Wattpad: https://my.w.tt/YJ8zpAc3a8 1 UWA UWACE... Bismillahir Rahmanir Rahim Batul Mamman SANARWA: Ina mai bawa masu jiran wannan littafi hakuri game da canjin da zaku gani a tare da labarin. Wasu dalilai sun sa na canja tsarin labarin sabanin yadda na fara shafin farko watannin baya. Allah Yasa mu amfana da darussan ciki Ya yafe min kurakuran da ajizancin dan Adam ba zai barni na tsallakesu ba. Amin Shimfida KIRIKASAMMA, JIGAWA 1983 Nishi take mai kama da gurnani saboda tsananin ciwon da take ji. Ko da wasa bata taba tsammanin ciwon nakudar da mata ke yawan fada ya kai haka ba. Mace ta kasa gane a wace duniyar take. Idan ba ta kama bakinta ba sai dai ka ji tana sumbatun da basu da kan gado. Addu'a kuwa bata san nawa ta kama ta saki kafin ta kai karshe ba. Yau Kulhuwallahu, Falaki da Nasin da ko cikin bacci basu bace mata ta kasa kai karshen ko daya. Sai ta karanta ayoyi biyu a nan ta kama wata. Halilala ma da kyar take cijewa ta kai karshe. Iska take furzarwa akai-akai ta baki ta hanci. Ashe shi yasa Malamin makarantar darensu ya ce duk wadda ta rasa rayuwarta wurin haihuwa tayi shahada. Ladanta daya da wanda ya rasu a wurin yaki. Mahaifiyarta ce ta fado mata a rai a wannan yanayin. "Allah Ya jikanki Inna. Inna idan na yi miki laifi ki yafeni. Innata bani da kamarki duk fadin duniya." Ciwo na tasowa ta ce "Inna ki ceceni." "Allah dai Ya ceceki Mari kada ki yi sabo mana." Ba da niyya ba ta kalli idanun surukarta Inna Mairo cikin radadin ciwo ta ce "kin san irin ciwon da nake ji ne Inna Mairo? Nan..." ta nuna mararta "...ne yake rabewa gida biyu. Yanzu kema a haka ki ka haifo Inuwa?" Dan murmushi Inna Mairo tayi saboda sanin cewa Mari ba a hayyacinta take ba. Ita da ta sha wannan wahalar sau goma sha uku sai dai ta bada labari. Wani irin ciwo ne ya damki mara da bayan Mari ta kai hannu ta cafko hannun Inna Mairo. Gani take kamar ba za ta tashi ba saboda azabar ciwo. Harira unguwae zoman ta sake danna gefe da gefen cikin sannan ta kuma lekawa. Kai ya taho amma da alama hanyar tayi masa kadan. Sabuwar rezarta ta dauko ta ce da Inna Mairo ta matso kusa da tochilan ta haska mata da kyau. Acibalbal din da aka kunna bata da hasken da zai wadaceta tayi abin da ya kamata. Mari ciwo bai barta taga abin da ake shirin yi mata ba. Harira ta saka tochilan din a cikin dankwalinta ita kuma Inna Mairo ta rike hannuwan Mari. Rezar ta dan kara a jikin wutar acibalbal din ta dauke ta danna kowane gefe a jikin zaninta. Ji ka ke kit-kit ta kara Mari ta hagu da dama. Wannan izaya bata da kalmar kwatance. A kan ce mata basu ganewa idan an karasu saboda ciwon nakuda amma Mari kam taji komai. Budar bakinta za ta yi ihu wani nannauyan nishi ya taso mata. Da dan sauran kuzarin da ya rage mata ta cije baki tayi nishin. Hamdala Harira tayi tare da karfafa mata gwiwa akan ta kara wani domin ga kan jariri nan ya kara turowa gaba. Ta daddage tayi kuwa sai ji tayi an canyara kuka irin na sabbin haihuwa bakin duniya. A take ta nemi wannan azababben ciwo ta rasa sai son ganin abinda ta haifa. "Sannu Mari. Sannu da kokari. Allah Ya raya shi Ya baki lafiyar shayarwa." Inna Mairo ta furta tana share mata gumi. Kunya taji ta lullubeta da ta tuna cewa ba don dan ya fito ba sakon tsinuwa da Allah Ya isa ta shirya bata domin ta isar ga Inusa maigidanta. Harira ta nade jinjirin a zani ta mikowa Inna Mairo. Da saurinta ta mika hannu za ta amshe shi hannun ya yi 'yar kara. Fuskar Mari wadda ta dago kai tana son satar kallon dan nata ta kalla tayi murmushi ganin Marin ta kawar da kai gefe. "Da dai korafin karya min hannu zan miki amma na fasa. Dauke shi ku ji dumin juna kafin na dawo." Da hannu Mari ta rufe fuskarta mai dauke da murmushin da ya gagara buya. A hankali ta bawa Inna Mairo hakurin rikon da tayi mata wanda da alama ya janyo mata rauni. Wani murmushin ta sake yi mata sannan ta tashi domin dora ruwan wanka tana murza hannun da take jin ya yi mata nauyi. Tana tausayin matar dan nata saboda ta tashi marainiya mara gata a wurin danginta. Shi yasa bata yarda an tafi da ita wankan jego ba lokacin da matar kawunta ta matsa akan hakan. Harira ma fita tayi aka bar Mari da jaririnta. Sai da ta tabbatar babu sawunsu a kusa ta matso dashi kirjinta ta rungume. Hannunta yana dan rawa ta bude fuskarsa da kyau. Hawaye taji ya ciko idanunta saboda kaunarsa da ta shigeta farat daya. Bata jin za ta iya hada shi da kowa sai dai idan a gaba ta sake haihuwa. Tunanin kadai sai da yasa tsigar jikinta tashi da ta tuna halin da take ciki mintuna kadan da suka wuce. Addu'a tayi masa ta neman tsari da kariya tare da albarkar rayuwa. Kafin a fara shigowa dakin har ta gama kissima rayuwarsa har aure. Burinta ya zama da nagari abin kwatance. Ya yi ilimi mai zurfi irin wanda taga ana yi a birni lokacin da take aikatau kafin tayi aure. Idan so samu ne ma ya zama babban likita ko lauya. "Dinkin nan zan zo in cigaba in tara kudin siya maka duk abin da za a nema a makaranta na karatun." Ta fada masa kamar yana fahimta. Guda ta jiyo ta tabbata yanzu duka matan gidan sun sami labarin haihuwarta. Yanzu dakin zai cika duk da asuba ce da matan 'yan uwan mijinta da sauran kannensu da basu yi aure ba. Ajiye jaririn tayi da sauri kar a ganshi a hannunta a kirata mara kunya. Can kasa kamar mai yi masa rada tayi magana tana murmushin tsananin farinciki da jindadi. "Bi'izinillahi sai kayi arabi da boko. Kayi sauka sannan kayi digirin digirgir irin na dan Hajiyar da na yiwa aiki." Rana na soma fitowa ruwan wanka ya yi zafi. Matar kanin Malam wato kawu ga mijinta Inuwa ce ta zaga bayan gida da ita inda za'ayi mata wanka. Jaririn kuma saboda hannun Inna Mairo da alama ya sami gocewa ko targade sai matar wan Inusa ce tayi masa wanka. Tana murnar rabuwa da ciwon haihuwa ashe akwai wani a gaba. Ruwan wankan da zafi sosai ake yarba mata darbejiyar da take ciki. Tun tana daurewa har ta hada da ihu. Ciki da baya sun sha matsa da dannawa. Bayan an gama wankan ta miko mata wani kwabi da kyallen kunguzu. Kallon kwabin da yafi kama da lalle tayi ta tamutsa fuska. "Me zan yi dashi Gwaggo?" Idan bata yi da gaske ba take taken Mari ba za ta saka ba saboda haka ta amshe ta ce yaba mata da kanta. Lalle ne aka kwaba da kauri da wani garin magani aka cusa mata. Mari sai gumi kawai take yi na wahala da ciwo. Bayan an gama sakawa kuma aka toshe wurin da kyallen kunzugu sannan aka bata zani ta daura. Tare suka fito tana taku da kyar zuwa daki. A haka aka ce ta shayar da jaririn bayan ko zaman kirki ta kasa. Haka aka cigaba da yi mata kwabin lallen nan na tsahon kwana shida sai ta nemi tsagar wurin karin ta rasa. Ciwo ya hade tsaf ya warke (don Allah kada wacce ta gwada). Ranar suna jariri yaci sunan kakansa Auwalu aka yi masa lakabi da Abbati. *** DALA, KANO 1985 Kukan ya ishe shi. Idan ya bari suka kara minti biyar a dakin yana da tabbacin zai sami tabin hankali. Bai so Innayo ta karbi girki daga yin arba'in ba. Jiya ma haka suka kwana jaririyarta Hasiya tana ta canyara kuka. A fusace yasa kafa ya haureta tana baccin da ana gani za'a gane cewa a gajiye take likis. Da yake muryar Hasiyan ba karfi gareta ba shi yasa bata ji kukan da ta shafe mintuna tana yi ba. "Dalla can malama tashi ki dauki 'yarki." Bugun ya shigeta sai dai kukan da ta ji ya dauke zafin dukan. Hannu ta kai da sauri ta lalubi 'yarta cikin hasken farin watan da ya ratso ta tagar dakin. Rarrashinta tayi nata idanun suna yi mata yajin bacci ta soma shayar da ita. Jin yarinyar tana ta ajiyar zuciya yasa ta jin babu dadi a ranta. Maganin mura ta sha ya saka mata nannauyan bacci ga kuma gajiyar aikin da tayi. "Baiwar Allah kin dade kina kukan nan da alama ban ji ba. Ayi hakuri" ta kare maganar tana shafa mata kai. "Mtsew" Alh Rabi'u ya buga tsaki. A cikin duhun dakin ya tashi ya lalubo wandon kayan da ya dawo dasu daga kasuwa ya saka hannu a aljihu. Sautin sulalla na karo da juna Innayo taji ta kalli bangaren da yake tsaye. "Alhaji idan wani abu kake nema bari ta gama na kunna maka fitilar kwan. A duhun nan ba ganin..." Kasa karasawa tayi ganin ya nufota. Duk da ba ganin fuskarsa take yi ba amma ta fahimci ransa a bace yake. Hannunta ya kama ya zube mata sulallan da bata san ko nawa bane. Da kakkausar murya ya yi mata magana cikin fushi. "Gashi nan na saya sai ki tashi ki koma dakinki." Sam bata fahimce shi ba. "Me ka saya?" Daurewa ya yi saboda dare ya raba ya bata amsa ba tare da ya kara daga sautin muryarsa ba. "Kwananki na saya Innayo! Ki dauki 'yarki ku koma dakinki. Zan dinga biyanki daga yau har ki kara wata arba'in din." Hankali a tashi ta fara tambayarsa laifin da tayi masa. Lokacin kuma Hasiya ta zabi ta sake bare baki tana kuka. Kan Innayo har wani sarawa yake saboda rashin isasshen bacci da gajiya. Wuni take a gaban murhu ga fama da yara. Biyar nata har jaririyarta ga kuma hudu na matarsa ta farko da ya saka shekara biyu da suka wuce. A yanzu su biyu ne a wurin maigidan nasu Alh Rabi'u kuma ita ce matsayin uwargida. Amaryar tasa Asabe ma ta dan kwana biyu tunda haihuwarta biyu yanzu. Iyakarsu da shi ya aunawa maigirki hatsi ga icce jingim a gidan. Sauran abin da za'a hada da hatsin a tayar da abinci kuwa sai dai mace ta nema. Asabe ko wata bata cika ba ta fitittike ta nemi ya raba musu girki. Kowacce tayi nata. Wadda miji ke hannunta ranar tayi da shi. Ita da ta zo cin arziki gani tayi sadakinta ma idan bata yi wasa ba a cefanen ciyar da 'ya'yan koshiyoyi zai kare. Haka kuwa akayi. Ya amince ya raba ya bar masu 'ya'ya da wahala. Bayan rabuwarsa da uwargidan taki daukar ko guda cikin 'ya'yanta. Har yau basu san me ya hadasu ba amma ko tantama laifin ba zai wuce nasa ba. Mahaifiyarsa ya kaiwa yaran da fari yayansa ya ce bai isa ba. Ga tsufa da tayi ga sanin halinsa na son banza. Jibge mata su zai yi sai an ganshi. A dole ya dawo dasu gidan ya rabawa matansa. Asabe tayi tsalle ta dire a gaban yaran ta ce ba za ta dauki ko daya ba. Tausayi suka bawa Innayo ana rabonsu a tsakar gida kamar ba mutane ba ta karba ta hada da nata. Zancen irin wahalar da take sha wurin ciyar dasu ma bai taso ba. "Nufinka bani da girki har sai mun kara wasu kwanaki arba'in din?" Ta tambaye shi da mamaki. "Ashe kin fahimta ki ke wani neman ba'asi." Shimfidar Hasiya ya tattaro mata "tashi ki tafi bacci ne a idona. Kuma ki kwantar da hankalinki ba wai Asabe zan baiwa kwanakin naki ba. Kukan nan ne kawai ba zan jura ba." Maganganunsa sun bata mata rai amma ta daure taki bashi amsar da za ta sa taji sauki a zuciyarta. Tashi tayi jiki ba kwari ta fice ya kada kai a wurin ya kwanta. Kamar kullum washe-gari karfe bakwai a bakin murhu tayi mata da goyon Hasiya. Da safe 'yar tsala take sayarwa da kuli-kuli. Da rana kuma dambu. Daidai lokacin tasowar yara daga islamiyya kuma tayi danmalele. Don ciniki kam sai dai tayi hamdala. Kudin ne dai duk yawansu basa isarta. Yara tara ne a gabanta da ita kanta cikon ta goma. Ga kudin laraba ga sayen abinda ba a rasa ba na boko. Ta sallami yaron karshe da bokiti cike da 'yar tsala da zai kai kasuwa taga fitowar Asabe daga dakin Alh Rabi'u da danta a hannu. Suna hada ido ta gatsina fuska gami da murguda mata baki ta shige dakinta. Bata bi ta kanta ba ta sauke tandar ta dora ruwan wanka. Yaran gidan duka sun tafi makaranta sai wadda ta yaye tana bacci a daki. Alh Rabi'u ta gani ya fito cikin shirin tafiya kasuwa. Dauke kai tayi kamar ba za ta yi masa magana ba saboda haushin abin da ya yi mata, sai kuma dai ta daure ta ce, "Sannu Alhaji." Da yake ba shi da gaskiya sai ya hau sababin borin kunya. "Na dai biyaki kin kuma cake kudin bare ki ce an ci amanarki." Zama tayi akan tabarma ta kwanto goyonta kafin tayi magana cikin rashin jindadi. "Wani abin kaji na ce?" Hannuwan babbar rigarsa ya nade fuskar nan tasa a hade. Bai so haduwarsu ba shi yasa ya zauna a daki niyarsa sai ta bar tsakar gidan ya fito. Daina jin motsinta da suka yi ne tasa shi cewa Asabe ta duba musu. Ita kuma don ta tura mata haushi ta fito sai ya zata ta gama suyarta ta shige daki ne. Muryarsa a sama tunda ya san yaran masu wayo suna makaranta yake mata magana. "Banda fitina ma irin taki Innayo daga yin arba'in ringidi-ringidi kin kwaso jiki kin dawo turakar maigida..." Maganganunsa a take suka fara tunzura ziciyarta domin ta fahimci ci mata mutumci yake son yi. Kalamansa na gaba basu bata damar yin wani tunanin kirki ba sama da zubar da hawaye. "...karfe takwas da rabi don bala'i duk kin saka yara bacci kin taho dakina ke mai girki. To magana ta gaskiya ni ba zan dinga kwana da wannan yarinyar tana yi min kuka ba." Ganin tana ta zubar da hawaye yasa shi cewa "Idan arba'in din ne baki son maimaitawa sai ki dinga barinta a dakinki ko ruwa A'i ta dinga bata. A shekarunta yanzu yaci a ce za ta iya kulawa da jinjinya." Ido sharbe da hawayen bakincikin wannan terere da ya yi mata kuma a kunnuwan Asabe ta ce "yanzu Alhaji kayi min adalci kenan? Ka dakeni kuma ka hanani kuka. Ita Asaben ba goyo gareta ba?" "Ban san kina kishi da namijin da ta haifa min ba sai yanzu. Yaro dan wata biyar da an kwantar dashi baka sake jin kukansa sai gari ya waye. Wai ma da ki ke zancen adalci ke shi kika yi min da kika haifi mata har biyar?" Zancen kenan kullum! Ita da babarsu A'i sun haifa masa 'ya'ya mata. Asabe ma ta farkon ta mace ce cikon ta goman matan. Na shadaya ne ya fito namijin da ake muradi. Idan ta biye masa ita zai cigaba da konawa zuciya a banza. Tashi tayi ta shige daki ko amsa bata bashi ba. 'Ya'ya mata Allah Yaso bata kuma ta gode. Sake kudurin ganin ta inganta rayuwarsu tayi. Idan ta kama ta kara wata sana'ar za ta kara. Burinta a rayuwa su ginu su zama mutanen da sai dai a rabesu a sha inuwarsu. Ta yarda ita kadai ta gama shan wahalar rayuwar duniya indai 'ya'yanta za su jidadi a gaba. *** BARNAWA, KADUNA 2000 Zazzage akwatin da ta ajiye akan gadon tayi ta sake bin kayan ciki daya bayan daya tana jerawa a nutse. Tafiya ko da unguwa ce mara nisa tana da wani abu guda, sai mutum ya bincika kayansa sau goma kafin ya bar gida amma yana zuwa inda zai je sai ya tuna wani abu mai mahimmanci da ya manta. Hayaniyar yaranta ta ji daga falo da alama fada suke yi. Ba sai an fada ba kusan kodayaushe suka yi fada mai laifin daya ne. "Lilu zo nan" Ta daga murya tana kiran danta na uku. Bai zo din ba kamar yadda tayi tsammani sai ma ambaton "sai na rama" da yake yi cikin kuka. Sanin halinsa na rashin kunya yasa ta tashi da kyar saboda nauyin ciki ta bisu falon. Babban mai suna Suhaib akwai saurin fushi. Farha mai binsa sarkin tsokana. Sai Khalil da kowa yake kira Lilu mara kunya, ga taurin kai da saurin kuka. "Allah nagode Maka" ta ce tana kallon yadda suka hargitsa falon kamar gidan mahaukata. Abubuwa kalilan ne a muhallinsu na asali. Yaran na ganinta suka shiga taitayinsu don sun san hali. Tana sonsu tana tattalinsu amma bata yarda da sakarci ba. Cikin hikima ta iya bi dasu duka da halayensu. Idan kayi abin fada ko duka kuma baka tsira. Khadija mace ce mai zafin nama da sanin ya kamata. Idan suka yi kiriniyar ta gama fadan sai ta koma gefe tana yi musu addu'ar shiriya. Fatanta kowannensu yana girma halinsa mara kyau yana raguwa har ya barshi gabadaya. Yanzu ma sulhu tayi musu ta kuma ja kunnen Farha akan tsokanar kaninta saboda raini da ya gama shiga tsakaninsu. Falon ta sake kallo sannan ta cira kafa ta taka kitchen ta leka ta dawo. "Ina Nasima?" "Ban ganta ba." Yaran suka hada baki wurin fada. A falo ta bar 'yar budurwar mai aikin nata tare da yaran ta tafi sake hada kayan tafiya asibiti. So take ta tabbatar komai yana ciki kada ayi irin na haihuwar Lilu. Sai da aka gama shirya yaro babu shawul babu zanin nade shi saboda tana tsakar nakuda ta hada kayan. "Ku taso ku kwashe tarkacen kayan wasanku kafin na kira Nasima ta zo ta share falon." "Wash Mami hannuna..." fadin Lilu yana yarfe hannu. Hade rai tayi tun kafin tayi magana ya mike tsaye "tashi makyuyaci. Idan aikin baki ne naka yafi na kowa tashi. Amma da an ce za a more ka sai ka dinga langabewa." Fita tayi tana cije lebe jin kafarta tana rikewa ta zaga bayan gidan tana kwalawa Nasima kira. Nasima tayi matukar razana da jin muryar uwardakin nata a kurkusa da inda take kwance. Hannuwan mutumin da suke bin jikinta ta doke da sauri tana mikewa tsaye. A razane shi ma ya dauki jakar da ya dawo da ita daga office yana gyara zaman necktie dinsa. Gaba ya yi yana yiwa Nasima inkiya da ta dakata kada ta biyo bayansa. Bata bari ya tafi ba ta bishi da sauri ta ware hannuwanta a gabansa. Mamakin karfin halinta ya yi a wannan yanayin da matarsa take gab da kamasu ya yi saurin zaro kudin da ya san su take nufi ya dora mata. "Yaya Tahir?" Khadija ta kira shi da mamakin rashin sanin dawowarsa. Da saurinsa ya tareta ya kama fadan borin kunya. "Me ya fito dake kina jan kafa ke da likita ya ce kina bukatar absolute bed rest? Meye amfanin Nasima a gidan da ba zaki huta ba?" Murmushi tayi tana yabon irin kulawar da yake bata a ranta. "Nasima nazo kira." Hararar Nasiman ya yi "idan kin gaji da aikin ne sai a nemi wata." Hakuri ta bawa Khadija kai a kasa cikin sassanyar muryarta ta makiran yara. Duka duka da kadan ta haura shekara sha shida, amma fitinarta a boye tafi ta wata 'yar arba'in din. Tamkar hawainiya haka ta kware wurin boye halayenta. Sumumu kasau, macijin sari ka noke shi ne tashenta a wurin saurayinta na farko wani Alhaji a kasan layin. Sai da suka shiga daki yake cewa Khadija wai yau yaji wa'azin da ake cewa kayi kyauta da dama hagu ba sai ta sani ba. "Shi ne fa ina shigowa na hango wannan kazamar 'yar aikin taki tayi baya. Da yake kanta kamar dusa aka zuba maimakon kwakwalwa inata kiranta na bata sadaka bata ji ba. Ni kuma na riga nayi niyar yi da fatan Allah Ya saukeki lafiya. Shi yasa na bita bayan." Kwalla taji ta sauko mata ta farinciki. Tana alfahari da mijinta domin ta san sai an tona ake samun irinsa. A da kam ta wahala akan 'yan matansa amma da dabara ya nuna mata ya bari. Baya son ta wahala kuma baya son damuwarta. Tana cewa wash zai bar duk abinda yake yi yazo gareta. Ga saurin bata hakuri idan ya bata mata rai. Kulawa sosai yake bata duk da mai aikin da ta dauko 'yar makotansu tun tana laulayi. Da zarar ya dawo gida bayan yara sun tafi Islamiyya yake turata daki tayi bacci. Wai nan so yake ta huta da kyau kafin su dawo. A wannan lokacin yake samun kebewa da Nasima ba tare da saninta ba. Nuna mata yake ya tsani yarinyar domin kada ya bar kofar zargi a tsakaninsu. "Nagode Yayana amma don Allah ka rage hantarar Nasima. Kaga amana take a hannunmu." Ruwa ya tashi watsawa jikinsa ya nuna mata kamar baya son zancen. Yana bandaki shi kadai yake tsakin zuwanta bayan gidan dazu. Bin mata sana'arsa ce tun yana matashi. Khadija 'yar kanwar babansa ce aka hadasu wai ana ganin idan ya yi aure zai rage. Babu wanda ya bata zabi kawai aka ce ta auri dan uwanta don ya shiryu. Ya kuwa nuna musu shiriyar tasa kamar gaske saboda yana son Khadijan. Da yake kwararren dan duniya ne babu wanda ya san ya cigaba da harkokinsa a waje. Dawowarsu unguwar nan abin nasa ya kara baci tunda ya ga Nasima komai ya kwance masa. A zahiri yake nuna mata kyama amma a badini tafi kowa. Ita ce kawai a gabansa kuma bashi da burin da ya wuce ganin lokutan da suke samun kebewa a gidan ko a wuraren da ya saba kai 'yan matansa. Khadija bata san wainar da ake toyawa ba. Da zuciya daya take zaune da kowa. Gidansu Nasima a can kasan layinsu yake kuma sun fi kowa karamin karfi. Abinci a rana bai fi su ci sau daya ba idan an sami faraga. Shi ne fa ta nemi Nasima ta dinga tayata aiki suna biyanta karshen wata. A ranar da daddare ta sake yi masa maganar dauko kanwarta ko tasa su tayata zama ko da zuwa tayi arba'in ne idan ta haihu. "Na fada miki ba zuwansu ne bana so ba amma a gani na me zai hana ki dauko waccan yarinyar?" Ya ce da sigar laluma. Dan jim tayi tana tunani kafin ta fada masa dalilinta na neman ta gida. "Na fara tunanin sallamarta ne kawai." Gabansa ne ya fadi zai yi magana ta dora da cewa "ka san ko Lilu da yake dana muna fada akan rashin kunya balle Nasima. 'Yan kwanakin nan sai tayi zamanta a baya taki aikin. Idan na kirata a murya sai ka ji lafiya amma a fuska sai in ga kamar tana hararata." Dariya ya kwashe da ita duk kuwa da fargabarsa ta cikas da korar Nasiman zai kawo masa. "Shi yasa nifa bana sonta. Ke kuwa da anyi magana sai ki ce marainiya ce. To kema dai naga alama kin gaji da aikin ladan kenan." "Ba gajiya nayi ba." Ta amsa masa ganin kamar yana ganin asarar kudi yake da biyanta bayan aikin nata babu yawa. "Zan yiwa mamanta magana ta fara kwana. Idan ta cigaba da halinta sai mu rabu." Zuciyarsa kamar an zuba ruwan sanyi don farinciki. Nasima tana gara shi a 'yar haduwarsu ta bayan gida. Minti biyar idan tayi sai ya biyata. Idan ta fara kwanan zai fi samun lokaci tare da ita. Bayan ya tafi aiki washegari Khadija ta je gidansu Nasima da misalin shabiyun rana. Lokacin yara suna makaranta ta barota ita kadai tana wanke-wanke. Tarba ta girmamawa ta samu daga wurin mahaifiyar Nasima. Bayan sun gaisa ta fada mata abinda ya kawota. Ladidi ta dan bata rai "haba Mamin Suhaib? Yanzu don kina son Nasima ta dinga kwana har sai kin fito a wannan yanayin da kike? Ai cewa za ki yi kawai ta fada min magana ta zauna." Dan murmushi Khadija tayi tare da girgiza kai. Don tana taimaka musu ba shi ne dalilin da zai sa su juyata son rai ba. "A'a gara dai na zo da kaina. Ban fada mata ba ma na ce sai naji amsarki." "Allah Sarki Mamin Suhaib. Yasin shi yasa nake kara ganin girmanki. Kina da mutumci kuma kin san mutumci. Allah na tuba banda ma kin dage ai da ko kwandalarku ba zan karba a matsayin albashinta ba. Ciyarwar da kuke mata damu kanmu ta wadace mu." A zatonta sai washegari ko nan da kwana biyu Nasima za ta taho sai gata ta dawo da kaya niki-niki kafin magariba. Lokacin ko cikakkun mintuna talatin bata yi ba da tafiya. Da mamaki Khadija take kallonta tana turo katuwar jaka da wata karama sai ghana must-go. "Ashe da shirinki." Tabe baki tayi Nasima tayi ta ce "uhm". Khadija ta daure zuciyarta daga take taken fitsarar da take gani a wurin Nasima. Shirin nata cikin kankanin lokaci ya bata mamaki ganin bata san da zuwan ba sai da ta gama aiki za ta tafi ta fada mata. Ita kuwa tuni sun gama shirinsu da Tahir. Mamakin Khadija ninkuwa ya yi da taga Nasima ta nufi dakin baki da kofarsa take a cikin falon da kayanta. Idan tayi tunanin ko mamanta ce ta hada mata kaya kafin ta koma gida to da ya akayi ta san dakin da za ta zauna bayan ko su Suhaib basu sani ba. Kama bakinta dai tayi tana kallon ikon Allah. Nasima kuwa tana shiga dakin ta buga wani uban tsaki. Ta lura Khadijan sai wani fiffika take yi ita mai miji. Mijin da yake a tafin hannunta matarsa har wani daga kai za ta yi mata? Sake yin tsaki tayi da ta kula tsohuwar katifarsu Lilu ce aka ajiye mata a dakin da wankakken bedsheet da pillow. "Kut! Ai wallahi gado za ka zo ka saka min a dakin nan ko na kama gabana. Lallai ma Khadijan nan kin rainani." Shu'umin murmushi tayi da ta tuna tuggun da ta shirya mata. Lokaci ya yi da Tahir zai bata nata 'yancin ko ta kwata ta karfi. Ba zai yiwu bane ya cigaba da raina mata wayo. A gaban matarsa ya fada mata magana a bayan idonta kuma ya dinga lallabata. Da Tahir ya dawo Nasima tana daki ta ji hayaniyar yaran. Da saurinta ta mike ta gyara kwalliyarta ta fesa turare ta fito. Shirt dinsa ce a jikinta ta hada da zani da dankwali iri daya. "Daddy oyoyo" ta ce da karamar murya kai a kasa. Kallonta ya yi sama da kasa wani abu na fizgarsa gareta. Ba don idon yara ba da sai ya biya ladan wannan ado. Gwalo tayi masa karaf a idon Khadija wadda ta fito daga kitchen da tray a hannu. Nasima sai ta wayance ta kuma yin gwalon. "Nima na rama Lilu." A zuwan wasa suke yi dashi. Tahir sai ya karbe da cewa "anya Khadija ba rainon mutum hudu ki ke ba? Ita da ta zo taimaka miki ta buge da wasan yara." Bai bawa Khadija damar yin magana ba ya bukaci ta tara masa ruwan wanka. Daki ta nufa zuciyarta cike da wasi-wasin abin da ba ta son zargi. Abincin ma daki ta kai masa a ranar. Sai da suka kwanta ta sako zancen shirt din. "Ni fa kamar shirt dinnan taka da nayita nema wancan wankin na gani a jikin Nasima dazu." 'Jaraba sai da ta gane' ya ce a zuciyarsa. "Oh ashe bamu yi maganar ba. Rannan na tsinceta a bayan mota tayi datti. Ina jin daga kayan wankin ta fado. Na dauko zan yar shi ne da ta gani ta ce tana so." "Ka dai san ina bata kaya. Idan kari take bukata ai da sai kayi min magana. Rigarka ai ba abin sawarta bace." Da bacin rai take magana ya soma bata hakuri. Zuciyarta sam babu dadi har wani zazzabi taji yana neman kamata. Abubuwan da take ta son turewa game da Nasima sun sami wuri sun manne mata a rai. Bayan kamar minti arba'in tana fama da guntun ciwon marar dake tsungulinta taji kamar hannun Tahir a saman fuskarta. Da alama karkada hannun yake ya gani ko tayi bacci. Da gangan tayi motsi ai kuwa ya dauke hannu ya kwanta da sauri. Juya mata baya ya yi ta bude ido ta tabbatar baccin karya yake yi. A hankali tayi kwafa ta sake rufe ido. Ba afi minti goma ba ya sake kada hannun. Wannan karon luf tayi takaici na nukurkusarta. Akwai abin da yake boye mata. Fatanta Allah Yasa ba Nasima bace. Tana jinsa ya tashi ya shiga bandaki. A cikin kunnuwanta taji ana bude dakinsu shi ma ya bude bandakin. Sannu a hankali ta bude ido kadan don kada a san ta farka ta hango Nasima a bakin kofar. Abin ya daina bata mamaki ma tunda har take da karfin gwiwar zuwa dakin. Da yatsa Nasima take yafito Tahir da ya fito daga bandaki, shi kuma yana nuna mata Khadija wadda duhun dakin yasa basu gane ta bude ido ba. Barazanar shigowa Nasima tayi masa ya yi murmushi yana yi mata inkiya ta karaso mana. Ba kunya ta sako kafa a kofar dakin ya yi saurin karasawa ya dagata a kafadarsa suka yi gaba. Kememe Nasima taki yarda a koma dakinta wai ita a gadonsa za ta kwanta. Sanin rigimarta yasa ya ce da Khadija su kwana a nata dakin. Rufe kofar da ya yi a hankali ya yi daidai da matsanancin bugun zuciyar Khadija. Hawaye take yi ba tare da ta sani ba ta tashi da kyar ta bude kofar ta fita. Dakin Nasima ta nufa bata same su ba sai ta nufi na Tahir. Daga bakin kofa take jin dariyar Nasiman tana rokonsa ya daina yi mata cakulkuli. Shi kuma yana cewa ta rage murya. Sai da ta tsaya ta hadiyi wani yawu mai daci sannan ta murda kofar da karfinta. Ganin da tayi musu yasa komai na jikinta tsayawa cak. Murdawar cikinta ce ta dawo da ita duniyar mutane ta rike ciki tana salati.Wattpad: https://my.w.tt/Fae5U4oHh8 UWA UWACE...2 Batul Mamman💖 Duk hukuncin da uwa za ta yanke akan 'ya'yanta tana yi ne da tunanin hakan shi ne maslaha a rayuwarsu ko da kuwa a gaba shi zai zamto mafarin kukansu. *** Kwakwalwarta babu abin da take hasko mata sai yanayin da ta ganshi tare da Nasima lokacin da ta farfado. Idanunta a rufe amma hawaye yana sintiri daga kwarmin idanun zuwa kunne ya sauka akan pillow. Daga kamshin da take ji na dakin kadai ta fahimci a gadon asibiti take. Sakayau take jin jikinta babu wani nauyi sai na zuciyarta da ta koma tamkar dashen dutse. Cikinta ta shafo a hankali taji babu tokarewar nan ta dan da ya kusa zuwa duniya. A firgice ta tashi wani irin radadi na ban mamaki ya soki mararta. "Bar garaje Khadija jikinki da danyen ciwo." Cewar Yakumbo mahaifiyar Tahir. Da yake bata san da ciwon ba tashin bai wahalar da ita ba kamar komawa ta kwanta. Ita ba a kwance ba ita kuma ba a zaune ba haka ta saka hannuwanta ta dafe gefen gadon don kada ta fada da karfi. Yakumbo ce ta taimaka mata ta koma ta kwanta tana rarraba idanu. Tambayoyi ne akan harshenta ta kasa amayar dasu saboda sabon al'amarin da take ji a jikinta. Yakumbo ta sake cewa "Bari na fadawa nos kin farfado" har ta kusa kofa ta dawo ta dafa mata kai "sannu kin ji. Allah Ya baki lafiya." Khadija ta kula da hawayen da Yakumbon ta dauke daga gefen idonta kafin ya sauko. Jikinta sai ya kara yin sanyi da tunanin ko me yake faruwa ba alkhairi bane. Yakumbo bata jima da fita ba Mamanta ta shigo tare da kannenta da su Farha. Kowa sannu yake yi mata tana amsawa da ka. Sallamar Tahir taji ta dawo mata da duk wasu lokuta da sai a yanzu take fahimtar raina mata wayo suka yi shi da Nasima. Runtse idanu tayi tana jin Mamanta tana tambayarta ko cikin ke mata ciwo ta girgiza kai. Shi kan shi Tahir din ganin idonta biyu sai da yaji kamar ya koma saboda firgici. Saukinsa daya yaransa da suke wurin Mama jikinsu a sanyaye da yanayin Maminsu. Yana da tabbacin ba za ta yi wani abu a gaban 'ya'yanta ba. "Ku bashi wuri mana ya zauna kun yi ďare-ďare akan gadon." Mama ta furta tana nunawa kannen Khadija hanyar fita daga dakin. Mutum biyu ne dama suka zauna a gefe sai suka tashi amma basu fita ba. Tahir ya kalli Khadija ba shiri yau shi ne da sauke kai kasa. Tsoronta ne ya mamaye masa zuciya saboda irin kallon da take yi masa babu komai a cikinsa sai tsana da disappointment. Mama kuma ta kara masa zafi da cewa "Ina mai-aikin taku yau? Kodayake ya kamata yau ta huta." Dawowar Yakumbo da likita ce ta taimaka masa bai bayar da amsar da za ta zama zallar karya ba. Kukan jinjiri ne ya biyo bayan shigarsu dakin a hannun Matron. Da dan murmushinta ta nufi gadon bayan gaisawa da jama'ar dakin. "Ina nan ni dai. Doctor ki gama dubata ta bawa bebina abincinta mun gaji da shan madara." Kallon kunshin shawul din Khadija take yi a lokacin da likitar ke yi mata tambayoyi game da jikinta. Babu abin da take fahimta sai gyada kai da take yi idanunta fal hawaye akan dan da bata ganin fuskarsa. Likitar sai ta kalli Yakumbo da alamar tambaya "Maman Khadija ya naga kamar bata san me ya faru da ita ba?" "Farfadowarta kenan na taho kiran Nos sai na hadu dake." Da ido Maman ta kalli kannenta suka fice tare da su Suhaib. Tahir kamar ya nutse ya kasa kallonta. Likitan ce ta karbi bebin ta dora mata a cinya. "Khadija kin san cewa tun farkon cikin nan akwai matsala har kina yawan zubar da jini ko?" Bata amsa ba sai bin fuskar yarinyar da har kunne an bula mata take da kallo. "Yau kwana kenan..." da sauri ta daga kai ta kalli likitan jin cewa kwananta biyu bata hayyacinta "maigidanki da mai-aiki sun kawoki cikin dare kina ta zubar da jini a sume. Ta ce zamewa ki ka yi a toilet wurin faduwa cikin ya bugu da sink. Kafin ki farfado faya ta fashe ga jinin bai tsaya ba." "Hummm" ta ce da guntun murmushi idanunta akan Tahir. Yakumbo tana kallonsu ta kuma ha yadda yaki daga kai ya kalli matarsa. "Ba cs din bane kadai Khadija harda mahaifar muka cire." Sautin da taji ya ziyarci kunnuwanta ga dukkan alamu shi ake kira saukar aradu a yanayin tashin hankali. Zabura tayi za ta tashi a karo na biyu tana fama dinkin kasan mararta. "Kwanta don Allah kada ki yiwa kanki rauni. Kaddara bata wuce kowa. Gashi an ciro miki jaririyarki lafiya kalau." 'Yar ta rungume ta fashe da matsanancin kuka. "Ki yi hakuri Khadija. Mun yi iya yinmu amma jinin yaki tsayawa. Taimakon Allah ne kawai muka sami baby din tunda sun ce basu san tun yaushe ki ka fada kan cikin ba." Likitar ta karasa yi mata bayani. Kukanta bai tsaya ba kowa na dakin ya tausaya mata. Yakumbo kuwa haka kawai tun farkon labarin dama bata wani yarda ba. Yanayin Khadijan a yanzu sai ya karfafa mata zarginta. Don ta tabbatar sai cewa tayi da Tahir ya rarrasheta mana. Mugun kallon da Khadija ta watsa masa wanda ya dakatar dashi ya bata amsarta. "Mijin naki ki ke yiwa wannan kallon don rashin hankali kamar shi ya dora miki lalurar." Mama ta ce da ita cikin fada. "Allah sarki" inji Matron "kar ki ga laifinsa da kyar ya yarda yasa hannu. Yarinyar da suka zo tare ce ma ta dinga tausarsa akan ya amince a cire saboda kada a rasa ki." Numfashinta neman daukewa ya yi a wannan lokaci. Wato duka karairayin zuwanta asibitin sai da Nasima ta ingiza shi ya yarda aka cire mata mahaifa. Bata san me za ta yi musu ta huce ba. Ya ci amanarta ya kuma cutar da ita. Gani tayi su Mama na fita daga dakin tayi murmushin takaici. Ta san irin abin nan ne ace a basu wuri ita da mijinta. Ana rufo kofar ya taho gareta da sauri. "Nasima don Allah kiyi hakuri ki rufa min asiri. Na san ban kyauta ba amma don Allah in ci darajar 'ya'yanmu." Tahir ya cika babban munafuki har tana mamakin yadda akayi ta kasa daukan haske ko sau daya. Saboda nisan da ya yi shi yasa bai ji kunyar kiranta da sunan mai-aikinta ba. "Khadija. Suna na Khadija." Ta ce dashi muryarta a dake. Bakinsa ya doke da sauri ya sauka kan gwiwoyinsa. "Ki yafeni Khadija." Ba shi take kallo ba. 'Yarta ta karshe a duniya take kalla tana nadamar biyayyarta a baya. Da bata amince ta aure shi ba da basu hada jini da mazinaci ba. "Na yafe maka tun kafin ka roka duk da baka yi nadama ba." "Nayi. Wallahi nayi nadama sosai." "Baka yi ba. Na rantse da Allah da kayi nadama da baka taho da ita kawoni asibiti ba. Da bata zauna jinyata har ana cigiyar rashin zuwanta a yau ba." Busassun labbansa ya lasa a hankali. Ya san ba za ta taba yarda ba amma shi ya san cewa ya yi nadama. Yana dai yiwa Nasima irin son da ba zai iya hakura da ita ba. Idan kurar nan ta lafa aurenta zai yi ya kama mata gida daban. Zai cigaba da zama da Khadija saboda wani sashe na zuciyarsa yana ganin girmanta. 'Ya'yan da ta haifa masa kuma duk munin halinsa yana sonsu kuma ya san suna da hakki a kansa. Muryarta ce ta katse masa tunani. "Kafin a sallameni ka rubuta min takardar saki. Ba zan tona maka asiri ba saboda bana son duniya ta nunawa 'ya'yana yatsa akan halinka. Kai dai ka tanadi abin da za ka fadawa iyayenmu tunda karya a jininka take. Sharadi na daya ne." Kallonta ya yi "kada ka yarda ka dora min laifi a matsayin dalilin rabuwarmu. Ina fata ka fahimceni." "Ba zan iya sakinki ba. Khadija ina sonki." "Ka daina yiwa kanka karya akan abin da baya zuciyarka." Zancen gabadaya baya so ayi shi a asibiti amma ya san ba shi da hurumin cewa tayi shiru. Yana son cigaba da zama da ita amma ba ya jin zai zama adalci gareta ya tursasata ta cigaba da zama tare dashi bayan yanzu ya fara son Nasima. Tunda dai za ta rufa masa asiri ya san komai zai zo da sauki. Juyawa ya yi zai fita ta kira sunansa. "Tahir! Za ka yi nadama a nan gaba sai dai ina tsoron kada ta zo a lokacin da komai ya lalace. Ina gudun kada hakkin 'ya'yan da ka batawa rayuwa ya rataya a wuyan 'ya'yana." Da yake maganar ta tsorata shi bai san lokacin da ya ce "wallahi ba ni na bata Nasima ba a haka na sameta." Kallon da tayi masa ne ya sa shi jin nauyin furucinsa. Sunkuyar da kai kawai ya yi yana jiran ya ji me za ta ce sai yaji shiru. Juya masa baya tayi tana zubar da zazzafar kwalla. Ta so Tahir a lokacin da bata da zabin da ya wuce bin umarnin iyaye. Ta sadaukar da farincikinta na son waninsa saboda tsira daga azabar Allah. A yau ta rasa mahaifi da kuma igiyar auren da take jira ya datse duk a dalilinsa. Ita mai iya tsaya masa ce ya kara aure idan yana so. Shi yasa take mamakin dalilinsa na yin zina. Zinar ma ta fuskar wulakanci gareta. Kalaman mahaifiyarta take tunawa a wani lokaci da ya wuce tana yiwa kaninta fada zai tafi jami'a a wani garin. "Zina masifa ce. Idan ka yi da 'yar wani kai ma sai ta zagayo jikinka inda za ka ji ciwo mai radadi. Ko ni, ko 'yan uwanka, ko iyalinka ko 'ya'yan cikinka" Addu'a ta soma yi musu tana fatan Allah Ya karesu daga wannan mummunar dabi'a. Za ta sadaukar da rayuwarta wurin kula da tarbiyarsu da fatan rufowar asirin mahaifinsu. Aure kuwa ta yi ta gama. Abin da ya yi saura ba rayuwarta za ta yi amfani dasho ne wurin ganin yaranta sun sami ingantacciyar rayuwa. Bayan kwana biyu suka sake kebewa da Tahir a dakin. Tuni tayi masa akan takardar sakin ya ce da ya saketa gara ta tona masa asiri. Amsarsa ta tayar mata da hankali ta kuma sanyata tunanin dalilinsa na sauyawa bayan da ya amince. Yanayinta ya kalla a ransa yana yabon kaifin basirar Nasima. Yana fada mata zai saki Khadija ya aureta ta fitittike ta ce sam bata yarda ba. Nuna masa tayi duniya za ta zagesu idan suka yi haka. A ranta kuwa gudun kada ya bata rikon 'ya'ya take yi. Tafi son ayi auren a gaban Khadijan ta ganta suna masu matsayi daya a gidan. Ita ta bashi shawarar wadancan kalamai domin a cewarta Khadija za ta zauna don 'ya'ya. Tunda aka kai yanzu maganar ganinsu bata tashi ba to ya sani cewa indai akan 'ya'yanta ne za ta rufa masa asiri. Ga zahiri ya gani. Sai ga Khadija tana kuka tana rokonsa saki kamar ba ita ya yiwa laifi ba. Da aka murda kofar dakin da sauri ta share hawayenta harda karyar ciwo ke cinta. Da wannan barazanar ya samu ya rufe bakinta har aka yi sallama. Da wani ya san abinda uban 'ya'yanta ya aikata ko da kuwa mahaifuyarta ce gara ta cigaba da zama dashi ko babu soyayya. Ba za ta so labarin gamon da tayi ya taso a lokacin da wani alkhairi ya doso rayuwar 'ya'yanta ya wargaza ba. KHADIJA: A jerin ire-iren iyaye mata ta fado a jinsin masu shanye komai domin 'ya'yansu. Ta yarda ta fanshi zubar hawayensu ta hanyar sadaukar da farincikinta. Karesu zata yi muddin rai kada kazantar mahaifinsu ta wargaza rayuwarsu a gaba. ***** KIRIKASAMMA 1995 Ta san ya ji ta sarai amma bata sare ba ta cigaba da binsa da roko da laluma saboda muddin ya sa kafa ya fita yau to magana ta kare. Kiran sunansa tayi da dan karfi ganin ya kusa kofar fita. Indai bukatarta za ta biya tayi alkawarin jure duk wani jan rai da wulakanci daga Inuwa. "Malam inata magana baka ce komai ba har za ka fita." A fusace ya juyu kamar zai mangareta ya soma fada. "Ke dai Mari da mayya ce ki ka kama mutum Yasin sai buzunsa. Haba! Ni na taba ganin bakin naci irin wannan? To duk jarabarki sai ya tafi yadda ake tura 'ya'yan kowa." Hargaginsa ya fito da sauran matan gidan daga bangarorinsu. Zaman kauye babu abin yi har jiran barkewar rikici suke don a bawa ido abinci. Gidan nasu kuwa an sami karuwar jama'a, kama daga matan da ake kara aurowa zuwa hayayyafar da ake yi kusan duk shekara. "Rigimar me ku ke yi da rana tsaka Inuwa?" Mal. Sa'idu babban wa ga mazam gidan ya tambayesu amma aka rasa mai bashi amsa. Mari sadda kai tayi kasa zuciyarta tana bata cewa hakuri kawai za ta yi wannan karon a tari gaba. Mal Sa'adu da sauran 'yan uwan Inuwa babu mai goyon bayanta. Maganar nan kuma ko Inna Mairo ba bayanta za ta bi ba. "Kya yi shiru kuma yanzu? Ai sai ki bude baki ki fada musu abinda ki ke rokona" cewar Inuwa yana duban yayansa "wai makaranta ce bata so a tura Abbati." "La haila ha illallahu..." Mata sai tafa hannuwa kamar sun ji gagarumin sabo. Shi kuwa Mal Sa'adu cewa ya yi maganar ba ta tsaye bace su biyo shi sashensa. Durkuso Mari tayi a gefen tabarmar da Inuwa ya zauna. Bata ma yi niyyar zama ba domin rashin kunya za ace tayi. Mal Sa'adu ne ya yi magana cikin jimami. "Yanzu ke Mari karatun Muhammadiyyar ne ba kya so? To ko dai kin canja addini ne bamu da masaniya?" Kai da hannuwa ta karkada a tare "a'a Malam. Cewa nayi a barshi ya cigaba da karatun a nan ba sai an kai shi Kano ba almajiranci ba." Matan gidan dama ba kaunarta suke sosai ba saboda fifikon da Inna Mairo ke nunawa a kanta. Gashi tayi karatu har matakin aji uku a firamare kafin Inuwa ya aurota. Su kuwa babu arabi ba boko. Anyi musu baiko tun tana shekara goma. Sai ta tafi aikatau Dutse inda ta sami wayewar kai. Gidan da tayi aikin suka saka ta a makaranta. Sun so a barta ta karasa amma gidan su Inuwa suka ce idan bata dawo anyi auren ba a dawo musu da kudinsu. Haka nan tana ji tana gani aka rabota da ilimin da ta fara jindadinsa. Wannan ne yasa ta dage aka kai 'ya'yanta firamaren garin sannan suna zuwa makarantar allo da ta dare. Da sana'ar dinkimta da take dan samun kudi take yi musu hidimar makaranta. Su biyar ne yanzu. Abbati babba da mai binsa Sani sai 'yan mata uku. Al'adar gidan ta tura yara maza almajiranci kwatakwata bata burgeta. Ta ga yadda almajirai ke watangaririya idan sun tafi karatu, bata marmarin 'ya'yanta suyi irin wannan rayuwa. "Lallai Mari. Ke ko 'yar kunyar nan ta dan fari ma ba kya ji har kike kallon idon Malam kina cewa a bar miki da a gabanki?" Uwargidan Mal Sa'adu ta furta da sigar nuna tayi ba daidai ba. "Ko ma dai mene ne wannan sabon abin da ki ka zo dashi ba al'adar gidanmu bace. Zuri'ar gidan nan suna zuwa almajiranci tun talan-tale. Naki dan da bai fi na kowa ba shi ma zai je. Sai dai kuma idan zaki sake masa uba." Mal Sa'adu ya kare da tsorata ta. Idan aka ce ta sake masa uba tamkar ana tuhumarta da laifin haifar dan da ba na sunna bane. Muryarta a karye ta bashi hakuri "Allah Yasa hakan shi ne mafi alheri." "Karatun allo hairan ne! Abbati zai je kamar sauran 'yan uwansa ya rubuce sittin kuma ya haddace shi." 'Nima haka nake fata' Mari ta ce a ranta tana mikewa tsaye. Jiki ba kwari ta shiga dakinta tana jin kamar an zare mata laka. Wannan karon an mata fin karfi amma ba za ta yarda badi a kai Sani ba. Kafin ranar tafiya ta shanya kanzo gari guda ta gyara masa. Man gyada ma ta soye shi da albasa ta kuma daka masa yaji. Tayi kuli-kuli, carbin malam, hallaka kwabo da duk wani abu da take tunanin zai ci daidai karfinta. Nasiha kuwa har ya soma gajiya da ji. "Ka yiwa malaminka biyayya Abbati." "Banda kwadayi ko dauke dauke." "Idan an turaku bara ka ce na hana. Ga kayan abinci nan ina ta hada maka hatsi. Zan fadawa Babanka ya bawa malamin. Idan ya so in sun dora sanwa a dinga dibar maka." "Abbati kada ka je bara fa. Daga cikin gidan wani zubin sai an zageka an zagi uwar da ta kawoka duniya kafin a baka kwantai." "To Baaba" yake cewa ga duk nasihar da fadan nata. Har yanzu bai san ma'anar karatu da ake cewa za'a kaishi tare da sa'ansa dan yayan Inuwa ba. Yayyansa da suka tafi garuruwa daban daban yake sha'awa. Idan zasu zo suna dan kullo tsarabar birni su kawo. Kuma shi da Baaba ke son ya zama likita yanzu ne zai yi karatu na 'yan birni ya fara allura. Mari tayi kuka sosai ranar da zasu tafi. Bai taba nisa da ita ba musamman saboda tsoron fadansa. Indai rigima ake yi da wuya ka ga Abbati a ciki. A gidan manya da yara idan ka cire mahaifansa da 'yan uwan babansa ana tsokanarsa da Abbati solobiyo. Rashin kuzarinsa yana daga cikin manyan dalilanta na son ya zauna a gida. Kazalika shi ne ya kara rura wutar kiyayyarta da zuwansa almajiranci. Banda iyayen sun riga sun farlantawa kansu kai yaransu maza akwai makarantu yanzu a garin nasu na ilimin islama. Har soro ta fito tana kuka da zasu shiga a-kori-kurar da ta zo daukarsu. Hawaye take wani na bin wani tana ta nanata masa abubuwan da ta fada masa. "Mu kuwa kamar tsinar namu 'ya'yan muke bamu san zafin nakuda ba." Cewar guda cikin faccalolinta. Wata ta amshe da cewa "mu da aka jima ana daukar namu ba." "Wai kuma a haka fa don dan fari ne. Wannan da Sani ne zai tafi sai tayi mana karamin hauka." A gigice ta kalli amaryarta da ko haihuwar fari bata yi ba tana neman ballo mata ruwa. Ranta a bace ta ce, "Bakin ki ya sari danyen kashi. Sani ba zai je bara ba da yardar Allah. Wannan ma don anfi karfina ne." "Ai kuwa zan nuna miki babu dan da za ki fi karfinmu a kansa. Kai Inuwa.." Mal Sa'adu dake bayan matan ba tare da saninsu ba ya yafito kaninsa "tsayar da direban nan ka hado kayan Sani." Ba Mari ba shi ma sai da ya razana. Sani shekararsa tara ga karamin jiki kamar dan bakwai. Mal Sa'adu ya juya a fusace ya kira ragowar kannensa. Duk wanda dansa sai badi zai tafi ya ce a hada masa kaya yau. Sauran matan basu ji dadi bane saboda basu shirya ba. Mari kuwa da ta gama magana da kanwar Inuwa dake aure a Kazaure sai da ta kusa haukan da ake kira mata. Sun gama shiri za ta dawo ta ce a bata Sani saboda bata da namiji sai ta tura mata kudi a kaishi bodin. A buhu Inuwa ya cusa kayansa tana kuka tana tumami amma Mal Sa'adu ko gezau. Inna Mairo ma tayi masa magana ya ce babu matar da za a auro tafi karfinsu. Idan bai yi haka ba sauran ma zasu raina mazajensu ne. Kukan Mari a kofar gida har makota ana ji. Ana saka Sani a mota ta sauko dashi tana magiyar a barshi ta yarda a tafi da Abbatin. Ita a nufinta ko shi kadai ya yi bokon ya zama wani abu a gaba zai taimakawa yayansa. Shi kuwa Abbati da zuciyar kuruciya sai ta ayyana masa mahaifiyarsu bata kaunarsa tafi son kaninsa. Kukan shi ma ya saka ta mika hannu za ta sauko dashi Inuwa ya daka mata tsawa. "Ki mayar dasu ko su sauko ku kama hanyar gidanku tare." Ransa ne ya baci da jama'ar da ta tara musu ana ta gulmarta wai bata da rikon addini. Mutanenmu da matukar tsoron kalmar saki. Ba arziki ta saki yaran tana zaman 'yan bori a kasa. Tana ji tana gani motar nan tayi gaba aka tafi da 'ya'yanta. Abbati za'a sauke shi a Kano shi kuma Sani da sauran yaran a Zaria saboda can ne suke da manyan yayye. MARI: Ga Mari ba mutuwar auren kadai take tsoro ba harda inda za ta kai yaran. Iyaye basa raye ga talaucin kauye. Idan aurenta ya mutu kannensu ma masomin tagayyarar rayuwarsu kenan. A wannan lokacin maslahar da ta hango bata wuce ta sadaukar da mafarkin cigaban manyan 'ya'yanta akan rayuwar kannensu ba. ***** KANO 1995 "Masu gida. Magadan Alhaji. Ku zo ku dauka na gama rabawa" Asabe ta kira 'ya'yanta tana rangwada murya. Gajeren tsaki gami da murmushi Innayo tayi ta cigaba da barar albasar gabanta. Ina abin gado a tattare da Alh Rabi'u har da mutum zai yi tinkaho? Tabbas arzikinsa ya karu a shekarun nan haka kuma tsiya ta rashin son wadata iyalinsa ta kankama. Innayo bata sake haihuwa ba tun Hasiya. Asabe kuwa ta jera maza uku bayan wanda suka yi goyo tare lokacin Hasiya. Salon kishin Asabe ya dade da dena bata mata rai. Ita bata yarda bane sai ta cusa mata haushi ta kowane hali. Innayo kuma bata da wannan lokacin. Har yanzu da ta aurar da duka 'ya'yan uwargidan Alh Rabi'u bata hakura da dena neman kudi ba. Yadda ta gina su haka take ta fafutukar gina nata. Dukkansu sai da suka gama sakandire da guminta aka yi bikinsu. Abu daya ke yi mata ciwo a rai wanda yasa ta dada jajircewa akan 'ya'yanta. Tun lokacin bikin A'i babbar 'yar Alh Rabi'u mahaifiyarsu ta sake bayyana a rayuwarsu. Mijinta Kansila ne a lokacin suna ta damashere da dukiyar talakawa. Innayo bata son auren ta kuma fadawa A'i, amma sai ta tsallake ta sanar da mahaifiyarta Laraba. Ita kuma ta tsaya mata sun ga mai arziki. Alh Rabi'u dama tuni ya mika wuya ya yi mubaya'a ga wannan hadi. Tana ji tana gani akayi auren. A'i da kannenta suka koma jikin mahaifiyarsu. Ita dai bata fasa yi musu komai da ta saba ba amma tsakaninsu babu wannan mu'amalar ta uwa da 'ya'yanta. Komai nasu na shawara da Laraba suke yi. A ranta ta kan ce uwa uwace! Shekara na zagayowa Kansila ya biyawa A'i, Alh Rabi'u da Laraba hajji. A gabanta kannen A'i suka shigo da tsaraba mai tarin yawa ita kuwa da 'ya'yanta aka bisu da dan madina da bagaruwa. Alh Rabi'u kuwa 'yan mazansa ya gwangwaje ya bata robar zam-zam irin 'yan kulalan nan adadin 'ya'yanta. "A sha a sami tubarrakin Annabi Isma'ila." Ya ce lokacin da ya ajiye mata a gefen katifa. Idan ta ce wannan abu bai yi mata ciwo ba tayi karya. Ita ma za ta so nata 'ya'yan su zame mata inuwar hutawa a gaba. Auren irin su Kansila da ta san dukiyar yawanci zuwa take ta tafi da an gama gwamnatinka ne bata so. Sai ya zamana bata da dare bata da rana. Sana'ar abinci ta iya kuma ita ta kara fadadawa. Muryar Zara ta ji wadda Hasiya take bi tana magana bakin tsiwar nan a gaba ta zumburo shi. "Ni dai gaskiya ki canja sana'a Innayo wallahi gulmarmu ake yi a makaranta. Ko? Ko Hasiya?" Ta waiga bayanta inda Hasiya ta tsaya jikin kofa. "Ni dai ban sani ba." Hasiya ta ce tana ja da baya gudun fadan Innayo. Haushi ya turnuke Zara ganin Hasiya za ta bata mata shiri ta harareta. "Banza kawai. Ke kin fi so a dinga jin tsamin geron 'yar tsala a jikinki duk safiya a makaranta" Ita da gaske take son mahaifiyar tasu ta sami wata sana'ar ba ta abinci ba. Sai da Innayo ta gama barar albasar ta daga kai "yau ke ce da yin danmalelen dare. Ga albasar nan ki yanka kanana Hasiya za ta karbo tumatir ki hada." "Innayo" Zara ta kira ta kamar tayi kuka. "Mai abinci ta fi almajira kuma ta fi mai shiga makota tana bani bani. Idan kin raina min sana'a ni ki ka raina." Ta bata amsa ko kadan muryarta bata daga ba. Daga gefensu Asabe ta tsoma baki tana dariyar shakiyanci "sunan wani wai shi girkau. An tasa yara a gaba ana ta kone musu sinadarin kyau da wutar icce ai dole su yi bore. Shiga makota bani bani kuwa dabara ce sai mai wayo. In mutum ya isa ya gwada mana." Innayo bata kula ta ba sai 'ya'yanta da ta bi da kallo daidai suka fahimci ma'anar kallon. Daki suka shige Zara tana botsarewa ita a dole bata son aikin. "Tara ki nake yi Zara. Idan ki ka kaini bango kin san sauran" cewar Innayo daga bakin kofa. Zara bata kara cewa komai ba. Innayo na fita kamun bikin 'yar kanwarta da yamma ta turawa Hasiya aikin da jan kunnen kada ta sake ta ce ita tayi. Bayan Hasiya ta gama ta fita waje kiran almajirin da yake kai musu bakin hanyar wata makarantar dare tayi. A kofar gidansu yake zama da an yi magariba. Tana jiran karasowarsa daga daya tsallaken layinsu a-kori-kurar da ta dauko su Abbati ta zo ta wucesu zuwa makarantar dake cikin unguwar. "Kai ina Munzali?" Suka ji muryar Asabe daga bayansu. Rabonta da shi tun kafin ta sauke abincin rana. Shi ne babban danta namiji. "Ban gan shi ba" yaron ya bata amsa. "An ce min tare ku ke zuwa filin kwallo." "Bai je ba yau. Su Shazali ya bi yawo." Da ta bi ba'asi sai ta gane su Shazalin wasu matasa ne almajirai kamar yaron Innayo din. Hankalinta ne ya soma tashi saboda an kusa Isha'i. *** "Cire wandonka na ce" Shazali ya ce da fada saboda bata masa lokaci da Munzali ke neman yi. Idanu a waje cike da tsoro Munzali ya sake kama wandonsa ya kankame. "Na ce maka bana jin komai. Ni gida zani Asabe za ta dakeni idan ban koma ba." "Kai ma ka tsaya sai wani lallaba shi kake yi. Dalla bani wuri na nuna maka yadda ake yiwa sababbin shiga." Cewar wani dan kwaya abokin Shazalin. Matsawa ya yi ya turo masa Munzalin da ya fara turjiya gabansa. Shi ya rike hannuwan abokinsa kuma ya dauke Munzali da mari kafin ya zare wandon ya yi wurgi dashi. Dariyarsu ce ta fara karade kangon kafin ihun azaba da Munzali ya saka yana kiran AsabI just published "3" of my story "UWA UWACE...". https://my.w.tt/jlkjBC37l8 UWA UWA CE...3 Batul Mamman💖 Duk duniya babu mai rufa maka asiri sama da mahaifiyarka. Komai lalacewar da sai ta kure sai kuma ta jure za ta iya fadawa duniya. Da mai kyakkyawar zuciya da ma mai akasinta duka suna yi ne domin kada rayuwar dansu ta lalace a wani mataki. Amfani ko kuskuren yin hakan ga dan da akayi dominsa kuwa gaba ce kadai za ta nuna. *** Tsohuwar naira biyar da ta gama shan wahala tsakanin kwandastoci da direbobin tasi ta yayyage Shazali ya dauko daga aljihunsa. "Ungo ka tafi gida." Ya sakawa Munzali a aljihun gaban rigarsa. Yaron da kyar yake tsayuwa saboda bakar azabar da ya sha a hannunsu. Da ya tashi tsaye ma kafafunsa duka rawa suke yi. Warce kudin abokin nasa da suka tafka ta'asar tare ya yi yana magana irin ta takadiran 'yan kwaya. "Kai da talo-talo ne wani sa'in. Banda hauka ya za ka ce ya tafi gida bamu yanka masa wainin (warning) ba" kwalar Munzali ya ci ya fizgo shi gabansa ta karfin tsiya sai da ya yi kara "idan ka sake ka fadawa wani abin da muka yi maka sai na yanka uwarka. Ka san dai na santa ko? Ko ba Asabe Gantali ba ce gyatumar taka?" Ya karashe da yi masa tsawa. "Ita ce" Munzali ya amsa da sauri jikinsa na bari. Ga ciwo ga tsoro. Sai da suka tabbarar ya gama tsorata sannan suka kama gabansu. Tsoro bai bari ya zauna a wurin da sunan ciwo ba. Ga duhu ga kukan kwari da kananan dabbobin da suka mamaye kangon. Da jan kafa ya fito yana cije baki tare da runtse idanu. Idan hawaye ya taho sai ya sharesu da sauri saboda ya rike kashedin da aka yi masa. Tafiyar minti shabiyar zuwa gidansu sai da ya rubanya ta. Asabe sai kai gwauro da mari take yi wurin neman Munzali. Ta shiga duka makota gidajen da yake da abokai bata same shi ba. Nemansa take yi saboda nutsuwar kanta ba wai don Alh Rabi'u zai yi mata fada ba. Tarbiyar yaran a wuyan uwar da ta kawosu duniya ya rataya a nasa tunanin. Ummakati yayarsa ta gama karantawa wasu gidajen da za ta je ta fita ita ma ta sake daukar mayafi. Tana isa soro Munzali na shigowa. Basu da wutar nepa amma akwai hasken farin wata saboda wurin babu rufi. Kunnensa ta jawo iya karfinta sai da ta durkusar dashi a gabanta sannan ta hau shi da fada tana jibgarsa. Bata taba yarda hukunya 'ya'yanta a gaban Innayo. Kullum nunawa take nata 'ya'yan basa laifi. Munzali bai yi kuka ba ko ya roketa tayi hakuri kamar yadda ya saba idan ya yi mata laifi. Zazzabi yake ji ga ciwo babu wani sauran kuzari ko da na kuka ne a tare dashi. "Shegen yawon tsiya kamar wanda makiya suka sako a gaba. Ban hanaka yin dare a waje ba? So ka ke babanku ya sani ya daina baka kudin makaranta?" Naira biyar din da Shazali ya bashi ce ta fado ta kyalla ido ta gani ta dauka ta karkade. A kirjinta ta soke kudin sannan ta cigaba da yi masa fada kunnensa a tsakanin yatsunta tana ja. "Ki yi hakuri Asabe." Ya iya cewa da kyar yana jan jiki. Bayansa ta bi tana cewa gara ma ya saki jikinsa domin bata yi masa dukan da zai saka shi irin wannan tafiya ba. Ko kadan tunaninta bai bata ta binciki inda ya sami kudin ba. Ita bata ma son tayi zancensu bare ta ji cewa ba wadanda za ta iya ci bane. Inda ya je ma ba laifi bane indai zai dawo kafin duhun dare. Innayo ya wuce bai gaisheta ba kamar kullum. An koyar dasu kiyayyar kishiya da 'ya'yanta tun kafin su gama wayo. Yana shiga bandaki ya fashe da wani sabon kukan. Bai taba jin ciwo makamancin abin da yake ji yanzu ba. Ga cikinsa ya kulle amma yana tsoron yi ya tadowa kansa sabon ciwo. Kukansa ya sha ya dauki wandonsa da ya baci da jini ya jefa cikin shaddar (masan kasa) ya fito. Rigarsa ta wuce gwiwarsa ma saboda haka babu mai gani. "Munzali ina wandonka?" Muryar Alh Rabi'u ta karade tsakar gidan. Kafin ya bada amsa Asabe tayi saurin amshewa ta ce wai don ya ga babu wuta ne ba mai ganinsa shi yasa ya fito. "Zai gyara Alhaji. Da kaina zan yi masa fada." Ta ja hannunsa "Bashi hakuri ka wuce muje ka ci abinci." Da dassashiyar murya ya ce da Alh Rabi'u ba zai kara ba. Shi kuma jin muryarsa a haka ya tambaye shi me ya same shi. Nan ma Asabe bata bari ya yi magana ba saboda kada wani ma ya ji cewa tayi masa fada ya yi kuka. "Mura ce. Murar zafi ce Alhaji. Ka san ta da bakin naci." Gyaran murya ya yi abinsa ya wuce ba tare da ya sake kulasu ba. Da yaje daki ya tarar da abincinsa wanda Innayo ta kai ta ajiye kafin ya shiga dakin. Da kafa ya ture farantin da ta jera langar tuwo da miya a kai ya zauna yana sassauta daurin tazugen wandonsa. Daga gidan wata sananniyar mai danwake yake ya ciko ciki. A kasuwarsu magidanta kalilan ne basa sayen danwakenta. Ga tsire da ya saya ya hada dashi da lemon kwalba. Wata uwar gyatsa ma ya yi ya kwanta zai yi bacci. *** "Mungode fa da ka saukemu Malam har kwana biyu. Ba don kai ba da sai dai nayi kwanan tasha." Cewar Inuwa yana mikawa Mal Alto hannu. "Babu komai. Ni ke da godiya da ku ka kawo danku wannan makaranta mai tarin albarka." Tsamurarren malamin ya bashi amsa idanunsa akan buhu da kullin ledojin dake gaban Inuwa. Kamar Inuwan ya gane ma'anar kallon kuwa ya fada masa cewa kayan abinci ne ya kawo masa. Ya turo mafi girman buhun wanda shi ma ledoji ne a kukkule a ciki da murmushinsa. "Wannan kuma kayan abincin Abbati ne. Akwai kanzo da hatsi harda shinkafa. Da yake yana da 'yar matsalar shiririta shiyasa uwar ta ce don Allah kada a barshi ya je bara. Ko rana da dare ne kadai idan anyi girki daga cikin gidan a zuba masa. Wallahi ba ma shi da ci sosai." Wani irin kallo yaga Mal Alto yana binsa dashi ya yi maza ya kara da cewa "kuna iya saka shi wanki, shara ko aike. Fatanmu ya samu ilimi mai amfani kamar 'yan uwansa ba sai ya hada da barar ba." "Ba damuwa. Bara ce dai kadai baka so ko? Iyalina zasu dinga girki dashi. Kar ka damu." Haka nan zuciyar Inuwa bata aminta da kalaman Mal Alto ba amma bashi da zabin da ya wuce barin dansa a nan. Idan ya mayar dashi gida Mal Sa'adu ba zai masa ta dadi ba. Har ransa shi ma ba ya ra'ayin yaransa suyi barar amma bashi da zabin cewa a'a. Zuciyarsa ta kwankwashe shi akan ya tafi da dansa sau ba adadi amma ya ki ji. Nan gaba kadan yana sa ran a kira Abbatinsa da Gwani. Haka nan ya fice ya barshi kamar yadda ya baro Sani a Zaria ya kama hanyar tasha zai koma gida. Abbati kuwa ya yi kuka sosai. Bayan kimanin rabin awa da fitar Inuwa lokacin Mal Alto ya tabbatar duk inda yake yana hanyar Kirikasamma. Dorinarsa wani babban dalibinsa ya dauka ya zubawa Abbati a baya shi kuma bai ce komai ba. Dalibin da yake yin abin daya san malamin nasu ya yi na'am dashi ya ce, "Tashi shagwababbe. Ni ban san akwai sangartattu a kauye ba sai yau. Wai kada a bari kayi bara. To uban me ya kawoka birni idan ba shinkafa da miya ba? Babban naka ya raina Malam ma." A firgice Abbati ya tashi yana kuka hannuwansa na susar inda bulalar ta same shi. "Ku je a bashi roba ya bi 'yan uwansa bara idan an fito daga karatu shabiyun rana. Sannan ka fada masa duka tsare-tsaren tafiya barar don kada a sami matsala." Cewar Mal Alto kai a kasa yana jan wani katon carbi kamar ba shi yake maganar ba. Ba kowa ya san halin Mal Alto ba saboda iya kankantar da murya da nuna shi na kwarai ne. Ya goge sosai wurin ci da addini. Mutane suyi ta kawo masa yaransu yana bautar dasu. Idan an tashi komawa gida kuwa sai an yi dogon gargadi akan iya rike baki kada a fadi me yake faruwa a makarantar. Da yake yana taba tsibbu a boye har rubutun kafe yaran yake yi. Duk wanda yaje ganin gida sai ya dawo. Wadanda wahala ta zamewa jiki har suka rika suka fara yawo irinsu Shazali kuma suyi ta dauko masa magana. Akwai 'yan daba, 'yan kwaya, masu haura katanga da duk wani nau'in gagararren mutum a gidan. Karatu ne suke yi babu ikilasi ko kankani. Idan mutum yayi magana cikin 'yan unguwa ace yana kalubalantar karatun addini. Ana fitowa shabiyun rana aka bashi wata kodaddiyar roba. Kayansa kaf dinsu har na jikinsa an dauka an kai cikin gidan Malam. Akwai wadanda girmansu ya zo daya a cikin 'ya'yansa. Jakar kayansa ta koma babu komai sai wasu tsummukaran kaya da aka fito dasu daga cikin gidan. "Kafin karfe uku ka tabbatar ka dawo." Abbati ji yake kamar mafarki yake yi. Babu abin da ya fahimta a karatun har suka fito saboda fargaba. Ya dauki kwano ya bi bayan wasu yara da ya zauna kusa dasu da ana karatu. Wani lungu suka shiga ya daga kafa da saurinsa ya cimmusu. Babban cikinsu ya saka dariyar muguntap suka cigaba da tafiya har karshen lungun ashe bayan gidaje ne. Tarfa shi suka yi babban ya tattale masa keya. "Ba kaine aka ce ba za ka yi bara ba? Ya muka ganka da kwano?" Sauran suka sa dariya. Hannuwansa duka biyun a keyarsa yana kare dukan da suke yi masa na cin zali ya ce "Don Allah ku bari na biku." "Ai baka isa ba. Ka nemi hanyar da za ka dinga bi saboda gidajen nan wurin namu ne. Idan muka kara yawa abincin ba isarmu zai yi ba." Wasu na duka da kafa wasu da hannu a haka suka kore shi daga lungun jikinsa duk ya yi futu-futu da kasa. Gefen hanya ya samu da ya gaji da yawon ya zauna gashi ko wakar barar bai iya ba. A nan bacci ya yi awon gaba dashi kudaje suna ta kai kawo a jikinsa. Munzali ne ya fito daga gidansu da jan kafa ya hango Abbati yana bacci a karkashin bishiyar kofar gidansu. Yau kwana biyu kenan da gamonsa dasu Shazali. Rashin kula na Asabe yasa ta yarda da ya ce mata a wurin bal ya turgude kafa shi yasa baya tafiya da kyau. Da kafa ya shuri Abbati ya tashi a tsorace yana rarraba idanu. Kansa ne ya juye ya manta a ina yake sai da ya ga robar bararsa. Munzali ya kankance ido ya ce "kai dan makarantar Mal Alto ne?" "Eh." "Shi ne kayi kwanciyarka kana bacci gashi har anyi la'asar sun kusa fitowa. Tabdi. Wallahi duka ake yiwa marasa komawa da wuri." Ba a makarantar yake ba amma layin bayansu take. Yawancin abokan buga kwallonsa daliban can ne. Duk wanda ya makara wurin komawa ba karamin duka yake sha ba. Kwal-kwal idanun Abbati suka yi da hawaye sai ya bashi tausayi da ya ce masa ba zai gane hanya ba. "Muje na raka ka amma ba zan shiga layin ba." Ya ce don yana gudun sake haduwa dasu Shazali. Har farkon layin ya kai Abbati ya juya zai tafi ya hada ido da Shazali. Fitsari ne ya subuce masa tsabar fargaba ya fara ja da baya. Jan hannun Munzali da Shazali ya yi daidai da waigowar Abbati. Yana kallo har suka bacewa ganinsa. Bai san meye tsakaninsu ba kuma ba ihu Munzali yake yi ba shi yasa bai yi tunanin komai ba. Kangon suka koma babu mutane ko hayaniya a wurin. Hannu Shazali yasa ya toshe masa baki sannan ya kuma maimaita masa rashin imanin nan. Sai da ya gama ya lura da hawayen dake fuskar Munzali shabe-shabe da majina. "Allah Ya isa. Mugu. Azzalumi. Dan wuta." Cikin bacin rai Shazali ya riko habarsa ya matse "Ni kake zagi Munzali? Don ma ka samu ina sonka. Idan ka ce zaka yi min rashi kunya tattaka ka zanyi in taka banza a wurin nan." Da kafa ya shura masa daurin bakar ledar da ya riko tun kafin su zo wurin. Munzali ya bude yaga langa ce cike da shinkafa da miya harda nama yanka biyu. Ga salad an yanka da tumatir da albasa. Duk wannan bakar wahalar da ya sha sai ya nemeta ya rasa a lokacin. Ga zobo kullin naira bibbiyu guda biyu da sauran kankararsu. Hannu baka hannu kwarya yake danna shinkafar nan. Ba shi ya daga kai ba sai da ya sude kwanon tas. Rabonsa da shinkafa da miya tun sallah karama da A'i ta aiko gidansu. Wata hudu kenan. Wanda ake ci a dakin Innayo kuma Asabe ta ce ta tsine idan suka karba. Wai guba za ta saka musu saboda bata da maza. Tafi ganewa girka musu wulakantaccen abincin da Alh Rabi'u ke kawowa. Shazali na kallonsa ya saki murmushi "nima kudi na samu a wurin Alhajin da yake min irin abin da nayi maka. Idan kana zuwa wurina kullum har kaza zan saya maka da tsire." "Akwai ciwo don Allah kada ka sake." "Kai dalla can baka san idan ana yi kullum zaka daina jin zafin ba? Da kan ka za ka nemeni wataran." Ya yi masa wata irin dariya. Da wayo ya dinga hillatarsa har ya amince gobe zai zo kangon ya same shi. Da zai fita ya sake bashi naira biyar tare da gargadi. "Muddin ka sanar da wani da kai da duka 'yan gidanku zan kai gidan yankan kai!" Sai bayan kwana goma suka sake haduwa da Abbati da jikinsa duk tabo da sabbin ciwuka. Daga bara Abbatin yake bai samo komai ba zai koma makaranta. Ranar ta kama alhamis ba sa karatu. "Don Allah muje gidanku ko kanzo ne ka kankaro min." Ya roki Munzali. "Nima babata bata da abinci. Ka dawo anjima idan kun fito barar dare zan baka abinci Yasin harda nama." Cikin Abbati har wata kara yake saboda yunwa ya amince a guje. Kayan abincin da yazo dasu Mal Alto ke ci. Gashi bashi da aboki ko daya cikin 'yan uwansa almajirai kamar ma sun tsane shi. Hasashen Shazali ya zamo gaskiya. Kwana biyu Munzali yana riga shi zuwa kangon. Ya saba yanzu ko babu kudi so yake ayi. 'Yan biyar biyar da yake batarwa a sayen kayan kwadayi har yau Asabe bata tambayi inda yake samo 'yan canji ba. Ranar da ta tsinci naira goma a aljihunsa ma boyewa tayi da sauri tana murna. "Masu 'ya'ya mata ne da fargaba idan an gansu da kudi. Da namiji kuwa indai ba barawo bane babu inda zai samu sai wurin abokan arziki." Ta murmusa ita kadai "Munzali ba dai jama'a ba. Duk inda ya gifta sai an kira shi." Kamar yadda ya alkawartawa sabon abokinsa da ko sunan juna basu sani ba da kansa yau ma yaje kangon. Shazali da wannan abokin nasa yazo. Bayan sun gama aka mika masa langar abinci da naira goma. Dadi kamar ya kashe shi. Ya duka yana juye abincin a leda Shazali ya tambaye shi me yasa ba zai ci a nan kamar kullum ba. "Aboki nayi wani sabon zuwa a makarantarku. Abin tausayi idan ya yi bara ba ya samun abinci." Dan tsorata Shazali ya yi "ina fata baka fada masa me muke yi ba ko?" "A'a." Yana kallon kofa ya ce "In tafi? Na ce ya jirani." Sallamarsa suka yi ya tafi da murna. Bai shiga gida ba saboda ya san sai Asabe ta ci ko bata bawa 'yan uwansa ba. Bai jima ba kuwa ya hango Abbati yana layi kamar zai fadi saboda yunwa. Karancin shekarunsa basu hana shi tausaya masa ba. Zuciyarsa tana da saurin rauni wanda da ace ya sami kyakkyawar tarbiya da kulawa da anyi mutumin kirki abin alfahari. Shekarunsa goma amma ya san ya gane mabukaci kuma ya yi abin da zai sama masa mafita daga yunwar da yake ji. Cikin soron gidan makotansu da ba kasafai ake bi ba ya ja shi suka shiga ya bude langar. Abbati yawu ya tsinke jikinsa yana rawa ya tsoma hannu a ciki. Tare suka ci amma Munzali bai fi loma uku ya yi ba. Abbati ya barwa abincin. "Nagode. Nagode don Allah ka ce da mamanka nagode kaji." "Ba Asabe ce ta bani ba. Wani abu nake yiwa wasu sai su bani abinci idan an gama." Mamakin ashe akwai aikin dake kawo abinci irin wannan Abbati ya yi "zan yi. Don Allah kaje dani gobe." Cike da kuruciya Munzali ya ce "kai wallahi sun ce idan na fada zasu kaini gidan 'yan yankan kai." Jiki a sabule Abbati ya koma ya zauna murnarsa ta koma ciki. Wani tunani Munzali ya yi ya ce masa "kasan me? Ni suna bani kudi ko abinci. Idan naje aka yi dani kai ma sai nazo nayi maka sai na sammaka kudin ko abinci. Ka yarda?" Wata dariya Abbati ya saka ya washe bakin da ya bayyana gibin turamensa biyu. "Na yarda." Munzali ya mike tsaye yana cewa "amma fa idan ka fada zasu yankamu har babarka da babanka." "Ba zan fada ba." Abbati ya nanata yadda zai amince masa. "To tashi ka cire wandonka." A cikin soron da babu wadatar haske Abbati ya zaro idanu "cire kuma? Iskanci ne fa. Wai ma ya sunanka?" "Munzali." "Ni kuma Abbati. In fada maka Baaba ta ce duk wanda yake cewa a cire wando wuta zai je ba zai ga Annabi Muhammadu (SAW) ba." Dariya ce ta kama Munzali ya ce "kai nima haka na zata. Ashe wai idan aka yi da mace da namiji ne mutum zai shiga wuta. Irin wannan kuwa dadi ake ji kuma a baka abinci." "Baaba bata fada min namiji yana cewa namiji ya cire wandi ba. Kila da gaskiyarka shi ba na 'yan wuta bane." A wannan daren Abbati mai shekaru goma sha biyu amma babu wayo da idon uwa ya fara koyon wannan mummunar dabi'a saboda yunwa da rashin gata a wurin Munzali. Munzali da ya koya masa bai san muni da zunubin dake cikin wannan alfasha ba saboda rashin saka ido na uwa da uba. Daga wannan ranar abotarsu tayi karfi. Munzali zai jure ko mutum nawa Shazali yazo dasu ayi a bashi abin da za'a bashi saboda Abbati ya ci abinci. Ana fitowa barar dare Abbati zai zo suyi shima ya biya shi. Abincin tare suke ci sannan ya raba musu kudin daidai. Zuciyarsa bata taba raya masa ya cuci Abbati kada ya bashi kudin da ya samo ba. Abin taysayi. Abin kuka. An kulla abotar kuruciya da aka so ginawa bisa alkhairi amma mummunar alfasha ta zamo jigonsa. Kaico! Allah kadai Ya san Abbati da Munzali nawa ne a tare damu cikin wannan masifa bamu sani ba. Wasu suna mu'amala da 'ya'yanmu wasu da kannenmu. ***** "Ke kuwa Khadija kamar me haihuwar fari me ya fito dake yawon arba'in? Ko har kin gama warkewa?" Yakumbo ke wannan fadan tana karbar jaririya Sauda daga hannun Khadijan. Su Lilu kowa da murnarsa ya je jikinta suna tambayar ta ire iren cimar da take ajiyewa a dakin domin jikoki. Sai da ta sallamesu suka fita daga dakin sannan ta zauna suka sake gaisawa da Khadija. "Jiki ya yi kyau. Allah Ya kara miki lafiya. Naji dadi sosai da yadda ki ka karbi kaddararki. In sha Allahu wadannan yara zasu zame miki sanyin idaniya. Allah Ya muku albarka." "Amin" Khadija ta amsa tana kokawa da hawayen dake son zubowa. Ita kadai ta san irin bacin rai da bakincikin da take kunsa a wurin Tahir a kwanakin nan. Nasima bata kara zuwa gidan ba tunda ta koma. Sai dai ya fito mata da salon wulakanci irin na namijin da ya fahimci karin aure a matsayin lokacin cin zarafin ta gida. Bata yi sati da komawa ba ta canja shawara ta ce ya saketa. "Kin san abin da zai faru idan muka rabu. Kowa zai san me nake yi kuma kan 'ya'yanki zai koma." "Na sani Tahir amma duk da haka ina so ka sakeni kafin zuciyata ta buga. Kayi min adalci albarkacin zaman da muka yi a baya da yaran nan." "Zan miki. Ke ki je ma na sake ki saki daya. Amma ki sani nayi miki rantsuwa ko Yakumbo bata isa ta sakani baki yaran nan ba. Zan daukesu mu koma Lagos tare da Nasima." Cak ta tsaya tana kallonsa idanunta cike da hawaye. "Yaya dama haka kake ko duka son Nasiman ne ya mayar da kai haka?" "Ki dauki duk wanda yayi miki bani da damuwa. Na ce ki zauna mu rufawa juna asiri sai dawo da hannun agogo baya ki ke yi. To ga sakin nan kin samu ki tafi da Sauda idan kin yayeta zan zo na karbi abata." Da kyar ta lallaba ta zauna a bakin gado bayan ya fita. Ta kasa gaskata abubuwan da suke faruwa yanzu musamman sakin da ya furta mata. Halayensa ba bakinta bane a da amma ko a wancan lokacin da yake tashen akuyancinsa yana shakkar ta sani. Yanzu kuwa akan kankanuwar yarinya ya yanke igiyar auren shekara tara. Abin da basu sani ba daga shi har ita shi ne Nasima da Ladidi mahaifiyarta suna kauye ana yi musu aiki akan Tahir. Duk yadda za'ayi ya aureta ko babu izinin iyayensa suke so. Sannan ya fifita ta akan kowa. Shi ya bayar da wannan kofa daga ranar da ya fara nemanta. Ladidi ta san komai game da halayyar 'yarta amma tunda ta zame mata jari shi kenan. Fuskarta ta wanke ta fito falo ta sami kanwarta ta gama girki ta zubawa yaran. Dakinta inda Gwaggo kanwar mahaifiyarta mai kulawa da ita tayi masauki ta shiga. Kuka ta saka mata ta sanar da ita sakin da ya yi mata. Hankali a tashe ta zari mayafi ta tafi gidansu ta sanar da Mama. Tare suka dawo ta kora musu jawabin abin da ya faru. "Khadija na san Tahir bai kyauta ba amma shi ne rufin asirinki. Idan kin fito waye zai auri mace mara mahaifa?" Kai ta girgiza tana karyata cewa mahaifiyarta ce take fadin wannan magana bayan ta fada mata matsalarta. "Dena yi min wannan kallon na fiki sanin halin maza. Kwansu da kwarkwata ban dauke miki uban da ya kawoki duniya ba duk jirginsu daya." Kiris ya rage ta saki Sauda saboda firgici "Baba ma yana neman mata?" Mama tayi murmushin takaici "ban fada miki don ki daina ganin girmansa ba amma babu irin cin kashin da ban gani ba lokacin da yake manajan banki. Ni da yake kawosu har cikin gida ya ce abokan aikinsa ne in yi musu girki." "Me?" Zantukan sun kadata sun yi matukar bata mamaki. "Rayuwarku da tsoron kada ku tagayyara yasa na zauna. Kema kuma ina shawartarki da ki rungumi kaddararki kiyi zaman 'ya'ya." "Yanzu Mama saboda 'ya'ya sai mata su dinga zama da fasikai?" "Idan kin fita kin san gidan wa zaki fada? In kuma baki yi aure ba ina zaki kai wadannan yaran ke ba sana'a ba kuma babu aiki. Babanku ya yi ritaya kannenki ma da kyar ake biya musu kudin makaranta. Ga zumunci da zai lalace kuma karshenta a bar miki 'ya'ya a hannun kishiya ta gallaza musu. Shawara daya zan baki. Idan ya dawo ki roke shi ya mayar dake kafin kowa ma yaji. Dama can an san halinsa ai aka aura miki. Lokacin ba yadda banyi ba aka ce zan raba zumunci." Khadija na kuka Mama ta cigaba da tausarta akan tayi hakuri. Al'adarmu ta fifita farincikin namiji akan mace. Ko mun sani ko bamu sani ba mun nunawa maza zamu nemo dalilin zama dasu duk lalacewarsu saboda gudun zawarci. Babu uwar dake son 'yarta ta fito daga gidan aure amma addini ma ya halarta fitar domin a zauna lafiya. Tahir bai yi mamakin ganinta ba da ya dawo da yamma. Dauke kai ya yi ya shige dakinsa. Zuciyarta na kuna ta tashi ta bishi dakin. "Na amince zan zauna." "Ya dai fiye miki. Ki turo min kofar idan kin fita." Ya ce daga kwance. Bata san daga gidan Yakumbo yake ba ya kai mata zancen auren Nasima ta fattako shi. "Tunanin me kike yi ne Khadija? Inata magana kin yi shiru." Dago kai tayi ta kalli Yakumbo tayi murmushin dole. "Babu komai." Ba yarda tayi ba tunda ta san Tahir yana neman aure. A wannan yanayin ba Khadija ba duk wanda yaji zai kira shi butulu ne. Ace daga cirewa matarsa mahaifa yana kiran sake aure. Nasiha ta dinga yi mata akan karbar kaddararta ta cire mahaifar amma bata sako zancen auren nasa ba. A gidan suka yi azahar sannan suka tafi gidansu Khadija a bayan layin da kafa. Da yamma Tahir ya zo daukarsu ya fara biyawa ya gaishe da Yakumbo. Bai samu sakin fuska ba tunda ya ce mata zai yi aure. " 'Yar waye yarinyar da kake nema ne wai?" Sosa keya ya yi "ba fa bakuwa bace Yakumbo. Mai aikinmu ce Nasima..." Kaf...Yakumbo ta kwade masa baki cikin fushi "mai aikinku fa kace. Kenan ma Khadija ta sani. Wannan wane irin cin fuska ne haka?" Alamun zai mata tijara ta gani sai ta zabi lallaba shi akan dai ta yarda da wannan danyen aiki "Idan auren kake so ka bari Saudatu ta shekara sai ka nemi wata" "Nasima kadai nake so!" "To ba za ka aureta ba duk abinka." Tahir dagewa ya yi babu jin nauyi ya nunawa mahaifiyarsa fa bata isa ba. "Akan mace nake fada kana fada Tahir?" "Meye aibunta? Ba gara na auri wadda Khadijan ta sani ba." Tsananin bacin rai yasa ta samun wuri ta zauna tana rike kai. Wani tunani ne ya darsu a zuciyarta ta kalle shi a razane. "Wannan bakin naci da kake kafa min akan yarinyar nan anya wani abu bai shiga tsakaninku ba?" Kai ya sunkuyar yana wasa da mukulli bai musanta zarginta ba. Hawaye tuni ya balle mata ta nuna shi hannu na rawa "Khadija ta san ita kake neman aure ko?" Da ka ya amsa mata. "Ko dai ta kamaku ne?" Nan ma da ka ya amsa. Yakumbo taji kamar ya soka mata kaya a kahon zuciya. Tashi tayi tana kaiwa duk inda ta samu a jikinsa duka. "Bana so in yi maka baki Tahir, tun kuruciyarka kake gasa min zuciya. Allah Ya sani ban zubar da mutuncina a waje ba amma akanka meye banyi ba. Saboda ka shiryu na tursasa kanina ya baka 'ya. Mahaifiyarta har yaji tayi amma na dage ko ayi ko in saka shi ya saketa. Tahir duk kai na yiwa wannan" kuka ne yaci karfin Yakumbo ta kifa kai a cinyarta. Jikin Tahir ya dan yi sanyi amma a ganinsa akan me zata hana shi auren da addini bai shata masa layi a kai ba. "Idan nayi auren nan ba zan sake bin wasu ba." "Iya abin da za ka iya cewa kenan? Akwai hakkina, da na matarka da na zuri'arka mai zuwa a gaba ma da na gabanka ba a wuyanka. Tahir. Tahir. Tahir kaji tsoron Allah idan kayi auren nan." Da murnarsa ya tashi zai fita ta dakatar dashi "ban amince don kafi karfina ba. Nayi ne kawai saboda kada ka cigaba da cusgunawa Khadija. Ina jin kunyar iyayenta. Ina nadamar kafewa su baka ita. Kada ka bari Allah Ya sakawa fushina a kanka ko da ban kai kararka gareShi ba." Zuciyarta kamar ta ballo kirjinta take ji. Kalaman mahaifiyarsa sun dan tsaya masa a rai amma biyan bukatarsa ya zarce kwabar da zuciya take yi masa. Ko babu komai akwai zalunci mai girma tursasawa Khadija zaman kishi da Nasima bayan ta gansu ra'ayil aini. Bai san dalilin Nasima na son ya cigaba da zama da Khadija ba amma ba ya son bata mata rai. Asiri ke cin Tahir amma idan bera da sata to daddawa ma da wari. Da bai bawa Nasima kofar ganin tana da matsayin da zai ci amanar matarsa akanta ba da ba za ta taba tunanin mallakarsa ta wannan siga ba. Yakumbo kmar kowacce uwa ita ma ta haifi Tahir tana mai tattalinsa. Tayi fadi tashi dashi har ya zama mutum. Idan yana ciwo tayi kuka ko ta shiga damuwa. Murmushinsa daya tamkar mukullin aljanna yake a gareta. Soyayyarta gareshi bata bari ta sangarta shi ba. Yau fari gobe tsumma haka ta rayu da duka 'ya'yanta. Bata sani ba kuma ba da son ranta ba an wayi gari daya daga cikinsu ya zama mazinaci kuma mara jin magana. Duk da ko 'yar da ya tashi da wannan dabi'a har duniya ta tsane shi ya taba rayuwa a tsumma ana sambarka. Anyi wani zamani da ake mika shi daga wannan hannu zuwa wancan ana cewa 'Allah Ya raya.' Uwa tana ta murna bata san kaddarar da aka rubutowa rayuwarsa. Idan da adalci ba kowane lalataccen da bane za'a zargi mahaifiyarsa. Indai Uwa ce, to burinta yafi kowa shiryuwa ko da bata bada gudunmawar da ta dace wurin yiwuwar hakan ba. Sai mun hadu bayan sallah in sha Allah. Allah Yasa mu amfana da wadannan kwanaki masu daraja da albarka. #StaysafecoronaiWattpad: https://my.w.tt/rNemE3YfS8 UWA UWACE...4 Batul Mamman💖 *** Kwanaki sun zo sun wuce kamar kiftawar ido ya rage saura kwana shida Nasima ta tare. Abin kamar a mafarki haka ya zo wa Khadija. Rayuwarta, iyalinta, mafarkinta da komai nata lokaci guda ya sauya. Mata da yawa a irin wannan lokacin da mazajensu zasu kara aure suna shiga wani hali. Kalmar kishiyar kadai basa so amma idan akwai ilimi, tawakkali da hangen nesa sai mace ta karbi kaddararta har ma ta mori alkhairin da yake ciki. Wadda za'a aurowa mai-aikinta kamar Nasima nata bakincikin yana karuwa ne da tunanin cin fuska da miji ya yi mata. Shi ma da anyi auren an kwana biyu zuciya tana iya samun salama radadin ya gushe tare da shudewar lokaci. To amma idan amaryar ta kasance matar da ta gida ta kama kuru-kuru ce tare da maigidan fa?! Ta ina za ta fara kuma wane bangon za ta dafa domin jin sassauci? Tambayar da ta addabi zuciyar Khadija kenan a yau da Tahir ya fada mata za'a zo jeren Nasima. "Dakina yafi girma saboda haka shi Nasima ta zaba. Ki kwashe kayanki daga naki dakin kafin azahar don za'a jera min nawa kayan a ciki." Magana ce yake yi mata da sigar nuna isa don kada ma tayi tunanin kawo nata korafin. Wato dakinsa Nasima ta zaba. Kodayake babu mamaki tunda ta gama sanin dakunan gidan. Bayanin karshe da ya yi mata na rainin hankali murmushi tayi masa ta amsa shi da 'to'. "Kinga ke za ki tashi da dakuna biyu harda falo." Da hannu ya nuna mata bangaren dakunan yaransu wanda hanyar zuwansa take a gefen hagu na karamin falon gidan. Tsarin ginin na mai karamin iyali ne dama. Idan ka shigo babban falon ne a farko. A cikinsa akwai kofar karamin falon da Khadija kan shiga da bankinta idan Tahir yana da baki a lokacin. Shi sai ya zauna a babban. Dan korido ne a cikin falon da kofa uku. Dakuna biyu sun saka bandaki a tsakiya. Daki daya gadajen yaran ne irin siraran nan. Daya mai hawa biyu, Suhaib a sama Lilu a kasa. Mai hawa dayan kuma na Farha. Daya dakin kuwa karami ne sosai. Nan Tahir ya tsara idan sun kara datawa Farha za ta koma da kansa a da. Idan an koma falon akwai wani korido din mai zuwa dakin Tahir da na Khadija. Ga bandakin baki a falon da kofar kitchen duka a cikinsa. Manyan dakuna ne daidai iyayen gida da bandakunansu. Yanzu ya ce ta kwashe kaya. Bata ma san ta ina za ta fara ba balle yadda za ta yi dasu. A wurin ya barta baki bude. Watanta uku da haihuwa taji sauki sosai. Ra'ayoyin dangi sun kasu biyu game da auren nan. Dadaddun masu bakincikin hadin Tahir da Khadija kamar su zuba ruwa a kasa su sha. Kowa taso ya auri 'yarta saboda matashi ne da ya soma kama naira daga gama jami'a. Mafi yawansu kuwa sun aibata Yakumbo sun ga laifinta wurin bashi goyon baya. Abin da tayi domin tsare auren Khadija ba sani suka yi ba. Zahirin suke gani wato ta fifita dan da aka cuci Khadija aka aura mata. Unguwar Barnawa ma cikin kankanin lokaci ta dauki zancen wani magidanci da zai auri mai'aikin gidansa. Wanda suka san su kuwa sunayensu suke kamawa. Sun sha zagi da muggan fata a bakin mutane a dalilin auren cin amana da ake tunanin sun yi. Makota sun shaida Khadija ta kyautatawa gidansu Nasima sosai. Lokacin da suka tare ta leka duka gidajen layin ta gaisa da kowa. A sannan ta fuskanci bakin talaucin da ya yiwa gidansu Nasima kawanya. Saboda tsabar babu ko tabarmar da za ta zauna basu da ita sai dankwalin kan Nasiman Ladidi babarta ta ciro ta shimfida mata. A take tausayinsu ya shigeta. Kullum da rana tana yin girki ya zarce bukatarsu. Idan ta gama sai ta tura Suhaib ya kira kanwar Nasima ta zuba musu. Tahir ya kan ce kada tasa rai da kwashe ladan saboda yana da nasa kason na mai siyowa. Sai su yi dariya su mayar da zancen wasa. Anyi haka na kamar wata biyu sannan Nasima da Ladidi suka zo godiya da neman aiki. "Idan ya dawo zan sanar dashi sai na fada muku yadda muka yi." Ita ce amsar da ta basu a mutumce. Ba bukatar mai-aikin take yi ba saboda ita ba aiki take ba. Lilu ma shekararsa hudu lokacin. Tsakaninsa da yayyensa dai duka kwanika tayi. Daga kansa ne ta sami dogon hutu. Godiya suka yi mata Ladidi harda hawayenta tana godiya. Cewa ma tayi ko babu albashi indai zasu dauke mata baki daya cikin wadanda take ciyarwa ta gode. "Ni kuwa Nasima ba kya tsoron matan layin nan su tona miki asiri akan irin abin da ya faru a gidan Alhaji?" Cewar Ladidi bayan sun fito. Juya idanu tayi tafiyarta tana canjawa gabadaya zuwa irin ta masu turo kirji gaba. "Kafin su farga na gama dashi." Da sauran rashin yarda babarta ta ce "uhm uhm fa. Kin tuna uban dukan da Hajiya tayi miki da rashin abincin da muke fuskanta saboda babu mai baki kudi yanzu?" Yatsina fuska tayi irin na tantiran da basu ganin kimar iyayensu "wancan ma akasi aka samu kuma dai shi Alhaji matsoraci ne. Amma baban Suhaib dinnan...hmmm" Ladidi ta kece da dariyar jindadi "labarta min. Ko dai har kun fara haduwa ne? Naga kina abu kai tsaye kamar anyi an gama." Murmushi Nasima tayi. Bata son saurin sakawa Ladidi rai amma tabbas ita ta san irin kallon da Tahir yake yi mata duk ranar da suka ci karo a layin. Bayan kwana hudu ta fara aiki. Ladidi jiki na rawa take karanta mata littafin rashin albarka. "Ki bita da ladabi da biyayya. 'Ya'yanta ki jasu a jiki kamar naki. A bayan idonta kuma kada ki dagawa mijinta kafa. Na san indai surar mace na gigita namiji wannan mutumi ba zai gagara ba. Ki janyo hankalinsa sannan ki gara shi ta yadda zai rasa sukuni. Wannan karon gidan nake so ki shiga na gaji da barnar kudi wurin zubar miki da ciki." Dalilinsu daya na biyewa wannan kazamar rayuwa. Uba ya mutu ya barsu da bashi babu gadon komai sai gidan da shima ya gada a wurin nasa iyayen. Danginsa sun yi kokarin taimakawa Ladidi wurin raba 'ya'yan su rike taki amincewa. Ita so tayi su dinga bata kudi bayan suma din babu mai katabus. Girman zumunci ne ma yasa su wannan yunkurin. Ta zauna babu abin da ke shigo mata sai kawai ta nunawa 'ya'yanta cewa dangin babansu basa kaunarsu ne. Ita kuma nata dangin suna kauye ba zuwa za tayi ta zauna ba. 'Ya'yan ne jarinta tunda suna da kyaun fuska da daukar hankali duk talaucinsu. Babbar bata biyewa Ladidi ba. Tafi duka kannenta kyau da kyaun hali. Aurenta tayi a Kaura Namoda tana dan aikowa Ladidi abin da ya samu. Nasima ce ta dasa dan ba a fitina sai mai bi mata ita ma ta fara yawo yanzu. Fuska biyu ta kwararrun munafukai Nasima take nunawa a gidan. Khadija bata ganin wata kofar zargi sai gabanin dawowarta gidan tayata zama da ta fara yi mata rashin kunya. Tahir kuwa sai da yaji duk duniya babu macen da zuciyarsa ke kauna sama da ita. Da kananun shekaru ta kware a barikanci. Sai ya zo wucewa sai ta dinga bude jiki da dabara. "Wayyo kadangare" Ta dinga ihu watarana da Khadija ta fita cikin sauri da Farha ta kusan hadiyar kwankwalatin kwalbar fanta. Asibiti ta tafi kaita ta bar Nasima dasu Lilu a gida. Da yake makira ce tana jin dirin motar Tahir ta turasu daki. Yana bude kofar ta saki zanin tana tsalle-tsalle. "Kadangare ne a zanina" ta ce da kukan kissa tana makale masa a jiki. Tahir an sami abin da ake so ya matso yana cewa ta tsaya ya duba mata. Ya tabbatar Khadija bata gida tunda ta iya yi masa haka. Bai yi kasa a gwiwa ba ya biye mata tunda dama jira yake. Ranar ya fara kaita dakin Khadija yaci mutumcin aurensa a cikin gidansa. Sai da suka fito suna murmushi yake tambayarta inda Khadija take. Kwabe fuska tayi ta soma kikkifta idanu. Muryarta ta karyar kamar mai shirin kuka. "Tun yanzu ka fara nuna min iya matsayina." Jikinsa ya janyota "Me nayi?" "Yanzu yanzu fa kake tambayata matarka. Wato na gama nawa amfanin." Ganin tana hawaye gabadaya sai hankalinsa ya tashi. Rarrashinta ya dinga yi da kalamai masu dadi sannan ya dauki kudi ya damka mata. A fakaice tayi murmushin mugunta sannan ta maida masa kudin aljihunsa. "Ni ba kudinka nake so ba." Wani irin dadi ya mamaye zuciyarsa jin ba shi kadai yake hauka ba. Aljihunsa tas ya zazzage ya bata duka kudaden dake ciki. Suna wannan yanayin Suhaib ya fado falon daga dakinsu yana kiranta. "Inata nemanki Anti. Lilu ne na kasa cire masa belt ya yi kashi a wando." Da azamarta ta mike tana murmushi "Liluna kenan. Yau dai yana min shagwaba son rai." Sai da ta juyawa Tahir baya ta cigaba da magana "Ta wata kakarmu ta ce duk yaron da ya wuce shekara guda yana kashi a wando uwarsa tayi asara." Juyawa tayi suka hada ido da Tahir ta dora da cewa "ka san mutanenmu na kauye ba dai iya zagi ba da raina kokarin mutum ba. Shi Lilu ma da yake karami babu wani a gabansa." Tafiya tayi ta barshi yana juya zancen a zuciyarsa. Yafi sau biyar zai iya tunawa da Lilu ke yi a wando. Amma duka lokutan dukan gaske Khadija ta yi masa. Yayyensa babu wanda ya yi haka. Sai zuciyarsa ke bashi ko ta fara gazawa a tarbiya ne. Yana zaune Khadija ta shigo da Farha a bayanta. Da dankwalin kanta ta goyota saboda ta sha wahala. An ciro kwankwalatin da ya karce mata makwogaro sannan anyi mata allurai. Da sauri ya tashi yana tambayarta ina taje. Wani irin kallo tayi masa na mamaki sai yaji kamar ta fahimci halin da yake ciki. "Nasima bata fada maka abin da ya faru ba?" Ta ce tana shigewa daki ta kwantar da da ita akan gado. Ganinsa tayi a yamutse ba yadda ta barshi ba ta dawo falo tana labarta masa abin da ya faru. Tashi ya yi zai koma duba Farhan yana jin babu dadi da tsautsayin da ya sameta ya bashi kofar cin amanar mahaifiyarta. Zai daga labule Nasima ta fito tare dasu Suhaib. Khadija ta tashi ta kama kunnuwansu ta murde kowannensu ya saki kara. "Ban hanaku tsalle akan gado ba? Kuna ganin tsautsayin da ya sami Farha baku tsoron ku fado." Sai da gaban Tahir ya fadi ya kasa karasawa ciki. Yana jin Lilu ya fara rantsuwar basu bane ya juyo ya musu abin da bai taba ba. Marinsu ya yi duk su biyun saboda tsoron kada ta yarda dasu ta fara zargin wani abu. "Ba zan yarda da rashin kunya ba. Maminku tana magana kuna karyata ta. Idan ba ku ba waye zai hau gadon ya yi mata tsalle? Na sake ji ko gani sai na zaneku. Ku wuce ku bani wuri." Da kuka suka bar falon. Khadija tayi mamakin daukar zafinsa haka. Ta dade tana rokonsa ya dinga taimaka mata akan kwabar yaran idan sun yi laifi ya ki har ta hakura. Da ta biye masa da yanzu sun gama sangarcewa. Yau da laifin ba mai girma bane a idonta sai gashi ya yi musu marin da ko ita aka yiwa sai ta rike kumatu. Ba dai ta ce komai ba ta bar wurin. Da Nasima za ta tafi ta tambayeta me yasa bata fada masa inda taje ba. "Naji kin ce Farha amma ban ji sauran maganar ba Anti. Wani abin ne ya faru?" Ta tambayeta tana rarraba idanu. "Baki sani ba fa ki ka ce?" "Anti ko dai nayi laifine? Kiyi hakuri." Khadija bata ce komai ba. Sai yanzu ta tuna Nasima tana wurin abin ya faru amma bata juyo ba. "Allah Ya kyauta" kawai ta iya cewa saboda rashin sanin matakin dauka ta bar zancen. A haduwar Nasima da Tahir ta gaba ce tayi masa kukan da ya karyar masa da zuciya. "Na san za ka yi mamakin ganin ni ba budurwa bace. Ba zan maka karya ba da kaina na sayar da mutumcina. Talauci da yunwa sunyi mana yawa. Babu mai son taimakonmu. Da mutane suka gane cewa zan iya komai domin ciyar da mahaifiyata da kanne shi ne maza suka fara nemana. Na san cewa kaima kana cikinsu amma ba yadda zanyi saboda albashina ba zai ishemu ba." Daga ranar ya bude mata bakin aljihu sai yadda tayi. So yake ya nuna mata yafi sauran mazan. Kudi kam bata da matsalarsu. Tahir kuma ita take juya akalarsa. Khadija sun maida ta hoto suna badakalarsu a gidan bata sani ba. Kiyayyar da yake nunawa Nasima ta zame mata katangar hana hango komai a tsakaninsu. To gashi yanzu anyi aure! *** "Mari kin ji labarin ana neman masu casa a gidan Sarkin Noma?" Audugar da Mari take kadawa ta ajiye ta kalli kawarta Tasalla da murmushin da yafi kama da dariya. "Ki bari don Annabi." "Yasin da gaske nake. Wannan karon ina tsammanin mata sai sun cika tsakar gidan saboda alherin da ya yi bara." Tsam Mari ta tashi ta shiga daki ta dauko mayafi. Tasalla tana ta tsokanarta wai ladan aikinta wannan karon harda amaryarta zasu ci. "Ko Malam in fada miki sai dai kallo. Yaran nan zan rabewa in je in dubosu." Kwalla ce ta taho mata ta goge da habar mayafinta "Har mafarkin Sani nake Tasalla. Ya yi kankanta sosai da bara. Ga Abbati kin dai san halinsa. Duk inda ya shiga raina shi ake yi. Ba zan taba yafewa Mal Sa'adu ba." Da sauri Tasalla ta dora hannu a bakinta "bari fada kar a ji. Wan mijinki ne fa." "Wan miji ai ba uban miji bane. Don baki ji yadda nake nadamar haihuwar mazan ba. Da mata ne wa ya isa ya tura su almajiranci?" "Kul Mari. Ba'a yiwa Allah tawaye akan haihuwa." Cewar Tasalla. "Astangafirullah" Mari ta ce da sauri tare da yin tofi a gefe na neman barranta daga zunubin kalamanta. Sun yi sa'ar samun gurbi cikin mata goman da ake nema suyi aikin casar shinkafa da masara a gidan Sarkin Noma. Mari kason mutum biyu take karba ta wuni tana aiki. Banda wannan ta cigaba da dinkinta duk da kuwa ba wani mai tsada bane ga bashi a wurin mutanen kauye. Haka take musu dinkin ta shafawa idanunta toka sai an biyata kudinta. Tuni tayi suna kuwa. Ana cewa bata da lamuni wurin kudi amma ta iya dinki. Duk abin da ta samu sayayya take yiwa Abbati da Sani. Yaran dake gabanta ba komai take basu ba saboda ganin suna gaban mahaifinsu. Bayan sati uku ta nemi izinin Inuwa za ta je Zaria da Kano ganin 'ya'yanta. Shi kuma ya sanar da Mal Sa'adu. Nan da nan zance ya zagaye gidan aka yi ta aibata ta. Sauran matan babu wadda ta taba zuwa ganin nata. Idan lokacin komawarsu gida ya yi ana basu hutu su tafi su taimakawa iyayensu musamman da damina. "Wai ke Mari kanki aka fara haihuwa ko naki kadai aka kai almajiranci? Wannan rashin ta ido har ina?" Mai bin Mal Sa'adu ya ce da ita yana muzurai. Inna Mairo ce ta kawo mata dauki wannan karon. "Bana son bakin hali. Kun dauke yaran yanzu meye aibunta don ta ce zata ganinsu? Na rantse da za'a jarabceku da laulayin kwana daya kafin ma ayi batun nakuda bana jin da mai yarda dansa ya matsa ko nan da zaure. Ba ita ba ma duk mai so a barta taje ta ga nata." Ashe sauran ma suna so baki da zuciyar yi Mari ta fisu. Faccalolinta da suke da yara a wasu garuruwan kowacce sai ta fara shiri. Ba lokaci daya zasu je ba saboda kada a bar gidan babu mata. Kaya niki-niki haka Mari ta hadawa su Abbati. Don karfin hali harda shinkafa, kwan zabi da garin kunu. Da ta tashi kuma ta yiwa iyalan malamansu tasu tsarabar. Zabinta hudu ta tafi dasu suka fara wucewa Zaria ita da dan rakiyarta dan wajen kanwarsu Inuwa. Duhun dare ya kawo kai suka isa unguwar da makarantar take. A cikin layin sun yi arba da almajirai sun fi goma. Yawancinsu duk daga bara suka dawo da abincinsu. Can gabansu suke hango kura tana tashi ga ihun yara da alama dambe ake yi. Yayin da dan rakiyarta ya yi tsaki ita ido ta zuba tana tausayin yaran da karancin gata ya sa rayuwarsu walagigi irin haka. Yaro daya ne a kasa guda uku na tumurmusarsa. Baka jin komai sai kukansa gami da tsinuwa da zagin da yake aika musu. Sauri Mari ta kara da niyar ta isa ta rabasu sai ga wani gardi (babba cikin almajiran) da dorina. Yana zuwa ya shiga sambada musu kan mai uwa da wabi. Ji kake taf-taf ga ihun yaran suna sosa inda bulalar ta sauka. Na kwancen da ya kasa tashi ya fi tafka. Ya kuma daga hannu zai zuba masa Mari ta gane ko waye. Babu wanda zai ce ga lokacin da ta motsa kafa sai ganinta suka yi ta duka ta rufe Sani. Bulalar a gadon bayanta ta sauka ta gantsare kwalla mai zafi tana taruwa a idonta. "Baaba?" Sani ya ce da mamakin da ya gauraya da murna. Da ka ta amsa shi saboda radadin dukan nan. Ya kuwa kankameta yana kukan dadi. Almajiran da suke wurin suka ruga ana rige rigen fadawa Malam abin da ya faru. Ita dai Mari daga Sani tayi tana karkade masa jiki. Farinwata ya haska mata shi da kyau taga yadda ya rame kamar ba shi ba. Ya sake kankancewa sai kai shirim kamar ya kumbura. Lebensa sama da kasa a kumbure sannan karshen lebban ta kowane bari ga alamun ciwo. Wurin duk ya tsattsage. Su kauyawa ne amma ba kazamai ba. Zuciyarta tana kunci ta dauke shi yana ta warin rashin wanka. Nan kuma taji abu ya karci hannunta. Ta shafa kafarsa da kyau taji wani mummunan faso da ya mamaye 'yar kafar. Bata ma san ina za ta nufa ba a lokacin sai ga malamin makarantar tasu ya taho yana baza babbar riga. "Baiwar Allah daga ina? Ance kin yi rabon fada tsakanin dalibai na." Kula ya yi da Sani da ta dauka ya rungume wuyanta da 'yan hannayensa ya daka masa tsawa "to tambadadde daga ganin mata ka makale mata. Ai sai ka sauko tunda ba uwar da ta sallamoka daga kauye bace." Ya mayar da hankalinsa ga Mari yana dan murmushi "haka muke fama fa. Iyaye mata kamar basu san zafin haihuwa ba. Yara da kananun shekaru a kawo a jibge mana. Ba kuma wani kudin azo a gani suke biya ba. Shi wannan ma dai mai idon mayun sam bai kwanta min ba. Kar ki raina kuruciyarsa hatsabibin gaske ne." Ta so ace wadannan kalaman a kunnen Mal Sa'adu ake fadarsu ya ji da kyau ba ita ba. 'Ya'yan da suke haifa cikin gumi da jini ke irin wannan rayuwar kuma laifinsu ake gani. Zuciyarta ke bugawa da karfi tana son bashi amsa amma tana hango laifin nasu da ya fada. "Don Allah zamu sami masauki zuwa wayewar gari." Mari ta katse surutun da yake ta yi da wannan tambaya. Kallonta ya yi sama da kasa tare da dan rakiyarta ya girgiza kai. Haka kawai a wannan zamani da ake fama da 'yan yankan kai bai ga dalilin saukar bakuwar da bai sani ba. "Sai dai nasa a raka ki gidan Mai Unguwa." "Nagode, ina kayan Sani suke mu dauka?" "Baiwar Allah wai daga ina kike ne?" Ganin karfin halinta ya yi na son satar dan mutane a gabansa. "Mahaifiyar Sani ce daga Kirikasamma. In Allah Ya so ka bar ganin mai idanun mayu kamar yadda ka kira shi daga yau." Kunya mai tsanani ce ta rufe Malamin. Gidansa ya tafi dasu yasa iyalinsa suyi musu abinci. Da aka kawo ko hannu bata saka ba sai da ta kula Sani yana ta kallo ta janyo kwanon. A baki ta bashi ya ci ya koshi. Ta fita wanke hannu kafin ta dawo bacci ya dauke shi. Shafa shi ta dinga yi tana hawaye. Wai wannan ne Saninta. Yaro mai kiba da kuzari duk ya lalace. Kayan Sani duka sunyi datti ga wari. Wando da riga ta samu tun asuba ta roki sabulu ta wanke masa. Da yake ana zafi sosai kafin su tashi tafiya sun bushe. Da kanta tayi masa wanka ta dirje masa jiki. Suna shan koko taji ana cewa yaran da suka yi masa duka jiya biyu cikinsu sun kwana suna zawo. Ana tsammanin abincin da suke fadan a kai lalatacce ne. "Sani ka ci abincin?" Ta tambaye shi hankali a tashe. "Loma daya nayi suka kwace." 'Kemis zan fara zuwa na saya masa ja da yalo kafin muje tasha' ta ayyana a zuci. Da zasu tafi bata fasa ba ta ajiye musu tsarabar da ta kawo. Neman magani ta dinga yi ido rufe amma bata sami kemis ba sai a tashar ta sayi maganin zawo a wurin wani mai tallan magunguna. Irinsu kemis guda ne a kansu suna sayar da kusan kowane irin magani na bukatar yau da gobe. Ita ba ilimin abin ba haka zalika mai maganin ma sayarwa kawai yake yi. Haka ya hado mata magunguna kala biyar wai duka na zawo da ciwon ciki. Filagil kadai ta gane sai magnesium na ruwa da ake girgizawa kafin a sha. Sauran kuwa kafinol ne hade da boscopon da panadol extra. Burinta kada wani abu ya sami danta saboda haka kai tsaye ta bashi na ruwan. Hakura tayi da zuwa ganin Abbati zata koma gida har sai Sani ya dan murmure. A hanya ya soma ciwon ciki yana ta amai. Daga baya sai zawo duk ya fita hayyacinsa. Shi yake ciwon amma Mari ke kuka. Sauran fasinjoji kuma suka dinga hantararsu saboda wari ya ishesu. Babu wanda ya san lalurar da ta kawosu wannan matsayi aka dinga cin mutumcin 'yan kauye a gaban idonsu. Kafin su isa Kirikasamma Sani ya fara sankamewa idanunsa a waje gwanin ban tausayi. Mari tayi kuka har muryarta ta dashe wurin yi masa sannu. "Baaba cikina zai tsinke ki kara min magani." Sam ta manta da magungunan da ta saya ai kuwa ta roki ruwa a wurin wata da ta kulla a farar leda. Ta ballo bibbiyu kowanne kamar yadda mai maganin ya ce mata ta bashi. Cikin zakuwa take tambayarsa "Ka fara jin sauki?" "Eh" ya amsa idanunsa suna kakkafewa. A zaton Mari bacci ne. Rungume shi tayi tana dan jijjiga shi har rai yayi halinsa bata sani ba. Ashe rabon su gana ne ya kaita Zaria. Da zasu fita daga motar wata ta ce mata jikinsa kamar ya saki. Da murmushi ta ce "bacci ya samu." Goya shi tayi ta dauko wasu kayayyakin. Sauran kuma dan rakiyarta ya dauka suka dauki hanyar gida a kafa. Lokaci lokaci take gyara goyon ta yi masa sannu. Rashin amsawarsa a wurinta saboda bacci ne. Sun kusa isa gida ta hango Inuwa a majalisarsu ta karkashin bishiyar darbejiya. Mamakin dawowarta a yau yayi tunda kwana uku ta ce za ta yi. Silifas dinsa ya zura ya taso da sauri da ya fahimci goyo tayi. "Ba dai Sani kika dauko ba Mari? Me kike so na cewa Malam?" "Maganar ba ta hanya bace ka bari muje gida. Bashi da lafiya ba zan iya barin shi a can ba." Dan murmushi ya yi sanin cewa ita ma akwai taurin kai. Yana son yin yadda take so amma ba zai iya sabawa yayansa ba. "To kwanto min shi na dauke shi naga kema a gajiye kike." Ba musu ta kwance goyon Inuwa ya tare zai saba shi a kafada yaji yanayin jikin wani iri. Mutum biyu cikin abokansa suka taso jin ba'asi ganin ana kwance goyo. "Sani ne jikin ba dadi ta taho dashi gida." Inuwa ya fada musu. "To kawo shi mana ka tayata da sauran kayan." Mijin Tasalla ne Lukumanu ya karbe shi sai ya dago shi da sauri jin ya tafi baki daya. Hannunsa na rawa ya ce, "Sani. Sani bude ido..." Mari sai ta tsaya tana son cewa bacci yake taga duk sun rufa a kansa ana jijjiga shi. Inuwa da karfi yake kiransa jikinsa yana tsuma. "Sai dai hakuri Inuwa amma Sani ya amsa kira." Kalaman Lukumanu kenan da suka shiga kunnuwan Mari. Duniyar tsayawa tayi cak bata iya tuna komai sai ranar da ta haife shi. Ranar da taji ciwon nakudar da ya zarce na Abbati. Lokutan da ta dinga sake-saken burikanta akan kyakkyawar rayuwar da take masa fata kamar yadda ta yiwa Abbati. Fuskar Saninta wanda yake ta kuka ba zai je almajiranci ba take gani. Yaron da jiya jiyan nan ta ganshi ana turmususa a cikin kasa akan lomar abinci. A kwana na biyu da rasuwar ta dan dawo hayyacinta. Kuka take yi ta rungume ledar magungunan da ta bashi. Muryarsa ke yi mata amsa amo tana jin lokacin da yake rokonta ta kara masa magani. A yayin da wasu zafafan hawaye ke kwarara a idanun Mari sai ta bawa Inuwa tausayi. Shi ma din zuciyarsa ta dinga raya masa lallai su dawo da Abbati gida. Wani abin ban tausayi ga wannan mata bai wuce har ita ma ta koma ga Allah SWT ba za ta taba sanin ainihin sanadin ajalin danta ba. Komai a rayuwa yana da sila. Hakkin ran Sani yana rataye a wuyan jama'a da dama. Babban cikinsu Mal Sa'adu mai ingiza kai yara almajiranci. Ga Inuwa da ya kasa jajircewa wurin kare amanar da Allah Ya bashi ta 'ya'ya daga dan uwansa. A gefe guda ga Malamin tsangayarsu da bai rike amanar da aka bashi ba ta yaran mutane. Matar da yayi bara a gidanta ta bashi lalataccen abinci saboda rashin sanin girman hakkin bil adama. Yaran da karancin tarbiya da kulawa ya janyo suka yi masa duka akan abincin da ya samo. Mai sayar da maganin da bashi da iliminsu ga mutane saboda neman kudi. Gwamnatin da ta yarje masa yawo a tituna da kwararo yana sayarwa bayan bashi da lasisin bada magani. Kaico! Hatta Mari da ta bawa Sani magungunan nan bisa rashin sani da tsantsar soyayya irin ta uwa da ďa bata tsira ba. A takaice dai the society killed Sani! *** Kalmar hutu kanta tana da dadin fada a baki balle kuma idan jiki zai same shi a aikace. A wurin Innayo kuwa daga mai arziki sai wanda bai san ciwon kansa ba kamar Asabe ke hutawa. 'Yan mata biyar a gabanta babu mai basu sai abin da Allah Ya hore mata daga kasuwancinta. Biki ko suna da wuya yake hanata dora tukunya. Abin da ya kama dole taje to lallai wata cikin 'yan matan za ta zauna a gida. Yau kuwa dole ta saka ta zaman gida tana hutun dole. Ranar ta kama litinin. Ta tashi da ciwon kirjin da ya kan damketa lokaci zuwa lokaci. Yaran nata kuma duka suna makaranta. Zara da bata kaunar karatu sai gayu ta so zaman jinya amma Innayo ta kora ta. Hudu suna zango na uku a makaranta. Jarabawa ake yi ta canjin aji ba za ta so a sanadiyarta wata ta maimaita ba. Babbar kuwa shekararta ta farko kenan a School of Nursing. Ayyukan da basu zama dole ba Innayo ta dauke mata a gidan saboda kawai ta sami isasshen lokacin karatu. Tsakar gidan nasu tsit sai ita kadai a daki. Alh Rabi'u yana kasuwa. Asabe kuma makota ta shiga saboda an kusa sauke sanwar rana. A can za ta ciko cikinta su kuma yaran ta dafa musu gurjiya kowa ya ci ya sha ruwa babu ruwanta. Zumbur Innayo ta tashi da ta tuna ta sa a jika mata gero tun dare amma ciwo ya hana ta wanke a kai nika. Idan ta barshi zai lalace gashi har kwano uku. Tashi tayi da kyar tana dafa bango ko ruwan ne ta samu ta canja. Bandaki ta fara zagawa domin rage mara taji taku da 'yan maganganu anayi. Gida na jama'a bata wani damu ba ta kammala ta fito. Babu kowa har yanzu a tsakar gidan ta zauna tana wankin geronta. Kwana biyu da suka wuce Munzali ya yi wata magana da dan kanwar Asabe da yazo musu hutu. Shi satin da ya gabata suka gama tasu jarabawar. Yaron mai suna Halliru ya girme shi da kusan shekara biyu. "Idan ka yarda muka yi aradu yau abincinka da nama" ya ce saboda ya fahimci amfani da kayan kwadayi yana taimakawa wurin samun biyan bukata. Halliru ya kai masa duka a kafada yana dariya"ashe kai gara ne ban sani ba" karkada hannu ya yi tare da jijjiga kai yana yi masa kallon rainin wayo "to bari kaji in fada maka da mata ake yi ba maza ba. Na taba gani a lungun gidan Mai kalanzir din unguwarmu." Dan jim Munzali ya yi yana nazari daidai kwakwalwarsa kafin ya ce "kai ka taba yi da macen ne?" A kunne Halliru ya rada masa cewa suna yi da kanwarsa idan babu kowa a gida. Ya kara da yi masa bayanin yadda suke jindadi. Shi ma 'yar makota ce da ta girme shi ta koya masa shi kuma ya koyawa kanwar. Da 'yan shekarunsu ya kwadaitawa Munzali son gwadawa. Shi ne fa ya bawa 'yar makotansu inda Asabe ta shiga kwadayi kafi-kaza ya taho da ita gida lokacin da Innayo ta zaga. Tare suka je gidan da Asabe ta kore shi da mugun kallo "shegen yaro kwalamamme. Ka biyoni salon taga munyi mata yawa taki zuba min abincin. Banda abinka idan ta bani ba zan rago muku ba?" Cike da tsiwa ya ce "za dai ki rago musu. Yaushe rabona da cin abincin makiyalla." Baki ta sake maganar ta shigeta ta daga hannu za ta kai masa mari "kut! Nice ma nake makiyalla?" Juyawa ya yi zai tafi idonsa caraf akan 'yar gidan da bata fi shekara shida ba. Da sauri ya dago ledar kafi-kazan yana kiranta. Kafin ta iso sai da Asabe ta karba ta barbada a tafin hannunta ta lashe. "Munzali kenan. Kai dai ba dai mutane masu insani ba. Kwanakin nan har wani kumatu ka dire." Ta kai hannu ta yi masa dukan wasa "ni ko saura ne ka dinga rago min a leda mana. Sai bakin hali irin na ubansa." Shigewa tayi shi kuma Munzali ya sami damar hillatar yarinyar suka tafi gida. Ya zata gidan ba kowa. Dakin Asabe ya shiga da ita inda babu kowa ya ce ta zo ya koya mata wani abu. Da kananun shekarunsa shaidanci ya shige shi har ya sami amincewarta ta cire kaya yadda ya umarceta. Karatun Halliru ya soma aiwatarwa akan yarinyar da bata san me ake yi ba. "Kar ki fadawa kowa kinji. Zan dinga baki tsamiyar biri da kafi-kaza." "Harda tsamiya gaye?" Ta tambaye shi da murmushi. "Duk abin da kike so zan dinga baki indai baki fada ba." A can gidansu kuwa Asabe tana ta sharbar faten tsakin da babarta ta bata. Innayo tana wankin gero taji kamar ana magana kasa-kasa. Gajiya tayi da sharewa ta tashi ta nufi dakin. Duk a zatonta abokan Munzali ne. Satin da ya wuce Asabe ta tafi yawonta aka zo aka dauke mata kudin dashi. Tayi ta rantsuwa wai cikin 'ya'yan Innayo ne. Shi ne ta tashi ta leka don kada a sake sakata biyan kudin da ta san karya ake musu. Tana daga labule tayi mummunan gamo. Da sauri ta afka dakin ta cakumi wuyan Munzali ta kifa masa wani gigitaccen mari. Tana dukansa amma jikinta ke rawa kuma ita ke fitar da hawaye. Idanunsa kyamas abin sa ya ja wandonsa ya mayar. Yarinyar kuwa ko a jikinta. Kafi-kaza ne tayi dumu-dumu dashi tana ta lasa. Ta baya Innayo taji an riko mata wuya tana juyowa Asabe ta dauketa da mari ita ma. "Kashe min dan zaki yi?" Ta kwance dankwali taci dammara "muguwa, makira. Ba tun yau na san magadan Alhaji sun tsole miki ido ba. Wato niyarki ki karshi a daka babu kowa ki fice." Yau daya Innayo ba ta kishi take ba. Tausayin Asabe ma take ji saboda wannan halayya idan Munzali ya tashi da ita ba karamar masifa bace. "Ai dai kya tambayeni me ya yi kafin ki fara sababi. Ganinsa fa nayi akan wannan yarinyar daga shi har ita ba wando...." Wani irin bugu Asabe ta yiwa kasa da hannu ta tafa hannuwan tana hargagi "ahayyeeeee....anyi walkiya na ganki Innayo. Yau dai rigar munafunci ta sauka an miki tsirara a idona. Wato kiyayyar taki da 'ya'yana har ta kai kiyi musu irin wannan sharri mai muni." "Asabe. Asabe ki ajiye maganar kishi ki duba tarbiyar 'ya'yanki. Meye ribata idan nayi masa sharri." Juyo dashi Asabe tayi duk da fargabar dake zuciyarta amma sam ba za ta yarda Innayo tayi mata dariya ba. "Kai Munzali wai da gaske ne?" Sai da ya kumburo baki ya ce "Biyoni tayi fa shi ne ta ce in kaita bayi tayi fitsari. Kawai ina cire mata wandon ta hau dukana." Ajiyar zuciya Asabe ta sauke ta kalli Innayo "to kin dai ji. Haka kawai za ki kulla masa sharri. Yo Allah na tuba yaron nan nawa ma yake? Me ya sani? Ko an fada miki kowa ma irin wadancan shirgin ne da ki ka tara a daka suna yawon ta zubar?" Lokacin ya yi! Tana kai karshen maganar Innayo ta rama marin dazu. Ba lafiya gareta ba amma tuni ta manta da ciwon. Zagi ba irin wanda Asabe bata yi mata ba ta ja gefe tana kallonta. Damben da take so ta biye mata suyi ne ba za tayi ba. Munzali salin alin ya ja hannun yarinyar ya kai ta kofar gidansu ya kara gaba. Dare ya raba Asabe ta kasa baccin kirki. Tashi tayi ta koma rumfarta ta taba Munzali. "Ka tabbata dazu Innayo karya tayi maka?" Sai da ya murza ido saboda bacci sannan ya ce "Halliru ne ya ce wai da mata yafi dadi." A baya ta daka masa duka a razane "bude ido don ubanka. Kayi da gaske?" Lokacin ya wartsake ya girgiza kai "ni ban yi mata komai ba." Jinjina kai tayi ta ce ya kwanta. Ta san karya yake. Har kasan zuciyarta ta yarda da Innayo da subutar bakinsa ta dazu. Sai dai kuma ko ana muzuru ana shaho ba za ta taba yarda ace laifinsa bane. Wannan magana anyi an gamata daga yau.https://my.w.tt/seH8zVi968 UWA UWACE...5 Batul Mamman💖 Assalam alaikum ma'abota bin wannan labari. Ina alfahari daku kuma ina godiya. Ayi min hakuri saboda dogon jinkirin da ake samu ba post. Yau da gobe sai godiyar Allah. In sha Allah duk lokacin da na samu dama zan dinga typing har komai ya daidaita na dinga yi a kai a kai. Abu na gaba mutum biyu sun ankarar dani cewa akwai wani littafin mai suna Uwa Uwace a manhajar okada. Kasancewar sunansu daya coincidence ne. Nawa kyauta ne wancan kuma na kudi. Saboda haka zan dinga kara inkiya a gaban nawa sunan domin a daina samun rudani. Ina godiya Ina muku SonSo Stay Safe *** Kwana goma cif da tarewar Nasima a gidan Tahir. Amarci suke irin wanda iyayen gida ke tsoron ayi musu kishiya su ga irinsa. Kullum sabon nau'in fitsara da rashin kunya Nasima ke kirkira wanda zai batawa Khadija rai. Abin da bata sani ba kuwa shi ne fitar Tahir da aurensa kacokan daga zuciyar Khadijan. Zaman 'ya'ya take yi kamar yadda matan aure da yawa suke yi. Bata da dogon buri ko hangen komai sama da inganta musu rayuwa. Ba don su ba komai wuya da tuni ta koma gidan mahaifinta. Sati guda ta sani addini ya bawa amarya budurwa tayi tare da ango kafin a raba kwana tsakaninta da ta gidan. A sati dayan sai take yi musu girki na kyautatawa ba don ta burgesu ba sai don ta sami ladan rama sharri da alkhairi. Anyi satin an wuce shiru Tahir bai yi mata maganar su raba kwana ba. Girki kuma bata ga alamun Nasima za ta shiga kitchen ba sai ta cigaba da yi saboda yaranta. Tana cikin wanke salad Nasima ta shigo kitchen din dauke da kwalin sabon food flask. Tukunyar shinkafar da Khadija ta bari ta karasa turara ta nufa kai tsaye. Khadija bata nuna ta san da wanzuwarta a wurin ba sai da taji ta bude tukunyar. Don karfin hali ma harda cokalinta a hannu ta danna shi kasa domin ta tabbatar ruwan ya tsotse. "Lafiya?" Baki ta murguda mata gami da fari da idanu "lafiya kamar ya?" Ran ta ya soma baci sai dai tayi alkawarin Nasima tayi kadan tayi fada da ita. "Abincina naga kina shirin budewa." "Abincinki ko abincin mijinmu? Naga dai shi ya saya don kin girka hakan ba ya nufin ba zamu ci ba." 'Kar ki biye mata' Zuciyarta ta kwabeta a lokacin da taji kamar ta mareta. Suturar jikinta da tun tarewarta irinsu take sakawa ta kalla ta kawar da kai. Gajeren wando ne da bai kai rabin cinyarta ba sai damammiyar vest. Anayi ne don ta tofa ace ta ce shi yasa take bawa iska ajiyarta. "Ki jira na dibarwa yara tukunna." Wani irin kallon raini Nasima tayi mata ta soma cewa "ke kin i..." sai taji an bude kofa kuma ta tabbatar Tahir ne. Langabe kai tayi ta kwantar da murya tana bubbuga kafa duk jikinta na rawa "ni dai don Allah Anti Khadija ki karba haka nan. Wayon hutawa kawai kike yi min kin barni inata fama ni kadai." Kitchen din Tahir ya shigo Nasima ta kwabe fuska tana yi masa shagwaba "Diya (Dear) wai kaji ta kara mana satin amarci ba yanzu za'a fara rabawa ba." Ko ita ta sarawa kissar Nasima. Jinjina kai tayi harda 'yar dariya. "Sai fa ba Diya ba" "Me ki ka ce?" Tahir ya tambayeta ta da murmushin jindadi a zatonsa sun fara hada kai ne. "Ban ce komai ba" sai ta mayar da dubanta ga Nasima "na baku wata guda don Allah kada ki ce baki karba ba. Da so samu ne ma zan fi son karba idan ki ka fara tofe-tofe da tashin zuciya." Ta karasa maganar ne tana dibar abinci. Da ta gama ta zo fita ta dakata a gaban Tahir. "Af...Diya" ta furta kalmar yadda Nasima ke fada da tsantsar rashin wayewa "na ce kada ka manta yaba kyauta tukwuci. Zan zo amsar nawa idan mun gama cin abinci. Da yake ma mu ba mayunwata bane idan za ka saurareni yanzu na san zasu iya jira." Lebensa ya cije. Magana Khadija ta yaba musu daga shi har Nasima. Haushi ya kama shi ya nemi yunwar ya rasa. Data kawo musu daki ko kallo kwanukan basu ishe shi ba. Tunanin maganganun Khadija ne ya addabe shi. "Waye ya bata izinin karin kwanakin ma?" Ya yi kwafa shi kadai. Kila fushi tayi don ya kara kwana uku akan bakwai din. Nasima ya kalla wadda har yau bata dena yiwa abinci cin yunwa ba ya tashi. A daki ya sameta ta goya Sauda. Tana ganinsa ta dauko form din JAMB ta mika masa. Ta riga ta cike komai, izininsa kawai take nema. Kallon rashin gamsuwa ya fara yi mata ta hade hannuwanta biyu a kirji. Fuskarta babu alamun za ta yarda da kalmar a'a. "Da can me yasa baki taba cewa zaki koma makaranta ba da na hana sai yanzu. Don nayi aure kina tunanin bani da sauran hurumin sawa da hanawa a gidana?" "Kana dashi matsawar ina amsa sunan matarka. Amma ina so kayi min adalci guda daya. Kar ka manta har na koma ga Mahaliccina hotonku kai da matarka ba zai taba..." Baya so ta kai karshen maganar saboda kar ta ga alamun kunya a tare dashi. Karanta form din ya shiga yi da karfi har sai da tayi dan murmushi. "Bari nayi sauri naje banki kafin su rufe na ciro miki kudin registration. Allah Ya bada sa'a." Anyi an gama komai cikin nasara. Khadija ta sami gurbin karanta Business Administration a ABU Zaria. Shirinta take yi hankali kwance ta manta da duka wata damuwar gidansa. Nasima tana ta fama da laulayi. A gabanta take wasu abubuwan kamar su tara yawu da yunkurin amai. Idan tana yi da tsantsar tausayi zaka ga Khadija tana yi mata sannu. Ko daga murya bata taba yi mata. Haushin da take son bata karshe ita take ji. Gida Tahir ya kama mata a Zaria mai daki biyu da falo. Ana saura kwana uku ta tafi ya shiga dakinta yaga akwatunan da ya tabbatar ba nata bane ita kadai. "Kada ki ce min da su Suhaib za ki tafi." Murmushi ya gani a fuskarta da ta dago kai. Ya fara tsanar murmushin saboda yadda bakar magana cikin nutsuwa take biyo bayansa. "Haba Diya. Kada ka ce min kayi zaton zan barsu a wajen amarya. Yanzu don Allah idan kai ne ita zaka so na bar maka 'ya'yana? Idan kaine ni za ka bar mata 'ya'yanka?" Shiru ya yi ta fita daga dakin ya bi bayanta da sauri. Tsohon dakinsa wanda ya zama na Nasima ta shiga. Rabonta da dakin tun tana kwashe 'yan tarkacenta. Zuciyarta wani irin kunci tayi mata. Bakinta har yana daci saboda tunawa da yanayin da ta taba ganinsu amma ta daure. Sallama tayi Nasima ta zo ta bude kofar tana yatsina. Ganin Tahir a bayanta sai ta saki fuska. "Anti nemana kike? Ai da kin turo su Lilu sun kirani." Sai da Khadija ta kallesu su biyun sannan ta ce "dama Diya ne ya ce na bar miki yara nace gara dai mu koma Zariyan tare. Kina fama da laulayi ba iya wahalarsu zaki yi ba. Duk da haka dai na ce bari naji ta bakinki." Langabewa Nasima tayi don bata ga dalilin da zai sa ta karbi yaran ba. Daga haka ma tana fatan maganinsu ya ci tayi gaba kenan har abada. "Zan so zama dasu Anti. Bari dai na sauke nauyin nan da kaina zan zo na dawo dasu." "To kai kaji Diya. Za ta so zama dasu amma sai ta haife nata. Bari na barku zan karasa hada kayan." Tafiyarta tayi ta barsu Nasima na rungumo shi yana kwacewa. Fada ya soma yi mata ba ji ba gani. "Yanzu ke ko kunyar idona baki ji ba ki ke nuna ba za ki iya zama da 'ya'yana ba?" Turo masa baki tayi da tsiwarta ita ma. "Haka ka ji na ce? Kuma nima dai haihuwar nan zanyi. Idan ma takama ake yi da 'ya'ya nima zan haifa maka wasu." Ransa yake ji a jagule. Dama gashi ta fara sire masa. Abin da yake doki ya riga ya samu har ya fara tunanin komawa titi abin sa. Ga Khadija duk ta canja. Da yatsa ya nunata kamar zai tsokane mata ido. "Bar ganina haka wadannan yaran basu da na biyu. Ina son abuna kuma idan kina neman zaman lafiya a gidan nan dole ki so su." Bai kara saurararta ba ya tafi dakinsa ya banko kofa cikin bacin rai. Zama ya yi yana tunanin me yasa yake ganin kamar Khadija ta daina sonsa? Ba haka yake so ta dinga yi masa ba. Kishin da ya tsammaci gani wanda zai tabbatar masa da sauran matsayinsa a zuciyarta duk babu. Baya mantawa kafin wata dayan nan da ta kara musu ya cika gabadaya Nasima sai da ta gundure shi. Don ma yana jin sonta a zuciyarsa ne da bai san me zai faru ba. Yana ta tuhumar kansa me yasa ya yi saurin aurenta. Da ya sani kuruciyarta kawai ya mora ya bata abin da zai bata a waje. Yarinyar sam bata da aji. "Wai Diya...sai kace wani dabba. Mtseww" Tunawa ya yi Khadija ma tana fada idan ta so cusa masa haushi ya yi dan murmushi. Tunda dai bata tafi ba zai cigaba da lallaba abarsa. Da tsohuwar zuma ake magani. Mata nawa ya nema bayan aurensu amma duk inda ya gama yawonsa wurinta yake dawowa. Da yake ita keda girki ranar da ya koma dakinta ta cigaba da yi masa komai yadda ta saba. Kallonsa tayi yana ta biyewa yaransa suna wasa tayi kwafa. Ba za ta taba bari ya gane kudurinta ba. Da kudinsa za tayi karatu. Burinta ta sami jari ko aiki a gaba wanda za ta iya rike kanta da 'ya'yanta. Komai dadewar lokaci, komai tsufa, za ta bar gidan Tahir. Nasima kuwa ta dade a tsaye inda Tahir ya barta. Tsoro ya gama mamaye zuciyarta domin ta kula ba tun yau Tahir yake hantararta ba. "Na rantse kayi karya Tahir. Ni da kai yanzu muka fara zaman aure." A ranar ta tambaye shi zuwa gida ya amince. Washegari yana fita ta tafi wurin Laraba. 'Yan kudaden da yake bata ta fiddo duka aka bawa wani malamin tsibbu. Ya hado mata magunguna da bayanin cewa da basu zo ba a ranar zai saketa. Wai bokan Khadija ne yake musu farraku. "Laraba kin ji ko? Na fada miki yanzu kamar bana burge shi ga yawan fada." Ta ce cike da gamsuwar karyar bokan. Kulle-kullen da ya basu ta dauka ta tafi dasu gida tayi amfani dasu yadda ya ce. To gidan dai rayuwa ake yau fari gobe tsumma. Khadija tana Zaria da yaranta sai dai Tahir ya ziyarce su. Ko suna hutu sai ta fake da karatun yaran. Sai lokutan hutu gama-gari take zuwa gidan. Karatunta take yi hankali kwance sannan tana sayar da zobo da ginger. Tun tana kullasu a leda har ta koma yin na roba. Kasuwa ta karbu har freezer ta kara saya da ribar cinikin. *** "Ina cewa matarka bata da hankali ashe kaine babban mara hankalin. Inuwa! Inuwa ka bani kunya." Mal. Sa'adu ya furta rai a bace. Sunkuyar da kai Inuwa ya yi kunya ta mamaye shi. Yayan nasa bai tashi yi masa tijara ba sai da yaga sauran matan kannensa sun zo wucewa. Ai kuwa tsayuwa suka yi a fakaice aka gama jin fadan. "Amma saboda Allah Yaya kana ganin irin mutuwar da Sani ya yi. Idan bamu yi wani abu ba shi ma Abbatin haka zamu rasa shi" Murya har dakuna mafiya kusa ake jin fadan Mal. Sa'adu yana cewa "Wanda ya rasu a wurin neman ilimi yana cikin jerin shahidai idan baka sani ba. Kuma tunda mutuwar ta kuruciya ce idan an je lashirar ba kai da Marin za'a fara cewa ya ceto ba. Kila ni da na assasa tafiyar ma sai ya gama daku zai ambaceni." Inuwa dagewa ya yi shi ma"Ni dai gaskiya zan dauko shi na saka shi a ta allo da boko a nan." "Ahap...tushen magana ya hito da za ka zauna kana yi min kwana-kwana. Daga makarantar 'yan aljanna za ka kaishi ta 'yan wuta. Wai ma shin 'ya'yanka aka fara kaiwa ne? Gidan nan kowa yana kaiwa. Don naka ya rasu sai ka kasa karbar kaddara?" Fadan Mal. Sa'adu yaki karewa. Inuwa tun yana mayarwa har ya kasa katabus. Sauran 'yan uwansa ne suka hade masa kai aka fara yi masa nuni da cewa Mari tafi karfinsa kuma ita take juya shi. Bahaushen mutum da jiji da kai da gudun raini sai yaji tsoron kada su raina shi. Har kasan zuciyarsa ba ya so amma kuma rashin son ayi masa kallon mijin-tace ya danne komai. Sun kunno shi sosai sannan ya shiga ciki ya hau Mari da fada. "Abbati ba zai dawo gida ba kuma ban yarda ki je Kano ganinsa ba. Tunda dai zasu zo hutun Takutaha nima ba zuwa zanyi ba." Wani abu ta hadiye da ya tokare mata wuya da kyar sannan ta daga kai ta kalle shi. An kusa wata biyu da rasuwar Sani amma har yau ta kasa komawa daidai. Da ciwo mai raunana zuciya da ruhi a tare da ita. Dashi take kwana dashi take tashi. Duniyar sam ta daina yi mata dadi. Gani take ta gaza a matsayinta na uwa. Kwanakin farkon rasuwar saboda ta sa abin a rai har mafarkinsa take yi yana tuhumarta da wulakanta amanar Allah. Shekararsa bakwai kacal a duniya. Sa'anninsa da suke cikin gata wasu ko kyakkyawan tsarki basu iya ba. Wasu su dawo daga makaranta suna bore suna ihun sun girma uwa ta kamasu tayi musu wanka da kanta. Wasu a basu abinci a baki. Wasu uwa ta shagwabasu da soyayya ba don su lalace a tarbiyya ba. Almajiri kuwa sai yadda Allah Ya yi. Ga kuruciya, ga rashin gata kuma a haka cuta za ta kama shi. Babu magani babu kuzarin yin bara sannan ba lallai a sami mai damuwa da halin da yake ciki ba balle a taimaka masa. Idan da tsananin ciwo zai saka shi amai a makwancinsu babu abin mamaki wurin samun masu yi masa tsawa da hantara kuma ace ya goge wurin. Idan ya yi zawo a jikinsa sauran dalibai su toshe hanci su guje shi. (Ke da yake da yake yiwa shara, wanke-wanke ko zuwa aike idan ya yi fashi ki hau shi da fada. Cikin dan albashin da kike bashi ki cire na kwanakin da bai zo ba. Ya wuni a rana yana wanki ki bashi ragowar abincin jiya kila ko dumamawa baki yi ba. Hakika tallafawa almajirai kafin gwamnati da masu ruwa da tsaki su dakatar da wannan al'adar jihadi ne. Idan wani mahaifiyarsa tana da rai kuma ta yarda yazo wani tasa uwar irin su Mari ce ko maraya ne. Idan wasu duniya ta lalatasu kamar Abbati wani kuma is innocent kamar Sani.) "Allah Ya kaimu Takutahan" ta iya cewa kadai. Watannin sun wuce a yayin da bawa yake ta fadi tashin neman na kai. Wannan mummunar alfasha ta gama shiga jikin Abbati da Munzali. Ranaku daidai ne basa haduwa. Shazali da abokansa suka koma amfani dasu biyun. Saboda haka yanzu abincin Abbatin ma ko bai hadu da Munzali ba zai samu a wurinsu. Ya murmure fiye da yadda ya zo daga kauye. Ya kuma zama fitsararre mara kunya da kawaici. Babu mai saka shi ko ya hana shi a makarantar saboda Shazali ya tsaya masa. Malaminsu ya dade da sallama su Shazali. Sun zame masa karfen kafa. Babu karatu kuma sun ki komawa gidajensu. Ana gobe hutun Abbati ne tare da Munzali dasu Shazali a kangon suna cin abinci. Tsire ne da biredi sai kwalbar lemo a hannun kowannensu. Shazali ya kusa sati yana juyayin gabatar musu da wata bukata amma yana gudun kada cikin surutu su fadawa wani. Amininsa ne ya ankarar dashi cewa ďa zasu fada fa da tuni wancan abu ya dade da yaduwa. Sai da ya kula duka suna jindadin abincin ya kawo zancen. "Da ace kullum ni nake baku kudin abinci ko na baku ba gara ku dinga bina inda nake samowa ba ku ma ku dinga shanawa da kyau." "Al'Qur'an ko ma ina ne ni dai zan bika." Cewar Abbati da zumudi. "Kai fa Munzali?" "Abbati ma zai yaje bare ni." "A wurin irin abin nan da muke yi zasu dinga yi daku sai a baku kudi. Idan ku ka fadawa wani a take zaku mutu." Wannan ba abin damuwa bane tunda sun riga sun saba. Abbati bai ji dadi ba saboda dole sai bayan ya dawo daga gida za'a kai shi. Ranar da zasu tafi 'yan uwansa na wasu makarantun a Kano ne suka hadu da 'ya'yan makota duk 'yan gari daya suka tafi tare. Yana shiga mota ya shafe shafin su Munzali. Hankalinsa ya yi gida Baaba Marinsa yake son gani da kannensa. A nasa haukan yake son ganin Sani ya fada masa abin da yake yi yana samun kudi da abinci. Zancen zuci yake wanda don dadin da abin ya yi masa har dan tsalle ya yi akan kujerar mota. 'Shi ma idan ya yi mu tara kudi mu kai Baaba Makka da Madina'. Bai san abin da yake ya munana ba. Ya dai san kila Mari tayi masa fada. Munzali ya ce manya ne kadai suke yi. *** Mari tana yayyafawa itacen da ta gama yiwa Abbati miyar zabi taji muryarsa. "Baaba. Baaba na dawo. Baaba Sani ma ya zo?" Murnar da ta tashi da ita sai ta nemi komawa ciwon rashin Sani. Murmushi tayi saurin yi domin kada ya zata bata murnar ganinsa har ya iso gareta. Da murnarsa ya taho zai rungumeta sai taji kunya. Tsakar gidan da mutane duk an zuba musu idanu. Yana isowa sai zai riketa sai ta dafa kansa. "Kun dawo lafiya?" Bai biye mata ba ya rungumeta yana dariya. "Lafiya kalau Baaba. Ina Sani? Ya zo gida?" Kwalla ta sake tarar mata a karo na biyu ta kawar da kai gefe "Sani kadai ka sani ba ka cigiyar sauran?" Uwargidan Mal. Sa'adu tana jinsu ta murmusa da gayya ta ce "Wai wane Sanin ake zance ne? Ko marigayi?" Mari ta dubeta cikin bacin rai ganin Abbati ya juya da sauri. "Haba Yaya Deluwa kya dai bari ko abin ci ne yaci mana." "Au, wai dama bai ji labarin mutuwar kanin nasa ba?" Deluwa ta furta kamar bata ji me Mari ta ce ba. Abbati sai ya matsa kusa da ita hankalinsa a tashe. "Iya Deluwa wane Sanin ne ya rasu?" Sauran matan gidan duk sai suka fito aka dinga cewa "Allah Sarki" da karyewar murya mai cike da alhini. Yanayin tashin muryarsu kadai sai yasa mutum yaji babu dadi. "Sani ai ya kusa arba'in biyu a kabari. Yaro yunwa da rashin gata suka yi ajalinsa." Inji wata faccalar ta ta. Deluwa ta cafe da saurin kwabarta "ko kiyaye bakinki dai. Ah to. Malam ya ce mutuwar jahadi ya yi tunda a bakin neman ilimi ne." Wani irin kuka Abbati ya saka yana zubewa a wurin. Mari da ta sami damar motsawa ba ita ta tsaya ba sai a tsakar dakinta. Ita ma nata kukan take yi har Abbati ya shigo ta share idonta da sauri. "Zauna in zubo maka abinci. 'Yan uwanka ma babu wanda yaci suna jiran dawowarka." "Baaba da gaske saboda yunwa Sani ya rasu?" Tambayar ta daki zuciyarta. Ta laluba ta rasa amsar da ta dace ta bashi. "Bana son yawan tambaya. Almajiranci ne anyi an gama. Ka dawo kenan ba za ka koma Kano ba." Nan fa Abbati ya yi wuf ya mike yana mai tuno Munzali da abin da suke yi sannan da irin abincin da suke ci wanda bai taba samu a kauyen. "Ni dai zan koma." Bata kawo komai ba a ranta illa gargadin da tayi tsammanin anyi masa akan kada ya zata ya gama karatun kenan. Kannensa mata ta kira suka hadu su hudu ta zuba musu abinci a babban farantin da ya kasance murfin fanteka. Shinkafa ta dafa musu wadda ta kwana hudu tana tsinta. Sai miyar dage-dagenta da tasha naman zabi taji gishiri da kafi zabo (vedan). Farincikin ragowar yaran a bayyane yake. Cikinsu babu wanda bai hadiyi yawu ba tun kafin ta ajiye musu abincin. Naman ta saka musu yanka dai-dai shi kuma Abbati guda uku. Abin dariya da ban tausayi ya hade duka lokaci guda. Ci suke kamar mayunwata yau an sami shinkafa. Abbati kuwa loma daya ya yi da kyar ya kasa ci. Ko kadan girkin da mahaifiyarsa ta sha wahalar hada kayan yinsa da wahalar girkawa bai burgeshi ba. Salam haka yake jin dandadon girkin. Miyar ma a idonsa bata yi kyau irin na wadda ya saba ci ba. Ga kannensa suna ta wawa shi kuwa shinkafa ma har ta soma gundurarsa. Mari ta lura baya ci sosai duk sai ta damu. Me yiwuwa ko zancen rasuwar Sani ke damunsa. Sai da suka gama tayi masa magana. Naman ma tana kallo ya bar musu suka cinye. "Abbati ka cire damuwa daga ranka ka dinga saka Sani a addu'a kaji. Yanzu me ka ke marmarin ci? Naga kamar ka kasa cin shinkafar." "Da kin sani tuwo ki ka yi min Baaba." Yana gama magana ta tashi. Iccen da ta zubawa ruwa ta tura gefe ta duba bata da isasshe. Yaran nata sun fice wasa dole ta saka mayafi ta fita. Da kanta ta karbo itace a wurin kanin Inuwa a waje tazo ta hura ta dora ruwan tuwo da miya. Kan kace meye wannan ta gama tuwon dawa da miyar busasshiyar kubewa. Dakunan faccalolinta dake kusa da ita sai leken tsakar gidan suke ana hadiyar yawu. Inuwa kansa da ya shigo bai iya daurewa ba ya bukaci ta zuba masa. "Malam ga fa naka abincin. Tuwon na Abbati ne." Zai sake magana ta bude tasar yaga shinkafa da miyar nan. Tuni ya manta da batun tuwo ya tsoma hannu ko wankewa bai yi ba. Loma manya manya ya dinga shirgawa kafin ta farga sai kwano babu kwayar shinkafa ko daya. Ya daga kwanon sha ya kurbi ruwa sannan ya yi mata godiya. Akuyarta ta sayar ta auno shinkafa, kayan miya, zabi da kayan abincin da ya san bai ajiye ba kuma bashi da kudinsu. Tana lura da yadda 'ya'yan gidan ke mata kai kawo a bangarenta saboda girkin da tayi. Da can ma tare suke cin abinci da nata yaran. Amma tun tafiyar su Abbati karatu aka dinga gulmarta ana cewa bata san darajar addini ba. Da kansu iyayen suka raba musu kwano. Gwaggo Mairo kadai ta kaiwa abincin ta sharesu. Da Abbati ya dawo daga gaishe da 'yan uwa da ganin abokansa ta ajiye masa tuwon fuskarta dauke da murmushi. Wani guntun kakide da aka bata a gidan Sarkin Noma da take ta janjani yau duka ta zuba masa. A zatonta yadda Sani ya zauna cikin wahala da rashin abinci shi ma hakan ne. "Ashe kakiden nan rabonka ne nake ta boyonsa sai ranakun daidai muke ci. Na san ka fimu bukata." Kallon tuwon nan ya yi yaji gabadaya zuciyarsa tana tashi. Miyar a idonsa tsululu tayi sai mai a sama. Ya kile fiye da zato da tsammani. Abincin sayarwa ma ba na kowacce 'yar talla suke ci ba. "Ci mana Abbati. Ko a baki ka ke jira na baka" ta ce tana 'yar dariya. Kwanon ya ja gabansa ya saka hannu. Kadan kadan yake gutsira sai Mari ta tashi ta bashi wuri. Karshenta dadewar da suka yi basu hadu ba ce take saka shi kunyarta. Tana tashi ya bi bayanta ya tabbatar ta bar harabar bangarensu sai ya dauko kwanon ya nufi garken awakinta. Dama tuwon ya yi da hannunsa tana kallo. Lokacin Inuwa ya aiko ta a bashi buta zai yi alwala a waje. Mamaki ne ya kamata yadda Abbati ya hade rai ya jagwalgwala tuwon ya juyewa awakin. Ita bata ci ba. Bata bawa mahaifinsa da kannensa ba amma ya wulakanta shi haka. A jikin kyaure ta labe tana kallonsa har awakin suka cinye sannan ya ajiye kwanon a wurin wanke-wanke. Kwalla ta mayar da ta cika idanun ta taho kamar shigowarta kenan. "Ba dai har ka gama ci daga fita ta ba?" "Na cinye shi tas Baaba." Da yake da akwai kuruciya a tare dashi bai yi lissafin tazarar lokacin da ta fita bai isa ace ya cinye ba. Kada kai kawai tayi bata nuna masa ta ganshi ba amma daga ranar ta sanyawa duk motsinsa ido. Abinci kullum ci yake kamar magani. Da ya dan sami wanda zai ji kuzari sai ya tashi. Hankalinta fa ya tashi ta tafi wurin Mai maganin shawara ta karbo masa. Mutumin ba kudi yake karba ba sai dan abin sadaka. Haka tazo gida ta dinga tafasa masa yana sha tana yi masa sirace. Babu wani chanji a tare dashi amma haka ta daure kullum ba fashi sai anyi. Ana haka Jummai kanwarsu Inuwa dake aure a Karkarna wani kauyen Jigawan ne shi ma tazo ganin gida. Ta taho da 'yan yaranta guda uku su ga kakarsu Inna Mairo. Babban namiji da bai fi sa'an Sani ba sai kannensa mata biyu. Ranar da ta kara wargaza farincikin Mari ta kama alhamis. Ita da Jummai ke gurfane gaban Mal. Sa'adu suna magiyar kar a mayar da Abbati Kano. "Yaya tunda Mari bata so kuma ga abin da ya faru da Sani don Allah a hakura mana" cewar Jummai kamar za tayi kuka. Ita da Mari sun kasance aminai tun kuruciya. Mari da take suruka ba zai iya zaginta ba amma Jummai sai da ta zubar da hawaye saboda kaifin maganganunsa gareta. Suna can suna roka masa ingantacciyar rayuwa ashe shi kuma jarabar tsiyar da ya koyo ta kwana biyu tana addabarsa. Ya rasa da wa zai yi a gidan ba tare da an tona masa asiri ba. Shigowarsa gida kenan daga wajen wasan gare-gare da suke yi da abokansa ya hango Hanne. Ita ce 'yar Jummai ta biyu. Ita kadai ce take kwaba kasa tana wasanta. Munzali ya bashi labarin ranar da ya yi da 'yar makotansu. "Ba don munafukar Innayo dinnan ba da kullum sai na daukota munyi. Amma kawai ta shigo mana daki don gulma." Bai manta yadda suka zauna suka zagi Innayo ba bayan Munzali ya ce masa matar uba ba uwa ba. Wannan karatun Asabe ne ya yi amfani dashi wurin sake batawa Abbati tarbiya. Bai taba raina amaryar babansa ba sai yanzu da yake jin da za ta shiga hurumin Mari zai rama mata. "Hanne zo ki karbi adua" ya kirata yana fito da aduar da suka tsinto a hanyar gida. "Bana sha." "To zo muyi wasan doki. Sai na goyaki mu shiga dakin baya." Dakin bayan kamar rumbu yake. Kayan abinci ne idan mazan gidan sun girbe amfanin gonarsu kowa nan yake ajiyewa. Da sauri ta taso ta dane bayansa. Yana ta gudu da ita da wayo da wayo ya tafi dakin bayan. ('Ya 'yar uwa, ban ce ki dora zargi akan 'ya'yanki ba. Amma yana kyau idan suna wasa a kebantaccen wuri lokaci zuwa lokaci ki dinga lekensu a boye. Zamani ne muke ciki mara dadi. Kina iya kokarinki wani ko wata azzalumi makiyin Allah zai koya musu mummunar dabi'ar nan tun da kuruciya..kada ki raba kan 'ya'yanki saboda mugun zargi amma kuma kar ki yarda ki shantake kina musu kallon basu san komai ba Tunda uba zai iya yiwa 'yar cikinsa ciki ta haihu to ki kaddara KOMAI IS POSSIBLE. Allah Ya karemu daga sharrin yai da gobe.) Daga wasan doki Abbati ya danne Hanne. Bata san me yake yi ba illa kashedin da yake ta nanata mata. Idan ta fada sai ya yanke mata baki. Suna wannan yanayin hankalinsa ya yi gaba sai ga matar guda cikin kawunansa ta kawo kai. Sai da gabanta ya fadi da ganin halin da yaran suke ciki. Amma saboda bakin hali da kishin faccaloli bata yi musu magana ba. Shi kuma bai ganta ba. Lallabawa tayi ta koma ta kira kawayenta cikin matan gidan. Su hudu suka dawo suna kallonsu suna sallallami. "Ai sai ku kirata tazo tagani. Tana can gaban Malam ana rokon kar ya koma ita da kawarta. Ashe 'ya'yan iska suka ajiye mana a gidan." 'Yar aiken Jummai ta kira "Zo ki ga Hanne." Yadda tayi maganar Mari ta fahimci babu lafiya. A wurinta da na kowa ne kuma ko wane yanayi Hanne ke ciki ba sai mahaifiyarta ce kadai ya kamata ta gani ba. Idan abun taimakawa ne ta taimaka mata. Kusan duka matan gidan ta gani a tagar dakin bayan. Jikinta sai ta hau rawa ko buhu ne ya fadowa Hannen. Da gudu ta tafi dakin kai tsaye Jummai na biye da ita. (Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Ya Allah kar Ka taba nuna mana 'ya'yanmu a cikin wannan yanayi. Ya Allah Ka tsare al'urarsu daga alfasha ta fin karfi ko ta ra'ayi. Amin). Abbati ta gani dare-dare akan Hanne yana mu'amala da ita cikin kwarewa. Kunnuwan Mari suka toshe bata ma ji ihun da Jummai ta saka ba. Idanunta suka makance. Jininta ya hau duk da ba asibiti taje ba domin duniyar cak ta tsaya mata. Bata san da yadda aka yi ta isa garesu ba sai sautin maruka kawai da suke tashi. Finciko Abbati tayi waje tana kai masa duka kamar an aikota. Magana take yi amma baka gane jumla ko daya saboda harshen ma ya harde. Hawaye kuwa ya sa ko ganin inda take kai dukan bata yi. Amma duk da haka soyayuar danta tana nan cikin zuciyarta domin ita din uwa ce mahaifiya gareshi! *** Daga shafi na gaba in sha Allahu zamu hadu da taurarin wannan labari a shekara guda.Wattpad https://my.w.tt/8NYyQD7zf9 UWA UWACE...6 (Da dadi ko ba dadi) Batul Mamman💖 Tun ana jin ihu da magiyarsa har muryar ta dauke sai nishi kawai yake fitarwa . Sai da ya kusa daina numfashi Mari ta barshi. Ita ma din gefe ta samu ta tsuguna tana nata kukan. A hankali ta daga kai ta saci kallonsa da ta daina jin nishin nasa. Duk tsiya duk lalacewa Abbati jininta ne, danta ne wanda take yiwa soyayyar da bata da kalmar kwatance. "Dan iskan yaro. Wallahi bari Malam ya zo komawa zai yi inda ya fito don bai isa ya zo ya lalata mana 'ya'ya ba" Muryar Deluwa ce ba wata ba. Tana fara magana sauran ma suka dinga tofa nasu ana ta kwashewa Abbati albarka. Jummai ta bar wurin tare da Hanne ta tafi dakin Inna Mairo. Abin da ya faru din ya girgiza Innar ta taso da kyar saboda ciwon kafa na girma ta taho bayan. Abbati ta gani a yashe kamar gawa ga matan gidan ana ta zage-zage. A can gefe kuwa Mari ce ta zuba masa ido. Lafiyarsa take son tabbatarwa amma tana tsoron nuna tausayinta gareshi a ce bata damu ba. Ajiyar zuciya ta sauke da taga Inna Mairo ta iso wurin. Abbati ta duka ta tayar yana numfarfashi ta gallawa Mari harara. Fada ta soma yi mata cikin bacin rai. "Kisan kai ki ka yi niyar yi ko me? Zo ki kama min shi a kaishi daki." Da sauri kuwa Mari ta taso. "Inna da kanki?" Cewar daya daga cikinsu tana matsowa gabansu za ta daga shi. "Ban son munafurcin banza da hofi. Kafin nazo da tana dukan nasa akwai wadda ta hana ne?" Deluwa ta tabe baki "yo Inna me zai sa mu hana uwa yiwa danta hukunci?" Ko ta kanta Inna Mairo bata bi ba ta nuna Abbati "Mari dauki danki muje dakina." Soyayyar uwa akwai ban mamaki! Mari so take danta ya shiryu. Tana son fahimtar dashi munin laifinsa amma hukuncin tana yi ne ba don tana so ba. Uwaye su kan yiwa 'ya'yansu hukunci mai tsauri wani zubin har ya zarta laifinsu domin kada a ga gazawarsu. Sau tari suna daukar wannan matakin ne domin a zuciyarsu suna hangowa 'ya'yan ceto daga wadanda suke wurin. Abin da Inna Mairo ta hango kenan wanda su Deluwa basu gani ba. Ta san cewa babu horon da uwa za ta yiwa danta ba tare da ya yi mata ciwo fiye da dan a zuci ba. Sannan su ma 'ya'yan zukatansu sun fi nadama da jin kunya idan hukunci ya tafi tare da tausayawa ko da ba daga mai horar dasu ba. Kunyar ganin Jummai a dakin Mari taji sai kawai ta sake shi don kada taga kamar bata damu da laifinsa ga Hanne ba. "Jummai don Allah kiyi hakuri" ta ce muryarta na rawa. "Ba komai fa Mari kar ki damu." Ta mayar mata amma ko ido ta kasa hadawa da ita. Ba laifin Mari bane ta sani amma 'yarta kuma fa? Ba don an gansu da wuri ba kila barnar da zai yi sai tafi haka. Muryar Mal. Sa'adu suka ji a kofar dakin yana doka sallama. "Ina yake tsinannen yaron nan?" Inna Mairo ta zaga wurin girki da kanta za ta dora ruwan zafin gasa masa jiki. Bata ji zuwan Mal. Sa'adu ba. Shi kuwa don kada su bata masa lokaci sai ya sa kai cikin dakin ya janyo Abbati waje. "Shegantakar da kake yi kenan Abbati? To Yasin ba dai a gidan nan ba. Daga yau idan kaga mace ma sai ka sauya hanya matsiyaci." Kausasan kalmominsa sun yiwa Mari zafi. Bata ki a hukunta shi ba amma da wannan sigar ba. Kara kuntata kawai zuciyarta take yi da takaicin silar lalacewarsa. Kofar dakin ta fito tana gani ya jefawa manyan 'ya'yansa Abbati ko kula da rashin karfin jikinsa bai yi ba. Dukan da Mari tayi masa kadai ya jigata shi. Yaran kuwa kamar jira suke suka dinga tafkarsa da tsumagiyar darbejiya. Abbati sai gurnani yake a wahale don kukan ma yaki fita. Zuciyar Mari ta dinga harbawa da tsoron kar shi ma yabi Sani. Da tafin hannunta ta toshe baki saboda kada sautin kukan da ya taho mata ya fito. Tana ji tana gani ake yiwa danta dukan-kawo-wuka. Tabbas ya yi laifi amma duk wurin aka rasa mai taimakonsa saboda ba nasu bane. Da abin ya yi yawa saboda dukansa suke babu digon tausayi tana gudun kar ayi masa lahani cikin kuka ta ce, "Malam na hukunta shi. Yanzu na gama dukansa." A harzuke ya mayar da dubansa gareta "ni kike fadawa haka? Ni za ki cewa kin hukunta shi?" "Nufinta a dena dukar mata da. Ai idan baku yi da gaske ba ma ina tsammanin yana daf da komawa dan mace duk da ubansa yana raye." Cewar Deluwa don ta kara zuga shi. Kafa daya daga cikin 'ya'yan nasa ya daga zai saukewa Abbati a ciki sai ga Inna Mairo ta dawo. Da karfinta ta ce "kwarankwatsa dubu idan kafarka ta same shi sai na tsinewa ubanka gashi nan" ta nuna Mal. Sa'adu "kuma duk ku bar min wuri taron marasa mutumci. Indai mugunta da bakin hali abin yi ne don Allah kar ku fasa." Ta juya ga amaryar Mari "ke kuma da hankali ya isheki da suna dukansa ke ya kamata ki agaje shi ki dauke shi." Sum-sum matan suka fice aka bar Mari hannunta har kaikayi yake tana son juya Abbati taga yanayin da yake ciki amma ido ya hana. Mal. Sa'adu yana yiwa Jummai tambaya game da halin da Hanne ke ciki sai ga Inuwa a guje da fatanya a hannu. A kan dansa ya sauke ido ya tafi da zafin nama zai taba shi Inna Mairo ta hana. Ta san zance ya kai gareshi ne yazo dukansa. "Don Allah Inna ki barni na zane masa jiki gobe ma ya kara..." Tsakin da Mal. Sa'adu ya buga ya janyo hankalinsa. "Da raina da lafiyata kake tunanin ba zan hukunta shi ba har sai ka zo? Kodayake kaima gara kayi masa naka domin ya san girman laifinsa." Ran Inna Mairo ya kai kololuwar baci da yadda Mal. Sa'adu yake nuna rashin mahimmancinta a wurin tana matsayin mahaifiyarsu. "Ku kashe shi ku huta tunda ban isa ba." Kamar ya yi kuka Inuwa ya ce "amma Inna har nawa Abbatin yake da za'a ce har ya san mace?" Juyo masa da Abbati tayi ya ga yadda fuskarsa ke fitar da jini kuma ta fara kumbura sai jikinsa ya yi sanyi. Zama suka yu jigum sai tashin sababin Mal. Sa'adu har Inna Mairo ta gasa masa jiki. A dakinta ya kwanta zazzabi ya rufe shi. Mari ko dakin bata shiga ba ta zauna a waje har lokacin bata bar hawaye ba. Ana la'asar duka mazan gidan suka hallara a bangaren Inna Mairo. Ita ta soma magana a matsayinta na babba a gidan. "Kun ga illar wannan almajirancin da karfi da yaji ku ka kakabawa 'ya'yanku yinsa ko?" "Gidan nan kowa ya san kin fi son matar Inuwa saboda ta dan zauna a birni. Banda haka Inna ba sai kin kushe lamarin addini ba don ki goyi bayanta." Mal. Sa'adu ne ya yi wannan maganar da gatsali. Kannensa kansu sun yi mamaki duk da ba tun yau yake kokarin nuna ya fita matsayi a gidan ba tunda shi ne namiji. Da yake mace ce mai saurin fahimta kuma kamar Mari ta jima abubuwa da dama na rayuwar bahaushe musamman na karkara yana damunta, sai kawai ta girgiza kai. "Malam ni fa ba matar ubanka bace, haihuwarka nayi saboda haka ba zan yarda ka fada min bakar magana a fakaice ba." Maganar ta dan dake shi sai dai nuna hakan zai iya sakawa kannensa su fara bijirewa umarninsa. "Gaskiya ce kawai na fada miki. Tunda dai mune maza ki bari muyi magana mu shawarta yadda zamu bullowa lamarin nan." Shiru tayi na wani dan lokaci sannan ta tashi jiki a sanyaye. Ta san haka suka tashi suna gani iyayensu mata basu da mahimmancin da ya wuce yi ko bari a idon mazajensu. Shi yasa idan sun girma suke raina uwayensu su kuma taka matansu. Sa'adu ya dade da rainata tun mahaifinsu yana da rai. Idan tayi magana ya ce jarumin namiji kenan. Kirjinta ke suya da bakincikin rayuwar da tana da yakinin idan an kokarta za'a iya wadda ta fita dadi. Za ta bari suyi shawararsu ko don kada sauran masu jin maganar tata cikin kannensa su ga suna sa'in'sa suma su bi sahu. Bayan tafiyarta Inuwa ya yi tsalle ya dire cewa Abbati ya gama karatu a Kano. 'Yan uwansa kuma suka dage suma sai ya koma domin ba zai zauna ya lalata musu nasu yaran ba. Tabe baki Mal. Sa'adu ya yi har suka gama gardamarsu sannan ya kwalawa Mari kira. Tana fitowa ya ce ta je ta taho da Abbati. Yaron ko tsayuwa akan kafafunsa ya kasa amma haka ta kawo shi ta zaunar. A zuciyarsa yake jin haushin kowa musamman Mari da ta bari aka sake yi masa duka. Idan ita tayi bai ga dalilin da zai sa ta bari ayi masa dukan da ya kusa ajalinsa ba. Duk yadda zai yi ya bar Kirikasamma zai yi don yanzu ya fahimci bashi da masoyi sama da Munzali. Shi ne farkon wanda bai hada jini dashi ba amma ya damu da damuwarsa. Kamar daga sama kuwa yaji Mal. Sa'adu yana tambayarsa a ina ya koyi wannan dabi'a. Bai yi wata-wata ba ya ce "Nan." Inuwa ya zabura ya ce "Nan? Nan garin kake nufi?" Kai ya gyada da kyar. Muryar Mari ya ji tana kuka a kusa dashi. "Karya yake Malam. Da a garin nan ne da na dade da sani. Ka yiwa Allah da ManzonSa ka bar shi a gabana." Basu san bata bar wurin ba sai yanzu. Mal. Sa'adu ya ce da Inuwa ya koreta daga wurin ko kuma shi ya tsame hannu daga abin da ya shafesu. Da rawar jiki Inuwa ya ce ta tafi. Gani tayi shirunta babu abin da zai haifar sai karin cuta ga danta. Tana mikewa ta hau masifa tana zubar da hawaye. "Babu inda zani. Haba! Da me kuke so naji ne? Wallahi Allah a Kano aka lalata yaron nan. Idan ya koma Allah kadai Ya san abin da zai zama kuma. Don Allah Malam ka barshi a gida mu saka masa ido." Galala suka tsaya kallonta kafin Mal. Sa'adu ya yi gyaran murya bayan ya tashi tsaye fuskarsa a hade. "Inuwa zabi yana gareka. Ko mutumcin gidan nan da addininka ko matarka amma Billahillazi yau dinnan sai ka zabi guda." Ya girgiza matuka ya kalleta tana tsuma da mugun bacin rai. Ta gaji ta kai makura akan mulkin Hitilan da Mal. Sa'adu yake gwada musu a gidan. "Mari ki bashi hakuri." "Ba zan bayar ba! Idan da wanda ya cancanci a bashi hakuri to a bayana yake." Sai kuma muryarta ta karye " Haba Maigida? In rasa Sani wannan kuma ya dawo a haka sannan ka ce in bashi hakuri? To hakurin me?" "Inuwa matarka bata da kunya." "Ba dole danta ya yi iskanci ba tana da irin wannan halin." "Dole ka rabata da 'ya'yanka." Shawarwarin sauran 'yan uwansa kenan da basu son abin da zai batawa Mal. Sa'adu rai har ya yi fushi dasu. Shi kadai ke sakawa da hanawa a gidan. Kallonsa suka dinga yi ana jiran jin me zai ce. "Ki je gida na sake ki saki daya." Kirjinta ne ya hau dukan uku-uku amma a haka ta kama Abbati za ta tafi bangarensu daukar gyale. "Sakar min da." Kallo mai tsayawa a rai ta yiwa Abbati. Kallon da zai yi ta tayar masa da tsigar jiki saboda tarin ma'anoninsa har a shekaru masu zuwa. Za ta iya dafa Izu sittin cewa karya yake yi a Kano ya koyo abinsa. Tun yanzu saboda wasu dalilai ya zabi komawa can akan zama da ita. Duk wani fadi tashinta yau ya katse shi a dalilin haduwa da Munzali. Murmushin biyan bukata Mal. Sa'adu ya yi. Yau dai ga karshen rashin kunyar Mari. Ba a taba surukar da take turjiya akan umarninsa ba sai ita. Idan ta zauna sauran ma zasu koyi bijire masa. Yanzu kuwa ko ta wane hali ba zai taba bari Inuwa ya dawo da ita ba. Kafin Magariba ta fita zuwa gidan wani kawunta a garin Maigatari. Inna Mairo har kuka tayi ta umarci Inuwa ya mayar da ita amma yaki saboda maganar Mal. Sa'adu tafi ta kowa. Bayan sati biyu su Abbati suka koma Kano. Inuwa ya sani ba sai an fada masa ba cewa rabuwa da Mari kuskure ne sai dai kuma ya yarda cewa hana almajiranci sabawa addini ne. Wanda baya son addini kuwa ba abokin rayuwa bane. Shi da 'yan uwansa suka dunguma Karkarna gidan Jummai. Mal. Sa'adu ya sake baiwa mijinta hakuri akan abin da ya faru. "Kuma matsawar ina raye yana kawo girma za'a daura musu aure. Kai Inuwa ka rubuta ka ajiye. Abbati ba shi da mata sai Hanne." *** "Wai Ladidi tace ki dafa mata shinkafa da miya, sannan ki tura a sanar da ita da wuri don bata so ya huce." Kalaman Jiddo kenan ga Nasima tana fada mata sakon mahaifiyarta. Sakuwarta ce sai dai ba ciki daya suka fito ba. Jiddo 'ya ce ga yayar Ladidi daga garinsu Soba. Dan kudin da ake ganin ta fara kamawa tun bayan auren Nasima da Tahir shi ne aka turota cin arziki. A haka duk wani aikin wahala ita take yi musu a gidan. Kallon wulakancin da ta saba ta yiwa Jiddo, tana jin kamar ta sa hannu ta mare ta saboda takaicin da take kwasa na Ladidi a 'yan kwanakin nan. Ta tsiro da wata sabuwar dabi'a ta cewa anan gidan za ta dinga cin abincin rana. Da ace da hali ma ba dan Tahir ya kan dawo da wuri ba to na dare da na safe ma nan za ta so ta dinga ci. Ita dai ta zauna a saka mata kaset a bidiyo tana kallo tana kwasar gara, ta ce a miko mata wannan a miko mata wancan. Cikin bacin rai Nasiman tace mata "ki gayamata cewa nima fita zanyi idan na dafa zan aiko mata dashi gida." Nan Jiddo ta juya ta fice. Ba jimawa ta dawo, tace ladidi tace a bar mata makulli idan ta gama zata tafi da makullin gida idan yaso Nasima in ta dawo sai ta biya can gidan ta karba. Takaici ya sake kama Nasima, tayi kwafa ta tashi ta shiga kitchen ta dauko wata tukunya ta mikawa kanwar tata. "Gashi nan ki kai mata, ki ce jiya nayi amma na manta ban sa a firij ba shine tayi tsami. Ta saka kanwa in ta gyara miyar, ta dafa shinkafar da zataci." Tana gama fadar haka ta dangwarar mata da miyar ta koma ciki abinta. Shiru shiru da Jiddo taga bata fito ba ta zari tukunyar miyan ta kama hanyar gida. Ba dai haka taso ba amma haka nan ta karbi tukunyar rai a bace. Taci burin zuwa gidan Nasiman, gashi akwai wuta taje tai kallo tana cin abincinta a karkashin fanka. Da ta kai tukunya kitchen ta bude taga nama zuqu zuqu hankalinta gaba daya ya tashi, nan da nan ta jiqa kanwa ta gyare miya ta dafa shinkafa ta zauna ta ci. Saboda bakin hali ma bata rage wa kowa cikin yaran nata ba. Ta cinye abincin ta tas, naman ma bata bar musu ba. Sai dare tukunna cikinta ya soma ciwo, yanata kulululun kuka, kafin asuba tayi gudawa ya kai sau goma. Garin Allah na wayewa, ta sake tura Jiddo a fadawa Nasima bata da lafiya azo a kaita asibiti. Zazzafan bugun da ake yiwa gate din ne ya tashi Tahir a firgice daga bacci ya fita kofar gida. A nan ya tarar da kanwar Nasima suna magana da Mallam Ado maigadi. Bayan ta gaishe shi ta sanar da shi abun da yake faruwa. Ko a jikinsa don bai ma yarda ba. Ya dai ce Allah Ya bata lafiya tare da juyawa ya koma cikin gida. A zatonsa irin shirin da suka saba masa ne don tatsar kudi a jikinshi. Tuni ya riga ya dawo daga rakiyar su, auren ma ya fice masa rai don dai ba yadda zaiyi ya rabu da ita ne. Da kunnuwan sa ya ji wani lokacin da Ladidi take cewa Nasiman akawo mata Mardiya yaye don su samu hanyar cin kudin gurinsa. Shi kuwa daga jin haka kafin su farga washegari ya dauke ta ya kaita wurin Yakumbo. Gashi har yanzu kusan satin ta biyu gurin bai ma karbo ta ba. Lokacin haihuwarta sun tatse shi son rai. Shi da ya saba mu'amala da mata a waje ya san duk wadannan karairayin na cin kudi. Sai dai kawai ya kyalesu suka zata wankarsa suke. Daga lokacin ne ya dinkewa Nasima da ta dawo. "To sai ki tashi bakin naki ne. Daya daga cikin kannenki ni ba rike sunayensu nake ba." Bai ko damu da fada mata me ya faru ba kamar bai ji sakon ba haka ya ja bargo ya koma baccin sa. Da haushin kalamansa na rashin rike sunayen kannenta gami da tashinta daga bacci ta fita. Fitar tata ke da wuya sai gata ta dawo ta dan tattaba shi don ya tashi, "Wai Ladidi ce ba lafiya" "Tun a wajen na ce Allah ya bata lfy." Ya sake juyawa ya cigaba da baccinsa. Ta danyi kwafa a ranta ta fita da niyyar shirin tafiya. Bayan tayi wanka ta shirya ne ta shigo ta same shi yadda ta barshi yana baccinsa hankali kwance. Bata ji dadin yadda ya nuna halin ko in kula ba amma dama itama ba daraja bane da uwar a idonta. "Amma dai Diya yanzu fa nace maka Ladidi ba lafiya baka ce komai ba." "To me kikeso na ce miki?" Ya ce da alamun kosawa. "Kudin zuwa asibiti zaka bani mana." "Bani dasu, dan Allah ki barni na samu bacci me dadi kar ki dame ni." Ya juya mata baya yana tunanin ko idan ya tashi ya je Zaria wurin Khadija. Fuuuu ta fice tare da bugo masa kofa ta tafi gidan su. Halin da ta iske Ladidi ya wuce yadda tayi tsammani. Haka suka kwasa sukayi a asibiti ba yadda take. Allah dai ya taimaka akwai yan kudade hannun Nasiman dasu ta biya aka basu gado tare da saka mata ruwa. Suna zaune asibiti har la'asar. Ladidi jiki ya dan lafa ta samu ta lallaba ta tashi zaune. "Wash, Nasima me zamu samu ne na dan saka a ciki? Me kuka dafo ne a dan tarfa min naci." Shekrke ta kalli uwar tare da sakin wata yar dariya. "Amma dai wallahi Ladidi a gaishe ki. Ace kin kwana kina cikin wannan yanayi amma daga dan samun salama sai ki hau neman abinci." Marairaice fuska tayi "To yar nan ya za ayi? Kinga ko fa magungunan nan da ake narka ma ba za suyi aiki ba in babu abinci. Ni a bar zancen nan dan Allah ku zuba min na ci. Allah ma yasa dai ba mai da yaji ba ne. Nafi son harkar miya kun san akwai gina jiki." Rai a bace Nasima ta yarfe hannuwa "To ni dai babu wani abinci anan. Tun safe da muka kawo ki ko tashi ban daga nan ba balle wani zancen abinci." Tuni fuskan Ladidi ya rikide tai kicin kicin ta hade rai. "Yanzu kina nufin haka zan wuni na kwana ban ci abinci ba fisabilillahi. In zawon da na kwan inayi be kar ni ba ai sai yunwa tayi sanadi na." Nasima ta juya ta kalli Jiddo a wulakance. "To kinji dai sai ki tashi kije ki dafo ki kawo ko." Ba musu Jiddo ta ta mike har zata fita ta juyo ta nema kudin mota, Nasima ta ciro a wulakance ta dangwara mata a hannu tana cewa "saura in kinje ki dade". Jiddo bata ce komi ba ta fice abunta tana fatan Allah dai ya kai damo ga harawa Ya bata ikon cikar burinta dan tsaf sai ta rama duk wannan wulakanci da ake mata. Tana sauka daga bus a bakin layinsu maimakon ta wuce gida sai ta tsaya kofar gidan Nasima. Ta gaishe da Malam Ado tace masa Nasima ce ta aikota. Bsi hanata shiga ba tunda ya san kanwar matar gida ce. Ganin motar Tahir a farfajiyar gidan ba karami dadi yayi mata ba har da sakin dan murmushinta. Yadda duk aka kai aka kawo aka yi auren Nasima da Tahir din ai babu abun da basu sani ba. In dai kura na maganin zawo to shakka babu yau zan wa kaina magani ta fada a ranta tare da cusa kai cikin gidan A falo ta iske Tahir ta gaishe shi a ladabce tare da fada masa Nasima ce ta aiko ta yin girkin asibiti. Bai ce mata komai ba sai tunanin irin wannan karfin hali nasu, dan me ba za suyi a nasu gidan ba sai a nashi. Hanyar kitchen ya nuna mata ya kau da kai ya cigaba da abun da yakeyi. Kafin ta wuce sai ta cire mayafi ta aje kan kujera, ta wani hau yarfe gumi daga su wuya da kirjinta. Jujjuya jiki ta dinga yi na daukar hankali. Tahir kamar baisan tana gun ba, ita ko bata fasa ba har sai da ta tabbatar ya waigo ya kallo inda take nan ta juya masa baya ta wuce kitchen din. Bata jima da shiga ba ta saki wata kara har sai da Tahir ya dan firgita ya taho da azama zuwa kitchen din dan ganin me ya faru. Tsalle ya sameta tana yi tana direwa ita nan a dole hannun ta ya kone. Sai ya tuna da lokacin da Nasima ta fara rungumar sa a cikin gidan da irin wannan sigar. Sabanin Nasima, ita Jiddo bata nufo shi ba. Yayi dan murmushi a ransa tare da yi mata sannu ya juya zai fice kawai ta saka kuka. Hakan ya sashi dawowa. "Naga hannun" ya umarceta. Kamar jira take ta mika masa. Yasa hannu ya riko hannun nata ba kunya ba tsoron Allah. Daman yaya lafiyar kura balle yaga abin da rai ya biya. Ya hau hura mata yana kallon cikin idonta, ita kuma tana wani sussune kai. "Ko muje daki na shafa miki magani ne." Ta sunkuyar da kanta tana matse ido wasu hawayen na zuba "A'a ka barshi ma ba zafi." "To kukan na meye?" Ya tambaya hannunsa a bayanta yana shafawa. Suna hada ido ya kanne mata nasa yana murmushin 'yan duniya. "Babu komai" ta ce baki na rawa. Dakinsa ya ja ta tana binsa kamar bata sani ba tana kuka. Rarrashinta ya yi ya sake tambayar dalilin kukan. "Hannuna zugi yake yi min da wuya na iya girkin. Idan na koma haka kuma Nasima da Laraba ba kyaleni zasu yi ba." "Kar ki damu. Muje na saya musu sai ki kai." "To ai za ta yi min fada idan taji kai ka saya." Ta ce a shageabe. "Zan yi mata bayani." Godiya ta dinga yi masa har suka bar gidan. Da dai bai yi niyyar zuwa asibitin ba amma tunda yana son samun kan Jiddo sai ya bi a sannu. Da suka isa asibitin shi ya dauko ledojin abincin tana biye dashi a baya. Ta bude masa kofar kafin ya shigo Nasima ta soma zaginta. "Uban me ya tsayar dake daga zuwa girki bayan babu nisa." Hawaye ta sake tarawa a idon tana rawar murya ta bata hakuri. Tahir kuma yaji ransa ya baci. Ita da Ladidi suna ganinsa suka fara murna. Duk da Nasima taga abinci ya kawo amma sai da ta tambayi Jiddo ina wanda ta dafa. "Konewa nayi Nasima. Shi ne Abban Mardiya ya ce na barshi zai siyo." Mantawa tayi da yadda take ladabin kura a gabansa ta hau zazzaga mata bala'i. "Wani salon karuwancin ne wannan ko me? Gidana na tura ki? Me ki ka je yi?" Ai sai Jiddo ta fashe da kuka "Naji kin ce naje gida nayi girki. Na zata gidanki ki ke nufi." Sake bude baki tayi Tahir ya mike a fusace sai tayi shiru tana taune lebe saboda bacin rai. Ta fi Jiddo iya bariki. Idan ta ce za ta shiga huruminta sai ta kwashi kashinta a hannu. Daga ranar ta ja mata kunne akan kada ta sake zuwa gidanta ko da wasa. Ladidi ta sake matsa mata. Ba don tana morarta da aiki ba da ta korata inda ta fito. Jiddo ta amsa da to. Aka kwashi kwanaki Tahir baya ganinta. Sai rannan bayan ta gama fakonsa ya hangota a gefen gidansa tana share hawaye. Da sauri ya taka burki ya fita wurinta. "Ke lafiya?" Bai rike sunanta ba. Fashewa tayi kuka ta rike ciki tana matsawa. "Don Allah ka taimakeni. Cikina, cikina." "Muje ciki wurin Nasima. Ko kuma shiga mota bari na kira ta mu kai ki asibiti." Hannunsa ta kamo da sauri tana zubewa a kasa "ni dai la taimaka min ka mayar dani garinmu." Kallon rashin fahimta ya yi mata ta ce masa tun ranar da ya kaita asibiti da abinci Nasima ta hanata shiga gidanta. A can gidansu kuma Ladidi ta matsanta mata. Abinci ma sai da kyar ake bata. Yanzu haka ma ciwon na yunwa ne. Da yake idanunsa sun rufe sai yaga kamar da gaske ta fada. Ransa ya mugun baci ya shiga da ita gidan. Nasima bata nan bai san inda taje ba. Khadija kuma ta zo hutu da yara saboda bikin kanwarta bai san suna ciki ba. Akan idon Suhaib ya shigar da ita dakinsa. Ya koma ya hada mata abincin da Nasima ta ajiye masa ya kai mata. Ta ci ta koshi sannan ya ce ta taso zai kaita hotel ta kwana gobe sai ya kaita gidansu. Khadija ta gama yiwa Sauda wanka kenan Suhaib ya fada mata Abbansu ya dawo. "Amma Mami naga ya shiga dakinsa da bakuwa maimakon ta zauna a falo ta jira ki fito." Gabanta taji ya fadi. Ba abin mamaki bane daga halayyar Tahir amma tayi zaton ya yi hankalin da zai daina kawo tarkacensa gidan aurensa. Yadda fuskarta ta sauya a idon Suhaib ya gane akwai matsala. Da ta ce ya zauna ya kular mata da Sauda tana zuwa sai yabi bayanta ba tare da ta sani ba. Batun zuwa hotel kadai taji a kofar dakin ta kwankwasa. Ya zata Nasima ce saboda haka kai tsaye ya bude. Ganin Khadija a tsaye sai yaji kunya ta lullube shi. "Ko don lafiyarka idan ma baka tsoron Allah Ya kamata ka yiwa kanka fada." Da sauri ya ce "ba fa abin da kike zato bane. Taimakonta kawai nayi." "Hmmm, taimako a uwar daka? Ina jiye maka ranar nadama domin wallahi hakkin duka matan da ka ke lalata dasu ba zai barka ba." Haushi yaji tunda bai yi din ba kuma take gaya masa magana. Kafin ya ce wani abu Nasima da ta dawo ta shigo wurin. Bata san me yake faruwa ba ta taho da gadara da tsiwarta. "Duk jarabar mutum dai yau girkina ne tunda ban san zaki zo ba. Sai ki koma sai gobe." "Ke miji ya dama Nasima. Idan kin shiga kya yi maganar girki da ta ciki ba ni ba." Ai kamar ta watsawa Tahir wuta ya ji takaicin abin da ta ce. Hannu yasa ya janyota za ta bar wurin ya kwasheta da mari. "Wato ban dameki ba? To idan kin isa ki saki kanki." Hannuwa yaji daidai kugunsa aka dage aka hankada shi sai da ya daki kofar dakin ya fadi. Yana tashi yaga Suhaib yana huci kamar maciji. "Ni ka ture Suhaib?" Ya ce da tsantsar mamaki. "Me yasa ka mari Mami?" Yaron ya bashi amsa kai tsaye. Bakinsa Khadija ta doke da sauri tana cewa ya bawa babansa hakuri. "Khadija halayyar da ki ke koya musu kenan?" Za ta yi magana suka ji sautin ihun Jiddo ya fada dakin yayin da Khadija taja hannun Suhaib. Amma kunnuwansa sun jiyo masa kalmar 'karuwa' da Nasima ke kiran Jiddo. Lokacin da Khadija ta ce suyi magana da ta ciki ta fada dakin da sauri. Jiddo dama tana jin muryarta ta kwanta akan gado ta kwaye zani har cinya. Bata ma gane ko wace ce ba saboda azabar kishi sai da ta finciko wuyanta. "Jiddo?" Ta ce da rawar baki "ni za ki yiwa haka? Mijin nawa zaki nema saboda ke 'karuwa ce'." "Nasima kiyi hakuri babu abin da muka yi." Ta ce tana kukan munafurci. Idanunta sun rufe ta shiga dukanta ba ji ba gani. Da kyar Tahir ya kwaceta ya kuma tsinkawa Nasiman mari. "Ki je gida sai na nemeki. Zan zo na karbi Mardiya don ba za ta zauna a gidanku na marasa tarbiyya ba." Hauka ne kadai Nasima bata yi ba. Tana ta kokarin sake kamo Jiddo ya shiga tsakani. Da kuka ta bar gidan da alwashin sai taga bayan Jiddo. Ita kuma tana ganin fitarta ta soma kukan rayuwarta ta kare domin ba ita ba hatta mahaifiyarta sai Ladidi ta ciwa mutumci. "Zan baki matsayin da basu isa su tabaki ba." Ya kuwa aikata abin da ya ce! Sati hudu a tsakani sai ga Jiddo ta dawo gidan a matsayin amarya. Dakinsa ya zama nata. Nasima da Ladidi suka haukace wurin bin bokaye da malaman tsibbu. Zumuncinsu da 'yan uwa da yawa ya lalace. Da kyar da sudin goshi bayan wata biyar ya yarda ta dawo gidansa. Kazamin kishi suke bugawa ita da Jiddo kamar zasu ga hanjin juna. Tun daga kan Mardiya bata sake haihuwa ba. Jiddo ta zubar da ciki yafi a kirga a kauye har ya taba mahaifarta. Ita ko haihuwar bata yi ba. Khadija ba ta shiga sabgarsu daga su har mijin da suke rigima a kansa. Tana gama karatu kamfanin da tayi bautar kasa suka riketa. Albashinta ta shiga tarawa har ya isa sayen fili. A hankali ta soma gina kayanta saboda ta matsu ta raba 'ya'yanta da kazamin gida irin na mahaifinsu. Duk da haka tana kokari sosai wurin shanye abubuwa da rufawa Tahir asiri don kada su san halinsa. Kusan babban burinta a rayuwa bai wuce nesanta su daga sanin halinsa da kwatanta aikatawa ba. Sai dai tunda kudi suka sake zama a hannunsa rashin mutumcinsa ga duka matan ma ya karu. Ita da yake ragawa darajar 'ya'ya ma ya daina. Nasima da Jiddo dama basu da wanban darajar. Gida ne tambadadde wanda mai shi ya lalata da hannunsa. Abu daya suka tsira dashi wato makauniyar soyayyarsa ga 'ya'yansa. Su biyar dinnan bashi da na biyunsu. Don ma Suhaib ba ya sakin jiki dashi ko kadan. Tun ranar da ya mari Khadija ya dauki karan tsana ya dorawa mahaifinsa. Da sannu yana kara wayo ya gane halinsa ciki da bai. Sai yake jin inama wani ne can Abbansa ba wannan manemin matan ba. Khadijan da yake yi dominta kuma kullum fada take masa akan ya bi mahaifinsa don neman rabauta ranar lahira. Sai yake ganin kamar cin kashin da ake mata baya damunta. Yana shekara goma sha biyar ya fara zukar tabar wiwi a boye saboda yawan damuwa da halin da iyayensa ke ciki. Lilu kuma ya zama mugun fitinanne mai yawan dauko magana. Duk kaffa-kaffa da Khadija take yi da rayuwar 'ya'yanta saboda mahaifinsu ba zai hana kaddara ta cimmusu ba wata rana. Wannan kenan! ***Wattpad https://my.w.tt/Fc8knjdAf9 UWA UWACE...7 (Da dadi ko ba dadi) Batul Mamman💖 *** Kwance tashi ba wuya a wurin Allah, yaran Innayo duk sun girma amma har kawo yau sana'o'in da takeyi babu wanda ta daina. Girma ya soma kama ta, ga wahalhalun ayyukan da takeyi domin ta rufawa kanta da ahalinta asiri. Sannu a hankali lafiyar idanunta ya soma tabuwa sakamakon yawan zama gaba murhun da takeyi. Amma haka nan take daurewa don samar wa yaranta ingattacciyar rayuwa. A kullum burinta Yaranta manyan uku duk sunyi aure Uwani, Maimuna da Salima, saura Zara da Hasiya a gabanta. A yadda rayuwa take gara musu tsugunne bata karewa Innayo ba. Uwani ta gama School of Nursing abinta har ma ta kama aiki a Abdullahi Wase Specialist Hospital Kano wanda ake yiwa lakabi da asibitin Nasarawa. Tana samun kudi sosai sai dai anyi rashin sa'a. Halinta yana neman zarta na mahaifinta. Mugun mako da kyashi gareta. Mijinta yana da rufin asiri daidai gwargwado. Lab Technician ne a asibitin nasu. Bai taba dora mata nauyin da ba nata ba na kula da gida ko 'ya'yansu guda uku. Tana da wadatar da za iya taimakawa mahaifiyarta musamman ta harkar lafiyarta amma kullum cikin kiran babu take. Don ma kada Innayo ta dinga tambayarta kudi sai wata ya raba ta kan leko gidan. Tana zama bata da zance sai na bukatunta wadanda kudin hannunta ba sa su isa ta biya ba. Ita kuma Maimuna lokacin da Allah ya kawo mijin rimi-rimi ya amince za ta cigaba da karatun da take a Legal. Sai dai anayin aure ko wata biyu ba a rufa ba zance ya juye. Innayo tace indai don kudin ne zata cigaba da daukan nauyin 'yarta. Yace yaji ya amince dama kudin ne baya so ya biya. To kuma sai mahaifiyar sa ta ce bata yarda ba ko dai tayi zaman aure ko ta fita taje tayi karatun ta. Nan kuwa yace to sai dai ra ajiye karatun. Maimuna shaukin soyayya na dawainiya da ita a lokacin tuni ta amince da bukatarsa. Innayo taji ciwon wannan abun amma ba yadda zatayi haka ta hakura. Haihuwa biyu duk ta tsufa ta lalace. Babu cima mai kyau ga tashin hankalin uwar miji da talauci. A hankali nauyinta ya sake komawa wuyan Innayo kuma bata yi mata komai da kyashi domin 'yarta ce. Salima kuwa watarana suna zaune kwatsam Alh Rabiu yazo wai yayi mata miji kuma aure nan da nan zaayi ba bata lokaci. Nan fa innayo da Alh Rabiu suka hau suka duro ta dage tana so yar ta tayi karatu ko don gudun abin da ya sami Maimuna amma yaki yarda sam. Karshe dai haka wannan ma ta hakura akai auren. Ashe basu sani ba auren biyan bashi yayi mata ga mijin mashayi ne na bugawa a jarida. Yau duka gobe tsangwama haka dai itama Salima rayuwar ta kare babu wani cigaba. Banda lalurar ido tsabar damuwa da halin da 'ya'yanta suke ciki sai hawan jini ya sarketa. Innayo bata fasa komai ba. Tashi karfe hudu na asuba har jikinta ya saba. Kwata-kwata bata san hutu ba. Zara da Hasiya da suka rage take take fatan ko za a samu wani abu na cigaba a rayuwarsu. To matsalar Zara karya ce sama da kasa take dawainiya da ita. A dole ita sai tayi rayuwar da za'a ce ita 'yar wani ce, ita dai kar a rainata. Hasiya kuwa ba sawa ba fitarwa. Yadda bata son rigima haka take kin halayyar Uwani da Zara. Maimuna da Salima kuwa tausayi suke bata. Zara ta gama sakandire da wata shida aka kawo kudin aurenta. Lokacin Hasiya tana aji shida ita kuma ita ma ta kusa gamawa. Saurayin nata da ne ga guda cikin mashahuran 'yan kasuwar da Kano take ji dasu a Singa. Alh. Rabi'u kamar ya zuba ruwa a kasa ya sha. Yadda yake jindadi da mijin A'i haka yake fata daga mijin Zara. Asabe kuwa hadiyar zuciya ne kawai bata yi ba. Hankalinta in ya yi dubu ya tashi wurin nemarwa Ummakati miji na wuce sa'a. An sanya biki wata biyu masu zuwa. Innayo ce zaune a daki da Uwani da Hasiya ga kayan amfanin gida irin su kuka da daddawa da ta siyo tana rabawa gida uku. Uwani dake kashingide akan gadonta ta dago kai. "Ki dan kara min kukar Innayo kin san Usman bai ki kullum na kada masa ba." Murmushi Innayo tayi ta debi cokali bibbiyu a sauran kaso biyun ta kara a daya. A zahiri ita ba da Uwani take rabon ba. Ta san tana da kudin saye. Nata ne da Maimuna da Salima. Ba yadda ta iya ta hakura da natan. 'Yan kudaden hannunta duk sun kare wurin siyayyar auren Zara. Wadannan din ma cikin nata ne ta dibar musu. Dan gyaran murya tayi tana juyayin samun biyan bukata a wurin Uwanin. "Uhmmn. Dama abin da yasa nace ki zo saboda maganar Zara ne." Tashi tayi zaune tana hade fuska "Wallahi indai harkar kudi ce sai dai kiyi hakuri. Na fada miki adashi nake yi kuma sai nan da wata hudu zan dauka." "Yanzu ba za ki iya rokon arziki a baki daukar watan nan ba? Kinga bikin ya matso ko bamu sayi kujeru ba." Tashi Uwani tayi. Da ta san dalilin kiran ma da ta kirkiri dalilin kin zuwa. "Ki nema a wurin Baba ko a rokesu a daga bikin. Ni wallahi yanzu dubu ashirin ma ba zance za a samu a jikina ba. Gobe nake shirin ranto talatin a asibiti. Sai na raba muku ke da Baba kuyi hidimar bikin." Muryar Innayo kamar za ta yi kuka ta ce "iya gudunwamarki kenan a bikin kanwarki? Uwani idan baki tausaya min ba waye kuma zai min? Sauran 'yan uwanki duka abin a tausayawa ne a gidajen mazajensu amma ban taba cewa ki kawo wani abu na basu ba. Na zata kina da hankalin duba yanayin da suke ciki ki ..." Yanzu taji magana. Ta rasa dalilin da yasa Innayo ta kawo ido ta saka akan albashinta. Lokacin da take hana idanunta bacci tana kwana karatu me Maimunan da Saliman suke yi? Basu tsaya sun gina rayuwarsu ba kowace tayi aure. Sai kuma ake tunanin ita za ta dauki dawainiyarsu saboda bata san zafin nema ba. Muryarta a sama ta soma magana. "To ni dai ba zan dauki nauyin kowacce katuwa ba wallahi. Dubu talatin kuma ita kadai zan iya fitarwa saboda nima bani dashi. In don nace ki kara min kuka ne to ki bar abarki. Haba! Ba damar nazo gidan nan kin dinga tasowa da bukatun kudi..." Tasss...taji saukar gigitaccen mari. Da kyar ta bude idonta da ya kanne saboda zafin shigar marin tana neman wanda ya yi mata wannan aikin. Hasiya da Innayo ne a gabanta. Kalaman autar tasu ne ya nuna mata hannun waye ya sauka a kuncinta. "Idan su Yaya A'i sun wulakanta rikon da Innayo tayi musu basa dubanta yanzu ke kina da wata uwar ne bayan ita?" Cewar Hasiya lokaci guda tana fashewa da kuka. Muryarta ta dinga yin sama-sama saboda taki yin shiru. "Kullum ki ka zo gidannan kin dinga kiran babu kenan saboda kada ki taimakawa uwar da ta biya miki kudin makaranta. To Allah Ya hadaki da babun nan da kike kira don girman..." "Hasiya kama gabanki. Fita kada ranki ya baci. A gidan wa ki ka koyi rashin kunya haka?" Innayo ta furta da kwalla a idonta. Kwallar ta sake tunzara zuciyar Hasiya. Rainin wayon yayarta ta ya kaita makura. Idan bata amayar da ranta ba tana jin zuciyarta sai ta buga. "Innayo ki barni don Allah. Dubi dakinki don Allah." Ta nuna kowacce kusurwa da hannunta "Dakin da Yaya Uwani ta mayar kemis a gidanta fanka biyu ce da ta bango da ta tsaye. Ke kuwa fankar tsayen ma da kyar take juyawa. Nima tashi nayi na ganta a gidan nan." Bakincikin marin da Hasiya tayi mata yasa ta kasa cewa komai. Duk abin da ta fada gaske ne to amma gaskiya tana tsoron talauci. Idan tana bada kudin sai su koma matsayin da ta tashi a ciki. Innayo ce ta kama hannun Hasiya ta fita da ita daga dakin. Tana juyowa taga Uwani ta saba jakarta tana gyara mayafi. "Uwani." Ta kira ta a sanyaye. Banda kudin bikin Zara da take nema harda na zuwa asibiti. Kwanakin nan sam bata jindadin jikinta daurewa kawai take yi. Dan abin da take dashi idan ta taba a zuwa asibiti dame za ta aurar da Zara? Danginta suna kauye a haka ta fi da yawa rufin asiri. Shi kuwa Alh. Rabi'u bakin hali ya raba shi da nasa sai jefi-jefi. "Innayo sai naci mutumcin Hasiya. Dani take zancen. Kar ma ki bani hakuri don wallahi ba zan hakura ba." "Zan yi mata fada. Yanzu dai ki taimaka min da ko dubu biyu ne in je asibiti gobe. Bani da kudi a hannu duk nayi sayayya dasu." 'Innayo ba dai naci ba' Uwani ta fada a zuciyarta. A ganinta duk abubuwan da take yi sun isa su sa tayi fushi ta daina tambayarta komai. Ba dole su A'i suka gujeta ba. Kila su ma roko ta damesu dashi. Dubu daya da dari biyar ta bata tasa kai ta fita. "Nima ba kudin gareni ba." Hasiya tayi kukan bakinciki a ranar. Bata ga me Innayo tayi da ya cancanci wannan wulakancin daga 'yar cikinta ba. Washegari ta rakata asibiti. Hawan jininta ne ya tashi tana daf da samun stroke idan bata huta ba. Sannan likita ya bada shawarar ta rage damuwa daga ranta. Da ta fadawa su Maimuna babu abin da suka iya zuwa dashi dubiya sai sannu da fatar baki. Innayo din ce ma ta ce ta basu kullin kayan da ta ajiye musu. Zara kuwa bata zama ana ta shirin biki da kawayenta 'yan karya. Da daddare ne ma da ta dawo daga rabon kati ta saka Innayo a gaba da kuka. "Wancan gadon na soro ne gadon da ki ka saya? Dangin Unais raina ni zasu yi. Kuma har yau ban ga kujerun ba. Idan auren ba zai yiwu ba kawai zan ce masa na fasa." Tana jin motsin Hasiya tayi shiru. Tunda Uwani ta dawo ta fadawa Alh. Rabi'u marin da tayi mata itama take shakkarta. Shi kuwa har uwar daka ya kirata ya zazzageta tunda Uwani ta bashi dubu shabiyar tayi mutumci a idonsa. Da maganganun Zara Innayo ta kwana a ranta. Gari na wayewa taje gidan A'i. Tangamemen gida ne na zamani. A wani karamin falo aka ajiyeta har A'in ta sakko bayan kusan minti arba'in. "Innayo kece a gidan namu? Nima ina son zuwa kawo gudunmawata ta bikin Zara." Juyawa tayi ta koma sama. Bata dade ba ta dawo da leda mai baka da yalo ta bata. Godiya tayi tun kafin ta bude sannan ta fadi abin da ya kawota. "Don Allah rance nake so A'i. Kujeru zan sayawa kanwar taki da sauran kayayyakin da basu samu ba." Kallon tausayi ta bita dashi kamar gaske "banda abinki Innayo kiyi mata komai daidai karfinki mana. Kodayake naji ance dan masu kudi ne. Zara da rawar kai maimakon ta kawo tsaranta shi ne ta dauko wanda yafi karfinta." Daurewa tayi bata ce komai ba tunda nema take. Wai A'i ce take yi mata haka? Lallai duniya baka shaidar da ko da naka ne bare na wani. Ta sami bashin tayi ta murna ta karba ta tafi gandun albasa inda kafintoci ke kware basirarsu. Ta sayi kujeru aka biyota dasu hae gida. Zara na gani ta tabe baki alamun basu yi mata ba. Innayo sai ta shige daki kawai ta fashe da kuka. "Allah kar kasa 'ya'yana su maye gurbin mahaifinsu wurin wulakantani. Idan nayi kuskuren tarbiyarsu Allah Ka shirya min su. Ya Allah na yafe musu. Da wanda suka yi da wanda zasu yi a gaba." (Haka rayuwa ta kan zo wa bayin Allah. Sai mu wahala akan wani abu da tunanin samun jindadi a tare dashi nan gaba. Idan lokacin girbar dadin ya zo lokuta da dama sai mutum ya kare da shan mamaki. Babu abin da Innayo bata yiwa 'ya'yanta ba na kyautatawa amma har yanzu bata ga wani abin buga kirji game da cigaban da ta jima tana yi musu fata. Duk da su din jininta ne to amma kar mu manta jinin Alh. Rabi'u ne. Basu tashi sun ga mahaifiyarsu tana da kima ba. Wannan zai iya rage mata daraja a idanunsu. A wahale suka ganta kuma dabi'ar dan Adam ce gudun wahala da talauci. Sai mai hankali, hangen nesa, tuna baya da tsoron Allah ne yake jajircewa wurin sakawa iyaye musamman uwa da alkhairi.) Anyi bikin Zara ba yadda take so ba amma dai ta bar gidan kamar yadda ta jima tana buri. Sai jifa jifa take zuwa gidan nasu saboda tana kunyar a ce Innayo mahaifiyarta ce. Ga talauci ga rashin wayewa. Mijinta ko a jikinsa. Bata nuna masa tana ganin girman mahaifiyarta ba shi ma bai ga dalilin girmamata ba. Abu na karshe da ya karasa kashewa Innayo jiki ta fitar da rai daga samun saukin rayuwa shi ne auren Hasiya. Wata uku bayan bikin Zara aka aiko musu da mummunan labari. A'i tayi hatsari ta rasu. Shi kuma babban danta da suke tare ya sami rauni a kansa. Wannan labari ya gigita Innayo ya kusa zarar da Laraba mahaifiyar A'in. An sha koke-koke an hakura. Ranar da aka yi sadakar uku Innayo ta sayar da filin da shi kadai ya rage mata kadara ta biya bashin da A'i take binta na kudin kujerun Zara. Mijinta Hon. Habu ya ce ya yafe, idan ma adadinsu ya shiga gadon 'ya'yansu zai biya a madadinta. Kafin ta isa gida Laraba har ta je ta ce ta bata kudin. Ba musu ta dauko ta bata. Kafin ayi bakwai ashe Alh. Rabi'u yana can yana kulle-kullen yadda zai cigaba da ci daga jikin Hon. Habu. "Ga kanwarta Hasiya ba sai ta maye gurbinta ba. 'Ya'yanka suna bukatar uwa da za ta kula dasu tsakani da Allah." Da mahaifiyarsa ya yi shawara ta ce ya amince. Dama ta kula a 'ya'yan Innayo din Hasiya ta fita daban. Basu san hawa ba basu san sauka ba sai sadaki aka miko musu ranar da A'i tayi arba'in. Da uwa da 'ya aka rasa mai rarrashin juna. Asabe ta dinga habaici da zage-zage wai wa ya san me suka kulla har haka ta faru? Sai da Allah Ya kawowa Ummakati miji mai rufin asiri bayan shekara guda sannan ta daina zaginsu. Hasiya ta tare da bakincikin auren dole da katse mata karatu. Mahaifiyarsu bata da mataimaki a gidan ga yawan rashin lafiya. Kaddara ta mayar da ita uwar 'ya'ya hudu da kananun shekaru. Bata taba zaton zama zai hadata inuwa guda da 'ya'yan da suka raina mahaifiyarta ba. Sai gashi Abbas, Ummi, Murja da 'yar karamarsu Hajara (Ayaah) sun koma karkashin iko da kulawarta. A wannan lokacin ne kuma Innayo ta tashi tsaye wurin son ganin ta kashe wannan aure. A idanunta Hasiya ta maye gurbinta ne tamkar tarihi yana neman maimaita kansa. Asabe kuma ta canja sheka daga yawon makota ta zamar da mijin Ummakati injin tatsa. Munzali ya kawo karfi ya yi kudi amma iyakarta dashi ta ce danta ne a baki ko ya bata idan ya yi niyya. *** 2018 A yayin da uwa ta haifi danta bata san gobensa ba ko anjima ba amma tana gina kyakkyawan buri aka rayuwarsa. Idan so samu ne ya fi kowa nutsuwa, kyaun hali, kudi da kyaun halitta. Ita dai ace nata ya yi zarra akan duk wani abu da zuciya take muradin samu. Burika ba kasafai suke cika ba. Da dadi ko ba dadi koda da nakudar haihuwa ce kadai dole a jinjinawa gudunmawar uwa akan danta. Tabbataccen abu ne cewa kaddara ita ce kashin bayan rayuwar kowanne dan Adam. Akwai mai dadi da mara dadi wanda sau tari tafiyar rayuwa daga ranar haihuwa ke kai mutum ga tasa. Waye yake tare da mutum a wadannan lokutan sama da UWA? Kokarinta wurin bada kyakkyawar tarbiya kadai ba shi zai kare mutum daga afkawa ga kaddarar cizon yatsa ba. Addu'a da taimakon Allah su ne jigo. Wata za ta kokarta amma akasin mafarkinta ne zai faru. Wata za ta shantake amma duk da haka kyakkyawan alkalami ya rinjayi mummuna akan zuri'arta. Wata tayi mai kyau taga mai kyau. Wata tayi mara kyau taga mara kyau. A karshe dai ba a canjawa tuwo suna. Mari uwa ce Innayo uwa ce Khadija uwa ce Asabe da Nasima ma dukkanninsu uwaye ne. Shekarar ta kama dubu biyu da sha takwas. An sha gwagwarmaya an yi fama. Iyaye, gari (society), abokai da ma ainihin halayyar da aka haifi mutum da ita sun kai manya da kananan taurarinmu ga matsI think you'd like this story: "UWA UWACE..." by BatulMamman17 on Wattpad https://my.w.tt/DwuHp8HW49 UWA UWACE...8 Batul Mamman💖 (Domin samun post da comment shiga wannan link din) https://chat.whatsapp.com/G5l0oQUZAFi37K0TXGggd5 {Kamar yadda na nemi uzurinku a baya sai kun dinga hakuri da rashin samun post a kai a kai. Zan cigaba da kokari da zarar na sami hali zan yi typing. Nagode da kulawar masu kira da masu text da dukkan masoya labaran Batul.} Thank you Maryam AD Baffa. You know why I know why They know why (A friend in need....) *** LAGOS 2018 Mukullai da cheque bibbiyu mutumin ya ajiye akan hadadden teburin gilas din dake gabansa yana kallonsu. Dukkaninsu kyawawa ne ga cikar halitta da kwarewa a gayu. Haduwarsu ta hudu kenan amma bai taba ganinsu da sutura daban daban ba. Hatta safa wannan iri daya suke sakawa. "Ga tukwicinku nan. Kun shigo da kafar dama domin na kwana biyu ban ji sun yabawa wani kamarku ba. Kudin kuma ku chanja wardrobe saboda akwai baki wata mai zuwa." Abbati da Munzali suka yi murmushi kowannensu ya dauki check da mukullin da yafi kusa dashi suka fita tare kamar 'yan biyu. Wandon jikinsu baki ne 3-quarter. Suka dora yellow din (hooded vest) riga mai karamin hannu hade da hula. Kafarsu bakaken original nike slippers ne irin na shakatawa. Agogo da askin kansu komai iri daya. Kyawawan matasa ne da suke ji da duk wani abu da cikakken matashi zai yi tinkaho dashi a wannan zamani. Abbati yana da shekara talatin da biyar yayin da Munzali yake da talatin da hudu. Suna zuwa farfajiyar gidan shakatawar suka ga an bude motocin da suka wuce a lullube lokacin shigarsu. Lexus ne RX 2015 biege iri daya guda biyu. Wani irin ihun murna suka saka tare da rungume juna suna tsalle. "Mutumin, yau akwai shagali fa" cewar Munzali yana yiwa Abbati kallon bani da na biyunka. "Ai dole. Ba don maganar nadin sarautar nan ba da munje Dubai." Abbati ya mayar masa yana kallon cheque din. Miliyan goma goma ne a jiki. "Kai dai kawai ka ce za ka je ganin uwargida Hanne." Wawan duka Abbati ya kai masa da muguwar harara. "Uwar Hanne zan gani ba Hanne ba." Munzali ya kwashe da dariyar jindadi. Baya hada kowa da Abbatinsa. Yana kuma kishinsa kamar yadda kowane masoyi ke kishin abin da yake so. Iya tsahon rayuwarsa wani mahaluki bai taba nuna masa soyayya kamar Abbati ba. Shi dai ya san cewa yana da uwa da uba. Suna raye har yau amma cikinsu babu wanda zai ce ya san shi sani na hakika. Haihuwarsa suka yi suka bar wa duniya tarbiyarsa. Yadda Abbati yake ga Munzali shi ma haka ya dauke shi. Bambancinsu bai wuce Baaba Mari da matsayinta bai tawaya a zuciyar danta ba. Munzali tamkar tsani yake ko kuma madogara a gareshi. A lokacin da iyaye suka watso shi hannun duniya babu wanda ya kama shi ya rungume sai Munzali. Shi ne gatansa wanda bai taba bari ya yi kewar iyayensa ba tunda suka hadu. Ya ciyar dashi kuma ya hana rayuwarsa tagayyara kamar ta sauran almajirai. Indai halacci yana sa dan Adam ya riki wani ya so shi kamar kansa to hakika bai ga ta inda Munzalinsa ya cancanci juya baya ba. Sau tari iyaye maza suna son kasancewa cikin rayuwar 'ya'yansu amma sai neman abincin da zasu ci ya dauke uba ya nesantasu dashi. Irin wannan uba za ka same shi mai yawan dokin lokutan zuwa gida domin ya saurari kuruciya, shirme da zallar soyayyarsu gareshi. Akwai kuma kishiyoyinsu irin su Alh. Rabi'u. Shi a gida daya suke kwana amma rabonsa da bada kudin sayawa dan cikinsa panadol ma ya manta. Bai san komai ba sai cikinsa da biyan bukatarsa. Idan aka sami uba irinsa ko wanda dole ta raba shi da gida da wahala ace uwa bata nan. Ita ke kokarin maye gurbin uban kuma ta taka tata rawar. Asabe bata cikin wannan sahun! Burinta daya ne. Me za ta samu a jikin 'ya'yan da tayi wata tara tana dakonsu a cikinta. Indai za ta ci ta koshi ta saka mai kyau to komai nafila ne. Munzali kamar sauran 'ya'yanmu yana bukatar kulawar majibintansa. Ayi tattalinsa a shagwaba shi. Ayi masa fada idan ya kuskure. A taka masa burki idan yana neman tsallake layin da dabi'ar dan Adam da addini suka shata masa. Bai sami wadannan ba sai a wurin Abbati. Tun kafin su gama gane rayuwa Abbati yake son sa da zuciya daya. Ba zai tuna lokaci na karshe da Asabe ta san bashi da lafiya ba musamman idan ciwonsa na namoniya ya tashi. Amma tun kafin ya daina kwana a gida Abbati ke jinyarsa. Wani lokaci da ya tashi sai da ya kwana biyu bata leka dakinsu ba inda yake kwana da kaninsa. A rana ta uku ne ma da lalitarta ta kone kurmus babu 'yan canji yaji muryarta tana yiwa Innayo bala'i. "An sako min da a gaba saboda hassada da bakinciki. 'Yar fitar nan da yake yana roro min abin arziki a wurin mutanensa kina neman saka masa hannu." Dariyar da Innayo tayi kafin ta bata amsa sai da ta bata haushi. "Asabe kenan. Yau kuma rigimar dani kike ji? Da nice ke gyale zan dauka na bazama nemansa ba zaman karyar son 'ya'ya amma ban san halin da suke ciki ba." Gyalen kuwa ta janyo akan kyauren dakinta tana mai cigaba da kumfar baka da borin kunya ta kare da cewa, "Dama fitar zanyi." Kugu ta kama tana karkada hannu daya kamar 'yan mata a wurin gaďa "Kuma ki gaggauta fadawa bokanki ya yi karya don bashi da rabo akan ahalina ehe." Har ta kusa rijiyar dake daf da kofar gidan taja tunga ta tsaya. Tuno wani abin karin haushin tayi ta kuwa kalli Innayo ta kwashe da dariya. "Su 'ya'yan so din wai uwar me suka tsinanawa wahalalliya? Ai in fada miki dadin haihuwa bai wuce ki haifa ki mora ba. Amma ka haifa kuma a more kuruciya da lafiyarka a gujeka wai....uhumm bari nayi gaba." Daskarewa Innayo tayi tana jiyo sautin Asabe tana rangada ahayye nanaye da salon wulakanci. Zafafan hawaye ta goge ta duka ta cigaba da tatar gero. "Wata rana zan huta. Balle ma indai sun huta basu yi irin rayuwata ba ni bani da sauran damuwa." Ta fadi da dan karfi tana baiwa kanta kwarin gwiwar cigaba da aikin gabanta. Munzali yana dakinsu ya gama jin zantukansu. Bai jidadin kalaman Asabe ga Innayo ba. A ransa yake jin inama ita ta haife shi. Ya tabbata da zai ga gata mara misaltuwa kamar su Hasiya. Sai da yaji tsakar gidan shiru ya lallaba ya fita. Murmushi ya karade ramammiyar fuskarsa ta kwana biyu da ya yi tozali da Abbati ya rakube a dakalin gidan. Shi ma yana ganinsa ya taso da saurinsa. "Ya jikin? Ga abinci na samo maka. Akwai sauran kudi in siyo maka lemon kwalba? Ko kunun zaki? Kafi son lamurje ko?" Dariya ce ta subucewa Munzali ganin Abbati duk ya rude. Kwana biyu da yake ciwon sai Asabe ta fita yake fitowa. A wurinsa yake wuni yana jinyarsa. Don kokari har kemis yaje ya siyo magungunan mura don a zatonsa mura ce da zazzabi ke damun Munzalin. Wannan kadan daga irin abubuwan da suka kara masa kaunar Abbati kenan. Kulawa yake so kuma babu ta inda Abbatin ya gaza nuna masa ita. Abbati has always been there. Babu mai yi masa fada ko gyara masa wani abu sai shi. Tasgaron da ya mamayi wannan kyakkyawar alaka ba komai bane illa alfashar luwadi. Saboda sakar masa ragamar rayuwar da iyayensa suka yi da kananun shekara daga Asabe har baban nasa babu wanda yake gani da mutumci har ya girma. Sai dai ya kawo kudi su karba babu bincike ko damuwa. Tunda ya ce kasuwanci yake magana ta kare. Yunwa, bala'i ce wadda mutum zai iya komai domin kawar da ita idan ba ya kai zuciya nesa ba. Munzali ne ya mikowa Abbati hannun taimako a lokacin da take neman kassara shi. Halinsa na tsoro da rashin son rigima sauran daliban suke dogara dashi suna cutar dashi. Shi ma Munzali da baya makarantar ya tsaya masa. Sai da ta kai hatta manyansu suna shakkar taba shi saboda fadan Munzali. Duk kulawa da soyayyar Mari gare shi bai hana shi jin zafin barinsa da suka yi zuwa bara ba ita da mahaifin shi. A lokacin da ta so ya zauna a gida bayan rasuwar Sani ya riga ya saba da abin da suke yi. Amma ba shi ne makasudin kin zamansa ba. Bai ga yadda zai iya rayuwa babu Munzali a cikinta ba. Shekaru suna gaba yana dan yin karatun addini sama-sama. Bai jima ba ya gane muni da girman abin da suke yi. Lokacin da ya kai shekara ashirin abin ya dame shi matuka. Shazali yana kaisu wurin manyan mutane ana amfani dasu a basu kudi sosai. Tuni Shazalin ya bar makarantar ya zama kawalin almajirai mai gidan kansa. Wannan sana'a tasu ta dami zuciyar Abbati. Ya yi nufin ya fadawa Munzali su daina su nemi sana'a ko ta wankin mota ce. Kullum abin yana ransa amma ya rasa yadda zai fito masa da maganar. Tsoronsa kada yaji haushi ya nemi rabuwa dashi. Wata rana yana zaune jiran isowar Munzali su je su sami Shazali tunani ya dame shi. Bai ji zuwan Munzalin ba sai da ya taba masa kafada. "Allah Yasa ban barka jira ba. Matar nan (Asabe) ce wai na ranta mata dubu biyu." "Ka bata ko?" Abbati ya tambaye shi yana tashi tsaye. "Kudin da muka samo a gidan nan ne fa na shekaranjiya ta gani ta saka min ido. Ni kuma na riga nayi amfani dasu." Idanu Abbati ya zaro. Dubu biyar biyar aka basu shi ko dari biyar bai cinye ba. Zai tambaye shi me ya yi da kudin ya miko masa leda. Atamfa ce guda daya da lesuka biyu. Kallon tuhuma Abbati ya yi masa "Na meye wannan?" "Kayan sallar da ka ce zaka sayawa Baaba dasu Atine (kannen Abbatin)" Zuciyarsa yaji tayi nauyi ya kasa magana. Abu daya ya sani. Munzali yana matukar kaunarsa. Ko kyamar almajirai bai taba yi masa ba. "Kai da ka ce baka da kudi duk ka kashe naka?" Murmushi Munzali ya yi. Shi ba maraya ba amma yana da wanda yafi uwa da uba a zuciyarsa saboda sakacinsu. "Ka fini bukata kai da zaka je gida gobe. Na hannunka sai kayi kudin mota da wanda zaka bawa Baaba ta rike. Kafin ka dawo kullum zan dinga fita in tara mana." Abbati yaje gida da tsaraba. Baaba Mari tana gidan kawunta a Maigatari. Ta kasa gaba ta kasa baya sai tunani. Duk sanda yazo hutu yaje ganinta sai ta tuna masa kada ya kusanci zina. Kar ya manta abin da ya faru shekarun baya. Idan 'yan matan sun zo su ma maganar kenan. A wahale suke rayuwa ana gasa su a gaban mahaifinsu. Da Abbati ya fara girma ne idan yazo ake daga musu kafa tunda da 'yan canjinsa a hannu. Ya je gaishe ta wannan karon ma ya bata kayan ta tsatstsare shi da ido. "Sana'ar me kake yi ne?" "Jiran shago nake hadawa da karatun" Ya amsa mata kai tsaye "Wannan ma ubangidana ne ya baki." Ya mayar da hannunsa da ya riko kudin da yake niyar bata ya dunkule. "A kula dai. Banda daukar kayan mutane. Banda ha'inci ko cuta." "To Baaba." Kwanansa biyar a garin ya koma Kirikasamma. Da isarsa gida da Gwaggonsu Deluwa ya fara cin karo a zaure. Guda ta saki tana ganinsa ta fara habaicin da ta saba wanda ya saka shi dakata karfi da yaji. "Ango manya, na Hanne ka sha kamhi. Da Malan har iya cewa a bika Maigatarin ai...hummm, su Mari idan aka ga d'a sai ayi bulunbukwi a manta da an tsani almajiranci. Ledar da ka tafi da ita can ka barota kenan?" Sauran surutan nata ba shigarsa suke ba. Kalmar 'na Hanne ka sha kamhi' ke kai wa da komowa a kwanyarsa. Me hakan yake nufi? Bai furta tambayar ba ya shige ciki da sauri. Kafin ya kai bangarensu tuni gudar Deluwa ta sanar da Mal. Sa'adu dawowarsa. Yana ajiye jaka dan aike na fada masa sakon kira. Gabansa ne ya fadi. Bai manta ba! Ta ina zai taba manta dalilin mutuwar auren Baaba Mari? "Wa ka fadawa za ka je Maigatari?" Cewar Mal. Sa'adu fuska a daure bayan Abbati ya amsa kiran nasa. A dakile ya bashi amsa da cewa "Babu kowa." A ganinsa baya neman izinin kowa musamman na wan mahaifinsa kafin yaje wurin mahaifiyarsa. "To ba zan dauki raini ba. Sai kazo ko kwana biyu baka iyawa a gidan ubanka amma ka iya tafiya dangin dangiro ka kai musu dan abin da ka tara. Ita kuma ko kunya babu ta karbe bayan ta gama aibatamu da karatun da aka tura ka." "Baaba ce Dangin dangiro din? Baaba Marin da ta haifeni?" Yadda ya fadi maganar da bacin rai muraran a idanunsa sai yasa Mal. Sa'adu yin lakwas. Tabarmar kunya ya nade da hauka ya sako bakunan kannensa cikin maganar yana cewa su taya shi gani Mari ta zugo danta ya raina shi. Da kyar aka bashi hakuri sai da Baba Inuwa ya zazzagi Abbati a gabansa. Baki Mal. Sa'adu ya turo gaba shi a dole ransa ya baci ya ce "sai ka shirya gobe ka je kaga amaryarka. Da baka dawo ba munje an daura aurenka da Hanne jiya. Ai baka manta alkawarin da muka yiwa shi uban nata ba hekarun baya." Dif Abbati yaji kamar an sara masa guduma a ka. Aure?! Shi kuwa me zai yi da mace yanzu? Macen ma wadda rabon da ya sanyata a ido tun tana shekara hudu. Tunaninsa ya tsaya a inda ya auno shekarunta na yanzu. Shadaya shi ne har an aurar da ita kamar zai gudu. Lokacin da mallam Saidu yace masa sai bayan shekara biyu zata tare bai damu ba. Sai kuma wani tunani ya darsu a zuciyarsa wanda yasa shi sakin guntun murmushi. Ko ba komai ya sami hanyar da zai fadawa Munzali aibun abin da suke aikatawa tunda dalilin bari ya samu. Abu ne da babu ko sabanin fahimtar malamai game da haramcinsa saboda haka bari ya zama wajibi. Washe gari suka shirya tare da dan Mal. Sa'adu don zuwa ganin Hanne. Haka ta fito tana ta sussune kai wai ita nan amarya a gaban angonta, bakin nan ya sha jan baki ga fuska da dige digen jagira. Yarinya karama amma wai ta san shi mijinta ne, abin ma dariya ya bashi. Bayan ya koma da yan kwanaki kadan ya shirya dawo Kano da farinciki zai ga Munzali dan yi masa fada da fatan kubutar dashi shi ma amma nan ya tarar da mummunan labari. An kama Munzali yana police station. Sanadin rufe shin ba komai bane kamar yadda ya ji daga bakin wani dan makarantarsu da ya san abotarsu illa sumamen 'yan kwaya da aka kawo unguwar. Hankalin Abbati in ya yi dubu ya tashi. Munzali ko taba baya sha. Shan kayan maye bai kasance cikin dabi'unsu ba. Jin kwanansa hudu a can ya daďa jefa shi cikin tararrabin halin da yake ciki yanzu. Bai yi kasa a gwiwa ba ya nufi gidansu. Ya dai san ba a maraba dashi domin Asabe ta gargade shi da rabar danta tunda ta gane almajiri ne. So yake yaje ya tabbatar ba a sake shi ba sai ya nemi station din da yake. Ya dade yana sallama kafin yaji wata murya ta amsa a fusace. Da azamarsa ya shiga soron gidan ya tsaya turus sakamakon maganganun dake tashi a tsakar gidan. Muryar da ta amsa sallamar shi ya gane ta Alh. Rabi'u ce saboda hango shi da yake yi a tsaye yana sababi. " Dan iskan yaro kai, ni zai zubarwa da mutunci a unguwar nan? Ashe wai a wani kango aka same shi da talatainin dare. Kuma jama'a sun yi ittifaki akan yawan ganinsa a wurin kamar kangon ubansa." 'Shazali yake jira' Abbati ya ce a zuci. Babu abin da ke kaisu kangon nan yanzu sai jiran zuwan Shazali ya kaisu wurin mutanensa. "To ni dai ka kawo kudin sai naje nayi belinsa" Asabe ta ce a sakalce. Ta riga ta gama bincike dakin Munzali tas babu kudi. Da ace ta samu dama rabonta za ta dauka sai ta fito dashi. Ta rasa uwar me yake boyo a dakin da ya kori kaninsa ma daga ciki. "Nawa ne kudin?" Cewar Alh. Rabi'u a fusace kamar an ce ya bada ransa. "Dubu ishirin da biyar ne. Ka bada ishirin sai na cike sauran." Sake bata rai ya yi cike da fushi sai kuma ya fashe da wata irin dariya. Kudi irin wannan indai ba kodarsa take so ya sayar ba a ina zai samu. "Kisan kai ya yi da zan biya talatin da biyar? To babu! Ya zauna su koya masa tarbiyar da ki ka kasa koya masa. Aikin banza. Baki da aiki sai yawon makota kina kwadayi. Ke dai kin shiga uku. Ko kishin yadda Innayo take tsaye kan nata 'ya'yan ba kya yi." Habawa! Ran Asabe ya fi nasa baci saboda hadata da Innayo da ya yi akan kudi. Hannuwa ta tafa ta rike kugu tana sauke nata ruwan bala'in. "Aikin 'bur in ji tusa. Kai dai anyi lusarin namiji. Ka haifi 'ya'yan ka bar mata da wahalar rayuwarsu. Kuma 'ya'yan Innayo din akwai wata ta dukan kirji a kai ne? Ba gara nawa ba akalla ko banza yana bani kudi." Kanta ya yi kamar zai kai mata duka "ni kike fadawa wannan maganar?" "An fada din lusari ko karya nayi?" "To Yasin ba zan bada ko kwabo ba." Hannu daya ta saka ta rufe bakinta tana masa ihu "Wohhhhh, anji kunya. Lusari. Dama me zaka iya fitarwa bayan kayi gadon bakin hali." Shi dai bai tanka ba tunda ya sabule ba zai bayar da kudin ba. Dakinsa ya shige ita kuma ta yi rantsuwar sai dai a barshi a kulle don bata da kadarar sayarwa akan dan da dama ba wani tausayinta yake ba. Mayafi ta dauko ta sanar da sauran yaranta wadanda a kunnuwansu aka gama bala'in zata je gidan Ummakati. A lokacin auren duka duka bai yi shekara ba. Hasiya ce ma take neman shekara ta biyu a nata gidan. Innayo kuwa tun safe da take ganin take taken rigimar kudin belin ta fita. Uwani da Zara ko ba a hada da sauran kannen A'i ba zasu iya hada kudin belin dan uwansu. To amma ta san fakewa zasu yi da rashin halin Asabe su ki taimakawa. Wannan kenan. Yau idanun Abbati sun gane masa abin da yasa Munzali baya kaunar iyayensa. Gabadaya son kai ya musu katutu babu mai cikakkiyar damuwa dashi. Kudin belin ne ma ya dame shi. Dubu ashirin da biyar da yawa. Bai je station din ba ya tafi gidan Shazali. Cikin sa'a ya same shi. Ko gaisawa basu yi ba ya ce, "Rance nake nema don Allah na dubu ashirin da biyar." Shazali ya kanne ido "babu sai dai akwai manya da suka shigo gari. Kayi sa a domin kuwa harda mataimakin wani gwamna cikinsu. Idan zaka iya aikin na tabbata nan da gobe ka tara dari ma ko sama da haka." Bashi da zabin da ya wuce karbar wannan tayin. Munzali ne fa. A wuni da daren ranar sai da ya ziyarci mutum biyar. Kudi kuwa don ma sun san ba wayayye bane amma duk da haka dubu dari biyar ya saka a gabansa yana kallo. Jikinsa har bari ya dinga yi saboda kudaden sun bashi tsoro. Haka ya hau titi zuciyarsa na fat-fat da fargaba. Gani yake kowa ya kalle shi zai gano adadin kudaden. Shazali ne ya fada masa wane station ne yaje da kudin belinsa a hannu. Sergent din da yake wurin ya fadawa sunan wanda yazo fitarwa. "Kawo dubu goma saboda da daddare aka gan shi. Da da rana ne sai mu karbi biyar." A haka shi Sergent din mugunta ya yi masa. Shi kuma muryar Asabe ce ta dawo masa. Kenan karya tayi da masifar da ta hau danta. Da gaske Munzali bashi da kowa sai shi. Wani irin tausayinsa ya sake mamayarsa. Kwalla ya dinga zubarwa da aka turo keyar Munzalin. Ya yi dukun dukun ga dingishi yana yi. "Dama na san zaka zo Abbati. Na san wallahi ba za ka barni a nan ba. Nagode..." Rungume shi Abbati ya yi suka fashe da kuka. Sergent ya tabe baki yana tunanin shakuwa ce ta 'yan uwa. Abbati~Munzali ya yi masa gata tun bai san me ake kira gatan ba. Ba zai taba iya barinsa ba bayan ya san shi kadai ne tsaye a rayuwarsa. Munzali~Abbati ne kadai ya taba bashi daraja ta dan Adam. Shi kadai yake kaunarsa da zuciya daya ba don wani abu ba. Iyayensa basu damu da kowa ba sai kansu. Fita suka yi Abbati ya tallafi nauyinsa. Asibiti suka fara zuwa ya biya kudin gado don ya ce a kwantar dashi ya huta. Wani karamin private ne da suka gani a hanya. A nan aka gyara targaden aka saka masa ruwa. Abinci mai rai da lafiya suka ci sannan bacci ya dauke Munzalin. Sai da safe Abbati ya nuna masa kudin da ya samo. "Me ya kamata muyi dasu?" Abbati ya tambayi Munzali. Munzali ba amsa. Bakincikin iyayensa ke damunsa. A gefe guda yana taya amininsa farincikin samun abin da zai iya raba shi da talauci. Ya jima yana tunani sai jin muryar Abbati ya yi. "To ga naka nan. Kowa ya dauki dari biyu. Wannan kuma.." ya nuna chanjin darin da ya taba yana musu hidima ciki "sai mu dinga cin abinci da sauran bukatu." "Kudinka ne Abbati. Ka dai bani na abincin ka san cikina babu juriya" ya kare da dariya. Sun yi ta kai ruwa rana akan Munzali da yaki daukar kudin. Shi yana ganin Abbati ya fishi bukata tunda yana da iyaye a kauye. Da dai ya tabbatar Munzali bazai dauki kudin ba duk abun da ya ce, kawai sai ya dauki jakar ya fice. Kai tsaye gidan Shazali ya nufa, ya ci sa a kuwa ya same shi. Nan ya shaida masa yazo neman alfarma gunsa dan Allah ya sama masa gidan haya wadda yake mara tsada sosai. Daki biyu da bandaki ko da daya ne. Shi bai ma yi tunanin kitchen ba ko wani yadda za a ci abinci shi dai gidan yake so a sama musu ko da ma daki daya ne kuma yana so ya zama nea da gidan unguwar da aka sansu. Wani murmushin gefen baki Shazali ya saki " dan gari, ashe ka gane abun da nake ta so ku fahimta tuntuni" nan ya amshe kudin ya kuma shaida masa in Allah ya yarda nan da sati daya gida ya samu. Bai ma yi tunanin zai cutar shi ba ko raba daya biyu haka ya dunkule duka kudin Naira dubu dari hudu cus ya mika masa yayi gaba bayan yayi masa godia sosai. Da ya koma asibiti Munzali yayi ta tambayarsa ina kudin, me yayi dasu? Ya ce masa ba komai. Fita ya yi ya koma wurin likitan ya nemi alfarmar lallai a bar Munzali ya kara ko sati daya ne a asibitin dan yana so ya samu hutu sosai. Shima likita dai yaga kudi, abinka da private hospital iya kudinka iya shagalinka. Muddin zasu biya to fa shi babu damuwa. Qka bar Munzali ana ta sa mishi ruwa lokaci zuwa lokaci, yana samun kulawa mai kyau jikin sa yana kara kwari. Bayan sati daya kuwa ya koma gidan Shazali, da kansa ya dauke shi a babur dinsa ya kai shi rijiyar zaki wurin gidan da ya sama musu din dan ya gani, a lokacin babu gidaje sosai a wurin. Gida ne ba laifi dan har da dan gate dinsa. Gidan dubu dari aka kama haya, ya biya dillalai da sauransu de komai ya kama dubu dari dari da arbain sai canjin sa dubu dari biyu da sittin ya mika masa duka. Ya ce "ga canjin ka ni bazan dauki komai a ciki ba. Ku rike wataran zai muku amfani. Aiki kuma duk randa kuke son ku cigaba da samun kudi to kun san inda zaku sameni." Ya damka masa mukulli da takardun da akayi cike cike (tenancy agreement) yace gobe kazo ka sameni zamuje kaima ka sa hannu a gaban maigidan a karkare komai da komai. Farinciki a gurin Abbati a wannan lokacin ma bazai misaltu ba. Ya koma asibitin, ya sanar da Munzali halin da aka ciki. Shi kanshi mamaki ya ishe shi. Yanzu gida ma Abbati ya kama musu kawai don saboda yana jiye masa komawa gaban iyayen shi tunda da idon sa ya gani cewa ba kaunarsa sukeyi ba. A cikin sati guda suka tarkata suka koma can. Shi dai Munzali ya koma gida Asabe, har ta fara murna tana fadin ashe har an fito da kai, tana neman ta fara mai zancen ko za a samu kudi a wurinsa ko wani abu, yace mata ya samu aiki ne, an basu gida a Rijiyar Zaki da shi da abokin aikin sa, kasuwanci sukeyi zasu dinga tafiya Abuja da Lagos. Farinciki ya isheta tana ta murna hadi da yadawa Innayo habaici ita uwar mai shi. Danta ya samu aiki zai dinga shiga cikin manyan mutane. Munzali bai wani jima ba ya tattara yan komatsan sa ya fice ko tunanin ta tasa kaninsa ya bi ya gano inda ya koma bata yi ba. Sannan bata damu da mahaifinsa ya san halin da ake ciki ba. Shi ko Abbati daman ba abin da ya cewa Malamin makarantar su, kawai shafawa akayi aka neme shi aka rasa. Ya san yanda zaiyi da iyayensa duk ranar da ya koma gida. A kwana a tashi ba wuya a wajen Allah. Shekaru hudu da soma rayuwarsu su kadai haramtaccen arzikinsu ya bunkasa. Da fari Abbati ya so su bar mu'amala da Shazali amma abu yaci tura. Sun riga sun saba da wannan masifa sannan rashin kudi a hannunsu ba abu bane da zasu jure. Musamman ma shi Abbati da su Mal Sa'adu suka taso a gaba da bani-bani. Lokacin Inna Mairo ta rasu. Deluwa ta zige Jummai mahaifiyar Hanne cewa kudi ne dashi amma Mari kadai yake bawa. Jummai da kullum abin da ya yiwa 'yarta a shekarun baya yake dasa mata jin haushinsa sai ta hau dokin shaidan. Ba dama yaje ganin gida sai sun tatike shi. Bayan Hanne ta tare ya fahimci ashe kukan dadi yake da farko. Da yake a cikin gidansu aka basu daki Deluwa ce ta zama uwardakinta. Hanne har laluben aljihu tana yi masa. Sannan basu da sirri komai sai ta fada mata. Saboda haka duk abin da yazo dashi gidan kowa sai ya sani. Bai isa kuma ya ce babu ba sai zagi ya koma kan mahaifiyarsa. Ita ake dorawa laifin hana shi yi musu alkhairi da karbe komai nasa. Wannan abu yana ci masa tuwo a kwarya. Dalilinsa kenan na cigaba da wannan mummunar alfasha. A ganinsa da kudin da suke mutuntawa zai samawa Baaba Mari lafiya daga sharrinsu. Yau da wata sana'ar ya koya a wurin Munzali sabanin wannan da kila wani karatun za a biya ba wannan ba. A bangaren Baaba Mari kuwa da ta fuskanci irin kudaden da Abbati yake facaka dasu musamman lokacin auren kannensa sai da tsoro ya darsu a zuciyarta. Rufo kai tayi bayan an gama bikin tazo har gidan neman Baba Inuwa. Ranar ta sha habaici a wurinsu musamman matarsa da suka dan yi zaman kishi. Toshe kunnuwa tayi a gidan wata makociyarsu da tayi masauki ta jira ya dawo. "Ni kuwa Malam ka taba zuwa ganin ubangidan yaron nan a Kano? Wace irin riba suke samu har yake iya daukar nauyin abubuwan da suka fi karfinsa?" Ta furta cikin girmama lamarin. Jinjina kai ya yi yana tunani, lokaci guda shi ma yaji zuciyarsa ta dora masa alhakin rashin binciken dan nasa. Bai kai ga bata amsa ba suka ga Mal. Sa'adu ya nufosu a kofar gidan fakam-fakam yana baza babbar riga. "Salamma alekun. Kai Inuwa tashi ka wuce gida." Ya ce fuska a murtuke sannan ya kalli Baaba Mari "kin dai ji kunya. Ni tunda nake ban taba ganin rashin kunya irin wannan ba. Ki taso kafa da kafa tun daga Maigatari ki biyo bazawari. Don kin haifa masa yara shi kenan kuma bashi da sauran rayuwa?" Baba Inuwa har yanzu shi da 'yan uwansa basu da katabus sai abin da yayansu ya ce ya tashi da sauri. "Ba abin da ka ke zato bane. Magana tazo akan irin kudaden da Abbati yake juyawa da bamu san... " Hannu ya daga kamar yana magana da dan karamin yaro "kai arrr. Kinibibin matan ne ban sani ba ko me? Ta taho dai bikonka tana so ayi kome tunda ta rasa manemi shi ne za ta fake da sakawa yaro ido." Ido cikin ido ya kalli Baaba Mari tayi saurin dukar da kai "ko kin ki ko kin so Abbati jininmu ne kuma mun fiki iko dashi. Dan abin da yake kashe mana ki ke bakinciki shi ne zaki soma tada zaune tsaye da tsugudidinku na mata. To ahir dinki. Idan baki da kalamin san barka a gare shi ki kama bakinki akan aibata shi." Ranta in ya yi dubu ya baci. Ta gaji da wannan fin karfi mara fasali akan 'ya'yanta. Auren ma da akayi duka matan a nan cikin gidan ake rabawa'ya'yan 'yan uwa. "Allah Ya san zuciyata. Yaran nan amana ce Ta bamu nake kokarin saukewa kun hana. Idan har Abbati yana mugun abu ina masa fatan shiriya. Ina addu'a Allah Ya bude idanunku ku gane gaskiya komai tsawaitar lokaci." "Rashin kunya za ki min?" Cewar Mal Sa'adu cike da mamakinta. Baba Inuwa don kada ya bata mishi rai shi ma ya hauta da fada "rashin kunya za ki yi masa Mari?" Bata ce komai ba ta koma cikin gidan da ta fito. Su Baba Inuwa ma suka koma nasu gidan yana jin yayansa yana mayar da zance akanta. Karya da gaskiya haka ya hada ya kara mata bakin jini. Daga ranar Abbati ya ci alwashin yin kudi sosai domin ya saya mata mutumci a idon duniya. Ya kuma yi sa a. Tunda ragamar gidan ta dawo wuyansa ya koma mai sawa da hanawa. Hatta Mal Sa'adu komai sai ya ce a jira Abbati ya zo. Da karfin ikonsa yasa aka mayar da auren Baaba Mari da Baba Inuwa. Ita dai bata so ba amma ta dawo ne saboda saka ido akansa. Zancen da ake yanzu nadin sarautar Sarkin Samari za ayi masa a garin Kirikasamma. Haihuwar Hanne uku duka yaran kafin suna suke komawa. Duk da baya sonta yana son haihuwa. Kudi ne sun tara sun tada kai. An kai iyaye Hajji an rushe gida an sabunta shi. Karafaren gida mai bangare biyu suka saya a Sharada cikin Kano suka tayar da ginin zamani guda biyu iri daya sak. Kamar Abbati shi ma Munzali da kudi ya sayawa kansa soyayyar iyayensa. Asabe jiki kullum yana rawa akan bukatunsa. Shekara biyar baya ya auri 'yar kanwarta mai suna Zakiyya. Dangi duk sun dawo jikinsa sai yadda ya ce. Daga haihuwar farko suka rabu saboda tana da wayo. Ta matsu kwarai ta gano ainihin sana'arsa. Ganin ta fara zarginsa ya saketa daga zuwa gida wanka. Yarinyar kuwa ya saka mata Mariya saboda soyayyarsa ga Abbati. Komai na sunanta Abbati ne ya yi. Ya bata yarinyar da shagwaba da gata. Qibdiyya suke kiranta. Bata rasa komai ba. Idan suka yi tafiya har gasar yi mata siyayya suke yi. Duk wanda tafi son kayansa ya dinga tsokanar dayan kenan. Tuni suka daina neman juna. Sun mayar da alfashar sana'arsu kadai suna cewq kawunansu idan sun tara da yawa zasu tuba. Qibdiyya ce farincikin Munzali da Abbati. Qibdiyya sanyin zuciya da idanuwansu. Qibdiyya ta kara kusancinsu. Qibdiyya ce JARABAWARSU! *** A cikin kunnuwan Innayo aka yi kiran sallar asuba na farko da na biyu amma har aka idar bata iya mikewa daga gado ba. Ilahirin jikinta ke ciwo kamar ana soka mata allurai. Wannan yana da nasaba da ciwon hakorin da take fama dashi tun shekaranjiya. Mukamukinta na dama, bangaren hakorin mai ciwo ya kumbura suntum. Uwa uba kwanakin nan saboda zafin da ake fama dashi kusan kullum da ciwon kai take kwana ta wuni. Taje asibitin sha-ka-tafi na unguwar satin da ya wuce an ce jininta ya kuma hawa. Ba dole ya hau ba?! Ita kadai take kwana ta wuni kamar mayya. Rayuwarta a matsayin matar aure suna kawai ta amsa amma babu alamunta idan ka cire rabon 'ya'ya. Asaben ma bata gaban Alh. Rabi'u. Shi dai ya ci banza da hofi a titi ya zauna gulma a majalisa. Idan ya dawo maigirki ta mika masa abinci idan ya ga dama ya tsakura. Dan na cefanen ma ya daina basu, a cewarsa 'ya'yansu sun kawo karfi. Lamarin Uwani har yanzu da take matsayin Metiron (matron) a asibitin Nasarawa bai chanja zani ba. Sai an kai ruwa rana ihsani ke giftawa tsakaninta da Innayo. 'Ya'yanta kuwa basu saba da kakarsu ba. Da wahala ta saka su a ido. Idan ta leka gidan saboda dadewar da Uwanin take bata zo ba sai ace suna makaranta. Maimuna da Salima ba cas ba as! Saboda tabarbarewar rayuwarsu da ta 'ya'yansu Innayo ta kasa daina sana'a. Ranakun da jikinta ya motsa ne kadai bata 'yar tsala. Cinikin a jikinsu yake karewa. Nasu 'ya'yan suna yawan zuwa domin a wurinta sun fi samun abin ci. Idan sun zo ba komai take karuwa dashi ba sai dadin wahala. Amma haka take jurewa da wasa da dariya su tayata aikin abincin ta basu su ci su kaiwa uwayensu. Zara? Hmmm, babu abin da ya canja a tattare da ita sai kudi da mijinta ya sake yi. A yanzu haka har gidan mai gareshi. Ga shaguna da motocin haya. Yana sakar mata sosai amma kunyar a dinga rabata da Innayo yasa sai ta dade bata waiwayeta ba. Ya kara aure kuma matar 'yar masu kumbar susa ce. Idan ana taro 'yan uwan surukan gidan suyi ta shiga da fita cikin kayan alfarma ana kece raini. Ita da bata da na nunawa sai ta zabi kawai ta rayu babu su da dai su matso jikinta taji kunya. Su duka hudun nan Innayo tana zubar da hawaye akan rayuwarsu ta yanzu sabanin mafarkinta. Sai dai duk kukanta a kansu bai kai wanda take yiwa Hasiya ba. Tarihin da take gudu ne yake maimaita kansa akan 'yarta mai jin kanta. Hon. Habu ya shiga gagarin 'yan siyasar da aka daina damawa dasu kafin shekara da aurensa da Hasiya. Kan kace kwabo ya sayar da duk wata kadararsa sun dawo rungumar hannu. Ga Abbas a kwance har yau jiki yaki lafiya. Hasiya sai ta koyi kunshi take yi a unguwa. Sannu a hankali tayi suna mutane suke zuwa sosai. A rana sai ta sami dubu biyu ko uku. Idan satin biki ne kuwa har takwas tana hadawa. Lallen nata dari biyu dari uku take karba. Da wannan kudin suke cin abinci har ta bawa Honorable na sokewa a aljihu. A nasa bangaren shi ma yana fafutuka sai dai babu canji. 'Ya'yansa sun dauki Hasiya uwa banda Ayaah. Ita ce karama amma tafi kowa daukar zugar kakarsu Laraba da sauran kannen mahaifiyarta. An nuna mata Hasiya bata kaunarsu da zuciya daya, nema take ta rabasu da mahaifinsu. Wannan bauta da Hasiya take yi a ganin Innayo babu abin da zai biyo bayanta sai kwatankwacin wanda ya sameta. Yau an wayi gari wadanda ta karar da karfinta akansu duka sun gujeta. Shi yass ta ari halin da ba nata ba tana kuntatawa Honorable da 'ya'yansa kawai don ya gaji ya sako mata 'yarta. Gwiwoyinta sun dade da sarewa akan ganin hasken rayuwa. Ta jima da karbar kaddararta amma bata yarda Hasiyanta ta zama Innayo ta biyu ba. Za ta yi iya yinta taga wannan aure mai tsahon rai ya turgude kowa ya huta. ('Yar uwa ko kin san cewa yanayin gidan miji yana taimakawa wurin shaping din wace irin uwa mace za ta zama? Mata da yawa na aure da kyakkyawar zuciya amma abin da suke tararwa a gidan aure sai ya sauya musu zukata. Kuna tunanin da Alh. Rabi'u ya cika namiji Asabe ta isa ta zama ballagar uwa? Ba don bakin halinsa ba me zai sa Innayo mai kyakkyawar zuciya ta dage zai auren Hasiya ya mutu duk da su Ayaah 'ya'yanta ne?) Ummi da Murja sun gama sakandire da gumin Anti Hasiya. Magungunan Abbas ita take saya. Kudin makarantar Ayaah yana wuyanta har yanzu. Honorable yana bakin kokarinsa amma samunta a kunshin nan yafi nasa nesa ba kusa ba. Jarabawa ta Allah dai har yanzu ita ko batan wata bata yi ba. Jarabawar Innayo da Anti Hasiya ta shallake dukkan danginsu ta fada akan Hajaratu Ayar Allah. **** Sautin muryar shugaban tsangayar kimiya da fasaha a jami'ar Ahmadu Bello Zaria (ABU) ce ta karade dakin taron inda yake cewa "And lastly, the award for best research goes to none other than the reknowned Pharmacologist in person of Dr. Khadija Khalid." Yana dariya ya kara da cewa "Please keep clapping until she comes to the stage." Zuciyarta sai da ta doka dan tsallen murna gami da faduwar gaban dake tattare da sanin cewa yanzu idanu zasu yi mata caa. Cike da farincikin ganin wannan rana da ta kammala PhD dinta har gashi ana yi musu convocation ta mike tsaye. Mazaunin maigidanta Alh.Tahir a teburin manyan baki ta kalla da tunanin ganin zai dan karfafa mata gwiwa koda da gyada kai ne kafin ta hau. Bata yi mamakin ganin ba ita yake kallo ba. Za ta iya rantsewa ma bai ji lokacin da aka kira sunanta ba. Cikin dandazon mutanen da suka zo domin iyalansu ta nemo babban danta da ido. Dan halak din ita yake kallo yana dago mata hannuwansa bibbiyu fuskarsa dauke da madaukakin murmushi. Wannan kadai ya isheta. Ta tashi cikin takun girma ta hau stage din. Sanye take da doguwar riga da zani na swiss voile navy blue mai adon yellow din fulawa. Ta daura dankwali irin na Maryam Babangida sannan ta yane kanta mayafin kashka mai kauri yellow. Komai na jikinta ido zai nuna maka na kudi ne. Fuskarta babu kwalliya mai hayaniya. Sauda autarta taso fente mata fuska taki yarda. Suna waje saboda mutum biyu aka yarda a shiga dasu dakin karbar takardar shaidar gama karatun. Suhaib na ganin ta hau ya mayar da idanunsa ga mahaifinsa. A take duk wata fara'arsa ta dauke. Alh. Tahir ne yake yiwa wata inyamura dake zaune a bangaren ragowar baki magana. Kujerar da yake a teburin manyan baki tayi kusa da bangaren inda su Suhaib din suke kuma ita ma yarinyar nan take. Kayan jikinta sun dameta ga uban attachment a ka. Vice Chancellor (VC) din University of Nigeria (Nsukka) ne zai bata award din. Sai da ya gama kwarzanta kwazonta sannan ya damka mata. Ta karba da murmushi ta juya koda wasa bata yi gangancin sake kai idanunta inda Alh. Tahir yake ba. Yau ranar farinciki ce wadda ta kara kusanta ta da cikar burinta. Bayan an gama kowa ya watse ita kadai ta fita daga hall din. Ta zata Suhaib na bayanta sai da tayi masa magana taji bai amsa ba. A ciki Alh. Tahir bai san Suhaib din na kusa dashi ba. Complimentary card dinsa ya mikawa inyamurar bayan ya rubuta nambar da tabbas za ta same shi idan ta kira. "Kar ki manta ki kirani." Ya kanne mata ido "sai kin fini farincikin amsa wannan gayyata." "My Alaji..dole zan kira" ta ce da gurguwar hausarta tana mika hannu. Basu ankara ba daga ita har Alh. Tahir din sai ganin hannu suka yi a tsakiyarsu. Ya warce katin ya dukunkune shi a hannunsa sannan ya sakarwa yarinyar murmushi. "Kin fadi jarabawar da Babana ya yi miki. Da baki karba ba kyautar kudi zai yi baki." Yarinya ta zaro idanu waje na rashin fahimta. Alh. Tahir kuwa sai uban murmushin dole yake kamar sauna yaga wawan zama. Da turanci yadda za ta fahimta da kyau Suhaib ya ce "Abba ya ce 'yan matan yanzu duk basu da tarbiyya indai sun ga kudi basa jin komai wurin bin dattijai marasa tsoron Allah." Hankali a tashe jin ta kusa yiwa kanta sawarwara ta shiga jijjiga kai "nooo, ahhh. Abeg na the name I wan see. Alaji shebi I say I no go follow you." Suhaib ya kalleta ya kalli mahaifinsa ya yi gajeren tsaki ya sa kai ya fita. Duk tsiya da jaraba dai ya tabbata dole Abban nasu ya hakura da ita. A waje kuwa zuciya cike da farinciki Mami Khadija ta fito daga hall din, tana ta waige waigen neman 'ya'yanta cikin daruruwan jama'ar da suka cika harabar wurin, kowa yazo convocation din 'yan uwan sa. Tana tsaye tana kallon su dai dai ta ji an taba kafadarta. Ta waiga nan ta ga Suhaib tsaye yana sakar mata murmushin nan da ya saba yi mata mai cike da tausayin ta hadi da nuna sanin halin da take ciki. Har kullum Suhaib ya kasance mai shiga damuwa akan yanayin da ta tsinci kanta a hannun maihaifinsu. Murmushi ta maida masa tana kara jin tausayin dan ta a cikin zuciyarta. Iya tsahon rayuwarsa tana ganin bai taba damuwa da wani abu ba sama da ita da kuma halin da take ciki, komai nasa ita ce. Bangaren mu'amalarsa da mahaifinsa kuwa, a lokuta da dama tana ganin kamar laifinta ne da ya raina shi. Sai dai kuma babu yadda zatayi, duk iya kokarinta na ganin ta dauke damuwa daga fuskarta yayinda take tare da Suhaib, tabbas sai ya gane halin da take ciki. Wannan yasa ya raina Mahaifinsa fiye da tsammani baya ganin girman sa ko na miskala zarratin, tayi fadan, tayi nasihar, ta ja shi a jiki duk dan taga ya aje wannan matsalar ta Tahir a gefe yayi masa kallon uba dan ta san sharrin da ke tattare da kin yin biyayya da kyautatawa ga mahaifa amma abu ya ci tura. Addu'a kawai take yawaita yi masa. Babban kalubalenta a kan rayuwarsa bai wuce shaye shayen da ya sa a gaba ba domin neman saukin bacin rai. Gashi har yanzu babu alamun dainawa a tare dashi. Sa'arsu daya Ya gama makaranta har yayi bautar kasa. A lokacin Alh. Tahir yaso kwarai ya tura shi yaje yayi Masters a kasar waje amma fir taki yadda saboda ta san cewa a kan idon ta ma ya aka kare da shaye shayen balle idan yayi nesa da ita. Shima kansa baya son tafiyar, saboda gani yake babu wanda ya damu da yanayin mahaifiyar tasu sama dashi. Wannan ita ce rayuwarta da Suhaib. Tana matukar son shi, kusan ma duk cikin 'yayanta tafi nuna masa so da kulawa, saboda yadda tasan yana sadaukar da duk wani abu na rayuwarsa dan ganin murmushi shimfide akan fuskarta. Bayan ta gama kallonsa tana wannan tunanin, ta maida dubanta ga Farha dake tahowa gare ta. 'Allah sarki Farha', ta ce a cikin zuciyarta. Yarinya kyakkyawa ga kyawun sura. Duk wani cikar zati na 'ya mace da za ayi sha'awa ace ana so kama daga kyan hali, dabi'a, yawan fara'a, ladabi da biyayya, iya girki babu ta inda Farha ta gaza. Amma har yanzu ko da wasa babu wanda ya taba sallama kofar gidan su da sunan manemin aure. Wannan abu yana matukar damunta yana ci mata tuwo a kwarya. Ita ma Farhan yanzu take bautar kasa amma babu mashinshini kwata kwata a rayuwar ta. A duk sanda ta dubeta tana jin wani irin kunci da bacin rai a zuciyarta. Mai yiyuwa ma abin da mahaifinsu yake wa 'yayan mutane ne yake dawowa kan yaranta. Haka take yawan ayyanawa a cikin zuciyarta. A bangaren Farha abin itama yana damunta fiye da yadda za'ayi tunani. Sai dai kuma tana nata kokarin ganin cewa iyayenta basu rage ta da komai ba ta dinga nuna hakan bai dame ta ba. Lokuta da dama takan tsinci kanta cikin kuncin rai har takai ga kwana tana kuka da tunane tunane kala kala. Son auren bai dameta ba kamar yawan tunanin ta ina ta gaza, mene bata dashi da ya janyo mata bakin jini. Ko irin saurayi yazo taji bata so ta kora ma babu. Irin samarin unguwa ma haka ko yan class daya da zasu nuna suna sonka ko da ba da aure ba irin dai school soyayyar nan duk babu. Kawayenta su zauna ana ta hirar saurayi, haka za tayi zugum tana jinsu ba za ta iya cewa uffan ba akai. Daga karshe ma har gani suke ko ta sawa kanta boko ne ganin mahaifiyarta lecturer ce ko itama bokon ta sa a gaba. Zolayarta suka koma yi ana kiranta Farha Boko addini. Sai ta biye musu kawai aka tafi a hakan, kamar da gaske abin bai dameta bane ba ko baya gabanta. Nan kuwa tafi kowa son taji wani ya zo da kokon barar neman soyayyarta. Itama ace yau dai ta taba yin saurayi. Bayan ita, sai da Mami tayi dogon juyi tukunna da idanuwanta sannan ta hango Lilu can tsaye da abokai. Wani murmushin takaici ta yi a ranta, wato abun da ta kwana tana yi masa fada akai har suka kwanta bacci ta bayan kunnuwansa ya wuce. Ta rasa gane irin kin ji da masifar kiriniya irinta Lilu. Kunnuwansa kamar an cusa masa duwatsu an toshesu, baya ji kwata kwata. Fitinanne ne na bugawa a jarida. Shima duk sanda ya yi abubuwansa, Tahir take hangowa, takan ga karshen ta abubuwan da yayi ne Allah ya jarabce shi da 'ya'ya haka. Khalil bashi da tsawo, har takanyi mamakin yanayinsa jikinsa kamar mutumin ruga. Karamin jiki gareshi babu kiba sai fadin rai da jin shi ma ya isa. Ya fi sauran 'yan uwansa kyau har mutane kan ce masa mai baby face. Da wannan fuskar kamar ta salihan bayi yake yaudarar mutane, idan yayi abu mutane kanyi mamaki har suga kamar ma karya ne ace wai shi ya aikata hakan. Iya saninta game da halayyarsa ta san baya shaye shaye. Amma akwai hulda da abokan banza, har club yana zuwa. Ga kuma azabar son mata har mamakin sa ma ta ke, shekaru ba wani abun azo a gani ba amma idonsa idon mace sai yayi yadda yayi ya tsarata. Ko da bai fara aikata me gabadayan ba to fa ya dau hanya gadan gadan wurin gadon halin ubansa. A gida ma duk wani abu na fitina, ko abun da za ace bari ko wani abu mara dadi a to sunan sa ake ambata. Yanzu haka da take hangoshi tsaye yake tare da wasu abokansa yana ta zuba zance daga inda take tana iya jiyo muryarsa ana shewa ana dariya. Ga gashin kan san nan yayi wani irin askin gefe da gefe anyi lowcut, tsakiya ya tara gashi kamar kan zakara. Ita dai ta san ba buzu ta haifa ba amma idan ka ganshi banbace shi da buzu tabbas zai baka wahala. Gashin gaban ne ya wani nannade ya kwanta luf luf yana sheki. Wannan ne dalilin fadan su a daren jiya. Tayi tayi ya fadacmata me yake shafawa haka, har tana ce masa idan ma relaxer ya fara sawa to Allah ya tsinewa mai kamanceceniya da mata. Sannan ta ce idan zai zo taron convocation din to ya tabbatar ya aske kansa askin mutunci. To gashi dai yazo babu askin da alama kuwa har ya fita nuna farinciki ma yadda yake ta shewa da abokai. Bayan shi kuma sai autar ta Sauda. Ita yanzu suke shirin gama secondary tare da Mardiyan Nasima, don tare aka saka su makaranta. Sanda aka saka Sauda, duk da Mardiya bata kai shekarun shiga ba haka Nasima ta nace sai an sakata tsabar masifar kishi dake azalzalarta. Matsalar Sauda shi ne raina duka matan Abbansu. Bata ragawa kowa indai zai shiga gonar Maminta. Amma Allah Ya hada jininta da Mardiya. Nasima tayi kokarin ranasu har ta gaji. Sannan sabanin yayarta Farha da ta rasa manema, ita kuma har sun mata yawa. Shi yasa Allah Allah take ma ta gama makaranta ayi mata aure kafin masifar Tahir ya rabe ta. Tunda manema ne da ita ta ko ina babu babba babu yaro kowa Sauda. Ita da ta haifo su ma bata ga da me saudat din ta dara Yar uwarta ba to amma abu na ubangiji baka da ta cewa se Hamdala. A gefensu kuwa Mardiya ce a tsaye tana murmushin yake. So take ta karaso wurin Mami amma tana jin nauyi. Sauda ta figo hannun kanwarta suka taho tare ta rungume su daya bayan daya. Mardiya ita ce babban misali na rayayye ya fita a cikin matacce. Iyayenta basu da halin yabo ko daya amma ita dabi'unta ababen burgewa ne. Tana son 'yan uwanta da mahaifi sannan a gefe tana yakin boye mummunan halin mamanta Nasima. Su biyar Abba Tahir ya mallaka. Ya dauki son duniya ya dorawa 'ya'yansa. Hatta Suhaib da shi kadai ya san boyayyen halinsa yana son abin sa. Duk wani so da gata da barin kudi ba ta inda ya ragesu. Tunda ya yi kudi arziki ya habbaka. Bayan gama daukar hotuna iyalin suka hadu a motoci biyu. Ta Alh. Tahir ce ta fara fita saboda takura da ya yi da kallon da Suhaib yake watsa masa. Dayar kuwa Lilu ne ya ja su zuwa gida... Kaddarar shekarun da Alh. Tahir ya diba yana tafka ashararancinsa da 'ya'yan mutane a yau ne za ta rabi dukkan 'ya'yansa. Domin a wannan rana ne Munzali da Abbati suka shigo garin Kaduna akan hanyaWattpad https://my.w.tt/mod4Kht3cab UWA UWACE...9 Batul Mamman💖 *** Tun kafin ta iso bangaren da 'yan kunshin suke zama wanda yake hanyar kofar fita Anti Hasiya ta san takun waye. Sautin kwas-kwas da takalminta mai mugun tsini yake yi har tsakar kan mutane ake ji. Dunduniyar duka takalman ta cire wurin tsinin sai qusa ke kartar fasassun tiles din da aka saka a wurin . Budurwa ce da take cikin ganiyar shekarun 'yan matancinta. Tana da kyaun kirar jiki da na fuska. Kayan jikinta sun matseta don siket din sai da ta dinga tsalle tana jan shi sama kafin ya shiga. Rigarta kuwa ko anyi rantsuwa babu kaffara kana gani ka san da kyar take sauke numfashi. Ga rabin kirji duk a waje haka ma bayanta. Kanta babu dankwali sai wani yalolon mayafi sa ta yane kan dashi. Ana ganin zara-zaran kalbar da tayi da zaren lilo a cewarta shi ba haram bane. "A haka zaki fita?" Cewar Anti Hasiya ganin tana niyar fita kai tsaye. Maimakon amsa Ayaah gatsina fuska tayi ta nufi kofar gidan gadan gadan za ta fita. Anti Hasiya tayi murmushin takaicin wannan hali nata. Wani salon fitsara da rani bata tunawa dasu sai taga tsakar gidansu cike da 'yan kunshi. A lokacin take yunkurin taka matar da take matsayin uwa a gareta don kawai ta zubar mata da mutumci. Bukatarta ta dade da biya domin dadaddun kwastamominta kusan kowa ya san tana da 'yar da take neman fin karfinta ba don a tsaye take ba. Murja dake gefe tana tata sana'ar ta kitso ta saki kan matar gabanta ta taso a harzuke. "Ba dake Anti take ba?" Ayaah tayi mata kallon raini tana jujjuya idanu "ai fa tunda ki ka fara kama matsabbai bakinki ya bude. To haka zan fita uwata ko zaki hana ne?" Wata mata ta kada baki ta ce "ke kuwa 'yan mata idan baki ga girman yayarki ba bai kamata kiyi haka a gaban mahaifiyarki ba." Dukan kunnuwanta tayi a tare tana murguda baki hagu da dama tare da farfari da ido kamar sabon kamun aljanu. "Mahaifiya? Tabdi. To ni mahaifiyata tana kasa Hajiya. Wannan matar..." "HAJARA!" Ba Ayaah ba kusan duka matan wurin harda Anti Hasiya kuwa sai da tsawar Honorable ta kada musu ciki. "Baki da bakin amsawa ne?" Ya sake cewa a harzuke yana tsaye a kofar da ta raba ainihin tsakar gidan da barandar da ake zaman kunshin. "Gani Baba" ta ce da sauri lokaci guda kwalla na zubo mata. "Share wadannan munafukan hawayen kizo ki wuce mara kunyar banza." "Baba gidan Anti Hasina (kanwar A'i kuma yaya ga Hasiya) zani." "Kin wuce ko kuwa?" Bata jira ya kuma magana ba ta bi ta gefensa ta shige ciki tana kuka. Dan dukar da kai ya yi ya bawa matan hakuri. "Ai shekarun nan sai an kai zuciya nesa. Allah Ya shirya mana zuri'a." Matar dazu ta furta da dan murmushinta. Ciki ya koma zuciyarsa tana tukukin bacin rai. Tsakaninsa da Hasiya yafi kowa sanin cewa ba soyayya bace. Ya sakawa zuciyarsa Allah ne Ya kawota cikin rayuwarsu domin ta zame masa bangon jingina. Idan ya tuna yadda har A'i ta rasu bai taba taka kafarsa gidansu ya gaishe da Innayo ba kunya kan rufe shi. Shi yasa baya ganin laifinta da taki goyon bayan auren nasu har yanzu. A yayinda mutane da yawa marasa tawakkali zasu alakanta aurensa da Hasiya a matsayin silar karayar arzikinsa shi alkhairi ya hango. Ya sani sarai cewa ko uwar 'ya'yansa da wuya ta zauna tsahon shekarun nan tana dawainiya dashi. Ba yadda zaiyi ya raba 'ya'yansa da kakarsu Laraba da kannen mahaifiyarsu amma yana bakincikin alakarsu. Yaji dadi da sauran basa daukar zuga amma Ayaah zugar ce ta tadda hali. Da fada yana fitowa mutum kila ba za ta ganu ba yanzu. A kanta ya fara dukan 'ya'yansa amma kullum dada kangarewa take yi. Shekararta goma sha shida da watanni, yanzu take ajin karshe a sakandire. Bayan sun shige ciki sai da Anti Hasiya ta dauki mintuna kafin ta ita cigaba da zanawa matar gabanta lalle. Lokuta marasa adadi ta kan ji kamar ta yiwa Ayaah dukan tsiya amma sai ta daure. Maraicinta take dubawa da kuma sanin cewa duk ranar da ta kai mata hannu akwai yiwuwar ta karairayata. Bata iya fushi ba sam. Sai ta dade tana tara mutum kafin ta dauki mataki. Abu na biyu kuwa bai wuce fargabar da take fama da ita akan kalaman Innayo ba. Tana yawan fada mata cewa yadda su A'i suka watsa mata kasa a ido ta tabbatar da wuya idan ba haka su Ummi zasu yi ba. Gashi ita bata haihu ba ma balle tasa rai da samun mai jinkanta a gaba. 'Ba duka aka taru aka zama daya ba. Dan da zai ji kan mutum ba lallai ya fito daga cikinsa ba.' Haka take yawan fadawa zuciyarta. Daga karfe uku ta rufe karbar 'yan kunshin ranar. Sai bayan la'asar ta gama ta shiga ciki tayi wanka. Ummi tayi abinci ta ci sannan taje ta duba Abbas. Yana yawonsa ko ina sai dai kwakwalwar ce ta dan tabu. Maganarsa ta hankali bata tsayi yake komawa shirme. Kwanakin nan yana yawan tashi da ciwon kai irin wanda yake yi tun bayan hatsarinsu. Ganin har lokacin yana kwance ta koma dakin Honorable. Kudin da take tarawa ta dauko. Dubu hamsin ne da 'yan kai suka rage bayan sun sayi kayan abinci sannan ta biyawa Ayaah kudin NECO da WAEC. Dubu shabiyar ta cire zata kaiwa Innayo washe-gari. Wata shabiyar din ta bawa Honorable a kai Abbas asibiti. Ashirin din kuma zata rike goma sai goman kai ta siyo kayan lalle. Dama haka take yi duk karshen wata ta raba musu ribarta. "Hasiya ki bar kudinki. Na yiwa wani abokina dan majalisa magana zai bamu tallafi akai Abbas asibiti a duba shi sosai." Kin karbar kudin da ya miko tayi, "ka fara kaishi ko magani su bashi na saukin ciwo kafin tallafin yazo." Da kyar ta samu ya karba a daidai lokacin da suke jin ihun Abbas din cikin azabar ciwo. Da gudu-gudu Honorable ya fita ya samo mai adaidaita sahu suka kaishi asibiti. Sai karfe tara na dare aka sallamosu. Kafin su dawo saurayin Ayaah ya kawo mata ziyara. Tunda babu idon babba a gidan tayi shiga irin wadda take so ta fita ba tare da sauraron gargadin Ummi da Murja ba. "Wowwww baby so ki ke ki kasheni ne da wannan kwalliyar? Kin san ina matukar son kwalliya. Ganinki haka ya cire min duk wani bacin rai da na taho dashi." Ya ce tana isowa jikin motarsa. Kanta taji yayi gingirin ya kara girma saboda tsabar dadin da taji da yabawarsa. Hankalinta kwance ta gillo masa karya da suka soma hira saboda yadda da soyayyarsa da tayi. "Babanmu ya ce ka fito." Sarai ya fahimceta sai ya bagarar ya gyara tsayuwarsa. "In shigo dai ko Baby?" Kallonsa tayi da rashin fahimta ta ce "ka shiga ina?" "Oh, ba kina nufin na shiga ciki mu gaisa bane?" Da saurinta ta gyara masa "nufina ya ce ka turo ayi magana saboda asa rana." Rabeel sai ya mike tsaye da kyau yadda za ta ga tsayinsa ya daure fuska yana jera mata tambayoyi "amma ba dai ce masa kika yi mun tsayar da maganar aure ba ko? Yaushe muka hadu? Ke da kike karatu me zaki yi da aure?" Tsoron kar shi ma ya kufce kamar sauran yasa ta kwantar da murya tana bashi hakuri "Dama ba wai auren za a daura yanzu ba. Kawai dai don ya san da kai ne kafin na gama makaranta." Kofar motarsa ya kama zai shige yana sababin da ya kwana biyu yana neman damar yi. Ya gaji da gafara sa bai ga kaho ba. Ta kware wurin kwadaita masa jikinta da irin shigarta amma taki bari ya dara daga rike mata hannu. Ya zata a waye take yazo kwasar ganima ashe kidahuma ce. Ga damar sulalewa ya gudu ya samu ba bata lokaci kuwa ya cafketa. "Yadda bana son a katsewa kannena mata karatu kema ba zan katse miki ba. Na zata Baba zai yarda kiyi zurfin ilimin da zamu yi alfahari dashi ni dake da 'ya'yanmu amma na fahimci ba haka ba. Tunda da wuri yake son aurar dake gaskiya ki nemi wani." Hankalin Ayaah in yayi dubu to duka ya mike tsaye. Bata da burin da ya wuce tayi aure ta bar gidansu. Gwaggo Laraba dama ta fada mata Anti Hasiya ce ta hana Murja da Ummi aure sannan sun kasa shiga jami'a. Daga mai dinki Ummi sai Murja dake kitso. Ga babansu ta hana arziki ya zauna masa domin ta juya shi. Shi yasa ita ta dage da karatu sosai don ta sha alwashin shiga jami'a. Abin kaddara duk kokarinta bata ci kwalifayin (qualifying) ba shi yasa Anti Hasiyan ta biya mata kudin NECO da WAEC. Ta fara murna wannan saurayin sun yi wata biyu shi ma yana shirin subucewa. Murmushi ta kirkiro na dole ta ce "Lahhh, wasa fa nake maka. Baba so yake na zama likita ma." Ai kuwa ya hade girar sama da kasa "Ayaah ni kam ba zan iya hada inuwa da makaryaci ba. Kamar baki san haramcin karya ba ki kalleni ki yiwa mahaifinki karya da sunan wasa?" Hawaye ta soma tana bashi hakuri ya shige motarsa yaja. A ransa yana cewa ta fiye bakin naci. Tun satin farko da yazo ya fahimci ita aure kawai take so. "A nemi wani wahalallen ba ni ba" ya ce yana dukan sitiyari. Kamar kiftawa da bude ido Ayaah ta neme shi ta rasa. Kuka sosai ta fashe dashi tana mai gasgakata Gwaggo Laraba. Lallai bokan Anti Hasiya ya iya aiki. Yanzu yanzu ta fito yana dariya amma ko rabin awa basu yi ba ya tafi. Rabeel bai zame ko ina ba sai gidansu abokinsa Danliti wanda ya bashi aron mota. Waya yayi masa ya fito karbar makulli. "Amma Rabilu yau kayi sauri ko baka sameta ba?" Dariya ya yi sannan ya kwashe yadda suka yi da Ayaah ya fada masa. "Kuma sai ka barta?" Cewar Danliti da mugun mamaki. "To zama kake so nayi a sani auren da ban shirya ba?" "Kai dai gaula ne. Irinsu ai da sa musu rai da aure ake moresu. Yarinya danya shakaf kamar wannan ka tsallake ka barwa wani?" Maganar ta shigi Rabeel ya cije yatsa yana maganar 'yan tasha yadda ya saba "ban yi tunani ba Yasin. To yanzu meye shawara?" Danliti ya lashe lebensa na kasa "sa'arka ta kare saura tawa. Can zani na gwangwaje son rai..." "Wannan yarinyar kamar kifi ba bari zata yi ka mori komai ba." Danliti ya shige motar da ya gyara zai mayar gareji kafin ubangidansa ya fahimci bata kwana a can ba "muje ka rakani na mayar da motar nan na baka satar ansa domin gaba." *** Jirgin Abuja su Munzali suka shiga. A can suka dauko motarsu wadda suka ajiye a gidan shakatawar daya daga cikin mutanen da suka ziyarta a Lagos. Babu bata lokaci suka kamo hanyar Kano saboda shirin bikin nadin sarautar Abbati sati mai zuwa. "Wai kuwa ya maganar mai yiwa Qibdiyya alkyabba ne? Ka tabo shi mana muji idan ya gama mu tsaya a Zariyan" Abbati ya tambayi Munzali suna daf da shiga Kaduna. Da sauri Munzali ya dauki waya ya kira mutumin da ya bawa aikin dinkunansu shi da Abbati da 'yarsu. Telan kwarrare a dinkuna irin na kayan sarauta. Kwatanta musu wata plaza ya yi mai suna Diamond plaza. "Kwananmu hudu da kama shago a nan mun baro Zariya. Ban fada maka bane Alh. Munzali saboda idan na gama da kaina zan kawo muku Kanon." "Ka gama na Qibdiyya? Babanta ya dameni wallahi." Munzali ya ce yana dariyar hararar da Abbati ke jefa masa. "An hada komai saura takalman." "Zamu biyo" *** Sau biyar Mardiyya tana kin daukar wayar Mamanta Nasima saboda tsoron me zata ce mata. A na shidan sai ta tura mata text wanda yasa da kanta ta kira a tsorace. (Idan baki dauka ba zamu hadu ne a gida. Shashasha mara mutumci.) Ringing din farko Mama Nasima ta dauki wayar ta fara surfa mata zagi. "Saboda baki daukeni a bakin komai ba ki ka shirya ki ka bisu ko? Tun ranar da babanki ya fada ban ce babu inda zaki ba?" Mardiyya sai ta wayance kamar bata ji me ta ce ba "Mama muna hanya" Rai a bace ta ce "Au, baki ma ji me na ce ba kenan. To ki ce su saukeki a shago yanzun nan." Mardiyya ta kashe wayar ta taba Sauda dake gefenta. "Mama tana nemana a shago." Sauda ta dan zura kanta gaban motar ta ce "Ya Lilu don Allah mu biya shagon Mama a ajiye Mardiyya." Bai so ba sai dai kuma Mardiyya tafi karfin haka a wurinsa. Tana kaunar 'yan uwanta suma suna sonta ciki kiwa harda Suhaib. "A ina yake?" "Diamond plaza" Farha ta bashi amsa. U-turn ya yi ya koma titin da suka baro domin sun bar hanyar plazar a can baya. Farha ce ta kira Mami Khadija ta sanar da ita inda zasu fara zuwa ta ce babu matsala. Ta ma jidadi domin abin da take son yiwa Alh. Tahir zai fi a bayan idon 'ya'yansa. Suna shiga harabar plaza din Lilu ya hango wata jar mercedes benz ya daki sitiyari yana dariya. "O.M.G! Wayyo Ya Suhaib mintsine ni na farka." Suhaib ya girgiza kai yana dan murmushi "kana da matsala Lilu. Yanzu zaka yi sauri mu ajiyeta ne ko mota zaka tsaya kallo?" Kallon rashin yarda da maganar da ta fito daga bakinsa Lilu ya yi masa. "Mercedes benz E class, E dinma 350. Ya Suhaib dream car dina ce fa kake yi mata kallon raini." Su Farha dake baya suka bushe da dariya don Lilu kamar zai yi kuka. "Tunda dai iyakarka da ita bai wuce dream din ba ai shi kenan." Ya zura hannu ta taga ya dagawa motar da ta sha tint glass hannu "ke dream car Lilu na gaisheki." "Ya Suhaib ka sace min gwiwa. Burina na mallakin motar nan kasa kafa ka dagargaza da wannan abin da kayi." 'Yan matan suka cigaba da dariya yayinda Lilu yake ta mita kamar ya ari baki. Kusa da motar yaje ya yi parking yana cewa sai ya shafata ko za ayi kararsa. "Muje na raka ka Lilun Mami." Farha ta ce hannunta a jikin hannun kofa. Mardiyya ta janyo hannun Sauda bayan ta fito daga motar. "Zo ki rakani muma mu taba." Kamar ba su Suhaib yake kira ba duka kannen nasa suka fice suna dariyar yadda jikin Lilu ke rawa yana zaro wayarsa. Jingina ya yi a jikin motar ya gyara kwalar rigarsa. Farha ya mikawa wayar ta karba tana murmushi. "Allah Sarki 'yan matan KASU zasu shiga uku da hotunan karya." Yana zura hannayensa a aljihu idanun Abbati dake zaune a mazaunin direba yana ta dariyar hirarrakinsu suka sauka akan Farha. "Ya Ladif" ya sami kansa da furtawa a hankali yana shafar sumar kansa da take shan gyara. 'So ne? Wannan ce soyayya?' Karon farko a rayuwarsa mace ta burge shi. Mace ta dauki hankalinsa. Ganin Farha ya yi tamkar tauraruwar da wata ba ya cika sai da kasantuwarta kusa dashi. It was love at firI just published "10" of my story "UWA UWACE...". https://my.w.tt/ZvVtc6Nojab UWA UWACE...10 Batul Mamman💖 Allah don isar da tafi kowacce isa Allah don mulkin da bashi da wa'adi Allah don rahamar da bata yankewa Allah don girman zatinKa Allah don kadaitar mulkinKa Allah don buwayarKa Ka karawa Annabi SAW daraja Ya Rabbi mamallakin sammai da kassai Ka kare mana zuri'a daga dukkan sharri. Ya Allah Ka karesu daga sharrin masharranta da sharrin kawunansu domin hakika kowane dan Adam akwai dabi'ar da aka halicce shi da ita mai kyau ko akasinta. Ya Allah kar Ka buga misalin Allah wadai damu ko 'ya'yanmu. Ya Allah Ka azurta iyayenmu da mafi girman daraja da daukaka daga cikin AljannarKa. Allah Ka yafe musu, Ka jikansu, Ka kara musu lafiya, Ka kyautata halayensu, Ka inganta mu'amalarmu dasu da kuma sauran mutane. Amin RABBIR HAMHUMA KAMA RABBAYANI SAGHIRA *** Babu sautin da kunnuwan Abbati suke ji sama da bugun zuciyarsa. Sassanyan murmushi ya kufce masa a lokacin da ya dora hannun damansa akan kirji saitin zuciyarsa. "Ya Farha kawo kema na dauke ki" muryar Lilu ta katse tunaninsa. "Farha" ya gwada kiran sunan akan harshensa. Daga wajen murmushi tayi wanda ya kara narkar da zuciyarsa ta ce "Haka kawai ina tsaya masu motar su fito a tsareni in sha kunya." Mardiyya da Sauda ya dauka har lokacin Munzali bai fito daga wajen tela ba. Farha ta gaji da surutunsa na rokon ta dauka ta jingina da motar bangaren direba. "Irin abin nan zanyi kamar nice mai motar na zo shopping." Hannun ta kama kamar za ta bude, Lilu ya saita ta zai dauka Abbati kuma ya cire lock. Tana dan daga handle din kofar ta bude. Daga ciki ya turota ai sai ta gigice su duka hudun suka kwasa a guje suka nufi shagon Mama Nasima. Suhaib na ganin haka ya fito daga mota da sauri. Wurin Abbati dake tsaye yana dariya ya karasa ya mika masa hannu. "Don Allah kayi hakuri" Abbati ya saki fuska sosai "ni zan baka hakuri saboda na tsorata maka kanne. Muje na tayaka kiransu" ya nuna hanyar matattakalar da suka hau. "Kar ka damu na san inda suka je" Suhaib ya bashi amsa yana hawa benen. A ransa yake ayyana mutumin yana da saukin kai duk kuwa da cewa kana ganinsa tun daga sutura har fatar jiki ka san akwai kudi. Shagon Nasima da take sayar da kayan kitchen suka shiga. Allah Yaso babu kwastoma ko daya a ciki sai 'yar budurwar dake tayata aiki. Mardiyya ce ta fara shiga ta hau ta da fadan da ta fara a waya. "Tsinannen yawo da rashin kishin uwarki yasa ki ka bijerewa maganata ko? Wace uwar za a baki a wurin da yasa ki fita da sassafe kafin na tashi?" Tuni idanun Mardiyya suka kada suka yi ja tana shirin yin kuka. Farha, Lilu da Sauda sai suka yi turus. Mama Nasiman kanta ta dan ji kunyar ganinsu amma sai ta fuske. Fuska ba wani annuri ta ce "yau kune a nan? Ince dai lafiya." "Lafiyar kenan. Kanwarmu wadda babu mai iko da ita sama da Alh. Tahir mahaifinta muka kawo" Lilu ya bata amsa shi ma fuska a hade. "Rashin kunya zaka yi min? Khadija ma..." "Wallahi kar ki soma. Da fa bamu san asalin balbela bane." Farha da bata da hayaniya ta ce a tsiwace. Ita da 'yan uwanta basa gani su kyale in dai abu ya shafi mahaifiyarsu. Mardiyya kuka ta saka. Ita ma ta san labarin auren cin amanar da mahaifiyarta tayi da babansu. Ba dai su san da maganar suna neman juna ba amma sun san mai'aikin gidan ce. Haka zalika sun san Anti Jiddo 'yar uwarta ce. Sauda ma kukan take tayata. Ana haka Suhaib ya shigo. Mama Nasima ta nuna masa kannensa cikin bacin rai. "Ka fita dasu kafin na kira Alhaji. Ba zan yarda ku zo har nan ku min rashin kunya ba." Da ido kawai ya kallesu suka fice daya bayan daya. "Kiyi hakuri" Ya ce da ita bayan sauran sun fita. Maminsu ta gargade shi sosai akan yiwa matan babansa rashin kunya. Mota suka nufa ya karbe mukullin daga hannun Lilu. Bai ce dasu komai ba yaja suka tafi. Suna fita Abbati da Munzali suna shiga shagon Mama Nasima. Yawun bakinta taji ya kafe ta nemi na hadiya ta rasa saboda ganin matasan masu kudi a gabanta. Komai da komai na suturar jikinsu da ido ke gani iri daya ne. A cikin 'yan dakiku ta gama lissafin tsadar kayansu ta gane sun tsallake raini nesa ba kusa ba. Harara ta gallawa Mardiyya wadda take jin zafin zuwanta a mace gashi bata sake haihuwa bayanta ba. Jikinta na rawa saboda rashin sanin daraja da kimar kai ta matsa gabansu. "Alhaji me ku ke so? Ke Debora miko musu katalog (catalogue) dinnan su duba kaya." Kamar wani zai rigata da sassarfa ta ce su biyota office dinta. Wani dan daki ne da aka sakaye daga gefe da kofar gilas. A nan take zama idan ta shigo shagon. Waige waige Abbati ya dinga yi yane neman su Farha. Munzali yana 'yar dariya ya tura shi gaba zuwa ofishin Mama Nasima tana fesa airfreshner. "Tunda ka kawomu ko kofi ne sai ka saya." Ya rada masa a kunne. Da suka shiga sun sameta tana goge kujerun zaman baki da dankwalin kanta. Murmushi take ta dokawa ta nuna musu su zauna. "Mardiyya. Ke Mardiyya kawo musu abin sha. Alhaji me zaku sha? Idan babu sai Debora ta sauka ta siyo." Sai da Mardiyya ta goge hawayenta ta taho zuciyarta tana zafi. Haka ta tashi ta fahimci mahaifiyarta tana bare-bare da zubar da mutumci gaban masu kudi. Idan ta sansano kudi a jikin mutum to babu ya shi a wurinta. Yaro sa'an Mardiyya ma sai ta duka masa. Neman kudi take kamar tayi sata. Tunda bata da magajin da zai tatso mata da yawa a jikin Alh. Tahir sai ta fake da kasuwanci tana kwasar kudi son rai. Duk da haka tana son kasuwancin domin yana hadata da manyan mutane. Shigowar Mardiyya keda wuya idanun Abbati suka sauka a kanta. Murmushi ya yi sosai. " 'Yan mata ashe nan ku ka gudu. Dama ku muka biyo. Ina 'yan uwan maki?" A darare ta kalli Mama Nasima sai taga ta kyafta mata ido da sauri. Da dariya ta ce dasu "Ba dai Mardiyya ku ka biyo ba? Ikon Allah. Ai 'yata ce ta cikina. Waye surukin nawa a cikinku?" Mardiyya ji tayi ina ma kasa za ta tsage a lokacin ta shige ciki. Daga ganin mutane ta kasa zaune ta kasa tsaye. Ita kuwa Mama Nasima ko amsa bata jira sun bayar ba ta dora da cewa "zo ki zauna bari na kawo lemon da kaina." Da taga Mardiyyan ta kasa daga kafa ma saboda takaici ta soma fada "meye haka ne zaki barsu jira kamar sa'anninki?" Ta dube su da dan murmushi "kuyi hakuri fa. Yaran yanzu da ka ce kana son su sai su dinga ganin kamar kun zama sa'anni." Tana fita Mardiyya tayi saurin zagayawa yadda zata fuskancesu da kyau. "Don Allah kuyi hakuri da maganar Mama. Sannan kayi hakuri da muka tsaya a jikin motarka." Murmushi Abbati ya yi yana jin tausayinta. Yanayin abin da mahaifiyarta tayi ba kowa ya kawo masa rai ba sai Munzali. Haka Asabe take gigicewa idan suka je gidan. Yanzu kamar ta goya shi bayan da almajiri take kiransa. Munzalin ya kalla yaga ya yi shiru. Ya tabbata shi ma ta bashi tausayi ne. "Ga mai motar nan ni dan rakiya ne." Caraf a kunnen Mama Nasima. Da saurinta ta karaso ta zuzzuba musu maltina mai sanyi a kofunan tangaran da yanzu ta bude daga kwali cikin kayan shagon. Da zata basu har wani dan durkuso tayi wanda ya tsayawa Mardiyya a zuci don takaici. "Ma sha Allahu. Ai nima mota ta tana nan a waje. Zaku ganta wata koriya koriya nan. 3.8 miliyan maigidanmu ya saya mana ni da kishiyoyina. Mu uku ne nice ta biyu." Ta dan yi shiru na abin da bai kai sakan biyar ba sannan ta cigaba da magana tana tura musu tray din da ta dora kofunan "ku sha mana ai an zama daya. Ya sunanku ne?" Ta kare da tambaya tana doka murmushinta mai ban haushi. Munzali zai yi magana Abbati ya take masa kafa ya nuna kansa "Ni suna na Abbati shi kuma Munzali." Kacokan ta mayar da hankali gare shi "Allah Sarki Alhaji Munzali. Ya su Mummy? Ya fama da jama'a?" Kasa jurewa Mardiyya tayi ta fice. Wannan zub da kimar ya yi yawa. Abbati da Munzali kuwa da kyar suka danne dariyarsu. Munzali ne ma ya yi karfin halin cewa zasu tafi. "Kun dai karbi nambar wayarta ko?" "Yanzu zamu karba" Munzali ya bada amsa yana yin gaba. Tana ganin Abbati ma zai fita ta dakatar dashi "Alh. Abbati ai da ka jira shi a nan. Sai da irin haka zasu fuskanci juna." "Haka ne" ya ce yana tsayuwar dole. Suna fita Munzali ya karbi nambarta. Hakuri ne dai take ta bayarwa ya ce kada ta damu. Nambar ma ya karba ne saboda kiran gaggawa da Abbatin yayi masa. Bai sani ba ko zai bukaci hakan. A ciki tambayoyi ta tsare Abbati dasu ya dinga bata amsoshin da ya ga dama. Ba jimawa Munzali ya kira shi ya ce mata zasu tafi. Haka ta taso Mardiyya a gaba har bakin mota suka rakosu. "Ka gaishe da Mummy da Daddy don Allah. Ka turowa Mardiyya nambarsu sai na kira mu gaisa a fara sabawa da juna." Munzali da Abbati na ganin sun bar wurin suka hada ido suka kwashe da dariya. "Mutumina ka gaishe da Mummy da Daddy" cewar Abbati yana kyakyatawa. "Ya kaga Asabe tana amsa sunan Mummy" shi kuma Munzali ya ce yana tasa dariyar. Sai da maganar ta fito ya yi saurin kallon Abbati ya doki bakinsa da kansa "sorry Abban Qibdiyya Allah subul da baka ne." Abbati ya girgiza kai "ni dai na fada maka UWA UWACE. Tunda ta kawoka duniya tayi maka komai." Duk da Munzali yaso daurewa amma sai da muryarsa ta dan yi rawa ya ce "Komai fa ka ce Abbati. Asaben ce tayi min komai?" Wani zazzafan hawaye ne ya sauko masa gashi shi yake tukin lokacin ya share ido da karfi "na rantse maka idan yau za a bani zabi kai zan zaba akan uwar da ta haifeni. Bata damu da komai nawa ba sai aljihu." Yana maganar yana hawaye sosai. Haka Allah Ya yi shi mai matukar son kulawa. Kuma duk yadda ya kai da basarwa ba karamin kwadayin ranar da Asabe za ta nuna masa mahimmancinsa yafi karfin kudi yake ba. Hawayensa ya tayarwa da Abbati hankali ba shiri ya sake karbar tukin. Shiru suka yi a motar har suka wuce Zariya sannan Abbati ya katse shirun motar. "Munzali" "Na'am" ya amsa yana ciccijewa irin na wanda ransa ya baci yana jiran rarrashi. "Dadina da kai ka ki girma. Ko kunya babu kake faman kuka kamar karamin yaro." "Allah abin ne da haushi." Kawai ya sake fashewa da kuka. Abbati yana tuki ya daga hannu ya make shi a kafada "ka min shiru don ubanka. Haka kawai za ka dinga min kuka kamar na dauko rikakken rago." A take Munzali ya soma dariya ya karkace baki ya ce "ɓaaaaa, ɓaaaaa, ɓaaaaa" Abbatin ma dariyar ya kama yi. Sai da suka yi mai isarsu sannan ya yi gyaran murya wanda yasa Munzali mayar da hankali gareshi. "Misali a kawo maka mace da namiji duka kyawawa ace ka zabi daya wanne za ka zaba?" "Me yasa ka tambaya?" "Maganar sai mun zauna ka bari muje gida" "Nifa ka san bana son jan rai kawai ka fada." Bakinsa ya ji ya dan yi nauyi amma yana ganin dole ya yi magana. "Munzali yaushe zamu daina wannan sana'ar?" idanunsa akan titi ya cigaba da magana tunda ya samu hankalin Munzalin na gareshi "ina tsoron kada mu dore a haka har asirinmu ya tono mu gogawa Qibdiyya abin da ba zai kankaru ba." A hankali Munzali ya ce "ka sami macen da ka ke so ne? Ko yarinyar dazu ce da kaimu shagonsu?" "Ko daya" ya sami kansa da cewa saboda yadda zuciyarsa ta raya masa cewa bashi da tsaftar jiki da ruhin da suka isa bashi dama ya furtawa Farha kalmar so. "Idan kana so mu daina ka sani ba zan tsallake maganarka ba. Nima fa na san haramun ne amma hanyar da na sani kenan ta samun kudi." "Munzali bamu da maraba da karuwai fa. Biyawa mutane bukata muke yi su biyamu. Bana so mu tabbata akan wannan abu" ya ce yana dan tsare shi da ido. Jikin Munzali ya dan yi sanyi. Yana son bari shi ma amma yana tsoron kada haka ya zama dalilin rabuwarsa da Abbati. "Idan mun daina me zamu yi?" Abbati ya ce "yanzu zamu ga amfanin adult education (yaki da jahilcin) din da muka yi. Kudaden da muke samu muyi amfani dasu mu bunkasa shagunanmu na kasuwa. Ko mu bude irin super store dinnan ko mall." "Kai kana sha'awar mata ne?" Munzali ya kasa hakuri sai da ya tambaye shi. "Na zata bana yi Munzali amma daga baya na gane nafi son mace akan namiji. Nifa sana'a na dauki abin da muke yi sai kuma sabo. Amma ina ji a jikina zamu iya dainawa idan mun sa kanmu. Mu dai yi tunani a kai mu nemi mafita." Kai tsaye Munzali ya amsa masa sai dai yana ji a jikinsa zasu wahala. Sun girma cikin wannan dabi'a har ta kai da kyar yake iya zuwa ga matarsa. Cikin Qibdiyya ma rabo ne kawai ya sani. Shi kuwa Abbati rashin so da mugun halin Hanne na dauke dauke yasa duk zuwansa gareta baya wuce rabo. Sai gashi 'ya'yan ma basa zama. Dadin dadawa sun saba da rike manyan kudi. Suna cikin matasan dake tashen kudi da 'connection' na sannin manya a yanzu (Ina so 'yan uwa su sani cewa mutane masu neman jinsinsu kala biyu ne. Akwai homosexuals masu neman jinsinsu kadai. Basa taba sha'awar wani daban. Akwai kuma bisexuals. Sune masu sha'awar jinsinsu walau mace ko namiji da kuma wanda ba nasu ba. Suna iya mu'amala da kowanne su jidadi. Abbati da Munzali sun kasance cikin wannan jerin. Sabo yasa basu damuwa da mata, ba wai don matan sun daina daukar hankalinsu ba.) *** Kayanta ta rage ta saka wata doguwar rigar yadi mai laushi sannan ta fito falonta inda aminiyarta a wurin aiki take zaune. Da fara'a ta sake tashi a karo na biyu ta rungumeta. "Congratulations Dr. Khadija." "Godiya nake Assistant Prof. Zuwaira" ita ma ta kirata da nata mukamin suka dara. Suna zama Dr. Zuwaira kamar yadda kowa ya santa a wurin aiki ta mike " 'yar uwa guduwa zan yi fa tunda naga tare da maigidan ku ka dawo. Dama makara nayi ban samu na zo miki a makaranta ba na ce bari na biyo gida." Dan bata rai Mami Khadija tayi "ba za ki zauna walimar da 'ya'yanki suka shirya min ba? Saboda ita mutane da yawa basu je Zariyan ba. Ana la'asar za a fara." "Zan dawo Doctor. Babban abin da ya kawoni akan maganar gidan nan ne. Na san kin ce a yau dinnan za ki yi masa idan ya kawo zancen komawarku sabon gida." Da tausayi ta kalli kawarta da ta dauka tamkar kanwarta "Khadija fight for your marriage don Allah kada hakurinki na shekaru ya tashi a banza. Ki duba ki gani ido rufe nake neman aure da shekaruna da komai saboda shi ne babban martabarmu." Murmushin takaici Mami Khadija tayi idanunta na cikowa da kwalla. Ba don suna shigowa gidan motar Dr. Zuwaira ta shigo ba da tuni kila ta karbi takardarta a hannun Alh. Tahir. "Magana fa nake kin tafi duniyar tunani" A gajiye da lamarin aurenta ta soma magana. "Kin san komai Anti Zuwaira. Abin da na kasa fadawa 'yan uwana ban boye miki ba. Don Allah kada ki shiga sahun masu bawa mata shawarar zama da mazinaci." Kwalla ce a idanuwanta. Kuka take son yi ko zata sami sassauci. Ta wahala matuka kafin ganin cikar burinta. Aiki ba dare ba rana har ta tara isassun kudi tayi gini a nan cikin Kaduna. Gidan da Alh. Tahir ya kama mata haya a Zariya tun lokacin karatunta har ta soma aiki ya dade da saya. Da sunanta ya saya ya bata takardun gidan. Wanda ta gina yanzu zai wadace su ita da 'ya'yanta har suyi aure. Daki hudu ne. Mazan kowa daya sai matan a guda ita ma a daya. Takaicinta daya ta gama ginin daidai lokacin da shi ma Alh. Tahir ya gama tsantsara gida na kece raini. Kafin yasa ranar tarewa take so ta karbi takardarta ta bar shi da matansa na aure da 'yan matansa na titi. "Khadija" Anti Zuwaira ta kirata a hankali da sigar laluma "idan kun rabu kin san da wa zaki hadu a gaba? Yawancin maza haka suke sai dai na wani yafi na wani. Ga 'ya'ya har hudu tsakaninku. Me zaki ce musu shi ne silar rabuwarku? Abin da hakuri bai bamu ba Khadija rashinsa ba zai bamu ba. Na isheki misali. Tun da sauran kuruciya na fito amma miji yaki samuwa. Ke banda tsoron Allah da sai na fada wani hali. A yadda nake ji yanzu ina dana sanin kai kararsa har aka rabamu." Khadija ta dakatar da ita da cewa "dukan Anti Zuwaira? Yanzu har kina nadamar fita daga gidan wanda ya miki dukan da ki ka kusa rasa rayuwarki?" Da dan karfi ta ce "ba dole maza suke cigaba da cusgunawa mata ba. Suna yi muna turewa kawai saboda kar a kiramu zawarawa ko a rabamu da 'ya'ya." "Khadija wace uwa ce mai hankali zata so barin 'ya'yanta a gidan da ita ta kasa zama?" "Haka ne. Nima zamansu nayi domin dasu ya yi min barazana a lokacin." Anti Zuwaira ta ce "yawanci duk hakurin da muke yi kenan. Fight to save your marriage and your husband." Kuka mai ciwo Mami Khadija ta fashe dashi tana jin zuciyarta tana tukukin bacin rai "wane auren? Wane mijin? Anti da idanuna ba labari ba na kama shi da Nasima. Har yau ..." ta fada tana dukan kirjinta dake suya "ban manta da hoton da na gani ba. Zama gida daya dasu muna kallon juna tsayin shekarun nan ya isheni bala'i. Ko matarsa ce na fada musu daki ya ya zanji ballatana mai'aikina yarinyar da ta bada shawara aka cire min mahaifa! Bai kuma tsaya nan ba na kuma same su suna rigima akan kanwarta da ya kai daki. Gasu nan duk ya ajiye a gidan amma har yanzu bai daina yawon bin mata ba. Mutumin da ya ce ya ji ya gani akan sabon Allah din ne zan wahalar da kaina wurin kwatowa? To na kwato shi daga hannun wa? Shi ne fa wanda ya kamata a dinga neman tsari da haduwa dashi. Na riga nayi masa alfarma a idon 'ya'yansa. Banda Suhaib babu wanda ya san halinsa a cikinsu. Rashin abin rike kai da 'ya'ya ke sa mata daurewa suyi ta zama to Alhamdulillah naci moriyar wannan zama. Wai Anti har kin manta silar haduwa da dalilin amincinmu? Kin san komai Anti Zuwaira ki daina bani shawarar cutar kaina. Kaddara ta riga ta hada jinina da nashi mun haihu amma wallahi ina tsoro. Ina matukar tsoron hakkin 'ya'yan mutane kada ya bibiyi 'ya'yana da Mardiyya. " Jinjina mata Anti Zuwaira tayi domin ta san cewa Khadija jarumar mace ce. Wata biyar da fara aikinta a jami'ar ABU suka hadu a masallaci. Allah sai Ya hada jininsu daga gaisawa suka kulla zumunci. Lokacin graduation din Sauda da Mardiyya daga JS3 Alh. Tahir ya shirya musu gagarumar walima a gida. Anti Zuwaira ta sami zuwa da 'yan matan 'ya'yanta su uku. A ranar Alh Tahir ya kyalla ido yaga babbar mai suna Siyama. Bai san 'yar waye ba shi dai ya ganta a wurin taro. Sai da ya san yadda ya yi ya nemi nambar wayarta. Yarinya ita ma bata san waye ba ya soma kiranta a waya da fuskar soyayya. Tafiya na gaba ya fito da maitarsa fili ya dinga tura mata kazaman sakwanni. Da yake Allah Ya kareta kuma akwai tarbiyya da kanta ta nunawa mahaifiyarta. Ita kuma ta kwafi nambar tunda bata tare da mijinta washegari a wurin aiki ta nunawa Mami Khadija. Hankalinta duk ya tashi tana tsoron kar a bata mata 'ya. "Ta wace hanya ya kamata mu bullo masa? Idan wani abu ya sameta ta ina zan fara? Ka kwashi shekaru kana tarbiyya da tattali wani mara tsoron Allah Ya wargaza maka." Tausayi ta bawa Mami Khadija domin ta shaida jajircewar Anti Zuwaira wurin tarbiyar 'ya'yanta. "Bani nambar na kira shi." "Keeee, raba kanki. Wai baki ga messages din da nayi miki forwarding ba? Mutumin nan da gani kwararren dan iska ne. Da aurenki kada matsalata ta janyo miki jangwam." "Tsorata shi zan yi in ce mun yi bincike a kansa zamu turo masa 'yan sanda idan ya sake kiranta." Kamar da wasa ta saka nambar a wayarta. Suna bai fito ba tunda Alh. Tahir bai taba kiran matansa da layin ba. Ringing biyu ya dauka a zatonsa cikin 'yan matan da yake bawa nambar ce. Kashe murya ya yi yana wani jan haruffa irin na kwararrun 'yan bariki "Hello baby girl." Bata gane shi ba a lokacin ta ce "babar Siyama ce yarinyar da ka ke ta yiwa barin kudi. Idan baka rabu...." Maimakon ya ja bakinsa ya katse kiran saboda mamaki da kaduwa sai cewa ya yi "Khadija?" Da ainihin muryarsa. "Abban Suhaib?" Ita ma ta ce nata mamakin ya ninninka nashi. Anti Zuwaira sai ta matso kusa da ita. Jikinta ya yi mugun sanyi kamar anyi mata wanka da ruwan kankara haka. Kukan ma da take jin zai kawo mata salama kasawa tayi. "Abban Suhaib abin naka har ya kai kan 'ya'yan kawayena?" "Tsaya kiji Khadija" ya ce a gigice. "Kaji tsoron Allah kada watarana abokan shashancinka su turawa naka 'ya'yan irin kazantar da ka turawa 'yarta. Ka kiyayi ranar da zaka ji inama baka zo duniya da lafiya ba bare ka dinga lalata 'ya'yan mutane." Kif ta ajiye wayar. Anti Zuwaira ta matso kusa da ita a tsorace "mijinki ne? Babansu Farha ne?" "Shi ne" ta ce a hankali sai ta yunkura kamar za ta tashi ta fadi yaraf a kasa. Anti Zuwaira taga tashin hankali muraran a ranar. Ta zata Mami Khadija ta cika ra dinga girgizata. Ganin abin yafi karfinta ta fita ta kira abokan aikinsu. Basu jima ba aka kawo ambulance daga asibitin koyarwa na Shika. Ma'aikatan su ma da fari sun zata ta rasu sai daga baya ta numfasa da karfi. Shabe-shabe da hawaye Anti Zuwaira ta rungumeta tana kuka. A asibiti likita ya ce jininta ya hau sosai saura kadan ta sami stroke (mutuwar barin jiki). "Kar ki bari ciwo ya kassaraki Khadija. Idan kina da damuwa ki fada min, ko bani da maganinta da shawara zan tayaki jimami. Barin kashi a ciki baya maganin yunwa. Ki dinga fadar damuwarki don Allah." Cikin kuka Mami Khadija ta ce "damuwar ina auren mijin da bai dauki zina a bakin komai ba saboda rashin tsoron Allah?" Ita kuka Anti Zuwaira kuka. A ranar suka kulla aminta. A yau kuma Mami Khadija ta gama shirin ba za ta kara kwana a gidan Alh. Tahir ba da aure ko babu. *** Hasiya ce mai zuwa duk satin ta duba lafiyar Innayo. Bata tafiya sai tayi mata miyar sati da girkin da zata ci ranar sannan ta gyara mata daki ta wanke bandaki. Ba don Innayo din bata son ganin su Ummi ba da su ne zasu dinga yi mata aikin. Salima da Maimuna kuma kamar hadin baki kananun 'ya'yansu ne mata. Manyan duk maza ne. Na Uwani da Zara kuma sai sallah sallah suke zuwa. Munzali ya yi gyara a gidan yanzu kowace mace tana da bandaki a cikin dakinta. Asabe bakincikin kamar ta mutu da ya ce zai hada da bangaren Innayo. Gori kuwa har ta gaji da damuwa ta saba. Kwana na uku kenan ciwon hakori ko bacci baya barin Innayo. Tunda Hasiya bata zo ba ta san cewa dole matsala ce ta taso mata. 'Tana can tana bautar 'ya'yan miji' ta ce a zuciyarta. Wayar da Hasiyan ta saya mata ta dauka ta kira Maimuna da sanyin safiya. "Shallo, shallo Memuna kina jina?" Ta ce da kyar hannunta dafe da mukamukinta bangaren dake ciwo. A dan tsorace saboda ganin wayar ta sammako Maimuna "Innayo ina kwana?" "Lafiya kalau. Ina mazajen nawa marasa cefane?" Ita ma ta amsa murya a sake. Da dai Maimuna ta tabbatar ba matsala bace sai ta saki rai suka gaisa sosai. Da tayi tunanin ko wani abu mara dadi ne ya faru a gidan. Suna gama gaisawar dama shiri take ta ce "Innayo Doguwa zamu tafi yanzu. An yo waya Iya (surukarta) ta zame a bayangida" (Nima ciwon hakori nake Memuna) Innayo ta furta a zuciyarta. A zahiri kuwa addu'a da fatan sauka lafiya tayi mata. Suna gamawa ta kira Salima. Mai rakata asibiti take nema cikinsu. Mijinta ne ya bata wayar tana gaban murhu sai fama da hayaki take za ta dumama tuwo. "Ungo Innayo ce ke kira. Ki dauka ki tambayeta dubu goman da na ce miki. Banza karbi mana." Tsuke baki Salima tayi domin idan tayi magana kuka ne zai taho. Sosai Hasiya ke taimakon 'yan uwanta da mahaifiyarsu sai dai samun nata ita ma ba wani mai yawa bane. Ita Salima ta san yanzu Innayo da Hssiyan ta dogara. Mijinta kuwa kamar an kwashe masa albarka. Aure har yau bata taba jindadinsa ba saboda mahaifinta bai saya mata mutumci ba. Ta kuma kasa fadawa Innayo saboda kada ta cigaba da tayar mata da hankali. Murya can kasa ta amsa wayar bayan ya zungure mata keya "Innayo..." "Ya naji muryarki a shake Salima?" Ta amsa a firgice. "Da ciwon kai na kwana. Yanzu ma nasha magani amma bai sauka ba." Mijin nata yana jin mai take cewa ya damki dankwalinta wanda ya hada da gashinta ya matse iya karfinsa. Haushi kamar ya rufeta da duka saboda taki nema masa kudin zuwa caca. "Sannu Salima. Zan fita idan na dawo zan biyo gidan naki." Uwani da Zara ne suka rage bata kira ba. Gabanta har dan faduwa ya yi da tayi tunaninsu. Ita ta haifesu amma kalaman da suke yi mata ke sa bata yawan kiransu. Duk da haka a gefe suna nan cikin zuciyarta. 'Yan uwan Innayo mata kaf suna kauyensu a karkashin karamar hukumar Garunmalam. Akwai kadan cikin 'ya'yansu dake aure ko kananan sana'o'i a Kano. A ganinta nemansu su rakata asibiti tamkar kwayewa kanta baya ne. Wurin Alh. Rabi'u taje neman kudin ganin likita ya ce babu. Kudin da Hasiya ta bata satin da ya wuce tayi barka dasu. Don kokari sai ta bayar da duka ta ce wai gudunmawar 'ya'yanta ce. Ba za ta iya zama da ciwo ba. Ruwan alwala ma da ya shiga bakinta da asuba ta kusa sakin fitsari saboda azaba. Shiryawa tayi ta tafi asibitin Sir Sunusi inda Uwani ta kai matsayin Metron (matron) a bangaren karbar haihuwa. Fatanta dai Allah Yasa tana nan tayi mata jagora bangaren hakori a duba mata. Nisan tafiyar zuwa asibitin wanda yake kan titin Hadeja daga unguwar Dala sai mazauni ko wanda ya san Kano zai gane. Adaidaita sahu ta shiga ya cajeta kudi mai tsoka kuwa saboda nisa da goslow. Yana sauketa a bakin gate ta tambayi bangaren haihuwa guda cikin masu gadin ya nuna mata. Tana tafe tana jin yadda duk taku daya sai kunnenta ya amsa na bangaren hakorin. Wasu nurses ta gani su hudu a bakin kofar wurin ta duka ta gaishesu saboda ganin girman masu farin kaya da mutanenmu ke yi. " 'Ya'yan nan don Allah Uwani nake tambaya. Wata 'yar jika-jika. Ta ce min a bangaren nan take aiki." Zaro idanu suka yi suka hada baki wurin cewa "Matron Uwani bala'i" Daya ta ce "Iya in dai mai haihuwa ki ka kawo gara kawai ki bi tsarin asibiti kar ki daka Metron dinnan." Innayo taji jikinta ya yi sanyi da kalaman da ake fada game da 'yarta. Ta tambayesu "akwai matsala ne ta bangarenta?" "Ai ba kya ji mutuwar sarki a bakinmu ba. Zamu fada mata idan mun ganta" suka yi gaba abinsu. Zaman minti ashirin a karkashin zafin rana da azabar ciwo Innayo tayi kafin Allah Ya kawo Uwani daga dakin hutunsu. Taku daidai take yi cikin kasaita ta yatsina fuska ta ce "Wace ce aka ce tana nemana?" Innayo ta daga kai da kyar. Bata san da yadda za ta kwatanta ciwon da take ji ba. Hasiyanta bata san da ciwon hakorin ba. Ita kuma taki fada mata saboda ta san irin nauyin dake wuyanta. Uwani na ganinta ta karaso da sassarfa. Idanunta basu gane mata canjawar fuskar mahaifiyarta saboda kumburi ba. Ita dai kada wani ya gansu tare duk masu tsoronta cikin abokan aikinta su rainata. "Innayo lafiya? Me yasa ki ka zo nan maimakon ki kirani a waya." "Wurin hakori zaki kaini Uwani. Kwana biyu ko runtsawa bana iyawa." Murya a sama sama Uwani ta ce "ni dai da kin kirani. Nan fa wurin aikina ne. Muna ta kokarin dakilar da neman alfarma da abokan aikinmu kan yiwa 'yan uwansu yanzu ni kuma zaki sani." "Nima ba alfarma nazo nema ba. Wurin za ki rakani sai ki kara min kudi saboda sayen magani da ganin likita. Mai adaidaita baki ga yadda ya cajeni ba ya cinye kusan rabin kudin komawa gida gashi na so biyawa duba Salima" Dariyar takaici Uwani tayi "Innayo kenan. Ki ce kudi ki ka zo karba. To ni wallahi haka na fito sikau don ko na man mota ma sai na ranta. Wata ya yi nisa." "Uwani" Innayo ta kalleta ido cikin ido wanda hakan ya dan razanata "idan nayi miki baki wallahil azimu sai ya biki. Na bi uwata har ta koma ga Allah. Don Ya jarabceni da haihuwarki ba zan butulce maSa ba. Ke dai ki kiyayi hudowar rana da faduwarta. Shiga ki kawo min kudin ganin likita shashashar banza." Tunda ta taso kusan yau ta taba jin Innayo tayi mata fada na gaske. Ranta a jagule ta koma ciki ta dauko dubu hudu ta kawo mata. Ita kuwa Innayo sai taji tsoron kar fushinta ya zama silar mummunan abu ya sami Uwanin. Fatan shiriya ta dinga yi mata a zuci da cewa ta yafe mata. Tana bata kudin ta ce "Allah Ya yi muku albarka Ya shirya min ku." Juyawa tayi ta tafi Uwanin ta biyota ta ce "koma bakin aikinki gida zan koma." Da yake bata da tunani sai ta koma tana fadawa kanta ai dai tayi nata kokarin. Innayo kuwa karkashin wata bishiya ta samu ta zauna ta kira Hasiya. A duke take kan Abbas yana amai amma ganin wayar ta Innayo ce ta amsa da sauri. "Hasiya" Sai kuka. Anti Hasiya bata san dalilin kukan mahaifiyarta ba amma tana jin kukan ita ma ta fara. "Innayo gani nan zuwa. Daina kukan. Me ya faru?" "Ki zo inda yayarku take aiki." "Gani nan" ta ce tana mikewa tsaye a gigice. (Uwa ta kira ki ta ce yi min kaza sai ki ji a ranki ta takuraki. Bata san uzurinki ba. Ko ta manta aure ki ke kina karkashin ikon wani? Allah Sarki...ita ma baki san uzurinta ba. Kila a wannan lokacin ke dai ce za ki iya kawo mata agaji. Kila kuma kulawarki take mararin samu. Kila kunya take so ki fitar da ita. Kila ajizancin da aka san dan Adam dashi ne ta gwada a kanki. Kila...Kila...ita dai uwa uwace ko da ta buzuzu ce.) Idan kin karanta wannan post din yau za ki biyani da dayan abu biyu rak. Ki kira mahaifiyarki ki gaisheta ki yi mata kyakkyawar addu'a taji dadi. Idan ta rigamu gidan gaskiya ki yi mata addu'a sannan ki hada da sadaka. She deserves the best you can offer! #UWAUWACEI just published "11" of my story "UWA UWACE...". https://my.w.tt/RpX6BXVbqab UWA UWACE...11 Batul Mamman💖 Astagfirullah wa atubu ilaika. La'ilaha Illa Anta Subhanaka Inni Kuntu Minazzalimeen. Allahumma Inna Nas'alukal Afeeya *** "Abu, Abu...KE ABU" Da dan karamin gudu Abu mai'aikin Zara ta shigo dakinta ta sami wuri ta dan durkusa. Kafin ma ta soma yi mata fadan da ta saba ta ce, "Ayi hakuri muna gyaran bangaren Hajiyan Fatakwal ne ban ji kiran da wuri ba." Maganar kuwa ta sake fusata Zara wadda ke zaune akan gado ta dora kafafu akan filo saboda taruwar jinin da suke yi "amma ai kin san yau ba girkina bane saboda haka ba aikin bangarena bane gyara mata wurin zama." Gyada kai Abu tayi bata ko mamakin halayyar uwardakinta yanzu. "Ayi hakuri dai. Na kamawa Gaji ne saboda baki da ...." Da hannu Zara ta dakatar da ita "ni ba surutu na tambayeki ba. Ga leda nan a kasa ki miko min." Da azama ta dauko ledar ta mika mata sannan ta fita daga dakin. Tana zuwa bangarensu na masu aiki suka tuntsire da dariya. Duk sun san bakar kyuya da son jiki irin na Haj. Zara. Ko kadan bata son motsa jikinta a dole ita matar Alhaji. Komai sai mai'aiki tayi mata. Ba komai bane dalilinta na yin haka illa son nesanta kanta da tunawa da asalinta. Ba za ta ce ga wani lokacin kirki da Innayo ke zama da suna gida. Kullum ita ce karshen bacci kuma farkon tashi kuma har yau bata huta ba. Ita kuwa za ta mori arzikin mijinta son rai. Ba don shi din ma ba mai son bada kudi bane da ta fi haka fantamawa. Tsarin Alh. Unais shi ne wadata iyali da duk kayan jindadin rayuwa amma kafin su ji kudi hannunsu sai a dade. Da yake amaryarta ta fito daga gidan arziki ko kadan bata damu ba. Ita kuma girman kai da gudun asali sun hanata nemawa mahaifiyarta agaji. Aurensu da wata biyu mahaifinsa ya fitar da zakka. Da kansa ya tambayeta idan babu laifi a bawa Innayo duk da ya kula ba wani damuwa tayi da ita ba. "Allah Ya sauwake. Sai kace almajira? Ko so ka ke 'yan uwanka su cigaba da raina ni?" Ta zauna a kusa dashi "don Allah kar ka taba karbar komai ka kai gidanmu. Idan zance ya zagayo ni ce darajata za ta zube a idanunsu." Haka take zaune duk abin da take so indai bai saya ba bata yarda ta tambaya. A haukanta duk ranar da ta tambaya zai zama kamar ta amince ita din 'yar talakawa ce. Wata rana zai iya goranta mata ko kishiya ko wani a danginsa. Ledar zazzage a gefenta ta karewa kayan ciki kallo. Turaruka ne da suka amsa sunayensu har guda goma. "Ga turaruka ki zabi biyar ko kuma ki zuba duka a akwatin zuwa asibitin. Bana so ko da wasa a dauki dana ace anji wani abu ba kamshi ba" Ta tuna kalaman Alh. Unais lokacin da ya ajiye ledar da zai fita kasuwa. Daya bayan daya tabi ta fesa domin tantance kamshinsu. Ta gama ta shafa cikinta tana murmushin jindadi. Sai yanzu a haihuwa ta shida da ake jira ko yau ko gobe likita ya tabbatar musu da cewa da namiji ne. 'Yan matanta biyar na kishiyarta uku. Alh. Unais ya kwallafa rai akan samun namiji. Tun cikin yana wata hudu da aka fada musu mene ne yake bata kulawa ta musamman. Babu abin da ta nema ta rasa. America ma yaso kaita haihuwa amma Hajiyar Fatakwal mahaifiyarsa ta hana. A cewarta lokaci ne na nunawa dangi ya sami magaji. Idan sun bar kasar dokin dan zai iya raguwa a zukatan dangi. Abubuwan alkhairin da Zara ta samu a tsukin lokacin ita kanta bata san adadinsu ba. Ga dan Adam da son idan yana cikin farinciki ko samuwa ya sami mai taya shi murna. 'Yan uwanta da ta wofintar take kewa sosai. Su take son burgewa su tayata murna amma da kunya ta fara binsu yanzu. Uwani ce dama suke mu'amala to ita kuma rokon tsiya gareta. Ga aiki ga albashi amma kullum kiran babu da tambayarta abubuwa take. Ba don taso ba ta tashi ta bude wasu akwatuna da suke shakare da sutura sababbi marasa dinki. Ciki harda na barka da take samu na haihuwa da kuma na wurin mijin da abokansa. Tunda hannunta a kame yake irin na Alh. Rabi'u ba kasafai take kyauta ba. Idan barka ta tashi kuma mijinta yana saya ya bata ta kai. Wasu lesuka ta dauko masu tsada amma wadanda aka ci yayinsu kimanin shekaru shida da suka wuce lokacin haihuwarta ta hudu. Komai na akwatin ma na barkar yarinyar ne wadda bayan haihuwarta tayi rashin lafiya. Shi yasa bata diddinka kayan sosai ba. Guda hudu ta zabo za ta bawa Innayo, Hasiya, Salima da Maimuna su dinka su saka ranar sunan danta. Tana zuba su a leda ta tuno bala'in Hasiya ta karo atampa daya za ta karawa Innayo da ita. A kalla babu mai rainasu wannan karon ba kamar sunan 'ya'yanta na baya ba. Haihuwa ta biyar da kanta ta ce musu babu taro don kawai kada a maimaita irin na da. Basu zo ba kuwa aka ci suna aka watse. Kowa ya yi cigiyar danginta sai ta ce Innayo ba lafiya. Wayarta ta janyo ta kira Uwani bayan ta kwanta saboda bata jurar aiki. Lokacin kusan rabin awa kenan da rabuwar Innayo da Uwanin a cikin asibitinsu. Ranta duk a jagule saboda rashin nutsuwar da ta saukar mata sakamakon rashin kyautatawa mahaifiyarta. Ganin wayar Zara sai ta saki ranta ta dauka da murmushi. "Haj. Zara ikon Allah. Matar Alh. Unais uwar Maryama." Zara ta murmusa "duk ni kadai Yaya Uwani?" "Kin isa ne kanwata." Uwani ta saba yi mata bambadanci saboda kwadayin samun wani abu a jikinta bata san irin zaman da take ba. "To ni dai ya ku ke?" "Lafiya kalau. Muna nan zamu fara shirye shiryen tafiya Saudiyya. Allah Ya yi Hajjin bana mun amsa kira." Dan yamutsa fuska Zara tayi saboda bata son yawan surutu kuma ta san shi Uwanin zata yi mata. "Na tayaki murna. Allah Yasa ayi maqabuliya." Uwani ta murmusa amma da dukkan gaskiyarta ta ce "Amin. Zan zo karbar 'yan riyalan da ku ke dawowa dasu dai." "Hala kin manta na fada miki watan nan zan haihu?" Jin kamar ranta ya baci Uwani ta kwantar da murya tana tambayarta lafiyarta. Basu dade ba fushin ya gushe Zara ta labarta mata tanadin da maigidan yake yiwa haihuwarta. "A Afficent za ayi suna. Ya biya kudi ko da sunan ya kama rana daya da masu biki zai biyasu kuma ya kama musu wani wurin. Ni abin da yasa na kira ki dama kaya ne za ki zo ki karbarwa su Innayo" Fadin maganar ya yi daidai da shigowar Hajiyan Fatakwal falon Zara. Isowarta garin kenan ta taho bangarenta ta duba ta taji tana waya. Zama tayi a kujerar da tafi kusa da kofar dakin tana dan danna kafafunta da zummar jira ta kammala. "Bana so wannan karon su zo a tsummokara ayi ta kallonsu." Uwani tayi 'yar dariyar kalmar tsummokara sannan ta fada mata zuwan Innayo din asibitinsu. "Wai ciwon hakori take kuma na ce muje a duba taki." "Kar ma ki damu indai ciwon hakori ne da kanta za ta nemeki. Ba ma dole su yi ciwo ba. Ni kaina wallahi ina kyamar kalar hakoran nan nata." Zara ta fada tana bata rai. "Kin san da ciwon sai da ta karbi dubu hudu a hannuna. 'Yan gulmar abokan aikina suka dinga tambayar wace na bawa kudi ni kuwa na ce matar makocinmu." Haushi ya kama Zara. Ko me yasa Innayo ta auri mutum irin mahaifinsu bata sani ba. Hatta sauran 'yan uwanta tana bakincikin yadda suka auri talakawa. Ba dole su lalace ba. Ace maza ba za su fita su nema yadda masu kudi suke yi ba. Kalaman Uwani basu dameta ba bare su bata mata rai. "Ni dai ki zo ki karbar musu su dinka da wuri don wallahi INA JIN KUNYAR NUNA INNAYO A MATSAYIN MAHAIFIYATA. Duk ta tsufa fiye da shekarunta. Rannan da muka je da su Maryam fa tana kiransu kin zuwa suka yi. Da muka fito Mas'uda harda amai kuma duk akan fatar jikinta da kalar hakora. Daki sai wani bashi bashi ni kaina da kyar na dinga hadiyar yawu." Hajiyan Fatakwal mamaki kamar ya kasheta a zaune. Tuni ta manta da matsar kafa ta kasa kunne da kyau tana ji. Kalaman karshen ne suka tunzurata ta tashi ba shiri ta bankada labulen dakin ta shiga. Ba shiri Zara ta katse wayar ta tashi tarbarta harda su runguma. "A'a kar ki kuskura ki tabani" cewar Hajiyan Fatakwal tana ja da baya "ina naga mutumcin da zai sa ki kaunaceni da zuciya daya tunda ki ke kunyar nuna uwar da ta haifeki." Baki daya jikin Zara sai ya hau rawa. Hajiyan Fatakwal kuwa ta dinga surfa mata ruwan bala'i. "Da wannan mummunar zuciyar a kirjinki ki ke haifa min jikoki? Wannan ba don nima a tsaye nake ba kila da Unais ne zai ce shi ma yana kunyar nuna ni." "Hajiya don Allah ki yi hakuri" Zara ta furta a hankali tana kuka. Kukan tsoron kada surukarta ta tsaneta ko tayi mata iyaka da daular gidan. "Wa? Ni? Ai ba ni zaki bawa hakuri ba." Ficewa tayi tana mamakin wannan abu. Ka haifi da a cikinka ya dinga cewa yana kunyar kasancewarka uwa gareshi. Tabbas ta sani wasu iyaye matan suna abin da zai sa 'ya'yansu gudunsu musamman hali mara kyau. Amma wannan fa zancen kalar hakori da yamushewar fata take yi. Bangaren da take zama idan ta zo gidan ta tafi tana ta juya zancen a zuci. *** Anti Hasiya ta tarar da Innayo ba yadda take saboda ciwo. A daidaita sahun da ta shigo ko tsayuwa bai gama ba ta diro saboda sauri. "Hajiya kudinki dari biyar." Sai a lokacin ta ankare da yadda ta fito daga ita sai waya babu jaka. Salati ta soma yi shi kuwa zai fara tijara Innayo ta taso da kyar ta mika masa dubu daya cikin kudin da Uwani ta bata. Chanji ya mika musu ya tafi yana surutan samari marasa kunya. Ido cike da kwallar kumburin fuskar Innayo Anti Hasiya ta ce "Da kudi a hannunki ne? Na manto jakata garin sauri." Abin da take dashi ta nuna mata sai Anti Hasiyan ta ce bari ta kira Uwani tazo. "Kyaleta Hasiya. Bana ma son ganin likitan a wannan asibitin." Anti Hasiya bata matsa mata ba ta ce "to bari na ranci kudi a wurinta sai mu wuce asibitin Nasarawa." Suna haka sai ga wayar Honorable ya kira ya fada mata ta manta jaka. Da ta gaya masa halin da Innayo take ciki ya ce zai turo Ayaah ta kawo mata tunda asibiti dole sai da kudi. "Ka ce ta wuce Nasarawa sai mu hadu a can" Sai da ta gama wayar ta tambayi Innayo me Uwani tayi mata ganin har lokacin tana kwalla. Da kyar ta iya fada mata tana zubar da hawaye. Zuciya na zafi ta juya ta tambayi wani hanyar wurin karbar haihuwa ya nuna mata. Innayo na kiranta taki tsayawa. Salama tayi a wurin ko amsawa ba ayi ba ta banka kai ciki. "Uwani Rabi'u nake nema" ta ce da wata 'yar matashiyar Nos a hasale. Teburin nurses din take duka da hannunta irin na wanda hakuri ya yiwa karanci "Metron Uwani tana break sai anjima za ta fito." Anti Hasiya kawai sai ta daga murya "Uwani Rabi'u. Uwani..." Shiru tayi bayan katse wayarsu da Zara tayi tana son gaskata ita ake yiwa wannan kiran na rashin girmamawa ko kuwa. "Uwani..." 'Kamar Hasiya' Da sauri ta fito ai kuwa ta hango Hasiyan ta hade girar sama da ta kasa. Take takenta ta san indai ta kyaleta sai ta zubar mata da mutumci a wurin. Ga abokan aikinta sun firfito jin gulma. "Muje waje Hasiya" ta kama hannunta za ta ja ta taji ta coge. "Ba inda zani. Kudi za ki bani na kai Innayo asibiti." Daure fuska tayi saboda ta san cewa ta bawa Innayo kudi ita ma Hasiyan sarkin nuna tafi kowa jinkai ba sai ta kawo ba. "Wata ya yi nisa ba..." Da yatsa Anti Hasiya ta nunata "wallahi ki ka kira min babu sai na tara miki mutane a wurin nan." Kirjinta ta nuna tana kokarin danne fushinta kada su yi fada a wurin "Hasiya ni fa yayarki ce." "Indai ke yayata ce to lallai Munzali (sakonta ne a haihuwa) da su Fati (wadanda suka hada uwa da marigayiya A'i ma yayyena ne)" ta kare maganarta da jan tsaki mai sauti. Kasa kasa da murya Uwani tayi, dan kada a ji. Ta kula gaba daya yawancin abokan aikin kamar su matso inda suke dan tsabar son jin gulma. "Ni kike gayawa magana Hasiya?" Hasiya ta ce "dake nake Uwani. Kinga ki dauko kudi ki bani na kai Innayo asibiti idan kuma ba za ki bayar ba sai na ranta a wurin abokan aikin ki." Uwani na jin haka ta sha jinin jikinta dan ta san ba ko shakka wannan ba karamin aikin Hasiya bane aikata abun da ta fada. Da sauri ta dauko jakarta, ta zaro dubu biyar ta mika mata. Hasiya ta karba ta jujjuya su cike da takaicin hali irin na yayarta. "Indai dubu biyar ce nima ina da abin da ya fita, don na yi fitowar gaggawa ba na manto jakata a gida. Ki bani dubu goma, da zarar na koma gida zan aiko miki kudin ki in sha Allahu." Haka Uwani ba yadda ta iya ta zaro wasu biyar din ta bawa Hasiya, tana so ta jaddada mata ita bashi ta bayar ba kyauta bane, amma kuma tana tsoron ta tabo Hasiya kada tayi mata tsiya a gurin nan. Haka nan ta hakura ta hadiye zancen a ranta ta juya da niyyar barin wurin. Batayi taku uku ba Hasiya ta kasa hakuri da wannan halin ko in kulan nata. Sautin muryarta a karye ta ce mata "Yanzu Uwani ba za ki zo ki ko kallon halin da take ciki kiyi ba?" Kafin ta bata amsa ta fice abinta ta nufi inda ta baro Innayo. Wasu a cikin abokan aikin Uwanin har sun riga su yin gaba, suna kallon inda Hasiya ta nufa suka ga ta riko Innayo nan suka fara kuskus. Daya daga cikin su wacce Innayo ta fara tambayar Uwani lokacin da ta zo asibitin ta ce, "A'a wannan ba matar nan bace ta dazu da ta zo neman Metron Uwani?" Hasiya ta juyo ta kalle ta, ta ce "mata kuma? Ita matron din taku bata gaya muku alakar su ba kenan." Uwani ta cika tayi fam, ranta ya gama kai kololuwa wurin baci. Shike nan an kwaye mata baya a idon makiya. Ita ko Nos da zakuwa ta tce "a'a bata fada mana ba." Hasiya ta dubi Innayo taga kiris ya rage ta fashe da kuka. Girgiza mata kai take yi don tayi shiru gami da yafito ta da hannu tazo su tafi. "Ba ma tafi ba Innayo ga abokan aikin 'yarki suna son saninki" ta matsa jikin Innayo din ta dafa kafadarta "ga MAHAIFIYARMU. Uwani yayata ce uwa daya uba daya." "Ban gane ba fa. Ke da wa kenan?" Daya daga cikinsu tai mata tambayar cike da mamaki. Hasiya ta ce "ni da matron din ta ku mana." Ta cuna Uwani da baki. Ta juya tai tafiyar ta. Nan ko wuri ya kaure da salallami, suna tafa hannuwa,mata an samu abun da ake so. Hasiya na tafiya daya ta yiwa Uwani kallon mara hankali duk da kasa take da ita. " Matron kika ce mana matar makocinku ce." Innalillahi wa inna ilaihir raji'un ta iya cewa a zuci saboda kallon mujiyar da wanda ya isa da wanda bai isa ba ke jifanta dashi. Su kuwa juyawa suka yi kan ka ce meye wannan kusan kowa ya samu labarin abin da ta yiwa mahaifiyarta. Wadanda suka ga Innayo cikinsu sun fahimci bata son asan cewa mahaifiyarta ce duba da yadda take. k Kana ganinta kaga mutum dake fama da talauci daga yanayin jiki har sutura. Hasiya kuwa kai tsaye asibitin Nasarawa ta dauke ta suka wuce. A take aka cire mata turame biyun dake azabtar da ita. Anyi mata allurai an kuma bata magunguna. Har suka kammala suka koma gidan can Dala babu Ayaah babu dalilinta ballantana ta kawo mata jakarta da ta manta a gida. Kunun gyada mai dadi Hasiya ta dama mata ta sha da kyar. "Ki barni haka ya isa" Innayo ta ture cokalin da ta kawo bakinta. Tayi kicin kicin da fuska kuwa. "Allah sai kin kara." Sai kuma ta soma mita "Haka kawai kina fama da ciwo ki kasa fada min?" "Da ki ka zo din me ki ka yi banda kunyata 'yar uwarki? Na dauka kin fi kowa jin maganata amma ina...kina kallo ina cewa kizo mu tafi ki ka ki sai da ki ka amayar da cikinki. Mece ce ribarki?" Hasiya ta saki murmushi "ai kuwa ni ce da riba. Yau an yi jana'izar girman kan Matron Uwani a Sir Sunusi." Sai kuma ta yi dariya ganin Innayo tana murmushi "banda abinki ma dai Innayo meye na damuwa. Ni da nake son ki bani hadin kai mu fara bincike." Sai da ta kashingida akan gadon da autar tata ta karkarde ta gyara sannan ta ce "na me?" "Neman 'yarki ta fari. Ina tsammanin wannan Uwanin dai musanyen asibiti ce." "Kaniyarki" Fadin Innayo tana son yin dariya ciwo ya hana. A cikin zuciyarta ta dinga rokawa Hasiya albarka tare da fatan ganin zuri'arta. A gefe daya kuwa kukan zuci take yi. Bata san da me ta ragi Uwani da Zara ba da suke gudunta saboda arziki. Ashe wahalar duk da tayi daga ciki har aurar dasu aikin banza ne? Ita Uwani ke kunyar nunawa duniya. Akwai Allah! *** Irin kwalliyar da Ayaah ta sha ta zuwa asibiti kai jaka sai ka rantse gidan biki zata je. Bikin ma na masu kumbar susa ko 'yan karya. Idan ka ganta ba za ka ce tana tare da damuwar rabuwa da masoyinta Rabeel ba. Ga haushin Babansu ya rasa wanda zai aika kai kodaddiyar jakar Anti Hasiya sai ita. "Idan nayi aure naga mai iko dani sama da mijina" ta fadawa kanta ta. Tun fitowarta wani saurayi da ake kira Dangwarzo da suke harka dasu Rabilu ya kira Danliti a waya. Dama a sanadiyarsa Rabilun ya hadu da Ayaah duk da bata taba sani ba. "Malama Ayaah sai ina" ya ce bayan ya iso kusa da ita. Yatsina fuska tayi tana fatan kada Allah Ya kawo wanda ya santa ya gansu tare. Ta tsani Dangwarzo tsana mai girma. "Sai inda ka aikeni." "Maida wukar ba fada ya kawoni ba. Saukata kenan daga adaidaita na hango ki." Ya nuno mata wani cikin abokansu zaune a cikin dan sahu yana tazar kai "idan sauri kike ki shiga wancan abokina ne direban ba sai kin biya ba." Kamar ta ce a'a sai kuma ta tuna ya ce ba sai ta biya ba. Tana faman rangwada da zuba kamshi taje ta shige ta fada masa inda zai kaita. Tafiyar minti biyar suka yi ya kira waya yana maganar da bata fahimta ba. Ita dai taji ya ce 'asibitin nasarawa' sai kuma 'idan ciniki ya fada nima zan zo d'ani '. Danliti ya yi matukar murnar samun biyan bukata wato samun damar ganawa da Ayaah. Motar da tafi kowacce kyau a garejinsu ya dauka ya canja kaya zuwa jampa da wando da ya aro a wurin wanki. Ogansa bai san ya fita da mota ba sabòda girman garejin. Sun kusa zuwa junction din Dan agundi direban ya dinga taka burki da gangan kamar adaidaita sahun yana da matsala. Ayaah son bati maimakon ta fita ta tari wani sai tayi zamanta. Direban ya fita yana ta 'yan kwale kwalensa nan kuwa Danliti yake jira. Haushi ya fara kama Ayaah saboda wayar Honorable yana tambayar ko ta sami su Hasiya. Mata duk tabi ta asirce musu uba ya tada hankalin kamar tashi babar ce babu lafiya. Gajiya tayi ta fito bayan kamar minti ashirin daidai da dosowar wata mota da ta dauke mata ido da hankali. Danliti ya rage motar ya tsaya a gefensu ya sauke gilas. Kansa babu hula amma ya taje sumar da ya dan tara ta kwanta. Ta bi fuskarsa da kallo taji gabanta ya doka. Wannan yafi Rabeel kyau. A nutse ta gangara jikinsa da ido ta karewa yadin da ya saka kallo. "Malam don Allah kwanar Wanzamai nake nema a sabuwar kofa." Danliti ya yi kamar bai ganta ba ya tambayi direban. Da baki ya yi masa kwatancen karya saboda babu wata kwanar Wanzamai ya ce bai gane ba. "Ni kuma mashin din nawa ya sami matsala ga fasinja ma ban san yadda zan yi da ita ba." Sai a lokacin Danliti ya kalli Ayaah. Da gaske ta hadu yadda yake son ganin mace. Kawar da kai ya yi ya ce tazo ya rage mata hanya idan hanyarsu daya. "Malam ita fa wannan asibitin nasarawa za ta je." "Sai na sami lada ko 'yan mata?" Sai a lokacin ya kalli idonta kuma ya yi mata murmushi. Ayaah ta nemi hankalinta ta rasa. Gabadaya zuciyarta ta tafi wurin Danliti har tana hango 'yan dagwai dagwai dinsu suna wasan tsere a idanunta. Ta manta da Anti Hasiya bare jakarta da ta bari a adaidaita sahun. Jiki na rawa ta shiga gaban motar ta zauna. *** Su hudu ne a falon kowa da abin da ya saka a gaba. Mami Khadija ta dinga bin su daidai da kallo tana rayawa a ranta daga yau sai yau anyi an gama. Tunda Mamanta ta amince da kudurinta ba za ta taba yarda shawarar zaman hakuri tayi tasiri a kanta ba. Alh. Tahir ne ya tara matansa a gabansa amma tunda suka shigo yake danna waya yana doka murmushi. Mami Khadija za ta iya rantsuwa da wata budurwar yake chatting. Nasima da waya ta shigo a kunne har yanzu bata gama ba. Zancen shiga da fitar kaya ne sai kudaden da suka shafi kasuwancinta. Jiddo ma selfie take ta kashewa tana dariya idan ta tura. Ko wa take turawa Allah Masani. Mami Khadija ta girgiza kai. Wannan ba gidan aure bane. Za dai ta zauna har ya gama ya yi musu maganar da yasa ya tarasu.I just published "12" of my story "UWA UWACE...". https://my.w.tt/w5mYwrfiGab UWA UWACE...12 Batul Mamman 💖 Godiya ta musamman ga duk masu comment a kafafen da nake dora labarin nan. Allah Yasa mu cigaba da karuwa da alkhairin dake cikin labarin Ya yafe mana kurakuran dake ciki. Amin *** Abin ba na kare bane. Awa guda cur ta kusa rufuwa amma har yanzu Alh. Tahir bai yiwa matansa da ya tara a falonsa maganar da ta sanya ya tarasu ba. Mami Khadija ta gaji da kallon fuskokinsu ta mike tsaye. Hanyar kofa da ta nufa ne ya dawo dashi daga duniyar jindadin zafafan kalaman da yarinyar da suke chatting take aiko masa. "Mami ina zuwa?" ya yi maganar da kokarin saita hankalinsa gareta. Amsarta takaitacciya ce gareshi don bata son fallasa kanta a gaban matansa. "Dakina." Ya dan ji kunyar abin da ya yi da ya kula da lokaci. "Ayi hakuri Mamin yara yanzu zan sallameku, dawo ki zauna." Fuskarta babu yabo babu fallasa ta dawo inda ta tashi ta kuma zama. Alh. Tahir mai neman hanyar kawar da fushin da ya san kokarin dannewa take yi sai ya tambayeta uzurin da zai mayar da ita daki da wuri. "Hada kaya muke yi ni da yara." Da murmushi ya ce "Ina mamakin yadda ake wani lokacin tunaninmu ke zuwa daya. Nima zancen da nake son yi muku kenan. Ga wannan kowa ta dauki daya." Ya karashe maganarsa tare da zube mukullai guda uku akan teburin gabansa. Anti Jiddo da Mama Nasima ne kadai suka dauka. Mama Nasiman tana kai hannu tana magana kasa kasa amma yadda ta san kowa zai ji. "Ba dole ku dinga tunani iri daya ba tunda bokanta ya buga ya sanar da ita." "Ke Nasima!" Alh. Tahir ya yi mata tsawar da tasa ta sakin mukullin da ta dauka "Khadija sa'arki ce ko me? Wato wuyanki ya yi kauri ko? Ki bar ganin ina kyaleki wallahi ba zan zuba ido ki rainata ba." Ta baya ta rago shi ne abin da kalamansa suka sanya Mami Khadija fadi a zuci. Waye ya bayar da wannan kofar sama da shi? Shi yake nunawa matansa cewa wadanda suka tarar a gidan basu da kima a idanunsa ta hanyar nemansu a waje. Bata taba kulasu dai saboda babu sa'ar yinta a shekaru, ilimi da wayewa. Jiya ma fada sosai ta yiwa su Farha akan rashin kunyar da suka yiwa Mama Nasiman a shagonta. "Idan baku raga mata don darajar tana auren mahaifinku ba ai kwa kyautata mata a matsayin mahaifiyar Mardiyya. Har abada bana fatan abin da zai zo ya raba kawunanku da kanwarku. Ta taso da kaunarku da girmamani shi ne ku kuma don rashin kunya zaku dinga fadawa mahaifiyarta magana akan idonta? Uwa uwa ce fa. Baku san abin da kuke yi zai iya tunzurata ta koma bin umarninta ko da ya sabawa addini da dabi'a ba? Ku tashi ku je dakinta ku bata hakuri." Lilu da Farha ta bawa wannan umarnin. Suka tashi suna kunkuni gami da hararar Suhaib da ya kawo kararsu. Zuwan nasu da bada hakurin bai canja komai na tsanarsu a zuciyar Mama Nasima ba. Mardiyya kuwa sai ta kara kaunarsu a ranta har ta dinga doka murmushi. Farha sai taji dadi ita ma. Lilu kuwa tana biyo bayansu ya shiga tsokanarta domin ya kara wanke laifinsu. Da hannuwansa duka biyu yake wasa da kumatunta. "An Mardiyya, Mardiyya. Kamota nan kamota nan." Ai kuwa ta kwashe da dariya sannan suka taru shi da ita suna bin Farha tana gudu. "Kamota nan, kamota nan.." Da Alh. Tahir ya shigo ya gansu sun hade su hudu suna bin Suhaib har wata guntuwar kwallar farinciki ya yi. Yana son su, yana kaunarsu. Su ne mafi girman arzikinsa a duniya. * "Mukullan na meye ne?" Anti Jiddo ta katse fadan nasa saboda tana son tashi. Gasar tura hotuna da shigar kece raini ake yi a wani group dinsu na whatsapp. Gabadaya ta rikice tana gudun idan bata tura da wuri ba za a iya zargin bata kai matsayin zaman group din ba. "Na dakunanku ne a sabon gidan. Kowacce bangaren da mukullinta ya bude shi ne nata. Ku fara shiri ranar Juma'a zamu tashi. Kuna da kwana uku na packing." Ya tashi zai fita saboda karar text da ya shigo wayarsa yana saurin zuwa ya bude yaji saukar mukulli akan centre table din. Dan wigowa ya yi sai yaga Mami Khadija ce ta ajiye nata. "Ina son magana da kai." Yadda Anti Jiddo da Mama Nasima suka ci burki sai ka rantse cewa tayi ina son magana daku. Alh. Tahir ya mayar da wayar da har ya zaro daga aljihu ya bude sakon. Baya son rigima shi yasa ya zube musu mukullai amma indai wani bangare take so a ranta zai bata dama. Ta cancanci fiye da haka ma. "Ku kawo mukullan. Idan munje sai a zaba. A fara ta kan babba." "Bar musu kayansu." Tsayuwa ya yi da kyau yana kallonta "to ki dauki naki mana." "Ba zan dauka ba. Maganar da ta kawoni kenan. Na gama gini kayi min izini na koma can tare da yara ko kuma ka sauwake min. Duk wanda ka zaba dai a ciki zan koma gidana ne." Ta ce a hasale ganin ya sake kai hannu ya shafo wayarsa da wani sakon ya sake shigowa. 'Yan mintuna kalilan din da take nema ma ba zai iya bata ba saboda matan titi. Kalamanta sun saukar masa kamar dirar aradu ne. Ba shiri ya mayar da wayar. Hajiyoyin gulma suka dawo abinsu kowacce tana ayyana idan Mami Khadija ta fita zata jidadin korar 'yar uwarta. "Wace irin magana ce wannan Khadija? Kina cikin hankalinki kuwa." Bata zauna ba. Zuciyarta ke tunkudarta akan ta amayar da bacin ranta a yau ko zata ji sauki. Abubuwan da suka yi ta faruwa shekara da shekaru suka dinga dawo mata. Mafi muni a cikinsu bai wuce yadda mijinta ya shafawa idanunsa toka yake tozarta addinin musulunci ba. Haram haram ce babu ruwanta da jinsi. To akan me za a dinga yiwa maza uzuri akan zina? Sabon Allah ne fa! "Duk abin da ka dauka game da hankalina daidai ne. Zaman gidanka ne na gama." Ya kankace idanu da mugun bacin rai "saboda ke butulu ce? Sai yau, washe garin ranar da ki ke ganin kin sami duniya za ki fito da wannan maganar? Me ma aka yi miki?" Rashin kunyarsa bata bata mamaki ba tunda ance zina tana daukewa dan Adam kunya. "Wanda ka yi min na yafe amma bari na tuna maka kadan a cikinsu. Ka ha'inceni. Ka cutar da lafiyata. Kaci amanata. Lalura ta sameni a rasa mai zabar min abin da ya dace sai wadda na kama ka akan gado da ita? Wannan wulakancin yafi komai yi min ciwo. Ni Nasima tasa aka cirewa mahaifa." Idanu jazur ta kalli Mama Nasiman "da yake Ubangijina adalin sarki ne sai ya barki da taki mahaifar Ya kuma hana wani dan kwanciya a ciki. Gashi nan da bakinsa yake fada min asibitoci da kudaden da ku ke kashewa wurin neman haihuwa." A haukace Mama Nasima ta kalli Alh. Tahir ranta a bace. Ta yaya zai dinga fallasa sirrinta a wurin matarsa. Ga wata shewa da Anti Jiddo tayi tana tafa hannaye. Ita kam a bangarenta komai zam. Duk su bar mata gidan ta ci karenta ba babbaka. Tashin masifar Mama Nasima ko dis bai shiga kunnuwan Alh. Tahir ba. Zantukan Mami Khadija ne suke kai kawo a kowanne sassa na jikinsa. Don yana bin mata sai me? Mata nawa ne zaune da maza irinsa? Wasu ma kannensu ciki daya mazajensu suke bi kuma ayi sulhu a zauna lafiya. "Meye ban miki ba Khadija? Wace irin kyautatawa ce ban yi miki ba a tsayin rayuwar aurenmu? Karatun da kike son fara yi min takama dashi waye sila?" Ba taso ya ga rauninta ba amma hawaye ne suka balle mata. Yau daya ta daga muryarta sama da ta mijinta. Ta gaji da hakurin gaibu. Babu abin da kokarinta a kansa ya haifar na canji sai kara tabarbarewa. "Kai har kana da bakin goranta min akan abin da kayi min? Ni da aka datsewa farinciki aka rabani da masoyina saboda ana neman shiriyarka in ce me? Kamar yadda mahaifiyata ta yiwa Baba biyayya ta amince da aurenmu haka nima na dinga yi maka. Ni ce shan banza da hofi duk domin ka sami gamsuwar da za ta rabaka da matan titi. Wani abin na sha na kwana na wuni gudawa, wani ya kulle min ciki, wani ya sani jiri amma duk a banza. Har yau ban dace da maganin infection ba saboda zama da kai. Ban gajiya da zuwa kunshi da gyaran kai saboda ance idan na dage da kwalliya zan karkato da kanka. Kai kanka ka sani babu irin kwalliyar da bana yi maka. Ka tara min abokanka nayi ta dora tukunya ina saukewa bana nuna maka gajiyata. Ladabi da biyayya har bayan na kama ka da mai aikina ban daina ba. WALLAHI MAZA IRINKA SUNA DAGA CIKIN MASU KAI MATANSU WUTA. Ba don kariyar Allah ba da tuni na dade da fara gurfana gaban malaman tsibbu ina karbo asiri. Kuma duk da na dade da kudurin barinka amma wallahi inata kyautata maka zato. Fatana ka shiryu mu cigaba da rayuwa da 'ya'yanmu har karshen rayuwarmu. Haba TAHIR! Idan ka tsarkake kan ka daga dattin zina ba Khadija ka yiwa ba. Bani da wuta da aljanna. Kanka kadai za ka taimaka da 'ya'yan da kake ikirarin so. Su ne nake jiyewa kada hakkin alfasharka ya fara bibiya." Zuwa yanzu fuskar Alh. Tahir a tamke take baya ma gani da kyau. Wai shi matar da yake kokarin ganin ta tsallake kowa a matsayi da mukami ce take gasawa maganganu haka. Da ya rasa abin cewa sai ya yi mata tambayar da yayi nadamar yi saboda amsar da ta soma bashi. "Duk wata nasara ta rayuwarki ba a jikina ki ka samu ba?" Shekeke ta kalle shi har lokacin idanunta suna zubar da hawaye "nasara? Dama akwai nasara a auren wanda baya tsoron Allah? In dai auren irinka nasara ce ga mata to ina fata Allah Ya hada 'ya'yanka da maza irin..." "Kina hauka ne?" Ya ce da dukkan karfinsa. Sannan ya dauketa da mari, wani abu da bai taba shiga tsakaninsu ba. Idanunta sun rine da bakinciki shi kuma da bacin rai. Da ya barta ko kadan bata da niyyar karasa addu'ar ita ma. Ko ba ita ta haifesu ba ba za ta musu wannan addu'ar ba. Marin bai sakata kuka ba sai dariya. "Ashe dai kana sane ka ke take sanin. Da na dauka kallon waliyyai ka ke yiwa masu halinka shi ne zan rokawa zuri'arka" Da dan allinsa ya nunata cikin fushi yana kumfar baka "ya isheki haka nan. Kuma babu inda zaki je. Ki hada kayanki jibi zan turo mota." Ya karashe a kufule. "Idan ta kama na kaika kotu ne zan kai ka. Babu wani dalili na shari'a da ya ce wajibi ne zama da kai." Nan yaji zuciyarsa ta dan girgiza. Dama ta fada ne don ta tayar masa da hankali. A daidai lokacin kuma waya ta shigo masa a wadda tun dazu ake turo masa sako. Wayar taki tsahirtawa duk da anji bai dauka ba. A kira na hudu yana faman babatun nuna mata wajibcin bin sa tunda shi ne namiji ya amsa kiran da sauri. "Zan kira ki...ka anjima" Bai ankara ba Mami Khadija ta warce wayar daga hannunsa. Katse kiran tayi da rawar hannu duk jikinta yana tsuma. Ace har a wannan matakin akwai wata tsagera a waje da ba zai iya hakura da bacin ranta ya shawo kan iyalinsa ba. Ta sake jin alamun shigar sako a lokacin da ya hayayyako mata da fadan ta bashi wayarsa. Daga Anti Jiddo har Mama Nasima sun kula da yanayin tsoratar da ya yi. "Ki bani wayata na ce." Bata saurare shi ba sai hannu da ta daga masa tana yi masa alamar ya dakata daga matsowa kusa da ita. Da daya hannun ta bude bangaren sakonnin whatsapp wanda ta tabbatar dashi suke hirar. (Mr Rufus) Ta gani a sama alamun shi ne wanda ya turo sako mafi kusa da lokacin da suke ciki. Da kyar ta mallaki nutsuwarta ta bude. "Khadija, Manzon Allah SAW ya ce wata tajassasu" ya fada muryarsa na karyewa. "Ya kuma isar da sakon Allah SWT da Ya ce Wala taqrabuzzina." (Gasu nan su tayaka bacci yau. Idan kuma dattijan gidanka sun barka fitowa ka tsaya a bayan layinmu ka daukeni.) Shi ne abin da aka rubuta na karshe Mami Khadija bata so bude hotonan da suka fara bata tsoro ba tun a haka ma sai dai biyun da ya bude a sama sun kadata. A guje ta bude daya ta dago kai ta kalle shi a sanyaye. She felt disappointed. Lalacewar tasa har ta kai nan? Me yasa maza masu wannan halayyar basa tsoron Allah ne? Ina hakki zai kai su? Mika masa wayar tayi jikinta a sake "Yumna? Yumna aminiyar Farha. Tahir ita ma baka bari ba? Ita kadai da iyayenta suka mallaka sai da ka lalata musu 'ya? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un." Fita tayi ko gabanta bata gani da kyau tana jiyo hayaniyarsa da amarensa. *** "Daddy ni Papa ne zai bani." Cewar wata karamar yarinya da bature ke yiwa lakabi da cute. Duka duka bata fi shekara biyar ba. Tana sanye da kayan bacci riga da wando na cotton. Kanta sabon kitso ne yiri-yiri anyi mata shuku biyu hagu da dama. Ko a haka ka kalleta sai ta shiga ranka balle idan surutunta ya hadaku. Bata da haske sosai kamar mahaifiyarta domin Munzali ya dan fi ta haske ma. Amma akwai idanu dara dara da dan karamin baki daidai fuskarta. Hancinta yana da dan tsini kamar na Munzali. Rike take da plate din indomie da kwai wanda mai girkin gidan Audu ya dafa. Daga bakin kofar kawataccen wurin cin abincin (dinning area) a tsaye Iya Kande ce dattijuwar dake kula da ita. "Daddy ka kira min Papa pleaseeee." Munzali ya dora hannu a ka kamar ya yi ihu. Kwata kwata ta hana shi baccin safe ga gajiyar da suka kwaso jiya. Kuma suna isowa Kano suka wuce gidansu Zakiyya mahaifiyarta suka daukota. Dama ita ma ta sani indai Munzalin na gari a gidansa Qibdiyya take zama ko lokacin makaranta ne su suke kaita. Bai yarda rabuwar auren ta kawo gibi tsakaninsa da ita ba. Yanzu breakfast suka zo yi karfe bakwai da 'yan mintuna saboda sammakon tashin da tayi amma take yi masa rigimar sai ya kira Abbati. "Papa bacci yake yi idan ya tashi zai shigo. Ki ci wannan sai a sake dafa miki wani abincin idan ya zo." Ya ce da sigar lallashi. Noke kafada tayi "ni dai a'a. Iya ta bude min kofa naje wurinsa." Ransa ya soma baci ya zaro mata ido "zan zaneki fa Qibdiyya. Ki zauna ki ci abincin nan nace kafin ya tashi." Sai kawai ta fashe da kuka kamar dukanta ya yi "Daddy sorry. Daddy ka ce ka hakura. Daddy..." "Na hakura" ya ce a kagauce da gajiyar magiyarta "zauna ki ci." "Kayi dariya" "Hihihi" ya yi yak'e kansa na sarawa. Gadonsa yake muradin hayewa ya nutse cikin lallausan bedsheet.... Murmushinta tayi masa jin ya hakura don ita bata son ana fushi da ita "yauwa Daddy to in dauko maka waya ka kira Papana? Pleaaasee" Ido ya tsura mata ya saki murmushin da bai yi niyya ba. Tana tsaye a gabansa tana rangwada kai gefe da gefe. Duk wanda ya san Qibdiyya zai shaida manyance da tsantsar wayonta. Idan ma akwai tashi a hannun kaka wato Gwaggo Lami kanwar Asabe harda halinta. Wani abin idan tayi shekara goma ko ma fi za ka bata. "Daddyna please fa nake ta cewa" ta dan turo baki alamar gajiyawa. Daukota ya yi ya dorata a cinyarsa "ki zo na baki don Allah ki ci mu je mu kwanta." Ita ma hakurinta ya kare tana ganin ba za ta sami abin da take so ba. Tafi son kwana a gidan Abbati amma tun bayan ya tura Hanne Kirikasamma sai ya ce ta dinga kwana a gidan Munzali tare da Iya Kande. "Ni Papa. Papanaaaa" Tun Munzali da Iya na rarrashi har ya koma fada. Bata yi shiru ba sai ciwon kai da ta kara masa. Wayarsa ya tashi ya dauko ya kira Abbati ba shiri. * Tun farkon kwanciyarsa har bayan asuba da ya koma bacci mafarkin Farha yake yi. Sunanta kuwa ya ambata a mafarkin da kuma a farke yafi a kirga. Wayar Munzali ce ta tashe shi ya yi guntun tsaki. "Idan na shigo sai ranka ya baci. Ka san me ka katse min da wannan wayar kuwa?" "Ba matsala duk abin da zaka yi na shirya in dai za ka dauki 'yarka. Yadda ka san in yi bacci a zaune amma kamar da gangan ta isheni da rigima." Murmushi ne ya mamaye fuskar Abbati yayinda yasa kafa ya shure katon duvet din da ya lulluba dashi. Sanyin dakin ya sauka a jikinsa ya mike da gaggawa ya dora riga mai madauri akan dogon wandon baccin jikinsa. Girarsa ta tattare da fushin da ya maye gurbin fara'arsa "me yasa ka tasheta da sassafe haka? Ko takwas fa bata yi ba. Yara suna bukatar isasshen hutu. Asabar din ma yaro ba zai huta ba to sai yaushe?" "Sannu mai 'ya. Dadin abin dai nima ba daga bishiya aka tsinkoni ba. Haka kawai ta hana mutane bacci ka zo kana yi min fada..." Dariyar da bai yi niyya ba ce ta kama shi. Wani zubin ya kan rasa gane da Munzali da Qibdiyya waye 'ya waye uba. Munzali har kishi yake da ita idan ya ga yaki kula shi. Ba don komai ba kuwa sai don ya tashi da yunwar kulawa irin ta iyaye. Shi ne komai na aminin nasa shi yasa yake ganin lokaci ya yi da zai yi amfani da wannan damar su saita rayuwarsu. A nasa bangaren dole sai ya je gida gobe. Munzali kuwa tunda iyayensa suna gari yanzu zai fara yi masa maganar abin da ya kamata ace ya yi tuntuni. Wannan rayuwar ta ishe shi. Suna bukatar iyali na kurkusa wanda zasu rayu tare. Farincikinsa daya yaki da jahilcin da suka dage sosai suka yi. A lokacin sun yi ne domin samun kasuwarsu ta daga a idon manya. Yanzu zai musu amfani wurin yin kasuwanci a ilimance. Wayewa dai irin wadda mutum zai je ko'ina kai tsaye ya saje sun samu. Haka nan manyan kasa ke biya musu su je kasashen waje domin idan sun iso su amfana dasu. A haka suka sami wayewa sosai idanunsu suka bude. * "Papaaa" Qibdiyya ta ce tana yin tsalle. Abbati ya dagata sama ya juya suna kyalkyala dariya. Munzali na ganin haka ya tashi zai gudu daki. "Malam dawo magana zamu yi fa. Me Audu ya dafa ne?" Ya yi maganar lokacin da ya dire Qibdiyya. A marairaice Munzali ya kalle shi "kayi min rai dan Mariya uban Mariya. Kaina wani yammm yake yi irin na mai shirin zarewa saboda rashin bacci." Kafe shi da ido Abbati ya yi wanda ya nuna masa zaman nasa dole ne. Sai da ya harare shi ya koma ya zauna. "Ka dai ci sa a ina tsoron masifarka wallahi da ba zan zauna ba." Iya Kande ta dube su tayi dariya. Abokan suna matukar burgeta. Tana fatan kowanne ya sami matar da zasu yi zaman lafiya tare. Ta san wani abu cikin zaman Abbati da Hanne mara dadi. Wauta take ganin ta yiwa Hannen yawa tunda duk kokarin Abbatin na son kyautata mata ta 'buge da yi masa sace sace a gida. "Mutum ma yaki zama mana idan ya isa." Cewar Abbatin bayan ya zauna a kujerar kusa dashi. Iya Kande sai ta ja hannun Qibdiyya da dabara suka bar falon. Bread da kwai Audu ya kawo musu domin bai kammala suyar doya da farfesun da yake ba. Ka'idarsu sai wuraren sha daya suke karyawa shi yasa bai fara da wuri ba. "Ni wallahi jikina duk ya yi sanyi. Ka sanni idan an ce za ayi magana amma don mugunta ka tayar min da hankali kafin na ci abinci." "Idan baka ci ba ma maganar sai jibi." Munzali na jin haka ya shiga tuttura abinci yana kurbar tea. Yana gamawa ya ture harda na gaban Abbati dake cin nasa a nutse. "Yauwa fadi don Allah." "Ban koshi ba" "Ba kyau abin da kake yi min." Sai kuma ya dan muskuta tare da rage murya "ko dai ya shafi maganarmu ta jiya? A shirye nake mu daina da gaske." Wannan yanayin na zance mai mahimmanci Abbati ya yi da fuska sannan ya ce "Wannan maganar zamu yi ta sosai amma kafin nan Munzali gidanku kai ne namiji babba ko ba haka ba? Duk yawan yayyenka mata ka fisu iko saboda kasancewarka namiji. Saboda haka alhakin gyara zumuncinku yana wuyanka. Ka nemi 'yan uwanka ka san su sani na jini da jini. Kaga ni dasu Atine bamu da shamaki. Babu wadda ban san halin da take ciki ba duk da suna gidan miji." "Ummakati ce babba kuma tayi aure mijinta yana da abin hannunsa." "Ina ruwan zumunci da abin hannun mijinta? Kuma fa muna tare fa babbar yar ku ta rasu kuma ka ce min akwai wasu." "Wadanda ba dakinmu daya ba su tara ne duka mata." "Sai kuma aka ce sun sauya suna daga matsayin 'yan uwanka don baku fito daki daya ba? Nima muna da 'yan uba kuma duk na hadesu. Magana ta gaskiya Qibdiyya ba mu kadai take bukata a rayuwarta ba. Banda 'yan gidan su Zakiyya bata saba da kowa ba." Kallo sosai na nutsuwa da fahimtar mutum Munzali ya yi masa. Kullum shi ne mai hango masa matsala kuma ya taya shi gyarata. Shi kam ko yau ya bar duniya ya yarda da soyayyar dake tsakaninsu ya san Qibdiyyansa ba za ta taba maraicin uba ba. "Naji zan kokarta. Amma sai ka tayani don ka san Asabe ita kudi kawai take so. Su kuma wallahi idan na bi wata ta gayan bak'a sai na rama." "Ka kwana biyu baka yi muryar 'yan tasha ba ai." "Kut...ni ne dan tashar?" Munzali ya tashi ya yo kansa a guje shi ma ya mike yana neman tsira. Idan ya zauna karshenta sai ya nemi panadol. Gajiya Munzalin zai tara masa don a jikinsa yake fanshe wasan kokawarsa da bai yi ba da kuruciya. "Ka dawo kawai mu gwabza mutumina ko na goge nambar yarinyar nan ta Diamond plaza." "Da gaske ka karbo?" Farinciki mara misaltuwa ya bayyana a fuskar Abbati lokacin da Munzali ya gyada kai. Bai jira komai ba ya je ya riko shi suka fara gwada kwanji. Yau dai Munzali ne ya ji jiki don bai san me Abbati ya sha ba har yake jin karfi irin haka. *** Sai da ta kusa isa dakinta wani tunani da ya karasa dagula mata lissafi ya darsu a ranta. "Yumna. Yumna aminiyar Farhata?" A guje ta shiga dakin 'yan matan har tana tuntube saboda sauri. "Farha bani wayarki" Ta umarceta fuskarta babu wasa. Bakinciki da taraddadin dake kai kawo a kirjinta kuwa baki ba zai iya kwatanta shi ba. Wani irin sauti kamar bugun kararrawa take ji a kunnuwanta. A tsaye take tana haki amma cike da dauriya ta kai hannunta dake rawa bangaren hotunan wayar. Bata ga komai ba saboda haka ta mika mata "Baki isa ki ha'inceni ba wallahi. Ungo ki budo min wadanda ki ke tura masa." "Shi wa?" Lilu ya tambaya suna shigowa dakin shi da Sauda da Suhaib. Akwati ta kira shi ya zo ya sauko musu dashi daga kan wardrobe. Tun a hanya ya ce ta san ba tsayi gareshi ba kawai ta kira shi don suyi dariya. Da kansa ya kira Suhaib suka taho tare. Mami Khadija ta kallesu ta ce "duk ku jirani zan zo gareku daya bayan daya." Ta mayar da hankalinta ga Farha "idan ba za ki bude ba bani nambarsa ko waye shi in kira." Farha ta karasa rudewa sai kuka take yi tana juya wayarta a hannu. Ran Mami Khadija ya sake baci ta daka mata tsawa nata jikin yana 'bari da tsoro. "Har kin isa ki yaudareni? Ina ta kaffa kaffa daku ashe ni aka mayar shashasha. Kuna can kuna turawa mutanen banza tsiraicinku." "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un." Su duka yaran abin da suka ambata kenan amma sautin muryar Farha tafi ta kowa. Kuka take yi iyakar karfinta Sauda tana tayata. Mamin tasu ta hargitse basu san musabbabin hakan ba. Kirjinta ta shiga nunawa wasu sababbin hawayen suna wanke mata fuska. "Mami ni? Ni din? Wallahi, wallahi karya yake ko waye shi. Saboda gudun fadawa halaka da tsoron bata miki Mami watana biyu bana kula Yumna." Da kyar Mami ta dan saita kanta ta nuna bata san komai ba "ina magana akanki me ya kawo zancen Yumna. Me tayi?" " 'Yar kawunta ce tazo hutu gidansu ta koya mata bin sugar daddies. Nayi ta mata nasiha taki ji shine na rabu da ita bayan ta ce za ta hadani da wani." "Ta hadaki da wani don mugunta? Me yasa ma baki sanar dani ba?" Farha ta share kwalla "ce mata nayi zan fada miki ki gayawa Ummanta sai ta ce min wai in na fada miki sai me? Shi ne naji haushi na kyaleta." A zuci Mami Khadija ta iya cewa 'Ba dole ta ce miki sai me ba tunda mahaifinki ya zubar mana da mutumci?' "Naji kuma na yarda amma na rantse duk ranar da ki ka afkawa irin wannan sharin ki kuka da kanki." Sauda ta nuno da hannu tana labe bayan Suhaib duk ta tsure. "Wallahi Mami bana komai ni. Masu zuwan ma nace su rabu dani sun ki." "Ki daina kokarsu tunda lokaci ne da Allah Ya kawo miki. Na baki kwana uku kiyi shawara da zuciyarki da 'yan uwanki ki fidda wanda ya kwanta miki. Kina gama secondary zan miki aure." Da yake bata ga fuskar musu ba ko tari bata yi ba sai aukin gyada kai. "Kai kuma Lilu idan na sake jin an ce kana bibiyar mata sai na saba maka. Yaro tun baka tafasa ba kana neman konewa. Kar kayi tunanin cututtukan zamani ne kadai sharrin dake cikin yawon banza. Lahirar mutum ce kacokan take gurbacewa. Duniyar ma kuma duk kudinka ba za ka taba samun nutsuwa da jindadin da kamilalle zai samu ba. Wadannan abokan banzan naka ku raba jaha kowa ya kama gabansa. Sai kun fi jindadin shiryuwa." Duk maganganun nan tana yinsu ne cikin haki da kunar zuciya. Suhaib yaji duniyar tayi masa zafi. Kusa da ita ya karaso ya dora hannayensa akan kafadunta ya sallami kannensa. "Ki kwantar ta hankalinki Mami in sha Allahu komai zai daidaita" "Komai zai daidaita a ina? Shaye shayen da kake ka shirya dainawa? Idan kana tunanin kana sha domin batawa mahaifinka rai ne to ka sake tunani. Bai san kana yi ba. Ko ma ya sani babu mai dora masa zunubanka tunda ba shi ya kama hannunka ya kai gaban 'yan kwaya ba" Idanunsa a kanta yana kara samun tabbacin Abban nasu ya yi wani abu mai girma ya ce "In Allah Ya yarda ba za ki kuma yi min maganar nan ba." Farha, Lilu da Sauda sai suka ji kansu ya kulle. Kalaman Mami na karshe ga Suhaib sun hasko musu wata kofa da basu san akwai ba. Kofar sirri tsakanin mahaifiyarsu da babban wansu. Kofar da suka kwadaitu su bude don ganin me aka rufe a cikinta. *** "Kayi hakuri don Allah. Zan yi mata magana da kaina." Anti Hasiya ta furta da sauri domin ceton Ayaah daga fushin Honorable. Ba don tayi magana ba daf yake da kai hannunsa jikinta. Amma duk da haka wani kallon kasa-kasa na raini Ayaah ta bata tukwici. "Hakuri kamar yaya? Kina ji fa jiya da na tambayeta a ina ta manta jakar cewa tayi a daidaita sahu. Daga baya kuma ta ce motar wanda ya rage mata hanya." "Zan mata magana don Allah ka sassautawa zuciyarka." Ta rarrashe shi. Tafi kowa sanin yawan hidindimun gabansa da rashin kudi. Ga matsalar Abbas. Takalmansa ya zura ya nufi kofar dakin zai fita "ki yi mata magana Hasiya. Zan dauki komai na halayyar da take mana a gidan nan, amma wallahi banda yawo. Idan ta ce yawo zata yi babu wanda ya isa ya kwaceta a hannuna." Sai da ya fita Ayaah ta taso tana kumbura baki zata fita daga dakin. "Dawo ki zauna." Murguda baki tayi ta juya idanu sannan ta ce "a zaunar dani mana idan an isa." Maganar ta daki Anti Hasiya sosai. Fuskarta ta hade da bacin rai ta daka mata tsawar da ta zaunar da ita ba shiri. Wani gululun abu ya tsayawa Ayaah a rai saboda tana son bijirewa amma a tsorace take sai kawai ta soma hawaye. "Kar ki soma yi min wannan kukan gulmar taki." Dan shiru tayi ta jira Ayaah ta share hawayenta da bayan hannu sannan ta cigaba da yi mata fada. Sam babu alamun lallabawa ko rarrashi a yadda kalamanta ke fita. "Ni ba kishiyar babarki bace da zaki zauna kina kishi dani Hajara. Da Yaya A'i tana doron kasa ko sama da kasa za ta hade ba zan auri mahaifinki ba tunda jininmu daya. Saboda haka ki ajiye makaman da ake baki na kishi dani a gefe. Ko kina so ko ba kya so, da auren babanku a kaina ko babu ni Hasiya uwa ce a gareki. Sannan ko babu alaka tsakanina da Yaya A'i bani da dalilin cutar daku domin mahaifinku bai cuceni ba. Na san kina da hankali ko da ba kya tunani sai abin da aka ce kiyi. To a cikin hankalinki ki zauna ki fada min me na taba yi muku a gidan nan na rashin kyautawa. Idan kuma jira kike bayan duk fadi tashin da nake a gidan nan in dawo na kwanta ki takani ba za ki ganin wannan ranar ba in sha Allahu. Idan ban ci darajar komai ba a wurinki in ci ta uba da na hada da wadda ki ke ganin zuwana gidan nan cin amana ne a gareta. Karshe ina so ki san cewa ba soyayya bace kike yiwa Yaya A'i da wannan halayyar. Kina tozarta tarbiyarta ne wadda Allah zai muku shari'a ranar lahira, ai kin sani idan abin da ki ke yi daidai ne ko akasinsa. Tashi ki bani wuri." (Iyaye mata mu sani cewa 'ya'yanmu komai kankantarsu suna lura da abubuwan da muke yi. Mu daure muyi namu kokarin wurin koyawa musu kyawawan dabi'un da zamu wanke kanmu a kai ko a gaban Allah. Abin da wuya kyma ba iyawarmu bace amma mu yi iya yinmu. Ayaah bata da wani wayo ta rasa mahaifiyarta. Amma bata manta cewa babu alaka mai kyau tsakaninta da Innayo da 'ya'yanta ba. Yau babu A'i amma tarbiyarta bata bar autarta ba. Sannan a gefe ga Laraba da sauran kannen A'i suna ingizata. Su Ummi da suka fara wayo sun rigata fahimtar wace Hasiya a tare dasu. Ita kuwa da akidar kiyayya suka raineta a gefe. Allah Yasa 'ya'yanmu su zama silar samun rahamarmu ba kishiyarta ba. Amin) Jiki a sanyaye Ayaah ta tashi ta bar dakin. Tana shiga dakinsu Murja da Ummi suka fice suka barta bayan tsakin da kowaccensu ta buga. Ai sai taji kuncin zuciyarta ya karu. Kukan gaske ta kama yi ba ji ba gani. Tabbas bata kyautawa ta sani. Tun jiya ake zancen jakar Anti Hasiya da ta manta a adaidaita sahu amma ita mai jakar bata ce komai ba. Sannan ga tunanin mai motar da ya kaita asibitin Nasarawa ya isheta. Komai nasa ya burgeta amma ko sunanta bai tambaya ba har suka rabu. Ko babu komai zuciyarta ta cika da shakkar Anti Hasiya. Bata taba yi mata fada kamar na yau ba. Lallabawa za ta yi ta nuna musu ta shiryu zuwa ta samu tayi aurenta ta bar gidan ta huta. Yadda kowa ya tsaneta (a tunaninta) barin gidan shi ne mafi a'ala. A bangaren Anti Hasiya kuwa duk yadda take son zuwa duba Innayo yau hakan ba zai samu ba sai can yamma ko dare idan ta gama lalle. Musamman saboda tun safe Uwani ta rangado mata kira. "Idan na taso daga aiki zan biya duba Innayo. Dama kira nayi in tuna miki kada ki manta da sakona." Da azahar ta sake kira shi ne musabbabin fadan da Honorable ya sake yiwa Ayaah. "Karfe uku zan fito Hasiya. Idan ba da wuri zaki je wurin Innayo ba sai na biyo gidanki na karba." Taji zafin kalaman amma ta daure bata mayar mata ba saboda nata kudin sun bata. Duk 'yar ajiyarta ce a ciki Ayaah ta salwantar. Wai akan kudin da ba a cikinta ta ci ba Uwanin ke kiranta bayan rabon da su gaisa a waya ta manta. Wani irin nauyi zuciyarta tayi saboda damuwa da hanyar da Uwani ta dage sai ta bi ta sabawa iyaye. Inda suke lallen ta koma ta cigaba da sakawa matan. Ana kiraye kirayen Isha ta sami shiga gidansu da abincin da ta dafowa Innayo. "Ki yi hakuri. Wallahi jakata ce ta bata babu ko sisi a jikina." Innayo ta murmusa da kyar. Idanunta duk sun zurma ciki saboda tsabar wahalar da tasha kwana biyu "A waya ma fa na ce miki kar ki damu. Uwani ta zo kuma sai da aka yi magariba kamar Salima ta bar gidan nan. Fuskarta dai duk a kumbure ko kadan ban ji dadin ganinta ba." "In Allah Ya yarda cikin satin nan zan ziyarceta. Mutumin nan baya tsoron Allah. Ko albarkacin 'ya'ya yaci ace yana raga mata wannan rashin mutumci." "Hmmm" Innayo ta iya cewa kawai. Anti Hasiya sai tayi shiru saboda ta san cewa cigaba da maganar zai kara bata ran Innayo ne. Salima bata taba sanar dasu mijinta yana dukanta ba amma sun dade da sani. Wahala kawai take sha amma Alh. Rabi'u ya ce ba zai iya riketa da 'ya'yanta ba idan ta kaso auren. "Faten tsaki nayi miki. In zuba yanzu ko sai anjima?" "Zuba min sai ki leka wurin Asabe ku gaisa ki zo ki tafi dare na kara yi." "Baban Ummi zai biyo ya duba ki. Shi zan jira." "Da ma kar ya wahalar da kansa. Taki wahalar ma ta isa." Anti Hasiya sai ta mike ba don tana son zuwa dakin Asaben ba. Zamanta zai sa Innayo ta koma nuna rashin son aurenta da kullum ta sami dama sai tayi. Ita kuma ta riga ta karbi kaddararta hannu bibbiyu. Zaman lafiya da aminci suke yi dashi wanda yafi karfin zaman soyayya. Ya girme mata sosai amma yanayin zama ya mayar dasu tamkar aminan juna. *** Riga da skirt na atampa aka sakawa Qibdiyya da zasu fito bayan Magrib. Ita ta dage wai kayan 'yan mata take so. Iya Kande tayi mata dauri ta kwance ta sake yin nata a cewarta na Iya na tsofaffi ne. Natan ma dai sai dai a gimtse dariya kawai. Tayi abinta Abbati yana ta kwarzanta kyaunta har suka fito. Kowa da motarsa suka fito daga gidan ita tana ta Munzali shi kuma Abbati yana tasa shi kadai. Daga wurin Asabe zai je gidan Shazali ne ya fara gabatar masa da kudurinsu na daina wannan mummunar alfasha. Shi kuma Munzali zai dawo da Qibdiyya gida. *** "Salamu alaikum" Anti Hasiya ta sake doka sallama ta biyar a kofar falon Asabe. Da karfi da alamar kosawa Asabe ta ce "Wai waye ne haka ake ta yi min sallama kamar an biyo bashi?" Ba don Innayo ce ta turota ba da babu abin da zai kawota. Danne bacin ranta tayi ta ce "Hasiya ce." "Wace Hasiyan" ta kuma tambaya a wulakance. Zuciyarta har wani harbawa take saboda bacin rai. Juyawa tayi za ta bar wurin taji an tura kafadunta cikin dakin. Asabe dake zaune rashe rashe tana kallo ga farantin da ta dora ledar tsire a kai ta mike tsaye tana gyara zani. "Meye haka za ki fado..." sai kuma ta kula da wanda Hasiyan take yiwa kallon mamaki bayan ya turota dakin. Fuska ta saki ta kama dariya "Alhaji Munzali sannu da zuwa, sannu da zuwa. Lale marhabin. Ai ban san tare ku ke ba. Ita ma kuma da sai ta ce Hasiya matar Honorable Habun A'i sai nafi saurin daukar haske." Munzali ya yiwa Abbati irin kallon nan na kaga abin da nake fada maka ko. Duk maganganunsu sun ji shi yasa ma ya turota dakin. Abbati dake dauke da Qibdiyya ya yi dan murmushi kawai. Anti Hasiya sai ta gaishe ta domin ta basu wuri amma maimakon ta amsa sai ta karkata kai ga Abbati. "Alhaji Abbati ina wuni? Ya fama da jama'a? Ya kasuwar? 'Yan uwa duka lafiya ko?" Ran Munzali ya sosu da wannan barar da kai na Asabe da kuma wulakanta Hasiya da tayi. "Baki ji Hasiya na gaishe ki ba?" "Au...hankali na ne ya tafi wurin Mariya." Ta janyo Qibdiyya jikinta. Ko daga kai ta kalli Hasiya bata yi ba ta ce "ya mijin naki da yara? Dazu ma naga Salima da Uwani ince dai lafiya." Wani mamakin ya sake kama Hasiya. Jiya baki da baki ta fadawa Babansu an cire hakwaran Innayo har biyu. Shi kuma ya san da lalurar ma kudi ne da ba zai bayar ba. Bata sani ba yanzu shi ne bai fadawa Asaben ba ko kuwa shaftarta ce da ta saba. "Innayo ce bata jindadi." "Allah Ya sauwake. Mariya mu je ciki na baki alawa" ta kama hannun Qibdiyya ta shige ciki da ita. Gwiwa a sage da wannan wulakancin har a gaban bakon ido Anti Hasiya ta juya ta fita. Munzali ya bita da sauri ya cimmata kafin ta karasa dakin Innayo. "Hasiya tsaya mana." Tsayuwa tayi bata juya ba. Dan uwanta ne da ya bata 'yan watanni amma rabon da su hadu ta manta. Fuska ya saki da ya iso gabanta "saurin me kike yi ko gaisawa bamu yi ba?" Murmushin da tayi masa mai ciwo ne. Gabadaya jikinsa ya yi wani irin sanyi. Bata ce masa komai ba amma a fuskarta yake karanto damuwarta. "Don Allah kiyi hakuri. Dukkanku ku yi hakuri akan duk wani rashin kyautawa daga gareni ko Asabe da duka 'yan dakinmu. Laifin namu ne don na san Innayo bata son wannan zaman da muke da juna." Kwalla ce ta taru har tana barazanar zuba daga idanunta ta ce "Ba komai. Biyonin da kayi ma wallahi naji dadi" Hannu ya mika ya karbi wayarta yana cewa "kawo in saka miki nambata". Ya fara saka nambar yaga sunansa ya fito "kaiiii, ashe kina da nambata amma baki taba kirana ba." "In kiraka in ce me?" 'Yar dariya ya yi ya ce "Ki ce kin kira mu gaisa." Nambarsa ya kira domin ya sami ta ta sai yaji ana cewa "your account is too low for this call" Dama a kunnensa ya kara wayar sai kawai ya wayance don kar ya kunyata ta ya ce babu service mai kyau. Da ka ta karanto masa nambar ya bita har dakin Innayo. "Munzali kai ne a dakin nan? Hasiya daga cewa ki je ki gaishe da Asabe kin dauko min magana ko?" Innayo ta ce a dan tsorace. Kunya kamar an zuba masa ruwan sanyi haka yaji. Yanzu ace ganinsa bai haifar da komai ba a wurin matar babansa sai tsoro. Sunkuyar da kai ya yi bayan ya zauna a gabanta. "Ba haka bane Innayo. Kiyi hakuri don Allah. Na dade bana kyautawa amma in sha Allahu zan gyara. Zan daidaita zumunci da 'yan uwana." Ya dubi Anti Hasiya "taimaka ki karanto min nambobi su Yaya Uwani da kaina zan kirasu. Idan da hali mu hadu a nan ranar asabar mai zuwa. Kowa ta taho da 'ya'yanta. Zan kira ki dai mu tsara yadda abin zai kasance." Kwallar da ta danne tun farkon maganarsa ce ta sauko. Tana son 'yan uwanta kuma tana kwadayin su yi zumunci da juna kamar kowanne dan uwa. Gasu da yawa amma babu jituwar kirki tsakaninsu da juna tamkar sun hada jini da Malamijo (KU DUBE MU). Mahaifinsu ta dorawa alhakin lalacewar lamuran gidansu. Babu ruwansa da komai na iyalinsa indai zai dawo a bashi abin ci. Ta rasa gane wace irin rayuwa yake yi. Tarbiyar jowa a gidan saitinta daban. Matansa ya kamata ya daidaita tuntuni domin su hada kan 'ya'yansu amma ya bari a daki daya ma ana gaba. Munzali sai ya matsa ya rungumota a barin jikinsa "in sha Allah Hasiya komai zai daidaita tsakaninmu. Nayi sakaci a baya kuma ina da na sani." Bambarakwai taji rungumar ta yi murmushi tana kokarin ture shi. Shi kuwa ya rike kafadarta gam yaki saki yana dariya " 'Yar kauye meye haka? Irinku ne masu rungumar miji sau daya a wata ko?" Innayo bata san lokacin da tayi dariya ba. Dariyar da bata iya karasawa ba saboda banko kofar dakinta da Asabe tayi tana huci. "Billahillazi huwar rahmanu Bokanki ya yi karya Innayo. Ni? Ni Asabe da raina ki ke neman yi min farraku da d'an da baki san lokacin da nake fadi tashin gina shi ya zama mutum ba?" Wani irin kallo Munzali ya bita dashi zuciyarsa tana zafi. Bai taba ganin uwar da bata san darajar kanta da 'ya'yanta ba sai ita...sai kuma babar yarinyar nan ta Diamond plaza wani sashe na zuciyarsa ya tunatar dashi. (Akwai kuskure mai girma ga iyaye musamman mata su dinga gilla karya a gaban 'ya'yansu. Sosai hakan yake taimakawa wurin zubar musu da girma a idanunsu. Mu kiyaye.) ********* Masu karatu kar ku ga kamar labari yana ta tafiya amma lokaci ba ya ja a cikinsa. Hakan yana faruwa ne saboda yawan jaruman labarin wadanda suke da rawar takawa ba 'yan karo ba. Kuma abubuwan da zasu faru a dan takin lokacin nan suna da nasaba da yadda labarinmu zai tafi a gaba. Sai mun hadu a shafi na gaba da izinin Allah. #SonSoI just published "13" of my story "UWA UWACE...". https://my.w.tt/H7FJkqEvQab UWA UWACE...13 Batul Mamman💖 "Hasiya muje daga waje muyi magana please. Ina so mu tsayar da rana ne a yau dinnan." Innayo ta kalla da Asabe wadda take shirin hadiyar zuciya. Maganar me Munzali zai yi da Hasiya har yake neman su kebe? "Bishi ku je. Allah Ya kara muku zumunci." Cewar Innayo tana murmushi. Allah Ya sani har zuciyarta ko Munzali yafi kowa talauci tana maraba dashi da 'yan uwansa wurin zumunci da nata 'ya'yan. Yau idan babu su a raye bata jin ko shi uban gayyar mahaifinsu zai so ace kowa tasa rayuwar yake yi. A tsakar gidan suka zauna ya sake bata hakuri. Ita mamaki ma ya kashe nata bakin sai murmushi take dokawa. Basu taba zaman hira ba da 'ya'yan dakin Asabe tun kuruciya. "Weekend dinnan zan yi tafiya da wanda ki ka ganmu tare a dakin Asabe. Aminina ne sosai sosai Hasiya." Wai Munzali ke fada mata wani abu nashi mai mahimmanci? Lallai duniya inda ranka ka sha kallo. Ita ma zata bashi labarin tata rayuwar kuwa ta ayyana a ranta. "Allah sarki. Yaya sunan shi?" "Abbati" Daga yadda ya fadi sunan ma ta fahimci alakar ba ta wasa bace. Dan tunani tayi ta dago kai tana ware idanu. "Ba dai wanda Asabe ta taba dukanka akan kana kula shi ba?" Dariya ya kwashe da ita "ashe kin tuna..oh su Hasiya muguwa...ai na kullaceku lokacin. Kuna kallo tana neman kaini kiyama aka rasa mai cetona." Ita ma bata san lokacin da ta soma dariyar ba. A nan Abbati ya samesu suka sake gaisawa yana murna da canjin da aka fara samu a rayuwar Munzali tun yanzu. "Ina Qibdiyyan?" Munzali ya tambaye shi. "Asabe ta ce idan zamu tafi kaje ka daukota. Ni bari naje wurin Shazali zan sameku a gida." Sallama ya musu ya tafi. Munzali ya san fada ne Asaben ke ji kuma ba zai bari ta sake raba kansu ba. Ummakati ya tuno ita ma ko a waya sai ayi watanni basu gaisa ba. Kananun ne dama masu damunsa saboda roko da Asabe ta koya musu. "Wai don Allah bebin da muka zo barkarta ce wannan? Mariya sunanta ko?" Anti Hasiya ta ce tana rike baki. "Allah wadaran gida irin namu. Yanzu fa babu abin mamaki ki ganta a waje ku wuce juna. Wallahi Baba bai yi ba..." "Kar mu fara aikin alheri da aibata iyaye. Shi Baba sai dai addu'a kawai." "Da Asabe ma..." "Da Uwani.." "Da Mahe (kaninsa wanda Asabe ke cewa sune magadan Alhaji Rabiu)" "Da Zara." "Da duka ahalin Laraba (babarsu A'i)" Wata dariyar suka yi. Gidansu kamar ba gidan mutane ba. A gabanta ya tura mata katin waya na dubu biyar ya ce ta kira duka 'yan uwan nasu suyi shawara. Idan asabar ko lahadi ta sama tayi musu duk su hallara a gidan da 'ya'yansu. "Allah Ya kara budi Ya kuma kyautata zumincinmu." Cewar Anti Hasiya. "Amin" "Dan dauko min Mariyan in dauketa. Ya ma naji kuna kiranta?" "Qibdiyya" ya ce da murmushi. Asabe tana ta masifa ya dauko 'yarsa ya kai dakin Innayo wurin Anti Hasiya. Yarinya kuwa tuni ta ware saboda Hasiya tana da son yara. Kafin ya fita Honorable Habu ya shigo suka gaisa. Innayo bata nuna halin ba saboda farincikinta na soma gani hadin kan 'ya'yansu. Fatanta Uwani da Zara ma su bada hadin kai. Da Abbati yaje wurin Shazali ya fada masa bukatarsu nuna masa ya yi babu komai har ya ce zai bisu bikin nadin saurautarsa. A badini kuwa ya hau lissafin asarar da zasu tafka da kuma kalubalen da ka iya biyo baya. Manyan 'yan siyasa da masu kudin da suke mu'amala dasu ba yarda zasu yi su rabu haka ba. Gani zasu yi kamar dama turo su akayi ko kuma sun gama sanin sirrinsu zasu tona musu asiri. Rabuwar sam ba za ta zo yadda suke tsammani ba. *** Tunani da zubar hawaye sune suka taya Mami Khadija kwana. Bata san kulle kullen da Alh. Tahir ya yi ba tun a jiyan sai washe gari da misalin karfe takwas na safe. Farha ya aiko kiranta amma sai ta kasa tashinta ganin yanayin yadda take baccin. A inda tayi sallar asuba bacci ya dauketa a zaune. Komawa tayi ta sanar da Abbansu tana bacci sai ta tarar da'irar kakaninta da abokan Alh. Tahir duk a falon. Gabanta ne ya fadi, da gani ba lafiya. Gaishesu tayi ta koma dakin ta taso ta. Tsabar ta rude ma harda hawayenta. Nata hankalin har yafi na uwar tashi wai amma a haka take kokarin kwantar mata da hankali. "Mami ki kwantar da hankalinki ki shiga falon a nutse. Kin san komai kaddara ne. Naga Mama da Baban Kawo tare da Yakumbo. Kuma su Lilu suna dakinsu kowa lafiyarsa kalau." Zuwa yanzu jikinta har karkarwa yake "Mami harda Yakumbo fa. Me zai kawosu gidan nan da sassafe haka?" Mami Khadija ta murmusa da ta fahimci inda zancen ya dosa "ki kwantar da naki hankalin kuma kar ki yarda ke ko wani cikin 'yan uwanki yazo falon Abbanku." Idanu kamar su fado saboda tsorata Farha ta ce "Mami ko dai sakinki Abba ya yi?" "Wuce ki fadawa yayanku nace" Mami ta furta da dan karfi don ta tsorata ta. Tare suka fito Farha ta ruga dakinsu Suhaib ta fada musu kai tsaye tare da sallama. Tayi sa a kuwa kowannensu da suturarsa. Lilu lecture gareshi da karfe tara shi kuma Suhaib yunwa ce ta tashe shi. "Are you crazy?" Suhaib ya ce fuska a hade. Ya hana kannen nasa mata shigo musu daki babu sallama kamar yadda ya hana Lilu shiga nasu kai tsaye. Hawayenta ya gani ya cillar da wayarsa ya mike daga kan gadon. "Ya Suhaib wani abu na shirin faruwa...." Muryarta da sauri-sauri ta dinga fita wurin fada musu abin da ta gani. "Taso min Mardiyya da Sauda." Ya ce yana yin hanyar kofar dakin. Bayansa tabi Lilu yana take musu baya. Da kansa ya bude dakin yana kiran kannen nasa. Duk tsoronsa bai wuce kada abin da za a tattauna a falon ya fito har ya shiga kunnuwansu ba. A firgice yake da gudun halin da zasu shiga idan suka san waye mahaifinsu. A duniya bai ga wani abu mai saurin zubar da mutumcin mai mutumci ba sama da zina. Bai san me yake faruwa ba amma ya san da maganar Maminsu na son su koma nata gidan. "Ku tashi Lilu zai kai ku gidan Mama." "Maman fa tana falon Abba na ce maka" Farha tayi saurin fada. "Na sani. Ku tafi zan biyoku nima." Gardama Farha da Lilu suka so yi masa ya jugo garesu a birkice. Sauda da Mardiyya ba ganin haka suka tashi duk da basu san me yake faruwa ba suka saka hijabansu. "Ya Suhaib please ka yi min bayani." Farha ta ce da rawar murya. Ita fargabarta bata wuce tunanin ko Mamin ce tayi laifi ba. Gyara yanayin fuskarsa ya yi domin ya kwantar musu da hankali baki daya. "Ku daina damuwa ba wani abu bane" yana fadin haka suka hada ido da Lilu wanda ya tabbatar idan bai basu gamsasshiyar amsa ba yaron zai fara tone-tone. Dan murmushi ya yi sannan ya ce "Kun san Abba ya gama gini zamu tashi daga nan. Ita kuma Mami ta riga shi farawa ita ma ta gama nata. To shi ne take so ita ta koma wanda ta gina ba na Abban ba." Gabadaya a tare fuskokinsu suka sauya zuwa yanayin da yake fatan gani. "Fadan da babu ruwanka dadin kallo ne dashi" Lilu ya furta yana dariyar shakiyanci. Harara ya samu daga Sauda ta ce "Fadan su Mamin ne da dadin kallo Ya Lilu?" "Idan ba dadin kallo ba me zan ce? Mu dai babu wanda zamu ce zamu shigarwa tunda matsayinsu daya. Kuma na tabbatar miki suna shiryawa sai masu shiga fadan sun ji kunya." Farha da bata yi saurin yarda kamar kannenta ba ta nisa ta ce "wai kun manta yadda ta shigo daki jiya tanata yi mana fada. Ni nawa ma yafi na kowa" ta karashe maganar da raunin murya. Suhaib ya yi saurin kawar da tunaninta da cewa "tun jiyan fa suka fara rigimar. Ni na zata ma a lokacin zai fadawa su Mama. Anyways mu zauna a nan don kun san Yakumbo tana ganin mun fita zamu sha fada." "Yaran zamani ba kunya..." Suka hada baki suka fada cikin salon kwaikwayon kakar tasu. * Da cikakken confidence Mami Khadija ta shiga falon da sallama. Dogon hijabi ne mai hannu har kasa ta dora akan kayan baccinta. Suna hada ido da Alh. Tahir ya kawar da nasa saboda kwarjinin da tayi masa. Dan tabe baki tayi ta wuce gaban Yakumbo ta gaisheta. Fuska a gimtse ta amsa mata. Bata nuna damuwa ba ta matsa gefen Mama (mahaifiyarta). "Rike gaisuwarki tunda har kin yi girman zama 'yar kanki." Motsa baki tayi za ta bata hakuri Baba ya katseta ta hanyar nuna mata yatsa "baki isa ki bijerewa umarnina ba matsawar kina amsa sunan 'yata wallahi. Wato kin fara shiga cikin manyan matan dake zaman kansu sun hure miki kunne. Da hankalinki da ilimin addini ki ke neman rabuwa da miji akan abin da bai taka kara ta karya ba. Shin namiji ba mijin mace hudu bane? Menene aibu don ya nemi auren kawar Farha? Ba sunna ya dabbak'a ba? Ko baki da masaniyar cewa 'ya'yan Nana Khadija (RA) su Sayyada Zainab da Ruqayya sun girmi Nana Aisha Allah Ya kara yarda dasu baki daya." Maganganun sai suka daure mata kai. Ido ta sake kaiwa ga Alh. Tahir wannan karon bai yarda ya kalleta ba. Ita kuwa bata yi shiru ba ta ce, "Baba me ya ce nayi ne?" Ran Mama ya sake baci kuwa ta kalleta a harzuke "Khadija ko dai da gaske kin fara kawance da matan da basu san girman na gaba dasu ba? Mijinki ya kwana yana fushi dake amma don kokari a gabanmu ki ke son shashantar da zance." "Ku kyaleta don Allah da fadan nan. Kishi dole ne. Khadija matso nan.." Mami ta matsa kusa da surukarta kuma yayar mahaifinta "kiyi hakuri tunda dai auren ba haramun bane. Abin da yake haramtacce shi ne mace ta dinga neman mijinta ya saketa ba da dalilin da shari'a ta yarda dashi ba. Na san irin auren nan babu dadi amma kar ki manta ba haram bane." Ta soma hasashen abin da ya faru amma duk da haka shi ta kalla kai tsaye. Zai kawar da kansa ta daga murya rai a matukar bace. "Kar ka kuma kawar da kanka ka kalleni ka fada min abin da ka sanar da iyayenmu." Tana kare maganar Mama ta tashi za ta mareta cike da takaicin zubar mata da mutumci da take ganin Mamin tayi. Kafin tayi marin Alh. Tahir ya taso da sauri ya rike hannun. "Kiyi hakuri Mama don Allah. Ban nemeku domin haka ta faru ba. Hakuri kawai nake so ku bata sannan ta san cewa na janye." "Wallahi ba za ka janye ba. Wannan aure kamar anyi an gama kuma ni zan maka waliccinsa ma. Idan an daura ta mutu tunda bata da tawakkali" cewar Baba. Nan fa gaban Alh. Tahir ya fadi. Shi da ya yiwa kansa garkuwa da auren karya wannan tsohon (wato Baban Mami Khadija) yana neman ballo masa ruwa. Da aminansa na shashanci su biyu wadanda ke zaune a falon suka kulla komai. * Daren Jiya (Dakin Nasima) "Zabi ya rage naki. Ko dai ki goyi bayana ki ce auren yarinyar na nema Khadija ta tubure ko kuma na rantse miki zan SHEGANTA Mardiyya." Dif taji kunnuwanta sun daina daukar kowane sauti sai gudun jininta a cikin jijiyoyin jikinta. "Me...me? Me kake nufi Diya?" Ta fara zuwa hannu ya fada a ransa sannan ya murtuke fuska "an fada miki ni sauna ne ban san me nake ba? Daga aurenki ko wata taran cif bamu yi ba ki ka haifeta. Na san tawa ce dai amma..." Dankwalinta ta cire ta daure kugu dashi jikinta na rawa kamar ana yi mata allurai. Gabadaya ta haukace masa ta soma masifa ido rufe tana zufa. "Wallahi kayi mugun kadan Tahir. Kambu..ni zaka yiwa haka?...to bari kaji in gaya maka. Zan jure komai banda wannan. Wallahi Mardiyya 'yar sunna ce. Ba a waje nayi cikinta ba" sai kuka ya kwace mata. Iyakar abin da Mardiyya zata tsira dashi na mutumci kenan a duniya. Shi ne kawai abin arzikin da ta san ta yiwa 'yarta da bata sami cikinta a waje ba. Nata dangin babu wani asali na bugawa a misali. Ga miji bashi da maraba da bunsuru. Ai ita ba mahaukaciya bace. Ta dade da sanin barin Mardiyya cikin 'yan uwanta gata ne gareta. Duk wannan hargagin na son ta rabasu ba komai bane sai barazana da kishi. Kukanta kuwa ya faranta ran Alh. Tahir "Za ki iya bani hadin kai na ceci aurena da Khadija ta hanyar karyata ta gobe ko kuma ki fadi gaskiyar abin da ya faru 'yarki ta shiga sahun marasa asali...that is bayan mutuwar naki auren da karbe shagona dake hannunki." Bata daina kukan ba ta ce "Ka karba. Ko yanzu ka ke son zan baka amma idan ka taba mutumcin Mardiyya sai na nuna maka haukan da har ka mutu idan kaji sunan Nasima sai zuciyarka ta girgiza." "Nasima kenan. Bakinki ba ya mutuwa. To ni dai kin amince ko kuwa?" "Na yarda." (Ai na fada muku komai lalacewa Nasima ma uwa ce. Duk barazanarsa babu abin da ya dameta illa asalin 'yarta da zai lalace. Babu wani abu komai dadinsa a gareta da zai sa ta yarda hakan ta faru. Saboda Mardiyya ta amince da wannan shiri.) * Daren Jiya (dakin Jiddo) "Ina magana kin yi shiru. Idan ba za ki bani hadin kai ba ki fara hada kayanki domin dama zamanki bashi da amfani sai karin nauyi. Ke ko barin nan da mata keyi baki taba yi ba." Shekeke ta kalle shi "kaga ni babu ruwana da sabgarka. Yawon tambada ai ba yanzu ka fara ba..." Marinta ya so yi ta kauce kafin hannun ya iso kuncinta. "Kaga Malam kar ka taba lafiyata. Idan kana so ma ka aurota da gaske ba matsalata bace" Hankali kwance ya fice daga dakin. Dogon tsaki Jiddo ta bishi dashi kafin ta mike ta saka mukulli ta kulle dakinta. Ruwa ta watsa ta saka wata figigiyar rigar bacci sannan ta bi fuskarta da heavy make up. Selfies ta kashe sun fi ashirin. Ta zabi biyar da suka fi kyau da nuna jiki ta tura whatsapp dinta. (Danliti Makanike) shi ne sunan da ya bayyana. Tura masa hotunan tayi ta kwanta tana jiran waya ko amsarsa ta nan. A lokacin Danliti yana zaune tsakiyar abokansa su Rabilu da direban adaidaita sahun da ya dauki Ayaah. Jakar Anti Hasiya suka zazzage suna shirin raba kudin dake cike Danlitin ya hanasu. "Ni da zan yi amfani da jakar na koma gareta ai zaku zubar min da girma idan aka taba kudin.." Ihun basu yarda ba suka fara yaji shigar sakwanni a wayarsa. Budewa ya yi ya doka uban tsalle sannan ya cillawa Rabilu wayar. "Wayyo Bobo ina ka samo wannan kayan dadin?" "Wohooho...kai kaga wata dakakkiyar haja. Shegen ina ka samota?" cewar direban. "Matar da nace muku motarsu ta lalace a wurin Ciromawa (Zaria road) aka daukoni na gyara musu. Daga hira fa tana ce min biki suka zo za su koma Kaduna sai gani da lambar wayarta. Sai ma kun ji irin hirar da muke yi." Ya kare da lumshe ido yana mantawa da batun Ayaah. "Bobo kawai kaje asha shagali. Wannan fa katin gayyata take turo maka da hotunan nan." Kada kai Danliti ya yi "inaaa, matar aure ce. Haka kawai azal ta kaini asiri ya tono a batar dani ban gama morar duniya ba." "Banza dan bakinciki. Ni ka hadamu kawai" cewar Rabilu. Basu tashi ba sai da kowannensu ya tura hotunan a wayarsa suna ta fasalta ta tare da amfani da kazaman kalamai akan mummunar alakar da suke son kullawa da ita. (Komai mutumci, girma da kimar mutum tsirara yake komawa da zarar ya kulla abota da zina. Ya Allah ka nesantamu da zuri'armu daga wannan kazamar alfasha. Amin) * Bakin Mami Khadija kasa rufuwa ya yi a lokacin da Anti Jiddo da Mama Nasima suka hada baki wurin bada shaidar zur. Su biyun sun ce rigimar ta faru ne lokacin da Alh. Tahir ya fada musu zai auri kawar Farha idan sun tare a sabon gida. Sai da iyayenta suka gama yi mata tatas sannan ta iya cira baki ta ce "Allah Ya sanya alkhairi a tsakaninsu. Bari naje mu cigaba da parking kafin goben." Ficewa tayi ba tare da ta sake kallon kowa a falon ba. Jikin Mamanta sai ya yi sanyi ta soma tunanin ko akwai wata a kasa. Ta san halin Khadijanta amma jiya fa Tahir din da abokansa yazo gidansu kamar zai zubar da hawaye. Yayinda zuciyarta take wannan tunanin sai wani sashe ya tunatar da ita cewa idan aurenta ya mutu yanzu tamkar ta bata rawarta da tsalle ne. Mata kowacce fa hakuri take a gidan aurenta. Me zasu ce da 'yan uwansu ya raba auren shekara da shekaru? Jikin Yakumbo yafi nata sanyaya. Tafi kowa sanin halin dan nata. Kafafu babu kwari haka ta tashi ta dogara zuwa dakin Mamin. Kofar a rufe take. Daga ciki taji an ce, "Ko waye ku fadawa sauran bana son damu. Kar wanda ya shigo sai na nemeku." "Ni ce" cewar Yakumbo a raunane. Da sauri Mami Khadija ta taso ta bude mata kofar duk da dama ba mukulli ta saka mata ba. Sai da suka zauna sannan Yakumbo ta soma magana. "Khadija fada min tsakani da Allah me ya faru." Sai da ta hada da roko sosai sannan ta sami amsar da tazo nema. Hawaye ne ya balle mata ita kuwa Mami dama nata ya kare. "Kiyi hakuri shi ne kadai abin da zan iya cewa. Wallahi ba don kun tara zuri'a ba da da kaina zan karbar miki takardarki. To amma yanzu kina fita me zaki fadawa 'ya'yanki ya rabaki da mahaifinsu? Dukkansu fa aqilai ne babu karamin yaro a ciki. Ko kin boye da sannu magana za ta fito. Yaya zasu ji ace uban da basu da madadinsa ne da wannan halayyar? Da girmansa ya zube a idonsu ace ya nemu kanwar 'yarsa a waje ai gara ace aurenta ya yi. Kina kallon halin da Suhaib ya shiga. Tahir din da kansa ya fada min da na matsa da tambaya. Ki daure ku karasa rayuwarku tare don Allah." Ga mamakinta sai ji tayi Mami Khadija ta ce "Yakumbo zan zauna. Wannan shawarar na san ita ce dai zaki bawa Amina ko Asama'u ( ya da kanwa ga Tahir). Kamar yadda nake tsammanin zasu yi miki biyayya nima zanyi. Zan zauna har Allah Ya kawo masa shiriya." Kalamanta sai suka bar Yakumbo da bude baki da rufewa. Ta rasa me za ta cewa Mami. Ba abin ta ce tayi mata rashin kunya ba ta san cewa gaskiya ce ta fada kuma dama wanzami baya son jarfa. Fita tayi Mami Khadija ko kofar daki bata rakata ba. Irin ciwon da zuciyarta take yi a lokacin tana tsammanin zai iya kwanyar da ita. Wannan wace irin duniya ce muke ciki mai cike da son zuciya da son kai. Sab'o ya tashi daga abin kunya ya koma abin rarrabewa tsakanin mata da maza. Jinsi mafi rauni idan ya aikata shi ne laifi. Bayan tafiyar iyayen nasu Alh. Tahir ya kai gwauro ya kai mari yana ta safa da marwa a falonsa. Baba ya ballo masa teku ba ma ruwa ba. Yakumbo tayi rantsuwar idan bai auri Yumna ba sai ta tsine masa kafin ta tafi. "Me zan ce da yaran nan? Me zan cewa Farha?" *** Da safiyar wannan ranar ne kuma 'ya'ya da jikoki harma da tattaba kunnen Marigayi Mal. Auwalu Sarkin Dori suka tashi da shirye shiryen isowar Farinwatan (Zahra Tabi'u) gidan. Kwai da kwarkwatansu babu wanda baya ci daga arzikin Auwal wato Abbati. Kafatanin danginsa na uwa da uba babu mai arzikinsa gashi babu rowa balle nuna kyashi. Washe garin ranar ne za ayi masa nadin sarautar da ayyukan alherinsa a garin suka saya masa. Sardaunan Matasan Kirikasamma. Da yake ba wasu abokai gareshi ba daga shi sai Munzali, Shazali wanda ba a son ransu ya biyosu ba, Iya Kande da Audu kukunsu sai shalelensu Qibdiyya. Katafaren ginin da ya yi a jikin katangar ainihin gidansu nan Hanne take zaune tun bayan ya maidota da kansa. Zama suke wanda babu soyayya ko kadan sai bakaken halayen da take nuna masa. Shi ma kuma yana sane da nasa mummunan aikin da ya shallake 'yan sace sacen da take yi masan. Nesanta da juna a tunaninsa shi zai raga musu yawan fadan da suke yi. Da ya dawo da ita Gwaggo Jummai gidan tazo ta sha kukanta akan lallai ya mayar da ita. Mal. Sa'adu ya shafawa idanunsa toka kamar ba ciki daya suka kwanta da ita ba ya ce maganar Abbati ce abar dubawa. Idan Hanne ba za ta kwantar da kai taci arziki duk da rashin haihuwa ba zasu bashi wata. Tana jin haka ta gane autarsu suke son bashi. Lokacin halin Deluwa ya fito musu zahiri. Rigima sosai aka yi wadda har yanzu da burbushinta domin gaba lamarin ya haddasa. 'Yan fadar Deluwa suna goyon bayan asa Abbati ya auri 'Yashshafa. Masu amana na hannun daman Gwaggo Jummai suna tuna mafarin hadin auren Hanne da Abbati suna sukar abin. Mal. Sa'adu bai ce komai ba saboda shi ma ransa yana so. Baaba Mari abin duniya ya isheta. Tayi ta kiransa ya zo a sulhunta yaki zuwa. Kowacce kamar za ta kwanta mata a kasa. Hanne da 'Yashshafa su wuni suna girki da zuwa yi mata shara da duk wani aikin bangarenta wanda ya koma aljannar Kirikasamma. "Ayiririiiiii. Kai jama'a, mai hanci ta buga mana gud'a mai doguwar gunna mana. Ga Shafa'atu ikon Allah. Kainuwa dashen Allah. Zinariyar gidan Alh. Sa'adu mai kyauta bata kirgawa. An buga an barki an sake bugawa an kuma barinki. Sannu uwa ga jikokin Haj. Mariya ta Alh. Inuwa gatan marasa galihu. Muna nan muna jira badi war haka sai an saki guda kala hudu a jere na saukar irin da zaki dasa a gidan Alh. Abbati. Na ce ina gaisuwa da babbar murya ga Alh. Abbati Sardaunan Matasan Kirikasamma..." Ta tagar wani falo dake saman nasu gidan Hanne ta leko cikin gidan iyayen nasu. Su ma basu fara ba sai da suka daidaici jikin katanga inda suka san ana yi zata jiyo. Tana lekowa kuwa 'Yashshafa da kawarta mai wannan kirarin suka kwashe da dariya gami da tafawa. Ta kule iyakar kulewa ta koma kasa inda kannenta ke tayata girke girke da gyaran gida na tarbar mijinta da bakinsa. "Ki barmu kawai Hanne muje ayita ta kare wallahi." Cewar wata kanwarta tana yanka ganyen salad din da ko wanke shi ba ayi ba. A tasu fahimtar sai an gama yankawa ake wankewa (datti da kwari idan akwai ba lallai su fita duka ba) "Ni fa jikina har tsuma yake Yasin. So nake kawai wata ta dan bangajeni ko da bisa kuskure ne inyi mata zugar zogale." Murmushi Hanne tayi ta kada kai "kar wacce ta kuskura ta taba kowa. Ina da maganin wannan rawar kan kuma zaku ce na fada muku. Su gama haukansu su hakura domin ni na tabbata ba zai taba kara aure ba." (Mutumin da take tunanin ba don rabon cikin da ta dinga samu a baya ana samun matsala ba da tayi rantsuwar bashi da lafiya. Duk wani abu da zata yi na daukar hankali sai ta ga kamar baya gani. Ta jima da sakawa ranta akwai matsalar da ta shafi lafiya a tare dashi.) Ana gama aikin 'yan matan suka yi wanka suka koma can gidan aka barta ita kadai. 'Yan kulle kullen magungunan mallaka da Gwaggo Jummai ta karbo mata ta zauna ta zuzzuba na abinci da na abin sha. Cikin irin juice din da yake girke mata a gidan ta bude daya ta tsiyaya ruwan maganin. Za ta kula ta tabbatar shi ya sha. 'Ba don mayen nan ba (Munzali) ai da kana gama ci zan saka ka zuwa yiwa Baba Sa'adu rashin mutumci' take zancen zuci ita kadai tana murmushi. Sai yamma likis taji dirin motoci wanda ya yi daidai da iface-iface daga bangaren iyayensu. Ta katanga ta leka ta hango kannenta mata da wasu cikin 'ya'yan Mal. Sa'adu ciki harda 'Yasshafa suna dambe. 'Yashshafa na kwance a kasa ana tumurmursata ko hannu bata daga ba. Wannan shiri ne na Deluwa akan suna isowa ta bari ya ga abin da ake mata. Fadan ma su suka takala. Motarsu na tsayuwa yaga 'yar wani kawun nasa kuma aminiya ga 'Yashshafa tana ihu tana tumami a kasa. Da sauri ya fito "ke Baito lafiya?" "Ina fa lafiya? Gashi can Anti (kalmar da bata taba fada ba) Hanne tasa kannenta suna nema kashe 'Yashshafa." Dogon tsaki ya ja ya juya yana cewa su Munzali su fara shiga gidansa yanzu zai fito. Bayan Baito yabi suna shiga katuwar tsakar gidan 'Yashshafa ta soma zunduma ihu. A guje ta ture 'yan matan da suke dukanta ta yi kansa da gudu kowa yana kallo. Saura kadan ta fada jikinsa ya dan ja baya tare da zaro idanu. "Ki ka tabani sai na wanka miki mari" Turus ta ja tunga ta tsaya. Deluwa taji wata irin muzanta da bata taba jiba. Da sauri ta bar wurin. Sauran iyayen nasu mata 'yan kallo ma kowacce ta sulale aka bar 'yan mata da kananan samari. "Ku kuma tunda karfi kuke ji kowaccenku ta samo tsintsiya ku share gidan nan tas. Ina nufin a shiga bangaren kowa da kowa har soron waje. Zani gida nayi wanka. Don Allah idan na fito ace min ga wadda bata yi ba taga yadda zanyi da ita." A gurguje suka dinga watsewa ya saki guntun murmushi. Wai 'Yashshafan da bata dade da daina yawo da majina bace aka koyawa irin wannan abin. Babu abin da bai ji ba a wurin Baaba Mari. Zai saitasu ne su duka su fita hanyarsa. Bangaren iyayensa ya wuce yana mai fadada murmushinsa. Babu kowa a falon ya shiga da sallama. Daga cikin daki Baaba Mari ta amsa ya bita can. Yana sallama ko amsawa bata yi ba ta soma fada. "Kaga abin da ka haddasa a gidan nan ko? Nayi nayi kazo sai yau kaga damar zuwa don ra'ayin kanka. To ka fadawa Hanne ta shirya ku koma tare zaman ya isa haka. Su Deluwa ma ka san yadda zaka yi dasu amma na gaji." "Ayi hakuri Baaba komai zai daidaita in sha Allahu." Kallonsa tayi ta danyi murmushi "haka nake so. Idan ka huta kazo ina da magana da kai." Tatsuniyar gizo bata wuce ta koki. Zancen Baaba Mari baya taba wuce kwakkwafinta akan silar arzikinsa. Ita dai burinta ta san me yake yi ko taji sukuni a zuciyarta. "Nima na taho miki da albishir. Ni da Munzali zamu bar kamfanin da muke yiwa aiki mu bude namu a Kano." "Cewa zaka yi an daina bani labarin gaibu. Zan ga kamfanin da idona kenan." Ta ce tana washe baki. "Kwanan nan kuwa da yardar Allah" ya amsa mata yana murmushi. "Kai Madalla..." Addu'a ta dinga binsa da ita kamar ba za ta daina ba. A can kasan ranta tana jin kamar an sauke mata nauyi. Tana son danta kuma babu abin farinciki sama da ganin dan cikinka ya zama gatan wasu ba ma kai kadai ba. Amma sabanin wasu iyayen ita sanin silar kudin shi ne kwanciyar hankalinta. Fargabarta kullum idan baya gari shi ne kada azo ace mata an kama shi tare da 'yan fashi ko barayi. Da wannan zulumi take kwana ta tashi. Ta sani cewa shi ma yana sane da rashin gaskata shi da tayi. Shi yasa tana dauko zancen yake nemo abin zillewa. Iyayensa maza kuma ko a jikinsu. Babansa ma da yake tayata damuwa ya sallamawa Ma. Sa'adu. Tunda ya ce a kyale shi ya san jininsu duk inda ya shiga ba zai yi abin assha ba. * Ya shiga gidansa ya sami bakinsa a zaune a falo su kadai. "Ina Hannen?" "Gani nan Yaya. Barka da zuwa. Ina kitchen na shiga hado abinci ne." "Amma ko ruwa da ba sai basu ba" "Ayya, ban ji shigowarsu ba." Zai sake magana Munzali ya kada masa kai sai ya fasa. Abinci ta fara kawowa Abbati ya ce ta bari suyi wanka. Dakunan da ya ce ta gyara ya leka babu wanda aka share. Da kyar ya hadiye fushinsa ya dauki jakar Qibdiyya. "Iya Kande muje bangaren Baaba ku kwana a can. Nan takura zaki yi. Qibdiyya ma za ta fi sakewa don akwai 'ya'yan kannena." Iya Kande ba musu ta mike. Ta kula da irin kallon da matar tasa take jifansu dashi na rashin maraba da zuwansu. Tare suka fita su duka sauran ma sun ce zasu gaishe da Baaba Mari. Sai da suka zazzauna a falonta tana ta haba-haba dasu sannan Abbati ya fita ya kira Hanne. Ransa a bace ya ce ya bata minti talatin ta gyara dakunan. Kuma ta aika musu abincin suci a can. Hada komai tayi ta kalli juice din da ta zubawa magani kamar tayi kuka. Malamin ya ce ta tabbatar shi ne abu na farko da ya fara sha bayan shigowarsa gida. Ta tabbatar wannan dai sai dai a hakura domin bata san waye zai sha ba idan an fitar. Na abincin ma a miya ta saka. Dolenta ta canja miyar don kada a sami matsala idan wasu suka ci. Tayi tsaki yafi cikin carbi tana jin haushin aikin da ya saka ta ga asarar kudi. Dadinta ma ba duka ta juye magungunan ba da ta sha bacin rai. * Lomar farko Abbati ya tauna kasa harda tsakuwa a cikin salad. Miyar kuwa tsabar tattasai ya yi yawa har wani daci take yi. Ga garin nasu ba wani restaurant zai samu ya sayawa bakinsa abinci ba. Allah Ya taimake shi ya riga kowa zuba abincin. Qibdiyya na kan cinyarsa zai bata sai ya ce bari ya dandana miyar ko da yaji. Munzali ya kalla yana neman ceto. Tuni ya fahimta ya karbi plate din hannun Shazali yana cewa yaji kamar muryar baban Abbati su je su gaishe shi. Audu dama bai riga ya dauka ba shi ma ya mike suka fice. Iya Kande ta kalli yanayin Abbati ita da take da wayo kuma ta fahimci wulakancin da Hannen tayi musu kafin ya shigo dazu. Idanunsa sun yi jazur ga jijiyoyin kansa sun tashi. "Sai hakuri baban Qibdiyya." Murmushi kawai ya yi ya shiga daki. Wurin da ya tabbatar ba zai ji kunya ba ya je ya zauna a gefen Baaba Mari. "Ni dai wallahi bana son wannan dabi'ar. Baka jin komai kake zama a jikina. Wannan ba sai ka sa a fara cewa rashin kunya ka koya a birnin ba." A da idan tayi maganar sake nanikarta yake sai ta ture shi. Yanzu kuwa murmushin yake ya yi. "Baaba ko zan sami abinci na bawa bakina?" Bai fada ba amma sarai ta fahimci me ya faru. "Kira Atine ta kawo abincin wurinta. Dama kannen naka sun yi muku abinci na ce su cinye kayansu kana da mata." Maimakon ya kira Atinen wadda dan kawunsu take aure ita ma a gidan aka yankar musu wuri sai kawai ya tafi da kansa. Tayi murnar ganinsa sosai ta kinkimo kwanuka ta biyo shi. Audu na hangosu ya baro su Munzali yazo ya karbi na hannunsa. Godiya Abbati ya yi masa ya ji dadi. A duniya bai taba ganin mutum mai saukin kai kamar Abbati ba. Ga kyau ga kudi kuma ga dangi rututu amma shi mutum ne mai yiwa kansa abu. Bai dade da fara aiki tare dasu ba ya soma zargin iyayen gidan nasa ko Sojojin baya ne (maza masu neman maza) saboda wasu abubuwa da ya gani. Har yau bashi da kwakkwarar shaida amma yana saka su a addu'a idan gaske ne Allah Ya yaye musu. Bai san kaddarar da ta kaisu ga wannan fitinar ba amma tabbas ya yarda da kyakkyawar amintar dake tsakaninsa da Munzali. Zama suka yi suka ci suka koshi sannan suka tafi gidansa. Hanne ta burbura gyara don ba wani abin kirki tayi ba. Har dare kuwa bata ga fara'ar mijin nata ba. Ana sallar Isha Audu da Shazali suka nemi makwanci. Abbati har lokacin yana ta kumburi akan abin da Hanne tayi musu. Munzali ya taso daga inda suka yi sallah a wajen gidan ya zauna a kusa dashi. "Mutumina inata jira ka gama shan kunun nan mu kira 'yar budurwar nan ta Diamond plaza naga kuma abin yaki karewa. Abin takaici ban san wadda ta burgeka ba da wurinta zan garzaya da kokon bara." Harara Abbati ya wurga masa yana dauke murmushin da ya soma jin Munzali ya gama ja masa rai akan nambar. "Kokon bara wane iri?" Dariya ya dinga yi masa "maida wukar idan bayi barar kai zan kawowa zuciyar ta ta." Abbati ya lumshe idanu "sunanta Farha. Ina jin sister din wadda muka bi ce." "Ai yarinyar ta bani tausayi. Tashi a gaban Asabe part two ba karamar jarabawa bace." Dundu mai shiga Abbati ya sakar masa a baya ya dinga shafa bayan yana harararsa. "Mugu kawai" "Naji din. Tunda kunnenka baya ji mu tafi a haka. Na fada maka Asabe ba abar rainawa bace. Iyaye sun fi gaban wasa tunda sune tsananinmu na samun rahama. Kuma banda abinka duk tsiya ai ta haifeka kai kuma ka haifa min Qibdiyya." Murmushi Munzali ya yi. Abbati daban yake har kullum. Shi ma Abbatin sai ya mayar masa yana ji a ransa ba zai taba jindadin rayuwar da babu Munzali a cikinta ba. "Allah Ya baka hakuri Mutumina na tuba. Yanzu dai matso mu danna kira.." Wayar da ta kasance mafarin komai! *** "Alhamdulillah ta sauka. Hajiya ku bamu kayan baby." Hajiyan Fatakwal ta sake fadada murmushinta sannan ta ce "Nos bani jaririn zan gyara jikana da kaina. Ita dai ga jakarta nan.." Jakar kayan Zara ta tura mata ita da Alh. Unais aka rasa mai iya mallakar kansa. Dukkaninsu murna ta cika su yau burinsu ya cika. Ganin wannan ranar ne ma ya hana Hajiyan sake tayar da zancen maganganun da taji Zaran tayi a waya. Nos ta koma cikin dakin haihuwar ta sami Zara tana rizgar kuka. Da gudu ta karasa gaban gadon duk da cewa ga likitoci biyu tsaye a kanta suna bata hakuri. "Me ya faru? Ina baby din? Ko wani wurin yana mata ciwo ne?" Ta dinga jera tambayoyi ba tare da samun amsar ko daya ba. "Ina kayan?" 'Yar dattijuwar likitan ta tambaya ranta yana baci da kukan Zara. "Kakar ta ce a in kai mata." Idanu cike da hawaye Zara ta dago kai ta ce "kin fada musu mace ce?" "A'a fa. Basu ma jira ba suka ce in dauko musu." "Na shiga uku. Doctor kin cuceni wallahi. Sau nawa kina ce min namiji ne?" Ta fada a zafafe tana wani kukan. "Haj. Zara ni ba zan baki hakuri don nayi kuskuren fadar jinsi ba domin ba ni na halicci abin da ke cikinki ba. Kuma tun farko muna fada muku ana iya samun canji." Zare safar hannunta tayi ta jefa a shara ta fice rai a bace. Yarinya kamar wannan za ta kawo mata raini akan abin da bata da hannu akan yiwuwa ko akasinsa. Tana fita Alh. Unais da Hajiyan Fatakwal suka matso. Ganin ba bebin bane a hannunta sai ya zaro kudi. "Dakta ga tukwicinki inji Imran dani babansa. Mungode sosai." Dan dagowa tayi ta kalleshi da kyau "wane Imran din?" 'Yar dariya mai fallasa tsananin farincikinsa "jaririna na ciki" "Oh..ashe fa Nos din bata fada muku ba. Ai mace ta haifa. Ko ba Zara Rabi'u ba?" In sun tanka to lallai kujerun wajen ma sun tanka.UWA UWACE...14 Batul Mamman💖 * Kafin isowarsu gida kishiyar Zara ta sanar da duka maaikatan gidan uwargidan Alhaji ta haifi da namiji. Labari da dumi duminsa yazo gareta daga wajen kanwar Alh. Unais wadda ta kasance aminiyarta cewa mace aka haifa. Dariyarta ta sha a daka harda rawa sannan ta fito rama wulakancin da Zara ta dinga yi mata da cikin. Dama saboda doki Alhajin da kansa ya tuka su zuwa asibiti ita da Hajiyan Fatakwal bai bari direba ya kaisu ba. Hancin motarsa na shigowa katafariyar farfajiyar gidan 'yan dattijan masu aikin gidan mata suka soma guda. "Allah shi raya Imarana magajin Alhaji Unaisu" inji mai girkin gidan. "Aminnnn" sauran suka amsa a tare. Hajiyan Fatakwal ta fito fuska a hade ta daka musu tsawa. "Ku matsa ku bani wuri duk kun cikawa mutane kunne. Waye ya ce muku namiji ne?" Sai suka yi tsuru-tsuru dasu. Hajiyan Fatakwal ta shige bangarenta ko waige babu balle ta sake kallon Zara. Jaririyar ma bata karbeta ba tun a asibitin ita suka bari ta dauko abarta. Ko tausayin yadda take daga kafa da kyar Alh. Unais bai ji ba ya ce tazo su tafi tunda kalau take. Hutun da ake yi bayan haihuwa tayi a gida don bai ga dalilin zama ba. Kasa magana tayi saboda yadda suka canja mata lokaci guda. Gashi ta sha dinki irin wanda ba a taba yi mata ba duk haihuwarta amma dole ta sauko jiki ba kwari. Alh. Unais bin bayan mahaifiyarsa ya yi suka barta da masu aiki. Laurat kishiyarta ta dubeta ta tabe baki. "Ya aka haihu a ragaya uwar Imran? Bari na dauko wayata don har na canja muku suna ke da maigidan zuwa Abu wa Ummu Imran." Tana dariyar shakiyanci ta wuce. Masu aikin ma ganin kamar Alhajin cikin fushi yake sai aka rasa mai karbar 'yar. Akwatin kayanta kawai aka daukar mata. Sai da kowa ya fice daga dakin ta kwantar da jaririyarta ta sami damar fashewa da kuka. Kirjinta har wani irin dokawa yake saboda bacin ran abin da aka yi mata tun daga asibiti har gida akan haihuwar mace. Bata yi mamakin ganin haka daga surukarta ba amma ta zata Alh. Unais yana sonta ko da bata taba haihuwa ba ma. Cikin radadin ciwo ta tashi ta tara ruwan zafi bayan kimanin minti talatin da ganin Hajiyan Fatakwal bata shigo ba. Jikinta ya yi tsami sannan 'yar ma tana bukatar wanka. Setin robor wankar jaririyar ta dauko ta ajiye a dakinta daga bangaren da yafi kusa da bandakin. Haka ta dinga dibar ruwa tana takawa da kyar har ta ajiye komai a wurin. Ta tashi za ta dauko bebin kafarta ta turgude ta tale gabadaya. Wata irin razananniyar kara ta saki lokacin da dinkin da tasha wuyarsa ya kece kyat! A wurin ta fadi jini na zuba cikin dan kankanin lokaci ta fice hayyacinta. Maryama da kannenta sai karfe shida suke tasowa daga islamiyya. Basu da masaniyar Mummyn tasu taje asibiti har ta haihu. Bakwai da rabi suke tafiya makarantar boko daga can su wuce islamiyyar. Mas'uda ce ta fara shiga falon Zara daukar wani abu taji kukan jariri. Da gudu ta karasa ciki ta hango jaririyar akan gado tana ta tsala ihu ga mahaifiyarsu kwance a kasa. Kanta tayi ta dinga jijjigata amma ta kasa tashi sai da kyar ta ce ta kira Hajiyan Fatakwal. Kafin wani lokaci dakin ya cika da 'ya'yanta sai Alh. Unais da Hajiyarsa. Masu aiki ne suka taimaka mata tayi wanka da kyar jikinta babu kwari. Duban yanayinta Hajiyan Fatakwal tayi gami da yin karamin tsakin da ya shiga kunnuwan mutanen dakin. Zara bata da hankali a ganinta. Irin maganganunta na rannan a waya su suka tabbatar mata da haka. Tayi mata lamuni ne dama albarkacin cikin da namiji da ake tunanin za ta haifa. Amma tunda abu yazo da haka ta sami damar raba danta da bakar kadara irin wannan. Dinbin asarar da Zara ta saka Alh. Unais akan hasashen gaibu ba kadan bane. Bakin gadon ta samu ta zauna ta dora kafa daya kan daya. Hannuwanta dake dauke da zobban gwal ta dauko guda ta nuna Zaran dashi. "Wai har yanzu baki sanar da kowa haihuwarki cikin danginki bane?" Gabanta ne ya yanke ya fadi ta kalli Hajiyan a tsorace "zan kirasu." "To ya dai kamata. Ba zai yiwu bane ace duk haihuwa sai dai ayi miki komai a nan. Dubi yadda ki ka fadin yanzu har dinki ya bude. Ya dace iyayenki su dinga tabuka nasu kokarin komai talaucinsu." "Umhumm" Zara ta furta kamar taci madaci. "Da dai nayi wa Unais magana akan daga can su samo miki mai zama har kiyi arba'in, to amma tunda ga wannan lalura da dole sai an sake miki dinki gara ki tafi gida. Kira min maman taki nayi mata magana." "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Zara ta furta da dan karfi hannunta akan kirji "gida fa ki ka ce Hajiya?" "Akwai matsala ne? Gidanku fa nake nufi." Zara ji tayi ta gwammaci kar a turo kowa tayi aikin komai na jegonta da kanta akan dai ta koma gida. Ta zauna da Innayo a wannan dakin da iskarsa ma bata mata dadi? Tunanin kadai ya sake dagula lissafinta. "Hajiya ki barni a nan zan iya..." Hannu ta nuna mata fuska a hade "bana son wata magana. Ko akwai magana ne?" Ta dubi danta. Kai ya girgiza don shima haushinta yake ji "yauwa to ki shirya direba sai ya mika ki yanzu. Kar ki manta da batun dinkin dai." Jikinta ya yi sanyin da ko baki ta kasa motsawa. Wane irin wankan jego zata je gida haihuwa ta biyar? Anya ba za a zata auren ya mutu bane? Babu sarki sai Allah dolenta ta shirya 'yan kayanta ta lallaba zuwa dakin maigidan. Tare da Laurat ta same shi ta nuna tana son magana dashi ya ce Bismillah. Laurat ta kalla ya hade fuska kuwa. "Kin kuma yi kadan ki zo ki sameta kiyi tsammanin zan ce ta fita saboda ke." Laurat ta murmusa tare da mikewa. "Kila sirri ne bari na baku guri." "Dawo ki zauna nace." A fakaice ta yiwa Zara gwalo ta koma kusa dashi ta zauna. Kirjin Zara ya dinga harbawa saboda tsananin bacin rai amma haka ta danne. "Uhmm dama cewa nayi kayan bebi din kadan ne unisex duk na maza ne. Ko za ka bani kudi...." "Ba zan yi asara ba. Ki saka mata duk wadanda aka farke kafin na sami sararin sayan na matan" Gyada kai tayi tana kokawa da hawayen da bata son zubarwa a gaban kishiya. "To in dauko maka ita kayi mata huduba?" "Idan kin je gida kakanta ya yi mata ya kuma saka mata sunan da yake so." Hannuwanta ta dunkule har suka soma zafi saboda rashin gudun jini. So take ko ta halin yaya ta farka daga mafarkin da take yi. Lokaci guda mafarkinta ya sauya game da haihuwa. Ta saka rai za ta haihu su dawo gida miji yana nan nan da ita sai gashi ko mutum daya bai karbi jaririyar ba cikinsu. Duk rashin kunyarta bata san da idon da za ta kalli Innayo ba. Asibitin da ta haihu ta ce da direban ya ajiyeta suna fita. Da kafarta ta kai kanta wurin likitar da ta gama yiwa rashin kunya ta nemi a dubata. Duk irin haushinta da likitan take ji sai da ta tausaya mata. Mirgina kai kawai ta dinga yi hagu da dama tana hawaye da ake sake yi mata dinkin. Azaba ce kan azaba don ta gwammace ace sake haihuwa tayi akan wannan wahalar da bata da na biyu. Ana cikin yi tana jin kukan jaririyar da har yanzu ko wanka ba ayi mata ba. "Wai ina 'yan uwanki ki ka dawo ke kadai?" "Wayata ce babu chaji shi yasa ban kirasu ba" ta iya cewa tana kawar da kanta don kar a gano karyarta. Likitan bata takura ba amma jikinta ya bata akwai wata a kasa. Boye mamakinta tayi lokacin da Zara ta ajiye kunya a gefe ta roketa ta bata gado ko da na kwana biyu ne. Tunda file dinsu kudi kawai Alh. Unais yake sakawa bata da matsalar biyan kudin komai. Kudin hannunta ko dubu biyar basu kai ba saboda baya basu kudi a hannu sai dai ka gani a kasa. *** "Wai Ayaah ta zo inji Dani." Muryar wani dan almajiri ya karade tsakar gidan Honorable. Murja ce ta amsa masa saboda tana wanki a wurin. Dakinsu ta shiga ta sami Ayaah ta tura earpiece a kunne tana fama da koyon turanci a gidan rediyo. Makarantar gwamnati suke zuwa turancin babu sosai gashi tana son cigaba da karatu. Shi ne ta daukarwa kanta sauraron wani shiri da ake darusan turanci a gidan rediyo. "Helflesslyyy" "Aimlesslyyy" "Hofelesslyyy" Take ta maimaita kalmomin da ake fada da kokarinta na ganin ta tace turancinta. Sai karya murya take tana magana da hanci. Duka Murja ta daka mata a cinya ta tashi a zabure. "To tashi alhudahuda ana kiranki a waje. Ki je ki kore shi kafin Baba ya dawo wallahi" "Daga sallama sai kora saboda ba wurinki yazo ba?" Ta maida mata a tsiwace. "To kar ki kore shi. Ki bari Baba ya dawo ya tarar da kasurgumim kafiri a kofar gidan nan ki sha mamaki." "Kafiri?" Ayaah ta ce tana kai hannu kirjinta ta dafe. Murja bata amsa mata ba sai ta janyo hijabi ta dora akan rigarta ta fita da sauri. Ko ba Baban nasu ba bata so Anti Hasiya ta dawo daga wurin Innayo da ta sake tafiya yau ta ganshi. Karshenta ta fadawa baban nasu don ayi mata fada tunda ba kaunarta take ba. Tuno fadan da tayi mata rannan tayi ta dan yi murmushi. Ita bata ma san laifin da Antin tayi musu ba har ta tashi da tsanarta. Lallabawa zata yi ta soma yi mata biyayya ko don kayan daki... Ido, baki da hanci duk ta bude tana kallon Danliti a kofar gidansu. Bai tashi zuwa kawo jakar ba sai da aka sake samun rantsatsiyar motar kece raini a garejinsu. Ya sha shadda mai kyau sai daukar ido take. Kan nan nasa a kwance luf yana sheki ya sha man alayyadi wanda ya hada da ruwan turare dan d'uri domin ya danne warinsa. Shi da kansa ya san ya yi barna a zuciyarta saboda yadda ta kasa mallakar kanta a gabansa. "Malama Ayaah sai ki ka ganni a kofar gidanku ko?" Muryar da ya daddage ya kashe domin ta kara dadi ta shiga kunnuwanta wanda tsabar rudewa sai cewa tayi "cewa akayi in zo in ji Dani." Kansa ya shafa da dan murmushi "sorry you know rannan sunanki na tambaya ban samu na fada miki nawa ba muka rabu. Suna na Abubakar amma a gida kakanni suka saka min Danliti. Abokai na kuma suke cewa Dani. Sunan nawa dai na san ba zai miki dadi ba." "Nooo" Ayaah ta cije baki wurin fadar kalmar saboda ya gane ita ma ba baya ba a turancin. "Sunan da dadi mana. Dad dina sunanku daya amma Hon. Habu ake kiransa shi ma." "Nice" inji Danliti. Jakar ya mika mata tare da zuba mata karairayin yadda ya dinga nemanta bayan ya ganta a motarsa. Abin ya so daure mata kai saboda duk lissafinta jaka tana adaidaita sahu. Za ta iya rantsuwa bata shiga da ita motar ba. Saurin kawar da tunanin tayi tunda dai ta dawo sannan ga Dani a gabanta. "Ban san me ki ka yi min ba Malama Ayaah amma tunda muka rabu na kasa sukuni. Zuwa nayi da bakinki kiyi min bayani." Wayyo Allah. Ko balam-balam ba za ta gayawa Ayaah kumburi ba a wannan lokaci. Tsaf ta fahimci inda ya dosa. Jirkita idanu tayi tana masa fari. Zuciyarta fes sai farinciki Allah Ya kawo mata mijin aure tayi ta bar gidan nan. "Ni ban maka komai ba" ta fada tana dan tura baki. Danliti ya kunshe murnarsa zai mata magana wayarsa ta shiga ringing. Saboda rayuwar karya da cutar 'ya'yan mutane da suka saka a gaba wayar mai tsada ce. Dauka ya yi ya kara a kunne maganarsa na fita da sigar rarrashi ga wanda ya kira shi. Ayaah ta kusa kuka da hirar tasa tayi gaba ta gane da wa yake magana. "Kiyi hakuri ba dadewa zan yi ba." "Ba shekaranjiya na tura miki 50k ba?" "To, to...naji kiyi hakuri. Yadda ki ke so Honey haka zan turo." Ya dan saurara kadan sannan ya ce "har dubu dari biyu? Ok zan miki transfer." Wayar ya tura aljihu idanunsa a kanta yana murmushi. "Sorry wife dina ce." "Ok" ta amsa da yanayin ko in kula. Muryarsa a sanyaye ya ce "Ku mata sai da lallabawa. Bakwa son gaskiya ko kadan. Da an so nuna muku laifinku sai ku hau bori." "Wasu matan dai ba duka ba" Dariya ya yi "dama kun saba karewa juna." Wata wayar ta sake shigowa ya dauka murya a sake. "Gambo ka siyo min abincin?" "Yauwa dama cewa zan yi ka biya Yahuza suya tsire ka siyo na dubu biyar saboda tayi baki kuma bata yi girki ba. Abincin kuma duka friedrice mai hantar nan suke so plate takwas. Sai coleslaw da lemon kankana." Yawun Ayaah ya tsinke saboda tsabar yadda ranta ya biya har kamshin abincin kwakwalwarta ta zayyano mata. "Sorry fa na cika ki da waya. Yau Madam dina ke jin rigima shi yasa nace ku mata sai da lallabawa." Daga iya bayaninsa ta fahimci kamar baya jindadin abin da matar tasa take yi masa. Ga kudi zai tura ga abinci zai saya. Kuma a haka aka sake masa flashing ya dauka ya sake bata hakuri yana cewa yanzu zai tura. Danne danne ya yi a waya ya sake yin alamun kira ya ce ya turo. Da ya gama gabadaya ya sake fuskantar Ayaah. "To Malama Ayaah ni zan gudu gashi baki bani amsar tambayar da nayi miki ba." Wayarsa ce ta hau ruri ba kakkautawa tana soma magana. Da sauri ya dauka ya sake bada hakurin cewa gashi nan zuwa. "Madam ta matsa kambon zan tafi sai na sake kawo miki ziyara." Ranta bakikkirin da takaicin wannan mata mai hana ruwa gudu ta ce, "tafiya ko ruwa baka sha ba?" "Kar ki wahalar da kanki akwai a mota." Wata wayar ta shigo wannan karon daga garejinsu. Dauka yayi abokin aikinsa na sanar dashi mai motar yazo dauka amma an fada masa anje testing. Hakuri ya kuma bayarwa yadda ba za ta gane ba. Bayan mutumin ya ajiye wayar ya cigaba da magana ba tare da ya cire daga kunnensa ba. "Don Allah kiyi min tuwon ko leda biyu ne." "Haba Honey. Ko baki da lokacin yin miya ni dai kiyi tuwon zan yi miyar da kaina ko in ci da mai." "Babu komai Allah Ya kaimu weekend din." Ayaah taji tausayin Danliti kamar tayi kuka sannan ga mamakin saukinsa. Ji yadda yake bin matar tana wulakanta shi. Idan ita ta same shi ba zai rasa komai ba. Samun kanta tayi da tambayarsa. "Tuwo ka ke so ne?" "Na cire rai Madam ta gaji." Ayaah taji kamar ta nemota ya shako wuyanta. Sosai take jin tausayinsa. Ji wannan bata show ta hana shi hira da ita ma. Tayi sa'a ya karbi nambar wayarta dai. Yana tafiya don karfin hali ta ce, "Idan na shigo gidan nan sai kin raina kanki." Shi kuwa Danliti yana haduwa dasu Rabilu ya labarta musu yadda suka yi. "Irinsu zuma ne da wuta ake cinsu. Na darsa mata tausayina da yawan arzikina ga hakuri. Indai ba fyade kake son yiwa mace ba to da irin haka sai kayi mata wayo ta kawo kanta har ta roki kayi eh ya ne..." Dariya suka kwashe suna tafawa. Danliti ya kira matarsa da ko shekara basu yi ba ya kasheta da kalaman soyayya da alkawarin taho mata da tsire saboda laulayi da take. "Mugu dan masara. Ka gama da wata ka koma lallaba ta gida." Inji Rabilu "Ta gida ce dahir kaji. Wadannan kawai a samu garabasa ne a wuce wajen. Bari ma na tashi sai gobe." *** "Haba Malam. Wannan irin sakin baki tun ban kira ba." Cewar Munzali yatsansa na laluben nambar Mardiyya "idan ka fiye washe baki zan fasa kira sai gobe. Ina tsoron kar ka zubar mana da girma garin rawar kai" Ba don yana tsoron kar Munzali ya yi masa sanadin rasa abin da zai hada shi da Farha ba da a take zai rama. Kwafa ya yi kawai. "Fadi ko kaji dadi" Munzali ya sake kokarin tunzura shi. Abbati ya nuna masa gidansa ya ce "Ka kira ko ka kwana a waje yau. Ai dai ka san wancan gidana ne." "Gidan Hanne da 'Yashshafa ba." Karar da wayar ta soma yi alamun kiran ya shiga ne ya dakatar da Abbati daga bashi amsa. Mardiyya na taya Sauda tsifa kiran ya shigo. Har yanzu basu san me yake faruwa a gidan ba sama da abin da Suhaib ya fada musu. Wayarta da Saudan ke dannawa ta hau kuka ta mika mata. Ganin bakuwar namba sai ta dan jinkirta dauka har ta kusa katsewa. "Salamu alaikum" ta ce da siririyar muryarta. Munzali ya dan numfasa kafin ya amsa da murmushi "amin wa alaikum salam. Diamond girl ce?" Mardiyya ta tabo Sauda ita ma ta taso don jin waye mai kiran. "Diamond girl kuma?" "Eh. Mardiyya wadda muka hadu farkon satin nan a Diamond plaza Kaduna." "Waye don Allah?" Ta tambaya duk da ta so gane muryar. Sai dai bata fatan wata matsala ta taso sakamakon tsayuwarsu yin hoto a jikin motarsu. Abin da ta guda ne ya faru taji ya ce "dama ranar da ku ka yi hoto a jikin motarmu yayana yana ciki. Shi ne ya ce na kira ki zai yi miki magana. Shi ne ma dalilinmu na biyoki shagon." Mardiyya taji cikinta ya kulle. Daga daukar hoto abu na neman zame musu matsala kamar sun saci motar. Jiki a sanyaye ta ce "Hoto ne fa kawai muka dauka." "Mirror din bangaren direba yana rawa, motar ma a gareji ta kwana." Abbati ya zungure shi da gwiwar hannu yana balla masa harara "Sannu kanya uwar zuba. Haka kawai ka ke yi musu karya" Sai da ya toshe kan wayar sannan ya ce "ka kyaleni nayi yadda nake so. Kai dai ba Farha kake nema ba? To za ka samu in sha Allah." Cigaba ya yi da wayar sai yaji murya daban tana cewa "daga cin arziki sai ku ce an taba mirror? Ko an gaya maka ba za mu iya biya bane" "Ke kuma ya sunanki?" "Sauda" ta amsa a tsiwace "ai ba mu ya kamata ku nema ba. Mu ma muna da yayye sai mu hadaku dasu." Munzali ya kunshe dariyarsa. Da gani 'yan matan a tsorace suke amma suna gudun nunawa don kada matsalar ta girmi yadda take yanzu. "Zan ma fi son haka. Hadani da babba sai na bawa yayan nawa." Kashe wayar Sauda tayi ta rike haba "Mardiyya me yasa kika basu nambarki?" "Biyoni suka yi" ta iya cewa ba tare da tayi bayanin abubuwan da Mamanta tayi musu ba. Duk lalacewarta da kunya ta dinga kwaye mata baya. "To mu kaiwa Ya Suhaib?" Mardiyya ta mike da sauri "kina bashi zan tafi na kwanta. Haka kawai ki sa ya shekara yana yi mana mita" Dariya suka zauna yi wayar ta kara shigowa. Da sauri suka kaiwa Farha a kitchen. Takaitaccen bayanin kiran suka yi mata sannan ta amsa wayar da sallama. Sunanta Munzali ya tamnaya tana fada ya maimaita da cewa, "Ya Farha" kamar yadda yaji Mardiyya ta fada kafin ta bata wayar "ga yayana Abbati" ya karawa Abbati a kunne ya tashi. "Ya Farha" Abbati ya ambaci sunan a kasalance. To ita dinma kamar kannenta taji tsoron wannan binbini. "Yanzu shi kaninka da ya hadamu da kai ba arziki bane ace yana da motar da za a dauki hoto a jikinta?" Murmushi ya yi yana jin jikinsa sakayau kamar zai tashi sama. "Ni ban ce daukar hoton laifi bane." "To menene? Su Sauda sun ce wai mirror yana rawa. To ko dai motar gidanku ku ka dauko ta sami matsala ku ke neman kudin gyara a jikinmu? Ko irin 'yan karyar nan ne masu aro mota su je burge 'yan mata? Duk fa mun san halin ire-irenku." Sosai yadda take magana ya sanya shi nishadi. Jinginar da kansa ya yi da bayan bishiya yana sauraron muryar dake zagawa sassan jikina. "Da gaske Ya Farha." "Ka dena ce min Ya Farha ni ba yayarka bace." "Allah Ya Farha?" Abbati ya kuma fadan sunan da 'yar dariya. Ita ma Farha sai ta sauko da ta fahimci kamar zolayarta ma yake yi. "Ya sunanka?" "Kina iya kirana Abbati." "Sai dai in ce maka Uncle Abbati. Wai don Allah me yasa ka kira kanwata." "Neman rigima kawai Ya Farha. Yadda motar ta burgeku shi ne na fito ko Allah zai sa nima na burgeku ayi hoton dani sai kawai ina bude kofa ki ka gudu." Yana son ya kara da cewa ta gudu da zuciyarsa ya fasa. Ba yanzu ba. A gaba kadan za ta gane matsayin da ta taka farat daya a zuciyarsa. "Idan na baka hakuri magana za ta wuce? Idan aka ji a gida fada za'a yi mana." "Tun ranar ma na hakura Ya Farha." Dan hade fuska tayi ta ce "nifa ko rabin shekarunka ban yi ba ka ke ce min yaya." "Kin sanni ne? Ko kin san shekaruna?" "Na ganka lokacin da ka bude motar." "Wane irin mutum ki ka gani?" Ya tambayeta da dan tararrabi a muryarsa. "Mai kyau" ta ce kai tsaye. Zuciyarsa dokawa tayi da abin da bai san sunansa ba. Dumi ne ya lullube shi tun daga tsakar kansa har tafin kafa. Ita Farha tunda take bata taba hira makamanciyar wannan da saurayi na shi yasa take fadin duk abin da yazo bakinta. Kalmar karshe ce dai sai da ta fito ita kanta taji nauyinta. A karon farko taji kunya ta mamayeta. Harshenta ya yi nauyi a bakinta da kyar ta juya shi ta sake hada wasu kalmomin da suka fito kamar mai rada. "Ba haka nake nufi ba." "Bani da kyau kenan? Allah Sarki Abbati..." ya furta yana mayar da muryarsa irin ta mai shirin kuka. Da sauri Farha ta ce "kana da kyau mana." "To za ki yi hoton dani? Please Ya Farha." "Idan Allah Ya sake hadamu." Ta ce tana murmushi sosai. "Zai hadamu. Ina ji a jikina in sha Allah idan na sake zuwa Kaduna zan nemeki ki cika alkawari. Wace kala ki ka fi so?" Duk da ta soma rikicewa sa zantukansa amma ta bashi amsa. "Orange" "Ina fatan ganinki cikin kaya masu wannan kalar a haduwarmu ta gaba. Mu kwana lafiya Ya Farha." Da kyar ta iya cewa "Allah Ya bamu alkhairi." Kafin ya ce Amin ta kashe wayar. Juyawa tayi za ta bar kitchen din ta hada ido da kannenta sun zuba mata nasu idanun. "Ya ku ka kare ne Ya Farha?" Cewar Sauda tana kanne ido. "An kare a matakin ina karbar wayar nan in tura number dinta mana" Mardiyya ta bata amsa. Kasa ce musu komai tayi kuma bata ji tana son hana a tura nambarta ba. Bata san me take ji ba har suka fice suja barta. Haka ya karasa daren har ta kwanta tana tariyo hirarsu tana murmushin da bata san dalilinsa ba. Could this be love knocking at her door? Da ta kwanta ranar mafarkin Abbati ta dinga yi a daidai lokacin da ya bude motar nan ya fito suka gudu. Bambamcinsa da haduwarsu ya zahiri shi ne (Ya Farha) da ya dinga kiranta... * Bacci yaki zuwa kamar yadda Shazali ya yi niyya saboda aikin tunani da ya bawa kwakwalwarsa. Neman hanya yake komai kankantarta da zai dauwamar da su Munzali akan sana'ar da ya zama sanadin fadawarsu gareta. Abbati bashi da hankali da har zai tunkare shi da maganar tuba. Dariya ce ma ta taho masa da ya tuna yanayin fuskarsa a jiya da ya fada masa. Idan sun san wata basu san wata ba ai. Shi mutum ne da zai iya komai domin biyan bukatarsa. Da ya ce zai biyosu nadin sarautar tudun dafawa yazo nema kuma ya dace da samu. A sanin da ya yiwa Munzali tun kuruciya ya fahimci shi yaro ne da ya rasa sa ido da kulawar iyaye. Sai aka yi sa a sakacinsu ya cire masa tsoron sab'a musu da kaunar faranta musu. Yana da yakini mai girma cewa ko a gaba kwai ya fashe daga Munzalin har iyayensa ba za su ji ciwo kwatankwacin na Abbati ba. Sudaddiyar habarsa da babu alamun gashi ya shafa, murmushi na mamaye fuskarsa. Ya shiga har falon uwar Abbati. Kirjinsa har dokawa sai da ya yi saboda tsantsar haiba da tawali'u irin na matar. Bai hango komai tattare da ita ba sai kyawun hali saboda yadda ya kula mutan gidan suna shiga taitayinsu a gabanta. Kudin danta zai iya saya mata rigar mutumci amma bai isa ya saye shi duka ba. Dole ne ma kyawawan halayen da a haduwar farko ya tsammaceta dasu su taka tasu rawar. Mahaifinsa kuwa tare suka yi sallar magariba da isha'i a masallacin kofar gidan. Bai yi masa kama da mutane masu hayaniya ba. Ya dai karanci akwai shakuwa irin ta uba da babban dansa a tsakaninsu. Shi ma din zai iya cewa ba kudi kadai ya kawo musu wannan jituwa ba. Uban yana kaunar dansa. Kuskuren iyayensa daya. Almajiranci da suka tura shi! A gefe guda kuma ga kawunnai da 'yan unguwar da zai rantse da Abbati zai tsaya takarar siyasa baya jin za a sami kuri'ar wata jami'ar daban da tasa daga garesu. Karara ake ganin yadda kowa yake kaunarsa. He has everything to loose idan asirinsa ya tono. Kwafa Shazali ya yi ya zauna jiran shigowarsu. Lokaci bai tsawaita ba Munzali ya shigo falon zai wuce dakin da ya zama nasa duk lokacin da suka zo tare. Bai kula da Shazali a falon ba saboda an kashe fitila mafi haske sai wata mai dan duhu daga can gefe. Hankalinsa yana can duniyar tunanin samun masoyiya da Abbati ya yi. Dadi yake ji tare da fatan Allah Ya daidaita zukatansu ita ma ta so shi. Da sai tafi kowace mace dacewa da mutum mai kyaun hali da iya kulawa da wanda yake so. Gashi ta zo a daidai lokacin da zasu gyara rayuwarsu. Babu abin da zasu ce da Allah sai godiya. Yana shiga daki ya yi shirin bacci don ba zai jira shigowarsa ba balle su tsaya hirar da zai shiga hakkin Hanne. Rabin awa da shigowar Munzali sannan Abbati ya shigo. Fuskarsa bata yi kokarin sakaya farincikin da ya lullube zuciya da ruhinsa ba. Hirarsa da Farha ya dinga tariyowa yana murmushi shi kadai, sai ka rantse hirar soyayya ce. Karon farko a rayuwarsa da yaji zuciyarsa tayi nauyi saboda cika da soyayya irin wadda ta halatta tsakanin masoya. Feeling ne da yafi karfin kwatancen baki ko rubutun alkalami. A gareshi Farha tamkar numfashi take tun yanzu. Yana ji a jikinsa ita din alkhairi ce mai dorewa a rayuwarsa. Zai yi bakin kokarinsa su gyara rayuwarsu shi da Munzali domin tsaftatacciyar rayuwa yake yi musu fata daga wannan lokaci. "Abbati in babu damuwa ina son magana da kai." Muryar Shazali ce ta katse masa tunanin da yake neman kaishi duniyar taurari shi da Farha. Cak ya tsaya ya juya bangaren da ya ji muryar domin da fari bai kula yana wurin ba. Wayarsa ya miko masa ya karba sai dai ko sakan talatin bata yi ba a hannun nasa ya saketa a kasa a gigice. "Shazali meye wannan?" Ya furta a hankali baki na rawa. Guntun murmushi ya yi kafin ya ce "Abbati ne da His Excellency gwamnan..." Toshe masa baki Abbati ya yi da sauri yana cewa "Baka da hankali ne? Gidana ne nan fa akwai mata ta a ciki." "Oh haka ne fa" Shazali ya ce da sigar shakiyanci "gudun kar ta ji ta fita ta tona maka asiri a gidanku sai ka bani aron lokaci muyi magana." Da wani irin yanayi mai ban tausayi ya nuna kansa "Ni za ka yiwa haka? Shike nan mu fita daga waje" Abbati ya ce yana yin hanyar kofa a yayinda duk wata na'ura mai sadar da sako a jikinsa ta dauki zazzafan caji. Abinka da kauye goma saura na dare amma kusan babu kowa duk an shige gida. "Menene ma'anar wannan vidiyon? Jiya baka nuna min komai na rashin dadi ba har na baro gidanka" Abbati ya tambaya suna tsayuwa a bangaren hagu da gidansu jikin wata bishiyar dabino. "Saboda ban riga na fahimci sagegeduwar da kake son ku yi min bane. Abbati kai da Munzali ba za ku iya barin sana'ar nan ba. Nayi magana da Mr. Lewis abin ya wuce tunaninka." Bai sani ba da kirjinsa da zuciyarsa waye ya kumbura. Shi dai ya ji kamar baya iya jan numfashi saboda takurar da kirjin ya yi gabadaya. Yawun bakinsa ya kafe da kyar ya iya tambayarsa cikakken bayani. A take Shazali ya hada masa kaso sittin na gaskiya ya gwama da kaso arba'in na karya aka tashi dari. "Jiya kana tafiya na fadawa Mr. Lewis yadda muka yi da kai. Idan da kaji irin masifar da ya dinga yi min da barazana sai ka tausaya min. Abbati da manya kuke mu'amala. Mutanen da suke juya kasar nan tamkar kwallon wasan yara. Kun gama sanin sirrinsu kila harda wanda bai shafi abin da kuke yi tare ba. Shi ya turon bidiyon nan da wasu ma na Munzali" Jikin Abbati ya soma sanyi domin ya fara dauko hasken inda maganar ta dosa. "...janyewarku a yanzu da kuke ganiyar samun kudi da yin suna a tsakaninsu ba komai zai harfar ba sai zargi inji Mr. Lewis. Mutanen nan zasu iya tunanin ko abokan hamayyarsu a siyasance ko kuma ta bangaren kasuwanci ne suka biyaku domin ku tona musu asiri. Idan kuma gajiya kuka yi to ka sani sune a sama. Gajiyawarsu ce gajiya ba taku ba. A takaice ina jiye muku tsoro domin tabbas rayuwarku tana daf da zuwa karshe" dan shiru ya yi yana nazarin Abbati wanda banda bugun zuciya komai ya tsaya masa. "Maganar daya ce wadda gudun faruwarta ya kawoni gareku yanzu. Zaku iya daina amsa kiransu to amma wallahi babu abin mamaki idan aka ji kun yi hatsari ko gobara an sallaci gawarku. Ko kuma wadannan bidiyon su zaga danginku. Kar kaji haushina. Turo ni akayi na yi muku barazana idan ba haka ba harda ni zata kwabewa. Kuma yau ko mutuwa kuka yi sirrin nan dole ya fito domin maganar gaskiya mutanen nan suna da makiya. Kuma makiyan nasu da hannunsu yawanci wurin fitar musu da sirri. Wannan bidiyon ma a wurin mai kawo abincin hotel din da kuka je aka samu. Na san ka fi Munzali nutsuwa shi yasa na zabi fada maka. Abbati guguwar da ta tunkaroku da wannan niyar taku bala'i ce..." Kwalla ce mai zafi ta cika idanun Abbati har ta soma saukowa bai sani ba. Ko gezau bai ji ba da ya ce za'a iya kawar dasu a doron kasa. Amma maganar tonon asiri ta kada hanji da hantarsa. Kafin kowa ya fado masa a rai sunan mahaifiyarsa ya soma amsa kuwwa a kwakwalwarsa. Wallahi ya gwammaci tayi arba da gawarsa da dai ta sami labarin yadda yaci zamanin kuruciyarsa da silar arzikinsa. Zuciyarta za ta iya bugawa amma ba wannan bane kadai matsalar. Yana ji kamar ko a lahira Baaba Mari ba za ta yarda ta hada hanya dashi ba bare har ta yafe masa ya sami rahamar Allah. Zinar da bata so yake aikatawa. Mafi muninta ma. Sannan ya kasance bashi da maraba da karuwa mai biyawa mutane bukata a biyata. Budar bakinsa zai yi magana sai hawaye ya soma ambaliya a kuncinsa. Bai damu da hana zubarsu ba. "Ni kadai zan iya zuwa?" "Me kake nufi?" Abin da zuciyarsa ta karanto masa a matakin karshe ya furta. Abin da yake jin shi ne karshen soyayyarsa ga Munzali. "Sirrina iyayena kadai zai batawa rai amma kuma ba ni kadai suka haifa ba. Zuwa wani lokaci zasu iya mantawa. Amma Munzali uba ne. Ba Qibdiyya ba ina jin har jikokinta idan ta sami mai aurenta kenan sai an goranta musu." Shazali ya murmusa yana danne dariyar da ta taho masa. A wannan fagen karan Munzali ya kai tsaiko amma Abbati ne tauraron shi ma ya sani (wa iyazu billah). Bashi da asara indai Abbatin zai cigaba da zuwa yana samun nasa kamshon kudin. A munafunce ya ce "Ayi haka Abbati? Wahalar za ta yi maka yawa." 'Qibdiyya batayi laifin amsa sunan diyar fasiki mai neman maza ba' wata karamar murya ta jaddada masa. Sannan yana da yakinin cewa idan Munzali ne a wannan gabar abin da zai zaba kenan. 'Kila ya hada da kaiwa Shazalin naushi ma kafin ya taka martabar' wani sashen ya ankarar dashi. Shazali shigewa ya yi gidansa bayan ya fada masa cewa gobe da sassafe zai bar garin don ba zuwa ya yi domin ayi wani nadin sarauta dashi ba. Bai damu da hana shi shigar masa gida ko jin zafin maganar ba. Masifar da ya kunna masa tafi komai daga masa hankali. Bayan shekara da shekaru cikin jindadi da fantamawa da kudi Abbati ya sami kansa da shiga tsakar da kudi ba zai maganinta ba. Kuka ya soma a hankali har yaci karfinsa ya durkushe a wurin. Su suka cuci kansu ko rayuwar da aka jefasu a kuruciya? Sanda suka farga da illar abin kuma komai ya lalace sun saba. Ya san bai yi kuskuren ceton Munzali ba domin shi kadai ke fada masa yaji. Tunda ya samu ya amince zasu bar komai tare bai dace ya dawo dashi ruwa ba. Bayan shi Munzali bai dauki wani abu da daraja ba sama da 'yarsa. 'Shin akwai adalci idan na bari mutumcin uba ya zuba a idon 'ya kamar yadda na kakanta ya zube a idon dansa?' Ya furta daidai jin kunnuwansa a yayinda hawaye masu dumi suka makanta ganinsa. Runtse ido ya yi suka sauko zuwa kuncinsa. * Washe gari har akayi nadin a fada suka dawo nan kofar gidansu Abbati domin yin walima Munzali bai ga walwalarsa ba. Hasalima tamkar gangar jikinsa kadai ke tare dasu amma shi yana wata duniyar daban. Munzali sai ya takura shi ma fara'a ta dauke masa. Da suka shiga ciki ne a dakin Baaba Mari danginta suna yi masa addu'a ta tuntubi Munzalin game da abokinsa. "Kace masa ya saki fuskar don sarauta ba tana nufin dinke fuska kamar damammiyar fura ba." Tayi ne domin ayi dariya kuma kowa ya dara banda Abbatin. Allah Yasa fuskarsa nade take da rawani sai ya dan dukar da kai saboda dariyar tasu kuka ta kusa saka shi. Gani yake idan ya yi dariya tamkar yana maraba da cigaba da wannan sabon ne. Bai yi aune ba hawayen da bashi da niyar zubarwa suka soma diga a gaban farin rawaninsa. Munzali ya matso kusa dashi ya dago kansa sai kawai ya fashe da kukan. Wannan wace irin rayuwa ce suka tsunduma kawunansu ciki gashi fita ya zame masa matsala. Ta ina zai fara ambaton sunayen mutanen da ya sani ta wannan hanya? Waye zai yarda dashi kafin azo batun taimaka masa? "Don Allah Baaba a dan bamu wuri" cewar Munzali idanunsa sun kada sun yi ja. Bai san damuwar Abbati ba amma ya san cewa duk damuwar danuwan nasa tasa ce shi ma. Da kanta ta sallami matan dakin ana ta gulmar abin da ya saka shi kuka a wannan lokacin. Wasu har sun fara cewa dama akwai masu harin kujerar me yiwuwa asiri aka fara jefo masa. Jiki a sanyaye Baaba Mari ta ce "Me ya same ka har ka ke zubar da hawaye a gaban mutane haka?" Munzali ma zuba masa ido ya yi shi kuwa sai ya ce "Baaba ji nake dama ban karbi sarautar nan ba. Haka kawai hankalina bai kwanta ba ina ganin kamar wani nauyi na karba. Kasa daurewa nayi da na tuna abubuwan da Liman ya fada min akan hakkin mutane." Murmushi tayi ta koma ta zauna "Nauyi ne mana Abbati. Amma da yardar Allah da kuma addu'armu za ka rike amanar da aka baka. Kai dai ka yawaita addu'a da kuma kiyaye hakkokin Allah." Nasiha sosai ta dinga yi musu mai ratsa jiki har Munzali ya dinga jin muguwar tsanar kansa. Wannan mata mai kyaun hali ya cutarwa da d'a ta hanyar koya masa mafi munin zina. Kukan da ya dinga yi bai da alaka da zantukan Abbati don ko kadan bai yarda ba. Nasa laifin ne ya dame shi yaji kamar da biyu take magana. Da ta kare maganarta ta sako zancen hakkin Hanne. "Idan kun tashi komawa jibi ka tafi da matarka. Wannan zaman da take ya isa haka. Yana daga cikin dalilan da suke ta kawo rikici a gidan nan. Sannan kaje na yarje maka ka takawa Deluwa birki haka nan. Na gaji da shari'a ba gaira babu dalili." Dan murmusawa ya yi ya mata alkawarin cika umarninta sannan suka tashi zasu koma waje. A daidai soron da zai sadasu da matasan da suka yi dafifi a waje Munzali ya ce, "Ga fa mutanenka suna jiranka Ya Sardaunan Makaryata." Da sauri Abbati ya dube shi sai ya ga ya dinke fuska. "Ni kake kira makaryaci?" "Kar ma ka fara sha min kunu don ka san gaskiya na fada. Yadda ka ninke Baaba Mari ni ba za ka min ba. Tun fa kafin aje fada nake tambayarka damuwarka kaki fada yanzu ka zo kana zancen wai maganar Liman...maganar da ko awa daya ba ayi da yinta ba." Da yake bashi da kuzarin rigima da Munzalin sai ya bashi hakuri kawai. "Da ciwon kai na kwana ga case din Hanne da maganar Inna Deluwa da 'Yashshafanta..." "Duk kuma so kake na yarda da abin da ka ce ko? Zan kyaleka dai sai mun koma" "Nagode. Kuma Allah Ya kaimu abubuwa su daidaita sai na gurje bakinka. Wai ni kake kira makaryaci. Wallahi Munzali ka raina ni. Ko rawanin kaina bai isa tsorataka ba?" Dariya suka yi baki daya sannan Munzali ya daukesu selfies a wayarsa suka fita waje. * Kwana biyu da dawowarsu Kano Hanne taga canjin kulawa daga wajen Abbati. A nata tunanin ayyukan malaminta ne suke ci. A bangarensa kuwa ya zabi daukan shawarar Baaba Mari ta sauke nauyin da ya dauka na matarsa da mutane. Babu soyayyarta ko digo a ransa amma akwai kyautatawa. Yana sa ran samun canjin halayya gareta sakamakon gyara zamantakewarsu da ya dauki niyar yi. Ita din ce dai ban san alkiblar da take fuskanta ba balle ya gane inda ta dosa. Yau da sassafe suka fita tare da Munzali duba fili. Sun yi ta tufka suna warwarewa kafin su yanke shawarar gina makarantar boko primary amma Islamic oriented (wadda tafi bada karfi a fannin addini). Tunda suka fara tafiya Abbati ya zurfafa a tunanin yadda zai yi ya sabule ya tafi Abuja saboda kiran da Shazali ya yi masa da safe. Munzali ya gaji da janyo hira yana barinsa da zance shi kadai. Ga kauce-kauce akan maganar damuwarsa ta Kirikasamma. "Wai kuwa ka samu ka karbi nambar Farha a wurin Mardiyya?" Saukar guduma maganar tayi masa. Farhan da ta hana zuciyarsa sakat amma ya kasa kiranta bayan Mardiyya ta turo nambar saboda kyamar kansa da yake. Me zata yi da kazami irinsa wanda ya zama bolar masu kudi? Idan ya aureta anya bai cika mugu kuma mara imani ba? A da dai da ya zata tubansa mai sauki ne ya kudiri niyar hada rayuwarsa da tata amma banda yanzu. Kallon mamaki Munzali ya dinga yi masa. Kwanakin nan ya rasa abin da yake damun Abbati. Kullum suna tare suna shawarwarinsu amma iyakarta kenan. Shi ya san ba Abbatin da ya saba dashi bane. Wannan bashi da aiki sai yawan tunani da damuwar da ta fito baro-baro akan fuskarsa. Ya gaji da wannan sabon yanayin da ya jefa shi wasiwasi da tuhumar kansa ko shi ya masa laifi. Tanadin da ya yi musu wanda a ka'ida zai shawarce shi ma ya kasa fada masa. Kudin da suka samo a Abuja kaf ya kwashe nasa miliyan goma harda ciko ya tura wani asibiti mai zaman kansa a kasar Italy. Asibitin ya shahara wurin canjawa mutane halittar jinsi kazalika suna da bangare guda da yake gudanar da theraphy na masu son komawa yadda suke. A bincikensa ya gano wannan bangaren zai iya taimaka musu wurin kawar musu da sha'awar da za ta iya mayar dasu ruwa. Har magana ya yi da daya daya cikin manyan likitocin asibitin domin ya samu gamsashen bayani. Akwai wadanda ake haifa saboda genetic defect su kasance a zahiri wani jinsi a badini kishiyarsa. Sai ka sami zabgegen saurayi da muryar mata yana karairaya (dan daudu). Ko mace da katuwar murya tana tafe tana bokarewa kamar wani dan ball. Irin wadannan yawanci aiki ake yi musu a kwantar da jinsin dake da rauni domin su zama abu daya. Kaso na biyu kuwa wanda a nan suka fada sune 'yan taka haye. Koya musu akayi ta karfi da yaji tun kafin ma su san ma'anar wannan mu'amala. Su ne suke iya aure har su hayayyafa sannan a gefe suna bibiyar 'yan uwan jinsinsu. Matsalar da irinsu kan samu ita ce ta sha'awar da kan taso lokaci zuwa lokaci saboda sabo. Wannan sha'awar Munzali yake son nema musu maganinta domin ya san suna da ita. A yadda ya fuskanci Farha ta tafi da tunanin Abbati ba zai so ko kadan gurbatacciyar rayuwarsu ta baya ta sami kafar nuna kanta bayan ya aureta ba. Kiiiii ya taka wani wawan burki motar ta yi gaba kamar za ta jefar dasu ta gilas sannan ta tsaya da karfinta a gefen titi. Sai lokacin Abbati ya yi firgigit ya kalle shi yana kuma dube dube na neman abin da ya kawo haka "lafiya? Birkin ne da matsala ko me?" Cikin yanayin ko in kula Munzali ya ce "Ko daya. Naga ina ta magana baka ji bane shi ne nayi haka domin dawo da kai duniyar mutane." "Yi hakuri kan nawa ne ya yi wani wuri." Haushin boye boyen da yake yi masa ya sanya shi magana da bacin rai "Wurin da bai kamata na bika ba bare na san damuwarka mu magance ta? Kai ni ban ma damu da na sani ba. Ba dole bane sai ka fada min komai naka tunda dan Adam yana da sirri amma a kalla ka fadawa Baaba Mari ko wani da kake ganin zai tayaka neman mafita." Kallom tsaf Abbati ya yi masa sannan ya ce "kana nufin akwai abin da kake boye min?" "Ai ba kai kadai ne ka san ma'anar maganar nan da ake cewa ciki ba'ayi shi don abinci ba kadai. Ka rike damuwarka a cikinka amma wallahi ka daina nunata a gabana. Ba za ka sa kullum na kebe in dinga tunanin matsalarka ba. Ga 'ya muna da ita ga kuma aure nima ina son yi. A bar mutum idan ya kebe ya yi tunanin 'yar budurwarsa mana da hanyoyin tsarata." 'Munzali kenan' Abbati ya ce a zuciyarsa yana murmushi "dan'anace ba dai zan fada maka ba. Da girmana ka dinga kokarin yi min wayo. Wannan blackmail din bai ba, ka koma inda ka koyo ka karbo kudinka." Dariya sosai Munzali ya yi ganin ya yi nasarar dawo dashi daga ko ma ina tunaninsa ya kai shi. Dan daidaita fuskarsa ya yi ya daina dariyar. "Maganar gaskiya ko dai har ka fadawa Farha kana sonta ne taki amincewa?" Goshinsa ya dan matse tare da kada kai "a'a, ni ne dai ma na fasa saboda bana jin mutum irina dake lullube da kazanta ya cancanci samun soyayyar mace irinta. Don baka ganta bane Munzali amma ko kadan babu alamun shashanci a tare da ita." Shiru Munzali ya yi na wucin gadi har Abbati ya dinga kiran sunansa. Da ya amsa kwalla ce ta cika idanunsa har tana saukowa. Muryarsa ba rawa ya ce "Abbati za ka taba yafe min kuwa? Ni ne sanadiyar shigarka wannan rayuwar. Na cuceka na cuci kaina cuta mai girma." Zuciyarsa radadi ta dinga yi masa ta cigaba da magana yana kuka tamkar karamin yaro. "Na dade ina son rokon gafararka amma sai nake jin tsoron kada ka barni. Abbati ban rasa iyaye ba amma marayu da yawa sun fini gata. Mahaifana basu yi min komai ba a rayuwa sai kawoni duniya. Duk wadanda muka fito ciki daya ina jin Ummakati ce kadai rayuwarta dama-dama. Sauran kannena kowa ta kansa yake yi. Shi yasa bana kyashin basu kudi don kar su nema duk da kudin ba shi zai basu tarbiyya ba. Navso kaina daya akanka tunda nayi amfani da soyayyarka gareni muka dauwama cikin sabo..." Kuka suke duk su biyun kowanne yana cike da nadama da tsanar kai. Ina ma ana komawa baya da Munzali zai zabi yin bara akan karbar abinci wurin Shazali. "Ka bar kukan nan haka in sha Allahu zamu sami rayuwa mai kyau a gaba ko babu kudi." "Wace irin rayuwa mai kyau bayan nayi sanadin abin da zai iya hanaka samun wadda ka ke so?" Shan kunu Abbati ya yi ya ce "dalla can murya kamar kosasshen zakara ka daina kukan duk ka cika min kunne." Kyabe fuska Munzali ya yi yana fyatar hanci da gangan "Allah sarki ashe baka tsaneni ba." "Ban tsaneka ba amma na tsani irin wannan fyace hancin kaima ka sani. Ni ka ja motar mu tafi kar ka sakani amai." Ya dage hancinsa. Munzali don mugunta sai ya mika masa hannu "to mu gaisa in tabbatar ina ranka ko bayan raina" "Allah Ya kiyaye in taba hannun da aka kai hanci" ya doke hannun. Motar tana tafiya baka jin komai sai dariyarsu da fadan da baya karewa kamar mage da bera. Munzali ya yarda damuwar Farha ce ta tsayawa Abbati shi yasa ya yanke shawarar neman Mardiyya ya aura. Da haka zai taimaka ya rabata da mamanta sannan yaji dadin cusawa Abbati Farha har sai yaga an shafa FaI just published "15" of my story "UWA UWACE...". https://my.w.tt/nvrHssbTfbb UWA UWACE...15 Batul Mamman💖 Maula Ya Salli Wa Sallim Da'iman Abada Ala Habibika Khairil Khalqi Kulli himi MUHAMMADUN SAYYADUL KAWNAINI WA SAQALAIN WAL FARIQAINI MIN URBIN WA MIN AJAMI Oh my Master, send your salutations and blessings forever Upon your beloved, the best of the whole creation MUHAMMAD IS THE LEADER OF BOTH WORLDS AND OF MAN AND JINN LEADER OF THE ARABS AND NON-ARABS AND THEIR KIN. OUR RASUL, OUR HONOUR Sallallahu alaihi wa sallam. *** "Dakta yaushe za ki sallami matar nan ta room 3 ne? Ba shishshigi zan miki ba amma gara taje gida ta karasa jinyar nan ko don jinjirarta. Yau kwana hudu babu wanda yazo dubiya balle a kawo abinci. Kullum sai dai ta bada naira dari biyu a siyo mata bons da ruwa." Tafiya likitan take yi da fari amma jin abin da sub-staff (karamar ma'aikaciyar) take fadi ya dakatar da ita. "Wace mata? Akwai mutum a room 3 ne?" Dan zaro ido mai aikin shara da wankin bandakin tayi "Dakta ba dai kin manta da ita ba? Haba ko da naji. Shi yasa naga ba a shiga ashe." Ta fada da tausayawa "Matar nan da ki ka yiwa dinki fa." Hanyar dakin likitan ta nufa. Tana budewa ta hade rai gabadaya. Dakin zafi ga wani irin kuka da tun kafin su shiga dakin take ji na baby. "Haj Zara?" Ta ce da mamaki wanda ya gauraye da bacin rai "wata lalurar ce ta sake dawo dake?" Zara ta dan murmusa tana kokarin tashi zaune amma ta kasa. Bebi dinta tana can gefen gado babu wani lullubin kirki sai cilla kafafu take tana kukan yunwa. "Ban tafi ba tun ranar nan ina jiran sallama" Ta ce da murmushin yake. A harzuke likitan ta soma magana ta zura hannu cikin aljihun labcoat dinta ta dauko wayarta "Tunda nayi miki dinki na ce miki ba zan kwantar dake ba saboda baki zubar da jinin da zaki bukaci kari ba. Ga 'yarki..." Yarinyar ta dauka ta shafa fatarta da hannunta taji wani mugun bacin rai. Ba ayi mata wanka ba tunda tazo duniya. Layin reception ta kira ta bukaci a lalubo nambar Alh. Unais a file dinsu a tura mata. Zara na jin haka hankalinta ya tashi. Niyarta ta zauna ranar suna ta koma nata gidan. "Doctor da kin kyale shi. Zamu iya maneji har jibi sai na tafi." Ta ce a sakarce. "Anya kina da hankali kuwa? Daga ke har bebinki babu wanka tunda ki ka haihu. Ance bons kike ci kullum ta ina za ta sami ruwan nono mai kyau?" Bata san hankalin nan da sauki ba a wurin Zara. Tunda aka gyara dinki ta kwana biyu ta soma jin wani irin mugun ciwo a wurin. Idan taje fitsari da kyar take yi ta dan shafa ruwa saboda ciwo. Wuri ya ruruce saboda rashin kulawar da bai samu ba. Kwayoyin cuta na neman kama wurin (infection). Ciwon da take ji ne ya yi tsamari har yana neman taba mata kai. Kwakwkwarar hira da za ta bukaci aiki da hankali yanzu tafi karfin tunanin Zara. Sako daya take fahimta-ciwo. Alh. Unais na amsa wayar likitan nan ta dinga surfa ruwan bala'i akan sakacinsa da lafiyar iyalinsa. "Ka zo ka dauketa yau dinnan. Kuma a biya duka kudin kwanakin da tayi." Ta ajiye wayarta shi kuma ya shiga wurin mahaifuyarsa ya fada mata. Haj. Fatakwal ta ce kuea da wa Allah Ya hadata. Banda Zara bata gabanta da kila sai ta hada mata da hannu. "Babu inda za ka je. Ka tura direba a kaita gaban iyayenta. Shi kuma wanda ya kaita asibitin ka kore shi. Ni da Zara ne a gidan nan. Na rantse sai ta zauna a gidan iyayenta. In ta san wata bata san wata ba." Dan wani tunani tayi ta tashi da sauri ta ce su tafi gidan Innayo kafin ya tura direban. Alh. Unais bai fahimci hikimar haka ba sai da suka isa gidan. Mahaifiyarsa tayi dabarar sabule kanta da shi daga zargi a gaban iyayen Zara. Innayo ce kadai a daki tana sauraron rediyo taji sallama gami da kamshin turaren da ya gauraye kofar dakinta. Muryar ba ta Munzali ba ce. Shi ne mai shigowa kwana biyun nan ya cika su da kamshin turare mai dadi. Amsa sallamar tayi ta janyo mayafi za ta lullube jikinta ta leka sai kawai aka shigo. Girgiza kai tayi ganin ko waye bai dauki bata lokaci tayi izinin a shigo da mahimmanci ba. Alh. Unais da ta gani daga bayan matar da ta luluka tunanin inda ta san fuskarta ya bata mamaki matuka. Mikewa tayi jikinta na rawa da tunanin ko wani abu ne ya sami Zara. Rabonsa da takowa dakinta tana jin tun gaisheta da suka zo bayan auren. "Ina masu jegon naji dakin naki shiru?" Cewar Hajiyan Fatakwal tana murmushin dole. Ita dai hankalinta a tashe ta ce "wane masu jegon kuma? Waye ya haihu?" Hajiyan Fatakwal sai ta fiddo idanu kamar gaske "bangane ba Maman Zara. Ya ina maganar Zara da 'yarta da suka taho nan wankan jego yau kwana biyar kina cewa waye ya haihu?" Allah Sarki Innayo. A gigice ta mike tsaye, zaninta na sabulewa tana kamo shi da kyar. "Kuyi min bayani yadda zan gane. Zara bata zo gidan nan ba kuma babu wanda yake da labarin haihuwarta." A gabanta Alh. Unais ya kira direban da aka umarta kawota gida ya ce ai asibiti ta ce ya kaita tun ranar. Innayo sai taji kamar an dora mata dutse a kanta. Me yake faruwa? Mayafin da ta dauko lokacin da taji sallama tayi saurin yafawa tana tambayarsu sunan asibitin. Yana fada ta kira Hasiya ta fada mata. Ita kuma lokacin Maimuna tana gidanta. "Ke da Maimunan ku sameni a can." 'Yar pos dinta ta dauko akwai kudi a ciki saboda Munzali ya bata dubu ashirin shekaranjiya da ya zo. Ashe kudin zai mata rana. Ko mukulli bata saka ta rufe dakinta ba tabi bayansu Hajiyan Fatakwal. Duk tsiya hankalin Alh. Unais yana kan matarsa ita kuwa Hajiyan Fatakwal dama burinta ta sada bak'ar k'aya sunan da ta lakabawa Zara da gidansu. Ko danta zai dawo da ita ba yanzu ba. Tunda ko kusa bata da niyar shiga asibitin Innayo na isowa jikin motar da sassarfa za ta bude baya ta dakatar da ita. Ita ba za ta iya zaman mota tare da wannan matar da ta kode da wahalar rayuwa ba. Karshenta ta cika motar da wari. "Maman Zara ina ga gara fa ki shiga adaidaita sahu saboda daga asibitin gida zamu wuce." Innayo sai tayi turus. Matsananciyar kunya ta kama ta sakamakon wannan cin fuska. Ta fahimci motar ce ba a so ta shiga. Banda haka ko ma ina zasu wuce tunda wuri daya zasu yanzu me zai hana a tafi da ita. Wani abu mai kaifi ya soki zuciyarta saboda tunawa da cewa wadannan mutanen Zara ta fifita akanta. 'Yar dariya ta kirkiro "laa babu komai ku wuce ai na gane sunan asibitin." Hajiyan Fatakwal ta tabe baki "to sai kin iso" Innayo na kallo suka ja mota. Hanyar titi ta nufa da zafin nama idanunta cike suke taf da hawaye. Bata zaci Zara ta kaskantar da ita ta yadda surukanta zasu kyamaci hada abin hawa da ita ba. Duk da haka kuma bata fasa adduar samunta lafiya ba. Za ta shiga adaidaita sahu kenan taji kira daga bayanta. "Innayo ina zuwa?" Munzali ne don ta gane muryar tun kafin ta juya. Da hannu ya sallami mai adaidaitan ya fito a ladabce ya bude mata bayan motarsa. Tana shiga ta soma kwararo masa addu'a har ya zagayo ya zauna. "Allah Ya tsare jinka da ganinka Munzali Ya rabaka da duniya lafiya. Nagode. Nagode. Nagode." Ta ce tana danne kwallarta. In wani ya ki ka wani zai so ka. Wadda ta haifa ta ja mata wulakanci. Ga kuma dan mijin da bai damu da komai nasu ba ya martaba ta. Yaji dadi har ya kasa boyewa. Asabe bata yi masa addu'a irin haka. Kudi ne dai idan ya bata mai yawa ta ce 'nagode'. Idan ta raina ta ce 'an gode'. "Ina za ki da ranar nan?" Yadda suka yi da mijin Zara ta fada masa. Ransa kuwa ya baci da salon wulakancinsu ya hau fada. "Bar bata bakinka. Zara ce ta nuna musu bamu da wata kima a idonta. Rabonta da zuwa gida wata goma kenan." Haka suka yi ta tattaunawa akan tabarbarewar gidansu har suka isa. Da bata ga motarsu a waje inda ake ajiye motoci ba sai ta fara tunanin ko ba daidai taji sunan ba. Suna shawarar zuwa gidan Zaran tambayar sunan asibitin tunda babu nambar da zasu iya kira sai ga su Hasiya. Munzali ya fita ya tarosu yana fada musu babu tabbas nan ne. "Ina jin fa nan ne" cewar Hasiya "bari mu shiga mu tambaya." Munzali na fadin sunan Zara a reception idanuwa suka yi kansu. Sai surutai ana nuna su da baki da hannu da masu yi da wutsiyar ido. Ashe Zara tana da dangi a kusa take zaman asibiti a yashe. Har dakin da take aka kaisu. Zuciyoyinsu duka sai da suka karye da ganin Zara. Tayi wani irin duhun da kana gani za ka gane wahala da dauda ya kawo shi. Lebe ya bushe fatar ta daddago kamar wadda ta shekara a kwance. Idanunta kuwa sun yi zuru duk ta zabure. Duk wannan bai kama kafar halin da 'yar talikar jaririyarta take ciki ba. Wani tsami take bugawa sosai. Maimuna tayi saurin dorata a cinyarta ta bude diaper (pampas) da nufin canja mata. Gabanta ya yanke ya fadi da abin da ta gani. Cikin rawar murya ta soma salati. "La'ila ha ilallahu...Zara?" Innayo da ta bada hankalinta tana sauraron bayanin likita game da Zara sai ta juyo. Munzali da Hasiya ma suka kallota. "Menene kuma?" Innayo ta tambaya da alamun rashin hakuri. Hannu na rawa Maimuma ta bude pampas din yarinyar ta tsanyara wata irin kara kamar ba jaririya ba. A tunaninsu ma ko fatar gabanta ta biyo pampas din sabods tsabar jikewa da cika da tayi. Alamu sun bayyana karara ba ta yau bace. Duk abin da tayi a ciki ya canja launi zuwa wani abu daban. Ya ci fatar jikinta da danshi ya d'ad'e jikinta. Likitan ta fita ba jimawa ta turo mai shara da filas din ruwan zafin office dinta saboda kafin a dafa ma zai bata lokaci. Maimuna ta shiga da yarinyar bandaki tana yi mata tsarki Hasiya na zuba ruwan. Su biyun aka rasa mai hana 'yar uwarta zubar hawaye. Innayo kuwa kirjinta ke zafi amma taki kuka. Wace irin masifa ce wannan da Alh. Rabi'u ya sanya gidansa a ciki? Su kadai ya bari su tarbiyantar da 'ya'yansu. "Allah Ya gani nayi bakin kokarina Zara. Ban rageku da komai cikin abin da Allah Ya hore min ba. Amma yau gudun zama dani kar ace babarki talaka ce mara ilimin zamani ya kawoki nan." Baki Zara ta zumburo "me kuma nayi?" Janyo hannunta Innayo tayi daga kan gadon tana cijewa saboda ciwo. "Babu abin da kika yi Zara. Zo mu tafi gida. Ba zan bata bakina akan ki ba tunda na san sarai ba kya cikin hayyacinki." Bayan an gama tsarkin ko pant basu nema sun sakawa yarinyar ba saboda yanayin jikinta sai zani aka dan rufa. Munzali yana kasa ya nemi bill din Zara aka ce masa ai family file ne. "Ku bani daga ranar da dawo ita kadai" Aka lissafa masa ya basu kati suka cire. Zai so ganin mijinta da wallahi sai ya naushe shi. Ace matarsa tana asibiti amma don wulakanci suka yiwa Innayo alkawarin karya suka ki zuwa. Kayanta gabadaya suka saka a mota suka tafi gida. A hanya Innayo ta ce Hasiya ta duba mata Sahad na cikin gari ta siyo madara mai kyau ta yara. Pos dinta ta bawa Hasiyan amma Munzali ya hana. A gurguje ya shiga ya siyo kala uku saboda rashin sannin wadda zasu fi so. Zai yi rantsuwa bai taba jinsa ya cika mutum ba irin yau. Gashi yana ta kai kawo wurin kyautatawa jininsa. A duniya ba zai taba mantawa da Abbati ba. Suna isa gida Innayo da kanta ta hada itace murhu biyu ta dora ruwa a manyan tukwane. Asabe tayi mamakin ganin shigowarsu tare da Munzali sai dai ganin Zara da son jin kwaf ya hanata yi masa fada. Tana jinsa ya kira Ummakati ya ce tazo gida yau ko gobe Zara ta haihu. Tsaki tayi da karfi "meye sabo a haihuwarta da ka ke kira min 'ya daga gidan miji?" Bai ce komai ba saboda ya san sai ta janyo rigima idan ta fara maimaita zancen tana rashin arziki. Kafin ruwan ya tafasa Innayo ta rufe kofar dakinta ta duba jikin Zara. Ajiyar zuciya kawai tayi ta kira Uwani a waya. "Kun tashi daga wajen aiki?" Uwani ta dan yi jim tana tsoron amsar da za ta bayar saboda bata san dalilin tambayar ba. Can dai ta ce "Eh mun tashi ina gida." Jin kamar Innayo za ta yi magana ta kara da cewa "wallahi kin ga wata ya yi nisa dan abin hannuna duk ya kare." "Ajiye karyarki wata rana kila in tayi fure tayi miki amfani. Yanzu dai ki fadawa mijinki ina nemanki da gaggawa. Ki taho da kayan aikinki. Dinki za ki gyarawa ...." Uwani taji kamar ta dora hannu a ka. Ta dade tana gudun ranar da Innayo za ta dinga kiranta taimakawa wani saboda aikinta. Kamar su allura ko karin ruwa da ta kan saka ta kafin tayi aure. Idan an yi lokacin ba kasafai take bari a biya ba. Sai dai ta dinga addu'a tana cewa arziki ne wasu na amfana da iliminta. Tana aure ta nuna bata son cigaba da wannan sadakar dolen. Idan ba za a biya ba kowa yaje asibiti. Bata jira jin karshen maganar ba ta ce "Gaskiya Innayo ki ce su tanadi kudi. Dinkin ma idan ba haihuwar farko bace ni har dubu goma ina karba." "Allah ba zai hana ni abin da zan biyaki ba. Ki yi sauri." Kawai ta iya cewa ta kashe wayar. Uwani sai jiki ya dan yi sanyi. Amma tunda za a biya bata ja lokaci ba ta shiga motarta ta taho gidan. Sanda ta iso Maimuna ta gama yiwa jaririyar nan wanka. 'Yar na kuka ita ma tana yi saboda tausayin jikinta. Zara kamar mutum mutumi tana zaune a daki har aka gama. Hasiya ta bude akwatin ta daga kaya duk na maza. Cikin unisex ta samu guda daya ta kaiwa Maimuna ta saka mata. Pampas kuwa bayan an shafe wurin da man kade sai aka barta a bude domin ta sha iska. Ana shiryata Hasiya ta hada mata madara tunda da feeder a kayanta. Maimuna ta bata ta sha sosai sai bacci. Duk sai ta basu tausayi. Innayo sai lokacin tayi kwalla. Tashi tayi ta bar wurin saboda bata son zuciyarta ta karye. Zara ta bata mata rai fiye da duka wani abu da ta taba yi a baya. Da Uwani ta iso Innayo ta gama hada ruwan wankanta a bandaki. "Maimuna dauki 'yarki ku koma bangaren Asabe don na sanki da raguwar zuciya. Kar ki kuskura ki zo min kofar daki sai an gama." Da sauri-sauri kuwa Maimuna ta mike. Tunda taji ana zancen gyara dinki hankalinta ya tashi. Dakin Asaben ta je ta gaisheta ta sami wuri ta zauna. "Lafiya dai ko? Naga mun gaisa har 'yar na gani amma kin gaza tashi." "Aiki za ayi a dakin Innayo zan tafi idan an gama" Kasa cewa komai tayi ta barta don bata ga alamun za ta fita ba. Munzali ya fita tunda ya kawosu amma ya ce zai dawo. Innayo ce tsaye da Zara a bandaki ta soma gasa mata jiki da tawul. Zafin ruwan bai sa tayi niyar gudu ko korafi ba sai da hannun Innayo ya kai cikinta. Nan fa ta kwala kara wadda tasa Asabe zabura a gigice. "Ke Maimuna gayan gaskiya. Me ake yi a dakin Innayo? Wannan dai duk ragwantar mace ba tayi shi a matsayin kukan wankan jego ba." Ita ma dai a tsoracen ta ce "naji ta ce Uwani tazo da kayan aiki" "To ni dai ina nan. Babu inda zan leka wallahi. Banda daukan hakki ai da ta fada min na tafi unguwa yau...uhmmm bari na shiga makota" ta tashi ta figi mayafi. Ihun Zara duk ya tayar mata da hankali. Cikin Zara Innayo ta dinga dannawa iyakar karfinta da tawul. Hasiya ta rike hannuwanta saboda taki tsayuwa da kyau. Cikin sa a kuwa sai ga audugar da aka bar mata a ciki tun ranar da ta haihu ta fado ta cika wurin da wari. Tuni ta koma bakikkirin babu kyan gani. An barta ne tun lokacin da ta kasa zama ana cikin kwashe mata jini da taji sakon Hajiyan Fatakwal game da haihuwar mace. Fadowar audugar yayi daidai da wata ajiyar zuciya da ta sauke da karfi. Innayo ta cigaba da yi mata wanka ta gasa jikin sosai. Sannan babu batun kyama ta zauna ta wanketa da ruwa mai zafin da bai yi yawa ba. A nan taji yadda wurin dinkin yake yauki saboda rashin kula. Da ta gama suka fito ta umarci Uwani ta duba idan ana bukatar sake dinkin ne ayi mata. Hasiya ficewa tayi ta koma falo. Uwani tana dubawa Innayo na kallonta. "Kin yi shiru. Tana bukatar sabo ne ko kuwa?" "Wannan din ya dauko hanyar warkewa. Idan aka ci gaba da tsaftace shi ba za ta bukaci sabo ba." "Da kudina Uwani kar ki cutar min da 'ya. Idan kin san wannan zai iya bata matsala ki ware shi ki sake mata wani." "Haba Innayo nima fa kanwata ce. Ta yaya zan cuceta? Tun zuwana kun ki fada min abin da ya faru da ita." "Idan ta dawo daidai ta fada miki da bakinta. Naga kuna dasawa labarin ba zai miki wuyar samuwa ba. Nawa kike chaji in an kiraki amma baki yi aiki ba?" Innayo ta fada fuskarta babu wasa. Magana ce ta fahimta kuma ita ma sai yanzu taga wautar abin da tayi dazun a waya. "Ko ina karba ai banda wannan. Don ban san Zara bace da ba zan yi zancen kudin ba Innayo. Naga kamar baki jidadi ba." "To Allah Ya bada lada." Daga haka Innayo bata sake bi ta kanta ba. Tuwon da tayi da rana wanda tasa Hasiya ta dumama ta zuba ta dinga bawa Zara a baki. Tana karba hawaye wani na bin wani a kumatunta. Tunda audugar nan ta fito taji kamar an tasheta daga bacci. Duk abin da ya biyo bayan nan ta sani ta kuma tuna me ya faru dalla dalla. "Wani wurin na yi miki ciwo ne?" Cewar Innayo lokaci guda tana kai hannu wuyan Zara taji ko akwai zazzabi. "A'a" ta amsa a raunane "To madalla. Ci abincin ko kya samu ki ji kwarin jikinki." Daga haka bata sake cewa komai ba. Zara ta dinga kallonta tamkar wata sabuwar halitta da bata taba gani ba. Kukanta bai tsagaita ba amma da za a saka mata wuka a wuya ba za ta iya cewa ga takamaimai abin da yake yawo a ranta ba. Abubuwan da yawa. Malmala daya da rabi ta cinye ta sha kunu fiye da rabin kofi sannan tayi gyatsa. Innayo ta dauke kofin daga bakinta sannan ta mika mata wayarta da suka dauko daga asibitin. "Kira mijinki yazo ya daukeki." Ba Zara ba hatta Maimuna, Hasiya da Uwanin da bata gama sanin me ya faru ba maganar ta basu mamaki. Idanu cike da hawaye Zara ta ce "Innayo a hakan zan tafi?" "Ba a hakan ki ka zabi asibiti akan wannan dakin ba? Kije gidanki ki karasa jinya Zara. Allah Ya raya miki 'yarki." "Don Allah Innayo..." Maimuna ta fara roko ta juyo kuwa tayi mata wani irin kallon da yasa bakinta rufewa gum. Da zasu fice ma baki dayansu daga dakin da taji dadi. Kuka take son yi. Kukan tausayin Fatima Zahranta. Kukan rashin sanin laifinta a wurin tarbiya da rainon 'yarta. Kukan matakin da take son dauka domin nunawa Zaran cewa dama can talala take yi mata. A daidai lokacin kuma Alh. Rabi'u ya daga labulen kofar ya leko dakin... *** Shiru Yumna tayi har Alh. Tahir ya gama magana sannan ta tashi daga jikinsa tana yi masa wani banzan kallo. "Aure fa kace? Ni za ka aura? Gaskiya nafi son auren yaro daidai dani." Mamaki sosai ya kama shi da karfin halinta na yi masa rashin kunya. Yarinyar da take sa'ar 'yarsa. Wato don ya sakar mata jiki da fuska take ganin kamar yanzu kansu daya. Ba don Yakumbo ta sake jaddada masa batun auren nan ba da tuni ya saka ta a bolar da yake jefa wadanda ya gama cin moriyarsu. "Kinga samu wuri ki zauna ba maganar wasa bace. Hotonan da ki ka turo duka matana sun gani." Rawa jikinta ya dauka ta saki wayarta a kasa ta kuma bi bayanta ta zube a gabansa. "Me? Ka ce min basa taba wayar. Na shiga ukuna. Idan suka fadawa Mummy wallahi kasheni zata yi kawai." Ta fashe da kukan firgici. Shi ma ba zai so tonawa kansa asiri ya fada mata gaskiya ba sai ya ce "da suka tuhume ni a kai na nuna musu cewa aurenki nake son yi. Yanzu duk sun zuba ido suna jiran jin batun aure ko hoto ya tafi gaban mahaifanki." "Na shiga uku" ta sake fadi cike da jimani "yanzu me zan ce da Farha?" Gabansa ya fadi shi ma amma sai ya dake. "Bana son munafurci. Baki san da Farhan ba ki ke bina duk inda na nema?" Murguda masa baki tayi "ai dai ba ni na kawo kaina ba kai ka nemeni." Tashi ya yi ya kimtsa jikinsa sannan suka karkare magana. "Matashin da ki ke son aure babu wanda zai yarda ya zauna da irinki. Ko an fada miki mazan yanzu jahilai ne? Gane masu yawo ba wahala yake musu ba. Gara ma ki yarda kina watanni zan sako ki. Kinga mun kashe bakin 'yan gulma. Wannan abu fa duk saboda ke nake yi saboda kada a gaba ki sami matsala da mijinki. Sannan zaki sami yadda kike so a wurina. Duk kasar da ki ke son zuwa zaki je. Infact na ma daina daukar matana rakiya sai ke." Da kudin ya sayeta duk da ba shi ya fara mu'amala da ita ba. Da su zai sake ninketa ya aureta saboda tsira daga bakin uwa. Alkawuran sun mata dadi. Ba musu ta bada kai bori ya hau. Tunda ta amince bata ga dalilin auren ya zama na takaitaccen lokaci ba. Yadda ya yake da kudin nan gara taje ta kwashi rabonta da hujja. Iyayenta dai take ji sai dai kuma komai ya zo ba yadda ta zata ba. Alh. Tahir ya nuna mata da gaske yake. A ranar da suka yi maganar da daddare yaje tsohuwar unguwarsu tare da Kawunsa daya da abokai biyu. Aka yi musu sallama da babanta wanda ya tarbesu da mutuntawa a falo. Yumna ce mai kawo ruwa da lemo ta shigo a nutse kamar ba ita ba. Tana fita abokin Alh. Tahir ya fadi abin da ya kawosu. Baban Yumna da mamaki ya ce, "Alh. Tahir din da kansa ko dansa Suhaib?" "Alh. Tahir din dai" cewar kawunsa. Babanta sai yaji kansa ya yi nauyi. "Abin ne ban fahimta ba. Soyayya ta aure kuke yi da ita Yumnan amma bani da labari?" "Ko daya Alh Kabiru. Yanzu ne dai Allah Ya dora min son hakan shi ne na ce gara mu zo da manya ayi magana ta fahimta. Idan tana da miji ne babu wani abu. Na kawo Kawuna ne da abokai dama domin ka san da gaske nake." "Ina zuwa" ya ce yana mikewa. A falon ya barsu ya shiga wurin iyalinsa. Ya yi mamaki kwarai da Yumna ta ce ta amince kai tsaye. Mahaifiyarta kuwa tsalle tayi ta dire ta ce wannan cin amana babu hannunta a ciki. Komawa ya yi ya barsu a dakin tana ta yi mata fada. Zancen duniya baya buya. Yana da labarin kafin su dawo wannan unguwar Alh. Tahir ya auri mai'aikin gidansa da 'yar uwarta. Sun yi zama na 'yan shekaru a nan gashi sun sake tashi. Mutumcin dole ne ya shiga tsakaninsu dalilin 'ya'ya amma sam mutumin bai masa ba. A 'yan watannin da suka gabata ya fahimci wata irin rayuwa da 'yarsa ta fara. Zuciyarsa sam bata son yarda da abin da ya tabbatar halayyar 'ya'yan yayansa ita ma take bi. Zuwan Alh. Tahir bai kara masa komai ba sai tsoratar dashi. Aurar da ita zai yi kawai domin tsananta bincike zai iya haifar masa da ciwon zuciya. Ya kwallafa ransa akan tilon diyarsa. Ko kadan zuciyarsa ba za ta dauki tabbatuwar zarginsa ba. Yana shiga falon ya ce musu ya amince kuma baya son a dauki lokaci. Su ma tunda a shirye suke sun sanar dashi zasu dawo nan da sati tare da kudin aure. Ana kammala wannan Alh. Tahir ya shiga tashin hankalin yadda kwan nan zai fashe a wurin 'ya'yansa. Matan gidan sun riga sun sani. Bai san da idon da zai kallesu ba. A zahiri aurensu ba haramun bane amma ji yake kamar zasu san boyayyar alakarsa da ita. *** Kwanaki sun zo sun wuce babu sako ko waya daga mutumin da ya kira kansa da Abbati a wurin Farha. Yafi sau hudu tana tankwara zuciyarta wurin son tambayar Mardiyya ko ta tura masa nambarta daidai. Da kanta take kwabar kanta cewa kar ta zubar da mutumcinta na 'ya mace. Daga cewa yana son su dauki hoto meye nata na kawo rai da buri ta dora a kansa? Karshenta ma yana da iyali. Yadda bata taba burge sauran maza ba bai ma kamata ta sakawa zuciyarta cewa kila ta burge shi ba. Mami ta ce ta cigaba da hakuri ta jira zuwan mijinta idan tana da rabon aure a duniya. "Idan Allah bai kawo ba ki gode Masa akan sauran ni'imomin da Ya yi miki. Bana kin aure Farha amma akwai matan da zasu rantse miki da gidan mijinsu gara su tsofe a gaban iyayensu. Duk yadda nake son in ganki a dakinki da zuri'arki ba zan taba gurfana gaban malami domin nema miki miji ba. Allah ba Ya dorawa rai abin da ba zai iya dauka ba. Ki rike wannan." Nasihar Mami Khadija kenan ta karshe a gareta ranar bikin 'yar kanwar Mamin da suka taso tare. Rashin aure daban da ace mace ta taso babu mashinshini inji bahaushe. Wannan yana tayarwa kowace irin dakakkiyar zuciya hankali ya sanya mata wasiwasi game da tsarin halitta da lafiyarta. Sun tare a sabon gidansu wanda Alh. Tahir ya zuba musu kayan alatu kamar baya tunanin aurar dasu. Da kanwarsa ta tuhume shi akan hakan lokacin da suka zo ganin gidan cewa ya yi aure ba sayar da 'ya'ya bane. Duk wadda abu ya kawota gida koda ziyarar wuni ce tana da dakinta inda zata wataya tare da 'ya'yanta. Idan kuwa kwana ne babu mai cewa sun takura masa. A bangaren 'yan matan wanda yake kusa da na Maminsu akwai falo madaidaici da kofofi uku na dakunansu. Kowacce da bandakinta a ciki kuma an kawata shi kamar na amaryar gata. Su kuwa mazan kowa da nasa. Duk da a manne suke da juna amma kowa kofarsa daban. Akwai falo da katon daki da bandaki a ciki. Matansa ma dakuna bibbiyu kowane da bandaki ga kitchen da store. Da yake kowacce kudi ya bata ta sayi abin da take so ita Mami Khadija sai ta adana nata a banki. Ta riga ta gama duk wata siyayya saboda gidan da ta gina. Yanzu ma 'yan haya take nema ta saka kafin ta ga me gaba za ta haifar. Mardiyya da Sauda na kallo a falonsu Farha kuma na dakinta tana chatting. Sanye take da doguwar riga ta material wadda tabi jikinta ta fiddo da cikar tsarin halittarta. Gashinta wanda ya zarta kafada da kadan ta raba shi biyu ta tufke kowanne tana jiran shigowar maikitsonsu. Muhawara suke tafkawa a wani group game da wasu matsaloli ta whatsapp Yumna ta kirata ta dauka da dan murmushi. Kawar ta ta bata da matsayi kamar da a zuciyarta tunda ta fara harka da manyan maza. Sai dai tana kewarta sosai. "Hajiya Farha meye duniya ne? Sai dai na ganki online ba hi ba hello." "Kin yada ni ne Yumna daga fadar gaskiya" ta ce da dokin da yafi na lokacin da kiran ya shigo. Yumna ta gatsina fuska sannan ta ce "to dai fada tsakaninmu ya kare. Duba status dina." Kashe wayar tayi tana dariyar mugunta ta bar Farha da waya a kunne. A ganinta ko ma meye tunda har ta kirata ai da ta fada da baki. Kada kai tayi ta fara laluben sunan Yumnan a jerin sunaye dake bangaren status din. (Alhamdulillah my lion has proposed. Wedding bells ringing) Murmushin Farha sai ya koma dariya. Falo ta koma wurin kannenta tana tsallen murna ta nuna musu. "Korafi ya kare Ya Farha ta shirya da aminiyarta." Cewar Sauda ita ma tana tayata murna. Mardiyya kuwa rungume Farha tayi "congrats Sis. Ai na san sharrin fada da kawa. Ni da muka yi da Jamila har zazzabi na dinga yi" Yadda ta fada ya sanyasu dariya. Farha ta zauna a nan inda suke ta kira Yumna. "Wane lucky guy din (mai sa'ar) ne ya sace zuciyarki? Gaskiya sai nayi review na danna nawa stamp din." Yumna taji dadin farincikin da ta tsammata daga Farha. Wannan zai taimakawa shirinta na farko wajen soma wargaza gidan. Ita yanzu hatta Mamin da take yiwa kallon uwa bata da sauran gashi a idonta. Mulkin da take zubawa a waje shi za ta dora a cikin gidan don ma kada a sami mishkila. Ba za ta ragawa kowa ba balantana ta bada kofar da wani zai takata a gaba. Wannan shawarar cousin dinta ce wadda suke yawonsu tare. Numfasawa tayi zuciyarta tana dan dokawa da tsoro ta daure ta ce "sake duba status din na saka hotonsa. Zan dai zo har gida muyi shawara don ya ce nan da sati biyu yake son ayi komai." "Sati biyu? Lallai ki ce zama bai ganmu ba. Amma kin san mun tashi. Ki bari zan zo kawai sai mu taho tare ki ga gidan." So take ta ce mata ta riga saka kafa a gidan domin sun zo ita da Alh. Tahir yafi a kirga sai ta fasa. "To shike nan. Sai na ganki." Farha ta katse kiran ta koma kan status din Yumna ta sake budewa. (My Lion and I {ni da zakina}) kadai aka rubuta slide din da ya biyo bayan wanda Farha ta fara gani. Na gabansa ya sanya zuciyarta mummunar dokawar da bata taba yi ba tunda tazo duniya. Mahaifinta ne Alh. Tahir sanye da singileti da dogon wandon shadda ya zauna akan wata doguwar kujera. Akan cinyarsa ba kowa bace illa Yumna daga ita sai wasu figaggun kananun kaya. Ga hannuwanta sakale da wuyansa yana dariya. Bidiyo ne na sakan biyar mafi tsaho da ciwo a zuciyar Farha. Mummunan gamo ne wanda ko Suhaib da Lilu bata fatan ganin dayansu da wata mace a haka. Zazzabi, ciwon kai, tsananin bugun zuciya tare da sanyin jiki suka kamata. Jijiyoyinta suka neme daina kai sako yadda ya dace. Bata ji muryar kannenta ba lokacin da suke cewa ta nuna musu hoton mijin Yumna su gani. Bata ji bata ganin komai sai wannan bakin hoto da ya yi zaman dirshan a kwakwalwarta. Hawaye kuwa kamar ruwan famfo suka dinga ambaliya a saman kuncinta. "Allahumma ajirni fi musibati....Allahumma. Innalillahi..." take furtawa ta kasa kai karshen ko daya. A zabure Sauda da Mardiyya suka tashi suna tambayarta abin da ke faruwa bata kulasu ba. Mardiyya ta damke hannunta ta fizge wayar ta duba amma Yumna ta riga ta cire status din. Farha na gani ta danna musu delete. Bata san tafiya take yi ba. Yaushe ta je bakin kofar bangarensu? Allah Masani. Ta dai tuna lokacin da ta mika hannu da nufin bude kofar domin ta fita. Daga nan komai ya dauke cak sai ihun Mardiyya da Sauda suna kiran sunanta. ***** ~Don Allah 'yan uwa lokacin saka facemask ya yi yanzu fiye da baya. Mu daina fita mu da yaranmu babu ita. Akwai hazo, akwai kura sannan akwai CORONA. Kafin sanyi ya kankama kurar nan za ta yi ta damun mutane musamman yaran dake zuwa makaranta. Stay Safe~ #Comment #Share #VoteI just published "16" of my story "UWA UWACE...". https://my.w.tt/2soFKdUdtbb UWA UWACE...16 Batul Mamman💖 Rahman Ya Rahman Sa'idni Ya Rahman Ishrah qalbi Qur'an Imlah sadri Qur'an Wasli hayati Qur'an ~~~~~Mishary Rashid Alafasay "Ya naga kun yi carko carko kamar masu barin gari, lafiya?" Alh. Rabi'u ya ce idanunsa na binsu daidai da kallo. Baki ya saki da ya hango alamun jariri ne a hannun Maimuna ba kunshin kayan da ya zata da farko ba. Tambayar mai haihuwa cikinsu ya yi Uwani ta nuna Zara. "Shi ne ki ka taho nan maimakon ki wuce gidan mijinki daga asibitin? Me za ayi miki a nan wanda ba za ki sami dubunsa a gidan Alh. Unaisu ba?" Innayo tayi kwafa hade da murmushi mai ciwo. "Dama me za ta samu a gidan uban da bai san ci da shanta ba tun zuwanta duniya bare a kai ga batun hidimar aure?" Magana ce irin wadda bai taba ji daga gareta ba, shi yasa shigarta kunnuwansa ta gigita shi. Sake kallonta ya yi ko zai ga ta inda ta kuskure da wadda ya sani mai hakuri da kawar da kai tsayin shekaru. Ita kuwa Zara ta kalla. "Ki kira mijinki ko direbanki ko ki tura a samo miki abin hawa ki tafi." Zara ta sake fashewa da kuka ta koma rokon Alh. Rabi'u. "Baba ka bata hakuri na zauna a nan kamar yadda su Hajiyan Fatakwal suka ce. Idan na tafi yanzu wallahi matsala zan samu. Sun ce lallai sai na zauna nayi wankan jego..." "Laifi kika yi? Ko sakin ki ya yi?" Ya tambayeta cikin tashin hankalin kalamanta da na Innayo. "Saboda na sake haihuwar mace.." ta fada a kunyace murya a kasa. Maganar ta shigi Innayo sosai don ji tayi kamar da ita ake. Ita ce ake gorantawa haihuwar mata. Alh. Rabi'u sai ya yi nufin burge Innayo yau daya dai tunda ya fahimci ranta a bace yake. Fada ya soma ba ji ba gani. "Amma wannan yaro anyi dan iska. Ita macen ba 'ya bace?" "Ta ina mace take 'ya? Ai ka barshi ya wulakanta matarsa yadda aka yiwa uwar da ta raina lokacin da take ta haifar mata. Ita kuma ka barta ta koma inda ya fi gidan mahaifinta dadi. Banda abinka ai duniya tafi bagaruwa iya jima." Juyawa tayi ta shige dakin baccinta ta barsu a tsatstsaye su da mahaifinsu. Yana son cewa wani abu domin kallon neman agaji suke yi masa sai dai bai saba ba. Matsayinsa a gidan suna ne kawai. Ba ya bi ta kan yaran sai bukatarsa ta tashi kamar yadda ya yiwa Salima da Hasiya. Basu bar wurin ba wani almajiri ya ce ana sallama da Zara. Alh. Rabi'u sai ya leka a zatonsa mijinta ne. Maimakon ya ganshi sai direba ya gani an aiko shi da kayan tea, ruwan roba da maltina masu yawa. Zuciya ta kwadayi sai ya basu hanya suka fara shigo dasu. Kafin su gama Munzali ya dawo. Tasa motar ma shake take da duk wani kayan bukatar maijego. "Meye wannan?" Ya ce da yaci karo da ledar kayan tea din. Madara da milo manyan gwangwani bibbiyu. Sugar na kwali guda hudu sai su ruwan. Alh. Rabi'u da sauri ya ce "Mijin Zara ne ya aiko mata. Ku shiga dashi falona saboda 'yan barka kada su gani ayi ta hada shayi ba kai ba ...." Ai kuwa Munzali ya hasala. A iya saninsa yana bawa mahaifinsa kudin da bai ci ace gwangwanin madara zai daga masa hankali ba. Da karfinsa kuwa yasa kafa ya yi ball dasu. Direban da ya kawo da almajirin daya taya shi shigo dasu suka saki baki. Maimuna da Hasiya kuwa hakan ya musu daidai. "Ka dauka ka mayar ka fada musu nan ba gidan matsiyata bane. Zara kuma ta dawo gida kenan. Ita dashi sai ya zo gaban mahaifiyarta ya bata hakuri. Ka ce masa wannan sakon UBAN Zara ne!" "Ni?" Alh. Rabi'u ya ce yana dan ja da baya. Wannan ai sanadi zai masa ya toshe kofa daya ta arzikinsa. Ya kalli direban ya ce "kai wallahi ban fada ba. Alh. Unaisun nan ba wani ganin girmana yake ba za ka janyo min matsala dashi" ya kare yana hararar Munzali. Kallon tsanar da bai yi niyya ba ya jefawa mahaifinsa sannan ya kalli Zara. "Ke malama ki fa daina wannan kukan. Idan kin ga kin koma gidan wannan mara mutumcin to da yawun Innayo." Ransa na kuna ya fita ya nemo masu taya shi kwashe kayan tasa motar aka shiga dasu ciki. Uwani na kallon wannan dirama yadda Innayo ta tsame hannu akan Zara da kuma irin rokon da Maimuna, Munzali da Hasiya suka yi ta fama har ta kyaleta. Hada kayanta tayi ta shiga motarta ta bar gidan kafin a gama daidaitawa. Ita kadai a motarta take magana kamar sabon kamu. "Dole ma na karasa gini saboda bacin rana. Ji yadda Innayo take mata kamar ba 'yarta ba. Ita ma Zara banza. Da tana da hanyar samun kudi wallahi tafi karfin wannan wulakancin. Hummm. Ba gashi Munzali na shiga maganar Innayo ta sauko ba?" Allah Sarki Innayo. Duk barazanarta bata fatan kora Zara inda bata da daraja. Tabbas ranta ya baci amma tauna tsakuwa kawai take yi. Ta jira asa baki a bata hakuri domin Zaran ta gane da gaske take yi ne. Magiyar su Munzali taje mata akan gaba ne ba wai don nauyin aljihun dayansu ba. *** 'Yar karamar jakarsa mai cin kayan da basu fi seti uku ba ya zuge sannan kamar wanda ya yi aikin karfi ya zauna akan gadon a gajiye. Rashin kuzarin zuciyarsa ne ya harbi duka gabobinsa har ya haddasa masa wannan yanayin kamar na mai ciwo. Babu sauran jirgi mai zuwa Abuja yau. Shi kuma halin da yake ciki ba zai barshi yaji dadin tuka mota zuwa Abujan ba. Kansa yaji ya sara kamar an buga guduma lokacin da Hanne ta shigo dakin ta buga kofar da karfinta. Damuwa ce fal a ransa ya rasa wanda zai iya fadawa domin ya sami mafita. "Ashe daki ka shigo ina ta faman jiranka na zata kana wurin Munzali." Kansa ya rike da hannu biyu saboda magana ma kara masa ciwo take ga wayar Shazali dake shigowa babu kakkautawa. Hanne bata kula da yanayin nasa ba ta soma fada masa tasa an kawo mata mai-aiki ya kawo kudin sallamar wadda ta kawota. Da kyar Abbati ya iya bude bakinsa ya ce "yaushe muka yi dake zaki dauki mai-aiki da har zata zo ban sani ba?" Tabe baki tayi kafin ta ce "tohhh, daukar mai aikin ma sai na fada maka? Naga ba sabon abu bane tunda dama akwai tafiya tayi." Abin da ke ransa yafi karfin wata rashin kunya da Hanne za ta yi masa. Kada kai kawai ya yi ya bata kudin da ta tambaya sannan ya tashi. "Abuja zan tafi yanzu. Ban san kwana nawa zan yi ba amma bana sa ran yin sati in sha Allahu." "Adawo lafiya" Hanne ta ce hankalinta yana ga kudin da take kirgawa. Shi ma bai kulata ba ya dauki jakarsa ya fice. Sai da ya zauna a mota ya saka wani hadadden bakin gilas sannan ya tayar ya fita daga gidan. Ya kusa Unguwa Uku wayar Munzali ta shigo masa. Gidan mai ya shiga ya bi gajeren layin dake ciki sannan ya gyara murya ya amsa wayar. Munzali da shigarsa gida kenan "ina kaje ne? Na dawo babu motarka." Abbati ya dan kaurara murya yana murmushi "kai fa ka fiye naci. Yanzu daga baka ganni ba sai kira. Wannan idan kayi aure matarka ta shiga goma bama uku ba." "Naji. Ni dai ka fada min inda kaje. Wallahi ina ganin babu motarka gabana ya fadi shi yasa na kira ba wai don na damu da kai ba. Banda ni ma waye zai iya zama da masifaffe. Ka wani zama mafadacin karfi da yaji kwanakin nan. To dai ina kake in zo?" Munzali ya yi maganar yana shiga motarsa. Dariyar da Abbati bai son yi ce ta kubuce masa har Munzali yaji sautinta. "Ina hanyar Abuja." "In kaje ka gaida Zuma rock." Ya san bai yarda ba sai ya rantse masa tare da fadin karyar da ya shirya tunda Shazali ya kira shi kwanaki biyu da suka wuce. "Chief Harrison ke nemanmu. Shazali ya yi masa bayanin mun daina yaki yarda. Shi ne yace gara daya daga cikinmu yaje muyi masa bayani baki da baki. Wai a haka yana iya zargin ko hadin baki ne muka yi da abokin nan nasa da suka yi fada." Saboda yadda yake fitar da maganar daki daki da sanin cewa karya ce ya sharo har wani irin bugu yake jin zuciyarsa tana yi. Da wahala idan akwai watarana da suka taba yiwa juna karya shi da Munzali. Munzali ya saurari dogon bayanin amma abu daya ne yafi daukar hankalinsa. Hade girar sama da kasa ya yi kamar Abbati na kallonsa ya ce "Wait! Ba mun ce ko waya ba za ta sake hadamu da Shazali ba? Menene nasa na kiranka yanzu?" "Na fada maka..." Abbati ya soma fada yana jan motarsa gaban bututun zuba man. "Yes ka fada naji amma ban yarda ba. Haba Abbati! Shazali dan is** ne kuma gogaggen makaryaci. Ka sani ko wata manakisar ya shirya maka tunda ya san Chief yana mutuwar sonka." "Nima nayi tunanin haka sai na ce gara naje dai muyita ta kare dasu kawai." Shi ma da yake maganar ba shigarsa take ba saboda raunin hujjar da ya bayar. Da wane baki zai fada masa cewa kwanaki biyu kenan da ya sami alert mai tsoka kuma ana jiran yaje ya yu aikin kudin? "To amma me yasa baka fada min ba? Me yasa kuma baka jira mun tafi tare ba?" Abbati sai ya amsa masa da cewa baya so ya kawo masa matsalar da zata sa ya bar 'yan uwansa a yanayin da gidansu yake. Ya dora da nuna masa illar rashin ganin ko mutum daya cikinsu saboda matsayin irin mutanen da suke bi a da. Munzali tun yana ta kokarin kure shi da tambaya saboda rashin gamsuwa har ya hakura ya amince. "Don Allah ka kiyaye kar suyi maka wayo don na sanka sarai." Abbati ya saki rai jin Munzalin ya dauko wasa. "Ai baka da kunya dama kuma yau tun safe bamu hadu kayi min ba. Zan kira ka idan na kuma tsayawa yanzu zan hau titi." Sun gama sallama Munzali zai katse kiran ya fasa. Haka nan yake jin wani irin nauyi a ransa. "Abbati wallahi idan ka bari suka yi wani abu da kai ALLAH YA ISA." Wani irin radadi ya rike duka jijiyoyin idanun Abbati saboda kukan da yake jin zai iya yi. Tafiyarsa daidai take da cin amanar Munzali, Baaba Mari da tuban da ya kuduri niyar yi. "Me ka ce?" "Allah Ya isa na ce. Mutumina kayi duk yadda zaka yi ka fito lafiya. Kaga ka jirani in zo mu tafi tare mana" ya kare a raunane yana mai jin tsoron kada ayi amfani da saukin kan Abbatin. Sai da ya dake ya iya cewa "kaima ka san zan kiyaye. Idan na sami damar ganinsa a daren yau ma to gobe zan dawo in sha Allahu." "No..a'a fa. Wane irin da daddare? Ka jira gobe ku hadu koda a restaurant ne da rana tsaka kuma a wuri mai mutane. Ka fada masa komai ka. Kuma ka tsaya akan bakanka ka ce musu mun daina duk aure zamu yi." Ya dan sako wasa yana dariya kasa-kasa "Idan kana dawowa ka jirani a Kaduna inje wurin Diamond girl." "Wai da gaske ka ke akan yarinyar nan?" Kyakkyawar fuskar Farha na dawo masa tar a idanunsa. "Tausayinta naji ranar nan. Sai nake ganin kamar irina ce ta tashi uwa bata damu da ita ba. Tunda kai ka fasa da yayarta ni dai ina ciki da kanwar. Allah Ya kiyaye hanya." Daga haka ya ajiye wayar zuciyarsa babu dadi. Abbati kuwa kwalar idonsa ya hana zuba sai zafin dake yawo a ilahirin jikinsa. Dama can sun san haram suke aikatawa amma shaidan yafi karfin zukatansu. Yanzu kuma da suke jin sun shirya komawa ga Allah sai shaidanu suke neman hanasu. Wani irin abu ne ya soki kokon ransa da ya ayyana a ransa ko bashi da rabon tuba ne? Ko dai baya cikin masu dacewa da rahamar Allah? Zuciyarsa sai ta sare. Karfin gwiwarsa ya ragu. Tsoro da fargaba suka mamaye dukkan tunaninsa. Me yasa suka biyewa son zuciya a wancan lokacin? Ya akayi ya zama daga cikin masu raya zunubin mutanen Annabi Luďu AS? Tabbas ya san basu da alhakin dulmiyar da kowa amma idan ya tuna sun rayu kwatankwacin rayuwar karuwa sai yaji ya tsani kansa. Sun bi musulmi sun bi kirista. Manyan masu fada aji a kasar nan duk suna tafin hannunsu domin sun san sirrinsu. Kafin ya isa Kaduna zazzabi ya rufe shi. Tukin gagararsa yake neman yi don sau biyu yana auna arziki bai karawa wani ba. Da tambaya ya samu aka kwatanta masa asibiti mafi kusa da titin da yake bi na fita gari. DOCTORS HAVEN Shi ne sunan da ya gani an rubuta kato a jikin bangon dake kallonsa na asibitin. (Yana daga cikin kokarin Shaidan la'ananne akan bayin Allah ya sarar musu da gwiwa yayin tuba. Ya kan sanyawa mutane hopelessness har kaji kamar tuban ba zai amfaneka ba. A bangare guda kuma Allah SWT zai iya jarabtar bawa da kalubale domin Ya kara masa ladan hakuri da jajircewa wurin tuba. Muhallishshahid shi ne kada mu karaya. Mu dage iyakar dagewa mu tsaya akan bakanmu. Idan Allah Yaso sai mu rayu cikin zunubi kuma Ya saukaka mana tuba da komawa gareShi. Sannan rahamarSa ce idan Ya so ya kawo mana nau'ikan jarabawa akan hanyar tubanmu domin mu kara imani. ALLAH SHI KADAI NE BASHI DA ABOKIN TARAYYA. Ya bamu ISTIGFARI domin Ya daukaka darajarmu rana gobe kiyama. Idan mun tsaya da ikilasi to lallai Allah zai bamu mafita da izininSa.) *** Mami Khadija na daki tana aikin tsara slides (power point) na lecture din da take dashi da 'yan masters sati mai zuwa taji kamar ana kiranta a waje. Gilashin idonta ta tura ciki sosai ta tashi daga gaban teburin aikinta da sauri. "Sauda? Farha? Mardiyya? Kai waye yake min wannan kiran ne kamar ana kuka?" Hanyar fita zuwa bangarensu tabi inda take jin muryoyin. Sai da tayo kusa ta fahimci Sauda da Mardiyya ne suke kukan. A bakin kofa taci karo da Sauda wadda ta taho domin kiranta. Nan kuma idanunta suka sauka akan Mardiyya tana girgiza Farha tare da kiran sunanta cikin kuka. Da gudu gudu ta karasa gabansu ta durkusa a wurin. "Me ya sameta?" "Bamu sani ba Mami. Daga duba status din Yumna ta fadi." Cewar Mardiyya hannunta na rawa wurin shafawa Farha ruwa a fuska. Ran Mami Khadija ya baci sosai ta ce "Yumna? Gaya min yadda abin ya faru. Sauda dubo min mazan nan mu kaita asibiti." Bayan fitar Sauda ne Mardiyya ta fadawa Mami abin da suka sani. "Na duba banga hoton ba amma na tabbata ganinsa ne ya sumar da ita." Fuskar Mami tamkar bata taba murmushi ba baŕe dariya ta tashi tsaye. Lilu ne ya shigo lokacin Farha ta bude ido da kyar. "Ku bani wayata" ta ce a tsorace tana gudun kada su ma su gani. Yadda tayi ya tabbatarwa Mami Khadija cewa lallai hoton ya shafi mahaifinsu. Wayar ta mika mata don ta sami saukin rai har tana nuna mata kamar ranta ya baci ganin bata da lafiya amma tana neman waya. Farha bata ce komai ba sai kai da ta sunkuyar. Kunyar mahaifiyar tasu take ji sosai da tausayi. Ga wata irin tsana mara takunkumi da take hauhawa a zuciyarta ta mahaifinsu. Mota ta ce su wuce ta tafi dauko mayafinta a daki. Ta dauko jakarta ta saka wayarta a ciki. Ji take kamar ana caccakarta da allura saboda bakin cikin halin da Alh. Tahir ya sakasu a ciki. Albarkacin 'ya'yan nan yaci kuma yake kan ci da tuni ta bar gidansa. Ba za ta yarda ya lalata mata tasu rayuwar da rashin kamun kansa ba. Doctors Haven asibitin da suke zuwa duka gidan Lilu ya kaisu. Farha da kafarta ta shiga kuma tana ta rokon Mami akan su koma gida. "Zan saba miki idan ki ka sake magana Farha." Bata sake cewa uffan ba har aka kira sunan file dinsu suka shiga wajen likita. Abu na farko da likitan ya fara gani shi ne jininta dake barazanar haure mizanin zaman lafiyar dan Adam. "Hawan jini nema yake ya tashi daga ciwon manya zuwa na kowa da kowa."ya ce a kokarinsa na yiwa Mami Khadija bayani "ki saka mata ido ta cire damuwa daga ranta kada a gaba ya zame mata ciwo." "In sha Allahu zan kula doctor. Nagode." 'Yan rubuce rubuce ya yi a takardar gabansu ya mikawa Farha takardar. Magungunan da zasu saya ne ya rubuta. Shiru suka fito babu mai magana sai hannunta da Mamin ta rike. Gani take kamar idan ta saketa damuwar dawowa za ta yi har ta kuma sumar da ita. "Jeki mota ki huta na karbo magungunan." Muryarta can kasa duk tayi laushi ta ce "zan iya Mami ki je ki zauna." Lilu yana bangaren da aka jere kujeru ya hangosu ya taso. Mami ta ce ya tafi da Farha mota su jirata. So take kawai su bar inda take ta samu ta fito da zahirin halin da zuciyarta take ciki babu rufa rufa. Tana kallo suka sauka daga matattakalar kofar fita waje sannan ta sami wuri ta zauna maimakon sayen maganin. Hawayenta ta bari suka sauko a lokacin da ta sanya fuskarta a kan tafukan hannayenta. Yana daga cikin abin da take gudu ace duka 'ya'yanta sun san halin mahaifinsu. Sai gashi bayan Suhaib ga dukkan alamu Farha ma ta sani yau. Rayuwarta da ta sadaukar saboda karesu tana shirin zama shirme da bacin lokaci muddin aka tafi a haka. Yaranta zasu daina ganin girman mahaifinsu. Tarbiyarsu za ta tawaya domin yana da hakkin matsayin uba a wuyansu. Wace irin rayuwa zasu yi a gaba? Wane irin mutum Allah Ya jarabceta da aure? Yana da damar karin aure. Ga kudi. Kai idan ya so ma ya sake su duka ya sake sabon zubi a gidansa da dai wannan kazamar rayuwa mara fasali. A cikin motar Lilu ne yake ta damun Farha akan ta fada masa wane irin hoto Yumna ta turo mata. Tausayin yayar tasa yake ji har yana hasashen ko dai mutumin wani ne da Farhan take so a gefe. Maganar hankali irin wadda bai saba ba yake yi mata tare da ban baki "Kin san dai babu wanda zai auri matar da ba tasa ba. Ki bar mata shi kawai. Naki mijin fa idan ya tashi zuwa sai Kaduna ta girgiza." Murmushi tayi wanda ya hade da zubowar hawaye. Za ta barshi ya cigaba da wannan tunanin har zuwa lokacin da kowa zai sani. Iyaka dai bata fata ko kadan wani ya fahimci akwai mummunar alaka tsakaninsu tun a waje. A lokacin da suke 'yar hirarsu ne kuma idanun Lilu suka kai bakin gate din asibitin. Motar Suhaib ce take shigowa yana waya dasu Sauda masu damunsa yaya jikin Farha. Motar bayansa wanda ya zata mai ita yana jiran ya wuce ne shi ma ya yi nasa parking din ta soma karar horn da karfi. Tsaki ya ja da karfi saboda anki daina danna horn din "Zan kiraku Sauda" ya jefa wayar gefensa ya kauce. Har ya gama parking babu sassauci a karar horn din. Mutane suka fara kallon motar ana 'yan surutai. Kimanin minti biyu a tsakani da suka fahimci ko motsi motar bata yi sai hankula suka fara tashi. Suhaib yana so ya shiga ya ga halin da kanwarsa ke ciki ya dakata. Shi ya fara zuwa gefen direban ya kama hannun zai bude yaji a rufe. Gashi gilas din da duhu baya ganin komai. Farha da Lilu da 'yan tsirarun mutanen wurin sun firfito an tsaya a wurin. Ta gilas din gaban motar suke iya ganin kan matukinta akan sitiyarin kuma baya motsi. "Ki koma mota Farha bari mu gani ko zamu iya balle kofar a fito dashi" cewar Suhaib ganin tana tangadi kamar za ta fadi. Bata san me ya fito da ita ba kamar yadda Abbati bai san ya akayi ya iya daga kansa dake tsananin ciwo a lokacin ba. Sannu a hankali yake dagawa saboda kwankwasa gilas din da ake yi ta kowane gefe ana cewa ya bude domin a taimaka masa. Sakan daya, biyu, uku...goma, talatin...idanun Abbati suka sarke cikin na Farha suna kallon juna. Bata tabbatar shi ne na diamond plaza ba amma fuskar ba bakuwarta bace. Abbati kuwa mamaki ne ya kashe shi a zaune. Da ace bai ga Lilu yaron da ya fara tsayuwa yin hoto a motarsu ba, da Suhaib wanda ya bashi hakuri da sai ya ce lallai gizo take yi masa. Kai ya girgiza a hankali ya runtse idanunsa sannan ya sake budewa yana kallon inda take. Fuskar da ta zame masa hoton zuciya ya sake gani ta dan yamutsata tare da dafa gaban motar don kada ta fadi. Rana ce ta take sosai mai zafi. 'Uncle Abbati?' Ta yiwa kanta tambayar da sunan da ta lakaba masa lokacin da ya dinga kiranta Ya Farha. 'Bata da lafiya' shi kuma wani sashe na zuciyarsa ya sanar dashi yana mai jin karfi na zuwar masa. Cire lock din kofar ya yi Suhaib ya bude da sauri. Ya zuro kafarsa waje hasken rana na saka shi kare fuskarsa da hannu saboda yadda yaji kamar ta kara masa ciwon kai. "Lilu kula da Farha kafin mu shigar da mutumin nan ciki" Sune kalaman da Abbayi yaji matashin da ya bude kofar yana kokarin rike shi ya fada. Dubansa ya kai gareta yaga yadda take takawa a hankali duk da daya saurayin wanda yake tsammanin shi ne Lilu din ya riketa. Takunta da duk wani motsinta ya dinga zama a zuciyarsa tamkar ana zana shi da kakkaifan alkalami. Yana da tarin matsaloli a kansa amma sake ganinta sai ya kankantar da komai. Tubalin dan guntun ginin da ya soma yiwa zuciyarsa katanga daga barin soyayyarta ya ruguje baki daya. Irin wannan coincidence din yafi karfin rainawa. Bai iya dauke ido daga kallonsu ba har ta shiga mota ta kwanta a baya. Bin Suhaib da wani Security din asibitin ya yi ciki. A hanya suka hadu da Mami Khadija, wata mace da ya gani mai cike da haiba da nutsuwa tamkar mahaifiyarsa Baaba Mari. Wannan kam da gani babu tambaya uwa ce ga wadannan bayin Allah. Fuskarta kamar ba ita tasha kuka ba. Bandaki ta shiga ta wanketa sannan ta goge kwarmin idonta da kwalli ya bata ta daidaita shi. Kallon Abbati tayi wanda ko ba a fada ba ta san bashi da lafiya sannan ta tambayi Suhaib ko waye shi. A takaice ya labarta mata yadda suka hadu ta kalle shi da tausayawa. "Bari na kaiwa Farha maganin sai naja motar shi kuma Lilu ya jiraka. Ka zauna dashi har ya dan sami kuzari sai ku kira 'yan uwansa." Ta sake kallon Abbati "Allah Ya sauwake kaji." Tafiya tayi suka karasa reception. A nan Suhaib ya fahimci Abbati bashi da file a asibitin da ya amsawa matar wurin cewa babu amma zai iya budewa yanzu. "Kiyi masa amfani da namu" cewar Suhaib yana tura mata file din da ta dauko lokacin "idan yana bukatar budewa ayi daga baya. He needs a doctor now (yanzu likita yake bukata)" Abbati ya yi masa godiya sosai. Da zai shiga wurin likita sai Suhaib ya tambaye shi wanda ya kamata a sanarwa yana asibitin. "Daga Kano nake kuma Abuja zan wuce. Idan na fito zan kira kanina" ita ce amsar da ya bashi. Suhaib sai yaji ba zai iya tafiya ya barshi ba. Jira ya yi har likitan ya leko ya ce waye ya kawo Auwal. Tunda bai san sunansa ba sai ya dan yi daburce kafin ta tuna cewa wanda ya rako shi kadai ne ya shiga ciki. "Gani" ya fada yana mikewa. "Yauwa Suhaib ashe dan uwanka ne. Koda yake naga file din gidanku. Me yake faruwa ne ake ta zuwa da hawan jini. Nasa is very bad damuwa tayi masa yawa dole zan kwantar dashi don nayi monitoring dinsa." Bin bayansa Suhaib ya yi. Nan ya tarar da Abbati a zaune amma ya kifa kansa a teburin likitan. Da fitar likitan wayar Shazali ya amsa wanda ya fada masa maganganu masu tada hankali. Yayi haka ne saboda gudun kada Chief Harrison ya nemi Shazalin ya maido da nasa kamashon kudin. "Ran Chief ya baci fiye da zatonka. Yanzu haka ya tura gidanka na Kano a taho da kai. Mutanen sun tabbatar masa baka gida ya ce a dauko Munzali tunda tare kuke." Abbati yana da saukin kai. Saukin kan da yawansa ya sanya Baaba Mari gudun tafiyarsa almajiranci. Gashi yau dashi Shazali yake amfani. A raunane ya yi magana "Na fada maka ina hanya. Gani a Kaduna da kyar na karaso asibiti. Bani da lafiya Shazali." Kausasa murya ya yi duk da bata fita da karfi ya ce "Idan ka shigo da Munzali cikin abin kuma wallahi sai na nuna maka nawa kalar haukan". Ya san Abbati sarai. Ba zai taba yi masa karya ba saboda shi mutum ne kaifi daya kuma mai yawan kyautata zato. Ba dabi'arsa bace bincike da bin kwaf balle ya gano karyar da ya yi masa. Hasali ma Chief Harrison ya bashi damar kawo masa kowane irin namiji. Da ya ce zai kawo Abbati ne ya kara nasa dubu dari akan abin da ya bashi. "Tsakaninmu bata baci Abbati. Ka maida wukar. Zan yi masa bayani sai na hada shi da wani." Suhaib ne ya taimaka masa zuwa dakin da aka bashi ya kwanta. Yana wurin aka zo aka dibi jininsa domin gwaje gwajen cututtuka irinsu maleriya. Bayan an gama an soma yi masa karin ruwa aka hada da allurar bacci. Baccin na fizgarsa Suhaib yana son sake tambayarsa wanda zasu nema ya kula baya cikin hayyacinsa saboda karfin allurar. Likitan ya ce yana bukatar hutu sosai. Waje ya koma inda Lilu yake zaune akan mota yana jiransa. Mukullin ya cilla masa yana yi masa bayani. "Ya yi bacci kafin ya bani nambar wani nasa na kira. Zan zauna kaje gida ka karbo bedsheet da bargo don na kula akwai hadari." Lilu ya tafi shi kuma ya koma ciki. Har Lilu ya dawo da kaya niki niki wanda Mami Khadija ta hado domin kwanciya Abbati bai farka ba. Suhaib ya duba wayarsa amma a rufe take bare ya dan duba sunaye. Hakura ya yi tunda Mami ta ce ya jira ya tabbatar wani nasa ya zo. Ba jimawa da Suhaib ya ajiye wayar a kan wani tebur da ake ajiye kayan abinci na mara lafiya Munzali ya kira. Sun yi dashi zai kira shi idan ya tsaya amma shiru. Daya layin nasa wanda wayar tana mota yana shiga shi ma bai ji an dauka ba. Haka ya dinga kira babu kakkautawa saboda hankalinsa dama bai kwanta da tafiyar ba. Haka kawai tunane tunanen ban tsoro suka far masa ya kasa sukuni. Kasa zama ya yi ya tashi ya tafi gidan Shazali. Ya san da wuya ya ce masa yana gida idan kira ya fara yi. Maigadinsa bai hana Munzali shiga ba tunda ba bako bane. "Ka dage kafi Abbati bashi farinciki. Ina mai tabbatar maka duniya sabuwa za ka bude idan ka kama manyan nan a hannu." Kalaman da suka sauka a kunnuwan Munzali kenan yana shirin yin sallama a budaddiyar kofar shiga gidan Shazali. A shirye yake yana takowa bakin kofar yana waya zai fita. Idanunsa na sauka akan na Munzali da yake bashi da gaskiya sai ya ja baya. Munzali kuwa ya ce da wa Allah Ya hada shi....cakumar wuyan Shazali ya yi gami da yi masa mummunar shaka. Da ihu yake masa magana idanunsa sun gama kankancewa. "Ina Abbati?" "Wane Abbatin?" Rufe bakinsa ya yi daidai da saukar naushi a bakin. "Wane Abbati? Ni ka ke tambaya wane Abbati?" Shazali sai ya fara kokawar kwatar kansa saboda Munzali zai iya yi masa lahani. "Kaga Malam nima da na ce yaje Abuja ya musu bayani bai karasa ba. Dazu muka yi waya ya ce min yana asibiti wai bashi da lafiya." "In na yarda Allah Ya tsine min. Kai Shazali! Dubeni da kyau wallahi. Munzali ne. Ka sanni ba tun yau ba. Bani da mutunci ko kadan akan abin da ya shafi Abbati. Ina yake?" ya furta a fusace. Jijiyar kansa tuni sun firfito idanu sun yi ja. Cikin jin haushin naushin da ya masa ya ce "Dama ta ina zaka yi mutumci a kansa tunda har yanzu kana begen ku cigaba da..." Wannan karon bai gama hada kalamansa ba wani naushin ya sauka. Munzali ta dinga dukansa a haukace yana cewa ya fada masa inda Abbati yake. "Indai kana tunanin waccan soyayyar nake yiwa Abbati to kayi kuskure. Ni da Abbati ma'abota inuwar Al'arshi ne in Allah Ya yarda (duba hadisin Qudsi dake magana akan mutanen da Allah zai sanya a inuwar Al'arshi ranar lahira. Allah Ya amintar damu da masoyanmu na gaskiya da wannan ni'ima. Amin). Wannan shi ne tsakanina da Abbati!" * Karfe bakwai da rabi Abbati ya tashi. Ya farka kansa ya yi nauyi amma babu ciwo sosai. Munzali ne ya fara fado masa a rai da ya hango duhun waje. Da sauri ya shiga laluben wayarsa saboda ya san dole yana can cikin tashin hankalin jinsa shiru. Inda Suhaib ya ajiyeta ya hangota. Zai dauka Suhaib din ya dawo daga masallacin kofar asibitin. Godiya sosai Abbati ya sake yi masa. "Babu komai. Za ka samu ka kira wani ko?" "Eh yanzu zan kira. Nagode." "To ga abinci nan. Zan dawo da safe in sha Allah. Ko in zuba maka?" Saukowa daga gadon Abbati ya yi "ka barshi naji kwari ai. Zan fara yin sallolina tukunnan." Suhaib ya fita shi kuma ya shiga bandaki. Da ya idar da sallah ya dauko wayar domin ya kira aka yi rashin sa a chaji ya kare. Aljihunsa da inda ya ga wayar ya duba babu mukullin motar balle ya je ya dauko chaja da daya wayar. Fita ya yi cikin sa a ya sami motar an gyara mata parking. Duk yadda aka yi wanda ya gyara din bashi da nufin cutarsa. Zuwa wayewar gari idan ba a kawo ba sai ya yi cigiya. A reception din ta sake tsayuwa ya tambayi wadda take kan aiki aron waya. Mata ta hade girar sama da kasa. "Ba sai kin bani ba. Zan fada miki nambar idan an dauka ki ce a kira Abbati ne." Kunkuninta tayi ta gama sannan a wulakance ta ce ya fadi nambar. Bai nuna jin haushin abin da tayi ba ya fada mata ta kira. Munzali na dauka a dakile ta ce "ka kira layin nan wani Abbati yana son magana da kai." Yana dakinsa lokacin ya rasa me yake masa dadi. A gefe ga jaka ya hada kaya da duka atm cards dinsa a ciki. Waya kuwa baya nisa da ita yana ta adduar Allah Yasa ba mugun hannu Abbati ya fada ba a hanya. Wannan wayar ta shigo a kan gaba. Matar na kashewa ya kira hannunsa har rawa yake. Da wayar kamar bata so haka ta mika masa. "Munzali kayi hakuri" Ya fara cewa sannan ya fada masa abin da ya same shi. "Yanzu yaya jikin naka? Zan taho na san in sha Allahu kafin sha biyu na iso." "Kar ka soma tafiyar dare. Bani da wata matsala yanzu." Duk yadda Munzali ya so Abbati hana shi tahowa ta yi. Da bacin rai karara a muryarsa ta ce "Da asuba zan taso." "Naji. Allah Ya tsare hanya." Abbati ya amsa da murmushi. Mai waya dai sai cika take tana batsewa wayar tasa ta kusa minti shabiyar. Da ya gama ya mika mata ta dan murguda baki. Wani murmushin ya yi sannan ya zura hannu a aljihu ya ciro dubu uku ya bata. "Ga ladan aron waya" Kunya ta kama ta amma bata sa ta mayar da kudin ba. Sai ma dannesu da tayi da hannu. "Laahhh babu komai fa. Idan baka gama ba ka kira shi ma." (Kudin wayar bai wuce naira hamsin ba) "Mun gama. Nagode" Ya fara bin hanyar dakin da yake yaji tana cewa "ni suna na Rufaida. Idan kana so ka dinga zuwa aron wayar kafin a sallameka." * Da sauri sauri har yana tuntube Alh. Tahir ya nufi bangaren Mami Khadija inda aka ce masa Farha tana kwance. Ya saba duka yaransa banda Suhaib yana waya da kowa kafin ya baro office. Shi yasa babu matsalarsu da bai sani ba. Rashin miji a wajen Farha kuwa nasihun da yake mata suna matukar tasiri a ranta. Yau da bai sameta ba sai ya shiga damuwa. Idan ya kirata kiran na shiga take rejecting call din. Shi ne ya kira Sauda take fada masa bata da lafiya har sun je asibiti sun dawo. Meeting suke yi mai matukar mahimmanci amma haka ya fito ya ce gobe a cigaba. Ya kusa kofar dakin daga bayansa yaji kira daga Mami Khadija. "Ina son magana da kai amma a dakinka." Kallon mara tunani ya yi mata. Wace irin magana zasu yi a kebe Farha ba lafiya "Ko ma meye ki jira don Allah in duba yarinyata." Hannuwanta ta harde a kirji ta ce "abu mafi muni da za ka yi mata a yanzu shi ne ka nuna mata fuskarka a yau." A tsorace ya juyo "fada mata zan auri Yumna kika yi? Haba Khadija! Ba na ce zan yi musu magana da kaina ba?" Gaba tayi abinta. Bashi da zabin da ya wuce binta dakinsa. Suna shiga ta ce ya dauko wayarsa ya kira Yumna. "A wane dalili?" "Ka kirata ko ni na kira." Da gaske take yaga alama. Kiran ya yi ai kuwa Yumna ta dauka da salon muryar da take yi masa idan suna tare. "Zakina" Mami Khadija ta tabe baki "daga Diya kuma yanzu Zaki ka koma? Tafe tafe sai an sami mai kiranka kadangare." Harara ya jefa mata ransa na baci. Zai yi magana ta karbi wayarsa. "Yumna ki saurareni da kyau ki ji abin da zan fada miki." Hantar cikin Yumna ta kada amma ta kasa kashe wayar. Mami Khadija ba sa'ar yinta bace. Akwai layin da duk rashin kunyarta bata isa ta ketare ba. "Babu ruwana da abin da ya hadaki da Maigidan nan. Duk wani shirme da shiriritar da ki ke yi da rayuwarki ya tsaya kanki da abokan shaidancinki" tayi maganar idanunta a kansa. Wani irin sanyi yaji ya ratsa shi na tsantsar kunya. Amma bai ce komai ba har ta cigaba da magana. "Ki fita harkar 'ya'yana. Babu ke babu Farha. Bana bakinciki da shigowarki gidan nan a matsayin matar aure amma muddin ki ka dasawa ranki taba min yara to ki saka a ranki ke da Tahir sai dai a titi. Bana magana biyu saboda haka don't try me." Wayarsa ta ajiye masa a kusa dashi ta fice daga dakin. Jiki na rawa ya kuma kiran Yumna. "Turo min abin da ki ka turawa Farha har ya sumar da ita." "Zakina.." ta ce tana shekar kukan kissa. "Zakin uw**ki. Ki turo min yanzu yanzu kafin na tambayeta." Ya daka mata tsawa. Yumna sai ta rikice. Gumi ya dinga karyo mata. A haka ta tura masa video din jiki ba kwari. Alh. Tahir zabura ya yi da ya bude. Nasa gumin tamkar an kwara masa ruwa. Yanzu ace wannan abu Farha ta gani? Mutumcinsa kaf ya zube tunda ya san cewa ta gama ganinsa a wannan yanayi. Kulle kansa ya yi a daki ya rasa tudun dafawa. Yana son Farha amma ya tabbata yadda Suhaib ya guje shi ita ma haka za ta yi. Tun Yumna na jiran ya kirata yayi masifa har ta hakura. Bata san abin zai hada da asibiti ba. Sannan gashi a gabansa kuma da wayarsa Mami Khadija tayi mata magana. Hakan na nuni da cewa wanda take yi dominsa shi ma yana shakkarta. Status din nata dama ta rufe babu mai gani sai Farha saboda kar ta sami matsala a gida. To gashi ta sami matsala da wanda take shirin shiga gidansa. * Bacci rabi da rabi Farha tayi a daren ranar saboda tana rufe ido abu daya take gani a mafarki. Mami Khadija bata matsa mata da tambayar me ta gani ba. Ta dai ce mata kar ta ja da hukuncin Allah game da mijin da Yumna za ta aura. Addu'a ce kawai tasu tunda basu isa su haramta halal ba. A gefe daya ga tunanin mutumin nan na asibiti da ya addabeta. Ji take ta tsani maza babu sauran nagari tunda mahaifinta ma bai tsira daga tarkon shaidan ba. To amma ta kasa cire yanayin da ta ganshi na rashin lafiya daga tunaninta. So take taji halin da yake ciki ko za ta sami sauki a zuciyarta. Abin gabadaya sai ya dinga bata haushi. Emotions sun yi mata yawa suna ta karo da juna. Da gari ya waye sai ta tashi da ciwon barin kai saboda rashin isasshen bacci. Mami Khadija ta bata magani tun asuba. Karfe bakwai da rabi ta gama shiri saboda tana da aji karfe goma a ABU. Direbanta har ya iso ita yake jira sai ga Suhaib. "Ina zuwa da sassafen nan na ganka a shirye?" "Wallahi Mami mukullin motar mutumin jiya ne na gani a aljihuna da asuba. Ya barshi a motar da na gyara masa parking ashe ban ajiye a dakin ba." "Ai kuwa gara kayi maza ka kai masa." Ta kalli Farha wadda ana ambatonsa taji faduwar gaba "yi maza ki shirya ki bishi." Sannan ta juya ga danta "Suhaib ta sake ganin likita. Da ciwon kai ta kwana. Hawan jini yana sa ciwon kai. Bana so ya zame mata ciwo tun da kuruciyarta. Gara taje ta sake yiwa doctor din complain. Ga wannan ku tafi wa mara lafiyar dashi" ta ajiye kwandon abincin da aka hada mata na zuwa office. Damuwar Farha ta mantar da ita tasa ayi abincin safe dashi. Cikin minti ashirin ta shirya cikin riga da sket na atampa. Hijabi mai hannu ta saka navy blue wanda ya kusa kwaurinta. Fuskarta tayi fayau babu kwalliya sai hoda da kwalli. A mota Suhaib yake ce mata kamar ya taba ganin mutumin. "Kamar shi ne mai motar nan na diamond plaza." "Ikon Allah" ya dinga cewa yana murmushi "idan kuwa haka ne ai ku bashi hakuri wannan karon tunda wancan lokacin kun gudu." Da suka shiga asibitin Suhaib sai ya wuce dakin da Abbati yake ya ce in ta gama ta biyo shi sai su gaisa. Ita ma bata sami ganin likitan ba ance sai karfe tara zai zauna. Yanke shawarar bin Suhaib ya zo ya kaita gida kawai tayi. Kila idan tayi bacci za ta ji sauki. * "Jiki ya yi kyau gashi har kayi wanka" Suhaib ya ce da ya shiga dakin ya ajiye kwandon hannunsa. "Alhamdulillah. Nagode sosai da taimakonku gareni." Munzali wanda ya iso awa daya da ta wuce ya taso ya mikawa Suhaib hannu suka sake gaisawa. Wayar matar jiya ya kira ta kwatanta masa asibitin. "Nagode sosai. Daga yau ka zama dan uwanmu kaima. Ni sunana Munzali, kai fa?" "Suhaib" Mukullin motar ya mikawa Munzali yana basu hakurin mantuwarsa. Sun nuna masa babu komai har suka soma taba hira. A dan wannan lokacin ya fahimci yadda suke son juna. A haka dai kamar su ga hanjin juna da mara lafiyar da mai jinya. Sai kawai ya dinga murmushi yana kallonsu. Su ukun suka kalli kofar dakin da aka kwankwasa gami da yin sallama da tattausar murya amma ba a bude ba. Abbati ji ya yi duk wata na'urar jikinsa ta tsaya. Ashe dadin muryarta da yaji a waya ba komai bane. Yanzu ya san yaji muryarta domin duk wani gashi na jikinsa ya mike kamar zasu amsa sallamar. "Yi hakuri kanwata ce. Na ce ta sameni a nan ne idan ta ga likita." "Meye abin bada hakuri? Kanwar dan uwanmu fa kanwarmu ce" Cewar Munzali ya daga murya ya ce "shigo." A hankali ta turo kofar kamar tana jin tsoron. Kanta a kasa ta shiga ta sake wata sallamar. Munzali da Suhaib kadai suka amsa. Abbati kuwa yawun bakinsa ma ya kafe. "Kanwarmu ya jiki? Kin sami ganin likitan?" Kallon mai tambayar tayi niyar yi sai idanunta suka sauka akan na Abbati. Da sauri ta kawar da kanta gefe ta amsawa Munzali wanda yake mata fara'a. "Da sauki amma sai tara Doctor din zai zauna. Ya Suhaib ko za ka kaini gida kawai?" Ta marairaicewa Suhaib saboda a takure take jin kanta. "Sai dai ki rakani ATM . Maybe kafin mu dawo taran ta yi" Munzali ya kalleta ya girgiza kai "bata da lafiyan za ka kwasheta wani wajen? Barta kawai ta zauna a nan ko ka kaita gidan idan babu nisa. Amma kafin nan don Allah rakani in kama mana hotel idan akwai a nan kusa. Da alama yau za a sallamemu. Gashi bana son mu kama hanyar Kano sai ya kara jin sauki. Ni kuma ban san kan garin nan ba." Suhaib ya ce akwai wani kurkusa dasu su je ya nuna masa. Mukullin motar da suka zo ya mikawa Farha ya ce ta jira shi a motar kafin su dawo. Munzali ne ya fara fita sai Suhaib din. Farha ta kusa bakin kofa Abbati ya kirata. Zuciyarsa taki bashi hadin kai na kar ya kula ta. "Ya Farha" Abbati ya furta da wata irin siga da ta tsaya mata a zuci. Tsayuwa tayi gabanta na harbawa da sauri. "Yaya jikin naki?" Kunya sai ta lullubeta. Shi da ya kwana a asibiti ko gaishe shi da jiki bata yi ba. Bata san me yake damunta ba. Murmushi tayi ta juyo amma kanta tana kasa. "Ina kwana? Ya jikin? Allah Ya kara sauki." "Lafiya kalau. Jiki da sauki. Amin Ya Rabb." Ya amsa da murmushi. Yadda ta jero tambayoyin haka ya amsa su. Dariya hakan ya bata amma sai tayi murmushi kawai. "Subhanallah" ya furta da sauri saboda yadda murmushin ya daki ko'ina a jikinsa. Farha sai ta kalle shi saboda bata ji me ya ce sosai ba "Na'am?" "Babu komai Ya Farha." "Ka daina ce min Ya Farha." Dumi dumi yaji a zuciyarsa. Salon maganar ya burge shi. A lokaci guda ya hau musu da zuciyarsa. 'Bata san shagwaba take bane? Anya ba kasheni yarinyar nan take son yi ba? Dama haka ake son mutum? Wannan ya zan ji idan ta ce tana sona?' "Ka ji." Ta maimaita a zatonta bai ji bane. "To me kike so na kira ki wanda zai kusantoki gareni ba tare da na bata miki rai ko na cutar dake ba?" Babu wata kalma da ya fada da bata ji ba amma bata gane komai ba. Ta dai ji ya ce 'kusantoki gareni'. Sauran kuwa kamar ba da hausa ya yi ba. "Kin yi shiru." "Me ka ce?" "Cewa nayi in dinga kiranki Farha-ta?" ya tsokaneta ganin ta tafi duniyar tunani. Yana ganin yadda idanunta suka kara girma da mamaki ta yi saurin cewa "wallahi ba haka kace ba." "Kin tabbata?" Ya tambayeta yana dariya. Soyayyar Farha ta zame masa jinin da yake yawo a jikinsa. Anya daidai ne ya biyewa zuciyarsa?I just published "17" of my story "UWA UWACE...". https://my.w.tt/7cEOGqDTzbb UWA UWACE...17 Batul Mamman💖 Ta san tsokana ce amma bata da karfin ikon hana zuciyarta dokawa tana wani irin tsallen murna wanda bata san ana irinsa ba. Da ta tuna tasirin da wayarsu ta farko tayi a kanta, da yadda ta jima tana jiran wayarsa har ta fidda rai sai ta zabi dakile hirar tasu yanzu. Banda Allah Ya hadasu yanzu da bashi da lafiya kila da ba za ta kuma ji daga gare shi ba. Ba abu bane da take son ta amince tayi ba amma tabbas ta kasance cikin dokin lokacin da zasu dauki hoton da ya fada. Tana tsoron sanyawa ranta abin da zai yi wuyar samuwa gareta. Wani irin kallo tayi masa mai kama da harara sai ya fadada murmushinsa. Bata iya hararar ba da alama. Ita kuwa kunya ce ta isheta tana neman hanyar gudu. "Baki ce komai ba. Kenan kin yarda haka na ce?" Marairaice fuska tayi ta ce "ina da karamar lalura fa. Wani lokacin idan an yi magana sai in ji dif. Kunnuwana suna zabar abin da zasu ji. Kaga duk abin da ka ce bayan mun gaisa ba komai naji ba." Tashi ya yi daga kan kujerar gefen gadon zai dauko wayarsa da ta soma ringing ya dakata ba shiri. A fuska ya nuna mata kamar zancen ya jefa shi cikin alhini. Nan kuwa dariya yake son dannewa. "Da gaske Ya Farha? Allah Sarki lovely Farha. Yanzu Sweet Farha ba komai ki ke ji ba? Farhata har kin bani tausayi...." Ciwon kan da ya kawota asibiti tun dazu ta manta dashi. Rashin kuzarin ma ta neme shi ko sama ko kasa. Da wani irin sauri ta bar dakin tana jiyo dariyarsa har cikin kokon ranta. "Tunda idanunki kalau suke zamu dinga chatting Farhataaaa" ya dan dago murya yadda za ta ji. Sai da ta waiga gefe da gefe don ma ta tabbatar babu wanda ya ji abin da ya ce. Butterflies din da take ji ana cewa suna yawo a ciki lokacin da mashin so ya harbi zuciya suka kai mata farmaki. Har ta isa motarsu gabanta yana faduwa sannan tana murmushi. Zamanta ke da wuya Suhaib ya kirata yana tambayar ko likitan ya iso. "Ka manta ance sai karfe tara?" "Hala bacci ne ya daukeki a motar? Duba wayarki." Hannu ta kai ta rufe bakinta "ahhh" ta ce da mamaki. Tara da minti ashirin. Bata san minti nawa tayi a dakin Abbati ba. Gani take kamar suna fita ita ma ta fito. Abbati bai san lokacin da murmushinsa ya kara cika annurin fuskarsa ba. Shi kadai a daki bakinsa yaki rufuwa. Sake kiransa aka yi ya duba yaga Mal. Sa'idu ne. Yana amsawa yaji ya ce. "Kirani" da sigar umarni. Shi yake saka masa kudi amma baya taba kiransa. Kullum haka yake yi idan yana bukatar magana dashi. "Gwoggwonka Deluwa ta ce tun jiya take kiranka baka amsa ba kuma baka bi kiran ba." Girgiza kai Abbati ya yi. Mal. Sa'idu ya dawo da gadara da umarninsa kansa kwanakin nan. Da dai sai lallabawa saboda abin hannu. Bai san me ya faru ba abin ya canja zani. "Ina asibiti a kwance ne." "Ai hoo..amma dai tunda ka iya amsa wayar na san jikin da sauki." Muryar Deluwa ya ji tana cewa "kayi sauri kayi masa maganar" Shi kuma Mal. Sa'adu ya ce "anjima zaka tura tasha a dauko 'Yashshafa. Yanzu za ta taho ta dinga kamawa 'yar uwarta ayyukan gida tunda ita ba haihuwa take ba balle ta sami mataimaki." Maganar ta daure masa kai sosai. Yanzu ya fara fahimtar sabuwar gadarar kawun nasa. Ya san ba zai taba yarda ba ace 'Yashshafa ta zo. Amma a haka ana magana da iko dole ya amince. Ransa a bace kuwa ya ce "Kawu nace maka ina kwance a asibiti. Sannan a Kaduna nake ba Kano ba. Ku kira Hanne ta tura a daukota." Yana kaiwa nan ya katse kiran ya bar Mal. Sa'adu da waya a hannu. "Wai a kira Hanne shi ba ya gari" ya ce da Deluwa da ta dame shi da tambaya. "Shi ba zai je ba? Malam ka ga illar saken da ka yiwa yaron nan da ya yi kudi ko? Yanzu waye zai kira Hanne taje ta daukota?" Sai kuma ta zauna dabas a gefensa "Malam ita ma Hannen motar gareta? Ya sanar da kai kafin ya saya? Kaga irinta ko? Allah kadai Ya san me da me ya mallakawa yarinyar nan." Sai da ta dan dakata taga yanayin tasirin maganarta a fuskarsa sannan ta cigaba da cewa "kar ka ga kamar na damu ko bakinciki. Ko kadan ba shi bane a raina. Danku ne Abbati. Yana ta faman hidima babu magaji ga raini da tayi masa. Na tabbata babu mai bashi kulawa sama da jininka. 'Yashshafan dai ita ce daidai dashi." "Ki barni dasu daga shi har Hannen da iyayensu babu wanda ya isa ya ketare maganata. Zan daina yi masa sako-sako saboda ya gane kudinsa ba zai sa na karbi raini ba." Dariya tayi muryar nan ta fito kamar ta-macen kozon kwad'o. "Me zai hana kawai a samo mota ko Buba (mijin Habi kanwar Abbati) ya kaimu kuma ba za a biya shi ba tunda Abbatin ne ya saya masa yake haya. Kaga ni da 'Yashshafa da uwarsa sai mu je can inda yake asibitin? Dole ya karbe mu da kyau darajar Mari. Daga can sai mu tafi Kanon. In mun kwan biyu mu taho mu barta a can har su saba?" "Ku tafi ku kadai. Mari ba kirki gareta ba. Da wuya ta bari a bar 'Yashshafa a can." "Ai kuwa dole mu hada da ita. Shakiyin yaro ne kana ganinsa ba karamin aikinsa bane yasa a juyo damu muna isa." Wuka da nama ya bar mata a hannunta. Tana tashi taje ta samu 'Yashshafa har ta gama shiri. Fuskar nan ta dau kwalliya kamar fatalwa za ta zance. Sanar da ita canjin da aka samu na tafiya tayi sannan suka rankaya bangaren Baaba Mari. * Bata dade da dawowa daga makarantar islamiyar da ta shiga ba ta matan aure. Ajinta daya amma bata damu ba. Ta mayar da hankali sosai wurin neman ilimi. A karatun da take ne ta fahimci ashe ba karamin jahilci suka rayu ciki ba. Shi yasa ta tasa 'ya'yanta a gaba da izinin mazajensu suke zuwa. Abbati ya gyara sorayen da ake karatun saboda ba ginanniyar makaranta bace. Dalilin zuwanta makarantar ne yasa ta tashi tsaye akan yiwa 'ya'yanta addu'a musamman Abbati. Ta rasa menene game da sana'arsa ya tsaya mata a wuya. Daidai da rana daya bata taba jin gamsuwa game da arzikinsa ba. Dare daya Allah kan yi bature inji Hausawa. To amma komai yana da sila. Silar arzikinsa kuma bata sani ba! Yau sun dawo da wuri saboda hutun da aka basu na sati biyu. Ta kama hijabi za ta cire kenan taji muryar Deluwa tana kuka. Labule ta daga za ta duba suka ci karo tayi baya. Kuka Deluwa take harda majina "mun banu mun lalace. Mun shiga ukun mu. Wayyo Allah.." "Lafiya Deluwa? Ba kyau irin wannan kukan fa. Mutuwa aka yi ne?" 'Ai fa tunda kika fara zuwa makarantar nan muke ganin sanabe' ta ce a zuci. Sai da ta fyace hanci babu dadin sauraro sannan ta ce "Abbati ne." Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Hanjin cikin Baaba Mari ya cure wuri guda saboda fargaba. Jikinta duk ya saki. Deluwa ta dinga dariya a zuci. "Mari kar ki sume min mana. Rashin lafiya ce ta kama shi yana wani asibiti a Kaduna. Ki shirya don Malam ya ce yanzu zamu tafi." Tafiya yanzu yanzu daga jin labarin rashin lafiya? Sai hankakinta ya kara tashi. Takalmin da ta cire ta mayar ko hijabin islamiyar bata cire ba ta fito. Tana son kiran Abbatin ma amma babu kowa kusa da zai nemo mata nambar a kira. Ita kuma ba iya karatu tayi ba. Mal. Sa'adu ya sanar da mutanen gidan halin da ake ciki. Da Baba Inuwa ya ce zai bisu sai ya ce ya bari tunda ga Buba tare dasu. Su ma ya amince su tafi ne saboda ganin hankalin Baaba Mari ya tashi. Tana ji tana gani yayi wannan karyar amma sai ta kyale tunda bata san manufarsu ba. Ta nemi su Atine su biyo su Mal. Sa'adu ya ce wai za a takura mazajensu. Sai kawai Buba ya ce da Habi ta taho su tafi tare. Su Deluwa dai ba haka aka so ba amma gudun kar a gano su ko ace menene dalilin tafiya da 'Yashshafa sai ta kama bakinta. Cikin awa daya suka dauki hanyar Kaduna. 'Yashshafa doki da murna kamar bakinta ya yage. Deluwa tamkar mai zuwa Makkah. Banda garuruwan kusa dasu bata taba zuwa ko'ina ba. Kanon ma Allah bai yi zata je ganin daular Abbati ba. Baaba Mari da Habi ne kadai cikin damuwa sai Buba. Sun sha tafiya kamar ba za ta kare ba. Jikin kowa ya yi la'asar. Wuraren tara na dare suka iso garin Kaduna. Sannan ne kuma Deluwa ta ce 'Yashshafa ta kira mata Hanne. "Latso min ita inji ko tayi mana girki. Yunwa nake ji kamar naci babu. Duk 'ya yame yamen da muka yi a hanya ba rikeni suka yi ba." "Gida garesu a nan din da zata yi girki? Ba suna asibiti ba?" Cewar Baaba Mari. "In basu da gida ba sai ta aika a siyo ba. Ni naga sai wani gani-gani kike min don na taho duba danki." Baaba Mari sai ta ki magana. Ko babu komai Buba surikinta ne. "A wane asibitin yake na tambayar mana kwatance?" Inji Buba Deluwa ce ta amshe da cewa "yanzu dai ai kya bari a kira Hannen ko?" Ita Baaba Mari ba waya. Habi ma babu duk sun barosu a gida. Abbati ya yi ta kiranta amma dama bai yi niyar fadin yana asibiti ba kada hankalinta ya tashi. Kullum dai suna waya shi yasa yayi ta kira bai samu ba. Ya nemi Atine ita ta fada masa suna hanya. Ita ma din sai yamma ya kirata. Ransa ya yi matukar baci kuwa. "Akan me zai taso min uwa tayi wannan doguwar tafiyar? Yanzu ina zan kaisu su kwana? Me zasu ci?" Yake ce da Munzali cikin bacin rai. Gashi bai samu sallamar ba ance sai gobe saboda ya kara hutawa. Tun yamman suke kiran Buba basu samu ba saboda rashin network a hanya har dan cajin nasa ya kare. 'Yashshafa ce ta kira Hanne. Tana zaune a falo ta ajiye tray din kayan marmari tana dauka ta yanka da 'yar wukarta ta kai baki. Bata san nambar ba haka nan ta dauka tana yatsina. "Hello" Deluwa ta ce "ke ni ba shalo ba gaya min sunan asibitin gamu nan mun shigo gari. Kuma da uwarmijinki muke a tanadi abinci ko don ita." Hanne sai ta mike tsaye da sauri. "Gwaggo Deluwa wane asibitin?" "Kuji min lusara. Inda mijinki yake kwance mana." "Kai Gwaggo Deluwa ko dai kun yi batan kai ne? Shi fa ya tafi Abuja tun jiya." "Da ya tafi baku yi shalo dashi ba?" "Ya kirani dazu ya ce min baya jindadi to amma ban ji batun asibiti ba." Deluwa an sami yadda ake so "an gaisheki tinkiya uwar tambele. Mijinki ya kwan a gadon asibiti baki sani ba. Ya kira ya fada miki baki bada hankali kin saurara ba. Ungo 'Yashshafa latso min Abbatin" Hanne na jin sunan 'Yashshafa bata san lokacin da ta kifar da farantin gabanta ba. Wato da ita aka tafi bayan ta gama sanin kudirinsu. Abbati ta kira harda kukanta. "Wallahi gobe zan taho nima. Ai dazu baka ce min kana asibiti ba-" Kashe wayarsa ya yi saboda takaicinta. Yana cikin fada mata ta ce wai tayi baki daga makota. Kafin ya farga ta katse kiran kuma bata sake a bi ta kansa ba. Deluwa tasa aka kira shi ya ce da Buba ya sami mai adaidaita sahu ta musu jagora zuwa asibitin. Tun yamman Munzali ya kama musu dakuna a guest inn din da Suhaib ya nuna masa. Sannan ya siyo abin ci da abin sha ya ajiye musu. Suna isowa shi ya fita ya biya mai adaidaita sahun sannan ya kaisu dakin da Abbati yake. "Sannunku Baaba kun sha hanya." Murmushi tayi "kai ma kana ta fama da jinya Munzali. Allah Ya kara hada kawunanku." "Amin amin. Ai Yaya Munzali ba daga nan ba." Cewar 'Yashshafa wai ita mai abokin miji. Ganin alamun wahala, yunwa da gajiya a tattare da Baaba Mari ya sa Abbati jin kwalla a idanunsa. Tsanar Mal Sa'adu kuwa ta karu a ransa. Banda son zuciya ba maza ne ya kamata su zo ba idan ma sai an taho? "Ina bayi (toilet) yake ne? Marata cike take taf" Deluwa ta ce tana dukawa saboda matsuwa. Munzali ya nuna mata kofar ta fada a guje. "Baaba ya hanya? Habi harda ke a wannan wahalar?" Abbati ya ce yana kirkiro murmushi. "Alhamdulillahi. Ya jikin naka?" "Da sauki." Zai fara korafin zuwansu ta girgiza kai sai ya yi shiru. Bai yarda ma sun dade ba yace su tafi masauki. Deluwa na jin haka ta kada baki ta ce "To ke 'Yashshafa a tafi dake kuwa ke da ki ka taho jinyar dan 'uwanki?" Ta dubi Munzali " A gida baka ga kuka ba duk tabi ta tayar da hankalinta. Indai da wurin kwanan mata tayi zamanta don na san kukan za ta dameni dashi cikin dare. Ni kuwa na gaji ina bukatar hutu...hehhhehh" tayi wata dariya mara fasali. Tsabar takaici Baaba Mari sai cewa tayi "Munzali zo ka kaimu. Ke ma Deluwa idan nan za ki kwana sai ku kwana tare da ita." Fita tayi kawai Habi ta biyo bayanta. Deluwa jiki a sabule ita ma ta fito. Tana kuma ji Abbati ya ce da 'Yashshafa "ke ba za ki tafi ba sai na zo na sameki a nan wurin?" Turo baki tayi irin na marasa kunya, ya yunkura kamar zai taso ta fice da sauri. Abin nasu yana neman wuce gona da iri ya koma hauka. Wace irin kwakwalwa ce da Deluwa da za ta ce 'yarta ta kwana jinyarsa kamar a garin mahaukata? Ko Habi ai ba za ta kwana ba balle ita. Daki guda Munzali ya kamawa Baaba Mari. Habi da Buba daya sai su Deluwa a guda. "Nima daya nake so don 'Yashshafa bata iya kwanciya ba duk sai ta bubbuge mutum." Ta ce dashi fuska a hade. Da yake shi ma kwararre ne sai ya miko mata hannu. Diriricewa tayi ta kalli Baaba Mari sannan ta ce masa "Me za ayi?" "Kudin dakin da zan kama miki za ki kawo. Dubu ashirin da biyar ne kwana daya." Sai ta hau hargagi don a bar maganar "Ashirin da biyar? Dakin aljannah ne? Barshi kawai zan kwana da Mari." "Ita Baaba umarnin Abbati nake bi. Ya ce ta kwana daki daya saboda an saka ta tafiyar dole." Babu wata magana da suka yi da Abbati. Hasali ma bai san komai game da inda ya kama musu ba. Sanin halinta ne yasa ya zabi raba musu wurin kwana. Ba dai haka taso ba don tana tunanin ko abincin dakin Baaba Mari yafi wanda aka ajiye musu shi yasa taso komawa can. Tunda babu fuska sai ta rungumi abin da ya samu. Da Munzali ya koma asibitin yana bashi labarin yadda suka yi da ita suka dinga dariya. "Amma wane daki ne dubu ashirin da biyar? Babban hotel ne?" "Guest inn ne. Dubu goma ne fa" Dariya suka sake yi sannan Abbati ya bashi labarin hirarsa ta dazu da Farha wadda bai samu sun yi ba saboda jin tahowar su Baaba Mari. *** "Yaushe rabonki da hutawa Hasiya?" Honourable ne ke maganar yana bubbuga mata kafadunta da suka rike saboda dukawa yin lalle. Murmushi tayi. Ita kanta ta san cewa ta gaji. Yau ciwon wuya, gobe kafada, jibi kai. Ga rashin isasshen bacci. Tana tsakar fama da zuwa gida saboda lamarin Zara yau kuma manemin Ummita ya aiko cewa iyayensa zasu zo sati mai zuwa. Ita da kanta take ganin cewa da gaske sawun Innayo take bi. Wahala da fadi tashi tun farkon aure. Kila gobe hutun yazo, kila kuma wahalar goben tafi ta yau. Allah Masani. Ta dai san ba kowa ke da rabon jindadi a wannan rudaddiyar duniyar da zunubi ya yi mata kanta ba. Fatan bawa bai wuce samun dacewa da cin jarabawa a duk yadda tazo ba. "Ina hutu ga mai shirin aurar da 'ya?" Sai yaji nauyi a zuciyarsa. Tunda ta aure shi take wahala da 'ya'yansa ba gajiyawa. "Ina jin kunyarki Hasiya. Abin da ki ke kawowa domin tafiyar da gidan nan yafi nawa yawa. Sai yanzu nake sake ganin wauta ta. Dama ance don tuwon gobe ake wanke tukunya. Ban san a gaba zaki maye gurbin A'i ba. Lokacin da nake da wadata ban damu da me yake faruwa a gidan nan ba balle na gyara. Allah Yasa Innayo ta yafewa A'i.." "Ta yafe mata tuntuni." "Nifa? Ni da ban san girmanta ba sai da na aureki. Gashi ko da wuka ba zan taba barinki ba" Dariya maganar tasa ta bata suka yi tare. "Allah Ya yi miki albarka maman Ayaah." Kallon yanayinta ya yi ko za ta canja fuska sai ya ga ta sake murmushi. "Mun zama abin tsokana ko?" "Ai na rasa me ya kamata muyi mata kuma ta dawo hanya. Ina jiye mata kar tayi irin nawa. Sai a gaba idan Allah Ya sanya samuwar farincikinta a tattare da wani abu naki tazo tana bin bango yadda nake yi a gaban Innayo." Hasiya bata da zabin da ya wuce bushewa da dariya. Ranar har suka kwanta tana tsokanarsa da Honourable Mai bin bango. Yana jindadin ganin ya faranta mata saboda iyakar abin da yake iya yi mata kenan. Akwai abin da yake ta fafutukar samu. Ba dai ya son fada mata ne kada ta saka rai kuma bukata taki biya. Gobe zai koma wurin mutumin ko za a dace. * "Dama kira nayi mu gaisa." Ayaah ta ce da karamar murya tana wani murmushi tamkar yana ganinta. Danladi ya yi juyi akan katifarsa yana harba kafafu cike da farinciki. Dama shi kadai ne a gidan matarsa ta tafi unguwa. Saboda haka zai sake ya gillawa Ayaah karya son rai. "Thank you Ayaah. Wannan wayar ta shigo a lokacinnda nake tsananin bukatar mai sauraron damuwata ya bani shawara." Daga magana kawai ta fuskanci rauni da damuwarsa ta yanayin fitar muryarsa. "Me yake faruwa." Numfashi ya ja da karfi wanda ya sake dagula mata lissafi. "Amanata zan baki Ayaah. Ban san me yasa nake jin zan iya yarda dake ba." Kamar za tayi kuka don yanayinsa duk ya karyar mata da zuciya ta ce "ba zan cutar da kai ba Danny. Ka fada min abin da ke damunka." Sake salon muryarsa ya yi yadda ya san zai kara janyo tausayinsa gareta sannan ya ce "Bana jindadin aurena Ayaah. Auren soyayya muka yi amma na rasa kulawa ta kowacce fanni" ('yan mata a kula!) 'Yar dariya tayi. Wannan mata tamkar tana share mata waje ne. Tunda ita bata iya rikon abin da take dashi ba kwatarsa a hannunta ba zai mata wuya ba. Wayancewa tayi taki nuna maitarta a fili. "Ku fa maza haka kuke. Baku da aiki sai korafi akanmu. Ni dai ina bayan Antina don na san ba za tayi laifi ba" "Don dai baki san zaman da muke bane. Duk girman gidan nan kishi ya hanata daukar maaiki. Ita kuma taki gyarawa. Abinci kuwa tafi ganewa na siyo a waje. Rabona da cin abincin gidan an kwana biyu. Yanzu ma ta fice tun safe ko ruwan zafi bata bar min ba. Kodayake laifin Mum ne. Tun muna yara an cika mana gida da Kuku masu aiki. Da ace ta koya mana duk da muna maza hakan ba za ta faru ba. Da Mum tana da rai wallahi babu macen da ta isa ta tauye min rayuwa haka." Ayaah sai kwallah, sai kuka wanda Danny ya zaci duk a cikin tausayinsa ne. Nan kuwa mahaifiyar da bata gama sani ba take tunawa. Karyar Danny sai ta kara masa kusanci da zuciyarta domin ba karamin tausayi ya bata ba. "Yanzu kana nufin baka ci abinci ba tun safe?" "To me zan ci? Ga freezer cike da nama. Na kasa cire ko kulli daya da sai ki koya min yadda zan yi ko dan peppersoup ne." "Ba don kada ka ce nayi maka shishshigi ba da nace ka zo bayan kafin Isha. Sai dai kuma ban sani ba ko kana iya cin abincin talakawa." Danladi ya yi wata super a katifarsa ya kankame waya. Wannan yarinyar ba zai dauki lokaci wurin samun kanta ba. "Ayaah kar ki wahalar da kanki." "Sai dai idan ka raina abincinmu." "Zan zo Ayaah. Thank you very much." Ranar Murja ce ya kamata tayi girkin dare amma Ayaah sai ta ce za ta yi. Naira dubu biyu ta fitar cikin kudin hular turban da ta fara sayarwa ta je tayi cefanen kayan miya. Ta hado da kayan salad da balangun dari biyar wanda ta boye cikin riga. Sannan ta biya wani shago can hanyar titi ta karbo bashin foodflask mai kyau guda daya dan madaidaici. Irin mai mazubin miyar nan a ciki. "Ayaah yau take sallah ne? Ina kika sami kudi nan haka?" Ummita ta tambayeta da ta ganta tana gyaran kayan miya. "Wallahi ribar huluna ne nace yau dai bari muci dadi." "Allah Ya amfana Ayaah Ya karo ciniki." Hasiya ta ce da taji me suke tattaunawa. "Amin" ta amsa ta cigaba da aikinta sai kuma ta ce "uhmm Anti in debi shinkafa ko na dafa taliya?" "Duk wanda ya yi miki. Shinkafar tana da dan yawa za ta ishemu girki uku ma." Da zuciya daya taji dadin sauyin da ta gani wurin Ayaah. Ba wai na siyan kayan miya ba. Yadda take magana da girmamawa babu wannan tsiwar. Daren ranar shinkafa da miya suka ci harda salad. Honourable ya bayar aka siyo kifi kowa yaci. Abinci yaji maggi kowa ya dinga santi. Yana tafiya sallar Magariba ta dauko flask din da ta zubawa Danladi abincinsa ta watsa balangun a cikin miyar. Yanka daya kawai ta jefa a baki ta maida yawu. Salad din ta zuba a farar leda don kar ya jike akan shinkafar. A bakar leda ta saka ta daure ta kai soro ba tare da kowa ya gani ba ta ajiye can jikin bango. Wurin da duhu babu wanda ya lura. Ta san mahaifinta sai bayan isha zai dawo shi yasa ta ce ya zo kafin ishar. Ana idar da magariba kuwa taji wayarsa. Sulalewa tayi don kowa yana daki wasu ma basu idar ba. Ta dauki ledar ta mika masa. "Naga duk ka fad'a." Ya yi murmushi mai ciwo kamar gaske "ba dole ba. Damuwa ce tayi min yawa harda irin wadda bai kamata na fada miki ba. Sunan ina da aure ne kawai Ayaah amma gwauraye da yawa sun fini gata." Sai taji kamar tayi kuka. Ga mutum cikakke ya sha kananan kaya da gani masu tsada ne. Soronsu kuwa sai kamshi yake kamar anyi barin turare amma rayuwar gidansa ba dadi. "Ka kara hakuri komai mai wucewa ne." Flask din ya dan jijjiga yaji da nauyinsa. Yawunsa ya tsinke tun bai bude ba. Ji yake kamar ya tashi sama ya ganshi a dakin Rabilu inda zasu ci su gyatse kafin ya tafi gida. Surutan tausayin da Ayaah take masa duk suka gundure shi. Ana idar da sallar ishar taji anyi sallama ta sallame shi. Bata sa rai sosai ba amma a zatonta zai bata tukwicin wahalarta. "Karshenta sai ya dawo da filas din zai min kyautar godiya" tace da kanta lokacin da take komawa cikin gida. I just published "18" of my story "UWA UWACE...". https://my.w.tt/thKZS9SmObb UWA UWACE...18 Batul Mamman💖 Allahummagfir li hayyina wa mayyitina.... A madadin daukacin 'yan group din UWA UWACE muna mika sakon ta'aziyyarmu ga 'yan uwanmu da suka yi rashin iyaye. Meena Parrot (mahaifi) da Amina Abdullahi Shu'aib (mahaifiya). Muna rokon Allah Ya jikansu Ya kyautata makwacinsu. Mu kuma Ya bamu kyakkyawan karshe. ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~Amin *** "Habibu ya maganar Agent dinnan? Naga har yanzu baka ce min komai ba." "Uwani kenan. Tsakaninmu da watan Hajji akwai watanni 5 kwarara." Hankalinta bai kwanta ba. Ta gaji da gafara sa bata ga kaho ba. Wata uku da bayar da kudinta na kujerar Hajji amma har yau bata ga komai na shaida ba. Habibu mutuminta ne tun farkon fara aikinta a asibitin. Shi yake mata shige da fice duk lokacin da aka turo mata transfer ta cigaba da zama a Sir Sunusi. Ta riga ta kafa ta tsare. A nan take cin kasuwarta. Sai mace ta haihu ta ce ta tafi gida za ta zo tayi mata dinki mai kyau a can. "Yawancin yaran nurses dinnan duk lalata muku jiki suke in an zo wata haihuwar sai an kara budeku. Indai ba ni nazo karbar haihuwarki ba kada ku yarda ayi muku dinki ko kun karu. Ga nambata ki nemeni da an sallameki sai ki kwatanta min gidanki nazo nayi miki. Dubu shabiyar ne amma ina miki rantsuwa mijinki ma sai ya gode min ba ke ba." Tsarin hudubarta kenan tun a wurin awo. Irin matan da ta yiwa dinki a gida basu kirguwa. Da yake kuma ta kware din sai matan suke turo 'yan uwa da kawayensu. Kasuwa ta bude mata sosai a waje. Manyan mata ko basu haihu ba suna neman Metron Uwani ta gyarasu. Ana iya cewa wannan shi ne babbar silar samun kudinta fiye da na aikin asibitin. Matan masu kudi tana yi musu suji dadi ayi mata ihsani mai tsoka. Ga karbar haihuwa da take yi a waje. Duk wata Nos da ta san sirrinta ta nemi tona mata asiri bata kara sati biyu Habibu zai tsaya har sai an yi mata transfer. "Yanzu sai yaushe zan sa rai? Gobe sunan kanwata. Kuma a son raina inje musu da zancen Hajjin yadda duk wani dan bakinciki sai dai ya hadiyi zuciya wallahi (tana fada, fuskar Hasiya take hangowa)" "Kice dai 'yan bani na iya basu barki ba har yau." Nan ta labarta masa haihuwar Zara da komai. Sirrinta da na 'yan uwanta da ya sani wani ma ya tabbata ta manta anyi. "Ina kuma shi na gaban motar" ya tambayeta mijinta yana kyalkyala dariyar raini gareshi. Uwani ta yi guntun tsaki, "wa yake ta wannan? Wai ni zai kalla ya ce in biya kudin makarantar yara bashi. Ya kwashe kudi yana ta uban gini, bayan na san karshenta da amarya zamu tare. Gani mahaukaciya in biya a gaba mu zo muna babatu. Nima kuma ba kudin nan gareni ba." "Uwani sarkin babu. Ki daina kiranta wallahi kada ta shammaceki." Harara ta doka masa "Allah Ya kiyaye. Ni babu ai garkuwa ce a wurina. Masu saka ido akan arzikin da Allah Yayi min sai dai su gaji su mayar da kwadayinsu." "Allah Ya bar min ke Matron...au, au, Hajiya Uwani ya kamata na fara kiranki fa." Wata shewa tayi cike da jindadi ta sabi jakarta. "Don Allah Habibu ka maida hankali in zo na fara shiri. Bana so a fara bita ina gida." "Kwantar da hankalinki Hajiya Uwani. Bana kam sai dai na ce Allah Yasa maqabuliya ce." Tana tada mota ya buga uban tsaki ya gyara kwanciyarsa akan benci kasan bishiya. Shegen kudin nata ma ko albarka babu. Ko da wuka ba ya ce ga wani abin azo a gani da ya yi dasu ba sun bi ruwa sun bi iska. Rigima bata kisa bare ya tsorata ranar da kwai zai fashe. *** Washe-garin zuwan su Baaba Mari Kaduna Mami Khadija ta sake aika abinci asibiti. Banda wanda su Farha suka tafi dashi da safe Suhaib ya kai na rana. Sannan yaji Abbati da Munzali suna tattaunawa game da tahowar su Baaba Mari. Iya abin da ya fahimta shi ne 'yan uwan Abbati sun taho kuma bashi da kowa da zai saukesu a nan. Ya koma gida da niyar fadawa Mami Khadija amma bata dawo daga wurin aiki ba sai bayan isha. Ta biya gidansu ne akan shirin bikin autansu da ake yi. Tana dawowa ya fada mata. Kallonsa tayi da kyau ta kada kai "yanzu Suhaib maimakon ka kirani tun dazu sai yanzu da dare ya yi?" "Yanzu ban burge ba? Cewa za ki yi nayi wauta ko?" Ya tambayeta yana tsuke baki. Dariya tayi kafin ta amsa masa "ta ina ka burge? Kuma banda wauta da ka kirani ai zan ce ka tuntubesu ko suna bukatar taimako. Ba ka ce ka karbi nambobinsu shi da dan uwansa ba? Kira dayansu mu ji me zamu iya yi musu." Da ya kira Munzali ya sanar dashi ya kama musu dakuna a Guest Inn din da ya raka shi da safe. Sannan ya riga ya sayi abinci. Suka yi sallama cikin aminci suna masu nanata godiyarsu a gare shi. Mami Khadija tana da wani ajin da safe ranar, saboda haka sammakon tashin Sauda tayi. Mardiyya ta kwana a bangaren Nasima, dama ta saba yi mata haka tun a wancan gidan. Idan ta je wurinta kusan raba dare suke tana bugun cikinta domin ta san me da me Mami Khadija da 'ya'yanta suke ciki. Tunda da wayonta sai kawai take biye mata tayi ta hada mata zantukan da basu da kan gado tana fada. Tsomen doya da kwai Sauda tayi wanda ya gajiyar da ita saboda yawansa. Mamin tasu tayi farfesun kaza sannan mai-aikinta ta dafa tea aka zuba a flask din gida sai na asibiti da na 'yan uwan Abbati. Ga kuma bread an hada musu dashi. Bayan sun gama a gajiye Sauda take cewa "Mami wai waye a asibitin ne? Jiya da shekaranjiya ma an kai ga na yau kamar masu tarbar baki." " 'Yan uwanki basu fada miki mutumin da suka gani a asibiti mara lafiya ba?" Da dokinta ta ce "Sun fada ban san shi ake kaiwa ba" sannan ta hau bata labarin abin da ya faru kafin ta dawo gidan "Ai jiya kafin ki dawo ne Ya Farha ta fada mana ashe wanda muka yi hoto jikin motarsu ne a plazar su Mama...Mami zo ki ga ihu wurin Ya Lilu wai mutumin ya burge shi." "Rabani da wannan mashiriricin. Karasa hada kowanne yadda na nuna miki ki taso Suhaib tunda shi ya san dakin da mara lafiyar yake." Tsabar son ganin kwaf Sauda ta ce "Mami ki ce yaje dani don Allah. Sai na daukar masa basket din." "A dawo lafiya. Idan ki ka yi masa rawar kai ya make ki" Mami Khadija ta furta tana yin gaba ta fita daga kitchen din. Kafin goma na safe sun kai abincin dakin Abbati wanda ganin Suhaib ya saka masa rai da sake ganin Farha. Da ya ga fuska daban bai nuna rashin jindadinsa ba sai aikin godiya. Haka kuma Munzali ya musu rakiya har dakin Baaba Mari. Wannan abu ya yi mata dadi fiye da zato da tsammani. Ta dinga yi musu kyawawan addu'o'i. Wani bangare na zuciyarta yana haska mata cewa karshenta Abbatinta mutumin kirki ne sabanin zarginta. Mutanen kwarai basa rasa mataimaki a inda basa zato. A matsayinta na uwa haka yafi komai yi mata dadi. Babu mai son rab'a danta da mummunan abu ko yaya yake sai dole. Babu wata uwa dake duka ko yiwa danta fada domin rashin so. A takaice ma tsabar soyayyar ke janyowa mu dinga kwab'ar 'ya'yanmu domin su zama nagari. Habi ta saka ta dibar musu abincin sannan ta ce ta kai ragowar dakin su Deluwa. Sai da suka ci suka koshi sannan Munzali ya daukesu suka tafi asibitin. Suna zuwa ana sallamarsa. "Baaba za ki iya sake kwanan inda na kai ku jiya ko mu kama hanyar Kano idan mun yi azahar?" Munzali ne ya tambayi Baaba Mari bayan sun gama gaisawa da Abbati an harhada kaya. "Mu tafi din dai zai fi." Deluwa taji zai bata mata shiri don so tayi su kara kwanaki ko biyu ne ta cusawa Abbati 'Yashshafa kafin su tafi Kanon. A gidansa Hanne za ta iya hana ruwa gudu. "Kai dai wannan yaro da zakalkalewa ka ke? Ai dai ka bari wadda ta fika iko dashi tayi magana?" Baaba Mari sai ta dauke kai kamar bata ji ba, su ma sai suka yi yadda tayi din. "Kafin mu tafi din zai kyautu muje gidan wadannan bayin Allah muyi musu godiya. Bai dace su biyomu karbar kwanukansu ba." Ta ce da Munzali. A ransa Abbati yake cewa kamar ta shiga zuciyarsa ta san abin da yake tunani. "Kayan shimfidar ma duka nasu ne." "Allah Sarki. Mutanen kirki basa karewa a duniya." Deluwa ta jinjina kai bayan sun gama kwashe komai suna shirin shiga mota ta soma sababi. Habi da 'Yashshafa suna motar Buba. Ita da Baaba Mari ne zasu shiga baya a ta Munzali. "Dole ki wulakantani mana Mari. Baki da laifi tunda ni na nace sai nazo duba danki. Wannan cin kashin da ki ke yi min Billahillazi kaf sai na fadawa Malam" ta kare tana yi mata kashedi da hannu. A karo na biyu Baaba Mari ta sake bawa banza ajiyar Deluwa ta ce "Na san halinka da nawa idan ka so Abbati. Don Allah ka hanzarta yin wanka ka kimtsa yadda zamu je mu kama hanya da wuri" Munzali sai ya kama murmushi. Da can ma Abbati komai nasa da shiri cikin tsari yake yi ballantana yanzu da zasu je gidansu Farha. Waya ya daga ya kira Suhaib ya fada masa. Sai kuma ya roke shi idan zasu iya ajiye motar Abbati a gidansu. Sati mai zuwa su zo su dauka saboda ba ya son Abbati ya gwada tuki mai nisa da fitowarsa daga asibiti. * Mami Khadija ya fara kira ya fada mata bakin da zasu yi. Tana hanya don goma ta fito daga aji kuma bata zauna ba ta taho saboda maganar bikin gidansu. Farha ta fara kira bayan sun gama magana ya fada mata karfe nawa zasu iso. "Idan kina jin kwarin jikinki yau kisa hannu a hada musu abincin rana. Aikin zai yiwa Sauda yawa a kankanin lokaci. Mardiyya kuma tun jiya na kula da take taken Nasima saboda haka kar ki kirata har ta sami yadda take so ayi rigima. In kuma ba za ki iya ba sai a siyo musu kawai." Bata san cewa kafin ma ta gama bayaninta ba Farha ta mike tsaye. Wannan yanayin na farinciki mara misaltuwa ya mamaye kirjinta. "Zan iya Mami. Sai kin iso. Allah Ya kiyaye hanya." Babu sauran ciwo bare damuwa. Dakin Sauda ta wuce ta tasota. Karatu take yi na gwajin da take dashi washe-gari litinin. "Ayyaaaa Ya Farha test gareni. Yaushe zamu gama nayi karatu? Ni wallahi ban iya komai ba kar naci zero." "Yi zamanki. Amma wallahi ki baza kunnuwa don Mami tana hanya. Kina jin motarta ki taho kitchen." Sauda tayi mamakin wannan abu. Yau yayarta da kanta take gudun dan tayi? Ba wai kyuya gareta ba amma bata son shiga kitchen ita kadai. Ko baka tayata da komai ba ta dinga jin motsi ko a ayi hira. Sai kuma ta tuna hasashensu ita da Mardiyya akan wanda Munzali ya bawa wayarsa rannan. Mutumin da Farha ta ce mata shi ne mara lafiya. Shu'umin murmushi tayi ta wurgar da littafin tana dirowa daga gado tabi bayanta. Zaman daki bai kama ta ba indai akwai wainar da ake toyawa tsakaninsu gara ayi a gabanta. Akan hanyar zuwa kitchen din ta turawa Mardiyya text ta tsegumta mata. (Ki kirani idan sun zo please) Ta tura mata amsa idanunta akan Mama Nasima. Fatanta kada a sami akasi akan fitar da ta ce zata yi. Ta kasa gane yawan tambayar da take yi mata yau akan Yumna kawar Farha. A zuciyar Mardiyya bata kaunar wannan hali mai kama da gulma na mahaifiyarta. Kafin ta girma duk abin da ta tambayeta take fada mata. Sai ta kula idan ta so takalar Mami Khadija rigima da wannan take amfani tayi ta sakin maganganu. Mamin ta gane abin da Nasima take yi amma bata taba nunawa yaranta su guji Mardiyya ba. Suhaib har CID ya saka mata lokacin wanda akan idonta Mami tayi masa kaca-kaca. Da shekarunta suka karu tayi hankali sai ta fahimci illar abin da take yi ta daina. Duk lalacewar Nasima a tata zuciyar wannan karon ba da gulma take tambayoyin ba. Laluben hanya mafi sauki da za ta fadawa 'yarta auren da mahaifinta zai yi take. Yaran duka suna son babansu a iya saninta. Wannan labarin ba komai zai yi ba sai wargaza farincikinsu. Sannan tana sane da yadda Yumna ta zame musu makusanciya a dalilim Farha. Bata sani ba ko ita ma Farha tana yawo. Kada ya zamana an koyawa 'yarta bata sani ba. She was just being a Mom a yau. Sai dai rashin sabo da rashin kyawun zuciya tun farko yasa ta kasa gabatar da niyarta. * Zuwan Sauda yasa aikin nasu saurin karewa. Tuwon shinkafa Saudan tayi ita kuma Farha hadaddiyar miyar agushi. Lilu ya siyo frozen springrolls da samosa aka soya da kuma lemuka. Sai kayan marmari da aka hada fruit salad. A gurguje Farha ta shiga wanka. Kafin ta fito Mami Khadija ta dawo taje ta duba inda aka tanadi kayan tarbar bakinsu. Komai ya yi yadda take so domin 'ya'yan nata ba daga nan ba. * "Kai Mutumina, wannan kamshi kamar gaisuwa zamu je kai wa ba godiya ba?" Abbati ya cigaba da fesa turare yana murmushi kafin ya bawa Munzali amsa. "Sa ido sana'ar su waye ma?" "Zagina za ka yi saboda ka warke?" Cewar Munzali yana tasowa ya karbe turaren ya shiga fesawa "wai ma da kananan kaya za ka je gidan surukai?" Abbati ya kalli kayan jikinsa ya dan hade gira. Jeans ya saka baki da jar riga shirt. Agogonsa na fata da takalmi covershoe duka bakake. "So ka ke ka rage min farincikin da nake ciki shi ne za ka fara korafi akan kayana?" "Rashin dacewa na gani. Tunda babu a kayanka idan ka amince kawai mu wuce Kano sai mu dawo daga baya idan an sami lokaci..." Sauran maganar tasa bata sami fita ba a dalilin kansa da Abbati ya taho shi kuwa ya ja da baya yana dariya. Sauran kiris su fara halin nasu na kokawa kamar yara Buba ya kwankwasa kofar. "Baaba ta ce in duba ku taji shiru." Sai da Abbati ya harari Munzali sannan ya bude kofar yana cewa "ka ci sa a." "Kai dai ka ci sa a ba don haka ba yau da sai nayi maka John Cena (sunan dan wasan wrestling ne) a gadon baya." Yana fadin haka ya fice da sauri suna dariya harda Buba da yawan tsokanar junansu ke matukar burge shi. Kamar yadda suka dawo masaukinsu haka suka sake shiga mota da kayayyakinsu yanzu. Habi da 'Yashshafa suna motar Buba. Habi tayi shigarta fes ita kuwa yallab'iyar kwalliyarta ta rambada tayi bajau. Banda uwar hoda da foundation wanda suka mayar da ita mutum mutumi ta kawo wata foundation din mai haske ta zana tun daga tsakanin girarta har karshen karan hanci. Irin abin nan da masu make up suke yi domin a karawa hanci tsini. Sai fuskar tayi daban daban. Jambakinta kuwa purple ne an zagaye shi da jar jagira. Abin dai sai godiya kawai. A son ranta Abbati ya karbi tukin sai ta shiga gaba. Sauran su taru a motar Buba. Deluwa da Baaba Mari suna motar Munzali a baya. Abbati yana gefensa suna ji ya gama waya da Suhaib wanda ya ce su je asibitin Doctors Haven yana jiransu a waje. Da isarsu kuwa suka hango shi a mota ya tayar su kuma suna bin bayansa. Maganar Munzali game da kayan jikinsa ta dawowa Abbati ya dubi Munzali wanda hankalinsa yake titi don kada Suhaib ya bace masa. Yadi ne a jikinsa wanda yasa domin tsokana ga Abbati. "Idan mun je ka zauna a mota kawai" Munzali ya karkace kai ya ce "saboda?" "Saboda na isa. Ko so ka ke a dinga yabonka shigarka ace tawa bata yi ba?" ya bashi amsa. Dan waigawa baya Munzali ya yi ya ce da Baaba Mari "ki shiga tsakanina da mutumin nan. Cin zalina yake yi duk sanda ya sami dama." Dariya suka bata ta murmusa "haka dai ku ka iya kamar kananan yara." "Haba Baaba ina da kamar Qibdiyya ki ke ce min yaro?" Inji Abbati "A baki ba! Kodayake gara ma kai wannan karon. Kai kuwa Munzali dama taraka nake yi. Kai baka mayar da mahaifiyar Mariya (sunan gaskiyarta take kiran Qibdiyya) ba kuma baka nemi wata ba..." Caraf Deluwa wadda tun dazu take neman shiga hirar ta ce "shi ma Abbatin ai sammakal. Har ma gara Munzali tunda ya ajiye kwai duniya ta shaida. Kai kuwa ka ajiye juya a gida bata komai sai ta ci ta sha tayi kashi. Ai Mari aure ya kamata ya kara ko Allah zai sa ya sami magaji." "Ku ne 'yan birni. Me ya kamata mu kaiwa mutanen nan ne a matsayin tukwicin kyautatawarsu?" Baaba Mari tayi tambayar ga 'ya'yanta tana mai kawar da kai ga maganar Deluwa a karo na uku. Ranta yana baci ne idan tayi maganganunta to amma bata son ta biye mata. Yin hakan zai zubar musu da kima a idanun 'ya'yansu da wadanda suke tare. Ba ta son tayi abin da ko da wasa Buba zai gorantawa Habi idan sabanin yau da gobe ya hada shi da ita. Sannan ga Munzali da uwa uba 'Yashshafa wadda tayi imanin komai rashin kan gadonta, idan taga ana saitawa mahaifiyarta zama sai taji babu dadi. Abbati ne ya amsa mata da cewa sai dai su ajiye musu kudi tunda sun riga sun biyo bayan Suhaib babu damar tsayuwa. Ita kuma ta ce ba kowa ke karbar kudi ba siyayyar za ta fi. Basu ankara ba suna shawara sai gani suka yi Suhaib ya saka trafficator ta bangaren dama. Munzali sai ya ce mata kada ta damu in Allah Ya yarda zasu kawo tukwicin ko ba yau ba. Deluwa aka hangame baki da kofofin hanci ana kallon tafkeken gida irin wanda bata taba gani ba. To Baaba Mari ma dai sai da taji faduwar gaba. Masu kudi irin haka ne suka taimakawa danta. Anya in sun san cewa su kauyawa ne zasu kallesu ma kuwa? "Baaba fito mana" Muryar Abbati ce ta katse mata tunanin da bata san ma ta dulmiya a duniyar yinsa ba. Shi ma kuma suna fitowar hada ido suka yi da Munzali kowanne ya jinjina kai. Basa bukatar furta zantukan da zukatansu suke yi. Maganar daya ce tak. Gidan nan yafi karfinsu. * "Ya Farha sun iso." Cikinta ya sake bada sauti bayan na farko da ya yi lokacin da taji an bude gate. Waskewa tayi don jikinta har wani dan rawa yake yi kamar mai shirin kamuwa da masassara. "To kuma sai aka ce idan sun zo ki fada min? Bakin Mami ne ki je ki sanar da ita mana." Sauda ta kama dariya "gani nayi wai kin sha wahalar yi musu girki." Farha ta sha kunu "to biyana za su yi?" "Eh mana. Ko dan murmushi aka cillo miki na san za ki kwana kina juyi." Tana kare magana ta fita da sauri kafin Farha ta iskota. A can waje bangaren da aka yi domin ajiye motoci Mama Nasima ce za ta shiga motarta. Mardiyya tana gefenta ta dauko mata jaka. Suna wurin su Abbati suka shigo. Suhaib ya ajiye motarsa a inda ya saba sannan ya tafi inda suka tsaya baya kadan dashi suna jiransa. Kamar da wasa Mama Nasima ta kalli bakin da take tunanin na makiyarta ne sai idanunta suka sauka akan Munzali sannan Abbati. Motar da bata shiga ba kenan ta bude baki ta soma cewa "Alh. Munzali" kamar ita ta rada masa sunan. Su duka suka waiga har ta karaso wurin tana kallon mutanen da suka zo tare. Kan Mardiyya ta dungure wadda tana jin ta kira sunan Munzali hankalinta ya tashi ta biyo bayanta. "Wai yarinyar nan sai yanzu take fada min kuna tafe kuma harda manyanka. Shi ne fa na fito da kaina zan tarbeku." Ta dubi su Baaba Mari jikinta a dan sanyaye da yanayinsu da ya fallasa rangwamen wayewa a tare dasu. "Sannunku da zuwa Inna." Suka amsa fuska a sake don basu san wurin wa suka zo ba dama. Mardiyya tayi karfin halin cewa "Mama ba fa..." "Wuce muje ki hado musu juice sannan ki dora abu mai sauki (bata taba daukar mai-aiki ba saboda gudun kar a ramawa kura aniyarta)." Duk abin da ake yi Munzali kallon Mardiyya yake wadda idanuwanta suka cicciko da kwalla. Tana magana hawaye na kokarin sauka. "Mama kinga tare da Ya Suhaib..." Munzali sai ya girgiza kai da sauri saboda fahimtar halin da mahaifiyarta ta sakata. Irin wannan ai ba bakonsa bane tunda ya tashi a gaban Asabe. "Abbati ku je da Suhaib zan shigo daga baya." Mama Nasima ta yamutsa fuska tana hararar Suhaib "au, kun sansu ne?" Hanya kawai Suhaib ya nunawa su Abbati "Bismillah muje." Abbati sai ya kalli Mardiyya ya yi mata alama da tayi murmushi ga Munzali nan. Murmushin kuwa tayi ya hado da zubowar hawaye. "Mama muje dama zan kawo miki karar Diamond girl" Munzali ya ce domin kawar da hankalin Mama Nasima daga kansu Abbati. Ai kuwa ya yi nasara domin yana kiran 'yarta Diamond girl ta soma dariya. "Yaran yanzu ba kwa kunyar kowa. Duk da dai kamar ma zamu yi sa'anni da kai Alhaji. Amma babu komai. Aure babu inda ba ya kai mutum. Abbanta ya girmeni sosai. Kusan kamar kai da ita." Kallon ban hakuri Mardiyya take yi masa. Shi kuma ya nuna mata ko kadan bai shiga damuwa ba. Da ido kadai yake karfafa mata gwiwa har taji saukin zuciyarta akan abin da mahaifiyarta tayi. Basu sani ba ashe kallonsu Mama Nasima take. Ta sake kallon motar da Munzalin ya tuko taji sanyi a ranta. Watanni kalilan suka ragewa Mardiyya da Sauda su gama secondary. Ranar jarabawar karshe in sha Allahu za ayi kamun 'yarta. Aurar da ita zata yi ga kamilallan mutum ko hankalinta ya kwanta. Bangaren zuciyarta da bai manta rayuwarta da ta mahaifin Mardiyya ta baya ba yana cike fal da tsoron kada wata rana kaddara ta giftawa tilon 'yarta. Suna shiga falonta ta yar da mayafi akan kujera ta fada kitchen. Sai lokacin Mardiyya ta iya yi masa magana. "Ni wallahi ban ma san me zan ce maka ba. Don Allah kayi hakuri." Kashe mata ido ya yi fuskarsa a sake ya ce "Kar ki damu Diamond girl. Ina jin fa gara wannan maman tamu akan wadda na baro a Kano." Abin sai yaje mata bambarakwai. A iya saninta mahaifiyarta ce kadai me wannan halin. "Da gaske?" "Zan kaiki ki ganta sai ki tabbatar." 'Yar dariya tayi, yaji wani irin sanyi a ruhinsa sai da ya kai ga lumshe ido. Kamar da wasa ya cewa Abbati zai nemeta sai dai bai taba zaton zai ji komai a ransa ba game da ita. Ya zata tausayi ne kawai... "Ka kaini ka ce mata wa? Bamu da 'yan uwa a Kano na san ma Abba ba zai bari muje ba." Muryar Mama Nasima suka ji tana cewa "kina nan kin saka shi a gaba da zance maimakon ki biyoni kitchen ko? Wannan ni kike son ki tozarta a zaci ban miki tarbiyya ba. Alh. Munzali sai kayi hakuri fa. Matar taka akwai kuruciya ga autanci yana damunta." Tamkar Mardiyya ta nutse a kasa don kunyar mahaifiyarta. Sai gashi Munzali ya kara mata da cewa "kinji Mama ta bada amsar idan na kaiki Kano da wane suna zan gabatar dake ga iyaye da 'yan uwana." * "Sannunku da zuwa. Sannunku. Ku zauna don Allah" Mami Khadija kenan take yiwa su Baaba Mari barka da zuwa cike da fara'a da kyautatawa. Baaba ta saki fuska ita kuwa Deluwa duk ta gigice da sanyin falon. Haushin shareta da Baaba Mari ta dinga yi ya bace a lokacin. Suhaib take kallo tana sake kallon zinariyar 'yarta wani abu yana darsuwa a zuciyarta. "Shafa'a (tana jin kamar idan ta kara 'tu' din sunan zai yi kauyanci) koma motar ki shigo da kwanukan da suka yi ta mana hidima dasu mana." 'Yashshafa ta tashi ta fara zumbura baki sai ji tayi Deluwa ta ce da Suhaib "Sha'aib rakata kaji dan albarka." Abbati ya harbo jirgin ya ce 'Allah Ya 'yantani' a ransa sannan ya mike kafin ta sake magana. "Muje na tayaki." Deluwa ta hade rai kamar ta rufe shi da duka. Sanda taso ya kula 'yarta yaki, yanzu ta sami wani zata cusawa yana neman hana ruwa gudu. 'Yashshafa tayi waje tana ta karairaya sai ka rantse kugunta bai zauna daidai ba. Abbati ya tabe baki yana dariya a ransa. Banda rigimar Deluwa daga ganin mutum ta fara tunanin hada shi da 'yarta. Kafin ta karasa kunyatasu gara ma suyi su bar gidan. Sai da suka isa jikin motar Suhaib ya fito ya karbi mukullin motar Abbati dake asibiti. Lilu zai dauko a gidansu abokinsa sai ya kai shi ya dauko motar. Bakin Abbati baya gajiya da yi musu godiya. Bayan ya tafi ne ya mikowa 'Yashshafa tissue. "Goge fuskarki kafin mu koma. Da ace naga wannan adon bararojin tun kafin mu fito ba zan yardi ki biyomu a haka ba." "Ni dai gaskiya Yaya Abbati ka bar min kayana ina so. Duk wata mace da ta amsa sunanta yanzu sai da me-uf (make up)." Magana zai sake yi mata kawai ya hango Farha ta fito daga wata kofa da bata da nisa da wadda suka fito. Doguwar rigar atampa ce a jikinta sai mayafin mai kauri wanda ta dora a ka ba tare da ta saka dankwali ba. Bata san ya ganta ba tayi saurin buya a bayan wasu fulawoyi masu tsayi da suka cike tazarar dake tsakanin bangarensu da na Mami Khadija. Kwando daya ya mika mata ya ce "jeki, iyaka dai duk wanda ya yi mafarkin fuskarki a gidan nan yau alhaki a kanki." Tana soma tafiya ya hango Farha ta kuma lekawa sannan ta buya a zatonta tare zasu koma ciki. Har ya lallabo ta gefen bangaren Mami Khadija ya tsaya a bayanta bata sani ba. Kallonta ya dinga yi kamar babu kowa a duniya sai su kadai. Farha da bata san yana wurin ba ta sake lekawa sai bata ga kowa ba. Sauke ajiyar zuciya tayi kanta cunkushe da tarin tambayoyi. Bata san ma'anar wannan bakon yanayi da take tsintar kanta game da Abbati ba. Sai tuhumar zuciyarta ma da take yi wurin azalzalarta da yawan tunaninsa. Kafa ta daga za ta bar wurin ta bangaren nasu dakin Abbati ya yi mata magana da sauri. "Abin da muke buyarwa din har ya tafi ne?" Ba karamin tsorata tayi ba harda ja baya. Tabbas taji kamshin turare mai ratsa zuciya amma bata kawo cewa a bayanta mai shi yake ba. Ga kunya ga kuma mamakin yadda yazo wurin bata sani ba, basarwa tayi ta ce masa, "Me kake yi a nan?" Takowa ya dinga yi a hankali zuwa inda take. Ta rufe ido har ya karaso domin tamkar a tsakiyar kanta take jin sautin duk takunsa. "Naga kin buya ne shi ne nima na taho kar abin da kike gudu ya kamani." Tura baki tayi don ta boye kunyar da ta kama ta ta ce "babu abin da nake gudu ni." "Da gaske? To ko ni ki ke kallo?" Ba shiri ta daga kai ta zuba masa kyawawan idanunta "me zai sani kallonka?" Hannuwansa duka biyu suna aljihun wando, ya jikina da bango ya dubeta da kyau kafin ya ce "Nima haka nacewa kaina. Me zai sa ki kallona?" Karkata kai tayi ta dan kalli yanayinsa da ido daya sai taji babu dadi. "Wai haushi kaji?" Shi da zai yi fushin wasa tana neman saka shi dariya. Da kalma daya ya amsa mata kada dariyar ta subuce masa "Eh" Farha ta sake ware idanu wanda ya fahimci tana yin hakan cikin mamaki ko tsoro. Yadda yake ji a ransa a lokacin zai iya rantsuwa babu wanda ya taba son wata mace kwatankwacin yadda yake jin Farha a ransa. "Fushin gaske ko na wasa?" Ya marairaice mata fuska "na gaske mana. Abbati bashi da abin da zai sa Ya Farha ta kalle shi ai dole in ji babu dadi." "Ni yaushe nace maka haka?" Ta fada hankalinta yana neman tashi. Abbati kuwa kamar ya zuba ruwa a kasa ya sha saboda ya amince ba haukansa yake shi kadai ba. "Kin yarda ni ki ke kallon? Uhmm?" Yadda ya tsareta da ido sai taji kamar tayi tsuntsuwa ta bar wurin. Motarsu ta nuna da hannu ta fice daga wurin yana bin bayanta. "Motar nan nake kallo ina tunanin kafin ku fito na zo na dauki hoto..." "Cewa za ki yi baki manta alkawarinmu ba. Ina fata baki manta ba?" Ko kadan bakinta da zuciya basa son yi masa musu. Sai dai bata saba ba sannan tana jin kunya. Kofar bangaren Mami ta kalla ta ce, "Zan kirga goma duk wanda ya fara fitowa shi zai daukemu. Idan na gama ba a fito ba sai dai ka hakura." "Na yarda. Bari na taya ki kirgawa." Idanunsu akan kofar ta fara kiran 'daya' yana tayata. Suna kaiwa shida ya ce a sake wai da sauri take yi. Haka nan ta amince saboda bata son ta fara bada kanta a gabansa. Ta fahimci nan gaba kadan za ta kasa jurewa rashin kallonsa da ta tilasta kanta. "Daya, da digo daya, digo biyu, digo..." "Wannan kirgen naka ya sunansa?" "Farhan Abbati style" ya fada kai tsaye yana yi mata wanu irin kallo. Kai ta sunkuyar ba tare da ta bashi amsa ba. Ya kawo ido ya zuba mata yana ta doka murmushi. "Yaya Abbati ka zo in ji Mooomina" 'Yashshafa ce ta fito tana wannan tafiyar irin ta wanda ya sha da kyar daga kamuwa da cutar shan inna. Haushi ya kama shi na yadda ta bata daddadan moment dinsa da Farha. "Mominki kuma 'Yash..." "Shafa'a. Suna na Shafa'a" ta gabatar da kanta ga Farha da sauri kafin ya karasa fadin sunanta. Abbati ya kada kai ya ce "to Shafa'a wace momin ke kirana?" Ta san ya gane yake son bada ita a gaban wannan kyakkyawar matar. "Moomina dai da muka zo tare." Sai ya yi kamar lokacin ya fahimta "Au wai Gwaggo Deluwa?" 'Yashshafa ta juya a fusace ta bar wurin tana buga kafa don takaici. Farha sai da tayi dariya sannan ta ce masa "baka kyauta ba. Ka fahimceta amma ka nuna baka gane ba?" "Laifin naki ne don ke take son burgewa. Haka kawai muna 'yan kauyenmu don ta ganki ta fara kiran Innarta da Moomi" ya kuma fada yadda 'Yashshafan take cewa. Farha dai hannu ta sa ta kare bakinta tana dariya kasa kasa. "Kana da abin dariya" ta ce a hankali da suka shiga falon Mami Khadija daga bakin kofa. "Zan yi komai domin ganin dariyarki Ya Farha. Idan kin bani damar zama abokin raba duk wani yanayi da za ki tsinci kanki daga yau har karshen rayuwarki ga mahaifiyata can..." ya nuna Baaba Mari wadda suke hira da Mami Khadija tamkar sun dade da sanin juna "zuwanki gabanta ku gaisa shi ne zai tabbatar min da cewa wannan Ya Farha Farhata ce" A hankali ya yi maganar daidai jinta domin ita ce a gaba yana biye da ita a baya. Kalamansa sun fito da sigar roko, tararrabin rashin samun karbuwa da zallar soyayya. A duniyar Farha bata taba shiga yanayi makamancin wannan ba. Idan haka ake soyayya bata fatan ta sake yiwa kowa bayan Abbati. Wucewa ciki tayi ba tare da ta juya ko ta amsa masa da baki ba. Maimakon ta wuce ta damanta inda zai fi saurin sadata da Baaba Mari sai ta zaga ta hagu. Abbati yaji kamar ana ajiye masa duwatsu a zuciyarsa don tsoro. Sai da ta gama ja masa rai sannan tayi takun karshe ta zube a gaban Baaba Mari. Sama sama yake jin muryoyinsu suna gaisawa. Farinciki ya mamaye zuciyarsa har yana neman yi masa yawa. Inda ya tashi ya je zai zauna waya ta shigo masa. Bakuwar namba ya gani ya dauka da sallama. Muryar wani da bai gane ba yaji. "Idan kai ne Abbati ina tare da matarka ta ce sunnanta...ke ya ma sunanki?" "Hanne" ya ji muryarta tar tana bada amsa. "Yauwa Hanne. Wai wayarta babu chaji tana nan tashar Kawo ka tura a daukota. Sannan ta ci shinkafa da miya a wurin Esther, ni kuma ta sha lemo da ruwa a shagona. Kudin da ake binta dubu daya da dari uku ta ce za ka biya." Ransa in ya yi dubu kuwa ya baci. Me yasa za ta wulakanta shi haka? Banda tahowa ba da izininsa ba harda cin abinci a tasha...kuma bashi! Tashi ya yi bayan ya fadawa mutumin cewa gashi nan zuwa. "Ina za ka je mu da muke jiranka mu kama hanya?" Baaba Mari ta tambaye shi. "Wane irin kama hanya ko ruwa baku sha ba balle aci abinci? Don Allah ku zauna. Sauda duba ki gani idan plates din zasu isa." Inji Mami Khadija tana tashi. Sai Abbati ya mata bayani a takaice "Baaba ku zauna Hanne zan dauko a tasha wai yanzu ta iso. Idan na dawo sai ku fito mu tafi." Ta gane ransa a bace yake sai ta ce masa sai ya dawo. Ta san zai yi mata bayanin komai idan sun kebe. Yana daf da fita Mami Khadija ta ce "ba dai wata 'yar uwar taku bace ta iso? Allah Yaso baku kama hanya ba da kunyi sabani." Deluwa fadi ba a tambayeka ba tayi tsagal ta ce "matarsa ce." Bai gama fita ba saboda haka yaji abin da ta ce. Tsayuwar dole ce ta kama shi ya waigo a hankali yana neman idanun Farha domin ya gane tasirin maganar aurensa gareta. *** Anti Hasiya ta gama shirinta da yamma za ta je gidan Salima. Washe-gari ne zai kama sunan Zara. Anyi mata waya an fada mata batun haihuwar amma har yanzu bata leka gidan ba. Shi ne Innayo ta ce taje ta duba mata. Maimuna ta zama mai wankan jaririya da kanwarta. Innayo ko kallo Zaran bata isheta ba. Jaririyar kuwa ko sau daya bata dauketa ba. Abin da ya tsayawa Zara a kahon zuci har ya zarta damuwarta na shariya daga Innayo. Abinci dai mai rai da lafiya da kanta take dafawa ta kuma tabbatar ta ci. Daga nan bata sake bi ta kanta sai wani girki. Zara taji ta muzanta ta tsani kanta. Ko hira ta dauko Innayo ba ta taba amsa mata. 'Yan uwanta sun san me yake faruwa amma sun zabi su zuba ido 'ya da uwa su daidaita da kansu. Da Anti Hasiya ta kira Honourable ta fada masa ta shirya sai ya ce ta tafi da Ayaah. Ta so yi masa musu sai ya nuna mata ya yi haka ne domin ta dinga shiga cikin ragowar kannen mahaifiyarta. Ba zai yiwu su zuba mata ido sai yadda take so ba. Amincewa tayi da kudurin idan Ayaah ta kawo mata raini za ta dauki mataki. "Ke da wadda zamu gidan nata waye babba?" Mamakin tambayar tayi tunda tun fitowarsu take zumbura baki. Anti Hasiya ta dauke kai ne kawai don bata son abin da zai janyo Ayaah tayi mata rashin kunya a adaidaita sahu. "Daga Yaya Maimuna sai ita sannan Zara." "Ita ce farar nan ramammiya kamar tsohuwa da muka gani a dakin Innayo da sallah?" Anti Hasiya ta daga yatsa tana kada shi a gaban Ayaah. "Ki kiyayeni Ayaah. Ban fito dake don ki ci mutumcin 'yan uwana ba." Da yake bakinta bashi da linzami sai ta rage murya amma yadda ta san Antinta za ta ji. "Ai dai kin san gaskiya na fada." Anti Hasiya sai taki kula ta. Gaskiya Ayaah ta fada. Duk gidansu babu wanda ya kai Salima lalacewa a gidan miji. A kalla duk talaucin mijin Maimuna yana kaunar matarsa. Ita kuwa Salima Alh. Rabi'u ya gama cutarta. Duk dan Adam din da za a biya bashi dashi ina yaga daraja? Daga soron gidan suke jin hargagin Maigidan Ale Gambo yana ta zaginta. " 'Yar bakinciki, muguwa, azzaluma. Ban fada miki kafin na dawo ki je gida ba? Ace 'yar uwarki ta haihu kin kasa zuwa barka balle ki karbo min..." Niyar Anti Hasiya ta gama jin dalilin wannan tijara. Idan ba haka ba Salima ba za ta taba fada da bakinta ba. Ayaah kuwa sai ta fada gidan tana doka sallama iya karfinta. Ta san duk abinsa dole ya sararawa matarsa a idon baki. "Salamu alaikum. Anti Salima kina ina ne? Ina ta doka sallama naji shiru." Baki Anti Hasiya ta rike tana biye da ita har tsukakkiyar tsakar gidan. Wai tana ta doka sallama. Harda wani Anti Salima kamar gaske. Salima na ganinsu ta share hawayenta da sauri amma duk sun gani. Ale Gambo ba kunya ya amsa sallamar ya dora da karyar ceton kai. "Yauwa Hasiya naji dadin ganinki. Don Allah ki fadawa Innayo babu hannuna a ciki. Tun ranar da aka sanar da batun haihuwar Zara nake cewa ta tafi gida barka taki." Salima ta kalle shi da jajayen idanunta ka kawar da kai. Ale Gambo ya karar da duk wani kuzarinta. Fadan da damuwa tayi har sun haddasa mata hawan jini. Zaman 'ya'ya ukun da suka haifa take yi sai ko gudun karawa Innayo nauyi. A haka ma ita ce karfinta, ina ga ta koma gidan da yara? Dalilinta kenan na daina tanka masa duk bala'insa. Ta daina yin yadda yake so tun lokacin da Innayo tayi ciwon hakori. Duka da zagi babu irin wanda bai yi mata ba a tsukin lokacin. Yau ma tashi ya yi babu komai a jikinsa sai naira dari. Shi ne ya dauka ya bata wai taje gida barka sai ta fadawa Innayo tana son kudi. Ko dubu goma ce ta samo masa kamar ya bata ajiya. Kin tafiyarta be ya janyo mata abin da su Ayaah suka tarar. "Zan yi mata magana." Kawai ta ce yasa kai ya fita. Hannun Salima ta ja rai a bace suka shiga dan mitsitsin falonta. Yadda ta san halin Hasiya sai ta fara bata hakuri tun kafin tayi magana. "Zan je barkar fa. Dama saboda halin Zara ne na ce sai na sami lokaci." Hasiya ta dage gira ta sha kunu "sannu shugabar kasar Najeriya. Karshen aiki dai kenan da rashin samun lokaci." "Baki yarda ba kenan?" Salima ta tambayeta tana kirkiro dariyar dole. "Kema da ki ka fada baki yarda da kanki ba sai ni? Tun yaushe yake dukanki?" Da tayi shiru bata amsa ba sai Hasiya ta canja tambayar da cewa "me yasa baki taba fadawa kowa ba?" Fashewa Salima tayi da kuka mai cin rai. Tana yi tana sheshsheka saboda yadda ya dade yana ci mata rai. "Baba dai babu abin da zai yi min idan na fada. Innayo kuma in dai ba ajalinta kike so nayi ba ai ya kamata na hakura haka. Ita ba za ta huta ba Hasiya? Kullum cikin nema banda ma ciwon ido da hawan jini sun hanata sukuni kina tunanin da har yanzu bata cigaba da abinci ba?" Hasiyan ma sai hawayen tausayin Innayo da Salima. Ta san da Innayo tana da karfi da tuni ta raba 'yarta da wannan kaddararren auren. Share ido tayi ta kalli Salima "kin san dai bai kamata ki cigaba da zama a haka ba. Idan ya kuma zuwa zai dake ki kar ki yard. Ki kokarta ki kwaci kanki ko da cizo ne." Ayaah na gefe da 'yat kwallarta saboda tausayin halin da Salima take ciki. Bata taba sanin abin da ya shafesu zai dameta ba amma yau da akayi a kunnenta taji sai ya tsaya mata a rai. Tana jin gurguwar shawarar Anti Hasiya a cewarta ta shiga zancen nasu ba jiran gayyata. "Wane irin ta kwaci kanta Anti Hasiya? Ko dai baki kula da girmansa bane? Jibgege ne, wannan idan aka sami akasi ta iya cizonsa wallahi karshenta ya zubar mata da hakora. Bai yi ruwan imani ba ko kadan." Da hawayen sai da tasa Salima yin murmushi da ta ce wai bai yi ruwan imani ba. Hasiya ta ma manta tare suke saboda basu saba hada fita ba. Daure fuska tayi a zatonta Ayaah rashin kunya za ta yi musu. "Sai ki kawo taki shawarar tunda baki san idan manya suna magana ki kama bakinki ba." Ayaah ta tsuke bakin tsiwarta "naga nima dai kanwar mamana ce Anti Saliman nan. Abin da ya shafeta ai ya shafeni." "Haka! Wanda ya shafeni ne bai shafeki ba ko?" Salima me zata yi banda dariya. Rabonta da ganin Ayaah an kwana biyu. Amma idan ta hadu da Hasiya da wuya su rabu bata dauko zancenta ba. Abin mamaki shi ne kullum hirar korafi ce akan rashin ji da rashin kunyar Ayaah gareta, amma fa ko Innayo ta fahimci ba karamin so take yi mata ba. Irin son da akasarin uwaye suke yiwa tabararrun 'yan autansu. "Nima ai baki damu da abin da ya shafeni ba." "Ayaah banda rashin kunya mana. Shi yasa kuke fada da babarki. Wane dan arzikin ne iyayensa suna fada yana fada banda abinki? Bata hakuri." Salima ta umarceta. Sai da ta yatsina baki ta bada hakurin. Hasiya za tayi magana Salima ta girgiza mata kai da sauri sai tayi shiru. "Sai ki kawo taki shawarar tunda tawa bata yi ba." "In yi magana kuma ace bani da kunya?" Ayaah ta fada idonta akan Anti Hasiya. "Tunda ita ta baki dama ki fada mana. Idan baki fadi taki ba zan dauki ta Hasiya. Iyaka dai ya zubar min da hakora ku zo dubiya." Anti Hasiya da Ayaah suka yi dariya tare. Sannan Ayaah ta ce, "Anti Salima idan ya sake zuwa dukanki kar ki gudu kuma kada ki kare. In zaki iya ma ki takali fadan don ayi a wuce wurin. Daga nan dukan farko ki zube kasa ki daina motsi. Don Allah Anti duk yadda zai yi kar ki motsa. Wai baki da 'ya'ya ne?" Ta tambaya tana duba cikin falon kamar lokacin zasu bayyana. "Allah dai Ya shiryeki. Su Murja sun san kowa cikin 'yan uwansu banda ke. Su uku ne. Babban namiji yana makarantar kwana. 'Yan matan kuma suna islamiyya." "Sun kai shekara goma?" "Goma da sha uku." Ayaah tayi dariya "sun san yana dukanki?" "Sun sani." "Anti Hasiya don Allah mu zauna har su taso in yi musu karatun ceton uwa." Salima da Hasiya sai suka jidadi. Ko me zata ce zasu saurara domin su kara janyota jikinsu ta san mahimmancinsu. A nata bangaren kuwa hasashen yadda zata taimaki kanwar mahaifiyarta take yi. For once in her life Ayaah sai taji dadi wai yau ita Anti Hasiya ta bawa dama har take saurarenta haka. Akan hanyarsu ta zuwa gidan Innayo, bayan sun bawa Ayaah dama ta yiwa kannenta hudubar taimakawa mahaifiyarsu ne Hasiya ta dinga maimaita kalan Salima a zuciyarta "Wasu yaran tsabar son ki sauraresu yake saka su fandarewa ko yin abun daukar magana. Da gangan Ayaah take tunzuraki dazu don kawai ki kulata taji dadi. Da alama mai son kulawarce sai aka yi rashin sa'a masu sauraronta basu dorata a turba mai kyau ba har zamanku ya kasance irin haka. Daga yanzu ki dinga janta a jiki kamar yadda kike yiwa 'yan uwanta kina nuna mata cewa tana da matsayi a wurinki ita ma." I just published "19" of my story "UWA UWACE...". https://my.w.tt/IK4e2j4j0bb UWA UWACE...19 Batul Mamman💖 *** Duk kokarinsa babu abin da Abbati ya iya karantowa a fuskar Farha. Abu daya kacal ya lura dashi. Wannan annurin na fuskarta yayinda take gaisawa da Baaba Mari ya dauke. Banda shi da ya san da zamansa ma babu wanda zai lura da cewa yanzu ta koma kadaran kadahan. Babu alamun bakinciki ko fushi, babu alamar tambaya ko neman karin bayani. Irin abin nan ne kawai da mutum zai iya dangantawa da dauke wuta. Iya nacinsa na takaitaccen lokaci ya yi domin ta kalli inda yake amma kamar tana sane ta fuskanci wadda yake tunanin ita ma kanwarta ce tana yi mata magana. Fita ya yi jikinsa kamar anyi masa duka ya tsaya a jikin motar ya kira Munzali. * Yana zaune baki bude yana ganin ikon Allah. Fruits Mama Nasima ta yanko masa ta kuma tura Mardiyya yi masa girki. Ya rage su biyu a falon ta zauna a kujerar dake fuskantar shi jikinta babu lullubi har lokacin sai farincikinta da yaki boyuwa. "Wato kuna ta shan soyayya ban sani ba. Gashi kun dace. M da M. Zai yi kyau kuwa a soveniya (souvenir) da katin biki. Irin a saka katuwar M daya sai a jona karashen sunayenku." 'Yar damuwa ya gani a fuskarta ta ce wai yaushe za ka turo ne? Kai ba yaro baq. A shekarun nan naka kana bukatar iyali domin cikar kamala. Bana so ka sami shakku a zuciyarka game da Mardiyya. Na horata sosai da aikin gida. Ko kusa ban sangarta ta ba don ita kadai gareni. Girki, tsafta, kwalliya duka ta kware. Kuma ina da yakinin sauran mu'amala ma ba za ta bani kunya ba. Tun tana da kananun shekaru nake gyara abata." Ta kare magana tana dage masa gira gami da guntuwar dariyar shakiyanci. Ita ke magana shi ne da kunya. Da za ace masa akwai ranar dai zai so kasa ta bude ya shige ciki don kunya tsaf zai karyata harda rantsuwa ma. Sai gashi a bagas ya gamu da gamonsa. "Ahhhhhh. Wayyoooo. Cikinaaaa" Mardiyya ta kwala ihu iya karfinta bayan ta fahimci wace irin hira Mamanta ta dauko. Haka kawai ta matso jikin kofa da taji ana ambaton kwalliya. Sai gata tana zazzare idanu da jin abin da Mama Nasima ke fada. Kunya ta kama ta sai dai babu muhallin biye mata. Idan bata dakatar da hirar nan ba to gaskiya bata san inda za ta tsaya ba. Ita shaida ce kakarta Gwaggo Ladidi ma idan suna wata hirar da 'ya'yanta mata sai ka nemi gudu. Ido ne ya bude tun da jajayen sawu ga rashin ilimin kirki. Sai suyi ta tafka rashin kunyarsu a tunaninsu wayewa ce. Tare da Mama Nasiman suka isa kitchen din, don yadda tayi karar dole mutum ya firgita. Shame-shame suka sameta a kasa. "Mardiyya lafiya? Me ya sami cikin naki?" Mama Nasima ke tambayarta cikin tashin hankali. Ta dago kanta ta dora a cinya tana salati. Ita kuwa Mardiyya ta cigaba da murkususu tana nuna ciki. "Mama ciwon cikina ne ya tashi." Mama Nasima ta bita da kallon mamaki "Dama kina da ciwon ciki ne? Ko menses kike." Yadda Mardiyya ta kwabe fuska kamar tayi kuka ya kusa saka Munzali dariya. Daga bakin kofa ya tsaya saboda suna hada ido ya gane ciwon karya take yi. Ta bashi tausayi sosai gami da dariyar diramarsu ita da mahaifiyarta. Juyo da fuskar Mardiyya tayi suna fuskantar juna hankalinta tamkar ya bar jikinta. Ira kenan 'yar, tsoka daya a miya. "Mardiyya kalle ni nan. Na ce menses ne? Naga baki taba ciwon mara mai tsananin wannan ba." Gara ace al'ada sau dubu da a ce menses saboda yadda ta tsani kalmar. Amma yanzu sau biyu tana jinta kuma a gaban mutumin da basu yiwa wani sanin kirki ba. Kai ta gyada don ta barta da tambayar. Sannan ta ce akwai maganin da take sha a dakinta dake can bangarensu. Mama Nasima ta mike a sukwane ta fice zuwa neman magani. "Sai ki tashi tunda ta tafi" cewar Munzali yana dariya a hankali. Mardiyya ta cukule fuska "dole kayi dariya tunda ka sani karya." Tana magana suna komawa falon "ka zo ka tafi don Allah kafin ta dawo." "Korata kike yi?" Ya furta bayan ya mayar da fuskarsa kalar ban tausayi. "Eh" Zamansa ya yi yana danna waya "babu inda zani tunda ba ke ki ka gayyatoni ba." A kujera mafi kusa dashi ta zauna idonta yana yawo tsakanin fuskarsa da kofa. Kuka take neman yi. "Don Allah ka tafi. Wallahi bana jindadin abin da Mama take yi a gabanka. Da wuya ka dinga ganin mutumcinta." "Mardiyya" Munzali ya kira sunanta na gaskiya cike da kulawar da bai san daga ina ya samota ba. Kallonsa kawai tayi ta dauke kai saboda jin nauyi a kowacce gabar jikinta. "Kar ki aibata mahaifiyarki. Damu da iyayenmu babu wanda yake cikakken dan Adam wanda baya kuskure. Suna hakuri damu, muna hakuri dasu. A tsakanin wannan hakurin ake neman balance don a zauna lafiya." Wani irin rauni ne ya ziyarceta. Tana son mahaifiyarta kuma tana kyamar halayyarta. Duk da haka bata taba jin a ranta wai za ta iya jin kunyar nunawa duniya tsatsonta ba. Abin da Allah Ya baka shi ne naka, dan Adam mai Hamdala shi ne zai kokarin rike tasa kyautar da daraja. "To kai ta yaya ka nemi balance din?" "Yanzu nake neman samu albarkacin amini kuma dan uwa nagari Abbati. Da fari da rashin biyayya, rashin girmamawa da nesanta kaina da mahaifiyata na fara sai naga ba a dace ba. Rayuwar taki albarka yadda nake muradi." Dokin jin yadda yake yi yanzu da tsoron dawowar Mama Nasima yasa ta cewa "yanzu fa? Me kake yi yanzu?" "Tare zamu nemo Diamond girl. Daga yau sai mu zama abokan shawarar juna game da matan da ya kamata su fi kowa daraja a idanunmu." Murmushi suka yiwa juna. Mardiyya ta kasa jurewa kallon da yake mata ta tashi da sauri ta shige inda yake tunanin hanyar daki ne. Wayar yaji kuma ya san Abbati ne sai bai kirata kamar yadda ya yi niyya ba. Labarin bakuwarsu ya bashi da yadda Farha tayi bayan Deluwa ta ce matarsa ce. * "Subhanallahi. Please kar ka damu. Dama dole ta sani. Zamu bata hakurin jinkirin da aka samu bata ji da wuri ba. Bari dai na fito muje. Amma ni wallahi ban san ina ne hanyar tashar Kawo ba. Ko Suhaib na kusa ka fada masa ya sake taimaka mana?" Abbati ya girgiza kai kamar Munzali na gabansa. Kansa ya dauki chaji mai wuyar sauka. Zuwan Hanne ba tare da izininsa ba ko kadan bai yi masa ciwo kamar wayar da aka yi masa akan abin da tayi a tashar ba. Wane mai hankalin ne zai so ya amsa sunan mijin ballagaza? Aikin Hanne kenan! Yayi nasa kokarin a kanta tunda har makarantar yaki da jahilci ita ma ya kaita kamar yadda suka yi shi da Munzali. Bata koyo komai ba banda danna waya da yi masa bincike kamar wakiliyar EFCC. Bai manta silar aurensu ba shi yasa bai raba matsayinta da na takalmin kaza ba. Yana can duniyar tunani Munzali ya isko shi. "Mutumina muje ko. Da kwatance ba za mu bata hanya ba in sha Allahu." Mukullin Abbati ya mikawa Munzali ya zagaya daya barin zai shiga sai ga Sauda ta fito da sauri. Ba don Mami tayi magana a gaban su Baaba Mari ba da ba za ta zo ba. Ita bata yarda ba ta fara taya yayarta kishi ne akan matar Abbati. "Uhmm dama Mami ta ce na tambayeku ko kun san tashar daga nan." "Daga ko ina ma bamu sani ba." Munzali ya bata amsa. "To ku jira" Komawa tayi ta fadawa Mami Khadija amsarsu. "Farha idan motarku da mai kuyi gaba ke da Sauda sai su biyoku a baya." (Mami Khadija ko tana hauka ba za ta yarda ace ta turasu a mota daya alhalin bata sansu ba. Sannan kuma gasu maza. Yadda take kaffa kaffa da 'yan matanta) Sauda ta tafi bangarensu inda suke ajiye mukullin tasu motar. Guda daya ce Alh. Tahir ya saya musu saboda uzurinsu musamman na makaranta. Farha kadai ya yarda ta tuka kafin su ma su gama secondary. A can ta hadu da Mama Nasima ta fito daga dakin Mardiyya duk ta hada zufa. "Yauwa Sauda zo don Allah ki tayani duba maganin Mardiyya. Gata can ba yadda take ciwon ciki ya murda mata. Nayi neman har na gaji" Kana ganinka ka san tana tare da damuwa. Idanunta sun yi zuru saboda firgici. "Wane irin magani ne?" Sauda ta tambayeta da mamaki. "Ciwon ciki ne dai ta ce yana yawan tashi." Sauda sai ta shiga suka dan bincika babu. Ita ta kawo shawarar su tafi asibiti. Ta dauki mukullin motar ta kaiwa Farha sannan ta fadawa Mami Khadija cewa su Mama Nasima za ta bi. Ta bata goyon baya suka fita tare domin ita ma ta duba Mardiyyan. "Kuyi hakuri an tsayar daku. 'Yar uwarsu ce babu lafiya. Ga Farha nan zata kaiku har tashar." Mami Khadija ta fada musu bayan sun fito. Ita da Sauda suka wuce bangaren Mama Nasima. Abbati ya dubi Munzali da mamakin baro mara lafiya. Sai da yaji ciwon karya ne ya dan yi murmushi. Ta kusa dasu Farha ta zo ta wuce ta nufi motarta. Ko kallon inda suke bata yi ba sai faduwar gabanta da ya tsananta da tazo giftawa ta gefensu. Munzali ne ya yi karfin halin kiran sunanta yadda Abbati yake fada da zolaya. "Barka da rana Ya Farha." Watsa masa wata muguwar hararar da ita kanta bata ma san ta iya ba tayi. Abbati yana lura da duk wani motsinta. Bakinta ta dan turo kamar za ta yi magana, maganar da alamu sun nuna a tsiwace za ta fito. Sai kuma kawai ta wuce zuciyarta na dokawa da sauri da sauri. Wani irin abu take ji game da Abbati da yafi karfin tunaninta. Ya kuma sanya jin yana da aure yi mata nauyi. Me yasa basu fada mata tun farko ba ta shirya zuciyarta? Allah Ya sani indai wannan abin da take ji shi ne so to kuwa ba kankani take yiwa Abbati ba. Gara ta kama kanta haka nan...karshenta ma matar ba daya bace. Ko yaransa nawa? Saurin girgiza kai tayi da ta fahimci inda tunaninta ya nausa bayan ta zauna a motar. Tayarwa tayi tayi ribas tana cin taya. A guje ta fice daga gidan ko tunanin na bayanta bata yi ba... 'Ina tunaninsa mana.' ' Idan na bace musu ai dole ya kirani.' 'Sai in rama nima.' 'Me za ki rama?' 'Da me za ki rama?' Zantukan zuciyarta kenan lokacin da ta daidaita akan titi. Tana zama a motar dama Abbati ya karbe mukullin daga hannun Munzali ya shiga mazaunin direba shi ma ya fizgi motar don kada ta bace masa. Dariyar mugunta Munzali ya fashe da ita "Mutumina kana ruwa, a bulallen kwale-kwale, kusa da mayunwaciyar kadar da 'ya'yanta suka bata. Hodijan inji Fillo. Farha tayi fushi amma kuma naji dadi." Abbati ya galla masa harara "ko baka fada ba na san kaji dadi mana. Ji wannan fara'a da kake yi kamar ka tsinci hakori." Dariya ya bashi saboda kana ganinsa ka san yana tare da damuwa. Abu ne goma da ashirin, bai san ta ina zai fara ba. "Dariya ma kake yi ko Munzali?" "Wai kuka zaka yi ne duk ka bi ka bata rai?" Kwafa Abbati ya yi yana dana sanin karbar tukin. Banda tsoron kada Farha ta bace masa da tuni ya kaiwa Munzali duka. Wata kwafar ya sake Munzali ya ce, "Wallahi in ka tabani sai nayi kararka wurin Farha. Na san wannan cije leben ba zai wuce lissafin yadda za ka taba lafiyata bane idan mun tsaya. Banda haka da tuni ka fahimci nasarar dake tattare da fushin Ya Farha" ya kare maganar da zolaya. Cike da rashin yarda Abbati ya ce "Nasara?" "Nasara mana. Mutumina me yake saurin batawa mata rai idan suna son namiji?" "Zancen kishiya." "To ana kishin abin da ba a so ne?" Kyakkyawan murmushi ne ya bayyana akan fuskar Abbati a take. Me yasa bai yi wannan tunanin ba? Munzali ya yi ta tsokanarsa har suka yi parking a gefen Farha. Tun kafin motarsu ta tsaya take hango fuskokinsu suna dariya. Wani abu ya zo ya tokare mata wuya yaki sauka. Kishi ne wanda bata san daga ina yake tasowa ba. Gefe da gefe motocinsu suke. Sai ya zamana idan suka bude kofa ita da Abbati zasu gogi bayan motar juna. Yana sane ya matseta a wurin gashi daya barin ma akwai mota. "Ka matsa zan tafi." Ta furta lokacin da ta harare shi. Murmushi ya yi mata. Murmushinsa mai kyau ya ce "Idan ki ka tafi b'ata zan yi a hanyar komawa." Har cikin ranta taji murmushin nan. Sai dai kishin ya ci galaba a kanta domin ya saka ta fadin abin da taji kunyar amsarsa "Dariyarku ta kai ku gida." Taji haushi ashe. Munzali kuwa me zai yi banda dariya. Tana kallo Abbati ya harare shi kwatankwacin yadda tayi. Sadda kai tayi kasa don saura kiris ya saka ta dariya. "Mugu, ka ce min inyi murna kishina take yi. Gashi ka sa na kuma bata mata rai. Ni wallahi da zuciya daya na damu da kai. Ko a mafarki ba zan baka gurguwar shawara ba." Ba shiri Farha ta kawar da kanta gefe ta danne dariyarta. "Ya Farha ki juyo don Allah." Girgiza kai tayi don ba za ta iya kallonsa ba tare da tayi dariyar ba. "Fita ka bata hakuri mana" cewar Abbati yana budewa Munzali kofa, duk hankalinsa ya tashi "harda wani cewa wanda ake so ake kishi." Farha na jin abin da ya fada ta juyo da sauri suka hada ido. Bude nata tayi yadda ta saba yaji kamar ana fizgarsa cikin idanun. Kafin ya farga ta lumshe nata tana murmushi. Shi ma murmushin ya yi har zuciyarsa yana jin wata irin nutsuwa. "Ya Farha ki tausaya min mana. Fushin nan na kishin ne ko na gaske?" Munzali ta kalla yana tsaye tsakanin motocin biyu. Kallonsu yake suna burge shi. Abbatinsa ya sami mata in sha Allahu. "Ka ce masa ya bar ta a ciki?" Ta furta a hankali. Sannu a hankali Abbati yaji kamar zuciyarsa ta kara girma saboda jindadi. "Za ki jiramu?" Ya tambayeta bayan ya fito. "Zan jira." Sai da suka yiwa juna murmushi sannan ya juya. Munzali ya dawo jikin tagarta ta daya barin. "Farha.." ya kira sunanta a nutse. Waigawa tayi har taji kunyar kila ya kula da kallon Abbati da ya shiga tashar da take yi. "Don Allah ki so Abbati. Ban san ko kina da wasu samarin ba amma da wahala ki sami mai sonki kamar shi. Tunda ya ganki na daina gane kansa. Mutumin kirki ne. Idan zan fara fada miki karuwar da nayi da zama dashi sai mun bata lokaci a wurin nan." "Dadin baki ya ce ka zauna yi min?" Ta tsokane shi. Yadda tayi sosai ya sake burge shi. "Kut...wallahi kun dace! Bakinsa baya mutuwa shi ma amma a zuci saukin kansa har ya kusa yi masa yawa. Sau nawa ina masa wayo bai gane ba.." ya ce yana dariya. "Ai kuwa ka daina daga yau..." "Dalili?" "Zan tare masa." Farinciki ya mamaye Munzali. Burinsa ya cika. Abbati ya sami Farha. Hannu ya saka a kasan habarsa ya kalli gate din tashar da Farha lokaci guda ya kada kai "Wallahi kun dace. Sosai, sosai, sosai. Mungode Ya Farhan Abbati." * Nambar da aka kira shi Abbati yake nema zai tambayi inda Hanne take kamar an ce ya kalli hagunsa, ya hangota zaune akan benci. Hannunta tasa tana bubbuga kanta yadda ta kanyi a gida idan amosaninta ya dameta da kaikayi. Yana bata kudin zuwa salon amma don bakin hali, kamar wadda take cikin rashi sai ta soke abinta. Shampoo ma idan ya siyo ba ya sanin inda yake tafiya. Kan dai kullum dankare da amosani. Makotansu inda take zuwa kitso, tayi fada da matar duk akan tayi mata maganar neman maganin amosani. Ga gashin himili guda da tsaho da cika amma gyara sai taga dama. Da ya gaji da magana ne ya yi mata rantsuwar idan ta sake yin susa a gabansa sai ya aske shi. Shi ne ta koma bubbugawa har ta saba. Mayafinta yana kafada. Daurinta bai rufe tsofaffin jelunan gashinta ba. A kusa da ita namiji ne yake cin abinci daga shi sai gajeren wando. Rabin cinyarsa ma a waje yake daf da jikinta. Gashi da cibiri-cibirin gashin kai mara kyawun gani. Sauran mutum biyun dake daga barin duka mata ne amma suna cin abinci ana buga shewa. Gabansa ne ya fadi. Zuciyarsa ta tsinke har yaji kamar ya karasa ya dauketa da mari. Matsalolin Hanne suna da yawa. Ba zai taba yarda wai tashi a kauye da rashin wayewa ne suke damunta ba. Ya yi mata duk abin da ya dace domin ta gyara rayuwarta a matsayinta na mace. Da 'Yashshafa ce ta sami rabi-rabin abin da ta samu ya tabbata sai an ga canji. Duk da haka a yau dai abu daya ne ya tsaya masa a rai. Kazamar rayuwarsa ce ta gifta ta gaban kwakwalwa da zuciyarsa. Da sauri ya ja istigfari yana fesar da numfashi. Matsanancin tsoro ya mamaye zuciyarsa a lokacin da ya tuna cewa ba don rashin lafiyar da ya yi ba kila da yanzu ya koma inda yake son bari. Da bai je ba sai Allah Ya musanya masa da samun mallakar zuciyar abar sonsa. Wani abu da bai hango faruwarsa nan kusa ba in ma yana da rabo. Hango shi Hanne tayi ya nufo inda take ta tashi da sauri. Jikinta har rawa yake saboda tsabar masifar dake cin ranta. Tsayuwa tayi a gabansa ta sanya hannuwanta a kugu tana girgiza. " Ina 'Yashshafan take? Hmmm, wallahi kada ma ta gwadani don ba mutumci ne gareni ba." Abbati kam sai da ya daure zuciyarsa sosai ya iya cewa "su waye suke binki bashi a nan?" Shekeke ta kalle shi a zuwan ya ma raina mata wayo "Auuuu, wai nan bagarar dani zaka yi don na barta? To Yasin uban kuturu ma ya yi kadan. Kowa yaci tuwo da ni miya ya sha wallahi tallahi" Mutane har sun soma kallonsu ya jinjina kai cikin son ya hadiye fushinsa. "Nine kuturun kenan, mahaifina kuma bai isa ba?" Fahimtar katobararta tayi sai ta kama bakinta ta tsuke. Mutumin da ya kira shi a waya ya taso da ya ga ta tsaya dashi. Kudinsa ya fada da na mai abinci duka Abbati ya basu sannan suka kamo hanyar fita daga tashar. Munzali da Farha suna can suna hira kamar sun saba. Dama ya fi Abbati saurin jan mutane. A haka ya gane Farha ma ba baya ba. She is very friendly ga iya magana. "Yanzu nan gaba kuma idan ya hadu da wata, haka za ka tsaya kana wasa shi a gabanta ko?" "Ba fa zan gaji da cewa kun dace ba. Wato nan bugun cikina za ki yi ki ji ko akwai wata. Abbati ake yiwa wannan wayon ba ni ba." "Shi ma din ai ka gama yi masa wayon daga yau." "Na yarda fa. Amma ki kwantar da hankalinki. Daga ke babu kari." Mahaifinta ta tuno taji kunci na neman rufe farincikinta. Karin aure ba shi bane matsalarta. Munzali da ya kula da fuskarta sai ya ce, "Matarsa ma bata da matsala, in sha Allahu zaku zauna lafiya." Tunda yake bai taba jin Abbati ya zagi Hanne ba shi ma ba zai fara ba a bayan idonsa. Yana dai kawo masa korafi idan abu ya ishe shi amma iyakarta kenan. Ita ta fara hango su saboda tana fuskantar gate din tashar. Gabanta faduwa ya yi taji ta karaya. Yau dai bata shirya ganin matarsa ba. Kuma bata ga dacewar su hadu a tasha ba. Munzali da ya bada baya kuwa sai hira yake mata yana jingine da tasu motar. "Zan yi gaba kafin su karaso in jira ku a can" ta nuna titin da yake kallonsu wanda shi zasu bi su koma. "Ba za ki jira ku gaisa ba?" "Idan munje gida sai mu gaisa." Ta amsa a hankali. So take kawai ta bar wurin kafin su iso. Abbati yana tunanin da kalmar da zai gabatar dasu da juna kawai ya ga motarta tayi ribas kuma ko ta juya ta kallesu. Numfashi ya sauke ya mikawa Munzali mukulli. Shi ma bai tambaye shi dalili ba saboda yana iya ganin damuwa da bacin rai shimfide a fuskarsa. "Ka kora su 'Yashshafan ne?" Hanne ta tambayi Abbati da dan hope dinta. " 'Yashshafa zan kora ko su 'Yashshafa? Ita mutum daya ce. Su kuma yana nufin harda surukarki wadda ta tsuguna ta haifeni." Gefe ta muskuta saboda kunyar da ta sake ji sai tayi shiru. Lokaci lokaci take yin tsaki ko tayi kwafa cikin bacin rai. Mai rabata da 'Yashshafa yau sai ya shirya. Da shirun ya gagara tana gudun zuciyarta kar ta fashe ita daya sai ta soma surutai "Wai ni za a yiwa bariki? Hmmm. Har tayi girman sanin kissa? Yarinyar da a gabana ta fara kirgar dangi..." Fadan da baya son yi ya hau ta dashi. Don wata tsawa da ya yi mata sai da ta kusa sakin fitsari a zaune. "Hanne!!!" Ya kira sunanta da karfi da kuma alamun gargadi. Ko kula da yadda take zazzaro idanu bai yi ba ya cigaba da yi mata masifa "Wallahi zan fasa miki baki kuma na mayar dake tashar ki koma Kano. Kin sha burkutu ne da za ki shigo mota kina yi min wannan haukan? Ya dace kiyi magana irin wannan a gaban Munzali?" Girgiza kai tayi da sauri. "Bude baki za ki kiyi min magana. Nace ya dace?" "Bai dace ba" Hanne ta bashi amsa baki na rawa. Bata zata zai tanka ba tunda ta saba debo shirmen haukanta tana yi baya kulawa. Duk abin da suke yi Munzali bai tanka ba. In da akwai wurin da suka shatawa juna layi duk da basu furta da baki ba to zamantakewarsu da matansu ce. Suna kaiwa juna korafi da neman shawara. Amma babu zaman zubarwa matan da mutumci. Ko babu komai dukkaninsu 'yan uwansu na jini suka aura. Yanzu ma parking ya yi ya fita daga motar. Farha bata kula sun daina binta ba don tunda ta ga ba Abbati ke tukin ba ta daina kallon motar ta madubi. "Yanzu me nayi da har za ka ci mutumcina a gaban Munzali? Saboda Allah a dakeni a hanani kuka?" "Ni ne ma na zubar miki da mutumcin Hanne? Yau ko ciki daya muka fito da Munzali ya dace ki dinga zancen kirgar nono a gabansa?" "Kirgar dangi na ce." "Kar kisa in zageki Hanne. Ko kirgar kindirmo ne ai ya san me kike nufi. Wannan shirmen ne ya kawoki dama ba duba mijinki ba?" "Sannu ya jikin?" Ta ce a sakarce. Madadin ya amsa sai ya ce "tsabar kishinki na banza ya saka ki fitowa ko kaya babu? Da ba yau zamu koma ba haka za ki zauna?" Gefen kafafunta ta hau lalube tana cewa "Da kayana. Na taho da kaya." Sai ta dafe kai "washhh, Yasin suna shagon mai shinkafar nan." Yi mata magana ma bata lokaci ne. Fada ko duka asarar energy. Fita kawai ya yi ya fadawa Munzali ta baro kayanta. "Ku wuce can zan koma tashar na dauko. Tafiyar tamu kamar da wuya dai a yau. Bana son fitar yamma bare ta dare." "Ba ayi haka ba." Munzali ya ce da Abbati. A dalilin Hanne tayi tafiya ya dace ya kaita ta dan huta kafin su kuma daukar hanya. Sannan suna bukatar yin magana a junanau. Wanda ya kira Abbati akan bashin da Hanne ta ci suka sake kira aka kwatanta masa jakar. Suka yi masa alkawarin dubu biyar idan babu abin da ya salwanta ciki sannan suka rabu. Munzali ya koma tashar, Abbati ya wuce gidan Alh. Tahir da Hanne. Su biyun sun gane hanyar a bi daya tak. *** Fafur Mardiyya taki zuwa asibiti saboda ciwon karya ne. Ta dai nuna taji sauki. Sai da Mami Khadija ta fita daga dakin sannan Mardiyya ta yiwa Sauda bayanin abin da ya faru. Dundu ta yi mata a baya "Amma dai baki kyauta ba, baki ga yadda hankalin Mama ya tashi ba." "Haka shi ma ya ce." Da shakiyanci Sauda ta ce "Shi? Har kin fara ce masa shi? Lallai Abba ya fara tari auta ta isa aure." "Ba fa haka bane. Kinga babba ne. Bai dace na kira sunansa kai tsaye ba." Mardiyya ta ce da nufin kare kanta. "Hakkun. Ladabi da biyayya akwai dadi." Shan kunu tayi don tsokanar Sauda bata karewa. Idan ta saka mutum a gaba sai ya kusa kuka. "Bana so...abokan shawara kawai ya ce mu zama kar ma ki fassara." "Hakka!" Ta ce bayan ta tashi tsaye tana dariya "su abota manya." Tsokanar da take gudu Sauda ta sami kofar yi har sai da ta nuna kamar ranta bai baci ba. Sannan ne Saudan ta turawa Farha text wadda a lokacin suka isa tashar ta fada mata Mardiyya kalau take. Sauran bayani sai ta dawo. * Lilu ne ya tuko motar Suhaib, shi kuma ta Abbati wadda take asibiti suka dawo gidan tare. Wurin parking suka nufa kowa ya daidaita motar da yake ciki bisa tsari. Kafin shigowarsu Baaba Mari ta dinga jin kamar suna takurawa masu gidan. Sun zauna jiran su Abbati batare da sanin ko masu gidan suna da uzuri ba. Dadin dad'awa ga an ce 'yar gidan babu lafiya. Babu alamun canjin fuska ko kadan a tattare da matar gidan amma da yake bata saba ba sai take jinta a takure. Ga Deluwa da 'Yashshafa sai kai hannu suke cikin tray din snacks suna dauki daidai. "Kiyi hakuri mun zo mun dora miki dawainiya." Mami Khadija ta sake fadada fara'arta "Me ya kawo wannan magana? Ni wallahi baki ji yadda nayi farincikin zuwanku ba. A haka fa ake kulla zumunci kiga har 'ya'ya." Baaba Mari sai dariya "kayya Hajiya. Mu fa 'yan kauye ne. 'Yan birni suna zuwa kauye?" "Har kinsa naji babu dadi. Muma ai zama ne ya kawo mu nan amma silar kakaninmu kauyen ne. Mu 'yan Soba ne kuma har yanzu muna ziyartar dangi a can. Garinmu a karkashin Kaduna yake." Uwar azarbabi Hajiya Deluwa mai hangen surukuta za ta hadata da Mami tayi saurin shiga hirar. "Mu kuma daga Kirikasamma muke. Amma ita Mari aure ne ya kawota. Ita 'yar Maigatari ce." Baaba Mari bata gwasaleta ba. Hirar sai ta tafi su uku. Deluwa ta rasa inda za ta saka kanta don murna. Da mace mai aji irin Mami Khadija take hira. Takaicinta ma na rashin bude kwanukan abincin da Baaba Mari bata bada fuskar yi ba ya yi sauki. Sai kayan fulawa suke ta gabza. Mami Khadija ce ta sake komawa bangaren Mama Nasima tunda bata san ciwon karya bane. Ta damu da Mardiyya kamar yadda ta damu da nata 'ya'yan. Da ta dawo Baaba Mari ta ce ta kaisu su gaishe da marar lafiyar. Mami Khadija kuwa taji dadin kyawun tunanin Baaba Mari. Su biyu suka bi ta. 'Yashshafa anyi gamo da samosa ta kasa hakura ta bisu. Tun dazu Deluwa take yi mata inkiya da hannu akan ta barshi haka don ita ma ta ci amma taki. Sai da suka fita taji falon ya yi tsit sai karar AC. Ita kadai ta firgita kanta da muggab tunani. "Wannan shuuuuuu haka kamar wucewar fatalwa?" ta ce da rawar baki. Guntuwar samosar hannunta ta ajiye ta tashi a hankali ta sulale waje. Da baya da baya take tafiya tana kiran Deluwa a tsorace. * Kai tsaye Lilu ya danno kai bangaren Mami Khadija sai ganin yarinya ya yi a gabansa a bakin kofar shiga. Gewayen fuskarta da dan karan hancin nan sun yi fari saboda hoda da foundation. Bakin da ya ci samosa kuma maiko ya zagaye shi. Idan ka kalleta dole kayi dariya ko baka so. Mami Khadija kanta girma ne kawai da sanin mutumcin bako ya hanata darawa. Sauda tayi a fakaice. Idanunta ta zaro tana kalle-kalle a farfajiyar gidan ko za ta hango mahaifiyarta. Lilu sai ya sauka daga matattakalar ya jira Suhaib ya karaso. Hab'a ya rike ya ce da yayansa, "Ya Suhaib, yaushe watan Ramadan ya tsaya har goman farko ta wuce ban sani ba?" "Ban gane ba." "Kaga karfin hali" ya nuna 'Yashshafa "masu Iya duba-duba na gani a kofar Mami. Yanzu ashe har cikin falo suke shiga in sun zo. Shi ma ya hau next level kenan." "Kai fa ka fiye shiririta. Gabadaya ban fahimci kalma daya cikin zantukanka ba." Hannu ya mika masa yana dariyar da ta bawa 'Yashshafa haushi. "Bani canji ko dari biyu ce in sallameta tukunna." Sai lokacin Suhaib ya karasa hawa matattakalar ya kalleta. Duka ya kaiwa Lilu ya goce da sauri. "Kanwar Abbati ce fa." Da ya soma dariya sai da ya durkushe a wajen "Wannan din? Kalleta da kyau Ya Suhaib 'yan Iya duba-duba ne." Kyale shi Suhaib ya yi ya dubeta duk tayi wuru-wuri kamar wadda ta yiwa Sarki karya. Rangwadar nan ma babu alamunta. Dole Lilu ya cr tashe tazo. Kalmar ce ta bace masa yake ta cewa Iya duba-duba. "Me ya fito dake?" "Innata. Inna Deluwa nake nema." Lilu ya sake kwashewa da dariya "kana ji fa Imna Deluwa take nema sannan ka ce ba ..." "Ya isheka Lilu" Suhaib ya ce rai a bace. 'Yashshafa ya tambaya inda suka je har aka barta ita kadai. "Wai wata ce bata da lafiya shi ne suka tafi da matar gidan nan" ta nuna bangaren Mami "cikin kuma sai nake jin kamar fatalwa tana shawagi. Sai shuu, shuu ake yi." Shi ma mai fadan dariyar sai gashi yana yi harda kyakyatawa. Cikin sa'a kuwa sai ga su Mami sun fito. 'Yashshafa tana hangosu ta sauka da sauri. Gayun ya dawo da karfinsa tunda yanzu dai ta san ba gidan yan kan kai bane yadda ta soma hasashe. "Mooomi. Moomii" Hanjin cikin Deluwa a take ya bada wani irin sauti mai karfi. Tsinuwa ta shiga yarfawa aljanun 'Yashshafa wanda ta kwaso a makatantar kwana. Kunya kamar ta nutse. Sai kuma dole ta nema mata sauki domin indai sune suna wahalar da ita. Wani zubin sai tayi wata guda a gida ana tsakar zangon karatu. "Me ki ka ce Shafa'a?" Ta riko hannayenta tana jin kamar ta fashe da kuka. Yanzu idan Sha'aib ya gujeta dole sai dai ta komawa Abbati. 'Yashshafa tayi murmushi a zatonta sunan ne ya burge Deluwa. "Moomi." Kowa yana ji ta ce ''oh ni 'yasu. Makaranki su rasa wurin tashi sai nan?" "Makarai? Aljanu ne da ita?" Cewar Mami Khadija tana dan matsowa da taussyawa. Lilu kuwa bayan Suhaib ya koma ya labe a firgice har yana tuntube. Cartoon ma baya kallon mai dodanni saboda kafirin tsoro bare kuma a ce gashi kusa da mai aljanu. "A makarantar kwana ta kwaso su. Da alama yau bafillatani ne ya tashi kenan." Cewar Deluwa tana marairaicewa "Karshenta shanunsa ne suka bata ya fito nema. Banda haka me zai kai budurwa kiran wata Moomi ana zaune kalau?" Lilu na jin tsoro amma bai hana shi dariya ba. Suhaib ya figi hannunsa saboda kallon da Mami Khadija tayi musu. 'Yashshafa tana son yiwa Deluwa bayani amma kuma Mami Khadija tana gefensu sai sannu take yi mata. Cikin falon suka koma Baaba Mari ta dinga girgiza kai. Tana ji tamkar ta janyo su Abbati su zo su bar gidan nan. Duk wani abu da zasu yi takama dashi na kare mutumci Deluwa ta zubar dashi. Bata ganin laifin 'Yashshafa domin kuwa yarinya ce mai bin maganar uwa sau da kafa. Duk abin da take yi bai wuce dorar da tarbiyar mahaifiyarta ba. *** Manyan mata ne a zazzaune suna hira ana ciye ciye da shan lemuka. Manyan mata a matsayin arziki domin ba dukkansu bane masu shekaru. Babu 'yar kass da talatin dai cikinsu. Suturunsu da duk wani abu da yake jikinsu ya isa shaidar cewa suna ganiyar jin dadin rayuwa. Su tara ne kuma kowacce cikin lemon gabanta anyi masa hadi da kwaya daidai ra'ayinta. Wasu har sun fara tambele suna magana irin ta gogaggun 'yan duniya. Wata hamshakiya da ta gama tumsewa ce ta mike tana wata irin rawa ta tsantsar rashin kamun kai. Suka tashi suna ihu aka soma tayata da liki. "Ku barni in warwasa kawayena. Jiya na hadu da namijin da ya amsa sunansa ba irin dan rakiyar da nake aure ba..." "Yeeeeyyyy" Suka hau shewa ana dariya. Ta cigaba da cewa, "Saurayin kanwata ne amma ina ganinsa na san dan harka ne. Bugu daya ya kawo min kansa hotel jiya." Wata shewar ta cika falon da suke. Matar gidan wadda tayi musu masauki ta doki cinyar Jiddo tana dariya. "Jiddo ta Alhaji Tahir bamu labarin naki mutumin. Ya ku ka kare da makaniken nan na Kano?" Jiddo bata son a ce ta gaza. Ba yau suka fara harkokinsu ba. Yanzu dai duk sun chanja samari ne. Ta fada musu haduwarta da Danladi amma shiru bata labarta musu yadda aka kare ba. "Sai zama na gaba za ku ji bayani." "Amma dai ya turo miki hotuna bayan kin tura naki ko?" Karya ta gillo musu mai jirwaye da gaskiya "ai tun bayan ganin hoton shegiyar nan a wayar Alhaji nake kaffa kaffa da wayata. Ya turo" sai ihu har sun fara matsowa ganin gulma ta kara da cewa "ina gani na goge." Mata ne wadda kowacce take dauke da tabo ko bacin ran namiji. A nasu jahilcin da bacewar basirar ne suke tunanin wannan rayuwar ce za ta wanke musu zukata. Neman matan Alh Tahir bai wani dami Jiddo ba. Amma rashin haihuwa ya mata karan tsaye. Tun tana nema har ta saduda. Duk tarin arzikinsa ba za ta tsira da komai ba sai tumunin takaba in ya mutu...a zatonta! I just published "20" of my story "UWA UWACE...". https://my.w.tt/XYPGlg7tvcb UWA UWACE...20 Batul Mamman💖 ~Na san kuna hakuri. Hakurin dai zan yi ta baku akan rashin regular post. Nagode da bin rubutuna da kuke yi. ~Afuwan, wadda ta bamu award sunanta Maryam Muhammad Labaran, nayi kuskuren rubuta sunanta a sakon godiya da nayi. This page is for you sister Habiba Haruna (Mantis Kitchen). Allah Ya kara lafiya. *** Buba da Habi sun shigo gidan sun tarar da Deluwa cikin tashin hankali da fargabar abin da ya sami 'Yashshafa. Sai fada take tana nanatawa lalura ce kuma babu wanda yafi karfin ta kama shi. Talaka da maikudi. Dan kauye da dan birni babu inda ba a aljanu. Su gidan wani abokin Buba suka je. Mutumin da kansa ya zo ya tafi dasu tun kafin fitarsu Abbati. Habi tana jin abin da ya faru ta yi 'yar dariya. Kafadar 'Yashshafa ta dafa ta ce, "Gwaggo Deluwa dake take fa. 'Yashshafa ko ba Momi kike nufi ba na 'yan gayu?" 'Yashshafa dai kamar ta nutse a kasa. Idanuwa duka a kanta. Dadinta daya ma wannan mai dariyar da yayansa basu biyosu ba. Mami Khadija ma dariyar tayi ta tashi ta shiga ciki za ta hado musu 'yar tsaraba, musamman ma dai 'yar budurwar nan mai abin dariya. Deluwa na ganin ta rufe kofar koriďo din da zai sada ta da dakinta ta kaiwa 'Yashshafa duka a baya rai duk a bace. "Yanzu ke Momi din ne baki iya fada ba ki ka hau kukan saniya? Ca nake 'yar gidan Bibalo ba momi suke ce mata. Kawai sai mooo, mooo ake ji kamar saniya ta tsinke daga turkenta. Mtseww" Buba da Habi suka bushe da dariya. Sallamar Farha suka ji Baaba Mari ta soma hamdala. Tafiya zasu yi yanzu yanzu in Allah Ya yarda. Bata bukatar Hanne ta zo ta bar nata abin fadin kamar na Deluwa da 'Yashshafa. Kafin ta shigo tun a waje Lilu ya tareta ya bata labarin gamonsa da 'yar tashe. Dariya taso yi aka kuma bude gate Abbati ya shigo. Zuciyarta tayi wani irin dokawa mai wuyar fassara. Abin sai ya bata mamaki tunda a hanya ta san Munzali ke jan motar. Bata ga alamun Munzalin ba sai mace. Shi ne ta shige bangaren Mami da sauri don ma kada su hadu. Ya kula da irin saurin da take yi wanda yake da nasaba da gudun haduwa da Hanne. Da gaskiyar Munzali dai da ya ce masa kishinsa take. "Wai shiga ka ke so nayi na kirasu? To wane bangaren zan je?" Hanne ta katse masa tunani da ta bude kofa za ta fita. "Don Allah Hanne ki kama kanki. Kin san abubuwan da bana so. Kar ki gwada musu a gidan nan. Godiya kawai muka zo yi musu na kyautatar da suka yi mana." Ya san halinta. Ko babu komai tsakaninsa da Farha ba zai so ta shiga tayi abin da zai zubar mata da kima a idonsu ba. Idan Farha rabonsa ce zai so ta shigo gidansa tana ganin mutumcin wadda ta tarar kuma kanwa gareshi. "Naji" ta amsa da kunkuni. Abbati dakatawa ya yi aka yi musu izinin shiga bayan ya yi sallama. Yana saka kafarsa Farha na shigewa wata kofa da yake tunanin kitchen ne. Murmushi kawai ya yi sannan aka gabatar da Hanne ga Mami. Anyi sa a Mami Khadija tayi mata kwarjini shi yasa ta gaisheta a mutumce. Da kyar Mami Khadija ta samu suka ci abincin don sun matsu su tafi Kano a ranar. Basu dade suna jiran Munzali ba ya iso. Wurin Mardiyya ya fara zuwa suka yi sallama. Mama Nasima tana son tambayarsa alakarsa da abokan tafiyarsa da Mami Khadija amma yau ba hali. Ciwon karyar Mardiyya duk ya tsaya mata a rai. Da zasu bar gidan Abbati ya so Farha ta fito ko yaya ya sake ganin fuskarta amma taki. Tsoron ganin matarsa take yi. A yadda ta ganshi hadadde dan gayu da wuya ace matarsa ba haka take ba. Idan kuwa haka ne kila sai ta raina kanta. Karshenta kuma tafiyar da bata taba irinta da wani d'a namiji ba ta sami tangarda. Gara dai kada ta kai kanta kallon abin da zai iya tada mata hankali. *** Fitar su Hasiya ba dadewa Ale Gambo ya dawo. Salima na durkushe bakin murhu tana faman hura wutar itace cike da tashin hankali saboda daren da girkin ya yi. Gashi itacen danyene, yaki kamawa sai hayaki yake ta fitarwa. Daga bakin rariyarsu 'yan matanta ne suke wanke wanke. Takunsa dif-dif tamkar wani doki mai ji da karfi ya shigo tsakar gidan. Sannu da zuwan da yaran suke yi masa ma bai ji ba sai kira yake kwalawa Salima. A razane ta fito domin da wuya suke wanyewa lafiya idan ya shigo a wannan yanayin. Cikin tsananin fushi da mamakin rainin da ya soma shiga tsakaninsu ya nuna ta da dan allinsa. Har wani haki yake ga feshin yawun da ya kan yi in yana magana cikin fushi. "Hasiya na gani ta fita." "Wani abin ne ya sameta?" Salima ta tambaye shi da firgici. "Nawa ta baki?" Maganar ta doketa sosai ba kuma don yau aka fara ba. Mijin aurenta ne, uban 'ya'yanta, wanda bai taba sanin darajarta ba yake yi mata wannan tambayar. Duk inda mutumci yake sun dade da yin hannun riga da Ale Gambo. Maganganunsu dasu Hasiya na dazu suka dawo mata. Tabbas zancen Ayaah gaskiya ne, babu wanda zai iya k'watar mata 'yanci a wannan yanayi sai ita da kanta. Tana jin tsoronsa har cikin kasusuwanta domin dukanta yake kamar ya sami gardi daidai dashi. Amma haka ta daure ta yatsina fuska tana magana cikin bacin rai ita ma. "Ajiya ka bata ko bashi?" Hagu da damansa ya waiga babu kowa sai yaransu suna kallonsa. Ya dawo da idonsa kanta tare da nuna kirjinsa. "Wai dani kike Salima?" Haka kawai taji kwarin gwiwa yana ciccibata. Daurin zaninta da yake neman kwancewa ta gyara tana cewa, "Idan akwai wani Gambon a gidan nan bayan kai to dashi nake." Jikinsa sai ya hau tsuma kamar mazari. A zatonsa ko hauka take bata isa ta maida masa magana haka ba. Daga shi har ita sun ji karar kwanukan wanke wanken domin a tsorace yaran suka mike. Sun tabbata sai ya dakar musu uwa. Hularsa ya cire ya yar a gefe. Kodaddiyar babbar rigarsa tabi bayanta. "Baba kayi hakuri" Ko kallonsu bai yi ba ya dubeta yana jinjina kai. A firgice take sosai amma tayi alkawarin daukar mataki. "Dama ina da labarin Hasiya" ya ce yana kumfar baka "ance tafi kowa rashin kunya a cikinku. Wato zuwa tayi ta kitsa miki gaibu tace kiyi min rashin kunya ko? Tunda baki da hankali har ki ka karbi shawararta za ki ga abin da zai biyo baya. Wallahi Salima daga yau ko daga ido ki kalleni kin daina.." "Idan ka isa ka kasheni kawai ka huta." Ta bashi amsa da kuka. "Mama kiyi shiru don Allah" cewar autarta. Ita da yaran babu wanda ya kula da lokacin da ya hanyo igiyar gugar rijiya. Murdeta kawai ya yi ya kama daidai inda zai masa dadin riko ya shiga lafta mata. Salima taki yin ihu kamar yadda ta saba. Tsayuwa tayi kyam dukan yana sauka a jikinta amma zuciyarta ke karbar zafinsa. Shi kuma gogan rashin jin magiyarta ya sake tunzura shi. Hannu ya daga ya kai mata dukan da yafi kama da naushi a gefen fuska. A lokaci ne kuma ta aiwatar da shawarar Ayaah. Tafiya tayi luuu ta zube a kasa. Yaran suka yo kanta suna kuka. Ale Gambo ya soma masifa yana jiran ta tashi yaji shiru. "Ke Salima. Salima? Tashi mana" ya ce jikinsa na yin sanyi. Igiyar ya saki ya dan ja baya. Babbar 'yar tasu mai shekaru sha uku Ihsan tana ganin ta fadi ta ruga makota a guje tana kuka. Duk da haka Ayaah ta ce suyi amma a tsorace take ko suman gaske Ummanta tayi. Kuka take tana kururuwa kamar yadda Ayaah ta fada mata a dan tsukin lungunsu. "Wayyo Allah. Baba ya kashe mana Umma" Hankalin Ale Gambo ya tashi sosai da yaji me take cewa. Girgiza Salima ya shiga yi yana faman kiranta kamar mahaukaci. Durkushe a wurin makotan da suka fara shigowa suka same shi. "Haka kawai naga ta fadi nima." Ya dubi yaransa a darare "ai ban mata komai ba ko?" Basu amsa masa ba sai ihun da suka cigaba da yi. "Baba ya kashe Ummanmu da duka." Salati kawai ake ji sai matan da suke neman taimaka wa Salima. Shi kuma Ale Gambo sai huci yake da surutai mara sa kan gado. Duk wanda ya gan shi a wannan lokacin ya san ya shiga rudani, amma yana kokarin boyewa don kada ya tonawa kansa asiri. Hannuwa yake ta dagawa kamar mai shirin tashi sama. "Ni ban mata komai ba! Daga maganar fatar baki sai mutum ya suma? Salima ki ji tsoron Allah ki mike. Wai me nayi miki?" Ba a dauki lokaci ba ta dan farfado musu amma taki ta sha ko da ruwa ne ga kuma baki duk sai fitar da jini yake. Gefen fuskar nan inda ya daka ya kumburo suntum kamar alkubus. Kan a ce me gida ya kacame da 'yan jaje cikin daren, daman makotan ta da dama suna da masaniyar ba yau ya fara bugun ta ba. Wani dan tsoho da yake yawan zama nan gindin bishiyar kofar gidan nasu ne yace to ya zama tilas su nemo iyayenta a sanar dasu kafin ya kashe musu 'ya wataran sai dai a kai musu gawa. Kowa ya yi na'am da zancen. Shi ya saka wasu magidanta biyu tare da Ihsan suka hau adaidata zasu je a fada wa iyayenta halin da ake ciki. Ale Gambo yana neman yi musu taurin kai domin ya gudu samarin layin suka kama shi. An tsayar da magana cewa da an dawo da iyayenta zasu wuce dashi ofishin 'yan sanda. *** Idanu ta runtse tana mai jin haushin kanta. Shigowar Innayo ta bakwai kenan dakin amma ta kasa motsa baki tayi mata tambayar dake cin ranta. Dangin Babansu da makota da dama sun zo mata barka. Amma yadda babu kowa daga gidan mijinta haka nan babu daga dangin Innayo. Hatta na cikin Kanon babu wadda ta zo. Abin ya yi mata ciwo. Indai ba su ma din sun tsaneta ba me zai hanasu zuwa? Ga yaranta da take masifar kewa kamar tayi hauka. Sallamar Uwani ta jiyo tayi saurin share kwallarta. Sai dai tuni Uwanin ta gani lokacin da ta bankado labulen dakin. "Kuka Zara? Naga uban kayan abinci su akarambana (Hasiya) suna gyarawa wai na suna. Ba dai rigima ku ka yi da Alh. Unais ba?" Bangare daya na fatan haka ne ko don tayi mata dariya. Ta jima tana fada mata kudin miji ba a tinkaho dashi. Burgewa shi ne ki tashi ki nemi na kanki. Daya bangaren kuma mai sauran imani yana fatan ba haka bane. Shi ma kuma domin kada 'yan bani-bani su kara yi mata yawa idan Zaran ta durkushe ita ma. "Bama waya ma" ta amsa mata muryarta tana karyewa "sai dai matsalarsa bata gabana. Na san yadda zan yi na rama duk abubuwan da suka yi min shi da Haj. Fatakwal." "To meye kike hawaye?" * A waje Maimuna, Hasiya, da Murja da Ummita wadanda daga gida suka wuto nan din kai tsaye ke ta aikin kayan miya da nama. Yaran Maimuna duka maza ne. Biyu cikinsu, manyan sune masu yayyanka nama. Hira suke yi cike da nishadi Ayaah sai ta dinga jin kanta kamar bare. Gefe ta koma tana daddanna waya amma ko kadan abin baya burgeta. So take ayi da ita amma bata san kan hirar ba. Zantuka ne da dukkansu suka san wani abu a kai. Hasiya tana ta lura da ita. Yanzu kam tana sane ta ki sakota cikin hirar saboda ta kara gaskata maganar Salima. Ta kuma samu abin da take so. Ayaah ta bata rai sai wani karkada kafa take wanda ta san da wata cikin yayyenta za ta yi mata magana karshenta a kare da rigima. "Ayaah." Kamar jira take ta amsa kiran Antinsu Maimuna da sauri. "Na'am" "Jeki ki karbo jaririyar nan wurin Zara na goya miki ita. Kin dai iya goyo ko?" Yanzu ma da saurinta ta gyada kai "na iya" "Dan wa ki ka taba goyawa?" "Aji tsoron Allah dai banda karya" Cewar Ummita da Murja suna mamakin yadda ma ta amsa mata a ladabce. A zatonsu gefen da ta kebe kanta tana danna waya duk cikin rashin kunyarta ne. "Ku kuma don baku taba gani ba sai ku yanke mata hukunci da rashin iyawa?" Mamaki ya kara kamasu. Anti Hasiya ce fa ta kare mata! Anya yau lafiya kuwa? Kara musu mamakin tayi ta hanyar kallon Antin tasu suka yiwa juna murmushi sannan ta kallesu ta murguda baki. Da sauri ta ta juya ganin Anti Hasiyan ta bude baki. Bata so tayi mata fada yau. Kullum ita ce mai laifi idan abu ya hada da yayunta. Yau dai ita aka tarewa. Duniya tayi mata dadi. * Innayo ta fito daga bandaki ta jiyo muryar Uwani da Zara a cikin daki. Bata ji shigowar Uwanin ba ta shiga wanka bayan ta gama hadin sabulun salo na jaririyar da take nuna bata damu da ita ba. Hannun kofar ta kama za ta bude ta ji zancen da suke yi wanda ya sake tsinka mata zuciya game da sha'anin 'ya'ya. "Yo don dangin Innayo basu zo miki barka ba sai ki hau kuka? To ko dai kin ji wata magana ne?" Uwani ta furta da bacin ran ashe duk kukan Zaran ma mara dalili ne a ganinta. "A cikin gidan fa nake amma ko mutum daya ban ji ta kira ta fada musu haihuwar ba. Ai dole abin ya yi min ciwo. Kuma ita ma bata taba daukan yarinyar nan duk kukan da za ta yi." "Kinga Zara bana son munafunci fa. Ni ce ba wata ba da za ki fake da rashin zuwan dangin Innayo don ki boye 'yar tsamar dake tsakaninki da mijinki. Daukar jika kuma ina ce haka kike so?" Daidai lokacin Ayaah ta shigo. Murmushi ta yiwa Innayo tunda sun gaisa lokacin da suka zo. Tashin maganganun da ta ji ita ma sai ta kasa karasawa dakin. Fita ya kamata tayi amma ta kasa lokacin da ta kula idanun Innayo a birkice suke. Akwai boyayyen bacin rai da damuwa a cikinsu. Sai kuma kwallar da ta cika shi taf amma taki bari ta zubo. "...ba har gidanki ki ka kirani akan in zo in karbarwa su Innayo tsofaffin kayan da baki dinka ba don kada su zama abin kallo wurin taron suna ba?Ko baki dinga yamutsa fuska da na baki labarin tana ciwon hakori ki ka ce kazanta bace? Shi ne yanzu za ki dinga kukan karya kamar kin fi kowa damuwa da ita..wai ma da kin taba gayyayarsu suna ne?" "Meye na daga muryar? Kuma duk abin da ki ka fada ai bai canjata daga zama uwata ba." Zara ta ce da sanyin muryar wanda hankali ya fara ziyarta. Uwani tayi wata irin dariya ganin kamar rainin hankali Zara take yi mata. "Daga baya kenan amma kin san sai dai ki fadawa wanda bai sani ba ko? Na san Innayo za ta ji dadi. Ko ba komai yadda ta dade tana son ki dinga rabarta sosai yau ta samu tunda baki da tudun dafawa." Allah Sarki Innayo, kwallar sai ta sauko a guje. 'Ya'yan cikinka su yi maka irin haka ba karamin ciwo gare shi ba. Ji tayi kafafunta suna neman sakinta a kasa sai hannuwan Ayaah suka tareta. Tausayin Innayo ya tsirga mata. Tunda suka shigo matar nan tana kan kafafunta. Amma ita ce 'ya'yanta suke yiwa haka. Daga ciki suka ji Zara na cewa "Ko ma me za ki fada kiyi ta fada. Na riga na fara ganin nawa sakamakon, ki jira naki." "Ba zan ga komai ba sai alheri. Wato rashin kunyar da ki ka kwana biyu baki yi ba saboda kin dawo gida mai soro ce tasa ki cewa nazo dama?" Zara ta share kwallar da ba za ta ce ga aihinin dalilinta ba. "Ki barshi kawai." Ayaah kasa jurewa ganin hawayen Innayo tayi ta juya za ta fita. A yau ta fahimci me yasa a gida ake bukatar wanda ba ya shakkar kowa. "Ina za ki?" Innayo ta tambayeta cikin dusashewar murya. Kofar dakinta ta harara tukunna sannan ta ce "Anti Hasiya zan kira." Innayo ta murmusa ganin ran Ayaah yana neman fin nata baci "Dawo abinki Hajara. Idan babarki ta zo raina sai yafi yanzu baci. Ba wani hakuri gareta ba bare jin magana a irin wannan yanayin." Ayaah bata san lokacin da tayi murmushi ba "da gaske ita ma bata jin magana?" "Ban ce ba" Innayo ta amsata cike da kulawa. Sautin tsakin Uwani wadda ta mike suka jiyo tana mai cewa "Aikin banza. Kin san abubuwan da na katse na zo? To wallahi sai kin biyani tunda a bakin aiki nake ki ka sani fitowa." Zara ta auna ta ga a neman lafiya babu ji da kai. Idan tayi shiru kanta za ta cuta. A yadda ta wahala kwanakin farkon haihuwarta ba za ta so a maimaita ba. "Wurin dinkin nan nake so ki duba min. Ina jin kamar bai yi ba." Metiron Uwani ba mutumci. Banda tana tsoron kada kasuwar ta watse da sai tayi dariya. Ai tun ranar da Innayo ta saka ta duba Zaran ta kula dinkin zai iya samun matsala saboda rashin kulawar da ya samu. Duk da cewa a ranar a tsorace take amma ta san muddin Hasiya tana wurin bata isa ta karbi kwandalar Innayo ba. Ashe kuwa tana da rabo. Tunda Zara ta sake kawo kanta wallahi sai taci kudinta. Tashi tayi kamar za ta fita daga dakin a zuwan bata damu ba ta ce "Aiki ne na kuďi Zara. Sannan dole ki san karyar da zaki yi ki zo ki sameni a gida. A nan Innayo..." Innayo kawai ta bude kofar. Su biyun kowacce ta zaro idanu. Jaririyar ta nunawa Ayaah. "Dauki kanwarki ki fita kuma kada ki manta abin da na fada miki." Umarni ta bi ta koma tsakar gida da 'yar jaririyar wadda ta sake nannadewa a shawul. "Uwani" Cikin Uwani sai da ya tsirga don tsoro ne ya cika mata zuciya. Yanayin Innayo yasa taji kamar tayi tsuntsuwa ta ganta a nata gidan. "Ba dake nake ba?" Innayo ta yi mata tsawa. "Na'am" Muryarta har rawa take da ta amsa. "Ban ce ki duba min Zara zan biya ki ba rannan?" "Kin ce." "Isa ne ban yi ba ko? Saboda bani da wannan mutumcin a idonki." Maganarta ta biyu babu hargagi balle daga murya. Amma zukatan fitinannu cikin 'ya'yan nata sun girgiza. Duk abinsu bata taba nuna musu wannan bangaren nata ba. Sai suka zata duk wani rashin albarkarsu za ta karba saboda tana son su. "Wallahi Inn..." Katseta tayi da cewa "Duba ta." Zara ta kwanta da tsoron kada fadan ya dawo kanta. Uwani na dubawa ta ce sai an sake dinkin. Hawaye ta soma fitarwa kawai saboda tuna irin azabar da tasha a 'yan kwanakin da suka wuce. Tana ji Innayo ta ce da Uwani ta je ta dauko kayan aikinta. A gurguje ta fice. Duk da dan akwatin tafi da gidanka da take yawo dashi yana mota ita dai burinta ta ganta a waje. Bayan fitarta ne Zara ta kasa daurewa ta kira Innayo a raunane. "Innayo." Bata amsa ba ta fita daga dakin. Wurinsu Hasiya ta tafi ta ce komai suka gyara su adana shi suna sai wani satin. "Wani abin ne ya faru?" Cewar Maimuna. "Maijego babu lafiya. Banda ma sun dorawa kansu waye yake wani taron suna a haihuwa ta biyar?" Hasiya kamar bata yarda ba. Dama ta kula da wani irin yanayi da Ayaah ta fito dashi kamar tayi kuka. Ana haka Uwani ta dawo. Bata cewa kowa komai ba ta shige ciki. Innayo ta bi bayanta ta rufe kofar falonta. Kafin a fara tasa Zara kiran Alh. Unais. Sai da tayi masa kira hudu sannan ya dauka a wulakance. "Ina fata ba cewa za ki yi kayan abincin sun yi kadan ba. Sannan ki fadawa Innayo dinnan don Allah ayi abinci maidadi saboda dangina da zasu zo da na Laurat. Ayi abin fita kunya." Taji zafi kwarai da jin kalamansa. Sai dai kuma har duniya ta nade Zara bata da wata uwar sama da ita. Babu mai daukar wannan bakin halin duk son da yake mata ya ce zai jure ya cigaba da kulawa da ita irin na uwa da 'ya. Ita din cw dai dolenta. "Innayo dinnan ce ba Zara ba. Ka fadawa danginka suna sai wani satin. Idan kuma za ku iya hakura gabadaya zai ma fi." A hanyar komawa gida yake daga kasuwa. Yana baya direbansa yana ja. Jin muryar Innayo ba shiri ya tashi zaune daga kashingidar da ya yi. "Wani abin ne ya faru?" "Ba ta da lafiya." Ya san Haj. Fatakwal ba za ta lamunce ba shi yasa ya ce zai sanar dasu yadda idan sun zo ba za su takura mata ba. Gaban Zara yana dukan uku uku ta ji Innayo ta cigaba da cewa "Baka fahimceni ba kenan. Kwata kwata bana son danginka su zo gidan nan gobe. Bayan wulakancin da ku ka yi min akan zamanta a asibiti da rashin lekowar waninku dubata sai ace za a zo suna? Ga kayan abincinku nan 'yan uwanta sun muku kara sun gyara. Ka aiko a dauka tunda matar taka bata nuna maka mutumcin mazaunan gidan nan ba balle ka zo da kanka. Sannan kasa a kawo mata 'ya'yanta su dubata." Dammmm...Zara da Alh. Unais da ma Uwani dake tsaye a gefe kowa yaji gabansa ya fadi. Tsoro ya ji kada ta ce ya sakar mata 'ya ya soma bata hakuri. Yana son Zara har yanzu. "Kiyi hakuri zan zo. Amma don Allah ayi sunan saboda Hajiyata." Wato saboda Hajiyarsa. Matar da bata san ciwon tata 'yar ba. "Suna kam babu shi Unaisu. Idan kun zo ma ba za ku sameta a gidan ba" Ta kashe wayar ta ce da Uwani tayi aikinta. "Kinga ya soma warwarewa ne Innayo. Ko in ware duka na sake sabo?" Uwani ta tambaya gudun yin laifi. "Ni da ban taba shiga aji ba ina zan sani? Ke dai kiyi aikinki zan biya." Uwani ta san gatse ne. Yau bata san me ya faru ba amma tsoron bacin ran Innayo take irin wanda bata taba ji ba a baya. Haka nan dai ta duka tayi aikinta gabanta yana faduwar da bata san musabbabinsa ba. Kafin a gama Zara ta kusa suma. Ihu ko surutu irin na mai jin jiyo bata sami zarafin yinsa ba. Tsoron sake batawa mahaifiyarta rai take yi. Wani abu da ya dade bai ziyarci zuciyarta ba. Innayo na ganin yadda take cije lebe da damkar gefen katifa sai ta matsa kusa da gadon. Hannunta kadai ta rike tana girgiza mata kai da rarrashi amma sai taji salama. Ciwon ya ragu sai wani irin abu da take ji game da matar da ta kawota duniya. Hawaye ne ya balle mata bata sharesu ba kuma babu niyar tsayuwarsu. Fuskar nan da ta tashi tana gani a bakin murhu a yau ta maye mata gurbin duk wata allurar kashe ciwo. Bata sani ba ko rashin kula ne amma kamar yau ta fara tantace komai na fuskar Innayo. Idanuwanta sun fada ciki ana gani za a gane wahalar rayuwa ce ta kawosu. Farar fatar da suka gada ta dusashe sosai. Wanda ya san kuruciyarta kadai zai iya bada shaidar ita din fara ce a da. Ga layukan girma don ba a ce tsufa ba sun zane mata fuska. Hannun da ta riketa dashi kuwa ba ka ce na mace bane. Babu kanta kamar da tunda ta daina kaso tamanin cikin ayyukan da take a baya. Amma fatar ayi wani irin tauri kamar na kakkarfan namijin da ya sha aikin hannu. Hannuwa ne da suka raini tare da aurar da mata har guda tara! Mata da masu kudin cikinsu suka juyawa hannun alkhairi baya. Matan da ita Zara take cikinsu! Kawai sai ta fashe da kuka. Ta sake yiwa hannun Innayo wani irin riko tamkar tare da rayuwarta yake tafe. A haka baccin wahala ya dauketa ga gumi ya wanke mata fuska. Uwani ta gama tattara kayanta ta ajiye pain reliever din da Zara za ta sha idan bukatarsa ta taso. Tsakar gida ta fito za ta tafi daidai lokacin da Ummakati ta shigo gidan da sallama. Ita ma tunda Munzali ya yi mata magana akan gyaran zumuntarsu da 'yan uwansu ba karamin dadi taji ba. Baudadden miji gareta sai da kyar da sudin goshi ya barta ta fito barka da yamman nan. Ta tsaya suna gaisawa Asabe ta jiyo muryarta tayo waje. Bata ga dalilin wannan shishshigi da 'ya'yanta suka fara ba cikin kwanakin nan. Fadan da ta taso yiwa Ummakati bai samu ba ta tsaya kallon wasan kwaikwayo a cewarta. Innayo ce tayi saurin fitowa kafin Uwani ta bar gidan. "Nawa ne kudinki?" Sai taji kunyar idanun dake kansu. Ko babu su ita yau tsoron Innayo din ma take. "Ki barshi ba zan karba ba." Innayo ta hade rai sosai ta ce "Idan baki tsaya kin karba ba daga yau in kin zo gidan nan kar ki kuma shigar min daki." Maimuna sai ta tashi da sauri "Subhanallahi. Innayo me ya yi zafi?" "Kar ku saka min baki." Ta kuma kallon Uwani wadda duk ta tsure "nawa ne?" "Dubu shabiyar. Don Allah ki barshi Innayo." Ta ce kamar za tayi kuka. Kowa ita yake kallo kamar basu santa ba. Innayo bata saurareta ba ta kwance gefen zaninta. Dubu takwas ta hado dama ta san bata da shabiyar din. A rashin hankali na Uwani idan ta so kin karba da sai ta yanko kudin kasa sosai. Ita dai Innayo sai ta kalli Hasiya da Maimuna, "Nawa zan samu wurinku?" Hasiya ta so cewa kar ta biya sai dai ta kama bakinta. Dubu uku ta bayar ta bar dari biyu da zasu yi kudin adaidaita sahu ita da Ayaah. Maimuna ta bada dubu biyun da Innayo din ta bata dazu. Samarin 'ya'yanta kamar hadin baki kowa ya ciro dari biyar kudin da aka basu sallama na aikin kafinta da suke koyo. Murja ta dauko jakarta ta mika dubu daya. Ummita dari bakwai gareta a hannu ita ma ta mika. Ummakati ma da bata san silar abin ba ta bayar da dubu biyu. Ayaah ta bada dari ukun da ita kadai ta rage mata. Uwani ta kasa motsi balle magana. Kannenta ne da 'ya'ya su duka amma haka suka hada kudin domin fitar da Innayo kunya. Da taki mika hannu ta karba sai Innayo ta kamo hannun ta dora mata kudin a tsakiya. "Ai na ce miki zan biya ki. Allah ba zai bari naji kunya ba." Ranar farko da Uwani ta ji muguwar kunya kenan a rayuwarta. Abin da ya faru yanzu shi ne asalin kaskanci a gareta. Tafi kowa kudi cikinsu. Amma sun hada sun bata. Bata iya kwakkwaran motsi ba sai da aka fara kiraye kirayen sallar magariba. Sannan ta farga ashe duk sun watse. Babu kowa a tsakar gidan duk suna falon Innayo sai ita kadai. Kwalla taji tana neman zubo mata tayi saurin sharewa ta fita a fusace. Innayo sai ta saki labulen dakinta ta koma ta zauna. Tayi minti goma tana karantar yanayin Uwani. Addua take Allah Yasa shiriyarta ce za ta zo ita ma. Ko kusa bata ji dadi abin da tayi mata ba. Sai dai Uwani tana bukatar sabon karatu game da sanin hakki da darajar mutane ba ma mahaifiyarta ba ita kadai. Kudi sinadari ne amma ko kusa ba shi ne rayuwa ba kamar yadda ta zata. *** "Kwarankwatsa dubu na gaji shika nake bida. Wannan wane irin aure ne? Ki don daga kauye ka auroni?" Tashin hankalinta yafi tsoro akan na uwargidansa. Bai hango wani dalili nan kusa da zai sa ya saki Ummule ba. Balle yanzu ma da take dauke da cikinsa. Zaunar da ita ya yi a gefensa yana bata hakuri ta soma kuka. Zabi biyu ta bashi kuma kowanne mai tsauri ne a gareshi. Salihi ya san cewa ta fi shi gaskiya sai dai kuma ya rasa yadda zai bullowa lamarin balle ya iya fadawa Uwani cewa ya yi mata kishiya watanni biyar da suka gabata. Yana jin kwarewa wurin iya masifa da kaskantar da mutum da Uwani take gwada masa ne suka mayar dashi lusarin namiji. Ba ya iya sakata ba kuma ya iya hanata. Dama kuma shi mutum ne mai yakana da hakuri. Ko kadan baya son hayaniya. Yana da rufin asiri daidai gwargwado, wannan ne ma yasa zaman nasu ya yi karko. Daidai da ashana Uwani bata taba karar saya idan bai bayar da kudin ba. Ita fa a dole ba za ta yi rayuwa irin ta Innayo ba. Miji ba zai kwanta ya mori arzikinta ba. Ita da kyautatawa ta miji da mata sai suka yi hannun riga. Babu wata riba cikin aurensu da zai d'orar banda yaran da suka haifa guda hudu. Su ma yaran bata basu mahimmanci kamar yadda take bawa aikinta. Tsabar son kudi a asibitinsu duk wadda bata son yin aikin dare kudi kawai za ta bata tayi mata. Haka suka tashi babu shakuwa tsakaninsu da ita. Shi kuma Salihi babu kulawa daga matarsa. Watarana anyi jinkirin biyan albashi ya roketa bashi zai biya kudin makarantar yaran. Yana dan yin rance wurinta amma wannan kudin yafi na ko yaushe yawa. Kamar ba za ta bashi ba tana ta kiran babu don kada ya soma saka ido akan abin da take tarawa. Sai da yaran suka yi sati a gida, gashi ta dauki hutun shekara. Rashin sabo da zama dasu sai take jin sun caza mata kai. Hutun da take nema babu. Hayaniya taki karewa. Ba shiri ta ce ta dauki adashi ya zo ya karba. Sunyi akan ana albashi zai biyata sai gashi har an soma zancen jarabawar karshen zangon. Uwani panicked! A zatonta ya yi sama da fadi da kudinta. Ai kuwa ta tayar masa da hankali. Shaf ta manta ya aurar da kannensa biyu mata a wannan tsukin lokacin. Albashin nasa ma bai ishe shi ba sai da ya ci wani bashin. Ita dai kudinta kawai. Takanas ta taka har gidansu. Mahaifiyarsa tayi mamakin zuwanta ta kuma tsorata. Saboda Uwani bata zuwa sai da dalili. Ba kunya ta fada mata halin da suke ciki. "Wallahi idan bai bani a watan nan ba hukuma za ta shiga tsakaninmu. Ni ba irin sakarkarun matan da ake yiwa wayo suyi ta bautawa miji da 'ya'ya a banza bace." Kwantar da kai tayi ta bata hakuri. Ita kuma sai wani jijjiga jiki take kar ta sassauta a fara kira mata ta yafe tunda mijinta ne. "Gobe in sha Allahu za a kawo miki kudinki Uwani. Nawa ne?" "Dubu dari biyu da tamanin da hudu." "Kije gida ba zai gagara ba in Allah Ya so." Babu sallama ta fice abinta. Mahaifiyar Salihi bata tsaya nemansa ba tunda ta san lokacin da ya ranta da dalilin da ya hanashi biya. Ranta dai ya baci sosai. Sarkar zinarenta ta karshe da maigidanta ya bata kafin rasuwarsa ta dauko daga ma'ajiyarta. Kai tsaye gidan Dillaliyar unguwarsu ta nufa. Haka ta bata sarkar jingina ta karbo bashin dubu dari uku. Da Salihi ya zo da yamma ta kulle a leda ta bashi. "Idan Allah Ya hore maka da wuri ka kawo kudin na maidawa Dillaliya." Sunkuyar da kai ya yi cike da kunya da takaicin Uwani. Karshe ma yaji kamar zai zubar da kwalla. A tausashe mahaifiyarsa ta ce, "Kada ka bari zancen nan ya tsaya maka rai. Maganar guda ce. Ba zan saka ka saki matarka ba amma indai ka haifu za ka kara aure. Ka nemo 'yar masu mutumci ka aura (haka kawai 'ya'ya su dinga janyowa ana aibata dattakon iyayensu)." Ya nuna mata ya haifu kuwa. A cikin wata guda ya hada kudin nan ya kai aka karbo mata sarkarta. Tayi ta saka masa albarka kuwa. Bayan wata uku ya ce su tura kauyen 'Yar gaya ya sami mata. Ita da 'yan uwansa basu kyamaci 'yar kauyen da ya kawo ba. Yarinya ce mai saurin shiga rai da faram faram da jama'a. Matsalar farko da suka fuskanta shi ne rashin samun kwarin gwiwar fadawa Uwani zai yi aure har aka yi. Tsoron tashin hankalin da za ta yi masa yake ji. Sai gashi ya buge da rokom Ummule tayi hakuri har ya sami damar fada. Gida ya kama mata a wata sabuwar unguwa. Daga office yake biyawa amma bai taba kwana ba. Haka take ta hakuri. Aurensu na da wata biyu barayi suka haura mata cikin dare. Tsananin firgita da tayi yasa ta suma. Sun kwashe kayan kallo da kudi amma basu tabata ba. Koda ya iso gidan bayan anyi masa waya daga makota tana da zubar jini. Ashe ciki gareta basu sani ba har ya zube. Musabbabin rigimarsu ta yanzu kenan. Ta roki ya raba musu kwana a kalla barayin da aka san 'yan unguwa ne zasu ga namiji na kwana. Idan ba zai iya ba kuma za ta koma gidansu. Da kyar ya lallabata da alkawarin zai fadawa Uwani yau ya tafi. Yana fita Ummule ta zari mayafi tabi bayansa a adaidaita sahu. Ba za ta yarda ta zauna tana cutuwa ba. 'Yancinsu ita da dan cikinta take neman karewa. * Samari ne su hudu cikin wani tafkeken daki wanda ya wadata da kayan alatu. Daki ne wanda uku daga cikinsu suke haya a ciki a matsayinsu na daliban jami'ar Bayero. Uku a cikinsi babu wanda zai kai shekara ashirin da biyar. Tun daga suturarsu da ta juyawa mutumci baya har zuwa wayoyin hannuwansu za ka san 'ya'yan masu hannu da shuni ne. Kawunansu babu kyawun gani kuma wai nan duk a cikin gayu ne. Cikon na hudun nasu dan saurayi ne wanda da alama sun girme shi. Shi riga da wando na yadi ne a jikinsa. Ko kadan babu alamun shashanci tare dashi sai damuwa shimfide a fuskarsa. Daya daga cikin samarin ne ya tsaya a gabansa yana magana yana jejjefa hannuwa kamar mai rapping. Wandonsa ya kusa gwiwa sai na cikin da ya bayyana cikin wani salon wulakanta kai mai suna ass-down. "Oh boy ya ka ke mana yawa ne? Nifa gaskiya bana son eh-yane, ai ka gane. Kawai idan maiko ba zai samu ba ka ware. Clique (kungiyar abokai) dinmu ba na yawa-boys bane." Tashin hankali ne ya kara bayyana a fuskar yaron da yaji sauran suna cewa ya tafi. Ya matsantawa kansa son yin abota dasu saboda duk makarantar babu masu tashe irinsu. Kowa ya sansu kuma yana shakkarsu. A gidansu shi da 'yan uwansa tamkar babu wanzuwarsu. Mahaifiyarsu neman kudi tasa a gaba. Babansu bashi da katabus sai tsoronta. Gashi bata nuna musu shiga dangi ba. Basu saba da kowa ba balle su ji dadin mu'amala da makusantansu. Yara kala kala ne. Akwai masu son ayi feeling presence dinsu idan suna waje. Suna son a yaba musu ko ayi musu fada. Su dai ka nuna ka san dasu kuma suna da mahimmanci a wurinka. Idan suka kasa samu a gida sai su fita. Irin haka ce ta faru da Mubasshir Salihi. Rayuwar gidansu babu dadi. Daga karatu sai karatu. Tun suna yara idan suka fara wasa Uwani ke hanawa tayi ta fada har suka daina yi da junansu. Yanzu shiga dari fita dari sai dai ka samesu kowanne rike da waya kamar ibada. "Nawa zan kawo to?" Ya tambayi mai yi masa magana. "Contribution ne kawai na daidai kudin gidansu mutum.." sauran suka kwashe da dariya "kada dai ka kawo kasa da 50k domin zamu tafi da babes. Ka san mata da son ayi musu barin kudi." "Shike nan, zan kawo." Fita ya yi da rawar jiki kada a fasa zuwa yawan bude idon da suka shirya zuwa Tiga dam dashi. Yana fita suka kwashe da dariya suna tafawa. Mubasshir ba ajinsu bane. Za dai su tatse shi da kyau su yar ne kawai. Babur dinsa ya hau wanda da kyar da sudin goshi Uwani ta saya masa. Shi ne danta na fari. Yana level one. Ya san yau aikin kwana gareta. Kannensa mata duka ukun suna makarantar kwana. Da mukullinsa ya bude gidan. Kofar dakinta a kulle da mukulli. Guntun tsaki ya yi ya dauko spare wanda abokan nasa suka sa ya yanka. Ashe ga ranarsu nan. Hankalinsa a kwance ya dinga sauke mata akwatuna yana bincike saboda bai sa ran dawowarta yau ba. Babansu ma kwanakin nan idan tana da aikin dare baya dawowa da wuri. Wani envelop ya samu a can kasan wardrobe dinta ya dauko ya zazzage akan gado. Bai san ko nawa bane don yawan bandiran da ya gani. Ga kuma kananun box din sarkar gwal guda uku. Dariyar shakiyanci ya yi da ya kwatanta bawa duk yarinyar da za a hada shi da ita a Tiga da ita matsayin kyauta. Ya san sai ya doke ragowar abokan nasu wurin samun fada da kulawa. Mubasshir yana dakin Uwani yana barna ta iso gida. Tana gyara parking Salihi ya iso. Jira yake ta gyara motar shi ma ya ajiye tasa sai ga adaidaita sahu ya tsaya a jikin katangarsu. Ummule ce ta fito ta nufi motarsa tana cewa ya bata dari uku ta biya mai adaidaita sahu. Uwani da ta dawo gida da bakincikin abin da ya faru a gidan Innayo sai ta tsaya tana kallon ikon Allah. Yarinyar da ta fito daga adaidaita sahu murmushi take yi. Salihi kuwa a firgice yake! UWA UWACE...21 Batul Mamman💖 Assalam alaikum wa rahmatullah wa barakatuhu. Da farko ina godiya gareku masu kira da turo sako ta sms da whatsapp, wattpad da facebook. Nagode da shiruna bai sa kun manta dani ba. Allah Ya sakawa kowa da alkhairi. Na so sai na kammala labarin nan gabadaya zan sake post amma yawan tambaya da kuma rashin sanin me ya boyeni yasa ni fito da iya abin da ya samu. Duk da haka ina mai baku hakuri domin daga wadannan shafukan zamu sake wani zangon kafin cigaba. Addu'arku nake roko don Allah. Akwai abu da ya tunkaroni, ina rokon Allah sa'a da salama a cikinsa. Allah Yasa a dace. Allah Ya biyawa kowa bukatunsu na alkhairi. Ina muku SonSo. *** A zuciye Uwani ta isa gabansu tana muzurai. Kafadar Ummule ta riko ta yadda dole sai da tasa ta juyo suka fuskanci juna. Bata cire hannun ba ta nunata da dayan. "Ke bariki ma fa iyawa ce. Naga kuma kamar baki iya ba tunda kin yi shuka a idon makwarwa. Idan sadaka ko taimako ki ke nema me ya hanaki tambayata ina mace 'yar uwarki? Ai mu biyu ne a wurin. Don tsabar is.. sai ki bi namiji?" Dama Ummule tana fita daga adaidaita sahun ta gane Uwani. Akwai hotunanta a wayar Salihi. Kafadarta ta gotar hannun Uwani ya koma lilo. "Akan me zan nemi taimakonki bayan ga mijina..." Uwani ta kan ji ana cewa kunne ya toshe na 'yan dakiku sakamakon jin zance mara dadi. Ashe gaske ne. Daina ji ko gane komai tayi na wani lokaci sai kalmar miji dake neman mazauni a cikin kwanyarta. Karfin hali Salihi ya yi ya ce "Uwani. Ummule. Ku shiga ciki muyi magana bai dace ana jin muryoyinku a waje ba." A haukace Uwani ta isa bakin karamin gate din nasu wanda mota bata shiga, shi yasa suke ajiye motocinsu a waje. Tare shi tayi da hannuwanta biyu ta soma masifa ido rufe. "In ta shiga Allah Ya ..." "Kar ki karasa tsinuwar nan. Gida dai nawa ne kuma ku duka matana ne" cewar Salihi yayinda ya matso zai cire hannuwan da tasa ta tare hanya. Duhu ya mamaye unguwar sai hasken kwayayen fitilu. Su ukun duka babu wanda ya yi sallar magariba saboda ta riskesu a titi. Ga isha an soma kira. Baya son makotansu masu zuwa masallaci wani ya ga abin da yake faruwa a kofar gidansa. Kallon baka da hankali Uwani tayi masa kafin ta iya hada labbanta ta ce, "Su waye matan naka? Aure kayi da gaske ban sani ba?" "Na ce miki mu shiga ciki ko" ya ce yana dan daga murya. Mubasshir na cikin tura kudi a aljihunsa yaji muryoyin iyayensa kamar suna fada. Da sauri sauri ya tattara komai ya mayar inda yake. Aljihunsa kam bandiran dubu dai-dai guda uku ya tura. Ga sarkar da ya dauka daya. Ya kuma rufe mata daki kamar ba a shiga ba ya fito. "Wallahi kayi kadan Salihi. Amanata ka ci? To ka je ka tambayi malamai wannan auren bai dauro ba tunda ban sani ba balle na amince." "Ki ce kawai idan ki ka tsine masa za ta kama shi." Cewar Ummule, haushin lallabawar da Salihi yake mata a wannan yanayin da suke cik na kara kamata. "Kar ki yi min rashin kunya! Bani da kyau wallahi" Uwani ta ce a harzuke kamar za ta kai mata duka. Akan ce idan babba ya yada girmansa sai yaro ya taka ya hau. Ummule ba mai takalar rigima bace amma bata ga dalilin ragawa haukan da Uwani take musu ba. "Daidai nake dake. Gidan mijina ne saboda haka a matsa min na shiga." "Wanda ya auroki ma bai isa ya shiga ba." Shi dai hankalinsa ya gama tashi saboda bai iya hayaniya ba. Da kyar ya cire hannunta ya janyeta suka shigo tare da Ummule. Ita haushi da tausayi ya bata. Yadda yake bin Uwanin a hankali har ta soma tara musu mutane ya kular da ita. Banda tana gudun bacin ransa da tuni ta hankadeta kowa ya huta. Suna shiga suka ci karo da Mubasshir wanda rashin gaskiya ya fito a fuskarsa baro baro. Amma da yake suna tare da damuwa su duka babu wanda ya kula. Muryar Uwani a sama tana ta zazzaga masifa ba ji ba gani. "Kaga Salihi ka sallami yarinyar nan kafin na illata ta." "Mu illata juna dai" cewar Ummule tana jijjiga kafa. "Kaji ko? A gabanka take yi min rashin kunya." Ihu ne kawai bai yi ba amma kansa ya dauki chaji sosai. "Uwani ki saurareni kiji." "Anki a saurareka din..." Mubasahir sai yaji wani iri. Mahaifinsa take yiwa magana haka a gabansa. "Mama don Allah kiyi shiru..." Dama a wuya take sai kawai ta janyo shi ta kai masa duka a gefen fuska ko ta huce. Ransa kuwa ya baci . Ta kara yiwa kanta bakin fenti a idonsa. "Munafukai daga kai har uban naka. Saboda baka damu dani ba ko a jikinka an kawo 'yar shila da sunan kishiyata." Bata tsaya kallon fuskar dan nata da miji ba bayan ta kira su munafukai ta harari Ummule. "Idan ma dadiro kuke yi ya miki ciki a waje ake son kawo min cikin gida ne to kunyi karya." Dama kallo daya ta fahimci Ummule tana da ciki. Sai da ta gaji da masifar don kanta ta nufi dakinta ta soma dauko akwatuna tana budewa. Saboda gudun bacin rana da cin amana irin ta da namiji take ta tanadi. Gininta a Zawaciki filasta kadai ya rage da fenti. An kawata gidan sosai ya dace da zamani ta kowace fuska. Gida ne dan madaidaici wanda ta kudurta niyar komawa idan bai yi musu gyara a nasu na yanzu ba. To ashe mai gabadaya ya tasarma yi. Ajiyayyun kudadenta za ta dauko ta bayar a gama komai cikin watan da ake ciki. Tana ganin idan ta tashi daga shi har kurar da ta kwaso matarsa za tafi karfinsu. Akwatin da kudaden suke ta durkusa ta bude kudi suka ce daukarmu inda kika ajiye mu! *** Bayan tafiyar Uwani da aka idar da sallar Magariba wasu makotansu Innayo suka shigo. Zama na mutumci ne tsakaninsu shi yasa suka shigo tambayar ayyukan da take so su tayata na sunan gobe. Kafin ma ta fada musu babu taro suka fahimci halin da Zara take ciki. Sun tausaya mata sosai kuwa. Da yake Innayo ba mai yawan magana bace bata taba zaman sukar 'ya'yan nata ba. Sai dai wanda ya gani da idonsa ya fahimci irin zaman da suke yi. 'Yar hira suka taba yayinda su Hasiya suka gama kimtsa komai suna shirin tafiya. Innayo ta fito raka bakinta kenan adaidaita sahun da ya dauko 'yan sakon gidan Salima ya tsaya a kofar gidan. Ihsan da kuka ta fito ta fada jikinta. Gabanta ya yi mummunan faduwa. Dago Ihsan din tayi daga jikinta hankali a tashe. "Ina Salima? Me ya kawo ki da magaribar nan? Kukan me kike yi?" Ihsan ta kasa magana sai shesshekar kuka. A tsorace take ko mutuwar gaske mahaifiyarta tayi. Daya daga cikin 'yan rakiyar ne ya yi mata bayani. Kuka ne ya kwace mata, nan da nan idanunta suka dinga zubar da kwalla. Bata ga ranar hutu akan lamuran 'ya'yanta ba. Kuma tana tsammanin wannan ranar ba za ta taba zuwa ba. Daga ranar da mace ta fara amsa sunan uwa to har abada sunanta kenan. Da damuwar Zara ta wuni, bakincikin Uwani ga kuma tararrabin halin da Salima take ciki ya risketa a farkon dare. A yadda ta fito rakiyar nan haka ta kutsa kai cikin adaidaita sahun da ya kawosu ko cikin gidan bata koma ba. Silifas ne a kafafunta sai hijabin da tayi sallah wanda da shi makotan suka risketa. Hannun Ihsan kawai ta rike tana karanto addu'a a zuci suka koma cikin adaidaitan. Su Hasiya sai ganin wadanda Innayo ta fita rakawa sun dawo su kadai suka yi. Kusan a tare suke rige rigen fada musu abin da suka ji da gani. Maimuna har ta soma kuka Hasiya ta tabata. Sai da matan suka fita ta sanar da ita yadda suka yi dazu. "Duk da haka Hasiya idan kuma na gaske ne fa. Ni dai ki zo muje." * "Ban gane wannan sabon shishigi da ku ka soma yiwa matar nan ba ke da Munzali." Ummakati shiru tayi ta dafe kanta da hannu daya kamar mai ciwon kai tana sauraren Asabe. Tun shigowarta dakin take ta yi mata fadan zuwan da tayi da magariba kamar dole. Sannan ana karo karon kudi ita ma ta dauka ta bayar ko shawara da ita bata yi ba. "Tunda kin bawa banza ajiyata ai gara ki tashi ki tafi" Asabe ta furta cikin fushi. Bata ga dalilin wannan binbini da Innayo ta fara yiwa yaranta ba. Ta dade da sanin darajar daukar ciki da haihuwa take ci a wurin Munzali amma bata gabansa. Ummakatin da take mace kuma cikin rufin asiri ita kuma bakar rowa gareta a nata tunanin. Amma don neman suna ta dauki kudi ta bawa Innayo. Gatse ne ko shagube, kalaman ba suyiwa Ummakati dadi ba. Tayi bayanin har ta gaji amma Asabe taki yarda. Surukarta ta ninka Asabe a komai ma. Ga rigima ga fitina. Dan nata ma tsoronta yake ji. Kuma a haka kiris take jira ta saka shi sakin Ummakatin saboda wai gidan da ta fito bai yi mata ba. Daga Alh. Rabi'u har Asabe babu mai daraja a idonta. "Ki yi hakuri." Tsaki Asabe ta ja tana mai cigaba da sakin maganganu. "Bani abin da kika kawo min ki tashi ki tafi kafin babanku ya san kin zo don cewa zai yi sai mun raba. Ko yana ina lokacin da nake fadi tashin gina ku ban sani ba." "Hmmm" Ummakati ta furta a hankali hannunta a jikin zip din jakarta. Dubu biyar din da ta lalube aljihun mijinta ta dauko ta mika mata. Idan bata bayar ba ta san watan kwasar bakincikinta ne zai tsaya. Har gida za ta dinga zuwa tana zubar da mutumci a gaban jikoki da babansu. Ba za ta yarda cewa Asabe ta manta da yadda suka tashi babu kulawarta ba. Banda tsarewa ta Allah da ta dade da shiga duniya kamar kawarta da suka yi 'yammatanci tare. A hanyarta ta fita ne ta tsaya yiwa su Innayo sallama. Nan ta ji abin da ke faruwa a bakin Maimuna. Ta ce su taso su tafi tare. Ayaah kawai aka bari a dakin ta kula da Zara da jinjirarta. Asabe da ta san ba sauraronta Ummakati za ta yi ba ko ta ce kada ta kaisu sai cewa tayi, "Yau dai ranar ta Innayo ce. Ana ta ganin bacin rai akan 'ya'yan da ake cika mana baki a kansu. An gama gulmata akan tarbiyar 'ya'ya sai gashi sune da arzikin da ake ci. Munzali ya sakar muku bakin aljihu yanzu gashi motar Ummakati za ku shiga. Duk wani asiri kuma da surkullen mutum zai yi ya gama ne. Kurkuwarmu kurrrr....." ta bisu har soro tana fada. Dama can ba ayi musu tarbiyar mayar mata da magana ba ballantana kuma yanzu da 'yarta take wajen. Hasiya da Maimuna sai suka kama bakunansu. Murja da Ummi su ma basu tanka ba. Yaran Maimuna kuwa basa wurin. Su aka tura shigo da adaidaita sahu kafin shigar Ummakati dakin. A zaune suka sami Salima da suka isa gidan. Fuskarta a kumbure ta sha kuka. Mata kuwa harda wasu mazan sun cika 'yar tsakar gidan babu masaka tsinke. Kowa bayanin abin da ya sani yake yiwa Innayo. "Mama ku ma kun yi sakaci tunda abu ne na shekara da shekaru. Ba don tana da tsahon rai ba ma da tuni labari ya dade da shan bamban." Matar da tayi maganar Innayo ta duba ta jinjina kai. Tabbas da laifinta. Duk da Salima bata fada ba amma ta jima tana hasashen hakan saboda irin ciwukan da take gani a jikinta. Karairayin Saliman na kare Ale Gambo dai ta zabi karba don ta kwantarwa da kanta hankali. Damuwar 'ya'yan sai tayi mata yawa idan kowacce cikinsu bata da sukuni. "Ina Gambon yake?" Nan da nan aka shigo dashi a daddaure kamar huhun goro. Bata kula cewa ta wuto shi a waje ba inda samarin layin suka yi cincirindo. Motar 'yan sanda suke jira azo a tafi dashi. Yana ganin Innayo da Salima a zaune ya fara kici-kicin son a kwance shi. "Dama na fada! Sharri suke son kulla min ita da 'yan uwanta. Banda haka ai ba yau na fara dukanta ba amma suna tafiya ta zube min a kasa bayan ko rabin dukan da na saba ban mata ba?" "La ilaha Illallahu..." Mata suka hau sallallami don ga dukkan alamu bai san asirinsa yake tonawa ba. "Kin ji yana fada da bakinsa ko Innayo? Wallahi na gama zama da shi ko kotu zamu shiga sai dai aje" Cewar Salima cike da kwarin gwiwa ganin kowa ita yake karewa. Don masifa Ale Gambo ji yayi kamar ya kwance daurin yaje ya mareta. Shi fa a tunaninsa bata isa ta taba ketare zancensa ba balle ta kaisu ga sa'insa. "Ki bar ganin idanun mutane wallahi sai na tattakaki na taka banza idan suka tafi. Ni dake aure yanzu aka fara." Hasiya da Maimuna harma da Ummakati sun so mayar masa da martani amma fafur Innayo ta hanasu magana. Yaran kawai ta cewa su shiga daki su dauko kayan sawarsu. Washe gari sai a dawo a kwashe kayan gidan. Hankalin Ale Gambo sai lokacin ya tashi da yaga sun fara fita. Mutane irinsa masu mulkin mallaka ga wadanda suka fi karfi basu fiye son a gudu a barsu ba. Duk wannan power din da yake takama da ita dama na samun wuri ne a jikin Salima. Yau da tayi bore sai yake jin yafi kowa kaskanci. Kiran sunanta ya dinga yi da karfi da kalaman tsoratarwa akan irin hukuncin da zaiyi mata idan ta dawo. Babu wanda ya waiwaye shi har 'ya'yansa. Innayo ce kadai ta dakata sai da iyalinta suka fice sannan ta dawo inda yake tsaye an daure masa hannuwa ta wanka masa wani irin gigitaccen mari. Kamar an dauke wuta haka mazan da suka yi saura a wajen suka dauke numfashi. Shi kuwa hantar cikinsa sai da ta kada domin bai taba zaton za ta iya yi masa wani abu sama da mugun kallo ba. "Idan takamarka wanda ya baka aurenta bai san darajarta ba shi yasa kaima kake takawa to kayi karya. Muddin ina numfashi da yardar Allah ka gama taba lafiyar Salima. Shari'a kuma akan hakkinta da ka dade kana dauka ko zamu shekara anayi in Allah Ya so ba za mu karaya ba." Juyawa tayi ta fita ran ta yana kuna. A bakin kofa suka yi kicibis da 'yan sandan da aka kira. Haka suka bi bayansu domin sun ce dole Salima taje ta bada statement kafin su daure shi. * Daki guda Abbati ya zage da kansa yana gyarawa Baaba Mari. Gidansa kato ne. Akwai rashin adalci idan aka ce matar gidan kullum sai ta bi dakuna da bandaki ta gyara. Shi yasa ya sa rai da ganin kura kadai ta rashin amfani. Shi ma kuma ko don kada kaya su lalace a kalla ko sau daya a sati ne ya kamata ace an share. Sai ya sha mugun mamaki. Datti dakal-dakal ya tarar da kura harda yana. Basu fiye bakin kwana ba saboda kishinta duk da masu zuwan duka 'yan uwansu ne. Bandakin kuwa harda kwari suna yawo wasu kuma sun mutu. Bawan Allah bai hango laifin kowa ba sai nasa. Da bai salwantar da rayuwarsa wurin yawo ba kila da yafi kula da lamuran gidansa. Yanzu kuwa ko sannu bai samu ba daga Hanne tayi hayewarta sama. 'Yashshafa ma duk shirmenta sai da taga rashin dacewar haka. Dukkaninsu sun gaji musamman Hannen da tayi jeka ka dawo a rana daya. To amma har ace ta manta mijinta a ranar aka sallamo shi daga asibiti? Akalla ko da ba yi za ta yi ba ai ta nuna masa cewa tana da hankali ta hanyar cewa ya bata tsintsiyar ta share. A yadda ta fahimti Abbati ta san da kansa zai ce taje ta huta. Jinjina kai tayi ta tashi daga kan doguwar kujerar da ta dan kwanta tabi bayansa bayan ya wuce da tsumman goge-goge. "Ina zaki kuma?" Deluwa ta tambayeta da sauri. "Karbar gyaran dakin zan yi." "Dawo ki zauna ai ba sanin darajarki ya yi ba. Na gano miki miji dan gidan arziki ba taka haye irin na wasu ba." Ta furta tana kai dubanta ga Baaba Mari wadda maganar ta yiwa dirar mikiya. Ko a farcenta don Deluwa ta hana 'yarta taya Abbati gyaran daki. Abin da ya tsaya mata bai wuce kiransa wanda ya yiwa arziki taka haye ba. Kenan ba ita kadai sauri da habbakar arzikinsa yake yiwa kai kawo a kirji ba? Kamar Deluwa taji tunaninta ta bata amsa tana faman tabe baki. "Kar fa kiji haushin maganata Mari kin san ba karya nayi ba. Almajiri da tamfatsetsen gida irin wannan akwai ayar tambaya. Anata cewa yana kasuwanci gashi har rana irin ta yau bamu taba ganin samfurin hajar tasu ba." Baaba Mari bata iya cewa uffan ba har Habi ta shigo daga bangaren Munzali inda aka yi musu masauki. Daki ya basu a cewarsa bai yarda su dawo tare a barshi a nasa gidan shi kadai ba. Iya Kande ba zama take sosai ba indai Qibdiyya bata nan. Habi ce ta karbi gyaran dakin a wurin Abbati shi kuma ya hau sama. Deluwa ma da 'Yashshafa suka shige dakin da aka basu suna jiran kuku ya gama girki. Tunani, damuwa da zancen zuci aka bar Baaba Mari tana yi akan tarin dukiyar Abbati. Kasantuwarsa dan fari ba shi ne ya sanya soyayyarsa tafi ta 'yan uwansa a zuciyarta ba. Saukin kansa wanda mutane musamman na gidan suke amfani dashi wurin cusguna masa tun kuruciya ne. Tunda aka gane lagonsa ake saka shi kuka. Tun tana kawaici har ta koma musayar yawo da duk wanda zai taba shi saboda bashi da baki. Wannan saukin kan yasa ta guji ya tafi almajiranci. In an barta ma za ta ce wannan halin zai janyo masa wahalar rayuwa fiye da a gabanta. Sai gashi abin mamaki maimakon ci baya sai ya yi gaba. A gaban ma ya yiwa da yawa fintinkau. Wata irin zabura tayi ta mike lokacin da taji takunsa yana saukowa daga sama. Haka ta kura masa idanu tana kallonsa cike da firgici. Tsoron yarda da hasashenta take yi. A cikin zuciyarta take addu'a kamar haka. "Ya Allah Kasa ba sata ko fashi yaron nan yake yi ba." UWA UWACE...22 Batul Mamman💖 *** Su uku ne zaune a dakin Alh. Rabi'u. Shi, Innayo da Asabe. Tray din abinci ne a gabansa yana ta kwasar girki yana gumi. Hannun malum-malum dinsa yasa ya goge shi bayan gama ya janyo tsintsiyar kwakwa a gefen gadonsa. Dan tsinke ya karyo ya danna a baki yana sakato naman da ya makale yana tofarwa. Magana ya kirasu suyi wadda gabadaya akan 'ya'yan Innayo ne. Shi yasa taji haushin kiran Asabe da ya yi dakin nasa. Ta san ya yi ne domin neman fada a wurin Munzali tunda dan Asabe ne. Duk tsiya idan ya kyautata mata ta hanyar nuna mata gazawar Innayo za ta yiwa Munzali magana akan bukatunsa. Ya kula yanzu bakin gwargwado Munzali yana dan yi mata magana da tattausan lafazi. Hirar arzikin Munzalin ya dauko suke ta yi da Asabe har sai da Innayo ta magantu. "Zan koma idan kun gama tadin ayi min magana." Mikewa tayi abinta za ta fita Alh. Rabi'u ya dubeta fuska a hade kamar ba shi ya gama yiwa Asabe dariya ba. "Bakin halin da ki ka koyawa 'ya'yanki za ki gwada min?" Dadi ya kama Asabe ta karbe zancen don ta kara zuga shi. "Ka dai bi a sannu kar ka manta da bakinka ka fada min Ale Gambo ya ce ta mare shi." Kamar an kunno shi kuwa ya hau masifa yana fadawa Innayo maganganu. "Banda lalacewa ace har kin iya dora hannuwanki a fuskar baligi kamar Ale Gambo kamar baki san haramcin yin hakan ba?" Saboda yadda take jin ta muzanta sai take gani kamar tsirara ya yi mata a gaban matarsa. Jikinta ya yi sanyi kalau yayinda zuciyarta take tafarfasa. Haka nan idanunta suka rine da bacin rai mara misaltuwa. "Yanzu Alhaji me ya kawo magana irin wannan? Gambo tamkar dan cikina fa yake tunda ya auri Salima." "Tamkar 'yar cikinki dai...ke da baki san ma'anar haihuwar namiji ba ina ke ina kwatanta dan wata da naki?" Asabe ce tayi maganar dankwalinta a gaba tana neman takalar fada. Haushin yadda su Munzali ke bin Innayo take son fanshewa. "Fada mata dai. 'Ya'yan da ta cusawa kiyayyata basa ganin girmana. Gashi tun ba aje ko ina ba an fara dawo min gida." Asabe ta murmusa cike da jindadi. "A'a fa Alhaji. Kar kayi butulci. Nima shaida ce ana kawo maka dari da kwabo idan Hasiya mai lalle tayi ciniki. Su kankamoji (Zara da Uwani) dai ko ita sha-wuyar basa bawa." Dariya suka kwashe da ita wadda tayi sanadiyar zubowar hawayen da Innayo take ta kokarin dannewa. Habar zaninta ta saka ta goge idanunta amma haka wani hawayen ya maye gurbinsa. Dan kuka mai ja wa mahaifiyarsa jifa. A haka ta fita tana jiyo sautin dariyarsu. Bata karasa dakinta ba ta juyo a fusace ta koma dakin Alh. Rabi'u. Tuni ta fahimci cewa sadaukarwa da hakuri daban suke da kawar da kai. Ta sadaukar da kuruciya, lafiya da jindadinta a bautar aure da kula da yara. Tayi hakuri da rashin kyautatawar miji da wasu cikin 'ya'yanta. Duka wadannan akwai riba a duniya da lahira. Amma kawar da kai akan abubuwa na bacin rai kam cutarwa ne gareta dasu wadanda take kyalewa. Anyi abin da aka yi a baya. Yanzu kuwa daidai take da kowa. Bata da nufin cutar da kowa, sai dai ba za ta yarda tayi ta hadiyar bakincikin kowa ba. Bankada labulen tayi ta shiga ta zauna a gaban Alh. Rabi'u. Hannayensa duka biyu ta kamo ta shimfida tafukan akan fuskarta. Asabe mamaki ne ya kamata na zuci da zahiri. Shi kuwa sai ya sami kansa da shiga taitayinsa ya kasa yi mata magana. Cikin muryar lumana babu wani hargagi kamar yadda ta yiwa su Zara ta soma magana. "Kaji dumin hawayena?" Ya gyada kai kamar sakarai. "Bai kama kafar zafin zuciyata da barazanar bugawar da take a kirjina ba. Alhaji...." "Na'am" ya amsa da rawar baki. "Allah zai bi min hakkin hawayen da na zubar maka ba da hakki ba." Ta tashi ta juya za ta fita sai ta tsaya ta kara da cewa " 'ya'ya amana ne kuma daidai iyawata nayi kokarin sauke wannan amanar. Ba komai da nayi bane zai zama daidai amma nayi imanin Allah zai sakawa kokarina. Zai shirya min 'ya'yana. Zai daidaita min lamurana." Da ta koma dakinta duka 'ya'yanta suna nan harda Uwani da ta shigo bayan fitarta. Kare musu kallo tayi daya bayan daya tana tuna ranar da ta haifi kowacce. Uwar dakin ta shiga ta barsu ba tare da ta amsa maganganun da suke yi mata ba. Hannu na rawa ta tura kofar ta rufe da sauri sannan ta zube a kasa saboda zafin kirji. Miji babu dadi, kishiya ba zaman lafiya, 'ya'yanta kuma kowacce da tata matsalar. Matsalolin nasu da suka zame mata abin tunani da shiga damuwa. Kwana biyar kenan da ta dauko Salima. Ga Zara har yau mijinta bai zo ba. Maimuna nata mijin ya ce ya gaji da yawan zarya da take yi zuwa gidan iyayenta, ga talaucinsa da yafi na Ale Gambo. Uwani tun washegarin zuwan Ummule ta fada mata anyi mata kishiya. Gabadaya ta sauya tana neman susucewa. Sai dai taki fada mata ba zuwan kishiyar bane kadai damuwarta ba. Kudin da take yawan cewa babu ta nema ta rasa. Ta kuma kasa cigiya a gida saboda babu wanda ya san dasu. Hasiya kuma nauyi ya mata yawa. Bata morar kudin sana'arta ko kadan yanzu. Duk ta rame saboda wahala da rashin isasshen bacci. Sannan rashin haihuwarta yana matukar damunta. Ita ce uwa garesu. Bata hango ranar hutun jiki da na zuciya ba kila sai ta bar duniyar. Alh. Rabi'u da Asabe kuwa har Innayo ta ware a dakinta basu dawo daidai ba. Maganarta takaitacciya ce amma ta zauna saram a kwakwalensu. *** "Kace masa Habu ne." Masinjan ya bishi da wani irin kallon kwaf kafin ya ce "Habun ai da yawa. Baka da inkiya ko cikakken suna?" Honorable ya yi dan murmushi don fushi ba nasa bane. Satinsa guda yana zuwa ma'aikatar wurin shugabansu Alh. Bala ana jirga shi. Ba kuma zuwan kansa bane. Mutumin ya kasance abokinsa lokacin da yake da abin hannu. Tunda ya sami karayar arziki bai taba bibiyar tsofaffin abokan huldarsa neman taimako ba. Wulakanci ne baya so. Yanzu ma dole ce ta kawo shi. Ya boyewa duka iyalinsa ne musamman Hasiya amma likitan da yake duba Abbas a asibitin kwakwalwa na Dawanau ya tabbatar masa da cewa idan ba ayi masa aiki cikin kankanin lokaci ba da wuya ya warke ko anyi. Jijiyoyin da suka sami matsala sun fara gajiya a yanayin da suke ciki. A wannan yanayin ne ya hadu da tsohon abokin nasa a wajen daurin aure. Bai yi kasa a gwiwa ba ya nemi taimako kuma ya yi sa a ya amsa masa. Fatan samun warakar Abbas din shi ne albishir din da yake ta boyewa Hasiya. Sai gashi har yau ko ciki bai sami shiga ba. Kullum da abin da ake fada masa. Yau ne ma ya yi sa'ar haduwa da masinjan Alh. Bala din shi ne har aka tambayi sunansa. "Habu Danmalam za ka ce masa. " Masinjan ya sake kura masa ido kamar me neman wani abu. Cikin 'yan dakiku ya sanya hannu ya bugi kansa da takaicin rashin gane shi da wuri. Sakin fuska ya yi sosai ga mamakin yanayin da ya ganshi. "Habu Danmalam dai da na sani?" "Ni ne" ya amsa da murmushi. "Ikon Allah. Ai wallahi da na san kaine da tun zuwan farko nayi cuku-cukun hada ka da Yallabai" Hannu ya mika masa suka gaisa ya ce " Amma ina zuwa. Bari naje na fada masa idan Minista ya tafi sai ka shiga." Wani karamin ma'aikaci a wurin yana jin furucin masinjan ya janyo shi gefe. "Yallabai fa ya ce kada a bar kowa ya shiga yau. Idan Ministan ya tafi shi ma tashi zai yi." Honorable Habu yana jinsu ya ja gefe da nauyin zuciya. Gwargwadon iyawarsa bai yi amfani da mukamansa na baya ya wulakanta kowa ba. Amma duk da haka yanzu idanunsa sun kara budewa da bambancin masu mukami da talakawa. Mafi yawan masu kawo korafi basu da yadda zasu yi ne. In an barsu ba za sy zabi kaskantar da kai suna roko ba. Amma sai su keta billensu suyi rokon bayan an hanasu a kara da wulakanci. Masinjan ya amsawa mutumin da cewa "Honorable Habu Danmalam ne fa." "Kai ka san shi" cewar wancan irin 'yan rijiya ta bayar guga ta hana dinnan. "Ni kuwa na san shi. Kuma Yallabai ma ya san shi domin tare suka yi siyasa." Bai kara saurarar mutumin ba ya wuce cikin ofishin Alh. Bala. Ya san suna tare da Ministan (Land, Housing and Urban Development) sai dai kuma idan har bai sanar dashi bakon nasa ba karshenta ya fice ta baya idan sun gama tattaunawa. Sallama ya yi ya sake gaishe da Ministan kamar ba shi ya yi masa rakiya har nan din ba. "Yallabai dama na ce bari na leko ko kuna bukatar wani abu." "Idan ina bukata ma ai ka san Surayya (sakatariyarsa) tana nan." Masinja ya gyada kai "Eh haka ne kuma. To ku tashi lafiya." Juyawa ya yi kamar zai tafi sai kuma ya dawo "af...Yallabai kar na manta kana da bako fa." Alh. Bala ya kirne fuska saboda wannan shishigi zai iya sawa ya rasa alkhairin da Ministan ya zo dashi. Hannuwansa ya dora akan teburin gabansa yana maganar da babu kofar ja'inja cikinta. "Ba zan ga kowa ba idan mun gama tafiya zan yi. Ko waye ka ce ya dawo gobe." Ya san za a rina shi yasa ya ce "babu komai. Yau da gobe duk daya ne. Don ya kara kwana daya akan ragowar kwanakin da ya yi yana zuwa babu matsala." Wani mugun kallo Alh. Bala ya jefa masa kafin ya kai ga ambaton sunan bakon a dole ya fita. Addu'a yake shi kadai yana fatan bai yiwa kansa sanadin aiki ba. Sai bayan fitar Masinjan Minista ya ajiye karamin kyakkyawan kofin shayin da yake rike dashi tun shigowarsa. Yadda ya buga kofin ya tayar da hankalin Alh. Bala domin alama ce ta bacin rai. "Kayi hakuri Ranka ya dade. Na san ka ma fini haduwa da 'yan maula masu hana mutane hutawa. Mutumin da ya zo din na san ba kowa bane illa wani tsohon dan siyasa da muka zauna jam'iyya guda a baya. Gwamnatin da ta maye gurbin tamu tun a wancan lokacin tayi watsi dasu. Shi kuma bai iya kwantar da kai irinmu ba...hahahhha" Har lokacin fuskar Minista babu wani annuri sai ya dora da, "Harda laifinsa gaskiya da ya kasa samun wani mukami da aka sake samun canji tsohuwar gwamnatinmu ta dawo. Ya dauki girman kai da dagawa shi a dole mai tsantseni. Ashe abin nasa duk buge ne, gashi daga haduwa wurin daurin aure ya makale min." 'Allah na gode Maka da Ka nuna min waye Alh. Bala tun kafin na sanar dashi makasudin zuwana.' Furucin Minista kenan a zuciyarsa. Idan yawan aiki ne da yawan 'yan maula ya ninka Alh. Bala nesa ba kusa ba. Sai dai shi mutum ne da ya tsani wulakanci. Tarba mai kyau wadda ta dace da matsayinsa ya samu kuma akan idonsa wani ya sami kishiyarta. Wannan abu ne da ba zai iya dauke kai ba. Maganar aure ce ta kawo shi. Ya hadu da wata yarinya a gidan abokinsa wadda bayan gajeren bincike aka fada masa 'yar Alh. Balan ce. Muradinsa na son auren mata biyu yaso cikewa akanta. Dalilinsa kenan na zuwa ya same shi saboda shi mutum ne mai tsari. Ba ya son ya fara yi mata magana a waje ta amince saboda mukaminsa bayan akwai wani. Halin mahaifin nata da ya gani yasa shi yanke shawarar zurfafa tunani da bincike. Tashi ya yi ya gyara zaman babbar rigarsa. "Ba dai tafiya ba? Bamu tattauna maganar da ka ce mai mahimmanci bace ba ma" Cewar Alh. Bala shi ma yana tashi tsaye. "Kada ka damu zan kira ka a waya. Ina da appointment ne da naso mantawa dashi gashi har lokaci ya kusa." "Au tohhh..." Alh. Bala ya ce yana sakin fuska "ai na zata zuwan dan anacen can ne ya bata maka rai." Minista bai ce komai ba har suka fito waje. Alh. Bala kuwa sai zuba masa surutu yake yana ta kwantar da kai kamar ya durkusa masa. * Da Masinjan nan ya fito bai iya komawa wurin Honorable Habu ba. Zaman jiran bai dame shi ba. Ya zabi ya fadawa zuciyarsa aiki ne ya yiwa Alh. Bala yawa ba wai da gangan yaki ganinsa ba. Tashin wasu security da sassarfa suna komawa wurin jerin wasu bakaken motoci da ya samu a wurin yasa shi kallon hanya. Farinciki ya wadatu a fuskarsa yayinda ya yi tozali da Alh. Bala. Da sauri ya tashi yana son yi masa magana kafin ya shiga mota. Da ya tashi sai yaga ba shi kadai bane ya nufi Alh. Bala din da wanda suke tare. Sai kalaman fadanci ake ta zubawa ana cewa "Allah Ya kiyayeka" Da dai ya gane ba da ubangidansu suke ba sai ya kalli abokin tafiyar sosai wanda shi ma kallonsa yake yi. Baki ya hangame sai kuma dariya da murna suka hana shi magana. Ministan ne da kansa ya ambaci sunansa cikin wani irin shauki da kewa. "Habu Kansila? Honorable Namu? Kai ne?" Honorable ya dinga gyada kai har suka cimma juna. Hannuwansa Minista ya rike yana ta murmushi. "Abdulkarim kaine haka?" Sunkuyar da kai ya yi na kunyar rashin kyautawarsa kafin ya ce, "Naji kunya sosai Honorable duk da dai wallahi na nemeka sosai bayan dawowata aka ce ka bar unguwar. Laifina shi ne na rashin mayar da hankali wurin binciken inda ka koma din." Alh. Bala sai yaji kamar an sare masa gwiwoyi. Alamun sanayyar dake tsakaninsu barazana ce a gareshi. Hanyar da suka baro ya nuna da hannu yana kiransu. "Ku zo mu koma ciki don da alamu kuna bukatar zantawa cikin sirri." Minista Abdulkarim Mamman Diso bai bashi amsa ba sai nunawa Honorable motar da zasu shiga ya yi. "Bismillah. Kodayake ban tsaya naji uzurin da ya kawoka nan din ba." Honorable ya kalli Alh. Bala ya kawar da kai "Wanda nazo gani bai saurareni ba" Da haka Minista ya gane shi ne wanda yazo ganin Alh. Bala. A motar suna tafiya Minista yake sake bashi hakurin yankewar zumuntarsu. Ba abokai bane domin kuwa Honorable ya girme shi nesa ba kusa ba. Lokacin da yake ganiyar cin zamarsa ne su Abdulkarim suka fitini unguwa. Rashin kudi ya hana iyayensa tura shi makarantar gaba da sakandire. Kafin wani ya kai zancen kunnuwan Honorable Habu shi ya gani da idanunsa. Har gida ya tura aka kira masa iyayensu maza ya ce zai dauki nauyin karatunsu shi da abokansa su uku. Haka kuwa aka yi. Suka sake JAMB cikin ikon Allah shi kadai ya haye. Yaji dadi sosai ya biya masa kudin karatun. Abokan masa kuma ya basu jari. Rayuwa tayi ta tafiya har ya kammala digirinsa na farko. Honourable Habu ya soma cuku cukun nema masa aiki sai ya sami tallafi na zuwa kasar waje karo karatu. A can ya zauna ya yi masters da Phd. Kuma nan ne dai ya hadu da dan wani mai bawa shugaban kasa shawara. Da taimakonsa aka sama masa aiki ya fara yana dawowa. Ya nemi Honorable Habu a ranar da ya sanya kafarsa a unguwarsu Diso sai ya sami labarin ya tashi. Da zuci zucin ya kara nemansa ya koma Abuja. Daga nan kuma kujiba kujibar duniya da kai kawo suka dauke masa hankali. Sai gashi sun sake haduwa a inda bai yi zato ba. "Ina su Abbas kuwa? Ya gama karatu yanzu ko?" Tambayar sai ta zama fami ga Honorable. Nan ya labarta masa halin da suke ciki. Abdulkarim sai ya kara jin haushin kansa. Bai ce masa komai ba amma tuni ya gama yanke shawarar irin taimakon da zai yiwa Hoborable da iyalinsa. *** A gidan Alh. Tahir kuwa Mami Khadija ta cigaba da shirye shiryen bikin autansu. Mama Nasima kuma ta matsawa Mardiyya lamba da tambayar yaushe Munzali zai dawo. "Kinga ya tafi kafin mu samu ayi maganar da ta dace. Ni ba so nake kuyi ta batawa juna lokaci da hirar waya ba." Ire iren zantukanta kenan kullum. Ita kuwa Jiddo ta shiga tsaka mai wuya a wurin kawaye. Karyar da ta zuga musu akan hadin kai da jindadi da ta samu a wurin Danliti makanike ce take neman tarar da ita. Mutum biyu cikinsu kuma harda shugabarsu a ciki sun nemi ta hadasu dashi. A cewarsu harka da talakawa marasa galihu tafi dadi. Komai kika yi musu yanzu sai su ji kamar duniya babu kamar ki. Ladabi da biyayya da kuma bin hanyoyin farantawa mace sai kin zaba kin darje. Sannan uwa uba sun fi rike sirri. Zancen da ake yanzu dai shugabar tasu tana son yaje Abuja ya sameta sati mai zuwa. Mijinta zai yi tafiya kasar waje kuma tana da yakinin da daya daga cikin 'yan matansa zai tafi. To ita ma ta kirkiri tata tafiyar ya kuma amince. Nan kuwa dan gidan holewa ta saya ba tare da saninsa ba inda take kai kwartayenta. Dubu hamsin ta turawa Jiddo ta ce ta bashi ya yi kudin mota. Jiddo ta rasa inda za ta saka kanta. Tun ranar da ta tura masa hotuna bai kara nemanta ba. Ta saka masa kati na dubu goma babu godi bare na gode. Yanzu kuma har shugabar wadda ake yiwa lakabi da Sarauniya ta fara cewa idan ma taki hadasu ne saboda tana kishinsa zasu saita mata zama. Ai ta san dokarsu babu rowa. Kowacce tana da damar neman saurayin 'yar uwarta. Shi yasa ma suke fadawa juna yadda ta kaya ko wata za ta so. Uban gayya Alh. Tahir kuwa yana cikin fushin Yakumbo. Ya tsayar da duk wata magana ta auren Yumna saboda abin da tayi masa. A yadda ya tsara idan an fasa akalla nauyin Farha zai ragu a ransa har ya samu su yi magana. Rabin hankalinsa a kwance yake tunda sauran 'ya'yansa babu wanda ya canja masa fuska. Ya san bata fada ba. Ita kadai ce dai har yau bata yarda sun hadu ba. Motsin motarsa ma idan taji daki take shigewa ta kulle kofa. Yakumbo kuma tayi rantsuwar idan bai auri Yumna ba to ya shirya ganin bacin rai domin babu shi babu ita. A can wani bangare na zuciyarsa wanda soyayyar 'ya'ya ta rinjaya sai yake jin gara fushin Yakumbo akan na 'ya'yansa. Yakumbo uwa ce. Uwa kuwa a saninsa za ta iya jure komai kuma ta hadiyi komai domin 'ya'yanta. Idan ta kama ya yi mata kuka ne ma zai yi don ya san za ta yafe masa ta janye zancenta. * Dan madaidaicin akwati mai taya hudu Farha ta daga ta saka a booth din motarta. Idanunta ta kai kan motar Abbati wadda take lullube a wurin ajiye motocin gidan taji zuciyarta ta harba. Zai yau zai zo gidan daukar motar amma ba zai sameta kamar yadda tayi masa alkawari ba. Sakon da ya turo mata jiya da daddare ta sake maimaitawa a cikin kanta a hanyarta ta zuwa wurin Maminta. (Zan zo mu yi magana Ya Farha. Maganar baki da baki kafin nayi shirin daukar mataki na gaba wurin mallakawa Auwal muradinsa. Kin mamaye ko'ina a tare dani. Allah Yasa kina tuna ni ko sau daya ne a rana.) Wani abu mai kama da ana yiwa mutum yawo a ciki taji ya tsirga mata a lokacin don dadi. Ita kadai ta dinga zuba murmushi tana kuma jin kunya kamar yana gabanta. Ashe sunansa Auwal ta fadawa kanta kamar da wani take. Sai da ya soma fitar da rai da samun amsa sannan tayi masa reply. (Ban san Auwal ba shi yasa bana tunaninsa) Da wurwuri ya sake turo mata wani (Amma dai kin san Abbati?) Kasa rubuta komai tayi tana dariya kasa-kasa. A bangaren Abbati shirunta sai ya dame shi. Shi fa kaifi daya ne baya son jan rai. Kiranta ya yi kai tsaye ta dauka da wayar da kusa tsinkewa. "Ya Farha baki san Abbati ba?" Yadda ya yi tambayar da damuwa yasa ta fasa cigaba da ja masa rai. "Na san shi." Ta rage murya sannan ta kara da cewa " Kuma ina tunaninsa kullum." Ajiyar zuciya ya saki tare da lumshe idanu "To ai ni ne Auwal din. Suna na na gaskiya na fada miki." Bata san lokacin da tayi dariya ba har tana tunanin ko dan fari ne. Dariyar da ta dinga kurdawa ko ina a cikin Abbati tana saka shi daukar dumi. Tun yanzu yake fatan idan ya sami Farha Allah Ya bashi ita har aljanna. Da wata irin murya mai dadin amo da tsayuwa a rai ya ce "Ina sonki Ya Farha" Yadda ya dauke numfashi yana jiran amsarta haka ta dauke nata saboda girman lafazinsa. Ta dade kwarai da cire rai da jin wannan kalmar a kanta. "Kin barni da faduwar gaba." "Nima nawa gaban faduwa yake" ta bashi amsa da dukkan gaskiyarta. "To yanzu ya za ayi kenan? Da sai nan da kwana uku zan zo daukar motata amma na fasa. Tunda gabanki na faduwa gobe zan zo in sha Allahu." Kunya ta ji ta sake yin shiru har sai da ya tambayeta me yasa bata son yi masa magana sosai. Bai san hira irin wannan gabadaya bakon abu bane a gareta. Kawar da zancensa tayi ta sako wata hirar daban. "Yaya su Baaba? Don Allah ka ce ina gaisheta." Sai da ta yi dariya ya ce "ba damuwa don kin bagarar da zancen. Gobe kinga sai ki bani amsa muna kallon juna. Kinga ni na huta tunda dama ba iya fada zan yi a gabanki ba don nima ina jin kunya. Baaba kuma tana lafiya. Zuciyata tana ninka son mai mutunta Baaba. Ki gaishe min da Maminmu." Katse wayar ya yi ya barta da murmushin da masana zasu gane na sabon shigar soyayya ne. Sai dai nishadin da take ciki bai dade ba ya rugurguje. Alh. Tahir ne ya kirata sau biyu bata daga ba sai ya kira Mami Khadija ya fada mata sako ta bata. Suna gama magana kuwa ta kirata ta sanar da ita. "Abbanku ya ce ki same shi a falonsa goma na safe." Kuka ta soma tun kafin ta gama jin sakon. "Mami don Allah..." Daurewa Mami Khadija tayi domin ta san abin da zata fada mata shi ne daidai. "Wasan buyar da kike dashi ya isa haka. Kije kiji kiran me yake miki" "Mami?" ta furta da kyar saboda kukan da yaci karfinta. "Sai da safe Farha." Ita ma kukan ne ya taho mata shi yasa ta katse kiran. A daren Farha ta hada kayanta a akwati. Gari na wayewa ta karasa shiryawa. Ita ta tashi Mami Khadija da ta shiga dakinta. "Gidan Mama zan tafi na zauna har a gama bikin Kawu." Ta san za a rina dama. Farha can be stubborn idan abu bai yi mata ba. "Da izinin wa za ki tafi?" Zubewa tayi a gaban gadon ta marairaice mata. "Don Allah ki barni in tafi Mami. Idan naji zuciyata za ta iya daurewa inyi magana da Abba zan dawo." Tayi maganar kwalla na zubo mata. "Au...bama ki da niyar dawowa in an gama bikin kenan?" "Please Mami" "Naji. Allah Ya tsare. Kada dai ki manta duk dadi ko rashinsa ba a canjawa tuwo suna." Kai ta gyada ta mike. Har ta fita bata bar fassara kalaman Mami na karshe ba. Jinjinawa mahaifiyarta ta tayi domin ta fahimci ko da bata fadi me ta gani ba ita ma ta san ko meye. Ita kam bata son fasiki kuma bata jin zuciyarta tana da kwarin daukar cin amanar namiji. Kofa a bude take yayi aure amma banda yawon bin matan titi. Bata fatan abin da zai zo ya gifta har ya sata hakurin zama da mazinaci! UWA UWACE...23 Batul Mamman💖 Amrah Auwal Mashi da Phary BB ina muku sonso domin Allah. (Ga duk masoyan Uwa Uwace, masu hakuri tare bibiyar shafukan da nake posting dinsa ina godiya. Dubun gaisuwa a gareku baki daya. In sha Allahu na dawo kenan sai mun ga kwal uwar daka akan labarin nan.....lets go!) *** Da mukulli Jiddo ta rufe kofarta bayan mai yi mata aiki ta fita ta shige daki. Missed calls din Sarauniya sun fi goma. Sai sakwanni wadanda tun bata bude ba ta san kwanan zancen. Surutu ne da zagi duk akan rashin hadasu da Danladi. Kayanta ta cire bayan ta rurrufe tagogi ta haye gado ta dauki hotuna kala kala wanda muninsu yafi na farko. Ta dai tabbatar bata hada da fuskarta ba. Wayar Danladi ta kira yana gani bai dauka ba sai kawai ta tura hotunan tare da sakon magiyar ya amsa gayyatarta. Ta kara da fada masa nemansa da Sarauniya take yi. (Ta bani dubu hamsin na baka kayi kudin mota zuwa Abuja. Ladan aikinka zai iya fidda kai daga talauci. Ni da kai duka zamu karo da abin da za ta biya. Sai naji shawarar da ka yanke.) A kwance yake ya gama karewa hotunan kallo ya karanta sakon nata. A gigice ya tashi har ya barar da dan kofin silba din da matarsa ta ajiye masa ruwa a ciki. Dubu hamsin kuma kudin mota kadai?! Hannunsa kaikayi ya kama yi yana son kiranta amma wata zuciyar ta hana. Wai kada ya nuna mata shi din kwadayayye ne. Jiddo kuwa da ta tabbata yaga hotunan sai ta kira shi. Da irin salonsu na gogaggun mata take masa magana. "Danladi mata aka sani da jan aji amma sai gashi lokaci guda kana ta dagula min lissafi. Shin ko dai abin da na turo bai burgeka bane?" Sai da ya hadiyi yawu da kyar saboda muryar ta tuna masa irin hotunan sannan ya dan yamutsa fuska ya amsa mata kamar ba ya so. "No ba haka bane. Kawai ina busy ne." Jiddo ta murmusa. Dan hannu ne babu tantama. Kyale shi za tayi ya ja ajin sannan ta fadi bukatunta. Danladi ya gama kwanakwanarsa ya mika wuya. Ba wai son zuwa ne baya yi ba tun farko dama. Kawai dai yana tsoro ne ganin cewa matar manya ce. In bai manta ba, motar da ya gyara musu da kayan jikinta babu alamar talauci ko kadan a tare da ita. "Ku sa min rana amma banda satin nan." "An gama" cewar Jiddo cike da nishadi. Jan shi ta dinga yi da hira har ya dan saki jiki. Suna gama wayar hankalinsa ya karkata kan Ayaah. Ita ce irin macen da ya dade yana muradi. Irinsu Jiddo sai dai aje aci kudi kawai a dawo. Ayaah kuwa su ake kashewa kudin idan akwai su. Dakin matarsa Raiha ya shiga tana zaune da yaransu biyu tana basu kunu. Aikin sa yana kawo masa rufin asiri daidai gwargwado amma saboda karya da yawon bin 'yan mata ya kasa wadata gidansa. Yau tashi suka yi babu ko sisi a jikinsa sai makota ta shiga ta karbo bashin kunu. Shi ne suka sha da safe, rana da kuma yammacin yanzu da ya gama sanyi kalau. "Wani abin kake so ne?" Ta tambaye shi a ladabce ganin ya tsaya a bakin kofa yana ta binsu da kallo. Tabe baki ya yi kafin ya ce "bani darin da na baki dazu zan dan fita." Danne zuciyarta tayi ta ciro darin daga cikin riga ta mika masa. Bai ce mata komai ba ya juya abinsa. Ludayin da take bawa yaran kunu taji ya mata nauyi ya sabule daga hannunta saboda bakinciki. Dan kudin da ya bata take cancanawa za ta saya musu awara suci mai dan nauyi da daddare shi ne ya karbe. Kamar kiftawar ido da bude shi don ko gyara zama bata yi ba ya sake shigowa ya wuce dakinsa. Katin naira dari ya siyo ya saka a wayar ya dannawa Ayaah kira. Yaci alwashin yau zai fara dorata akan manufarsa. Ba zai bar gidansu ba sai ya rungumeta. * Wanki take ta kunna rediyo tana sauraron wani shiri da akeyi a tashar Freedom mai suna Sabon Shafi. Shirin yana burgeta matuka domin ana hira ne da mata da suka yi fice a fannoni daban daban. Burinta wata rana ace za ayi hira da Hajara Habu Danmalam, fitacciyar.... Tunaninta ne ya katse ba tare da ta gama tsara matakin da take son kaiwa a gaba ba sakamakon shigowar waya. Daga kai tayi kan dan dakalin da suke ajiye guga inda wayar take taga sunan mai kiran. Da sauri ta goge hannunwanta da zanin jikinta ta amsa kafin ta katse. Sai da tace hello sau hudu Danladi bai amsa ba. Yana jin ciwon tafiyar kudinsa a banza amma dole ya hakura idan yana son cin wannan yakin. Wani jan numfashi ya yi kamar wanda ya yi muguwar gajiya sannan ya kira sunanta da kwantacciyar murya. "Ayaahhhh. Me na yiwa mata suke guduna haka?" Daburcewa tayi da salon maganarsa. A lokaci guda kuma kalamansa suna tayar mata da hankali. Duk yadda akayi matarsa ta kuma guma masa wani abin. "Mata har nawa ke gudunka?" "Wadda kika sani dai ta gidana, sai kuma ke da na daukeki wata babbar jigon rayuwata. Kwana nawa baki ji daga gareni ba amma ko dan tes dinnan ya gagara ki ji lafiyata." Kanta yayi gingirin kamar an dora farantin kwai tana tsoron ya fado ya fashe. Zuciyarta kuwa shawagi ta dinga yi mata a kirji saboda tsananin farinciki. Da tattausan lafazi ta soma bashi hakuri. Da ya san katin yana daf da karewa sai ya katseta. "Na san dai ina takura miki da matsalolina amma don Allah I am sorry. Bana son Mom ta sani. Ke kadai zuciyata ta amince ta dinga fallasawa sirrinta. Idan kina gida zan zo da anyi magariba." Cikinsa a take ya bada wani sauti kamar yana rokon shi ma a kaishi gareta ya sami abinci. Shu'umin murmushi ya yi ya dan daga murya, "Dalin, kin dafa min indomie din ne?" Ya dan yi jim kadan "naji. Allah Ya baki hakuri. Idan na fita zan nema. Kina son wani abu ne na taho miki dashi?" Ana fara warning na yanzu kudin zai kare ya ce da Ayaah "sorry na barki ina magana. Idan nazo zan kiraki." Mace mai tunani za ta fassara hirarsu Ayaah da cewa Danladi (Dani) ya cancanci a tausaya masa saboda rashin samun kulawar iyalinsa. Da kudinsa da komai amma abinci ma sai dai ya saya. Mai zurfin tunani kuwa za ta tausaya masa da farko. Idan an gama wayar sai ta koma tunanin dalilinsa na fada mata laifin matarsa. Daga nan za ta gane akwai wata a kasa. Sauran binciken zai nuna mata shi abin yarda ne ko akasin haka. Wankin da Ayaah bata gama ba kenan. Inda Hasiya take tare da 'yan lallenta taje ta durkusa. Sosai alakarsu tana ta gyaruwa yanzu sai dai duk da haka aure Ayaah take so. Ita dai ta bar gidan ta huta da zugar su Anti Fati kannen mamanta da kuma mitar yayyenta. Sannan ta kula baban nasu ba iya biya mata zai yi ta cigaba da karatu yadda take so ba. "Anti me za a dora ne? Naga yamma tayi sosai." Hasiya tayi murmushin jindadi. Canjin da Ayaah tayi yana faranta zuciyarta sosai. "Kin manta yau Ummita ce a kitchen? Kice tayi mana jallof din shinkafa." Ta zaro dari uku ta mika mata ta ce a siyo kifi a saka a ciki. Ayaah ta karba harda godiya ta shiga ciki. Mayafi ta dauko ta tafi ta siyo kifin ko Ummita bata nema ba. Kifin dari biyu da hamsin ta siyo sai alayyauhu da albasa mai lawashi na hamsin. Sauran kayan bukatar duka akwai a gidan. Albasa ma suna da ita sai da mai lawashin take bukata. Wankesu tayi ta yanka tare da alayyahun ta sake wankewa ta ajiye ya tsane. Ta debo wake yadda take bukata ta dora. Sannan tayi jajjagen kayan miya da citta da tafarnuwa ta soya ta tsayar da ruwan abinci. Kamshin ne yasa Ummita lekowa daga daki. Tun dazu take son fitowa dora girkin ciwon kai ya hana. Ta dauka Murja ce ta gama kitso ta zo taimaka mata sai ganin Ayaah tayi. Wani dadi ya shigeta na canjin kanwar tasu tayi mata gofiya ta koma ciki. Da ruwa ya tafasa Ayaah ta zuba shinkafa tare da waken da ya soma dahuwa su dahu tare. Sai da ta kusa gama turara bayan ta rage wutar ta zuba lawashin da alayyahu tare da kifin da ta ciccirewa kaya. Yau ma kafin kowa ya farga ta dibarwa Dani sannan ta kwashe sauran. Tayi sa'ar gama komai kafin a fara kiran sallah. Sai ta fake da alwala ta samu ta wanke fuska taje tayi kwaskwarima. * Honorable yaga ranar taimakawa na kasa a lokacin da bai zata ba. Da suka bar ma'aikatar su Alh. Bala, gidan Minista Abdulkarim suka wuce. Tamfatsetsen gida wanda ko lokacin da yake ganiyar arzikinsa bai taba tunanin mallakar irinsa ba. An kawo masa abinci mai rai da lafiya ga kuma girmamawa ta musamman daga maigidan. Matarsa tana Abuja da yara shi kadai ya zo ganin iyayensa da magana da Alh. Bala. Wannan yasa masu hidimar gidan su ma suka zage damtse anata kai kawo. "Naga kamar umarninka kadai suke bi. Don Allah ka ce kada ta zubawa wallahi na koshi." Furucin Honorable kenan bayan duk abin da yaci kuma aka sake kawo masa farfafesun jelar saniya. Abdulkarim ya dagawa mai aikin hannu da murmushi a fuskarsa sannan ta fasa zubawa. Kallon Honorable ya yi yana mai kara jin tsoron Allah ta yadda rayuwa take jujjuyawa ga bayi. "Gani nayi duk ka rame. Don Allah ka sake cin wani abu." Honorable ya tuntsire da dariya "banda abinka kuma sai aka ce a cin abinci guda zan yi kiba?" Dariya suka yi tare suka taba hira sannan Honorable ya tashi zai tafi. Abdulkarim ya ce bai san zance ba. Yana son jin me ya faru dashi tsayin lokaci har rayuwa ta koma haka. Tiryan tiryan ya labarta masa komai. Ba kuma don maula ba sai don dalili guda wanda ya fada masa kamar haka, "Duniya bata da tabbas Abdulkarim. Ba komai ne yake zama tabbatacce ba a rayuwa. Saboda haka ka daure ka rike gaskiya a duk inda ka sami kanka. Idan duniya ta ciyar da kai gaba fiye da nan sai ka dinga kallon kasa kana kara godiya ga Allah. Bana maka fata amma ko da za ta kawoka inda ta ajiyeni to kada ka karaya da samun rahama. Allah ba Ya dorawa bawa abin da yafi karfinsa. Ba zan boye maka ba da farko na shiga kunci saboda rashin sabo da babu ga Abbas a kwance. Da ilimina na fara hasashen ko auren Hasiya ne ya jaza min talauci. Sai gashi ashe ita za ta rike gidana da 'ya'yana. Duk zafin talauci idan Allah Ya baka mace ta gari to tabbas Ya kwashe maka radadinsa." "Zan so ganinta. Muje da kaina zan kai ka gida." Cewar Abdulkarim, zantukan suna shigarsa da kyau. Honorable ya dage baya so. Shi ma Abdulkarim ya dage sai yaje. Daga nan ya tashi ya bi wata hanya zuwa bangarensa. Da envelop ya dawo ya mika masa. Allah Sarki! Yawun bakinsa ya kafe. Idanuwansa suka kada suka yi ja....a wani shudadden lokaci shi ne yake bawa Abdulkarim. Yau duniya ta nuna masa cewa tables can always turn. (Ya Allah Ka rabamu da talauci da karayar arziki. Duk abin da zai taso mana na kudi Allah Kasa mu fi karfinsa.) "Duk ni kadai? Basu yi yawa ba?" Ya ce da murya tana rawa. Raba kudin ya yi gida biyu ya mika masa rabi. Abdulkarim sai yaji wani abu mai nauyi a zuciyarsa. Honorable Habu yafi karfin wulakanci a wurinsa. Laifin kansa ya gani da ya yi sakaci da zumunci har ta kai bai san mawuyacin halin da tsohon ubangidansa yake ciki ba. Ace har ya kai matsayin da dubu dari za ta kawo masa kwalla a ido. "Kada kayi min haka Honorable. Ban kyauta ba a baya na sani amma ka dauka Allah ne bai shirya haduwarmu ba sai a yanzu da muke sa ran alkhairi ya biyo bayanta." "Haka ne. Nagode.." Godiyar ma katseta Abdulkarim ya yi suka fita zuwa mota tare. Wannan karon daga su biyu a bayan mota sai direba. A hanya ne yake tambayarsa irin sana'ar da yake son yi. Lokaci ya ja babu batun komawa siyasa. Idan an manta da mutum sai ya zo da kwakkwara kuma kyakkyawan shiri tafiyar take sake armashi. In ba haka ba kudinsa kawai zai yi asara. "Zan yi shawara da Hasiya sai na fada maka" Ya ce da murmushi a fuskarsa. Abdulkarim ya kama dariya sannan ya ce "Allah Yasa bata aurar da duka 'ya'yanta ba ta bani guda. Don naga alama idan na auri rainonta kila sai nayi shugaban kasa." Honorable ya girgiza kai "abin kuma harda zolaya?" Abdulkarim bai ce komai ba. Ba kuma zai ce ba har sai yaje gidan ya ga 'yan matan da ya sani a baya tun suna yara. Kudurcewa ya yi a zuciyarsa indai ba rashin tarbiya wanda baya tsammani ya gani ba ko su suce basu son aurensa ba zai nemi guda. *** Mardiyya da Sauda ne tare da Suhaib da Lilu tsaye a jikin motar Abbati. Sun rako su bakin mota shi da Munzali bayan sun shiga sun gaisa da Mami Khadija. Mama Nasima bata nan kuma Mardiyya sai addu'a take yi su yi su bar gidan kafin ta shigo. Sau biyun da ta zubar da kimarta a gaban Munzali bata yi a gaban yayyenta ba. Ba kuma ta son a fara daga yau. Hirar motoci suke yi wadda Lilu da Munzali ne karfinta. Lilu ya shafa motar yana binta da kallon bege "Ni dai ba don yau za ku tafi ba ai da na dana ko zuwa karshen layinmu ne in kashe arna." Keyarsa Suhaib ya kwade ya kuma ce idan bai kama kansa ba sai ya fadawa Mami. Mardiyya da Sauda zasu yi dariya ya hade rai zai yi kaza huce kan dami. "Wai me ma ya fito daku ne? Wurinku suka zo? Ku koma ciki." Munzali ne ya shigar musu domin Abbati kamar baya wurin. Hankalinsa yana kan hanya yana dakon ganin ta ina Farha za ta bullo. Da sauri Munzali ya ce "Ya za ka korar min kanne?" Dan nesa kadan da inda suke tsaye ya nuna da hannu yana mai cewa "In ganki mana Diamond girl." Karashen maganar ya yi ne idanunsa a cikin na Mardiyya. Kawar da kai tayi da sauri gabanta na wata irin faduwa ta daban. Bata san yadda akayi yau take jin Munzali a ranta haka ba. Tun dazu take satar kallonsa sai ta ga shi ma ita yake kallo. Juyawa tayi za ta gudu saboda kunya Sauda ta rike mata hannu. Shi kuma gogan ya basar kamar ba daga bakinsa maganar ta fito ba. Abbati ma dake son tambayarsu game da Farha amma ya kasa sai da yaji kunyar. Wato duk yanzu halinsu yake fitowa game da mata da suka hadu da wadanda suke so. Suhaib ma dai daskarewa ya yi don kusan yafi kanwar tasa jin kunya. Gyaran murya ya dinga yi ba kakkautawa don ya kasa magana. Lilu kuma ya dinga kikkifta idanu na shakiyanci sannan ya ce, "Diamond dai da na sani mai shegen tsadar nan ka kira Mardiyya?" Hannu ya sakalo a kafadarta ya tako kusa da Munzali dake ta murmushi ya tsaya da ita a gefensa. Hannuwa ya hada kamar mai shirin daukar hoto yana aunosu ta cikin zagayen da yatsunsa suka bayar. Ya dawo kunnenta yayi magana kamar rada amma kowa na ji "Baby Sis kin matso mana class wallahi." Ya koma ga Munzali " Kai ma Alh. Munzali ka more. Hummm don ma kada ka ce yabon kai da sai in ce duk 'yan matan Kaduna babu kamar na gidanmu." Hannun Mardiyya ya fara kamawa suka ti musabaha sannan ya saki ya koma kan na Munzali yana faman murmushi gami da nanata kalmar "congratulations." Suhaib ji ya yi kamar ya daga shi a kafada su bar wurin. Lilu ba ya jin magana ya ce a ransa kafin kuma a zahiri ya biyo shi. Zillewa Lilu ya yi bai bari ya kama shi ba ana ta dariya. "Baka da kunya ko kadan." Suhaib ya furta yana fuskantar bangaren Abbati. Nauyin Munzali ne ya kama shi saboda a gabansu yake yiwa Mardiyya wani irin kallo. Gashi sun girme shi sosai balle ya yi irin jan idon nan na yayan budurwa. Abbati kafadar Munzali ya ture da tasa har sai da yasa shi rankwafawa yana mita. "Munzalin ma ai ba kunyar gare shi ba da ya yi mata magana a gabanmu." Daure fuska Munzali ya yi cikin wasa yana hadawa da hararar Abbati. "Ai dama ba ayi maka gwaninta. Sharar fage nayi maka don duk su watse kafin ta fito." "Wa?" Lilu da Suhaib suka hada baki wurin tambaya. "Ya Farha" Sauda da Mardiyya suka basu amsa a tare. Suhaib bai san lokacin da wani irin murmushi mai cike da tsantsar annashuwa ya bayyana akan fuskarsa ba. Farha ce yau da kunnuwansa yaji ance namiji yana jiranta? Ganin murnar na neman yi masa yawa kuma bashi da tabbacin me yake faruwa sai ya ce, "Yanzu duka nan dama zance ku ka zo ba daukar mota ba?" Sauda da Lilu har ma da Munzali sai dariya. "Diamond girl kanwata ce kuma abokiyar shawara ko?" Munzali ya yi magana yana kannewa Mardiyya ido sannan ya dora da cewa "wasu ne dai har a cikin bacci za ka ji suna kiran Ya..." Bakinsa Abbati ya rufe da hannu su Lilu aka sami nayi sai dariyarsu suke. Munzali na kokarin kwatar kansa Abbati kuma yana faman yi masa alkawura akan idan ya kama bakinsa zai cika masa su. "Zan tuka motar har Kano!" Ya fadi abin da ya san zai yiwa Munzali dadi. A take Munzali ya daina kokarin janye hannun Abbatin ya nutsu. Yana sakinsa yasa dariya. Da gaske wautar Abbati bata wani buya lokuta da dama. "Riba biyu kenan. Kaga dai kowa ya fahimci menene baka son na fada. Alkawari kuma dole ka cika tunda ban fada da bakina ba" Mukullin ya dorawa Abbati a tafin hannu ya yafito Mardiyya da hannu. "Kina ta sani dibar kunyar Ya Suhaib kuma kin ki zuwa." * Gate din gidan aka wangale direban Alh. Tahir ya shigo ciki. Wurin ajiye nasa motocin ya dan yi nisa da inda yake hango 'ya'yansa da wasu baki biyu suna dariya. Motar da ya gani a kusa dasu kuma a bude ce tasa ya gane su waye. Mami Khadija bata tauye masa hakkinsa na maigida ba, ta sanar dashi game dasu tun ranar da suka ajiye motar a gidan. "Ga sirikinku nan" cewar Lilu yana yin gaba wurin mahaifinsa. Mardiyya da Sauda ma da sauri suka mara masa baya suna kiran "Abba" tamkar wanda ya yi tafiya. Kafin su karasa ya ware hannuwansa ya rungume kowacce a bari daya. Kirjinsa yaji ya takure saboda rashin Farha. Indai su uku suka zo tarbarsa to ita a bayansa take tsayawa ta riko wuyansa da hannuwanta biyu. Daga nan haka suke raka shi har daki. Wani lokacin ma su taya shi cin abinci. Lilu kuma idan yana gida shi yake dauko masa jaka da wayoyi. Yanzu ma ya dauko harda babbar rigar da ya bari a motar ya ratayota a kafada. Tun tashinsu Suhaib baya zuwa sai suke ganin kamar irin abin nan ne na babban yaya. Farha kuma tunda taga bidiyon nan take kirkirar abin da zai hanata fitowa idan ya dawo ko ya aika a kirata. Yanayin soyayyar uban da 'ya'yansa ya burge Munzali da Abbati matuka saboda basu tashi a haka ba. Gara ma Abbati ya san nasa mahaifin yana dan kokartawa amma babu zancen wata runguma ko sakin fuska makamanciyar wannan. Duk ranar da suka kwatanta haka karshenta Mal. Sa'idu sai ya tsire masa uba. Shi kuwa Munzali ina ma suka hadu balle a nuna an damu dashi. "Manyan yayye basa zuwa oyoyo?" Munzali ne ya tambayi Suhaib amma Abbati ne ya lura da yanayinsa a lokacin da yake bayarda amsa. "Mu ai mun girma an barwa kanana" Ba da niyar nuna musu komai ya yi ba amma bakidaya annurin fuskarsa ya bace. Irin kallon da ya yiwa mahaifin nasa ya kawar da kai Abbati ya kasa fassarawa. Kamar kallon tsana, kiyayya ko jin haushi. Kallo mai nuni da cewa akwai wani kwamtaccen abu na bacin rai tsakanin uban da d'ansa. Bai bar tunanin ma ya zauna masa ba ya kawar dashi ta hanyar sakin fuska suka karasa wurinsu shi da Munzali. Da fara'a ya tarbesu ya kuma dinga jansu da hira. Dama ransa a bace yake daga office amma ganin yaransa kadai ya wanke masa komai. Wata sabuwar ma'aikaciya suka dauka shi ne daga zuwanta ta fara nuna masa alamun tana so su kulla mu'amala. Matsalarsa da Farha ta janyo masa rashin kwanciyar hankalin neman yarinyar duk da ya kwadaitu da ita tun farkon zuwanta. Abin da ya bashi haushi kuwa bai wuce kukan da ta saka masa a office ba bayan ta gaji da dabarunta ya daka mata tsawa ya ce ta fita. "Amma sauran duk sun ce ba haka kake yi musu ba. Ni me na rasa?" Wannan magana ta hana shi hadiyar yawu a lokacin saboda dacin da ya taso masa. Sauran da take nufi ba wasu bane illa matan kamfanin nasa da ya nema a baya. Kenan duk kudaden da yake kashe musu da gargadin su rike bakunansu ya tashi a iska. Suna hirar da juna harda yi masa cune...in ba cune ba ta ya akayi yarinyar ta san ta nemi jan ra'ayinsa tunda ba shi ya fara nemanta ba? Har suka iso gida yana tunanin mutum nawa aka fadawa? Mutane nawa ne suke yi masa kallon tsirara mara kima ba tare da ya sani ba? Farha da baya tsammanin gani a cikinsu ya tambaya Sauda ta fada masa tana gidan Mama. Ba shi kadai yaji babu dadi ba harda Abbati da suka yi alkawarin haduwa yau. Alh. Tahir murmushi ya yi ya ce "ta fi ku dokin bikin nan naga alama." "Abba bata fada maka za ta tafi ba?" Mardiyya ta tambaye shi don tayi mamakin tambayar tasa. "Yau meeting muka yi tayi amma naga missed calls dinta zan kira." Sallama ya yiwa su Munzali ya wuce nasa bangaren kafin a kara wata tambayar da za ta fallasa karyar da ya musu. Abbati kam jikinsa ya yi sanyi tunda bata sanar dashi ba kuma ta san zuwan a yau dominta ne. Farha ta fi karfinsa ta kowacce fuska idan ya dubi tarayyarsu. 'Yar masu kudi duk da dai ya san indai don kudi ne ba zai wahala ba. To amma cikakkiyar 'yar boko ce mai tsaftataccen asali. Sirrin rayuwarsa ya sanya bai sami damar jin bacin ran kin fada masa ba. Zuciyarsa dai ta raya masa cewa bashi da wannan matsayin. Tunani ne ya yi masa yawa sai kawai ya yi sallama dasu Suhaib ya shige mota bangaren direba . Munzali dake son magana da Mardiyya sai ya fasa ya ce zai kirata. "Mutumina kayi hakuri. Karshenta inda taje din ba za ta iya haduwa da kai ba shi yasa bata fada maka bata nan ba ko ta ce ka biyota" Munzali ya fadi a kokarinsa na kwantar masa da hankali bayan ya zauna. Da sanyin jikin da bai so ko Munzali ya gani ba ya ce "Kar ka damu." Suna tafiya Suhaib ya tafi wurin Mami Khadija. Albishir ya yi mata don yafi kowa sanin damuwarta akan Farha. "Amma Mami yarinyar nan don wulakanci sai ta tafi gidan Mama bata fada masa bata nan ba? Wallahi duk yadda yaso boyewa sai da na gane rashin jindadinsa." "Ai kuwa zan gamu da ita. Ta barmu da damuwa Allah Yasa ba ita take korarsu ba muke tunanin su suke kin zuwa." Zancen yana da mata da kuma tsoron kada a sami matsala a gaba ta fara yi masa suka shiga wata hirar daban. A waje kuwa sai da kowa ya tafi sannan Lilu ya nufi dakin Abbansu da kayansa da ya dauko a mota. Tunawa ya yi da katin daurin auren wan abokinsa a dakinsa ya juya. Ya san ba zuwa zai yi ba tunda rana daya ne da na kanin Mami da za ayi a Kano. Duk da haka amintarsa da abokin nasa tasa yana son Abban nasa ya sani kuma ya kira baban angon ya masa fatan alkhairi. Akan gadonsa ya ajiye kayan Alh. Tahir ya bude durowar gaban madubi ya dauko envelop din katin. Jakar office din ya fara dauka sannan wayoyin. Ya dago babbar rigar biruka da wallet suka fado daga aljihun jakar. Guntun tsaki ya yi na bata lokaci ya duka ya daukosu. Hannu kawai ya zura a aljihun ya mayar dasu sannan ya kama zip din zai ja sai yaji ya rike yaki motsawa. Jibge kayan hannunsa ya yi ya juyo da jakar yadda zai ga zip din da kyau. Abu ne kamar takarda ya makale yasa taki zuguwa. A lokacin da ya zube kayan hannunsa akan gadon ne wayar Alh. Tahir wadda yake amfani da ita wurin kiran 'yan matansa ta fado daga aljihun babbar rigarsa. Lilu bai kula ba ya gama gyara zip ya kwashe wayoyin da yazo dasu a hannu ya yi gaba. Alh. Tahir bai tashi sanin wayar bata nan ba sai dare bayan Jiddo mai girki a ranar tayi bacci. Hankalinsa kuwa a take ya tashi. Ko a office ba zai so barinta ba saboda gudun fadawa hannun da zai ji kunya, ballantana kuma gida. A daren nan wurin daya saura ya fita yaje motar ya dudduba tunda ya san a hanya ma ya amsa waya da ita. Motsin wucewarsa Lilu yaji a lokacin yana kallo ya tashi ya leka taga. Ya yi mamakin me Abban nasu yake nema a mota a daren. Kamar ya fita tambayarsa sai yaga ya koma. Laptop dinsa ya kashe ya kade bargonsa ba tare da kula da wayar da ta fado daga kai ba ya haye gado ya kwanta. Wurin karfe tara ya fito zai tafi makaranta yaga Alh. Tahir tsaye da jallabiya ga direbansa yana ta bankade mota yana dube dube. Karasawa ya yi ya gaishesu duka. "Abba me ake nema ne? Jiya ma cikin dare na ganka kana duba motar nan." Murmushin dole Alh. Tahir ya yi saboda kada ya nuna ya damu da wayar. "Babu komai jeka abinka" ya ce masa. Shi kuma direban ya ce "wayar Alhaji" a lokaci guda. "Abba ka duba. Jiya duka wayoyinka na kawo maka daki." Kamar gaske Alh. Tahir sai ya saki fuska "bari naje na duba. Sai ka dawo." Ana rufe gate din gidan ya dawo da idanunsa da suke nuna tsantsar bacin rai ga direbansa. Hankalinsa ya matukar tashi. "Idan wayar nan ta fada hannun wani saboda sakacinka a bakin aikinka." Direba cigaba da bincike ya yi yana mamakin wannan abu. Shi ko kalar wayar ba zai ce ya sani ba amma an dora masa laifin batanta. Ana gobe zasu tafi Kano Mami Khadija ta kafa sharadin duk wanda bai gyara dakinsa ba babu inda zai je. Kamun amarya ne wanda aka hada da mother's eve da dinner za ayi a Kanon. Babu mai son a barshi da kallon hotuna yana cizon yatsa. Ita kanta ta san da wa take dama. Lilu ne dakinsa sai tayi da gaske yale gyarawa. Alh. Tahir ya so masu aiki su dinga gyara musu ta ce sam bata yarda ba. Tana barin wurin ya fice daga gidan. Shawarma ya siyo guda biyu manya manya da robobin yoghurt ya shige wurinsu Sauda. Mardiyya ce ta fara jin kamshin shawarmar ta tashi da murna za ta karbi ledar ya boye abarsa. "Kun dai ji me Mami ta ce. A gyara min palace dina a ci dadi. Bari na saka muku yoghurt din a fridge kafin ku gama." Da gudu gudu suka bi bayansa. Wasu kaya ya dauka a leda ya tafi dakin Suhaib ya shirya. Dinner din gidansu abokinsa ya tafi. Sauda ta fada toilet aka bar Mardiyya da uban shirgin kayansa. Tana cikin ninki taci karo da waya a kasan gado. Lilu bai san da ita ba balle ya kula da faduwarta. Daukewa tayi ta jona masa tunda taga chaja a jikin bango. Da suka gama aikin ta kunna masa kafin ta fita. Shi kuma da ya dawo ko bi ta kan wurin bai yi ba ya kwanta saboda gajiya. Da safe bayan sun gama shiri sun dauki hanya Yumna ta dinga kiran wayar. *** 0UWA UWACE...24 Batul Mamman💖 Shafin na Baaba Jummai (Minna) ne. Ina godiya tare da turo tawa dubun gaisuwar da fatan alkhairi. *** Flashing ya kai shida Danladi ya yiwa Ayaah. Tsabar kwarewa wasu a ciki ma bata jin karar wayar sai dai taga haske kamar walkiya ya bace. Hakura tayi da son dauka ta kira shi da kanta. Abin da ya fara cewa yana daukar wayar shi ne, "Gaskiya kuna da matsalar netwok a unguwar nan. Zuwana nan na kira ki ya fi sau goma. Har na fara tunanin turo yaro a kira min ke tunda ba zan iya tafiya ban ga murmushinki ba." Da sanyin murya ya yi magana. Cikin wani irin yanayi mai sa mutum ya ji kamar ya aikata gagarumin laifi. Ayaah taji babu dadi ta shiga bashi hakuri duk da a bangare guda tana cike da farinciki game da kalamansa. Da ya nuna mata kamar komai ya wuce sai ta ce ya ajiye mota a bayan layinsu za ta zo nan ta same shi. "Yanzu Babanmu ya kira Anti cewa yana hanya tare da bako. To ban sani ba ko bakon da zai kai ciki ne ko mai tsayawa a soro. Kuma kaga baku taba haduwa ba zai fi kyau ku hadu yana shi kadai." Cije lebe Danladi ya yi ransa na kuna. A soron nan nasu mai dan duhu ya so ya fara koya mata gurbatacciyar soyayyarsa. Gashi bai sami motar da tayi masa a garejin ba. A ina zai sami wannan damar idan suka hadu a filin Allah? Da muryarsa da ya kware wurin kwantarwa domin ya sanyawa 'yan mata tausayinsa ya yi mata magana. "To babu komai Ayaah. Ba zan so na takuraki ko na sanyaki cikin yanayi mara dadi ba. Banda zuciyata da ta kasa sukuni saboda tunaninki da na hakura sai lokacin da kike so na zo." Numfashi taja wanda ya bashi damar yin murmushin samun nasara tun kafin ta furta ta bakinta. Yadda yaso haka ta ce za ayi. Duk da tana jin nauyi haka ta daure taje ta fadawa Hasiya za tayi bako. Murmushi Antin tasu tayi gami da 'yar tsokana. "Gilashi zan saka domin na tantance ko ya cancanci zama surukina. To amma wani hanzari ba gudu ba. Ki bashi hakuri ya jira zuwa gobe. Kinga Babanku yana hanya da bako." Ko kadan Ayaah bata son batawa Dani rai. A tunaninta zai fassara rashin sauraronsa daidai da abin da yake fada mata matarsa tana yi. Zai shiga damuwa idan basu hadu ba kuma bata son haka. "Anti ko inje gidan Mal. Tasi ya sameni a can sai na bashi hakuri tunda ya riga ya zo?" Katangarsu daya da ta gidan Mal. Tasi din. Yadda ta marairaice fuska sai Hasiya ta amince. Dakin Abbas ta koma suna hira da Murja mai bashi abinci. A zuciyarta take tunanin lallai Ayaah tana son bakon nata. Za ta sanar da Honorable tun wuri ayi binciken da ya dace. Ayaah kuwa da saurinta ta sake kiran Dani ta fada masa inda zasu hadu. Ba haka yaso ba amma ya fiye masa waje. Tana cikin gaisawa da matar Mal. Tasi tare da fada mata abin da ya kawota taji sallamarsa. Wani iri ta dan ji tunda ta zata zai kirata ne. Da babu alaka mai kyau tsakanin gidan da nasu kuma ba ayi mata izini ba haka zai zo kenan? Ta tambayi kanta. Haka nan dai ta tashi da ledar da ta sako madaidaicin filas din da ta zuba masa abinci. Tana doso soron kamshi ya dinga hawa kanta. Yau ma turaruka 'yan duri ya bulbula sai dai hannu ya so zarcewa. Kamshin ya yi yawa har yana neman sakawa mai shaka mak'ak'in wuya. Suna hada ido ta manta da komai sakamakon murmushin da ya sakar mata. Yana da nashi kyawun amma babban abin da ya zame masa jari bai wuce yanayin jikinsa ba. Ga tsayi ga kaurin da bai kai a kira shi kiba ba. A idonta gani tayi kamar ya fad'a. Haushin matarsa ya kamata. Ta yaya mace za tayi sake mijinta ya dinga ramewa saboda rashin kulawa da abinci? "Mom dina tana gaishe ki" Rausayar da kai tayi gefe tana murmushin jindadi ta ce "ta sanni ne?" Dariya ya yi mata yana mai cewa babu wani abu nasa da mom din bata sani ba. "Idan ta dawo daga Dubai har gida zamu je ki gaisheta." Ayaah sai tayi murmushi. Ina ita ina zuwa gaishe da uwar saurayi? Ba Anti Hasiya da Babansu ba ko su Anti Fati da kakarta Larai sai sun kusa yankata. Yawo ba tarbiyarsu bace. Idan ya sake tayar da zancen a gaba za ta kirkiro hanyar fitar da kanta don babu inda za ta je. Ledar hannunta ta mika masa ya dinga godiya da shi mata albarka. Harda cewa wai ya akayi ta san yana jin yunwa? Filas din wan can karon da na yau ya yi mata alkawarin kawowa duka a washegari. Wurin karbar ledar ne ya samu ya hada da hannunta ya matse. Gabanta taji ya yi mummunar faduwa taja hannun da sauri amma ta kasa kwacewa saboda ya rike gam. Ja ta sake yaki saki sai ma wani irin shafawa da ya dinga yi a hankali yana mai bin kwayar idanunta da kallo da nasa da suka yi alamun tausayi. Ilahirin jikinta babu inda baya rawa kamar mazari. Cikin dabara ya rage tazarar dake tsakaninsu. "Ki dago ki kalleni Ayaah" ya ce a kasalance. Kasawa tayi sai girgiza kai da take yi tana son cewa ya saketa. Danladi sai ya saka yatsunsa biyu ya dago kanta. Runtse idanu tayi da sauri taji ya yi karamar dariya. "Kunya ki ke ji? Gashi ni kuma mutum ne mai son kulawa. Kulawar da na rasa a gida. Ina fata da addu'ar ki cike min wannan gurbin ki hanani tunawa akwai kowacce mace bayan ke. Idan kin amince min zan yiwa Mom magana kawunnai na su zo ganin Baba." Runguntsumi sunan abin da Danladi ya yiwa Ayaah domin yaji dadin isar da mummunan kudurinsa. A lokacin da yake son bude mata ido da haramtacciyar mu'amala ya kama zuciyarta a hannu ta hanyar nuna mata yana sonta. Banda haka ya hada da maganar aure da mata ke so a wannan zamani. Sannan ya rufeta ruf da ya nuna mata cewa za ta zo gidansa a matsayin mai share hawaye. Wannan tunani ke sanya mata mugun tausayin namiji da ganin ba zai rayu babu su ba. Da kyar ta iya mallakar tunaninta ta ja jikinta baya. Muryarta ko fita bata yi sosai ta ce, "Ka sakar min hannu don Allah. Kaga babu kyau." "Nima ba zan so yin abu mara da ke ba. Kiyi hakuri" ya ce yana sakin hannun. Ko sallama bata yi masa ba ta fita daga soron. Ya kwashe da dariya "Kin kusa samuwa." Ficewa ya yi abinsa da ledar abinci ya tafi gida. Yana zuwa ya bawa Raiha yana wani cin magani. "Sai ki saki ran ai. Baki san irin kokarin da nake domin samar muku abinci ba. Don na karbi darin dazu ki ke ta kumbure kumbure. Ki zuba min ku ci sauran" Bude filas din tayi ta ganshi shakare da abinci sai kamshi yake. Cikinta ya bada wani uban sautin yunwa. Da sauri ta samo faranti ta dibar masa sannan ta taso yaranta tana basu tana ci. Tambayar inda ya samo abincin bai zo mata ba don ta zata sayowa ya yi. * A dakin Abbas iyalin Honorable Habu suka hadu ya nuna su ga Abdulkarim wanda tausayin Abbas ya kusa saka shi kuka. Addu'ar samun lafiya ya yi masa tare da jaddadawa Honorable lallai ranar litinin a mayar dashi asibiti. Duk abin da ake ciki a sanar dashi. Hasiya tsabar farinciki sai da tayi kuka. Da zai tafi tayi masa tayin abinci sai ya ce a zuba masa ya tafi dashi. Dan filas din da yake madaidaici mai kyau shi Ayaah ta kai wa Danladi. Aka yi neman duniya aka rasa. Murja sai rantsuwar ta wanke shi take yi. Hasiya ta ce babu komai su bar maganar kada bakon yaji. Na maigidan ta saka a leda aka bashi. Bayan tafiyarsa ne ta rutsa Ayaah a kitchen ta tambayeta inda ta kai shi. "Lokacin da zaki fita wurin bakonki na ganki da leda da abu kamar shi sai dai ban zata abinci ki ka diba ba shi yasa ban miki magana ba." Sunkuyar da kai Ayaah tayi. Hasiya ta daure fuska saboda bata so hasashenta ya zama gaskiya ba. "Na zata mun wuce wannan matakin Ayaah. Kin sani sarai rowa ba halin gidan nan bace amma ba zan lamunci yiwa saurayi girki ba! Wato dalilinki na karbar girkin Ummita kenan? Bai ji komai ba ya karbi abinci a hannunki ko mahaifinki bai taba gaisarwa ba?" Tuni zuciya ta soma tunzurata. Ba za ta iya jure kalamai marasa dadi a kansa ba. Idan ba a tayata tausayinsa ba ai bai dace a aibata shi ba. "Anti matarsa ce fa bata girki. Shi ne na zuba mishi ba roka ya yi ba. Bata yi masa komai ko ya roka sai taga dama." Hasiya sai ta hadiye fadanta ta kirkiro murmushi ganin abin ya girmi abincin da ta bayar. "Kin kyauta da ki ka taimaka masa amma nan gaba ki dinga tambayata kinji ko? Kuma ki ce lallai zuwa na gaba ya zo mu ganshi." Ayaah sai murmushi. Tasa hannu ta rufe fuska sannan ta tashi a guje tana yiwa Hasiya godiya. Ita kuwa bayan tafiyar Ayaah daki ta koma ta rafka tagumi. Gabadaya saurayin bai yi mata ba daga jin furucin Ayaah. Maza masu tonawa iyalansu na gida asiri ba mazan kwarai bane mafiya yawan lokuta. Ta kuma fuskanci ya riga ya fara dasa mata wani tunani. Tashi guda idan ta nemi rabasu za a iya samun matsala. Gida za taje suyi shawara da Salima don ta fita fahimtar halayyar yara. Shawarar data bata kwanaki ita ce ta taimaka wurin kara kusantasu da juna. *** Ginin shopping mall din su Abbati ya yi nisa. Hankali kwance komai yake tafiya yadda suke so. Ga tafiyarsu Italy asibiti tana ta matsowa. A lissafi nan da kwanaki goma sha bakwai zasu tashi. Suna fata idan an dace babu wani abu da zai yi saura a tare dasu na bukatar jinsinsu. A gefe guda suna cike da farincikin daina jin motsin Shazali. Tun zuwan da Munzali ya yi gidansa ya masa dukan nan akan tafiyar Abbati bai sake nemansu ba. A zatonsu an rabu kenan... Yau ta kama Alhamis suna site din gininsu tare da masu aiki ana ta lissafin kudaden da zasu kawo domin siyan wasu kayan aikin. Hankulansu sun raja'a kan abin da ke gabansu wayar Abbati ta soma ringing. A hannunsa take ya juyo da ita yaga sunan Farha ya bayyana a screen din. A take zuciyarsa ta doka dan tsalle sai kuma ta koma ta kwanta. Tun zuwansu Kaduna da bai hadu da ita ba yake kiran wayarta a kashe. Yau kwana biyar sannan za ta kira shi. Yana son dauka yana jin tsoron me za ta ce. Muryar Munzali yaji wanda ya zuro kai ta kafadarsa. "A haka dai kamar za kayi abin arziki amma daukan waya ya gagareka. Tsoron me kake ji ne?" "Ni kar ka kara min tension ka matsa ka bani wuri" Abbati ya bashi amsa yana kokarin matsawa gefe domin yaji dadin amsa wayar. "Ita ma fa tana sonka" Tsayuwa Abbati ya yi ya juyo ya kalli Munzali da murmushi kamar Farha da kanta ta fada masa. "Ai fa na kasheka da dadi to dauki kada ta kuma tsinkewa" Munzali ya ce yana kara yi masa dariya. "Kaima ka ce wani abu. Bari na sallameta zan gamu da kai." Gefe ya matsa don idan Munzali ya saka shi a gaba kila hirar ba za tayi armashi da kyau ba. Yana dauka yaji zazzakar muryarta mai taushi tana magana. "Ya Auwal" Shiru...Abbati ya sake nutsewa cikin kogin son Ya Farha. "Ko dai wrong number na kira?" Tayi tambayar da murmushin da yake kan fuskarta tun lokacin da ta yanke shawarar kiransa da sunan gaskiyarsa idan ya dauki wayar. "Ki ka ce baki san shi ba" Abbati ya fada a hankali da ya rasa me zai ce. "Na san shi. Kararsa ma na kawo maka" Sai da ya jingina da bango ya cigaba da sauraron bayaninta. Korafi tayi masa na rashin nemanta ranar da yaje Kaduna a wurin 'yan uwanta. Ta tabbata da ya yi hakan dole zasu kai shi gidan kakaninta. Ita kuma wayarta ce gida na taro aka nema aka rasa a ranar. Ba ita tayi sabuwar waya ba sai da safe kafin su taho Kano. Kin fadawa Alh. Tahir wanda zai saya mata sabuwa a guje tayi. Sai da safen Mami Khadija ta bata kudi ta saya. "Kina nufin iskar gari daya muke shaka? Shi yasa yau nake jina daban." "Uhummm. Wane canji aka samu?" "Iska mai dadi, gari yana kamshi, zuciya kuma sakayau." Farha sai ta kama dariyar yadda yake magana. Kwatancen inda suka yi masauki ya nema ta ce ba za ta iya gane komai a hanyar ba. Wata 'yar uwarsu ta samu 'yar gidan da suke tayi masa kwatancen. Hira suka yi inda take fada masa daurin auren kanin Maminsu ne za ayi ta kuma gayyacesu. Hoton IV din za ta tura masa ta whatsapp don bata san unguwannin Kano ba. "Idan kun fita ki dinga kallon hanya tunda zama ya kusa kawo ki." Kunya kuwa ta kamata ta ce "Ni sai anjima". "Mu jima da yawa Ya Farha sarkin kunya. Yau dai tunda bikin na yamma ne ba zan zo ba. Amma gobe da jibi kafin ku koma in sha Allahu zan zo." * Anyi kamu ranar Alhamis din tare dasu Mami Khadija da suka iso ita da sauran yaran. Ranar Juma'a kuma sai bayan magariba za a tafi wurin dinner. Farha ta sami Lilu tayi masa famfo akan ya tambayi Mami ko zasu sami kati guda biyu tunda event din card admit ne. Shakiyanci ya yi mata kuwa son rai tana shanyewa sannan ya tafi wurin Mami. Yana gama fada mata zancen da ya tsara ta girgiza kai tana murmushi. "Dama kai ai ko ba aiko ka aka yi ba nayi tunanin za ka iya nema musu." Shafa kansa ya yi yana dariya "wallahi Mami don ba ki yi musu kallon kwaf bane amma sun hadu." "Allah Ya tsareni da yi musu kallon kwaf" ta ce tana mikewa da dariya. Babu wanda ya san irin farincikin da take ciki sakamakon soyayyar da taji akwai a tsakanin Abbati da Farha. Sun yi sa'ar samun katuna a wadace daga wurin dangin amarya masu shirya dinar. Hakan kuwa ya faru ne saboda suma zasu yi tasu a Kaduna idan an kai amarya. Yadda suka basu da yawa shi ne aka ramawa kura. Guda biyun ta bashi ya tafi yana murna. Suhaib ya kaiwa domin su ji dadin karbar gayyatar shi kuma ya kira ya fada musu. * Kafin lokacin masallaci dama Munzali yake da nufin zuwa dauko Qibdiyya yau. Tunanin zuwansu dinner din gashi Kande bata dawo ba sai washegari sai ya kira Abbati ya fada masa. "Kada ma ka fara tunanin soke daukota zuwa gobe. Ko so kake a fara ganin kamar akwai uzurin da za ka dinga fifitawa akanta?" Cewar Abbati yana tsaye a cikin wani bakery. Duk wani cake da ya san tana so ya saya yana jiran turn dinsa ya biya. Munzali ya sha kunu kamar suna tare ya ce "Ka gama kashewa yayarmu murya ni kuma ka dinga yi min masifa. Ya yi kyau!" Daga inda Abbati yake har hasko fuskar tasa ya yi. Dariya ya dinga yi masa, "Ai kaine da wani zance kawai don za ka je tsara budurwa baka son babyna ta bata show." Shi ma dariyar ya yi "Dadin abun kaima tsarin nan dai zaka je. Tun wuri na fada maka idan mun tafi da ita a wurinka zata zauna ku kare kalau." Da haka suka yi sallama. Munzali ya kira Mardiyya shi kuma Abbati gudun kada Munzali ya shashantar da dauko Qibdiyyan yau ya kira Zakiyya ya ce mata yana hanya. Abu ne da suka saba dama. A wajen kaita gidan ko daukota daya daga cikinsu ke zuwa ko suje tare. Tunda Zakiyya ta san da tafiyar tun kwanaki biyu ta riga ta hada mata 'yan kayanta. A can dinma tana da kaya domin dakinta guda. Hatta uniform akwai koda watarana dalili zai sa ba a mayar da ita da wuri ba. Fitowa tayi daga daki tana kwala mata kira domin ta zo ta shiryata. Duk inda take tunanin samunta ta duba babu Qibdiyya babu dalilinta. Hankalinta tuni ya fara tashi tunda ta tabbatar tare suka shigo gidan daga gidan kitso. Dakin mahaifiyarta ta sake shiga ta gama tashin hankalinta. "Umma kamar fa bata gidan nan. Kuma ga kofar gida a rufe." Umman tasu kanwa ga Asabe ta mike ita ma cikin firgici. "Taso min Daddy ya zo ya fita a dubota. Ba har gara Munzali ya zo ace bata nan ba da wannan Abbatin." Daddy din kanin Zakiyya ne. Hanyar dakinsa ta nufa da gudu gudu sai gashi tana kama kofar dakin shi ma ya kama ya bude. Wata mayyar jallabiya ce da ya nacewa a jikinsa yana murmushin yake. A gefensa kuwa Qibdiyya ce tayi tsilli tsilli da ido. Dariyar da bata kai zuci ba Daddy ya yiwa yayarsa. "Oji-oji (hide and seek) muka yi miki kuma baki kama mu da wuri ba ko Qibdiyya?" Ya furta yana tsare yarinyar 'yar shekara biyar da idanu. "Eh" ta amsa babu wani kuzarin kirki a tare da ita. Zakiyya haushi ya kamata duk bata kula da yanayin fuskokinsu masu dauke da labarai iri-iri ba. Hannunta tasa ta tankado kan Qibdiyya gabanta. "Bana son irin wannan wasan, kada ki sake. Wuce muje ki canja kaya." Tana sake turata Qibdiyya taji wani irin azababben ciwo ya tsirga ta tsakanin kafafunta. "Washhh Mama." Kafin Zakiyya ta gama juyowa har Daddy ya sunkuceta ya yi gaba. "Daga yi miki wasa sai ki dinga hankadeta? In wasan ne ba kya so an daina yi dake." "Ku wasa ya dama. Kayanta suna kam gado. Kayi sauri ka shiryata kafin azo daukarta, dama karatu nake Abbatin ya kirani." Falo ta koma inda ta bar wayarta ta dauka ta cigaba da karanta novel din da aka yi update gabanin wayarsu da Abbati. Bata ji komai ba ta nutse cikin karatun ta bar kankanuwar 'yarta a hannun baligin namiji wai ya shiryata don kawai tana takamar shakikinta ne. Ba yau ta fara ba. Son jiki ne ko sakaci? Allah Masani. "Saka mata pant." "Jeki Uncle Daddy ya yi miki wanka kafin na gama." "Daddy shafa mata mai." Aikin Zakiyya kenan. Idan ka bibiya kuma zaka samu ba wani abin kirki ne ya tsareta ba da har kula da tilon 'yarta yake yi mata wahala. Gashi bata son takura. A haka ma don anyi sa a Ummansu tana tsawatarwa duk lokacin da ta gani. Ta kan ce mata wannan zamani da uba yake haikewa 'yar cikinsa bau dace tana sakacin sakarwa kaninta ragamae Qibdiyya haka ba. Kowane dan Adam baya rasa makusa. Wannan dabi'ar ita ce ta Zakiyya. To shi ma Daddy ba yau ya fara latse 'yar yayar tasa ba tare da barazana. Na yau dinne sai yaso wuce gona da iri. A cikin dakin daure fuska ya yi katamau yana yiwa Qibdiyya kallo mai ban tsoro. "Kina fadawa wani zan sani kuma sai nasa wukata mai kaifi na yanka wuyan Daddy dinki (Munzali) da Papa (Abbati)." Girgiza kai tayi da sauri tana mayar da kwallarta. Bidiyo din da yake nuna mata na yadda aka yanka wani mutum ta tuna ta runtse ido "Allah ba zan fada ba." "Ko kefa " Ya dan kalli jikinta "babu zafi ko?" "Uhmm" ta ce da saurinta tana gyada kai. "Good girl." Abbati na zuwa Daddy ne ya rakota har mota suka gaisa sannan ya ja suka tafi. Abin mamaki a gareshi bai wuce rashin kuzari ko digo a tattare da Qibdiyya ba. Kafin su isa gida ta cure jikinta a bayan mota tayi bacci. UWA UWACE...25 Batul Mamman💖 A kafada Abbati ya saba Qibdiyya daya hannun kuma ya dauko ledar kayan ciye ciyen da ya siyo mata suka shiga gida. Hanne tana zaune a falo tana kallo. Ganinsa da 'ya a hannu da kaya bai sa ta tashi ba balle ta rage masa wani abin. Sannu kawai ta ce masa ta mayar da idanunta kan tv. Ko ta kanta bai bi ba ya shiga dakin da Baaba Mari ta zauna kafin su koma Kirikasamma ya kwantar da ita akan gado. Sama ya haye ya yi shirin masallaci ya sauko har lokacin Hanne bata motsa ba. Shi ya fara yi mata magana yana daura links. Sallahun kula da Qibdiyya ya bar mata ya fita. Tsaki ta buga bayan taji tashin motarsa. Yadda ya bata mata rai shekaranjiya da tafiyarsu Baaba Mari ita ma ba zai ji dadinta ba kuwa. Sama ta haye ta bar Qibdiyyan har suka dawo. Allah Yasa Munzali gidansa ya shiga da tare zasu ji kukanta tana ta kiran Abbati da Anti Hanne. Ransa kuwa ya sosu ba kadan ba. Yana gama rarrashin ya kaita wurin Munzalin sannan ya dawo ya sameta rai a bace. "Idan Qibdiyya 'yar cikinki ce haka zaki tafi ki barta ta tashi tana kuka?" Baki ta murguda bata san ya gani ba ta bashi amsa da rashin kunya. "Sai kaji in da dadi mutum ya nemi abu aki yi masa bayan akwai halin yin hakan." Ya fara gane inda ta dosa amma ya kyaleta ta cigaba da magana domin ya tabbatar. Zancen shekaranjiyan ne dai ta tayar. Tunda Baaba Mari ta zo tayi 'yan kwanaki ita ma sai tata uwar ta zo. "Ai uwa bata fi uwa ba" Daure fuska ya yi da takaicin halayenta. "Gwaggo Jumai ba kishiyar Baaba bace kina jina. Haka kawai idan ta so zuwa gidan nan ba zan hana ba. Amma ba zan yarda ki tsiro min da abin da zai iya zama rigima a gaba ba. Zuwan daya ba zai zama dalilin zuwan daya ba." "To kuwa wallahi...." Dan murmushi ya yi sannan ya katseta "ki cigaba da biyewa Gwaggo Deluwa ta kashe miki aure." Gabanta ne ya dan fadi saboda bai yi kuskure ba. Gwaggo Deluwa ce zugata akan cewa ya kamata innarta ta zo ta kwashi romon arzikin gidan. Abbati sai ya sami damar cigaba da fadin abin da yake jin zai taimaka masa ya dan dawo da ita kan hanya. "Ki bar ganin tana ta cewa ta samarwa 'Yashshafa miji a Kaduna. Idan yaki aurenta kin san ni din dai za a kuma kawowa. Shi yasa take so tayi sharae fage yadda idan can bai samu ba nan din ba za ki kawo musu matsala ba." "Cabdijan" ta furta cikin bacin rai "amma Gwaggo Deluwa ta raina min...." Bai tsaya jin sauran sababin nata ba ya sake ficewa yana murmushi. Sai da suka yi magariba suka tashi shiryawa zuwa dinar. Hanne da rawar jiki yana cewa ta shirya Qibdiyya ta kamata tayi mata wanka. Wurin tsarki ne ta kula tana kanne ido sai ta alakanta hakan da zafin ruwan. Tsaf ta shiryata cikin riga da skirt na lace tayi mata dauri. 'Yar kwalliyar da taso yi mata da ja gira a hada da jambaki da foundation ba tun yau Abbati ya hana ba. Ya kan ce mata komai da lokacinsa. A bar yarinya taci kuruciyarta idan ta isa adon ba sai an koya mata ba. A mota kwanciya Qibdiyya tayi a jikin Munzali, Abbati kuma yana tuki. "Wai ni baka ga canji a wurin Mamana ba? Dan taba wuyanta ko zazabi take yi? Shirun ya yi yawa." Dago kanta Munzali ya yi ya taba wuyan da goshi. "Babyn Daddy akwai inda yake miki ciwo?" Kamar ta nuna masa sai ta tuna kashedi ta fasa. Yanzu ma dai da sauki sosai tunda bai yi mata mai gabadayan ba. Firgici ne ya zauna mata a rai ta rasa walwala saboda bidiyo din da Daddy ya nuna mata. Kai ta girgiza ta sake kwanciya. Gajeren tsaki Abbati ya yi yana cewa "ka gani ta sake kwanciya ko? Kawai kar mu dade mu biya a dubata. Ni dama saboda shirun ne ma nace mu fito da ita ko ta sha iska." *** "Nifa ba soyayya muke ba" Mardiyya ta sake nanatawa Farha da Sauda mai bada labari. "Shi yasa naji yana kiranki Diamond girl" Sauda ta fada tana harararta ganin za ta raina musu wayo. "Saboda a diamond plaza muka hadu ko kun manta?" Sauda bata hakura ba ta sake cewa "Amma ai ke ya fadawa zasu zo da 'yarsu." "Saboda yaga kamar na fiki son yara ne." "Tunda a rubuce yake a goshi ba! Ke dai idan biki ya tashi kada ma ki nemeni don ba zan miki komai ba tunda tsakaninmu an fara boye boye." Farha dariya tayi yadda suke hararar juna kowacce tana son a yarda da zancenta. Su ukun sanye suke da skirt da riga na lace fari da purple. Kowacce kamar sauran 'ya'yan dangi taci gwaggwaronta da kwalliya irin ta zamani saisa-saisa. Dokar Maminsu kuma ta tabbata a kansu don bata yarje musu yawo babu lullubi ba saboda biki. "Duk wadda ta ajiye tarbiyarta tayi yadda take so a bayan idona Allah na kallonta." Da haka ta kashe musu jiki domin da fari har Sauda da Mardiyya sun fara son bin sahun 'yan mata 'yan uwansu. Da suka kiyaye mutumcinsu kuwa sai suka dinga jinsu a sama a wurin bikin sabanin marasa mayafi. Sun yi matukar kyau kamar a daukesu. Hankalinsu kwance basu da damuwar komai. Jiddo da Mama Nasima ma duka sun zo saboda biki dai na kanin Alh. Tahir ne ko bai auri Mami Khadija ba. Inda suka zauna ma dai taron 'yan uwa ne daga masu sabbin goyo sai marasa aure anata hira. Kiran Abbati da sanarwa Farha da ya yi cewa sun iso ya kara karfin shewarsu. "Farha da saurayi? Lallai yau zamu yi farin gani a wurin nan." Cewar wata sa'arta wadda a yanzu take da ciki na biyu. Idanu suka dawo gareta kowa na fadin albarkacin bakinsa. Abin ne da mamaki saboda duk lokacin da ake haduwa irin haka ana hirar samar sai dai tayi murmushi. Idanu suka saka mata suna jiran ganin waye ya ciri tuta. 'Yar kwallarta ta samu ta danne saboda ganin yadda suke ta murna. A baya din ma basu san babu bane ba wai tana boye shi ba. Zuga guda ce ta biyo su suka tsaya daga bakin kofar shiga inda ake nuna kati ana jiran su shigo da bakinsu. Farha da ta fisu tsiya sai ta fadawa Lilu ta ce ya shigo dasu. Idan akwai saukin mutane ma ya fara kaisu su gaisa da Mami Khadija. Shi kuma sai ya kira Suhaib saboda katinansu suna wurinsa. * Ba tare da wata shan wahala ba Danliti ya iso venue din da Anti Jiddo ta fada masa ya zo ya sameta. Yau bai yi karambanin daukar motar garejinsu ba saboda ta san ko shi waye. Gara ma ya nuna mata fakirancinsa da kyau domin ta kara sakar masa bakin jaka. Yana sauka daga adaidaita sahu ya kirata ta fito waje. Ba karamar kwalliya tasha ba. Mayafinta a kafada daya ta rataya shi sai karamar jaka a daya hannun. Ba ciki take son su shiga ba. Hasali ma idan ta sami faraga so take su dan zaga hotel kafin a tashi daga taron. Shi yasa ma ta san yadda tayi Alh. Tahir ya yarda aka taho da motarta. Dan kanwarsa ne ya tuko kuma ana zuwa ta karbe mukullinta. (ZINA kenan. Ma'abocinta baya taba cin bulus. Da wuya ne idan bata dawo jikinsa yadda zai yi masa ciwo ba.) Kasa dauke ido daga kallonta Danliti ya yi har ta iso tana girgiza masa jiki. "Ka san kana so amma nake turo maka hotuna kana ja min aji" Jiddo ta furta tana kashe masa idanu. Busassun labbansa ya lasa cike da shu'umanci a zuciyarsa ya ce "ba so ne bana yi ba karfina kawai aka fi." A kagauce ta ce "Akwai inda zamu iya zuwa kurkusa don na dawo da wuri?" Da ka ya amsa mata saboda irin kallon da take masa da motsin jikinta duk sun hargitsa masa lissafi. Danna remote tayi motarta dake gefe tayi kara alamun lock din ya bude. Da ido ta nunawa Danliti ya shiga tana wani irin kakkashe masa idanu kamar wadda ta sha kayan maye. Danliti ya kama hannun kofa zai bude kenan Suhaib ya isko su. Ta gabansa Anti Jiddo ta fito tana waya da Danliti ya zo bata kula dashi ba. Fitowarsa kenan zai shigo dasu Munzali. Uzurinsa yaso karasawa da ta wuce sai dai karairayar da ya hango tana yi da girgiza jiki ya matukar kada hanjinsa. Yau ko mahaifinsa ne baya jin akwai dacewar tayi haka a gabansa a waje irin wannan ba. Jikinsa ya yi matukar sanyi da yaga irin kallon da Danlitin yake binta dashi shi ma. Maganganunsa basu isa kunnuwansa ba sai dai ganin suna neman shiga mota ya karar da hakurinsa. Baya son dasa musu zargi bisa hasashe amma duk da haka baya jin zai iya dauke kai. "Anti Jiddo ina zuwa haka ana ta nemanki a ciki." Sakin mukullin tayi ba shiri sakamakon gumin da ya karyo mata ba shiri har tafin hannu. Daburcewa tayi gabadayanta ta juyo. "Me ya fito da kai ana tsakar taro Suhaib?" Kallon tuhuma ya yi musu duk suka ji kamar ya yi musu tsirara a waje. "Baki gareni zan shiga dasu." "Oh...to sai ka dawo." Anti Jiddo ta ce da murmushin yake tana fatan ba zai yiwa Danliti magana ba. "Kai kuma fa?" Ya ce da Danliti fuska a murtuke. "Am, ammm" Wani mugun kallo Suhaib ya dinga yi masa sai ya rasa abin fada duk kwarewarsa a karya. Anti Jiddo da ta san koma meye ita ce a ruwa sai ta ce makanike ne zai duba mata mota. "Waye ya turo miki shi?" Tambayar ta fito babu digon fara'a a fuskar Suhaib gareta. "Kawata. Eh kawata ce ta turo shi." Ta amsa da rawar murya. Hannu kawai ya mika mata "bani mukullin naki. Idan na raka bakin ciki sai na bi shi. Gani ga Lilu ace kin tafi gareji a daren nan Abba ma ba zai barmu ba." Jikinta sanyi ya yi ga wani irin bacin rai da yake cinta. Danliti zuciyarsa kamar ta fado don tsoro. A haka ya daure ya ce, "Kawo na tayar na fara dubawa kafin ka dawo. Idan dole sai mun je garejin zan gani." Shiga motar ya yi ya tayar ya shiga danna totir ya leko da kansa da ya jike da gumi. "Ina jin ma ba sai mun je ba." Ya dubi Anti Jiddo "Hajiya bakin mai kawai za ki canja." A firgice ya mikawa Suhaib mukullin ya kara gaba ko waige babu. Suhaib ma sai ya bawa Anti Jiddo ya tafi inda su Abbati suka yi parking ko kallon kirki bai kara yi mata ba. Kwafa kawai tayi tana tsine masa a ranta. Uban da ya haife shi ma yawo yake bata ga wanda zai hanata more rayuwarta ba. * Gaban Farha ne ya fadi da su Abbati suka shigo hall din. Bata jin rashin samun masoyi da wuri ne yasa take ganin ya burgeta a komai. Yanzu kam shigarsa take kallo. Kayansu iri daya da Munzali. Yadi ne ruwan toka anyi musu dinki mai gajeren hannu. Kawunansu da hula ita ma iri daya babu bambanci. Wurinsu Mami Khadija Suhaib ya fara kaisu suka gaisheta. Lilu yana wurin ya dauki Qibdiyya wadda take makale a hannun Abbati yana tambayarta sunanta. "Lilu sarkin yara. Tun yanzu zan fara yi maka addu'ar bibbiyu da uku uku." Cewar matar wani kanin Mami din. "Ai kuwa matata ba sai ta dauko mai raino ba Anti. Ta dauki daya na dauki daya." Mami Khadija ta girgiza kai tana kiransa mara kunya su Abbati suka yi murmushi. Iyayensa dake wurin kuwa dariya suka dinga yi masa anata tuna kuruciyarsa da yadda yake daukar musu yara yana musu wasa. "Kaisu su zauna mana" Mami ta ce da Suhaib wanda ya kafe Anti Jiddo da ido a inda take zaune. Bayan sun zauna Lilu ya kira Farha ya kwatanta mata inda suka zauna. Tare suka mike da yan uwanta har mutum hudu. Duk yadda taso sai da suka bi bayanta suna dariya. "Gashi can mai sajen" Sauda ta nuna musu shi. Kan kace meye wannan sun riga Farha isa. Kunya ta kamata da taji suna ta yi masa tsiya. "Allah banga laifinki ba Farha. Wannan da ya bayyana da wuri ai da tuni an miki kwace." Wata mai baki ta fada. Abbati kuwa sai ya kada baki ya ce "ba zan kwato ba fa. Ni nan sai Ya Farha." Kafin kowa ya farga Suhaib ya bar wurin saboda wata irin shewa da suka saka. An tara masu baki ne a wurin wadanda duk taro sune iyayen zance. Farha kamar ta nutse a kasa ta juya zata bar wurin. " 'Yan uwanmu kunga ban gama shigar da kaina ba kuna neman korar min ita ko Mun...." Yana waigawa babu alamun Munzali a wurin sai Lilu da yake bawa Qibdiyya meatpie. Ashe wurin zama daban ya ce Mardiyya ta sama musu tun kafin su shigo. 'Yan matan suka gama dariyarsu suka watse. Ya rage su hudu har Qibdiyya. Lilu ma sai ya mike ya dorata akan cinyar Farha. "Zan bika" ta ce da sauri tana daga hannuwa. (ABIN LURA: Yaran da kan gamu da sharrin makusanta ta fannin fyade ko koya musu munanan dabi'u sukan saba da abin fiye da tunanin iyaye. Ba ranar Daddy ya fara taba Qibdiyya ba sai dai ranar ne ya fara nufin zarcewa. Wannan ne ya haddasa masa tsoronsa har ta kaishi ga yi mata barazana. Idan uwa bata kula da 'yar alawa da biskit kadai ake toshe bakunan yara musamman masu wayo ace kada su fadawa kowa. Ba tare da sani ba kwakwalwar Qibdiyya ta saba da abin da Daddy yake yi mata. Lilu da yake kusan tsaransa kuma lokaci guda ya jata jiki sai wancan abu yake neman tasiri a kan karamar yarinya. Gani take abin da Daddy yake mata shi ma kila zai yi. Kuma tunda ya fara da kyautatawa me yiwuwa ba zai kaisu da zancen yanka iyayenta ko ya yi mata mai zafi ba.) Girgiza kai Lilu ya yi ya bata hakuri cewa zai je ya dawo ne sai ga Sauda tazo ta dauketa. Shiru kan Farha yana kasa haka kawai take jin kunyar Abbati fiye da ta kullum. Nasa shirun bashi da nasaba da kunya sai nazarin yanayinta. Zuciyarsa ce take kara nanata masa lallai yabi a hankali saboda ba lallai bayan anyi binciken asalinsa a mallaka masa ita ba. "Ya Farha dago kanki muyi magana" *** Kayan daki gabadaya Uwani tasa Mubasshir fitar mata wurin neman kudadenta. Ko digo bata zargin Salihi saboda haka bai taba faruwa ba. Mubasshir din kuma ta san da wuya yake shigar mata daki. Tafi yarda da cewa wuri ta canja musu amma har yanzu shiru. Ga dadin bakincikinta yadda Ummule take tararta gaba da gaba babu shakka ko tsoro. Da taga wankin hula yana neman kaita dare kawai sai ta nemi Habibu. Ta kikkira wayarsa a iya kwanakin da take neman kudin bata samu ba. Shi ne yau kawai ta same shi a office. "Hajiya, Hajiya" ya dinga yi mata kirari tun kafin ta iso gabansa. Murmushi tayi kanta na fashewa ta sami wuri ta zauna. Bayan sun gaisa ta bijiro masa da bukatarta. Kudinta take so na Hajji ta fasa zuwa. So take ya bata taje ta karasa gyaran gida ta tashi. "Ikon Allah. Metiron lafiya kuwa? Wannan indai ba fitar rabo ba waye ya taba fasa Hajji saboda gyaran gida?" Cike da bacin rai ta ce "ba za ka gane bane Habibu. Wai ni Salihi ya yiwa kishiya? Kishiyar ma kuma wai gida daya zamu zauna. Bana son yin wani tashin tashina dasu domin nafi karfin haka. So nake ya gani a aikace cewa na haifu cikin uwa da uba. Sannan wannan aikin ba gumin banza nake fitowa nayi ba." Yawu ya hadiya. Ta ina zai fara nemo wadannan makudan kudade yanzu? Dama jira yake a fara kiran maniyata ya samfe ba za ta kara jin duriyarsa ba sai an gama dawowa. Wannan ba za ta har ina? "Gaskiya Metiron akwai matsala. Kudi ba zai dawo ba. Na fada miki cewa na riga na biya har Agents sun gama komai. Lokaci ake jira a baku passport dinku." Huci ta kama sai ta ya tsorata. Ta buga ta raya ya daure ya cigaba da cewa sai dai tayi hakuri. Haka ta hakura ta koma wurin aikinta tana ta tufka da warwara. Da shigarta ba dadewa aka kawo mai haihuwa. Matan manyan mutane sun fi ganewa asibitin kudi akan na gwamnati. Yau sai ga tsuntsuwa daga sama gasashshiya. Matar kwamishinan raya karkara ce da kanta ta kawo surukarta. Nakuda ta kamata kuma suna ganin kafin su isa asibitin da take awo za a iya samun matsala saboda ta soma zubar da jini. Shi yasa suka kawota nan saboda yafi kusa. Uwani kuwa sai tayi uwa tayi makarbiya ta hana kowa tsayuwa kan mai nakudar. Kafin likitoci biyun da aka sanar su shigo har ta gama shirinta. Kudi kawai take gani har ta samu indai tayi aikinta yadda ya kamata. "Haihuwa ta nawa ce?" Da kyar yarinyar ta amsa mata "ta biyu." Rage murya tayi ta matsa kusa da ita kamar cikin za ta taba sai ta duka yadda za ta ji ta sosai. "Naga babu dinki a haihuwarki ta farko kuma da alama da kanki ki ka karu." "Washhh Allah..." "Ko" "Likitan ta ce ban karu shi yasa ba ayi ba." Uwani ta dago kai kamar gaske "wace irin likita ce wannan mai neman kashe miki aure? Ke baki dinga jin jikinki a sake ba?" "Innalillahi...wayyo Mamaaa" Jira tayi ciwon ya dan kara sauki ta kuma ingizota. "Zan taimaka miki. Idan kin haihu yanzu da kari kada ki yarda ko kadan ayi miki dinki. Zan jira ki haihu na baki nambata. Wallahi gyara zan miki giredi amma a gida. sai kinfi budurwa a wurin mijinki." "Lahaula wala quwwata illa billah....ki rabu dani don Allah" yarinyar ta furta cikin tsananin azabar ciwo. Ana haka likitocin suka iso. Kafin ma su fara dubata kan d'a ya danno. Ba haka Uwani taso ba haka tana ji tana gani likitocin suka karbi haihuwa. Abin dadi ga maijego wannan ma bata karu ba ko kadan. Uwani sai ta makale a dakin da sunan taimaka mata ta gyara jikinta kafin a fito da ita. "Kar ki cuci kanki na san zafi ne babban abin da yake saka ku gudun dinki. Allura zan miki wadda zata kashe duk wani ciwo. Mazan yanzu masu dan banzan yawo sai da gyara ake samun kansu." Bacin rai muraran ta gani a fuskar yarinyar a lokacin da ta tashi za ta fita daga dakin haihuwar tana cewa "Baiwar Allah ki kyaleni don girman Allah" Tana fita Uwani ta ciji lebe za ta fara zaginta sai ji tayi ance "ni ina so. A nawa za ki min na dawo kamar budurwa?" "Dubu ...." ta soma cewa bayan ta bude labulen da ya raba gadon wadda ta haihu da na mai maganar. Ita ma tsohon ciki ne da ita. Ta sanar da ira cewa an kawota tun dazu anyi inducing amma har lokacin bata fara jin ciwo ba. "Barshi ma. Zan baki dubu hamsin kiyi min aiki mai kyau." Sama ta kalla tayi kwafa "sai na shayar da kai mamaki. Wallahi nafi karfin zama da kishiya." An tabo inda yake yiwa Uwani masifar kaikayi. Nan ta zauna tana yiwa matar da bata sani ba famfo da nuna mata illar rashin gyara irin wannan ga matan aure. Ranar fafur taki tafiya gida sai wuraren uku na dare matar ta haihu. Ta so suyi magana tun lokacin amma ganin manyan likitoci suna ta kai kawo sai ta hakura. Ranta fari kal domin ta tabbata dai matar wani ce. Bayan ta kimtsa an kaita dakin hutu da kanta ta ce a kira mata Metiron Uwani. Da zumudinta kuwa ta shiga ta kara yi mata barka. Matar ta karbi nambar wayarta. "An riga anyi min dinki amma." "Karki damu. Kwancewa zanyi nayi miki nawa. Wallahi na yiwa mata sun fi a kirga masu haihuwa a nan da haihuwar gida ko wasu asibitocin." Ajiyar zuciya ta samun nutsuwa matar tayi sannan suka yi alkawarin ana sallamarta washegari za ta kirata ta bata kwatancen gidanta. Jikin Uwani har rawa ya dinga yi saboda taji kudi. Tana fita matar nan ta dauki waya ta kira maigidanta. Hakuri ta bashi saboda yana ta kiranta lokacin da suke maganar da Uwani bata dauka ba. Farincikinsa na sake samun karuwar zuri'arsu ya nuna mata da tambayar bukatunta idan akwai a lokacin. Murmushi tayi ta gyarawa jaririnta kwanciya sannan ta ce "Akwai mai girma CMD (Chief Medical Director). Ana badakala a asibitin nan karkashin shugabancinka baka sani ba. Nayi karambani na kama maka daya. Za dai muyi maganar a gida. Amma please my dear ya kamata kasa ido sosai." Dariya ya kwashe da ita ta tausayin mai tsautsayin da tayi shuka a idon makwarwa. Matarsa lauya ce mai zaman kanta wadda take hadawa da aikin sa kai na kare hakkin bil adama. I just published "26" of my story "UWA UWACE...". https://www.wattpad.com/1025814941?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=BatulMamman17&wp_originator=f3dsiNVHQhnPpmsrf6Za7OnPVDBoe2EVQfBDpc9b5%2BNiVBLLjSXjNFjYmWPLib9NKigpf3Pq5gfayzx%2BVgnUFyXLVDLaYKjwlmS6DyEDcbfmbovhnzp33%2FJT2vhpPR%2BV UWA UWACE...26 Batul Mamman💖 *** Karfe shida da kwata a kofar gidan Alh. Rabi'u ta yiwa Salihi. Garin da sauran duhu hasken rana bai fara fitowa ba. Wasu magidantan ma basu riga sun koma muhallansu daga masallaci ba. Daga ganin yadda ya ajiye mota zaka san baya tare da nutsuwa. Kasheta kawai ya yi ba tare da ya rufe ba ya fita ya soma doka sallama a kofar gidan. Sallamar tasa ba karamin tsinka zuciyar Salima wadda ko tashi daga kan abin sallah bata yi ba tayi. A hanzarce ta mike suka kusa yin karo da Zara don ita ma ta gane muryar waye. Innayo kuwa iccen da take kokarin turawa a murhu tayi jifa dashi su ukun suka hado a kofar gidan da ko budeta ba ayi ba. "Karbo min mukulli a wurin Alhaji" Innayo ta furta muryarta tana fallasa fargabarta. Babu wani abu ko daya da zai kawo Salihi gidan nan da duku dukun asuba mai dadi. Tare da Alh. Rabi'u Salima ta dawo ya sako babbar riga yana murza idanu don ko sallah bai yi ba. Innayo ya kalla ta jingina da bango zuciyarta tana ta dukan kirjinta. "Aka ce Salihi ne yake sallama." "Ni ne Alhaji" ya amsa daga waje. Nasa hannun ma rawa ya kama yi sai Zara ce ta iya budewa Salihi ya shigo. Daga soron ya durkusa ya gaishesu sannan ya dan sosa keya. Salima da Zara sai suka bar wurin tunda kowa ya fahimci ba tashin hankalin da suke taraddadi bane. "Innayo ki bata hakuri tazo mu koma. Indai akan Ummule ne zan raba musu gida." Alh. Rabi'u ya kalli Innayo kallo na wulakanci sannan ya yi wata irin banzar dariya. "Hajiya Hauwa kenan. Kin nunawa kowa a gidan nan cewa kin fi kowa iya tarbiya da kyawun hali. Rannan har magana ki ka fada mana ni da Asabe akan 'ya'yanki. Sai gashi a tsukin abin da bai kai wata guda ba uku sun dawo gida. Allah Ya kyauta." Wucewarsa ya yi ko waige babu. Salihi kunya ta lullube shi yaji kamar ya nutse a wajen. Numfasawa Innayo tayi ta dube shi da murmushin da ya tsaya a fatar bakinta saboda bacin ran Uwani. "Salihi aure kayi?" Da sauri ya kalleta ba tare da ya iya boye mamakinsa ba. "Uwanin bata fada miki ba?" "Bata fada ba. Allah Ya sanya alkhairi. Sai dai kuma bata zo gidan nan ba." Kansa da ya yi niyar yin kasa dashi ya sake dagowa da sauri hankalinsa a mugun tashe. Jiya bata da aikin kwana. A ka'ida ma kafin la'asar take dawowa a ranaku irin wannan. Sai gashi har bayan isha babu duriyarta. Ya dinga kiran wayarta babu amsa, wanda kuma tana sane don kada ya katse mata jiran mai haihuwar da zata zame mata alkhairi. Abu kamar wasa har goman dare. Nan fa yaji ba zai iya bacci ba dole ya tafi asibitin nemanta. Nos din da suke da aikin kwana ranar suka ce masa ta tafi. Basu san tana nan ba tunda kafin zuwansu ma 'yan yamma sunyi nasu sun tashi. Sai da ya tafi ne daya daga cikinsu ta ganta take fada mata wani yazo nemanta. Haka nan taji a ranta maigidanta ne amma sai taki kiransa. Dole zai yi mata ta dawo gida ita kuwa bata cikin masu wasa da neman kudi. Haka ya koma gida ko runtsawa bai yi ba. Tunaninsa ya tafi akan ko tayi yaji ne saboda zuwan Ummule. Shi ne ya taho gidan da sassafe saboda baya son kowa ma hatta Ummule ta fuskanci da b'araka irin wannan tsakaninsu. "Ikon Allah" ya ce lokacin da yake jin wani irin tsoro a ransa "nima nayi jinkirin zuwan ne saboda tunanin ko ta karbarwa wata aikin kwana ne..." Innayo ba shiri tayi 'yar dariya tana cewa "banda abinka Salihi yaushe zaka dinga magana kamar yau ka san Uwani? Ita da ba wasu kawayen kirki ba ai da wuya ne ta karbarwa kowa aiki." Murmusawa ya yi shi ma. Wayar suka sake kira shiru dai ta ma daina shiga. Innayo daurewa kawai take yi amma gabanta sai faduwa yake yi. Salihi yana tafiya taje ta ballo magungunan hawan jininta tasha. Sun yi dashi zai koma asibitin ya sake dubawa. Idan an tabbatar masa ba a nan ta kwana ba zai kirata ya sanar da ita su san matakin dauka na gaba. Jiri ne ma ya yi mata sallama dole ta nemi wuri ta kwanta. * Wuraren bakwai da rabi Metiron Uwani ta fito daga dakin Haj. Salma wato matar CMD. Bakinta kamar gonar auduga domin Hajiyar tayi mata alkawarin idan aiki ya yi kyau tana da mutane a kalla shida wadanda zata hadata dasu. Duka kawayenta ne a cewarta da suka hayayyafa ana neman tayar da komad'a. Kudin aikin kowacce sun tsayar a dubu talatin. Nuna mata tayi duka matan manya ne sannan ai suna sayen kayan gyara na sama da wannan kudin sosai. Kai tsaye dakin da suke kwanciya ko ajiye kayansu ta nufa ta dauko wayarta. Tabe baki tayi ganin yawan kiran da Salihi ya dinga yi mata. Da yana sonta ba zai munafunceta ya karo aure ba ta ayyana a zuci. Kiransa tayi yana bakin danja zai karaso asibitin. "Naga missed calls ne" ta ce dashi da ya dauki wayar da yanayi na nuna kosawa da kiran nasa. Haushi ya kama shi ya daure ya boye fushinsa. "A ina kika kwana?" "Wace irin tambaya ce wannan bayan ka san ina zuwa aiki? To ina asibiti yanzu zan taho gida." "Sai kin dawo" Yau kam ya yi niyar nuna mata idan ma da gangan take wannan rashin hankalin to bashi da juriyar cigaba da dauka. Ace ko kadan bata ma san tayi masa ba daidai ba? Ta kwana a waje ba waya ba text sai amsa waya da gadara. Wayar Innayo ya kira ya fada mata sun yi magana sai ta roke shi da ya kawo Uwanin gidanta idan ta koma. Ita kuma Uwani wayar kafintanta ta kira cikin sa'a kuwa ya dauka. Kayan gado da kujerun da ta saya a wurinsa ta ce tana bukatar aje a kafa mata yau. Dama ta saya ne saboda tayi gyaran daki idan ta dawo daga Hajji. "Idan kun kusa titin Kofar Famfo ga nambar dana ku kira zai kaiku gidan." Bayan ta gama dashi ta kira mai labule shi ma ya dinka mata ne na iya falo da dakin baccinta. Karin yadi ta ce ya nema irin wadancan za ta zo bayan la'asar suje ya auna labulen sabon gidan a kara. Kafin nan ta san masu gado sun yi nisa a nasu aikin. A son ranta a gama komai cikin kwana biyu ta tare. Ginin da kuma wadannan kayayyakin da ta saya su suka cinye mata kudade. Dalilin da yasa ta shiga rudani kenan akan bacewarsa sarka da kudadenta na daki. Shawarar da ta yanke tun kwana biyu da bacewar kudin ce ta sake fado mata taji kwarin gwiwa. A jikin Salihi za ta fanshi kudinta komai runtsi. Da wadannan lissafe lissafen ta kama hanyar BUK oldsite inda Mubashir yake karatu. Da ta kira shi a waya tsorata ya yi da farko sai yaji ba zancen kudinta bane. Haduwa suka yi ta bashi mukullin gidan nata da bayanin abin da zai yi. Saboda halin rayuwa ta jima da nuna masa gidan tun yana fuloti. Daga nan gida ta nufa zuciyarta kamar an yayyafa ruwan sanyi. Tana tura gate din suka yi ido hudu da Salihi. "Fita zaka yi ne?" Tayi masa tambayar rainin wayo a zuwan ita har lokacin bata san tayi masa laifi ba. "Ke nake jira" Kallonsa tayi shekeke ta wuce ciki tana cewa "wai meye ne kake ta wani bata rai don na kwana a asibiti kamar wani bakon abu?" Dan tunani tayi ta dawo da baya ta ce "Idan saboda ban kiraka bane aiki ne ya min yawa. " Tsabar takaicinta bai bashi damar amsa mata ba. Daki ta wuce tayi wanka ta fito ta sha shayi a gurguje saboda kada Haj. Salma ta kirata bata gama ba. Tana tashi Salihi da Ummule suka fito daga dakinsa. Dakin nata ya bita shi kadai ya sameta tana sauko da akwatuna. "Lafiya?" "Lafiyar kenan" ta ce a yayinda ta dauko wata leda da 'yan mukullaye a ciki. Kwancewa tayi ta dauko wasu masu guda hurhudu ta cirar masa d'ai-d'ai ta damka masa. "Gasu nan mukullin gate ne da na kofar gida. Idan kayi kwanakin cin amanarka a nan sai ka dinga biyoni nawa muhallin ranar girkina." Mamakinta yana neman zarta bacin ransa. Sam ya kasa fahimtar inda ta dosa. "Ban fahimceki ba." Kugu ta rike da hannu daya bayan ta turo dauri gaban goshi. "Na gama gini na ina shirin saka 'yan haya kazo min da waccan abar wai kishiyata kuma kana sa rai na karbeta mu zauna a nan. Sai dai ina so ka sani cewa nafi karfin wannan wulakancin. In Allah Yaso ba zan kara sati ba a gidan nan zan koma nawa. Ba kuma zan yafe maka hakkina ko daya dake kanka ba." "Yanzu Uwani har gida ne dake ban sani ba?" Kwaikwayonsa tayi tana dariya "yanzu Salihi har aure ne da kai amma sai da matar tayi ciki na sani?" Ganin ya kasa cewa komai ta dora da cewa "da ne maza suke taka mata su zauna lafiya amma yanzu kan mage ya waye. Ko an fada maka kudin da nake nema ina yi ne don na mutu ku ci gado kai da 'ya'yanka?" "A tare lafiya Uwani" Daga yanayin fitar muryarsa ma ta gane ba da niyya ya yi mata adduar ba. Shi yasa ita ma ta amsa masa yadda zai ji haushi. "Amin dai. In ka sami sukuni sai ka kawo kudi ko ka sayo gadon da zaka sa a dakinka na can." Ya daina mamaki kamar yadda ya daina jin bacin rai. Hukuncinta sai ya zauna ya yi shawara da kwakwalwarsa sosai. Tafiya ya soma yi ta biyo bayansa da sauri. "Af...baka ji ba. Na ce akwai lissafin da zan maka na abubuwan da bakuwarka ta sace min." Dage gira taga ya yi sai ta hau bayanin cewa ranar da ya kawo Ummule gidan bata ga alamun bakunta a tare da ita ba. Shiyasa rake ganin ba ranar ya fara zuwa da ita ba. A takaice tana zargin ita tayi mata satar kudi da sarka. Katse zantukan da yake ganin matsalar kwalwalwa ce ta kawo mata su ya yi "Idan kin gama shiryawa ki zo muje Innayo tana nemanki." "Ina da uzuri zan biya idan na gama. Maganar sark...." "UWANI!" Hadiye sauran maganarta tayi ba shiri saboda karfin tsawar da ya daka mata. "Ki dauko mayafinki yanzun nan ina jiranki a mota." Bata gama dawowa daidai daga firgicin da ta shiga ba Mubashir ya kirata. Saurin dawo da nutsuwarta daga tunanin me ya sami Salihi tayi ta amsa wayar. "Umma gamu a bakin gate amma KNUPDA sun yi alamar a dakatar da aiki a gidan." Kwakwalwarta ce ta toshe na 'yan dakiku ta dinga maimaitawa Mubashir tambaya daya kamar mai bitar karatu. "Su waye kuma KNUPDA?" *** Farha bata dago da kanta ba har Abbati ya gama fada mata asalinsa da musabbabin zuwansa Kano. Labarin nasa ya sami sauyi ne a wurin silar arzikinsa inda ya ce mata kasuwanci suke yi amma yanzu sun balle daga jikin ubangidan nasu. Ya fada mata unguwar da suke ginin shopping mall da ire iren kayayyakin da suke son zubawa a ciki. A lokacin da yazo gabar da dole karya ce kadai za ta iya rufa masa asiri sai da ya hadiyi yawu mai daci. Da kansa yake jin tsana da kyamar dabi'ar da suka rayu cikinta. Yana son Farha so mai girma. Burinsa idan har ya mallaketa su zamewa juna tamkar warin takalma masu cike junansu. Yadda bashi da sirri da Munzali yana fatan kusancinsa da ita yafi wannan. Ba don komai ba kuwa face sanin cewa duk matsayin aboki matar aure ta fishi. Ita da mijinta aminai ne, masoya kuma ma'aurata. Kimanin minti uku da yin shirunsa amma har lokacin bata dago kanta ba. Tuni ya fara sarewa yana jin ya rasata kenan har abada. Magana mai girma irin wannan ya so ace a gida aka yita. Sai dai kuma tazo masa bagatatan ne da Farha tayi masa tambayar cikin hirarsu. "Don Allah ki dago kan ki ko sallamata zaki yi kada ki ce ba za ki sake iya kallon wannan almajirin dan kauyen wanda ko kwalin primary bai mallaka ba." Muryarsa ce tayi wani irin rauni mai fallasa ruhi da zuciya tana raurawa saboda tasirin soyayyarta a zuciyarsa. Bai gaji ba ya sake yi mata magana domin ya kagara ya san matsayinsa duk da ya gama sallamawa. "Ni ba tsaran aurenki bane Ya Farha, amma wallahi ina sonki da dukkan zuciyata." Farha bata san yadda zata kwatanta halin da Abbati ya jefa zuciyarta ba da kalamansa na karshe. Zuciyarta kara fadi take a cikin kirjinta tana kuma cikewa da wannan bawan Allah dake gabanta. Kosawa ya yi da rudanin da zuciyarsa ta shiga a sakamakon shirunta. "Ko in tafi?" Sai lokacin ta dago da taji ya dan tura kujerarsa baya alamun zai tashi. "Idan ka tafi kana tunanin tsaran auren nawa zai zo?" Ta ce a raunane. Kansa ya gyada da murmushin da ya tsaya a labbansa. Wurin kawai yake son ya bari kafin ya tsinci kansa a kan gwiwoyinsa yana rokon soyayya. Hawaye ne ya zubo mata ba shiri da ta hada ido dashi. Wannan wace irin zazzafar soyayyace suke yiwa juna haka? Da jikakkun idanunta ta dube shi. "Yazo ya aureni kana ji kana gani?" "Kin yarda idan yazo na kore shi ko waye?" Ita ma kai ta gyada masa amma nata murmushin mai sauti ne da jindadi. "Kina ganin su Mami zasu yarda ki aureni?" Ya tambayeta da sabuwar damuwa. "In sha Allahu babu matsala." Gyara zamansa ya yi gami da sakin ajiyar zuciya. Suka kalli juna suka yi murmushi a tare. Abbati ya kasa dauke ido daga kan kyakkyawar fuskarta. "Kin san me?" "Ina dai so in sani" ta lumshe idanunta sannan ta bashi amsa. "Na dan kware a Ingilishi." Farha bata san lokacin da ta kama dariya ba. "To ko mu kara ne?" "Me ya yi zafi daga wasa" Dariya suka yi tare a idanun Mami Khadija wadda ta zo wucewa can nesa dasu da kawayenta. Murmushi tayi ta dauke kanta kafin su farga cewa ta gansu. Fatanta Allah Ya cikawa 'ya'yanta farincikinsu. A zuciyar Abbati kuwa tunani yake kada Allah Ya kawo abin da zai raba shi da Farha. Shi kan shi tsoron girman soyayyar da yake yi mata yake yi. Idan ya rasa ta......baya son sanin halin da zai shiga idan ya rasa ta. * Can daya bangaren inda Munzali da Mardiyya suka zauna suma tasu hirar suke gwanin sha'awa. Hirar irin son da Abbati yake yiwa Farha yake mata tana bashi amsa da tabbacin yayarta ita ma tana kaunar aminin nasa. "Da gaske dai ba sona kike ba ko Mardiyya?" Ya furta daga sama suna tsakar magana. Gabanta ne ya fadi domin tun haduwarsu bai taba kiranta da sunanta ba. Kallon ma kamar tayi masa laifi haka ya tsareta da idanu duk sai ta daburce. "Me nayi don Allah?" Yanayin tsoratar da tayi sha'awa ya bashi. Yarintarta ta fito sosai sai kara shiga zuciyarsa take yi. "Tunda muka zauna nake yi miki zancen su Abbati amma ko ki bata rai ki ce a canja hira. Kamata ya yi nima naci ribar lokacin nan nayi miki hirar zuciyarta da yadda take kaunarki." Sunkuyar da kai tayi tana wasa da wayar hannunta. A haduwarsu da yawan wayarsu ta gane Munzali yana da son wasa da tsokana. Wannan ma yana daga cikin abubuwan da suka sa take son sa. "Baki ce komai ba." Mardiyya sai ta zabi ta rama ita ma ta nuna masa wace ce ita. "To ni me zan ce? Ka kebe 'yar karamar yarinya kana yi mata zancen soyayya." Dariya sosai ya dinga yi yana bude baki ya rufe kafin ya ce "kin ce wani abu. Wato yarinya ko? Bari na tashi na nemi daidai dani a cikin taron nan" Hannuwanta ta daga kamar mai addu'a da ya mike ta soma cewa "Allahumma..." Tsayuwa ya yi yana kallonta cikin wani irin yanayi mai kashe jiki "karasa mana." Sai ta daure fuska ta cigaba "Allah Kasa duk wadda Daddyn Qibdiyya ya gani ya yiwa magana ta ce an kawo kudin aurenta." "Diamond girl" ya ce yana dariya sosai "I love you." A guje ta tashi ta bar wurin har tana tuntube da kujera akan hanya. Munzali ya dinga murmushi yana mai mamakin yadda zukatansu suka zama mallakin yaya da kanwarta lokaci guda. * Filin rawa Lilu yaje ya yi abarsa son rai ya dawo inda Sauda take tare da Qibdiyya. Yarinyar ta sake abinta tana ta yi musu hira. Tana ganin Lilu ta gudu wurinsa. Sauda ta ce. "Baban yara ita ma ka sayeta kenan" Ranar har su Abbati suka tashi tafiya Qibdiyya tana hannun Lilu. Kowa sai da ya shaida yadda tasu tazo daya daga haduwa. Da ya zo sakata a mota shi da iyayen nata babu wanda ya kula cewa kiss ta so yi masa a baki. Dama ce bata samu ba saboda tana yunkurowa ya sauketa a jikin Abbati. Kuruciya bata barta ta dauke shi komai ba. Uncle Daddy ne kadai yake yi mata. Sai kuma mutanen cikin ire iren bidiyo da yake kunna mata ya ce tayi masa abin da ta gani. Ta fanin kallo Zakiyya tana matular kokari don ko fim ta daina kallo a gaban 'yarta saboda kaifin basirar yarinyar. Shi yasa bata da aiki sai karatun waya. Sakacinta a bangaren saka ido ne a cikin gida. A zatonta tunda suka fito ciki daya da Daddy ba zai taba cutar da ita ba balle 'yarta. (Ya ke UWA mai dimbin daraja da martaba. Ba a ce ki sanya zargi da kokonto a tsakanin mu'amalar 'ya'yanki da 'yan uwanki ba. Nagari masu sonmu da gaskiya sun ninka shaidanun. Yana da kyau amma ki kula da irin shakuwarsu ko tsoronsu da yara ke ji. Idan tayi yawa to wajibi ki bi abin cikin laluma ki gano musabbabinsa. Ita alakar da aka gina da taba jikin juna a waje tana da wuyar bari. Shi yasa ma yaran da ake yiwa fyade ko koya musu mummunar dabi'a ake samun wahalar hanasu. Sai kin dinke baraka tsakaninsu da mai koya musu sai suje suna nema a wurin wasu da kansu. ZINA MASIFA CE GA BABBA DA YARO! Rabuwa da ita sai an dage sosai.) *** KIRIKASAMMA Dakin Baaba Mari babu haske sosai saboda ta gama shirin bacci. A kwance take tana ta juye juye akan gado. Jikarta ta wajen Atine da suke kwana tare sai munshari take abinta. Gajiya tayi da tunanin da ya addabeta ta tashi za ta dauro alwala kamar yadda aka koyar dasu a islamiyya. Babu wani abu da ya gagari addu'a, musamman a hada da qiyamul laili. Alwala taje ta dauro a bandakinta wanda Abbati ya yi mata a falo. Da yake fitilar chaji ta kunna tana iya hango tsakar gidansu sosai. Maigidanta ne har yanzu shadaya da kwata na dare zaune tare da Mal. Sa'adu wanda ya yi uwa ya yi makarb'iya akan bakon da suka yini dashi. Su uku har bakon hira suke suna dariyar wani abu da ya fada. Daki ta wuce ta dauki hijabi da abin sallah. Komai a sanyaye take yi saboda wani kwantacwn abu da bata san a ina yake ba yana fada mata akwai matsala. Ko Munzali bai taba zuwa Kirikasamma shi kadai ba. To me zai sa 'yan satittika da nad'in sarautar Abbati shi wannan Shazalin ya dawo? I just published "27" of my story "UWA UWACE...". https://www.wattpad.com/1029251873?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=BatulMamman17&wp_originator=A%2FjBKEA%2FIPJkMQcFon9sHPKf%2BYzihwobswtFyypgUAcyHfG1WzcO47tsfx%2F1d5kzPijXW4%2BSo5KkOcwf5xJ%2BR4xf0WysWT1dYqEA%2BVvMqaK%2FRzw%2BmqlRdh6rqVmac01t UWA UWACE...27 Batul Mamman💖 *** Gari ya waye, rana ta fito tun karfe shida da rabi. Zuwa goma na safiyar Asabar jama'ar dake waje har sun fara jin zafinta. Sai dai wannan zafin ba zai hana masu uzuri a waje fita su gabatar dashi ba. Kamar kowacce rana ga dan Adam, ita ma wannan Asabar ta zo a matsayin ranar kuka, farinciki, dariya, bakinciki, fargaba, alhini da kowane irin yanayi da mutane ke tsintar kawunansu. A safiyar wannan Asabar din ne Uwani ta amsa wayar Mubashir mai tafe da mummunan labari akan gininta. A ranar ne kuma Shazali ya wayi gari a Kirikasamma bayan ziyarar bazata da ya kaiwa gidansu Abbati. Ita ce kuma ranar da Hasiya ta zaba domin kai wa Salima kukanta akan saurayin Ayaah. Duka dai kuma a wannan ranar ne Abbati da Munzali suka je daurin auren kanin Mami Khadija bayan dinner din da suka je ranar Juma'a da daddare. Dinner din da basu baro ba sai da suka tabbatar an sami musayar zukata tsakaninsu da 'ya'yan Alh. Tahir guda biyu. *** Ana kiraye kirayen sallar Magariba Shazali ya isa Kirikasamma. Girkin abokiyar zaman Baaba Mari ne. Tana jin an ce abokin Abbati ne ta fito daga rumfar da suke girki tana fadin maganganu. Ciki har tana cewa "Ban san da zuwan bako ba saboda haka ban girka dashi ba."  Baaba Mari ko tari bata yi ba har ta juya ta tafi. Bakinciki da hassada ba bakon abu bane gareta daga wurin kishiyar dake morar arzikin Abbati. Niyarta idan an kawo mata nata abincin ta bashi. Sai gashi an hada masa gara guda daga bangaren Mal. Sa'adu. Atine da Habi su ma ba a barsu a baya ba saboda kada mahaifiyarsu ta wahala. Kowacce ta aiko da abinci. Ashe kusan karfin girkin ma 'Yashshafa ce tayi. Deluwa ta rasa inda za ta saka ranta domin a burge wannan bako. Mahaukaciyar motar da yazo da ita kadai ta ishi bawa shiga rudani. Akan Shazali ita mai iya hakura da Sha'aib ce kamar yadda take kiransa. Kafin lokacin kwanciya baccin da Baaba Mari ta kasa runtsawa Mal. Inuwa ya shigo dakinta. K'aidarsa ce zaga matansa da asuba da kuma bayan Isha. Da murna ya shigo mata yana yabawa baiwar dansu wanda har masu kudi ke ziyartar iyayensa. "Idan aka kirani da Uban Abbati sai naji duk garin nan babu ya ni. Dubi dai ace mutum mai arziki kamar wannan ne a gidanmu..." Kula ya yi hankalinta ba ya gare shi ya bata rai. "To yanzu kuma me ya faru? Tunane tunanenki na banza akan arzikin danki ne ya sake dawowa?" Murmushin yake tayi tare da kawar da kai domin ko za ta kwana tana bayani baya taba fahimta. "Malam kenan." Komawa ya yi ya zauna yana dubanta cikin yanayin da yaki jinin ganinta. "Ki fadi damuwarki tunda nayi imanin akwai. Yau da ace ba Inna Mairo ce ta karbi haihuwar dan nan ba sai ince ba naki bane shi yasa kike gwada masa halin matar uba ko dan riko. Ni ko da wasa ban taba jin uwar da take yiwa dan cikinta bakincikin samun arziki ba sai ke Mari." "Har yanzu kana ganin laifina don na damu da son sanin silar kudin da mu da danginmu muke ci? Daga zuwa almajiranci sai kudi kamar suna zuba daga sama?" Ransa ya soma baci amma ya danne domin baya son rigima a daren nan. "To meye a ciki? Arziki ba na Allah bane? Kuma yana baiwa wanda ya so bi ghairi hisaba. 'Yan kasuwa nawa ne suka fara a matakin da yafi bara kaskanci amma yanzu sun wuce sa'a?" "Cikinsu kuma kowanne idan an tashi zaka ji an cewa abu kaza yake sayarwa ko yake kerawa. Shin ka taba tambayar kanka me Abbati yake sayarwa? Ka taba ganin wani abu cikin kayan sayarwarsu ya kawo gidan nan?" Shirunsa ya bata damar cigaba da magana cikin lumana. "Malam ni da kai mun sani cewa yaron nan duk fadi tashinsa yana yi ne domin ya inganta rayuwarmu. Kafatanin gidan nan babu wanda Abbati bai shiga rayuwarsa ba." Muryarta sai ya karye tun kafin ta fadi abin da ke zuciyarta "dan nan yaron kirki ne ba don ni na haife shi ba. Amma ina tsoron kada haram..." "Ya isa!" Mal. Inuwa ya furta yana mikewa. Zargin ta dasa masa wanda ko kadan bai so ba. A duk lokacin da son bincikar dan nasa ya bijiro masa sai tsoron abin da zai tarar ya hana shi. Amma yau yaji wani irin nauyi ya sauka a zuciyarsa mai tayar da hankali. "Allah Ya huci zuciyarka. Mu kwana lafiya." Daga wadannan kalaman ya shige uwar daka ta barshi. Ya fita zuciyarsa tana ta wasiwasi. Amma yana zuwa wurin Mal. Sa'adu da ya same shi da Shazali suna hira sai ya tura zarginsa baya. Da safe Deluwa har dakin da aka sauke Shazali  ta tura 'Yashshafa ta kai masa abinci. Ta hada mata da hudubar kwarkwasa domin daukar hankalinsa. To 'Yashshafa ko kadan baiyi mata ba daga kallon farko. Akwai kudi ta gani daga sutura da motarsa. Bashi da wani muni amma mummuman nufin dake zuciyarsa ya tasirantu a cikin ji da ganinsa. Ko murmushi yake idan ka kalle shi zuciya sai ta harba saboda shaidan ya gama dashi. Da zumbura baki tayi sallama kuma yana amsawa ta ajiye a bakin kofa ta gudu abinta. Gara dai a mayar da ita Kadunan ko sa saba da Suhaib. Matsalarta daya akansa bata wuce kaninsa da ya kirata Iya duba-duba ba. Idan ta auri yayansa sai ta tashi tsaye ta saita shi don kada ya rainata. Wajajen biyu da rabi aka raka Shazali  bangaren Baaba Mari zai yi mata sallama. Ita kadai ce a falon nata tana sauraron rediyo.  'Saboda ke Abbati bai isa ya jika min aiki ba. Munzali baya ketare maganarsa. Idan ya ce su komo gareni karshenta da gudu zai biye masa ya amince.' "Zauna mana"  Baaba Mari ta furta da dan karfi domin ta dawo dashi daga duniyar da ya luluk'a. Jikinta har sanyi ya soma yi da ya shigo saboda kallon da ya kafeta dashi yana tunanin yadda zai bata mata da. Gaisheta ya yi da girmamawa da zai tafi ya kawo dubu hamsin ya ajiyeta a kusa da ita. Kudin ma tsoro ya bata tunda bata san manufarsa ba. Haka kawai ya zo ya kwana kuma gari ya waye zai tafi ya hadata da kudi.  "Daukesu don Allah." Nunawa ya yi kamar bai ji dadi ba ya yi magana cikin rashin walwala. "Don Allah ki dauka kisa mana albarka. Na san da Abbati ne ba za ki ce ya dauke ba." "Duk da haka ai kai bakonmu ne. Ni dai don Allah ka dauke nagode." Wayarsa ya zaro yana cewa "tunda baki daukeni d'a ba bari na kira Abbati da kansa ya fada miki matsayina." Matsawa tayi daga inda kudin suke tana sauraron alamar shigar kira saboda speaker ya saka. Sau hudu ya kira Abbati bai dauka ba saboda suna zaune da Munzali suna amsa tambayoyin Alh. Tahir da wasu yayyensa. Sakon text Shazalin ya tura masa wanda ya saka shi kira hannu na rawa bayan ya tashi ya fita. (Ina dakin Baaba Mari a Kirikasamma) Shazali sai ya dauka ya kuma danna speaker a lokacin da Abbati yake magana hankali a tashe. Ya gama birkicewa gami da tsorata. Magana kawai yake yi yana mai jin inama zai iya bude ido ya ganshi a gidan. "Ban gane kana dakin Baaba ba? Shazali me zai kaika gidanmu." "Zumunci mana." "Zumunci? Ko da can ka taba jin na nemi yin zumunci da kai da balle yanzu?" Shazali sai ya kalli Baaba Mari ya marairaice kamar kalaman sun bashi mamaki shi ma.  "Ka bari na fita nan ba wurin wannan maganar bane. Ni kararka na kawo mata akan kasuwancinmu. Sana'ar tana kawo kudi kana neman durk'usar damu." Daga bayan fage (background) Abbati yaji ana kiran sunan wata ya kuma gane muryar mai kiran da sunan wadda aka kiran duka 'yan gidansu ne. Hankalinsa sai ya nemi gushewa saboda tsananin tashin hankali da ya gane da gasken yana gidan. Gargadin da yake yi masa ma a raunane ya fito domin yana daf da fita daga hayyacinsa. "Shazali! na rantse idan ka fada mata wata magana sai ka raina kanka. Hummm....Kai bari kaji in fada maka, idan ka sake ka fada mata abin da zai tayar mata da hankali sai na dauki mummunan mataki a kanka."  Baaba Mari tana daga zaune amma jiri ke dibarta. Hannuwanta ta sanya ta rike gefe da gefen kujerar two seater da take kai a zaune. Idanunta a rufe taji muryar Shazali yana bawa Abbati amsa. Tasa muryar a nutse take fita da wani abu da za a iya kira da nasara. "Kwantar da hankalinka ni hanya ce ta biyo dani na zo muka gaisa. Ban san sadar da zumunci da iyayen aboki laifi bane da ban zo ba." Kashe wayarsa ya yi ya juya ya fita ko sallama bai yiwa Baaba Mari ba. Bukatarsa ta riga ta biya. Ko yanzu kasuwa ta tashi Dankoli ya ci riba. Bukatunsa akan Abbati biyu ne. Ko dai tsoron tonon asiri a wurin mahaifiya da danginsa yasa shi komawa ruwa ko kuma asirin ya tono ya zubar masa da mutumci kamar yadda ya hana shi cigaba da samun kudi. Yadda ya san Munzali yana jin maganar Abbati ko uwar da ta haife shi baya jin ta isa dashi. Umarnin da hani a hannunsa suke. Shi yasa ya zabi biyo masa ta bayan gida. Abbati ya dinga kiransa wani kiran na tarar da wani amma yaki dauka sai da ya shiga mota. Idanunsa na kallon Mal. Inuwa da Mal. Sa'adu tare da wasu kawunnan Abbatin suna ta dago masa hannu. Murmushin mugunta ya yi sannan ya amsa wayar. Shi ya fara magana bai ma saurare shi ba, kuma yana gamawa ya katse kiran. "Zabi ya rage naka Abbati. Kafi kowa sanin cewa ina da abubuwan da zan nunawa tsohuwarka wanda zai sa ta tsine maka yau dinnan ba gobe ba. Ka fadawa Munzali na ce ku same ni a Port Harcourt jibi." *** Awanni uku da rabi kafin waccan mummunar wayar sun zo wa Abbati da Munzali tare da masoyansu da abubuwa daban daban. Ga Abbati da Farha, wata kofa ta karin sani da fahimtar juna ce ta bude musu bayan an dawo daga daurin aure. Sai ta kurewa Suhaib a waje yake yarda magana ta hada shi da mahaifinsa. Sai dai yau ta sha bamban da kowacce rana. Jiya bayan sun dawo daga dinner Farha ta fada masa yadda suka yi da Abbati. Shi da Mami wadda ya fadawa zancen duk sun yi mamakin jin bai yi karatu ba sai na yaki da jahilci.  Tabbas Mami Khadija za ta so 'yarta ta auri mai ilimin boko bayan na addini sai dai kuma ta duba abubuwa da yawa. Na farko dadewar Farha a gida babu wanda ya taba cewa yana sonta (kadan daga cikin shukar Alh. Tahir da zuri'arsa suke girbewa). Yabawa da hankalinsa da mutumcin mahaifiyarsa. Sai kuma ganin girman soyayyar da Farha take yi masa.  Dasu aka daura auren sannan suka bi su Lilu gidan Kawunsu inda aka shiryawa Ango reception. Suhaib ya hango Alh. Tahir cikin mutane. Sai da yaga ya bar jama'ar dake tare dashi ya fito daga karkashin katuwar canopy din ya bishi a baya. "Ga bakin Farha da Mardiyya zasu gaisheka." "Suhaib kenan. To ina kwana?" Cewar Alh. Tahir yana mai jindadin maganar da dan nasa ya yi masa ko a wane yanayi ne. Shi ma Suhaib sai yaji kunya ya dan rissina da murmushi a fuskarsa. Murnar alakar dake tsakanin Abbati da Farha ta cire masa damuwa sosai. Wannan kuwa ya biyo bayan nishadin da yake ganin Mami Khadija tana yi saboda ganin walwalar 'yarta. Kansa ya dan shafa ya ce, "Abba ina wuni? Ya taro?" Bai iya boye jindadinsa ba kuwa "Lafiya kalau. Suna ina bakin? Ko na rannan ne da suka zo gida?" Da Suhaib ya tabbatar masa su din ne sai ya ce su dan jira shi minti kadan zai je ciki ya gaisa da kakaninsu da suka zo. Sannan tunda akwai 'yan uwan Alh. Tahir din mazauna Kano, zai fi son su gaisa dashi a gabansu domin a taya shi bincike. * Munzali ya kasa nutsuwa da Suhaib ya fada musu zasu gaisa da Alh. Tahir da kawunnansu. "Idan wani ya san mu ko wanda ya san mu fa?" Ya ce jikinsa a sanyaye ga wani tsoro yana shigarsa. Idan ka cire Qibdiyya, to Mardiyya ce mace ta biyu da yake matukar so. Asabe darajar haihuwa kadai ta samu a wurinsa saboda watsi dashi da tayi. "In sha Allahu babu komai" Abbati ya sami kansa da karfafawa Munzali gwiwa duk da a zahiri ya fi shi jin tsoro.  Manyan mutane sun halarci daurin auren saboda baban amaryar dan siyasa ne. Shi kuma ango danginsa manya ne a ma'aikatun gwamnati daban daban. Dole su tsorata saboda ire irensu sune abokan mu'amalarsu a baya. * Mardiyya ta gama shiri za ta fito su gaisa da Munzali kafin Alh. Tahir ya kirasu Mama Nasima ta tsayar da ita. Dakin da babu kowa ta shigar da ita ta damka mata wata 'yar leda. "Yi maza ki bude ki saka kwallin kafin wani ya shigo." "Kwalli kuma? Kinga idona fa na saka." Ta matso da fuskar gaban mahaifiyarta sosai. Mama Nasima ta daure fuska da sauri ta kwance ledar ta miko mata abubuwan dake ciki. "Kwallin mallaka ne. Ki saka sannan ki shafa hodar ki fita wurin Alh. Munzali." Ja da baya Mardiyya tayi da sauri bayan ta mayar da kullin ledar tafin hannun mamanta. "Ba zan saka ba." Kiris ya rage Mama Nasima ta mareta  "To shashashar banza. An fada miki mazan yanzu ana sanya a kansu ne? Tun yanzu idan bamu tashi tsaye ba kina ji kina gani wata za ta kwace shi a hannunki. Yau da sassafe Dini (kaninta) ya shigo mota domin ya kawo amma za ki fara yi min shirme." Kwalla sai ta taru a idon Mardiyya. Tana son mahaifiyarta amma taki jinin halayen da ta tashi ta ganta a kansu.  Mama Nasima da ta fuskanci kamar abin bai mata dadi ba sai ta wayance ta koma lallabata. "Kafin ki fara yi min wa'azi tun wuri ki sani ba kayan boka bane. Haba Mardiyya, kamar baki sanni ba? Wannan wani malami ne wanda ya dogara da Qur'ani. Ko kasa zai buga miki sai ya kama sunan Allah." "Mama ni dai ki daina wasa da lahirarki a kaina. Malamin Allah babu ruwansa da duba ko buga kasa." Ba don bakunta da idanun mutane ba da  Mama Nasima ta kai mata duka don haushi. "Baki ji na ce yana Bisimillah kafin ya fara don ya kori shaidanu ba?" Cigaba da maganar zai iya saka Mardiyya yi mata rashin kunya wanda ba halinta bane. Sai kawai ta zabi fita daga dakin cikin kunar rai ta iske Munzali da Abbati a inda Suhaib ya ce suna tsaye.  Tun daga nesa Munzali ya gane tana cikin bacin rai. Wurin wata mota ta tsaya ya ka a ya sameta. Yana isowa wayarta ta hau ruri. Sunan (Mama) ya gani a jikin wayar kafin tayi saurin kashewa. Murmushin yake tayi masa wanda akan ce yafi kuka ciwo. A zuciyarta kuwa tana tararrabin kada Maman ta biyo bayanta. Yanayinta na mai son boye zahirin halin da take ciki ya fi komai damunsa. Karamar yarinya ce da ta dauki nauyin saita mahaifiyarta da boye aibunta. Abin da shi Munzali mai shekaru da suka kusa rubanya nata bai yi ba duk kuwa da shawara da fadan amininsa. A lokacin da Abbati yake masa wannan fadan yana ganin tamkar bai gama fahimtar matsalarsa bane tunda ya tashi gaban uwa tagari. Sai gashi ya hadu da Mardiyya cikin yanayin dake kusanci da wanda ya taso a ciki. Kuma tana gwada sabanin abin da ya dinga yiwa tasa mahaifiyar.  Girmanta ne ya karu a idanunsa tare da wata irin soyayya mai ratsa zuciya. Murmushi ya yi mata ganin duk ta takura kanta tana ta waige waige. "Ashe nayi kuskuren tunanin zan zama mai baki shawara game da abin da ya shafi rayuwarki Diamond girl." A razane ta dube shi sai ta sadda kanta kasa saboda kallon da yake mata ya nuna maganarsa ta jindadi da yabawa ce. "Idan baka bani ba wa ka samu da zai bani?" Ido cikin ido ya kalleta ya kuma kada yatsansa yana mai gargadinta da kada ta kaucewa kallonsa. Daurewa tayi ta cigaba da kallonsa zuciyarta tana rawa. "Zuciyarki ce za ta dinga bamu shawara Mardiyya. Da ka nake tafiyar da personal matsalolina. Amma na gane kan yana kuskure domin a zuciya ne akwai jin kai da tausayi. Tawa zuciyar kuma karama ce akan taki ta wannan fanin. Shin za ki karbi amanar wannan bawan Allahn dake neman hasken bin iyaye ki gyara masa rayuwa? Kin amince na gabatar da kaina a matsayin manemin aurenki? Za ki iya aurena nan da wata hudu da kin kammala secondary?" Murmushi tayi ta cukwikuye fuskarta cikin mayafi. Ga duka tambayoyinsa tana gyada kai na amincewa. * Farha kuwa da ledoji biyu masu dauke da abincin da aka raba na reception ta fito. An yi packaging abincin cikin mazubin roba mai kyau sai lemon ginger da zobo a robobi suma duka masu kyau da dadin rikewa. Ledar da aka saka su a ciki ta gaba sunan ango ne da amaryarsa. A baya kuwa tana dauke da tambarin /D Delight/ kwararru wajen girkin taro tare da abin sha (online cooking classes for Ramadan coming soon in sha Allah. Come and patronize Batul Mamman please.) Abbati kadai ta hango saboda Munzali yana tare Mardiyya. Tun kafin ta karaso suke yiwa juna murmushi.  "Ya Farha kin tayar min da duka kishina da wannan kwalliyar. Ina tafiya ki je ki goge indai ba a ciki zaki zauna ba." Dariya tayi a hankali "so ka ke na dauka da gaske kake har na fara jin nima na isa? Harararta ya yi da jin furucinta ta cigaba da yi masa dariya. Dolensa ya soma tayata domin  gabadaya yana neman shagala da kallonta. "Kin yi yawa ma. Kin kuma san da haka. Fatana kawai kada Allah Ya kawo abin da zai iya shiga tsakaninmu." "Kana ganin akwai?" Sai kuma tayi murmushi "kodayake yawancin kullum sai naci karo da sakon Malama hide my ID idan an kawo kararku." "In sha Allahu ba zan taba yi miki abin da zaki kaini kotun social media ba." Ya furta da alamun tsoron da ta zata na wasa ne. "Allah Yasa" Kasa hakuri ya yi ya dora da cewa "ko kin ji wani abu nayi miki rantsuwa ko meye ya zama tarihi. Zan zame miki miji nagari in Allah Ya so." "Allah Ya yarda" ta amsa da karamar murya. "Da gaske nake sonki Ya Farha. Burina na zama mijin da babu abin da zaki ji a kaina ki yarda kai tsaye ba tare da bincike ba." Kalaman nasa sun fara bata tsoro. Shi kuma firgicinsa akan tunanin idan gaskiya tayi halinta watarana ne. Rokonsa tayi da sigar da bai ga kofar kubucewa ba. "Kayi min alkawari daya Ya Abbati..." "Kina son wani abu ne bayan ni?" Girgiza kai tayi tana murmushi "kwantar da hankalinka ba mutum bane." "Au tohh. Ina jin ki. Nayi alkawarin." "Babu zancen sirri ko rufe wani abu da zai zo tsakaninmu nan gaba. Ko aure ka ke son karawa ka fada min da wuri ba don neman izini ba sai don bani da boye boye kuma bana son ayi min." Jikinsa ya yi sanyi kalau yaji tsana fiye da ta baya game da rayuwarsa. "In sha Allahu irin zaman da zamu yi kenan. Kuma tunda kin amince min zan sanar da iyalina game dake tun kafin iyaye su zo." Hira suka soma gwanin sha'awa basu ankara ba ashe Alh. Tahir ya fito kiran Suhaib domin kiransu Abbati cikin falon. Da ya hango Farhansa tare da Abbati sai da yaji zuciyarsa ta wani takure a kirjinsa. Abu ne dai bai taba ji ko gani ba tun tasowarta. Damuwar da suke da ita shi da Mami akan wannan matsala yana sa ran cewa ta kau. Tahowa ya yi garesu fuskarsa a sake ya ma manta da fushin Farha. Ita ta fara ganinsa ta daure fuska sosai. Bata da yadda zata yi da zuciyarta akan bakincikin  hoton da kwakwalwa ta kasa gogewa. Mahaifinta dauke da kawarta akan cinya daga shi sai dogon wando da singeleti. Wannan abu har ta koma ga Allah bata jin zai taba fita daga ranta. A yadda kuma abin yake mata ciwo har yanzu ta san bata da karfin gwiwar fuskantarsa ba tare da tayi abin da za ta yi nadama a gaba ba. Gajeren tsakin da zuciya tafi karfinta a kai ne ya fito ba shiri a lokacin da take cewa Abbati, "Don Allah zo mu koma daga can saboda idon mutane." Yaji tsakin sannan kuma muryarta ta sauya lokaci guda. Juyawa ya nufi yi domin ganin wanda ya bata mata rai sai yaji ta ce, "Kar ka juya mana.." Sai dai ya riga ya ga Alh. Tahir din wanda fuskarsa take tamkar gonar auduga. Ya juya ga Farha ita kuma tata babu annuri ko digo sai ma kwalla da ta cika mata ido. Sai yaki motsawa daga inda yake.  Yana ganin ta fara tafiya bai san lokacin da tasa muryar ta fito da sigar umarni ba. "Dawo ki tsaya." Sau daya ta kalli fuskarsa wadda ta sauya shi ma babu wasa ko kadan taji kafafunta sun daskare a wurin.  Alh. Tahir yana karasowa Abbati ya durkusa cike da ladabi ya gaishe shi. Ya amsa masa tare da mikar dashi tsaye ta hanyar dago hannuwansu da suka yi musabaha. Wanda kuma Alh. Tahir din ne ya mika masa. "Tashi tashi ai ka zama dana." Wajen sati guda sai yau yasa Farha a idonsa. Amfani ya yi da albarkacin idon Abbati ya janyota barin jikinsa. "Farhan Abba wato tun yanzu za ki min ritaya ko?" Da kyar ta saki jiki ta rabu da jikinsa amma har runtse idanu tayi saboda tsigar jikinta da ta tashi. Mahaifi! Sanin mahaifinka yana zina daban da ganin mahaifinka a yanayin da ya kusanci zina. Yanayi mai nuni da cewa anyi ko ana gabar yi. Its devastating! Kada Allah Ya hadamu ko zuri'armu da mummunan gani irin wannan. Abbati dake dariyar kalaman Alh. Tahir bai fasa la'akari da yanayinta ba. Hakan ya tuna masa da abin da Suhaib ya yi rannan a gabansu na kin zuwa gaishe shi. Ko ba a fada ba ya gane akwai matsala kenan. "Ki bamu aronsa kakaninki da baffani zasu gaisa dashi." Cewar Alh Tahir. Sannan ya dubi Abbati "ina fata kai da abokinka da gaske kuke akan 'ya'yana. Idan akasin fahimtarmu ne a gabanku don Allah kada ku yaudaresu." "In sha Allahu ba za mu baka kunya ba" Abbati ya furta kai a kasa. Alh. Tahir sai ya murmusa "Allah Ya muku albarka. Bari na nemi Suhaib a waya ya shigo daku wurin 'yan uwana." Da haka ya tafi. Farha ma sai ta daga kafa tana shirin barin wurin. Da muryar dazu ya ce, "Farha." Kiran ya fadar mata da gaba. Ya tuna mata cewa Abbati babba ne ta kowacce fuska akanta. Ko Suhaib bai isa ya kara dashi a shekaru ba balle ita. A hankali ta juyo suna hada ido sai hawaye ya soma gudu a kumatunta. Kallon roko da magiya tayi masa sannan ta fadesu da baki. "Don Allah kada ka tambayeni komai." Sai ya sami kansa da yin murmushi "bani da niyar tambaya. Amma duk da haka ina da abin cewa idan kin bani dama." Sai ta dawo ta tsaya sosai lokaci lokaci tana goge hawayenta da bayan hannu. "Yanzu kin ga idan ba ni ba babu wanda zai ce kin burge shi da wannan fuskar da ta baci da kwalli." Sai da yaga murmushinta ya soma magana a nutse. "Ya Farha darajar mahaifi da mahaifiya ta girmi komai da kowa banda da'a ga Allah da ManzonSa SAW." "Na sani" ta ce a raunane wani hawayen yana zubowa. "Ina mai baki shawara da kiyi amfani da wannan ilimin ki bi hanyar da ta dace ta mu'amalarki da Abba."  Babu wasa ko damar tayi masa musu a maganganunsa. Cigaba ya yi har sai da ta fashe da kuka sosai. "Allah SWT Ya yi mana dukkan gata da bai watso mu cikin duniya ba tare da iyaye ba. Daga Mahaliccinmu sai Annabinmu sannan iyaye a girman daraja. Allah Ya ambaci yi Masa biyayya tare da da'a ga iyaye a wurare daban daban cikin littafinsa mai tsarki. Karshe ma dai iyayen nan kin sani saboda adalcin musulunci ya horemu da kyautata musu ta kowacce siga koda mushirikai ne. Illa iyaka kada mu yi musu biyayya wurin saba Masa. Tunda sune abu mafi kusanci da suke tuna mana da Girma da Buwayar Allah. Cikin hikimarSa ya hado mutane biyu mabanbanta jinsi da komai Ya ce musu ga amanar bayiNa wato 'ya'ya. Sai ki ga mutum har sata ya kan yi domin ciyarwa ko dauke wata lalurar wannan amanar. Wani ayi ta cin zarafinsa a wurin aiki amma ya yi ta jurewa saboda albashinsa shi ne abincin 'ya'yansa. So many things dai da ba sai na fada ba. Wasu irinmu mu da bai bawa 'ya'yan ba har kuka muke muna fargabar ko girman zunubanmu ne yasa Allah bai bamu amanar bayinSa su zo a matsayin 'ya'yanmu ba..." Kuka ta fashe dashi domin ya gama daureta da jijiyoyinta. Ta san Qibdiyya ba 'yarsa bace kuma bai ce mata yana da d'a ba. Amma da ya fada da bakinsa sai da ya tabata fiye da zato. "Kayi shiru don Allah, za ka haihu in Allah Ya so....na fahimci kuskurena kuma Allah zan gyara." "A yau ba gobe ba?" "A yau ba gobe ba." Murmushi ya yi ya ce "Allah Yasa ke dinnan rabona ce ta duniya da lahira"  Amin ta ce yadda zai ji domin ita kam bata jin kunyar ya san cewa tana yi masa soyayya mai girma. Duk mutumin da zai gan ka a irin yadda ya ganta ya kuma zauna yana kokarin ganin ka gyara lahirarka baka da na biyunsa. Basu gama hirar ba Suhaib ya zo suka wuce cikin falon tare da Munzali. Da wasa da dariya  dattijan suke yi musu tambayoyi har aka gangaro kan sana'a. Bakinsu a hade suka ce kasuwanci suke yi. Iyayen sun yaba da halayyar da suka gansu  a kai aka shiga barkwanci. Wannan lokacin Shazali ya zaba ya kira Abbati. Kiran da Munzali ya fito ya same shi a mawuyacin yanayi a dalilinsa. Jijiyoyin kansa duka sun fito sai gumi da yake tsatstsafo masa saboda firgici.  "Allah mun tuba. Allah Ka rufa mana asiri" Kalmominsa kenan har suka shiga mota a gigice suka tafi ko sallama basu koma sun yiwa kowa ba. "Idan ya fada mata wallahi da kyar in bata tsine min ba. Munzali yaya zanyi da rayuwata kuma? Me zai rage min idan Baaba taji wannan zancen?" Abbati kuka yake yi. Kuka kamar karamin yaro. Irin kukan da ya manta rabonsa da yin makamancinsa. Bai hada iyaye musamman Baaba Mari da kowa ba. Ita ce mafi girman gatan da Allah Ya bashi domin ba don ita ba kila bayan waccan dabi'a sai ya hada da wasu munanan alfashar. Munzali ma kukan yake yi ya kuma kasa rarrashin Abbati. In ta kwabewa daya ta kwabe musu ne su duka. Hanyar Kirikasamma ya dauka ba tare da tunanin komai ba. *** I just published "28" of my story "UWA UWACE...". https://www.wattpad.com/1069889361?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=BatulMamman17&wp_originator=KFjeRCEYOeCCop1KZemoqtrxbYnKdEUt%2BN3vuRslVOGHXeVyvRctm2H9e2ieXQp2h5na2H8%2FZfP%2Fo%2BHnu2uzK%2BqpwO8SvawBfcO53XyKaH3pEGnYSjnrlqziEAz69pxG UWA UWACE...28 Batul Mamman💖 KULLU AMIN WA ANTUM BIKHAIR. EID MUBARAK✨🌙 (Yau da gobe tasa na fahimci cewa kowane littafi shi yake rubuta kansa. Marubuci zai gama tsari labari da lokacin da yake hasashen kammalawa. Amma da zarar ya dora alkalami ya fara rubutu, sai yadda labari ya yi dashi. A yadda naso da yanzu tuni na kusa gama wani labarin bayan UWA UWACE, Allah bai nufa ba. Labarin ya zo lokaci guda da jinkiri kala kala. Na gode da hakurinku tare da bibiyar lafiyata da kuka dinga yi.) *********** Kallon jan fentin da aka yiwa alamar (×) a jikin gidanta Uwani tayi taji jiri yana dibarta. Tambayar Salihi ta dinga yi cikin sarkewar harshe kamar ya san wani abu a kai. "Me nayi? Ina da takardun filin nan da sa hannu wanda na saya a wurinsa. Kai hatta Mai unguwa sai da muka je yasa hannu a matsayin shaida." Duk da yana cike da haushinta sai ta dan bashi tausayi a lokacin. Ba kuka take ba domin tana da bala'in dakakkiyar zuciya. Jikinta ne kawai ya saki sannan sautin muryarta ya fallasa tsoro da tashin hankalinta. "Ki kwantar da hankalinki tunda akwai takardu za a warware cikin sauki in sha Allahu." Sambatu ta dinga yi kamar ba da ita yake ba. Katangar gidan ta nuna masa inda tasa aka yi baya da ita kawai don tana son ayi mata rela samma tana tsoron kar ta shiga filin gwamnati. Shi dai hakuri ya bata har suka koma mota tare da Mubashir a baya. Niyarsa su je gida ta amsa kiran Innayo sai ta kafe akan lallai ofishinsu can Ministry of Health zata je ta sami Habibu. "Shi ne ya jagoranci sayen filin da komai. Zuwa zai yi ayita ta kare don wallahi asara bata kamani ba." "Waye kuma Habibu?" Salihi ya tambayeta. Bacin ransa na dawowa sabo fil. "Abokin aikina ne. Shi ya tallata min filin ya kuma shige min gaba." "Tunda kin auri lusari ai dole wani kato ya fini sanin halin da kike ciki Uwani." A kausashe Salihi yayi maganar wanda yasa Uwani shan jinin jikinta. Borin kunya ta soma yi masa saboda ta san bata da gaskiya. "Damuwa kayi dani da zaka san me nake ciki? Ko kai ba aure kayi ba tare da sanina ba? Habibu duk inda yaji harkar karuwa zai nemeni. Kafin ka ce ban fada maka ba ma shi na bawa ya biya min kudin Hajji. Bana damu za ayi 'yan bakinciki su daina hura mana hanci." Da kannensa mata take ya sani. Shi yasa bai ce komai ba har suka isa gate din BUK ya sauke Mubashir. Kai tsaye ministry din ya nufa sai ga waya an kirata. Koda ta duba sunan (Costumer) ta gani ya bayyana. Murmushi a take ya maye gurbin bacin ranta. Amsa kiran tayi taji muryar Hajiyar nan da ta haihu tana yi mata magana cikin nutsuwa. Uwani ta ajiye komai a gefe ta saurari kwatancen gidan da matar tayi mata. "Ka saukeni 'Yan Kaba zani" cewar Uwani ga Salihi. "Ai ko direba nake ya kamata ki rissina lafazinki gareni." Yatsina fuska tayi ta gyara lullubi sannan ta hayyako masa da fada tana jin kanta daidai da kowa tunda ta tabbatar zata sami kudi. Cikin kudin za ta bawa Habibu a kashe kurar dake neman tashi a gidanta su sallami KNUPDA. "Sau nawa nake cin arzikin shiga motar taka da har zaka min gori? " Girgiza kai kawai ya yi "wurin wa zaki a 'Yan kabar?" "Stitches zan yiwa wata." "Allah Ya kiyaye hanya." Sauketa ya yi ta fita ta shiga adaidaita sahu. Yadda yake jin bacin rai ba zai juri ja in ja da ita ba. A yau kadai ya gane har yawon dinke mata take zuwa bai sani ba. Sai yake jin kamar ma bai san wace ce yake aure ba. Karya kwana ya yi ya nufi Ministry din yana son ganin wannan Habibun domin zuciyarsa taki nutsuwa. Ba wai zarginta yake ba domin ya yarda da ita dari bisa dari. Duk bakin halinta ya yarda za ta tsare mutumcinta duk inda take. Harka dai ta kudi ce bashi da tabbas. Idan yana son gyara lamuranta ya kamata ya fara da sanin abokan huldarta. Da kwatance da kiran waya Uwani ta isa gidan CMD. Bata wani sha wahala ba saboda kwatancen dalla dalla ne duk da ba a fada mata sunan maigidan ba. Hankali kwance ta shiga wani makeken falo bayan anyi mata iso. Gida ne babba irin wanda take burin mallaka wataran. Nan da nan ta sake ganin kimar hajiyar tana tunanin yadda za ta tatsi naira jikinta da kawayenta matan masu kudi. "Haj. Umma ta ce ki shigo ciki"  Muryar mai aikin da ta shigo da ita ta katse tunaninta. Sai lokacin taji sunan matar. Wata kofa suka bi sai gasu a wani falon da ya shafe shafin inda ta baro. Sai da ta zauna akan wata luntsumemiyar kujera sannan matar ta tafi. Kimanin minti bakwai sai taji sallamar Hajiyar. Fuska ta saki tana mai kara raina kanta. Kama daga sutura zuwa su sarka babu ta inda Haj. Umma bata burgeta ba. Tashi tayi cikin girmamawa tana yi mata sannu. "Ya karfin jiki da jaririnmu?" "Alhamdulillah Matron Uwani. Ya gajiyarki?" ta amsa fuska a sake. Zama suka yi Haj. Umma ta ce bari ta kira Maigidan su gaisa sai su shiga daki ayi. Uwani taji kamar kakarta ta yanke saka yau. Idan tayi sa'a mijin mai alheri ne ai kila shi ma ya bata wani abu. Irin wannan mutanen idan sun yi maka kyauta baka cewa a'a. Kamshi ta fara ji kafin sallamar babban mutum cikin wani irin yanayi na seriousness. Kasa dagowa tayi har ya zauna ta gaishe shi. Muryarsa babu alamun wasa ko digo taji ya kirata da cikakken sunanta. Wani abu da yasa hanjin cikinta kanannadewa da juna cikin azama. "Matron Uwani Rabi'u!" Haka ta daga kai jiki na tsuma. Fuskar da ta gani sai da ta kusa sakin zawo. Basu taba haduwa kurkusa ba amma karya take ta ce bata san kamannin CMD dinsu ba.  "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ta dinga maimaitawa ba ji ba gani da karfi ga gumi yana bin sassan jikinta. Dakewa ya yi domin ba abu bane mai wuya ya tausaya mata ya fasa hukuncin da ya dauka. Bai manta da zantukansu da maidakin nasa ba. Inda take cewa yiwa Uwani sako sako tamkar an ce ita ko wasu su cigaba da haka ne. Dole ne ya tauna tsakuwa domin aya taji tsoro. Laifin Uwani mai girma ne. Gara ace matan ke nemanta da abin da take yi. Akalla idan su suka nemeta a waje babu ruwan asibiti. Yanzu kuwa ana samun tangarda basu da mai kwatarsu a hannun hukuma tunda ma'aikaciyarsu ce. Envelop ya nuna mata akan karamin teburin gilas na gabanta. "Dauki ki tafi." "Ranka. Ranka. Ya dade. Ranka ya dade.." ta soma magana tana waigawa ko matar tasa zata fito. Katseta ya yi ganin za ta bata masa lokaci. "Idan hukuncin da yake ciki bai yi miki ba kina iya kai batun Ministry." Kafin ta samu bakin magana ya fice abinsa. Kasa bude takardar tayi saboda faduwar gaba. Kafafunta kamar an kwashe mata kasusuwa don kiris ya rahe ta zube a kasa. Kirjinta kawai ke dukawa tare da azababben ciwon kai. Ko a mafarki abubuwan da suka faru yau suke samunta ta san cewa sai ta tashi da hawan jini. Shigowar Haj. Umma wannan karon fuska a tamke ya kara tayar mata da hankali. Ita mamakin kasadar Uwani ma take yi.  "Allah Yaso ki duk wadanda kike yiwa aiki ta wannan sigar babu wadda nata ya baci ta shigar da kara kotu. Da license dinki ya dade da barin hannunki. Idan private practice kike son budewa kin san akwai hanyoyi da matakan da ya kamata ki bi domin samun sahalewar gwamnati. Amma son zuciya ya hana. Ace mace tana tsakar nakuda don tsabar rashin tausayi kina tallata mata muguwar sana'arki?" Kalaman cin mutumci ne suka taba fita daga bakinta ga abokiyar aikinta lokacin da ta taba  yunkurin hanata wannan sana'a. Ashe kura ta san gidan mai babbar sanda. A gaban Haj. Umma ko tari bata iya yi ba har ta gama magana. "Ki bashi hakuri Hajiya. Tunda ki ka ga ina wannan abu kin san cewa kudi nake nema." "Kiyi me dashi? Yasa anyi bincike akanki Uwani don kar ya dauki hukunci bisa rashin uzuri. Kina da miji mai rufin asiri. Har mota gareki balle ace kuncin rayuwa ne ya tasoki a gaba. Neman kudi ba hauka bane so kar ma kiyi kokarin justifying laifinki. Ko kina da wata kebantacciyar bukata hanyar da kika biyo bata dace ba." A shekaru wannan matar bata fi kanwarta ta uku ba Salima. Don tana auren maikudi shi ne za ta tasata a gaba da bakaken maganganu? Wannan abu ya tunzura zuciyarta taji ba za ta bar gidan bayan an koreta daga aiki ba tare da ta rama ba. Yatsina fuska tayi tana hura hanci ita a dole girmanta bai zube ba. "Don kin sa an koreni daga aiki kina tunanin zan daina walwala ne? Ana kiran ciwon 'ya mace na 'yar uwarta ne kamar ba a san mata sun fi kowa son ganin karshen junansu ba? Banda munafunci ai bake nake yiwa tallan ba jiya amma kika yi katsalandan kika ce kina so. Auren maikudi ba zai raba mace da talauci ba ehe. Idan kina son burgewa ki nemi na kanki ki wuce wulakancin namiji." Tun farko Haj. Umma bata ga alamun mutumci a tare da Uwani ba. Sai dai ko kadan bata kawo a ranta abin ya kai haka ba. Ranta ya sosu matuka amma haka ta daure taki magana har Uwani ta dire tana yi mata kallon banza. Hannu ta kai ta dauki envelop din da Uwanin bata kai ga dauka ba ta yaga shi gida hudu ta watsar a kasa. Uwani tabi takardun da kallo tana kissimawa a ranta rashin nuna tsoronta ya yi rana. Karshenta matar ta tsorata ne taga gara a bar mata aikinta. Murmushi ta soma yi sai dai bai kai ko ina ba idanunta suka soma cikowa da kwalla sa'ilin da Haj. Umma ta soma magana. Tsaye take kyam kana ganinta ka san mace ce da ta san kanta. Sai tayi mata wani irin kwarjini. "Suspension ne na wata hudu hukuncin da aka yi miki ba tare da kai zancenki ministry ba. Anyi miki haka ne domin kada mu rabaki da aikin da bamu san irin WAHALAR DA IYAYE suka yi wurin karatunki ba. To amma Uwani kin yi kuskuren fada min maganganu son ranki a cikin gidana. Ki koma bakin aikinki daga yanzu idan kin so. Sai dai ina so ki sani cewa in sha Allahu indai ni Barr. Umma Jibril ina numfashi sai kin rasa license dinki ba ma aiki ba." Wuta ce dif ta dauke a kwanyar Uwani 'Barr. Umma Jibril din da kusan duk mai jin Rediyo Kano ya sani?' ta tambayi kanta a zuci. Amsa ta bawa kanta domin tana jin sunan ta alakanta muryar da wadda take ji a rediyon. Da tangadi ta bar gidan don ji take kamar duniyar da ta sani aka kifar. 'Yan uwa da iyaye da mijinta bata ga wanda ba zai yiwa halin da take ciki dariya ba. Zasu samo mafita ko ta wane hali ita da Habibu. Ya san manya a matakai daban daban na gwanati. Idan ta rasa aikinta ta rasa matattakalar rayuwarta ne. Shi ne abin da ta dogara dashi wanda zai kangeta daga talauci. Habibu ta kira. A lokacin yana tsaye a gaban Salihi yayi tsilli tsilli da idanu. Tambayarsa ya yi akan ya hada shi da ainihin dillalan filin da tayi gini sannan ya bashi shaidar biya mata kudin kujera.  Mintuna arba'in da suka wuce Salihi ya tambayi masu gadi ko akwai Habibu a wurin. Tashi daya suka amsa da cewa akwaisu har uku. Biyu manyan ma'aikatane. Daya kuwa sub-staff ne mai shigewa manyan. Yana jin haka ya ce a nuna masa shi. Da ya sanar dashi cewa shi ne mijin Uwani ba karamin mamaki da tsoro ya gani a tare dashi ba. Tambayoyin da ya yi masa suka sashi daburcewa ya kasa bada kwakkwarar amsa. Sai gashi ta kira a wannan lokacin. Gefe ya dan matsa da niyar bude mata wuta da borin kunya. "Habibu akwai matsala. Zan shigo ministry yanzu." Tana cikin tashin hankali a yadda yaji muryarta. Sai ya fasa fadan ya ce  "Don akwai matsala sai ki turo min mijinki ya titsiyeni a cikin mutane?" Adaidaita sahun da ta tare ta hau. Abin da ya dameta daban da zancen da yake yi shi yasa ta amsa shi ba tare da nuna damuwa ba  "Zuwa ya yi? Yace maka me?" Habibu sai ya murmusa ya zabi amfani da amsarta ya tada tarnaki tsakaninsu. In ba hakan ya yi ba yau shi za ta karewa. "Takardun filinki ya ce na bashi da kuma kudin kujerarki. Har yana ikirarin ban isa na fishi sanin matarsa ba. A matsayinsa na mijinki yaba da hakki akan dukiyarki amma ke ce harda yin gini bai sani ba." Abin ya zo mata bambarakwai saboda sanin Salihi shi yasa ta ce "inji Salihin?" "Yasin gashi a nan, na baro shi a gefe da zan amsa wayarki. In kin ce na bashi kwafin takardun sai na bayar." Ya rage murya yadda za ta tausaya masa. "Ka barni dashi. Kada ka bashi komai. Kai kaga ma yi tafiyarka ka bar saurarensa. Wannan wace irin masifa ce?" Maimakon ya wuce gaba sai ya dawo gaban Salihi ya tunkuda hularsa gaban goshi. "Da kai bada izinin matar taka kazo yi mata kutse a harkokinta ba? Ta ce kada na baka komai. Ko kunya baka ji ba bayan kayi aure matar ta sami ciki sannan ta sani, shi ne za ka lallabo rabata da arzikinta. Ku kuke janyowa ana zaginmu ace bamu da tausayi. Haka fa kwanakin baya ka matsa mata da sai ta ranta kudin makarantar yara." Salihi bai taba danasanin auren Uwani kamar yau ba. Banda barin Habibu ya zama uwa da uba gareta yana juyata da sunan shawara harda sirrin gidansa duk ya sani. Allah Kadai Ya san yawan abubuwan da ta sanar dashi. Kala bai iya sake cewa ba ya kama hanyar motarsa yana jiyo dariyar Habibu. Yana hanya  Uwani ta kira shi da tambayar rainin hankali. "Me kaje yi wurin Habibu?" "Na baki rabin awa duk inda kike ki sameni a gidan iyayenki." Da ya ajiye wayar sai kawai ta kama a'uziyya domin ta yarda dari bisa cewa jifa ne ko sihiri aka yi mata. Idan komai zai kwaba bata taba kawowa harda Salihi ba. A zatonta har abada zai kasance tare da ita yana hadiyar bacin rai. Kwafa tayi tare da mugun tsaki lokaci guda da wani tunani ya fado mata. "Tsafi gaskiyar mai shi. Lallai Mulmule kike ko wa? Ni zaki tarwatsawa rayuwa daga zuwanki?" Sai kawai ta soma dariya wanda har ya janyo direban adaidaitan ya dinga kallonta ta madubi. Ita kuwa karfin halin amaryar Salihi ne ya saka ta dariyar. A bayyane yake gareta Ummule ce tayi mata asiri. Banda haka me yasa komai bai faru ba sai da tazo gidan? Wata kwafar tayi ta ce da direban Adaidatan ya kaita Dala. *** "Hummm inji mai ciwon hakori. Ka magantu azo a fara narai-narai da ido ana neman janyo maka zunubin da ba naka ba." Furucin Asabe kenan bayan Hasiya da 'yan matanta sun gaisheta sun wuce dakin Innayo. Alh. Rabi'u sai ya zata dashi take saboda sun yi sa'in'sa akan  'yar dangin wa ya kamata a sake hadawa da Munzali cikinsu.  Labule ya daga ya leko da kansa ya watsa mata mugun kallo. "Dake da Munzalin duka kuna karkashin ikona. Sannan Zakiyyan da suka rabo ba 'yar kanwarki bace ciki daya?..." Dakatar dashi tayi ta nuna masa dakin Innayo da bakin da ta turo gaba. "Maida wukar. 'Ya'yan matarka ne naga suna ta sintiri a gidan nan abin ya soma yawa."  Ta tashi ta koma dakinta yana biye da ita. So tayi ta daga murya wurin fadin maganganu amma Munzali ya ce mata ko labari yaji ta sake takalar Innayo sa rigima zai hanata kudin wata. "Kwanaki Zara ce ta haihu kullum sai sun zo. Auren Salima ya mutu shima kamar wata uwar zasu iya yi mata suka dinga zuwa. Dazu kuma akan idona Maimuna tazo ta wuce da ledoji harda jakar bacco. Ga Hasiya ita ma ta wuce yanzu. Kar ka manta zuwan mijin waccan kankamojin Uwani shi ma ya ce bai ganta ba. Ni dai ka dauki mataki kafin a fara zaginmu a unguwa." Buguzum buguzum ya fice daga dakinta ya tafi na Innayo. Ta saka dariya ta zauna jiran tashin muryarsa idan yana fada.   Hira ya samu suna yi ga kayan kad'in miya danginsu kuka da daddawa ana ta zuzzubawa a ledoji. A gefe ma akwai ledojin viva biyu cike har baka da danyar masara. Sai kwan zabi cike da katuwar kwarya. Fuska a sake Innayo ta nuna masa uban kayan dake gabansu. "Idan kun hadu da Musbahu (mijin Maimuna) kayi masa godiya. Kauye yaje shi ne ya hadomu da abin arziki." "Ya hadoki dai ke da kike shagwaba shi. Duk wata dawainiyarsu kin dauka kamar ke ki ke auren Maimunan" cewar Alh. Rabi'u cikin fushi yasa kafa ya shure ledar masara guda daya "wai masara kamar wasu mabarata?" 'Ya'yan nasa yabi da kallo saboda duk sun dinke fuska yaja dogon tsaki. Duk tsiyarsu dai shi ne ubansu. Kuma dadin abin yana da Munzali. Tabe baki ya yi kamar anyi masa dole kafin ya fita ya ce "In kun dafa ki miko min inji idan noman ya yi kyau dai."  Tun a gida Maimuna take cikin farincikin wannan kyautatawa ta mijinta ga iyayenta. Kullum sune masu karba a hannun Innayo ko Hasiya, yau gashi ita ma tana da abin kaiwa gìda asa albarka. Sai gashi tun ba aje ko ina ba Alh. Rabi'u ya yi nasarar kawar da murmushinta. 'Yan uwanta duk sun kawar da kai basa son hada ido da ita don kada su karasa sarar mata da gwiwa.  "Ina da itace. Zara tashi kije ki dora masarar nan." Idanuwan sai suka koma kan Zara. Salima ta mike da hanzari tana cewa bari ta dora. Ga mamakinsu sai Zara ta tashi da rawar jiki. Irin rawar jikin nan na mai son burge wanda ya bashi umarni ba na tsoro ba. Ledojin ta kwasa tayi waje ga uban murmushi ta kasa dainawa.  Sai da ta fita Innayo tayi murmushi tana girgiza kai ta furta kalmar "Zara kenan" da kulawa. Ita kuwa Zara tana isa waje sai da ta share kwalla. Shareta da Innayo take yi yafi duk wani abu da ya sameta ciwo a yanzu. Daki daya suke kwana amma takaitattun kalmomi ke shiga tsakaninsu. Ta riga ta sauke duk wani dakon rashin albarka da ta dauka akan ahalinta. Shiri take nema da kowa a cikinsu. Da ta dora kin komawa ciki tayi tana ta faman tura icce don tayi saurin dahuwa. Sa'arta daya ma iccen bai nuna mata kurenta ba. Tashin farko ya kama ba tare da ya hada mata hawaye da majina na yaushe gamo ba. Tana jin kukan jaririyarta taki shiga ciki har sai da Hasiya tazo ta kirata.  "Ke kuma daga hura wuta sai kiyi zamanki ki barta tana kuka?" Cewar Maimuna tana mika mata 'yar. "Naga duk kwadayin cin masara ya kamaku shi ne na zauna ina ta fifita don ku samu da wuri." Wasa take son shigarwa tsakaninsu. Basu sace mata gwiwa ba kuwa suka dinga dariya suna cewa ko dai akwai sauran bebi a cikinta. "Ku barta dani take tunda ni na ce a dora." Zara sai idanu suka raina fata. Gabanta ya fadi. A tsorace ita dasu Mqimuna suka kalli Innayo ta fara cewa "Wallahi, wallahi..." Innayo sai tayi dariyar da ta bawa 'ya'yan nata mamaki.  "Lallai ma Zara. Ke ki tsokani 'yan uwanki amma ni ba zan tsokaneki ba?" Ajiyar zuciya Zara ta sauke su Hasiya ma duk sai suka saki rai. Sun san yadda Innayo ta dauki zafi da ita. A gaban ido da baya duk suna bata hakuri da son ganin ta sakarwa Zara.  "Tsoron bata miki rai nake Innayo." Ta ce a sanyaye wanda ya soki zuciyar mahaifiyar da bata da tamkarta. Harararta tayi cikin wasa ta ce "Ai kuwa dai ya soma baci tunda kin bar min jika da yunwa."  A gaggauce Zara ta gyara zama ta rungume 'yar a jikinta sosai. Ta kalli su Salima kowa murmushi yake mata. Innayo ta sake shayar da ita mamaki da ta ce, "Komai ya wuce Zara ki daina saka damuwa a ranki. Allah shaida na yafe miki duniya da lahira. Rashin zuwan maigidanki da yara duk ba wani abu bane indai kin sami lafiya. Muna nan da yardar Allah zaki ganshi dasu." Allah Sarki, Zara sai hawaye "na gode Innayo. Salima kuma ku yafe min. Don bakin halina yarinyar nan ko suna bai saka mata ba har yau." "Allah Ya san sunan da Ya halittota dashi. Kada ki sake tambayarsa." Cewar Innayo ta sake sako wasa don ta kawar da damuwarsu "ni dai a dafa min masara in mayar da mugun yawu." Kusan tare yaran nata da ita kanta suka saka dariya. A zuciyarta tana jin wani irin farinciki wanda yafi kudi da duk abin da kudi zai saya. Dariyarsu ce ta kawo Asabe wadda take mamakin ko Alh. Rabi'u bai yi musu yadda ta ce ba. Zuwanta ya yi daidai da tambayar da Hasiya ta yiwa Innayo akan dalilinta na cewa a dafa masara bayan abin da babansu ya yi mata. Su duka sun kasa gane dalilin rashin nuna fushinta da abin da ya yi. Asabe ta kasa kunne da kyau domin kwasar gulma ta kara hada fada. "Allah ne fa Ya ce kada mu zata don mun ce munyi imani ba zai jarabcemu game da 'ya'ya da dukiyoyinmu ba. Da rayuwa tana tafiya da burin dan Adam da babu wanda zai yi kuka da komai. To amma yawan jarabawa da hakuri da ita karin daraja ne a aljannah. Tunda Allah bai bani kudin yin sadaka ba ba zan butulce don Ya dora min wannan rayuwa ba." Hawaye ta sanya 'ya'yan nata. Suka kara ganin kima da darajar mahaifiyarsu. Ana haka  Salihi ya iso. Bai jira isowar Uwani ba ya ce da Innayo idan ta zo ta ce mata ta zauna.  Abin da ya fadi ya tabata sai dai dama ta san dole akwai ranar da tura zata kai bango. Ya yi hakuri na ban mamaki a zamansa da Uwani. "Wani abin ta sake yi?" Murmushin bacin rai ya yi "ta dai zauna. Idan zuciyata ta sanyaya zan zo ki mana hukunci. Mubashir zai kawo mata kayanta." Bata taba ganin suruki irin Salihi ba. Nauyinsa ta kara ji. Yana da iyaye da 'yan uwa amma har kullum bai gazawa wurin kokarin rufa asirin matarsa. Ta rasa wace irin zuciya ce a kirjinsa mai matukar hakuri da zurfin tunani. Ba shi ta haifa ba amma ya iya zuwa debe mata kewar 'yarta yana kuma bata hakuri akan halayyarta. Yau kam ta tabbatar Uwani bata yi masa da wasa ba wajen bata masa rai. Za ta bashi hakuri ya ce don Allah ta bari. Uwani ce mai laifi don ta haifeta ba za ta dauki nauyin laifinta ba. Bai jima da fita ba uwar gayyar ta iso.  Innayo taji kamar ta rufeta da duka akan amsar da ta bayar bayan ta fada mata abin da Salihi ya ce. "Ba zan yi mamakin duk wani abu da zai yi min ba yanzu tunda ya auro matsiya... " "Rufe min baki shashashar banza. Kina girma halinki yana kara tabarbarewa. Akanki ni ba sai dai na ce banga ranar boko ba? Ke kadai kika same shi mai yawa a cikin 'yan uwanki amma banda hauka bai kareki da komai ba." Haukan ta nuna ziryan inda ta kada baki tana hurawa kannenta hanci ta ce "ai kuwa boko ya min komai Innayo. Na sayi mota, nayi gini sannan na biya kujerar Hajji." 'Ikon Allah' Innayo ta sami kanta da cewa cikin wani irin yanayi a zuciyarta. Bata cikin iyaye masu saka ido akan kudin 'ya'yansu amma bata jin duk hakurinta zata so ace bata san cigaban yaranta ba. Babu abu daya da Uwani ta lissafa wanda zata yi mata shamaki da mallakarsa. To me ya hanata fada mata ko addua ta tayata da fatan alkhairi. Abin bai yi mata dadi ba ko kadan. Murmushin fatar baki tayi mata tare da fadin, "Sai ki wuce gidan naki kafin mijin naki ya sakko." "KNUPDA sun kwace" Uwani ta ce tana tura baki kafin kuma cikin sauri ta dora da yi musu bayanin cewa zata je a daidaita don kada suyi mata dariya. Dariyar da ta guda ita Innayo tayi.  *** Bayan tafiyar kimanin awa daya da rabi sai ga wayar Suhaib. Munzali ya samu a lokacin. Ya jima yana kiran layukansu shi da Abbati amma duka sun ki shiga saboda raunin service na hanya. Da ya same su kuma aka rasa mai daukar wayar cikin su biyun. Gara ma Munzali tuki yake. Abbati kuwa ragowar karfin halinsa ne yaji yana neman kufce masa da yaga sunan mai kiran. Kira hudu ya musu a jere ta wayar kowa sau bibbiyu sannan ya hakura.  A gidan bikin iyayen nasu duk sun damu saboda an san cewa wayar da Abbati ya amsa ce ta tayar musu da hankali har suka tafi. Yayinda Mardiyya take ta kiran Munzali saboda halin da ta shiga na taya shi jimamin damuwar da ake tsammanin suna da ita, Farha  bata kira Abbati ba ko sau daya. Ko ma mene ne ta fahimci gagarumi ne tunda ya bar gidan ba tare da ya yiwa iyayensu da suke tare sallama ba. Za ta jira zuwa gobe idan ba a ji daga garesu ba ta bangarenta ko 'yan uwanta kafin ta kira. Addu'a kawai ta zauna tana yi don bikin ya fice mata a kai. Da Suhaib ya ce wayoyinsu na shiga ba a amsawa sai ta tura masa text. (Allah baya dorawa bawa abin da yafi karfinsa. Wannan alkawari ne daga  Mamallakin dukkan halitta. Ina fata Allah Ya kawo muku saukin abin da yake gabanku. Luv, Ya Farha) Karar shigowar sakon ya kada duk wani abu dake yawo a jikin Abbati. Fargabar barnar da yake tunanin Shazali ya yi masa ta shafe komai a kwakwalwarsa. Wayar tana aljihunsa amma jikinsa ya bashi daga ina sakon yake. Jiki a sake ya dauki wayar ya bude sakon. Numfashi kawai ya dinga ja yana saukewa da sauri da sauri.  "Shazali ne? Me ya ce?" Munzali ya tambaye shi da yaga yadda ya kara birkicewa. "Farha ce." "Nima tun dazu Mardiyya take kirana." Shiru suka yi na lokaci har suka isa Gumel. Fadan irin tashin hankali da tsoron da suka sami kawunansu a tsukin lokacin ma bata baki ne. Gidan mai suka shiga suka kara mai tare da yin sallah. Sun kusa barin garin Abbati ya ce da Munzali ya yi parking. Gefe ya gangara ya fuskanci Abbati ba tare da kashe motar ba. Yana tsayawa Abbati ya kama kofar ya bude. Kafarsa daya a waje ya juyo ya kalli Munzali mai binsa da ido da alamun tambaya. "Ka koma Kano zan wuce ni kadai." A razane Munzali ya dube shi maganar tana dukansa ta ko ina.  "Me ka ke nufi?" Kadaici yake bukata? Tsoron haduwarsa da Baaba Mari? Tabbacin rasa Farha na har abada? Hasashen girman tashin hankalin da zai wanzu a gida da garinsu? Babu abin da ahi kadai bai isa ya haukata tunanin shi ba. Sai gashi su duka da ma wasu suna jiransa. Bai san ta ina zai fara ba, amma gara ko meye ya tunkareshi shi kadai tukunna. "Don Allah Munzali ka koma. Tunda kaji na ce ka barni ni kadai ka san bani da zabi ne." Yawu mai daci ne ya wuce ta makoshin Munzali. Ko ba a fada ba ya san cewa Abbati ya gama sarewa da komai. Yau din rana ce da za ta zama mafarin wani abu da bashi da suna a rayuwarsu. Kuma har ga Allah Yafi kowa sanin cewa tonowar asirin Abbati ba kamar nasa bane. Abbati ya tashi cikin dangi da iyaye. Duk wani rikicin cikin gida bai raba kan iyayensa ba. Shi kuwa ko yau iyayensa suka ji bashi da abin da ya wuce dora musu alhakin komai. Darajar Qibdiyya da kuma 'yan uwansa da ya fara sabunta zumunci dasu ne ababen dubawa. Sai kuma masoyiyarsa Mardiyya wadda ko kadan baya son abin da zai shata layi tsakaninsu. Mafi girman damuwarsa kuwa tana tattare da bakincikin shi ya batawa Abbati rayuwa. Numfasawa ya yi bayan ya dan yi nazari.  "Kana nufin za ka je ka tonawa kanka asiri ne ni kuma na zauna? Waye silar shigarka wannan rayuwa." Hannu Abbati ya nuna masa "kada muje nan wajen." Rai ya soma baci Munzali ya ce "to ina zamu je? Ba ni bane? Ba don ka hadu dani ba da yanzu kana rayuwarka cikin kwanciyar hankali." Kafin ya gama maganar idanunsa sun yi jajir. Zuciyarsa a kuntacce take yana jin yadda take zafi. Ya sake bude baki zai yi magana Abbati ya dakatar dashi da cewa, "Don Allah kayi tuki a hankali." Duk yadda Munzali yake son yi masa musu haka ya hakura ya tafi bayan shigar Abbatin motar haya. *** Mummunan faduwar gaba ne ya sami Baaba Mari har ta saki butar hannunta da taji muryar yaran gidan suna yiwa Abbati barka da zuwa. Sake dibar ruwa tayi cikin rawar jiki duk tana zuzzubarwa ma ta kuma cika botar ta zauna za tayi alwalar Isha'i. Jikinta har wani karkawa yake saboda tashin hankali. Tunda ya iya biyo dare ya taho garin a yau da basu kwana da shirin zuwansa ba ta san babu lafiya. Tabbas babu ko tantama Abbatinta bashi da gaskiya. Da babu wata a kasa tun dazu zai kirata ya karyata zantukan da taji sunyi a waya da Shazali. A yadda zuciyarta take dakan lugude a kirjinta kuwa a lokacin ko me ya fada a waya zata amince. Yardar ta zame mata wajibi ko don kada bakincikin jin gaskiya ya kwantar da ita.  Shi kuwa a bakin kofar da zata sada shi da sashen mahaifinsa ya tsaya tun shigowarsa. Idanunsa da suke cike da kwalla suka sauka akan Baaba Mari tana alwala. Ya gama karanta da fahimtar duk wani motsinta. A firgice take! Alwala take yi amma sam hankalinta baya jikinta. Shafar kai kadai wadda da wuya ake kuskure adadinta saboda sau daya ce sai da tayi biyar akan idonsa. Ya lura duk gabar da ta kama sai ta dawo hayyacinta take tafiya ta gabanta. Bai san kuka yake ba sai da yaji ruwan da zafinsa yafi wuta a zuciyarsa yana bin kumatunsa. Asalin kunci da damuwa ne suka rufe shi ya juya a hankali ya fita daga gidan. Kofar gidansa yaje tun daga dan nesa yake hango hasken tocilan din wayoyi guda uku a wurin. Bai yi mamakin ganin 'Yashshafa da wasu 'yan mata sa'o'inta biyu ba. Su ma duka kannensa ne kowcce da tsintsiya a hannu. "Gwaggo Deluwa ce ta aikomu muyi maka shara kafin a kawo abinci." Guda cikinsu ta fada bayan ta gaishe shi. Mukullin kawai ya mika musu ya juya masallaci. 'Yashshafa bata manta gargadin Deluwa ba tayi saurin cewa a dawo lafiya. "Ki kwantar da kai ki kyautata masa domin mu sami biyan bukata." Cewar Deluwa mintuna kalilan da sallamar Abbati cikin gidan. 'Yashshafa tana dirzar kafarta da dutsen goge kaushi ta daga kai tana zumburo baki. "To wai ni Inna haka za kiyi ta min ne? Yau ki ce in daina sakar masa fuska gobe in saki? Yaushe zai soni a haka?" Deluwa ta murmusa tana wani jijjiga kai "Yaro man kaza. Banda abin ki 'Yashshafa idan baki kwantar da kan ba ta yaya zamu samu ya baki lambar shi Sha'aib din cikin sauki?" Cigaba da dirzar kafarta tayi cikin yanayin ko in kula ta ce "Inna ki bar batunsa don a ranar ko kallo ban ishe shi ba." Harara mai kyau ta samu kuwa sannan cikin fushi Deluwa ta ce mata, "Ta yaya zaki san me yake faruwa a lokacin nan kina can kina kukan shanu? Kar ma ki zata dominki na damu. Tausayin yaron da mutumcin uwar tasa ne yasa nake ta kokari. Ni kadai na san me na gano a kwayar idanunsa game dake. Jikina ya bani suna ta nemanki ta wurin Abbati. Amma don mugunta yaki hadaku. Su kuma 'yan birni ba wuya ciwon zuciya ya kwantar dasu saboda da gaske suke soyayya." Tabe baki 'Yashshafa tayi bayan tafiyarsa tabi 'yan uwanta cikin gidan. Daga Abbatin har Suhaib ta san bata gabansu. Ita din ma ta turesu daga gabanta. Kwanakin nan mutum daya take yawan tunawa tana jin ina ma zasu hadu ta rama dariyar da ya yi mata.  Da Abbati ya dawo bai koma gidansu ba. A waje ya gaisa da sauran iyayensa maza ya ce kansa ne yake ciwo zai kwanta. Harda nanatawa Mal. Inuwa ya sanar da Baaba bashi da lafiya kada ta ji shi shiru. Nan kuwa karfin gwiwar hada ido da ita a daren ne bashi dashi. Abinci kala biyu ya gani a falonsa. Wanda ya tabbata daga wurin Baaba Mari aka turo ya tsakura kadan ya yi shirin bacci. Sun dan taba shawarwari da Munzali a waya sannan ya kwanta.  *** Tafiyarsu Munzali ta gaggawa ta dagawa iyaye da 'yan uwan Alh Tahir wadanda Allah Yasa suka gamu dasu jiya hankali. Saboda haka suka dinga kiransa ana tambayar ko yaji daga garesu. Shi ma ya damu haka Mami Khadija da Mama Nasima. Wuraren tara na safe yaci sa'a Munzali ya dauki waya. I just published "29" of my story "UWA UWACE...". https://www.wattpad.com/1069890147?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=BatulMamman17&wp_originator=HEUJmsOYglY3kZgRbXSElahoP5O7Gz9YEvViSnSSKsmjyDvaje5RtEr7HvxDXafaYphpjZJAgd0Hp1y2h4lNwKgQgH4AuufTWYBhuc3haYtNjFvXB3eIrX9CBO7iJXay UWA UWACE...29 Batul Mamman💖 Tafiyarsu Munzali ta gaggawa ta dagawa iyaye da 'yan uwan Alh Tahir wadanda Allah Yasa suka gamu dasu jiya hankali. Saboda haka suka dinga kiran Alhajin ana tambayar ko yaji daga garesu. Shi ma ya damu haka Mami Khadija da Mama Nasima. Wuraren tara na safe yaci sa'a Munzali ya dauki waya. Munzalin kwanan zaune yayi inda yake ta tufka da warwara. An wayi gari kansa yana wani irin ciwo saboda rashin bacci da alhinin me zai faru tsakanin Abbati da Baaba Mari. Irin wannan lokacin sallah da kankantar da kai a gaban Allah SWT  shi ne yafi dacewa da bawa. Sai aka yi rashin sa a munin dabi'ar da suka rayu cikinta ya danne tunaninsu daga shi har Abbati. Asalin kalmar da bature yake kira despire ita ce ta wanzu a kawunansu. Suna jin tamkar basu da sauran rabo. A duniyar sai sun ji kunya sannan a lahira da wuya su sami dacewa da rahama. Wannan shi ne tunanin kowannensu. Shi ne fargabar da suke da yakinin ganin ranar faruwarsa. Da farko bai yi niyar amsa wayar kowa ba sai ta Abbati. Amma karar kiran da ya shigo tamkar ana kada kararrawa a cikin kansa ya saka shi mika hannu ya daukota a gefensa.  Katse kiran yaso yi tunda bai san nambar ba, bisa kuskure sai ya zamana ya amsa ne. "Alhamdulillahi ya dauka" Shi ne abin da Munzali yaji an fada daga dayan bangaren. Bai sha wahalar gane mamallakin muryar ba. Hakan ya tilasta masa tattaro duk wata nutsuwarsa ya gyara murya suka gaisa sosai. "Me ya faru jiya Munzali? Kun tafi kun barmu da fargaba. Ina shi Abbatin?" Murmushin fatar baki Munzali ya yi da ya hasko tonuwar asirinsu da irin yadda zasu wulakanta bayan rabuwa da masoyansu. Karya ce kadai rufin asirinsu kuma ita ya gilla kamar yadda suka saba domin kare kai. "Ku yi hakuri. Wan Baban Abbati ne aka kira babu lafiya ...." Alh. Tahir ya katse shi tun kafin ya gama da cewa "Subhanallahi, ciwon ya yi tsanani kenan duba da yadda ku ka tafi." "Eh suma yake yi kamar ba zai tashi ba." "Kuna ina ne yanzu?" Munzali sai da ya dauke wuta na wucin gadi kafin ya iya bayar da gamsashiyar amsa. A yadda suke dai bai kamata ya ce Abbati ne kadai ya tafi ba. Sannan idan ya yi gaggawar binsa yanzu bai san me hakan zai janyo ba. A takaice ma dai dole ya zauna domin ya dakile yunkurin da yake hasashen Alh. Tahir ya fara. "Muna Gumel nima aka kirani Qibdiyya ta fadi ana zaton karaya ce." (Da safe ranar ta fadi amma ko kuka bata yi ba) "Sannunku kaji. Ya jikin nasu?" "Kawu Sa'idu ya fara samun sauki. Qibdiyya kuwa mai kula da ita ce ta firgita. Buguwa ce kawai." Nutsuwar da Alh. Tahir ya rasa tun jiya ce ta dawo masa. Ya sake jajantawa Munzalin sannan suka yi sallama.  Munzali har ya fara jin sanyi a ransa na rabuwa dashi lafiya sai ya sake kira. Bayan ya fada musu me yake faruwa ne Mama Nasima ta ce ayi musu kwatance zasu je dubiya. Ita a nufinta taje har gidan Munzali ta kara gane ina zata kai Mardiyya. Alh Tahir bai ki ba saboda shi ma baya son wadannan zaratan matasa su kufcewa zuri'arsa. Tunda Allah Yasa suna Kanon gara ma da aka yi haka. Sai suje domin a karfafa magana. "Amma ya dace muje gidansa? Babu mace fa a ciki. Idan akwai ma kuma ai bai kyauta iyayen wadda yake son aure suje duba mata 'ya ba." Mami Khadija ce taja hankulansu kan kuskuren zuwa gidansa. Mama Nasima sai ta hau borin kunya. "Mutum kullum burinsa ya nuna yafi mu sani da iyawa. Da an fimu din kuma da bamu zo gidan ba. Ki kwantar da hankalinki bance sai kinje ba. Yanzu nake shirin cewa a fada masa ya kaita gidan iyayensa sai muje can." Mami Khadija sai ta girgiza kai kawai. Ba don tayi magana ba tsaf gidansa zasu je. Yanzu kuwa ko don a bata kunya dole a canja salo.  Ba bata lokaci Alh. Tahir ya kuma kiransa ya fada masa shawararsu. Suna gama wayar Munzali ya tashi a gaggauce ya fada bandaki. Cikin mintuna biyar har kaya ya saka. Yana makala links din hannun riga wayarsa tana gefen kunne ya danneta da kafada. Asabe ya fara kira ya tambayeta ko tana gida ta ce ta tafi sunan wata 'yar uwarsu a kauyen Kuyen Ta'inna da sassafe. "Idan zuwa zaka yi bari in taho gida yanzu. Ka san kauyen a cikin gari yake zan iso da wuri." "A'a yi zamanki. Zan zo da daddare ko gobe." A wurinsa gara ta zauna kada su hadu da Mama Nasima ayi abin da shi da Mardiyya zasu dade basu manta ba. Zara ya kira ya fada mata bakin da zai yi da matsayinsu.  Asabe kuwa sai ta kasa zama. Idan kudi ne gara ta koma gida tayi masa waya ya zo ya kawo mata. Kada tayi sake goben ya ce ya taba. Takalmanta ta saka ta sallami maijego ta fito neman abin hawa. *** Yau ma Abbati ya kasa shiga bangaren Baaba Mari. Ya leka ya gaisar da kawunnansa. Ita kuwa yana zuwa kofar dakinta ya tambayi wani yaro dan wajen Habi ko ta tashi. "Ta tashi tun dazu. Kunu take sha." Kirjin Abbati ya sake matse zuciyarsa saboda tsoron hada ido da ita. Cikin hanzari ya ce da yaron "Tunda kunu take sha ka ce ina gaishe ta. Bana son shiga in katseta. Zan dawo anjima." Daga cikin dakin Baaba Mari tana sauraronsu tun farkon tsayuwarsa a wurin. Maganarsa ta karshe tasa ludayin hannunta ya yi mata nauyi a hannu. Abbatin da ko wanka take yi yana jiranta shi ne mai cewa baya son katse mata shan kunu? So take ya bata dalilin karyata duk wani zargi da ya darsu a zuciyarta amma ya kasa. Daga wayarsu ta jiya kafin yazo zuwa yanzu bai yi komai ba sai tarwatsa mata zuciya da fargaba. Akwai matsala ta riga ta sani sai dai bata san girmanta ba. Wannan shi ne tashin hankalinta.  Tsayuwa Abbati ya yi a jikin bangon dakin ya kasa tafiya. Komai na duniya ya tsaya masa cak. Baaba Mari kawai yake so ta dube shi, duba na tsausayi da soyayyar uwa ta ce masa ta yafe. Ta roka masa rahamar Allah wadda a yanzu yake taraddadin samu. Idanunsa ya rufe sa'ilin da kwala ta cikasu har tasa suke zafi. A sanyaye ya juya zai tafi sai yaji wayar Baaba Mari tana ruri. Sautin ne ya dawo da ita daga duniyar tunani tayi saurin share kwallarta sannan ta dauka da sallama. Muryar mace mai kamala ce ta amsa mata cikin walwala da son janta a jiki. "Wa alaikum salam wa rahmatullah. Allah Yasa baki manta Khadija kanwarki ta Kaduna ba." Baaba Mari tayi murmushin jindadi "yaushe zan manta mace mai kirki da mutuntunta dan Adam kamar ki Mami Khadija?" Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Cikin sakan daya Abbati ya bayyana a gaban Baaba Mari a hargitse.  Kallo guda taji ya matukar bata tausayi. Duk ya sauya babu komai a idanuwansa sai fargaba da tashin hankali. Bakinsa na rawa saboda bai san me aka ce musu ba tunda ya gama tsorata da Shazali ya ce, "Baaba kashe wayar don Allah" a hankali. Dauke kai tayi kamar bata ganshi ba tana tambayar Mami Khadija yara. "Kowa lafiya kalau Alhamdulillah. Ya mai jiki kuma? Jiya Abbati ya tafi ya barmu da fargaba. Ashe kawunsa ne babu lafiya." Kallonsa Baaba Mari tayi ta tabe baki. Abin har ya kai ga karya kenan. Shi da bai ma san abin da Munzali ya fada musu ba sai ya daburce ganin tana masa kallon tuhuma. Da bakinsa ya kasa hada kwakkwarar kalma balle ya yi magana sai ta cigaba da wayar. Rufa masa asiri tayi kamar yadda kowace uwa za ta yi ta ce "Ai jiki ya yi kyau sai hamdala. Tsorata muka yi shi yasa aka kira shi." Cikin jimami Mami Khadija ta ce "haka Munzali ya ce. An kira an ce yana suma ai dole hankula su tashi. Don Allah kiyi masa sannu." "In sha Allahu Mami. Mun gode sosai." "Haba ai an zama daya. Allah Ya kara hada kawunansu." Amin ta ce sannan suka yi sallama. Abbati ya kalleta cikin sauri ya sauke ido. Inda ya tashi ya koma ya gurfana gabanta hankalinsa ya sake tashi. Baaba Mari ta kasa tambayarsa komai. Tsoron amsarsa take ji ga kuma tausayin yadda ya firgice mata. A hasashenta ma daga maganganun Mami Khadija ta fahimci akwai alaka tsakaninsa da daya daga cikin 'yan matanta. Wayarsu ta karshe kafin zuwan Shazali dama ya fada mata akwai maganar da yake son yi da ita. Kawar da tunanin tayi domin bashi da muhalli a yanzu cikin damuwarsu. Can ta nisa tayi masa tambaya amma a sakaye. "Kai da Munzali sana'arku daya?" Sai da taji hadiyar yawunsa tare da hawa da saukar Adam's apple dinsa kafin ya iya bata amsa. "Eh" ya dora da cewa "amma wallahi Allah mun tuba mun daina" yana mai nunin girman maganar da yatsansa. Hannu ta daga ta dakatar dashi nata jikin yayi sanyi kalau. Kunnuwanta kuwa kamar an toshesu domin bata jin komai sai karar bugun fargabar zuciyarta. "Bana son jin koma mene ne Abbati. Duk wanda yake kan tafarkin gaskiya ya sani. Wanda ya saba ma yana sane. Ka tashi ka koma gida. Zamanka a nan ba zai karemu da komai ba." Samun kansa ya yi da fashe mata da kuka. Babu sauti sai dai ilahirin jikinsa duka rawa yake kamar an kwara masa ruwan sanyi. "A tare dake aljannata take Baaba. Idan kin yafe min ina sa ran samun gafarar Ubangijina." Nata kukan ta danne. Ya zama wajibi a gareta ta karfafi zuciyarta indai tana son danta ya sami karfin gwiwar tuban da yace ya yi. "Na yafe hakkina idan akwai a cikin sana'arka. Sai dai ban san yadda zaku yi da hakkin mutane ba." "Baaba ban fahimta ba." Ya tambayeta da dukkan gaskiyarsa. Rikicewarsa ta kai ya manta bata san ainihin sana'ar ba. "Ba da sana'arku ku ka yi kudi ba?" "Da ita ne." Ya amsa kansa a kasa. "Kuma sana'ar haramtacciya ce?" Kai ya sunkuyar ya gyada shi a hankali. Yanayinsa sai ya soma bata haushi. Yafi ta sanin me suke aikatawa to don me zai nuna mata rashin sanin girman laifin? Duk mai daukar kayan da ba nasa ba yafi kowa sanin hakkin wasu ne yake dannewa. Hakkin da sai an tambayeshi ranar lahira. "Kafi ni sanin cewa dukiyar haram ce kake kwance a kai. Idan akwai halin ka mayarwa wasu cikinsu dukiyoyinsu gara ka gaggauta yin hakan." Abinka da dan fari kuma mutum wanda tun asali bashi da saurin fahimtar abubuwa makamantan wannan. Da Munzali ne tabbas zai cigaba da tafiyar da Baaba Mari ne akan zarginta na cewa sata ce suke yi. Abbati kuwa cikin kidima da tsoron zargin da take musu sai cewa ya yi bai taba satar kudin kowa ba. Baaba Mari taji zuciyarta ta daka wani mugun tsalle a kirjinta yana fadin haka. Da sassarfa ta tashi ta tura kofar dakinta ta saki labule sannan ta dawo ta kama hannunsa suka zauna. Kallon ido cikin ido take yi masa cikin yanayi na fargaba da taraddadi. Muryarta a shake ta fito saboda nauyin tambayar da take shirin yi masa. "Yankan. Yankan? Kai? Yankan kai? Abbati ku 'yan yankan kai ne?" Bata jira amsarsa ba ta shiga yarfe hannuwa "na shiga ukuna ni Mariya. Abbati rashin imanin naku ya tsallake sata ya hada da zubar da jini?" Sakin hannuwansa tayi ta hanyar bigesu daga cikin nata tayi baya a zabure. Hakan yasa shi yaji kamar ba za ta kara son ya kusanta gareta ba. Ita kuwa zafi ta soma ji fiye da kima ga gumi yana tsatstsafo mata kamar an kunna famfo. Wannan kaddara da nauyi take. Dan cikinta ne a gabanta amma bata san shi ba. Tana tuhumarsa da daya daga cikin masifun wannan zamani amma yaki cewa komai sai ido da yake binta dasu. Tana hawaye ta doki gefen kirjinsa, cikin gunjin kuka ta ce, "Bakinka zaka bude kayi min magana. Wato da baka da niyar fadin gaskiya sai ranar da aka bukaci jininmu a kungiyar ...." "Baaba ki yarda dani wallahil Azeem bana cikin kowacce irin kungiyar asiri ko yankan kai" ya fada dalla dalla duk da kukan da yake cinsa domin ta yarda da gaskiyarsa. Komai ya kulle mata. Ta rasa tudun dafawa. Tsoron abin da zai fada yasa take jin gara ma ace satar ce. Sassauta murya tayi ta sake mika hannu ta damko hannunsa daya. Da dayan hannun nata ta share kwallarta sannan ta fuskance shi da kallo na tausayi garesu baki daya. "Fada min sana'arka!" Saukar aradu yaji. Zuciyarsa ta tsaya na 'yan dakiku kafin ta cigaba da bugu cikin yanayi na faduwar gaba. "Baaba...."  Sai kuka. Kuka. Kuka...sannan ya fayyace mata komai tun daga haduwarsa da Munzali. Ko da ya gama ya sake kiran sunanta bata amsa ba. Dama kansa a duke yake sai ya dago a hankali. Shi take fuskanta amma ba shi take kallo ba. Bakin kwayar idanunta a birkice ya gansu, sun juye kamar babu su. Suman zaune tayi bai sani ba.  *** Datar MTN ta dari uku wadda suke bayar da 1GB na kwana daya Danliti ya saka a wayarsa. Whatsapp ya bude cikin rashin sa'a bai ga sunan Ayaah ba. Guntun tsaki ya yi domin ya so ganin hotunanta yau. Kwana biyu kenan da zuwansa wurin dinner inda ya hadu da Suhaib amma har yanzu bai manta da fuskarsa ba. Sai da ya koma gida haushi ya ishe shi. Da gani ya girme shi wai amma shi ne ya yi masa barazanar da ta tsorata shi haka.  "Idona idon matsiyaci sai na nuna masa tashancin 'yan Kano." Danliti ya yi kwafa gami da jinjina kai cikin bacin rai. Duk da cewa baya jin akwai wata mace da ta kama kafar Ayaah cikin matan da yake son mu'amala dasu, amma yaci burin samun hajiyar Kadunan nan wato Jiddo. Da bukata bata samu ba. Ya laluba babu halin ganin hoton Ayaah a yau. Sai kawai ya saka katin dari biyu ya kirata.  Shirin fita suke ita da Murja zuwa gidan Innayo. Murja ce za ta yiwa Zara kitso kamar yadda ta fadawa Hasiya jiya. Shi ne ita kuma ta hadasu da Ayaah ta ce su tafi tare. Shake murya ya yi yana magana ciki ciki irin na mayaudara. "Baby nayi missing dinki da yawa. Anjima zan zo. Me ki ke so na taho miki dashi?" Ya fada a karshe don ya san ba za ta ce komai ba. Ita kuwa sanyi taji a ranta da sabon sunan da ya rada mata. "Babu komai. Fita ma za muyi da Murja." "Ina zaku je baki fada min ba? Nifa gaskiya bana son kina fita ana gane min ke. Da kin fada min sai na zo na kai ku. Anywhere dai ku jirani please zan taho now now." Satar kallon Murja tayi ta bar wurin da sauri kafin taji me yake cewa. "Ka barshi bani kadai bace. A gida fada za ayi min. Gidan kakanninmu zamu." A lissafinsa anci rabin kudin wayar sai kawai ya fake da nuna bacin rai ya mata sallama. Hankalinta sai ya tashi tayi maza ta kira shi da ragowar canjinta. "Kayi hakuri mana don Allah." Kamar ba zai ce komai ba har ta fara kosawa sannan ya ce "Naji. Amma har ku isa muna chatting. Ki kwatanta min gidan sai na sameku a can ko fuskarki na gani naji dadi. Da kudi a wayar ko na turo miki?" "Akwai" ta bashi amsa duk da ta san sun kare.  A danja ta sayi kati ita ma na dari biyu ta saka ta tura masa amsar sakonsa wanda ya rubuta kamar haka, (Wane kaya ki ka saka?) (Atampa ce) (Kwatanta min daga sama har kasa domin naji kamar kina gabana.) Kwatancen tayi masa na riga da skirt da hijabin da ta saka mai hannu wanda ya zarta gwiwarta kadan. Abin bai yi masa armashi yadda yake so ba. Wanda a idon namiji mai mutumci zai ga tayi matukar kyau. Canja salo ya yi cikin kwarewa da iya hillata. (Da wane irin kaya ki ka fi son yin bacci?) Kallon wayar tayi kamar ba tata ba na dan lokaci har sai da Murja ta tambayeta ko akwai matsala ne. Dena juya wayar tayi a kasan ranta tana yi masa uzuri da cewa kila lefe yake tunanin fara hadawa. (Doguwar riga) Danliti yaja tsaki ganin taki daukar haske. (Ni kuwa kinga nafi son kwanciya da wandon bacci kadai. Idan ma sanyi ake nan gaba kadan na san kina kusa dani ba zai dameni ba. Kema ki shirya ba zaki zo min da doguwar riga bed ba.) Wani dumi dumi Ayaah ta fara ji. Ita kadai ta dinga tsarguwa ko Murja ta fahimci irin sakwanin da yake turo mata. Hirar ta daina yi mata dadi amma ta rasa me ya hanata dakatar dashi ko ta daina bashi amsa. Wani sakon ne ya sake shigowa sai da ta dan zabura da ta karanta. (Ina son mace mai kunya. Shirunki yasa na kara sonki. Amma fa ki sani nan gaba kadan zaki nemi kunyar ki rasa. Zaki fara rungumeni da kanki ba sai na nema ba. Kafin aurenmu ina son mu sake da juna sosai ta yadda tun yanzu zamu san abubuwan da zasu faranta mana.) Ayaah bata iya sake tura masa amsa ba. Tambayoyin nauyi suka yi mata. 'Yar fara'ar da ta soma ta nema ta rasa.  Danliti da kansa ya gano zai yiwa kansa sagegeduwa ta wannan hanyar. Kifin rijiya ce ba kamar yadda ya yi zaton irin makwadaitan 'yan matan nan bane masu mummunar wayewar zamani a soro. (Kiyi hakuri Baby. Ina jin kamar na dauko hirar da bata kamata mu fara tun yanzu ba. Ina tsananin kewar irin wannan kusancin da iyalina. Ke kadai ce zan iya fitowa da damuwata hankali kwance domin nayi imanin zaki saurareni kuma ki fahimceni. I love you) Shi kenan! Kyakkyawan tunanin da ya fara ginuwa a zuciyarta ya rugurguje da sakonsa na karshe. Tausayinsa ya sake kamata. Ta kara jinsa a rai fiye da kullum. Matarsa kuma ta sha bakaken addu'o'i domin har gani take ba don haduwarsa da ita ba kila da yanzu ya fara bin matan titi. * Dubu ashirin Alh. Tahir ya baiwa Mama Nasima domin yiwa Qibdiyya sayayyar dubiya. Ita da Mami Khadija zasu je. Sai 'ya'yansu. An nemi Jiddo a waya bata dauka. Tana can gidan wata 'yar kungiyarsu 'yar Kano an kawo musu samari suna keta dokar Allah. Ta gama tsara karyar da zata yi idan ta dawo kafin lokacin tafiyarsu Kaduna. Mota biyu suka yi. Daya direban gidan da ake bikin ne yake jan Mama Nasima da Mami Khadija tund shi dan gari ne.Ta bayan kuwa motar gidan Alh. Tahir ce. Suhaib ke tuka kannensa suna biye dasu a baya.  A son ran Mami Khadija su biyu kadai zasu je sai ko 'yan mazan. Saboda mata da kunya aka sansu. Tana ganin iyaye da 'yan uwa sun isa su wakilci 'yarsu kafin a daura aure. Dadin dadawa ma maganar bata riga ta zama ta gemu da gemu ba. Zai iya zama kamar suna son cusa 'yarsu ne ta karfi. To Mama Nasima ta dage sai Mardiyya taje. Shi yasa ta hada da Farha da Sauda don kada ido ya yiwa Mardiyyan yawa idan aka fahimci matsayinta. *** Kayan tarbar baki lodi guda Munzali ya kawo dakin Innayo. A nan ya sami Uwani tana ta buge bugen waya tana tsaki. Tun safe take kiran Habibu waya taki shiga. Za ta fita kuma Innayo tayi rantsuwar idan bata nemi izinin mijinta ba in ta fita kar ta dawo. Ita Salima dama yaji labarin komai. Sunyi magana da ita a waya ya kwantar mata da hankali tare da goyon bayanta akan son raba auren. Zara ce ta gyara falon Innayo ta sakewa Qibdiyya kaya sannan ta jera komai a tray. Salima ta shimfida tabarma saboda basu san mutum nawa bane. Haj Uwani tana uwar daka ta kira Mubashir a waya tana kwatanta masa kamanin Habibu. So take yaje ministry ya kira mata shi. Innayo kuma tana gefe ita da Munzali yana yi mata bayanin Mardiyya da iyayenta. "To amma duk wannan bayanin da kake ni banga farinciki a fuskarka ba. Baka son yarinyar ne ko akwai wata matsalar ne daban?" Ta tambaye shi bayan ya gama. Bata ga wani doki ko murna a tare dashi ba. Kusan ma kamar rabin hankalinsa yana wani wajen daban. "Ba haka bane Innayo. Abbati ne ya ce min zai taho daga Kirikasamma yau. Shi ne nake tunanin zuwan bakin da isowarsa. Kada ya iso basu tafi ba. Kinga babu mai dauko shi daga tasha." Zancen bai yi tasiri a kanta ba saboda bashi da madogara. Abbati ba yaro ba kuma ba bako ba me zai same shi idan ya shiga mota daga tasha zuwa gida? Akwai damuwa sosai tana gani a idanunsa. Munzali mai yawan fara'a yau idanunsa kamar an dauke wuta. Rabuwa zata yi dashi har bakin su tafi sai ta kuma tuntubarsa. Idan ba abin da ya kamata ta sani bane zata bishi da addua. * Uku da rabi saura suka isa kofar gidan Alh. Rabi'u. Sauda ce mai tsokanar Mardiyya tana cewa, "Ke zaki shiga gaba mu take miki baya tunda gidanku ne." "To parrot kaddai mu shiga ki dinga nunata." Farha da tayi maganar ita ma bata tsira daga tsokanar kanwarta ta ba. "Kai Ya Farha daga wasa? To ko daga nan a biya garinsu ne shi ma." Suhaib da Lilu aka bari da dariya. Suka taka zuwa inda iyayensu suke tsaye bayan sun fito daga mota. Tsayuwarsu keda wuya Munzali ya fito tare da Ayaah a gefensa. Ita za ta rakasu dakin Innayo shi kuma zai shiga dasu Suhaib falon Asabe tunda babu kowa a ciki. I just published "30" of my story "UWA UWACE...". https://www.wattpad.com/1069890589?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=BatulMamman17&wp_originator=YYjueliRY%2Fur%2FdO5hYF6vB8QgjdvACtjcuW8JNTTky0CZQly4P%2B0Nqj0vZ7rPuLcyWAm9XBuv2o4lHOPXPp57ixksHVniR4WoKc4ZZoxJWeL3q9OW0OjNxfh6EOncFdV UWA UWACE...30 Batul Mamman💖 Innayo da 'ya'yanta sun karrama su Mami Khadija fiye da zaton Munzali. Shi ya kawo duk wani abin ci da sha to amma bai kai rabi rabin kyautatawar su Salima garesu ba. Farha tana ganin jaririyar Zara ta karbeta. Mardiyya da Sauda suka karaci nacinsu suka hakura. Uwani har lokacin tana daki ko lekowa a gaisa bata yi ba. Duniyar ce take ta hajijiya da ita. Bata da lokacin kanta balle na wani. Lokacin da suka shigo Murja tana ta sauri sauri ta kai karshen kitso biyun da ya rage musu, saboda haka kan Zara a bude yake. Suna sallama ana gamawa. To bayan sun zauna an gama gaisawa Sauda ta dinga taba Mami Khadija har sai da Innayo ta kula da hararar da Mamin take yi mata. Da hannu ta kira Saudan fuskarta dauke da murmushi. Bakin da gani sun baiwa kalmar 'babu' hutun shekara da shekaru ma. Amma babu alamun wulakanci ko girman kai. Mama Nasima ce ma dai ta hadiye rashin gamsuwarta ta hanyar kama bakinta tana jiran tabbatacen bayani game da gidan da matar dakin. "Zo ki fada min me kike so ake hanaki kamar ba dakin mamanki ba." Mami Khadija tayi saurin cewa "don Allah kar ki biye mata." "Sai dai a tari gaba." Yadda Innayo tayi maganar sai ya basu dariya. Sauda na tsoron batawa Mami Khadija wadda bata daina hararta ba, sannan tana kunyar badawa Innayo kasa a ido. Su biyun duka idanunsu na kanta. Ta kalli wannan ta kalli waccan ta dukar da kai. Farha da Mardiyya da ma su Zara da Ayaah wadda 'yan matan suka burgeta ana ta dariya. Mama Nasima kuwa cin magani take rai a bace sai ga Munzali ya shigo. Sauda ta hau murmushi da ajiyar zuciya. "Yauwa don Allah taimakeni." "Da me?" Ya amsa yana dube duben fuskokin mutanen dakin. Mami da Innayo ma sai da suka yi dariya wannan karon. Salima ce ta labarta masa me yake faruwa.  "Saboda haka ka taimaketa idan ba haka ba daya daga cikinsu zata hukunta ta." Halin rashin nutsuwar da yake ciki bai hana shi  biye musu ya yi murmushi ba.  "Nima dai babu ruwana. Kawai ki kwato kanki don duka ina tsoron fushinsu." "To ke kinji, kin kama kafar wala" cewar Mami Khadija da murmushi. Sauda ta turo baki ta soma cewa "Ai don dai ba Mar....." Kafin ta gama shi da Mardiyya sun kama kansu domin cikin sauri suka dinga cewa ta fadi abin da take so. Nan da nan dakin ya sake kaurewa da dariya. Sai da suka nutsu ne ta fada musu kitson da ta gani ne ya burgeta. Ayaah ta mike da sauri tana cewa "bari na kirawo miki wadda tayi." Sauda ta kalli Mami ita kuma ta ce ba za su jira ayi mata kitso ba. Munzali na jin haka ya ce "Mami ba a waje za a nemo mai kitson ba. 'Yata ce ita ma. Bari su zo na gabatar muku dasu" ya kare maganar da murmushi. Zara da Salima harda Innayo ne suka hadu suna rokar alfarmar Mami ta bari ayi kitson. Murmushi kawai tayi domin nauyinsu ne ya kamata ta kasa kafewa akan bakanta. Halayyarsu ta burgeta matuka don daga uwar har 'ya'yanta sun iya saka bako yaji kamar a gida yake. Shi yasa ta ce ba hanawa tayi ba sai dai da kunya zuwan farko su zauna ayi kitso. "Duk gida ne Hajiya kuma na fahimceki sosai. Amma don Allah ki bari ko manya tayi mata. Ki ajiye dalilin zuwanku ki dauka mu daku  daya ne." Mami Khadija ba yadda ta iya da furucin Innayo wanda tayi cikin sigar rarrashi da sanin ya kamata. A dole ta ce ta hakura amma fa manyan za ayi kuma tun wuri Innayo ta sani cewa idan sun je gida sai ta yiwa Sauda fada. "Ba zan hana wannan ba. Amma dai kar kiyi da yawa. Na tabbata jin da tayi kamar tana tare da 'yan uwanta ne yasa bata boye abin da take so ba. In wani gidan ne ita ma ba za ta soma ba ko Saudatu?". Sauda ta gyada kai tana kallon kasa. Farha ta tashi ta ce bari ta fadawa Suhaib. Saudan sai ta bita aka bar Mardiyya da ta karbi baby din Zara da Munzali tare da sauran mutanen falon.  Mardiyya kunyar kasancewar Munzali a wurin ta hanata sakat. Sau biyu suna hada ido. Murmushi yake mata wanda a kasan ransa yake jin zai iya zama na bankwana. Tunda Shazali ya kunno musu wuta yanzu basu san iya inda zata tsaya ba. Don kada kowa ya fahimci kallon me suke yiwa juna sai ta dubi Zara ta tambayeta sunan baby.  Kafin Zara ta san me za ta ce mata Mami Khadija ta sako tambayar waye babba tsakanin Munzali dasu Salima. Ba kuma haka kawai tayi ba sai don ta kawar da hankulansu daga tsakin da Mama Nasima take yi jifa jifa. Sautin na yanzu yafi karfi shi ne tayi tambayar da dan karfi ita ma. Har kasan ranta bata da niyar idan sun zo ta zake da yawa tunda ta san halin abokiyar zaman nata. Kar ta ce surukanta ne Mamin take shige musu. Kyawun mu'amalar 'yan uwan Munzalin ya bata sha'awa amma ta kula ba haka bane a wurin mai shirin zama surukarsu. Yatsine yatsine take ta yi da tsaki na gajiya da kosawa daga zamansu. Dalilinta kenan na jan maganar kitson da Sauda ta nuna mata kawai don kada su kunyata kansu. Munzali ya nuna mata Salima ya ce ta girme shi amma Zara kanwar bayansa ce. Ai fa nan suka soma musu da Zara akan waye babba har ya hakura ya karbi kankantarsa. * Da Ayaah ta fito kiran Murja samunta tayi tana waya. Gira ta dage tana yi mata dariyar shakiyanci saboda gane wanda ake wayar dashi. Mahiru ne saurayin da ya kai kudin aurenta. "Haba nifa naji shiru daga kaiwa baki abin sha baki dawo ba ashe ashe..." Sallama Murja tayi da Mahiru tayi dariya "gulmammiya indai ba labe ki ka yi min ba me ki ka ji na ce da zaki gane da wa nake waya?" Ayaah ta rausayar da kai hannunta daya akan kugu ta ce "gani nayi kina ta bin bango kina malalewa kamar ruwa irin abin nan na Indiyawa a lambun soyayya. Na ce duk yadda aka yi Yaya Mahiru ya fadi abin da ya susuta Murjanatu 'yar Baba."  Haushi ya kama Murja da Ayaah ta kwatanta irin tsayuwarta a jikin bangon harda waka. Iska ce ta debi maganganunsu har falon Asabe saboda sun fi kusa da wurin. Lilu ya kama dariya harda rike ciki. Suhaib ya kai masa duka yana nuna masa alamar ya yi shiru da dan yatsa. Shi ma hirar nishadi ta sanya shi har yaji yana son ganin fuskar mai tsokanar. "Kai fa baka da kan gado wallahi." A lokacin wakar da Ayaah take yi ta shiga kunnuwansa sai da ya murmusa. Gyara zama ya yi yana saurarensu tare da kallon Qibdiyya da Lilu yana biye mata kamar yaro dan uwanta. Waka take abinta babu kyakkyawan kari. Duk baitin da yazo kanta take fada. "Sai ruwa ruwa na malaleeeee. Ashe ruwan bana ya ci su Murjaaaa. Kinsan ya dade yana sonki ruwa na ...." "Zan malale bakinki a wurin nan" cewar Murja a fusace tana galla mata harara sai kuma ta kama dariya "murya kamar gogen tsumma."  Ayaah ta sha kunu tsiwar ta motsa ta ce "kin dai fada ne kawai don kiji dadi amma ke kin san muryata da dadi. Idan ina magana Dani kasa dauke ido yake daga kaina." "Waye kuma Dani kamar wani arne?" Furucin Murja kenan domin yau ta fara jin sunansa. Ran Ayaah in yayi dubu kuwa a take ya baci. Maganar tayi mata zafi don sai da taji kwalla na neman kwace mata. Dani din nata ake kamantawa da arne. A bangaren su Suhaib ma sai suka hada ido da jin kalmar Murja ta karshe da shirun Ayaah. Ba tantama ya da kanwa ne. Sai da Farha ta fito tana tambayarsu inda su Lilu suke sannan Ayaah ta fadawa Murja sakon da ya kawota.  Rashin sanin da mutane a kurkusa dasu ya sake bawa Ayaah haushi da Murja ta nuna falon Asabe. Da suka fito bayan gama jin bayanin Farha suka fito Ayaah ta basu baya tayi hanyar kofar gida da waya a kunne. Danliti ne ya iso yana neman karin kwatance. Basu ga fuskarta ba har suka karasa ciki wurinsu Innayo. *** Mami Khadija bata son barin 'yan matan dasu Lilu kadai a gidan. Sannan take taken Mama Nasima tun farkon zuwansu ya nuna mata zasu iya samun matsala akan jiran kitso. Cije lebe tayi ta rasa me zata ce da Innayo ba tare da ta bata mata rai ba.  To ita ma Innayo din duk ta karanci rudanin da Mami Khadijan ta shiga. Ita kadai a zuciyarta ta yabawa wannan uwa. Tunanin maslaha ta tayata inda bayan dan nazari na kankanin lokaci ta bude baki tayi musu magana. "Munzali ko zaka bisu da Murja sai Ayaah ta rakata. Kitson mutum daya dai na san kafin Magariba in Allah Ya so sun gama. Ko kuwa? Kunga sai a sami zumunci sosai tsakaninsu ko?" Kai Mami Khadija ta daga ta kalleta da murmushi sannan tayi mata godiya sosai. "Haka ne. Nima ba zaman kitson ne bana so ba amma kinga ..." tana son cewa su matsayin dangin mata suke kuma gashi ko iyaye maza basu gana ba. Ita da tun farko bata goyi bayan zuwan ba kuma harda Mardiyya bai kamata ta assasa dadewarsu ba. "Karki damu duk na fahimta. Bari ta kirawo kanwarta sai su biku tare." A lokacin Lilu ya bukaci Suhaib ya bashi mukullin mota yana da chakulet zai daukowa Qibdiyya. Nan ta soma tsalle. Munzali ya ce shan zakinta ya yi yawa kada ya dauko. Da ido Lilu ya yiwa Suhaib alamar ya taimaka ya dauko masa. Shi kuma sai ya sami kansa da biye masa yabi bayan Murja da ta fito kiran Ayaah. *** Turare Danliti ya sake mitsikawa a hannunsa yabi jikinsa ya shafe sannan ya sako kai soron da Ayaah ta shiga bayan ta hango shi. Tuni ya ce mata a bakin titi ya ajiye mota saboda ya zata layin nasu mota bata shiga. Ita ma a ciki hijabinta ta gyarawa zama tasa hannu ta dan goge fuska. Idanun iyayenta da bakin dakin Innayo ne suka hanata sabunta kwalliya domin tarbarsa. A tare suka sakarwa juna murmushi da ya shigo. Idanunsu sarke da juna kunya duk ta kamata. "Baby kin yi min kyau sosai." Kalman da Suhaib yaji kenan da ya tunkaro kofar. Can ya baro Murja tayi cikin gida tana ta kwala kiran Ayaah. Bai san wace ce ba amma zuciyarsa ta bashi abokiyar fadanta ta dazu ce wadda aka ce zasu tafi tare. Fari tayi masa da ido sannan tayi godiya. "Na gode Dani." 'Dani?' Suhaib ya ambaci sunan a ransa yana mai tuna abin da ya hada 'yan uwan rigima. Curiosity bai barshi ya cigaba da tsayuwa inda ya dakata ba. Yanke shawarar wucesu don yaga fuskokinsu su biyun ya yi. Murmushi ya bayyana akan fuskarsa da ya ayyana me Lilu zai yi da shi ne ya fito. Ya daga kafa zai cike tazarar dake tsakaninsa da kofar soron sai yaji abin da bai zata ba. Muryar mai suna Dani ce take fita a raunane cike da makirci irin wanda ba kowa zai gane ba. "Baby yau ma ina cikin damuwa. Shi yasa ma kika ga na matsa sai mun hadu." Bai kuma jira jin cewarta ba don ya kula ta fara yi masa kallon tausayin nan ya dora da "wai ko kinsan yanzu matar nan ta daina zuwa shimfidata sai na biya?" A saukar aradu maganar ta shiga kunnuwan Ayaah da Suhaib. Ita nauyi da kunya ne suka kama ta gami da fara jin haushin me yasa hirarsa bata wuce irin wadannan maganganun. Suhaib kuwa zuciyarsa yaji ta soma tafarfasa. Ya yiwa zina da duk wani ma'abocinta mummunar tsana. Salon hirar nan kuwa ba komai bane illa dauko hanyar bude kofar da za a iya fadawa gareta. Yarinyar da yaji muryarta kila ba za ta wuce sa'arsu Sauda ba ita ake fadawa wadannan kalamai. Jikinsa har yana tsuma don bacin rai ya iso daidai bakin kofar amma sun juya masa baya sannan yaji amsarta. Muryarta har raurawa take yi saboda an kure rashin kunyarta ta ce "Dani ina ga ba ni ya kamata ka fadawa wannan matsalar ba. Gara dai ka kaiwa magabatanku a nemi mafita." Danliti ya gane ta fara jin tsoro daga muryarta ya yi murmushin gefen baki. Da tsoron wanda bai hana cigaba da soyayya ake samun kan irinta. Sake kwantar da murya ya yi abinsa harda langabe kai. "Wa zan fadawa matsalata bayan Mum idan ba ke ba? Ita kuma saboda bata kasar bana son yawan tayar mata da hankali. Kece dai wadda nake shirin aura nake ganin ya dace ki san matsalolina tun yanzu domin ki tanadi hanyoyin magancesu." Maganar tasa tana fita ne daidai da takunsa da yake ta kusanto shi gareta. Idanun Ayaah sun yi wuri wuri amma ta rasa me ya hanata ja da baya. Tausayinsa take ji har kokon ranta tana kuma gudun kar ya nemi wata idan taki taimaka masa. Bata yi aune ba ta ji shi daf da ita har tana jin dumin numfashinsa. "Baby ko dan huk (hug) ne don Allah in samu domin na rage zafi. Ina tsananin bukatar mace. Jiya na tura mata dubu dari ta ce ya mata kadan. Ni kuma shi ne naji haushi ban sake yi mata magana ba. Kudin bai dame ni ba amma na gaji da rainin wayo." Sai ga Suhaib yana tafa hannuwa kamar mace saboda tsabar mamakin da ya sarke shi. Bai taba ganin dan is... kamar wannan mai sunan arnan ba. Duk da haka ya tsaya yana son ganin irin tarbar da Ayaah zata yiwa yunkurinsa domin ya san matsayin da zai ajiyeta. Duk abin da ake yi ko fuskarta bai gani ba har yanzu.  Akan idonsa ta ja baya kadan tayi magana kamar mai shirin kuka. "Ka kara hakuri. Ba ka ce idan Mum din ta dawo za a turo ba? Ka bari ayi auren." Hannu ya daga yana son shafa fuskarta ta goce da sauri. So yake su wuce wannan matakin ya sami yadda yake so. Yawancin mata wuyarta a sami kansu na farko. Daga basu da zabin da ya wuce amincewa a gaba saboda gudun kada a ki aurensu. Ya dade da yadda da wannan shi yasa yake cin karensa babu babbaka.  Cikin muryar dake nuni da tsantsar karaya da neman agaji ya ce  "Har sai wannan lokacin Ayaah? Idan na shiga wani hali kafin nan ba laifinta bane ita kadai har dake. Naki ma yafi nata domin zuciyata da gangar jiki duka ke suke so.  Nayi zaton zuwa yanzu nafi karfin komai a wurinki. Ashe ni kadai nake haukana. Yadda na daukeki daban da matsayin da kika bani."  "Ba haka bane. Kai ma ka san ina sonka." "To ki nuna min a aikace. Ki mantar dani bakincikin da matata take kunsa min. Ki cire tsoro a ranki domin wallahi ko raina ki ka nema zan iya baki. Sannan kada ki manta dama ya halatta na ganki tunda maganar aure ce tsakaninmu. Gani babu hijabi balle mayafi. Hakkina ne kike neman dannewa Baby. Kin yi min adalci kenan?" Runtse idanu Ayaah tayi da ya sake daga hannu zai shafa fuskarta. Bata so ko kadan amma zuciyarta ta gama aminta da halatta haramun din da yake neman yi. Ba zina zata yi ba. Nutsuwar da yake nema kawai take son taimaka masa ya samu. Suhaib bai san lokacin da ya iso gabansu ba. Danliti da ya gama sakawa ransa cewa daga shafa fuskar zai zarce da koya mata wani karatun daban sai ji ya yi hannunsa ya makale a iska. Daga kai ya yi yana kallon gefen fuskar mutumin da ya rike shi a firgice. Ayaah kuwa da taji shiru bai taba ta ba sai ta bude idanunta a hankali. Nan suka yi ido hudu da mutumin da bata sani ba. Kwayar idonsa tamkar maganadisu aka zuba saboda yadda ta kasa dauke nata. Mugun kallo yake yi mata mai kama da na tsana. Zuciyarta sai da tayi wani irin tsalle don tsoratar da tayi. Suhaib ya kuma ware mata idanuwansa da suka kara firgita ta. "Get out of here (bar wurin nan)" ya umarceta da tsawa. A guje tayi cikin gida tana haki. Murja har ta fitar da rai da ganinta suka yi karo. Bata kula da yanayinta ba ta fada mata sakon Innayo. Bayan tafiyarta Suhaib ya kalli Danliti wanda yake ta kokawar kwace hannunsa ya kasa. Tuno inda ya san fuskarsa ya yi ba shiri ya saki hannun baki a bude. "Kai? Ba kai bane makaniken...." Bai iya karasa magana ba sakamakon ture shi da Danliti ya yi da karfi ya kwasa a guje ya fita daga soron. Tunda ya fita ba shi ya tsaya ba sai da yaje titi. Ya tsaya mayar da numfashi bai yi aune ba wani mai kurar ruwa ya kwashe shi ya watsar a gefe.  * Innayo da iyalinta har bakin mota suka rako su Mami Khadija. Su suna godiyar ziyara ita tana ta kyautata musu da aka yi. Ita dai Mama Nasima mota ta shige kai tsaye ko waige babu. Tuni ta fara musu da zuciyarta akan amincewa alakar Munzali da Mardiyya. Ta raina gidan da ahalin gidan. An rarrabu kowa ya shiga mota. Ayaah kamar wadda ta yiwa Sarki karya gabadaya ta kasa sakewa. Duk inda ta motsa sai taga kamar idanun mutumin da taji Kawunta ya kira Suhaib suna kanta. A gaban motar Munzali ta zauna ta hade hannuwanta a tsakiyar cinya. Murja tana baya suka bi bayan motar Suhaib din. Ita dai har suka isa gidan bata san inda tunaninta yake ba. Tsakin da taji lokacin da ta fito daga motar ne ma yasa ta karewa gidan da suka iso kallo. Ido suka kuma hadawa da Suhaib ya sake yin tsaki a karo na biyu sannan ya kawar da kai tamkar yana kyamar kallonta.  Hawaye taji yana neman sauko mata ta daure ta hadiye shi. Da tabi 'yan matan cikin gidan shi tsayuwa ya yi wurin Munzali suna magana. Hankalinta a tashe tana tsoron ko abin da ya gani yake fada masa. Ana ta janta da hira sai dai tayi yake. Cikin abin da bai kai minti talatin ba har an gama kitson. Mami Khadija ta basu kudi suka ki karba. Har ta nuna bacin rai amma suka ki. Sai suka sake burgeta. Dama da a gida suka hadu ba kudi zata bayar ba. Kyauta zata yi musu irin wadda ta dace da 'yan mata. "Ku karbi nambar juna ku dinga gaisawa. A haka ake fara zumunci." Abin da tace musu kenan sannan ta juya ta barsu dasu Sauda. Da yake 'ya'yan nata babu girman kai a take suka fara aiwatar da shawararta, aka yi musayar nambobi tsakaninsu. Ayaah jiki ya kasa daina rawa saboda ganin har lokacin Munzali da Suhaib suna magana. Da Munzali ya kallo inda take kuwa sai da taji kamar ta saki fitsari a wurin.  "Ku zo mu tafi"  Kasa daga kafa tayi sai da Murja ta ja hannunta. Da suka isa bakin motar Suhaib ya bata mamaki da ya bude mata gaban sannan ya hada da yi mata murmushi. Kura masa idanu tayi ba shiri domin tabbatar da abin da take gani. Ya kuwa sake yi mata murmushi a karo na biyu. Farha tana yi musu sallama shi ma ya yi harda cewa su gaida gida. Murmushinsa bai hanata satar kallon Munzali ba a hanya tana jiran ya fara fada. Gani take kamar na mugunta yake mata bayan ya gama hada mata bomb. Kallon hanya da zurfi cikin tunani da take ganin Munzali ya yi bashi da alaka da abin da take tunani. Suhaib ya yi masa magana ne akan baffaninsu maza da suka yaba dasu har suka bukaci a sanar dasu cewa su turo iyayensu indai da gaske suke. Ya kira Abbati yafi sau shurin masaki amma bai dauka ba tunda gari ya waye. Abin ya karu domin yanzu wayar ko shiga bata yi. Haka ya rufe ido ya kira layin Baaba Mari shi ma shiru. Kafin ya isa kofar gidan Hasiya ya kira mutum ya kai shida a gidansu Abbati. A kalla kowanne ya kira sau uku ko hudu. Hankalinsa ya tashi sosai har ta kai kwatancen gidansu da Murja take yi masa baya ganewa sosai. Sau biyu yana yin kwana sabanin wadda take fada masa. Tsayuwarsa da mota ke da wuya Ummita ta fito rike da Hasiya a jikinta. Tangadi suke duk su biyun. Hasiya na ciwo, Ummita na firgicin irin aman da taga tana yi. Cikin kankanin lokaci ta fita daga hayyacinta. Ko kashe motar bai yi ba Ayaah da Murja suka fita da sauri.  "Me ya sameta?" Ummita tana kuka ta fada masa yadda Hasiya ta dinga amai daga kwabin lalle. Babansu kuma tun safe Abdulkarim ya turo aka tafi dashi asibiti tare da Abbas. Duk wannan bayanin a hanya aka yi shi. Gudu irin na  ganganci ya dinga yi saboda kakarin da Hasiya take yi a galabaice.  Kiran Abbatin da bai sake samun damar yi ba kenan a ranar domin suna zuwa asibitin emergency aka nufa da ita. *** "Gabadaya na kasa fahimtar bayaninka Abbati. Haka kawai ta suma bayan bata kwana da ciwon komai ba?" Mal. Inuwa ya furta hankalinsa yana ga Baaba Mari dake kwance akan gadon asibiti rai kwakwai, mutu kwakwai. Atine ce tayi karfin halin cewa "Ya ce magana suke fa yaji ta daina amsawa" Duka 'ya'yan Baaba Mari suna dakin da aka kwantar da ita a babban asibitin garin Kirikasamma. Abbati ya rasa me yake masa dadi a duniya. Gefe guda ya samu ya zauna ya hada kai da gwiwa cikin tunani. Tare suke da mahaifinsu Mal. Inuwa da wasu cikin Gwoggoninsu matan 'yan uwansa. Shi Mal. Inuwa yafi kowa nuna gigita saboda yadda yaga Abbati ya fito da ita waje a hannu ko motsi bata yi. Daga shi har 'yan majalisarsa sun dauka bata da rai. Kowa yana tofa albarkacin bakinsa game da ciwon da ba a san silarsa ba likita ya dawo. Wasu gwaje gwajen jini ya sake rubutawa ya bukaci Abbati ya biyo shi waje. Da sauri Mal. Inuwa ya ce "Fadi ko ma mene ne Dafta. Nan wajen duka babu bare. Me ya sami Mari?" Likitan ya dubi Abbati wanda ya gyada masa kai sannan ya fada musu abin da suka gano. "A gaskiya jininta ya hau fiye da kima har yana barazanar taba mata zuciya. Idan ba a dauki matakin da ya dace ba zata iya samun stroke (mutuwar barin jiki) ko ...." "Allah ma Ya kiyaye" cewar Mal. Inuwa da rawar murya "indai kudi ne sha Allahu ba zai gagara ba. Ayi mata duk abin da ya dace ga danta nan." "Malam. Malam" Ba Mal. Inuwa da ta kira ba, duka wanda yake dakin sai da ya juya da farincikin ganin Baaba Mari ta farfado. Da hannu ta yafito shi ya matso kusa da gadon ya duka kansa ganin tana ta motsa baki. "Ku mayar dani gida." Wani irin kallo ya mata cikin tashin hankali ya daga kansa ya yiwa Abbati inkiya da ya matso. Su Habi duk sai suka fice. "Kaji taurin kan mata ko? Wai a mayar da ita gida." Murmushi tayi masa "Idan an kaini asibitin waye zai biya kudin?" "Wace irin magana ce wannan? Ko kin sami makuwa ne saboda ciwo?" Muryarta ta kara dusashewa ta ce "kana da sauran kadara ne Malam da zaka sayar ka nema min magani?" Duk da ya soma harzuka haka ya daure saboda ba lafiya gareta ba ya ce "Wai ba ga Abbati ba? Mari lafiyarki kuwa?" Idanun Abbatin ta lalubo da nata. Ya zabge tamkar shi ne kwance a gadon asibitin. Kalamanta na gaba a gareshi ita kanta basu yi mata dadi ba sai dai babu gudu ba ja da baya. "Ban yafe ba idan ya sake kashe min kwandalarsa. Ban yarda kaima ka kashe min daga kudin da ya baka ba. Sannan idan ban tashi ba ka isar da sakona ga dan uwanka Sa'idu. Ni MARIYA BA YAFE MASA BA!" I just published "31" of my story "UWA UWACE...". https://www.wattpad.com/1072817053?utm_medium=com.whatsapp&utm_source=android&utm_content=share_published UWA UWACE...31 Batul Mamman💖 "Anya Mari baki yi gamo ba? Yaya Sa'idun kike ja wa Allah Ya isa?" Wani bacin rai ne ya turnuke kirjinta. Wato bai ma damu da abin da tace akan dan cikinsa ba sai yayansa wanda ya zama silar rushewar rayuwar 'ya'yanta maza. "Ko in hada da kai ne?" Mal. Inuwa ba arziki ya saita fuskarsa daga fushin da ya yi da farko "Ni kuma me nayi?" Ko kula shi bata yi ba ta dubi Abbati da murmushi. Wannan karon kallon yana cike da soyayyar uwa da danta. Yadda ya koma yafi mata ciwo akan shi kansa. Dukiyarsa take son ta raba shi da ita domin babu amfani su cigaba da ninkaya cikin haram. Sabuwar rayuwa za ta tura shi da taimakon Allah wadda bai taso cikinta ba tunda ya fara sana'arsa. A yanzu yafi bukatar soyayyarta da tausayawa kuma a shirye take ta nuna masa domin yaji dadin tuba. "Kirawo 'yan uwanka su taimaka min na tashi." Kai ya gyada daidai da saukowar hawaye a idanunsa. Tana kallon yadda yasa bayan hannunsa ya dauke hawayen sai dai bai hana wasu gudana suna maye gurbin wanda yake sharewa ba. Haka ya fita bai yi musu akan rashin son zamanta ba. Ya fahimceta sarai. A shirye yake ya bi umarninta. Da hannu ya kara goge idanunsa sannan ya kira kannen nasa. Da ya fita Mal. Inuwa kallon tuhuma ya dinga yi mata. Tabbas akwai abin da yake faruwa tsakaninta da Abbati. A matse yake da son ji. Sai dai yanayin fuskarta ya sanya tayi masa kwarjinin da ba zai iya yi mata titsiye ba. Likitan da ya dubata har bakin mota ya bisu yana nanata musu gangancin dake tattare da dauketa a yanzu. "Bai kamata ku biye mata don ta ce ba za ta zauna ba" ya dubi matan da ya tabbatar 'ya'yanta ne saboda kukan da suke da rokon yayansu akan su zauna "za ta iya shiga yanayin da dukkanku nan sai kun yi dana sanin kin karbar shawarata." Habi sai ta koma kusa da mahaifinsu tana kuka. "Kaji abin da yake cewa Baba. Don Allah ka tilasta mata ta zauna." "Abbati?" "Baba muje gidan. Da kaina zan dawo da ita asibiti in Allah Ya yarda." Iyakar abin da yace kenan ya shiga gaban motar da zata mayar dasu gida. * Deluwa ce kan gaba wurin zuwa bangaren Baaba Mari bayan sun dawo. Daga ita sai daurin kirji da dankwali a ka. Tabe baki tayi tana soshe-soshen jiki. "Yo aka ce mana ranga- ranga aka fitar dake ashe ma ciwon ba wani na azo a gani bane." Ci-kan-ki wannan bata samu daga bakin kowa ba. Ta gaji da maganganunta ta kama hanya za ta fita. "Ki kirawo min mijinki idan kin fita" Wata irin juyowa Deluwa tayi ta kalli bakin Baaba Mari da ya furta wannan maganar. Har wani duka ta kaiwa kunnenta domin tabbatarwa. "Ki ka ce?" "Ki turo min mijinki! Da jikina da kwari da kaina zan je na same shi." Mal. Inuwa dama ya matsu yaji me yake faruwa. To amma shi ma yadda tayi maganar ba karamin tsorata shi ya yi ba. Musamman da ta sallami duka 'ya'yanta da jama'ar gidan da suke sashen nasu ta bar Abbati shi kadai. Dadin dadawa kuma sai shi ma Abbatin ya yi wata magana da ta sabule masa kuzarinsa ya kara shiga firgici akan me yake faruwa. Hadiyar yawu mai masifaffen daci ya yi, idanunsa duk sun shige ciki ya dubeta. "Baaba tona min asiri zaki yi? Na rantse miki ba yau na tuba ba. Ni da Munzali har..." Runtse idanuwa tayi da ya ambaci sunan Munzali. Allah Ya sani ko sunansa bata son ji balle ayi hirarsa. Ya fice mata a rai lokaci guda kamar anyi ruwa an dauke. Akwai laifin mijinta da yayansa dumu dumu amma nasa mai girma ne. Bata jin zata taba manta cewa shi ya koya masa....karshenta ma har yanzu suna yi. Tsigar jikinta a take ta mimmike da wannan tunanin. "Idan ban yiwa tufkar hanci ba ka san irinka nawa zasu samar mana a dangi?" Abin da ta ce kenan. Sai ya koma jikin bango ya tsaya tare da jingina bayansa. Babu wani abu ko digo da yake yi masa dadi a duniyar nan. Nadama iyakar nadama ya kara yi. Ya tsani ranakun da ya mika jikinsa ga marasa tsoron Allah cikin manyan mutane masu fada a ji a kasar nan. Farincikin da kudaden suka saka shi ya koma bakinciki. Sallamar Mal. Sa'idu da kakkaurar murya mai nuni da girman bacin ransa sai da tasa hanjin cikinsa kanannadewa. Zazzabi mai zafi har cikin 'bargo ya afka masa. Daga wannan lokacin zai sanya kafa guda da sabon shafin rayuwa. Idan har zai iya cigaba da rayuwar. Shikenan! *** "Wa nake gani kamar Mariya?" Asabe ta takawa kafafunta burki a daidai kofar dakin Innayo. Laluben dakin da yake sakale akan dokin kofa ta sake dagawa da hannunta ta leka ciki. Tabbas jikarta ce take hangowa zaune akan cinyar Salima tana ta zuba surutu. Ranta ya sosu ta taka cikin falon ko sallama babu sai ganin hannunta Salima tayi tana kokarin fincikar Qibdiyyan. "Tashi ki wuce muje." Noke kafada tayi ta kwace hannunta. Salima ta murmusa kawai ta ce mata "tashi mana Qibdiyya. Sannu da zuwa Asabe." "Ban son munafunci. Ki rike sannunki ki sakar min jika" Sababi ta hau yi akan dalilinsu na riketa a dakin. "Shi ma Munzalin zai zo ya sameni. Akan me zai kawota bai fada min ba?" Innayo da Zara duka suna falon amma yadda bata nuna ta gansu ba haka su ma basu kulata ba. Ta gaji da fadanta ta dauki Qibdiyya da karfi ta nufi bangarenta. Ihunta suka ji da ta tura kofar ta bude ba tare da ta saka mukulli ba. "Jar uban nan! Wallahi gidan nan baku so zaman lafiya ba. Wace mai kokarin ce ta bude min daki?" "Daddyna ne ya budewa su Uncle Lilu." Asabe ta gatsina fuska "waye kuma Unku Lihu?" "Uncle Lilu da yake min doki a bayansa... " Cewar Qibdiyya da mamakinta irin na yara idan aka kasa gane abu mai mahimmanci a wurinsu. Asabe hakura tayi da neman ba'asi. Duk inda yake ta san dole zai dawo daukan 'yarsa. Zata nemi karin bayani a wurinsa. Sannan kuma ta samu ta karbi kudin da take tunanin shi ya zo bata. Mayafinta ta kama za ta cire Qibdiyya ta ce zata yi fitsari. Sunkutarta tayi gabadayanta ta shiga bandaki. Yarinya fes da ita amma saboda son burge mahaifinta kamar ba dan cikinta ba ta tube mata kaya. "Wanka zan miki kada ya dawo ya ganki haka kamar wadda tayi dambe." Bata da ruwan dumi amma don kar ya dawo bata gama ba idan ta tsaya dafawa sai tayi mata da mai sanyi. Qibdiyya harda kukanta don garin babu wannan zafin da zai sa mutum wanka da ruwan sanyi. Aka zo shafa mai tabi ta mulketa da man kadanya sai kyalli take. Ta kawo kwalli aka rambada mata a ido. Ta tafi dauko pant din da ta cire mata a bandaki Qibdiyya ta kai hannu gabanta tana susa. Wanka ne aka yi aka koro maikon jiki amma ba ayi mata tsarki ba. Dan datti da ruwan sabulun da ya wuce ta wajen da fitsarin da tayi ba a wanke ba. Wannan susa akan idon Asabe da ta dawo daga bandakin. "Kalau kike kartar jiki haka da karfi? Kwanta mu gani ko kurji ne a wajen." Da kanta ta kwantar da ita ta kai hannu za ta raba kafafunta taji ta cafke mata hannun. Idanuwa Qibdiyya ke binta dasu tana yi mata kallon tsoro. "Kema hannu zaki saka min a nan? Kiyi min a hankali ba mai zafi ba. Kuma ba zan fadawa kowa ba don kada ki yanka min Daddy da Papa." Asabe ido kawai ta zuba mata ta kasa kwakkwaran motsi saboda firgici. Qibdiyya kuwa tuni ta rufe ido tana jira ayi a gama. Da taji shiru sai ta bude idon a hankali. Da karamar muryarta ta ce da Asabe, "Ni ce zan yi miki?" Kamar wadda aka kwadawa mari sai lokacin Asabe ta dawo hayyacinta. Kuka ta kama yi ba tare da ta sani ba ga jikinta ya soma rawa kamar mazari. Furucin Qibdiyya ya matukar tayar mata da hankali fiye da tunani. Shi yasa bata ma san lokacin da ta d'aka mata wani mugun duka a cinya ba. "Ki yi min uwar me? Na bonu ni Asabe. Kiyi min me? Tashi don uban...." Qibdiyya ta tashi zaune a razane tana son yin kuka amma tsoro ya hana. Daddy ya hanata kuka ko taji zafi idan yana yi mata abu irin wannan. Cewa yake hawayenta na fita za a saka mamanta a rami a rufe da kasa. Tun bata iya ba har ta kware wurin danne hawayenta. Idanu tsilli tsilli ta kafe Asabe dasu babu alamar kuka duk zafin dukan. "Daina kallona" wani tunani tayi ta sake kwantar da Qibdiyya ta soma dubata. Allah ne kadai Ya taimaketa bata suma ba akan abin da ta gani. Kankanuwar yarinya ta kusa gama budewa. Kafafunta kasa daukarta suka yi bata ankara ba tayi zaman 'yan bori a kasa. Kai ta dago dankwalinta ya karkace saura kadan ya fadi ta kalli jikarta. "Waye yake taba miki nan?" Ta nunawa Qibdiyya inda take tambaya da hannu. Razanar da tayi a dalilin dukan da tayi mata dazu da kuma tsoron kada a rufe mata uwa a rami sai taki fada. Jikinta yana bata cewa idan ta fada din ma ba tsira zata yi ba. Asabe ta gaji da tambaya ta soma dukanta. Amma ko digon hawaye babu sai ajiyar zuciya. Hargagin muryarta tana cewa "ba za ki fada min ba?" har tsakar gida. Uwani ta fito tana waya taji. Hanyar dakin ta nufa sai dai kafin ta isa Innayo ta fito daga nata dakin ta ce mata kada ta soma zuwa. "Bana son gulma ki zo ki wuce naki uzurin kada ki ja min magana". Komawa tayi din amma haka kawai taji ta kwadaitu da son sanin me yake faruwa. Maganar dai kamar da Qibdiyya ake yi amma bata ji ko tarin yarinyar ba. * "Munzali kana ina?" Sautin muryarta banda alamun tashin hankali harda kuka yake iya ji. "Muna asibiti da Hasiya ne amma na kusa tahowa. Wani abin ne?" Karo na farko a rayuwar Asabe da ta dakata tayi tunani kenan da kwakwalwarta. Wannan sam ba maganar waya bace. "Ka taho da sauri ina son ganinka yanzun nan." Bayan ajiye wayar hankalinsa ya kasa kwanciya. Yasa rai da jin mitarta akan zuwa wurin 'ya'yan Innayo. Kudi ya damkawa Ummita kafin shigowar Hon. Habu ya ce musu zai je gida ya dawo. Akan hanya ya dinga kiran Abbati shiru bai dauka ba. Kansa ya sake daukar chaji kamar ana buga guduma. Ya san Abbati ba yaro bane da za a zane bayan ya fadi gaskiya. To amma me ya biyo bayan fadin tunda ya tabbatar da wahala idan bai fada din ba. *** Sanyi da daddadan kamshi ke tashi a wani katafaren falo. Duk inda ake neman ni'ima mai shiga zuci an gama samu a nan. Mazauna wurin maza ne su biyar wadanda shekarunsu suka tura. Ga kuma shaida a jikinsu na cewa sun kama kasa. Daga 'yan siyasa sai 'yan kasuwa sai kuwa masu manyan mukamai a gwomnati. Dukkaninsu sanye suke da manyan kaya harda babbar riga illa mutum daya. Daga gani shi ne mai masaukin baki saboda yadda ya bararraje. Hula da babbar rigarsa duk suna gefe guda can nesa dashi. Bayani yake yiwa babban bakonsu. Amininsu ne ta fanin harkokin 'yan mata. Sai gashi a Kano garin yake gida ga sauran hudun. "Yanzu sai da kana shirin komawa Kaduna zaka sanar damu zuwanka Alh. Tahir? Karramawar nan da ake yiwa manyan baki ma baka bamu damar yi maka ba." Cewar mai gidan hutun (guest house) din da suke ciki. Dariya Alh. Tahir ya yi masa "banda abinka ni da na taho da taurarina guda uku ina ni ina bin kwararo?" Kwashewa suka yi da dariyar shakiyanci suna zolayar juna. Nan hira ta kacame da ciye ciyen kayan abinci na alfarma. Maigidan aka kira ya amsa ya bayar da umarni ga mai kiran da ya shigo. Alh. Tahir na jin haka ya san ba zai wuce mace aka kawo ba. Murmushi ya yi yana gyada kai. "Ni dai bari na gudu don na tuba." Wani Alhaji mai tulun ciki ya tafa da na kusa dashi suka yi masa dariya "Kowa ya tuba don wuya ba lada." Alh. Tahir ya kada kai "da lada fa. Abubuwa sun cabe min. 'Yar banzar yarinyar nan kawar Farha da nake fada muku yanzu fa Yakumbo ta rantse sai na aureta. Yarinyar da take yawonta da kananan yara kuma duk na sani." Mai gidan yaja guntun tsaki "duk laifinka ne. Na fada maka wallahi Malamina yana aiki akansu maganar nan zata bi ruwa. Ita Yakumbon da kanta za ta ce a bar maganar. Yarinyar kuwa duk iskancinta sai an sauke mata shi. Ba za ta sake yin wani yunkuri domin bata maka suna ba." "Wai kai Alh. Tahir tsoron me kake ne? Ka amince mana ka yar da kwallon mangwaro. Yarinyar nan a bariki ta sameka tayi kadan ta kawo maka cikas da girmanka da komai." Wani da bai ce komai ba tun dazu ya tofa albarkacin bakinsa. Mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki. Basu wani jima ba suka shawo kansa. Nan take Maigidan wanda aka fi sani da Comared ya kira Malamin tsibbunsa a waya. Suna kan magana wani mutum sanye da kufta da wando ya zo ya shige cikin dakin Comared din da dan matashi da bai fi shekaru sha takwas ba. Bayan ya gama wayar ne Alh. Tahir ya tsare shi da idanu yana nuni da dakin nasa. "Comared ba dai kaima ka fara daya harkar ba da maza?" Kkamar dazu, yanzu ma dariya sauran suka yi masa. Comared ya gyara zama yana shafar gemunsa. "Wannan Malamin da na kira shi ya dorani a harkar nan. Naki fada maka ne kawai saboda naga kamar kana kyamar abin. Magana ta gaskiya wani aiki aka yi min shi ne yace na nemi namiji. Washegari aikin ya ci to amma abin ya zarce...." Ya kare da shu'umar dariya. Alh. Tahir ya kada kai "kace ya hadani da mata goma ni dai akan namiji guda." Wata dariyar Comared ya yi domin aikinsa kenan. Dariya kamar dan akuya. "Ai kuwa ka makaro domin kuwa namiji ya ce ka nema ranar laraba kafin rana tayi zawali. Indai kayi yadda ya ce da kanka za ka nemeni. Zai aiko da magani da zaka hada kafin kayi abin." Hula Alh. Tahir ya cire ya shafi sumar kansa wadda ta fara samun bakin furfura. Ko kadan baya son auren Yumna musamman saboda abin da ta nunawa Farha. A bangare daya kuma ko yana shan giyar wake ba zai so tsinuwar Yakumbo ba. Sau daya dai don ya nemi namiji ba zai rage shi da komai ba. Yana tunanin abin yaji tsigar jikinsa ta mike har amai na neman taso masa. Wayarsa ya dauka ya tashi yana yi musu sallama. Comared ya dakatar dashi daga tafiya "bari nasa ayi maka booking wanda ya san me yake yi tunda kai sabon shiga ne" waya ya dauka ya sake kira sai ga mai kuftar da ya shige dakinsa ya fito. Zubewa ya yi kamar mai rokon gafara a gabansa "Yallabai kana da wata bukatar ne?" Kofar dakinsa ya kalla ya hadiyi yawu "yaron da ka kawo daga gani ya yi kawai. Kwararre a harkar nan nake so kayi min booking ranar laraba mai zuwa. Ina son irin wanda idan sabon kamu ya samu gobe da kansa zai koma. Daga aljihuna kadai zan baka dubu dari biyar. Shi kuma uban gayyar ba mai rowa bane. Ka sa rai da farin gani." Shazali ya saki murmushi har hakoransa suka fito. Ya san inda zai samo musu kalar wadanda suke so. Shi da yake da shaidar da zata tarwatsa musu rayuwa, dolensu su zo ko sun ki ko sun so. I just published "30" of my story "UWA UWACE...". https://www.wattpad.com/1069890589?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=BatulMamman17&wp_originator=YYjueliRY%2Fur%2FdO5hYF6vB8QgjdvACtjcuW8JNTTky0CZQly4P%2B0Nqj0vZ7rPuLcyWAm9XBuv2o4lHOPXPp57ixksHVniR4WoKc4ZZoxJWeL3q9OW0OjNxfh6EOncFdV UWA UWACE...30 Batul Mamman💖 Innayo da 'ya'yanta sun karrama su Mami Khadija fiye da zaton Munzali. Shi ya kawo duk wani abin ci da sha to amma bai kai rabi rabin kyautatawar su Salima garesu ba. Farha tana ganin jaririyar Zara ta karbeta. Mardiyya da Sauda suka karaci nacinsu suka hakura. Uwani har lokacin tana daki ko lekowa a gaisa bata yi ba. Duniyar ce take ta hajijiya da ita. Bata da lokacin kanta balle na wani. Lokacin da suka shigo Murja tana ta sauri sauri ta kai karshen kitso biyun da ya rage musu, saboda haka kan Zara a bude yake. Suna sallama ana gamawa. To bayan sun zauna an gama gaisawa Sauda ta dinga taba Mami Khadija har sai da Innayo ta kula da hararar da Mamin take yi mata. Da hannu ta kira Saudan fuskarta dauke da murmushi. Bakin da gani sun baiwa kalmar 'babu' hutun shekara da shekaru ma. Amma babu alamun wulakanci ko girman kai. Mama Nasima ce ma dai ta hadiye rashin gamsuwarta ta hanyar kama bakinta tana jiran tabbatacen bayani game da gidan da matar dakin. "Zo ki fada min me kike so ake hanaki kamar ba dakin mamanki ba." Mami Khadija tayi saurin cewa "don Allah kar ki biye mata." "Sai dai a tari gaba." Yadda Innayo tayi maganar sai ya basu dariya. Sauda na tsoron batawa Mami Khadija wadda bata daina hararta ba, sannan tana kunyar badawa Innayo kasa a ido. Su biyun duka idanunsu na kanta. Ta kalli wannan ta kalli waccan ta dukar da kai. Farha da Mardiyya da ma su Zara da Ayaah wadda 'yan matan suka burgeta ana ta dariya. Mama Nasima kuwa cin magani take rai a bace sai ga Munzali ya shigo. Sauda ta hau murmushi da ajiyar zuciya. "Yauwa don Allah taimakeni." "Da me?" Ya amsa yana dube duben fuskokin mutanen dakin. Mami da Innayo ma sai da suka yi dariya wannan karon. Salima ce ta labarta masa me yake faruwa.  "Saboda haka ka taimaketa idan ba haka ba daya daga cikinsu zata hukunta ta." Halin rashin nutsuwar da yake ciki bai hana shi  biye musu ya yi murmushi ba.  "Nima dai babu ruwana. Kawai ki kwato kanki don duka ina tsoron fushinsu." "To ke kinji, kin kama kafar wala" cewar Mami Khadija da murmushi. Sauda ta turo baki ta soma cewa "Ai don dai ba Mar....." Kafin ta gama shi da Mardiyya sun kama kansu domin cikin sauri suka dinga cewa ta fadi abin da take so. Nan da nan dakin ya sake kaurewa da dariya. Sai da suka nutsu ne ta fada musu kitson da ta gani ne ya burgeta. Ayaah ta mike da sauri tana cewa "bari na kirawo miki wadda tayi." Sauda ta kalli Mami ita kuma ta ce ba za su jira ayi mata kitso ba. Munzali na jin haka ya ce "Mami ba a waje za a nemo mai kitson ba. 'Yata ce ita ma. Bari su zo na gabatar muku dasu" ya kare maganar da murmushi. Zara da Salima harda Innayo ne suka hadu suna rokar alfarmar Mami ta bari ayi kitson. Murmushi kawai tayi domin nauyinsu ne ya kamata ta kasa kafewa akan bakanta. Halayyarsu ta burgeta matuka don daga uwar har 'ya'yanta sun iya saka bako yaji kamar a gida yake. Shi yasa ta ce ba hanawa tayi ba sai dai da kunya zuwan farko su zauna ayi kitso. "Duk gida ne Hajiya kuma na fahimceki sosai. Amma don Allah ki bari ko manya tayi mata. Ki ajiye dalilin zuwanku ki dauka mu daku  daya ne." Mami Khadija ba yadda ta iya da furucin Innayo wanda tayi cikin sigar rarrashi da sanin ya kamata. A dole ta ce ta hakura amma fa manyan za ayi kuma tun wuri Innayo ta sani cewa idan sun je gida sai ta yiwa Sauda fada. "Ba zan hana wannan ba. Amma dai kar kiyi da yawa. Na tabbata jin da tayi kamar tana tare da 'yan uwanta ne yasa bata boye abin da take so ba. In wani gidan ne ita ma ba za ta soma ba ko Saudatu?". Sauda ta gyada kai tana kallon kasa. Farha ta tashi ta ce bari ta fadawa Suhaib. Saudan sai ta bita aka bar Mardiyya da ta karbi baby din Zara da Munzali tare da sauran mutanen falon.  Mardiyya kunyar kasancewar Munzali a wurin ta hanata sakat. Sau biyu suna hada ido. Murmushi yake mata wanda a kasan ransa yake jin zai iya zama na bankwana. Tunda Shazali ya kunno musu wuta yanzu basu san iya inda zata tsaya ba. Don kada kowa ya fahimci kallon me suke yiwa juna sai ta dubi Zara ta tambayeta sunan baby.  Kafin Zara ta san me za ta ce mata Mami Khadija ta sako tambayar waye babba tsakanin Munzali dasu Salima. Ba kuma haka kawai tayi ba sai don ta kawar da hankulansu daga tsakin da Mama Nasima take yi jifa jifa. Sautin na yanzu yafi karfi shi ne tayi tambayar da dan karfi ita ma. Har kasan ranta bata da niyar idan sun zo ta zake da yawa tunda ta san halin abokiyar zaman nata. Kar ta ce surukanta ne Mamin take shige musu. Kyawun mu'amalar 'yan uwan Munzalin ya bata sha'awa amma ta kula ba haka bane a wurin mai shirin zama surukarsu. Yatsine yatsine take ta yi da tsaki na gajiya da kosawa daga zamansu. Dalilinta kenan na jan maganar kitson da Sauda ta nuna mata kawai don kada su kunyata kansu. Munzali ya nuna mata Salima ya ce ta girme shi amma Zara kanwar bayansa ce. Ai fa nan suka soma musu da Zara akan waye babba har ya hakura ya karbi kankantarsa. * Da Ayaah ta fito kiran Murja samunta tayi tana waya. Gira ta dage tana yi mata dariyar shakiyanci saboda gane wanda ake wayar dashi. Mahiru ne saurayin da ya kai kudin aurenta. "Haba nifa naji shiru daga kaiwa baki abin sha baki dawo ba ashe ashe..." Sallama Murja tayi da Mahiru tayi dariya "gulmammiya indai ba labe ki ka yi min ba me ki ka ji na ce da zaki gane da wa nake waya?" Ayaah ta rausayar da kai hannunta daya akan kugu ta ce "gani nayi kina ta bin bango kina malalewa kamar ruwa irin abin nan na Indiyawa a lambun soyayya. Na ce duk yadda aka yi Yaya Mahiru ya fadi abin da ya susuta Murjanatu 'yar Baba."  Haushi ya kama Murja da Ayaah ta kwatanta irin tsayuwarta a jikin bangon harda waka. Iska ce ta debi maganganunsu har falon Asabe saboda sun fi kusa da wurin. Lilu ya kama dariya harda rike ciki. Suhaib ya kai masa duka yana nuna masa alamar ya yi shiru da dan yatsa. Shi ma hirar nishadi ta sanya shi har yaji yana son ganin fuskar mai tsokanar. "Kai fa baka da kan gado wallahi." A lokacin wakar da Ayaah take yi ta shiga kunnuwansa sai da ya murmusa. Gyara zama ya yi yana saurarensu tare da kallon Qibdiyya da Lilu yana biye mata kamar yaro dan uwanta. Waka take abinta babu kyakkyawan kari. Duk baitin da yazo kanta take fada. "Sai ruwa ruwa na malaleeeee. Ashe ruwan bana ya ci su Murjaaaa. Kinsan ya dade yana sonki ruwa na ...." "Zan malale bakinki a wurin nan" cewar Murja a fusace tana galla mata harara sai kuma ta kama dariya "murya kamar gogen tsumma."  Ayaah ta sha kunu tsiwar ta motsa ta ce "kin dai fada ne kawai don kiji dadi amma ke kin san muryata da dadi. Idan ina magana Dani kasa dauke ido yake daga kaina." "Waye kuma Dani kamar wani arne?" Furucin Murja kenan domin yau ta fara jin sunansa. Ran Ayaah in yayi dubu kuwa a take ya baci. Maganar tayi mata zafi don sai da taji kwalla na neman kwace mata. Dani din nata ake kamantawa da arne. A bangaren su Suhaib ma sai suka hada ido da jin kalmar Murja ta karshe da shirun Ayaah. Ba tantama ya da kanwa ne. Sai da Farha ta fito tana tambayarsu inda su Lilu suke sannan Ayaah ta fadawa Murja sakon da ya kawota.  Rashin sanin da mutane a kurkusa dasu ya sake bawa Ayaah haushi da Murja ta nuna falon Asabe. Da suka fito bayan gama jin bayanin Farha suka fito Ayaah ta basu baya tayi hanyar kofar gida da waya a kunne. Danliti ne ya iso yana neman karin kwatance. Basu ga fuskarta ba har suka karasa ciki wurinsu Innayo. *** Mami Khadija bata son barin 'yan matan dasu Lilu kadai a gidan. Sannan take taken Mama Nasima tun farkon zuwansu ya nuna mata zasu iya samun matsala akan jiran kitso. Cije lebe tayi ta rasa me zata ce da Innayo ba tare da ta bata mata rai ba.  To ita ma Innayo din duk ta karanci rudanin da Mami Khadijan ta shiga. Ita kadai a zuciyarta ta yabawa wannan uwa. Tunanin maslaha ta tayata inda bayan dan nazari na kankanin lokaci ta bude baki tayi musu magana. "Munzali ko zaka bisu da Murja sai Ayaah ta rakata. Kitson mutum daya dai na san kafin Magariba in Allah Ya so sun gama. Ko kuwa? Kunga sai a sami zumunci sosai tsakaninsu ko?" Kai Mami Khadija ta daga ta kalleta da murmushi sannan tayi mata godiya sosai. "Haka ne. Nima ba zaman kitson ne bana so ba amma kinga ..." tana son cewa su matsayin dangin mata suke kuma gashi ko iyaye maza basu gana ba. Ita da tun farko bata goyi bayan zuwan ba kuma harda Mardiyya bai kamata ta assasa dadewarsu ba. "Karki damu duk na fahimta. Bari ta kirawo kanwarta sai su biku tare." A lokacin Lilu ya bukaci Suhaib ya bashi mukullin mota yana da chakulet zai daukowa Qibdiyya. Nan ta soma tsalle. Munzali ya ce shan zakinta ya yi yawa kada ya dauko. Da ido Lilu ya yiwa Suhaib alamar ya taimaka ya dauko masa. Shi kuma sai ya sami kansa da biye masa yabi bayan Murja da ta fito kiran Ayaah. *** Turare Danliti ya sake mitsikawa a hannunsa yabi jikinsa ya shafe sannan ya sako kai soron da Ayaah ta shiga bayan ta hango shi. Tuni ya ce mata a bakin titi ya ajiye mota saboda ya zata layin nasu mota bata shiga. Ita ma a ciki hijabinta ta gyarawa zama tasa hannu ta dan goge fuska. Idanun iyayenta da bakin dakin Innayo ne suka hanata sabunta kwalliya domin tarbarsa. A tare suka sakarwa juna murmushi da ya shigo. Idanunsu sarke da juna kunya duk ta kamata. "Baby kin yi min kyau sosai." Kalman da Suhaib yaji kenan da ya tunkaro kofar. Can ya baro Murja tayi cikin gida tana ta kwala kiran Ayaah. Bai san wace ce ba amma zuciyarsa ta bashi abokiyar fadanta ta dazu ce wadda aka ce zasu tafi tare. Fari tayi masa da ido sannan tayi godiya. "Na gode Dani." 'Dani?' Suhaib ya ambaci sunan a ransa yana mai tuna abin da ya hada 'yan uwan rigima. Curiosity bai barshi ya cigaba da tsayuwa inda ya dakata ba. Yanke shawarar wucesu don yaga fuskokinsu su biyun ya yi. Murmushi ya bayyana akan fuskarsa da ya ayyana me Lilu zai yi da shi ne ya fito. Ya daga kafa zai cike tazarar dake tsakaninsa da kofar soron sai yaji abin da bai zata ba. Muryar mai suna Dani ce take fita a raunane cike da makirci irin wanda ba kowa zai gane ba. "Baby yau ma ina cikin damuwa. Shi yasa ma kika ga na matsa sai mun hadu." Bai kuma jira jin cewarta ba don ya kula ta fara yi masa kallon tausayin nan ya dora da "wai ko kinsan yanzu matar nan ta daina zuwa shimfidata sai na biya?" A saukar aradu maganar ta shiga kunnuwan Ayaah da Suhaib. Ita nauyi da kunya ne suka kama ta gami da fara jin haushin me yasa hirarsa bata wuce irin wadannan maganganun. Suhaib kuwa zuciyarsa yaji ta soma tafarfasa. Ya yiwa zina da duk wani ma'abocinta mummunar tsana. Salon hirar nan kuwa ba komai bane illa dauko hanyar bude kofar da za a iya fadawa gareta. Yarinyar da yaji muryarta kila ba za ta wuce sa'arsu Sauda ba ita ake fadawa wadannan kalamai. Jikinsa har yana tsuma don bacin rai ya iso daidai bakin kofar amma sun juya masa baya sannan yaji amsarta. Muryarta har raurawa take yi saboda an kure rashin kunyarta ta ce "Dani ina ga ba ni ya kamata ka fadawa wannan matsalar ba. Gara dai ka kaiwa magabatanku a nemi mafita." Danliti ya gane ta fara jin tsoro daga muryarta ya yi murmushin gefen baki. Da tsoron wanda bai hana cigaba da soyayya ake samun kan irinta. Sake kwantar da murya ya yi abinsa harda langabe kai. "Wa zan fadawa matsalata bayan Mum idan ba ke ba? Ita kuma saboda bata kasar bana son yawan tayar mata da hankali. Kece dai wadda nake shirin aura nake ganin ya dace ki san matsalolina tun yanzu domin ki tanadi hanyoyin magancesu." Maganar tasa tana fita ne daidai da takunsa da yake ta kusanto shi gareta. Idanun Ayaah sun yi wuri wuri amma ta rasa me ya hanata ja da baya. Tausayinsa take ji har kokon ranta tana kuma gudun kar ya nemi wata idan taki taimaka masa. Bata yi aune ba ta ji shi daf da ita har tana jin dumin numfashinsa. "Baby ko dan huk (hug) ne don Allah in samu domin na rage zafi. Ina tsananin bukatar mace. Jiya na tura mata dubu dari ta ce ya mata kadan. Ni kuma shi ne naji haushi ban sake yi mata magana ba. Kudin bai dame ni ba amma na gaji da rainin wayo." Sai ga Suhaib yana tafa hannuwa kamar mace saboda tsabar mamakin da ya sarke shi. Bai taba ganin dan is... kamar wannan mai sunan arnan ba. Duk da haka ya tsaya yana son ganin irin tarbar da Ayaah zata yiwa yunkurinsa domin ya san matsayin da zai ajiyeta. Duk abin da ake yi ko fuskarta bai gani ba har yanzu.  Akan idonsa ta ja baya kadan tayi magana kamar mai shirin kuka. "Ka kara hakuri. Ba ka ce idan Mum din ta dawo za a turo ba? Ka bari ayi auren." Hannu ya daga yana son shafa fuskarta ta goce da sauri. So yake su wuce wannan matakin ya sami yadda yake so. Yawancin mata wuyarta a sami kansu na farko. Daga basu da zabin da ya wuce amincewa a gaba saboda gudun kada a ki aurensu. Ya dade da yadda da wannan shi yasa yake cin karensa babu babbaka.  Cikin muryar dake nuni da tsantsar karaya da neman agaji ya ce  "Har sai wannan lokacin Ayaah? Idan na shiga wani hali kafin nan ba laifinta bane ita kadai har dake. Naki ma yafi nata domin zuciyata da gangar jiki duka ke suke so.  Nayi zaton zuwa yanzu nafi karfin komai a wurinki. Ashe ni kadai nake haukana. Yadda na daukeki daban da matsayin da kika bani."  "Ba haka bane. Kai ma ka san ina sonka." "To ki nuna min a aikace. Ki mantar dani bakincikin da matata take kunsa min. Ki cire tsoro a ranki domin wallahi ko raina ki ka nema zan iya baki. Sannan kada ki manta dama ya halatta na ganki tunda maganar aure ce tsakaninmu. Gani babu hijabi balle mayafi. Hakkina ne kike neman dannewa Baby. Kin yi min adalci kenan?" Runtse idanu Ayaah tayi da ya sake daga hannu zai shafa fuskarta. Bata so ko kadan amma zuciyarta ta gama aminta da halatta haramun din da yake neman yi. Ba zina zata yi ba. Nutsuwar da yake nema kawai take son taimaka masa ya samu. Suhaib bai san lokacin da ya iso gabansu ba. Danliti da ya gama sakawa ransa cewa daga shafa fuskar zai zarce da koya mata wani karatun daban sai ji ya yi hannunsa ya makale a iska. Daga kai ya yi yana kallon gefen fuskar mutumin da ya rike shi a firgice. Ayaah kuwa da taji shiru bai taba ta ba sai ta bude idanunta a hankali. Nan suka yi ido hudu da mutumin da bata sani ba. Kwayar idonsa tamkar maganadisu aka zuba saboda yadda ta kasa dauke nata. Mugun kallo yake yi mata mai kama da na tsana. Zuciyarta sai da tayi wani irin tsalle don tsoratar da tayi. Suhaib ya kuma ware mata idanuwansa da suka kara firgita ta. "Get out of here (bar wurin nan)" ya umarceta da tsawa. A guje tayi cikin gida tana haki. Murja har ta fitar da rai da ganinta suka yi karo. Bata kula da yanayinta ba ta fada mata sakon Innayo. Bayan tafiyarta Suhaib ya kalli Danliti wanda yake ta kokawar kwace hannunsa ya kasa. Tuno inda ya san fuskarsa ya yi ba shiri ya saki hannun baki a bude. "Kai? Ba kai bane makaniken...." Bai iya karasa magana ba sakamakon ture shi da Danliti ya yi da karfi ya kwasa a guje ya fita daga soron. Tunda ya fita ba shi ya tsaya ba sai da yaje titi. Ya tsaya mayar da numfashi bai yi aune ba wani mai kurar ruwa ya kwashe shi ya watsar a gefe.  * Innayo da iyalinta har bakin mota suka rako su Mami Khadija. Su suna godiyar ziyara ita tana ta kyautata musu da aka yi. Ita dai Mama Nasima mota ta shige kai tsaye ko waige babu. Tuni ta fara musu da zuciyarta akan amincewa alakar Munzali da Mardiyya. Ta raina gidan da ahalin gidan. An rarrabu kowa ya shiga mota. Ayaah kamar wadda ta yiwa Sarki karya gabadaya ta kasa sakewa. Duk inda ta motsa sai taga kamar idanun mutumin da taji Kawunta ya kira Suhaib suna kanta. A gaban motar Munzali ta zauna ta hade hannuwanta a tsakiyar cinya. Murja tana baya suka bi bayan motar Suhaib din. Ita dai har suka isa gidan bata san inda tunaninta yake ba. Tsakin da taji lokacin da ta fito daga motar ne ma yasa ta karewa gidan da suka iso kallo. Ido suka kuma hadawa da Suhaib ya sake yin tsaki a karo na biyu sannan ya kawar da kai tamkar yana kyamar kallonta.  Hawaye taji yana neman sauko mata ta daure ta hadiye shi. Da tabi 'yan matan cikin gidan shi tsayuwa ya yi wurin Munzali suna magana. Hankalinta a tashe tana tsoron ko abin da ya gani yake fada masa. Ana ta janta da hira sai dai tayi yake. Cikin abin da bai kai minti talatin ba har an gama kitson. Mami Khadija ta basu kudi suka ki karba. Har ta nuna bacin rai amma suka ki. Sai suka sake burgeta. Dama da a gida suka hadu ba kudi zata bayar ba. Kyauta zata yi musu irin wadda ta dace da 'yan mata. "Ku karbi nambar juna ku dinga gaisawa. A haka ake fara zumunci." Abin da tace musu kenan sannan ta juya ta barsu dasu Sauda. Da yake 'ya'yan nata babu girman kai a take suka fara aiwatar da shawararta, aka yi musayar nambobi tsakaninsu. Ayaah jiki ya kasa daina rawa saboda ganin har lokacin Munzali da Suhaib suna magana. Da Munzali ya kallo inda take kuwa sai da taji kamar ta saki fitsari a wurin.  "Ku zo mu tafi"  Kasa daga kafa tayi sai da Murja ta ja hannunta. Da suka isa bakin motar Suhaib ya bata mamaki da ya bude mata gaban sannan ya hada da yi mata murmushi. Kura masa idanu tayi ba shiri domin tabbatar da abin da take gani. Ya kuwa sake yi mata murmushi a karo na biyu. Farha tana yi musu sallama shi ma ya yi harda cewa su gaida gida. Murmushinsa bai hanata satar kallon Munzali ba a hanya tana jiran ya fara fada. Gani take kamar na mugunta yake mata bayan ya gama hada mata bomb. Kallon hanya da zurfi cikin tunani da take ganin Munzali ya yi bashi da alaka da abin da take tunani. Suhaib ya yi masa magana ne akan baffaninsu maza da suka yaba dasu har suka bukaci a sanar dasu cewa su turo iyayensu indai da gaske suke. Ya kira Abbati yafi sau shurin masaki amma bai dauka ba tunda gari ya waye. Abin ya karu domin yanzu wayar ko shiga bata yi. Haka ya rufe ido ya kira layin Baaba Mari shi ma shiru. Kafin ya isa kofar gidan Hasiya ya kira mutum ya kai shida a gidansu Abbati. A kalla kowanne ya kira sau uku ko hudu. Hankalinsa ya tashi sosai har ta kai kwatancen gidansu da Murja take yi masa baya ganewa sosai. Sau biyu yana yin kwana sabanin wadda take fada masa. Tsayuwarsa da mota ke da wuya Ummita ta fito rike da Hasiya a jikinta. Tangadi suke duk su biyun. Hasiya na ciwo, Ummita na firgicin irin aman da taga tana yi. Cikin kankanin lokaci ta fita daga hayyacinta. Ko kashe motar bai yi ba Ayaah da Murja suka fita da sauri.  "Me ya sameta?" Ummita tana kuka ta fada masa yadda Hasiya ta dinga amai daga kwabin lalle. Babansu kuma tun safe Abdulkarim ya turo aka tafi dashi asibiti tare da Abbas. Duk wannan bayanin a hanya aka yi shi. Gudu irin na  ganganci ya dinga yi saboda kakarin da Hasiya take yi a galabaice.  Kiran Abbatin da bai sake samun damar yi ba kenan a ranar domin suna zuwa asibitin emergency aka nufa da ita. *** "Gabadaya na kasa fahimtar bayaninka Abbati. Haka kawai ta suma bayan bata kwana da ciwon komai ba?" Mal. Inuwa ya furta hankalinsa yana ga Baaba Mari dake kwance akan gadon asibiti rai kwakwai, mutu kwakwai. Atine ce tayi karfin halin cewa "Ya ce magana suke fa yaji ta daina amsawa" Duka 'ya'yan Baaba Mari suna dakin da aka kwantar da ita a babban asibitin garin Kirikasamma. Abbati ya rasa me yake masa dadi a duniya. Gefe guda ya samu ya zauna ya hada kai da gwiwa cikin tunani. Tare suke da mahaifinsu Mal. Inuwa da wasu cikin Gwoggoninsu matan 'yan uwansa. Shi Mal. Inuwa yafi kowa nuna gigita saboda yadda yaga Abbati ya fito da ita waje a hannu ko motsi bata yi. Daga shi har 'yan majalisarsa sun dauka bata da rai. Kowa yana tofa albarkacin bakinsa game da ciwon da ba a san silarsa ba likita ya dawo. Wasu gwaje gwajen jini ya sake rubutawa ya bukaci Abbati ya biyo shi waje. Da sauri Mal. Inuwa ya ce "Fadi ko ma mene ne Dafta. Nan wajen duka babu bare. Me ya sami Mari?" Likitan ya dubi Abbati wanda ya gyada masa kai sannan ya fada musu abin da suka gano. "A gaskiya jininta ya hau fiye da kima har yana barazanar taba mata zuciya. Idan ba a dauki matakin da ya dace ba zata iya samun stroke (mutuwar barin jiki) ko ...." "Allah ma Ya kiyaye" cewar Mal. Inuwa da rawar murya "indai kudi ne sha Allahu ba zai gagara ba. Ayi mata duk abin da ya dace ga danta nan." "Malam. Malam" Ba Mal. Inuwa da ta kira ba, duka wanda yake dakin sai da ya juya da farincikin ganin Baaba Mari ta farfado. Da hannu ta yafito shi ya matso kusa da gadon ya duka kansa ganin tana ta motsa baki. "Ku mayar dani gida." Wani irin kallo ya mata cikin tashin hankali ya daga kansa ya yiwa Abbati inkiya da ya matso. Su Habi duk sai suka fice. "Kaji taurin kan mata ko? Wai a mayar da ita gida." Murmushi tayi masa "Idan an kaini asibitin waye zai biya kudin?" "Wace irin magana ce wannan? Ko kin sami makuwa ne saboda ciwo?" Muryarta ta kara dusashewa ta ce "kana da sauran kadara ne Malam da zaka sayar ka nema min magani?" Duk da ya soma harzuka haka ya daure saboda ba lafiya gareta ba ya ce "Wai ba ga Abbati ba? Mari lafiyarki kuwa?" Idanun Abbatin ta lalubo da nata. Ya zabge tamkar shi ne kwance a gadon asibitin. Kalamanta na gaba a gareshi ita kanta basu yi mata dadi ba sai dai babu gudu ba ja da baya. "Ban yafe ba idan ya sake kashe min kwandalarsa. Ban yarda kaima ka kashe min daga kudin da ya baka ba. Sannan idan ban tashi ba ka isar da sakona ga dan uwanka Sa'idu. Ni MARIYA BA YAFE MASA BA!" I just published "32" of my story "UWA UWACE...". https://www.wattpad.com/1075498851?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=BatulMamman17&wp_originator=ch%2BCj6HFMGZric%2F0AziznjzpnsGFTeE6FcqyK47HiPNU9s7kTIdx2UmGGuBfIR%2BD6eifgeyno%2B%2FW1iPy3eGVxAoWDWZFgyOGfdmHjoCLwlZRaoqPmxHi7hxgWfHl7GQb QUWA UWACE...32 Batul Mamman💖 Akwai uwa kuma akwai uwa! Wadansu uwayen sun san cewa 'ya'ya amanar Allah ne kuma suna kokari wurin ganin sun sauke in nauyin. A cikinsu wasu suna yin nasara wurin aikata daidai a wannan tafiya mai dadi da wahala. Wasu kuwa kuskure suke aikatawa wanda soyayyar 'ya'yan ne yake zama sanadiyarsa. A shagwaba 'ya'ya fiye da kima. A kasa tsawatarwa kurakurensu, sannan a karshe a biyewa ra'ayoyinsu koda zuciya da kwakwalwa sun san hakan bai dace ba. Kaso na biyu cikin uwayen bayan wannan rabe raben na masu son sauke nauyi sune masu fifita kawunansu da bukatunsu akan na 'ya'yansu. Irinsu ake yiwa lakabi da ballagaza. Kwakwalwarta kalau take balle ace lalura ke hanata bawa 'ya'yanta kulawa. Ita bata ma san cewa kuskure take aikatawa ba. A lissafinta kodayaushe ita ce farko kafin danta. Shi yasa take gabatar da farincikinta kafin na danta. Ita fa ko yunwa ke damunsu ita da 'ya'yanta sai ta fara koshi take tunawa dasu. Idan abincin babu yawa sai su kare da sudin hannu. Kulawa wadda ke karkata zukata ga nuna tausayi da damuwa ga mai bayar da ita bata fiya shiga tsakaninta da nata ba. Wannan sakacin nata zai iya zama kalubale kuma babbar jarabawa ga 'ya'yanta da duk wanda ya rab'e su. A karshe da za ta rigasu komawa ga Allah da wahala su ji kewa irin wadda 'ya'ya ke ji idan sun rasa uwa. Albarkacin wata tara, nakuda da shayarwa kadai za ta ci. Ya ke Uwa! Ki koyawa 'ya'yanki sonki ta hanyar kulawa, tausayi, jinkai, ladabtarwa da soyayya. Idan a gaba kin sami sabanin tarbiyar da kika yi musu ki sani cewa kowane bawa yana tafe da kaddararsa. Ke dai ki tabbatar cewa kin yi iya yinki har a gaban Allah ta yadda ba za ki zama wata Asaben ba. Kin bata naki ki bata na wasu da basu ji ba basu gani ba. Kada ku manta laifin ba na Uwa bane ita kadai. *** Ya dauki kimanin minti goma sha biyar a dakin bata ce komai ba. Hasali ma ko motsi daga inda take bata yi ba. Qibdiyya ce a gefenta idanunta a kumbure sun yi ja, da gani tasha kuka. Ya yi mata magana bata amsa masa ba. Tun shigowarsa da ta taso a guje Asabe tayi mata tsawa ta koma ta zauna. Gajiya ya yi da shirun. Ya san halin mahaifiyarsa. Karshenta kudi take son karba a hannunsa take ta kirkiro wannan dabarar. Hannu ya zira a aljihu ya zaro dubu goman da ta rage a hannunsa ya dora mata a hannun kujera. "Qibdiyya taso mu tafi" ya furta a yayinda ya mika mata hannunsa don ta kama. Sannan Asabe ta tashi da fada bayan ta kwashe kudin "ince ka zo amma don raini baka tsaya kaji me ya faru ba za ka tafi." Hannu yasa ya matse kansa da yake ciwo. Haka ya soma magana kamar zai yi kuka. Bai san wata damuwar da ta zarce rashin ji daga Abbati ba. Washegari yake son bin sa, ko ma me za ayi gara ayi musu tare. Ko kuma ya bishi a yau....tunaninsa ne ya katse lokacin da Asabe ta sakar masa harsashin da ya bula kwakwalwa da zuciyarsa. "Ban san wane irin sakaci kake yi da 'yarka har wani tsinanne ya..ya" sai taji bakinta ya sarke sakamakon idanun da Munzali ya zuba mata. "Me aka yi?" Ya furta da sautin da yafi kama da umarni. Bai ma san ya yi amfani dashi ba saboda yadda ya soma tsorata tun kafin yaji karshen zancen. Asabe ta hadiyi yawu "ina jin fyade aka yi..." "Qibdiyyan???" Ya tambaya a razane kafin ma ta kai karshe. 'Yarsa ya dauka da zafin nama yana neman dubata mata jiki. Asabe tayi azamar karbeta "baka da hankali ne za ka bude mata jiki? Na riga na duba kuma wallahi namiji ya kusanci..." Innalillahi wa inna ilaihi raji'un....hawaye ne suka ballewa Munzali. Zancen ya dinga bin sassan jikinsa tamkar ana huda shi da alluran da aka kona a wuta. A wurin ya durkushe yana kuka mai sauti. Kuka irin wanda bai taba yin kwatankwacinsa ba. Da zai ci karo da ko ma waye ya tabbata sai dai ayi masa takwara a dangi domin shi kam tasa ta kare. Kashe shi zai yi idan ya so shi ma a hukunta shi. Asabe gani tayi ya dora hannu a kahon zuci yana bugun kirjinsa. Idanunsa basu bar fitar da hawaye ba. "Kashe kanka zaka yi ko kuwa zaka tambayeta waye ya mata wannan aikin?" Sannan ta kara da cewa "kuma ina zargin ba abin kwana daya bane domin kuwa alamu sun nuna ta soma sabawa." Runtse idanuwansa kawai ya yi. Yawancin maza idan 'ya'yansu mata suka isa aure sai kaga suna ja wa manemansu aji. Ba don komai ba kuwa illa tunanin cewa idan ka auri 'yata fa ga abin da zaka yi mata. Wannan kishin yadda uba yake yiwa 'yarsa haka 'ya'ya maza suke yiwa uwayensu idan kaddarar sake aure ta gifta musu. Munzali yaji zuciyarsa tana suya a kirjinsa. 'Yarsa mai shekaru biyar ake cewa ta saba...ta saba da namiji a kananun shekarunta. Shi da ransa, mahaifiyarta ma da ranta. Garin yaya??? (Zina bashi ce Munzali. Kaga Allah Ya bamu 'ya. Idan bamu tuba ba wata rana ita za ta girbe abin da muka shuka) Kalaman Abbati a wani lokaci da yake yi masa maganar tuba daga wannan alfashar suka dawo masa. A hankali ya tashi yaje gaban Qibdiyya ya durkusa. Ya mika hannuwansa gareta duk ta firgice. Asabe tayi mata dukan da ba a taba yi mata ba a dalilin kin fadan wanda yake mata. Shi yasa ta tsorata ko shi ma dukanta zai yi. Ga mamakinta da Asaben sai ya rungume Qibdiyya. Riketa ya yi sosai a jikinsa yana jin kamar ranar suka fara haduwa bayan haihuwarta. She will always be his baby duk girmanta. Kasancewarta tsatsonsa bai kara mata komai ba sai masifa. Ya cuceta cuta ta har abada domin an bar mata tabo daga barnar da ya kasance yana aikatawa. "Ki yafe min Mariya. Ki ce kin yafe min." A razane Asabe ta taso har tana tuntube da kujera. "Me kake cewa. Na shigesu. Munzali kai ne ka bata..." Magana ya cigaba da yiwa Qibdiyya da taushin murya. "Ki yafewa uban da bai bar alkhairin da zaki mora a rayuwarki ba sai sharri. Nayi miki alkawarin gyarawa. Zan yi ta tuba har karshen rayuwata. Ina fatan Allah Ya haskaka rayuwarki Ya wanke miki duhun da na janyo miki." "Munzali kayi min gwari gwari don Allah. Shin kai ne ka bata 'yar nan?" "Allah ba zai dora min wannan kaddarar ba in sha Allahu." "Washhh har hankalina ya kwanta" tace tare da sauke ajiyar zuciya "yadda ka ke magana ne sai a zata kai ne." Da Qibdiyya a hannunsa ya juyo ya fuskanceta "Hankalinki kar ya kwanta Asabe. Ke ki ka assasa komai." "Kar ka dora min laifin da ba nawa ba. Dubata fa kawai nayi na sanar da kai. Banda sakarci ita kadai kwal amma kun kasa kula da ita." Murmushin bacin rai ya yi "kamar yadda ki ka kasa kula dani da 'yan uwana?" Ba ta zaci wadannan kalaman daga bakinsa ba shi yasa ta dinga bude baki tana rufewa don mamaki. Da kyar ta iya yin magana muryarta tana fita kamar an shake mata wuya. "Me kake nufi?" "Bayan haihuwata da suna da ku ka saka min ke da Baba kuna da wani abin kare kai a wajen Allah game da tarbiyyata? Kin san sana'ata? Kin san silar arzikina?" A yanzu sababbin hawaye sun cika idanunsa har suna zuba amma dariya yake yi "ina dauke da zunubina ga na Abbati da nayi silar fadawarsa mummunar rayuwa. Ba mamaki shi yasa Allah Ya jarabceni akan Qibdiyya." 'Kada kayi sab'o' ya fadawa kansa da ya tuna da cewa da a gaban Abbati ya fadi wannan maganar haka zai ce masa. Tunanin Asabe sai ya luluka da ita duniya daban da wadda Munzali yake son haska mata. Gani take kamar abin da ya sami Qibdiyya ne yake neman taba masa kai. Banda haka kaf zantukansa basu yi ma'ana ba a cewarta. Tana kallo ya murda kofar dakinta ya fita. Sai dai me? Yana fita suka yi ido hudu da guda cikin 'yan uwansa mata. Idanunta kadai ya kalla ya san ta gama jin komai. Abin mamaki shi ne yadda zuciyarsa bata ji komai ba. To me zai ji bayan ciwon da yake ciki a yanzu? Matsalarsa bata wuce rashin sanin halin da Abbati yake ciki ba. Sai kuma tunanin irin hukuncin da zai yiwa wanda ya soma ketawa diyarsa haddi. *** Zaune akan kujera Mal. Sa'idu ne yana karkada kafafunsa. Su hudu ne a falon Baba Mari. Daga ita sai Abbati, Mal. Inuwa da shi babban bako na musamman. Bacin ransa baya bukatar ya bude baki ya yi magana. Yanayinsa kadai ya isa tsorata jama'ar gidan. Mal. Inuwa kansa a takure yake don idan fadan ya tashi babu mai tsira. Da ya dubi Baaba Mari sai ta bashi tausayi. Duk yadda aka yi zafin ciwo ne ya kaita ga yin wannan kasadar. Gyaran murya Mal. Sa'idu ya yi gami da yin kwafa. "Inuwa gani a gaban isasshiyar matarka. Ka umarceta da ta fadi abin da yasa ta aika NI SA'IDU in zo inda take." "Mari..." Mal. Inuwa ya fada a hankali kamar yana rokonta da ta kawo karshen zaman nan. Mal. Sa'idu ne ya katse shi "Idan kuma takamarta haihuwar Abbati ne to ka tuna mata cewa ni da ake zagi, ni ne silar arzikinsa. Bayan duk tijarar da ta gama yi akan tura shi karatu gashi tafi kowa girbar samunsa" ya daga hannu yana kadawa domin kashedi "duk da haka babu wata mace da ta isa ta nuna min iko da danta domin iyayensu maza ma umarni na suke bi. Abbati da duk abin da ya samu nine sila..." "To Alhamdulillahi..." Baaba Mari ta katse shi. Kowa sai ya kalleta da tayi magana. Abbati kuwa ji yayi kamar kasa ta bude ya shige ciki kada a sake jin ko da sunansa balle labarinsa. Ya amince da ko ma me zata yi amma hakan ba zai hana shi jin tamkar tsirara yake a gabansu ba. Kamar tana jin rurin da zuciyarsa take yi sai ta kira shi da hannu. Kafafunsa da yake ji kamar ba nasa ba haka suka kaishi gefenta ya sulale ya zauna. Dan murmushi tayi masa wanda ya sake nutsar da zuciyarsa sannan ta fuskanci Mal. Sa'idu. "Fashin baki nake son yi muku akan wani abu da kuke yi mara tushe kafin na fadi illar da ya janyo min." Mal. Sa'idu ya yi dariya "Magana kike son yi akan zuwa almajiranci ko? Ke a dole ba za ki karbi addini a yadda ya zo miki ba?" "A yadda yazo muku dai. Wannan fitinar da kuka farlanta bata cikin shika shikan musulunci. A takaice ma dai baku yiwa addinin komai ba sai bacin suna." "Mari wai sai yaushe zaki daina janyowa kanki matsala da Yaya Sa'idu?" Cewar Mal Inuwa cikin fushi. "Kila yau! Yau din da nake so kai dashi ku san cewa kun dade ana rubuta muku zunubi a matsayin wadanda suka jagoranci aikin alfashar da dansu yake yi saboda mummunar akida." Falon sai ya yi tsit. Baka jin komai sai hawa da saukar numfashi. Kan Abbati a kasa yayinda Mal. Sa'idu yaji lokaci ya yi da zai saurari Mari. Kalamanta ba karamin zargi bane wanda yake jin dole sai da hujja za ta yi shi. "Addinin Musulunci da kalmar Karatu ya fara zuwa garemu. Wannan yake nuni da cewa ko kadan jahilci bashi da muhalli a cikinsa. Allah ma Ya ce mu san Shi kafin mu bauta Masa. Duk musulmin kwarai bai dace ya yi gaba da neman ilimi ba." Mal. Inuwa ya ce "to amma ai ke kina yi." "A fahimtarku ba" ta nuna Abbati da yatsanta "ga danku nan. Kamar kowane bawa shi ma da tasa kaddarar yazo duniya amma kune sila. 'Ya'yanmu amana ne. Babu inda aka ce mu sakesu da kananun shekaru neman karatu ba tare da kyakkyawar kulawa ba. Kun turasu gidan malamai da sunan neman ilimi amma babu abinci. Yunwa ba kanwar uwar kowa bace. Idan ta taso dole a kawar da ita ko a ji jiki. Babba ma idan ka kai shi karatu babu abinci ka hada shi da jidali balle yaro. Wani sai ya wuni yana barar bai samu ba. Mutane su ci karo dasu wasu su zagesu wasu su tsine musu tare da mu iyayensu saboda sun dame su da bara. Ba dole su nemi abinci ta hanyar da ta fi musu sauki ba? Wasu su dace da halal, da yawa su fadawa haram. Hatta masu kwacewa na kasa dasu kana ganin laifinsu? Sun yi girma da bara kuma da gaske babu abincin. Sannan sun tafi babu tunanin ranakun da zasu tashi ba lafiya. Waye zai kula dasu idan suna ciwo? Wa zai basu magani? Ko kun manta ranar da na shigo garin nan da gawar Sani ba tare da na san ya rasu ba?" Sai ta fashe da kuka. A haka ta cigaba da cewa "Uwa uba baku ajiyesu a inda za a basu tarbiyya ba. Iyakarsu da malamansu a biya musu karatu su bayar da hadda. Idan sun yi laifi a zane su. To amma tarbiyyar fa? Sai abin da suka tsinta a titi? Da yawansu basu tashi sun ga jinkai da tausayi ba. Dan shekara shida yana yawo a unguwa neman abinci a lokacin muku-mukun sanyi ko damuna. Wani idan ka ganshi saboda rashin kulawa da zama cikin hazo sai dai ka dinga ja masa Innahu min Sulaimanu. Wallahi zato zaka yi aljani ne. A makarantar babu mai tausaya musu sai kalilan idan anyi sa'a. Mu da muka haifesu mun riga mun bata rawarmu da tsalle da muka rabu dasu da kuruciya. A karshe zukatansu su bushe. Idan anyi dace yaro ya zama nagari, idan ba a dace ba ya buwayi al'umma." "Yanzu ki ka ce kowa da kaddararsa. Ni tun tasowata banda Sani da jikan Mai-adua ban taba jin labarin yaron da yaje karatu ya rasu ba. Gidan nan yara nawa muka tura kuma gasu nan duk sun dawo kamar ba ayi ba?" Mal. Sa'idu kenan. Ya fadi haka ne ba don zuciyarsa bata soms zuwa inda Baaba Mari take son kai shi ba. Ba dai ya son ya karbi gyaran ne daga gareta. "Ashe baka ji lokacin da nace kowane bawa da kaddararsa yake zuwa ba? Amma akwai sila. Kuma dole ne silar ya karbi sakamakon abin da ya zama tushen faruwarsa mai kyau ko akasinsa." "Kai Abbati. Wace irin sana'a kake yi? Sata ko fashi?" Cewar Mal. Sa'idu muryarsa ta soma sauyawa daga dakiyar da yayi da farko. Abbati bai iya amsawa ba. Ba zai iya cewa ga takamaimai abin da yake cikin zuciyarsa ba. "Ba da kai nake ba!" Ya daka masa tsawar da zata firgita mai karamin tunani "nace wace irin sana'a kake yi?" Baaba Mari ta daga masa hannu duk da kwarin jikinta yana ta raguwa. Tsawar da ya yi ta bata rai itama ta koma yi masa magana tana daga murya. "Baka da hurumin yiwa dana tsawa Yaya Sa'idu. Wannan damar ta saraya a wuyanka. Abin da ya rage tsakaninmu bai wuce ALLAH YA ISA ba. Ni da d'ana bamu yafe mak...." "Mari!" Mal. Inuwa ya kirata da karfi. "Kaima da ka kasa tsayawa 'ya'yanka ka tanadi amsar fitar da kai ranar lahira." Dakin ya yi shiru na wani lokaci. Iyayen maza biyu mamakin kalamanta ya ishe su. Baaba Mari kuma ciwo ke neman dawowa sabo. Abbati ya matsa kusa da ita da sauri. Filo ya kara mata a bayanta domin ta zauna da kyau. Mal. Sa'idu ya rasa me zai ce ya kare kansa sai "Yanzu ke da ace barinki aka yi da yaran nan za ki iya kula dasu ba tare da uba ba? Uwa ai ba ita kadai ce madogarar 'ya'yanta ba. Sannan karatun nan da kike ta suka ba shi ne yake taimaka musu wurin iya rike kawunansu a duk inda suka sami kansu ba saboda sun horu?" maganar ma a hankali ta fito. "Rike kai..." Baaba Mari ta furta da murmushin da tun dazu take yawan yi domin ragewa Abbati damuwa "Allah bai halicci kananan yara domin su rike kawunansu ba. Da haka ne kuwa to kowannemmu zai fado daga sama idan lokacin haihuwarsa ya yi. Yaya, cikin daukar ciki da haihuwa akwai mabanbatan wuya irin wadda bakunan mata kadai ke iya labartasu. Wannan azabar mai kama da mutuwa bata taba hana uwa mai cikakken hankali son 'ya'yanta ba. Ashe baka san.." ta dubi idanun Mal. Sa'idu babu tsoro ko shayi "soyayyar uwa da 'ya'ya aya ce cikin ayoyin Ubangijinmu ba? Cikinsu ya hanamu lafiya, haihuwarsu ta gadar mana da ciwo da sauyin halitta, tarbiyarsu ta janyo mana zagi da aibatawa komai kokarinmu amma duk da haka bamu fasa son kayanmu ba. Me yasa karatu yazo mana da cewa Allah Yana kunyar wadanda bai bawa haihuwa ba? Kuma Ya umarcemu da kyautatawa marayu domin samun lada. Lallai Ubangijin da Ya samar da wannan ladan ba zai so a tauyewa uwa zamewa 'ya'yanta uwa ba. Munfi kowa son cigaban 'ya'yanmu. Idan suka zama manyan malamai sai nafi kowa cikinku farinciki. Amma zama malamin ko wani kwararre a fannin da Allah Ya dorasu yana tafe da kulawarmu. 'Ya'yanmu suna bukatarmu kafin su shiga duniya su iya rike kawunansu. Baka bani damar kulawa dasu a lokacin da suka fi bukata ta ba. Yaya Sa'idu jawabina da yawa. Gashi na gaji bana jindadi. Kuje kai da dan uwanka na barku da ...." Caraf Mal. Inuwa ya hanata karasa magana "haba Mari karki karasa mana. Ni duk zancen ma baki fada mana me yake yi ba." Ta kalli fuskar Abbati sai kawai ta tashi ta barsu a wurin ta shige dakinta. Shi da ta bari taji nauyin karasa labarin da kansa ya zayyane musu komai. Mahaifinsa ya dinga kukan da ko ranar da iyayensa suka bar duniya bai yi irinsa ba. Daga cikin dakin Baaba Mari tana jinsa ita ma kukan take yi. Hawaye wani yana min wani babu kakkautawa. Mal Sa'idu ne ma bata ji koda tarinsa ba sai daga baya taji alamun faduwa da kuma kiransa da karfi da Abbati da Mal. Inuwa suka yi. *** Honourable ya kai ya kawo a dakin asibiti ya kasa zaune ya kasa tsaye har likitan da ya sake shiga ya fito. "Baku yi min bayani ba sai shiga kuke kuna fita. Me ya sameta?" "Alhaji muje ofis muyi magana." 'Yan matan aka bari a kanta yabi bayan likitan. Ana cewa ya zauna bai ji ba don hankalinsa baya tare dashi. "Yallabai matarka ciki gareta na wata uku." Cikin wani gigitaccen farinciki Honourable ya ce "Allah Hakimu, Hasiya ke da ciki? Alhamdulillah. Allah Ka karawa Annabi SAW daraja." "Amin" cewar Likitan "sai dai akwai 'yar matsala." Nan da nan Honourable ya zauna hannuwansa akan teburin likitan. Murna tana neman komawa ciki. "Zubewa ya yi?" Gamsashen bayani likitan ya yi masa akan halin da take ciki. Mahaifarta bata da kwari ne tana barazanar zubar da cikin. Idan ba a daure mahaifar ba zai iya zubewa. Sannan tana bukatar bed rest na wani lokaci. Kuma ta daina komai har ya yi kwari a gani. Honourable ya ce musu ya amince ayi duk abin da ya dace. Yana fitowa masallacin asibitin ya nufa ya yi sallah raka'a biyu domin godiya ga Allah. Hasiya ke rike da gidansa da sanaarta. Da ace wata biyu da suka wuce ta sami cikin nan mai matsala bai san yadda zai yi ba. Yana neman kudi sosai amma kamar kofofin samun sun toshe masa. Yanzu gashi tayi cikin a lokacin da yake da abin kula da ita. Minista Abdulkarim ya bashi kudi a hannu banda wanda ya zuba a account din asibitin da aka kai Abbas. "Allah Ka kara mana hakuri da kaddara kowace iri." Daga nan bai koma cikin asibitin ba. Adaidaita sahu ya tare ya ce a kai shi Dala. Sai dai akira shi duk abin da aka ga dama amma da bakinsa zai yiwa Innayo wannan albishir. Ita ce mutum ta farko da ya san Hasiya za ta so gani idan ta tashi. Kuma bai ga wanda zai yi masa tattali da jinyarta kamar mahaifiyarta ba. *** Kankanin daki ne kamar akurkin kaji, ba taga ko daya sai kofar shigowa. Babu komai a cikinsa sai tarkacen gyaran mota irinsu spanner, sukun direba da matattun tayoyi. Iskar dakin kuwa warin fetur take da bak'in mai. Daga bayan inda aka jere wasu tayoyi suka yi tsini muryoyi ke tashi a hankali. Daya tana magiya dayar kuma tana bayar da hadin kai. Cikin sassarfa Suhaib ya shigo dakin ya isa bayan tayoyin ya leka. Mummunan gamun da ya yi bai sa shi ja da baya ba sai ma cakumo wuyan rigar namijin da ya yi. Dani ne sanye da kayan makanikai ya yi duqun-duqun. Suturarsa da fatar jikinsa duka suna neman agajin wanka da wanki. A tare dashi kuwa ba kowa bace illa Ayaah. Fuskarta babu kwalliya amma tayi kyau. Hijabin jikinta kuwa dama shi Dani ya kamo saura kadan ya gama cire mata shi. Ya gama hillatarta da alkawarin aure idan ta yarda ta bashi hadin kai kamar yadda Suhaib yaji. Kunnenta Suhaib ya murde iya karfinsa yana yi mata fada cikin bacin rai. "Ban yi miki magana ba dazu?" Ayaah ta turo baki "wai kai ina ruwanka? Kuma ba ya ce zai aureni idan Mummy ta dawo." "Mooooommiiii" Yaji an ce daga gefensa. Kunnen Ayaah ya saki ya juya. Yarinyar nan mai kwalliyar aljanu cousin din Abbati ya gani. Bata fasa kiran Mooomiii ba. Lilu a kusa da ita ya dinga dariya yana kiranta Iya duba duba. * A zabure Suhaib ya tashi daga bacci yana salati. Kansa ya yi wani irin nauyi kamar an dora masa dutse. Baccin dauke shi ya yi bai sani ba. Fuskar Ayaah ce ta zauna masa daram a kansa lokacin da ya gansu Dani zai cire mata hijabi. Murmushi take yi kamar abin da suke niyar yi daidai ne. "You have the guts to smile (har kina da damar yin murmushi)" ya furta tare da yin kwafa ya yi wurgi da filo. Sake kwanciya ya yi niyar yi wani tunanin ya fado masa. What if yarinyar nan ta bi mutumin yaje ya bata mata rayuwa? Daga hirarsu ta dazu ya fahimci kamar yanzu ne yake neman amincewarta. "Wannan kanta baya ja da gani" Tsaki ya yi ya tashi a gurguje ya zura takalmi ya fita zuwa cikin gidan. Yawancin 'yan biki sun watse tunda yau aka tafi da amarya Kaduna. Yana shiga suka yi kicibus da Mardiyya. "Bani wayarki." "Wallahi Ya Suhaib babu komai a ciki mara kyau." Murmushi ya mata duk hankalinsa yana kan wayar. "Karki damu Auta na yarda dake." Wayar ta bashi ya laluba contact dinta. Da yazo kan numbar Ayaah da sunanta da ya zauna masa daram a ka ya ganeta. Yana wurin suka karbi nambar juna. Kallo biyu ya yiwa numbar ya haddaceta. Mardiyya tana jiran taga me zai yi sai gani tayi ya miko mata wayar. Dakin da suka yi masauki ya koma ya samu wuri ya zauna a gefen gado. Yana danna kira ta shiga. Sai yaji wani bakon yanayi ja sarkewar harshe ya ziyarce shi. Me zai ce mata matsayin dalilin kiran? I just published "33" of my story "UWA UWACE...". https://www.wattpad.com/1095386077?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=BatulMamman17&wp_originator=wsvg1y6wjXkjc%2BsoHY%2FGAgyROXyp%2BY%2F6LAbeHHjA%2Biw0477%2B48VGV%2F8yOfEUfjTePvzgNLOgDlVDMm3xWUvdH978a2xKHrFdotfVZAjOUHbes%2FelWEJ2MliWyG77rSUB UWA UWACE...33 Batul Mamman💖 Kunyarku nake ji wallah. Haka dai zaku dinga hakuri dani saboda Son So dake tsakaninmu. Allah Ya barmu tare har aljanna. Amin *** "Ranka ya dade kana da bako." DPO Yahaya ya dago kai cikin bacin rai ya kalli Sergent din da ya yi maganar a tsorace. "Me na ce muku dazu?" "Duk wanda yazo ace ka dan fita" ya ce sannan ya gyara tsayuwa rabin jikinsa a bayan kofa "Yallabai mun nemi ya sanar damu matsalar da ta kawo shi ya kafe lallai kai yake son gani." Girgiza kai ya yi ya fasa yin fadan da da ya yi niyya. Yau din kamar hadin baki tun sassafe ake abu daya. Daga wannan case din sai wancan. Wani abin ma sai kayi tunanin al'ummar tamu ta rasa alkibla. Cuta, ha'inci, mugunta, magudi da uwa uba zina. Kansa ya dauki caji yana ta ciwo. Shi yasa ya bayar da umarnin ace baya nan domin ya huta. Tunda an riga an fada masa bashi da zabin da ya wuce sauraron mutumin. Sallamar kadai yaji ya gane surukinsa, babban wa ga matarsa. Ba shiri ya mike domin nuna girmamawa a gareshi. Mutumin akwai mutumci da halin girma. Ilai kuwa da shigowarsa kalmar hakuri ya fara amfani da ita "ayi min hakuri Yahaya. Na san aikinku babu hutu." "Haba Yaya Salihi ai sai kasa naji babu dadi" ya amsa masa a yayinda suke musabaha. Bayan 'yan gaishe gaishe Salihi ya zayyane masa duk abin da ya sani game da Habibu na ma'aikatar lafiya. DPO Yahaya ya dinga gyada kai har ya gama. "Akwai wani mugun dan ta kife mai cin kudaden mutane a cikin ministry of health. Ka san ai jurisdiction dinmu ne .." "Dalilin kenan da na kawo maka case din." DPO Yahaya ya ce ya kwantar da hankalinsa zai bi kanun komai "Sunan ne naji ya zo daya ina tsammanin wanda nake zargi ne. Sau biyu yana zuwa nan amma sai kaji daga sama an ce a sake shi." Salihi ya dan cije lebe "kana nufin idan shi ne sakinsa zaka yi?" Da sauri DPO Yahaya ya gyara zancensa domin kuwa ya jima yana son Habibu ya shiga gonar da ta kusance shi. Irin gonar da idan Habibu ya sallami na sama dashi da kudi shi kuma zai nuna bacin ransa akan rashin goyon baya daga abokan aikinsa. "Duk yadda akayi dubunsa ce zata cika. Yaya Salihi ka dawo gobe kawai in sha Allahu iwar haka yana cell." Shawara suka zauna yi akan yadda zasu bullo masa a saka shi fiddo kudaden Uwani. DPO Yahaya ya dan muskutu gaban kujerarsa cikin muryar da babu cin fuska a tattare da ita ya ce, "Amma don Allah garin yaya Maman Mubashir tayi wannan sakacin? A gaskiya ko babu addini a al'adance ma banga dalilin da zaisa mace ta riki wani namiji amini idan ba shakikinta ko miji ba. Duk da na san cewa muma mazan bamu cika kyautawa ba. Idan harkar kudi ta hadamu da mace sai muyi taking advantage din kyautatawarta mu danne mata kudi. To amma duk da haka wannan ba hujja bace da za ta dinga budewa wani shirgegen kato sirrin da mijinta bai sani ba." Salihi sai ya yi murmushi. Kafin ya tashi ya ce masa zai dauki kwakkwaran mataki akanta. Sai dai yafi kowa sanin Uwaninsa. Duka abubuwan da tayi babu guda da zai yi mata uzuri akan shi. Bata kyauta ba iya rashin kyautawa. Duk da haka gidan da ta taso ya taka muhimmiyar rawa wurin shaping din rayuwarta. Bakin halinta na rowa ba komai bane illa nason da halin mahaifinta ya yi a jikinta da kuma tsoron kada a maimaita wata Innayo din da ita. Domin ya sami cikakkiyar yarda tsakaninsa da ita da sauyin hali sai ya nuna mata cewa ba kowane namiji bane Alh. Rabi'u. Dukiyar matarsa ba tasa bace kuma nauyin dawainiyarta da ta yaransu a wuyansa yake shi namiji. A karshe yana son ta bambance tsakanin kyautatawar da mata kan iya yiwa mazajensu domin lada da rainin wayon maza marasa tsoron Allah. Irin mazan dake sarayar da ayyukan da suka wajaba a garesu su barwa mace daga taimako. Sune suke tsorata mata da yawa su kasa taimakon mazajensu koda suna da halin yin hakan. *** Kwalla fal idanun Innayo a lokacin da Honourable Habu yayi mata kyakkyawan albishir. "Hasiyan ce dai da ciki ko?" Kunyar da ya manta da ita a lokacin da ya iso gidan har ya fada mata da bakinsa ce ta kama shi. Ya dan dukar da kai yana murmushi. Ita ma murmushin ta mayar masa wanda ya koma dariyar farinciki. "Fadi komai kan ka tsaye ai auta ce babu mai cewa mun yi rashin kunya." Honourable dai sai dariya mai hade da kunya. Asibitin da Hasiyan take kwance ta tambaye shi sai ga Asabe a kansu kamar daga sama ta fado. Daga dakinta taji kamar suna ambaton Mariya domin 'ya' kawai taji da kuma asibiti. Bayan abin da ta gani dazu a firgice ta fito. "Me ya sami Mariyan? Ina Munzalin?" Ta ce yayinda take waigawa hagu da dama tana dube dube. Innayo tayi mamakin abin da ya tayar mata da hankali haka. Ba abin ta tambaya ba ta san tsaf za ta gwasaleta. "Hasiya ce a asibiti." "Au tooo...to Allah Ya sauwake" ta ce a sanyaye tana juyawa dakinta. Innayo bata ma bi ta kanta ba ta shirya ita da su Salima zasu tafi asibitin. Dakinta ta koma inda ta baro Uwani tana ta kai gwauro da mari ita kadai. "Na san cewa a karkashin wani kike nima ba zan so ki dinga yawo da aurenki ba. Amma ai ko sakon gaisuwa ga kanwarki kya bayar. Zumuncin da kike wulakantawa Uwani shi ne gatanki. Ba don kinsa kafa kin tattaka shi ba da bamu ga rana irin ta yau ba akan aurenki." Kunyar rashin tunaninta taji da kanta. "Kiyi hakuri Innayo. Ku gaisheta kafin na zo." Murmushin takaici Innayo din tayi ta fita tana cewa "da girmanki baki san gatse ba. A yadda Hasiya ta dade tana neman haihuwa na zata kiran mijinki zaki yi ki nemi izinin zuwa dubota. Komai girman farincikin da zai gilma a gidan nan indai ba ke ya raba ba wato ba za kiyi murna ba..." Har tayi waje Uwani tana jiyota. Abin ma sai ya sata murmushin da bata yi niyya ba. Autar Innayo da ciki kuma bata je dubiya ba. Ta san ba makawa yau sai ta kwana tana jin mitar mahaifiyarta. Sai dai kuma abin da yake damunta yafi karfin samun cikin Hasiya a yanzu dai. Hakuri ta sake bayarwa da sakon gaisuwar ta koma ciki. Suna fita ta fito ita ma ta shiga dakin Asabe. Daga bakin kofa ta tsaya cikin shiri don har mayafi ta yafa. Abin da ya kaita ta fada ba tare da kwana kwana ba. "Gidan Munzali za ki kwatanta min ko ki rakani." Da tsananin mamaki Asabe tayi mata duba irin na wanda ake tsammanin ya yi makuwa "gidan Munzali kuma?" Uwani sai ta dauko waya ta mika hannu gareta don bata ga dalilin mamakin da Asabe ta nuna ba. Ta rasa gane me yasa kowa yake ganin kamar bata son zumunci. Waye cikinsu yake zumuncin da ita? "Bani nambarsa idan kwatancen ba zai samo ba" Asabe sai ta sabi mayafi. Yau din gani take kamar duniya tana hajijiya da ita. Ba kuma don abin da ta gani a tattare da Qibdiyya ba kadai. Harda maganganun Munzali. Tunaninta ya kasa hasko mata inda zantukansa suka dosa. Da yake mai hali ba ya fasawa suna samun adaidaita sahu Asabe sai cewa tayi "amma dai ke za ki biya min ko? Tunda dai ke zan raka." Uwani ta hade girar sama "Munzalin ba danki bane? To nima ba kudi gareni ba. In ba za ki biya ba ki kwatanta min." Asabe tayi azamar gyara zama tana kallon idanun Uwani "Idan baki nuna min halinki ba ai bana ce ke din tsatson Alh. Rabi'u bace." Direban da yaji irin maganganunsu sai ya tsaya cak a tsakar titi. "Hajiyoyi ku sauka don Allah kafin mu isa mu soma rigima daku akan kudi." "Muje zan biya" cewar Uwani tana hararar Asabe da gefen ido. "Wai ma me zaki je yi a gidan Munzali?" "Abin da yasa kika biyoni maimakon yi min kwatance ne zai kaini." Asabe ta hangame baki "kema ya fada miki?" "Labe nayi muku duk da dai hargaginki ne ya sani zuwa ba wai nayi niyya bane." Uwani ta bata amsa kai tsaye. "Nice nake hargagin? Lallai Uwani baki da mutumci. Koda yake ki ka yiwa gyatumarki ma wace ni?" Cewar Asabe tana kara kulewa. Uwani bata kulata ba. Hankalinta ya yi gaba cikin tunanin nawa zata caji Munzali idan ta duba 'yarsa. Ko babu komai yadda ake labarin arzikinsa da son da yakewa 'yar dole ya mata hasafi. Kila ma ya hada da toshiyar baki. *** Banda 'ya'yan cikinta da jikoki babu wanda ya yi saura a bangaren Baaba Mari. Jama'ar gidan manya suna asibitin da Mal. Inuwa ya jagoranci kai Mal. Sa'adu. Sauran kuwa musamman mata suna bangarensu a tsorace. Labari yazo musu cewa Baaba Mari da kanta ta aika kiran Mal Sa'adu. Gashi daga shigarsa bai fito da kafarsa ba sai gadon asibiti. A asibitin kuwa tunda Mal. Sa'adu ya dan farfado ya soma cewa a kai shi gida yana son ganin Baaba Mari. Wannan abu ya harzuka Deluwa musamman taga ko sannun da take ta ce masa bai amsa ba. "Jama'a ku kawo min dauki. Mari ta fito da maitarta fili ta lashe kurwar Malam." 'Yan koranta da na Mal. Sa'adu suka dinga jinjina kai alamun amincewa. Shi kuwa wanda ake yi dominsa ransa sai ya baci. Abu ne da bai taba zato zai ji a ransa ba sai gashi a yau duk kalmar batanci da za a fada akan matar kaninsa sai yaji tamkar an loda masa kaya ne a kansa. Tuntuni ya fahimci illolin da take son nuna masa game da bara. Sai ya zabi ya take gaskiya saboda bata kai matsayin da zai dauki shawararta ba. Kuma sauran yaransu masu zuwa ai kowa ya dawo lafiya. Gabansa ya fadi da wani tunanin ya mamaye kwanyarsa. Shi ganau ne ba jiyau ba akan canjin da aka samu cikin 'ya'yansu da na makota. Akwai uban da yake zuwa wurinsa yana yiwa dansa rubutu domin neman a raba shi da dauke dauke. Ya gallabi gidansu da makota babu damar mutum ya yi ajiya. Wani kuma dan ya addabesu da haurawa matan aure cikin dare yana musu fyade. Ga kwararren malamin tsibbu wanda matan aure suke tarawa arzikinsu akan mallakar miji da korar kishiya. Suna da dan kwaya wanda har a kwata ana tsinto shi. Akwai wanda ya koyo mugunta da tsantsar cin zali. Sau biyu yana zubarwa matarsa ciki da duka sannan ya karya mata cinya. Wani ma dan damfara ya zama. Yana can Dubai ana damawa dashi Wasu sun bata har yau babu su babu labarinsu. A karshe akwai wadanda suka rasu sai dai a kawo gawa. Wani ma sai dai labari ya riski iyayensa bayan an binne shi. Wadannan halaye hatta a makaratun boko na kwana ba baki bane saboda wahalar dake cikin tarbiyya. A can safe, rana, yamma da dare duka akwai ido akan yaran. Amma basu tsira ba. Idanun masu kular sun yiwa daliban kadan. Dalibai sama da arba'in a karkashin kulawar mutum daya na wani lokaci. Dole a sami masu kangarewa ba tare da sani ba. To ina ga makarantar allo wadda idon bai wuce na malami ba? Yaran kuma suna fita a duk lokutan cin abinci neman na kansu? Duk da haka akwai wadanda suka yi dacen samun alkhairi daga zuwa karatu. 'DACE suka yi' Mal. Sa'adu ya tunatar da kansa. Irin dacen da wadanda suka fadawa halaka basu yi ba. Karatu ba zai taba tafiya babu tarbiyya ba. Tarbiyya kuwa tana samun kwakkwaran tubali ne a inda ake bayar da kulawa. Ita kuwa kulawa sai an jure an daure domin bayar da tarbiyar akwai wuya. Zamanin baya ido kadai d'a zai hada da mahaifiyarsa ya fahimci sakon dake cikinsa kuma ya yi aiki dashi. Yanzu kuwa sai ka zare idon shi ma ya bude maka nasa kirikiri yana dariya. Ka dake shi cikin sakan talatin ya manta ya sake maimaita laifin. Akwai wuya...ke uwa kina yi ma ya aka kare balle an kai dan nesa babu mai kwabarsa. Mari ta ce ba za ta yafe masa ba. Abbati ya zama dan luwadi...Wa Iyazu Billah. Da me zai ji? Tsatson gidansu da yake alfahari da kyawunsa shi ne aka sami reshe guda ya lalace. Bayan sadaukar da rayuwarsa wurin ganin gidansu ya cigaba da amsa sunan gidan Malamai yanzu wannan masifa ta bullo. Zuciyarsa bata son karba amma kwakwalwarsa ta san gaskiya. Idan ma yaki neman gyara shi ne babban mai kwana ciki. Ba don ya so ba ya yiwa Deluwa magana akan kalamanta. "Ba zan lamunci wannan shirmen ba Deluwa. Idan ba za ki iya kama bakinki daga barin aibata Mari ba ki wuce gida. Kirji ta dafe ba shiri kamar tana gudun faduwarsa. Ta dube shi idanu a waje. "Malam Mari ka ke karewa? Mari dai wadda muke raba dare muna kwashewa albarka ni da kai? Kaiiii..." Ta fada da karfi tana girgiza kai "Yasin da wata a kasa. Mari ta karawa bokanta kudi aiki ya ci." Mal. Sa'adu da ya san shiru sosai yake bukata domin samun nutsuwar tunani da neman mafita tamke fuska ya yi. Bai bata damar roko ba ya ce lallai ta koma gida baya son zamanta a asibitin. Bata yi masa musu ba ta tafi gidan. Amma tana zuwa dakin Baaba Mari ta nufa tana danna ashariya. *** Yamma tayi, gari ya soma duhun da dakuna suke bukatar haske. Lokacin da Asabe da Uwani suka yi sallama a falon gidan Munzali basa ganin kofofi da matattalar dake wurin. Ko ina dund'um an saki labulaye. Kwada sallama suka dinga yi da karfi tunda Maigadi ya tabbatar musu cewa ya shigo sannan ga motar da ya fita da ita a wurin parking. Uwani ta so shagala da kallon tsala tsalan motocin dake zube a wurin. Ga gidajen daga waje ma sun hadu. Tsarin fuskantar juna da suke yi dana Abbati ya sake burgeta. Shigowar Kande ce ta kawo karshen sallamar tasu. Da yake ta san Asabe sai ta gaishesu da girmamawa. "Alhamdulillahi kun zo Hajiya. Yanzu nake fakon idan aka yi Magriba Alh. Munzali bai fito ba zan taho gidan naki." "Me ya faru kuma?" Cewar Asabe da saurinta. Kande ta labarta musu yanayin da Munzali ya shigo gidan yana harhada hanya. Da ganinsa baya cikin nutsuwa ko kadan. Qibdiyya tana kafadarsa tayi bacci. Da ta nemi karbarta har wata tsawa ya daka mata. Dole taja baya ta zuba masa ido. Hawaye ne tabbas taga saukowarsu daga idanunsa. Sai dai kafin ta gama janyo tunanin da ya dace tayi, ya haye sama sai karar buga kofa taji. "Ki hau ki kira min shi da Qibdiyyan" inji Uwani ga Asabe tana ajiye dan akwatin tafi da gidanka na kayan asibiti. Hantar cikinta sai da ta dan kada don bata manta maganganunsa na dazu ba. "Ban gane in hau ba? Don rashin tausayi tsofai-tsofai dani zaki sani hawan bene." Uwani ta tabe baki. Abin kirki tazo yi amma halinta kam ya zanu akan dutse. "Gidan danki ne fa kuma ni ban taba zuwa ba. Ke ya dace ki hau." "Sai an magana ku dinga cewa ubanku daya. Da su Maimuna ne ai ba za ki ce yau kika fara..." Sauran maganar makalewa tayi don tuni Uwani ta kusa kure benen. Kankanin lokaci ya sadata da wani katafaren falo wanda yake cike da ababen more rayuwa. Kofofin dake cikinsa ta dinga kallo tana neman kofar dakinsa. Cikin sa a sai ta hango takalmin Qibdiyya a bakin kofar daya daga ciki. Duk yadda aka yi nan suke. Bata ji ko dar ba don dakakkiyar zuciya gareta ta karasa kofar dakin tana kwankwasawa gami da yin sallama. Munzali yana zaune a gaban gadonsa inda ya shimfide Qibdiyya ya hada kai da gwiwa yaji sallamarta. Yayi matukar mamaki duk da ya san taji komai bayan haduwarsu ta dazu. Bai motsa daga inda yake ba kawai ya dago kai. "Shigo." *** I just published "34" of my story "UWA UWACE...". https://www.wattpad.com/1095387462?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=BatulMamman17&wp_originator=Y6Whd7vibxZO3ov2%2FPsLYwHTGqHbwm%2FcSizoY4fzcwOV0cAQganfcuU6IofLueJEMdtJpryQscJyFE6EhHul9y%2FCQlLqNPPExesSATjzSneThshj7TIDLT4mdnC%2FGc82 UWA UWACE...34 Batul Mamman💖 Yan uwa muna barar adduarku ga mahaifin 'yar uwa Massouda Moulaye. Wanda Allah Ya yiwa rasuwa ranar larabar da ta gabata. Allah Ya jikanshi Ya gafarta masa. Allah Ya kyautata makwancinsa. Ya bamu ikon tarar dasu cikin aminci. Amin ****** Wata sallamar tayi ta kutsa kai cikin dakin da sanyinsa ya busa har kasusuwanta. A take taji kwarin gwiwarta ya dadu. Sai da ta shiga daga inda yake zaune ya danna remote kwayayen fitilu uku suka kama. Haske ya gauraye dakin da zaka rantse ba namiji ke gyara kayansa ba. Komai tsaf ga kamshi ga kyau. "Ke da waye?" Ya tambayeta yayinda ta kai ido inda Qibdiyya take bacci. "Asabe. Tana kasa." Shiru suka yi na dan lokaci suna yiwa juna kallon kallo. Ita tana ganin wautarta na rashin kusantar kanin nata tun da dewa. Shi kuwa abubuwa da dama ne suka cunkushe kirjinsa. Zazzabi yake ji da matsanancin ciwon kai. "Na san abin da ya kawoki Uwani zan kuma baki domin ki taimaki Qibdiyya. Sai dai abu daya ne ba zan miki ba..." Idanunsu suka sarke da juna. Magana yake yi mata ba da wasa ba. Bata jin ma banda gaisuwa sun taba yin wata doguwar magana dashi banda yanzu. Idanun nasa sai suka zame mata tamkar masu wadanda ke huda sassan jikinta. Gabadaya sai ta tsargu ta kasa sakewa. Don ma tana da baki ne ta ce, "Ban gane ka san me ya kawoni ba? Daga zuwa taimako sai ka soma fada min magana saboda raini." Dan murmushi ya yi cikin son nuna burgarta bata je masa ko ina ba. Ya dora maganarsa ba tare da ya damu da bata amsar maganarta ba. "Kamar yadda na ce zan biya ki dubata amma ko kwandala ba zan baki ba domin ki bar maganar nan a matsayin sirri." "Me yasa?" Ta fara cewa tana zaro ido sai kuma tayi saurin gyara zancen "yaushe na ce maka idan baka biya ba zan tona maka asiri?" Mikewa ya yi kansa na cigaba da sarawa ya matso da Qibdiyya bakin gadon yana cewa, "Baki fi kowa so da damuwa dani ba Uwani amma sai gaki ke kadai a gidana a wannan lokacin. Ina Innayo ina su Zara? Me yasa baki fada musu kun fito tare ba?" Hade rai tayi na borin kunya ta saka safar hannu. "Saboda irin wannan abin ba abu bane da ake so ayi ta yamadidi dashi ba." Wani dan murmushi ya yi mai sauti "Qibdiyya dai 'yarki ce, tonon asirinta naki ne. Kuma magana dole zata fito idan aka tsinci tsinannen da ya yi mata wannan abin da rai ko babu." Fita ya yi yaja kofar dakin ya barta da tunanin kalamansa. Taji zafin maganganun duk da gaskiya ce ziryan bai mata sharri ba. Qibdiyyan ta tasa a hankali don kada yarinyar ta firgita idan taji ana tabata cikin bacci. Cikin yan uwan mahaifinta Uwani tana sahun gaba na wadanda bata saba dasu ba kuma suke bata tsoro. A firgice take kallonta amma Uwani bata fahimta ba saboda sabgar yara ba tata bace. A hankali dai take yi mata magana domin ta kwantar da hankalinta. "Yi kwanciyarki dubaki zanyi." Tana kai hannu zata cire mata pant, Qibdiyya ta runtse ido yadda ta yiwa Asabe. "Kema hannu zaki saka min a nan? Idan an saka wannan safar ba zai min zafi ba?" Hannuwan Uwani sai suka fara rawa ta kasa cire pant din. Wannan wadanne irin maganganu ne suke fita daga bakin karamar yarinya irin wannan? Tana can tana tunani caraf idanun Qibdiyya akan alluran dake cikin first aid box din. Jikinta ya kama rawa ta soma kuka. Munzali yana jin kukan ya bude kofar. Sai dai yaci karo da abinda yasa shi jin ina ma bai zo duniya ba. Qibdiyya ce take cewa, "Don Allah kada kiyi min allura wallahi ba zan fadawa Daddy ba. Abin nan ne bana so ki tura min da karfi yana min ciwo kinji" kallon da taga tana yi mata ta kasa cewa uffan ne ya bata damar tashi zaune don ko kadan bata so ayi mata "Kwanta ni inyi miki. Nima na iya." Tsigar jikinsa har tashi take yaji kansa kamar k'wari suna yawo. Da dan allinsa ya nunata yana daga murya ba tare da ya sani ba. "Me kika iya? Me zaki yi? Qibidiyya waye ya koya miki wannan abin?" Baiwar Allah a gigice ta tashi idanunta suna zubar da hawaye. Idan da abin da yafi komai daga mata hankali bai wuce shi ko Abbati su sani ba. Uncle Daddy alkawarin kisa ya yi musu. Zai yanka mata su irin yadda aka yi a bidiyon da ya nuna mata. A zafafe Munzali ya sake cewa "nace waye ya koya miki? Da wa kuke yi? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un." Ya rike kansa "Uwani kin ji abin da tace kuwa?" Qibdiyya dai ba abin da take sai kuka. Haka ma Munzali wanda ya dubkule hannu yana dukan bango. Yatsunsa har kara suke amma bai daina ba. Uwani kanta ta kidime. Sai a lokacin taji wani girma ya sauko mata. Idan bata tari abin da yake faruwa ba da uban da 'yarsa duka zasu shiga wani hali. Hannunta ta kama ta zaunar da ita a kan cinyarta. "Daina kuka Qibdiyya ki fada min waye yake saka miki hannu a cikin pant." Cikin faduwar gaba Qibdiyya ta kalli Daddy dinta ta girgiza kai. Wata irin tsawa ya yi mata wadda har Uwanin sai da taji cikinta ya kada. Kaiwa da kawowa kawai yake a dakin jikinsa na tsuma. So yake ya samu wani abu ya matse ko ya yi ta duka har sai kuzarinsa ya kare. A lokacin azal ta fada kan wanda bai ji ba bai gani ba. Hakika Allah ba azzalumin Sarki bane. Sai dai kuma Yana nuna ishara ko aya akan wasu domin ya zama gargadi ga majibintansu. "Uncle Lilu" Amon muryarta ya fito lokaci guda da kiran sallan da Ladanin masallacin kusa dasu ya soma na Magariba. Yawun bakinsa kafewa ya yi ya kasa hada harufan da zai kira sunan Lilu. Ga wani abu mai daci yana bin busasshen wuyansa yana saukar masa a ciki. Zuciyarsa kuwa tamkar farantin tangaran haka yaji tayi rugu rugu. A karamar kwakwalwar Mariyatul Qibdiyya kuwa, tayi tunanin kama sunan Lilu tsira ne gareta da iyayenta. Shi yana da kirki ba zai yanka su ba. Uncle Daddy da yace yana ganinta duk inda take yanzu ba zai mata komai ba. (Ba da niyya Munzali ya taka muhimmiyar rawa wurin janyowa Lilu laifin da ba nasa ba. Yarinya ce wadda aka tsorata tun lokacin da ake batawa rayuwa. Yanzu kuma an sake firgita ta da fada da tsawa. Wannan kadai ya isheta dalilin yin shiru ko ta kira sunan wani daban. Da wane mataki aka fi saurin samun bayyanar gaskiya a irin wannan yanayin da ba a fata? Rarrashi da laluma musamman ga kananun yara. Idan sun kama suna iyaye a bincika a sake bincikawa. Yara ma suna karya! Wani domin kwatar kai, wani kuma domin maslahar da yake ganin canja gaskiyar zai kawo.) *** Washegari bakwai a hanya ta yiwa iyalan Alh. Tahir. Ana sallame sallar Asuba suka shirya. Lilu da Mardiyya ma ko wanka basu yi ba saboda iyayen sun matsu su tafi. Awa biyu ta kaisu gida. Shi Alh. Tahir kai tsaye office ya wuce. Yana shiga ya shiga dube dube yana daga abubuwa. Wannan wayar da yake kiran 'yan matansa yake nema ido rufe. Fatansa kada ta fada hannun da asirinsa zai tono. Da ya gaji da neman sai ya kira direbansa da masinja. Shi direban umarnin kai mota wanki ya bashi. Ya ce a cire duka kujerun a duba masa wayar. Masinja kuma ya kira masu shara a fitar da komai na cikin office din a duba masa. Amma fa koda ya bayar da wannan aikin yana da tabbaci dari bisa dari bai barta a office ba. Motar yafi zargi. Kawai dai ya yi amfani da karin maganar bahaushe da ake cewa idan kana neman rakuminka ka duba har cikin allura. Dakin da suke meeting ya shiga ya zauna yana jin zuciyarsa tana wani irin bugu. Ya rasa me yake damunsa tun wayewar garin yau. Ransa a jagule yake ga fargabar da bai san dalilinta ba. Ya san dai yana matukar tsoron wayar nan ta fada hannun wani a cikin gidansa. Mutumcinsa ne zai zube wanwar. Matansa sun san komai amma ba zai so su gani kamar yadda suka ga sakon Yumna ba. Amma 'ya'yansa fa? Wanda Farha ta gani ya ishe shi jin kunya har ya mutu. Tunanin Yumna da ya yi sai ya sake kad'a shi wata duniyar. Rabonsa da ita tun ranar da wayarsa ta bata. Kamar sauran 'yan matansa ita ba bata da numbar kowane layi sai na wannan wayar. Yadda take babu hankalin nan yana tsoron kar ta zo gidan ta ce tana nemansa. Wuni ya yi yana ta tufka da warwara har aka gama ayyukan da ya saka ba a ga wayar ba. Bai iya tabuka komai ba ya tafi gida. * Kurar da bata taka kara ta karya ba a dakinsa ya fara karkadewa kafin ya shiga wanka. Idan bai yi da kansa ba ya san Mami ba za ta bar Sauda ko Mardiyya suyi masa ba. Musamman da yake daga tafiya suka dawo za ta ce suma sun gaji. Yana gama shiryawa ya dare gado zai yi ramuwar bacci sai ya bige da chatting. Hirar kwallon kafa ce suka kusa yin awa guda suna fafata musu shi da abokansa a group dinsu. Daga kwance sai da ya koma ya zauna. Can aka turo hoton jerin wasannin da suke magana a kai da sakamakon. Lilu bai san lokacin da ya yi ihun murna ba. Club dinsu ne suka yi nasara kamar yadda suka fada. Sun cinye musun. Yana cikin murnarsa Suhaib ya shigo sanye da wandon bacci da singileti. Da gani shi ma wanka ya sake yi zai kwanta. "Ka fa hanani bacci da ihu." Lilu ya daga hannuwa irin na masu saranda yana murmushi. "Takawarka lafiya dan rigimar Mami yanzu nima zan kwanta." Suhaib bashi da zabin da ya wuce yin murmushi. "Kai kuma Dan-ta-kife din Mami ko?" "Kada ka dora min sunan da ba halina ba." Suhaib ya gyara tsayuwa gami da yin kwafa "ni rigimar halina ce kenan?" "Banda rigima tun dazu me ya hanaka bacci sai yanzu daga yin ihuna za ka fito?" Tsuke baki Suhaib ya yi ya juya yana murmushi. Me kuwa ya hana shi bacci sama da tunanin yarinyar da ya gani tare da makaniken nan? Haushinta ya kamata yaji a ganinsa. Sai aka yi rashin sa a ta cike tunaninsa da wasu abubuwa da bai saba kai kansa garesu ba. Wai yau shi ne yake tunanin wace makarantar gaba da sakandire ce za ta fi kusa da gidansa (Alh. Tahir ya mallaka musu filaye shi da Lilu wadanda ake kan aikin ginawa) idan matarsa iyakarta sakandire kafin auren. Dariya ya kama yiwa kansa na yadda aka yi daga haduwar rana daya ya san cewa iyakarta sakandire. Koda ya koma daki maimakon ya kwanta kamar yadda ya yi niyya sai ya zura jallabiya ya nufi bangaren Jiddo. A dakin Lilu bayan fitar Suhaib da karewar musun nasu sai ya soma hamma. Gajiyar biki da ta tafiya tayi masa rubdugu lokaci guda. Mikewa ya yi ya nufi gaban socket din da yake saka chaji. A nan yaga chajarsa da bakuwar waya. Tsorata ya yi don bai ga ta inda za a ce wayar ta shigo dakinsa ta jona kanta ba. Yan uwansa kuma duka ya san babu mai irinta. Kamar ya tafi kiran Suhaib sai ya fasa. Yanzu kowa zai kara raina shi ace bai iya komai ba duk bakinsa. Ya daure zuciyarsa ya daga hannuwansa ya karanta musu Ayatul Kursiyyu ya tottofe. "Kun dai san nan dakina ne amma duk da haka ban ji haushi don kun jona chaji da chajata ba" ya rage murya da salon rokon arziki "ina neman izini in cire in saka tawa ko rabin awa ne?" 'dillll' Yana rufe bakinsa text ya shigo wayar. Hanjinsa gabadaya ya kanannade saboda tsoro ya koma kan gadonsa ya haye har kafafunsa. "Daga magana sai ku turo min text? Indai chaji ne na hakura har abada." Ya zuro kafarsa yana kallon kofa gabansa na faduwa "don Allah zan fita inje dakin yayana. In je?" 'dillll' Wani text din ya kuma shigowa. Dole ya fasa fita yana fadawa kansa cewa gargadi ne ake yi masa. Ya koma yana mika hannu yana janyewa duk a tsorace "Bari in duba don kada ace nayi rashin kunya. Ni din banza in ja daku? Ku da ake cewa sai kun shekara dari kuke fara samartaka...." 'dillll' "Naji. Naji! Ya dauki wayar sai dai a kulle take. Abinka da fitinannen matashin zamani. Ya manta da tsoron da yake ji ya koma kokarin gano pattern din budeta. Bai sha wata wahala ba ya samu bayan yan dabaru. Abin da ya daure masa kai bai wuce ganin pattern din sak irin na Abbansu ba. Kai tsaye wurin messages ya shiga. Ya tarar da sakonni sun tasarma dari. Kuma wani abin al'ajabi na layin basu fi a kirga ba. Sauran kuwa harrufa ne wasu D, V, J, gasu nan dai. Na sama saman da suka yi alamar sune aka yi yanzu ya bude. Harafin dake jiki Y ne. (Naji labarin tafiya kayi da tsofaffin matanka. Shi ne ka kasa daukar wayata saboda kana jin tsoronsu? Anyways an tabbatar min yau ka dawo. Na baka zuwa azahar idan baka kirani ba zan zo har gidan ai ba bakona bane. Aure ne dai ko ana so ko ba a so sai na amsa sunan matar Alh. Tahir) "Abba?" Ya ambata a raunane, hawaye na zubo masa. Duk wani kuzarinsa ya kau sai zafin kirji. Tarin tambayoyi ne a kansa na son sanin yadda aka kwana a ragaya. Neman amsa ya shiga yi ta hanyar bin text din yana maimaitawa. Bai samo amsar komai ba sama da haddace mummunan sakon. A kasan ransa kuma sai tunanin me zai fi dacewa ya yiwa wannan mai tsautsayin da ta iya shafawa idonta toka ta turo wannan sakon. Cikin sauri ya koma baya ya soma bin sauran harrufan da aka adana sunan mutane dasu ya bude nasu sakonnin. Sannan ne kuma jikinsa ya yi mugun sanyi. Hira ce tsakanin Abbansu da 'HARUFFA' daban daban ta rashin da'a. A haka ma ya kula amsoshin Abban basu da tsayi sosai. Wannan kuma dama ya yi ne domin tsira daga forwarding chat ko screenshot da ake yi a whatsapp. Dena binsu ya yi ya koma saman wanda suka yi musaya da Y. Nata da yawa korafi ne akan rashin zuwansa da maganganun aure. Har tana cewa mahaifinta ya ce idan bai zo ba a satin zasu fasa bashi ita. Ko kadan Lilu bai damu ba idan Abban aure zai yi. Salon hirar ce tafi daga masa hankali domin alamu sun nuna cewa ba a hira aka tsaya ba. Yaci karo da inda aka yi zancen hotel da guest house. Da kuma godiyar 'yan matan akan tarin kudaden da ya basu. Whatsapp yaso dubawa sai dai babu shi akan wayar. Yana nan kansa ya rarrabu wurin fassara abubuwan da ya gani yaji shigowar wani sakon. Y din ce dai. Kamar dama jiranta yake yana shigowa ya bude. (Kaga fa ina tunanin ciki ne ma dani. Zan yi test a gida idan positive ne zan turawa Farha hoton ta whatsapp. Sai a yiwa tsofaffin gwangwanye albishir sun kusa samun karuwa.) Kuka Lilu yake tamkar yaron goye. Karshen sakon ma da kyar ya iya karantawa saboda cikar hawaye. Nambar ya kwashe ya zuba a wayarsa. Tunda ya kai nambobi shidan farko sunaye masu shigen nambar suka dinga raguwa. Yana saka ta bakwai sai ya rage suna daya. YA YUMNA kamar yadda suke kiranta shi dasu Sauda a matsayinta na aminyar yayarsu. Kin tsayawa ya yi sai da ya rubuce ta duka ya tabbatar da sunan da ya gani. Yana jin lokacin da zazzabi ya rufe shi hade da wani irin sanyin jiki. Bashi da hujjar karyatawa saboda harafin da ya gani a wayar Alh. Tahir ya kara bashi tabbaci. "La haula wala quwwata illa billa. Abba? Ya Yumna?" A gigice ya mike da ya tuna ma'anar sakon karshe. Indai Yumna ciki ne da ita kenan komai ma ya faru tsakaninsu. Zuciyarsa a take ta tashi saboda kyamar hakan da yaji. Ya fada bandaki ya amayar da duk abin da ke cikinsa. Baki kawai ya kuskure bayan ya gama ya fita daga dakin. * Duk gidan Alh. Tahir babu wanda Jiddo ta tsana a tsukin kwanakin nan kamar Suhaib. Da can da baya shiga shirginta mantawa ma take dashi. Iyakarsu da juna idan zasu wuce kuma suna kusa taji sautin tsakinsa. Tsakin da tun aurenta da ubansa take ji kuma bai taba damunta ba. Ba kuma wani abu ne ya janyo yake yi mata shi ba sai kamasu da aka yi a daki wanda shi ma yaje wurin. Abubuwan da suka biyo baya da auren nasu sun taimaka kwarai wurin dasa masa tsanarta. Sai gashi bayan shekaru sun shude ta sake bude kofar sabunta zarginta a zuciyarsa. Alal hakika bai yi wani mamaki ba lokacin da yaga tana shirin barin wurin dinner da makaniken nan. Sanannen abu ne cewa indai bawa ya kulla aminci da zina to ba makawa sai ta kawo masa ziyara watarana. Mahaifinsu yace yaji ya gani wurin sabon Allah. Dolensa kuwa ya girbi shukar da yayi ko ba dade ko ba jima. Shi dai adduarsa kullum bata wuce Allah Ya tsare masa mahaifiyarsa da kannensa. Sallama hade da kwankwasa kofa ya yi da ya isa bangarenta. Mai'aikinta ce ta amsa ta bude masa. A hakimce kan two-seater yaganta tana waya. Ganinsa a tsakar falonta ya mugun firgitata. Lafiya ko rashinta basu taba kawo shi inda take ba. Yau da yazo ta san lallai akwai matsala. Wayar faduwa tayi daga hannunta ta kuma gyara zama ba shiri. "Nambar makaniken nan zaki bani." Cewar Suhaib, fuska babu annuri. Jiddo sai ta daburce duk saboda gudun tonon asiri. A haka ta cije ta harare shi. "Rashin kunyarka ta isheni Suhaib. Idan ban ci darajar shekaruna ba ai ya kamata in ci na matsayina a gidan nan." Surutunta bashi da gurbi a kwakwalwarsa balle yaci darajar neman ta maimaita domin ya fahimta. "Zan samu ko in tafi?" Rainin wayonsa ya sake bata haushi. Wato ma bai ji abin da tace ba bare ta san ran zai yi aiki dashi. Yatsina fuska tayi ita a dole bata san me yake nufi ba ta ce, "Wane makaniken?" Wannan karon Suhaib ne ya hango rainin wayonta. Sai da ya dage girarsa daya sama ya murmusa. Harsashi zai hada mata a wurin Alh. Tahir don ranar tada bom din bata zo ba. Wannan ba aikinsa bane. Lokaci da talalar Ubangiji ga bawan da ya dage akan aikin sabo zai cimmata wataran. Wata irin murya ya yi amfani da ita sai a rantse sangartaccen da ne a gaban mahaifiyarsa yana zuba shagwaba. "Don Allah ki bani Anti Jiddo." Ita kanta da taji muryar sai da ta kara tsorata fiye da farkon zuwansa. Ta san dole akwai abin da yake nufi da haka. Ba dai ta zata maigidan ne da kansa ya shigo falon ba tare da ta kula ba sai yanzu. Ran Alh. Tahir fari kal kamar takarda yau ga Suhaib a bangaren Jiddo. Yadda yake magana ya nuna masa sun jima da daidaitawa. Ya dinga zuba murmushi kamar sakarai har yana mantawa da halin da yake ciki. "Wato kin saka danki a daki yana ta shagwaba aka rasa wanda zai amsa min sallama ko? Wai ma mene ne yake faruwa zan yi alkalanci." Suhaib ya yi saurin bashi amsa kafin ta sami damar juya zancen. "Nambar makanikenta na Kano nake so Abba shi ne taki bani wai sai na yarda gobe zan rakata shopping" Wohohooo. Alh. Tahir da shi ma ba wani samun hira daga Suhaib din yake ba duk irin son da yake masa sai yaji kansa ya yi gingirin. Murmushi yaki yankewa a fuskarsa. "To ai sai ka amince dan Jiddo" 'I reject it! Tuff, tuff' cewar Suhaib a zuci yana jin tsigar jikinsa na tashi saboda an kira shi dan Jiddo. "Na amince. Don Allah ki bani" Tsabar mamaki sai ta kasa cewa komai banda kai da take gyadawa kamar kadangaruwa taga manja. Sunan Danliti ta lalubo tunda Alh. Tahir ya musu karan tsaye yaki tafiya. Dama al'adarsa ce shiga bangaren kowa idan zai fita ko ya dawo. Bayan Suhaib ya kwafe nambar ne Alh. Tahir yake tambayarsa me zai hada shi da makanike a Kano. "Wani case ne babba ya taso tsakaninmu dashi." Alh. Tahir ya dan bata fuska "Ban gane ba? Wani abu ya yi maka?" Suhaib ya yi hanyar kofa yana cewa "a'a, motar Anti Jiddo yaso lalatawa ba don Allah Ya kaini wurin da suke ba da wuri." Sautin cikin Jiddo har kunnuwansu saboda tsoro. Suhaib kuwa ya fice yana jin Alh. Tahir na tambayarta me ya sami motar har aka nemo makanike shi bai sani ba. Rantse rantsenta kadai ya jiyo ya kara gaba don bashi da lokacin jin karairayin da zata yi. * Lilu kuma da ya fito bai zame ko ina ba sai bangarenta Mami Khadija. Ya yi zaton samunta ta kwanta ko shirin kwanciyar kamar kowa sai yaga sabanin haka. Laptop ce a gabanta ga tulin takardu ta soma barbazawa tana aiki. Gaban table din da aka yi mata musamman saboda aikinta yaje ya mika mata wayar. "Ga wayar mijinki idan ya dawo ki bashi." Tun shigowarsa take kallonsa amma furucinsa yasa ta koma yi masa firgitaccen kallo. "Mijina? Mijina fa ka ce Lilu. Ko dai nice ban ji ba da kyau?" Ta furta a sanyaye. Lilu ya cije lebe cikin bacin ran tuna abubuwan da ya gani. "Mijinki maigidan nan nake nufi." Laptop din ta tura gefe ta tashi tsaye tana dubansa. "Ko agolanci nazo da kai gidan nan bana tunanin za ka iya budar baki ka kira wanda nake aure Mijina." Duk shashancin Lilu bai taba zina ba. Mami Khadija ta dasa musu tsananin kyamar wannan laifin tun basu san kawunansu ba. Yafi kowa fitina a gidan amma akwai iyakokin da ko a mafarki bai hango kansa da ketaresu ba. Kalaman Mamin murmushi suka saka shi. "Mamina kinfi karfin haka a wajena. Wallahi indai mai mutumci wanda ya san darajar kansa data iyalinsa kika aura ni mai tayaki yi masa biyayya ne." Da ya gama maganar ya dora wayar a kusa da tata ya fice da sauri. Zama a gabanta karyar masa da zuciya zai sake yi ya kaishi ga kuka. Tausayinta yake ji sai dai kuma jikinsa ya bashi ta jima da sani. A hanyar zuwa dakin ya dinga tuno irin nasihunta da fada da suna yara har kawo ga yanzu. Kusan komai yafi ta'allaka akan zina. 'Ba halinsa bane!' shi ne abin da Mami Khadija ta fara fadawa kanta a lokacin da taji kamar ta kwashe shi da mari. Kwalla ce ta taho mata saboda jikinta yana bata da wuya idan ba sirrin boye ne ya fito fili a wurinsa ba. Yadda Farha ta sani bayan Suhaib gashi yau shi ma ya sani. A ranta ta dinga tsarkake Mulkin Ubangijin da ya haramta zina. Hakika wannan kaba'ira tana zubar da mutumcin mai mutumci. Yau Lilu da bakinsa yake kiran mahaifinsa da wani suna ba Abba ba. Kallon wayar tayi sau daya ta kawar da kanta. Alh. Tahir na shigowa bangarenta daga wurin Jiddo ta damka masa wayar daga bakin kofar da ta tare don kada ya shigo ciki. "Lilu ne ya kawo" Gumi a take ya tsatstsafo akan goshinsa. "Ya ce wani abu ne?" Mami Khadija ta kalle shi ido cikin ido ta ce "ya ce ga wayar mijina na bashi idan ya dawo" Alh. Tahir ya karkata gefen fuskarshi gareta yana son tabbatar da abin da ta ce. "Mijinki? Dani yake?" Cikin ko in kula ta ce "a iya sani na ba." Daga haka ta rufe kofarta ta barshi a wurin yana jinjina girman abin da yake samunsa a tsukin nan. I just published "35" of my story "UWA UWACE...". https://www.wattpad.com/1095418785?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=BatulMamman17&wp_originator=WH2D39oPR5sYCfkLu1mXT4fL9GeLPbHp2QiULVor2y52dl9oH29pjmjeOiXFaGwOC1HqE1U%2BRuVJYskywLegMBvivLLBGM9JeCauF9Iqcg5jKRTG62XjxazG0mL2u3NB UWA UWACE...35 Batul Mamman💖 Yaa Rabbi! Naji korafe korafe kai tsaye da ma na aike kala kala game da dorawa Lilu laifin da ba nasa ba. Na so kamewa daga bayar da amsa sai dai ku gani a rubuce. To amma wasu har ikirarin barin karatun suke. Jama'a idan kun barwa Batul labaranta ina ta kama? Sakon da nake fatan Allah Ya bani ikon isarwa bai je ko ina ba kenan. Ya zama dole na magantu. Kafin na fara wanke kaina, ina so inyi amfani da wannan damar wurin yi muku godiya. Akwai gajiya matuka idan marubuci yana daukan dogon zango kafin ya yi post. Sai dai kamar kullum hakuri dai zan cigaba da baku. Ba da gangan bane. Yau da gobe ce wadda take nukurkusar daukacin al'ummar kasar duniya ba ma kasar nan ba. Allah Mabuwayi Ya kawo mana saukin lamura. Amin To mu koma ga labarinmu. Kwanakin baya korafin akan yawan wahalhalun Innayo da rashin cin moriyar guminta ne suka yi yawa. Wasu har suna ganin kamar zan sagar musu da gwiwa wajen kulawa da amanar da Allah Ya bamu ta zuri'a. Ko daya ba nufina ba kenan. Labarin nan kacokan ban yi shi domin tsantsar nishadi ba. Wasu lamura nayi ta nazari a rayuwarmu shi yasa nake son yinsa ta yadda zaiyi kamanceceniya da zahirin rayuwa. Akwai Innayo bila'adadin a cikin al'ummarmu. Mace ta wahaltawa miji ta kuma wahaltawa 'ya'ya. Amma a karshe haka zata koma ga Allah da bakincikin dukkansu. Ta rayu a talauce ta mutu cikin talauci. To amma fa shafin rayuwarta ba zai kare a wurin Maqaginta ba muddin ta koma gareshi tana mai gaskata kadaitar mulkinSa. Daga lokacin ne ma zata fara shan romon ladan ayyuka da hakurinta har zuwa tashin qiyama. Sai dai taji ance ta wuce Aljanna gidan dauwamamen farincki. Game da Lilu kada mu manta su waye iyayensa. Uba mazinaci wanda har yanzu babu wata kwakkwarar nadama a tattare dashi. Shin idan zina bata dawo masa a inda zai yi masa ciwo ba kuna ganin zai san Annabi ya faku? Zai ji ciwon da iyayen 'ya'yan da ya mu'amalanta suka ji? Zai yi nadamar ayyukansa har ma ya tuba? Sanin tsohuwar sana'ar maneman 'ya'yansa ba ta da babban tasiri indai ba an riga an daura aure ba. A yanzu kam ba zai wuce ya soke auren ba ya cigaba da yawonsa. Wanda kuma duk ya yi zina da ahalin wani shi ma sai anyi da nasa. A gefe guda kuma mahaifiya ga Lilu mace ce tagari. Uwa ce da ta amsa sunanta wurin tarbiyya da yawan yiwa 'ya'yanta addua. Ga Ubangijin da take mikawa lamuranta Mai ji ne ga kukan bayinSa. Al Hayyu, Al Qayyumu ba zai bata kunya ba. Gamu ga Sarkin da baya saba alkawari. Mahaliccin da Adalci ya kasance cikin suffofinSa. Duk da cewa labari ne amma ina son tunatar damu uwaye karfin addua. Tabbas alkawarin Allah na dawowa mazinata da sharrinsu ta hanyar da zasu koka ba zai tashi ba. Sannan kuma adduar Uwa ta gari ga 'ya'yanta wannan kaifiyan ce. Indai haka ne kuwa to lallai Alh. Tahir sai ya yi kuka akan sharrin da aka yiwa Lilu. Sannan Mami Khadija sai ta kara mika wuya ga Allah a yayinda Ya kubutar mata da danta daga dabaibayin da bai isa ya kwance ba. Ya Rabbi ka karawa Annabinka daraja, Ka azurta shi da kololuwar daukaka. Amin. *** Mami Khadija kiran Lilu tayi bayan ta rufe kofarta. A zatonta Alh. Tahir ya bar wurin ashe yana tsaye. Kafafunsa sun yi masa nauyi ya kasa dagasu. Lalacewarsa bata yi kamarin da zai iya cigaba da jure juya baya daga tsatsonsa ba. Bazuwar zancen nan zuwa kunnuwan ragowar 'ya'yansa ba karamar barazana bane ga mutumcinsa a idanunsu. Shi kuwa zai iya komai domin kare wannan martabar. A tsarinsa miji ko mata kada ya fishi girman masauki a zuciyarsu. Yana son ya zama babban amininsu kamar yadda suka faro tun kuruciya. Wannan dalilin ne ma yasa Farha da Lilu suka ji ciwon laifin nasa fiye da yadda zasu misalta. Muryar Mami yaji cikin dakiyar da ya saba gani a tare da ita tana magana da Lilu. "Ina ka tafi?" Bai ji amsar ba sai abin da ta mayar masa. Yadda tayi magana babu alamun wasa ko wargi. Umarni ne take bayarwa domin ta kare dan nata. "Yana daga cikin rahamomin Ubangiji garemu da Ya halatta mana yin abota. Lokuta da dama suna maye gurbi ko ma su fi family dinmu tsaya mana akan matsaloli. Sai dai kuma ba kowacce irin matsala ya kamata a fadawa aboki ba. Wani abin sirrinka ne har lahira. Idan yau kaje wurin abokai da damuwar nan har ka fada musu komai ka cuci kanka. Ba kai kadai ba hatta 'yan uwanka ka tozartasu a idon duniya. Saboda haka duk mummunan sirrinka da Allah bai tona ba kada ka zama mai fitar dashi. Zai zama tamkar ka cakawa kanka wuka ne da kanka. Shi mahaifi sutura ne ga zuri'arsa. Abu kadan idan ya faru wanda ya dauke uba daga muhallinsa a wurin 'ya'ya sai kaji ana kiransu 'ya'yan mace. Kuskure guda daya tak zasu aikata sai a kusa shekara ana goranta musu duk don babu uba kuma babu madadin uban. To ina ga kai da kanka ka tona halin naka? Abokanka karshenta suyi maka tayin kayan maye. A halin da kake ciki na san karba zaka yi" Shiru suka yi na 'yan dakiku kafin Mami Khadija ta ambaci alkunyarsa wadda mutane suka bar kiransa da ita. "Khalil?" "Na'am" ya amsa da muryar da ta makale a makoshi saboda damuwa. "Ina fata sunanka zai jagoranci hukuncin da za ka yanke domin ni kam bani da sauran abin cewa gareka. Banda iyayena dominku nake komai. Don Allah kada ku sa bayan kukan miji na dora da na 'ya'ya." Lilu sai ya fashe da kuka. Mami Khadija ta dinga rarrashinsa da kalmomi masu dadi. Ba don gargadin da tayi masa ba tabbas idan yaje wurin abokan nasa sai ya farkewa mahaifinsa laya. A ganinsa hakan ba zai zama komai ga mutumin da bai iya daraja kansa ba. Ya manta bayan shi akwai 'yan uwansa. 'Yan uwan ma mata masu rauni. Gashi babu wadda tayi aure. Wane dan mutumcin ne zai so auren 'yar mutumin da aminiyar 'yarsa take ikirarin yayi mata ciki? Da wannan tunanin ya sauyawa shawararsa akala. Alwala ya dauro ya sanya dogon wando da tsaftatacciyar jallabiya ya dauki littafi mai tsarki ya soma karantawa. (Babu wani abu mai canja kaddarar bawa ko ya sassauta ta kamar addua. Duk takun da bawa zai yi domin kusanta kansa da Mahalicci, Sarkin da bashi da wa'adin zamani zai zo gareshi da fiye da wannan.) *** Shi kuwa Alh. Tahir kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki haka ya bar kofar dakin. Kamar da wasa haka ya shigo tariyo wasu kazaman mu'amala da ya yi da mata daban daban. Tunanin kuwa yayi sanadiyar radadi mai azaba a cikin zuciyarsa. Yana cike da tsoro matuka a wayi gari duka 'ya'yansa suna yi masa kallon fasiki. Wannan rana ya tabbata zata fi kowacce muni a gareshi. Ba zai jure kallon kyama irin wanda Suhaib da Farha suka bishi dashi ba daga dukkansu. Shi bai ma san soyayyarsu tayi masa irin wannan kamun ba sai yau. Har musu ya yi da zuciyarsa akan cewa yanzu son da fargabar kiyayyarsu ya ninku sau adadin da bai sani ba a ransa. Zazzabi ya soma ji tun kafin ya isa nasa bangaren. Tunani ya sha masa kai bai ga isowar Suhaib gabansa ba sai muryarsa wadda ta dawo dashi hayyacinsa yaji. "Ina son zuwa Kano gobe in sha Allahu." Alh. Tahir ya ware idanunsa sosai da son dawo da nutsuwarsa jikinsa. Bashi da lokacin zurfafa tambaya ko binciken me dan nasa zai je yi a Kano daga dawowarsu yau. Ya dai aminta dashi ya san ba shashanci ne zai kai shi ba. 'To ma idan shashancin ne ai a wurinka ya gada' wani sashe na zuciyarsa ya tuna masa. Shi dai Suhaib yanayin sanyin da ya gani a wurin mahaifin nasa ya bashi mamaki. Domin Alh. Tahir mutum ne mai yin komai da kuzari. Sai ya sami kansa da kasa sharewa. "Abba lafiya dai?" Alh. Tahir yayi murmushin jindadi har hakoransa suka fito. Yau shi ne Suhaib yake nuna damuwa akan damuwarsa. "Lafiya kalau. Kaina ke ciwo shi yasa ma na dawo da wuri. Anjima kazo in kara maka guzuri" "Na gode. Kuma Allah Ya kara sauki" cewar Suhaib yana yin gaba. Wurin Mami Khadija ya wuce don baya son sai dare yaje yace zai yi tafiya da safe. Tunda taji sallamarsa bata yarda ya karaso dakin ya sameta a yanayin da take ciki ba. Fuska ta saki har ya shigo ya fada mata zancen tafiyar. Ba karamin dadi taji ba kuwa saboda ko kadan bata so ya fuskanci abin da ya faru. Tafiyar tasa tamkar rage karfin rikicin da take gudu ne. Dagula komai zai yi da fushinsa da zuciya. "Allah Ya kiyaye hanya. Kwana nawa zaka yi?" Suhaib wani irin kallo ya yi mata na rashin gamsuwa. Maminsa mai bin kwakkwafin yara normally cewa zata yi me zai je yi. "Mami lafiya kuwa? Ko baki da lafiya?" Fahimtar inda ya dagota da tayi yasa ta nemo murmushi ta dora akan fuskarta. "Wai don kaga ban tambayeka komai game da tafiyar ba?" Kai ya gyada kawai yana yi mata kallo na son gano inda baraka take idan akwai ta. Murmushi ta sake yi sosai ta ce "jikina ne ya bani kamar surukata daga Kanon zata zo. Ko dai wurinta zaka je ko kuma idan ka tafi yau zaku hadu." Suhaib dai bai san kujerar da Ayaah ta samu a zuciyarsa ba amma kalaman Mami sun saka shi jin kunya. Shi din ba ma'abocin harkar mata bane saboda tsoronsa na zama tamkar babansa. Faffadan murmushin kama kai ya shiga yi gami da susar keya. Mami Khadija ta mike cike da farinciki tana dariyar da ta bayyana hakora. "Hasashena ya zama gaskiya akwaita kenan. Alhamdulillahi. Na santa?" "Nifa Mami ki ma daina wannan batu don ban girma ba." Kallon ka-ma-rainani tayi masa tana cewa "to bari nayi addu'a ga wadda zaka je wurinta din. Allah Ya kawo mata santalelen miji wanda zai aureta nan ba da jim...." Abin da yayi a lokacin har ya koma dakinsa yana mamakin kansa. Katse addu'ar Mami ya yi da saurinsa yana mai bata fuska. "Ba amin ba." Ta dage gira tana leken fuskarsa da yayi kicin kicin da ita. "Koda kaine mijin?" Shi ma sai sannan ya gano tasa katobarar. Gaggawar fita daga dakin nata ya yi cike da jin kunya yana cewa ba abin da take zato bane. Sai da ta tabbatar ya fita ta iya sauke ajiyar zuciya. Farha ce kuma a ranta yanzu. Yarinyar tana da dauriya fiye da zato da tsammani. Da ta matsa mata da tambaya tabbas ta sanar da ita cewa har yanzu bata ji daga Abbati ba. Bai daga wayarta ba sannan kuma bai nemeta ba. Hankalinta taji ya tashi da tsoron kada zuwansa rayuwar Farha ya zama tamkar lasawa yaro zuma a baki. Da ace abin da ya saka shi komawa gida ya girmama bata jin mahaifiyarsa zata boye mata lokacin da suka yi waya. Tunanin ba zai fissheta komai ba shi yasa ta fita zuwa dakin 'yan matan. * (Allah Ya zama gatanka akan duk abin da baka da iko akansa) Sakon sms da Farha ta turawa Abbati kenan taji an murda kofar dakinta. Mami Khadija ce ta shigo da sallama. Farha tayi saurin gyara zama daga kashingiden da tayi. "Ya naga kowa ido biyu ne? Na zata zan sameku duk kun kwanta saboda sammakon da akayi." Dan murmushi Farha tayi tana cewa kwanciyar zata yi yanzu. Mami sai ta sami wuri a bakin ta zauna. "Farha" ta kirata a tausashe. Ba da baki Farhan ta amsa ba, sai dai ta tattaro hankalinta da nutsuwa ta mikawa mahaifiyarta. Mami Khadija ta cigaba da magana "kafin faruwar abin nan, ina nufin tafiyarsu gida babu shiri ranar da suke ganawa dasu Abbanku kun samu sabani ne?" "A'a Mami" cewar Farha tana danne kwallarta. Kewa da damuwa akan rashin sanin halin da Abbati yake ciki sun yi mata yawa. Karfin hali da dauriyar tata sun kai makurarsu. "Ki kwantar da hankalinki ki kuma yawaita addu'a. Ba komai da muke so bane alkhairi a garemu. Miji kuma babu matar da zata auri wanda ba nata ba" da dan sauri Farha ta dago ta dubeta tana son ta ce ita dai Abbatin kadai take so amma ta kasa. Mamin ma dai murmushi tayi "ke dai ki kasance mai mika wuya wurin karbar kaddara. Mijinki da yardar Allah wanda zaku kama hannun juna ne har aljanna. Bana miki fatan haduwa da abokin rayuwa wanda zaki so tatayyarku ta kare a duniya kadai." Farha ta san da wa Mami take shi yasa ta dinga zubar da hawaye. Duniyar gabadaya sauki ne da ita amma mazauna cikinta suyi ta jajibowa kansu matsaloli ta hanyar sabon Allah. A daren ranar Jiddo ta kira Danliti ta fada masa Suhaib ya karbi nambarsa a wurinta. Ta kara da cewa bata san manufarsa ba saboda haka tana mai gargadinsa da ya yi taka tsantsan. Ya kuwa yi mata alkawarin kiyayewa. Sai dai kuma ta riga ta makaro. Tun bayan komawar Suhaib dakinsa ya kira shi. Sauya murya ya yi yadda ba zai saurin gano shi ba ya ce kwatancen garejinsu yake nema. "Kwanaki mun zo tare da wani abokina daga Abuja har ka bashi nambarka. Na shigo gari ne mota take ta bani matsala. Idan zan sami gyaran da wuri ina son kawo maka ita gobe." Kalmar Abuja kadai da Danliti yaji tasa shi bayar da cikakken kwatance harda wata nambar idan bai same shi a wannan ba. A gefe guda kuma maganar Jiddo ta sanya shi yiwa Ayaah mugun tanadi. Indai akwai wata alaka tsakaninta da Suhaib da wannan shirin nasa zai bakanta masa rai. Ita kuma ya zama ladan bata masa lokaci kamar bata san me ya kawo shi ba tun farko. *** Duk wani taimako da Uwani zata iya bawa Qibdiyya tayi a lokacin wanda bashi da wani yawa. Mafi a'ala a kaita asibiti wurin kwakrarren likita domin a dubata yadda ya dace. Shawarar da ta bawa Munzali kenan bayan sun fito daga dakin. Kai ya gyada mata ba tare da ya iya magana ba. Zazzabi yake ji yana bin lungu da sako na jikinsa kamar ana gasawa akan garwashi. Numfashi da iskar da yake fesarwa ta baki ta hanci duk zafine dasu. Daki ya nuna musu a kasa ya ce idan zasu kwana ne ga wuri nan idan sun idar da sallar magariba. In kuma zasu tafi ne shi ma ga kudin mota don ba zai iya tuki ba. Ficewa ya yi daga gidan bayan ya yi tasa sallar a daddafe yana taku kamar a iska saboda rashin nauyin jiki yaje kofar gidan Abbati. Shi kadai kawai yake son fadawa abin da yake faruwa domin ya dauki mataki. Don sai yanzu ya kara yarda cewa Abbatin ya fishi tunani. Duk inda ya laluba sai yaga kamar idan ya taba Lilu sai ya kashe shi. Ya san zafin fyade tunda Shazali ya yi masa a shekarun da suka fi na Qibdiyya ma. Ya san ciwon da rai ke rikewa a yayinda ya san cewa shi ne sanadiyar dulmiyar wani a aikin sabo. Wannan ya tilasta masa yin sanyin da yake ganin yanzu ba muhallinsa bane. Salamar da ya san Abbati zai cusawa ransa ko yaki ko yaso ya tattaro ya sanyawa zuciyarsa. Saboda idan bai nutsu ba yana da yakinin cewa sai ya yi abin da zai yi nadama a gaba. Gara ya nemi uban Qibdiyya ya nemi shawararsa kafin ya zartar da nasa hukuncin. Ya debi kusan mintuna goma yana sallama da kwankwansa kofa kafin Hanne ta bude masa. Yadda ta bude kofar da dankwali a hannu zai sanar da duk wanda ya ganta cewa daga bacci ta tashi. Yatsina fuska tayi da ta ganshi taja guntun tsaki. Murmushi mai ciwo ya yi mata. A ransa yake jin kinsa da take yi tuntuni ba zai rasa nasaba da kasancewarsa sanadiyar bata rayuwar mijinta ba. "Don Allah kin yi waya da Abbati? Na neme shi na kasa samunsa." "Rabona dashi tun ranar asabar da kuka fita tare" ta bashi amsa tana cika tana batsewa. Ganin bai ce mata uffan ba ya juya zai tafi sai ta ce "kayi ka gama munafurcinka na son saka shi ya min kishiya. Ta Allah ba taka ba." Bai ko waiga ba balle ya kalleta. Yana ji ta buga kofa da karfinta kamar za ta balleta. Gida ya koma ya shige daki bayan sallama da su Uwani sun ce ba zasu kwana ba. Asabe ta so ya bata Qibdiyya su koma ya ki. Bayan tafiyarsu ya karbi abinci a wajen Kande ya bawa Qibdiyya. Yarinyar jikinta duk yayi sanyi ta kasa sakin jiki tayi wasa saboda yanayin da taga babanta. A jikinsa kawai ta sami wuri ta kwanta tayi lakwas. Munzali ya dinga kallonta yana kara tsinewa Shazali. Ya kuma kara tsanar Alh. Rabi'u wanda sakacinsa ya zama masomin lalacewar tarbiyar gidansu. Duk abin da ya samesu da shi 'yan uwansa babansu ne sila. Sakarwa iyalansa mata ragamar gidansa da hadasu da nauyi da hakkokin da ba nasu ba shi ne matakin farko na tabarbarewar lamuransu. Tsatson Innayo sun dace da uwa ta gari amma halin uba ya zama jirwaye ga tarbiyar irinsu Uwani. Shi kuwa da 'yan uwansa da basu yi sa'ar uwa ba sai dukan ya zame musu biyu. Waya ya dauka ya sake kiran Abbati duk da bai sa ran cewa za a amsa ba. Jikinsa yana bashi cewa Abbati yana cikin koshin lafiyar jiki. Sai dai bashi da tabbacin ta ruhi. Washegari litinin dama ya yi niyyar binsa idan shirun ya yi yawa. Ya tabbata sirrin boye ya riga ya fito fili. Wannan lokacin ne Abbati yafi bukatarsa. Su Baaba Mari zasu yafewa Abbati idan suka ji cewa shi ne ya fara saka shi a wannan hanyar zasu dauki laifin su dawo masa dashi. * A cikin halin ciwo Baaba Mari take sosai don sun sake komawa asibiti. 'Yan uwa da basu san me yake faruwa ba suna ta al'ajabin wannan abu. Ace mutum kamar Abbati ya kasa kai mahaifiyarsa babban asibiti a halin da take ciki. Tun ana kananun maganganu da safe har aka fara tararsa gaba da gaba ana fada masa zuwa yamma. Kannensa ma sai da suka nuna bacin ransu sosai. Ya rasa inda zai saka ransa yaji dadi. Ciwo yana cinta amma ta ce indai ba halal ya nemo ba ya barta ta mutu ta huta. Wuraren Isha sai ga Mal. Inuwa ya shigo dakin kamar an koro shi. Kullin leda ya dauko daga aljihun 'yar sharar jikinsa ya mikawa Abbati. "Ga wannan dubu talatin da hudu ne mu mayar da ita babban asibiti." Da kyar Baaba Mari ta iya bude idanunta ta dube su. Mal. Inuwa yana ganin fasalin kallon mai kama da na tuhuma ya hau rantse rantse. Yanzu tsoron bacin ranta yake yi da gaske. "Gonarmu da wajen gari na sayar. Da shike ba girma gareta ba shi yasa bata yi kudi sosai ba. Nan an warewa duka 'ya'yan Malam (yan uwansa da suka hada uba) kasonsu. Wannan ne nawa." Ya sake nuna ledar. Da Abbati ya karba sai da yaji kamar bai taba rike rabi rabinsu ba a rayuwarsa. Kudi dai ya baya miliyan biyar baya a asusunsa na bankin da atm din yake jikinsa a yanzu haka. Da za a tara abin da ya tara da kadarorinsa shi ma ba zai ce ga adadin abin da za a samu ba. Sai dai duk wannan arziki tubalin toka ne. Kwakkwarar iska guda ta hure komai saboda haram dama bata da nauyi. Da zarar mutum ya dauki damarar rabuwa da ita indai da zuciya daya ne to tafi komai saukin saukewa. Suna shirin tafiya don har an samu musu mota kwatsam sai ga Mal. Sa'idu a kofar dakin yana sallama. Kallon kallo aka soma tsakanin Abbati da kannensa. Dame kuma yazo? Mal. Inuwa ne ya leka sai dai bai jima ba ya dawo yace Abbati yaje. "Gani" Leda sak irin ta hannun Mal. Inuwa ya mika masa. Da ace hankalin Abbati a kwance yake da yaga yadda tsufan kawun nasa ya sake bayyana. Ya zabge sosai a tashin hankalin kwana daya. Allah Ya ragewa aya zakinta akwai hannunsa dumu dumu a cikin rayuwar duka 'ya'yan gidan. Ba don haka ba da tuni ya lakabawa Baaba Mari laifin bata danta. Kila ma zuwa yanzu duka gidan da garin sun gama ji har an karar da tofin Allah tsinen da za ayi masa. Da yake shi ne uban gayya mai daukar credit din cigaban duka 'ya'yan gidan dole ya karbi lalacewarsu ma. Ta Abbati dai ta fito fili, zuciyarsa kuma tana nan tana raya masa cewa ba shi kadai bane ya fada tarkon shaidan daga zuwa karatu. "Gashi nan ka kara a kudin asibitin" Karba kawai Abbati ya yi ya koma ciki ko daga kai ya kalle shi bai yi ba. Haka suka fita ana ta juyayin wannan lamari na ciwon Baaba Mari da Mal. Sa'idu a cikin gidan. Deluwa tayi nacin har ta saduda aka son jin kwaf. Habi da Abbati ne kadai masu tafiya tare da mahaifansu. Babban asibitin gwamnatin Dutse suka tafi. Cikin dare sosai suka isa garin. An kuma karbi Baaba Mari an fara bata taimakon da ya dace. Zuwa safiya jikinta ya soma daidaita sosai sai hamdala. Bayan azahar ne da Abbati ya tabbatar an sami kanta yadda yake bukata ya iya dauko wayarsa. Ashe ta shiga silent ba tare da saninsa ba. Missed calls ya gani rututu. Na Munzali sun fi na kowa yawa. Sai na wanda suka nada yake kular musu da ginin plaza. Plazar da sai dai idan gwamnati ta gaji da ganinta ta san yadda zata yi da ita tunda komai na samuwarta haram ne. Na Farha basu fi biyar ba. Ya san lallai ita din ba mai takurawa bace. Tunda ya tafi a irin wannan yanayin kuma bai nemeta ba ta tabbata abin ya girmama. Babu na Hanne ko daya. Dama ita bukata ke sanyata nemansa ko zai yi sati bata ganshi ba. Wani irin yanayi na shaukin soyayyar da mai yinta ya san bata tafe da cikar buri ne ya shige shi. Abubuwan da ya yi ta gudu a baya game da rasata sun bayyana. Ko yana hauka baya jin zai iya sake komawa gareta. Arzikin da ya zame masa garkuwar neman aurenta ya kau. Yanzu bashi da maraba da almajirin kan hanya mai jiran sadaka. Messages din ta turo masa har sunfi kiran yawa. A kalla a rana ta turo uku. Nasihohi ne da maganganun kwantar da hankali. Zuciyarsa ta sake karaya. Ba don karfin addu'ar mahaifiya ba da jajircewarsa wurin son ya kyautata tuba da ya koma gareta. Zai kirata ya jaddada mata girman soyayyarta da alkawarin aure. "Allah Ya baki wanda ya fini a wurinsa. Allah Ya cire min kaunarkiba don na daina sonki ba Ya Farha." Adduar da ya yi kenan iya jin kunnuwansa sai dai Baaba Mari tana ganin motsin bakinsa. Adadin kiran da Munzali ya yi masa ne ya dakatar dashi daga rufe wayar. Munzali ya san me ya kawo shi gida. Ya san abubuwa marasa dadi dole zasu faru. Ya kuma san cewa zai neme shi da zarar abubuwa sunyi sauki. Babu lafiya jikinsa ya bashi. Bai yi tunanin komai ba ya kira shi tare da fatan ya amsa da gaggawa. Ringing din farko ma bai gama shiga ba Munzali ya dauki wayar da sauri. Hannunsa yana rawa ya kara wayar a kunnensa. Zazzabi yake mai zafi da matsanancin ciwon kai ya kasa tashi zaune ma balle ya nemi agajin kukunsu a kai shi asibiti ko a bashi magani. Yadda numfashinsa yake fita da sauti da kuma canjin muryarsa kadai suka ganar da Abbati cewa bashi da lafiya. "Munzali me ya sameka? Kana ina?" "Qibdiyya aka yiwa .. " Sallah Baaba Mari zata tayar daga zaune ba shiri ta katse kabbarar haramarta ta kira Abbati a fusace. "Abbati. Bani wayar nan!" Ta kalli Habi wadda ta tsorata "bamu wuri". Da saurinta kuwa ta fice duk da tana son jin me ake boye musu. Tashi Abbati ya yi yaje gabanta ya durkusa sannan ya bata wayar. A wurin ya cigaba da durkuso ita kuma ta kara wayar a kunnenta. Kafin tayi magana Munzali dama yaji kiran da ta yiwa Abbati saboda haka bai yi mamakin jin muryarta ba. "Munzali..." Da fada taso kiransa domin ya san duk abin da zata fada ba wasa bane. Sai dai kuma yana amsawa taji tausayinsa ya tsirga mata. Gaisheta ya yi da faduwar gaba "Baaba ina wuni?" Bata amsa ba. Sai ma kai tsaye fada masa abin da yake gabanta. "Don sonka da Allah da ManzonSa (SAW) babu kai babu Abbati indai da gaske tuban kuka saka a gaba." Tunda Abbati yake bai taba yiwa Baaba Mari musu ba amma yanzu bai san lokacin da ya kira sunanta da karfi ba. Jikinsa ya kama rawa ya sanya hannuwa ya dafa cinyarta. "Baaba don Allah kada kice haka. Nayi miki rantsuwa da sunayen Allah tsarkaka wallahi bama neman juna. Abotarmu ita kadai ce halattaciyar dangantakar dake tsakaninmu. Domin Allah muke yinta ba don..." Fuskarta babu annuri ko miskala zarratin amma ga hawaye suna gudu akan nagartacciyar fuskarta. A lokacin da Abbati yake nasa maganganun tana jinsa da kunne daya shi ma Munzali nasa yake yi mata. Magana yake cikin dakewar murya domin kuwa iya abin da ya rage masa kenan. Mutuwa yake yiwa kansa fata domin yana ganim idan har Allah Ya karbi tubansa to lallai can din zai fiye masa akan rayuwa ba tare da aminin kwarai ba. Ashe alkhairi na karshe da zai gifta a tsakaninsa da Abbati shi ne assasa masa tuban da bai hangowa nan kusa ba. Kamar wanda ake cakawa mashi a kahon zuci haka ya dinga ji a lokacin da yake yi mata magana. "In sha Allahu zaki sameni mai biyayya a gareki Baaba. Babu ni banu Abbati. Zan tashi daga gidan da nake kafin ya dawo Kano." "Shi ma ba zai dawo ba. Ku nesanta da juna sannan ku nesanta da dukiyar haram. Sannan ne zaku yi tuba da kyakkyawar zuciya. Wala Allah zaku samu rabauta a nan duniya da lahira." Kuka ya fashe dashi ba tare da sanin cewa Abbati ma kukan yake mata ba. "Ki yafeni Baaba. Don Allah kada ki kai karata wurin Allah akan Abbati. Ko naki hakkin na rage ina sa ran samun sauki ko yaya yake a wurin Mahaliccina." Rufe ido tayi wasu hawayen suka sauko a guje masu zafi. "Na yafe maka. Allah Ya yi muku albarka." Abbati na jin haka sai ya ce "Baaba don Allah ki tambaye shi me ya sami Qibdiyyan" Munazali yaji tambayar da yayi. Wani daci ne ya taso masa daga makogaro har wuya a sanda ya ce "Fyade aka yi mata Baaba amma don Allah kada ki fada masa. Bata ji ba bata gani ba ta soma girbar shukata tun kafin ta fahimci duniyar kanta." "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Baaba Mari ta fada tana jin kamar ciwonta zai dawo. Masifun zamanin nan sun yi matukar yawa. A gigice Abbati ya ce "mutuwa tayi?" Da ta girgiza masa kai sai ya ce "Baaba ki bani don Allah ko sallama ne muyi dashi." Tausayi ya bata ta mika masa wayar sai dai yana karawa a kunne yaji kit Munzali ya katse kiran. Kiransa ya yi amma taki shiga domin kuwa yana katsewar ya kasheta. Ya kuma lallaba ya kashe sauran ukun ma wadanda duka Abbati yana da lambobin. Da Abbati ya gaji da gwada kiransa ya dubi Baaba Mari tamkar karamin yaro ya ce "kinga ya kashe wayoyinsa." "Saboda yana son ka shiga sahun masu bin maganar iyayensu." Bai iya cewa komai ba sai kifa kai da yayi akan cinyarta yana sheshekar kuka. Ita ma nata hawayen take yi saboda nauyin raba wannan abota. A bangaren Munzali kuwa shi ma kwanciya ya yi yana jin yadda hawaye suke gangarawa cikin kunnuwansa. * Gari ya waye yau ta kama litinin. A garin Kaduna Mardiyya da Sauda sun shirya sun tafi makaranta. A Kano ma Ayaah tana shirin tafiya tasu makarantar. Dukkaninsu suna aji shida ne a makarantar sakandire. Kwanaki kalilan suka rage su fara jarabawar NECO. Ayaah bata sami damar yin JAMB ba sabods rashin kudi amma su sunyi. Kunun tsamiya Ayaah ta damawa Anti Hasiya kafin ta fita. Tana sanye da farin dogon wando da shudiyar rigar da ta kawo mata har gwiwa sun sha karin guga. Fitina irin ta dalibai rigar ta kamata tsam sai ka rasa yadda ma take iya numfashi. A gaban Anti Hasiya ta durkusa da flask din kunu tana tambayarta ko ta zuba mata kafin ta tafi makaranta. Yamutsa fuska Anti Hasiya tayi saboda rashin dadin baki. Jikinta gabadaya babu dadi ta rasa gane a wace duniyar take. Tunda aka sallamota ta kasa tabuka komai a cikin gidan. Daga amai sai kwanciya. Ita ce zazzabi ita ce ciwon kai. Honourable kansa ya zama kamar mai jinyar. Hasiya ita ce zuciyar gidansa. Matar rufin asiri ce wadda baya fatan ya shiga cikin sahun mazaje masu butulcewa a lokacin samu. Shi da yaransa duka rige rigen kyautata mata suke yi. Ga Abbas an sanya ranar aikinsa nan da sati hudu. An hado shi da magunguna kuma ana ganin amfaninsu. Sai da ta gama yi mata fadan dinkin rigarta wanda bata san lokacin da aka tsuke shi ba da kashedin tana dawowa yau ta bayar a budeta sannan ta bata amsa. "Kadan zaki zuba amma ki matsa min lemon tsami a ciki" Ayaah ta fiddo ido waje ba shiri da taji abin da ta ce. "Tsamiyar ta fito fa yadda kike so. Don Allah ki hakura ki sha a haka." "In kin tafi ma Murja zata bani, gara ma ki saka min kawai." Rabin wani dan karami Ayaah ta matse mata sannan ta dauke ledar lemon tsamin ta tura a jaka akan idon Anti Hasiya. Ita kuwa ta marairaice mata saboda tsamin kadai ke taimaka mata ta sanya wani abu a cikinta. Murja da ta zama raguwar karfi da yaji saboda tsabar tausayin halin da antinsu take ciki ta taso za ta duba jakar Ayaah ta dauki lemon tsamin. Ayaah ta galla mata harara tana kankame jakarta. Cikin fushi ta ce no "Tunda ba ke za a haifawa kanin ko kanwar ba ai gara ki bata tasha ta haifo mai yamushasshiyar fata irin na Altine. Kin manta yadda muka dinga tsoron daukar dan saboda kamaninsa da tsofaffi?" Murja ta ja tsaki "sai aka ce miki lemon tsami ne ya busar masa da fata?" "Idan ma dai ba shi kadai bane wallahi kika bata bayan na tafi makaranta ban yaf..." Anti Hasiya bata san lokacin da tayi murmushi ba. "Ya isa Ayaah ba ma zan sha ba kada Allah Ya isan ta bini nima." Duk sai suka yi dariya har Ummi da ke wankin wake. Bayan fitar Ayaah shiru Anti Hasiya tayi tana mai al'ajabin kudurar Ubangiji. Watanni biyu da suka wuce idan ance Ayaah zata sauko daga dokin da ta hau su zauna lafiya zata karyata. Sai gashi cikin lokaci kankani da ta dage da addua da kuma bin shawarwarin Salima komai ya sauya. Ko yanzu sai dai tayi ta hamdala ga Allah. Rayuwa kam tayi juyin alkhairi dasu. Zuwan Minister Abdulkarim ya kawo musu canji a rayuwa. Abbas ana sa masa rai da samun lafiya. Kan 'ya'yanta kuma a hade yanzu sannan uwa uba wannan gagarumar kyauta ta samun ciki. Ayaah na adaidaita sahu wayarta ta dauki ruri. Lokuta da dama tafiyar kafa take yi kusan mintuna talatin a hanya zuwa da dawowa. Yanzu kuwa kudin mota na sati aka bata wannan satin. Mamakin mai kiranta da sanyin safiyar nan me ya kama ta. Cikin aljihun wandonta inda ta boye wayar ta zura hannu ta lalubota. Dama ta tafi da ita ne domin kawarta ta saka mata fim. Sunan Dani ta gani baro baro a jiki. Gabanta ya yi mummunar faduwa da ta tuna haduwarsu ta karshe. Amma abin da yafi tsaya mata a rai kuma ya sanyata tsorata bai wuce fuskar wannan saurayin da taji kannensa sun kira shi da Ya Suhaib ba. Ta shaida irin bacin ransa lokacin da Dani yake neman tabata. Tayi ta kokarin hana kanta tunanin abubuwan da suka faru ranar sai gashi wannan wayar ta dagula mata lissafi. Wani kiran ne ya sake shigowa wancan na tsinkewa. Numfashi ta sauke da karfi sannan ta amsa. Cikin kwantacciyar muryar da ya saba hillatarta da ita ya yi magana. Sai dai wannan karon fushi ya nuna mata. "Baby ni zaki kai gidan kakanninki ki wulakanta?" Daburcewa tayi ta ce "wulakanci kuma Dani? Me nayi maka?" "Au tambayata ma kike yi? Don na bude miki cikina kin san sirrin gidana shi ne kika kira yayanki yazo ya wulakantani. Me ya hanaki tsayuwa kiyi masa bayanin alakarmu banda kina min kallon dan iska?" Gabadaya hankalin Ayaah sai ya tashi ta soma bashi hakuri. Ya dinga ja mata rai har sai da direban adaidaita sahun ya dan waiga ya kalleta saboda jin yadda take magiya. A gadarance Danliti ya ce "Abu daya ne zai sa na hakura Baby. Zan zo makarantarku na daukeki anjima ki zo ki gaishe da Mummy" Da murnar ganin rikicinsu yazo karshe Ayaah ta ce "ta dawo ne?" "Ta dawo kuma na fada mata komai game dake. Tana son ganinki ne domin gobe ta yiwa kawunnai na magana. Wikent (weekend) dinnan sai su zo su ga Baba asa mana rana." Dan jim Ayaah tayi kafin ta ce "yanzu makaranta zanje kuma gaskiya Anti Hasiya ba za ta yarda na bika ko ina ba." "Matar da kika ce bata sonki." Ita ta fada masa da bakinta amma da ya maimaita sai da taji mugun haushi. Yanzu kam uwa ta dauki Anti Hasiya kuma ba za ta yarda wani ya fadi maganar batanci akanta ba. Kwalla taji a idanunta ta daukesu da yatsanta. Danliti tuni ya gane zuciyarta a karye take. Hakuri kawai ya bata ya cigaba da dorata a keken bera. "Ban san me nayi miki wanda ya dauke duk wata daraja da girmana da kike gani ba a baya. Ni dai alfarma nake nema ko daga makarantar ne ki zo muje taga zabina. In Allah Ya yarda nan da sati biyu ko ba ayi biki ba na tabbata an daura mana aure" Sunan makarantar ta bashi tare da fada masa yadda zasu hadu idan an fito break karfe goma da minti arba'in da biyar. Goma daidai Suhaib yana cikin wani gareji a unguwar Na'ibawa wanda ya dace da kwatancen da Danliti ya yi masa. Wani Dan bumburutu ya samu ya kai shi wurin tun daga gadar da zata sada bako da farkon garin Kano daga titin Zaria. Garejin nasu sananne ne saboda kusancinsa da babban titin fita gari. Matafiya da yawa suna tsayawa ko a dauko musu makanike daga nan. Bayan ya sallami yaron da ya kawo shi ya karasa wurin ma'aikatan da suka yi da'ira ana ta mayar da zance da wani Alhaji. Sallama ya yi musu sannan ya ce "Don Allah Danliti nake nema." Kusan mutum hudu a tare suka ce masa ya fita. Wani ne ya kara da cewa, "Kaima wani abu ya hadaka dashi ne?" "Eh" Suhaib ya ce kai tsaye ganin kowa ya zuba masa ido da alamun bacin rai. Taron sai ya karkato ya hada dashi inda a take yaji rigimar da ake yi. Motar da ya gama gyarawa ya dauka ya sanar da abokinsa na garejin wai budurwarsa ce bata da lafiya a makaranta shi ne zai je ya kaita gida. Gaban Suhaib ya yi muguwar faduwar da bai san ainihin dalilinta ba. "Don Allah waye ya san inda zan same shi?" Ya kara da cewa "me yace sunan budurwar?" Abokin masa da aka tsare yana bada amsa kamar shi ne Danlitin ya dan jinjina kai kafin ya ce "baby dai naji yana ta cewa. Amma kafin ya tafi ya kira wani abokinsa da suke yawan zuwa nan tare Rabilu ya ce masa wai yau zai rufe shafin Ayaah. Sai dai gaskiya ni ban san abin da yake nufi ba." Kwatanta irin rudanin da Suhaib ya shiga ba zai misaltu ba. Su kansu mutanen wurin sun tsorata da yanayinsa. Musamman da ya ce, "Ku san yadda zaku yi ku hadani dashi kafin ya cuci yarinyar mutane domin wallahi idan ya taba mutumcinta gabadayanku sai na daureku." Hargaginsa bai basu damar binciken ko shi waye ba. Suturarsa da motar da yazo da ita sun ishesu amsa. Dan garejin nasu da bai taka kara ya karya ba basu ga mai kwarjinin ja da Suhaib din ba. Shi ma kuma mai motar da Danlitin ya dauka yabi bayan Suhaib ya ce kararsa zai yi. Saboda haka nan da nan wurin ya kacame ana tattauna yadda za a same shi tunda yaki daukar waya kafin ya ida nufi. I just published "36" of my story "UWA UWACE...". https://www.wattpad.com/1106315246?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=BatulMamman17&wp_originator=%2FLt7cLBxCRjebLsBmlyCxirOQgEcocfxDAt12Yz5fTsGj3B%2BnR2rWBg4fLQ5qQ7JSNGYb7aSCF5dRDpjzrAlyImKmw8hPKZYgskdQUUwjuHe%2B4YjRcBozvRpvA2rlViA UWA UWACE...36 Batul Mamman💖 Addu'ar samun rahama da kyakkyawan makwanci ga iyayen 'yan uwa da muke tare. Sisters Teema (mahaifi), Hadiza Yauri (mahaifi) da Hashal (mahaifi da 'yan uwa maza uku). Allah Ya jikansu da rahama Yasa sun huta. *** Da sallamar da ya san babu mai amsawa ya murda hannun kofar dakin. Fitila a kunne take da alama cikin sauri aka manta ta. Ga kaya watse a ko'ina. Riguna ne da wanduna harda kwalaban turare na jiki da na kaya. Salihi ya yi ajiyar zuciya ransa duk babu dadi. Da kunnuwansa yaji Mubashir yana waya da abokinsa suna shirya yadda zasu fita party shadayan dare. Bai yi masa magana ba domin yana son tabbatarwa kansa Mubashir din zai je ko kuwa. Fitar da ya yi niyya ya fasa ya zauna a gidan ba tare da sanin dan nasa ba. Goma da rabi kuwa sai gashi ya fita daga gidan da sand'a a zatonsa babu kowa sai Ummule da ta dade da kwanciya. Wata leda mai kyau Salihi ya gani a saman tebur din da Mubashir yake ajiye tarkacen makarantarsa. Ya dauka ya bude yaga sababbin takalma kala biyu da risit din sayayya. Abin da aka kashe na sayayyar ya girgiza shi. Bill ne na dubu casa'in da yan canji a sayayyar kaya. Shi dai bashi da kudin da zai iya bashi ya yi sayayya mai tsada haka. To a ina ya sami kudin? A dakin yayi zaman jiransa har bacci ya kwashe. Goshin asuba ana tsaka da kiran sallah sai gashi ya shigo da sand'a. Rufe kofar yayi da sauri ya murda mukulli sannan ya kwantar da bayansa a jikinta yana ajiyar zuciyar tsira. "Allah Ya soni Baba bai tashi ba" "Ko kuma ni Ya soni da na kwana a dakinka ba." Wani wawan juyi Mubashir ya yi a matukar razane yana kokarin murda mukullin kofar ya fita amma ya kasa. Ilahirin jikinsa babu inda baya ji yana rawa. "Juyo ka dubeni Mubashir." Maimakon ya juyo sai ya cigaba da kokarin fita har Salihin ya tadda shi inda ya juya masa baya. Hannunsa dake rike da mukullin ya kama ya rabasu da yatsun nasa. Sau daya ya murda su duka suka ji sautin budewar kofar. Mubashir dake faman gumi zuwa yanzu ya sake kama hannun kofa wannan karon. Shi fa burinsa ya bar gaban uban ko ta wane hali. Saboda shi da kansa ya san cewa bai taba yin laifi kwatankwacin wannan ba, shi yasa hankalinsa gabadaya ya tashi. Gani yake suna hada ido zai gano duk abubuwan da suka wakana a wurin party din. "Irin wannan patin kuke kira till dawn ko?" Shiru babu amsa daga Mubashir kuma har yanzu hannunsa yana jikin hannun kofar amma ya daina murdawa. "Ban hanaka zuwa ba jiya bayan na gama jin shirinka da wani a waya." Ras, ras, ras...haka gaban Mubashir ya cigaba da faduwa yana sauraron mahaifinsa a tsorace. Salihi ya daure zuciyarsa iyakar dauriya saboda warin hayaki iri iri da yake ji a jikin Mubashir. Da wahala idan bai sha kayan maye ba ko tarkacen hayakin. Sassauta murya ya yi sai ka rantse kuka ne zai kwace masa a kowane lokaci. "Tsakaninka da Allah Mubashir idan ka kwatanta abin da akayi a wurin da kaje da tarbiyar addini da ma maslahar zamantakewar dan Adam kana tunanin Annabin Rahama zai yi maraba da kai?" Fada, mari, zagi, tsinuwa ko duka sune abubuwan da yasa rai dasu. Ko kadan bai yi zaton wadancan kalaman ba. Daga kai ya sami kansa da yi ya kalli babansa. Duk wani zafin kai na matasa sa'anninsa sai ya kufce masa. Rashin kunyar da aka koya masa koda zata baci irin yanzu yaji babu guda da zai iya. Allah SWT Yafi komai da kowa. Sunansa kadai da aka ambata gami da kwallar disappointment a idanun mahaifinsa sun dagula masa lissafi. Ba yadda ya iya dole ya girgiza kai a matsayin amsa ga tambayar da aka yi masa. Ta yaya ma zai yaudari kansa yace inda yaje bai sabawa musulunci ba? Kogin tunanin da ya fada da mabambantan yanayin dake bayyana a fuskarsa kowace dakika sun sanyaya ran Salihi. Alamu ne na cewa tarkonsa ya kama kada. Da shirinsa ya shigo dakin Mubashir domin yana fata yau ta zama rana ta farko kuma ta karshe da irin wannan fadan zai shiga tsakaninsa da dansa. Wayarsa ya kunna har yanzu suna tsaye a bakin kofar ya kunno abin da yake so ya nuna masa. Bidiyo ne wanda ke nuni da jama'a suna jam'in sallah. Bayan kamar sakan goma anyi kabbarar dagowa daga sujjada amma wani matashi a sahun gaba bai tashi ba. Koda aka sallame aka duba ashe rai yayi halinsa. Mutane suka yi ta kabbara da ambaton Innalillahi. Mubashir bai san lokacin da ya soma kuka wiwi ba yana cewa, "Baba kaga fa ya rasu" "Kamar haka ne ajali ke riskar kowane bawa a lokacin da bai yi zato ba. Da ace naka lokacin yayi a jiya karshenta da sai dai yanzu a kirani inda kaje party ace inzo in karbi gawa" tsigar jikin Mubashir ta tashi da tunanin hakan kawai. Salihi kuwa dafa kafadarsa ya yi suna fuskantar juna. "Abin tunani shi ne da ace kaine na cikin bidiyon nan da kila har nima na koma ga Allah ina bada labarin mutuwarka. Kai nayi imani 'yan bakinciki sai sun mutu saboda sun san cewa nayi babban rabo. Ranar lahira mune 'yan hura hanci saboda nayi dacen samun dan da Allah Yake so har ya karbe shi a sujjada. Haka zaka karbi cetonmu ka kaimu aljanna idan ayyukan alkhairinmu sunyi karanci" Sai da ya ja numfashi sannan ya dora da "da kuma ace ka mutu a wurin patin haka zanyi ta boye fuska kada idon sani su ganni. Kuma ina mai imani da cewa zan dawo gida nayi ta gillawa mutane karya. Ba zan taba yarda a san a inda ajali ya riskeka ba. Kaga anyi biyu babu. Ka tafi a banza ka bar ubanka zai tafi a hofi tunda ya zama makaryaci" Jikinsa Mubashir ya fada yana kuka duka jiki na bari. Salihi ya dinga bubbuga masa baya da rarrashi. Sai da ya kula nutsuwa ta zo masa sannan ya yi masa tambayar da ta zo masa a ba zata. "A ina ka sami kudin da kayi waccan soyayyar? " *** Bacci mara dadi Uwani tayi sakamakon abubuwan da suka faru a gidan Munzali jiya. Da suka dawo gida tare da Asabe tayi mamaki sosai da Innayo bata tambayeta daga ina suke ko dalilin fitarsu tare ba. Kalmar 'kema 'yarki ce' da Munzali ya yi amfani da ita lokacin da yake cewa ba zai roketa rufin asirin Qibdiyya ba tayi mata karan tsaye a wuya. Makomar rayuwar yarinyar a gaba ya sanyata cikin damuwa. Shikenan rayuwarta ta baci tun yanzu? Sai kuma nata 'ya'yan da basu wani dameta ba suka fado mata. Anya ta ma san wani abu cikin rayuwarsu sama da dan abin da ba a rasawa? Irin abin da kowa ma zai sani muddin ya zauna dasu. Ita dai a matsayinta na uwa ba za ta dorar da komai ba. Babbar 'yarta Amira ta tuna. Yarinyar da har almajiri take sawa yi mata tsarki lokacin da take karama saboda bata son tashi daga kemis dinta. Sai ta bawa almajirinta mukullin gidanta ya tafi ya gyaro mata jiki su dawo. Kudi ne kawai a gabanta sannan bata son mai aiki mace don kada ta dauke hankalin mijinta. Ta biyun kuma Anisa a lokacin tata kuruciyar wani kanin Salihi da yake karatu ta sakarwa ragamarta. Sai da Salihin ya yi mata tatas lokacin da ya farga. Idan ma da mugun nufi kila har anyi an gama. Yaran basa kaiwa shekara biyar take barinsu su fara wanka. Saboda ita ce Uwani ina kika fito neman kudi, ina zaki neman kudi. Mubashir ne ma ya dan samu kulawa a matsayinsa na dan fari kafin ta gaji ta watsar. Duk wannan tunanin sai ya kare a inda take ganin cewa ai kudi take nema musu. 'Kudin da baki iya kashe musu' zuciyarta ta tuna mata. 'Kudin da suke neman salwanta a banza?' Kamar an tsikareta haka ta tashi firgigit ta janyo wayarta. Nambar Habibu ta dannawa kira ta kara a kunne. Ta shiga har ta katse bai dauka ba. Ta cigaba da gwadawa missed calls sun kai goma zai gani amma duka shiru. Lokaci ta kalla sai taji bari tayi masa uzuri kila bai tashi ba. Nan kuma ta canja akalar kiran ga Salihi. Kiran yaje gareshi lokacin da Mubashir cikin kuka ya fada masa da kudin wa yayi sayayya. Sam bata yi la'akari da cewa yanzu ake sallar asuba ba. Kudadenta kadai take tunani. Yana amsa kiran Uwani ta hau fada kamar ta ari ba. Bakinta yana kumfa saboda tsabar bala'i amma ko jan numfashi ta gaza yi. "Wallahi Salihi ka fadawa matarka ta dawo min da kudadena da sarkoki. Ba yau muke tare da kai ba na san baka taba daukar min komai ba idan baka dashi. Ka fada mata ta dawo dasu idan ba haka ba police station zan kai maganar nan su kwatar min hakkina" Ba speaker Salihi ya saka ba amma yadda Uwani take daga murya babu abin da Mubashir bai ji ba. Jikinsa sai ya sake yin sanyi. Kunyar mahaifinsa ta sake lullube shi. Hannu yasa ya karbi wayar ya kara a kunnensa. "Umma ni na dauki kudin da sarka sai dai abin da ya rage babu yawa." Yana gama magana ya mikawa Salihi wayar ya shige bandaki. To shi ma dai Salihin bai ce komai ba ya katse kiran ya fita yin alwala. Uwani tafi minti biyar a zaune da waya a hannu. Ta san waye Salihi. Ta san abin da zai yi da wanda ba zai yi ba. Sanya Mubashir karbar laifin da ba nasa ba baya cikin abin da zata taba yarda zai yi. Idan ta kure zai iya karbar laifin amma ba dai yace wani ya karba ba. 'Mubashir?' ta dinga maimaita sunan a zuciyarta kamar yau ta fara ji. "Kai! Ina! Sata?" "Idan kin gama surutan ki tashi kiyi alwala ko ki rufe mana baki muyi sallah a nutse" Juyawa tayi taga Innayo akan abin sallah. Bata san lokacin da ta shigo ba. Da azamarta ta tashi amma ta kasa fita yin alwalar. Kanta ya dauki mugun caji ne yana daf da bugawa. Yadda zuciyarta take zafi ko duka aka yi mata da itacen darbejiya ba za ta ji wannan radadin ba. Ayi maka gagarumar sata kuma ka gane dan cikinka ne ya aikata? Kamar sakarya haka ta dan tsaya galala da ta tuna yace abin da ya rage saura kadan. Tuntuni satar bata wani dameta ba saboda tasa ran Ummule ce. Ko ana tsiya tsiya sai ta fito da kudin domin kararta zata yi. A kwato mata kudinta sannan a nunawa Salihi kuskuren tunanin zai iya mata kishiya ya kwana lafiya. Jikinta, zuciyarta, ruhin dake rike da ranta da ma tunaninta a take suka koma na kankanuwar yarinyar dake tsananin bukatar mahaifiyarta. Ji tayi kamar an mata tsirara duk sanyin duniya ita yake duka. Uwa ce kadai zata fahimceta ta suturta ta. Aikin da take takama dashi karshenta sun rabu kenan, kudin da ya rage dan cikinta ya sace. Kudin Hajji kuma wani sashe na zuciyarta mai dan hankali ya dage akan ta nemi Habibu komai rintsi. Zargin da mijinta yake masa ya sanyata wasiwasi. A zatonta a dake ta soma magana, bata san tun a kalmar farko komai nata ya ruguje ba. "Kiji wani abin mamaki Innayo. Sata aka yi min ta kudade masu yawa da 'yan sarkokina wai amma Mubashir yace shi ne. Ni kuwa me nayi masa da zai min sata irin wannan? Na wahala sosai ina hada kudin nan" sai hawaye sharrrr kamar famfo. "Allah Ya kyauta. Matsa zan tayar da sallah." Uwani ta girgiza kai ta dafa kafadun Innayo "baki gane ba Innayo. Ba labari nake baki ba ya faru ne a gaske. Kudin nan dashi nasa ran biyan KNUPDA su sakar min gidana. Bani da komai duk na kashe a gini da biyan Hajji. Wurin aikin ma sun dakatar dani saboda mugunta irin ta masu kudi." Salima da Zara duk sun ji maganganun Uwani. Salima sai ta kasa hakuri ta shiga dakin. Da Innayo suka hada ido saboda ta juyawa Uwani baya tana share tata kwallar. Kwalla ce ba ta tausayin Uwani ba kadai harda ta kara ganin girman Allah. Soyayyar 'ya'yanta bata hanata hango cewa abin da ya sami Uwani harma da matsar bakinta ta tonawa kanta asiri duk yana cikin sakayyar Allah ba. Irin wannan lokacin take ta jiye mata. Halin rayuwa ya juyo wanda zaisa ta dawo gareta ba domin Allah ba. Kai Salima ta girgiza mata don ta daina hawayen sannan ta da daga hannuwanta sama tana dariyar takaici. "Allah Ya jikan Hasiya ba don ta mutu ba. Ta ce Allah Ya hadaki da babun da kike yawan kira watarana. Yau gashi kun gamu har ta fara saka ki kuka. To kadan ma kika gani wallahi" tayi kwafa da karfi "Baki ga komai ba. Uwa? Ke har kina tunanin kin ci bulus kenan akan hawayen Inn.." "Salima ya isa!" Innayo ta fada tana riko hannunta. Hannun ta janye ta cigaba da tsayuwa a gaban Uwani. "Ki barni in sauke mata kafin Hasiya taji banyi komai ba tayi min Allah Ya isa." "Nace ya isa haka. Idan kuma kema shaidanun ne dake shi yasa ku ke neman hanani yin sallar asuba to Bisimillah" Bayan tafiyar Salima har Innayo ta idar da sallah Uwani tana tsaye. Da gaske kanta ya rikice har bata iya gane mai yake faruwa a kusa da ita. Zuciyarta ta kasa rabe mata tsakanin sace kudin da wanda ya sata wanne yafi dimauta hankalinta. Kai a takaice ma duk wani labari mara dadi da ta samu game da dukiyarta sai yanzu ya yi zaman dirshan a kwanyarta kamar wadda ta farka daga magagin bacci. * Da Innayo ta idar da sallah ta zauna tana addu'o'inta amma hankalinta yana kan Uwani. Abin da take gani shimfide akan fuskarta yafi karfin damuwa sai dai a kira shi tashin hankali. Tausayinta ne ya tsirga mata. Sai kuma kamar wadda aka girgiza tayi kokarin kawar da tausayi daga zuciyarta. Uwani ce fa! 'Yar cikinta wadda ta wahaltawa amma ta dinga wulakanta ta. Kalmar wulakanci ita ta dace da duk abubuwan da ta dinga yi mata a baya. Ta tuna mugun ciwon hakorin da idan ya tashi sai ta kusa fitsari a jikinta. Amma Uwani ta rufe ido tace bata da kudi. Kuma taki kaita ganin likita don kada a alakantasu da juna. Duk wata soyayya da uwa zata yiwa da itama tana yiwa Uwani, amma hakan ba zai sa zuciyarta ta kankare mikin da ta bar mata ba. Ba za ta taba yi mata baki ba amma ta san cewa lokaci zai musu alkalanci. Tana so Uwani ta rarrabe tsakanin zare da abawa, me yiwuwa hakan zai sa tayi hankalin da ta jima tana yi mata fata. Da wannan ta mike domin tunaninta ya karkata zuwa ga autarta magamin kukanta. Hasiyatu mai zuciyar zinare. Hasiya takwarar Asiya matar da ta gagari shaidancin Fir'auna. Jarumar matar da ta zama majinginar Annabin Allah Musa AS. Ita Innayo taga ranar sanyawa yaro sunan magabatan kwarai. Ta kasance cikin farinciki domin kuwa da kyawun hali da addu'a gashi matsalolin gidan Hasiyan sun kau. Suna cikin ganiyar samun rufin asiri, ana saka rai da samun lafiyar Abbas, gashi zuciyar Ayaah ta karkato daga hudubar shaidan. Sannan uwa uba ga rabo Allah zai basu na zuri'a. "Salima idan kin sallami 'yan makarantar (yan matan 'ya'yanta) nan ki zo ki tayani yiwa kanwarki dambu." Zara sai tayi saurin tashi ta goya 'yarta "Kawo in yi mata Innayo." "Yi zamanki kada ki kwasar mata sanyi sanyin safiyar nan" Kwance goyon tayi ta kwantar da ita a kusa da Salima. "Gata nan bari inje in taya Innayo aiki" Bata jira cewarsu ba ta fice. Tana isa rumfar da suke amfani da ita a matsayin madafi ta dinga share kwallar dake bin idanuwanta. Ita Zara me zata ce da duniya banda NAGODE. Ta koyar da ita darasi mai wuyar fassara. Mijin da take takama dashi har take wulakanta mahaifiyarta dominsa ya juya mata baya. A zahiri ya nuna mata har yanzu yana sonta. Amma ko kusa yaki sab'awa mahaifiyarsa akanta. Yaki kawo mata 'ya'yanta sannan yaki sanyawa jaririyarta suna. Innayo ce ta tsaya mata har tayi masa magana akan haka. Wayarsu ta karshe da ita bayan ta gama sauraron bayaninsa abu daya ta fadawa Zaran wanda ya sakata zubar da kwalla. "Biyayya yake yiwa mahaifiyarsa wadda komai rashin dadinta gareni da tawa 'yar dole muyi hakuri. Ita Uwa ta wuce tunanin duk mai tunani. Allah ne kadai Ya san fadi tashin da tayi dashi kafin ya kai yanzu. Idan na ce ya sab'a mata dominki ina ganin ban yi musu adalci ba. Ki mikawa Allah lamuranki ki zuba ido ki ga yadda Ubangiji Yake shigarwa bayinSa fadan da yafi karfinsu" Da yammacin ranar Innayo tayi sadakar kosai tayi tawassuli dashi akan nemawa Zara zabin alkhairi. Kukan da tayi a ranar ko digo bashi da nasaba da halin da take ciki da mijinta. Hawayen na nadama ne da dana-sani. Sai kuma tsantsar godiya ga Allah da Ya ara musu rayuwa ita da Innayo din. Dole ne tayi amfani da wannan damar ta daidaita da mahaifiyarta. Bata ji isowar Innayo ba sai muryarta da taji tana cewa "kin tuna lokacin da ake cewa kin fi kowa iya girki a gidan nan? To kiyi mata farfesu da naman kazar can na firij, ni kuma zanyi dambun. Duk na wanda tafi ci to mai shi tafi iya girki sai a daina cika mana baki." Zara ta juyo da murmushi mai hade da hawaye. Innayo din ma da guntuwar kwallarta domin kuwa ta dan jima tana kallonta. Abin da ba kasafai mutanen da suke yi ba Zara tayi a lokacin. Rungume Innayo tayi tana cigaba da kukanta. A haka take magana da dusashshiyar muryar da ta cakude da kuka. "Don Allah Innayo ki ce kin yafe min. Ba wai don na koma gidansu Maryam ba. Sai don kawai wannan kullutun hakkin naki da na daukarwa kaina ya sauka daga kirjina" Ta dago kai tana mai nuni da kirjinta. "Na sani sarai cewa ban kyauta ba amma kaina na yiwa ba ke ba. Don Allah ki yafe min." Innayo ta dan tura baki duk ta rikice da kunya "to cikani don Allah kada a ganmu" "Sai kin ce kin yafe" "Zara zan ci kaniyarki fa. Cikani nace" Zara ta cikata tana dariya kasa kasa. "Baki ce komai ba." Innayo ta numfasa tana kallonta tana girgiza kai tare da murmushi. "Indai nice ki sani cewa hatta waccan yayar taku mai rangwamen tunani na dade da yafe mata. Babban burina dama bai wuce ku fahimci kuskurenku ba. Wallahi Zara ba kudinku nake so ba. Ku din da na haifa a halin maraici ba uwa ba uba ku nake so." Kwalla ta sake taruwa a idon Zara. Innayo kuwa sai tayi gaba ta fara tattaro abubuwan da take bukata na girki. Yau dai gidan Hasiyan zata je da kanta ba aike ba. Da suka gama Maimuna ce ta daukar mata kwandon da aka zuzzuba abincin. Kiranta tayi a waya tace ta nemi izinin mijinta yau sai gidan Hasiya. Zara da Saliman sun so zuwa ta hana. A cewarta bata son yawo kawai don suna gida. Wuraren shabiyu suka fita. *** Awa guda da fitar Ayaah, Hasiya ta kula da 'yar pos dinta a inda ta durkusa ta zuba mata kunu. Dauka tayi ta bude taga 'yan kudaden da basu kai dari uku ba a ciki. Ta san ba za su wuce kudin motarta bane ta manta a gida. Idan kuwa haka ne in ba a kai mata ba karshenta ta dawo a kafa ko ta kare da rance. Wannan ma bai dameta ba sai da taga takardar da Ayaah ta nannade kudin WAEC dinta a ciki dubu sha biyar. Daren jiya Honorable ya bata saboda yau din ne rana ta karshe da zasu biya. Duk da tana jin jiri haka ta daddafa bango ta tashi tana kiran Murja da Ummita. "Don Allah wata cikinku ta zo tabi Ayaah makaranta da pos dinta da ta manta." Murja ta ce yanzu suka yi waya da wata mata zata zo kitso. Ummita na jin haka ta san ita ce mai zuwa. Hanzarin shiga wanka tayi ta fito ta shirya da sauri. Bata son lokacin break ya yi taje ta wahala wurin neman Ayaah cikin dalibai. Idan ta isa da wuri ajinsu kadai zata nema. Ta gama shiri ta fito Honourable ya bata kudin adaidaita suka ji sallama. Direban Minister ne wato Abdulkarim. A soro suka hadu da Honourable Habu ya mika masa wani envelop. "Oga ya ce jiya likitan Abbas ya turo masa. Gwaje gwaje ne da ake son ku sake kai shi ayi yau dinnan. Idan sakamakon ya fito zasu gane aikin da za ayi dole sai an bude kan ko kuwa irin wanda ake soka na'ura ne tayi. Ya ce kuje kai tsaye ya biya kudin." Honourable Habu ya ma rasa irin na'u'im godiyar da zai yi. Shi kuwa direba fadi yake ai bai ga komai ba cikin dimbin alkhairin wannan bawan Allah. Direban na fita Ummita ta fito. Riga da siket ne a jikinta na atampa. Ta yane kanta da mayafin pashmina wanda ya sha jiki ba laifi. Sai dai a wanke yake ya kuma sha guga. Ta hango mota a farkon layinsu ikayar inda mota ke tsayuwa amma bata yi mata kallo biyu ba ma. Kanta a kasa tana tafe hankalinta yana kan cimma titi da wuri ta sami abin hawa. Bayanta gefenta taji ana horn sai ta kara rabewa kusa da kwatar dake gefe, a zatonta ko ta tsaya akan hanyar motar ne. Sake horn aka yi ta kuma matsawa. Da aka yi na uku sai ta juya baya cike da tsiwa. Direban na bude kofa ta ce, "Malam ko kwatar kake so na fada ne sannan ka sami hanyar wucewa?" Ganin dan dattijon da ta gaisar dazu tare da mahaifinta sai kunya ta kama ta. Kasa tayi ta rissina mayafinta ya rufe mata gefen fuska ta sake gaishe shi tare da bashi hakuri. Murmushi ya yi don ko da ya dameta da horn din sai da Maigidansa ya ce kada ya firgita 'yar mutane. "Shigo a rage miki hanya" Girgiza kai tayi da sauri "Baba zai yi fada. Na gode" Abdulkarim yaji abin da tace sai yaji ta burge shi. Idan bai yi kuskure ba ita ce Ummi babbar diyar Honourable. Bude bayan ya yi ya fito da kafarsa daya ya tsaya. "Zo muje a fara sauke ki ina sauri ne." Yawu ta hadiya da kyar da taga mai maganar. Sake yin kasa tayi zata gaishe shi ya ce, "Shigo motar sai mu gaisa" Ummita ta daburce "Allah Baba da Anti Hasiya sun hana" Abdulkarim sai ya dauki waya ya kira Honourable Habu. Yana tsaye bai mayar da jikinsa ciki ba har wayar ta shiga. Gaisawa suka yi sannan ya kada baki ya ce, "Tare muke da Mal. Amadu amma sai nace kada ya fada muka ina mota saboda bana son ka fito da safe haka. To yanzu mun hadu da Ummi nace ta shigo mu kaita inda zata je amma taki. A takaice dai neman izini na kira" Honourable ya dan ji nauyi domin harga Allah baya son take dokarsa. Sai dai kuma yana kyautata zato ga Ministan. Ba wai kuma don sakar masa bakin aljihu da yayi yanzu ba. Tuntuni bai taba saninsa da mugun hali ba. Duk da dadewarsu basu hadu ba, baya jin zai kira shi domin neman izinin cutar masa da 'ya. Dariya ya yi ya ce "Tana karkashin ikonka babu ruwana." Kallonta Abdulkarim ya yi tana kallon kasa ya ce "to sai ki bar kirgen kasar kizo mu tafi ya bayar da izini" Ummita ta dan tsuke baki tana mamakin salon yadda ya yi mata magana kamar yaji haushin kin shigarta. Daya barin ta zagaya zata shiga amma ga mamakinta sai taga kofar baya a bude. Direban ta kalla galala tana ware idanuwanta ta dan rage murya ta nuna kofar a tsorace. "Wai nima bayan zan shiga?" "Baki yarda da azkar dinki na safe ba kenan, ko baki yi bane kike wannan tsoro?" Mamakin wannan Minista yana neman zauta ta. Shi da yake abokin babanta ya akayi yake yi mata magana kamar ta yiwa tsaranta laifi? Kuma ma da wane kunnen yaji abin da ta fada a hankali. Dan murguden bakin da tayi duk akan idon Abdulkarim din. Dariyarsa ya gimtse don kuwa da gayya yake yi mata magana a haka. Baya son ta shigo a darare kamar tana tare da uba. Bashi da masaniyar ko anyi mata miji amma haka nan yake jin wani kwarin gwiwar tunkararta. Idan da mijin a hannu sai ya hakura. Bai san lokacin da dariya dai ta subuce masa bane a yayin da ya hangota ta kai hannu baki tayi tofi. Ba kunya tabi jikinta ta shafe ta kuma tofawa motar sannan ta shiga da kafar dama gami da Bisimilla da dan karfi. Har ta shiga yana dariya. Mal. Amadu ma sai da ya dara. Ta zauna a dofane tana kallonsu. Dariyar masu kudi ma daban take, babu sauti mai karfi ko hargagi ta ayyana a ranta. Tambayar da ya yi mata ce ta maidota hankalinta "Wai me da me kika karanta kika tofa mana ne?" "Su Au'zu bi kalimatillahi...." Sai tayi azamar dora hannunta akan labbanta "ba daku nake ba. Tunawa nayi ban yi ba kafin na fito" Hannu ya mika mata yana murmushi "to sai ki bani abin sadaka ladan yi miki tuni ko. Don da farko na zata mu kike tofewa don kada mu gudu dake." Mayafi ta janyo abin da ya lura ko dabi'arta ne ta rufe rabin fuska tana dan murmushi. "Wai ya sunanki ne?" Ya tambayeta saboda yana son sake jin muryarta. "Ummita" "Ummi-ta? Tawa kenan ko ta mutane da yawa?" Hanjin cikinta taji ya yi wani juyin waina a tanda ta manta da kunya ta kalle shi cikin ido. Ba shiri ta sauke nata ta dukar da kai kamar mai shirin kwanciya akan cinyarta. Basu sake magana ba sai kwatancen da take yi har suka isa makarantar. Ga mamakinta dana Mal. Amadu sai suka ji Abdulkarim yace a jirata. Ta kusa minti ashirin a cikin makarantar kafin ta fito a guje tayi bakin titi. Shaf ta manta da wanda ya kawota kuma yake jiranta. Hannu bibbiyu tasa tana tsayar da adaidaita sahu. Abdulkarim na ganin yanayinta harda hawaye kwance a fuskarta ya fito da sauri. "Ummita" Ganinsa yasa kukan nata ya karu. Ta dawo da baya suka hadu domin shi din ma nufota ya yi. Kafin ma ya tambayeta ta fada masa abin da ke faruwa. "Ba a ga Ayaah ba. Wai ta kusa awa biyu da fita fitsari har yanzu bata dawo ba. Kuma ga jakarta a ajin. Anje duka bandakunan da lab da ko ina bata nan" shirun sakan biyar tayi wani tunani yazo mata "ko dai aljanun bandakin sun dauketa?" "Bama mutane ba aljanu Ummita?" Abdulkarim ya tambayeta yana kada kai don kada ta saka shi dariya a halin da ake ciki "Muje bandakin mu duba. Allah Yasa dai kin iya rukiyya sai na tsaya daga bayanki ko?" Duk da tashin hankalin da suke ciki bai hanata fassara shi a ranta ba. 'Mutumin nan ba dai bakar magana ba'. Ita da kanta kuma ta hango wautarta ta ce, "Ko masu satar mutane" ta dan tafa hannu irin na ta canka daidai "ai fa an ga kana zuwa gidanmu shi kenan za a fara kawo mana hari." Abdulkarim bai ma san lokacin da ya ya balla mata harara ba. "Ji mun yarinya. Ni kuma zaki dorawa laifin?" "To ai ..." Kai ya girgiza kawai ya ce ta zo su koma cikin makarantar. Suna tafe zuwa ofishin Principal ta daga waya zata kira gida ya hanata. Idan sun san aihinin me yake faruwa sai su fada. A haka hankula ne zasu tashi babu sanin madafa. A ofishin Principal din banda ita akwai malamai biyar ana ta mayar da zance. Kowa ya shiga rudani har wasu suna cewa a tashi yaran kowa ya tafi kada a hada dasu. Yana shiga mutum uku suka gane ko waye. Da radar da bata buya ba suka sanar da ragowar. Nan da nan kuwa aka dinga raba idanu tsakaninsa da Ummita wadda ke biye dashi sau da kafa. Kallon ne ya tunzura shi kafin ma ya tambayi ya ake ciki ya fara da bayanin da ya baiwa Ummita dasu kansu mamaki. "Wannan 'yar tsohon Ubangidana ce. Mun dade da rabuwa sai kwanakin nan Allah Ya sake hadamu. Yanzu ma daga gidansa nake kuma da izininsa muka taho nan." Principal sai ta hau borin kunya "ranka ya dade me ya kawo wannan bayanin?" Ya dage kafadu sannan ya ce "zuciya abar banza ce wani zubin. Yanzun nan sai ta shiga yiwa mutum sake sake ta sanya shi zargi a gurbin da bai dace ba." Kowa kuma sai ya shiga gyara tsayuwa ana gyaran murya. Bai kulasu ba ya tambayi ba'asin sanda aka farga da batan Ayaah. Bayanin da aka yiwa Ummita aka sake yi masa. Ya gyara zama tamkar a ofishinsa ya nuna wani Malami. "Kirawo min Maigadinku" "Su uku ne" "Duka su biyoka sai ku saka wasu malamai a wurin saboda kada yaran su fice" Masu gadi duk sun tsumu kowa ya rantse bai ga fitar wani bako ba ko na dalibar da ake magana a kai. Guda cikinsu yafi kowa dagewa aka rantsuwarsa. Gashi a shekaru alamu sun nuna ya girmi wadancan sosai. Yadda ya gabatar da kansa ya sanya Abdulkarim dora masa ayar tambaya. Dalilinsa kenan ma na daga waya yace zai kira Kwamishinan 'yan sanda domin a zo ayi bincike. Hakuri aka soma bashi ya rufe ido yana fada akan sakacinsu da amanar 'ya'yan mutane. "Idan sun zo zasu tafi da masu gadin a kullesu na a kalla sati koda an ganta kuwa. Wannan ai sakaci ne da rashin sanin aiki." Dan dattijon maigadin yana jin haka ya soma muzurai. Rashin fara'a da ya gani ko digo a fuskar bakon nasu ta tsorata shi. Haka kawai da iyalinsa azo a kulle shi yana zaman zaman sa. Hularsa ya cire ya dan firfita fuskarsa wadda ta soma tsatatsafo da gumi sannan ya rankwafo a gaban Minista. "Yallabai ai ba ayi haka ba. Yarinya dai babu wanda ya saceta. Duba min nan..." Ya zaro wata kodaddiyar naira dari biyu "ka gani wani matsiyacin Alhaji ne yazo da katuwar mota ya dauketa. Wannan abar ya iya bani don na barta ta tafi da alkawarin zata dawo kafin a tashi." Dan ofishin Principal a take ya karade da sallallamin malamai mata da fadan malamai maza. Dattijo kamar a cinye shi danye. Principal ta ce barin aikinsa yazo domin bata san tun yaushe ake haka ba. "Wallahi Hajiya yanzu ma tsautsayi ne. Wata yayi nisa nayi haka ne da tunanin zan dan samu na cefane. Ni yarinyar ko wayewa da fuskarta ma banyi ba sosai." Ummita dai sai kuka kawai take yayinda Abdulkarim ya ce ba zai tafi ba har sai 'yan sanda sun zo. *** Goshi Suhaib ya dinga murzawa ya rasa wane irin tunane ya kamata yayi. Ta ina zai fara nemanta? Baya son Munzali duk da ya san 'yar yayarsa ce amma yana gudun halin da zasu shiga kafin a ganta. "Idan ta bishi kanta ta yiwa" ya furta a zafafe. Sai dai kuma can kasan zuciyarsa ya san cewa ba zai taba iya kawar da kai ba. Haka kawai yana zamansa yarinyar tayi masa karan tsaye a rayuwa. Banda mahaifiyarsa da kanne babu wata mace da ya taba damuwa da shirginta sai wannan yarinyar mai idanu a tsaye. Mota ya shiga ya zauna ya bar abokan aikin Danliti da mayar da zance. Kusan minti goma ya yi kansa na kan sitiyari yana tunanin mafita kafin dabara tazo masa. Waya ya dauka ya kira nambar Ayaah yana ta addu'ar ta dauka. *** Kokarin danne tsoro Ayaah take yi amma ya bayyana karara. Ta fara nadamar biyo shi tun kafin su bar layin makarantarsu amma ta rasa bakin cewa ya tsaya ta sauka. Banda ragon azanci ta yaya ma zata je gaishe da suruka da kayan makaranta? Idan matar mai hankali ce tana ganinta karshenta tayi mata fada. "Wai ina zamu je ne naga muna yin bayan gari." "Walalamb'e" Danliti ya bata amsa kai tsaye. "Walame?" Ayaah ta tambaye shi da sauri don tana jin kamar bata ji me yace bane da kyau. Danliti ya sake maimaitawa wannan karon harda dariyarsa. "Kada ki damu Baby. Yanzu zaki gani da idanunki." Tun daga Hotoro ta daina gane ina suke tafiya. Ta dai ga wani roundabout daga nan suka yi hagu gefen wani gidan mai. Jikinta ya yi sanyi kalau kamar mara lafiya. Gashi yau gabadaya tsoronsa ma take ji. Suna zuwa kofar gidan zata gudu kawai. Don kada ya gane ta kakalo murmushin dole. Ana haka 'yar wayarta ta soma vibrating. Bata san nambar ba amma da sauri ta dauka. Don ta san yanzu da wuya idan ba a fara nemanta ba. Danliti bai damu da wayar da zata amsa ba saboda ya gama yanke hukuncin cewa ko me zai faru yau sai ya kusanceta. Ikon a hannunsa yake kamar yadda ya fadawa kansa. Da sallama ta dauki wayar, muryarta tana dan rawa. Suhaib yana jin yanayinta wani abu ya taso masa a kokon rai. "Ayaah kina tare da Danliti? Zaki iya magana sosai?" "Eh amma ba zan iya ba" ta amsa masa tana kokarin kin kallon inda Danliti yake. "Kin gane ni ko?" "Eh" "Good, ki saurareni da kyau kuma kada kiyi abin da zai gano ki. Mutumin da ya daukeki wallahi makanike ne yanzu ma ina garejinsu. Mutumin banza ne. Ya fadawa abokin aikinsa zai zo daukarki ya kaiki inda zai..." Sai ya kasa karasawa. Ayaah ta sake tsorata sosai jikinta ya soma rawa. Yawu ta hadiya da kyar a hankali ta ce "ba na fada miki mumminsa zai kaini na gaisar ba? Yanzu muna hanyar gidansu ne. Kar ki bari a gane bana aji kinji" Ba karamin burgeshi yaji tayi ba. Ga tsoron yana iya rarrabewa cikin zancenta amma a haka ta fada masa abin da ya dace ya sani. "Na fahimta. Ki kokarta ki turo min address din inda kuke ta sms saboda kada ya gane." "In sha Allahu. Ni dai ki dauko min jakata ki jirani a bakin gate ko an tashi." Danliti ya dan kalleta ya murmusa yana kiran "Baby na kenan! Ki gama wayar nan ki fada min kalaman da zasu sanyaya min rai" "Kiji min dan iska..." Saboda yanayin da take ciki murmushi kadai ta iya yi amma duk da haka Suhaib yaji sautinsa. Shi kuwa gogan ya zata dashi take. "Dariya ma na baki?" Suhaib ya ce yana shan kunu "A'a. Don Allah ni dai kiyi sauri. Zan turo miki nambar registration din tawa ki cike min form din." Kafin ya ajiye wayar ya sami kansa da cewa "Ki kula da mutumcinki Ayaah. Kada ki yarda ya taba min jikinki." Shi da ya fada ya yi mamakin karfin halinsa sai dai kuma yanzu ba lokacin hakan bane. Haduwar kwana daya ce amma zuciyarsa taki bashi hadin kan yakiceta daga tunaninsa. Ita ma a nata bangaren wani irin nauyi kalamansa suka yi mata. Haka nan ta cije ta sake yanko karya ta fadawa Danliti bayan ta kashe wayar. "Wai nambarmu ta NECO ake bukata daga ofishin Principal. Shi ne kawata ta kira don kada a neme ni." Mutumin da ko sakandiren bai gama ba sam bai fahimci karyar ba. Hankalinsa bai bashi yasa ido akan abin da take rubutawa ba. Iya abin da ta gane a hanyar da suka bi da sunan unguwar da ya fada wanda bata ma rike daidai ba ta rubuta. Suhaib ya koma wurin sauran makaniken ya karanta musu text dinta. "Da mamaki dai amma wannan kwatancen ya dace da hanyar gidansa. A can unguwar Walalamb'e yake da zama" "Muje ka nuna min" Mutum uku ne suka shiga motar. Harda shugabansu cikon na hudu. Rayukansu duka sun baci akan abin da yake yi. Ga daukar abin hawan masu kawo gyara sannan kuma ya dauki mace yana shirin bata mata rayuwa. * Bangaren inda suka nufa wawakeken filin unguwa ne da gidaje tsilli-tsilli basu matse juna ba. Gidajen wurin kaf babu bene ma a iya ganinta. Duk sunfi kama da gidajen gargajiya. A takaice dai unguwa ce ta masu karamin karfi sosai. Cikin Ayaah ya sake kullewa da mugun tsoro a lokacin da faka motar a kofar wani dan tsakon gida. "Ina ne nan?" Ta dan dake ta tambaye shi. "Gidan mai ban ruwan fulawa a gidan Mummy. Kiyi hakuri zan shiga in duba shi ne yanzu na fito" Tunda dai bai kirata ba sai taji dama dama a ranta. Fita ya yi ya rufeta a cikin motar ya shige gidansa da sauri. Mukullin dakin Rabilu abokinsa da ya bashi aro tun jiya ya manta a aljihu yazo dauka. Sun yi da Rabilun can dakinsa dake kusa da unguwarsu Ayaah zai kaita. Kuma idan shi Danliti ya gama biyan bukatarsa da ita shi ma mai dakin zai yi. Kafin ya fito ta sake turawa Suhaib wani sakon. (Ya kulleni a mota wai wani wurin zamu je ba inda na turo maka ba. Don Allah kayi sauri wallahi tsoro nake ji.) (Ki kula da duk inda kuke bi ki sake turo min. Please take care of yourself.) Amsar ta karanta ta gyada kai kamar yana kallonta. A ciki kuma matar Danliti da murna ta tashi tana yi masa maraba ya doka wani uban tsaki da ya saka ta ja da baya. Naira dari biyu irin wadda ya bawa maigadin makarantarsu Ayaah ya jefa mata a wulakance. "Gashi nan na san abin da kike yiwa kenan. Ke dai a baki kudi ku ci abinci da 'ya'yanki." Hawaye taji ya taho mata tayi saurin tarewa da hannunta. Kudin ta duka ta dauka ta ce, "An gode. Allah amfana" Tsaki ya sake yi mata ya shige daki yana neman wandon da ya cire jiya. Ita kuma mayafinta ta zara a kan igiya. Ta goya karamar ta rike hannun mai wayon ta fice tana ce masa zata karbo kayan miya. "Na ajiye mota a waje ta mutane. Kada ki kuskura kije kusa da ita. Ke dawo idan na tafi sai ki fita." Sarai ta ji abin da yace amma tayi biris ta fita soro ta leka. Abin da tayi tsammani ta samu. Yarinya ce mai fuskar kamala a cikin motar. Takaicin halinsa ya turnuketa. Babu wani bakon abu a halayyarsa da bata sani ba. Bakon abin da shi bai sani ba tare da ita shi ne a yau ta gama hadiyar bakincikinsa in Allah Ya so. Komawa tayi cikin gidan suka yi kicibis a bakin kofa. Rai a bala'in bace ya dinga yi mata masifa. "Me yasa kika fita? Da kika fitan me yasa kika dawo?" Hakuri tayi ta bashi tana cewa taji kamar ya kirata ne. Sai da ya gama fadan ya koma dakin yana cilli da kaya. "Me kake nema ne in tayaka?" "Mukullin dakin Rabilu nake nema wanda na bari a cikin wando" Kai ta jinjina tana tunanin wato can zai je da yarinyar. Dauko mukullin da ta gani da tana ninke wandon tayi ta mika masa. Haka ya warce shi a hannunta ya fita da gargadin ta jira sai ya tafi. * Sakon da Ayaah ta turawa Suhaib ya riske shi ne suna kurkusa da unguwarsu Danliti. Tun fitowarsu har yanzu bai fasa ambaton Allah cikin addu'a da fatan nasara ba. Da ya gama tura mata amsa ya sanar da abokan tafiyar tasa abin da ta ce. Guda a cikinsu sai ya ce su karasa gidan nasa. Kila suyi sa'ar samunsa ko su tambayi matarsa ina yake. "Muna ma iya cewa ta kira shi ta ce anzo nemansa akan motar da ya dauka da 'yan sanda. Na san da wuya idan bai tsorata ba" Shawararsa ta sami karbuwa suka karasa. Da yake Allah Maji roko ne sai gashi sun sami fiye da abin da suka saka rai. Wanda ya bada shawarar ne ya yi sallama a kofar gidan. Ta fito da yaranta da 'yar ghana must-go wadda ta zubawa kaya. Ta ganinsa ta dan saki fuska suka gaisa. Ba tare da bata lokaci ba ya ce, "Idan kin san inda Danliti yake ki fada min don Allah. Daga gyaran mota ya dauko motar wani mutum. Yanzu haka yace 'yan sanda zai kawo mana." Sauke jakarta tayi daga dakalin kofar gidan tana cewa "ba zan fada ba don laifin nasa ya kara yawa a dukkan dakikar da 'yan sandan suka wahala nemansa. Sannan idan kun hadu ka fada masa ya aiko min da takardata." A rikice ya ce "kiyi hakuri ki taimaka mana" Su Suhaib suka firfito ta dubesu ta kau da kai. Suhaib din ne ya tako gabanta ya dubeta a mutumce ya ce "don Allah ki taimakeni kada ya keta haddin 'yar mutane. Har makaranta ya bita ya daukota yana shirin bata mata rayuwa." Da sauri ta dago kai tana mai tono yarinyar da ta gani. "Bari na shiga adaidaita sahu ku biyoni in kaiku inda nake tunanin zai kaita" Suhaib ya ce na gaban ya koma baya ita da yaranta su zauna. Su da suke makanikai basu fitar da warin jiki irin nata da na yaran ba. A haka kuma ba karamin kokari take ba. Duk albashin Danliti a cin banza da hofi sai yan mata yake karewa. Sabulun wanka da wanki sai tayi kamar ta ari baki. Ruwa ma iya na girki kadai yake saya mata. A haka take cancanawa suyi wanka bayan kwana bibbiyu ko uku. Ga zafin gari da ake fama. Kai kawai Suhaib ya dinga kadawa cikin takaicin wai wannan matar aurece. Mace da ake son a mutunta amma ita ce nata mijin har yake da guts din zuwa kofar gidansa da yarinyar da zai nema ta gani. Kodayake ba kansa farau ba da ya tuna nasa uban. Neman tsari ya dinga yi akan fadawa wannan kaba'ira ta zina har suka kai kofar dakin Rabilu. Ya kuwa laluba aljihunsa ya bawa yaran dubu goma ya ce ga kudin mota. Bata cuci kanta ba ta karba tana ta godiya. *** Da kuka Ummita ta shiga gida duk da irin gargadin da Abdulkarim ya yi mata akan tayarwa iyayenta hankali. Kasa daurewa tayi tana shiga ta fada kan Innayo tana kuka. Hasiya ta saki cokalin dambun da take ci ta tashi da sauri tana tambayarta me ya faru. Maimuna da Innayo basu dade da shigowa gidan ba. Kuma hirar dadewar Ummita da rashin samunta a waya ake yi sai gata ta fado. "Ki yi min magana Ummita me ya same ki?" Hasiya ta sake tambayarta tana hawaye tun kafin taji me ya faru. "Anti an sace Ayaah. Har makaranta wani yazo ya bawa maigadinsu kudi ya tafi da ita" Hankalinsu ashe bai tashi da kukan Ummita ba sai yanzu da tayi magana. Kan kace meye wannan gidan ya rude da kukan mata. Murja, Hasiya, Ummita da Maimuna babu mai rarrashin wani. Innayo ce tayi ta maza ta daure tana basu hakuri. Suna kukan suka ji sallamar Honourable da yaron da ya taya shi rike Abbas suka je aka yi test. Kukansu ya saka shi shigowa tun kafin su amsa. A nan yaji labari mara dadi. Gidan ya sake cika da Larai (mahaifiyar A'i) dasu Hasina kannenta. Sun zo duba Abbas ne saboda Honourable ya fada musu za ayi masa aiki. Wannan ya sake dagula lamarin domin fada ne kuma yaso kacamewa. Larai tana kuka ta ce "Hasiya naji labarin kina da ciki ai. Wato kafin ki haifa zaki fara daidaita 'ya'yan marigayiya saboda kina tunanin samun gado tunda maigidan ya soma farfadowa." Hasiya bata iya cewa komai ba da yayyenta suka hada baki ana ta fada mata maganganu. Innayo ta hana Maimuna da ma Murja da Ummita din mayar da martani. Batan Ayaah ne a gabansu ba zantuka marasa amfani a gaban suruki ba. Maigidan kansa kasa tsawatarwa ya yi saboda yawunsu da kuma damuwar da yake ciki. Tunda ya ce suyi shiru suka ki sai kawai ya fita zai tafi makarantar. 'Yar nutsuwar da ya samu ma ta biyo bayan kiransa da Abdulkarim ya yi suka shigo gidan tare. Shi ya fada masa case na hannun 'yan sanda ana bincike. Ko sau daya babu wanda ya yi tunanin kiran wayarta saboda gargadi da jan kunnen da Hasiya take mata akan zuwa da ita makaranta. Duk sun zata wayar tana gida saboda haka babu amfanin kiran. *** "Shigo mana Baby" Danliti ya ce da Ayaah bayan ya zura mukulli ya bude dakin shagon Rabilu. Rainin wayon nasa ne ya bata mamaki ta ce "ban gane in shiga ba? Ya zaka ce min zan je gaishe da mahaifiyarka ka kawoni nan?" Hagu da dama ya dan waiga bai ga idon kowa a kansu ba kawai ya fizgota cikin dakin ya rufe kofa. Budar bakinta zata yi ihu ta rufe sakamakon tozali da hoton tsohon saurayinta Rabeel (Rabilun Danliti). Cikin kidima ta ce "Dani dama ka san Rabeel?" Danliti ya kwashe da wata irin dariya harda tafa hannuwa kamar biri a hannun mai wasa dashi. "Idan ya shigo anjima zai yi miki bayanin da zaki gamsu. Ni nan cire hijabi zaki yi mu farantawa juna rai." Kallonsa tayi taji dukkan wata tsana ta duniya ta tattara a kansa. Ga haushin rashin hankalinta da ta bari ya yi wasa da tunaninta. "Ashe abin da aka fada min gaskiya ne duk da dama bana tunanin mai fadar zai yi min karya." Danliti bai wani damu da maganarta ba ya kama kayan aron jikinsa ya soma cirewa. Ayaah ta juya ta fara dukan kofa da ihu taji ya daka mata tsawa. "Juyo nan ki gani" Ta juya a fusace ai kuwa tayi tozali da kakkaifar wukar da yake nuna mata. Shi ma cikin fada ya ce, "Ki kama bakinki ko idan na gama wallahi in kashe ki in kashe banza." Durkusawa tayi a wurin ta fashe da kuka "me nayi maka da ka zabi cutar dani?" Kishingida ya yi akan katifar daga shi sai singileti da gajeren wando masu dan banzan datti yana wasa da tsinin wukar ya zuba mata idanu. Sau daya ta kalle shi taji amai ya taso mata. Wani uban gashi ne a hammatarsa wanda da gani har kitso zai yi. "Bana son munafunci bayan na san kema kina so. Banda gulma me zai sa ki biyoni wai zaki gaishe da Mummy? Ni Innata tana kauyenmu." "Naji na cuci kaina don Allah kayi hakuri ka barni na tafi" Danliti ya sake yin dariya "dama ai ba kwana na dauko ki kiyi mana ba. Za dai mu gwangwaje a jikinki ne kawai mu kaiki gidan tsohonki." Kula ya yi kamar tana danne amai ya dinga dariya "wai nan kyamata kike ji? Tabdi. Yarinya wannan jikin yau zai kafa miki tambarin da har ki mutu ba zai goge ba" "Allah Ya fika" ta ce cikin kuka tana tofar da yawu." "Ke dai anyi azzaluma. Kina ta kada jiki a gabana amma kin kasa karasowa ki bani kasona? Ki taso kafin na farde kayanki da wukar nan" Duk wata magiyarta bata yi tasiri ba. Gashi babu halin buga waya. Karshe kayanta ya umarceta da ta cire ta zo ta same shi akan katifar. Da taki ya taso ya kamata ya tsarge hijabin ya wurgar dashi. Ayaah ta fashe da wani irin marayan kuka mai ban tausayi. Duk wata hudubar Anti Hasiya ta dinga dawo mata. Matsatsiyar rigarta ya gani yana karewa surar jikinta kallo harda lasar labba. Ta sake dukawa tana bashi hakuri ya dagota ta mike ya dalla mata mari saboda ransa ya kai makura sannan hakurinsa ya kare. "Ni ban daukoki domin na gwada miki karfi ba. Soyayya mai zafi nake son mu shayar da juna amma kin tsaya kina neman yi min taurin kai. Wallahi idan kika bari na saka miki karfi yau ko uwar da ta haifeki ba za ta ganeki." Hankadeta gefe ya yi ya koma ya kwanta rigingine da wukarsa a gefe ya dauko tecno dinsa ya kunna wata mahaukaciyar waka ya kure sautin. "To maza ki cire kayan ki zo muyi rawa." Ayaah taga cin mutumcin da tozarcin nasa sun wuce tunaninta. Yadda zata samu ta karbi wukar hannunsa ma dabara ta kare mata. Bata daddara ba kawai ta juya tayi masa ba zata wurin dukan kofar dakin da hannuwa biyu, iyakar karfinta. Danliti ya taso a guje bayan ya jefar da wukar zai kamota. Iskancin nasa na matsorata ne domin kuwa yana tsoron 'yan layin su farga a dauki mataki. Sun saba kawo yan matan da suka amince ne ba jjc irinta ba. * Ayaah na wannan bugun Suhaib na gama mikawa matar Danliti kudi. Kusan a tare shi da tawagar makanikai da ita suka kalli kofar. Baiwar Allah sai ta kada danta tabar wurin. Duk lalacewa bata son yaron yaga ubansa a yanayin da ta tabbatar zai shiga na muzanci nan da dan lokaci. Jikin Suhaib na tsuma ya karasa jikin kofar suna biye dashi ya soma bugawa iyakar karfinsa. Danliti da Ayaah suka kalli kofar a tare. Dankwalinta da gashinta ya hada ya yiwa mugun riko dama yana shirin fizga yadda zata ji zafi aka yi bugun. "Waye?" Ya tambaya muryarsa ta fito kamar ta kyanwa don ya tsorata. Ogansa ya yiwa Suhaib alamar ya yi shiru sannan shi ya yi magana da kaushin murya. "Mutumin banza bude ka bani mukullin mutane don tare muke da 'yan sanda" Yawu ya hadiya ba shiri " 'yan sanda kuma?" Sake buga kofar Suhaib ya yi da karfi Danliti yaji kamar ya saki fitsari a wurin. Yana can hankalinsa a rabe da tunani bai farga ba Ayaah ta dauki wukar da ya yar sai kawai gani ya yi ta nuna shi da ita. "Ko ka bude kofar nan wallahi ko na burma maka wukar nan a cikinka" Shi ya jiyota, na waje ma kowa yaji abin da ta ce. Jikin kofar Suhaib ya raba da sauri ya ce "Ayaah?" da taushin murya. Kuka ta fashe dashi tsabar farinciki "na'am?" "Kada kiyi abin da zamu yi regretting kinji ko?" Kai ta gyada tana wani kukan ta dubi Danliti "ka bude ni" Gaba kura baya sayaki. Wukar hannunta bata dame shi kamar jin muryar shegen yaron nan ba. Idan bai bude ba ma zasu balle kofar ne ayi masa abin da aka ga dama. Saboda haka babu yadda ya iya haka ya zura mukullin ya murda kofar. Mukullin yana yin karar ta bude kafin ma ya zare sakatar da ya saka ta sama yaji sun yi baya tare da kofar. Wawan bugu Suhaib yayi mata da kafa sai da ya jijjigeta gabadaya ta balle. Ayaah na ganin hasken waje bata yi wata wata ba ta danna kai a guje sai ji tayi sun yi karo da mutum har suna shirin faduwa. Dole ya saka hannuwa ya tarota. Tsigar jikinta da nasa suka tashi lokaci guda da suka hada ido cikin ido karo na farko tun haduwarsu. Da sauri Suhaib ya sanya hannu ya rabata da jikinsa. Kallo guda ya sake yi mata ya runtse idanu. Rigarta ko kadan bata dace da ganin idanunsa ba balle na wasu. Bai yi tunanin komai ba ya shiga balle maballan shirt din jikinsa. Rigar dogon hannu ne da ita. Cireta ya yi ya rage farar T-shirt din jikinsa. Ayaah bata ankara ba taji ya dora mata rigar ta gaban kirjinta. "Rufe jikinki ki jirani a waje" ya ce ba tare da ya kalleta ba. Da sauri ta fice kuwa ta koma gefe tana share hawaye. Kansa tsaye ya fada cikin kazamin dakin mai warin kazantar kaya da ta fasikancin da aka jima ana yi a cikinsa. Da kafa ya doke kofar daga kan Danliti yasa kafarsa dake cikin hadadden cover shoe ya danne tsakiyar kafafun Danlitin. Razanannen ihun da Danliti ya yi sai da yaje kunnuwan makotan shagon. Mutane suka firfito ana kallon ikon Allah. Ayaah kanta durkushewa tayi ta cusa yatsunta a cikin kunne. Tsinuwa da zagi kala kala daga bakin jama'a ana fadin yadda suka mayar da dakin dandalin yan mata. Suhaib kuwa bai ragawa Danliti ba don ko kadan bai yi niyar cire kafarsa nan kusa ba. Ogan makanikan ne ma ya ji tsoro yaje ya riko shi. "Yallabai ka yi hakuri ka bari a hadashi da hukuma kada ka dauki mataki a hannunka." Kamar ba zai dauke kafar ba sai ya cire. Sauran mazan kamar su ya yiwa suka dinga sauke ajiyar zuciya. Suhaib ya shammacesu ya sake daga kafar kawai kuma buga masa. Ihun Danliti har yafi na dazu don suma ne kawai bai yi ba saboda azaba. Biyu cikin makanikan suka leka waje wurin Ayaah. "Ki zo ki yi masa magana kada yayi kisa" A hanzarce ta tashi ta koma kofar dakin. Ta san sunan shi tunda kannensa sun fada taji. Amma bata san ita me ya dace ta kira shi ba. Wasu hawayen ta goge ta sami kanta da cewa, "Yaya" Suhaib ya juyo ransa a matukar bace "Ban ce ki fita ba?" "Ka zo ka kaini gidanmu don Allah" Yadda tayi maganar da sanyin murya ya taba shi sosai. Cije lebensa ya yi don bai so barin Danliti haka ba ya biyo bayanta. Haka ya tasata a gaba har bakin motarsa don baya son kowa yaga bayanta. Da kansa ya bude motar har ta shiga sannan ya rufe ya zagaya barin direba ya zauna. Yana tuki yana kula da hawayen da take gogewa lokaci-lokaci da rigarsa mai kamshi. Sai da suka bullo titi ya yi mata magana. "Ina zamu bi?" "Dama" Shiru ya sake mamaye motar na 'yan dakiku sannan ya ce, "Ba kya jin magana ko? Abin da ya faru shekaranjiya bai isheki ba sai da ki ka biyo shi"? Da jajayen idanunta da suka rine saboda kuka Ayaah ta dube shi. "Kayi hakuri don Allah." "Ya tabaki?" Ya tambayeta idanunsa na kallon titi. Ta girgiza kai tana wani kukan. Ba don sun zo ba da yanzu tana can ya gama da ita. "Dago kanki ki dinga yi min kwatance" Umarninsa tabi ta dinga kwatanta masa har suka shiga layinsu. Nan ta tarar da motar 'yan sanda har biyu a kan layin. "Kinga abin da kika janyo a gidan ko?" "Ai ba zan kara ba" Suhaib ya taka burki ba shiri ya kalleta "tunanin karawa dama kike yi?" "A'a" ta amsa masa da sauri. Da ya tsaya tare suka fito daga motar. Shi da ita duka kunyar suturar jikinsu ta kamasu. "Kinga abin da kika ja mana ko?" Kunkuni yake don bai san da yaya ma zai shiga gidansu ba. Tsayuwa ya yi a hanya yace ta karasa. Tayi narai narai da idanu za ta yi kuka. "Don Allah kazo kayi musu bayani. Yau ina jin Baba sai ya yi min duka." "Banda abinki Ayaah, ance miki bana so a dake ki ne?" Baki ta bude amma bata iya cewa komai ba ta rufe. Ta zata ba zai karasa din ba sai gashi ya cigaba da bin bayanta har kofar gidan. A tsorace ta saka kafa sai ta dawo da baya. Gabanta ke faduwa bata san abin da iyayenta zasu yi mata ba. "It will be okay. Ki shiga" "Wallahi zuciyata kamar za ta fito ta baki." Tausayi ta bawa Suhaib sosai. Bai san tun yaushe take ta kuka ba yau ga wani ta fara na tsoro. Rab'awa ya yi ta gefenta ya shiga kofar farkon sosai. "Assalam alaikum wa rahmatullah." Murya tafi biyar da ta amsa. Amma a ciki Ayaah ta bambance ta babanta da Anti Hasiya. I just published "37" of my story "UWA UWACE...". https://www.wattpad.com/1133888814?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=BatulMamman17&wp_originator=8bORFMwuNDQyr%2BfdoI7yxGIK4CEE8lbtGac2Zw5bWunyGWNSmVrSo5i2xfNSEwWAqh9k101JzBETDaJ4m%2FU5XfSegbkS4kRSc%2Bon%2FQk3gZry7YcyktZ%2BmwMkk%2FSCjmwv UWA UWACE...37 Batul Mamman💖 {Fatan alkhairi ga masu bibiya tare da hakurin jiran post. Ba zan gaji da bayar da hakuri ba. Ciwon hannu ya sakoni a gaba. Wadanda muke group tare da masu turo sako private duk sun daina ji na sai jifa-jifa. Sakonninku birjik a whatsapp da wattpad harma da instagram amma dubawa ta gagareni. Masu kira Allah Ya saka muku da alkhairi. Babu dama na daga waya sai nayi jinyar hannu. Ina kan magani yanzu kuma Alhamdulillah sauki yana samuwa. Shi yasa nake ta lallaba hannun. Na so kwarai sai na kammala tas kafin na kara post. To amma na sami kiran wasu da sako wadanda suka ce na turo abin da ya samu ko babu yawa. Bana son zama mai karya alkawari tunda na kan ce na kusa a yayinda nake jin saukin hannun. Da zarar ciwo ya dawo sai na bar rubutun. Ku kara hakuri mu lallaba har mu kai karshen Uwa Uwace.} For THE QUEENS, because they deserve it. Na gode *** Abbati ya zagaye gidansa yafi a kirga. Babu wani lungu da sako da bai leka ba bayan fitowarsa daga wurin Baaba Mari. Akwai wuraren da rabonsa da taka kafarsa tun ana ginin. Wasu irin tunane tunane suka dinga zarya a cikin kansa. Son muhallin nasa ya darsu a zuciyarsa irin wanda bai taba ji ba. Sai idanu sun zaga sosai a cikin garin nasu ma za a sami gida makamancin nasa. Lallai shi yasa ake cewa idan an ga matashi da kudi bayan bashi da kwakkwarar sana'a ya kamata a bincike shi. To wai ma ya aka yi bai taba jin korafi ko da wasa game da tarin arzikinsa da wadak'ar da yake da kudi ba a garin? Ko ana tsegungumi a bayan idonsa ne bai sani ba? Yau daya da ya yiwa gidan kallon tsanaki sai ya fahimci yawan titsiyen da Baaba Mari take yi masa akan wurin aiki. Wajibi ne uwa ta matsu da son jin silar rayuwa irin tasa. Ga gida ga motoci ga kudi kamar bai san ciwonsu ba. Samarin garin da dama idan sun kawo kawunansu ko iyayensu sun musu jagora akan ya saka su a hanyar sana'arsa sai da ya cikasu da kudi. Ana karbe kudin zaka ga mutum ya ja gefe an koma kasuwanci ko a cinyesu a banza. Ya gode Allah da ya kasance ba shi da alhakin sanya d'an kowa a layinsu. Da yanzu bai san yadda zai yi da lodin zunubai ba. Ga nasa da yake fatan samun gafara ga na wasu da babu lallai su so tuba. Kan kasaitacciyar kujerar kushin din dakin da aka yi domin kwanciya ya tafi ya kwanta rigingine. Tunani bai barshi ba har ya luluka yana tuna masa yadda aka yi suka kawo zuwa yanzu. Yayinda Munzali ya zama mukullin bude masa wannan duniyar, shi Abbati, shi ne ya fara mayar musu da ita sana'a a lokacin da Munzali ya kwanta ciwo. Shi ne ya nemi Shazali wanda ya kaishi wurin wani babban mutum. Tunanin komai da kowa ya yakice ya sanya kansa a faifan zuciyarsa yana tuhuma. Shin yana wannan dabiar ne a matsayin sana'a ko matsayin namijin da yake jindadi mu'amala da jinsinsa? Amsarsa ita ce zabi na biyu. Hakika ya yi mugun sabo da wannan dabi'a wadda ta sanya har yanzu sha'awar mu'amalar ta kan taso masa. A kalla kusan bayan kwana bibbiyu ko uku ya kan sami kansa a mugun yanayin son wannan abu. Yana jin wahala har ma ya kai ga siyan magani don wani zubin ko bacci kasawa yake. Haka kuma take a wurin Munzali shi ne ma dalilinsa na biya musu makudan kudade domin samun lafiya. Matsalar irin wannsn zinar ya wuce mutum ya tashi watarana kawai yace ya tuba. Ita jiki take bi tana yi masa illah. Idan bukatarta ta taso mutum dole ya nemi hanyar biyanta ko ya wahala. Allah ne shaidarsu amma rabonsu da neman juna tun gabanin ciwon Munzalin. Shamaki ne Allah Ya saka musu sannan Ya maye musu zukata da tsaftatacciyar kaunar juna domin lokaci irin wannan. Duk wannan abu zuciyarsa bata fasa fada masa cewa shi din har yanzu namiji bane. Soyayya dai ta zuciya da zuciya Farha yake yiwa. Tunaninta kadai sai da yasa tsigar jikinsa ta tashi. Yana sonta da dukkan abin da zuciya za ta iya bawa wanda take kauna. Burinsa na duniya akan mace ahi ne ya mallaketa a matsayin matar aure. A wayi gari wasu yara suna kiransa Baba suna kiranta Mama. Duk mazan da yake mu'amala dasu kallon maza yake yi musu. Mata kuma suna nan a mata. Bai taba sanya kansa a ajin 'yan daudu ko wadanda suke karyar cewa da son jinsinsu aka haifesu ba. Shi lafiyayyen namiji ne wanda ya mayar da kusantar maza 'yan uwansa sana'a. Idan babu namiji zai rayu sarai da mace sai dai kawai illar wancan abu zai dinga damunsa kafin Allah Ya yaye masa jarabar. Infact yana daga cikin dalilansa na cigaba da zama da Hanne duk irin rashin dadin zamansu kuwa. Tuntuni auren ya wuce na umarnin Mal. Sa'idu, domin kuwa a irin kudinsa da ya saketa idan har da mai ce masa don me ba zai wuce Baaba Mari da Gwaggo Jummai mahaifiyarta ba. Sauran kowa so yake ya zo ya auri tasa 'yar. Abin da ya hada auren nasu ma tuni an manta dashi. Shi da ita suna zaune ne kawai saboda auren rai gareshi. Babu soyayya, babu shakuwa sannan babu damuwa. Gara ma shi yana bata kulawa domin sauke nauyin hakki. Ita kuwa tsakaninta dashi bai wuce kudi idan har ta neme shi. Ga misali yanzu rabonsa da gida tun asabar daga zuwa daurin aure. Amma har yau ko flashing bata yi masa ba. A kasalance ya tashi ya shiga hada kayansa na sakawa a wasu manyan akwatuna. Ya zabi aikin ne domin rage radadin rashin Munzali da Qibdiyya. Sai dai ko kusa bai sami abin da yake so ba. Komai ya taba indai nasa ne to Munzali ma yana da irinsa sak. Haka ya gama loda kaya masu muguwar tsada a jakunkuna da akwatuna ya jeresu a gefe. Sai da ya gama da nasa ya soma tunanin ta ina zai fara sabuwar rayuwa? Duk abin da ya mallaka da kudin zina mafi muni ne don haka dole su rabu. To yanzu me zai ce da duniya? Yaya mutane zasu kalle shi? Da ya dauki aniyar sauya rayuwarsa sai ya ga ashe abu ne mai matukar wahala. Ashe rayuwar da ya bari lokacin yana dan shekara goma sha biyu sai bayan shekaru ashirin da hudu zai cigaba da ita. Abbati almajiri ne zai taso ya dora rayuwarsa daga inda Abbatin Munzali ya yi masa katsalandan. Abin da wuya....da matukar wuya. Shaidan ya shiga kai kawo wurin nuna masa tarin kalubalen da zai fuskanta da zarar ya sanya kafarsa a waje. Ya shawarta zuwa ya baiwa Baaba Mari hakuri akan ta barshi da iya abin da ya tara yafi a kirga amma ya fasa. Dukiyar ta haram ce. Indai ba yana so daga shi har mata da 'ya'yan da yake fatan haifa a gaba su zama cikin wadanda Allah ba zai ji kukansu ba dole ya hakura. Shaidan din yana nan amma so da addu'ar uwa sun yi matukar tasiri a zuciyarda da gaske Allah take fuskanta. Faduwa ya yi cikin sujjada domin neman karfin zuciya daga Sarkin dake jujjuya zukatan bayi. "Ya Rabbi kada Ka barmu. Idan Ka barmu munyi asara. Allah Ka haska min hanyar da zata bulle dani kamar yadda nake fatan Ka haskawa Munzali. Duk wani abin da zai lullube mana zuciya daga barin yi maka da'a Ya Allah Ka nesantamu dashi. Ya Allah Ka jagoranci sabuwar rayuwarmu kada Ka kunyata tubanmu a duniya da lahira. Ya Allah Ka rufe sirrinmu kada Ka bari mu tozarta a idon duniya." Adduarsa kenan. Kuma ya yita cikin kuka da kankantar da kai hade da yakinin ganin kudurar Ubangiji akan lamarinsu. Abin da Allah Ya hukunta ba zai wuce bawanSa ba. Abin bukata bai wuce tsayuwa akan imani da kyautatawa Allah zato ba. Yana tashi sai ga wayar Baaba Mari. Sarkin da baya bacci Ya juya zuciyarta. Hakika tun bayan fitarsa da abin da Munzali ya ce ya sami takwararta sai ta rasa sukuni. Hukuncinta na rabasu tun farko domin su jidadin tuba yana nan. A matsayinta na uwa dole ne tayi duk wani abu da ta san cewa zai taimakawa danta ya tuba. Tabbas d'a na kowa ne to amma fa game da naka Allah zai fara tambayarka ranar lahira kafin na wani. Sannan yana daga cikin sharudan tuba da aka koyar da ita a Islamiyya, bawa ya nesanci wurin da yake aikata wani sab'o, ko ya canja abokai ko abin da zai kusanta shi da hakan a yayin tuba. Shin ta so kanta kenan don tana nemawarwa danta tsira daga azabar wuta? Kwalla mai zafi ta silalo mata ta share. Zuciyarta a kuntace take. Lallai ita Mari tafi uwar da 'yarta take yawon karuwanci shiga tashin hankali. Luwadi? Luwadin da Allah Yasa aka kife al'ummar Annabi guda a sanadinta amma ace dan da tayi rainon cikinsa ta haifa kuma ta shayar ita ce sana'arsa? Kaico! 'ya'yan mutane da suke cikin wannan mummunar rayuwa ba zasu kirgu ba. Wadanda suka shigeta a matsayin sana'a ko hanyar jindadi a sanadiyar almajiranci sun ninka masu shiga a gaban iyayensu. Babu dalili komai dadin bakin mutum da za a fada mata wanda zai sa ta taba goyon bayan a cigaba da tura yara almajiranci. (Wannan gaba zaman fayyace halin da almajirai suke ciki zai iya cinye ragowar labarin namu. Na dai yi imanin cewa mun sani ko mun saba jin labarai marasa dadi akan yaran da suka tsinci kansu a nesa da iyaye da sunan neman karatu. Fatanmu Allah Yasa masu ruwa da tsaki su kawo gyaran da ya dace game da rayuwar al'ummar nan a kowane fanni.) Munzali! Matsayin Munzali ta tuno a wurin Abbati ba rawar da ya taka a rayuwarsa ba. Lokuta babu adadi Abbati zai turo mata katin waya ko da tana dashi ya ce don Allah ta kira Munzali. "Ki yi hira dashi Baaba irin ta uwa da danta. Ki dinga yi masa fada kina bashi shawara. Yana bukatar hakan." Tun tana kiran bayan Abbati ya saka ta har ta koma yi a karan kanta. A duk lokacin da ta kira sai ta kara jin kaunarsa a zuciyarta. Yaro ne mai saukin kai ga wanda ya fahimce shi. Mutum ne shi wanda yake fama da k'ishin (thirst) uwa a rayuwarsa. A hirarrakinsu yana bude mata sirrinsa da damuwa akan gidansu. A dalilin haka ta yi yunkurin hada zumunci da Asabe amma abin bai yi nisa ba. Lokacin 'ya'yan nasu basu yi kudi kamar yanzu ba. Asabe ta dinga yi mata lakabi da Uwar Almajiri. Ko a waya suke gaisawa da wannan sunan take kiranta. Da aka yi masa haihuwa ya sanyawa diyarsa Mariyatul Qibdiyya kuwa kiranta tayi ta ci mata mutumci. Bata fadawa kowa ba har Abbati amma ta janye jikinta. Sai dai abin da ya sami takwararta ya mata karan tsaye. Fyade ta furta kazamar kalmar a raunane. Tufka da warwara basu barta ba sai dai tunaninta ya tsaya wuri guda. A takaice raba Abbati da Munzali ba zai zama mafita ba. Hadasu da nuna musu hanya a tare shi ne jigo. (Wato 'yan uwa na fa sha korafi akan dalilin sanya Baaba Mari ta umarci Abbati da rabuwa da Munzali. Da yawa basu san manufar yin haka ba. Na so nuna muku hukuncin farko da iyaye kan zartarwa yaransu ne a duk lokacin da aka sami bullowar mummunan hali. Za ka sami uwar abokin barawo da son raba danta da barawon harma tana ikirarin zai bata mata d'a. Sau tari bata ma san cewa nata shi ne ya bata na wani ba. Illar rabawar musamman ga masu wayo shi ne su dinga haduwa a bayan idon uwa. Idan da zata zurfafa tunani sai ta gano matakin farko shi ne ta kokarta wurin taimakawa duka yaran da suka yi tarayya a barna. Ita da iyayensu su hada kai su gyara. A inda aka kasa samun haka sai guda daya ta gwada. Sai taga hakan ya kasa zama maslaha sannan ta canja tsari. Idan zamansu tare da fadan da nasihu yaki aiki sai a shigo da shawarar rabuwarsu. Wannan shi ne abin da naso nunawa da hukuncin farkon. Wallahu Ta'ala A'alam) "Zo ina son ganinka" Da sauri ya mike domin ya zata jikin ne. Ya sameta a zaune a dakinta ita kadai. Ta nuna masa wurin zama da hannu. "Abbati na baka amanar kanka da ta Munzali. Na yarje muku zamewa juna jagora a kokarinku na inganta tuba. Na amince ku hada kai ku nemi taimakon Allah akan umarnin da na baku na rabuwa da duk wata dukiyar haram. Wallahi Abbati albarka ba za ta bi ku ba alhali kuna ci kuna sha da kudin zina. Rayuwarku za ta tafi akan tsarin da zai haskaka zukatanku ne a lokacin da ku ke cikin halalinku komai kankantarsa. Ita haram banda tarin zunubi harda kuncin zuciya take sakawa." Ko kusa bai zata abin da zata fada masa ba kenan. A bazata mafi girma kalamanta suka dirar masa. Hawaye ya cika idanunsa har ya zubo a lokacin da ya matsa ya kama hannunta ya rike cikin nasa. "Allahu Akbar. Allahu Akbar. Baaba kin sani cewa ban taba kokwonta akan Sarautar Allah ba amma yau na kara imani. Na roki Allah kuma hakika Ya taba zuciyarki. Na gode. Mun gode" Hancinta ta ja ta hanyar shaka alamun kukanta bai kare ba ta murmusa. "Allah Ya karawa Annabinmu SAW daraja." "Amin" "Ka bar duk abin da kake yi ka tafi Kano domin Munzali yana bukatarka. Ni shaida ce ba don matsalar da ta taso ba da tuni ya biyoka." Abbati yaji gabansa ya fadi "akan Qibdiyya da ya ambata ne?" Baaba Mari ta gyada kai. "Fyade aka yi mata" "La haula wala quwwata..." Abbati ya ce a yayinda ya yi wata irin mikewa cikin mummunan tashin hankali. "Ka nutsu domin a yanzu kai ne kwakwalwar tunaninsa. Idan kaima ka makance babu lallai ku iya daukar matakin da ya dace. Ka tafi Allah Ya tsare." Cikin minti goma sha biyar har ya isa tasha. Wurin mutum uku ya biya domin motar tayi saurin tashi. **** Ana amsa sallamar Suhaib Ayaah ma sai tayi cikin muryarta da ta dusashe saboda kukan da tayi. Ba a amsa ba. Sai dai cikin abin da bai fi sakan biyar ba ilahirin jama'ar dake cikin gidan Honourable a wannan lokaci suka tsaya a bakin kofa. Sunan Ayaah kawai ake kira ana kukan murna da hamdala. Jikin Hasiya ta fada tana kuka sosai. Kukanta ya tayar musu da hankali. Farincikin da suke yi na ganinta ya koma alhinin jin daga ina take da kuma abin da ya sami suturar jikinta. Honourable kurawa Suhaib ido ya yi yana neman fassara yanayin da ya gansu a ciki. Matashi mai jini a jika sanye da 'yar singiletin da ta bi jiki da damatsansa. Ga 'yarsa ta suturta jikinta da rigar da ya yi imanin ta matashin ce. Me yake faruwa? Gabansa ya shiga faduwa yana fatan ba abin da yake tunani bane. "Ya kamata mu zauna aji me yake tafe da yaron nan ko?" Larai ce tayi magana tana janyo Ayaah daga jikin Hasiya ta rungume. Gani take ta fi kowa damuwa da son jikokin nata na wurin marigayiya A'i. Ita dai Ayaah hawaye kawai take yi tare da yayyenta Ummita da Murja har suka shiga cikin dan falon da ba zai dauki mutanen gidan ba. Basu san me ya sami kanwar tasu ba amma hankalinsu a tashe kamar na kowa. Mazan duka suna waje. Honourable wayar Abdulkarim ya kira ya fada masa dawowar Ayaah tare da tsawaita godiya akan taimakonsu da ya yi. Zamansu Ayaah ke da wuya sai ga Anti Hasiya da kwanukan abinci. Murja ce ta karbi tray din ta ajiye a kasa ita kuma ta koma kusa da Ayaah ta zauna. Tana zaman Ayaah ta dora kanta a cinyarta ta cigaba da kuka. Kasa daurewa tayi ta biye mata suna yi tare har sai da Innayo tayi magana. "Kun bar mutum a waje kin zo kin sakata a gaba da kuka maimakon ki rarrasheta." Larai ta harareta saboda so take ace ita ce mai rarrashin. Bata son duk wani abu da zai nuna Innayo ko Hasiya sun fi ta sanin me ya kamata akan jikokin. Sai cewa tayi, "Wani irin rarrashi a wannan yanayin da ake ciki? Ai ki barta tayi kuka ko zata sami sa'ida." A tsakar gidan kuma Honourable ne ya ce da Suhaib idan babu damuwa ya zauna zasu yi magana. Bai yi mamakin jin hakan ba shi yasa ya zauna akan tabarmar dake shimfide a wurin. Honourable ya shiga falon ya ce don Allah su fito waje amma yana son a dan jira zuwan Abdulkarim. A ganinsa yadda ya kokarta masa yau dinnan ya kashe duk lalurar gabansa ya dace shi ma ya san me ya faru. Ita dai Ayaah ji tayi kamar wata igiya ta kwance daga wuyanta zuwa kafafu. Yawun bakinta duk ya kafe ta rasa na jika lebenta ma. Rawar jiki kawai take yi saboda firgici. Da Salima ta kula da yanayinta sai ta yiwa Honourable magana cikin hikima. Mutumin da yake a tsorace bai dace idanu su yi masa yawa ba a irin wannan lokacin. Tana gudun tayi musu karya saboda rashin sakewa. Shi yasa taga gara ace mahaifinta ne kawai da Hasiya. "Inaga duk abin da za a tattauna gara ayi a nan. A kira saurayin da ya kawota ya shigo ciki sai mu baku wuri." Larai da 'ya'yanta sun so kin tashi sai dai Salima bata barsu ba. Musamman ma dai 'yan uwan nasu. Ai kuwa ta hau fada akan cewa a madadin uwa tafi kowa cancanta da zaman jin bayanin Ayaah da bakonta. "Don Allah mu koma dakin yaran nan tunda ya dan fi yin ciki. Sai kuyi shawarar a can ko don bakon da bamu san ko waye ba." Honourable ne da kansa ya yi magana saboda ya san halin Larai. Jan zance zata yi, gashi shi kuma a matse yake yaji bayani. Da suka fito Hasiya ta nunawa Suhaib kofar falon ta ce ya shiga suna zuwa. Suna zuwa Honourable ya ce da Hasiya, Innayo da Larai zasu zauna da yaran. Sai Abdulkarim idan ya iso. Daga jin haka Larai tayi gaba tana mitar ai 'ya'yan cikinta ya kamata ya kira ba Innayo ba. Babu wanda ya ce mata komai a cikinsu. Suna zuwa bakin kofar Abdulkarim ya yi sallama ya shigo gidan suka rankaya ciki tare. * Suhaib ya shiga ya sami Ayaah tana faman goge hawaye da rigar jikinta-rigarsa! Haka nan yaji hakan ya zo masa a matsayin kusanci da ita. Kasa yi mata magana ya yi bayan sallamar da ya yi sai kallon yadda ta take kuka. A nata bangaren kuma ganinsa yasa taji wani kwarin gwiwa fiye da farkon shigowarta. Wasu hawayen ta goge ta dago kai ta dube shi. "Don Allah ka rufa min asiri kada ka fadawa su Baba abin da ya faru. Ban san me zasu yi min ba." Kwayar idanunta wadanda suka yi jazur gami da kankancewa Suhaib ya kalla ya dan yi murmushi. "Kada ki firgitani yadda kika firgita kanki mana. Nace ki kwantar da hankalinki komai zai daidaita in sha Allahu" Amsarsa bata bata nutsuwar da take nema ba domin ba abin da take muradi ya fada ba. Jikinta duk ya yi sanyi ta marairaice fuska. "Kenan fada musu gaskiya zaka yi?" "Banda gaskiya babu wani abu da zai fitar dake. Me zamu ce a matsayin dalilin da ya hadamu har na kawoki gida? Banga wani abu da zamu fada wanda zai gamsar damu kanmu ba balle su." Bata hakura ba ta ce "Iyayena zasu ji kamar naci amanarsu. Don Allah..." A tausashe ya ce "I will be here Ayaah. Zan yi musu bayani yadda zasu gamsu in sha Allahu." Abubuwa taji suna shiga zuciyarta daga sautin kalaman har zuwa sakon da suke tafe dashi. Hankalinta ya dan kwanta amma tsoron bai barta ba. Turo baki tayi ganin magiyarta taki tasiri cikin kunkuni ta ce, "Ni wallahi na zata ma sona kake shi yasa ka taimaka min." Tun bayan zuwansa Kano a yau sai yanzu Suhaib ya yi dariya. Dariya mara karfin amo amma mai nuni da har cikin zuciya mai yinta yana cikin nishadi. "Wato kin zata sonki nake?" Ayaah ta murguda baki da kumburarrun idanunta ta ce "Dariya ma na baka?" "Ai dole nayi dariya." Ance wai mai hali baya fasawa. To Ayaah ma bata manta tsiwarta ba tunda Danliti bai sami damar koya mata hankali ba. Juya idanu taso yi amma nauyinsu ya hanasu bata hadin kai. Sai ma zafi da suka yi wanda yasa ta runtsesu da sauri. Duk da haka bata hakura ba sai da ta ce, "Ko a nan gaba kaji kana sona kada ma ka fada don ba zan baka hadin kai ba." "Zamu gani" ya ce yana cigaba da murmushi. Kofar da aka taba ta danyi kara ce ta kawo karshen maganar tasu. Honourable ne a gaba sai Minista, matan suna biye dasu. An zazzauna kowa ya fuskanci Ayaah wadda ta rakube a jikin Anti Hasiya. Honourable ne ya soma magana cikin nutsuwar da ya arawa kansa ta dole. "Kun san zaman me muke yi a nan? Ku dubi girman Allah ku fada mana gaskiyar abin da ya faru." Ayaah baki sai ya soma rawa. Dauriyar da taso yi ta kasa sai kuka. Wannan yasa Suhaib ya karbi ragamar jawabin daga inda ya sani. "Suna na Suhaib Tahir kuma a Kaduna nake da zama. Kanwata Mardiyya ita ce Alh. Munzali yake nema..." Innayo ta gyada kai saboda tun dazu take yi masa kallon sani. Ya cigaba da fada musu ranar da ya fara ganin Danliti a wurin dinner. Sai ya sakaya ya ce matar dan uwansa ce ba matar babansa ba. Irin abubuwan da ya gani da maganganun da Danlitin ya yiwa Jiddo da Ayaah duk ya fada. Akan haka ne hankalinsa bai kwanta ba har ya karbi nambarsa a wurin Jiddo da zuwansa Kano. Dama duka abubuwan da suka biyo baya har ya sami damar kubutar da ita da taimakon Allah. La haula wala quwwata illa billah. Suhaib yana bayani Anti Hasiya da Larai suna kuka. Innayo ma ba a barta a baya ba domin tabbas ba don tsarewar Ubangiji ba da yanzu suna kukan bakinciki. Honourable kuwa sunkuyar da kansa ya yi kasa. Shi kadai ya san halin da zuciyarsa take ciki. Sam ya kasa magana sai Abdulkarim ne ya dauki matsayin uban. Godiya ya fara yiwa Suhaib sannan ya koma kan Ayaah. "Saura ke" "Don Allah ku yi hakuri" ta fara cewa Larai ta daka mata tsawa. "Za kiyi bayani ko sai na saba miki? Mutuniyar banza mutuniyar hofi." Idanunta a kasa ta fadi abin da ya kamata ta fada. Tana magana hannunta yana cikin na Hasiya wadda ta rike domin bata kwarin gwiwa. Labarin bai yi mata dadi ba amma kuma bata so tsoro ya hanasu gane bakin zaren. Kunyar duniya yau Ayaah ta gama sha. Da bakinta take maimaita yadda abubuwa suka kasance a gaban iyayenta da Suhaib. Ko ba a fada ba ita da kanta ta dinga ganin wautarta na yarda da zantukansa baro baro. Honourable ya dago kai a fusace bayan ta gama magana. "Taso ki zo nan?" Suhaib ya kula da bacin ransa sosai. Shi ma zuciyarsa a cunkushe take da takaici amma bai bar tausayinta ba. Yana jin kiran da mahaifinta ya yi mata sai ya mike tsam. Hukunci ya zama wajibi sannan shi din bashi da hurumin hanawa. "Bari na baku wuri" Bai jira yaji abin da zasu ce ba ya fita daga falon. Haka Ayaah ta rarrafa gaban babanta ta kama kafafunsa tana kuka. Hakan bai hana shi tureta ba ya daga hannu zai mareta Abdulkarim ya hana. "Bata kyauta ba amma don Allah kayi hakuri. Mace kamar wannan ta wuce ladabtarwa da duka" "Inji wa?" Cewar Larai tana face majina "yau ba don yaron can dan albarka ba da yanzu muna cizon yatsa" "Duk da haka dukan bashi da amfani. Kamata ya yi mu godewa Allah da Ya tsare mutumcinta" "Sai kuma ayi mata me bayan addu'ar? In kyaleta gobe ma ta bi wani katon banzan?" Honourable ya tambaya cikin fushi. Kafafunsa Ayaah ta sake dafawa ta ce "Don Allah kayi hakuri Baba ka yafe min. Wallahi ba zan kara ba." Girgiza kai ya yi da disappointment karara a fuskarsa "kin bani mamaki Ayaah. Kamarki ace kin iya hada baki da namiji ya zo makaranta ya daukeki. To ma wa ya san tun yaushe hakan take faruwa?" A gigice ta dora hannu a baki tana rantsuwa "wallahi yau ne kadai." "Kina tunanin zan yarda ne?" Bata fuska Larai tayi "ban gane ba Habu, me kake son cewa? Tun dazu nake ta bata laifi tunda na san bata kyauta ba. Amma ba zan zuba ido ka jefeta da kazafi ba." Ta juya bangaren Anti Hasiya "dama na fada da sa hannunki akan abin da Ayaah tayi. Banda haka wace uwa ce zata kasa gane irin wadannan abubuwan? Da ace kina kula da marayun nan ai da kin fahimci abin da take yi tun kafin ya yi nisa. Ki bari ki haihu din kafin ki wargaza rayuwar 'ya'yan gidan." "Maganganu irin wadannan basu dace da gab'ar da muke kai ba Larai." Innayo ta furta cikin lumana. Na farko Honourable Habu suruki ne sannan ga bakonsa. Bai dace magana irin wannan ma ta raso a yanayin da ake ciki ba. Sannan ta gaji da daure zuciyarta kan kalaman Larai akan Hasiya. Tana tsoron kada a kai ta bango ta rama duk su taru su bawa kansu kunya. Mayar da kallonta tayi ga Ayaah ta ce "ina ji a jikina abin da ya faru yau ya isheki darasi da ishara akan rayuwar da kika so jefa kanki a baya. Ki kiyayi maimaituwar yau din a rayuwarki domin duk ranar da namiji a sami galaba a kanki walau da son ranki ko babu indai babu aure a tsakaninku ya cuceki har abada. Wani tsautsayin kirawo shi ake yi da sakaci. Allah Ya kiyaye gaba." Amin suka amsa su duka har Larai din. Abdulkarim ya yi murmushi a ransa yana kara yabawa da tsatson da Hasiya ta fito wanda ya yi tasiri akan 'ya'yan Honourable. Dolensa ma ya zage damtse akan Ummita don bai ga wadda ta dace ya nema da gaske ba kamar ita. Innayo sallama ta yi musu ta ce zata tafi. Honourable sai ya ce yana son su zama shaida akan hukuncin da zai yankewa Ayaah. Jin batunsa Anti Hasiya da Ayaan suka dinga bashi hakuri. Suna cike da tsoron abin da zai ce. Sun san shi mutum ne mai hakuri da kawaici amma bashi da dadi idan ya kai bango. Ummita da Murja yasa Ayaah ta fita ta kirawo masa. Babu bata lokaci sai gasu duka a tare kowacce ciki ya duri ruwa. Fadan baban nasu bashi da dadi ko kadan. "Ku zama shaida" ya ce dasu Innayo, "ban yarda Ayaah ta sake fita in ba tare da wani daga cikin gidan nan ba. Makaranta ma in sha Allahu ta bar zuwa sai ranakun jarabawa. Shi ma da kaina zan dinga rakata na daukota. Sannan in sha Allahu sati daya da gama jarabawar Ayaah zan aurar dasu. Duk wadda bata da manemi zan samar mata kafin lokacin. Ke kuma..." Ya nuna Murja "ki fadawa Mahiru tunda dama ni suke jira. Ku tashi ku tafi." Murja ta mike. Ayaah da Ummita suka kasa kwakkwaran motsi. Maganar abin da bai fi wata uku ake ba. Kuma basu da maneman a hannu. Anti Hasiya ma maganar dirar mikiya tayi mata. Ayaah kam tayi laifi mai girma sai dai ko kusa ba za ta yarda ya yiwa yaran nan auren dole ba. Ita da nata mahaifin ya yi mata, Allah ne kawai Ya dubi zukatansu ita da mahaifiyarta Ya daidaita zaman. Sai ya kasance Honourable din ya zarce duka tunaninsu a fagen kyautatawa sabanin sanin da suke tunanin sun yi masa lokacin yana auren A'i. "Ku tashi mu tafi" ta ce da 'ya'yan nata ganin hatta Ummita ita ma kukan take. Suka bi bayanta kuwa suna tafe kamar kwai ya fashe musu a ciki. Da fitarsu Honourable ya bawa kowa mamaki da ya yi 'yar dariya. Innayo ma da Abdulkarim sai da suka murmusa. Ita nata ya dace da na Honourable. Fushi ne suke gani muraran Hasiya tana yi na sanya mata yara a tsaka mai wuya. Shi kuwa Abdulkarim na farincikin fahimtar cewa Ummita bata da kowa a hannu yake. Lallai zai ci karensa babu babbaka. Tunda babu wani yaro a hannu da zai masa shigar sauri ya hure mata kunne. Dakin da suka baro su Maimuna suka shiga, Ummita da Ayaah suna kuka babar tasu ma tana yi. Maimuna ta gaji da rarrashinsu ta koma fada. "Tunda baku san hakuri ba sai kuyi ta yi. Amma ki sa Ayaah ta cire rigar d'an mutane ta mika masa" Sai a lokacin ta tuna da rigar. Da sauri ta shiga balle maballan ta cire ta mikawa Murja. "Don Allah ki kai masa" Anti Hasiya ta kai mata duka ta kauce "Amma baki da kirki Ayaah. Mutum ya yi miki irin wannan taimakon amma godiya ta kasa shiga tsakaninku. Tashi maza ki kai masa da kanki." Hijab ta dora ta fita tana jiyo muryar Larai tana bada labarin abin da ya faru. Duk inda take tunanin ganinsa kama daga tsakar gidan, soro da kofar gida. Bata manta da gargadin babanta ba saboda haka bata yarda ta fita ba. Ciki ta dawo da niyar daukar wayarta ta kira shi sai ta kula da takalminsa a kofar falon. Kenan Baba ne ya sake kiransa ta ambata a zuciyarta. Kamar wadda tayi magana da karfi sai ji tayi Babanta ya kwala mata kira. Da hanzari ta shiga don yanzu bata kaunar abin da zai bata masa rai. "Dama rigarsa zan ce ki kawo ashe ma kin dauko." Abdulkarim sai cewa yayi "muje waje in ganka kafin na wuce Honourable." Hon. Habu ya dan yi turus sai da ya sake maimaitawa ya mike. Suna fita Abdulkarim din ya ce da Suhaib idan ya fito zasu yi sallah don har biyu da rabi. Rigar ta mika masa bayan sun fita ta furta kalmar godiya a hankali. "Ya naga duk kin yi laushi ne? Ko hukuncin da Baba ya ce min ya yanke ne bai yi miki ba?" Dago rinannun idanunta tayj da sauri ta ce "yanzu sai da ya fada maka zai min auren dole?" "A'a" ya ce yana mai girgiza kansa "cewa ya yi kawai za ki daina fita har zuwa school sai kina da paper" ya kare da dan murmushi. "Auren dolen ka ke yiwa dariya ko hanani fita?" "Kina da rigima" Suhaib ya furta da wani irin yanayi sannan ya tashi tsaye "ni zan wuce. Sai in ce sai mun zo biki ko?" Shiru tayi bata kula shi ba don ta kula yana jindadin zolayarta. "Au ba za ki amsa ba?" "Kana farinciki da auren dolen da za ayi min ya za ayi na amsa?" Sai da ya je bakin kofa sannan ya juyo ya kalleta cikin ido ya ce "dazun nan ki ka yi warning dina da cewa ko ina sonki kada na fada domin ba za ki yarda ba. Ba don haka ba da na sake introducing kaina a wurinsa a matsayin...." Ya lumshe ido ya budesu a gajiye "idan kin bani matsayin da ya dace na sake gabatar da kaina a wurinsa ki kirani kafin lokaci ya kure mana. Take care." Har ya fita su Ummita suka shigo bata sani ba don ba karamin kashe mata jiki da zuciya kalamansa suka yi ba. Sallah ya tsaya suka yi sannan ya ce zai tafi. Ba yadda Honourable bai yi dashi ba akan ya zauna yaci abinci yace ya koshi. Da fitarsa bai zame ko ina ba sai garejin su Danliti. Ogansu ne ya kira shi yana shiga mota zai bar unguwarsu Ayaah. "Mal. Suhaib muna kara godiya akan taimakon da kayi mana. Dalilin kiran naka kuwa yanzu ba wani abu bane illa wayarsa da nake son baka kafin 'yan sanda su nema." "Waya kuma?" Suhaib ya furta yana yamutsa fuska saboda son sanin dalili. Mutumin ya ce "Kwarai kuwa. 'Yan sandan da suka zo basu kula da ita ba sai wani cikin yarana ne ya dauko. Yanzu suka budeta har sun cire lock din ma. A garin bibiyar hirarrakinsa na chatting muka ci karo da hirarsa da wata mata suna kuma yawan ambaton sunanka. Matar har tana cewa idan ka zo Kano ya sake maka kamanni da duka. Shi ne nace gara dai ka zo ka gani kada ya cuci wata" 'Alhamdulillah' Suhaib ya ce yana mai fadada murmushin fuskarsa domin wannan batu ba karamin taimako zai yi masa ba. Shaida ce guda da zai samu ya nunawa Abbansu akan Jiddo. In anyi sa'a yaga cewa matarsa ma tana yin yadda yake ko kusa da kila ya canja hali. Da wannan tunanin ya wuce garejin. Kafin ya karasa kafarsa ta dama ta soma wani irin tsukku kamar ana cakarta da allura. Da kyar ya iya karasawa sai dai yana fitowa ya kasa takata da kyau. Ogansu Danliti yana ganin yanayin tafiyarsa ya ce, "Dama na san a rina. Wannan duka da ka yiwa kofar dakin nan da wuya idan baka bugu ba ko targade. Don da karaya ce da wuri zaka fara jin ciwon." Wasa-wasa Suhaib kasa jan motar ya yi. Shi da ya yi niyar komawa Kaduna a lokacin sai gashi wani aka samu ya mayar dashi gidan kawunsu inda aka yi zaman biki. Abinci ma kasa ci yayi dole suka tafi wani asibitin kashi na kudi. Har x-ray aka yi masa saboda kafar ta fara kumbura ta wurin idon sawu. Dunduniyar kuma tana ciwo. Babu karaya yadda suke tsammani sai tsabar buguwa. Irin leg brace dinnan aka daura masa bayan an yi mata gashi sannan suka koma gida. Matan gidan suna can suna kiran Mami Khadija su sanar da ita shi kuwa ya kira Lilu ya ce ya taho washegari su koma tare. *** Zara taga ikon Allah zamansu da Uwani bayan fitar su Innayo. Surutai take yi ita kadai kamar wadda ta sami tabin hankali. Kalma ko daya ba za ta iya cewa ta gane ba amma ga bakinta nan yana ta motsi da sauri-sauri. Abin tsoro ya soma bata ta tashi daga dakin ta koma falo. Kafin ta zauna Uwani ta fito tana mai cigaba da maganganunta. Babu zato taji ta ce mata, "Kiyayyar da kuke min har ta kai a rasa mai tambayata damuwata Zara?" "Idan na tambaya za ki fada min ne?" Uwani na jin haka ta dawo kusa da ita ta zauna. Da gaske neman wanda zata saukewa damuwarta take. Innayo din da ta zata har abada ba za ta taba juya mata baya ba yau gashi tana magana taki sauraronta da kyau. Kanta ta dinga dunguri da yatsanta manuni. "Zara ina ji wadansu notina suna kwancewa a kwakwalwata wallahi. Daf nake da zarewa idan Habibu bai dauki wayata ba" "Habibu kuma ko Salihi?" Uwani ta maimaita sunan da karfi "Habibu nace. Ai ce miki nayi kaina zai kwance ba wai ya kwance din ba" Mikewa Zara tayi "me yayi zafi za ki sauke min fadanki. A kira Habibu lafiya" Da sauri Uwani ta riko hannunta ta dawo ta zauna. Bata boye mata komai ba cikin matsalolin da suka fuskantota a dan kankanin lokaci. "Idan na rasa komai wallahi zuciyata za ta iya bugawa. Zara gabadaya rayuwata fa akan yadda zan gujewa rayuwa irin ta Innayo na yita. Sai yanzu bayan na gama shan wahalar har ina hango soma cin arzikin sai komai ya rushe? Meye marabata da Innayo yanzu? Karatun da aikin duka babu riba." Kwalla ce ta taru a idon Zara saboda ita kanta ta hango tsagwaron rashin hankali a zantukan Uwani. "Ko kadan baki yi kuskure ba don kin yi fatan gujewa irin rayuwar Innayo. Babu wani mai hankali da zai so bayan ya tashi a wahale ya cigaba da rayuwa a haka. To amma kuskurenmu daya ne ni da ke. Mun so gujewa rayuwar ne mu kadai ba tare da tunanin wadda tayi sanadiyar rabamu da ita ba. Da gumin wa muka rayu? Wa ya ciyar dake? Waye ya kai ki makaranta? Wa ya aurar dake? Addu'ar waye ya zame miki garkuwa tsahon rayuwarki? Sai ace kuma da kika sami dadi ita ce mutum ta farko da kike gudu tamkar ita ta zabawa kanta kuncin da take ciki. Ke din wayonki ne yasa ki ka sami duka nasarorin da kike tinkaho dasu? Idan wayonki ne to ki sake tsallake wannan ramin dake gabanki. Ni dai na dawo daga rakiyar shaidanin da ya taba min zuciya. Uwata ita ce madubin rayuwata. Ranar da kika gane haka kuma ki ka roketa gafara shi ne lokacin da zaki fara ganin haske." Tun zuwanta gidan ta kula da yadda Zara take neman shiri da Innayo. A zatonta abin na ganin ido ne kadai. Sai gashi taji daga bakinta. Wannan yasa tayi wata irin dariya. So take ta san waye mara hankali tsakanin ita da kanwar ta ta. "Da bambanci sosai tsakanin matsalata da taki. Baki san juya kudi ba sai dai a dauka a baki. Shi yasa da miji ya juya miki baya ki ka yi saurin laushi a hannun Innayo tunda arzikinta kike ci. Ni kuwa gumina ne. Nafi karfin tozarcin da namiji wallahi." "Hakka!" Cewar Zara da gatsali. "Don kin ganni a gida ki ke min magana haka? Hala baki ji na fada miki ina da gidan kaina ba?" "Kan ki kuma ake ji" Zara dama ba kyalle bace. Da ta fuskanci Uwani bata da niyyar bin hanyar da take nuna mata sai taji gara a bar maganar kafin su fara fada. Tashi tayi ta fito falo. Uwani sai ta biyota rai a bace. "Ni kike cewa kaina ake ji saboda ga 'yar macukule ko? Har kina da bakin fadawa wani magana ma ke da kike goyon 'ya mara suna?" "Wai in tambayeki Uwani. Anya kin taba zama kin karewa Innayo kallo kuwa? Kin ma santa kuwa? Sani na wace ce ita a matsayin 'yar Adam ba na matsayinta na uwa a gareki ba." Shiru Uwani tayi tana sauraron zancen da Zara ta dauko. "Innayo bata sami gatan uwa da uba ba a dalilin maraici amma mu ta zame mana uwa da uba harda kari. Mu tara ta aurar Uwani. Mata tara wata na bin wata. Ta sadaukar da lafiyarta da jindadinta domin rayuwarmu ta inganta. Amma cikinmu banda Hasiya waye take jindadi a jikinsa? Salima da Maimuna suna kyautata mata amma ai har yau guminta suke ci. Su Hasina dama tun zamanin marigayiya Allah Ya jikanta suka juya mata baya. Me tayi mana da zafi Uwani? Saboda ta auri ubanmu ta haifemu shi ne laifi? Ko don ta jure wahalar gidansa domin ta zauna damu don kada rayuwarmu ta tagayyara? Kiyi tunani idan har kina da rabon jindadin duniya da lahira. Innayo jininta ne kadai bata zubar domin mu ci, mu sha kuma mu sami ilimi ba. Tun karfe hudu take tashi amma babu ita babu sake kwanciya sai wuraren shadaya ko shabiyun dare. Hannunta kullum a ruwa, ido a gaban murhu. Haba Uwani? Kamar baki rike ciki kin yi nakuda ba? UWA, UWACE komai lalacewarta. Balle kyautar Allah irin Innayo." Bata kara tofa komai ba bayan haka ta shige daki saboda kukan da yaci karfinta. Uwani kuwa zama tayi dabas akan kujera duka jikinta babu kwari. Ta kwashi kusan minti ashirin tana juyayin maganganun Zara kafin wani irin bacci ya dauketa. Tabbas sau tari mutum yana ganin abin dake zuciyarsa ne a cikin bacci. A yadda take a zaunen ko gyara zama bata yi ba baccin nata ya dauketa zuwa duniyar mafarki mai ban tsoro. A cikin baccin take fatan Allah Ya kawo mai tashinta saboda firgicin da ba za ta ce ga abin da ya kawo mata shi ba. * "Shazali ya maganarmu ne? Ranar laraba muka yi da Alh. Tahir gashi har yau litinin baka ce min komai ba" Gefen titi Shazali ya gangara da motarsa domin maganar da zai yi da Comared tana bukatar nutsuwarsa sosai. "Ranka ya dade akwai shirin da nake yi ne. Hatsaniya ta shiga tsakanina da mutumin da nake son kawo masa ne, saboda haka sai na lallaba shi a hankali." Tsaki Comared ya ja ya kuma kama yi nasa fada harda zagi. "Ka tabbata yaron ya zo domin idan aka sami akasi raina da naka duk sai sun baci" Hakuri Shazali ya bashi a ransa yana ta tufka da warwarar yadda zai yi ya sami kan Abbati cikin lumana. Aikin Comared din da ya yi masa bayani ya wuce biyawa Alhajin da zai zo bukata kadai. Aiki ne na sihiri wanda Alh. Tahir ya zata za ayi ne domin toshiyar baki (Yumna). Bai san cewa Comared tasa tukunyar yake son gyarawa ba. Sharri yake son kulla masa ya watsa hotunansa ta yadda zai rasa duk wata kwangilar dake hannunsa. Sai a bawa Comared don dama irin sana'arsu daya. Lokaci guda Alh. Tahir din ya yi musu zarra, sunansa kadai ake ji. Abotar sai ta koma murmushin gaban ido da gulmar bayan ido, batare da saninsa ba. To shi ma Shazali burinsa ya yi amfani da wannan damar ya tozarta Abbati. Duk da cewa a gaskiyar lamari yafi jin haushin Munzali saboda yafi baki. To amma wulakantar Abbati sai tafi ta Munzali ciwo kamar yadda ya yi hasashen tonon asirinsu. Abbati dan dangi ne. Munzali kuwa da danginsa da babu duk daya a tunaninsa. Sannan son da Munzali yake yiwa Abbati zai sa yaji ciwon abin sosai. Dama ce ya samu da zai nuna musu shi din ba kanwar lasa bane. A matsayinsa na silar arzikinsu bai kamata su juya masa baya ba. Sai da suke ganiyar samun kudi kamar hauka sannan zasu ce wai sun tuba. Ko waye ya fada musu cewa shi baya son samun rahama bai sani ba. Lokacin tubansu idan ya zo ba sai kowa ya fada musu ba. Tsufansu ya ishesu sanin cewa ya kamata a koma ga Allah. Su gina masallatai su dinga bayar da sadaka. A haka zasu koma lahira kamar jarirai. (Babu bawan da Allah Ya yiwa alkawarin jinkirta masa rayuwa zuwa wani wa'adi. Lokaci yana zuwa ne ko da tsufa ko babu. Ko an tuba ko ba a tuba ba sai an tafi. Ya Rabbi Ka yafe mana zunubanmu na zahiri da badini. Amin) Da waccan magana ya katse kiran Comared ya shiga laluben layin Abbati. Cikin sa'a kuwa ta shiga sai fatan a dauka. Abbati na ganin sunansa a jikin wayarsa ya ja tsaki ya mayar da ita aljihu. Sun kusa Jogana motar tasu ta soma hayaki suka tsaya. Abin duniya ya taru ya yi masa yawa domin ya kasa samun mota mai tsayuwa ta dauke shi. Ga yamma ta kawo kai. A gefe guda kuma ya kasa samun Munzali. Hanne da yake tunanin zata hadasu ita ma wayarta a kashe. Daga baya ne ya yi tunanin kiran Kukunsu. Cikin sa'a kuwa ya sameta. Shazali da bai hakura da nemansa ba ya dinga jin wayar tana shiga number busy. Kalmar lafiya kalau kadai Abbati ya iya cewa ga dukkan tarin kalaman gaisuwa da kukun yake jefa masa. Jin zai fara tambayarsa mutanen gida ya yi saurin katse shi. "Don Allah hadani da Munzali" Kuku ya dubi hanyar bene ya ce "yau ko sau daya bai fito ba. Sannan yaki barin Qibdiyya ma ta sauko. Abincinsu ma ni ban sani ba ko sun ci don ya kulle kofarsa" Dunkule hannu Abbati ya yi ya daddaki goshinsa cikin rashin sanin abin yi. Can dai ya ce masa yana zuwa ya kashe wayarsa. Hannunsa yana rawa ga gumin tashin hankali ya shiga scrolling din sunaye a wayarsa. So yake ya gani ko zai yi dacen samun nambar 'yan uwan Munzali amma babu ko daya. Tsoronsa kada ya dauki mummunan mataki musamman da Kukun yace yana tare da Qibdiyya. Kiran kukun ya sake yi da wata shawara ta zo ransa. "Ka san gidan iyayen Munzali ko?" "Na sani ranka ya dade" "Ka je gidan ka nemi mahaifiyarsa Asabe ka fada mata. Ita zata san me ya kamata ayi kafin na iso. Ka tabbatar ita ka samu" A kofar gidan Alh. Rabi'u kukun ya tsayar da mashin dinsa ya sauka ya dinga kwada sallama. A cikin gidan Asabe tana kuryar dakinta abin duniya ya yi mata yawa. Zantukan Munzali basu da ma'anar da zata iya cewa ga dalilin da yasa yake rokon Qibdiyya gafara don an mata fyade. Ta so tahowa ma da ita a jiya a hana. Yau kuma yaki daukar wayarta. Daga baya ita ma bata samunsa. Ga sunan yaron da Qibdiyya ta ambata ma ya kwanta mata don bata taba jinsa ba. Shawara tayi tafi dari akan ta kira su Ummakati ta fada musu ko tayi shiru. She was never a Mom to all of them. Ta dai san wahalar daukar ciki da nakuda. Ta kuma dan san wahalar raino musamman kafin yaro ya fara zama. Daga nan kuma sai abin da hali ya yi. Allah Mai rayawa Shi ya raya mata zuri'arta cikin mugun sakaci da rashin sanin ciwon kai. Da Innayo ce tabbas ta san da tuni ta lalubo abin da ya dace har ma ta aiwatar. Yinin ranar bata tsinana komai ba sai kullawa da kwancewa. Ga ranar da duk girman d'a yake bukatar mahaifiyarsa. Gata da rai da lafiya amma bata san me ya kamata ta yiwa Munzali ba. * Tashin da Uwani tayi daga firgitaccen baccinta yana da alaka da karfin sallamar Kuku. A razane ta tashi tayi hanyar kofa da sauri. Zara ta kalleta ta girgiza kai. Ita ma sallamar ce ta fito da ita. Kallon ina-na-sanka Uwani ta dinga yiwa masa. Shi bai ma ganeta ba sai Asabe da ya tambayeta. Juyawa tayi kamar ta koma daki sai dai ta karasa ta fadawa Asaben. Tare suka dawo bakin kofar. A gabanta ya fada mata halin da Munzali yake ciki. Cikin tsantsar rudani kuwa Asabe ta soma kuka. Ita kuma Uwani wani case ta tuna a asibitinsu inda uba ya kusa kashe 'yarsa saboda bakincikin an mata fyade a kauye. Ya ce gara ta mutu akan duniya taji wannan labari. Ba tare da tunanin komai ba sama da ran kaninta da 'yarsa ta koma daki da gudu. Mayafin dake jikin Zara wanda ta lulluba zata fito tun zuwan Kuku ta warware ta yafa. Ta ruga daki ta dauko jakarta mai dauke da kayan aikin gaggawa ta fito. "Ki fadawa Innayo na tafi gidan Munzali" Zara ta bita da sauri "gidan Munzali kuma? Me ya faru?" Uwani bata ce komai ba ta fita. Asabe har lokacin tana tsaye tana koke koke bata iya cewa komai ba ga kuku. Isowar Uwani ce ma ta ankarar da its cewa ya kamata tayi wani abu. "Malam muje don ba gane gidan zanyi ba" Kuku ya dan ja baya "ke ce Asaben?" Rai a bace da ganin yana bata mata lokaci ta ce "ni yayar Munzali ce. Ka wuce mu tafi" Asabe sai ta gyada masa kai ta koma ciki da zummar dauko mayafi. Kafin ta fito sun bar wurin. Duk da tsoro irin na Uwani haka ta hau mashin din tana salati har suka isa. I just published "38" of my story "UWA UWACE...". https://www.wattpad.com/1133889152?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=BatulMamman17&wp_originator=VZ0iecln71g4e%2B3XyeweYBP%2F5nkH%2BcNoWrBHfg6iF2vPrMxcsWcPxWRResAX78c51fQElDFikz8lba2nyxXA4uHandgvdjrxFJT0p%2BYtGV68AukxrUibEQ9qpTux2mxt UWA UWACE...38 Batul Mamman💖 Karfe goma na safe Habibu ya shigo cikin ministry da wata 'yar jaka a hannunsa. Kayan sawarsa ne da abubuwan bukata na kurkusa ya hada a ciki. Zaman Kano ba nasa bane ya sani tun ranar da Salihi ya titsiye shi. Babu shakka bayani ya kai kunnen Uwani. Sanin da ya yi mata na son kudi ba na yau bane. Abu mafi karanci da zata yi masa shi ne ta hada shi da 'yan sanda. Shi yasa zai yiwa tufkar hanci ya gudu. Ba kudinta ne kadai ya jike a hannunsa ba, harda na wasu da dama. Da ace kudaden suna da albarka a hannun macuci kuma maha'inci irinsa da tuni ya zama wani. Shekara da shekaru da 'yan dabaru yake kwatar kudi a hannun mutane ya danne. Haduwarsa da Uwani da amincinsu ne yasa ya rage rarakar aljihun wasu. Bai taba shan wahala ko ta anini ba wurin tatsarta. Ita take kawowa tana bashi, shi kuma yana gina kansa. 'Algungumi, an dai fadi ba nauyi' ya ambaci maigidanta Salihi dashi a lokaci guda yana jan tsaki. Duk shi ne ya bata komai da ya far masa kamar ita ta aiko shi. Tunda ya san gaban kansa yake yi gara ya gaggauta guduwa kauyensu har kura ta lafa. Manyansa a harkar magudi ba za su bari ya rasa aikinsa ba. Yanzu ma daya daga cikinsu ne ya ce ya biyo ya karbi rabonsa na wasu kudade da suka yi kashe mu raba da hakkin talakawa. Hagu da damansa ya waiga don yana ji kamar ana kallonsa sai dai bai ga bakuwar fuska ba. Hakan yasa shi sakin jiki ya shiga office din mutumin. Yana rufo kofa wani masinja ya kira wayar DPO Yahaya kai tsaye ya sanar dashi shigowar Habibun. "Ka san yadda zaka yi ka rike min shi idan kaga zai tafi har mu iso." "Yallabai kada ku dade domin da jaka na ganshi" "In sha Allahu ba za mu wuce minti ashirin zuwa talatin ba." Masinja ya cika aiki kuwa. A matsayinsa me da ma'aikacin da aka fi gani tare da Habibu, DPO Yahaya yasa aka kai shi station. Bayan guntuwar tsoratarwa suka gano da gaske bashi da hannu wajen ha'incin Habibu. Ya dai san yana yi kuma kamar yadda ya dinga yi musu rantsuwa yana yawan yi masa fada. Alakar tasu ba wata mai zurfi bace sama da yawan musayar yawu game da bambancin ra'ayin siyasa. "Muna so ka bamu hadin kai ka taimaki abokinka ya daina cutar mutane" abin da DPO din ya fada masa kenan da ya bashi lambar wayarsa. Bai fi minti bakwai ya rage a lokacin da Masinja yake tsammanin isowar 'yan sandan ba sai ga Habibu ya fito yana fara'a. Masinja ya karaso suka gaisa ya soma jansa da hira. Idanun Habibu akan gate yana daddaga wuya ya zaro dari biyar "sauri nake ga wannan ka sha ruwa" "Yi hakuri ka saurareni Habibu. Matsala ce ta taso a unguwarmu." "Ka ganni nan? Garin zan bari yau dinnan. Ka nemi gidan Dagaci ko Mai unguwa ku kashe matsalar" Masinja bai hakura ba ya bi bayansa ya rage murya kamar sirri zasu yi. "Na san kana dan taba harkar nan. Ka taimakeni ko wani abu ne sai na biya." Saurin takun Habibu sai ya ragu. Masinja kuwa ya gimtse dariyarsa da yaji me yace. "Wace irin matsala ce? Yadda na dauke ka dan uwa kaima ka san ba zan iya dauke kai akan matsalarka ba" Masinja ya kirkiro labari ya shiga zuba masa. Wai fili ya sayar ba tare da sanin mai shi ba miliyan biyar. An gama biyan kudi amma balli na neman tashi. Shi ne yake neman mafita. Hannu Habibu ya dora akan kafadar Masinja yana murmushin mugunta. "Ina kudin yake yanzu? Allah Yasa baka kaisu banki ba" A madadin amsar Masinja da yake jira sai jiniyar 'yan sanda ta ziyarci kunnuwansa. Saboda tsabar kaduwa, hannun nasa da ya dora a kafadarsa ya kasa saukewa. Jikinsa ya yi sanyi kalau amma haka ya daure domin a zatonsa motar wucewa tazo yi ta unguwar. Dif ya daina jin karar har ya samu damar sauke numfashi. A ransa yake tunawa kansa cewa mijin Uwani a yadda take fada masa yafi kama da marasa wayo. Ita kuma tunda bata san ainihin me ya mata ba da wuya tayi kararsa. Wayar da tayi masa da asubar ranar dama ita ta kara saka masa son guduwa sai kura ta lafa. Yana can yana zancen zuci sai ji ya yi an damki hannuwansa. Ya zabura ya kalli masu rike shi yaga duka kayan gida ne a jikinsu. Wannan kuwa dabarar DPO Yahaya ce domin kada Habibu ya farga ya yi tunanin gudu. "Lafiya? Ku su waye? Satar mutane kuma da safiyar Allah a gaban jama'a?" Daya daga cikinsu ya dauko ID card ya nuna masa "mal. Habibu, ana tuhumarka da satar kudin Uwani Rabi'u ta hanyar yaudara" "Bangane ba!" Da ya fada a tsorace ta nuna cewa ya gane tsaf. "Idan mun station za ayi maka cikakken bayani. Muna neman hadin kanka ko mu tafi da kai ta karfin tsiya" Mutanen da suka fara tsayuwa kallo ya kalla sai kawai ya hakura yabi su. Bai san da sa hannun Masinja ba tunda gefe yaja ya tsaya. Ana tafiya da Habibu station DPO din ya sanar da Salihi. Shi ne ya bukaci ya zo da Uwani domin jin ta bakinta. A lokacin ya tafi gidansu daukarta sai yaci karo da ita a bayan mashin din Kukun su Munzali. Hawa mashin ba dabi'arta bace. Ganin da ya mata ya tayar masa da hankali. Ko dai fitar da tayi ta son zuciyarta ce ko kuma ta emergency ce na abin da ya shafi wani. Zuciyarsa sai tafi karkata da tunanin farko tunda ya santa da son kai. Babu bata lokaci yabi bayansu har gate din gidan Munzali. Akan idonsa ta dira da sauri don saura kiris ta fadi ta tura karamar kofar jikin gate ta shiga da gudu gudu. Shi ma sai ya kashe motarsa ya bi kukun da sauri ganin an bude masa gate zai shiga da mashin din. "Me yake faruwa ne a nan? Ni ne mijin matar da ta shiga yanzu Uwani." Kuku ya ce "Alh. Munzali ne babu lafiya" *** A cikin dakin Munzali kuwa a kwance yake yana rawar sanyi. Zazzabi yayi masa mummunan kamu. Har ta kai yana jin kamar ana kwankwatsa masa kasusuwa. Ciwon kai kuwa bai san daga wane bangare yafi sukarsa ba. Tunani barkatai sun addabi zuciyarsa. Mafi girma a ciki bai wuce jin tsoron ko tubansa ne bai karbu ba. Da tubansa ya karbu da babu wanda ya isa ya ketawa Qibdiyya haddi. "Da tubana ya karbu da Allah Ya tsare min ke ko bana raye" ya furta a kasan makoshi yana shafa kan Qibdiyya. Sake nanike mahaifinta tayi ta ce "Daddy har yanzu Papa bai zo ba" Kwalla ta taho masa ya yi saurin riketa saboda kallon kurillar da take yi masa. "Zai zo. Watarana zai zo...in Allah Ya yarda" saboda bai dade da gama wayar da ta kara masa ciwo da Baaba Mari ba. "Daddy..." Wata tambayar ce ya riga ya sani. Tun safe take faman damunsa. Da yace ta fita saboda ciwon kansa sai ta kulle kofar da mukulli maimakon ta bude bisa kuskure. Shi kuma azabar ciwon kai ya hana shi tashi. "Kaina ciwo yake don Allah kiyi shiru" Can gefe ta koma ta dauki biskit da juice wanda ya zame mata abinci tun safiyar yau din ta cigaba da ci. Wasa-wasa sai ga Munzali yana zubar da hawaye saboda ciwo. Komai ya jagule har yana tunanin rayuwarsa ce ta zo karewa. Sai dai yana tsoron tafiyar ba tare da sanin ko akwai nakasu a tubansa ba. Duk masu kwankwasa masa kofa ana kiransa yana ji amma ya kasa daga koda hannunsa ne. Ita kuma Qibdiyya bacci ne ma ya dauketa. A wannan halin Uwani ta iso gidan. Da sassarfa ta hau saman tana buga kofa amma shiru. Ana haka Salihi ya shigo Kuku yana yi masa jagora. Kiran da bugun da take yi ne ya kai hankalinsu gareta. Salihi yabi bayanta da sauri. Shi da Kuku suka hadu suna bugun kofa amma ko gezau taki motsi. "Qibdiyya" Munzali ya tabota da muryarsa da ta dashe bata fita sosai. Gyara kwanciya tayi abinta ta juya masa baya. Ya sake kai hannu ya tabata idanunsa na fitar da kwallar azabar ciwon kai. Da kyar ya samu ta farka tana zuba masa magagi. "Jeki ki bude kofa" Zuwa tayi ta kama mukullin tana ta murda shi ba daidai ba. Hamdalar Uwani da Asabe da bata jima da isowa ba ta tsaya a dalilin rashin buduwar kofar. Salihi ne ya yi dabarar cewa a miko mukullin ta kasa. "Na kasa cirewa" ita ce amsar Qibdiyya saboda ta kasa murda shi ya koma yadda zai fita. Sai da suka kwashe kusan minti goma sha biyar ana kwatanta mata yadda zata yi tana kasawa. "Ina babanki?" Asabe ta tambayeta a firgice. "Yana kwance. Kuma kuka yake yi" Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. A zaton Asabe ya ma mutu. Cigaba da juya mukullin Qibdiyya tayi har ta gaji. Ta cire hannu kenan Munzali ya taso da bin bango ya bude kofar. A tare Uwani da Asabe suka tura kofar ya fado gabadayansa akan Uwani saboda ita ce a gaba. "Munzali? Munzali tashi. Na shiga uku na lalace. Ku taimakeni" Zantukan Asabe kenan tana faman jijjiga shi bayan Salihi ya daga shi daga jikin Uwani. Da ta tashi jakarta ta dauko a kofar dakin ta soma auna shi. Jininsa ya hau ta yadda ita kanta ta tsorata sosai. "Asibiti zamu kai shi" Ta ce da Salihi tana mikewa tsaye. Ko tunanin daga ina yake ma bata yi ba. Shi da kukun dai suka saka shi a motarsa. Asabe, Uwani da Qibdiyya kuma suka shige bayan mota. Hayaniyar fitarsu ce ta taso Hanne har ta leka ta taga. Akan idonta aka sanya Munzali a mota. Jiki na rawa ta sami abin fadi ta dauko wayarta ta kira Abbati. Rabonta dashi tun yana shirin tafiya daurin auren kanin Mami Khadija. Tunda akwai kudi a hannunta bata ga dalilin kiransa ba. Shi ne mai kokarin kiran duk inda yake koda sau daya ne a rana saboda hakki. Neman kudi kadai ke sanyata kiransa. Yau da yake gulma ce sai bata ji kyashin kiran ba. Yana dauka ta saki baki ko tauna magana babu. "Yanzu naga an dauko Munzali an saka shi a mota kamar matacce" Razanar da yayi zai rantse ko tonuwae asirinsa bata sa yaji makamanciyarta ba. "Me kika ce?" Ya tambayeta da muryar da take fita kamar ba tasa ba. Sai kuma ta dan yi jim da ta hango wautarta "bani da tabbas fa" Kashe wayarsa ya yi ya sake kiran Kuku. A nan yaji cikakken bayani. Tashin hankalinsa ba zai misaltu ba. Allah Yasa lokacin suna Jogana. Daga nan tafiyar bata da yawa sosai za a shigo garin Kano. Bayan minti arba'in Abbati ya shiga wani babban asibitin kudi wanda suke zuwa tare da iyalansu shi da Munzali. Sai dai ya daki gurbi domin kuwa ba nan aka kai shi ba. * Bangaren A & E na asibitin Sir Sunusi Salihi ya nufa. Sai lokacin Uwani ta farga da ina suke. Kaddara za a kira shafewar tunaninta a game da hukuncin da CMD ya yanke mata har aka shigo. Ta dade da gane hanyar nan din Salihi ya dauko tun a baya amma tunanin an dakatar da ita daga aiki bai zo ba sai yanzu. Da ta fito daga motar sai taji kafafunta tamkar ba za su iya daukar nauyin jikinta ba. Shi kuwa Salihi tunda bai san halin da take ciki ba sai cewa yayi, "Shiga kiyi musu magana mana a zo a dauke shi. Idan ke ki ka shiga na san ba za a bata mana lokaci ba" Sati biyu da suka gabata da ita ce ta shiga tana da yakinin cewa a lalace mutum biyar su biyo bayanta. Idan kuwa aka san cewa kaninta ne to Allah kadai Ya san irin kulawar da zai samu. Sai gashi a dalilin son zuciyarta yau ta zo amma tana kunyar shiga. Labari ya risketa daga masu kiranta jajen gaske da na karya cewa kowa ya san an dakatar da ita. Matron Uwani Rabi'u sananniya ce a asbitin sosai. Akwai kwazon aiki da shige shige. Ga masifa kamar da Alh. Rabi'u aka gina asibitin. Shi yasa ta tara makiya da yawa masu son ganinta a kasa. To yau ga ranar. Taimakon wadanda take nunawa dagawa ne zai sa kaninta ya sami kulawar da ta dace. "Matron Uwani me kike yi a nan?" Da sauri ta juya suka hada ido da wata Matron din. Kallo daya ta yiwa Munzali ta dubi matar. "Wallahi kani na ne babu lafiya. Yana bukatar emergency care." "Ai kuwa nan dai cike yake da jama'a saboda an kawo masu accident." "Innalillahi. To don Allah Matron ki taimaka min don yanayinsa ba zai yiwu mu fita dashi ba" "Sai dai ki fara kulawa dashi kafin likita ya zo" Har ta fara murmushi ta sake tunawa da suspension dinta. Amma haka ta daure tabi bayanta tana cewa su shigo dashi. Da gaske wurin a cike yake. Wheelchair (kujerar guragu) wani sub-staff (karamin ma'aikaci) ya kawo za a dora shi sai yaja baya da ya hada ido da Uwani tana kokarin sokawa Munzali allura a hannu inda za a kara masa ruwa. "Matron? Ko ba Matron Uwani bace?" Ya furta da karfi har aka fara kallonsu. "Nice. Don Allah yi sauri ka kawo ya zauna" Mutumin ya dakata yana yi mata kallon biyu-ahu "In baki kiyi aiki aji dadin korata?" Ya kara daga murya ya kira Matron din da ta shigo da ita wurin yana cewa " da alama dai baki san an dakatar da matar nan har na tsahon wata shida ba ko? To wallahi babu ruwana don dokar daga sama aka aiko da ita. Uwani ta kalli Munzali ko tsayuwa ya kasa yi. Yana tsakiyar Salihi da Asabe ne sun rirrike shi yana neman faduwa. Harbawa zuciyarta ta kama yi ta dubi mutumin rai a bace. "Wannan ba patient din kowa bane nawa ne. Kanina ne wallahi. Don Allah ka bani kujerar a zaunar dashi" "In na baki Allah Ya tsinan..." Ya tabe baki "ko doka bata hau kanki ba Matron wallahi yau dai sai dai wani ya taimaka miki. An fada miki na manta tarin rashin mutumcin da kika yiwa matar kanina a labour room ne? Ga kuruciya gashi haihuwar fari ce amma kika dinga yi mata tsawa kamar wata baiwar da kika saya da arha." Daga bandakin bangaren emergency din wata dattijuwa mai aikin shara da wanke bandakuna ta fito. Duk zancen da ake yi taji kuma ta kara da nata. "Ashe ba ni kadai matar nan ta yiwa diban albarka ba. Nifa matar makocin dana aka kawo sai a baranda ta haihu. Kememe Matron Uwanin nan ta dage sai an biya kudin gado wai na gwamnati sun kare saura na kudi. Yaron wajena yazo muka tafi nace mata nima nan nake aiki sai cewa tayi wai tayi ragin dari biyu albarkacina. Su biya dubu tara da dari takwas." "Uwani Rabi'u ake fada muku. Matar da ta kasa biyawa uwar da ta haifeta kudin ganin likitan hakori? Nan asibitin suka zo babarta ko bude baki ta kasa amma Uwani ta ce bata da kudi. Kai ranar naga rashin mutumci ajin karshe. Wallahi sai da na godewa Allah da bai bani haihuwa ba. Da haihuwar dan da ba zai ji kanka ba gara kayi ta shafa fatiha." Uwani ta juya suka hada ido da daya daga cikin nurses din bangarensu na haihuwa. An kirata ne saboda cikin masu hatsarin harda mai ciki. Muzanta da tozarci irin wanda ko a labari bata taba ji ba ne suka saukar mata. Idanu sun fi a kirga a kanta. Ciki harda na Salihi da Asabe. Ga maganganun 'yan kallo harda majinyata ana zundenta tana ji. Jikinta a take ya yi sanyi kalau kamar an jefata a ruwa. Gumi ne kawai yake karyo mata sakamakon zafin da take ji yana bin jikinta. Ta kuma kasa yin motsi don ji take kamar an zare mata laka. Kai ta sunkuyar kasa ta dunkule 'yar robar daure hannun wanda za a sakawa allurar karin ruwa a hannunta da karfi. A hankali ganinta ya ragu a dalilin kwallar da ta cika idanun. Hannu taji a kan na damanta an riketa ana jijjigawa. "Mu fita mu nemi private hospital (asibitin kudi)" Da kyar ta iya daga ido ta kalli Salihi sai ta mayar da kanta ga Munzali. Idanunsa ne suke yin luuu yana shirin suma. Ganin haka bata san lokacin da ta dauko wayarta ta duba nambar Barr. Umma Jibril. Ringing hudu ta amsa kiran. "Matron Uwani?" Ta ambata cike da mamaki. Yawu Uwani ta hadiya mai daci. Bata manta da haushin matar da take ji ba da yadda ta rufta ta a gidanta da sunan dinki za ta yi mata. Bacin ranta ba wai don tana tantamar rashin gaskiyarta bane. Ta san ita din mai laifi ce sosai. To amma yadda aka bi aka kunyata ta duk da ba a gaban mutane bane ya tsaya mata a rai. Ga matsalolin daban daban da suka kunno mata kai lokaci guda. Amma hakan bai hanata jin cewa Barr. Umma ita kadai ce hope dinta ba a yanzu. Muddin ta tsaya girman kai ta ce su tafi wani asibitin Munzali zai iya shiga mawuyacin hali fiye da yanzu. Barr. Umma sai ta ce "Ko ba Uwani bace?" Da taji shirun ya yi yawa. "Nice" ta amsa da sanyin murya tana kallon kaninta. Kanin da ba wani abu na zumunci da zata ce ya taba giftawa tsakaninsu tun kuruciya. Sai gashi a yau tana jin damuwarsa ta danne tata. Ga ciwo ga maganganunsa da bata gane ba sannan ga babbar lamari game da 'yarsa....'yarmu ta gyara a zuci. "Hajiya don Allah ina rokonki da ki taimaka ko na yinin yau ne kisa CMD ya janye dokar suspension dina" Karaya da nadamar da ba a son bayyanawa Barr. Umma take ji daga muryar Uwani. Da yake ba halinta bane sai ta kasa jan zancen ta hanyar nuna mata dama rana irin yau sai ta zo dole. "Me yake faruwa?" "Kanina ne muka kawo gashi babu wanda zai iya duba shi a emergency saboda yawan patients. Ki taimaka min don Allah." Yau wai ita Uwani ce take magana da roko har tana jin taruwar kwalla a idanunta. Ina zuwa taji Barr. Umma ta ce. Ba a yi minti goma ba aka kira babban likitan dake emergency din. Da kansa ya zo inda Uwani take kai gwauro da mari ya mika mata dan akwatin awon bp. "Ki daukar min duk wani relevant detail ki fara kara masa ruwa kafin na gama da wadanda suke kan layi." Murmushin da yafi kama da dariya gami da fitowar kwalla duka suka sauko mata a lokaci daya. Asabe tana ta hamdali yayi da Salihi ya karbe wheelchair din da sub-staff din nan yaki basu da farko ya zaunar da Munzali. Ita kuma ta kama hannunsa ta dauki bp. Sakamakon da ta gani ya tsorata ta sosai. Lokuta kalilan ta taba ganin wadanda jininsu ya hau haka a bangaren haihuwa. Zafin zazzabin shi ma ya haura ka'idar da aka saba. Da taimakon Salihi ta samu ta saka masa ruwa shi kuma ya rike ledar saboda stand din ma babu a kusa. Tayi masa allurai da duk wani agajin da ya dace da halin da yake ciki. Bayan ta gama iya nata ta ruga duk infa likitan nan ya saka kafa tana biye. Bata so ya manta da dan uwanta akan layi. Da ya ce a miko wani abu sai tayi azamar yi duk don idan yazo kansu ya kyautata. Asabe tana tsaye rike da hannun Qibdiyya amma idanunta suna biye da duk takun Uwani. Sanda kwalla ta silalo mata ita kanta bata sani ba. "Innayo bata yi asarar haihuwa ba" ta fada da raunanniyar murya. Salihi ya gyada kai a inda yake tsaye yana kulawa da Munzali wanda bacci ya fara daukarsa. Uwani baudaddiyar mace ce. Shi kan shi bai taba zaton akwai ranar da zai ga tambarin mahaifiyarta a tattare da ita ba. Indai mara kirki wanda ya amsa sunansa mutum yake nema to lallai in yazo kan Uwani ba zai matsa ba. Zai ce ya sami abin da yake nema ne kai tsaye. Inama Innayo tana kusa ta ganewa idanunta. *** "Mami zani Kano gobe in sha Allah" Wayar da aka yi mata daga Kanon ta fasa amsawa ta kalli Lilu da sauri. "Wani abin ne ya faru?" "Ya Suhaib ne ya buge a kafa ba zai iya tuki ba" "Kada ka boye min komai Lilu" ta furta cike da tsoro. Murmushi ya yi kawai ya kira Suhaib a wayarsa ya bata. Da kansa ya fada iya abin da zai iya. Kofar daki ya daka ya bugu a kafar. Hankalinta ya dan kwanta amma ta san Suhaib da dauriya akan abin da yake ganin zai janyo mata damuwa. Ga Lilu kuma shi ma bata jin yana cikin nutsuwar jan mota shi kadai har Kano. "Zan bika amma ka san ni ina son sammako" Dage gira ya yi harda 'yar dariya "dan farin kuma Mami? Ai na zata za ki daure har ya iso gida" " Fita ka bani wuri" ta ce ita ma tana dariyar. Fitarsa keda wuya ta kira Alh. Tahir ta fada masa abin da ya sami Suhaib. Izinin tafiya ya yi mata. Ya kara da cewa shi ma jibi abu mai mahimmanci zai kai shi Kanon. Su jira shi sai su dawo tare. Da ta ajiye wayar kwakwalwarta aikin tunani ta shiga. Lamarin 'ya'yanta yana matukar damunta. Kowa da irin tasa damuwar. Yanzu da tace tana son zuwa Kano bata ce ga dalilinta ba. Indai buguwa ce tabbas abu ne da zata iya jiran a dawo mata da Suhaib din gida. To amma zuciyarta ta gaza sukuni. Kanon dai take son zuwa. I just published "39" of my story "UWA UWACE...". https://www.wattpad.com/1133889480?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=BatulMamman17&wp_originator=6I7qwMcRV%2FprvkCAkOvGj81Y%2BmQoj3hi1UT3OuzitQizPjHSDqCAybTI7a5GOCA3ThRlgbmz%2BAmhOE1LwaV8L5ikM6vN4nYTiiRNW6SjyqWr0FoHDqOW%2FWW1CPbmrqkE UWA UWACE...39 Batul Mamman💖 Su Innayo basu san wainar da ake toyawa a gidan ba sai da suka dawo ita da Salima. Tambayar inda Uwani ta shiga ta yiwa Zara ta fada mata duk yadda suka yi har fitarta. "Ban san me yake faruwa ba amma tana fita Asabe ma ta fita" Dama da tunanin halin da ta bar Uwanin a gida ta wuni. Wannan labari sam bai mata dadi ba. Duban 'ya'yan nata tayi ta ce daya daga cikinsu ta kira mata Uwanin a waya. Salima ce ta kira da aka amsa ta mika mata. "Ban hana ki fita ba Uwani?" Fita tayi daga dakin da aka kwantar da Munzali don kada ta tashe shi daga bacci. Kofar ma a hankali ta rufeta sannan ta ce, "Muna asibiti da Munzali an kwantar dashi" "Me ya same shi?" "Bayanin ba zai yiwu ta waya ba Innayo" Muryarta babu wannan gadarar da ta saba da nuna isa. Kamar ma da sigar rarrashi Innayo take jin amsoshin Uwani. Da taji a wane asibiti suke sallar magariba kawai tayi ta sake tashi. Sai da Salima tayi da gaske wurin hanata fita bata ci komai ba. A lokacin ne ta fadawa Zara abin da ya faru da Ayaah. Suka gama jajantawa sannan suka fita zasu tafi asibitin. Wannan karon dai Zara sam taki yarda su barta a gida. Ciwon dan uwansu da zai kai Uwani asibiti ko biyanta zai yi ba abin rainawa bane. Innayo ta girgiza kai kawai don bata ga alamun zata ji maganarta ba suka tafi. Basu wani sha wahala ba suka iso dakin da Uwani ta kwatanta musu. Mamakin ganin Salihi a wurin ne ya kama Innayo. Ya gaisheta da fara'arsa sannan ya bata kujerar da yake zaune. Sai da ta zauna sannan ta kalli inda Asabe take tayi lakwas. Ta kira kannin Munzali namijin mai suna Bature akan yazo ya kwana amma kememe yaki. Uzuri mara tushe ya dinga bata. Dama rabonta da ta sanya shi a ido an tasarma sati. Da dai rabon kudi yake ba zai yi fashin zuwa. Ummakati kuma mijinta yace dare ya yi za su zo gobe, duk da lokacin da aka fada mata shida bata karasa ba. A gidanta autarsu mace ta tare saboda kwadayi. Gashi mijin Ummakati yana mata kulle. Sai abin ya shafi kanwar da ya kula tana yawo. 'Ya'yan Innayo mata wadanda kullum take aibatawa tare da yi musu kallon rashin galihu sune a tare da ita. "Asabe ya mai jikin?" "Da sauki, gashi ya sami bacci." Dakin sai ya yi shiru tunda hirar kirki dai bata taba hada duka mazaunan cikinsa a lokaci guda ba. Uwani waya take yi da wata mai shara tana bata sautun irin abincin da za a siyo da adadin mutanen dakin. Jin haka Innayo ta ce, "Mu kam a koshe muke" "Sai a tafi dashi gida. Guda bakwai za ki karbo kinji" ta karkare wayar tana duban Qibdiyya wadda ke faman matse kafa. "Kina jin fitsari ne?" Ta tambayeta. Da ka ta amsa don ta matsu sosai. Tashi tayi domin ta kai ta sai Asabe ta riga. Dakin ya zame mata kamar akurki. Kwarjinin Innayo da zuri'arta yasa ta kara jin kanta kamar wata 'yar kora. Suna fitowa taji ance, "Barka da dare Asabe" Sakin fuska tayi da ganin fuskar da ta sani. "Barkanmu dai dannan. Shiga ciki ga dakin da aka kwantar dashi." Qibdiyya da ya gani tare da ita ya jefa tunaninsa a mizanin aune-aunen hanya mafi saukin bullewa. Babu bata lokaci kuwa ya cafki damar da ta zo gareshi da gaggawa. "Ina zaki je ne?" Hagu da damanta ta dinga kalla ta ce "wallahi inda zan sami piya wata (pure water) nake nema wai fitsari Qibdiyya take ji" Dan waro idanu yayi "babu bandaki a ciki ne?" "Ka san bangaren maza ne bai yiwuwa na shiga" "Haka ne. To bari na dauko miki a mota" Ya dan soma tafiya kenan ya tsaya. "Qibdiyya zo muje ki rakani" Wai aka ce tsaytsayi baya wuce ranarsa sannan mai halo baya fasawa. Asabe ta manta da halin da Qibdiyya take ciki har ta iya bari wani namijin ya tafi da ita mota. Sai da suka fara tafiya kawai taji kamar an sharara mata mari ta dawo hankalinta. Da gudu tabi hanyar da taga sun yi sai dai har ta isa wurin motocin babu shi babu alamunsa. Kin yarda da tunanin dauke mata jika tayi ta koma ta tsaya a inda ya barta tana jiransu. Bata jima ba kuwa su Innayo suka fito. Uwani ce karshen fitowa tana yiwa Nos din da ta rakosu godiya. A ka'ida tun shida ya kamata 'yan dubiya su fita. Amma ganin dan uwanta ne shi ne aka barsu. "Ina Qibdiyyan?" Zara ta tambayi Asabe tana gyarawa Salima goyon jinjirarta. "Ina fitowa naga wani abokin Munzali. Shi ne ya ce zai dauko piya wata a motarsa" "Abbati ne?" Innayo ce tayi tambayar. Kafin ma ta karasa Asabe ta girgiza kai. "Sunansa Shazali. Su kan dan zo gaisheni tare dashi jifa-jifa" Sai suka tsaya aka koma shawarar zuwa a dauko kukunsu Munzali ya zo ya kwana dashi. Minti shabiyar, talatin, talatin da biyar...a daidai mintuna talatin da bakwai da tafiyar Shazali da Qibdiyya sai ga Abbati ya fado gabansu kamar an jeho shi. "Ina Qibdiyya?" * Awa daya da rabi kafin zuwan Shazali asibiti gidansu Abbati ya fara zuwa. Rashin samun kowannensu a waya ya kawo shi gidan babu shiri. Kwana daya ya rage a lokacin da Comared ya bashi gashi ya kasa samun su. Yana zuwa maigida ya sanar da shi an kai Munzali asibiti. Hankalinsa kuwa ya tashi domin ya tabbata idan Munzali yana asibiti ba makawa Abbati ma yana can. Kenan ba shi da abin da zai tilasta musu zuwa don ko yafi kuda naci bai ga dalilin da zai raba Abbati da asibiti idan Munzali yana kwance. Wautar saurin tonawa Abbatin asiri da ya yi a wurin Baaba Mari ya gani. Ganin abubuwa suna neman rikice masa sai ya tambayi wani asibiti ne. Idan ya yi sa a suka fada tarkonsa na tsoron watsuwar sirrinsu a duniya kila ko Abbatin shi kadai ya je. Kuku ne ya kira Uwani domin ya karbi nambarta kafin su tafi bisa umarnin Abbati. A wurinta ya sami kwatancen da ya yi masa. Babu bata lokaci ya nufi asibitin cikin gaggawa. Sai da ya kusa shiga ya dinga kiran Abbati amma ba a dauka. Ya san za a rina saboda abubuwan da suka shiga tsakaninsu. Bai damu ba ya shiga da niyyar yi musu barazana. Da shigarsa kuma ya hadu da Asabe shi ne ya canja shawara ya gudu da Qibdiyya. Sai da ya yi tafiyar minti goma sha biyar ya tabbatar ya yi nisa da asibitin sosai sannan ya turawa Abbati message. (Idan kana son sake ganin Qibdiyya ka zo ka same ni a Guest house din Comared gobe.) * Kiran Shazali a wayar Abbati yafi goma amma yana sane yaki dauka. To me ya rage a tsakaninsu ma da zai sa shi yawan kiransa? Kunnuwan da yafi tsoron su ji irin gurbatacciyar sana'arsa sun riga sun ji. A tunaninsa babu wata sauran barazana da Shazali zai zo da ita wadda tafi tashin hankalin da ya gani a cikin 'yan kwanakin nan. Shi yasa yaki dauka domin alkawari ne sun bar shi har abada. Ba don son sanin halin da Munzali yake ciki ba ma da tuni ya kashe wayar tasa. Suna shigowa gari ya sami adaidaita sahun da zai kai shi gida. A gurguje ya shiga ciki ya fada bangarensa da sallama. Hanne ya gani tayi daidai a falo tana kallo. Sanye take da kayan bacci wadanda bashi da masaniya yau ta saka su ko tun na jiya ne. Kai ta dago ta ce masa sannu da zuwa ta cigaba da kallonta. A yau sai bai ga laifinta ba. Mutum irinsa ta yaya ma zai yi zaton cewa komai na rayuwarsa zai zo da sauki? In zai yi mata adalci ma a ganinsa ita din abar tausayi ce. Yana dai sauke hakkokinta dake wuyansa amma daga nan babu wata shakuwa ko soyayya. Laifina ne ya ce a hankali yayinda a zahiri ya tambayeta ya gida. "Lafiya lau" ita ce amsar da ta bashi ta mayar da kai ga tv. Bai tsaya a wurin ba ya karasa sama. Mukullin mota kawai ya dauko ya dawo ya ce mata zai tafi asibiti wurin Munzali. "A dawo lafiya" Daga nan bata kara cewa komai ba ta kuma mayar da hankalinta ga talabijin. Zamansa ke da wuya a mota Shazali ya sake kira. Da yaga sunan tsaki ya yi. Sai kuma ya kula da shigowar text da sunan Shazalin. Budewa ya yi yana mamakin bakin naci irin na wannan mutumi. Maigadi gani ya yi motar ta yo kansa gadan-gadan. Ihunsa ya dawo da Abbati hayyacinsa. Bai san ya saki hand break ba sai a lokacin. Cikin sauri ya tsayar da motar sannan ya leka da kansa ta taga. "Bude min gate da sauri" "Yallabai kamar bai dace kayi tuki a yanayin..." "Na ce ka bude min!" Ya fada da tsawa. Gumi kawai yake yi yana kiran Shazali wanda a lokacin banda kyakyata dariya babu abin da yake yi. "Shege ashe yana da hannun daukar waya" Kafin yaje nasa gidan Abbati ya kira sau ashirin da 'yan kai. Ya tura text yafi goma. Shazali dai dariya kawai yake yi kamar mahaukaci. Ba gidansa da su Abbati suka sani ya nufa ba. Wani dan karamin gida yaje a wata unguwa da bata gama cika ba. Kafin ya fita daga motar ya turawa Abbati sako ya kuma kashe wayarsa a take. (Aiki ne ya samu wanda yinsa ne kadai zai fanshi 'yarku. Idan kuma ka ki to ka kwana da sanin cewa ni Shazali zan sayar da ita ga duk wanda yake da bukata.) A motar ma ya kulle wayar da Abbati yake da layin ya dauki sauran biyun ya watsa a aljihu. Ya fito ya zagaya inda Qibdiyya take bacci ya dagota yaga ta jike sharkaf da fitsari. Sau biyu kafin tayi baccin tana sake tuna masa fitsari take ji. Daga baya ta soma kukan kiran Paapa da Daddy da Asabe har bacci ya dauketa. Tsaki ya dinga yi da kananun zage-zage. Baya son harkar yara ko kadan. Ba don kada ta mutu a motar ba da a ciki zai kulleta ta kwana. Haka nan ya sabata a kafada ya yi amfani da nasa mukullin ya bude gidan. Wani yaro matashi da bai fi shekara goma sha shida zuwa sha bakwai ba ya fito sanye da gajeren wando da fara'arsa zai tarbe shi. Ganin yarinya a hannunsa yaja tunga ya tsaya. "Zo ka karbeta mana" Shazali ya ce dashi da dan fada-fada. Yaro ya noke kafada harda buga kafa. "Wallahi ba zan karbeta ba sai na tabbatar ba 'yarka bace" Shazali ya yi dariyar jindadi ya mika hannu guda ya rungumo yaron a jikinsa yana bubbuga masa baya. "Da mace da buhun siminti duk abu daya ne a wurina. Basu taba burgeni ba balle a kai ga sha'awa..." Ya kashewa yaron ido. A falo ya kwantar da Qibdiyya suka shige daki shi da yaron suna dariya. (Mai karatu wannan yaron dan wata makarantar kwana ne ta maza. Shazali ya jima kwarai da daina mu'amala da idon sani. Ya kuma fi son yaran da suke ganiyar tasawa. Bisa shawarar wani abokinsa a irin wannan harkar suke zuwa makarantun kwana suna biyan masu gadi ko malamai sai a fito musu da yara. Wani zubin washegari yake mayar dasu da sassafe. Wasu ma basa kwana. Amma wannan yaron tun haduwarsu gabanin hutun makaranta ya kasa rabuwa dashi. Dubu hamsin ya biya ya dauko shi ranar da aka koma hutu wato lahadi. Yana so ya kai wata lahadin sannan ya mayar dashi. A cewarsa ya yi kewar yaron.) * Wani irin ciwon kai ne ya kama Abbati yayinda ya fahimci da gaske Shazali ya dauke Qibdiyya. Ga Asabe a gefe ta soma kuka tunda taga halin da ya shiga ta san babu lafiya. "Shi yaron ba abokinku bane?" Amsar da zai bayar yafi kowa sanin cewa karya ce. Sai dai karyar ita ce cigaban rufin asirinsu. Yana bayar da amsa yana mai Allah wadai da sana'a ko dabi'ar da muninta zai sa mutum ya dinga karya da gangan. "Abokinmu ne a baya. Rigimar kasuwanci ce ta hadomu. Ya cinye mana kudi ya kuma ki yarda mu hadu balle ya yi mana gamsashen bayani game da kudin. Shi ne muka yi masa barazana da zuwa kotu. Saboda yana so mu janye karar da zamu kai shi ne ya dauketa." "Amma anyi lalataccen yaro. Na rasa gane inda duniyar nan take dosa damu" cewar Innayo ita ma tana share kwallar tausayin dauke 'yar karamar yarinya. Salihi ya dafa kafadar Abbati ya ce "Zama bai kama mu ba. Muje a kai raport ofishin 'yan sanda" A razane ya dubi Salihi. Shigowar 'yan sanda cikin lamarin nan a yanzu ba komai bane zai faru illa allura da za ta tono garma. "Ya ce gobe naje na same shi tare da takarda mai sa hannu cewa mun yafe masa kudin. Idan ba haka ba zai sayar da ita. Ka bari naje tukunna mu gani. Idan ya saba alkawari sai mu nemi 'yan sandan. Yanzu ya kashe waya ne kawai saboda ya tayar mana da hankali sannan ba gidansa ya tafi ba." Zukatansu ba duka suka yi na'am da shawarar Abbati ba. Sai dai kuma sun san cewa a yanzu ko masu satar mutane suna gaggauta cutar dasu ne idan suka fuskanci hukuma za ta damkesu. Da wannan aka samu suka bar maganar haka. Abbati ya fadawa Uwani shi ne zai kwana da Munzali. Ya kuma jaddada musu mahimmancin iame bakunansu daga zancen abin da ya faru. In ya nemeta ace masa tana wurin Asabe. Hankalin kowa sai ya kwanta suka tafi gida ana tararrabin me zai faru washegari. A gaban gadon Munzali ya tsaya yana kare masa kallo. Ya zabge sosai kamar ba shi ba. Gashi dai bacci yake yi amma ana iya ganin yadda fuskarsa ta tattare kamar wanda ya fada tunani mai zurfi saboda damuwa. Tausayinsa ya sake kama shi da ya tuna abin da aka yi mata da dauketa da Shazali ya yi. Iska mai zafi ya fesar ya fita daga dakin ya koma mota. Ya dauko abin sallah sannan ya sayi ruwa ya dauro alwala ya koma. Tashin hankali ya hana shi jin yunwa. Da ya idar da sallar dorawa ya yi da nafilfili cikin kankantar da kai da cikakken tawali'u. Addu'oinsa basu da yawa sosai. Istigfari ce yake ta yi domin neman gafarar Ubangiji gare shi da amininsa. Idan sun samu rabauta ya yi imani komai zai zo da sauki. Asirinsu zai rufu, iyayensu zasu yafe musu. Sannan Allah zai tsare Qibdiyya a duk inda take. Yayi nisa cikin ibadarsa yaji muryar Munzali tana fitowa a hankali. "Ka yafe min ko zan sami sassaucin kunar dake raina." Dago kai ya yi suka hada ido. Abin da ya gani a idanun Munzali ya bashi tsoro. Irin yanayin nan ne da zaka ga mutum bashi da maraba da mutum-mutumi. Total hopelessness and helplessness. Mikewa ya yi ya ja kujerar gaban gadon nasa ya zauna suna kallon juna. Munzali ya zauna ya jingina bayansa da bango. "Ni kake cewa in yafe maka Munzali?" Murmushin karfin hali ya yi da yaga kamar ran Abbati ya sosu ya ce "To ko sai na durkusa?" "Ka ajiye wasanka muyi magana. Me zaisa ka ce na yafe maka bayan ni da kai muka yi laifin kuma Allah Ya kamata mu roka gafara?" Kodaddun idanun Munzali sai suka ciko da kwalla. Yana so ya yi magana ba tare da ya nuna karayarsa ba amma ya kasa. "Ina ta rokon Allah gafara kamar yadda ka ce amma zuciyata tana raya min tubana ba zai karbu ba. Ga nauyin zunubina ga na lalata maka taka rayuwar daga zuwa karatu." Rai a bace Abbati ya ce "dakata haka" Girgiza masa kai Munzali ya yi yana murmushi wanda ya koma kuka kafin ya kai karshen maganarsa "ka barni na karasa magana. Laifinmu yana da girma. Abin da aka kifar da al'umma guda a dalilinsa. Shi ne nayi silar fadawarka gare shi har muka mayar dashi sana'a. Wallahi zuciyata har kokonto ta soma akan amintarmu. Shin Abbati amincin Allah da Annabi ne tsakaninmu ko kuwa kazamar soyayya nake yi maka? So nake a shafe babina a doron kasa domin ban san waye ni ba. Da wannan nauyin kana tunanin har ina da darajar dukawa gaban Allah in roki gafara? Baka ganin tun yanzu na soma ganin bala'i? Qibdiyya me ta sani a duniyar da har ..." Abbati ma kwalla ya soma fitarwa yana ta girgiza masa kai don ya yi shiru. "Ka daina irin wadannan maganganun Munzali kada kayi sabo." "Sabawa Allah ai na riga nayi. Gashi yanzu ina jin kaina kamar mafi kaskanci a cikin halittun Sa. Idan na tuna kwanciyar kabari sai naji na karaya fiye da tunaninka. Abin da ya sami Qibdiyya bai min ciwo kamar tsoron mutuwata. Me zan ce da Allah?" Wani irin kuka Munzali ya fashe dashi wanda ya janyo makotan gadonsa a dakin suka fara kallonsu. Abbati ya gama sauraron dukkan zantukansa sannan ya kama hannunsa na dama ya rike. "Na rantse maka da wanda rayuwarmu take hannunsa gafarar Allah ta ninninka azabarSa. Sannan wadannan tunanin na banza da suke damunka ba komai bane illa wasiwasin shaidan. Idan ka bari rayuwarka ta kare a haka to tabbas zaka mutu cikin nadama..." Munzali ya galla masa harara ya ce "a dinga tauna harshe idan za ayi nasiha don likita ya ce jinina ya mugun hawa" Shi ma Abbatin harararsa ya yi yana jin kamar ya mangare shi ya ce, "Gara ka tsorata kada kayi min sanadin rashin samun wuri a karkashin inuwar al'arshi" Munzali sai ya yi kasake yana sauraronsa. Wannan ya bashi damar yi masa bayani gamsashshe. "Tsahon lokacin da muke tare cikin sabon Allah kai shaida ne ina yawan karatu. Karatun ne ya taimaka min wurin kara fahimtar munin abin da tuntuni muka san haramun ne. Shi yasa na damu da son mu tuba. Amma kafin na cigaba da magana zan yi maka tambaya guda daya. Kana jin da bamu tuba ba za ka iya yin mu'amala dani Munzali?" Wata irin zabura ya yi ya ce "A'uzubillah minash shaidanir rajim" Abbati ya ce "to Shaidan sai a nemi wani gaulan wannan dai ya tsira" Dole Munzali ya yi dariya. Abbati ya yi murmushi ya dora da cewa "Masha Allah. Abotarmu ta Allah ce ba ta shaidanci ba. Da ace zukatanmu suna marmarin haka a tsakaninmu to ina mai tabbatar maka tubanmu ba zai cika ba sai mun nesanta da juna kamar yadda Baaba ta fara bamu shawara domin samun nutsuwar zuciya" Munzali ya hau ambaton "Alhamdulillah" da yaji wannan bayani mara wahala. "Abu na biyu kuma mafi mahimmanci shi ne ka daina raina rahamar Allah. Ta yaya ma za ka dinga tunanin ba zai yafe maka ba bayan ya yi alkawarin gafara ga bawa idan ya tuba. Inda na karanta fa cewa aka yi zunubi ko ya kai kumfar kogi Allah zai yafe idan aka tuba." Cikin rauni Munzali ya sake cewa "Amma gafarar ba sai ga wanda yaso ba? Idan bana ciki fa? Alfarmar wa zana hau a cikin mutane wanda zanci albarkacinsa har a yafe min?" Abbati ya dauke duk wani burbushin fara'a a fuskarsa ya ce "in ka sake magana wallahi sai na bata maka rai. Ta yaya ina fada maka girman Allah kana dawo da hannun agogo baya? Tudun da za ka ci ya wuce na kasancewarka daya daga cikin halittun Allah? Ko kana tunanin akwai wanda Allah zai yafewa zunubai a dalilin aikin wani ahalinsa alhalin shi bai mika wuya da gaskiya ba? Tsarki ya tabbata ga Sarkin da yake yafewa bayi a kan kowane zunubi indai sun tuba. Munzali da za ka tuba yau gobe ka komawa zunubi ka sake tuba zai yafe maka (hakan ba yana nufin bawa ya yi ta wasa da damar tuba bisa izgilanci da tunanin gobe ma za a yafe masa ba. Idan mutuwa ta wafce mutum a cikin halin sabo kafin ya tuba shikenan!). Kai..." Ya tabo kafadar Munzali domin ya sami cikakken hankalinsa a tare dashi "akwai wani sahabi kuma surikin Annabi SAW mai suna Abu Sufyan. Ko ka san irin taskun da suka sanya musulmi kuwa? Yana cikin jagororin yakin musulunci na farko wato Badar. Matarsa kuma a yaki na biyu (Uhud) ta hayi wani ya kashe mata kawun Manzon Allah SAW. Kawunsa fa wanda yake matukar so. Sunansa Hamza. Kuma bayan an kashe shi aka ciro mata hantarsa ta tauna. Sannan ta lalata gawar ta hanyar yayyanka sassan jikinsa. Da Allah baya yafe laifuka da bai basu damar karbar musulunci ba duk su ukun." Zaro idanu Munzali ya yi "sun musulunta?" Abbati ya gyada kai "da Abu Sufyan din, da matarsa (Hind bint Utbah) da wanda ya yi kisan (Wahshi ibn Harb) na dai manta sunayensu. Amma wallahi duk sun shiga inuwar musulunci kafin su bar duniya. Sahabbai ma suka zama tunda sun rayu da Annabi SAW. Duk sahabi daya kuwa darajarsa ta ketare tamu akan kowane aikin ibada." "Allahu Akbar" cewar Munzali da wani irin shaukin fahimtar addininsa. "Dalla can. Sau nawa ina kawo mana littafin tarihi kana kin karantawa sai aukin danna waya?" "To ai dai na daina. Ni islamiyya ma zan shiga wallahi." "Zamu shiga dai. Kaga irin wannan kambana girman zunubin da jin kamar baka da rabo ba komai bane illa aikin shaidan. So yake mu dauwama a zunubi. Idan muka tashi tuba kuma ya nuna mana kamar laifinmu yafi karfin a yafe mana. Kaga imani sai ya sami rauni. Muje lahira ..." "A tutar babu" Munzali ya karasa masa. Maimakon su kwanta sai suka koma tattauna abubuwan da suka danganci laifi da tuba. A nan ne Abbati ya sake fayyace masa kowane bawa da aikinsa zai dogara ba kusancinsa da waliyyi ko asharari ba. Ya bashi misali da tarayyar Fir'auna da Asiya Allah Ya kara yarda da ita. Ga Annabi Nuhu AS da Annabi Lud' AS da matansu wadanda Qur'ani ya tabbatar mana cewa 'yan wuta ne. "Duk da haka amma fa musulmi masu imani suna cin darajar juna indai kowannensu ya yarda Allah da zuciya daya. Misali wanda dansa ya mutu kafin shekarun balaga indai yayi hakuri akwai sa ran dan zai cece shi (ina kara mika ta'aziyya ga Ummu Sadiq da Ummu Abdurrahman na Sparkling, Sanah Matazu Fikra da Halima Siyama H2H da duk wadanda suka rasa 'ya'ya. Allah Yasa rashin da muka yi masu ceto ne a garemu) , ko idan kana da d'a hafizin al-Qur'ani zai daga darajarka a aljannah. Sannan Allah zai bawa wasu ceto ranar lahira" Bakin Munzali a bude har Abbati ya gama magana sannan ya ce "to wai ni ina ina ka tara wannan ilimin? Wallahi ganinka nake kamar wani shaihin malami." Dariya babu shiri ta kama Abbati ya ce masa "Allah Ya shiryeka. Babu bashin salloli akan ka ko?" "Akwai wallahi" ya amsa yana mai jin kunyar kansa. Da taimakon Abbatin ya shiga bandaki ya yi alwala. A zaune ya gabatar da sallolinsa ya jima yana neman gafarar Allah. Sa'annan ya hada da godiya da Ya hada shi da Abbati. Lallai a cikin abota akwai riba idan an dace. Kuma masu cewa zama da madaukin kanwa yana kawo farin kai basu yi kuskure ba. Halin da ya tsinci rayuwarsa ya yi jirwaye a rayuwar Abbati. Yanzu kuma an zo wakafin da halin rayuwar Abbatin zai wanke musu duka jirwayen. Karatu ne ya kawo Abbati Kano kuma cikin kudurar Allah Ya samu ya yi. Babbar illar da ya samu ita ce ta rashin idon mafadi da rashin kulawar iyaye a shekarun da ake bukatarsu. Allah Ya hada shi da mutum mai saukin kai da tausayi irin Munzali. Da ace Munzali ya tashi da kulawar iyaye tabbas da an yi bawa mai yawan kyautatawa na kasa dashi. A cikin halin kuruciya da rashin ilimin da iyaye suka barshi ya iya janyo almajiri jikinsa. Ya nuna masa sana'ar da yake yi domin yaci abinci. Sannan bai taba yi masa hassada ko kyashi ba. Wannan rayuwar bata hana Abbati cigaba da karatunsa ba wanda zamu iya alakanta shi da yawan addu'ar da mahaifiyarsa take yi masa da nasiha. Shi ne yaja hannun Munzali zuwa makarantar yaki da jahilci. A gefe guda yana ta bibiyar duk wani littafin da ya danganci addini wanda zai iya karantawa. Zuciyarsa bata nutsu da sana'arsu ba sai dai kuma a lokacin bashi da karsashin son su barta ko don kudin da suke samu. Munzali bai taso da akidar karatu daga wurin uwa da uba ba shi yasa baya ma mararin karanta irin litattafan Abbati. Ashe zasu yi musu rana. Ashe abotar irin wadda ake fatan ta kai ma'abotanta karkashin inuwar al'arshi ce. Da ya shafa addu'arsa bacci Abbati ya tilasta masa yi. Yana son jin bayani game da fyaden da aka yiwa Qibdiyya sai dai dan saukin da Munzali ya samu yana bukatar a tattala shi. Tambayar damuwa za ta dawo masa da ita. Haka ya hakura sai dai har gari ya waye bai rintsa ba. Yana ta faman tufka da warwara akan yadda ya kamata ya fuskanci Shazali. *** Alh. Rabi'u ya dawo gida daga wurin da suke buga karta da abokansa shadaya da rabi na dare. Innayo dama ba kwana gareta ba. Babbar rigarsa ya cire ya nufi bangaren Asabe. Kudi yake so a wurin Munzali ya kasa samunsa a waya. Ba za a rasa wani abu a hannun Asabe ba ko yaya ne. Shi ne ya taho da dan kunshin tsirensa ya kai mata. Ko kallo ledar bata isheta ba har ya ajiye. Rashin kulawarta ya bashi mamaki domin ko mage bata fita jin kamshin nama ba. Ledar ya kama ya shiga kwancewa yana 'yar dariya. "Hala mura kike baki ji yadda kamshin tsiren nan ya cika dakinki ba. Nace wai ina Munzali ne kwana biyu" A hautsine ta kalle shi da jajayen idanunta tana kada kai. "Ga mayya ba. Ai dole in juyo tunda maigida ya kawo nama" Ledar ya dire ya kare mata kallo a tsorace sannan ya ce "wani abin Innayo tayi miki?" Asabe bata amsa ba sai ma juya masa baya da tayi. Da ya san yadda zuciyarta take a jagule da ya fita ya bar mata dakin. Shi kuma a wautarsa sai ya zata da gaske Innayo din ce. "Ai kuwa yau daga ita har wadancan zaurawan da ta tara a dakinta ba za su kwana lafiya ba." Hanyar fita yabi Asabe ta tashi tayi saurin dakatar dashi da taji ya fara kiran sunan Innayo. "Dakata min Malam don wannan hargagin naka ba zai burgeni ba. Innayo kuma da kake magana da taron zaurawan dakinta a yini guda sun yi min abin da baka taba yi min ba a iya tsayin shekarun aurenmu. Duk wanda ya damu da naka ba don abin hannu ba shi ne cikakken masoyi." Kirjinsa ya shiga nunawa cike da kokonto yana cewa "dani kike Asabe?" Dama can zuciyarta tana wuya. Wannan borin kunyar nasa sai ya kara tunzurata. Da yatsa ta nuna shi tamkar dan cikinta. "Da kai nake Rabi'u. Da kai nake sako tumaki ballo jakai." Tas ya dauke fuskarta da wawan mari yana huci. "Ni kike zagi a cikin gidana?" Ita kuwa rike kumatu tayi tana kuka ta ce, "An zageka din. Wannan ginin kuma billahillazi ba gida bane. Gida ai inda miji da mata suke tattalin 'ya'yansu ne. Nan kuwa bashi da maraba da bariki gidan ka zo na zo. Gara ma Innayo tana yiwa 'ya'yanta. Amma da yake jini baya karya ai bata fara jindadinsu ba sai da duniya ta koya musu hankali. Sun so gadon bakin hali a jikinka ba don Allah Ya tarfawa garinsu nono ba." "Wai Asabe ko kin fara shaye shaye ne?" "Zancen kake so kuma zan yi maka shi filla-filla. Munzali yana kwance a gadon asibiti. Jiya ya yi min wasu zantuka da na kasa fahimtarsu amma sun yi matukar razana ni. Sannan wani dan iska ya yiwa Mariya fyade kuma an saceta ma amma duk halin da muke ciki babu wanda yaji a ransa wai ya kamata a sanar da kai. Saboda me?" ta sake nuna shi da dan allinta "saboda kai da babu sammakal. Amfaninka daya a gidan nan shi ne ka yiwa mace ciki ta haihu..." Tunda suka fara rigimarsu Innayo, Salima, Zara da Uwani suka yi shiru suna sauraronsu. Kalmar Asabe ta karshe ta janyowa Zara da Salima harma da Innayo muguwar kunya. Su biyun suka tashi suka shige daki da dimbin mamakin fyaden Qibdiyya. Uwani kuwa ko gezau ta cigaba da zama tana kallon yadda Innayo ta takura. Kofar dakin da su Salima suka shiga tabi da ido ta ce, "Ai ba karya tayi ba duk suka wani watse don munafunci." Innayo ta kada kai ta ce "Uwani kenan" Ta kuwa yi kicin kicin da fuska "to banda sunansa da muke karawa a gaban namu akwai wata riba ne?" Kafin ta dauko abin da zai karasa kunyata ta sai ta tambayeta ko tana da masaniya game da abin da Asabe ta ce ya sami Qibdiyya. Nan da nan fuskarta ta canja kuwa. Al'amarin da ya faru tun zuwanta gidan na farko ta labartawa Innayo. Bayan ta gama gani tayi Innayo din tayi ajiyar zuciya amma bata ce komai ba. "Kin san wani abu ne akan abin da ya same shi?" Da hanzarinta ta girgiza kai "ko kusa. Kawai dai ina rokon Allah da Ya kawo mana komai cikin sauki ne" Uwani bata gamsu ba ta ce "amma na fada miki cewa ya dinga yi ta yafe masa wai laifinsa ne" "Duk iyayen da suke kaunar 'ya'yansu suna dorawa kansu laifi ne idan wani abu mara dadi ya faru dasu." Ita ce amsar da Innayo ta bata. A fuska kuwa kana iya gane zancen ya tayar mata da hankali fiye da yadda take son nunawa. Mikewa Uwani tayi ta dan bata rai "da yake ba su Hasiya bane sai nema kike ki katse 'yar hirar da na samu kina yi dani." Tayi hanyar daki "Bari naje na mike bayana yau na sha tsayuwar aikin lada. Allah Yayi mana albarka." Innayo bata san lokacin da ta tuntsire da dariya ba. Uwani tayi kasake tana kallonta. Abin sai ya taba mata zuciya fiye da zatonta. Ji tayi kamar an tsikareta a kahon zuci. Bata san tayi kewar fara'ar mahaifiyarta ba sai yau. Yaushe rabon da taga ko murmushi ne daga Innayo akanta? Bayan ta gama dariyar ta ce "Allah Ya bada lada Yayi albarka". Kafin Uwani ta sami damar magana ta tashi ta shige bandaki. A ciki ta share wata kwalla ta bata ma san ta taru a idanunta ba sai yanzu. Da a wuri mai tsarki take tabbas babu abin da zai hanata sujjadar godiya ga Allah. Bayan shekaru masu yawa ace wai ita ce take hango yunwar mahaifiya a idanun Uwani. 'Yar da tasa kafa ta take duk wani kusanci dake tsakanin uwa da 'yarta. Uwanin da take nuna mata kyama kirikiri saboda ta sami abin duniya. Kaico! Duniya abar banza. Dan adam ya yi ta daga kafada yana nuna izza a doron kasa. Lokaci guda Allah Yana nuna masa iko sai ya yi lakwas. Tana son furtawa Uwani kalmar yafiya sai dai tana tsoron kada a koma gidan jiya idan duniyarta ta sake zukar iskar wadata. Wanka tayi amma har ta fito tunanin rayuwa bai barta ba. Munzali da Qibdiyya ne a ranta fiye da komai. Bata son fadawa kowa ne amma ta dade da dora alamar zargi akan sa. Yaron da bai yi boko ko islamiyya ba sai yawo cikin unguwa ace lokaci guda ya yi kazamin kudi. Tabbas da dan cikinta ne da ta jima da kwankwasarsa akan sana'arsa. Shi kuwa yanayin gidansu yasa ta kame bakinta. Tun da ta taba magana Asabe ta ce ta saka masa ido ta janye jikinta. Banda Allah Ya taimaka da kansa ya sake waiwayo ahalinsa da yanzu haka zai shiga halin nan shi kadai. Dalili mai karfi ne zai sa ya ambaci fyaden Qibdiyya a matsayin laifinsa. Kamar Baaba Mari sai gashi ita ma tana tunanin ko sata yake yi. * KWAYAYE ZASU FASHE...tabbas dole su fashe ko sakon da nake burin isarwa a karshen labarin da yardar Allah zai sami damar bayyana kansa. Ku dakaci shafukan karshe masu zuwa gareku soon in sha Allahu. Jazakumullahu khaira I just published "40" of my story "UWA UWACE...". https://www.wattpad.com/1221353320?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=BatulMamman17&wp_originator=NYezbORxrG%2Bh%2BigXx3DygdDpPU0OhBETkTnfRmjQZewRsbUh%2F0BZd4OGN8VCL3tmlLZfj4%2BWNmhHzFlgcXZlsN7%2FqVYIdxEMPJ4W3EGm5KsQVuVFxQaVt%2BcUvr%2FAdNp%2B UWA UWACE...40 Batul Mamman💖 EID MUBARAK~Kullu amin wa antum bikhair. An sha jira. Ayi hakuri ba da niyya bane. Yanayin chanjin rayuwa ne wanda ya zama silar birkita yadda mafi yawanmu muke sarrafa lokutanmu. Fatanmu Allah Yasa mu rabauta duniya da lahira. Littafin UWA UWACE tukwici ne ga dukkan masu karatun da suka sha jiran kammaluwarsa. Musamman masu kira da turo sakonni ta whatsapp, wattpad da instagram. Kun yi min halacci. Nagode H2H The Queens KDM Sisters The Sparkle Antina Prof. Asabe Habiba (Mantis kitchen) Lubabatu S. Shayi Maman Fatima Aisha Lagos Mamin Fadil Pherty BB Anti Fauziyya Bindawa Anti Binta DB Anti Samira DB Da sauran da ban sami damar ambata ba duka nagode. ***Safiyar Talata*** ~A gidan Innayo ita da 'ya'yanta sun yi sammakon tashi domin hada abincin asibiti. Gabadayansu 'yan dakin babu wadda tayi baccin kirki saboda batan Qibdiyya. Duk sun matsu da son ganin an dawo da ita lafiya a yau kamar yadda Abbati ya sanar dasu. Asabe da Alh. Rabi'u kuwa tun rigimar da ta barke tsakaninsu da daddare babu wanda ya kara jin duriyarsu. ~Gidan Mami Khadija kuwa ita da Lilu tare da Farha ne a mota suke shirin tafiya Kano. Sai da gari ya waye su Sauda na shirin tafiya makaranta sannan Mami ta ce da Farha ta shirya. Basu da niyar kwana sai dai ita tafiya ta Allah ce. Shi yasa suka dauki kaya na kwana dai-dai koda bukatar hakan zata taso. ~Baaba Mari ta tashi da karfin jiki a yau har taji zama ba nata bane alhalin Abbati da Munzali suna cikin wannan yanayi. Bata ma da labarin dauke Qibdiyya amma taji zancen kwanciyar Munzalin a asibiti. Garin Allah na wayewa ta nemi izinin Mal. Inuwa. Da ya so hanata saboda yanayin jiki sai ta dage ba za ta iya zama ba. Muryar Munzali a lokacin da ya fada mata abin da aka yiwa takwararta da ma rokon gafararta da yayi suna ranta. Tare suka shirya domin lokacin sakar mata ragamar 'ya'ya ita kadai ya riga ya wuce. Makauniyar biyayyar da yake yiwa Mal. Sa'idu bata yi masa rana ba. To kuma sai Mal. Sa'idun ma ya ce zai je. Haka aka fito dashi ba yadda yake ya zauna a gaba da yar sandarsa. ***** Damuwa ce karara a fuskar Zakiyya lokacin da ta tashi daga bacci. Irin baccin nan rabi da rabi wanda kusan duk abin da ake yi a kusa da mutum zai ji tayi. Ba komai ya haddasa mata wannan rashin kwanciyar hankali ba sai rashin dawo da Qibdiyya da Munzali ya yi. Indai ba lokacin hutu ba a ka'ida bata wuce lahadi idan tana wurinsa. Hutun da ya wuce da bai zauna a gari sosai ba da kansa ya maidota kafin a koma makaranta. Sai kuma daukarta da Abbati ya yi ranar Juma'a. Tunda kowa ya san litinin za a koma makarantu ta zata zai yi aiki da hankali. Daren lahadi tunda aka yi isha take kiransa shiru baya dauka. Litinin ma haka. Yau gashi talata. Me yake nufi? Tana can duniyar tunani bata ji shigowar Ummansu ba sai da ta kai mata duka a kafada. "Raba kanki da yawan tunani tun da kananun shekaru ba alkhairi bane" ta sami wuri kusa da ita akan gadon ta zauna sannan ta cigaba da magana "wai akan rashin dawowar Qibdiyya ne kika kasa baccin safen naki na jaraba?" Kwabe fuskarta tayi ta ce "Umma daga cewa zata kwana biyu sai in ji shiru sannan yaki daukar waya?" Maganar haushi ta bawa Umman ta ce "tunda dawa ta tafi ai dole ki tada hankali." A sanyaye Zakiyya ta ce "ba haka bane. Kinsan makarantarsu da tsauri. Yanzu sai kiji ana cewa za a maye gurbinta da wani dalibin idan bata dawo ba." "Na dauka don Allah kika damu da ita ashe don tijarar makarantarsu ne. To Allah Ya kyauta. Kin bi kin sakwarkwace daga haihuwa daya. Babu wani kulawa sai aukin hada lanci bus (lunch box) a kai yarinya makaranta." Ta mike tana tabe haki "Sai ki sake kiransa ko ita Yaya Asaben don ni dai babu wanda zan nema." "Umma na sakwarkwace fa kika ce?" Zakiyya ta ce a shagwabe. Da fada Umman ta karanto mata abin da yake damunta wanda a karshe ta kai ta daga murya sosai. "Yo sakwarkwacewa mana. Da kina da kula sosai akan abubuwa amma yanzu idan kika fara danna waya da kyar kike tashi sallah. Kin bari ta namaye miki rayuwa baki da katabus kan lamuran rayuwarki. Yarinya daya ba don ina gidan ba ni ban san yaya zaki yi da ita ba. Maganar gaskiya ko yau Munzali ya yi aure ya bukaci 'yarsa wallahi ko ba kya so sai na bashi. Kulawar da take samu in taje hutu ta ninka taki kuma kema kin sani. Shi ne zaki wani dami mutane don ta kara kwanaki don wawanci? Mtsewww" Fadan Umman bai karawa Zakiyya komai ba face sake shiga rudani. Tabbas tafi kowa sanin yadda taja baya wurin kula da 'yarta. Mafarkinta na jiya ya sake dagula mata lissafi. Ganin Qibdiyya tayi a yanayi mara dadi har tana neman taimakonta. Anya idan ta cigaba da zama ba za ta amsa sunan sakarai bayan wawiya da Ummanta ta kirata a cikin fada ba? Da wannan tunanin ta mike a gurguje tayi wanka ta shirya. "Sai ina kuma?" Cewar Umma ba tare da ta sakar mata fuska ba. "Gidan zanje in daukota" "Yanzu ba za ki bari ya dawo da ita don kansa ba?" "Umma gara inje dai. Daddy zai kaini" Cikin minti goma sha biyar Daddy da Zakiyya suka dauki hanyar gidan Munzali. *** Alh. Sadisu Nakano rikakken dan bangar siyasa ne wanda ya iya takunsa a wajen iyayen gidansa. Da abin da ya dinga tarawa a jikinsu ya hada jarin da ake yi masa kasuwanci kala kala. Duk fadin Kano babu wanda zai ce bai taba jin sunansa ko labarinsa ba. Yana da baki kamar reza. Idan ya sako mutum a gaba to kashinsa ya bushe. Idan yana yi da kai kuma da wuya ka fadi takara ma. Da karfin cin tuwo ya mayar da kansa uban 'yan siyasa da 'yan jagaliyarsu a Kano. Mutum ne shi wanda baya yafiya, komai daren dadewa sai ya fanshe idan aka yi masa laifi. An alakanta shi da muggan laifuka iri iri wadanda suka hada da safarar hodar ibilis da yankan kai saboda kudinsa da k'aurin suna. Gashi bashi da tsoro ko digo. Kai har cewa aka yi ya taba sawa an dauko masa gwamna cikin dare ya yanka masa warning akan wani kuduri da ya sabawa aikinsa. Jita jita mara dadi kullum cikinta yake. Wata gaskiya ce wata kuma ana kara gishiri. Duniyarsa dai tana garawa yadda yake so ta kowane fanni illa lamarin zuri'a. Dansa daya mai suna Abdul. Yana ji dashi kamar rai. Matansa hudu amma ta biyun ce ta haife shi. Sai dai wani abu na ban mamaki shi ne duk irin kishin gidan gabadaya matan suna kaunar Abdul. Kowacce tana kokarin faranta masa ko don gyara fadarta a zuciyar maigida. Saboda yanayi na sa ido daga abokan hamayya a dalilin karatowar zab'e da rashin tsaro Alh. Sadisu ya dauke Abdul daga makarantar da yake ya mayar dashi zuwa wata 'yar kadaran kadahan ta kwana. Masu matsayi irin nasa a jam'iyun gaba suna neman sako shi a gaba ta hanyar dansa. Duk wata yana bayar da kudi mai tsoka domin a kula masa da gudan jininsa. Burinsa ya kai shi waje da zarar ya gama sakandire. A makarantar aka sami wadansu fitinannu suka koyawa Abdul mummunar dabi'ar luwadi. A nan ne kuma malamai marasa tsoron Allah da hadin bakin maigadi suke sana'ar tura kyawawan samari masu wannan hali wurin shaidanun mutane a waje. A takaice dai, Abdul Sadisu wanda aka boyewa inkiyar Nakano yana gidan Shazali! A washegarin da Qibdiyya ta kwana a gidan shashancin Shazali ta tashi ne da kuka. Ta waiga hagu da dama bata gane inda take ba ga sanyi sanyin safiya sai ta fara kiran iyayenta. A lokacin Abdul ya fito daga wanka kenan. Falon ya fito ya sameta a bakin kofa tana bubbugawa da karfinta. Sai ta bashi tausayi. Ya san ba huruminsa bane yin bincike akan duk wani abu da ya shafi personal rayuwar Shazali. Duk da haka sai yaji ba zai iya dauke kai daga yarinya karama irin wannan ba. Me ya hadata da Shazali har ya kawota gidansa? Nufota ya yi da dan murmushi ya ce "Zo, ya sunanki?" Ai tana juyawa da ta ganshi da tawul a kugu sai ta firgice fiye da ganin kanta a bakon wuri. Uncle Daddy ne ya fado mata a rai taji tsoron ko shi ma abin nan yake shirin yi mata. Da yaga yadda ta tsorata sai ya yi nufin tuntubar Shazali domin a bata koda shayi ne tasha. Yana kawo kai yaji wayar da shi kanshi ta kada masa ciki har ya kasa motsi. * Comared yana kwance tsakanin 'yan mata biyu yaji kiran Shazali. Rabonsa da gidansa yau kwana uku. Ya sanar da matansa ya tafi Lagos aikin sati daya. Basu san yana garin a guest house din da kalilan ne suka san da wanzuwarsa. Muryarsa a shake kamar basamuden kwad'o ya ce, "Shazali ya ake ciki?" "Comared an samu sai dai ina rokon idan da hali yazo ayi yau dinnan kawai. Da kyar na sami kan mutum daya daga cikinsu don sai da na hada da dauke musu yarinya" "Dauke 'ya kuma Shazali? Nifa bana son abin da zai je ya dawo gareni." Shazali ya yi dariya ya ce "kada ka damu. Akwai tamu dasu ne. Yarinyar ce kadai tikitin samun hadin kansu. Da azahar zamu zo." Comared ya shafa kurcin cikinsa yana dariyar shakiyanci. "Idan bai sami zuwa ba ni ka kawo min yarinyar na dana mana." "Comared bata fi shekara shida ba fa" "Irinsu sunfi...kai dai kawai nayi shiru. Ni dai ina so" "An gama. Zan kawota indai bai zo ba. Amma sai dai daga wurinka a san inda za ayi da ita don babu hannuna kuma." Jikin Abdul ya yi mugun sanyi da ya fuskanci girman abin da ke gaban Qibdiyya. Kafafu babu kwari ya koma da baya da sauri ba tare da ya shiga dakin ba. Bai san tun tsayuwarsa Shazali ya ankare dashi ba. Da ya fito ya kusa dariya ganin Abdul ya firgice a kokarinsa na son basarwa, shi a dole bai ji komai ba. Duk yadda yake son yaron dole ne ya dauki mataki a kansa tunda har ya san gidansa. Da niyarsa yace masa tsintota yayi kawai a bar maganar a haka. *** Bayan Alh. Tahir ya gama waya da Comared bashi da zabin da ya wuce bin hanyar Kano a yau dinnan. Bayani daya aka yi masa shi ne cewa yau da yamma mutumin da zai zo suyi abin zai yi tafiya zuwa wata kasa. Shi kuma Comared a cewarsa wai shi kadai ya sani wanda zai rike musu sirri a kankanin lokaci. Sannan tunda shi din bai saba ba dole aka nemo masa kwararre. Har zuciyarsa yake kyamar wannan abu to amma idan ya tuna da kalaman mahaifiyarsa akan auren Yumna sai yaji wani irin kwarin gwiwa. Ko ta wane hali sai ya kifar da maganar aurenta sannan yaci mata mutumci akan wulakanta shi da tayi a gaban 'ya'yansa. Allah wadaran bariki. Banda haka me zai sa yarinyar da take durkusawa har kasa ta gaishe shi ta koma abokiyar sa'in'sarsa? Har ta kai yana fada tana fada. Yau da ta halali ya nemi aurenta komai son da yake mata ya san dole ta bashi girmansa na mijinta kuma sa'an uban da ya haifeta. Suna hanya da direbansa ya kira Mami Khadija ya fada mata aikin da zai yi a Kano ya dawo yau. Zai fara zuwa duba Suhaib da sun shigo gari sannan ya wuce. Tana jiran ya fara ajiye wayar bayan tayi musu fatan sauka lafiya su duka sai taji ya fara cigiyar 'ya'yansa. "Bani su mu gaisa" ya tambaya da dan jin nauyi. "Lilu yana tuki, Farha kuma tayi bacci" ta kashe wayarta bata jira taji me zai ce ba. Su biyun duka sai suka juya bayan motar inda take zaune ita kadai suna kallonta. Ta dauke kai abinta ta lumshe idanu tana 'yan tunane tunanen da suka zame mata jiki. Idanunsu da ta dinga ji jifa-jifa yasa tayi dan murmushi ta bude nata a kansu. Ba shiri suka mayar da kallonsu gaba lokaci guda. "Lilu rami kake son tura mu ne kake kallon baya haka?" Kai ya shafo da 'yar dariya "wane ni in kai Ya Farha rami saurayinta yasa a kulleni?" "Dama ka gama raina ni shi yasa ka rasa amsar fada sai wannan" cewar Farha tana kai masa duka shi kuma yana karewa. "Bana son ganganci ana tuki." Nutsuwa suka yi na dan lokaci kafin Lilu ya soma magana. "Wai Mami musulunci ya wajabtawa mata zama da miji mai bin mata ne?" Gaban Farha ya fadi da tsoron kada Mami ta zata ita ta sanar dashi abinda ta sani. Ta kalle shi ta kalli Mamin a fakaice. To shi ma din bakinsa ya rufe da hannu saboda shirmen da yake tunanin ya yi na maganar a gaban Farha. Yadda suka koma kallon kallo suna tuhumar juna da ido sai kawai Mami Khadija ta ce "don Allah ku rike sirrin nan kada ya kai kunnuwan Sauda da Mardiyya. A kalla ko su biyu ne a samu su dore da yiwa mahaifinku kallon nagartaccen uba." "Ya Suhaib ya sani?" Farha ce tayi tambayar sai dai kafin ma taji amsar Mami ta fahimci ya sani din. Biri yayi kama da mutum. Tsahon lokaci suna mamakin rashin shakuwar babansu da babban wansu duk yadda Abban yake da jan yara a jiki. Abin ya dade yana damunsu. Ashe ba a banza ruwa ya yi tsami ba. Tunda Mami Khadija ta rufe ido bata kara cewa dasu uffan ba. A tunaninsu tayi bacci ne shi yasa suka fadawa juna abin da suka sani. Farha harda kwalla. Tana jinsu suna ta maganar mutum mafi soyuwa a garesu a 'yan kwanakin baya da sigar kyama da bakinciki. Me yafi wannan tashin hankali da ciwo a wurin uwa? Ashe zaman da iyaye suka tursasata ake yi masa kallon rufin asirin miji fanko ne? Da ta bar gidan sun yi nesa dashi da matukar wuya su san halinsa. Ko sun sani ba zai musu ciwo kamar yanzu ba da suke rayuwa tare suna yi masa kallon nutsatstse. Da karshenta yana nan da darajarsa ta uba. Duk lalacewarsa mijinta ne shi dai uban 'ya'yanta. Babu yadda za ayi uwa tayi maraba da raini ko tsana ta gifta tsakanin mijinta da 'ya'yansu. Uwaye da dama sun sadaukar da manyan burikansu domin 'ya'yansu su tashi a happy home. Ayi ta jure mugun halin miji domin kada gurbin mahaifi ya sami tawaya a rayuwar yara. Ita dai sadaukarwar bata yi mata rana ba. Amsa sunan matar fasiki mai gadara da sab'on Allah ba hakuri bane....! (Ya Rabbi kada Ka jarabcemu ko mazaje/matayenmu da alfasha. Wadanda Ka hada da fasikai Ya Allah Ka basu ikon daukar matakin da zaka yi farinciki dasu rana gobe kiyama. Amin) Hukunci ta yanke a take a zuciyarta. Wannan karon babu gudu babu ja da baya. *** Karfe bakwai Abbati ya gama kimtsa dan abin da ba a rasa ba mallakinsu a dakin asibitin. Munzali ya kafe kai da fata ba zai kuma kwana ba. Jinyarsa ta ruhi ce ba gangar jiki ba. Idan zai sami nutsuwa a zuciyarsa babu abin da zai hana lafiyarsa dawowa. Sai shadaya da kwata da likitoci suka zo round aka sallamesu. Tare suka tafi gida da Innayo, Salima da Uwani. Sai kuma Salihi wanda shi ma da wuri ya iso saboda kwana da suka yi da fargabar halin da Qibdiyya take ciki. Asabe bata zo ba suna gida ita da Zara saboda Abbati yace ta zauna a gida a matsayin tana kula da Qibdiyya. Da suka fito zasu tafi ya kasance inda Abbati ya ajiye motarsa da tazara da inda Salihi ya aje tasa. Abbati sai ya ce su Innayo su shigo motarsu. Idan gida zasu koma zai kai su. Baya suka fara shiga sai ga Salihi ya zo bangaren da Uwani take ya yi mata magana. "Muje ina son magana dake." Tsuke baki tayi sai da Innayo ta leka tayi mata kallon da ya sanyata bin sa babu shiri. Munzali yana fama da kansa amma hakan bai hana shi yin dariya ba. "Wai ni Uwani yaji tayi ne kamar wata karamar yarinya?" "Kaima ka fada Munzali. Sai kun taru kun sauke mata Al-Qur'ani izzu sittin ina jin." Dariya aka sake yi yayinda Abbati ya tayar da motar suka wuce gidansu kai tsaye. Munzali ya tambaye shi me zai hana su fara sauke su Innayo maimakon yaje Rijiyar zaki sannan ya koma Dala. Motar sai tayi dif na takaitaccen wa'adi kowa yana tunanin amsar da ba za ta fallasa abin da suke kokarin boyewa ba. Abbatin ne ya amsa masa da cewa zai taho da Asabe dasu Ummakati tunda basu sami zuwa asibitin yau ba. Cike da farincikin hangen nesan amininsa Munzali ya yarda da amsar har ma ya murmusa. Da isarsu gidan bayan maigadi ya bude gate suka ga mota a ajiye a kusa da bangaren Munzali. Su Innayo basu shiga cikin gidan ba amma Abbati ya bi bayan Munzali har cikin falo. Zaune a ciki kuwa ba kowa bane illa Daddy da Zakiyya suna gaisawa da Kande mai kula da Qibdiyya. An janyo centre table gabansu inda Kuku ya ajiye musu kayan motsa baki. Daddy yana shan juice sai wani gadara da fizgar kai yake irin na matasa masu zafin kai ko gaishe da maigidan bai yi ba. Abbati kuwa gabansa ne ya buga sosai har sai da ya dafa kujera yana mai fargabar ko Shazali ya nemi Zakiyya ne. Munzali bai bi ta kan Daddy ba don sam baya son girman kan yaron. Amsa gaisuwar Zakiyya ya yi tayi masa sannu da jiki tunda taji labarin rashin lafiyarsa a wurin masu aikin gidan. "Amma dai bana jin dubani kika zo yi ko?" Ya tambayeta bayan ya zauna. Abbati ya cigaba da tsayuwa a bayan kujera yana jiran jin amsarta. Maganar da Zakiyyan tayi masa maimakon amsa tambayar Munzali kusan kara tsorata shi tayi. "Abbati ina kwana? Ya wajen Hanne?" Bakinsa yana sarkewa ya ce "lafiya kalau" Dan dukar da kai tayi saboda jin kunyar rashin hakurinta da zargin wani abu ta ce "dama naga har an koma makaranta ne baka dawo da Qibdiyya ba" Nasa gaban ne ya fadi yanzu. Ya kalli Abbati a fakaice ya daure ya daidaita fuskarsa don kada ta gane da matsala. (Fyaden da yake tunanin Lilu ya yi mata) "Saboda yanayin jikina Asabe ta dauketa..." Daddy ya katse masa magana da sigar izgilanci yana tabe baki. "Asaben ce za ta wani iya kula da ita?" Duk wanda yake falon harda Zakiyya yaji rashin dacewar furucinsa da sigar da aka furta shi. Munzali yaji bacin rai sosai akan hakan. Ko hauka take baya jin ya dace dan kanwarta ya yi magana irin haka a kanta. Cikin fushi ya nunawa Daddy kofa yana fada. "Malam get out! Idan bata ci darajar komai ba a wurinka ai taci ta zama silar mallakar motar da kake karade garin nan da ita. Bayan kuma ka san na saya ne don ka dinga kai min 'ya makaranta. Ko an fada maka ban san irin yawo da gangancin da kake da ita wanda ni ke biyan kudin gyara ba? Duk kuma a cikin alfarmar Asabe da tasa ni auren yayarka?" Kafadarsa Abbati ya dafo "ya isa haka ba lafiya gareka ba" "Don Allah kayi hakuri" cewar Zakiyya a tsorace da fadan nasa. "Ya fita kawai za a kawota da weekend. Sai ki fadawa makarantar zata yi fashin sati daya." Rashin kunya Daddy yaso yi musu sai dai dukkaninsu sun yi masa kwarjini. Yanayin jikinsu ma ba daya ba. Ya san uwa da ubansa zai ci la'ada waje idan ya kara magana. A hanyarsa ta fita ne dai ya yi magana da kunkuni ya ce, "A jikin 'yarka zan fashe" Kalaman sun sami nasarar shiga kunnuwan Abbati. Matsalolin gabansa basu hana shi juyayin maganar a zuciyarsa ba a hanyarsa ta kai su Innayo gida. Dukanta zai yi? * Bakin Uwani bushewa yayi har ta rasa yawun hadiya da Salihi ya ajiye motarsa a jikin katangar police station ya ce ta fito. Hannunta yana rawa ta murda hannun kofar ta fita ta fara bin bayansa. A daidai gate din da zasu shiga kafafunta suka yi mata nauyi saboda tsabar tsoro. Jiki a mace ta coje a wurin don ji take kamar ta kwasa da gudu. Muryarta ta fito kamar mai shirin kuka ta nuna kirjinta da rawar jiki. "Karata kayi? To me nayi maka? In kana so na dawo gidanka ai ka san umarni kadai zaka bani ba sai ka hadani da hukuma ba." Kiris ya rage ya kwashe da dariyar kalamai da yanayin fuskarta. Kuma don karfin hali so take ta nuna masa cewa bata ji komai ba. "DPO ne yake son ganinki" Habar mayafinta kamar yaji me aka ce ta sabule ta rasa yadda zata gyara shi tsabar firgici. Da kansa ya saita mata mayafin a kafada yadda zai zauna ya ce "muje" Suna tafiya mayafin ya kara cirewa ta dube shi idanunta suna shirin zubar da kwalla. "Da ka fada min inda zamu zo ai da na saka hijabi. Ko babu komai zan shiga da mutumcina" a fusace ta wurga gefen mayafin kafadarta tare da cewa "in zaka zauna ka zauna ko in cireka kowa ya huta" "Ina ruwan mayafi za a huce a kansa" Allah ne Ya taimake shi yana gaba da ita da tuni ta ga dariyar da yake dannewa. Maganar da ya yi ce ma ta kara kular da ita. Yawancin 'yan sandan da suka tarar a wurin counter sun gaishe shi da girmamawa saboda DPO Yahaya ya fada musu cewa surikinsa ne tun zuwansa na farko. Uwani bata sami sukuni ba sai da suka shiga cikin ofishin DPO din taji yana gaisheta tare da kiran Salihi da yaya. "Bari nasa a kawo shi" cewar DPO bayan sun gama gaisawar. Ba a jima ba kuwa sai ga wani dan sanda ya taso keyar Habibu wanda alamu sun nuna anyi lugude da jikinsa. Yana ganinta ya sunkuyar da kai don ya sha gargadi akan ko hada ido ya sake yi da ita sai an masa fin dukan yanzu. Ita kuwa mamaki ne sosai ya kama ta. DPO Yahaya ne ya yi magana domin warware mata me yake faruwa. "Kin san wannan mutumin?" "Eh" ta amsa da baki tare da gyada kai. "Good. Kamar nawa ne kudinki da yake hannunsa?" Tunda ta fahimci ba tuhumarta aka zo yi ba sai ta hau lissafi. Akwai kudin kujerar Hajji, kudin sallamar agent, kudin hotel din da za a kama mata a Makka da Madina (bata san cewa duk a cikin kudin da ta bayar ake cire na kujera dana masauki ba), kudin fili, kudin masu gini ma ta hannunsa suke bi, kudin sallamar dillalai.... Lissafi ya dinga tafiya a yayinda ta cigaba da fadin nawa ta bawa Habibu. Da aka tambaye shi bai musa ba. "Sai kayi musu bayani game da komai kamar yadda kayi mana." Kai ya dukar ba don kunya ba sai tsoron hukuma. Da farko babu batun dukansa a lissafinsu. Sai da ya yi kokarin sayesu da kudi domin a kashe maganar. Sannan ne suka nuna masa cewa akwai bambanci tsakanin 'yan sanda da muna 'ya'yan sanda. "Kudin Hajji babu su gabadaya nayi amfani dasu, filin da kika yi gini kuma ku biyar na sayarwa wurin. Ban san waye ainihin mai wurin ba ma. Sannan..." Gajiya tayi da jin bayanin nasa mai neman sanya mata hawan jini ta ce "ya isa! Ya isheni haka. Allah zai saka min." Ta dubi DPO Yahaya ta dan rissina kai tayi masa godiya sannan ta tashi ko bangaren Salihi bata kalla ba. Da sauro ya tashi ya bi bayanta. Daga kafa kawai take tana saukewa ba tare da sanin ina ta nufa ba. A zuci take kukan bakinciki. Tanadin da ta soma tun ranar da ta fara daukar albashi ya rugurguje. Darasin da ta kasa tsayuwa ta koya yau duniya ta fahimtar da ita a cikin 'yan tsirarun dakiku. 'Duk gudun mutum ba zai wuce kafafunsa ba'. Babu wani bawa da ya isa ya tsallake kaddararsa. Talauci da babu take gudu kuma gashi sun zo sun risketa. Kai ta girgiza ta gyarawa kanta da cewa taje ta riskesu dai. Aikin da take takama dashi bata san makomarta ba akan shi. Kudi kuwa yanzu da matukar wahala ta fito da dubu hamsin indai ba motarta za ta sayar ba. A karshe dai mutum biyun da take ta kokarin ta wuce a rayuwa su ne dai suka rage wadanda zata koma garesu. Uwa da Miji. "Shigo mota mu tafi." Gefenta ta kalla inda Salihi yake binta da mota ta kawar da kai. Ransa ya baci ya daga mata murya. "Meye haka kike yi ne kamar wata mara tawakkali? Ki zo mu tafi nace." Ba musu ta zagaya ta shiga. Suna tafiya tana goge hawayen da yake ta yi mata zarya a kumatu. Sai da ya saita motar yadda za ta iya shiga gida sannan ya yi mata magana. Muryarsa ba da karfi ta fito ba kamar dazu amma tana iya gane zancen nasa ba da wasa yake so ta dauke shi ba. "Ke ba Innayo bace. Bana jin har abada za ki taba zama ita. Mutane masu irin zuciyar mahaifiyarki kalilan ne" Daga kai tayi ta dube shi sai taji a karon farko bayan wasu shekaru wai tana jin nauyinsa. Salihi ya yi mata kwarjinin da ko zamanin samartaka bata jin ta taba jin haka a kansa. A dole ta mayar da kanta kasa ta cigaba da sauraron shi. "Ni ba mahaifinki bane. Ban taba aibata miki uba a gabanki ko bayan ido ba amma na san halinsa gaba da baya. Ta yiwu bisa kuskure na taba yin wani abu da yasa kika ji kamar tarihin iyayenki zai maimaita kansa a naki gidan auren..." "A'a" ita ce amsarta da sauri. Dan murmushi ya yi ya nuna mata kofar gidansu. "Ki je ki roki gafarar Innayo gwargwadon girman laifukanki. Idan kin tabbata ta yafe miki ki kirani zan zo na daukeki mu koma gida" Kama kofar tayi za ta fita ta dawo ta kuma zama cikin rashin kuzari. "Za ta yafe min kuwa?" Dariya ta bashi ya ce "zan iya rantsewa ko yanzu ma ta yafe tun kafin ki roka. Ai ba ita bace abin ji ba, ni ne." "Au, baka yafe min ba?" "Kin rokeni ne?" Fuskarsa a sake take. Hakan ne ya bata damar yin murmushi ita ma. Jikinta a sake kamar burodin da ya tsumu cikin ruwan shayi ta bude motar ta shiga gida. *** Tunanin Abbati akan manufar kalaman Daddy ya katse a lokacin da Innayo ta soma labarta masa abin da ya sami Ayaah da suka isa gida. Rokonsa tayi da su sake yiwa Suhaib da iyayensa godiya. Ta sanar dashi cewa Munzali bai sani ba. Kuma taki fada masa ne saboda halin da suka riske shi a ciki a asibiti. Amma don Allah tana so kada Abbati ya manta wurin yi musu godiya. Hakan zai sa suji cewa lallai sun ji dadin abin da dansu ya yi musu. Ya soma mamakin inda suka san juna sai ta fada masa zuwansu duba Qibdiyya harda babarsu. Murmushi mai ciwo ya sami kansa da yi. Halin Mami da 'ya'yanta na karrama mutane abin yabawa ne. Zai so ace ya hada zuri'a da wadannan kamilallun mutane. Ina ma kaddara bata riga fata ba? Da ace shi ma mai tsafta ne kamarsu da zai yi duk abin da ya dace domin samun amincewarsu wurin bashi 'ya. Yana ajiye su ya kira Shazali ya nemi ya bashi adireshin inda zasu hadu. "Da azahar nace maka zamu hadu ba yanzu ba" yace da shi a gadarance. "Allah Ya kaimu azahar din." Danne zuciyarsa ya yi wurin bayar da waccan amsa. Baya son ya nuna tsantsar damuwa da tashin hankalinsa a zahiri. Abu ne mai sauki Shazali ya yi amfani da wannan damar ya wulakanta shi. Gashi bashi da juriyar wulakanci. Karshe idan abin ya kare da rikici sune zasu kwana a ciki tunda Qibdiyya tana hannunsa. Maganganunsu da Innayo ya tuno yaji ya kamata ya kira kamar yadda ta bukata. Akalla ko godiya ne ya yi. *** Cije lebe Mami Khadija tayi a yayinda ta gama sauraron bayanin Suhaib game da Danliti. Wayarsa da ya karbo ya mika mata bayan ya budo mata chats dinsa da Jiddo. "Mami" ya ambaci sunanta a tausashe saboda yadda ya fuskanci abin data gani ya tabata. Sakin fuska tayi ta kai hannu kan bandejin da aka nade masa kafa. "Allah Ya baka lafiya Suhaib. I am proud of you. Ka tseratar da mutumcin wata kaima in sha Allahu babu mai taba mutumcinka dana 'yan uwanka ." Kawar da zancen take son yi sai dai ko kadan bai yi niyyar barin maganar haka ba. "Mami jiya kusan kwana nayi ina neman fatawar da ta tilasta miki zama da ...." Bata bari ya gama magana ba ta dakatar dashi da hannu a lokaci guda tana mikewa. "Zanyi abin da ya dace Suhaib. Abin da ya kamata nayi tun da dadewa." Ta karashe maganar a hankali tana fita daga dakin. Da taimakon Allah ta isa dakin da aka saukesu ita da Farha. I just published "41" of my story "UWA UWACE...". https://www.wattpad.com/1221353664?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=BatulMamman17&wp_originator=dmTI6%2Bd4xW4ySQC9IZSN5Ctp1ECDjPlql7uEEwxNyy6mwmTs5Ncm6yv57bRsBRlDWFHVlr6suRV3pFd4sJuu9eSkRnJfcM3791OugVz9A24ZB4FNIQX9hKS8ACJWWt%2FZ UWA UWACE...41 Batul Mamman💖 *** Suhaib ya kamata ya kira amma gangar jiki da ruhi suka ki bawa Abbati hadin kai. Haka yatsansa ya dinga jujjuyawa akan sunan Farha yana tuhumar zuciyarsa da rashin jin magana har ya kai ga kira bai ankara ba. Cikin sauri ya kai hannu zai katse kiran sai dannawar tasa tayi daidai da sallamar muradin rayuwarsa. Zuciyarsa wani irin dokawa tayi sai da ya dafe kirjinsa. Ba yadda ya iya dole yayi saurin bin kiran da wani. Sake dauka Farha tayi cikin macewar jiki da faduwar gaba. Sallamar da ta kuma yi ta riski kunnen Abbati da sautin karaya da tsoro. A take yaji tausayi da soyayyarta sun taso masa. Baya bukatar tuni yana sane da cewa shi mai laifi ne. Cikin kankanin lokaci ya sanya mata rai da soyayya harma da tunanin rayuwa a karkashin inuwa guda. Sai kuma ya soke mafarkin da ta fara ba tare da ya bata gamsashen bayani ba. Barinta cikin rashin sanin tudun dafawa ba karamin cutarwa bane. Bai tashi sanin hakan ba sai yanzu. Ajiyar zuciya suka sauke a tare wanda sautin ya shiga kunnuwan junansu. Hakan ya sanyasu yin murmushi a lokaci guda. Farha ce ta fara yin magana da cewa "nayi sallama baka amsa ba" Tunanin Qibdiyya ne kadai ya hana shi nuna mata zahirin halin da zuciyarsa ta shiga sakamakon jin muryarta kadai. "Kiyi hakuri. Wa alaikum salam. Kina lafiya?" "Alhamdulillah. Kai fa?" "Nima Alhamdulillah" Shiru suka dan sake yi sannan ya yi ta maza ya ce "Ya Farha muna cikin wani yanayi ne yanzu dake tsananin bukatar addu'a. Don Allah ina neman alfarma ko sau daya ne ki roka mana sauki a wurin Allah." Tausayi taji ya bata. Ta matsu taji mene ne ya yiwa kyakkyawar alakar da suka fara ginawa shamaki har tazara irin wannan ta wanzu a tsakaninsu. "In sha Allahu zan yi" "Baki tambayeni ko meye ba?" Ya ce da dan murmushin karfin hali. "Na san idan ya kamata naji ba za ka boye ba" Allah Sarki zuciya. Kalaman Farha kara nutsar da ita suka yi cikin zuciyar Abbati. A kullum yana kara yabawa da irin tarbiya da tsaftar tsatson da ta fito. Kafin ya manta ainihin dalilin kiran nasa ya ce ta yiwa Mami godiya akan taimakon da Suhaib ya yiwa Ayaah kafin su zo Kaduna suyi da kansu. Tunanin sake ganinsa nan kusa yasa ta fada masa cewa suna Kano ga kuma halin da Suhaib din yake ciki. "Kuna gidan da muka zo biki?" "Eh" "Zan zo koda ni kadai ne saboda Munzali ma yau ya fito daga asibiti idan baku koma ba zuwa gobe ko jibi. Don Allah kada ki manta da adduar." Zai katse wayar kenan yaji ta ce "baka bani abin sadaka ba. Naji ance ku Kanawa ko me zaku yi sai an biyaku" Dariya ce ta kama shi ya ce "dadin abin kauyenmu a Jigawa yake nima bakon Kano ne" Da murmushi Farha ta ce "Ai shikenan tunda ka fara rowa" Da kyar ya iya sallama da ita suka ajiye wayar kowannensu yana jin matsananciyar kewar dan uwansa. Daga nan zagaye ya dinga yi a titi domin zaman wuri daya ninka masa damuwa yake yi. Wani masallaci ya tsaya a gefen titi da aka kira azahar ya yi sallarsa tare da fatan samun nasara daga wurin Maikowa da komai. Akwai mutane da dama da zai iya kira su wulakanta masa rayuwar Shazali ba tare da ya daga hannu ba. Ya san manyan da zasu yi komai domin farincikinsa. Amma ko kusa ba zai nemi kowa ba. Domin kofar da yake son rufewa ce zata sake budewa. Shi yasa ya zabi kai kukansa inda ba a barin mutum ya dawo empty handed. Kamar jiransa Shazali yake yi kuwa sai ga waya. Sanar dashi adireshin inda zai je yayi da dariyar mugunta. Wannan yasa ya figi motar a guje da fargabar me ya sami 'yarsu. *** Minti arba'in kafin Shazali ya kira Abbati ya amsa wayar wani kusan gwamnati wanda yake yiwa kawalcin 'yan mata. Da yake zancen nasu ya hada da yadda zasu koma biyan malaman makarantun kwana kamar yadda suke yi a ta maza ana basu dalibai sai ya fita daga gidan. Hirar sirri ce baya so ko Abdul ya san me yake ciki. Mukullan mota ya dauka ya ce masa zai je siyo wani abu ya dawo. Minti goma da fitarsa kuwa Abdul ya kamo hannun Qibdiyya yace ta zo ya kaita wurin mamanta. Bata yi musun binsa ba don ta soma galabaita. Sam taki cin abinci sannan ga rashin iyaye ko wani idon sani. Abdul gani ya yi tana jan kafafu ya sunkuceta ya goya. Durowar da ya taba gani Shazali ya ajiye mukulli ya duba yaci sa'ar ganin mukullai daban daban a ciki. Lokutan baya bai taba tunanin dauka ba duk da idan Shazali zai fita yana rufe shi a ciki. Wurin kala shida ya soka a jikin kofar saboda kusan duka girmansu daya kafin ya yi sa'ar jin ta bude. Ajiyar zuciya ya saki gami da sake ruko kafafun Qibdiyya a cikin hannuwansa. Yana sako kafa a waje yaji kamar an dauke masa kansa sakamakon hada kan da bango da Shazali ya yi. A kofar gida ya zauna yana wayarsa. Duk gwajin mukullan da Abdul yake yana ji. Haka ya shigo gidan a harzuke ya banka kofar ta rufe da karfi kafin ya hankada shi. Da kyar Abdul ya iya tsayuwa akan kafarsa don gudun kada ya kifa da baya ya danne Qibdiyya. Bayan ya sauketa kafafunsa ta rike ta buya a bayansa tana kuka. Shi kuwa kunnen bangaren da ya hadu da bangon yaji ya dauke dif sai wata kararrawa ce take bugawa kamar an kada tara a firamare. "Har kayi tsaurin idon shiga lamarina Abdul? Waye ubanka a garin nan da kake jin ko kasheka nayi za a tada magana ma?" Abdul babu amsa sai kunnensa da yake ta bubbugawa ko jinsa zai dawo daidai. Kafadunsa Shazali ya rirrike ya shiga jijjiga shi yana masifa. Abu biyu ke damunsa. Na farko ya san duk kaunar da yake yiwa Abdul ya rasa shi kenan domin ba zai kuma kawo shi gidan nan ba. Na biyu kuwa wani mutum ya wuce ta kofar gidan a daidai lokacin da Abdul din ya tura kofar gidan. Babu tantama ya san cewa an ganshi. Bayan kuma ba a taba jin duriyar kowa a gidan ba. Da kansa da ya gaji ya sake shi ya nuna shi da yatsa. Har lokacin dai bai dawo daidai ba. Kana ganin kwayar idanunsa zaka gane a cikin dimuwa yake. "Ka jawowa kanka bala'i don na fuskanci akwai ganganci idan na mayar da kai makarantarku. Ka jirani in kai yarinyar nan wurin ubanta na dawo." Cikin gidan ya wuce ya tafi dakinsa ya barsu a dan sararin tsakar gidan. Kukan Qibdiyya tuni ya dauke sai ajiyar zuciya saboda tsorata da tayi. A gabanta Abdul ya durkushe ya fiddo wata 'yar karamar waya kirar samsung mai torchlight. A makaranta ma ba a san yana da ita ba. Bai taba kiran kowa ba sai Shazali da suke musayar text messsage. Shi ma kuma bai san yazo gidan da ita ba. Gefen siket din Qibdiyya ya samu ya saka ta ya yi mata nadi biyu. Siket din sai ya dage sama amma ba za a gane da wayar ba saboda dan fadin rigarta. "Ki boye wayar nan in kin hadu da babanki ki ce ya kira babana." Da ka ta amsa tana rike dashi har Shazali ya dawo. Hannunta ya fincika ya fita da ita a ransa yana tunanin ko wa zai hadu dashi cikin makota ba zai damu ba domin yana dawowa zai fita da Abdul ya bar gidan gabadaya. Fitarsu ke da wuya Abdul ya fadi a tsakar gidan. Jini kuma ya dinga silalowa daga cikin kunnen da ya bugi bango ta bangarensa. *** Duk wata addua da Abbati ya sani ya karanta ta a hanyarsa ta zuwa gidan shakatawar Comared. Manyan motoci ya gani har biyar a harabar gidan. Da yake gidan gona ne mai dan karen girma. A kusa da ta Shazali ya ajiye tasa ya fito ya kira shi a waya. Maimakon ya dauka sai ya fito ya yi masa jagora zuwa ciki. Karfin zuciya ne ya hana shi far masa da duka tun a lokacin saboda bai san me zai sami Qibdiyya ba idan haka ta faru. A cikin gidan kuwa Alh. Tahir ne zaune a wani daki wanda kofarsa take cikin falon suna magana da Comared. "Har yanzu babu wani canji dole sai da namijin?" Ya sake maimaita tambayar da bai san sau nawa ya yiwa Comared ba. Fuska ya kyabe kamar mai jin tausayinsa har zuci ya ce "ko dazu sai da na sake kiransa har nace ko ni zan iya yi maka aikin yace a'a" "Allah Sarki mutumina. A hakan ma nagode sosai. Na san kai mai taimaka min ne har inda karfinka ya kare." Comared ya tashi daga bakin gado ya ce "so nake ka kwantar da hankalinka. Yaron kwararre ne ya san me yake yi. Kafin ka farga anyi an gama" Suna ciki suka jiyo sallamar Abbati domin dai shi Shazali bata gabansa. Hasali ma hankalinsa yana wurin Abdul. So yake ya koma gida ya yiwa yaron rashin mutumci kafin ya watsar dashi a titi. Falon wayam babu kowa sai kayan ciye ciye da karar tv data AC. Qibdiyya Abbati ya nema da ido babu ita babu dalilinta. Cikin zafin nama da gajiya da danne bacin ransa ya riko Shazali ya tsayar dashi a gabansa. Da kakkausar muryar da shi kansa bai san bacin rai zai taba bashi irinta ba ya ce, "Shazali ina Qibdiyya?" To shi ma Shazalin bai san dakin da Comared da Alh. Tahir suke yana kusa dasu ba, shi yasa ya bashi amsa babu kwana-kwana. Dariyar mugunta ya fara da ita kafin ya ce, "Tana nan kalau ko farcenta ban taba ba. Nan da awa guda idan kaso zaka tafi da 'yarka gida. Bukatarmu kawai kabi umarnin da aka baka" Murya kasa-kasa Alh. Tahir ya tambayi Comared me yake faruwa. Ganin babu wata mafita sannan ya san a cikin matsi abokin nasa yake shi ne ya yi masa takaitaccen bayani. Bai kai ga yin magana ba suka ji Abbati ya daka wata irin tsawa. Su biyun duka jikinsu ya amsa duk da ba dasu yake ba. Barin ma Comared wanda tun isowarsu gidan yasa aka bata maganin bacci. Tana dakinsa na sama yana jiran Abbati da Alh. Tahir su shiga daki shi ma yaje ya afka mata. "Shazali! Ka fito min da Qibdiyya idan ba haka...." Cike da dakiyar 'yan barikin da suka yi nisa Shazali ya katse shi da cewa "in ba haka ba sai me Abbati? Kana da abin da zaka iya ne? Duk wani k'usan gwamnati ko maikudin da kake takama dashi ta dalilin wa ka sanshi?" "Ana takama da Allah waye yake ta mutane? Wawa irinka ne zai dogara da halitta mai kayyadajjen wa'adi bayan akwai Maihalittar da bashi da karshe. Da nace maka ni da Munzali mun tuba ba da wasa nake ba." "Aikin banza. Wane d'an son zuciyar ne ya ce muku Allah zai karbi irin wannan tuban naku? Shekararku nawa a wannan rayuwar? Kudi da duk wani connection dinku a kasar nan ba jikinku bane sanadinsa? Sai yanzu kuna tunanin kun gama tara abin da kuke so zaku wani ce kun tuba? Malam in zaka sha giya kasha ta duba. Allah Gafurur Rahim ne kowa ya san wannan. Kawai ku cigaba da gashi suya sai ranar sallah. Idan mutuwa tazo ka gaggauta istinginfari me yiwuwa a dace." Karkada kai Abbati ya yi da murmushin takaici. A matsayinsa na bawa mai tarin zunubi kuma mai neman rahama ya yi imanin cewa shi din ba kowa bane. Amma duk da haka bakinciki mara misaltuwa ya danne zuciyarsa saboda maganar Shazali. Tsanarsa ta kara ruruwa a zuciyarsa saboda kalaman izgilancin da yaji daga bakinsa. Nasa imanin da tawakkalin kuma suka karu domin ya yarda cewa lallai shiriya ta Allah ce. Su da suka tuba ba wayo ko dabararsu bane. Cike da kosawa ya ce, "Don Allah Shazali ka fito min da ita mu tafi. Bana son wannan case din ya kaimu gaban police." Sama Shazali ya nuna masa yana yi masa kallon wulakanci "To ni waye yace maka ina tsoron police? Kaga Abbati ka amince kayi abin nan ka zo ka tafi don nima uzuri ne a gabana. Mutumin nan ya riga ya saba sakarwa mata kudi kamar hauka. Wannan harkar ma don bako ne shi a cikinta shi yasa na nemo ka. " "Babu ruwana da sanin ko shi waye. Da Allah fa nake hadaka akan ka bani 'yata mu tafi. Mece ce ribarka idan na koma wannan kazamar rayuwar?" "Riba? Eh to ina da riba gaskiya. Zan jidadi na rabaku da tuban da kuke ikirari wanda yasa kuke yi min kallon dan wuta. Munafunci ne tuban naku tunda sai da aljihunku ya yi nauyi da haram zaku ce wai kun komawa Allah. Indai ina numfashi sai kun koma ruwa." Murmushi Abbati ya yi mai ciwo. Bin Shazali ta laluma ba zai kara masa komai ba sai bacin rai. Idanuwansa ya daga yana kallon fanka wanda a zahiri zuciyarsa ce take fuskantar Mak'aginta. "Ya Allah idan tubana dominKa ne, kuma niyyata ta barin dukkan abin da na mallaka ta haramtacciyar hanya dominKa ce ina rokonKa da ka tsare Qibdiyya. Kasa su fito da ita da kansu. Ya Allah kada Ka bawa Makiyanka dama a kaina da abokina. Kada Ka basu ikon sake mayar damu kazamar rayuwar da ka haramtawa bayinKa." Kafada Shazali ya kada irin na ka yiwa kanka ya ce "Tunda baka da rabon arzikin nan to ka zauna ka jira Qibdiyya. Tana can ubangidana yana morar jikinta. Na san zamu sami fiye da abin da ya kamata a biyaka" A guje Abbati ya tashi ya yi hanyar benen jikinsa yana rawa ga gumin da ya wanke shi a take. Ko rabin benen bai kai ba Shazali ya finciko shi ya fado. Akan hannunsa daya ya fada kuma yaji karar da ya yi amma hakan bai hana shi mikewa da zafin nama ba ya bangaje Shazali ya sake nufar benen. "Qibdiyya! Qibdiyya!!" Da Shazali ya sake riko shi rufe masa baki ya so yi saboda gudun kada Comared yaji hayaniyar. Idan ya rasa kudin wahalarsa ta kawo Abbati gidan nan ba karamin abu zai yi masa ba domin huce haushi. Hannun da ya kai da nufin toshe masa baki Abbati ya damko ya sami sa'ar janyo shi ya kifar dashi a kasa. Bai dakata ba saboda tsananin bacin rai da kunar zuciya ya haye kansa ya shiga kai masa duka ko ta ina a fuska da lafiyayyen hannunsa. Cikin kankanin lokaci baki da hanci suka soma fitar da jini. Duk kokarin Shazali da son ture shi ya kasa. Ihun neman ceton da yake yi da kyar yake fita saboda wahala. Tun farkon maganganunsu Alh. Tahir yaji jikinsa yayi sanyi da Comared ya fada masa wanda aka kawo yayi ikirarin tuba. Kuma hakan ne ma ya zama dalilinsu na dauke 'yar amininsa wadda bata da maraba da matsayin 'yar cikinsa. Zai iya yin komai dominta. Sai kuma kwatsam yaji ya ce Munzali. Sannan ya kara da ambaton tuba da zantuka masu taba zuciya. Irin zantukan da ya saba jinsu da kalamai masu tasiri fiye da na Abbati daga matarsa. Amma a yau ne kadai ya fara shiga hankalinsa. Harbawar zuciya da gudun jininsa a cikin jijiyoyi ya dadu. Ya san suna Munzali da Abbati da kuma kasancewar Munzali uba ga wata yarinya da bai rike sunanta ba. Matasan samarin dake shirin zama surukansa. Idan ya fita Abbatin da ya kasance saurayin Farha na farko zai gani? Bai san yadda aka yi ba ya iso kofar dakin zai murda Comared ya kama hannunsa. "Alhaji kada ka fita don na fuskanci dan iskan yaron nan zai iya bamu matsala. Idan yaga fuskarka bai mana aiki ba tabbas zai iya tona mana asiri. Kuma yadda zuciyarsa take a kusan nan mu kanmu bamu san me zai mana ba. Ka jira in kira security." Fizge hannunsa ya yi ko amsa bai iya bawa Comared ba ya fita. A halin da ya sami Shazali da Abbati bai san lokacin da ya kwalawa Abbati kira ba bayan ya gama razana da ganin da gaske shi din ne. "Abbati sake shi kada kayi kisa" Bai san waye ya yi magana ba amma wuyan Shazali da yake neman shakewa yana maganganu a zauce don duk tunaninsa da gaske ana can ana cin zarafin Qibdiyya ya saki farat daya. Idanunsa hawaye suke fitarwa ya tashi a firgice da tsanar aika-aikan da yaso yi ba don an dakatar dashi ba. Da kakkausar murya ya nuna Shazalin dake kwance sannan ya juya ga mutane biyun da suke tsaye a hagunsa. "Kai ne mutum na farko da ya fara sakamu cikin wannan masifa Shazali. Kuma har yanzu ka kasa hakura ka barmu mu koma ga Allah. Idan wani abu ya sami Qibdiyya wallahi zaku ga rashin ...." Bai sami damar karasa maganar ba a sakamakon ido hudu da suka yi da Alh. Tahir. Idanuwansa ne kadai suka kara girma a yayinda wani kololon abu mai daci ya taso daga cikinsa ya tsaya masa a wuya. Cikinsa ya kulle tamau har sai da shiga da fitar iska cikin hancinsa suka soma wahalar dashi. Kafafunsa da yake umarta da su zaga dakunan gidan su nemo Qibdiyya sannan ya fita kuwa suka ki motsawa. 'Zina 'yar aike ce. Duk inda ka turata zata dawo ta isar maka da sako. Bana yi mana fata domin dawowarta gidan nan ba zai taba zama alkhairi ba. Sai dai ina so ka sani koda tayi batan kai da sannu wata rana za a sami mai nuna mata hanya. A lokacin ko bata tuna cikakken sakon ba saboda shudewar lokaci, sallamarta kadai zata hargitsa tunaninmu. Na barka lafiya!' Ga Alh. Tahir kuwa, wannan sakon na Mami Khadija wanda ta tura masa tun washegarin ranar da Yumna ta fallasa komai ga Farha ne ya dawo masa tar. Ko batan wasali bai yi ba wurin tunano kalmomin daki-daki tamkar yanzu yake karanta su. Hantar cikinsa ta buga a tsorace da ya yiwa sakon fahimtar da ta dace dashi. Tun kafin ya bincika yaji ko akwai wanzuwar haramtacciyar alaka tsakanin su Abbati da 'ya'yansa ya gama shiga tashin hankali. Sanin cewa sun taba yin luwadi duk da a yanzu kunnuwansa sun jiye masa nadama da tubansu kadai ba karamin bala'i ya jefa zuciyarsa ba. Ko shi da zina ta gama bin jinin jikinsa ba karamin kyama yake yiwa wannan nau'in nata ba. Haka ya dinga jin kamar ana sassara adda a sassan jikinsa. Bai san wanne daga cikin masifun da suke gabansa ya kamata ya fara yiwa kukan bakinciki ba. Ganin Abbati a wannan gida da sanin waye shi ko kuwa ganin da Abbati ya yi masa da sanin nasa sirrin? Kallon kallo da suka tsaya yiwa juna ne ya bawa Comared damar tayar da Shazali ya zaunar dashi akan kujera. Da yaga kallon yaki karewa ne ya dubesu da mamaki sosai. "Alh. Tahir ko kun san juna ne?" Yawu yaso hadiya domin bayar da amsa amma ya laluba yaji babu danshi a bakin nasa. Kansa yaso kadawa shi ma yaji ya yi masa nauyi. Comared kawai sai ya ce, "Shi ne yaron da aka dauko 'yarsu ai domin ya amince da aikinka." Yana gama magana ya juya ga Abbati "wannan haukan da kayi a gidan nan baka ci bulus ba wallahi. Idan kana takama da zafin kai ka tarar da ubangidansa. Sai na daureka igiya tayi rara." A sanyaye Alh. Tahir ya daga kai ya kalli dakunan dake sama ya ce "Comared a wane daki yarinyar take?" Wani irin duba Comared din ya yi masa sai dai bai iya yin musu ba ya nuna masa kofar da hannu. Abbati ya kalla fuskokinsu duka babu digon nutsuwa. "Daukota ka zo ku tafi" "A'a Alh. Tahir, bangane ba. Ya zaka sallamesu batare da shawarta ta ba?" "Nawa ne zai fanshi uba da 'yar Comared? Nawa zan baku ku kyalesu har abada?" Sakin Shazali Comared ya yi ya taso har gaban Alh. Tahir cike da dumbin mamaki. "Alhaji ka san shi din da gaske?" "Da ne a wurina. Iyaka abin da zan iya fada maka kenan" Kai Comared ya kada alamun ya amince Abbati ya hau saman. A gurguje kuwa ya haye ya bude dakin da aka rufe ta waje amma key na jikin kofar. A tsakiyar gadon ya sameta ta dukunkune jiki tana bacci. Kwalla mai zafi ta zubo masa a lokacin da ya rankwafa ya daukota. Jikinta zafi rau da zazzabi. Yana dorata a kafadarsa yaji dumin zafin yana nasar nasa jikin. Ba shiri ya dagota ya dorata akan kafar damansa da ya dora a bakin gadon. "Qibdiyya. Bude idonki Papa ne" Da kyar ta bude idon saboda gajiya, yunwa da kuma aikin maganin baccin da Comared ya dura mata. Yadda kanta yake kifewa da kansa kamar 'yar maye ya sake daga masa hankali. Jikinta yabi da hannu daya ya mammatsa domin son ya farkar da ita. A nan ne kuma yaji ya tabo wani abu mai dan tauri a kugunta A razane ya dan daga rigarta ya ciro shi daga cikin siket dinta. Bakinsa da kyar ya iya hada tambayar wayar waye gareta. Cikin yanayin rashin kuzarin da take ta ce masa, "Cewa ya yi na baka" Aljihunsa ya tura wayar ya mayar da ita kafadarsa ya sauka. Idan ta dawo daidai zai tambayeta waye ya bata. Da ya sauko babu wanda ya kalla haka ya fita daga falon. Sai da ya isa bakin motar har ya kwantar da Qibdiyya a baya sannan yaji an ambaci sunansa da murya mai rauni sosai. Gabansa ya yanke ya fadi domin bai san da wane ido zasu kalli juna ba balle har su yi bayanin fidda kai. *** Minti goma sha biyar da isar Alh. Sadisu Nakano makarantarsu Abdul ta hargitse kamar ana cin kasuwa. Tun daga Principal har Masinja babu wanda bai shiga sahun zagaye makarantar ba ana neman Abdul. Principal din yafi kowa rikicewa don sai yau ya san akwai dan Alh. Sadisun a makarantar. Tun lokacin da yasa aka kawo shi makarantar dama ya bukaci a boye ko dan waye. Kudin da yake turowa domin kulawa dashi kuwa bai bambanta da wanda wasu iyayen kan yi ba sai ta adadi. Malamin ajinsu wanda kudin ke biyowa ta hannunsa yana isar da sako tare da yin tasa bushashar son rai. Daya daga cikin masu gadi ne ya ruga ya sanar da Principal bakon da suka yi tun kafin su shigo ciki. Principal din ya tashi da sauri ya shiga kankanta ofishinsa domin yana da labarin zuwan bazata da Alh. Sadisu ya kan yi makarantu. A zatonsa yau sallarsa ce ta kama don yasa rai da samun wani abu mai nauyi daga babban bako. Bai tashi shiga tashin hankali ba sai bayan sun gaisa Alh. Sadisu ya bukaci a kira masa dansa. Dan aike wato Masinjansa ya dawo da mummunan labari cewa wai washegarin dawowarsu makaranta ya koma gida bashi da lafiya. Daga nan aka soma diramar! Tashi Alh. Sadisu yayi tsaye cikin fushi da kaduwa ya hankada teburin Principal din dake gabansa. Ji kake kiyyyy, ya tafi ya daki bango. Abubuwan da suke kai wadanda suka yi zaman dakin kishiyar da ba a shiri da ita suka rufto kasa. "Bana son zancen banza da hofi. Yaron wajena nake nema Abdul. SS2 B yake. Sunan form master dinsu Sir Balarabe. Hostel dinsu kuma Sardauna House. Ya ce min a kwanar da gadonsa yake akwai Victor da Faisal" Jinjina kai Masinjan da Principal suka yi na mamakin yadda ya rike komai da ya shafi dansa. Direbansa da PA da suka zo tare basu dauki hakan komai ba. Saurin rike abubuwa suna daga cikin manyan jarinsa da suka kawo shi inda yake yanzu. "Ranka ya dade zauna bari naje ajinsu da kaina na kirawo shi. Ina jin sakon ne bai fahinta da kyau ba." Principal dai bai sami damar dawowa ba sakamakon matsalar da ya tarar. Lokacin ba a tashi daga aji ba. Yana zuwa Monita da sauran 'yan aji suka tabbatar masa da cewa kamar yadda aka bukaci su dawo asabar saboda damina ana bukatar gyara makaranta, Abdul ya dawo amma ba a wayi garin lahadi dashi ba. "Me yasa ban san labarin nan ba sai yau?" Cewar Principal yana gumi tare da tsare malamar dake ajin tana koyarwa a lokacin. "Ranka ya dade Mal. Balarabe ya kamata ka tambaya. Nima ban san komai ba" Tare da Monitan ajin da Assistant dinsa ya tafi staffroom din malamai maza. Yana shiga ya kira sunan Mal. Balarabe sai dai nan take aka sanar dashi baya nan shi da wasu malamai biyu abokansa. "Bangane ba? Ina ya tafi ana cikin wannan yanayin?" Wani malami ne ya bashi amsa da cewa "babu yadda za ayi ya zauna alhalin duka makaranta ta dauka cewa dan Alh. Sadisu ya bata." "To shi ya batar dashi da zai gudu?" Ya tambaya a fusace. Malaman dai basu ce komai ba tunda basu san me yake faruwa ba. Haka ya koma ofishinsa da yaran nan biyu cike da fargabar yadda zai fara yiwa Alh. Sadisu bayani. A inda ya barshi tsaye ya dawo ya same shi yana kai gauro da mari. Yana ganinsa kuwa ya ce ina Abdul. "Yallabai ka zauna kaji daga bakin yaran nan. Daga nan sai mu san abin yi." Rainin wayo Alh. Sadisu ya dauki zancen Principal din. Sai dai kuma ance idan rakuminka ya bata ka duba har cikin hudar allura. Bisa wannan dalilin ya saurari Monitan wanda ya maimaita sak abin da ya fadawa Principal. "Yanzu kai baka ji kunyar cewa na tsaya jin wannan wasan yaran ba? Cewa zaka yi makarantarka babu tsaro har ana shigowa a sace 'ya'yan mutane. To wallahi banda dana. Kai, ina tsammanin baka gane ni ba ko? Suna na Alh. Sadisu Nakano kuma ko uban mutum ne yake mulkin kasar nan bai isa ya hanani koya masa hankali ba." Ya nuna kofa da hannu "kaje ka nemo maigadin da ya kwana ranar asabar din. Da malamin ajinsu duk inda yake..ku hadu ku nemo min dana" Da Principal da mataimakansa biyu tare da malaman da suka yi cirko-cirko a kofar ofishin kowa hankalinsa ya tashi. Alh. Sadisu ma dauriya kawai yake domin zuciyarsa tuni ta fara karanto masa sunayen abokan hamayyarsa wadanda zasu iya dauke masa da a matsayin fansa ko garkuwa. "Sir?" Kowa juyowa yayi don jin wa dalibin dake matsayin mataimakin monita yake kira. Kai tsaye Principal din nasu yake duba ya ce, "Ina jin fa ba bata ya yi ba. Tun kafin hutu yawanci da daddare ranar juma'a Sir Balarabe yana zuwa kiran wasu a hostel. Yawancinsu da safe suke dawowa. Wasu kuma sai lahadi..." Ya kalli monitan "ba shi ne muke cewa ko lesson ake musu banda mu ba?" Da ace kunnuwa suna jin gaibu yau da ofishin Principal dinnan ya cika da bugun zukata. Duk wani mai hankali a cikin wurin tunaninsa ya karkata daidai da na uban yaron da ake nema. Wannan kuwa ba bakon abu bane tunda akan ji labarai makamantan haka a makarantun kwana. Cijewa Alh. Sadisu ya yi ya daure ya tambayi yaron ko mutum nawa ne suka bar makaranta rana daya da Abdul. Babu musu kuwa ya lissafo masa su biyar. "Amma sauran hudun duka ranar lahadi suka dawo da daddare. Shi kadai ne Sir Balarabe ya ce gida ya koma" Cikin karaji da gigita Alh. Sadisu ya ce "A nemo min Balaraben da masu gadi" "Sir Balarabe ya fita" "Mal. Bawa maigadi baya nan" "Malaman dake abota da Sir Balarabe ma basa nan" Wadannan ne amsoshin da suka biyo bayan umarnin da Alh. Sadisu ya bayar. Da aka gama fada dariya ya kwashe da ita. Wata irin dariya mai dauke da bakinciki da bacin rai gami da tsoro. Kamar yadda ya fara ta kuma a bazata haka yayi dif ya daina lokaci guda. Kallo mai ban tsoro yabi mutanen da suke gabansa sannan ya daga waya ya kara a kunne. "Ku fara aikinku" Cikin kankanin lokaci gabadaya makarantar ta kasance a zagaye da 'yan sanda. Wasu suka shigo aka fara yiwa duk mai ruwa da tsaki tambayoyi. Ya kira su ne tun kafin Principal din ya dawo daga binciko masa me ya faru. Ma'aikatan jarida kama daga na gidajen rediyo zuwa tv suma suka soma dafifi. Alh. Sadisu ya tsaya a kofar ofishin Principal da na'u'rorin daukar magana kala kala a saitin bakinsa ya ce, "Ba roko nake ba shawara ce. Na bada awa biyu kacal a dawo min da dana inda aka dauke shi." *** Ayaah, Murja da Ummita ne suka tashi daga gaban mahaifinsu da Abdulkarim bayan sun gaishe shi. Kafin su fita ya sake jajantawa Ayaah abin da ya faru jiya tare da shawara gareta da 'yan uwanta akan tsare mutumci saboda gurbacewar zamani. Bayan sun koma wurin Anti Hasiya aikin gabansu suka cigaba. Ayaah kuwa kusa da antinta ta koma ta kwanta ta rufe ido. "Dalla can tashi, ai kin san yau kece da wanke-wanken safe" Baki Ayaah ta turo ta tashi rai a bace za ta soma gunaguni Anti Hasiya ta ce ta koma ta kwanta. "Haba Murja! Yanzu har kin manta abin da ya sameta jiya kike kira mata wanke-wanke? Duka duka yaushe garin ma ya waye?" Murja da Ummita suka dubi juna suka bushe da dariya. Karfe goma shadaya harda minti bakwai. Shi ne Antinsu take cewa yaushe gari ya waye. Sannan bata tashi ba Ayaah da Murja suka yi fada kamar zasu ari baki a kofar bandaki. Ita kuma tana tasowa ta cigaba da lallabata. Labarin fadan suka bata ta koma yiwa Ayaah kallon tuhuma. Amma da yake ba a cinyeta da baki sai da ta magantu. "Dauriya ce fa kawai nake Anti amma har yanzu ban dawo daidai ba. Kuma bana son ki shiga damuwa shi yasa nayi kokarin dawowa daidai." "Yanzu tsiwa ce daidai dinki Ayaah? Allah nagode Maka" cewar Anti Hasiya tana dariya. Raharsu suka cigaba da yi cike da so da kaunar juna. Anti Hasiya ta dubesu daya bayan daya ta sake mika godiyarta ga Allah. Irin wannan zaman na ahali daya kuma da zuciya daya tayi ta buri. Sai gashi lokaci guda Allah Ya amsa addu'o'i'nta. Kan yaranta ya hadu sannan ita ma ta sami rabon da zata kira nata. Uwa uba an Abbas yana shirin samun lafiya da yardar Allah. * "Ina ta sa ran jin ka tambayeni me yasa na nacewa gidanka naji shiru" Abdulkarim ne ya yiwa Honourable tambayar bayan sun gama gaisawa sannan ya fada masa daren yau ake bukatar kwantar da Abbas a asibiti. Washegari ake sa ran yi masa aikin da safe. Likitan da zai jagoranci aikin ya iso Kano. Da yake Honourable ya fishi kwarewa a sakin magana sai cewa ya yi "Wata kake so cikin 'yan matan gidana ko?" Yadda ya yi maganar kai tsaye ya bawa Abdulkarim mamaki domin bai yi maganar da kowa ba sai zuciyarsa. Zaro idanun da ya yi ba tare da ya ce komai ba yasa Honourable bude baki. "Don Allah wai da gaske kake?" Kwarjini Honourable ya yi masa fiye da kullum amma ya san ranar wanka ba a boyon cibi. Tunda dai Ummita ba za ta aurar da kanta ba dole ne ya fadawa mahaifinta. "Da gaske nake" Honourable ya gyara zama yana dariyar kunya da takurar da yake gani a tattare da Abdulkarim. "Murja dai an kawo kudinta. Ya rage Ayaah da Ummita" Abdulkarim ya dan tura hularsa baya kadan ya ce "Umminmu din nake so. Allah Yasa wani bai rigani ba. Kuma don Allah kada ka sako zancen shekaru wallahi da sauran tafiya kafin nayi hamsin ma." Dariya sosai ta kama Honourable. Farincikinsa ba zai misaltu ba. Wato da gaske bayan kowane tsanani akwai sauki. Sai dai wani hanzari ba gudu ba... " Abdulkarim anya baka yiwa Ummita nisa ba. Ba batun shekara nake maka ba. Ina nufin a zamantakewa ta wayewar rayuwa da arziki. Ina jin tsoron kada ku sami rashin daidaito a dalilin ..." Dakatar dashi Abdulkarim ya yi ya nuna masa rashin jindadin furucinsa. "Ka sanni kafin na zama wannan Abdulkarim din. Duk abin da na samu a sakamakon kusanci da kai ne a lokacin da nima ban dace da kusantar mutum irinka ba. Amincewarka nazo nema domin na nemi soyayyarta. Ba zan so ayi mata fin karfi ba saboda wani abu da na samu na takaitaccen lokaci" Fuskar Honourable dai babu komai cikinta sai annuri. Tashi ya yi ya ce masa idan sun gama shiri anjima zasu tafi asibitin zai kira shi. Abdulkarim sai ya shiga rudani ya ce "maganar Umminmu din fa?" Wata dariyar Honourable ya sake yi "Naga dai yanzu ba lokacin tadi bane da rana tsaka amma dai bari na turota kwashe kwanuka." Kunya ce ta kama Abdulkarim amma abinka da manya sai ya fuske. Ba jimawa kuwa yaji sallamarta a kofar falon. Da ya amsa ya yi zaton zata shigo amma shiru har kusan minti biyu. Ga alamun tsayuwarta a bayan labule yana gani amma taki motsi. Babu mamaki babanta ya fada mata yadda suka yi. Banda haka me zai hanata shigowa don yana ciki? "Nifa dan gata ne a gidan nan. Idan baki shigo da kafafunki ba ko Ayaah na kira zasu hadu da Murja su daukoki a ka" Ja da baya tayi cike da tararrabin me ya kamata tayi. Bayan kusan sakan talatin ta matso jikin labulen ta damke shi da hannu ba tare da ta bude ba ta ce, "Ni wallahi kunya nake ji" Murmushi ya sami kansa da yi ya taso ya dawo bakin kofar ya tsaya ta yadda suke iya ganin shatin juna. Ummita bata ma san ya iso wurin ba sai da taji amsarsa a kurkusa. "Banda abinki idan baki ji kunyata ba ai sai ki sa na fara kokwonton zabina" A wautarta ji tayi amsar tasa bata cika ba. "Ni kadai ce mai jin kunyar?" "A iya sanina dai mata sun fi son namiji mai karancin kunya akansu." "Wai naga kamar 'ya nake a wajenka" "Wai idan kin dauka kallon 'ya nake yi miki ki ajiye." Hannu kawai Ummita ta kai ta rufe bakinta saboda murmushin da ta kasa daina yi. Gabadaya nauyinsa take ji sannan tana mamakin yadda ya sake abinsa ya ma manta ita wace ce. Duk da cewa ba yau ta fara sanin soyayya ba, wannan tazo mata da salo mai girman da yafi karfin shekaru da tunaninta. Zurfafa da tayi a tunani ya bashi damar kallon irin tsayuwar da tayi. A jikin kofar ta dan jinkina sai gefen labulen da ta rike amma taki budewa. Kusa da inda hannunta yake ya kama bata lura ba sai ganin fuskarsa tayi ta bayyana a gabanta. Ja tayi da baya zata gudu ya girgiza kai wanda yanayin fuskarsa da tayi mata kwarjini ta hanata kin bin umarninsa. "Gajiya nayi da hirar bayan labulen kamar wani mara gaskiya" "To ka koma zan shigo na zauna" "Na yafe. Zan dawo anjima idan za a kai Abbas asibiti." "To Allah Ya kaimu." Ta furta da azama tana son tafiya. "Dawo Aminatu ban sallameki ba tukunna." Dagowa tayi a hankali da niyar kallonsa ta kasa. Ya san mamakin sunanta da ya fada take yi. Shima ya yi mamakin rashin mantawa. Kodayake bai taba manta duk abin da ya shafi Honourable ba. "Nace ba, wai nayi miki kuwa?" "Innalillahi ..." Furta tare da rufe fuska tana dariya kasa-kasa. "Ya kike ja min Innalillahi? Nayi?" Dariyar dai ta cigaba da yi cike da kunya ya ce "in dauki wannan kunyar a matsayin amincewarki kenan?" Da ka ta amsa masa. "Nagode Ummi-ta. In sha Allahu ba zan baki kunya ba daga ranar da zama ya hadamu a inuwar aure." Kafin ta daga kafa har ya fito. Kunya bata barta tayi masa sallama ba. I just published "42" of my story "UWA UWACE...". https://www.wattpad.com/1221353933?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=BatulMamman17&wp_originator=OAnyjBkYebmtwXfikQ2gExZ08J47W5rzKWjy6t9da0IA7fmudaAWLyyy%2BRSKqIo%2BqhsMo27LctTWW83%2BNlZI7Y0o1BXRgBOlazLJnfP8XBOylR4Ue7I09hup3DQsxy4j UWA UWACE...42 Batul Mamman💖 *** Kan Abbati a kasa ya kasance har Alh. Tahir ya isko shi a bakin motar. A bakinsa wani irin daci yake ji mai naci domin duk yadda ya kai ga hadiyar yawu yaki wucewa. Halin da ya tsinci kansa baki ba zai taba iya fada ko ya kwatanta ba. Zuciyarsa ce kawai take harbawa fiye da ka'ida. Bai ga wata maraba tsakanin sanin sirrinsa da Alh. Tahir ya yi ba da Farha. Tunda uba ya sani, me zai hana 'yar ta sani? So ya yi su rabu asirinsa a rufe. Gara ta dinga tuna shi a matsayin mayaudari akan fasiki...fasikin ma kuma manemin maza. Firgici da tashin hankalinsa ko kusa basu kai rabin abin da Alh. Tahir yake ji a dukkan gabbansa ba. Ko tafiyar da yake ba zai iya cewa ga da yadda aka yi yake iya daga kafa ba. Ya dai dawo hayyacinsa da yaga bai fi taku biyar ya rage tsakaninsu ba. "Abbati..." A tunanin Abbati maganar da Alh. Tahir zai yi masa ba za ta wuce tuhuma akan 'ya'yansa ba. Saboda haka bai bari ya kai karshen abin da zai fada ba ya ce, "Babu abin da ya taba mutumcin su Farha a a hannunmu. Ban kuma kawo kaina da niyyar aurenta ba kamar yadda yake a wurin Munzali sai da muka tuba" ya ciji lebensa na kasa wanda yake nuni da karayarsa yayinda ya cigaba da cewa "mun yi nadama, mun tuba har muna shirin barinsu kafin duniya taji a dalilin barazanar da Shazali yake yi mana...amma ban san me yasa Allah Yasa asirinmu ya tono ba a irin wannan yanayi." "Asirina ne ya tono ba naku ba Abbati. Ni Allah Ya gwadawa IkonSa ba kai ba." Da sauri ya daga kai ya dubi Alh. Tahir. Shi ma din Abbatin yake kallo. Idanunsa sun cicciko da kwallar da ya manta rabonsa da yinta. Haka ya cigaba da magana jikinsa yana mutuwa da kowacce kalma. A jikin motar ya jingina saboda babu sauran karfi a tare dashi. Ya daure dai ya fada masa cewa maganin bacci ne aka shakawa Qibdiyya saboda haka ya kwantar da hankalinsa zata dawo daidai nan da awa daya ko kasa da haka kamar yadda Comared ya fada masa. Yana ganin yadda Abbati ya shafa fuskarta cike da kulawa. A ganinsa wannan ita ce soyayyar iyaye da 'ya'ya ta gaskiya ba wadda yake ikirarin yiwa nasa ba. Zantukan da suka biyo baya kuwa ya yi su ba a cikakken hankalinsa ba. "Ban taba tuba ba. Shekara da shekaru Khadija tana kuka tana hakuri dani. Sai yanzu ne ma wani dan dalili yasa ni nadama. Bukatar kawar da wannan dalilin ce ta kawo wannan lokaci. Kafin zuwanka ina tunanin akwai lokaci a gaba da zan sami damar yin hakan in tsufa ya kamani. Ashe lokacin zai biyoni yau? Suhaib ya sani! Farha ta sani!! Lilu ma ya sani!!! Amma hawayen 'ya'yana dana mahaifiyarsu bai sa naji lokacin tubana ya yi ba. Ba don abubuwan da suka faru ba a ciki da yanzu kila na amince anyi..." Karshen maganar nauyi ya yiwa bakinsa dole ya datse zancen. Kamar saukar guduma maganganun suka dinga shigar Abbati. Farha ta san mahaifinta yana zina? Ko shi ne musabbabin ganin canjin da ya yi a gareta kwanakin baya da Alh. Tahir ya dawo gida suna wurin? "Ban taba mu'amala da maza ba. Na yau din ma dalili ne" kamar an matsi bakinsa ya fadawa Abbati abin da yasa ya zo Kano yau da kuma dalilin nadamarsa. Wato sanin da Farha tayi cewa yana neman aminiyarta wanda da ace aurenta yake nema kadai ma da sauki. "Mayafin da ya lullube soyayyar da 'ya'yana suke yi min naso yayewa. Na tabbatar fasa auren Yumna zai iya dawo min da martabata a idanunsu. Ashe Yumna ba ita ce matsalata ba. Ni ne matsalar kaina. Wallahi Abbati ina jin kamar na bude ido naji an shafeni baki daya." Shi dai Abbati kasa cewa uffan yayi saboda shi ma din mai laifi ne. A nutse dai ya saurari dukkan maganganun Alh. Tahir wanda ya sake dauka a matsayin izina. Babban mutum, mai kudi, iyali, da kima a idanun al'umma ya tasa shi a gaba yana ta sumbatu. Ashe idan basu tuba ba nan gaba suna da rabon ganin rana makamanciyar wannan ko ma wadda ta fita muni. Duk wata daraja da kimarsa shi da kansa yake jin sun gudu sun bar shi a dalilin haduwarsa da Abbati a gidan nan. Zuciyarsa har lokacin bata huta da kakkarfan harbin da take yi masa a kirji ba. Wace irin masifa ce tafi wannan? Ya aka yi bai ji girman laifinsa ba a lokacin da 'ya'yan cikinsa suka san sirrinsa sai yanzu a gaban mutumin da bai riga ya zama surukinsa ba? Kalmar surukin da ya ayyana a ransa ita ta sanya shi yin wani tunani. Babu bata lokaci kuwa domin tabbatarwa ya nuna saitin jerin wasu motoci guda hudu ya ce, "Don Allah taimaka ka miko min wayata a cikin mota in kira likitana" Durkushewa ya fara yi wanda hakan yasa Abbati yin saurin zuwa wurin motocin ba tare da ya tambayi wacce bace cikin hudun. Da d'ai-d'ai ya dinga bin tagogin motocin yana lekawa ko zai hango wayar amma bai samu ba. Ya taba hannun babu wadda ta bude. Ya dawo da sauri ya tambaye shi , "Wacce ce a ciki? Duka a rufe suke." Maimakon ya bashi amsa sai yaji ya ce "Zina bata yarda taci bashi bata biya ba komai daren dadewa. Naji dadi da kunnuwana suka jiye min kalaman tuba daga gareka wanda yanzu na tabbatar baka fadesu domin ka san ina ciki ba." Yana gama magana cikin gidan ya koma. Abbati ya sake taba jikin Qibdiyya sau daya bayan ya shiga mota ya zauna sannan ya tayar ya tafi. *** Wani irin ihu Zakiyya tayi da Abbati ya shigo da Qibdiyya cikin falon Munzali tamkar bata da rai. Ya manta ta zo gidan da bai shigo kai tsaye ba. Munzalin ma hankalinsa ba karamin tashi ya yi ba da yaga hannuwanta suna kadawa su kadai. "Me ya sameta kuma? Tare da Asaben ka daukosu? Ko ita kadai ta biyoka bayan ka ajiye su Innayo?" Akan doguwar kujerar da Zakiyya ta tashi ya kwantar da ita. "Maganin bacci aka shaka mata. Nan da. .."ya dubi agogon hannunsa "minti talatin idan bata tashi bane zamu nemi likita" "Ka kara sakani a duhu. Me yake faruwa ne?" Cewar Munzali yana tattaba jikin Qibdiyya. "Zakiyya bamu wuri don Allah" Gyara zama tayi abinta a kusa da Qibdiyya tare da rike mata hannu. "Gara ma ka fadi ko ma mene ne don babu inda zani alhali akan 'yata zaka yi magana." "Zaki tashi ko sai na mugun bata miki rai" Tsawar Munzali ta tsorata ta amma bai kai yadda zata iya bin umarninsa ba. Zai sake magana Abbati ya ce, "Zakiyya ki dauketa ku je sama ki yi mata wanka. Nayi miki alkawari zaki ji duk wani abu da ya kamata idan na gama magana dashi." Ba haka taso ba sai dai kuma a yau din Abbati ya yi mata kwarjinin da bata taba gani a tare dashi ba. Tashi tayi da Qibdiyya a kafadarta sai Munzali ya zo ya karbeta. Dakinsa ya kaisu ya fito ya rufe kofar. Da sauri ya dawo ya zauna a gaban Abbati. Shi kuma sai ya kama hannunsa suka fito waje ya bude mota suka shiga. Tafiyar kimanin minti goma suka yi wadda ta dan nesantasu da gida sannan Abbati ya tsaya. "Ina so ka saurareni da kyau Munzali." "Don Allah ka daina ja min rai haka. Wallahi kiris nake jira zuciyata ta buga kawai. Me ya faru?" Tiryan tiryan Abbati ya shiga labarta masa abin da ya faru a daren jiya da yana kwance a asibiti har zuwa yanzu. Kai ya rike wanda yake azabtar dashi da bala'in ciwo da yaji karfin halin Shazali na daukar musu 'ya. Ga kuma bacin ran son tilasta Abbati ya koma ruwa. Murfin motar ya kama ya ji ta a rufe. "Bude min Abbati. Ina jin nine ajalin Shazali." Ya furta a fusace idanunsa sun kankance sun kara yin jazur. "Munzali ka daina magana irin wannan" Abbati ya ce dashi a tausashe. Kallon takaici Munzali ya bishi da shi yana taune labbansa. "Wacce iri ya kamata in yi? Fatan alkhairi zan masa ko me? Da ka amince fa? Da shegen ubangidan nasa ya taba Qibdiyya fa? Da me zan ji? Da me zan ji??" Karshen maganar muryarsa karyewa tayi sakamakon hawayen da ya soma bin fuskarsa. "Idan kana irin wannan abin bana jin zan sami kwarin gwiwar karasa maka labarin nan." Idanunsa fayau kamar fanko ya dubi Abbati ya ce "ina jin ka. Har akwai wani mummunan labari da zai kara tayar min da hankali makamancin wannan?" Abbati bai bar komai ba game da haduwarsu da Alh. Tahir da kuma abin da Innayo ta fada masa na Ayaah da Suhaib. Sai ga Munzali ya kasa cewa komai sama da bude baki da rufe shi. Mamaki da kaduwarsa suka ninku dari bisa dari da ya fada masa abin da Innayo ta ce Suhaib ya yi na taimakon Ayaah. Da kuma wayarsa da Farha. "Tabbas akwai kudurin Allah a cikin haduwarmu da iyalin nan. Ka duba kaga alakarmu da 'ya'yan gidan, da haduwata da babansu wanda ba don shi ba kila da Allah kadai Ya san halin da zamu shiga yau. Sannan ga taimakon tsare mutumcin Ayaah da ... Yana cikin magana kawai yaga Munzali ya zura hannu ta gabansa ya bude lock. Hakan ya bashi damar bude bangarensa ya fita da sauri ya zagaya ya bude shi. "Fito in tuka" "Ina zamu je?" "Don Allah ka fito. Wannan labarin ya bude min tunanina akan abubuwa da dama" A zaton Abbati tunanin Munzali ya tafi daidai da nasa akan ganin akwai abin da Allah Ya yi nufi da Ya hadasu da mutanen nan. Bai san cewa a nasa lissafin ya kara gaskata cewa lallai Lilu ne ya bata masa 'ya ba. *** Anti Hasiya da kanta ta hada kayan Abbas dana Honourable na tafiya asibiti. Ranakun farkon aikin ne zai dinga kwana. Daga nan kuma sai dan mai bin A'i ya cigaba da kwana. Larai ce ta dage bata yarda ya nemo mai kwana da jikanta ba a cikin danginsa. Mutanen da basu iya taimaka musu da hatsi ba a lokacin da komai ya jagule masa. Ita ma Anti Hasiya tayi na'am da shawarar. Ta san yaron ba zai kuskura ya yi wasa da lafiyar dan uwansa ba ko don gudun fadan kakarsa. Sun gama ta kira Innayo ta fada mata karfe nawa duka zasu rankaya asibitin. Ba za su dawo gida ba a cewarta sai an fito dashi. "Inji waye ya ce ba za ku dawo gida ba? Ke fa na lura ganin kanki kike yi daidai da kowa" Honourable ya ce yana mai daure mata fuska da wasa bayan ta gama wayar. Tuni ta gano korafin nasa bai rasa nasaba da cikinta ba. "Don Allah kada ka koroni gida wallahi fargaba ba za ta barni ba" Illolin zaman asibiti da yanzun nan ya tattarasu a kansa saboda rashin son ta wahala ya shiga jero mata. Daga karshe ya hada da rarrashi. "Hasiya bana son mu yi sakaci da taki lafiyar. Allah bai hana ni 'ya'ya ba kuma nagode Masa akan wannan ni'ima. Hakan bai hana ni kwadayin son ganin irin da zaki haifa min ba." Murmushi ta bige da yi don ta riga ta san cewa ya gama cin wannan yakin. Da lokacin tafiya asibitin ya yi baki dayansu suka tafi aka rufe gida. Larai ma iyalanta a asibitin suka riskesu. *** Ba karamin dadi Suhaib yaji ba da zuwan su Mami. Abin da bai saba yi mata ba ma ya dinga yi lokacin, wato raki da shagwaba. Damuwa da kulawar da take nuna masa ne bai gaji da gani ba. Ko yaya ya motsa kafar sai ya ce wash. Ita kuwa jiki na rawa ta dinga ambaton sannu, ko ta ce a koma asibiti. Mayafi ta yafa ta riga kowa mikewa tana cewa gara dai a je ayi x-ray a kafar. Matan gidan dasu Farha suka taru suna yi mata dariya da suka fahimci yana yi ne da gangan. "Ki yi zamanki Mami tsokanarki kawai yake yi." Cewar Farha bayan kowa ya fita daga dakin an bar uwa da 'ya'yanta. Kan Suhaib ta shafa cike da kulawa ta ce "idan ma karyar ciwo yake babu ruwanku. In yana so yau har goyo zamu yi." Lilu da Farha basu san lokacin da suka sake kwashewa da dariya ba. Suhaib kuwa pillow ya dauka ya kare fuskarsa yana cewa, "Haba Mami a gaban yara ki ke kiramin goyo don su raina ni?" Daure fuska tayi cikin wasa ta ce "Kai ba a gaban yaran ka ke ta wash-wash ba saboda samun wuri?" 'Yan uwansa ya kalla suna ta dariya ya wulla pillow din saitinsu "Da daya daga cikinsu ne ba za ki ce suna yi don samun wuri ba" Sai da suka gama zolayarsa ita da Farha da Lilu sannan ta dawo gefen gadon ta zauna. A ranta take kara jin cewa tabbas haihuwa kyautace daga falalar Ubangiji. Duk tarin bacin ran da babansu yake haddasa mata da ta kebe da yaranta sai ta manta da wanzuwarsa. Murmushi ta sakar masa tare da mika masa wayarsa. "Saki ranka ka kira wadda tayi nasarar canja min kai daga sarkin zafin kai zuwa wannan Suhaib din dake gabana." "Ummmmm" Lilu da Farha suka fitar da sautin shakiyanci a tare. Mami babu bata lokaci ta nuna musu kofa tana shan kunu. Ficewa suka yi ana jiyo dariyarsu. Sai da suka rufo kofar sannan ta ce, "Ayaah ce ko?" Kallon rashin fahimta Suhaib ya yi mata ya amsa da cewa "tayi me?" "Ta taba zuciyarka har kake yi min abin da ban taba gani ba tun tasowarka." Kai ya shiga sosawa irin na marasa gaskiya "nifa babu komai a tsakaninmu" "Sai ka dage ka gina abu a tsakanin naku kafin wani ya riga ka." "Kai Mami..." Suhaib ya furta a kunyace yana kawar da kai. Da kafarsa kalau take ma da ficewa zai yi daga dakin a guje. Zuciyarta tamkar an zuba ruwan sanyi ta dube shi ba tare da alamun wasa ba. "Suhaib ka cinye kuruciyarka wurin dauke damuwata da kulawa da 'yan uwanka. Shi yasa ba ka san wasa ba balle yadda ake yinsa. You were too serious. Yau gashi Allah Ya amshi addu'ata. Da kan ka kake kirkiro wasa a tsakaninmu ba tare da ka san kana yi ba. Na san ba zai wuce haduwarka da niece din Munzali ba. Kana sonta ko?" "Mami sa'ar su Sauda ce fa. Yanzu take shirin gama secondary school" "And so?" Kada kai ya yi yana dariya ya ce "wannan hirar tayi min nauyi Mami a canja wata" "An canja Suhaib. Ai ni yarinyar nan ta gama min komai. Allah dai Ya rabaka da sharrin late-comer. Idan ka tsaya wasa labari zai sha bamban." "Allah ma Ya kiyaye" Sai da maganar ta fito ya kama bakinsa. Karo na biyu kenan da ya fadi kalmar nan garera akan Ayaah. Tare suka yi murmushin farinciki. Mami ta sake dubansa, shi ma sai ya nutsu da ya gane magana take son su yi. Wayarta ta mika masa daidai sakon da ta turawa Abbansa. Ya karanta sau daya ya ajiye wayar a sanyaye ya ambaci sunanta "Mami?" "Na taba yunkurin neman sakin har sau biyu amma iyaye suka hana ni. Sai dai wannan karon kamar yadda na tura masa text dinnan to in sha Allahu babu gudu babu ja da baya." "Su Yakumbo zasu amince?" "Da Allah kadai na dogara. Shi ne Ya haramta zama tsakaninmu. Allah ne shaidata ban taba kusantar kowa a waje ba. Na killace kaina da taimakonSa. Kuma nayi imanin zai taimakeni akan kudirina." Hannunta kawai ya rike yana jin wani irin nauyi a zuciyarsa. Ba don rabon haihuwarsu ba da wannan baiwar Allah bata zauna ta kwashi bakinciki irin wannan ba. "Na rasa kalmar da zan yi amfani da ita domin kwantar miki da hankali Mami" "Kayi mana addu'a ni da ku Allah Yasa hakan alkhairi ne a garemu baki daya. Zaman da ake ta cewa nayi domin ku bai amfana komai ba sai tonon silili. Farha da Lilu na fada maka sun san komai. Da ace na tafi tun kuna yara da har yanzu kuna ganin mutumcin Abbanku. Akwai ciwo a dan da zai san mahaifinsa yana yawo a waje. Har gara mata akan dan cikinka." Kwalla ce ta zubo mata Suhaib ya soma bata hakuri. Lokacin kuma Farha ta bude kofar saboda ta manta wayarta. Halin da ta riskesu ya daga mata hankali. Da sauri ta shigo tana kukan da ta riga ta gane musabbabinsa. Wayar Danliti dake gefensa Suhaib ya budo ya mikawa Mami. "Kinga sakayyar Allah. Ki daina damun kanki. Gara mu tafi kafin muma wata rana dattin ya shafemu." Da ta karanta irin kazaman chats din Danliti da Jiddo bata san lokacin da ta kankame Suhaib da Farha ba. "Kada ku kusanci zina. Wallahi a cikinta akwai tozarci da kaskanci. Ko da raina ko babu don Allah kada ku yarda shaidan yaci galaba akanku. Ba zan yafewa duk wanda ya aikata ta ba cikinku." Suna cikin wannan yanayin Prof. Zuwaira aminiyar Mami Khadija ta kirata. Sai a kira na uku bayan ta saita kanta ta iya daukar wayar. "Dr. Khadija kun iso?" "Eh, a nan shadaya tayi mana." "Kin ganni mun gama shiri zan bar Kanon yanzu ni kuma. Kwatanta min gidan sai na biyo na duba d'ana kafin mu wuce" Cikin yaran gidan Mami ta samu aka turawa Prof. Zuwaira text na kwatancen gidan. A falo suka hadu da kowa ana taba hira. Suhaib kuwa zamansa ya yi a daki ya dauki wayarsa yana jujjuyawa. Muryar Ayaah yake son ji tana tsiwar nan. Har zai kira ya tuna ta ce babansu ya karbe mata waya. Komai tsaya masa ya yi da tunaninta. Anya zai iya barin Kano bai ganta ba? Waya Mami ta cigaba da yi da Prof. Zuwaira inda take kara yi mata kwatance saboda sun kasa gane layin. Ta nemi Lilu domin ya fita hanya bata gan shi ba. Sauran yaran cikin gidan duka mata ne. "Gidan shi ne mai bakin gate a close din. Bari na fito waje kila ku hango ni" Tashi tayi ana cewa ta bari a tura wata cikin yan matan ta ce babu komai. Da wayar a kunnenta ta taho bakin gate din suna waya da Prof. Zuwaira. Zuwan Lilu ne ya taimaka wurin saukaka musu. Location dinsu ya turawa Prof. Zuwaira ta whatsapp din Mami. Ba jimawa kuwa sai ga kiranta ta ce layi daban suka shiga amma yanzu zasu juyo. Tare suka tsaya jiran isowarsu a bakin gate ta ciki yana ta tsokanarta wai zamani ya canja waye yake zaman cewa a bi hagu a karkata dama. *** Saboda mugun gudun da Munzali yake saura kadan ya wuce gidan Kawunsu Suhaib sannan ya farga. Da sauri ya taka wani wawan burki sai da taya tayi kara sannan shi da Abbati suka yo gaba kamar an hankado su. Cikin fushi kuwa Abbati ya hau shi da fada. "Lafiyarka kuwa Munzali? Wane irin tukin ganganci ne kake yi?" "Kira Farha ka ce mata ta turo Lilu ya zo ya shiga damu." Abbati ya kalle shi a tsanake ya adana bacin ransa domin son fahimtar inda matsalar take. "Me yake faruwa? Don zamu zo duba Suhaib sai mu fito a haka? Jallabiya ce fa a jikinka. Kalli yadda Shazali ya yi min da riga." Ya nuna masa kayansa da suka dukunkune kamar sun fito daga rami. Ficewa Munzali ya yi daga motar idanunsa a rufe da bacin rai ya nufi gate din gidan ko kallonsa bai yi ba. Yana fita Abbati ma ya fito. Yana ganin ya daga hannu har ya buga gate din sau daya yayi saurin riko masa hannuwa. "Munzali meye haka wai?" "Sake ni Abbati. Ka sakeni in kamo dan iskan yaron nan..." Gaban Mami Khadija yankewa yayi ya fadi ta damki hannun Lilu a tsorace. "Muryoyin nan ba na Munzali da Abbati bane?" Kafin ya iya cewa komai Abbati ya sake yin magana. Ransa a bace yake matuka don duka kafadun Munzali ya riko ya juyo dashi suka fuskanci juna. Zuciya ta tunzura shi ya daga murya yana fada. "Wane yaro? Sai tambayarka me yake faruwa nake ka ki kayi magana. Me muke yi a kofar gidan nan?" "Lilu zan kashe." "Me???" Abbati ya sake shi babu shiri yana yi masa kallon mara hankali. "Yadda bai iya tausayawa Qibdiyya ba nima..." Da sauri Abbati ya dora hannunsa ya toshe bakin Munzali sannan ya ce, "Shi ne? Qibdiyya ce ta fada maka?" Munzali ya gyada kai hawaye yana zubo masa. Mamaki ya kama Abbati ya ce "A yaushe? Duka duka sau nawa suka taba haduwa? Kaga zo mu koma gida..." Zuciya da bata da kashi. A take ta Munzali ta shiga kuncin ganin kokonto a fuskar Abbati. Bai san lokacin da ya fuzge hannunsa daga gareshi ba ya ja baya. "Nufinka karya nake yi?" Sassauta murya Abbati ya sake yi saboda ko kadan baya so wani yaji sirrinsu. Da lallashi ya ce, "Ba haka nake nufi ba Munzali. Wannan maganar tana da girma. Ka zo mu tafi mu fara yin shawara a gida." Zuciyar Munzali ta kara zuwa wuya. Wace irin shawara kuma zasu yi a gida bayan gasu a kofar gidan da zasu sami Lilu? A tunaninsa jin sunan wanda ya bata Qibdiyya sai ya batawa Abbati rai fiye dashi. Me Abbati yake nufi da nuna sanya akan lalurar 'yarsu? Sai yanzu ma ya tuna cewa tun zuwan Abbati jiya ko sau daya bai tambaye shi waye ya keta mata haddi ba. Wani hawayen ne ya zubo daga idanunsa da suka rine kamar garwashi ya yiwa Abbati kallon takaici. Kallo irin wanda bai taba tsammanin zai gifta tsakaninsu ba. "Sanin waye ubansu da kayi a yau dinnan bai isheka hujjar yarda da maganata ba? Ko soyayyar da kake yiwa Farha ce tasa kake kokarin kare kaninta ko kuwa don baka san zafin haihu.." Tsayuwar gaggawa ce ta kama numfashin Abbati da bugawar zuciyarsa. Jikinsa ya hau bari saboda tsananin bacin ran sanin abin da Munzali yake shirin fada. Gumi ne kawai yake zubo masa kamar ruwa ga wani uban sanyi da yake ratsa kasusuwansa. Bai barshi ya karasa maganar ba ya dakatar dashi cikin zafin rai. "KAR KA SOMA WALLAHI! Kada ka kuskura kayi min gorin haihuwar Qibdiyya don bacin ran da zamu shiga sai ya ninka wanda muke ciki a yanzu" Munzali kasa motsawa ya yi ko kadan sai idanu da ya kafe Abbati dasu. Shi kuwa Abbati jikinsa sai karkarwa yake kamar wanda zazzabi ya yiwa mummunan kamu. Bai haifa ba ya sani. Qibdiyya ba jininsa bace wannan ma ya sani. Fargabar da ya shiga ba komai ya janyota ba sai tsoron kada wannan masifar ta zama silar watsewar alakarsu da dan uwansa don ya wuce amini. Zai iya daukar komai banda gorin haihuwarta. Domin da zarar ya fito daga bakin mahaifinta kai tsaye zuwa gare shi, ya tabbata babu sauran zama a tsakaninsu. Munzali ba zai taba yi masa furuci irin wannan a halin rashin sani. Idan ya yi to tabbas daga zuciyarsa ne. Cikin sanyin gwiwa ya juya ya fara nufar motar. "Ina za ka?" Munzali ya fada da wata irin murya tamkar ba tasa ba. Yawun bakinsa ma daci yake yi masa saboda masifar halin da yake ciki. "Ka same ni a gida idan ka aiwatar da abin da zuciyarka ta raya maka." Yana rufe baki wani adaidaita sahu ya tsaya a gabansa wanda Munzali bai kula da lokacin da ya daga masa hannu domin ya karaso ba. A guje kuwa ya bi bayansa yana kwala kiran Abbati. Da suka ki tsayawa ya durkushe a wajen ya dauki hannu ya dinga dukan goshinsa da cikin tafin. Idan bai yi a hankali ba yana jin yana daf da zarewa. Banda haka me ya kai shi furta wandannan kalamai ga Abbati? * Gudun jinin Mami Khadija ya ninku, bugun zuciyarta ya zarce ka'ida. Tashin hankalin da ta shiga ya zarce tunani balle a fade shi. Duk wata kalma da ta fito daga bakin Abbati da Munzali ta sami damar shiga kunnuwansu ita da Lilu. Ma'anar zantukan nasu ya fita dalla-dalla basa bukatar karin bayani. Daga gabar da suka fahimci inda maganganun suka dosa Lilu ya saki wayarsa a fusace ya nufi gate din. Kunnuwansa sun kurmance, haka nan idanunsa sun makance. Abu daya kawai yake hangowa shi ne hannuwansa a wuyan Munzali a yayinda zai tuhume shi dalilinsa na yi masa sharri. "Me kake shirin yi? Ina za ka?" Mami ta tambaye shi a firgice lokaci guda ta riko hannun shi domin hana shi bude gate. Sa'arsu daya maigadin ya zaga bayan gidan zai cirowa matar gidan zogale. Muryarsa tamkar ba tashi ba saboda tashin hankali ya dube ta da mamakin tambayar da tayi masa. "Baki ji me ya ce ba? Ki barni in je..." "Kada ka fita" ta furta tana girgiza masa kai. Shi ma kan ya girgiza kuma sai lokacin hawaye ya sauko masa ya ce "idan ki ka hana ni fita zuciyata za ta iya bugawa Mami. Wallahi baki san yadda nake ji ba. Zan iya mutuwa...Mami ni ba Abbanmu bane. Ba zan taba yarda ko da wasa wani ya jefeni da irin abin da ya dade yana sanyaki kuka akan Abba ba. Kina ji fa akan sanin halinsa aka dogara da cewa ni nayi." Daga nan bai kuma sauraronta ba ya fita da sauri. Cikin sa'a yana fita ya sami Munzali ya shiga mota kenan har ya tayar. Ba tare da bata lokaci ba kuwa ya zagaya daya barin ya bude. Kallo daya Munzali wanda idanunsa suka yi masa nauyi saboda tsabar zubar hawayen da suke ya yi masa ya kashe motar. Mamakin karfin halinsa ya ma hana shi cewa komai. Sai Lilu ne da kansa ya ce, "Ka kaini gidanka. Ka kaini gaban Qibdiyya in ji yadda aka yi na yi mata fyade." "Kada ka sake ambaton sunanta. Kuma ka fice min daga mota don ban san me zan maka ba." Wata irin dariya Lilu ya yi yace "kaga nayi kama da matsoraci ne?" Domin samun damar wanke kansa a gaban Abbati ya fizgi motar a guje. Tashin motar ya faru akan idon Farha, Mami Khadija da Suhaib wanda ya fito yana jan kafa. Sai Prof Zuwaira da suka iso lokacin. Jama'ar gidan da suka biyosu bayan shigar Mami tana kiran Farha duka sun shiga tashin hankali. Da ta bawa Farhan mukullin mota akan su bi bayansu sai da matar kawun nasu ta ce ga direba ko ma mene ne gara wani ya kai su. "Kiyi hakuri Anti. Idan Allah Yasa wutar ta mutu da kaina zan baki labari. Ki ara min yau ta zama sirrin gidana don Allah." Ta juya ta bawa Prof. Zuwaira hakuri da alkawarin zasu yi magana a waya in Allah Ya yarda. Dole kowa ya hakura. Suna kallo Mami ta taimakawa Suhaib suka shiga baya, Farha taja mota da gudu. Kafin ta karasa kan titi ta kira Abbati bisa umarnin Mami. Da yake shima suna tsaye a junction ba a basu hannu ba shi yasa yaji kiran. Ganin sunan Farha ya bashi tsoro ko Munzali ya yi wani abu. Yana amsawa yaji muryar Mami. "Kwatanta min gidanku" "Lafiya kuwa Mami?" Ya ce a razane. " Munzali ya tafi da Lilu." "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Kuna ina yanzu? Bari na juyo. Ko dan gari ne zai kawo ku?" "Mu kadai ne" Inda suke kawai ya bukaci sani ya ce su jira shi a nan. Tsayuwar minti goma sha biyar suka yi domin ya hadu da goslow a hanyar dawowa. Kafin isowarsa ne Mami ta sami damar sanar dasu Suhaib abin da suka ji ita da Lilu. Hankulansu duk a tashe har Abbati ya iso. Yana zuwa bangaren direba ya nufa ya bude kofar. Farha tayi masa wani irin kallo wanda ko kusa bai bata masa rai ba. "Ki bashi wuri ya tuka" taji muryar Mami a kunnuwanta. Ba don ta so ba ta fita ta koma daya barin. Abbati ya dinga tukin 'yan Kano saboda tsoron abin da zai iya faruwa a gidan kafin su isa. I just published "43" of my story "UWA UWACE...". https://www.wattpad.com/1221354829?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=BatulMamman17&wp_originator=JWAJxTZASApy6wCWp2SxqyncmVPlR75j0u6mfsma%2FRA4DJkEWK8dcy4Cd6t6X1KPZVzn7xOh%2Bvb%2Fvr04iNZxbfE14IvfhaUcIRPlHUyKV%2BAl3wqSUqBjA8wf8A%2F9Kn7%2B UWA UWACE...43 Batul Mamman💖 *** Fitar su Munzali ba jimawa su Mal. Inuwa suka iso. Maigadi ya bisu har bangaren Abbati yana yi musu maraba bayan ya rufe gate din. Bai gane Mal. Inuwa da Mal. Sa'idu ba. Amma Habu ba bakonsa bane tunda yana yawan zuwa gidan. Sannan ya hadu da Baaba Mari sau biyu. A wurinsa suka ji cewa Abbati da Munzali basa gida amma Hanne tana nan. Da murnarsa ya dinga kwada sallama a kofar gidan tare da bubbuga dan hannun kwankwasa kofa da yake daga wajen. Hanne tana tsakar cin abinci taji bugu. Tsaki ta jejjera sun kai goma sannan ta mike ta ajiye plate din da ta gama shakarewa da abinci. "Waye ne?" Ta ce bayan sautin wani tsakin nata ya karade kunnuwan su Baaba Mari. A gajiye suke su duka musamman ita da Mal. Sa'idu saboda yanayi na rashin lafiya. "Iyayenki ne" Mal. Sa'idu ya furta da fada. Faduwar da gabanta ya yi a lokacin ba na wasa bane. A iya saninta idan ka cire tafiyarsu Hajji bata taba ganin kawun nasu a Kano ba. Mantawa tayi da hannu ta fara cin abinci ta damki hannun kofar ta bude. Da d'ai-d'ai ta bisu da ido har suka shiga suka zazzauna. Habu ne kawai bai biyo su ciki ba ya tsaya suna sake gaisawa da maigadin. Hanne ta rufo kofar ta durkusa ta gaishesu. Babu yabo babu fallasa suka amsa. Na iyaye mazan bai dameta ba sai na Baaba Mari. Tunda suke bata taba ganin ta canja mata fuska daga faram-faram ba. Shi yasa taji gabanta ya soma faduwa ta fara tunane tunane barkatai. Gauron numfashi da Mal. Sa'idu ya sauke da kyar na ciwon jiki ne yasa ta mayar da hankali gareshi a k'agauce. "Ina yayan naki" "Ya fita" Mal. Inuwa ya ce "ya yi miki bayani akan abin da yake faruwa?" Kafadarta ta daga da fari alamun ko-in-kula, sai kuma taga rashin dacewar hakan tayi saurin cewa bai yi ba. Ita Baaba Mari ta riga ta san za a rina. Komai dangane da zaman Abbati da Hanne ba bakonta bane. Mal. Sa'idu ne ma yanayin nata ya dan bashi mamaki har ya kai ga tambaya. "Wane irin zama kuke yi da dan uwan naki ne?" Hanne na jin haka ta jinjina kai da cije lebe. Zuciyarta ta raya mata kila auren Abbati aka yi da 'Yashshafa shi ne iyayen suka zo da kansu don kada ta tada balli. Ido a rufe kuwa ta ajiye tsoronsa a gefe ta soma kuka da fadin maganganu. "Haihuwa ta Allah ce ba ni na dorawa kaina ba. Tuntuni Baaba Deluwa take son amfani da hakan domin ta hada shi da 'Yashshafa..." Ta sake fashewa da kuka tana jan hanci "ashe sai da ku ka hadasu" 'yar karamar dariyar farinciki tayi da ta tuna wani abu wanda kuma bata barwa cikinta ba "Sai ta shirya, yadda na san ko zan hadiyi Al'Qur'ani ba zan kaffara ba cewa babu soyayyata a ransa na rantse har gwara ni akanta. " "Bana son zancen banza. Me ya kawo zancen karin aure kuma?" Cewar Mal. Inuwa domin katse soki burutsun Hanne wanda zai iya janyo mata mummunan hukunci a wurin Mal. Sa'idu. Shi kuwa gogan hannu kawai ya dan daga yace masa ya barta "yaran nan duk abin da suka yi basu da laifi. Tun farko na riga na fahimci zaman nasu babu armashi sai dai ban yi tunanin kawo musu maslaha ba. Idanuna sun da son ta zauna domin maganar abin da ya wuce a baya kada ta sake tashi." Cikin tashin hankalin tsoron tabbatuwar hasashenta Hanne ta waro idanu tana cewa "Maslahar ce tasa ka bashi 'yarka?" Rashin da'arta ya kara bawa Mal. Inuwa haushi ya daga hannu kamar zai kai mata mari. "Za ki rufe mana baki ko kuwa? Idan auren aka yi masa ke kin isa ki kalubalancemu ne? Ko ruwa baki iya bamu ba sai surutan banza. Ko baki auri Abbati ma na zata zamu ci darajar zama yayyen mahaifiyarki" 'Shikenan! Ta tabbata an cikawa 'Yashshafa burinta. Yanzu Gwaggo Deluwa za ta yi yadda take so da Abbati. Karshenta ma tasa ya saketa' tunanin da yazo zuciyar Hanne kenan. A fili kuwa mikewa tayi cike da fitsara domin yau dai babu sauran tsoron Mal. Sa'idu a ranta ta ce "Da kuna kaunar mahaifiyata da baku sa anyi min irin wannan kishiyar ba" idanunta akan Mal. Inuwa ta kara da cewa "irin wannan biyayyar da kake yiwa Baba Sa'idu wallahi sai...." "Ke! Hanne? Baki san su waye a gabanki bane?" Babu wanda ya kula da shigowar Habu sai da ya yi magana. Furucin nasa muguwar harara ya janyo masa daga Hanne. Ta dube shi sama da kasa ta tabe baki. "Harda su kaza a cin danko? Idan ma kana tunanin kai wa Yaya Abbati gulmar abin da na fada ne to ka kwana da sanin cewa ko sakina ya yi ni ba zan saku ba. Wallahi zama daram a gidan nan ni dashi mutu ka raba." Alamun tsoro ne ya bayyana a fuskar Mal. Inuwa ya dubi Baaba Mari da damuwa "Kina ganin abin da yarinyar nan take yi kuwa? Ko tana da mutanen boye ne bani da labari?" Bahaushe ya kan ce a juri zuwa rafi wataran tulu zai fashe. Baaba Mari da bata tanka musu ba ko kadan sai yanzu ta daga kai ta ce "uhmm?" alamun bata ma san me suke yi ba. Yau da ace babu matsalar da ta kunno kai a rayuwar Abbati da har dariya sai tayi domin ko surukarsu wato mahaifiyarsu Mal. Sa'idu da tana raye bata taba yi masa magana irin haka ba. A gidansu kam shi kadai ne ya isa, ragowar jama'ar 'yan bin umarni ne kawai. Sai gashi da ranta da lafiyarta ba a labari ba taga mutuwar bakin Sarkin gida Mal. Sa'idu. Yana zaune gurum ya kasa cewa uffan sai girgiza kai kawai da yake yi. "Nace ko tana da mutanen boye ne?" Mal. Inuwa ya sake nanata tambayarsa. Baaba Mari ba shi ta bawa amsa ba. Hanne da ta soma cewa garau take tana tsaka da son murguda baki domin cikar tsiwar ta dakatar. "Ya isa haka Hanne. Abin da kike gudu ba shi ya faru ba. Dalilin zuwanmu ya zarce batun kishiya ko sakin aure." Yanayin nutsuwa da haibar Baaba Mari a lokacin da tayi maganar saukarwa da Hanne wata irin kunya da jin nauyi tayi. Ta kalli iyayen nata maza ta sunkuyar da kai da fargabar me zai biyo baya. Ita kanta bata san me ya shiga kanta ya bata karfin gwiwar sakin baki haka ba. Kokarin durkusawa ta soma bada hakurin gaggawa take yi suka ji ana kiran sunanta da karfi da bugu kamar za a balle kofar gidan. *** Sai da aka kwashi kusan minti goma da Zakiyya taji karar tada mota sannan Qibdiyya ta soma mutsu mutsu. Da sauri kuwa ta kai hannu domin ta dagata sai gani tayi ta soma buge-buge da ihu tana cewa "ka kai ni wurin Daddy na" Firgicin da ta gani a tattare da ita ya bata tsoro ta tsaya ta kare mata kallo da kyau bayan ta rirrike hannuwan. "Qibdiyya bude idanunki nice. Mummy ce" Tarrr ta bude idon ta tabbatar da abin da kunnuwanta suka ji. Ba shiri ta kai 'yan hannuwanta ta rungumo mahaifiyarta tana fashewa da kuka. "Mummy ki boyeni kada ya sake tafiya dani." "Waye?" Zakiyya ta tambayeta tana waige waige a dakin. "Wanda ya gudu dani ya boyeni a gidansa jiya, kuma ya dokeni." Tsoro ya sake kama Zakiyya. Gabanta na faduwa ta fara tariyo yadda Abbati ya shigo da ita gidan. Kamar an zabureta zuciyarta ta tsinke da mummunan tunani. Irin tunanin da yake zuwa kan kowace uwa a yayinda taga danta ko 'ya cikin yanayi mai cike da ayoyin tambaya. Babu bata lokaci ta dage mata siketa ta kai hannuwanta wadanda tsoro yasa suka yi sanyi kalau ta dubata. Wata irin gigitacciyar kara ta saki da ta tabbatar da abin da tayi zargi ya sami 'yarta. A lokacin bata ma iya tantance yanzu aka yi ko ya dade ba. Abu daya ne dai ta fahimta. Tabbas an raba 'yarta da darajarta tun bata san me duniya take ciki ba. A haka ta sabata a kafada ta fito a guje tana kiran Munzali. Da bata ganshi ba ta kira mahaifiyarta tana kuka amma ta kasa fadin me ya faru. A haka tayi hanyar gidan Abbati tana kiran Hanne. *** Hanne dasu Baaba Mari babu wanda bai tako zuwa kofar gidan ba saboda karfin kiran da tashin hankalin dake tattare da muryar. Tana bude kofar Zakiyya ta fado ciki bata kula da kowa ba ta kama kokarin bude jikin Qibdiyya. "Zo ki gani Hanne. An cuceni. An cuci ni Hanne" Hannunta taji an rike kafin ta kai ga bude jikin. Ta juyo a birkice suka hada ido da Baaba Mari. A lokacin ta kula da mutanen dake cikin falon. Ta san kowa tunda suna zuwa Kirikasamma sosai a lokacin da take auren Munzali. Hawaye ne ya sake jika mata kumatu ta dora hannun Baaban a jikin Qibdiyya. "Baaba Mari duba ki gani. Allah Yasa ni din ce ban gani daidai ba" "Daukota mu shiga ciki" Hanne ce ta dauko Qibdiyyan suka shiga wani daki a kasa aka bar su Mal. Inuwa da tunani. *** Sai da ta gama shirinta tsaf wanda bai wuce wanka da mulka basilin ba ta nufi dakinsa. A kwance ta same shi ya yi shame-shame a kasan fanka yana jan minshari. Duk shige da ficen da aka dinga yi a gidan tun safe akan batan Qibdiyya ko a jikinsa. Ranta ya sake baci ta cije lebe ta kai hannu ta janye filon. Ba arziki kuwa Alh. Rabi'u ya tashi cikin dimuwar kasa tantance inda yake. Ido da suka hada ne ya sanya shi yin kwafa da wani bahagon tsaki. "Ki adana rashin mutumcinki zuwa in gama baccin nan don wallahi idan ki ka kunno ni yanzu sai na saba miki. Bar ganin jiya kin min yadda kike so ban tanka ba. Tara ki nake." Yana gama magana ya sake mayar da kai kan shimfida. Tsaki tayi cike da bakinciki ta ce "Malam ka tashi mu tafi gidan Munzali. Yanzu su Innayo suka dawo an sallame shi yana gida." A fusace ya tashi zaune ya kai wa katifa naushi "Wohoho Asabe!...Allah dai Ya jikan Innayo ba don ta mutu ba. Ko kusa tarbiyarku ba daya bace. Bata san musu da miji ba balle tsaki. Banda shirmenki ma a ina kika taba ganin namiji yana rawar jiki akan ciwon 'ya'yansa kamar wani dan daudu?" Asabe bata san lokacin da dariya ta kwace mata ba. Ta daga murya kuwa ta kwalawa Innayo kira. Ba jimawa kuwa ta iso. A tunaninta wani fadan suke yi wanda karshenta ya janyo Alh. Rabi'u ya taba lafiyar jikinta. Da ta gansu kalau sai ta juya za ta koma. Asabe ta yi azamar dakatar da ita ta bata labarin abin da yake faruwa. "Da satin da ya wuce ne naji yabonki daga bakin Alhaji da nace kila malami ki ka canja." Murmushi ne ya subucewa Innayo. Asabe kuwa ta hararai Alh. Rabi'u sannan ta ce "wannan magana har zuciyata nake fada miki" Kafadarta Innayo ta dan tura tana mai cewa "Mu bashi wuri ya shirya sai ku tafi" Haushi kuwa ya turnuke shi har wuya ganin da gaske 'yar maganar nan ta Innayo tasa ta daina yi masa tijarar da ta fara har tana shirin fita. A da tasu ta zo daya har ta kai suna kulla yadda zasu bakantawa Innayo rai a cikin hirarsu. Amma cikin kankanin lokaci komai yana neman sauyawa. Idan ya bar Innayo ta cigaba da shigewa Asabe ya san za a wayi gari ta karta masa rashin albarka fiye da yanzu. Karshen matsalar ba zai wuce ta hana Munzali bashi kudi ba wamda ko kusa ba zai jura ba. Zai zama cikakken lusari kuwa idan ya bari haka ta kasance. Dakin Innayo dake cike da 'ya'yanta da wasu cikin jikoki duk sun ji lokacin da Asabe ta kirata. Uwani ma a hanyar fitarta daga dakin suka yi kicibus da ta shigo gidan. Hasiya kuma daga asibiti wurin Abbas suka wutu nan domin jajen batan Qibdiyya. Maimuna ma abin da ya kawota kenan. To dukkaninsu ko gaisuwar kirki basu samu yi da mahaifiyar tasu ba ta fita. Shi yasa da suka ji shiru bata dawo ba sai suka fito duka su biyar din da tunanin tabbas akwai matsala. Da isarsu kofar dakin ne kuma wanda ya yi daidai da sanyo kan Asabe da Innayo zasu fito sai furucin Alh. Rabi'u wanda ke duban Asabe yasa su cin burki. "Dama na dade da sanin cewa kina da karancin hangen nesa. Banda haka har me ya faru da zai sa ki fara jin maganar Innayo akan tawa? Amma ance jiki magayi, ga ki ga ta nan. Ranar da munafuncinta ya bayyana kansa gareki za ki hankalta." "Ke kuma" ya juya ga Innayo wadda jikinta ya yi sanyi akan maganganunsa "Kin bi kin cika min gida da zawarawan 'ya'yanki da basa tsinanawa kowa abin azo a gani. Masu takamar kudin cikinsu me suka taba yi miki na bajinta banda wulakanci da raini. Talakawan ne kawai a nanike dake saboda har yanzu suna morarki" ya daga yatsa kurkusa da fuskarta cikin fushi "baki isa ki shiga tsakanina da matata ba saboda haka ki fita idona in rufe." Yatsan ya sake matsowa dashi kamar zai shigar cikin idonta tayi saurin runtsesu. Alh Rabi'u ya bita da kallon raini sannan ya dubi su Uwani da suka gama shigowa daya bayan daya. Da yake suma din a wuyansa suke tuntuni sai yaga dama ce ta amayar musu da cikinsa. "Tunda muke dake ko naira dari cikin 'ya'yan nan babu wadda ta taba bani ta neman albarka. Abin ya jima yana ci min tuwo a kwarya sai kace ba jinina ba" "RABI'U!!!" Innayo ta kira sunansa da karfi, da kaushin murya da kuma sigar gargadin kada ya dora wata magana daga nan. Su Hasiya ma kowacce 'Baba' take ambata cikin tashin hankali banda Uwani. Ita kadai ta taka har gabansa ta dube shi duba irin wanda ko kusa bai kamata ya gilma tsakanin uba da 'ya ba. "Mu ne kake zargin ba jininka ba ko kuwa duka 'ya'yanka da ka sakarwa uwayensu ragamar kula dasu tamkar marayun da basu da galihu?," "Mahaifin naki kike fadawa haka Uwani? To indai don nice bana son ki shigar min na yafe. Ki ja kannenki ku fita." Kalaman Salihi ne suka dawowa Uwani ta dubi Innayo da kishiyar kallon da ta yiwa mahaifinta dakiku kalilan da suka wuce. Kwalla ce taf ta cike idanun dattijuwar da ta kawota duniya har ta fara saukowa. A take taji ta kara tsanar kanta da dukkan halayyar da ta gwada mata a shekarun baya. "Nayi miki alkawari daga yau ba zan kara sabawa umarninki ba. Don Allah ki yafe wa rashin biyayyata ta yau domin idan ban yi ta ba bana jin zan taba yafewa kaina balle in roki gafararki akan abin da ya gabata. Tuni kawai nake son yi masa akan abin da na tabbatar ya sani." Maimuna, Salima, Zara da Hasiya basu iya boye mamakinsu akan furucin Uwani ba. Asabe kanta sai da ta jinjinawa lokaci da dan Adam yake cewa bai bar komai ba. Yau Uwani ce tayi laushi irin haka a gaban uwar da kowa ya san bata gani da kima. Innayo kuwa dan murmushi tayi wanda babu wanda ya fahimci ma'anarsa. Ta dai gyada kai alamun lamuncewa Uwani tayi abin da tayi niya ga mamakin dukansu sannan ta sami wuri akan tilon kujerar mai dakin ta zauna. Kallon baki da hankali Alh. Rabi'u ya yi mata ya ce "kina nufin kin amince ta yi min rashin albarka?" "Baba" Sunan a tausashe ya fito daga bakin Uwani. Shi Alh. Rabi'u ma hantar cikinsa sai da ta kada saboda tana bude baki ya tsorata. A iya sanin da ya yi mata ba bata da tsoro balle kunya. Tunda ta iya yiwa Innayo shi waye da ba za ta yi masa ba? "Naaaa...na'amm?" "Allah Ya azurtaka da 'ya'ya goma sha uku. Cikinmu wa za ka bugi kirji ka ce ka taba siyawa magani ko da na ciwon kai ne ?" Shiru ba amsa. "Rai tara a cikin 'ya'yanka kuma duka mata Innayo ce ta dauki ragamar komai da komai namu har aure. Idan akwai wadda ka sayawa cokalin tafiya gidan miji ka kama sunanta a gaban matanka." Idanusa kamar 'ya'yan bararriyar gurjiya ya yi tsilli-tsilli dasu ya kasa hada ido da kowa a dakin. "Banda fitowa daga tsatsonka babu wani abu komai kankantarsa da za ka yi tutiyar cewa ka taba yi mana a matsayinka na mahaifinmu." "Ya isa haka Uwani" cewar Maimuna saboda tsoron kada tayi rashin kunyar da zata koma ta taba mutumcin mahaifiyarsu. "Ki barni Maimuna. Ni ba Innayo bace da zan zauna ina hadiyar bakinciki da bacin ran da zai iya haifar min da ciwon zuciya ba. Ba kuma Asabe bace da zan biyewa rashin kulawar miji in sakarwa duniya 'ya'ya ba. Banda shiriya ta Ubangiji ce da tuni munyi qaurin suna cikin gantalallun mata." A salube Asabe ta ce "nima harda ni Uwani? Na zata tunda mun shirya da Innayo ba sai kin fadi aibuna ba." Kaza huce kan dami. Maganar Asabe kofa ta budewa Alh. Rabi'u ya hauta da fadan borin kunya. "Wato ni ta cigaba da fadan nawa kenan?" Ya kalli Uwani a fakaice ya ce "To duk tsiyar mutum sai na daga kafa uwarsa za ta shiga aljanna. " "Haba dai Baba" cewar Uwani tana murmushi "Fir'auna ma duk kudi da mulkinsa wallahi yana ji yana gani Asiya RA za ta wuce aljanna kuma babu yadda ya iya." Duk inda bacin rai yake yau ya sarkafi zuciyar Alh. Rabi'u. Abin takaicin ma dariyar da Asabe ta kece da ita wadda tayi sanadiyar murmushin su Zara. Baki yana fitar da kumfa kuwa ya ce "ni kike hadawa da Fir'auna? Innayo kina jin abinda 'yarki take cewa ko? Kina kuma kallon ragowar 'ya'yan naki suna yi min dariya." Kallonsu tayi tana mamakin har a wannan lokacin ita kadai yake jingina wa su tamkar dasu ta zo gidan. "Ku shige mu tafi" Uwani sai cewa tayi "Allah dai Yasa ba wani laifin na kara yi ba. Ni gaskiya ce kawai nake son fada masa a matsayinsa na wanda ya yi sanadiyar kawomu duniya." Zara tayi saurin karbe zancen da fadin, "Baba ba komai Uwani take son fada maka ba illa ka sani cewa Allah baya zalunci. Babu ta yadda mutum zai cutar da abokiyar zamansa sannan ya yi zaton idan anje lahira sai an shawarce shi za ta ji dadi. Tsaf za ta wuce aljanna ta bar miji akan layi" "Dani kike Zara?" Alh. Rabi'u ya ce cike da mamaki. Wato baki dayansu suna ankare dashi kawai sun yi shiru ne duk tsayin shekarun nan. Anya idan ya yi sake ba za su karasa kwance masa zani ba? Salima ma tunanin gidansu da gashin k'umar da Ale Gambo ya yi mata yasa ta ce "ba kowacce mace bace take da zuciyar yafiya. Idan an fadawa mutum kuskurensa ya kamata ya yi ya karba. Sai ya bayar da hakuri tare da rayawa a zuciyarsa cewa ya daina. Domin duk wani bacin rai ko hawaye komai kankantarsa da miji zai dasawa matarsa ba bisa hakki ba sai an fitar mata da hakkinta." "Sanin hakki da kyautatawa ke rike aure ba kudi ko talauci ba Baba. Idan neman na kai ne babu wanda ya kai Innayo. Kyawun hali da hakurinta kuwa hatta 'ya'yanmu suna jinjinawa. Amma mun tashi da ganin babu wata mu'amala a tsakaninku sama da kyara da hantara" inji Maimuna tayi maganar idanunta suna ciccikowa da kwalla. Hasiya ce ta rufe zancen gabadaya da cewa "Baba iyaye su suke koyawa 'ya'yansu tausayi da jinkansu. Innayo tayi iya yinta sai dai ance zama da madaukin kanwa shi ke kawo farin kai. Kamar yadda Maimuna ta ce ne, mun tashi mun san cewa mahaifiyarmu tafi borar mata kaskanci a wurinka. Wannan ya yi sanadiyar kyamarta daga 'yan uwana na haihuwa da ma wadanda ta tayaka sauke hakkinsu ('ya'yan Larai)" "Ina miki kallon mai hankali ashe duk uwar darin ce ke da Uwani?" "Ko kusa Baba. Ita fa da a namiji ta zo na tabbata halayenku sai sun yi tagwaitaka" A kufule Uwani ta ce "Innayo kina jinta fa" Hasiya ta ce "nima gaskiya zan fada muku kamar yadda ki ka faro. Baba kaga duk wanda ya zama sanadiyar aikin alkhairin wani yana da lada gwargwadon aikin. Haka ma zunubi. Mun riga mun girma kowa yana da littafin ayyukansa. Amma hakan ba zai hana wadanda suka bada gudunmawar aikin ladan ko akasinsa samun rabonsu ba. To ka duba adadin matanka da 'ya'ya...baki dayanmu sai Allah Ya tambayeka game da amanarmu da Ya baka. Baka san rayuwar kowa a cikinmu ba balle ka san ko za ka iya fidda kanka a ranar. Ina jiye maka tsoron komawa ga Allah a wannan yanayin. Kada ka manta duk hawayen Innayo a lokutan da Zara da Uwani suka cusguna mata saboda sun koyi kinta daga wurinka sai Allah Ya saka mata. Kuma..." Hannu ya daga ya dakatar da ita "ya isa haka! Ba dai Munzali bane ake maganar zuwa duba shi? Zani. A bani wuri na shirya." A tsakar gida Asabe ta tari Innayo ta ce mata ta zo su tafi gidan Munzali tare. Tayin ya zo mata a bazata. Tabbas ta matsu ta san halin da Qibdiyya take ciki. Satar dan mutum harda baraza akan rayuwa da lafiyarsa abu ne mai ban tsoro. Sai dai sabanin amsa gayyatar da Asabe tayi mata sai ta girgiza kai. "Ke da Alhaji kadai ya kamata ku je" Asabe tayi turus tana kallonta kafin ta ce "ni wallahi na dauka mun fara shiri ashe ba haka yake a gun ki ba?" Dariya ta so bawa Innayo sai ta buge da murmushi. "Mun shirya mana Asabe. Bana son zuwana yasa Alhaji sake botsare mana a hanya ko a can. Gara ku tafi ku biyun ko a samu ya je yaga halin da dansa yake ciki. Asabe bata wani gamsu ba. Hasali ma dai tunani ta shiga yi akan ko yadda take hango matsala haka Innayo din ita ma. Sai tayi saurin cewa, "Kema kina hasashen akwai matsala a gidan ko? Nayi zaton sanin hakan ne ma zai sa ki biyomu domin jin mene ne yake faruwa." "Ba ayi ciki domin abinci ba kadai. Ku biyun dai ya cancanta ku fara zuwa ku san damuwarsa. Wani sirrin tsakanin uwa da yaranta ko uba ba'a so ya ji. Zuwana zai iya zame muku karan tsaye. Fatana ki jiyo alkhairi irin wanda da kanki ma zaki zo ki bani labari". I just published "44" of my story "UWA UWACE...". https://www.wattpad.com/1221355520?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=BatulMamman17&wp_originator=mpYDskUeiEG9CDOyYcH9FvuBE0%2BCoe14jmvbGzpiBRqafRYhxsXC16Ye3NBepzEEktaVzMIHCAjQYFg6eqHR9XLj0QFKsEQwC5UNTmz7wRiPUkR9mR7KjaZ7sSHP9RXu UWA UWACE...44 Batul Mamman💖 *** Baba Mari bata yi mamakin jin halin da Qibdiyya take ciki ba tunda Munzali ya riga ya fada mata. Yadda Zakiyya ta shiga damuwa ga Hanne duk ta tsorata yasa bata nuna musu ta sani ba, saboda gudun tambayar da bata san amsarta ba. Jikin Qibdiyya da Zakiyya ta so bude musu su gani ta hana. Yawan bude jikin babu alkhairi indai ba gyara zai kawo ba. Hakuri ta dinga basu a yayinda suke ta hasashen abin da ya faru har suka ji karuwar muryoyi a falon. Zakiyya kuwa da zafin nama ta fita da ta tantance ta Munzali a cikin wadanda suka shigo. Ganin ya shigo da wani matashi sai ta hadiye abin da ta so fada. Fuskarta kawai ya kalla ya gane cewa ta san halin da Qibdiyya take ciki. Ba tare da yi mata magana ba ya gaishe da su Mal. Inuwa. Ya kuma sanar dasu cewa Abbati yana hanya. Tun shigowarsa gidan da yaga motar Buba ya fara tunanin akwai baki daga Kirikasamma. Sai kuwa maigadi ya tabbatar masa da hakan da ma su waye bakin. Kafin ya shiga ciki ya kira shi. Kin dauka ya yi kamar yadda ya yi hasashe, sai kawai ya tura masa sako. Shi kuma bai tashi dubawa ba ma sai da ya tsaya a danja. Kansa ya sake daukar chaji. Wannan rana ta ki karewa tamkar ita ce ranar wankan da ake cewa ba a boyon cibi. Mika wuya kawai ya yi ga sarautar Allah tare da fatan nutsuwar zuciya ya ziyarce shi a duk sa'ilin da ya tuna wannan ranar a gaba. Yana shiga harabar gidan ya hango Asabe da Alh. Rabi'u a tsaye suna magana. Ba shiri ya kashe motar ya fito a lokaci guda yana cewa su Mami su biyo shi. Ba don hankula a tashe suke ba da dukkaninsu sai sun yaba da tsarin gidan duk da kasancewarsu masu arziki. Asabe na ganinsa ta tare shi da tambayar ko Qibdiyya ta dawo. "Tana ciki na daukota" Ajiyar zuciya ta saki sannan ta hau sababi da yiwa Shazali mugun fata. "Abota da wannan la'anannen bata yi muku rana ba Abbati. Amma in sha Allahu yadda ya hanamu sukuni da ya sace Mariya sai ya riski bakincikin da ya ninka namu sau dari" "Sata? Me yake faruwa ne Abbati?" Mami Khadija ce tayi magana tana mai yi masa kallon tuhuma. Indai sace Qibdiyya aka yi ai babu mamaki a can aka bata mata rayuwa. A matsayinta na uwa, duk da satar mutum ba abin so bane amma a gareta kofa ce da danta zai iya tsira daga zargin da ake yi masa. Kallon rashin sani Asabe tayi mata ya hada amsoshin ga baki daya ya basu a jumla guda. "Mu shiga ciki sai a warware komai da yardar Allah" Alh. Rabi'u wanda ya kosa da tsayuwar tasu amma tasirin kalaman 'ya'yan Innayo ya hana shi ya magantu ya ce "wanne ne bangaren naka? Maigadinku ya ce duka suna can." Da hannu ya nuna musu tare da basu hanya su fara yin gaba. Jikin motar ya koma domin taimakawa Suhaib tunda da akwai matattakala kafin a shiga kowane sashe sai yaga Farha ta dawo za ta zauna. "Muje mana" ya ce bayan Suhaib ya dafa kafadarsa. "Zan jira ku a nan" ita ce amsar da ta bayar tana dan daure fuska. Bata son bashi damar ya ce dole sai ta shiga. Ai sam bata ga tsari a shigar masa gida ba alhalin akwai abu a tsakaninsu sannan matarsa da iyayensa kamar yadda taji maigadi na fada masa suna ciki. Gabanta har wani faduwa ya dinga yi saboda tsoron kada Mami ta ce sai ta shiga dole. Ji ya yi baya son barinta a wurin ya sake bude baki zai yi magana sai Suhaib ya yi belinta don ya gano inda ta dosa. "Zai dai fi ta jira a wajen" Kai Abbati ya gyada na fahimta. Ya so ya kalleta su hada ido sai yaji nauyinta ya sake rufar masa. Lallai wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa. Da taimakonsa Suhaib ya shiga falon. Sun sami kowa a zazzaune ana gaisawa. Ganin Baaba Mari a falon ya taimaka wurin ragewa Mami Khadija zulumi. Don ma dukkaninsu babu mai kwanciyar hankalin tsawaita hira sabanin haduwarsu ta farko. Bayan gaisuwar ta tsahirta ne Abbati ya gabatarwa da Mami Khadija da duka wadanda suke wurin. Zuciyarta kuwa ta tsinke cikin fargabar abin da zai iya samun Lilu. Da ya kula da sanyin da tayi sai ya ce "Mami wallahi ba na tsoron komai don ban aikata ba" iya jinta ita kadai. Jinjina kai tayi a hankali cikin zuciyarta tana rokon Allah da neman tsarinSa akan wannan musiba da ta tunkaro su. Kwarin gwiwar da yawan jama'ar da suka gani a gidan yasa ta kusa rasawa ne ya dawo mata. *** Maigadi na shiga bandaki Daddy da Umman Zakiyya suka turo karamar kofar gate din suka shigo. Umman tasu afujajan take tafe da zaninta a hannu ga hawaye ya jike mata fuska. Gidan Munzali suka nufa sai Farha dake cikin mota taga rashin dacewar barinsu su tafi bayan Maigadin ya fadi inda jama'ar gidan suke. Kafin su karasa ta bude motar ta fita ta dan daga murya yadda zasu ji. "Suna wancan gidan" ta fada tare da nuna inda su Mami suka shiga da Abbati. Umma ta dawo da sauri ta ce "don Allah rakani baiwar Allah." "Wancan kofar ce" Farha ta furta da sauri don bata son shiga. Daddy ya dubeta da shanyayyun idanunsa na 'yan duniya ya ce "ki taimaka ki rakata zan koma in shigo da mota naga maigadin ya fito" Yawu Farha ta hadiya ta kalli gate din. Tabbas maigadin ta gano yana yiwa dan saurayin da bai fi Lilu ba inkiya da ya zo zai bude masa gate. A gefe guda Umma Lami ta cigaba da sharar hawaye. Ba yadda ta iya dole ta taka kafafunta inda take ganin kamar bai kamata ta je ba. Shi kuma Daddy da yake bai san me ya faru ba ga kyakkyawar fuskar Farha da ta hargitsa tunaninsa tuni ya shigo da motar ya take musu baya. Umma cewa tayi babu lafiya a gidan Munzali. Tunda bai manta yanayin da suka riski gidan da ya kai Zakiyya ba sai bai alakanta abin da barnar da ya aikata ba. *** "Mu baka fada mana su waye bakin ba." Alh. Rabi'u ne ya yi tambayar yana mai yiwa Mami kallon kurilla. Tashi tsaye Abbati yayi ya ce masa "Munzali zai yi muku cikakken bayani" sannan ya yiwa Hanne da iyayensa nuni da kofar dakin da suka fito "mu shiga ciki mu basu wuri." Wani irin abu mara fasali ne ya sami damar tokare wuyan Munzali da jin furucin Abbati. Gwiwa a sake yana jin jiri na dibarsa ya sami wuri a kusa da Suhaib ya zauna. Falon baki dayansa daga iyayensa har na Abbatin suka shiga cikin rudani. Ba don komai ba kuwa sai kasancewar ba a taba ji ko ganin gilmawar wani abu makamancin wannan a tsakaninsu ba. Ko sallamar su Farha babu wanda ya ji sai idanu da aka kafe Abbati da Munzali dasu. "Da me kake so naji Abbati?" Munzali ya dago kai yana dubansa ya yi masa tambayar a zuciye. "Da abin da ka ke jin kai kadai Allah Ya bawa wuyan dauka mana" shi ma ya mayar masa da amsa cikin fushi. Dama ya san dole ran Abbati ya baci. Amma bai yi zaton abin ya yi masa zafin da zai tona musu asiri a gaban kowa ba. Muryarsa yaji ta karye, kuka na barazanar kwace masa. Idan Abbati ya fita daga rayuwarsa tabbas rayuwarsa za ta tawaya. Rabuwarsu bata da muhalli a kowace mahanga ya dube ta. Tashi ya yi ya karasa har inda Abbati yake tsaye ya ce "A waje na b'ata maka rai, don me za ka kawo maganar gaban iyayenmu?" "Saboda su shaida cewa ..." Katse shi ya yi kafin ya kai karshe ya ce "kalamaina kuskure ne kuma kai ma ka sani. Ashe ban kai matsayin da za ka yafe min idan nayi maka laifi ko da ban baka hakuri ba?" Yadda murya da yanayin Munzali suka sauya a lokacin da ya yiwa Abbati wannan tambaya sai da ya sanya kwalla zuwa idanun duka matan wurin. Harda Asabe kuwa domin jikinsa ya nuna asalin sallamawa ga abin da yake neman fin karfinsa. Gorin haihuwa akwai ciwo. Takalmin wanda bai haihu ba baya taba yiwa wanda ya haifa daidai. Shi yasa fahimtar halin da zukatansu suke shiga a lokacin da aka goranta musu yake da matukar wahala. Ciwon yana ninkuwa ne a yayinda gorin ya fito daga bakin wanda kake tunanin matsalarka tashi ce. Shi yasa duk dauriya irin ta Abbati ya kasa hakura. Wani kuskuren yinsa ma babban kuskure ne! "Fadin abin da yake zuciyarka ba shi ne laifin ba. Zuciyata ta kasa nutsuwa da tunanin kila na saba yi maka wasu abubuwan da suke sa kayi tunanin don ban haifa bane nake aikatasu." Magana Mal. Inuwa ya so yi sai Mal. Sa'idu ya hanashi. Ya kuma nunawa kowa alama da hannu akan kada su shiga wannan rigimar. Baaba Mari kwalla kawai ta dinga sharewa. Tsaftatacciyar alaka ma ba a rabata da sharin shaidanu daga aljanu da mutane balle kuma tasu. Tausayi suka kara bata ta kuma godewa Allah da bata gaggauta rabasu kamar yadda tayi niyya ba. Maganar da Munzali ya yi a wannan gabar wadda ta tab'a zukatansu ita tayi sanadiyar dawo da zaman na abin da aka yi dominsa tun farko. Da idanuwansa wadanda suka kada kamar garwashi ya dubesu ya ce "bani da wata kalmar kare kai ko ban hakuri da zan fada maka. Idanuna ne suka rufe dazu har nake ganin kamar ciwon da nake ji baka jin irinsa shi yasa ka kasa fahimta ta. Sai yanzu na gane cewa a cikin komai akwai hikimar Ubangiji. Ya bani haihuwa amma bana cikin mutane masu bin komai cikin lumana domin samun maslaha musamman akan abin da ya shafi wadanda nake so. Sai Ya hadani da kai. Ya baka nutsuwa da hangen nesa domin ka nuna min hanya idan na makance. Abbati wannan bai isheka dalilin yafe min ba? In kuma ba za ka yafe ba ai ka san cewa baka da ikon rabani dasu Baaba. Saboda haka duk abin da ya shafi Qibdiyya dole ne su sani." Kallo sai ya koma kan Abbati. Murmushi ya soma yi wanda yake tafe da dariyar farinciki. Ba yace ga kalmar da ta haska masa zuciya ba a zantukan Munzali. Ya dai san kawai komai ya wuce har kasan zuciyarsa. "Baka ce komai ba?" Munzali ya tsokane shi shima yana dariya. Hankalin kowa sai ya kwanta har nutsuwa ta maye gurbin tension din da ya gauraye da iskar falon. Kujerar da Munzali yake shi ma Abbati ya zauna suka saka Suhaib a tsakiya. Da Abbati zai fara yi musu bayani sai murmushin fuskarsa ya bace sai damuwa da alhini. "Jarabawa ce Allah Ya dora mana irin wadda bamu taba tsammani ba ko a mafarki. An wayi gari an sami wani mara tsoron Allah ya raba Qibdiyya da mutumcinta." Da wanda ya sani da wanda ya sami labari yanzu baki dayansu sai da suka ambaci kalmar Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Gumi kamar ruwa a take ya fesowa Daddy. Cikinsa ya kulle yayinda ya fara tunanin hanyar gudu. Yadda yake rarraba idanu yana cilla kai kamar kadangare ne ya dauki hankalin Farha. Ita da shi daga bakin kofa dama suka tsaya. Abbati ne bata son ya ganta shi kuma mara kunyar karyar Munzali yake gudu saboda karonsu na dazu. Duk wata alama ta rashin gaskiya da firgici ta nuna kanta a tattare dashi. Wannan yasa Farha taji wani abu ya darsu a ranta. Suna jin an fara tambayar waye ya yi sai taga ya juyo da sauri da nufin fita. Ta kalle shi ta tabbatar bata yi kuskuren ganin tashin hankali mara misaltuwa a tare da shi ba. Alamun rashin gaskiya sun dabaibaye fuskarsa ta yadda mutum ba zai fassara tashin hankalinsa da damuwa akan yarinya ba kadai. Ba tare da dogon tunani ba kawai tayi shahada tayi abin da zuciyarta ta raya mata. Qibdiyya ta kwallawa kira wanda hakan ya yi sanadiyar da kowa ya kallo bakin kofar. Qibdiyya dake zaune a jikin Zakiyya daga kai tayi ta hango mai kiran da na kusa da ita. Nan da nan tayi mummunar razana. Farha ta dad'a samun yakini akan zarginta. Daddy bai yi aune ba tayi saurin rufo kofar ta rike hannun taki matsawa. Ai da ya fahimci me tayi bai san lokacin da ya yi wasu kwararan taku biyu ya isketa ba. A wajen Qibdiyya zaman da akayi da zantukan da suke yi babu wanda ta fahimta. Abu daya ne ta sani shi ne yawan tambayar da aka dinga yi mata akan abin da yake mata. Shi yasa tana hango shi ta soma kuka tana cewa "Ban fada ba Uncle Daddy. Don Allah kada ka yanka min Mummy da Daddy da Papa" ta dubi Munzali wanda ya yi mutuwar zaune da idanuwanta wadanda suke nuni da jigatar da tayi daga jiya zuwa yau ta ce "Daddy kaima ai ban fada maka ba ko? Kaima haka ko Papa" ta kare tana duban Abbati. "Baki fada ba Mamana" Abbati ya amsa da kyar don magana ma baya son yi. Shi da Munzali da Lilu da uwar gayya Zakiyya duk kofar suka nufo cikin sauri. Daddy yasa karfinsa zai ture Farha ya fita ita kuma taki sakin hannun kofar. "Ki bani wuri kafin nayi miki lahani" Ya yi maganar a fusace yana mai dunkule hannu zai kai mata naushi a inda ya san za ta wahala. Jikinsa ko ta ina rawa yake saboda tsoro. Fuskarsa duk ta canza ta rikice da fargaba. Amma ko gezau taki saki. Tunda Allah Ya kubutar mata da kani tana jin abu na karshe da za ta yi shi ne bayar da gudunmawar kama ainihin mai laifin. Hannun nasa ya kusa sauka a cikinta don har ta runtse idanu taji shiru. Tana bude ido taga Abbati ne ya rike hannun naushin. Munzali kuma ya sauke masa wani wawan mari wanda sautinsa ya karade falon. Yayinda Lilu ya janyeta zuwa gefe. Zakiyya kuwa da babu wanda ya kula kujerar dinning table ta kinkimo. Munzali na sauke hannunsa ta rotsawa Daddy kujerar a kansa. Ta gaban kansa inda ya tara wata uwar suma a dukunkune kamar mahaukaci sabon kamu ya dinga tsarto da jini. Durkushewar da yayi da jinin dake zuba basu sa taji sassauci ko digo a ranta ba. Shi yasa ya sake daga kujerar za ta kuma buga masa. "Kada ki yi kisa 'yar nan. Ki bari a bi komai cikin lumana" Ashar ta debo za ta saukewa mai ambaton lumana bayan abin da aka yiwa gudan jininta sai tayi ido hudu da Mal. Inuwa. Albarkacin furfura da yaci yasa ta saki kujerar ta kara fashewa da kuka. Ganin yadda falon ya koma da sauri Baaba Mari ta dauke Qibdiyya ta koma dakin da suka fito. Duk wannan abin da akeyi ashe Lami suma tayi tun yunkurin Daddy na farko wurin fita. Mami Khadija tana tsakar godiya ga Allah da Ya wanke mata d'a tun kafin ayi nisa ce ta fara lura saboda a kusa da ita take zaune. Kanta ta gani ya langabe gefe guda ta rufe idanu. Da hanzari ta tabo Asabe wadda daga gani ta fahimci 'yan uwa ne saboda kamanninsu. Ita kuma da kuka ta hau ihu tana kiran sunan kanwarta. Da kyar aka samu ta dawo hayyacinta. Tana bude ido ta yunkuro ta zauna kowa yana yi mata sannu. Mutum guda ta nema da ido tayi sa'ar gani, wato Zakiyya. Ta isketa tayi kuka har ta gaji. Fuskar nan ta cabe da hawaye da majina. "Matso" ta kirata da hannu. Zakiyya na matsowa kuwa ta cire hannu ta tsinketa da mari. "Baki da hankali ne Lami?" Asabe ta furta da mamakin wannan hukunci "ga wanda za ki mara can fa" ta nuna Daddy a zaune a kan kafet da jini a fuska. "Ita zan mara Yaya Asabe. Zakiyya zan fara hukuntawa domin ita ce silar komai." "Umma ni kuma?" Zakiyya Mami Khadija na jin haka sai ta mike. Duka 'ya'yanta ma suka tashi. Baaba Mari ma ta ce da Hanne ta samo abinci ta biyota ciki a bawa Qibdiyya. Umma Lami ta gyara zama ta hanyar sauko da kafafuwanta daga kan kujera ta ce "ina za ku? In kowa zai fita ke Hanne da wannan budurwar..." Ta nuna Farha "ku dawo ku zauna. Abin da zan fada zai iya amfanarku tunda baku wuce shekarun haihuwa ba". Ko ba a fada ba a kallon fuska kawai mutum zai karanto ciwon da yake cin zuciyar dattijuwar nan. "Zakiyya kin cuceni kin cuci kaninki da 'yar cikinki. Komai lalacewar dan iska a kullum yana kokarin yin abinsa ne a nesa da gida. Ma'ana cikin gidansu ko inda idon sani zai iya gani. Amma yau a dalilin sakacinki irin wannan kwad'on mara dadin ambato ya faru a tsakanin zuri'ata" Hakuri 'yan dattijan suka dinga bata ta girgiza kai tana cije baki. "Gado ne kadai Allah bai shardanta tsakanin Daddy da Qibdiyya ba. Banda shi duk wani hukuncin da ya hau wuyan mahaifinta na halacci da haramci shi ma yana kansa. Wane irin hakuri zan yi? Wallahi da ganin irin wannan bakar rana gara ace mijina na kama da mace akan gadona." Mami Khadija taji gabanta ya fadi domin kalaman karshen sun ratsa ko ina a jikinta. Ji tayi kamar da ita matar nan take. Zakiyya kuwa cikin kuka ta ce da maihafiyarta "Mene ne laifina Umma? Ta yaya bacin rayuwar Qibdiyya zai zama laifina alhalin ni ba mazinaciya bace?" Numfashi mai tafe da zazzafar iska mara dadi Umma Lami tayi fashin baki akan bakincikin da ya sark'esu muddin rai. "Zakiyya kowane bawa bai isa ya tsallake kaddararsa ba ni na san wannan. Na kuma yarda kaddarar yarinyar nan kenan. Matsalar shi ne ke kika zama silar tabbatuwar kaddarar. Akan mutuwar aurenki kin zo kin ce Munzali yana yi miki boye-boye. Don kin matsa da tambaya ya koroki gida. Amma ni nafi tunanin shegiyar kyuya da gandarki ce ta kashe miki aure. Babu abin da yake kayatar dake sama da danna waya, kallo da bacci. Sau nawa Qibdiyya za ta dinga kwala miki kira daga bandaki kiyi ta jera mata ina zuwa akan uzurin banza? Ko kin manta ranar da kika bari har bayangida ya soma bushewa a jikinta saboda bana nan. Sai da na shigo nace miki zai maidota gidan ubanta?" "Naji ban kyauta ba amma Umma meye hadin laifina da abin da Daddy yayi?" "Son zuciya. Yawan fadan da nake yi miki sai ki ka mika masa matsayinki na uwa. Daga bata abinci aka koma cire uniform da sakawa (bata san idan bata gida harda tsarki da wanka Zakiyya take saka shi ba). Ko shi ya kawota duniya ai akwai abubuwan da basu dace uba ya yiwa diya mace ba. Kuna son haihuwa amma ba kwa jure raino. Da yawan matan da irin haka yake faruwa da yaransu idan an bi sila baya rasa nasaba da sakaci ko yaya ne (Ban ce duka ba! Mau'du'in labarinmu yana magana ne akan sakacin). Muna cikin zamanin da uba mahaifi yake iya ajiye mutumcinsa ya taki tsatsonsa mace ko namiji. Kinga kuwa halin ko in kula ba na uwa bane. Sai kin yi da dukkan gabbanki ki kuma hada da tsananta addu'a wadda bana jin ke kina ma tunawa da cewa ya kamata ki dinga yiwa 'yarki. A soyayyar baki da daukarta a hoto ki ka fi kauri." Dukar da kai Zakiyya tayi yayinda kukanta ya kara tsananta. Tabbas mahaifiyarta ta fadi gaskiya. Kuma ita shaida ce cewa indai ta gani sai tayi mata fada akai. "Baki yi mana adalci ba Zakiyya. Abu irin wannan ya faru amma na rasa kukan me zan yi? Sannan ina ji ina gani dole in cigaba da kwana gida daya da wanda ya yiwa jikata haka tunda nice uwa a gare shi. Duk bacin ran da zan shiga ba zan iya korar shi daga gida ba kada yafi haka lalacewa." Maganganun Umma Lami sun bawa kowa tausayi harda masu kuka. Musamman Farha da Hanne wadda ta kara tsorata da sharrin kyuya. Daga nan iyayen suka saka baki aka jajantawa juna. Wadannan zantuka musamman na Umma sun tsayawa Munzali kwarai a zuci. Kansa ya kara dorawa laifin abin da ya faru. Ya kuma gaskata cewa lallai bawa bai isa ya yiwa Mahaliccinsa wayo ba. A lokacin da rayuwa take gara musu, suna tsaka da samun kudi kamar ruwan sama ya aureta bisa umarnin Asabe. Na farko babu soyayya sannan sam aure baya gabansa. Saboda haka ba shi da lokacinta. Tun tana kuka da korafi har ta saba. Waya da tv suka zama abokan hirarta. Ga masu aiki har biyu ya dauko sannan ga kudi baya yankewa. So ya yi ya dauke mata hankali da jindadin duniya. Sai dai bata jima ba cikin rayuwar ba-cas-ba-as ta gaji ta sake kafa masa kahon zuka. Shi ne dalilin sakin. To ashe da wannan sabon na rayuwar da ya koya mata ta tafi. Gashi 'yarsa ce ta kwana a ciki. Shi yasa da ya kalleta yaga yadda take zubar da hawaye ta bashi tausayi. Kallonsa ya mayar ga Daddy ya hadiyi yawu da kyar. "Tsakaninka da Allah tun yaushe ka fara bata Qibdiyya?" Amsar tambayar famin ciwo zata zama shi yasa Abbati ya nemi dakatar dashi. "Munzali.." Runtse ido Munzali ya yi ya gyada kai alamun ya hakura da tambayar sai ya canja wata "Me yasa sai ita? Ya aka yi ka iya keta haddin yarinyar da idan kaf matan duniya sun kare ba za ta taba halatta a gareka ba." "Ku yafe min" ita ce kadai amsar da ya iya hadawa da busassun labbansa. "Kada ka yaudari kanka. Duk fadin duniya babu wanda ya isa ya yafe maka a madadin Qibdiyya. Ka roki Allah tsahon kwana domin ka roketa da kanka." Daga wannan bai sake cewa komai ba ya tashi ya bawa su Mami hakuri sannan ya fita daga bangaren. Sam zuciyarsa babu dadi. Yana son ya hada Daddy da hukuma a sauya masa kamanni amma cikin ransa yana jin kamar bai cancanci yin haka ba. A matsayinsa na uban Qibdiyya wanda jirwayen kazantar rayuwarsa yabi 'yarsa ina shi ina ganin laifin wani? Gwiwoyi a sake Umma da Zakiyya suka tashi zasu tafi. Baaba Mari ta riko hannun Qibdiyya ta damkawa Zakiyya tare da cewa, "Ki tafi da ita domin yau tafi bukatarki akan kullum" Da zasu fita ne Qibdiyya ta ce "Papa ina wayar da na baka?" "Subhanallah" ya furta da sauri don shaf ya manta ta bashi waya ta ce ya kira. Aljihunsa ya laluba ya daukota ya kunna. Cikin sa'a ya samu akwai chaji. Ya duba wurin sunaye yaga 'Alhajina' da wannan ya yi tunanin ko waye kila yana da alaka da mai wayar sai ya kira. I just published "45" of my story "UWA UWACE...". https://www.wattpad.com/1221355822?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=BatulMamman17&wp_originator=vwihQZy0W9YXQvP7R%2FtMltmxa%2F15b2tHeN1txxBjr5ZBvikcf3aylzrsi7bsEL83RMwgrLdcJNzrbHKFPZyf7VdK9pZmM8onmizYpGjR2yXyiR2cyhJyZU8jw%2F6BvX%2B%2B UWA UWACE...45 Batul Mamman💖 Da shigar kiran ko dan sautin nan na alamun ta shiga da mutum yake ji idan tana ringing bai kare ba aka dauka. "Abdul?" Abbati ya ji an ambata da muryar da ake iya gane tana cikin tsananin tashin hankali. "Ba Abdul bane. Na sami..." Katse shi Alh. Sadisu ya yi cikin matsanancin bacin rai ya ce "Waye kai? Ina dana? Wallahi duk inda kuke a kasar nan sai an nemo min ku" Duk inda aka yi shi ma dansa Shazali ya dauka, Abbati ya ayyana a ransa. Tunanin hakan yasa shi kashe wayar ya duka a gaban Qibdiyya ya ce ta fada masa a yanayin da ta baro mai wayar cikin dabara. "A gidan da Uncle dinnan ya kaini na ganshi. Kuma har ya daukoni zai kawoni gida. Sai Uncle dinnan ya buga masa kai da bango ya yi jini. Sai ya bani ya ce ka kira Daddy dinsa a zo a dauke shi." Tiryan tiryan ta fada kowa yana ji. Cikin kuka Zakiyya ta roki Abbati da ya fada mata tsakani da Allah me yake faruwa. Ita tunda basu mayar da Qibdiyya gida ba ta san akwai matsala. Kansa sake daukar chaji yayi. Ya waiga babu Munzali a wajen. Ya dubi su Mami wadanda sai yanzu da hankalinsa ya daidaita ya tuna gamuwarsa da Alh. Tahir. Yawu ya hadiya ya fadi iya abin da zai iya. "Abokinmu Shazali ne ya dauketa jiya domin ya yi mana barazana ni da Munzali. Daga inda na karbota nake shi yasa ma ku ka ganni haka" ya nuna suturarsa wadda bai san tuni kowa yake tunanin inda yaje aka yamutsasu haka harda yagewa ta wuya ba "Sauran bayanin sai na dawo. Da alama ba ita kadai ya dauka ba." Wayar da tunda ya katse take faman ruri ya dauka tare da bayar da hakuri. "Na tsaya neman bayani ne game da mai wayar don ban san shi ba. Ka fada min inda zamu hadu domin zancen ba na waya bane" "Dole ka ce ba na waya bane mana don kada ayi tracing dinku. Idan kudi ne ka fadi ko nawa kuke so a wuce wurin." Alh. Sadisu ya kare magana cikin fushi yana bubbuga kafarsa daya a kasa. Babu nutsuwa ko kusa a tare dashi. Duk sakan guda gani yake kamar zai rasa dansa har abada. Shi kuwa Abbati da ya tuna yadda yaji kafin ya dawo gida da Qibdiyya sai ya yi masa uzuri. "Kayi hakuri. Idan na zo zan yi maka bayani gwargadon abin da na sani." Wayar a speaker take dama saboda 'yan sanda da suke wurin. Saboda haka da rad'a da inkiya da komai na kwatance suka nunawa Alh. Sadisu abin da suke bukata ya yi. Ya kuwa fada yadda suke so din. "Ka same ni a gate din makarantarsu Abdul." "Ina ne?" "Kada ka nemi ka raina min hankali mana.." Wani dan sanda ya sake yi masa alama da hannu. Ba don ya so ba ya fadi sunan makarantar da unguwar da take. Kallon iyayensa da duk wadanda suke wurin Abbati ya yi ya ce, "Zan je na sami mahaifin yaron" Mal. Sa'idu ya dube shi da damuwa a fuskarsa ya ce "anya ayi haka kuwa? Daga yanayin maganarku naga kamar kai yake zargi" "Babu komai in sha Allahu. Bari na canja kaya na je" Mami Khadija ya sake bawa hakuri da Lilu. Suka yi musabaha da shi da Suhaib sannan suka ce masa zasu koma gida. "Za ku gane hanya kuwa? Ko za ki biyoni a baya na kai ku sai na wuce daga can?" Ya yi maganar yana duban Farha. Mami tayi la'akari da halin da ake ciki ta ce "Kada mu wahalar da kai. Idan mun bace hanya zamu kira gidan. Allah Ya rufa asiri Ya kare gaba". "Babu wata wahala. Makarantar a hanyar take. Sai ma mun wuceta kafin mu karasa gidan" Baaba Mari ta saka baki ta ce su amince su bishi. Idan ya fadawa mutumin abin da ya sani sai su wuce. Bai kamata a barsu su tafi bayan abin da ya faru ba. Haka kuwa aka yi. Cikin minti goma Abbati ya kimtsa ya sauko suka tafi. Bai nemi Munzali ba saboda ya san a yau zuciyarsa ko kusa babu dadi. Lilu ne yake jan motar. Farha na gaba su Mami da Suhaib na baya. Kafin su isa Alh. Sadisu ya kira Abbati yafi a kirga. Wani ya dauka ya ce su yi hakuri yana hanya, wani zubin ya share saboda ransa ya fara baci. Suna isa ya hango motocin 'yan sanda fal a gate din makarantar. A ransa ya ce dan wani babba ne Shazali ya tabo. Wuri ya samu ya yi parking su Lilu ma suka yi a bayansa a waje. Yana fitowa aka sake kira. Ya kara wayar kenan a kunnensa daga bakin gate din kawai yaga 'yan sanda sun yi masa da'ira. Kafin ya gama sanin me yake faruwa sun fara dukansa. Cikin abin da bai wuce kifta ido da budewa ba suka tura shi cikin motarsu. Farha bata san lokacin da ta fito daga tasu motar ba da aka fara dukan shi. Lilu ma ya biyota. Haka Mami Suhaib daga baya. Mami ta rasa da wane suna za ta yiwa wannan rana lakabi. Kafin su iso motar da aka saka Abbati tuni tayi gaba. Sauran ne a baya. Farha kuka kawai ta fashe dashi. Lilu ya tsayar da daya daga cikin motocin yana yi musu bayani cewa ba Abbati ne ya dauke yaron ba. "Yaro ka kama bakinka ko kai ma a tafi da kai wallahi." Wanda ya bashi amsa ya kallo gate din ya ce da direbansu "ga Alhajin nan ya fito muje" Su Mami suka juya a tare. Alh. Sadisu ne ya fito yana tafiya da sauri kamar zai tashi sama. Ga 'yan kazanginsa da securities da malaman makarantar suna biye dashi a baya. Kwakkwaran kallo guda Mami tayi masa ta kara sauri tun kafin ya shige motar da aka riga aka bude masa. "Alh. Sadisu?" "Don Allah ku rabu dani" ya amsa a fusace don ya gaji da amsa mutane. Burinsa ya gan shi a station din da aka kai mutumin da ya kira shi a waya. Da ta fahimci da wuya idan zai juyo balle ya kalleta ne ta kara da cewa "Alhaji Khadija ce, Maman Suhaib" Ai kuwa da saurinsa ya leko kansa ta taga. "Hajiya Khadija me kike yi a nan?" Ya yi wa direbansa alama da su tafi yana cewa da ita "Za dai mu yi magana daga baya, yanzu ina cikin tashin hankali ne wallahi" Da sauri ta ce "na sani.Abdul aka dauke ko? Manemin 'yarka ne aka kama yanzu. Ba shi ne ya dauke shi ba" Kallonta ya yi a tsanake sannan sautin Innalillahi da Farha take ta ambato cikin hawaye ya soma shiga kunnens. "A mota kuke?" "Eh" "To ku biyo mu don Allah." Suna shiga mota tasa Suhaib ya kira mata Munzali. Ita da kanta tayi masa magana ta kuma umarce shi da ya boyewa su Baaba Mari kafin a san me yake faruwa. Sai dai tuni hankulan iyayen ya tashi tunda ya amsa wayar ne a gabansu. Suna gama wayar suka nemi jin ba'asi. A dole ya sanar dasu. Haka suka tashi babu wanda ko ruwa ya shiga bakinsa tun zuwansu suka bishi. A hanya ya kira Alh. Tahir. Yana can gidan Comared har lokacin bai tafi ba. Ya yi bakincikin rashin zuwa da direba gidan saboda har yanzu babu kuzarin tuka mota a tare dashi. Kansa ya rufe ruf ya rasa zaren kamawa tun tafiyar Abbati. Da yaji kira kamar ba zai dauka ba yadda ya yiwa sauran kiran da suke ta shigo masa. Sunan mai kiran da ya gani ne ya sauya masa tunani. Abokinsa ne da suka hadu ta dalilin ayyukan kwangila. Duk zafin zuciya da kwarjinin da Alh. Sadisu yake yiwa mutane sai tasu tazo daya dashi. Har ta kai suna ziyartar juna a gida. "Alhaji kaji labarin na shigo Kano ne?" Ya ce da kokarin kawo raha tsakaninsu. "Kana ina Alh. Tahir? Don Allah duk inda kake ka taho police station din Gadon K'aya. Akwai matsala an sace Abdul kuma muna tare da iyalinka Haj. Khadija." Satar Abdul din da yaji ta firgita shi. Sai dai ko kusa bata kai kidimar da ya shiga da yaji sunan Mami ba. Ya nemi jin cikakken bayani amma shi ma Alh. Sadisun bashi da abin cewa. Mukullin motarsa da waya kadai ya dauko ko hula da babbar rigar da ya cire bai tuna ba ya fito. A harabar gidan ya tarar da Comared da Shazali kowa rai a bace suna ta musayar yawu. Comared ya dora masa laifin duk abin da ya faru shi kuma Shazali yana cewa ba zai fita ba sai an bashi kudin da aka alkawarta masa ko ya baza sirrinsu a ahafukan sada zumunta. "Kai karamin kwaro ne Shazali. Karyar rashin mutumci kake shi yasa har ka sami kwarin gwiwar mayar min da magana. Harma da barazana. Amma yanzu zan tuna maka waye ubangidan kuma waye bawa." Kira ya kwala da karfi wasu garadan maza biyu suka fito ya umarcesu da su kulle masa Shazali a store din gidan. Da yake jikinsa ya riga ya yi tsami saboda dukan da Abbati ya yi masa sai ya kasa kwatar kansa. Alh. Tahir yana gani aka ciccibe shi aka yi ciki dashi. Da Comared ya nemi jin ina zai je da sauri haka kin fada ya so yi. Sai kuma ya tuna cewa ta dalilinsa ya hadu da Alh. Sadisu. A takaice ma dai yana cikin yaransa na hannun dama. Saboda haka babu bata lokaci ya zayyane masa iyakar abin da yaji daga bakin Alh. Sadisun. Comared ko cikin gidan bai koma ba ya kira direbansa suka tafi tare. *** Kafin su Alh. Sadisu su iso har an fara dukan Abbati a cell. Lokacin ya daina kokarin kare kansa daga zargin da ake yi masa balle dukan. Irin tunanin Munzali wanda yake ta kwabarsa a kai ne ya shige shi. Kokwonto da tsoron ko tubansu bai karbu ba shi yasa da an toshe kofa daya sai wata daban ta bude ta bakin ciki. Ba su suka sarara masa ba sai da wani ya leko ya yi musu magana. "Kai Sergent, ku taho da shi ofishin DPO yanzun nan ana jira" Suna jin haka sun san cewa Alh. Sadisu ma ya iso. Jiki na rawa saboda kwadayin samun wani abu suka fito. Dukan da suka yi masa ma dama don su burge shi ne in yaji dadi ya yi musu ihsani. Hankada shi su ka yi har ciki. Tausayinsa ya sake tsirga zuciyar Farha da taga yadda ya koma cikin kankanin lokaci. Fita taji tana son yi daga office din saboda ba za ta iya jurar kallon sa a a cikin wannan yanayin ba. Tana share hawaye suka hada ido sai ya yi murmushi yana yi mata alama da ta bar kuka. Bai ankara ba yaji an kai masa wata mahaukaciyar a wuya. Yana kici-kicin kwacewa sai saukar duka a gefen idonsa. Farha ta sake saka kuka yayimda Lilu da DPO suke kicikicin kwace Abbati daga hannun Alh. Sadisu wanda yake ta ihun a fito masa da dansa. Da kyar bayan an rabasu DPO din ya ce da Abbati "Malam ina mai baka shawara da kada ka wahalar da kan ka da mu ka fada min yadda aka yi ka dauke dan Alh. Sadisu da dalilinka na daukarsa" Zai fara bayar da amsa su Munzali suka shigo suka same su. Hankalinsa ya kara tashi da yaga yadda aka sab'a masa kamanni a lokacin. Wannan abu fa a dalilin dawo da 'yarsa ya same shi. Shi kadai yaga ribar zama da Abbati yayinda Abbatin yake shiga tarin matsaloli tun farkon haduwarsu. Baaba Mari da Mal. Inuwa suka rasa abin cewa saboda tsananin tashin hankali. Mal. Sa'idu ne ya hau bayanin cewa dansa ba zai taba cutar da wani ba balle a kai ga sace shi. DPO ya tambayi matsayinsu tare da yiwa Sergent din da ya shigo dasu fadan cika mutane a wurin. Jin cewa iyayen wanda suke tuhuma ne sai ya ce lallai a ragu. Office din ya rage daga Alh. Sadisu sai Mal. Inuwa, Munzali (a matsayin mahaifin yarinyar da ta kawo waya) da Abbati. Su Baaba Mari, Hanne da Mami Khadija da su Asabe duka suka koma reception. Mal. Sa'idu kuwa jinjina kai ya dinga yi. Duk takamarsa akan 'ya'yan 'yan uwansa yana ji yana gani DPO ya ce ainihin mahaifin Abbati kadai ake bukata. Wannan ya kara karya lagonsa da yaga ko kara babu Mal. Inuwa ya ce shi ne uban. Shi Abbati Allah kadai Ya san irin ciwon da kansa, jiki da ruhi suke yi masa a wannan lokacin. Idonsa daya har ya tara jini don ya kasa bude shi sosai. Ya daure ya fada musu iya abin da ya sani DPO ya bubbuga kan bironsa akan tebur ya sake yi masa wata tambayar. "To kai me yasa ya dauki taka 'yar? Sannan ina ya kaita har ta hadu da Abdul?" "Ban san inda ya kaisu ba. Kamar yadda na fada maka ya yi amfani ne da abotarmu ya tafi da ita daga hannun kakarta a asibiti." Abbati ya amsa masa cikin wani irin yanayi na kosawa da komai. "Wannan bayanin naka bana jin ko alkali ka fadawa zai karbi uzurinka balle ni." Munzali ya galla wa DPO din harara ya ce "Karya kake so ya yi maka ko me?" "Kaga DPO a mayar dashi cell mana a dauko Shazali din" Alh. Sadisu ya fada ganin lokaci na tafiya an kasa cimma matsaya guda "idan wani abu ya sami d'ana ku ma da kuke ta jan kafa ba tsira zaku yi ba" ya kare magana yana tashi tsaye. Fita ya yi da waya a hannu yana waya wadda da alama da wani babba cikin 'yan sanda. DPO din da kansa ya taso Abbati a gaba zai mayar dashi cell. Suna fitowa duka jama'ar da ya zata sun fita waje suka taso lokaci guda. Kowannensu da irin tambayar da yake jefowa domin son jin ko ya kubuta ne. "Naga alama kana da tarin masoya" cewar DPO ya mayar da hankalinsa garesu "ku bashi shawara ya fadi gaskiya. Wallahi akan yaron nan case din yafi karfin tunaninku. Komishinanmu ma yana hanya kuma ko shi bai isa ya ja da umarnin Alh. Sadisu Nakano ba." Jiki sam babu kwari Abbati ya dubi DPO din ya ce "iyakar gaskiyata na fada muku. Bani da zabi idan baku yarda ba sama da na cigaba da addu'ar neman taimakon Allah. A cikin kwanakin nan ina cikin jarabawar Ubangiji. Abubuwa suna ta tasowa wadanda suke barazanar rabani da duk wani abu da nake so. Babban burina bai wuce in rufe ido ko da na minti biyar bane idan na farka in ga ashe duka kwanakin nan mafarkinsu nayi." Sai ga Mami Khadija da Asabe suna share kwalla. Farha ta fita ta sami wani dan dandamali ta zauna tana kuka. Ana dawowa daga rufe shi Alh. Sadisu ya dawo. Munzali ya tari gabansa ya ce shi ya san gidan Shazali. "Me yasa baka fada ba tuntuni? Officer a hada shi da mutane mu tafi" Basu bar wurin ba Alh. Tahir da Comared suka shigo reception din. Mami Khadija da 'ya'yanta suka fara kallon kofa da tarin mamakin me ya kawo shi nan. Tana yin ido hudu da Comared taji zuciyarta ta tsinke. Babu ko tantama abin da suka saba na tara 'yan mata a guest house a kwana ana sharholiya ne take jin ya hadasu. Takaici ya sake kama ta da ta tuna cewa duba dansu fa suka zo yi amma ya kare da zuwa wurin Comared. "Ina Abbatin yake?" Ya fara tambayar Munzali. "Kai kuma waye?" DPO ya tambaya ganin shima nasa hankalin a tashe yake. Alh. Sadisu ya bashi amsa da cewa abokinsa ne. Shi kuma Alh. Tahir ya ce da DPO su shiga office dinsa yana da magana. Alh. Sadisu ya yi saurin cewa "A'a ka bari tukunna. Gidan wani Shazali zamu je Abbati din ya ce wai 'yarsa a can ta hadu da Abdul." Comared ya ce "Shazali kuma?" "Ka san shi ne?" DPO da Alh. Sadisu suka yi masa tambayar a jere. "Kwarai kuwa. Yallabai muje office din naka" "Comared wallahi ba zan iya sake bata lokaci ba. Ka fadi ko ma mene ne a nan bani da damuwa." Alh. Sadisu ya furta a kagauce. Alh. Tahir da Comared suka hada ido. Munzali kansa ya tsorata don bai san me zasu ce ba. Jikinsa ya gama sanyi yana jiran a farke musu laya. "Shazalin nan da ake magana gagarumin kawali ne mai fada a wurin manyan mutane. Yana kai maza da mata duk inda ake da bukata. Bana fata amma indai shi ya dauke Abdul akwai yiwuwar ..." A hargitse Alh. Sadisu ya ce "kai dakata min nan kada ka karasa wannan maganar banzan da ka dauko." Baaba Mari, Mal. Inuwa da Mal. Sa'idu sun san waye Shazali da rawar da ya taka a rayuwarsu Abbati. Shi yasa furucin wannan mutumin bai basu mamaki ba. Sun dai kara shiga rudani ne akan dalilin da yasa Shazalin ya dauke Qibdiyya tunda basu sami zama anyi maganar ba. Cikin lumana DPO ya lallaba Alh. Sadisu da cewa "Yallabai kada muyi saurin katse masa hanzari. Irin wannan abin yana cikin manya manyan matsalolin da muke fuskanta daga makarantun kwana. Lallai zamu je gidan shi Shazali din. Kuma yanzu zan tura mota a taho min da Principal, masu gadi da malaman makarantar tasu." Gyaran murya Comared ya sake yi ya ce "ina da magana" "Ina jinka" Alh Sadisu ya bashi amsa rai a bace kamar shi ne Shazalin. "Ku bani kimanin rabin awa zan kawo muku Shazali har nan." Alh. Sadisu ya nisa ya ce " kowane sakan guda yana da mahimmanci a gareni. Ni dai na fi son mu rankaya gidan nasa in ga halin da dana yake ciki" "Ka sanni ba tun yau ba. Abin da ya shafi jininka nima ya shafeni. Ka bani lokacin da na bukata kawai. Komai zai zo karshe in sha Allah. Shazali shu'umi ne. Na rantse maka zai gwammace a kulle shi akan ya fadi gaskiya idan muguntarsa ta tashi." "To meye alakarku da Abbati da shi wannan Shazalin da ake ta fada?" DPO ya jefawa Comared tambayar da take cin zuciyar kowa. Alh. Tahir ne ya bashi amsa da cewa "Ni zan baka amsar tambayar nan idan komai ya lafa." *** Babu wani abu da zai sami bawa face da sanin Mahaliccinsa. A wannan rana taimako ya zo wa Abbati da Munzali a yanayin da basu taba zato ko tsammani ba. Waye zai taba kawowa a ransa cikinsu cewa duk ranar da asirinsu ya tasarma tonowa Alh. Tahir zai zame musu garkuwa? Sai gashi ya zama wata katanga wadda ta tokare bayyanar sirrinsu da tozarcinsu a idon duniya ba tare shi kansa ya shirya hakan ba. Kamar yadda DPO ya fada, ya tura motoci biyu an taho da duk wani mai kusanci da aji ko hostel din su Abdul daga makarantarsu. Masu gadi ma sai police aka zuba aka taho da su. Jigum-jigum aka zauna jiran dawowar Comared. Alh. Sadisu kamar zai zare a tsokin lokacin saboda rabin awa ta gota. Abin da yake faruwa kuwa shi ne da Comared ya koma gida sawa ya yi aka fito da Shazali. Ya kare masa kallo a ransa yana tausaya masa. Indai ta tabbata dan Alh. Sadisu yana gidansa to kashinsa ya gama bushewa. Ta wani fannin ma sune da riba domin duk abin da yake takama dashi na sirrinsu bai isa ta fito dashi ba idan yaje hannu. "Kayi hakuri. Bai kamata na bari bacin rai ya sani tsare ka ba. Sai dai kana sane da matsayina. Ba zan so duk wani abu da zai shafi mutumcina ba" "Ina iya tafiya?" Kawai Shazali ya iya tambayarsa saboda ransa ya riga ya gama baci. A gefe guda yana ta tunanin Abdul da ya hada da bango kafin ya fito. Ya rasa dalilin da yasa yake ta fado masa a rai tunda aka rufe shi a daki. Bai sani ba ko don son da yake masa ne har ransa. Da dingishi ya karasa motarsa ya fice daga gidan. Yana tuki ana biye dashi a baya ba tare da ya sani ba. Motar amittacen yaron Comared ce wanda yasa bin Shazali gida. Shi a nasa zaton ma a can ainihin gidansa da kowa ya sani ne ya ajiye shi. Sai da yaron ya kira ya fada masa suna hanyar wata unguwa mai cikowar mutane da yawan gidajen gargajiya. "Bishi kawai. Gamu nan a bayanku. Ka kwatanta min inda ku ka bi" Bai yi mamaki ba don kuwa Shazali ya taba fada masa cewa yana da gida a unguwar inda yake shagalinsa. Suna hanya ya kira Alh. Tahir. Shi kuma ya sanar da DPO da Alh. Sadisu. Nan da nan aka yi ayari aka bisu. Shazali bai san me yake jiransa a waje ba ya shiga gidansa kai tsaye. "Abdul na dawo" Shiru babu amsa. Ya murmusa a ransa yana tunanin ko har yanzu fushi yake saboda yanayin rabuwarsu da zai fita da Qibdiyya. Yana sanya kafarsa a karshen soron ya hango shi kwance cikin jini a inda ya barshi da zai fita. Rawa jikinsa ya dauka tamkar mazari a yayinda ya duka a kansa yana kiran sunansa cikin sarkewar murya. "Abbbbbduuu...llll?" Shiru mai hargitsa tunani ne kadai ya bakunci kunnuwansa. A take duk wani ciwon jiki da yake ji sakamakon dukan da yasha ya kau. Ya dago kan Abdul wanda kasansa babu komai sai jini ya jijjiga shi. Jikinsa gabadaya a sake yake. Fuska tayi fayau saboda rashin jini. 'Na shiga uku' ya dinga ambata a ransa don ko sau daya bai tuna da sunan Sarkin da ke warware dukkan matsala ba. "Mutuwa kayi?" Ya yi tambayar da bai sa ran samun amsarta ba. Jinin wajen ya sake kallo wani ya bushe ma. A lissafinsa ya yi wajen awa hudu da barin gida. Cikin sauri-sauri ya tashi ya shiga daki ya dauko duk wani abu da zai iya tunawa wanda zai iya tona masa asiri ya saka a wata jaka. Dama ba wasu kayan kirki yake ajiyewa ba tunda lalatarsa kadai yake yi da kananun yara a wurin. Yaran da ko da zata kwabe a gaba iyakarsu nan gidan wanda ya saya da sunan wani dan uwansa na kauye. Kallo daya ya sake yiwa Abdul ya bude kofar gidan da niyar idan ya tafi ya tafi kenan har abada. Sai dai me??? Ko minti goma bai yi da shiga gidan ba Comared da motocin 'yan sanda wadanda aka ki kunnawa jiniya suka iso tare da Alh. Sadisu. Ba don an rirrike shi ba ma da tuni ya afka gidan. Idanun kowa akan kofa. Ga wasu 'yan sandan sun tokare kofar gidan ta yadda ko jinjiri ba zai iya wucewa ta tsakaninsu ba. Shazali yana bude kofa ya yi ido hurhudu dasu. Cikin dimaucewar tunani ya koma ciki da sauri zai rufo kofar. Sai dai tuni mutum biyu sun riga sun sanya hannuwa sun dannota ciki. Na ukunsu ya tura da kafa. Na karshen kuma ya zura hancin bindiga. "Idan ka sake yunkurin rufe kofar nan sai na fasa maka kai da harsashi" Baya ya yi ya daga hannuwansa sama. Ya nemi yawu zai hadiya yaji bakin a bushe. Tunaninsa ya dauke sai hanya da ya bayar domin 'yan sandan su wuce. Abu daya yake takama dashi. Manyan mutanensa ba za su bari ya rayu a kulle ba. "Ku bani hanya, ku bani hanya." Abin da yaji ana fada kenan daga kofar gidan. Ya zuba ido domin ganin mai shigowa sai yaga Comared da Alh. Tahir. Budar bakinsa zai yi musu tambayar abin da ya kawosu nan sai ya hada ido da mutumin da ko baka taba haduwa dashi ba a zahiri to lallai an sha gamuwa a TV ko kafafen sada zumunta. Kai hatta muryarsa ba bakuwa bace. Wani irin sanyi mai hade da zafi a tare suka fara binsa daga tsakar kansa har tafin kafa. Me ya kawo Alh. Sadisu Nakano gidansa? Shi Alh. Sadisu ba tsayawa ya yi ba. Ciki ya bi 'yan sandan. Yana zuwa ya gansu akan Abdul suna salati. Kirjinsa yaji ya takure. Gumi ya wanke masa jiki. Gwiwa a sake ya durkusa a gaban Abdul ya janyo shi jikinsa. A daidai nan Shazali ya juyo domin ganin me ake yi. Hoton da idonsa ya dauka da kalaman Alh. Sadisu suka kusa sanya shi hadiyar zuciya. Duk da cewa ko uffan bai ce masa ba saboda rayuwar dansa ce a gabansa tukunna. "Abdul tashi domin Allah kada ka mutu ka barni. Me zan fadawa mahaifiyarka? Me zan fadawa uwayenka? Wace rayuwa ce kuma za ta rage min idan na rasaka? Kai kadai na mallaka. Abdul ka tashi Baba ne da kansa ya zo" Da kyar da sudin goshi kwakwalwar Shazali ta bude har yaji a ransa cewa muddin ya cigaba da tsayuwa babu abin da zai hana a dauki tasa gawar. Duk fadin kasar nan babu mai tsaya masa ya bar Alh. Sadisu. Mutumin da shugaban kasar dake kan kujera ma babban yaronsa ne a siyasa. Kofa ya kalla babu ko tunani ya nufeta a guje ya fita. Kafarsa na fita yaji hanya ta kare. 'yan sanda sunfi biyar da suka cafke shi. Ana kokarin daukar Abdul a ciki Alh. Sadisu ya ce su bari. Da kansa ya dago shi ya saba shi a kafada. Idanuwansa suna zubar da kwallar da rabonsa da yin irinta tun ranar haihuwar Abdul din ya yi ta farinciki. Hanya aka bashi ya fita da shi ya sanya shi a bayan mota. Ya juya da niyar fadawa DPO cewa gida zai wuce sai yaji an kamo hannunsa. Rikon dai babu karfi saboda rashin kuzari. "Baba.." Abdul ya furta a hankali. "Alhamdulillah. Ya Allah Ka bani ikon aikata alkhairin da za Ka yi farinciki dani albarkacin raya min Abdul da kayi" Wannan shi ne furucin Alh. Sadisu kafin cikin gaggawa su bar wurin zuwa asibiti. 'Yan unguwa suna kallo aka jefa Shazali a bayan mota. Wadanda idanuwansu suka taba ganin lokutan da yake kawo yara sannan bakinsu ya bude suka dinga bada shaida. Sai da aka gama bawa Abdul taimakon da ya dace kafin ayi maganar 'yan sanda. Alh. Sadisu yasa aka duba masa kuma likita ya tabbatar cewa lallai ana amfani da dansa don har ya dauko hanyar gamuwa da cuta. Kansa kuma ya bugu sannan ya zubar da jini. An matukar auna arziki da rayuwarsa bata salwanta ba. Bayan komai ya daidaita ya bar Abdul tare da matansa ya koma police station. Abin mamaki babu mutum ko daya da ya tafi cikin wadanda suka zo domin Abbati. Ga kwamishinan yan sanda shi ma ya zo. Alh. Sadisu ya fada masa yana so a gaggauta shigar da makarantarsu Abdul da Shazali kotu. "Ina gudun daukar mataki a hannuna. Ku yi abin da ya dace da wuri kafin a kira ku daukar gawar da hukuma bata bada umarnin kashewa ba" Office daban aka ware domin sauraron wannan batu. DPO yasa aka fito da Abbati. A reception din Alh. Sadisu ya taresu ya rike masa hannu tare da raba shi a jikinsa. "Ka yafe min. Da taimakon Allah da jajircewarka akan wanda baka sani ba dana ya kubuta." Abbati bai ce komai ba. Alh. Sadisu ya juya ya ce idan yana da uwa a wurin nan a nuna masa ita. Mami Khadija tayi murmushi ta nuna masa Baaba Mari. Akan idon kowa ya karasa gabanta ya sauke gwiwarsa daya a kasa. "Duk wanda ya sanni zai shaida duk zafina bani da girman kai. Ina rokon gafararki akan tozarcin da aka yiwa danki. Wallahi babu mai gane halin da na shiga dazu da wanda nake ciki yanzu sai wanda ya dandana shi. Don Allah ki roka min yafiyar Abbati. Dalilinsa Allah Ya raya min Abdul. Da ya jinkirta ko bai ma kira ba da karshenta bayana ya yanke kenan har abada" Duk dauriyarta sai da kwalla ta zubo mata. "Ya yafe maka har abada ba zai kara kallonka da laifin yau ba" Tunda uwa ta yafe waye d'a da ba zai yafe ba? Tana fada zuciyarsa ta wanke fushinsa zuwa ga fatan kaffara. Munzali ya riko shi domin bashi madogara. Hanne tayi gaba tana kuka zasu tafi. Alh. Sadisu ya dakatar dasu. "Ina neman alfarma. Don Allah kafin ku tafi ina son ganinka Abbati tare da baban yarinyar nan da Shazali ya dauka" "Nima ina da magana dasu game da alakarsu da Shazali da satar diyarsu da aka yi." In ji DPO A wannan lokacin ne kuma Alh. Tahir ya taka rawar da ta shafe tunanin kowa akan laifinsu na baya. Office din DPO dai aka koma. Alh. Tahir da Comared, Munzali da Abbati sai kuma Alh. Sadisu da DPO din. "Dazu Alh. Tahir kayi mana alkawarin warware abin da ya hada samarin nan da wancan matsiyacin. Na dawo da tambayar nan ne saboda ina son a hukunta shi akan Abdul da yarinyar wajenku." "Wani labarin sirri ne wanda jinsa zai iya cutar da mai shi" Alh. Tahir ne ya yi magana . DPO kuma ya bashi amsa da cewa rashin sanin gaskiya a hukumance zai mayar da Abbati sahun wadanda ake zargi. Wanda a karshe dole shi ma a kai shi kotu. Basu da zabi. Kofofi sun toshe. Dole su fadi komai da bakunansu yau. Bisa wannan dalilin suka nemi a shigo da iyayensu. Abbati ya ce a hado da Mal. Sa'idu. Abbati ne ya fara magana yana duban amininsa. "Ranar wanka ce yau fa Munzali." "Na sani. Ba a boyon cibi idan ta zo" "Wadannan sune iyayena" Abbati ya nuna su Baaba Mari, ya dora da cewa "daga Kirikasamma aka turo ni Kano almajiranci. Da karancin shekaru da rashin wayo na zamewa kaina uwa da uba a dalilin haka." "Ga nawa iyayen. A gabansu na tashi. A cikin gidanmu. Amma daidai banda wurin kwanciya babu abin da zanyi tinkaho dashi a matsayin kulawar uwa da uba." Shiru akayi. Hankula da kawuna suka karkata garesu a yayin da kowannensu ya bayar da labarin yadda rayuwarsu ta wanzu tun farkon haduwarsu. Baaba Mari tana kuka, Asabe tana tumami. Alh. Rabi'u kuwa kunya tamkar kasa ta tsage ya fada ciki. "Namiji ya nemi dan uwansa alfasha ce wadda Allah Ya la'anci ma'abotanta. Ya yi fushi da wadanda suka fara ta. Ya kuma gargademu akan koyi da su." Muryar Abbati ta karade kunnuwansu da kaifi. Munzali ya cigaba da cewa "Mu kuma da ita muka rayu, muka inganta rayuwarmu. Muka yi hajji da umra harma muka kai iyayenmu. Muka yi aure sannan muke kara neman aure. Kuma a ciki muke rainon 'yarmu" "Da ace iyayena basu turoni almajiranci ba, da ban hadu da Munzali ba. Rashin haduwarmu ina sa rai zai tsameni daga cikin mutanen da Allah Ya tsinewa tun a duniya" wannan karon da kuka Abbati ya karashe maganarsa. Kafadarsa Munzali ya dafa yana duban iyayensa " da na sami kulawar da ta dace da 'ya'ya bisa koyarwa shari'a, da ban hadu da Shazali ba. Nima da na tsira daga cikin mutane marasa rabo" Banda hawayen da Asabe da Baaba Mari suke yi, dukkan mazan wurin babu wanda hankalinsa bai tashi ba. Tsigar jikinsu ta tashi. Abbati ya dubi Alh. Sadisu "kune masu fada a ji a kasar nan. Idan kun kafa doka ina tsammanin za tayi tasiri." "Doka akan me?" "Almajiranci. Da farko dai duk musulmi ya san cewa neman ilimi wajibi ne ga mata da maza. To amma duk duniya a arewacin Nigeria ne kadai ake musulunci? Me yasa mu ne kadai muke wulakanta zuri'armu da sunan neman ilimi? Wane irin tunani ne yake shige wa iyaye har su iya turo dan da bai shekara biyar ba ya zamewa kansa gata? A ina yake kwanciya iyaye basu sani ba. Me yake ci? Wadanne ranaku ne ba shi da lafiya? Su waye abokan huldarsa? Mene ne hali da dabi'arsa marasa kyau wadanda ya kamata iyaye su tsawatar? Babu guda da aka sani!" Munzali ya tausayawa Abbati sai dai shi ma ba wani cikakken bambanci bane a tsakaninsu. Shi yasa yana shiru shi kuma ya karbe ragamar zancen. "Almajiranci ba shi ne silar lalacewarmu ko ta ragowar dalibai ba. RASHIN MAFADI shi ne yake jagorantar duk wata barna. Yadda almajiri zai iya tashi da gurbatacciyar rayuwa saboda rashin gata haka dan dake gaban iyayensa idan basu kula dashi ba. A suna ne Abbati yake almajiri amma ni da shi bamu da bambanci sai na wurin kwana. A gidanmu idan ka cire ginin gidan babu wani abu da mahaifinmu yake yi mana na tsakanin uba da da. Hatta abinci sai mun nema. Karatu sai mai ra'ayi ko wanda mahaifiyarsa ta tsaya masa. Kafin na shekara sha biyu mahaifiyata ta fara karbar kudin icce, maggi da mai a wurina. Ina nake samowa ba damuwarta bane." Ya dan numfasa kafin ya cigaba da cewa "da ace makarantun allo anyi su a killace, yaran kamar kowanne dalibi su sami kulawa. Abinci kuma duk malamin da ya bude tsangaya sai ya tabbatar cewa yana da masu girki da wurin kwana. A killace yaran nan daga yawo cikin unguwa da tituna. Da tabbas makarantun allo sun amsa sunansu na cibiyar karantar da Al'Qur'ani da samun nagartacciyar tarbiya. Duk dan da ba a tsarewa cikinsa da lafiyarsa ba muddin iyayensa suna da rai komai talaucinsu sun zalunce shi. Domin duka wadannan abubuwan idon iyaye kadai yana rage radadinsu a zuciyar 'ya'ya." "Ni duk zuwa da abinci ake turo ni. Almajirai da yawa iyayensu suna yi musu wannan kokarin. To amma waye zai dafa mana? Manyanmu a makaranta da su kansu malaman suna da bukata. Yawanci wanda ya kawoka yana tafiya za ka yi sallama da abincin harma da suturar sawarka. Kwace da rashin tausayin na k'asa ya zama ba komai ba saboda yanayin da muka tsinci kawunanmu." Abbati ya fada idanuwansa suna kan Mal. Sa'idu wanda ya dukar da kai. "Ba wanda zai dauki nauyin zunubanmu muke nema ba. Kowa ya sayi rariya ya san zata zubar da ruwa. Amma komai yana da sila. Silar da muke fatan a kawar da ita ko masu tasowa a bayanmu zasu sami tsira daga mummunar kaddara. Kamar yadda muka fada, ba almajiranci bane kawai. Hasali ma almajiran suna cutuwa ne mafiya yawan lokuta ta hanyar 'ya'yan da suke gaban iyayensu irina." (Mai karatu wannan ita ce matsayata game da tura yara almajiranci. Kowa yana da ra'ayinsa na sani. To amma illar dake cikin karatun da aka mayar addini ne ma yinsa tana neman fin alkhairin cikinta. Yaran da uwa take rainon cikinsu ta haifa a wahale ne ake saki suyi ta walagigi kamar ba a san ciwon samunsu ba. Wasu saboda kuruciya da rashin wayo ko sunan garinsu basa rikewa. Sai a shekara biyu yaro bai je gida ba. Duk kuma masu kare irin wannan karatu idan ka duba babu dansu ko daya da zasu iya turowa. Na tabbata iyaye mata da yawa zasu yarda dani akan son a dakile wannan tsohon system din da kullum yake kara tabarbarewa. Duk lokacin da muka yi ido hudu da almajiri sa'annin yaranmu kananu sai mun shiga damuwa. Saboda ya zama dandalin yada mumanan dabi'un da sai sun baci ake sani. Allah Ya kawo mana mafita ta alkhairi akan duk abin da ya damemu. Amin) Last page shortly in sha Allah. UWA UWACE...Karshe Batul Mamman💖 Shiru ne ya ratsa office din na wani lokaci bayan su Abbati sun gama bayaninsu. Baka jin komai sai jan hancin Asabe da saukar numfashin mazan da karfi. Hakika wannan zama ya zama tamkar daukar darasi ne ga dukkanin wadanda Allah Yasa aka yi a gabansu. Kowa ya kalli labarin ta fuskar da ya shafe shi. Baaba Mari fin karfi ne. Mal. Inuwa makauniyar biyayya. Mal. Sa'idu kasa bambance neman ilimi (almajiranci) da bara (rokon abinci, da kudin gabatar da bukatun rayuwa). (Jama'a da yawa sun jahilci kiyayyar da ake nunawa wannan na'u'in karatun domin sun hada shi wuri guda da littafi mai tsarki. Abin da basu gane ba shi ne da makaho, da gurgu, da kuturu da dan malam wato almajiri dukkaninsu mabarata ne. Gyaran da muke nema shi ne a gatancewa yaran da ake turowa karatu ta yadda karatun kadai zasu yi cikin aminci da kulawa. Ita kanta bara tana kashe zuciyar ma'abocinta ne. Kenan tana rage darajar ilimin da suke nema. Duk inda almajiri mai roko yake ba shi da wata kima a idon mutane saboda kullum shi ne hannun karba.) Asabe sakarar uwa wadda ta biyewa sawun miji wurin banzatar da 'ya'ya. Alh. Rabi'u irin uban da ake yiwa yawancin hausawa kudin goro da halayyarsa. A haifa a kasa rikewa saboda son zuciya da zalunci. Irinsu da yawa 'ya'yansu lalacewa suke yi kuma su zama silar lalacewar 'ya'yan wasu. Alh. Tahir magidancin da ya dauka zai ci bulus a tattare da alfashar da ya rayu cikin biyewa zuciya wurin kosar da ita. A yau duk wani tunaninsa ya ruguje. Ashe ita zina ba a cin bulus. Ko ayi a inda zai maka radadi ko aje lahira a girbe shuka. Ko a hadawa bawa duka biyun. Sanin zahirin su Abbati ya firgita shi fiye da zato. Gashi kuma suma bashi da sauran kima a idons. Alh. Sadisu masu madafan iko wadanda nasu kadai suka sani. Duka matsalolin yau zasu iya zama tarihi idan gwamnati ta saka hannu tayi abin da ya dace. Maimakon haka sai suka zabi amfani da gurbatattun cikin al'umma wurin cimma burikansu na siyasa. Sai gashi daya daga cikin baragurbin ya harbi tilon dansa har ma yana shirin rasa shi baki daya. * Da aka rasa mai fara tashi ko kara cewa komai bayan sun yi shiru sai Munzali ya tambaya ko zasu iya tafiya domin yana son ya kai Abbati asibiti. DPO ya cike takardun da suka dace wadanda suka wanke Abbati daga zargi ya ce zasu iya tafiya. Gabadayansu tare suka firfito waje. Jikkunan su Asabe a sanyaye. Yayinda wadanda basu san abin da aka tattauna a ciki ba suke ta farinciki. Kasancewar Hanne tana wurin, Farha bata yi gigin matsowa inda ake ta yiwa Abbati murnar kubuta ba. Amma rashin samun yin hakan ya bayyana tsantsar damuwar da Mami Khadija tayi saurin fahimta a tattare da ita. Tausayi taji ta bata. Tunda bata amsa sunan matarsa ba tabbas bai dace tayi abin da zai sosa ran matar tasa a yanayin da ake ciki ba. A wani bangaren na zuciyarta kuma sai ta shiga wasiwasi akan al'amuran da suka faru a yau. Tabbas idan ta ce babu zargin lauje cikin nadi a game da su waye Abbati da Munzali ta yiwa kanta karya. Babbar damuwarta bata wuce alakarsu da wanda ya sace Qibdiyya da kuma dalilinsa na sace ta ba. Alhalin da kunnuwansu duka sun ji daga bakin Comared cewa kawali ne na kusoshin kasar nan. Abbati ya ce shi almajiri ne amma ji gidansa da irin motocinsu. Shin ko dai su ma kawalan ne??? "Mami?" Firgigit ta dawo daga duniyar tunanin da take sakamakon tabata da kiran sunanta da Lilu yayi. "Na bude motar ke muke jira" Kallon motar tasu tayi taga ashe duk sun shiga bayan sun yi sallama dasu Abbati. Ta shiga baya kusa da Suhaib ta zauna. Sun iso kusa da gate din station din Abbati da ya rufewa Baaba Mari kofar motar Munzali ya tari motar tasu kafin su fita. Saitin tagar gaba inda Farha take zaune ya tsaya amma idanunsa baya suke fuskanta wurin Mami Khadija. "Mami ku yi hakuri da abin da ya faru dazu da ma damuwar da muka janyo muku yanzu." Murmushi tayi tana mai kara yabawa da sanyin halinsa. "Ka bar wannan magana Abbati ta riga ta wuce. Allah Ya tsare gaba. Gara ku samu ku tafi don ka ga likita da wuri." "In sha Allahu. Nagode..." Ya kallo Suhaib da Lilu ya sake cewa "Nagode" Farha ce kadai bai yiwa magana ba. Sai murmushi kadai saboda idon Mami. Waje suka yi da motar suka bi bayan Comared wanda yake tare da Alh. Tahir. Kuma shi zai yi musu jagora su koma gida. A ranar Asabe gidan Lami ta wuce. Bata iya komawa gida ba sannan ba za ta iya fuskantar Munzali ba. Duniyar ce kaf ta daina yi mata dadi. Ta rasa tudun dafawa. Yau ko mashi aka caka mata a zuci iyakar ciwon da za ta ji kenan. Dole bahaushe yake cewa gaskiya tana da daci. Maganganun da taji daga bakin danta basu yi mata dadi ba ko kusa. Amma cikinsu babu karya. Idan Alh. Rabi'u halinsa ne tsallake iyalinsa ya barsu suyi ta kansu da zarar sun fito duniya, ita mene ne nata uzurin? Bata taka rawarta ta uwa a wurin 'ya'yanta ba. Duk wata alamar mace ko uwa ta gari babu a tattare da ita. Kaiconta! Ta ina za ta fara? Alh. Rabi'u da ya koma gida shi kuma ko runtsawa bai iya yi ba. Dakinsa ya shige ya rufe kofa tun dawowarsa. Gabanin magariba Innayo da su Uwani suka shirya tafiya asibiti dubo Abbas. Aikin nasa karfe bakwai ne da an idar da sallah. Ta cikin dakin ya iya cewa su gaishe su. Yanayinsa da rashin dawowar Asabe ya sanyata shiga damuwa. Damuwa ba akansu ba. Tunaninta ya tafi kan Munzali da take da yakinin akwai abin da yake faruwa dashi. Da kuma Qibdiyya. Aikin da aka shiga da Abbas ne yasa kowa tsammanin shi ne damuwarta. Shi yasa babu wanda ya dameta da tambaya. Tare dasu Hasiya suka zauna har aka fito dashi suka tabbatar lafiyarsa kalau sannan kowa ya kama hanyar gida. *** Allah Ya yi dare, gari ya waye. Kowane mahaluki safiyarsa tana zuwa da fuskar da Allah Ya kaddara masa. Wani da dariya wani da kuka. Wani da damuwa wani kuma zuciyarsa fes. Shi bawa har kullum idan yana kwadayin dacewa sai ya zama mai karban rayuwa a duk halin ta zo masa. A wannan rana wadda ta biyo rana mai tarihi a rayuwarsu Abbati, sun wayi gari da ciwon da jiya ta bar musu. Daga asibitin da Munzali ya kai Abbati, gida suka dawo dukkaninsu. Munzali ya fita ya nemi gidan abinci mai kyau ya sayo musu. Aka taru aka ci kamar ana tura magani. Hanne da Habu kadai ne suka zata shirun nasu yana da nasaba da dukan da aka yiwa Abbati. Ko da suka shishshiga daki domin bawa jiki hakkinsa, babu wanda ya runtsa sai mutum biyun can dai. Juye juye kowa ya dinga yi har aka kira assalatu. Kowa ya tashi kamar jira suke yi. Kafin takwas duk sun hallara a falo. Zamansu ke da wuya maigadi ya shigo ya fadawa Munzali mahaifinsa yana nemansa. Dan murmushi ya sami kansa da yi domin ya tabbata yau dai neman da yake yi masa na damuwa da lamarinsa ne ba na neman kudi ba. Bai so ace karon farko da mahaifinsa zai damu haka dashi ya kasance akan abu makamancin wannan bane. Bangaren Abbati ya ce a kawo shi. Ya zo ya zauna suka fara gaisawa da su Mal. Inuwa sai ga Asabe. Kayan jiya ne a jikinta da alamun rashin wanka ma. Tayi wuri wuri da ita gwanin ban tausayi. "Hanne da Habu ku dan bamu wuri don Allah" cewar Mal. Sa'idu yana mai dubansu da mutuntawa. Bambarakwai suka ga abin tunda bai saba lallaba dan kowa ba. Habu ya fita waje. Hanne kuma ta haye sama. Munzali da Abbati suka zazzauna a kasa domin girmamawa ga iyayensu sannan Mal. Sa'idu ya soma magana cike da rauni. "Ba don wannan al'amari mai muni bane wanda nake fatan daga yau kada a sake tayar da maganar ba, da sai in ce ina son sauran kannena su kasance a wannan zama." Caraf maganar ta shiga kunnuwan Hanne. Kafafuwanta kuwa suka ci burki a bakin kofar shiga saman daga ciki. Sannu a hankali ta sakaya kofar ta sami wuri ta labe abinta. Mal. Sa'idu ya cigaba da cewa "Allah shi ne shaida cewa ni Sa'idu ina kaunar 'yan uwana da 'ya'yansu da zuciya daya. A tawa wautar soyayya ce tasa nake juya kowa a gidan a matsayina na babba. Girman kai yasa nake ganin tunda gaba nake da kowa yi min biyayya wajibi ne. Sannan kowa bai san daidai ba sai ni kadai." Ya dubi Baaba Mari, duba na mai jin nauyin wanda ya sabawa. "Ki yi min aikin gafara duk da cewa na roka a makare. Tun ranar da ki ka dawo da gawar Sani a bayanki ya dace ace na zauna nayi tunanin halin da na jefamu a ciki. Son zuciya da girman kan da na ambata a baya suka sanya nake jin baki isa na janye kudurina ba. Yin haka tamkar kin yi galaba ne a kaina. Wannan dalilin yasa na kara tamke dammarar juya duk wani abu da kike tunanin kina da iko dashi. Musamman rayuwar Abbati. Sannan magana ta gaskiya, a duk lokacin da ki ka tayar da maganar son sannin sana'ar Abbati, nima ina kwadaituwa da haka. Na kan riski kaina cikin halin tunani da rashin bacci a wadannan lokuta domin nima a tsorace nake. Gudun kada abin da nake gudu ya tabbata yasa bana kaunar jin kina tayar da wannan zancen." Bayan ya yi shiru Mal. Inuwa ya yi gyaran murya ya ce "laifi ba naka bane kai kadai Yaya. Harda mu da duka wadanda suke da alhakin sanyawa ko hana irin wannan na'u'in karatun. Hakika bana jin akwai wani mai sanya gaba gabas da zai kalubalanci tura 'ya'yan musulmi neman ilimin islama. To amma wannan hanya da aka biyo ba mai bullewa bace. A da can zan yarda idan aka ce mu iyaye maza muna tura yaranmu ne domin karatun Muhammadiya. Yawancin 'yan kasuwa da masu kudin da ake ji dasu a arewacin kasar nan akwai almajiranci a cikin tarihinsu. Su nemi ilimi su hada da koyon sana'a'o'in hannu komai kankantarsu. Yanzu kuwa babu tantama abin ya koma hanyar gujewa daukar nauyin da Allah Ya dora mana na 'ya'yanmu ne. Muna fakewa a bayan addini muna wulakanta rayuwar yaranmu. Ko babu komai duk mai roko baya daraja da kima a idon mutane. Zuciyarsa mutuwa take wurin jiran a bashi. Sannan ta kangare idan bai samu ba, ya dinga ganin laifin duka duniyar baki daya wurin kin nuna masa tausayi." Baaba Mari dai bata ce komai ba sai sauraron Mal. Inuwa da Mal. Sa'idu suna bankado rawar da suka taka wurin bata rayuwar Abbati. Munzali kuma ya tsurawa iyayensa ido. Da ya gaji da shirunsu ya kasa hakuri dole sai da ya yi magana. "Baku ce komai ba Baba" Asabe ta dukar da kai cikin jin nauyin kowa. Kunya da bakinciki sun mamaye zuciyarta. Tana mamakin yadda akayi ta makance da son duniya a baya har ta iya aikata wannan danyen aikin na sakaci da rayuwar 'ya'yanta. "Me zan ce Munzali? Ina cike da kunya da nadama amma hakan ba zai canja komai ba. Laifinmu ni da mahaifinka yafi na kowa yawa a wurin nan. Bamu bar muku komai na tinkaho ba sai yawanku wanda ba don kun yi yunkuri da kanku ba da bai amfaneku da komai ba. Kalmar hakuri kadai bana jin za ta yi wani tasiri wurin rage maka radadin wannan al'amari" Kalaminta ya zaburar da Alh. Rabi'u ga yin magana tana rufe bakinta. "Mene ne aibun 'ya'yana? A iya sani na arziki ne yawan haihuwar domin kuwa rana gobe kiyama da irina Annabin Rahama zai yi alfahari" Sallallahu alaihi wa sallam ya ji falon ya karade da ambata kafin muryar Munzali ta doki kunnuwansa cikin fushi. "Ina abin alfaharin Baba? Waye cikinmu za ka iya fitarwa ka nuna hankali kwance har ma ka yi zaton za ayi alfahari da shi" "Munzali meye haka ne?" Abbati ya ce dashi da alamun rashin jindadi. " Gaskiyar da 'yan uwa, makota, surukai, abokai da mu kanmu 'ya'yansa muka kasa fada masa da wuri zan sanar da shi." Ya mayar da hankalinsa ga Alh. Rabi'u wanda shi ma kallonsa yake da mamaki. Duk jahilcin da yake tunanin Munzali yana fama dashi bai yi tsammanin zai kasance cikin masu kokonto akan hadisan Ma'aiki ba. Hadisi ma irin wannan da ya dade da karade al'ummar da ya taso a cikinta. "Baba idan anje lahirar za ka tsame wasu cikinmu ne ka nuna a matsayin 'ya'yanka?" "Munzali kada ka yi sa6o mana" Asabe ta gargade shi ganin kamar zai saki layi. "Allah Ya tsareni. Laifukana na baya ma sun isheni. Da yardar Allah ba zan sake afkawa zunubi da gangan ba. Ina dai so in ji shin da wa Baba zai yi alfahirin." Ya soma lissafi da yatsun hannunsa "Da 'yan dakin su Marigayiya A'i wadanda suka butulcewa hannun da ya ciccibi rayuwarsu a lokacin da basu da gata zai yi (Innayo)? Su suka fi morar lafiya da kuruciyarta amma saboda rashin uba tsayayye suka manta alkhairi. Ko Uwani da Zara da suka zabi kyama da tozarci ga mahaifiya kamar Innayo saboda gudun talauci? Ko ni da nafi kowa kazanta? Ko Bature da baka san a gidan wa yake kwana ba? Ko Lawisa dake canja samari kamar hula ta kuma gagara zaman gidanka? Ko Ummakati dake jin kunyar a hadata da ku a matsayin iyaye?" Alh. Rabi'u shiru ba amsa sai muguwar kunyar da ta mamaye shi. Su Mal. Inuwa kuwa nauyi yasa suka ji ina ma kafin a fara maganar suka fita. Idanu cike da kwalla Munzali ya dubi Baaba Mari ya ce "ki fada musu babu abin alfahiri a haihuwar da 'ya'ya basu sami kulawa, soyayya da kwab'a ba. Wadannan abubuwan masu saukin samuwa ne tunda babu ruwansu da da kudi ko talauci balle mutum ya dorawa halin rayuwa laifi. Annabi SAW ba haihuwar yuyuyu yace ayi ba. Me zai yi da taron al'ummar da fiye da rabinta suka zabi hanyar shaidan a matsayin tafarkin da zasu bi saboda rashin kulawar iyaye? Da kun sauke hakkina da na 'yan uwana da yake kanku da a yau iyayen Abbati ba suyi kukan fadawarsa harkar neman maza ba." "Neman maza?" Hanne ta yiwa kanta tambayar a hankali tamkar tana jira wani ya sake fassara mata abin da ta riga ta sani. Ta sake maimaita kalmar tana cije lebe kafin kuma a hankali ta dora hannuwa a ka ta dinga nanata "na shiga uku" tana mai buga kafafunta a kasa a hankali don kada a ji. Matsanancin tsoro da fargabar da suka kama ta basu kawar mata da tunani ta yadda za ta so ta bayyana kanta a garesu kafin ta gama jin komai ba. "Munzali yawan tada maganar nan ba shi da amfani tunda mai afkuwa ta afku. Ku yafi juna kai da iyayenka a cigaba da addu'a" cewar Mal. Sa'idu wanda hasashen halin da Alh. Rabi'u yake ciki na kunya yasa shi magana. Shi kuwa Mal. Inuwa sai cewa ya yi "tada zancen akwai amfani Yaya Sa'idu. Ai zaman zubeben kwarya ake. A fitar da komai don kowa ya gane ta inda ya kuskure saboda a ji dadin gyarawa" idanun Munzali ya kalla dake cike da zallar bacin rai da tarin damuwa ya kuma kalli Asabe da Alh. Rabi'u "har yanzu da mu daku bamu makara ba. Dama ce muka samu domin shafe abin da ya faru da yaranmu. Don ko mun ki ko mun so, mu ma muna da namu kason a cikin zunubinsu tunda sakenmu ne sila. Musamman mu iyaye maza." Asabe ta share hawaye ta ce "haka ne." Shi kuwa Alh. Rabi'u daure fuska ya yi. Yadda bahaushe yakan ce gaskiya tana da daci to shi ma wannan ba karamin dacinta ya ji ba. Ba kuma ya jin zai bari a cigaba da fadarta balle tayi tasiri a zuciyarsa. "Dakata Malam wa kake da suna?...wace irin magana ce wannan za ka ce muna da rabo a zunubinsu? Na san lokacin da ya fara ne? Ko ni na aike shi? "Alhaji mene ne haka kuma?" Asabe ta furta ranta ya soma baci. Ko ba komai mahaifin Abbati bai cancanci irin wannan maganar ta rashin girmamawa ba. Harararta ya yi kafin ya ce "dama tunda kika fara sauraron Innayo na soma kasa gane kanki. Idan ke kina maraba da a qaqaba miki zunubin irin mutanen Annabi Ludu ni bana so" ya mike tsaye yana baza babbar riga "ban san me ya dawo dani gidan nan ba. Na dai tabbata ba wannan maganar bace don wallahi da ba zan zo ba." Mal. Inuwa ba shiri ya ce "kayi hakuri ban fada da wata manufa ba" Munzali cije lebensa ya yi bayan ka karewa yanayin da Abbati ya shiga tunda Alh. Rabi'u ya soma magana. Takaicinsa ya karu da ya fahimci har yanzu akwai sauran gyara a lamarin mahaifinsa. "Har a yanzu da nake kan siratsi irin wannan na rayuwa ba zan ji ni kamar kowane d'a mai iyaye ba?" Asabe ta yi saurin cewa "Kada ka dauki maganganun Alhaji cikin fushi ya fada. Ka yafe mana don Allah" "Kada Allah Yasa ya yafe. Aikin banza. Kaje ka gama iskancinka sannan ka dawo kana neman wanda za ka dorawa alhakin aikin da gabbanka suka aikata." Su Mal. Sa'idu jiki duka ya yi sanyi. Ana neman gyara ga alamun sake tabarbarewar lamari ya taso. Idan ya cigaba da sauraron mahaifinsa yana jin tabbas zuciyarsa sai tayi bugawar da take ta shirin yi tunda abubuwan nan suka soma faruwa. Shi yasa ya murje idanunsa ya fadi abin da yake ganin daidai ne. "Idan ka so Baba ka cireni daga cikin 'ya'yanka. Wannan shi ne kadai nake jin abin da zai rabaka da amsa tambaya akan halin rayuwata..." "Munzali mahaifinka ne fa..." Cewar Asabe tana jan hannunsa don ya kalleta" "A suna ba. Na cinye kuruciyata sanda nake matukar bukatarsa ma na rayuwa balle yanzu" "Munzali" Mal. Sa'idu da Baaba Mari suka kira shi kusan lokaci guda. "Ku barshi ya nuna min iyakata. Dama can kawunanku yafi gani da gashi ba nawa ba" "Ka taba yi min wani abu da zan gan ka da kimar da Allah Ya baka ta ubana..." Da karfi Abbati ya ce "Munzali? Hauka kake ko me? Alhaji ne fa! Zo ka tafi gida gani nan zuwa." Maganar da Munzali bai karasa ba kenan domin baya jin akwai ranar da Abbati zai saka shi ko ya hana shi ya kuma musantawa. Tuntuben bakin da ya yi akan Qibdiyya yake gudu kada Allah Yasa ya kuma maimaitawa. Alh. Rabi'u da su Baaba Mari kowa ya ji kuma ya gani cewa Munzali bai bar fadi in fada da babansa ba sai da Abbati ya tsawatar. Hakan ya zama sanadin da Alh. Rabi'u ya sake samun abin aibata dan nasa. Kujerar da ya tashi ya koma ya zauna a dofane yana kare musu kallo shi da Abbati. "Ikon Mai Sama. Yanzu Munzali duk fadin wurin nan da jama'ar ciki babu wanda ya isa ya hanaka ka hanu sai wannan almajirin? Ka dubi tsabar idanuna ka dinga cab'a min magana son rai." "Wallahi Abbati ya isa dani" "Tabdijan!" Ya dubi su Mal. Inuwa "to Billahillazi da sake. Yaran nan basu tuba ba. Sannan ina tsammanin mu'amalarsu bata sauya ba tun kuruciya. Iya shegenku kuke yi har kwanan gobe." Ya kalli Asabe tana sharbar hawaye "ki adana kukanki don basu cancance shi ba. Alhaki kwikuyo gashi nan ya bi kan 'yarku ai. Shi ne don borin kunya ku ka tara mu a nan kuna karanta mana karya da gaskiya." "A'uzubillahi" cewar Mal. Sa'idu yana mai duban mutuwar tsayen da Abbati da Munzali suka yi "Alhaji wace irin magana ce wannan? Ana kokarin kawo gyara ya za ka sake jifansu da abin da su da kansu suke neman tsari daga gareshi?" "Baka ji me yake cewa ba? Wai fa ni yake fadawa cewa Abbati ya isa da shi. Koda yake ba damuwa zaku yi ba tunda wanda ya zaba akan mu iyayensa danku ne." Asabe kuka kawai take yi. Yayinda Hanne ta sulale a kasa bakin kofar da take labe ta zauna. Wani sashe na zuciyarta yana kokarin karbar zancen Alh. Rabi'u. Domin alal hakika ta dade da rashin son alakarsu duba da yadda komai zasu yi sai sun tuntubi juna. Sutura wannan daidaikun ranaku ne suke bambantawa. Bata ganin kowa sai muryar Munzali da ta karade falon cikin rauni, karaya da bakinciki ya mayar da martani ga zargin da mahaifinsa yake yi musu. "Ba zan janye kalamaina ba. Abbati ya isa dani. Haihuwata ce kadai bai yi ba amma duk wani abu da ya kamata uwa da uba su yiwa d'a ya yi min. A kuma matsayinsa na ALMAJIRI" Alh Rabi'u ya fuskanta da tambaya "ka taba sanin cewa da ina karami ina yawan fama da ciwon namoniya (pneumonia)? Duk lokacin da ya tashi Abbati ke jinyata. Ita Asabe ai ta sani. Ya nemo kudi ta kazamar hanya ya kaini asibiti. Bata taba son sanin a ina yake nema ba tunda ba ita yake tambaya ba." "Ke, yaushe aka yi haka ban sani ba?" Ya tambayi Asabe a zafafe. "Ban sani ba" ita ce amsar da ta bashi. "Kun gani ko?" Ya nuna iyayen nasa yana girgiza kai "Abbati ne ya kaini makarantar boko ta yaki da jahilci. Yasa muka koma zuwa makarantar dare duk da mun san cewa mu din masu aikata laifi ne. Sannan tuban da muke hanyar yi shi ne dai sila kuma jagora. Ya yi min komai wallahi. Ya cancanci girmamawa da mutuntawa. Tunda ya ce na tafi gida kuma zan tafi domin wannan almajirin yana da iko da ni" yana kaiwa nan yasa kai ya fita ko waige babu. "Malam ina neman izinin yin magana" Abbati ya kai idanunsa ga Baaba Mari ita kuma tana fuskantar Mal. Inuwa. Kai ya gyada mata da sauri sauri don ya san zancenta a kullum abin duba ne. Asabe da Alh. Rabi'u ta yiwa magana da cewa "Da farko ina son baku hakuri akan duk wani abu da Munzali da Abbati suka yi wanda ya bata muku rai. Abu na biyu kuma ina son tunatar da mu duka cewa zama iyaye ba a ciki da haihuwa bane kadai kamar yadda Munzali ya yi ta nanatawa. Shiriya da 'bata ba a hannun iyaye yake ba. Amma akwai kokari da dagewa. So, kulawa, sawa da hanawa duk namu ne. Su din basu isa su gyara mana 'ya'ya ba. Amma kuma aikatasu yana kosar da zuciya. Yana sanya nutsuwa da kwanciyar hankali domin mutum ya san idan ya koma ga Allah yana da hujjar da za ta cece shi daga azabar tozarta amana." "Ni wallahi na karbi laifina Maman Abbati. Zanyi duk abin da ya dace domin gyara kuskure na" "Ki je wurinsa" Abbati ya ce da ita da farinciki. Tana fita Alh. Rabi'u ya fita kamar zai tashi sama yana faman hardewa da babbar riga. *** An fi ganin nisan daren da washegarinsa bawa yake da burin aiwatar da wani aikin da dole sai an jira gushewar daren. Haka mutum zai kwana zuciyarsa tana azalzalarsa da son ganin lokaci duk bayan gilmawar hannun agogo. Wani zai iya kwana yana buga tsaki da k'wafa. Yayinda mai wayo yake dauro alwala ya gana da Mahalicci. Idan hakan bai samu ba ayi ta tasbihi da tahmidi ana neman agajin Maiduka wurin ganin safiyar ta zo daidai da burin mai jiranta. Mami Khadija a wannan dare bayan sun dawo daga ofishin 'yan sanda ko tunanin kwanciya bata iya yi ba. Duhun dare shi ya bawa Alh. Tahir mafaka ya sami damar sabulewa tuhume tuhumen da suke dankare a kokon zuciyarta. "Ina da magana da kai" ta ce a lokacin da ta ga yana shirin ficewa daga gidan bayan sun kawosu shi da Comared. "Ba a nan ba Khadija. Ki yi min alfarmar mu jira gari ya waye mu koma Kaduna" Rokonta yake. Taji hakan a muryarsa ta kuma gani a yanayinsa. Ba don ta so ba ta amince saboda rufin asirinsu tunda akan ce bango ma yana da kunne. Kwana tayi sallah da jan ambaton Allah har aka kira Assalatu. Nan ma bayan tayi sallah tayi wanka gani tayi rana taki fitowa da wuri. Ba ita ta sami salama ba sai da motarsa ta shigo gidan ya nemi da ta fito su tafi. "Ba zan bar su Farha su taho su kadai ba saboda tukin Lilu" "Magana zamu yi kawai na dawo dake" Ta kula gudun rigima yake. Jikinsa ma duk ya yi sanyi. Sannan ga dukkan alamu yadda bata runtsa ba shi ma haka ya kwana. Ba musu ta bishi. Matan gidan wadanda tuni suka karbi uzurin da Suhaib ya basu na jiya cewar Lilu ya bi saurayin Farha ne ba tare da yiwa Mamin tasu bayanin dalili ba. Shi yasa hankulansu suka tashi. Sai da suka je suka samu 'yarsa aka sace kuma basu dawo ba sai da aka ganta. Shi yasa yau tsokanar Mamin kawai suka dinga yi akan za ta bi mijinta cikin raha ba tare da tayar da zancen jiyan ba. Da zasu tafi har dakin samarin taje ta dauko wayar Danliti dama Suhaib ya cire lock din. Gidan Comared ya tafi da ita kai tsaye. Suka shiga har falon da Abbati da Shazali suka duku akan boye Qibdiyya. "Ina ne nan? Me yasa ka kawoni?" Ta tambaya rai a hade tana karewa hargitsin wurin kallo. Wuri ya nuna mata ta zauna sannan ya bude baki ya fadi abin da yake jin shi ne rufin asirinsa da na su Abbati. Karfin kalaman da ya zube mata sun tafi akan boye laifin matasan ne wadanda zuwa yanzu ya amince da cewa komai na Allah akwai manufa. Wala Allah rufa musu asiri akan yakinin da ya samu na tubansu zai iya rage masa nasa nauyin. Ya fara da tuna mata shi waye ta fannin mu'amala da mata. Ya cigaba da cewa ya zo gidan ne jiya domin haduwa da 'yan matan sai ya gamu da Abbati. Katse shi tayi a firgice ta ce "Innalillahi. Kaddai su ma din..." "Ko kusa" Alh. Tahir ya sami kansa da wani irin karfin gwiwa "kinsan Abbatin ma almajiri ne. Irinsu yawanci babu gata da kulawar babba a kusa. A nan suka hadu da shi wannan Shazalin dake unguwarsu Munzali. Abinka da kuruciya da rayuwar da abinci ma sai ka roka. Bai wahala ba wurin jan ra'ayinsu ya hadasu da manya aka dinga sakar musu kudi suna kasuwanci. Sai da aka bari kudin ya zauna musu sannan aka bijiro musu da irin aikin Shazali na kawalcin maza da mata. Da suka ki amincewa ne fa Shazalin ya dauke musu yarinya. Shi ne abin da ki ka gani jiya" Mami ta dinga salati da hailala "To amma kana da tabbas akan basu taba yi ba" Tunawa yayi da irin rantsuwar da Abbati ya yi da kuma fushin da ya yi akan gara mutuwarsu da su komawa tsohuwar sana'arsu. Sai ya sake zabo kalmomin da zasu kwantar mata da hankali sannan a lokaci guda basu kaucewa abin da ya ji ba. "Khadija wallahi Abbati bai san ina cikin gidan nan ba da farko. Amma ya yi ta rantsuwa akan gara ya rasa komai akan ya sabawa Mahaliccinsa." Ajiyar zuciya tayi. Wani abu da ya kwana a wuyanta ya sauka ba tare da ta farga ba. Ta mika godiyarta ga Allah a fili da zahiri da Ya sanya basu cikin masu sabon Allah. Alh. Tahir shi ma hakan ce ta kasance dashi. Zuciyarsa ta amince da tafiya da sirrinsu Abbati kushewa. Ba komai ya janyo hakan ba kuwa sai ganin cewa izina ce abin da ya faru jiya a gare shi. Kazamin mazinaci irinsa bai isa ya tserewa abin da ya shuka ba. To Amma Allah Buwayi Ya dubi zuciyar uwar 'ya'yan da su kansu Ya kangesu daga zinar. Shin wannan bai ishe shi godiya ba? Da kunnuwansa yaji kalaman tuba da nadamar Abbati. Idan ya hana shi 'yarsa ya san wane irin fasikin za ta hadu dashi? Rayuwarsu curarren zare ne mai wahalar warwara. To amma idan mutum ya nutsu zai gane cewa Allah Shi ne Gwani mai jujjuya lamura domin su dace da rubutun kaddarar allon kowane bawa. "Ya ganka a nan din?" Muryar Mami ta sauka a gare shi cike da alhinin amsarsa. "Ya ganni. Ya kuma alkawarta min ba zasu taba tayar da maganar ba." Wata kwalla yaji ta cika idanunsa ya ce "kinga irin abin da ki ka jima kina fada min duk ya faru ko? 'Ya'yana sun san ko ni waye sannan maneman 'ya'yana ma sun sani" An dawo inda ya dade yana mata kaikayi. Wayar Danliti ta damka masa bayan ta bude sakonnin da suke musaya shi da Jiddo. Jijiyoyin wuyansa suka tashi suka firfito saboda bakinciki. Ta fara magana da fada masa zargin da ama yiwa Lilu na bata Qibdiyya. Da tsoron da take kada watarana gangan ta zama gaske. Sai ta koma batun Jiddo "Tonon asirin wani ba abin kirki bane. Ban taba tunanin yin haka ga kowa ba. To amma ina gudun yadda kaddara ta fada mata nima wata rana za ta zo ta riskeni. Duk wata kamewata da yawan nasihar da nake yi maka ai ba iyawata bace. Ko kadan ban fi karfin Allah Ya jarabceni da aikata wani na'u'i na alfasha ba. Musamman na zina ko danginta wanda kubuce musu yake da wuya. Shi yasa na zabi ka sahale min wannan auren d..." Mikewa ya yi ba shiri ya ce "Haba Khadija? In kina yiwa Allah ki bar maganar nan zan tuba" Mami Khadija ta tashi ita ma "Allah Ya haramta zama da fasiki. Aurenmu tuntuni ya dace a raba shi domin in tsira da mutumcina. Zaman nawa me ya haifar banda kwaye maka baya a idon 'ya'yan cikinka?" "Na tuba" "Bukata daya ce yanzu ta rage a tsakaninmu. Ina rokonka arziki ka barni in yi maka idda mu rabu a mutumce. Zan yi bakinciki mafi girma da muni ace na mutu ka sanya hannu wurin sakani a makwancina a matsayinka na mijina. Haka kuma zan yi shi ace ina zaman yi maka takaba alhalin baka kasance cikin masu kunyar mummunan aikinsu ba" Shiru ya yi na dan lokaci maganar ta sami kowace kusurwa a jikinsa ta shiga. Sannu a hankali ya daga kai ya dubeta ya ce, "Tsanar da ki ka yi min har ta kai haka?" "Ko kusa. Me zai sa na tsani mijina uban 'ya'yana? Mutumin da ya kyautata rayuwata da ta 'ya'yana da dukiyarsa da soyayya. Kyamar halinka nake yi domin duk dadin mu'amalar mu ta gidan duniya akwai ta lahira. Wadda zata nuna ina mutum ya nufa bayan an kare wannan gajeruwar rayuwar da bata da tabbas. Ina tsoron kada jindadin more rayuwa yasa in daina ganin aibun laifinka harma zuciyata ta daina yi masa kallon haram." Kuka take yi. Kuka sosai. Ta durkushe akan gwiwoyinta ta daga hannuwa gareshi. A dimauce Alh. Tahir ya tayar da ita tsaye ya yi nufin rungumeta don lallashi amma ta kame jikinta wuri daya. Jikinsa ya kara yin sanyi. Yaushe rabonta da amince masa a matsayin miji? Shi kansa ya manta. "Ki yi shiru" "Ka taimakeni ka sauwake min." Kamar wani mahaukaci ya dubeta ya ce "Khadija wallahi zan tuba. Ke na ma tuba. Astagfirullah" "Don Allah. Ka dubi darajar mai cikakkiyar daraja SAW. Ka raba ko igiya daya ce a tsakaninmu don Allah" "Nace miki na tuba" ya furta hawaye na sauko masa. Bai taba sanin zafin soyayyarta ba sai a wannan gabar "ta yaya zan rayu babu ke? Ta yaya zan zuba ido ki zama mallakin wani?" Mami Khadija ta daure ta kamo hannunsa ta rike tamkar suna musabiha. "Ban san gobe ba. Bani da masaniya akan gaibu. Sai dai ina rokon Allah Sarkin Sarakuna. Idan akwai sauran zama a tsakaninmu, kada Ya bani ikon sake aure har na koma gareshi. Ya baka ikon tuba wanda ya cika dukkan sharudda. Ya tsayar da digadiganka akan siradil mustaqim. Ya tasheka cikin bayin da Ya aminta dasu. Ya kuma sake hada aurenmu a aljannah. Amma a duniya kam na gama auren nan in sha Allahu." "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" a gabanta ya durkushe yana nanata wannan kalma sannan da kyar bayan ta soma fitar da rai ya ce "na sake ki saki daya. Don Allahn da kika sa na sake ki kada ki auri wani. Ki jirani. Ko a duniya ko a lahira zan tuba. Wallahi na tuba. Kai...me ya kaini? Wannan wane irin zalunci na yiwa kaina?" Jikinta ya dauki rawa da jin kalmar sakin. Ta jima tana nema. Ashe duk dauriyar da take tunanin tana da ita bata kai ta kawo ba? "Ina da gida a Kabala zan baki. Ki jira a gyara takardun in sanya sunanki kafin ki tashi." "Nagode" "Batun yara fa? Na san ke zasu bi. Da wuya su zauna a inda nake. Ina nufin ya zanyi in dawo da koda rabin ko kwatan mutumcina a idonsu?" "Ka tuba. Allah zai yi maka sauran indai dominSa kayi." Bai san shi dan gata bane kuma asararrarre sai yau. Yau ne ya nutsu ya saurari Khadija. Yau ne kuma igiyar aurensu ta sami targade. Ya Allah Ka shafe mana kurakuran da suka gabata. Ka hanemu aikata wasu. Amin 47 Iyalin Innayo sun tashi da alhinin aikin da aka yiwa Abbas. Kowa yana farinciki da jin cewa anyi aikin cikin nasara. To amma duk wanda ya ganshi bayan ya farfado a daren jiya cikin magagin ciwo sai ya tausaya masa. Hasiya tayi kuka tamkar ranta zai fita. Kiran sunayensu yake yana rokonsu da su cire masa ciwon da yake ji. Duka sai gwiwoyinsu suka yi sanyi. Da wuri 'yan dakin Innayo suka gama shiri zasu tafi dubiya washegari. Hasiya ma man ta taho da sassafe saboda bata yarda ta bar asibitin ba. Da tursasawar Honourable ta taho gida yin wanka tunda nan din yafi kusa da asibitin akan gidansu. Uwani ta riga kowa gamawa. Ta sami wuri ta zauna ta kira Munzali. Muryarsa ta dakushe ba ma a jinsa sosai. "Kira nayi inji jikin Qibdiyya da naka. Jiya ban wuni cikin kwanciyar hankali ba. Kuma Innayo ta ce akwai sirrin da bai dace mu ji ba ko don mutunta juna shi yasa bamu zo ba". " 'Baram'barama" cewar Zara dake zaune a dakin tana shayar da diyarta "Hasiya taho ga Metron Uwani tana sakin baki" "Da yake Hasiyan uwata ce ko? Wai me yasa ku ka raina ni ne?" Uwani ta hau ta da masifa ita kuwa sai dariya. Tun bayan faruwar lamarin nan sai yau Munzali ya yi dariya. Dariya harda kyakyatawa. Da furucin Uwanin da abin da Zara ta ce duka ya ji. Ya kuma kara kaunar Innayo domin hakika ta karramasu da ta basu damar adana sirrinsu ga mahaifansu kadai. Sai da ya gama dariyar ya ce "Jiki da sauki. In sha Allahu zan kawota wurinku yau ki dubata sai ki fada min abin da ya dace mu yi." "Kai ni fa anyi suspending dina. Ranar da muka kai ka ma sai da na barar da girmana wurin roko.Ka kaita na kudi kawai a dubata a sirrance. Irin asibitinmu ai da baki ma za a dinga nuna ni idan na koma aiki. Dama kuma can ba kaunata suke yi ba balle an sami abin gorantawa." Wata dariyar ya yi sannan ya tambayeta Innayo. A bakinta yaji batun aikin da aka yiwa Abbas. Shi ne ma ta bashi shawarar ko asibitin zai kai Qibdiyya tunda na kudi ne kuma ta yaba da likitocin. Da alkawarin zuwan nasu suka rabu. Ko tashi bata yi ba daga wurin Zara tana ta yi mata tsiya suka ji sallamar 'ya'yan Zaran. Wayyo dadi! Zara ta kusa sakin jinjirarta saboda tsananin farinciki da taji Salima tana cewa "marhabin da su Maryam, maza ku shiga ciki ki ga kanwarku" 'Yan matan Zara su hudu suka shigo falon Innayo suna ta rab'e-rab'e a jikin bango. Yanayinsu ya nuna sam basu so shigowa ba. Duk da haka Salima ta cije ta dinga cewa "Ku shiga mana" Taku daya biyu a daddafe suka sake jan burki. Zara ta taso ta tsaya a gabansu da farincikinta. A zatonta wallahi suna ganinta zasu rufeta don murna. Sai taga sun sake jan tunga an rasa mai fara zuwa jikinta. Wani irin kallo ma suke yi mata mai kama da kyama. Kwala taji ta taho mata ta kuma kasa tareta. Innayo ta kawar da kanta gefe kawai don 'yarta ba karamin tausayi ta bata ba. Sai ta tuna mata da lokutan da ita Zaran take yi mata haka. Cikin bacin rai Uwani ta daka musu tsawa bayan ta gama karantarsu da kanwarta. A ranta ta kissima irin bakincikin da zata ji idan nata 'ya'yan suka gwada yi mata haka. Ta sake jinjinawa hakurin Innayo. "Kun wuce jikin uwarku taji duminku kun ji nata ko sai na taso muku?" Jiki na rawa kuwa suka tafi wurinta amma a bayanta suka labe saboda tsawar Uwani ba don farincikin d'a ya ga mahaifiyarsa ba. Karamar da yake babu hankali sai cewa tayi "hummm, Mummy ba kya wanka ko?" Mai bi mata kuma ta ce "ba Aunty ta fada mana a gidansu Mummy ba..." Mas'uda ce babbar, ta sa hannu ta buge bakin kanwarta tana mai cewa "ba ta ce kada mu fada ba?" Ta dubi mamanta ta tabe baki "tare da Daddy muke. Ya ce ki zo." Ta kuma ce da kannenta "ku zo mu koma mota" Salima ta hadiye nata fushin ta ce "ku zo ga kanwarku ku ganta. Sai mu ga da wa take kama" Maryam har ta fara murna ta soma takawa wurinta sai ta fasa. "Karaso mana" "Aunty ta ce kada mu taba komai a gid..." Mas'uda ta janyo hannunta tana gargadinta "ba ta hanaki surutu ba? Ni ku zo mu tafi kafin mu fara warin talauci" "Ke???" Uwani ta yi musu tsawa a karo na biyu. Zara sai kuka. Jikinta har rawa yake. Ta ruga gaban Innayo ta durkusa akan gwiwoyinta. "Wane mutum Innayo? Waye zai buga kirji ya ce ya zama sanadin hawayen iyayensa kuma ya gama da duniya lafiya? Ki yafe min. Ki yafe daga kasan zuciyarki don girma da isa da tsarkin Mulkin Allah. Nayi miki rantsuwa idan yaran nan suka gwada min abin da nayi miki na sati guda zuciyata za ta buga. Kaicona. Ba zan iya addu'ar cewa Allah Yasa yarana su ji kaina kamar yadda nayi miki ba" Hawaye Innayo take ita ma. Ta rike hannuwan Zara ta ce "na yafe muku ke da 'yan uwanki tun kafin ku roka. Babu komai a zuciyata game daku sai fatan alkhairi da albarkar rayuwar duniya da ta lahira." Da hannu ta yafito 'ya'yan tasa suka zauna a gefen mahaifiyarsu. Da har sun fara matsawa don kada jikinsu ya gogi nata Uwani ta watsa musu kallon ku shiga hankalinku. Ana haka Hasiya ta fito daga bandaki daga ita sai daurin kirji. Fiye da rabin jikinta duk kumfa. Bala'i ya ciwota a bandakin na maganganun da suke tashi ta kasa tsayawa tayi wankan a nutse. "Wace ce Anti?" Ta tambayesu rai a hade. "Anti Laurat matar Daddynmu" Mas'uda ta bada amsa da sauri saboda tsoron tsawar Uwani. Fuuu....Hasiya tayi waje a fusace. Innayo kuma ta dubi yaran ta nuna musu Zara "wace ce wannan a wurinku?" Da yake rabonta da haihuwa bayan tayi ta ruguntsumin kwanika shekara biyar ne, babu wadda bata fahimci tambayar ba a cikinsu. "Mummy ce" "Mummy" " suka amsa tare. "Na san kuna zuwa Islamiyya. Mene ne hukuncin masu sabawa iyaye har su sanyasu kuka? Ina Allah zai saka shi?" Tayi tambayar ga manyan. Maryam da Mas'uda sai da suka zaro idanu a tsorace sannan suka ce "wuta" Uwani na jin haka hantar cikinta ta tsirga. "Mu dai mun roki gafara kuma ance an yafe mana ko Zara?" Zara ta murmusa don idanun Uwani sosai suka bayyana tsoratar da tayi. Innayo ma sai da tayi murmushi sannan ta ce da yaran idan ba wutar suke so ba kada su kara yin abin da zai bata mata rai. A hankali suka shiga matsawa jikinta. A karo na biyu Salima ta sake nuna musu kanwarsu. Ba bata lokaci suka tafi. Tun suna dan ja baya har suka ware. Ganin haka Innayo ta ce da Zara sai ta tashi tsaye wurin dawo dasu turbar da ta dace. In ba haka ba nan gaba ba za ta iya tankawarasu ba. Kanta ta sake tunawa da yadda tayi ta ta rayuwar. Cikin rashin gajiyawa ta sake bawa Innayo hakuri. A waje kuma Hasiya ce tsaye akan dakalin gidansu tana fuskantar Alh. Unaisu. "Saboda ka kara aure sai ku koyawa yara tsanar mahaifiyarsu? Kaga irin kukan da Zara take yi kuwa? Hakkinta ba zai barku ba." ta kare da goge kwallar tausayin yayarta. Alh. Unaisu ba shi da zabin da ya wuce yin murmushi bayan ta gama magana. Dalili kuwa shi ne tunawa da labaranta da ya kan ji daga Zara tun ma kafin su yi aure. Tana yawan fadin masifar Hasiya musamman idan aka taba nata. Bai taba zaton za ta damu da damuwar Zara ba duba da rashin jituwarsu. A nan dole ya godewa Hajiyan Fatakwal da ta zama sanadiyar komawar Zara gida. "Dariya ma na baka?" Hasiya ta tambaye shi a hasale da taga yaki magana. " Yi hakuri Hasiya kuma ina so ki saurareni game da Laurat da kin zuwana" "Don kana auren yayata bani da hurumin son sanin dalilin karin aurenka. Rashin zuwa kuwa ni ban san me ya hadoku ba. Matsalata shi ne komai lalacewar uwa ko uba babu ruwan dayan wurin dasawa yaran kiyayyar dan uwansa." Jajirtacciyar mace ce kuma kaifi daya babu karya ya ayyana a ransa. Sannan ya zauna ya yi mata bayannin duk abin da ya faru har zuwa yanzu. Domin kara horar da Zara da karya lagonta Hajiyan Fatakwal ta sanya shi mikawa Laurat uwargidansa yaran. Zaman Zara ne tuntuni yake karya matsayinta tunda ita bata haihu ba. Shi yasa da wannan damar da ta samu ta fito da makirci kala kala tana juya kan jama'ar gidan. 'Ya'yansa da masu aiki kamar su kwanta mata saboda yadda take kyautata musu. Suka daina ganin girman kowa sai yadda ta ce. Hajiyan Fatakwal na ganin haka ta ce zama bai ganta ba. Da alama da abubuwan da take yi ba wai da kisisina ta dogara ba kadai ba. Shi ne ta ce ya dawo da matarsa tunda yaran ko su yanzu basa gaisarwa sai ta amince. Tare suka koma ciki. Zara na jin muryarsa gabanta ya fadi. Ta tashi da sauri za ta shige daki. Alh. Unaisu da nasa saurin ya tareta zai karbi jinjirar ta karkace gefe guda tare da rankwafawa da nufin hana shi. "Bana son sakarci Zara." Cewar Innayo tana kallon kafafunsa da ya shigo mata har nan da takalma. Kafar ya bi da kallo shi ma ya koma da baya ya cire takalman. Da ya dawo ya zauna Zara taki mika masa 'yar ta kuma ki kallonsa. Sai ma yaran da ta cewa su shige dakin su jirata. Shi ma din sai bai bi ta kanta ba. Innayo ya fara gaisarwa sannan ya dora da ban hakuri akan rashin waiwayo iyalinsa. "Matsayin aurenku nake son sani kafin komai." Shi ne abin da ta ce da shi. Sai da ta fada ya auna ya ga lallai fa dole ayi tunanin ya daina auren. "Aure yana nan Innayo. Ku gafarceni akan abin da ya faru" nan ya fada mata abin da ya sanar da Hasiya a waje "zancen da nake muku Hajiya ta ce kada na koma gida ba tare da Zara ba. Ta karbi kuskurenta na hukunta ta ta wannan hanyar akan abubuwan da take ganin halayya ce da bata son jikokinta su koya. Gyara ba zai yiwu da banzatar da matata a cikin halin danyen jego ba." "Mu kam tsakaninmu da Hajiyarka sai godiya domin kuwa dawowar Zara gida ta haifi d'a mai ido." Inji Uwani. Innayo sai ta yi musu inkiya da su basu wuri tana mai cewa "gata nan ku sasanta amma babu inda zata tafi yanzu kamar wadda bata da gata" ta kalli fuskar Zara don ta gani shin amsarta ta sami karbuwa ko kuwa son bin miji zai sa ta nuna bacin rai. Suna hada ido murmushi da alamun godiya ta yiwa mahaifiyarta. Innayo ta cigaba da cewa "yadda ka bamu hakurin wulakanta min rayuwar 'ya da wasa da lafiyarta, zan so Hajiyar taka ita ma ta zo. Zara ta jima tana bata min rai tabbas, amma duk inda bacin raina ya kai akan halayyarta ba zan taba zuba ido ina kallo ana cin zarafinta ba. 'Yar talakawa ce ka aura amma darajarta tafi karfin in baka ita haka sikau kamar kwanakin da suka gabata basu faru ba." Kai ya gyada tare da cewa "to" da saurinsa. Zai tashi Innayo ta ce a bashi jaririyar. Zara ta dora masa ita a cinya tana aika masa da mugun kallo. Innayo dauke kai tayi don ko yaya dama ya dace Zaran ta nuna bacin ranta ko don gujewa maimaici idan yaga kamar bata damu ba. Kurawa yarinyar idanu ya yi har sai da yaji kwalla ta taru. "Allah Ya baki hakurin jinkirin ganin wannan rana Ummulkhairi. Allah Ya rayaki Yasa ki yi koyi da halin mai sunanki" Innayo, Uwani, Salima, Hasiya da maijego Zara duk sai da suka yi mamakin wannan irin karamci da ya yiwa Innayo. Wasu cikinsu ma irin Hasiya da Uwani basu zata ya san ainihin sunanta ba. Ita kuwa Zara murmushin da tayi mai hade da dariyar farinciki su kadai suka yi nuni da cewa ta gama yafewa mijinta. Su Innayo fita suka yi aka basu wuri. Ya kara bata hakuri da nuna mata cewa shi da ita da Hajiyarsa duk sun yi kuskure a baya. Sannan ba a gyara barna da wata barnar. "Ba jimawa zan yi ba. Ga wannan ki rike. Anjima zan dawo da duk wani abu da ya dace ace nayi tun farkon haihuwar. Na baki dama ki zabi ranar da kike so ayi taron sunanta a gidan nan. Sai anyi za ki koma." "Na cancanci haka kuwa Daddyn Mas'uda? Laifukana ga mahaifiyata suna da tarin yawa." Ta furta cikin kuka. "Ki dauki duk abin da zamu yi yanzu a matsayin lallashi da ban hakuri ga Innayo." "Kai kuma me kayi banda guje min da kayi..?" "A bar tada zancen gudun nan mana maman Khairi." Ai kuwa alkunyar da ya kira sunan 'yar tasu dashi ya matukar burgeta har sai da ta sake yin murmushi. "Nima da laifina sosai. Ban cika masoyi ba tunda ban damu da daidaita tunaninki akan mahaifiyarki ba." Bayan tafiyarsa Hasiya ta kebe da Zara kafin su tafi asibiti. Maganganun da ta saba yi mata a baya ta kara maimaitawa. Sai dai wannan karon sun sami gurbi mai kyau sun zauna a zuciyar Zara. "Miji abokin rayuwa ne kuma mahadin rayuwa. Duk wanda Allah Ya zaba miki a matsayin miji, ki sani cewa alakar ta zarce ke da shi da 'ya'yan da zaku haifa. Aure haduwar dangi shida ce. Naki na uwa da uba, nasa na uba da uba, sai kuma abokan arzikinki da nasa. Idan aka sami matsala tsakaninki da guda cikin nasa ko shi da naki, wajibi ne sai ya taba jindadin rayuwar auren mutum. Musamman abin da ya shafi dangi domin su kawaye ko abokan arziki ana iya canjasu. To amma fa duk wanda kika kawo a matsayin makusanci na jini ko na abota, dole ke ce za ki nunawa miji ko shi ya nuna miki mahimmancin dayan a gare shi. Wanda ka mutunta, abokin zamanka ya tayaka mutuntawa. Wanda ka tozarta ko ka wulakanta, wani sai ya fiki ci musu zarafi. Cikin mutanen da na ambata, UWA ita ce tubalin komai. Innayo uwa ce a gareki. Ina fata kin gane me nake nufi." "Mun gane, kuma mungode." Tare suka juya suka ga Uwani. Ta karaso ciki ta dubi Hasiya, "Meye za ki bata shawara ita kadai banda ni?" "Allah Ya huci zuciyar metiron" cewar Hasiya tana dariya. "Kin raina ni. Amma muje zuwa. Ba ciki gareki ba? Allah Ya kaimu ranar fafe gora in..." "Kada ma ki karasa..." Innayo ta shigo cikin dakin ita ma "idan ki ka ci zalin auta rama mata zanyi la'ada waje" Dakin kaurewa ya yi da dariya kafin kuma su tashi cikin hanzari su cigaba da shirin zuwa asibiti. *** Tunda Abbati ya san Asabe ta tafi wurin Munzali, Alh. Rabi'u na tafiya ya haye sama. Wanka yake son yi ya dan gasa jikinsa. Dukan da ya sha a police station da fadansu da Shazali sun sa jikinsa yin tsami. Su Baaba Mari ma dakunan da aka saukesu suka shiga. Fito da komai fili da aka yi yasa zukatansu sun sami sukuni. Abin da ya rage yanzu shi ne kawai a tabbatar da cewa sun nesanta daga wannan rayuwa har abada. Takun Abbati bai sa Hanne yunkurin tashi ba har ya hawo. Gabansa sai da ya yi mummunar bugawa da ya ganta zaune da jajayen idanun da kuka ya rina. Cikin mutuwar jiki ya karasa hawa ya zo gabanta ya zauna shima jingine da bango. Muskutawa tayi ba tare da tunanin komai ba sai kyankyamin abin da taji game da shi. Sanin cewa za ta iya tona masa asiri bai hana shi yin murmushi mai ciwo ba. Da kansa ya ja jiki ya sake bada tazara a tsakaninsu. "Zamanki a nan ya nuna min cewa kin ji komai" "Naji" ta bashi amsa a dakile. "Ki saki ranki Hanne. Babu sauran bacin rai ko fargabar da ta rage min a dalilin wannan abu. Duk abin da za ki yi ba komai bane illa tishi akan wanda iyayena suka yi. Allah na sabawa, fargabar ko Ya karbi tubana ya danne duk wani abu mara dadi da ya sameni a sakamakon abin nan" Gashi dai a hankali yake maganar, amma kalamansa ba karamin haushi suka bata ba. Ta tashi tsaye tana masifa. "Kana nufin bacin raina ba shi da mahimmanci a wurinka? Kodayake dama ba tun yau na san cewa ba ka sona ba." Tsareta ya yi da ido ya ce "tsakaninki da Allah ke kina so na?" Bata zata zai yi mata irin wannan tambayar ba. Sai ta sami kanta da bude baki tana rufewa. Shi kuwa bai yi mamaki ba. "Kada ki tuhumi zuciyata don nima ba zan tuhumi taki ba." Kuka kawai ta fashe da shi. Ranta a jagule da bakinciki. Abubuwa da dama ne dankare a zuciyarta wadanda suka haddasa mata bacin rai. Abbati sai ya mika mata hannu. A zatonsa za ta sake nuna kyama. Sai yaga ta miko nata. Ya rike hannunta suka sauka kasa. Baya son sake kwana da komai a ransa. Idan ta kama duk wani nauyi da hakki ya daidaita shi a yau to zai yi domin gobe ta zama goben dake tattare da budewar sabon shafi. Dakin da su Mal. Sa'idu suke ciki ya kwankwasa tare da yin sallama. Mal. Inuwa ne ya amsa don shi Mal. Sa'idu har ya soma gyangyadi. Suna ganinsu tare suka tashi zumbur kowa ya zauna. "Abbati fada mata kayi?" Mal. Sa'idu ya tambaye shi yana hankalinsa a tashe "me ya kai ka? Wannan sirrin ai tsakaninka da Allah ne" "Baba ku yi hakuri." Ya rufa mata asiri bai ce tsayuwa tayi ba bayan ance su tashi ita da Habu. Zama suka yi akan kafet suna fuskantar gadon da su Mal. Inuwa suke kai a zaune. Abbati ya dubi Hanne ya nuna mata iyayensu, "Tsayin shekarun da muka dauka a matsayin ma'aurata bisa biyayyar iyayenmu bana jin akwai wanda ya taba damuwa da son sanin ainihin bukata da burinki. Yau gashi kin san abu mafi muni a kaina. Ina so ki yiwa kanki adalci a gaban wanda ya hadamu auren nan ki fadi abin da yake ranki" "Kamar yaya?" Ta tambaye shi saboda kanta ya kulle ta kasa fahimtarsa. "A wane matsayi ki ka dauki aurena a da da yanzu?" Sunkuyar da kai tayi. Mal. Inuwa ya ce kada ta cuci kanta suna sauraronta. Kasa magana tayi har lokacin. Sai da Mal. Sa'idu ya hada da jan idonsa mai sa ayi ko ba a so sannan ta magantu a tsorace. "Na so auren nan duk da cewa hadamu aka yi. Nayi ta kokarin ganin cewa mun zauna kamar wadanda suka yi auren soyayya amma ban samu ba. Babu abin da na nema na rasa a gidan nan. Sai dai kai da nake zamanka duk kokarinka na sauke hakkina bai hanani jin kamar nesa muke da juna ba. Ra'ayi da tsarin rayuwarmu duka ba iri daya bane. Ko hira muke akan abu daya fuskar da muke kallonsa ta bambanta. Shi yasa tun ina kokarin ganin na shawo kan matsalar har na hakura." "Ba laifinki bane. Laifin rayuwar da nake yi ce wadda ta hanani ganin aibun nawa tsarin. A ganina ci, sha da sutura da sauran 'yan abubuwan da nake yi sun isa su gamsar dake" cewar Abbati. "To wai ni yanzu mene ne matsalar? Banda tashin hankalin jin mummunan sirrin mijinki kina son rabuwa da shi ne?" Sunkuyar da kai tayi da sauri. Abbati ya roki Mal. Sa'idu da ya sassauta mata domin tana da damar nuna bacin ranta. Mal. Inuwa kuma ya ce ta fadi abin da take so shi kuma ya yi alkawarin tsaya mata. "Babu farinciki a cikin gidan nan. Zaman hakuri kawai muke yi cikin wadata amma kowa rayuwarsa daban. Kudin shi ya rikeni har na kai yanzu. Amma tunda na san silar samuwarsa, wallahi gara min rayuwar kauye da nan. Don Allah Baba ina rokon arzikin komawa gaban iyayena. Zamanmu a lokacin da ban san sirrinsa ba ma bai yi min dadi ba balle yanzu?" Ta daga kai a hankali ta kalli Mal. Sa'idu "Baba ku gafarceni. Abin da naji ba zai taba fita daga zuciyata ba. Ba zan iya zama gida daya da Yaya Abbati da Munzali ba. Zuciyata cikin zargi za ta dawwama matsawar zan gansu a inuwa daya. Nayi imani kuma ba zai taba barin Munzali a kan kowacce mace ba." Kimamin mintuna biyar ne suka wuce kafin Mal. Sa'idu ya ce "Abbati rubuta mata takardarta. Gobe in sha Allahu zamu tafi tare da ita." Jikinsu duka su biyun ya yi matukar sanyi. Zaman sama da shekara goma duk rashin dadinsa dole mutum yaji wani iri lokacin rabuwa. Rayuwa suka yi babu duka babu zagi. Babu rashin kunya babu fitsara. Sai gidadancin Hanne da wauta da kuma rashin soyayyar Abbati. Amma su biyun babu wanda yake nufin dan uwansa da sharri. Matsalarsu guda ita ce rashin wannan karsashin da zai sa mutum ya shiga ranka ko babu soyayya. A takure suke da juna, kowa yana gwada sauke hakkin dan uwansa a iya damar da Allah Ya bashi. Irin wannan zaman musamman tunda babu yara sai mutum yaji kamar yana kurkuku. Arziki da wadata basa cike gurbin bukatar zuciya na son samun abokin rayuwar da ya dace da ita. Abbati ya jima da sanin wannan shi ne kuma dalilinsa na amfani da wannan damar wurin sauwakewa Hanne maimakon neman ta zauna. Idan ya zauna da ita yanzu cutar sai tafi ta da. Domin yanzu aure baya gabansa. Akwai abu mai matukar mahimmanci da ya kamata su fara yi kafin suyi tunanin zama da mata. *** "Baka ganin dazu kayi amfani da kausasan lafuza akan mahaifinka? A haka kake so ka ja ra'ayinsa wurin sauke akidar da yafi shekara arba'in da biyar a kai?" Asabe ce tayi maganar tana zaune akan kujera yayinda Munzali ya takure a kasa. A haka tazo ta same shi dama. "Ki gafarce ni amma ko kalmomi na basu dace ba ina ganin bai kamata ki ga laifina ba." "Haka ne. Bamu koya muku ba sannan bamu kaiku inda za ku koya ba." Da bai ce komai ba sama da kada kansa gefe ta fahimci amsarta tayi daidai. Tambaya take so tayi masa amma tana tsoron kada su karke kamar yadda ya yi da mahaifinsa. Sai da taga yana shirin tashi ta ce, "Munzali ka fada min tsakani da Allah wane irin so kake yiwa Abbati. Na san ya kyautata maka sosai. Amma anya saboda wannan dalilin kadai ya dace ka fadawa Alhaji maganganun da ka fada dazu?" Taune lebensa ya yi gami da rufe jajayen idanunsa. Yana ganin idan bai yi da gaske ba da wuya ya wayi gari saboda zafin zuciya. Me yasa kowa yake yi masa wannan tambayar ne? Ko dai abin da suke zargi game dashi gaskiya ne? Shin mene ne ainihin abin da yake zuciyarsa? "Zan baki amsa idan na nemota in sha Allahu." "Munzali?" "Kiyi hakuri Asabe." Daga haka ya janyo filon guda daga kan kujera ya ajiye akan kafet ya kwanta a kai. Ko minti goma bai yi vmba bacci ya dauke shi. *** Da gudu Sauda da Mardiyya suka fito tarbarsu Mami Khadija. Mardiyya harda kukan ganin kafar Suhaib. "Yaya accident kayi ne?" Ta tsare shi da tambaya tana tattaba kafar. "Buguwa ce Mardiyya" Sauda ta ce "Da me?" "Ku muje ciki" Farha ta katse su tana bin bayan Mami. Tun tasowarsu daga Kano Mamin ta canja. Su duka sun san wani abu ya faru kuma yana da nasaba da babansu tunda suna tashi aka sanar dasu sun fita tare. Alh. Tahir bai shigo gidan ba sai bayan la'asar. Yanayinsa ya nuna yana cikin tsananin tashin hankali. Bangarensa ya wuce yau bai tsaya jiran kowa fitowa ayi masa sannu da zuwa ba. Sauda da Mardiyya ne kadai ya san ko ya tsaya zasu iya fitowa. Sam bai kula da Mama Nasima dake tsaye a bangaren dinning table da tray a hannu ba sai da tayi magana. "Diya duk gajiyar ce ka shigo haka babu sallama?" "Uhm" ya amsa kamar baya so yana mai cigaba da tafiya hanyar dakinsa. "Ina ka wuce ne? Nayi zaton tare ku ka taso dasu." Maimakon amsa sai ya tsura mata idanu yana kallonta daga sama har kasa. Ya tuna cin mutumcin da suka yiwa Mami shi da ita a dakinsu. Ya kuma tuna cewa ita ta bayar da shawarar a cirewa Mamin mahaifa kuma ya karba. Tirr da Allah wadai ya yiwa kansa. Tabbas yana daga cikin bambancin halittar namiji da mace son tarayya da mutum sama da daya. Hakan iko ne da ayar Ubangiji SWT. To amma shi wane irin mutum ne da bai san kawaici ba? Me zai sa ya yi masha'arsa a cikin gida da matarsa da 'ya'ya? Be tsaya nan ba duk gatan da Allah Ya yi musu na damar karin aure amma yake yawon bin mata kamar bunsuru. "Lafiya kuwa Diya?" Muryar Mama Nasima ce ta katse masa tunani. Ya yi firgigit ya dubeta sannan ya ce ta fita ta kirawo Mami Khadija da Jiddo. "Kayi musu waya mana" ta ce tana dan murguda baki. "Ki fita ki yi abin da na saka ki kafin na fito daga wanka" Da wane bakin zai yiwa Mami magana shi da ita a waya?! Cikin minti ashirin ya gama kimtsawa sannan matansa duk sun hallara a falon. Ya dauko takardu biyu wadanda ya rubuta ya mikawa Jiddo daya, Mami Khadija ma daya. Mama Nasima ta cika fam da ta tabbatar biyu ne. "Ina tawa? Alhaji me yasa sam baka son yin adalci ne?" Za ta kara magana Jiddo ta kwarma wani irin ihu wanda ya fita har wurin masu gadi. Ta tashi tana rawar jiki ta kawo masa takardar gabansa ta saketa a kasa. "Wallahi, na rantse, wallahi babu inda zani." Ta nuna kanta "ni za ka saka? Ni din? Ko don kaga bana haihuwa?" Da sauri Mama Nasima ta koma ta zauna nata jikin ita ma yana rawa. Ta kalli Mami Khadija a fakaice amma ta kawar da kai don bata ma son sanin me takardarta ta kunsa. Sai da Jiddo ta gama hargaginta sannan Alh. Tahir ya zaro wayar Danliti daga aljihunsa. "Ki godewa Allah baki haihu ba don da yau babu abin da zai hanani bawa danki wannan wayar" ya fada yana mika mata. Hannu ta noke ta ce "wayar waye?" "Na zata za ki fini sani. Amma tunda da alama kin manta bari na bawa yayarki Nasima ta karanta" Kafin ya rufe bakinsa ta karbe wayar. "Whatsapp za ki bude. Ki nemo sunan da aka sa Kaduna account" Jikinta ya fara sanyi ta nemo sunan. Tana bude chat din gabanta ya yi mummunan faduwa. Ba hirar ta karanta ba. Hoton farko da idonta ya kai gareshi kirjinta ne tsirara da ta turawa Danliti. "Na shiga uku na" ta furta a dimauce tana kallonsa "wallahi. Kaga ni. Ban san..." "Adana zancenki don ba zai min amfani ba. Ina fata dai kin tuna waye" Nan fa ake yinta. Samari nawa ne suka yi irin wannan hirar dasu? Ai ba za su kirgu ba. Don sun fi wadanda tayi mu'amalar zahiri dasu. Mama Nasima dai jiki sai bari yake. Ta gama firgicewa don ko ba a fada ba ta fara harbo inda jirgin ya dosa. Dama ta jima tana zargin Jiddo tana yawo sai dai bata da shaida ko guda. Jiddo tasowa tayi tazo gaban Alh. Tahir tana kuka ta fara cewa sharri ne ake son yi mata. Jikinta ne ta yarda amma bata san waye ya dauka har ya tura ba. Rainin wayon nata ya sosa masa zuciya kuwa. Yana son nuna mata bacin ransa sai ya tuna ba shi da wannan hurumin. A takaice ma ya san cewa sakamako ne ya soma girba tun yanzu. Ya ma godewa Allah da ba 'yar cikinsa bace da bai san inda zai tsoma ransa ba. Janye kafarsa ya yi daga rikon da tayi masa ya ce "Idan kin gama ganin sakarcin naki bani wayar domin ana bukatar amfani da ita wurin gurfanar da Danliti makanike a kotu" Kiris ya rage ta kwarma ihu lokacin da ta maimaita sunan da karfi. "Danliti? Kotu? Wallahi ni dai babu ruwana ko me ya yi" Tsaki kawai ya yi. Bai kara tanka mata ba ya dubi Mami Khadija da Mama Nasima. "Khadija ga sakin da kika bukata kamar yadda na alkawarta miki zan yi. Alfarmar da na roka ta ki zauna kafin komai ya kammala na gidan kawai nake nema" "In sha Allah" ta bashi amsa gami da mikewa. "Me za ki ce da yaran?" Ya tambaya a raunane. "Idan ka gama ka same mu a falona" Ficewa tayi abinta don bata bukatar sanin ragowar me zai tattauna da sauran matansa. Tana fita Mama Nasima ta cigaba da tsuma. Ita dai ta san indai ba mazan da ta sani kafin aurenta ba, babu wani da namiji da za a danganta ta dashi. Daga ranar da ta haifi Mardiyya ta san cewa gantali ba nata bane. Shi ne ta fada neman kudi ka'in da na'in. Laifinta guda a yanzu wanda shi ma tana ganin namiji zai iya saki dominsa. Shi yasa ba bata lokaci ta zamo daga kan kujera ta hau bashi hakuri. "Me kika yi ke kuma?" Ya ce da dan murmushi. Ya dade da sanin tana yi. Yana dai kawar da kai ne saboda ganin damarsa. "Kudi" ta ce tana zufa " idan kayi ajiya ina dauka Diya. Ina maka lalube a jaka da walet. "Tashi ki tafi." "Ni dai babu sakin ko? Idan ka sakeni ina zani?" "Babu. Jeki Nasima. Ina bukatar hutu." Ai ko bai ce ba dole ta fita. Bata son jimawa kada a fito da dalilin sallamarta. Ita da shi duka sun manta da Jiddo dake sharbar kuka. Sai da ta tafi ya ce da ita, "Duk abin da na saka a bangarenki da wanda na baki ki tattara ki tafi dasu. Wannan shi ne abu na karshe da zan iya yi miki" *** Su Farha ne zaune a kasa iyayensu akan kujera sun yi jigum. Alh. Tahir ya rasa me zai ce. Mami Khadija sai da ta tabbatar ba zai iya magana ba saboda tsoron halin za zasu shiga sannan tayi magana. "A matsayinku na musulmai masu hankali na san kun san kaddara. Wannan kaddarar ita ce ta kawo mu wannan rana da aurena da mahaifinku ya kare." Sauda da Mardiyya suka fashe da kuka. Su Suhaib da suka san dalili su ma babu wanda zuciyarsa bata kadu ba. "Mami me yasa? Don Allah ku yi hakuri ku koma" cewar Mardiyya. "Ya Suhaib ba za ka ce komai ba kana jin abin da take cewa" inji Sauda. Alh. Tahir sai ya hau gumi. Tunaninsa abin da zai ce shi ne dalilin da ya san yaran zasu yi ta tambaya. Mami Khadija ce tayi belinsa da dabaibayin da ya zargowa kansa tun farko. "Aure zai yi. Kun kuma san cewa ba haramun bane. Wacce zai aura din ce dai nayi rantsuwar ba zan taba zama da ita ba. Yakumbo kuma ta ce tunda har ya yi magana da iyayen yarinyar ita ma bata yarda a janye ba. Rabuwarmu ita kadai ce maslaha a yanzu." "Wace ce?" Sauda da Mardiyya suka tambaya a tare. Farha wadda amsar Mami ta farantawa rai domin bata son kannenta su san halin babansu ce ta bada amsa. "Yumna ce. Kawata Yumna" Sauda da Mardiyya ko kallon uban basu sake ba suka fice daga falon suna kuka. Mami Khadija ta dubi su Lilu da ko tari basu yi ba ta ce, "Ina rokon arzikin ku rufawa mahaifinku asiri a wurin kannenku. Fushinsu yanzu na dan lokaci ne zai wuce sabanin idan suka san abubuwan da ku ka sani" Daga nan ta fada musu zancen tashi da zasu yi bisa umarmin baban nasu. Basu ce masa komai ba suka tashi suka fice su ma. "Na gode Khadija. Na gode kwarai da gaske. Ina fatan Allah Ya yi miki sakayya da mafificin alkhairi" Dakinsa ya koma yana tunanin yadda zasu kwashe da iyayensu idan suka ji sakin. Ran kowa zai baci to amma wuyarta a kwana a tashi, komai me wucewa ne. *** Gwaggo Jummai mahaifiyar Hanne kuma kanwa ga su Mal. Sa'idu ta shiga ta fito don a mayar da aurenta da Abbati abu yaci tura. Sati guda kenan da komawarta gida. Da ta kasa shawo kan 'yarta ta amince a gyara auren sai ta koma wurin yayyenta. Goyon bayan da taga sun bawa Hanne ranar da tazo gidan ya dagula mata lissafi. Abin har ya kaita ga fitowa tsakar gida tana yada magana. "Anje an gama kullo munafunci an kaso auren 'yata." Nan da nan tsakar gida da cika ta jama'ar gidan. Dama tun dawowarsu Baaba Mari da fitowar zancen mutuwar auren ake ta kus-kus a kowacce kusurwa. Don ma ita Gwaggo Jummai ba a gidan take ba. Da bakinciki sai ya kusa buga mata zuciya. Da Hanne ta koma gida tayi ta kokarin samun Abbati a waya sai dai bisa umarnin Mal. Sa'idu baya dauka. Yace masa ya bari su zasu yi mata bayani ba tare da tonon asirinsa ba. Suna gudun kada ya fadi wani abin da zai iya darsa mata zargi. Ko kuma ta tilasta masa mayar da auren saboda ganin girmanta. Sai taki zuwa gidan amsa kiran yayanta. Kullum tana faman kiran Abbati. Ga Hanne taki cewa komai. A takaice ma dai tafi walwala. Ga uban kayan abinci da kudi da ya bata. Zuciyarta fes tunda ta san aurensu kam ko a lahira bata muradinsa. Zaman wa da kanwar yafi mata dadi. Cikin rumfarsa Mal. Sa'idu ya ce ta dawo su yi magana ta ki. "Ba zan shigo a ninke ni baibai ba. Ni gabadaya zantukan da kuke yi kai da Yaya Inuwa basu da ma'ana. Ai na jima da sanin Deluwa tana son saka 'yarta a gidan Abbati. Kuna fakewa da rashin haihuwarta bayan ni na san kwadayi ne da hassada." Deluwa tafa hannuwa tayi don dama itama a matse take da son sanin dalilin sakin. Da canjin da ta gani farat daya a wurin murdadden maigidanta. "Bana fada da kanwar miji Jummai. Ba don haka ba da kin ji ta wuraren da 'yarki ta gaza har Abbati ya kasa zama da ita." "Zan saba miki Deluwa" ya fada yana yi mata kallon da yasa ta rufe baki ba shiri. Kanwarsa ya kalla da 'yan ganin kwaf ya ce "rabuwar auren bata da alaka da kowa a gidan nan. Hasali ma 'Yashshafa da kike magana a kanta na riga nayi mata miji" Deluwa ta san bashi da labarin Sha'aib (Suhaib) na Kaduna. Shi yasa cikinta ya wani murde da taji me yace. 'Ya'yan 'yan uwansa maza da suka rage babu wani mai dan romon da za a sha a cikinsu. Magana ta so yi ya ce tana kara bude baki a bakin aurenta. Haka ta cije lebe ta bar wurin cikin bacin rai. Tafiyarta ke da wuya Hanne ta shigo. Bata san fitar Gwaggo Jummai ba sai da kaninta ya fada mata. Shi ne ta biyo sawu. Ta iske sun koma rumfar Mal. Sa'idu. Hakuri dai suke ta bata taki yarda saboda har yanzu bata ji kwakkwaran dalili ba. A yau yawan kallon Hanne ya yi mata rana. Zama tayi ta dubi iyayenta. Mal. Inuwa duk ya fita hayyacinsa saboda tsoron kada karshe Mal. Sa'idu ya rasa zabin da ya wuce fada mata gaskiya. Baaba Mari kuwa dama ko uffan bata ce ba. "Gwaggo ki yi hakuri. Sakin nan ni na nema. Munje asibiti likita ya ce akwai wani abu a jininmu wanda ya sa da matukar wuya mu haihu tare. Masu irin jininmu basa zama da juna. Shi yasa nake yawan bari. Ya so.mu cigaba da zama. Ni kuma gaskiya ina gudun cinye kuruciyata babu d'a ko daya" Tunda ta bude baki sai yanzu wani abu da ya tokare wuyan Mal. Sa'idu ya sauka. A take fuskar Gwaggo Jummai ta koma kalar tausayi. Ta girgiza kai tana cewa "ban san abin haka yake ba. Yaya ku gafarce ni. Tabbas lalura idan ta shafi haihuwa maslaha ake nema. Amma me yasa baki fada min ba?" Ta kare da tambayar Hanne. Hanne bata yarda ta kwashe laifin karyarta ba. Idan bata gyara zancen ba zasu dade Gwaggonta tana mita. Nuna mata tayi basu dade da yin gwajin ba. Abbati yaki yarda ya saketa da ta nema. Shi ne ya kira iyaye don ayi sulhu. Su kuma suka goyi bayanta. Gwaggo Jummai ta dinga bada hakuri. Da Baaba Mari ta tashi har daki ta bita tana ta rokon tayi hakuri akan kalaman da ta dinga yi. Ita kuwa da ta san cewa ita ce ta karu da abin da ya faru, da wuri ta nuna komai ya wuce. Bayan tafiyarta ta kira Abbati ta sanar dashi. Ta kuma jaddada masa ya yiwa Hanne godiya sannan ya cigaba da tuba. *** 48 Zaune yake gaban likita na goma sha uku cikin jerin likitocin da ya ziyarta domin magance matsalarsa. Amsa yake nema don ya san a wane babi zai ajiye lafiyar kwakwalwa da tunaninsa. Ya gama bayani tsaf akan yadda ya dauki Abbati da zargin da mutane makusantansa suke yi masa kamar yadda ya yiwa sauran likitocin. Ya kare da cewa, "Bayani nake so a mahanga ta addini. Idan bani da rabon samun rahama ne saboda irin tunanina gara..." "Subhanallahi" cewar likitan da sauri "Munzali wannan magana taka bata dace da dan musulmi ba. Ni ba malamim addini bane. Amma tabbas har yau ban bar gaban malamai ba. Na kuma godewa Allah da malumanmu na yanzu suka kasance masu ilimin boko wanda yake taimaka musu wurin warware matsalolin da suke tafe da zamani. Idan za ka iya gobe ka zo nan da la'asar. In sha Allah zan kai ka wurin Dr. Abdallah Saraki. Kawu ne kuma siriki a wurin abokina Dr. Huzaifa." Tun bayan zaman nan da aka yi a gidan Abbati sati biyu da suka wuce, sai yau Munzali ya yi murmushi. Da ya tashi zai tafi likitan nasa ya ce su taho tare da Abbati da iyayensa. "Hakan ne zai sa kowa ya sami gamsuwa akan amsar da zai baka" Yana shiga mota ya kira Abbati. A lokacin shi kuma yana cikin ofishin Alh. Sadisu. Kiran na shiga ya dauka da sauri. "Munzali lafiya dai ko?" "Lafiya kalau. Kana gida ne?" "Ina office din Alh. Sadisu ne. Yanzu muka dawo daga duba Abdul" Munzali yaji kunya ta kama shi. Ba irin lallashi, fada da nasihar da Abbati bai yi masa ba amma kememe ya daina yarda ko zaman minti biyar suyi a wuri daya. Abbati ya yi fushi sosai saboda ya fuskanci akwai abin da yake boye masa. Shi kuma baya son fada saboda a take Abbatin zai soke masa zargin. Gashi zuciyarsa ta riga ta fara rawa akan maganganun iyayensa. Ya zama wajibi ya san me yake ciki. "Kwatanta min wurin zan zo na same ka" Minti ashirin ya kaishi. Suka zauna tare da Alh. Sadisu. A yau godiya mai tarin yawa ya sake yi musu sannan ya koma kan batun abubuwan da yaji a police station din. "Kuna ganin da gaske zaku iya dainawa? Nayi bimcike ance da wahala rabuwa da wannan dabi'ar. Idan Abdul ya tashi a haka ban san yadda zan yi ba" Munzali bai yi kasa a gwiwa ba ya fada masa shirinsu na zuwa asibiti a Italy. Rashin zuwa a duba lafiyarsu da kuma neman hanyar rabuwa da lalurar har abada ba karamin kalubale bane ga tubansu. Ita wannan dabi'a tana tattare da matsaloli da yawa ga lafiya. Ciki kuwa harda kasa jurewa rashin samun biyan bukata ta inda aka saba. Wannan abu ya kan fi karfin furtawar baki da yakinin zuci. Wani duk dauriyarsa idan abin ya ciwo shi sai ya biya bukatar yake jin dadi. "Abdul yaro ne. Sake komawarsa ba abu bane mai wahala. Mafi a'ala shi ma ka kai shi asibiti" inji Abbati. Godiya ya yi musu da zasu tafi da alkawarin tsaya musu a duk lokacin da suke da bukatar taimakonsa. "Magana nake son muyi Abbati." Munzali ya ce da suka fito waje. "Dama jikina ya bani tunda ka kira. Ka gaji da yajin ne kazo biko da kanka?" Da sauri Munzali ya ce "don Allah ka bar amfani da kalmar yaji da biko kamar wasu mata da miji" Abbati na jin haka ya gano inda matsalar take. Motarsa ya bude suka shiga ya tayar. Gida ya wuce kai tsaye. Yanzu babu kowa daga kuku sai Maigadi. Iya Kande bata dawo ba tun tafiyar Qibdiyya gida. A waje suka zauna wurin wasu kujeru da 'yar rumfa. Munzali ya fadawa Abbati dukkanin damuwarsa. "Na san za ka iya cewa ba komai bane. To amma hankalina ba zai taba kwanciya ba. Don Allah gobe ka zo muje wurin malamin." Kamar uwa da d'a. Tausayin Munzali ya kama Abbati sosai. Don gudun kara masa damuwa sai bai yi masa yadda ya saba ba idan yana cikin yanayi mara dadi. Lokutan da yake yi masa fada ko nasiha da rarrashi har sai ya sauko. "Allah Ya kaimu goben. Dama nima ina son yi maka magana akan mu nemi fatawa kan dukiyarmu. Goben sai muje masa da komai muji me zai ce." Munzali ya mike zai shiga ciki. Abbati ya kai hannu zai taba kafadarsa don ya tsaya sai ya fasa. "Munzali." Juyowa ya yi fuskarsa duk ta rame kamar ya dade yana ciwo. "Ina so ka sani cewa ko yaya makomar alakarmu ta kasance gobe ba zan taba barinka ba" "Ko da ya tabbata wannan kazantar bata barni ba" "Zama da kazanta fa sai ka so. A matsayin kani kuma amini na daukeka. Banda an riga an dasa maka wani irin tunani a zuciyarka da na fada maka matsayinka a wurina. Yanzu kuwa ina magana za ka iya tsoron kada nace gobe zan kawo sadaki" Murmushi suka yi a tare sannan kowa ya nufi gidansa. *** Washegari basu hadu da safe ba. Munzali ya tafi gida dauko su Asabe. Ya sami gidan a cike makil. Larai da su Fati sun zo dukkaninsu kwai da kwarkwata. Gaban Innayo ta zauna ta roki gafararta na rashin kyautawa da tasa 'ya'yanta yi mata. Ta karbi laifinta kamar yadda 'ya'yanta su ma suka karba. Aka yafi juna tare da alkawarin sabunta zumumci. Hasiya ce kadai bai samu ba. Hakan ya yi masa dadi domin yana jin kunyarta saboda rashin samun sukunin zuwa duba Abbas. Uwani kuwa tana jin muryarsa ta fito ta tare shi a gefe. Mita ta soma yi masa na rashin kiranta da ya ce zai yi domin ta duba Qibdiyya. Hakuri zai bata sai ta kula da ramar da ya yi. Mantawa tayi da fadan ta koma tambayarsa damuwarsa. "Na manta gidanmu ba irin da bane, da na sani ban zauna abubuwa suna ta damuna ba a cikin kwanakin nan" yace ba tare da wasa a fuskarsa ba. "Komai mai wucewa ne Munzali. Tunda muka dinke da Innayo kaima kawai ka jira lokaci. Kafin ka farga zaka ga ya koma tarihi. Ko ka bayar dashi ko rike abinka a zuci" Karfin gwiwa ya samu daga gareta wadda da ita ya yi amfani wajen jajircewa iyayensa suka bi shi. *** Sheikh Dr. Abdallah Saraki ya saurari jawabin Munzali da Abbati da dukkan nutsuwar da ake bukata daga malami. Labarinsu gabadaya izina ce kuma babban darasi ga iyaye da su kansu 'ya'yan. (Ni din ba Malamar addini bace. Daliba ce mai koyo har yanzu. Bakin gwargwado ina nazari da bincike kafin na kawo wani batu mai girma cikin labaraina. A nan ma na duba matsayar malamai na kuma hada da tawa fahimtar. Saboda haka idan mai karatu yaci karo da abin da ya sabawa nasa ilimin, kada a manta cewa wannan labari ne. Abin da ya shafi fatawa a nemi sahihancinsa a wajen maluma. Rabbi Yasa mu dace da khairi duniya da lahira. Amin) Da Alh. Rabi'u ya ga zai fara magana, hankalinsa kacokan ya mika masa. Yana so yaji malamin ya wanke shi daga abin da Munzali ya ce, wato yana da hannu a cikin lalacewar rayuwarsa. Dr. Abdallah ya fara jawabinsa da sallama tare da addu'ar bude taro ko wani zama da za a tattauna abu mai mahimmanci. Sannan ya karkare da yiwa fiyayyen halitta salati SAW. "Da farko zan fara da yaba muku tare da kara muku karfin gwiwa. Duk wanda ya nufi Allah SWT da kyakkyawar zuciya, to ya sani cewa Allah ba zai tab'ar dashi ba. Saboda haka ku cigaba akan niyyarku. Ko a duniya ko a lahira sai kun yi mamakin falala da girman Mahaliccinmu. Zai baku fiye da rokonku. Ya yafe fiye da tubanku domin Shi din gagara misali ne wajen jink'ai da tausayi." Ya gyara zama saboda su san cewa zancena gaba yana da mahimmanci. "Munzali ina so kai da iyayenka ku sani cewa tsaftatacciyar soyayya ce tsakaninka da Abbati. Irin soyayyar da Allah SWT Yayi alkawarin inuwar Al'arshi rana gobe kiyama ga ma'abotanta. Wato mutum biyu masu kaunar juna domin Allah Shi kadai." Munzali ya hau murmushi yayinda Abbati ya dinga kiran sunan Allah a iya a lebbensa. "Malam baka ji inda ya ce yana son Abbati fiye da kowa ba? Ma'ana fa harda mu. Babu jin nauyi ko kadan yake nuna min cewa yaron nan ya fini a wurinsa." Cewar Alh. Rabi'u yana huci. Dr. Abdallah ya ayyana a ransa cewa lallai Alh. Rabi'u akwai gagarumin gyara a lamarinsa. "Aikin sab'o sakamako ne na raunin dan Adam. Shi kuma rauni ana gane shi ne daga zuciya. Idan aka haneta ga barin abin da take so sai ta ce ta kasa. Idan aka umarceta da abin da bata so nan ma ta nuna gazawarta. To da zarar mamallakinta ya biyewa ra'ayinta ba tare da dora shi a mizanin hankali, dabi'a da addini ba, dole nadama ta saukar masa watarana. Alh Rabi'u, ka yi godiya muddin rai ga Allah da Ya bawa yaran nan damar fin karfin zukatansu a lokaci irin wannan. Gurbacewar zamanin nan ta kai ta kawo. An kawata zina ana tallatawa mutane. Tserewa tarkonta wallahi sai wanda Allah Ya azurta da jarumar zuciya. Wadda tana so din kuma tana tsoron mummunar makoma. Zuciya ta ma'abota tsoron Allah da kwadayin rahamarSa." Asabe ta dinga gyada kai tana yiwa Munzali da Abbati kallon tausayi. Alh. Rabi'u kuwa cikin kosawa ya ce, "Nifa so nake naji inda aka halattawa baligin namiji kaunar kato kamarsa har ma kake ganin cewa hakan ba laifi bane. Addinin nan bakin gwargwado nima fa na san shi. Maluman zamanin nan banda son zuciya da kwadayin abin hannun masu neman fatawa basu iya komai ba. Sai ayi ta halatta haram don kada ran mai kudi ya baci" Kunya sosai ta rufe Abbati da Munzali. Asabe ta dinga bawa Dr. Abdallah hakuri. Shi kuwa ko a jikinsa. Mutane irin wannan da wadanda ma suka fi shi nawa ya gani? "Soyayya tana samuwa ne daga kyautatawa. Babu ruwanta da jini ko alaka. A inda aka samar da ita a nan take samun wurin zama. Ku duba hikimar Ubangijinmu a wurin zamantakewar rayuwa. Da farko Ya sanya soyayyar da a zukatan iyayensa tun yana ciki. Wannan ita ce ainihin sunnar rayuwa game da iyaye da 'ya'ya. Duk wanda Allah Ya bamu mai kyau ko akasinsa. Nagari ko shakiyi sai kaga muna son kayanmu. Har muna jin ciwon hukuncin da mukan yi musu idan sun yi laifi. Su kuma 'ya'ya ana haifarsu ne ba tare da ilimin komai ba. Tunda anyi zuciya da kaunar mai kyautata mata, fuskar da mutum ya nufeta da ita, itama za ta je da kwatankwacinta. Yaro baya sanin wace uwa a gareshi a farkon rayuwa. Shi dai kawai wannan mai kawar masa da yunwa da kula da damuwarsa ita ce mutum a wurinsa. Wannan dalilin yasa wadanda maraici ke riskarsu tun a zanin goyo suke tashi da kaunar marikansu indai an yi musu rikon amana." Daga nan Alh. Rabi' u ya soma shan jinin jikinsa. Asabe kuma ta soma hawaye. "Yaran nan sun hadu a lokacin kuruciya. A shekarun da ko iyaye suna kokarinsu sai sun kara sun dage sannan an hada da addu'a. Dalili kuwa shine wannan shekara shabiyu zuwa sama mataki ne na farkon balaga. Lokaci ne da yara suke fara sanin kawunansu. Munzali yana da zuciyar tausayi da jinkai. Amma ya tashi da kishirwa da yunwar kulawa. Wannan shi ma a tsarin halitta zaka ga wani yafi wani cikin yara son kulawa. Wasu yaran tun kuruciya suna son a dinga basu damar yin komai su kadai. Wani kuwa burinsa na gaba ya sanya shi a hanya kullum. Yana son ayi ta ririta shi. In kun duba Munzali da ya san ya taimakawa wani tun kuruciya tabbas shi mutum ne mai raunin zuciya. Duk wanda zai ja shi a jiki shi ne mutum mafi girman kima a idonsa. Ya zo ya hadu da Abbati. Wanda shi kuma bai kasance daga cikin butulun mutane masu manta alkhairi ba. A zamanin nan duk wanda ya kawar maka da yunwa babu ya shi. Kyautatawa junansu a lokacin da ido da sawun iyaye baya garesu shi ya janyo musu shakuwa. Babu ce ta hadasu ba arziki ba balle ace wani yana kwadayin abin hannun dan uwansa. Kune ku ka kora danku zuwa ga mai kaunarsa da zuciya daya. Misalin haka kan faru tsakanin iyaye mata da masu raino. Idan mace ta sakarwa mai raino ragamar komai na danta, watarana sai ta mika hannu ya noke kafada. In ta dauke shi ta karfi ya yi mata ihun da jama'a zasu iya yi mata kallon mai satar yara." "Tabbas malam kayi gaskiya" Asabe ta furta tana kuka "sakacinmu ya janyo Munzali ya hada Abbati da miyagun mutane. Dole yake kukan cewa ya yi sanadin bata rayuwar Abbati." "Don Allah ku daina zancen wani ya bata wani cikinmu. Kaddara ce irin wadda bawa bai isa ya kauce mata ba" Munzali ya kalli Abbati ya yi murmushi. Dama ya san haka zai ce. "Ni dai duk da haka ka yafe min" "Nima ka yafe min" Asabe ta ce "Allah Ya yafe mana baki daya" ta dubi Alh. Rabi'u "Alhaji ka dai ji abin da Malam ya fada. Duka abin da ya ce babu wanda bamu aikata ba. Mu karbi laifinmu kawai mu tuba shi ne maslaha. Wani borin kunya ba namu bane" "Ke, bana son rashin kunya. Kin sa danki da bare sun kawo ni nan domin a ci min mutumci ne dama?" Ya tashi tsaye yana karkade riga yadda ya saba idan ransa ya baci "tunda bani da amfani a gareku da 'ya'yanku yau dinnan ba gobe ba zan sauwake muku. Kuma ku zuba ido ku gani idan ban auro yara sa'annin jikokina ba. Wadanda zasu karbi irin kulawar da nake baku hannu bibbiyu suna son barka" Maza irin Alh. Rabi'u masu kafiya, taurin kai, yiwa addini raguwar fahimta da karan tsaye suna daga cikin babbar matsalar arewacin kasarmu. Suna yin ba daidai ba. Sun sani sarai, kuma in an gyara musu sun san kurakuransu. Amma saboda bahagon tunani basa yarda su karbi gyaran. Kuma a haka wani mai zuciya irin tasu zai basu 'ya su aura. Ukubar da za ta fuskanta da sunan aure ba matsalar mijin da uba bace. "Ba ayi haka ba Alhaji. In zaman nan bai kawo gyara ba ina ganin bai kamata ya kara lalata lamura ba." Dr. Abdallah ya ce dashi. A ransa yana mai cigaba da nazarin hanyoyin karkato tunanin dattijon. "Na gama zama. Ki sameni a gida idan kun gama" Abbati ne ya hana shi fita "Alhaji ka zauna ka yi mana shaida akan kudirinmu na gaba. Malam mece ce makomar dukiyarmu a yanzu da muka tuba?" "A shari'ance dukiya kala biyu ce. Halattacciya da haramtacciya. Tunda kokontonku yana ga son sanin ko dukiyarku ta haram ce to akan ta biyun zamu yi magana. Ita dukiyar haram an kasata biyu. Akwai ta haramci a dalilin abin mallakar mai cutarwa ne kamar giya, naman alade ko mushe. Da kuma wadda ta haramta a dalilin hanyar samuwarta da izini ko babu izinin mai ita. Misali dukiyar da aka sata ko ta bokanci, kwangilar kisan kai, caca, sayar da kayan maye, karuwanci da ribaa. Kun ga irin taku dukiyar ta fado cikin aji daya da karuwanci. To game da wannan nau'in dukiyar wadda ake samu da izinin mai ita amma sanadin samuwarta haram ne, dukkanin malaman mazhabobinmu wato Imam Hannafi, Imam Hanbali, Imam Malik da Imam Shafi'i sun tafi akan cewa wajibi ne a rabu da ita. Ko dai a mayar da ita ga mai ita ko ayi sadakarta ga mabukata idan babu halin mayarwa. Ibnul Qayyim Aljauzi ma yana cewa a bayar din shi ya fi. Domin a lokacin samunta wanda ya bayar ya amfana da abin da ya biya kudinsa ne duk da cewa abin haram ne. A wani kaulin, Imam Al-Ghazali ma ya ce sadaka, zakka ko Hajji basu wajaba akan wanda duka dukiyarsa ta kasance haramtacciya ba. Duka maluman nan sun yi duba ne ga ayoyin Alqur'ani da Hadisan Annabi SAW wurin fitar da fatawar. Misali, akwai wani hadisi wanda Imam Bukhari, Muslim, Ibn Majah, Nasa'i, Abu Dawud da Tirmizi duka suka rawaito [an karbo daga Abi Mas'ud Uqbah bin Amr RA cewa Manzon Allah SAW ya haramta kudin cinikin kare, kudin karuwanci da kudin bokanci.] (Ownership of Unlawful Wealth from Islamic Legal Perspective. Badruddin HjIbrahim da Azizah Mohd, 2017) Hakika ba zan gushe ba wurin yaba muku matuka. Ina kuma yi muku albishir da cewa dukkan wanda ya bar wani abu da yake so domin Allah, to ladan wannan aikin yana ga Allah (Annawawi hadisi na daya). Zaku kwashi rabonku na alkhairi a duniya ko lahira. Ku sani dai cewa wallahi baku yi asara ba." Kallon juna suka yi suka gyada kai a tare. In sha Allahu ba za su bari son duniya ya rufe musu ido daga barin mummunan alkaba'in da suka jima suna aikatawa ba. "Akaramakallah akwai wani batu guda daya da ya rage. Ka san wannan abin yana tattare da matsaloli da dama da suka shafi lafiya. Musamman ga wanda ya tasarma barinta. A haka dai bamu da wani ciwo cikin ciwukan da ake dauka ta wannan hanyar. To amma mu dan yi bincike ana samun abin da ya shafi kwakwalwa. Hanyoyin da ya kamata mu bi a likitance domin kauracewa sha'awar da ta kan taso mana saboda sabo. Rashin kulawa zai iya janyo mana rubewa ko fitar tsutsa..." kasa karasawa ya yi saboda takaicin halin da suke ciki. Abbati ne ya cigaba da bayanin "mun biya miliyoyin kudi ga wani asibiti a Italy wanda suka kware wurin dakilar da sha'awar sake fadawa zunubin. Sannan duk wata lalura da ta shafi lafiya wadda da wuya mu tsallakewa samunta a nan gaba kadan zasu magance ta. Tambayarmu a nan shi ne zamu iya zuwa? Idan bamu je ba Allah kadai Ya san halin da zamu iya tsintar kawunanmu. Sannan bamu da halin sake samun kudin da zamu biya. Duk abin da muka mallaka yanzu hatta waya zamu rabu da ita saboda duka da kudin muka samu" Iska Dr. Abdallah ya fesar daga bakinsa. Wannan tambaya akwai rudani a cikinta. Ya dubi matasan ya auna duka maganganun da suka yi. Ya tambayi nawa suka biya yaji kudin ba na kusa bane. Bayan nazari ya fada musu abin da yake ganin shi ne mafita. "Ku je ku nemi lafiyar ku. Domin sai da ita ne kadai zaku iya barin wannan abu har abada. Idan nace ku zauna ban yi muku adalci ba. Bani da halin sama muku irin wannan kudi. Iyakar shawarar da zan baku shi ne ku kiyaye. Kada ku dauki kari akan abin da ku kw san lallai zai isheku iya zamanku a can." (Wannan ba fatawa bace. Fahimtata ce ba fadin malami ba) Ragowar bayanin da aka yi shi ne ya dan taba zuciyar Alh. Rabi'u. Ya auna da kwakwalwarsa ba son zuciya ba ya tabbatar duk a kokarin samun lahira Munzali yake wannan abu. Shi kuwa wane irin shaidan ne a kansa da zai sa ya cigaba da riko da mummunar akidar da har mahaifiyarsa ta rasu bata taba goyon bayansa a kai ba? *** Bayan Wata Hudu Sannu sannu bata hana zuwa, sai dai a dade ba a je ba. Abubuwa da yawa sun faru a cikin watannin nan ga jaruman labarinmu. Mami Khadija ta koma hadadden gidan da Alh. Tahir ya mallaka mata ita da 'ya'yanta. Ta cigaba da aikinta cikin kwanciyar hankali. Iyayenta da Yakumbo sun yi fushi har sun sauko. Mardiyya bata yarda an barta ita kadai ba. Kamar yadda suma yaran basu kwashe duka kayansu daga wancan gidan ba. Musamman Sauda da Mardiyya da basa rabuwa. Kullum in basa wannan gidan suna wancan. Jiddo ta dade da tafiya. Gida ta kama mai kyau ta cigaba da shashancinta bisa zugar kawaye. Gidan ya zama dandalin fitinannun mata. Ba a dade ba kuwa suka cinye fiye da rabin kudin da Alh. Tahir ya bata. Tunda bata iya juyasu ba sai bushasha. A halin yanzu ta gamu da ciwon gonoriya. Kuraje manya manya masu dan karen kaikayi da kazamin ruwa sun firfito mata. Ga kudin asibiti ya soma gagararta. Alh. Tahir ya auri Yumna domin biyayya ga umarnin Yakumbo. Da kuma rufin asirinsa akan abin da Mami Khadija ta fadawa 'ya'yanta. Ya daina bin mata kamar anyi ruwa an dauke. Rayuwarsa babu wani farinciki a ciki saboda rashin Mami da zubar girmansa a idon manyan 'ya'yansa. Mama Nasima ta rage rashin zaman gida saboda tsoron kada ita ma ayi waje da ita. Yumna kuwa babu wannan fadar da take tsammanin samu. Ga kudi ga komai amma mijin bashi da lokacin biye mwa shirmenta. Lilu ya mayar da hankali akan karatu. Suhaib kafa ta warke ya koma bakin aikinsa. Ayaah tana nan a ransa. Suna yawan gaisawa a waya wadda bata wuce ya gida, jikin Abbas da jarabawarta (a tsarinsa sai ta gama jarabawa zai nemi soyayyarta wadda ya gama nutsewa a ciki). Farha ce ta koma abar tausayi a wurin Mami. A zahiri ta cigaba da gudanar da rayuwarta kamar da. A badini kuwa kewar Abbati tana neman wargaza tuninta. Kara son shi tayi bayan Mami ta fayyace musu komai kamar yadda Alh. Tahir ya fada mata. Ta dai sakaya yanayin haduwarsu da babansu. Sai ta ce wurin abokinsa yaje yaga Abbatin. Wayar duniya ta buga bata samunsa. Tunda tayi na sati ta hakura ta fawwalawa Allah. A Kano gidan Innayo sai san barka. Kansu ya hadu 'ya'yan suna ta zumuncinsu. Asabe da Innayo ma kamar 'yan uwa. Maigidan ne dai sai a hankali. Yau fari gobe tsumma. Wata dabi'ar barinta yana da wuya. Tuni Zara ta koma gidanta bayan Hajiyan Fatakwal ta zo da kanta sun sasanta da Innayo. Aka yiwa Ummulkhairi taron sunan da ya shiga bakin 'yan unguwa. Da wuya a hadu ayi hira mai tsayi ba ayi zancensa ba. Uwani ma da kanta ta koma. Salihi dawowa ya yi gida kawai ya sameta a falo da Mubasshir suna hira. Yayi murna kwarai da irin canjin da aka samu a tattare da ita. Ya hadasu da Ummule ya musu nasihar zaman lafiyar da kowane magidanci yake yi. Har yanzu dai babu wani abu mara dadi da ya faru gashi har Ummule ta haihu. Uwani ce ta karbi haihuwar tayi komai babu ha'inci a gida. Saura wata daya suspension dinta ya kare. Sannan ba tare da sanin kowa ba sai mijinta ta dauki Zakiyya da Qibdiyya sun je asibiti. Duk wani abu da ya dace ayi Salihi ne ya dauki nauyin biyan kudin. Ita da 'yan uwanta duk sun karbi zancen da yabi bakin kowa na cewa karayar arziki ce ta sami su Munzali. Asabe ta gina zancen akan wanda Mami Khadija tace mata taji a wurin Alh. Tahir lokacin da ta kira tayi musu jaje. Salima dai aure ya mutu murus. Ale Gambo ya yi rantsuwar idan bata koma ba cikin kayadadden lokacin da ya bata tana da damar sake aure domin babu shi babu ita. Innayo ta lamunce mata tayi abin da zuciyarta take so. Cikin farinciki don har ta murmure ta ce ta gama zama dashi. Kwanaki kadan da suka wuce ta gama iddarta. Abbas ya warke ya koma gida. Sauki ya samu don ya fara magana kuma yana tafiya da kansa. Tsakanin su Honourable da Abdulkarim sai tarin godiya. Shi da Ummita soyayya suke yi mai ban sha'awa. Biki saura sati biyu. Ayaah ma ta gama NECO sauran WAEC wadda jarabawa biyu suka rage su kammala baki daya. Anti Hasiya ciki ya fito. Laulayi ya yi sauki sosai. Tana samun riritawa daga mijinta, mahaifiya, 'yan uwa da 'ya'ya. Haihuwa kawai ake jira. Karshen abin farinciki shine kulle Danliti da Shazali da Alh. Sadisu yasa aka yi. Duka malamai da masu gadin makarantar da sukw da hannu su ma an rufe su. Shi Shazali ma a kurkukun bai tsira ba domin kusan kullum sai an yi masa duka. Tunda Baaba Mari take bata taba samun kwanciyar hankali dari bisa dari ba sai yanzu. Alkawarin Allah Ya cika. Bayan kowanne tsanani akwai sauki tafe. Damuwarta ta shekara da shekaru ta kau. Sauran 'ya'yanta dama basu da matsala irin wadda ta jima tana damunta akan Abbati. Yanzu da komai ya daidaita ta sami nutsuwa. Mal. Sa'idu ya soke karatun Allah. Sauran 'ya'ya da jikoki duk yasa an dawo dasu gaban iyayensu. Ya kuma aurar da 'Yashshafa ga wani tsohon saurayinta. Deluwa kamar ta hadiyi zuciya. Tana ta mitar yaya zasu yi ida Sha'aib ya zo. Hanne ma ta gama idda har manema sun fara kawo caffa. Ta cigaba da rayuwarta sannan ta rike sirrin Abbati. *** Wata biyu kenan Abbati da Munzali suna karbar treatment akan hanyoyin tsira daga komawa tsohuwar rayuwarsu. Kafin su taho duk wani abu da suka mallaka sun damka shi a hannun Dr. Abdallah Saraki. Zunzurutun kudi da kadarori. Sutura da takalma kadai ne basu bayar duka ba. Amma hatta zobe da agogo basu bari ba. Motocinsu sun sayar. Gidan ma a satin aka sami mai saya. Sauran abin da basu kammala ba suka bar masa amanar sayarwa. Cikin kankanin lokaci aka dinga gina rijiyoyin burtsatse a kauyukan da suke tsananin bukata. Aka biyawa marasa lafiya da yawa kudin asibiti. Kudi ya zaga inds ya kamata. Dr. Abdallah ya taimaka musu kwarai wurin sauke nauyin da yake wuyansu. Hankulansu kwance a inda suke. Wayoyin hannunsu ma shi ya saya musu kafin su tafi. Bayan tafiyarsu Alh. Sadisu ya neme su a waya shiru. Sai ya tuntubi Alh. Tahir. Shi ma bai san inda suke ba. A wurin Mami Khadija ya sami numbar Baaba Mari. Takanas ya tafi Kano inda suka hadu shi da Alh. Sadisu suka kirata. Ta hadasu da Mal. Inuwa shi kuma ya faygace musu halin da ake ciki. "Alhaji da zuciya daya nake kaunar yaran nan. Idan suka dawo kana ganin zasu yarda in saka su cikin siyasa? Ba wai 'yan banga ko makamancin haka ba. Ina so in daga su a idon duniya. Su fara da zama PA dina ko Secretary. Ta yadda duk inda nasa kafa muna tare. A hankali har a sansu wata rana idan muna raye in daga hannuwansu a zaben manyan mukamai" Alh. Sadisu ya ce da Alh. Tahir bayan sun koma gidan Alh. Sadisun. "Nima nayi tunanin janyo su aikin kwangilata. Amma ina gudun kada su ki amincewa saboda yarana da suka nema a baya. Sannan bani da wani mutumci a tunani a idanunsu. Dama auren zai yiwu da naji dadi. Musamman na Farha." Shi ma Alh. Tahir ya fadi nasa kudirin. Jari zai basu mai tsoka da zai ishesu tsayuwa akan kafafunsu. Amma kuma Alh. Sadisu zai bawa "ina gudun kada su ki karba. Ko kuma su ga kamar nayi ne da wata manufa" "Hakika haduwarka da yaran nan izina ce garemu baki daya Alh. Tahir. Duba ka gani yadda rayuwarka ta canja. Ina fada ba don izgilanci ba. Yadda ka rabu da harkar mata haka idanuna suka bude na rabu da duk wani abu na haramci a siyasata. Don gani nake kamar hakki ne ya kama Abdul. Kuma naga fa'ida domin na kara samun masoya. Kwarjinin da nake fata na kara yinsa ba tare da na bawa kowa tsoro saboda cin zali ba." *** Garin Parioli wanda yake cikin babban birnin Italy wato Rome shi ne inda ake da babban masallacin kasar. Saboda girmansa zai iya daukar masallata dubu goma sha biyu a lokaci guda. A daya daga cikin wuraren alwalar maza Abbati da Munzali ne suke alwala. Sun cika burinsu na ziyartarsa kafin su bar kasar. Abbati sanye yake da shudin wando da shudiyar shet wadda ya dorawa jacket sea green. Munzali kuwa bakin wando ne da polo shet ruwan madara a jikinsa. Su biyun sun yi kumari sosai. Ashe duk yadda jikinsu yake wannan abu yana tsotsesu basu sani ba. Sai yanzu suka kara zama cikakkun maza masu cikar kamala. Kowanne ya ajiye gashi a fuska wanda ya kara musu haiba. Alwala suke Munzali yana ta rawar dari. Abbati da ya gama ya koma gefe yana yi masa dariya. "Nace maka ka k'ara riga akan ta jikinka amma ka dage wai da alamun rana a waje. Yanzu kuma ka zo ka sani a gaba kana makyarkyata kamar wanda ya kulla abota da DJ" Munzali ya ciko hannu da ruwa zai watsa masa ya kauce yana kara yi masa dariya. A hasale Munzali ya ce, "Ka dai ji kunya. Wai a matsayin wa na kake amma ka kasa sadaukar min da rigar sanyi. Sai surutu kake min kamar ..." Kunnensu Abbati ya kamo yana cewa "ban hanaka rashin kunya ba?" Munzali ya karkace kai saboda zafi yana magiya "me yasa baka san wasa bane. Don Allah ka saki kada kayi min kunne daya" Zungure masa kai Abbati ya yi sannan ya cire rigar ya mika masa. "Minti talatin zata yi a jikinka ka bani" Da farinciki Munzali ya karba ya saka suka shiga masallacin domin yin sallar azahar. Da suka idar hotuna suka dinga dauka domin tarihi. Ba su suka tafi ba sai da suka yi sallar la'asar. Lokacin jacket din ta koma jikin Abbati. Kowa minti talatin din yake ya bawa dan uwansa. Suna ta atishawa. Abbati ya yi ta mita. Munzali yana tunzura shi da cewa don kada ya barshi da jinya ne ma fa yake karbar aron rigar sanyin. Da zasu tafi addu'a kowannensu ya yi. Kusan abu daya suke roko. Cigaba da samun rufin asiri akan abin da ya gabata na rayuwarsu. Samun sana'ar yi sai kuma kowa ya yiwa dan uwansa fatan samun abokiyar zama tagari ba tare da sanin dayan ba. Ranar da zasu tafi a airport dukkaninsu dokin ganin Qibdiyya suke yi. Sabo da rigima kamar yara harda fadan waye zai fara daukarta. "Bayan ma yau baka kira mana ita ba" Abbati ya harari Munzali. Zama suka yi akan kujerunsu daga jikin juna a jirgi sannan Munzali ya ce "na fada maka kashe min murya Zakiyya take yi. Sai ta kusa cinye kudin da surutu. Kai kuma ka wani dage ba za ka dinga kiranta ba sai kace surukarka" "Ka sani ko ayi kome?" Seatbelt din da yake kokarin sakawa ya saki ba shiri ya kalli Abbati. "Kome a ina? Ni nace maka ina son aure ne ko kuwa ina son Zakiyya?" Abbati ya ce "ko daya. Aure dolenmu ne Munzali. Indai ba so kake iyaye su sake fara zargin ko mun koma ruwa ne. Ba don na san mun rabu kenan dasu Diamond girl dinka ba ai da ita zan ce ka aura. To amma kaga babu wadda ya dace ka zauna da ita kamar Zakiyya. Ita ce ta haifi Qibdiyya. Ita ta san me ya faru da ita. Ita ce kuma zata san hanyar hana maimaici." "Shawara ce kake bani?" "Eh" "Kana ganin akwai alkhairi idan aka daina rabawa Qibdiyya hankali?" "Tana bukatar tsayayyen gida da uwa da uba." "To kai yaushe za ka yi auren?" "Wa yake ta tawa? Da Hanne tana nan da yanzu bakina alaikum. Yanzu kuwa dole in nema can nesa da gida." Zancen Farha ya so yi masa amma ya fasa saboda baya son yi masa fami. "To Allah Ya kawo tagari. Amma ka daina zancen Hanne baiwar Allah. Ni na san ko kadan baka sonta. Shi yasa kana samun dama ka sallameta" cewar Munzali yana dariya. Shi ma Abbatin dariya ya yi yace "Cutar juna muke kawai. Tana jin haushina ina jin nata." Jirgin na shirin tashi suka kira Dr. Abdallah, Alh. Sadisu wanda yanzu yake yawan kiransu sannan kowa ya kira iyayensa. Munzali kadaran kadahan suka gaisa da babansa. A hakan ma sun sami cigaba ne a alakarsu saboda jajircewar Munzalin. *** Tafiyar awa biyar da minti hudu ce ta kawosu Nnamdi Azikiwe International Airport Abuja. Suna fitowa daga ciki mota tazo ta daukesu kamar yadda Alh. Sadisu ya ce musu ya bada umarni da suka yi waya. "Zai kai ku hotel. Gobe zan zo garin ganin party chairman. Sai mu juya jibi tare. Ina fatan hakan ba zai zama takura a gareku ba" Wannan shi ne abin da ya fada musu a wayar. Cike da girmamawa suka yi masa godiya. Da zasu fita daga motar bayan sun isa hotel din kudi direban ya basu a envelop. "Yallabai ya ce ku rike kafin ya iso" Suka sake yin godiya sannan kamar lokacin tasowarsu duk da dare ya yi sai da suka kira iyayensu. Cikin daren suka tattauna yadda zasu yi idan Alhaji Sadisu ya zo musu da wani abu da zai iya bata musu rayuwa. A yanzu sun hankalta suna matukar tsoron shigewa masu kudi. Babu dangin Iya babu na Baba. Watakila wani abin ake nema a garesu. Washegari sai bayan isha Alh. Sadisu ya iso. Tare suka je suka ci abinci. Dakinsa a hotel din yace su biyo shi. Gabansu ya fadi amma suka daure. Yana zaune a kan kujera suna kasa a gefensa ya yi musu magana. "Na san cewa zukatanku suna cike da tambayoyi da fargabar manufar janyoku da nayi a jiki. Dom Allah ku kwantar da hankalinku. Ko babu komai ceton rayuwar Abdul da ku ka yi ya isheni dalilin son saka musu da abin alkhairi. A dalilinku ya sami sauki har ina shirye shiryen tura shi kasa mai tsarki da biyu cikin iyayensa mata. Sai ya yi a kalla shekara guda yana karatun addini zai dawo gabana ya karasa sakandire. " Murna suka taya shi yaji dadi kuwa "Magana ta gaskiya labarinku ya tsaya min a zuciya. Ban taba ganin almara irin wannan ba. Giyar kudi bala'i ce. Musamman ga matasa irinku wadanda kuruciya take diba. Yaran yanzu zasu yi komai domin kudi. Sai gaku na hadu daku zahiri ba labari ba. Kun bude min ido da kusanto da tunanin lahira a dukkan lamurana. A takaice rayuwata duka na canjata kuma duka kune sila. Wannan yasa na daukarwa kaina alkawarin ba zan bari ku tagayyara ba. Rashin abin yi da rashin kudi a hannun wanda ya saba rikewa ba karamar jarabawa bace. Tsananin rabo da tsoron Allah ne kadai zai dakushe zukatanku daga tunanin hanyoyin samun kudi ko ta wace siga. Saboda haka idan kuna da ra'ayi ni Alh. Sadisu Nakano nayi muku alkawarin muddin ina raye da rai da lafiya, zan yi iya yina domin ganin kun zama wasu ababen misali da alkhairi a cikin al'ummarmu. Ina burin duniya ta amfana da alkhairin da nake da yakinin Allah Ya wanzar muku sakamakon mika wuya gareShi. Me ku ka ce?" Basu ce komai ba sai kwalla. Ikon Allah akwai ban tsoro. Duka duka awanni nawa da suka wuce ne suka zauna suna tunanin yadda zasu yi da rayuwarsu yanzu? Sai gashi mafita tazo daga inda basu tsammani. Alh. Sadisu ya yi murmushi "in dauki shirunku a matsayin amincewa?" "Alhaji ko za ka bamu zuwa gobe domin mu shawarci iyayenmu" "Ka cika babba Abbati. Dama gaggawa daga shaidan take. Ku yi shawara da duk wanda ya dace. Fatana Allah Yasa ku bani damar zame muku uwa da ubs a siyasance. Da yardar Allah ni daku babu mai yin nadama." Dr. Abdallah suka fara kira. Ya ce idan sun shigo Kano gobe su zo su same shi a gida. Da makomar tattaunawarsu da shi zasu yiwa iyayensu bayani. Daga nan su nemi amincewarsu. Direban da ya daukosu daga airport shi ne ya kuma zuwa daukarsu. Alh. Sadisu ya sanar dasu cewa zasu tsaya a Kaduna zai ga abokinsa kafin su wuce. Haka suka jera suna biye dashi a baya. *** Suhaib, Farha, Lilu, Sauda da Mardiyya ne suka fito daga wani babban shopping mall wanda yake makwabtaka da ofishin Alh. Tahir. Mami Khadija ya kuma roka akan burinsa na daidaitawa da yaran. Tayi musu magana harma da fada akan lallai su cire abin da yake ransu su kyautatawa mahaifinsu. "Shi kadai gareku. Ba zai yiwu don ya auri Yumna kowa ya dauki gaba dashi ba. Duk alkhairinsa gareku bai kyautu ku manta ba saboda wani abu guda daya da bai sabawa shari'a ba" Fadan a gaban kannensu ne. Su manyan sun san me take nufi. Hakuri suka bata tace to tana so bishi office su nuna masa komai ya wuce. Da yake kullum cikin kokarin janyosu jiki yake suna yakicewa sai kowa yaji babu dadi. Shi ne Suhaib ya ce su fara zuwa kowa ya sayi gift guda daya su bashi. Sauda da Mardiyya sai tsalle da murna. Ji suke kamar sun dade basu ga Abbansu ba. Kowa ya yi kewarsa. Harda Suhaib kuwa. Abbati da Munzali a hadadden reception din office din suka zauna suna hira. Alh. Sadisu ya shiga wurin Alh. Tahir ba tare da sun san wurinwa ya zo ba. Yana ciki suna tattauna makomar rayuwar yaran. Niyarsu sai sun gama magana sannan Alh. Sadisu zai kirasu ciki domin su sami fahimta da Alh. Tahir. Yana so su dauke shi a matsayin makusancinsu. Waya suke yi da Qibdiyya ta cikasu da surutu mai bude kofar ya hangameta. Basu dago sun kalli su waye suka shigo ba koda suka ji ma'aikatan dake wucewa suna ta yi musu maraba. "Oga yana tare da bako." Wani masinja ya fada musu. "Bari mu jira shi a nan" Suhaib ya nuna kujerun reception din. Kafin su karasa duka su biyar din sun ga su waye a zaune. Farha ji tayi kamar zazzabi zai kama ta. Kujerar farko ta gabanta ta dafa yayinda Suhaib da Lilu suka karasa gabansu. Earpiece ne a kunnen Abbati yana kallon video din Qibdiyya na zuwa sabuwar makaranta wanda tasa mamanta tura musu a lokacin. Munzali ne ya daga kai da yaji alamun ana tahowa gabansu. Mamakin dake fuskarsu Suhaib shi ne a tasa. Da hannu ya zunguri gefen hannun Abbati. Yana daga kai idanunsa a bangaren hagu suka sauka. Duniyar sai ta tsaya cak. Numfashinsa ya dinga fita da sauri da sauri da yayi tozali da Farha. Jikinsa nauyi ya yi masa saboda bai san me zai ce mata ba. Akwai tarin tambayoyi da ma bayani da zata bukata wanda bashi dasu. Kwanciyar hankalinsa daya shi ne sanin cewa Alh. Tahir ya rufa musu asiri. Yana can duniyar tunani da kallonta har Munzali suka gama gaisawa dasu Suhaib. Ya rike hannun Lilu yana cewa "ka gafarceni. Kunya ta hanani nemanka." "Komai ya wuce. Naga message dinka tun lokacin" Lilu ya bashi amsa da fara'a. Sauda ta turo Mardiyya gaba don su gaisa tana ta nokewa. "Diamond girl da Hasanarta kuna lafiya? Ya kwana biyu?" Sama sama suka amsa, hankulansu sun karkata ga Abbati da ya yi mutuwar zaune ga Farha tana takowa wurinsu a hankali. Har ta iso Abbati bai dauke idonsa daga gareta ba. Tana zuwa gefen Munzali taje ta tsaya tayi masa sallama. "Don Allah ko za ka iya bani wuri in zauna kusa da dan uwanka?" Ta nuna inda yake zaune kusa da Abbati. Idanu ya dan ware ya ce "na'am?" Idanun Abbati basu bar kanta ba duk da taki juyowa. "Hoto nake so a daukemu" ta furta a dake. Hannunta ne ma ya soma rawa wurin kokarin bude jaka domin ta dauko wayarta. Idan ta kama dan karfen budewar sai ta kasa juya shi yadda ya dace. Saboda dauriyarta ta kusa karewa. "Bashi wannan" Abbati ya mika mata wayarsa ko earpiece din jiki bai cire ba. Ta mika hannu ta karba kanta a kasa bata yarda sun sake hada ido ba. Lilu ta mikawa don hannunsa tuni ya yo gaba. Ta koma ta zauna a inda Munzali ya tashi. "Ya Farha" Ko da wasa bata yi yunkurin amsa kiran da ya yi mata iya jin kunnuwanta ba don ta san muryar ta bace. Daga kai tayi kawai aka yi dace shi ma ita din yake kallo. A haka Lilu ya daukesu hoton suna yiwa juna kallo mai cike da sakonni kala kala. Ana dauka ta mika hannu ta karbo masa wayarsa. 'Yan uwanta da Munzali suna ta kallon ikon Allah. Numbarta ta soma sakawa sai gani tayi sunanta ya fito baro-baro a jikin screen din. (Ya Farhata) Kwalla mai zafi ya sauko mata kowa yana gani tasa hannu ta dauketa. Cikin whtsapp dinsa ta shiga ta bude sunanta ta tura hoton da suka dauka sannan ta mika masa. Yana karba ta haye sama. Su Mardiyya suka bi bayanta da sauri. Office din Alh. Tahir taje. Ta bude da sallama ta fada kai tsaye. Yana ganinta ya tashi ta iso ta rungume shi sai kuka. Lilu ya rike baki a hankali ya ce "see love" "Me ya sameta?" Alh Tahir ya tambayi su Suhaib hankalinsa a tashe. Amsar ya gani da idonsa da isowar su Abbati kofar office din. Alh. Sadisu ya saki murmushi "Munzali me ku ka yi mata?" "Babu ruwana fa. Aikin Abbati ne." Abbati yaji kamar yana kan k'aya a inda yake. Ta daina kukan amma ko fuskarta baya hangowa. Alh. Tahir dadi kamar ya yi yaya. Farincikin da ya rasa na watanni ya samu da ganin yaransa. Gashi alamu sun nuna Farha da Abbati suna son juna har lokacin. Alfarma ya roki Alh. Sadisu akan su je gidansa kafin su wuce. "Abba da alama mun kusa shan biki a gida" Sauda ta ce tana tafa hannuwa. Aka yi dariya sannan kowa cikinsu ya mikawa Alh. Tahir kyautar da ya kawo masa. Bawan Allah sai yaji yana neman yin kuka. Sauda da Mardiyya ya rungume don kada a gane suka fita tare. Idan Abbati da Munzali sun yi mamakin sabon gidan da suka gani na Alh. Tahir sam basu nuna ba. Mami Khadija tasa mai aikinta ta kawo musu lemo da ruwa sannan ta fito. Ita kanta taji dadin sake ganinsu Abbati. "Shikenan sai kuka bace Munzali?" "Dawowarsu kenan kasar tun bayan faruwar wannan abin" Alh. Tahir ya bata amsa. Bayan tambayoyin yaushe gamo, Sauda da Mardiyya kadai aka sallama daga falon sannan Alh. Tahir ya sake nanata abin da ya fada a gabansu. "Alh. Sadisu ne ya basu shawarar barin kasar har kura ta lafa. Dukiyar da aka basu kuma sun tattara komai sun mayar ga masu ita. Shi ne suka gujemu a tunaninsu zumunci zai kare tunda yanzu basu da komai." Wannan abu ya kara tausayinsu ga su Mami Khadija. "Bawa bai taba yi domin Allah Ya tabe ba. Ba kowa zai iya abin da kuka yi ba Abbati. Mara tsoron Allah ne kadai zai gujeku" Dama tunda Alh. Tahir ya kirata a waya ya fada mata zai kawo nan shi ne tasa aka kara abinci. Falon cikin gidan tasa Lilu ya shigo dasu Munzali domin su ci abinci. Alh. Tahir kuma ya ce zai tafi da Alh. Sadisu don gujewa kananun magana kamar yadda Mami ta ce. Harda direbobin zasu tafi. Idan suka gama zasu dawo su daukesu su wuce. Mai aiki ce tayi jigilar kai kayan abincin falo. A ciki kuma ba babba ba yaro an hadu ana bawa Mami Khadija labarin hoton Farha da Abbati. Ita da tayi hoton ma sai yanzu kunya ta rufeta. Dariyar da Mami Khadija tayi ne yasa "Mami sharri ne fa. In akwai su nuna miki." "Lallai ma Ya Farha. Bari naje na karbo wayarsa" inji Lilu uban gayya. Suhaib ya janyo hannunsa "dawo gadanga abinci zasu ci" Falon Mami Khadija ta tura mazan. Su Mardiyya ta saka su aikin hada fruitsalad sannan ta tsare Farha a daki. "Na jima rabona da ganinki cikin yanayi irin wannan na zallar farinciki Farha." Kai Farha ta sunkuyar. Mami ta cigaba da cewa "bana so ki zura jiki da yawa. Tun haduwar farko na lura Abbati yana da hankali. Na tabbata faruwar wannan lamari ne ya koresu. Kin ji ance basu da komai yanzu. Sai dai nayi imani tunda Alh. Sadisu yake bibiyarsu he has a plan for them. Abbanku ma ya ce akwai abin da ya shirya. Tambayata a nan Farha za ki iya zama da Abbati sabanin yanda kike zatonsa?" Idan tayi shiru tabbas za ta kwari kanta. Sannan bata kasance cikin masu zurfafawa da naci ba tare da neman zabin Allah ba. "Ina addu'a sosai Mami. Sai gashi na ganshi a wurin da ban taba zato ba. Indai kin yarda dashi in sha Allah zan iya zama dashi. Cikin farinciki Mami Khadija ta ce "Alhamdulillah. Abbanku ne ya ce na tambayeki kafin su dawo don yana so a yau a tsayar da magana guda." Da gudu Farha ta bar dakin saboda kunya. Dakinta ta shiga tayi sallah ta sake gyara fuska. Tana gaban mudubi taji kira ya shigo. Haka kawai jikinta ya bata Abbati ne. Da ta duba kuwa sai taga bakuwar namba. Sake kira aka yi still taki dauka. Sai ma haushi da taji cewa yana da nambarta amma bai taba kira ba. Fitowa tayi daga dakin suka kusa karo da Lilu. A ranta tace dama ya saba rawar jiki idan ya gansu. "Yauwa dama ke nake nema. Wai ya ce ki fito ku yi zance" Bakin Lilu ta rufe da sauri ta waiga hanyar kitchen. Ai kuwa masu aikinsu biyu suna wurin kuma sun ji. Ga Sauda da Mardiyya. Sai suka hau yi mata dariyar shakiyanci. 49 Bakin Lilu ta rufe da sauri ta waiga hanyar kitchen. Ai kuwa masu aikinsu biyu suna wurin kuma sun ji. Ga Sauda da Mardiyya. Sai suka hau yi mata dariyar shakiyanci. Falon ta nufa zuciyarta tana dukan uku uku. Tana yin sallama Abbati ya ajiye cokalin hannunsa ya bita da ido. Munzali ya hada ido da Suhaib sai kawai suka tashi. Ya zo bakin kofa ya juyo ya kalli plate dinsa wanda ya cinye abincin tun kafin shigowarta. "Abbati ban koshi ba fa. Na dawo na karasa?" Jinjina kai Abbati ya yi rai a bace. Munzali ya rasa lokacin yi masa haka sai a gaban Farha. Bai san lokacin da harare shi tare da gargadi ba. "Kada ka bari na tashi Munzali" "Za ki iya da wannan mafadacin? Ko dai za ki koma ciki ni na karasa cin abincina?" Munzali ya sake zolayarsa kafin ya fita da sauri da Abbati ya yunkura zai tashi. Kujerar farko idan an shigo Farha ta samu ta zauna. Abbati sai ya ajiye nasa plate din akan tray ya taso ya dawo ta kusa da ita. Yana kallon alamun takura a tare da ita. Ta hade yatsunta tana ta wasa dasu. "Ya Farha" Tsigar jikinta tashi tayi saboda yadda tayi kewar sunan a bakin wanda ya furta shi. "Uhm" "Ina neman alfarma. Farha-ta nake son magana da ita. Wadda ta sauke min alkawarin da nayi na daukar hoto da ita" "Me yasa kake nemanta bayan baka damu da ita ba?" Ta furta a raunane. Yana ji ya san ranta ya baci da shirunsa. Dole ya rarrasheta in yana son ta fahimce shi. "Bana bukatar fada miki matsayinki a wurina. Amma ina so ki sani cewa zuciyata bata taba samun hutu ba tun ranar da na fara ganinki" "Ta yaya zan yarda bayan kai kadai kake yadda kake so. Lokacin da ka ga dama kawai kake nemana" tayi maganar cikin zubar hawaye. "Ki yi hakuri. Nayi zaton hakan shi ne mafi alkhairi saboda halin da muka tsinci kanmu ni da Munzali" Sai ya kara bata tausayi. Ta dube shi da hawayen idanunta "kana ganin ya dace kai kadai ka yanke hukunci akan abin da ya dace ba tare da jin ta bakina ba?" Idanunta dake cike da kwalla ya fara kallo sannan duka fuskar da kuka ya fara kumburawa. Wani abu mai girma ya sake motsa zuciyarsa. Sonta da burin mallakarta a matsayin matar aure ya mamaye tunaninsa. A cikin nutsuwa ya ce mata, "Kiyi hakuri Ya Farha. Farha-ta. My Angel. Zan iya kiranki Angel ko?" Ya marairaice murya. Da wadannan kalaman ya tarwatsa tunaninta. Zuciyarta ta kara cika da tsaftatacciyar soyayyarsa. "A'a" ta bashi amsa kai tsaye. "Me yasa?" "Saboda ban sani ba ko nan da kwanaki kadan zan sake nemanka na rasa" Murmushi ya yi ya ce "na hakura. Zan jira ranar da za ki kirani da kwatankwacin wannan sunan. A lokacin na san kin shirya karbar Abbati." Dan muskutawa ya yi ya ce "Zamu iya magana a gaggauce kafin su Abba su dawo?" Da ka ta amsa. Abbati ya dauko mata zancen abin da ta sani. A kasan zuciyarsa yana bakincikin boye mata ainihin labarinsa. Sai ya tuna cewa ko babu tsoron rasa soyayyarta bai kamata ya dinga kwayewa kansa baya ba. Takaicinsa sai ya rage na sanya mahaifinta da duk masu son rufa musu asiri yin karya. "Rayuwata ta koma baya. Bana ajin irin mazan da suka dace su kiraki matarsu. Wannan ne dalilin da yasa ban kara nemanki ba" "Angel" ta ambata a can ciki don da kyar ma yaji. Cike da annashuwa kuwa ya kalleta. "Na'am" "Kada ka sake guduwa!" Daga haka ta tashi ta fita. Ba jimawa Munzali ya shigo. Sai kuma su Alh. Tahir suma suka dawo. Fitar da Munzali ya yi yasa Sauda ta kira masa Mardiyya. Sun sami wuri sun zauna ya yi amfani da rufin asirin da babanta ya musu ya fada mata duk abin da ya faru. Ba tare da jan zance ba ya ce, "Baki cancanci soma rayuwar sadaukarwa da kuruciyarki ba. Zan cigaba da kasancewa tare dake a matsayin dan uwa. Amma ina so ki cigaba da normal rayuwarki har muga ikon Allah" Kuka yaga tana son yi ya ce "kada mu yi haka dake. Ba datse alakarmu nayi gabadaya ba. Ina bukatar lokaci. Bayan abin da ya faru da Qibdiyya yanzu zamu daidaita da mamanta. Ki yafe min bacin lokacin da nayi miki" "Nagode Ya Munzali" Mardiyya ta kirkiro murmushi. Karancin shekaru basu sa ta kasa fahimtarsa ba. Su hudu suka zauna a falon. Alh. Tahir ya fara da tambayarsu game da 'ya'yansa. Kai tsaye Munzali ya ce ya janye. "Bayan duk abin da ya faru ina ganin ya dace na dawo da matata da muka rabu. Zan cigaba da daukar Mardiyya kamar kanwata. Allah Ya kawo musu miji nagari. "Kai fa Abbati?" Kai a kasa ya fada musu yana son auren Farha amma ba yanzu da bashi da komai ba. Ya kuma san cewa ta jira shi ba karamin son kai bane. Rasata kuma is not an option. Manyan dariya suka yi. Sun riga sun gane halin da yake ciki. Alh. Tahir ya ce idan ya je gida ya bawa mahaifinsa nambarsa don ya kira suyi magana. Sauran abubuwan da yake tsoro kuma Ya barwa Allah. Da suka tashi tafiya Mami ta sake fitowa. Su Suhaib ma har mota suka zo, Farha ce kadai bata fito ba. Kunyar da rashinsa yasa ta iya ajiyewa dazu ita ce ta dawo bayan samunsa. *** Ko akwai, ko babu, indai dangi suna da yawa kuma da hadin kai to kuwa da wuya idan uzurin juna ya tashi a ji kunya. Cikin 'yan watannin nan da aka sami wadatar farinciki da kyautata zumunci a gidan Alh. Rabi'u, 'yan uwan sun dauki juna da matukar mahimmanci. Abu ya zo akan gaba. Za ayi bikin Ummita da Murja. Kowa ya zage damtse. In baka yi bani wuri. Da talaka da mai kudi babu wanda bai kawo wani abu domin a saka a dakin amaren ba. Abdulkarim yaso sakar musu kudi sosai amma sam Honourable yaki yarda. Wanda aka yi ma ya isa. Kada su zama marasa tunani. Sannan dole su kiyaye mutumcin 'yarsu. Munzali ne ma ya dinga jin ba dadi. Zasu aurar da 'ya'ya amma duk abin da ya saya rabin kudin Abbati ne ya bashi cikin wanda Alh. Sabi'u ya basu. "Banza, akan haramtacciyar dukiyar kake ta kunkuni tun jiya ko? Idan kana so sai na kai ka inda aka sakaya Shazali ku gana" Kukan kura Munzali ya yi ya tashi zai cakumo shi sai ga Qibdiyya ta shigo. "Daddy me za ka yiwa Papa?" "Maballi ne ya shake shi zan gyara masa" Munzali ya ce da sauri. Abbati da Asabe dake zaune a falon nata suka kwashe da dariya. Tare suka fito daga gidan da Asabe da Innayo a bayan mota. Sai Qibdiyya akan cinyar Munzali. Abbati ya jasu zuwa wurin da ake taron kamu. Taro ya yi kyau sosai. Da aka bukaci uwar amare ta fito domin kai 'ya'yanta kan shimfidar da aka tanada domin kamu duka 'ya'yan Larai sai cewa suka yi Uwani taje. Ta tashi cikin farincikin da bata taba ji ba ta rungumosu a jikinta har wurin. Da ta dawo ta zauna Hasiya ta dan tabota ta ce, "Metiron kuka kika yi ne?" Uwani ta maka mata harara bayan ta karewa wajen kallo ta tabbatar babu wanda yaji. "Bani da lokacinki yanzu. Nan da wata biyu zaki ga Metiron Uwani a gabanki ra'ayil aini." Jikinsa Hasiya tuni ya yi sanyi. Tsokanar da ta fara ta hadiye ta tsurawa katon cikinta kallo. Can dai ta kasa daurewa ta riko hannun Uwani. "Don Allah da ciwo sosai yadda ake fada? Taba wuyana ki ji. Wallahi zazzabi ke neman kamani" Uwani ta tuntsire da dariya. DJ na cewa uwar amarya ta fito ta janyo hannun Hasiya filin rawa tana jujjuyata. Innayo ta kallosu su biyar, da su Ummakati da Fati duka suturar jikinsu iri daya, sun yi kyau. Karo na farko da wani zai gansu ya ce jininsu guda. Cikin aminci aka yi taro aka gama. Washegari daurin aure. Ranar ne kuma Suhaib da Lilu suka zo. A masallacin daurin auren suka hadu dasu Abbati. Munzali ya yi murna da suka karbi gayyatarsu. "Ba dole ba. Idan naki zuwa Ya Farha da Ya Suhaib zasu iya tsireni" Lilu ya ce yans dagewa Abbati da Suhaib gira. Munzali ya ce "ban gane ba. Abbati dai na san an gama da zuciyarsa. Suhaib ne dai sai ka bani haske" " 'Yarka ce Ayaah" Munzali sai murna. Suhaib ya ce to dai gaskiya kada su bata masa show. Su yi shiru a jira su daidaita. "Ashe a jaririn mataki kuke. To ga Romeo nan sai ka tambaye shi satar amsa" cewar Munzali da shakiyanci. "Allah Ya tsareni da zama Romeo. Shi da bai dorar da soyayya ba. Ka dai kirani ...." "Wa?" Suhaib, Lilu da Munzali suka tambaya. Abbati ya tashi ya barsu yana cewa duk basu da kunya sun raina shi. *** Da kaiwa baki abinci Munzali ya samu ya tura Ayaah wurin Suhaib. Tayi kwalliya mara hayaniya wadda ta fiddo da kyawunta. Tray din hannunta lemuka ne da ruwa a kai. Tana tafe wurin da Munzali yace mata ya bar mota tana yangar 'yan mata. Suhaib ne kadai a motar yana ta dariyar yadda take fama tura baki a dole kayan sun mata nauyi. " 'Yan mata na tayaki ne?" Bata kula dashi ba sai murya taji. Dama kuwa ta gama fushi don ya ce mata ba zai zo bikin ba. A saman boot ta ajiye ta murguda baki cike da shagwaba. "Bana so." "To tsayuwar me kike a nan?" "Saurayina nake jira" ta amsa tana waige waigen baya. Suhaib ya dauki lacasera mai sanyi ya bude ya sha kadan sannan ya ce "Har ya bani tausayi" "Wa?" "Saurayin naki mana. Zai kwashi tsiwa. Gashi ma ba sonsa kike ba?" Ayaah ta daure fuska. Fushi take dashi maimakon ya bata hakuri ya zauna tsokanarta. "Inji wa yace bana son sa?" "Inji wanda kike so" Kusan faduwa Ayaah tayi don dama inda take tsaye dan tudu ne mara fadi. Sannu Suhaib ya ce mata da ta gyara tsayuwa a gefensa. "Na zata kin fara sona ne fa kamar yadda na dade da sonki" Kunya da farinciki suka rufeta ta ce "Ni wallahi..." "Ke me?" "Me yasa kace ba za ka sami zuwa ba?" "You are not serious. Amsar abin da na fada miki kenan?" Rufe idanu tayi da tafukan hannunta ta ce "kunyarka nake ji" Girgiza kai ya yi don ba haka yake son ji ba "ya batun amincewa ko babu? Dazu Baba yake fada min ya dage bikinki sai yaron da ya zaba miki ya dawo daga cirani." Yana kallonta duk ta fara rikicewa "Kin tuna ni kuma kin ce kada ma nace ina sonki a baya ko?" "Lokacin ma fa wasa nake? Kace masa..." Dariya taga yana yi shi yasa ta kasa karasa magana. Yana kiranta ta dinga sauri ga takalminta mai tsini. **** A yau cikin hukuncin Allah aka daura auren Auwal (Abbati) da Farha, Munzali da Zakiyya da kuma Suhaib da Haajara (Ayaah). Bikin ya zo wata biyu daidai bayan Hasiya ta haifi santaleliyar 'yarta wadda aka radawa suna Aisha kamar yadda Innayo ta roka. Anyi biki na masu ilimi da aji. Alh. Sadisu ya tsaya tsayin daka a matsayin uban angwaye. Iyayensu basu da abin cewa sai godiya da addua. Kamar yadda ya yi alkawari ya basu aiki a jikinsa. A gefe guda sun soma kasuwanci kuma suna ganin alkhairi. Sun kara gaskata zancen da ake cewa Na Allah baya tabewa. Rabon kwado kuma baya hawa sama. Zakiyya dai auren a bazata yazo mata. Munzali wanda yake jin zai iya sadaukar da komai domin Qibdiyya ya je gidansu wata daya kafin bikin ya yi magana da Gwaggo Lami. Ya fada mata taja kunnen Zakiyya saboda ko kusa ba zai dauki sakaci da rayuwar 'yarsa da wasa ba. Daddy kuma wanda ya koma hostel saboda tsangwamar Gwaggo da kiyayyar da Zakiyya ke nuna masa ya ce a fada masa ko da wasa kada ya yi gigin zuwa inda yake da sunan ganin yayarsa. Bai kulleshi ba saboda kawai yana ganin shi ma mai laifi ne. A gefe guda ya auna yaga da wahala idan ya auro wata ba za ta gorantawa Qibdiyya wataran ta ce kanin babarta ya bata ta ba. Ya kuma san wannan abin ne yasa Abbati cewa ya dawo da Zakiyya. Kafin magariba amare duk sun shiga dakunansu. Gidan Abbati yana Farm center, na Munzali yana Lodge road. Dukkaninsu cikin gidajen hayan Alh. Sadisu wadanda suke apartments ya basu daidai su zauna. Ya nuna musu cewa lokaci kuma ya yi da zasu koyi rayuwa su kadai domin samun damar kulawa da iyalansu. Ayaah kuma Kaduna aka kaita. Gidanta babu nisa da na Mami Khadija. Shima na Alh. Tahir ne. Suhaib ya yi mata alkawarin cigaba da karatu kamar kannensa. SHEKARA KWANA Baaba Mari, Innayo, Asabe da Mami Khadija suna zaune a tsakar gidan Alh. Rabi'u. Yau ake yinin bikin Salima da wani abokin Alh. Unaisu. Baaba Mari tana dauke da Maama (Khadija) 'yar wajen Suhaib da Ayaah. Akan cinyar Innayo kuwa Auwal din Munzali da Zakiyya ne. Mami Khadija kuma ta goya sarkin rigima Sa'id din Abbati da Farha. Asabe kuma tana ta kai kawo wurin kaiwa baki abinci. UWA UWACE... Tammat Bihamdulillah