BANI DA HUJJA!! By Maimoon BISMILLAHIRRAHMANNIRRAHEEM Godiya ga Allah buwayi gagara misali da ya sake bani damar dawo muku da sabuwar littafina mai suna BANI DA HUJJA!! "Kamar yadda tafiyar TANGLED HEARTS (RUƊAƊƊUN ZUƘATA) ta kasance smooth and full of wonderful memories, ina fatan BANI DA HUJJA ma zai samu matsuguni a cikin zukatanmu gabaki" ɗaya daga ni har ku. "To ga dai BANI DA HUJJA nan. Allah Ubangiji ya sa yadda muka fara lafiya, mu ƙarƙare lafiya." #ARYAAN UMAR TURAKI #SALWA AMEENU TURAKI #FAMILY SAGA 1. "A hankali, cikin nutsuwa ya ke sauƙowa daga benen, but at the same time cikin kuzari da" "taku irin na cikakkun mazaje, that confident masculine stride of a man da ya san worth ɗinsa." "ƙarasowa falon yayi, ba tare da ya ko kalli sashen da suke tsaye cirko cirko ba yayi wucewar sa ya buɗe ƙofar palourn ya fice kamar bai gansu ba ko bai san da su a palourn ba, da idanu duk suka bisa kowa da irin abinda ya ke saƙawa a zuciyarsa gabaki ɗayansu ɓacin rai ya bayyana ƙarara akan fuskokinsu, har ya fito babban farfajiyar gidan da akayi parking motoci na alfarma guda 2 banda nasa da ke usual spot din da yake parking a gidan, direct motar tasa ya nufa mai matuƙar kyau da tsada ya buɗe motar ya shiga sannan ya maida murfin ya rufe tare da sauƙe gajeren ajiyar zuciya, whatever emotions he was carrying, he wasnt ready to share it with the world ya dannesa a cikin ƙirjinsa, har lokacin ba'a iya ganin furkarsa, bare asalin yanayin da fuskar ke ciki, saboda p-cap din da ke kansa, da kuma shade ɗin idanunsa, sannan ga nose mask ɗin da ya sa ya" toshe hancinsa da bakinsa. "A hankali ya soma driving har ya fice a gidan bayan mai gadi ya wangale masa gate ɗin, ya cilla motar titi, tafiyar da baifi ta minti ashirin ba, ta kawo sa ƙofar wani restaurant, wanda daga samansa aka rubuta Amaira Restaurant and co, sauka yayi tare da nufar ciki kai tsaye yana tafiya a nutse, ƙananun kaya ne a jikinsa as usual dan kafin ka gansa da manyan kaya zaka daɗe he’s" "always simple on ƙananun kaya, mostly ma white ko kuma black shirt," "cikin sauri wani ma'aikaci da ke sanye cikin uniform na ma'aikatan wajen ya ƙaraso wajensa, ya gaishesa tare da miƙa masa wata leda at the same time yana mamakin shigowarsa ciki da kansa yau kuma, dan on normal days yana isowa yake kira a kai masa har mota." "karɓa yayi bayan ya amsa gaisuwar ciki ciki, ba lallai wanda yayi gaisuwar ma yaji amsar ba ya" "juya ya fice a wajen ba tareda ya sake ce masa komai ba, shi dai ya bisa da kallo kawai." "Motar ya koma ya shiga ya tada ya bar wajen, sai da yayi tafiya aƙalla ta mintuna ashirin zuwa ashirin da biyar kafin yayi parking a ƙofar wani ƙaramin gida ɗan madaidaici mai kyau, sauka yayi ya tura gate ɗin kasancewar babu mai gadi, sannan ya dawo ya shigar da motarsa, ya maida gate ɗin ya rufe, ledan ya ɗauka sannan ya rufe motar ya nufi hanyar shiga cikin gidan kai tsaye, a bakin ƙofar falon ya tsaya ya ciro makulli a aljihunsa ya buɗe kofar ya nufi cikin falon da ke da duhu kasancewar labulayen ɗakin masu kauri duka a sake suke, karasawa yayi ba tare da ya kunna fitila ba, har ya kai tsakiyar falon, kafin ya ciro wayarsa tare da kunna haske, ɗakuna biyu ne a cikin falon dake kallon juna, ƙarasawa yayi kai tsaye jikin ɗaya daga cikin ɗakunan, ya buɗe ƙofar ɗakin ya zura kafafunsa ciki, yana haskawa da fitilar wayarsa kasancewar nan ɗin ma" ba hasken kirki Sai da kalli labulayen ɗakin da suke sake suma kafin ya Hasketa da fitila yana kallonta ba tare da ya ƙarasa cikin ɗakin sosai ba yana tsaye daga bakin ƙofa ya harɗe hannunsa a ƙirji girarsa a ha ɗe. "A zaune take a gefen gado, ta sanya kanta a tsakanin kafafunta, kanta babu ɗankwali, kasancewar ta haɗa kai da gwuiwa ne ya Sanya gashinta ya sauƙo ya rufe fuskarta har yana taɓa gwuiwarta," "baka iya ganin furkarta sam, saboda irin zaman da tayi a cikin duhun ɗakin." "second 5 yayi yana kallonta then as if forced ya Ƙarasa cikin ɗakin ya tsaya akanta yana cigaba da kallonta, idanunsa suka sauƙa akan hularta da hijab ɗinta da ta ajiye a gefenta, juyawa kawai yayi ba tare da yace komai ba ya fice a ɗakin, kusan mintuna 3 da fitarsa sai ga hasken wutan lantarki ya gauraye ko ina na gidan ya dawo cikin ɗakin still with his nose mask and shades on" yace """ke""" "bata ɗago ba, kuma bata da niyyar ɗagowar bare ta kulashi, sai kuka da take ƙasa ƙasa, bai sake tanka mata ba ya ajiye ledan hannunsa dake ɗauke da take away ɗin abinci a bedside daga haka ya nufi ƙofa, a hankali ta buɗe idanunta ta ɗagosu daga gwuiwarta da ta kifa ta bisa da kallo idanunta duk sun kumbure saboda kuka, she couldnt believe he is leaving again, sake tafiya zaiyi yanzu ya barta a wajennan?, ta tura baki tana binsa da kallo da manyan idanunta da ke tsiyayar da hawaye, ita babban damuwarta ma yanzu ta san sai ya kashe power ɗin gidan kafin ya tafi, ta shiga uku, gashi yamma ya soma yi sosai dan its past 4, har ya fice a ɗakin kafin ta kalli hularta da hijab ɗinta da tayi sallar la’asar da shi, miƙewa tayi ta sauƙa daga kan gadon ta wuce toilet idanunta na sake cikowa da hawayen takaici da baƙin ciki, gabaki ɗaya duk wani baki da tsiwa nata ya mutu murus kamar ba ita ba, wanke fuskarta tayi ta wanko hannunta tana kallon" "fingers ɗinta that are so fyn and fragile yadda ruwa ke zuba a tsakaninsu a ƙarƙashin tap ɗin," "kafin ta cire su under tap ɗin ta fito cikin ɗakin tana tafiya a hankali kamar mara bone sanin har yanzu yana gidan bai tafi ba tunda ga wuta nan bai kashe ba, dan punishment ɗin da yake mata shine kashe wutan gidan gabaki ɗaya idan zai fita duk da yadda take da mugun tsoro kamar farar kura haka take zama ita kaɗai kamar mayya gashi ya ƙi bata wayarta, wannan punishment" ɗinnasa scares her more than anything. "ƙaramin ƙugi da cikinta yayi yasa ta dafe shi a hankali, ba ƙaramin yunwa take ji ba don abincin safe da ya kawo mata da tayi taurin kai ta ƙi ci ɗaukewa yayi ya tafi da shi bayan uban aikin gyaran gida da ya saka ta, bata da zaɓi than ta ci wannan ɗin yanzu, ta ƙarasa gefen bed ta zauna ta ja abincin ta soma ci hawaye na sake cikowa idanunta, sam ba abinda take so bane a takeaway ɗin, kaɗan ta ci ta sha ruwa da ke ciki ta sake jingina da gado tana matsar hawaye, kamar kuma wadda aka tsikara ta saka kuka tana shure shure akan gadon, gabaki ɗaya ji take kamar ba ita ba, kwata kwata bata jin daɗin rayuwarta, duk duniya bata jin akwai wanda ya" "tsaneta irinsa, kuka ta dinga rairawa kamar an aiko ta ne dama ta yi shi tana yi tana kiran Daddy." Yana jinta daga kwance da yake a dogon kujera a palour yana danna wayarsa amma ko kallon "hanyar ƙofar ɗakin baiyi ba, jin kukan ya ishe shi ya sa ya miƙe ya fice a falon tare da rufe gidan gabaɗaya this time around bai kashe wutan gidan ba ya shige motarsa ya bar unguwar gabaki ɗaya ya nufi gidansa." "Parking yayi a space ya buɗe motar ya sauƙo bayan ya kashe ta ya nufi cikin gidan yana sake tamke fuska ganin har sannan motocinsu na nan a farfajiyar gidan alamar basu tafi ba suna nan suna jiran dawowarsa, gabaɗaya shi sam ya ma manta da ya barsu a gidan ba don motocinsu da" ya gani a farfajiyar ba har sannan alamun suna gidan shi wallahi ya mance da su. "a falo ya same su, ga baki ɗayan su fuskarsu babu yabo babu fallasa, infact zunzurutun ɓacin rai" ne ma a kwance akan duka fuskokinsu. "Ciki ciki yayi sallama, ta yadda bayi da tabbacin wani acikin su ya ji shi, bai bi ta kansu ba ya nufi" sama. """Aryan!”" "Ya ji an faɗa a bayansa wanda yana da yaƙinin cousin brother ɗinsa hamza ne, ba tareda ya bi" "takan hamzan ba ya sake cigaba da tafiya, uncle Ameenu ya sha gabansa yana faɗin" """Ba ka ji kiran da yayanka ya maka bane? Ko bai kai ya dakatar da kai ba?, iyakar mu kake so ka" "nuna mana kamar yadda ka saba? Ina tambayar ka?"" ya faɗa tare da saka hannu ya hankaɗa kafaɗ ar sa, ko gezau bai yi ba, sai idanunsa da suka soma kaɗawa daga farare tass suna surkawa da ja dan yanzu babu shades a idanunsa tun kan ya shigo ya cire shi, ya sauƙe idanunnasa ƙasa ya ƙi ya kalleshi, Uncle muhammad da ke tsaye gefe shima ransa a ɓace ya karɓe da faɗin" """Me ka mayar da mu ? mutanen banza? Kiran duniya an maka kaƙi ɗaukar waya, mu tako Muzo" "wajenka takanas amma dan raini da wulaƙanci ka sauko ka ganmu, sai ka fita ba tare da kace" "uffan ba, sannan ka dawo zaka sake hayewa sama, wato ga ƴan iska koh? Kai waye, me kake jin" kanka? Me kake taƙama da shi? Yaushe ma aka haifeka Aryan?” Uncle Muhammad ya ƙarasa faɗa ransa a mugun ɓace dan ba ƙaramin zafi abin ya masa ba. "Har lokacin bai da alaman zai furta wata kalma, sai ma lumshe idanunsa da yayi yanajin wani" mugun raɗaɗi a zuciyarsa Hamza ne yayi ƙwafa yana kallon mahaifinsa uncle muhammad ya ce """Dad ka gani koh? na faɗa maka wallahi ba zai ce muku ƙala ba, uwarsa ce ta koya masa duk wannan halin gaba ɗaya, yaro an koya masa raini da rashin girmama na gaba da shi, ba iya mu" "yayunsa ba har ku iyayensa, mara tarbiyya kawai""" "ya faɗa yana huci tare da kallon sa har lokacin yana tsaye ƙiƙam, sai dai wannan karan yayi" "folding hannayensa a ƙirji yana sauraron duk abinda suke cewa, jin Hamza ya ambaci umminsa yasa ya ɗago idanunsa ya dube sa," """ƙarya yayi ne? Kake kallonsa da waɗannan idanunnaka maye? Ko ƙarya ya mata ne?”" "Uncle Ameenu ya faɗa yana kallonshi , a yanda idanunshi suka kaɗa sukayi ja a lokacin zai tabbatar maka da ranshi ne yake ɓaci da tafasa a ƙarƙashin ƙirjinsa amma duk da haka bashi da" niyyar cewa komai. cikin jin daɗin zai tanka ganin reaction ɗinsa Hamza ya sake faɗin """Oh sorry, the mistress ya kamata ince, dan na tabbata tana can tana abinda ta saba, ta gagara" "zaman aure!, matar da ke zaman kanta, waya sani ko kaima abinda kake yi kenan, ka biyo footstep" "ɗinta shiyasa ka keɓe kanka, ka rabu da family house ka dawo gidanka kai kaɗai """ "Kasa ƙarasawa yayi jin numfashin shi na shirin rabuwa da gangar jikinsa, sakamakon wani irin fizgosa da yayi ya buga da bango ya bishi ya shaƙe da iya ƙarfinsa, zuciyarsa har wani racing take yi, nose mask ɗin da ya sa ya toshe fuskarsa da shi ya zame ya dawo ƙasan wuyansa, cikin idanun Hamza yake kalla kamar yadda shima yake kallon nasa da idanunsa da ya zaro waje" sakamakon shaƙar da ya masa. In a very shaky voice ya buɗe baki yana cigaba da kallon Hamza cike da warning yana ƙara shaƙ esa da iya ƙarfinsa yace "“Don't you dare, stay within ur limit......"" Sai kuma ya kasa ƙarasawa ya cije lips ɗinsa kawai yana haɗiye wani irin takaici da ya taso masa yana kallon idanun hamza da suka soma kaɗawa, Hamza da yaji ƙamshin lahira, idanunsa duk sun firfito waje gabaki ɗaya ga wani yawu da yake ji na taruwa a maƙogoronsa da ya kasa haɗiyewa, ya saka hannayensa biyu ya rirriƙe hannunsa" dake wuyansa yana ƙoƙarin cirewa amma ya kasa. """Aryaan!!"" uncle Ameenu da uncle muhammad da ya ga ana ƙoƙarin hallaka masa ɗa suka shiga" kiran sunan sa ganin kamar baya cikin hayyacinsa sai sake tightening shaƙar yake yi """kashe shi zaka yi? Baka da hankali ne Aryaan?, ka sake shi na ce!”" "sam babu alamar ma yana jin su dan yanda yake sake shaƙe Hamza da gini, da ƙyar suka iya raba shi da wuyan Hamza da shima ke iya ƙoƙarinsa ganin ya ƙwaci kansa a hannunsa amma ya hanasa ƙwaƙƙwaron motsi saboda yadda yayi cornering ɗinsa a jikin bango, zuwa lokacin ƙoƙ arin shurawa kawai yake idanunsa duk sunyi jajir, sai ƙoƙarin dambe yake da shi amma yaƙi bashi space da damar yin hakan." "wani wawan mari uncle Ameenu ya sauƙe ma Aryan a fuska, yana faɗin" "“lallai wuyanka ya isa yanka Aryaan, la shakka Asiya ce uwarka, to bari kaji ni da kyau ka faro" "abinda bazaka iya karasashi ba Aryaan, ka jira hukuncin wannan abin da ka aikata, abin kuma da ya kawo mu dama bai wuce sanar maka da cewa mun baka nan da watanni da basu haura 2 ba ka nemo mata muyi maka aure ko kuma kaga mata a gidannan a cikin dangin da kake gudu, dan wallahi baka isa kana yawo kana abinda ka ga dama da yaran mutane a garinnan ba yana dawowa kunnenmu kana ɓata mana suna ba, da darajarmu da mutuncinmu a garinnan, baka isa ba, idan mu baka jin tsoronmu sannan baka ɗauke mu a bakin komai ba ka raina mu baka ganin mutuncinmu, to tabbass zaka ji kira daga mai kankat wato mahaifinka UMAR kuma na tabbata kasan haduwarku da shi, dan gwara mu da ka raina a kansa, haduwarka da shi ba zai maka daɗi" "ba mara mutuncin yaro, ɗan iska”" "Daga haka ya kama hannun Hamza da uncle Muhammad ke bama ruwa ko ta kansu bai bi ba," idanunsa sunyi jajir suka fice a gidan gabaki ɗayansu suka barshi nan tsaye yana huci da sauƙe ajiyar numfashi. #banidahujja #Maimoon 09041426598 BANI DA HUJJA!! 2. Iskar da ya cika bakinsa ya furzar cikin matuƙar ƙunar rai yana cigaba da bin ƙofar da suka fita da kallo. Two months? Is this a joke? Mata a wata biyu? wannan ma ai ba mai yiwuwa bane kamar wani "shirin film, a ta ina zai nemo matar a wata biyu kacal, infact shi bai ma shirya zama tied to ko wace mace yanzu ba at all, baya buƙatar aure kwata kwata a rayuwarsa a yanzu, juyawa yayi ya wuce sama jikinsa har tsuma yake." """Yaya UMAR baka ga abinda ɗanka ya mana ba, wallahi ko kare bazai ci ba, tabbass yaron nan shaiɗani ne fiye da yanda muka yi zato, bashi da mutunci bashi da tarbiyya sannan bashi da hankali"" Uncle Aminu ya faɗa yana huci, uncle muhammad da shima ranshi har sannan ke ɓace" ya karɓe da faɗin """Kai ba ma wannan ba, ka ga dukan da ya ma Hamza?ya shaƙeshi yana neman kashe shi kawai dan ya faɗa masa gaskiya, gashi nan duk wuyansa yayi jajir sai da aka shafa masa man zafi, kuma a gabanmu saboda bai ɗauke mu a bakin komai ba ya gama raina mu, wallahi tallahi bazan taɓa" "barin wannan abin ya wuce a banza ba, kawai dan ya faɗa masa gaskiya, wallahi bai isa ba""" uncle Muhammad ya ƙarasa faɗa yana nuna masa wuyan Hamza da yayi mugun ja abinku da fari sai ƙyallin man zafi yake. "Dad dake zaune ƙafarsa ɗaya akan ɗaya, da cup na coffee a hannunsa wanda shansa ya kasance al'adarsa ya ajiye cup ɗin hannunsa a kan center table tare da gyara zaman newspaper dake kan table ɗin kafin ya miƙe tsaye, sam bazaka iya karantar a wani yanayi fuskarsa take ba, baya ya juya musu tare da folding hannunsa duka biyu ta baya kafin a hankali cikin kamilalliyar muryarsa" yace """kun isar masa da saƙo na?”" "Cikin zafin yanda baice komai akan abinda Aryaan yayi ma hamza ba, uncle Muhammad yace" """Ameenu ya isar masa """ "bai sake cewa komai ba yayi wucewar sa ya barsu a tsaye a wajen, zuciyoyinsu cike da takaici, da" baƙin cikinsa. "Tun daga bakin ƙofa take kare masa kallo tana wani irin shu'umin murmushi, a hankali ta soma takowa zuwa cikin ɗakin tana tafiya a hankali saboda yanda kayan jikinta ya kamata duk da atampa ce a jikinta amma an mata wani irin ɗinki na rakani gantali, ga wani uban hill da ke ƙ afarta,ta zubo da kitson da aka mata da gashin kantin da yayi matuƙar mata kyau har gadon bayanta, sai wani ɗan siririn gyale sharara da ta ɗaura bisa kai wanda da shi da babu duk uwar" "ubansu ɗaya, black beauty ce kyakkyawar gaske, komai yaji masha Allah da ita." "a hankali take tafiya tana murmushi ganin yanda yake kwance akan gadon ko takalman ƙafafunsa bai cire ba, daga gani baccin ya ɗaukesa ne ba tare da ya shirya ba dan half ƙafafunsa na ƙasa gefen gadon other half na jikinsa kuma yana kan gadon, gashin kansa ya rufe masa kusan rabin" goshinsa saboda yanda ya kwanta a rigingine. "A hankali ta zauna a gefen gadon tare da shafa fuskarsa tana murmushi, gashin nasa da take" mugun so ta sa hannu ta shafa a hankali kafin ta cigaba da shafa gashin da ke da matuƙar santsi "ba sai an faɗa ba ya ci kuɗi, tana yi tana kallon fuskarsa cike da nishaɗi, a hankali ya soma buɗe" "idanunsa da suka yi ja, saboda bacci da ɓacin ran da bai gama sakinsa ba, akanta ya sauƙe idanunnasa kafin a hankali ya yunƙura ya miƙe zaune" """Hi My love""." "Ta faɗa tana kallon sa, da faffaɗan murmushi ɗauke a fuskarta, lumshe idanunsa yayi ba tare da ya amsa ta ba, yana jin yanda kansa ya masa nauyi, sai kuma a hankali ya miƙa hannu da" "niyyar ɗaukan wayarsa dake gefenta, da sauri ta rigashi ɗauka ta miƙa masa tana faɗin" """Love gani a kusa, komai kake so ka faɗamin in baka mana miye anfanina? Ga matarka a kusa ai" baka bukatar yin komai da kanka” ta faɗa tana kashe masa ido still smiling "Wayar ya karɓa ba tare da yace mata komai ba, da wani irin sauri ya dirga daga kan gadon ganin yadda time ya wuce sosai yana bacci gashi ko sallah bai yi ba, itama da sauri ta miƙe tana kallon" "sa, ganin wanka zai shiga ya sa ta faɗin" """Can i join u?""" Har kamar bazai tanka ta ba amma sanin irin baƙin nacinta kamar tsohuwar mayya ya sa yace """Aneela! i am not in the mood, so i will appreciate if you leave me alone""." daga haka ya shige bayi tare da rufo ƙofar "Binshi tayi da ido murmushin fuskarta na raguwa, ƙarar sauƙar ruwa da taji ya sa ta miƙe a hankali dan ta tabbata tunda yace mata ta tafi politely to idan har ya fito ya sameta he won’t welcome that, sai da ta tattare masa duk abinda ya zuzzubar a ɗakin which are very few, sannan ta gyara masa gadon kafin ta bar ɗakin tare da ja masa ƙofa, falon ƙasa ta koma ta zauna tana" danna wayarta. "takun sakkowarsa da taji yasa ta dago kanta a hankali tana kallonsa, kamar yadda tayi tsammani" "farar shirt ce tass a jikinsa da jeans harda pcap, tayi shiru tana kallonsa lost in thought, Aryaan mai kyau ne, tasan ana cewa tana da kyau sannan tana ji da kyawunta, but Aryaan ƙarshe ne ga kyau ga iya ɗaukan wanka, bata San ya zata kwatanta shi ba but he’s just sooo different da" sauran. "har ya gama sakkowa bata lura ba, bai bi ta kanta ba ya nufi ƙofar fita a palourn, ƙamshinsa da taji na yin nesa ya sata saurin buɗe idanunta sa ta lumshe tana faman murmushi, rufe ƙ ofarsa kawai ta gani, da sauri ta miƙe ta bi bayanshi, har ya buɗe mota tayi saurin zuwa gabansa" "ta tsaya, ta marairece cike da shagwaɓa tace" """Love"" ya ɗage girarsa alamun “what?” Ganin sai kallonsa take zata ɓata masa lokaci yasa" "hannu ya mayar da ita gefe, zata yi magana ya rigata" """Aneela!!""" "Yanda yayi maganan ya sa ta fasa tata maganar, ta dinga kallonsa ta tabbata wani ne ya taɓosa a can wani wajen daban cause thats not how he behaves with her, tana kallonsa har ya shiga mota ya tayar tare da barin gidan, ta bubbuga ƙafanta a ƙasa kafin ta juya a hankali ta shiga tata" motar itama ta fice a gidan. "A bakin restaurant ɗin ya tsaya, ba tare da ya shiga ba ya ɗau wayansa, bugu ɗaya ya ɗaga, a ta" ƙaice yace """Jameel kawo min ina waje""" "cikin mintuna 3 Jameel ya fito da uniform a jikinsa, da leda a hannunsa, window ya sauƙe sannan" ya amshi ledan ya ja motarsa ya bar wajen. "A ƙofar gidan ya tsaya, ba tare da ya shigar da motar ba, ya ƙarasa ya shiga gidan, buɗe ɗakin yayi bayan ya saka black shades a idanunsa, a zaune ya sameta tana wasa da roban takeaway ɗin" "da yayi mata da safe, ta ɓaɓɓarka ledan gabaɗaya." "Ba tare da yayi magana ba ya tura mata ledan hannunshi gabanta," "bata ko kalli ledan ba ta ci gaba da wasa da yatsunta, har ya kai ƙofa zai fice sai kuma ya juyo yana kallonta," """SALWA!!""" Ya kira sunanta strictly yana folding hannayensa a ƙirji "Idanunta da zuwa yanzu sun koɗe da kuka ta ɗago tana kallonsa da su, wani irin very Innocent face take dashi, wanda zaka yi tunanin ko yatsa aka saka mata bazata taɓa cizawa ba, wanda ke ɗ auke da round face da big eye balls ɗinta masu masifar ɗaukar hankali, tana da hasken fata tare da very cute ƙaramin baki ga dimples guda biyu wanda ko da magana take ko kuka ko dariya lotsawa suke a hankali." "kallon second 10 tayi masa ta mayarda kanta ƙasa tana wasa da ƴan siraran yatsunta masu kyau, wasu hawayen da take ta riƙewa tuntuni kar su zubo suna biyowa shar agefen fuskarta." "daurewa yayi kamar baya so, ya furta" "“Eat ur food""" "daga haka ya juya, har ya ɗaura hannu akan handle ɗin sai kuma ya tsaya cak sakamakon tsinkayo sassanyar muryarta da yayi, Cikin rawar murya na kukan baƙinciki da ke cinta ta" soma magana """Yaya Please ka mayar da ni wajen Ammina, ka min rai, zan mutu anan, ni bana son wajennan," "tsoro nake ji wallahi yaya kullum idan baka nan, ni kam ka kaini wajen daddyna "" tana kaiwa" nan ta fashe da shagwabaɓɓen kuka that irritates him. "Sai da ya jira ta kai aya kafin ya buɗe ƙofar ya fice abinsa, Wani irin kuka ta sake fashewa da shi tana kallon ƙofa, wannan wace irin rayuwa ce, idan kasheta zai yi gwara mata ya kashe ta ta huta, idan har lissafinta dai-dai ne to aƙalla zata yi sati ɗaya da kwana ɗaya kenan a wannan gidan" "da ko falo bata ƙaunar fita, eight days fa kenan innalillahi wa inna ilahi raji’un." Ganin idanunta har wani zafi suke mata da wani irin hazo hazo ya sata lumshe su a hankali tana jinginar da kanta a jikin bangon ɗakin. A hankali take furta “daddy…” cike da shagwaɓa wanda nature ɗinta ne magana a haka. "Sai da ya tsaya yayi isha’i kafin ya wuce gidan, a ranshi yana jin kamar ya fasa zuwa ya wuce" gidansa. "Sauƙe glass ɗin motarsa yayi yana kallon soldier ɗin da ke riƙe da bindiga fuskarsa a matuƙar ha ɗe, ɗaya daga cikin abinda ya sa ya tsani gidannan kenan, ba tare da ya kula maganar da yake masa ba ko na sauran soldiers ɗin da ke gadin wajen ya zuge glass ɗin ganin sun basa hanya ya" wuce ciki "A tangamemen gate ɗin estate ɗin yayi horn, ɗaya daga cikin sojojin da ke gadin gate ɗin ya leƙo da kansa, ƙaramin tsaki ya ja ƙasa ƙasa yana kallonsa daga cikin motar, ganin motar Aryaan ɗin ya sa sojan buɗe masa ƙofa da sauri, babban family house ne ko ince estate na gasken gaske wanda yaji komai na rayuwa, ajikin makeken plate name ɗin da ke gefensa an rubuta ‘THE TURAKI'S’. kai tsaye cikin gidan da yake nan tarrr da haske kamar ba dare ba ya nufa da motarsa, sai da yayi tafiya ta atleast 15 minutes akan shinfiɗaɗɗiyar titi dake ko ta ina a cikin gidan yana wuce gine gine wanda dukansu iri ɗaya ne, sai dai banbancin girma da decorations da wasu suka fi wasu, sannan ko wani gidan yana da gate ɗin da zai sada ka da shi, da security mai gadin wannan gate ɗin, a ko wani gate da sunan mai shi a jikinsa wanda duka" ƙarshensa ke ƙarewa da TURAKI. "Tun da ya tunkaro gate ɗin gidan mahaifinsa yake jan tsaki ƙasa ƙasa saboda sojoji da ke nan burjik suna gadin gate ɗin kamar zasu hana waɗanda ke ciki mutuwa, tun kafin ya ƙaraso ya fara horn har ya iso gaban gate ɗin wanda da alama ginin wannan gidan yafi na kowa a cikin Family" "house ɗin gabaki ɗaya, duk kuwa da yawan gidajen dake cikin estate ɗin." "Buɗe masa gate ɗin sukayi ba tare da sun kula shi ba kamar yadda shima bai kula kowa a cikinsu ba, gate ɗin mai kyau sai dai bai kai na Main entrance na gidan girma ba, a gaban wannan part an rubuta CDS. UMAR WAZEER TURAKI, a babban parking space ɗin da zai iya haɗiye a ƙalla motoci 10 ko ma fiye yayi parking, sannan ya fito daga motar yana sake haɗe fuskarsa, a hankali yake tafiya kamar baya son yayi ya nufi main entrance na wani babban part wanda yafi ko wani part girma a gidan, murɗa ƙofan falon yayi a hankali ya shiga bayan ya zare glasses ɗin idanunsa," "ya ƙare ma babban falon da ya gaji da tsaruwa kallo, ƙamshi ne kawai ke tashi a falon mai sa" "nutsuwa ga sanyin ac da ya ƙarama wajen wani pleasant daɗi, ba tare da ya zauna ba kawai ya wuce ya fara hawa stairs don ya tabbata kowa na gidan na ɗakinsa, sanin yanayin mai gidan na rashin son hayaniya sam yasa komai a nutse a keyi a gidan. har yakai sama sannan ya dakata yana kallon ɗakunan da ke jere a saman guda uku ta gefen daman sa bai bi ta kansu ba ya murɗa wata ƙofa dake gefen hagunsa, wata haɗaddiyar falo ne ta bayyane mai matukar kyau wanda ke ɗauke da ɗakuna biyu kacal a cikinta, sai wani ƙofa da zai sada ka da falo na biyu, sosai ya lumshe idanunsa jin kamshin da ke tashi a falon kafin ya ƙarasa ciki, nan ma babu kowa, ɗan jim" yayi kafin ya nufi ɗayan falon yana addu'ar samun Dad anan. "Tura ƙofan yayi a hankali da sallama ɗauke a bakinsa, a zaune ya samesa a kan ɗaya daga cikin manyan kujeru na alfarma, a falon da ya ma gaji da tsaruwa, dan ya ma fi falon farko kyau sai dai bai kaisa girma ba, ƙafansa ɗaya akan ɗaya ga cup akan center table ɗin gabansa, da wata ƴar" karamar littafi da yake rubutu a ciki that looks like jotter or a diary book. "ɗago idanunsa dake cikin fararen medicated glasses yayi ya zuba ma ɗan nasa idanu, kafin ya kawar da kai daga kallonsa ya cigaba da abinda yake yi ba tare da ya amsa sallaman ba, a hankali Aryaan ya ƙaraso gabansa, ya zauna a ƙasa ya sunkuyar da kansa yana kallon haɗaɗɗen carpet ɗ" "in dake malale a ƙasa, cikin sanyin murya yace" """Ina wuni DAD""" "bai amsa ba sannan bashi da niyyar amsawa sai ma miƙewa da yayi, yayi folding hannuwansa a" baya ya soma tafiya towards ɗakin dake cikin falon. Cikin sauri muryarsa har rawa take Aryaan yace """Dad please!""" ɗan dakatawa yayi kafin cikin dakakkiyar voice ɗinsa da ke cike da command yace """ARYAAN UMAR TURAKI! Leave immediately, sannan saƙon da baffaninka suka isar maka, make sure ka cika umarni, kwanaki 59 suka rage cikin sittin ɗin da na ɗibar maka, bring a wife before then if not you will leave me with no choice bayan na ɗaura maka aure da koma wacece, in" "tura maka gidanka, since ka fi ƙarfin zama a cikin ƴan uwanka""." daga haka yayi shigewarsa ɗaki tare da rufo ƙofan. "Wani irin zuciya ke cinsa yana dannewa, why! Me yasa shi da mahaifinsa are not in good terms at" "all, ya zo ne ya gana da shi akan aurennan but sam yaƙi sauraransa, ya ake so yayi? Ta ina zai nemo mata a wata 2 kamar wani magnet? Aneela ce ta faɗo ransa cikin sauri ya shiga girgiza kai" """Nooo banda Aneela"" sai kuma ya miƙe dan yasan bayi da choice bayan Aneela ɗin." #banidahujja #Maimoon 09041426598 https://whatsapp.com/channel/0029VbB1qGBFMqrVuPRZ5f2Q BANI DA HUJJAH!! By Maimoon 3. "Zuciyarsa a dagule, fuskarsa a haɗe ya fito daga sashen mahaifinnasa, yana kokarin ficewa daga ɓ" "angaren gabaɗaya suka kusa cin karo da mummy ya matsa baya a hankali ya bata hanya ganin shiga zata yi wajen Daddy, a taƙaice ya gaishe ta shima ciki ciki" "“ina wuni” ko kallonsa bata yi ba ta shige ciki abinta ya bita da side eye kafin ya buɗe ƙofar shima ya fice a gidan, ba tare da kallen kallen komai ba ya buɗe motarsa ya shiga ciki ya tayar aka buɗe masa gate ɗin Cds. Umar wazeer turaki ya fice yana driving gently, a gaban gate ɗin barr Ameena wazeer turaki yayi horn ba tareda ya ko kalli opposite house ɗin da shi kuma aka rubutu DR Ameenu Wazeer turaki ba, aka buɗe masa gate ɗin ya shiga yayi parking yana kallon motar AMEEN dake parking space ɗin which means yana gida as expected. Bai samu kowa a palourn ba sai sanyin ac da ƙamshin turaren wuta mai daɗi nan ma, stairs ya nufa kanshi tsaye yana jujjuya" key ɗin hannunsa. "“Aryaan?” Dakatawa yayi tare da juyowa yana kallon Mami da fitowarta kenan daga kitchen, ta" ɗan buɗa ido tana kallonsa tace “ashe dai kai ɗinne hamshaƙi” ɗan murmushi yayi kaɗan ya fasa haurawa ya dawo palourn ya zauna a kujera yana sake ƙirƙiro murmushi “ina wuni Mami” “Da ban wuni ba zaga ganni ne aryaan?” Shiru yayi kawai dan ya san dama dole sai tayi ranting "in dai ta gansa, rabonsa da gidan ya kwana biyu tayi mita har ta gaji." "“Yau kuma Allah yayi ka tuna mu kenan Aryaan, yanzu abinda kake yi ya kyautu kenan? Yaro ɗ" "an gata amma ka mayar da kanka kamar maraya?” Ta faɗa tana zagayowa ta zauna a kujerar da ke facing ɗinshi tana ta kallonsa keenly, Nan ma bai ce mata komai ba sai murmushi kawai da yayi," ta sauƙe ajiyar zuciya a hankali tace "“To Allah ya kyauta, ya kake toh? How have u been?” Sai a sannan ya amsa da" “Alhamdulillah Mami” "“Are u sure?” Gyaɗa mata kai yayi, tace" "“Toh Allah yayi albarka, ya tsare gabanku da bayanku, ya baku abinda kuke nema duniya wa" "lahira, a cigaba da hakuri a kuma cigaba da yayyafawa zuciya ruwan sanyi, zama lafiya da kowa ya" "fi zama ɗan sarki, komai lokaci ne da shi haka zaka ga watarana kamar ba’a yi ba”" "“Amin Mami” ya amsa yana jinginar da kansa da kujera, miƙewa tayi tana kallonsa tace" “AMEEN ɗin ai yana sama kaje bari nima in duba girki ya kusa gamuwa ma su lailerh zasu "kawo muku” gyaɗa mata kai kawai yayi bashi da niyyar tashi, ta miƙe ta wuce kitchen, 10 minutes later ta kuma fitowa, da mamaki take kallonsa ganin har sannan yana zaune a wajen yana danna wayarsa, hakan yasa bata kulashi ba ta wuce sama dan kiran Ameen ɗin da kanta, tare suka sauƙo da wani matashin saurayi kyakkyawa wanda zasu yi sa’o’i da Aryaan sai dai ya fi Aryaan hasken fata da glasses a idanunsa dressed casual, ya kalli Ammi bayan ya sauƙo cikin" palourn yace “Ammi where is he?” Ammi ta ƙaraso cikin palourn tana kallonsa tace “Ji iskanci! Anan fa na barsa shine ya kama hanya ya wuce bai ce min zai wuce ba? Kuma fa har abinci nace ya jira amma shine ya wuce ya tafi abinsa koh? Kirawo min shi kace nace ya dawo yanzu ya zo yaci abinci”. Ameen ya ɗan sauƙe ajiyar zuciya yana zama a kujera yace “Ki ƙyaleshi kawai tunda ya tafi ba juyowa zaiyi ba kin sani” zama tayi itama a kusa da shi tace “Al’ameen me ke damun ɗan uwanka ne?” Ya buɗa mata hannu alamun bai sani ba shima "yana murmushi," "“Ya zaka ce min baka sani ba, bayan ure closer to him than anyone”" "“Allah Ammi ban sani ba, but bari na watsa ruwa inje gida in same sa inji if there’s anything i" should know” gyaɗa masa kai tayi tace “Idan ya faɗa maka pls ka zo ka faɗa min” “Okay Mami” ya faɗa yana miƙewa ya wuce sama murmushi kwance a fuskarsa “Lailerh ta kawo maka abinci yanzu?” “Ah ah idan na dawo zanci” “Toh” ta faɗa tana kallonsa har ya haura kafin ta wuce kitchen dan duba abinda su lailerh da siyama ke yi. Yana driving yayi dialing lambarsa yana ajiye wayar a gefensa bayan yayi connecting da speaker ɗ "in motar, sai da kiran ya kusa yankewa kafin ya ɗaga, Al’ameen yayi gyaran murya yace" “Malam kana ina ne?” “Why?” “Ban sani ba! Kana gida ko baka gida?” “Bana gida!” “Kana ina?” “Doesnt concern u!” Murmushi Ameen yayi kawai ya katse kiran yana nufan gidan nashi bayan ya kalli agogo ƙarfe 10 saura. "Buɗe masa gate mai gadi yayi bayan yayi horn once, ya shiga yayi parking a kusa da motar Aryaan dake space kafin ya fito ya nufi cikin gidan, ba tare da knocking ba ya tura ƙofar palourn ya shiga ciki yana kallon ko ina, ganin baya ciki ya gyara glasses ɗin idanunsa ya nufi hanyar sama da takalmansa, motsi da yaji a kitchen ya sa ya dawo da baya ya nufi kitchen ɗin, a bakin ƙofa ya tsaya ya harɗe hannu a ƙirji yana kallonsa, yana tsaye a jikin counter da singlet baƙa a jikinsa against fair skin ɗinsa, yayi pairing ɗinshi da three quarter iya guiwarsa dat looks loose, Al’ ameen ya kalli plate ɗin scrambled egg dake plate da toasted bread guda biyu a gefe, black tea" da yake haɗa ma kanshi a lokacin ya kalla kafin yace "“Yaushe ka koyi girki bawan Allah” ko kallonsa baiyi ba, barin jikin ƙofan yayi ya nufe shi yana" faɗin "“Wulaƙanci ne bana so, sai in juya in koma in da na fito, da ina da zuciya ma wallahi ba zaka ganni a nan ba, ko da yake Mami ce tace na zo ka je kana acting weird a gida kuma before in sauƙ" "o ka wani wuce ka tafi, idan ka san baka so in zo waya ce ka zo gidanmu nemana?”" “Says who kai naje nema?” Ameen ya hararesa yace “To me kaje yi?” Sai da ya ajiye cup ɗin a gefen tray ɗin kafin yace “Mami naje gaisarwa” Al’ameen yayi wani dariya da ya sa Aryaan kallonsa yace "“Ko ba gaishe da Mami ba, u that i know ɗin koh? Kai dai faɗi me ya kaika kawai, amma" "kafinnan haɗa black tea ɗin da ni banci abinci ba na fito” ko kulasa baiyi ba ya ɗauki tray ɗin ya fita a kitchen ɗin, Ameen ya ƙarasa ya ɗauki well cleaned cup da spoon ya biyo bayansa yana fa" ɗin "“Wannan ɗin zai ishemu ne?” Bai kulasa ba ya ajiye tray ɗin akan dinning, tun kafin ya zauna" "Ameen ya ja kujera ya zauna tare da ɗaukar toasted bread guda ɗaya ya bar masa ɗaya, ya saka spoon ya ɗibi scrambled egg ɗin ya kai baki, zama kawai shima yayi ya ɗauki ɗayan bread ɗin ya soma ci, Al’ameen ya ɗauki cup ɗin black tea ɗin ya zuba a cup ɗinsa ya raba musu daidai da daidai, kafin ya tura masa nasa gabansa, komai bai ce masa ba ya ja ya fara sha yana ɗan danna wayarsa fuskarsa a haɗe, sai da suka conye duka kafin ya miƙe ya koma cikin palour ya zauna yana danna wayarsa, kwashe kayan Al’ameen yayi ya kai kitchen ya ajiye a sink ya buɗe fridge ya ɗauko bottled water guda biyu ya fito da su a hannunsa, jefa masa ɗaya yayi ya cafe shi kuma ya ƙaraso yana shan ɗaya, ya zauna a wani kujeran daban ba wanda Aryaan ke kai ba yana cigaba da shan ruwan, sai da ya gama sha ya ajiye sauran a center table kafin ya kalli Aryaan dake" "buɗe ruwan hannunsa a lokacin zai sha, yace" “What happened bro? Tell me mana why are u acting all up haka?” Aryaan ya rufe ruwan ya "ajiye tare da ɗan dafe kansa, hakan yasa Ameen putting serious face ya miƙe ya dawo kujeran da" yake zaune yace “Me ya faru ɗan uwa?”Ajiyar zuciya ya sauƙe a hankali ya ɗago ya kalli Ameen da idanunsa da suka ɗan yi ja yace “I’m tired Ameen! Please tell me miye nayi ma Daddy?” “What happened?” Ameen ya tambaya sounding concerned! Duk abinda ya faru ya kwashe ya "faɗa masa from zuwan su uncle Ameenu zuwa zuwanshi gidan, Al’ameen ya sauƙe ajiyar zuciya yana kallonsa har ya kai aya kafin ya dafa kafaɗarsa yace" “Calm down bro! Yanzu iya wannan abinne ya saka ka ɗaga hankalinka haka? Har ya nuna a face ɗinka cewa ure tensed? Haba aryaan” wani mugun kallo Aryaan ya masa yana ƙwace kafaɗarsa yace "“Bangane iya wannan abin ba, shey u no comprehend abinda nace maka? Cewa fa nayi Dad and" "his brothers so suke in kawo mata nan da two months, how is this possible Ameen? Meyasa sai ni kaɗai suka gani? What happen to u and hamza and the others? Kai da hamza da kuka girmeni ba’ a ce ku kawo mata in so so so time ba sai ni?” Al’ameen ya gumtse dariyarsa yana kallonsa" yace "“Wato yanzu ka yarda mun girmeka da yake zancen is not in ur favour, what happened to" "watanni ba girma bane? Kuma da kake zancen mu ba’a ce mu kawo mata ba, kai ai ka san dalilin da ya sa suka ce ka kawo mata, baka jin magana Aryaan, i’ll be so happy wallahi idan ma kayi auren ko wasu abubuwanka zasu saitu” Ganin yadda ya haɗe rai ya sa Ameen ya ɗan bubbuga" kafaɗarsa yace "“Sorry bro, ka kwantar da hankalinka za fa ka samu mata nan da wata 2” jingina kansa yayi a" jikin kujera yana kallonsa yace “I was thinking about Aneela…” tun kafin ya kai ƙarshe Al’ameen ya haɗe rai tare da hararansa yace "“Over my dead body ne zaka auri yarinyar nan, kai tsakaninka da Allah idan aka barka sai ka auri" "yarinyarnan? Sai kace ma yaranka wace irin uwa ka zaɓa musu kenan?” Kallonsa kawai Aryaan yake baice komai ba, Al’ameen ya ɗauko wayarsa dake ringing ganin Mami yace" "“Mami ce, let me come and get going home”" "“Spend the night here mana” ya faɗa yana kallonsa, ɗan shiru yayi sai kuma ya ɗaga wayan" "yana sauraren Mami tare da kallon Aryaan da ya lumshe idanunsa, can yace" "“Eh Mami, ill spend the night here gobe zamu shigo tare da shi” shiru yayi sai kuma ya amsa da" “Amin” daga haka ya katse wayar yana kallonsa yace “Duk ta damu ta ɗauka wani babban abu ke damunka” “Okay yanzu ƙarami ne ke damuna kenan” "“Eh mana daɗi ne yayi maka yawa, ni ace in fito da matar a gani mana da tuni na kai an wuce" wajen” “To yanzu ma idan ka kai ai ba zasu ƙi yi maka ba” ya faɗa yana miƙewa "“Ah ah barsu dai su tambayeni first ni ai ina da wacce nake so, jira kawai nake a tambayeni in" "gabatar da ita gaban kowa da kowa, ba irinka bane ni da kake tunanin auren mace irin zaleena" sunanta ko aleena….” "“Aneeela..” suka tsinkawo muryarta daga bakin ƙofa, duk suka ɗaga kai suna kallonta, idanunta cike taf da hawaye take kallonsu hannunta rike da jakarta sai wayarta a ɗaya hannun tana sanye da tshirt mai maɓallai fara da blue jeans, attachment ɗinta ya xubo har gadon" "bayanta, sai siririn ɗankwali da ta ɗaura a kai as usual." "Kallo ɗaya Al’ameen ya mata ya haɗe rai tare da miƙewa da nufin haurawa sama yana mamakin irin rashin kamun kanta, yo rashin kamun kai mana idan ba haka mai zai kawo mace da ta san darajar kanta gidan mijin da ba nata ba da wannan daren? Halinta disgust him, Ko da yake its not entirely her fault har da na mai gayya mai aikin dan shi ya bata daman haka shi yayi welcoming ɗ inta a gidansa anytime idan ba haka ba ai bazata zo ba, wani takaici ya takure shi a wuya ya ja tsaki tare da ɗaukan wayarsa zai wuce sama, ajiye jakar tayi ta ƙaraso palourn tare da shan" gaban Ameen tana kallon cikin idanunsa tace “Al’ameen miye na taɓa yi maka a rayuwarnan da ka tsane ni? Baka ƙaunata baka ƙaunar gani "na tare da farincikin rayuwata, mai nayi maka da zafi har haka da kake ikirarin over your dead" body ya aureni” wani kallo yake mata irin na malama na miki kama da wanda kika zo wajensa "ne, kamar bazai kulata ba sai kuma yace" "“I’m glad uve been eavesdropping tun ɗazu kuma kinji duk abinda nace, aryaan bazai taɓa" "auren mace irinki ba God forbid” juyawa tayi ta kalli Aryaan dake kallonsu kansa a kishingiɗe da kujera, kafin ta juyo ta bawa Ameen amsa ya raɓata ya wuce sama abinsa, ta bishi da kallon tsana" kafin ta juyo ta dawo kujerar da Aryaan ke zaune tace "“Love ka ji abinda yake faɗa koh? Pls dont listen to him, ure my life ka sani” miƙewa yayi shima zai wuce sama tayi saurin kamo hannunsa ya juyo yana kallonta, ganin yanda take kallonsa idonta cike da hawaye ya sa ya janyo ta jikinsa yana kallon face ɗinta ya sa finger ɗinshi yana" "share mata hawayen dake kumatunta, ƙasa ƙasa yace" "“Go home zamuyi magana later okay?” Ta gyaɗa masa kai tana kallonsa, ya sake ta ya ja da" "baya yana kallonta da guntun murmushi akan fuskarsa, ƙarasawa tayi ta ɗauki jakarta har ta buɗ e ƙofa ta sake juyowa ta kalleshi, kashe mata ido ɗaya yayi, tayi murmushi tana share hawayenta ta fice tare da jan ƙofar, yana juyawa ya ga Al’ameen a tsaye a jikin stairs ya harɗe hannu yana kallonsa, suna haɗa ido ya haɗe rai, kallonsa kawai Ameen keyi har ya zo zai wuce kafin ya ja tsaki" da ya tabbatar yaji ransa a ɓace ya furta "“kayi asara” ko kulashi bai yi murmushi kwance a fuskarsa ya wuce sama, juyawa yayi ya bi" bayansa saman ransa a mugun ɓace. Not edited #Banidahujjah #Maimoon 09041426598 https://whatsapp.com/channel/0029VbB1qGBFMqrVuPRZ5f2Q BANI DA HUJJAH!! 4. Al’ameen na fitowa daga bayi da pyjamas ɗin Aryaan a jikinsa ya zauna a gefen bed yana kallon "Aryaan dake zaune a kan bed yayi resting bayanshi da headboard, macbook a buɗe akan cinyansa," hankalinsa duka yana kan abinda yake yi a ciki “Wai haryanzu baka gama project ɗinnan ba?” "“Uhm” ya amsa a taƙaice, jin Al’ameen yayi shiru ya ɗago ya kalleshi yace “ko zaka ƙarasa" min?” “Hmm” kawai Ameen yace yana miƙewa ya dawo bedside ya leƙa screen ɗin yana kallo yace “Still on commercial complex?” Aryaan ya bashi side eye ba tare da ya amsa ba yana zooming "da adjusting kyakkyawan zane dake screen ɗin, Ameen yayi murmushi yana kallon abinda Aryaan ɗin ke nuna masa a screen ɗin, 3D model ne na building ɗin da yake aikinsa yanzu ya dinga rotating yana nuna ma Ameen ɗin ba tare da yace komai ba, sai da ya gama nuna masa kafin ba" tare da ya kalleshi ba yace “Kasan mutuminnan canja facade ɗin ya sake yi?” Ameen yayi guntun murmushi yana kallonshi yace "“Sau uku fa kenan yana canzawa, wannan client ɗin naka sai kai”" "“Fourth…” ya faɗa calmly yana jan wani layi across screen ɗin, kafin ya canza zuwa wani tab ɗ" "in daban wanda ke ɗauke da finishing materials, shi dai Ameen jingina bayansa kawai yayi yana" kallon aikin cike da burgewa. "“Previous design ɗin kwata kwata baiyi balancing da structural load ɗin ba, idan na biye masa" "na bi irin abinda yake so blindly, kwata kwata ginin bazai yi making sense ba” Ameen ya gyaɗa kai yana miƙewa feeling impressed but not suprised dan ba tun yau ba yasan Aryaan is perfect at" what he does. "“Kaga barmu a bar da cases, mun bar muku buildings ɗin”" “Gobe zaka rakani somewhere” Aryaan ya faɗa yana ɗago kanshi “Where?” “Zaka gani goben” “Hope its after mun je gida?” Ganin ya maida kanshi zai cigaba da abinda yake Ameen yace “serious Mami cewa tayi mu zo tare gobe” “Allah ya kaimu” ya faɗa a taƙaice "Haurawa gadon Ameen yayi ya kwanta dan bacci sosai yake ji, amma yana kwanciya maganar" "Aneela ya faɗo masa a rai dan ɗazu suna haurowa toilet Aryaan ya shige da ya fito kuma still shima ya shiga so bai ma yi masa maganan ba, juyawa yayi ya fuskance shi yace" “Aryaan!” Ya juyo ya kalleshi “Are u really going to do it?” Fuskarsa da yaga ya nuna alamun bai gane inda maganar ta dosa ba yasa yace “Da gaske kana so ka auri yarinyar can?” Ɗauke kansa yayi ya cigaba da abinda yake yi muryarsa ƙasa ƙasa yace “As if i have a choice!” "“Kar ka raina ma kanka hankali mana, baka da choice as how? Who force u yace dole sai ka" "aureta, ka kawo wata daban mana, ko yaushe ka fara sonta bani da labari”" Aryaan ya kalleshi yayi shiru kamar zai yi magana sai kuma ya fasa ya miƙe ya ɗauki macbook ɗ "insa ya nufi ƙofa, Ameen ya gyaɗa kai yana kallonsa yace" "“Allah ya baka sa’a, and dont even bother explaining later” kashe masa wutan ɗakin Aryaan" yayi ya koma palour ya ajiye laptop ɗin ya sauƙa ya haɗa ma kansa black tea ya dawo ya baje ya cigaba da aikinsa peacefully cike da natsuwa dan kwata kwata ko zancen aurennan ba so yake yi a masa ba at all. Washegari suna dawowa daga fajr Ameen ya kunna tv din palourn tare da kwanciya akan kujera "yana rage volumn, shima aryaan da kamar zai wuce bedroom sai kuma ya fasa ya kwabe jallabiya da ya daura kan wandon pj dake jikinsa dan shi dama bai iya bacci da riga ba, pillow ya janyo ya sauke kan lallausan carpet ya kwanta yana kallon wrestling da Ameen ya kunna a haka bacci ya sake yin awun gaba da su, sai wajen tara kafin Al’ameen Yayi miƙa daga saman kujeran da yake kwance ya tashi zaune yana sake yin miƙa tare da kokarin miƙewa tsaye sanye da jallabiya da yaje sallah da ita da asuba, komawa yayi ya zauna yana kallon Aryaan da ke kwance akan carpet da dogon wandon pj a jikinsa ba riga yayi matashin kai da pillow ɗin kujera da ya sauƙe ƙasa, ya sa ƙafa ya ɗan shure ƙafarsa da ke kusa da tasa, hakan ya sa ya buɗe idanunsa a hankali ya" kalli Ameen da su. wayarsa ya juya masa yana nuna masa agogo yace "“Tashi ka shirya muje gida” ya miƙe zaune tare da saka fuskarsa cikin palm ɗinsa na kamar 2 minutes kafin ya miƙe tsaye ya ɗaga pillow ɗin ya mayar mazauninta ya juya ya wuce ɗaki," Ameen ya bishi da ido kafin shima ya mike ya bi bayansa. "Aryaan ne ke tuƙi Ameen na zaune a gefe yana danna wayarsa, ganin ba hanyar gida suka nufa ba" ya ɗaga kai ya kalleshi yace “Malam ya naga ba hanyar gida muka nufa ba” “Yes zamu fara zuwa inda zaka rakani ne ba zamu daɗe ba sai mu wuce gidan” shiru yayi yana "kallonsa bai ce masa komai ba dan ba haka suka yi da shi ba amma dai ya share bai ce komai ba," "har suka iso kofar gidan, kallon gidan yayi ya juya ya kalleshi yace" “Ba kace ka sayar da gidannan ba?” “Eh na sayar” "“So..?” Bai kulashi ba ya sauka a motar bayan yayi parking da kyau a waje, Ameen ya bishi da" "kallo across motar har yaga ya buɗe gate ɗin ya shige ciki kafin ya sauƙo ya bishi a baya. A tsaye ya ganshi a compound ɗin yana jiransa, yana hangosa ya shigo ya cigaba da tafiya towards ƙofar palourn, Ameen yabi bayansa still wondering dama ashe bai sayar da gidan ba, ya sa makulli yana" buɗe ƙofar palourn Ameen da ya iso wajen yana kallonsa yace “What are we doing here” yana tura ƙofar palourn yace “Sayar da kai na zo yi” Ameen yayi murmushi yana binshi ciki “Wane kai” "“To sa wasa” ya ƙarasa yana kallon labulayen palourn that are hanged ya ƙarasa kujera ya zauna yana kallon Ameen da ke ƙare ma madaidaicin palourn kallo, buɗe ƙofar kitchen ɗin da ke cikin palourn akayi, kwata kwata bata lura da Ameen ba, dan straight kujerar da yake yawan zama idan ya zo ta kalla jin motsi a palourn, suka kuwa haɗa ido da shi, da gudu ta wuce ɗakinta hannunta riƙe da ruwan gora kanta ba ɗankwali, Ameen da ya daskare a inda yake tsaye ya kalli hanyar da ta bi da kallo kafin ya mayarda kallonsa kan Aryaan dan he seriously couldnt believe his eyes, Aryaan yayi kamar bai san shi yake kallo ba sai ma wayarsa da ya fara dannawa, nufar ɗakin da ta rufe Ameen yayi dan bai gama yarda da abinda ya gani ba ko dai idonsa ke masa gizo? To ko Aneela ce a gidannan ɗin idanunsa ke nuna masa wata daban da ya tabbata babu dai abinda zai kawota nan ɗin, Aryaan ya bishi da kallo ta ƙasan glasses ɗinsa har ya tura ƙofar ɗakin da ta shiga, a tsaye ya ganta a tsakiyar ɗakin riƙe da ruwan tana kallon ƙofa kamar mai expecting shigowar wani, suna haɗa ido da Ameen ta wani zaro ido tayi cilli da goran ruwan ta nufosa a guje ta shige jikinsa ta rungumesa ta fashe da sabon kuka, gyaɗa kai kawai Ameen yake still in shock" yace "“SALWA!?” Ajiyar zuciyar kuka kawai take sauƙewa taƙi ta amsa, ya ɗagota daga jikinsa yana" kallonta yace “Me kike yi anan? What happened to morocco? Birthday ɗin kenan?” Shagwaɓe fuska ta kuma yi tana kallonsa a shagwaɓe tace "“I never went” tana faɗa wasu hawaye na rige rige a kumatunta, ya gyaɗa kai kawai yana lissafa" "irin tsantsar rashin gudun zuciya da gudun magana irin na Aryaan, shi yanzu idan ba tsantsan nema wa kai fitina ba ko da kudi aka ce ya shiga harkar yar uncle Ameenu sai ya shiga? ba ƙ aramin mamaki abin ya bashi ba har hakan ya nuna ƙarara a fuskarsa, sake zuwa tayi zata shige jikinsa ya riƙe hannunta yana kallon face ɗinta da duk ya kumbura tsabar kuka, to dama mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki, salwa on normal days ma ya take da kuka bare kuma an taɓa ta, ya dinga kallon face ɗinta lost in thought, har wata rama tayi fuskarta look somehow" ko dan kukanne kasancewarta fara sai fuskar tayi ja ta ɗan kumbura. Cire hannunshi yayi a nata "ya juya ya nufi palour ransa a matuƙar ɓace sai dai wayam ya samu palourn babu ko mai kama da Aryaan, yayi ƙwafa a hankali ya juya yana kallon salwa da ta biyo shi palourn tana share ido har sannan kanta ba ko ɗankwali, ƙofa ya nufa ganin zata biyo sa a haka ya dakata yana kallonta" yace “Je ki ɗauko veil ɗinki” "“Babu sai dai hijab” ta faɗa tana kallonsa, gyaɗa mata kai yayi yace" "“Je ki ɗauko yi sauri” juyawa tayi walking slowly ta tafi ɗakin, hijab ɗinta da Aryaan ne ya" "kawo mata su guda biyu take sallah da su ta ɗauko guda ɗaya ba tare da ta kula akwatin kananun kayan da ta kwasa that she was suppose to travel to morocco da shi ba ta fito a ɗakin, Ameen ya kalle ta ganin ta sako hijab ɗin har yana jan ƙasa ya nufi ƙofa, bin bayansa tayi tana" tattare hijab ɗin kamar zata faɗi tace "“Yaya i dont want to wear this” bai kulata ba har suka fito haraba, ta ja ta tsaya tana kallonsa" "har ya buɗe gate ya leƙa yana kallon inda suka yi parking ɗazu amma babu motar, ya riƙe kunkumi kawai yana kallon wajen, bai san sanda ya furta “wow!” Ba, da ya ɗauki mota ya barsa da ita anan me yake nufi kenan? Ya juya ya kalli salwa da ta haɗa rai ta ɓata fuska harda tura baki," ranshi yaji yana ƙara ɓaci yana kallonta yace “Zo ki wuce mana” ta soma takowa tana riƙe hijab ɗin tace “Yaya wai da wannan abin zan je har gida?” Wani harara ya galla mata bai kulata ba ya kama "hannunta ganin ta iso shi ya soma tafiya da ita, binsa kawai take tana tattare hijab ɗin da ke jan ƙasa kamar zata faɗi banda hawaye babu abinda take yi ganin yadda mutanen unguwan suke kallonsu, sai da suka iso titi kafin ya sake hannunta ya fara ƙoƙarin tare abin hawa yana laluba aljihunsa yaji ko yana tare da wallet ɗinsa amma babu kamar yanda ya bar wayarsa a mota haka ya bar wallet ɗin ma, kallon keken da ya tsaya a gabansu tayi in disbelieve kafin ta kalli Ameen da" sauri tace “I dont understand? Meyasa bazamu shiga mota ba? Ni gaskiya bazan shiga abinnan ba” me keke ya wani kalleta daga sama har ƙasa kafin ya ja tsaki kawai ya ja kekensa yayi gaba tun "kafin ma Ameen yayi magana, Ameen ya bishi da kallo sai kuma ya kalleta, tayi murmushi tace" “All this poor people and short temper” "“Tunda kin kore shi sai ki tare wani, where’s your phone?”" Tura baki tayi tace “shima ya ƙwace” "Ameen ya gyaɗa kai kawai yana sake ƙoƙarin tare wani keke," “Yaya pls mu shiga mota” "“Kina da kudin motan?” Shiru tayi tana kallonsa, ya kama keke ya shiga bayan ya tsaya yana faɗ" "a masa inda zasu, kallonta yayi ganin tana tsaye yace" “Kina ɓata mana lokaci ko in tafi in barki ne?” Ganin still tana tsaye yace “Me keke mu je” me keke ya tayar kuwa zai tafi da sauri tace “Wait..” kamar zata yi kuka ta shiga kusa da Ameen tana zama a ɗosane kamar ta zauna akan "ƙaya, mai keke dai ya ja kekensa yayi gaba bai tanka su ba, sai a lokacin Al’ameen ya kalleta yace" “Tun yaushe ne kike nan ɗin” ta kwantar da kanta a shoulder ɗinsa tace "“Nace maka i never went to morocco yaya Ameen, ai wallahi Allah ya isa na, abinda ya fi bani" "haushi ma wayata, Raliya will kill me, haka zata ce fake promise na mata banje birthday ɗinta ba bayan we planned everything together, ai bazan taɓa yafe masa ba ko kabarinsa yana balbali da" wuta” "“Keee…” Ameen ya dakatar da ita yana dariya, ta tashi zaune da kyau tana kallonsa tace" “Its not funny yaya Ameen” "“Its not daddy’s princess” ya faɗa yana jan hancinta, sake mayarda kanta tayi kafaɗarsa ta" "kwantar tana kallon hanya, Allah Allah take su iso gida." tun kafin su iso road block ɗin da zai sada su da estate ɗinsu me keke yace “Ba ma ƙarasawa can fa” kallon salwa Ameen yayi ta wani zaro ido tana kallonsa tace “da ƙafa? Duk soldiers ɗincan su ganni a haka da wannan abin?no pls yaya” ta faɗa tana "nuna masa hijab ɗin jikinta, ajiyar zuciya ya sauke ya kalli me keke da harya ja ya tsaya yace" “Dont worry muje zan musu magana” "“Toh oga” me keke ya faɗa yana sake tada keken ya nufi sojojin, tasowa sukayi suka nufosa" "ganin wajen ya tunkaro suna daka masa tsawa, Al’ameen ya leƙo daga ciki da murmushi a fuskarsa yace" “Sorry its me” cikin fara’a da girmama juna suka gaisa ya faɗa musu he’s going in with the me "keke, hakan yasa suka basu hanya ita dai salwa haɗa rai tayi tana kallonsu ƙasa ƙasa har suka wuce, ko da suka zo gate ɗinma sammakal sai da ya sake musu magana kafin suka buɗe, me keke ya shigar da su har ƙofar “Ameena wazeer turaki” yana yaba yanda masu kuɗi suke sha’aninsu" "ji wani gida dan Allah, yana gama parking salwa ta sauƙa shima Ameen haka, ganin zata nufi gate" "ɗin gidansu da ke kallon na su Ameen ɗin, Ameen yayi saurin riƙo hannunta tare da yafito mai" "gadin gate ɗinsu da ɗayan hannun ganin ya leƙo jin keke a ƙofar part ɗin abinda bai taɓa ji ba," “Lawal bashi kuɗinshi pls idan akwai cash jikinka” da sauri ya fito yana faɗin “Akwai ranka ya daɗe” shi kuma ya ja hannun Salwa zuwa cikin gidansu dan ko giyar wake ya "sha yanzu bazai bari Salwa ta tafi gidansu a haka ba, Babanta ya ganta a haka su shiga uku." A palour ya tarar da Mami da yaranta Lailerh da Siyama suna kallo duk suka ɗaga kai suna "kallonsa kafin su kalli Salwa da ta sha hijab, miƙewa zaune su siyama sukayi har suna haɗa baki wajen faɗin" “SALWA!!” #Banidahujja #Maimoon 09041426598 https://whatsapp.com/channel/0029VbB1qGBFMqrVuPRZ5f2Q BANI DA HUJJAH 5. "Tana tsane gashin kanta da ta wanke shi sosai ba kaɗan ba ta fito daga toilet, baby pink towel ɗ aure a chest ɗinta, very fair skin ɗinta sai glowing yake, ta zauna a gaban dresser tana ƙarema ɗakinsu siyama da su kansu su siyama ɗin kallo, ɗakinsu siyama babba ne sosai kuma kasancewar su masu banbancin ra’ayi akan komai yasa ɗakin ya zama kamar wanda akayi splitting gida biyu, ko wacce da side ɗinta with her bed da study area ɗinta, kasancewar lailerh is more girly yasa gefenta nuna hakan, sashinta sai ya kasance is more aesthetic dan har ƙaramin vanity table take da shi a gefenta cike da skin cares ɗinta da perfumes kamar mai sayar da su, itama gefen siyama tana da same table amma nata laptop ɗinta da notebooks da frames na motivational quotes ne akai, kai kana kallo kai tsaye zaka gane cewa ita siyama is a bookworm ita kuma lailerh soft girl life, sai dai duk da haka same dresser da siff suke sharing, Lailerh da tayi" tagumi akan gadonta tana kallon Salwa tace “Wai bazaki faɗa mana what happened ba” "“Eh!, bazan faɗa ba” ta faɗa tana matso cream ɗin Lailerh ɗin da ta zo ta ɗauka a table ɗinta" "kasancewar same cream suke using unlike siyama da ba irin nasu take anfani da shi ba, ko shower" "gel da na Lailerh tayi using, ta zauna ta fara lailaye jikinta da cream ɗin kamar tana shafa ƙwai, siyama dake kan gadonta itama tace" "“Haba Princess, ki faɗa mana pls”" "“Mtsw, sai kuma kuyi, ba dai ni kuka yi ma dariya ba ɗazu! Billah bazan faɗa ba”" "“Stop swearing mana ai da Mami ta ce mu bar dariya mun bari, pls tell us what happened," "kullum sai na duba status ɗinki har snapchat da insta story ɗinki u didnt post anything about birthday ɗin raliya, pls tell us what happened” kamar ba da ita suke ba ta ƙarasa shafa mai ɗ in ta buɗe drawer ta fara duba kaya a cikin nasu zata saka, kamar kuma wacce aka yi wa wahayi ta" juyo tana kallonsu tace “Wallahi bazan taɓa yafewa Aryaan ba” duk buɗe ido sukayi suna kallonta jin ko yayan ma bata "sakaya ba wai Aryaan, ji sukayi kamar ta tafka zunubi ambatar sunansa without yaya, kafin su" gama comprehending wannan ta cigaba “I hate him! Stubborn.. arrogant.. st…” "“Ke salwa, are u in your right senses kuwa? Shi yayan?”" Sai da tayi rolling idanunta kafin tace “Eh shi? Waye shi? Tunda ba mala’ikan ɗaukan rai bane ai "da sauƙi, ni na daina jin tsoronsa wallahi, kuma wannan abin da ya min koh hmm…”" Da ƙyar suka rufe bakunansu da suka sake suna sauraronta “Me yayan ya miki wai toh?” "“Ku barni da shi, wallahi zai san ni yayi ma haka, wallahi duk abinda ya mini sai na rama” sai a" lokacin Siyama ta ɗan ja guntun tsaki tace "“Ko kuma ki rame ba, Shegen cika baki, Salwa duk duniya wa ya fiki tsoron yaya Aryaan, ki faɗa" "mana me ya haɗaki da shi sai kame kame kike kina zaginsa, Allah ya sa ya jiki”" “To ya jini mana! Sai me?” “Wai a ina kika ga yayan? Ni fa na kusa two weeks rabon da na gansa” “Dama a ta ina zaki gansa yana can yana walakantani saboda ni ce karamar katangarsa daɗin tsallakewa” “Ban gane ba” Lailerh ta faɗa cike da son jin labari. "Ƙin amsawa tayi ta juya ta cigaba da zaɓen kaya da zata saka, da ƙyar ta samu wani plain gown" cikin kayan lailerh su dai kallonta kawai suke yi yadda garin ɗaukan kayan take ta wargaza musu "siff, yanzu suyi magana cibi ya zama ƙari tunda Mami ce tace tayi wanka anan ta ci abinci kafin ta" tafi gida. "Saka rigan tayi ta zauna ta fara drying gashinta, ta gama tayi styling ɗinshi tana yi tana tunanin" wayanta da ke wajenshi idan ta tuno ji take kamar ta hadiyi zuciya ta mutu. "Tana gamawa ta miƙe ta nufi ƙofa duk suka bita da kallo, siyama ta miƙe ta tafi siff ɗin ta leƙa" "taga bata ko taɓa part ɗin kayanta ba, ta ɗan yi murmushi ta kalli lailerh tace" "“Sai ki tashi ki gyara kayanki” daga haka ta nufi ƙofa itama, miƙewa lailerh tayi ta bita ba tare da ta gyara ɗin ba itama gudun kar ta tsaya gyarawa Salwa ta je ta faɗa ma siyama abinda ya faru" ita kaɗai. "Mami na ganin sun sauko ta nuna musu hanyar dining da hannu, ko kallon dinning din salwa bata" "yi ba ta nufi hanyar ƙofa, Mami ta bita da kallo kafin tace" “Salwa bazaki ci abinci ba?” “Bani da appetite Mami i just want to see daddy” "“a haka zaki tafi babu ɗankwali…?” Ko kafin ta ƙarasa har ta fice a palourn, Mami ta sauƙe" ajiyar zuciya kawai kafin ta juya wajen su lailerh tace “Kuje ku ci abinci” "Al’ameen ne ya shigo ɗakin Mami bayan sallar magrib, ganin tana waya ya sa ya ƙarasa ya zauna a kujera yana jiran ta gama, ganin expression ɗinta yasa ya bada hankalinsa kan abinda" take faɗa a wayar "“Eh, na gane! Na gane, to ba damuwa idan baku dawo ba zan sa Al’ameen ya kawo ni”" Ameen dai ya zuba mata ido har ta sauƙe wayar ta dafe kanta a hankali “What happened?” Ya tambaya yana kallonta worried “Salwa ce wai take hospital” “Hospital kuma? Me ya same ta?” “da Amminta muke magana yanzu wai bata iya cin abinci babanta ya kaita asibiti” "“Saboda kawai bata ci abinci ba shine za’a kaita hospital to yaushe ma ta dawo ɗin, kuma sau" nawa ne bata ci abincin ba?” "“Anan ma ai ƙin ci tayi ina jin da ta je gidan ma bata ci bane kuma dai ka san yanda Yaya Ameenu yake akan Salwa, ni wallahi sam ban ji daɗin abinda Aryaan ya aikata ba har fargaba nake" ji na abinda zai faru wlh” “Ikon Allah” Ameen ya faɗa though ba wai hes very suprised bane kowa ya sani a duka family ɗ "innan Uncle Ameenu ko kaɗan baya wasa da lamarin only daughter ɗinshi Salwa, akanta bashi da kara, dama asali ba kirki ya cika ba to akanta kuwa rashin kirkin ninkuwa yake, ko Amminta ba sha take yi ba a wajensa in dai akan Salwa ne, shiyasa yarinyar take abinda taga dama kowa tsoron mata faɗa yake saboda jaraban ubanta dan a gurinshi fa bata laifi, the only people da suke iya mata magana akan abu Mami ne twin sister ɗin Uncle Ameenu, tunda babansu Ameen ya mutu ta dawo gida da yaranta da dadewa tun kafin su Ameen su kai haka, to itace ma atimes takan yi wa Salwa nasiha idan ya kama harda faɗa sai kuma Bappah, thats Wazeer Turaki himself, grandfather ɗinsu shi kuma dama mutuminta ne duk da tsaurinsa amma sosai take sonshi akwai shakuwa sosai tsakaninta da shi, sai kuma Amminta da take shakkah only idan daddynta baya" wajen. Maganar Mami ce ta katse masa tunanin da ya tafi “Amminta tace wai hypoglycemia ke damunta wai sugar level ɗinta yayi dropping! Toh ban dai "sani ba since babanta ne dr ɗin komai ma zai iya cewa, kuma ka san already ya kira meeting!” Ameen ya sauƙe ajiyar zuciya yace" “Shiyasa ma na zo yanzu in ce Mami as his twin sister pls babu yadda za’a yi ki ɗan masa "magana yayi hakuri da meeting ɗinnan? Lokacin general meeting baiyi ba amma yawanci idan kaji emergency meeting toh its always him, yanzu wannan issue ɗin bazaku iya settling a hankali" ba sai an sakko bappah a ciki” "“Kira min Aryaan” Mami ta faɗa ba tare da ta amsa maganar da yake mata ba, wayarsa ya zaro" ya shiga dialing lambar Aryaan amma baya connecting ya dube ta yace “Baya shiga” "“Ai ya kyauta saboda ya san bai shuga abin kirki ba shiyasa ya rufe layukansa, idan kayi sallah" "isha’i kaje ku taho tare da shi, saboda zai iya cewa gobe ba zai zo meeting ɗin ba, ya ƙara ma kansa wani laifin akan laifi, wallahi ni har yaya Umar tsoron yaji maganar nan nake”" Miƙewa Ameen yayi yana kallonta yace "“Ke dai ki kwantar da hankalinki Mami, duk abinda sukayi babu ruwanki kar ma ki saka ma kanki" "damuwa please, ai ya san irin haka zai faru amma ya gwammace ya jawo ma kannasa magana”. Daga haka ya fice a ɗakin ta bishi da kallo kawai," Ummah dake zaune a palour ta kalli uncle muhammad dake sauƙowa daga sama da waya a kunnensa har ya ƙaraso cikin palourn ya zauna a kujera ranshi a ɓace yana faɗin "“Tabbass! To wallahi sai yayi dana sanin taɓa ta Allah ya kaimu goben, toh, toh, shikenan”" Ummah ta taɓe baki tana kallonsa tace “wa kuma aka taɓa” gyara zama yayi yana kallonta yace "“Wannan ɗan iskan yaron Aryaan ne wai ya je ya kulle Salwa dan bashi da mutunci, ni dai na" cewa Ameenu ya duba ta da kyau kar dai ya mata wani abin dan ɗan iska ne yaronnan kowa ya sani” "“Mtsw, dama na san wallahi bazai wuce ita ba, kai ai idan anga kana ɗaga jijiyoyin wuya to akan" "Ameenu ne, kana yayansa amma wai ƙaninka ke juya ka, daga yayanka har ƙaninka su zauna suna juyaka yadda suka ga dama ba abinda ya dame ka suyi ta passing ɗinka kamar ƙwallon ƙ afa kowa yana anfani da kai, ga dai hamza ga nan shaheeda sune dolenka amma inaaa ka ƙare a gindin brothers ɗinka da basu san darajarka ba kowa ɗansa ya sani a cikinsu, nan Aryaan ya shaƙ e Hamza ka dinga hayagaga bazaka yarda ba amma shiru kake ji babu abinda kayi akan hakan ya daki banza amma da yake salwa ya taɓa yanzu gashi nan har babanta ya kira emergency meeting an taba ƴar gold, kai kuma kana taya sa kana tada jijiyoyin wuya bayan da aka taɓa naka ɗan shi bai yi wannan baloƙoƙon ba, ka cigaba wallahi takaicinka bazai kashe ni ba” tana gamawa ta mi ƙe ta wuce sama mugun takaicin halin mijinta yana ƙona mata rai, duk cikin brothers ɗin sun fishi kuɗi, sun fishi alƙibla da sanin abinda sukeyi, they are the leaders shi kawai sai yadda suka yi" "da shi a ganinta, sun fishi iko da say a gidan." "Aryaan ne a zaune, Mami na tsaye a kansa ta inda take shiga ba ta nan take fita ba" "“What u did is not right, its very very wrong Aryaan, ko ba komai ai yar uwarka ce amma ka ɗ" "auketa ka kaita ka kulle kamar wata mara galihu? Bayan ka san halin mahaifinta sarai? Meyasa duk abinda zaka janyo ma kanka magana shi ka fi so Aryaan, dama gashi nan kana baki already amma kullum sake saka kanka kake a bakin kowa Aryaan, na tambayeka why u did that kuma ka" min shiru koh” "Ɗaga idanunsa yayi ya kalleta ya sauƙe kan still saying nothing, ta koma ta zauna tana kallonsa" tace “Shikenan tunda bazaka faɗa min ba gobe ai dole ka faɗa a gaban kowa Allah ya kyauta” shiru yayi kamar bazai ce komai ba sai kuma can yace "“Kiyi hakuri Mami” Al’ameen takaici kamar ya kashe sa yana zaune dai yana kallonsa, Mami ta" girgiza kai tana kallonsa tace "“Ah ah ni kuma ina ruwa na, duk abinda zaka yi dai ni dai ina mai tabbatar maka ka dinga tunani," yanzu na tabbata umminka bata ji ba bata gani ba zaka jawo mata magana dan kai ka sani ko miye "zaka yi a wajensu fa Umminka ce ta saka ka, bata nan ɗinma bata tsira ba kullum cikin sakata a" bakin yan gidannan kake ka dinga mata adalci ni dai na faɗa maka” shiru yayi bai ɗago kansa ba tace “Yaushe rabonka da kaje wajenta?” Sai a lokacin ya ɗago ido ya kalleta yayi shiru “Tambayarka nake” “Three days ago naje” “Kunyi magana da ita?” Girgiza kai yayi alamar “ah ah” "“And why is that” shiru yayi bai ce komai ba, ta sauƙe ajiyar zuciya tace" “Tashi kaje sama ka kwanta” ya ɗago kanshi ya kalleta “Mami zan zo goben i promise” "“Story for the Gods, ka ga ni kar ka saka ni magana, kaje sama ka kwanta gobe after meeting ɗ" in sai ka tafi” "Ɗan kallon Ameen yayi, Ameen ya ɗauke kansa daga kallonsa yana pressing phone hakan ya sa" ya kalli Mami yace “Zan ɗauko kaya” “Use Al’ameen’s” gyaɗa kai yayi ba don ransa ya so ba yace “Okay” ganin yanayinsa tace "“Idan kuma zaka tafin, amma promise zaka zo goben”" “Ah ah i’ll stay back” "“Toh shikenan, Allah yayi albarka”" Ya amsa da “Amin” ba tare da ya kalli Ameen ba kawai ya mike ya nufi ƙofa Mami ta bishi da kallo. Ba’a jima ba Ameen ma ya miƙe yabi bayansa shima ya nufi ƙofa ta raka su da ido kafin ta sauke ajiyar zuciya ta miƙe ta wuce sama. Kujera da ke compound Ameen ya ɗauka ya kai har gaban motar Aryaan da ya bar door ɗin gefen a buɗe ya zagaya side ɗin da ke buɗen which is not facing the compound ya ajiye kujeran ya zauna yana kallon Aryaan da ke zaune a driver’s seat kafafunsa na ta waje da cigarette a "hannunsa da ya kunna yana sha a hankali, Ameen ya zauna yana kallonsa yace" “Har yanzu baka yi niyyar faɗa mini me ta maka ba kenan?” Ko kula Ameen baiyi ba sai yatsarsa da ya sa yana kaɗe jikin tabar tokar ta zube ya mayar bakinsa yana sha a hankali yana furzar da "hayakin, shi kaɗai ya san irin ƙunan da ke damun zuciyarsa." Ameen ya kai hannu ya zare taba ɗaya daga kwalin da Aryaan ya ajiye a gefensa ya sa a baki ya kalle shi yace "“ina lighter ɗin?” Kamar bazai tanka sa ba sai kuma ya ciro a aljihunsa ya jefa masa, ya ɗauka" "ya kunna shima yana sha yana taɓa wayarsa, sai da suka kusa shanye duka kwalin kafin Aryaan ya" "miƙe zai wuce ciki, Ameen yace" “Mami will perceive the smell stay back a little” "Komawa yayi ya zauna yana haɗe rai ya jingina kansa da kujera, shima Ameen ɗin bai kulasa ba" ya cigaba da chat ɗinsa abinsa. "Murmushi Ameen yayi bayan wani lokaci ya kalleshi kafin ya ɗaga kiran dake shigowa wayarsa," Aryaan da idanunsa ke lumshe ya buɗe su yana kallon Ameen jin yace “Kin samu kin ci abincin?” Ganin waya yake ya sa ya mayarda idanunsa ya rufe sai kuma kawai ya miƙe yayi wucewarsa cikin gida ya barshi a nan zaune. #Banidahujja #Maimoon 09041426598 https://whatsapp.com/channel/0029VbB1qGBFMqrVuPRZ5f2Q BANI DA HUJJAH "Assalamu alaikum lovelies Bani da hujjah is a paid book, free pages kuma basu da yawa sosai, pls" "support me by making your payments kafin end of free pages! Thank you so much as you do, ga masu bukatar biya zasu tura 500 kacal zuwaga" 7039695535 "Palmpay," Maimunatu Abdullahi muhd Sai ku tura min evidence of payment ta 09041426598 on whatsapp Idan kuma katin waya ne zaku tura 500 zuwa ga 07039695535 Thank you 6. "A cike Babban hall din yake, duk wanda ke cikin gidan turaki yara da manya sun hallara saboda" "kiran gaggawa da Ameenu wazeer turaki ya Kira, the only people da basa nan are wadanda ke aure outside, hayaniya sai tashi yake kasa kasa a hall din da ke nan well structured, komai" "co-ordinated, kasancewar kujerun in rows a jejjere gwanin sha’awa kuma kowa ya zauna a inda ya kamata da iyalansa yasa suka yi looking rich and beautiful kana ganinsu kaga one big family, tun farkon ginin Wannan gida aka gina Wannan hall a cikin gidan kasancewar duk bayan wata shida sukan hadu dan tattauna dukkanin matsaltsalu da cigaba da ya faru a cikin gidan, idan disputes ne ayi settling, idan damuwa wani ke da shi a magance masa, wanda hakan ba karamin hadin kai ya janyo ba tsakaninsu over the years, Ba iya ahalin wazeer turaki bane a cikin estate din hasalima shi wazeer turaki and two of his brothers Lameer turaki da Nazeer turaki sune suka hadu suka Samar da Turaki family house! Sai dai Allah bai yi musu tsawon rai ba hakan yasa bayan rasuwarsu ya kasance kamar Wazeer shine Uba kuma kaka ga dukkanin ahalinnashi da na yan" uwansa. Duk da sai bayan wata shida ne scheduled lokacin meeting wanda Akan gayyato har wadanda "aure ya rabasu da gidan, amma duk da haka a duk lokacin da wani ya Kira meeting din gaggawa Akan amsa ko da kuwa waye ne dan sauraran matsalarsa. Kamar dai yadda a yanzu aka taru saboda uncle Ameenu." da yawa sunzo amma still wasu sai uzuri suka bada a cewarsu ya fiye korafi yanzu haka Ba wani Abu mai muhimmancin azo a gani bane. "Salwa ta ɗago daga danna sabuwar wayarta da daddy ya bata jiya bayan ta baro hospital saboda yadda ta saka su gaba da ƙorafin Aryaan ya ƙwace mata wayarta, ta kalli Ammi da ke gaisawa da Mami dake row ɗin bayansu tare da su siyama, juyawa tayi ta kalli su siyama amma" before they could wave ta ɗauke kai ta cigaba da danna wayarta tana tauna cingam. “Tofar da cingam ɗinnan kafin na mareki” taji Amminta ta faɗa tana hararanta ganin yadda take cin cingam ɗin tana ƙas ƙas da shi "Ɓata rai tayi amma dai ta cire ta riƙe a hannunta tana kallon Amminta da ta mayarda hankalinta suna gaisawa da other relatives da ke side ɗinta, ji tayi zaman ya isheta tun kafin a fara meeting ɗin, ita bata ma san meyasa daddy ya kira meeting ɗinnan ba, bata taba son meeting ɗinnan ba" its always boring to her. "jin hall ɗin ya ɗauki tsit sosai ya sa ta ɗaga idanunta da a hankali tana kallon farin tsoho mai ran ƙarfe, katanga kuma madogara ga duk wani ahalin Turaki, wato Wazeer turaki da kansa yana shigowa cikin hall ɗin da ke cike da ahalinsa, Escorted by Maza huɗu da suka kasance inuwa ga duka ahalin, wato Umar wazeer turaki, Aminu wazeer turaki, muhammad wazeer turaki sai lawal Nazeer turaki. kanta ta sunkuyar a hankali har Bappah ya samu waje a gaban hall ɗin ya zauna ya fuskanci ahalinsa for the countless time since them, as always kyakkyawar murmushi kwance akan kyakkyawa kuma kamilalliyar fuskarsa, su Uncle Ameenu ma duk zama sukayi, soldiers ɗin da escorts Umar wazeer turaki suka fice daga hall ɗin dan during that meeting su kaɗai suke" kasancewa ahali ɗaya gabaɗaya babu bare. "Sai da bappah yayi adjusting mic ɗinsa kaɗan zai fara Magana duk cikin hall ɗin kowa yayi tsit kafin ya shigo hall ɗin, shirun da hall ɗin ya ɗauka ya sa duk aka juya ana kallonshi aga wani hamshaƙi ne har Bappah ya riga shi isowa, Salwa ta ɗaga idanunta itama tana kallonshi da mamakin ganinsa yau cikin manyan kaya though babu hula akansa amma ba ƙaramin kyau shaddar ɗinkin half jampa ta masa ba, sai dai kamar kullum kamar ko yaushe fuskarnan kamar wanda aka aikowa da saƙon mutuwa, har ya samu waje kusa da Ameen ya zauna a row ɗin farko ɓangaren maza kafin ta ɗauke kanta tare da ɗan jan guntun tsaki ciki ciki, shi dai bappah binsa kawai yake da kallo still da murmushi a fuskarsa har ya zauna unlike uncle Ameenu da kuma" daddy Umar da suka haɗe rayukansu kamar basu taɓa murmushi ba. "Sai a lokacin Bappah ya gyara mic ɗin yana kallon dukkanin ahalinsa cike da alfahari da su ya musu sallama suka amsa ya soma da buɗe taron da addu’a kamar ko da yaushe! Duk da yadda shekaru ya ja amma cike da kamala yake magana, with same aura da yake musu magana da shi" each and every meeting. "Briefly ya musu nasiha akan haɗin kansu, akan tsoron Allah da kiyaye hakkokin Allah a lamuransu wanda wannan jawabi ne da sun saba jinsa daga bakinsa baya taɓa gajiya da nanata musu" wannan. Sai da ya gama jawabinsa kafin ya juya ya kalli uncle Ameenu dake zaune ya haɗe rai yana hura "hanci yana jira a iso gaɓar dalilin da ya sa ya kirawo taron, Bappah yayi gyaran murya yace" “Duk da akwai muhimmin dalili da ya sa aka kira taron but kafin in bada daman gabatar da wannan Umar will add one or two to abubuwan da na faɗa as usual” "Daddy Umar ya gyara mic ɗin gabansa fuskarsa ba yabo ba fallasa ya musu sallama suka amsa, ya soma magana a nitse wanda kamar ko yaushe ƙari ne akan Nasihar da bappah ya riga yayi, shi dai uncle Ameenu ko jin abinda yake faɗa baya yi dan takaici ne ya turnuƙeshi, shi fa ya kira meeting ɗin so meyasa dole sai an bawa wanda ba shi ya kira meeting ba damar magana kafin shi a basa, yanda daga shi har uncle muhammad suka zuba masa idanu zaka ɗauka sauraronsa" suke yi amma kowannensu da saƙar da ke cikin zuciyayoyinsu. Ko da aka bashi damar magana sake haɗe rai yayi kamar yanda ya kanyi idan ya shirya rashin "mutunci kafin ya gyara zamansa akan kujera tare da sallama, aka amsa masa ana jiran jin dalilin wanann kira na gaggawa, kowa ya zuba masa idanu banda Aryaan da ko kallon stage ɗin baya yi." "“Ku sani ban kira wannan taro for jokes ba, na kira wannan meeting ɗinne saboda my daughter" "was kidnapped, locked up, and treated like bata da dangi bata da gata bata da dignity”" Ya juya ya kalli Aryaan dake zaune kamar ba akansa ake magana ba yace “If anything should happen to my daughter ina so a sani cewa it would not be a family matter "anymore! So nake a yi ma Aryaan iyaka da salwa, babu ruwanshi da ita! Bana bukatar ace wai za’ a yi ma ƴata discipline i can do that myself, he was reckless with my daughters life da saboda stress da rashin cin abincin kirki sugar level ɗinta yayi dropping drastically, yesterday she" coulndnt even stand da kanta! Sannan ina so Aryaan ya kalle ni ya faɗa min dalilinsa na aikata mata hakan” "Gyaɗa kai bappah yayi kafin ya maida dubansa ga Aryaan, Muryarsa calmly yace" "“Aryaan” ya ɗaga idanunsa ya kalli bappah, kafin ya miƙe a hankali ya nufe shi, kwata kwata yanayinsa bai nuna damuwa ba sam, bappah dai kallonsa yake har ya ƙaraso ya tsaya a gefensa" ya sunkuyar da kansa a hankali. Sai da bappah ya ɗanyi shiru yana kallonshi na sakwanni kafin yace “What happened?” "Kowa ya zuba ma Aryaan idanu yana jiran amsarsa, banda uncle Ameenu da yake jin bai ma" kamata a tambayi Aryaan what happened ba kamata yayi kawai a yanke masa hukunci dai dai da abinda ya aikata ma Salwa. Jin yayi shiru Bappah ya kuma magana yana kallonsa yace “me ya faru Aryaan menene dalilinka "na aikata hakan?” Shiru ya kuma yi bashi da niyyar amsawa, daddy Umar da ke kallonsa shima yace" "“Ba da kai ake magana bane?” Girgiza kansa kawai yayi a hankali ba tare da yace komai ba still," Bappah yayi murmushi yana kallonsa yace “Je ka zauna” "“thank u” ya faɗa ƙasa ƙasa kafin ya wuce ya koma wajen zamansa, uncle Ameenu ya bishi da kallo kafin ya kalli mahaifinsa ransa idan yayi dubu to ya ɓaci duka sai dai babu daman magana, sai a yanzu yake da ya sanin kiran meeting ɗinnan, da ya sani da da kanshi ya ci uban Aryaan, ai" ya manta cewa shi Aryaan ɗan favourite child ne kuma favourite jika babu abinda za’a masa. "“Salwa” kiran da Bappah ya mata ya katse tunanin da ya tafi, ta taso a hankali with her phone" "in hand ta iso har gabansa, yana murmushi yace" “Me ya faru ne Salwa tsakaninki da yayanki?” Sai da ta ɗan tura baki kaɗan kafin tace "“Babu!” Ba uncle Ameenu kaɗai ba har shi Aryaan sai da ya kalleta, Amminta ta yi ƙwafa kawai" "a hankali dan dama ta san za’a rina sai da tace masa kar ya kira meeting ɗinnan ƙaramin aikin Salwa ne ta kunyatasa gaban kowa da kowa, Bappah yace" “Tell me the truth! Me ya haɗa ki da shi? Me kuma ya miki?” “Babu bappah” ta faɗa tana wasa da phone ɗin hannunta ba tare da ta kalli side ɗin babanta ba. Daddy Umar ya haɗe rai yana kallonta yace “ke ba wasa aka kiraki ba tell us what happened” "“daddy babu fa” ta faɗa tana kallonsu duka, Daddy Umar zai kuma magana Bappah ya dakatar" "da shi tare da umartarta da taje ta zauna, tayi godiya itama ta nufi mazauninta tana ƙin haɗa ido da su Siyama da suke kallonta with mouth agape, duk da kowa a wajen ya san thats not what happened amma since ita wadda aka ma tace babu dole kowa yayi shiru kawai yana jiran hukuncin Bappah, uncle Ameenu ya bi ƴarsa da kallo ransa na kuma ɓaci da abinda Salwa ta" "aikata, toh ko dai he threatened her ne Aryaan ɗin dan zai aikata fiye da haka ma." "Bappah dai Nasiha ya shiga musu once again cike da fasahar sarrafa magana, ya musu nasiha" "akan fushi! Ɗaukar hukunci a hannu, da kuma barin emotions ɗinsu yana shiga tsakanin zumuncinsu, ba ko wani issue bane ya kamata yayi turning into war, ƴaƴa duka nasu ne sannan duka iyayensu ne suma, ya sake tabbatar musu da cewa ba’a shiga tsakanin yara dan yanda sukayi handling case ɗin is far better than yadda iyayensu sukayi! Sosai yayi magana kafin ya bada damar a cigaba da gudanar da meeting ɗin kamar yadda aka saba idan akwai wani mai" matsala ya gabatar da shi da dai sauran abubuwa da aka saba yi a kowace meeting! Ba’a jima sosai da cigaba da meeting ɗinba Aryaan yayi excusing ɗin kansa Ameen na "tambayarsa inda zashi ma bai basa amsa ba ya fice a hall ɗin dan ji yayi ya gaji da zama a ciki, ya" ɗan tsaya a wajen hall ɗin yana kallon motoci birjik dake harabar kafin ya fara tafiya a hankali da ƙafa expression ɗinshi unreadable. Bai nisa a tafiyar ba ya jiyo kamar murya a bayan motar da ke pake a ƙofar Muhammad wazeer "turaki, hakan ya sa ya ɗan dakata." “Haba sweetheart! Ke fa daɗina da ke you look and act like kin waye amma sam baki waye ba! Ke kinsan ina sonki amma kiyi ta wani behaving kamar yar ghetto” Harararsa tayi tace “ni dai ka sake mini hannuna yaya hamza bana so or else i’ll tell daddy” ya sake mata hannunta yana murmushi yace “To komai ne sai kin faɗa ma daddy ehn daddy’s princess! Amma tell me meyasa kika rufa ma yaroncan asiri bayan duk abinda ya aikata miki” jingina tayi da ɗaya motar da ke wajen tana pressing phone ɗinta tace “Cause da kaina nake so in rama ai na san ko na faɗa babu abinda za’a masa da ya wuce nasiha "ko faɗa ni kuma i want to make his life a living hell, zai san ni yayi ma……” maƙalewa maganan yayi bayan haɗa ido da shi a tsaye a wajen facing them! Ta miƙe daga jikin motan tana kallonsa tare da ɗan ja da baya, hamza ma ya ɗaga idanunsa ya kalli direction ɗin da take kallo ganin" Aryaan ya miƙe shima daga jikin motar yana haɗe rai yace “Whats the meaning of that?”Ko kallonsa baiyi ba sai Salwa da yake kallo da ta saka hannu ta ri "ƙe gefe da gefen gown ɗinta, ya ƙare mata kallo daga sama har ƙasa dan shi bai ma san sanda" ta fice a hall ɗin ba kafin yace “Zo ki wuce ki koma” ta ɗan ja baya tana kallonsa tare da shagwaɓe fuska!” "“Are you deaf? Dumb? Both?” Ya tambaya strictly yana kallonta, da sauri ta zo ta wuce shi" tana tura baki idanunta cike taf da hawaye. Hamza ya kalleshi rai ɓace yace “kai a su waye zaka ce sai ta koma? Miye haɗinka da ita” kallo ɗaya kawai ya masa ya juya bi "bayanta, sai sauri take yi kar ya cimmata gashi heels ne a ƙafafunta, ya harɗe hannunsa a bayansa yana tafiya a hankali a bayanta ba tare da ya kulata ba, saurin da take yi ya sa ta take gefen gown ɗinta tayi baya baya zata faɗi yayi saurin ja da baya ta faɗi a ƙasa ta fasa ƙara tana yarfe hannunta hawaye na gangarowa kan kuncinta, tana kallonsa ganin yadda ya ɗan ja baya ya barta ta faɗi, he didnt even attempt to help her kuma fa da yayi niyya da zai iya tare ta tunda ba wani nisa ke tsakaninsa da ita ba amma shine ya matsa ya barta ta faɗi har ƙasa, ganin tana ƙoƙ" arin kifa kanta ta cigaba da kuka yace “Ta shi ki wuce ciki” ta ɗago idanunta da ya jiƙe da hawaye tace “Ni bazan iya ba!” Ganin kallon da yake mata ya sa tace “Ƙafana ne ya bugu fa yaya” "“Tashi nace before i slap you” ya faɗa yana mata mugun kallo, a hankali ta soma ƙoƙarin miƙ ewa yana kallonta har ta miƙe kafin yayi gaba ya barta a tsaye, ta bishi a baya tana tafiya a hankali a cikin zuciyarta kuwa Allah ya isa kawai take ja masa tana karkaɗe jikin gown ɗinta da ya taɓa ƙ asa, haka ta bishi a baya har cikin hall ɗin tana kallon yadda yake tafiya a nutse gashin kansa ya kwanta ta bayan kansa da yake babu hula kayan jikinsa kamar wanda yayi highlighting haske da" haibarsa. "Shi ya fara shiga cikin hall ɗin kafin ta shigo tana biye da shi a baya, Ameen ya dinga kallonsu da" mamaki kamar yadda Su lailerh ke kallonsu don basu yi kama da dominsu aka haɗa wanann meeting ɗin ba. 7039695535 "Palmpay," Maimunatu Abdullahi muhd N500 Thank you #banidahujja #Maimoon 09041426598 https://whatsapp.com/channel/0029VbB1qGBFMqrVuPRZ5f2Q BANI DA HUJJAH "Assalamu alaikum lovelies Bani da hujjah is a paid book, free pages kuma basu da yawa sosai, pls" "support me by making your payments kafin end of free pages! Thank you so much as you do, ga masu bukatar biya zasu tura 500 kacal zuwaga" 7039695535 "Palmpay," Maimunatu Abdullahi muhd Sai ku tura min evidence of payment ta 09041426598 on whatsapp Idan kuma katin waya ne zaku tura 500 zuwa ga 07039695535 Thank you 7. "Tun bayan meeting Aryaan ke zaune a cikin motarsa, ya ƙure ac ya kwantar da kansa kawai" tunani kala kala na yawo a zuciyarsa. Knocking glass ɗin da akayi ya sa ya buɗe idanunsa da ke lumshe ya kalli sashen da ake knocking "ɗin, Ameen ya gani a tsaye a wajen yana ƙoƙarin sake knocking! Ya miƙe zaune tare da winding down yana kallon Ameen yace" “Ɗume?” (Miye?) in his native language wato fulani. Ameen yayi murmushi yace “Yau kuma?” Bai jira amsarsa ba yace “Bappah na nemanka……yanzu!” Mayarda kansa yayi ya jinginar after some seconds kuma ya buɗe motar ya fice ya nufi part ɗin bappah Sallama yayi a ƙofar palourn aka amsa tare da bashi izinin shiga! Bappah dake zaune tare da daddy umar ya ɗaga ido yana kallonsa har ya ƙaraso ya zauna a ƙasa ya sunkuyar da kansa dan kwata kwata baya son haɗa ido da Dad ɗinsa not after everything that happened earlier. Bappah yana murmushi yace “babban mutum ina ka tsaya har Aminullahi ya shigo kai banganka ba sai da na aika shi nemanka?” "“Ina mota bappah” ya faɗa a hankali yana ƙaƙalo murmushi, bappah ya gyaɗa kai" “To yayi kyau!” Ya faɗa yana mayar da hankalinsa kan ɗansa suk cigaba da maganan da suke yi hakan ya sa Aryaan ya miƙe ya nufi cikin ɗakin grandmum ɗinsu dan basu waje idan sun gama sai ya dawo! "A zaune ya sameta gefen gado tana lazimi, tana ganinshi murmushi ya bayyana a fuskarta tana" cigaba da jan cazbah tace “Wata sabon gani” murmushi shima yayi this time genuine murmushi yana ƙarasawa gabanta yace “Ba wani wata sabon gani ai baki nemeni ba” tsohuwar cikin wasa ta kawo masa carbi ya kauce yana dariya ya zauna a ƙasa kusa da ita yana cigaba da dariya kafin yace “Ba dai don halinki ba ina wuni” "“Ka manta da ni Aryaan” ta faɗa tana kallonsa fuskarta na nuna damuwa, ya kamo hannunta" yace "“Ni na isa Daada, ya jikinki?”" "“Liar! Ka manta da ni mana” Ta faɗa tana ƙwace hannunta, ya sake dariya yana faɗin" “Zaki fara drama ɗinki koh? Ta yaya zan manta ki loml” "“Uhm naji, ya aikin naka? Ya Asiya kana zuwa kana dubata kuwa” ta faɗa tana rage" "murmushinta, yanda tayi tambayar doesnt show she really cares idan yana zuwa ɗin kawai dai ta" "tambaya ne, shima murmushin fuskarsa ce ta ɗan fara fading yana matsa mata hannunta yace" "“Alhamdulillah Daada, ina zuwa”" "“Hmm, To Allah ya kyauta!, yayi albarka” ya amsa da" "“Ameen, meyasa baki zo meeting ba kika barshi shi kaɗai ya zo?”" "“Uhm bazan iya bane bayana ciwo yake kaikam, ga ƙafa ma ya sakani a gaba” ta faɗa tana ƙo" ƙarin miƙewa ta ɗauko masa ruwa a fridge Ganin abinda take shirin yi yace "“Kinga bar ruwanki, ke bazaki bawa mutum abu mai daɗi ba sai ruwa!”" “To me kake so in baka mai daɗi muhammad” Ta faɗa tana komawa ta zauna tana kallonsa “Kinsan me nake so?” Ta girgiza kai tana kallonsa “Kudi…” dariya tayi tana ɗan tari kaɗan tace "“Kudi kuma wanne kake so Aryaan? Me zakayi da kuɗi, ai akan kuɗi gwara ma kace mata kake so" "in sama maka kayi aure tunda ka gagara samowa da kanka, Your dad and uncles kullum cikin" complain ɗinka suke Aryaan” kallonta yayi sai kuma yayi shiru walwalarsa na ɓacewa kamar bashi ke murmushi yanzu ba. Ta zuba masa idanu tana ta kallonsa tace “Idan kana da wata damuwa ne Aryaan ka faɗa ma Daada” ya lumshe idanunsa ya buɗe yana kallonta yace “Babu” zata yi magana kenan sai ga bappah ya shigo cikin ɗakin yana kallonsu yace “Miye ake tattaunawa” Daada ta kalleshi tace “Maganar dai da baya so ita nake mai shine ya wani ɓata fuska kamar wanda nake bashi "mummunan labari” bappah ya ƙarasa ya zauna a kujera yana kallon yanda Aryaan yayi kicin kicin da face, yace" “What is your problem Aryaan! Yanzu maganan da muke yi da Umar kenan akanka! Yace ya gaji da halinka kuma lokacin da ya ɗiba maka na aure idan ya kai bazai ƙara maka ba dole sai kayi "auren, you will soon be thirty what is the issue?” Shiru yayi yaƙi cewa komai, bappah ya dubi daada yace" “Ko ya faɗa miki matsalar” girgiza masa kai tayi alamun "“Ah, ah” bappah ya sauƙe ajiyar zuciya yana kallonsa yace" “Aryaan! Why do you make things difficult for yourself?meyasa bazaka buɗe baki ka faɗi abinda ke damunka ba kamar yadda kowa ke yi? Duk abinda zaka aikata baka duba miye zai biyo baya sai "dai kawai ka aikata, your dad is very angry at you! daga nan dama kaje can ka bashi haƙuri kaji koh?”" "Gyaɗa kai yayi a hankali ba tare da ya kallesu ba, bappah ya cigaba yana kallonsa" “Now tell me miye salwa ɗin ta maka uhm sarkin ɗaukan hukunci a hannu?” Bai san sanda ya "ɗanyi murmushi ba, Daada ma murmushi tayi tana kallonsa cike da sonsa." Ya gyara zamansa yana kallon bappah yace “Bappah ni fa ba kidnapping ɗinta nayi ba” “To me kayi?” Ya sake gyara zamansa yana kallon bappah yace "“Ban san me yasa duk abinda yarinyar nan za tayi a gidannan kuke kyaleta ba bappah, infact she’" s becoming a bad influence to sauran yaran gidannan! Babu mai mata faɗa babu mai taka mata birki fisabilillah?” "“Inji wa ba’a mata faɗa” daada ta katse shi tana kallonsa, ya mayarda kallonsa gareta yace" "“Okay kinsan cewa morocco zata je wani stupid birthday wai na friend ɗinta, bday ya wuce all" states na nigeria har sai sunyi flying out? Kuma kowa ya zuba mata idanu babu mai kwaɓanta? As small as she’s har zata iya flying out alone for birthday tsakani da Allah fa?” Da mamaki bappah da Daada suke kallonsa dan sam basu san da maganar ba ko da suka ji ta shiru fiye da sati bata lekosu ba Ameenu cewa yayi ta tafi relative ɗin Amminta! Daada ta tafa hannuwa tana kallonsa tace “Amma Ameenu dai bashi da hankali! Kai innalillahi” ta juya ta kalli mijinta da shima ita yake kallo tace “Kuma fa babanne ya goya mata baya haka wallahi na sani yanzu haka Amminta ta hana suka ƙi hanuwa” Bappah ya gyaɗa kai yace “you did right amma da ka sani you report to me or your dad ba ka ɗ "auke ta ka kaita wani waje for this long ba, duk da anyi avoiding drama ɗin da suka faru saboda" hakan” Aryaan ya gyaɗa kai a hankali tare da faɗin “toh ayi hakuri in sha Allah it wont repeat itself” a "zuciyarsa kuwa shi ya san ba iya wannan dalilin bane ya sa ya rufeta! Ya jima sosai yana tarata dama already kwata kwata yarinyar bata yi masa ba rawan kanta da rashin kunyarta yayi yawa da ya sa ko kadan baya son yarinyar! Duk cikin ƙannensa she’s one da baya son ko ganinta saboda ya tsani sangarta a rayuwarsa, but duk da haka ba zai iya canza ta a matsayin jininsa ba hakan ya sa da yaji labarin she’s flying out for birthday a bakinsu lailerh kuma wai har Amminta ta hanata" amma Uncle Ameenu yace a barta tayi abinda take so ya ƙudurta bazata je ba! dan birthday ne "irin na marasa ji marasa kuma Kamun kai zasu je yi can ɗin! Hakan ya sa ya aikata abinda ya aikata, kuma ya tabbatar sai after birthday ɗin kafin yayi releasing ɗinta shima kuma cause of her school da zasu yi resuming cikin week ɗin, cikin satin da take wannan gida ko kaɗan Uncle Ameenu bai kawo Salwa bata Morocco bane saboda Aryaan always replies his messages da yake turawa salwa time to time! Wannan yana cikin dalilin da ya sake harzuƙa uncle Ameenu ganin rainin wayon ya kai rainin wayo! Aryaan wish yarinya ce da zai iya hukuntawa kamar su lailerh da tabbass duk wani rashin ji wallahi sai ta daina shi saboda yadda zai gyara mata zama amma inaa, duk wani abu da ya haɗa da Uncle Ameenu baya son shigarshi, shima wannan ɗin dana sanin" shiga maganar yake da ya sani ya barta taje duk abinda tayi ruwanta ita da babanta. "“Allah ya kyauta” muryar bappah ya katsesa dan duk maganar da suke ma shi bai ji ba, bappah" yana kallonsa yace "“To kai kuma back to maganar da baka so, akwai ko babu”" Murmushi yayi yana shafa kansa ya kishingiɗa da kujera yace “Babu Allah bappah” bappah ya daina murmushin da yake yi yana kallonsa yace “Ban gane babu ba ka ɗauki abinnan wasa koh?” Langaɓe kai yayi yana kallon bappah yace “Dan Allah bappah kayi ma daddy magana wallahi ni bani da kowa ni ban shirya ma aure ba "bappah, Daada pls talk to them! Ga nan Ameen shima ace ya kawo mata mana bappah”" “Sai yaushe kenan zaka shirya ɗin? Banda shashanci shekara kusan talatin kace baka shirya ba! Shi Aminullah ai baya rashin ji shiyasa basu damu ba ko da yaushe ya gabatar da mata is fyn amma kai kam dole kayi aure idan ka ajiye iyali zaka fi natsuwa i’m with your dad and uncles on this” “Innalillahi! Daada talk to him pls he listens to you! Wallahi idan ba dai auren dole zaku mini ba "ni bani da wata i’m serious, kuma a wata biyu ni bansan a ina zan samo ba”" Shiru bappah yayi yana kallonsa kamar wanda wani tunani ya zo masa sai kuma yayi murmushi yace “Its alright! Tashi kaje ka bawa babanka hakuri kaje sai da safe” ganin yanda bappah ke murmushi yasa yace "“Thank you bappah for understanding me, dan Allah ka musu magana”" "“Zan musu, tashi kaje” tashi yayi yana shafa kansa yace" "“Nagode bappah, sai da safe! Sai da safe Daada!” Suka amsa masa da" "“Allah ya tashe mu” ya juya ya nufi barin ɗakin, sai da ya fice kafin Daada ta kalli bappah" “Amma da ka bari yayi auren wallahi ni bana son rashin jinnan da yake yi wallahi” “Zaiyi! Kafin ma wata biyunnan zaiyi kar ki damu” “Ta yaya?” Ta tambaya tana kallonsa “I just thought of something yanzunnan ” "Later that day da dare suna zaune a dining suna cin abinci, Mami ta kalli Aryaan dake ta juya" "cokali amma ko loma ɗaya baiyi ba har sannan, kallon Ameen tayi da ke cin abincinsa a nutse ta ajiye cokali tace" “Aryaan ci abinci mana” Ameen ya ɗaga ido ya kalleshi sai kuma ya fara dariya! Mami ta kalli Ameen tace “Kai kuma fa?” “Wai fa Daddy Umar ne yace masa ya kwaso kayansa ya dawo cikin gida ya bar wancan gidan nasa with immediate effect shine tun da ya baro wajensa yake ta cika yana batsewa!” Mami ta ɗanyi murmushi tana kallon Aryaan da ya ɗaga idanunsa yana kallon Ameen fuskarsa a mugun haɗe. "“Da yaushe ne yace maka hakan Aryaan?” Mami ta faɗa tana kallonsa, ya sauƙe idanunsa yana" juya rice yace “Ɗazu ne” “To miye abin damuwan dan ance ka dawo cikin gatanka Aryaan! Cikin ƴan uwanka!” Shiru "yayi bai ce komai ba, ta zuba masa ido tana kallonsa kafin tace" “Idan ma baka son zama can part ɗinku ga nan gidan sai ka tattaro kayanka ka dawo nan kawai "kaaji” sai a sannan ya kalleta ya gyaɗa kansa a hankali, feeling a little bit relieved dan tunda Dad yace ya tattaro ya dawo gidan babu abinda yake tunani irin zaman gidan Dad ɗinnasa da baya jin" zai iya! Ameen dake murmushi yace “Gaskiya ya tafi gidansu kar ya takura mini” “Sai dai kai ka tafi gidanku shikam nan ne gidansu” Mami ta faɗa tana murmushi. “Yanzu yaushe zaka kwaso kayannaka?” “Gobe in sha Allah” “To Alllah ya kaimu” duk suka amsa da “Amin” Salwa ce ke saukowa daga sama waya kare a kunnenta tana magana da raliya da sai jiya suka "dawo daga morocco ashe, tana sanye da girlfriend jeans da top mai kyau da ya nuna flat tommy da perfect figure ɗinta, kanta ba ɗankwali sai siririn headband da ta sa a ta gaban gashin, ganin Amminta a palour tayi ma Raliya sallama tana ƙarasawa cikin palourn ta ɗan rungume Ammi ta baya kafin ta zagayo ta zauna a ƙasa kusa da ita, Ammi na kallonta tace" “Kinyi isha’i?” “Nayi Ammi” “Tsakaninki da Allah kinyi” “Wallahi Ammi fa nayi” ta faɗa a shagwaɓe "“Idan ma baki yi ba ke kika sani! Tsakaninki da ubangijinki, kuma kin sani Allah yana kallonki”" “Ammi nayi fa” Ammi bata sake kulata ba ta cigaba sauraron voice note ɗin da only sister ɗ inta ta mata on whatsapp. Miƙewa Salwa tayi ta nufi hanyar ƙofa Ammi ta kalleta tace “Ina zaki da darennan!” “Wajen Siyama zan duba abu ne a anatomy textbook ɗinta” “A haka zaki fita babu ɗankwali? Ke kam miye ɗankwali ya miki ne a rayuwarki Salwa? Wallahi "ni banga anfanin islamiyyar da kike zuwa ba Salwa kin fi so ki dinga yawo da kai a buɗe mala’iku na tsine miki koh? Kin fi so ki je ki kwaso ma kanki abinda bazaki iya ba koh salwa! Wallahi na gaji da magana akanki ki kiyayi randa zan fara saka hannu a jikinki saboda ɗankwali Salwa!” Tsayawa tayi a bakin ƙofa tana kallon Ammi a shagwaɓe kamar zata yi kuka, ganin Ammi ta miƙe" "ya sa ta wuce sama da gudu tana hawaye, Ammi ta bita da kallo tana faɗin" “kuma ki cire cingam ɗinnan a bakinki dan ubanki..” ganin har ta riga ta haura ya sa ta koma ta zauna tana cigaba da replying sister ɗinta wanda ba maganan kowa suke ba face na Salwa still. #banidahujja #Maimoon 09041426598 https://whatsapp.com/channel/0029VbB1qGBFMqrVuPRZ5f2Q BANI DA HUJJAH "Assalamu alaikum lovelies Bani da hujjah is a paid book, free pages kuma basu da yawa sosai, pls" "support me by making your payments kafin end of free pages! Thank you so much as you do, ga masu bukatar biya zasu tura 500 kacal zuwaga" 7039695535 "Palmpay," Maimunatu Abdullahi muhd Sai ku tura min evidence of payment ta 09041426598 on whatsapp Idan kuma katin waya ne zaku tura 500 zuwa ga 07039695535 Thank you 8. "Kamar yadda ya faɗa ma Mami washegari ya je gidan dan ɗauko boxes ɗinshi, har cikin zuciyarsa" "ba son komawa family house ɗinnan yake ba amma yadda ran Dad ke ɓace ba yadda ya iya, babu any room for musu." Boxes uku yayi na kayansa waɗanda zai buƙata dan ya riga ya sa a ransa ba wai ya koma gidannan "bane forever, ko ya zaiyi zai shawo kan dad ya barsa ya bar gidannan, yanzu dai he’ll be there for the meantime tukunnan." "Dakatawa yayi da haɗa kayan ya riƙe jikin siff ɗin yana kallon akwatunan sai kuma ya ɗan ja tsaki ƙasa ƙasa, kwata kwata rayuwarsa is messed up! Baya jin daɗin rayuwarsa ko misƙala zarratin! Duk da kasancewar mahaifinsa babban soja, family ɗinsa well reputed sunansu ya zaga ko ina, amma deep inside of him ya rasa what is the missing piece da babu a rayuwarsa da yake sa yake jin rayuwar a wargaje, menene wannan missing piece ɗin da ya kamata ya tattaro" rayuwarsa duka ya saka glue ya manne su waje ɗaya. "Yana saukowa da akwatinan palour ya fara kakkashe appliances na gidan aka buɗe ƙofa, ya juya ya kalli Aneela da ta shigo cikin palourn tana kallon boxes ɗin da ke palourn kafin ta mayarda idanunta kansa ganin ya kashe tv da wutan passage ɗin yana ƙoƙarin kashe wutan palourn gaba" ɗaya tace "“Love”kamar bai ji ta ba ya wuce kitchen few seconds later ya fito, tana nan tsaye inda ya barta" tana ta kallonsa confused. “Baby whats going on?” Ta faɗa finally bayan tayi mastering enough courage ta ajiye jakarta ta ƙarasa ta riƙo hannunsa. “Ina zaka haka da duka boxes ɗinnan?” “Gida” ya bata amsa a taƙaice “Wani gida?” Ɗan kallonta yayi ya zare hannunsa a nata ya ɗauki box ɗin ya kai bakin ƙofa ya dawo sai sake ɗaukar wani “Okay kafin ka tafi can i talk to you for a moment?” Ya ajiye akwati ya rungume hannunsa yana "kallonta da idanunsa da ya sa taji jikinta ya mutu, ta ɗan langaɓe kai ta ƙaraso ta rungumesa a" hankali duk da baiyi hugging ɗinta back ba amma bata damu ba ta cigaba da magana "“Baby ka min magana mana, me yake damunka? Yaushe rabon da ka ɗaga wayata? Yaushe" "rabon da ka zo apartment ɗina ko school ɗinma na manta rabon da ka zo da sunan ganina, dan Allah dont punish me for laifin da bansan na aikata ba kaji kasan ina sonka sosai kai ne rayuwata ka sani” ta faɗa tana zagayo hannunta a wuyansa ta ɗago face ɗinta tana kallon nasa, ta ɗan" ɗaga ƙafarta to match his height da niyyar sumbatarsa. Sai a lokacin ya warware hannunsa yayi wrapping around bayanta ba tare da ya bari ta sumbace "shi ɗin ba, ya juyata ya jingina ta da bango yana kallon cikin idanunta, murmushi tayi tana kallonsa itama tare da cije lips ɗinta, ta kama hannunsa ta ɗaura akan ƙirjinta a hankali tana kallon idanunsa, ya sauƙe idanunsa ya kalli inda ta ɗaura hannunnasa kafin ya saketa ya ɗan ja baya a hankali, da mamaki ta dinga kallonsa ya ƙarasa zai ɗauki akwatin da bai ɗauka ba ɗazu tayi saurin riƙo hannunsa idanunta cike taf da hawaye tace" "“Aryaan! zaka aureni pls?” Ɗan kallonta yayi na few seconds cause bai tsammaci wannnan tambayan ba, sai kuma ya kamo hannunta ya jata har kujera ya zauna ya zaunar da ita, ya kamo" fuskarta ya ɗan sunkuya ya sumbaci goshinta kafin ya ɗago yana kallonta yace “Lets talk” ta gyaɗa masa kai kawai tana kallonsa dan a halin yanzu babu abinda take son sani irin abinda ke zuciyarsa game da ita. "“Aneela ba tun yau ba kin tambayi this same question idan zan aureki ko ah ah, the answer is" No! Aneela kuma kema kin san dalilin da yasa amsata ya kasance haka!” Hawaye ya gangaro idanunta tace “Saboda Al’ameen yace kar ka aureni koh? Saboda yace maka ni ƴar iska ce koh? Idan ma iskancinne ai tare mukeyi meyasa ni kaɗai zan karɓi consequence ɗin banda kai” guntun murmushi yayi ya ɗan kau da kansa daga kallonta kafin ya koma yayi relaxing da kujera yana kallonta yace "“Da ni kike iskanci?” Tayi shiru tana kallonsa," "“okay lets get this over with, na farko! Ameen ba shi zai faɗa mini wacce zan aura da wacce" "bazan aura ba since ba shi zai zauna mini da matar ba! I never said i was gonna marry you Aneela, kuma ke kinsan dalilin da ya sa bazan aureki ba, kinsan dalilin da ya sa i never crossed the line with you, saboda duk abinda i cant own i dont keep, duk abinda is not fully and completely mine i" dont attach myself to it.” "Kallonsa kawai take, kafin tace “bangane nufinka ba?”" "“Kinga no need for tone tone! I’m been honest with you, idan har kina da wanda kike ganin is" more serious gwara ki bashi chance” yana faɗin haka ya miƙe itama miƙewa tayi tana kallonsa tace “Amma you are a wicked person Aryaan! Ni zaka ci amana? Bayan ka gama ruguza mini "rayuwata, bayan komai da na sadaukar saboda kai? Bayan duk soyayyar da na nuna maka? This is what you say? This is how you pay back my love for you? To wallahi billahi Aryaan idan har ina doron duniya kuma ina numfashi ni ce nan matarka kuma baka isa ka auri wata mace a duniya" bayan ni ba!” "Daga sama har ƙasa ya ƙare mata kallo kafin ya harɗe hannunsa a ƙirji," “Na ruguza miki rayuwa in what way? By paying your rent and your school fees? By sponsoring "your lifestyle? Sadaukarwa saboda ni? Wanne kenan enlighten me, kinga Aneela i’m not in for this rubbish!”" Katsesa tayi saurin yi tana kallonsa tace "“na baka lokaci na, na baka jikina, na baka respect da duka emotions ɗina” bai san sanda yayi" dariya ba yana kallonta yace “Dont deceive yourself kika bani jikinki? Sanin kanki ne i never crossed that line! Saboda kamar yadda na faɗa miki duk abinda ba nawa bane completely bana buƙata” “Wai kana nufin i sleep around ko miye?” Bai tankata ba ya ɗauki other boxes ɗin ya fitar a "palourn ta biyosa tana cigaba da magana, komawa yayi ya rufe ƙofar palourn bayan ya kashe sauran appliances ɗin duka ya ɗauko jakarta ya ajiye a waje, tana biye da shi tana maganganu marasa kai da gindi tana hawaye, ya fito compound ɗin ya nufi motarsa ya buɗe ya saka boxes ɗ in, yana saka box na ƙarshe a baya ya rufe motar tare da buɗe murfin gaban motarsa zai shiga" ya bar gidan sai a lokacin ta fara kukan gaske ta riƙo hannunshi tana kallonsa tace “Are u breaking up with me?” Ya wafce hannunsa yace “I already did! Goodbye” fashewa tayi da kuka tana riƙosa tace “Pls baby No! Ko bazaka aureni ba na yarda amma kar ka rabu da ni pls” wafce hannunsa yayi "ya shiga motarsa ya rufe ta fara buga glass ɗin kamar mahaukaciya tana kiran sunansa, reverse yayi da ya sa ta matsa daga jikin motar tana zunduma kuka ya nufi gate, mai gadi dake zaune tuntuni yana kallon drama ɗinsu ya taso da sauri ya buɗe masa gate! ya dakata ya sauƙe glass ɗ" in yana kallon mai gadin yace "“Ta fita ka rufe mini gida! Kar wanda ya sake shigo mini gida without consent ɗina, nima zanyi" tafiya i wont be around idan kana so zaka iya zuwa kaga gida”gyaɗa kai kawai mai gadi yake yana amsawa da “Toh ranka ya daɗe” ganin Aneela ta nufo gate ɗin da saurinta ganin yana magana da mai gadi "ya sa ya ɗauki kuɗin da ke dashboard ɗinsa ya miƙa masa yana karɓa ya ja motar ya fice a gidan bai ko tsaya sauraren godiya da yake ta masa ba, ficewarshi yayi dai dai da isowar Aneela gate ɗin, ta dakata tana kallon motar har ya ɓace kafin ta rushe da kuka, ta tsuguna a wajen tana tayi, shi dai mai gadi komawa yayi ya zauna yana kallonta, tausayin mata masu hali irin nata na ratsashi, dama a haka suke ƙarewa kullum suna hanyar zuwa wajen maza ƙarshe mazan su wulaƙanta su saboda dama tun farko basu ɗauke su a masu daraja ba, girma, mutunci, ƙima da daraja da" "Allah yayi ma ɗiya mace duk sun zubar da tasu a gaban mazan, ta yaya bazasu bi kai su taka su" wuce ba? “Allah ya shirya mana haula” ya faɗa a hankali yana gyara zamansa a kujera yana kallonta. Sai "da tayi kukanta mai isarta kafin ta miƙe ta tafi ta ɗauko jakarta da ke yashe a compound ɗin ta nufi gate fuuuu, kamar zata tashi sama dan wallahi yayi kaɗan yace bazai aureta ba, wallahi bashi" da mata a doron duniya bayan ita zata iya zuwa ko wani extent dan ganin hakan ya faru. "From there Aryaan gidansu Umminsa ya wuce straight, Gidansu Umminsa madaidaicin gidane" "mai kyau single storey building, yayi horn mai gadi ya buɗe masa ya shigo da motarsa compound ɗin yayi parking. Sai da ya ɗauki kusan three minutes cikin motar kafin ya buɗe motar ya sauƙo ri ƙe da wayarsa ya nufi cikin gidan." "Tun kafin ya ƙarasa palourn yake jin hayaniyan yara sama sama, ya tura ƙofar palourn da sallama ƙasa ƙasa ya shiga, Umminsa na zaune a kan kujera hannunta riƙe da Marwah tana bata indomie sai juya kanta take bata son ci, Maman marwah ƙanwar umminsa na zaune itama a palourn tana dariya ganin yadda marwah ke kuka bazata ci ba ummi kuma tace sai fa taci yarinya kwata kwata taƙi abinci sai Nono ƙatuwa da ita, babban yayan su Ummi dake zaune shima a" palourn yace “Asiya ki rabu da ita idan bazata ci ba dan Allah” sauƙeta tayi ta ɗan daki jikin pampers ɗinta da wasa tace "“jeki ƴar ƙaniya” dai dai lokacin suka ji sallamarsa, duk suka ɗaga ido suna amsa sallaman." Ganin wanda ya shigo ya sa Abbah Usman sakin fuskarsa sosai yana faɗin “Ahh Aryaan kaine?” Ya cire glasses ɗin idanunsa yana ƙarasowa ya zauna a ƙasa yace “Ina wuni Abba..” ya juya yana kallon maman marwah yace “ina wuni ummah” itama tana murmushi tace “Ahh lallai Aryaan yau dai da rabon zamu haɗu ashe a gidannan! Wato sai dai a haɗu da kai a hanya kai baza dai kazo ma mutum har gida ba koh?” Murmushi yayi ya juya ya kalli umminsa da ta daina murmushin da take yi tun shigowarsa yace “Ina wuni Ummi” “Lfy lau” ta faɗa tana miƙewa ta nufi kitchen dan taimakawa anty husaina matar Abbah usman dan yau full house gidan yake sun zo duba jikin gwaggo. Ummah ta miƙe ta nufi ɗakin gwaggo tana faɗin “Gwaggo guess wa ya zo gaishe ki…?” Shi dai Aryaan binta da ido yayi har ta shige ɗakin kafin ya kalli Yayan Umminnasa yace "“Abbah haidar fa?” Second son ɗin Abbah sa’an Aryaan ɗin, dan ya ma bawa Aryaan ɗin" watanni. "“Tare muke da shi ai, yaje kai Malam check up ne na san sun kusa dawowa ma, bakwa magana a" waya da shi ne” “Munayi” Aryaan ya amsa yana gyara zamansa "Abbah yace “to yayi kyau, Ka shiga ka duba gwaggon”" "gyaɗa kai yayi a hankali ya miƙe ya nufi ɗakin gwaggo,mahaifiyar umminsa," "farar tsohuwan na kwance a kan gado kana ganinta kasan tana ɗan jin jiki duk da yadda Ummi ke kula sosai da ita, tana ganinsa ta miƙa masa hannu tana murmushi, ya ƙarasa ya zauna a gefen bed tare da sa hannunshi a nata ita dai ummah na zaune a bedside tana kallonsu ɗauke da" "murmushi, hannun ya kai bakinsa ya sumbata yace" “Ya jikin gwaggo?” "“To Alhamdulillah muhammad, ina ta cigiyarka shiru abinka”" “Aiki ne ya ɓoye ni gwaggo kuma bansan baki da lafiya ba” "“Aikam dai jiki yaƙi daɗi, sai fatan Allah ya sa mu cika da imani”" “To ke wa ya faɗa miki cuta mutuwa ce? Sai ki ga na rigaki mutuwa ma..” da sauri ta girgiza masa kai tana kallonsa tace "“Kul, in sha Allah ba yanzu zaku mutu ba Aryaan sai ka ga ƴaƴanka har da jikoki, nima in sha" "Allah sai na ga har ƴaƴanka in sha Allah” murmushi yayi ya ɗaga idanunsa ya kalli Ummah ta harareshi, ya shafa kansa a hankali yace" “Ummah tun yaushe ne bata da lafiya?” "“Ban sani ba, ai da ka damu da sani da ka sani” shiru yayi bai sake cewa komai ba," After some seconds ya kalli gwaggo yace “kina son wani abu ne gwaggo in je in samo miki?” Shiru tayi tana kallonsa sai kuma girgiza masa kai "“In sayo miki fruit?” Ɗan murmushi tayi kafin ta jinjina masa kai, yayi murmushi shima ya miƙe" ya nufi hanyar fita Ummah ta bishi da idanu. Fita yayi a palourn Abbah na tambayarsa inda zashi yace yana dawowa. Bayan Thirty minutes ya "dawo gidan da niƙi niƙin kaya, Abbah ya zuba masa idanu har ya gama shigowa da duka cefanen da yayi kafin yace" “Yanzu wa ya saka ka wannan aiki Aryaan” ya sunkuyar da kansa yayi shiru “Toh Allah yayi albarka” da “Amin” ya amsa ya ɗauki ledan fruits ɗin gwaggo ya wuce ɗ "akinta," sai a lokacin Abbah ya kalli Ummi dake zaune a palourn yace “Asiya meyasa kike haka ne? Idan baki ja ɗanki a jiki ba wa zai ja miki shi ne wai” shiru tayi "bata ce komai ba, ya sauƙe ajiyar zuciya yana miƙewa yace" “Allah ya kyauta! Bari in ɗauko su malam a hospital wai motar Haidar is faulty” "“No wonder naji su haryanzu shiru” ta faɗa tana kallon yayannata , bai ce mata komai ba dan" haushin yanda take treating ɗanta yake ji har ransa ya nufi ƙofa ya fice abinsa. "Bayan fitansa Ummah da anty husaina suka fito daga ɗakin gwaggo, ummah ta zauna tana kallon Ummi ganin yadda tayi shiru lost in thought kuma tasan baya rasa nasaba da zuwan Aryaan" gidan. Anty husaina tace “Yanzu Asiya har yanzu bazaki cire abinnan a ranki ki nunawa ɗanki soyayya ba? Kina wahalar da kanki kina cutar da yaro?” Ummah tayi ƙwafa tace “wallahi anty husaina lamarin yaya Asiya sai ita! Dan Allah shi miye laifinsa a duk abubuwan da suka faru yana ƙarami! Me ma ya sani shikam?” Kafin ta basu amsa Aryaan ya fito a ɗakin wanda hakan yayi dai dai da shigowar malam tare da Abbah da yana fita yaci karo da sunyi bolt ma ashe har sun iso sai kawai ya dawo ciki tare da Malam ɗin ya bar Haidar a waje yana waya. Malam na ganin Aryaan ya buɗe ido yana faɗin "“Ahhh lallai manyan baƙi ne a gidannamu ashe” murmushi yayi a hankali yana gaishe sa," Malam ya zauna a kujera yana faɗin “Kuma a cikinku a rasa mai sanarmin Muhammad ya zo?” Ya faɗa yana directing question ɗin to su Ummi. "“Ban daɗe da zuwa ba ai” ya faɗa yana ƙarasowa ya zauna a ƙasa gefensa," "“Toh masha Allah ya gidannaku? Ya bappahnku da su Daada, how’s your Dad? Da kowa kowa?”" “Lafiyansu lau Alhamdulillah suna gaishe ku” "“Muna amsawa masha Allah, amma zaka kai dare ai koh tunda gashi naga har yamma ta fara yi”" “Ah ah yanzu zan wuce but zan dawo gobe in sha Allah” Sai a lokacin Umminsa tayi magana tana kallonsa tace “Ce maka akayi kar kayi dare a nan ɗin kenan” ya dubeta a hankali amma bai ce komai ba. "“Da sun sani ai kar ma su barka ka zo kwata kwata, ko da kai ko ba kai zan rayu” tana faɗa ta mi" "ƙe zata wuce ɗaki, Aryaan ya miƙe ya tsaya yana kallonta yace" "“Ummi..” juyowa tayi tana kallonsa, yana kallonta shima yace" “What wrong have i ever done to you? Miye laifina a duk abubuwan da suka faru? Meyasa laifin "wasu ke shafana? Meyasa kika tsaneni? Me na miki?” Kallonsa kawai take idanunta yayi ja, har ta juya sai kuma ta dawo tana kallonsa tace" “Idan har abinda zai kawo ka kenan Aryaan kar ka sake zuwa inda nake! Kaje can wajen dangin "ubanka da suka fini, zuwan ganin daman da kake mini ma bana so na yafe!” Tana kaiwa nan ta juya zata wuce, Aryaan yayi wani murmushi mai ciwo kafin yace" "“Ko da ban zo ba na san ba zai dame ki ba ummi.. cause u never cared, idan da ace u cared" "bazaki barni at five years ba, da zan iya da na jima da daina zuwa inda kike…” pauuu marin da ta" ɗauke shi da shi ya sa ya tsayarda maganar ba tare da ya ƙarasa ba da sauri Ummah ta taso tana "ƙoƙarin riƙeta, Malam yana kallonta yace" “What kind of behaviour is this Asiya” tana huci ta kalli Aryaan tace “Idan ka kuma mini magana in that tone zaka san ni ce nan na haifeka ba kai ka haife ni ba! Rashin tarbiyyarku ta gidanku ta tsaya iya gidan ubanka! And get out of my house!” "Malam zai kuma magana Abbah ya masa alama da ya barta, tsayawa Aryaan yayi dafe da kuncinsa" "idanunsa sun yi ja, Ummi ta fizge hannunta daga na ummah ta tafi ta kama hannunsa ta ja shi har" "ƙofa a zuciye, binta kawai yake yi dafe da kuncinsa ta buɗe ƙofa ta tunkuɗa sa waje tana kallonsa tace" “Sanda ka koyi respecting uwarka da iya magana da ni u come back! I’m still your mother ko ma miye za’a yi brainwashing ɗinka a nuna maka ba zai taɓa canza matsayina na uwarka ba and for that bazan ɗauki disrespect from my own child ba” tana gama faɗa ta rufe ƙofan. #banidahujjah #Maimoon 09041426598 https://whatsapp.com/channel/0029VbB1qGBFMqrVuPRZ5f2Q BANI DA HUJJAH "Assalamu alaikum lovelies Bani da hujjah is a paid book, free pages kuma basu da yawa sosai, pls" "support me by making your payments kafin end of free pages! Thank you so much as you do, ga masu bukatar biya zasu tura 500 kacal zuwaga" 7039695535 "Palmpay," Maimunatu Abdullahi muhd Sai ku tura min evidence of payment ta 09041426598 on whatsapp Idan kuma katin waya ne zaku tura 500 zuwa ga 07039695535 Thank you 9. Ya kai three minutes a tsaye dafe da kumatunsa kafin ya juya a zuciye ya nufi motarsa kamar zai "tashi sama, ba tare da ya ko kalli Haidar da ke zaune yana waya a compound ɗin ba ya buɗe motar ya shiga mai gadi ya buɗe masa gate ya fice a gidan Haidar ya bishi da kallo." "Driving kawai yake amma zuciyarsa wani irin mugun bugawa da ƙuna da ciwo take masa, dukan steering yayi karo na babu adadi wanda instead of hakan ya sanyaya masa zuciya sai ma sake zafi" da zuciyarsa ke yi! Ganin idanunsa ya fara zama blurry yasa ya gangara gefen hanya ya fara bincika cikin motar inda "yakan ajiye cigarette ɗinsa har ya samo kwalin, ya buɗe motar ya fito ya zaga gefe ya fara kokarin kunna lighter a jikin tabar, da ƙyar ya iya kunna cigarette ɗin da ya saka a baki saboda yadda hannunsa ke shaking ya zuƙa tabar sosai kafin ya furzar da hayaƙin yana jin kamar" zuciyarsa zata kama da wuta. "Sai Wajen ƙarfe shida ya shigo gidan, sau ɗaya ya kalli motar hamza da ya kusa bumping into him wajen gate saboda how reckless yake driving amma ko kaɗan bai biye masa ko ya bi ta kansa ba ya wuce part ɗin Mami, yana gama parking ya fito har sannan idanunsa bai washe daga jan da yayi ba, ƙofar shiga gidan ya nufa dai dai lokacin salwa ta fito daga cikin gidan riƙe da babban textbook na anatomy da wayarta a hannunta Siyama dake bayanta tana tambayarta ko zata shiga school gobe dan a goben zasu yi resuming, dama ita da siyama suke studying same thing madicine suna 200level yanzu haka, apart from rashin ji Salwa is a gifted child, in dai ƙwaƙ walwar kwashe karatu ne Allah ya bata, Lailerh kuma mass communication take yi itama tana" 200level ɗin. "Ko amsa gaisuwar da Siyama take masa bai yi ba ya wuce cikin gida, Salwa tayi dariyar mugunta" tana kallon siyama tace “Ba ke iyayi ba? Ni kinga na gaishe sa ne? Wani yaya ina wuni.. gashi nan ai ya dizga ki maganinki wallahi Allah ya ƙara” Siyama tace “sai miye idan bai amsa ba ni dai ba ruwana gwara ke wallahi bazan ƙi gaishe sa ba ya ci ubana…” "Salwa zata yi magana lailerh ta fito tana tura baki da key ɗin motar Aryaan a hannunta, ta ƙ" "araso inda suke dan dama gidansu Salwa zasu karatu, tana kallonsu tace" “Yaya yace mu kwaso masa boxes ɗinsa mu shigar ciki” Siyama ta tsaya sororo tana kallon "Lailerh da ta nufi motar, Salwa tayi wani dariya tana tauna chewing gum ɗin bakinta tace" “ƙannen yaya ku je ku kai masa kayansa ciki ni kinga tafiyata” da sauri Siyama ta riƙo hannunta tana kallonta tace "“Dan Allah ki jirani, gashi can lailerh ta fito da shi guda uku ne kawai yanzu zan shigar in zo mu" tafi…” Kallon hanyar gate tayi kamar bazata haƙura ta jirata ba sai kuma tace "“yi sauri toh, let me sit there” ta faɗa tana nufar kujera da ke compound can ƙarƙashin flowers, da sauri siyama ta juya ta nufi motar, ta ɗauki akwati ɗaya cikin biyu dake wajen dan lailerh har ta shigar da ɗaya, lailerh ce ta sake fitowa ta ɗauki na ƙarshe tana kallon Salwa irin kallon kin shiga uku sai kuma ta koma ciki ba tare da ta ce mata komai ba, kusan five minutes shiru basu fito ba ta ja tsaki ƙasa ƙasa tare da miƙewa ta nufi gate, har zata fita sai kuma ta fasa" ta juya ta nufi cikin gidan dan ganin uban abinda ya riƙe siyama ɗin. "Buɗe ƙofar palourn tayi bata lura da shi ba har sai da ta shigo tsakiyan palourn ta ganshi a zaune babu kuma siyama bare lailerh a palourn sai akwatunan da suka shigo dashi duka uku a palourn a gabansa, tana ganinsa ta juya da sauri zata nufi ƙofa, buɗe idanunsa da ke lumshe yayi yana" kallonta idanunsa sun sake kaɗawa yace “Come back here! Ke wato kin fi ƙarfin ki ɗauko boxes ɗin right?” Juyowa tayi ta kalleshi amma ta gagara magana! Fuskarsa kaɗai ta kalla ta san akwai abunda ke damunsa daban bayan zancen akwatuna! Ya daka mata tsawa yana kallonta yace “Ba dake nake magana ba!” “Lailerh fa bata ce da ni ba” ta faɗa a shagwaɓe hawaye na ciko idanunta tana dana sanin "shigowa gidannan, da ta sani tayi wucewarta bakinta alaikum." “Kwashesu ki kai sama kafin in fara ball dake” ya faɗa babu wasa a tone ɗinshi. "“Duka?” Ta tambay tana ɗan zaro masa idanu irin sun mata yawa ɗinnan, shiru yayi yana" "kallonta , ganin irin kallon da yake mata ta yarfe hannu tare da ajiye textbook ɗin hannunta da wayarta hawaye na gangarowa ta nufi boxes ɗin ta kama ɗaya, mai da kanshi yayi ya jinginar ya lumshe idanunsa sai dai duk kiciniyar da take da boxes ɗin yana kallonta sarai ta ƙasan idanunsa, tanayi tana yarfe hannu tana hawaye! Da ƙyar ta kai ɗaya sama zuwa bedroom ɗin Ameen, ta sake saukowa tana kallon palm ɗinta wai ko yayi ja, haka ta sake ɗaukar ɗayan tana yi tana kallonshi amma taga idanunsa a lumshe,ta tura baki ta ja akwatin ta fara ƙoƙarin hawa da shi sama, daga ta koma ta gaban akwatin ta tura sai ta koma ta baya ta ja shi ƙiii, danne zuciyarsa kawai ya dinga yi kar ya tashi ya kife ta da mari ganin abinda take masa da akwati amma dai ya shareta, haka ta kai na biyun ta sauƙo zuwa lokacin kukan gaske takeyi dan hannunta da gaske" zafi ya kama yi mata gashi yayi ja. "Tana kuka ta kama na ukun, ta dinga ja da ƙyar ta kaishi rabin stairs, ta zauna a wajen tayi shiru tana kallon tafin hannunta, bata ankara ba ta ga ya miƙe daga kwance da yake da sauri sauri ta mi ƙe tsaya ta kama akwatin tana kallonsa a marairaice, bata san sanda ta sake akwatin ba ganin ya nufota ta kwasa da gudu tayi sama, ya ja tsaki ƙasa ƙasa ba tare da ya bi ta kanta ba ya wuce ɗ" "akin Ameen ya kwanta, kusan ten minutes sai gata nan ta shigo da last akwatin, ta lallaɓa ta ajiye" "shi kusa da ƴan uwansa ta juya ta fice a ɗakin a hankali, dan a zatonta bacci ne ya ɗauke shi, shi" kuwa sarai yana jinta kawai baya son huce haushin da yake ji ne a akanta dan zai iya karya waɗ annan kararen hannuwan nata. “Kai wa yace maka Aryaan ya dawo gidannan?” "“Mummy wallahi ya dawo! Yanzu ma saura kaɗan muyi clashing a gate, ai na so na bi ta kan ɗan" iska da mota kuma dama naji ƙishin ƙishin wajensu kamal wai Dad ɗinsu yace musu Aryaan was instructed da ya dawo cikin gida….” Katseshi mummy tayi ba tare da ta ƙarasa ji ba dan hankalinta na ka first sentence ɗinsa da yace sun kusa clashing da Aryaan ɗin. "“Ni bana son shahshanci kana mota yana mota kake gangancinnan, idan abu ya same ka kuma" fa?” “Ba abinda zai same nj mummy” hamza ya faɗa yana ɗaukan slice ɗaya na Apple cikin wanda "mummyn tasa ke ci, Abida da ke danna wayarta ta miƙe zaune tace" “Yaya Hamza da gaske yaya Aryaan ya dawo?” “Ban sani ba dan ubanki! Dama in ganki kina nane masa ɗinnan wallahi sai na taka wuyanki wawuya” mummy ta haɗe rai tana kallonsa tace "“Miye haka hamza? Kai meyasa bazaka ja ƙanwarka a jiki ba? Kana da wacce ta fita ne? Ku biyunnan fa kune gatan juna ko bayan raina, miye ne dan tana murnar ya dawo? Haba hantarar ai" yayi yawa kuma” "“Mummy kin mance haukan yarinyarnan koh? Wai sonshi fa take yi dan bata da hankali, ki rasa" wanda zaki so sai maƙiyina” “To ina ruwanka idan tana sonshi? Kai da ubanka halinku ɗaya hamza sam hankalinku baya kan "abinda nake so! Hanyar da zaku mulki gidannan ya dawo sai abindq kuka ce! Ba gwara ita bama tunda ko ba komai wanda take so matakala ne na cikan burina, kai kuma fa? Ka rasa wacce zaka" ce kana so a cikin family ɗinnan sai Salwa! Allah ya sauwaƙe in haɗa iri da Ameenu wallahi” "“Taɓdi maganar kuma kike so mummy! Ai wallahi kinma haɗa an gama, ni fa Salwa ita zan aura" "gwara ma ki daina wannan maganar taki, kowa ma yaje ya auri wanda yake so in dai dan na hana" Abida auren ɗan iskan can ne to taje ta aureshi a bar mini salwata” Abida ta taɓe baki dan ita da salwa ko ga maciji basa yi tana kallon hamza tace “Taɓdi wallahi yaya da ka auri salwa gwara….” Ko ƙarasawa bata yi ba yayi kanta yana faɗin “Kutumar ubanki shegiya annamimiya! da in aureta gwara miye? Wato ke kike zuga mummy koh dan uwarki” "“Hamzaa” mummy ta buga masa tsaya, ya dakata ba tare da ya doki Abida ba kawai ya wuce" "fuu ya fice, ita kuma Abida ta bishi da harara harda tsaki, duk da can ƙasan zuciyarta zumuɗi ne da son ganin Yaya Aryaan da ta mallaka ma zuciyarta ya dasa kujera ya zauna a cikin zuciyarta ya ɗaura ƙafa ɗaya akan ɗaya yayi kane kane, kuma mummynta ta mata alƙawari cewa bata da miji" bayanshi. "Washegari Mami na zaune a palour tana kallon daily soap Salwa ta shigo cikin palourn, tana sanye" "da pencil skirt da top, braid guda huɗu da amminta ta mata da gashinta ta sakosu ta gaba, ta ɗ" "aura veil ɗinta kamar ɗankwali hannunta riƙe da wayarta ta shigo cikin palourn, Mami ta ɗaga kai tana kallonta tace" “Baki je school ɗin bane Salwa?” Ɓata fuska tayi tana ƙarasowa ciki tace “Bani da lafiya” Mami ta mayar da hankalinta sosai kanta tana kallonta tace “Subhanallah me ya sameki?” Gefen kujeran da Mami ke zaune ta zauna tana nuna mata hannunta tace "“Ba yaya Aryan bane ya sani kai akwati sama jiya shine hannuna yayi red sai da na shafa balm," da asuba da Ammi ta tashe kuma naji kamar zazzaɓi shine daddy yace kar inje in bari gobe” Mami dai kallonta kawai take yi har ta kai aya kafin tace “Toh sannu Allah ya ƙara sauƙi” “Amin” ta amsa tana kai hannu bowl ɗin dake center table ta ɗauki chocolate guda ɗaya. Mami ta cigaba da kallon da take yi can kuma tace “Ko zaki rakani gidan baffanku Sageer? Wai Tahir bai ji daɗi ba kuma an kawo kayan auren safna "kinje kin gani?” Girgiza kai tayi tana ɗaukan wani chocolate ɗin shekaran jiya Amminta taje kuma sai da tace tazo suje taƙi zuwa, duk da duka gida ɗaya ne amma mutane dayawa cikin ahalinnan sai su jima basu ga salwa ba, dama gidan da tafi shiga daga na Mami sai kuma part ɗin" grandparents ɗinta. "“Ya kamata ki je ki gani ai ki mata Allah ya sanya alkhairi, bari musa ya dawo na aikesa sai ya" kaimu yanzu” Gyaɗa kai tayi sai kuma ta miƙe tana kallon Mami tace “Let me go change my clothes da sauri kafin ya dawo!” “Me ya samu waɗannan ɗin” "“Nikam zan canza…” ta faɗa tana nufar ƙofa da sauri! Tana buɗe ƙofa ta kusa cin karo da shi dan ya kawo hannu zai buɗe kenan yaga an buɗe ƙofar, kallo ɗaya tayi masa ta ɗauke kanta yana sanye da black tshirt da ash sweatpants ƙafafunshi cikin sneakers, daga gani kasan daga workout yake, fuskarnan kamar kullum kamar ko yaushe a haɗe, haɗe ranta tayi itama tana matsawa daga bakin ƙofar ta bashi hanya ya wuce ta ya shige ciki ba tare da ya bata second look ba, ta bi bayanshi da harara kafin ta fice a gidan tana ayyana a ranta abinda zata masa ta rama" duk abubuwan da ya mata. "Da yammacin ranan Aryaan na kwance yana duba project ɗin da yake aiki akai, Ameen kuma na toilet yana wanka dan tun da ya dawo daga office ya kwanta bacci sai yanzu ya farka shine ya" shiga wanka. "Gajiya yayi da duba project ɗin ya ajiye laptop ɗin ya janyo wayarsa, ya fara scrolling a IG har yanzu mood ɗinshi is very off. Har ya wuce post ɗin ya dawo yana kallon hoton da tayi posting twenty minutes ago, da ita da wata da bai san wacece ba yarinyar ta rungumota ta baya ita kuma ta buɗe haƙora duka tana dariya, sosai hoton ya fita yayi matuƙar kyau amma sam ko misƙala zarratin bai burgesa ba ya duba caption ɗin yaga ta sa BFF sai kuma tag na account ɗin wacce ke hoton tare da ita wato Raliya, ga nan likes da yawa da comments kaca kaca wanda mostly na" maza ne masu yaba kyawunta. "Tsaki kawai yaja ya fice a instagram ɗin, yau da su lailerh ne da tabbass sai ya taka wuyansu akan" "post ɗinnan amma anything that involve Salwa and her dad ya tsame hannunsa a ciki, tayi duk abinda pleases her." "Wayar da ya ajiye ya lumshe idanunsa ne ya fara ringing, buɗe idanun ganin sunan Dad ɗinsa a screm ɗin ya sa ya tashi zaune da sauri! Ta ɗauki wayan yayi picking ya kai kunne tare da sallama." Ko amsa sallamar Dad baiyi ba yace “Meet me now a part ɗin bappah! Immediately” yana gama faɗin haka ya katse wayarsa ya ri ƙe wayar a hannunsa yana kallo da tunanin what happened kuma again this time around dan he can sense ɓacin rai sosai ba kaɗan ba a voice ɗin Dad ɗin nasa. Ameen da ya fito yana tsane kansa yace "“Me ya faru?” Ya buɗa masa hannu alamun bai sani ba, sai kuma ya sauƙa a gadon ya nufi ƙ" ofa!” Aryaan ya bishi da kallo yana wucewa dan ɗaukan kayan da zai saka. "Mutanen da ya tarar a palourn ya sa bugun zuciyarsa ƙaruwa dan ya tabbata ba lafiya ba, dan uncles ɗinsa kaf suna zaune a palourn kuma dukkaninsu fuskarsu babu fara’a suke kallonsa, babu wanda nasa yafi basa mamaki irin bappah, ya ƙaraso ciki da sallama sai a loakcin ya lura da" Aneela da ke zaune can other corner na ɗakin idanunta jajir a kumbure suntum. #banidahujja #Maimoon #09041426598 https://whatsapp.com/channel/0029VbB1qGBFMqrVuPRZ5f2Q BANI DA HUJJAH . "Assalamu alaikum lovelies Bani da hujjah is a paid book, free pages kuma basu da yawa sosai, pls" "support me by making your payments kafin end of free pages! Thank you so much as you do, ga masu bukatar biya zasu tura 500 kacal zuwaga" 7039695535 "Palmpay," Maimunatu Abdullahi muhd Sai ku tura min evidence of payment ta 09041426598 on whatsapp Idan kuma katin waya ne zaku tura 500 zuwa ga 07039695535 Thank you 10. Gyara zamansa Aryaan yayi yana sauraren Aneela da ke magana bayan bappah ya bata izinin "maimaita abinda duk ta faɗa, he is not even suprised at all bai san meyasa ba, ba kunya babu tsoron Allah take labarta ƙarya da sharri a gabansa da iyayensa without thinking about the consequence, the only thing da yake yawo a kansa a lokacin shine Al’ameen was damn right ta yaya ma yayi tunanin zai iya auren Aneela in the first place? Wannan abinda da ta aikata ya sake tabbatar masa cewa he made the perfect choice by breaking up with her, mamaki ma yake yadda ta iya shigowa cikin gidan har gaban bappah who allows her in? ya tabbata dole da saka hannun wani cikin family ɗinnan kafin ta iya isowa har gaban bappah, ya ɗaga idanunsa ya kalli uncle Ameenu da uncle muhammad da ke zaune suna kallonta tana bayani, idan ba idanunsa suka masa gizo ba gani yayi ma kamar murmushi ne tucked a lips ɗin uncle Ameenu, ɗauke idanunsa yayi a hankali daga kallonsu ya mayar ƙasa ba tare da ya yarda ya sake kallon face ɗinsu Dad ɗ insa ba dan sosai suka nutsu suna saurarar ƙaryar da take shirga musu suma ransu a ɓace, wani smirk yayi a hankali jin wai har abotion ya sha sakata tana yi and that babanta sent her to school here amma shi ya hanata ya ajiyeta yana biyan bukatarsa da ita with the promise cewa zai aureta! Girgiza kai yayi a hankali yana jinjina hauka da rashin lissafi irin na Aneela, a tunaninta all these da" tayi zai saka ya aureta ne? Ko su zasu tursasa shi ya aureta ne? Infact his own family dai da ya sani this alone da tayi ko shine da kansa yanzu yace zai aureta bazasu taɓa lamunta ba! This is the height of rashin kunya da rashin tarbiyya shi a ganinsa. "Maganarta ne ya katse masa tunaninsa, tana shesheƙar kuka take faɗin" "“Shiyasa na kawo kukana gareku, dan Allah ku mini adalci sir” ta faɗa tana share hawaye" Ajiyar zuciya bappah ya sauƙe bayan ta kai aya ya juya ya kalli Aryaan da har sannan ya kasa haɗa idanu da kowa kamar yadda Aneela taƙi yarda ta kalli sashin da yake. "“Muhammad” bappah ya kira sunansa, a hankali ya ɗago kansa yana kallon bappah yace" “Na’am bappah” "“Ka san wannan yarinyar?” Ya tamabaya yana nuna masa Aneela, gyaɗa kansa yayi a hankali ba" "tare da yace komai ba, Dad ɗinsa ya dinga kallonsa da mamaki tare da takaici duk a haɗe!" "“Ka santa kace?” Ya sake gyaɗa kansa ba tare da ya ce komai ba," "“Duk abinda ta faɗa gaskiya ne kenan?” Girgiza kai yayi a hankali ba tare da ya ɗago ba," Uncle Ameenu yayi caraf yana kallon Aryaan rai ɓace yace "“Maƙaryacin banza maƙaryacin hofi!” Dad Umar ya kalli Ameenu bai dai ce komai ba," “Sharri kake so kace tayi maka? Mu ba ce mana kayi baka da wata mace da kake nema ba? Ba "zaka kuma iya providing mata a wata biyu ba, mu zaka zubar wa mutunci? Mu zaka ɓatawa suna? To wallahi billahi baka isa ba! Tunda har kace ka santa that means duk abinda ta faɗa akanka gaskiya ne, kuma zaka aikata” Uncle Ameenu ya cigaba yana yi yana nuna Aryaan ɗin da yayi" shiru kawai yana saurarensa ba tare da yace komai ba. "Bappah ma kallon Aryaan ɗin kawai yake yi, duk labaran da ake kawo masa na rashin jin Aryaan bai taɓa yarda one hundred percent ba sai yau, he’s so disappointed in him, wai ace jininsa ne ke irin wannan bayahudiyar rayuwa! Da ƙyar yayi composing kansa ya dubi Aneela dake share" hawayen har sannan yace "“I’m deeply sorry for this my daughter!” Da sauri Aryaan ya ɗaga kai ya kalleshi, he cant" "believe wai bappah haƙuri yake bawa Aneela, ya buɗe baki da ƙyar yace" "“Bappah….” Ɗaga masa hannu bappah yayi, ya cigaba da maganarsa yana kallon Aneela yace" “Idan har everything you have said is true ni na miki alƙawari i will not let it go..”ta gyaɗa masa kai a hankali tana wani sussunkuyar da kai "“But for now ina so ki bamu time, ki je gida we will handle this” gyaɗa kai ta kuma yi duk da" "ba haka ranta ya so ba, so tayi su ce dole sai ya aureta bayan abinda ya aikata mata, ta ɗan kalli side ɗin uncle Muhammad da Ameenu da ba ita suke kalla ba dan ba haka tayi da su ba amma dai sai bata musa ba ta miƙe a hankali ba tare da ta sake kallon kowa a palourn ba ta nufi ƙofa" "tana jan ƙafa ta fice, duk suka bita da kallo banda Aryaan da dad ɗinsa." Shiru palourn ya ɗauka na few seconds kafin dad Umar yana kallon bappah yace “i’ll head to "barrack now akwai abinda zanyi yanzu a can bappah” gyaɗa masa kai bappah yayi dan yasan ba ƙaramin ɓaci ran Umar ɗin yayi ba, Dad Umar ya miƙe ya nufi ƙofa ba tare da ya kalli sashin da Aryaan ke zaune ba, bin mahaifinnasa yayi da idanu, deep down yana jin disappointment in himself for constantly hurting his Dad, ya sauƙe idanunsa ƙasa yana jin wani kalan tsanan Aneela har ƙasan ransa, da dana sanin irin rayuwar saɓon Allah da suka yi da ita dan tabbass wannan ne" ya bata lasisin yi masa wannan akuyancin. Miƙewa Uncle Ameenu yayi yana kallon bappah yace "“I’ll also take my leave” yana faɗin haka ya nufi ƙofa, uncle muhammad ya miƙe ya bi bayansa, dan suna buƙatar iske Aneela kafin ta bar estate ɗin, dama can su suka shigo da ita, uncle muhammad ya zo zai shigo ya ganta a tsaye sojoji sun hanata shiga suna ƙoƙarin humiliating ɗ inta, ya sauƙe glass ya tambayi whats happenening suka ce masa wai wajen Aryaan ta zo amma" "ta gagara kiran line ɗinsa, jin Aryaan yasa yace su barta ta shigo, suka kuwa barta ta shiga motarta ta bi bayansa, sai da ya fara tabbatar da abinda ya kawota zai musu anfani kafin ya sanar da Ameenu shi kuma ya escalating maganar har gaban bappah tare da mata alƙawarin Aryaan ya aureta an gama, now that ta ga ba haka ba they need to silence her ko da kuɗi ne dan su dama burinsu ba wai Aryaan ya aureta bane burinsu Umar da bappah su ga this side of Aryaan da kyau," amma sam Aneela ba dai a zuri’arsu ba. "Bayan fitarsu palourn shiru ya sake ɗauka, daga Aryaan har bappah babu wanda yace komai, kusan mintuna uku kafin Aryaan ya miƙe tsaye a hankali, bappah ya bishi da kallo dan a tunaninsa tafiya zaiyi amma ga mamakinsa sai ya ga ya tafi bookshelf ɗin da ke palourn dake cike da littafan" addini ya ɗauko Al’ƙur’anin bappah ya dawo ya zauna yana kallon bappah yace "“I know you are disappointed in me bappah, kuma nasan you wont believe ko miye zance," amma wallahi..” ya faɗa yana raising alƙur’anin slightly "“Ban taɓa having anything with her ba, ba wai ita kaɗai ba, ive never had anything with any" "woman!” Shiru bappah yayi yana ta kallonsa, ganin yayi shiru ya sa ya sake faɗin" “Trust me pls” gyara zamansa bappah yayi yana jin kaso mai yawa cikin ɓacin ransa na evaporating "“Meyasa baka faɗi haka a gaban parents ɗinka ba?” Shiru yayi ya gagara amsawa, bappah ya" jinjina kai yana kallonsa yace "“Toh naji! Yanzu ina so ka faɗa min da bakinka who she is, miye kuma haɗinka da ita?”" "“She was my girlfriend, kuma na san na aikata kuskure da hanyar bata too much access to" "rayuwata, da yin abubuwa da yawa da addinina bai lamunce mini in yi da ita ba amma wallahi" bappah babu zina cikinsu duka” "Studying ɗinshi kawai bappah yake yi, duk da yasan ƙarya ba halin Aryaan bane dan tun yana ƙ arami he’s a very straight forward person idan yayi abu yayi ne ko yanka shi za’a yi zai ce yayi, haka idan bai yi ba ko za’a halakasa bai yi ba. Ganin bappah yayi shiru yana ta kallonsa ya sake" cewa “I’m not lying!” "“I know!..” bappah ya faɗa yana cigaba da kallonsa," “But still ina so in san dalilinta na aikata hakan” “Saboda nace i cant marry her” "“Why cant you marry her?” Shiru yayi, bappah ya ɗanyi guntun murmushi yace" "“Tashi kaje, i know exactly me zanyi ya kawo ƙarshen komai, idan ma gaskiya kake faɗa ko akasinsa” gyaɗa masa kai yayi a hankali ya miƙe ya mayar da Qur’an ɗin ya dawo ya nufi ɗakin" Daada walking slowly…. Karatun alƙur’ani ya sameta tana yi tana ganinshi ta ƙarasa ayar da take karantawa tana murmushi tace “Muhammad” "“Na’am” ya amsa ƙasa ƙasa yana ƙarasawa dogon kujera dake ɗakin ya kwanta ya lumshe idanunsa, shiru tayi tana kallonsa kamar zata masa magana kuma ta fasa ta cigaba da karatunta a" "hankali, tun yana jin karatun ƙasa ƙasa har bacci ya ɗauke shi.." "Ko minti goma baccin baiyi da ɗaukarsa ba muryarta ya tashe shi, Har tsakiyar kansa yake jin muryar kamar wata gyare banda surutu babu abinda takeyi, tun daga palourn Bappah har ɗakin daada ana jiyota! Kuma ya san bazai wuce ita da bappah ɗin ba dan wannan wasa na jika da kaka" tafi kowa yinsa da bappah kuma shima yake biye mata. "Tashi yayi zaune a hankali ya dafe kansa da hannu biyu, Daada ta dubeshi tana rufe alƙur’anin" tace “Ta tasheka koh? Ai wannan yarinya Salwa kam sai a hankali” shiru ya mata bai ce komai ba "saboda ciwon da kannasa ya fara masa, dai dai lokacin ta buɗe ƙofar ɗakin Daada, tun daga" bakin ƙofa tace "“Daada am” tana shigowa cikin ɗakin ta nufi Daada, sai dai wanda ta gani a zaune dafe da" "kansa yasa ta ja ta tsaya sai kuma ta juya ta nufi ƙofa, Daada na mata magana ma ko juyowa batayi ba ta fice a ɗakin, ya ɗan ja guntun tsaki tare da miƙewa ya nufi ƙofa shima Daada ta" bishi da kallo… "Yana fitowa palour ya tarar bata nan, bappah yace “kai ka korota hala?”" "“Ita wa?” Ya tambaya a hankali yana zama a kujera," "“Zaka santa soon” shiru yayi bai ce komai ba, bappah yace" “Baka da lafiya ne?” Ya ɗan gyaɗa masa kai yana nuna masa kansa "“Sannu kaje ka sha magani ka kwanta, bari in ga ko daada na da paracetamol” ya faɗa yana mi" ƙewa ya nufi ɗakin Daada. Sai da ya sha maganin kafin ya wuce masallaci tare da bappah dan sallar Maghriba kafin ya wuce gida. "A hankali salwa ke haura stairs ɗin without making any sound dan bata son ko su Lailerh su san ta shigo, sannan sai da ta tabbatar Ameen ya tafi masallaci kafin ta shigo, successfully ta gama haura benen ta buɗe ƙofar ɗakin Ameen ta shige ta rufo ƙofar tare da riƙe kunkumi tana kallon ɗakin, bata ma san miye ya kawota ko miye take nema ba abinda kawai ta sani shine duk wani abu nashi mai muhimmanci yana nan, ta fara kalle kalle, ɗakin is very clean babu tarkace bare ta gane inda kayansa suke, wadrobe ta buɗe ta ƙare ma kayan ciki kallo kafin ta rufe, ta ɗan ja tsaki dan" bata ga wani abu mai muhimmanci da idan ta lalata masa zai ji haushi ba. "Har ta juya zata fita idanunta ya sauƙa akan laptop ɗinsa dake gefen bed, ta san wannan ba laptop ɗin Ameen bane so definitely nasa ne, haka kawai taji this is it, ta nufi laptop ɗin da sauri ta zauna gefen bed ta janyo laptop ɗin ta buɗe tana faɗin" “Lets see what u got here” wani murmushi tayi ganin screen ɗin babu password this seems easier than she imagine. "“He’s actually stupid, wa ke barin stuffs ɗinsa without password yanzu..” ta faɗa a hankali" tana gyara zamanta a kan gadon. "Tana buɗe screen ɗin taga already it was opened to his work, ta zuba ma screen ɗin idanu tana" "kallon kyakkyawan 3D model na zane dake kan screen ɗin da bata wani gane kansa ba, abinda" "kawai ta sani shine it was beautiful and massive too, ɗan matso da fuskarta tayi kusa da screen ɗ" in sosai tana kallo ba ƙaramin birgeta zanen yayi ba "“Whats this..” ta faɗa amused, ba wai building bane kawai, zane ne da ta gagara gane miye ne," "abubuwan da ta gane a ciki kawai highways da yayi mapping, inda yayi indicating ruwa, da kuma skyscrappers, ko ma dai menene wannan ba ƙaramin abu bane, komai was engineered to" perfection. a can saman screen ɗin taga an rubuta Arewa crown development pan african financial and cultural district Lead architect: Aryaan Umar Turaki Ɗan buɗa idanunta tayi tana cigaba da kallo a zuciyarta tana mamakin shi yayi duka wannan ɗin? "Tanƙwashe ƙafafunta tayi ta cigaba da kallo tana clicking tana buɗe other files ɗin, babu abinda bai tsara ba, interior layouts, phase of construction, and many more." Babu tsoron komai ta hau deleting files ɗin tana yi tana kallon ƙofa sai da ta goge su tass har wa ɗanda bata buɗe ba kafin ta miƙe da sauri jin taku outside door ɗin dai dai lokacin ya turo ƙofar ɗakin ya shigo…. #Banidahujja #Maimoon 09041426598 https://whatsapp.com/channel/0029VbB1qGBFMqrVuPRZ5f2Q BANI DA HUJJAH "Assalamu alaikum lovelies Bani da hujjah is a paid book, free pages kuma basu da yawa sosai, pls" "support me by making your payments kafin end of free pages! Thank you so much as you do, ga masu bukatar biya zasu tura 500 kacal zuwaga" 7039695535 "Palmpay," Maimunatu Abdullahi muhd Sai ku tura min evidence of payment ta 09041426598 on whatsapp Idan kuma katin waya ne zaku tura 500 zuwa ga 07039695535 Thank you 11. "Daga sama har ƙasa ya ƙare mata kallo ganin yadda tayi tsuru tsuru a tsaye, kana ganin idanunta ka ga mara gaskiya kafin ya juya ya kalli gadon inda laptop ɗinsa ke ajiye a buɗe, bai san sanda ya haɗe girar sama da ta ƙasa ba yana takawa zuwa cikin ɗakin sosai, Ameen dake biye da shi a" baya shima ya ƙaraso ciki yana kallon Salwa yace “Me kike yi anan?” "“I….i…na zo ne… ina so..” ganin Aryaan ya ɗauki laptop ɗin tayi hanyar ƙofa da gudu zata fita, shi dai Ameen bai ga sanda Aryaan ya ajiye laptop ba sai gani yayi ya cafko ta, ta fasa ihu tare" da tsugunawa ƙasa tana kallonsa har ta fara hawaye “Wallahi ban sani bane yaya…” da Sauri Ameen ya matso yana faɗin “Sake mata hannu mana dan Allah kar ka karyata miye ta maka?” Janyota ya soma yi zai mayar "da ita gaban laptop ɗin, ta lanƙwashe a ƙasa tare da taƙarƙarewa ta kurma ihu ko Mami zata ji" ta ta zo ta taimaketa! Ameen that is confused ya sake biyo sa yana faɗin "“Wai miye ta maka ne? Meyasa idan bakayi mugunta ba baka jin daɗi” ko kula Ameen baiyi ba," "yana riƙe da hannunta da hannunsa ɗaya ita kuma tana tsugune a ƙasa ya buɗe laptop ɗin, he was so shocked da bai san sanda ya sake hannunta ya dafe bakinsa ba, tunda ya ga laptop ɗinsa a buɗe yasan ta taɓa kuma ganin zata gudu ya san ɓarna ta masa amma bai taɓa expecting abinda ta aikata kenan ba, project ɗinsa na wata da watanni? Idan bai halaka ta ba sai dai idan ba sunansa Aryaan ba, a zuciye ya juyo sai dai wayam har ta tattare skirt ɗinta ta gudu ta bar ɗakin," Ameen ya matso ya leƙa screen ɗin yana faɗin "“Wai miye tayi ne” kanshi da already ke ciwo yaji ya sake sara masa, idanunsa suka kaɗa lokaci" ɗaya yana kallon Aryaan kamar wanda baya son yayi believing abinda ya gani yace “She deleted Arewa crown development project” zaro idanu Ameen yayi yana kallonsa yace "“No way! you dont mean it… innalillahi” ya faɗa yana janyo laptop ɗin yana dubawa, Aryaan" "ya samu waje ya zauna a gefen bed ya dafe kansa, project ɗinnan bai taɓa babban project irinsa" "ba, his hardwork for months ta goge cikin mintuna? Wace iriyar yarinya ce Salwa?" Fuskar Ameen cike da alhini yace “Subhanallah kuma baka da any back up” shiru yayi kawai ya gagara magana.. Ameen ya miƙe yana sake jinjina lamarin yace “Kayi haƙuri haka Allah ya ƙaddara…” wani banzan kallo ya masa daga sama har ƙasa kafin ya miƙe yana kallon Ameen yace "“Ai wallahi idan kaga abinda ya hanani karya yarinyarnan rasuwa nayi, gobe ko tsinke aka ce" "mata nawa ne zata kiyaye sa..” yana gama faɗin haka ya nufi ƙofa zai fita, Ameen yayi saurin shan gabansa yana kallonsa yace" “Kar ka taɓata please yarinya ce…” bai san sanda ya hankaɗa Ameen ba yana huci yace "“Motsin gado ce ba yarinya ba, kasan girman Allah ko da kuɗi aka bata ta bi hanyar da na bi ma" bazata sake bi ba..” Ameen dake ta kallonsa yace “Akan project ɗin banza zaka taɓa lafiyarta ta?” "“Ba na banza bane, its my hardwork, wahalata ce na months, why am i even explaining it to you?" Ka zauna kana son Yarinya ƙarama shiyasa duk inda raini yake ta rainaka to billahi ƙaryarta ta rainani ba sunana Al’ameen ba kuma banyi mata kama da saurayinta ba..” sororo Ameen ya tsaya yana kallonsa har ya kai ƙarshe kafin yace "“Bismillah je ka, idan ka barta da rai yau baka cika Aryaan ba, kuma sanin kanka ne ni ba soyayya" "nake da ita ba bare kace saboda haka ta raina ni infact respect ke tsakanina da ita more than you could imagine, to idan ma soyayyarce why is it your problem? Ko dan Albarkacin son da ka san ina" mata ba zaka mini kara ka mata uzuri ba? Amma a gabana kake cewa zaka daketa?” “Ai ka san girman Allah ko kai ne ka goge abinnan duka zan maka bare wata wacce kake so na banza da hofi…” yana faɗa ya raɓa gefensa ya fice a ɗakin Al’ameen ya bishi da kallo Ganin yadda ta shigo cikin palourn tana ƙoƙarin haurawa sama da gudu ya sa Ammi dake shirya dining faɗin "“Zo nan..” sai da ta kalli sama ta kalli ƙofa kafin ta nufi wajen Ammi jikinta na mazari, dan daga" yadda taga yayi reacting ba ƙaramin ɓarna ta aikata masa ba “Miye haka? Meyasa zaki shigo mini gida da gudu wa ya biyo ki?” Tana yi tana kallo ƙofa tace “Babu!” “Bazaki faɗa mini wa ya biyo ki ba sai na kwaɗa miki cokalinnan...” Ammi ta faɗa tana dakatawa da jera abincin.. "“Ammi dama yaya ne ban sani ba na…..” dai dai lokacin ya buɗe ƙofar palourn ya shigo, ta kurma ihu ta nufi sama da gudu, Ammi ta bita da kallo, amma ga mamakinta sai taga Aryaan ya" "bita saman, Ammi tayi saurin ajiye spoon dake hannunta tana faɗin" "“Lafiyanku kam?” Ta faɗa tana nufar saman itama, a bakin ƙofar ɗakinta ta same shi salwa ta" "shige ta rufe da makulli, Ammi ta tsaya tana kallonsa kafin tace" “Laifi tayi hala?” Sai da ya sauƙe ajiyar zuciya kana ganinsa kasan ransa a ɓace yake kafin ya juyo ya kalli Ammi yace “Ina wuni” “Lafiya lau miye tayi maka?..” ta sake tambaya tana kallonsa “Babu!”Kawai ya faɗa yana nufar stairs ta bishi da kallo har ya gama sauƙa ƙasa kafin ta nufi ƙ ofar salwa ta buga tace “Zo ki buɗe mini..” “Ammi yaya yana nan?” “Ban sani ba ki zo ki buɗe mini nace” a hankali ta buɗe ƙofar Ammi ta tura ta shiga tana kallonta tace “Me ya haɗaki da shi da ya biyo ki har nan?” “Wallahi Ammi ni babu abinda na masa kawai dan na ɗan taɓa laptop ɗinsa ne shine….” "“Ƙarya kike yi akan haka ba zai biyo ki har nan ba na san halinsa, ba za dai ki raba kanki da wasan banza da mazan gidannan ba koh? Ban hanaki ba? Idan ya karyaki a banza wa yake da asara? Ki janyo babanki yayi ta jarabar da ya saba koh bayan ke kike fita kike nemo duk wani abu da ke samunki koh? Na rabaki da hamza kinki ji yanzu kuma Aryaan kike neman maganarsa? Baki san har yanzu haushin ɗaukarki da yayi nake ji ba? Da kinji maganata a lokacin kin hakura da zuwa da zai ɗauke ki ne? Yanzu uban miye ya haɗaki da laptop ɗinsa ko sa’anki ne shi da kike" wasan banza da shi har yake biyoki har nan zai dokeki” “Ammi fa…” gwaɓe mata baki Ammi tayi ta dafe bakin tare da fashewa da kuka “Na rabaki da su wallahi in banda gaisuwa na sake ganinki da su kina wasan banza sai na ci miki mutunci mara hankali kawai” tana gamawa ta fice a ɗakin ta barta a durƙushe tana kuka.. sake leƙowa Ammi tayi tana harararta tace “kuma wallahi ki rufa mini baki tunda ba dukanki nayi ba kar ki fusata ni in miki shegen duka "dan ubanki, tunda dalilin kuka kike so ni zan baki dalilin yin kukan mai lasisi..” tana faɗa ta rufe ƙ" ofar ta sauƙa ƙasa dan ƙarasa aikinta. "Ƙunshe kanta salwa tayi a ɗaki taƙi saukowa har sai da Daddynta ya dawo, itama Ammi ko bi ta" kanta bata sake yi ba. "Uncle Ameenu bayan yayi wanka ya sauƙo dan cin abinci, har ya zauna ya kalli Ammi dake ƙoƙ" arin serving ɗinsa yace “Ina princess..” “Tana ɗaki” Ammi ta faɗa fuskarta ba yabo ba fallasa “Why is she in her bedroom by this time? Bata da lafiya ne?” “Lafiyarta ƙalau yallaɓai..” tura kujerar yayi baya ya miƙe ba tare da ya kuma kula Ammi ba ya "nufi sama, Ammi ta bishi da kallo kawai dan ta san miye zai biyo baya…" "A kwance ya sameta ta lulluɓa da bargo har kanta, ya ƙarasa ya zaune gefen gadon yana kallonta" yace "“Princess” jin shiru ya sauƙe bargon kanta, gani yayi idanunta a lumshe tana bacci, tayi parking gashinta Ya kwanta lub a goshinta, shiru uncle Ameenu yayi yana kallonta kafin ya kai hannu ya taɓa goshinta jin ba zafi ya taɓa wuyanta shima ba zafi hakan ya sa ya miƙe ya nufi ƙofa, Ammi na ta jira taji ya fara faɗa dan ta tabbata kukan da ta wuni tanayi tun magribh idanunta ya kumbura amma taji shiru. Ta ɗaga kanta tana kallonsa jin takunsa har ya ƙaraso ya zauna a kujerar da ya tashi ya soma cin abincinsa, bata tambayesa ba itama kawai ta zauna ta soma cin" "nata, two spoons kaɗai yayi ya sake kallonta yace" “Amma taci abinci ne kafin ta kwanta..” Ammi ta girgiza kai bata ce komai ba “Ta yaya za’a yi ki bar yarinya tayi bacci bata ci abinci ba fisabilillah? Idan ulcer ya kamata what "are you going to tell me? Kina abu kamar ba ke kika haife ta ba? Haba dan Allah” ko kallonshi Ammi bata yi ba ta cigaba da cin abincinta, ya ture kujeran ya miƙe tare da goge bakinsa da tissue ya kurɓi ruwa ya wuce sama abinsa, sai da ta kalli abincin da ya bari kafin ta cigaba da cin" abincinta abinta…. "“Happy birthday to you! Happy birthday to you…” pausing yayi yana kallon Al’ameen, siyama" "da Lailerh a palourn dukansu kayan bacci ne a jikinsu sai hular birthday dake kansu da cake a hannun Siyama, shi kwata kwata ya manta ma birthday ɗinsa yau ne, ya ƙarasa saukowa ƙasa" sanye da workout wears ɗinshi yana ƙaƙalo murmushi yace “Ba zaku makaranta bane?” Lailerh ta ƙaraso tana ƙoƙarin saka masa birthday cap tace “Bamu da early lectures dukanmu! Happy birthday Yaya” ya bari ta gama saka masa cap ɗin kafin ya ɗan bata side hug yace “Thank you lil sis” itama siyama ajiye cake ɗin tayi ta zo gabansa tana faɗin "“Happy 30th birthday Yaya, Allah ya ƙaro shekaru masu albarka”" “Thank you” ya faɗa yana kallon Ameen da shima yace “Happy birthday” a taƙaice ya amsa da “tnks” yana cire cap ɗin ya ajiye yace "“Ku je ku shirya ku tafi school” Mami ta fito daga kitchen tana kallonsu da murmushi a fuskarta," ƙarasawa yayi kusa da ita yace “Good morning Mami” "“Morning, Allah ya ƙara maka shekaru masu albarka, ya ƙaro maka hankali ya baka mata ta" gari cikin shekararnan”. "“Amin” ya amsa a hankali.. dai dai lokacin kuma aka turo ƙofar palourn aka shigo, duk kallonta" "suka kamayi, Abida ta shigo cikin palourn tana shining teeth tace" "“Happy birthday yaya Aryaan, my favourite cousin” yana murmushi yace" “Thank you Abida how are you” “I’m fyn fav” kafin ta juya ta kalli Mami tace “Good morning” “Morning” Mami ta amsa tana kallonta rabonta da gidan ta manta amma bata yi mamaki ba dan ba ita Mami kaɗai ba kowa ma ya san meya kawota! ‘Aryaan’ Ɗan kallon Ameen tayi tace “good morning yaya Ameen” "“Morning Abida, ya shaheeda kuna waya?”" "“Eh munayi” ta faɗa tana bin bayan Aryaan da ya nufi ƙofa zai fita, duk suka bisu da kallo," Lailerh da siyama suka taɓe baki tare da nufar sama abinsu… "Jerawa Abida tayi da shi tana ta masa hira telling him how much she missed him da baya gidan," ya ɗan kalleta yace “Ke baki da school yau ne” “Kawai bazan je bane yaya i’m tired of this school wallahi” ya gyaɗa kai kawai bai ce mata "komai ba suna cigaba da tafiya a jere, Salwa dake saman balcony ɗin gidansu sanye da kayan bacci dan tashinta kenan Ammi tace taje tayi watering flowers dake wajen sai hamma take yi, hammar ce ta katse hangosu da tayi suna tafiya a jere suna magana ta bisu da kallo tana zuba ruwa a flowers ɗin, haka kawai jininta sam bai haɗu da Abida ba, ko ga maciji basa yi ita da Abida ganinsu yanzu tare da Aryaan yasa ta ja dogon tsaki ta ajiye butan ruwan, a ƙasan ranta tana faɗ" in "“Birds of the same feather…” ta wuce ta buɗe slide door dake wajen zata shige cikin gidansu," "dai dai lokacin ya kalli side ɗin balcony ɗinsu, bayanta kawai ya gani da gashinta da ta tufke ta shige ciki ta juyo zata rufe door ɗin suka haɗa ido, murguɗa masa baki tayi ta rufe ƙofar, yayi shiru yana kallon door ɗin da ta rufe kafin ya ɗauke idanunsa tare da gyaɗa kai kawai ya cigaba" da tafiya sam baya ko jin abinda Abida ke faɗa…. "Har sai da ya gama duk wani workout da zaiyi Abida na biye da shi, ji yayi kamar ya kore ta amma" dai ya rabu da ita. “Wai yaya har ka gama” ta faɗa ganin he’s heading home "“Eh” ya bata amsa a taƙaice fuskarsa a haɗe, ta bishi a baya jikinta a sanyaye ganin yanda ya" amsata kamar suna faɗa. "Suna shigowa layin ya hango motar driver ɗin salwa a pake a wajen gate ɗinsu yana jiranta, ya juya ya kalli inda ya ganta ɗazu kafin ya kalli gate ɗinsu, daidai lokacin ta fito dressed beautifully ta rataya expensive tote bag hannunta riƙe da labcoat da dama shi ta manta ta shiga ɗaukowa," kallo ɗaya ta musu ta shige motar tana kallon driver ɗinta tace “Yi sauri mu tafi kafin su yaya su iso” tada motar yayi yana amsa mata da “toh” ya ja suka "wuce su, Aryaan yayi guntun smirk dan a yanzu ko lokacinta bayi da shi amma tabbass zaiyi" lokacintane ta gama guje gujen… Abida ta tsaya a bakin gate ɗin Mami tana kallonsa tace “Zan wuce gida Yaya Aryaan” “Okay” kawai ya faɗa yana tura gate ɗin ta bishi da kallo har ya shige kafin ta wuce abinta. "A compound ya tarar da Siyama da Lailerh musa zai kaisu makaranta suma, ya wuce su ya shige" cikin gidan ba tare da ya ce musu komai ba dan gabaki ɗaya idan ya tuno project ɗinnan ji yake ransa na lalacewa. #Banidahujja #Maimoon 09041426598 https://whatsapp.com/channel/0029VbB1qGBFMqrVuPRZ5f2Q BANI DA HUJJAH Last free page…. "Assalamu alaikum lovelies Bani da hujjah is a paid book, free pages kuma basu da yawa sosai, pls" "support me by making your payments kafin end of free pages! Thank you so much as you do, ga masu bukatar biya zasu tura 500 kacal zuwaga" 7039695535 "Palmpay," Maimunatu Abdullahi muhd Sai ku tura min evidence of payment ta 09041426598 on whatsapp Idan kuma katin waya ne zaku tura 500 zuwa ga 07039695535 Thank you 12. "Sai da yayi wanka kafin ya zauna ya janyo laptop ɗinsa trying to see idan zai iya recovering wani abin, ya buɗe screen ɗin ya tsaya yana kallon folder ɗin aikinsa amma empty ba komai a ciki, ɗ aya bayan ɗaya ya duba files ɗin duka empty ya lumshe idanunsa a hankali tare da jingina kansa da headboard sai da yayi taking deep breath kafin ya buɗe idanunsa ya maida su kan laptop ɗ insa ya fara danne danne, duba recycle bin da recently deleted yayi yaga duk ta goge a wajen, ya shiga duba system files da temporary folders amma duk babu wani abu mai anfani a wajajen, at that moment ya sake tabbatar da cewa its gone! Wayarsa ya janyo a hankali ya buɗe ya fara scrolling bai san sanda ya sauƙe gajeren ajiyar zuciya ba, duk da ba wai duka komai ne yake kan wayartasa ba but atleast wasu abubuwan na nan ɗin, hotuna, screenshots da folders da ya tura wayarsa weeks ago ba dan yana saka ran zai yi anfani da su ba yanzu gashi sune zasu yi saving life" ɗinsa.. "Ya shiga zooming yana bin detail ɗin komai da ke jiki da kallo kamar mai haddacewa, thank God" yana da structural note a wayarsa still shima zai taimaka duk da theyre still not enough amma theyll go a long way. "Ajiye wayar yayi ya koma kan laptop ɗin ya buɗe sabon file ya fara sabon aiki afresh, ya san ba" lallai ya gama before date ɗin presenting ba which is next week! Amma duk da haka he’ll try his luck sannan zai demanding for extention of submission ɗin idan Allah ya taimakesa he’ll make it. "Wuni yayi aikin, sau ɗaya ya sauƙa yaci abinci shima Mami ce ta zo har ɗaki ta matsa masa ya zo yaci abinci, ciwon da kansa yake masa ya ƙaru sosai dole ya ajiye laptop ɗin around four dan zuwa Sallahn la’asar, a palour ya tarar da Ameen da ya dawo aiki ya baje a palour yana gisting" Ammi akan law firm ɗinsu tunda itama retired lawyer ce kuma field ɗinta ne. Ganin Aryaan zashi masallaci ya miƙe shima ya ɗauro Alwala a banɗakin palour ya bi bayansa zuwa mosque.. suna dawowa Aryaan ya kuma haurawa sama Ameen kuma ya yi zamansa ƙasa. Mami tana kallonsa tace “Aikin miye Aryaan kam yake yi ne? Yau fa wuni yayi aiki da ƙyar na samu yaci abinci..” "“Hmm” kawai Ameen ya faɗa yana danna wayarsa, Mami tace" “Why humming?” “Salwa ce wallahi ta goge masa wani project da yake yi kusan wata huɗu fa kenan kuma next week zaiyi submitting ɗinsa..” Mami ta ɗan buɗa ido tana kallonsa tace “Kai haba dai? Subhanallah amma gaskiya bata kyauta ba miye ma ya aiketa taɓa masa aikinsa ko bata sani bane?” "“Ta sani wallahi” ya faɗa yana miƙewa tsaye, Mami ta yi shiru tana ta kallonsa har ya fara" haurawa kafin tace "“Amma zai iya sakewa ne a wannan guntun lokacin, tunda kace next week ya kamata ya bayar?”" Ameen ya ɗanyi murmushi kawai yana haurawa yace "“Maybe zai iya, kinsan shi da naci kamar kuturu, amma gaskiya fa kamar wuya…”" "“Kai Allah ya kyauta, amma gaskiya ban ji daɗi ba wallahi”Ammi ta faɗa tana jin haushin abinda" salwa ta aikata masa da kuɗira aniyar idan dai ta shigo sai ta mata faɗa. "A zaune Ameen ya tarar da shi still yana aikinsa, Ameen ya zauna gefen bed yana cire takalminsa" yace "“Take it easy on yourself pls, kaima kasan bazaka iya sake yinshi kafin due date ɗin ba…” ko" "kulasa Aryaan bai yi ba, Ameen ya shiga wanka." Bayan Sallar isha’i Aryaan ya fito toilet yana gyara gashin kansa da ya jiƙo da ruwa ya zauna a gaban side mirrow yana goge gashin da towel! Ameen da ke shan coffee yayi murmushi yana kallonsa yace "“Toh wa yace maka zuba ruwa a kai yana rage ciwon kai ai sai dai ma ya ƙara!” Shiru ya masa," Ameen ya kuma murmushi yana cigaba da kallonsa yace “To ni yanzu laifin miye na maka kake wani shashshareni sai kace ni na goge maka aikinnaka…” "sai a lokacin ya kallesa, fuskarsa a haɗe yace" “Kasan Allah either you ko babanta gwara ku fara neman kuɗin biyana abinda ta mini asara idan ba haka ba wallahi duk abinda nayi ma yarinyarnan a gidannan babu ruwan kowa da ni..” "“Mu biyaka? Mu biyaka fa ka ce…” Ameen ya faɗa yana dariya, kafin Aryaan ya amsa, wayar" Ameen ya hau ringing ganin bappah ya ɗaga tare da gaishe shi har sannan da murmushi fuskarsa… “Eh muna tare da shi gashi nan…Okay..toh” kallon Aryaan yayi bayan ya katse kiran yace “Meyasa ka kashe wayarka ana ta nemanka” ya ɗaga idanunshi ya kalli Ameen “Wa ke nemana?” “bappah ne ya kirani yanzu wai idan muna tare da kai kaje yana nemanka yanzu” ɗauke kansa Aryaan yayi yana ajiye towel ɗin da ya gama goge kansa “Kaji ina?” Ameen ya maimaita masa yana kallonsa da sipping coffee ɗinsa “Ba zuwa zanyi ba.” Ya faɗa yana miƙewa daga gaban mirrow ya nufi kan gado.. “Kiran bappahn?” “Eh” ya amsa a taƙaice “And why is that” kamar bazai amsa ba sai kuma yace “Aneela ce ta je ta same su wai na mata ciki na sa tayi aborting and many other sharri su kuma "they believed her, bappah yace ta je zai ɗauki mataki shine wato har ta dawo saboda ita mayya" ce.” Ameen ya buɗa ido sosai yana kallonsa yace "“Is she Mad?, why on earth will she do that!”" "“Yes She’s indeed Mad, a kuma gabana ta faɗa”" "“Amma lallai yarinyar nan ta cika mahaukaciya, kai kuma sai kace musu miye? Kaga irin yarinyar" da kake so ka aura ina koh? yanzu a gaban su bappah tace ka mata ciki?.” “You dont have to remind me” ya faɗa yana jingina kansa da allon gado.. "“Yanzu dai tunda na riga na ce masa ga ka nan kawai kaje kar ka ƙara ma kanka laifi, da na san" hakane da cewa nayi ma bama tare..” “Ka rakani toh…” Aryaan ya faɗa yana kallonsa daga kwance “Ah ah kaje dai zan zo kafin ka dawo bari na gama shan wannan..” ya faɗa yana ɗaga masa cup "ɗin hannunsa, amma a zahiri shima tsoron zuwa yake yi kar a je a haɗa da shi" shiru yayi kamar ba zai tashi ya je ɗin ba sai kuma ya miƙe kawai ya nufi ƙofa yana gyara white shirt ɗin jikinsa Ameen ya bishi da kallon yana kai cup bakinsa.. "Duk da dare ne amma ko ina tarr da haske ƙoyayen fitulun waje, a nutse yake tafiyarsa ransa duka a dagule, abubuwa ne da yawa suka haɗe masa a yanzu da ya rasa yadda zaiyi da su, kamar ance ya ɗaga kai ya hango salwa zaune saman motar Hamza, shi kuma yana tsaye a ƙasa, ta tanƙ washe ƙafafunta tana danna waya suna hira, ya kalli agogon hannunsa ƙarfe takwas da rabi, kasancewar dole ta gabansu zai wuce yasa suka hangosa tun kafin ma ya iso, buɗa idanunta Salwa tayi ta soma ƙoƙarin sauƙa a saman motar tayi ta kanta Hamza na mata magana ma ko kulashi bata yi ba ta samu ta sauƙa zata ɗiba da gudu, dan bata san meyasa ba haka kawai wani irin tsoronsa ne ya ɗarsu a ranta tun bayan abinda ta aikata masa, tana ƙoƙarin guduwa amma tuni Aryaan har ya iso wajen saboda yadda Hamza ke ƙoƙarin hanata guduwa yana tambayarta abinda ya haɗata da Aryaan ɗin da zata gudu dan ta gansa.. wafce hannunta tayi daga na hamza bayan ta galla masa uwar harara ta ɗiba da gudu Aryaan ya rufa mata baya, ko kaɗan bata kai labari ba dan bata yi nisa a gudun nata ba Aryaan ya cafkota tare da haɗe hannayenta biyu waje ɗaya ya ɗauke fuskarta da Mari, da sauri hamza ya nufo su kafin ya ƙaraso har Aryaan ya ƙara ɗ auke ɗaya gefen da mari ya ƙara mata da ranƙwashi mai azababben zafi ta kurmu ihu tare da" "fashewa da mugun kuka, Hamza ya hankaɗa Aryaan ɗin yana faɗin" “Kai mahaukacin ina ne? Uban miye ta maka” dai dai lokacin Ameen da ya biyo bayansa ya "hango abinda ke faruwa, ya nufosu da sauri yana faɗin “Subhanallah” Aryaan ya sa hannu duka biyu ya hankaɗa Hamza har sai da ya bugu da mota, ya juya ya koma kan Salwa da ke kuka wiwi tana bashi haƙuri, ganin yana ƙoƙarin zare belt ta fara ƙoƙarin riƙe hannunsa amma sam ta" gagara miƙewa tsaye bare ta saka ran guduwa. Ameen yayi saurin riƙe belt ɗin da ya ɗaga zai sauƙe a jikinta yana faɗin “Aryaan miye haka!” Wani kallon banza ya masa tare da sake masa belt ɗin da ya riƙe ya kalli Salwa da ke hawaye ga shatin hannunsa kwance a farin kumatunta ya nuna ta da yatsa cike da kashedi yace “Ban gama da ke ba…” yana gama faɗin haka ya nufi part ɗin bappah! Ameen ya ɗago "Salwa da ta ƙara ƙarfin kukanta kamar zata shiɗe, Hamza ya miƙe zai bi bayan Aryaan Ameen" yayi saurin hanashi yana faɗin "“Dan Allah ka rabu da shi kar ka biye masa, ba girmanka bane” kallon banza shima yayi wa" "Ameen ɗin zuciyarsa na tafarfasa ya juya ya nufi part ɗinsu, Salwa dai banda gunjin kuka babu abinda take yi, Ameen ya sa hannu yana duba face ɗinta da yayi ja yatsun Aryaan kwance ɓaro ɓ" aro yace "“Salwa bakya ji, yanzu dubi abinda kika ja ya miki, baki kyauta ba, wata da watanni ya ɗauka" "yana aikinnan kuma cikin sati mai kamawa zai yi submitting gashi kin masa asararsa, yanzu gashi" kin ja ya doke ki a banza da hofi… sorry!” Ya faɗa cike da rarrashi "Sheshsheƙan kuka kawai take yi tana sauƙe ajiyar zuciya kamar zata mutu tana kallon wrist ɗin both hannayenta da suma suka yi ja saboda riƙon da yayi mata, rabonta da a dake ta har ta manta lokacin, shi dai Ameen ya cigaba da rarrashinta dan ko kaɗan baya son kukanta amma kuma this" time around bashi da bakin magana tunda itace bata da gaskiya… "Sai da ya tsaya yayi composing kansa kafin yayi sallama tare da shiga palourn bappah, yanayin" "fuskokin parents ɗinsa a yau ya sa haka kawai yaji zuciyarsa ta buga da ƙarfi! Bappah na zaune fuskarsa expressionless, Uncle Ameenu ma na zaune idanunsa sunyi jajir har wani ruwa ruwa ne a cikin idanun na ɓacin rai, kasancewarsa fari yasa farar fuskarsa har jajaja tayi tsabar ɓacin rai, Dad ɗinsa ma fuskarsa a matuƙar haɗe, ransa a ɓace irin ɓacin ran da ya jima bai gani tattare da shi ba, uncle muhammad sammakal, kai harta uncle lawal da bai cika ɓacin rai ba shima yau fuskarsa a haɗe yake tamau! This time around harda Daada a zaune gefen Bappah itama fuskarta" babu yabo babu fallasa… Waje ya samu a ƙasa ya zauna yana lissafa duk wani laifi da he possibly did da zai ɓata musu rai har haka amma bai iya tuno ko da ɗaya ba. "A nutse ya gaishe su, bappah da Daadah ne kaɗai suka amsa sai uncle lawal. Bappah ya gyara zamansa ya fuskancesa tare da fara magana, daga yadda yake magana kaɗai ya tsinci ɓacin rai" shima a muryarsa.. "“Muhammad!” Bappah ya kira sunansa, amsawa yayi yana ɗaga idanunsa ya kalli bappah," strictly bappah ya soma magana “Na yanke hukunci muhammad mai girma wa rayuwarka wanda bai yi ma iyayenka daɗi ba! Sai "dai ina mai tabbatar maka cikinsu duka babu wanda ya isa ya hana hukuncin da na yanke! Ina kuma fatan kai bazaka yi jayayya da hukuncin da na yanke akan rayuwarka ba dan sanin kanka ne bazan taɓa cutar da rayuwarka ba” gyaɗa kanshi yayi a hankali ya gagara cewa komai,yawun bakinsa ma ji yayi ya ƙafe rashin sanin wani hukunci ne wanann da ya shafi rayuwarsa da har ya" ɓata ran kowa har haka? “Muhammad Aryaan ni bappahnka Wazeer na ɗaura maka aure a yau da Salwa Ameenu "Wazeer, auren da nake buƙatar ku kasance tare ƙarƙashin inuwarta har ƙarshen rayuwarku!” Dummmm kansa ya sara da ƙarfin gaske yayi dai dai da bugun da zuciyarsa yayi kamar zai faso" ƙirjinsa ya fito! "Ya ɗago idanunsa yana kallon bappah speechless, gyaɗa kansa bappah yayi yana kallonsa yace" “Idan kuma kaima iyakata zaka nuna mini bismillah!” Girgiza kai ya hauyi amma ya gagara "magana! Salwa? Why Salwa? Cikin duka matan duniya a rasa wa za’a aura masa na dole sai Salwa? Salwa fa? Inaaaa bazai yiwu ba, ba zai taɓa yiwuba, ba zai taɓa iya rayuwa da salwa a matsayin" matarsa ba kwata kwata bazai yiwu ba… “Ka tashi kuma ka je ka taho da matarka yanzu ina so in yi magana da ku a tare!” "Alhamdulillah anan na kawo ƙarshen free pages from the book bani da hujjah, ku garzayo ku zo" "kuyi making payments dan kar ayi tafiyarnan ba tare da ku ba, amsoshi ga tambayoyinku duk zaku same su ne idan kunyi subscribing" Ya makomar auren Aryaan da salwa? Shin iyayensu zasu amince da zamansu? Su kansu couples ɗin zasu zauna ɗin? Menene tarihin Turaki Family And many more….. Support me pls Zamu ɗauki hutun posting na sati ɗaya both on whatsapp and arewabooks dan tantance "payments, nagode sai na ji ku.. " 7039695535 "Palmpay," Maimunatu Abdullahi muhd Sai ku tura min evidence of payment ta 09041426598 on whatsapp Idan kuma katin waya ne zaku tura 500 zuwa ga 07039695535 Thank you #banidahujja #Maimoon 09041426598