🕸🕸TARKO🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 1⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA YAURI Da sunan Allah mai,rahama mai jin kyai, duk kan godiya da yabo ya tabbata a gare shi, wanda ya yi mu ya wadata mu da ni,imomin sa, Wanda ya shari,anta yin addu,a zuwa gare sa, ,kuma yai muna ni,ima da baiwan shi, akan mu roke shi duk bukatocin mu,, Ubangijin,mu wanda ya ce idan su ka tambaya a gamay da ni, To ka basu labarin cewa ni din makusancin ne a gare su, Ina karba adduan mai addu,ar mai, addu,a idan ya roke ni, Ya Allah tsira da amincin ka su tabbata ga fiyayyen talikai, Annabi rahama Muhammad S A W, da halaiyen sa da sahabban sa da ma duk wani musulmi wanda yabi tafarkin gaskiya har izuwa ranan Alkiyama,,,,,,, Ya Allah ina rokon ka da da gode maka da ka bani wanan daman na rubuta wanan dan gajeren labari, Ya Allah yadda ka nufeni da farawa lafiya Allah ka bani ikon kammalashi lafiya, Ya Allah dani da na rubuta da wanda duk kabawa ikon karantawa, Allah ka yafe muna kurakuren mu, Allah ka sada mu da rahamomin ka da ni,imomin ka , Ya Allah kasa Aljannan fiddausi tazamo makomar mu,,,,,,,,, BARKAN MU DA SALLAH YAN UWA,,,,,, A hankali ya sa hannun shi saman kan shi ya cire farin rawanin dake saye a kan shi, Farin rawanin da a kasar hausawa sai wani mai, sarauta ko malami ko wani babban mutum ke sawa kan su shi, Gefen guda daga inda yake zaune saman shimfidar dake a cikin rufan da ke kofar gidan shi, Rumfar wanda ya a kayi manne da ginar zauren gidan, a ta gefe guda, Sai shimfidar da akayi wa wani gadon kara dake a cikin rufar, Shimfidar ya sha kayan laushi irin daddumar nan na da ja,jayen kala, Daga gefe guda littatafan addini ne kala kala tare a guri guda, Sai kuma wasu allunan katako, dake tare a guri guda, Wanan abubuwan zai nuna wa mutum cewa runfar na wani malamin irin kasar hausa ne, A hankali dan tsohon ya dan jawo jikin shi daga saman shimfidar da yake a zaune, Gurin da wata butar silver mai ruwan gold yake a je da ruwa ya nufa, a hankali ya fara gabatar da alwala a tsanake, kamar yadda addini ya umur ta, Bayan ya gama alwal ne ya kara gunda ruwa ga baki yayin da yake mikewa tsaye ya zubar a saman bangon shiga cikin gidan shi A hankali ya ke dan takawa zuwa kofar fita cikin rumfar tashi, Jama,a ne a,waje da alamar shi suke jira, daman yafito gaba dayan su , suka mike tsaye, Bata lokaci aka fara gabatar da sallah azahar na ranan, Bayan idar da sallah tsohon yadan kai wani lokaci a gurin zaune yana tasbihi, Duk wanan jimawan da yayi a zaune bai hana mutane zanan jiran fitowar shi ba, Ya fito fuskan shi dauke da annuri mai kama da murmushi a koda yaushe, Yara ne daga gefe guda suna ta taruwa da alama karatu zasu yi a gurin, Saboda irin yadda suke ta tururuwan fitowa daga cikin gidan, Hakan ya nuna cewa gidan na malam Manya, babba gida ne mai tarin jama,a acikin sa,, Tarin wanke wanke ne a gefe guda kuda na bin su, Daidai lokacin da wata mata yar kimanin shekaru, hamsin da tafi daga dakin ta, tana kokarin gyara daurin zanin ta, Gani kwanonin da ba,a wanke ba har izuwa yanzu yasa matar sake wani irin wawan tsuki, a lokaci guda ,,, Takalman silifas din ta dake a kofan dakin ta take kokari zurawa kafan ta sai faman mita takeyi, tana cewa ace izuwa yanzu ba,a wanke kwanonin da akaci abinci a cikin sa ba,,, Amma yau idan na kama wanan Yarinyan sai rayuwar ta ya baci, Cikin gidan babbane mai sassa guda dai,dai har goma sha, biyar, duk sassan gidan na 'ya'yan malam Manya ne, sai mutum uku ne kawai diyan yan uwan shi da ya karantar kuma yai masu aure suna zaune a tare dashi, Duk diyan malam suna da aure sai mutum guda wanda shine autan malam wanda ake cewa Isah, Amma Abdullahi ya bace wada suke kiran shi, da shi saboda acewar mahaifiyar shi tun haihuwar shi da tasamu kudin suna ta, sai dabbobi tana kiwo shine suke ta kawo mata kudi, Mahaifiyar Audi, itace matar malam na karshe wacce daga ita bai kara wani aure ba,, Dan malam na farko shine baba Buhari, sai na biyu Sha,ibu, sai Musa, sai Gwago, Laira, gwago Lanto, sai Hamza,, Yahaya, duk diyan mace guda ne, Ismail, shi da Habiba uwar daya amma ta rasu dadewa, tun gurin wani haihuwa, Asiya, Rabi, da Audi su kuma diyan mama Rukaiyya ce Amaryam malam, ta yanzu, Wanan babban gidan na malam manya, yana nan a cikin uguwar da ake kira da Shiyan Sarakuna, dake a cikin garin Birnin Kebbi, Wanan shiyan kowa yasan cewa shiya ce ta haifaffun gari da kuma baki masu asali, ke zama gurin, Yanzu haka, zaka samu mazauna unguwar duk kowa yasan kowane gasu da yawan ilimin addini tare da na zamani, A tsakiyar unguwan zaka samu gidan malam Manya, wanda shi da daukacin iyalin shi suke a ciki,, Babban diyarn Buhari mariya, sai, Abubakar wanda ya ke bi matan sai mata ne har su biyu, su ke bi mashi, sai daga baya mahaifiyar tasu ta samu maza,biyu da mata biyu,,, Don haka yaranta sune manya a gidan gaba dayan, saboda, a kusan jere tai ta haihuwan ta, Ba karamin kokari malam Manya keyi ba gurin ganin cewa hankalin iyalin shi, ya zamo guri guda, Amma duk da haka akwai, baraka a tsakanin matan wanan babban gidan don sun kashi kashi dakashi a tsakanin su,,,,, Yanzu haka ita matar malam wace a,ke,cewa maman Audi, Kansu a hade yake da Amaryan malam watau maman Audi, Wanda hakan ya samu asaline don kusan a lokacin da malam ya auro ta ita mahaifiyar su Audi,,,, A tare suke hurda da mama Ladi, wace da ma bata kaunar zama da mahaifiyar mijin ta, Hakan yasa da malam ya auro maman Audi, sai Ladi ta jata a jiki, Shiko Ismail da kaunar shi wace da mahaifiyar su bata da rai, a gidan sai aka ware su, Hakan ya sa Shi Ismail yake da kwazo da neman na kan shi, A can cikin dangin mahaifiyar su gwandu ya auro matar shi, Wace take zaman hakkuri a gidan tare da yaran ta, Sai dai sauran matan yan uwan Buhari sam basu yarda, da wulakancin mama Ladi ba sam, saboda suna ganin cewa bata fisu ba, Ya sa sam ba su yarda da da wanan cin fuskan da,takewa sauran matan gidan, Sashin mata daban a makarantan sashin maza da ban Matan suna zaune kusa da kakan su inda suke daukan karatu, Malam baya yarda yarinya ta girma batare da ta sauke alkur,ani maigirma ba, Don duk wace zaiwa aure a gidan dole sai ya kasan ce ta sauke littafi mai tsarki, Don haka komai kankantar yarinya dole tana zama da zaran lokacin karatu yayi don gudun makara saboda bulalan da malam ke dan shada masu a hannun su idan sunzo a lati,,, Sauri takeyi don gudun makara don tasan cewa malam yanzu ya fito daga cikin massalaci, Saboda agogon bango dake sagale dakin mahaifiyar ta ya nuna mata cewa, biyu da minti talatin daidai, A cikin saurin da ta keyi ne suka hade hanya da mama Ladi wace ta zo sa shen nasu don neman Meenat din Meena wace ganin mama ladi yasa gaban ta faduwa don tasan cewa ko banza sai kunuwar ta yasha murda gurin mama, Da sauri Meena ta ja baya daidai inda mama ta kai mata bugu ta gwauce, Gaba ta sata da masifa inda dole ta aje Alon ta zuwa sashen mama ladin, Sai da ta wanke kwanonin tas sanan ta, dauki allon ta zuwa kofan gida, Tun fitowar ta hankalin malam Manya, yake a kan yariyar wace, ke ta dan sharan kwalla, da habar hijabin ta, Malam,Yasan duk abinda ke gudana agidan Amma hali irin na manya yasa shi, kawar da kai tankar bai san may ke gudana ba, Azaton Meena malam zai mata bulala yau sosai saboda irin makaran da tayi, ga kuma sauran yan uwan ta duk sun zuro mata ido suga yaya zasu kwashe ita, da malam, Sai dai tana zuwa sai malam ya nuna mata, gurin, da zata zauna a hankali ta zauna a tsorace don gudun kada ya fyedo mata bulala daga inda yake zaune a gefen su, Da guda guda su kai ta zuwa gaban shi suna biya allon su, Meenat tana isowa agaban malam, maimakon ya fara biya mata sai yace mata cikin tausa murya Amina ki dinga kula daga yau da duk wani aikin da za,a saki, a gida bana son kina makara haka don gudun kar a barki a baya,,, Kai kawai ta gyada mai don a zaton ta har yanzu zai mata bulala da ta makara, Amma har aka tashi, bai mata bulalan ba, hakan yasa ta sakin jikin ta, Ba komai asa Meena take tsoron bulalan malam don ganin irin yadda bai kaunar dukan ta duk cikin su,,, Hakan yasa Meena ke jin nauyin ace, tana cikin masu makara, Dawowan ta sashen su, ta yi dakin mahaifiyar ta inda ta samu mahaiyar ta na gyara dakin ta don ganin yamma ya gabato, Hijabin ta ta cire tana kokarin karban tsintsiyar dake a hannun mahaifiyar ta, Jeki ki duba kigani idan da, sauran aikin da zakiyi, wa maman ku ki karasa mata, kafin dare yayi, Cikin sanyi jiki Meena ta bar sashen nasu zuwa,,, gurin ina ladi don ta share mata guri, Kamar yadda ta saba yi mata akoda yaushe, don dama takamar maman ladi shine taita bautar da yar mutane saboda mugun kiyayyan da takewa Meena din haushin uwar ta take ji,,,,,,, A yi hakkuri da wanan yan uwa barkan mu da sallah, Allah yasa wanan novel din ya samu karbu gurin fadakar da ku kamar kullun, Taku ZAINAB MAKAWA,,,,,,,,,,,,,,,,,,, 🕸🕸TARKO🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 2⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA YAURI SADAUKARWA Na, Sadaukar da wanan littafin ga Anty na yayana kuma masoyiyata Antyna Nafisa Harzami tare da duk sauran yan uwan mu maza da mata yan Harzami Family,,,,,, JINJINA Jin,jina gare ki MAMAN FARIDA TUKUICI Wanan littafin tukuici gareki Anty SAFEENA MAMUD, MAIDUGURI,,,,, FATAN ALHERI GAREKU DUK KA MASOYANA MASOYA NOVEL DIN ZEE MAKAWA,,, YA ALLAH Kabani ikon gama wanan littafin lafiya kare ni, da ga rubuta duk wani abin da bai dace aciki ba,,,, A karkashin babban itaciyar cediyar da ke a tsakan gidan gurin da matan gidan ke taruwa suyi hira, daka da sauran yan aikace, aikacen su, Yau ma zaune akasarin matan gidan suke a guri itacen Wasu na yan aiyukan su wasu kuma suna hira ne kawai saboda basu da aikin yi a lokacin, Mama ladi ce tafi don rakiyar kawar ta aminiyar ta kuma uwar matar da ta zabawa Abubakar din ta, Kusan matan gidan dake guri alokacin duk sun, wa hajja, sallama, Sai dai kusan duk idon matan akansu yake tun dai irin yadda suka ga mama ladi na washe baki don ganin Aminiyar nata, Daga cikin mata ukun dake zaune, suna hira duk suka bisu da kallo a lokacin da suka bada baya, Matar shaibu ce tace ni dai sam wanan matar bata kwanta min a zuciya na ba, wallahi, Sai dayar matar da suke a zaune tace ,"ke ki iya bakin ki da wanan zancen, Guda tace ke ina ruwan ki da zancen da bai shafe ki ba kina zaman ,zamanki ki jawa an kifitina, Hakan bai sa Maimuna shiru ba har sai da takara cewa Mata da wani iren fuska babu fara,a, walle, duk sanda nigga wagga mace hankali na tashi shi,kai,,, Daga haka zancen nasu ya tsaya don ganin mama Ladi da sukayi ta juyo zuwa cikin gida,,,, Abubakar ne zaune tare da malam a turakar shi suna hira, a washe garin da ya dawo daga karatun shi , Dama Abubakar sunan malam ne yaci don haka malam manya ke kiran shi da mai suna,,, Mai suna inji malam Yanzu kan Alhamdullahi ko? Tunda guri ya cika ankamala wagga karatu gashi har ankai ga aiki yau, Murmushi Abubakar yayi yadan sadan da kan shi kasa cikin girmamawa, A cikin taushin murya yace wa malam din malam da taimakon Allah da naku ai wanan gurin nawa ya cika, Nagode ma Allah da yanufe ni yau kana raye malam saboda irin yadda kai min tarbiya da kokari a cikin rayuwana, Kudi ya ciro masu yawa daga cikin aljihun shi, ya a je su a,gaban malam din, Ido malam ya dan tsurawa kudin da Abubakar ya aje a gaban shi, Cikin tambaya yace kudin maye wanan kuma mai suna, Abubakar yace kudin da akafara bani na albashina ne, shine nace barin kawo ma don asan yadda za,ayi da su, Shiru malam yayi yana nazarin wani abu a cikin zuciyar shi, Gyaran murya malam yayi da farko tare da gyara zaman shi kadan, Mai suna inji malam Abubakar din yadan dago da kan shi kadan yana mai kallon malam, Wanan kudin ka kasa shi kashi hudu, Kashi biyu ka kwasa nakane,da sauri ya dago kai ya kalli malam don shi a ganin shi ai kudin sun mai yawa duka don ba wani abu yake saye ba ai, Malam ya gyada kai yace kwarai kashi biyu kai zaka a je a gurin ka, Kashi guda kabawa mahaifinka da mahaifiyar ka, Sauran kashi daya sai a rabawa sauran iyayyenka maza da mata, Cikin sauri Abubakar yace amma malam sai naga kamar ace na baba Samaila zai fi yawa, don bazan manta da irin halarcin da yai min ba gurin ganin ci gaban karatuna, Kwarai malam yaji dadin wanan zancen don da alama jikan nashi zai yi jin kai ga yan uwa, da sauran al,umma, Abubakar bai tashi gurin malam ba har sai da suka cirewa kowa abinda ya dace tundaga ubannen shi har zuwa matan gidan,,, Zaune take wanan karon a gaban malamin ta tana fada mai irin yadda take son sanar ta ya bunkasa a cikin lokaci guda, Malamin yai yar murmushi yace ai wanan ba komai bane zan maki kokari inga cewa, duk wanan nahiyar ansan da ke, Hajja ta gyara zama cikin jin dadin zancen malamin nata, Sun dauki lokaci malam yana mata bayani tace duk taji zata iya abinda yace, mata, Ta dawo gidan ta da farin ciki, da jin dadi don tana ganin kamar har komai ya kammala ma ko Yar ta Sadiya ce a zaune tsakar gida tana karatun novel, Tai mata,sannu da zuwa tare da kawo wa mahaifiyar ta ruwan sha wanda aka surka da kunu, koko, Tunda hajja ta kafa kai ga kwanon ruwan bata sauke ba har sai da ta shanye ruwan kwanon dukka, Hakan yasa yar nata tagane cewa ba karamin kishin ruwa mahaifiyar ta ta kwaso ba, Don haka abinci ta kara gabatar mata, Hajja na zaune tana cin abincine Sadiya ta kawo wa hajja wani leda baki da ke dauke da sabulan wanka dana wanki, Tace wai inji mama Ladi tace akawo maki a fada maki cewa danta Abubakar ne yazo jiya da dare daga inda ya samu aiki, Cak hajja taja ta tsaya don jin sakon da yar ta ke fada mata, Cikin sauri tace Abubakar din yazo gidan nan ne ,kai sadiya ta gyada mata alamar a,a baizo ba, May Ladi take nufi da rashin zuwan dan nata gurinki bayn mun riga da munyi magana akan hakan,,,,, Wanan zuwan mahaifiyar Abubakar bata bata bari ya koma ba,sai da ta gabatar mai da zancen auren da take son hada shi da yar kawar ta aminiyar ta, Abubakar baida zabi a rayuwar shi don shi ba mutum bane mai,rigima, Hakan yasa uwar ta samu sa,an shi saboda ita Sadiya irin matan nan ne da basu da fasali, Doguwa ce baka mai dan kiba hancinta a baje saman fuska, kanta baida gashi mai yawa aciki, Itama Sadiya mace irin masu mugun hali wa yan da sam basu kaunar na kusa da su ya rabe su, Ba wai don wani abuba, a,a halin natane kawai a hakan, Zaku iya kwana guri guda da ita amma ba za zatai ma mutum magana ba, sai in ta kama dole, Sai dai dama ita tana mutuwan son Abubakar a rayuwar ta, tun farko, Sam malam Manya bai so wanan hadin ba amma sanin da yayi cewa yanzu mutum bai zagewa sarakan zamani yasa shi jan bakin shi yai shiru, So sai ake shirin buki daga bangaren amarya da na ango, Sai dai rashin samun wadattacen lokaci da ango bai yi ba yasa bukin ya dan rage armashi, Amma duk da hakan ba laifi, don, yan uwa da abokan arziki sun nuna farin cikkin su da wanan bukin gida ya cika sosai a ranan, Bayan buki da kwana biyu ango da amarya suka kama hanyar Lagos can inda Abubakar yake, aikin sa yake kuma zaune,, Sai dai da amarya zata bar gidan ma haifiyan ta uwar nata taba wani ruwa tare da yin hayaki, a cewar ta na neman tsari ne, da samun sa,an daki, Gidane ma daidaici suke a ciki, acikin rufin asiri da wadata, Zama sukeyi na,rufawa juna, asiri da mutun tawa a tsakanin su, Sai dai matsala daya shine Sadiya bata da kuzarin aiki, sam, don haka bata damu da wai dafa abinci ba,, Zata iya kai wani lokaci tana barcin abinta ba tare da ta dafa ko mai taci ba,, Gyaran gida kusan weekend take yin shi don ita sam kazanta bai damay taba, Don a gida neman kudi ne kawai a gaban su shine tun safe za,ai tayi batare da an yi wani girki ko gyaran gida ba , Saukin al,amarin babu yan uwan Abubakar da suke ziyaran su a lokacin, Wanan shine, shimfidar labari da zan bayar,,,, Mama ladi, ce zaune a tare da aminiyar ta, suna dan tataunawa, Mama, Ladi ta marairai ce kai tana fadawa aminiyar ta, da muwar ta, Sai da Hajja ta gama sauraron maganar da Aminiyar ta tazo mata da shi,,, Hajja ta ce tau,Ladi yanzu yarda da mutum abin tsoro ne, Da sauri Hajja ta dago kai cikin nuna mamakin da jin abinda Hajja tace, Cikin mamaki tace Hajja ashe yanzu har akwai wani abinda zaki ji shakkun gaya min a tsakanin mu, Ba hakana ba,ne Ladi abin ne bai son yawan surutu kuma,siri ne mai girma a tsakani, Kinga ke nan ba zanso har wani yaji wanan zancen ba gaskiya, Kara matsowa Ladi tayi kusa da Hajja don ganewan da tayi cewa, maganan da zasu yi, mai, muhin mancine sosai Hajja tace wa Ladi, ki bari zuwa jibi in,Allah ya kai mu akwai inda zan kai ki, Da murna ladi tabar gidan don farin cikin ta kusa samun mafita, Buhari yana a majalissan malam mahaifin shi ya hango, dawowan maidakin nashi acikin zafin rana, Cikin rayuwan shi yake masifa da ita yana fadan rashin zaman gida irin na Ladi, Amma tana iso gurin da suke sai cewa tayi a gaishe ku, Yan kadan ne suka karba mata, da ingwaiyya Ladi ke dawo,? Ta ansa da fadar Awo, Allah ya maisan da ni lafiya, Daga haka ta,shigewan ta ciki, inda malam da dan shi buhari, takaicin ya hana,su cewa kala, Acikin gida ma, haka mata suka dinga gaida Ladi da dawo, Idan sunce mata Aho, yaya, Ita ko sai cewa takeyi ingwaiyya, agaishe ku, dai,,, Tas, ta samu shiyan ta don Meena ta gyara mata shi tas,, Amma halin kiyayya irin na Ladi sai cewa tayi wai Meenat, bata zuba mata ruwa a randar kasar ta ba, Tun daga inda take take, kwadawa yarinyar kira, A gigice Meenat tafito tana kokarin daura dan kwalin atamfar dake kan ta, Cikin masifa take cewa wa kike son ya cika radan ruwan da naga baki debo ruwa ke, zuba min ba? Meenat ta bude baki da niyar tayi magana amma kuma sai kawai ta kasa saboda idon ta da ya kawo ruwa, Salati Ladi tasa a lokaci guda tana tafa hannayen ta, cikin mamaki, Meena ko uwar ki ta hana ki min dan aikin da kike tayani ne kuma, Cikin mamaki Meenat tadaga kai ta dan kali Ladi don jin cewan da tayi wai aikin da tasha dan ka dan ne,,, Hakan ya ne yasa Meenat jin wani irin gululu a zuciyan, Ita dai gaskiya ta gaji da wanan kawaicin da ina ke sa tanayi wa mama Ladi Wace kuma duk cin mutum cin ta a kan sune yake karewa ko yau she, Saboda mugun tsanar da mama,Ladi takewa mahaifiyar abin har ya shafi diyan ta, Wanda hakan ba karamin batawa Meenat rayuwa yakeyi ba, Don haka azuciyar ta sha alwashin cewa daga yau zata san abin yi akan mama, Ladi,,,,,,,, Wacce duk wanan aikin da ta sha tun safe bata gani ba, sai ko karin cima uwar ta fuska takeyi,,,,,, ZEE MAKAWA YELWA ,🕸🕸TARKO🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 3⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA YAURI Bayan yan bayanin da malamin su yai masu amma ita mama Ladi, ba wai ta fahinci abinda yake nufi bane, Wani kwalla mai marfi wanda ita mama Ladi din take gani a cikin jeran dakin Hajja tasan shi, Shine malamin ya rufe da wani bakin kyalle yace su dauka zuwa gida , Amma kada su bude sai bayan kwana arba,in cif sanan ta bude, Daga wananranan da zata bude kwallan duk kukan abinda taji aciki shine zata dinga yankawa, Dajin an ambaci yanka gaban mama Ladi ya yanke ya fadi ras, Saboda jin an abaci yanka acikin al,amarin, don dai ita dai a iya sanin ta yanka wani abune na mushirikanci,,, Tana son tambaya amma Hajja ta tattare da godiya gurin malamin, Haka suka biyo hanya hajja nata koda malam da aikin shi Tana kuma yiwa mama Ladi barka da samun wanan abin acikin sauki, Da yake dare ne mama Ladi bata samu wani matsala ba gurin shiga da kwallan gida, Can ta samu karkashin gadon ta tatura shi ta boye batare da ta bude ba kamar yadda malam ya umurce ta dayi, Sai dai tun ranan tasa yarq suka debo mata duwatsu, ta boye. A kullun tana kidayawa guda guda tana jefawa don gudun mantuwa,, Sai dai duk abinda take yi sam mama Ladi bata yarda tayi nisa da dakin ta , Don gudun kada kaddara ya kai wani gurin kwallah ya bude ya bata mata tsari,, Wanan kafa kafan da takeyi yasa mutanen gidan gane cewa mama ladi tana acikkin wani yanayi a yan kwanakin nan, Rana akeyi yau kamar kullun don yanayin garin ke nan da yawan zafin rana, Daga makarantar boko suke tafe kowacen su sauri takeyi tasamu ta isa gida, Makarantar jeka,ka dawo ta yan mata dake Badariya suke zuwa watau Salamatu Husaini, Dake cikin tsohon makarantar Abdullahi Fodio, Isar su gida acikin gajiya yasa,su kowace ta nufi sashen su, Meenat na isa, ta samu ta cire takalmin sadal din dake a kafan ta tun a waje ta fara cire hijab din ta, Saboda bata,son shiga dakin su da kayan makaranta ajikin ta, Acewan ta, rigar yakan yi warin jemage ne dake makarantan su, Daga ita sai unders din ta tashige daki inda ta dauro zani zuwa wurin wanka,, Wani yaro ne cikin masu daukan karatu, yake ce mata wai mama Ladi tana kiran ta, Kamar bata ji shi ba har zata wuce yaron dan aiken mama ladin, Saboda wani irin mugun haushi da taji a cikin ranta mutum yadawo ko sallah bai yi ba za,a fara sashi aiki, ke nan, Muryan mahaifiyarta ce taji tana cewa cikin irin sanyin maganar ta, Dake fa ake magana yar mama, kin yi kamar bakiji shi ba, Baki gaba Meenat tace, mama kofa sallah banyi banci abinci ba, Kai mahaifiyar ta takada kawai don takaici, bazaki je kiji ko may take kiranki akai ba, Muryan Baba Samaila ne sukaji, a bayan su yana cewa , Yanzu fa naga shigowar su daga makaranta bata ko ci abinci baza ki ce yarinya ta je don dole, Ko ta tafi can wani abinci Ladi zata bata, halan, ? A,a malam wai gani nayi dama kada yaya tace kuma ba,a tura ta ba, Anki tura din , Ba tana da yara a dakin taba wai taje ma na duk abinda Amina kayi mata tasu suyi mata, Walle na gaji da,wagga irin bakar dabi,a Yaro ya dawo ma baida hutu shin,? Duk yadda akayi haka dan aiken mama Ladi ya zayyana mata zancen, Inda ba bata lokaci ta nufi sashin na Baba samaila, Agaida may "ya shin, Ni ta,zaka gwada ma haihuwa shin? Au ashe ke haihu Ladi an? Banga alama ba tunda banga kina gwada masu rashin mutunci kaman wadda kika wa sauran diyan mutane ba,? O Lailai Samaila yanzu akan "ya ka ta fari ka,kak fada shi, ? Tai ka jika ta kasha tunda kumya bai i,shi ijjiyanka ba, Banduk jikata amma yanzu kam da dawon ta da makaranta ko abinci da sallah ba ta yi ba Kika zuwa kice wai atai zuwa yi maki aikin wahala, Mamaki sosai ya kama mama Ladi ganin cewa yau wai itace ke magana ana mayar mata da ansa, Don ita a tunanen ta,duk ta shanye mutanen gidan gabadayan su, Shiyasa take taka kowa yadda taso, Abinda bata sani ba shine duk gidan kawici ake mata akan mijin ta baba Buhari, Dattijon kirki mai mutunci da zumunci da sanin ya kamata, "Dan kowa agidan tankar nashi yake dauka bai banbanta tsakani sam,, Wanan dalili ya sa dadewa baba samaila yake wa mama Ladi halar ci akan "yar shi Amina wace mutanen gidan dana shiya suke cewa Meenat,,,, Juyawa mama Ladi tayi da suraitai abakin ta, zuwa sashen su, Yar da suka dawo tare da su Meenat daga makaranta, Tana zaune saman kofar dakin su tana juya shinkafa da miyan manja da nama, Gefe guda cup ne wanda ta debo, fura mai sanyi aciki ga goran dake dauke da ruwan sanyi, Tambayar mama takeyi akan yaya akayi don jira takeyi mama ta taso Meena a gaba tazo ta ci mata mutunci, Ke rufen min baki kin ke ji ya, Gani da tayi cewa rayuwar mahaifiyar ta ya baci sosai yasa ta ja bakin ta tai shiru,, Sai dai tanayi tana dan daga kai tana duban hanya shigowa ko zata ga Meenata shigo, sashen nasu, Daga inda malam yake zaune yaga fitowan Meenat, da wuri zuwa cikin daukan karatu, Malam yai mamaki kwarai don ganin cewa yau jikan nashi ta fito daukan karatu dawuri ba tare da ta makara ba, Duk da suna da manyan dakuma wa yanda suka dan dara,su amma hakan bai hana wanan yariyar cinma manyasu ba , ga karatu, Hakan ke kara,sa kakan nasu najin ta ajikin shi sosai, Gashi kuma bawai wani dadi mahaifanta ke ji acikin gidan ba, Hakan ko ya samu asaline na rashin dan uwan haihuwa da shi baba samailan baida acikin gidan, Gwago hafsi ce kuma tayi aure ita a garin Kalgo bako a cikin gari ba sai in ta shigo gari,, Baba samaila ba karamin jurumi bane don har aikin soja yatafi, amma bai wani dadeba ya bari saboda mahaifin shi da bayason wanan aikin, Yanzu mota ya saye yana shiga kauyu ka yana dauko itace da sauran kayayyaki yana shigowa dasu gari,,,, Amina yau yaya ankayi kin kafito da,wuri ko uwar taki bata nan ne, Malam ke tambayar ta acikin wasan jika da kaka da yakan mata wani lokaci, Murmushi tayi tadan noke kan ta acikin hijabin ta ba tare da tabashi ansa ba, Sai can tace baba na yace min intahowa na makaranta, Wai daga yau ya yanke aikin nan, da nika zuwa yi wa mama kullun, don kada a wuce ni ga karatu,, Murmushi malam yayi kawai don yadade da sanin cewa wata rana hakan zai faru, Don dai irin yadda mama take nuwa bai dace ba sam saboda babu adalci acikin tafiyan, Baba Buhari ne ya shigo gida dauke da buta a hannun shi, da alamar ruwa yake so acikin butar, Gurin randar ruwa ya nufa daniyar diban ruwa, don ya zuba a butar, Muryan mama Ladi ce ta bayan shi take cewa yau kan ai mai diya ya hana diya tai diban ruwa, Yau samaila ya gwada min baida kunya don ko nauyi bai ji ya kalli ijjiya ta yaka ce wa wai diya tai tadawo ko hutawa batayi zan damay ta da bakin kira, Sororo yayi tsaye da buta a hannun shi yana sauraren ta, Saida ya tabbatar tagama ya nunata da hannun shi dake dauke da mudar radan ruwan yace, Ke, Ladi ke Ladi, Walle kiji tsoron Allah, daga dai yau Samaila yai magana kan Amina kikacewa wai ya gwada,maki rashin kunya, yai fada kan "ya tai ta fari, Walle Ladi an,kiji tsoron Allah ga al,amarinki, Duk yadda mutanen ga ka kauda kan su ga al,amarin diyar su, bai,ishe keep ba, sai keyi masu kazafi To, to ta ka shigan ma dan uwaka ke nan ko don ba yau ba nasan bakason abinda Yarinya taka min, Dauri ai sai ka hwada min in sani ko, To ai yanzu ke sani ko ? To katai zuwa inda zaka samu ruwan zuba ma butan ka tunda bata taho ta debo muna ba, Wanan maganan shi ne sanadin daina duk wani wahala da meenat keyiwa mama Ladi, Sai kuma kiyayya abin ya koma masu sosai don sam daga mahaifin da matar har yaran su ba shiri tsakanin su da sahen mama Ladi Dan dama dama gurin ita kishiyar mama din baraka wace babu ruwan ta da zancen su, A gajiye yadawo daga gurin aiki, tare da ledoji manya a hannayen shi, Da kyat ya samu ya shigo gidan nashi don nauyin kayan da ya dauko, A falo take zaune daga ita sai yar shimi a jikin ta sai littafin dake hannun ta tana karan tawa kanta babu hula ko dan kwali, Da sallama ya shigo gidan, Ita ma Sadiya sau guda ta daga kai ta kalle shi takawar izuwa abinda takeyi, Batare da ta kara daga kai ko ta mike ta taya shi karban kayan ba tace mai sannu da dawo, Umhumm ya ce mata cikin rashin sakin fuska ko walwala,, Kayan ya aje a gaban ta saman tebur ya wuce direct gurin fridge, Goran ruwa mai sanyi yafito dashi daga cikin fridge din, Kai ya kafa har sai da ya shanye ruwan, sanan ya cilla goran ta bayan shi, Shi da kan shi yadawo gurin kayan da ya,aje yafara fitar da su guda guda, Duk hakan baisa ta aje littafin ba ta dube shi saima kara mike kafa da tayi tana kadawa, Sadiya, Abubakar ya kira sunan ta acikin nuna son ta maida hankalinta zuwa gare shi, Littafin ta aza saman cinyan ta tadan dawo da diban ta gare shi, Hankali ta ga ba daya ya koma gare shi, don son jin may zaice, mata, Da farko kayan siturun da ya,sayo mata,su ya fara turawa gaban ta Dago kai tayi tana son jin karin bayani daga bakin maigidan nata, Wanan kayan naki ne ki dinga amfani dasu, pls, sai kuma wa yan nan kayan Ya nuna mata kayan leda kayan abincine ki kai su duk inda ya dace a aje ko wani daga cikin su, Daga haka Abubakar ya mike zuwa dakin kwanan su don yadan watsa ruwa ajikin shi, Abubakar bai fitoba sai gab da sallah magrib don ahi mutum ne mai son yin sallah a cikin jam,i kamar yadda sunna yai ko yi,,,,, A gurin da ya bar kayan a gurin ya samay su kamar yadda ya barsu, dazun, Mamaki sosai ya kamashi don shi a iya sanin shi agida idan mahaifan su ,sun shigo da kaya Tun daga nesa mace zata zo cikin ladabi takarbi leda ko kayan, akai su inda ya dace, Amma shi sai gashi yau , ya sayowa matar shi abu anma ta nuna mai halin ko in kula, da su, Agurin da ya barsu a gurin ya samay su kamar dazun, Shim ko don bata san kudin da ya kashe bane akan sayayyan da ta wulakanta, Wata zuciya tace, mai kawai rashin da,a da tarbiyan kwarai ne bata samu ba, Sai bayan ya je sallah ne ya dawo, ya kwashi kayan abinci zuwa inda ya dace akai ko, wani,,, Daga wanan ranan ne, ya sa wa rayuwan shi hakkuri akan duk wani al,amari na zaman takewan wasu, Abubakar mutum ne mai kwazo agurin aikin shi don shi dama irin mutanen nan talent ne, Sosai Yai fice gurin manyan ma,aikatan su wanda hakan yasa yana halar ta seminar kala kala akasan har kasa shen, waje, Don haka kudi ke shigo mai ta hanyoyi da dama daga gurin aikin,,,,,, ZEEE MAKAWA YELWA 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸 4⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA YAURI Tun safe yau idan ta shiga dakin ta sai ta dinga jin kamar kukan kaza, wace ta haihu, Amma ita ga tunanen ta kila kazace a bayan dakin ta ke kiwo har take ji a cikin dakin, Bayan shigar da fitan da takeyi a dakin sai ji take abin ya tsanan ta, Mamaki sosai takeyi ya akayi har kaza ta shigo mata daki batare da ta sani ba,, Neman gurin da kazar ke kuka mama Ladi ta fara yi, saboda kukan kara tsanan tawa yakeyi, Yar ta Samira ce ke taya ta duban kazan, dukawa tayi karkashin gado don taga ni ko da akwai kazar aciki, Sak kukan a karkashin gadon yake fitowa nan Samira, tadago kai tace wa mama ladi Mama inaga a nan na tta,boye, don kukan nan, na yaka fitowa, Shin wai minana a cikin wagga kwallan da nig gani , Gaban mama Ladi ne yaba da wani irin dam, a lokaci guda, Ba abinda yazo mata a rayuwa alokacin sai zancen kwallah da malamin su ya ce kwana arba,in cif ta bude, In ko ba demuwa ne ya kamata ba tana ganin yau kwana arbain ke nan cif ga lissafin da takeyi na kirga dutse, Da sauri ta ce wa yar ta ke maza kibar gurin ka ke jiya ko ? Sai yanzu nat tuna bakazata ba wallah daga waje na sautin ka hitowa ai, Da mamakin mahaifiyar ta, samira ta dago daga duken da take a karkashin gado, Kallon uwar takeyi ta ce cikin dan tsoro, mama walle cikin dakin ga na, Don kega wagga kwallah da nig gani kamar daga ciki naka jin motsi da kukan kazan, Kai yau Allah ya gwada min yarinya da dumin bazan , Shin bana hwada maki cewa ba kazata ba kuma aini hi ma ba anan kukan ka hitowa ba, Samira dai mikewa tare da nufar kofar fita wajen dakin, zuciyar ta fam da dan zargi da tsoro,,,, Ita ko mama Ladi, a lokacin tankar ta tsula fitsari a tsaye don tsoro, A hankali ta dan leka taga ni idan yar nata tabar gurin, Hanyar fita daga sashen na su ta hango Samiran, Kira ta sa wa yar nata da sauri Samira ta juyu zuwa kiran maman nata sai dai a zaton ta mama taga kazan da ke kukan ne. Don dai ita fa tabbas ta ji kukan kaza a gurin, da ta leka kasan gadon mahaifiyar su,, Mama tace in ni,ji ke hwada ma wani cewa ga abinda mun ka jiya, Walle yau sai na bata maki rayuwa yau don nasan ki da yawan bakin dumi, Baki samira ta turo gaba tana cewa kasa, kasa, Mi ruwa na da wagga maganan shin minzan tai zuwa hwadi ? Daga haka ta juya abinta tabar gurin zuciyar ta, na mai jin haushin cewan da mama tayi tana da bakin surutu,,, Da sauri mama taja kofan shigowa dakin ta ta rufe bakin ta dauke da kalman bissimillah ta mika, hannu ahankali ta jawo kwallah,,, Cikin dan tsoro ta bude bakin kwallah don ganin ko may ye a cikin yake wanan kukan,,, Zaune yake a office din shi aiki yai mai yawa, don a tsakiyan wata ake, Irin wanan time din ai,yuka kan yi wa ma,aikata yawa ne, sosai, Kan shi a duke yake yana fama da rubutu da ke gaban shi, Massagen su ne ya shigo office din da sallaman shi , Mutumin, ya na da kokarin girmama na,gaban shi sosai,, Duk da yasan cewa ya girmay masu so,sai ba kusa, Amma hakan bai sa yai masu girman kan kai ba akan aiki, Hakan ne ya jawo mai,samun alheri ga ma,aikantan da yake aiki tare da su, Abubakar yadan dago kai don jin anyi sallama an shigo mai office a wanan lokacin da kowa ya natsu ya na aiki, Duk da yawan daure fuska irin na Abubakar idan yaga baba masinja yakan sake fuska, A,a baba kai ne tafe shigo ma,na karaso, in ce dai lafiya ko ? Abubakar din ke tambayar shi ba tare da ya,daga,kan shi daga aikin da yakeyi ba, Lafiya lau malam sai alheri, dama wani bako ne ke tambayan ka, daga waje, Shine na ce, barin masa iso ko kasan da zuwan shi ? Mamaki ne sosai a fuskan Abubakar din don dai shi yasan cewa baida wani wanda zaizo ya samay shi, Asalima shi tun zuwan shi garin Lagos bai yi aboki da kowa ba, Iyakar shi daga gurin aiki sai gida sai kuma makwabtan shi da,suke dan gaisawa sama sama da shi, Cikin mamaki Abubakar din ya kara tambayar baba masinjan shin bakon shine kuwa, Baba ya dan gyara tsayuwar shi da kyau yace, kwarai kuwa don ma harda sunan ka,da kuma addreshin ka yazo, Dan shiru ya yi can kuma sai ya ce , ashigo dashi kawai malam mudi,, Da sauri malam mudi ya juya zuwa, inda ya fito don yai wa bako iso, Turo, kofan da akayi yasa Abubakar saurin daga kai, don ganin bakon, Cikin sauri da dago kai, ya mike tsaye,, tare da fadin Baba Wada, da karfi,, Shima dai Baba Wadan cikin jin dadin rashin shan wahalan da bai yi ba,sosai gurin neman gidan dan yayan nashi yasa shi saurin washe bakin shi,,, Cikin jin dadi da nuna kulawa sukayi ban hannu da junan su tankar wasu abokai, Baba daga ina haka, ? Abubakar ya tambaya cikin mamaki, ? Ganin bakon nasu ne yasa malam Mudi, masinja ya juya da sauri zuwa, waje, Ba ai wani dadewa ba sai gashi dauke da kwalban Martina da, take,away a hannun shi, Wanan Abin yasa Abubakar kara jin dadin malam mudi masinja, Malam mudi ya kawo wani dan tebur ya aje mai a gaban shi, Tare da aje abincin a saman tebur din yai wa baba wada wanda ke ta faman raba ido ga office din dan yayan nashi,,,,,, A tare suka juyo zuwa gida inda Abubakar ke nuna jin dadin shi, Sai tambayan Wada yake yi labarin kowa a gida, yana bashi ansa,, Sun iso gida inda suka samu matar gidan kamar kullum a falo zaune, tana kallon TV, ga kuma littafi da cup wanda ke nuna cewa wani abu ta sha acikin shi, amma bata kawar ba ko ta wanke, Ganin Baba wada bai wani sa Sadiya farin ciki ba sam duk da tagane shi tasan cewa zata iya jin labarin iyayyen ta agurin shi, Sun dai gaisa sama sama da shi inda hakan bai wa baba wada, dadi ba, sam, Amma sai dai ya dake saboda ya san cewa ba gurin ta yazo ba ai, Abinda baba Wada ya fara lura dashi shine, ganin da yayi Abubakar ke ta kokarin, yin hidima da shi,,, Da mamakin haka ya kwana a dakin da Abubakar ya gyara mai ya kuma kai mai yan abin bukata, na rayuwa,,,,, A gida hankalin ma haifiyar Wada duk ya tashi don rashin ganin shi da batayi ba tun daren jiya, Hakan yasa ta duk shiga cikin wani ya na yi don Wada bai taba yin hakan, ba, Bayan majalissan malam ya tashi ya dan dogaro sanda shi irin wanda malamai tsofaffin hausawa sukan yawan rikawa, zuwa cikin gida, Wanda sashin malam din kusan shine na farkon shiga gidan, Shimfidar shi dama a gyare ya ke tun kafin ya shigo, Da zaran ya shigo ya zauna matan gidan sarakan shi zasu dinga kawo mai gasuwa, Daga sashe, sashe na gidan suna cewa Baba ho, shiko yana cewa ingwaiyya, Idan kuma jikoki ne sai su ce A ho, Baba, sai yace shin wata, ta, Mai shi zai fadi sunan shi sai tsufon ya ce a,a to ke ta, Ko kuma ya ce kai na , ho dan nema, bakai barci ba, shin,? Sai bayan duk kusan yan gai da baba malam sun gama sintirin su, Sanan matan malam suka iso gurin shi, A lokacin yana kokarin gyara zama da kyau don Abinci da ta gabatar mai da ruwan sha, Sai bayan ya gama ci ne san,nan maman Wada ta kawo zancen rashin ganin dan ta tun daren jiya,, Shiru malam yayi don shi ya ma riga ta gane cewa Wada bai gida tun dare, don ba da shi suka yi sallah asuba ba yau, Maman tace walle tun dazun jiran ka dai ni kai ka, taho malam in hwada maka, Shin saratu inba abinki ba yanzu da dare na ki hwada min Wada bashi gida ko, ko ya bata, Da ina ki,ka son in, hwaro? Da sauri tace "Ko, ni an malam gani niyyi kana cikin jama,a shinas,sa ban hwada maka ba, malam an,, Nan malam ya fara fada sosai akan rashin fada mai da mama saratu taki yi da,wuri, Baba Buhari aka fara kira sai sauran yan uwa, inda atake hankalin mutane duk ya tashi a lokaci guda,,,,, Kusan a tsaye ranan yan gidan suka kwana don dai su a sanin su Wada bai san ko ina iyakar shi cikin gari, Baba Samaila wanda sai da safe yadawo daga kauyen da ya tafi lodin shanu don kawo wa kasuwan Kalgo da zata ci washegari, Shine ya fara cewa cewa shin ko dai Logos na Wada ya tai, Inda Abubakar,? Wa, gwada mai hanyan kurmi inji baba Shaibu, Baba Buhari ne yace, "Wane, ? Rabu da dan yau kaji, ai tunda kaji Samaila ya ce haka to a kawai dai, Malam dake jin muhawaran diyan nashi yace,, Missa ka ce haka ? Baba kwanakin baya da ni,ddawo yaka tambayana Wai nawa na,ka kai mutum Lagos da nan kebbi, ? Ni tambayai ko wa kazuwa Lagos din shina yace min wai wani abokinai kason zuwa,,,, Don Allah kuyi hakkuri da,wanan pls ban da caji ne yan uwa,,, ZEEE MAKAWA YELWA 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 5⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA YAURI ARRAHAMANIN RAHEEM A hankali take kokarin mika hannun ta don ta bude kwallah da aka bata, Sai duk a cikin tsoro take yin hakan, amma zuciyar ta ya kagu da ta bude saboda tana tsan manin KUDI,NE, ma su din bin yawa acikin, kwallah akai mata , na sihiri, kamar yadda take zato, Amma tunanen ta, ya fara harbawa ganin ta a cikin dukiya tana yadda take so da KUDI,,,,,,, Jawo kwallah tayi zuwa tsakiyan dakin ta a hankali, gurin da haske yake,, Daga tsugunen da take ta mika hannun ta ta bude kwallah a hankali, Cikin wani, irin gigicewa ta jefar da marfin kwallah a gefe guda tana mai, fadin INNA,LILLAHI, WA,INNA,ALAIHIM RAJ,UN,,, Yau naga shiga uku ne Ladidi may na daukowa kaina a gidan duniyar nan, Kara kai idon ta tayi a karo na biyu don ta dubi kwallah ta kara ganin abin da ke a cikki karo na biyu,, Amma ina sam bazata iya jure kallon wanan mugun halittan dake a cikin kwallah ba, Wani irin halittane tankar fuskan mutum dan Adam aciki, Amma da wasu irin abu bakikirin kamar gashin dabba ko kiya shi suna bin shi, Ga abin wani jalo,jalo da shi kamar jani in,jaka, yana wani irin yawau,yawau a cikin kwallah, Da farko taso ta nufi waje da gudu don neman agaji, Amma kuma sai dan natsuwa ya shigo take tunane yazo mata may zatace wa mutane, akan abin, Bayan an san cewa wanan kwallah ba nata bane, Motsi taji kamar za,a shigo sashen nata cikin wani iri dakiya ta jawo marfin kwallan ta rufeshi da sauri ta tura karkashin gado, Sai wani irin zufan tashin hankali ke tartso mata daga cikin jikin ta, Waje tayo don ko dakin yanzu bata bukatan wani ya,shiga ciki, Samira ce yar ta ta dawo daga sashen kanin mahaifin ta inda akwai yan mata har kusan mutum biyu sa,in ta, Duk da Samira yarinya ce to amma ta dan kula da rashin natsuwan hankalin mahaifiyarta a,wanan lokacin, Mama halan minana, shin,? Ko kukan kazan na ka damun ki ? Mi, kin,ka gani halan ?,,, A,gani kawai nayi awa hankalinki a tashe, shike, Ke Samira, walleh bani son diban albarka ke ji,,, Haka dai ki ka lakako sheri ki azamin,,, Ko ni mama Allah ya baki hakkuri walle gani niyyi awa, a hargitse ki ke, Yau Allah ya gwadamin mara,kumyah, yariny,,,,, Bata kai ga cewa yarinya ba,sai suka ji kukan kazan tankar a tsakiyan su, Mama Ladi ce ta riga Samira ja da baya a,cikin tsoro, Samira ma ta biyo bayan ta,a dan tsorace duk da dai ita bata ga abin tsoro a kaza ba,,,,, Abubakar shi da baba Wada suka shiga kasuwa inda yai mai sayayyan tsaraba masu kyau da tsada, Wada bai yi tsan,manin cewa Abubakar ya iya yi mai wanan irin tsaraban da yai mashi a yanzu, Don dai, shi a zaton shi Abubakar iya albashin da zai ishe shi ciyar da iyalan shi ne kawai a hannun shi, Amma sai yaga yayo mashi tsaraba kamar hauka, Tun daga malam Manya har, zuwa iyayyen su maza sai kuma matan gidan, Wada ya sa a,sayo mai yan kayayyaki da zai yi dan sana,a da,su irin wanda babu su anan arewa, Mota guda Akai mai sheta, har zuwa birnin kebbi shi kadai, Sai dai tun a mota Wada ke shawaran yadda zai bawa malam labarin irin yadda yaga zanan Abubakar da matan shi, a can Lagos, Amma kuma yana ganin kamar in ya fadi abin da ya gani a can bai kyautawa Abubakar din ba irin yadda yai mai wanan alherin mai yawa, Shi ko Abubakar ji yayi kamar kada, kanin mahaifin nashi ya tafi saboda yana son shi a ran shi, Sai dai kuma tafiyan nashi yai mai dadi don gudun kada ya dade tare da su har ya fahinci irin rayuwan sadiya, Hakan ne ma yasa baya, yarda, su ci abinci a gida gidan abincin da ke a unguwar su ya kai Wada ya ce duk sanda yake da bukatan abinci ko wqni abu na ci yaje gurin, Inda yai jinga da mutanen masu shagon abincin kan yadda zasu kula mai dashi,,,,, Sai da motan su Wada ta fara shigowa Arewa sai wani uban tsoro ya ziyarci zuciyar shi a lokaci guda,, Take malam Manya ya fado mai a rai, da kuma yadda yabar gida batare da ya fada wa kowa ba, Tsoro karara ya baiyyana a fuskan shi, jikin shi har dan rawa ya ke yi don bai san da wani fuska zai isa gida ba, Wata zuciya tace mai ya dake kawai tun da har ya samu bukatar shi ya biya, Kuma gashi ya samo jarin da zai dinga sana,a ya huta zaman banzan da suke a yar shiya shida abokan shi,,,,, Ita kan Samira fita tayi abinta inda Mama Ladi ta koma ciki a hankali cikin tsoro ta jawo hijabin ta tare da rufe kofan dakin ta da kwado, Gidan Hajja ta, sulale ta nufa hankali a tashe mata don duk ji takwyi tankar abin da tagani a kwallan ya na biye a bayan ta, Mama Ladi hankali a tashe hajja ta gan ta don haka ta ja ta zuwa daki saboda kada mutanen da ke gidan ta masu sayen kaya su ji, zancen su, Sai da ta gama koro wa Hajja yadda al,amarin nata yau ya wakana tas, Sai Hajja ta washe, bakin ta wanda ya rine saboda cin gora, Cikin jin dadi da farin ciki, tace ki ce min aiki yayi kyau ke nan Laduwa, Wane, irin aiki yayi kyau, in hwada miki abinda niggani da injiyana cikin kwalla, Aiki kan baci ya yi wallah, Mama Ladi ce ke fadawa Hajja haka,, Kamar wace zatai gulma ta matso kusa da, mama Ladi tace, Yanzu komawa zakiyi, duk inda kaza wadda tai sabon haihuwa wadda kin kaji dodon ki na kuka shi zaki samuwa kitai a yanka maki ko dan jinin shi kadan kin ka samu ki,ka zuba cikin kwallan ya wadatar da ke, Shi ke nan bukata tabiya Laduwa, Ido waje mama laduwa, ke kallon, Hajja cikin sarkewan Murya tace, Hajja, Shin mi, kki ce ? "Ke san ko mi ki ka hwadi, Shin, Ni Laduwa ta zan tai yin duk wagga abin da kin ka lissafo min, Cikin nuna bacin rai Hajja tace , To wa kika son ya tai yai maki, ? In kin ka samu kudin ki dawa za ki bushasha? Babu ko sallama, mama Ladi ta mike duk da taji muryan Hajja tana magana amma bai sa ta tsayawa ba don sauraren ta, Sai dai kunnuwan ta ya jiwo mata Hajha na cewa indai har baki bashi abin da yakaso ba walle yau kina rasa wani gidan ku, Tafe take tana hadawaa da tun tube sai faman sababi takeyi a hanya, Bayan ta koma gida ne duk abin duniya ya damay ta don tunawa da kalamin, Hajja na karshe da tayi, Alwala tayi inda ta shiga daki don gabatar da sallah azuhur saboda lokaci ya gabato, Bayan ta idar ne ta zauna ta dinga jero irin addu,oin tsari da tayi dama wanda ba na tsari ba, Hakan ne yasa taji wanan kwallan ya rage kukan da ya ke yi , Saidai duk da haka hankali mama bai kwanta ba sam, Yau, ce rana na farko da tai nadaman kulla kawance da Hajja a rayuwan ta, Mai gidan ta ya hane ta da hurda da hajja amma duk taki haka ma malam manya da kan shi yasha fada mata cewa ta rage zurewa Hajja amma sai taga kaman suna mata kyashine da hassada, Don sun gan ta tare da wace zata mai hanya ci gaba,,, Yadda taga dare haka taga rana, don ta kasa runtsawa, kuma ta hana kowa ranan kwana dakin ta, Dama malam Buhari ba a dark n ta yake ba, a ranan, Tun da asuba bayan idar da sallah kwalla ya fara maimata kukan shi irin na jiya sosai , Don na yau babu kakautawa, don kuka yakeyi bilhakki, Mama Ladi hankalinta ya kara tashi sosai gata duk ta zabge a lokaci guda ta,wani ramay wa, Bayan an idar da sallah baba buhari ya,gama ganawa da mahaifin shi, Direct sashen mama Ladi ya nufa don su, gaisa don haka dabi an shi yake dama, Zaune take a kofan dakin ta a cikin tashin hankali tayi tagumi da hannu guda, Tun daga nesa baba Buhari ya gane cewa babu lafiya, Ladi lahiya dai ko? Baba Buhari ke tambayar ta cikin sanyin murya irin nashi, Maimakon ta bashi ansa sai ta kasa daurewa ta sa kuka , hankalin Baba Buhari ya kara tashi inda yace, Subbahanallahi, halan mi,ya faru, ? Wa mutun shin ? Ta,na yi tana dan leken kofan sashen kishiyan ta tace cikin marairai,cewa, Walleh malam magana na ni, dauko maka, shina ka damun, Halan mi ankayi ? Sai kuma tasake sa kuka, Nan hankalin Baba Buhari ya kara tashin don yasan kukan ladi ba na wasa bane, Yau ko gata tana yi ido biyu, Hwada min mana mi,nana shin ? Malam am, mutai ciki ka jiya, Dakin suka shiga tare, da shi inda sai raraba ido ya keyi ko zaiga yaran dakin amma baiga kowa ba, Shin ina yaran sun ka tai,? Suna can inda Bagudo na tura su, Mama ladi ta bashi ansa da hakan, Mi kawo kaza har kuryan daki shin? Walle malam Ba kazata ba, Kaza ta ke bakijin kukan ta na,, Walleh malam nice maka ba kazata ba, "Sihiri" ta, Murmushi yayi yace wane irin sihiri shin ga kaza ina jin ta haihu tana kuka, Ko ni an malam nice ma sihiri na wallah, Sororo Baba Buhari ya tsaya tsaye yana kallon ta cikin mamaki, Wane irin sihira na haka, ? Bata boye mai komai ba ta fara fada mai , Dakatar da ita yayi don bai iya sauraren ta shi daya, Saboda mamakin abin da yaji ta fara fada mai da farko, Shin Ladi mi, kin ka rasa a rayuwan ki da har kin ka tai zuwa yin wagga harkan, Sai kuma maganar ta makale mai saboda takaicin da ya rufe shi,,,, Cikin bakin ciki da kunar zuciya ya zubawa mama Ladi ido, kuri, Sai kuma tunane ya zo mashi yanzu shi wa zai tun kara da wanga zancen abin kunya da mama Ladi ta jawo mai, Baba Samaila kanin shi wanda basu hada uwa guda ba dashi ya fado mai arai, Wanda yasan cewa bazai taba jin wanga zancen ba in har yayi shi da shi a gurin wani, Don haka Baba Buhari ya juya batare da kara magana ba, Yayi sa,a ranan Baba Sama,ila yana gari bai kwana daji ba,, Da sallama ya shiga har cikin Sashen Baba samailan, Da mamaki ya fito yana wa dan uwan shi kallon mamaki, Yau may ya kawo shi har cikin sashen shi abinda bai taba ga nin Baba Buhari yayi ba kenan zuwa sashen kannen shi, Don haka zuciyar shi ta ba shi cewa da magana ke nan yau,,, Yaya lahiya ko? Samaila, babu lahiya yau kan don dai walle matan ka Ladi ta dauko magana,, Nan yadan fara ba Baba Samaila labari kamar yadda ta fada mai da farko, Shiru yayi yana sauraron dan uwan nashi cikin na tsuwa, Sai da ya gama fada mai yace , Wanga zance shina Gaba kura baya Karen Daji,, Wa ka fadawa bayan ni ?, Baba Buhari ya ce cikin wata irin murya mai bantausayi, Wani ka hwada ma bayan kai, Da can wurin ta niyo nan, Inda kake, don babu wanda nika iya fadawa wagga magana, Ajiyan zuciya Baba Samaila ya yi tausayin dan uwan nashi ya kama ahi don yasan gaskiyan zancen ke nan ya fadi, Ina zuwa yace cikin sauri ya shiga dakin su bai jima ba ya hito saye da wata yar karamar riga ajikin shi, Mutai, yaya yace cikin karaji da sauri, inda dan uwan nashi yabi bayan hima da sauri, Mama ladi wace take a tsayen tun fitan Baba Buhari, Don a zaton ta Baba Buhari zai tara mata mutane ne a shiyan ta ya tina mata asiri,,, Sai ganin su tare, da Baba Samaila tayi girshi a Sashen ta, Cikin sauri Baba Samaila batare da ya tsaya dogon magana ba ya ce, Ina kwalla, yake, ? Kamar mai tsoro mama Ladi tadan nuna mai karkashin gadon ta da yatsa a hankali,,, Ba bata lokaci Baba,Samaila, ya duka karkashin gadon bakin shi dauke da addua, Ya sukuci, kwallah ba bata lokaci yai hanyar fita wajen gidan inda baba Buhari, shima yabi bayan shi da sauri suka bar gidan,,,, Da, sauri su duka biyun suka fada yar akwalan motar pekof din Baba samaila dake, can gefe guda ajiye, A bayan motan suka dire kwallah sai gudu baba Samaila, ya ke yi,,, Tunda ya dawo daga office ranshi yake a bace don baisan ko, wace irin mutum bace Sadiya, Ya za,ace mutum ya sauka agidan ka amma baka gan shi ba kuma baka tambaye shi, Da farko ya na ganin shine wanda bai da mu da hurda da mutane ba ko a gida, Amma sai yaga yanzu garama dashi bisa ga Sadiya wace bai taba jin ko tai hiran yan uwan ta ba , Daga inda yake zaune saman kujeran dake facing din nata, Ya ja wani rin tsaki mai tsananin karfi da kara, sannan ya ce, Wanan hali naki bai yi ba Sadiya idan zaki canza ki canza tun baki makara ba,,, Kallon shi Sadiya ke yi a cikin mamaki, don bata san ko fadan may yake mata ba haka, Yace ace mutum yai Bako bai gan shi ba kuma bai tambaya ba, Wanan wani irin rayuwane haka pls,? Mutumin nan fa kin sani sani kanin mahaifina ne,bawai wani bare ba, Amma kika nuna ko in kula a kan zuwan shi kika barni da dawai niya dashi, Maimakon tai magana sai kawai ta sake wani irin kuka mai karfi mai tsuma zuciya,,, Mamaki ta bashi saboda baiga abin kukaba acikin wanan zancen da yake mata ba a halin ywnzu,,,,, ZEEE MAKAWA YELWA,, 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 6⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA MALIKI, YUMEEDEEN Tafiya kawai sukeyi batare da wani yai wa dan uwa magana ba, Kowa da irin abin da ke a bakin shi, adduan sukeyi ta neman tsari daga shedanu ko wani iri mutum ko dabba ko Aljan, Hanyar JEGA, ya dauka don fita gari amma suna kai wa KALGO, sai ya dauki hanyar BUNZA,, Tafiya mai tsawo su kayi daga titi zuwa cikin wani daji, Sanan ya samu wani guru ya Parker motar suka fita ba tare da wani yai,wa dan uwa magana ba, Fatanyar dake a baya da shebur yadauka sai ya nufi wani kwazazaben rami inda ruwa ne acikin sa,daga gefe, Kuma a ko da yaushe ruwa zai iya cika gurin don damana ce, Rami mai zurfi ya haka agurin inda ya duka yai ta addua, a cikin ramin, Wasu irin manyan duwatsu da ke gefe ya kwasa, Shi dai Baba Buhari sai kallon ikon Allah ya ke yi a cikin mamaki, Mota Baba Samaila ya koma ya dauko wanan kwallah, Da farko a bakin ramin ya aje kwallah dake ta faman ihu da kuma kukan kaza, Cikin dakiyar zuciya Baba Samaila yace kai shedani daga yau babu mu babu kai, har abada, Idan kaga dama ka koma can gurin wanda ya kawo ka anna mu babu mu babukai babu iyalin mu, Kamar ana jira ya kare zancen shi sai sukaji wani irin tsaki mai karfi daga cikin kwallan a lokaci guda, ance, Matsiyata kawai a haka zaku kare ai , Arziki na binku kuna ki, Baba Buhari sai ya fara ja da baya don tsoro, Shiko Baba Samaila sai kawai ya duka ya sukkuci kwallah bai tsaya jiran komai ba sai ya juye wanan halittan a cikin wanan katon ramin da ya haka, Wani irin kuka wanan halittan ya kara sakewa kamar mutum a lokacin, Yace don Allah kada ka kashe ni zan bauta maku zan baku ko nawa kuke so, Zan dinga yo maku farautan duk abinda kuke so a duniya kada ku kasheni , Ina son in zauna a duniya nima kamar yan uwa na, Dutsen dake a gefen shi yadauka bakin shi na dauke da sunan Allah ya sake dutsen a cikin ramin da karfi,, Wayyo karku kasheni malam San,inna ne ya aiko ni gurin ta don in bata kudi, Wani dutsen Baba Samaila ya kara azama mai sama, Wani kara ya sake gami da yin tsuki ya ce wawaye kawai da kun barni da kun sha kudi da shanaye da hatsi,,,,,,, Kasa Baba samaila, ya mayar saman dutse tare da kara dora wasu irin manyan duwatsu akai yakara dabe gurin, Kana ya tofe gurin da addu,oi masu karfi sanann yadaga hannayen shi sama yai addu,a, Daga haka suka bargurin da sauri cikin tashin hankali, Sai a lokacin Baba Buhari ya samu bakin magana,,, Sai sharan gumi sukeyi suna ajiyan zuciya, ba tare da wani ya iya yiwa dan uwa magana ba,,,,, Da kyat Baba Samaila ya iya jawo mota, suka iso cikin gari, Saboda wani irin mugun zazzabi da ya rufe shi a lokaci guda,,,,,, Tun isan su ya shiga gida ido rufe ya cewa matar shi ta rufe shi sanyi yake ji,,,, Yai Barci yafi a kirga acikin motan kafin su iso Birnin Kebbi, Tun ganin sun fara jin kamshin gida sai barci ya fita daga idon shi, Babu abinda yake yi sai sakawa da warwalewa, na abinda zai cewa mahaifan shi a gida idan ya isa, Yace ba don sakon mutane da Abubakar ya bashi da bazai fadawa kowa cewa ya tafi har Lagos din ba, Shigan su garin Birnin kebbi da misalin magriba mota bata tsaya da shi ko ina ba sai uguwar su watau, shiyan Sarakuna,,,, Mutane suna alwalan sallah magrib suka ga tsayawar mota a sheke da kaya cikin ta,, Kowa idon shi na kai har malam wanda bai san ko wani bako ne ba a wanan lokacin, na huturo,,, Wada ya bude mota tare da ahi da driver suka fito a lokaci guda, Daga shi har driver haraman alwala suka fara yi duk da dinbin gajiyan dake a tare da su,,, Sai da ya karanto, yan addu,oin da ya iya wai kada malam yai mashi fada, a kan tafiyan shi, San,nan, ya tunkari gurin da malam yake a zaune ya jan casbi, Ganin yana lazimi yasa shi komawa baya a lokacin har driver ya fara sauke kanyan motan, Nan Wada ya kira yaran dake gurin don su kwashi kayan zuwa cikin gida, Mahaifiyae shi da tun isowar shi yara suka sheka suka fada mata tana cen cikin farin cikin ganin dan ta ya, dawo gida lafiya, Ganin irin kayan da ake ta faman shigowa da shi wai duk tsaraban Baba Wada, Shi yasa har matan wani lungu zuwa ganin gulma da sunan sun,zo taron Wada ne, Abin "da mahaifi, har mahaifiyar shi ta gabatar mai da abinci da su ruwan sha a daki, Sai daukan abincin yayi yace bari ya kai, waje su ci da driver, Sai a lokacin mahaifiyar shi wace jin dadi ya hana ta tun farko tambayan Dan, nata inda ya tafi, Kai tsaye batare da wani shakkunta ba ya ce mata, Lagos gurin Abubakar, Lagos Wada ? Da kai dawa shi katafi ? Ni kadai ya bata ansa a takaice,batare da jin wani darr, ba, Kafin tai wani magana ya sukkuci kolan abincin nashi zuwa waje gurin driver da ya ce, Ya samu har yana niyar tafiya alokacin amma sai wada ya tsaida shi da magiya don ya tsaya suci abinci, Da kyat driver ya tsaya inda sukaci abinci da abokin tafiyan shi na wanan ranan,, Wada ne a gaban malam kai a sunkuye, cikin tsananin tsoro malam karo na farko a rayuwan shi, Don haka ya yanke wa kan shi shawaran fadawa malam cewa Abubakar ne ya bukaci ya zo inda yake, Wanan zancen ya batawa malam rai inda yace a harzuke yaushe har ka ga Abubakar din yace kazo, Kai a sunkuye Wada ya ce tun lokacin da zai koma da yazo , Wanan zancen kawai ne inji malam watau kai ka girma har ka kai lokacin da zakai bugun gaban kan ka, ka ai,watar da abin da kaga dama,? Wada yai maza ya kara sunkuyar da kan shi a kasa,, Don jin may mahaifin shi yace, da kyat ya iya cewa ayi hakkuri malam, Malam yasan idan yace zaiyi magana rayuwan shi zai ci gaba da baci sai kawai yaja bakin shi yai shiru,,, Tsawon wani lokaci Wada ya na duke a wurin, malam bai ce komai ba sai can yaji muryan malam ya na cewa akira ma shi Samaila, Hakan ya sa wada gane cewa ba zancen shi malam ke yi ba,a yanzu, kuma, bai da halin yin maganar, Don haka ya mike a hankali zuwa dakin mahaifiyar shi,cikin sanyin jiki,, duk sai bai ji dadin abinda ya aikat ba, Dan sako yadawo yana sheda,wa Malam cewa Baba Samaila wai tun safe bai da lafiya, Cikin murya mai kama da fada Malam Manya yace,, Samaila yaro na ? da zai zauna da ciwo daki bai fadawa kowa ba, Baba Buhari malam yasa a kira mashi don ya je ya dubu Baba Samaila, ya ga ya jikin na shi, ya ke,? Sosai Baba Buhari hankalin shi ya tashi don dama duk yinin yau baida kwanciyar hankali, Rayuwan shi yau a,bace yake don bai ko son yaga mama ladi a fuskan shi yake ji,,,, Yadda Baba Buhari ya samu Baba Samaila yasa hankalin shi tashi a lokaci guda, Don a rufe yake tun daga kan shi harzuwa kafan shi cikin wani katon bargo, Take abinda yafaru da safe dasu ya fado mai a rayuwan shi, Cikin wani irin tausayi da kuma tsoron halin da dan uwan shi ya ke a ciki,,, Cikin sauri ya juya zuwa gurin Malam Manya mahaifin su don ya sanar da,shi abinda ke faruwa, Tsugune Baba Buhari ya ke agaban mahaifin su yana sheda mashi abinda yafaru dashi, Subbahanallahi inji Malam yace ya akayi baku sanar da ni ba tun farkon faruwan abin, Daga haka ya mike shima yau da kan shi har cikin Sashen Baba Samaila, Kamar yadda Baba Buhari yabar shi tun farko hakan suka samay shi, Kira biyu zuwa uku Baba Buhari yai ma Baba Samaila amma bai iya ansawa, ba, Hakan ya kara tayar masu da hankali sosai don haka ba bata lokaci malam ya,juya,zuwa Shiyan shi, Bayan wasu lokota,sai ga malam ya,dawo dauke da wani roba mai, ruwa aciki, shi,, Malam, yasa Baba Buhari ya kware mai bargon da ya ke a ciki, Kwance yake idon shi a kafe sai, rawan dari da yake yi, Daidai gurin kan shi malam ya nufa inda ya dafe goshin Baba,Samaila, a hankali, Adduoi, yafara jefo mai ya na tofa mai a goshi, sai kuma, ruwan da yake yayafa mai a duk kan sassan jikin shi a hankali, Ba,a gushe ana mai haka ba ya sake wani irin ajiyan zuciya mai karfi, tare da kokarin dagowa, Cikin sauri Baba Buhari ya dan danne shi ta mai da shi saman gadon, A hankali ya ke bude idon shi acikin wani yanayi na rashin fahinta, inda yake sosai yake kallon su, Ganin haka hankalin Baba Buhari yai matukar tashi, a take idon shi ya fara silalo da hawaye, Nan take gaba dayan su suka shiga karanto addu,o,i iri iri don neman tsari a gurin ubangiji mu, Sannu a hankali ya koma barcin da yake yi sai dai wanan karon numfashin shi yana sauka,a hankali ba kamar farko ba, Ganin ya samu barci kuma alamar da yar sauki a zancen Yasa malam yasa Baba Buhari ya debo mai garwashin wuta a waje, Cikin sauri baba ya nufi gurin samo garwashin, wutan da aka umurce shi, Wani dan kulli malam y bude ya debo hayaki aciki, Nan aka zuba duk da barci yakeyi amm sai da ya dinga sake atishawa, mai karfi har sau biyu, Malam manya da Baba Buhari dake gefe suka, sauke ajiya zuciya a hankali, Sai a lokacin malam ya juyo inda Baba Buhari yake a tsaye, ya ce, Ya samu sauki insha Allah, amma idan ya farka a bashi wanan ruwan ya sha, Har malam ya taka kamar zai bar dakin sai kuma ya juyo, inda Baba Buhari yake a tsaye Yanayin fuskan malam yasa gaban Baba Buhari ya yanke ya fadi, Malam yace,cikin wani irin yana yi wanan zancen yazama siri a tsakani ku da dan uwanka har matar ka, Cikin karfin hali Baba Buhari ya,ansa da kada kai gami da cewa to, a fili, Daga haka malam yabar shiya cikin sauri batare da ya kara furta wani abu,ba,,,,,, Mama Ladi wace tin safe ta kasa zaune ta kasa tsaye don maigidan nata bai ce mata kalla ba akan wanan mumunan halitan da suka dauka a dakin ta, wada za aiy da dodon kwallah a takaice,,, Ga sako tun da rana da Hajja ta damay ta da,shi wai tazo malam na San,inna na son ganin su, Wanan aiken ya kara tayar mata da hankali sosai don tana tsan,manin ko, dodon kwallah ya koma gurin shi ne, Amma ta san yau duk abinda zai faru sai dai ya faru don dai ba ta da wani kafa da hae zata samu fita zuwa Anguwa, Don a yinin ranan ba abinda takeyi sai rokon ubangiji Allah sauki,,, Ba karamin kidemawa mama Ladi tayi ba, don ganin irin aiken da Abubakar dan ta wanda suke kira da mai sunan malam, ya yi ba, Hakalinta ya tashi kwarai duk da tana cikin tashin hankalin dama, Sam bata taba tunanen cewa yana da irin wanan arzikin ba, Sai gashi zuwan Wada gurin shi yai ma kowa aike da ya tayae mata da hankali, Mama bata san lokacin da ta manta wancen zabcen Dodon kwallah nata ba, Sai ta hau sake maganganu kawai tana cewa wai anfara zuwa gurin dan ta yawon maula batare da sanin ta ba, Sai kuma cewa da takeyi ita bazata yarda a mallake mata "da ba har ya dinga abu batare da shawaranta ba, Hakan yasa tun tana yi ba wanda ya tanka mata har saida Baba,Buhari ya taka har kofan nata duk da haushin ta da yake ji, Daga labulen dakin yayi ya ce mata cikin fada, Ji mana Ladi, Kin dai san cewa dama ina da,ke a raina ko? Ba wai na manta da zancen bane,, Don a,sanadinki ga dan uwana can a kwance tun jiya, Don haka ki san zaman ki a gidan nan tun yanzu don ba, zan yarda ki zubar muna da darajan gida ba a cikin shiya,,, Tunda Baba Buhari ya fara magana sai mama ladi tai tsit don ta hango zancen gaskiya ya ke a idon shi,,,, Ganin bazata tanka masa ba yau ya sa shi kumtawa da karfi alamar zaki sani,,, Can cikin gida kuwa sai murna da farin cikine ya mamaye kowa don ba lungun gidan da,ba aiwa alheri ba, Abinka da babban gida kafin wani lokaci labari ya karade cewa mama Ladi batai farin ciki ba da,wanan baiwan da Allah yai mata,a dakin ta, Don dai ka haifi da yana wa mutane alheri wani abu ne na musan man,,,, Yau kimanin sati uku ke nan da komawan Baba Wada gida daga Lagos, Zama tsakanin Abubakar da matar shi ana dai yi ne kawai don kowa ma miskilin kanshine, ba mijin ba ba matar ba, Babu wani abinda ke burge shi daga halaiyan Sadiya din, Duk ta kowani gefe Sadiya bata da gurin da za,a yaba mata akai, Don haka, yau tun wayewar gari Abubakar ke son yiwa Sadiya magana akan ta je gurin gyaran kai ko kitso, Sai dai kuma yana dan shakkan yi mata zan cen don baya son ta fassara mai zancen shi, Don inhar son samu ne itace da kanta ya kamata ta san kanta yana bukatan gyara, Gashi kuma agaskiya dole ne yau ya daure ya fada mata ta gyara kan nata, Sai da ya dauko goran ruwa a fridge ya dawo inda ya ke zaune da farko, Muryan shi Sadiya taji yana cewa Ni kan dai Sadiya nace yau ya kamata ki shirya in kai gurin gyaran kai ko kamar yadda naga mata suna yi,, Abinda Abubakar ya fahinta shine tunda ya fara magana Sadiya tai yi kicin kincin da fuskan ta alamar maganar bai mata dai ba, Sai cewa tayi gaskiya ni ban son fita ban san kowa ba a gari Ai,kuma gashi, nakan iya kamawa na gyara da kauna, Murmushi yayi irin na takaici yace Sadiya ke nan In banda abinki ta yaya mutum zaiwa kan shi gyara kamar yadda wani zai mai yayi kyau, Kara bata rai tayi alamar yanzu bata yarda da zancen zuwa gurin gyara ba, Daga karshe sai cewa tayi ni banga rashin kyaun wanan din da nake lalabawa kaina ba, Galala ya yi ya saki baki yana kallonta don kuwa tagama bashi mamaki,,,, ZEEE MAKAWA YELWA 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 7⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA IYYAKA NA,ABBUDDU WA,IYAKA,NAS,TA,INN, SADAUKARWA Sadaaukar da wanan pages din a kullun gare ku yan family mu na ALIYU HARZAMI KANO FATAN, ALHERI GARE KU MAKARANTA WANAN NOVEL DIN MAI FADAKARWA, A kan wata katuwar shifidaddiyar tabar suke zaune, a sashen malam, Kallo guda zakaiwa Baba Samaila kagane cewa yai ciwo mai karfi a cikin yan kwanakin nan, Duk wanda yaga irin yadda aka shimfida wanan tabarman yau in dai har a gidan kake ba wani abin mamaki ba, Don duk wata maga tasamu mai muhinmanci za,ayita haka ake shimfida, Sai har matan sashen na malam dole a lokacin subar sashen har zuwa lokacin da za,a gama zancen, Zaune suke da alamar suna jiran wanine a lokacin, Mama Ladi ce tafe cikin tsoro da fargaba take tafiya don jin da tayi cewa malam ne yau da kan shi ke kiranta, Wasu zannuwa masu ruwan zuma da yan adon flowers kore da ja ne a jikin ta, Ta daura guda da dan kwalin shi da riga sauran sanda biyu kuma ta yafa a jikin ta har zuwa kai, Azaton mama ladi tunda taji shiru har kwana kusan goma ta dauka zancen ya wuce ne, Amma kiran da malam yai mata yau ya sa ta jin nauyi da fargaba don bata san ko may zai faru ba, Wani iri tsuki Baba Buhari ya ja tunda ta tunkaro gurin, Cikin tsawa ya ce mata ke dai san ke mu ka zaman jira tun dazun shina ki ka wagga tahiya, Malam Manya ne cikin murya irin ta manya ya ce mashi koni, "an, bita sannu, tunda ta taho,,, Can gefe guda,mama Ladi ta samu ta zauna ta gaida malam a hankali, Addu,a akafara bude taron dashi,, tare da neman wa zurian su gamawa lafiya, da fatan alheri ga ko wani musulmi,,,, Gyaran murya malam din yayi wanda ya kara dawo da hankali kowa zuwa gare shi, don sauraren abin da zaice, Malam ya fara da kiran sunan mama Ladi, da cewa, Ladi, Mama ta ansa kai a sunkuya da cewa naam Baba, Wanan zaman da ki ka ga mun,yi don ki muka yi shi badon komai ba sai don, mu tatauna mu ji yaya ankayi haka ya hwaru,? Shirune ya biyo baya tankar babu wani mahaluki a gurin zaune, Ganin baza tai magana ba yasa Baba Buhari cewa cikin bacin rai ko ni an malam bari dai in yanke alakata ga wagga bakin irin , Yar nema mugguyar shiya, Dibo wadda kinka mayar min da dan uwa saboda bakin kwadan ki, Mi kin ka rasa duniya ? da,,,,,,, Malam ne ya katse Baba Buhari cikin daga hannu tare da kiran sunan shi da karfi, Wanda hakan yasa baba saurin yin shiru don bin umurnin mahaifin shi,,, Malam ya ce Ladi an, magana zakiyi don musan ta ida zamu bullo ma,wagga zancen, Don ba karamar magana ta, ba ke ga aikina ta sihiri, Ko yaushe yana iya dawo wa, Gaban mama Ladi ne ya fadi ras don jin cewa wanan dodon kwallah zai iya dawo wa ko wani lokaci, Zama ta dan gyara tare da kara dukar da kan ta a kasa inda tafara cewa,,, Malam, walle sherin shedan na da kuma Hajja ,,, Gani ni, nayi ina zaman banza bani sana,a shina na tai inda Hajja, ni ce ta taimaka min, Walle bata fada min cewa sihirina za,a yi min ba sai dai bayan kwana biyu ta aiko min cewa in aiko da, kwalin, Lipton shayi guda uku, Sai na saye na aika mata dashi takara aikowa tace in dan bayar da ko nawa gare ni,, Sai na aika mata da dari biyar, bayan kwana hudu ta aiko cewa ranan laraba mai zuwa in taho da kwallah akwai inda zamuna Sainace mata banda kwallah mai dan kyawo tace min in bari tana dubawa cikin nata,, Sai kuma ta kasa karasa maganan tai shiru tare da dukar da kai, Muryan malam ce da ya jefo mata tanbaya yasa ta saurin dago kai, Wane malamina ko in ce boka kun ka tai wuri nai ? Nan ma shiru mama Ladi tayi saida Baba Buhari ya daka mata tsawa, Cikin dan i,iniya tace malam na San,Inna munkatai wuri nai Wa, akacewa hakana inji malam ke tambaya tace shina can kasan yar mayan ka shike da zama, Salati sukayi gaba dayan su yadda akayi tun daga shiyan sarakuna ace mace ta tashi har mayan ka,,, Malam ya ce Ladi baki kyauta ba gaskiya, ke manta da gidan da kika aure na,, A ce yau macen da ke gidan ga na, ta tai gurin Boka don dai rashin tawakkali, Ladi rashin tauhidi na har ya kai,ki ga wagga harkan, Yau idan kaga mutum na sha,ani nai iyakan ka dashi ijjiya, Amma tambaya ba shi shuka ma alheri ga wagga zamani da muke ciki, Ke de ga halin da dan uwan mijinki ya shiga ciki sanadiyar wagga abin, Sai a lokacin mama ladi ta daga kai ta dan kalli Baba Samaila wanda ya ramay ya wani zabge a lokaci guda, Nan da nan hankali mama Ladi yai matukar tashi ,, Tai matukar kidimewa don ganin irin yadda Baba Samaila ya koma a lokaci guda, Sai kawai ta shiga rusa kuka wi,wi tana cewa malam don Allah a yafe mata tayi kuskure, bazata sake ba insha Allah, Malam ya ce, yanzu da zaran zancen ga yai girma duk gari ji zasuyi a dauka cewa tana MAITA, Don ke ga Allah ya taimake ki da ace kin fara da bashi kazan da yaka so da shikenan ke bi hanya, Don wata,rana har mutun zaicewa ki bashi jinin shi yasha, ke ko idon ki ya rufe kin iya sihiri Baba Samaila dake zaune jingine da bango yace ai,duk zafin neman bai kawo samu, Kawai mutum ya hakkura ga duk yanayin da ya tsunci kan, shi, don yanzu badon Allah ya gyara ba da, ba,a san iya inda wanan abin zai tsaya ba,, Cikin muryan kuka mama Ladi kewa ku ya fe min don Allah Malam yace Allah dai ya yafe muna baki dayan mu,, Kuma wanan zancen ina son ya tsaya dai dai iya mu kada inji shi ga wani nan gaba, Hakan yaiwa mama dadi so,sai don malam ya kashe wutan zancen,,, Haka rayuwa ta kasance da ci gaba a gidan malam , Yanzu tsakanin mama Ladi da Hajja sai yar nisa da nisa don babu irin mugun shakuwar nan ta da, Ita ko Hajja ko a jikin ta don arzikin ta,sai gaba gaba ya ke yi a koda yaushe,,,, Rashin zuwan Abubakar gida akai akai ya fara da mun malam, Manya yanzu, Don a iya ka sanin tun lokacin da mai,sunan nashi yai aure har izuwa yanzu baizo gida ya kai sau uku ba, Gashi yanzu tasan ma,shekara, biyu da rabi da auren shi, Abu guda ne shine duk wani dan uwa ya je zai aiko masu da sako mai yawa a kawo masu, Ita ma fanin Sadiya matar shi haka ne,ko da yake mahaifiyar ta ba wai ta wani damuwa tayi da rashin zuwan yar nata gida ta yi ba,,,, Kuma yadda yan gidan su, Abubakar suka damu da rashin samun karuwan ma,auratan, Ita Hajja a nata bangare hakan bai wai damay ta ba sam,, Idan anyi magana cewa har yanzu dai sadiya bata haihu ba sai tace lokacine bai yi ba, Ita ko, bangaren mama Ladi ko in ce gidan su Abubakar rashin samun haihuwan shi na da mun su, Tun dai malam Manya wanda kance abokina dai har yanzu shiru ba labari, Bukin Sallah babba na bana Allah ya nufi Abubakar zuwa gida tare da mai,dakin shi watau sadiya, Daga shi har ita kallo guda za kai masu kasan cewa akwai kwanciyan hankali da wadata atare da su, Don hasken shi ya fito sosai gashi ya dan kara jiki da girma, gwanin ban sha,awa, Wanan zuwan da Abubakar yayi ya kara tayar wa malam manya hankali irin yadda yake jin labarin, jikan nashi abin yafi da nan so sai,, Gashi harda motar kanshi yazo lafiyya ga kuma tsaraba mai yawa, Sai,dai duk yawan wanan tsaraban da yazo da su a kofan dakin mahaifiyar shi, mama ladi a ka labta su,, Wanda shi Abubakar sam bai so haka ba yaso ne ace akai su can kofan dakin malam, Tun da malam ne wanda ya tashe shi tun yana yaro sai ko sauran iyayyen su maza musan,man Baba Samaila,,, Wanda tun baiyi aure ba duk abinda ya samo sai yace na Abubakar din shine , Mutanen gidane ke ta turuwan zuwa sashen Baba Buhari gurin gaida bakin Lagos da sukai saukan dare,, Don ba,a samu ganin su da dare ba sai yau da safe don haka ake ta zuwa, ganin su,,, Girman da yaran gidan nasu yayi yasa shi mamaki matuka don bai yi tsanmanin cewa sun,kai haka ba, Kusan duk wanda ya shigo indai dan gidane da tsaraban shi, Amma kuma sai wanda mama taso aba ma abin kwarai, Duk wanan rabon da akeyi babu dan shiyan Baba Samaila ko mutum guda da ya shigo sashen, har zuwa yanzu, Daidai shigowan ,Saratu matar Baba Samaila da iyalinta Abubakar wanda ba ma,abuci magana bane tun farko, daga shi har matar shi,,, Yana zaune, gefe guda yana wasa da wayan da ke a hannun shi, Wanda alokacin kusan a hannun shi yan gidan suka fara ganin wayan Mobile, A cikin natsuwa suka gaishe shi kamar kowa tare da masu yaya hanya, Ya amsa cikin dan sake fuska kadan, da cewa mama, mun samay ku lafiya,? Da ga haka bai kara cewa komai ba ita ma dai mama saratu juyawa tayi zuwa kofan waje da yaran ta, Shiko Abubakar sai kokarin duba kaya yake yi wanda zai basu, A daidai kofa duk wanda ke gurin a lokacin zai iyajin abinda uwa da Dan takeyi a dakin, Haba mama inji Abubakar ya ce yan uwanane fa na ji ko duka tsaraban zan basu ai sunci shi a guri,na, Kai ne dai ka dauke su a haka ni ko diyan shaibu, ban yarda da wanan ba balle diyan, Samaila masu daukan kai kaman wata tsiya, Murmushi kawai mama Saratu tayi a lokacin don jin abinda mama ladi ke fadawa dan ta, akan su, Haba mama kibar fadin haka don ni baba Samaila baida maraina a gurina, Kaine kasan may yai maka ni dai ban yarda ka dauki cikin wa yan nan leshin kaba su sai dai wancan na gefe da na cire ma, Suna hada ido da kishiyan mama Ladi sai wa mama saratu signal da ido ta wuce kawai, Isan su sashen su yayi daidai da lokacin da sakon Abubakar ya iso gare su, A lokaci guda mama saratu da yaranta Meenat da Awal su ke cewa amayar mashi ace abawa wasu yan uwa sun gode, su, Wanan sakon yasa Abubakar fitowa dauke da kayan a hannun shi, cikin bacin rai, Direct gurin mama Saratu ya nufa duk da yasan cewa bawai ta girmay shi bane amma a matsayinta na matar kanin mahaifin shi yana ba su ladabi,, A daidai lokacin Baba Samaila yashigo gida daga waje sai kuma ya samu Abubakar din da kan shi a sashen shi, Bakin Baba Samaila har kune don jin dadin ganin Abubakar da yayi yau, Sun kara gaisaw cikin nuna farin ciki inda Baba yasa akawo mai ,shimfida, Nan suka zauna da Abubakar kafin su fara magana Abubakar ke cewa mama don Allah kiyi hakkuri Kada zancen mama yasa ki yi fushi har kuki ansar kayan Sai a lokacin Baba Samaila yagane may ke faruwa, Murmushi yadan sake mai laushi sanan ya ce, haba dai Saratu, may zai sa har ki biye wa halin Ladi, Awal ne yace baba munji abida mama Ladi ke cewa da zamu fito shiyasa maman mu tace, abar kayan, Batare da,Baba Samaila ya,bukaci jin Komai daga bakin iyalin nashi ba ya karbi kayan a hannun Abubakar tare da yi mashi godiya,, Yana cewa Ladi ai mahaikaciyace wa ke bin ta nata balle yai fushi, Murmushi Abubakar yayi don tunawa da waban sunan da Baba samaila yakira maman shi dashi, Don tun yana karami idan sunyi fada abinda Baba samaila ke ce mata ke nan mahaukaciya,,, Murmishi yakarayi don tuna yadda suke kwasan riki abaya,, Gashi kuma idan harkan ta yazo shine a tsaye amma san ita mama bata ganin hakan,,, Sai kuma daga baya ya fara yi mai nasiha akan rashin kula da gida da bai yi Inda suka dauki tsawon lokaci yana mai nuni da rashin alherin da hakan ke da shi,, Abubakar yabar sashen Baba samaila cikin rashin jin dadin yadda mahaifiyar shi ta nuna masu tsana, Alhalin suna zaman yan uwan shine suma matsala kawai don wai ba ciki daya suka fito da mahaifin shi ba, Wanan wani abu wanda tun yana karami yake sane da wanan akidar na irin yadda ake gwadawa Baba Samaila yan ubanci a gidan, Amma da yake shi na mijin duniya ne duk yadda za a gwada mai zai iya shanyewa a ran shi, Abinda yake ji shi ga ahi yau har iyalin shi sun fara sanin wanan bakar tsanar da ake gwada ma su agidan,,, ZEE MAKAWA YELWA 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸 8⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA I,HIDDINAS SSIRATAL MUSTAQU,IN,,,,,,,,,,, A lokacin da Abubakar zai koma Lagos sai malam ya kafe akan cewa dole ya tafi da mutum guda daga cikin yan uwan shi,,, Don haka Abubakar bai ja ba don yasan cewa tun da tsohon ya ce haka yana da,wata manufane, Maganar farko sai malam yace a dauki daya daga cikin "yayan Baba Samaila, Aiko mama Ladi ta tuma ta kafe sam ita bata yarda ba , Ga Abubakar da kan,ne a dakin su shine za,a ce a tsallaka aje har sashen Baba samaila, Baba Buhari zai yi magana malam yace a,a ya bar,ta ta ba da yaro guda daga fan,ninta,, Ba kunya ba tsoro mama Ladi ta shirya Samira tace a tafi da ita,,, Jama,an gidan malam manya da yaran, su, su,ka taru kofan gidan malam don yiwa mutanen Lagos rakiya, Abubakar ya na zaune kafa tankwashe, saman tabarma a gefen malam. Inda malam din ke kara ja mai kune akan al,amarin duniya,, Ita kuma Sadiya tana tsaye jingine a gaban mota tana wani yatsunar fuska, Su,ko mutanen gidan sun daga gefe sai kallonta, su keyi suna yatsunar fuska su ma, Wasu kuma daga cikin su haushin yadda take masu kallon bazan suke ji, A can kuma gefe Samira ce da yara yan uwan ta suna ta yi mata suraita irin na ke kan Samira kinji dandin ki za,a dake har Lagos,,, Ita ko samira sai washe baki takeyi don jin dadi za tai wa yan uwan ta tazara,, Tun fara hanyar su Samira ta fara rena kan ta don Tambayar ta Abubakar ya fara yi da cewa, wani makaranta kike zuwa, Cikin dan nuna tsoro da kuma nauyi Samira tace, salamatu Husaini,government girls secondary school, A jinki nawa a can ?tace, aji uku zan je hudu, Sai kuma yai shiru ya ci gaba da tukin da ya,keyi, Da har Samira na murnan tamabayar ya kare, Sai taji an jefo mata wani tambaya again, Shekarun ki nawa yanzu, ? Cikin rawan murya tace mama tace wai goma sha, hudu nake yanzu, Suka yi ido biyu dashi tai saurin dukar da kai da sauri don tsoron fuskan shi take ji,, Izunki nawa yanzu,? Goma sha, takwass,,, Bata karasa fadi ba taji ya ce takkwala kawai, May kike jira har, yanzu baki sauka ba ? Haba ai tai kokari inji Sadiya wace, ke tauna chewingun, Common shut, up my friend ke nawa kike balle har ki sa min baki, Cikin sauri tai wani cewa Allah ya baka hakkuri ni dai, Allamun tsoro su ka kara baiyyana a fuskan samira wace tai da ta sani bata biyo yayan nata ba, Tun yanzu wanan tambayar haka kamar dan jarida Can kuma ya kara tambayar ta yaran baba wani nawa ne sai ta fada mai, Ita kuma gwago wance fa diyan ta nawa yanzu, shima sai ta fada mai, Har dai zuwa lokacin da tafiya yai nisa duk kan su su,kayi shiru don gajiya, A cikin dare suka isa garin Lagos wanda yawan cunkoson shi, Samira ba zata iya gane komai ba, a cikin ida suka dosa,,, A kofar wani gida mai hawa kusan uku suka tsaya, Gaskiya gidan ba laifi don ba yabo ba fallasa a cikin shi, Gaba dayan su har yayan nata suka fara kwasan kayan su zuwa cikin gidan, sashen da taga Abubakar ya sa dan makulli ya bude kofan, A hawa na biyu suke da zama su, don haka ba suyi wani shan wahalan hawa ba, A tsakiyan falon gidan sukai ta jibge kayan da sukayo tsaraba da ga gida da kuma nasu na sawan su, Duk da dai shi Abubakar ya ce wa mahaifiyar shi basai Samira tazo da kaya masu yawa ba, acan, Amma duk da haka tadan zo da yan gwargwado daga abinda take so, Wani daki yayan nata ya nuna mata ya ce ta kwashi kayan ta zuwa ciki a nan zata zauna,,, Dakin yana dauke da dan gado guda daya sai mirrow, a gefe, Samira na kallo Sadiya ta dauki dan trolley din ta ta nufi dakin kwanan su, Inda tabar sauran kayan nan gurin da aka zube su da farko,,, Baki bude Samira ke kallon yadda yayanta ke ta faman kwasan su zuwa ciki inda ya kamata ya kai komai, Ita ko Sadiya tun shigewar ta dakin bata kara fitowa waje ba, Take away din da ya saya masu tun a hanya shine ya bawa Samira, guda daga ciki tare da nuna mata kitchen din su, Shigan samira kitchen din sai da gaban ta ya fadi don shirgin da ta gani kamar ba,a ciki ake girki ba,,,, Zaune suke a saman tabarman roba wanda aka shimfida a rufar dake tsakiyan filin sashen nasu,,, Kasan cewa yau Jumma,a , ne duk kan su sunyi kwaliya, fes da su,, Ga kuma shiyan nasu fes da shi kamar babu yara aciki har biyar, Sallaya ne a hannun mama Sadiya tana kokarin nikewa da ga gurin da tai sallah, A daidai lokacin Baba Samaila ya shigo gida da yaran shi su uku, maza, da ke, biye da shi a baya acikin shigar su ta sallah Jumma,a,ga kuma shiga na fararen shadda sun yi don, Jumma,a,,,, Da sallamar su suka karaso cikin gidan, sannu da zuwa mama ke ma su inda su Meenat da ke daga ciki suka gane cewa mahainfin su ya dawo, Nan su ka yo, waje gaba dayan su suna masu barka da Jumma,a Bayan sun zauna a saman katon tabarman dake shimfede mama ta gabatar masu da abincin rana, Kowa anzuba mai a nashi, plate, tare da abokin cin shi, Tuwo ne na far shinkafa da miyar taushe, anzuba wa miyar kabewa bussashe, da kuma kulikuli, Sai manshanu da aka lema a saman miyan kamshin shi yana tashi sama, Mamace ta fara gane cewa yau Baba bai cikin farin rai, Da alamar zuciyar shi ba ta da dadi sam don tun safe haka take gani tare da shi,,, Loman da ya diba zai kai abakin shi ya tsaya a lokacin da ya ji muryan mama tana cewa, Ai da ka daure ka ci abinci ko bakajin dadin shi, A hankali Baba ya dago kai ya dube ta cikin dan sakin fuska mara walwala, Fuskan matar nashi ya tsurawa ido don ganin cewa, ta fahinci halin da yake ciki, Inda yaran su, suke zaune yadan kai kallon shi, gare su, Hakan yasa mama gane cewa bai son yin magana a,gaban su a lokacin,, Don haka sai mama tai shiru taci gaba da zubawa yaran maza miyan da suka shan ye, Amma azuciyan Baba sai ya kasa daurewa don yasan cewa matar ta shi don, ta damu da damuwar shi, Baba yai dan murmushi tare da yanko lomar tuwon ya ce, Saratu ke nan ai dole ki ganni haka don al,amarin kiyayyan da Ladi ke gwada min yai yawa, A lokacin ne ya jaye kulan abincin daga gaban shi ya jawo roban ruwan wanke hannu a,gaban shi,, Mama tace ko ma may take nufi ai Allah ya fita Baban Meenat, Na san da haka saratu to amma abin ne da daure kai don dai ni da da farko abin bai damu na sam, Amma yanzu wanan abun da tai muna yasa na fara jin tsoron ta akan yaran nan, Caraf Aliyu yaron su na uku ya sa masu baki azancen su da cewa, Wai ce muna takeyi irin fulani irin tsiya,,,, Murmushi Baba yayi a lokacin da Aliyu ya fadi haka nan, Baba ya ce kada wanda yadamu da duk wani abin da Ladi zatai maku, Nasiha Baba yaiwa ran sosai don irin yadda zasu zauna da mutane lafiya,, Jin Meenat tai shiru a lokacin kamar bata a gurin yasa mama dan juyawa gurin da take zaune, Ke lafiya kike kuwa kin yi shiru haka, kuma ko abincin ba,kya ci,, Ba komai mama Meenat tace cikin muryan tausayi, Muryan Baba ne ke cewa, Amina ina gani karama da ke kina aon sawa kan ki maganar manya ko ? Murmushi Meenat har dan sautin ya fita sanan tace, Baba ai ni nasaba da halin mama ba yau ba duk wani abinda zatayi nasan dashi ko , Takai hannun ta cikin plate din abincin dake gabanta tare da lumshe idon ta don takaicin irin yadda duk fadin gidan su ,su kawai mama tafi sawa a gaba, Baba samaila yadan girgiza kai, acikin zuciyar shi yana tausayawa yarinyar nashi, Ta,na da hakkuri da kuma, tausayin iyayyen ta dayan uwan ta,,, Ga shi duk wani wahakan da mama Ladi zata sata ba ta taba nuna bacin ranta akai, Baba Samaila ya Amina kwanan nan zan mai da karatunki Sakkwato, insha Allah, Ki koma can kiyi makarantar kwana ina ga hakan zaifi ko,? Murmushin jin dadi Meenat tayi don ta dade tana sha,awan makarantar kwana,,, Amma sai mama saratu tace malam makarantar kwana fa kace, ? Baba ya ce kwarai kuwa don hakan shine shirina ba yau ba don samun mafita, Meenat cikin sanyi murya ta dan dago kai ta kali Baba tace, Baba, malam tsoho ko zai yarda ? Zan san yadda zan bullo mai insha Allah,,, Hakan yasa Meena dan sake ajiyar zuciya a hankali,,,,, Washegari da isan mutanen Lagos Samira tana kwance tana jiran abin kayarwa, Jin shiru yai yawa yasa ta dan fitowa waje, don taga ko angama yana kitchen ne nata , Kamar yadda tabar kitchen din da dare haka ta samay shi ko yau da safe, Samira tana son shiga kitchen din don dafa abu amma bata san ya zatai amfani da irin gas din su ba,, Don haka tadawo falon ta zauna inda take bin kayan falon da kallo cikin mamaki, yadda kayan suke a jibge babu kulawa kamar ba mace agidan, ma sam, Da hannayen ta bibiyu tai tagumi tana tunanen sabuwar rayuwan da ta wayi gari dashi, Ita da a gida take da, yanzu ta na batun karyawa na biyune ko na uku,, Shigowan matar gidan falon alokacin yasa Samira saurin dago kan ta daga tagumi da tayi,daga zaunen da take, Cikin dan yake hakora tace ina kwana Sadiya? Wani kallo tai mata sanan tace, lafiya lau, daga haka ta wuce kawai abinta, Kitchen ta shiga sai ga ta tafito dauke da kufi a hannun ta, Kunsan a,tare suka jefowa juna tambaya a lokaci guda, Ita Sadiya na cewa kin karya ko ? Ita kuma Samira tana tambayar ta, yaya Abubakar fa, Ya fita office ai tun da safe, Sadiya ce taba Samira ansa haka na, Ita kuma Samira tambayar ne na Sadiya ya ba ta mamaki, Tace banga komai ba da zanci aii, ? Wani kallon mamaki Sadoya tai mata don jin may tace, Kin duba kitchen babu abinda zaki dafa ne, Ban an yayazan kuna gas din bane, Tsuki, tayi tace muje ingwada maki yadda zakiyi ko ? Jiki ba kwari duk yunwa ya ishe ta, tabi bayan Sadiya wace ke saye da wani shimi mara hannu, A tunanen Samira atare zasuyi girkin amma sai taga kawai sadiya ta juya batare da ta fada mata ko may zata dafa ba,,, A haka dai tai ta kokarin ko yo tana yi tana hawaye, tana gogewa da bayan hannu,,, Samira nada sati da zuwa Lagos yayanta yasata wani makaranta dake unguwar su, na jeka kadawo, Agida kuma yake dan samun time yana masu karatu, Samira ta fara fahintar irin halaiyar da yayanta suke aciki da matar shi, A wanan yan kwanakin ta gane cewa, Abubakar , yana da wani irin baudadden ra,ayi arayuwan shi, In har ba sanin halinsa kayi ba zakasha wuya gurin zama dashi, Gashi miskili na karshe ga saurin fushi, dan abu kankani zai iya sa shi fushi ya bata mai rai, Saidai dadin bai daukan lokaci mai tsawo acikin fushin, Sannan kuma bai yarda sam Sadiya ta wulakanta mai yar uwa,,,, Mama Ladi yau sai habaici take sakewa don jin cewa Meenat zata wuce sokoto karatu gobe, Kirikiri ta shiga cewa iyakar dai mutum nan sokoto, badai mutum yakai Lagos ba,, Kishiryar ta ce ta bata ansa yau da cewa hassada dai ga mairabo taki ce,,, Sai kuma ta juya gurin ta da cewa mutum dai ya tsaya matsayin sa, Idan kuma fitsari banza ce ai,kaza tayi mana,,,,, ZEEE. MAKAWA YELWA 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 9⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA SIRRATAL,LAZZINA, AL,ANTA ALAIHIM, A daidai wanan lokacin da mama Ladi ke wanan habaice, habaicen, Abubakar yana kwancen a falon shi saman dogon kujera, Zuciyar shi sai a cunkushe da bakin ciki da bacin rai, Irin yadda daga matar shi har sister din shi babu wace ke iya gyaran ko da falo ne ko kitchen din gidan, Hakan yasa yake jin wani irin radadi da zogi a lokaci guda, Idon shi sama yana kallon silin din falon yadda yanar gizo duk ya lulube silin din, Da sauri ya mike daga kwancen da yake kamar wanda aka mintsina, ya zauna, Zaman bai mashi ba ya kuma mike tsaye yafara dan zagaye dakin, Abind ya,gani jiya agidan abokin aikin shi wanda akaiwa kiran gagawa cewa yaron shi baida lafiya, Suka tafi gidan gaba dayan su don ganin jikin yaron, Duk da ga yara har biyu amma gidan fes yake kamar ba ataba zama acikin shi ba, Ga wani kamshi na daban na tashi, a sassan gidan, Duk da rana bai wani yi sosai ba a lokacin amna sun samu har tayi girki, rana nan aka zubo masu su ka kwasa, Idon shi ya lumshe don wani gululun takaici da ya ziyarci zuciya,shi, Don hango wasu tarin kayan wanki da yayi a kofan shiga bathroom din su,,, Alama ya nuna mai cewa ko Samira ba ta da tsabta ke nan don idan har Sadiya bata gyara ba ai ita ya kamata ta gyara, Sauki guda da ya samu yanzu shine Samira tana girka abinci su ci ya dai na yawon saye ko ya girka , Duk haka yake tilastawa kan shi cin abincin don rashin dadin shi,,,, *** *** *** *** Wanan ne karon ne farkon shigowar ta garin sokoto, iyakarta birnin kebbi sai ko gwandu ko kalgo gurin gwagon ta, Hakan yasa tun shigowar ta take raraba ido gurin kallon yanayin garin, Gidan dan uwar mahaiyarta Baba ya fara kai ta don ta san guri, Malam Nafi,u malamin asibiti a cikin garin sokoto, yake aiki, Yana da mata guda biyu da yara biyar, yana da dan rufin asirin shi, gwargwadon kima, A gidan Baba zaibar Meenat yadda su ka yanke shawara cewa shi uncle Nafi,u ne zai kai ta idan weekend ya kare,,, Ameenat tana tsaye kofan gidan uncle dauke da dan karamin yaron amaryan shi na goye, Ida tayo wa mahaifinta rakiya don ya ce bazai kwana ba ranan zai koma gida, Baba ya,ce tau, Amina ki kasance da halinki nagari da nasan ki dashi, Nakawo nan karatune don ci gaban ki duk da dai kin ga malam ba wai yaso hakan bane, Don Allah ki rike mutuncin ki, Ki rike ibada ki tuna da irin gidan da ki kafito kada ki sawa, zuciyan ki kwadan duniya ko kadan, Ki jira rabon ki don rabon mutum bai taba wuce shi, inji Allah, Nan da nan idon Meena ya kawo hawaye amma sai ta wayan,ce da sherewa da bayan hannun ta,, Ga wanan mahaifiyar ki nan duk abinda ya shige maki duhu ki sanar dashi don zai aiko min insha Allah, Nabar ku lafiya Allah ya bada sa,a yasa a dace duniya da lahira , Wani irin kuka ne yazowa Meenat duk yadda take son zuwa boarding da kuma sokoto sai taji yau bata so kwata,kwata, Kasan cewar yaune rana na farko da ta taba barin iyayyen ta zuwa wani gurin,, Tayi da ta sani da ma ba,ta,zo ba ta,zauna gida tare da mahaifanta da yan uwan ta,, Cikin gida takoma inda ta zauna folo don babu dakin wace zatace zata nufa daga cikin matan uncle din nata,, Har kayan ta duk a nan suka bar mata su afolon gidan nasu, Wanan bai hana Meenat mikewa don zuwa tattara kwanon da akaci abinci ta fara wankewa,,, Tare da ita ranan uwargidan tai girki don kusan aikin Meenat ce tayi shi don ta iya,,, Dan kwana biyun da Meenat tayi a gidan uncle din ta yasa amaryan shi Sakinat ta ja Meena ajiki don ta fahinci yarinyace wace bata son jikin ta, Ranan da za,a kai Meenat makaranta uncle Shafi,u ya dan kara mata sayayyan provision masu dan yawa da dai yan sauran abinda zata bukata wanda Baba bai sayo mata ba, *** *** *** Tun tafiyan Meenat sokoto Baba suke wasan boya da malam mahaifin shi, Da zaran anyi sallah asuba Baba ya fita bai,dawo,wa gida sai dare lokacin malam ya shige gida, Saboda tsoron haduwar su da malam din,wanda bai so tafiyan maryam karatu har wani gari ba, Sati guda cif da tafiyan Meenat ranan Baba yadawo daga gurin neman kudin shi da yake yar buga bugan shi, Baba Buhari ya tsayar dashi a kofan gida yana mai nasihan cewa ya tafi ya gaida malam don kwana biyu ke nan yana jin yana tambayar shi, Jikin Baba samaila yai sanyi don haka ya yanke shawaran shiga gurin malam din yau, Baba samaila bai yi sanyi a gwiwa ba yana gama gyara jikin shi ko abinci bai tsaya ci ba ya nufi sashen mahaifin shi, Bayan sun gaisa sai yar shiru ya biyo baya kadan, Muryan malam ce ta ratsa shirun da cewa Samaila guduna kakeyi kwanan nan ko don nace kada ka kai yar karatu wani gari, Baba samaila yadan gyara zaman shi cikin ladabi yace ba hakana bane malam aiyukane sukai min yawa shinassa, Murmushi malam ya yi tare da girgiza kan shi, yace, Duk da na san cewa yanzu zamani yana tafiya,ne da ilimin zamanin, To amma ita diya mace tarbiyan ta sai iyayen ta sune zasu tarbiyar da abin,su yadda ya kamata, To amma naso ace ka kalli lamarin ta fuska biyu, addini da kuma zamani, Don haka na kyale kane kawai don da gida biyu aka sanshi dama , Saboda kace gurin wan mahaifiyar ta zata zauna don yana garin, Don haka na kyale ka ka tafi da ita amma nan gaba ban son gardama akan diyan ku,, Baba Samaila yace a yi hakkuri malam baza,a sake ba insha Allah,,, Bakomai inji malam ai Ameena yarinya ce mai natsuwa da hakkuri Allah ya bada sa,a ,,,,, *** *** *** Yau Monday, ma,aikatar su Abubakar sun bude Monday su da, transfer a hannayen su, Wada daga ciki su har da Abubakar wanda ya samu karin girman bazata, saboda kwazon shi ga aiki, Gashi kuma an turo shi Abuja , babban headquarter su da ke can, da zama,,, Sosai sauran abokan aikin shi musaman hausawa suka fara farin ciki wani hanya kuma suna bakin ciki rabuwa da mutum kamili irin Abubakar din, Inda ba bata lokaci suka yai haraman zuwa yin reporting, *** *** *** Mama Ladi ne zaune daki da yaranta mata biyu da ke aure a cikin gari, Bukin suna akeyi a gidan can sashen baba su, guda, Mama Ladi ce ke magana, da yaran nata alokacin, Inda babban yar ta ta kawo zancen, dan uwan su Abubakar da cewa, Mama yanzu shi mai sunan malam haka zai zauna da mace bata haihuwa kuma bai damu ba, ? Cikin Fushi mama Ladi tace wa yar nata, shi da ke zama da ita ya ce maki yagaji da hakan ne, Binta wace itace ke bi wa Abubakar gurin haihuwa tace, Cikin murmushi, haba mama ke dai baki son sam ayi zancen wanan matar ta mai sunan malam, Mace sai dan banzan tsiwa, taurin kai da nakasa ga kekessasshiyar zuciya da rashin sanin ciwon kai, Idan Baba Wada yana bada labarin ta wallahi mama kare bai ja, Mama kin san fa shi ba wai zai taba zuwa gida ya fadi irin halin rayuwan da yake ciki da ita bane, Tafarkon mai suna maryam tace, nidai wallahi mama ke ce mai son wanan hadin tun farko, Don dai wallahi Abubakar bai dace da wanan matar ba sam,, Shin wai ina ruwanku da wanan zance ita naga ta dace da shi shiya sa na hada su, Shikuma Wada dama munafunci ya tafi yi shi yasa bai fadawa kowa ba lokacin da zai tafi, don da ban yarda ba, Gaba dayan su suka yi shiru da bakin su, don sun san cewa Sadiya bata taba baki a gurin maman su,,, Maryam ce tace ai Samira tana can zamu ji komai abakinta idan ta dawo,,, *** *** *** Saye yake cikin bakaken suit, kai tsaye ya ke tafiyan shi mai kama da ta kasaita da isa, Yana rike da wayar shi a hannun shi na dama sai briefcase din da ya rika a hannu guda, Idon shi ya na manne da farin glass mai kama da medicated, Tun daga nesa mutanen da ke zirga,zirga a maikatar suke satan kallon shi,, Kallo guda za kai mashi ka gano cewa namiji ne jan gwarzo don a cikin azama yake tafiyan shi,,, Office din shugaban su ya nufa kai tsaye tare da taimakon wani lebura, Abdullahi wanda suka hadu tun a bakin get, Abubakar ya yaba kwarai da kyawon gurin inda, girman gurin da kuma yawan ma,aikata yasashi gane cewa ba karamin guri yazo ba yanzu, Office din shi babban fiye da tsan manin shi don kusan ya kai wani taki mai tsawo, Bai wani tsaya bata lokaci ba don dama shi mutum ne mai kwazo ga aiki, Farin jinin jama,a ke gareshi duk inda yake to amma kuma gashi shi mutum ne wanda baida surutu,, Meenat yarinya mai hazaka inda ta hadu da wata Yarinya, Aisha,yar kauyen, sokoto Bodinga,, Meenat da Aisha sunyi mugun shakuwa a tare su ke komai nasu, kasancewan a rana guda aka kawosu makarantan, A haka rayuwan su yaci gaba da kasancewa a tare da junan su, Kokarin Meenat yasa aka santa cikin dan lokaci don duk wani abinda za,ayi a makarantar na kokarin, da ita a ciki, Wanan ne yasa mata farin jini gurin yan uwanta dalibai da malaman su, Baba yana yawan ziyaranta inda in yazo Meenat, zata dinga jawo mutane azo aga mahaifin ta, Shiko Baba samaila yanajin dadin hakan da yar na shi take yi mai a cikin yan uwanta, Saboda gudun surutu yasa idan an samu hutu mai gajeren zango Meenat bata zuwa birnin kebbi, Saidai idan dogon zango ne takan je tayi hutu a cikin yan uwanta,,,, *** *** *** Mama Ladi wace tun ganin yadda Meena ta koma da tazo hutu sai hankalinta ya tashi, Amma a fili sai cewa take yi sokoto fa kawai mutum ya tafi amma daga uwa har uba duk sun rude sunawa mutane wani zance wai diyar su na karatu sokoto, Wanan irin abin da, mama ke yi duk wanda yasan yadda matan wanan shiyan suke, ba wani bakon alamari ba ne wanan, Don haka abinta sam bai damu Zurian Baba Samaila, Ita mama Ladi bawai Baba samaila take wa wanan kyashin ba kowa ne na gidan idan taga mai da alamar dan haskawa, To fa da ita da mai shi kwana biyu sai anji su don sai sanadin da tai fada da mutum tai mai gori,, *** *** *** Salawatu wata matashiya ce ma aikaciya a ma,aikatan su Abubakar, Fittaciya ce agurin aman tana yawan ji da kan,ta gata yar gaye irin na karshen nan, Tana duke saman computer dake a gaban ta tana aiki, Muryan aminiyar ta kuma babban kawar ta, lubana, taji tana cewa kai, Amma wanan gayen karshe ke nan bai da inda yake da makusa, Ji tafiyan shima kawai don Allah, A hankali Salawatu ta dago kan ta daga abinda takeyi, Gaban ta ne ya ba da ras don ganin irin haduwar da guy din yayi,, Amma dai wanan bako ne ko ? Salawatu ce ke tambayar, Lubana ta bata ansa da cewa shine mana aka cenza mai,makon Emos,, Da mamaki suke kallon Abubakar har ya karaso inda suke ya wuce, Bayan shi suka bi gaba daya da kallo a lokaci guda, suna, mamakin halittan shi, Don dai su ya yi masu a rayuwan su sai dai matsala guda shine da alama baida sakin fuska, Salawatu tace Lubuna ki sa aranki daga yau cewa kamar na samo kan shi na gama, ko, Amma fa ni abinda na hango Salawatu kamar wanan bazai wani girmay ki sosai ba, And so what ? Ta fada cikin wani irin yin har da idon ta, Shine ma ai daidai move, di na, idan baki sani ba, A cikin hausan na yan yaren garin Abuja suke magana, *** *** *** Tun daga wanan ranan Salawatu ta fara shi,shigewa Abubakar, da gaisuwa ta fara mashi a cikin ladabi, Sai kuma ta fara dan canza shigar ta irin na yaran hausawa ainihi,,, Duk yadda tasan za tayi su hadu a rana sai Salawatu tayi don su hadu, da Abubakar , Sadiya da Samira duk sun dawo nan Abuja yanzu tare da shi, Inda ma,aikatar su, ta bashi gida maikyau ga kuma girma sai dai ba,a cikin kwatas din su bane, Sadiya yanzu da yake andawo arewa tana dan ganin yadda mata ke gyara , Hakan yasa ta itama tadan fara gyaran jikin ta amma sama,sama,,,,,, Yanayi yanzu ya canza sosai don cigaba ya samu sosai gurin Abubakar, Bin kwakwafi irin na Salawatu har saida ta gane gidan Abubakar, Da sannu har ta dan fara kaiwa matar shi sadiya ziyara agida,,,,, ZEEE MAKAWA YELWA 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 1⃣0⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA SIRAATAL- LAZEENA AN'AMTA `ALAIHIM,GHAYRIL-MAGHDOOBI `ALAIHIM WALAD-DA,AALLEEN (AMEEN) AFUWAN YAN UWA A POST DIN JIYA PLS GYARAN KU A GARENI YA NA KARA MIN KARFI DA KWAZO A KO DA YAU,SHE NAGODE KWARAI DA KULAWAN KU,,,,,,, A, zaune yake cikin office din shi wanda yasha kayan electronic din ma,aikata, Kan shi a duke yana faman aikin tun safe baida lokacin kan shi idan har yana office, din, Hakan ya sa ba kowa ne yasan da shi ba a ma,aikatan, nasu saboda girman gurin,, Abubakar yana hankalce da irin harin da matan ma,aikatan ke kawo mashi, Sai dai yakan gwada masu tankar bai fahinci manufar su ba,,, Don shi ko a gida bai faye son hulda da yan uwan shi mata ba, Don a ganin Abubakar sakewa mace fuska raini ne hakan ke jawo wa mutum so,sai,,, Hakan ya sa duk wata mace wace ta san ko waye Abubakar za ta shede shi da cewa mutum ne mai wulakanci sosai, Don abin ya zama mai jiki irin tsare gidan shi ba mata ba kawai har ma mazan, Tafiya, yake kamar mai hanzari, hannun shi guda saye a cikin Aljihun shi, hanyar zuwa, gurin saida abincin ma,aikatar nasu ya nufa, Ba kasafai zaka ga Abubakar a wanan gurin ba, Iya karshi, indan harka ganshi drink ne kawai zai sha sai snacks wani lokaci Sauri ya ke yi don ya karasa gurin saboda yunwa yakeji gashi kuma da aiki a office da yawa, Tun daga nesa,suka hango shi, a lokacin ita salawatu ta juya bayan ta tana waya, Ta,bota Lubuna tayi da dan yatsunta ta na gwada mata shi, Cikin sauri Salawatu ta juyo don idon ta ya gane mata shi , Shigan shi cikin restaurant din masu aikin gurin ya samay shi don jin ko may zai kawo mai, A daidai wanan lokacin Salawatu suka karasa karasowa gurin ita da Lubuna, Cikin wani, ladabi, na kissa suke gaishe shi harda dan rusun nawa, Sir inji Salawatu, ya mutanen gida ? Cikin mamaki yadan dago kai don jin abinda ta fada , Sai,dai yana mamaki wasu mutanen gida ne ta sani har take tambayar shi, Mamaki a fuskan shi karara yadago kai da niyar tambayar ta, A lokacin ne kuma drinks din da yai oda ya iso gare shi, Ganin su gurin ya sa ma,aikacin ya tambaye shi a cikin ladabi da cewa, Ko za,a kawo masu nasu abin shan ne, su ma, ? Sai ya dago don jin may za su ce, Lubuna tace kwarai kuwa mungode kwarai Sir, Bayan wucewan ma,aikacin ne Lubuna tace, Wanan sunan, ta Salawatu , nikuma Lubuna nake, Mun yaba kwarai da mutuncin ka a wanan ma,aikatan , Muna ganin ka shine yau nace bari muzo don mu gaida kai, Sai da ya kurba drinks din dake a cikin cup din dake hannun shi tukun tare da lumshe idon shi , Saboda mamakin irin karfin halin da su kayi na taron shi haka kai tsaye, Dama yana da labarin yan matan Abuja tun lokacin da akai mai transfer ake bashi labarin su, A takaice ya bata ansa da cewa nagode, Lubuna da mutuntawan ku, Daga haka mai,kawo masu drinks, din ya iso dauke, da tiren drinks din su,,, Daidai lokacin da zasu fara sha ne shikuma Abubakar ya mike da niyar barin gurin,,, Cikin wani irin muryan kissa suke cewa mungode Sir, Hannu ya daga masu alamar, is,ok, daga haka kawai ya sa kai abinshi ya bar gurin,, *** *** *** Dawowan Abubakar Abuja yasa izuwa yanzu mutanen gidan su suna samun labarisa akai,akai, Bakamar lokacin da yake zaune a Lagos ba da mai jin duriyan su, Hakan yaza yanzu labaran ci gaban da Abubakar ke yawan samu yake isowa garin birnin kebbi, Sai dai wanan labarin a gurin mutane har da kari sikeyi a kai, Sadiya tafi Abubakar, rashin kula da,gida don ita indon ta na,ta ne ma suyi zaman su a can ba,tare da sun shigo kebbi ba, Abu guda ne shi duk wanda yasan Abubakar idan har yai sa,an ganin shi zai dan iya wa mutum alheri kadan, Sai dai kuma idan har sako zai yi zuwa gida, to fa mama Ladi, ita ce za tai kato,kato da sakon sai wanda ranta yaso abawa, Duk da ko malam tsoho sai taga dama bashi abinda taga dama, Hakan da takeyi shi ya kara tayarwa da malam tsoho hankali don yasan cewa nan gaba gaba,daya kan zurian nashi zai kasu ne daban,daban,,, Yanzu kwata,kwata ta daina, bawa yan gidan alheri sai dai takai waje don bidan suna, ***** ***** ***** Zaune yau yake a office din shi aiki yai mai yawa kamar kullun, Don yanzu komai kara bunkasa gaba gaba yake mai, Dawowan shi daga gurin meeting ke nan yana kokarin ganin, ya shigar da abinda sukai meeting akai cikin net, Sakatariyar office din su, ce ta turo kofa, ta shigo tana saye da wando da riga bakake, Batare da ya dago kai ba, ya ke ce mata, yadai Ruth ? Tace Sir cikin harshen turanci kana da bako kusan kwana biyu ke nan yana zuwa wai yana son ganin ka ne, Cikin sauri ya dago kan shi yana mai kallonta, Inda ya kara maimaitawa da cewa kwana biyu shine baki fada min ba Ruth sai yau, Ruth ta dan sosa kai tace cikin rusunnawa, Gani nayi miutumin bai cancanci ya ganka bane don baiyi kama da abokin hurda ba, Ya fi yi kama da Beggars, Cikin dan daka tsawa ya katse ta da cewa, ki ce ya shigo pls, Umurni na baki daga yau kada ki kara hana bako na gani na kowani iri ne, Umurni na baki kada ki kara kawo min naki uzurin, Irin yadda yai magana yaba Ruth tsoro don haka jiki na rawa tafita da sauri don yiwa bakon iso, Don tunda sabon boss din na su yazo bata taba ganin bacin ranshi ba irin yau, Karan bude kofan tayi don shigowa da bakon da tace din yana ta ziyaran su,, Ba, wani bane bakon illa Baba masijan su na Lagos watau, malam mudi,, A cikin mamaki yace malam Mudi kaine a nan kuma ? Barka da zuwa, Kasa malam Muddi din yazube yana cewa Rankaidade barka da warhaka,? Yau she kazo garin nan tashi mana Bissimilla ga guri kazauna yana mai nuna mai gurin zama, A dan ta kure malam mudi ya zauna saboda yana ganin bai dace ya zaune kusa da shugaban shi ba, Bayan ya sha rruwan da Ruth takawo maine dan kadan Sai kuma yadago kai yana mai kallon Abubakar din, Hawaye suka zubo mai inda yake cewa don Allah gurinka, nazo rankai dade ka tausaya min , Kai min hanyar da zandawo nan Arewa a cikin yan uwa na in har da halin yin hakan, ? Dama sana,a nakeyi acan bayan yar kariyar arzikin da na samu shine wani yai mun hanyar wanan aikin, Sai kuma ya kara sa yar sheshejan kuka, alokaci guda, Subbahanallah haba malam ai zancen bai kai na kuka ba, Ka tsaya muyi maganar fahinta kawai ina ga zaifi,,,, ***** ***** ***** So,sai duk wani girma na diya mace ya baiyyanawa Meenat, Da ka ganta kasan cewa daga zurian gidan malam Manya take sabode ta debo irin jikin iyayyen ta maza, a gurin tsayi, Sai dai ita abin nata ya raba gida biyu ne don duk fuskan ta da launin jikin ta na fulanin gwandu, ne,,, Wanda yasan Meenat a baya yanzu idan ya ganta yasan cewa a kwai canji sosai ga lamarinta, Ta waye ta zama yar birni sosai, ga turanci a bakin ta, kamar wace ta taso gidan da ake turanci tun tana karama, Wayen Meenat ya karawa mama Ladi hassadan ta sosai a ranta don tasan cewa ko yar ta Samira wace ke can Abuja gidan yayan ta batai wanan kyaun ba, Gashi duk Meenat zata zo gida sai Uncle Shafi,u yaba da motar shi ankawo ta cikin mutunci, tare da dan tsaraban ta duk da ba yawa amma sai ankasa an,bawa kowa tsaraban, a gidan,, Ita ko mama wanan abin ke kara sa ta yanzu jin haushin Samaila da iyalan shi,, Don duk wani motsi na, su da wani tako na,su duk idon mama Ladi yana kan su, Babu karin haushi sai yadda Malam ke alfahari da yar jikar nashi, Tundai da aka nuna su suna wani gasan karatu a NTA sokoto, Wanda kowa ke murnan ganin ta cikin TV tana wasa kwakwalwa da sauran dalibai, yan uwan ta,, Don haka ta raya arayuwan ta cewa bazata taba barin Samaila har yai nisa akan harkokin ci gaban shi ba, ***** ***** ***** Wanan zuwan hutu da yan makaranta suka samu na dogonzango, shi ya sa duk yan gidan a wanan lokacin suna gida tare da mahaifan su, Ganin irin yadda karatun addinin jikan nashi ya samu ci gaba fiye da tsanmani shi, Yasa shi kara yin alfahari da ita acikin zuciyar shi kamar yadda ya ke yi wa duk wani daga cikin iyalinshi da ya kyauta,ta mai, Samira ma tasamu zuwa wanan hutun na dogon zango daga Abuja, kamar kowa, sai dai kuma zuwanta da kamar sati sai ga sakon yayan nata watau Abubakar yana bukatan komawan ta, don matar shi bata da lafiya wai, Kuma ana zaton ko karuwa ne ta samu, na aure, Hakan yasa Samira tayar da hankalinta sosai akan cewa bazata koma ba ita, Asalima daga wanan dawowan ita tadawo gida ke nan kwata,kwata, Ganin yadda samira taki yarda ta koma yasa malam manya yanke hukuncin cewa duk yan matan gidan su shirya tunda su cikin hutu ne su tafi gidan yayan nasu Abuja,,,, Wanan tafiyan yasa rayuka da dama agidan sun baci saboda yawancin iyayyen yaran basu so ba, Badon komai ba sai don mama Ladi wace sam bata son aje a gogi dan ta, Amma malam ya rufe idon shi yace duk Abuja zasu tafi hutu,, Abubakar baida labarin wanan tafiyan nasu sam don haka, Bama zuan na kannen nashi wani tanadi yadda ya kamata ba, Motar da Malam yai masu shata sai musalin karfe biyar na yamma ya shigo garin Abujan inda duk kan su su biyar a gajiye suke, Direct gidan shi dake NYanya suka nufa akan jagoran Samira wace ta san gidan, Tun saukan su gashi a gajiye suke amma tun a lokacin suka fara fuskantar matsala daga matar gidan, Don da isar su gidan suka kwankwasa sai da aka dauki mintoci kafin suji anbude kofan, Ganin haka a lokaci guda yasa ta waro idon ta waje tana mamakin hakan, Abinda ya fito a bakin ta shi kune haka tafe ? Daga haka ta samu guri ta zauna abinta, Samira,ce ta ce masu su zauna ga guri nan, inda duk kan su sukabi kujerun da kallo don kuran da sukayi, Nan take wani irin kazantar gidan ya dira a zuciyar Meenat, Ido tabi falon dashi da kallo inda a take ta hango ko may gidan ke ciki, Ruwa samira ta gabatar masu na sha tare da wucewa dakin da take zaune, a cikin , Kayan su ta umurci su kai don su, ajiye aciki kafin su san na yi,,, A dadafe Meenat tai alwala a ban dakin nasu saboda kazantar shi,,, Idar da sallah su abuna farko da gidan ya fara cin karo dashi shine gyaran bandakin su, dukka biyu, Dare yayi don haka Meenat ta bari sai zuwa gobe ta gyara falon, Amma duk da haka sai da ta dan taba gyara, sama sama ita,ma, Dawo wan Abubakar ya samu bakin shi unexpected a gidan nashi, Cikin mamaki yake tambayar su yadda akayi sukazo gaba dayan su, A lokacin Meenat tana can dakin samira tana dan gyaran inda zasu kwanta, Wanan training din Meenat ta kara samun shine a zaman da takeyi tare da amaryan uncle din ta na sokoto ,,, Uwa uba kuma ga maman ta mace mai mugun tsabta iyaka dai ace ita a local waje take da zama, Shima dai maigidan tun bayan ganin da sukai mai basu kara ganin shi har kwana biyu da zuwan shi,,,,,,,,,, ZEEE MAKAWA YELWA [7/2, 12:55] Anty Lantana: 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 1⃣1⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA, MAALIKI YAWMID-DEEN,,,,,,,,, A, zaune suke a dakin na Samira da ke acikin gidan yayan nasu Abubakar, Kusan duk kan su biyar idan ka dubi fuskan su babu an,nuri a cikin sa, Murja diyan baba shaibu itace ta fara kau da,shirun da dakin yayi da cewa, Yanzu Samira ana nufin cewa a haka kike zama da wa yan nan mutane har tsawon shekara kusan biyu fa ake neman yi yanzu , Samira wace tana zaune tana gyaran kumbar kafan ta ta,ce hmm murja ke nan, Ai saukin abin ma kawai, wani lokacin nakan dan samu kulawa daga shi yayan namu, An ma ita wanan mai kama da an shuka dusar a haka rayuwan ta yake, Hmmm ni wanan matar tun farko ban taba jin son ta azuciya na ba wallahi, Meenat cikin mamaki ta dago kai da sauri ta kalli Aisha tace, Haba dai Anty Aisha bai,dace kice haka ba ga matar dan uwan mu, Ita,ma yanzu fa a matsayin yar uwa take gare mu, Wani harara, Nafisa ta watso mata tace ke ko Meenat, zaki fara irin zancen ki ke nan, Yau,she zata zama yar uwan mu a haka,? Ki duba fa tun ranan da muka zo yau kwanan biyar a gidan nan amma ko sau guda wanan matar bata samu time din mu, Kina gani da ace mu yan uwanta ne zatai muna haka ? Ni dan Allah daga ita har mijin ta kuma daina mun zancen su pls, Wallahi badon kawai ina,son inzo inga Abuja ba da ba,abinda zai sani zuwa wanan wajen, Wasila, da itama karo na farko ke nan da ta fara magana tun zaman nasu sai cewa tayi, Kamar babana yasan may zamu tarar da zamuzo yaba kudi yace duk yadda muka gani in samu abinda zan saye, To yanzu may zaki gani wanda zaki saye anan bayan ko kofan gida bamu taba lekawa, ba, Ke ni fa in badon malam tsoho da rikicin shi ba da ba abinda zai sani zuwa, Murja tace wa ya isa yace wa malam bazamu zo ba cikin su baba,, Baki ganin ko mama Ladi dole ido tasa mai don ba yadda, zatayi da masifan baba idan ya tashi, Inko, badon haka ba da, mama ba,zata bari muzo ba, sam, Meenat ce ta numfasa don jin hiran su tace gaskiya yamma tayi ya kamata ace mun shiga kitchen fa, Ganin ba su da niyar tashi yasa Meenat shiga kitchen din don dora masu abincin dare, Ga garin sai lema ruwan sama akeyi wanan ya,nayin ya,sa mutane jin sanyi,, Tuwon semovita, ta tuka masu da miyar egusi, wanda ya sha, nama da tagani a cikin fridge duk ya kankare, Sai kusan gaba aikin tane Samira ta shigo kitchen din don taya Meenat din aiki, Amma kuma sai ta samu ta kusan gamawa don saura kadan, Don haka ta dan taimaka mata da dan abu kalilan, Suna kitchen a lokacin da sukaji sallaman yayan su Abubakar, Meenat wace, sai,mamakin yadda mutum ya iya tukin mota cikin wanan ruwan da ake tsulawa, Daga kofan kitchen din suka dan hango bayan shi yana shigewa a lokacin bedroom din su hannu shi dauke da yar briefcase, din shi,,,, Mamaki ne ya kama Meenat ganin irin yadda yayan nasu ya shigo cikin gidan ba tare da nuna wani damuwa akan su bakin shi ba, Kuma, ma ga Sadiya a falon zaune tana kallon season's film, amma sai ta ga bai tsaya ba, Mugun hali ta furta a zuciyan ta tare da cewa wanan ai, ba halin sunna bane, A take uncle din ta na soko, ya fado mata a rai irin yadda yakeyi masu idan yadawo daga gurin aiki, Amma kuma ai har da laifin ita Sadiyan don dai tun jiya take ganin ta a cikin wanan dogon rigar ai , Ita abinda, ta gani tun a gidan su har izuwa gidan uncle din ta shine, Da zaran yamma ta yi dai dai lokacin da mazaje ke dawo wa gida daga gurin neman kudi, ko aiki, A lokacin ne zaki ga mace tai wanka ta chaba ado tankar wace zata anguwa ko, gurin wani gagarumin buki, Shima kuma Uncle idsn zai dawo zai sayo dan tsara ko da bana ci ba ko dangin kayan miya ne, Da kuma duk wani abu wanda ake yayinsa a lokacin, Kamar rake, yalo agwalama, lemo kankana, gyada,dafafa, masara gasassa, caras, da,sauran su,,, Wani lokaci ma ganye zai kwaso masu dafaffa irin su zogala da kuli ganayen rama, dinki, tafasa, da,sauran su dai,,, Duk da ba wani tsada garesu ba zaki ga mata da yara suna murnan cewa baba ya dawo sai a shiga rabo, A lokacin kuma za a fara kaeo mai gaisuwa dagida dagu da ana mai sannu da dawowa, Wani lokaci kuma shi da kan shi yake leka ko, wani daki don jin damuwar iyanlishi idan yadawo daga aikin, Kusan kuma hakane ai ta gani a gidan iyayyen su duk da gidane na talkawa, Amma suna kokarin kula da iyalin su sosai kamar yadda sharia, yace, Wani lokaci kuma malam tsoho shi da kanshi zai saye kwaryan nono da fura akai cikin gida a raba ko wani sashe na gidan, Amma ga wanan shi ko halin kowa bai kwasa ba shi wani irin mugune haka, Kwana biyar a gidan ka amma ace ba kasan wanda yazo gurin ka ba ma ba ma balle karramawa, Tsuki ta sake wanda har ya baiyyana a fili ba tare da ta sani ba, Sai jin muryan Samira tayi tana fadin may ya faru Meenan su,Baba,, Ajinyan zuciya ta sauke tare da cewa ke dai bari sister, ***** ***** ***** Zaune yake bayan ya dawo daga gurin sallah yana cin abincin da Samira ta gabatar mai da sunan abincin shi,, Tun a lomar farko ya san cewa ba daga hannun sadiya ko Samira kaunar shi wanan abincin ya fito ba, To idan ma ba su bane kar dai ya ce wanan abincin daga cikin yan bakin yaran nan da malam ya turo suka cika mai gida wata tayi,,, Sosai ya cin ye abincin nashi wanda rabon da ya zauna agida ya, ci abincin gida haka har ya manta da lokacin, Ya godewa Allah da ruwan sama ya hana shi tsaya wa baici abincin restaurant ba, Tun daga wanan ranan ya fara dawo wa gida don cin abinci, ***** ***** ***** Zaune take a gaban mirror tana gyaran jikin ta, Kayan jikin ta suna da shiny,shiny wanda duk ta juya suna walkiya,sosai, turare ta fesa kusan kala biyar a jikin ta alokaci guda, Jan baki ta dauko ta dan zizirawa bakinta sai kuma tadan kara gyara fuskan duk da kwaliyan shi yayi kyau tun farko amma sai da ta sake yin wani, Wasu takalminta masu tudu dake gefe guda ta jawa su ta dan shiga goge su don su, dan kara haske, Gyalenta da ke saman gadon ta, ta, dauko ta sagala, a saman wuyan ta, Yar jakar ta ta dauko, tare da keys din dakin ta dake a saman mirror ta, Tun shigan ta ma,aikatan tai arba da motan shi daidai, gurin da ya saba parking din motan, a kullun,,, Kallon motar tayi tankar shi take kallo a fili, ba wai motar ba, A cikin dan damuwa ta karasa har office din su, cikin dan nuna yanayin damuwa, Zaune take amma tana yi tana duban time din wayan ta dake a gaban ta, Lubuna ce ta zo har inda take ta zauna a saman tebur din da ke gaban Salawatun, Cikin wani irin murya irin ta goggagun mata tana kashe ido guda, Salawa, yau ya akayi ne wai ? Nasan dai, zancen ba zai wuce na mutumin naki ba ko, Mr No Name, Ki bari kawai Lubuna, yau ban samu barci ba saboda tunanen shi, A tafe yake kamar kullun baida abokin hurda, dabian,sa ne daga gurin sallah azahar sai ya wuce gurin cin lunch din shi wanda kuma muna iya cewa breakfast, Da dan saurin ta ta karasa inda yake gab da ya shiga, restaurant din, Salamu Alaikum, Sir ko ba komai wanan muryan yanzu ya dan saba da jin sa ako da yaushe, Cak ya tsaya don ya kula tafe take gare shi da dan saurin ta, Fuskan shi cike da mamakin ganin gurin shi ta nufo direct, Cikin dan rusunawa ta gaishe shi tare da cewa cikin dakewa, Sir nobar ka nake so pls, ? Cikin mamaki yake mata wani irin kallo na bai fahince ta ba, Cikin wata irin murya tace ba wani abu ba ne kawai ina son indinga kiranka muna gaisawa ne, Shiru yayi da farko kamar ya wuce yabar ta amma yana daga kai suna ido biyu, Sai yaji bakin shi kawai yana karanto mata noban wayar nashi,,, Daga haka ya juya da sauri kamar wanda aka kora,kawai, sai ya,shige gurin da ya nufa,,,, Salawatu wace ke tsaye tabi bayan Abubakar da kallo tare da sauke wani irin ajiyan zuciya, ***** ***** ***** Abincin ne aka jera a cikin tiren silver round, daga dangin jug na ruwa, kulan tuwo da miya, sai gishiri a gefe, Tabar da, ke a shimfede a cikin yar rumfar sashen ta tanufa da kayan abincin, Baba Buhari yana zaune daga gefe guda, yana kokarin cire hular da ke a kan shi, Isowan ta gurin yasa shi da furzar da iska daga bakin shi yana cewa sannu da aiki, Yawwa malam inji mama Ladi wace takai gurfane a lokacin don aje abincin,, Gefe guda mama Ladi ce, wace duk da ta manyanta hakan bai hanata tarairaiyan mijin nata ba, Shinkafa da wake ne dafafa, a,cikin kulan sai mai da yaji, Cibi biyu gana uku mama Ladi tace wa Baba Buhari, Shin malam yaushe yaran nan da malam ya turawa mai sunan malam zasu dawo,? Cak Baba ya tsaida cibin da ya debo shinkafa da niyar kaiwa bakin shi , Ladi wani irin tambayane wanan haka,? Malam gani nayi sun yi yawa mana duk kan su ace a gidan shi zasu tare, Innalillahi inji Baba Buhari cikin mamaki Ladi waye bare acikin wa "yan nan yaran ?,,,, To malam ai gani nayi kamar sunyiwa matar nashi yawa ace har da su murja da Meena, da,,, Ke dakata yace wa mama ladi cikin daga hannu da daga murya,, Tunda sun,yi yawa sai ki shiga mota ki je ki kwaso su ko ? Abincin da Baba Buhari bai tsaya ciba ke nan don rayuwan shi ya baci, Ya mike tsaye yana sa taklmi yana fada da ita yace Mai sunan malam dai dan uwan su ne ko kina so ko baki so ? Ya nufi hanyar fita waje yana mai bambami shi kadai,, ***** ***** ***** Sun zage iya karfin su sai faman goge , goge da share share sukeyi duk inda ya kamata a gyara agidan sun gyaro shi gaba daya, Kasan cewa yau weekend ne sun san cewa yayan nazu yana gida don bai faye fita ba irin wanan ranan, Ko zai fita sai zuwa yamma lokacin rana yai sanyi, Suna cikin gyara, suka jiwo, Sallamar yayan nasu su,kaji wanda ya su gaba daya waigowa amma banda Meenat wace ke kitchen tana gyara, Daya daga cikin kujerun falon ya nufa ya zauna, inda ya dan daura kafan shi guda sama dan stoll din dake gaban shi, A daidai lokacin ne Meenat ta fito daga kitchen dauke da bukitin da tai moping, Ganin shi ta yi azaue girshi agaban ta, batare da tasan da shi a falon ba, Tun zuwan su yaune farkon ganin shi da ta yi a baya sai dai taji muryan shi kawai, Ji tayi kamar ta juya baya batare da ta gaisheshi ba Amma sai yai mata wani irin kwarji a fuska taji kawai ta gaida yayan nasu, Tankar a cikin mafarki Abubakar ya tsinkayi zazzakan muryan Meenat tana gaishe shi, Kallon mamaki ya ware idon shi yana mata don sam tunzuwan su yau kwana goma sha takwas bai san da ita ake ba, Da kyar ya iya bude bakin shi ya ansa mata cikin mamaki, Ita kan Meenat tasa kai abinta da niyar wucewa inda zata, Yau,she kikazo ke ? Ya tambaya cikin mamaki, Samirace daga bayan shi taba shi ansa da cewa ai tare mukazo da ita yaya, Amma shine ban sani ba ya tambaya cikin mamaki Ita bata fitowa waje ne idan ba aiki zatayi ba sai kuma kitchen da take shiga, Zai yi magana sai wayar shi tai kara a gefen da ya ajeta saman kujeran da yake akai,, ZEEE MAKAWA YELWA [7/2, 13:11] Anty Lantana: 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 1⃣2⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA ALLAH- ARRAHAMAN Layin MTN, ne ya,gani bakuwar noba wanda bai san mai ita, ba, Da sallama abakin shi ya dauki wayar dake mai tsuwan, Muryan wata mace ce ya daki kunnuwar shi a lokacin da take ansa mai sallaman shi, Hausan ta yasa ya gane cewa bada ga cikin yan uwan shi bane ke kiran shi,,, Cikin wani irin kashe murya ta fara gaishe shi inda ya ansa mata adan daburce, Cikin mamaki ya ce don Allah ko da wa nake magana pls ,? Sai da ta dan sake wani sautin yar dariya irin na gwanaye sanan tace cikin wata irin murya, Sir kana magana ne da Salawatu daga ma,aikatan ku, Nice wace ta karbi nobar ka two days ago, Ajiyan zuciya ya sauke a lokacin tare da dan dago kai ya kallo gurin da sisters din shi suke kamar mara gaskiya, Ok, Ok yace sai ya dan mike tsaye daga haka yabar falon zuwa bayan back yard din gidan, Meenat ce da Murja agurin suna kokarin shanya wasu kyalayen kujeru da suka wanke, Nesa da su yadan taka inda ya zuba hannun shi guda, a cikin aljihun wandon shi ya na sauraren may salawatu ke cewa, Sam yaran basu damu da may yayan su ke yi ba alokacin don su har kan gaban su kawai suke yi, Maganar na Salawatu ne yadan sashi jin yar kunya sai yake ganin ai yaran suna sauraren zancen shi, Duk da yasan cewa baza su taba jiwo shi ba daga inda suke tsaye, Matsan na karshe Meenat ke yi a lokacin ne kuma ta,dago daga duken da ta ke, tun farko, Caraf idon ta acikin nashi wanda hakan yasa tai saurin kau da nata idon, Tare da daukan bukitin da su kai amfani da shi agurin shanyan, Ido yabi su da shi tare da ci gaba da wayan shi da Salawatu wace ke ta kokarin tsara shi,,, ***** ***** ***** Malam mudi wanda yanzu aikin shi ya, dawo Abuja shima A,sanadin Abubakar wanda yai mai hanyar hakan, Don haka malam mudi tare da Abdullahi sabon masinjan shi Abubakar din su ka zama kamar abokai da junan su yanzu, Duk wani abin,da ya dace daga aiki ko wani hidima duk su keyi wa Abubakar, Abu gudane shi ne rashin samun fuska a gurin matar gidan da basu yi ba,, Shiyasa ko iyalen su basu iya kawo wa gidan maigidan nasu,, Su biyu ne yau,ma azaune a karkashin icen dogon yaron dake mai,aikatar don sauda yawa sukan zauna atare idan har babu aiki sosai,,, Salawatu ce tare da Lubuna ke wuce,wa cikin tako irin ta yan gayu, Hmmm inji malam Abdullahi tare da dan tabe bakin shi yana jijiga kan shi, Hmm,ummm ya,kara cewa tare da dan rage sautin uryan shi,,, Malam Mudi wai,ko ka kula da wani abin kaiyya dake shirin faruwa,? Malam Mudi wanda ya wugat da ledan pure,water da ya gama zuka, Yace kamar may fa,? Mlm Abdullahi ya kara tausa muryan shi yace , Waccen yar iskan ce na ga duk kwanakin nan tana shigewa ubangidan mu, Jiya ma a office din shi na gan,ta tana wani magana tana har da idanuwar ta mai kama dana kwankwanbishi,,, Hmmm,ummm,inji malam Mudi yace cikin kada kai, Yo ai wanan ba yarinya bace, kwaskwari,ma ce kawai irin na matan zamani ya boye mata shekaru, Amma Allah na tuba aikila zasu yi yan sa,a guda da mai gidan, Dariyan kyata malam Abdullahi ya sa har da buga kafa , Yace ashe kaima kagane abinda na gano ke nan dan uwa ? Yo wlh Allah wanan da wuya maigida ya girmay mata, Wayo kawai zatai masu shi da wanan gidahumar matar tashi mara dariya, To, to to ashe kaima har ka gano halinta ke nan don dai ni shiru nayi da bakina don kar ace nafaye sa ido, Haba dai aiko ita sam bata dace dashi ba don bata da marmari sam wanan matar, Malam Abdullahi yakara nuna Salawatu da hannun shi daidai lokacin da zata shiga cikin wani office, ***** ****** ***** Malam tsoho ne zaune a majalisar kofan gidan shi, Yara da kuma manya masu zuwa gurin shi daukan karatu lokaci, lokaci, suna zaune suna ta bibiyawa, Baba Samaila ne ya fito daga cikin yar akwalar akuri,kurar shi, jikin shi duk butu,butu, da kura da ganin shi kasan daga gurin aikin wahala ya fito a lokacin, Tun daga nesa mahaifin nasu, ya tsura mai ido cikin ban tausayi, Dan nashi shida yar uwan shi suna bashi tausayi harkullun in ya tuna da watsin da yan uwan mahaifiyar su sukayi dasu sai su bashi tausayi, Anan gida kuma bawai wani dadin yan uwa, haihuwan su, suke jiba, don ssun ware su a gefe guda, Don ma dai shi Baba samaila ya zama na mijin duniya ne don a tsaye yake kem da kafan shi gurin neman abin rufawa, kan shi da iyalin shi asiri, Direct inda malam tsiho yake Baba Samaila yanufa, Tun daga nesa sosai ya cire silifas din dake akafan shi duk sun goge akasa saboda tsufa, Gwiwa bibiyu a kasa ya tsugun na yana gaida mahaifin nashi, Daga bisani kuma yadaga yadawo gefen tabarman da dake gefe guda yadan zauna, Cikin dukan da kai da ladabi Baba Samaila ya dukar da kan shi a kasa, Wanda hakan yasa malam tsoho fahitar dan nashi nada magana a lokacin, Samaila, ya, ya akayi ne ? Cikin dan sosa kai, Baba Samaila yace, malam dama zancen su yar Baba, da ke can gurin yayan su ? Dazun ina daji shi kawun nata ya bugo min waya yana min tuni, kan hutun su ya kare, wai, wani sati zasu koma,,, Murmushi malam tsoho yayi tare da dan gyara zaman shi Baba Buhari wanda ke gefe yace a,a,a hutu ya kare aiko gara su dawo don kada su, makara, Aikaga waccan mahaukacin tun kwanan baya ta damay ni akan zancen dawowan su, Wai an,kaiwa yaran dawainiya da yawa, don zaman bariki ba zaman nan bane, Ko wa zata gwada ma zaman bariki,? Mata babu tunane sam a kwakwalwan ta, ita yanzu inda tana da wayo hakan ba abin alfahari bane gare ta, Yau ace an, wayi gari har yan gidan nan sun je gun dan da ta haifa da cikin ta sada zumun ta, Murmushi Baba Samaila yayi tare da kada kan shi, cikin takaici, Yace ai nasan dama, Ladi sai tayi wanan korafin akan wanan tafiyan, Don dai kawai malam ne yace ai,ni da babu inda zasu gaba dayan su,,, Malam tsoho dai bai tankawa diyan nashi ba duk zancen da sukeyi sai murmushi yakeyi ya na girgiza kai, har zuwa lokacin da duk kan su su kai shiru, Cikin murya irin na tsufa yake cewa, zan yi magana dashi Abubakar din insha Allah, Daga haka Baba Samaila yai wa mahaifin nashi sallama ya tashi ya bar gurin, ***** ****** ***** Abin da tasaba yi duk lokacin da kwanan wata yakai irin wanan lokacin yau ma shine take ko,karin yi, din kamar kullun, Kamar yadda tasaba, bawa yaran shiya da sadakan naman kaji, da kuma na Naman rago, Yau ma wani irin murdaden ragone kato, aka shigo dashi daga mahauta inda aka yanka aka kuma gyara, shi,, Ba, bata lokaci aka shiga yan kawa ana kaiwa makwabta sadakan naman ,, Masu karba su karba wa, yan da suka camfa wanan sadakar na Hajja kuma suki karba,, Su kuma har neman kari sukeyi don wanda aka kai masu bai ishesu ba, Duk a,kai wanan yan kan abuguda Hajja ke dauka daga cikin tunkiyan ko rago,,, Daga shi bata daukan komai daga ciki kuma ita bata cin naman, Duk abinda take ciki tana ganin cewa mutane basu hankalta da abinda takeyi, Batasan cewa labari iri iri akan ta yabi gari ba kowa da irin abinda yake cewa, ***** ****** ***** Zaune take a falon da daya daga cikin takardun ta na karatu da tazo dashi, Tana dan dubawa don gudun mantuwa, kada ya shige mata, wanan dabiar Meenat ce yawan bitan littatafan ta, akai akai, Samira ce ta sa ma ta kira daga dakin su don haka ta mike tabar takardun nata a guri, Shigan,ta dakin da kamar minti uku Abubakar ya shigo gidan agajiye, daga gurin mai gyaran mota yake, Don haka saman kujeran tree sitters din da Meenat ta tashi ya hau, don yadan sha iska ya huta, Takardun da yagani akaine ya dauka yana dubawa inda ya fahinci cewa takardan daya daga cikin sisters din nashine, Wace ce wanan mai wanan rubuta mai kyau haka gashi kuma ta iya bayanin kowani sashe da kan ta, Tambayar da yaiwa kan shi ke nan a cikin zuciyar shi, Don haka ya aje takardun a saman tabur din dake a gaban shi, Kwantawa yayi ya mike tare da dagwara hannayen shi akan shi , idon shi a lumshe suke tankar mai barci,, Meenat tafito daga dakin don taci gaba da karatun ta inda ta tsaya, Sai ta ja ta tsaya guri guda don ganin yayan nasu da tayi a kwance gurin da ta tashi yanzu, yanzu, Komawa baya tai niyar yi don ganin shi da tayi a gurin , Amma sai idon ta ya hango mata takardun ta a saman dan tebur din dake gaban shi, Sadaf, sadaf ta nufi gurin don azaton ta irin yadda ta ganshi ta dauka barci yake yi, Daukan takardun nata yai daidai da bude idon shi inda ya sauke su a cikin nata, Fuskan shi a murtuke kamar kullun yadda take ganin shi, Wani iri taji kamar ta koma baya tabar takardun don tsoron shi da taji, Kawai sai tai nufin juyawa, amma kuma muryan shi da taji yana cewa ke dauki mana ki tafi, Yasa ta saurin dauka cikin makyarkyatan hannu kama za a rike ta, Da sauri tabar guri inda shikuma ya maida idon shi ya lumshe kamar yadda ta samay shi da farko, Ita ko Meenat cikin zuciyan ta sai cewa tayi mugu kawai wanda yai gadon mugun hali gurin mama,Ladi,, Kai tsaye, dakin su ta nufa, Ganin irin yanayi da ta shigo da shi a dakin ne yasa Aisha tambayar ta ko lafiya, Batare da taba ta ansa ba ta samu gyafen gadon da suke zaune itama ta zauna tare da yin tagumi, Tunane barkatai ta dinga yi a kwakwalwanta tana cewa, Watan da gaske ne da ake cewa mutum na gadon abubuwa daga mahaifan shi, Inko haka lalai wanan yayan nasu ya gado mahaifiyar shi da tsanani sosai, Mutum haka da girman kai, ga ahare mutane kamar mai jin warin su, Ga isa da izza kamar wani dan gidan sarkin gwandu, Sjigowan Samira dakin tare da kiran sunan ta shi, ya tsayar mata da zancen zucin da takeyi, Meena wai yayan mu ne ke tambaya na wai waya hada mai zobo ranan nan, Anty samira ke baki hada mai da kan ki aiduk dayane ko,? Tafadi haka cikin yanayin damuwa, To Meena ai tambayana yayi shine na fada mashi cewa kece, kike hada muna kullun,, Don haka sai kizo muje ki hada mai kafin ya kara tambaya, Barin je in fara jika maki kàfin ki taso ko don in rage maki aiki, Ganin Samira ta juya ta nufi hanyar fita daga dakin, Meenat, ta mike tsaye tai saurin da sauri ta sha gaban Samira tace, Pls anty Samira ki taimaka ki hada masa don ban son fita idan yaya na falo, Dariya ne ya kama Samira tace, kamar wace zai daka ko yai mata fada,? Zo muje tare ke babu komai dan Allah Badon taso ba tabi bayan Samira simi simi da ita kamar wace za,a kama, Yana cikin falon still saidai wanan karon a tsaye yake yana waya, ba kamar yadda ta barshi dazun ba, Daga kuma wanda yake wayan dashi yana da mutunci matuka agare shi, Saboda irin yadda yake magana cikin girmamawa tankar a gaban mai shi yake, Ta gefen shi sukabi suka wuce batare da sun gaishe shi ba, Ba,a dauki wasu lokutaba suka hado mai zobon mai sanyi yaji kayan hadi kamar yadda tasaba yi a gida don sana,ar mama Saratu ne kayan sanyi,,, Sunan Samira yakira inda ya dakatar da ita, sai dai ita Meenat kan har ta shige abinta, Tambayar ta yayi da cewa, Wai cikin yaran nan wace ce diyar Baba Samaila,? Tace yaya Meenat ce ai diyar shi, Wacece Meenat din daga cikin su,? Itace mana wqnan da muka hadama zobon da ita ai, Cikin mamaki ya ce itace wana yarinyar dake bin babban dan shi ko, ? Ita ce kuwa inji Samira ta bashi ansa, Wani irin faduwar gabane ya ji tamkar zuciyan shi zai yi rawa, Yace yanzu dama da diyar Baba na Samaila a cikin ku shine ban sani ba, Samira ta dan mai,da hankalin ta gare shi da kyau tace eh yaya, Subbahanallah inji yayan nasu ya fadi cikin kidimaywa, Ita kan Samira tai shigewanta tabar shi nan gurin da yake zaune, Kusa da Meenat ta zauna tana cewa ke Meenat wai fa tayan mu bai san dake acikin mu ba, Sai yanzu yake tambayana wai wacece diyar Baba samaila daga cikin mu, Meenat cikin zuciyan ta, ta ce mugu kawai ai,gara da bai,sani ba tun da farko,, Washe garine suna falo sai gashi ya fito acikin shigar shi ta zuwa office, Gaba dayan su su ke rige rigen ce masa ina kwana yaya, Cikin daga hannu ya ansa masu gaisuwa tare da cewa a takaice, lafiya, A gurguje ya dan kurba tea din da ya hada wanda ga mamakin shi ya sha kayan kamshi kamar yadda iyayyen su ke yi, Har ya fara tafiya sai yake cewa batare da ya kalle su ba, Malam tsoho ya bugo waya jiya yace a tura ku ku koma gida don hutun wasun ku ya kare wai, Daga haka kawai yasa kai ya wuce inda suke ta ce mai adawo lafiya yaya, Fitan shi yai daidai da juyowan Samira gurin Meenat tace inaga saboda kene aka bugo mai waya,,,,, ***** ****** ***** Zaune take tana kokarin jawo wani file dake karkashin takardun dake saman tebur din ta,, Wayan tane yai kara alamar kira ya shigo mata alokacin Kamar kada ta duba amma sai wata zuciya tace mata ta duba mana taga ko waye ke damun ta haka, Da yar tsukin ta ta jawo wayan don ganin ko waye ke damunta tana tsakan aikin ta haka, Cikin wani irin mamaki takai zaune saman kujeranta don ganin noban dake kiran ta, Cikin rawan hannu ta dauki wayan don karba kiran na bazata da yai mata a yau,, Wani irin kashe murya tai sallama dashi tare da kara gigita mashi zuciya, Salawatu indan antashi daga aiki zakki rakani wurin shopping akwai wasu yaran da sukazo hutu gurina ina son in masu sayayan komawa gida, Cikin sauri sauri tace ok sir insha Allah zan shirya da wuri mutafi,,,,, ZEEE MAKAWA YELWA,,, [7/2, 13:11] Anty Lantana: 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 1⃣3⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA,,, ALLAH_ AR-RAHEEM,,,, Wani irin uban tsale Salawatu, ta daka tare da mikewa da sauri ta suri jakar ta, Gida ta koma inda ta kara yin shiga ta alfarma ta gyara duk sassan jikin ta tsab, Ta dawo, office duk wanda yaga ta canza shiga daga cikin abokan ta sai sun tsaya mamakin ya haka kuma ? Sai tai masu far da ido tace abin ai sirine kawai basu gane ba yanzu,, Har kusan zuwa tashi office, sanan ta dauko jakar hannunta takara dauko madubi ta gyara duk inda ya dace, Wani turare ta shafa a jikin ta mai wani irin mugun kamshi, Sai kuma daurin dan kwalin ta da ta gyara da kyau, tare da sabale gyalen nata, Wayan ta ta aje gefe guda tana jiran kiran shi kawai, Shiko dama dan over time ne yana can yana over din shi, Har ya manta da zancen zasu fita da ita, sai aikin gaban shi ne yake kokarin yi kawai, Malam Abdullahi masinja ne ya hango ta a tsaye bakin motar shi tana ta kallon agogon wayan ta cikin bacin rai,,, Shigan malam Abdullahi office din yasa shi dago kan shi a cikin sauri Da mamaki ya ce malam baka tafi gida bane har yanzu, A haba dai yallabai ai jira nake har ka rarage sai in kulle ko ina , Allah sarki hakene fa malam Abdu don Allah kayi hakkuri, dani shap na manta da ka na jirana ne, wallahi, Ba matsala ai,na san baka gama bane yanzun ma nazo ne in sheda maka cewa kamar naga ana jiran ka a waje ko ? Cikin mamaki Abubakar ya ce ni ta alamar nuna hannun shi a jikin shi, Saida Abdullahi yadan yi shiru tukun sai yace kuma yarinyar nan mai yawan tsayawa dajai nan ma,aikatar, Cikin wani iri Abubakar ya ce Subbahanallah wallahi ni nace ta tsaya min zata rakani in saiwa yaran nan da su kazo hutu wurina tsaraba, Daga haka ya mike tsaye yabar gurin cikin daukan yar briefcase din shi, ***** ****** ***** Daga gurin da take kwance tai mafarki kamar yadda ta saba yi a,duk tsakiyan wata,, Ciwon maran da tasaba yi shine har zuwa yau ma ya tayar da ita daga barcin da takeyi, a dakin ta, Nishi takeyi sama, sama ta murdewa guri guda kamar macijiya ,, Sai kuma wani irin kugi da takeyi ga jikin ta na wani irin rawa, A daidai bayan dakin da suke suna hiran su da kuma wanki, murja ta fara jiwo wanan kugin har sai,da tace wa yan uwa suyi shiru su saurara, Daga dakin kwanan Sadiya ne wanan sautin ke fitowa, Kallon juna sukayi a lokaci guda inda kuma suka kwasa gaba dayan su zuwa cikin gida, Samira ce suka kai karo da ita zata fito gurin da da suke hannun ta dauke da sabulun wanki, Murja ke sheda mata abinda suka ji daga dakin Sadiya, Tsuki tayi cikin rashin nuna tausayi tace ai aikin ta ke nan duk lokacin da zatai period ko ta kare, Acikin mamaki duk suke kallon ta inda take kokarin wucewa abinta zuwa waje batare da ta damu ba, Meenat ce ta sa kai zuwa cikin gidan inda sauran suka mara mata baya, Irin yanayin da take ciki yasa su gaba dayan su rudewa sai kiran sunan ta suke,yi,,, Da sauri Aisha ta koma falo inda ta dauko goran ruwa da cup ta dawo dakin , Tsugunnawa tayi tafara karanto addu,oin da kakan su malam Manya ya koya masu, Ganin haka yasa ita ma Meenat zuwa daidai inda Sadiyan take kwance cure guri guda, kamar wace zata mutu, Addu,oi suka fara mata suna tofawa duk da dai a tsorace suke, Aisha tace su taimaka su daga mata ita, su bata ruwan da tai addua,n aciki, Komawa sukayi tsatsaye suna kallon ikon Allah kawai, Can sai sukaji tayi wani irin getsawa da karfi sai ga zufa ya keto mata a goshin ta, Daga haka tafara sakewa tankar mai shirin yin barci ko somaywa, Sai faman sannu, Anty sannu Anty suke mata, Ita ko kai, kawai take iya kada masu saboda azaba, ***** ****** ***** I am sorry pls abinda ya furta ke nan da isowar shi gurin da take a tsaye, Batare da ya tsaya wani magana ba kawai ya bude motar nashi, suka shiga, Tuki Abubakar keyi a hankali kamar wanda ke tausayin sitiyarin motar, Wanan yanayin tukin nashi yasa Salawatu jin dadin yanayin da ta tsinci kan ta yau tare da Abubakar din, A hankali ya mika hannun shi inda ya kara volume din redio motar kira,ar shuriem ne ke tashi a cikin suratul AN-NISAN, A hankali Abubakar yake bin kira,an malamin cikin wata irin murya, Salawatu wace batasan may zatayi ba awanan lokacin sai gyara zaman ta tayi a hankali tare da bin lafiyan kujeran mota, Tafiya sukeyi batare da wani yaiwa dan uwa magana ba, Shi Abubakar din ne yadan kau,da shirun ta hanyar juyowa gurin da take zaune yace, Wani shagone zamu tafi, ? Hakan yaiwa Salawatu dadi don haka bata lokaci tace mai mutafi sahad, aiko, Tace hakane don tasan matatara ne wanan shago dole ne ma wani yaganta tare da Abubakar kafin su fito, Daga haka bai kara magana ba inda ya juya kan motan shi zuwa sahad store din, Shigan su shagon ne sai taga Abubakar yace mata bissimillah ko sai ki zaba masu, Da farko English wear ta fara dauko masu, masu kyau, don taji yace kada ta damu da kudin kayan ta dai zaba masu, Tambayar shi tayi da cewa ko su nawane yaran inda ya sheda mata cewa su biyar ne, Kai ta kada cikin mamaki tace wani abu sai malam bahaushe, Har mutum biyar za,a turo hutu a garin Abuja haka ? Ganin bata zabi kayan da yasan yaran hausawa suna sawa ba yasa shi kiran sunan ta Karo na farko kega tun lokacin da tafada mai sunan ta,, Wani irin dadi salawa taji don aganin ta ko mahaifanta da suka rada mata suna basu kai shi iya kiran sunan ta, ba,, Wasu dinkakkun kaya readymade, ya nuna mata dinkin shadda ne masu kyau zani da riga da dan kwali akwai kuma masu siket, da riga, Sai kuma gurin turamayn zannuwa inda ya ce mata tazaba mashi masu kyau da kuma tsada, Ganin tana ta dauka baice komai ba yasa ta dan juya tare da daga kai ta kalle shi, Tambayan ta yayi da cewa sun ishe,su ko ? Mamaki taji a zuciyan ta tace shi wanan wani irin so yakewa yan uwan shi haka,? Da,bai jin zafin kashe masu kudi, ? Lailai za,a rina awanan gurin, don haka dole ne tayi kokari ta kutsa kanta gareshi, Daga karshe itama yace ta dauki duk abinda take so, Ba karamin mamaki salawatu tayi ba don jin irin kudin da aka caje shi, Amma ba bata rai yasa hannu ga Aljihu ya biya su atake, Masu kwasan kayan store din suka kwasa zuwa inda suka Parker motar su, Sun fara tafiya ba,a dadeba taji muryan shi yana cewa, Sannu da kokari miss salawatu, na gajiyar dake da yawa ko ? Nagode kwarai, Cikn jin dadi da rausaya kai, tace ma shi,, You are welcome,, Murmushi yayi alamar maganar ta ya gamsheshi har zuciya, Yace godiya nake, Yar siririyar dariya ta sake tace Sir, kamar wanda nai wani abu wanan godiyan haka,? Saida ya sake murmushi ya furzar da iskar bakin shi yace mata, Lokacin ki fa kika bani salawati, Aikin ga dole na gode maki ko ? Da kwatance ya isa gidan su Salawa din inda ya fahinci bawasu masu karfi bane gidan su, Rufin asirine kawai irin na Allah, ke tare da ita, Kayan da ya siya mata ya bude but din motar takwashe ya kara mata godiya ya sa kai zuwa nashi gidan da kayan tsaraban yan hutu niki,niki, ***** ****** ***** Jin yau cikin ikon Allah, ciwon baiyi mata tsanani irin yadda ya saba yi mata ba, Tadan rarafo zuwa falo inda ta samu dogon kujera ta kwanta, Sai,dai daga kwanciyar zaka gane cewa tana cikin wani irin yanayi gaskiya, Da sallama kamar kullun yadda ya saba shiga gidan nashi ya shigo, Duk da yasan ba lalaine ya samu ansawan sallamar tashi ba, Tun daga kofa ya hango ta daga yanayin kwanciyar ta yasa shi gane cewa ba lafiya, Sai bai kula da yan kan,nenshi dake zaune falon ba cikin yanayin damuwa, Da wata irin murya ya kira sunan ta cikin nuna kulawa, Ba tare da ta dago ba ta, ansa mai kiran nashi da naam, Tsungunawa yayi daidai kanta yana mata magana kasa kasa ta yadda ba dole ba ne wani yaji may yake cewa,, Hannu ya kai daidai wuyan ta yana taba jikin nata don jin lafiyan ta, Muryan Aisha ne ya katse mai tabe taben da yakeyi a jikin matar na shi, Yaya dazun mun ji tsoro sosai irin halin da mukaga anty sadiya ta shiga , Sai da Allah ya bamu ikon yi mata addua, da kuma tofi irin yadda malam tsoho ya gwada muna akan ciwon mara, Daidai lokacin da yake dagowa tsaye da ga duken da yake ne yace mata Ok, Daga haka yasa kai abinshi ya wuce zuwa ciki, Gaba dayan su kallon mamaki suka bishi dashi a lokacin irin yadda yai masu, Kallon kallo suka bi junan su dashi don dai irin yadda ya basar da su, Sosai abin ya bata masu rai saidai babu halin su nuna tunda yayan su ne, Kuma kadan daga cikin irin rayuwan shi ke nan, don mai ba hagon hali suke jin iyayyen su na ce mai, A dakin su inda suke zaune suna ta kus,kus, kowan su a gajiye yake da ya koma gida, Tun dai manyan su irin su Aisha da murja masu samari Gashi sun bar,su can ba hira,,nan kuma tunda su,kazo babu inda suka taba zuwa , ***** ****** ***** Baba Buhari ne tafe cikin wanan ranan da aka famtsama yau, rigar shi uk ta jike da zufa da alamar da kàfa yai yawo cikin wanan ranan, Daidai zai shigo sashen nashi ne yaji muryan mama Ladi tana cewa, Su wa yan nan yan jakar uban basu da ranan dawo wa tunda sunji dadi sun samu gidan ci da sha, mai galmi,, Kai Allah dai ya sau,waka da wanan irin rayuwan na rashin sanin ciwon kai, Zagi haka har kowa naji suwa kika samu haka ne wai ladi? Wa yan nan yan jakar uban yara mana da suka tafi gulma, Wani irin mugun bacin rai Baba Buhari yaji alokacin Don har sai da gaban shi ya fadi gudun kada iyayyen yaran su ji, Wani irin kunya ya lulubeshi a lokacin da ya hango matar kanin shi gufa ta lungun su tana kada kai, Mama taci gaba da cewa wanan yaron ai wahala ta samay shi tunda ya nuna yana dashi, Haka kawai a dinga yiwa mutum iko inga tausayi ai bai kamata atura mai su dukkan, su ba Ke Ladi cikin wani irin daka tsawa baba ya kira sunan ta yace ahir din ki wallahi, Naga abin naki tabin hankaline, Shin ke ka dai keda yaron gane wai shin? To wallahi ki iya kan ki akan wanan zancen don zan bata maki rai fiye da tsanmanin ki, Ganin irin yadda rayuwan shi ya baci yasa mama tai shiru don tasan irin zuciyan baba yanzu zai iya mata abinda yace din, ***** ****** ***** Dukkan sune a falon inda yasa Samira da Murja suka kasa kayan gida biyar, Baki yabasu akan kowa ta zaba daga cikin, sanin cewa sune manya gare ta, Tana zaune gurin da take har suka gama zaben su, Komai itace ta karshen dauka daga cikin abinda aka saya masu din, Sai murna da farin ciki sukeyi don ganin irin wanan tsaraban mai tarin yawa da tsada da akasaya masu, Cak tamike har zuwa bakin hannun kujeran da yake zaune akai tadan dafa, Cikin girmamawa tace yaya mungode Allah ya kara bude ya kara rufa asiri, Kai ya kada mata alamar bakomai, dama tasan cewa ba lailaine ya ansa mata ba, Ganin hakane ne suma tan uwan daga gurin da suke suke tacewa yaya mungode mungode, Sauran kayan da zasu kaiwa sauran mutanen gidana kuma nan ya shiga dan yi masu bayani sama sama, Kiran Salawatu ne ya shigo a lokacin don haka bai karasa zamcen shi ba yadauki wayan, Cikin murmushi a fuskan shi yake magana da ita, Rankashi dade ka isa gida lafiya ko ? Ya madam ya bakin ka ko ince bakin mu, Don nima ai sun zama yan uwana yanzu, Sai tai shiru taji yaya zaiyi re,action, Duk lafiya suke suna gasheki sun kuma yaba da sakon ki sosai, Kai, Sir har fa naji dadin wanan zancen da na ji ZEEE MAKAWA YELWA,,,, 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 1⃣4⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA, ALLAH_AL-MALIK,,,, BANZAN MANTA DA KAUNAR KU GARENI BA,,, SAFIYA ABDULLAHI HUGUMA MARIYA SB HAFSAT YUSUF NAFISAT HARZAMI, MAMAN FARIDA SAFENAT MAHMUD MAIDUGURI (ABUJA) PRECIOUS HINDU KB MAIJIDDA HARZAMI, FATIMA YAHAYA NASAWA, FATIMA GARBA LUV, MAMA WALID DA WALIDA,,, DAMA DUK WANCE BANKAI GURIN SUNAN TA BA, NAGODE MAKU KWARAI DA GASKE GA TAIMAKON DA KUKE BANI A KULLUN,,,, Duk yadda suka so tafiya a karshen mako hakan bai samu ba don ciwon da Sadiya take fama dashi, Dole tafiyan nasu ya dage zuwa wani lokaci don tana jin jiki, Ga Samira fafir taki zama agurin su itama tashirya dawowa gida, gurin yan uwan ta, Gado a,kabawa Sadiya don haka su Aisha da murja da suke manyan su, Su ke zauna da ita a sibiti Ganin irin yadda take wahala yasa yaran hankalin su tashi, sosai, Suna tsaye a kanta har zuwa lokacin da abin yadan lafa mata, Yayan su ya umurce su da su zauna da ita i je yadauko masu abin bukata a gida, Barci Sadiyan takeyi i,yanzu don haka suma suka samu kujera su ka dan za,zauna a gefen ta, A gida su Samira ne ke faman kokatin girka abinci kafin su dawo asibiti, Kwatsan sai ga yayan su yashigo yanayin ba dadin gani don fuskan shi babu annuri ko kadan, Hakan ya tayarwa yaran da hankali do sun matsu suji wani irin hali matar yayan nasu take cikine ? Ba wani sakin fuska kamar kulkun fuskan shi a,daure, tam, Kai tsaye yace masu ku sa min ruwan zafi a flasks, da kuma yan kayan da ake bukata a,asibiti, Wanan dalilin yasa su gane cewa, an kwantar da ita a,asibitin ke nan, Daga haka ya wuce, direct zuwa dakin kwanan shi, Ido suka bishi dashi cikin jin takaicin irin halin yayan nasu, Meenat dake daga cikin kitchen tana jin duk yadda suka yi tare da yan uwan ta, Sai ga Samira tafado kitchen din tana cewa Meena kinji wanan matar wai gado aka bata, ashe,? Ni wanan abin wallahi haushi yake bani,sai da mutane suka shirya zuwa gida, sanan zata wani kakalo ciwo ta narke a gado,,, Sai ta karasa da jan guntun tsuki tana kokarin duba flask din dake gefe a jiye, *** *** *** Duk wani abinda ya umurce su da su hada mai don tafiya asibitin da su, Sun hada mai a cikin wani basket da ke cikin kitchen din, Yadda ya shiga fuska babu walwala hakan ya fito masu, Yana kokarin sa bottom din hannun rigar shi fuskan shi a kan kayan da suka hada, Inda Samira take zaune ya dan kalla yana cewa naga kayan da yawa mana , yaya haka, ? Cikin dan girmamawa tace dama har da abincine muka hadawa su, Aisha, Bai tankawa kowa ba sai kokarin da yakeyi na daukan basket din, Samirace tace yaya dama wai muna son mu, bi ka zuwa asibitin ne, Kamar bai ji may take fada ba ya sakai fuuu ya wuce abinshi, Samira wace ta kai iyakan sai cewa tayi a fili, mugunta, har kan shi ya ke yi wa,,, Nafisa wace ke zaune a cikin shirin bin yayan nasu zuwa asibitin da suka sa rai tace, Ni tun farko ban so kisa musa ran mu ga zuwa ba wallahi don na san yaya bazai ko saurare mu ba, don dai kawai ina son ganin gari ne, Hon din motar shi ne suke ji daga waje cikin karfi ya ke masu, Samira wace ta san halin shi da sauri tace ashe, miskilin bai wuce ba mu yake jira a waje fa, Meenat wace tana zaune har yanzu batai wani alamar motsawa ba yasa Samira cikin sauri tace mata taso mana Meena don kin san fa ba jiran mu zaiyi ba yana iya wucewa, Kai ta gyada mata tare da kokarin shafa addu,a a fuskan ta sanan tace, Anty Samira idan nace in biku wa zai zauna gida yayi muna girkin dare, Baki Samira ta tabe gami da fisgan gyalen ta da sauri taja hannun Nafisa suka fita, Su biyu Abubakar ya hango tun,daga nesa sun tunkaro gurin da yake, Mamaki yayi na rashin ganin diyar Baba Samaila a tare da su, Kamar zai masu maganar ta sai dai kuma ya share su kawai suka bude mota suka tafi, ***** ****** ***** Fitan su babu dadewa Meenat tafito tsakar falon gidan da nan tafara inda ta gyara shi tas takawo kamshi ta fesa, Girkn dare ta dora sai kuma ta fara gyaran dakun gidan tun daga nasu har zuwa na matar gidan da na yayan su Abubakar din, Ba, ita tasamu kanta ba sai zuwa gab da magrib a lokacin duk ta hada komai, Kiran sallahbda akeyi a ko ina ina ya sanar da ita cewa,lokacin sallah yayi , Don haka babu bata lokaci Meena ta fada dakin su ta dauro alwala don tai sallah, Falon gidan ta dawo can wani dan angul ta tsaya don,tai sallah, saboda yau gidan yai mata girma, A gurin da take zaune ne taji sallaman shi yadawo, Tun daga kofa Abubakar ya gane cewa gidan yasha gyara yau, Kamshi biyu ne suka daki hanncin shi, a lokaci guda, gana air fresh ga na girki, Ganin tana sallah yasa shi shigewa dakin shi direct, Tsowon lokaci ya dauka da shigan shi dakin nashi, Don ganin irin yadda dan lokaci guda dakin shi ya sauya kama, dakin ya bi da kallo ko ina tsab, Ko bai tambaya ba yasan cewa meena ce tai wanan aikin haka, Ita ko Meena tana zaune tana karatun Alkur,ani maigirma izu, biyu, Jin muryan shi tayi kamar daga sama yana cewa ina, ina abincin da za,a kai asibintin, ? Da sauri Meena ta dago daga duken da take tana karatu, don ta bashi ansa, Voil ce a jikin shi mai ruwan madara, ya,na ta kyalli, Mamakin wanan irin kwalliyan da ya sauya takeyi, Don dai ita, tun zuwan su gidan shi, bata ga yana sa manyan kaya irin haka ba, Kan ta, ta marya kasa da sauri cike da kunya da ladibi, Sai kuma nauyin da ta dan jin don wani daure fuska da yayi da yaga irin kallon da taimai, Don shi azaton shi yarinyar miskilace ta karshe , Mikewa ta yi inda kai tsaye ta wuce gurin da basket din abincin yake, Cikin mamaki yake kallon irin yadda yar yarinya kamar meena ta iya wanan aikin haka, ? Unlike matar shi Sadiya wace ko wankin toilet aikine a gurin ta balle daki, Ya dauka har ya kai kofa ba tare da ya juyo ba yake cewa i hope baki sa masu plates da yawa ba don akwai na dazun a can, Kan ta dake kasa ta girgiza alamar a,a tare da dn cewa a,a a asanyaye, Daga haka yabar falo ya na dauke da basket din abincin, Inda dama Meena a matse take don gani take duk a takure take dan tsayin da yayi a gaban ta, ***** ****** ***** Shiga na gani na fada, tayi cikin wasu tsaddadun material masu daukan ido, Dinkin dogon riga ne sai shara, sharan hannun da akai, ma,su,, sai kuma saukan da rigan yi har kasa, Ga jakar su, da takalman shigen kalar kayan, da ta sa, sai kayan su kai mata wani irin kyau, ajikin ta, Ita da kawarta aminiyar ta watau lubuna, suke tafe don zuwa duba mara lafiyan, Kayan fruits ne,suka tsaya a hanya suka siya don kaiwa mara lafiyan, Basu wani sha, wuya ba sosai gurin gane dakin da Sadiyan take kwance aciki, Saboda tambayan noban dakin da ta,ke kwance aciki, Gaba daya yan mata suna cikin dakin sun barbaje sai kwasan girkin da kaunar su ta tsaya gida ta girko ma su,su keyi abin su da kuma shan "ya"yan fruits , wanda yayan su, ya siyo wa mara lafiya, Tun kafin su shigo dakin kamshin turaren su ya sanarwa duk wanda ke a cikin dakin a lokacin zuwan su gurin, Gaba daya hankalin na cikin dakin ya koma gurin masu shigowan dakin a lokacin, Saboda kamshi da kuma sautin, takon takalman su,, Da sallama suka shigo dakin a lokacin, Sadiya wace ke kwance tana facing din kofan dakin, Mata ne yan gayu, su biyu da ganin su gogagun Abuja ne basai an fada maka ba, Sun yi wankan mai sunyi wani irin fari wanda har ya fara canza masu kalar fatan jikin su, Aisha ce tafa yi masu sannun da zuwa inda murja tafara mikewa saman kujeran da take zaune akai, ta basu, Samira ce saman dayan kujeran, don haka ta tsaya wani dan shan kamshi kafin ta tashi sama, ta mika masu,,, Fuskan su gurin Sadiya wace ke kwance saman gado wani kimdin da ita kanta wanda ba kitso ba kuma gyara yai wani chushewa guri guda, Ya ya jiki ? Inji Salawatu wace ke wani kallon mutane uku saura, Da sauki inji Sadiya inda ta juya kan,ta don bazata jure irin kallon da suke mata ba na kurullah, Dakin yai wani tsit a lokacin kamar ba kowa acikin shi, Ko wacen su da abinda take, sakawa a zuciyar ta don zaman kallon kallon akeyi, Yaya Abubakar nr ya shigo dakin a lokacin shima sai kamshi ke tashi a jikin shi, Hannun shi dauke da ledan maganin da ganin shi kasan daga gurin sayo magani yake, Abin mamaki sai ga yaya Abubakar yana yar murmusawa don ganin wa yan nan matan, da yayi, Cikin mamaki sisters din nashi suke mai wani irin satan kallo, Muryan shi sukaji yana cewa sannu ku da zuwa ashe har kun kara so, ne, ? Da hausan su na yan Abuja suke cewa eh amma dai bamu wani dade da zuwa ba ai, Ashe yan hutu basu samu tafiya ba ? Eh ciwon madam ne,ya hana su tafiya wallahi,amma yan,zu ta samu sauki zuwa wanan lokacin, sosai, Allah ya sauwaka suka ce tare da kokarin mikewa inda Lubuna take kokarin tura ledan da suka shigo dashi a gaban su, Salawatu wace tasa hannu a cikin jakarta ta debo kudi yan dubu guda guda,, Samira wace ke kusa da ita tsaye tun bayan mika mata kujeran da tayi ta miko ma kudin, Karba tayi cikin rashin wani nuna zumudi kamar yadda Salawatu ke tsan manin zasu nuna kwadayin kudi a fili, Tacewa Samira ga wanan ku kara a tsaraba ko ? Murja ne ta ansa da cewa mun gode , Cikin wani kashe murya daidai lokacin da suke mikewa tsaye Salawatu ta ce, Sir zamu koma ke nan Allah ya sauwaka, Abubakar ya gyara tsayuwan shi da cewa barin sauke ku mana, Koda mota ku,kazo abinda yasa har su sisters din nashi suka dago kai don su kara kallon matan, No Sir motar tana wurin service wallahi kuma munga idan mun tsaya dare zai yi , Amma ka barshi kawai zamu dauki drop ai ba wani matsala, No mu je kawai na sauke ku sai in dawo in kai, wa yan nan gida su ma, Ba wani musu suka mike suna mai cewa Allah kara sauki, Su kuma wasu daga cikin yan matan suna cewa mun gode Allah kai lafiya, Da haka suka bar dakin cikin karairaiyan kwankwaso da kafadan su, ***** ******* ***** Leda ne rike a hannun shi babu komai a ciki sai kayan cefane irin su alaifo, tumatir, albasa, da tatasai, Daidai lokacin da zai shiga cikin kofan shiga babban gidan nasu A,daidai wanan lokacin mama Ladi ta ke kokarin fitowa cikin wani katon hijab, baki, Kamar kada ta gaida shi da dawo wa amma sai ta dake tace, "Illah ho,, Ingwaiyyah,inji baba samaila, ya ansa mata gaisuwan da ta ansa mai, Fuskan shi a daure kamarkullun idan sun hadu don haduwar su bai faye dadi ba,, Yadan zarta ta kadan da niyyan shiga ciki sai yaji muryan mama Ladi tana cewa, Shin yaushe yaran nan da kuka tura can gurin yaron nan zasu dawo ne wai, Kaga gaskiya an takurawa wanan yaron da yawa don dai ace rai har biyar a lokaci guda, Ai sai su ja mashi matsala, ga matar shi ko ga inda yake samu, Inba hali irin na son kai ba da ganin iyaka wanan ai son ganin karshen mutum ne kawai , Cikin wani tsawa Baba Samaila yace mata ke dakata Ladi, Wawiyar banza mala hankali da tunane, ke in har kina da kunya har zaki iya tarona ki ce wai bamu da hankali mun tura wa Dan ko yara, Baki ta rike cikin shirin bada ansa sai muryan mijin ta baba buhari ta ji daga bayan ta, Yana cewa ke kan Ladi tir da halinki mara hankali da wayo , Shin wai Ladi yau in tambaye ki Dan ga ke kadai adda shi ko kuwa,?,,, Muryan ta na rawa tace don dai, na tambaya shine zakuyi min taron dangi, Hakan ya jawo hankalin wasu daga cikin mutanen gidan, Ganin an fara taruwa masu yasa ta wucewa inda ta nufa simi simi, da Da wanan bacin ran Baba Samaila ya karasa shiga ashen shi cikin fada da mamakinnirin wanan karfin hali na mama Ladi, Mama Saratu ce tai kokarin kwanatar mai da hankali da cewa Malam ai wanan zancen bada kai ta ke yi ba don ba kai ka tura su zuwa inda yake ba, Da malam take son tai jayayya kawai shi da ya tura su zuwa can, Huci yayi tare da yin kwaffa mai karfi yace ai kyale ta kawai Bari kawai yace ladi zata gane kuren ta, Don duniya ka shirin bashe ta, ***** ****** ***** Zaune suke adakin su sunyi dadaya sai iran mamaki sukeyi irin yadda suka gani a gurin yayan nasu yau a asibiti, Gulma yakai gulma don har gwada yadda kowa daga cikin su yayi sukeyi suna ta kwasan dariya, Inda kuma suka juya suna sifanta irin yadda Salawatu take yi da taga Abubakar, Muryan shine su,kaji a falo yana kiran samira acikin natsuwa, yake magana, Abinci yake da bukatan ta hado mai don bai iya cin abinci a asibiti, shi,,,, ZEEE MAKAWA YELWA 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 1⃣5⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA ALLAH AL-QUDDUS,,,, KAUNA TA A GAREKU DAGA ALLAH NE,,,,,,,,, BABY ISAH SAFIYA HUGUMA FIDDAUSI SODANG BABY, DEEN MAMAN FARIDA NAFISA HARZAMI Ya kai wani lokaci zaune a falon batare da sanin su ba, Duk zancen da sukeyi a lokacin yayan nasu Abubakar yana sauraron ,su, Bawani zance bane sai zancen wa yan nan bakin matan da suka kawo wa sadiya ziyaran dubiya a asibiti dazun da yamma, A daidai lokacin da yake shirin magana ne yaji muryan da tun fara zancen bata ce komai ba tana cewa, To ke anty Samira may ye abin kushewa a wanan zancen ? Ina dai wa yan nan matan da kike zance akai da sanin yayan mu sukazo, gurin ko Kuma ai yayan mu idan kin kula yai farin cikin zuwan nasu, Don haka kama yayi mu ma muyi farin ciki ga duk wani abinda da dan uwan mu ke son don taya shi, jin dadin abin, Amma ni sai banga wani abin kushewa ba sam ga re su, tunda don dan uwan mu suka zo gurin, Bafa ke ce zaki zauna mai da su ba shike ra,ayin abin shi don haka namu addu,a kawai idan da alheri a ciki, Allah ya,,,,,, Da sauri Aisha ta dakawa Meena tsawa tace Alheri a cikin may fa ? Amma ko dai ke Meena ke bani mamaki kwarai da gaske, Wa yan,ga yan barikin zakiwa yaya Abubakar kwadayin su, Kallon mamaki Meena taiwa yar uwar nata kamar za tai magana sai kuma Mike don kokarin barin dakin don zuwa bayi, ta watsa ruwa har takai kofa sai ta dan juyo tace Ai da ku san cewa ba,kwa son su sai ku,ki karban kudin su da su ka baku, Daga haka tabar dakin zuwa abinda take kokarin yi kai tsaye, Daga gurin da Abubakar yake zaune yana jiyo hiran yan uwan nashi cikin fahintar ko wacen su,,, Huci yayi tare da furzar da iskan dake a bakin shi zuciyar shi na mai suya, tankar ya fada dakin da yaran suke a ciki, ***** ****** ***** Bayan kwana biyu an sallamo matar yayan nasu daga asibiti bayan dan jiyan da tayi saboda ciwon maran dake yawan damun ta akai, akai, idan tana period, Sai dai wanan karon ya fi na kullun matsala shine dalilin kwanciyar ta asibitin, Sosai yaiwa malam tsoho tsaraba don jin dadin wanan tsohon, Wanda ya sha wahala dashi alokacin da yake yaro da kuma lokacin da yake bukatan taimako, Motar ma,aikatar su ce ya dauko don ta mayar mai da yaran da suka zo mai hutu daga gida, Inda yaiwa kowacen su tsaraba daidai gwargwado, Ranan Jumma, da safe sukai shirin tafiya komawa birnin kebbi, da lodin kayan su, Yaso samira ta tsaya da su har zuwa wani lokaci amma fafir tace ita bazata kara zama ba inda tasa mai kuka da tashin hankali, Yana tsaye yana kallon su har suka shiga mota inda Meena ce can baya zaune, Driver ya ja mota suna dagawa yayan nasu hannu cikin bankwana, Bacewar motar su yasa shi sauke ajiyan zuciya cikin sanyi, Ya juya zuwa cikin gidan shi don shirin fita gurin aiki,,, ***** ******* ***** A sai musalin magriba suka isa saboda lalacewan da motar su ta dan yi a hanya, Duk wanda ke gida ko haraban wajen gidan yasan da isowan yan matan gidan, Don hayaniyar yan kannen su tare da sauran yan uwa da ya kaure shiyan, Malam tsoho daga cikin massalacin shi inda ya ke zaune yana jiran lokacin sallah yai murmushi kawai, Don jin dadin Allah ya kawo mai yan jikokin shi gida lafiya, daga sada zumuncin da suka tafi yi gurin dan uwan shi, Duk wani tsaraban da suka iso da shi tun daga kayan su har na sako duk a sashen mama Ladi a ka jibge su, Hand bags din sune kawai kowa ta samu karasawa dashi sashen su, Meena dai sallah ta ga,batar a lokacin, don gudun kada lokaci ya kure mata, Sai da ta tabbatar da cewa, i,zuwa yanzu mutane sun dan rarage a gurin, Sannan ta nufi sashen mama Ladi don ta gaida ita ta dauko kayan ta,,, Hannu Meena rike da yar uwan ta tare da kanin su guda wanda ke binta a bayan ta, Tun dan kwanar da zai sadaka da sashen na mama Ladi zaka iya jiyo muryan ta kamar fada, Sannu a hankali Meena ta karasa gurin inda ta samu anyi dai, dai da kayan cikin da trolley din ta, Ga kuma mahaifiyar murja ita ma a tsaye cikin tujara da nuna masifa a idon ta, A hankali, Meena tace mama sannu da gida mun samay ku, lafiya ? Mama Ladi wace bataji Meena ba alokacin saboda masifan da maman murja ke yi da ita cewa don may zata budewa yara kayan su ta kamar wa yanda sukayo sata, a can, ? Idon Meena ne ya ciciko da hawaye don takaici da bakin ciki a hankali ta duka gurin tana dan tattara kayan ta cikin kunan rai, Duk wani abinda ya danganci abinda aka saya masu a Abuja gefe guda Meena ta ahe wanan abin Inda ta tattara yan kayan ta dama ba wasu shirgi ta tafidasu masu yawa ba don haka tamike tabar gurin Meena na shiga sashen mahaifin ta wanda aka kewaye da dan guntun katangar jan laka, Sai yar rufa ta kara wanda akayi tankar barandan kwano inda suke shan iska, Dakin da take zama da yan uwanta can ta nufa a cikin bacin rai, Kan,nen ta da sukaje tare sune ke fadawa mahaifiyar su cewa mama ladi ta budewa Meena kaya tana bincike ga maman Murja can ta na fada akai, Duk da rayuwan mama Saratu ya baci amma sai ta kan,ne a cikin zuciyar ta kawai, Daga gurin da take tsaye ne take wa yar nata fada akan to may zai bata mata rai har ta,shiga damuwa kamar wace bata san may ake a ciki ba,, Mama ni ba fushi nake akan kayan ba yadda dai mama ta watsar muna da kaya a tsakar gida tana tone tone tankar munyi sata acan, Baba Samaila ne ya shigo gida da murnan shi don ganin yarsa da yake ji da ita ta dawo, gida lafiya, Bakin Baba Samaila har kunne don murna sai,dai kuma a irin halin da ya samu yar nashi a ciki sai murnan ya koma mai ciki, Ladi ladi ladi Allah dai ya shirye ki abinda Baba ya iya furtawa ke nan a lokacin, Ina kike Amina, ? Gani Baba ko Ladi takawo maki kayan nan kada ki fara ki karbe su kin ji ko, To Baba inji Meena cikin sanyin murya ta ansa wa mahaifin nata,,, ***** ****** ***** Mama Ladi bayan ta gama fada da mahaifiyar murja wace tai ma mama Ladi tas, kuma ta dauki kayan yaran ta tafi da shi cikin gori, Sai a lokacin ne idon ta ya bude inda take neman jakar kayan Meena don ta mai da kayan nata ciki, Samira ce ke fada mata cewa ai Meena tazo ta dauki kayan ta ta tafi tun dazun, Idon ya kai gurin kayan da ta,zube kasa wanda dan ta Abubakar ya,sayawa su Meena din, a matsayin tsaraba, Cikin tsawa tace wa Samira ta kwashi English wear takaiwa Meena ta bar mata turamen zannun , Center carpet da sautan kayan da ya aiko wa malam tsoho tana so , asa mata su a cikin daki, Samira tace amma mama yaya fa cewa yayi akawo wa malam tsoho su yasa guda dakin shi guda kuma ya aje a waje gurin da yake bada karatu, Shin wai Samira ke ta kin ka haihwa min mai sunan malam ko niya,? Kayan Meena Samira ta kwasa don ta kaiwa yar uwan nata, Sai dai tana shiga Baba Samaila yace Samira ta koma da kayan tace wa mama a bar su kawai, Meena ta gode don bata cikin ragga,, Samira tana fada,wa mama sakon Baba samaila sai cewa mama tayi mahaukaci kawai, Alluran sojan na ya motsa mai hita batune don rigima shika so, Kaya dai na amshe su bashi kuma da wadda zai yi da ni don dana yai gaba ko , Shehu ya roka muna Allah ya amsa muna, Abinda dawiwa shikai ya kwasa tunda ba shi iya sai mata irin su, Washe gari tun da safe aka tashi da gyaran dakin mama Ladi inda aka shimfida mata carpet din da ta mamaye,,, Sauran sakon mutane kuma sai wanda ta ba don son ran ta, Meenat ko tun daren jiya tasawa kan ta hakkuri akan kayan nata badon komai sai don irin wanan cin fuskan, da mama Ladi tai masu ita da mahaifanta, Don haka ranan shirin komawa sokoto ta yi ni dashi don duk wani abin da za,a bukata na tafiyan ta baba ya shirya mata su tsab, Washegari tun da Safe tabat garin birnin kebbi zuwa Sokoto, A cikin shirin ta ta tafi sallaman malam tsoho wanda a lokacin har yafito majalisar shi ko yana dan kishi gide yana lazimi a hankali Inda yaji sallamar jikan nashi da sauri yadago kai yana kallon ta cikin mamaki, ya ce, Amina badai tahiya zaki yi yau ba da dawowan ki baki ko huta ba, ? Dauri ki bari wani sati ke ga sai ki shi makarantan ko ? Meena wace take kokarin gyara jakar hannun ta don ta durkusa ta gaida tsohon tace, Malam walleh ban tsayi kaga an, wuce ni ga karatu kusan sati biyu ke nan, Me nika tsayawa yi gida in tai in isko notes da yawa, Malam tsoho yadan kada kai cikin jimamyn zancen jikan nashi ya na kokarin tura hannu shi cikin aljihun wando shi Yace to baku kun,katai birnin taraiyya kun kai ,zaman ku ba, ? Hmm inji Meena wace ke duke a gaban tsohon kakan nasu mai farin gemu, Ta,ce malam ko ni an bazama munkayi ba mata tai ta a bata da lahiya shina mun ka tsaya har taji sauki, Subbahanallah halan missa may ta inji malam tsoho ya na tambayan jikan nashi cikin son jin karin bayani, Walleh malam ban sani ba yadda dai niji suna hwadi shi na wai duk wata haka takai, Mika mata kudin da ya ciro daga aljihun shi yakeyi ya fadin i maza ki boye tun yan sa idon ga ba su tai ciki hwada ma uwayen su ba,,, Meena takarba tana cewa ta gode inda tabi umurnin malam tai sauri ta tura kudin cikin jakar hannun ta, Tambayan ta yayi da cewa to Amina an, nan da sokoto shina ki kai wanga sakko haka? Kafin taba da ansa daya daga cikin yan rakiyan ta yaba da ansa da cewa, Don tana son kafin ta shiga makaranta ta dan tsaya gidan uncle din ta, ta, huta,,,,, Tsohuwar motar akori,kura na Baban ta shine za,a kaita tasha daahi suna tafe hayaki na tashi motar na wani kara, booooooooooo,,,,, ***** ****** ***** Lokacin da duk ake wanan zancen Baba Buhari baya gari sai da ya dawo ne ya samu labari gurin kishiyar mama Ladi din, A cikin bacin rai ya nufi gurin da mama Ladi take a bakin murhu tana tankaden garin dawa na tuwo ga karkashi a gefe guda wanda ta gama gyarawa zatai miya dashi,,,,, Ladi, ke wace irin mahaukaciyan mata ce wai, Shin ko kauyan cina har yanzu ka cin ki na ladi ko rashin mutunci irin naku Ginbanawa ka da mun ki, Sai a lokacin mama Ladi ta dago kai ita ma a cikin masifa take don ta riga ta shirya akan wanan zancen , Don bazata dauki wanan rainin ba a dinga zuwa cin arzikin Dan ta kai tsaye, Ita kan sam ba zata yarda da hakan ba sai dai duk wani sako ko aike yazo ta gurin ta direct ki kuma taba wanda ranta ke so,,, Malam shin sau nawa kake son in fada maka cewa Dan ga dai dana ne ba wani na ya haifa min shi ba,, Sakona ina so don haka sai a jira wani ko ? Takare she zancen cikin muguda baki irin na mata kauye, Tare da dukawa gurin murhun ta don ci gaba da aikin girkin da takeyi, Tsaye Baba Buhari ya yi cike da mamakin irin wanan karfin halin na mama Ladi da kuma rashin kunya, Ya san cewa idan ya tanka a lokacin za, ayi batatta don haka ya juya direct zuwa gurin mahaifin shi, Don ya sanar dashi saboda malam tsoho yai ma duk diyan shi shamaki akan saurin daukan mataki ga iyalin su,,,, ****** ******* ****** Anty Meena oyoyo Anty Meena oyoyo yaran gidan uncle ke wanan ihun lokacin da mai yar besfa ya aje Meena da kayan ta a kofan gidan su dake a cikin Sama,Road, Ihun yaran ne yasa iyayen su gane cewa Meena tadawo Meena sarkin aiki ga tsabta da iya girki, Haka matan gidan na uncle din ta ke ce mata, a duk lokacin da ta tsiri yin wani aiki,,, Anty Amarya wace itace tafi bawa Meena fuska agidan ta kwaso da saurin ta daga dakin ta cikin farin cikj da ganin Meena din, Ja tayi ta tsaya a daidai lokacin da sukai kicibis da Meenatun a kofan shigowa falon su, Meena wace ta duka tana daukan dan karamin dan Anty amarya wanda yaga meena yake murmushin nuna yasan ta fa, Shin Meenatu ba dai mai kin kafara shafawa ba ko ? Meena wace ta ji maganar uwar dakin ta kamar a mafarki tai saurin dagowa cikin dariya tana cewa, A, a,a wallah anty mikaini ? Ke koga yadda kin ka koma Meenatu an ? Dariya Meena tayi don jin zolayan da amaryan uncle din nata ke mata, Sai a lokacin uwar gidan wace ke zaune tun shigowan Meena din saman dining table tana shan abu a cup tai magana, Walleh Meeana an duk ke canza kamar ba ke ta ba, ? Ko mummy ? Inji Meena din wace ke ta faman murmushi saboda jin dadin ganin yan uwan ta, Gaskiya inba, don gida gida bane da sai tace nan gidan uncle din ta yafi mata dadin zama don ba wani sa ido ko tsangwama a gidan Ba kamar gidan su ba da duk abinda mutum keyi idon mutane na gare shi,,,,,,, ZEEE MAKAWA YELWA 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸 1⃣6⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA ALLAH- AS-SALAAM,,,,,, Baba Buhari ne zaune a gaban mahaifin shi malam tsoho, inda yake koro mai duk yadda al,amuran da suka faru, akayi, Malam tsoho sai faman kada kai ya ke yi don mamaki koda yake bai dauki sarakuwan nashi cikin mutanen kirki ba dama, Tun farko bai ra,ayin ta sam da dan nashi abudai ne in yaro yace yana ra,ayi sai a kyaleshi yayi, Ina kake malami Naam Baba ya ansa wa mahaifin nashi a cikin ladabi, Katai kayi hakkuri kajiya ? Halin Ladi sai ita,, To amma Baba , Hannu malam tsoho ya daga mai alaman ya isa haka nan, Shiru Baba buhari yayi a vikin biyayya yanà mai dukar da kan shi a lokacin, Magana gudane shine kayan yatinyar ga Aminatu wanda an,kan ansa, Hakan baiyi dadi ba sam wallahi sai dai kawai ayi hakkuri abar zancen, Shi kuma Samaila zan ganshi in mai magana don kada ya dauki abin da zafi a ran shi, To amma yarinyar ga Aminatu yau ta koma makaranta sam banga wani bacin rai a tare da ita ba, Baba ai kasan yarinyar yarinyar kirki ce ba zata taba nunawa ba,, Amma zanga sauran abokan tafiyan nata don inji ko may yafaru acan gidan dan naka, Saboda naji cewa wai matar, mai suna batada lafiya, Baba shima cikin mamaki ya tambaya, ya ce, may ke damun ta, Bari dai mu bincika a hankali, Kasan matar taka bata da kwanciyar hankali balle a ce, ayi zancen kai tsaye, Hakane Baba inji Baba buhari ya ba mahaifin shi ansa atakaice, Cikin kwantar da harshe Baba buhari ya ce, to baba Su wa yan nan kayan na wurin ka fada ta mamaye yaya za,ayi da su? Cikin sauri malam tsoho ya ce, kai, kai dama ai wanan kayan yara ne kabar mata kawai Allah sa albarka kaji, To ,Baba inji Baba buhari ya ansa acikin ladabi, ****** ****** ****** Wanan labarin da yazo ma Abubakar yai matukar bata mashi rayuwa, sosai Ya dade yana tambayar Baba Wadda wanda ya bugo mai waya yana sheda mai abinda ke faruwa, Sam baji dadin jin wai mama ta karbe kayan yar gurin kanin mahaifin shi, Yariyar da duk kusan zaman su a gurin shi ya na hankalce da cewa ita ce mafi wahala agidan, nashi, Amma sai gashi wai ita ce kuma mama ta karbewa kayan, Ba komai kamar yadda yai wa Baba wadda alkawarin zai aikowa Baba samaila da wani abu don ya dan rage zafi,,,, Kiran Salawatu ce ya,shigo a wayan shi abinda ya dan washe mai zuciya ke nan, Daukar wayan yayi a cikin jin dadi yana mai cewa ya akayi ne Salawa, kamar yadda yakan kirata Cikin lumshe ido don jin dadin sautin muryan dan matashin da tayi tace, Babu komai Sir na dai kiraka ne kawai don inji muryan ka, Tooooo, fa inji Abubakar din wanda ya fadi haka acikin yar dariya da nuna mamaki, Cikin lumshe ido yace ni har na isa babban yarinya kamar ki, ki ce kina son jin murya na, Sir ai har ka wuce hakan a gurina, Tau na gode inji Abubakar ya fadi haka a cikin jin dadi da nuna kulawa, ****** ******* ****** Aisha wace ke zaune kusa da kakan ta wace ya turawa kwalban zuma da tazo roko gurin shi wai zataci masa dashi, Malam tsoho yace wai ke Aisha, may matar yayan naku ta bakune haka kowan ku yai kiba da haske haka,? Da sauri Aisha ta dago kai cikin jin mamakin maganar kakanta, Ta ce malam muka dai bawa kan mu ko ? Matar da bata iya ko da kula da kanta ba balle wani, Ai in fada maka malam wanan matar sam wallahi bata dace da yaya Abubakar ba, Malam ya dauko mata wani guntun kilishi a leda wanda yaji kuli kuli, da yaji yace karbi wanan, Karki tashi ki zauna sai kin cinye don kar ki fita dashi wani yagani gashi iyakar shi ke nan, Nan Aisha ta samu guri tafara yagan kilishi a hankali, Malam tsoho yace to shi yayan na ku may yake ci da bata girki, Samira tace wai sayowa yakeyi ko kuma ita samiran ta dafa amma yace wai ba dadi girkin Samira, Shine da muka tafi kasan halin Meena da son aiki itace ta kirkiro muna girki da sauran aiyuka har mukeyi, Malam yace toshi yayan naku yana ci ko ? Ta ce malam cikindago kai tare da tsaida cin kilishin ta tace sosai ma har fa da cefanai yake yo,wa daga baya, sai mu girka, Kai malam tsoho ya kada, don al,ajabi ace wai mace bata girki a gidan ta, Bai kai ga karasa tunanen shi ba sai yaji muryan Aisha tana cewa, Wallahi, malam yaya Abubakar sam bai yi sa,an mata ba, Ga mace wata iri ba fasali ba zuben suffan mata ko kadan,, Wai ma malam baka san wani abuba yanzun haka wata tsohuwar yar bariki tana nan ta lakewa yaya Abubakar gam, kamar chewing gun, Gaban malam ne ya fadi don jin sabon masifan da ke shirin kara bullowa jikan nashi, Ya na tunanen yadda zai bullowa zancen Sadiya sai kuma ga wani sabon zance anzo mai da shi, Gaskiya dole ne yasan abin yi akai, Bazai hana shi aure ba amma yar kirki yar asali wace ta fito daga zuria mai mutunci, To amma shi Abubakar din yana ra,ayin ita matar da ki kace yanzu din ? Daidai lokacin da Aisha ke kokarin tura kilishin karshe abaki tace, Malam matar fa mai kudi ce, don ko da zamu dawo dubu ashirin taba mu sabbi fill da su, Wani iri malam ya ji amma afili sai cewa yayi Allah ya kyauta kawai,,, ****** ****** ****** Meenat yanzu tun zuwan ta Abuja ta canza kamar da ga irin yadda take a da don yanzu komai nata na siffan manyan matane, Amma a bangaren ta sam ita bata san da wanan girman da canza kama, da ake mata ikirarin tayi, Hutun meet time break suka samu don haka ta dawo gidan uncle din ta don birnin kebbi yai mata nisa, Sun samu Anty amarya suna shagalin buki a gidan su inda kaunar ta ke aure, Hakan yasa yan gidan su uncle gaba daya banda mummy wacce ke tsayawa gida suke halarta wanan bukin, Sosai anty Amarya taji dafin zuwan Meena a wanan lokacin don ko ba komai zata kula mata da yaran ta ai, a gurin, Duk da ba wani sutura mai tsada ke ga Meena ba hakan bai hana ta fitowa cas a gurin bukin ba, Ya wancin yan uwan anty amarya sun san da zaman mina agidan uncle don a tare suke da anty amaryan, Hakan yasa a yanzu da tazo cikin su bata zama wata bakuwa ba, Wata sister su anty amarya da tazo daga Kaduna tana kwance saman gado ta hakince, Alokacin Meena ta shigo dakin dauke da jakar kayan da ta can,zawa salim dan wurin anty amarya, Matar anty Zainab tace Fatima wai ina kika samu wanan yar kyakyawan buduruwar ce haka ? Anty amarya tadan kalli gurin da Meena ta ke tana zuge zip din jakar tace wallahi diyar Nafi,u ne , Yarinyar senior sister di shi ce daga kebbi take tazo karatune nan sokoto, Kai amma gaskiya akwai mace a wanan gurin wallahi, Ke zaki auri yaro na,? Dariya akasawa matar duk dakin don jin abinda tace, A lokacin Meena take kokarin fita daga dakin, Amma sai Anty Zainab din tace tsaya mana yan mata ba wasa nakeyi ba, Wata daga cikin matan dake dakin tace wani yaro naki badai Amir ba, Kai haba wane Amur da wana ai tai ma Amur girma sosai, Ina da yaro faruk dan yayan Man ne yazo daga chadi,,, 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 1⃣7⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA, ALLAH- AL- MU,MIN Casbi ya ke ja a zahiri amma azuciyar shi tunane acikin fam, Daga kishingide yake kwance inda ya mimike kafan shi, Yai makari da kafadan shi na dama hannayen nashi sai jan casbin suke yi, Idon shi a lumshe suke bakin shine kawai ke motsi, Hakan kawai ne mutun zai gane cewa ba barci ya keyi ba a lokacin, Baba Wadda ne yai salma a lokacin cikin girmamawa ya kai durkushe yana gaida mahaifin na shi, Idon shi ya bude ya na kallon dan autan nashi kamar mai nazarin wani abu, Sai ya furta sunan shi a hankali, Wadda mun,kwan lahiya, ? Cikin dukar da kai Wadda yace lahiya lau Baba, A,a dare da jama,a ? Wallahi duk lahiya lau Wadda an, Mikewa Baba Wadda yai niyar yi don tafiya wurin tsabagar gaban shi, Amma sai ya ji murya mahaifin nashi na cewa yaka Wadda ne mi guri kazauna dama ina son ganin ka na, Gaban Baba Wadda ne ya fadi don shi a zaton shi yaiwa malam tsoho mahaifin shi wani laifi ne, Amma sai yaji mahaifin nashi nacewa da ma tambayan ka na naka son yi, Akan iyalin Abubakar can wajen su ? Cikin mamaki Wadda ya dago kai don tunanen may tsohon ke son ji akan iyalin yaron yayan nashi , Tambayar da malam ya watso mai sune suka dakatar mai da tunanen nashi, Shin Wadda wai a,a kka ga zaman mai, suna na da matar shi ne, Yaran ga na da sun ka dawo , sun ka hwada min cewa wai, Zaman takwarana da maidakin shi sam babu dadi, ? Shin ,a,a, zance shike na ? Shin gaskiya na su,kai ko ko a,a na ? Zama Baba Wadda ya gyara da kyau inda ya fuskanci mahaifin nashi yace, To walleh maganar gaskiya ita, ta haka zancen shike, Don dai duk wani kulawa wanda ankasan mata da shiya, Sam wanan macen batayi, Kai baba ingajarce ma walleh zaune dai take dusha da ita kamar wata gwakyanya,, Malam Manya wanda rayuwar shi ta baci matuka, Kai kawai ya iya gyadawa a lokacin tare da cewa jeka dai Wadda am na gode, Ya mike yana cewa mahaifin nashi mu yini lahiya ba, Allah shiba da sa,a da rabo na alheri, inji tsohon wanda duk yaron da yazo sallaman shi don zuwa gurin aiki, ko wani harka, hakana suke samun wanan adduan daga bakin shi, Wanda su kuma al,umman gidan wanan adduan na masu dadi don ko fita za su yi za kaji yara na cewa mu je gurin baba neman tubarki,,,, ****** ******* ****** Shakuwa mai karfi ne ya shiga tsakanin Abubakar da Salawatu zuwa yanzu, Shakuwar da har takai dan uwa idan baiga dan uwa ba zai iya shiga damuwa sosai, Kusan zuwa yanzu mutane sun san wanan alakar dake tsakanin Abubakar da salawatu din, Abu guda,ne shine Abubakar bai iya aikata alfasha a waje ba sam , Don duk yadda salawatu ke kokarin gwada mai hanyan lalacewa sai ya nuna mata tankar bai bahince ta ba, Haka yasa tafara shiga cikin halin damuwa saboda tana ganin cewa ba zata iya samun abin da take so ba, Don dai a zaton ta na ganin cewa, Abubakar ba zai taba auren ta, ba, Hakan ne ya kara tayar mata da hankali sosai, har ta fara shawaran shiga malaman Abuja,, Ranan da ta fara zuwa gurin malamin ta don ai mata aiki, Tun kafin akai ga aikin da ta bayar din ai mata sai ga dan halas din na cewa,,, A lokacin da suka kama hanya don zuwa gida bayan sun tashi daga gurin aiki, Abubakar wanda ke tuki tankar yana tsoron sitiyarin motar Fuskan shi na kallon titi inda kira,a ke tashi daga cikin motar nashi, Salawa ya kira sunan a cikin wani irin shaukin so da kulawa, Itama amsawa tayi batare da ta kalle shi ba cikin wani yanayi, Tambayar bazata ne ya jefo mata alokacin da cewa, When are we getting, marriage ? Sai da Salawata gigice don jin wanan tambayan da Abubakar ya jefo ta dashi,,, Hannu takai ga gaban ta tana kokarin nuna kan ta da yar yatsar hannun ta alamar ita, ? Yake nufi, da zancen aure, Kai Abubakar ya kada cikin nuna alamar eh yana mai lumshe mata idon shi masu kama da yana jin laziness, Yau don jin dadi Salawatu bata iya cewa Sir din ba sai cewa tayi Abubakar kana nufin zaka iya aure na, ? yanzu haka ? Yes, Of course May ya yasa kike mamaki ko zan iya auren ki ? Sai a lokacin ta dan hada natsuwan ta a guri daya san nan ta dan kalle shi acikin kunya tace, Naga most of the hausa fulani Guy's basa aure haka a waje da wuri, Sai dai su yi a gida a cikin dangi, Waya fada maki hakane ? Kawai a kwai dalilin da yasa mutane su kafi yin aure a garin su,,, Wani dadi har acikin ranta ya ratsa ta don hakan ta ya kusa cin ma ruwa ke nan, very soon, So daga yau ina fatan zaki zauna a cikin shiri don any time aure zai iya zuwa, Kunya taji don jin zancen shi don haka sai ta dan dukar da kai tana wasa da ya tsun hannun ta Jin tayi shiru yasa Abubakar kara jefo mata tambaya da cewa ko Ban isa in aje irin wanan madam din a gidana bane ? Kai haba Sir wace ni da zance ma haka ? Kawai dai ban san bakin da zanyi ma godiyan hakan da shi bane, Ki aje wanan godiyan naki har ki shigo hannu na ina ga zai fi ai, Dariya da yar kunya ya bata wanda ya sa ta saurin rufe,fuskan ta da hannun, ta ,,,,,,,, ****** ******* ****** Zaune suke a saman wani katon tabarman kaba,mai mai ruwan kala,kala, Duk da yake zuwa yanzu sama sama suke da junan su ba kamar da ba da suke kut, da kut, Mama Ladi wace ta wanko takalman ta har zuwa gidan Hajja din don su tatauna akan yaran nasu ma,auratan juna, Mama Ladi din ke cewa Hajja gani nayi ya kamata ace mun san abin yi akan yaran nan haka kafin idan mu dangin uban shi masu tsurku su fara tofa miyon su akan abin da bai shafe su ba, Don ke ga matan yaron ga dan wurin shaibu gashi ammare, jiya, jiya ga ciki Allah ya basuwa ankai ga ribar ammare, Kai ke ji min Ladi da wata magana shin cikin ga ni ka basuwa ko Allah ka basuwa, ? Da zaki taho na, nanga da wata magana mara dadin sauraro, Walleh da nasan cewa wagga magana ta at, tahe dake da ban tsaya sauraronki ba,, Shin Hajja maganan ga da na taho da ita ba maganan da aka zama adubata ta ba ? Ammre shekara kusan shidda ace ba wani karuwa acikinai ? Gaskiya nikan na hwara shiga maganar da nikawa mutane ruhwa ruhwa, (rufa,rufa) akanta Don yanzu banda abin cewa in ana wagga zancen a gabana, Abin da kashrin faruwa ne nazo maki akan zancen shi, To ba sai ki tai ke da mutanen gidan naku kuyi abinda Allah bai tashi yi ba,,,, Mama Ladi , wace bata taba data sani ada na hada auren da tayi tsakanin dan ta da diyar Hajja din, Auren da yanzu ta ke jin dan wani iri akan shi duk da dai duk sallah ko azumi sai Hajja ta kawo mata, garan sallah gudan mai yawa, Duk da ba aikawa wasu Abubakar din takeyi da kayan ba, Kayan garan kamar su shinkafa, mangyada manja maggi gishiri dadawa, gero da masara, duk a matsayin garan sallah wa yar ta sadiya,,,,, ****** ******* ****** Kusan dangin Anty amarya duk sun san Meena yar albarka kamar yadda suka lakaka mata sunan, Meena yatinya ce mara girman kai ga aiki ga sanin ya kamata, ga girmama na gaban ta, duk yadda yake, Wanan halin ne ya jawo mata samun farin jini da kuma alheri ga yan zurian, su anty amaryan,din, Gama secondary din ta uncle din ta ya samo mata guribin cigaba a Shehu shagari, COE, Ba bata lokaci Meena ta fara karatun hankali kwance, Hakan ne ya jawo mata rashin zuwa gida birnin kebbi a kai,akai, Yanzu takan dauki lokaci mai tsawo batare da ta je ziyara gida ba, Badon komai ba sai don gudun irin hassadan da mama ladi ke yawan gwada masu ita da iyayenta a fili karara,, Ga habaici da suke mata wai bata isa ace ta kare, karatun ta ba shi ne za,ace takai har gaba da secondary, Wanan abin da mutanen gidan su ke ya,wan nuna mata idan ta je kebbi din shi yasa sam yanzu bata faye son zuwa can din ba , Sai dai in dogon hutu a,kasamu zata iya zuwa tayi kusan rabin shi a can din, Zuwa yanzu da girma yazo mata har yakai Meena ta fahinci irin kiyayyan da mutanen gidan su ke nuna ma mahaifanta, Tagane cewa kishine kawai irin na matan hausa ba komai bane sai yan ubanci, Saboda mahaifin ta ya kasance shi daban ne daga shi sai gwagon su wace ke aure, a kalgo, Wanan dalilin ne kawai ya jawo wa, masu bakin jini harsu, Acewan mutanen gidan wai malam bai taba auren macen da yake so kamar kakan su Meena ba sai kuma Allah bai mata tsowon rai ba ta rasu,,,,, Jin wanan dalilin yasa Meena tafara kenkeshe idon ta ga duk wani mai kawowa iyayyen ta suka da sara akan rayuwan su,,, Zaune take a gaban mirror dakin Anty amarya tana kwalliya don yau ba kara tu Abdulhamed saurayin ta zaizo kawo mata ziyara kamar yadda yai alkawari zuwa, Tsab tafito cikin wani dinkin atamfa masu ruwan blue da ratsin fari ajikinsu, Dinkin buje da riga ne akai masu wanda ya fitar mata da surar ta tsab, Ita kanta ta yaba da wanan kwalliyan da tayi don sai take gani kamar ba ita bace Meena diyan gidan baba Samaila, Anty Amarya ce ta shigo dakin tana cewa, a,a a shin wata,ta an nan,? (Wacece nan haka) ? Murmushi Meena tayi alokacin da take kokarin dauko zumbodeden hijab din ta fari don ta sa, Shin me zakiyi kuma da wanga hijaba,? Makin kisa gyale don kara fito da ke shar shar da ke ya, A,a inji Meena walleh anty am ban iya fita dashi ko nan da kofan gida da gyale,, Don ji nike awa ban rufe jikina ba sam kamar haka na nake tafiya, Ke kinka sani da halinku na diyan gidan malamai, Murmushi meena tayi alokacin da take zumbuda hijabin nata, a wuyan ta, Zaune yake a cikin motar shi kafa guda waje yana dan dane danen a motar, Assalamu Alaikum tace acikin muryan ta mai kama da busa sarwan sharo, Firgigit Abduhamed yadawo daga abinda yake yi amotar inda ya dago kai da murmushi yace, Ameen wa alaikis salam giyabata, Yar murmushi Meena ta sake cikin jin dadi tana cewa karaso mana daga can waje, A,a Meena ai nan ma yai min ki zagayo ki shiga mota kawai ki zauna ko ? Kai ta girgiza mai alamar a,a tana cewa ai na fada ma ba darajata bane shiga mota yin hira, Murmushi Abdull din yayi don sanin irin ba,hagon halin meena don dai ita kulun takar mutumiyar da take, Bata taba nuna waye wa ga al,amarin ta sam, Sai dai ta nuna gidadanci, Ok tunda hakakike so ba matsala ai barin fito mutafi can din, Kafin duk yafito a motar har meena ta juya da sauri ta nufi gurin don gudun kada ta ya ga tafiyan ta, Murmushi Abdullahameed din yayi don ya gane nufin Meena din, Nisa kadan ta zauna akan saman tabarman da ta shimfida mai, Inda take wasa da dan wani kara a hannun ta, ****** ******* ****** Shiri sosai Abubakar keyi wa wanan tafiyan dake gaban shi don a kwai abubuwa da dama da yake kokarin yi idan yaje, Saboda kasancewar shi na wanda ya dade bai zo gida ba sai dai yayo aike kawai ga wanda Allah ya ba rabo, Ga labarin da yan uwa ke ji akan shi cewa yazama wani irin baba a ma,aikatar su, matsala dai guda ne rashin kula gida da yan uwa da baiyi, Yasan cewa idan yazo zasu kwashi rikici da dan tsohon kakan nashi sosai don dai yasan cewa shi mai laifine sosai agaresu, Ga kuma sabon zancen auren da zai zo masu dashi don su tafi agabatar da komai acan kauyen salawatu dake cikin jahar nasarawa,,,, ZEEE MAKAWA YELWA [7/13, 07:17] Anty Lantana: 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 1⃣8⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA,, ALLAH-AL-MUHAYMIN,,, Tuki yake a cikin natsuwa, da gwanin ta, sai dai hankalin shi na ga irin yadda zai tunkari mahaifan shi da zancen karin auren da yake son yi, Musanman mahaifiyar shi mama Ladi wace yake gani tankar tama fi son matar shi Sadiya sama da shi, Hannun shi ya daga guda ya shafo kyakyawan fuskan shi dashi tare da sauke ajiyan zuciya mai karfi, Abubakar Buhari Birnin Kebbi kenan kyakyawan matashi mai,tashe ga kyau ga ilimi, ga Naira ,,,, Daidai kofan gidan su inda malam tsoho kakan shi, da jama,ar sa suke zaune suka daukan karatun marance, Duk wanda ke gurin a lokacin idon shi naga wanan kyakyawan bakar motar da ta tsaya a kofan gidan dattijon malamin, Sannu a hankali ya bude motar inda ya sako kafar shi guda waje yana kokarin dauko wayoyin shi daga gaban motar, Kafar shi kawai ya isawa wanda ke gurin ko waye zai fito a motar mai, ji da kansa ne, Fitowar shi daga motar gaba daya yasa mutanen dake gurin gane cewa ai Abubakar ne, watau (mai sunan Malam), Ai nsn take mutane suka gane cewa shi ne kusan gaba daya suka tashi zuwa mashi murnan da barka da zuwa,,, Malam tsoho wanda ke daga zaune yana biya wa wani tsohon bafillace karatu, Sai murmushi yake yi yana gyada kai don jin dadin ganin yadda jikan nashi ya koma a lokaci guda, Direct daga gurin da masu taron shi suke, gurin tsohon ya nufa, Takalman da ke a kafan shi yake kokarin cirewa don girmamawa, Wanan ya,na daya daga cikin dabi,un duk, wani yaron gidan malam Manya, Babba da karami dole ne idan zaka wuce ta gurin ka cire takalmin ka, Cikin jin dadin ganin jikan nashi bai yarda tarbiyan gida ba, Yake dan yake fararen hakoran shi wanda akasarin jikokin gida duk shi suka biyo, da fararen hakora, da kyau, Abubakar kai ne tafe babu labatin zuwan ka a yau din,? Murmushi yayi ya cewa kakan nashi nayi marmarin ganin ka ne malam shi yasa na taso don in duba ka, Nan ya samu gefen tabarman da malam din yake, zaune, Gaisawa sukayi a cikin girmamawa, inda malam yace ai sauri a shiga gida wurin maman Wadda a karbo ma Abubakar ruwa da fura,mai sanyi, Ga mamakinbmalam tsoho sai ga Abubakar ya sha kusan rabin kufin furan da aka kawo mashi, Wani sabon gaisawa suka kara shiga yi inda yake tambayan shi lafiyan mai dakin shi da kuma gurin aikin shi,,, ****** ****** ****** A can cikin gida kuwa labarin zuwan Abubakar ya iske mama Ladi wace duk ta kasa boye farin cikin ta afili, Sai, rawan jiki ta,keyi tana cewa a yi sauri a aje a anso mata dan drinks ta bashi da kuma sakon abin miya wanda zata dafa mai abinci, Duk da idan yazo daga ko wani sashe na gidan a na kawo mashi abinci, har izuwa ranan da ya tashi komawa, Amma duk wanan bai sa mama Ladi ta daina dafa mai abinci da kanta,ba idan yazo, Da sauri ta tura yaro gidan su Sadiya matar shi gurin Hajja don a sanar da ita, Hajja tabawa yaron Naira hamsi wai ya sha Sweet da shi idan ya koma, Yaro ya koma da murnan shi gida ya na, farin ciki, Bai nuwa mama Ladi Naira hamsin din ba don yasan idan ya nuna mata zata iya cewa suraba shi da ita, Sai bayan Sallah isha,i Abubakar ya shigo cikin gidan don ya gaisa da mahaifiyar shi da sauran, mutanen gidan, Nan fa yai ido biyu da jerin kwanonin abincin da aka aiko mai da shi daga kowa shiya na gidan A hankali ya samu gefen tabarman da aka shimfida mai,a tsakar dakin na mama,Ladi ya ksi zaune, Cikin murna da farin cikin ganin dan nata take cewa, Mai sunan malam kana tafe shine baka sanar da kowa cewa kana saman hanya ba, Sai dai kawai mu ka gan ka kwatsam ba tsanmanin ka a yau din, Murmushi yayi don yasan cewa duk a lokacin da mama ta ganshi tana cikin farin ciki da jin dadi, Shima haka yana jin dadin kasan cewa mahaifiyar tashi sosai duk yasan cewa wasu daga cikin halaiyan mama tun suna yara baida dadi sam, Tambayar shi mama tayi labarin matar shi Sadiya, Tana cewa har yanzu dai shiru a gidan ka mai sunan malam ? A hankali ya dago kai ya dube mahaifiyar wace ta tsura mashi ido don jin ansar da zai bata,, Yadda ya kalli mama sai ya bata tausayi don ko bai yi magana ba tasan cewa ba wani ansa gamsasshe daga bakin shi, Murmushi ya danyi tare da cewa mama har yanzu dai muna baran adduan ku , Akan Allah ya kawao muna mai albarka insha Allah, Daga haka Abubakar yajawo daya daga cikin kulolin abincinbdake a gaban shi wanda yasan cewa,shi aka ajewa wanan abincin, Mama dake gefe tace cikin sauri a,a aida ka dakata har a karasa abincin da nasa Samira ta dafa maka,,, No, mama ki barshi kawai wanan din ma ai is Ok, Kawai dai dama ina son cin abincin gida ne wanda nai missing dadewa, Kai idon mama taga ko wani kulane yajawo sai idon ta ya sauka akan kulan da mama Saratu ta aiko mai dasu,,, Kai, mai sunan malam ga kuloli da yawa masu dadi zakaci wanan ? Yace cikin kai hannu ga kulan da ya bude din yana cewa, Wanan din ma ai zai yi mama bari kawai inci, don bada yawa zanci ba, Tuwon dawa, surfafe ne, da miyar karkashi danye, wanda yaji nama da man shanu, Fuska mama ta daure don jin haushin daukan kulan sashen Baba buhari da yayi, Daga sunan kadan zaici sai ga Abubakar ya buge fiye da rabin kulan abincin, Ganin irin yadda ya kwashi wanan girkin da mama ke dauka mara dadi, agare ta, Wanan girkin yaiwa Abubakar dadi sosai don rabo da yaci irin wanan girkin tun yana yawan zuwa gida hutu daga makaranta Wayar shi ce tai kuka, wanda hakan ce ta da katar dashi daga cin abincin da yake yi,, Yadaga don ganin mai kiran nashi a wanan lokacin da yake kwasan girki mai dadi, Salawatu ce ke kiran shi a lokacin don haka ya dauki wayan a cikin murmusawa, Mikewa yayi tare da kallon gurin da mama take zaune tana mai kallon kurulla, Tun a gaban ta ya dauki, wayan sai dai a cikin harshen turanci yake magana,, Don haka mama wace bataji may yake cewa ba sai bin bayan shi tayi da kallo kawai, Amna dai gabanta ya fadi don hasashen da zuciyar ta yai mata akancewa Abubakar da wata mace yake zance, fa, Idan ko hakane gaskiya za a dauko wani sabon zance ke nan agidan, Don tasan cewa da yawa daga cikin yan uwanshi dama uban,nen su zasuyi farin ciki da wanan abin,,,, ****** ****** ****** Zaune take da tarin littatafai a gaban ta tana dubawa, Kanta yana dan saye da farin gyale wanda ta dan yane fuskanta da shi, Bitan littafan ta takeyi saboda , jarrabawan su da ke kara gabatowa, Don haka tai matukar mai da hankalinta akan karatun ta yanzu, Shigowan shi kenan gidan ya hango Meena zaune gurin da take bitan karatun ta, Ya fi tsayin yan mintuna tsaye agurin yana kallon wanan yarinyar, Ko kifta, idanuwansa ba ya yi farat daya yaji son ta da kaunar ta sun shige mai zuciya, Kai tsaye yaji zuciyan shi na bashi shawaran ya tunkare ta don ya ji ita ko wacece, Kamar kuma ya juya zuwa inda zashi bangaren yayan nashi sai ya ji sam bazai iya ba, Sabosa haka gadan gadan ya cike da karfin zuciya ya nufi inda take, Meen wace take duke , Zuciyan ta ya bata cewa tankar akwai wani mutum tsaye a kanta a lokacin, Daidai wanan lokacin ne ta tsinkayi muryan shi yana mata sallama, A dan firgice ta kara dagowa da sauri tana kallon shi Daga gurin da yake a tsaye ya zura hannayen shi duk biyu acikin aljihun wandon shi, Idon shi a cikin nata yake cewa kiyi hakkuri pls don naga kamar nadakatar dake daga karatun ki,, Cikin maganar da yake yi ne ya tako izuwa gare ta, Gap da inda take zaune ya karaso, inda har Meena zata iya dan jin hucin shi, Mamakine kwarai ya kama Meenat din don haka ta kasa ko da wani kwakwaran motsi don fargaba, Don dai ita asanin ta ga bakin dake zuwa gidan uncle din ta ba, Ganin kamar ba zai iya dakatawa a inda yake ba yasa Meena tai saurin mikewa don barin gurin, Muryan shi taji cikin wani irin yanayi yana cewa Kiwa Allah da son manzon tsira ki dan bani minti biyu pls, Cikin rintse ido da jin abinda bakon yace ta tsaya agurin da take, Muryan shi takara ji a karo na biyu yana cewa don Allah a nan gidan kike da zama ne ? Da sauri Meena ta dago kai ta dube shi ta ce, a hankali, "Eh, Ya kara gyara tsayin shi yace to amma ban sankiba beauty ? Beauty kuma inji Meena ? Cikin wani irin daga gira irin na mazauna kasan turai ya ce yes beauty, mana, Kin ko gan ki kuwa, takar ke ce kika halitta kan ki, A fusace Meena dake zaune tun shigowar shi ta mike tsaye, Fuskan ta a daure tankar bata taba dariya ba a rayuwanta, Rayuwan ta yai mata bakikirin a take idanuwan Meena suka kada, zuwa ja, do yazuba mata still yana kallon irin yanayin da ta sauya atake, Cikin dakewan murya Meena tace wani ne ya aiko ka ka tambaye ni, ko ? Cikin murmushi yace mata kinga nayi kama da wanda za,a aiko ? Kanta kawar gefe guda daniyar ta dan gezashi ta wuce abinta, Gyalen kan tane ya dan silalo daga saman kanta zuwa kafadar ta, A take gashin kan ta dake daure da wani ribbon ya baiyyana a fili Wani iri ya na yi ya shiga cikin dan lokaci kadan, Sai tsayawa ya yi yana mai kara kallon wanan yar matashiyàr budurwa da idon shi ya ga nan mai, Ganin zata wuce ne ya iya bude bakin shi yace ,,,,,, Iam ALI-ABBAS, MAHMUD, KA,OJE, Cikin wani irin kallo Meena ke kallon shi don jin Mahmud din daya ambata, Tasan cewa daga family din nasu yafito saboda su fulanin Ka,oje ne, ma,zauna sokoto, Daga haka Meena ta dan gwauta shi ta wuce abin,ta Kamshin turaren jikin ta da ta shafa, black s,s ya shaka, A hankali ya dan lumshe, idon shi, don kamshin yai mai dadi so sai, har cikin ran shi, Part din da take na Anty amarya can tanufa inda ta,samu babu kowa a,dakin nasu na yara,, Sunan Ali,Abbas take nanatawa a zuciyan ta tankar mai mamakin sunan, Hayaniya taji a falo hakan ne ya bata tabbacin cewa masu gidan sun dawo ke nan daga unguwar da suka fita, Sai kuma ihun da taji duk ya gauraye falon da gidan alokaci guda, Fitowa Meena tayi don tai masu sannu da zuwa da kuma ganin may sukewa ihu haka ? Daidai gurin da ta tashi a nan wanan bakon yake zaune ga dan hankicin ta da tabari da sauran takardun ta a hannun shi, Ido suka hada daga fitowan ta wanda hakan yai daidai da kai hankicin ta a hancin shi yana dan shaka tankar mai mura, Wani irin shu,umin murmushi ya sauke mata a lokaci guda, Wanda tai tankar bata fahince shi ba sai cewa tayi a kasalance mummy sannun ku da dawowa, Mummy wace ke ta murnan ganin dan kanin nata a lokacin sun kaure da harshen fulanci, Tankar ba shi ne dan gayen da zaka ce banda turanci bai iya komai ba abakin sa, Mummy tace yawa, Meena sannu ko don Allah ki taimaka ki hadowa bakona drinks da abinci pls, Hannu ya daga cikin muryan nan nashi maikama da sallo ya ce, No ki barshi kawai ki bani cool water in dan sha pls, ? A hankali Meena ta juya zuwa dauko mai ruwan sanyin da yace, Don keta ruwa masu mugun sanyi har sun fara alamar kankara Meena ta dauko mai a cikin freezer su, Tai hakane don taga iyakar turai da karyan sanyi, Abin mamaki cikin rashin damu taga ya balle murfin goran ruwan, Kai ya kafa ya fara kwankwada har saida ya kai karshen goran yan kankaru kawai suka rage a cikin goran, Sannan ya aje goran a saman table din dake gaban shi, kusa da littafin Meenat din,,,,, Ànty amarya ce ta fara mikewa don barin falon inda Meenatu ta mike don tabi bayan ta, Wata yar sassanyar ajiyan zuciya taji Ali,Abbas ya sauke, sanan yace ina kuka samu wanan Beauty, Queen din a gidan ku, Gurin da Meenatu take mummy ta dan kalla inda tace a cikin fulanci kar dai ka fara kace kana son ta don kasan diyan gwago Buriji, nan na jiran ka, A take yanayin fuskan shi ya sake inda yake cewa, na fada maku, bana son wanan zancen sam, Mummy tana dariya take ce mashi ai sai, dai yayi hakkuri kawai don duk family din su ba wanda bai san da zancen ba, A dakin Anty amarya Meena ta samay ta tana cire dankunne a kunen ta, A lokacin ta dan waigo tana kallon Meena tace kinga bakon turai ko ? Brother din Asma,u ne a England ya ke zaune yana karatu bayan ya gama ya fara aiki a can, Yanzu ya dawo nan Nigeria ne don gwaunati tana bukatan yai mata aiki, Allah sarki inji Meena batare da tacewa uwar dakin nata komai ba, Ta juya abin ta da nufin komawa dakin su da suke kwana, Yar wayan ta Nokia wacce uncle din ta ya saya mata, don kiran mutanen gida, Abdulhameed ne ya kirata a lokacin don haka sai bata karasa fita daga dakin ba , Nan ta tsaya a kofan dakin tana ansa wayan ce mata yayi ta fito gashi a waje don zai yi tafiya zuwa Lagos gurin saro kaya, Komawa Meenan tayi dakin Anty a gaban mirror ta dan gyara fuskan ta sama sama, A falo ta kara samun wa yan nan yan uwan junan watau mummy da brother din ta, A cikin yanayin takun ta mai kama da na yanga, ta dan fito daga cikin gida don ta ratsa su, gurin da suke zaune a falon, Sannu, kawai tai masu inda ta sa kai zuwa hanyar fita waje,, Bayan ta, Ali, Abba's yabi da kallo inda ya kara ganin halittan ta da kyau, abin sai da yai touching din zuciyar shi, Saboda irin yarinyar da yadade yana cigiyar samun irinta ke nan a kasar hausa, Abdulhameed ta hango a yar farfajiyar gidan uncle din nata Yana zaune a bayan motar , jikin shi saye da wasu kananan kaya, sai jacket da ya dora daga sama, wanda hakan ya nuna mata a cikin shirin tafiya yake Hannun shi rike da keys din motar shi yana kadawa, a hankali, A cikin irin takun nata ta karaso gurin da yake a kunyace Tai masa sallama, Wani irin kallon na can kasan ido yai mata yana mai sake murmushi a fuskan shi, Sannu da zuwa, Dan uwa, Hmm yar uwa sai kika gan ni yau a wanan lokacin kuma ko? Murmushi Meenatu tadan sauke a daidai lokacin da ta dan kwanta kadan a bayan motan, Kasan hakan ai daurowa ce da ban ganka a yanzu din ba, don nasan baku da lokaci a cikin irin time din nan, Murmushi ya yi don jin abin da ta ce a lokacin don yasan cewa gaskiya ta fadi basu da time sam da rana sai dai da dare kawai, Yace wlh kaya aka shigo muna dasu daga waje kuma wanan ne farkon shigowa dasu kasan, Don hakane muke son zuwa mu kwaso su don mu samu su shiga da wuri, A hankali tace Allah ya taimaka Allah ya bada sa,a da rabo na alheri, Ameen ya Allah yar uwa,ta nagode kwarai da wanan addu,an da ki kai min , Amma insha Allah idan nadawo za mu shiga gurin hajiya ta don su gan ki, Murmushi Meenat tayi gami da dafe bakin ta da sauri tadan dago kai ta kalle shi ida sukayi ido cikin ido, Meenat tai saurin cewa rufa min asiri don Allah ai bazan iya zuwa gidan ku yanzu ba dan uwa na, A, haba dai saboda may, ? Meena, ta dan Allah mu ma bar wanan zancen kawai, don dai gaskiya ba zan iya zuwa ba, Abdulhameed ya ji dadi har a cikin ran shi saboda irin wanan halin ya ke kara alfahari da Meena din , Sosai suka nutsa a cikin hiran da sukeyi don Abdulhamed yana ta kokarin kara, kafa,wa kan shi tubali, a zuciyar Meenatu, Ali, Abba's ne ya fito daga cikin gidan uncle yana kokarin gyara kwalar rigar sa, Caraf idon shi ya sauka akan Meenat da Abdull din wa yan da suka yi nisa a cikin soyayya, Gaba daya hankalin sa ya koma akan su kallon Abdul yake yi a zuciyar shi ya, ce wanan guy din shine ashe Yarinyar nan ke, kin sauraron kowa, Wani irin kishi ne wanda bai taba jin kwatankwacin irin sa ba arayuwar shi, Wani gumi mai zafi ne yaji ya keto mai a goshi alokaci guda, Don haka da sauri ya kau da kansa gefe guda inda yataka da karfi zuwa gurin da ya aje motar shi, Zuciyar shi sai faman tukuki yake yi bai san may yasa ba yau ,yau da ganin yarinya har ya fara jin feeling a kan ta, Duk wana abin da yakeyi Abdullahameed wanda ke zaune saman motar shi yana dan kada kafar shi a hankali, Meena waye kuma wanan bakon da nagani agidan ku, Gurin da Ali, Abba's yake yana kokarin ta da mota Meena ta dan kalla Juyawa tayi gurin Abdull tace mai nima ban san shi ba yanzu nagan shi da zan fito, Amma ina ga dangin matan uncle ne tunda har ya shiga cikin gida,,,,, ZEEE MAKAWA YELWA [7/13, 07:21] Anty Lantana: 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 1⃣9⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA ALLAH- AL-A'ZEEZ,,, Tun zuwan Abubakar sai washegari musalin karfe goma na safe suka dan samu kebewa da kakan nashi malam tsoho, Malam tsoho yana saman shifidar shi na gadon kara da ke kofan gidan shi, Inda Abubakar din ke saman tabarman roba a kusa dashi zaune, Daganin su kasan cewa ganawa sukeyi na musan man, Don irin yadda suke zaune mutum zai iya gane hakan tun daga nesa, Yan maganganu suka fara yi akan irin al,amuran da ke gudana acikin gidan su, Sai kuma zancen gurin aiki, shi da suka saba yi da malam din a,duk lokacin da yazo garin, Daga karshe ne shi Abubakar din ya jefo zancen son ya kara aure saboda wasu dalilai da bai fadi ba, Malam tsoho wanda ke daga kishingide ya dan murmusa don dama yasan da cewa komai dadin dadewa irin wanan ranan zai zo, Shiru yayi bayan ya gabatar da bukatan shi ga malam din don jin mai zai ce a lokacin, Malam tsoho yadan gyara murya a hankali cikin natsuwa ya kai duban shi gare shi yace madalla maisuna nayi murna kwarai da jin wanan zancen daga bakin ka, Ina mai adduan kulun kafin in kwanta dama in ga zurian ka a duniya, Murmushi Abubakar yayi don dai shi a gaskiya irin wanan zancen ba wai ya damay shi ba ne a rayuwan shi, Abubakar ya cigaba da cewa don haka akwai wata wace muka shirya da ita acan Abuja, Dama ita ce nake son ko za a shirya sai su Baba su samu lokaci su tafi ayi duk wani abinda ya dace ayi ? Jin malam tsoho yai shiru yasa shi dago kai ya dan dube shi don jin abinda zai ce, Ganin yanayin fuskan tsohon kawai yasa shi gane cewa baiyi na,am da zancen ba, A hankali Malam ya kira sunan Abubakar din sai yai shiru na dan wani lokaci, Can yace mai zai hana ka duba nan gida ko a,cikin dangi kasamu wacce tai ma ku shirya, Ina ga hakan zaifi ma don kaga mu a nan din ai muna da kyawawan yan mata irin yadda zaka so,, Abubakar ya dubi kakan shi cikin yar natsuwa da kuma mamakin maganar shi ya ce, Malam nifa bazan iya aure daga nan gida ba don ban son fitina da kuma raini, Katse shi malam din yayi da cewa ai ba dole a nan gida zaka zaba ba ka zagaya acikin dangi ka duba ko, don akwai kyawawa nasani, Malam inji Abubakar banda ra,ayin auren mace don kyaun ta ko wani abu, Ni kwanciyar hankali kawai nake bukata, arayuwa na , Malam ya girgiza kai kawai don jin may Abubakar din yace a lokacin cikin takaici, Shike nan Jeka mai suna zan zauna uban nen naka muga yaya za,ayi su samu lokacin zuwa kan zancen, Godiya sosai Abubakar din yai mashi saboda yasan cewa tunda ya samu kan malam tsoho ya gama da kowa agidan ke nan ,,,,, Daga haka ya bar gurin malam din zuwa gidan sarakuwar shi hajja, ****** ******* ****** Baba Buharine zaune tare da mahaifin shi suna magana akan zancen da Abubakar din ya zo dashi na son karin aure a can birni,, Sai da Baba buhari yagama sauraren zancen da mahaifin shi ke koro mai a kan dan shi Abubakar, A jiyan zuciya yayi inda ya dago kai a fusace yace wa mahaifin shi, Amma malam wana shawaran na a,yar darwa yaron nan sam bai yi ba saboda babu alheri ko kadan ga auren bariki, Murmushin jin dadi Malam Manya ya sauke saboda fahintar shi da danshi Buhari ya yi ,, Amma a fili cewa yayi wa Baba Buhari abi shi a sannu don kaga ai auren shi na fari yai muna biyayya ko, Baba Buhari ya ce amma malam sai naga bai fi yaran gidan da wani kama ba ko, Malam ya ce ai shi ya ce ba ra,ayin shi bane auren mace kyakyawa don haka kaga yana da nashi irin zabin ke nan, Don haka sai kuje ku fara shirin zuwa nema mashi aure kamar yadda ya bukata, Baba Buhari ya dago kai kamar wanda zai yi magana, a lokacin sai kuma ya maida kan shi kasa yai shiru don biyayya saboda yaga ba wasa ga zancen tsohon, Kusan duk iyayyen su Abubakar sun yi rashin aman na da wanan auren da zaiyi a birni ba acikin gida ba, Amma yadda zasu yi don dole suka ja bankin su sukai shiru, Baba Hamza da Baba samaila da Baba yahayya sune zasu tafi sai wani makwabcin su wanda shima anan cikin unguwar shiyar sarakuna yake da zama akusan shakuwar gidajen biyu ya koma zumunta, sosa,,,, ****** ******** ****** Tun da safe take kokarin kiran layin wayan shi amma not reachable ake ce mata, Har zuwa yanzu da wayan mobile din ta ya nuna mata karfe biyar da rabi na marance, Don haka ta sake kiran layin shi din don taji ko zai shiga, A cikin sa,a ta ji layin yana ringing alamar kiran na shiga, Allah Allah salawatu takeyi ya dauki wayan amna sai ba,a dauka ba, Wanan abin ne ya tayar mata da hankali sosai har ya sa ta shiga wani dan hali, Azaton Salawatu ko a gida iyayyen Abubakar sun yi rejected din zancen ta da shi ne, Dole badon taso ba ta dai,na kiran shi acikin damuwa take sosai , Sai musalin karfe takwas na dare ne taji call a wayan ta tana dubawa taga ashe Abubakar ne a layin Cikin zumudi ta dauki wayan tana mai kashe murya, ta, Da sallama yafara zance kamar kullun don hakan akidar shi ce shi, Ina,shiga gari da,zun naga kiran wayan ki a lokacin a kwai go slow sosai a hanya, Ya hanya Sir ya mutanen gida,? Ya kabar su mama da sauran jama,a, Sosai yaji dadin wanan maganar da takeyi mai don ta nuna mai kulawar ta akan yan uwan shi, Shiru ne yadan biyo bayan hirar nasu sai ita salawa din ce ta kau da shirun tana tambayan aka maganar da ta kai shi gida, Dariya yai mata inda yaje cewa ai nasan cewa shine dalilin kiranki haka tunda,zun, Cikin jin kunya tace No sir ba hakana bane , Saidai dama don ina son inji ko zasu yarda dani ne in zama surukar su ko Nan dai ya ce mata gajar ce ki zauna ashiri don anytime zamu iya ganin parents di na agarin nan akan issue din mu,, Wani irin dadi ne ya ziyarci zuciyar salawatu a lokacin, Inda harda dan ihun ta don jin dadi wanda har ta kasa boyewa, Murmushi Abubakar yayi a bangaren shi don dai shi dariya ta bashi sosai, ****** ******** ****** Saye take a cikkn rigar barcin ta wani mai ruwan ja, jajir, Kanta yana daure da ribon wanda ta kama kan tun daren jiya da zata kwanta, Kitchen din ta shiga don ta kama ma mummy girkin safe kasan cewar itace da girki yau kuma tana dakin maigidan Idan abin ta mummy bazata fito ba sai rana ya haska sosai, Wayan ta dake gefe guda gurin da take tsaye tana fere dankalin turawa, Idanun ta kawai ta dora akan screen din wayan ba tare da ta dauka ba, Dan uwa tagani a rubuce, kan screen din wayan nata, Wani lalausar murmushi ta sake, a lokaci guda tare da saurin kokarin aje yukan da ke a hannun ta na firar dankalin da takeyi Bayan ta ta jingina da abin zinc din dake cikin kitchen din, Fuskanta dauke da murmushi tace Assalamu Alaikum Tankar Abdulhamed din ya na gurin a lokacin Meenat wacs haduwar ta da Abdul ya kawo mata wasu sauyin ra,ayi da dama, yanzu,,, A cikin wanan zazzakar muryan nata tai masa sallama tare da lumshe ido, Abdull wanda a lokacin yana tsaye da yar three quarter wando yana kallon Birch daga masaukin su, Bayan sun gaisa ne take cewa cikin muryan nata mai sanyi, Ya hanya dan uwa da fatan ka isa lafiya dai ko ya gajiya da jama,a Gajiya Alhamdullah sai dai ta kasa samun sukuni saboda ke Meena, Kai dan uwa saboda ni fa kace. ? Murmshi ta sake mai tare da cewa kai dan uwa fadi dai gaskiya ko dai gajiyar wanan dogon hanya da ka sha, Au to baka yarda ba to bari ki ji da kunnuwar ki ko zaki gaskan ta, No barshi kawai ai na yarda don nasan baka fada min karya Murmushi yai mata don yardan da tayi a lokacin guda Tabbas yasan cewa meena tana son shi sosai kamar yadda shima yake sonta,, Hira sosai sukayi na ina kwana ya gajiya ya kewan dan uwa ? Daga karshe take fada mai cewa tana kitchen zata hada break fast ne, don haka ya kyale ta badon yaso ba, ****** ******** ****** Dukkan su hudu a vikin shigar manyar riguna suke, don girmamawa, Sun isa garin lafiya cikin gajiya, don haka masaukin da Abubakar yai masu a wani hotel da aida nisa da uguwar dasuke, Sai dai su basu so hakan ba tun ma dai da aka ce wai har abinci duk na hotel zasuci, Baba hamza ne yafara magana yana cewa gaskiya Abubakar ka tona muna asiri yanzu a ce abinci da kafirai sunka dafa shina zamu, Baba Samaila wanda yake kokarin nade hannun rigar shi yace cikin shirin daura alwala, Don yin sallolin dake gaban su tun rana,.suke saman hanya, Washe gari ne da safe suka je yin abinda ya kawo su watsu ne man aure, Tun kafin su shiga suka fara ganin abin assha aciki don yawanci a cikin shi Duk jikin su ba sitirun karai ga kuma gidan da kazanta, Sai kuma babu wani babba mai tsayayye a gurin du taron yara ne, Duk a matse suke da su bargida don basuga wani sbin kwarai ba da har dan su zai so hada zuria da irin wa yan nsn mutane , Daidai da zasu wuce shi baba hamza ke tambayar wacece sarakuwar tashi, Wata babban mace da ke saye da dogon rigar atamfa ya dan dane mata jiki wai itace dan nasu ke so hada zuria da ita , Tun a hanyar su ta dawowa masauki suke suka fara sauke numfashi an rasa wanda zai fara magana daga cikin su,,,, Shiko Abubakar din sai jin dadi yakeyi Salawatu ta kusa dawowa hannun shi, Zai zama tankar kamar kowani magidanci shima yayi yadda masu aure keyi, Sam idon shi ya rufe bai hango abinda iyayyen shi suka hango mai ba, Baba yahaya yace ko shi dai da yake uba ga Abzai kwashi wanan tsohuwar mace ba wai mata, Baba Samaila ne yai masu magana akan su daina don komai ra,ayine,, ZEEE MAKAWA YELWA [7/14, 07:07] Anty Lantana: 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 2⃣0⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA ALLAH AL-JABBAAR Duk kan su hudu ne zaune cikin ladabi a gaban malam, Dawowar su ke nan ko gida basu shigaba a lokacin , Sun tsaya don su sanar wa da malam sakon gabacin da aka,aike su yi, a can Baba Sanaila ne yai saurin tare yan uwan nashi don gudun kada su aiban ta zancen a gaban malam mahaifin su kamar yadda su ksi tayi a can, Dafarko ya fara cewa malam Allah ya dawo damu lafiya, Abubakar da iyalinshi su na gashe ka kwarai da gaske, Ya ce muyi masa godiya sosai a gurin ka kafin yazo, Can kuma gidan ita matar muntafi gaskiya sun karbe mu hannu bibiyu sun kuma yi munar sosai, don haka muma muka gabatar da komai kamar yadda ya kamata ayi, Baba Hamza' cikin wani irin kallo da yakewa dan uwan shi ya kasa hakkuri yace, Haba samaila may zai sa ka boyewa malam gaskiyan zancen, Tunda tura mu yayi don mu wakilci gidan mu, mun kuma je munga akasi a gara mu fada mai don ya san yadda za,a bullowa abin ko ? Haba yaya Hamza' haka bai dace a gare mu a matsayin mu na iyayye ga Abubakar , Ganin yadda suka fara kaulewa da gardama yasa malam tsoho dakatar da su a cikin daga hannu irin na manya, Inda ya ce haba ba aiken ku nayi ba,aigara ku tsaya ku fada min gaskiya don kar sai abu ya baci adawo kuma ana da,an sani,,, Gaskiya kan inji wanan dattijon guda da suka tafi tarr da shi Abuja, watau makwabcin su, Yanzu kai malam sani fada min duk yadda akai don Allah saboda hakan ne ai na hada ka da su, Gyara murya malam sani yayi yafara da cewa to a gaskiya malam ba irin arziki za a dauko a gidan ka ba, Darajan gidan ka da mutuncin gidan ka bai,dace a ce yaron irin wanan zirian ya auro mace irin wancan matar da muka gani don sam babu tarbiya, Baba yahaya ne yajefa baki da cewa ga shi kuma ta girmi shi Abubakar din, SUBBAHANALLAH inji malam tsoho shi Abubakar din ke kuma son ta a hakan ? Kwarai kuwa don da muka tafi ya nuna muna jin dadin shi kwarai da gaske a lokacin, Shiru malam tsoho yayi batare da ya iya cewa ufan ba saboda atake zuciyar shi ta baci Baba Buhari wanda tun,fara magana bai iya cewa komai ba sai kai yake kadawa kawai a lokacin Can ya ce watau shi mai sunan malam sabon al,amari yake son kawo muna kuma ke nan? Gaskiya hakan ba zai yuyu ba sam dole ne idan har aure yake son karawa ya dawo gida ya zaba a cikin dangi ko yan wanan yankin, Ido kawai malam tsoho ya kura masu baki dayan su yana nazarin abubawa daga zancen kowan su, Baba Hamza yace aiko a nan gida muna da yara sai ya zaba daga sashen shaibu ko yahaya da hamza, Sam bai kawo sunan Baba Samaila ba wanda ke da yar matashiyar diya guda acikin su,, Shima din sam bai damu ba don dama ba wai wanan karon bane suka fara numai haka ba, Komai a yasu,yasun su suke abin su sai, dai su ware shi shi kadai koda yar uwar shi Mikewa yayi don jin inda zancen ya juta akala yana mai ce masu to jama,a mukwana lafiya fa, Dag haka ya shige abin shi cikin gida zuwa gurin iyalin shi, Ido malam tsoho wanda ke daga kishigide yabi dan nashi dashi kawai don yasan halun samaila sai shi, Samaila mutum ne mai murdaden halin wanda ba ruwan shi da shiga shirgin wani arayuwan shi,,, ****** ******** ****** Tafiya take yi a hankali kasancewa rana yau yai zafi, Wanda hakan yasa masu abin hawa sukai karanci a saman titin a lokacin, Tafe take da irin takon ta tankar tana tausayin kasa, ne Wata bakar mota lafiyyaya ta zo ta harba a saman titin, Can kuma Meena ta hango motar na yowa baya baya Har zuwa daidai inda take batare da ta waiga ba don ganin gurin da motar take Sai ji tayi mai motar na dan dana mata hon din motar, A hankali ya sauke glass din motan inda yake cewa, Beauty daga ina kike haka a cikin wanan ranan ? Sai a lokacin Meena tajuyo don ta ga waye ke mata magana, Ta tsura masa manyan idanuwan nan na ta , wanda ke rikita duk mai kallon ta, Ali,Abbas ne taga yana sakar mata irin shu,umin murmushin nan nashi,na ranan, Bakin shi na yar kyarma cikin rawan murya da ganin fuskan ta ya ce kizo in rage maki hanya pls, Ranan nan yai yawa kada ya illanta mun ke pls, Meenatu wace ta kada idon ta wai ita harara ta dan rausaya kanta gefe guda cikin yar yatsune fuska, tace, Kayi hakkuri malam don ni bana shiga mota da namiji dagani sai shi,, Daga haka ta juya abinta taci gaba da tafiyan ta,. Murmushi Ali, Abbas yayi, don yasan abinda ta fadi har cikin ranta haka zancen yake, Don haka sai bai matsa mata ba yasa kai abin shi zuwa gurin da ya nufa, Meena wacce tasha tafiya donbdaga karshe hakkura tayi da ta sara da kafa kawai tun da har takawo nan babu yar vespa, Da kyat taga gida don haka ido rufe ta iso, sai dai gidan na tsit a lokacin, Batai mamaki ba don tasan yaran gidan suna makarantan islamiya a wanan lokacin , Gurin Fridge ta nufa don ta sha ruwa ta duka ta dauko goran ruwa masu sanyi ta kafa kai da niyar sha, Har tasha takai rabin yar, goran, sai taji an rungumo ta ta baya, Wa, iyazu billah,,, Cikin sauri Meena ta furzar da ruwan da ke a bakin ta lokacin, Ta juyo a fusace, don ganin ko waye mai wanan dabiar banzan Ali,Abba's ne ya na sakar mata wani irin shu,umin murmushi a fuskan shi, Idon ta dan rutse inda tadaga hannu da niyar kai mashi mari, Cikin sauri ya gwauce, sai bata samay shi ba ta samu iska, A lokacin wasu irin hawaye masu zafi suka ziyar ci fuskan Meena, A cikin masifa ta nunashi da dan yatsan ta tace, Cikin daga murya tace daga yau daga rana mai kamar ta yau kada ka kara shiga tsabagata ko ka nuna ka san ni Kasa ni cewa ni ba yar iska bace irin ka wanda ya tashi cikin rashin tarbiya, Kuma ina neman tsarin Allah daga duk wani sheri daga ire, iren ku shedanun mutane, Daga haka taja wani irin dogon tsaki gami da hararan shi ta watsar gefe guda, Sai a lokacin hawayen idon ta suka fara yawa a fuskan ta, Wani kallo ta watsa mai , mai tatare da tsana da kiyayya, Baki bude Ali,Abbas, ya tsaya yana kallon yadda yar yarinya, karama ke gaya mashi, magana son ranta, A fusace Meenatu tabi ta gaban shi ta wuce zuwa cikin gida, rai bace, Direct dakin Anty amarya ta nufa da shiga ta zauna a,bakin gado idon ta na mai zubar da hawaye kawai, Anty tana fitowa daga bathroom taga Meena acikin wanan halin, Take hankalin ta ya tashi da sauri ta karaso gurin da Meenat take zaune ta na tambayar ta cikin tashin hankali, Amma Meenat ta kasa bude baki tayi magana don bakin ciki, da ya mamaye mata rai, Da tambayar yai mata yawa ne ta kwanta ga kafadar uwar dakin nata cikin kuka take fada mata abinda ya faru, Rayuwan amarya ya baci sosai nan ta shiga bawa Meena hakkuri har ta samu ta dan sasauta kukan nata, Shiko Ali,Abbas shigar Meenat ciki yasa shi sauke yar ajiyan zuciya cikin takaici, A lokacin ne yasan cewa ya tabka babban kuskure don nan kasar hausane ba wai turai ba, Gashi kuma ko banza Meenat still karamar yarinya ce tukun ba wani girma tayi ba Gashi Allah yasa mai son wanan yarinyar a rayuwan shitun ranan da ya ganta, Sam ba zai iya jure rashin taba a halin yanzu don haka dole ne ya jure duk wani cin fuska da zai gani a gurin ta, Cikin yanayi na rashin kuzari da kyat ya ja kafan shi da yaje jin sunyi masa nauyi, Tankar bazasu dauke shi ba, ya nufi hanyar fita wajen gidan ran shi a bace,,,,, ****** ******** ****** A cikin gidan malam tsoho ko wani sashe sai kokarin ganin ance yar su za ai wa Abubakar kamay, Daga sashen Baba Hamza' da Baba Shaibu har da Baba yahaya, Sai kuma bangaren gidajen gwagwan,nin su suma suna son wanan hadin, Duk wanan wainar yan gidan Baba Samaila basu da labari sam, Ko ma suna da a yanzu yar shi bata cikin jerin manyan yan matan gidan, tukun na don duk sun girmay mata sosai, Malam tsoho wanda yau da kan shi yasa aka kira mai wayan jikan shi na fari Abubakar, Bayan sallama da gaisawa ne, malam tsoho ke cewa jikan nashi Kana magana ne da Abubakar manya mai almajirai, Murmushi Abubakar yayi a bangaren shi sai da malam din yaji tankar yana agaban shi ne, Abubakar magana nake son yi ta fahinta da kai don mu fahinci junar mu, Abubakar wanda a lokacin yana zaune yana cin abincin dare, ne , Yadan dago kai ya kalli gurin da Sadiya take zaune tana kallon wani shiri a African, magic, Malam din ya soma da cewa akan zancen auren da kake da burin karawa ne mai suna, Banji dadin yadda iyayen ka suka dawo suna fada min irin zurian da kake son mu hada iri da su, Shin mai suna ina tarbiyan ka da sanin ya kamatan ka suka shige da har zaka kwaso wa kan ka irin wanan macen, Tun a wanan ookacin rayuwar Abubakar ta baci yaji wani iri a zuciyar shi, Muryan malam din ce ya dan dakatar dashi daga tunanen shi, Malam yace kazo gida cikin dangin ka da yan uwa kaduba iri mai kyau kaza ba Don dai a gaskiya ba zan yarda tun ina da rayuwa ba, ace wai jikana ne ya auro irin wanan zurian agidan mu,,, Abubakar wanda tun fara maganar kakan nashi yake sauraren shi ya ce malam A gaskiya na fada maka akwai kalar matar da nake bukatar in aura tun farko, Don haka yanzu kuma naga wacce nake so don Allah kubar ni inyi abin da rayuwana ke muradi, Malam ya ce badai ita wanan din ba sai dai ka dawo nan gida kebbi ka duba kalar ta,,, Daga haka tsohon ya kashe wayar shi batare da yajira yaji mai jikan nashi zaice ba, Innalillahi kawai Abubakar ya iya nanatawa a lokacin don tun daga kafan shi har kai wani irin abu yake ji tankar ya fadi, May zai sa suyi mashi hakane bayan tun yana yaro baida zabin kanshi komai akan umurni yake tafiyar da shi, Rai bace ya lalabo noban Baba Samaila duk da dai ai har da shi a cikin masu zuwa su fadawa malam mumunar labari akan salawatu, Bayan sun gaisa ne sai zancen da yasa ya bugo mai waya yafara da cewa, Baba a gaskiya ban ji dadin abinda aka fadawa malam ba a kan wanan yarinyar da na tura ku nemar min, Baba Samaila wanda a lokacin shima ya na zaune ya fara cin abinci a take yaji abinci ya fita ran shi, Baba Samaila ya ce haba mai sunan malam ka kwantar da hankalin ka mana ka fahinci komai, yadda yake, Koda zamu bata zancen ka ne ai kasan bakamar yadda kake nufi ba ko ? Kaifa ba jahili bane ya kamata ace kasan yadda zancen yake, To baba in banda abin malam auren zumunci auren sunna ne ? Manzon Allah S A W babu yar uwar sa acikin matan shi ko da akwai ma bai tilasta yin hakan ba ko da acikin sunna Kuma ai matan sa bawai duk yan kabilar sa bane, Don haka ita dai wanan din itace zabina ita nake so in aura koma yaya take, Kana ko cikin hankalinka mai sunan malam ? Kada zancen mace ya sa ka koma mara biyayya ga iyayyen ka ? To bara kaji wanan karon babazan goyi bayanvka muddin kace zaka bijerwa mahaifan ka, Kabari abi abin asannu don a samu a rabu lafiya ai naga ko anan gida birnin kebbi akwai yan mata kyawawa da zaka so, Baba har yanzu baku fahince ni sosai ba, ni fa ba wai al,adace a gaba na ba Addini nake son koyi akai nasan cewa yaran mu suna da kyau da asali da tarbiya irin wanda yan birni basu da shi, To amma ko wani namiji da akwai abinda ya ke so ga mace ,,, To ka bari abi abin a sannu ko ina ga zaifi sauki sosai,,,,, ZEEE MAKAWA YELWA,,, 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 2⃣1⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA ALLAH-AL-MUTAKABBIR Sheshekan kukan da Meenatu ke yi yatayar wa amarya da hankali sosai cikin fada take cewa kiyi shiru Meenatu an, In uncle din ki ya dawo zan fada mai yai masa iya ka dake, Don su ba kunya bane garesu, ya dauka cewa ke irin dabi,un yaran gidan su ke gare ki, Dabiar da za aita rugumar juna da dan uwa wai dabiun wayewa wanan ai lalacewa ne da watse, Wanan maganar ya sa Meenatu dan dakata wa don ta saurari zancen amarya, Anan ta shiga bata labarin rayuwar turawan da sukeyi a gidan su,, Sai a lokacin meena cikin murya mai kuka tace to ni iyayye na ba yan aron al,adun wasu bane su yarda koyarwan iyayye da kakan,ni, Mu gidan mu muna koyi da sunanan maikin Allah ne mazon rahama, To kin ga ai hakan da kikai masa gobe bazai kara ba don ya san tarbiya ba daya,,, A haka ta samu har meenat din tai shiru daga kuka da bacin ran da take ciki, Sosai rayuwan uncle Nafi,u ya baci don jin abinda ya faru tsakanin Meenatu da kanin matar shi, Duk irin mutuncin da ke a tsakanin Nafi,u da Ali,Abbas sai da wanan zancen yaso ya hada su fada sosai, Amma da yake mazane sai suka kai rayukan su nisa suka sasanta da junan su, Inda shi Ali, Abbas ya kwantar da kai gurin Nafi,u yana cewa shi wallahi auren Meena yake son yi ba wai yai mata haka da wani manufa bane,,,,, Daga karshe dai uncle Nafi,u ya ce ya bari abi abin a sannu don har yanzu Meenat yarinya ce,,,,,,,,, ****** ******** ****** Abubakar yayi shiru yaji duk jikin shi yai sanyi lankwas, Wanan sabon al,amarin da ya bolle mai maigirma ne sosai, Don haka maganar Baba Samaila kuma gaskiya ne, A hankali dole zai bi da malam tsoho ya samu ya lalaba shi akan zancen, Shi in fa badon mahaifan shi ba bai ga dalilin da zai sa malam tsoho ya dinga taka mai burki ga al,amarin shi ba, Duk yan kwanakin nan duk wanda yasan Abubakar yasan da cewa ya canza sosai,, Ga kuma aiyuka da suka taso mai daga gurin aikin su, A bangare Salawatu kuma duk da ba wani abinda tagani na canji daga Abubakar amma jikin ta ya bata cewa tun zuwan iyayyen shi Abuja akwai matsala sosai, Don a irin yadda da farko yake nuna mata cewa bada dadewa ba zasu yi aure sam yanzu ya daina hakan, Kwatakwata ma bai zancen auren su a yanzu din sai dai yana yawan nuna mata kulawa da kuma kashe mata kudi,,, Abubakar yana sane da cewa hankalin salawatu a zuwa yanzu ya tashi matuka don dai bata ga fuska yadda zatai mai korafi bane, Tun bayan wani rana da ta faraxmai magana suna acikin mota a hanyar su ta dawowa daga gurin aiki, Tsawa ya daka mata tare da mata kashedin yi mai katsalandar ga harkan shi, Yace bani nace maki naji zanyi ba koke ce kika sani , Salawa sai hakkuri kawai take ba shi a lokacin don ganin irin yadda idon shi ya rine a lokaci guda yai wani ja kamar garwashin wuta, Mtsss ya ja wani dogon tsaki tare da rike kanshi da yake ji a lokacin tankar zai tsage, Hannayen shi guda biyu da suje a cure guri guda yake dan dukka kadan kadan, A wanan yanayin, shi kadai yasan,irin abinda yake ji a zuciyar shi Zaune yake a office din shi saman kujerar shi duk da tolin aikin dake gaban shi ya kasa aiwatar da komai akai, Mtsew ya sake jan wani sabon tsaki, tare da furzar da iska daga cikin bakin shi a lokacin,,,,, Yasan duk inda wanan sherin yafito daga bakin kannen mahaifin shi ne,,, Baba yahaya ko baba hamza don koda rantsuwa yayi bazaiyi kaffara ba , Baba samaila bazai taba yi mai wanan gamin ba a surin tsoho,,, Ajiyan zuciya ya sauke a lokaci guda don tunawa da shawaran da Baba Samaila ya bashi yasan cewa shima Baba samailan zai yi wani abu akai ke nan,,,, ****** ******** ****** Tun faruwan wanan zance Meena bata wani sake jiki a gidan ba, Kwatakwata ma hankalinta ya koma gida birnin kebbi ba abinda take so kamar taje taga kakan ta malam tsoho, mai bata sudin kwanon fura da waina,,da, baban ta da maman su da yan uwanta,, Kasan cewar zasu kwana biyu ba su da lacca, Musalin karfe goma na safe sai kawai ta yanke shawaran ta wuce birnin kebbi kawai ta gano gida, Gurin anty amarya ta wuce ta sheda mata cewa zata je birnin kebbi yau, Da mamaki uwar dakin nata ke kallon ta, tana tunanen kodai Meenatu nason zuwa gida tafadi abinda ya faru da ita ne, Ido ta dan tsurawa meenatu din sannan ta kira sunan ta , "Meeena, Meeenat wacce ta dan dago kai ta kalle ta a hankali, Anty, tace kardai ince abinda yafaru tsakanin ki da Ali Abbas zai saki tafiyagida ? Kai meenat ta kada a hankali alamar a,a badon shi ba zata tafi,,, Murmushi anty ta, sake a lokaci guda tace, don Allah meenatu kada ki fadawa iyayyen ki don rayuwan su zai baci suga kamar ba,a ai maki rikon kwarai a nan,,, Meena ta dubi anty amarya tace insha Allah anty ba zan taba fada masu wanan zancen ba, Karfe daya saura Meenatu ta na cikin garin birnin kebbi, a cikin shiga ta mutunci, Kallo guda zakai mata ka ga canji sosai daga gare ta saboda yanauin canjin gurin zama, Mai mashin na sauketa a kofan gida da yar jakar ta da tasa kayan ta aciki sai kuma wani jakar vaco da ta saka tsaraban da su Anty amarya da mummy suka bayar ta kawo wa mahaifiyar ta da kannen ta,, Tun daga nesa malam tsoho ya hango ta yaga irin yadda yarinyar ta canza a lokaci guda, Su baba Buhari da ta sama a kofan gida su ta fara gayar wa dacewa Baba ina wunin ku ? Meeenatu ke, ta tahe yanzu, "Ni ta Baba' Ina wajen su kawun naki duk suna lahiya ko ? Walleh duk lahiya muke Baba,, To, a gaishe ki, ke ji Da murmushi a fuskan ta, ta karasa gurin malam din ta na cewa malam ina fatan akwai sudin fura mai sanyi, Ho yar nema kina son sudin fura kika tafi kika bar ni da fura na, Meeena tai murmushi tace to ai gani naji kewar ka na dawo don in gan ka insha kuma fura,,, Ke ta att ta he yau, ? Ya ya gurin kawon naki da sauran jama,an ku,, Lahiya lau muke malam tsoho, Wani kamshi ne mai ma,ana yaji yana tashi a jikin jikar tashi, Wanda hakan ya nuna mai cewa yanzu akwai canji mai yawa daga jikan tashi, sosai, Mikewa tayi cikin fara,an ta zuwa cikin gida rataye da yar jakar ta a kafadar ta, Da murnan ta tashiga ciki tana cewa Salamu,Alaikum, A,a a maraba da mutan sakoto kece a tafe yau Meenatu, ? Mutanen da ta ke cin karo da su a hanyar ta ta shiga cikin sashen su ke nan, Murna sosai na jin dadi meena keyi don wani irin yanayi sa ta tsunci kanta aciki, Matar baba yahaya, tace a a maraba da Meenatu, wallahibdazun nagama zancen ki, Murmushi Meenatayi don tasan gaskiya ce saboda suna dasawa da ita sosai, Daga haka Meenat ta wuce zuwa cikin shiyar su, A bakin murhu ta samu mama,Saratu tana kokarin raba abincin rana, A,a ke ta tahe yanzu ? Darabon yau muci abincin rana da ke ? Murmushi tayi kawai tana kokarin aje jakar hannun ta a cikin rumfar dake tsakar gidan ku,, Ya wajen su kawun na ku da iyalin shi ? Wani irin Meenat taji a lokacin da mama take mata wanan tambayar, Duk yadda taso ta boye bacin ranta abin ya kiya don a daidai lokacin mama ta dago kai don ta kara tambayar ta, Amma sai ta fahinci a kwai matsala ga zuciyar yar nata Saboa irin yadda fuskanta ya sauya a lokaci guda, A may kuma ya faru don naga kamar daga tambayar su kin canza fuska, Murmushi Meenat ta kakaro na karfin hali don kawar da zargi daga mama, Tace a haba dai mama gajiyane kawai nayi saboda motar da na shigo yar karamace duk a matse muka iso garin nan,, To ki dan watsa ruwa mana ko zaki walware ko ? To mama amma barin shiga in gaida su mama kafin in huta ko ? Hakan yayi inji mama wace ke kokarin rufe tukunyar da ta gama raba tuwon shinkafa da miya yakuwa, da ya ji kulikuli,,, Sashen su mama Ladi dake can ta karshen gida ta ziyarta karshe, Mama Ladi wace tun sallamar Meena ta kalleta tun daga kasar ta har saman ta sanan ta bata fuska gami da karba sallamar ta, Samira ce tafito a daidai lokacin da Meenat ta kai kasa tana gaida mama ladin, A,a mutanen sokoto kune yau a garin namu, haka ? Anty Samira kina ciki ashe,? Ai na zata ko kin koma Abuja ne ai , Samira tayi dariya tace kai Meenatu akwai ki da zolaya Ai nida Abuja ko ziyar balle leke indai da zamane, ? Dariya suka sa gaba sayan su a lokaci guda meenat tace haka dai ki kace Mama ladi dake daga gefe guda cikin kushewa ta ce, Aiduk diya, ta gari a gidan uban ta an kasan ta ba yawo kalar dagi ba don kwadayi gashi kuma wasu har yanzu banda canza halitta basu zama komai ba, Duk da Meena tasan da ita mama keyi amma sai tai dariya kawai tankar bata fahinci mama ladin ba, Samira ce wace da jin abinda mahaifiyar ta tace ta bata fuska tadan joyo gurin Meenat tace dama ko ina son ganin ki kaina ta, Akwai labari mai, dadi amna sai kin huta zan shigo har lungun ku in gan ki, Wai ko Meenatu ke ga wadda kin ka koma kuwa ? Walleh ke yi wani irin fresh da keyyah kamar ba keta ba, Shin mi aa,r sirrin na muma mu shige ciki ? Haba anty samira Hadda keyya wurin yi min sheri? Walleh ba sheri ba na Meena ke san ankusa bukin mu , Cikin budan ido da mamaki Meenat tace da gaske, shin ? Mama Ladi wace ke tsaye ta na wa meena wani kallon kaskanci sanan tace, To mayye na fadawa meenatu me zatayi maki? Me ar gare ta ? Sosai wanan maganar ya so ki zuciyar meena Meenat tadan dago kai cikin murmushi tankar maganar bai zafe ta ba tace, Mama na gaishe ku zanna in huta gajiya anty Samira sai ke taho, Meenat na fita tun bata kai kofa ba taji muryan mama tana cewa , Samira so kike kizubar min da mutunci me zaki bida ga wagga diyan matsiyatan ? Haba mama nida yar uwata zakice min haka na kedai san tsakan mu sai Allah ko ? Rai a bace meenatabar sashen maladi da mamaki azuciyar ta yaushe mama zata canza halinta ne ? Ba abin mamaki bane ganin yadda meena ta dawo cikin bacin rai ko ba,a fada ba tasan sun kwaso da mamaladi ke nan ? Baba yaji dadin ganin meenatu gida da ya dawo, Don haka sun kai wani lokaci zaune tare suna hira har ibrahim shima yayan ta ya dawo ya samay ta sukaci gaba da hiran su, Sai dare lokacin da meenat ta san cewa malam ya shigo gida daga majalissan shi na kofan gida, Lokacin ne taje gurin shi don su gaisà da shi din kamar yadda ta saba yi idan tadawo,,, Malam na murmushi da ya gan,ta yana cewa mutanen sokoto baki barci bane,? A,a malam ina jiran ka shigo mu gaisa ne kafin in kwanta, ne, Murmushi malam yayi yace ke yar nema kedai taho ki shanye min fura kawai Dariya tayi don tuna baya irin yadda takan zauna don tasha furan malam tai,ya mai hira, Ke da Abubakar dai kamin wanan halin duk cikin jikokina, Sai a lokacin ta tuna da ta na da dan uwa Abubakar agidan su Tambayar malam tayi ina yayan nasu da iyalin shi, Malam yadan gyada kai yace yanan nan, Kwanan nan yadauko rigima wai aure zai kara, Allah sarki in,ji meena gaskiya yana da bukatar hakan, ****** ******** ****** Jin shiru da malam yayai Abubakar bai tuntube shi da zancen komai aasa shi tunanen ko ya canza shawara ne Amma sai yace bari ya tun,tube shi yaji komay yake ciki a kan shawaran da yabashi na yazo gida ya nema anan, Baba Samaila wanda yazo gaida malam din da safe kafin ya fita zuwa gurin neman kudin shi, Baba Samaila yana shirin wucewa malam tsoho yace Samaila dauki waya ka kira min danka Abubakar muyi magana, A take yadauki wayan malam dake gefe yakira mashi Abubakar din, Wanda alokacin yana zaune office din shi yana kokarin fara aiki, Ganin nobar malam tsoho ke kiran shi tun da safe haka Yasa gaban shi faduwa don yana tunanen ba lafiya ba kila, kira haka da safe, Gaisawa suka fara sai kuma yar shiru da ya biyo baya Can ya ke cewa dama na bugo makane don inji yazancen mu ya kwana ne, Jiki a sanyaye ya cewa kakan nashi malam ina nan akan zance na, Amma zan tafi England wurin karo ilimi na wata shidda sai na dawo zamu kai karshen maganar, To shike nan Allah ya kai mu, Allah kuma ya kaika lafiya yabada sa,a, To ameen malam nagode,,, Daga haka suka kashe wayan suna mai sallama da junar su,,, A lokacin malam ne wanda ke daga kwance yake dan kada kai a hankali,,, ZEEE MAKAWA YELWA,, 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 2⃣2⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA ALLAH-AL-KHAALIQ,,,, Bayan dawowar ta daga birnin kebbi, washegari, Meenat ta,shirya musalin karfe goma tana,son zuwa makaranta, Falo ta nufa don ta samu ta danyi breakfast a lokacin kafin ta tafi, school, Zaune yake a falon da waya shi a hannun shi, yana magana da wani adayan bangaren, Rigar dake a jikin ta dogo ne har kasa yadan fitar mata da,sharp din ta a fili, Dinkin rigar yai matukar yi mata kyau sosai, sister din anty a marya ce ta dinko mata shi daga kaduna, Tun daga kofan falon ta hango shi a zaune ya na wayan, Sai dai duk da wayan da yake yi hankalin shi gaba daya yana akan ta,, Ji tayi kamar ta juya sai dai ta jure kawai ta karasa, karasowa cikin falon, Inda ya zuba mata idanuwan, shi gaba daya, kamar wani tsohon maye, Ya so ace yai mata magana amma sai ya tuna da yadda su kayi da uncle Nafi,u,, a kanta last two weeks,, A haka tazo har ta gaban shi ta wuce batare da yai mata maganar komai ba, Bayan ta yabi da kallo a cikin sha,awan irin kira da siffan jikin ta, Ita ko Meena ganin yana waya yasa ta wuce,wa, batare da ta gaishe shi ba , Milk, take zubawa a cup, a lokacin ne taji yayi shiru ga wayar da ya keyi, Don haka ta waigo don ta gaishe shi saboda kawai mutuncin yayar shi watau, mummy, Ifon shi kar akanta a lokacin tankar maye wanda hakan yadan bata, tsoro, Amma cikin daurewa ta ce, masa ina kwana uncle kamar yadda taji yaran gidan na kiran shi,, Cikin dan i,iniya ya ansa mata da cewa lafiya kalau Beauty ya kika dawo,? Lafiya tace masa a takaice, , Sai dai a cikin zuciyar ta tana mamakin wai har yasan cewa tayi tafiya kwana biyu,, Ci gaba tayi da abinda takeyi na kokarin hada shayin da take yi,,, Daga gurin da take tajiyo ajiyar zuciyar shi kamar wanda yai dogon tunane, Muryan mummy ne taji daga bayan ta tana cewa brother, May yasa kake son zubarwa kanka da mutunci ne ga diyan talkawa haka Meenat wace ke kokarin juya tea din da ta hada a cup taji abinda mummy tace a kan ta, Idon ta tadan rintse a hankali yayin da zuciyar ta ke mata dan kuna, A gaskiya badon wanan karatun na cikin dadadawa mahaifan ta rai ba kamar yadda su ke burin suga tayi ilimi don cigaban rayuwar ta watarana, A gaskiya da akan mummy da dan, uwanta zata iya barin sokoto gaba daya ta koma gidan mahaifan ta da ake kira da talkawa, Eh to tamaji din su talkawa,ne to amma wai ita mummy damay suka fi su ne wai ? Iya kan dai tarbiya Alhamdullah tana dashi wanda su diyan masu kudin suka kasa samu a yanzu, Zaka ga dan talka yafi dan mai kudi tarbiyar da kuma sanin ya kamata, To wai ita ma mummy dake cewa masu kudi har ina kudin yake a gurin su, Tsukin da taja daga cikin ranta wanda har ya baiyana a fili, Da sauri gaba dayan su suka waigo ta don ganin may takewa tsukin Cup din ta dauka da nufin barin falon don ta basu guri, Cikin wani irin murya taji Mummy ta kira sunan dashi tana cewa, Ke Meenatu waki wa wanan tsukin newai,? Shin may kike nufi da nine agidan nan ? Tun farkon zuwan ki naga duk take, taken ki ba yau ba , Ido kawai na sa maki don inga iya gudun ki daga ke har wace ta kama maki a,gidan nan, Kuma bari ki ji duk iya, yinki da kisisinar ki bazai yi tasiri a kaina ba nida dan uwa na da aka turo ki ,gare shi don ki bata mashi suna, Ke har ina mace da zaki wani ce wai Ali,Abba's ya rugumay ki da niyar iskan ci, Haba sister a gaskiya bakiyi wa,wanan yarinyae adalci ba, Wanan ai sheri ne kawai irin naku na mata kike kokarin yi, Na fada maki cewa ni nace ina son ta, nafada maku son ta nakeyi son nake in aure ta, Sai a lokacin Meenat ta dago kai da fuskanta wanda ya jike dahawaye a lokacin, Cikin wani sanyi murya ta bude baki niyar maga don har ta soma cewa mummy, Sai taji muryan anty amarya a gaban ta tana cewa Meenat wuce,war ki zuwa inda zakina "ke ji, Simi,simi meenat tabi ta gaban su gaba daya ta wuce zuwa ciki da cup din tea a hannun ta,,, Wani mugun kallon rainin hankali Anty amarya ta watsawa masu, Bata ce komai ba ta bibayan meenat ranta a bace, ****** ******** ****** Ba wani issashen lokaci yake da shi ba so,sai saboda tafiyan da ya taso mai a gagauce zuwa England, Don, haka ya zo gida, a bazata don yai masu sallama duk yadda yaso ya wuce batare da yazo ba saboda baida issashen time, Amma sai ya ga haka bazai yuyuba ba agare shi dole ne yai squeezing din time din shi ko na kwana gudane, Azaune yake cikin daren da ya iso agaban malam suna dan ganawa, Bayan ya gama fadawa malam din dalilin wanan tafiyan da zaiyi zuwa kasashen ketare, Malam din yai mashi addu,a tare da fatan alheri, Malam ne ya jefo mai tambaya akan cewa ya zancen maidakin shi Sadiya, Abubakar ya dan gyara zaman shi a hankali ya ce a canzata zauna har zuwa lokacin da zan dawo, Ita da wa ke nan zata zauna acan din ? Batare da wani damuwa ba yace wata,ce yar uwar ta zasu zauna tare, "Tau, Inji malam wanda yaji zafin wanan zance na jikan nashi, A ce mutum bai shawara da kowa acikin yan uwan shi, Yanzu duk yawan yan uwan shi amma ace wai sai an fita waje an samo, mai zama da matar shi,, Duk yadda malam yaso a lokacin yai magana irin wacce, za, a fahita abin ya kakara, Sanoda yasan cewa bazasu fahinta ba a yanzu don haka ma ya ja bakin shi yai shiru, kawai, Abubakar zaune a dakin mahaifiyar shi mama Ladi suna bankwana, Sai addu,a da fatan alheri take kwarara ma dan nata, Can kuma ta dan kashe murya tankar akwai wani wanda zai jin may zata ce a wanan lokacin, May ake ciki akan zancen auren da naji ance zaka kara wai ? Shiru Abubakar yai mata a wanan lokacin tare da dan dukar da kanshi a kasa, Tau, saurara kaji koda kai wani aure ka kokarta ka kula, da matar ka sosai, Don ban son ace kayi aure ka wulkanta diyar aminiyata, Saboda ban son mu samu matsala da uwarta akan wanan auren ? A cikin ladabi ya ansa mata da cewa, insha Allah babu abinda zai faru a kan haka, Sosai mama Ladi taji dadin ansan da dan nata ya ba akan diyar aminiyar ta, Zancen auren yar, uwar shi Samira wanda za,ayi baya kasan mama ta kawo a lokacin, Abubakar yace ba kudi kukace na aiko maku dashi wanda zaku sai mata kayan daki dashi ba, Ma kin san fa yanzu babu kudi sosai na riga da na yi duk wani planing akan tafiya na, ko, Cikin dan marairaice murya mama tace amna aikasan dole ne sai mun kai kayan gara irin wanda mutane zasu sheda ko ? Shiru yay tare da sa hannun shi a cikin aljihun shi, Inda ya ciro kudi hannu suna rawa mama ta mika ta karbi kudin daga hannun shi,, Tafiya yake yi alokacin zuwa sashen amaryan mahaifiyar shi wanda kusan a manne su ke da junan, su, said ai yar katangar da akayi a tsakanin su, Tunane yake yi wai may yasa mama tafidamuwa da Safiya fiye dashi, Yadda mama take nuna mai tankar Sadiya ce ta haifa a tsakanin su ba shi ba, Duk irin mugun rayuwan zaman auren da suke yi a tsakanin shi da Sadiya mama bata taba ganin laifin hakan ba sam, Saidai ita gurin ta kawai a gyarawa Sadiya rayuwanta sai kuma zancen ya ba da kudi aiwa gidan su Sadiya abu, A haka yai sallama da duk kusan wanda ya kamata yai sallama da shi a wanan lokacin ya yi saboda safe zai wuce, Da Baba samaila suka gana akarshe inda yake fadawa Baba samaila kudirin auren shi da yadawo daga England insha Allahu, Inda baba Samaila yai mai alkawarin cewa zai tsaya mai akan zancen auren har komai ya tabbata, Mama Saratu tana jin duk zancen da sukeyi a lokacin, Don haka take mamaki da cewa wanan karon akan mace Abubakar ke niyar saba, wa mahaifan shi, A nan taji muryan maigidan ta inda yake kara nanata wa Abubakar da ya kwanatar da hankalin shi yabawa Yarinya hakkuri, har zuwa dawowan shi Sai a lokacin ne Abubakar ya tuna da cewa ai Baba samaila yana da yara masu dan girma akwai Ibrahim da kuma mace ai, Wanda gaba dayan su baya jin duriyan su acikin zurian gidan nasu, ****** ******** ****** Wata uku ke nan yanzu da suka wuce rabon Meenat da zuwa gida birnin kebbi, Sai,dai a ko da yau,she suna waya da yan uwan ta sosai, Musan man Samira wace ke aiko mata da kudi ta na siyo mata abubuwan bukatu a garin sokoto, Zaune ke da yar wayar ta a hannugama wayar ta ke nan da Abdullhameed, Wanda zuwa yanzu sun rage irin hurda da su keyi a da dashi, Wanda ita sam hakan bawai ya damay ta bane don tasan cewa yanzu take don abune mawuyaci tafi batare da ta dawo da sabon yyi ba, Duk da TV dake a dakin su yana aiki kamar y tsage mutanen ciki su fito, Hakan bai sa Meeenatu daga kai ta kalli TV ba ita hankalin ta, na ga wayan ta , Text take karantawa wanda duk kusan yan kwanakin nan mai text din na yawqn damunta da turowa, A hankali har ta iso inda meenat din take zaune daidai inda take a zaunen, Takai hannun ta, a hankali ta dafa ma ta kafadar ta, Hakan yai sanadiyar dawo da ita acikin hankalin ta Tadago kai suka hada ido da uwar dakin nata watau Anty amarya, Ajiyan zuciya Meenat ta sauke tare da dan yin yake a fuskanta, Da ganin dariyan bai kai ciki ba tadai yi shi ne kawai, Gefen ta amarya ta samu ta zauna tana cewa Meenat auren yan uwanki ya matso banga kina wani shiri ba akai, Ido meenat ta lumshe kadan sanan tace anty ina ga fa sai kila ne ma in samu zuwa don ina da test awanan lokacin, A ,a ke ko meena za ai buki a gidan ku kuce bazaki samu zuwa ba nan da birnin kebbi, Anty Amarya ta dubi meena da kyau tace sai dai in akwai abinda zai hana ki zuwa Fuska meena ta bata tace Anty kin san fa yar wajen mama Ladi ce fa da diyar baba shaibu, Ni wallahi Anty ban son tozartawa sam wallahi saboda hakane kawai ban sa zan tafi ba, Murmushi Anty tayi tace zaki tafi mana don in baki tafi ba basu ji dadiba musam man samira din, Ai badon ita mama ladi zaki tafi ba ko ? Ido ta tsurawa wa meenat din inda yarinyar ta ba ta tausayi sosai, Yarinya kamar meena ace bata da kwanciyan hankali saboda kawai hassada Hannu ta sa ta dauko ledar dake gefen ta kayane tafara ciro daga ciki Kayane har kala uku Anty ta a mata wai tasha buki da su, Baki bude Meena ke kallon uwar dakin nata wace a ko da yaushe tana ko karin ganin farin cikin ta, Sabanin mummy wace ji takeyi tankar ta shake meena din yanzu Wai ta yiwa dan uwan ta sheri, don ta bata mashi suna, ZEEE MAKAWA YELWA 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 ²³ and ²⁴ ZAINAB IDRIS MAKAWA ALLAH-AL-BAARI Gaisuwa gare ku da fatan alheri masoyya wanan novel TARKO,,, Allah ya sada mu da rahamomin sa na wana ranan, Ga irin al,adun buki na garin birnin kebbi, a, da sati biyu ne, amma i, zuwa yanzu an rage zuwa sati ko kwana hudu, A cikin wa "yan nan kwanakin ne ake gudanar da abubuwa da dama, Musali zuwa gyaran dakin amarya kafin a sakata a lalai, Daukan darasin amarya ga malamar da zata koyar da ita, zamantakewa aure, mutane daban daban zasu dingawa amarya huduba kala kala, Tun buki da sauran sati biyu za,a fara gyara amarya da kayan hadi na gargajiya masu kyau da ma,ana, Hakan ya kasance a gidan malam tsoho wanan satin, Don jikokin shi biyu da akasa a lalai a lokacin wanda duk dangi na kusa da na nisa sun iso wanan gidan, Sai hidima kawai ke ta kankama akowani sashe na gida, Sashen Baba Samaila ba wasu bakine sosai suka zo ba, Don bukin ba na yan dakin su bane sanan ba wai wani zaman lafiya bane a tsakani balle yan uwan su na sashen mahaifiyar su su zo masu kara, Wana sai in Allah ya gwada muna auren yar lelen baba watau Meenatun sa, Duk wanan abin dake gudana hankalin Anty Samira yana gurin yar uwar ta Meenat, Shakuwan Samira da Meenat ya samo asaline ga tashin da Meenat tafara yi a gurin Baba Buhari, Watau a hannun mama Ladi wacce ta yayye ta daga nono, Sai dai daga baya da matsi yai matsine Baba samaila yashafawa idon shi toka ya karbe diyan shi wacce aka mayar tankar boya, Mutane da yawa sukan ce wa meenat yar dakin Samira don samira bata yarda aiwa meenat wani abu, idan ta na gurin, Haka ke sa mama kara jin haushin yarta Samira akan yadda take nunawa meenat zumunta mai karfi a tsakanin su, Samira wace, itace ta saka meenat a cikin manyan yan matan gidan da karfi da yaji badon ta isa ba, Kuma babu yadda zasu yi dole suka kyale Meenat ta bi su don masifan Samira, Masu zuwa gyara dakin amare yau suka tafi don su gyaro mata inda duk da samira ce babba itace ya kamata a fara gyarowa Amma sai mama tai tsaye tace sam sai andawo gurin gyarawa Murja nata tukun, Hikimar mama da yin hakan shine, wai kada a fara jerawa Samira kaya suga wani abu suce suma zasu sayawa yar su, Don haka mutane sun san masifa take so dole aka nufi gidan murja dake bayan Owando aka fara gyarawa, Sosai ba laifi gidan murja yayi kyau don mijin yayi kokari, Yaro ne matashi yana aikin gwaunati a gidan taki, Andawo cikin murna da sambarka tun a kofa mama ta kasa hakkuri sai tambaya takeyi ya aka ga gidan na murja, Yar guda ce Safiya ta ja ta zuwa gefe tana cewa ha dai Innar mu shin mi ki ka yi haka wai ? Da Samira,da murja ai duk guda na ko? Ansa mama Ladi ta bata da cewa a gurin ku suke guda ko? Nikan a guri na ai diyan kishiyoyi na, na, To Allah shi kyauta innar mu, Amma don Allah ki ko karta ki boye kishin ki a kai, Diyar ta guda mai suna habiba itace tazo gurin da suke tsaye tana cewa, Innar mu ke ji dai ko kwatan Samira murja bata kama ba ko, Ai da sunga an fara fitar da kayan Samira nasan du girgiza zasuyi, Habiba had ke ya,? Shi ita Murja wai ba yar uwar ki ta ba ? Ko yar uwata ta hwa,? Sai inki nawwa in kama ta ? To Allah shi kyauta inji safiya, wacce ta kula da cewa baza su daina abinda su keyi ba, Jeran samira abinyaba wa mutane mamaki sosai don an nuna mata gats an, nunawa mutane cewa ita yar dangi ce,,, Don kamai da akewa amare masu gata anmata agidan ta, Sai,dai matsala guda shine, Murja tafita samun miji na kwarai sosai kuma tafita samun gidan aure, Gara na gani na fada aka kai masu wanda malam tsohone da kan shi ya hada masu wanan garan , Sai,dai ita mama ladi wacce ta kara akan wanda malam din yai masu, Zaune take tana gyara yan yatsun kafan ta wanda suka sha zane, Da kwalliya, anty amarya ce takira mai mata zane har gida tazo ta zana masu ita yar ta da zasu,yi wa meena rakiya gurin buki, Kitso da kumshi yar asali akai masu zanen dashi, Wayan ta Nokia da ke gefe yai kara, da sauri takai hannun ta ta dauka ANTYNA SAMIRA, Shine baro baro ga screen din wayan ke boring, Murmushi meenat ta sa,ke tana cewa sai Anty na Da Assalamu Alaikum kamar kullun ta daga wayan tana mai yi wa antyn ta dariya, Amma Meena walleh ke ban mamaki ace har anfara program baki taho ba, Gashi nasan cewa Anty amarya zata ba da sakon da ta ce ki kawo min, Ba hakana na ba Anty Samira, Tsayawa nayi in rubuta test yau gobe tun da safe in sha Allahu zamu tahowa, Ke da suwa na zaku taho ? Ni daina kataho mana, mtss taja tsaki aza nayi da Anty amarya zaki tahowa, To ai ke san mama bata gaiyyace su na ba, da sun taho ko da yini na, To goben sakko zakiyyi ko ? Awo, insha Allahu koda sha biyu kayi muna cikinkin garin birnin kebbi to da ke kyauta gaskiya, Don dai kesan kuna na hannun damana ga wagga harkan, Kai anty Samira, ga manyan yan mata mi akai da yan kananun yara iri na, To ke dai ji na hwada maki sai ke taho ke nan, To Anty samira agaida gida,,, Ajiyan zuciya Meena tayi gami da lumshe idon ta, Allah sarki Anty Samira yanzu zata bar gidan mu ke nan ta fada acikin sabon rayuwa, Ita ma , watarana irin haka zaizo kanta ranan da zata bar gida tabar baba da maman ta da yan uwan ta zuwa gidan auren ta, Ajiyan zuciyar tayi don tasan cewa akwai aiki ga irin haka don ba karamin tashin hankali bane , Aure sha kan yaro inji manya, masu karin magana, A lokacin ne anty ta zo da leda ga hannun ta tace munyi waya da samira wai in baki sako ki kai masu shine na hado har da ita dayan amaryan tunda duk yan uwanki ne, Godiya Meenat tai mata, a cikin mutun tawa, Karfe sha daya da rabi suna Ambursa, kafin, sha biyu cif sun shigo gida, Tun a kofan su meenat ta gane cewa buki ake sha a gidan su, Saboda bakin fuskokin yara da manya da bata sani ba da ya cika katon iccen dake kofan gidan nasu, Acan kuma dan nisa da gidan su gidan makwabtan su kidan D,J ne ke tashi yara da yan mata suna ta kwasan rawa, Murmushi Meenat tayi don tasan cewa malam tsoho ke nan ya hana a kunna masa kida a kofan gida,,, Saboda diyan Anty amarya Meenat tazo shi yasa uncle ya bada motar shi wani dattijo driver makwabcin su yakawo mashi su, har birnin, kebbi, Idan kuma sun gama buki sai ya dawo ya kwashe su komawa gida, Cikin wani yadin Swiss material blue colour take, dinkin dogon riga mai dogon hannu, shara,shara, Sai farin gyale dan karami, wanda tai rolling din kan,ta da shi,, takalmin masu dan tu,du,, ta saka a kafan ta,, Kayan jikin na ta sun matukar karban jikin ta sosai sai dan farin glass da ta, saka a idon ta don kare, kurar hanya, a idon ta, Yaran cikin gidan su ta samu,su kwashe mata kayan su, zuwa cikin gida, Gurin da rufar malam tsoho yake a ciki,ta nufa tana rike da hannun yan kan,nen ta da suka nace sai sun biyo Anty zuwa buki gida, birnin kebbi, Ita kuma anty amarya saboda ta mayar wa Meenat da mahaifiyar ta da irin ko,karin da suke masu wajen zumunci ta yarda aka tafi da yaran ta, Da sallamar ta da murmushi manne a fuskan ta ta karasa zuwa gurin da yake zaune, da littafi mai rubutun warash, a hannun shi yana dubawa, "A hho, malam ; Har ya ce in,gwaiyya kan shi a duke azaton shi daga cikin yan jikokin shi dake agari ne masu shige da fice, suke gaishe shi, Sai kuma yaji muryan kamar na wacce ya dade da sani a da can, Da,sauri ya dago kai daga kallon littafin da ya ke yi na, Risala,,,, Ameenatu shin ? "Ke ta atta tahe yanzun ? Awo malam nita a,daidai lokacin da suke cire takalman kafar su don karasawa gurin malam din, Har kasa gwiwa bibiyu suka rusun na ita da yaran da ta zo da su yusura da didi, Gaisuwa sosai sukayi da tsohon kakan nata inda ya ke tambayan ta mutanen sokoto,, Yaran da take tare da su ya kallla yara masu kyau da su bulbul dasu gwanin ban sha,awa,, Nan yake tambayar ta diyan gurin kawun ta ne wa yan nan yaran ko,? Meenat taba shi ansa da fadin en malam duk kan su diyan amaryan shi ne da take gurin ta,, Ya jinjina kai irin na manya tare da kara masu sannu da hanya, Daga haka ta mike ta na rike da hannun yaran har zuwa sashin su inda takeyi tana gaisawa da duk wanda ta hadu da shi wanda ta sani,,, Mama Saratu tai murna kwarai da zuwan diyan yan uwan ta gurin ta, Alokaci guda aka fara gwada wa yara gata da kauna, Meenat bayan ta huta tamike tsaye tana cewa mahaifiyar zata ta gaida mutanen gida sai taga su anty samira, Jinan Inkyau, sunan da take kiran meenat da shi ke nan, Kiyi nisa da maman ku Ladi don bata jin kunyar tozarta ki cikin mutane, Balle ma mama ai nasan sai tayi babu mutane ma tai mun balle yau ga jama,a,,, To ki dai bi sannu ban son abin magana sam a rayuwana, To mama insha Allah Kusan duk sashen da ta leka suna gaisawa cikin mutunci dakuma yi mata sannu da hanya, A kofan shiga sashen mama Ladi suka hadu da Samira wace ke shirin fita daga lungun nasu, Ihu samira ta sa don murnan ganin Meenatu alokacin Ihun da ya jawo hankalin mutanen dake daga cikin sashen mama Ladi, Mama ladi wace take zaune tare da yaran ta suna kokarin hada kudin sayen robobin rabawa mutane, masu zuwa walima yau, Gaba daya hankalin su ya koma gurin su Samira da meenatu da suka makale junan, su don murna, Wacce tta ayar can ? Inji habiba antyn Samira sai Safiya ta ba da ansa da cewa killa kawar ta ,ta taho ko ? Caraf mama tace wacce kawar ta Amenatu ta fa diyar baban ku Samaila, Gaba dayan su lokaci guda suke cewa, Amina shim? Yanzu Amina ta, ta,koma haka ? Mama Ladi tace, badole ba tunda iyayyenta sun sake ma duniya ita, Wai wata yar bariki karikon ta matar kanin uwar ta, Daidai lokacin da Meenat ta karaso zuwa gurin da suke zaune , Har kasa Meenat takai tana gaida su a cikin ladabi, Sai cewa suke yi Shin Meenatu, ke ta haka ? Yaushe rabon da mugan ki a idon mu , Dariya kawai meenatu tayi gami da mikewa tsaye a lokaci guda, Rungomota Samira takara yi tana cewa gaskiya kamata yayi in fushi da rashin zuwan ki da wuri haka? Anty Samira na fada maki test nayi jiya shi ya hanani zuwa da wuri, ok, haka ne kin kuru, Bakomai tun da gashi kin zo yau din kinga ai ayi wasu events da ke,, Ok Meenat barin je in fara shiri kin san yau zamuyi kauyawa day, A gurin program din ne take jin cewa wai za,a hada Aisha ko,yar wurin baba shaibu aure da Yaya Abubakar idan yadawo,daga England wurin karo ilimi, Meenat azuciyar ta tace aiko da mai shi ta shiga uku,,,,, ****** ******** ****** Anty Sadiya wace mijin ta ya bari Abuja zaune ya wuce zuwa England, Daga can ya kara turo mata da kudi ta hannun Salawatu, Wanda zata tafi birnin kebbi don halartar bukin kaunar shi Samira da sauran sisters din shi, Inda ya bata sakon wasu kudi don ta karawa mama,Ladi idan taje, gurin bukin don buki akwai cin kudi sosai tun dai irin bukin mutanen su na hausa, Wanda za,a kashe zarahi kamar ba gobe kuma ? Isowar Sadiya garin nasu gidan mahaifiyar ta Hajja ta nufa direct, Duk sha,anin da akeyi bata leka ba sai yau da za,a yi sisters day, Ko shi bata so zuwa ba saida yan uwanta suka dinga mata korafi da cewa halin nan nata baida kyau ace mutum yazo buki a gidan mijin shi amma bai taka ba ko sau guda, Wanan ne dalilin halarta da tayi yau a tare da yan uwan ta su biyar, Jama,a sai wani kallon ta sukeyi, don ba wani canji a tare da ita, Ankon din pink lace akayi da blue din goggoro , Baba Samaila shine ya sayawa Meenatu kuma yabawa wata matar wani abokin shi soja ta dinka mata, Kowa kagani aranan cikin pink lace da gwaggoro blue,, Amarene kawai aka banban ta su da sauran mutane inda suka sa Fararen lace masu kyau da daukan ido, Meenat wace ta gyara jikin ta tsab tafito kamar wata tauraruwa, Don ba karamin kyau shigar yaiwa meenat ba don duk wanda ya ganta dole ya yaba da shigar ta ga kyau ga diri, da zati,,, Mutane sai zolayar ta sukeyi da tafito suna cewa wanan kyau haka meenatu sai kace kece amaryan, Murmushi kawai meenatu take masu duk wanda yace mata kai kin yi kyau sai tace nagode kawai,, Tun daga nesa ta hango matar yayan su Abubakar zaune tare da yan uwan ta, Yar su habiba tana tsaye tana magana da su, a lokacin, Gaba daya suka waigo suna kallon meenat din wace alamar hakan na nuna cewa ana yin zancen mutum a gurin, Gurin su ta nufa kai tsaye inda ta gaishe su cikin girmamawa, Ga mamakin Meenat sai taga Sadiya ta nuna tankar bata san ta ba, Hakan bai wani bata mamaki ba don sanin halin ko inkula da mutane irin na Sadiyan, Tana rike da hannun yan kannen ta suka kara gaba abin su, Anyi ta rawa da cashewa amma sam meenatu ta ki yarda tai rawa ko sau guda acewar ta su jikokin malam ne, yin rawa gare su zubar da darajan gidan su ne, Washegari wankin amare don haka ranan buki ne sosai, Kamar yadda kowa yasan yadda al,adan bukin birnin kebbi yake ranan jumma,a ake wanke amare, Asabar ayi wanka, to shi wanan yasha bambam don malam tsoho yayi tsaye yace sai dai ayi wanka Alhamis, saboda shi jumma,a zai daura auren yayan shi, Inda yace mutane ne basu gane ba da,suke daurawa yaran su aure ranan asabar sabanin da da akafiyi ranan jumma,a, Inda yake cewa ta ya ya zakuji cewa an hana yin abubuwa a wanan ranan asabar din sai kuma hankalin ku ya gushe shedan ya rude ku, ku koma daura auren diyan ku a sabar din, Asabar fa wata rana ce da hatta wanki da yankan akai fa da kitso ko gyaran kai a hanemu dayi a wanan ranan don gujewa masifofi, Amma wai shine a yanzu jama,ar mu suka mayar wai ranan daurawa diyan su aure, Don haka shi yace jumma,a ce za daurawa su Samira da murja aure, Dole aka maida wankin amarya ranan Alhamis, a can G,R,A za ayi wankin amaren kamar yadda aka saba, Buki yakai buki inda jamaa yan uwa da abokan arziki aka hadu aka gwadawa wa yan nan ma,aurata gata duk kowani fannin both angwaye da amare, Meenat wace Allah ka,dai yasan yawan masoyan da ta samu a wanan shagalin Cikin ma tana boyewa bata faye fita fili ba sai can ba,a rasa ba,,,, ZEEE MAKAWA YELWA 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 2⃣4⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA ALLAHA-AL-MUSAWWIR Bayan an sauko daga sallah jumma,a ne, din,bin al umman Annabi suka taru a kofar gidan malam manya don sheda daurin auren jiko kin shi,,, Mutane da kauyu kan garin birnin kebbi, dama cikin garin sun shigo saboda sanayyan dake tsakanin su da wanan tsoho An taru inda tsohon malami, ya bukaci manya diyan shi da su wakilce shi, ga daura auren, Abin mamaki sai ga Malam din ya,bukaci Baba hamza da Baba shaibu da su matso gaba yace su yake son su fara karban auren, A take gurin yai tsit, ana sauraron tsohon dattijon irin yadda ga Baba Buhari a zaune amma ya gabatar da yan kan,nin shi a gaba, Anan ya umurci Baba Shaibu da ya amshi waliyancin dan shi Abubakar shi kuma Baba Hamza ya karbi na diyar shi Aminatu, A take jama,an gurin suka fara kalon kalo suna mamaki kowa da irin abin da ya ke fada agurin, A bokan Abubakar da suka zo daurin auren kan,nen abokin nasu, ta sanadin shi, sai mamaki suke yi a lokacin, Ba baki ba har yan gida sun shiga cikin rudani, saboda sam basu zaci cewa,, Ameenatu malam tsoho zai ce zai aurawa Abubakar ba, Saboda ai ba daki guda mahaifan su suke ba ,ga su , su da suke daki daya da mahaifin shi, ai, "ya,"yan su ne ya kamata a hada dashi, din, ba sai anyi wani dogon shako ba, har zuwa sashen Baba Samaila, Dole badon sun so ba aka daura wanan auren mutane na ta mamaki, Baba Samaila wanda yai mutuwan zaune saboda duk ilahirin jikin shi zufa ke fita, don tashin hankali, Shiko Baba Buhari sai cewa yayi Alhamdulillahi, Allah mungode maka da kabar muna,wanan tsohon namu maitarin alheri, Daga haka kuma akasa baba Samaila ya bada auren Samira, inda Baba Buhari tabada auren Murja, Wanan abin yai wa din,bin jama,a sha,awa irin yadda tsohon yai hikimar hadin kai a cikin zuri,ar shi, Sadakin kowace diya mace dubu sittin ne don haka kowace a ka mikawa waliyin ta, Daga haka masu sanarwa suka fara shedawa al,umman dake daga nesa, Maroka mata sukayo cikin gida suna guda da shewa yau Allah yayi an,daura auren Magajin malam Abubakar da Aminatu Samira da Aliyu, Murja da Dauda, jama,a sun sheda yau kun zama amaren angwayen ku,,,,,,,, ****** ******** ****** Meenatu da gwago Habiba wace suke cewa gwago Habi, ita kadai ce kauna ga mahaifin meenat din, Hira sukeyi akan yadda mamata hana aba gwago Habi abinci tun zuwan ta gurin bukin, Mama Saratu mahaifiyar Meenat tace gare ku wanan abin yake bako ko? Naga hakan ai kadan ke nan daga cikin halin mama Ladi, Baku ganin ko mariya diyar ta da yake bata da komai kuma a kauye take zaune ai kun ga bata hurdan komai da ita, Gwago Habi tace ai tayi abin ta wata rana sai labari don Allah bai manta da kowa ba, Muryan maroka matan da sukaji ya kaule gida shine ya dakata da su daga hiran da sukeyi, Kamar amafarki wata mai murya rarara, ta sake cewa yau Aminatu ta zama matar Abubakar inji Allah Samira matar Aliyu Murja matar Dauda, Gwago Habi tace ji mashiririciyar can abin da take cewa bata ko san sunayen amaren ba,,, Again wata mai babban murya daga cikin marokan ta,kara maimaita abinda ta farkon tafadi, Wanan marokiyar bata kara fadin zancen su samira ba sai ganin Meena Gwago Habi tayi ta mike zubur, Itama din mikewa tayi don mamakin abinda sukeji a na fadi daga wajen marokan, Guda mai karfi wata daga cikin dangin malam, tsoho da ta zo daga kauye ta rangada, zuwa sashen Baba Samaila din, Abin da ya kara tayar masu da hankali kenan gaba daya, Isowar matar tana wanan guda tare da,wasu daga cikin dangi yasa,Meenat cewa Ya Abubakar shin ? Sai ganin ta kawai gwago Habiba tayi tai kasa, a somay, Kururuwa jama,a suka sa wanda ya jawo hankalin sauran al,umman gidan, Ruwa aka zubawa,meenat din masu sanyi wanda yasa ta farfado cikin dan bude idon ta ahankali, Sai ganin jama,a tayi still, a kanta dafifi, abinda marokiyar nan da gudar matan nan ya fado mata a rai, Hakan ya kara,sata sumay wa again, a take duk gidan ya rude, Wanan karon duk jikin meenat a jike yake, da ruwa Amma shiru bata farko ba don haka aka fadawa maza a waje, Ba bata lokaci mahaifin ta ya sukkuce ta zuwa motar shi, Asibitin Sir Yahaiya ya nufa da ita, inda aka bata tai makon gagawa, Bude idon ta sukai arba da mahaifin ta wanda fuskan shi kawai zaka kalla kasan yana cikin mumunar ashin hankali a lokacin shi ma, Sannu Amenatu Baki ta bude da zumar zatai magana amma sai ta kasa saboda kukan da yazo mata, Muryan gwago Habi ce taji a lokacin wadda batasan tana gurin ba alokacin sai yanzu, Gwago Habiba tana cewa haba Amenatu kibi abin a sannu mana wanan irin tashin hankali haka, ? Mikewa take kokarin yi daga kwancen da take tana cewa Gwago Habi kiwa Allah ku cece ni ku ceci rayuwa na ban iya zama da mutum irin yaya Abubakar, Gwago Habi ce ke cewa Baba ya akayi haka ya faru ne yaya,? Bai kai ga bata ansa ba wayar shi tai kara, yana dauka yaji muryan Ibrahim yana cewa baba don Allah duk inda kake ka dawo gida ga mama Ladi nan tana tawa maman mu masifa da kidan zari a cikin gida, Da sauri Baba ya juya yana fadin ina zuwa habi ki kula da Amenatu kafin in dawo, ****** ******** ****** Tun a wajen gida yake jiwo muryan mama Ladi yadda ta ke budan baki, Wallahi wanan zancen baiko yuyuwa wanan ma ai karya ne, Duk muna funci da kilibibin da kuka kulla a gidan nan, Kan ku zai kare may ake da irin fulanin gwandu irin tsiya, Wallahi wanan sherin sai kusan yadda zakuyi da yar ku, Badai in hada zuri,a da irin ku ba wanan ma karya ne, Ke Ladi tajiyo muryan baba Samaila daga bayan ta yana kiran sunan ta, Wallahi ki kama kan ki ki iya bakin ki, Abinda kika sani ne in badon magabata ba bu abin da zai sa in hada wani alaka dake, Baki masan may kikeyi ba da baki zagi mutanen gwandu ba, Don ko mutanen gwandu sun gama maki komai a rayuwa, Sanan ki sani duk na karajin kin yi wani mumunan furci akan wanan abin yanzu zan gwada maki cewa karyan hauka ki ke yi, Nan mama lafi ta juya da fadin mahaukaci kawai wanda Alluran soja tai ma yawa a jiki, Nadai fada maku kusan yadda zakuyi da yar ku don ni dana yafi karfin lalataciyar yar ku,,, Juyawa tayi zuwa sashen ta a cikin masifa da jidali a bakin ta da zuciyar ta, Mama saratu tayi kuka sosai ta shiga cikin tashin hankali, Tana rike da hannun yaran da Meenat tazo da su daga sokoto, Su ma yaran ganin halin da antyn su ta shiga yasa su yin kuka da ihu, Duk wanan abin da akeyi malam tsoho ya sane da komai amma kala bai ce ba, Don dama abinda yake son ya shawo kan shi ke nan agidan tun yana da rai, Baba Buhari wanda ke zaune, kusa da malam wanda aka hana shi shiga cikin gida don gudun masifan mama ladi Saboda shigan shi cikin gidan babban fitina ne tsakanin shi da matar nashi, Haka yasa malam tsoho ya hanashi motsawa ko nan da can, Daga gadon da meenatu ta ke kwance ba abin da takeyi sai hawaye da kiran sunan Allah, Baba yadawo nan meenatu tadage a kan don Allah amaida ita gida, bata jin ciwon komai ita, Ba mussu aka sallamay ta zuwa gida inda tun a hanya Baba Samaila yake fadawa, gwago habi yadda suka kwashe da mama ladi a gida, dazun bayan zuwan su asibiti, Maganar manya ce ita meenatu sai ajiyan zuciya kawai takeyi don abin ma izuwa yanzu ya wuce tunanen, ta, Tankar a mafarki ta ke ganin zancen wai ita meenatu ce yau wai mata a gurin yayan su miskili Abubakar dan mama Ladi masifaffa da ko mazan gidan su iyayyen su tsoron fitinar ta suke yi Saboda bata da kunya a cikin al,amarin ta sam, don haka ne ma kowa ke mata daukar mara mutunci, ko mara hankali,,, Daidai lokacin da take ajiyar ziciya yaji muryan mahaifin ta yana cewa , Duk iskanci ne da hankalin ta guri ta samu takewa mutane wanan iskan cin Yau ai badon ta gudu ba da taga karyan haukar da take kira min, Gwagwa Habbi ta ce kafita batun ta kawai yaya don babu yadda zata yi da mu acikin hidan mu, Bari kiji habbi, duk Ladi ta taba min diya wallahi sai ta gane kuren ta, Duk wanda ke a kofan gidan a lokacin da aka dawo da meenat daga asibiti sai tabaka tausayi, Gwago Habbi tace kija mayafin ki zuwa kai don yanzu kina da nauyin akanki hakkin aure ya rataya a wuyan ki, Ita da kanta tasa hannun tana gyarawa meenat gyalen da ta dan yafa ajinkin ta, Wasu irin hawaye masu zafi suka fito daga idon ta, Yau don takaicin tsohon kakan ta ko kallon gefen da yake zama batayi ba haka tashige cikki rungumay a jikin gwagon ta. A sauran sassa gidan kuma wasu harda habaici suke sakewa wai ai dama mutum kurum kurum mugune, Yawan shirun mama saratu na mugun tane don itace tabi dare tabi rana gurin shige da fice irin nasu na fulani har tasa aka aurawa Abubakar yar su, Wasu kuma suce ai baba Samaila ma tsohon mugu ne don shiga dajin da yakeyi ba na banza bane, Ai mama kawai nata ya samay ta tunda ta hada irin mu acikin jikin ta yanzu, Wanan zancen nasu ya kara haukata mama Ladi sai,kawai ta figi mayafin ta sai wurin malam tsoho da kukan ta Tana cewa ita don Allah malam ya walware wanan hadin da yayi ya bawa Abubakar ko wacece amma dai Meenatu ba wace har gaba da secondary iyayyen ta suka tura ta har sokoto, Sai a wanan lokacin ne malam tsoho yai magana tun lokacin da take ta faman hauka a cikin gida da zafe zage, Cikin maganar shi irin tamanyan jiya yace, To Ladi haukar taki da akace kina dashi ne kika taho ki geada min har nan waje, Kunya taji tafara cewa ba haka bane malam gaskiya bazan taba yarda a hada min zuri,a da irin diyan su samaila ba, Murmushi Malam yayi ya ce ko kina da hujja akan hakan ? Shiru tayi yace to ki ta shi kije kiyi hakkuri, idan kuma baki hakkuri duk abinda zaki yi kije kiyi, aure ne kuma andaura babu mai rabawa sai mutuwa, Ganin duk kusan diyan malam suna gurin azaune lokacin yasa ta jan bakin ta tai shiru don tasan bazasu kyaleta ta zagi mahaifin suba agaban su, Gida duk ya rikice da surutu wasu naganin rashin dacewar haka wasu kuma basuga illa ga hakan ba, Meenat kan tun shigewar ta dakin mahaifiyar ta bata fito ko kofa ba tana can kuryan uwar ta saman dan gadon kata kon dake dakin ta takure, guri daya sai kuka takeyi a cikin gumza, Ita ma mama saratu kukan takeyi zaune daga kofa saboda bata kaunar fitina arayuwar ta sam, Anty Samirace tashigo tun daga kofa take cewa ina matar yayan nawa nazo muyi bankwana kafin in wuce don nasan da wuya mu hadu anjima, Ganin yadda meenat take kwance bakajin sautin komai sai kukanta dake tashi a kuryan uwar, Dan dafata tayi cikin tausaya mata tace Meenat don Allah kiyi hakkuri ki daina wanan kuka har asan abin yi, Amma ni hakkuri kawai zan baki don kin san halin malam tsoho, Tunda yadaura ya daura ke nan sai hakkuri, Kamar ta yayafa mata fetur a take takarasa wani sabon sautin kuka a lokaci guda, Haka Samira tamike zuciyar ta sam ba dadi taiwa mama saratu sallama da gwago habi ta wuce ran ta a bace,,,, ZEEE MAKAWA YELWA 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 3⃣3⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA ALLAH-AL-BAASIT,,,, Duk musumi na kwarai idan har,lokacin tashin sallah asuba ya yi Da zaran wanan time din yayi zaka ji tankar an tashe kane, daga barci komai nauyin barcin da kake yi, A irin wanan yanayin ne ni Meenat na farka daga barcin da ya dauke ni tun daren jiya cikin kuka da magiya, wa yaya na, Abubakar, Akan wasu abubuwa da tun muna yara ake muna horo akan su na mu kiyayyi yin su da wasu mazan Amma sai gashi yau yayana dan uwana jini,na yana kokarin yi min shi acikin wani irin yanayi, Farkawa na, nayi duk jikin na ya na,man, nauyi, don ban taba sanin irin wanan rayuwar ba,,, Na dade a kwance ina son tashi amma nauyin jiki ya hana ni,,, Gashi ina tsinkayo kiran sallah a can nesa da anguwar mu kadan, A cikin dauri ya na dan iya mikewa zaune daga kwancen da nake, Wani irin zazzabine naji ya ziyar ci jikin na wanda ya kara man nauyin jikin,a lokaci guda, Da taimakon bangon dakin na samu har na kai bayin kamar yadda Anty na cikin hikima tai man hiran wata yarinya da irin abinda yasamay ni a yanzu yafaru da ita, Heater ruwan zafi, na kunna, wananda shi ya taimaka man har na dan ji daman jikin na,wa, Sallah na gabatar inda nake zaune a takure na nade kafanna babu abinda nakeyi sai hawaye, shar, shar shar, Tiryan tiryan abinda ya faru da ni a,daren jiya tsakanin na da yayan mu mafi daraja da kima a idon kowa na gidan mu abubuwan ne yazo man, a,zuciya, wani irin tashin hankali naji, Kara runtse idon na nayi ida wasu sabbin hawaye masu zafi suna gangaro man a fuska, Macen kwarai ba, ta son jikin ta Meena duk halin da take ciki zata san yadda ta yi ta taimakawa rayuwan mijin ta, Don haka kada ki zama ragguwa a gidan ki ke ma ki zage ki zama cikin mata masu kwazo da fasahan aure, Maganar Anty Amarya ne ya fado man zuciya na cikin ire iren nasihan da take min a lokacin da nake a gida Don haka still jiki ba kwari na mike tsaye tare da nade sallayan da nai sallah akai wanda Uncle dina na ne yabani da zanzo,,,,, Kitchen na nufa inda na kunna gas, na dora ruwan shayi cikin daurewa, A rish din da na gani gefe guda cikin store har sun fara rubewa na zabo na fara herewa a hankali jiki na duk ba kwari,,,, Kafin wani lokaci gida duk ya gauraye da kamshin dadi, saboda sanadarin da sa acikin girkin, Da kyat na samu na kamalla hada komai saman dinning table, din don zuwa lokacin zazzabi mai karfi ya rufe man ido, Ban yarda na kwanta ba alokacin, sai,da nai wanka Na dauko wani bakin jallabiya mai laishi da yawan stone a gaban rigan nasa,, Ido rufe na fada gado jikin na,na rawan sanyi sai wani iri nake ji, du kuma a tsorace nake a lokacin,, Bargon dake a gefen gadon na na jawo na nade kaina a,ciki inda na rufe fuskan na lif, da shi, Tun dawowan yaya Abubakar, daga massalaci, Yau yaji jikin shi yai mai wani irin nauyi, da kuma kasala da ya sauka mai, Ba dabi ar shi bane komawa barcin safe, sai gashi yau, ya tsinci kan shi da kara komawa barcin da safe, Kwance yake amma mafarki yake yi da wanan yarinyar kaunar shi da jiya tasa shi cikin wani halin rayuwa, Macijine mai wani irin suffa keta kokarin sai ya shiga karkashin wanan yarinya, dake ta fama neman taimako, Muryan yarinyar ne yaji daga cikin mafarki tana cewa La,illaha,Illah,Anta,Subbahanaka Inni kuntu minal Zalimin ,,,,, Da karfi yaga macijjn ya juya kamar hayaki yabar gurin Ita kuma ta zube akasan gurin a sumay babu numfashi atare da ita,,, Zubur ya mike don mumunan mafarkin da ya yi da safen nan Bakin shi na dauke da fadin A,uzubillahi, Innalillahi wainna,alaihim raj,un, Zauna,wa ya,yi a bakin gadon sannu a hankali ya fara dan tariyo mafarkin na, shi, Wani katon maccijine ke kokarin shigewa a jikin wanan yarinyar da ta shayar dashi abin mamakin da bai taba tsanmani samun shi gurin mace ba,,, A take kuma zancen mafarkin ya gushe mashi don tunawa da abin da ya faru tsakanin shi da yarinyar a a,daren jiyan, No, wander yake ganin wasu maza kamar sakarkaru ga matan su Abinda shi da farko bai taba sanin a kwashi ga mace ba da gaske ? Ya,dauka kawai cewa yan son mata ne da ke cewa wai mata suna suka tara, Wai wata tafi wata,, Daren jiya ya yarda daban yake acikin dararen da ya sani a rayuwan shi, Bathroom ya fada don yai wanka saboda yau a kwai aiki, monday ne, ga shi bai dauki hutu ba tun dawowan shi daga England bai huta ba,,,, Saye yake cikin wasu fararen suit masu manya manyan anini ,guda uku a gaban court din, su, Falo ya tunkara ya na dauke da yar jakar aikin shi a hannun shi, Agogon hannun shi ya ke ta ko karin daurawa a lokacin,,, Sai kuma hancin shi ya shako, mai kamshi maidadin shaka, a folon, Cikin mamaki ya kai idon shi a dining table din, su, Abinci ya hango yau a gidan shi, har an kamallah dafawa an,aje duk wani abin bukata, da wanan safiyan Bai tsaya yai mamaki ba don yasan cewa aikin bakuwar kaunar shi ce badai Sadiya, ba, In har bai manta ba al,adan iyayyen su matane tin shidda na safe angama hada abin breakfast,, Shi tun auren shi da Sadiya, shekar biyar da watan ni kenan bata taba hada mai breakfast ba wai don zai tafi office, ko kuma sun yi baki,, Babu kowa a gurin don haka ya aje yar case din shi a falon cikin takon shi na kasai ta ya nufi sashen dakin ta, Akwance nake kamar yadda, nake tun kwanciya na, ina ta makyarkytar sanyi daga cikin bargo,,, Daga cikin bargon yake hango yadda nake yi a fili, Da sauri ya karaso guri na yana fadin Subbahanallahi, Bargon ya yye fuskan ta ya baiyana ina kwance nade wuri guda cikin neman taimako, Mafarkin da yayi da ita da asuba ne ya fado mashi a rai, ya tuna irin yadda wanan macijin ke ta kokarin son ya cuta mata acikin mafarkin, shi, Da sauri ya rikoni zuwa jinkin shi abinda ya sani dan bude idona daga barcin wahalan da na ke yi a lokacin, Hannun shi ya kai ya fara tataba min jiki cikin kidimay wa yake cewa ba,kyajin dadi kuma ki ka fita yin girki, ? A hankali ya kara kwantar da ni gurin da nake a kwance, da farko,, Falon ya koma ya hado tea mai zafi tare magani pain relief Sai da ya tabbatar da cewa nasha shayin da ya hado min, Sai ya, miko min magani tare da dan yimin addu,oi a saman kai na, Ido ya tsura min duk da a rufe idona su ke amma sai da na gane hakan saboda yadda naji a jikina, A hankali ya mayar min da kaina saman filo tare da gyara min kwanciya ya jawo min bargo a hankali, Falo ya koma inda ya kwashi kalacin shi hankali kwance, Dakin Sadiya ya nufa ya tura kofa a hankali tana kwance saman gadon ta kaya ne ko ina a yashe a kasan dakin da saman kujeran dake daki,, Wani tsamin dauda ne kamar kullun ya daki hancin shi don bayau ne farkon jin haka ba adakin na ta,,,, Kwance take rub da ciki ta sake ko ina nata wai tana barci, Cikin takaicin wanan kwanciyar ya kalle ta Sunan ta ya ya ke kira a,cikin yar hasala "Ke; Sadiya manene haka wai, dallah gyara kwanciyar ki mana, Mika tayi tare da yin wani irin nishi sai kuma tafara yar soshe soshe, Ta dan dago kai tana kallon shi sai cewa tayi katafi kawai idan na tashi zan rufe gidan, Ke dan Allah tashi kin ji , cikin bacin rai, yace hakan a kuma hasale, Mika takara yi tare da mirginowa tana fuskantar shi, Har zaka tafi ke nan? Ke tashi ki rufe kofa ban son yawan surutu please ? Mikewa tayi dan sanin cewa ba wasa azancen shi ta ,mike ba don taso tashi zuwa rufe gidan ba, Tafe yake ta na bin bayan shi har zuwa falo ida kamshin girkin da ya kwasa ya shige hancin ta,. Gurin dining ta juya ta dan kalla a hankali inda ta hango kulolin abinci a saman table din, Har yasa kai zuwa fita waje, sai kuma ya ja ya tsaya, yana ce mata, Wanan yarinyar bata jin dadin jikin ta please ki dan kula da ita kafin na dawo,, Wani kallon raini tai mai batare da ta yi magana ba Ta koma daga gefen alamar tana jiran shi ya fita ta rufe kofan, gidan,,, ****** ********* ****** Tasha kwalliya kamar mai zuwa unguwa, ga makeup da taiwa fuskan ta,, Ànty Amarya ta na daga kwance a dakin ta bayan barcin da ta sha har ta gaji, ta tashi,, Wayan ta da ke saman side drower ta jawo, tare da duba sakon ni, da take da su, Sai kuma ta koma gurin contact din ta, don ta duba sunan wata yar uwar su, Sunan Meenat din ta ne, ta gani kusa da gurin sunan maimunan, Sai taga ai ya kamta ta, kira ta taji lafiyan ta, zuwa yanzu don tun dawowar su basuyi magana ba, Kamar ta kirata sai ga uncle ya shigo dakin ta cikin jin dadi da ganin irin yadda Sumaiyyan shi mace mai kwazo da kuma hankali uwa uba tarbiya ga tsabta da sanin ya kamata, ya caba ado badon kowa ba sai saboda shi,, Zaunawa, ya yi a bakin mirror suna fuskantar junan su shi da ita, Yace cikin murmushi, wanan kwalliyan ya kama ta a ba tukwuicin sa fa, Wani far tai mashi da idon ta tace aiko ba tukwaici tunda ka yaba shike nan, Tambaya ya jefo mata da cewa, Kina kewan yar ki ce halan,? Naga kin wani kwanta kin lafe kamar mai tunanen wani Abu a zuciyar ta, Murmushi tayi tana kokarin mikewa zaune tana fadin, Ai dole ne inyi kewan Meenatu, yarinya ce mai kirki ga ta da mutunci sosai, Amma kuma sai naga bata samu abokan zaman kirki ba daga matar har mijin,, Murmushin Uncle yayi don jin may tace mai a lokacin, Aganin ki ko ? Ni kan a bangare na ban ga matsalar komai ba gaskiya, Indai don ganin da ki kaiwa mijin ta ne haka na ai, ko ita Meenat din haka take, Kallon Uncle Anty tayi don taji yace haka Meenatu take ita ma, Uncle yace yes hakan Daga jinin, jikin yan gidan su, ne haka na din zaki gan su kamar ba su da sakewa, da mutane Amma sai idan ka zauna dasu zaka gane cewa, suna da sabo, so,sai Don kinga mun dan zaman da muka yi dashi na lokaci kadan mun fahinci juna dashi sosai, Anty Amarya ta nisa tana cewa tau ni dai, Allah ya, dau,kaka min diya ta, akan su, Uncle yace kaji masu diya ba son kai dai ba kyau, Cikin murmusawa da kallon irin na ya nayin kissan mata, tace mai,, Ai kai,ma, addu,an, zaka ta ya mu yi please,,,, ****** ********* ****** Zufa na diga jin yana tartso min daga cikin barcin da na keyi,, A hankali na yaye bargon da nake a cikki lulube, tun da safe, Ido na, bude a,hankali, inda nafara kallon silin din dakin a hankali, Launin silin din daki ya sa ,ni saurin tuna inda nake a halin yanzu, Ido,na na dawo dashi ga dakin a hankali ina kallon ko ina, A lokacin fankan Sama ne kawai ke dan aiki a hankali, cikin dakin, Karan waya na Nokia naji daga gefe na tana dan tsuwa, Hannu na mika daga cikin bargo na dauko wayan a gefen filo na, Bakuwar noba ce na,gani ke kirana, ban daga ba har kiran ya katse, 3 miss called na gani a wayan kuma duk dsame noba, ke kirana, Ina cikin tunanen ko laban waye ke kirana' haka ,? Sai naji an kara kiran na dakuma, wanan bakuwar, nobar dai, Dauka nayi batare da na ansa ba , Muryan namiji ne ,ke magana, Kin farka daga barcin ke nan ko ? Zazzabin ya bari ko ? Kin ci wani abu kuwa da kika tashi,? Tambaya uku a lokaci guda abinda yasa idona ya watsake har na gane mai magana alokacin,,, A cikin dan daburcewa na mike daga kwancen da nake ina kokarin mayar mai da ansa a cikin girmamawa,, Idon shi ya lumshe tankar ya na a gabana to ki,yi kokari ki ci wani abu a bakin ki, Na ansa da cewa to na gode, Mamaki yayi daga magana sai nagode,? Kashen wayan yayi inda ya mai da kan shi saman marikar kujeran shi yana dan juyawa a hankali, a cikin wani yanayin jin dadi, Irin abinda ya faru a daren jiya ya,sa shi lumshe idon shi, Malam Mudi ya shigo office din yana kokarin rufe kofan office din, Shugaban nashi ne yasa mu, a cikin wani irin yanayi na shaukki, Sai da ya kara sallama ya bude idon shi da yai ja kamar mai jin barci,, A hankali ya ce malam Mudi lafiya dai ko ? Cikin girmamawa da kallon yana yin ogan nashi, ya sashi dan tunane, Akwai wani sabon yanayi da shugaban shi yau yake ciki, Tun safe yake ganin shi cikkin cool action, Takardan da ke a hannun shi ya tura mai a gaban shi yana cewa yanzu, a kabani in kawo maka, Tarone watau, meeting na gagawa daga office din shugaban su, Acikin su uku da aka tura kasashen duniya karo ilimi ana da bukatan mutum guda wanda zai zama masu babban a counter, A karshe taron Allah ya bawa Yaya Abubakar sa,an cin wanan interview din Nan aka bashi wanan mukamin na a,counter din su na N,N,P,C, A take guri ya dauki murna da ihu cewa mukami ya dawo gurin dan arewa, Dama wani IBO ne ke rike da wanan mukamin tsawon shekaru masu yawa, Daga gurin meeting din ya na fitowa ya nufi Mosque din ma,aikatar su, Inda yai sallolin da ake bin shi, ****** ********** ****** Ban jin komai a jikina sai dai nauyin da yai min tun wayewan garin, Kitchen na fada inda nai muna abincin rana, sai dai kuma still akwai na daren jiya saura da kuma na safen yau da ya dan rage, Gashi babu wanda zan sa ya kira min almajiri abashi, sadaka, Kuma ban san ya zanyi da wanan abincin ba don gudun kar ya baci, Hijjab na dauko daga daki na sa na dan tsaya daga cikin garejin mota gidan, Daga ida nake tsaye ina jin motsin samarin nan, masu zama gaban gidan Wa yan da muka gani a kofan gida ranan da mukazo, Kamar an jefo wani daga cikin su ya dan zo ta kofan shigowa gidan namu yana dariya , Gani na yayi a tsaye abinda ya dan sashi cewa a, Ina wuni na ansa da lafiya, Tambayar shi nayi da cewa, Don Allah almajiri nake nema in abashi wanan abincin, Kallon kulan abincin yayi sai ya ce ok barin karba in fita da shi, Na mika mai na nufi cikin gida inda naci gaba da ai,yukana, don hada abincin dare da wuri tare da gyaran gida,,,,, ****** *********** ****** Wanan Saurayin yana fita da kulolin abincin duk sai sauran, suka zubo mai ido, har ya iso gare su, Abinci,ne inji, Amaryan gidan nan wai abawa almajirai,, Kulolin suka shiga budewa a hankali abincin dake cikine yasa su kallon junan su, Sai daya daga cikin su yace waiko kasan cewa tun safe rabon da in ci wani abu ,,, To ai kuwa yau gashi Allah ya tsaga da rabon mu ba bata lokaci suka hau abinci da ci, Gaba daya har na jiyan suka tashi dashi tas tare da zuwa gurin famfom gidan namu dake ta cikin gareji suka sha ruwa suka kuma wanke min kulana tasa, Bugun cikin shi ya yi yana cewa yau wanan matar ta ceci gayu wallahi, Allah ya saka mata tare da maigidan ta da alheri sauran suka ansa da fadim Amin Ina daga kitchen naji ya na kwada sallama yana cewa ga kula ya dawo dashi sun gode fa,, Karba nayi nakara wankewa na kife, Tun safe ban ga Anty Sadiya waje ba don haka na shirya cikin atamfa dinkin zanin rapper, Da Sallama na shiga sashen nata wani irin tsamin dauda yadan daki hanci na, Tana kwance a three seaters, ga plate din da ta debo abinci da ga falo har ya dan bushe,, Da cup din da tasha tea tun na safe, Ina wuni Anty ? Lafiya ta ansa a,takaice Shiru mukayi batare da wani yai wa wani magana ba, Ganin da nayi cewa shirun yai yawa ga kuma tsami na dukan hancina yasani cewa sai anjima, Ban tsan manin cewa ta ansa min ba a,lokacin don duk hankalin ta naga kallo, tv,,, Sai dai kuma tayi hakane don ta wulakanta ni, Saboda ita gani takeyi wai na aure mata mijin ta don rashin mutinci ****** *********** ****** Ko karin yake ya sa takalman shi a kafan shi, a daidai,kofan massalacin, Wayar shi tai kara inda ya dan dago yana karasa ,sa takalman nashi daga tsaye,, Sweet Mum ya,gani rubuce, a screen din wayan shi cikin murna da jin dadi ya dauki wayan don su gaisa,da mahaifiyar shi, Amma sai yaji muryan mahaifiyar nashi babu ko gaisuwa balle yaji dadin fada mata, alherin da ya samay shi,, yau, Muryan Mama a cikin fada, ya tare shi da cewa mai sunan malam ka bani mamaki, Yanzu ace an dauki wanan yarinyar har an,kai maka ita, gidan ka ba tare da na sani ba, Mama baki sani ba fa ? Yaya ko za,a bari in sani tunda ba alheri bace, Gaskiya mama na zata kina da labari saboda na ai mutanen gida ne suka kawo ta, Mama Ladi takara cewa cikin hasala mutanen gida muna fukai ko ? Saurare ni kaji da kyau ina son katurowa wanan tsohon da munafukin uban ta da yar su kafin jibi, Da karfi yace Jibi mama gaskiya sai kuma yai shiru don yasan maganar shi ma fitina ne, a gurin ta yanzu yadda ta hassahaka? Nafada maka cewa kada ka fara ka taba yarinyar nan, Ka turo ta gida ta dawo gurin iyayye ta, su kama abinsu ZEEE MAKAWA YELW@ 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 3⃣4⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA ALLAH-AL-KHAAFID Mamaki da,tashin hankali suka sauka mai a lokaci guda, Da farko yana mamakin,irin rayuwar mahaifiyar su, Wace, a,koda yaushe cikin fitànà take da tashin hankali da kowa na gidan, Bakamar Mama Saratu ba,wace take saliha da kowa mutunci takeyi a gidan, dashi, Ga halin alkunya irin na diyan fulanin asali, ko ba ka kaunar ta zata iya yi ma alheri ita, Sabanin mahaifiyar da har makwabta hakkuri sukeyi da ita a shiya, Wanan kalaman da mama tai mai sun matukar girgiza shi, ainun,, A hankali ya taka har zuwa office din shi inda jama,an ma,aikatan su ke ta zuwa yimashi murna, Sai,da aka dan rarage ne ya dan fara dawo da tunanen shi, Akan irin sharadin da Mama ta gidaya mashi akan Meenatu, Ya zai yi da umurnin da su Baba suka bashi akan yarinyar, Ya zai yi da alkawarin da ya dauka akan wanan auren, Waiko Mama tana tausaya mashi akan bukatocin ta Shigowa Salawatu tare da yan gungiyar ta mata ma,aikatan gurin aikin nasu, Yasa shi dakatar da tunanen da yake yi akan Mama, Murna sosai sukai mai tare da nuna fatin cikin su akan samun cigaban shi, A nan su ke gaya mai cewa zasu hada mai yar party don nuna farin cikin su, Tafiyan su bada dadewa ba shi ma ya shirya zuwa gida, Mamaki malam Mudi ya,yi da yaga cewa, yau zasu rufe da wuri zuwa gida, Sai da ya tsaya hanya yasai masu kayan da yasan za,a bukata a gida, Shi da kanshi ke kokarin shigo da kayan da ya siyo a hanya, Yaron da ya bude mai get na gani ya zo da sauri ya kama mai kayan zuwa cikin gida, da su,,, A gajiye ya karaso zuwa cikin gida yana dauke da case din shi, Zubewa yayi saman kujeran dake kofan shigowa falin shi, Yayin da yake ko,karin sauke Nick tie da ke daure a wuyan shi, Makullin buth din shi yaron da ya kwaso mashi kaya, ya mika mashi a cikkin ladabi, Minti kamar biyu yayi a zaune sai kuma ya mike tsaye, zuwa ciki, don bai ji motsin kowa ba acikin gidan, Ruwa ya watsa majikin shi don yaji sanyi, daga nan ya dan gyara dakin kwanan shi kamar yadda ya saba yi idan ya dawo daga office, Zaune take tana waya a saman kujera, kayan da ya barta da,sune a jikin ta tun safe har zuwa yanzu a jikin ta, Ba gaisuwa ko wani zance sai daga kai tayi takalle shi yayin da ta ci gaba da maganan ta a waya, Ganin irin yadda tai mai yasa juyawa ya koma falon shi duk da dai ya saba da halin ko in kula na Sadiyan, ****** ********** ****** Tsaye nake ina kokarin gyara filolin saman gadona duk da bawai sun yi wani abu bane, Jin shigowan mutum dakin yasani saurin dago kai,na da ke duke, Tsaye yake jingine da ban gon kofan dakin idon shi na zagaye dakin da kallo, Yana saye da wani farin jamfa, da wandon shi mai budaden hammata, kafan shi saye da wasu plat shoes, Idon shi ya sauke a kai na gurin da nake a tsaye bakin gado rike da filo a hannu na, Har kasa nakai, tsugunne ina mai cewa cikin sanyin murya sannu da dawowa ? Ansa yabani a takaice da cewa barka da gida? Wani irin nauyi da kunya sa ne suka lullubeni a lokacin, Bakina naji ya na cewa akawo maka ruwa ne, saboda yadda naga a gida idan iyayyen mu maza, sun dawo ake kawo masu ruwan sha,,, Cike da fara,a fuskan shi ya ce Alhamdullahi nasha ruwa don har wanka nayi, ko, Kaina yana duke a kasa har zuwa lokacin da naji muryan shi yana cewa, Ya jikin naki yayi sauki ko? Ban samu dawowa da rana in dubaki ba don yau meeting mukayi har zuwa wani lokaci, A dan kunyace cikin satan kallon shi nace ai ba komai naji sauki, A, hankali kamar wanda ya gaji yace Alhamdullahi, sai,dai ki kara shan maganin ki pls, Cikin kwantar da murya na ansa mashi da toh,,, Ido ya zuba min tare da cewa Meenatu kunyi waya da malam ? Damm naji gabana ya bada , Amma a cikin dakewa tare da boye razana na nace bai kirani ba,, Ok kawai ya iya cewa sai naga ya juya zuwa falo, Bayan shi nabi da kallon mamaki don sai naga kamar a mafarkine muke zancen nan,, Ban fitoba sai da gyara dakina tas nakara feshe ko ina da kamshin da Anty Amarya ta saya min , ****** ********** ****** Gidan ta a rufe yake don shiyan ta can yake daban da na mutane, Yinin yau mutanen gidan sun ga sai sintiri takeyi ta ta fama diban ruwa zuwa cikin sashen ta, Sai dai babu mai ikon tambayan ta don gudun masifar ta, Hankalin ta atashe sai masifa takeyi a cin ranta tana cewa malam tsoho aiko zaka san cewa ni Hajja ce, Karya kake wallahi, sam baza ka bata min shirina ba Ma zai taba yuyuwa ba ace Abubakar ya kauce muna, Shekara nawa ina amfana da al,amarin shi da zaka kawo min cikas, Kugin Dodon ta ne da ke jinya yau yasa tagane cewa ruwa yake bukata, Roban penti ta dauka zuwa bakin famfo inda take debo ruwan, Sai da ta cika katon radan roban da yake a ciki da ruwan san,nan ta huta, Abinda tai tayi ke nan rana saboda ruwa Dodo ke son ya shiga viki yau don yaji sanyi, Sai zuwa dare ta samu hutu sosai akan wanan bakar wahalan da jikanyar malam tsoho ta jawo mata yau, Dole ne gobe tunda safe ta tafi gurin boka ta sheda mai, TARKO da malam tsoho take ganin ya haka mata, Ita a yanzu tafi ganin laifin Mama Ladi da wace ta kasa tsawatawa dan ta, A gaskiya itama tayi kuskure da har ta yarda ta bada sunan gidan Abubakar da iyalin shi,,,, ****** ********** ****** Malam ya kamata ace mun kira yar baba don muji lafiyan ta aiko? Loman tuwon da baba ya diba daga cikin kula ya mayar, Cikin wani irin murya mai razanarwa ya,ce karki fara shi Saratu, Kada inji cewa kin kira wanan yarinyar a yanzu kubarta har ta kiramu da kanta, Mama Saratu sai kuma tafara cewa maigidan nata wanda taga ya hasala, Tace kayi hakkuri malam ban yi tunanen haka zai iya tayar mata da hankali bane, Tou kin dai ji abinda na fada maki kar wanda ya kirata, muddin ba ita ce ta kira ku ba, Abincin da bai ciba Mama Saratu ke kallo bata dauki cewa maganan zai iya bata mashi rai haka ba, Da batai zancen a lokacin da yake kokarin cin abincin shi ba, Muryan Mama Ladi ce suka jiyo daga cikin gida tana fada da kishiyar ta Mama Sa a Wai bata sa masu abin miya ba acikin miyan da ta aiko masu dashi, Mama Sa,a tace yau ba,a sayo abin miya ba sauran wanda ya ragene shekaran jiya na murje muna a ciki, Sai masifan fada takeyi a cikin daga harshs take sababin, Baba Buhari ya shigo gida tun daga nesa yake cewa ke arr da halinki ladi, Yanzun bakiji kunya ba ace harshenki har wajen gida saboda fadan abin miya, Kunya shin kunya fa kace ? Don na tambayi hakkina shine kunya malam ? Eh lalai kuwa Sa,a kin shigo da sa,a tunda har kin iya sa adanne ma wasu hakkin su haka, Ke dakata mara kunya inji Baba Buhari baki san kuya ba sam a rayuwan ki, Ace ina da Da kamar Abubakar amma sai naje yawon maula gurin jama,an Annabi, Wani kallon raini tajefo su dashi tace oho in da ka dogara ke nan dama, Yana can yana wahala yana turo maka ku na ci da wata mai babban duwawu, To na hana din baza a ci ba, To inkin hana kinyiwa kan,ki ai don gaki kina fadan naman miya ko kifi, Juyawa yayi gurin Mama Sa,a dake tsaye tana kallon ikon Allah yace ke shige ciki kar nakara jin muryan ki kuma, Shima wucewa yayi ba tare da ya tsaya kara ce mata wani abuba can ? Mama Ladi a cikin fada take cewa, ni nace kada ya kara taimakawa in dai har ba nawa zaifi yawa ba, Kuma yana aikowa din ni ce ke karbe naka in kana da karfi ka kwata mana, Allah ya shirye ki inji Mama Sa,a wace ke daga shiyan ta tana jin muryan Mama ladi ratatatata,,,,,, ****** ********** ****** Zaune nake bayan na idar da sallah ina karatun Alkur,ani maigirma kamar yadda munkayi agida, Muryan ta kawai naji don ban tsan manin tayi sallama da zata shigo dakin, Cewa tayi acikin wani irin murya Ki zo yana neman ki a falo wai,? Nima dai ban ansa mata ba sai ci gaba na yi da karatuna har nakai aya, Nashafa tare da mikewa don zuwa katba kiran da ake min,a falon,, Da sallama a dauke a bakina a lokacin da na karaso gurin da suke zaunen, Jugun jugun ba mai wa wani magana ita idon ta kuri a tv kamar bakauya, Shiko sai faman dannan wayar shi yake hankali kwance abin shi, Gaishe shi da wuni na karayi Sai a,lokavin yaya Abubakar ya dago idon shi ya dan dube ni Yace ya kike ? Na ansa a sanyaye da cewa lafiya lau, Ki zauna yace min a lokacin da ya mai da fuskan shi ga abin da yakeyi, Gefe na samu a kasa center carpet na zauna inda yadan dago kai ya kalle ni tare da sauke murmushi mai sauti, Gyaran muryan da ya yi ne yadawo da hankalin mu gaba daya gare shi,,, Ya soma da cewa Alhamdullahi na godewa Allah da ya hadani da ku a matsayin abokan zama, Nakirakune don in sheda makucewa yau Allah ya nufa an kara min girma a ma,aikatar mu, Cikin murna da jin dadin abinda yace, ya sani dago kai na, na kalle shi cikin farin, Wani irin sanyi da dadi gami da murna suka ratsa min zuciya na alokaci guda, Har na kasa boye farin ciki na afili, Kunshi na da anty amarya tasa akai min da zamuzo wanda har yau ya ke sheki kamar yau akayi shi, Saboda ya yi baki wulk da dashi ya zauna min akafa gwanin ban sha,awa, Shi nake kallo cikin mutnan jin dan uwa ya samu karuwa, Ban san lokacin da nace yaya mutanen gida ko sun sani ? Sai kuma nai saurin toshe bakina don ban san lokacin da tambayan yazo min ba, Ga mamaki na sai naga yai saurin girgiza kai alamar bai fada masu ba, Sharp ya manta da zancen yafadawa iyayyen shi asa mai albarka, ga al,amarin,,, Wayan shi dake hannun shi ya shiga dadan,nawa don kiran malam tsoho kakan mu Ji kawai nayi ya na cewa Allah Gafarta malam mun wuni lafiya, ? Da sauri na dago kaina don fahintar danayi da malam tsoho yake waya a ,lokacin, Gaisawa su kayi a cikin mutunci, tare da yar taba hiran tambayan lafiyan iyali, Shiru yadan biyo bayan sai yaya Abubakar ne yace malam dama na bugone in sheda maku cewa yu na samu karin girma a ma,aikatar mu Masha Allah Masha, Allah, Allah ya kara dauka ya rufa asiri, Allah sa wa zuri a albarka, Wani dadi yaya Abubakar yaji a lokacin don tun yana yaro rabon da suyi irin haka da malam, din, Malam yaci gaba da cewa, Sai ka kula da Amana, kwarai da gaske saboda nauyi ya kara hawan kan ka, takwarana, Wani irin dadi yake ji yana kara,shigan shi sosai don sam shi bai kawo fasan cewa ya fada masu ba tun rana, Amma ga yarinya karama ta bashi shawara mai amfani, Niko sam ban kawo komai araina ba danace hakan, Muna daga zane ni da Anty Sadiya wace tai tankar bata gurin ma lokacin don tabi lafiyan cushion tana kallon seasons film , Lokacin da na ga yagama wayan nace Allah ya sanya alheri acikin al,amarin tare da mikewa don barin gurin, Da katar dani yaya Abubakar ya yi da cewa , ji nan, Abinda yasani dawowa na zauna ke nan cikin natsuwa, Daga yau duk dare karfe takwas kowace daga cikin ku ta tabbatar da cewa tana falon nan har zuwa tara da rabi, Wanan doka ne da umurni na bayar bawai, fade ba, A tare za mu dinga cin abinci gaba dayan mu a nan dining, Saboda haka daga yanzu sai ku tashi mu je aci abinci, A nutse na dago kai ina kallon shi don dai ni a koshe nake,, Nasan yaya ya fahince ni, amna ba fuskan da zan yi comment, Dole na mike nabi bayan su inda ya umurce ni da in fara zuba masu tunda nice na girka, Kamshi ne kawai ke tashi gurin don kulolin da na bude,na girkin dare, Kafin na zuba wa yayan mu Anty Sadiya tace in miko mata plate ta zubawa kan ta, Saida ta shake plate bam da tuwon farin shinkafa miyan shuwaka, Kafin mubar gurin cin abinci, wayan mutanen gidane yafara zariya a wayan yaya, Babana shine mutum na uku daya fara kiran yaya Abubakar don yai mashi murna, Jin ya ambaci sunan mahaifina ya sani alokacin ina kokatin kwashe kuloli da plate din abincin, Da sauri na dan dago kai cikkin dan sauraren su ina jin dadin gani irin yadda yaya ke, magana tankar mahaifinn nawa yana a gaban shi ne, Lokacin da naga yaya ya dago ya dubi gurin da nake nai sauri na sadda kai na kasa, Saboda naji kunyan irin yadda nayi mashi a lokacin don na kasa boye murnan jin hiran su da mahaifina, A sanyaye nai saurin kwashe kayan don barin gurin don kar yai min magana, Sosai yaya Abubakar ke tajin dadin yau yan uwa sun nuna mashi kauna sosai, Fuskan shi dauke da yalwataccen fara,a yake kallon gurin da muke zaune, Ni dai tankar a takure nake gurin don duk ban iya sakewa a cikin su, Dan juyowa yayi inda nake zaune, tare da dan kura min ido, Kaina na kara dukarwa kasa ina wasa da yan yatsuna Muryan yaya Abubakar ne yana cewa hado min ruwa,insha, pls A cikin natsuwa namike zuwa kitchen sai yunane nakeyi, Ina shiga Kitchen na rasa may zan yi can nace to bari dai na dan hado mashi, simply drink,, Zobo drinks dana hada da rana shina juyo a jug na dora masu cups a saman tire, din A gaban su tsakiya nadire tire din ina mai cewa gashi yaya, Anty Sadiya wace tun zaman mu take wani basarwa, Anty ga drinks din nan, Kan ta, takawar gefe cike da jin haushi na ita a ganin ta muna hanata kallon ta alokacin ****** ********** ****** Malam tsoho wanda ke zaune yana dan murmusawa Saboda ganin cewa TARKO shi ya fara kama kurciya, Meenatu zaki iya, zaki iya na sani da zuciya guda zaki taimaka muna, Lalai idan ba ita yasa ba a halin yanzu babu wanda zai mashi yadda yake so, Wanan aikin sai mai hakkuri da juriya da kuma sanin ya kamata, Bawai sauran yaran ba su iyawa bane zasu iya amma da wata manufa, Bada irin manufar shi tayadda yake bukatan yayi kamu a,cikin ruwan sanyi, sosai,, Godiya yakara yiwa Allah Ubangiji Subbahanahu Wata,allah da tun ba akai ko ina ba har yafara samun yadda yakeso, Yasan cewa a sannu komai zai zo daidai insaha Allahu, Matsala guda shine irin yadda yasan cewa jikokin nashi na cikkin wani TARKO mai wuyan wallawala, Yasan cewa zasu yi daga sosai da Hajja a gurare da dama don ta dade tana mai barna acikkin zuri,an shi, Duk da yasan cewa bazata iya yin komai ba shine ma dalilin da ya bullo mata ta inda bata zata ba,, Ita azaton ta bai fahinci abinda take aiwatarwa ba kamar yadda take ganin duk gari kamar ba,a fahinci halin da take ciki ba, Da sannu zai nuna mata cewa wutsiyan rakumi yafi gaban yaro, Don shi malam tun farkon ganin ta yagane cewa muguwa ce, Abuguda saboda sun fito yanki guda da sarrakuwar shi kuma suna zumunci,, Hakan,ne yasa ya kyale ta yasa mata idon sai gashi har sunkai ga hada zuria dashi , Tunfarko ko haihuwa akayi agidan shi sai yasan abinda yayi agidan do shi mugu baya shiga gidan shi sam, Wanan dalilin ne yasa hajja bata zuwa gidan malam tsoho sam,,, ZEEE MAKAWA YELWA [7/27, 07:03] Anty Lantana: 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 3⃣5⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA ALLAH- AR- RAAFI,,,, JIN,JINA GARE KI UWAR MARAYU DA TAL,LAKAWAN KEBBI HJY DR ZAINAB UMAR SHIMKAFI ATIKU ABUBAKAR, MATAR GWAUNAN KEBBI STATE,,, KINYI MUN GANI WALLAHI AIKIN,KI NA KYAUGA MATA ALLAH YAJA ZAMANI KIN SA MATA ACIKIN HANYOYI RAYUWAN NA ALHERI,, MUNGODE KWARAI DA GASKE,,,,, Gidan yayi tsit baka jin komai sai karan na,urori dake cikin gidana kunne, sai kuma tsuntsayen dare da ke kuka jefi jefi, A zaune nake, saboda a kida tace hakan yar tocilar wayana ne nake hassakawa, Karatun na keyi a cikin littafi mai tsarki don tsoron da nake yawan ji a lokacin, Muryw kasa, kasa, acikin sautin karatuna da ba yabo ba don dadin sauraro, Ww Har ya turo kofan dakin ya shigo,kaina yana aduke, Daga kofa ya tsaya ya tsura min ido yana dubana da sauraro, Natsuwata da kwarewa na ga,karatu ya dauki hankalin shi ga saurarona, Bai katse ni ba sai da yaji nakai karshen sura dai dai lokacin da zan shafa ne mu kayi ar,raba da yayana a tsaye akofan dakin, a lokacin shi ma zai shafa,,,, Da sauri na dukar da kaina sai da kuma acikin zuciya na ina tuna nen may ya kawo shi dakina, Don a gidan mu da gidan Uncle da na zauna ai naga miji ba ya shiga dakin wace ya kwana again ,,,, Tafiyan shi naji ya na takowa zuwa gare ni kaina aduke ina kokarin aje littafina, inda yake, Cikin yar siriri yan murya nake mashi ina wuni, Zaman shi da ansawan shi sunyi daidai da daga kaina acikin mamaki, Wani irin kallo a cikin shu,umin murmushi yake sake min Ke nan ana nufin kin yi har da tulawa, a gurin malam Sai a lokcin na dan sake fusakana kadan nace ai dole, ne in dai agidan malam ne, Ya ai Babana yace min kai babban malami ne agidan mu don haka naji yana wa yaya Ibrahim fada Sai naji ya saki yar dariya yace to ai, Baba samaila Baba na ne ba naki ba ke kadai, Murmushi na danyi tare da gyada kai na ce shima Baban haka naji yana cewa, wai kai dan shine da yake ji da kai aduk gidan mu, Da alaman zance yai wa yaya Abubakar dadi a irin yadda naga ya lumshe idon shi, Can kuma ya bude idon shi a hankali ya kalli gurin da nake tsugune a takure, Da hannun shi yai amfani gurin buga gefen katifan da yake zaune, Ya mai kallo na kai tsaye yace zo nan ki zauna, Idon shi ya na kokarin mu hada ido cikin ido dashi, Daidai Gurin da ya dan buga da nufin wai in zo inzauna nake kallo a cikin mamaki, Dago kai nayi don in kalle shi amma sai ya daga min gira alamar eh,da dan rausaya kan shi, Yace ina malam yace ne kizo ki kula da yayan naki ne wai ? Wani iri naji a take hankali na ya tashi, abinda ya faru jiya ya fado min a rai, irin yadda yayan namu ya jagwalgwalani a daren jiyan, Kasa nayi da kaina yayin da wasu zafafun, hawaye suka ziyarci ido na, Saboda tuno min da abinda ya faru a tsakanin mu a daren jiya, No, No, bana son ganin wanan hawayen daga yau muddin kina gidan nan, Ban aune ba sai ji nayi hannun shi a jikin nawa ya,namai jawo ni izuwa gare shi, Saman ciyan shi, ya zaunar da ni, ya yin da ya ke kokarin daga fuskana, Subbahanallah, Meenat kukan may kuma a haka zaki kuladain din kina wanan hawaye haka, ? A hankali yasa hannayen shi yana share min hawayen, Yana mai kallon fuskana, ya ce, kin ga dakata muyi magana, da ke, Naga hankalin ki a tashe ya ke da ni Meena har yanzu, Ko dai, ba kya son zama da mune wai ? Idan har bakya son yanzu fada min in kira malam da su baba in fada masu sai su san yadda zasu yi da mu,,, Da sauri na shiga goge hawayen fuskana ina cewa cikin murya mai kama da rada, dan Allah yaya kayi hakkuri kada ka fada masu, Dariya na ba shi amma sai ya daure yana cewa cikin murmushi, No ai kawai ki bari na fada ma malam tsoho din kawai don ya aiko a dauke ki, Da Allah yaya kayi hakuri kada ka fada masu don naiwa Babana alkawari bazan kunya ta su ba, insha Allah, Tausayi na ne ya kamashi a lokacin da yaji ko may na ce, To daga yau idan kin gani ki daina tsorata ni ba dodo bane ko mugu, ni yanzu mijin ki ne mai bukatan kulawan ki da kuma neman taimakon ki gurin kula da al,amarin rayuwa na, Kai na gyada mai alaman na yarda da zancen shi insha Allah zan kula, Rigar barcin da ke a jikina mai baiyyana surar jiki a fili, don haka komai gashi nan free, Shi na ga ya tsura wa ido, jikin nawa ido a lokaci guda, Gurin da ya,ke kallo nai saurin kallo sai na gane cewa kirjina ya tsura wa ido, wanda kunya ne ya kamani, Idon shi naga ya lumshe tare da sauke ajiyan zuciya Babu zato sai jina nayi a tsakiyar kirjin yaya Abubakar ya matse ni gam yana wani sauke ajiyan zuciya, Dadircewa nayi kasancewar hakan sabon abune a guri na, Amma shi yaya Abubakar, tuni yai nisa da inda yake, Bai taba samun irin wanan rayuwan ba da har ya gigice a lokaci guda saboda mace, Sosai hankalina ya tashi amma babu yadda zan yi in kwaci kaina, a lokacin,, Kawai sai na sakar mashi kuka kamar jiya amma abinda bambanci don yau bai sarara min ba sam, Kuka sosai nake mai da magiya da kyat na samu yaya ya sarara min Ya koma, saman gado yana sauke numfashi guda,guda,, Ya kai minti goma sha a gurin yana sauke nufashi guda guda, Kukan da na keyi ne ya ke cin zuciyar shi ya mika hannu da niyar ya lalashe ni amma kuma sai ya kasa kai hannun shi gareni, Don bai san may zai ce indan ya tabani da niyar bada hakkuri ba Jikin sa duk a dake kamar ya yini a gona, yana aiki, Gefen da nake kwance ya kalla idon shi ga kitson kaina wanda ya hargitse, Lalai Aminatu daban ce daban take da sauran mata komai na yarinyar burgeshi ya keyi sosai, komai nata tun tana yarinya special, ne,,, Dole ne yanzu ya sawa kan shi zama da ita kamar yadda iyayyen su ke bukata, Da kyat ya mike ya mai,da rigar shi da ke yashe a kasa, Bargo ya jawo ya rufa min har kai yana mai jin kukan har a cikin ran shi, Falo ya nufa don ya sha ruwa a fridge saboda zuciyar shi da ya ke jin yana mai kuna, ****** *********** ****** Direct gurin fridge ya nufa ya dauko goran ruwa mai sanyi ya balle marfi ya sawa bakin shi, Sai da ya kusa shaye ruwan ne yaga kamar Innuwar mutum zaune a saman kujera, Goran ruwan yai saurin cirewa ya kallon gurin cikin mamaki, Inda ya taka har zuwa gurin, Sadiya ce zaune cikin wani farin nightgown har kasa, A hankali yaya, Abubakar, ya ce Sadiya lafiya may kike yi anan cikin wanan lokacin, haka ? Dago kai tayi fuskanta duk hawaye shabe shabe sai she,shekan kuka takeyi, Sai wani kallo take masa mai cike da zargi ganin yanayin ta yasa shi daure fuskan shi tama,u,, Kara maimaita tambayan shi yayi gare ta da cewa lafiya dai ko ? Cikin wani irin murya tace yanzu Abubakar don ka auri yar uwar ka,shine har zaka fara wulakantani, Subbahanallahi yace a hanzarce, May nai maki Sadiya, Cikin wani irin ya mutsar fuska tace, Girkina ne yau fa ka barni ka tako zuwa dakin yar uwanka don ku nuna min bambanci, Tsaki ya ja mai karfi yace ke wace irin mahaukaciya wai Sadiya ? Sam baki da wayo baki da hankali baki san komai ba banda kwanciya kiyi kallo, Baya ga rashi ilimin addini harda ma rashin sani ka,idar komai baki sani ba,? Ita yarinyar da kike ikirarin yar uwa ta ce wace iri ce ita, Budurwa ko bazawara? Kwana nawa aka yankewa wa budurwa a yi da ita indan an aure ta, Sannan Bazawara kwana nawa za,a yi a ta re da ita ? Tabe baki tayi tare da gyara tsayuwar ta wani bakin kishi ke cin ta a lokacin, Ta ce yanzu kana nufin cewa sai, ka yi sati a tare da ita ? Ke dakata na fada maki sai wanan yarinyar ta cika sati guda sanan zan dawo gurin ki, Zubur ta mike tsaye tana cewa, dama nasan abinda za kuyi min ke nan , Gashi ba a,kai ko ina ba har kun fara nuna min, Rai a bace yaya Abubakar yace, look Sadiya ban son abin surutu na fada maki yadda akeyi kije ki tambaya fakat, Ya daga goran ruwan shi ya shiga kwankwada kamar yadda ya fito yi, Nan ya barta ya juya zuwa hanyar dakin na, Meenatu, Wanda tun fara rikincin su na kargamay kofana don gudun kar ta,shigo tai mun masifan ni ma, Jin na rufe kofa yasa shi saurin juyawa inda ya fito nan yabar Sadiya tana ta rusa kuka wai ya cuce ta, Dakin shi ya fada ya wuce zuwa bathroom kai tsaye yai wanka, ****** ********** ****** Hajja ce a cikin damuwa saboda yau gaba daya Dodo ya hana ta shakat kamar zai halakata, Saboda kwana biyu bai samu abin da tai mai alkawarin samu ba, Gashi duk yadda yaso shiga gidan wanan bakuwar yarinyar ta hanashi duk ta kona shi da abinda ta keyi duk dare, Allah Allah ta keyi Asuba yayi tabar gidan zuwa gidan mai,lassa, Ta yi diban ruwa har ta gaji ta hakkura, takoma gefe tana mai nadama da wanan rayuwan da ta jefa kan ta, a ciki, saboda kwadayin duniya, Don yanzu ta koma kamar mujiya a cikin mutanen gari, Ko yaro ke abu yanzu za,ace akai shi wurin hajja manya, Bata da dama ta shiga taron mata yan uwanta sai su watse su ce ai ita muguwa ce, Ga dukiya kamar ya kashe ta amma bata iya ci don bata iya amfani dashi, Gashi yar ta Sadiya dake a birnin taraiya Abuja tana aiko mta da sako jefi jefi, Idan da tasan da hak gaskiya da bata sa anta acikin fitina ba, Yanzu tana da buhuhunan shikafa sukai dari, biyu, taa da wake tana da gyada da diyan dorawa, Amma bata iya kashe su ga harkokin ta idan ka ganta mutsu,mutsu da ita, kamar mahaukaciya don wahala, Wani kugi da wanan abin boyen nata yayi don azaban da yake ji, shiya kara firgita ta, Kusan duk mutanen dake a farke lokacin a unguwar nasu sai da su kaji wanan kugin,a dodon Hajja, mutane suka tsorace,,,, Bai samu shakat ba sai zuwa sallah asuba yasu ya dan lafa acikin randan roban da yake ciki,,,,,, ****** ********** ****** Yau kan a cikin daurewa na, mike saboda karfin hali irin na fulani, Ina jin jiki amma dole indaure in fita don hadawa yaya abin kari kafin ya fita, Sai da na tabatar da na gama dafa komai na koma daki na watso ruwa, Nafito daure da dan guntun towel sanin cewa ni ka dai ce a dakin nawa, ina kokarin daukan wani sabulu don wanda ke aciki ya fadi kasa, Zaune yake saman sabon zanin gafon dana kara shimfidawa da safe, bayan nai sallah, Wayana ne a hannun shi yana game din snake a ciki, Gabanane ya fadi don ganin shi da nayi a daki lokacin, Wani irin dip naji kamar in dauke wuta ko in shige kasa, don kunyan yadda ya ganni a haka, Ido ya zuba min, duk sai na rude nakasa koda motsawa, Da kyat na iya cira kafana zuwa bakin drower mirro, don in dauko sabulun, Daidai zan taso naji an riko ni tabaya na ji na yi ya rungumay ni tsam a jikin shi, Ido na a runtse ya zagayo dani muna fuskantar junar mu, Cikin wata irin murya nake cewa don Allah yaya kayi hakkuri na saka hijabina pls,duk a cikin runtse ido na. A daidai saitin kunnuwa na naji muryan shi ya na cewa a hannun shi a gashin kaina yana dan yamutsawa a hankali, May yasa jiya don nafita shan ruwa kika rufe min kofan daki,? Naji shi ya kara cewa Uhmmm? Kai na a kasa ido a runtse na ce kayi hakkuri yaya nazata ka wuce ne, Abinda naji a lokacin ya hanani ko da motsin da kafana, Ina jin lokacin da ya cire dan guntun towel din dake a jikina, Inda kyakyawan surar jikina ya baiyyana afili ta yadda zai iya ganin komai nawa, Wani irin ajiyan zuciya naji ya sauke da karfi hankalisa kamar baya a jikin shi, Duk abin da ya keyi idona yana a rufe don bazan iya budewa na kalleshi ba, saboda nauyi da kunya, Hawaye naji suna biyu fuska na a hankali Kuka again Meenat ? Why pls? Ko ba kya so na ne ? Kai na girgiza mai cikin rufe ido , To ki daina kuka Meena ni mijin ki ne a yanzu ina da right din da zanyi duk yadda nake so dake, Iya wahala na shashi ranan a gurin yayan nawa kuma miji na inji Allah, Ina jin lokacin da ya gama abinda zai yi yafita dakin nawa, Da kyat na samu na tashi zuwa bathroom, sosai na gasa jikin ina kiran mugu macuci kawai, jarababbe, Malam tsoho da su baba sun cuce ni sun hada ni dan barikin mutum, Wando ko kunya baiji a matsayi na yar uwar shi kuma kaunar shi yake bude min tsiraici haka agaban shi, Sai naji wasu sabbin hawaye sun kara biyo fuska na masu zafi, nasa bayan hannu na na goge, Kallo guda zakai min yau kasan na fada sosai don fuskana yai wani zurun,zurun, kamar nai ciwo, Ina kokarin zura riga a wuya na, naji shigowar shi dakin Tun daga nesa na fara kokarin mikewa inja baya don kaduwa da tsoron da nayi, Haba Meenat sai kace kinga dodo ki saki jikin ki da ni please ba zan cuce ki ba fa, ko in zalunce ki, Cikin wani irin murya nace don Allah yaya kayi hakkuri, ka kyaleni hakana please, Murmushi ya yi mai nuna yarinya ai yanzu nake ni, Sa kaya kizo mu karya ke muke jira, awaje, Ina fitowa mukayi arba da Anty Sadiya wace idon ta yai ja don kuka, Kau da kai nayi gefe tankar ban ga yanayin ta ba sai da nace ina kwana Anty Sadiya, Ta ansa min ciki,ciki da cewa, Lafiya, Ta wani kau da kai gefe da sauri, Yaya da ke a gefe ya girgiza kai don takai ci Kujera na jawo na dan zauna a hankali gefe guda, Sam na kasa sakin jiki inci abincin sai wasa da spoon din hannuna nake yi, Kur da ido yaya yai min bazaki daure ki kici koda kadan,ne ba ? Anty Sadiya ce naji ta dangwaran da plate din da take cin irish ta mike zuwa part dinta, Gaba dayan mu muka bita da ido har ta bace zuwa ciki, Murya yaya naji ya na cewa, ko inzo in baki a baki ne? Da sauri nakai spoon guda abaki na, badon naso ba,,,, ,, ZEEE MAKAWA YELWA,,, [7/28, 05:45] Anty Lantana: 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 3⃣6⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA,, ALLAH-AL-MU`IZ,,, Zaune take a farfajiyan gidan su ita kadai tana tunane, Duk da a lokacin duhun dare ya tsala ko ina bakikirin za ka ga guri amma ita duhun bai damay taba a lokacin,, Yau idan zata iya lissafawa kwana kusan hudu ke nan rabon da ta ga Yallabai kamar yadda take kiran shi, Don dai tun ranan da a,kace anbashi, rikon a counter din su gaba daya, A yan kwanakin da su ka wuce bai tafiya gida sai tare da ita, Amma yanzu sai kawai ta ga ya sa kai abin shi ya wuce before ta iso, gurin motan shi, Mutumin da aka san shi da ko,karin over work a ma,aikantan baki daya, amma yanzu sam ya daina, wanan cikin kwanakin nan gaba daya, Shi wai wace irin yarinyace ko kuma mata Yallabai din ya aura ne wai da har zata saurin jaye mai hankali haka,? Dole ta bincika taji ko ya wanan matar take, shin yarinya ce, tsohuwa ce yar kauye ce, ko kuma wai ma yaya take, ne wai ? Malam Audullahi masinja ne ya fado mata a,rai, gurin shine za ta dan samu wanan labarin amma fa sai ta hanyar, zolaya don taji komai a gurin shi,,, Da wanan shawaran ne ta mike zuwa cikin dakn kwanan su don ta kwanta kamar yadda kowa ya natsu, don yanzu karfe daya da rabi ke nan na dare, Washegari a gurin aiko kowa sai harkokin gaban shi ya keyi a lokacin, Amma ita tunane takeyi yadda zata dan kebe da mudi ko malam Audullahi, Don duk cikin ma,aikatan su da su biyu ne kawai yake hurda sosai ta gani, Kamar kullun a zaune suke su biyu suna hira kamar yadda suka saba, Salawatu ce ta zo cikin shigan irin nasu na yan gayu, Buje ne na atamfa amai tsaga ta baya har zuwa sharaban ta, Idan tai tako daya zaka iya ganin naman kafarta a fili, Dinkin rigar mai umbrella ne har kusan gwaiwan ta mai dan tsawon hannu, Tana rataye da handbag mai shige da launin kayan, Daurin dan kwali har a gaban goshin ta, fuskanta ya sha makeup kamar kullun, Takalman kafarta tsinin shi kamar marfin biro ya ke,, Tun daga nesa malam mudi ya hade ran shi don dai shi sam baya kaunar wanan yarinyar da bawan Allah ga , Saboda ba irin tarbiyan su guda ba kai shi agurin shi basu ma dace ba sam gaskiya, Da takon ta mai kama da karan kofato ta iso gare su, Yau, ba, ta tsaya har su gaishe ta ba , Ita,ce ta dan sakata a gaban su tana cewa sannu ku fa, Ya kuke ya kwanan iyali,? Shikan malam Mudi ya sha toka bai son wani alaka da ita ta ko ina, amma shi malam Abudullahi cikin washe baki ta ke cewa, Malam Abudullahi duk shan miyar amarya ne yasa yanzu daga ku har Yallabai ba,a ganin ku ko ? Gaba daya suka jiyo suna kallon ta a cikin mamaki don sam basu da labarin cewa ubangidan nasu yai aure, A cikin nuna yar zakuwa da son jin zancen malam Abdullahi ke cewa kai hjy yaushd akayi haka ? Tace au boye min kuma zakayi bayan shi da kan shi angon ke fada min cewa, Amaryan shi ta tare acikin satin nan da ya shige, Gaskiya bamu da labarin cewa yai aure don dai bai fada muna ba, Amma kila shi abokin aikin nawa ya samu labari ban sani ba ko ? Malam Mudi yace cikin yar matsewa ai ba sai na sani ba don bani na biya mai sadaki ba, Sam bata ra,ayin wanan bakin bakanen a rayuwan ta don ta na sane da cewa ya tsane ta, Muryan malam Abdullahi ne ya ratsa mata kunnuwa da cewa aiko, Abin yai kyau, wallahi ga amarya ga karin girma, Sai shi malam Mudi ya ce kaga ke nan amarya tazo da nasarorin rayuwa ta shigo da far kafa ke nan,,, Sai kuma taji sun bala,in bata haushe da abinda suke fadi, Watau auren yarinyar shi ya kawo wa Yallabai good luck,,, Wuf ta fada cikin office din Abubakar ran ta a bace Ama a irin yadda ta hango shi zaune a cikin annuri da annu shuwa yana aikin shi hankali a kwance, Ga wani irin kwarji da haske da dan kiba da ta ga ya kara mata, Gaban ta ya ba da dammm kar dai ace zance munafukan mutanen da ta baro waje gaskiyane, Da takon da girgizan dole ta karasa gareshe cikin dan sakin fuska, Oh, Salawa how are you? Sorry, please two days bamu hadu ba saboda ban samun tsayawa Don new wife dina bata faye lafiya ba, Wani irin kishine ya turnike mata girjin ta alokaci guda, Da kyat ta iya seta kan ta, har ta dawo normal, sai dan dariyan yake da tayi afili,, A sorry sir ashe new madam ce ba lafiya kardai har an samu yan baribari ne ko ? Fuskan shi ya daure don baiga abin da zai sa ta ce haka ba? Da ta ga haka sai tai saurin cewa Allah sarki wata kila bakunta ne, takeyi hakan, Ci gaba yayi da aikin shi sai kuma ya dan dago kan shi ya ce barin kira malam Abdullahi ya baki drink ko ? No ka barshi kawai I am ok, Ta mike tana dan gyara bayan bujen ta koda yadan tatare zaman da tayi, Sai ya dago kai sukayi arba dashi yadan sake mata guntun murmushi ya ce I will called you back indan na rarage yanzunan ina busy ne pls, Ita,ma dai yar dariyan da bata kai ciki bane ta sake a lokaci guda, tana cewa zan tafi ba matsala ai, Sai gaban ta wani irin mugun faduwa yakeyi tankar zata shude a gurin saboda bacin rai, Saboda wani irin bala,in da take ji sai take ganin ma,aikatan yau yana juya mata, Tafiya takeyi tana cewa Yallabai ne, yau yake nuna min cewa yana son yarinyan nan ke na, Yarinya da shi da bakin shi yake ce min a gidane aka hadasu bai ma san ta ba, Kai lalai,ma namiji abin tsoro ne gaskiya, Wai yau Yallabai din tane da bakin shi ke fada mata zance akan wata mace, Tunda har yake bata lokacin shi, haka sosai bai ko iya boye wa, Zaune take a cikin office din su duk rayuwan ta yai mata kunci ta rasa may ta ke ciki ne wai, Idan ba tayi da gaske ba fa abin zai bashe ta, gaskiya ita bazata iya zama batare da ta mallaki miji irin yallabai ba, Gashi ta samu kuma yana batun kurce mata daga hannun ta, Lubuna ce tsaye a kanta tana karewa kawar nata kallo a cikin mamaki lokaci guda ta ga duk ta canza mata, Kafadan ta, ta,dafa sai da Salawatu ta dan girgiza kadan don tayi zurfi a cikin tunane ko Dago idanuwan ta da sukayi jawur tayi saboda bacin rai, ta dan sauke ajiyan zuciya, Tace Lubuna Abubakar yana son yai min yawo da hankali na wallahi, Bayan ya gama sani na yarda dashi 100%, sai gashi yana son ya kawo min sabon zance kuma, Cikin wani irin takaici lubuna ke kallon aminiyar nata , Irin yadda ta tsaya saboda so tana son wahal da rayuwan ta ga banza, A gaskiya Salawatu ki na bani mamaki kwarai da gaske, Wai shim Oga Abubakar shi kadaine namiji a Abuja? Kar ki manta kina da masoya da yawa fa akan maye zaki tsaya kina son batawa kan ki lokaci ne haka,? Kodai kawai don shi yaki ku tsaya kuyi Roncy a waje kamar sauran maza, Ke kuma kin riga da kin mutu a kan shi, idan ba kin dandana shiba bazaki iya hakuri da shi ba, Hawaye ne suka biyu fuskan ta zuwa sauka kasan fuskan ta, A cikin takaici take cewa Lubuna ina son wanan guy din kema kin sani Kuma I am lucky yace zai aure ni, Idan bashi din da yazo min da zancen aure ba kinga wani wanda yazo muna da zancen aure ne, Dubi irin zaman da mukayi da oga,Yusuf har wuce kinji zance aure ga bakin shi, Gaskiya Lubuna bazan so in kare rayuwana a haka ba? Don lokaci yayi da ya kamata mutum yaiwa kansa fada , A yanzu bani da burin da ya wuce in auri Yallabai Abubakar, Amma gidan su da yan uwan shi suna son suyi muna tsakani, da shi, Tausayi taba aminiyar nata don haka takai zaune tana mai kallon ta acikin tausayi, Mutun mai karfin hali da dauriya irin Salawa ace yana kuka haka akan soyayya, Salawatu ke nan inji Lubuna tana murmushi irin na bacin rai, A gaskiya ni nasan cewa dama zaki fuskanci irin wanan matsalan gurin mai mata sai gashi kuma ya kara yin wata matar, Don a gaskiya yan Yallabai sun nuna maki cewa basu kaunarki acikin su, Don zancen auren ki yana gaba da na wanan da suka daura mashi, Yanzu tunda har kin nuna cewa zaki iya zama dashi a hakana da mata dayawa ai ba matsala sai mu san yadda mukayi, ai, Da sauri Salawatu ta daga kai ta kalle ta cikin mamakin jin abinda ta ce, Kiyi shiru kawai mugani in har ya ce zai guje ki zai gamu da aikin mu sosai, Munyiwa banza ma balle wanda muke son zama dashi,,,, ****** *********** ****** Yau, satina gudu atare da yaya Abubakar, wanda dan zaman da mukayi a tare yadan jawo muna yar shakuwa kadan a tsakanin, Koda yake shakuwar tamu sai idan muna atare ne saman gado inda ba haka ba, Sam bazaka gane farin cikin dan uwan nawa ba don a koda yaushe fuskan shi a daure nake ganin ta, Nasan cewa kwana bakwain da mukayi tare da yaya Abubakar, Ya dan bude min wani sabin babin rayuwan da Anty Amarya ta dade tana lurar da ni amma ban fahinta ba, Ya Abubakar gwarzon namij ne, wanda yasan yadda zai tafiyar da macd a cikin ruwan sanyi, Har ta mantar da damuwan ta don sannu a hankali yadan kawar min da damuwar irin zaman da ada nake hage dashi, Yau Anty Sadiya ce zata karbi girki a gidan don haka kamar yadda na tsamani sai ban ga wani alamar karban girki daga gare ta ba, Saboda banga fitowan ta zuwa dora muna girki ba kamar yadda yake, Ina zaune saboda rashin abin yi na gyara daki na da bayi yafi a kirga, sai kamshi ke tashi ta ko ina,, Karan shigowar motan yaya Abubakar cikin haraban ne yasani gane cewa ya dawo a lokacin, A hankali ya turo kofan falon gidan hannu shi guda dauke da yar briefcase din shi guda kuma acikin aljihun wandon shi, Shiru yau ya samu falon don kwana biyu kamshin turaren falo da na girki ne kan tare shi,, Mamaki ne ya kama shi don ba haka yasaba gani kwana biyu ba, A hankalo ya tako zuwa cikin falon inda ya aje yar case din shi saman center table, Dakina ya nufa da ganin shi a gajiye yake, don daga tafiyan shi zaka gane hakan, Daga kofa ya tsaya inda ya dan jingina jikin shi da dan katangar kofan dakin, Zaune nake saman stol din dressing mirror dina ina gyara gurin, Jin shigowan shi dakin nawa ne yasani dan juyowa ina kallon shi, Cikin jin yar kun ya nake ce mai sannu da dawo yaya, Sai da yadan tako har zuwa bakin gado yadan zauna yana cewa Yauwa ya gida, da aiki Meena,? Ban bashi ansa ba sai murmushi da na dan yi, kawai, Nagaji wanka nake son yi kafin in dan fita inyo muna shopping, Yau banga drinks din taro na a saman dining table ba shine nazo jin dalili, Kaina yana duke a kasa nace cikin yar siririyar murya, Yau bani ce ya kamata in tare ka ba yaya Anty Sadiya ce da girki, A take naga annurin fuskan yaya ya gushe waya fada maki hakan? Yau satinka guda a dakina shi yasa nasan da hakan, Ok kawai naji ya iya cewa tare da mikewa tsaye lokaci guda, Sai da ya kai gaf da kofan fita daki yace ke kuma kina ta faman kidayawa ko ? Daga haka yasa kai yafita batare da ya kara cewa komai ba, Fafadan bayan shi nabi da kallo har ya shige ma gani na, Na sauke ajiyan zuciya a hankali tare da cigaba da abinda na keyi, Dakin shi ya wuce direct inda, bai tsaya bata lokaci ba ya shiga wanka, kamar yadda yace, Ya shirya tsab cikin kananin kaya, da suka karbe shi suka fitar mai da kurciyar sa, afili,, Dakin Anty Sadiya ya shiga inda ya samay ta zaune, tana kokarin dauko wayan ta dake gefen ta, Gefen dressing mirror din ta yai niyar tsayawa amma sai yaga kura tab a gurin, Hannu ya dan kai ya lakato kuran da yar yatsan shi yana ce mata, Haba Sadiya wai ke yaushe zakiwa kanki fada ne har ki koyi tsabta,? Yanzu duk irin wanan gyaran da yar karamar yarinya ke yi a gidan nan kwana biyu, Baisa ki fahinci cewa gyara ga mace yana da wani amfani ba,, Abubakar, dakata haka please ? Kada ka dinga hada da wanan karamar yarinyar da ka susuce akan ta haka Tayi irin rayuwar ta in yi kalar tawa don haka daga yau kada ka kara hadani da ita Dakata kiji Sadiya don naga kin dauko hanyar yi min rashi mutunci ina fadi kina fadi, Kin san bazan yarda ba sam da wanan sabon halin don bani daukan wulakancin mace sam,,, Ya fara tafiya a hasale yana cewa Idan kinga dama ki gyara, idan bazaki gyaraba cikin ki tayi, Kuma ki tashi ki girka muna abinda zamuci don kin san kece da girki yau, Da sauri ta dago kai tana kallon shi fuskan shi ba wasa acikin shi sam Abinda yasa tai shiru kenan har ya fita, daga dakin nata ba tare da ta ce komai , Sai dai acikin zuciyar ta sai mita takeyi don may zaice sai ta girka bayan ba haka suka saba yi ba, Suna kai sati biyu uku ba tare da sun girka komai a,gidan ba,, ****** ********** ****** Zaune suke daga ita har shi rayuwan su babu dadi sam alokacin , Can dago kai fuska adaure yace gaskiya ba karamin kuskure ki kayi ba Hajja na barin wanan yarinyar ta shiga gidan, Hajja ta dan gyara zama tana cewa wallahi Mai lassa ba mu san da zancen auren nan ba har tarewan, Don shammatar mu mugun tsohon nan yayi ta ko ina bai bari mun san da zancen ba, Gaskiya Hajja sai dai mu bi a sannu don idan mun matsa wanan zancen cikin mu yayi sosai, Karki manta cewa wa yan nan mutanen sune suka kashe min dayan dodon da, aka hada wa matar gidan, Duk yadda naso mu dauki fansa akan su abin baiyi ba , fole na kyale su , Yanzu kuma kinga ita wanan yarinya ita ma daga cikin su take, Don haka akwai babban alamari maigirma atare da ita Malam nima naga alamar haka don ko shi mijin yar nawa har yanzu ban samu yadda nake so ba gare shi Yace yanzu ba matsala nasan hanyar da zamu bullowa al,amarin, Sai a lokacin Hajja ta dan saki murshin jin dadi don da duk a rude take,,, Wasu garin magani tayabata har kala uku wanda zata zubawa dodon ta don samun sauki,, ****** ********* ****** Zaune muke gaba dayan mu saman dinning table din gidan, Ita da ta girka abincin itace a tsaye tana zubawa cikin daure fuska, Adole tai girki ta gaji da aiki yau, Jealoup din taliyane yai wani fari fait, ya cucure guri guda, Kallo guda nai mai naji hankalina ya tashi sosai saboda yadda na hango shi, Bayan ta gama zubawa mai gidan ne taturo min kulan agaba na wai in zuba nawa, Serving spoon guda na dan zuba na tura mata agaban ta, Da sauri yayana ya dago kan shi yana kallon na da mamaki, Itako sai naga tana lodawa kamar yadda ta loda mashi, Na daga hannu a hankali nakai spoon guda a baki, na, Amaine yaso ya taso min amma sai Allah ya tai make ni na samu na hadiye shi da kyat, Ruwa dake cikin cup din glass a kusa dani na dauka da sauri nakaiwa baki na samu ya wuce min, Yayana ma ya diba ya kai abakin shi ya dan kai wani lokaci da shi a cikin bakin shi ya kasa hadewa, Da karfi naga ya fuzo shi yana cewa Sadiya zaki kashe mune, Ga tankwa ga gishiri ga kuma maggi bai narke ba kin sa na tura maggi a baki ? May kake nufi kana nufin bai yi dadiba ko may, Idan yai dadi sai ki cinye ke,? Wai ke bazakiyi wa kanki fada bane Sadiya, Taliya da, daren nan shi zamu ci ? Bakya ganin yar uwar ki tuwo take muna har kice leda biyu da kusan rabi, Amma ke don ke ta zakiyi muna taliya taliyan kuma ba ko test abu haka kamar dahuwar jariri, Gaba dayan mu shiru mukayi kowa kanshi a kasa saboda irin yadda yake magana acikin fada, Haka kike son mukwana da yuwan wanan yaji ai sai ya halaka mutum abanza, To ni gaskiya ban san ya kake son inyi ba don dai ni banga abinda wanan taliyan yayi ba, Ta diba takai a bakin ta da sauri tadawo dashi tare da daukan ruwa takama kwankwada da karfi, Nikan mikewa nayi tare da daukan plate din wanda na zuba zuwa kitchen, Ina fitowa na wuce daki na da niyar in kwanta don yau ni kadai ce adakin, Ban dade da shiga ba naji fitan yaya Abubakar da mota , Kayan jikina na sauya zuwa na barci don in yi shirin kwanciya, wayanane yai kara, Noban anty amaryace takirani , Da murna na dauka ina cewa cikin shagwaba,gaskiya Anty kin daina sona yanzu tunda kika tafi sai yau kika kirani, Dariya tayi tana cewa ba wata ya bayan ke my daughter, Gaisawa mukayi natambaye ta yaran gidan mu kaf din su, Sai da muka dan lafane take tambaya na ya zaman mu yake, Yar dariya nayi nace la Anty babu komai lafiya kalau muke, Kin tabbatar Meena, Gaskiya Anty babu komai , To haka nake son ji don wallahi kawun ki ne ya hana in kira ki kwana biyu, Ko yau da kyat na samu ya yarda in kiraki wai kina shan amarci kada in damay ki, Kunya ne ya kamani kamar tana gabana nace haba anty please ki bari ba wani amarci da nake sha ban da kewan ku, Ke tafadi da karfi kada kisa inzo abuja gobe in tambayi in-law nawa ko lafiya yake,? Wayan takashe daga haka batare da mun koyi sallama ba, Sai dai ina tsanmanin Uncle dina yana kusa da itane alokacin, Mikewa nayi don in sawa kaina ribon, sai naji anturo kofa, Yayane hannu dauke da leda guda biyu, ya aje min wanda baikai sauran yawa ba a saman mirror na, Idon shi kar a kaina yana min wani irin shu,umin kallo, Godiya nai matare da cewa su anty suna gaishe shi,,,,, Da yar fara,an shi ga fuska ya ce au yau sun bugo waya ke nan? Nadaga kai a hankali alamar Eh,,, ZEEE MAKAWA YELWA [7/29, 12:38] Anty Lantana: 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 3⃣7⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA ALLAH-AL-MU,ZIL,,,, Sai da na tabbatar da nagama gyaran dakina na fada wanka, Wani material lace ne milk da adon flower purple kanana, ajikin shi sai duwatsu jefi jefi jikin shi, dinkin buje da riga ne, Kaina da ya kai kusan kwana goma akitse yadamay ni da kaikayi, sosai, A hankali nake kokarin daure dankwali a kan naji shigowqn yayana dakin, Fuskan shi yau yafi na ko yaushe rashin walwala don tamau, yake a daure, Yana saye cikin wasu yadi fari mau laushi wanda har zaka iya hango farin singilatin shi a fili, Tun kafin ya karaso dakin na kai kasa cikin ladabi, ina gaishe shi, cikin yar siririyar, murya na, Sai a lokacin naga ya dan sake fuskan shi ka dan yana amsa min,, Ya ce lafiya kalau ya dare? Dakin na ga yaiwa wani irin kallo sai kuma ya fara tafiya yana cewa zan tafi office, sai na dawo Allah ya tsare yaba da sa,an fita, adawo lafiya, Murshi yadan yi don jin dadin adduan da na jero mashi da wanan safiyan, Abinda tun zaman su da Anty Sadiya bai taba jin ta furta ba ko da a wasa ne, Cikin rawan murya da kuma tsoro da shakka nace mai yaya don Allah ina son inda shiga nan makwabta a min kitso ko kadan ne, Da sauri naga ya daga kai ya kalli kaina shi a ganin shi ai kitson baiyi komai ba, Shima da bai saba ganin ana kitso a gidan shi ba balle yasan tsufan shi, Tambayana yayi da cewa kin san mutanen gidan ne ? Shiru nayi don ban da ansa bayarwa komay ya tuna kuma sai ya ce anyway ki shiga ki gani idan babu masu yi sai ki bari gobe akai ki, saloon, Nagode nace mai tare da karayi mai adawo lafiya, Bayan tafiyan ya da yan mintoci na fito falo don inga komay aka hada muna breakfast in dan ci kafin in fita, Babu komai a saman table din sai robobin take awaya din da ya siyo muna jiya dadare, Anciye abin da ke a,ciki ba a kwashe su an,zubar ba a dustbin, Nawa na tuna dashi wanda nasa a fridge daren jiyan, Da sauri na nufi hanyar kitchen din na bude fridge na dauko su, A cikin microwave na sa nadan yi stemming din shi, Kitchen din yaiwani hargitsewa kamar ba jiya da rana na goge shi ba bayan na gama girki, Ga taliyan jiya yakara komawa wani iri acikin plate, zaban kazan ta, Da sauri na kwashe su na zuba a dustbin din baya inda wari bazai damay mu ba, saboda taliyan baida dadin gani, Nadawo nadan gyara kitchen din tsab yakara komawa daidai, Najawo abinda na sa a cikin microwave na kashe, shi ta baya, Da shi na karya kumallo rana na dauko goran five alive, na dan tsiyaya na maida sauran, Ban karasa cinyewa ba naji fitowan matar gidan acikin nightgown take har zuwa yanzu, yai dauda so,sai don har yar bashi ya,keyi, Kallon take away din dake gabana tayi sai kuma naga ta kalli kitchen din, Ina kwana anty Sadiya duk da batai min sallama ba, Murya cikin alamar mai tasowa daga barci tace, wai yau ba,a dafa komai bane gidan, Banyi magana ba sai naji tayi yar tsaki tana cewa nifa bazan iya wanan harkan girki, girkin nan ba, Kawai idan zamu hada girki mu hada don gaskiya da matsala idan ance sai nayi, Bance mata komai ba sai ci gaba da taunar naman kazan da nakeyi a hankali, don cin dole manakeyi saboda cin abu mai nauyi haka tunda safe, Take away din bai saura bane ki bani in ci naji tace cikin yin hamma, Gaba daya na gabana na tura mata gaban ta tare da kokarin mikewa tsaye, Kin gamane ke nace mata a hankali na ko shi, sainaga ta jawo tafara ci, Mamaki ne ya kamani sosai , Wai ita wace irin mata ce shim? Bata iya sallama ba balle maganar girma da arziki, Sai zuwa goma da rabi na sa hijab dina wanda ya sauka har kasa, Najawo kofan dakina na kulle da key, tare da kashe duk wani na,uran wuta, Dakin Anty Sadiya na nufa don in mata sallama, Wanka tafito tana daure da zani atamfa jikin ta duk ruwane, Da sallamana nashiga dakin gani na yasa ta wani daure fuskan ta, Anty zan dan shiga nan makwabtar mu inyi kitso yanzu, Ok kawai tace min, Nima ban tsan mani komai ba daga gurin ta na juya na,fita, ****** ********** ****** Ina fita kofan get din gidan nai,wa anguwar kallon tsab, ko ina gidaje ne na gani na fada, masu matukar kyau sai dai wani yafi wan kyawo, Wani gida na hango a gefen gidan mu ginan shi baikai na kowa kyau ba a layin, Gidan nada iccen umbrella, a kofan shiga get din gidan, ba a,yi plaster bangon gidan ba, Gidan na tun,kara,, a hankali, na tura kofan shiga cikin gidan wanda wani tsohon, gambun karfe ne ja, Da sallama dauke a bakina na shiga gidan, wanda babu kowa a tsakar gidan sai, kayayya kin aiki, a waje, tsakar gida, A hankali na kara yin sallama a karo na biyu cikin gidan,, Ina tsaye daga kofa shigowa gidan, Mutum biyu ne su ka karba min a,lokaci guda kusan tare su ka laiko kowa daga dakin shi, Wata dattijuwa ce Baka ta na rufe da gyale ja,a kanta har kasa, Wanda zai nuna maka cewa da ga gabashin Nigeria take, watau shiyoyin kasan maiduguri,,, Sai kuma wani dan matashi yafi yaya Ibrahim di na shekaru, Ban sheda shi ba amma shi ya shedani sai cewa yayi ah, Amarya ? Naji ya nacewa amaryan da aka kawo gidan mutanen nan ne da ba ruwan su da kowa, Mamaki matar keyi don irin kallon da take min yai matukan bani tsoro, Hausan ta ba pure hausa ba ne sai cewa tayi, Yarinya lafiya dai ? Sai a lokacin nace, ina kwana ? Daga gurin da nake na,ke tsaye saboda sabon, da nayi da yin gaisuwa , In dai mutum ya girmay ni sai mun gaishe ka, wanan dokar malam tsoho ne, A sama sama ta karba min da cewa, lafia, Nace don Allah ina tambayan gidan da ake kitso a wanan area ? Magana tayi kaman a cikin yaren su sai naji ana kiran wata, Fattu, Fattu fattu kira daya biyu mai sunan Fattun ta fito daga daki tana kokarin daura zanin ta da goyon ta a hannu, Ganin bakuwa a tsaye tsakar gidan su mai dan filin da baifi tako uku ba yasa ta tsayawa muna kallon kallo, Gaishe ta nayi tankar na san ta dama, wanan saurayin ne ya dauko min wani farin kujeran roba, yana cewa ki zauna nan, Inda nake fattu ta iso tana cewa cikin sakin fuska, Daga ina yar uwa,? Daga nan makwabtar ku na ke nazo don Allah tambaya ko ina zan samu kitso, ? Ki,tso yar uwa ? Nace eh a hankali, Gaskiya ni a cikin gari nake zuwa amma in ba mai yawa kike so ba zan dan gwada yi maki ki gani, Awaje muka zauna batare da bata lokaci ba tafara min kitso, Kitso mai suna suna SHADE tai mun yan kakana a kaina, Rana guda ake sabo don haka sakin fuska daga bangare na da nasu yasa muka dan saki jiki da junan, mu, Dan zaman da nayi a gidan na fahinci cewa zama ne na uwar miji da sarakkuwar ta, Fattu ce ke auren dan ita wanan dattijiwan watau Maman Bi,u kamar yadda na ji suna kiran ta, Sai kuma kanin mijin ita Fattun mai suna Hamza wanan saurayin masu zama kofan gidan mu, Na kuma fahinci cewa zama sukeyi na fahitar junan su sosai, Don girkin ranan Maman ,Bi,u ce tai girkin idan ta girka masu Birabisco, Ta karbi girkin ne don kawai, a samu ai min kitso, Dan yaron da Fattu ke goyo Maman Bi,u ta dauki yaron ta goya abayan ta don yabar uwar shi, tai, min kitso, Na kuma fahinci cewa Maman Bi,u bata jin hausa sosai don haka da tafara sai ta sa yare a ciki, Bayan mun kamala kitson ne ina kokarin kakabe jikina, A lokacin ne ita wanan Dattijuwar Maman Bi,u ta kawo min wani abu a cikin bakin leda, Karban ledan nayi da hannu bibiyu ina mata godiya, Da harshen yaren su take cewa Fattu wai in dinga amfani dashi turare ne dan maiduguri dana daki da na jiki, Fattu ce ke fassara min da cewa, wai tace kada in dinga zama babu kamshi a jiki na, Koda yaushe namiji zai iya shakan kamshin matar shi, Nai dan murmushi nakara cewa na gode kwarai da gaske, Dubu daya naba Fattu a matsayin kudin kitso Amma sai tace ita bazata karba ba, Daga can bayan mu, mukaji muryan Maman Bi,u tana cewa, A,a,a kada Fattu ta karbi kudina, Wai ina laifi gida nawa ke a cikin uguwar amma na shigo nasu kai tsaye Murmushi kawai nayi na kara gode masu sosai sai dai da zan wuce, Yaron Fattu da Maman Bi,u kebawa abinci na saka mai kudin a cikin rigan shi nace asai mashi Pampers, A gidan mu nasamu kofan gidan a sake kamar yadda na jawo shi da zan fita, Hakan ne ya sani gane cewa tun fitana Anty Sadiya bata fito ba ke nan balle ta rufe gida, Dakin ta na nufa don in sheda mata cewa na dawo daga gurin kitson da na tafi, Na samay ta a kwance tana ta sharar barcin ta hankali kwance, Najawo baya cikin mamakin ta na juya zuwa sashe na, A falo na hadu da Hamza dan gidan da na fito kitso dauke da kula a hannun shi, Sallama ya kara yi na ansa mai cikin mamaki daga gurin da yake tsaye ta kofa yake cewa , Mama tace wai in kawo maki Biski ne wai idan tai maki tayi acan ba,aki ci ba, Banda yadda zan yi dole na karba na,dauko wani kula daga kitchen na juye aciki, Daki na shiga na debo sabulu da omo nasa aleda nace ya kaiwa Fattu, yace na gode Shi kuma na bashi dari biyu saboda dauko abincin da yai min,, Saman dinning table na aje abincin na wuce zuwa daki, Har na zauna sai na tuna da maganar Anty Amarya da tace duk lokacin da nake da girki in tabbatar da cewa na gyarawa maigida dakin shi tsab, Don haka namike da sauri don zuwa na fara gyarawa kafin lokacin sallah ya karaso, Kofan shigowa gidan mu na jawo,na rufe da key don kada wani ya shigo muna, A hankali nake hawa saman benen da nake zaton dakin maigidan ne a can, Kasan,cewar yace rana na farko da zan fara shiga dakin nashi, Nayi zaton cewa zan samu dakin a rufe amma kuma sai na samu abude yake, Abin yabani mamaki don azatona rufewa ya ke yi , Gashi matar gidan na ta sharan barci abin ta batare da ta damu ko wani zai iya shigo masu ba, Kayane birjit ko ina acikin dakin babu gyara ko kadan Zanin gadon yai wani motsu, mutsu saboda rashin gyara, Dole na cire hijab dina na shiga aiki ba shiri, na kai wani lokaci acikin dakin, Don har sallah aciki na gabatar na tara kayan wankin da suke gefen tarshe a kasa guri guda, na daure cikin zanin gadon da na kwashe, Kafin wani lokaci dakin ya koma kamar ba shi ba don nan take yafara kamshi, Sai karfe uku na sauko saboda unders din dana tsaya wankewa,, A hankali nake tafiya zuwa kasa, don duk jikina yana ciwo saboda gajiyan aikin da na sha, Don ina zaton tun tarewan su gidan ba,a taba gyaran dakin ba, Tun saura steps biyu in sauko na hango Anty Sadiya a zaune saman kujeran dining tana cin Biskin da Maman Bi,u ta aiko min da shi, Tafiya na da taji yasa ta dago kai don taga kowaye, Wani kallo mai kama da harara tai min tare da dauke kai, taci gaba da cin abincin ta,, Acikin sakin fuska nace har kin tashi,? Acikin wani irin murya dasasshe tace eh, Kanta a duke tace, A,she har kin dawo har kin girka muna abinci, yanzu da na farka na,fitone nagani, Amsa na bata da cewa ba,nice na girka ba , Gidan da na tafi kitso ne suka aiko min dashi, dazun, Nazaci cewa bazata ci gaba da cin abincin ba amma sai naga kawai tana ci gaba da ci,abin ta, Ban zauna ba sai da na gama hada muna abincin dare, Nai sallah sanan nazo na zauna don inci abinci, tare, dan hutawa, Ba laifi don girkin tsohuwar yai dadi sosai, ashe abin da ya sa Anty Sadiya ta ci fiye da rabin kulan, abincin ke nan, ****** ********* ****** Malam tsoho zaune tare da yaran shi da suke shawaran don zuwa Abuja su taya dan su murnan samun karin girma, Sai da tsohon ya gama sauraren shawaran da baba Samaila suka kawo mashi shi da sauran yan uwan shi, Sanan ya dan nisa a cikin jin dadi ya ce gaskiya yaji dadin wanan shawaran badon komai ba,sai don a nuwa jikan nashi irin kaunar da suke mai, Amma kuma ga shawara guda ya kamata a fadawa mahaifiyar shi ko akwai daga cikin yan uwan ta da zasu, Haka kuma can 2urin ita matar tashi don kada sai mun tafi su zo suce basu da labari, Kowa yaji dadin wanan shawaran da malam tsoho ya kara kawo wa, Baba Buhari yagama zaiyanawa Mama Ladi sakon malam amma sai cewa tayi ita gaskiya babu wani dan uwanta dazata fadawa cewa ya zo a tafi, Baba Buhari yace har yayan ki bazaki fadawa ba ko zai samu zuwa, Amma sai mama Ladi tace ita fa kada aiwa yara gaiyya zuwa gida yana fama da kan shi, Baba Buhari yace wai ke Ladi, shin yaron ga ke kadai kika haife shi ne da kike nuna min haka, To bari kiji yadda kike ganin cewa zaki yi iko da shi haka nan nake iya iko dashi ina dai kyaleki ne kawai don ba hankali gare ki ba, Ai baka sanin banda hankali sai na sa yaturo maku da yar ku gida tukun, Yanzu haka ma ina tsan manin ya a ko ta dai can gidan da take zaune ne a sokoto, Nunata Baba Buhari yayi da hannu yana fadin ji mahaukaciya, Ai in,kinga auren yaran nan ya mutu to babu gudan su ne, Daga haka Baba ya wuce abinshi dama malam tsoho ne ya matsa akan wai yazo dai ya shawarce ta don a fitar mata da hakkin ta, ****** ********* ****** Wanka nayi inda na tsala kwalliya kamar yadda Anty ta fada mun in dinga yi,, da zaran mun raba girki, Tun daga haraban gidan falon, gidan har zuwa kitchen da kuma,sauran sassan gidan yau fes,suke, sun sha gyara, Uwa uba kuma dakin maigidan da bai taba ganin an mai hakaba, Kafin shigowan shi gidan su Hamza ne suka kamo mai TV daga cikin kwalin shi sabo fil, Anty Sadiya wace ke zaune a falon tana kallo season film kamar kullun a wanan lokacin, Ta dan dago kan ta, tana gani tai saurin kau da kai gefe don takaici, Da Sallama yaya Abubakar ya shigo gidan yana sagale da corth din shi ga kafadar shi, Gaba daya yau sai ya ga gidan duk ya canza ma a lokaci guda, Kitchen na fito dauke da jug, din ruwan sanyi hade da cup,a hannu na, Daidai lokavin da ya ke zama saman kujera a falon, Idon shi kyam a kaina baya ko kyaftawa, Anty Sadiya wace ke kallon shi ta wutsiyan ido taja dogon tsuki, Murmushi yaya ya sake saboda ya fahinci abinda takewa tsakin, Sai alokacin yadan kau da kan shi gareni cikin zuciyar shi fadi yakeyi ita dai wanan yarinyar komai nata daban , Har tafiyan ta da kuma iya ladabin ta nadaban ne, Sai da nakai kasa na nafara tsiyaya mashi ruwa a,cikin cup nace mai sannu da dawowa yaya, Shiru ba ansa yasani saurin daga kai yana rike sa goshin shi tankar yana masa ciwo, Hakan ya tabbatar min da cewa yana dan cikin damuwa ne kila alokacin, Ga ruwan nace masa abinda ya sa shin firgigi ya dan dago kai, tare da yin dan takai,taccen murmushi a lokaci guda, Sosai naga yasha ruwan tare da sauke ajiyan ziciya yayin da uake aje cup din saman table, Dago kai yayi ya dubeni sosai sai yace a kasalance, Kedawa kukai wanan aikin haka ? Kaina na dan dukar a kasa ina wasa da hannun jug din dake gaba na nace ni kadai, tare da kara sunkuyar da kai na akasa, A hankali yace ki daina wanan wahalan idan ina gida zanyi da kaina. Don Bake kadai bace ke batawa don haka kinfa wahalan zai maki yawa, Daga haka ya mike zuwa sama inda dakin shi yake, Gaba daya sai yaga dakin ya canza mashi, don bai taba zaton abinda ke ciki suna da haske haka ba, Da mamaki a fuskan shi ya tsaya yana karewa dakin kallon cikin sha,awa, Wanka yayi yafito cikin kananin kaya ajikkn shi sai kamshi ke tashi, Tv da ya shigo dashine yakira mai hakawa don a haka a daki na,,,,, ZEEE MAKAWA YELWA [7/30, 07:13] Anty Lantana: 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 3⃣8⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA ALLAH-AS-SAMI, Tv plasma, yar madaidai ciya ta bango yaya Abubakar yasa a ka hada min a daki na, Naji dadin wanan abin da, yaya yai min Ko banza zan samu abokin hira a daki na, A yan kwanakin da na yi a gidan yayan mu na fahinci cewa yanzu komai ya canza agidan nashi bakamar wancan zuwan da mukayi da yan uwa na ba, Ba sai an fadawa mutun cewa yanzu yaya Abubakar yana cikin walwala ba da falala da nasarorin rayuwa, Hakan kan sa in,zauna ina tunanen shi yaya Abubakar wani irin mutum ne wai ? Ace duk wanan tatin dukiyan da Allah ya bashi tun yana cikin kurciyan shi amma bai damu da iyayyen mu na gida ba, sam, Irin halin rayuwan da nasan su na fama da shi kamar may ? Amma shi kuma gashi cikin jin, dadin rayuwa, ya tara wasu irin motoci har guda uku a farfajiyan gidan shi, Sai kyali da daukan ido sukeyi da ka tunkari gidan, Yanzu falon gidan da ke samun gyara ko da yaushe, shima abin sha,awa ne, Amma kuma fa, iyayyen na can a cikin wahala sai sun samo abinda za,aci agida,ko wace rana, Girgiza kaina nayi saboda takaici, da bakin ciki, Wasu siraran hawaye suka zubo daga idona saboda bacin rai, Gefen bayan hannu na sa, na,shafe dan guntun hawaye, Aiki nake a kitchen amma ina tunanen yadda zan fadakar da yaya mun cewa mutanen gidan mu suna bukatan taimakon shi, Babu fuska agurin yaya Abubakar dan iya fada mashi wanan maganan, Haka naci gaba da aikina batare da na samu wani mafita ba daga zancen, Yanzu duk wani girkin gidan da gyaran gida ni ke yin don Anty Sadiya tace wa maigidan bazata iya ba ita, Don duk tayi sai ace ba a iya ci, Ya yace ai ba, ance bane don har da ke baki iya ci idan kinyi, Tun da naga sun fara wanan gardaman na mike tsam nabar gurin don bazan tsaya agabana yana wa mace kamar Anty Sadiya fadan girki ba, Wani lokaci kuma yaya zai ce kada na girka komai zai bada take away akawo muna, Yau ma kamar kullun kasan cewa ranan jumma ,a ce, tun safe na tashi na gyara ko ina na gidan nai muna breakfast lafiyayye, Kafin duk su fito har na gama hada komai, na gyara muna ko ina gidan sai faman kamshi turaren da Maman Bi,u tabani nasa ga yar boner, Cikin wasu fararen material nake masu dan adon silver flowers a jikin su, dinkin dogon rigane har kasa da dogon hannu, sai dan kwalin su dana daura duk da yana sulbewa, Abin da nafara kula dashi, shine yaya Abubakar yajin dadin irin yanayi da yanzu gidan shi yake ciki, Saboda bai iya boye murnan shi da farincikin shi a duk lokacin da yaga ko yaji gidan ya dauki kamshi, Ada na zaci daga shi gar matar duk kaza mai ne tundai irin yadda naga dakin kwanan shi kacakaca, Sai yanzu nagane cewa gyaran guri bana namiji bane aikin mace ce, cikin ma yana kokarin gyarawa ke nan shi, Tun fitowa daga daki na hango, yaya Abubakar acikin annuri , Ga kwar jini kalar nashi da ya kara hasaka shi, yafitar mai da surar shi sosai, Voil ce mai kyau da tsada fara a jikin shi sai kyalli yakeyi, Kokarin zuba kunun kokon da kosai da na dama muna yake yi a cup duk kamshin kosai ya kama dining area din, Fitowa na ke nan daga dakin ina cikin kwalliya bazaka ce nice nai wanan aiyukan ba, Jin karan rufe kofa na yasa shi saurin dago kai yana kallon inda nake tafen, Kunya ne ya kamani saboda irin kallon da yayan nawa ke min don ya ki ko kifta idon shi a kaina, Da sauri na dukar da kaina kasa don kunyar kamani da yai ina mai kallon tantancewa, Anty Sadiya wace take zaune tana dan juya kokon ta a hankali da spoon ta dago ido ta dube shi, Wani irin mamaki da haushin shi ne ya rufe ta wai a ce Abubakar sadaukin da ta sani ne ke irin wanan abin agaban yar karamar yarinya, irina, A gefen shi kadan na dan rusun na ina cewa yaya ina kwana,? Ajiyan zuciya ya sauke tare da cewa lafiya kalau Meenatu, Juyawa nayi da niyar in gaida Anty Sadiya, sai naji muryan yayana yana cewa, Ke yaushe har kika tashi kikayi wanan ai,yukan haka, ne ? Murmushi kawai nai masa ba tare da na bashi ansa ba, Na juya gurin ta na ce ina kwana Anty ? Nasan cewa tun da yaya yana zaune zan samu ta karba min , Inda dai daga ni sai ita ne to ba lalai,ne ta ansa min ba, Yaya Abubakar ya dan motsa kadan daga inda yake zaune, Zauna ki karya ka da, kuma ki tsaya wani aiki har yai sanyi, Da kan shi ya jawo jug din kokon zuwa gabana yana kokarin dauko cup Anty Sadiya ta buga wani tsaki tare da,buga mai harara, Kosai kwara uku ta dauka tare da cup din kokon ta zuwa dakin ta, Batare da kowan mu ya kulata ba mukaci gaba da kwasan breakfast dinmu sai dai gaskiya bazan iya sake jiki na ba, Yaya Abubakar wanda ya tsura min ido yana kallon yadda nake wasa da bakin cup din dake gabana A hankali naji yace, Meenatu , A bazata naji kiran nashi don haka sai na kasa dago kai na in kalle shi, Kaina a kasa na dan ansa cikii,ciki da Na,am,, May yasa baki son cin abinci ne, wai ? Sai a lokacin na dan dago kaina, na kalle shi, Gira ya daga min tare da daure fuskan shi yana cewa, Ko kin fi son idan mutanen gida sun gan ki suce kin ramay sosai, Ga yunwa ga aiki, ? Dagowa nayi da sauri na dube shi don mamaki sai kuma, na dan yi Murmushi tare da girgiza kai na kawai, alaman a,a, Kafin wanin mu yayi magana sai sallama mukaji daga kofan falo, Gaba dayan mu ka juya muna kallon kofan don muga mai muna sallama , Don babu masu shigowa gidan mu saboda masu gidan basu hurda da kowa nake gani, Mace tafara shigowa dauke da yar,ta a hannu ga kuma wani dan namiji yana bin ta, Da mamaki muke kallon ta inda namike tsaye daga inda nakr zaune, Ina cewa Sannun ku da zuwa cikin yar sake fuska, Ganin nayi fara,a yasa matar yin fara,a itama tana cewa ina kwana na ansa cikin harshen mu na sakkwatawa da lahiya lau, Gurin da yaya Abubakar yake zaune ta ke kallo tana ce mai ina kwana,? Ya amsa mata sama,sama da lafiya, Cikin nuna jin kunya da nauyi kanta a kasa take cewa, Ya,ce nace ma wai yana waje, A cikin yar mamaki yaya Abubakar ke cewa wake nan? Batai magana ba sai yar murmushin da tayo kawai, Mikewa yaya yayi zuwa waje don yaga ko waye ke mai sallama, Malam Mudi ne ashe yaron wajen aikin su yaya , Shine yazo da maidakin shi don ta gaida mu, Sun taba zuwa alokacin suna tsohon gida sai Anty Sadiya ta bar su a falo zaune ta shige daki abin ta, A cikin yar fara,a nace mata, ga kujera ku zauna don ban san ko daga ina take ba, A tare da malam Mudi, yaya yashigo gidan, Yana cewa shigo mana ai ban san cewa kasan anguwar ba, Yace ai kwatance malam Abdullahi yai masa, da haka yagane gurin, Shi ne su kazo yi muna barka da jumma,a gurin da nake kokarin fitowa daga daki bayan na saka hijjabi, Suke kallo na a cikin mutumci na gaida shi tare da girmamawa, Zai dan girmay ma yaya Abubakar kadan ga shekaru, Addu,a ya dinga yi yana mai rokan muna zama lafiya tare fatan samun zuri,a masu albarka, Yaya Abubakar ne kawai ke cewa Ameen Ameen, cikon jin dadin addu,an, Anty Sadiya ta fito dakin ta dauke da cup din da tasha kunun a ciki, daga dakin ta Ganin bakin mu yasa ta kallon su a cikin mamaki, tana kokarin tuna kamar ta san su Shiga kitchen, take kokarin yi don aje kayan dake hannun ta, Yar rigar barci ne ajikin ta mai guntun hannu sai zani da ta daura saman rigan, A take naga annurin fuskan yaya Abubakar ya gushe saboda ganin yadda Sadiya ta fito waje ga bako hakans, Ta gane abinda yake nufi don haka naga ta shige kitchen da sauri, Yaya ne ke cewa zasu zauna anan zasu yi ni damu har su dawo gurin aiki, Sosai naji dadin jin yau muna da abokan fira a gidan babu zaman kadai ci yau, Suna fita Anty Sadiya wace ta boye a kitchen don hararan da tasha tai saurin fitowa, Ina kwana matar ke mata amma bata tsaya amsawa ba tashige dakin ta, Kallon matar nayi tàre da kokarin daukan yarinyar ta ina cewa zo mu shiga ciki, Dakina muka shiga ida matar ta fara kallon yadda na dan gyara dakin nawa, Dakin yaba sha,awa sosai don yadda ko ina yake tsab ga kamshi na tashi Kitchen na koma na dauko sauran kosai da kokon na kawo wa yaran tare da sugar, Ina gyara yarinya, na ke cewa ya sunan ki yan mata,? Uwar ce tace min Hanifa don sunan mahaifiyar shi ce, Nace tau na gyarawa yarinyan, rigan ta tare da mika mata kosai guda daga, Tv na kunna masu inda muka kai mbc 3, don yaran su kalli cartoon, Anan gari kuke ne ? Tambayan da nai mata ke nan don mu kauda shirun , Tace eh aida tare muke can Lagos da su sai daga baya, baban su ya dawo nan garin saboda maigidan ga. Amma kinga matan nan kamar bata san mu ba ina gashe ta tana shigewa, Yar dariya nayi ina kokarin zama a bakin gadona, Nace ko dai bata gane ku bane ? Hmm ke ce dai bakuwan ta don bata da hali wanan matar, Murmushi kawai na yi, don ban son muyi zancen ta sam, Don mu kau da maganan sai cewa nayi, kin san kowa da irin halinsa Ita Anty ba mai yawan son hayaniya bace, Kafin tace wani abu sai cewa nayi, Wa yaron ta ya ko in dauko maka ruwa ne kasha, Kun san uwa da dan ta sai murmushin jin dadi, matar ta ke yi, Bayan na gama zance da yaranta ne nadan dago ina dariya Matar tadan dube ni cikin nuna sakewan ta, dani tana cewa, May ye sunan ki ne nace mata Amina, amma Meena ake ce min, A a,a ashe sunan mutanen da ke gare ki ? Nace sunan kwarai mai asali ba, Sunan mahaifiyar Manzo Allah ne fa kin ko ga ba karamin suna bane, Matar tace min nikin ga sunana Hajjara, ke ashe duk mune nace acikin wasa, Nan muka shiga hiran suna yen zamani da kuma irin yadda malamai ke fadakar da mu Musanman mata akan sa sunan da baida ma,ana wa yaran su, Daga mace taji suna tana sha,awan shi kawai sai ta sawa yaron ta batare da sanin ma,anar shi ba, Kosan da na ajewa yaran ta takai guda abaki tace amma kuna da masu kosan kwairai a unguwar nan, Ai bana sayarwa bane nafada mata cikin murmushi, Da sauri ta dago kai tana min kallon mamaki jin cewa wai nice nayi, Nake fada mata cewa ai da blender nai amfani na markaden tankwa shi yasa yai lau,shi da kyau, Gaskiya kin yi kokari, don kin ga zaman birni irin Abuja ba wani abincin irin na gida mutum ke samun yi ba, Nace mata, amma ai sai in mace bataso sarrafa abincin ba ko Kinga ai shinkafa zaki iya, sarrafata kamar yin dambu, fate, tuwo dafaduka shinkafa da wake, waina, sai da miya kamar yadda akasarin mata sukagi yi, Wake kuma zaki iya yin faten wake, alale, dan wake da maida yaji, tubani, da sauran su, Ka,fin,in ce wani abu maman Hanifa tace min wai amma gurin tsohuwa kika tashi ko, Dariya tabani sosai nace acikin dariya maman Hanifa sai ka tashi gurin tsofi zaka iya girkin gargajiya, ? Yar ta da ke kuka tana son shan mama ta dan jawo zuwa jikin ta tana kokarin bude riga ta, Tacewa kin san ko wasu uwayen namu ba damuwa sukayi da su koyar da girkin ba, Nai dariya nace mata zama a cikin babban gida yasani iya girkin gargajiya, Girkin zamani kuma a wajen anty amarya na koyi yin su,,, A tare mu kayi girkin rana da ita, don mun san cewa yau,jumma,a ne yasa muka girka da mazajen mu, don zasu dawo dawuri gida , Wa yan nan kayan mata da anty Amarya ta hadamin cikin wani katon bucket din roba kalakala suna debawa Maman Hanifa, tsara da su sabulai, Kamar yadda anty amarya tace min idan nai bako in tabbatar da cewa nabashi koda Sabulaine na wanka ko wanki, Don wai bako rahamane sosai shigan bako a gurin ka wani irin rahamane da kariya,,, Munyi sallama da ita cikin jin dadi da kainan junan mu,,,, ZEEE MAKAWA YELWA [7/31, 17:16] Anty Lantana: 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 3⃣9⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA ALLAH-AL-BASEER' Daga massalaci yake, wayan shi dake saman side, drower din shi a daki ce ke kuka, Da sauri ya dauka don gudun kar ya katse, bai dauka ba, Mama Ladi ce, ke kiran shi a lokacin kafin ya dauka sai da yai dan murmushi don yasan cewa, wani sabon magana ya taso ke nan, Da sallama ya dauki wayan a dadare ta, karba mashi sallaman na shi, Sai kuma hau fadin , Mai sunan malam, watau nace ka sako masu munafukar yar su ashe baka sako ta ba,? Shiru taji yayi don bai da amsan bata a lokacin don haka yaja bakin shi yai shiru, Tambayan ka fa na keyi ? Mama bawai naki turo ta bane , Akwai abinda nake shiri ne akai don kada su san cewa da sanin ki, na turo ta, Ban son kowa yasan cewa da hannun ki aciki don kada su zarge ki musanman malam tsoho, wanda shi ne yai wanan hadin, Ajiyan zuciya tayi tana cewa yanzu naji Allah yai maka Albarka ya ce Ameen, Mama kada ki da,mu zan yi yadda kike son ayi, Murmushi tayi har yana iya jin ta, Kamar zata aje wayan sai kuma tace e,he, sai kuma wani shawara da Baban ka ya shigo min dashi wai zasu zo taya ka murnan samun girma, To bara kaji ban,yarda da wanan ba adinga kwaso jiki ana,zowa har a,kaika abaro, Mama ai kyale su kawai malam ya fada min cewa wai zasu zo, Ni banga abinda zasu zo yi ba ma,? Ashe kaima kayi wanan tunanen, don haka idan sun zo kasan yadda zaka kakabesu gobe bazasu so zuwa ba, Kada ki damu Mama zan yi yadda kike so nagode da shawaran ki acigaba da muna addu,a dai,, To ya su baba da sauran jama,a, Kamar a fili yaji tai dan tsuki, Tace kaima baka da zuciya mai sunan malam dafa hadin kan shi aka hada wanan auren har ya na ikirarin cewa idan na matsa akan sai ka sako yarinyar nan nima a bakin aurena, Subbahanallahi Mama har abin yakai can,? Inji yaya Abubakar ke tambayar ta,, Mama tace,To ina son in nuna mashi cewa nafi shi iko da kai, ne Yaya Abubakar yace cikin yar murya, Mama don Allah kuyi hakkuri, da ke da Baba,, don duk kan ku Allah yace in maku biyayya,, Amma ai shi bai dauke ka da muhinmanci ba, alokacin da muke ta wahala akan karatun ka may yayi shi aciki,? Wani iri yaya Abubakar yaji akan abinda Mama tace wa mahaifin shi,, A hankali yafurta mata dacewa Mama don Allah abarvirin zancen nan don kowa ma yai kokari akai, Cikin hasala tace to nadai fada maka kaji abinda nace mako ? Ajiyan zuciya ya sauke bayan sun gama wayan, da mahaifiyan shi, Komawa yayi bakin gadon shi ya zauna yana mai lumshe idon,shi, Anty Sadiya ce ta shigo dakin a lokacin don tambayan shi, wasu kudi da take so, Tsaye take a gefen shi take cewa Abubakar kudin da nai ma magana ina son sayen, kayan lalura na tun kwana biyu da suka wuce, Bai iya cemata komai ba don tasamu gaba daya ranshi a jagule yake, Da kyat ya iya bude, jajayen idon shi ya sauke a kan ta, Jikin shi tankar anmasa duka yaje ji a lokacin da magan ganun mama sundan taba mai zuciya amma baida yadda zai yi, Da kyat ya iya bude bakin shi yace mata, amma yanzu kin san cewa bake kadai ba ce ko ? Dole ku biyu zanba kowa tayi abinda zata yi da nata, Na kuma fada maki cewa, ban son rashin hadin kai acikin gida na, Tambaya tayi cikin nuna damuwa tana cewa, yanzu don nace ina son sayan yan kayayyakin amfanina shine zakace atare zaka saya muna, Da kai mata kayan aure ni kayi min ne ko tunawa dani baka yi ba, Dariyan takaicine yaya Abubakar yadan sauke yana mata wani irin kallo, Yace ni naira biyar dina bai shiga cikin wanan auren ba, Idan ma har kina tuhumane to banyiwa Amina ko kyaleba tukun, Iyayyen tane sukai mata komai da kike gani sai na samu lokaci zan mata nawa Wani kallo ne ta watsomai tana cewa zakai muna dai ainima irin kayan mutanen da kai min, Yace badai nayi maki ba ada din? Don haka kibani wuri in huta please idan na sauko zamu yi maganan anjima, Cikin fisgan jiki tabar dakin tana yan maganganu ciki,ciki, ****** ********* ****** Shiri sukayi sosai cikin shiga irin mai firgitar da mata, Da ganin su ka ga yan matan birnin irin classic ladies din nan, Su uku ne a,cikin tafiyan kasaita su ke tafe, p0motan Hadi ce kawar sukazo da Ganin cewa yamma tayi yasani yin kwalliya kamar yadda na saba tun zuwana, Cikin wani dogon rigan mutanen kasan Mali shia,, Tsaraban da yaya ya,siyo muna na barka da jumma, nake dan lakata da dancibin shi a falo, Ina zaune a saman kujera, ni kadai a falo saboda yaya Abubakar tun bayan tafiyan bakin muda yaje sallah la,asar Ya shige daki bai fitoba har yanzu, Ita kuma Anty Sadiya un shiga sallamar ta mun samay ta zaune tana, waya, A nan tabarmu, tsaye nida Maman Hanifa da taje sallamar ta Har saida muka gaji mukai mata sai anjima mu ka fita dakin,, Gyara zamana nayi don inji dadin shan icce cream dina, Sai mutane kawai nagani a falon cikin wani irin shiga na tantiran matan zamani, Da mamaki nake kallon su, duk da dai bawai nasan mutanen da masu gidan ke hurda da su ba ne,, Cikin sakin fuska ga taron bako nake masu sannu da zuwa,, Sai wani taunan chewing gun suke yi suna min wani irin kallon kurullah, Mai dauke da tsana da kuma kishi mai zafi a idanuwan su,,,, Kujera nake nuna masu still a cikin sakin fuska ina cewa bisimillah kuzauna, Duk da falon a tsabtace yake amma sai nuna kamar suna jin kazan tan mu, Ruwan gora nadauko masu acikin fridge masu sanyi nadora a saman turen, silver golding, Ke ce Amaryan gidan ko ? Ban basu amsa ba sai dai yar murmushin da nayi kawai, Ina wuni nace masu alokacin da na koma saman daya daga cikkn kujerun falon, A lokacin ne dayan su ke ce min maigidan ko yana ciki, Acikin sakin fuska nace masu eh yana ciki, Ok yi muna sallama dashi please ? Nace tau acikin rashin nuna ko in kula, don dai banga abinda yayana zai yi da irin wa yan nan ba, Ina tashi gaba dayan su sukabi bayana da kallon ban ko yi nisa da su ba, Suka fara zance akaina, very young, Bari ke dai wanan na kusa haihuwar ta ma ai lalai ashe akwai aiki, Hadi wace bata ce masu komai bane sai yanzu tace amma da alaman yarinyar simply ce, A hankali na tura kofan dakin tun daga kofa na hango shi a kwance rigingine saman gadon shi, Hannun shi dafe da goshin shi, zuwa fuskan shi, Idon shi suna a lumshe tankar mai barci, a lokacin , Ganin yanayin kwancin shi yasani juyawa don in sanar masu cewa yana barci, Juyawa nayi don in koma falon , MEENA naji ya fadi a cikin wani irin murya mai ya nayin kasala,, Saurin juyowa nayi ina kallon shi, still yana kwance kamar yadda na samay shi da farko, Cikin dan daurewa tare da nuna dan rudewa nace bakine falon suke jiran ka, Sai alokacin ya sauke hannun a saman goshin shi, Ya sako min idon shi da sukai mai jawur alokaci guda, Fuskan shi dauke da mamaki yake tambayana waye yazo ? Kaina aduke nake cewa wasu matane su uku, su kazo, Mata kuma ya tambaya cikin mamaki, Na daga kai a hankali alaman eh, Tashi ya yi daga kwancen da yake, ya yar tsuki da alamar antakura mashi dai, Juyawa nayi zuwa falon yana bayana cikin tako irin na gajiya, Aninin rigarshi ta sama a dan balle, fuskan shi adan ya mutse, Ganin irin yanayi da yaya Abubakar yafito ni kuma ina ta gaban shi muna saukowa daga steps din, A take Salawatu ta anyana zuciyar ta cewa shiga dakin gurin yayana har munyi wani abu dashi, A cikin mamaki, yake kallon su tun yana saman steps din, Da yar fara,a dauke ga fuskokin su daga shi har su, yake ce masu surprise visiting ? Dariya suka kama yi atare suna cewa muna zancen zamu zo har gida muyi ma murna, bamu samu time,ba Shine yau dai mu kace bari mu rako madam tazo har gida muyi ma murna biyu ke nan ko ? Ga Amarya ga kuma karin girma,, Murmushi naga yaya ya yi don jin dadin abin da suka ce mai, Inda nake tsaye dan nisa kadan, dasu ina kokarin, kauda, remote din de a saman wani kujera, Yaya Abubakar yake ce min Meena kizo ku gaisa da next Amaryana, Azaton su zan yi wani sad re,action, ko shock amma sai sukaga ina dariya da murna na, Nace a ashe Anty na ce tazo gidan ? Yaya Abubakar yace min zo ki zauna ku gaisa yana kokarin nuna min gefen saman kujeran da yake a sama,, Ba musu nazo na zauna yar fara,a na ina cewa, ashe amaryan yayana ne ban sani ba,? Mamaki na ba su sosai karama dani wai na iya barkadon manyan mata, Kira Sadiya su gaisa yaya Abubakar ke bani umurni da hakan,, Mikewa nayi zuwa kiranta ida suka kara bin bayana da kallo gaba dayan su har maigidan, Sauke idon shi da ajiyan zuciyar shi yai daidai a cikin na Salawatu wace duk kishi ya turnuke ta alokacin, Murmushi irin mai kashe jiki ya sake mata, oole bata san lokacin da ta mayar maida irin murmushin ba,,, Bayan na fada mata cewa yaya yace tazo su gaisa da baki a falo, Inajin lokacin da tai tsuki alaman an damay ta fa,, Nadawo falon ina cewa barin dauko maku abinci ko ? No, No ,No ki barshi kawai we are ok ? Anty Sadiya tafito fuska adaure babu walwala kamar kullun, Ganin su yasa ta kara daure fuska tana cewa au, ku ne ma, ? Shine tace wai baki, Sun gaisa sama sama da ita suna mata wani kallon raini,, Basu wani dade ba su kace za su tafi, Na ce tun yanzu ku kuwa aida kubari dan anjima mana, Kudi Lubuna ta debo daga cikin jakar ta tanacewa to amarya gashi kiyi hakkuri da su ba yawa mun sayi baki dai ko? Gaskiya bazan karba na ce ai,kozuwan da kukayi ya wadatar, don mun gode gaskiya, Haba dai ki karba mana kada ki raina please, ko bakiyi farin ciki da zuwan mu bane,? A,uzubillahi mina,shedanin, rajin nafadi azuciya na na karba da Bissimillah, To wacece Anty nawa ne wai na tambaya alokacin da suka mike tsaye don tafiya, Dariya sukayi ba tare da sun nuna min ita ba, Harkofan fita falo mukai masu rakiya dukkan mu har may gidan Wanda a tare suka fita waje dashi yana masu rakiya, ****** ********** ****** A gurin da na sallamay sallah magrib nake zaune ina addu,a, Tunane na keyi na matan dazu da yaya Abubakar yakira da wai wace zai aura, Wanan ai duk manyan matane, Babu tamtama sungirmay mu har shi, don babu warin shi aciki, Mamakin may yagani agurin da har ya jashi haka ? Naja yar tsuki nace kai namiji, ina cewa Anty Sadiya ta tsofe min ashe ga mamawo nan shigowa, Gaskiya ni kan tawa ta samay ni zama cikin manyan mata, May zan gane anan ? Dawani zanjine wai,? Allah ka kawo min dauki, ya Allah, Banniya koda motaswa ba daga inda nake zaune takure, saboda damuwan da na shiga, Kudin da suka bani yana zube saman gadona ina jiran maigidan ya dawo in kai may, Don nasan cewa idan an ma alheri ta hanyan mutum to yakamata kaba shi sai in shi yace bai so, Da farko anty sadiya naso inba kudin, amma sai naga bayan rakiyan da mukai masu ta wuce cikin part din ta da karfi, To shi yaya Abubakar bai ko jin nauyin fada muna cewa wai matar da zai, aura ce haka ??? Munazaune falo da daren kamar yadda ya umurce mu da yi duk dare, Tv ke ta aiki inda dani da Anty idanuwan mu su na kan TV, Yaya Abubakar ya na daga duke saman laptop din shi ya na duba sakon ni, ciki,,, Yan dubu dubu ne guda ashirin sabbi fil da su sai kamshin banki su keyi da na turare, A saman dan table din da system din yaya yake na aje kudin a gefe,,, Da sauri yadago kai yana dan kallo na, Na may ye kuma nace kudin da suka bamu ne dazun, To aike su ka ba bamu ba ko ? Gefen da Anty Sadiya take zaune nadan waiga ina kokarin mika mata kudin, Ki barshi kawai tunda ke suka ko ? Ban iya cewa komai ba don irin yadda naga tayi da fuskan ta, Gefen kujeran da yake naga yafito da wasu kudi masu yawa, a hannun shi, Duk lokacin a takure nake don dai ni wanan zaman falon yazama min zaman takura gaskiya,, Kirga kudi naga yanayi, sai da suka kai yadda yake so sai naga ya mikawa Anty Sadiya, Sauran kuma ya miko min yana cewa kowa tasai abin amfanin ta dashi , Kudine masu yawa koda ban kirgaba sai da naji tsoro, Ya dan kara dago da fuskan shi yana cewa zan samu wani driver ya kai ku kuyi sayayyan ,,,, Kudin nake kallo a hannu na kara juya su cikin mamaki waini Meenatu yar Baba keda wanan kudin da sunan nawa hallal malal,,,, ZEEE MAKAWA YELWA [8/1, 06:33] Anty Lantana: 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 4⃣0⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA ALLAH-AL-HAKAM Assalamu Alaikum yan uwa musulmai, ku taya mu adduan ga yar uwar mu masoyiyar mu, SAFIYA ABDULLAHI HUGUMA , marubuciyar WAYASAN GOBE,,, DA DAN GAN,TAKARZUCIYA,,, Ta haifi diya mace yau sai dai munyi missing din lovely BABY Din namu, Allah yajikan ta yai mata Rahama,,,, Ita kuma Uwar Allah ya bata lafiya,,,,,👏👏👏👏 Tafiyan babu maihafin yaya Abubakar babu nawa mahaifin a ciki, Daga Baba Musa sai Baba Shaibu da Baba Hamza sai Baba Wadda, sai kuma malam Jibrin ladan, sai dai a hikima irin ta malam tsoho sai yace yayana Ibrahim ya zo a madadin Baba na, Wanan abin yan gidan mu basu ji dadin shi ba sosai, Saboda muna da uban nai da ba su zo muna dakuma manyan yayye da basu zo ba, Amma shine za,ace wai Ibrahim yazo, bayan gasu su ma sunan son zuwa, Mama Ladi a ranan kamar tayi ihu don dai kawai anfi karfin ta ne, Don har aike taiwa diyan ta dake aure a cikin gari mata suzo tana neman su, Cikin tashin hankali suka iso gidan don su azaton su wani abune yafaru, Cikin muryan tashin hankali ta zaiyyana masu komai, Anty Safiya ce ta katse ta da cewa to Mama don iyayyen maza sun tafi gurin yaya Abubakar shine kuma abin ya da hankali, Mama irin wanan abin shine fa ke kara sa yaya bai damu da kowa ba a cikin dangi, Ke rufe min baki Safiya wani lokaci saboda irin halin rayuwan ki ke da samira sai nake ganin kamar bani na shayar daku nono ba, Ida asibiti na haife ku da sai ince ancanza min ku ne, don sam babu inda kuka biyo ni, Anty Samira wace ke ta fama da laluran cikin ta ta ce, Mama, Wanga zance ma in har wani taji ta aikunya zamuji Duk mutumin da baida yan uwa aduniya ai ba kowa bane, Shege ma yana da dangi balle mai iyayye haka kamar yaya Abubakar, Walle da nasan kan wagga managa aka kirana da ban zo ba, Inkin hana yaya ya turo wa iyayyen mu alheri ai ita Sadiya naga tana aikowa nata yan uwan, Kuma suna zuwa suma su ci arzikin su dawo, May yasa baki hana su ba,? Sai,kadan daga cikin diyan nata ne suka dan mara mata baya da cewa wai harda Ibrahim shim ? Lalai yanzu sun samu guri ke nan? Indai Sadiya na ai Meenatu bataga gidan zama ba, Don Walleh turo waje zatayi, Wanan ka zama da kishiya, ? Basu dai gane komai ba tunda bazasu iya hana abinda malam tsoho ya kulla ba don ba wuri, Don shi bai wasan jika da kaka da yara sai in ya so hakan, ****** ********* ****** Washegari na tashi duk jikina yana min ciwo saboda yadda yayana ya tafiyar dani a gado daren jiya abin bai misaltuwa, Don har tsoro yabani irin yadda naga ya koma kamar wani tsohon driver da ya samu sabuwar mota, Sam yau banda kuzari a jikina hakan ne yasani dan kwantawa, À gurin da nai sallah asuba anan barci mai nauyi ya dauke ni, Bayan su baba sun kamo hanya ne, Baba Wadda ya bugo mai waya cewa gasu a hanya, Bai so zuwan su ba acikin ran shi don mutum ne wanda baya son takura ko kadan, Kuma bai saba da irin haka ba kayi baki suzo maka da yawa, Yayi tunanen to zuwan su may zai karashi da shi inma murna ne ai sun mashi a waya ya isa ko,? Kai malam tsoho badai rigima ba,yanzu haka shi ya daukan masu shatan mota yasan da kudin shi, Malam malam yace acikin zuciyar shi wanan tsoho da yayi ilimin zamani da ai san yaya zaiyi ba don wayo da hikima, Lumshe idon shi yayi tare da dan murmusawa don tuna wa da Meena a daren jiya, Bai taba samun daren da ya rayashi cikin jindadi da walwala ba irin daren jiyan adakin shi da Meenatu, Gaskiya malam tsoho ba karamin gudun mawan rayuwa yai mashi ba anan, Dan zaman yarinyar nan a cikin su, a iya kwanakin da tayi atare da su, Yasa shi gane cewa mace wani rahamane ga da namiji so sai, Yarinyar nada wani bawai na bam mamaki a tare da ita sosai,, Dan rufe idon shi yakarayi yana tuno abubuwa akan ta da dama, Barcine yai awon gaba dashi a cikin irin tunanen,da yake ba tare da ya sani ba, Don shi ma yana jin gabobin shi ba lakka a lokacin yana bukatan dan maimaita barcin, Ya kai dan wani lokaci yana barcin shi hankali a kwance ya farka , Ganin irin harzuwa lokacin safiyane yasashi mikewa Su biyar ne chur su ka, kamo hanya tare da tsaraba irin kayan amfanin mu na gargajiya, daga gurin mahaifana, da malam tsoho, Sai dai duk gaba dayan su a motar sai tsan mani sukeyi idan sunzo gidan yaya Abubakar za su samay,ni a rakube gefe guda, Ko kuma acikin rashin walwala da kuma rashin sakin jiki Don a cikin su ba bu sa,a yi na dole in koma abin tausayi acikin su,, Babu dai irin zancen da basu nasawa zukatan su ba akai na,, Saboda, a ganin su ban kai matsayin da zan zauna a cikin jin dadi gidan dan uwan nawa ba, Ina farkawa naga rana yayi sosai a lokacin abinda ya sa ban damu ba saboda yau ya kasance weekend ne, Babu zancen zuwa aiki a gurin yaya Abubakar sai dai idan yana da wani uzuri a can din, Wanka na shiga bayan na fito ne na zauna na gyara jiki na cikin wasu atamfa zani da riga, Ina kokarin daurin dan kwali ne yaya shigo dakin yake ce min, Wai su Baba Musa suna hanya tare da sauran yan uwa, A yadda na fahinci fuskan shi duk da dama rashin walwala dabi,ar shi ce hakan, Amma na hango rashin jin dadin haka a tare dashi sai kawai naji banji dadi ba Don dai nasan cewa wanan tafiyan tunda nashi ne da wuya idan babu mahaifina aciki, Kamar in tambaye shi may za ai masu sai kawai na share shi don inga iya gudun shi, Kokarin fita ya keyi daga dakin nawa, nace mai a hankali don Allah yaya ina son in da shiga gidan Maman Bi,u in bada sako, Juyowa yayi tare da dan tsura min ido kamar zai yi magana, sai kuma ya juya yana cewa kada ki dade please, ****** ********* ****** Maman Bi,u ne da Fattu a zaune tsakar gidan su, suna gani na suka shiga washe baki, Nagaishe su inda nadan rike hannun yaron Fattu ina wasa dashi, Gurin da Fattu take zaune nake kallo inda nace mata nazo ne don Allah idan Hamza yana gida ya sayo min sako a kasuwa, Ban boye masu ba naje sheda masu cewa mahaifan mune zasu zo daga gida taya maigida murna, Maman Bi,u ce ke tambaya mu yan uwa ne da mijina nan na sheda masu yadda muke da shi, Itace da kan ta tabani shawarwn abinda zan sayo ai masu kafin su iso, Naji dadin hakan sosai don dama Anty amarya ta fada min cewa uwar daki da tasan ciwon kan ta ke karasa mace hanya nagari, Ba uwar dakin da zatai maka wayo ba tadinga cuta maka, A tare da fattu muka koma gidan mu, ida muka fara masu girkin na taron bakin mu, Hamza wanda nake cewa Babana shi ne yai tazuwa sayo muna duk abinda muke bukata, Sai musalin la,asar suka shigo gari inda duk na rasa yadda zanyi saboda murna, Basu shigo ba sun tafi yin sallah a massalacin unguwar mu, Kafin su zo mun gyara masu dining table yadda zasu wallah, Sai a lokacin yaya Abubakar yadawo gidan cikin yar rudewa yana cewa wai ya tafi kai mota service ne sai kuma ya tafi gidan abokin shi, Ganin irin yadda na aiwatar da komai yasa shi dan tsayawa da mamaki a fuskan shi, Don da farko har ya fara cewa, to gasu sun iso yaya za,ayi da abinci don yaga agajiye suke, Sai idon shi yai arba da kulolin roban da na bawa Hamza kudi ya sayo min da rana, A hankali yadinga budewa, abinda yagani a ciki ne ya bashi mamaki, Cikin mamaki yake kokarin magana amma sai mukaji sallaman su shigowa, ciki, Da murna nake masu sannu da zuwa, inda, suke ta kokarin kallon yadda nake Gwiwa bibiyu a kasa na kai ina masu sannu da zuwa,, Amina ke ta kezam mutane Abuja da, da ko ? Gani yayana Ibrahim nayi acikin a lokacin da nake raraba ido inga Baba na, daga cikin su, Murna sosai nayi tare da kasa boye farin cikina a fili, Abinsha dana tanadar masu agaban su sun fara dauka Anty Sadiya wace, yaya Abubakar ya taso agaba tafito falon cikin yar sakin fuska, tana cewa, A,Baba kune tafe ashe ? Sannun ku da zuwa ? Nan suka shiga gaisawa da su tare da mata ya kwana biyu, Abokin tafiyan su Baba makwabcin mu da malam ya turo tare da su ne ke cewa, Abubakar munyi murna munyi farin ciki da wanan karin girma da a,kasamu Allah ya kara daukaka , Sai sauran su Baba su ma suka dauka kowa da abinda yake cewa gurin iyin addu,an shi, Gani su babane zallah yaya na Ibrahim ne kawai yaro yasani cewa barin kai mashi abinci daki na, ****** ********* ****** Zaune a dakina tare da dan uwana yana cin abinci, Sai kallon mamaki yake min a lokacin ya na cewa Meena kega yadda kinka koma kuwa, Murmushi nayi ina tsiyaya mashi lemo a cup, nace kai haba ya Ibrahim har yaushe nabar ku dazaka wani ce na canza, Tambayan shi labarin kowa agidan mu nayi tundai mamana da Baba na sai malam tsoho, Nan yaje sheda min yadda malam tsoho ya dage da cewa sai anzo dashi, dole don ya dubu ma shi ni,, Yaya Abubakar ne ya shivo dakin yana waya kuma hankali na gare mu, Da hannu yai min alamar inzo, nadan taso da sauri zuwa kiran da yai min, A bakin kofa ya tsaya ni kuma ina daga cikin labulen dakin na dan daga labulen fuskana yana facing din shi, Ya Ibrahim daga cikin daki sai mamaki yakeyi haka kuma su baba su da wutsiyan ido suke satan kallon mu, Tambaya na yaya Abubakar keyi wai yaron nan da yaga ina aike hamza yaken son suje su diba masauki, tare, Nace O,Babana Hamza batin ce Fattu ta turo min shi, A waya na fada mata cewa ta turo shi inji yaya Abubakar, Ba bata lokaci ya zo ya samay shi suka fita tare, zuwa wani masaukin baki mafi kusa, Yayana Ibrahim tare da Baba Wadda suka bisu zuwa gurin don su ga gari da kyau duk da dai yamma ya yi a lokacin, Sosai su Baba su kaji dadin wanan ziyaran da suka kawo muna, Anty Sadiya itace da girki amma sai ta ki fitowa ta yi wani abu, Har dare nake ta faman dawainiya dasu batare da gajiya ba, Suko sai faman samin albarka sukeyi don jin dadi, Bayan sun dawo daga sallah Isha,i ne ina dakina a lokacin, Na gama gyara ko ina na gidan don haka na samu na gyara jiki, tsab, Ajiyan zuciya na saukar a hankali ganin cewa na gama hada komai har zuwa abinda zan yi da safe gobe idan Allah yakai mu, Jin shigowan yaya Abubakar dakin cikin shigar kananan kaya sai faman kamshi yakeyi, Kaina sunkuyar kasa daga inda nake kwance bakin gado, Kokarin mikewa nake yi zaune amma sai ya dakatar dani ta hanyan dan rankwafo min, Daf da fuskana yakawo fuskan shi ta yadda zamu iya shakan numfashin junan mu, A hankali kamar da wani adakin yake ce min wanan kayan sun karbi jikin ki har na kasa daurewa, Sai naji ya hada bakinshi da nawa ya fara tsotsawa, a hankali, Idona na kara lumshe saboda bakon abinda ya ziyarce ni, Kanshi nadan shafo daga baya abinda ya bashi mamaki da daurewa ke nan Kokarin kara shige min jiki yake yi amma sai na daure nace , mai cikin murya mai kama da kasala, Yaya kayi hakkuri banice da kai ba ba yau kuma gamu da baki a falo fa, Wani tsaki naji ya ja tare da mikewa daga samana gaba daya yana maida numfashi guda guda, Muryan shi naji a yayinda idona yake dan lumshe, saboda re,action din da na samu a lokacin Zan tafi da su in kaisu masauki kizo kuyi sallama da su kafin su tafi, Mikewa nayi tare da gyara rigana da yaya ya mutsuke min, Najawo hijjab dina har kasa nazumbuda sama a tare muka fito falon nidashi, Wanda duk wanda ya ganmu a lokacin dole yaji sha,awan mu, Daga bayan kujera na dan tsaya ina masu saida safe, cikin girmamawa, Ina tsaye har suka gama fita daga falon gaba dayan su, Yaya Abubakar kusan shine mutum na karshen fita daga falon, Kada ki kwanta kidan jirani indawo please yafadi cikin daure fuska, Nikan ina jin tashin motar su nai saurin komawa dakina nakullo, kofa, Dama agajiye nake barci ne ya daukeni mai karfi, Ban tashi farkawa ba sai zuwa karfe daya na dawani abuna dare, nadan bude idona, Gaba daya kaman a mafarki nake jin kamar nishi akeyi aduk gidan namu, ta ko ina, A hankali nadan fare bude idona dake tare da barci acikin shi, Sai kara jin wanan sautin daya tayar dani barci nake ji, Addu,a nafara jerowa don nai man tsari daga sherin shedan, Tsoro sosai ya kamani don ban ko iya motsa koda yatsan hannu na alokacin saboda tsoro, Wani abu nake ji dadaren kamar guguwa ya turnike ko ina, Gashi fitsari nake ji sosai a lokacin kuma ban iya shiga bandaki don tsoro, Addu,an naci gaba da yi can naji wanan abin yana lafawa a hankali, Da fitsarin ya matse hakana namike a cikin tsoro na shiga bandakin, nasake shi , Wani irin mugun kara naji daga waje tabayan bathroom din nawa, Da sauri nafito najawa kofan bathroom din na fada gado don tsoro,, Sai kusan asuba shedan ya rudeni barci ya kwashe ni, Abinda ya jawo min makara ke nan aranan, sai da haske yadan yi na farka da ga barci, Koshi saida yaya yadawo daga sallah yaga har zuwa lokacin ban fitoba shine ysi ta bufamin kofa har na farka, Da kyat na iya mikewa zuwa kofan dakin na bude kofa, Tsaye yake kofan yana saye da farar jallabiyan sa da yar fulla fara kal, akanshi, Hannu shi dauke da tasbaha yana ja a hankali, Yadda ya ganni a hargitse ya sa shi saurin cewa subbahanallah may ya faru Meena ? A hankali cikin daurewa nake ce mai babu komai bawai ya yarda bane amma sai ke ce min kinyi sallah, Yanzu zanyi nace tare da kokarin shigewa na nufi hanyar bathroom,, Kallon zargi yake min har na shige, bathroom din, girgiza kan shi yayi tare da komawa sashen shi batare da ya yarda da ansan dana bashi ba,, Kafin wani lokaci har na,gama hada ma bakin mu breakfast ko, A ranan zasu koma birnin kebbi don haka yaya ke ta zirga,zirga akan su da motar da su kazo da ita,, A zaune nake ina son in karya a daki na saboda falo akwai su baba aciki, Zan iyacewa, tun safe yau banga Anty Sadiya ga idona ba, Wanan dan zamana dasu yazama mata tankae dabi,a aduk ranan da tai girki takwana dakin maigidan bata fitowa da wuri, Kuma haka zata wuni acikin wani orin yanayi atare da ita, Shigowan shi dakin yasani dan dago kai na kalleshi ga abincin da na tasa gaba ina kallo na kasa ci. Saboda damuwan da na tashi dashi yau, a raina, don nakasa fitar da tunanen abinda naji agidan daren jiya ,,, A hankali ya karaso har zuwa inda nake zaune, irish da kwan da nazuba a plate na kasa ci Shi yasa hannun shi ya dauki spoon din abincin ya, debo , A,zato,na shi zai ci amma sai naga yamiko min alamar in bude baki, Ba musu don banga fuskan haka ba na bude bakina a hankali yasa mun, Sai dana tane ina kokarin hadewa shima ya mai da spoon din yadebo yasawa bakin shi, Bayan ya hadiye ya na shirin debo wani ne yake cewa, Na rasa abinda zan ba su Baba Musa wallahi don sunce lalai yau zasu tafi, ba fashi, Ido na dan dago nadan kalleshi sai kuma nai saurin saukewa Yaya ka basu kudi mana sai su je su sayi abinda suke bukata, dashi, Don ka ga za sufi bukatan kudin akan wani tarkace, Kallo na yayi tare da nisawa, yace amma kin sa innace zan basu kudi to kaman nawa ke nan, Nace yaya ai kaike da aljihunka , don haka sai ka kiyasta, Yadda zasu iya sayen tsaraba a hanya da kuma in su isa gida su sai abinci da sauran kudin Wani iska naji ya furzar daga baki shi tare da sauke ajiyan zuciya, Kudi kaman nawa sai naga ya mike ba tare da ya ji may zance ba, Fitan shi dakin ba,a da deba yayana Ibrahim yashigo dakin, nawa da sallaman shi, Bayan mun gaisa ne da shi na mike na nufi wardrobe dina na dauko kudin da ke ciki, Gaba daya kudin da suke a hannu na na mikawa, yaya Ibrahim su, Sai naga ya bude baki yana mamaki, Zaunawa nayi ina cewa ka kaiwa baba kace ya sai abinci saura sai ya gyara motar shi, Meena ina kika samo wanan kudin haka masu yawa, ? A takaice nabashi ansa da cewa yaya ne yabamu su jiya wai musai abinda muke bukata, To ni may zanyi dasu, ni da zan koma sokoto kwanan nan, inshà Allah, Ok tau yayi zan masu bayani nan yake fada min bayanin sokon kayan da sukazo min dashi, Shima dubu biyar nabashi na ce kuma yaba Baba wada da suke tare dubu biyu, A tare muka fito falo da yayana a lokacin ne nake jin su Baba Musa suna ta zabga godiya, Suna ganina naji suna cewa Amina kiyi muna godiya gurin mai sunan malam, Yaba kudi masu yawa, muda mukazo murna kuma mun kawo mashi dawainiya, Kudi yaba yaya Ibrahim wai yakai ma Baba na da kuma sako akaiwa nashi mahaifan, Sun tafi sun barmu acikin jin kewan su Tafiyan su bada dadewa ba zazzabi ya rufe ni saboda rashin barcin da ban samu ba,,, ZEEE MAKAWA YELWA,,, [8/2, 07:04] Anty Lantana: 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 4⃣1⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA ALLAH-AL-A'DL Sai yama lis su Baba Musa suka isa Birnin Kebbi, Kowanen su dauke da tsaraban shi kamar su Manja, Doya, da sauran su, Nan take gida ya hargitse da murna cewa sun,dawo, sundawo, Mama Ladi da sauri ta tura jikanta,waje don tagano mata ko da may suka dawo,, Wanan tafiyan kowa sashe na gidan mu sunyi farinciki dashi sosai Da wanda ya tafi da wanda bai tafi ba ma ya sheda cewa an tafi, din, Malam tsoho wanda yan aiken nashi su na zaune a gaban shi suna bashi sakon shi da labarin abin da suka gano mai acan, Sai kada kai ya keyi ya na dan murmusawa a hankali, Labari suke bashi amma zuciyan shi sai hamdala ya ke yi saboda TARKO shi ya fara kamawa ko, Sakon kudin da suka zube mai agaban shi kuma suke sheda mai abinda Abubakar yace, akan sakon, Murmushi yayi bayan yagama sanin cewa TARKO shine yai aiki, In ba haka ba sau nawa Abubakar ke zuwa amma bai ce ya sha fruit's da kaji ba da kudin shi , Lalai wanan zancen daga aikin Meenatu ce don duk cikin jikokin,shi itace tasan cewa yana shan fruit sosai don mahaifin ta na yawan sayo mai idan ya tafi kauye, Itace ke kawo mai idan an sawo takan ce mashi mai kwadan diyan icce, Kuma alhalin idan ta kawo bata wucewa sai an,sha shi tare da ita, Murmushi ya karayi yana cewa nasan cewa zaki iya Meenatu don hakkurin ko zai kai ki ga cin riba, gabadayan mu, Amma duk yanzu ba,za,a gane may ya ke nufi da wanan hadin ba sam, ****** ********* ****** Daga Baba har Mama na shiru su kayi suna kallon sakon kudin da na turo masu dashi, Kowa da abinda yake kiyastawa a zuciyar shi a lokacin har zuwa lokacin da yaya Ibrahim ya gama masu bayani kamar yadda nai mashi, Ajiyan zuciya Baba na ya sauke tare da numfasawa, Yace wa yaya Ibrahim ita Aminatun ce taba ka duk wanan kudin duka, Yaya Ibrahim ya ce wallahi ba, Nima abin sai da ya bani tsoro nake tambayan ta ina ta samo kudi masu yawa haka? Sai tace min wai shine ya basu ranan Jumma,a yace ko,wacen su ta sai abin bukatan ta, To ita kuma taga cewa ai sokoto zata dawo makaranta Bazata yi komai da su ba shiyasa tace in kawo maka ka gyara motar ka da shi,, saura kuma kasai muna abinci, Dubu Dari da hamsim ke nan har wanda yaya Abubakar ya aiko masu dashi, Shi kuma yaya Ibrahim ya tashi da dubu,sha biyar, Ni na bashi dubu biyae yaya ya basu goma,goma shida Baba Wadda, Daga inda Mama na take zaune ta kurawa kudin ido tace malam a dai bincika tukun kafin ataba, Baba yace mata ai dole duk da nasan irin tarbiyan da nai ma diya na amma dai dan yau ne baka shedan shi,, Kudin ne ya hada gaba daya tare da mikewa zuwa gurin malam, da,su, Saida baba ya gama mashi bayani komai sanan malam tsoho ya dan tofar da miyaun goron dake bakin shi, Yace, masha Allahu Aminatu Allah yai maki albarka, Yanzu sai kaje kayi yadda tace dasu saboda babu dadi mutum yana taimaka maka bai ga kayi abinda yake son kayi ba da kudin, Yarinyar ka irin tarbiyan da kai matane take aiwatar wa, Don haka addu,a zaku bita dashi Allah ya kare muna ita daga sherin masu sheri, Ameen inji Baba na wanda ya mike jikin shi duk ya mutu saboda murna, Shekara nawa yana neman kudi amma bai iya tara su haka ba alokaci guda, Yau sai gashi yar shi Allah ya azurta , ta jikin dan uwan ta, Kamar yadda malam yai mashi bayani shima haka yaiwa Mama na wace ya samu a cikin damuwa, tana ta faman tunane kala,kala, Baba bai tsaya wani dogon guri ba fitar da kudin da zai shiga kasuwa don sayen abinci, dasu, Saura kuma ya kasafa su ta yadda ya dace ayi da komai, ****** ********* ****** Mama ladi wace take ji kamar ta suke don bacin rai , Yadda yar rahoton ta tai mata bayanin irin kayan da taga matafiya sun shigo dasu gidajen su, Har sashen ta Baba Musa ya shigo yabata sakon da Yaya Abubakar ya bashi ya kawo mata tare da fada mata sakon baki, Ya juya zai tafine yaji muryan Mama Ladi tana ce mashi, Baka fada min ko may ku,ka samo ba a gurin shi da kukaje, Don yara sun fada min sun,gan ku da tsarba kaya masu yawa kun shigo gida da su, A hasale Baba musa wanda babu ruwan shi dama da harkan kowa a gidan don bai son raini Haka yake kamar Baba gurin rashin kula kowa acikin gidan mu, Dam Baba na ya dan mutunci da babban wansu watau Baba Buhari,, Cikin irin muryan shi na masu saurin magana yace ai sai kije ki tambaya ko gurin wanda ya ba mu don yafi maki sauki, Fuuuuu, ya wuce batare da ya tsaya kara sauraren may zatace ba, Nan Mama ta hau sababi tana kumfan baki ita adole anje gurin dan ta an yi mai maula, Amma shi Baba Buhari da Baba musa ya kai mai nashi sakon yadade yana kallon gudin, Can dai ya nisa yana cewa tau musa nagode Allah yai masu albarka ya kara rufa asiri, Ameen, Ameen inji Baba Musa wanda ke tsaye tare da yayan shi, Ai Buhari baka ga irin taron da muka samu gurin yaranan ba wallahi, Kaga ikon Allah ko kai ai shi Wadda wanda ya saba zuwa yace, A gaskiya gidan mai sunan malam ya samu canji sosai, Ga abinci an,muna lafiyayye ga kuma gurin kwana mai kyau sanan ga wanan irin alheri haka,? Madalla inji Baba Buhari yace aiko abu yai kyau ke nan gaskiya, Suna watsewa da,ga gurin kowa ya tafi yin abin bukata da kudin,, Ganin yau Baba sai harkoki yakeyi yasa mama ladi jin wani irin bakin ciki a rayuwan ta, Idan akwai abinda taki jini shine taga Baba Buhari a cikin walwala yana sayen abu ana girkawa mama ladi na ci,,, ****** ********** ****** Kayan tsaraban da aka kawo min daga gida na dan bude su ina dubawa, Kayan yaji ne da man shanu da daddawa, kuka, suborodo, da bussashen kubewa,da kuma garin farar masara mai yawa, Abinda nasan zan mu bukata kafin in wuce kawai na bari sauran na kira nobar wayan, Fattu ta turo Baba na Hamza yazo ya daun masu , Ba,afi wasu mintina ba sai ga Maman, Bi,u da kanta ta shigo yi min godiya, Har kasa tsohuwar ke kokarin kai wa amma na hana ta sacewa haba dai Mama ba komai ai, A cikin daurewa na karasa,duk aiyukan dake gabana, Inda har zuwa lokacin abin da naji, daren jiya yana a cikin rai na, Saidai wazan fadawa wanan zancen ne ? Don haka na daure na rike abin a zuciya na ni kadai, Da dare na karbi girki inda nai ta faman dawainiya da Yayana Mijina, Daya daga cikin rigunan barcin da Anty Amarya tasayo min guda biyar ban taba amfani da shiba sai yau na jawo shi,daga kasan kaya na, Turaren da Maman Bi,u tabani na kara shafawa yau ma again, A hankali na tura keep fan shiga dakin yayana Abubakar Dakin yana ta faman kamshin room fresh din da na feshe shi dashi, Can na hango shi tsaye a bakin window dakin iska na dan kada fararen labulen sama, Ya na dan tsaye yajingina jikin shi da bangon dakin, Kafan shi guda ya na tokare ga bango ya dan dafe bayan shi ga gina, Tun kafin in karasa isowa gurin da yake na fahinci da wanda yake wayan, Mama Ladi ce don irin yadda naji yana ta bata hakkuri yana cewa mama kiyi hakkuri za,a yi yadda kikace din, Ai ba wani abu mai yawa na basu ba kawai na shan ruwa hanyane na basu, Tun lokacin da ya hangoni shigowa dakin na ji harshen shi ya fara sarkewa yana dan ce, mata,, Mama zan kiraki da safe in kara maki bayani insha Allah, Direct gurin da yake tsaye na nufa cikin irin tafiyan da ban san da cewa na iya shi ba sai yanzu, Hannu ya mika min alamar inzo gare shi gurin da yake tsayen, Ba musu nanufeshi a hankali, yayin da ya ware hannaye shi dukka biyu na shige ciki, Duk da waya ya,ke yi da mama bai hana shi sauke wani irin ajiyan zuciya ba, Tare da lumshe idon shi, yana shakan kamshi turaren da na shafawa jikina, a hankali sai faman sauke ajiyan zuciya yake yi, Ita ko Mama sai faman fada takeyi acikin waya tana cewa duk abinda kake shiryawa akan wanan yariyar kada ka wuce wanan satin da zamu shiga,, Abinda kunne na yajiwo min yasa nagane cewa dani mama take, Kai na na matsa a cikin fadaden kirjin yayan nawa, Yayinbda ya rugumoni da hannu guda yana dan shafa min kai a hankali kamar wata karamar baby, Mama zan turo ta zuwa jibi ma basai andauki lokaci ba, Albarka naji tana sa mashi yana cewa Ameen Mama nagode kwarai, Da haka tana sababi ya kashe wayan tare da sauke ajiyan zuciya mai karfin sauti, Abinda ya fado min arai shine zancen Mama lokacin da muka tafi da Anty Amarya sallamar su, Inda take ce min babu abinda da yawa mutanen gidan mu yanzu suke son ji da gani kamar ace, Aure na da yaya Abubakar ya samu matsala, nadawo gida na zauna batare da auren shi ba akaina, Cikin wani irin murya Mamana Saratu da takawo nan tadan sasauta muryan ta tana cewa yar Baba don Allah ki daure kiba marada kunya ga wanan al,amari, Don kinfi kowa sanin irin halin rayuwan da muke ciki agidan nan, Don gaba daya sun dauki tsanar duniya sun sa muna mu da ku, Kaina na tura a kirjin yayana tare da dora hannuwana abayan shi nai mai round dasu, Kara sauke ajiyan zuciya yayi tare da matse ni gam ajikin shi kamar wani na son kwace a jikin nashi, Meenatu ya furta acikin wani irin yana yi mai nuna kasala gamutum, Yace nasan cewa kinji abinda mama take fadi a wayan nan A hankali nadaga mashi kaina dake saman kirjin shi tare da dago kyawawan sexy eyes dina muka hada ido dashi, Murmushi mai kwantar da hankalin mutum na sake mai,, Don in samu damar shigar da kaina agare shi har ya manta da zancen Mama ladi, Don bawai ba a yanzu shirye nake da in rike mijina kamar yadda kowace mace mai sanin ilimin rike,miji ke kokarin yi, A daidai saitin kunne na yakara rada min Meenat duk ritse duk fitinar mama ban son ki barni, please, Nasan cewa idan fitinar mama ya ishi, Baba Samaila zai iya yunkurin raba wanan auren da malam ya daura, Kai na girgiza mai a hankali nace Baba bazaiyi hakaba don da zaiyi da bai bari ankawo ni gare ka ba, Murmushi naji yayi sanan yace Baba samaila babanane bazai so abinda zai tabani ba nasani Meenat, Yaya kada ka manta cewa nima fa Mama mamatace, Duk abinda kaji Mama tana fadi a kaina anmata wani abinda ba daidai bane, Saboda amatsayinta na mahaifiyar ka malam bai nemi shawan hada aurena da kai ba Bayan yasan cewa ba kaka guda muke da kai ba a,gurin uba, kamar yadda mutanen gidan mu ke fadi, Shiiii naji yace alamar inyi shiru da wanan zancen da nake kokarin fadi, Cikin rausaya kai na dago ina dan kokarin wasa da igiyar bathrobe din dake jikin shi, Nace yaya ai wan shine kawai kiyayyan mu da mutanen gidan mu, A take naga jikin shi ya hau,rawa yana tsumi, yace wanan ba hujja bane bai kamata su dauki wanan akidar har yazama masu abin dogaro akai, Ni gaba daya kowa na gidan mu guda na dauke shi, agareni, Nasha fadawa mama tun ina karami irin yadda take gwada wa Baba Samaila da ta daina don ba kyau, Gudun kar diyan shi su taso har ku gane hakan gashi ko ashe har kun gane ko may ke nan, Nace yaya ai koda muka san hakan bai yi tasiri akan mu ba don mu duk kowa nagidan mu guda muka dauke shi, Maganan ta shige shi sosai yace naji dadin jin,haka agare ku, Jikin shi ya kara manna ni, a take ya shiga sarafani irin yadda yake so, Lokaci mai,tsawo muka dauka ahakan ni da shi cikin wani irin ya,nayi da ba zance ga kamar shi ba, gare ku,, A hankali yake mai da numfashi guda guda sama gado, yana kwance rairai fuskan shi na kallon saman rufin dakin, Sunana ya kara kira akaro na biyu shigowa na dakin nashi, yace, Meenatu Uncle din ki ya kirani dazun da rana yana sheda min cewa kun koma school a wanan satin, da zamu shiga, insha Allah, Kara gyara murya naji yayi tankar maganan da zai fada ya makale mashi, Don haka acikin sati maizuwa,zan sallamay ki ki koma sokoto, Amma dai gaskiya ban so ance kin yi tafi a yanzu ba,, Saboda nasan cewa kafin ki dawo nan abubuwa zasu iya faruwa,masu muhinmanci, Sai dai babu yadda zanyi don karatun ki nada amfani agare mu gaba daya nan gaba, Wani irin dadi naji jin azuciya ta, cewa zan koma sokoto cikin yan uwa na, Za huta da zaman kadaicin da nake fama dashi nan inda ba abokan magana, Sai dai ina son injadda maki cewa ki kula da kanki, Don ni mutum ne mai kishin iyali na sosai, Kada ki ga kamar cewa bazan, san wani irin rayuwa kike ciki a can din ba, Duk da nasan cewa baki da wani halin assaha a tare da ke,, Shiru naji yayi nima dai shirun nayi ina sauraren shi, Meena kin san cewa ina son ki ba sai na tsaya fada maki da baki ba kamar karamin yaro, Burina bai wuce in nuna maki hankan ba da kuma iyayyen mu, Don haka kizama mai rikon amana ki kula da rayuwan ki acan, Sabosa hakkina yana akan ki, a koda yaushe, inda zaki fita inason sani daga nan, Don bazan so ace kin zama akuyar sake ba, a garin mutane, Sanan duk lokacin da na dana bukaci, zuwan ki nan zaki zo ne, A hankali na ji bakina nace mashi insha Allahu yaya zan ki,yayye, Murmushin nuna alamar jin,dadi ga zance na naji ya yi ,,, Ya jawo ni zuwa jikin shi yana cewa, sai ki fara shiri zuwa gobe, Don zuwa alhamis idan ran mu ya kai, zan sallamay ki, Don haka sai ki fara shiyaryawa yacigaba da sunsunan wuyana zuwa girji na, Sosai naji ya matse ni a jikin shi yana mai rada mun wasu zantuka, a kunne na, ****** ********** ****** A washegatin da yaya ya umurceni da in fara shirin tafiya na fara yi, Ranan ya kasance safiyan Monday ce, don haka akwai fita aiki a ranan ga yaya,na, Don haka da safe kafin nabar part din shi ya ke ce min Zanbaki kudi Meena kiyi duk wani shirin da ya kamata kafin ki wuce,, Kudi masu yawa yaya Abubakar ya bani sai da nai mamakin haka sosai, Yana daukan wani takardan shi dake saman table yace, Wanda na baki last Friday, nasan cewa dashi kikayi amfani gurin taron su Baba da su kazo, Cikin yar murya siririya nace baduka nai masu amfani dashi ba, Na aikawa Babana da sauran kudin ne yayi lalura dashi, Daidai lokacin da yake dagowa yakecewa nasani ai, Mamakin abinda ya ce na yi sai cewa yayi batare da ya kallo gurin da nake, zaune ba, Baba Samaila ya bugo min waya jiya da dare ya ke sheda min cewa kin aiko mai da kudin dana baku ke da Sadiya,, Nace mai ba komai ni agareni dama nakune na,baku, na amfanin ku, Kunyane ya kamani don ban tsanmanin cewa Babana zai min haka ba, Bakin gado ya koma ya zauna yake cewa kin san shi Baba Samaila rayuwan shi daban ne, Jeki yi aikin ki kada ki makara don rana ya soma yi, Godiya nai mashi tare da fatan alheri ga rayuwan shi, Murmushin jin dadi kawai yai min yana cewa haba ai ba komai bane wanan, Na juya don in tafi har, na fara tafiya sai na tsaya ina cewa Yaya don Allah inason inwa wanan makwabciyar tamu magana don ta rakani gurin gyaran jiki, Daku yin tsaraba wasu anty Amarya da yaran su,a kasuwa, Ok yace a yayin da yafara bude takardan hannun shi yana cewa Amma ba,a motar haya zaku tafi ba ko ? Kafin ince wani Abu yace ki dauki ga ke din mota can ku tafi da ita, Wanan yaton dake shigowa ya kai ku, Nagode yaya na kara furtawa a cikin ladabi Ina fita , da ga dakin yabi baya na yana kallo na cikin, tausayawa da jin wani iri azuciyar shi, ****** ********* ****** Wani Sallon ne na gyaran jiki da kai muka tafi ni da Fattu da dan ta nagoye, Matar mai gyara tana min gyara tana ta yabon irin kyau, halittan gashina da jikina, Nan taje tambayana cewa ni yar ina ce acikin arewa,? Nace mata ni yar Kebbi ce amma a gwandu nake , Tace kai zanso inga mutanen wanan yanki na ku na gwandu, Nai murmushi nace mata mu Fulani ne na asali bawai haye ba don samun irin mu sai a jahar mu ta Kebbi, Don mazan mu da matan mu duk kyawawane ga addini da tarbiya, akan addinin mu, Dariya su kayi min da cewa kai amma dai kin iya zuzuta garin ku ?, Nai mata yar murmushi mai kawatarwa nace, gaskiya nake fada maki anty, Don mu din na daban ne a, ko ina,,,,, Dariya sosai sukai min don jin dadin hiran mu, dasu, Har kafa,na sai da aka wanke min duk wani staining, dake a jikina na koma ina jin,kaina wata irin kamar bani ba ce,,,,, ZEEE MAKAWA YELWA,, [8/2, 22:09] Anty Lantana: 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 4⃣2⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA ALLAH-AL-LATEEF,,,,, Assalamu Alaikun yan uwa musulmai, muji tsoron Allah ga al,amuran mu, Mu daina yi wa Allah Ubangiji Izgili ga rayuwa kusani cewa, Rahaman Annabin Rahama, Annabi Mohammed S,A,W itace muke samu a gurin Allah Ubangiji Subbahanahu,ta,ala, Amma wai har shine mutum a zamanin nan zai san cewa ya aikata zunubi maigirma irin zunubin da, har wasu zamani saboda irin shi a juya wanan kasan tare da al,umman lokacin, Yau sai gashi saboda samun guri har muna fitowa a fili mu ikirarin yin sa, Wa,iyazubillah kuma a cijin diyan musulmai hausawa, Ya Allah ka yafe muna kurakuran mu kasa mu mu,fi karfi zukatan mu Ya Allah ka shiryar da duk kan Al,umman musulmi, Ya Allah ka kare mu daga rudin shedan Ya Allah kasa mugama da duniyar nan lafiya, 👏👏👏👏👏👏👏👏 Sayayya sosai nayi wa su, Anty Amarya da yaran ta harda ma Mummy da yaran ta, Uncle dina tare da yaya Abubakar na sayo masu unders irin na maza masu kyau, Tsab na shirya tare da hada kayan dakina wanda nasan cewa zasu yi min amfani gaba, I zuwa yan,zu komai na hada don tafiya da safe kawai,, Abinda nasan cewa idan na barshi a gidan yaya zai lalace na kwashe nakai wasu Fattu da Maman, Bi,u, Sai murna su keyi da sa min albarka da fatan samun cigaba da nasara arayuwa, A yadda na ke gani, kamar babu zancen yafiya na acikin wanan satin, Allah, Allah naje yi kada yaya Abubakar ya ce min an fasa tafiya don, Naga cewa bai kaunar zancen tafiyan nawa sam, Sai zuwa dare na ya shigo dakin nawa ko ina yabi dakin da kallon mamaki irin yadda na parking din komai, Murmushi naji yayi duk da fuskan shi yana a daure babu fara,a acikin ta, Na kalle shi a cikin natsuwa ina mashi sannu da zuwa, a cikin murya mai sanyi, ba tare da ya ansa min ba, Idanuwar shi ya zuba min zuwa wani lokaci sai yadan nisa, Gefen gado na ya samu yadan zauna, tare da sauke ajiyar zuciya, Meenatu naso ace na kaiki har Sokoto da kaina, sai dai gaskiya hakan bazai samu ba, A hankali na dago kaina nadan kalli inda yake zaune cikin dan dafe kai da hannun shi, Alamar ya na tare da gajiya a jikin shi, Murmushi mai kama da yake na dan sake mai, ina cewa ai ba komai yaya, Amma driver tare da malam Mudi zasu da matar shi zasu kaiki goben, insha Allah, Ina fatan idan kin je zaki bawa Uncle da Anty Amarya hakkuri rashin zuwa na, Kamar yadda nakara fada maki yau ma zan kara sheda maki, Ki kula min da kan ki kirike amana na dake kan ki,,,, A hankali na furta insha Allah, Daga karshe yaya yace nai maki yan sayayya don kije dasu gidan uncle, saidai, basu da wani yawa sosai, Har an riga ansa a motar da zaku tafi dashi gobe, Godiya na kara yi mai tare da fatan alheri, kudi ya kara cirowa daga cikin aljihun shi ya turo min a gabana yana, ce min kirike don yin amfanin ki, Da sauri na kalle shi ina cewa yaya da akwai kudi fa a hannu na har yanzu, Kai yagyada yanacewa nasa, ai amma kuma kin san yanzu ba da bane ko? Do ajwai bambanci garayun ki nada dana yanzu, So ki aje agurin ki don tare lalura ba sai uncle yayi maki ba, Ya mike tsaye yana cewa idan kinje ina gaida uncle da matar shi, Murya nane kawai zai isar da sakon da zuciya na ke ciki a lokacin, Don wani iri naji saboda rabuwan da zamuyi da yayana bayan dan sabon da mu kayi na dan lokaci,, Yana fita bayan tafiyan shi na adana kudin da ya bani, don tafiya, na, Mikewa nayi zuwa sashen Anty Sadiya don in sheda mata cewa zan koma, gobe,,, Na samay ta a zaune tana gyaran yatsun kafan ta a dakin ta, Sallamana da ta ji ya sata dago kai fuska a daure, ba fara,a ko ka dan,, Wani irin kallon kurulla naga tana min badon komai ba sai irin yadda gyaran jikin da nayi ya maidani, a lokaci guda,,, Gaishe ta nayi a daure ta amsa min a cikin da matse fuska, kadan, Anty nazo in sheda maki cewa, gobe zan koma insha Allah, Dan sasauta fuskan ta tayi tana cewa, gobe goben nan, za,a tafi, ? Sai da na,dan yi kamar zan wuce saina ce anty don Allah ki yafe, min, Acikin muryan nan nata maikama da agajiye take tace min, Allah ya yafe muna baki daya na ansa da Ameen nabar dakin, Bina tayi da kallon mamaki yadda cikin da lokaci taga na wani canza mata , Take wani irin kishi ya turnuke mata zuciya don sam bata san har yaushe na zama haka ba,, ****** ********* ****** Sanmako mu kayi kamar yadda yaya Abubakar ya umurce ni da yi, Motar hilux, ce ni da Maman Hanifa zaune abaya, Maigidan ta malam mudi wanda a yanzu yake na hannun daman yaya Abubakar, zaune tare da driver a gaban motar Driver wani yare ne don inaganin baya jin hausa sai turancin yan Lagos su,keyi da malam Mudi, Yadda yaya ya basu Umurni a ranan zasu dawo Abuja, kada su kwana wai su kai muna dawainiya, Tafiya ya fara ni sa inda kewar mijina da kuma kaunar shi ya fara min yawo azuciya, Sai yanzu nasan cewa mun dan shaku da yayana Abubakar, a dan zaman da mukayi, Yanzu na gane cewa kada ka fadi halin mutum muddin baka zauna dashi ba, Ada kallon mugu wanda baya da lokacin kowa, na ke,wa yaya Abubakar, Amma dan zaman da na,yi dashi yasa na,gane cewa Rashin sani ki shi waye yasa na ke mai itin wanan fassaran, da nai mai,,, Abinda ya zo min a zuciya shi ne yadda mutane ke ganin cewa bazan taba samun guri a cikin zuciyad yaya Abubakar ba, Ni kai,na nai tunane irin yadda zan zauna dashi a matsayin mijina, Mutum gogage abin shawa da kyau gani ace wai nice matar shi, Wanan irin tunanen ne nai tayi lokacin da malam yace wai ya daura min aure da yaya Abubakar,, Mama Ladi ce tafado min a rai har nakai ga lumshe idona, a hankali, Don ban san yaya zasu kwashe da dan nata ba zuwa yanzu, Haka nai ta tunane barkatai a hanya tare da dan lumshe ido na Acikin ikon Allah mun iso garin sokoto, da wuri sakamakon gudun da driver yai ta shararawa,da mu,,, Da kwatance nai ta ma su nuni da hanyar uguwar mu har zuwa gidan Uncle dina, Taka injin din motan da karfi driver yayi alaman cewa mun iso, Da guda yaran gidan Uncle su ka fito azaton su ko, Baban su ne, Gaba daya suka sa ihu da Eh Anty Meenat, Anty Meena, Abinda ya jawo hankalin iyayyen su daga cikin gida ke nan,, Da sauri Anty Amarya tafito hanyar shigowa cikin gidan , Inda mu kayi karo da ita rugumay juna mu kayi da yar ihun mu,, Sai kuma ta sakeni tana min wani irin kallon mamaki, Kunyane ya kamani nadan noke kaina acikin hannaye na, Muryan Maman Hanifa, ce ke gaida Anty daga bayan mu , Sai kuma hankalin mu ya koma gare ta cikin mamaki Anty Amarya ke kallon maman Hanifa, don bata san ta ba, Nan nai mata bayanin ko wace ita yayin da muke shiga gida, Kayana aka dinga jidowa ana shiga dasu sashen Anty Amarya, Sosai annuna minnkauna agidan uncle don ranan har da mummy cikin zuwa taro na sashen Anty na,, Abinci aka zuba wa su malam Mudi, da driver da ya kawo mu Ita kuma Maman Hanifa a tare aka zubo muna mukaci, A falon anty ta kira ni nan naga irin kayan da yaya ya jib go muna, Buhun shimkafane da jarkan manja da mangyada su taliya, da indomie, da su sweet, da sauran tarkace, Su malam mudi ba suyi wani dadewa ba suka kama hanya don gudun kada dare yai masu a hanya,, Abinda na bashi da kyat ya karba amna na nuna mashi banji dadin rashin ansan abin ba dole suka karba shi da driver, Maman Hanifa, Ita ma na bata nata rabon, da,kuma wasu kayan jikina kala biyu, tana ta zabga godiya, ****** ********* ****** Tunda ya dawo sai yake ganin gidan tankar ba kowa acikin shi, Yadda na tafi nabar shi da safe , shima yafita zuwa office haka yadawo ya samay shi, Yadan dade tsaye a tsakar falo yana kallon kofan shiga daki na, Kamar ya nufi can sai kuma ya juya zuwa, hawa saman part din shi, Har ya gama abinda yakeyi ya fito, ba motsin Sadiya, a falon, Alama ya nunamai cewa bazata girka masu komai ba ke nan yau, A fusace ya nufi dakin ta tana tsaye tana kokarin gyara gadon ta da,ya cikwikkuykuye, Bata iya ce masa sanun da zuwa, ba sa kawai tana kokarin ci gaba da abinda takeyi, Haushine ya kama yaya Abubakar mace kamar tunkiya, Bata san yakamata ba da bai kamata ba, Gefen mirror ta inda yadan saba tsayawa idan zai mata magana don ya jingina jikin shi,, Sadiya tadago ido ta kalleshi don jin yadda ya ambaci sunan ta, Ita azaton ta ya zo ne neman wani abu agurin ta don yaga yau ita kadai ce a gida, Tambayan da yai matane yasa ta saurin dago kai ta dan dube shi, Sadiya may kike nufi da rashin dafa muna abinci, da baki da niyan yi, Abinci zan dafa kuma kace bai yi kyau ba,? Idan nace bai yi kyau ba basai ki gyara ba ki koya ko zaki yi mai kyau, Gaskiya kada kace zaka kawo min wanan tun wuri bazan iya ba ni, Aiko dole ki iya don ba mai zama yana dafawa ki na ci,, Bari kiji in har kin samu Meenatu yarinya ce ko kuma tana yi maki a matsayin ta na yar uwar mu,, Wace zata zo gidan nan yanzu nasan ba zata daukan maki wanan akidar ba, Idan kace kar ta bani ko, Da mamaki ya kalle ta yace wai ko Sadiya kina da hankali kuwa ? Ki tashi ki fita ki girka muna abinda zamuci na dare, Kuma barin fada maki daga yau, bazan kara sayo maki take away ba agidan nan, Sai dai mu zauna ahaka idan ba za ki yi ba, Gani fuskan shi ba wasa yasa ta biyo bayan shi, don zuwa ta dafa masu abincin, Idomie ne ta dafa masu sai dai yayi yaji da yawa don bazai ciyu, bà sam, Dole drinks ya dan kara korawa sama ya samu guri ya kwanta, Zuciyar shi cunkushe da bakin ciki, don ya rasa may ke mashi dadi a ran shi, Shawara yake tayi akan yadda zai bullo ma wanan al,amarin na Sadiya,,, Ace, mace kamar Sadiya bata,san yadda zata tafiyar da gidan ta ba,, Amma wai har yarinya kamar Meenatu tasan yadda zata tafiyar da rayuwan shi acikin jin dadi batare da wani matsuwa ba, Dasafe ma ruwan tea kawai da burodi ta tanadar mashi, Irin abincin da nake muna na karyaw ne ya fado mashi arai,, Gefen da take zaune tana faman loda bread a cikin ya ya kalla yana cewa Harara yafara sakr mata sannan yace wai ke, Ko Irish din baki yiya soyaba ke nan Sadiya sadiya kiwa kan ki fada fa,, Wani jutar da kai tayi gefe guda kamar wace akai wa wani zance na daban, Tsaki ya ja tare da mikewa tsaye idon shi duk sun kada,, yana cewa kada kiga kamar kin min ne, Ya ce sam kan ki kiyiwa, do ke, ce zaki sha wuya nan gaba,, Daga haka yasa kai yabar gidan zuwa office abinshi,,,, ****** ********* ****** Falon yai shiru duk da yake dai sanyi safiyane, Uncle dina ne azaune, Tare da matan shi dukka kan su biyu, kayan da nazo da su ne zube a gefe gudan falon, Uncle ya kara min sannu da zuwa yaku ma tambayen ni akan kayan da nazo da su, Kamar yadda yaya Abubakar yai min baya haka na fadawa uncle dina, Shiru yayi zuwa wani dan lokaci, can yace cikin wata murya mai sanyi, Gaskiya banji dadin abinda Abubakar yai min ba, Ada dakike gidana shike bani abinda zan ciyar da ke ne ? Anty Amarya ce ta tare zancen da ce, Haba dai dear ba haka yake nufi ba , Idan har ka lura shi aganin shi ai yanzu yana da hakki akan Meenatu kuma nasan yana ganin hakan zai yi ya fitar da nauyin ta dake kan shi, Mummy ma tace nima dai abinda nagani ke nan ai, Uncle ya dan furza da iska may sanyi daga bakin shi yana cewa, Yanzu abinda za,a wanan shinkafa duk biyu zan turawa mahaifan ki suyi amfani dashi, Mai kuma sai ku diba ku bada saura akai masu Saratu, Zanyi magana Uncle yace min yadda ya ce haka za, ayi, da kayan dole na kyake ina kallo aka hada komai ya fita dasu zuwa tasha don ya turawa iyayye na, Sauran tsaraban da na sayo masu, naraba nabawa kowa nashi Atake gida ya rude da murna don kowa nasayo mai tsaraba mai muhinmanci, Sai da mukaxkoma daki ne nakara fitar wa da anty amarya da yaranta wasu tsaraban da na sayo masu na daban, Tsaye Anty Amarya take amma sai ta janyo, dan stol din mirror dakin ta zauna, Tana yi min wani irin duba nason jin bayani daga baki na, Kunya ne ya kamani amma sai na daure nake fada mata irin alherin da yaya Abubakar yai min a lokacin zamana dashi, Allah mungode ma Anty Amarya tace tare da daga hannun ta sama ta shafa a jikin ta, Meenatu takira suna na a hankali , Nasan cewa abu mai muhinmanci zata fada don haka na ansa mata da murya kasa,kasa, Tace da farko na tsorata ainun da auren ki da mutumin nan, Ga irin yadda nai ta jin labarin shi da kuma uwar shi, Gama kuma da nagan shi a fili sai na kara tsunkewa da al,amarin sa,, Amma kin ga abin Allah sai gashi duk zaton mu ba haka bane ashe, Don haka yanzu abinda nake so dake ahine ki kara zage damtse gurin dankr mijin ki, Yadda ba wata macen da zata iya shige maki gaba da komai, Kin san dai yadda makiya sukayi wa auren ku yawa, don haka kara daurewa zakiyi kibawa marada kunya, Na amsa da cewa insha Allah Anty, zan yi duk yadda kika ce din Nan muka dan dauka n zama Abuja tare da yadda na hadu da Fattu da Uwar mijin ta, Sai Monday na fara fita school sai da ban manta da maganan da yaya Abubakar yai min ba, Akan in kula da rayuwata, bakomai yake nufi da hakan sai in tsare mutuncin kai na, Wanda dama ni Allah ya rufa min asiri ban da wanan irin rayuwan, Don ni ko kawa ban yarda da yi ba,a makaranta, Abinda yakai ni shine nasa wa gabana don haka yanzu ma ba wasa don wani katon hijab baki na zumbuda ajikina wanda ya rufe min ko ina nawa, Sakon Uncle dina ya samu isa gurin iyayyena wanda mutane na ta mamaki daga ina wanan kayan ya fito haka ? Sai gulma akeyi ako, wani sashe, na gidan mu inda abin yadan yi sauki dan gidan Baba Shaibu da yaraka yayana Ibrahim gurin dauko kayan a tashar mota, Shike fada masu cewa,daga gurin Kanin Mama Saratu sakon ya fito, Hakan yasa zancen yadan lafa, Bayan dawowan Baba na gida yasau sakon kayan da Uncle ya turo mai dasu, Kwana biyar biyar,aka debawa ko wani sashe tare da zuba masu manjan a wani kwano, Sai shigowa sukeyi zuwa godiya mazan su da matan su, Wasu kuma na cewa, ta inda ake zaton abin ya fito sai gashi bai fito ta gurin ba,,, Zaune matan gidan suke suna zancen abin duniyar dake gudana musanman a gidan su, Matar Baba Shaibu ce ta fara cewa, ita waccan may, bakin cikin, Ta,na nan dan tana can na wa duniya, yayafin arzikin shi, Sai matan Baba musa take cewa ai, ko bakin cikin ta ita zaici don dai a yadda malam ke fadi, Yanzu wani irin daula ne na arziki ya taso mashi amma nan gashi tare tako ina kada wani yaje ya lakato, Matar Baba Hamza tace, aiko zata sha mamaki nan gaba don muddin yarinyar nan ta kara nan gaba bazata iya tare ta,ba, Ai dai gamu gani inda rayuwar mu zamu sha kallo a gidan nan, Baki gani yadda Saratu ta canza cikin kwanakin nan sai wani sheki takeyi kamar mai sabon ciki, Wace tafara maganar tace, to ita kan ta mama Ladin, ai a wahalce take,, Ace wai danka nada hali irin na mama ladi amma daki ko gurin zama babu ballr shimfidar kwarai, To wai ku kuna mamakine baku gani gidan ga kowace mace dan uwan ta na zuwa amma ban da dangin mama ladi, Duk tabi ta kakabe su, ba mai zuwa gurin ta saboda mugun hali, Yanzu ai Hajja ce dangin nata inji matar Baba musa, Dagin sheri ba tunda mugun abin su iri guda,ne ai shiyasa nasu yazo daya,, ****** ********** ****** A kwance yake saman gadon dakin shi sanyi AC kawai ke tashi a dakin, sai faman juyi ya keyi Daga inda yake kwance ne yake kallon yadda dakin ya hargitse babu gyara, tun bayan tafiyan Meenatu wace ke gyara mashi, a kullun take da girki Gyara kwanci ya kara yi rigingine sanyin na ratsa mai jikin shi, Kewar matarshi ne kawai ke damun shi don sai yanzu ne ya san cewa sun shaku da yariyan fiye da tsan manin shi, Gyara kwanciyar shi yayi don cigaba da tunanen shi, Idon shi ya lumshe saboda tuna abubuwa da dama akan ta, Tarbiya, tsabta, girki, iya soyayya cikin dabara, take tafiyar da komai, Wayan shi dake gefen shi, ya lalabo, tare da neman laban wayan ta, Kira yake wayar kamar zata katse, sai yaji na dauka acikin siririyar muryan nan tawa, Wani irin sanyi yaya Abubakar yaji ya ratsa zuciyar shi saboda jin murya na da yayi kawai, Jin muryan kawai ya jefa shi ackin wani irin nishadi a lokaci guda, A hankali nace ina wuni yaya ? Lumshe idon shi yayi çikin wani irin ya na yin jin dadi, Ya gajiyan aiki yaya? Da kyat ya iya tataro natsuwar shi guri guda ya amsa min da cewa, Tau da sauki dai, Acikin damuwa nace da sauri lafiya kuwa yaya,? Sai da yadan nisa yace ina fa lafiya Kaunar yaya kin wuce kin bar yaya acikin tunane da kewar ki, Kunya maganar tashi taba har nadan sake murmushin jindadi ta yadda zai iya jina a inda yake, Hakan yasa yaya Abubakar lumshe idon shi a hankali saboda wani irin abu dake fisgan shi , ZEEE MAKAWA YELWA [8/4, 21:37] Anty Lantana: 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 4⃣3⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA ALLAH- AL- KHABEER Jiki da jini yau Allah da ikon shi an wayi gari Mama Ladi ba lafiya, Tun safe Mama Ladi ta kasa koda fitowa kofan dakin ta, Ganin irin yadda jikin ya matsa mata Mama, Sa,a wace Mama ladi ke ji tankar ta shaketa kowa ya huta,, Itace taji shiru Mama Ladi bata leko ba kuma bata motsin ta ba a sashen ta, Don haka ta daure ta zagayo zuwa sashen mama Ladi din, Kwance ta samay ta acikin wani irin yanayi mai ban tausayi, Ta,yi amai duk jikin ta ya baci ko ina da aman, ga wari dakin kamar may, Da sauri ta karasa gurin Mama Lafin wace ke kwance cikin mawuyacin hali, Ganin dai abin bana wasa bane yasa ta komawa da sauri zuwa kiran maigidan su wanda ke waje gurin mahaifin shi suna karatu, Dan aike na fada mashi bai bata lokaci ba ya garzayo zuwa ciin gida, Da shi da Mama Sa,a ne suka gyara,mata jikin ta suka canza mata sutura, Da sauri Mama Sa,adatu ta, tada yaro yaje gidaje da yaran ta su ke aure ya fada masu halin da mahaifiyar su ke ciki yau, Ba bata lokaci sai gasu gabadayan su suncika gida, Hankalin kowa a tashe yake ganin irin yadda jikin ya matsawa, Mama Ladi, Samira ce ta dauki waya ta bugawa yayan su Abubakar , Nan ta ke sheda mashi irin halin da mahaifiyar su ke ciki tun safe, Waya yakira abokin shi Aliyu dake cikin Birnin Kebbi da yazo ta kai ta asibiti, Gado aka bawa Mama Ladi don ciwon yai mata tsanani, sosai, Mama Saratu itace ta farko aika masu da abinci asibitin,, Inda sauran mutanen gidan ba wanda ya kai mata komai, don sunce ko ciwo su keyi sai Mama ta ga dama take zuwa gaida kai, balle ma idan yaron kane baida lafiya,, Wanan dalilin suka rike yau su ma suka ce sai sun rama, Babana Samaila shine yazo da motar shi yace duk wace zata gaida ita tazo ta shiga su tafi, Wanan daman yasa matan gidan namu zuwa shiga mota don suje suyo gulma, A kai akai yaya Abubakar ke bugo waya ranan don jin ya karfin jikin mahaifiyar nasu, Andai tabbatar mai da cewa i yanzu ta dan samu sauki sai dai tana jin jikin har yanzu, Wanan zancen ne yasa yaya Abubakar, shiryawa zuwa kebbi dan ganin halin da mahaifiyar shi take aciki,bai tsaya wani shiri, washe gari ya kama hanya, Saboda yazo ya ganewa idon shi halin da mama take aciki idan ya kama a tafi da ita, Abuja ne gurin su sai ya wuce da ita,,, ****** ********* ****** Fitowa na daga lectures ke nan gurin da, nake yawan zama kusa da school mosque, na zauna ina jiran lokacin sallah azahar, yayi, Wayana dake acikin jakata ke ringing alamar kira ya shigo min, Ganin mai kiran nawa cikin wanan lokacin ne ya bani mamaki, Nomban yaya Abubakar ne kiran yai matukar ba ni mamaki sosai don baya kirana da rana sau dadare lokacin da yasan cewa ina free, Bayan na dauka mun gaisa yake sheda min cewa yana hanya ya kusa shigowa sokoto, zai tafi Birnin kebbi, A hankali na ke tambayan shi ko lafiya zai yi tafiya haka, shine ya ke tambayana acikin mamaki banda labarin mama tana asibiti kwana biyu kenan, Cikin wani irin murya nake cewa subbahanallahi, Banda labari gaskiya, ban san da zancen ciwon mama ba haka, gaskiya A take na nu damuwa da kullawa na ta hanya ce O ni Allah mama may yasamay ta haka, ? Allah ka dube mu da idon rahaman ka ya Allah, Sosai yaji dadin jin yadda na nuna concern di na akan mahaifiyar shi , Batare da na nuna bata kauna in nuna jin dadina akan ciwon ta ba Muryan yaya Abubakar ne naji yana cewa ban san ko kina free ba don ina son in tsaya indauke ki don mu je tare Ina school ne yaya amma zan kira Anty Amarya ta fadawa uncle dina, Ok zaki samu zuwa ko in wuce kawai ya fada cikin nuna dan bacin rai, Amsa na bashi da cewa zan tafi, Sai naji yai wani yar sanyayar ajiyan zuciya lokaci guda tare da cewa sai na shigo zan kira ki, Bayan kashe wayan ne nai shiru sai kuma naga banda enough time na tunane don haka na kira Anty Amarya na shedawa yadda mukayi da yayana, Murmushi naji tayi tare da cewa Meenatu akwai ki da shirmay, Uncle din ki yanzu yana da iko a kanki ne dazai ce bazaki bi mijin ki ba Balle gida zaku gurin mahaifiyar shi wace ke fama da jiki, Ki yi sauri duk inda kike ki dawo gida, ki shirya kanfi ya iso, Sosai Anty Amarya ta min shirin gagawa na ban mamaki, Don ina kallon yadda tai ta min jike jike da kuma yan sauran dabarun mata,, Sai bayan biyar ya shigo garin sokoto inda nai mashi kwatancen gidan uncle din mu, suka karaso, Driver ne ke jan motar shi kadai zaune, a bayan motar, Masha Allah, kalman da su Mummy suka furta ke nan Yayin da yaya Abubakar yasamay su waje tayowa yan uwan ta rakiya, Nan take sheda masu cewa ai, tana ganin shine Mijin meenatu, A lokacin anty Amarya tafito, daga cikin gida don tai min rakiya, Kafan shi wanda yasa wasu bakaken takalma sai wani irin walkiya yakeyi, Yafar fitarwa, daga cikin motan a hankali, sanan ya fito da gangan jikin shi wanda, ke saye cikin wsu yadin silky mai laushin da sulbi, Annurin shi duk ya cika gurin ga zatin shi mai daukan idon al,umma, Cikin wani irin tafiya na kasaita wanda bawai da gangan yakeyi ba halitta,ne hakana din, kawai, ya karaso gurin su mummy din, Ya gaisa da su Anty da mummy cikin mutunci da girmamawa, Muka kama hanya, zuwa gida garin mu Birnin Kebbi, Tun shigana motar inda yake zaune a baya cikin dan gyara zaman shi, Batare da ya kalli gurin da nake zaune ba naji hannu yaya daidai saitin kunkuruna, Ya kamoni zuwa jikin shi tare da sauke wani irin ajiyan zuciya, Ya kike yace yayin da yake kokarin sunsunar wuya da hancin shi, Ganin a kwai driver a gaban motan yasa ni dan kara kama jikina kadan daga abin da yaya ke min, Zance Anty Amarya ne ya fado min a raina cewan da tayi yau sai na daure, don zan ya bawa aya zaki, gurin yayana, A hankali nacewa yayan nawa ya hanya? Ya labarin jikin Mama kuma,? Hannu na ya damke a cikin nashi tare da dan matsewa a hankali, Sai ya dan ja ajiyar zuciya a fili yace Alhamdullahi cikin kada kai, Kafin muyi wani magana kuma wayan shi ce akakira, A yadda nake tsanmani daga gurin aikin sune wanan kiran saboda irin bayanan da naji yanayi da mai shi, Dankali da su tumatari din hanya danagani anasayar wa na saba dama idan zan tafi gida in tsaya insaiwa malam tsoho,,, Wanda shi a rayuwar shi baida abinda yafi mai cin dafafen dankalin hausa, da kulikuli dakakke, Ganin Dankalin fari fet saman hanya yasha wanki yayi wani irin kyau gasu manya manya, Ban san lokacin da na cewa yaya wanda ke waya har zuwa lokacin, Nace mashi cikin murya maikama da shagwaba, yaya don Allah, zan sayawa malam dankali please? Dakatar da wayan da ya keyi, a lokacin yayi cikin bada umurni yana cewa driver stop there please, Cikin wani irin jan burki driver ya taka burkin motan a gaban wani dan yakwamamay tsoho mai farin gemu, duk rigar shi ta mutu saboda tsufa, Yaran dan tsohon naganin mu suka taso suna cewa, Dankalin mu yana da zaki da gari ga gardin ci , na,nawa zakawo maku, Kokarin bude zip din jakata nakeyi, amma sai naji, Yaya Abubakar nacewa dan saurayin mai dankali kowa wancan kwanonin dukka gaba daya, Sai da ya shake bayan buth da dankalin manya,manya masu kyau sanan muka,wuce,, Mun shiga garin lokacin dare, ya soma don haka muka wuce direct asibitin Sir yahaya, inda mamatake kwance, cikin jin jiki, A mota muka dan tsaya yaya yakira abokin shi Aliyu, yana sheda mashi cewa mun shigo garin, Wani Ward mama take kwance, ne wai ? Females Ward take zakuga su Wadda ai a haraba asibitin idan zaku shiga, A,nan nake jin yaya na ba Aliyu umurnin ya kama mashi hotel mai kyau kafin ya karaso,, A cikin girmamawa naji Aliyu, na karbawa yaya Abubakar umurnin shi, Females Wards muka nufa, atafe muke tare da yaya Abubakar sai, Baba Wadda wanda ke gaba yana muna ja gora zuwa dakin,, Dakin su kadai ne aciki dakin kudi, aciki ba na taro bane, Duk ilahirin diyan Mama suna dakin a lokacin gaba dayan su, Tare da wasu sauran yan uwan mu yan mata da su ka zo gaida mama din a,lokacin, Jikin nata ba laifi don da dan dama amma akwance take rijib, Sallaman da yaya yai masu yasa gaba dayan su juyowa suna fuskantar kofan, dakin, A cikin mamaki su ke kallon mu suna muna sannu da zuwa,, Duk da dare ne amma gaba daya idon su na a kai na, Kowan su na kokarin ya ga yadda na koma, kamar yadda suka,ji labari Duk da a fuskan su akwai murnan ganin mu amma akwai kyashi ga zukatan wasun su,, Saboda irin kallon kurullah da suke min a lokacin, da na shigo, Ni dai ina bayan yaya Abubakar sim, sim dani kamar zan shige cikin sa, A bakin gadon da mama take a kwance muka, tsatsaya muna kallon yadda take barci numfashi sama sama take fitarwa, Ido na kafe mama da shi sai ruwan da ake kara mata wanda ke shiganta kamar digo, Jikina duk ya dauki rawa saboda tsoro da tausayin yadda mama ta koma acikin lokaci guda, Da baya baya na koma ta kofa, ina mai zubar da hawaye, hankali na a tashe,don bazan jure ganin wanan abin ba mama ce haka a,kwance kamar ba ita bace hakan duk ta ramay ta canza halitta, Daga gurin da yaya Abubakar yake tsaye idon shi kyar a kan mahaifiyar shi, Ganin ina kuka ya,dan sa shi, dago kai tare da juyawa yana kallon gurin da nake tsaye, Fuskan shi da gani babu dadi acikin ta ko kadan don shima hankalin shi a tashe yake, Irin halin da ya riski mahaifiayar shi a ciki, kwance, Anty Samira ce da dan karamin, cikin ta, da ya fara turo rigar ta, sai faman zubar da miyau,takeyi, Ita ce ta biyoni inda nake ta dan ja min hannu mu ka fito wajen dakin, tare da ita,, A hankali take ce min Meenatu ai kun samu Mama taji sauki, sosai inda ga kwana biyu da ya wuce ne ai baza ki iya ganin taba ashe, ? Subbahanallahi na furta a hankali ina mai yiwa Mama addu,an samun sauki , Sai kuma Anty Samira ta dan kara kallo na wanan karon fuskan ta da guntun murmushi makale, tace, Meenatu wai da ke da mijin naki may kuka ci ne haka wai? Kun wani sake kun canza a lokaci guda gaku kamar wasu larabawa, can, Sai lokacin na dan yi guntun murmushi na ce kai Anty Samira ho, May ko mu kaci idon ki dai ne ya nuna maki mun canza,kawai, Hararan, wasa ta jefo ni da shi, tana cewa tunda makauniya nake ba, koko in ce muke ba,, Meenatu kin yi wani irin girma ga haske, ga kuma waye,wa atare da ke duk a lokaci guda, Kai haba dai Anty Samira duk a lokaci guda haka gaba daya abinda kika lissafo min,, Baba Wadda ne ya leko daga kofan dakin yace in zo Mama ta farka daga barcin, Mum samu ita da yaya Abubakar suna magana haka na kutsa kai zuciya na tare da fargaba, zuwa har bakin gadon da take kwance, Mama sannu da jiki ya karfin jikin, ? Shiru Mama tayi tankar bata jini ba sai kuma dan annurin fuskan ta da ya gushe, a lokacin da ta ganni, Dakin yayi tsit ana sauraren mu gaba daya an sako muna ido a dakin, a ga yadda zamu yi, da ita, Yaya Abubakar ne yake cewa mama Meenatu na gaishe ki, Mama tai wani irin lumshe idon bakin ciki tace, lahiya, a takaice, Na ce Allah ya sauwaka ya bida lafiya daga haka na juya da zuman komawa gurin da nake tare da Antyna Samira,, Kujeran da Anty Mariya ta dauko mashi ya zauna ya nuna min yace zauna nan, Wani irin nauyi da kunya ne ya kamani don ganin yadda yayyene yan uwan haihuwan yaya su ka sako muna ido gaba dayan su dakin,, Kai na dago daniyar in,cewa wa yaya Abubakar ya bari in fita waje amma sai annurin shi da kwarjinin shi ya hanani iya bude bakina alokacin,, Still dai kujeran ya dan kara, matso min da ita gabana inda nake a tsaye gab da shi don in zauna da kyau, Ba mussu na zauna kamar yadda ya umurce ni da yi, Daidai zan zauna naji daga bayan mu daya daga cikin su Antyn nawa wata ta sauke wani irin ajiyan zuciya, Dakin gaba daya yai wani tsit a lokaci guda inda kowa mu yake kallo, Mamaki ne karara a tare da yan uwan mu wai yau ni Meenatu mutum kamar yaya Abubakar kebawa gurin zama, Hmmm,umm wani abu sai mace, kaina duk yai wani nauyi don nasan cewa akwai magana ke nan, agidan mu,, Shigowan Aminin yaya watau yaya Aliyu makwabcin mu ne shima, uguwar mu guda dashi Acikin shiyan Sarakuna tare sukayi tundaga primary har secondary da yaya Abubakar, Zuwa gaban secondary ne suka rabu, don shi yaya a lokacin gwaunatin jahar sokoto na lokacin ta dauki nauyin karatun yaya Abubakar din, Yasa hankalin kowa komawa gurin shi, don agaisa da shi, Sun gaisa da yaya ta hanya bawa juna hannu tare da tambayan gajiyan hanya, Sai lokacin yaya Aliyu yan da kula dani a zaune, cikin mamaki yace, A kace min tare kuke da Madam ashe,? Mama Ladi wace ke kwance tana bautan Allah ta ji wani irin haushi a ran ta hakama sauran yaran ta masu mara mata baya, haushin abinda yacd ya kama su, A cikin mutunci fuskana dauke da yar murmushi na gaida yaya Aliyu da cewa ina wuni yaya Aliyu, Ya ansa min cikin fara,a da jindadi ta hanyar cewa lafia kalau Meenatu,, Kun taho lafiya yaya hanya ya, karatu shin ko kina Abuja ,har yanzu ? Ban bashi ansaba sai murmushin dana dan yi kawai, Yaya Abubakar ne ke cewa yaya Aliyu da motan ka kazone, Ya amsa mai da cewa eh tana waje, yace ok bari Baba Wadda ya tafi da driver mu can gida, ya sauke ma Meenatu tsaraban ta, Ka kai mata sashen Baba Samaila, don kar ya lalace, Saboda na gaji baza mu iya shigowa gida yan,zuba dare yayi daga nan masauki zamu tafi, Yakara fuskan tar gurin da Baba Wadda yake yana cewa, idan an sauke kayan sai ka,kai driver inda Aliyu yai mashi masauki don ya huta, ko,,, A yake yan uwan mu dake a zaine sai suka fara kallon,kallo a tsakanin su don jin may yaya Abubakar yafadi a gaban su,, Ina zaune saman kujera idona kur akan Mama wace ke kwance shamay shamay saman gadon asibiti cikin ban tausayi, Sai dai har yanzu da alamar bata saduda ba ga al,amarin Ubangiji, don irin halin da alaman yanayin ta ya,nuna,,, Yaya Abubakar sun fita waje da yaya Aliyu, don haka ni da yan uwa na matane,a zaune dakin, Daga inda Anty Safiya take zaune tace min Meenatu mutanen Abuja dada kin tahiyar ki ke kyale kowa, ko? Murmushi nayi ina cewa Anty Safiya ba hakana bane,, Nomban wayar ki ta ban dashi ai da keji kira na,, Daga can bayan ta Anty Mariya tace a,a wallah ina taka kiran mutane ta samu maisunan malam ta kalalamay,shi Baki ga wadda shika rawan kafa akanta ba na? Daga baya kuma Anty hafsat tace to ko ke ce, aka rike ma kan maciji mika hanaki wasa da bindi nai,? Yanzu fa da kunnuwan ki kin kaji yace, tsaraba da yattaho da ita wai ta Meenatu ta, Lungun Baba Sama, za a aje mata suwa,, Samira ce tace kai jama,a asibitina fa muke ba gurin dadi rai ba,,, Shin mikkawo wagga magana wai,? Babane tare da Mama Sa,a su kazo akan babur din makwatan mu da ya aro, Cikin murna da jin dadin ganin mu gaba dayan su sai murmushi su keyi,, Amenatu ashe kuna hanya bamu da labari, na dan mike tsaye ina Kokarin ba Baba Buhari kujera, I zaman ki Aminatu ke ji, da kun ka kwaso gajiyan hanya, Na kai kujeran har gaban gadon da mama take dai inda Baba yake tsaye, Durkusawa, nayi har kasa na gaishe su shida matar shi na mike zan fita waje, Anty Safiyace ke tambayana ina zan tafi,? nace mata sallah zanyi don ba muyi sallah ba, daman,,,, Ita ce da kan ta ta taso tabani buta da sallaya sai kuma ta rakani tana nuna min inda zanyi tsarki, Gurin da na idar da Sallah muke zaune da Anty, Safiya da Samira, muna kara zance akan ciwon Mama, Samira ce ta kara jefo min tambaya cewa har yanzu ina Abuja ne ko na dawo sokoto, Nace mata ina Sokoto ai tun sati kusan uku, da suka shude, Sai naji ta nisa tana kallon yar uwar ta can dai tace, Gaskiya Anty Safiya idan har Meenatu bata Abuja za,a samu matsala sosai idan ance Mama zata can jinya,,, Anty Safita tana kallon yar uwar ta tace, matsalar may, Ai baza a samu matsalar komai ba kin manta cewa Sadiya diyar Mama ce, Ni Samira ta kalla amma sai nai kamar ban fahinci may take nufi ba don haka sai mukabar zancen kowa yai shiru a cikin mu, duk kan mu uku kowa da abinda yake kiyastawa a zuciyar shi, Daga inda muke zaune muka hango yaya Abubakar shi da Aliyu tare da wani doctor, sun nufi dakin da mama take kwance a ciki,, Ba,a dauki lokaci ba sauran yan uwan mu dake cikin dakin har mama Sa,a su ka fito waje daga dakin, Gurin da muke zaune, su ka dawo suna cewa likita zai duba Mama, ne, Nan kuma gurin aka sake hada wani sabon daban hira sai kace ba jinya a,kazoyi asibiti ba,,, Sun dauki lokaci adakin tare da likita ciki zuwa can likitan yafito yabar su yaya da Baba acikin dakin,, Sun dauki lokaci a ciki saiga su sun fito har Baba Buhari,, Gurin da muke a zaune,da yan uwa nan suka nufo mu gaba dayan su, Yan bayanai yaya ya kewa su Anty Mariya da cewa zasu bari zuwa gobe sugani idan mama ta dan kara samun sauki,sai su wuce Abuja da ita,, Ina daga can zaune tsakiyan anty,Safiya da Anty Samira, Yaya Abubakar ke cewa kizo muje ko zan samu indan huta, hakanan, Wani irin nauyi ne da kunya suka rufeni a lokacin don duk wanda ke gurin ya girmay ni don nice karaman su, Anty Safiya ce da Mama Sa,a suke cewa alokaci guda, Meenatu tashi kuje kinji yace duk ya gaji don Abuja ba kusa bane, A hankali na mike tsaye daga inda nike zaune saman sallaya, Barin raka matar yayana inji anty Safiya, anty Samira kuma cewa tayi barin bisu su sauke ni gida nikan ,, Bayan shigar mu motane, naga zamu tafi yqyq bai bar masu komai, ba, Daga can bayan motan nake cewa yaya ya kamata fa kabar masu dan wani abun kashewa, Bai yi musu ba ya ciro kudi daga aljihun shi yace wa Anty Safiya da batai nisa da motar mu ba tazo takarban masu, Anty Samira wace ke tare dani a bayan mota tace wa dan uwanta, Yaya shima Baba fa da mashin suka zo shi da mama Sa,a,,, O,o Allah na nace, daga gefen da nake zaune, nace Allah ya yaye muna wanan halin da muke ciki Anty Samirace takarba da fadin Ameen ke dai Meena, ZEEE MAKAWA YELWA,,, [8/4, 21:38] Anty Lantana: 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 4⃣4⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA ALLAH- AL-HALEEM,,,, Wanka na fito ina daure da tawul, fari na hotel din a jikina, Yaya Abubakar yana daga bakin gado zaune cikin wani dan wandon boxes na maza, Kokari nakeyi in daure kaina da ribon fin da na dauko daga cikin jakata, Muryan shi da abin da yake fadi yana kawowa daga gurin da nake a tsaye bakin mirror, Hakan ne yasani gane cewa da mace yake magana kuma ba Anty Sadiya bace, Saboda irin yadda naji yana bada amsa cikin shauki da so,, Wani irin abune naji yai min tsaye a zuciya ta,har naji kamar idona yana rufewa, Amma abinda yafado min arai shine zancen Anty, Amarya, alokacin da nai mata hira lokacin da Salawatu tazo gidan mu a Abuja, Anty Amarya tace min,Meenatu koda mata biyu yayan ki zai auro yanzu a lokaci guda babu ruwan ki don ba yadda zakiyi,, Don auren ki dashi aure ne na mutu ka raba ban ga dalilin da zai sa ki tayar da hankalinki ba,. Abu gudane yanzu agaban kishine kisan yadda zaki tafiyar da rayuwar ki dana Mijin ki ta yadda duk wace ma zai auro bazata iya dake ba sai dai ta barki, da shi,,, Ajiyan zuciya na sauke tare da dan kirkiro farin cikina a fili, Ban san zuwan yaya Abubakar kusa da ni ba sai dai jin hannun shi nayi a baya na, Daga haka muka dan yi tafiyan hazo a tare ba tare da na kara, tunazancen wata Salawatu can ba, ****** ********* ****** Karfe takwas na safe muna a haraban gidan mu kofan gidan malam tsoho dake uguwar shiyan Sarakuna cikin garin, Birnin Kebbi,, Idan na tsaya baiyyana irin farin cikin dake dauke a fuskan kakan mu malam tsoho da wasu daga cikin iyayyen mu dake gurin, Babu wanda yakai mahaifina farin cikin ganin mu a lokacin don dagani har yaya Abubakar ban san wanda yafi jin daddin gani ba a tsakanin mu, Nafito daga bayan mota tare da ni da yaya Abubakar cikin murna yau gani a gida, bayan dan dadewan da nayi batare da na shigo ba, Yaya Abubakar yana gaba ina biye dashi kamar yadda yake a gidan mu, Don kusan doka ne hakan don duk wani dan gidan idan har yai tafiya yadawo dole ne sai ya fara zuwa rufar malam tsoho ya kai gaisuwa da neman albarka, Sosai malam ya kasa boye irin farin cikin da yake ciki yau don ganin yadda TARKO shi yai kamu, Mun gaisa da shi cikin wasan jika da kaka inda yake cewa watau Abubakar wayau da kai min ke nan, ? Ka karbe min mata katafi da ita birni, kuka barni nan a cikin rumfa ko, Dariya sukayi atare inda yaya Abubakar yana zama yace mai, ai, kai ba jarumi bane sunan kawai muka ara maka, Don haka kaga da ni jarumin maza tadace shiya sa ka,sadaukar kabar min kawai, Atare suka kara sa dariya malam na cewa to haka zaka ce min yanzu ko, Tun da nai maka wanan, halarcin kake ganin kamar ban kai jarumi ba ko, A hankali yaya Abubakar ya dan sasauta muryan shi kasa kasa yace bance ba tuba nake, malam tsoho mai ran karfe, Nan nabarsu zaune a tare da malam din suna kara tataunawa a tsakanin su, Direct sashen mahaifana na wuce kai tsaye,, Na samu Mamana tana kokarin hada muna breakfast,, Da dan gudu na nakarasa gurin ta na rugumay ta, ta baya, nadade rungumay da mama ina jin dumin jikin mahaifiyata, Sai kuma ga hawaye sun zubo min shar ga ido na subbanallahi Yar Baba may ye haka kuma farin kisa wata tashigo taganki kina kuka ace ai, wani abin ne ya faru, dake kuma, Cikin muryan kuka nace mama naji marmarinku ne wallahi, Tace to yanzu ba gaki ga muba sai ki cinye mu tunda kinji marmarin mu, Kaina nakara nutsarwa a jikin ta nace, mama idan na cinye ku ingawa kuma, Muryan mahaifina ne mukaji daga bayan mu yana shigowa gidan, yana cewa, To ke Saratu tunda sun zo ai sai abarshi su karya anan ko? Anan kuma malam mama ta tambaya cikin mamaki, da fargaba, Nan muka zauna gaba dayan mu a yar barandar tsakar gidan mu ana hiran yaushe rabo,, Babana yakalleni yai murmushin jindadi yace, to ya wajen kawun naki, ina fatan duk suna lafiya ko,? Na ba Baba ansa da cewa duk lafiya suke suna gaisheku, Baba yace , Nafi,u dan rigima,saiga shimkafa da su mai, ya turo min dasu wai, muyi anfani da su, Shigowan yaya Abubakar a sashen mu yasa ma sauri dauko hijabin ta tasa, Wai kada suriki ya ga jikinta,surukin da tun ba mu zo duniya ba yake ganin ta a hakana, Shima afaninyaya Abubakar din yau sai yake jin wani irin nauyin Mama da Baba, Don haka sai ya kasa sake jikin shi kamar yadda ya saba, Baba ne yai mai umurni da ya zauna su karya a tare dashi, Bai fi minti biyar da zaunawa zai yi breakfast ba sai ga Baba Wadda yana sheda mashi cewa, wai ana sallama dashi a waje, Har zai mike sai baba yace dakata ka tsaya kaci abincin ka kafin ka fita, Don yanzu haka da ka tashi bazaka kara dawowa ka zauna ci ba, Masa ne da miya, sai, kunu koko, da kosai, da sugar, Sosai yaya yaci masa da miyan da aka siyo muna gudan mai yawa, sosai, Kafin ya kai karshe,sai ga yaya Aliyu ya shigo yana ce mai wasu daga cikin abokan su ne su kazo mashi murnan samun girman da yayi,,, Daga wanan fitan ban kara ganin yaya Abubakar ba har zuwa, wani lokaci, Nikuma ganin haka yasa nasamu sakewa da mahaifiyana da yan uwana munata hirar mu gwanin ban sha,awa,, A dakin mamana in kwance saman gadon ta mana tana zaune saman kujera, Mamana tace yar Baba naji dadin ganin kuna zaman lafiya da maigidan ki fiye da yadda muke tsanmani, Da farko zancen auren ku hankalina ya tashi sosai wallahi sai nake gani kamar zai wullakanta min ke, Amma tunda mahaifin ku ya ce min mubar wa Allah al,amarin sai kawai naji hankalina ya kwanta sosai Don haka nashiga rokan Allah da ya kara sanya alheri fa wanan al,amarin, Yakawar da duk wani sheri ko kulli dake tattare da wanan auren naku, Tambaya najefo mata da cewa amma Mama Ladi ta daina wanan irin zagin da take muna ko, Murmushi Mama tayi wanda ya nuna min cewa bata daina ba, har yanzu tana yi, Sai Mama tace inma har bata daina ba ai sai tayi da wanda ya kulata, Yanzu ai wanan ciwon kawai ya isheta ishara in tana da hankali, Haka mukai ta hira da mahaifiyata mu na yi muna girkin abincin rana, tare, Sai bayan Sallah azahar yaya Abubakar yabugo min waya yana cewa daga gida suka wuce, gaida mama sai kuma wani abokin su da gidan shi ya kone suka tafi mai jaje, Akarshe yake tambayana da cewa ba dai matsala ko ? Murmushi nasake ina cewa saidai na rashin ganin yayana a kusa dani, ba, Yaji dadin may na,ce haka yasa shi dan murmushi jindadi, Yace ai, gani zuwa don nasan mama tai min abinci rana, yanzu haka ko , Nace kaman kasani yaya amma dai tuwon shimkafa nace tai maka shine ta hada ma harda dan wake wai tasan kana son cin danwake da, Murna sosai naji yanayi yace wa kifara min godiya kafin in zo, don ban san yaushe, rabona da cin dan wake ba, Kafin yazo na dan tashi na shiga wasu sassan gidan mu ina gaida su,, Sai zuwa dare na samu shiga asibiti,gurin gaida mama, Gaskiya yau jikin ya dan yi dama sau don da alamar taji sauki, Tun shiga na mama wace ke zaune tana shan kunu acikin cup, Mu kayi arba da ita, sai naga ta kauda kai gefe guda, kaman bata kaunan gani na, Har gaban ta na karasa ina gaishe ta da jiki, Kamar bata son ansawa ta nsa min tare da kauda kanta gefe guda,, Nagane may take nufi amma sai naki gushewa daga gaban ta naja na tsaya, mata, Da ta gaji da aje kanta a gefe guda sai takai kwance , Anty, Safiya ce ke min magana daga bayana, tana cewa, Matar yayana jiyafa munga sako, daga yayan mun gode,, Da mamaki na juyo ina kallon Anty Safiya ina murmushi nace nikan anty ai wanan zancen kune ba nawa bane,, Sai da dare yaya zo dakin inda yake tambayan yan uwan haihuwan shi, koda wace cikin su za,ai tafiyan, Inajin yadda suke muhawara a tsakanin su, don anty ,Samira ce tafara magana tana cewa nidai kar ku sani don kun ga halin da nake ciki, Haka dai sukai ta cecekuce, inda anty mariya tadage akan cewa itace zata, Dole kowa ya kyale ta, ta tafi din su zasu zo daga baya suga jikin mama din insha Allah,, Motar asibiti ce yaya yai haya zata kai, Mama Ladi har Abuja, tare da baba Wadda da Anty mariya, Washe gari badon naso ba mukayi sallama da iyayyena da yan uwa da abokan arziki, Mun kusa shiga sokoto,ne na dan matsa kusa da yaya Abubakar,nadan kwantar da kaina ga kafadar shi, A hankali naji yana sauke ajiyan zuciya mai yar nauyi, A hankali nace mashi yaya Allah yaba wa mama, lafiya Ya ansa min da amin a hankali,, Inda naji ya dankara matse ni zuwa jikin shi yana cewa, kici gabada kula da kanki pls, Kudi ya mikomin don zasu kai kamar dubu hamsin, zanyi magana ya kada min kai dole nayi shiru bance komai ba sai dai ina rike a jikin shi,,, A sokoto yaya Abubakar suka saukeni a gida tare da tsarabar da nazo ma su da shi, Mun rabuzukatan mu babu dadi acikin ta don ga zancen ciwon mama ga kuma kewan rabuwa da junar mu da zamu kara yi, ****** ********* ****** Masu tafiya sun isa Abuja lafiya inda ba bata lokaci ya kai,ta Turkish hospital, Inda kwararu likitoci suka diba mashi ita, Baba Wadda tare dashi aketa faman wanan zirgazirgan asibitin, Salawatu tare da abokan ta sun zo gaida mama da abin arzikin su fam a leda, Sun dan zauna jim kadan sanan su kace zasu tafi, Kufi lubuna ta mikowa, Anty Mariya, tana cewa su zasu tafi Allah ya sauwaka, Anty Mariya tabi bayan su don yi masu rakiya, suna cewa ta tsaya amma saida ta bi su har bakin motan su, Sai da zasu tafine Anty mariya ke tambayar wace amaryan tasu ne daga cikin su, Lubuna ta nuna mata Salawatu, wace take kokarin shiga mota, daga dayan bangaren, Addu,an, Allah ya nuna masu anyi wanan abin arzikkin suke fata, kamar yadda tace, Ai mu mun fi son ki shigo ko gidan dan uwan mu zai gyaru, Bayan ta koma daki ta zaina kirga kudin da Lubuna ta miko mata dubu ashirin ne cif, Tace cafdi mace ke kyautar kudi haka masu yawa, don aso ta kawai,, ta maida kudin acikin aljihun bujen ta taja zip, ta rufe, Sun kwana sun wuni Sadiya bata lekasu ba, tun zuwan da tayi da dare ranan da akabawa mama gado, Tun abin bai damun Mama wace tafar murmurewa zuwa yanzu, Har takai ga cewa su Anty Mariya, da Baba Wadda, Shin Sadiya ko tazo ne tana barci? Anty Mariya tace tun ranan da mu kazo tun ranan tazo dubaki tare da yaya, Kagin su tafi duk ta ishe mu da tsaki tana tacewa yaya wai a kai,ta gida, ina jin sai da yai mata dan fada ta daina damun shi Mama tace ke Mariya, badai, Sadiya ba sai dai in akwai wani matsala da ya hanata zuwa kawai, Shiru Anty Mariya tayi don tasan cewa mama bazata taba yarda ai maganar Sadiya ba agaban ta, Don ita Sadiya bata laifi agurin ta, sai dai yaya Abubakar yayi laifi,, Sai bayan kwana biyu anty Sadiya tazo duba Mama yadda take wani ya tsune fuska tankar mai jin, warin su, Shigowan yaya Abubakar dakin ya sa hankalin su dawowa gareshi, Dauke yake da ledojin take away, din da ya sayo masu abinci, Daga gurin da mama take kwance ya karasa yana cewa mama tashi kidan ci abinci ko sai kisha maganin ki ki kwanta,, Mama ta ya mutsa fuska tana cewa, nagaji wanan shimkafa shimkafan maisunan malam, kace ma matarka tai muna tuwo mana haka, Gurin da Sadiya take yadan kalla yana mata wani kallon ke kin ji ko ? Ita ko Sadiya ko a jikinta don bata damu ba sam, don ba matsalar ta bane, Yan office, din su yaya Abubakar da kuma abokan arzikin shi haka suke zuwa, gaida Mama, Ladi tare da mata abin arziki, Wanda ganin haka yasa Mama Ladi kara mikewa saman gadon asibiti, Don ita bata da niyar tashi, zuwa gida sam, ranan da yaya Abubakar yazo fada mata cewa za,a sallamay ta sai cewa tayi,, Kada akawo mata bakin ciki a filin Allah don anga ta na samun abin arzikigurin mutanen arziki za aimata bakin ciki haka,? Sai da lalashi da ban baki aka samu mama tayarda zata koma gida, ****** ********* ****** Yaya Abubakar bai samu kwaso su, ba da kan shi zuwa gida, Don haka ya tura malam Mudi da driver don su kwaso su mama zuwa gidan shi bayan an sallamay su daga asibitin, A falo su ka yada zango don basu san inda zasu shiga ba, Ga yunwa na cin su don ba akai masu abin karin kumallo safe ba Tun da sallamar safiyane akai masu,daga asibitin, Tunda su ka shigo gidan ba kowa a falo malam Mudi, yai ta kwada sallama kamar tashin hankali, Bashiri Anty Sadiya ta fito falon don ganin mai wanan sallaman haka, Ganin su ne tai wani shekeke tsaye tana masu wani irin kallon, Sai, cewa tayi O,wo kune ashe,? Mama ya jikin naki,? Mama tadan ansa da kyat tana cewa taji sauki, Tun wanan lokacin da ta shige bata kara fitowa ba,su kadai ne zaune a falon sai kalle, kalle su keyi, Ganin yuwa zai halakasu Baba, Wadda ya fita waje, cikin Sa,a ya hadu da Hamzan maman Bi,u, Dama tun zuwan da sukayi da su Baba musa sun san juna, Nan Baba Wadda ke sheda mashi yunwa su keji, sun dawo daga asibiti matar gidan bata taresu ba, Gida ya koma ya fadawa Maman Bi,u da, Fattu Anyi sa,a angama abincin rana shi aka kwaso masu sukaci har suka bari, Sai bayan karfe uku yaya Abubakar ya fito daga meeting din da suka shiga na gagawa, A likacin ya bugowa Anty Sadiya waya ko ta,yiwa su mama wani dabara,, Saicewa tayi au suna nan gidan ne dama ? Wani irin abu ya ji a ran shi baisan lokacin da ya fisgi mota ba sai gida dauke da abincin take away, A lokacin suna zaune fali suna sallah la,asar bayan sunyo alwala can wajen get, din gidan, A falo ya samay su tarshe da kayan su zube duk sun gaji, Daki ya fada daga inda su ke suna jin, yadda yaya Abubakar wanda bai magana yau yana daga harshe gurin sababi, Dakin dake gefen na Sadiya yasa key ya bude masu dakin na bukatan gyara,sosai, Hamza ya kira awaje ya sheda mashi cewa, yazo ya taimaka mashi da aiki,. Kafin wani lokaci da Hamza da Baba Wadda sun gyara dakin nan tsab sun kwashe kayan su mama sun kai, ciki, Wanan abin ranan yabawa Mama Ladi mamaki matuka, Da yamma sai ga Maman Bi,u da Fattu dauke da kulolin abinci lafiyayye sun kawo wa mama, ladi, Lokacin da yaya Abubakar yadawo daga massalaci ya samay su zaune suna cin abincin da su Fattu suka kawo masu, Duk nauyi da kunya ya kamashi, mama cikin muryan mai ciwo take ce ma yaya Abubakar ya zauna yaci abinci, mana yace ya koshi,, Tausayi yaba mahaifiyar nashi don ada da bata gani ba sai take ganin ka,zafi ake wa Sadiya don ba,a kaunar auren shi da ita Amma sai gashi ta gani da idon ta, sam Sadiya bata wani damu da zancen, Basuga Sadiya ba sai washe gari da ta kawo masu, tea da breads kawai ba kwai ba Irish, Tun shi bata kara lekosu ba,daga gidan su Fattu aka kawo masu abin kari lafiyyaye, suka ci, Da rana Jeloup din macroni, ta dafa masu bai ko karasa dahuwa ba tsatsaye, Suna ta zullumin yadda zasuci shine sai ga maman Bi,u da kan ta ta kawo masu abinci tuwon garin farar masa da miyar danyen kubewa, ZEEE MAKAWA YELWA 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 4⃣5⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA ALLAH-AL-AZEEM,,,, Wanan irin wullakanci da tuzarci da Sadiya taima mahaifiyar shi da yan uwan shi, Yasa yadan shiga wani halin tunane acikin kwanakin nan, Kamar shi ace wai sai makwabta sun kawo abinci agidan shi, Amma koda yake madadi Mama ke fuskanta, Don ita ce ta hana shi auren wace yake so ta hada shi da Sadiya diyar kawarta, A lokacin shi Fatima kaunar Aliyu abokin shi yake so da da ita yai soyayya sosai, Amma sai mama tace madadin ya auri fatima wace boko ya ratsa ga Sadiya nan diyar aminiyar ta suyi auren su na rufin asiri, Alokacin abinda yasa ya yarda yana gudun irin tozarcin da mahaifiyar shi zata shiga ne, Ga Fatima yanzu inda take aure yaran ta biyu kuma ta zama yar business sosai, Tsuki ya ja tare da cewa Sadiya, Sadiya why please ? Kin zama min kayan kafa, babu inda nake jin daman ki, Wayan shi dake gefen side drower din shi ya jawo,, Noban Babana Samaila ya ke nema, yakira shi don ya san abin da yake ciki, Kira na uku Baba Samaila ya dauki wayan, tare da sallama wa dan shi surikin shi, Sun gaisa Baba Samaila ya ke tambayan, jikin Mama Ladi,? Inda yake sheda mashi cewa jiki Alhamdullahi da sauki sosai don har sun sami sallama Yana son sai jikin nata ya kara samun sauki ne su, dawo gida, Madallah madallah Alhamdullahi Allah ya tsare gaba inji Baba Samaila, Dan shirune ya biyo bayan zancen su sai shi yaya Abubakar din ya dan kau, da shirun ta cewa, Baba dama akan zancen auren da zankara da mukayi ne yasa na bugo maka waya, Duk da Baba na yaji wani iri acikin ran shi amma sai yadaure yana cewa, to, to, to, Zance ya taso ke nan dai ko ya Abubakar ya amsa da cewa eh Baba, don dama na ce bayan Wata biyu da auren Meenatu zan yi wanan din, Yanzu ga shi har ankusa ma wata biyar da auren meenat din,, To ba matsala zan yi magana da malam dashi yaya Buhari akan zancen, In yaso sai inkiraka asa lokaci ko? Tau Baba na gode da wanan kokarin nagode kwarai, A, a aiba damuwa yiwa kai ne hakan ai, ****** ********* ****** Bayan gama wayan su Baba na yakai wani lokaci tsaye bakin motar shi yana tunane, Ya tausayawa Meenatu sosai, yarinya karama kamar Meenatu tashiga cikin manyan mata haka,? A zaton shi yadda yaga ya karbi auren Meenatu yana zaton Abubakar din ya janye zancen auren shi da waccen yar barikin ne ai, Amma sai gashi yanzu gatsau ya tayar da zance idan har bai bashi goyon baya ba sai ace saboda yana auren yarshi ne bai son yayi auren, Amma shi gaskiya bai so ace Abubakar ya auri wanan irin mace ba gaskiya, Malam tsoho bayan ya gama sauren bayanin Baba, Samaila, Sai faman girgiza kai ya keyi, yana cewa,hmmm, hmmm kaiyya, Ta yaro kyau takai bata karko, amma bai kamata ace wanan halarcin da yai mashi kuma yanzu ya watsa masu kasa a ido ba, Ganin cewa malam zai hana zancen yasa Baba Samaila ba malam hakkuri akan ya bari ayi auren don kada su aikata sabo a dalilin hanasu yin auren, Yace kaga baba inda Abubakar mazinacine bazai kawo zancen aure ba sai dai suyi ta zaman banza a waje kawai, Amma tun,da yana son ta aduk yadda take abari kawai, suyi auren su zai fi,, Badon malam tsoho yaso ba ya yarda da zancen karin auren yaya Abubakar wanda za,a yi a karshen wata lokacin ina batun fara exam ke nan, ****** ********* ****** Bayan sallah isha,i malam tsoho ne ya kira yaya Abubakar da kan shi a wayan shi sabanin yaya Abubakar ne mai kiranshi su gaisa dama, Ganin mai kiran nashi yasa shi dan tsayawa gefen hanya don ya karba kiran, Bayan sallama da gaisawa, sai kuma yar shiru, Ga irin yadda yaji yanayi muryan malam sai yake jin badadi ba a rayuwar shi, Malam tsoho ne ya fara cewa, Abubakar, ina son in kara jaddada maka cewa Amanan yarinyar ga Aminatu na baka, Ko bayan raina ka cuta mata bazan yafe maka ba Abubakar,, Wani irin abu yaji azuciyar shi, tare da mutuwan gabban jikin shi, Tunda yake da malam tsoho maganan bacin rai bai taba shiga tsakanin su ba sai wanan zancen, Kafin yayi yunkurin yin wani magana sai yaji malam tsoho ya kashe wayan shi dif, A jiyan zuviya ya sauke tare da share gumin da ya dan feso mai a goshi da bayan hannun shi,, Ci gaba yayi da tukin motar shi sai dai hankalin shi duk a tashe yake, Gab da zai shiga get din gidan shine kiran wayana ya shigo mashi, Meenatu ya furta sunan a hankali, tare da tunanen zancen ne zan mashi, Ya dauka da Sallama tare da sauke numfashi, murya na babu fushi acikin ta ko sarkewa, Hakan yasa shi dan sake jiki yana tambayana ya nake,ya karatu, ya mutanen gida, Na bashi amsa cikin lumshe idona dan jin dadin muryan shi dana yi da fadin lafiya kalau, Tambayan jikin Mama Ladi nayi inda ya ke ce min ta samu lafiya sosai, Sai kuma yaje gamba ana da ba matsalan komai dai ko ? Na bashi ansa da fadin babu komai yaya, Murmushi naji yayi kawai tare da cewa fadi dai gaskiya yar kauna,ta Murmushi mai hade da dariya na sakar mashi tare da cewa Lah yaya gaskiya babu komai, Yace kedai kodai inzo in dauke ki ne ? Yaya ni da zan fara exam ina zani kuma, haka? Ai, to ba yanzu zaki fara exam din ba kibari kawai inzo in dauke ki kizo ki kwana muna biyu ko na ce a,a yaya sai munyi hutu dai, to kidai yi shawara zan kiraki inji may kika yan,ke akai? Da haka mu ka yi sallama dashi kamar kada mu rabu da junan mu,, Kafin in kashe wayan ina ta jin wani kira yana shigo min, Sai da na kashe sai naga ashe malam tsohone, ke kirana, Da sauri na kara kiran shi sai dai zuciya ta na cike da mamakin kiranshi a wanan lokacin,, Mungaisa acikin girmamawa kamar kullun, ina sauraren shi, Sai na ji muryan shi yana kiran suna na yana cewa Meenatu ki saurare ni da kyau ki ji abinda zan fada maki,, Kara natsuwa nayi guri guda don sauraren shi kamar yadda ya umurce ni da yi, A lokacin ne kuma sai ga Anty Amarya ta shigo dakin namu dauke da bakar leda, A cikin sa kayan tsaraban dare da Uncle ka siyo muna, kamar meat, chicking pepping, snacks drinks da sauran su, Ganin irin yanayin da nake ya sa ta tsayawa batai magana ba, Hand's free na wayan nasa don muji a tare don babu abinda zan boyewa Anty amarya na rayuwa na, Matar da take tsaye akan al,amari tankar ciki guda muka fito da ita, Malam tsoho yafara da kiran sunana da cewa Amina, Na,ansa da na,am malam yace kiyi hakkuri kinji ? Duk abinda kika gani a rayuwan bawa jarrabawa ne daga Allah, Don komai,mukaddari don haka ina son wanan auren da ki kaga mijin ku zai yi ban son ko kadan ki tayar da hankalin ki, Wani irin faduwan gaba naji ya ziyarce ni a lokacin amma sai kawai na daure na ci gaba da sauraren tsohon, Malam ya ce sai gaba zai gane dalilin hadin auren ku da nayi, Bama shi kadai ba har kowa dake gidan nan gaba daya koda a lokacin bana a raye nasan za a fada, insha Allah, Idona da suka sauya zuwa ja na daga na kalli Anty amarya wace ke tsaye muna sauraro, Kai ta kada min alamar kada inyi kuka na daure nace malam na gode insha Allah bazanyi komai ba, Ya ce to Allah yai maki albarka ya baku zuri,a dayyaba, Wanan ban iya ansawa afili ba sai nai shiru, malam ya ci gaba da cewa, Abarshi kawai yayi auren yaji abinda ke nan ga Wadda ya bugo waya yana fada min irin wullakancin da Ladi ke gani gurin ita wanan matar tashi dake gida, Yace ba ta ba su abinci sai dai ansayo masu ko kuma akawo masu daga makwabta, Daga idona nayi mu ka hada ido muna kallon junan ni da ita, Sai muka kadawa junan mu kai alaman, tooo,pa, Malam yaci gaba da cewa, Shine zai kara jajibowa kan shi wani auren wahala kuma,, Munyi shiru, muna ta sauraren nasihan tsohon har yai muna sallama na kashe wayan, Lokaci guda, muka numfasa ni da Anty Amarya tare da kallon juna, Anty Amarya tace ashe shi har yanzu bai fasa zancen auren ba ke nan,? Kada kisawa kan ki damuwar komai kowa tashi tafisshe shi kawai, Don haka ban son jin kin yi wani fitina a,kai ki,bari zamu tafi gida wurin Hajiya Mama muji may za tace, (Hajiya mama mahaifiyar su Anty,) To na amsa mata da shi tare da cewa nagode Anty, Ledan da tashigo min dashi na kayan tsaraban Uncle dina ta miko min tana cewa bari taje ta kwaso yara falo don kila sunyi barci, Fitan Anty banbi ta kan ledan ba na kwanta saman katifa na zuciya na duk ya cakushe min wuri guda, Tunane na keyi yaya zan zauna a tsakiyan wa yan nan manya matan, da suka ma kusa haihuwana, A haka barci yai gaba dani batare da nakara koda motsawa ba, Sai cikin dare na dan farka sai dai tunanen bai yi wani tasiri ba na koma barcin, ****** ********* ****** Baba Samaila da su Baba Musa da sauran jama,a suka tafi don nemawa dan su aure acan wani kauye cikin NASAWA STATE, Sai dai suna zuwa sai iyayyen Salawatu sukace sai dai a tsaya a daura aure gaba daya, Hakan akayi inda Baba na Samaila ya ba da dubu hamsin sadakin auren kamar yadda suka yanke masu, Sai daga bayane aka kawo zancen kayan lefe, amarya, Baba Musa yace ai mungaya maku cewa neman aure mukazo ba daurewa ba kuka ce, a daura, Yanzu wanan ya rage a tsakanin, su shi da matar shi, Iyayyen Salawatu sun yake cewa Sati biyu tarewa don haka, sai a shirya, Sai bayan su Baba sun dawo ne suke sheda masu yadda abin ya kaya a can, garin, Duk suna zaune a falo har Mama Ladi, suna sauraren abinda suke fadi, Mama Ladi tace ai dole su yi gagawan daura auren, don kar a ce anfasa, Amma ta yaya tana zaune a cikin gida zai daira aure bada sanin ta ba, Matar shima batada labarin auren sai kawai aji daga sama, To kiyi hakkuri Ladi haka Allah ya nufi ayi auren ba shiri, Ta ce tunda ya maryar da kan shi wanda bai daukan shawara ba, In ba shi ba dan may zai ce haka zaita aure ba da sanin ta ba,, Daga can baya Baba Musa yace to ai yanzu Ladi sai kiyi yadda zakiyi don mu samu akayi mun kuma aiwatar, don haka zance ya saura gare ki, Dakike cewa haka ita Meenatu ba matar shi bace, Wazo daurin auren ba mahaifin ta ba, ni wallahi irin rayuwan nan naki na jahilci shiyasa bazan taba shiri da ke ba, Dariya sauran mutanen gurin suka sa masu don sanin cewa sun saba wanan badakalar a tsakanin su dama, Su Baba basu tsatsaya ba washegari suka juyo zuwa Kebbi, abin su Baba Wadda yaso ya biyo su, su dawo amma yaya Abubakar, yace yadan dakata su dawo tare dasu Mama Ladi, Badon yaso ba yana gani suka juyo abin su zuwa gida, ****** ********* ****** Ànty Amarya ce bayan nadawo school take sheda min cewa har andaura auren yaya Abubakar da Salawatu, Duk labarin bai min dadi ba amma sai kawai na dake a zuciya na, A fili cewa nayi tau, Allah bada zaman lafiya, yasa ace gwanma da akayi, Wanka na shiga tare da dauro alwalan Sallah la,asar, Nakai wani lokaci zaune a gurin tun ina addu,a har na koma tunane, Irin halin rayuwan da zan yi cikin manyan mata yar karama dani, Yanzu duk irin zumudin da idan muna tare da yaya Abubakar yake nuna min ashe halin mazane, Shiko dai don an bashi ni ne yasa zai min haka ? Aure da wata hudu yace zai auro wata baya na, may narage shi dashi kamar yadda ake ta min nasiha akai, Wasu irin hawayen bakin ciki da takaici ne naji sun silalo daga cikin idona zuwa kumatuna, duk sun wanke min fuska, Waya na dake saman mirror dakin mu tana chaji naji tana kukan neman agaji, Hannu na mika a hankali na dauko wayan sunan, yaya Abubakar ne na gani jikin wayan, Ina kallon wayan har tagama ringing din ta tagaji ta katse don kanta, ban dauka ba, Kira uku ban daga ba har ya gaji naji ya daina kiran nawa, Daga karshs ma sai na kashe wayan gaba daya ta yadda ko ankira baza,a samay ni ba, Mikewa nayi na fara shirin kwanciya duk da dai nasan cewa ba barcin zanyi ba amma sai nake ga kwancin yafi min a lokacin,,, Anty Amarya ce ta shigo dakin tun daga kofa ta hangoni a kwance fuskana yana kallon rufin dakin, Muryan Anty naji tana cewa, Meenatu badai damuwa kikasa a ranki ba haka ko ? Murmushi na kirkiro a fuskana na dole, badon naso yin sa ba, Gefena tasamu tazauna tana ce min, Meenatu ban son kisa damuwa ga al,amarin mazan zamani, Duk namiji idan yana son aure, baijin has azamanin nan da muke a ciki, Sai fa idan sunyi sun ji abinda ke nan, sanan hankali su ya kwanta su fara neman hanyar ceto, Don haka tunda kikaga har iyayyen ku basu iya hana shi wanan auren ba ki sa masa ido, kawai kamar yadda na fada maki da farko, Ke dai kawai ki rike mutuncin ki da kuma ibada kina kai kukan ki ga Allah, Saboda haka idan ya kira ki dauka kar ki kara share ahi don Allah , Kyale shi ai shima yasan bai yi daidai ba tunda bai sanar da ke ba akai, Ido na dago ina kallon ta yadda har tasan cewa ban dauki wayar shi ba, Anty Amarya tace, yanzu ya bugo waya yana tambarya Uncle din ki ke wai ya kira baki daga waya ba, Shine nake ce masu kin kewaya ne shi yasa isan kin fito zan fada maki cewa ya bugo, ****** ********* ****** Yaya Abubakar da yaga cewa yai kira uku ban dauki wayan ba yasa shi dan yi murmshi don yasan cewa yayi laifi, sosai, tunda har ba,a daga mashi wayan shi, ba yau,, Don haka sai ya kira nomban Uncle dina don su gaisai kuma ya tambaya ko ina lafiya, A lokacin Anty Amarya tana kusa da Uncle dina shinw take fada masu cewa, ai ina bandaki ne a lokacin, Sai yake cewa Uncle ayi hakkuri fa auren ne nasa yazo mashi ba shiri, Sundan taba hira da Uncle dina sanan sukayi sallama ya kashe wayan, Shiru yadan yi tare da lumshe idon shi don yasan cewa kawai an dai kareni ne kawai, Amma ina cikin fushi ne kawai irin na mata, murmushi ya dan yi kawai don yasan cewa sai kana son mutum kake kishin sa, Wayan Salawatu ne daya shigo a lokacin ya katse shi ,, Acikin wani irin muryan shagwaba take mai magana yau, Sundauki lokaci mai tsawo suna hiran irin ta masoya, Washegari koda ya shiga office mutane sai murna suke mashi cewa Ango Ango, Shiko sai murmushi ya keyi baki yaki rufuwa sai nagode yake cewa jama,a kawai, Yau, Salawatu shigan zani da riga tayi na atamfa, zuwa office din nasu, Sai wani gyale mai shara,shara da ta yafa akanta har zuwa rabin kirjin ta, Ita a ganin ta ,tarufe jikin ta ke nan,a hakan ta yi shigan matan aure, Sai da tafara zuwa office din su suka gaisa da mutane suna ta mata, murna da fatan alheri, Sai, nagode nagode take cewa da kuma Allahuma Ameen, Acikin wani irin jin dadi ta isa office din maigidan nata, Yana zaune aiki yai mai yawa yana kokarin tura sakonni, Yaji an turo kofan shiga office din shi yadan dago don yaga kowaye yashigo mai batare da malam Abdullahi ya sheda mai shigowan mai shi ba,, Salawa ce su kayi arba dashi tun daga kofan office din, Wani irin dam yaji gaban shi ya yabada tankar ya fadi, Sai yaga yau Salawa ta kara mai wani irin kyau da kwarji a fuskan shi, Murmushi mai laushi mai sace zuciyan masoya suka sakewa junan su a lokaci guda, Wanda su kadai,su ka san irin yanayin da suka shiga alokacin, Da tafiyan jan hankalin maza ta karasa gaban table, din nashi, Tana zuwa ta zube gwiwa bibibyu a,kasa gaban shi tana cewa barka da safiya maigida, Cikin wani irin lumshe idon jin dadi ya amsa mata,, Tare da mikewa tsaye yadan rugumota zuwa jikin shi yana mai wani irin sauke zuciya, Cikin wani irin murya da sai ka saurara zakiji tace be my husband forever, dear ? A hankali shima ya rada mata da cewa i,will insha Allah, Suka kara rungumay juna cikin shauki da kaunar junar su,, A hankali yaya Abubakar yafara zare cikin shi daga gare ta yana mai ce mata, yana sa aiki da yawa amna idan ya gama zai mata waya su fita, ZEE MAKAWA YELWA,, 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 4⃣6⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA ALLAH-AL-GHAFOOR FATAN, ALHERI GAREKU KO DA YAUSHE MASOYA NOVEL DIN TARKO, BAZAN IYA LISSAFA SUNAYEN KU BA ANAN INA DAI MAKU FATAN ALHERI DA GAMAWA DA DUNIYA LAFIYA, ALLAH YASA MU DACE DA RAHAMAR SA ALLAHUMA AMEEN👏👏👏👏👏👏 Daga inda take kwance saman makeken gadon hotel din take kallon bayan shi, Cikin wani irin so da kauna da ke fisgan ta, alokacin Don zata iya cewa bata taba karo da namiji jan gwarzo irin Abubakar ba, Daga bathroom yake yafito wanka, yana ko,karin shirya jikin shi, cikin tufafin shi da ya watsar saman kujeran dake dakin, Sai a lokacin Salawatu ta dan zabura ta mike don ta fahinci cewa tafiya zai yi, A daidai lokacin da yake zura wandon shi ajikin shi yaji muryan ta tana cewa, Zaka tafi ne ? Batare da ya juyo inda take ba ya bata ansa da cewa, Eh a takai ce, Cikin wani irin kashe murya take ce mai tun yanzu dear,? Bai iya bata ansa ba sai da ya suri corth, din shi yana kokarin sawa, A lokacin Salawa har takai, tsaye tana kokarin daura, towel a jikin ta, Inda take ya juya ya nufa sai da ya mika hannu ya dauki keys din shi sanan ya dan riko ta yana cewa, Zai je gida kada hankalin Mama ya tashi saboda bai Sanar da su inda yake ba, Amma zai turo Bado driver ya dauke ta ya mayar da ita, Cikin kashe murya, tace dear I think we, are going to spend our night here? Murmushi mai kama da yake ya sake mata tare da kara gyara bottom din rigar shi, Yace bana son family di and my Mama su, shiga damuwa saboda ban sanar da kowa gurin da nake ba, See you next, Daga haka ya sa kai zuwa fita daga dakin batare da ya kara furta wani abu ba, Yana fita ta koma saman gado tana sauke numfashi sama sama, Don yau gaskiya ta samu abinda ta dade tana muradin samu a rayuwan ta, Yanzu abinda ya rage shine yadda zata mallake shi gaba daya yazama na ita kadai, Don yanzu bata jin zata iya sharing din Abubakar da kowa wace mace a duniyan nan, Burin ta shine ta mallake shi ita ka dai bada kowa ba,, Murmushin mugunta takara yi don gaba dayan su, sai tai waje road da su, ****** ********* ****** Tafe yake a motar shi, shi kadai sai faman tsuki, yake yi, Sai dai ya rasa dalilin yin tsukin da ya ke tayi har yanzu, don bazai ce ga dalili ba, Hamza ne ya bude mashi get, tare da yi mashi sannu da zuwa, A tare suka shiga gidan da Hamza wanda zuwa yanzu ya zama dan gida sosai yana yawan shiga gidan, A falo Mama su ke zaune ita da anty mariya,suna kallon TV da ke aiki, Yana shiga mama ta mike tsaye tana cewa mai sunan malam ina kashiga haka yau, tun safe, Ba waya ba, kuma aike balle mu san abinda, kake ciki, Murmushi yayi yana cewa, mama, ai ba abinda zai samay ni insha Allah, Kawai dai ai,yukane sukai min yawa yau na dan tsaya ti office, Tambayar mama yayi da cewa mama kunci abinci ko ? Ta tabe baki ta ce an kawo muna gidan wa yan nan bayin Allah masu bamu, Amma ai mariya ta fara dan koyon yadda ake girki da na ku kayan girkin, Ita Sadiya fa ba ta girka ba , Mama za tai magana ke nan sai ga, Sadiya tafito daga dakin tai kicin, kicin da fuskanta, Wanda tun zancen daurin auren Salawatu da shi Abubakar suke cikin matsala, Inda Sadiya ke fadin cewa bata taba sanin cewa wai Salawatu ce yake nufi zai aura ba, Tace wanan yar barikin zai kwaso masu gida, ya halakasu, baki daya har shi, Ashe dama zaman banza sukeyi da ita shiyasa komai nashi take shigewa gaba,gaba, Ita ta zaci cewa zaman mutunci su keyi na suna office guda da juna,,, Wanan maganan yaba Abubakar haushi sosai yace cikin kunan rai may kike nufi da muna tare, ashe,? Ni ban taba zina ba don ki sani don dani mazinaci ne da kece zaki fara sakani yin zina, Amma sai na godewa Allah bai yoni mai saba mashi ta wanan hanyan ba, Fitowan ta daga Sashen ta taji yana tambayan Mama ita,, Wani irin mugun kallo ta watso ma Mama tare da cewa, dama nasan anzone kawai don aga iyakar mutum, Wani irin bacin rai yaya Abubakar yaji baisan lokacin da yayo kan taba a fussace, Mama Ladi ce cikin karfin hali tace mashi kada ka fara ka taba ta kyale ta kawai, A cikin kunan zuciya ya haye sama yana jin bacin ran shi na dada karuwa mashi, Yana shigewa Sadiya tace ai kun kai ga yadda kuke so akai, Amma ce kunzo kun zubewa mutane agida duk kun hana mutum shakat, banda daman in hutu ace yi wanan a yi wancan, Ni gaskiya bazan iya ba don ba yar aikin kowa nake ba, Cikin mamaki Anty Mariya da Mama Ladi ke kallon ikon Allah, Don dazun da Anty Mariya ta shiga kitchen ta dauko, madaran peak zata hadawa Mama tea tace tana son sha, Sadiya tana fitowa sai cewa tayi kada Anty Mariya ta kara daukan wani abu batare da ta fada mata ba, Kuma ma ai wanan don ta aka siyo ba don su ba don ai da su kazo ba taga ya siyo wani ba da sunan su,, Dole suka koma zaman taka, tsantsan, a gidan suna gudun yin dogon motsi suyi laifi, ****** ********* ****** Zaune su ke saman wasu manyan kushin din kujeru, masu siffan kunkuru a falon, Yar tsohuwan tayi dani in zauna a saman daya daga cikin kujerun da ke falon kamar yadda suke zaune ita da yar ta amma na ki zama, Ina kasa zaune gefen kafan ta ga goran fura mai sanyi an aje muna agaban kowan mu, har ita yar dattijiwan, Sai da ta kurba furan daga gora ba tare da ta tsiyaya a cup ba tace, Meenatu hakkuri zakiyi kin ji, Aure bautan ubangiji ne, Don haka abarwa Allah, al,amarin sa kawai, don ko kin tayar da hankalinki indai namiji ne baya jin has, a lokacin sai fa yayi binda yai niyar yi, Balle nasan cewa ke bawai wani laifi kikai mashi ba har ya kai shi ga yin wanan auren ba, Illa kawai sun dade da ita yarinyar ne wata, kila zancen ta yana gaban na ki, Shiyasa yai haka don ya burge ta ko ya wanke laifinsa gare ta, Musan man ke Meenatu da ku ke yan uwa dashi, Dan ke fa yar uwar shi ce, bazai damu da cewa sai yayi ta rarashinki ba don dole dai ki zauna dashi, Kinga idan baki kwantar da hankalinki ba, tabbas rayuwanki zata shiga cikin tashin hankali da matsaloli mara misali, Don dole kuma kiyi hakkuri duk yadda ta kasance, da ke, Kibar komai ga Allah kirike ibadun ki ki taimaka mashi wurin taimakon yan uwan ku mabukata, dama wanda ba yan uwan ku ba, Haka zai kara maki haske sosai gareshi dama kowa na,ku Anty Amarya dake gefe zaune tana wasa da wayan ta zuciyan ta tana mai,jin haushin abinda mijin Meenatun yai masu, tace wa mahaifiyar ta Ni Mama hajiya, yanzu abin,da nake so shina Meenatu ta fahinci yadda zama cikin irin wayan nan manyan matan ya ke, Haka hajiya Mama ta fara min nasiha cike da kissa da kuma wayarwa akan zaman aure, A karshe take ce min dole ne in fara kwantar da kaina in fahinci halin kowacen su, Daga baya sai in koma nima karuwan dakin mijina sai sun girgiza, dankan su, Ina zaune cikin ladabi, ina sauren hajiya Mama take ce min Kar ki yarda ace girkin ki ya zo batare da kin wa mijin ki wani tana di ba daga jikin ki, Wanda hakan ne kawai zakiyi mashi ki kwato incenki ga kowan su, Duk da na san cewa, suma din ba bayaba gurin gyara irin nasu, Duk abinda zakiyi kada ki yawaita cushe cushe a jikin ki ya na ragewa mace daraja ga mijin ta idan har ya gane, hakan, Dan zai zaci cewa kina masa wani asirine don ki mallake shi, Akwai hanyoyi daban daban da zaki bi wanda zai kawo maki dau,ka ka, a,waje maigida ki koma, tankar yar leda,, A take ta dinga jero min irin dabarun su na mutanen baya wanda bai kawo wa mace illa, ajikin ta, Sai wanda zaki dinga hadawa da kan ki a gida ki,na sha, ga bakin ki a koda yaushe, , Anty Amarya ta dinga rubutawa inda taba hajiya mama kudi a sawo min goran zuma na ainifi kauye don inje dashi, Sai kudin da za,a siyo min sauran abubuwan bukata da hajiya mama zata tura kauye, Wanan zancen da hajiya mama, tai min yasa na dan rage jin zafin da nake ji araina,, Ba muje gida ba sai da anty ta kaimu shagon Gazali mai kayan mata a cikin kasuwa, ta sayo min yan kasan Indonesia masu kyau da tsada, Muna tafe Anty na jan mu a mota hanyan komawa gida, Ta ce min Meenatu na ansa a hankali da cewa Na,am Anty,, Tace kin,ga duk abubuwan nan da mama tafada maki to walle idan ki ka tsare yin su to ke more auren ki, Don ke gan,ni nan badon Allah ya ban uwa mai tawakkali da kuma hikima irin Mama ba, Da ina ganin gidan Uncle dinki nika shi don iyayin su, Samira ba kadan naba, Kin san dai kowa yasan yan gidan doctor, ka,oje nan garin, ko? Amma dole sun ka bar ni dakina tama, Amma fa haka bai samuwa kamar yadda mama ta fada makine, Addini sadaka alheri kyautatawa duk su shige maki gaba, kuma tsakani da Allah zakiyi badon ganin ido ba,,,, , Ki tai kiyi hakkuri keji,,insha Allahu babu abinda ka samuwan ki, sai alheri, Hawaye masu zafi ne suka tsiyayo daga idona a lokaci guda na ke furta kalman nagode Anty, Tace kai haba Meenatu mizaki godemawa tun da duk yiwa kai na, Allah dai yasa mu dace kawai, Na ansa da cewa Ameen a hankali ba wai lalai anty taji ba, ****** ********* ****** Tun bayan shigan shi dakin shi duk zuciyar shi tana mashi wani irin zafi da su ya, Wanka ya karayi ko zai dan samu relief a ran shi irin yadda yake ji, Zaune yake a bakin gadon shi inda ya dafe kai da tafin hannayen shi, Yabaro gurin salawatu da bacin rai ga kuma sadiya ta kara mashi wani, Numfasawa yayi irin na an,gufu ba,a tsiraba ke nan, May zaice da wanan damuwar ta shi ne wai karfa ace anazaton, wuta a makera sai gata a masaka, Da sauri yace kai hakan ba zai yuyu ba ai dama kowa yasai rariya yasan zatayi yoyo ai, Wanan sai in yaso mamaki acikin don mace kamar salawtu, dama ai,dole haka zai samu gare ta, Point din farko kenan da ya fara karo dashi daga gare ta,, yafurta a hankali SALAWATU,, Amma ita kuma Sadiya yasan mai gyarata sai Allah amma idan har zama yai zama ai dole ta canza wasu halaiyya nata, Amma kuma ai rashin mutuncin ta yai yawa har da mahaifiyar shi, za,taiwa rashin mutumci, Matar da tai Sanadin auren shi da ita, Matar,da, bata taba yarda wani ya aiban ta Sadiya a kusa da ita ko kadan, Duk da mama tai mashi fada akan kada yace mata komai, Gaskiya baiji cewa zai iya kyaleta taciwa mahaifiyar shi mutunci a,gaban shi,ba, Don haka ya aiyyana a rayuwan shi zata gane kuren ta sosai, Haka ya zauna daki batare da yafito gurin su mama sun dan,yi hiraba kamar yadda ya saba yi dasu duk dare, Kwance ya,kai ta baya cikin yanayin damu daga saman gadon da yake zaune, Idon shi ya dan ritse kamar gizo yaga Meenatu, cikin irin yanayin ta na alkunya kamar kullun tana dan murmushin nan nata kasa, kasa, Fitgigit ya bude ido yana tuna cewa rabon da yakira Meenatu fa yau kwana biyu ke nan, Dama ita ba gwana bacs gurin kiran shi, indai ba zuwan Mama ba da takan dan kira taji ya jikin Mama Wayan shi ya jawo tare da saurin neman nomban ta, Har kiran ya katse kamar ranan ba a dauka ba daga bangare na, Wayan na daga gefe na tana ruri koda ban duba ba nasan cewa shine awanan lokacin Don tunda rana munyi waya da iyayyena mun gaisa ko kamar kullun don neman albarkan nan da suke sa min idan munyi waya dasu, Wani sabon kira ne yashigo again daga gare shi, inna kallon wayan naki daga, Anty Amarya ce ta shigo dakin gab da wayan ya katse sai ta girgiza min kai alaman in dauka, Bamusu sai dai raina baiso daukan wayan ba a lokacin, Ina jin ya sauke ajiyan zuciya daga cikin wayan tankar a fili yake gaba na,, Cikin wata irin murya da ban san ina da ita ba nake cewa Assalamu Alaikum, Assalamu Alaikum Assalamu Alaikum, Ni kadai sai nake cewa ayya ba network sai na kashe daga ban,gare na, Kafin in kashe a lokacin da nake tacewa ba network wani irin murmushin kasaita naji yayi, Nasan cewa yan san ina jin shi bandai da niyar daukan wayan ne kawai, Murmushi sosai yaya Abubakar ya yi don ya fahinci ban dai son daukan wayan nashi ne, kawai, Don ya nuna min ya fini wayo da dubara sai ya kira ni ta layin Uncle dina, Da gudu karamin yaron mummy Ansar, ya kawo min wayanyan yaron na ta haki don gudun da ya yi, Da sallama again na karba wayan nashi inda yake tambaya na da cewa Yanzun dai kina jina ko ? Naam sa mai da eh, ina ji, Gaishe shi nafara yi sai kuma nai shiru, Sorry pls kuyi hakkuri da wanan banda da caji wlh, ZEEE MAKAWA YELWA 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 4⃣7⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA ALLAH - ASH - SHAKOOR Ya Allah muna rokon ka ka kawo muna karshen yin rawan yayan musulmai a cikin film din hausa 👏👏👏👏👏👏👏 Cikin wani irin murya mai tada hankalin maisauraron ta mai juya wa mutum lissafin tunanen sa, na ji ya ce, MEENATU,, May yayan ki yai maki bakya daukan wayan shi ne, ? Nace acikin siririyar murya na bakin dankan wayan nayi ba, network ne bakyau, Hmmmm na ji ya ce tare da numfasawa a hankali, Ya karatu ya mutanen gida,? Na amsa mashi da duk lafiya kalau Alhamdullahi, Daga inda yake kwance ya dago idon shi da suka kada sukayi jajir, yana kallon rufin darkin nashi, Yarasa may zai cewa yarinyan don haka jin yai shiru ne nace mai, Sai anjima tare da saurin kashe wayan batare da na tsaya sauraren may zai fada min ba, Tashi nayi na shirya a cikin wata yar farar rigar barci na, Ina kokarin daure dogon gashina da ribon ne Anty Amarya ta bude labulen kofan namu, tana cewa, Meenatu badai har zaki kwanta ba yanzu ? Nadago kai na a hankali na kalli inda Anty take tsaye nace, Eh ina son tashi da safe da wuri idan ran mu ya kai, Anty Amarya tace Meenatu bakyaji ko sai da nace ki dauki wayan bawan Allah nan idan ya bugo amma sai ki kaki, Gashi har uncle din ki ya fara suspecting din ko kin sawa kanko kishi ne, Da sauri nadan dago kaina ina kallon ta don jin abin da tace uncle yace a kai na, Jikina ne yai sanyi a lokacin nace cikin wata irin murya tankar zanyi kuka, Anty ni ba fushi nakeyi da shi ba, kawai dai, ban jin dadi ne, Hmmm naji tace taci gaba da cewa gaskiya meenatu, baki kyauta ba duk nasihan da mukai maki amma zaki, yi haka, A sanyaye na dago idona da suka fara cika da hawaye nace, Kiyi hakkuri Anty Insha Allahu bazan koma kindaukan wayan shi ba, Ji nayi ta safa min kafada na tana fadin kiyi hakkuri Meenatu nasan cewa hakan nada zafi, To amma shi namiji ba,a yi masa haka sai yai saurin gano takon ki ya raina ki, Kiyi a hankali bada garaje ba har ya shigo hannun ki, da dubara zaki wana shi, Don Allah ki kiyayye Meenatu, ni mai kaunar kice,shi yasa kikaga ina kokarin saki a hanya, Bawai don bana son ki ba ni dake guda nake daukan mu don kin gwada min kauna kuma ai ko dan kawun ki zan maki abu dole, meenatu, Na kara cewa don Allah Anty kiyi hakkuri Insha Allah zan kiyayye,, ****** ********* ****** Washegari su mama da Anty Mariya,suna falon gidan yaya, Abubakar zaune, Sai ganin wasu irin kattan mata yare sukayi sun shigo gidan babu ko Sallama, sai daya daga cikin su ce ta e Sarama,rekum, Mama Ladi kan tsoro taji da farko ganin irin shigar su kowace da gashin doki akai, an kara mata, Sannu ku fa kawai suka ce, sai suka fara kokarin shiga duba dakunan gidan, Suna ta faman gwalanci a tsakanin, su Kofan dakin da aka nunawa su Anty Mariya da Mama Ladi cewa nawa ne a nan sukaga mutanen sun tsaya sai faman murda marikar kofan su keyi suna jin ta a rufe, Anty Mariya ce hankali tashe ta nifi dakin anty Sadiya tana sheda mata cewa ga wasu irin kattan arna sun shigo masu gida ba sallama suna kokarin bude daki,, Da sauri suka fito waje tare da Anty Sadiya a cikin mamaki suke kallon matan, Tambayan su Anty Sadiya ta keyi da lafiya dai ko,, Watace daga cikin suke cewa suna son abasu keys din wanan kofan ne don su shiga su gani, Saboda suna son su shiga su gyara wa Salawatu daki ne, A cikin muryan mamaki, Sadiya ke ce masu maigidan yasan da zuwan su, ne ? No sai yasan da cewa zamu zo mu dai munzo ne don mu gyara mata part din da muke so, Kuma munga cewa wanan yafi saboda yafi tsari da kyau a,duk cikin dakunan da ke gidan, Ayyee inji Sadiya tace to gashi ko kun makara don wanan din dakin watace, Wata daga cikin su tayi farin bilicin har jinin jikin ta zaka iya gani da jijiyoyin ta saboda kwandewan da tayi, Ita ce ke cewa gaskiya sai dai mai dakin ta kwashe kayan ta zuwa wani part don mu wanan mu ke so, yafi kusa da ko ina na gidan, Wani irin kallon banza Sadiya ta watsa mata tare da cewa Over to you,, Ta juya kawai a binta sai taji muryan matar na cewa,komai bakin ciki dai mun shigo gida babu yadda za,a yi damu dai, Daidai lokacin ne Baba Wadda da Hamza makwabcin mu suka shigo gidan, Anty mariya ce ke fada masu abinda ya kawo matan gidan da kuma wai abinda suke son yi, Ga yan abu kaza inji Baba Wadda Ya,kara cewa ko matsafa suke wallahi basu shiga dakin Meenatu, Mama Ladi wace tsoro da fargaba duk sun kama ta don ganin balai,n da yafi nata, Hamza ne yai masu wani irin tsawa yace subar kofan dakin nan tun kafin ya karaso gurin, Sai tambaya sukeyi wai shi waye da zai hana su aiwatar da aikin su, Daki dai shi suke son sawa yar uwar su kayan ta a ciki, dole kuma abude masu, Baba Wadda ya ce bari yan iska in gwada masu hauka,, Wani wayan kebel din wuta yasamu yai cikin su dashi yafara lafta masu, shima hamza ya mara mai baya, Ihu suka sa da gudu suka fara fita gidan suna ihu, da neman taimako,? Salawatu ce su ka kira a waya, suna sheda mata karya da gaskiya, Ita kuma takira yaya Abubakar tana kukan kissa wai Ànty Sadiya tasa yan daban shiyan su sunyi wa yan uwan ta wullakanci har da duka, A fusace rai bace ya iso gidan tun daga kofa yake kwadawa, Sadiya kira, Batai wani damuwa ba don ita halin ta sai ita don irin mutanen nan masu halin ko in kula, Don may zata sa a wullakanta mutane bayan tasan cewa zasu zo gyara daki ma yar uwar su, Za tai magana ya wani kara daka mata tsawa, tasa kai batare da tai mashi bayani ba ta juya abin ta zuwa dakin ta,, Waya ya buga masu kaman wanda yai hauka wai su,zo suci gaba da aikin su, Su za bi duk dakin da take so agidan wanda taga yai mata, Still dai dakin nan nawa suka kara nuwa cewa shi zasu bude, Baba Wadda ya kira su Baba, hankali tashe yake sheda masu halin da ake ciki, A cikin tashin hankali Baba Buhari yakira wayan shi a karo na farko yana mashi kashedin muddin ya bude dakina ban gida yasa wata bai yafe mai ba, Sai a lokacin ne jikin yaya Abubakar yai sanyi tare da dan dawo wa cikin hankalin shi, Duk ya najin kanshi cewa bazai iya sabawa Salawatu aduk abinda tace ba to ya kuma zama dole ya,bi umurnin iyayyen shi, Malam.tsoho wanda tun lokacin da autan shi ya bugo waya yana sheda mai yadda su kayi da Abubakar akan dakin Meenatu, Duk da rayuwan shi a bace yake bai yarda ya nuna hakan a gaban yaran shi ba, Sai dai can cikin zuciyan shi yadade yana mamakin wanan rashin mutuncin na Abubakar, An gyara wa Salawatu daki, wanda ke fuskantar na Anty Sadiya suka zaba saboda girman shi,, Allah ke nan,lokacin da za,a kawo ni cewa Anty Sadiya tayi bata yarda in zauna a wanan dakin da yanzu Salawatu ke hasashe ba, Yanzu kuma sai gashi zasu yi zaman makwabtaka a tare, Washe gari salawatu daga ita sai Lubuna da da kawar ta guda suka rako ta, Ta dan yafa wani dan guntun mayafi mai shara,shara, a kan,ta, wai ita amarya, Wanan shine mafarin labarin zaman Salawatu a gidan yaya Abubakar, ****** ********* ****** Washegari da Amarya ta tare, har zuwa wani lokaci, ba wanda ya leko wajen gidan, Ga yuwan ya addabi Mama Ladi da Anty Mariya, wanda tun daren jiya basu ci abinci ba, Saboda mamakin yadda dan ta ya koma kamar ba Abubakar din ta ba, Sai zuwa wani lokaci Salawatu ta sauko daga sashen maigidan, Daga inda Mama take zaune ta hango ta ko gaisuwan arziki basu samu ba daga gare ta, Zuwa can sai gasu tare da, Abubakar sun fito daga dakin shi, Wanan karon tasha kwalliya sai kyalli takeyi don ado, Gurin Mama suka nufa a tare sai kauda kai Mama ke kokarin yi, don bazata juri ganin wanan irin fitsarar da Salawatu keyi a gaban ta ba, Duk Mama sai taji ta tsawala ta wani dabur ce, don ganin wanan irin mace wai itace yau sarrakuwar ta Gata tanka irin matan iya muran da suke gani a hanya idan zasu anguwa, Yau wai irin sune a gidan dan ta Abubakar a matsayin sarakuwan gidan malam tsoho, mai almajirai, Kamar yadda ya saba idan zai gaida Mama yau ma hakan yayi inda yadan zauna daga bakin kujera, yana cewa, Mama,ya kuka kwana ? ya dare, ? Ita ko salawatu can ta koma daga bayan kujera tana cewa Mama antashi lafiya ? Daga Mama Ladi Baba Wadda har Anty mariya sai da su kaji wani irin nauyi da kunya,, Amma sai sukaga shi Abubakar ko a jikin shi bai wani nuna damuwan rashin da,an da ta nunawa Mama ba, Mama Ladi dai kanta yana kasa duk takaici da imani ya rufe ta a lokacin, Anty Mariya ce tai karfin halin tambayan yaya Abubakar da cewa kai Abubukar Mama fa yunwa takaji, Da mamaki yake tambayan Sadiya bata baku abin kariba, Anty Mariya tace, mu yau ko ganin ta bamuyi ba tunda gari ya waye, A take rayuwan shi ya baci, ya dan kalli gurin da Salawatu take tsaye daga bayan shi,ya ce, Ki hada masu abin karyawa please ? Ba,tace ba,zatayi ba sai dan dan murmushi da ta sake mai daga haka ya tashi ya nufi hanyar fita daga gidan, Baba Wadda yabi bayan shi suka fita tare a lokaci guda, Yana tsaye daga waje har yaya Abubakar yaja motan shi yabar gidan, Baba Wadda gidan su Hamza ya shiga don ya gani ko Hamza' yana gida a lokacin, Mama Bi,u ce tai mashi tayin, kunun gyada, da sugar, Sai dai Baba Hamza ya kasa sha yana tunanen su Mama Ladi da Anty Mariya, Mama Ladi tagane nufin shi don haka ta zuba mashi cikin wani babban jug nasu, Ta kuma zuba masu faten Irish, da sukayi mai yawa acikin kula tace ya kai masu, Sosai suka ci wanan abinci da aka aiko masu har suka koshi, Anty Mariya ta juye saura anjima su bawa Mama taci, Salawatu tun shigan ta daki tafada saman lafiyayen gadon ta tana tun yadda daren su da Abubakar ya wakana jiya, Sadiya wace ba kunya ya ishe,ta ba sai kawai ta fito wai tana neman abin karyawa, Sauran abincin da Anty mariya ta ajewa mama lafi shi ta lashe gaba daya ta kora da goran fanta, Baba Wadda shi ke ba Hamza labari don haka hamza ya fadawa wa mama bi,u Dazasu dafa abincin rana aka dafa dasu da kan ta ta kawo mata tana kuma bata hakkuri akan sarrakan zamani, Anty Safiya ce ta bugo waya daga gida ta noban Baba Wadda saboda ta nan kawai ake samun su, Bauan sun gaisa ne Anry Mariya take dan kenkyasa mata, halin da,suke cikki kadan, Hankalin Anty Safiya yai mugun tashi tace su dawo gida da mama ta karasa jinyar ta a gida, Ta kara tabbatawa da Anty mariya da,su tayar wa yaya Abubakar da hankali don ya turo su, gida, ****** ********* ****** Tun rashin kiran da yaya Abubakar bai min ya na dan damu har nazo na basar nafitar da abin a rai na kawai, Karatuna nake facing yanzu ban da wani abu dana sawa gaba kamar karatun, A gajiye nake tafe don tun tea da nasha kafin mufita zuwa school ban kara cin komai ba har zuwa yanzu, Gab da zan shigo nake jin muryan mummy uwargidan Uncle nake ji daga falo tana bawa wasu da ban sani ba labari kamar haka, Ai bari kedai aure wata, uku da dan kai, amma wai har miji ya kara wani aure, Dama fa ba neman ta yayi ba kawai dai kwadayi ne irin na iyyayen su, Suka daura mata aure dashi, Ance ma wai mahaifinta shine ya roki kakan wai ya daura da yar shi , Yanzu a yadda nake gani, bai ko kulata balle ma yasan da wata Meenatu, can,,,,, Ido biyu,mu kayi da ita daidai lokacin da take kaiwa nan ga zance, A hankali nace masu sannun ku da aiki mummy, su kuma bakin na gashe,su cikin ladabi na shige abina, Da kyat na kai dakin kwanan mu na fada saman gado na sai kawai naji na fashe da kuka, Nasan dama dole ne mutane su zageni wasu ma harda zargi zasu hada min, Daga gurin da nake kwance ni kadai a dakin mu don yau Anty Amarya bata gidan ta, tafi taron Anty Zainab din su da tazo daga Kano, Wayana ne ya fara ringing a lokacin kamar kada in duba amma sai na mika hannu na na dauka, Yaya Abubakar nagani rubuce a screen din wayan nawa Wani irin haushin shi da takaicin shine suka rufe ni, sam sai naji bana son jin muryan shi balle ma ingane shi,, Mutumin da akan shi ake tamun ka,zafi iri iri a cikin yan uwa, Saboda kawai biyayyan iyayye na hakkura da duk wani yanayin rayuwa da nake gani,, Hudubar Anty Amarya ne ya fado min a rai don haka na dauki kiran nashi, badon naso ba zuciya na fam da takaicin shi, Muryan nan nashi dakkakiya mai kama da ta jaruman maza, ya ce, Assalamu Alaikum Meenat, Na ansa cikin dassashen murya na da nai kuka har ya isheni, da cewa, Wa,alaikas,salam, Kafin yai magana ni,ce na fara cewa ina wuni yaya, ? Ya sallam, naji yace a lokaci guda sai,kuma cikin daga murya yake cewa baki da lafiyane Meena ? Da kyat na dan seta muryana, nace lafiya na kalau yaya yanzu na dawo daga school na gaji ne kawai, Sai a lokacin naji yai wani irin ajiyar zuciya yana cewa, OK, ok, sorry sannu ko ? To ya kuke nan,? Still cikin dakiyan zuciya nace mai da Alhamdullahi duk muna lafiya, Yau shene zakuyi hutu ne wai,? Akwai sauran time nace a takaice, Ok, kawai ya amsa da shi, A hankali nace ya jikin Mama cikin daurewa, ya amsa gami da lumshe idon shi da cewa Alhamdullahi ta samu lafiya sosai yanzu, Agaishe su na ce batare da na kara furta wani abu ba, Daga haka nai shiru abina, ban kara cewa komai ba, Wani irin sha,awar ce ta saukowa, yaya Abubakar don bai san tsawon lokacin da ya dauka, yana kewan na ba, Sai yanzu ya fara gane cewa ba karamin missing din yar uwar haihuwar shi kuma matan shi yayi, ba, Jin yayi shiru ya dan sani ajiyar zuciya daga gurin da nake, , Yaya Abubakar ji yayi tankar ya jawo ni daga cikin wayan ya rungumay Ina jin irin yadda ya sauke ajiyan zuciya wanda hakan ya tabbatar min da cewa, ya dan shiga wani yanayi, Don in takaita shirun nace ina gaida kowa sai anjima, nakashe wayan, Murmushi kawai yayi don yasan cewa iyakar hiirar mu ke nan dama ba wani mai tsawo bane, Daga gaisuwa ne sai kuma tambayan lafiyan, junan mu, Ina katse wayan sai yasake yar murmushi tare da sosa kan shi da key din motar shi, Yasan dai watara dole aje wanan kunyan nawa zanyi a koma dai,,,, Wanan wayan da mukayi da yaya yadan sani mantawa da zancen mummy da yan uwan ta akaina,. Sai dare Uncle ya dauko Anty Amarya da yaran ta suka dawo gida, Kafin ta iso nagyara ko ina na sashen nata sai kamshi ke tashi, Da sallama ta shigo sashen nata, tun daga kofa taje cewa wai lalai Meenatu wanan irin kamshi haka ? Daga dakin mu na yara nafito ina mata sannu da zuwa, tare da rungumay yar ta da ta yo cikina da murnan oyoyo, Ledan dake hannun anty tamiko min tana cewa ga sakon ki inji Hajiya Mama, Sai mun zauna zan maki bayani akan kowanin su, Na amsa da fadin to Anty, Uncle dina yabiyo bayan ta rugumay da dan karamin yaron ta, wanda ke ta barci a kafadar mahaifin shi, Sannu da zuwa nai ma Uncle wanda,ke kokarin mikawa matar shi, yaron , Uncle yana bada baya cak, naga Anty ta tsaya da yaron a hannun ta tana kallon na cikin son tambayana, Muryan ta naji tana cewa, Meenatu may ya samay ki har ki kai kuka, Nace kuka Anty ? Eh kuka gashi har idon ki sun yi jajajir, don kuka, Na bude baki zanyi magana amma sai na kasa cewa komai, Illa ma hawayen da ya dan fara silalowa saga fuska na, Hmm kawai , tace tare da juyawa tashige nata dakin kwanan, Nima dakin mu na juya nashige da Ledan vacco da anty ta miko min , Ban tsaya jiran komai ba nayi kokarin samun guri in kwanta, Sai ga Anty dauke da,wani ledan mai tambarin shagon saida kaya, Naman kaza ne gasassa da fresh milk mai sanyi a kwali, Ta shi ki ci abinci tace min don nasan baki ci komai ba, Ba musu na mike zaunen ida Anty ke kokarin bude muna ledan da kan ta, tare da miko min nawa kwalin milk din a gabana, Nakai a baki sau guda sau biyu sai na ji muryan anty da ke zaune tana ta cin abin ta hankali kwance, tace, Meenatu Fada min gaskiyan abinda yasaki kuka haka yau, A hankali nace Anty don Allah abar wanan zancen don fadin shi ba alheri bane zai haifa Tambayana takarayi ina fatan ba zancen auren Abubakar bane ke damun ki har yanzu ? Da sauri nadago kai ina kallon ta cikikarshen za kai, na, anty ai na fita wanan zancen ko, Madallah nagane ida zancen ki ya nufa ko baki fadamin ba, Don yau yan rashin mutuncin ga sun yini gidan mu,,, ZEEE MAKAWA YELWA 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 4⃣8⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA ALLAH- AL-ALI Yanzu yaya Abubakar baida matsalar kwana agidan shi don ya fito cikin wanan kangin na Sadiya da,yadade yana azabantuwa akan ta,, Dakin shi ya fara samun gyara kaman lokacin da Meenatu ke a gidan, Salawatu ta na girki ba kamar Sadiya ba sai dai matsalan shine ba dadi sam, Ba test bai dahu, salt, oil, pepper, ruwa, da sauran su, Amma dole haka yake zama tasa shi a gaba ta zauna sai taga ya ci, A bangaren su Mama, Ladi suma hakana suke ci don kar yunwa ya kar su, Sai dai yakan dan hada yanzu da sayowa Mama dan kayan marmari, a waje, Tsakanin Sadiya da Salawatu zamane na ba,ruwan wani da wani kowa harkan gaban shi ya keyi agidan, Ganin salawatu bai sa Sadiya ta taimakawa Mama Ladi ba sam sai ma nu kamar tana kyamarta da takeyi, Don bata yarda su shiga mata daki idan ma magana yakai su dakin zata taso tana cewa muje falo ko ? Gurin abinci yanzu basu da matsala tunda Anty Safiya ta bugo mai waya tana cewa abin kunya ne ace Mama tazo gidan shi ba abinci kamar yadda duk wanda ya je yake dawo, wa da zancen horo da yunwa agidan,, Ya dawo gida ya tara su yai masu cin mutunci sosai tare da ja masu kunne, Ita salawatu, tana basu abinci amma babu sakin fuska atare da ita sam, Anty mariya wace taso ta shishige mata, a lokacin amma ta kakabe ta hanyan daure fuskan ta gare ta ****** ********* ****** Zaune muke a gida yau weekend ne ban shiga school, Dom haka muke ta zuba, hiran mu ni da Anty da,su Amira yaran anty, Anty Amarya ke ce min ashe haka akayi da Abubakar lokacin tarewan amaryan sa kan dakin ki, Kirjina naji ya bada dam duk da ban kai gajin may akayi, ba, Anty Amarya tace sai shekaran jiya muna hira da yaya Saratu take fada,min ai, Anty halan mi an,kayi ? Cikin kaguwa don son jin abinda ya faru da dakin nawa, Dariya Anty Amarya tayi tana cewa, abin ma ni walle dariya yaka bani, Wai samun wuri don kawai jan magana wai su alla dole sai dakin ki zata zama, Dariyan yake nayi nace to ai sai a bata tai tazama, ko Washi nan ai basu isa ba wallahi don ko yasa ta dasai takwashe kayan ta da hannun ta , Ai ance sai da mahaifin shi Abubakar ya buga mai wayan cin mutunci a kai, Ido na lumshe yayi da ni irin bakin ciki da bacun rai ya tokare min makoshi na, Sai kuma naga Anty na kwasan dariya ita kadai tace ance auta su Baban ku ya na cen shi da sarakuwar ku, A hankali na ce baba Wadda ko ? Anty Amarya tace to shiya, Shi da wani aboki nai makwabcin ku suka dinga zabga masu bulala sai da suka watse gidan, Nima abin ya dan bani dariya don nadan yake saboda nasan halin Baba Wadda zai iya yin hakana, Tsaki naji Anty taja tana cewa kyale banza wai so tayi ta ciza tagani inda jini, Ke ga da tasamu shiga dakin da shike nan ke baki da mutunci sam ga idon ta da kowa nata, kuma, Kuma ance tsohuwa ta don duk ta girmay maku wai ? A sanyaye nace gaskiya ne Anty don dai gaskiya ba yarinta ba, Ke ma san ta ke nan ko? Na ce ai tazo wai ganina da kuma yi mashi murnan samun girma, Anty tace yar iskan tsohuwa kawai, duk tagama zubewan ta a titi ta dawo ta nade dan yaro,, Gaskiya sai kunyi da gaske don irin su ba karamin sheri da kisisina sunka iya kullawa ga namiji ba, Yazaman to sauran basu gane komai gare shi sai dai ita uwar iyayi, Amma ta makaro wallahi don dai babu yadda zatayi dake, ke kan, A sanyaye na ce Anty ni wallahi har tunane nakeyi yadda zan zauna tsakiyan wa yan nan matan don dai gaskiya babu warin yi na cikin su, Da sauri na Anty ta girgiza min kai tace ki kwantar da hankalinki babu abinda zai, faru, dake sai alheri insha Allah kuma ki ce na fada maki, Ke dai ki fake duk abinda kowa ka fada maki, in ma har wani abu ya shige maki duhu ga wayanan ki kirani dashi, A sanyaye na ce ro Anty na gode, Fita anty tayi tabarni falon zaune, sai tunane nake yi yadda zan bullowa al,amarin nawa, Wata zuciya tace min haba meenatu duk wanan nasihan da akai maki kirasa na dauka dazai fishe ki, Bansan lokacin da nayi wani irin murmushi ba ni kadai, ****** ********* ****** Shirin sallaman su mamay ya keyi fon ta samu sauki sai dai check up din da zata dinga zuwa kawai yanzu, Bawani shirin azo a gani yai masu ba saboda babu mai bashi shawaran kwarai a kai, Amma ya basu kudi masu dan yawa su rika tare da yi masu alkawarin zuwa idan an kwana biyu, Motar ma,aikatar su yasa a kai su mama har binin kebbi, Sun isa gida, lafiya inda mutane ke zuwa, yiwa mama ladi barka da arziki da fatan Allah ya tsare gaba, Labarin zaman gidan yaya Abubakar mama ta hana duk su Anty mariya da Baba Wadda fadin yadda zaman su ya kasan,ce a gidan, Abinda bata sani ba shine labari ya riga su isowa ko kamar a gaban su akayi, Har a zuciyar mama ladi bata kaunar taji zancen gidan dan ta yanzu,, Yanzu yaya sai faman zuwa garuruwa yin aiyu ka yake yi dan haka bai samun zama garin sosai,yanzu saboda yawan tafiye tafiyen da yake yi, Wanan daman da suka samu yasa Salawatu yin yadda taga dama ita da abokan ta, a gidan batare da wani tsangwama ba, Daga Lagos, yau yake tafe bai fadawa kowa cewa zai dawo a ranan ba, Sai ganin shi kawai su kayi girshi a ranan, a lokacin Salawatu da mutanen suna zaune a falo sai shewa su keyi hankalin su a kwance, Batare da yace masu komai ba ya kutsa kanshi shigowa gida, wa yanda yasamu a falo sun fi wan da ya baro a wajen gidan,, Indon shi ya sauka a kan abincin da sukaci a falon sunyi baja, baja da shi, ko ina tsakiyan falon,, Direct ya wuce zuwa dakin shi batare da ya tanka masu ba,, A dakin shi yana shiga ya dafe bangon dakin tare da, dafe goshin shi saboda tsananin bacin rai, Jin an shigo dakin ne a lokacin, yadan sashi bude idon shi da sukayi ja, Salawatu ce, tashigo tana sake mai wani shu,umin dariya, Tana kokarin, zuwa rugunmar shi, ne yadakatar da ita cikin wani irin yanayi,. Dakatawa tayi don ganin yadda yanayin shi ya nuna Bai ya ce mata komai ba ya fada bathroom din shi tare da cire kayan jikin shi ya watso ruwa don yaji sanyi, Ita ko Salawa komawa tayi ta Sallami bakin ta cikin gagawa tana sheda masu cewa su tafi don Allah kafin oga ya fito, Da sauri tasa a ka gyara ko ina na gidan tankar babu abinda ya faru a gurin, Sallah yaya Abubakar yafara gabatarwa bayan fitowan shi yadan jima wurin sallah zaune, Sai ga Salawata dawo wanan karon fuskan ta da damuwa sosai acikin sa, Sau guda ya daga kai ya kalle ta bai iya cewa komai ba, Wayan shi ce tai kuka a lokacin don haka ya mika hannu ya dauka, ALIYU ne abokin shi ke magana dashi a lokacin, Zance sukeyi kan cewa mijin sister shi ya samu accident din mota suna asibin sokoto dashi, Sosai ya jajan tawa, Aliyun irin halin tashin hankalin da suke ciki, Salawatu dake tsaye, ta samu gefen bakin gadon shi ta zauba tana jiran shi, Yana gama waya da Aliyu, ya shiga neman noba na, a lokacin, Ina tsaye, a bakin laundry din gidan uncle ina kokarin a je kayana da zan wanke, Ganin wanda ke kirana yasani saurin barin gurin zuwa dakin mu, don in karba mai , Saman gadon dakin na kwanta nai rub da ciki ina mai kokarin kar ba sallama, Da sallama na dauki wayan na,shi tare da mashi barka da wuni,, Cikin dan yanayin murya ba walwala, ya an,sa, min Cike da zargin yadda naji yanayin shi nai, mai ya aiki ya iyali ? Sai lokacin naji ya dan sauke yar murmushi da ga yanayin shi, Ba wani magana sai tambaya ya jefo min da cewa, Yaushe ne zaki gama exam din kine wai Meenatu,? Cikin sauri Salawatu da ke zaune idon ta na kallon center carpet din dakin ta dago kanta tana kallon shi cikin mamakin jin ya kira wata agaban ta, Cikin dan ida,inda na ba shi ansa da ce wa yaya dama ai, ko da mun gama zamuyi continues semester ne, Murmushi na ji yayi alamar rashin yadda da zance na, Amma Uncle Nafi,u ya sheda min cewa idan kun gama zaku dan yi hutu ai ko ? Manya idanuna nazare tankar yana kallo na tare da gyada kai,, Ban bari ya cimma zancen ba na ce, mai ya jikin Mama tasamu sauki dai ko? Hmm najiya yace look Meenat ki zauna da shiri don zan zo anytime from now, in dauke ki,don zaki zo hutu nan ne, Saboda ba,zan yarda ace ko hutu bazaki dawo dakin ki kiyi ba,, Cikin son in dauki excuse naji yace, kinji na fada maki, don nasan cewa kun rufe school tun last week, Don ban gida ne yasa ban damu da ki dawo ba a lokacin, Nace amma yaya kasan yanzu karatu ya ke min sosai don ban da enough time da zan zauna, Baijira na gama magana naba naji ya kashe wayan ta hanyar cewa ki gaida kowa agidan sai nazo kenan, Ya kashe wayan tare da komawa ya jingina kan shi ga kujeran dake, kusa dashi yana mai lumshe idon shi, Da kyat Salawatu ta iya saita muryan ta tana cewa, Sir ka dawo lafiya ? Cikin daurewa yace mata lafiya, Wani tambaya ta jefo mashi da cewa, Meenatu zata dawo nan ne kuma ? A hassale ya dago kai yace mata Salawatu will you live me alone please ? Ganin cewa rayuwan shi duk a bace ya ke saboda, yadda ya samay su taf a gidan nashi daya dawo dazun, Sai kawai ta zube kasa gwiwa bibiyu tana mai daga hannayen ta sama tankar mai neman gafara tana cewa, Sir please iam so sorry yan uwa nane su kazo tayani murnan aure daga garin mu, But daga yau bazan kara shigo da baki batare da ka sani ba, Sai a lokacin yadan ji sanyi azuciyar shi ganin irin yadda tai mai ladabi saboda ta yi laifi taba da hakkuri, Abinda Sadiya bata taba yi mai ba duk da tsoron, shi da take dan ji, A hankali ya furta give me a cup of tea please ? ****** ******** ****** Bayan mungama wayan dashi, wayan nawa na bi da kallo tankar shine a tsaye maimakon wayan, wayan , ya koma min abin mamamaki Numfasawa nayi gami,da gyara zama, wata sabuwa nace a raina, Muryan Anty, Amarya ne naji tana shigowa dakin daga kitchen, da take girki, Ganin irin yanayin da ta ganin a ciki, yasa ta min wani irin kallon tuhuma tana cewa lafiya dai ko ? A sanyaye, nace Anty, yaya Abubakar ne ya kirani, Ta ce tau, pa Ya kukayi shiru nayi tare da dukar da kai, na kasa a hankali nace wai cewa yayi in shirya anytime zai zo ya dauke ni, Yar dariya Anty ta sake tace ashe zaki bamu kewa, don tun da yace zai zo zaizo din ne, Wayan ta na,ga ta hau dan nawa tana cewa hello hajiya Don Allah a hadawa meenatu gunba da tsumin ta don ta kusa wucewa, hutu,, Tsam na mike don komawa gurin laundry don in wanke kayana, Har zuwa lokacin da, nagama wakin na shanya, Bayan mugama komai da dare, muna zaune ne anty ta,dubeni cikin, Son yin magana mai muhinmanci, don zuba min idanuwan ta tayi cikin nawa, tace, Meenatu Nace na,am anty, Sai kuma naji tai shiru kamar may tunanen wani abu can daban, Sai tace ina fatan duk abinda aka fada maki yana a cikin zuciyar ki, Wani irin abu naji azuciya na kamar shakku, anya kuwa zan iya, ? Muryan Anty na ji ta kara kiran sunana a karona biyu, tana ce min Kar ki boye min komai ki daukeni tankar yayan ki na ciki daya, Fada min yadda kika fahinci zaman ki da Abubakar a kwanan baya da kika tai, hutu, can gurin su, Kaina kasa na fara labarta mata dan zaman da mukayi da su, sai da ba dukka ba, Saurare na takeyi inda ta zuba min idon ta har na kai karshe, Ajiyan zuciya naji tayi tana cewa Alhamdullahi don fa zancen ki idan kinci gaba akwai kyakyawan fahinta da zai biyo baya nan gaba, A sake na tambaye ta da cewa yanzu may zanyi Anty ? Don kinga cewa ita wanan matar da take gidan yanzu ba irin Anty Sadiya bace, Tsaki Anty amarya taja tana cewa kyale tsohuwar banza ai kurciyar ki zaki nuna mata kin fita iya bariki, Muma matan hausawa mun iya duk wani barkado da suke yi wajen kwace miji Fuska a daure tace ai kawai shi Abubakar, aki sakewa jiki ki kauda duk wani kunya a idon ki, Don fa rashin samun irin hadin kan da har ya kai shi da hangen gurin Salawatu zai samay shi, Don fa tunda kikaga har ya kiraki akwai matsala duk yadda akayi, Don haka rashin samun hadin kai daga gurin ki, zai iya haifar da matsalan da zai sa ya koma gurn ta, Na nisa nace to Anty zanko iya ashe,? Murmushi tayi tace min cikin girgiza kai, ke dallah wuce can sai kace ba yar Birnin Kebbi , Murmushi nayi tare da cewa na gode Anty, Takarashe da cewa gobe zan shiga kasuwa in sayo maki sabbin nightgown masu kyau, Da kuma kayan sawa sabbai don ki canza kin san kudin ki suna hannun uncle dinki yasa a banki, ****** ********** ****** Tun wanan ranan na,fara shan abubuwan hadin da mama hajiya ta hada min Sai anty ta tabbatar da na shanye abinda takawo min a cup san, nan zatabar dakin, Kafin wani lokaci jikina sai sheki da daukan ido ya ke ni kaina nasan na canza sososai irin yadda nake jin bakon al,amari a tare dani, Aikin komai, anty amarya bata yarda na yi, shi a cikin kwanakin nan, Dinkuna masu kyau da daukan ido anty ta dinko min tare da night gown masu kyau da tsada, ZEEE MAKAWA YELWA 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 4⃣9⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA ALLAH -AL-KABEER Shafikune yau uwa masu kauna Hajiya RABI, Assibitin Murtala sokoto, da Hawa,u Abdullahi school of health and Technology Gwadabawa, sokoto,state, Nutrition department,, Kaman yadda Anty ta umurce ni da kada in fassa shirin da nake don anytime din da yace zan iyaganin shi,kamar yadda ya fada, Don haka ban fasa ba kullun sai ta tsure ni da yan dabarun ta na mata, tana a tsaye zan shaye komai tas inbata kofi, Barci nake yi yayin da ake ta kwada ruwan Sama a gari wuri ya koma wani irin cool weather, Anty naji tana tashina daga barci ina bude ido sai ta miko men wani plate, da ke dauke da naman yan tsuntsaye guda biyu a plate, din, Naman na tsurawa ido zuwa wani dan lokaci ina nazarin ko maye haka ? Ki wanke bakin ki kizo ki ci naman tantabarane don naga kina masu wani irin kallon, Fuska na ya mutse alaman ban so haka ba, don dole na mike zuwa bathroom wanke bakina, Anty na saman kujera ina daga kasa zaune ina ci ina ya mutse, fuska, don ba dadi, Na dago kai inda anty take tana gyara wani abu a cikin roba, Nace fuska bace naci anty, tsuki tayi gami da daka min tsawa tace, Dalla malama cewa akayi ki cinye dukka ki kuma shanye romon gaba daya, Ido nafitar wajw sai kuma na kwabe fuska kamar zanyi kuka nace, Wallahi anty ba dadi ko kadan, a cikin shi, ta galla min harara tace baki dadi ko ? To ko babu dafi dai wanan sai kin shanye shi tas yau, Haka akayi inda na shanye na tara kassuwan a wani plate, Anty ta zuba su cikin wani leda ta fita dasu waje wai zata rufe su ne a cewan ta, Tun da na gama cin wanan naman nasha ruwa sai nafara jin wanu irin kasala yana rufe min jiki a hankali, Kara kwantawa nayi don dama weather ranan Alhamdullahi, Anty ta shigo dakin tana cewa hajiya Mama ce ta bugo waya take tambayana cewa, nadafa maki tantabarun kuwa kin ci? Nace cikin wasa ni dai ki fadawa wanan tsohuwar ta barni haka dai please ? Yar murmushin jin dadin yadda na mai da mahaifiyar ta tankar kakana tayi,, Tace don kin samu bat sa kishiba har tana gyaraki aida tabar ki da wa yancan maguzawan kishiyoyin naki , Nace aiko in gudo in dawo dakin ta direct don wanan Salawan da kike gani anty nasan za a sha daga da ita, Cikin muryan na Anty tace gwada mata cewa ke ma fa yar Kebbi ce ba Sanya don kin san mu matan kasan hausa sai wace taso zama bora agidan mijin ta, Meenatu muda ka bude ido da hudubar zama da miji har kishishiya tun muna kanana, Zan kai kai saman pillow in gyara kwanci wayana yai kara, A zatona Babana ne yakira saboxa naga cewa, safiya ne rana batai wani yi ba a lokacin sosai, Wata nombace da ban san,ta ba, na dauka ina mai kwarara sallama, Muryan Yaya Abubakar ne naji yana amsa min cikin irin dakewan nan nashi na kullun, Yaya ina kwana nace cikin siriri yar murya na ahankali, Sai da naji sauke ajiyan zuciyar shi sanan ya amsa min da cewa lafiya kalau Meenatu, Sai yai shiru, nima a nawa ban garen dan shirun nayi masa, Sunana naji ya ambata cikin wani irin murya mai saukewa mutun kasala da cewa, Meenatu, ina hanyan sokoto yanzu haka zan zo in dauke ki zamu tagi Niger Reporblic, Ban san lokacin da na maimaita maganan ba da cewa Niger ? Murmushi naji yayi yace eh Niger, ko bakya zuwa ne yai maki nisa, Na saki a jiyan zuciya nace zan tafi mana yaya Yace don kawai mu biyo ta nan mu dauke ki nai wanan tafiyan ta mota, Na lumshe idona ina tunanen yadda zan tafi Niger, din, Murya Yaya Abubakar naji yana ceea ko Uncle bazai bari in tafi mashi da yar shi wani kasa ba, A hankali na sake wani murmushi mai fitar da sautin cool, nace ,a,a ai Uncle baida iko dani kamar kai, ko banza, Allah dai ya kawo ku lafiya ?' Nace cikin kara lumshe idona, saboda wani irin abu da naji a lokacin, Na sauke numfashi bayan mun kashe wayan tare da kurawa hanya shigowa dakin ido, Ina tunanen yadda zan fadawa anty zancen tafiyan nawa, Kayan wanki yaran ta da aka wanke ta shigo dashi dauke a hannun ta, dakin namu, Tambayana tayi cikin son jin may yace yai maganan ranan da zaizo kuwa? Sai da na sada kaina kasa san nan na ce a hankali cewa yayi wai yana hanya zamu tafi Niger ne, Itama Anty acikin mamaki ta maimaita da cewa Niger shin? Na kada mata kai alaman eh, Ba bata lokaci naga anty Amarya ta hau shirya min kaya da kanta, Sai zuwa karfe daya na rana yaya ya iso shi da driver shin , Sai lokacin da na tabbatar da cewa tafiya fa zamu yi ne hawaye yazo min tab ga ido na, A lokacin Yaya Abubakar suna tare da Uncle dina a folo, suna dan shan drinks, A falo inda suke zaune da Uncle na samay su inda nadan zagaya gefen Uncle din na durkusa a gaban shi idon yana fitar da hawaye, Na kasa magana sai dan sheshekan kukan da nakeyi, kawai, A hankali na iya bude baki ina cewa, Uncle zan tafi, Kamshin turaren dake jikina Yaya Abubakar yadan shaka abinda hakan ua saukar mai da yar kasala a take har takai ga ya dan lumshe idon shi a hankali, Ga kukan da nakeyi yana torching din zuciyar shi, Cikin dakewa ya mike tsaye, tare da yi wata irin murya yai magana da uncle cewa To zamu kama hanya sai dai in Allah ya dawo damu lafiya sai mu biyo ta dauki kayan ta, Cikin dan kuka na juya inda su Anty suke tsaye na ce, a sanyaye anty mun tafi, Wani iri yaji a zuciyar shi don jin abin yakeyi kamar ya jawoni zuwa jikin shi a lokacin ya rarashe ni,, Mutanen gidan mu na Uncle suna daga min hannu kamar kullun, suna min bye, bye motar mu ta daga,, Daidai muna fita kwanar layin mu naji hannun Yaya Abubakar a cikin jiki na, Idona na lumshe lokacin da naji hannun shi a cikin jikina, A tare muka sauke ajiyan zuciyan lokaci guda, Muryan shi naji yana cewa bakya son tafiyan ne Meenat,? A hankali nadago kai na dan kalleshi karo na farko tun zuwan shi, Yayi wani haske fatan jikin shi sai sheki yakeyi don kyau, Yar,Sajen faskan shi da ya bari ya dan kwanta mai lub a saman kyakyawan fuskan shi, A lokacin da yake min maganar ashe idon shi yana a lumshe, ya kara bayan shi a makarin kujera, Batare da na kara kallon shi ba na ce cikin tausa murya, Kawai dai, ina jin kewan rabuwa na dasu ne da zamuyi, A kara cewa amma kuma baki jin dadin kasancewa da yayan ki da zakiyi ko ? Hmmm kawai na iya cewa batare dai nai magana da baki ba, Shima din bai kara cewa komai ba sai ji nayi ya kara matse ni a jikin shi tankar wani zai kwace may ni, Driver sai kwarara gudu yaje a saman titin dake cikin sahara, abin shi, ****** ********** ****** Sam yanzu bata ganewa dodon ta don ya dai yi mata kaman da, da farko, Irin abinda dafarko yake kawo mata yanzu sam bai kawo wa gashi kuma sai yawan shan ruwa fiye da da, Gurin bokan ta, ta koma tana sheda mashi irin abin da take ciki da dodon ta yanzu, Bayan yan dube duben da yayi yadan yi gyaran murya, yace, Abinda yake samu ga alkawarin da kikai may yanzu ya daina samu shi, Don kin ga da farko a koda yaushe, yana samu abubuwa irin yadda ya kamata, Amma kuma yanzu sai yai kwana ki da dama bai samu abin da kikai masa alkawari ba dashi, Shiru tayi don ba abinda yazo mata arai sai mugun tsohon nan da ya hanata shakat Watau malam, tsoho, wanda take ganin cewa shine wanda yai mata karan tsaye ga al,amurorin ta, Dole ne fa tasan abin yi kafin ya kai ta ga makara don idan har tabari ya kai ta bango to asirin ta zai tonu ne , Malam boka yace banda wani abinda zan iya maki a halin yanzu sai dai kawai ki yi kokarin aiwatar mashi da bukatan shi, Sosai zuciyar hajja ya sosu don hankali tashe tabar gidan boka zuwa gida don gudun kar dodo ya bukaci wani abu bata a gida, Bayan ta dawo gidane ta yanke shawaran zuwa gidan Mama Ladi, don tun,da ta dawo bata samu zuwa, gaishe ta ba, Sai yau da take da bukatan zuwa don jin halin da gidan na dan ta ke ciki watau gidan yaya Abubakar Tafe take,cikin shigan zani da riga inda tai mayafi da irin zanin da ke ajikin ta daure, Malam tsoho wanda tun shigowan hajja uguwar nasu, jikin shi yabashi cewa akwai mugun abinda zai faru, Bala babban almajirin shine yakira yace ya samo mashi rushin wuta da sauri, Acan cikin gida hajja na shiga kafin ta kara,sa sashen mama ladi Sukayi kicibis da matan gidan zaune a karkashin iccen darbejiyan da ya sake masu innuwa a gidan, suna zaman hira a gurin Atake Rakiya matar Baba Hamza taji kanta yai wani sarawa alokaci guda, Take tafara ganin guri yana juya mata a hankali hankalin ta ya fara gushewa daga jikin ta, Wani irin ihu, ta sake a lokaci guda tare da mikewa tsaye, Duk wanda ke acikin gidan malam tsoho alokacin da kewaye sai da yaji wanan ihun na Rakiya,,, Gurin hajja Rakiya ta nufa tana cewa ku yi ta kanku wallahi ga diyan macizai nan da kan kare suna lasan jikin ku, Ai take mata suka sa ihun gida ya rude, wayyo Allah Innalillahi, A,uzubillahi, Hajja dole ta ja tai tsaye jikin ta sai rawa yakeyi, don kaduwa, Wuyan ta, Rakiya matar Baba ta, riko dukk idon Rakiya fito waje sai wani yare takeyi, wanda ba wanda ya taba, jin tana wanan yaren, a duniya, Da guda aka kira mazan da ke kofan gida don su kawo a,gaji,,, Mama Ladi tafito daga sashen ta tana ta masifa wai an wa kawar kazafi don ana bakin, da ita Ba wanda ya kulata sai kokarin ganin an banbari Rakiya daga jikin Hajja, Saidai jama,a duk sun kassa banbaranta daga hannun Rakiya, Daga bayan Mama Ladi akaji kuwan anty Mariya cikin wani irin ihun tashin hankali wanda duk ya kara ruda gidan, Sai ihu takeyi tana çewa wayyo Allah ga sunan suna shiga jikin ku suna lassa, Take guri ya kara rudewa da tashin hankali,saboda, yadda Anty mariya take ihun baida dadin saurare sam, Malam ne yau ya tako da kan shi har zuwa cikin gidan sashen sarakunan shi, Wani abu ya yarfawa tarun jama,an dake gurin gaba dayan su,, Wani tsawa malam ya dakawa mariya da Rakiya, Bala daga bayan shi ya zuba wani hayaki a rushin wuta gaba daya wanda ke gurin ya fara atishawa,, Sai a lokacin Rakiya ta dan sassauta rikon da taiwa Hajja, Malam ya tako har zuwa garesu bakin shi dauke da addu,oin tsari, Cikin tsawa fuska a daure yace Rakiya ku sake mata wuya nace Ba mussau aka sake Hajja wacce idon ta duk yafito, waje saboda wuya,, Tana batun gudu malam tsoho ya daka, mata tsawa yace dakata kiji Cikin daure wan fuska malam ya kalleta abinda yasa hajjin cikin Hajja kadawa, Don sai tana ganin cewa malam zai tona mata asiri ne sosai, Ciki kadu malam yq ce ke, saurara ki ji may zan fada maki, Kinyi babban kuskure da har kika shigo gidana da nufin sheri, Kai Hajja ta kada alamar a,a Malam tsoho yace bari kiji ni Abubakar Sambo Manya, Mugu ko muguwa bazai taba shigowa gida na har gurin iyalai na ya wanye lafiya ba, Ko ina a raye ko a mace mugu bazai taba samun nasara a gida nan, ba, Kai ko a makwabtana balle har cikin gida, na ke ki sani cewa, ba yau ba nasan cewa ke muguwa ce ta sosai, amma da baki tabani ba sai ban taba ki ba,, Yakara kallon ta rai bace yace, daga yau kada ki sake ki kara shigo min gida cikin iyalina, Fice ki bamu guri muguwa kinji kunya kirasa inda zakiyi sheri wai sai wanan gidan, Simi, simi Hajja tabar gidan batare da ta waiga ba saboda tsoron malam din, Kafin wani lokaci har labari ya karade unguwa da gari baki daya cewa hajja mayya ce wai, Mamaladi duk jikin ta yai sanyi saboda abinda ya faru da aminiyar ta, Sosai yau tai nadaman zama da Hajja duk da ziciyar ta, na ce mata kazafi akai wa Hajja, Abu guda ke sa ta gaskan ta zancen saboda tunda ta haifi Mariya bata taba sanin cewa tana da iska ajikin ta ba ,sai yau, Wanan dalilin yasa Mama ladi ta dan yar da da sherin Hajja, Baba Buhari ya,shigo gida yana ta masifa da Mama cewa duk gurin kwashe, kwashen ta ta hadu da Hajja da ta zama masu matsala,, Gashi har kin yi sanadin hada zuri,a da ita yanzun haka kike son diyar ta ta haifa muna jikoki a gidan nan, ? ****** ********* ****** Sai dare muka shiga kasan Niger din,wani babban, hotel din da a kasan aka kama mu na, Direct, can muka nufa saboda duk sauran abokan tafiyan nashi suna a hotel din, Ko ina haske ne ya haska farfajiyar hotel din gwanin ban sha,awa, Tafe muke muna takawa guda guda, saboda steps din da akayi gurin shiga cikin hotel din, Duk wanda muka wuce sai yadan kara waiga mu saboda yadda mukayi kyau gashi kuma abu ga jini kamar mu guda da yaya Abubakar din, Muna shiga dakin wayan yaya Abubakar a na kiran shi a lokacin, Don haka yadan tsaya daga shigowa dakin, abinda na fahinta shine daya daga cikin matan shine yake waya da ita,a lokacin, Don haka na kara,sa shigewa cikin dakin, inda a hankali na ciren gyalen abaya na da na yafawa kaina, Saman gadon dakin na aje gyalen, a hankali nake kwabe abayan da na a,za saman kayana, Ya Abubakar wanda ke waya ina ganin how happy he's, Is ,, a lokacin, Tufin dana saka daga ciki wanda yadan matsen min jiki yai min kya surar jikina suka fito filli, Daga gurin da Yaya ya,ke tsaye ya lumshe idon shi don ganin irin yadda na koma a idon shi Mikewa nayi na jawo yar jakar da nazo da ita na fidda zanin daurin da nazo dashi da hijab, Yaya yaci gaba da kallona yana mai mamakin yadda a lokaci guda na juya na caza zuwa wata classic lady, Nai mashi wani irin kyau ga fuska,ko ina nawa ya ciciko a murje na yi wani fresh fatana sai sheki yakeyi, Lumshe idon shi ya karayi daidai lokacin da na fada bathroom din dakin, Wanka na yi don inji dadin jikina tare da dauro alwala don in gabatar da sallolin dake tare dani, A kwance na samu Yaya saman gadon dakin yadan kishingida kafan shiguda na tokare, fuskan shi na kallon kofan bathroom, Daurin zanin gaba nayi hannuna yana dauke dakayan da na cire a jikina, Yaya ga ruwan zafi can na hada maka, a bathroom, Bai amsa min ba sai wani irin kallo da yake min cikin mamaki, yana wani lumshe idon shi a hankali, Don gani yayi na yi mai wani irin girma a idon shi harda kiba, Duk wani abinda yake bukata ga irin macen da ya dade yana son ya mallaka a gidan sa ya baiyyana a jikina, Ganin da nayi cewa bazai bani ansa ba, kawai sai nafara war,ware hijab dina don in ta da Sallah, Alokacin ne naji muryan Yaya Abubakar yana cewa may yasa baki jirani mun shiga tare ba,? Murmushi mai sauti kawai nai masa batare da nai magana ba na tayar da Sallana kawai, Har zuwa lokacin da na kusa sallamay wa na,ga ya mike zuwa wanka, Bayan ya gama muna Odan abincin da zamuci daren da muka iso,,, Bayan na idar da sallah ne na mike tare da dan, gyara muna kayan mu, inda na zuba su cikin, Wardrobe din da nagani a dakin na nufa na sa kayan mu a ciki, Sai na fitarwa yaya Abubakar, wasu simply kaya don ya saka ajikin shi idan ya fito, Rigace mai yar guntun hannu da wando tree quarter, na samu acikin kayan na shi Suna fitar mai don ya saka idan ya fito daga wanka,na kuma feshe mashi su da turare, Dago kan da zanyi ashe Yaya ya fito, yana zaune a bakin gado daure da towel, sai wani dan karami, da yake ta gugan sumar kan shi da shi, Idon shi na akaina duk lokacin,, Kayan da na fitar mai su ya saka ajikin shi bai wani bata lokaci ba ya ta da sallah, Nagama gyara jikina tsaba yadda ya kama ta batare da na bari ya gane may nakeyi ba, ba, Daga gurin da yake zaune yana addu,a yadan waigo yana ce min, ki saka hijjab dinki don ga wani nan zai shigo ya kawo muna abinci, Bamusu da sauri na saka hijab dina akaina, na koma can bayan gefen gado nadan zauna, Wani buzu ne ya shigo bakin shi dauke da sallama, A binci ya kawo muna wanda ke dauke da abinsha mai sanyi, Abincin ba laifi don tankarka kalan namu na Nigeria, ZEEE MAKAWA YELWA,,,, [8/11, 05:43] Anty Lantana: 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 5⃣0⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA ALLAH- AL-HAFEEZ,,, Jumma,at Mubarak,,, Shafin yau na kine ke ka dai kuma bada kowa ba SADIYA SIDI MARUBCIYAR, SIDIYA, Nagode da irin kaunar da kike gwada min,,,,, Bayan mun karasa, cin abinci ni da kaina na gyara gurin na kawar da kayan abincin a can gefe, Hand bag dina na bude na ciro daya daga cikin Sweet's din da Anty ta sayo min masu kamshi, nasaka ga baki na, Wayan Yaya Abubakar yai kar da alamar daga cikin abokan tafiyan shine suke waya, Nikan sai da na kara kakabe gadon sanan nazauna ina gabatar da addu,oina kamar yadda na saba yi, A hankali na kai kafada na saman katifa saboda gajiya, na dan lumshe idona tankar mai barci, Tunanen matan Yaya Abubakar ne yazo min a rai yadda akayi baizo da dayan su ba mussanman ma amaryan sa, Nai zurfi ga tunane ban san cewa Yaya ya gama wayan shiba, Yana zaune a gefena ya kura min kyawawan idanun shi, Duk duniya ya fahinci ba macen da zai gani yaji sha,awan ta ya motsa mashi, kamar wanan yarinyar, Sai yanzu ya gane cewa komai na Meenatu daban yake da na sauran matan shi, kai dan das da shi gwanin sha,awa, Muryan shi kawai naji gab da kune na yana ce min, Meenat, nayi rashinki da yawa atare da ni, Firgigit na bude idona adan tsorace, Ashe gab yake dani kwance, idon shi sun canza kala zuwa wata irin muguwar sha,awa, A hankali na dan motsa dan in gyara kwanciya na alokacin, A hankali, naji hannun shi kuma a jikina yana wasu maganganu da zan iya cewa bai san may yake cewa ba ma, Wani irin mahaukacin soyayya ya gwada min ranan, Don duk yadda nake tsan manin cewa, yai amarya bazan samu wani doki ba sai gashi ya ma fi kullun, nuna min, duki, Don irin yadda Yaya ya gwada min ban san da cewa ana iya yiwa mace shi ba, balle ma shi da nake ganin bai dauki mace a wani matsayi ba, Sai kusan asuba nasamu Yaya ya sarara min nai barci, Daga ni har shi sai da muka makara ga sallah asuba ranan, Sai dai shi ya rigani tashi don haka sai da ya tabbatar da cewa na tashi sanan ya kyale ni, Sai da na idar da sallah na mike zuwa gaban mirror dake dakin ina gyara jikina, Zuciya ta fam da tunanen iri, irin, yadda Yaya ya canza min sallon soyayya, Shin kodai harda shawaran da Anty Amarya taba ni da cewa ni ma in gwada mai nawa, sallon, Murmushi nayi tare da dan rintse ido na ahankali ina anyana cewa mutum mai mata biyu, zaiyi wanan irin abu haka, Muryan Yaya Abubakar ne naji daidai satin kunnuwa na yana cewa my queen, Ya gajiyan hanya da na Yayan ki ? Murmushi kawai na sake mai tare da cewa sai hamdala, duk ka biyun, A can cikin kunni na ya rada min a hankali, Anty ce ta kara gyara,min ke ko Meenat ? Dif na dakatar da murza turaren da na keyi a jikina tare da dan sake murmushi, kadan, Mikewa yayi tsaye daga dan rankwafo min dayayi a kafada na, Jin ya mike a bayana yasani sauke dan ajiyan zuciya tare da dan lumshe ido na, Azuciya na nace No Wander, nasha wuya jiya hannun Yaya, Ashe yaji abin da yaji ne ajikin nawa, Idona na lumshe a hankali ina cewa a raina watau wanan gyaran da su, anty ke tamin da gaske yana da amfani ke nan, Mikewa nayi na shirya tsab cikin wasu, tsaddadun material dinkin riga, da skirt, a kai masu ya dan matse ni das don mazauna na sun fito tsab daga cikin shi, Dan kwalin su na daura a kaina sai dan kitson kaina da yadan fito da ribon din kai na, waje kadan daga baya, Wasu plat shoe's Anty ta sayo min don in hada su da kayan, Dan karamin gyale na, yafa a kaina , tare da kara shafa kamshi a jikina Saboda naji har malaman addini na cewa kamshi yana kara kauna tsakanin mata da mijin ta sai dai ban shafawa, a gurin da nasan cewa zai min illa kama saman nono, karkanshin nono da saman gashin kaina, saboda gudun cancer, Zaune Yaya Abubakar yake a bakin gado ya gama waya da masu kula da abincin mu, A hankali nake takowa har zuwa inda yake zaune ya tsura min ido, har na karaso gare shi, Gefen shi dan tsuguna har kara tare da dan dafa gadon da yake zaune akai, nace, Ina kwana Yaya ? Murshi yayi tare da dan kamo hannu na namike tsaye zuwa jikin shi ya zaunar dani a saman cinyar shi, A hankali yace Meenat ki karya ki kwanta ki huta kinji nasan cewa daren jiya ban kyauta maki ba don kina tare da gajiya kuma ban sarara maki ba,, Murmushi nadan sake ina mai dan dukar da kaina nace, Yaya nifa matar kace dole ne inyi hidimar ka duk sanda ka bukaci hakan daga gare ni, Murmushi yayi tare da dan rausaya kan shi azuciyar sa yace lalai meenat ta,sake ga yadda ya san ta, A hankali ya kai min kiss a goshina yana mai cewa Meenat ina mai alfahari dake, Meenatu, Nasan cewa iyayyen mu sun, muna hadin mafi, alheri a rayuwar mu, Fatana mu zauna lafiya, a tare dan, su kara alfahari da mu arayuwan su, A, hankali na ansa da Ameen ya Allah, Ranan kafin su fara fita abinda yakawo su haka na zama mai shagwaba, da wani irn langabewa, Take yaya duk ya wani bi ya susuce ya koma tankar karamin yaro,,,, ****** ********* ****** Rayuwa ke nan a yayin da muke kasar Niger Republic da Yaya Abubakar muna jin dadin rayuwan mu, Sai dai kuma iyayyen mu suna can a cikin halin, haula,i Don abin duniya ya kai ko ina Saboda rashin wadda ta da talkawan kasa ke a ciki, Don a bangaren mahaifina yar akwalar motar da mahaifina ke neman kudi dashi ya ja ya tsaya saboda tsufa, Sai malam tsoho ya taimakawa iyayyena da dan abin sayen abinci, Wani lokaci kuma sai Yaya Ibrahim ya dan je ya samu yunwar haya ta yar vespa, ya dan yo cefane, Shikuma Baba yakan tafi ya samo aikin karfi ya samu kudi, A cikin haka kuma yake tallafawa Baba Buhari don sai yake ganin ya fishi dan hanyar samu,wadata, Sam.iyayyen saboda irin tarbiyan da suka samu daga mahaifin su malam tsoho basu taba damuwa da cewa Dan su yana acikin waddata yaki ya taimaka masu, Sam basu sa rai ga dukiyan dan su ba balke ni mace wace auren shi kawai nake yi, Mutane ne kawai yan gani da dauka kan,ce Mama Ladi ta hana dan ta ya taimakawa mahaifin shi dan uwan shi, Wasu kuma sai suce daga dai Yaya Abubakar din ne baida halin kyauta don rayuwan turawa gare shi, Ance gidan shi ma wai idan ba notice ka tafi baza, a baka abinci ba, Kuma ba,a bari ma ka shiga cikin gidan sai dai wai mutum ya koma, Wasu kuma su ce wai baidai da halin yin alheri ne , ko kuma su ce bai samu matan kwarai wace zata dinga bashi hawara ba, shi yasa bai damu da gida da dangin shi ba, sam, ****** ********** ****** Izuwa yanzun mun kusa kai sati biyu a Niger, don aiki sosai su Yaya ke yi acan din aiki na tsakanin kasa da kasa, Yau ma kamar kullun ya,dawo da wuri daga gurin aikin saboda yana son mudan shiga garin muyi tsaraba kamar yadda na ce mai, Don ni yanzu na fara fahintar shi Yaya Abubakar mutum ne mai I don't care attitudes, ko a kansa balle wanin shi, Don haka nakan yawan jin yana waya da amaryan shi wace ina zaton bata san cewa tare muke da yaya ba kasan Niger din Takan yawan ce masa ya sayo masu tsaraban Niger, Ganin bai damu ba yasani cewa, idan zamu wuce zan shiga garin mu sayi tsaraba, Shaddodi masu kyau da tsada muka saye na mata da nashi sai kuma dinkankun kaya wanda suke har kasa sun sha design masu kyau wasu kuma zani da rigane hade, Wasi shago naga kayan suna da sauki don haka dan tsaya ina son inji saukin price din su, Daidai bayana Yaya Abubakar yadan dawo yana cewa har yanzu shadda basu isheni bane, Kai na langabe ina cewa wanan dinkin yaimin kyau a fuska ina son a sai wa malam tsoho ne yasamu na zuwa jumma,a, Murmushi Yaya yai min tare da cewa ai sai ki zaba mai ko? Kai na kara langabewa nace to Yaya idan da hali ai da ka sayawa su Baba don da wuya asamu irinsu acan da saukin kudi haka, Ba musu Yaya, yace idan zan iya daukan kaya ai Bissimillah ko ? Kaloli masu kyau na zabawa duk iyayyen mu maza gar Baba wadda, Azato Yaya zaice min kayan sunyi mashi kudi da yawa sai kawai naga ya biyya batare da wani gardama ba, Mamaki ne fal a zuciyana ina tunanen nafara sanin wasu daga cikin bahagon halaiyar shi da mutane basu gane, ba, Don tun ina karama nakan ji malam tsoho yana cewa Abubakar ai bahagon mutum ne, mai murdaden hali ,,,, A kasuwan na ga nonon rakumi na sayo su da yawa na kuma sayo chikwi da dabino da sauran kalar abinda bamu dashi a kasar mu, Ranan a gajiye muka dawo daga kasuwan sai korafi yayake min wai duk nice nasa shi yin wahala, Murmushi kawai nayi nace yaya aikin lada ne fa mukatsaya yi sai yakan ce min sai kuma akace a,wahala ko ? Ni kadai ce adakin don Yaya Abubakar yana gurin da suke zaman karshe, Yau sun,fi kullun dadewa don haka har zuwa lokacin barci don haka na tashi, nashirya cikin wasu jajjayen kayan barci iyakar tsayin su gwiwana, Na daure kaina, da wani ribon baki, sai, na koma bakin mirror na fara shafa turare ta ko ina ajikina,, A gajiye Yaya Abubakar ya shigo dakin yana rataye da couth din shi ga kafadan shi, Kokarin cire takalman shi yakeyi a lokacin nakaraso gurin shi cikin wani irin tako, rigar jikina yana shaking, Hannayen shi ya ware na shige ya mayar ya rufe hannayen dani a ciki, Ajiyan zuciyan zuciya muka sauke kusan atare, tankar mundade bamu ga junan mu ba, Bayan yai wanka yai sallah shafa,i da wutir, sai nagabatar mai da abinci Zaune nake a gaban shi na tsurawa abincin ido na kasa cin komai, sai faman tunane nakeyi Hannu shi na hagu yai amfani dashi gurin kada min hannu, Abinda yadawo dani daga duniyan tunanen da na shiga ke nan, May kike tunane haka bayan ga yayan ki a gaban ki kuma ? Murmushi nayi nace a hankalo ba komai yaya ina dai tunanen cewa gamu anan muna cin abinci mai kyau da lafiya amma , Har mu rage afita dashi batare da mun iya cinyewa ba, Amma gida suna can yanzu nasan a wanan irin lokacin na damana da abu kan yiwa mutane tsaye suna nema, Murmushi kawai Yaya Abubakar yai min tare da kokarin tsiyaya ruwa a cup ya sha Da sauri na karbi goran ruwan ina tsiyaya masa a cikin cup na mika mai, Sai da ya kora ruwan sanan ya dan kalle ni yace, Kina nufin cewa yanzu gida a matse suke cikin irin wanan lokacin ? Cikin yar murya irin ta mai shagwaba nace Yaya kasan fa ba wai suna wani aiki bane, Sai fa abinda Allah ya basu zasuyi amfani dashi, Ajiyan zuviya naji yayi a lokacin tare da sauke numfashi a hankali, Har ya gama cin abinci bai kara cewa komai ba na mika mashi tissue ya goge hannu da bakin shi, A irin yanayin da naga Yaya Abubakar tun zancen mu na abinci sai na dan shiga damuwa batare da na bari yagane ba, Don inaga baiji dadin zancen da nai masa ba a take nace wa kai na sannu dai Meena uwar rigima, Daga gani saki sai in kama talala, Daga gurin da nake a kwance ina kallon Yaya Abubakar tsaye a gaban mirror ya na shafa roll on a hammatar shi tare da dan, jefa mintin a bakin shi dan na zube muna saman mirror ne, idan zamu kwanta sai kowan mu ya dauki yar kallan da yake son tsotso, yasa abaki don sanya dan kamshi baki, Ina jin lokacin da ya hawo gadon tare sa rungumoni daga baya inda ya fara sunsunar wuyana har zuwa sumar kaina, Sai naji ya kira sunana acikin wani irin murya mai rauni, A hankali na amsa mashi da na,am Yaya,saboda na fuskanci magana ce ta muhinmin zai fada min, Tambaya naji ya jefo min da cewa shekaranki nawa yanzu ? Gaba yaba da dam don nasan dama na taba yan mazan yau ,, A hankali nace ina cikin na sha tara Yaya Hmmm naji ya ce tare da matseni yaci gaba da addu,oin kwanci, Barci ya fara dauka don nasan yau ba kan,ta don ran yan maza da alamar a jagule yake, Muryan shi naji yana cewa Meenatu banda abinda zance sai dai in kara godewa Allah ubangiji subbahanahu,wata,ala da ya bani ke amatsayin abokiyar rayuwa,, Meenat wanan zancen da kikai min a gamay da gidan mu ya kamata ace hankali na yakai can da dewa, Amma sai kawai shedan yasa na shagaltu da zance saboda aiyukan da sukai min yawa mutane kuma suna shakkan fada min gaskiya saboda su na ganin cewa wai ina dashi nafi karfin su yanzu, Wani irin ajiyan zuciya na sauke tare da dan kokarin juyowa na dan fuskance shi, Ai tuni idona ya ciko da kwalla, hankalin Yaya, Abubakar yadan kara tashi jindayayi ina hawaye, Janyoni yayi zuwa, jikin shi ya kara matse gam yana cewa, Kada kiyi hawaye Meenat, nasan cewa kece kwanciyar hankalina iyanzu, Saboda nadade ina neman mutumin da zai dunga sani a hanyoyin alheri arayuwana, Nasa gefen hannuna na share hàwaye da ke zubo min a hankali , Nace Yaya nadade ina shawaran yadda zan sanar da kai irin bukatar da mahaifan mu ke çiki a gida, Musanman ma Baba Buhari wanda mutane ke maka kallon baka kula dashi don tun ina karama nake ji a na fadar haka, Subbahanallah naji yace haka mutane ke kallo na Meenat nagyada kaina nace kwarai ma yaya don gashi ko dan abin hawa Kakasa saiya mashi don komai nisan guri akassa zakaga Baba yanatafiya zuwa, Innalillahi naji yaya yana ta maimaitawa don da alamar maganar ta daki zuciyar shi sosai har cikin rashi, Abin mamaki sai gani kawai nayi mutum kamar Yaya Abubakar yana hawaye, Yace Meenat, wallahi ban fara hawa abin hawa ba sai da na sayawa Baba mashin amma mama tace yace baison abin hawa indai bashi kudin shi, Kinji dalilin da yasa ban sha,awan saya masu abu sai in bashi kudin Innalillahi nace a raina don nasan sherin Mama Ladi haka, Gashikuma mahaifiyar shi ce ba dama in fada ma gaskiya akai, Don haka nace a fili yanzu ai kamata yayi kasai mashi kabashi hannu da hannu kaji mai zaice, Sai da yai ajiyan zuciya da karfi yace haka za,ayi meenat don mutane su sheda cewa shine bai so Na ansa da cewa kwarai kuwa yaya, hakan zaifi sauki sosai, Ban san lokacin danace nagode kwarai yaya Allah ya saka da alheri, Meeanat ni ya kamata in,gode maki ai saboda kin bani shawaran da kowa ya kasa bani arayuwa na,, Murmushi nayi tare da lumshe idona saboda jin dadin daya Banyi aune ba sai jinayi Yaya na kokarin nemo bakina ban bashi matsalaba hakan , Don haka muka manne guri daya inda muka tsinci kan,mu awani yanayi, Nagane Yaya Abubakar kan shi yadau zafi don haka bazan iya cewa ga irin yadda ya sarrafa ni a ranan ba, Washe gari mun shirya tsab don shirin tafiya komawa gida Nigeria, Yadda aka lodda kaya ga buth din motan yaya saida ko ina ya shake dam da kayan da na sayo muna tsaraba a Niger, Ina daga gefen Yaya Abubakar ina mai lfahari da mijina wanda duk inda mazaje suka kai zai iya shiga ya ratsa asan cewa ya shiga, Yana saye acikin wani yadi fari mai laushi da santsi dinkin rigar iya gwiwa,hannun shima dan gajeren hannu ne ya kafa wata farar hula mai gashigashi, sai kamshin turare kawai ke tashi a gurin,, Inda nake tsaye Yaya ya kalla ina saye cikin shigan dogon riga baki jallabiya na yafa dan kwallin shi nai rolling din kaina, duwatsun riga na walkiyan blue da fari, Yaya Abubakar ya ce yau na sheda cewa nai tafiya da mace wanan irin tsaraba haka ? Wayan shi ce tai kara a lokacin Aliyu ne anokin shi bayan sun gaisa ne yake sheda mai cewa, mijin Sister din shi da ake jinya a kano ya rasu, Salatin da naji Yaya yayi irin ta mutuwa yasa na maida hankalina gare shi don son jin may ke faruwa, Naji yaya yana cewa yaushe ke nan abin ya faru sai Aliyu ke bashi ansa dacewa, jiya ne a cikin dare, Yanzu haka ankawo gawan shi sokoto, inda za,aimai jana izza, Allahu Akbar naji, yaya fada tare da cewa Allah yai mai rahama, Nima daga gefe na ansa da fadin Ameen Allah yasa ya huta,, Tun lokacin sai naga jikin yaya Abubakar yai sanyi yana fadar Allahu Akbar, duniya bata da tabbas, Haka muka kamo hanyan Sahara desert, babu komai sai yashi da yan itatuwan sabara jefi, jefi, Bamuyi wani nisa da tafiya ba sai na fara jin kamar ban jin dadin jikina , Don haka na dunkule gefen jikin yaya saboda yadda nake ji, a haka barci ya dauke ni, Ganin da Yaya Abubakar yayi barci nake yi yasa shi dan sake murmushi don yasan cewa daren jiya nayi kokari sosai, Don haka yakara gyara min kwanci a jikin shi, don inji dadin yin barci da kyau, Wani gari muka tsaya don Yaya nason ya sai Kilishi da wani abunan da suke sayarwa, Sai a lokacin na,dan farka daga barcin a hankali sai naga aiduk a jikin Yaya na keyin shi,, Cikin yar murmushi yadan dagoni yana cewa Sarkin barci kin farka ko don ba AC, Daga wanan garin bamu kara tsayawa ba sai cikin garin sokoto lokaci yamma ya fara sosai Don haka , muka fara zuwa Yaya yai bucking, din daki shida driver shi, Duk ban jin dadi jikin wani iri nake ji sai daurewa na keyi kawai don ban son, Yaya ya gane hakan, Yaya yadan taboni jin nayi shiru yana cewa yarinya a garin Uncle din ta da Anty, amma bazata kwana gurin su ba, Da sauri yadago kai yana cewa Meenat lafiya kike kuwa, Cikin dakewa tare da langabe kaina nace ina ganin wahalan tafiya ne, Girgiza kansa yayi tare da cewa, dole kiga likita, don ya dubaki, A hankali na dan kara zuke jikina na, nade,sosai guri guda, nace, Gajiyane kawai don ban tafiya mai tsawo haka, shiyasa kawai, badon ya yarda yasa mufita zuwa dakin da ya kama muna, Kamar kada mu shiga dakin sai wani sanyi ya kara taso min a lokaci guda dole na dunkule guri guda, cikin bargo, Aliyu ya nema yazo nan masaukin namu shine yai kokarin samo wanda zai dubani, Likitan kamar abokin sune inda yai dan aune aunen shi ya shedawa yaya cewa gajiyane ya haifar min wanan zazzabin haka, Inajin lokacin da yaya yakira Uncle yana sheda mai cewa muna acimin garin sokoto saidai banda lafiya shiyasa banzo gida ba, Anty taso mu gaisa amma ina barci saboda maganin da nasha,,,, ZEEE MAKAWA YELWA [8/12, 05:33] Anty Lantana: 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 5⃣1⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA ALLAH - AL- MUQEET,,, Allah da ikon shi, washegari sai na samu sauki kamar bani bace, jiya ba lafiya, Ina zaune inda nai sallah Asubahi, Yaya Abubakar ya shigo hannun shi rike da tasbaha yana ja a hankali, Kafin in masa ina kwana shi yafara yi min da cewa Meeanat ya kika kwana ya kika kara ji ? Na,ansa da fadar Alhamdullahi Yaya naji sauki, ai Ya ce, ashe kaunar tawa bata,son wahala daga yanzu idan zamuyi tafiya sai dai mu shiga jirgi ke nan ko,? Murmushi nayi ina mikewa tsaye tare d nade Sallaya nace, ciwo daine yazo Yaya aikumaya bari, Gado na koma nadan kwanta na dunkule guri guda kamar yadda yaro ke kwanciya cikin ciki, Daga bathroom Yaya ya fito ya samu wayan shi da yasa caji tana kira, Uncle naji ya ce bayan ya dauki wayan Inajin haka nasan cewa Anty Amarya ce zata sa Uncle kira don jin ya jikin nawa, saboda nasan jiya batai barci ba da dadi, Yaya ya cewa Uncle na samu sauki ai don har na tashi nayi sallah, ko, Nan Uncle ke cewa wai kada mu ci abincin hotel an girka muna agidan shi, Godiya naji Yaya Abubakar ya zabgawa uncle a wayan, Nan naji yana fadin cewa bada safe zai wuce ba don yana son tsayawa yayi ta,aziya a nan sokoto don anwa abokin shi rasuwa,, Bayan sun kashe wayan ne ya dan juyo gurina yana taba wuya na don jin zafin jikin nawa, Alhamdullahi naji yace aijikin bazafi, zaki iya tafiya ke nan ko? Gabana ya fadi don jin may yace, don nasan cewa da zaran mun shiga Abuja shi ke nan duk wanan tarairayan bazan samay shi full ba, Mijin mai mata kenan komai na auren mai mata ragagge ne sosai wallahi, Nace su Anty Samira sunji dadin su su kadai a gurin maza jen su, Anty Aisha,ce ma naji ana cewa wai zata auri may mata inda nice ke da zabi ai bazan auri mai mata ba nace a rai na, Karfe tara, da rabi mukabar hotel zuwa gidan Uncle don mu karya, Dakin Anty na,shige na haye gado don sam zazzabin ya takura min sai dai banjin shi sosai sai alamomin shi kawai, nake ji, Antu shigo dakin dauke da nawa kayan a hannun ta tana cewa,a,a kwanciyar kuma kika karayi Meenatu, Wallahi Anty banjin kwarin jikin nawa sam ido ta kura min har dan wani lokaci sai take ce min tashi ki karya ko ? Daidai lokacin da take zuba min ruwan zafi a cup ni kuma ina son mikewa zaune take ce min, May likitan da ya duba ki yace ? Nace cewa yayi,wai,wahalan hanya ce tai min yawa tare da sanyin Ac sai yaja min zazzabi, Allah ya sauwaka tace tare da turo min cup din tea da plate din Irish da kwai soyayye, a gabana, Tea din na dauka ina kokarin kaiwa a bakina, amma sai naji tankar zanyi amai dole na cire cup din da sauri na, aje, Ido anty takara tsura min tace min lafiya cikin dan mararaice fuska nake ce mata, Wallahi sai kawai naji bana son warin milk din da naji, Anya kuwa Meenatu ? Ba ciki kin ka samu ba ? Wani iri naji datace hakan nace cikin shagwaba haba dai Anty don Allah daina zancen nan please, Tace cikin dariya,to na daina na koma na dan kwanta ina cewa Wallahi likita yace wahala ce tai min yawa tunda ban saba ba, Tace hakane fa kuma to amma aida kinci koda kwai ne da dan dankali ko ? Ba don naso ba na kara mikewa zaune a hankali ina yar tsuki gefe, don sam ban san may ke min dadi ba, Ba laifi don na dan ci Irish din da kwai, nacewa Anty barin sha ruwan Lipton zalla ingani ko zan iya sha, Anty tamike da kanta tana hada min Lipton din zallah, Tace min ance wai anwa mijin ku rasuwa a nan gari ko, ? Nace eh haka naji suna magana da Aliyu, mijin kaunan Aliyu ne abokin shi, Wace da ya tashi aure amma Mama ta hana wai yar boko ce, Dama anan sokoto take aure, shine mijin ta ya samu accident, ankai shi kano jinya Allah yai mai rasuwa jiya, Allah ya jikan shi na ce Ameen tamiko min cup din Lipton din na gyara don insha, Lipton din, Tsab Anty Amarya ta gada min kayana ga trolls dina guda biyu, da mamaki na kalli Anty Amarya nace bafa zandade sosai bane anty wanan kayan sun yi yawa ai da arage su kawai, Saida ta gama jan zip tai tsuki tace akai zaki dauka halan ? Sanan ke san ko may zaki iske a can din, yanzu fa ba daga ke sai Sadiya bace, Murmushi na yi tare da kokarin mikewa zaune nace, ai shiyasa surukin ki ya tambaya cewa halan kece ki ka gyara mai ni haka,? Ke Meenat don Allah dai bari namike zaune da kyau na dauki, Irish' guda na jefa bakina nace tun ranan da muka shiga kasan Niger waahegari yake tambayana hakan? Kunya ne ya kama Anty do komawa tayi saman gado tazauna tare da dafe fuskan ta, Nan na dan fada mata yadda muka kwasa da shi har zuwa dawowan mu, sai dain in brief ba gaba daya na fada mata ba, Uncle ne ya bude labulen dakin ta re da sallama yana cewa, maigidan ki yana falo yana magana da ke, Gyalen na dan aza akaina na nufi falon Yaya yana zaune saman kujera one, seater, da waya a hannun shi yana dakila, a hankali, Jin motsin fitowa na yasa shi dago kai ya tsura min ido kamar may son gano wani abu gare ni, Da dan murmushin karfin hali ga idona na karasa gurin shi, zan zauna a kasa yace min come,up, dawo nan kizauna tare da danbubuga min gefen kujerar shi, Kafada na dan make lokacin nakai zaune a kasan carpet ina cewa, nan gidan mune kada wani ya fito yagan mu hakana, Hmmm kawai naji yace tare da cewa to yaya jikin naki ne yanzu, Naji sauki nace tare da dan dago kai na kalli fuskan shi, Uncle ne ya shigo falon da sallama abakin shi yana cewa, nayi magana driver yace gashinan cikin gari zai zo, Sai lokacin Uncle ya, dan mai da kallon shi gurin da nake zaune yake cewa , Uhumm ki rubutawa kowa sunan shi a kayan shi yanzu driver zai zo ya kai masu sakon don kin ga baza mu wuce dashi har Abuja ba kuma, Set set mu kai ta rubuta sunan nida Anty sai da mu kafidda na kowa, Nafitar da wanda na sayowa Uncle da su anty sai hajiya Mama wace itin katon gyalen nan da manyan mata ke ya fawa na sayo mata, Nono Rakumin da cukkui din da na sayo nace ma anty ta aje su anan amma sai tabani gora biyu wai in tafi dasu can, Anty ta nosa tace Meenatu wanan irin tsaraba haka kamar wace ta tafi saudiya, Murmushi nayi nace to anty ai shine daidai tace gaskiya ne kuma, Kasamu kaci da wani shine samu inji Allah da mazon shi, Uncle ya zo tare da driver yaya da wani suka kwashi kayan zuwa motan da zata,kai Birnin Kebbi, Sai bayan tafiyan su ne Uncle ke sheda muna cewa, ai har da kayan masarufi ya tura masu da shi, Sai dai abinda ya bashi mamaki shine su tufafin yace ace wai inji ki, Murmushi nayi shine nake dan ba su uncle labarin yadda akayi sayen kayan, Uncle yace shi yasa yake samun cigaba sosai agurin aiki don kinga shi mutum ne mai gaskiya ga al,amarin shi, Don haka Meenatu, kisan yadda zaki zauna da wanan mutumin, kiji ko nace naji kawu, ****** ********* ****** Ba mu samu wuce Abuja ba a ranan don yan zirga zirgan da Yaya yayi shida Aliyu da Uncle dina, Sai zuwa yamma yazo ya dauke ni wai muje yiwa Fatima kaunar Aliyu da mijin ta ya rasu gaisuwa, Gidan jama,a ne ciki cimjin tako ina, yan uwanta da na maigidan, Aliyu ne yai muna jagora har dakin ta dakin yana da falo amma ita tana can daga kuryan dakin ta, Tafito cikin wani katon hijab har kasa hannu rike da tasba, Ta zauna gefen wata tsohuwa, tana muna sannun ku da zuwa, Mun mata gaisuwa inda Yaya ya jajanta mata tare da mata addu,an Allah yasawa yaranta Albarka, Idon ta sun kode sunyi ja saboda kuka, ta ansa a hankali da fadin Ameen, Aliyu ne kewa wa tsofin ga matar shi nan ai wace malam.tsoho ya hadasu auren gidan, Wani iri naji da yafadi hakan take idon kowa yayo kaina suna cewa Allah sarki tubarkallah Wata daga cikin su tace ai daga nin su jini guda ke aiki don kamar su yayi yawa, Sannu keji ai,ta hakkuri kin ji, zaman aure sai da hakkuri, Fatima wace ta dago ido a hankali ta kalle ni sai kuma ta dan kalli Yaya Abubakar ta maida fuskanta kasa da sauri don, ganin yadda yai mata wani kwarjini,, Wata tsohuwa ke tambayan cewa, daga Abuja yanzo ko ? Aliyu yace Niger suka fito shine ya tsaya suyi gaisuwa, Sai suka kama fadin aiko, angode angode, sannun ku da hanya, Yaya Abubakar yasa hannu ga aljihu yadebo kudi zasu kai dubu hamsi ya aje mata a gaban ta inda ya waiga gurin da nake ya yace muje ko, Na mike na bi bayan su shida Aliyu wanda ke muna jagoran fita daga gidan, Gidan Uncle na koma don wai zasu fita shida Aliyu, Acan gidan Uncle bayan nagama cin abinci mu kadan yi hira da Anty akan irin tausayin da Fatima kaunan Aliyu taba ni, Don muna hanya dawowa Aliyu ke ma Yaya Abubakar hira cewa wai yan uwan mijin dama basu son Fatima, a gidan saboda haka suka sashi ya kara wani aure, Baifi wata uku da auren matar ba ya samu accident din da yai sanadiyar shi,,, Yaya ya bugo waya lokacin ina barci wana kuma yana gurin caji dakin Anty, Don haka, dole ya kyaleni gidan Uncle na kwana ranan, Cikin dare zafin jiki ya tadani daga barci, amma zuwa asuba saina samu barci don sai naji zazzabin ya bari, Tun da safe bayan mun karya muka kama hanyar Abuja, inda driver yai ta sharan gudu damu don ya samu hanya, Duk yadda naso in boyewa Yaya Abubakar rashin jin dadin jikina hakan bai yi ba don zazzabin ya kara rufe ni a mota again,, Nan Yaya Abubakar yahau min fada cewa may yasa ban fada mashi tun can banji sauki ba likita ya kara dubani, na biyo hanya da ciwo, haka, A kofan gidan kamar kulun Samarin dake zama a kofan gidan suna nan, Tsayawar motan mu ya sa hankali su duk yayo kan mu baki dayan su, Nice ta karshen fitowa daga motar abinda yasa hamza saurin mikewa da sauri ke nan, Ya ce a Amarya tazo ke nan fa, ? Wani daga gefen shi cikin suke tambayan shi wata amarya yace mai wanan da ta ke bamu abinci mana, Sai suka mike gaba daya zuwa taron mu suna faman yi muna sannu da zuwa, Makullin dakina na,ciro daga cikin jakkana na mikawa Hamza wanda sai a lokacin ya kula da cewa banda lafiya ne, Cikin tausayawa yake mun sannu yayin da sauran abokan shi suka fara yi min sannu suma tare da cewa anzo lafiya, Tana zaune, a falo, cikin shigar wani dogon wandon jeans da wani bakin riga mai dogon hannu,, Hamzs ya shigo gidan da sallaman shi, da sauri ya nufi part dina yana budewa, Salawatu ta mike tsaye tana masa wani irin kallon rainin hankali, za tai magana ke nan na shigo gidan da Sallama na , Baki na ya sauke da addu,oin tsari kamar yadda kakana ya sanar dani, Kallon mamaki take min don da farko bata gane ni ba sai da taga shigowan Yaya Abubakar yana cewa akai kaya a part dina, Hamza ke daga kofa yana shiga da kayan cikin dakina, A hankali na ina bude bakina ina ce mata ina wuni acikin muryana da yasa ta kara sandarewa, tsaye, Ban san ko ta karba don ni wucewa nayi don in samu guri indan kwanta, Hamza ke cewa barin fadawa Fattu cewa kin zo ba lafiya daidai lokacin da na shiga dakin, Bai bata lokaci ba ya fita kiran Fattu a lokacin ne Yaya Abubaka ya shigo dakin nawa, Gadon ba zani gado saman shi, sai dai katifa hakana kwanta sama ina jin wani irin amai na taso min, Inna Allah Allah Yaya ya fita dakin in samu in shiga bayin dakin, Ganin yana kokarin taba ni yasa ni mikewa da sauri har ina ture shi na fada bandakin Amai nayi sosai sanan na samu sa,ida na wanke baki na da fuska na nafito dan kwalina a hannu, Yaya yana tsaye daga kofan bayin ya tsura min ido cikin tsarguwa, Yace Meenat har baki da lafiya haka kika bari mukabi wanan hanyan mai tsawo da ke, Sallaman Fattu a kofan dakin shi ya dakatar dashi, Yace mata bissimillah ko ? Tashigo tana cewa Amarya ba lafiya kuma kukai wanan tafiya haka, Dan dariyan yake nai mata nace a hanyane ciwon ya kamani ai, Fita Yaya yayi zuwa gurin sauran matan shi yabar mu da Fattu, Ita ce ta taimaka min da gyaran dakin take dakin ya koma neat, kamar bashi ba, takawo room Fresh ta fesa ko ina har bayi take guri ya dauki kamshi, Anty Sadiya ce ta shigo da Sallamanta fuskanta ba yabo ba fallasa a cikin sa, Ina zaune ina shan ruwan Lipton da Fattu tasa Hamza ya kawo min daga gidan su, Acikin muryan nan nata kamar bata son magana tace, , Meenatu ba lafiya kuma ga tafiya, a hankali nace sannu Anty, Tace yawa, kun zo lafiya ya mutanen gida ya karatu? Na ansa da Alhamdullahi, daga inda Fattu take tana kokarin sa min trolls dina guri guda tacewa Anty Ina wuni Anty,? A dasashe ta ansa wa Fattu ba a cikin dadin raiba, Daga haka anty ta juya tana cewa Allah ya sauwa ka, muka karba mata fadin ameen, Lafewa nayi saman gadon kamar may barci yayin da Fattu take zaunw daga gefe guda ta zura min ido, Yaya Abubakar ya shigo dakin yana cewa in tashi mu tafi asibiti, Badon naso ba muka tafi asibiti da shi, akai min alluran malaria da kuma kwayoyin sa akaba bani, Da na dawo na samu Mama Bi,u tazo tana zaune a dakina don haka ranan tsohuwar mai mutunci itace ta kula dani, Washe gari na tashi jikin nawa da sauki don muyi waya da Anty ina mata bayanin yadda jikin ya kasance min, Ta tambayeni ko ya muka kwashe da Salawatu, sai da na ja tsaki nace ni tun shigowa na ban ganta ba ma har yau, Kina nufin ba tazo dubaki ba ke nan na cewa Anty gaskiya hakane, Share muna fuka kawai ki kama harkokin ki bakin ciki takeyi dake don may ki kazo,, Kada ki yarda ki biyewa jikin ki ki mike kifara harkokin ki a cikin gida kamar kowa,, Na amsa mata da to Ànty na gode takara ce min kadafa kiji tsoron kowa ki dake kawai ki kama harkokinki na kara cewa to Anty nagode, Muna gama wayan da Anty sai naji tankar tabani wani magani ne a jikina don sai kawai na mike tsaye, na shiga yan gyare gyare a dakina har zuwa dan corridor din sashe na, Daga nan na fada kitchen don indan sa ruwan zafi wanda zan sha ruwan Lipton shayi, Salawatu tana cikin kitchen din tana aiki wanda hakan ne yasani gane cewa, ita ce da girki a gidan, Sallamu Alaikum na ce tare, cewa ina kwana lafiya kawai tabani ansa, Direct gurin Gas din da ba bu komai a sama na nufa don in kunna wuta,, Muryan Salawa naji daga baya na tana cewa, wanan dayan Gas din zan yi amfani dashi yanzu, Amsa na bata a takaice da cewa ruwa kawai zan dafa sama, Naci gaba da abinda nakeyi, sai dai bakina ya dauke da addu,an haduwa da muguwar kishiyya, Komai na hada daga Lipton har kayan yaji a cikin ruwan har ya fara batun tafasa, Muryan Yaya Abubakar naji daga baya na yana cewa,Sallawa har kin samu lafiyan fitowa hada girki, Dan murmushin irin ta ma,ana na sake nace ba girki bane Yaya dan ruwan Lipton zan dan dafa da kayan yaji inzuba a flasks dina, Ashe Salawa tana a bayan shi sai naji yana cewa bakin ce ta,tare maki gurin girki da nata girkin ba, ? Batare da na kula suba tankar basu gurin najawo flasks dina a gaban shi na fara daurayewa tare da daukan dan soyoyon tace ruwan zafi, nafara tace ruwan a cikin flasks, Ina jin lokacin da yaya ya juya yana cewa cikin murya kamar a zafi zuciya yace, bazan yarda da zaman fitina a gidana ba fa, Idan ke baki sani ba su sun sani ai don na riga na fada masu, tun farko So, Mind your self,,, Sororo Salawatu tayi tabi bayan mijin su da kallo don ita ba haka tazo ba, Daga in da nake tsaye na sake wani irin ajiyan zuciya,tare da numfasa, Na kashe Gas din tare da dauraye tukunyar na zubar da kayan yajin a dustbin, din kitchen,, Fitana daga kitchen din tabi bayan nawa nima da kallo har na bace mata ga gani, Dakina na fada na aje flasks din a gefen mirror na, Bakin gadona na zauna nafara tuna nen cewa ashe zancen Anty Amarya gaskiyane, na cewa sai nayi fama da kishin Salawatu, Na mike tsaye ina cewa ashe akwai aiki kenan a gaba na bari kawai in murjewa wanan macen ido, Abincin da yasa dokar cewa a tare za,a dinga ci sai naga ba,a kirani ci ba Tunda nadan sha ruwan Lipton dina tare da magani na sai na samu guri na kwan ta don dama ina bukatan hutu,, Sau kusan biyu Yaya Abubakar ya yana lekowa ya ga ko na farka daga barci, don yaji ko nasha magani na, Wanan abin ya matukar bakan tawa Salawatu rai don tun zuwan ta gidan ta, tare komai tana nuna kamar ita ka dai ce matar gidan,, Ita Anty Sadiya ko a jikinta, don ita har kan su baya gaban ta Duk wani duniyan cin da Salawatu zatayi bai a gaban ta, Hakan ke sa bata damu da fita waje ba don bata da lokacin su, Ita ko Salawatu sai take gani kamar duk a cikin samun gurine hakan agareta, Amma yau sai gashi kan yar karamar matar sa har yake ta zuwa da dawowa, ****** ********* ****** Driver yana shiga garin Birnin Kebbi bai tsaya ko ina ba sai kofan gidan malam , Abinda ya jawo hankalin al,umman uguwar ke nan zuwa kallon motan da ta tsaya kofar gidan tsohon, Driver wanda ya fito ya nufi wurin da malam yake cikin rufan kofar gidan shi, Babu abinda zaka hango sai farin gemun shi tun daga nesa, Shima kansa malam din kallon mamaki ya kewa driver motan, Sun gaisa da malam a cikin mutunci tare da taron hababa daga malam din har sauran mutanen dake gurin, Mutumin ya dubi malam yace sako ne da Alh Abubakar na gidan nan, Yace ina zo in,baka wanan sakon hannu da hannu ya mika masa envelope, Kudi ne acikin envelope din da yar takarda, mutumin yace, yace wa yancan kayan aba Wadda ya rabawa kowa ga takarda wai a bashi, Cikin mamaki malam yace a ina ka gan shi bawan Allah, Yace Sokoto sun fito Niger da shi da matar sa, saboda bai samun zuwa shi da matar sa yaba da sakon akawo, Take guri ya dauki zance cewa Abubakar ta turo wa iyayyen shi da abinci mota guda taf da kaya, Baba Wadda aka nemo a cikin gari yazo da sauri inda ya fara fitar ma da kowa da nasa rabon, Har zuwa makwabtan su da ya sa sunan su a cikin don sun zama tankar yan uwa, Sai kuma kudin sabon mashi wanda za a saiwa Baba Buhari,, Baba Wadda yaba kowa shadda da kudin dinkin da yaya Abubakar yace masu nice na sayo masu tsaraba a kasar Niger, Haba gari ya dauki ciri cewa, Abubakar ya aiko wa iyayyen shi da sako, Wasu ce ai yanzu ya daina daukan shawaran Mama Ladi ne, Wasu suce ai saboda yanzu yana auren yar gida yasa yafara kula da gida, tau kowa dai yasan halin dan Adam,,, Ranan Mama Ladi kamar zata kama da wuta don may zai yo sako bai fada mata ba sunyi shawara, Ita Meenatu aiki takeyi da zata samu kudin sayen irin wanan kayan haka? Sam baza ta yarda a mallake mata da ba kamar yadda uwata ta mallake ubana ya kasa kara aure ,sai abinda tace kuma take so akeyi a cikin gidan mu, Zagi dai kala kala mun sha shi gurin mama Ladi ni mahaifiyata a ranan, Malam tsoho yasa arabawa mutanen shiya mabukata kason shi tare da cewa Abubakar ne ya aiko masu dashi,, ****** ********* ****** Ina zaune a dakina ina dan shan faten wanken da Fattu ta,shigo min dashi don faten yai min dadin sha dosai, Ya Abubakar yabude labule ya shigo da sallamar shi, Na amsa tare da dan dago kaina plate din dake gaba yake kallo, Tambaya ya jefo min da cewa mayye wanan haka a gaban ki, Nai dan murmushi nace fate ne nake sha, Yakara kallon plate din yace, fate kuma,? Nace Fattu ce ta dafa min wai ko zanji dadin bakina sai naga fuskan shi ya matse da ga yar fara,ar da ya shigo da ita, da farko, Meenatu bana son mutanen nan suna shigo min da abinci dafafe a gida, Idan basu, dauka agidana ba ashe kuma baza,a kawo saga gidan su ba don dai ba alfahari ba nasan cewa nafi karfi, Jiki na yai sanyi sosai da jin zance Yaya Abubakar Don haka a hankali na dago kai nace masa nice nace ta da famin Don bazan iya dafa abinci yadda nake ji, jikina ba, Na fadi hakane don yasan cewa ba a, bani abinci ba agidan, Na karashe zance da kwantar da muryana na ce amma kayi hakkuri baza,a sake ba insha Allah, Ya juya batare da yace min komai ba ya nufi waje, cikin fushi, Nima murmushi nayi daga inda nake zaune don ko banza na rama abinda Salawatu tai min da safe, Dakin Salawa ya nufa ya samay ta zaune tana waya tana fadawa Salawtu ce nazo garin Abuja, Kallon da yai mata kawai yasa ta gane cewa da magana yazo, Don haka ta kashe wayan ba shiri tana mai kako murmushi a fuskan ta, Oga lafiya dai ko? Ko kana son wani abune ? Lafiya kalau yace, tare da fuskan tar ta da kyau ya ce ina abincin Meenat, Meenat ta tambaya cikin maimaita sunan, Yace eh Meenat my second wife, Kai tsaye tace ban sama mata ba saboda naga gaba daya ake zubawa agidan, aiko, Yace amma kin san aibata da lafiya ? May yahana ki kai mata a daki ? Ta katse shi da sauri cikin murya mai baiyana mama tace, Sir nice zan kaiwa wanan yarinyar abinci har daki ? Don kin kai mata abini laifine, ? Ba kishiyar ki bace ita,? Idan akwai abinda yafi muni Salawatu taji shine wanan kalman da ya fadi Gaba daya duk jikin ta sai yai sanyi rayuwar ta ya baci, Amma sai ta dake tace ma shi ban yi wanan tunanen ba gaskiya amma kayi hakuri please , Tashin hankali Salawatu duban Yaya Abubakar takeyi yadda ya sake mata a lokaci guda, Kamar ba Ogan ta ba da suke ta zuba soyayya da amarci tare, Juyawa yayi ya haye sama dakin shi rai bace don duk mun taba shi, Salawa ta dafa bakin gadon ta takai zaune da kyat, Idon ta sunjuye sunyi jajir akan wanan little baby din yau Oga ke batun ci mata mutunci haka ? Lai ko wani abu sai aure wanan yar karamar yarinya za,ace takaiwa abinci har daki nerve gaskiya da sake,,,,, ZEEE MAKAWA. YELWA🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 5⃣1⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA ALLAH - AL- MUQEET,,, Allah da ikon shi, washegari sai na samu sauki kamar bani bace, jiya ba lafiya, Ina zaune inda nai sallah Asubahi, Yaya Abubakar ya shigo hannun shi rike da tasbaha yana ja a hankali, Kafin in masa ina kwana shi yafara yi min da cewa Meeanat ya kika kwana ya kika kara ji ? Na,ansa da fadar Alhamdullahi Yaya naji sauki, ai Ya ce, ashe kaunar tawa bata,son wahala daga yanzu idan zamuyi tafiya sai dai mu shiga jirgi ke nan ko,? Murmushi nayi ina mikewa tsaye tare d nade Sallaya nace, ciwo daine yazo Yaya aikumaya bari, Gado na koma nadan kwanta na dunkule guri guda kamar yadda yaro ke kwanciya cikin ciki, Daga bathroom Yaya ya fito ya samu wayan shi da yasa caji tana kira, Uncle naji ya ce bayan ya dauki wayan Inajin haka nasan cewa Anty Amarya ce zata sa Uncle kira don jin ya jikin nawa, saboda nasan jiya batai barci ba da dadi, Yaya ya cewa Uncle na samu sauki ai don har na tashi nayi sallah, ko, Nan Uncle ke cewa wai kada mu ci abincin hotel an girka muna agidan shi, Godiya naji Yaya Abubakar ya zabgawa uncle a wayan, Nan naji yana fadin cewa bada safe zai wuce ba don yana son tsayawa yayi ta,aziya a nan sokoto don anwa abokin shi rasuwa,, Bayan sun kashe wayan ne ya dan juyo gurina yana taba wuya na don jin zafin jikin nawa, Alhamdullahi naji yace aijikin bazafi, zaki iya tafiya ke nan ko? Gabana ya fadi don jin may yace, don nasan cewa da zaran mun shiga Abuja shi ke nan duk wanan tarairayan bazan samay shi full ba, Mijin mai mata kenan komai na auren mai mata ragagge ne sosai wallahi, Nace su Anty Samira sunji dadin su su kadai a gurin maza jen su, Anty Aisha,ce ma naji ana cewa wai zata auri may mata inda nice ke da zabi ai bazan auri mai mata ba nace a rai na, Karfe tara, da rabi mukabar hotel zuwa gidan Uncle don mu karya, Dakin Anty na,shige na haye gado don sam zazzabin ya takura min sai dai banjin shi sosai sai alamomin shi kawai, nake ji, Antu shigo dakin dauke da nawa kayan a hannun ta tana cewa,a,a kwanciyar kuma kika karayi Meenatu, Wallahi Anty banjin kwarin jikin nawa sam ido ta kura min har dan wani lokaci sai take ce min tashi ki karya ko ? Daidai lokacin da take zuba min ruwan zafi a cup ni kuma ina son mikewa zaune take ce min, May likitan da ya duba ki yace ? Nace cewa yayi,wai,wahalan hanya ce tai min yawa tare da sanyin Ac sai yaja min zazzabi, Allah ya sauwaka tace tare da turo min cup din tea da plate din Irish da kwai soyayye, a gabana, Tea din na dauka ina kokarin kaiwa a bakina, amma sai naji tankar zanyi amai dole na cire cup din da sauri na, aje, Ido anty takara tsura min tace min lafiya cikin dan mararaice fuska nake ce mata, Wallahi sai kawai naji bana son warin milk din da naji, Anya kuwa Meenatu ? Ba ciki kin ka samu ba ? Wani iri naji datace hakan nace cikin shagwaba haba dai Anty don Allah daina zancen nan please, Tace cikin dariya,to na daina na koma na dan kwanta ina cewa Wallahi likita yace wahala ce tai min yawa tunda ban saba ba, Tace hakane fa kuma to amma aida kinci koda kwai ne da dan dankali ko ? Ba don naso ba na kara mikewa zaune a hankali ina yar tsuki gefe, don sam ban san may ke min dadi ba, Ba laifi don na dan ci Irish din da kwai, nacewa Anty barin sha ruwan Lipton zalla ingani ko zan iya sha, Anty tamike da kanta tana hada min Lipton din zallah, Tace min ance wai anwa mijin ku rasuwa a nan gari ko, ? Nace eh haka naji suna magana da Aliyu, mijin kaunan Aliyu ne abokin shi, Wace da ya tashi aure amma Mama ta hana wai yar boko ce, Dama anan sokoto take aure, shine mijin ta ya samu accident, ankai shi kano jinya Allah yai mai rasuwa jiya, Allah ya jikan shi na ce Ameen tamiko min cup din Lipton din na gyara don insha, Lipton din, Tsab Anty Amarya ta gada min kayana ga trolls dina guda biyu, da mamaki na kalli Anty Amarya nace bafa zandade sosai bane anty wanan kayan sun yi yawa ai da arage su kawai, Saida ta gama jan zip tai tsuki tace akai zaki dauka halan ? Sanan ke san ko may zaki iske a can din, yanzu fa ba daga ke sai Sadiya bace, Murmushi na yi tare da kokarin mikewa zaune nace, ai shiyasa surukin ki ya tambaya cewa halan kece ki ka gyara mai ni haka,? Ke Meenat don Allah dai bari namike zaune da kyau na dauki, Irish' guda na jefa bakina nace tun ranan da muka shiga kasan Niger waahegari yake tambayana hakan? Kunya ne ya kama Anty do komawa tayi saman gado tazauna tare da dafe fuskan ta, Nan na dan fada mata yadda muka kwasa da shi har zuwa dawowan mu, sai dain in brief ba gaba daya na fada mata ba, Uncle ne ya bude labulen dakin ta re da sallama yana cewa, maigidan ki yana falo yana magana da ke, Gyalen na dan aza akaina na nufi falon Yaya yana zaune saman kujera one, seater, da waya a hannun shi yana dakila, a hankali, Jin motsin fitowa na yasa shi dago kai ya tsura min ido kamar may son gano wani abu gare ni, Da dan murmushin karfin hali ga idona na karasa gurin shi, zan zauna a kasa yace min come,up, dawo nan kizauna tare da danbubuga min gefen kujerar shi, Kafada na dan make lokacin nakai zaune a kasan carpet ina cewa, nan gidan mune kada wani ya fito yagan mu hakana, Hmmm kawai naji yace tare da cewa to yaya jikin naki ne yanzu, Naji sauki nace tare da dan dago kai na kalli fuskan shi, Uncle ne ya shigo falon da sallama abakin shi yana cewa, nayi magana driver yace gashinan cikin gari zai zo, Sai lokacin Uncle ya, dan mai da kallon shi gurin da nake zaune yake cewa , Uhumm ki rubutawa kowa sunan shi a kayan shi yanzu driver zai zo ya kai masu sakon don kin ga baza mu wuce dashi har Abuja ba kuma, Set set mu kai ta rubuta sunan nida Anty sai da mu kafidda na kowa, Nafitar da wanda na sayowa Uncle da su anty sai hajiya Mama wace itin katon gyalen nan da manyan mata ke ya fawa na sayo mata, Nono Rakumin da cukkui din da na sayo nace ma anty ta aje su anan amma sai tabani gora biyu wai in tafi dasu can, Anty ta nosa tace Meenatu wanan irin tsaraba haka kamar wace ta tafi saudiya, Murmushi nayi nace to anty ai shine daidai tace gaskiya ne kuma, Kasamu kaci da wani shine samu inji Allah da mazon shi, Uncle ya zo tare da driver yaya da wani suka kwashi kayan zuwa motan da zata,kai Birnin Kebbi, Sai bayan tafiyan su ne Uncle ke sheda muna cewa, ai har da kayan masarufi ya tura masu da shi, Sai dai abinda ya bashi mamaki shine su tufafin yace ace wai inji ki, Murmushi nayi shine nake dan ba su uncle labarin yadda akayi sayen kayan, Uncle yace shi yasa yake samun cigaba sosai agurin aiki don kinga shi mutum ne mai gaskiya ga al,amarin shi, Don haka Meenatu, kisan yadda zaki zauna da wanan mutumin, kiji ko nace naji kawu, ****** ********* ****** Ba mu samu wuce Abuja ba a ranan don yan zirga zirgan da Yaya yayi shida Aliyu da Uncle dina, Sai zuwa yamma yazo ya dauke ni wai muje yiwa Fatima kaunar Aliyu da mijin ta ya rasu gaisuwa, Gidan jama,a ne ciki cimjin tako ina, yan uwanta da na maigidan, Aliyu ne yai muna jagora har dakin ta dakin yana da falo amma ita tana can daga kuryan dakin ta, Tafito cikin wani katon hijab har kasa hannu rike da tasba, Ta zauna gefen wata tsohuwa, tana muna sannun ku da zuwa, Mun mata gaisuwa inda Yaya ya jajanta mata tare da mata addu,an Allah yasawa yaranta Albarka, Idon ta sun kode sunyi ja saboda kuka, ta ansa a hankali da fadin Ameen, Aliyu ne kewa wa tsofin ga matar shi nan ai wace malam.tsoho ya hadasu auren gidan, Wani iri naji da yafadi hakan take idon kowa yayo kaina suna cewa Allah sarki tubarkallah Wata daga cikin su tace ai daga nin su jini guda ke aiki don kamar su yayi yawa, Sannu keji ai,ta hakkuri kin ji, zaman aure sai da hakkuri, Fatima wace ta dago ido a hankali ta kalle ni sai kuma ta dan kalli Yaya Abubakar ta maida fuskanta kasa da sauri don, ganin yadda yai mata wani kwarjini,, Wata tsohuwa ke tambayan cewa, daga Abuja yanzo ko ? Aliyu yace Niger suka fito shine ya tsaya suyi gaisuwa, Sai suka kama fadin aiko, angode angode, sannun ku da hanya, Yaya Abubakar yasa hannu ga aljihu yadebo kudi zasu kai dubu hamsi ya aje mata a gaban ta inda ya waiga gurin da nake ya yace muje ko, Na mike na bi bayan su shida Aliyu wanda ke muna jagoran fita daga gidan, Gidan Uncle na koma don wai zasu fita shida Aliyu, Acan gidan Uncle bayan nagama cin abinci mu kadan yi hira da Anty akan irin tausayin da Fatima kaunan Aliyu taba ni, Don muna hanya dawowa Aliyu ke ma Yaya Abubakar hira cewa wai yan uwan mijin dama basu son Fatima, a gidan saboda haka suka sashi ya kara wani aure, Baifi wata uku da auren matar ba ya samu accident din da yai sanadiyar shi,,, Yaya ya bugo waya lokacin ina barci wana kuma yana gurin caji dakin Anty, Don haka, dole ya kyaleni gidan Uncle na kwana ranan, Cikin dare zafin jiki ya tadani daga barci, amma zuwa asuba saina samu barci don sai naji zazzabin ya bari, Tun da safe bayan mun karya muka kama hanyar Abuja, inda driver yai ta sharan gudu damu don ya samu hanya, Duk yadda naso in boyewa Yaya Abubakar rashin jin dadin jikina hakan bai yi ba don zazzabin ya kara rufe ni a mota again,, Nan Yaya Abubakar yahau min fada cewa may yasa ban fada mashi tun can banji sauki ba likita ya kara dubani, na biyo hanya da ciwo, haka, A kofan gidan kamar kulun Samarin dake zama a kofan gidan suna nan, Tsayawar motan mu ya sa hankali su duk yayo kan mu baki dayan su, Nice ta karshen fitowa daga motar abinda yasa hamza saurin mikewa da sauri ke nan, Ya ce a Amarya tazo ke nan fa, ? Wani daga gefen shi cikin suke tambayan shi wata amarya yace mai wanan da ta ke bamu abinci mana, Sai suka mike gaba daya zuwa taron mu suna faman yi muna sannu da zuwa, Makullin dakina na,ciro daga cikin jakkana na mikawa Hamza wanda sai a lokacin ya kula da cewa banda lafiya ne, Cikin tausayawa yake mun sannu yayin da sauran abokan shi suka fara yi min sannu suma tare da cewa anzo lafiya, Tana zaune, a falo, cikin shigar wani dogon wandon jeans da wani bakin riga mai dogon hannu,, Hamzs ya shigo gidan da sallaman shi, da sauri ya nufi part dina yana budewa, Salawatu ta mike tsaye tana masa wani irin kallon rainin hankali, za tai magana ke nan na shigo gidan da Sallama na , Baki na ya sauke da addu,oin tsari kamar yadda kakana ya sanar dani, Kallon mamaki take min don da farko bata gane ni ba sai da taga shigowan Yaya Abubakar yana cewa akai kaya a part dina, Hamza ke daga kofa yana shiga da kayan cikin dakina, A hankali na ina bude bakina ina ce mata ina wuni acikin muryana da yasa ta kara sandarewa, tsaye, Ban san ko ta karba don ni wucewa nayi don in samu guri indan kwanta, Hamza ke cewa barin fadawa Fattu cewa kin zo ba lafiya daidai lokacin da na shiga dakin, Bai bata lokaci ba ya fita kiran Fattu a lokacin ne Yaya Abubaka ya shigo dakin nawa, Gadon ba zani gado saman shi, sai dai katifa hakana kwanta sama ina jin wani irin amai na taso min, Inna Allah Allah Yaya ya fita dakin in samu in shiga bayin dakin, Ganin yana kokarin taba ni yasa ni mikewa da sauri har ina ture shi na fada bandakin Amai nayi sosai sanan na samu sa,ida na wanke baki na da fuska na nafito dan kwalina a hannu, Yaya yana tsaye daga kofan bayin ya tsura min ido cikin tsarguwa, Yace Meenat har baki da lafiya haka kika bari mukabi wanan hanyan mai tsawo da ke, Sallaman Fattu a kofan dakin shi ya dakatar dashi, Yace mata bissimillah ko ? Tashigo tana cewa Amarya ba lafiya kuma kukai wanan tafiya haka, Dan dariyan yake nai mata nace a hanyane ciwon ya kamani ai, Fita Yaya yayi zuwa gurin sauran matan shi yabar mu da Fattu, Ita ce ta taimaka min da gyaran dakin take dakin ya koma neat, kamar bashi ba, takawo room Fresh ta fesa ko ina har bayi take guri ya dauki kamshi, Anty Sadiya ce ta shigo da Sallamanta fuskanta ba yabo ba fallasa a cikin sa, Ina zaune ina shan ruwan Lipton da Fattu tasa Hamza ya kawo min daga gidan su, Acikin muryan nan nata kamar bata son magana tace, , Meenatu ba lafiya kuma ga tafiya, a hankali nace sannu Anty, Tace yawa, kun zo lafiya ya mutanen gida ya karatu? Na ansa da Alhamdullahi, daga inda Fattu take tana kokarin sa min trolls dina guri guda tacewa Anty Ina wuni Anty,? A dasashe ta ansa wa Fattu ba a cikin dadin raiba, Daga haka anty ta juya tana cewa Allah ya sauwa ka, muka karba mata fadin ameen, Lafewa nayi saman gadon kamar may barci yayin da Fattu take zaunw daga gefe guda ta zura min ido, Yaya Abubakar ya shigo dakin yana cewa in tashi mu tafi asibiti, Badon naso ba muka tafi asibiti da shi, akai min alluran malaria da kuma kwayoyin sa akaba bani, Da na dawo na samu Mama Bi,u tazo tana zaune a dakina don haka ranan tsohuwar mai mutunci itace ta kula dani, Washe gari na tashi jikin nawa da sauki don muyi waya da Anty ina mata bayanin yadda jikin ya kasance min, Ta tambayeni ko ya muka kwashe da Salawatu, sai da na ja tsaki nace ni tun shigowa na ban ganta ba ma har yau, Kina nufin ba tazo dubaki ba ke nan na cewa Anty gaskiya hakane, Share muna fuka kawai ki kama harkokin ki bakin ciki takeyi dake don may ki kazo,, Kada ki yarda ki biyewa jikin ki ki mike kifara harkokin ki a cikin gida kamar kowa,, Na amsa mata da to Ànty na gode takara ce min kadafa kiji tsoron kowa ki dake kawai ki kama harkokinki na kara cewa to Anty nagode, Muna gama wayan da Anty sai naji tankar tabani wani magani ne a jikina don sai kawai na mike tsaye, na shiga yan gyare gyare a dakina har zuwa dan corridor din sashe na, Daga nan na fada kitchen don indan sa ruwan zafi wanda zan sha ruwan Lipton shayi, Salawatu tana cikin kitchen din tana aiki wanda hakan ne yasani gane cewa, ita ce da girki a gidan, Sallamu Alaikum na ce tare, cewa ina kwana lafiya kawai tabani ansa, Direct gurin Gas din da ba bu komai a sama na nufa don in kunna wuta,, Muryan Salawa naji daga baya na tana cewa, wanan dayan Gas din zan yi amfani dashi yanzu, Amsa na bata a takaice da cewa ruwa kawai zan dafa sama, Naci gaba da abinda nakeyi, sai dai bakina ya dauke da addu,an haduwa da muguwar kishiyya, Komai na hada daga Lipton har kayan yaji a cikin ruwan har ya fara batun tafasa, Muryan Yaya Abubakar naji daga baya na yana cewa,Sallawa har kin samu lafiyan fitowa hada girki, Dan murmushin irin ta ma,ana na sake nace ba girki bane Yaya dan ruwan Lipton zan dan dafa da kayan yaji inzuba a flasks dina, Ashe Salawa tana a bayan shi sai naji yana cewa bakin ce ta,tare maki gurin girki da nata girkin ba, ? Batare da na kula suba tankar basu gurin najawo flasks dina a gaban shi na fara daurayewa tare da daukan dan soyoyon tace ruwan zafi, nafara tace ruwan a cikin flasks, Ina jin lokacin da yaya ya juya yana cewa cikin murya kamar a zafi zuciya yace, bazan yarda da zaman fitina a gidana ba fa, Idan ke baki sani ba su sun sani ai don na riga na fada masu, tun farko So, Mind your self,,, Sororo Salawatu tayi tabi bayan mijin su da kallo don ita ba haka tazo ba, Daga in da nake tsaye na sake wani irin ajiyan zuciya,tare da numfasa, Na kashe Gas din tare da dauraye tukunyar na zubar da kayan yajin a dustbin, din kitchen,, Fitana daga kitchen din tabi bayan nawa nima da kallo har na bace mata ga gani, Dakina na fada na aje flasks din a gefen mirror na, Bakin gadona na zauna nafara tuna nen cewa ashe zancen Anty Amarya gaskiyane, na cewa sai nayi fama da kishin Salawatu, Na mike tsaye ina cewa ashe akwai aiki kenan a gaba na bari kawai in murjewa wanan macen ido, Abincin da yasa dokar cewa a tare za,a dinga ci sai naga ba,a kirani ci ba Tunda nadan sha ruwan Lipton dina tare da magani na sai na samu guri na kwan ta don dama ina bukatan hutu,, Sau kusan biyu Yaya Abubakar ya yana lekowa ya ga ko na farka daga barci, don yaji ko nasha magani na, Wanan abin ya matukar bakan tawa Salawatu rai don tun zuwan ta gidan ta, tare komai tana nuna kamar ita ka dai ce matar gidan,, Ita Anty Sadiya ko a jikinta, don ita har kan su baya gaban ta Duk wani duniyan cin da Salawatu zatayi bai a gaban ta, Hakan ke sa bata damu da fita waje ba don bata da lokacin su, Ita ko Salawatu sai take gani kamar duk a cikin samun gurine hakan agareta, Amma yau sai gashi kan yar karamar matar sa har yake ta zuwa da dawowa, ****** ********* ****** Driver yana shiga garin Birnin Kebbi bai tsaya ko ina ba sai kofan gidan malam , Abinda ya jawo hankalin al,umman uguwar ke nan zuwa kallon motan da ta tsaya kofar gidan tsohon, Driver wanda ya fito ya nufi wurin da malam yake cikin rufan kofar gidan shi, Babu abinda zaka hango sai farin gemun shi tun daga nesa, Shima kansa malam din kallon mamaki ya kewa driver motan, Sun gaisa da malam a cikin mutunci tare da taron hababa daga malam din har sauran mutanen dake gurin, Mutumin ya dubi malam yace sako ne da Alh Abubakar na gidan nan, Yace ina zo in,baka wanan sakon hannu da hannu ya mika masa envelope, Kudi ne acikin envelope din da yar takarda, mutumin yace, yace wa yancan kayan aba Wadda ya rabawa kowa ga takarda wai a bashi, Cikin mamaki malam yace a ina ka gan shi bawan Allah, Yace Sokoto sun fito Niger da shi da matar sa, saboda bai samun zuwa shi da matar sa yaba da sakon akawo, Take guri ya dauki zance cewa Abubakar ta turo wa iyayyen shi da abinci mota guda taf da kaya, Baba Wadda aka nemo a cikin gari yazo da sauri inda ya fara fitar ma da kowa da nasa rabon, Har zuwa makwabtan su da ya sa sunan su a cikin don sun zama tankar yan uwa, Sai kuma kudin sabon mashi wanda za a saiwa Baba Buhari,, Baba Wadda yaba kowa shadda da kudin dinkin da yaya Abubakar yace masu nice na sayo masu tsaraba a kasar Niger, Haba gari ya dauki ciri cewa, Abubakar ya aiko wa iyayyen shi da sako, Wasu ce ai yanzu ya daina daukan shawaran Mama Ladi ne, Wasu suce ai saboda yanzu yana auren yar gida yasa yafara kula da gida, tau kowa dai yasan halin dan Adam,,, Ranan Mama Ladi kamar zata kama da wuta don may zai yo sako bai fada mata ba sunyi shawara, Ita Meenatu aiki takeyi da zata samu kudin sayen irin wanan kayan haka? Sam baza ta yarda a mallake mata da ba kamar yadda uwata ta mallake ubana ya kasa kara aure ,sai abinda tace kuma take so akeyi a cikin gidan mu, Zagi dai kala kala mun sha shi gurin mama Ladi ni mahaifiyata a ranan, Malam tsoho yasa arabawa mutanen shiya mabukata kason shi tare da cewa Abubakar ne ya aiko masu dashi,, ****** ********* ****** Ina zaune a dakina ina dan shan faten wanken da Fattu ta,shigo min dashi don faten yai min dadin sha dosai, Ya Abubakar yabude labule ya shigo da sallamar shi, Na amsa tare da dan dago kaina plate din dake gaba yake kallo, Tambaya ya jefo min da cewa mayye wanan haka a gaban ki, Nai dan murmushi nace fate ne nake sha, Yakara kallon plate din yace, fate kuma,? Nace Fattu ce ta dafa min wai ko zanji dadin bakina sai naga fuskan shi ya matse da ga yar fara,ar da ya shigo da ita, da farko, Meenatu bana son mutanen nan suna shigo min da abinci dafafe a gida, Idan basu, dauka agidana ba ashe kuma baza,a kawo saga gidan su ba don dai ba alfahari ba nasan cewa nafi karfi, Jiki na yai sanyi sosai da jin zance Yaya Abubakar Don haka a hankali na dago kai nace masa nice nace ta da famin Don bazan iya dafa abinci yadda nake ji, jikina ba, Na fadi hakane don yasan cewa ba a, bani abinci ba agidan, Na karashe zance da kwantar da muryana na ce amma kayi hakkuri baza,a sake ba insha Allah, Ya juya batare da yace min komai ba ya nufi waje, cikin fushi, Nima murmushi nayi daga inda nake zaune don ko banza na rama abinda Salawatu tai min da safe, Dakin Salawa ya nufa ya samay ta zaune tana waya tana fadawa Salawtu ce nazo garin Abuja, Kallon da yai mata kawai yasa ta gane cewa da magana yazo, Don haka ta kashe wayan ba shiri tana mai kako murmushi a fuskan ta, Oga lafiya dai ko? Ko kana son wani abune ? Lafiya kalau yace, tare da fuskan tar ta da kyau ya ce ina abincin Meenat, Meenat ta tambaya cikin maimaita sunan, Yace eh Meenat my second wife, Kai tsaye tace ban sama mata ba saboda naga gaba daya ake zubawa agidan, aiko, Yace amma kin san aibata da lafiya ? May yahana ki kai mata a daki ? Ta katse shi da sauri cikin murya mai baiyana mama tace, Sir nice zan kaiwa wanan yarinyar abinci har daki ? Don kin kai mata abini laifine, ? Ba kishiyar ki bace ita,? Idan akwai abinda yafi muni Salawatu taji shine wanan kalman da ya fadi Gaba daya duk jikin ta sai yai sanyi rayuwar ta ya baci, Amma sai ta dake tace ma shi ban yi wanan tunanen ba gaskiya amma kayi hakuri please , Tashin hankali Salawatu duban Yaya Abubakar takeyi yadda ya sake mata a lokaci guda, Kamar ba Ogan ta ba da suke ta zuba soyayya da amarci tare, Juyawa yayi ya haye sama dakin shi rai bace don duk mun taba shi, Salawa ta dafa bakin gadon ta takai zaune da kyat, Idon ta sunjuye sunyi jajir akan wanan little baby din yau Oga ke batun ci mata mutunci haka ? Lai ko wani abu sai aure wanan yar karamar yarinya za,ace takaiwa abinci har daki nerve gaskiya da sake,,,,, ZEEE MAKAWA. YELWA [8/13, 07:03] Anty Lantana: 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 5⃣2⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA ALLAH- AL-HASEEB,,,,, Gaba dayan mu, mu uku, Yaya Abubakar ya bukaci da muzo falo gurin shi, Kusan nice ta karshen fitowa sai da na natsaya na gyara jiki na tsab, Nasa wani English wear, baki mai tsaga a kowani gefe ta kasa, Yana da yagwai iya kwankwaso, na daurewa, rigar ta matseni tafitar min da sharp dina tson, Tun kafin in karaso gurin su kamshina ya iso gare su, Kamar yadda Anty Amarya tai min baya cewa kamshin kishi yana sa kishiya tashin hankali, Hakan ne ashe don wani irin harara da mugun kallo nake sha tun da na nufo su, Ya Abubakar wanda ke zaune a saman kujerar tsakiya yana waya, Tun fitowa na hankalisa ya dauke gareni ido ya zuba min baba kawarwa Waya yakeyi don tun ban karaso ba nake jin alaman da yan gidan mu ya ke waya, Daidai karasowa na naji sunyi sallama, da mai wayan ya kashe, tare da ajitan zuciya, Kujeran da Yaya ke zaune sama ita na samu gefen kafar ta kasa saman center carpet na zauna, Cikin mamaki ya dan kalle ni yace, taso mana ga guri nan ki zauna, yana mai buga gefen kujeran da yake zaune, Kai na girgiza na dukar da fuskana kasa nace nan is ok Yaya, Ko da kaina ke a kasa nan san bakowa yai wani irin ajiyan zuciya mai baiyana takaici ba sai Salawatu, A hankali nace Yaya ina wuni,? Ya karba min a cikin sakin fuska da lafiya kalau Meenat ya jikin ki ? Alhamdullah, na amsa dashi, Sai na juya gurin da su Anty ke zaune sun sashi tsakiya kowace na saman kujeran da ke gefe, gefen shi, nasan ko cewa an tare guri ne kada in zauna akusa da Yaya din, Ce masu nayi ina wunin ku Anty, ? Ba laifi don ita Anty Sadiya ta katba da cewa lafiya Meenat jiki yai sauki ko ? Duk fuskan ta a hade yake wanan kuma aiba wani bakon al,amari bane ga Anty, Ji mu kayi Yaya Abubakar ya sauke wata kakkarfan ajiyan zuciya tare da sauya fuskan sa zuwa damuwa, Kowan mu na ganin yadda annurin fuskan Yaya ya dauke, a take kowa ta shiga natsuwa, Ina wasa da yan yatsun hannu na a hankali kai na duke a kasa, Magana ya fara a cikin wani irin murya mai nuna alamar serious a tare da shi, Dan gyaran murya ya fara yi wanda hankalin kowa ya koma gare shi gaba daya, Yafara da sallama da addu,a tare, da magana a cikin dakewa, kamar haka ? Ina son ku san cewa duk kan ku Allah ne ya hada zaman akan amana, Gaba dayan ku duk abu gudane ya hada mu, aure, babu daya daga cikin ku da zata fi karfi na, Abu na farko shine, ina son hadin kai daga gare ku kamar farko don ci gaban gidan , Ya nuna mu da yatsa nida Anty Sadiya yace, su wa yan nan biyun sun sanda irin dokokin da na sa agidan nan,, Don haka ina son a cigaba da yadda akeyi da farko, Kafin ya rufe bakin sa sai Salawatu ta ce amna aini ban san wanan dokan ba a gidan, Zaki sani yanzu ai don tun zuwan ki abinda yasa ban fada maki ba shine, don wanan bata gidan a lokacin, Dafarko idan baku man ta ba kun raba kwana a tsakanin ku, Sai kuma yadda girkin ku zai kasance duk a wanan can lokacin a dan samu matsala a gurin girkin da fatan wanan karon za,a gyara, Idan angama abinci wajibi,ne mai girki idan ta kare girki ta fadawa kowa donba fito a ci a tare, gaba daya har ni, idan kuma bana gida sai kuci a tare , Salawatu ta bude baki tace to amma Sir sai,nake ganin, Wani tsawa ya daga mata ya ce, shout, up my friend iam talking you are talking who is the master,, Cikin muzan ta Salawatu tai wani irin dukar da kai tana ajiyan zuciya, Kawunan mu na kasa ni da Anty Sadiya saboda, sanin halin gogan namu da mukayi, don mutum ne wanda bai son raini ko kadan, shi, Bayan dan shiru da yayi tare da kuraw Salawatu ido sai yaci gaba da cewa, Wajibine duk wata wace ke girki tafara yiwa yan uwa ina kwana da safe ranan itace zata guda nar da komai na gida alhakinn kowa yana gurin ta, Karfe, takwas zuwa tara da rabi kowacen ku ta tabbatar da cewa tana cikin falon nan da dare, Da sauri Salawatu ta kara dago kai ta na duban shi a cikin mamaki, Bazan taba lamuntar hayaniya a gida na a tsakanin ku, Duk wace akaiwa ba daidai a sanar dani don inbincike akai, Dafatan za ku kiyaye gaba daya abin da na sheda maku akai,, Shiru mu kayi gaba dayan mu kowa da abinda take tunane a rayuwan ta a lokacin, Tv da ke aiki a falon muka tsurawa idon muna kallo da saurare,, Don faba dayan mu ba wanda ke iya magana a lokacin duk jikin kowacen mu yai sanyi, Wayan Yaya Abubakar yai kara ya bar abinda yake a system din shi, yadauki wayan da sauri naga ya gyara zaman shi Jin da nayi yana cewa Baba ina wuni, yasa ni saurin dago kai na na dan dube shi, Batare da ya dube ni ba yaci gaba da maganan shi Ina tsan manin ko wani Baba,ne, mai shi godiya ya keyi don sai Ameen, Yaya Abubakar ke ta cewa tare da kada kai yana lumshe, idon shi a hankali, Sai ji mu kayi yana cewa su na lafiya, Baba, da alamar mai shi ya tambaye ni sai miko min wayan Yaya Abubakar yayi da sauri na karba ina cewa, Baba ina wuni ? Daga murya nagane cewa Baba Buhari ne maihaifin Yaya Abubakar don haka nakara dan magana acikin girmamawa,, Sai addu,a Baba yake muna akan Allah ya bamu zaman lafiya tare da samun zuria dayyaba, Baba Buhari yace Aminatu muna alfari dake don zuwan ki cikin rayuwan dan Uwan ki,ya kawo canji sosai, Hakki Aminatu Ubangiji shi yasan yadda yake tsara abinsa cikin ikon sa da mulkin sa, Baba na gode nace don in takaita maganan Saboda idona da ya kawo hawaye, a lokacin Saboda yadda nake jin maganar ta Baba Buhari yasa jikina yin sanyi, Baba Buhari yace, Aminatu idan Allah ya so mutum da alkhari ko arziki ba wanda ya isa ya hana, Hakana kana zaune zai kawo maka har inda kake zaune ta inda baka zata ba,, Nasan kina kokari sosai gurin gyara halaiyyan dan Uwanki, Zamanki a tare dashi ya kawo muna cigaba sosai a rayuwan gidan mu, Murmushi nayi wanda har sai da Yaya Abubakar yadago kai daga abin da ya keyi, ya dan kalle ni, tare da kura min ido , Salawatu dake daga gefe, ji take kamar ta shakeni a lokacin don batai zaton cewa zata samu matsala daga gare ni don tasan cewa auren hadi akai min da yaya Abubakar ba wani so a tsakanin mu, Na mika masa wayan tare da cewa to Baba mun gode Allah saka da alherin sa, Yaya ya karbi wayan tare da karawa a kunen s yana mai cewa Baba sai anjima mun gode fa, Salawatu dake zaune kamar mutum mutumi hankalin ta yai mumunan tashi, Laila yanzu ta gane ta kuma fahinci, cewa akwai matsala sosai daga bangaren Meenat Wace take wa kallo da farko ba komai bace ita a rayuwan Abubakar din, Sai yanzu ta kara tuna cewa Meenatu ce fa taso hanata shiva gidan Abubakar tun farko saboda auren ta da iyayyen shi ke son yayi, Lai tayi mantuwa abaya datake wa Meenatu kallon Dan Hakki,,,, Ba shakka ba kowa ya katse mata sanadin jin dadin ta da walwala ba sai wanan yariyar karamar alhaki, Don da farko akwai so da kauna mai karfi a tsakanin ta da Abubakar, din ta, Amma tun fara zancen yatinyar ta barar mata da gwaunatin daga gare shi saida tayi da kyet tasamu shiga gidan, Magana Yaya Abubakar ke mata yana tambayan ta, ruwan maganin da yace ta aje mai da rana, Amma hankalinta sam baya gurin ta don ta na can ta lula duniyan tunane, Firgigit ta ansa mai tare da mikewa don ta dauko mashi, maganin nashi, Ta, dawo ta aje maganin ta juya tana cewa tan zuwa don Allah, Ido Yaya Abubakar ya bita dashi don ya fahinci tana cikin yanayi, Wani irin gumi ne ta ji ya zubo mata agoshin ta kamar wace ke cikin ovon, Ita kadai a daki take cewa Meenat kin yi kuskure wallahi baki san ko wace Salawatu ba da ba tsaya a gabana ba, Baki isa ki tsaya min agaba har Abubakar ya kalle ki a matsayi mata ba wai, Dole tun yanzu tafara ya ki da duk wani abin da zai sai Abubakar ya kula da Meenatun, Zan iy kokari inga cewa babu wata mace a gaban sa bayan ni, Sai dai muna fukan iyayyen nan nasu da suka hada auren nan su raba shi nan ba dadewa ba A can falo kuma duk zaune muke a takure sai yaya Abubakar wanda ke ta faman aiki a cikin computer shi shi kadai, Muryan Anty Sadiya ce na ji ta kira sunana tana cewa, Meeanat jiki yai sauki ko ? Na,dan yi murmushi tare da dan dago kai na ina kallon ta nace,, Da sauki Anty, Ta ce Allah ya kara sauki Ameena, na ansa da shi, Ya Abubakar dake aikin shi yadan dago kai a lokacin yace hmmm Kin sha maganin ki da daren nan kuwa ? Nadan sunkuyar da kai,na kasa na fadin sai na koma zan sha, Jikina ya bani cewa ya tsureni da ido, don haka na kasa dago kai, don kada mu hada ido insha fada, Dan motsawa nayi kadan murya kasa kasa na,ce ai yanzu zan tafi in sha,, Salawatu da ke tafe tun daga nesa ta hango lokacin da yaya Abubakar ya tsura min ido yana kallo na Abinda ya kara tunzurata ya kona mata zuciya ainun, Zama tayi tare da cewa, ka,kare ne, da cup din in dauka, ? Ya zura mata ido can yace ba haka kika aje min shi ba kibarshi kawai sai zan kwanta zan sha ai, Namike da niyar in shiga insha magani ai in kwanta, Nadan waigo gurin da suke gaba dayan su ina cewa sai da safen ku ni zan shige, Salawatu ta wani bata rai, ta kauda kai gefe tana cewa, Allah tashe mu, Anty Sadiya tace a irin muryan na nata mai nuna kasala akoda yaushe, Allah bamu Alheri ? Na ansa da fadar Ameen ma, gaba dayan su,,, Maganin nafara sha sanan na gyara jikina don kwanciya, ****** ********* ****** Yau Anty Samira tun da safe take tashirin zuwa gida don ta wuni, Cikin ta zuwa yanzu ya fito sosai don haka, da ka ganta zaka san cewa ta kusa haihuwa,, Dan vesper tashigo daga Badariya zuwa unguwar su shiyan Sarakuna, Sai dai mai yar vespan ya kasa karasawa da ita har cikin uguwar nasu saboda yawan yashin da ke shiyan sosai, A hankali take tafiya da kafa don ta karasa gidan su, Baba Buhari saman sabuwar mashin din shi sabuwa fil, da ita, Tun daga nesa Samira ta hango Baban,azuciyar ta ke cewa kai Allah sarki Baba ho ko ina kuma ya samo sabuwan mashin haka ? Shikuma Baba ya hango diyar nashi wace ke tafiya guda guda don nauyin ciki, Cikin dan murmusawa yace a,a Samira ta? Ta amsa da fadin Ni ta Baba, Mun samay ku lafiya ko ? Wallahi Samira lafiya kalau Yau naka batun zuwa shiyan ku in gwada maki abin arzikin da Yayan ku ya sai min, Ido Samira tafitar tana iye Baba shin ka dai ince mashin dinga taka ta ? Samira Yayan ku ya sai min ita yau kwana uku ke na, A,a lailai kan Baba mun ko yi murna wallahi, to ki buga mai ki mashi godiya ke ji, Yace zan tafi inyo cefane a can yar kasuwa, Anty Samira tace Baba a dawo lafiya Allah ya tsare,, Ya ja mashin din shi Samira ta bi mahaifin su da kallon tausayi , Azuciyar ta ce Baba mutum mai saukin kai wanda ba ruwan shi da girman kai, A dan gajiye halin irin na masu ciki Samira ta karasa gidan su, Sai da ta fara gaida malam tsoho, wanda ke waje da jama,an shi, Inda yake ta mata ba,a akan cikin ta tare da tambayan lafiyan maigidan ta da jama,an gidan su, Sai da tafara zuwa sashen mama Saratu ta gaida su tare da sauran mutanen gida, Gurin Mama Sa,a tafara shiga kafin ta karasa gurin mahaifiyar su, Cikin fara,a da jin dadi Mama Sa,a ke cewa a,a lalai marhabin da mutanen Badarriya, Samira ke ta kikai nauyi haka ? Gaskiya tubarllaka ciki na miki kyau, Dariya Samira tayi tana cewa kai Mama ho, takau da zancen da cewa ashe Baba yai sabuwar amarya na ? Dariya suka gaba da yan su atare Samira tace Allah yasa a more, Ameen inji Mama Sa,a tace ai,dada fa huntuwa tayi zani, Dariya Samira tayi tana cewa ai yanzu sabuwan bazawara zata lake mai, sai tashigo, Mama Sa,a tana dariya tace tazo aiga gidan nan gwalmaddiya,i, Allah dai yakara daukaka Abubakar yasa amorewa saura Ameen inji Samira ta saikai tafita zuwa sashen Mama Ladi,, Sanan ta karasa sashen Mama Ladi a gajiye ta jawo kujera yar tsuguno na mata da ke gefen dakin Mama ta zauna, Tana cewa wasshi Allah walle duk nagaji sai kace da kafa nai tafiya, Mama Ladi wace ke zaune saman tabarma a kofan dakin ta tamike kafan ta don taji dadin zama, Ta ce wa yar nata yau kuna kun ka tuna da mu, Samira tace Mama yanzu banjin dadi komai wallahi ko dazan tashi kafin a ce haka komai ban yiba sai dai dare yayi, Mama Ladi tace me munafukanga ka fada maki ? Naji ta tun daga can tana ta tsiyaya adole taji dadi sun samu mashin din banza sai atai zuwa hawa yanzu ai kiga zuwa anguwa ya tashi, Dariya Samira tayi tare da kada kai tace mama in kina so aikema goyaki zaiyi, Allah dai ya sauwaka min, min zanyi saman mashin da malam Nan suka fara gaisawa Samira tana tambayar lafiyan jikin Mama, Sai kuma Mama Ladi ke cewa shin wane shiri kin kayi zuwa yanzu akan haihuwan ki ? Mama shirin mizanyi haihuwan farina fa zanyi, ? To, nan kin ka labe ko ? Kina jiran aimaki? To Mama mi zanyi, nawa nake dashi nida ba ni aikin komai, Har za,a sa ran, a samu wani abu gurina Mama ? Cikin daure fuska Mama Ladi tace ke tsaya kijiya keji, Inkina kawa abinda aggareki ki kawo aba yan uwan ki su kara suyi maki soye,soye da shi, Take Samira fuskan ta ya matse a lokaci guda don tasan cewa maganar gaskiya Mama Ladi tafadi abinda tace shi din za,ayi, Samira rayuwan ta yabaci matuka inda tafara fushi tana cewa yanzu ya akeson inyi banda kudi kuma shi ba aiki ya keyi ba, mama kin sani, Rayuwan Samira abace yake, har akai sallah zahar sai fushi take faman yi taki sake jiki ta, Daga inda take kwance tunanen Yayan ta fado mata, arai sai dai kuma zuciyan ta na tuna mata lokacin da yayanta ta Safiya ta haihu, Alokacin ya,na aiki a Lagos da ta buga mashi waya tana tambayan shi, akan ya taimaka mata da abinda zasu yi dawai niyar buki, Amma sai yace sai mama ta kirashi ta fada mai saboda ya na shakar ya bata mama tai masa fada, Don haka Mama ya turo wa, da kudin da ta nemi taimakon, Ita kuma Mama ta kuma karbi, na hannu Safiya ta hada batai mata koma ba,, Shiyasa take tunanen cewa ita irin na Anty Safiya ake son yi mata ke nan, Taso sai da yamma ta koma gida amma saboda zancen da mama ta tare ta dashi yasa ta komawa gida da karfe uku, na rana, Tanan har dare bata iya yin wani abin kwarai ba tana ta faman tunanen irin mahaifiyar da Allah ya basu, Yanzu ita yaya zatayi da wanan zancen gashi yan uwan ta kowa tana fama da laluran rayuwan ta, A take wani tunane yazo mata a zuciyar ta wanda taje ganin gara ta gwada taga sa,an ta,,,,,,, ****** ********* ****** Zaune nake a bakin Mirro na fitowa na ke nan daga wanka, ina son in shirya in, fita falo kafin mai gidan ya shigo,, Kasancewa yau nice da girki duk abin ya bani mamaki kwarai don kusan tare da Anty Sadiya mukai aikin, Don ita ce ta gyara min falo acewan ta banda lafiya bari ta taimaka min da aikin, Waya na dake caji saman mirro gefe guda dan nisa kadan da gurin da nake zaune, Da sauri na mika hannu na dauki wayan Anty Samira nagani baro, baro a saman screen din wayan, Da sauri nadauki wayan cikin murna da jin dadi ina cewa sai Anty na, Ta,ce a,a wallah wace Anty bayan an manta damu, Nadan tausa murya tare da langabe kai tankar tana gani na, Nace a,a fa anty Samira aiko dai kin san ina da kokarin bugo maki waya, Anty Samira tace yaushe rabon da ki bugo min waya Meena ? Anty keep n san munyi tafiya da yayane wallahi bamu kasan mun tafi makwabta, Kuma koda muka dawo wallahi ban da lafiya ne anty da fever na dawo , To na dai jiya yanzu ya kuke lafiya Anty, Takara tambaya keji sauki dai ko ? Nace insha Allahu Anty, Sai kuma tai shiru can na ce Anty ya Yaya Munbashir ? Tace yana lafiya, Nace to yaya tsufa Anty ? Sai naji ta nisa tai shiru kuma can tace cikin wani irin murya mai sa mutum yanayi, tace, Meena ke dai san halin Mama ba sai na fada maki komai ba, Wai zancen kayan haihuwa ne yau mun ka kwasa da Mama tace wai sai na kawa kudi sanan za ai min GARA,,, Uumm,Ummm nace itakodai mama ina zaki samo kudi hakana ? Nace, yanzu anty yaya za,ayi ga yan gidan mijin nan naki basu da mutunci, Kin san na aure ma har ankai wani lokaci suna gori akai, Ta nisa tare da cewa bari kedai Meenat shiru muka yi zuwa can nace Ke fadawa yaya ne ? Cikin wani irin dan ihu ta ce, wacce ? Niya, ? Barni in mutu ina Samira na, Baki san yadda akayi dashi ba lokacin haihuwan, Anty Safiya, Na katse ta da cewa kinsan yadda za,a yi zuwa karfe takwas daidai ki bugo waya kada ki bari a wuce takwasa din kinji Anty, Tace cikin jin dadi to Meenat nagode nagode kinji, Haba dai Anty may na godiya Allah dai ya sa mu dace, Mun kashe wayan zuciyana duk ba dadi saboda, irin abinda Anty Samira ke fada min Abinda nafara yi shine jin haushin wanan irin al,ada na mutanen mu na kashe zarahi, Abu tun iyaye da kakan ni har zuwa yanzu yaki mutuwa, Sai ma kara yiwa abin kwas kwarima da aketayi yanzu, Sai kuma Mama Ladi wace ban san wani irin rayuwa gareta ba da har da diyan cikin ta take ma mugun hali, Mikewa nayi naci gaba da abinda na keyi don gyara, ko ina , ****** ********* ****** Tsab na gyara jikina acikin wani material purple mai dan design din flower light, chuculate, Dinkin, riga da skirt akai mun, dan kwalinshi yana da sulbi sosai don haka daurin danayi mai sai yai kamar style nayi, Dan hill shoes kamar kullun na saka ma kafana, Don ance sa takalma mai dan hill yana kawo wa mace hip's, Mai mai kamshi na dan murza na daga rigana na shafa kasan nono na da sama har zuwa hamatana, Dama na feshe kaya na da turare masu kamshi da dadin shaka, Daga dakina naji tsayawan motan yaya Abubakar hakan yasa nasan yadawi daga sallah ke nan, Fitowa na yai daidai da shigowan shi falo Salawtu, tana zaune a falo ta kurawa kofan shigowa ido, Wani irin muguwan harara ta sake min tare da nuna kishin ta gareni filin Allah, Murmushi dauke a fuskana na nufi hanyan shigowa ina cewa, Sannu da dawowa Yaya,? Ina kokarin karban brief case din dake hannun shi, Murmushi ya sakar min har a cikn zuciyar shi yaji dadin ganina haka ? Daga inda take zaune take cewa you are welcome oga, How are you my dear ya amsa mata, Batare da ya tsaya, falon ba ya bi bayana alokacin na fara hawa steps din hawa saman shi, Wani uwar harara Salawatu tawatsa min tare da sake tsuki tana cewa yeye girl, You will know my true clour soon, Murmushi nakeyi daga infa nake ina cewa sai kace ba renon anty Amarya ba,,,,, ZEEE MAKAWA YELWA [8/14, 09:06] Anty Lantana: 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 5⃣3⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA ALLAH - AL-JALEEL,,,,, Already na riga na gyara mashi dakin sai kamshi ke tashi ta ko ina, Na,wuce gurin side drower, na aje yar briefcase din a hankali, Yana tsaye da ga kofan daki ya harde hannayen shi, kafafuwan shi ma a harde suke guri guda, Wani irin kallo yake min cikin nuna so da kauna acikin wani irin yanayi, Shidai har kull bai gajiya da mamakin irin yadda halittuna suke, Duk da wai wasu mutane kecewa muna da kama dashi sai dai tsayi ne da ya,ke shi namiji ne ,, A hankali na nake takawa har zuwa gurin shi,, Kafin in karaso ya ware hannayen shi biyu na shige ciki, Wani irin ajiyan zuciya naji yana saukewa ya fadi a hankali miss you sweet sister, Kara shigewa nayi cikin farfadan kirjin shi da yai min masauki dashi, Kamshin jikina naji yafara shaka yana wani lumshe ido kamar wanda ke cikin maye, Bakina ya nemo ya manna nashi a ciki abinda ya dan jawo min rawan jiki, Don ni har kullun jin Yaya Abubakar nakeyi kamar sabo a gareni, Yaya Abubakar din shi dayake tsohon hannu ne yana sane da irin re,action dina kullun, Hakan ne ma yasa yake kokarin ganin cewa ya kawar min da kunyan shi gaba daya, A cikin yanayin da muke ban aune ba sai jina nayi a saman gadon dakin Yaya Abubakar Bayan komai ya lafa a tsakanin mu a hankali na mike zaune ina kokarin saita kaina, Shiko ya Abubakar din mirginawa yayi gefe guda yana sauke numfashi a hankali, Zuciyar shi fam da tunane, Murmushi yayi irin mai ma,anan nan yana cewa hmmm,Meenat,,,, Wayan shi yai kara a daidai lokacin da nake kokarin mikewa don shiga bathroom in hada mai ruwa, Ji nayi ya jawone da hannun shi guda abin da yai sanadiyan nadan fado mashi a jiki, Ganin kiran wayan zai katse yasani mika hannu na dauko mashi wayan, Samira nagani an rubuta, don haka na mika mashi tare da cewa Anty Samiran gidan mu ce ke kira, Yaya Yar tsuki yayi tare da magana acikin yanayi yana cewa, May kuma ya faru take kirana, Da sauri ina kokarin tashi zaune, bakin shi na fidda tsuki ya dauki wayan nata acikin wani irin murya, Samira Yaya dai ? Ita kuma bayan sallama tana cewa Yaya ina wuni, A hankali natsuwan shi ke dawowa ajikin shi don haka na zauna bakin gado inji yaya zasu kwashe da yar uwan shi, Jina yi ya ce, look Samira, ni maye nawa a,ciki, ba Mama ce ke gudanar maku da wanan harkan ba, Da,sauri na kalleshi, muka hada ido sai na canza annurin fuska na gaba daya na hade rai, Anty Samira dai bata gane komai ba sai yar fadan da ta samu, sukayi sallama, Ban taka masa ba sai mikewa nayi zuwa bathroom na hada mashi ruwan wanka, Nafito ban tsaya,ba fuska a dan daure nace ga ruwan wanka can Yaya, Gurin Wardrobe din shi na nufa ina son in dauko mai kayan da zai sa, idan ya fito, Daga inda yake,tsaye, yake ce min, bazan samu cudawa ba ke nan, Gurin gado na nufa na,fara gyara,gadon don duk mun chukwikuye shi kamar bashine na gyara dazun tsab ba, Ya,shige bathroom ni kuma na fito zuwa, daki na don in kara kintsa jikina saboda Yaya ya bata min shiri, Salawatu bayan shigan mu, takai yan mintuna zaune a falon taga ai ban sauko ba, Don haka sai taji tankar ta kama da wuta don haushi, kishi nata azalzallar ta, Kusan sau uku taje ta dawo, taje ta dawo don taga ko na sauko sama, Abincin dake jere a saman dining table tariga da tun shigan mu tai masa ta,asa, ko, Wanka na shiga na gyara jikina tsab, kamar bani bace, dogon riga na sa wanan karon, Misscalle din Anty Samira na samu har uku, ta kirani don haka na,dauka ina ce mata, ta ai ina gurin naji yadda su kayi amma ta bari zan kirata insha Allah,, A gurguje na fito falon fuska hade don yau kan gaskiya mun makara sosai ba mu ci abinci ba, Anty Sadiya bata wasa da cikin ta tana falo zaune, tana jiran fitowan mu tare muka fito da maigidan don zan shiga kitchen naga saukowar shi, Jug na,dauko wanda na hada muna zobo,drinks a cikin sa, Salawatu ce karshen fitowa fuskan ta tamau, ba bu walwala a cikin sa, Ni dake da girki nice zaune a kusa da Yaya Abubakar, ina zuba mai abinci a plate, Sadiya itace tafara cin abincin tana kai cibi a baki sai tai saurin furzarwa, Cikin wani irin murya na mamaki tace Meena, ? Tana mai min wani irin kallo, Abincin na kalla sai kuma na,dago ido na kalleta, Kafin in sauke idona sai naji Yaya Abubakar daga gefe na ya furzar da nashi wanda ya fara kaiwa baki, Yaya akayi haka ne wai ? Ya tambaya cikin bacin rai da kuma mamaki fuskan shi a daure, Diba nayi daniyar inji may suka ji, gishiri ne kamar zai daye bakin mutun don kaifi, A hankali nace gishiri a girki na ? Sai kuma nai murmushi ce, to nima ban sani ba don ban girki da gishiri ni, Sai dai ban san ya akayi kuma gishiri ya shiga ba, haka don ban ko ga roban salt din ba ma ni, Salawatu tace bama zan ko ci ba don ban shiri da gishiri ni, Amma dai ai ya kamata ki kula da yadda zakiyi girki kada adinga barnan abinci, Sai da na rausaya kai kadan ina mai kokarin maida abinci a cikin kula nace, Sai dai kuma ba yaune farkon girkina a gidan miji ba ban taba samun akasi akan girki ba, Yau din ma dai kalau nai girki na don min ina da shedan hakan, Enough please na fada maku cewa ba zan lamunci, cacan baki ko wani abu irin haka a gida na ba, Gaba dayan mu shiru mukayi yayin da shi ya mike ya suri keys din motar shi yafita batare da ya ce wa kowa komai ba,, Na kwashe kayan rai bace na mayar kitchen, ga abinci lafiyayye amma na rasa yadda zanyi da shi, don bai ciyuwa, Daki na shiga na kira fatu ina tambayan ta ko hamza yana gida, tace yafita tun,da yagama cin abincin da na basu, Nace don Allah Fattu ko kinji yana cewa da gishiri a ciki tace a,a don cewa ma yayi zai kara gishi don baiji mai ba, Saida mama tai masa fadan cin gishiri shi ne ya fasa zubawa, Ajiyan zuciya nayi don nagane cewa sheri akai min a gidan don a hadani fada da Yaya Abubakar, ****** ********* ****** Cikin, murna ta daga wayan ta tana kiran noban Lubuna , A a matar Oga ya akayi ne wai, ? Hmmm bari ke dai Lubuna ai kwanan nan ina cikin yar damuwa wallahi kin san wanan shigiyar yarin matan Abubakar tazo, Wai kin samay irin yarinyar tana son ta raina min wayyo sai don wallahi ban taba tsanmanin zan samu matsala daga gare ta ba wai sai gashi akan ta Oga yana ta wani rawan kafa, Dariya mai sosa rai Lubuna taiwa Salawatu ta dan dakatar da dariyan tana cewa, Kema ai kinsan dole ne sai, kin samu irin wanan challenges din daga wurin shi, Nafarko fa yar uwar shi ce yarinyar and so what inji Salawatu,, Murmushi Lubbuna tayi tare da cewa becareful my friend, don komai zai iya faruwa fa, Daga haka Salawatu taci gaba da bata rabarin su irin yadda zaman su yake a yanzu da kuma sherin da fara kulla min a gidan, Da kyau nawa inji Lubbuna kawai dai ke ma don kina son sa ne in bashi ba may zai sa ki tsaya wahal da rayuwan Akan mutum guda har nawa zai iya baki da zaki wani tsaya har ana wullakanta ki haka ? Ni mamaki kike ba may yafi mazan da kike hurda dasu a baya, ? Look Lubbuna ban son yawan sa ido fa ni dai nace maki ina son abina haka na, Sai kin ji ni again bye ba zan iya sauren kina tofa bakin ki akan abin da nake kauna ba, Daga haka ta kashe wayan tare da jin haushin aminiyar ta wace ke kokarin zagin rabin ran ta,, Komawa tayi saman godon,ta ta zauna tare da bushewa da wani irin dariya tana cewa, Yarinya dani kike zance an fada maki cewa, ni din ta wasa ce, Don dole ki bar min a binda nake kauna ko kuma ki zama yar kallo a gidan nan, ****** ********** ****** Take away ne ya shigo dasu daga waje kowa guda guda da naman rago mai zafi irin na gargajiya mai yawa a leda kowancen mu da na ta kumshi,, Tun bayan abinda ya faru zuciya na yaki yi min dadi saboda irin yadda nake ji a raina, Saidai ma ko waye nabar mai shi da Allah abinda kawai na ce ke nan, don idan nace zan yi bincike ta ina zan fara, Amma dai muje zuwa da mai shi don nasan idan halin mai shine gobe ma karawa za,ayi, Tun daga nesa nake jiyo karan cibaben spoon su suna kara,, Kamshin naman ya doki hanci na har sai da naji shi har cikin rai na, Maimakon in nufi dining table din inda suke sai kawai, na, nufi gurin kujera na zauna, Fuskana babu yabo babu fallasa, acikin sa don haka bazasu iya gane halin da nake ciki ba, Ido Yaya Abubakar yabini dashi don bai fahinci may nake nufi ba, Anty Sadiya ce tace Meenatu zo mana ga abincin ki ki ci, Yayan ki ya leka ya samu kina sallah yace don haka muka fara ci, Cikin dan murmusawa nace anty bazan iya cin abinci ba yanzu, Yaya Abubakar dake kokarin kai abinci ga baki yai saurin juyowa yana na kallo na, Cikin daure fuska yace baza kici ba may ki ka ci da zaki ce bakya ci Na girgiza kaina ga da cewa babu ko mai kawai dai ban jin cin abinci ne, Ban yarda ba in ji Yaya Abubakar, don babu abinda kikaci balle ki ce bakya cin abinci, Murmushi na dan sake na ce wallahi Yaya kawai banjin cin abinci ne, Anty Sadiya tace ko jiyafa haka ki ka ki cin komai Meenatu, Ki dauki ko naman ki ci inji, Yaya Abubakar yace a cikin dan yanayin damuwa, Gaskiya inji Salawa don dai kinga, zai yi sanyu in baki ci yanzu ba, Na mike daniyar in dauki ledan naji sallaman Hamza, Kulan da na basu abinci shi da abokan shi ya dawo min da shi yana cewa Ina wuni Sir sai kuma yake cewa su Anty sannu ku fa ya gajiyan gida, Anty yake ce min duk da ya girmayni ni sa ba kusa ba amma saboda girmamawa ya ke ce min haka na Anty munfa gode abinci ma da wasoso muka cinye kin san kuraye na awajen, Nace, Baba Hamza da gishirin kuka ci abincin hakana ? Da mamaki ya dan tsayar da tafiyan da ya,keyi yana cewa gishiri ? Ai ba hishiri a ciki wallahi don har na aika mama ta bamu gishi taimin fada wai in daina vin gishiri hakana bakyau, Wallahi ba hishiri acikin sam, Gaba dayan su ido suka sako muna suna jin yadda muke zance da Baba Hamza, akan abincin da akace yana dagishiri aciki, Nace to mukan namu gishiri ya hana muci shi wallahi, Baba Hamza wanda nakewa karan suna saboda Baba Hamza kanin mahaifan mu, yace Kai wana maganace kawai don wallahi bani kadai na ci abincin ba gaba dayan mu awaje kowa ci babu kuma wanda ya ce gishiri, Wani irin shu umin mirmushi na sauke don ko yanzu Alhamdullahi na samu sheda Kitchen ya nufa ya ije kulan da na basu abinci a ciki yafito yana cewa Sir a rufe get don zamu watse zamu kallon Ball ne, Muryan yaya Abubakar ya na cewa Hamzo zoga wani abincin ka dauka ko? Take way dina na bashi tare da diban masa naman dake gaba na mai yawa so sai, Sai godiya yake ta zab gawa ya addu,a tare da fatan alheri ga maigidan da mu,,, Babana Hamza na fita daga falon na sauke wani irin gwauron numfashi take, nafara dancin nama na a hankali, Ina korawa da ruwan holandia, milk mai sanyi dake gabana, Zuciya na tai mun tas don Allah ya wanke ni daga TARKO da aka dana min Yaya Abubakar tunda ya duka ya fara aiki a system din shi bai dago kai ba, Ko ba,a fada ba nasan ran yan mazan ya baci ke nan yau, Nice ta farko mikewa daga bin dokan da akasa muna na zaman dole falon, Zaman da kusan duk a takure muke sai dai Sallawatu wace da farko tana dan jan shi da hira, Amma da taga tai magana daya biyu ba ansa tai shiru tama fara waya, wai tana gaisawa da mutanen gidan su, Daki na koma inda na fara shirin zuwa turakan maigida, Yana daga zaune ya hango ni lokacin da na shiga kitchen don in dan sa ruwan zafin Lipton a wuta, Don yanzu shan ruwan Lipton ya zama min kaman wani kwazaba shan shi na keyi sosai, Hakan yasa shi duba time din system din tare da dan sauke hamma, Tun fitowa Anty Sadiya ta mike tana kokarin hada yan abubuwan ta a hankali ta dan dubi gurin da Yaya Abubakar yake tana ce masa sai da safe ni zan tafi in kwanta, Kofan dakina na rufa ina saye cikin wani zumbulelen hijab sai kamshi ke tashi a jikina, Hannu na yana dauke da dan flasks dina da cup dan karami, Na tsaya inda Yaya yake zaune ina cewa zan kwanta Yaya Na juya gurin Sallawatu wace keta wayan karya da dariya nace to sai da safe ko ? Kai kawai ta gyada min ba tare da tace komai ba wai ita tana waya, Ban ko kai ga karasa hawa steps din ba naji shiru banji muryan ta ba, Ban dade da kwantawa ba naji shigowan Yaya Abubakar dakin, Bathroom yafara shiga yadan jima ciki yafito, yana saye da wani dan wandon boxer, Injin ya kashe fitilan dakin a lokacin har na dan fara barci, Ta baya naji ya rungomini yana cewa yau barci kike jine haka ? Cikin yanayin mayen barci nadan bude idanuwa na da suka fara nauyin saboda batci, Jikina gaba daya ban jin dadin shi, don haka nake kwanakin,nan idan dare yayi, sai inji zazzabi a jikina, Yaya Abubakar ya ce ga jikin naki da zafi mana Meena ? Dan murmushin karfin hali na sake nace haka nake duk kwanakin nan,ai, Cikin murya mai kama da fada yace shine baki fada min ba mu koma asibinti akara dubaki, Yaya haka yanayin zazzabina yake sai a hankali zai dai, Are you sure ? Nace wallahi ko Yaya da sannu zan daina jin shi ai, ya amsa da fadin OK Sai naji ya kara matse ni a jikin shi ya na sauke ajiyan zuciya a hankali, Cikin wata irin siririyar murya nace, Yaya ya amsa a hankali da fadin na,am , Nace dazun kaman da Anty Samira naji kana waya ko ? Ya ce itace mana, Nace haba Yaya yanzun fa kune iyayyen mu, don Allah ya hore maka shekaru ilimi da kuma abin duniya, Kamar yadda kowa ke kokarin ganin cigaban gidan su, At list ace akwai wani jigo wanda idan wani abu yw taso zai tare,, Ya ansa ciki ciki da fadin hakane , Nace to yaya ai ina tsan manin ba Anty Samira ba ko mu da bamu fito ciki guda da kai ba a yanzu zamu iya neman taimakon ka ka ba mu , Umhmmm inajinki ya ce, nace yaya don Allah ka taimakawa yar uwanka kamar yadda Allah ya taimake ka,, Shin kin manta da halin Mama ne Meena, yanzu ina bata Mama zata ce don may na bata, Sai a lokacin na juyo muna fuskantar junan mu nace, Taimakon tsakanin ka da mu yan uwa ka daban ne ba dole bane sai Mama taji In yaso ita kuma Mama sai ka tura mata da nata kace gashi ayi sha,anin haihuwan Samira dashi kaga ai baka tauye kowa ba, Nadan marairaice murya na nace, Ko ya kagani yaya ? Amsa kamar a ikin bacin rai da cewa, shike nan naji Kice ta turo da account nomban ta zuwa Wednesday nace to Yaya mun gode, Ban san lokacin da na kai hannuna a jikin shi ba nafara shafa,,,, ZEEE MAKAWA YELWA 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 5⃣4⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA ALLAH-AL-KAREEM Yan Uwa Massoya ZAINAB MAKAWA Da Novels, Dina Ina Kara Mika, Godiyana, A Gare Ku, Kau,nan Da Kuke Gwada Min Banda Bakin Da Zan Gode Maku Akan Shi Sai Dai, Ince Allah Ya Kara Rufa Muna Asiri, Don Na Samu Alheri Sosai Daga Gare Ku Massoya Na, Ubangiji Allah Ya kara Rufa Asiri Ya Sawa Sauran Dukiya Albarka,,,,,, Nagode Nagode Abin Daga Allah ne Kawai, Alhamdullilahi Ala Kulli, Halin👏👏👏👏 Ba sai na fadi sunayen ku ba duk inda kuke kun san kan ku nagode kwarai wlh,,,, Abin duniya duk ya taru yai mata yawa a rayuwa don babu dama tashiga taron mutane yanzu, Sai a fara gudu a na cewa ga manya, ga manya nan, Saboda banda gidan malam tsoho ta kara shiga wani gidan buki kusa da gidan ta, Iskan kusan mata biyar ya tashi a gidan ranan da kyat tasha don sun mata mugun shaka, a wuya, Hakan ya ba mutane tabbacin cewa ita muguwa ce ta sosai, Yanzu diyan ta da yan uwanta da ya zama ma dole sai sun shiga gurin ta ne kawai ke shiga gidan ta, Ta zama mujiya a cikin al,umma, sai dai maza su wa yanda take sana,a da su basu tsoron ta don sun ce ai in ma maya ce bata cin mutane akwai dai irin sihirin da take yi, Don haka su kan je neman hayan mashi ko yar vesper gurin ta don tana dasu tana bada hayansu, Abin da tafara hankalta (kula) da shi yanzu shi bata samu kamar farko, Yadda Dodon ta kan mata aman kudi da farko yanzu sam baya yi, Bai wuce a sati yai mata sau guda ba ko sau biyu kuma basu yawa irin farko, Kai ta gyada tare da kuftawa, tana cewa a ranta ba kowa ya fara jawo mata matsala ba sai wanan mugun tsohon malam Manya, Yanzu bata da aiki sai na wahalan jan ruwa daga rijiyan gidan ta ko famfo zuwa cikin randan da ta boye dodon ta a ciki, Matsala guda shine yanzu boka yai nisa dasu wai ya koma can dajin Bargu da zama,, Saboda yanzu baya samun wani alheri a nan addini ya ratsa zukatan mutane, ba kamar farko ba, Don yai wa wata mata aiki, bayan Mama Ladi itama matar ha gida ta mayar mai da kayan shi tai ta mai tujara da tonon asiri, Yadda akayi shine, matan tazo gurin shi da kukan tana son sana,a don duk abinda ta rika baya zama kudi, sai ya lalace, Shine yace ta kawo sabon kwarya wanda ba,a taba aiki dashi ba, Jiki na rawa takai masahi sabon kwaryan yace ta tafi bayan kwana uku, ta dawo, Da ta dawo ya bata kwarya da wasu duwatsu guda uku, acikin sa, yace ta boye inda babu mai gani, Dukiya sai dai agani a wajen ta ta bashi dubu uku kamar yadda ya bukata, Ta tafi gida tana murna da jindadi takai kwaryan ta can ta boye karkashin gadon karfen ta, Kaman kwana biyu cikin dare sai ji tayi wasu irin manyan tsuntsaye har guda uku sun tashi daga dakin ta zuwa, Saman rufin dakin basu bukatan wai saman ya bude duk da rufin kwano da dakin ke dashi, Bata kara barci ba tana zaune har zuwa asuba sai ganin tsuntayen nan sun dawo suna ta amai a tsakiyan dakin ta zaban tausayi, Hakalin matar ya tashi matuka saboda yadda taga wanan halittan suna amai, Kafin wani lokaci sai taga kamar hayaki sun koma cikin kwaryan da ta aje a bayan gadon ta sun zama kamar duwatsu, Juyowan da zatayi sai ganin wanan aman da sukayi tayi ya koma mata kudi gudan mai yawa, Innalillahi ta fara fadi ga bakin ta tana cewa wanan mugun maita ya bani ashe,? Badani ba sam bazan karbi wanan fitinar ba gaskiya sam da sake, Tun da safe da kudin da kwaryan ta kwasa ta mayar mai da abin shi tana kokarin tara mashi mutane a gida, ****** ********* ****** Anty Samira bata bata lokaci ta turo da account din wata kawar ta, Ya Abubakar ya tura mata da dubu dari a ciki, ina barci da rana musalin sha biyun rana, Saboda girkin Salawatu ce gaba dayan mu ni da Anty Sadiya muna daki kwance abin mu, Ta manta cewa mu mutanen hausa ne kishi dashi aka haife mu na tsabata bawai na sheri ba, don tun muna yara muke taya uwayen mu kishi, mun san kan zama da mutane iri, iri, Zaka fan mu kamar kauyawa amma zama da mu wahala gare shi don kar muke kallon ka, Karan wayan Anty Samira ya tayar dani barcin da na keyi badon naso ba, Cikin muryan barci nace Anty Samira ya kuke ya gajiya, Tace Meenatu an bansan ko me zancewa ba, don na rasa kalman da zan maki godiya, Na ce, a,a wallah na mi anaty ? Shin Meenatu ke ko ga kudin da yaya ya turo min? Har fa dubu, darin ya turomin dasuwa,, Nace cikin sakin fuska kai Anty Samira am nai maki murna, Sai atai zuwa shagali ko ? Cikin wani murya tace wani shagali zanyi da su duka, 'Dariya na sa mata don jin abin da tace, "Tace ke san dama ina son jari in fara yar sana,an gida irin na mata, Na, ansa da fadin gaskiya na Anty ke ga sai dai ki saro kayan su, turaren wuta, takalma da su manshafi masu dan dama, Tace Allah dai ya barki Meenatu, kaman kin san shawaran da ni ke nema ke nan, Cikin zolaya nace amma dai sai kin tai kin gwada ma Mama kudin ko kafin ki fara taba su,? Cikin wani irin murya da karfi tace, Wata,? Niya ? Ai in kin gani lahira maza su ka kaini,, ta dai jiya ga baki amma koshi sai angama sha,ani zan fada mata, Nace a,a ke ko Anty kaman yadda tace ki kai mata ko dubu goma kice ga su nan suna kin ka samu kawai, Shiru naji tayi can ta numfasa tace to shike nan ance ba,a kin shawara zan gwada yin haka mugani, Takara min godiya tare da kashe wayan ta, A hankali na juya ina mai lumshe idona wanda zuwa yanzu barcin da nake yi ya fita min ga ido ko, Don haka namike na bude drawer mirror na dauka comb da masillan kitso, Nafara sance kaina da ya fara yi min kaikayi don yana neman agaji, Tsab na sance na daure shi da ribon ta baya, sai dai ina a gaban mirror na ga ya dace inje wankin kai, haka nan, Waya na jawo na kira Fattu muka gaisa na dan tambaye ta mutanen gidan ta Sai take ce min Mama tana nan ta na biski wai zata kawo maki,, A take na tuna da zancen Yaya Abubakar gashi kuma ina sha,awancin wanan biskin da akai min tayi, a gidan Fattu, Don haka na kira Yaya Abubakar ina sheda mashi cewa ina son in dan mika kafa gidan su Fattu, Bai ha,na ni ba sai ce min da yayi a dawo lafiya na amsa da fadin Allah ya nufa na gode, A gidan su Fattu can na dan sake jikina muka ci abinci tare, da ita muna fira jafi, jefi,, Maman Bi,u sai dadi take ji na shigo gidan su duk ta rasa inda zata sani saboda murna, Munyi da Fattu zata rakani gurin wanke kai kamar yadda mu ka taba zuwa tare da , Sosai,naji dadin zama da su saboda sai nake ji tankar a gida Birnin Kebbi nake , Tunda na tunkari hanyar shigowa, gida sai naji duk jikina yai min sanyi , Zuciya na ya cunkushe min na dinga jin babu dadi, sam a rayuwata, Mutum yai ta zama batare da yai magana da kowa ba saboda kishi, da mugun hali, A falo na samu Salawatu, zaune tare da wata farar mace wace mai ya kodar da ita har zaka iya ganin kwancin jijiyoyin ta, Sallama nai ma su ban tsan mani sun karba min ba don haka ban tsaya ta kansu ba, Don ina kallon yadda gaba dayan su da zan shigo suke wurga min harara tare da jan dan guntu tsoki,, Nashige part dina ina kokarin bude dakina da key, Kunnena ya jiyo min lokacin da bakuwar Salawatu ke cewa wana ai batafi sha takwas ba ma, Murmushi nayi kawai na shige abina ba tare da na tsaya jin su ba don duk basu gaba na, Matar tace wa Sallawatu yanzu ma akan wanan kika tayar da hankalin ki haka, Shiru Sallawatu tayi tana sauraren abinda matar ke, fadi, can ta nisa tana cewa, Wata Adah baza ki gane bane aikin san dai koni wacece ko ? Matsalan na daga gurin maigidan nan don duk wasu dokoki da ya aza muna sai kiga komai a dole ya zama equal a gidan sa,, Matar tace ba matsalan komai na san yadda zamu fito mata, Sallawatu, ta gyara zama tace kin gane ne Adah nafi son ace, babu wata mace a tare da shi ko a gidan nan sai ni kadai, Matar da take kira da Adah tace kar ki samu damuwa, yanzu kifara kawo wanda zan fara zuwa dashi mu gani,, Yau manyan matane ke girki, a gidan don haka ta kasa ta tsare, taki gusa daga falon tana zaune don zan iya cewa a nan ta wuni ranan, A gajiye ya dawo gidan daga office don haka yau sai a hankali, Salawatu sai rawan kafa ta keyi da don ta na haka kada wata daga cikin mu ta samu kafan shige mashi, Ya shiga yai wanka ya fito duk muna daki babu wace ta fito, daga cikin mu, Hakan yadan sashi fara dube duben kofan shiga dakunan mu a lokacin, Anty Sadiya akai sa,a tafito daki a lokacin don tai mashi sannu da zuwa, Fuskan Sallawatu yana kicin,kicin, don may Anty Sadiya zata fito gaida maigidan, Ita ko Anty Sadiya kar take kallon ta don ta fahinci may take nufi da daure fuskan da tayi haka nan , Cikin irin sakin fuska shi da ba wani fara,a yace Sadiya ya gidan dai,? Yana saye da doguwar jallabiya a jikin shi kafanshi plat shoe's din mazane, Direct part dina ya dosa a lokacin don ganin halin da nake ciki, Wani kunci Salawa taji ya rufe ta tabi bayan shi da harara, Komawa tayi saman kujera ta zube don takaici, da bacin rai Ina zaune Tv na yana aiki na kai Africa TV 3, suna program na addu,oin marance, Daga gurin da nake a zaune ina dan bin su a hankali, kamar yadda suke yi idona a lumshi, Kamshin turaren Yaya Abubakar ne ya daki hanci abinda ya haddasa min bude idon nawa a hankali, Cak muka hada ido dashi yana tsaye kallo guda nai mashi na gane cewa tun dazu ya shigo kena, don har yai shirin fita sallah magrib can kasan mu Kokarin gyara zamana nayi ina cewa sannu da dawowa Yaya, Ya an,sa da cewa,, lafiya kike daki bangan kin fito gaidani da dawowa ba ? Lafiya lau Yaya na ba shi ansa da hakan ina cewa, wani program ne ya dauke min hankali ban san time yayi ba, Ya maida kallon shi ga tv don yaga kowani tasha nake kallo, Kan shi ya juya, yana cewa ai ina ce ko har yanzu jikin ne ? In ce mu tafi asibiti hakana dai, Na girgiza kaina da sauri ina cewa, ai naji sauki yaya don ko alaman fever na daina jin sa yanzu, Ya ce ni zan fita zuwa massalaci saina dawo, Allah ya tsare hanya nace tare da fatan adawo lafiya, Har ya kai kofan daki na na manta Yaya mun fa gode Allah ya saka da alheri Allah ya umfana dukiya, Murmushi yayi daga gurin da yake tsaye yace har ta sanar da ke, ke nan ko ? Nace Yaya kasan abin dan uwa ai yadda yake ko ? Daga haka ya sai kai ya fita dakin fuskan shi dauke da murmushi, Sallawatu wace ke zaune ta hau tayi fan a motar kishi, Sai faman jijiga kafa takeyi tana leken han fitowa daga part dina, Hango shi da tayi tafe, yana dan murmusawa, yasa ta mikewa tsaye, Kafin ya karaso gurin ta, ya kara daure fuskan shi tam, do ya gane nufin ta tun daga nesa, Dan dabur cewa tayi tana ce har kafito ga time ma yana son ya kure maka, Batare da yai magana ba ya sa kai yabar gida tare da turo kofan shiga falo, ****** ********** ****** A bangaren Mama Ladi Yaya Abubakar yakira ta sun gaisa yake tambayan ta akan zancen haihuwan Samira, Sai cewa tayi dama tana son fada mashi cewa ya turo da abinda za,ai mata, hidima dashi, Don dai yasan cewa yanzu ita bawai wani karfi ne da ita ba, Kuma gashi haihuwan Samira na farko ke nan a gidan, Don haka kaga ba karamin sha,ani za,a yi ba ke nan don haka katuro da abin kwarai,, Yace to Mama zan turo ma Baba Wadda sai ya kawo maki, Sai naga sakon ke nan ta fada kai tsaye kamar mai fada a lokacin, Suna kashe wayan ya numfasa tare da lumshe idon shi, don lamarin Mama yana bashi, mamaki sosai, Don ita ko diyan da ta haifa bata barsu ba sai tai mashi nasu kalan, Sam ko yan uwan haihuwan shi,mama bata kauna yai masu wani alheri a tsakanin su, Don sai dai sakon yafito ta hannun ta dole saboda tadan samu ta tsankwara,, daga ciki,, Amma yanzu wanan shawaran da Meenatu ta bashi haka zai dinga yi a tsakanin su,, Bayan ya dawo daga sallah ne, Salawatu wace ke zaune daga bakin gado, Ogana ina son zamuyi magana da kaine please idan har ba damuwa, Ba tare da ya kalle taba ya natsaye daga bakin wardrobe yana ciro kayan da zai saka a jikin shi, Gaskiya Ogana ina son inyi request a wurin ka irin yadda kaduty kana shiga wani daki please, Da sauri ya juyo yana mata wani irin kallon mamaki, Yace are you out of your mind,, Ta dan fadi a hassale, da cewa gaskiya mind dina is not styling idan kana haka,? Ya ce so da wanan kika shigo min gida ? To dakata kiji bazan yarda ki kawo min matsala acikin family na ba, Ke da su wa ya fara shigowa gidan nan first ? A hankali, tace sun rigani zuwa gidan, gaskiya, Yace may yasa su basuyi bakin ciki dake ba sai ke ce zaki nuna bakin cikin ki a kan su,, Shiru tayi tana cewa, gaskiya ni bana jin dadin hakan ? Amma kin san cewa suna gidan ki shigo ko don haka sai kiyi hakkuri amma idan bazaki iya ba hanya a bude yake gaskiya, Ni dai a ranan kaman nasan yadda sukayi da Yaya Abubakar, Haka kawai naji ban son fita falon kamar yadda ya ya umurce mu dayin haka kullun, Sai ma da na tabbatar da suna falon a lokacin na mike don in gabatar da Sallah da na idar kuma zan kwanta ne kawai abina, Saboda irin yadda naga take taken ta tun da rana yasa nace barin kama kaina, Ina kokarin shimfida sallaya Salawatun da kan ta tashigo dakin daga kofa tadan tsaya tana ce min Oga yana magana da ke a falo wai, Nace mata cikin alaman nuna ina sallah da cewa uhum, uhum, Ta juya batare da tace komai ba ta nufi fallon don ta sheda mashi cewa ina sallah, Bayan na idar na kawo nafilfili na dora akai, dafa bisani kuma nazauna naci gaba da yin addu,oi na,,, A takaice dai sai da na ga time ya kusa na barin falon yasani tashi don in tafi falon, Idona ya fara kawai ga kayan dake saman table din a cikin ledoji guda uku duk da alama iri dayane, Kamar kullun na nufi kasan carpet na zauna irin yadda na saba yi, Sai da ya gama tura sakon nan shi a,system yadago kai ya dubi time yana cewa, May kika tsaya yine haka baki fito ba yau da wuri haka ? Nace, Sallah na gabatar Yaya sai kuma, na tsaya nadan watsa ma jikina ruwa, Ok kawai ya furta, tare da kokarin jawo ledejon dake gaban shi, Inda Anty Sadiya take yace kizo ki zabi guda daga ciki, Anty Sadiya tamike tazo gaban table din ta mika hannu ta dauko wanda tagani can daga karshe, Sai ya juyo gurin da nake zaune saman carpet ya ce oya zaki zaba ko ? A lokacin ne naga Sallawa tana wani kada kafa, kamar yadda idan ran mutum ya baci yake yi, A hankali na dan karasa bakin table din na dauki ledan dake gabana, Tare da cewa cikin wata irin murya mun gode Yaya, Allah ya kara dukaka, Naji lokacin da Yaya yai wani irin ajiyan zuciya tare da cewa hmmmmm, Sai ya juyo gurin Sallawa wace ke ta wani irin taunan baki tagefe tana karkada kafa, Ta mike, jiki ba kwari zuwa gaban table ta dauki ledan karshe din , Nikan ina zaune na jingina bayana ga kujeran da nake zaune a kusa da shi, Kafana yana daga mike ina karkadawa a hankali batare da ma na kalli ledan ba, Hankalina yana gurin TV da,nda suke wasan tseren ruwa, Karan bude ledojin da ke gefen su nake jiin suna tayi, Nidai ban bude ba sai ma mikewan da nayi a hankali ina cewa zan kwanta sai da safen ku, Na mike tare da daukan leda na wanda Sallawatu ta kura,wa ido kamar tana son ta kwankwance abinda ke cikin Ledan nawa, Nikan ina shiga daki, na aje Ledan saman mirror dina na rufo kofana na kwanta kawai, Sai da na jero addu,oina na shafe ko ina na jiki na sanan na jabargo na kwanta, Barci na soma yi amma sai nake jin kamar hayaniya daga cikin gida, Tun ina daurewa har yakai na bude idona inajin muryan su su uku ana ta masifa a tsakani, Saida yaya ya daka masu wani irin tsawa su kayi tsit gaba dayan su,,, Magan ganun da nake ji jefi,jefi a kan ledan kayan da yaya ya siyo muna ne sukeyi,fada, Don naji anty Sadiya wace bata magana ma ko banza tana cewa daga kawai, Nshiga kitchen dauko ruwa zaki canza min leda an fada maki cewa ban gane kallah roban man dake ciki bane, Tsuki nayi kawai tare da gyara kwanciya na ina mai jin haushin su a zuciya na, Afuwan yau ba yawa sosai please,,,,,,,,,,, ZEEE MAKAWA YELWA,, 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 5⃣5⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA ALLAH- AL-RAQEEB,,,, Alheri, Rahama Ni,ima, Gafara, Daukaka, Daraja, Baiwa Dake a cikin wanan Watan mai albarka ya Allah muna rokon ka , ka sada mu da shi gaba dayan shi,,,,👏👏👏👏👏👏👏👏 Yau Anty Sadiya ce da girki, don, haka na tashi tun da safe na fara gyara gida, Kagin kowa ya tashi ko ina na gidan mu sai kamshi ya keyi,, Ko da Sallawatu tafito don ta sa girkin breakfast ta samu kitchen din mu na wani irin kyali saboda yasha gyara don har store din kitchen sai da na sharo, Gaba dayan su duk wanda ya fito sai ya ja ya tsaya don mamaki, saboda gyara shine gida, Dining table din mu har kafafuwan shi sai da nagoge su tas, don tun daga nesa zaka gane hakan, Wai duk wanan aikin da sha babu ko mutum daya da ya fito daga cikin gidan a lokacin, Na kare na koma dakina don in yi wanka indan sarara, Na dade zaune a gaban mirro ina gyara jikkina tare da yan shafe ,shafe, Sai a lokacin na hango ledan kayan da Yaya Abubakar ya bamu adaren jiya,, A hankali da gurin da nake na mika hannu na bude ledan don inga abinda ke ciki, Sabulai ne na wanka da man shafi,masu kamshi maclean, su tissue, cotton bund, da sauran su, Sai wani material mai kyau da dauka ido kalan nawa, light pink, Kalan yai min kyau sosai a idona don nakai wani lokaci ina ta shafan material din,, Namayar da kayan a leda na dauka na sa cikin wardrobe, dina,, Dogon riga na yan kasan Niger da na sayo ya ji aiki a gaban shi nasa,,, Nayi wanan kwalliyan ne don kin san idan kina da kishiya, bawai sai ranan da zaki karbi girki bane zakiyi kwalliya a,a Next day to kiyi girki zaki gyara jikin ki ta yadda mijin zai rude yaji kamar ace ke ce zakiyi, girki a ranan, Jin banji motsin kowa a waje ba yasa na koma saman gado na na haye,,, Gadon da yasha gyara cikin wani zani gado ja mai zanen flowers farare,,, Dakin yaji room fresh tunga labulen dakin zanin gado da bathroom don sune ake sawa room fresh, sai daki ya dade yana kamshi, Dan kwantawan da nayi ashe barci ya fara kwasa na saboda gajiya, Sai muryan Anty Sadiya naji kaman a mafarki, tana cewa Au, Meenatu kin kwanta ne,? A hankali na bude idona ina kokarin tashi daga zaune, ina kuma, cewa, yanzu fa na kwanta ashe barci ya dauke ni, ko Idon Ànty na saman rigan da nasa alokacin, yana daukan ido, , Anty ina kwana ? Tace Alhamdullahi Meenatu, Ya gajiyan aiki,? Na tashi naga ko ina gidan yau sai kyalli ya keyi murmushi nayi nace naga idan anyi tun da safe yafi sauki ne shi yasa nayi, Ta ce to nagode, murmushi nayi yayin da naga ta juya zata bar dakin don fita, Ni kuma sai na koma saman pillow da nake kwance da farko, Amma sai kuma Anty ta tsaya tare da juyo wa tana fuskan ta ta, Tace Meenatu dama yau, tuwon alkama naso in muna kuma sai dai nasan idan nayi zai sake ne, nace to babu matsala Allah ya kaimu anjima lafiya , Sai dai ina son idan anbarni zan tafi gurin wanke kai anytime na dawo sai muyi, Na karashe zancen cikin murmushi , Tace ai badamuwa ko sai kin dawo, ke nan don ni zan shige ciki, Komawa nayi na kwanta sai dai kuma barcin baizo ba again, don haka sai na lumshe ido,na,,, Tausayin irin rayuwan, Anty Sadiya nake,yi mutum ba ruwan shi da komai shi, Idan ba ka zauna da ita sosai ba sai ka dauka bata son mutane ne ita, Kamar tana kyaman zama da mutane don yawan, daure fuskan ta, Amma daga yau tunda har na fahince ta insha Allah a tare zamu dinga aiyukan mu na gida, Na nisa nace, aiko banza ita matar yayana ce kuma kaman yan uwa muke don zama gari guda, da muke, Idona yana daga lumshen da yake ina ta tunanen duniya, Alaman mutum ya na tsaye a kaina naji sai kuma kanshin turaren da hanci na ya shako, min, na dan baiwa, watau Yaya Abubakar, ke nan, Hakan yasa ni bude yan daradaran idona sai cikin na Yaya Abubakar wanda ke tsaye, a gaba na, fuska ba yabo ba fallasa, ya kura min idanun nan nashi masu firgita mata,, Kokarin mikewa nayi zaune ina mashi wani irin murmushin jan ra,ayi, Kafin in ka daga zaune sai naji muryan shi Tambaya ya jefo min Barci kike ne ko kuwa hutu ? Nace, kawai dai ina dan hutawa ne kawai, kafin in fita, Ina kwana Yaya ? Lafiya kalau ya kika tashi ,? Ko da yake naga ai lafiya kike tunda har kin yi wanan irin aikin haka ? Murmushi nayi nace gidan ne yai min ba dadin gani shi yasa na kamawa Anty gyaran shi, Kin kyauta yace tare da dan murmusawa, ya ce zai tafi shi sai ya dawo, Ban san lokacin da na jefo mashi tambaya ba da cewa kayi break fast ne ko Yaya ? Sai naga ya dan bata rai yana dan jiji ga kai yace yau bazan tsaya break ba agida kifita ku karya, Na ansa mashi da fadin to Yaya, Zai fara tafiya nace Don Allah Yaya ina son yau in tafi saloon gurin gyaran kai ? Cak ya tsaya yadan yi shiru zuwa can ya nisa yace, Ok ki dauki ki nan a saman drawer a dakina Hamza ya kai,ku, amma dan Allah ku kula kada yai tukin ganganci da ke , Nace tare da Fattu zamu tafi insha Allah zamu kulla,, Ya ciro kudi daga cikin ajihun wandon shi ya miko min,, yana cewa, Ba matsala yace yasa kai ya fita abin shi, Godiya nai masa, tare da fatan a dawo lafiya,,, Na nisa bayan fitan shi tare da komawa na kwanta, ****** ********** ****** Mun samu mata da yawa a cikin saloon din, don haka muma muka bi layin zama,, Matar mai shago tafito a take ta shedani, don bata manta da ni ba, Da murna tare da sakin fuska, ta, tare mu ta na jin dadi, Ta umurta da a kawo muna ruwan, sha duk yadda naso, kada ta wahal da kan ta gare mu amma sai taki, Bamu kadai ba ranan harda sauran mutanen da ke shagon ta saya muna ruwa masu sanyi,, Mata sai hiran duniya akeyi ana ta yan dararaku kowa da abinda ake mata, Wata daga cikin matan ta dan dubeni take cewa da za a wanke maki kafa, ai maki ado zai yi kyau, Murmushi nayi ina cewa ai naga kamar da layi da yawa yau, akwai jama,a agurin, Anty mai shagon tace barin maki da kaina kaunata, Ba bata lokaci a ka kawo roba a gaba aka fara gyara min kafa, Matar da tabani shawara a fara gyara min kafa wayan ta yai kara ta dauka suna magana, sai dai a cikin zafin rai take zancen ta, Bayan taga tafara fada ita kadai tana cewa ita za,a kawo iskan ci ? Sai Anty mai shago tace to ai shi wanda kike fadan dashi yanzu baya kusa, Matar tadan ja tsuki gefe tana mai kauda kan ta ,tace,,, Bari kawai Anty wata shegirya matace ke son shiga gona ta, Wata mace ce gurin aikin su guda da maigidana shine take ta kokarin shige masa, Yanzu wai kirana yayi yana ce min wai an kawo lace masu kyau a shagon su amma, Aliya ta zaba muna, Ina ruwan ta da ni da har zata zaba min a binda zan sa tasan colour din da nake so ne,? Anty mai Shago ta nisa tace aiko naki ya samay ki wallahi, Don kin san irin matan nan idan sun lakewa mijin ka sai Allah, Fattu daga gefena tace, irin amaryan gidan ku ke nan Meenatu, Nai murmushi kawai batare da nace komai ba don dariya abin ya bani, Anty mai shago tace, ke kardai ki ce min an ma kauna ta kishiya kuma, Da ba kun ce su biyu bane,? Fattu tace wallahi Anty, wata irin garmakekiyar mata na nan a cikin su wai itace amaryan su, Duk ta girmay masu har maigidan nasu, sai kishin bala,i,, Anty mai shago tace hmmm,ummm, amma gaskiya abin da mamaki sosai a ciki, Fattu tace ai ina ga dama kamar zancen auren ta yana gaban na Meenat don da alaman sun dade a tare,, Sai matar da tafara zancen tace itama wanan din wani brother din maigidana yace min wata mai kama da yar Togo ce, ba yarinya bace irin tsofin barikin nan ne, Fattu tace shima dai maigidan su Meenatu bazaka ce zai iya auren wanan mace ba wallahi, Sai Anty mai shago tace o kin mutu wallahi an fada maki cewa baki sake suke rike mazan, ? Ai sai sun dade suna masu shiri sosai kafin su tun kari na miji tukun, Wata taso taimin haka ga maigidana na bita har gida na ci ubanta na nuna mata nafita zaman bariki, Wai har abinci take kawo wa maigidana a office da kuma ziyar a gida idan ban gidan, Fattu tace ai ina ga ita Meenatu tasu ta samu shigane saboda yadda rayuwan uwargidan su yake na ko in kula, Abinci fa sai maigidan ya sayo masu take away, don bata iya dafa wa ita bata da time, Sai matar wace kekira da , Humaira, tace kinga kowa nima halina ke nan don ban da time da safe idan nafita gida ban dawo wa sai, after six kinga a lokacin duk nagaji, Anty mai shago tace yo kin mutu wallahi Humaira idan zaki gyara maza ki gyara kafin ai maki sakiyar da ba ruwa, Sai wanan lokacin nasa masu baki a hiran su daidai lokacin da nake kokarin gyara kafana, nace, Amma gaskiya don kina zuwa makaranta bashine zai baki excuses din kin dafawa maigidan ki abinci ba, Anji cewa da rana baku a gida gaba dayan ku, to da safe da kuma dare fa, ? Baki da right da zakice bazaki kula da mijin ki ba idan har kikayi sakaci yanzu ne wata sai ta dafe maki shi, Duk da dai mun san cewa mata hudu shari,a ta yarda masu dasuyi, To amma ai mutum sai yayi kokari ya gyara ta ban garen shi kafin yazama ma mitum to latet, Cikin dan marairai ce murya matar tace, to yaya zanyi ni don Allah wallahi har kunsa duk naji jikina ya mutu, Fattu tace wallahi wani lokaci mu matan sakacin mu ke kai mu ga halaka ai, Matar a take duk tashiga damuwa tace wallahi kamar kun sani cewa Yanzu duk hankalin shi na kula da yana gurin ta don ko da dare na zaki ga yana waya muku muku, da ya gan nin sai ya kashe yana cewa I will call you back,,, Cab,di,jam inji Anty, maishago, tace gaskiya a kwai aiki sosai Hummaira, Na ce ba wani aiki kawai, dai sai dai ta gyara mu,amulanta da mijin ta, Bakin su na haduwa gurin ce min kamar, yaya fa,? Nace,kamar ta kyautata tsakanin su mana ta yaya za,a ce mace sam bata da time din mijin ta kwata,kwata, Anty mai shago tace gaskiya Humaira baki da gaskiya anan, Don ma sai ince kece kika ba da kafa ai maki hakan ma, Humaira ta ce to, ya zan yi ne ni dan Allah duk na rasa ko may zanyi wallahi, Na dan ce masu hummm, gaskiya abubuwa da dama,, Kin ga da farko dai abinda zakiyi, shi ne ki fara sake jiki dashi, Kamar kuci abinci a tare, ko kuma idan kin rigashi ci idan ya zo zaici, sai, ki zauna gab dashi, Kece mai service din din shi, kamar suzuba abinci a plate, Kara miya idan da bukata hakan, kara gishiri ko maggi, Da farko ki tabbatar da tsabtar gidan ki a kullun kafin ki fita, Sai kuma ki tabatar da cewa, kin tanadi komai wanda zakiyi abincin dare, da idan, kin dawo daga makaranta, Sai kuma abinda zakiyi maku breakfast kada ki fara kibar, mijin ki yafita gidan ki bai karya ba, Don kada keep mantq cewa wanan bokon da kike zuwa yi iya karshi a duniya zaki bar shi,, Sai ke kuma kikai sakaci da gobe kiyaman ki kika kama duniya kawai, Shin bakya tunanen, cewa, Allah zai tambaye ki yadda kikai zama da Amanan mijin ki da ke kanki, Humaira ta wani nisa,wa tace, gaskiya ban san may ma zance ba, Nace to kinga wanan ke nan Humaira gaskiya akwai matsala gare mu matan yanzu, Gaba dayan su su kace gaskiya kan, Sainaci gaba da cewa sanan ki tabbatar da cewa idan kin gama girkin duk saurin da ki keyi ki ba mijin ki time tukun kafin fitar ki, Zuba ruwa a cup ko drinkis, Ki dan rika jan shi da fira jefi,jefi, idan ya gama sai ki, zuba ruwan wanke hannu, ko mika tissue, da toothpick, kwashe kayan abincin zuwa kitchen ki gyara gurin cin abincin, Ki tabbatar da kin tsabtace makwancin ku kin gyaro ko ina a dakin, Kada ki nuna gazawanki gare shi wurin mu,amulan aurataiyya, A jiyan zuciya Humaira ta sauke a lokaci guda tare da kallon mu gaba daya,, Kin ga dai in har zakici gaba dayin haka na insha Allah ba yar Okene ba ko yar Eteku ce dole ta barki, Tace Meenatu bani noban ki please zamuyi magana Tafara yi muna, godiya kaman zata fadi kasa, Nace sai mun kara haduwa zan fada maki yadda zakiyi mu,amullah da yan uwan maigidan ki, Tace ai kaji wani matsala Babba don sun sani gaba yanzu haka da muna funtata, Daga haka muka cigaba da kara tattaunawa a tsakanin mu akan yadda irin wayan nan matan masu zaman kansu ke kama mazan mutane su mayar nasu, Ta hanyar sakaci irin na mu matan hausawa musan,man matasan mu na yanzu,, Irin yadda mukafi karfi da neman duniya sama ga lahiran mu, Mun manta da maganan Allah da Annabin sa akan biyayyan aure, muna yawan shagala da rayuwan mu, Angama min gyaran jikina nafito wata irin shar dani tankar amarya a ranan, Don,ni kaina nasan cewa nayi kyau sosai tankar wata fure, Kudin da nabawa Anty mai shago na mu biyu sai cewa tayi bazata karba ba, Amma nace don Allah ta karba idan ba ta raina bane, takarba don Allah,, Tun muna saloon naba Baba Hamza, kudi ya sayo muna abin bukatan mu da na yau da gobe, Ina shigowa gidan Sallawatu ta kyalla ido taga yadda na ke ta wani haskaw ai sai kawai ta rude, Don haka daki kawai na shiga, na farayin sallah saina fito na nufi dakin Anty Sadiya ina ce mata nadawo, Tana zaune saman kujera tana kallo wani India Wani irin kallon mamaki naga tai min tare da saurin kau da kai gefe tana cewa kin dawo nace zan shiga kitchen kafin ki fito, Nai gaba abina ina murmushi a raina ina cewa kishi kumallon mata Anty Sadiya kuma kishina takeyi ne haka, Ina shiga kitchen din nafara gyara gurin da Sallawatu ta dan bata da tai girkin rana,, Sai da na kara wanke pot din gudun ko wani kwaro ya hau saman shi bamu sani ba, Na tara ruwan a zinc din direct zuwa pot, daga haka na kunna Gas, A lokacin da zan jawo Ledan da aka,siyo muna fresh, kayan miya don amfanin mu, Tace to har kin,fara ko nace eh Anty sai nake nuna mata kayan miyan da sayo muna inda nake gwada, mata komai yadda suke, Tare mukayi girkin mu tsab ranan da anty inda take nuna min gurin, da take nuna min inda take samun kuskuren girkin ta, Mun gama a cikin lokacin muka kai sama dining table din mu, Ina gyara kitchen ne sai ga anty tana ce min, ki tsaya, Meenatu intafi in gyara infito sai ke ki shiga, Ba ta dai fito fili ta fada min ba amma na fahinci manufar ta tana gufun wani abu yafaru da abincin namu, Kara gyara falo nayi ina kallon Salawatu sau biyu tana fitowa, falo, Sai ta gan,ni a falo ina aiki sai ta juya ta koma, anjima kadan kuma tafito kamar mai neman wani abu, sai kuma ta juya, Fitowan Anty Sadiya sanan, na, shige dakin nima na je don inyi sallah, Ban fito ba sai musalin, takwas da wani abu a lokacin har sun sun hadu don cin abincin su, Ina saye da wani, dogon riga mai yar karamar hannu iya hammata, Kaina yana saye da hullan net mai raga irin mai nuna kitson mutum, Na gaida Yaya Abubakar dazuwa naja kujera na zauna alokacin ya fara kai loma sai naga ya tsayar da hannun shi ya dan juyo gurin da nake tsaye, Kamar zaiyi, magana sai kuma yaci gaba da cin abincin shi batare da yace uffan ba, Gabadayan ranan duk mun ci abinci sosai Baba Hamza ne da nace yazo ya karbi abinci dazun shine ya shigo, Sannu Baba na nace ma Hamza din yakarba da cewa yawa anty sannun ku da gida ya gajiya, Sallawatu wace tun shigowan shi ta canza fuskan ta duk da haka sai da ya gaishe su gaba dayan su, Sanan ya shiga kitchen daukan abincin shi, yafito yana cewa saida safen ku, Nace ka gaida su Fattu da Mama , Yaya Abubakar yace kai Hamza da safe kazo akai motan ca baka gurin wanki, Hamza ya ansa da fadin tau maigida insha Allah zanzo, Yaya ya ce mashi sai kaikai ta can tukun gurin da ake min service din ta adan dubata, Yace tau maigida nagane gurin inda muka taba, zuwa kabar ni na karbi karfe ko? Kai yaya Abubakar ya gyada mai nasan don baison yawan magana yasa shi gyada kai din, Cup din tatacen kankana da muka gyara ya ce a miko mashi, Sai da ya kora ruwan kankanna da kyau sana ya aje cup din, Ina kokarin hada plate din gaba daya naji muryan Yaya Abubakar yana cewa, Wanan kitson fa Meenat kamar na yan Sudan aiko kin sha zama ko? Murmushi, nayi gami da cewa yar kanuri ce tai min dai, Ya ce uhumm ni kan nasani don su kadai ke wanan irin kitson haka ? Sallawatu wani irin mamakine ya kamata har ta kasa daurrewa, tace, Ina kuma namij yasan kan kitso har da kiran sunayen yan country, Yace tunda anfada maki cewa ban san komai nagamay da mata ba, Ba Sallawatu ba har Anty Sadiya saida zuciyar ta yadan sosu amma sai nai tankar ban fahinci su ba, Na wuce ina wani juyawa cikin karairayan kugu, rigan dama yafitar min da hip's dina dakyau, Sallawtu tace a cikin hausan Oga gobe ina so man ka kaini uguwa ? Bai tanka mataba sai cigaba da bude system din shi yayi don duba sakkon ne,,,,, Takara maimaita zancen ta yace kin taba ganin nakai mace anguwa a gidan nan, Ban wanan sakarci ni bance bankai mace anguwa ba amma sai mai dalili Don haka gobe sai ki fadawa Hamza ya kaiki idan kina so, Tace Nop kadai bari inyi driving da kai yafi min fita tare da wani wanda ban masan asalin sa ba, ZEEE MAKAW@ YELWA 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 5⃣6⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA ALLAH- AL- MUJEEB,,,, Haba mutane, baku min uzuri please, nida nai hakkurin zaunawa na rubuta na turo, Banyi fushi ba sai ku ne zakuyi fushin jiran network harda turo min zagi da bakaken magana, Ba komai na gode Allah ya,bani ikon gama wanan novel din lafiya don na yi alkawari, tun da na fara dole in yi hakkurin karasa shi,,, Zaune yake office din shi yana dan juyawa saman kujeran shi a hankali, Jikin shi ya saye da,farar tie shirt, mai dogon hannu da,aninaiyya jere har kasa, Wuyan shi nada necktie, daure mai dan tsawo har saman kirjin shi, Wandon jikin shi baki sai kafan shi dake saye a,cikin bakaken takalma, Hannuwan shi na saman goshin shi ya dafe dafe shi da shi, Kallo guda zakai mashi ka gane cewa,ya na dan cikin yanayin damuwa irin yadda yake zaune dafe da goshin shi, Idon shi ya kara lumshewa yana tuna irin bakaken maganganun da Sallawatu ta fada mashi a daren shekaran jiya, Idan akwai abinda baya so tun yana karami shine fitina da kuma mai yawan yin fitinan, Gaskiya sam bazai lamunci, ta wargaza masa gida ba suna zaune kalau da matan sa, ****** ********** ****** Matar yaya Awal dan wurin baba musa ta haihu, Sai barka mata ke zuwa yi a gidan tako ina yan uwa da abokan arziki, Haihuwan yazo wa Baba, Musa a bazata don haka ba wani shirin da akayi a kai, Yaya Awalu yana ganin dashi da mahaifin shi duk sun dan shiga damuwa, Saboda sanin irin yadda buki fari yake, a garin Birni Kebbi,, Mahaifiya na Saratu ita ce ta bugo min waya tana fada min cewa matar Yayan ki Awal ta haihu, Don haka ki bugo waya kiwa dan uwanki barka tare da mai jego nace cikin murna insha Allahu mama zan bugo mashi, Nace mama tace Yaya Ibrahim ya turo min da nomban nashi, An turomin ba,a wani dade ba na kira Yaya Awalu cikin jin dadi, A lokacin yana zaune a sashen mahaifan shi suna, dan tataunawa, Ganin bakuwar noba ce yasa shi cewa bari kawai ya share nomban, Har kiran ya katse bai dauka ba amma sai nace bari dai in kara kiran shi in gani, Nakara dialing din nomban Baba Musa yace dauka mana kaji ko waye, ke kiran ka, Mahaifiyar shi ta ce ai shima yasan musu barkana ka kira nai, Ya dauki wayan tare da cewa Assalamu Alaikum, naji dadi sosai da naji muryan dan uwan nawa a lokacin, Duk da nasan halin miskilancin shi iri gudane da na Yaya Abubakar don ko zubin halittan su iri guda ne, Amma hakan bai hanani yi masa dan ba,a bayan na karba sallaman nace cikin dan zolaya A Yaya Awal angon karni ashe mun samu karuwa na ? Allah yaraya muna yasa albarka Allah sa dadin musulma ta, Ya karba da fadin Ameen a dakile kamar yadda nai tunane, Nace Yaya ina gaida, Jamila ina mata barka Allah shi raya muna, Ya kara cewa Ameen, Nace ina gaida su Baba ya amsa da zasu ji, Mamaki yakeyi ko wacece take mai wanan waya haka, Tambaya yayi da cewa shin wai wace,ta, ka magana don ban gane ba, Yaya Meenatu ta fa, Cikin dan sake murya naji yana cewa a,a Meenatu ke ta, Wallahi, tallahi ban gane keta ba ? Murmushi nayi nace ai na gane Yaya nima mamata, ta bugomin taka fada min cewa ai mun samu karuwa, Yace walle gaskiya na ta yaya wajen maigidan naki ? Lafiya yake Yaya, Nace shin kako fada mashi,? Ya ce walle Meenatu ban fada mashi ba, Nace haba dai Yaya halan me ? Yaya don Allah buga mashi, don kaga kaina ya kamata ka fada mai, Yace to Meenatu zan kira shi insha Allah amma ina gudun kar mama Ladi ke dai san halin ta ai, Nace ,a,a Yaya kai dai fada babu komai insha Allahu, Nace zan kiraka yaya insha Allahu zuwa gobe da yamma, Yace Meenatu na gode keji,,, Allah yabar zumunci na ansa da fadin Ameen yaya sai anjima, Bayan mun,gama magana dashine ya dan juya gurin da mahaifan shi, suke, Ya ce, Meenatun Baba, Samaila ta wai Mama Sara ce ta buga mata waya tana sheda mata zancen haihuwan, Nan dai ya kwashe duk yadda mu,kayi ya fada ma,su, Baba Musa ya ce, tsoron Ladi mi? Ladi ta zata hana ka zumunci da dan uwan ka kira shi dai kafada mai halan wani abunai kake so? Yaya Awal shi malamin secondary ne gashi kuma ba,ai masu albashi ba don ana tsakiyan wata, A take a gurin ya kira Yaya Abubakar, wanda ke zaune a office cikin damuwa, Bayan sun gaisa yake ce mashi, ya bugone ya fada mashi matar shi ta haihu, Barka Yaya Abubakar yai mashi baidai nuna mai wani, murna ba a fili, Yadai mashi barka a dan dadare tare da Allah ya raya suka kashe wayan, ****** ********** ****** Ina ta murna har cikin rayuwa na da wanan haihuwa har cikin raina, Bayan dawowan Yaya Abubakar, gida ya shige dakin shi, Ban fito ba don nasan cewa, banice da girki ba a ranan, Ina daki abina ina kallon wasan yara tashan cartoon, Sallaman Yaya Abubakar ce ya naji a dakin nawa cikin wanan lokacin, Na daga kai, da mamaki ina kallon shi, don nasan baya shigowa dakin mutum a wanan lokacin, Kokarin mikewa nakeyi daga zaune,, Yace No koma ki zauna abinki, dama nazo in fada maki cewa ne, dan Allah kafin indawo ki dan dafa min ruwan Lipton mai kayan yaji please? Dan jim nayi sanin cewa yau ba ranan girki na bane,,, Har ya kai kofa yace, ina da right din da zan sa kowace mace aiki a gidan nan, Shiru nayi ba tare da nace komai ba har ya fita daga dakin nawa,, Nisawa na yi tare da kokarin mikewa don zuwa, yin abinda aka umurceni da yi, Kitchen din nafara shiga na har,hada kayan yaji na zuba a wani roba na fara wanke wa san nan na zuba a cikin pot tare da dauko Lipton guda biyu na kada acikin ruwan, Sosai na barshi yai ta dafuwa a saman wuta, don yayi masa dandano yadda yake so,, Bayan na gama hada komai a flask na dauka zuwa falo dashi, Sai dai babu kowa a falon abin yabani mamaki don da wuya irin wanan lokacin a samu Sallawatu bata falon, Amma sai gashi yau bata falon hakan ya bani mamaki matuka, Juyawa nayi da flask din na mayar kitchen na samu guri na boye , Dakina na koma na gabatar da Sallah sai kuma na dan kara gyara guri, Yan mintoci da dama aka dauka kowa bai fito ba nan na gane a kwai matsala a gidan, Anty Sadiya ce ta fara fitowa tana saye da rigan barcin ta fari na cotton, har kasa yake rigan, Bata jima ba Sallawatu tafito itama cikin wasu kaya kaman na yan ghana, ita agañin ta wayewa ne, Sai da na tabbatar da cewa nagama komai adakina nafito, wajen, Kitchen nafara zuwa nadauko mashi dan wani flask karami baki da yake amfani da shi, Tafe nake amma zaka ce ai rangwada na keyi a lokacin, don irin tafiyan nawa, Cikin dogayen rigunan da Anty Amarya ta sayo min na saka guda, Rigar irin in kana tafiya sai ya kama shocking yana wani dan fidda walkiya a jikin yadin, Da yake darene sai ya kara ma rigan kyau da daukan ido, Tun da na tunkaro hannu na yana dauke da flask din da cup duk hankalin su na a kaina,, Nakarasa takowa a hankali gaban shi na durkusa tare da aje flask din ruwan a gaban shi, Sai a lokacin ya dago kai yana cewa Ok har ya dafu ko ? Na ansa da fadar eh yaya, Kanshi yana duke ga system din shi yake cewa ki dauko min zuma a saman drawer a dakina please, Ban dauka cewa dani yake ba don haka sai na samu gurin ina kokarin zama, a gefe, Ya dan dago kanshi daga abinda yake yi yace bakiji bane wai ? Sai na dan daburce nadan kalli Sallawatu wace ke da girki a ranan, Yadda naga ta daure fuskanta tamau, ta wani hade rai, yasani mikewa, Sai naji muryan shi yana cewa ki hado min da spoon please, na ce toh na juya zuwa inda ya aike ni, Sallawatu wace ke kallon mu rai a bace tadan cije leben ta, tare da yin kwaffa, Ban karasa hawa sama ba najiyo muryan ta tana cewa Aiko baka nuna a fili ba kowa ya,san cewa, akan Meenatu zaka iya komai agidan nan , Yace au har kin manta da kince saboda tana yar uwana nake nuna mata hakan, To ina son in gwada maki cewa, Yar uwatace din ta kwarai don guri biyu take gare ni zuwa uku, Kinga na farko yar uwar haihuwana ce, Na biyu mata,ta,ce ta sunna, Na uku yaruwata ce ga musulunci don haka babu ta inda ban hada da ita ba, Don haka kalamin nan naki da kikafada shinake son gwada maki cewa, Meenatun zan iya sata zan iya hanata aduk sanda naso, Tai wani har da ido tace ai sai ta haifa maka yara, mu gani ka cika gida dasu kuna cewa yan uwa kuke, Sadiya wace tun fara zancen take sauraren su cikin bacin rai tace amma wanan abin naku bai kawo kallo ba, gaskiya Tana kokarin mikewa tsaye take fadan haka gare su, Ya nuna Sallawatu da yatsa adaidai lokacin da karaso dauke da kwalban zuma a hannuna yake cewa, Wanan macuciyar mata ce so take ta cuce inzalumci rayuwana in kone, Bazaki bani dokaba agidana don nina ajeki bakece kika ajeni ba, Kuma kin san ai ina da mata ki ka aure ni hakana da su, So sai ko kiyi hakkuri ki zauna kamar yadda kowa cen ku ke hakuri da dan uwa, Nikan ina aje kwallba na juya na nufi part dina cikin bacin rai , Muryan Sallawatu naji tana cewa, ashe dama kai haka kake ban sani ba, Ya Abubakar yace o da kinga yaro kin zo ki min wayyo ko, Look Sallawa the door is open, Yo can go and live us pls, Bazan taba bari ki cutamin aka rayuwana ba in kwashi dukiyar mutane in dinga narka maki any how, Dakina fada ina mai kiran innalillahi,wa,inna alai,him,raj,um, May ke faruwa haka tsakanin yaya da matar shi gaskiya abin baiyi kyau ba, Har zan rufe kofa sai na tuna da ban dauko goran ruwa sha ba, Don haka nafito don in dauka naji yaya yana cewa , I can't stay, with you, being my wife like dis, Abuse me like a ashawo woman in front of my family, Jikina yana rawa da gurin da nake na hango idon shi sun kada sunyi jajir a lokacin, Narasa may yai zafi har ya kawo wanan fadan tsakanin wa yan nan ma,auratan, haka ? Da sauri na karasa ina cewa Yaya kayiwa Allah kadaina wanan halin ba alheri bane please na karasa kamar zanyi kuka, Juyawa yayi ya dan kalle ni da rinanun Idanun shi da suka kada sukayi masa ja,,,, Ko may ya tuna sai naga ya dauki system din da flask din ruwan da na kawo mashi ya haye sama, Gurin Sallawatu na juya wace ke cike da masifa saidai kuma fuskan ta ya manne da nadama, sosai don irin yadda tabi bayan shi da kallo da yake hawa sama, Na juya gurin tare da mata wani irin kallo nace haba haba please hakan bai yi kyau ba gaskiya, Bai kamata ace kuna haka ba wanan ba alheri bane gaskiya hakan ba zai kawo alheri ba gaskiya, A cikin mamaki kamar ba sallawatu ba naji tana cewa Meenatu, Babu abinda zaki fada min tunda harda ke gurin son kuga bayana agidan nan, Murmushi mai daci na hade ina cewa badamu tunda kinsan da haka amma yanzu sai kiyi hakkuri saboda dare muryan ki zai iya kaiwa ko ina, Amma shawaran da zanbaki shine ke mace ce kiyi kokari ko sasanta da miji ki ina ga zaifi daga haka najuya abina wuce, ****** ********** ****** Washe gari tunda safe Sallawatu ce ta buga min kofa, Ina bude kofa nagan ta tsaye cikin wani dan yalalon hijjab dagage tun a kofa tace min ina kwana Meenatu, Hanya na kauce mata don na fahinci tana son shigowa dakin nawa, Tana raraaba ido ko ina adakin tana kallon yadda dakin nawa yake da tsari da tsabta, Bakin gado ta zauna yanayin idon ta y nuna cewa tayi kuka sosai da dare, Itace ta katse shirun da cewa Meenatu nazo ne in maki godiya akan abinda ya faru daren jiya, Nagode kwarai don kin bani shawaran da babu wanda yabani shi, Sai kuma don Allah ina mai baki hakkuri ga yadda nasa ki a cikin rikinci mu bakiji ba baki gani ba, Sai gashi kuma duk da ina maki kallon yarinya kinbani shawaran da yai min dadi, Don Allah kuma ina rokon ki da kikara ba yayan ki hakkuri akan abinda ya faru please, Nace a,a gaskiya tunda har kun sasanta a tsakanin ku komai ya wuce don Allah sai kuyi ta hakkuri please, Tace sherin shedan ne kawai don ba wani babban magana bane haka dai Allah ya kawo Na tare ta da cewa Allah ya kyauta ya tsare muna gaba don Allah muyi ta hakkuri da junan mu, Tamike tana cewa nagode nagode Meenatu, Tana fita nabi bayanta da kallo ina tuna maganan Anty Amarya da take cewa irin su Sallawatu baka gane kan su, Sai ka natsu sosai don yan duniya ne na karhe, Lalai Anty Amarya ta fadi gaskiya don dubi yadda wai yau Sallawatu ce kamar da gaske tazo min daki,, Daren jiyane fa take ta zumduma min zagi harda gorin haihuwa, Amma yau wai itace tazo take min dadin baki, kamar wata ta kawarai Allah ya sauka Na kara da cewa Allah yai min katangar tsari ga duk wani sheri na ta, Na nade sallaya na dama tasamay ni zaune ne ina karanta Hasbunallahu wani,iman wakeel kafa dari hudu da hamsi Gyaran safe nai ma dakina na koma na kwanta batare da nafito waje gyara ba, Barci nakara komawa batare da nasani ba har zuwa lokacin da Yaya Abubakar ya shigo dakin nawa, Yau shigan kanan kaya yayi wanda ya kara fito maahi da kurciyan shi a fili, Suman kanshi daya dan taru ya kwanta mai a kai bakikirin, yai lub Hannu shi ya na saye da wani agogon White, silver, sai kafan shi da ya sa wasu takalmi buth na maza masu tsada, Barci kikeyi ne Meenat ? Ya tambaya alokacin da yake kokarin juyawa daniyar fita daga dakin nawa ? A hankali na bude ido,na na kuma sauke su ga fadadar bayan ya Abubakar dake niyar juyawa, Murya na ya tsinkayo ina cewa Yaya ina kwana,? Juyowa yayi yana cewa kin tashi ne ? kwanta abinki ni zan fita ne, Nace Allah, ya tsare hanya,, Har zai fita na mike zaune daga kwance da nake, Yaya ya zance ya Awal ne ? Cikin mamaki yake kallo na yana cewa Awalu ? Nace eh Yaya bai fada maka cewa matar shi ta haihu bane, Cikin daure fuska yace ya fada min mana nai mashi barka, Na kara gyarawa nace amma Yaya ai ya kamata ka bada gudun mawan ka, Hannu ya daga min yana cewa look Meenat may kuma kike son in mashi, bayan barkan ? Cikin dan tsuke fuska nace amma dai Yaya kasan fa haihuwa wani abune na farin cikin rayuwa da tarihi irin wanda mutum bazai taba mantawa ba, Cikin dan hasala yace Meenat may kike son in mashi, ? Kaina na dukar kasa bance komai ba sai dai na hade fuskana abinda ban taba mashi ba, Sai ka dawo na fadi a hankali tare da kokarin juyawa ina lalaban filo na, da niyar kara kwantawa,,, Bai juyo ba yasa kai yafita abinshi Sam ban ji dadi yadda Yaya ya yi ba akan zancen haihuwan matar dan uwan mu, Yin ranan a haka nayi a cikin bacin rai don gaskiya idan Yaya Abubakar zaici gaba da yi wa yan uwan mu irin wanan halin gaskiya ba,za,a samu cigaba da zumunci maidaurewa ba, Don dai Babba shike hasa kan gida sanan na baya suji dadin biyo shi, Kamar yadda na saba taya Anty Sadiya aiki yau ma banki yi ba don a tare mukayi abinda duk ya dace, sai dai jikina ba walwala a,tare dani, Muna gama duk wanin abinda zamuyi sai da na tabbatar da cewa nayi, Don haka na,shige daki abina na dan yi abubuwan da ya dace in yi, Fattu na kira, muka gaisai mu kayi yaya kwana biyu, ? Mun kai wani lokaci muna dan tataunawa akan zance Humaira, Bayan kashe waya, ne ban kai ga ajewa ba sai na tuna cewa nace zan kira Yaya Awalu yau din, Kira daya nabiyu na uku yadauka ya na cewa Meenatu yaya kuke ya Abuja,, Nai dan murmushi na ce Yaya Awalu ya ruwan zafi ? Kai haba Meenatu masu ruwan zafi suna gidan su inda suke, Na ce a cikin mamaki, yaya gida ta haihune yace , Wallahi Meenatu daga asibiti suka wuce, da ita gidan su kinga yaya za,a yi, ba dole mu bar su ba, Nace to Allah shi kyauta ya ce Ameen yanzu kinga ga suna sai kara matsuwa yake yi, Gashi gwaunati batai albashi ba don banzaci haihuwan a yanzu ba, Sai kawai kwatsan gashi yazo muna a bazata, Nace akwai Allah yaya Allah zai rufa asiri insha Allah,, Ya Awal ya amsa da cewa ameen Meenatu nace zakaji mu insha Allah kafin sunan yaya abin ne bai yi ready ba, Mukayi sallama da Yayan nawa na kashe waya zancen shi suna damuna a rai na, Daga daki ina jin karan TV da alaman yaya na kallon network News,, Ban fita ba don tun gama girki mu naci shi a kitchen tsaye, Duk zaman falon sai yaji ya ishe shi don rashin ganin na fito waje, Sai dai yai kokarin danne damuwar tashi don gudun zargi daga sauran matan shi, Sai dai bai san cewa Sallawatu duk ta fahinci halin da yake ciki ba, Cikin dakewa yake cewa Sadiya Meenatu lafiya take bata fito ba, Ina ga gajiyane kawai don tun da muka gama girki,tashige bata kara fitowa ba, Ok kawai yace tare da ci gaba da abinda yakeyi a system din, Barci, ne ya dauke ni sosai, don daga kallon sunna tv barci ya daukeni ban sani ba, Kamar a mafarki naji maganan shi yana cewa barci baki kashe electronic, ba? Nadan mike firgigit nace cikin idon barci zan kashe yanzu ai, Tashi ki kashe ki rufe kofa, kafin barcin ya dauke ki, Ban kara furta komai ba sai sai dan tashin da nayi don inyi abinda ya umurce ni dayi, Maya hanaki fitowa falo yau,? Dan marairai cewa nayi nace kawai dai banjin dadi ne sai na dan kwanta, Batare da ya waiwayeni ba yace zancen Awalu kikewa fushi ko ? Cikin wata irin murya kasa kasa nace ni ba fushi nakeyi ba , Akan may zanyi fushi tunda kaima ai dan uwanka ne, Aini zan tura masu da abindake gate ni gobe insha Allah, Kallon mamaki yai min yace ashe kudi gare ki haka? Nace a,a kudin da kaba ni, in tafi,sallon ne mai sallon din ta raga nna ne zan hada da wanda ke gurina in aika mashi, Hmm kawai ya iya ce min daga haka ya juya fita yana ce min sai da safe, Yau ma kamar jiya na tashi fuskana a daure nafito daga wanka ina shafa mai ya shigo dakin cikin shirin tafiya office yau ya kasance juma,at, Don hakani shaddane mai kalan milki sai shining yakeyi, da kyalli, Ina kwana na,ce fuska ba yabo ba fallasa a cikin sa, Ina kwana nai masa adan sake batare da na kalle shi ba ina shafa mai a cinyoyi na, Ya saki ajiyan zuciya yana dubana cikin wani irin yanayi maradadi, Yace ni zan fita babane za,a ba kudin ko Awalun ? Nace cikin da murya karami da cewa karaba masu dai Yaya tunda kowa nada abin dai yi daga cikin su, Ok zan turo maki Hamza ko Abdullahi sai ki mashi bayani yaje ya tura masu, Ya dan duba agogon hannun sa yace ina ga bari a turawa shi Awalu da hamsin shi kuma baba talatin ko? Nadan juyo ina duban shi nace dadai kabasu kowa hamsim din don lalura da yawa, Ya amsa da cewa to shike nan zan ba shi ya tura masu sai kicewa Awalu ya turo da account Nace cikin nuna farin ciki da Allah ya saka da alheri angode, Yajuya yayin da nace Allah ya tsare cikin sakin fuska, ZEEE MAKAWA YELWA [8/18, 10:26] Anty Lantana: 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 5⃣7⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA ALLAH- AL- WASIYU,,,, Fatan Alheri gare ka da Zurian ka, Fatan gamawa da duniya Lafiya, Baba Alhaji Aliyu Harizami, Dan Amar Kano,,,, Gaba dai Gaba dai Baba Aliyu Dan Amar Kano,,,,,,,, Zaune, Baba Musa yake Yaya Awal ya shigo gidan cikin farin ciki da jin dadi yana cewa, Baba kaga ikon Allah ko ? Wallahi, Mai sunan malam na ya aiko muna da alheri, Masha Allahu, kai madallah aiko mun godema Allah, Allah abin godiya inji mama matar Baba Musa mahaifiyar su yaya Awal, Allahu Akbar inji Baba Musa lokacin da ya gama kidaya, kudin Ya ce ance gari da yawa maye baicin kan shi, Allah ya rufa,muna,wagga asiri, Wasu kudin yaya, Awal ya mikowa Baba yana cewa ga wanga, Baba ya ce kuma ? Wai an mari kumama, Yace Meenatu ta ce asai ma mai jego turmin zani wanga kuma naka na Baba,,, Masha Allah inji baba ya karbi kudin ya nata sa muna albarka dubu goma ya ce cif,, Allah kai ma wa yan ga diya albarka, Allah ka azurta, su zuri,a masu albarka, Yaya Awal da Mama su ka karba da fadin Ameen ya Allah, Kudin Baba Musa ya kaiwa malam tsoho ya nuna mashi tare da yi mashi bayanin komai, Murmushi malam tsoho yayi tare da dan kad kanshi yana mai lumshe ido ya ce Madallah madallah Allah mun gode maka da ka ba mu wannan yaro mai albarka acikin zuri,an mu, Allah nagode ma da ka bu ikon hada auren wanan yaron da wanan yarinyar, mai albarka da sanin ya kamata, Wana addu,an na karshe shi yasa Baba Musa saurin dago kai ya dubi malam, Malam tsoho ya gane nufin shi, don haka ya dagawa Baba Musa kai tare da,sauran iyayyen mu da ke gurin, Ya ce zaman Meenatu tare da mai suna,na wani babban TARKO ne na haka muna wanda gaba dayan ku baza ku gane hakan ba yanzu,, Gaskiyane inji Baba Buhari wanda ke sauraren zancen su, Yadan murmusa tare da fuskantar mahaifin su ya ce, Ai malam iyanzu na fara fahintar, gaskiyan zancen ka sosai, Don sanin halin yaran nan da,nayi gaba dayan su Don ka ga shi mai sunan malam zuciya da saurin fushi, Ita ko Meenatu uwayen hakkuri da sanin ya kamata, Malam yace to kun ji dalilin hada tarko nan da nayi ke nan badon komai sai hankalin wanan yaron ya dawo gida gare mu, Wanda idan kun kula ku kan ku za kusan cewa da, da, da yanzu nan ban daya ba ne,, Don da farko sam maisuna badamu da damuwar mu ba ko kadan, Yanzu kuma idan har kunyi la,akari sai kuga cewa, ai ba, duk wani harka yana dubuwa, Gaba dayan su sukace haka ne malam maganan ka gaskiya ne , Baba musa ya ce, ai watau, malam wanan mahaukaciyar uwar tashi ita ce duk ta kawo wanan matsalan wallahi,, Malam ya ce kusa ido kuyi kallo in akwai rayuwa ko bani da rai zaku ce na fada maku, Don Ladi na kallon bai boyewa zai dinga yiwa yan uwa da abokan arziki alheri babu yadda zata yi, Kuma shi kan shi duk wanan miskilancin nasa zai daina ya rabu da su a hankali, kudai sa ido a hankali zaku gane amfanin wanan hadin nawa, Malam Bashir makwabcin mu yace lalai malam kayi babban hikima guri wanan hadin ba karamin TARKO ka haka ba, Malam tsoho yace ai duk zage zagen da ake yi lokacin da nai wanan hadin auren ina ji ba wai ban ji bane, Su wa yan nan yaran da kuke ganin cewa ai sun girmi ita Aminatu, Su ya kama ta a hada da mai sunana, na ba gaskiya bane, Don da sune aka hada dashi da zuwa yanzu anfara kai ruwa rana ko Saboda ba zasu iya ratuwan mai sunana ba san nan ita Ladi irin wanan mugun fitinan da take yiwa Saratu da,shi kan shi samaila yana iya kawo karewan auren, Gaba daya sukace wanan gaskiya ne malam don dai duk matan mu in ba Saratu ba babu mai iya hade fitinar Ladi, Don,ko shi Samaila idan ya yunkura nasan cewa matar sa ke taushe shi yayi hakkuri, Kowa yace gaskiyane malam gaskiya abin yayi kyau sosai, Yace kun ga yanzu muna sani halinda suke ciki kamar yadda su ma suke sanin labarin gida a kai akai har yake taimaka mu na irin hakan, Ko wa ya karba da cewa, gaskiyane malam abin yayi kyau kwarai da gaske, Malam ya kare da cewa Allah ya kyauta Allah kuma ya raya muna su yasa albarka Daga, haka a ka fara zancen abinda ya kamata su yi tunda kudi sun samu yanzu, Baba Musa bai boye ba ya dinga fadin alherin da, Yaya Abubakar da Meenatu, suka turo masu, Mutane sai albarka akesawa yaya Abubakar din tare da fatan alheri ga rayuwa, Zance na yawo ya kewayawa har caraf a kunen Mama Ladi, Mariya ce ta jiyo zancen ta zo tana shedawa mama cewa ashe , Abubakar ya aiko masu da kudin hidima,? Mama Ladi tace bari zancen nan Mariya, akwaodai inda suka ranto (aro su) su , Walleh Mama shina ya aiko ma su da shiya kuma ance kudi na masu yawa ya aiko masu , Wai harda Meenatu sai da taturo da nata taimakon ita ma, A take rayuwan Mama Ladi ya baci may mutanen gidan nan ke nufi da har zasu rufe min alherin da dan cikina ya aiko da shiya, Mikewa tayi Anty Mariya tana dakar da ita amma ina wucewa tayi zuwa cikin gida, Bata tsaya ba sai, sashen Baba Musa tashiga surfa jidalin cewa an maishe ta batasan komai ba kenan Baba musa na jin ta yai wuf ya fito daga dakin shi, shi ya na cewa ke Ladi walle in kina cin kasa ki kiyayi na shurem,,, Don tafi karfin taunar ki saboda dankon ta, kedai san ni bani dauka shedanar ki, Don haka duk abinda kin ka jiya ba karyana ba gaskiya ta, Sai ki tai ki hana gobe shi basuwa, ki gani inzai hannu maki,,, ****** ********** ****** Tsafi gaskiyan mai shi don Hajja tun daga Birni Kebbi ta tashi har bargu tai tafitan yini don kwana bai yi gare ta, Ta samu bokan ta tai mashi bayanin irin rayuwan da take ciki yanzu inda take she da mashi duk irin abinda yanzu dodo ke ciki, Shiru boka yayi kamar mai nazari can ya nisa yace , Abinda kike mashi da farko shine, yanzi baya samu daga gare ki, Anyi alkawari dake kin amince yanzu kuma sai baya samun hakan, Tace to amma ai naga dai ta nawa bangaren babu matsala,, Don duk abinda, ya ke bukata na tsare mashi ina kokarin yi, Boka yace dole a kwai matsala, don haka kawai ba zai daina abinda yai ke yi ba, Muddin yana,samun biyan bukatun shi to shi kuma ba fashi ga abinda zai gudanar gare ki,, Hajja cikin magiya take cewa bokan ta don Allah dai ya taimaka mata akan dodo ya dawo kamar farko, Yan abubuwan surkulle boka, yai ma Hajja tare da mata albashir din komai zai dawo, daidai, Ta bashi abinda ya kamata,ta bashi tare da mashi godiya sosai, Ranan ta, juyo, daga can ta biyo ta garin illo don yafi mata saukin tafiya, Sai zuwa yamma sosai ta iso gida da kunshin abubuwan da bokan ta ya ba ta tayi,, Bata tsaya wani hutawa ba ta shiga aiwatar da abinda, boka ya bata tayin, Wani hayaki da ta turara har makwabta sai da suka shiga damuwa saboda mugun karfin shi, Amma sanin halin Hajja yasa kowa ya kama bakin shi da ita, don ba zasu iya jidali ba, Sai da ta tabbatar da cewa ta gama hada komai san nan hankalin ta ya kwanta, Ta ne mi abincin da zataci ta dan samu guri ta kwanta jiran tsan,mani,,,, ****** ********** ****** Kitchen na ke ina,aiki yau ni ce, ke da girki sai dai Anty Sadiya tace min bata jin dadin jikin ta, a yadda take fada min wai jikin tane ya mutu mata kai yai mata sanyi, Bayan na idar da sallah la,asar, na fito falo ina kara gyara yan wguraren da ya dace in kara gyarawa, Karan tafiyan takalmin naji shigowa gidan har mai shi ya kawo tsakiyan falo babu sallama, Sau guda na daga kaina na dan kalli, gurin da naji motsin mutun shigowa, Sallawatu ce wace tun safe tafita gidan sai yanzu tashigo, Ko da zata fita ma batai muna magana zata fita ba don haka ni ma, na maida kai na ga abinda na keyi, batare da nai mata magana ba, Don banga dalilin da zan mata sannu da zuwa ba bayan ba tai min sallama ba, da zata fita, Daga gurin da take tsaye ta ke cewa abincin rana fa Meena, Aikina naci gaba dayi batare da na nuna mata cewa najita ba, Sai ji nayi tace, ke Meenat dake fa nake magana, zaki wani share ni, Batare da na juya inda take tsaye da tana jiran abinci bayan yunwan da ta kwaso daga gurin gantalin ta, Ji min rainin hankali ga wanan yarinyar abincin ma kuma shi bakin cikin bani kikeyi, Nace sai kin dawo gurin koyon Sallama zan baki ansa ai, Wani irin takaici da mamaki ne suka rufe ta a lokaci guda, Karamar yarinya kamar Meenat, in badon rayuwan aure ba ina ita, ina yarinya kamar meenat, A fusace Salawatu ta juya zuwa, part din ta tana kokarin aje kayan da ke a hannun ta, Ta dan jima don lokacin har na karasa abinda na keyi ina kokarin shigewa, Ta dawo cikin wani irin yanayi wanan karon fuskan ta babu dafin kallo, Tace sai naga raini ya shiga tsakani na dake sosai don kina ganin cewa wai abu gudane ya aje mu agidan dake, Nadago fuska na nace au da make baki sani bane sai yan zun nan,? Cikin wani irin mamaki take kallon ta ce laila ma yarinyar na kin samu guri wallahi, To bari kiji yau babu kowa a gidan nan idan ki kai min tsiya wallahi kafin wani ya shigo sai na nada maki dukan tsiya tukun, Cikin wani irin rashin tsoro da karfin zuciya na ce Bissimillah uwata ,,, Aiko ban yi aune ba naji tayo kaina gadan gadan, da nufin duka, Ai take na Fulani ya ziyarce ni wani irin zuciya ya rufe min ido a lokaci guda, Wani irin zazzafan mari takawo min na kauce nikuma Allah yaban sa,an ta nadago ta tun daga kasa na makata a tsakiyan falo,, Zan kara yowa kanta naji an rike ni ta baya ban tasya ba nai cikin su ita da wanda ya rike ni ta baya, Gam naji an kara rikeni sai wani irin tsimi jikina keyi a lokaci guda , Najuyo cikin masifa sai naga Yaya Abubakar ne a tsaye bayana rike dani sai kuma Anty, Sadiya, wace ke daga gefe acikin tashin hankali, ita ma, A zuciye nake cewa a sakeni, dan Allah kafin wanan, mara mutuncin ta taso, Cikin wani irin tsawa yaya Abubakar ya ke ce,wa, Meenatu kina da hankali kuwa, Haushine da kishi ya kama Salawatu, dake kokarin mikewa ga kasan da nakai ta, Ita a ganin ta irin yadda yaya Abubakar yayi yana magana kamar bai son yi yaudarane yana son ya goyi bayana ne, Don haka take cewa Meenatu nice ki,kaiwa wanan abin haka? Abubakar kana ganin yadda tai min ko ? Yaya Abubakar cikin wata irin murya yace shout, up, my friend, ya ce cikin wani irin muryan daka tsawa, Tayo cikina da wani irin karfi har saboda wani irin kishi da ya turnike ta a lokaci guda, Ban hango alaman imani ba ko kadan ga fuskanta a lokacin, don haka, Ta na kawowa na daga kafa na kai mata shuri aiko takara yowa cikina haikan, Wani irin wawan mari Yaya Abubakar ya sake min tare da daka min tsawa, Dole na shiga hankalina, Anty Sadiya ce naji daga bayana ta riko ni tana cewa kadai so dukan tane Amma ai meenatu bata da laifi a wanan zancen don daga maganar fatan baki takai mata duka fa, A take anty Sadiya tashiga fada mashi abinda ya faru, tiryan tiryan, Daga gurin da Salawatu take kai yamutse tankar mahaukaciya take cewa, Aike dama Sadiya munafuka ce don na fahinci duk munafuncin ki ba yau ba, Anty Sadiya acikin muryan nan nata, tace ba komai amma ki sani babu wace nake tsoro daga cikin ku , Enough Yaya Abubakar yace ciki wani irin tsawa yana wani irin hucin bacin rai, Ya juya gurin Salawatu dake rera kuka acikin kissa yace stop dat please ? I don't want to hear your silly voice,, Ta wani langabe kai tankar yarinya tana cewa dama nasan sun hada min kai basu kaunan zamana a gidan nan don ina bare acikin ku,, Kallon ta mu kayi gaba dayan mu don saboda Sallawatu ta cika makiran mace, domin abinda tace, Maganan da tayi na cewa mun hada mata kkai mun maida ita bare yasa shi yasa shi wucewa batare da yai muna magana ba, Juyawa mukayi ni da Anty Sadiya muna kallon juna a cikin mamaki saboda duk inda makiran mace takai Salawatu ta wuce gurin, Ba wanda yaiwa juna magana daga cikin mu kowa ta nufi part din ta mu kabar muna fuka nan tana share hawayen munafunci,, Kamar kada in shiga dakina sai kawai naji wani irin kuka mai karfi yazo min a lokaci guda, Tausayin kaina ya kamani take tunanen iyayyena yazo min a rai, Nace ashe wanan shine manya kecewa aure sha kan yaro, Yau ni kadai ke cikin tashin hankali kuma babu mai bani hakkuri, Kuka nai tayi inda acikin kukan tunane yazo min da cewa, Sallawatu ni kadai takewa wanan halin don na fahinci duk ransn girki na sai ta kawo matsalan da zai sa duk zukatan mu ya baci a gidan, A hankali naci gaba da rera kukana batare da nasamu mai rarashina ba Anty Amarya ce ta fado min a rai don itace zata iya warware min wanan matsalan a ruwan sanyi, Wayana jawo daga inda nake na fara neman nomban Anty amaryan Ta dauki wayan cikin cewa babban diyar ya kuke ya gida, Inadai lafiya kika kirani cikin wanan daren, don ba halin ki bane, Kuka taji inayi tace subbahanallahi Meenatu, Watta ba ki shin? Missa may ki,? Wai may ankayi ne shin? Ban iya cewa komai ba sai kukan da naci gaba dayi kawai, Cikin dan rudewa tace shin ko in kaiwa uncle din ki na ? Nace a,a anty cikin dasasshen murya na fara labarta mata halin da muke ciki da Sallawatu tun zuwa na Shegiyar tsohuwa annaminiya, May ya kaiki Meenat ai hada jiki da kishi da sunan fada tsiya yake sawa wallahi, Daga yau ka da ki kara hada jiki da kowan su don walle baida kyau so sai Kuma tsiyata maigida shikayi irin hakan din gaskiya ba a son fitani na agida tsiyata gida shikai, Idan tayi ki dai rabu da ita don duk sherina hakan, Wai ita makira da gangan taka haka don dai ta bata maku tsarin dare ke da shiya, Nace nima Anty abinda na fahinta ke nan yanzu don ni kadai takewa hakan, Anty tace share hawayen ki ke jiya tashi ki kimtsa jikin ki ,(gyara jiki) kitai zuwa gurin mijin ki, Kuma ki sa ido ki kallo in Allah yayi duniya don manzon Allah sai Allah ya saka maki Meena am, Yanzu bari har gobe don kega dare yayi amma gobe in Allah ya kai mu zan kiraki mu kara tataunawa akai keji, Na,amsa cikiciki da cewa insha Allahu Anty, tace Allahi shi haushe ki kan su gaba daya nace Ameen Anty, Tace don walle babu kishiyar da kason kishi shiya saidai mutum kawai ya boye kishine shine saukin, Wanka na shiga inda na dan dauki lokaci gurin gyara jikina yau ban ko tsaya sa rigan barci ba saboda duk zuciya na a cakushe take min, Daurin kirji kawai nayi da zani na nakawo katon hijab dina na aza sama, Na jawo kofan dakina a hankali nasa key na rufe nakama hanyan hawa sama, Ashe Sallawatu taji motsin rufe kofana don haka ta tashi da sauri tana dan lekawa tagani ko kulle kofa nayi daga ciki, Sai ganina kawai tayi na gilmata kamshin turaren da na fesa duk ya rufe mata hanci, Wani irin kishi da takaici ya ziyarci zuciyan ta don bata zaci hakan ba yau, daga gare ni, Don dai tasan cewa ta rshe wanan plan din yau ke nan,, Zagi ta jefo da cewa yar iskan yarinya ta rushe min plan dina, ke nan, Amma ai dani kike zancen zaki gane ni ce,muje zuwa dai, Natura dakin a hankali batare da nai sallama ba inda na hango yaya Abubakar kwance saman gadon shi yadafe goshin shi da hannayen shi idon shi a lumshe, Idan baka sani ba sai kace barci yakeyi a lokacin amma ni tun shigowana nafahinci idon shi biyu, Don haka na koma daga can karshen gado na kwanta a hankali,, batare da nai wani kwakwaran motsi ba, Shima dai yau din yaya banji ya mirgino ya rike ni ba yadda ya saba yi min, Wani irin tunane nakeyi wanda hakan ya haddasa min ciwon kai a take, lokaci guda, A haka na samu barci ya saukeni ba tare da na sani ba, A cikin batci naji wani irin murdawan mara ya zo min lokaci guda na farka na bude idona, Murda sosai maran ke min a hankali na bude iddona yaya Abubakar yana daga kwance ya barcin shi hankali kwance,, Tunda nake ban taba irin wanan ciwon maran ba don duk yada naso in daure sai na kasa saboda wani irin yanka da marana keyi a lokacin, Kasan gadon na sauka ka ko zanji ya fada min kaina na daga saman gadon amma kamar karamin zugin sa akeyi a lokacin, Wani murda min da yayi da gurin da nake duke kaina saman katifa nace,wayyoni Allah na Nishi na ke yi da karfi abinda ya farkarda Yaya daga barcin ke nan, A hankali ya fara saurarawa sai yaje jin nice ke wanan irin nishi, Zubur ya mike zaune yana cewa ke lafiya haka may ya faru da ke ne wai, Nace Yaya marana ne kaman zai balle min wani irin murdan mara,naji nakara,sa kaina saman katifan gadon ina cewa wayyo Allah na zan mutu, Subbahanallahi ya,ce a,cikin kaduwa yai kaina yana ce sannu, sannu da,sauri ya jawo rigan sa ya zura ya kashi key din mota , In tafiya kafana ya ja ya rike guri guda ban iya daga kafa,ko kadan, Ai dauka na yayi cak muka,sauko zuwa,bai tsaya tada kowa ba daga cikin matan shi muka fita, Ja mota a guje bayan ya,wagale get muka,fita zuwa,, asibiti, Ban san shawaran da yayi ba sai gani nayi ya tsaya kofan gidan su Fattu yana kiran layin wayan Hamza, Ba,a bata lokacin Hamza ya dauki waya nan yake sheda mai famu waje zamu tafi, asibiti banda lafiya, Cikin yan mintuna duk suna waje gaba dayan su tare da Maman Bi,u muka tafi, asibitin, Sai dai tun bamu karasa ba Jini ya balle min faaaaa, Hankalin Yaya Abubakar yai mugun tashi da Mama ke cewa Jini ya zo min, Tafurta da harshen yare su tana cewa Hamza bari ciki nayi, Ya fadi da hausa yace barin ciki subbahanallahi, cikin damuwa da nuna tausayi, Da sauri Yaya Abubakar ya juyo yana cewa barin ciki Meenatu din,? Tana da cikine dama ? Innalillahi ya fara maimaitawa, cikin wani irin tashin hankali, Shigan mu asibiti ba bata lokaci aka karbe mu inda su ma suke sheda mai miscarriage ne na samu, Sai da sunyi min allurai tare da bani gado barcin wahala ya dauke ni ban san yadda akayi ba, Cikin wani irin tashin hankali yaya Abubakar yake don tun zuwan mu asibiti bai zauna ba Sai huci ya keyi yana wani furzar da iska cikin tashin hankali, Maman Bi,u taga yadda yake don haka ta nufi gurin shi cikin irin hausan ta tana cewa yayi hakkuri yazo ya zauna haka Allah ya nufa, Hamza ya karaso gurin yana cewa, maigida kayi hakkuri, tunda ta samu lafiya zuwa yanzu, Yana tsaye ya tokare hannaye shi a saman ginan asibitin kafan shi guda harde cikin guda, Idon shi duk su canza kala zuwa wani irin ja kamar garwa shin wuta, Ya najin kamar an rura mashi wuta a cikin jikin shi saboda zafin da ke fita mai, Ya nisa da karfi yace tare da furtawa kun cuce ni wallahi kun cuce ni, Gari yadan fara haske saiga Fattu da mijin ta sunzo muna da zannuwa da kuma abin karya wa, Yaya Abubakar a lokacin yana zaune wajen asibiti zaune saman dogon bencin da aka tanadarwa mutane, Ya dukar da kan shi sai faman tunane yakeyi cewa abinda ya dade yana nema aduniya ko da yaushe yake kai kukan shi ga Allah , Yau shine Allah ya karba masa,addu,an shi amma saboda mugun hali irin namu nai masa sakaci da shi har ya bare, Mijin Fattu wanda yaya baya gama wayewa dashi bane tsaye gurin shi yana cewa maigida ashe abinda ya faru ke nan kuma, To Allah ya sauwaka Allah ya kawo wani rabon mai albarka, na moriya, A hankali can cikin makogwaro Yaya Abubakar ya ce Ameen, daga haka bai kara magana ba, Sai duk wanda ya kalle shi yasan yana cikin tashin a lokacin don yadda yanayin sa ya nuna, kawai, Sai musalin tara na safe Anty Sadiya ta ji shiru bai shigo sallaman ta tafito daga dakin ta, Part dina ta fara dubawa shiru babu alamana a ciki, Ta dawo, kofan yaya Abubakar dakin a bude yake sai dai babu kowa har bathroom ta bude amma sai bataga alaman anyi amfani a ciki ba, Take wani irin kishi ya kamata sai tana ganin akwai inda muka tafi da yaya don jin dadi, Tafito kofan falo tagani a bude alaman asake ya kwana, Mamaki karara a fuskan ta don haka ta dauki waya takira nimban shi don taji yana inane, Dafarko kamar ta share kada ta kira sai dai tace bari taji su inane,? Itama Sallawatu wace ke saukowa daga stairs a lokacin sai ta ja ta tsaya don sauraro, Bayan ya dauki wayan babu sallama babu komai Anty Sadiya tace cikin gadara kuna inane haka,? Asibiti yabata ansa atakaice, Asibiti ta kara maimaita zancen yace eh Meenatu ce ta samu miscarriage, Subbahanallahi tace da sauki dai ko yace eh da sauki don jinin yanzu ya tsaya, Allah ya sauwaka tace wani asibiti ne kuke kuma baku da bukatan komai ko ? No ki barshi don muna tare da mutanen gidan su Hamza a nan,, Ok ta ce cikin mamaki da jin abinda ya ce don ita dai wa yan nan mutane sai take masu daukan munafukai, kawai, Sallawatu dake tsaye a bayan ta bata sani ba sai maganan ta taji har ta firgita, tana cewa, Su ina yake cewa ? A cikin hassala Sadiyaya tace mata asibiti a takaice Meenatu ce ta samu miscarriage, Cikin wani irin murya tace what miscarriage dama tana da cikine ? ZEEE MAKAWA YELWA,,,, [8/20, 09:10] Anty Lantana: 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 5⃣8⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA ALLAH-AL-HAKEEM,,, Nafarka daga barcin dolen da nayi inadan kokarin bude idon a hankali, Indon yai min nauyi don haka a hankali nake bude idon don sun min nauyi, Kallon mamaki nakewa gurin don naga ba dakina bane ai, Muryan Maman Bi,u da Fattu yasani karasa washe idon nawa Maman Bi,u wace ke cewa Meenatu kin tashi yaya jikin, Bakyajin komai yanzu ko ? Ai anyi arziki don abin yazo da sauki in ba haka ba ai bari wahala gare shi yafi haihuwa wasu suka ce, zafi, Ban fahknci may suke cewa ba sai ido kawai na zura wa Maman Bi,u din don ban fahince ta ba sam, Ganin irin yadda nake kallon mamaki yasa Fattu dan dukowa daidai saitin kaina tana cewa, Meenatu Mama na son fada maki cewa, kin yi barin ciki ne jiya cikin dare ya zube, Cikin mamaki na kai, hannu na saman mara na ina kallon Fattu, nace , Ciki, ? Ciki fa Fattu ni ce keda ciki ta gyada kai tace kwarai amma kuma ai ya zube, ko, Innalillahi, wa ina alaihim raj,um, Allahuma ajirni fi musibati wa,akkali,lif,li hairain min ha,,, Wasu hawaye masu dumi naji sun ziyarci ido duk yadda naso in controlling din su na kasa sai da suka tsiyayo min daga idona, Daidai lokacin da Yaya Abubakar ya shigo dakin ke nan yana saye da jallabiyan shi tun na dare a jikin shi, Kallo daya zakai mai kasan cewa yana cikin wani irin tashin hankali sosai, Yana ganin idona da hawaye yai saurin kau da kai tankar bai gan ni ba, Sai cewa yayi wa Maman Biu bata complaine, din komai ko da ta farka Mama tace mashi a,a ba komai, banji tace wani abu ba har yanzu, Yace Doctor ya ce idan babu matsalan komai zuwa anjima zai sallamay mu sai taje gida ta ci gaba da shan maganin, ta, So ni zan tafi gida inyi wanka in dan karya don banci komai ba, Tausayi Yaya Abubakar ya bani irin yadda naga ya canza min a lokaci guda, Don daga yanayin maganan shi zaka gane cewa ya cikin bacin rai sosai, Fattu ce tafara fita tanawa Mama yaren su sai naga Mama ita ma tafita yarage dagani sai Yaya Abubakar a dakin, A hankali na juya da niyar in da tashi in zauna sai naji jikin nawa still ba karfi, Don haka na koma na kwanta tare da lumshe ido na a hankali, Ya Abubakar ya kula da abinda nake son yi don haka na tsinkayo muryan shi yana ce min, Kibi jikin a hankali fa don ba karamin jini kika zubar ba, Idona na kara rintsewa nace Yaya wai da gaske Fattu ke yi bari nayi, Banji ya bani ansa ba abinda ya sani bude idona ke nan, Zaune yake a bakin gadon da nake sai hawaye kawai,nake gani yana tsiyayo mashi a fuska, Why Meenatu why kinsan kina da ciki kika ,,,, Sai ya kasa karasa zancen shi saboda hawayen da yazo mashi,,, Mikewa yayi yabar dakin cikin wani irin bacin rai don jin kan shi ya keyi tankar zai suke,, Yana fita nasa wani irin kuka mai tsuma rai tare da cin zuciya na saka alokaci guda, Na daina tausayin kaina sai na Yaya Abubakar don mutum babba kamar Yaya yana kuka aikasan abu yai nisa, ke nan, Mama Bi,u ce ta turo kofan dakin tana cewa haba, haba Meena kada kiyi kuka don, Allah ki yi hakkuri ki daina kuka, Ai munyi arziki tunda ya tafi ya barki lafiya don naga shima maigidan naki ya tafi rai bace,, A lokacin itama Fattu ta sako kai dakin tana cewa haba Meenat, ai ki godewa Allah da abin yazo maki da sauki kawai, Nace cikin muryan kuka Fattu ni ban ma san cewa ina da ciki ba wallahi, Da ban yarda na biyewa Salawatu mukai fada ba don ina ga shine sanadin wanan barin nawa, Gaba dayan su sukace cikin mamaki fada kukayi da ita? Nan na kwashe abinda ya faru na gaya masu yadda tayo cikina da nufin duka na nikuma na biye mata, mukai ta jidali da junan, mu, Allahu, Akbar inji Maman Bi,u tace ai Meenatu irin wanan fadan na kishiyo yi tsiya yake haddasawa a gida, Yanzu ma wanan abin kawai ya isheki ishara, don ke ta cuta, Nashare hawaye na, nace mama bansan cewa, ina dauke da ciki ba, Mama Bi,u tace, ciki har na wata daya da kwanaki shiyasa ma ki kai wanan jinin kadan, Ai wanan matar wallahi ta cuce mu don dai, kawai fadan kishine da naci mata mutunci, Fattu cikin dariya tace Mama ke ma ai yarki nada laifi da ta yatda har suka hada jiki da ita,, Nan dai akai,ta zance wanda nake jin shi kamar zuban ruwan zafi a zuciya na, ****** ********** ****** Falon gidan babu kowa sai na,urorin da ke aiki, a cikin sa, Ya fara hawa sama ya ji dan motsi a bayan shi abin da ya sa shi juyowa ke nan, Sallawatu ce saye cikin wasu yan, kanan kaya duk sun fitar mata da suran jikin ta, fili, kirjin ta ba komai ya shafe plat, Wani mugun kallo ya watso mata tare da saurin kauda kan shi gare ta, Sallawatu ta ganshi ta kuma fa irin kallon da yai mata, Take tasha jinin jikin ta don tasan cewa tun jiya a hake yake da ita ga kuma wani babban zance da ya ahigo ciki, Yaya Abubakar yana shiga daki ya fada bathroom din shi don ya watsa ruwa, Ya dauki lokaci sosai yana wanke jikin shi yana tuna irin jinin da yaga yana zuba min ajiki,, Sosai hankalin shi yakara tashi take yaji wani irin tausayi na ya kama shi, Don yasan kamar yadda na fadi cewa ban san ina da ciki ba gaskiyan zancen ke na, Shima da ya girmay ni bai sani ba tayaya ni zan san cewa ina dashi, Bakowa yaja mashi wanan hasaran ba sai Sallawatu, wace yanzu aure ta ya zama mashi da ya sani, Sai yanzu zancen malam tsoho kakan shi yake fado mashi a rai, Yadda malam yadage yana fada mashi cewa bai hanashi aure ba amma ya auri yar asali, Lalai malam yayi gaskiya auren yar asali shine aure don tarbiya da addini , Shi yanzu ba ma zai ce Sallawatu tana cika ibadan ta ba, don baya ganin tanayi, Amma abaki tana cewa ita musulmace, sai dai bata cika ibadun ta, Yana, fitowa daure da alwala, ya sa wata rigan ya fara sallah,, Ya dade zaune a gurin ya na kai kukan shi ga Allah,, Yunwa yake ji zuwa lokacin ya fito don ya samu abinda yaci, Nice da girkin a ranan don haka ban gida sai ba wanda yai breakfast daga cikin su, Har kitchen ya leka ko zai samu wani simple din abinci ya dan ci ba ko mai da zai iya ci gurin, Zai fito ne suka hade da Sadiya, itama kitchen din zata shiga alokacin, Au ka dawo a she ? Ya bata ansa a takaice da cewa Eh, Ya mai jikin da sauki ko ? Alhamdullahi ta samu sauki sosai, Bakuyi abinci ba, ke nan a gidan nan ? Gaskiya bamu yi ba don banzaci cewa zaku dade haka ba ? Mamaki kwarai tambayan ya bashi, don baima san ansan da zai bata ba a lokacin, Har ya kai tsakiya sai ya juto yana cewa kina nufin cewa baku dafa komai da za,a kai masu asibitin ba, ? Bata bashi amsa ba sai tai shiru don tasan cewa bata kyauta ba sam, Keys din shi ya kwasa ya bar gidan cikin bacin rai rayuwan shi na mai daci, Restaurant ya tsaya yasai abinci ya ci sai kuma yai muna takes ways din su, Ba laifi da ya dawo yasamu idona biyu sai dai ina cikin damuwa a lokacin don haka, Ya umarce ni da in tashi in ci abinci ba musu nadan mike tsaye duk da ina jinnjiri a lokacin, Dai taimakon Fattu na, shiga banda ki na gyara jikina,,saidai jinin zuwa yanzu ya tsane min bai zuwa sosai kuma Jikina dai ne ban jin kwarin shi sosai saboda jiri nake gani da na mike tsayen, Nadan fara cin abincin amma sai naji ban iyawa saboda yadda nake jin badadi a bakina ga zuciya na yai min baki badadi saboda bacin rai, Hawaye ne ya,silalo min daga idona duk yadda naso su tsaya min abin baiyi ba, Fattu ce ta matso kusa dani tana fadi a hankali Meenat kibar wanan hawayen haka please, Nace cikin dan daurewa Fattu abin da ke sani kuka,shine, idan na tuna da duk yawan hakkurin danayi amma wai saida Salawatu ta kaini ga kasa hakkuri ga al,amarin ta, Maman Bi,u tace babu komai haka Allah ya nufa wanan ba rabo bane, Duk yadda suka so inci abinci nakasa ci don haka nakai kwance ina mai rintse idona, A haka barci ya kara kwasa na yai gaba dani ban san inda nake ba, Sai zuwa yamma lis Allah ya bano ikon farkawa saidai wanan karon da wani itin matsakaicin yunwa na farka daga barcin,, Anyi daidai mijin Fattu ya kawo muna pepper soup din kasan rago yaji kayan yaji sosai a cikin sa, Sosai Maman Bi,u tazuba min kuma nasha da yawa,, Saura kadan in karasa Yaya Abubakar ya shigo dakin hannu shi daukw da ledoji, Fuskan shi na gare ni yaje cewa, kin tashi nace masa eh a hankali, Sai kuma yakai kallon shi ga plate din dake hannu na ina sha, Gab da gadona ya karaso yana tambayana may ke damuna yanzu nace masa babu komai, Nan yake cewa yaso a sallamay yau amma yace wa likita yabar ni har zuwa gobe idan na kara jin karfin jiki na, a lokacin, Maman Bi u tace gaskiyane hakan yana da kyau sosai, Tare suka fita da, mijin Fattu wanda yau ne haduwan su na farko Mijin Fattu bayan sun dan fita can kasan wani bishiyan mangoro da ke cikin asibitin, Yake cewa Yaya Abubakar gaskiya abin ma yazo da sauki don ba karamin tashin hankali bane zuban ciki, Saboda halin damuwa da Yaya Abubakar ke ciki yau shi da kan shi ke cewa mijin Fattu a cikin yar damuwa, Kunsan ance idan magana taima yawa kasamu wani yardadde ka fada mashi don samun shawara, ko dan warware damu saboda kunci, Abinda ya faru tsakanin mu da Sallawatu ya fada wa mijin Fattu din, inda ya kare da cewa shi yanzu ya rasa hukuncin da zai dauka akan mu, Mijin Fattu cikin kwantar da murya yace mashi, Hakkuri zakayi maigida don ka ga ita wanan dai itace aka zalunta, Saboda kaida bakin kace tasamay ta tana aiyukan gida ita kuma bata gidan ma tun safe, Kadai a takaice ita aka zalunta sosai don wanan barin çikin da tayi ba karamin rashi bane ai, Amma ita wacen matar, ya kama ka dan hukun tata don tasan batayi daidai ba, Yaya Abubakar ya kada kai, alaman ya gamsu da zancen mijin Fattu, Don haka ya mike yana cewa, yagode kwarai da wanan shawaran don shi da farko, so yayi ya sake ta gaba daya, ya huta da tashin hankali, Mijin Fattu yace a,a ba,a hakana ya dinga hakkuri da mata don su haka su ke, kamar tunkiyoyi, Daga haka ya ci gaba da bashi shawara akan abinda ya dace da kowacen, mu, A take Yaya Abubakar yaji dadin zama da mijin Fattu wanda a kullun sukan hadu massalaci amma ba wani, alaka a tsakanin su, Sai yau da dalili ya hada su har suka danfahinci junan su, Har zuwa dare suna tare don a tare su ka tafi gida ranan, Daga gurin da nake a kwance wayana ya fado min a rai sai na tunacewa Fattu ta bani, wayan da safe da ta zo, Don haka sai na lalaba wayan na a karkashin filon da nake kwance , Wayan baida wani enough caji sosai, amma dai zan iya kira dashi hakanan, Anty Amarya ce nakira ta dauki wayan tana magana acikin fada tana cewa , Meenatu wai yau ina kin ka shiga haka tun safe na ke kiran wayan ki amma bai zuwa,,? Nace cikin murya irin ta yanayin mara lafiya, Anty Walleh banda lafiya na yau, Cikin nuna damuwa tace missamay ki halan ? Sai da na dan cije bakina na dan hade wani abin bakin ciki na furta a hankali na ce, miscarriage na nassamu Anty, What ? Tafada cikin wani irin daga murya mai, kara tare da kara maimaita tambayan ta, Sai kuma tashiga cewa Innalillahi ,waina alaihim raj,un, Yan wagga bakar diya sai da tajawo muna wagga, irin hasara, Walle sai ta gani ga rabon ta, Sai kuma tace shin yanzu kina ina na ? Nace a hankali walleh ina asibiti anty tun daren jiya, Subbahanallahi takara fada sai kuma tace, To su asibiti shi mi sunka ce ? Saida na dan gyara kwanciya na sanan na ce ban san ko min sunka fada mai ba, Sai naji tana nanata ,a,a a miscarriage shi wagga diya anyi mugguyan shegiya, Dama du wadda ankayi tasan cewa kina da ciki kila shina tattaho maki da jidali don dai kuyi fada ta goga maki tsiya, To in Allah yayi duniya don Annabi kan ya za ya karewa, Don ke kin godema Allah ke gwada itako wassa sherin da taka kunsawa, Sannu Anty Amarya takara yi min tare da jamin kunne in samu mu rabu lafiya da ita, Nacewa Anty amarya to tace hutun mu ai ya kare in shirya in naji sauki indawo sokoto kawai abina nace mata insha Allahu danaji sauki zandawo sokoto da zamane, Ina jin kafin in kashe waya anty amarya tana ta surfawa Salawatu zagi na fitan arziki, ****** ********** ****** Ba laifi don zuwa yanzu Alhamdullahi na ji karfin jikina sosai, Don waye wangari sai na tashi jikin nawa Alhamdullahi, Wanan dalilin yasa likita da yazo dubani yabani Sallama Tare da yan magungunan da zan sha don su kara min karfin jiki na, Malam Abdullahi ne suka zo da driver suka maidani gida don Yaya Abubakar yana da Meeting a ranan, Nasamu Fattu a dakina ta gyara min shi fes sai kamshi ya keyi, tankar ina dakin a lokacin, Sai da na dawo gida Anty Sadiya tashigo har dakina na ta gashe ni, Abin bai wani bani mamaki ba don la,akari da irin yanayin, mutanen mu gurin kishi, Na mayi arziki da har tazo ta gaida ni ina matsayin kishiyar ta nayi barin ciki tazo gaisheni, Don inda agida mu ke bazan samu wanan daman ba, Sallawatu wace ban ma sa rai cewa zata zo gaida ni din ba don haka rashin ganin ta bai damay ni ba,, Itama dai din a daidai wanan lokacin suna ta kwasan rikicine da maigidan , Don yace sai tabar masa gidan shi don bazai iya zama da fitinanan mace ba shi, Sallawatu kan ta shiga tashin hankali sosai, don gaba daya ta rasa yadda zata shawo kan al,amarin, Duk yadda taso ya tsaya su fahinci junan su dashi yaya Abubakar yaki bat lokacin sa, Ta buga waya yafi a kirga yaki koda kallon wayan nata balle ya daga, Ta yi tunane barkatai ta yadda zata bullowa al,amarin amma ta rasa mafita akan zancen, Ta rasa tsaye ta kasa zaune a gidan don bata san abin yi ba, Gashi bata son fita ta koma gidan yan uwanta da take zaune, Don ko gida Lubbuna bata kaunar ta tafi don hakam tonon asirine agare ta, Sai faman sintiri kawai takeyi, don hankalin ta baya tare da ita,, Can daga inda take a zaune gefen mirror ta, taji karan shigowan motar shi gidan, Zubur ta mike, ta leka ta tagar dakinta, ta hangoshi yana kokarin zuwa parking space din gidan, Sosai tayi kokarin gurin tataro hankalinta, don samu ta fuskance shi, Daga labulen dakin ta take hango shi lokacin da ya shigo gidan dauke yar case din shi kamar kullun, Direct part dina ya nufa daga shigowan shi gidan abinda yasa Salawatu sake dan guntun tsuki ke nan a lokacin, A take numfashinta ya shiga kai da komo wani azabbaben kishi ya ziyarci zuciyar ta, sai ji take tankar numfashinta zai dauke,, Sai kuma ta tuna cewa yanzu fq ba lokacin kishi bane tukun dole ta aje komai a gefen, Ta fuskanci yadda zasu sasanta da maigidan nata wanda izuwa yanzu duk ya jagula mata lissafi, ****** ********** ****** Kwance nake cikin dakin nawa saman gado na sai kuma Maman Biu wace ke zaune daga kofa tana dan lazimi irin ta manya idan an fara girma, Da sallama a bakin shi ya shigo dakin inda yake kokarin gaida Maman Biu tare da mata ya gajiya, Ta ansa da fadin lafiya kalau ya kokari da aiki ? Dan murmushi Yaya yai mata yana cewa Alhamdullah, Ya maijikin ta ji sauki ko ? Ta bashi amsa da cewa ai jiki yai kyau, don yau kan Alhamdullahi gaskiya don babu matsalar komai, Kokarin tashi Maman Biu ke yi don ta fita, daga dakin, saboda ta bamu guri, Daga gurin da na ke kwance nace wa Yaya sanni da dawowa , Ya dan ya mutsa fuska yana kara matsowa gurina yace ya jikin naki ne ? Nai murmushi nace naji sauli sosai yaya, Alhamdullah, ban jin komai yanzu ai, Ya dan ya mutsa fuskan shi yana cewa naso nazo nadauke ku da kaina amma sai kuma ga meeting yazo muna, Nace yaya aiba komai tunda ga driver da malam Abdullahi sun zo ai, Yaya ya saki murmushi, ya ce ok barin tafi indan watsa ruwa in fito, Zandan fita in samo maki fruit don likita ya ce a dinga baki fruits da vegetables kina ci,, Nace cikin dan murmusawa ai nasamu lafiya Yaya ba sai naci ba, Har yakai kofa sai ya juyo ya kalleni tare da cewa hmmm kawai, Yasa kai ya fita daga dakin yayin da na sauke yar ajiyan zuciya Saboda nasan cewa yanzu yaya ya daina fushin da yakeyi dani, Yana shiga daki kamar yadda yace din bathroom ya shiga ya watso ruwa ajikin shi don yaji dadin kara fita,. Jin fitowan shi yasa Salkawatu da ke zaune tana jiran fitowar shi yin, Firgigit ta mike tsaye daga zaunen da take tana nufar sa, Duban ta yakeyi a cikin mamaki da ganin karfin halinta na zuwa dakin shi, Duk da irin kashedin da yayi mata na cewa kada ta yarda ya dawo ya samay ta a gidan shi Cikin daure fuska ya ke kokarin zuwa gurin wardrobe din shi don daukan kaya, Kasa takai da gwiwowin ta har biyu tana ce masa don Allah yayi hakkuri ya yafe mata, Haushi da takaicin ta ne suka rufe masa zuciyar shi,, Tayaya take nufin zai iya manta wanan abinda Salawa tai mashi a ratuwan shi, Takara cewa dullah dun Annabi Mohammed (S,A,W) kayi hakuri Oga sherin shedan ne Ta hada hannayen ta biyu guri guda tana cewa iam so sorry Oga Banyi haka da wani manufa wallahi just dai akasi aka samu kawai, Ya girgiza kan shi lokacin da tace hakan tare da mata wani irin mugun kallo, Yace look Salwa zan iya maki sauki saboda Allah da Annabi Mohammed, Don haka sai kinbar gidan nan na two days I am telling you,, Wani irin mugun shock taji don jin abind yace mata,na zancen barin gida, Yace cikin bacin rai I don't know who you are before , , Wani irin kallon mamaki tai mashi don jin abinda yace mata, tasan cewa rayuwan shi ya kai karshe ga baci, Ya ci gaba da cew kin bani mamaki Salwa do min banzaci haka ba daga gari don nazaci samun peace of mind daga gurin ki saboda you are mutual enough, Kokarin riko mashi hannu tayi yai sauri ya ja baya daga gurin ta, ke yana mai ture ta, Wasu irin hawayen takaici ne suka zubo mata alokacin don takaici, A take ta soma rera masa kuka adakin cikin wani irin murya mai ban tausayi, Yace ke ce kika boye min true colour dinki don ban san cewa haka kike ba, Yarinya karama acikin ku ma tafiku kwantar min da hankali a gida idan anyi magana sai kuce wai nafi son ta ne Abinda Meenat ke mun na kulawa duk cikin ku babu mai mun shi, For god sake Salwa live me alone please ? I want to be alone for now Yama kasa karasa zancen shi ya yasa kai yana mai barin dakin har ya kai kofa ya juyo yana ce mata kada ki bari indawo in samay ki a nan, Ganin zata nufo shi yai saurin fita yabar mata daki inda yabar gidan gaba daya, Wani sabon kuka Salawatu tasa a gurin inda ta durkusa ita kadai tana ta rusa kuka har sai da tagaji ta sauko daga sama zuwa part din ta, ****** ********** ****** Ina daga kwance naji motsin mutum anshigo dakina, A zato na ko Maman Biu ce tashigo batare da na juyo ba nake cewa Mama don Allah ki dan kashe min Ac din nan sayi nake ji, Naji an kashe AC din amma ba,ai magana ba don haka na juyo don ganin kowaye, Salawa ce tsaye da rinanun ifon ta da tasha kuka su kayi ja, Ganane ya fadi lokacin da na gan ta amma sai Allah ya bani ikon fadar kalman nan da akace yana tarwatsa muguwar kishiya, Watau La,illah,ha,illah Mohammed rasululah,,, A hankali naga ta tako zuwa inda nake kwance ta zauna Idon ta na mai zubar da hawayen nadama cikin wani irin ban tausayin yanayi, Kaina nakawar gefe saboda nasan cewa bata kaunana har cikin ran ta kawai dai muna funci ne ya kawo ta, Amma yadda naga babba da ita tana kuka agabana sai ta bani matukar tausayi, Takira sunana cikin muryan kuka tace Meenat nazo ne in baki hakkuri bisa ga abinda ya faru, Wallahi banayi shi bane intentionally, kawai dai haka Allah ya kawo, Ta dan dafani a hankali tace don Allah don Annabi Meenat kiyi hakkuri, sherin shedan ne, Nadago idanuna na kalle ta sai naji tausayin ta ya kamani Nace Salawa ina iya kokarina inga cewa inawa ko wacen ku biyayya don babu sa,a ta acikin ku, Ta dago idanunta sharkaf da hawaye tana dubana dasu, A idon nata sai naga babu alamar yaudara cikin su, Nace a hankali komai ya wuce insha Allah Allah ya yafe muna baki daya, Ta ansa da fadin nagode, Sai naga taci gaba da rusa kukanta hankali a tashe tace, Meenat Yayan ki ya dauki zafi dani sosai don yaki saurare na kamar yadda ke kika saurare ni, Nace kiyi hakkuri zai sauko shima insha Allahu, Ta kara cewa ta gode alokacin datake mikewa tsaye don barin dakin nawa, Daidai lokacin da Maman Bi,u ta shigo dakin tana ma Salawa kallon mamaki, Sallawa na fita Maman Bi u ta karaso gareni cikin damuwa tana cewa may wanan yazo yi gurin ka, ? Tanayi tana dan duduba min jikina tana yi kamar tana neman ganin wani abu, Mama tace Meena Meena kayi hankali fada wanan matan mugune sosai wallahi, Wanda yai ma dukan har ciki yafita may zaizo yi gurinka kuma don dadin baki,,,, Nadan murmusa nace Mama na sani nima dai don har dakina tana bani hakkuri,,,, ZEEE MAKAWA YELWA 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 5⃣9⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA ALLAH- AL- WADUDU,,, YAN UWA MUSULUMAI BARKAN MU DA WANAN RANAN MAI TARIN ALBARKA, YA ALLAH KA SADAMU DA RAHAMARKA YA ALLAH KA SADA MU DA NI,IMAN KA YA ALLAH KA SADA MU DA DARAJOJIN KA YA ALLAH KA SADA MU DA ALHERORIN KA, YA ALLAH KA SADA MU DA GAFARAN KA, YA ALLAH DARAJAN WANAN RANA KA SAUKE MASU CIKKAKAN MU LAFIYA, YA ALLAH WA YANDA BASU SAMU HAIHUWA BA ALLAH KA BASU, YA ALLAH MASU MAZA ALLAH KA KARA MASU ZAMAN LAFIYA DA KWANCIYAN HANKALI, YA ALLAH KA TAUSAYA MUNA KA BAMU MAZAJE MASU ALBAKA GA DUK WACE MA BATA DA,,, YA ALLAH KAI MAI,JIN KAN BAYINKA NE,ALLAH KA ANSA MUNA WANAN ADDU,OIN, KA SA MUNA JIN TSORON KA AZUKATAN MU KA BAMU IKON BAUTA MAKA BAUTA MAISTARKI YA ALLAH YA ALLAH MUN GODE MAKA MUN GODE MAKA DA KA YO MU MUSULMAI, ALLAH MUNGODE MA ALLAH MUN GODE MA, ALLAH KABA MU IKON CIKAWA DA KYAU DA IMANI, ALLAHUMA AMEEN👏👏👏👏👏👏👏👏👏👏 Kayan fruit's masu yawa Yaya Abubakar ya sayo min kuma na sha su so sai, ba kadan ba Naji dadin shan wanan fruit din da nayi don bakina yai min dadin test,, yanzu, Ganin na samu lafiya Maman Bi,u tace zata koma gida su kwana guda kawai tayi a gidan mu din, Gadiya sosai mu kai mata inda ita kuma kafin ta tafi sai da ta kara jamin kunne akan Sallawa, din, A lokacin da Mama zata tafi sai naji kamar a ce kada ta tafi gidan su anan zamuyi ta zama tare da ita, Tafiyan ta yasa na dan kara mikewa don kauda kadaici, na Ina zama ina kallon tv ina dan fita ina gyaran daki na, Da neman abinda zanci wa raina don ban girkawa gaba daya, gidan Ba,don komai ba sai ganin irin yadda har Anty Sadiya wace na ke gani kamar ta saduda, ashe har yanzu tana dani rike a zuciyar ta, Ta na min daukan kishiya a cikin rayuwan ta boyewa kawai take min, Sai da nai wanan ciwon na,kara sanin halin kishiya da kyau, Tsakanin Salawatu da Yaya Abubakar, wasan yar boya akeyi a gidan, Don haka bayan tazo dakina tai min magana akan inyi hakkuri aikin shedan ne, Sai ta bani tausayi sosai shigowan Yaya Abubakar dakina nake ce mashi don Allah yayi hakkuri abarwa Allah komai haka Allah ya kaddara, abin zai zo, Cikin wani kallo mai kama da hararan shiga hankalin ki tare da wani irin tsawa Yaya Abubakar ya daga min hannu yana ce min in masa shiru, Ni na aje masa ita ko shi ya aje ta da zan gwada mai yadda zan yi, da gidan shi, Kamar ruwa ya ci ni ban kara ko daga kaina ba tunda ya fara fadan shi kaina ya na a duke har ya fita, daga dakin nawa, Inda nima ya kara daukan zafi dani sosai don sai ban kara ganin sa ya shigo ba, ****** ********* ****** Iyanzu gidan mu komai lafiya ba wanda ke da lokacin wani, Idan gari ya waye maza sai su fita gurin neman kudi Don duk yawancin Iyayyen mu dan kudin da Yaya yake turo masu dubu hamsin hamsin sai suka dan fara sana,ar dogaro da kai da shi,,, Daga haka yanzu gaskiya abubuwan suyi dama sosai a gidan, Mama Ladi izuwa yanzu abin Yaya Abubakar ya fara daure mata kai sosai, Gashi tayi tayi dashi da ya saki Meenatu amma yaki sai ce mata ya keyi akwai abinda yake jirane, Idan lokaci yayi ai zai sakeni din, Ita kuma tasha alwashin cewa bazata yarda ta hada da irin zurian mu a cikin iyalin ta ba, Babana yanzu yan buga bugan shi sun kara yawa don yakan tafi kauye ya sayo abin da zai yi saurin shiga idan ya kawo Birni, Hakan yasa zaka fahinci samun walwala saosai a tare da shi yanzu sama ga farko, Hajja wace tun bayan dawo wanta kasan bargu wurin bokan ta batai wasa ba gurin ganin ta yi duk abinda ya umurce ta dayi don ganin dodo ya dawo daidai kamar farko, Yanzu din ko abin yana da dan dama dama don dodon nata iyanzu ya rage yawan langabewan nan sai aukin shan ruwa don yazu duk yadaina yawan shan ruwan nan sosai, Ta tara daki a kayan masarufi masu yawan gaske amma bata kaunan ta sai abin koda ashirin ne, tafitar da kudi, Bata kwantuwa ko kadan sai in ya kai mata dole dole zaka ga tafitar da kudin, ****** ********** ****** A gurin da na idar da Sallah don nafara dazun da rana da naga jini ya dauke min, Nan nake zaune bayan Salah isha,i ina tilawa a hankali, Nadauki lokaci mai tsawo ina karatun don babu abinda zanyi, a lokacin, Anty Sadiya itace da girki, a ranan bayan gama abincin tane, ta gyara guri sama sama, Aikin duk ya kai mata ko ina sai faman fada takeyi a cikin zuciyar ta, Tana cewa ita bazata iya wanan aikin wahala ba gaskiya, Yaya Abubakar ya zauna don ya ci abinci da ta girka masu, Ga ido abincin ya bashi sha awa sosai har yana jin dadin ganin ta, ta iya girki haka yanzu, Tun gurin diban abincin zuciyar shi ta fara tsinkewa, Don yana saka hannuwan shi yaji tuwon yai ruwa sosai, Bai so ba ya,kai ga bakin shi don azaton shi miya zaiyi dadi yasamu tuwon ya wuce mai, Ai da sauri ya dawo dashi ya kalli gurin da take a fusace yana cewa yo ga tsiya, Manene wanan haka Sadiya ? Sai ta tsuke fuska tace abinci mana , Abinci fa ki,kace ? Yanzu saboda Allah Sadiya shekarunki da zaman ki yar hausawa kuma tallaka ace wai baki iya tuwo ba kamar ki, ? Ya mike kawai ya sa kai ya wuce sama abin shi batare da ya juyo inda take ba, Sai cewa Sadiya tayi yanzu saboda Allah menene laifin wanan abinci dai ina dai tuwon ne bai yi karfi ba kawai, Saidai Itama da kan ta tana kai loman tuwon a bakin ta sai ta tsuke fuskan ta, Sai a lokacin ta tuna cewa bata saka maggi a miyan ba fa, Mikewa tayi tabar gurin tare da tatara kwanonin ta, Daga dakina bayan na tashi yunwa ya isheni don haka na,fito neman abinda zanci, Naga kula a rufe sai na bude tuwo na gani na shinkafa, saidai tun ga idona tuwon yai min ruwa tuwon sosai, Amma da yake ina son ci sai na yanka hakana na zubu miya mai yawa kin san mu mutanen hausa da son miyan vegetables,, Nazo saman dining na soma ci loman farko da kyat na samu na hade shi ya wuce, A take na kara kallon tulin abincin da ke gabana sai naji wani iri, Ga wani amai da ke taso min kamar zan kife, don gaba daya na ji zuciya, na ya rufe min ban da sukuni ko kadan, Da gudu na mike zuwa dakina, kafin in kai bathroom har na fara shekashi, a hanya, Na dauki lokaci duke ina zuba amai gurin sanan na mike daga tsugunen da nake ina cewa wai, wai ina maida numfashi, Sam ban san cewa Yaya Abubakar yana tsaye kaina ba sai da na juyo don komawa bedroom dina, Ya na tsaye hannayen shi harde a saman kirjin shi fuskan shi babu walwala a cikin ta, Wani kallon tuhuma naga yana min ya, ce mai yasamay ki may kikaci ne haka,? Ina kokarin goge fuskana da haban rigana sai kokarin kaiwa saman gadona nake yi a lokacin, Har inda na zube saman gadon ina cewa wai, wai Yaya ya tako yazo ya tsaya a kai,na yana cewa May ke faruwane haka wai ina tambayan ki ne fa don dai ba zazzabi bane ko, ? Da kyat na iya daga mashi kai nace ba zazzabi bane kawai dai, abinci naci shi zuciya na ya tashi, Cikin karaji ya tambayeni wani abincin badai wanda Sadiya ta girka ba ko, Na daga kai alaman shi daidai lokacin da nake kokarin gyara kaina ga filo, Sai kuma naji tankar wani aman zaizo min take na mike zaune da sauri aiko aman ne na nufi bathroom, Sai da na samu na amaye guntun wanda ya rage min a ciki sanan na samu saida, Yaya yana kaina sai faman tambayana may zanci yakeyi nace mai ban son komai na koma na kwanta, Sai sauke numfashi guda guda nakeyi a wahalce ina faman cewa wai, ina juyawa don indan ji dadi, Barcin dole ne ya dauke ba shiri ban san inda nake ba, Tausayi sosai na ba Yaya Abubakar wanda ke tsaye a kaina yana min duban tausayi, Shima abinci zai fita nema shine yazo ya tambayeni may nake son ci ? Daga stairs din da yake saukowa yagan ni na f da gudu, Bayan yasayo min abinci ya samu still ina barci sai ya aje min su a gefen gado na yajawo min kofan dakina, tare addu,a Acan cikin dare na farka da wani irin yuwan sai nake jin kamar banda ko hanji a cikina, Kokarin tashi nakeyi in fito don neman abinda zanci, Sai idona yakai ga ledan da yaya Abubakar ya aje min a gefen gado, Na mika hannu na na jawo ledan naji dadin ganin abin dake ciki, Kaza ce gassa irin na modern dinan yaji kayan hadi sosai sai drinks masu sanyi da kuma snacks, Kamar ance in kashe tocin wayana don na duba kofana nagan shi a rufe duk da haka saida na sa key daga ciki, tare da addu,a nayo fitsari, sai na hau cin kazan ina dan korawa da drinks din,,, Idan har ba ki manta ba na taba fada maki cewa nataba jin nishin wani abu a cikin gidan mu har sai da nai zazzabi washe gari A rin daidai lokacin da naji wancan din yau ma haka naji wanan nishi maiban tsoro, Tankar ana wani irin huci ne na gajiya ko na wahala, Dama saura kiris in gama don haka nai shiru ina sauraren shi, Inajin abin tankar bayan gurin parking space din motocin yaya hucin ke fitowa, A hankali na kauda ledan na dan jawo jikina tso nahaye gado naja bargo, Bakina yana dauke da addu,oi ina ja idona na rufesu, Gabana sai wani harbawa yakeyi tankar zai tsage, don tsoro, Can kamar minti talatin lokacin har barci ya fara daukana Sai jin wani irin ihu nayi tankar kunnuwa na zasu tsage, Numfashi na naji kamar zai dauke don tsoro, ihu nakara ji a karo nabiyu abinda ya tabbatar min da acikin gidan mu ihun nan yake, Ban san lokacin da nakai zaune ba don tsoro sai naji ihun da yafi na bayan karfi mikewa nayi wuf na nufi hanyan fitowa waje, Bakina dauke da addu,a, daga dakin Anty Sadiya waban ihun ke fitowa cikin tashin hankali, Ai gaba dayan mu muka nufi dakin nata dai lokacin da shima Yaya Abubakar ya sauko daga sama, Muna shiga dakin Sadiyan na hango abin kamar maciji tana kokarin fita ta window dakin ta, Shima yaya Abubakar ya hango wanan abin da idon shi , Sadiya tana tsaye hannuwa a kwandare kamar mahaukaciya sai ihun fitan hankali takeyi, Da sauri yaya Abubakar ya bi abin baya sai dai baiga komai ba, Ga Sadiya taki barin ihun da takeyi tankar zautata, hannu a kwandare mata, Yadawo ya samay mu adakin ina ta tofa mata addu,oi Shiya kamota yashiga karanto mata ayar Allah sai kallon shi nake yi da mamaki don zakace ko wani alaramma ne, A hankali nake bin abinda yake karanto mata daga inda nake zaune gefen su Sallawatu tafado dakin a firgice tana cewa, May ne may ke faruwa ne, wai ? Hannu yaya ya daga mata batare da ya tsaida karatun shi ba yana mata alaman tayi shiru, Muna tsaye cirko cirko sai mukaji Sadiya tafara nuna karkashin ta tana cewa a cece zai shige mata a gaba, A lokacin ji nayi tankar in tsula buli don tsoro daga gurin da nake, tsaye, Da sauri yaya yace a dauko mashi waya adakin shi, Daga cikin mu ba wacce ta motsa don tsoro ganin Sallawtu ba zata ba dole na mike don in tafi, Muryan shi naji yana cewa dakata in tafi nai wani dadeba ya dawo alokacin yana kokarin kiran nomban wani, Ashe mijin Fattu ce ya kira sai yafita da suka iso ya bude marsh kofan shigowa, Tare da mama suka shigo tana tambaya cikin damuwa may ke faruwa ne, Mama ce ta karasa gurin da yake rike da hannayen Sadiya da sukq zage a lokaci guda tankar ta taba ruwan zafi, Bayani yaya ke masu suma duk hankalin su a tashe yake suka kara fita suka zagaya gidan, Dai dai gurin window abinda suka iya gani shine tankar wani abu mai mai yabi gurin da jan jiki, Dole suka dawo aka dauke ta zuwa asibiti sai kokarin bude zanin ta takeyi wai abin yana nan yana kokarin shige mata a gaba, Tsoro duk ya kara kama mu a lokacin don haka akace Baba Hamza' ya tsaya atare da mu gida su kuma sai su tafi har mama,biu Mama itace bayan motan zaune tare Sadiya wace take tankar zautata, Mama tana rike da hanayen ta duka biyu tana tofa mata addua, Sun isa asibiti ba su gane komai ba sun daiyi mata alluran barci tare da cewa lafiyan ta kalau subari idan ta tash aga reaction din ta, Wanan abin yai mugun tayar wa kowa da hankali don abune na sihiri, Har safe muna zaunr a babban falon zaune kowa da abinda take sakawa akai Nidai a halin yanzu gaskiya gida nake son yaya Abubakar ya maidani Don kwata kwata duk garin da ya fita raina sam ban son zama Jinkiran sallah yasamu mikewa kowa ta futa zuwa sallah, Bayan na idar na shiga kitchen na hada masu breakfast don akai masu, Batare da tunanen komai ba na kira baba Hamza nace ya kai masu asibiti na bashi key din motan da mukan fita da ita anguwa, Sosai sunji mamakin ganin yadda na aiko masu da breakfast a cikin lokaci, Abin da ita kanta Sadiya amatsayin ta na babban a gare ni batai tunanen yi ba, Yaya Abubakar hankali duk a tashe, yake don abubuwa sun zo mai acikin tashin hankali, Duk abubuwa sun zo mai acikin tashin hankali gashi ba kowa akusa da mu, sai, abokan arziki, Yaji dadin yadda su Maman Biu ke gwada muna mutunci, abinda farko su da Sadiya basu san cewa zaman lafiya da makwabta yana sa azama daya, Sai yanzu da farko yaso ya hanani hurda da su amma sai yaga idan ya hanani bazan so ba sai ya kyaleni kawai, Sai gashi daga baya zama dasu yai mashi dadi sosai tunzuwan Mama Ladi jinya Dakuma kwanciyana asibiti sai gashi kuma yanzu sun mashi wanan halarcin , Don mijin Fattu shike ta zirga,zirga a cikin asibitin,, Saboda shi yaya duk jikin shi yai sanyi sai faman tunane yakeyi barkatai, Babu abinda ya ke mai yawo azuciya kaman wanan dodon sihirin da yaga fitan shi daga dakin Sadiya, Don da bai gani ba da sai yace kila dai mafarkine ko wanu abu, Sadiya ta farka cikin yanayin damuwa sai dai yanzu complain takeyi da cewa hannun ta, hannu ta na mata zugi da radadi, Ganin haka yasa mijin Fattu wanda Yaya ke kira da, Lawal, Yace wa Yaya su zo gefe su tatauna, akan zancen, A wani kauye can kauyen Suleja suka yanke shawaran zuwa tare, har ita Sadiyan da Mama, Basu wani dade ba suka iso gurin malamin, malami ne mai aiki da alkur,ani, Don haka yai mata addu,oi tare da bada abubuwan da za, adinga shafa mata da kuma hayaki, Tun anan ya bayar aka shafa mata wani abu a hannun nata, Cikin ikon Allah sai ta dan lafa jin zafin Sosai hakan yasa malamin samun yin magana da ita, Ta soma da cewa, Nafito daga dakin maigida zuwa nawa dakin don ban san may yasa ban son kwana can har safe ba, Bayan nashigo ne sai nadan kewaya daniyar inyi fitsari, Na duka shine naji kamar abu yana lasana koda na haska toci shine naga wani irin halitta, yana kokarin shige min a gaba, Ganin yana son shige min yasa nai kokarin rikeshi da hannuwa na ina ihu, neman ceto, Takarashe zance acikin kuka da neman mafita murmushi malamin yayi tare da kada kai yana cewa, cikin irin harshen su na gwari, Allahu Akbar wanan wani sihiri ne mai karfi gaskiya, To amma yanzu atafi a shafa wanan abubuwan da ya bata zuwa gobe in Allah ya kaimu sai su dawo harda ita don yana son yin istihara akai, Godiya Yaya Abubakar yai wa malamin tare da bashi kudi sai malamin ke cewa su bari kawai idan sun dawo sai su bashi, Amma sai yaya Abubakar ke cewa yadai karba ai sadaka ne ya bashi dole mutumin ya karba, Sunkamo hanya kowa da abinda yake sakawa azuciyar shi, A lokacin wayan Lawal mijin Fattu yai kara yadauka tare da Sallama Fattu ce a layin tana fada mashi cewa babu fa abinda zasu dafa agidan, Yadda Yaya Abubakar ya fahinci zancen mijin da matan sai suka bashi tausayi don ya fahinci sai ya fita gurin buga bugan shi yake samo masu abinda zasu ci, Don haka bayan sun kai su mama gida da Anty Sadiya inda muma muka bita dakin don mata sannu da jiki, Bayan kara yiwa, Mama bayanin magani Yaya yace wa Lawal yazo su fita tare,, Basu tsaya ko ina ba sai kasuwa nan suka sayi kayan stuff duk wani abin bukata sun saya aka loda wa mai Nape ya biyo su baya dashi, A gidan Lawal Yaya Abubakar ya tsaida mai Nepep inda ya umurci da a sauke kusan rabin sayayan da sukayo a kofan gidan Lawal, Mamaki sosai ya kama Lawal inda har ya kasa yin magana yakai wani lokaci tsaye a cikin mamaki, Sai da ya ji muryan Yaya Abubakar yana ce masa lokacin sallah magrib yayi, Yakamata su karasa massalaci don kada su rasa jam,i, Sunyi sallah sun ka fito don zuwa gida duba jikin Sadiya, Sai a lokacin Lawal ke cewa maigida ban sanbirin godiya da zan maka ba gaskiya, Don rabona da, samun irin haka tun lokacin da nake aikin Banki, Sai kwatsan wata rana aka turo muna da takardan sallama daga aiki har mu biyar, Batare da mun samu wani sallama da ga chan headquarter mu ba, Wanan dalilin yasa na sai da duk wani kaddaran dake gareni na dawo nan, nai muna wanan ginan, Sai nake fita kullun kasuwa ina yawon dillanci don mu samu abinda zamu ci, Yaya Abubakar yanisa tare da cewa ai aikin banki baida tabbas, Don idan tsiyan su ya tashi daga sama kawai zasu ce sun sallami mutum Ba don komai ba sai don kada suyiwa mutane sallaman barin aiki, kamaf kowa, Don haka ni sam ban dauki aikin banki acikin aiyukan kwarai ba, Lawal yace ai maigida mun sheda hakan sosai wallahi, don alokacin abin kamar zai tabamin kwakwalwa, Godiya na ga Allah daya bani mahaifiya irin mama wace tasan yadda zata kwantarwa da mutum hankali, Don da taimakon Allah da na ta har na dawo normal person dina, Takuma aura min Fattu diyar yar uwar ta don matar da na aura da farko fafir taki wai banda komai ita bazatai zaman wahala ba, dani, Tafi abinta tabar ni batare da ta tausaya min halin da nake ciki ba, Nisawa kawai yaya Abubakar yayi don ya fahinci matar bariki ce Lawal ya aura, Don haka ya ce Allah ya kyauta a ta kaice kawai, batare da ya kara cewa komai ba, Bayan fitowan su daga Sallah suka shigo a tare don duba jikin Sadiya, Sun samu tana zaune Mama tana shafa mata magani a hannayen ta da suka kunbura sukai wani irin jajir dasu, A daidai lokacin na shigo dakin dauke da kulolin abincin su ahannu, Bansan cewa su Yaya Abubakar suna dakin ba a lokacin don haka ina ganin su sai na koma baya da sauri , Hijjab dina na sa nafito na dawo dakin inda na gabatar masu da abincin su, Amma sai Sadiya take cewa bazata iya çiba don bata jin cin komai, Nadan koma kusa da ita ina cewa ko in hado maki tea mai zafi ki sha ta gyada mun kai kawai alaman eh, Bandade ba nadawo dakin dauke da cup din tea mai zafi da bread, Amma sai tace inbar bread din don ruwan tea din kawai zata sha, Gurin daYaya Abubakar yake tsaye ya kura mata ido dagani nazarin abubuwa da dama yakeyi a lokacin, Cikin dan tausa murya nace wa Yaya Abubakar Yaya abinci fa,? Sai da ya nisa tare da lumshe ido yake ce min Meenat zanci , Amma naso sai nai wanka tukun nace to barin hada maka ruwan zafi ko? Yadan lumshe idon shi kadan yace no kibarshi kawai kin san cewa ke ma ba lafiya bane dake, Kibi jikin ki a hankali don kada jikin ya tashi maki,don stress na iya saki kwanta again, Nai dan murmushi na ce, ai naji sauki Yaya zan iya insha Allah, Ya ce No ki dai bari kawai, a lokacin Salawa ta shigo dakin tana saye da wani dogon riga baka maidan karamin hannu kamar shimi, Kanta, ya saye da fullan mai net, wanda ke nuna kitson attachment din ta daga cikin sa, Sannu da zuwa tai masu yay Abubakar tare da jira mai zaice ba Ta juya tana duban inda Sadiya take tana cewa Sadiya ya jikin naki, ? Sai da Sadiya ta dan murmusa kadan sanan tace a hankali cikin daurewa Da sauki, Sai kuma dakin yai tsit a lokaci tankar babu kowa a gurin, Jin kada Salawatu ta juya yayin da zata bar dakin tana cewa Allah ya sauwaka,, Tabar dakin abinta zuwa dakin ta ba,ai wasu mintuna ba Yaya Abubakar yabi bayan ta, Kafin ya karasa fita nake cewa mijin Fattu malam abincin kaima sai yaya yafitone zakaci,? Yace kai haba aini yau maigida ya wadatar da mu Anan yake fadawa Mama irin alherin da Yaya Abubakar ya sai masu, Har dani dake gefe dakin sai da na taya su murna tare da godewa Allah Mun kai wani lokaci zaune mu na taya Sadiya da mama hira, Sai wani lokaci Fattu da maigidan ta sukai muna sai da safe, Bandade ba nima na nai masu saida safe na koma dakina sai dai zuciyata tab da tsoron abinda dare zai yi ywu, Na rufe kofana tare da jero addu,oin da duk na iya a bakina, Nabi duk wani kafa nq dakin na toshe da adduoin, A hankali na kwanta saman gadona a takure ina mai jin tsoron dare, Da haka har barci barawo yai gaba dani batare sa na sani ba, ZEEE MAKAWA YELWA [8/22, 08:10] Anty Lantana: 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 6⃣0⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA ALLAH-AL- MAJEED YA ALLAH MUNGODE MA DA KA NUFE MU DA GANIN WANAN RANAN MAI TARIN ALBAKA, YA ALLAH KA SA MUNA CIKIN YANTATTUN BAYINKA, YA ALLAH KA SADA MU DA RAHAMAN KA YA ALLAH KA TAUSAYA MUNA DUNIYA DA LAHIRA, YA ALLAH KA GAFARTAWA IYAYYEN MU, YA ALLAH KA KARA RUFA WA IYAYYEN MU ASIRI DUNIYA DA LAHIRA, YA ALLAH KA BAMU MAZA JE MASU MUTUNCI, ADINI SANIN YA KAMATA MASU, ALBARKA YA ALLAH KA GAFARTAWA DUKKAN QULLUMIN MUSULMIN ALLAH MAZA DA MATA BABBA DA YARO, TSOHO DA TSOHUWA , YA ALLAH MUN GODE MA YA ALLAH MUN GODEMA YA ALLAH MUN GODE MA DA KAYO MU MUSULMAI YA ALLAH KA KARBI TUBAN MU, KASA MU MUTU MUNA MUSULMAI ALLAH, AMEEN YA ALLAH 👏👏👏👏👏 BARKAN MU DA SALLAH YAN UWA Bayan tafiyan Lawal da iyalen shi Yaya Abubakar ya koma dakin shi don ya huta, Sai kuma zuciyar shi ta kasa barin shi ya huta din,don tunanen abin mamakin da ya auku yau a gidan nashi, Lalai badon da idon shi ya ga abin ba da bazai taba yarda ba , To may ye wanan abin ya tambaya da kan shi, daga ina yake haka, May ya kawo shi gidan shi mau yake so a cikkin iyalin shi Iska mai zafi ne ya furzar da ga bakin shi tare da kai ma hannayen shi naushi a,lokaci guda, Malam tsoho ne ya fado mashi a rai don dole ne ya fadawa tsohon wanan abin saddabarun da ke faruwa a gidan shi, Sai ya kai duban shi ga agogon wayan shi take yana sa a ran shi cewa dare yayi sosai a lokacin, Don haka dole ne ya bari har zuwa gobe da safe ya kira malam din, Da wanan shara ya shirin kwanciya barci inda ya bi lafiyan gadon shi, Sai bayan ya kwanta yake tunanen cewa Meenat bai ganta a waje ba tun bayan dawo wan shi gidan, Hakan yasa shi mikewa da nufin zuwa dakin nawa don ya duba ya ga halin da nake ciki, Salawatu ce ta shigo dakin, ta na saye cikin, wani rigan barci mai kama da babu komai a jikin ta a lokaci, Sau guda ya daga kai bai kara kallon ta ba, Zagayowa tayi ta bayan shi ta rungumo shi tana cewa, Sweet Oga har yanzu fushi kakeyi danine please ? Tana son su hada baki yai saurin ture ta yana cewa Salawa are you out of your sense ? Baki san halin da nake a ciki bane halan ? Har zaki shigo kina son in making love da ke a haka Cikin wani irin juya ido takara kwanti mashi a jiki tana cewa to amma ai sai naga taji sauki ko ? Wani mugun harara ya watsa mata yana cewa ok don ciwon ba a jikin ki yake ba ne har kike ganin cewa, zaki samu kai na a yau din, A gaskiya ni ban gane ba dear duk kwanakin nan baka da time dina sam, Kai ya kada yana cewa look Salawa, ban son yawan magana don ina a cikin yanayi yanzu haka , Sai dai duk da irin yadda Yaya Abubakar yake neman ta kyale shi Salawatu bata yarda ba don saida tai irin halin su na matan bariki ta hilance shi, Abinda yasa Yaya Abubakar ya manta da zancen zuwa duba ni a lokacin da yai niya yi ke nan, ****** ********* ****** Malam tsoho wanda tun a tsakar dare bayan ya idar da sallah nafilan shi kamar kulun daga gurin da yake a zaune barci ya dan fisgeshi, Mafarki yayi da wai gashi a gidan Yaya Abubakar, Inda yaga matan shi a cikin damuwa, sai kuma shi Abubakar din wanda, yafi kowa shiga hall n damuwa, Sai kuma aka dan nuna mashi fuskan mace tare da wata, tana, ta azabantar da ita ta hanyan sihiri, Firgigit ya farka sai yaga har tasbahan da ya ke rike a hannun shi yana ja ya fadi kasa,, Hankalin malam ne ya tashi inda ya kai indon shi ga mamakeken agogon bangon dake dakin don ya duba time, Karfe uku da wani abu na dare lokaci ya nuna mai hakan yana nufin cewa tsakiyan dare ake, Abinda ya keyi ne yaci gaba dayi tare yi wa family din jikan shi addu,an, neman tsari daga sherin shedan, Kamar yadda wa yan da ke kwana raye gurin kokarin kai kukan su ga Allah Ubangiji Subbahanahu wata, ala, mai jinkan bayin shi, Barci da shedan kan dan so rinjayen mutun a waau lokuta irin haka, Malam tsoho still, barcin ne kuma yaso yakara rinjayen shi har ya dan fara mafarki Kamar farko wanan katon da mamaki ya tashi don wace ya gani acimin mafarkin nashi a lokacin, Hakane ya tabbatar mai da cewa lalai akwai matsala sosai a gidan Jikan nashi duk yadda aka yi, Hakan ya kara sa malam qaimin gurin ganin yai wa jikokin nashi addu,oi,, ****** ********** ****** Ya Abubakar bai farka ba sai gabanin asuba inda ya sauke idon shi akan Sallawatu wace ke kwance rub da ciki tana barci a gefen shi, Dan tsuki yayi yana kokarin mikewa don ya duba time, I zuwa yan karfe biyar saura na asuba hakan yasa shi sauri mikewa da sauri don, bai zaci cewa lokaci ya kai haka ba, Don yaso ace cikin dare ya ziyarci su Maman Bi u da Sadiya don ya ga irin halin da su ke ciki Amma sai wanan shu,uman matar tashi ta ja hankalin shi har ta shagalar dashi, Bathroom ya fada inda yai wanka tare da dauro awala kafin ya fita massalaci sai da ya tafi dakin Sadiya, don ga kwanan su, Yasamu mama tanawa Sadiya fitara duk da sanyin Ac dake a dakin Amma sai korafi Sadiya keyi na cewa ita zafi takeji sosai, Cikin mamaki Yaya Abubakar wanda ke saye da jallabiya a jikin shi, Yake tambayan Maman Bi,u abinda ke faruwa take fada mashi irin halin da suke ciki, tun gabanin asuba,,, Gab da Sadiya ya nufa yana mata sannu da jiki tare da tambayan ta yadda take ji, Bayan yasamu tai dan mashi bayani sama,sama ya yi mata addu,, a Tare da tofa mata aruwa yabata tasha yadauko mata wani standarding fan yasa masu a dakin, Take tasamu barci daga haka ya wuce yin sallah asuba, Sai da gari yai haske sosai, sosai sanan Yaya Abubakar ya shigo gida Ya samu ina dakin gurin su Anty Sadiya ina masu yaya dare,? Ganin da yai min zaune a gefen carpet din da Mama take akai, na wani takure guri guda kamar mai jin sanyi, Ina kwana nai masa da,ga inda nake zaune a cikin ladabi tare da girmamawa, Gurim da nake yake duba na yana cewa to yaya jikin naki ? Na ansa mashi da cewa a cikin wani irin murya da Naji Sauki, Yace yanzu bakya dai jin komai ko ? Eh nace mashi kaina yana a duke, Sannu Mama ya maijikin bata farka ba har yanzu ko ? Eh mama tace mai ai Alhamdullahi tun dazun barcin takeyi, Kafin ya ce wani abu wayan shi ce tai kara alaman kira, ya shigo mai, Saida yai tsuki don yana mamakin wanda ke kiran shi da wanan safiyan haka ? Malam tsoho yagani a rubuce saman screen din nasa, Yai matukar mamakin ganin kiran malam din a wanan lokacin, Cikin mamaki yace malam tsoho Abinda yasani saurin dago kai ina duban shi ke nan, A take kuma naji gabana ya bada dam a lokaci guda, don jin sunan wanda ya ambata, Gaisawa naji sun fara yi tare da tambayan lafiyan mutanen gidan Sai da naji suna ci gaba da zance yasa hankali na yadan kwanta kadan, Don nasan cewa, lafiya babu wani abinda ya faru ke nan a gida, Saidai kuma ina tunanen dalilin wanan kiran da wanan safiya haka,, Mikewa Yaya Abubakar yayi zuwa waje inda suka fara zance da malam din, Malam ke tambayan Yaya Abubakar da cewa lafiya dai ko kake da iyalin ka? Yaya Abubakar yarasa abinda zaicewa malam din sai yai dan shiru Malam yakara tambaya yana cewa domin jiya cikin darai nai mumunqn mafarki a kan ku, Innalillahi Yaya Abubakar ya ce da yaji may malam din ya ce mashi, Cikin murya irin ta damuwa yake cewa wallahi malam abin sai a hankali domin gaskiya, Meenatu ce ta fara samun matsalan barin ciki satin da ya gabata, Bayan tadawo gida da kwana biyu sai kuma ita Sadiya tasamu wani matsala, Subbahanallahi malam ya furta a cikin damuwa, tare da nuna kulawan shi, Ya jikin ita Meenatun yanzu da sauki ko Yaya Abubakar ya amsa mashi da cewa taji sauki sosai don kwana guda tayi aka sallamay ta daga asibitin don jinin da yake zuba ya tsaya da wuri, Allah ya kawo rabo na moriya inji malam tsoho saidai yaya Abubakar yakasa ansa mai Ameen a fili sai dai a cikin zuciyar shi, Malam tsoho yace ita kuma dayar may ke damun tane fa,? Ya Abubakar yace malam al,amarin ne kamar na jinnu wallahi don abin ma ban san yaya zan fada maka ba, Amna dai gaskiya zan iya ce wa aikin jinnune kawai don yadda abinke mata, A take Yaya Abubakar ya kwashe duk yadda abin yafaru ya gayawa kakan nashi, Sai da malam ya gama sauraren sai ya nisa yana cewa lalai duniya tai nisa, sosai Abubakar, Da a kusa kake dani da akwai maganan da zamuyi na musan man akan wanan zancen Shiru yaya Abubakar yayi yana sauran malam din acikin tashin hankali Shiru su kayi na dan wani lokaci bayan malam din ya kare zancen shi, Ya Abubakar ne ya dan kau da shirun da cewa, yanzu malam may nene mafita,? Malam ya nisa yace Allah ya kare ya tsare amma gaskiya dole mu san abinyi, Malam tsoho yacs amma duk da haka Wadda zai taso yau din nan in sha Allah, Sai dai duk wani bayani sai bayan ya iso insha Allah zata samu lafiya, sai daga baya musan abin yi akan zancen, Yanzu lafiyan ta yafi muna komai don haka sai mu tashi muci gaba da mata addu,a, Ya Abubakar yace gaskiya ne malam nan ma akwai wani wanda mu ka fara zuwa gurin shi kuma da alaman aikin sa na da kyau. Malam tsoho ya ce hakan na da kyau, amma don Allah idan Allah ya kawo Wadda lafiya ka tabatar da cewa kasha magani, Insha Allah inji Yaya Abubakar yana mai cewa kakan nashi, Malam tsoho yakara tambayan jikin Meenatu da fatan babu wani matsala atare da ita, yanzu, Nan yaya ya tabbatar mashi da cewa na samu lafiya sosai,,, Sukayi Sallama inda yaya Abubakar ke ta godiya sai dai zuciyar shi fam da mamakin yadda akayi kakan na shi ya san zancen Sadiya, ****** ********** ****** Har zuwa wani lokaci babu abin kari a gidan don Salawatu tana can tana barci abin ta, Ga mara lafiya tana neman abinda zataci don yunwa, Sai bayan dawowansu Ya Abubakar daga kauyen da suka tafi karbo magani, suka, dawo, Yake tambayan abin karyawan shi Sadiya ce tafara mashi korafin rashin cin abinci tunda safe har yanzu sha dayan rana da wani abu, A fusace ya shiga dakin Sadiya wace ke kwance share,share saman gado, Tana kwasan barcin ta hankali a kwance da gani ko wanka batayi ba alokacin, Wani wawan duka ya kai mata abaya, ta mike a firgice tana cewa my dear, kadawo ne, Tambaya ya jefo mata da cewa ina breakfast din su Sai cewa tayi ban samu yi ba don nagaji sosai wallahi hakan ya sa ban tashi ba takarashe tana bata fuska, Ido Ya Abubakar ya kura mata cikin takaici yana cewa, Yanzu har da yar uwar ki da bata da lafiya baki masu breakfast ba ki ka bar su hakana, Mika tayi tare da daga hannayen ta sama ta hada su guri guda,, Tai wani mika wanda ya bayanar mata da duk wani sassan jikin ta, a fili, Wani irin tsukin takaici yayi yabar dakin cikin takaici, da bacin rai, Yana fitowa adaidai lokacin da nafito daga dakina zan shiga kitchen saboda wani irin yuwan da nake ji tankar banda komai a cikina don sai nike ji ko hanji babu,, Batare da nace mai komai ba na wuce gigice zuwa kitchen din, don neman abinda naci, Tun bayan dawowa na daga asibiti nake yawan jin wanan yuwan haka, Indomie na dafa nacika mai ruwa da yaji tun yana asaman wuta nafara diba ina ci, Ban juye a plate ba tun a cikin tukunya na cinye abina sai da na kusa gamawa na tuna da ruwa, Gurin fridge na nufa da sauri na balle goran ruwa na kafa kai,, Sai da na kusa rabin goran ruwan san na kula da Ya Abubakar wanda ke tsaye a kofan kitchen din hannayen shi a harde saman kirjin shi, Cikin dan kaduwa da firgita nace cikin dan in,in iniya Sannu yaya, Lafiya kike kuwa ina kokarin tatara natsuwa na nake cewa, Lafiya kalau nake yaya Kina lafiya kike cin abinvi haka kamar mayunwaciya, Nai murmushi kadan nace yuwan dai naji kawai shiyasa, Don tun da naji sauki sai na fara wanan yawan cin, Inaga kamar maganin da suka bani na karin jini ke sani wanan yawan cin da yawa, Ok kawai yace tare da tamvayana may Sadiya zataci ne mai sauki, Nace ko adafa mata noodles din itama ? Idan zataci a dafa mata shi din ko ? Na dafa mata nakai mata sai dai na samu kamar tana barci ne, Don haka na aje tare da juyawa, a lokacin naji fitowan Mama wace ashe tana bayi tana wankewa, Nan nake fada mata cewa idan ta tashi ga abinci nan, Maman Biu ta tabe baki tana cewa gidan ku babu tsari sam wallahi , Gida da mara lafiya za,a ce ba,a girka abincin safe ba har yanzun nan ? Murmushi nayi nace mama yanzu ne dai abin ya juta haka amma da farko ba haka zancen yake ba, Sadiyace ta bude idon ta daga gurin da take tana cewa tana son cin abinci, Ba bata lokaci aka bata abincin da na kawo mata tafara ci, Zan fita waje alokacin ne Sallawatu ta shigo dakin daniyar gaida Sadiya da jiki, Tun safe bata shigo gaida Sadiya da jikin ba wai sai yanzu, Ban tsan manin cewa Anty Sadiya ta karba mata gaisuwan nata ba, Don banji muryan ta ba agaskiya, Bata wani tsaya basai faman wani ya tsune fuska takeyi wai ita dakin ba ventilation, a cikin sa sam, Ni dai nai tankar ban fahinci abinda ke wakana a tdakanin su ba, Sai muryan Salawa mukaji tana cewa Ok Allah ya sauwaka ko, Ta sa kai ta fita tana wani irin karairaya ga tafiyan nata, Ina daga inda nake tsaye wani murmushine ya subbuce, min Sai naji Sadiya na cewa muguwa kawai sai ta cuci mutun tazo tana nuna ita bata san komai ba, Nan Sadiya ta fara cewa nasan babu inda wanan abin yake sai daga gurin Salawa, Don na fahinci muguwa ce ta karshe sosai, saboda, Ance idan mutun yai maka mugun asiri bazai zo gaisheka ba, Ban san ya akayi bakina yace to ai gata tazo gaishe ki ita, ko ? Inda nake tsaye Sadiya ta kalla tace cikin takaici, Meenatu baki san komai ba, Wanan matar da kike gani muguwa ce don ni sam ban yarda da ita ba tun farko, Baki ganin ko mutum yana ciwo bata damu da ta gaida mutum ba, Nace niko sai na dauka kishine yake sata yin hakana, Don idan kin kula ita ra,ayinta duk a watse abar mata Ya Abubakar ita kadai, Sadiya tace ai tasan yana da mata ta aure shi dn may bata tafi ta auri wanda baida mata ba, Murmushi nayi ina cewa kowa dai da halinsa wallahi mna ai zaman lafiya yafi zaman irin wanan, Kishiya fa idan ka hadu da ta kwarai abokiyar zamace, Sadiya tace kikace ko Meenatu ni ba zan taba yarda da kishiya ba, Don duk yadda kuke tana son jin sherin ka sabanin hairan, Wani irin mamaki naji a lokacin da ta fadi hakan don tana nufin har ni bata yarda dani ba don zan iya mata sheri, Muryan Maman Biu naji tana cewa ni dai wanan matar batai min ba gaskiya bata dace da maigidan ku ba, Ai duk matar da bata son kwanciyan hankalin mijin ta bata san may ta keyi ba ke nan, Sadiya tace ba kowa ke harin rayuwa na ba sai wanan makiran don nasan cewa kowa rantsuwa nayi ban kaffara, Mamakin ta daine ya kara kamani don jin ko may tace akan Sallawatu,, ****** ********** ****** Da yamman ranan suka koma gurin maimagani harda Sadiya, sai dai mama bata samu zuwa ba tace kan ta na ciwo, Sun samu malamin a gida sabanin dazun da safe da suka zo,, Amma yace ace da safe yamna su dawo su samay shi, Bayan yadan dade yana wasu yan abubuwa irin nasu na malamai, ya dago kai yana kallon su, Yace gaskiya Alhaji a kwai matsala sosai a gidan ka, Saboda idan har ba a fitar da wanan fitinar ba a gidan to irin haka zaku dinga gani, Wani irin nisawa Yaya Abubakar ya sauke don jin may malam yace, Don haka ya tambaya da cewa malam ai sai in sake gida ko, Don ina ganin cewa hakan zaifi man sauki don ba musan ina wana mugun abin yake aje ba, Malam wanda yai shiru yana kallon wani tasbaha dake hannun shi, Can ya nisa ya na cewa ai ba a ainifin gidan akasa wanan kullin ba, Asalima ba a wanan gatin da kuke yake ba, don haka kaga ba zanven gida bane, Yace tun can garin ku kazo da abinka, don haka sai katashi tsaye sosai don neman mafita, Saboda ai ba wanan ne karo na farko da hakan yafaru ba, Sai dai ku baku iya gane hakan kuma du inda kuka tafi wanan abin yana bibiyan ku, Yanzu duk yadda akayi akwai akasin da akasamu da har kuka gan shi da idon ku, Malamin yace barin fada maka gaskiya Alhaji idan har a gidan ka za ai ciki to ba zai taba samuwa ba ga matan ka, Sai dai idan har babu wanan kullin akusa za,a iya samun ciki bance maka a,a ba, Wani irin firgicin rayuwa suka shiga gabadayan su sai Lawal ne ya ke kara tambayan malamin da cewa, Yanzu malam baka fada muna yadda al,amarin yake ba sai magana kake muna adunkule Murmushi malam yayi yana cewa bazan ce komai ba amma bada dadewa ba komai zai walwale insha Allah,,, Kuje kuci gabada yin abinda na baku mu gani har Allah ya bata lafiya, Baba Wadda ya iso garin alokacin su yaya basu gida sun tafi gurin katban magani, Don haka ni kadaice agida saboda Salawa tafita ita ma alokacin, Nan Baba Wadda ya fitar da sakon da malam ya bayar akawo min harda zuma mai yawa acikin sakon nakarba tarr da godiya nakai dakina na boye, inda babu maigani, Abincin da na girka na debowa Baba Wadda, tare da bashi abin sanyi don jika makoshin sa, A hanya su Yaya Abubakar suna dawo wa daga suleja sai zufa yake faman sharewa, Don maganganun malamin yana mashi yawo a rai, Kenan ita Meenatu da ta samu ciki ba,a nan ta samay shi ba ke nan ko? Sai ya tuna cewa ai, duk yadda akayi kenan tafiyan mu kasar Niger Republic nasamu cikin da ya zube kenan, Bai san lokacin da ya furta Innalilahi, Wa,inna,Alaihim Raj,un Yanzu yaya zaiyi ke nan ana nufin crwa idan har zaiyi ciki da wata mace sai bai kusa dawa ke nan, Bayani dai ya nuna cewa, Meenatu dai bata aciki ke nan tunda har ta samu ciki, Innalillahi ya kara furtawa a filli, tare da goge gumin da ya karyo mai agoshi, Watau rashin haihuwa agidan shi yana da wani nasaba kenan da wanan abin sihirin da ya gani, Ashe zama bai gan shi ba ke nan don dole ne ya mike, on neman mafita akan al,amarin kafin yai yawa don gaskiya iyanzu yafara son haihuwa, a rayuwan shi,,, ZEEE MAKAWA YELWA,, [8/24, 05:58] Anty Lantana: 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 6⃣1⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA ALLAH-AL-BAAITH SAKON GAISUWA DA BARKA DA SALLAH GARE KU MASOYA ZAINAB MAKAWA, FATAN ALHERI ZUWA GARE KU KAMAR YADDA KU KE MIN, IDAN NACE ZAN TSAYA ZANA SUNAYEN KU BAZAMU SAMU ZANA LABARIN BA YAU, AMMA DUK MAI KAUNATA DAKU MA YAN UWA MUSULMAI NA DUNIYA ZAINAB NA MAKU BARKA DA SALLAH ALLAH YA MAIMAITA MUNA,,,,,, Tashin hankali wanda yafi karfin furta zance shi Yaya Abubakar ya shiga ciki, Don sai gumi ke feso mashi da kafafen jikin saboda irin yadda ya ke ji, a lokacin, Allah kawai ya tsare su don tuki kawai yakeyi batare da yasan may yakeyi ba, Tunane kala kala sun zo mai a lokaci guda batare da yasan yana yi ba, Sun iso gida sun samu Baba Wadda ya iso a lokacin don har yaci abinci yai sallah ko, Nan suka zauna da Baba Wadda a falon gaba dayan su a na gaisawa, Ina kitchen ina yan aiyu kana tare da kara rusa abincin a cikina, Jin shigowan su yasa na fito don in masu barka da dawowa, Kallo guda naiwa yanayin Yaya Abubakar nagane cewa yana cikin tashin hankali, A take naji banji dadi ba don gabadaya a rude yake sai faman mazurai da idanu yakeyi yana kallon ko wani sashe nagidan kamar mai nemqn wani abu, A lokacin da naji Baba Wadda zai fara mashi bayanin akan Sakon da yazo dashi sai na bargurin zuwa part dina, Ganin irin halin da Sadiya take ciki ne Baba Wadda wanda yaro ne sosai amma ya kawo shawaran cewa ya kamata fa asanar da yan uwan Sadiya don a samu wanda zaizo jinyar ta, Cikin murya mai nuna damuwa da kasala Yaya Abubakar kecewa saida nai tunanen hakan nima, Don kaga wanan tsohuwa dai tai muna mutunci sosai gaskiya, Ba kuma zatai ta zama a nan haka ba, don ita ma tana da nata laluran ai, Matsala guda yanzu shine ai kasan halin irin na Sadiya, ba kirki ne gare ta ba, Ba ruwan ta da yan uwanta bakajin tana zancen kowa daga cikin yan uwan ta, Ba ta damu sam da yan uwan ta ba balle wani daga cikin su yaji dadin zuwa gurin ta, Ai akwai wata wace ta taba zuwa lokacin da nafita karatun wata shidda amma kafin in dawo matar ta wuce saboda irin zaman da su kayi, Baba Wadda yace amma dai duk da haka ni sai nake gani da dai a sanar dasu zai fi, Don kada daga baya su zo su ce ai ba,a fada masu ba, Gaskiya ne kuma inji Yaya Abubakar wanda ya fada cikin bata rai, Yana cewa zan kirasu in sanar da su idan sun zo to idan babu wanda yazo kuma shi ke nan, A lokacin Salawatu ta shigo gidan saye da wani dogon riga sai dan wani yalalon gyale daidai wuyan ta, Gaba dayan su kallon ta sukeyi kowa da irin kallon mamakin da yake mata, Duk da ta sheda Baba Wadda amma sai batai masa sannu da zuwa ba tasa kai zata shige, Cikin wani murya Yaya Abubakar yace, Salawatu da karfi abinda yasa ta juyowa tare da dawowa baya, A cikin bacin rai yace baki ga Baba bane zaune ko baki san shi bane ? Kunya taji amma sai ta dake tana cewa, gaskitan kula dashi ba don ban kalle gurin ba, Sannu da zuwa ya hanya tace tare da wuce wa çiki, Yaya Abubakar ya dan rintse idon shi don shima halin shi kaman namune don bamu kaunan a taba yan uwan mu, Baba Wadda bayan shigewan wata ya dubi Yaya Abubakar yace Maisunan malam wanan matar taka ai ba sa,an yin ka bace, don da alama zatai wuyan saitituwa, kamar sauran mata, Murmushin yake kawai Yaya Abubakar yayiwa Baba Wadda don jin abinda yace, Ya san halin Baba Wadda shi bai boye zancen zuciyar shi sam Wayan shi ya jawo daga aljihun shi inda yafara neman layin wayan mahaifiyan Sadiya,, Kamar bazata daga wayan ba amma sai yaji muryan ta tana cewa Salamu Alaikum, Sun gaisa acikin mutunci sai dan shiru ya biyo baya, Can Yaya Abubakar yace Mama dama Sadiya ce ba lafiya yau kwana biyu ke nan, Gaban Hajja ne ya fadi don itama kwana biyu kenan da take fama da Dodon ta wan da ya dawo duk jikin shi ya salle saboda tabin da Sadiya tai masa, Amma karfin hali irin na Hajja sai cewa tayi yanzu may zan yi mata nida ke nan, ku kuna can, Allah dai ya bata lafiya Daga haka ta kashe wayan ta tabar gurin cikin kunan rai don a lokacin taji hamman Dodon ta wanda idan yai hamman zakaji wani irin wari, mai doyi, yana tashi, a guri, Wani irin mamakine ya kama Yaya Abubakar a lokaci guda, Yadade da sanin cewa,Sadiya halaiyan uwar ta ke gare ta, na rashin mutunci, Bai kara gaskan tawa ba sai yau din ya tabbatar da hakan , Ace yar ki ga halin rayuwan da take ciki amma sai ki cewai, ke ya zakiyi babu Allah ya sauwa sai kawai ki kashe waya don rashin imani,, Baba Wadda wanda ke daga gefe yana nazarin yadda suke waya da Hajja yace, Ya ce tayi ma halin nata ko ? Murmushi mai kama da yake Yaya yayi kawai tare da hade wasu miyau masu zafi, Daga gurin da yaya Abubakar yake zaune, kasan carpet, ya jingina bayan shi ga kujera, Ya sanya hannayen shi guda biyu ya dafe goshin sa da su, Zuciyar shi sai wani harbawa takeyi tana masa ciwo, da radadin saboda duk, abin duniya yai masa yawa, Falon na shigo da sallamana, ganin yanayin sa yasa na gaishe shi a sanyaye, Cikin dauriya Ya Abubakar ya cire hannu daga goshin shi ya,dago idon shi da,suka rine sukayi ja, Yake ce min a hankali Meenat kina kuwa shan maganin ki ? Na ansa ma shi da cewa ina sha yaya har sun kusa karewa ai, Baba Wadda wanda ke gefe sai cewa yayi Meenatu malam na cen duk ya tayarwa mutane da hankali yana cewa wai kina garin mutane babu mai kula da ke, Daga gurin da nake na sake wani irin murmushi ya subuce min, har ina yar darawa, nace malam ho, Ya Abubakar ya ce, daga gurin da yake zaune ai kasan malam baida kamar meenatu duk gidan nan, Ina fada mashi cewa ta yi bari ya na batun fasa min dodon kunena da wani irin salati, Wani irin duban wasa na sakewa yaya Abubakar ina cewa amma dai kowa yasan cewa kaine dan gaban goshin sa bani ba, Ni da watarana muke fada har ya hana min fura, ko zuman cin masa, Abin mamaki sai kiran malam din ya shigo a wayan yaya Abubakar, a lokacin, Cikin dan ya mutse fuska yaya Abubakar yace ga dan rigiman nan ya bugo ai, Nace, Allah sarki malam yana dai ji da kai Baba nasan ya bugone yaji ko ka iso, Bayan sun gaisa ne yake tambayan ma su jiki yaya Abubakar ke masa da,sauki, Sai kuma yafara mashi bayanin yadda zai da maganin da aka kawo mashi, Sai yake cewa yaya Abubakar ya tabbatar da cewa yai sadaka da masa mai zuma ranan jumma, Sai kuma gyadaw wanda akasoya, suya ruwa wanda zai ba wa yara kanana sadaka,, Sai sugar na kwali cubes yaraba yara kana shima yace duk wani abu wanda zakaba yaro yasha har yaji dadi dashi zaka hada ka basu sadaka, Amma ka tabbatar da duk yadda nai bayani kayi da wa yan nan sakon kayi Godiya sosai ya Abubakar yayiwa malam tsoho tare da fara mashi bayanin abinda malam dake kauyen da suka tafi yace masu, Malam tsoho ya kira sunan yaya na kwarai da cewa, ABUBAKAR, yaya ya amsa mashi da cewa na,am malam, Malam yace ba sai ka fada min ba don ni nasan komai ko, Don tun bayau ba nake hasashen wasu abubuwa da dama a gidan ka, Yanzu ne zargina ya tabbata cewa aike ne ake maka daga nesa, Don ni tun auren ku da Aminatu nagane cewa akwai wani bakon al,amari a tare da kai, Amma mutun karya yayi saidai Allah badai mutum ba wallahi, Tun lokacin da suka fara zancen abinda malam ya fada masu hankalina yai mugun tashi, Muryan Baba wada ne suka ji daga inda yake zaune yana cewa cikin dan kwantar da murya, Ai wanan mace muguwa ce yanzu mutane ko da kudi basu bi hanyan gidan ta, Yaya Abubakar ya ke tambaya da crwa wake nan ? Ba wani shakka ko tsoro a fuskan shi ya Hajja mana, Da sauri naga yaya Abubakar ya dan juta gurin da nake yana kallo na, Baba Wadda wanda bai san may ba sai ci gaba yayi da fadin Ai tun ranan da ta shigo gida da nufin gaida Maman mariya (Mama Ladi) Iskokin mata yai ta tashi harda mariya wace mun koma daga nan ba,a wani dade ba Mariya nada iskane ? Yaya Abubakar ya tambaya cikin jin haushin hiran shirmay da Baba Wadda keyi, Nan Baba Wadda yashiga zaiyana muna tiryan tiryan yadda al,amarin ya faru a ranan, Dagani har yaya Abubakar shiru mukayi tankar ruwa cimu muna sauraren abin al,ajabi, Idan hankalina ya kai dubu babu wanda bai tashi ba a ranan don tsoro, da fargaba, Don tun ina karama nake tsoron Hajja muna ji a,na cewa muguwa ce, Wanan labarin yasa na shiga wani irin hali wanda har na kasa boye, Ya Abubakar wanda sai Innalillahi yake maimaitawa, don mamaki, Duk da ba wai yarda da zancen yaya Abubakar yayi ba amma sai zance ya sosa mashi zuciyan shi sosai, Shigowa Sallawatu cikin wasu matsatsun kaya tana taunan chewing gun, da wani irin kara, wanda ya dawo masu da hankalin su gare ta,, Cikin wani irin murya take cewa Yaya Abubakar sweet Oga, na son,ganin ka ne fa , A hankali ya dan dago kai ya dubeta sai yake ce mata, naji ina zuwa, Bai wani dauki lokaci mai tsawo ba ya mike tare da dan tsuki, ya bi bayan shu,uman,,, Wani irin ajiyan zuciya na sauke, tare da kallon gurin dashupba Wadda yake zaune, a cikin mamaki, Nan nake tambayan shi zancen al,amarin Hajja ya ke bani labarin irin muggancin ta da takeyi,, Tsoro ya kara kamani sai naji ba ma zaman gidan ba duk garin gaba daya ya fita raina,,, Nace gaskiya Baba ni zan koma sokoto ne don duk garin nan ya isheni wallahi Baba Wadda yace Meenatu in sha Allahu babu abinda zai samay ki, Don Allah ya natare da bayin shi , ke dai kawai ki rike ibada da addu,oin neman tsari daga sherin mutun ko dabba ko, aljan ko kwaro, Nace ina yi duk wanda malam tsoho ya umurce ni da yin tun da farko, Yace Allah ya tsare ni kin ga wanan matar ta mai sunan malam batai min ba sam, Don duk take taken ta na ya zauna da ita ce ita kadai don wanan bata kaunar ta bude ido ta ganshi da wat mace daga cikin ku, Baba Wadda yace tun dai ke Meema don baki gari a lokacin zuwan ta gidan nan ida ta dage adole sai dakin ki, zata zauna wai yafi kyau da girma, Sai da,na nuna,mata ni da Hamza cewa mun fisu iya,iskanci, sannan aka zauna daidai... Nace Baba har yanzu bawai tabar ni bane ji take kamar ta daina ganina agidan nan kwata kwata wallahi, A hasale Baba Wadda yace sai dai tabar maki gida wallahi don babu inda zaki, Auren ki da mai sunan malam mutu ka raba bana rabuwane in ta sawa ran ta sauki ta, Nace cikin yar tausa murya wallahi Baba ka daina zancen ta don zaku iya batawa da Yaya a kan ta wallahi, Ai shi yasan cewa bani kaunar wanan matan a rayuwa na wallahi don ni sam batai min ba,, Saboda kallon yan Togo nike mata, knga waya dai ta taho tai mashi, Dariya sosai Baba Wadda ya bani nace cikin dariya Baba So ne fa haka na, son ta ya ke yi shinasa,, Baba Wadda yace kai wani irin So Meena son yaudara ko ? Yanzu fa debo tahowa dai tayi ta ce mai ya taso yatashi ya bita kamar Rakumi, Yanzu ke kina iya cewa Taso kazo ya taso zuwa inda kike haka kai tsaye, Sod di ya,i gwalmad,diya,i,,,, Dariya yasani shigewa dakina don Baba Wadda a cikin serious yake zancen shi, Na shiga don gabatar da Sallah nakai wani lokaci kamar kullun ina kai kukana ga Allah, Daga inda nake zaune zancen labarin Hajja da Baba Wadda ya bamu yazo min a rai, Nan gaba na ya shiga faduwa don nasan cewa tunda malam tsoho da kan shi har ya furta cewa da matsala a gidan to da matsala ke nan, Wani irin tsoro ne ya kara ziyara na yadda baba ya fada muna cewa wai mata nata ihu suna ce ga dodo da diyan shi na lasan mutane, Tsab na mike nadauko wayana dake caji a gefe guda, Noban malam tsoho na kira duk da nasan kila yana cikin masallaci yanzu suna wuridi, Cikin ikon Allah sai naji ya dauki wayan yana cewa Aminatu ke ta, Na ansa da wani irin murya na damuwa nace nita malam, Mun wuni lafiya ya ansa da fadin wallahi lahiya lau Aminatu, Ya jama,an wajen ku,? Suna lafiya malam, sai kuma nai shiru ba tare da nace komai, Aminatu Yaya ankayi na nace malam naga sako gurin Baba, Wadda nagode Malam yace kai haba babu komai ki dai yi amfani da suwa kinjiya, Nace to malam, Amma malam, ni gaskiya hankali ya daga ga gidan nan yanzu sosai gaskiya malam bazan iya zama ba zan dawo gida ne ni, Sai kawai kafin yai magana nasaka mashi kuka mai tsuma zuciya, Subbahanallahi naji ya na fadi, yana cewa ashha Amina , Mi zai tayar maki da hankali haka nace maki ki kwantar da hankalinki don Allah,, babu abinda zai samay ki insha Allah, Nace cikin kuka wallahi malam duk kwanakin nan bana barci a tsorace nake don da idona naga wanan abin sihirin da ya shigo dakin Sadiya lokacin da yake fita, Abin mamaki maimakon malam tsoho ya nuna damuwan shi sai naji ya yi murmushin manya yana cewa Amina kwantar da hankalin, ke jiya, insha Allah babu wani sihiri da zai yi tasiri akan ki, Ke dai ki tsare adduan da ke gaban ki don babu abinda zasuyi da ke, Wanan abin da kike gani ai bai isa yazo gare ki ba sai dai in Allah ya bashi iko hakan ? Don ke ba jinin su bace sai dai yazo gurin wace adda alaka da shi, Amma ke mi kin ka hada da suwa ? A,buguda da yanzu ka damuna, shine mijin ki Abubakar ina tsoron kada su illanta shi a sanadin zaman da yake dasu, a gida, Nace cikin muryan kuka kaman mai tausayi may ya faru da shi malam ? Yace, babu komai Meenatu kwantar da hankalin ki Zaman da yake yi da yar gidan Hajja na ke dan jiyewa don kin san mace shu,umace,, Saboda haka ki kwantar da hankalinki kamar yadda na fada maki tun farko ki dinga karanta, Lahaula wa,la,quwati, illa billahi aliyal,azeem kafa 41 Kafin ki fito waje, duk safe, sai hasbunalah shima 450, Babban makami wanda zai sa har basu kaunar hada ido dake shine, Kalman shahada,,,kamar yadda na fadi a baya, Idan kuma kin fita anguwa ko kin dawo kafin ki shiga gida kikaranta, Alam tarakaifa, kafa uku ahannuwan ki, sai ki shafe jikin ki, Naji yace hummm Amina bazasu iya komai da,ke ba wallahi, muddin kika tsare wanan abin , Ke wallahi ko shi Abubakar sai ya koma ya shakkan ki, Daga gurin da kika idar da Sallah magrib ki karanta Basmsla kafa 21 a kulun, Na ansa da cewa to malam nagode, Yace kin san kanufari na amsa da eh malam ina dashi, ma, ai, Ya ce masha Allah to wanan KANUN FARIN zaki kirga guda 41 sai ki nika su ya zama gari, A kullun sai kina lasawa a hankali har ya kare , Insha Allahu zai maki amfani ta hanyoyi daban daban Amina, Don tsarine mai amfani sosai don zai maki tarei dakuma gyaraki, Watau Amina,abinda ku yaran yanzu baku sani ba shine, Wa yan nan abubuwan da akai amfani dasu a da can baya sunfi aiki bisa ga wanda kuke yi yanzu, Don da mace zata tare yin su wallahi zataga fa,idan su so,sai don haka ki yi hakuri ki zauna tare da dan uwan ki,, Sauran bayani sai ki bari duk ranan da Allah ya kawo ki sai muyi shi a fayyace, Yakare zancen da tambayan yadda na kara jin karfin jikina, Na,ansa dafadan cewa Alhamdullahi malam naji sauki sosai,,, Bayan mungama waya da malam na mike don zuwa gaida Anty Sadiya, Na samay ta zaune tana hawaye ita kadai a daki, ta,na jin sallamana tai wani irin firgigit tana cewa Meenatu don Allah kizo ki taimakamin don tun dazu na ke son in kewaya babu wanda zai kaini, Tausayi tabani sosai irin yadda na sa may da kuma yadda tai min magana, Na kamata har zuwa bathroom na kuma samo leda nace ta da ita ta tura hanayen ta kadan daga cikin ledan , Sai dai ta kasa yin hakan sai da na kama hannun ta na saka a ledan da kaina, Wanka nai mata don ta danji daman jikin ta, sai faman yi min godiya take yi idon ta na zubar da hawaye, Na gyara mata inda zata kwanta, da kuma duk abinda ya dace da dakin nata, Ina shafa mata mai Yaya Abubakar ya shigo dakin cikin mamaki yake kallon mu, Tambayan Anty Sadiya ya jikin nata ya keyi sai take ce mai da sauki don yanzu ma Meenat tai min wanka, Tare da Yaya Abubakar muka shafa mata magani a jikkin ta, muka bata na sha, Ina kokarin yi masu saida safe ne Mama Bi,u ta shigo da sallamanta, Na tsaya muka gaisa da ita sanan nai masu sai da safe,na juya zuwa daki na, Ba Yaya Abubakar ba har Maman Bi,u ba taji dadin yadda taga yanayina ba, Don kallo guda mutun zai mun ya iya fahintar cewa ina cikin yanayin damuw daga fuska na, Ina shiga dakina na fada wanka don bazan iya kwanciya haka na ba, Ina fitowa sai naji wani irin yunwa ya ziyar ce bama zan iya kwantawa batare da naci wani abu ba, Ina shiga kitchen na samu inda na aje abinci an kwashe ko ban tambaya ba nasan cewa Salawatu ce, Raina yai matukar baci na fita zuwa part din ta inda na samu tana shafa man shafi jikin ta ma , saboda duk ashe wani dabbara dabbara jikin ta ya ke dashi , Nace Salawa ke dan Allah kika juye abincin kula dukka ? Sai cewa tayi cikin wani irin kashe ido wani ya aiko ki ki tambayeni,? Na ce eh to kaman hakane don bake, ce kika dafa ba ko ? Ok to shine akace don ban dafa ba kada inci ko ? Na murmusa kai nace Salawa ke nan ashe kina son ci kika ki tsayawa ki dafawa muna, Bayan kin san cewa kece da alhakin bamu abinci yau agidan kika fita batare da kin sauke hakkin ki akan mu ba, Mikewa tayi tare da cewa ke Meenat wallahi rashin kunyar ki ya isheni don bazan daukar maki raini ba, Wani irin harara na watsa mata na ke baki isa ba wallahi, Na juya zan bar dakin ina cewa kindai ji kunya wallahi mace bazata iya tsayawa tayi girki ba sai an girka tazo ta cinyewa mutane, don rashin kunya, Nafito daga dakin fuuu muka hade da Yaya Abubakar wanda yafito kai Baba Wadda masauki, Da mamaki yake kallon na ya na cewa a zuciyar shi may yakawo ni dakin Salawa a wanan lokacin haka ? Itace tafito bayana tana cewa wallahi ni sai in maki dukan tsiya, Ganin Ya Abubakar a tsaye tai saurin cewa yauwa Sweet Oga dama ina son in fada maka cewa Wallahi kajawa yarinyar nan kune, Don muna auren ka a tare, does not means raini da rashin mutunci zai shiga tsakanin mu, Yace cikin daga murya wai may ke faruwa ne haka duk kun kasa yi min bayani, Salawatu tace, wai kawai sai gata tafado min daki tana tambayana cewa ina abincin da ta aje a cooler, Ni ce har don samun guri zata zo har daki takawo min, rashin mutunci wai naci abinci, Ya Abubakar yace to ke kinci ne ? Tace na ci mana tunda angirkane don aci, Kece jika girka da zakici au dear don bani na girka ba kenan bazanci ba, Na fito daga kitchen ina cewa kawai na girka abinci sai ki zo min kamar shonike ki kwashe abincin, gaba daya batare da ma kin raga mun ko da kadan ne,, Wani tsawa Yaya Abubakar ya daka min yana cewa ke Meenat ban son hayaniya fani a gidan nan, Don kin dafa abinci taci shi har zai kawo fitina haka ? Nace to ai yaya itace ya kamata ta girka muna muci amma tasa kai tafita tabar gidan, Nima don zuwan Baba wadda yasani girkawa kada yazo aji kunya, Ya Abubakar yace OK shine, kuma akace bayan shi kada wani yaci abinci ko ? Nace yaya abinci na ne fa da nake son ci insha magani Look Meenat bana son fitina for god sake kubarni in huta please ban so banso Ban iya çewa komai ba sai idona da yakawo hawaye a lokaci guda, nake jin wani irin baci rai da mamaki suna cimin zuciya, Na juta kitchen ina hawaye tare da dan sharewa a hankalo da bayan hannuwana, Gashi bazan iya kwantawa ba banci ko mai ba saboda irin yadda nakejin cikina yana min, Na dafa tare da kwashewa na nufi dakina dasu, Sai da naci nasha sanan na kwashen kayan zua kitchen inda na samu ankashe wutan falon gaba daya , Haka ya tabbatar min da cewa maigidan ya kwanta ke nan a lokacin, Wani irin tsoro naji don duhun da ya mamaye falon gaba daya a lokacin, Da saurina aje kayan na juya zuwa dakina don sai ina ganin kamar wanan abin zai iya fito min a lokacin, ZEEE MAKAWA YELWA 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 6⃣2⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA ALLAH- ASH -SHAHEED Daga kwance nake rigingine fuskana yana kallon Ac din dakin da ke sako min ni ima wanda ke sani cikin wani yanayi mai dadi, ga kamshi dake tashi na turaren humra, daki, Duk da Motsin da naji na shigowa dakina a lokacin, bai,sani juyawa don ganin kowaye ba, Ya iso gab da gurin da na ke, zaune a bakin gado,,, yana min wani kallo acikin mamaki, Muryan shi naji yana cewa lafiya kike kuwa yau, ? Batare da na kalle shi ba nake cewa, lafiy kalau nake, Hmmm naji yace, Kamar zai juya amma sai naji muryan shi yana cewa, Breakfast din Baba Wadda fa,? Banyi ba na bashi ansa a takaice, Saboda may ? ya tambaya cikin mamaki Nace don banice da alhakin badawa ba nagani , yau din, May kike nufi da hakan ne,? Ai bani kadai bace da alhakin wanan laluran ko Wani irin tsawa ya daka min tare da cewa Ke ni zaki gaya wa magana haka kai tsaye kina rainawa hankali ina fadi ki na fadi ke ma, Ban yi magana ba sai hawayen da idona ke fitar wa shar a lokaci guda, Ki tashi ki fita ki girka mai abinda zai karya idan ya dawo, Daga haka yasakai ya fita dakin a fusace cikin bacin rai, Ban ce komai ba sai kokarin mikewa da na keyi don zuwa kitchen din, Na jawo dan karamin gyale na na rufawa kaina tare da gyara daura zani na, Abinci lafiyayye na hada mashi tare da ni da su Anty sadiya, Nasa saura a kula don nasan cewa zuwa anjima kadan yunwa zai iya zo min, Nakai abina daki na gyara gurin da nai aikin a lokacin na juya daki na shiga wanka, Bayan na fito ina zaune a bakin mirror ina shafa mai don yanzu ba zama yin kwaliya na keyi ba, Ina kokarin zura wani dogon rigan pepper lace da akaiwa combination,da shi, Yaya Abubakar ne ya shigo dakin yana min wani kallo amma fuskan shi acikin daurewa yake, Tambaya na abincin sa saboda yana son fita, ban kai ga bashi ansa ba idon shi ya kai, ga abincin da na zuba a plate saman mirror don yasha min isaka kafin in zauna ci,, A tsatsaye yafara kai spoon abakin sa,yakai kusan sau biyar da yaci a tsatsaye don da alama sauri yakeyi a lokacin, Bayan ya aje spoon din,Ya dan juyo gurin da nake tsaye ina gyara dankwalina yana cewa, Shi zai fita amma da Baba Wadda zasu fita don akwai inda zasu tare, Murya ciki, ciki nace Yaya lokacin komawa na sokoto fa yayi, Wani kallo naga yai min na yarinyarga fa kin rainani naci gaba da cewa, Don da mun koma zamu tafi final teaching practices din mu, inha Allah, Tankar baiji may nace ba don bai ma nuna yaji din ba sai sa kai yayi yabar dakin,, abin shi Ganin uana fita baice min komai ba nabi bayan shi da kallo, Yana fita daga dakin gaba daya nasa wani irin kuka mai tsuma zuciyan mai sauraro ta, Ina cikin kukan da babu mai rarashi na sai Allah naji anshigo dakin, Yaya Abubakar ne ya dawo dakin yana cewa inzo mu gaisa da Baba wadda kafin su fita, Ganin da yai min na kifa ciki ina kuka cikin filo ya sashi tsayawa yana kallo na acikin mamaki yana cewa, May ke faruwa ne wai Meenatu ? Banyi magana ba ya kara jefo min tambaya da cewa, An maki wani abune wai don tun jiya nake ganin damuwa a fuskan ki, Nadan tsakaita kukana ina cewa ni gida kawai nake son komawa yanzu, Murmushin takaici yayi tare da cewa bazaki ba idan kuma kika matsa min karatun ma gaba daya sai ince a fasa yin sa, Don dama banga amfanin shi ba don ba dai aiki zakiyi ba balle, jin haka yasa na, Kara gumzan kukana nayi yadda zai tayar mai da hankali, Da sauri ya juya ya bar dakin hankalin shi a tashe bai iya cewa Baba Wadda komai ba sai kawai ya nufi hanyar fita waje, Shima Baba Wadda yana ganin haka ya tashi ya mara mai baya suka fita tare,,, ****** ********** ****** Labarin ciwon Anty Sadiya ya iso Birnin Kebbi ko A, take zance ya fara yawo cikin gari kala,kala, don kowa da abinda yake fadi, Wasu suce ai kishiyoyine sukai mata su suce ai sherin uwar ta ce, Ranan da mama Ladi ta samu labari hankalin ta ya tashi sosai, don kada iyayyen Sadiya suji suce ba,a dauki mataki akan ta ba, Don haka bata tsaya bata lokaci ko ina ba sai gidan Aminiyar ta Hajja, Don kada taji labarin ga mutane tace ai ba,a fada mata ba, Amma bayan zuwan ta sai tai mamaki da taji Hajja na cewa ai mai sunan malam ya bugo mata waya Amma ta fada, ma shi cewa, ai basai ta tura,kowa daga nan ba, Don a can ai,basu rasa mutane ko amma haka dai zai sa in tura mashi mutun daga nan, Wama yasan ko may ke damun ta balle adawo nan ana yadda zance kan karya, Abinda mutum baiji ba bai gani ba ya taho yace shi ya gano acan, Don haka ni banga abinda za,a ce sai an tura wata ko wani daga nan ba, Hakane inji Mama Ladi tace amma dai duk da haka da daga cikin yan uwan ta a samu wata a turata, mata can ina ga haka zai fi, Don fa ranan wuya sai naka , Hajja ta tabe baki tana cewa, haka ne amma gaskiya ni babu wanda zan tura daga nan don Ai fanin, ku, da kuma mijin ta baku rage ta da komai don haka abar zancen tura wani, saboda tana samun kula daga mijin ta ai, Tun da Mama Ladi ta gane cewa Hajja bata kaunar zancen kwata kwata yasa ta kyale wa,, Sai suka fara hiran wani abu can daba don sam bata kaunar wanan zancen, Don zancen yana tayar mata da hankali saboda bata san may zatayi ba i yanzu akai,, Haka mama ladi tai sallama da ita batare da ta gane komai ba gare ta, Ga warin hamman Dodo da ya isheta tun zaman ta, Amma anan cikin gidan mu gidan malam tsoho sai zance ya canza da cewa, Ai sherin Hajja ce duk yadda akayi ke bibiyan don tunda har malam ya saka bakin shi ciki, zance, Zance yazowa Mama Ladi cewa ai nayi barin ciki, a kwanakin nan,, Anan Mama ta fara fitina tana zage,zage tana masifa, Ita Allah ya tsare ta, da ta hada zuri,a da zuri,an irin Baba samaila, Da kuma mahaifiyana ita dole Maisunan malam ya sako Meenatu, tun bata kara yin wani ciki ba, Yanzu shi mai suban malam har may yagani ajikin Meenatu da ya,rude shi har ya afka mata wai harda samun ciki, Aiko amanan ta ya ishi cikin ya zube don dai Allah yagani ita bazata hada da irin mu ba, Kuma wanan sherin na malan tsohone shi da yai uwa yai makarbiya harda hada aure tsakanin jikokin shi, Yakuma rasa wanda zai hada wai sai yar Samaila da na ta, Dan dama, dama dama ace a cikin diyan wa yanda suka fito ciki guda da Baba Buhari ne zata dan yarda, Dole sai Yaya Abubakar ya turoni gida kwanan nan inba haka ba zai hadu da fushin ta, ****** ********** ****** Tafiya ya keyi zuwa gida malam saboda karbo wa Sadiya magani shi da Baba Wadda, Wayan ce tai kara yaga ashe Mama Ladi ce ke kiran layin nashi, Sai da ya bari kiran ya tsaya kamar yadda yake mata kulun sai ya kara kiran ta, Mama bata bari sun gaisa ba tafara cewa Kai mai sunan malam shin batun ga da najiya da gaskiya na ? Yace cikin tambaya mama wane batu ke nan kika jiya ? Tace wai Aminati tasamu tagon kaya ? Kwanan nan shin ? Yace cikin dakewa hakane Mama gaskiya na yayi barin kwanan nan, Salati ya Abubakar yaji Mama ta sake a lokaci guda, Tana ewa da ka tona min asiri maisunan malam ace duk cikin zuka zukan matan ka ka rasa wace zakaiwa ciki sai waga yar ficikan yarinya, Me kagani gare ta shin ? Me zaka ganewa gurin wagga dagin bararo, Nace maza ka dawo da yarinyar nan gida kafin wani sati ya zagayo, Kajiya ko ? Shiru yayi Mama takara cewa shin kaji abinda na fada maka ko ? Najiya Mama ya bata ansa da fadar hakana, a takaice, To kadai jita nan zuwa wani sati ka turo masu ita gida su san wadda zasuyi da ita, Ya kara ansawa da fadin to Mama zanturo ta kafin lokacin, Su na kashe waya ya furzar da iska daga bakin shi yana mai dafe gefen kan shi da hannun shi guda da bai tuki dashi,, Ya ce kai, Mama ho, ba dai fitina ba Mama, don kawai ata da sabon fitina a gida, ta dawo da wanan zancen,, Baba Wadda wanda ke zaune daga gefe yace to wai ita, Maman Mariya dake cewa haka shin, may ye hujjan ta, Babu inji yaya Abubakar ya bashi ansa da cewa, kawai dai akidace ta su irin na mata, Wayan shi dake a gefe ya laluba ya na neman nomba Uncle, dina, Ya ce hello Uncle su ka gaisa a cikin mutunci da girmamawa,, Yace Uncle dama ina son don Allah a taimaka min a school din su Meenat don a bata excuse saboda tace zasu fara exam gashi kuma tana nan on medication, Uncle ya ke ce mai zai tafi school din na mu ya bin cika ya gani, inda yadda za,ayi,, Sukayi sallama acikin mutunci tare da yiwa juna fatan alheri, Baba Wadda wanda ke daga gefe ya dan murmusa ya ce kai o,o yanzu, ita maijiran dawowan Meenatu fa can gida, murmshi kawai yayi, Sun karbo maganin kamar yadda kullun ake zuwa karba , Ya tafi Baba Wadda ne don yaga wuri saboda ya dinga zuwa karba don shi baida enough time, Baba Wadda ne ke tunasar dashi zancen sadakan da malam tsoho ya cd su yi, Baba Wadda yace ina fa yin sa a wanan kauyen zaifi don ka ga acan cikin gari babu yaran da zaka bawa, Yays Abubakar yace gaskiyane Baba barin wa malam magana sai a sayo min, Shawaran Baba Wadda yai amfani sosai gurin, don yara har sunfito fiye da tsanmani saboda sun saba karban sadaka a gurin malam sun san da yana sada shiyasa da anfara cewa Ana Sadaka,,, zasu fito dayawa karba, ****** ********** ****** Sallaman Fattu naji a daidai lokacin da nike daga baya ina shanya kayan dana wanke muna, Dan saukin da na samu ita Sadiya bata amfani da kaya sosai, Sai godiya take min a lokacin da nashiga kwasan kayan wankin nata a dakin ta, Nawa na fara wankewa na shanya sai na fara nata na shaya a daidai wanan lokacin ne Fattu suka shigo gidan ita da Antyn Saloon, Da murna na tare su muka shiga ta falo don zuwa part dina, Salawatu tana zaune a falo tana kallon wani tashan wakoki ata faman raye raye a cikin sa, Da mamaki take kallon Anty mai Saloon don batai tsan manin cewa nasan irin ta ba, Natura kofan dakina da na sakaya lokacin da zan fita zuwa backyard gurin wanki, Sai kamshin dadi ke tashi tare da sanyin Ac daya gauraye dakin ,gwanin ban sha,awa, Ga dakin ta ko ina yasha gyara da daukan idi sai kyali yake yi, Bayan sun zauna na nufi kitchen don in hado masu drinks din sha, Cikin wani tiren silver mai ruwan golden na zuba hade da ruwa da cup,,, Ina direwa naji Antyn Saloon tana cewa yanzu ita wanan ce kishiyar kaunata, Fattu na fadin wallahi itace Anty wanan ai zata ma iya haihuwan ki Sai suka sa dariya irin na wayayyon mata nidai na aje masu ina murmushi, Na samu gefe guda na zauna ina masu sannu da zuwa a cikin murmushi, Àntyn Saloon ta dubeni tana cewa, kaunata duk kin ramay wallahi, Nidai ina daga zaune sai murmushi nake sake masu, Kawar Anty ce tace to ke ko ai dole ta ramay bakin ji abinda ya faru da ita ba, Anty tace wallahi fa a kasuwa muka hadu da Fattu shine nake tambayan ki sai take sheda min , Sorry ko Allah ya kawo sabon rabo nace Ameen Anty, ya kuke ? Ya kuke ya shago da yara tai murmushi tace komai Alhamdullahi kaunata, Sannu ko Nai murmushi kawai tare da cewa Anty kusha ruwan don Allah dai Munkai wani lokaci tare da su muna fira sai nake cewa Fattu ai na kusa komawa sokoto insha Allah, Fattu tace wallahi Meenat ni ban kan so tafiyan nan naki don idan kin tafi sai gidan nan naku ya koma tankar babu kowa a cikin sa, Nai murmushi nace hai Fattu wanan ai sheri ne gida da mata biyu zaki ce ya koma tankar ba kowa acikin sa, Kedai kawai don dani kika saba shiyasa kike cewa hakan, Fattu tace Allah yasa kada Yaya ya barki ki tafi muga tsiya, Da sauri nace ba amin ba Fattu aima dole ne ya barni tunda, karatu nakeyi, Tambayana kawar Anty tayi da cewa ina dayan kishiyar tawa take, Nake ce masu aitana daki bata da lafiya, suka tausaya mata sosai sai sukace idan zasu tafi sai su gaida ita, Daga cikin sabulan da yaya yake sigo muna ban komai da su na zuba masu a leda da drinks din su da basu sha ba, Dakin Anty Sadiya muka shiga tana daga zaune tana son ta tashi tundazun ta kewaya Fattu ce ta taimaka mata shiga bayin tare da tsayawa har ta karasa, Sai na fara gyara gadon da ta tashi sudai bakin suna kallon mu daga gefe zaune, Godiya Sadiya ke muna tana kokarin zama da kyat don irin yadda take jin jiki, Dayar matar da Antyn Saloon tashigo da ita ce ke cewa may ke damun Sadiya ne, Fattu ce ta fara basu labarin abinda ya faru da ita sai inda naga zata zure in gyara mata, Sun matukar tausaya mata har suke zancen mai kishiya bata mutuwar Allah, Suna cewa ai kila sherin kishiya ce yanzun haka kila aike akayo muna ni cikina ya zube ita kuma ai mata wani sherin, Nace a,a ni cikina fada mu kayi da Salawa, lokaci guda suka hada baki suna cewa fada har ciki ya zube, Fattu aka shiga labarta masu zancen da yadda na sha wahala sosai a daren har nai zuban jini, Nace to aike Fattu jiya mun tashi yin wani nabasu labarin abinda ya faru a tsakanina da Salawa, Gaba dayan su har Sadiya suke ce min daga yau in daina bin mutun har daki don yin hakan ba daidai bane, Hakan zai iya sa komai gaskiyan mutum ya dishe saboda kamar ai takaka na kai mata, a lokacin, Ni mutun ce mai daukan shawaran naga da ni in dai har shawaran mai amfani ne, Don haka nai masu godiya nan suke bani shawaran cewa, idan na girka har ina bukatan abina to in kwashe in boye kada inbarshi a fili, Sai matar guda ke cewa amma gaskiya kamata yayi a samu wace ke kula dake sai a dinga biyan ta ina ga zaifi, Fattu yar rigima kecewa maigidan kuwa zai yarda sai matar ke cewa ai ita wallahi da zata ganshi zata bashi shawara, Tace saboda kinga wahala takeyi fa sosai a haka dubi fa tundazun take son kewayawa amma babu wanda zai taimaka mata dole tana zaune, Anty Saloon tace dagama dai sun samu Meenatu yariyan ce mai kirki da tarbiya in ba hakaba aida tuni an bare wallahi, Sukai mata sallama mukafito daga dakin Anty Sadiya don in masu rakiya, Motar Yaya Abubakar ce ta Parker sun shigo shida Baba Wadda, Fattu ke cewa su Yaya sannun ku da zuwa Yaya kamar yadda nake ce mai ita ma haka take fada mai, Su Anty Sallon suka gaidashi a cikin girmamawa, tare da mutuntawa, Daya matar da ke tare da Antyn Saloon wace ban san sunan ta ba, Take cewa maigida ashe kuma madam ba lafiya haka cikin daure fuska Yaya ya amsa mata da cewa Eh, Sai take cewa a cikin rashin damuwa, gaskiya yakamata a samo mata supporter wace zata dan dinga taimaka mata, Saboda inda ka kula abin nason wanda zai zauna a kusa da ita akoda yaushe, Ok idan har ka yarda ni zan iya samo maku mace mutumiyar kirki don ta taimaka maku, Yana tafiya batare da ya tsaya ba ya ke cewa sai najiki, yashige abinshi yabar a tsaye muna bin bayan shi da kallo,, Murmushi nayi daga gefena nake cewa hmm anty kin dai matsa saida kikai wanan zancen Tace wallahi matar tabani tausayi ne sosai shiyasa na damu, Amma ai, zai yarda idan yaga matar don tanada mutunci sosai, saboda maigidan ta ya rasa dadaewa yaran ta biyu maza amma duk suna wai Lagos a zaune suna sana,a a can, Haka mu kayi sallama dasu har Fattu wace zata shige nata gidan daga can, Ina shiga falo na samu Yaya Abubaka shi da Baba Wadda a zaune Tambaya yaya ya jefo min da cewa, a ina kika san wa yan nan matan Meenat ? Naja na tsaya fuska a dan daure nace matar da take min gyaran kaine da kafa, ansar da na bashi ke nan a takaice, Zan wuce naji yana ce bana son yawan kwashe kwashe na fada maki, Nace bani na kirasu ba yaya sun dai zo gaida ni da jiki ne, Daga haka na shige ba tare da na tsaya jin may zaice ba, Ina shiga daki na kara gyara inda su Antyn Saloon suka zauna tare da sharo dakin nawa, Yaya Abubakar ne ya shigo dakin nawa yana mai cewa baki girkawa Baba abinci bane, Na aje filon dake hannu na saman gado nace Yaya gani nayi cewa banice da girki ba don haka yasa ban yi, Ya ce look Meenat ko da baki a matsayin mata ta nai bako ashe bazaki iya bashi abinci ba , Balle kanin mahaifin mu, da yazo idan wata bata bashi abinci bake ba mai bashi bane,? Kaina yana kasa ban daga ba nace Yaya amma kasan halin Salawatu zata iya cewa, ai don may na girka abincin tunda ni ba girki nakeyi ba, Ya ce ba tace bazata iya girki ba don bata son warin girki kuma tana fama da zazzabi , Nace ban san wanan zancen ba don haka shiyasa nake taka tsantsan kada tace don may, Ok kifito ki bashi abinda zaici, ya juya yabar dakin batare da yakara cewa komai ba kuma, Dama na girka abinci na aje inda babu mai sanin cewa nayi, Don haka na gabatar masu dashi a dining table , Har yaya Abubakar sai da ya ci abincin don baici komai ba shi ma, ****** ********** ****** Washe gari ina cikin wani material lace yellow da purple din flower a jikin shi sai stones a kasan shi, Dinkin dogon rigane akai min dashi, sai na dan zauna a gaban mirror nayi simple make up, a fuska na, Na dauko takalmana na saka akafana, sai kamshi turaren shekkah ke tashi a jikina, Dakin Anty Sadiya na nufa don in gaida ita, da jiki, don tun safe ina ta aikin gyaran falon mu da yai dauda, Sai kuma girkin da na hada don karyawan jama,an gidan, Karfin hali kawai nima na keyi don jiki na sam bana jin karfin sa, Abin karin ta nadauko daga kitchen zuwa dakin ta daga kofan dakin na tsaya ina sallama inda Yaya Abubakar dake acikin dakin yai min iso, A zaune take da alaman wanka tayi, don magani na ga yana shafa mata ajikin ta, Gefen da take zaune na nufa da tire din na aje mata ina fuskan tar ta nace ina kwana Anty Ya karfin jikin ya kuma dare ,? Ta amsa a hankali idon nakai ga hannayen ta sai na ga duk sun faffashe suna dan fidda ruwa,, Magani Yaya Abubakar ke kokarin kadawa ga cup na karba na kada na nufeta dashi, Da kaina na kafa mata a baki har saida ta shanye shi gaba dayan shi sannan cire cup din ina mata sannu da jiki, Shiru mu kayi dakin gaba dayan mu ba mai cewa komai daga cikin mu, idon mu ga hannayen Anty Sadiya dake fitar ruwa, Muryan Yaya Abubakar naji yana cewa wanan matar zuwa yaushe zata turo matar da take magana a kan ta, A hankali na dan dago kaina da fuskana mai nuna damuwa na ce ban san lokaci ba gaskiya . Najuya acikin rashin walwala na bar dakin don zuwa inci gaba da abinda na keyi,, Yaya Abubakar wanda ke daga tsaye gefen gadon ya bini da idanu har na fita daga dakin, Ina fitowa Salawace na gani tana fitowa daga kitchen ta hada tea da wani leda mai katon bread a cikin sa, Kala bata ce min ba sai kokatin gittawa take a gabana, Sanin cewa gaba baida kyau yasani daurewa cikin dakiyan zuciya nace, Ina kwana ya jikin ki ? Kamar bazata ansa min ba sainaji bayan ta dan gwautani kadan tana cewa lafiya, Ta wuce tana wani irin karairaya tare da dan matse fuskan ta, gare ni, Ni dariya ma tabani sai na tuna da zaginta da Antyn Saloon tayi jiya, Ban wani dade da shiga dakina ba naji muryan a kofan dakina a na kwada min sallama, Nafito don ganin ko waye kawar Antyn Saloon ce da wata mata baka, A cikin dan sakin fuska nake cewa a, Anty kece tafe yanzu,? Sannu ku da zuwa daga nan muka shiga gaisawa da su tare da tambayan yadda suka koma jiya, Nan take ce min jiya bayan ta koma gida taje gurin matar da take magana akai , Ba,a samu wani jayayya ba ta yarda da cewa zata zo tagwada ta gani, Kawar Anty saloon tace to ki saurara da,kyau tallo, Wanan din itace muka sani kamar yadda na fada maki da farko kishiyar ta ce ba lafiya muke son ki dinga taimaka mata dan Allah, Tambaya tayi da cewa ina mara lafiyan nace tana dakin ta , Nace amma fa kin san cewa jiya sai andaure don haka don Allah kiyi hakkuri please, Tace babu komai insha Allah zata yi kokarin tun madam ce ta kawo ni, Nace to mungode barin je inga maigidan in fada mashi cewa kin iso ko, Da sallama na tura kofan dakin yana tsaye yana daurawa hannuwan shi agogo a,hannu guda, Jin sallama na yasa shi dago kan shi ya na duba na daga inda yake tsaye, Ban karasa shiga daga dakin ba nace yaya matar ce tazo da mai aikin , Wani irin kallon ya watso min yace da karfi, ke, Zonan waye zaki tsaya daga can kina fadawa magana haka kai tsaye, Baki naturo gaba cikin nuna alaman fushi azuciya na, Dan nesa dashi kadan na tsaya ina dan kallon shi ganin irin yadda ya tsure ni da ido yasani dukar da kaina kasa, Banyi aune ba sai jin shi nayi ya rungumoni zuwa jikin shi , Kokarin kwacewa daga rikon da yai min na keyi, na ce, nika sake ni please ? Banyi aune ba sai ji nayi yana kokarin kai bakin shi a cikin nawa yana son yi min kiss, Duk kokarin da nakeyi in kwace kaina bai ma san inayi ba, shi, A tare muka fada saman mamakeken gadon dakin shi, Inda ya shiga jagwagwala ta yadda rashi yaso, Kamar wanda akaiwa tsawa naga ya sakeni ya juya da sauri gefe guda yai rub da ciki,, Yana maida numfashi guda guda, daga inda yake akwance, Da kyat na samu na tatara hankalina guri guda tare da saurin gyara gaban rigana da ya kware, Muryan Yaya Abubakar naji yana cewa ki fada mata cewa gani tafe Hannu na nasa na goge dan hawayen da ya zubo min, Nasamu su kawar Antyn saloon zaune suna kallo a dakina, Nace don Allah kuyi hakkuri na samu yana bayi ne shi yasa, Tai murmushi tace, haba ai ba komai tunda har munriga da munzo ko, ai, Ba ai wani daukan lokaci ba ya shigo dakin da sallaman shi , Suka gaisai faram faram tare da kara mashi ya mai jiki ? Fuska a daure yake cewa Alhamdullahi da sauki sosai, Tace ga matar da nake magana zata iya aikin tazo, Sai lokacin ya dubi matar ba wata tsohuwa ce ba sosai haka, Kara gaishe shi Ramatu tayi tana çewa barka da rana yallabai, Yace ina fatan zaki tsaya kiyi abinda ya kawo ki kamar yadda kikai alkawari, Don kinga aiki nan sai an,daure, ansa hakkuri a cikin sa sosai, Agina, kawar Antyn Saloon tace duk nai mata bayani sir, Yaya Abubakar yace, OK nawa ne kuka shirya da ita, ? Aginatu, tace gaskiya bamuyi wanan zancen ba tun farko iyaka dai makwabciya tace ita maigidan ta ya dade da rasuwa , Naga wahala yai mata yawa shine nace barin mata hanya tunda naga kamar yar shiyan state din kuce ita,, Yace, yanzu ke nawa ki ke ganin cewa zan baki ya fadi a kage don duk ya matsu yabar mu, kamar mai tsoron mata, Ramatu tace Alhaji duk abinda ka bani nagode Allah yasa masu albarka, Yace OK zan ganta sai muyi magana akai yana nufin wai zai gan ni sai muyi magana dashi, Daga haka yasa kai daniyar barin dakin har ya kai kofan fita sai ya dakata, Batare da ya juyo ba yace kisan cewa a tsakiyan mata uku zaki zauna sai ki kiyayye please ? Tace insha Allah zan kiyayye Alhaji nan inda aka daukeni zan tsaya da kafana, Bayan fitan yaya Abubakar ne muka kwasa zuwa dakin sadiya gaba dayan mu mu uku, Barci takeyi tun dazu nan nafara yiwa bakuwar mu Ramatu bayani abinda zata dinga yi, Muryan mu da Sadiya taji yasa ta bude idon ta, a hankali tana kallon mu, A kusan tare mu kai mata yaya jiki tace da sauki a hankali, Tana kokarin mikewa ne nasa filo nadan gyara mata a bayan ta, Kara gaisawa sukayi nan nake ce mata ai an kawo wace zata zauna da itane saboda Maman biu bazata iya ba, Sun gaisa da Ramatu tana cewa, ok zaki ko iya yi yar uwa don kinga da wahala abin, Ramatu cikin sakin fuska tace babu damuwa yar uwa zan iya insha Allahu Allah dai ya baki lafiya, Muka karba gaba dayan mu da Ameen Ameen, Munyi Sallama da Aginatu mata mai mutunci da tausayi, Inda na karbi nomban ta da cewa duk abinda ake ciki zan kirata in sheda mata, Duk abinda mukeyi madam din gidan mu tana kallon mu sai dai bata sa baki Kamar yadda ta nuna ciwon Sadiya bai damay ta ba kuma baya gaban ta ma sam, Sai wani nan nan yanzu naga Yaya Abubakar yana yi da ita wanda hankalina baigano ko may ye dalilin hakan ba, Gashi duk dare sai naga ya shigo mata da ledan kayan fruit masu kyau, Ina so amma dayake ita yake kawai ko a kitchen nagan su cikin fridge duk son da na ke masu ban sha, Sam iyanzu babu wani shiri a tsakanina da Salawatu don duk ta dauki tsanar duniya ta samin, Idan da farko tana boyewa yanzu sam bata iya boye don ko a hanya muka hadu cikin biyu sai na samu daya, Harara ko tsuki daga gare ta, abin dariya yake bani don nasan babu yadda zatayi dani dai, Kuma ganin irin rawan kafan da yaya keyi yasani kawo ido in sa masu, Dole aiyukan gida duk da bawai naji saukin jikina bane nice dai maiyin su, Sallah na idar ina zaune gurin ban kai ga dagawa ba naji waya ta tana kara, Yaya Abubakar ne yakirani daga office murya kasa kasa yake cewa, Meenat ina fatan yau zaki karbi girkin ki tunda kinji sauki ko ? A cikin marairai cewa nace don Allah yaya kayi hakkuri bazan iya ba , Don har yanzu nakanji marana yana min ciwo time to time, Yadan tausa muryan shi yace please Meenat for Allah sake ya kuke son inyi ne please ? Nace cikin murya kamar zanyi kuka wallahi yaya bawai naji sauki bane kawai dai karfin hali nakeyi don kada a zauna da yunwa a gidan, Yace look Meena bawai shawaran ki nake nema ba command ne na baki Naji fit ya kashe wayan inda nabi wayan da kallo tankar shi nake kallo, Wahalan da nasha aranan nan ne ya fado min a rai lokaci guda, Inda na rutse idona, cikin wani irin jin zafi azuciya nasan cewa tunda har yaya ya ce hakana to ya zama wajibi in kai masa kaina daren yau in har ina son kaina da lafiya, A haka naci gabada aiyukana batare da hankalina ya kwantaba saboda ina tunane yadda zanyi da Yaya Abubakar a daren yau, Don nasan cewa maganar gaskiya ke nan ya furta har cikin rashi, Dole nadan fara yin an abuwan shirin kwana dakin maigida kamar yadda mata keyi inda kanada kishiya ko kishiyoyi, agida, Kamar daga fara gyara dakin maigida yin yan gyare gyaren gida, sai kuma girki tare da tsala kwalliyan daren don taron maigida, Saidai duk ni yau acikin fargaba nakeyin nawa saboda yadda yanayin jikina yake, Duk abinda nakeyi yar sa idon gidan mu tana biye dani don ganin shirina, Na,gane may takeyi amma sai nai tankar ban fahince ta ba, Daga inda nake ina gyara kaya a dining table na hangota tafito a lokacin yayi daidai da time din dawowan Yaya Abubakar gida yayi, Har gaban table din da nake tafito tana wani taunan chewing gun irin na yan duniya , ZEEE MAKAWA YELWA🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 6⃣2⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA ALLAH- ASH -SHAHEED Daga kwance nake rigingine fuskana yana kallon Ac din dakin da ke sako min ni ima wanda ke sani cikin wani yanayi mai dadi, ga kamshi dake tashi na turaren humra, daki, Duk da Motsin da naji na shigowa dakina a lokacin, bai,sani juyawa don ganin kowaye ba, Ya iso gab da gurin da na ke, zaune a bakin gado,,, yana min wani kallo acikin mamaki, Muryan shi naji yana cewa lafiya kike kuwa yau, ? Batare da na kalle shi ba nake cewa, lafiy kalau nake, Hmmm naji yace, Kamar zai juya amma sai naji muryan shi yana cewa, Breakfast din Baba Wadda fa,? Banyi ba na bashi ansa a takaice, Saboda may ? ya tambaya cikin mamaki Nace don banice da alhakin badawa ba nagani , yau din, May kike nufi da hakan ne,? Ai bani kadai bace da alhakin wanan laluran ko Wani irin tsawa ya daka min tare da cewa Ke ni zaki gaya wa magana haka kai tsaye kina rainawa hankali ina fadi ki na fadi ke ma, Ban yi magana ba sai hawayen da idona ke fitar wa shar a lokaci guda, Ki tashi ki fita ki girka mai abinda zai karya idan ya dawo, Daga haka yasakai ya fita dakin a fusace cikin bacin rai, Ban ce komai ba sai kokarin mikewa da na keyi don zuwa kitchen din, Na jawo dan karamin gyale na na rufawa kaina tare da gyara daura zani na, Abinci lafiyayye na hada mashi tare da ni da su Anty sadiya, Nasa saura a kula don nasan cewa zuwa anjima kadan yunwa zai iya zo min, Nakai abina daki na gyara gurin da nai aikin a lokacin na juya daki na shiga wanka, Bayan na fito ina zaune a bakin mirror ina shafa mai don yanzu ba zama yin kwaliya na keyi ba, Ina kokarin zura wani dogon rigan pepper lace da akaiwa combination,da shi, Yaya Abubakar ne ya shigo dakin yana min wani kallo amma fuskan shi acikin daurewa yake, Tambaya na abincin sa saboda yana son fita, ban kai ga bashi ansa ba idon shi ya kai, ga abincin da na zuba a plate saman mirror don yasha min isaka kafin in zauna ci,, A tsatsaye yafara kai spoon abakin sa,yakai kusan sau biyar da yaci a tsatsaye don da alama sauri yakeyi a lokacin, Bayan ya aje spoon din,Ya dan juyo gurin da nake tsaye ina gyara dankwalina yana cewa, Shi zai fita amma da Baba Wadda zasu fita don akwai inda zasu tare, Murya ciki, ciki nace Yaya lokacin komawa na sokoto fa yayi, Wani kallo naga yai min na yarinyarga fa kin rainani naci gaba da cewa, Don da mun koma zamu tafi final teaching practices din mu, inha Allah, Tankar baiji may nace ba don bai ma nuna yaji din ba sai sa kai yayi yabar dakin,, abin shi Ganin uana fita baice min komai ba nabi bayan shi da kallo, Yana fita daga dakin gaba daya nasa wani irin kuka mai tsuma zuciyan mai sauraro ta, Ina cikin kukan da babu mai rarashi na sai Allah naji anshigo dakin, Yaya Abubakar ne ya dawo dakin yana cewa inzo mu gaisa da Baba wadda kafin su fita, Ganin da yai min na kifa ciki ina kuka cikin filo ya sashi tsayawa yana kallo na acikin mamaki yana cewa, May ke faruwa ne wai Meenatu ? Banyi magana ba ya kara jefo min tambaya da cewa, An maki wani abune wai don tun jiya nake ganin damuwa a fuskan ki, Nadan tsakaita kukana ina cewa ni gida kawai nake son komawa yanzu, Murmushin takaici yayi tare da cewa bazaki ba idan kuma kika matsa min karatun ma gaba daya sai ince a fasa yin sa, Don dama banga amfanin shi ba don ba dai aiki zakiyi ba balle, jin haka yasa na, Kara gumzan kukana nayi yadda zai tayar mai da hankali, Da sauri ya juya ya bar dakin hankalin shi a tashe bai iya cewa Baba Wadda komai ba sai kawai ya nufi hanyar fita waje, Shima Baba Wadda yana ganin haka ya tashi ya mara mai baya suka fita tare,,, ****** ********** ****** Labarin ciwon Anty Sadiya ya iso Birnin Kebbi ko A, take zance ya fara yawo cikin gari kala,kala, don kowa da abinda yake fadi, Wasu suce ai kishiyoyine sukai mata su suce ai sherin uwar ta ce, Ranan da mama Ladi ta samu labari hankalin ta ya tashi sosai, don kada iyayyen Sadiya suji suce ba,a dauki mataki akan ta ba, Don haka bata tsaya bata lokaci ko ina ba sai gidan Aminiyar ta Hajja, Don kada taji labarin ga mutane tace ai ba,a fada mata ba, Amma bayan zuwan ta sai tai mamaki da taji Hajja na cewa ai mai sunan malam ya bugo mata waya Amma ta fada, ma shi cewa, ai basai ta tura,kowa daga nan ba, Don a can ai,basu rasa mutane ko amma haka dai zai sa in tura mashi mutun daga nan, Wama yasan ko may ke damun ta balle adawo nan ana yadda zance kan karya, Abinda mutum baiji ba bai gani ba ya taho yace shi ya gano acan, Don haka ni banga abinda za,a ce sai an tura wata ko wani daga nan ba, Hakane inji Mama Ladi tace amma dai duk da haka da daga cikin yan uwan ta a samu wata a turata, mata can ina ga haka zai fi, Don fa ranan wuya sai naka , Hajja ta tabe baki tana cewa, haka ne amma gaskiya ni babu wanda zan tura daga nan don Ai fanin, ku, da kuma mijin ta baku rage ta da komai don haka abar zancen tura wani, saboda tana samun kula daga mijin ta ai, Tun da Mama Ladi ta gane cewa Hajja bata kaunar zancen kwata kwata yasa ta kyale wa,, Sai suka fara hiran wani abu can daba don sam bata kaunar wanan zancen, Don zancen yana tayar mata da hankali saboda bata san may zatayi ba i yanzu akai,, Haka mama ladi tai sallama da ita batare da ta gane komai ba gare ta, Ga warin hamman Dodo da ya isheta tun zaman ta, Amma anan cikin gidan mu gidan malam tsoho sai zance ya canza da cewa, Ai sherin Hajja ce duk yadda akayi ke bibiyan don tunda har malam ya saka bakin shi ciki, zance, Zance yazowa Mama Ladi cewa ai nayi barin ciki, a kwanakin nan,, Anan Mama ta fara fitina tana zage,zage tana masifa, Ita Allah ya tsare ta, da ta hada zuri,a da zuri,an irin Baba samaila, Da kuma mahaifiyana ita dole Maisunan malam ya sako Meenatu, tun bata kara yin wani ciki ba, Yanzu shi mai suban malam har may yagani ajikin Meenatu da ya,rude shi har ya afka mata wai harda samun ciki, Aiko amanan ta ya ishi cikin ya zube don dai Allah yagani ita bazata hada da irin mu ba, Kuma wanan sherin na malan tsohone shi da yai uwa yai makarbiya harda hada aure tsakanin jikokin shi, Yakuma rasa wanda zai hada wai sai yar Samaila da na ta, Dan dama, dama dama ace a cikin diyan wa yanda suka fito ciki guda da Baba Buhari ne zata dan yarda, Dole sai Yaya Abubakar ya turoni gida kwanan nan inba haka ba zai hadu da fushin ta, ****** ********** ****** Tafiya ya keyi zuwa gida malam saboda karbo wa Sadiya magani shi da Baba Wadda, Wayan ce tai kara yaga ashe Mama Ladi ce ke kiran layin nashi, Sai da ya bari kiran ya tsaya kamar yadda yake mata kulun sai ya kara kiran ta, Mama bata bari sun gaisa ba tafara cewa Kai mai sunan malam shin batun ga da najiya da gaskiya na ? Yace cikin tambaya mama wane batu ke nan kika jiya ? Tace wai Aminati tasamu tagon kaya ? Kwanan nan shin ? Yace cikin dakewa hakane Mama gaskiya na yayi barin kwanan nan, Salati ya Abubakar yaji Mama ta sake a lokaci guda, Tana ewa da ka tona min asiri maisunan malam ace duk cikin zuka zukan matan ka ka rasa wace zakaiwa ciki sai waga yar ficikan yarinya, Me kagani gare ta shin ? Me zaka ganewa gurin wagga dagin bararo, Nace maza ka dawo da yarinyar nan gida kafin wani sati ya zagayo, Kajiya ko ? Shiru yayi Mama takara cewa shin kaji abinda na fada maka ko ? Najiya Mama ya bata ansa da fadar hakana, a takaice, To kadai jita nan zuwa wani sati ka turo masu ita gida su san wadda zasuyi da ita, Ya kara ansawa da fadin to Mama zanturo ta kafin lokacin, Su na kashe waya ya furzar da iska daga bakin shi yana mai dafe gefen kan shi da hannun shi guda da bai tuki dashi,, Ya ce kai, Mama ho, ba dai fitina ba Mama, don kawai ata da sabon fitina a gida, ta dawo da wanan zancen,, Baba Wadda wanda ke zaune daga gefe yace to wai ita, Maman Mariya dake cewa haka shin, may ye hujjan ta, Babu inji yaya Abubakar ya bashi ansa da cewa, kawai dai akidace ta su irin na mata, Wayan shi dake a gefe ya laluba ya na neman nomba Uncle, dina, Ya ce hello Uncle su ka gaisa a cikin mutunci da girmamawa,, Yace Uncle dama ina son don Allah a taimaka min a school din su Meenat don a bata excuse saboda tace zasu fara exam gashi kuma tana nan on medication, Uncle ya ke ce mai zai tafi school din na mu ya bin cika ya gani, inda yadda za,ayi,, Sukayi sallama acikin mutunci tare da yiwa juna fatan alheri, Baba Wadda wanda ke daga gefe ya dan murmusa ya ce kai o,o yanzu, ita maijiran dawowan Meenatu fa can gida, murmshi kawai yayi, Sun karbo maganin kamar yadda kullun ake zuwa karba , Ya tafi Baba Wadda ne don yaga wuri saboda ya dinga zuwa karba don shi baida enough time, Baba Wadda ne ke tunasar dashi zancen sadakan da malam tsoho ya cd su yi, Baba Wadda yace ina fa yin sa a wanan kauyen zaifi don ka ga acan cikin gari babu yaran da zaka bawa, Yays Abubakar yace gaskiyane Baba barin wa malam magana sai a sayo min, Shawaran Baba Wadda yai amfani sosai gurin, don yara har sunfito fiye da tsanmani saboda sun saba karban sadaka a gurin malam sun san da yana sada shiyasa da anfara cewa Ana Sadaka,,, zasu fito dayawa karba, ****** ********** ****** Sallaman Fattu naji a daidai lokacin da nike daga baya ina shanya kayan dana wanke muna, Dan saukin da na samu ita Sadiya bata amfani da kaya sosai, Sai godiya take min a lokacin da nashiga kwasan kayan wankin nata a dakin ta, Nawa na fara wankewa na shanya sai na fara nata na shaya a daidai wanan lokacin ne Fattu suka shigo gidan ita da Antyn Saloon, Da murna na tare su muka shiga ta falo don zuwa part dina, Salawatu tana zaune a falo tana kallon wani tashan wakoki ata faman raye raye a cikin sa, Da mamaki take kallon Anty mai Saloon don batai tsan manin cewa nasan irin ta ba, Natura kofan dakina da na sakaya lokacin da zan fita zuwa backyard gurin wanki, Sai kamshin dadi ke tashi tare da sanyin Ac daya gauraye dakin ,gwanin ban sha,awa, Ga dakin ta ko ina yasha gyara da daukan idi sai kyali yake yi, Bayan sun zauna na nufi kitchen don in hado masu drinks din sha, Cikin wani tiren silver mai ruwan golden na zuba hade da ruwa da cup,,, Ina direwa naji Antyn Saloon tana cewa yanzu ita wanan ce kishiyar kaunata, Fattu na fadin wallahi itace Anty wanan ai zata ma iya haihuwan ki Sai suka sa dariya irin na wayayyon mata nidai na aje masu ina murmushi, Na samu gefe guda na zauna ina masu sannu da zuwa a cikin murmushi, Àntyn Saloon ta dubeni tana cewa, kaunata duk kin ramay wallahi, Nidai ina daga zaune sai murmushi nake sake masu, Kawar Anty ce tace to ke ko ai dole ta ramay bakin ji abinda ya faru da ita ba, Anty tace wallahi fa a kasuwa muka hadu da Fattu shine nake tambayan ki sai take sheda min , Sorry ko Allah ya kawo sabon rabo nace Ameen Anty, ya kuke ? Ya kuke ya shago da yara tai murmushi tace komai Alhamdullahi kaunata, Sannu ko Nai murmushi kawai tare da cewa Anty kusha ruwan don Allah dai Munkai wani lokaci tare da su muna fira sai nake cewa Fattu ai na kusa komawa sokoto insha Allah, Fattu tace wallahi Meenat ni ban kan so tafiyan nan naki don idan kin tafi sai gidan nan naku ya koma tankar babu kowa a cikin sa, Nai murmushi nace hai Fattu wanan ai sheri ne gida da mata biyu zaki ce ya koma tankar ba kowa acikin sa, Kedai kawai don dani kika saba shiyasa kike cewa hakan, Fattu tace Allah yasa kada Yaya ya barki ki tafi muga tsiya, Da sauri nace ba amin ba Fattu aima dole ne ya barni tunda, karatu nakeyi, Tambayana kawar Anty tayi da cewa ina dayan kishiyar tawa take, Nake ce masu aitana daki bata da lafiya, suka tausaya mata sosai sai sukace idan zasu tafi sai su gaida ita, Daga cikin sabulan da yaya yake sigo muna ban komai da su na zuba masu a leda da drinks din su da basu sha ba, Dakin Anty Sadiya muka shiga tana daga zaune tana son ta tashi tundazun ta kewaya Fattu ce ta taimaka mata shiga bayin tare da tsayawa har ta karasa, Sai na fara gyara gadon da ta tashi sudai bakin suna kallon mu daga gefe zaune, Godiya Sadiya ke muna tana kokarin zama da kyat don irin yadda take jin jiki, Dayar matar da Antyn Saloon tashigo da ita ce ke cewa may ke damun Sadiya ne, Fattu ce ta fara basu labarin abinda ya faru da ita sai inda naga zata zure in gyara mata, Sun matukar tausaya mata har suke zancen mai kishiya bata mutuwar Allah, Suna cewa ai kila sherin kishiya ce yanzun haka kila aike akayo muna ni cikina ya zube ita kuma ai mata wani sherin, Nace a,a ni cikina fada mu kayi da Salawa, lokaci guda suka hada baki suna cewa fada har ciki ya zube, Fattu aka shiga labarta masu zancen da yadda na sha wahala sosai a daren har nai zuban jini, Nace to aike Fattu jiya mun tashi yin wani nabasu labarin abinda ya faru a tsakanina da Salawa, Gaba dayan su har Sadiya suke ce min daga yau in daina bin mutun har daki don yin hakan ba daidai bane, Hakan zai iya sa komai gaskiyan mutum ya dishe saboda kamar ai takaka na kai mata, a lokacin, Ni mutun ce mai daukan shawaran naga da ni in dai har shawaran mai amfani ne, Don haka nai masu godiya nan suke bani shawaran cewa, idan na girka har ina bukatan abina to in kwashe in boye kada inbarshi a fili, Sai matar guda ke cewa amma gaskiya kamata yayi a samu wace ke kula dake sai a dinga biyan ta ina ga zaifi, Fattu yar rigima kecewa maigidan kuwa zai yarda sai matar ke cewa ai ita wallahi da zata ganshi zata bashi shawara, Tace saboda kinga wahala takeyi fa sosai a haka dubi fa tundazun take son kewayawa amma babu wanda zai taimaka mata dole tana zaune, Anty Saloon tace dagama dai sun samu Meenatu yariyan ce mai kirki da tarbiya in ba hakaba aida tuni an bare wallahi, Sukai mata sallama mukafito daga dakin Anty Sadiya don in masu rakiya, Motar Yaya Abubakar ce ta Parker sun shigo shida Baba Wadda, Fattu ke cewa su Yaya sannun ku da zuwa Yaya kamar yadda nake ce mai ita ma haka take fada mai, Su Anty Sallon suka gaidashi a cikin girmamawa, tare da mutuntawa, Daya matar da ke tare da Antyn Saloon wace ban san sunan ta ba, Take cewa maigida ashe kuma madam ba lafiya haka cikin daure fuska Yaya ya amsa mata da cewa Eh, Sai take cewa a cikin rashin damuwa, gaskiya yakamata a samo mata supporter wace zata dan dinga taimaka mata, Saboda inda ka kula abin nason wanda zai zauna a kusa da ita akoda yaushe, Ok idan har ka yarda ni zan iya samo maku mace mutumiyar kirki don ta taimaka maku, Yana tafiya batare da ya tsaya ba ya ke cewa sai najiki, yashige abinshi yabar a tsaye muna bin bayan shi da kallo,, Murmushi nayi daga gefena nake cewa hmm anty kin dai matsa saida kikai wanan zancen Tace wallahi matar tabani tausayi ne sosai shiyasa na damu, Amma ai, zai yarda idan yaga matar don tanada mutunci sosai, saboda maigidan ta ya rasa dadaewa yaran ta biyu maza amma duk suna wai Lagos a zaune suna sana,a a can, Haka mu kayi sallama dasu har Fattu wace zata shige nata gidan daga can, Ina shiga falo na samu Yaya Abubaka shi da Baba Wadda a zaune Tambaya yaya ya jefo min da cewa, a ina kika san wa yan nan matan Meenat ? Naja na tsaya fuska a dan daure nace matar da take min gyaran kaine da kafa, ansar da na bashi ke nan a takaice, Zan wuce naji yana ce bana son yawan kwashe kwashe na fada maki, Nace bani na kirasu ba yaya sun dai zo gaida ni da jiki ne, Daga haka na shige ba tare da na tsaya jin may zaice ba, Ina shiga daki na kara gyara inda su Antyn Saloon suka zauna tare da sharo dakin nawa, Yaya Abubakar ne ya shigo dakin nawa yana mai cewa baki girkawa Baba abinci bane, Na aje filon dake hannu na saman gado nace Yaya gani nayi cewa banice da girki ba don haka yasa ban yi, Ya ce look Meenat ko da baki a matsayin mata ta nai bako ashe bazaki iya bashi abinci ba , Balle kanin mahaifin mu, da yazo idan wata bata bashi abinci bake ba mai bashi bane,? Kaina yana kasa ban daga ba nace Yaya amma kasan halin Salawatu zata iya cewa, ai don may na girka abincin tunda ni ba girki nakeyi ba, Ya ce ba tace bazata iya girki ba don bata son warin girki kuma tana fama da zazzabi , Nace ban san wanan zancen ba don haka shiyasa nake taka tsantsan kada tace don may, Ok kifito ki bashi abinda zaici, ya juya yabar dakin batare da yakara cewa komai ba kuma, Dama na girka abinci na aje inda babu mai sanin cewa nayi, Don haka na gabatar masu dashi a dining table , Har yaya Abubakar sai da ya ci abincin don baici komai ba shi ma, ****** ********** ****** Washe gari ina cikin wani material lace yellow da purple din flower a jikin shi sai stones a kasan shi, Dinkin dogon rigane akai min dashi, sai na dan zauna a gaban mirror nayi simple make up, a fuska na, Na dauko takalmana na saka akafana, sai kamshi turaren shekkah ke tashi a jikina, Dakin Anty Sadiya na nufa don in gaida ita, da jiki, don tun safe ina ta aikin gyaran falon mu da yai dauda, Sai kuma girkin da na hada don karyawan jama,an gidan, Karfin hali kawai nima na keyi don jiki na sam bana jin karfin sa, Abin karin ta nadauko daga kitchen zuwa dakin ta daga kofan dakin na tsaya ina sallama inda Yaya Abubakar dake acikin dakin yai min iso, A zaune take da alaman wanka tayi, don magani na ga yana shafa mata ajikin ta, Gefen da take zaune na nufa da tire din na aje mata ina fuskan tar ta nace ina kwana Anty Ya karfin jikin ya kuma dare ,? Ta amsa a hankali idon nakai ga hannayen ta sai na ga duk sun faffashe suna dan fidda ruwa,, Magani Yaya Abubakar ke kokarin kadawa ga cup na karba na kada na nufeta dashi, Da kaina na kafa mata a baki har saida ta shanye shi gaba dayan shi sannan cire cup din ina mata sannu da jiki, Shiru mu kayi dakin gaba dayan mu ba mai cewa komai daga cikin mu, idon mu ga hannayen Anty Sadiya dake fitar ruwa, Muryan Yaya Abubakar naji yana cewa wanan matar zuwa yaushe zata turo matar da take magana a kan ta, A hankali na dan dago kaina da fuskana mai nuna damuwa na ce ban san lokaci ba gaskiya . Najuya acikin rashin walwala na bar dakin don zuwa inci gaba da abinda na keyi,, Yaya Abubakar wanda ke daga tsaye gefen gadon ya bini da idanu har na fita daga dakin, Ina fitowa Salawace na gani tana fitowa daga kitchen ta hada tea da wani leda mai katon bread a cikin sa, Kala bata ce min ba sai kokatin gittawa take a gabana, Sanin cewa gaba baida kyau yasani daurewa cikin dakiyan zuciya nace, Ina kwana ya jikin ki ? Kamar bazata ansa min ba sainaji bayan ta dan gwautani kadan tana cewa lafiya, Ta wuce tana wani irin karairaya tare da dan matse fuskan ta, gare ni, Ni dariya ma tabani sai na tuna da zaginta da Antyn Saloon tayi jiya, Ban wani dade da shiga dakina ba naji muryan a kofan dakina a na kwada min sallama, Nafito don ganin ko waye kawar Antyn Saloon ce da wata mata baka, A cikin dan sakin fuska nake cewa a, Anty kece tafe yanzu,? Sannu ku da zuwa daga nan muka shiga gaisawa da su tare da tambayan yadda suka koma jiya, Nan take ce min jiya bayan ta koma gida taje gurin matar da take magana akai , Ba,a samu wani jayayya ba ta yarda da cewa zata zo tagwada ta gani, Kawar Anty saloon tace to ki saurara da,kyau tallo, Wanan din itace muka sani kamar yadda na fada maki da farko kishiyar ta ce ba lafiya muke son ki dinga taimaka mata dan Allah, Tambaya tayi da cewa ina mara lafiyan nace tana dakin ta , Nace amma fa kin san cewa jiya sai andaure don haka don Allah kiyi hakkuri please, Tace babu komai insha Allah zata yi kokarin tun madam ce ta kawo ni, Nace to mungode barin je inga maigidan in fada mashi cewa kin iso ko, Da sallama na tura kofan dakin yana tsaye yana daurawa hannuwan shi agogo a,hannu guda, Jin sallama na yasa shi dago kan shi ya na duba na daga inda yake tsaye, Ban karasa shiga daga dakin ba nace yaya matar ce tazo da mai aikin , Wani irin kallon ya watso min yace da karfi, ke, Zonan waye zaki tsaya daga can kina fadawa magana haka kai tsaye, Baki naturo gaba cikin nuna alaman fushi azuciya na, Dan nesa dashi kadan na tsaya ina dan kallon shi ganin irin yadda ya tsure ni da ido yasani dukar da kaina kasa, Banyi aune ba sai jin shi nayi ya rungumoni zuwa jikin shi , Kokarin kwacewa daga rikon da yai min na keyi, na ce, nika sake ni please ? Banyi aune ba sai ji nayi yana kokarin kai bakin shi a cikin nawa yana son yi min kiss, Duk kokarin da nakeyi in kwace kaina bai ma san inayi ba, shi, A tare muka fada saman mamakeken gadon dakin shi, Inda ya shiga jagwagwala ta yadda rashi yaso, Kamar wanda akaiwa tsawa naga ya sakeni ya juya da sauri gefe guda yai rub da ciki,, Yana maida numfashi guda guda, daga inda yake akwance, Da kyat na samu na tatara hankalina guri guda tare da saurin gyara gaban rigana da ya kware, Muryan Yaya Abubakar naji yana cewa ki fada mata cewa gani tafe Hannu na nasa na goge dan hawayen da ya zubo min, Nasamu su kawar Antyn saloon zaune suna kallo a dakina, Nace don Allah kuyi hakkuri na samu yana bayi ne shi yasa, Tai murmushi tace, haba ai ba komai tunda har munriga da munzo ko, ai, Ba ai wani daukan lokaci ba ya shigo dakin da sallaman shi , Suka gaisai faram faram tare da kara mashi ya mai jiki ? Fuska a daure yake cewa Alhamdullahi da sauki sosai, Tace ga matar da nake magana zata iya aikin tazo, Sai lokacin ya dubi matar ba wata tsohuwa ce ba sosai haka, Kara gaishe shi Ramatu tayi tana çewa barka da rana yallabai, Yace ina fatan zaki tsaya kiyi abinda ya kawo ki kamar yadda kikai alkawari, Don kinga aiki nan sai an,daure, ansa hakkuri a cikin sa sosai, Agina, kawar Antyn Saloon tace duk nai mata bayani sir, Yaya Abubakar yace, OK nawa ne kuka shirya da ita, ? Aginatu, tace gaskiya bamuyi wanan zancen ba tun farko iyaka dai makwabciya tace ita maigidan ta ya dade da rasuwa , Naga wahala yai mata yawa shine nace barin mata hanya tunda naga kamar yar shiyan state din kuce ita,, Yace, yanzu ke nawa ki ke ganin cewa zan baki ya fadi a kage don duk ya matsu yabar mu, kamar mai tsoron mata, Ramatu tace Alhaji duk abinda ka bani nagode Allah yasa masu albarka, Yace OK zan ganta sai muyi magana akai yana nufin wai zai gan ni sai muyi magana dashi, Daga haka yasa kai daniyar barin dakin har ya kai kofan fita sai ya dakata, Batare da ya juyo ba yace kisan cewa a tsakiyan mata uku zaki zauna sai ki kiyayye please ? Tace insha Allah zan kiyayye Alhaji nan inda aka daukeni zan tsaya da kafana, Bayan fitan yaya Abubakar ne muka kwasa zuwa dakin sadiya gaba dayan mu mu uku, Barci takeyi tun dazu nan nafara yiwa bakuwar mu Ramatu bayani abinda zata dinga yi, Muryan mu da Sadiya taji yasa ta bude idon ta, a hankali tana kallon mu, A kusan tare mu kai mata yaya jiki tace da sauki a hankali, Tana kokarin mikewa ne nasa filo nadan gyara mata a bayan ta, Kara gaisawa sukayi nan nake ce mata ai an kawo wace zata zauna da itane saboda Maman biu bazata iya ba, Sun gaisa da Ramatu tana cewa, ok zaki ko iya yi yar uwa don kinga da wahala abin, Ramatu cikin sakin fuska tace babu damuwa yar uwa zan iya insha Allahu Allah dai ya baki lafiya, Muka karba gaba dayan mu da Ameen Ameen, Munyi Sallama da Aginatu mata mai mutunci da tausayi, Inda na karbi nomban ta da cewa duk abinda ake ciki zan kirata in sheda mata, Duk abinda mukeyi madam din gidan mu tana kallon mu sai dai bata sa baki Kamar yadda ta nuna ciwon Sadiya bai damay ta ba kuma baya gaban ta ma sam, Sai wani nan nan yanzu naga Yaya Abubakar yana yi da ita wanda hankalina baigano ko may ye dalilin hakan ba, Gashi duk dare sai naga ya shigo mata da ledan kayan fruit masu kyau, Ina so amma dayake ita yake kawai ko a kitchen nagan su cikin fridge duk son da na ke masu ban sha, Sam iyanzu babu wani shiri a tsakanina da Salawatu don duk ta dauki tsanar duniya ta samin, Idan da farko tana boyewa yanzu sam bata iya boye don ko a hanya muka hadu cikin biyu sai na samu daya, Harara ko tsuki daga gare ta, abin dariya yake bani don nasan babu yadda zatayi dani dai, Kuma ganin irin rawan kafan da yaya keyi yasani kawo ido in sa masu, Dole aiyukan gida duk da bawai naji saukin jikina bane nice dai maiyin su, Sallah na idar ina zaune gurin ban kai ga dagawa ba naji waya ta tana kara, Yaya Abubakar ne yakirani daga office murya kasa kasa yake cewa, Meenat ina fatan yau zaki karbi girkin ki tunda kinji sauki ko ? A cikin marairai cewa nace don Allah yaya kayi hakkuri bazan iya ba , Don har yanzu nakanji marana yana min ciwo time to time, Yadan tausa muryan shi yace please Meenat for Allah sake ya kuke son inyi ne please ? Nace cikin murya kamar zanyi kuka wallahi yaya bawai naji sauki bane kawai dai karfin hali nakeyi don kada a zauna da yunwa a gidan, Yace look Meena bawai shawaran ki nake nema ba command ne na baki Naji fit ya kashe wayan inda nabi wayan da kallo tankar shi nake kallo, Wahalan da nasha aranan nan ne ya fado min a rai lokaci guda, Inda na rutse idona, cikin wani irin jin zafi azuciya nasan cewa tunda har yaya ya ce hakana to ya zama wajibi in kai masa kaina daren yau in har ina son kaina da lafiya, A haka naci gabada aiyukana batare da hankalina ya kwantaba saboda ina tunane yadda zanyi da Yaya Abubakar a daren yau, Don nasan cewa maganar gaskiya ke nan ya furta har cikin rashi, Dole nadan fara yin an abuwan shirin kwana dakin maigida kamar yadda mata keyi inda kanada kishiya ko kishiyoyi, agida, Kamar daga fara gyara dakin maigida yin yan gyare gyaren gida, sai kuma girki tare da tsala kwalliyan daren don taron maigida, Saidai duk ni yau acikin fargaba nakeyin nawa saboda yadda yanayin jikina yake, Duk abinda nakeyi yar sa idon gidan mu tana biye dani don ganin shirina, Na,gane may takeyi amma sai nai tankar ban fahince ta ba, Daga inda nake ina gyara kaya a dining table na hangota tafito a lokacin yayi daidai da time din dawowan Yaya Abubakar gida yayi, Har gaban table din da nake tafito tana wani taunan chewing gun irin na yan duniya , ZEEE MAKAWA YELWA 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 6⃣3⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA ALLAH- AL HAQQ Zaune nake a gaban mirror na bayan fitowa na daga wanka, Saida nai sallah nafila, nazo gaban mirror na na zauna don gyara jiki kamar yadda duk wata macen aure da tasan kanta takeyi, Mai mai kamshi na fara lakatowa na shafe karkashin nono har zuwa saman shi, Sai na fara lakato turaren mai na kamfanin oud, ina shafawa a part, part din jikina, Nai mixed din kusan kala uku a guri guda na bude matsematse na na shafa, tako ina har zuwa mazauna na,, Na koma gurin man gashi da na sayo gurin anty saloon na shafe kaina dashi har zuwa baya, Na dan dankwala turare nashafe bayan kunnuwa na zuwa wuya na, Rigar barcin da na fitar zan sa na feshe shi da turaren feshi , tare da zanin da zan tafi dashi don sallah da hijjab, Ina saka miski bayan nasan cewa hayakin kanun farin da nayi ya shiga jiki na, Sai nakawo miski na dan dankgwala kadan bada yawa kwarai ba, Waya na,ne naji kira ya shigo min a lokacin daga inda nake na mika hannu na na,dauka, Yaya Abubakar ne a layi yana kirana , nadan tsura ma wayan ido kamar ba zan dauka ba,, Sai na mika hannu na a hankali na dan na received, Muryan shi cikin wani irin yanayi kasa, kasa yake cewa, Meena may kikeyi tun dazun baki zo ba bayan kin san cewa ke nake jira, Murya kamar ina rowa nace a cikin wani irin ja sallah na tsaya yi dama, naji yace ok, Bayan na aje wayan nai shiru na tsurawa wayan ido na dan wani lokaci, Sweet din dake acikin drawer dina nadauko guda biyu different colour na bare su na jefa a bakina, Namike a hankali tare da saka rigar barci a jikina na saka katon Hijab dina, akai, Na kaso wutan dakina tare da dauko wayana da zani a hannu, nasa key na kulle kofan dakin, Adaidai koridon da zai sada ni da part din Yaya muka hade da Salawa ta sa wasu shegun rigar barci komai nata a waje da alaman kamar shigarta ke nan tafito dakin nashi, Don ina daga kofa na ina rufewa, naji motsinta badadewa ba , Tankar ban ganta ba na sa kai na shige abina ina jin ta tana wani irin ajiyan zuciya bayan na dan wuce ta,, Dakin nashi babu kowa da alaman yana cikin bathroom a lokacin, don motsin da naji, Na kalli gadon yanan a gyare kamar yadda na gyarashi dazun da yamma, Bakin gado na samu na dan zauna kamar maijin tsoro, Fuskana yana mai bin ko ina nadakin da kallo a hankali, Motsin fitowan shi daga bathroom din shi yasa ni dan daga kai na kalleshi, Yana saye da bathroom robe din shi yadan daure igiyar shi, Wani irin kwara jini yai min a fuska na da sauri na kawar da kaina daga kallon shi, Gurin mirror din shi yanafa yana dan gyare, gyare irin ta maza, Daga gurin da yake a tsaye ya ke cecmin may kika tsaya yi ne baki sallah da wuri ba, I have been waiting for you since,? Nace na dan je gurin wanan bakuwar matar ce na gwada mata wasu abubuwa yadda akeyi, Yace OK sai kika shanya yayan ki a nan ko ? Murmshi nayi nace cikin murya kasa, kasa tare da dan wasa da yatsuna ,a,a ba haka bane nadaiga ita bakuwa ce, kawai, Inda nake zaune ya juyo yana kallo na yace shi kuma waban Hijab din fa na may ye? Sai da nai murmushi a hankali nafara sabule Hijab din daga jikina, Yar karuwan rigan barcin da nasaka mai kama da babu komai ajiki na ya baiyyana, Sai ganin, Yaya Abubakar nayi a gabana yana cewa masha Allah, Meenat you look so gratuitous, Na lumshe idona tare da hade wasu miyaun mintin da nake tsotso a bakina, A hankali naji hannuwan shi a saman wuya na yana dan tafiya dasu kamar tsutsa, a hankali har zuwa kaina, Harshen shi naji a kunnuwa na yana min magana daga ciki a hankali, Abinda ya saukar min da wani irin kasala a jikkina lokaci guda, A take ya fara amfani da harshen shi kamar wanda ya samu Sweet yana tsosa, Jikina yafara dan karkadawa kamar yaune farkon haduwa na dashi, Bansan ya akayiba sai jina nayi saman katafaren gadon yaya, yafa aika min da sakon ni, kala kala, a ciki na, Abinda ya jawo min mutuwan jiki da kasala ke nan a lokaci guda, Sai nake ga tankar yau ne farkon haduwan mu da Yaya Abubakar, Shi kadai ke kidan shi da rawan shi har zuwa lokacin da ya gaji don kan shi, Naji mirginawan shi yana mai maida numfashi a guda guda, daga gefe da yake kwance, A daidai lokacin da yadan koma normal naji ya damko hannuna ya hada da nashi ya matse guri guda, He sound in a soft, voice yace, Meena why the you act like this today ? Is something wrong with you, ? Runtse ido na nayi guri guda tare da fitar da wani dan siririn hawaye , Ban iya yi magana sai dai gyara kwanciyar dana yi a hankali, Ajiyan zuciya naji yayi daga gefen shi, yana cewa, You know that i love I don't want to hurt you, ki daina yi min rudeness, please, Cikin muryq mai kama da ta mai son kuka nace Yaya na fada ma cewa zamu fara teaching practice ne very soon, Naji ya sauke ajiyan zuciya yana cewa, nafada maki cewa ki bini sannu, Ya kike son inyi ina a cikin wanan irin tension a lokaci guda abubuwa sun zo min at the same time, Nima a nawa bangaren yadda naji ya fadi maganar sai tausayin shi ya kamani A hankali na furta cewa kayi hakkuri yaya dama don kada a wuce ni ga karatuna ne na shiga damuwa, Dai yana mikewa daga kwancen data ke kobai fada ba nasan cewa wanka zai shiga don baya kwana ba tsarki a jikin shi, Yace, idon karatu ne insha Allah zaki karas meena kawai ina son inyi styling din gida nane tukun, Daga haka ya shiga bathroom din don tsarkake jikin shi kamar kullun,, Sai bayan fitowan shi na shiga ni ma nai wanka nafito, na maida rigan barci nada zani nadake ta faman kamshi,,, ****** ********** ****** Salawatu wace daga dakin ta ke ji tankar tayi ihu don shedan na rudin ta yana anya na mata abubuwa a gamay da mu,, Waya ta dauka acikin daren nan take fadawa Lubuna cewa gaskiya har yanzu fa bata samu yadda take so a gurin Oga, ba, Don har yanzu yana rawan kafa ga shegiyar yarinyar nan fitsarara, Lubuna tace amma ai kin dai ji abinda wanan bokon na masaka yafada muna ko, Don haka wallahi in har kina son kan ki da lafiya Salawa ki rabu da wanan yarinyar ki sa mata ido, Tun kafin wani abu mara kyau yazo ya faru da akan son kai irin naki, Shima wai may nene matsalan ki tunda har kin samu yanzu yana fifita ki fiye da sauran, gaba daya, Ki fita batun yarinyar mana tunda babu abinda zata diba a gurin ki, Look Lubuna wallahi ban kaunar in bude idona inga shegiyar yarinyar nan a cikin gidan nan , Don idan har tana tare dashi to wallahi ina fada maki bazai ta ba kallon kowace mace ba da daraja, Idan nai magana sai yace wai banda hakkuri karamar yarinyace shima lalabata yake yi a zauna lafiya, Shiya sa ranan da tashigo min daki naso in mata dukan tsiya da ko iyayyen ta bazasu sheda ta ba, Lubuna tai yar dariya tana cewa ita ko tana a tsaye zaki mata irin wanan dukan haka, Salawatu tace ai ni in fada maki nafi kowa fatin cikin zubewan cikin shegiya, Da muna zaune muna kallon yar iska yar karama da ita tana haihuwa muna taya ta raino, Lubuna tace ai gara da kika zubar dashi kowa ma ya huta don abinda zaku gani sai yagi nan, A to kin mata ance kakan su matsafine shiyasa duk abinda zan masu zai kama su ba, Mutumin da akace ko ruwa ya duba yace ya zama kifi sai yazama, kifin, Ke Sallawa banda sheri fa tace wallahi nima malam Abudullahi masinger shi ke bani labarin su,, Aikin san karbi karbi,baibar ko wa ba, don mutanen yanzu idan kana son sanin abu mikama na kusa da su alheri kasha labari,, Yanzu ai baki san wani abuba pretending na ke mashi as, pregnant woman, Ihu Lubuna tasa tace, ke Sallawa kirage sheri wallahi, Kada yazo ya gane karya ki keyi fa ku hausama dashi, Ta ce ke don ba ki ga irin yadda da akace yarinyar nan tayi miscarriage yadda ya koma kaman zaiyi hauka,, Au to ke ki na ganin cewa zai yi wanan rawan kafan akan ki ne Salawa,,, Sundauki tsawon lokaci suna hira a tsakanin su abinda har yasa Salawa ta dan rage jin zafin da takeyi, ****** ********** ****** Bayan wasu yan awani ina cikin barci naji tankar an tashe ni daga barcin da nake yi, A hankali na bude idona inda nagane cewa a dakin Yaya Abubakar nake kwance, Yana daga gefena yana barcin shi acikin kwanciyan hankali, Wani amai ne ya taso min ya tokare min makoshina inaji tankar zan amaye hanji na, Cikin sauri na mike zaune don zuwa yin amain, da nake ji yanzu, Da sauri na isa bathroom din na fara sheka amai, kamar zan dauke, a lokacin, Da kyat bayan nagama na iya tasowa zuwa cikin daki, don in kwanta, Yaya Abubakar ne na gani a tsaye hannayen shi harde da juna yana min wani irin kallo acikun mamaki, Tafiya na keyi kamar zan fadi don irin yadda na kejin jiwa yana dibana,, Hannun Yaya Abubakar naji ya tallaboni ta bayana yakai ni bakin gado ya aje, Ya koma bathroom din ya gyara ya fesa abin kamshi,, Ai bai fito ba daga bayin sai ga ni na shigo da gudu in sheka wani sabon aman, A take, tausayi ya kama Yaya Abubakar yayi daya sani ya kyale ni kawai, Acikin wani irin murya mai sanyi yake cewa Meena dama baki da lafiya ne, ? Aman ne ya kara zo min faaaa da karfi duk na bata mai bathroom din dake a jikin shi,, Sai faman sannu sannu yake min a cikin nuna damuwan shi, gare ni, Shida kan shi ya kaini saman gadon shi ya shimfede ni sai karkadawa nake yi, A take jikina yai min wani irin zafi zazzabi mai karfi ya rufe ni a lokaci guda, Hankali Yaya Abubakar yai mugun tashi don bai san yadda zaiyi da daren nan ba, Paracetamol yabani nasha don samun dan sasautawan zafin jikin, Cikin ikon Allah nasamu dan sauki zuwa tasan ma asuba na samu barci ya kwashe ni, Daga haka ban farka ba sai kusan takwas na safe ranan ban samu Sallah safe ba, da wuri, Zaune ya ke a gefe na bayan ya dawo daga massalaci, Ya kura min ido yana kallon yadda nake maida numfashina a hankali, Fuska ya ramay sosai na koma wata yar feyau dani kaman na dade a kwance ina ciwo, A hankali na bude idona don jin nauyin mutum danayi daga cikin barci na a kusa dani, A hankali na bude idon da sukai min nauyi na furta cikin yanayin ciwo da cewa sannu Yaya, Na mai da idanuna a hankali na rufe don ci gaba da,barci na, Sallah ne ya fado min a rai nai zubur na bude idon tare da kokarin mikewa zaune,, Ina zaki ne kuma ya tambaya cikin yanayin damuwa, A hankali nace banyi Sallah ba Yaya kuma gashi har gari ya waye sosai, Yace ki bi a hankali don kin san jikin ki babu karfi sosai, don haka kibi a hankali, Ina kaiwa zaune na kara jin wani irin luuu kamar dakin yana juya min, Sai kuma wani irin yunwa da naji ya ziyarci cikina, Yaya yunwa nake ji sosai wallahi nafadi ina hamma alaman akwai barci a idona, Ya mike yana cewa kwanta ina zuwa tukun na barin samo maki abinda zaki sha, Yana fita har kwanta na rufe idon kamar zan koma barci amma sai naji bazan iya ba, don banyi sallah ba, Don haka namike ahankali na nufi bathroom don in yi alwala wanka nafara na watsa ruwa masu zafi a jiki na, Hakan ya dan sani jin karfin jikina har na samu nayi sallah , Ina zaune a gurin da nai sallah na dan zauna tare da, dan lumshe idona acikin yanayi na mai jin ciwon jiki, Yaya Abubakar yadauko tea da kwai da ya soya min da hannun shi a kitchen, Tun yana suyan kwan Salawa ta shigo kitchen ganin shi a tsaye yana hada breakfast da kan shi yasa ta mamaki tana tambayan lafiya yake kitchen da kan shi, A takaice ya ce Meena bata da lafiya shiyasa nake son in hada mata breakfast, Gabanta ne yaba da dammm tace cikin karaji may ya samay ta kuma ? Bai bata amsa ba sai juye kwan acikin plate dayayi tare da kashe gas din da yai amfani dashi, Ya dauko kwan zuwa gurin da ya hada min tea mai kauri ya nufi hanyar fita, Salawatu tana tsaya kamar gunki duk imani ya kashe ta kamar ba jiya jiya ta gama bata kudin ta gurin bokan su ba, A inda nake kwance saman sanyin ties ina jin dadin sanyin kasan, Kallon mamaki yake min har zuwa lokacin da ya karaso gurina yana cewa, kin samu yin sallah ne ? Na bude idona a hankali ina cewa eh yaya nayi sallah , Idona yana akan cup din dake rike a hannun shi don ji nakeyi tankar in kwace in kafa kai , Don irin yuwan da nake ji a lokacin kamar inyi ihu saboda shi,, Gaf dani ya zauna ya miko min cup din a bakina yana nufin insha daga hannun shi, Nagane nugin shi don haka banda zabi tun da na kafa kai ban dakata ba har sai da na shanye tea din, Yaya Abubakar yaji wani irin tausayi na mamakin yadda na shanye cup guda a lokaci guda yace ko akara hado maki ne, ? Nace a a yaya na gode na koshi sai yace to kici kwan ko kadan ne please ? Nafara cin kwan a hankali ina taunawa kamar bakina ciwo yake min,,, Zan kai na hudune naji wani irin tashin zuciya ya ziyarci zuciyana, a lokaci guda idona ya rufe da sauri na ke kokarin mikewa, Sai kokarin rikeni Yaya keyi ai ko nawanko masa jikin shi duk da amai a lokaci guda ina kokarin mikewa kuma wani aman ya kara zowa, Hankalin Yaya Abubakar yai mugun tashi a lokacin sai da yaga na dakatar da aman yake ce min sannu ko ? Da kyat na samu na ke kada kaina ina cewa wayyo Allah na cikina, cikina Ya Abubakar duk ya rude ya fita hayacin sa yana cewa tashi mu tafi asibiti kn ji Subbahanallahi wai may ke damun ki ne haka Meenat ? Kasan naji bazai min ba na mike zuwa saman gadon shi na kwanta na dunkule guri guda kamar jaririya, A take barci ya daukeni barci mai nauyi yai gaba dani lokaci guda, Ganin nasamu barci sai zufa na keyi a cikin barcin yasa shi dan sauke ajiyan zuciya, Nan ya barni a kwance ya fita zuwa, gurin aikin sa amma zuciyar sa tana acikin damuwa, ****** ********** ****** Zaune take a falo tun lokacin da taji fitan maigidan Idan ba karya zuciyar ta ke mata ba tana iya cewa yau tun safe ban fito daga part din Yaya Abubakar ba, Hakan ne ya bata daman ya kewa a zuciyan ta cewa ta tashi ta leka dakin Yaya Abubakar tagani, A kwance ta hangoni nadunkule guri guda ina barci, abina hankali kwance, Ta dade tana kallon zuciyar ta na kiyas ta mata abubuwa da dama akaina, Gyara kwanciyar da nayi yasa ta saurin ja da baya da sauri tasake labulen kofan tabar gurin, Tun kagin ta karasa saukowa daga stairs din ta hango Ramatu tafito daga dakin Anty Sadiya, Tana saye acikin hijab din ta har kasa tana dauke da flask din ruwan zafi a hannunta, Ganin ta doshi hanyar kitchen yasa Salawatu wani irin daka mata tsawa,, Ke dakata lafiya ina zaki shiga wa mutane haka ? Daga ina kike ne ma wai ? Ramatu wacce tsawan Salawatu yadan sata yar kaduwa tajuyo tana kare tamata kallo, Akaron farko da tafara ganin ta ke nan a gidan tun shigowanta jiya, Cikin dan rusunnawa tace, hajiya ina kwana ? Ya aiyuka, Kalafiya ta karba da cewa tare da watsa mata wani irin kallon rainin hankali na ke wacece, Daga ina kike na haka ? Cikin wani irin kallon tun daga sama har kasan ta, Ramatu tace daga sashen wacan Hajiya da bata da lafiya nice wace aka kawo don in dinga taimaka mata, Sai da tai mata wani kallon rainin wayo har zuwa kasa tace, Uummww kece dai mai kwadai da bata san ciwon kanta ba ko yan uwanta suna gudun ta ke don kwaidai kin zo kin tara ko ? Murmushi Ramatu tayi tace, ai taimako ne hajiya babu abinda zai faru insha Allah, Daga haka Salawatu ta,watso mata harara cikin kallon ke kika sani tajuya fuuu ta shige part din ta, Ramatu tabi ta da kallon mamaki har shigewan ta cikki ta kada kai tana cewa akwai magana ke nan a gidan nan suna da tantiriya, ashe, agidan haka ? ****** ********** ****** Hasken rana ne ya hasko min fuska na daga window dakin ta baya, Abinda ya sani bude idona kenan nauyi naji jikina yayi sosai , Sai daga baya nagane cewa ina dakin Yaya Abubakar ne har wanan lokacin, A hankali na yunkura na mike zaune nadan dade a zaune bakin gado kafin na yunkura namike tare da tattara duk kayayakina zuwa kasa part dina, A hankali na tako zuwa kasa inda na hadu da Ramatu ta dauko ruwan zafin da ta dafa , Tana ganina ta tsaya tana cewa sannu uwar daki na ashe yau kuma jikin ya tabu ne haka, Alhaji ne ke fada muna dazun da zai fita yace baki barci da dadi ba daren jiya, Nadam lumshe ido alamar ciwo nace ai naji sauki sosai, jikin dai ne ba karfi, Ta dan kauce min kadan duk da ba ko a kusa muke ba amma saboda girmamawa ta dan kauce gefe, guda, Ina shiga daki na fada saman gadona tare da lumshe idanuwa na Zuwa can na sauke ajiyan zuciya tare da bude idona, Sallaman Ramatu naji adakin nawa tana cewz ko akwai abinda zan taimaka maki dashine Hajiya, Cikin dan lumshe ido nace yuwan nake ji sosai wallahi, Tace ko may zaki ci yanzu nace ko tea ne ki hada min don Allah, Fitan ta don zuwa hado min tea din yai daidai da kiran wayan yaya Abubakar, Nadauka a hankali da cewa Sallamu Alaikum cikin yar siriri yan murya,, Muryan shi yana cewa Meenat kin tashi yaya jikin naki ne ? Na lumshe ido na tankar yana kusa dani don jin muryan shi da ya daji kunnuwa na, Nace eh yaya naji sauki ai, Kin sauko ne ko kina kwance har yanzu sama, nace ina daki na kwance ne zan sha tea ina jin yunwa ne sosai, Yace A,a wanan jin yuwa fa Meenat kamar mai Ulcer ? Murmushi nayi batare da na bashi ansa ba, nace hmmm kawai cikin lumshe ido, Bayan nasha tea din da Ramatu ta hado min nasha, Sai wani irin zufa ya fara karyo min duk jikina ta ko ina inajin wani irin zafi, Don haka na fada bathroom na watsa ruwan don inji dama ajikina, Bayan fitowan na ne na dan ji karfin jikina ba kamar yadda na tashi ba don haka na dan jawo wani dogon riga jallabiya na saka ajikina. Cikin daurewa na nufi dakin Anty Sadiya, don in duba lafiyan ta, Nasamu Ramatu tana hada mata abinci zata ci, da kuma dan gyara mata filo, Mungaisa da ita ina mai kallon hannuwa ta yau gaskiya babu laifi don hannu ya tsane sosai ba kamar baya ba, Nace cikin murya ta kasala anty ya jikin ta amsa cikin wani kushe fusaka da cewa, Da sauki yaya naki jikin dazu yake fadamin cewa wai daren jiya bakuyi barci ba, Nace cikin murmushin karfin hali wallahi fever ne ya kamani acikin dare mai karfi amma naji sauki ai yanzu sosai, Jikin nawane kawai nake jin shi wani iri kamar ba nawa ba, Tace Allah ya sauwaka na ansa da fadar amin tare da kurawa hannuwanta ido ina kallon su, Munyi shiru can take cewa wai ko matar gidan nan tana nan kuwa, Ban yi saurin kawo watake nufi ba don sai ina kallon ta ina mamaren kowa cece bayan ita, Sai Ramatuce ke cewa Hajiya aini dazun tabani tsoro sosai don yadda muka kwasa da ita da safe, Sai nagane cewa Salawatu take nufi nace tana nan mana , Anty Sadiya tace wai ciki gare ta maigidan ke fada jiya yana cewa wai kwanan duk bata jin dadi saboda duk abinda taci sai ta dinga jin tashin zuciya, Gabana ya fadi inda na tuna cewa cikin da ya zube min fa hakana nadinga amai alokacin shigar shi, Kardai ace jiya jiya da fara karban girkina har na dauki wani cikin nafara laulayi haka da sauri, Muryan Sadiya ce ke cewa, ai ni wanan matar ban dauke ta acikin masu hankali ba sam, Murmushi nayi ina mamaki araina irin mugu kishin dake a tsakanin anty da Salawatu, A raina nace aiko ni ban tsiraba kenan don nima aikishiyace, Namike batare da nakara cewa kallaba adakin ina cewa zandan tafi in kwanta, kadan, Daga haka nasa kai nabar dakin na nufi part dina, Nasamu misscalled din yaya Abubakar har biyu ban bata lokaci ba gurin kiran shi, Najiya nacewa ina kika shigane tun dazun baki dauki waya ba haka, Nace natafi gaida Anty Sadiya ce nabae wayan adaki , Yace alright, Yajikin naki yanzu I hope baki kara aman ba dai ko zuwa yanzu ? Nace bankara ba yaya naji sauki ai sosai don banajin komai yanzu, Amsa da cewa masha Allah may kikeso azo maku dashi, nace a hankali babu komai yaya, Hmmm kawai yace baikara cewa komai ba naji ya kashe wayan nashi, Nima nasaka tawa wayan a caji na dan saya kofar dakina na kwanta atake barci yai gaba dani,,,, ZEEE MAKAWA YELWA 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 6⃣4⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA ALLAH- AL-WAKEEL,,, Don Allah ina neman addu,an ku gareni nafatan alheri ga abinda nasa gabana, Ya Allah kataimaki boyar ka Zainab kaba ta miji nagari mai mutun ci da sanin ya kamata,,,, Allahuma Ameeen Allah Tun ranan da nai wanan ciwon sai na samu sauki sai abinda na lura dashi yanzu ina yawan yin zazabin dare, Sai dai kusan asuba sai kuma Allah ya kawo min sauki,, Don haka sai ban wani yawan damuwa da hakan sai ina ganin ai fever ne kawai,, Sai kuma nadawo da shan ruwan Lipton dina kamar farko, Anty Amarya nakira ina sheda mata irin halin yanayin da nake ciki yanzu, Cikin tausa murya tankar wani yana kusa da ita, tace, Shin Meenat ko dai cikin ki dama bai zube ba na ? Nace nima a hankali walle ban sani ba Anty ko bai zube ba , Tace kai duk yadda akanyi cikin nan yana nan jikin ki ki la dai bleeding na kawai kin kayi kwana ki, Tace shin ke san wani abu yanzu nace a,a anty ta ja bakin ki dai kiyi shiru don kesan halin bakar mugunyar kishiyar ki, bata da kyaun hali, Don haka kiyi shiru dai kar ki bari har shi maigidan yasan da zancen ki, Na amsa da fadar cewa to anty , Anty Amarya tace Allah dai yasa cikin nan baizube ba ma muga tsiya gurin munafukar kishiyar ki, Nace, Anty ai itama ciki ne da ita a yanzu haka sai fama shagwaba takeyi wa mijin ta, Tsuki mai kara sosai Anty tayi don jin haushin zancen, Tace wanan makira kilama karya takeyi wallahi yanzu haka kira ma makirci ne irin na tsufin mata, Mun dan dauki lokaci muna hiran da ita tana fada min yadda zanyi, Don tana bukatar in jagulawa Salawatu rayuwa ta yadda batai tsan mani ba daga gare ni,,,, ****** ********** ****** Kamar yadda Anty Amarya tace min in kauda komai a zuciya na in yi haka din nayi kuwa,, Don gaba daya ,nima yanzu na sake ma Salawatu , don ina gwada mata cewa nima fa A, ce, A kwance nake kasa dakina saman ties saboda inajin dadin irin sanyin dake fitowa daga kasan ties din, Ban san shigowan Yaya Abubakar a dakin nawa ba sai dai ganin shi nayi a gabana, Yadan dauki lokaci a tsaye gabana yana kare min kallo, cikin wani irin yanayi, Ganin shi tsaye a kaina yasani kokarin mikewa zaune daga kwancen da nake, Muryan shi naji yana cewa No kwanta abinki kawai, Sai ya duko ya tsugun na agaba da fuska na har muna iya jin numfashin junan mu, Cikin wani irin kallon sha,awa yake ce wa may yasa may ki kika kwanta haka a kasa, Duk da ba dadi nake ji a jikin na wa ba sai nayi kokarin kirikiro murmushin dole nace, Kawai dai na kwantane in dan huta don zaman haka ya ishe ni, Yaya Abubakar yace amma jikin ki kamar mara lafiya tare da kai hannun shi ajikina yana dan tabawa, Nace lafiya na kalau Yaya bandai gama walwarewa banre kawai, daga rashin lafiyan da nayi, Yai dan shiru can yana kokarin mikewa daga tsaye yake cewa,munyi waya da malam tsoho dazun yake tambayana ke, Murmushi na sake tare da kokarin mikewa daga zaune nace,, Allah sarki suna lafiya ko ? A gaban mirror dina ya tsaya ya dan jingina jikin shi da katakon mirror, yace, Autan shi wai yake tambaya yaushe ne zai dawo nake ce mai aikece kika tsaida shi, anan, Na dan langabe kaina nace cikin shagwaba yaya kada kasa malam ya rikeni fa, Duk wanda ya tambaya ina Wadsa sai yace ai yana wurin Meenatu Abuja, Lokacin da yaya yadago a mirror ya ke cewa kinga sai mutane suce ai yar tashi ta kosa, Kaina na kara langabewa cikin tausa murya kamar wata karamar yarinya nace hai ,Yaya , Zai fita daga dakin yake cewa zan shiga wanka yau a fito falo please ? Salawatu wace ke labe daga kofan daki tana sauraren mu da leke, saboda wai bata san may yasa yake yawan dadewa a dakina ba, Tai sauri tabar gurin zuwa can kasa stairs din part din shi tankar mai neman wani abu a gurin, Shiko yana fitowa ya na fitowa bai tsaya bata lokaci ba kawai ya haura sama abin shi, ****** ********* ****** Abin duniya ya taru yaiwa Hajja katutu azuciyar ta da fili saboda yadda Dodo yanzu al,amarin nashi duk ya riki ce mata, Ko ita kadai ce a zaune sai ta fara surutu kamar ta baba, Sai tai ta faman diban ruwa zuwa, cikin dakin da ta aje Dodon nata, Gashi yanzu sai take gani ai duk abin duniyar da ta tara kamar a ana zuke su ne, Ita dai ba tabasu takeyi ba don bata yarda tayi asaran kwandala daga kudin ta,, Bata sadaka bata kyauta bata hasara balle don Allah yi hakkuri, indan an mata barna, Don haka ta dauki alwashin sai ta ga bayan duk wani wanda ya ke kokarin kashe mata Dodon ta, Yanzu abubuwa take yankawa agidan ta tana ba mutane sadakar nama amma babu masu karban sadakan a shiyan nasu, Sai tai dabaran kawai wani uguwa don ita kawai, bukatan ta shine tayi yankan dabba da sunan zata bawa Dodon ta jini Da ta nasa hakan duk gurin da tai yankan daniyar haka jinin zai samay shi, yasha don samun waraka,,, Daga haka tasamu har ya dan samu sauki daga saluntar da jikin shi keyi don tabashin da akayi, Gashi kuma bokanta yai mata nisa yanzu ba kamar da farko a lokacin da yake a gari ba,, ****** ********** ****** Kaina da yasha gyara gurin Antyn Saloon na daura mai ribbon har gida uku, Wando tree quarter nasa tare da wani dan farin riga iya kuguna ,sai kamshi da na shafa ta ko ina ajikina, Yanzu na tabbatar da cewa, Baba Wadda ya bar falon namu saboda bai faye dadewa ba a gida da dare yana zuwa gurin fira tare da,su Baba Hamza,, don yace yafi son ya sauka a gidan su maman Biu,, Yaya Abubakar yana zaune a falon fuskan shi da hankalin shi yana saman system din shi, Takalmin da ke a kafa na suke kara kwas, kwas kwas, Anty Saloon ce ta sayar min dasu da naje gun wanki kai, Abinda yasa Yaya,Abubakar dago kai daga abinda yake yi a cikin system din shi, Salawatu wace ke daga kwance saman kujera two seaters, ta dago kai da sauri don ganin ko wacece, shigowa a lokacin saboda sam batai zaton haka ba Daga inda nake ina kallon yadda take taunar chewing gun kamar a solow, Ga duk rabin yan shamukkakun nonon ta a waje, Wai ita adole tasa rigan daukan hankalin maigida a dole,,, Ido Yaya Abubakar ya sako min tare da dan susucewa,, ga mi da barin abinda ya keyi, A hankali na karasa isowa gurin shi ina dan tsotson lollipop din dake a hannu na hankali, kamar wata Baby Gefen kujerar shi na zauna daidai saitin kafan shi, tare da cewa acikin wata zakkakan murya nace Yaya ina wuni ? Ina jin lokacin da, yai firgigit, tare, da wani irin ajiyan zuciya a hankali, Yace Meena yaya gajiya ? Ido na lumshe tare da yin wani har dasu nace akwai shi gaskiya yaya, Salawatu daga gurin da take a kwance cikin wani irin murya mai kama da mara lafiya,tace, dear yau ina son shan shawarma, Yaya Abubakar ya dubi time yace may yasa baki fada ba tun dazu sai yanzu, Tace yanzun ne ai shan shi yazo min a rai duk wani iri nake ji kamar zanyi amai, takara fadi a cikin shagwaba, A hankali na yunkura daniyar mikewa saboda bani bukatar yafita yabar ni da ita a falon mu biyu, Nace Yaya, don Allah idan ka fita ka taimakamin da Ice cream da fresh fruits please,,, Daga haka kawai na mike zuwa part dina cikin tako irin na jan aji,,, Daga gurin da Salawatu take a kwance tace zakici uban ki yar iskan yarinya, kawai, Sai nayi magani wanan shegeyar yarinyar mara kunya kawai, Unlucky Yaya Abubakar bai samu sakon Salawatu ba amma sai gashi da sakona niki niki a leda, Ina zaune bakin gado dagani sai daurin zani a gaba ina kokarin saka rigar barcina ajikina, Yashigo dakin bakin shi dauke da sallama yana mai kura min ido, Yace adaidai lokacin da yake aje ledan hannun shi a gefen gadona, Har zaki kwanta ke nan yanzu ? Nace, Yaya na gajine ina son indan kwanta in huta ne, wallahi, Yace Oya tashi kisha Ice cream, din kafin ya narke, uana kokarin bude ledan da ya shigo dashi dakin a lokacin, Roban Ice cream din ya dauko min yana kokarin budewa, ina kallon shi har sai da ya bude, yamiko min nakarba tare da fadar nagode yaya, Godiyan yai masa dadi sosai irin yadda naga ya lumshe idanuwan shi, yana murmushi, Abinda rai ke so a take na fara shan Ice, cream din kamar mayunwaciya, Irin yadda nake sha babu kakautawa yasa shi kura min ido acikin mamaki, Muryan Yaya Abubakar da samun Ice cream yasa na manta cewa yana dakin tsaye ya harde hannayen shi, guri guda ya kuramin ido yana gani irin yadda nake haukan sha, Yace haba Meenat yanzu kina son wanan abin haka kika kasa fada min, indinga sayo maki, Ya kamata ace kin saki jiki dani zuwa yanzu ace nasan bukatar ki, Don kada ki dinga sa ina zaluntar ki haka dubi yadda kike shan abu tankar mayunwaciya, Cikin shagwaba nace ni yaya ban san yadda zance a dinga sayo min abuba haka ni kadai, Sai inga cewa baka sayo wa sauran yan uwa na ba ai, gara sai a,sayo muna gaba dayan mu, Yai murmushi yace aikuwa kowace da abinda takance azo mata dashi, wanan ai abin ra,ayi ne , Don kinga ita Salawa ai abinda tace tana bukatar a sayo mata ko ? Yafara tafiya yake cewa ashe shiyasa kika kasa tuna min da zancen lefen ki da na manta banyi maki ba ko ? Murmushi nayi tare da dukar da kaina ina man cigaba da shan Ice cream dina sai dai wanan karon a hankali na fara sha, Yana mai dafa kofan gita dakina yake cewa kiyi hakkuri please wallah mantawa na shap da zance, Amma yanzu na bada sako a kasar Dubai za a hado maki duk abinda ya kamata, Kuma nasan cewa Anty Amarya zasu ga cewa kawai dai banda niyar maki ne shiyasa na share zancen,, Nace cikin kada kai gaskiya wallahi Yaya banta ba jin wanda yai wanan zancen ba, Yace ok hakan yayi yanzu dai ai zasu ga kayan ya riske su girshi ko ? Bugon kofan da Salawa takeyi tare da kwada Sallama da karfi yasa shi yin shiru, A zuciye yace, wai waye wai ta karba daga kofa da cewa Nice, Bai fita daga dakin ba sai daga labulr da yayi ta yadda zata iya hangoni, daga inda nake zaune, ina shan Ice cream di na, Yana bude labulen na hango Salawatu a tsaye cikin masifa, Ta zuba mai wani irin uban harara, tare da jefan sa da wani irin mugun kallo Mai cike da zargi akan yadda ta han goni daga bakin gado a zaune , Yaya Abubakar ya hade, ran shi yana mata wani irin duba yace Lafiya haka,? Ta wani ya mutsa fuska tace naga dawo wanka tun dazu kuma banga sakon nawa har yanzu,, Ya kara daure fuska yace tun da ni yaron aiken ki ne shine kika kasa hakkuri har izo in samay ki, Salawatu ta fahinci yanayin da Yaya Abubakar ya nuna mata na bacin ran shi, Watau ma yana nufin cewa tazo tana damuwar shi ke nan ko ? Saboda iya mu,amulan salawatu da maza zata iya gane k irin halin da namiji ke ciki tundai mashi da take mutuwar so, Wani irin kishine da bakin ciki suka ziyarci zuciyan ta Idanun ta suka canza launi a lokaci guda tare jin wani irin haushi da takaici, Ta tabe baki tace, duk dai abinda, mutum yayi ai Allah yana ganin sa, Yaya Abubakar, yasaki wani murmushin takaici yace, Idan zaki iya jiran inzo sai ki jirani idan bazaki iyaba kuma sai ki shigo ko ? Ta tabaki ta juya acikin bacin rai zuwa tsakiyan falo zuciyan ta tankar ya buga, saboda wani irin bakin kishi da ke cin ta,, Bayan ta ya bi da kallo a hasale yana maigirgiza kan sa a cikin takaici tare da yin tsuki, Ya juyo yana fuskanta ta na dukar da kaina da sauri naci gaba da shan Ice dina, Sai da ya dan dauki dan lokaci kadan a dakin nawa duk da ba komai yake yi ba inba wayan shi da yake ta faman dakila ba, sanan ya fito, yana mai min sai da safe, Yana hawa sama yafara Kokarin cire rigar jikin shi don yai shirin barci, Tashigo dakin a cikin dan daure fuska yai tankar bai ga shigowar ta ba, Tace wai ya zancen sakon nawa ne Sweet Oga ? Yaya Abubakar yayi saurin dakatar da ita acikin daga hannayen shi yana cewa, Wait Salawa ban son surutu da yawa, so please live me alone,? Salawa ta zubawa Yaya Abubakar ido kamar mai son ganin wani abu, Yayin da zuciyar ta ke tafarfasa tana anyana cewa lalai Yaya Abubakar zuciyar ta na gurin wanan munafukan yar karamar yarinya, Lai la ba shakka Oga hankalin shi yana a gurin matar shi yar uwar shi tabbas, Itace fa ta aika sako amma sai gashi ya sayowa wata ita ko zancen nata, Yazu Oga nice fa na baka sako amma baka sayo min ba ka sayowa wace bata ce tana so ba da farko, Yace look Salawa ban son yawa fitina na fada maki , A kinsan cewa kece kika bada sako nafita don may bazaki iya jirana har in dawo ba in baki naki tunsa aguri guda zamu kwana dake, To amma ai ba wai lalaine ace sai ka shiga dakin ta ba ko ? Ya Abubakar ya juyo a hasale yana cewa, Salawa please will you live me alone ? Ta zauna cikin bacin rai a bakin gado tana mai tsura mashi idanu, ta bayan shi yayin da yake kokarin daura towel a jikin shi don shiga wanka, Tace yanzun dai ina sakon nawa yake yace cikin hasala da fadan babu shi, Baki fada ba in time, don haka ban samu sai dai nabar kudi gobe zan karbo maki, Tace amma kasan cewa, yanzu ne cinsa ya zo min arai ko, don may zaka ce sai gobe kuma, Yace to ban sayo ba sai kifita kije ki sayo da kanki ko. ? Cikin mamaki take kallon shi tace Oh, haka kace ko ,? To, Babu inda zan tafi tunda ai bani kadace da wahalan cikin ba harda kai ma, Ya ce a yar hasale to ban siyo ba saiki kyaleni hakana please, Fanin fruit din sunada yawa sai na raba biyu na nufi dakin Anty Sadiya dashi don in basu su sha, in suna da bukata, Na samu Ramatu a zaune tana jan tasbaha anty tana daga kwance tana kallon TV, Nai masu Sallama ina mai mika ma Ramatu ledan Fruit din , Nace ga Fresh Fruit da aka siyo yanzu nace barin debo maku ko ? Daga gurin da Anty Sadiya take tace da watermelons a ciki ? Nace eh da akwai shi ta mike zaune Ramatu tajawo plate tafara zubawa a ciki, Nai masu sai da safe nadawo dakina, nai addua na rufe kofana, Ban wani dade a farke, bayan na gama yin addu,oi na da na saba yi kafin in kwanta barci, Duk da ina yi amma kuma tun ranan da matsala ya faru da anty Anty Sadiya ban yarda in yi barci banyi addu,oi na ba ****** ********** ****** Washe gari ban fito ba sai da nai wanka na gyara jikina tsaba acikin wani purple material, mai adon flowers ash, A Niger na sayo su da muka tafi shida kan shi Yaya Abubakar ya zaban min shi, Nasa su ne don nasan yana sha,awansu tunda har ya zaban min su, Ashe kenan zai ji dadin ganin nasaka su ajiki na da ina boyon su ne saboda banda kaya da yawa amma yanzu da naji cewa zai sayo min sutiru sai kawai nace barin saka abina ajiki inja aji, Suna zaune a dining don cin breakfast, din su wanda yanzu da karfi da yaji Salawatu ta hana aci a tare, Daidai lokacin da nake kokarin fitowa cikin tako irin nawa , Salawa ta zubu min ido, tana mai min wani irin kallon kamar manya, Nasan ba komai take kare min kallo akai ba sai wanan tufafin da na saka ajikina, masu daukan ido, Kamar yadda na hango ta ta ashe ni da ido nima din haka nai mata don wani irin kallo na watsa mata tare da harara, Daga gurin da Yaya Abubakar yake zaune ya tsuro min ido tare da sake min wani mayaudarin murmushi, Ya tataro dukkan hankalin sa gareni, yana ma sakemurmushin gani na, Nima dai muna hada ido murmushin nasakar mashi, mai narka zuciya don nima kaina ban san da cewa na iya irn sa ba, Tuni Salawatu ta tsura mashi ido acikin mamaki tana mamakin yadda yanzu bai ko iya boye feeling din shi kan wanan yarinyar, Wani harara ta wurga mashi tare da jan tsuki, batare da tace uffan ba taci gaba da kokarinkai cibi a bakin ta, Na karaso har gaban table din yayin da kamshin jikina dana tufafina ya daki hancin salawatu, Wani mugun haushi da takaicin wanan yariyanr ya ziyarci zuviyar ta Yaya ina kwana nace mashi yayin da nakai gwiwowi na kasa gab da kujeran da yake a zaune, Sai da ya dan hade abincin da ya deba ya kai a bakin shi, Yace lafiya kalau Meenat yaya dare ya karfin jikin ? Da sauri ta dago kai tana kallon inda nake a tsugune cikin harara, Sai kuma taci gaba da cin abincin ta tana wani murde fuska Yace kizo ki zauna muci abinci ko ko kuwa kin karyane ko ? Nadan dubi abinci nagan shi wani fari fate da shi da gani baiji wani ingredients ba, Sai naji kamar amai zai kamani a lokacin da sauri na kauda kaina daga kallon abincin ina cewa ba yanzu zan karya ba yaya, Ya ce O right amma dakin karya ki karasa shan maganin ki please ? Nace insha Allah a lokacin da nake mikewa tsayd da ga tsugunen da nake, Na wurga mata harara kamar yadda take wurgo min daga inda take zaune, Kitchen na shiga don hada abinda zanci don gaskiya bazan iya cin wanan abinda nagani ba wai jeloup din taliya, Ina kokarin Fere Irish yaya yaleko daga kofan kitchen din yana mi sai yadawo inajin wucewar shi dakin Sadiya,, Naci gaba da aiyukana kawai ban tsaya wani rakiyar shi ba don ina sauri in fara aikin na saboda yunwan da cikina yafara yi, Banyi aune ba sai muryan mutum kawai naji abayana cikin fada tana cewa, Ke Meenat gurinki nazo wallahi barin fada maki gaskiya ki fita a idona wallahi, Idan ba haka ba har kika bari muka sa kafan wado guda dake, agidanan wallahi zaki gane kuren ki sosai, Ke in ma badon hadin iyayye ba ma may zai yi dake yar kauye kawai kamar ki, Murmushi nayi kawai don sanin halinda nake ciki don ba zan bari ta kara cutana ba, Taji haushin murmushin da na keyi batare da na kula ta ba, Tace a hasale ai dole ki mayar dani mahaukaciya yar iska kawai macuciya azzauluma waike kina takama ke tar uwar shi ce, dake da munafukin tsohon kakan ku kukayi kutun kutun kuka aure shi don kada ya aureni, Cikin wani iriin tsawa nace mata ke yar iskan tsohuwa gantalala, Duk kika sake zagan min iyaye wallahi sai yau kingane koni wacece, Tana kokarin ta yo cikina Ramatu tazo da sauri ta shiga tsakanin mu,, ZEEE MAKAWA YELWA 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 6⃣5⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA ALLAH - AL -QAWI,,,, Ganin irin yadda yanayi Salawatu ya nuna min nasan cewa zata iya yin duk wani abinda ta furta a kai na alokacin Shigowan Ramatu a gare mu yasa Salawatu ta juya da fadan a gurin ta,. Ban san may Yaya Abubakar ya manta yadawo dauka ba don tun daga kofa yake jiyo muryan Salawatu tana cewa, Munafukin tsohon da ya hana aure ne don a aure ki wai ya yi maku hadin gida, In har shi yace ki takamu yadda ranki ke so to ki fada mashi aikin shi bai ci ba don ni Salawatu naci dubu sai ceto, Bata karasa abinda ta bude baki tafadi ba kamshi da takon Yaya Abubakar ya baiyyana a kitchen din namu, Maganan da ya makale a bakin Salawatu ke nan bata karasa ba, Ramatu ce tace to Alhamdullahi tunda Allah yadawo dakai Alhaji, Wallahi fitina baida kyau baida faida maida gida baya yake yi, Idan badon nima Allah ya kawoni ba aida ba asan yadda abin zai tsaya ba irin yadda ta taso ma, Ga kuma zagin iyayye wanda bai dace tunda iyayyen yarinyar nan ai sai nake gani kamar duk naku ne da dake tunda dan su kike aure ko ? Fuskan Yaya Abubakar wanda zakace bai ta yin dariya ba dashi ya hade guri guda, Salawata matso kusa dashi tana ceea yawa Oga gara da Allah ya dawo da kai, Kafadawa wanan fitsararan yarinyar tafita hatka wallahi don ni ba sa,ar ta bace, A zuciye ya juyo gare ta ya daka mata wani irin tsawa yana cewa, Shut up my friend I don't want to hear from you, Maza zoki fice min daga gida please,? Salawa ta juyo tana duban shi a cikin mamaki tace Oga ni kake kora daga cikin gidan ka don muna fada da wanan yarinyar, May wanan yarinyar zata gwada min ne wai da har kake kokarin ko yaushe kare ta, Ran Yaya Abubakar ya kara baci yace, a fusace tare da mata wani kallon rainin hankali, Wanan yarinyar ai kema kin san cewa tafi ki komai ko, Tunda har kika tsaya duk yawan shekarun ki a kanta wai kina fitina da ita, Tunda idon ka a rufe yake a kanta ai bazaka ga lafin ta ba ita, Yaya Abubakar ya watsa mata harara yace ni mata na sun fiki komai Salawatu tundaga mutunci, dakuma kamun kai, don babu wace ke jamin fitina da bacin rai a gida da waje sai ke, Wani irin mugun bacin rsi Salawatu taji a wanan kalaman nashi , Take taji gidan tankar yana juya mata, yau ita Salawatu ce ake fadawa haka cewa, Muryan shi taji yana ceea Get,out in my house please , Fuskan shi ta duba wanda babu alamar wasa a zancen shi dole fita zatayi Lailai ma watau namiji baida tabbas yau ita da tske ganin cewa duk ta dara sauran matan Abubakar a komai , Wai ta ce akewa wanan cin fuska a gaban kishiya da ar aiki, Hawaye ne na takaici ya zubo mata a fuska yanzu bata da wata magana tunda har ya kwnce mata zanin a gaban kowa don har Sadiya dake daki saida wanan hayaniyar ya fito da ita, Takasa koda motsawa agurin muryan shi stil yana cewa kuma ina mai tabbatar maki wanan tsohon da kika zaga har sai kin nemi gafaran shi ke da gidan nan, Don shine sillar zuwa na duniya har kika gani kika lake min, Da sauri ta daga kai ta kalli Abubakar wanda yau ya koma mata tankar zaki agabanta, Yace idan na kyale ki agidan nan wata rana zan dawo na samu kin min kissan kai a gidan nan tunda ke dabi,un ki na yan jagaliya ne , A hankali naga Salawatu ta juyo ta kali gurin da nake tsaye da yukan da nake fere dan kali, Sai kuma ta juya ranta abace tafice da ga kofan kitchen din hawaye na zuba mata a idon ta, Bayan ta Yaya Abubakar yabi a fusace ya cewa Iam tied with dis in my house please live us alone, Daga dakin ta yana tsaye daga kofa ya ke fadar hakan ta girgiza kai azuciyar ta tace tab dijam yau kan angama sance mata a kasuwa daga wani irin kallo za,a dinga yi mata agidan kuma, ****** ********** ****** Tafiyan salawatu bai min dadi ba a rai don ba dadi irin haka , duk da dai mahaifana ta zaga da kakana, Amma bai,kamata ace har ta bar gida akan hakan ba don saboda yaya Abubakar tsaye yai mata har sai da ta gita gidan, Shima ya fita, duk Anty Sadiya ta nuna cewa hakan shine daidai ni dai a gaskiya har cikin raina banji dadi ba, Maganar Ramatu ne ya dan hankaltan da ni inda take cewa to ke uwar daki na. Idan har Alhaji bai dauki mataki a kanta ba watarana babban magana zata jawo mai a gida, Sai a lokacin nagane cewa warning din ta yake son yayi don haka nace Allah ya kyauta kawai, Ganin da nayi cewa yanzu Anty Sadiya taji sauki sosai yasani cewa ta karbi girkin ta a ranan idan don cooking ne ni zan dinga yi gaba daya, Batayi musu ba ta karbi girkin ta tare da yi min godiya gurin Yaya Abubakar ne dai muka samu matsala, Don daya dawo yagane cewa Sadiya zata koma girki yai ta masifa yana cewa kamar abin gudu bazata bari taji sauki ba sossi , zata soma girki a yanzu, Amna sai na bashi hakkuri ina sheda mashi cewa nice zan diga cooking din gidan gaba day, . kuma indai yai haka Sadiya zata zaci ko wani abu yake nufi na daban, Dole ba don yaso ba ya hakkura ya barta taci gaba da yi duty din ta,, Bayan na kare aikin komai dake gabana sai na shige dakina don in huta, Ban kai minti biyu da kwantawa ba Anty Amarya tabugo min waya , Na dauka da sallama abakina ina mata gaisuwa tare da tambayan ta kan,nena, Nakuma tambaye ta lafiyan uncle dina tare da na su mummy, Anty ke ce min kwana biyu banji ta ba tana can gidan hajiya suna jin yarta kamfanta ke ciwo har sai da ta kwanta asibiti, Na tausayawa tsohuwan tare da yi mata sheri irin na jika da kaka, Nan Anty take ce min ai Abokin Uncle dina Nasir ya samu matsala da matar shi, don tana ganin kamar har sun rabo Nai Innalillahi tare da tambayan yaushe ? Anty Amarya take cewa ai ankwana biyu da yin case din yanzu haka tana gidan su kano, Yara kuma suna nan an dawo dasu sokoto gidan iyayyen shi, Allah sarki amma gaskiya banji dadin wanan labarin ba anty Tace ai kowa ma meenatu don kin san halin mu mata bamu tsaya muyi bincike ko muyi tunanen mafita ga al,amari. Sai dai kawai mu kama hauka akan dan abinda baikai ya kawo ba, Waifa wayan mijin ta ne taga photo wata mace a ciki ga kuma kafan wani namiji kwance, sai dai ba a dauki photo namijin full ba half body ne kawai, ya fito, Shine ta ce duk yadda akayi mijin tane a kwance ba kowa bane wai Nasir ne,, A take zuviyan ta ya hau ya na shigowa take tambayar shi ko wacece a picture yace mata ina ruwan ta da tambaya, Kinji abinda ya hada su fada ke nan Meenat, niko anty amma dai mata Uncle Nasir tai sakaci sosai wallahi , Mumata idan abu yazo sai bamu kwantar da hankali mu yi nazari sai kawai muce zamu yanke danyen hukunci, Yanzu Anty musalima ace full picture din shi ta gane ai sai tayi kokari na farko ta rufa mai asiri, Na biyu ta zauna tayi nazari may yakai shi gurin waccan matar da har ya ita tsalake ta, Kyawo ko dressing ko marking love, da sauran su, Amma wai sai ki ga mace tana ta hauka kamar ba diyar musulmai ba wace tun tana karama tana jin yadda, akecewa mata hudu Allah ya umarci maza da yi, Matsala dai da abin tsoro shine baka san ko wace ce za,a kawo maka ba, Wanan kuma ai sai naga mutun ya dukufa ga rokon Allah kawai don samun mafita,, Hakane inji Anty Amarya tace ai idan ido ya rufe komai, mace mai kishi tana iyayi, Yanzu da tai hakkuri ta tsaya tayi na zarin wa yan nan abubuwan da kika lissafa ai da baikaisu ga haka ba, Ni wallahi Meena da ni ita ce zan fara yiwa Uncle din ki duk wani abinda nasan najan ra,ayin maza ne, Don yanzu idan kin bibiya ma bata ko kama kafan matar Nasir din ba ita ta cikin photo, Nace ni yanzu anty bagashi ba kaman kin sani kikace in fita zancen Salawatu , Ba sai gashi ba kawai ta tunkare ni jiya, wai zata dake ni kuma again, Ina kitchen ina aiki sai da mai aikin mu ta ta shiga tsakanin mu da ita , Ta dinga surfa min zagi ta uwa ta uba har da dan bawan Allah tsohon mu malam tsoho jiya yasha surfa, Wanan mata dai anyi yar iskan banza wallahi mace kamar iblishiya haka, Nace Allah yasa ashe mai gidan da take tunanen ko ya fita bai kai ga wucewa ba yai mantuwa ya dawo, duk abinda takeyi a kan idon shi ne, Masha Allah inji Anty takara da cewa da kya wallahi ai gwamma da yaji ta da kunnuwan shi, To yaya akayi nan na kwashe duk yadda akayi na fada mata da cewan da yayi sai ta ta roki malam tsoho gafara sanan zata dawo gidan shi Kai amma ko dai Abubakar ya burgeni sosai wallahi yana son ya gwada mata cewa yasan darajan iyayyen shi sosai, Anty ta ce to in dai har haka gaskiya Meenatu aiki ja yasamay ki sosai wallahi, Don yanzu tunda ba imani ne da ita ba zata ce duk yadda zatayi taga cewa yai maki wulakanci zata yi, Don haka sai ki kara dagewa gurin addu,oin dakuma sadaka akan duk abinda ta dauko ya koma mata, Yanzu dai kinga kina da ciki babu zance amfani da kayan mata, Musaman na cusawa duk da nasan baki yin amfani dana cushe cushe dama, To amma shi wanan hayakin kanunfari ki dakartar da yin shi don Wallahi idan har mace nada ciki tai hayaki a gaban ta zubewa yakeyi tayi bari, Don haka kada ki fara kice zakiyi yi shi yanzu babban abinda zakiyi tunda kina a haka shine ki yawaita shan kayan sa ni ima, kawai, Da kuma dabarun gado sai ki sanyadda zaki kama mijin ko a wanan fannin, Don zata tafi ta kara jin huduban shedan gurin aminan ta na banza fiye da da, Don haka wallahi duk mace keda kishiya irin haka ko da tafiya tayi sai kiyi kokari kafin ta dawo kema ki kara naki fannin, Nace Anty aikuwa na gode wallahi tace maza ki maida kaimi gurin kara jawo mijinki a jikin ki, Nace insha Allahu Anty zan gyara don a gaskiya banyi dabaran yin haka ban sam, Tace aiko zaki kirani da kanki kisheda min idan har ta dawo, din, Tace na fada maki harda kwalliya yana sa namiji kara susucewa don wallahi mazan wanan zamanin sun banbanta da mazan da can Don mazan yanzu zakiga ko mata biyu gare su idan guda bata da karfin yar uwa sai kiga hankalin su ya koma ga wace keda shi, Mai kaya tab ga daki da kuma kayan sawa itace tauraruwan gida agare su,, Nace wallahi anty wanan maganan naki haka yake ba wai ba, don tun ina gida nake ganin haka ga mazajen garin mu,,, Munyi sallama ba don munso ba saboda Uncle danaji muryan shi ya shigo wurin anty ****** ********** ****** Ido a rufe Salawatu ta isa gidan Lubuna, wace ke kokarin shirin fita gurin aiki, Da mamaki tabi salawatu wace ta wuce direct saman kujera ta zaune rai a bace , Tsaya tayi tana kallon aminiyar nata duk da tasancewa ba lafiya ya fito da ita gida ba da wanan safe haka, Kuka Salawatu keyi riris kamar karamar yarinya, kamar ranta zaifita, A hankali Lubuna ta taka zuwa gare ta ta dafa ta cikin tausayawa tace, Wai may ke faruwa ne haka Salawa ni baki fada min abinda ya faru ba kin barni a duhu haka Cikin dan tsagaita kuka tace Lubuna Oga ya wulakantani ya cuceni don ya ci min mutunci agaban kowa nagidan Wani irin takaici Lubuna taji tai tsaye tana ma Salawa wani irin kallo, Tace gaskiya Salawa ban san irin ki ba wallahi shin Oga Abubakar ne namiji kadai a duniyan nan, ? Karki manta ko yau ya sake ki zaki samu masoya da yawa to may zai saki dinga wahalas da rayuwan ki akan shi haka wai, Bafa kwantai kikayi ba Salawa, kece dai da irin nacin ki kika lake masa, Har yana jin dadin wulakan ta ki yadda ran shi ya so a gaban kowa, Auren sa fa ba dole bane idan zaki rufawa kan ki asiri ki rabu dashi kirufawa kanki, Ki gwada mashi cewa kema fa din mace ce mai aji sosai, Kai ta daga tare da kallon Lubuna tace, ke ma kin san cewa ina son Oga ba zan iya ba sam, don shine kadai zai iya hakkuri dani yadda nake so, Lubuna ta tsuwa Salawa idanu tana kallon ta acikin takaici, Can tace saboda wana yarinyan ce again ko yai maki wani abu, Tace wallahi kanan kin sani fa don tane yai min cin fuska tun a daren jiya yafara, Don nace masa ina son cin shawarma, nako wani irin piza ne sai ita ma tace wai ya sayo mata Ice cream da fresh Fruit's , Bayan yadawo naga bai sayo min ba maimakon nida ce mai ina so ya fara zuwa guri na kuma fa nice da duty a ranan sai kawai ya nufi gurin ta dakin ra ya kai mata nata sakon, Da naji shiru shine na bishi tundaga can muka fara fada dashi wai don maye bazan jira shi har yazo ba,, Cikin takaici Lubuna tace you see akan karamar yarinya kina ganin wulakanci, haka, Yanzu dai tunda har ya kai ga haka ai sai ki kara zage damtsen ki, Don dama matan hausawa dinan kina ganin su haka wallahi is not easy kafi karfin su , Mistake dina shine da ban bari sai jima da fitaba sai kawai na samay ta kitchen daniyar inci mata mutunci sosai ashe yana gida bai fita ba, Yaji irin yadda na dinga zagin iyayyen su da kakan su wanda ya bashi auren yar iskan yarinyar, Yanzu dai dakata kiji inji Lubuna wace ke kokarin kawai, zaune gefen hannun kujeran da take a zaune, Tace yanzu fa dole ne sai mun mike tsaye so that we should rideout that foolish girl away, Salawatu ta ce hmm kin dai sai koda yaushe ko nawa nake kashewa akan irin hakan amma abin yaki, Murmushi Lubuna tati tace Salawatu ke nan ai yanzu tunda har kina son shi haka dole ne sai mun dage sosai don mu kwata maki shi, So kada ki damu ki dan bani time kadan please akwai inda zan tafi maki, Sai dai yanzu dole ne mu samu mu dan lalabashi ki koma dakin ki, Salawatace bakiji may yace bane cewa fa yayi sai natafi har garin su naba wanan witch din tsohon hakkuri, Da wani irin karfi Lubuna tace WHAT ? May yake nufi da hakan impossible, hakan ma ba zai yuyuba gaskiya,, Tace dole ne mu samu mutane anan wa yanda yake tare da su , subashi hakkuri gaskiya amma idan yace wai sai kin tafi can ai bai kyauta muna ba, Kuma wallahi yan uwan shi zasuyi hating naki ne sosai har ma yaran ki idan kin aihu dashi, Wani irin ajiyan zuciya ne Salawatu tayi tare da ce o,o wallahi Lubuna nayi hating din wanan yariyan sosai ,,, ****** ********* ****** Tun lokacin da wanan abin yafaru yaya Abubakar yake jin wani irin zafin Salawatu a ran shi har yake ji gara kawai ya sallamay ta tafita daga rayuwan shi don shi gaskiya bazai iya zama da macen da ke zagin iyayyen shi ba haka, Yayi nadama sosai ga hanashi da malam tsoho yayi amma ya dage akan sai yayi, Yanzu gashi baida kwanciyan hankali ko kadan da ga gare ta, duk ta hana gidan shi shakat, Yasan cewa babu wanda zai tunkara da wanan zancen , dole ya daukan wakanshi mataki akan fitinar ta, Driving yakeyi amma hankalin shi tankar baya a jikin shi a lokacin, Wayan shi tai kara sai dai bakuwar noba ce ya gani don haka ya dauka da sallama, Saidai murya mace ce yaji bayan sun gaisa tafara bashi hakkuri a kan case din su da Salawatu, Dif ya katse layin tare da sake guntun tsuki, yana cewa a fili rubbish , Yashigo gida a gajiye ya nayin tafiyan shi mutum zai gani ya fahinci hakan, Muna zaune gaba dayan mu a falo muna kallon wani season film na hausa, Jin shigowan shi yasa gaba dayan mu muka,waiga don ganin mai shigowa, A irin yadda ya samay mu zaune a falon har Ramatu mai aiki yasa shi jin dadi, Duk da dai ba wai fira mukeyi ba amma yanayin zaman mu ya nuna kwanciyan hankali, Mikewa nayi daga inda nake zaune, don zuwa gurin shi in karbi case din shi, Ya zuba min ido daga inda yake a tsaye har lokacin da na iso gare shi, Sannu da zuwa nai masa tare da dan rusunnawa kadan, Murmushi yasaki tare da sauke a jiyan zuciya yace Ya gida Meenatu, Alhamdullahi, Daga gurin da Anty Sadiya take a zaune ta mashi sannu da zuwa, A daya daga cikin kujerun falon ya zauna yana mai cewa wassh Allah na duk na gaji wallahi, Ina saukowa da part din shi nahango shi zaune afalo tare dasu Anty don haka na shiga kitchen, na dauko mashi ruwa, a gora tare da dora cup a ture din, Ina tafe cikin bakar jallabiya mai fitar da sharp, din mace Zakace ko wata yar larabawa ce, rigan yasa ina tafiya kamar da gaiyya nake rausaya , A gaban shi na aje ruwa a saman stol din dake gefen shi, Zan dauki ruwan da nufin in tsiyaya mashi a cup yace No barshi kawai kawo goran, Nayi saurin dago kaina na kalle shi da mamaki nace abar cup din kuma, Ya daga min kai kawai alamar eh, Daga haka ya dauka ya kafa goran a bakinshi bai cire ba saida ya kwankwade, shi gaba daya san nan ya aje goran a saman tire din yace min ya gode tare da dan lumshe idon shi ya koma saman kujeran ya zauna,, Nadauki turen da cup na mayar kitchen na wurga gora a dustbin, Ramatu tamike a hankali don tabar falon saboda ganin yaya Abubakar azaune, Yace No dawo kawai ki zauna abinki zau hau samane ni, Daga gurin da Sadiya take a zaune take cewa, maganin ta na sha ya kusa karewa fa, Yace ok zan tura Baba Wadda da Hamza gobe insha Allahu su karbo maki, Daga haka ya mike zuwa sama yana mai rike karfen da akai matagalin steps din dashi, Bayan shi nabi inda muka hau steps din a tare dashi don a tare muka shiga dakin, Daga gurin da Anty Sadiya take tabimu da kallon tare da sauke ido da sauri tana mai tabe baki, Ramatu na gani haka tai saurin kawar da kanta daga kallon ta ta ci gaba da kallon tv abinta, Amma can kasan zuciyar ta mamaki takeyi na yadda nake ma Anty halarci amma akwai burboshin kishina a zuciyar ta, Muna shiga daki na riko Yaya Abubakar tabayan shi na rungumo shi, tare da sauke ajiyan zuciya, Naji ya sauke ajiyan zuciya again akarona barkatai kenan tun shigowar shi,, Hankali cikin wani irin murya nace, Yaya Abubakar ka yi hakkuri damu please kasan mata sai hakkuri, Yaya yadan yi wani jim kamar yana tunane, sai naji ya juyo dani ta yadda zamu fuskanci juna, da shi, Kai minkiss yayi a goshi yana cewa Meenatu bana son fitina arayuwa na sam wallahi, Nakara dan narkar da murya na nace yaya kayi hakkuri don Allah ka yafe muna please, Yasa dan ya tsanshi a saman lebbana ya ce Shiiii alaman inyi shiru kawai, Yace gaba dayan ku nasan halaiyan kowan ku don haka nasan abinda nakeyi, Ina judge din kowa akan laifin shine, bazan yarda da yawan fitina ba agida na, sam, Azuciya na ce ashe zancen Anty Amarya gaskiya da tace koda namiji baya gida ya kan fahinci halaiya iyalin sa daya bayan daya, A hankali na ke kokarin zamay jikina daga rikon da yai min ina cewa barin hada maka ruwan wanka , Ya ce no ki barshi idan natashi zan hada da kaina, Ya shiga shinshinan wuyana har zuwa wasu part na jikina yayin da na lumshe idon cikin wani irin tsiga, yarrrr da na ji, Kokarin juyawa na keyi don barin dakin, naji ya riko min hannuwa , Najuyo muka hada ido naga idanuwan shi sun kade sunyi jawur, Nai saurin kauda idona daga gareshi sai naji yana rada min a hankali haba, Meenat, Ya kuma zaki wuce ki barni bayan nasan cewa kinzo ki ga farin ciki na, Na dan sunkayar da kaina kasa cikin jin nauyin shi nace bazan tafi bane girkine sa ban sauke ba nake son zuwa na sauke kada ya kone, Na san ba dai ya yarda bane, just kawai yabarni ne in fita kawai, ****** ********** ****** Salawatu da Lubuna agaban malamin su a zaune, Lubuna ce bayan sun gaisa da malamin nata take cewa, Boka ko malam mun zone gurin ka dama wanan kawar tawace ke da dan matsala da mijin ta shine nace muzo gurin ka, da ita ka duba mata, Don Allah ina son ka taimaka muna ai mata aiki mai zafi wanda zai girgiza abokiyar zamab nata. Boka ko malam yai murmushi yana mai gyara zaman shi tare da duban shi yana cewa, Yanzu may kike so ai mata a rabata da gidan ko a haukatata ko a barta a dambalata kawai, Salawtu tace ai matsalan shine, zuri,an su guda mana,ana gidan su guda don iyayyen su gudane, Amma in akwai yadda zaa ayi na mallakeshi ni kadai zan so hakan gaskiya duk su sauran biyu ayi waje da su, Murmushi Boka ko malam yayi yana cewa wanan ai ba wani babban aiki bane, Nan yashiga yin irin abinsu na bokaye sai da yadauki dan lokaci mai tsawo zuwa can ya dan dago kai ya kalle ta, Yace gaskiya akwai babban al, mai girma agidan ku, Don akwai abu akasa zube yanzu haka wanda ba wai lalai kusan da zancen ba a halin yanzu, Amma yanzu bari muyi binda ya kawo ki kawai saurin idan bukatan su ya taso zaki dawo, Ga jahilci irin na Salaqatu sam bata fahinci maganar mutumi saboda idon ta yarufe ita dai bukatar ta shine taga an fitar da Meena da Sadiya agidan, Yace amma dai ita wanan yariyar daga cikin su akwai ta da babban al,amari bawai lalaine kiga yadda kike bukata ba gaba daya, Lubuna tace kawai Boka malam kafita batun ko ma wacece kai mata aiki akan maigidan ta yadda ba wata agaban ta sai ita kadai kawai, Salawa da ke daga gefe tace gaskiya hakana ne Boka, Ni agaskiya idan son samu ne ai masu duk abinda ya dace da kowan su, Nan suka zube mai kudade masu yawa suka mike suna zabga godiya , Shi kuma yai masu alkawari tare da basu time, Salawatu taji dadin zuwa gurin wanan mutumin don har sai take ganin kamar ai har aiki yaci ko,, ****** ********** ****** Nagama shiri inda ban wani tsaya yau bata lokaci ba don nasan basai Yaya ya sauko ba, Yau ma kamar kullun don sai da na tabbatar da cewa na fitar da duk wani damuwa daga zuciyar Yaya Abubakar wanda sai faman ajiyan zuciya yake saukewa a hankali daga gefena,, Kamar wace aka sakowa wani irin amai nan na mike da sauri na hari hanyar bayi yabi ni da kallo acikin maki sai na rufo kofa don kada yaya yajini, Ganin na rufe kofa yashi sauke ajiyan zuciya don sai yake zaton ai toilet zan yi, Nafito duk jikina babu karfi yayin da zuciyana ke gaskanta zance Anty Amarya, Watau cikina yana ajiki a har yanzu bai fitaba kenan abinda yasani kai hannuna nashafa cikin a hankali tare da dan lumshe idona, Addu,anayi tare da neman tsari daga duk wani sheri , Hannun yaya Abubakar naji a saman marana yana dan shafawa a hankali ya na cewa, May kikaci cikin ki ya rude nasauke ajiyan zuciya nace kila fruits din da nake shane,, ****** ********** ****** Baba Wadda da Hamza sun isa gurin karban magani a nan ne mutumin ke cewa su fadawa yaya cewa sai yazo don fa akwai aiki a gaban shi sosai,, Bayan dawowan su basu tsaya komai ba suka fara fada mashi sakon mutumin, Bai samu zuwa a ranan ba sai washe gari ya tafi nan malamin yai masa bayani akan cewa akwai matsalonlin da zasu taso amma sai ya bashi addu a da sadaka da zaiyi don kaucewa fitana, Suna dawowa mijin Fattu ya fara yin yadda malamin nan bagware ya umurci suyi don tsari agidan, Nan kuma bayan ya shigo dakin shi yakira malam tsoho ya sheda mashi duk abinda wanan bagwaren ya fada mashi, Malam ya kwantar mashi da hankali ta hanya nuna mashi cewa, ba wai lalaine abin ya zama gaskiya ba kawsi da yai sadaka don riga kafin masifu masu taso, ZEEE MAKAWA YELWA