#LubnaSufyan ✨ #WomenOfWords #09035723778 (WhatsApp) Littafin nan na kudine akan #1k kacal, zaizo a manhajar Telegram ne kawai 20/06/2025 In Shaa Allaah, bayan mun kammala shafukan dandano. Zaku iya biya ta: 9035723778 Opay, Lubabatu Sufyan. NAGODE. * LABULE...Asirin mai daki 1 "Wacece Maryam Sa'id?" Tana aji uku ne taci karo da wannan tambayar a cikin slam book da ake ta zagayawa dashi tsakanin 'yan ajin, haka suka dinga kallon juna ita da littafin nan,  saboda ita dai tun asali ba gwanar bada labari bace ba, ko film ne ta kalla in kace ta baka labarin abinda ya faru saita rasa ta inda zata fara, akwai lokacin da suke kallon wani indian series mai suna "saloni ka safar", haka suke binshi kafa da kafa, in babu wuta za'a kunna generator, kamar wanda akayiwa asiri. Wani episode mai zafi akayi, duk basa nan sun tafi wajen sunan matar Khalifa da ita ba'aje da itaba saboda tana karambau, haka suka zagayeta suna jiran tayi musu bayani, data fara kamo tsakiya tana jonawa da farko, haka Shukra taja tsaki "Wallahi da gangan ma mukayi asarar lokacinmu muna tambayarki Maryam, ke an taba kulla abin kirki dake daman? In dai labaranki mutum zai jira ya hadu da takaici" Kuma tasan da gaske ne, tunda a ranar ta rasa ta inda zata fara amsa wannan tambayar, to wacece ita ta wacce fuska? Halaye? Tarihi? Halaye dai ai ba masu yawa bane ba, ba kuma boyayyu bane, tunda kowa za'a tambaya tashin farko zaice ita din mafadaciya ce ta kwatance, dan ko a lokacin da take primary ba'a cacar baki da ita, kafin ka numfasa ta sauke maka mari in yaso a kacame da dambe, wanda yafi wani karfi ya kwaci kanshi, tunda har wanda suka wuceta aji saida suka kiyayeta, haka ake cewa yanda take lange-lange kamar za'a iya kaita kasa, kashi dayane da ita. Haka 'yan gidansu in suka fadi wannan zasu kara da wani hali nata guda daya, kishi, tsananin kishin da har Hajjarsu take roka mata sauki akanshi. Dan kishine irin wanda bata kaunar taga wani ya rabi ko da 'yan uwantane, dan akansu nema Hajjar ta fara gane kishin da Maryam take dashi har takan ce "Allaah Ya rabaki da wannan kishin Maryam, 'yan uwanki ma kenan, inaga mijinki?" Kawayen Khairi kuwa da take ganin suna kusan sa'anni da ita sun sha wahala a wajenta, musamman na cikin unguwarsu, balle kuma a makaranta, baka isa a fito break ta ganku kuna cin abinci da ita ba, saita turmusaka cikin kasa, gashi ko taron dangi akayi mata sai anyi da gaske ake iya kaita kasa, shisa duk suka hakura da kawancen da Khairi, idan Hajja ta daketa kan abinda tayi kuwa saita je ta rama akansu, tunda halinta na uku taurin kaine, inta kafe ko kasheta za'ayi ba zata daina abinda takeyi ba, shisa ma Alhajinsu ya hana dukanta saiya kama dole "Kar yarinyar nan ta kangare muku, yara irinsu ja ajiki, soyayya da fahimta suke so ba kyara ba, ku fahimci abinda bataso din, idan abune da zai iya cutar da ita a gaba sai ayi kokarin fahimtar da ita a hankali..." Hakan kuwa aka cigaba da tafiya, amman kuma ai tana ganin yanda take kara girma tsoron halayen nata na cika idanuwan Hajja, amman kuma ai kamar kowa ba zata rasa halaye nagari bako? Kuma tana da yakinin sune suka rinjayi wanda suke hadata fada da kowa na gidan suka sakata shiga ransu sosai, wani abu da take alfahari dashi a ko ina, tunda yanzun zuciyar Maryam babu kowa a cikinta banda iyaye da 'yan uwa. Ita kawaye basu dameta ba, kawai 'yan uwanta su hadu su sota fiye da kowa, ko da wani zai rabesu tofa kar su damu dashi yanda suka damu da ita, kai gabaki dayama su din kar wani ya nuna yana sonsu fiye da ita, shine matsalarta. To duk ya zata takaita wannan tunda a hakama kadan ne a cikin halayenta ta sakasu a wannan slum book din da aka bata shafuka biyu kacal a ciki, idan kuma asali ake nufi ta ina zata fara? Ai asalinta ba zai cika batare da iyayenta ba, tushensu shine nata, babu ta inda zata bada tarihinta bata hada dasu a ciki ba. Alhaji Sa'id shine mahaifinta, kuma dan asalin kauyen Matazu ne ta jihar Katsina, su tara mahaifiyarsu ta haifa, amman su biyu suka rayu, dan tanayin wabi ne, sauran yaran duk rasuwa sukeyi kafin ayi suna, har a lokacin abinka da kauye akace watakila ta zagi mayya ne da take ganiyar kuruciya, shine take bibiyarta, wasu kuma suce ko asiri ne, kowa da abinda yake fada. Sa'id ne ya fara tsayawa, bayanshi ta kara guda biyu sannan Murtala, dagashi kuma sai haihuwar ta tsaya mata. Masu karamin karfine matuka, tunda gonar gado ce mahaifinsu da gabaki daya danginshi ake nomawa, a ciki ake duk wata hidima ta yau da kullum, annobar amai da gudawa da ta shiga garin a wata shekara, ana tsananin zafi, itace tayi ajalin mahaifinsu Sa'idu, inda mahaifiyarsu tabi shi kwanaki sha biyu tsakani, sai rikonsu ya koma hannun Kanin mahaifinsu Ya'u, shikuma duk karamin karfinshi mata hudune dashi, yara maza duk wanda yakai shekara biyar sai a watsa shi almajiranci, dan haka aka hada da Sa'idu da yake da shekara bakwai lokacin, da kuma Murtala da bai karasa cika hudu ba tunda shi kanshi Ya'u yasan cikin matanshi babu wadda zata dauki wahalar Murtalan. Da aka tashi kuma duk kukan da suka dingayi sai aka rarrabasu, shi Sa'idu akayi Zaria dashi, Murtala kuma garin Kano. Da yake Sa'id irin yaran nan ne masu shiga rai, yana da wani sanyi a tare dashi idan ka kalle shi, baiyi wahalar abokai da suke fita yawon bara tare ba, bai kuma rufa wata uku ba ya zamana ko shi kadai ma saiya fita yawonshi, tunda sunyi sa'a Malamin nasu nagari ne, banda karatu baya sakasu irin aikace-aikacen gona da wasu Malaman sukeyi. A irin yawon ne yaje wani gida a cikin unguwar samaru yawon bara, da aka bashi abinci, yaga shinkafa da miya harda salak, rabon da yaci abinci ya koshi irin ranar tun iyayenshi na da rai, yana gamawa saiya rabe kasan wata bishiya da take kofar gidan ya kwanta. Bacci ya kwashe shi, wani bacci da ya zame masa silar alkhairai masu tarin yawa, dan a wannan kwanciyar da yayi ne maigidan ya dawo ya same shi, kuma kankantarshi saita bashi tausayi matuka, ya shiga gidan nashi dashi, ya cewa matarshi kullum zai dinga zuwa ana bashi abinci, batayi musu ba ta amsa. Safe, rana, dare haka Sa'id yake zuwa karbar abinci, ya taba zuwa ya samu ganyayyaki duk sun zubo a harabar gidan yace ta bashi tsintsiya ya share, da taki tunda almajirin da yake zuwa yanayi mata wannan aikin a lokacin Babba ne, zazzabi yake fama dashi kwana biyu. Sai dai nacin da Sa'id ya saka saita bashi, tayi mamakin ganin ya share gidan kwal, sai gashi yana dan yi mata kananun aikace-aikace, sai aiken da ba'a rasa ba, a hakan kuma yayi sabo da dan gidan Mustafa, har iyayen saida suka dinga mamaki, tunda Mustafa kowa yasan kamar dage yake wajen fada, shisa duk ya kore abokan harna cikin unguwa, amman a ranakun da babu islamiyya, alhamis da juma'a har sautin dariyarshi zaka dinga jiyowa suna labari da Sa'id, akace mai da wawa, sannan su Alhaji Usman mutanen kirkine kwarai, irin kirkin da baya wahalar samu a zamaninsu, kirkin nan na maida dan wani naka, sai son inganta rayuwar Sa'id ta shiga rayukansu, da kanshi ya taka har makarantarsu Sa'id sukayi magana da Malaminshi, ya dauke shi ya sakashi a makarantar boko. Wannan shine mafarin samun ingantacciyar rayuwa. Sa'id, amman duk da haka yasan iyakarshi, yanda duk suke janshi a jiki yana kama kanshi na sanin fa har abada shidin almajirin gidansu ne, ya samu karatu har matakin NCE inda baisha wahalar samun aikin koyarwa ba a lokacin, sai dai ya samu aikin ne a garin Kaduna, shikuma Mustafa da yake yana da wata irin kwanya, kuma gurbin karatu a Ahmadu Bello ya samu, sai gashi ya samu scholarship zuwa kasar Ingila inda ya dora karatunshi, yayi dabarar yin duk wani aiki da ya samu yana adana kudadenshi, yana da burika masu yawan gaske, babban burinshi shine zama hamshakin mai kudi. Lokacin daya dawo har Sa'id yayi aure, ya auri Asma'u da kannenta dalibai ne a makarantar da yake koyarwa, a lokacin ita tana makarantar kwana ne aji uku, kuma sun taka har Matazu domin tabbatar da gaskiyar asalin Sa'id kafin su bashi aurenta. Haka dan uwanshi Murtala bayan gwagwarmaya daya sha, tunda shi karancin shekaru yasa kamar ba zai rayu ba a almajirancin da aka kaishi, ya fada harkar garuwa, ya samu nasibi a cikinta, dan da wannan sana'ar yayi aure, yana kama haya anan cikin kwaryar Kano, kafin daga baya ya bude gidan ruwan shi, inda ake dandazon dibar ruwa duk rana. Yanzun haka yaranshi biyar ne da matarshi Furaira data saka yaran suna kiranta da Mummy, dan kuwa macece da batayi ilimin boko ba, na addinin ma an samu na bautawa Ubangiji, amman tana matukar son harkar gayu, kullum gidanta tsaf zaka ganshi, haka ma yaranta guda biyar ne kacal, tunda taji labarin tsarin iyali ta karbe shi da hannu bibbiyu, so takeyi su samu ingantacciyar rayuwa irin wadda ta gani a tare da yaran Alhaji Sa'id lokacin da takai musu ziyara a garin Kaduna. Suyi ilimi na boko dana addini. Sunayensu ma itace take shigewa 'yan gayu tana adana duk sunan da yayi mata dadi, Asaad ta farayi, sannan Aminatu da taci sunan mahaifiyarta suna ce mata Minal, Ishaq, Hibba, sai Autarta da Murtala ya sakawa sunan mahaifiyarshi Zainab suke ce mata Khairi. Wannan sune iyalan Murtala kanin Alhaji Sa'id. A filin jirgi Mustafa ya hadu da Rumana da babban wanta, da kuma matarshi, tun daga kallon farko yaji cewar yaga abokiyar rayuwa, Kanuri ce, yar Maiduguri, baka kyakkyawa ta gaske. Duk da yaji dar saboda fuskantar da yayi na cewa 'yar masu kudi ce, haka dai yayi jarumtar karbar katin dan uwanta da yagansu tare. Kuma da yake akace matar mutum kabarinshi, bai samu wata matsala ba, saiga Bafullatanin usuli ya taka har Maiduguri neman aure,dan Mustafa farine kal, ko sumar kanshi ka kalla zaka san cewa bafulatani ne, iyayenshi tsatsonsu fulanin Yola ne. Anyi shagali dai-dai da zamanin, tunda bayan aiki daya samu a shekarar da aka bude gidan man NNPC, wato 1977, duk da baya fatan aiki a karkashin kowa, suka tare a garin Abuja. Ya fara binciken yanda zai kafa business dinshi na siyar da motoci da tun asali shine plan din da yake dashi. Da taimakon Allaah da kuma tsantsar naci irin na Mustafa ya kafa AU motors, inda daga baya ma ya ajiye aikin nashi da kudi suka fara zauna masa, kuma ya tattara ya baro garin Abuja ya dawo Kaduna ya kara kafa wani branch din na AU motors, yanzun haka yana da branches uku ne, Abuja, Kaduna, Kano, sai dai na Kadunan ma duk yafisu karfi. Jinkirin haihuwa suka samu shi da Rumana, wani abu daya saka iyayenshi matsa masa karin aure ganin irin dukiyar da yake ta tarawa babu magaji a fadarsu. 'Yar uwarshi ya aura Fadime, bayan tarin rikicin da suka sha da Rumana, dan macece ita mai izza da ji da kai, sannan tana matukar kaunarshi. A shekarar Fadime ta samu ciki, kuma saida tayi yara uku sannan Allaah Ya bawa Rumana ciki itama. A yanzun haka, Rumana na da suke kira Mami, na da yara uku ne, Munira, Anisa, sai Haris. Inda Fadime (Umma) take da guda bakwai, Aliya, Halima, Kubra, Shatu, Mukhtar, sai Ibrahim. Kuma Maryama da duk 'yan uwanta sunsan amintar da take tsakanin babansu Sa'id da kuma Mustafa, dan karin karfin arzikin Sa'id din kowa yasan sanadin Mustafa ne daya kara fadawa harkar noma, sai kuma ya zamana Sa'id din shine yake kula masa da wannan bangaren, in ba haka ba, da basu taso cikin rufin asirin da suke dashi ba, dan aikin koyarwar da yakeyi ba wani kudi bane da za'ace za'ayi hidimar yau da gobe a ciki har a adana wani abu. Dan rufin asirin da Sa'id din ya samu a lokacin, ya kuma karasa ginin daya daukeshi shekaru takwas yanayi, sai 'yan uwan da suka watsar dashi a baya suka dawo sunaji dashi, ciki kuwa harda Murtala da Sa'id din shine yake bibiyarshi sosai da zumuncin nasu ya jima da watsewa. Saima da akaji ya tafi aikin Hajji, bayan dawowarshi kuma Asma'u da suke kira da Hajja tun asali saboda Hajiyayye ake ce mata a gidansu da yake an haifeta ranar arfa, su sai suka takaita shi zuwa Hajja, sai dangi sukace dawa Allaah Ya hadasu ya dinga biya musu bukatu in ba Alhaji Sa'id ba. Su bakwai Asma'u ta haifa, Ahmad, Khalifa, AbdulKarim, Zahra, Yazid, Asiya sai auta Maryam. Amman tun tasowarsu kullum gidansu cikin jama'a yake, yaran dangi da sukazo hutu daga Matazu, wasu kuma na wajen Baba Murtala da sukazo daga Kano. A cikinsu kuwa wasu ma nan suka kwaso kayansu suka dawo da zama, su bakwai sai suka samu karin mutum biyar, Maimunatu, Sagir, Adnan, Saifullahi, da kuma Khairiyya da 'yar gidan Baba Murtala ce, kuma shekara daya da rabi ta bawa Maryam. Hajja duk ta hadasu ta rike kamar daga cikinta suka fito, tun tana samun matsala da wasu a cikinsu har suka warware suka saki jiki suna mata rikon uwa kamar yanda takeyi musu na 'ya'ya. A irin amincin da yake tsakanin Alhaji Sa'id da kuma Alhaji Mustafa da Zahra ce ta makala masa Baban Tudun Wada, saboda acan unguwar yayi katafaren gidanshi a garin Kaduna, sunan saiya bishi. Ya kamata ace matansu ma suna wannan amincin, amman babu, saboda Hajiya Rumana bata bada wannan damar ba, musamman da taji labarin wanene Alhaji Sa'id a bakin 'Yan gidansu Alhaji Mustafa, a raine take kallonshi, saboda har a zuciyarta ta kasa aminta dashi a matsayin aminin mijinta bayan yaronshi ya kamata ace ya zama. A karkashin shifa yake ci yana sha. Ita kuwa a irin izzarta me zaija mata kawance da matarshi. Shisa itama Hajjan ta kama kanta, duk kirki da hakurinta tana da gudun wulakanci, sannan daga ita har mijinta dabi'ar cusa kai ba halayyarsu bace ba, yanda duk Alhaji Mustafa yaso ya juya Hajiya Rumana akan sha'anin gidan aminin nashi dole ya gaji ya kyaleta, garama Fadime ita duk wata hidima da zata taso a gidan Alhaji Sa'id da ita ake wuni anayi har a kammala, duk da Hajja ta girmeta saita zame mata kamar wata Yayaa da bata da ita a kusa tunda duk yan uwanta suna can Yola. Wannan zumunci nasu yayiwa Hajiya Rumana tsaye a wuya yana kara saka mata tsanar duk wani abu daya danganci Alhaji Sa'id da ahalinshi. A lokacin bata hango wata alaka zata shiga tsakaninta da iyalan Alhaji Sa'id data wuce tunaninta ba. In su Maryam sunje gidan Alhaji Mustafa, in zasu karaci buga bangaren Hajiya Rumana dansu gaisheta, ba zata taba bude musu kofa ba, daga bayama sai suka daina zuwa, suyi zamansu bangaren Fadime, har su gama abinda ya kaisu a mayar dasu gida. Wannan shine tarihin da Maryama zatace nata, tunda ya hada duk wani abu kama daga asalinta, da kuma duk wasu mutane masu muhimmanci da suke da alaka ta kusa data nesa da ita. Maryam taso ace ta samu Kakanninta, tunda a halin yanzun Malam Ya'u kawun mahaifinta ya jima da rasuwa, sai matarshi Hajiya Inna, kuma sosai Maryam takejin dadin zama a wajenta duk idan sukaje Matazu, saboda labaran da take basu masu abin dariya da ban al'ajabi. Tana aji uku na a makarnatar Sakandire Hajiya Inna ta rasu, kusan tafi kowa jin mutuwar 'yar tsohuwar a gidansu, ta jima tana kuka, har saida kowa ya dinga mamakinta. Kuma kusan Maryam zatace a wannan lokacin ne mutuwar ta bude mata ido, tasa ta fara fahimtar rayuwar gabaki daya dama abinda ta kunsa. Dan a lokacin ana gab da bikin Adda Maimunatu ne, tunda ita taki karatun, dakyar tayi diploma, tunda ta hadu da Yasir dashi sojane, ta rufe idonta, sonshi takeyi har bata iya boyewa a gaban kowa, haka Maryam zata dinga lekensu idan yazo zance, labarin Hajiya Inna na fado mata. Wani labari da yaki barinta har yau, lokacin tana aji daya a sakandire Hajiya Innar ta basu shi, amman ko yau ta rufe idanuwanta tar muryar Hajiyar ke dawo mata "Ai mu da Allaah Yayiwa tsahon rai muna ganin abinda ya ishemu, mu lokacinmu ai sai kayi sa'a ne ma za'a fada maka anyi maka miji, koni nan bansan kalar Alhaji ba sai bayan an daura mana aure, saboda yanda iyayenmu suka san cewa sun isa damu, ba zamu koyi numfashi mai karfi ba balle muyi musu kan hukuncin da suka yanke mana" Da yake maganar ta zauna mata, duk da karancin shekarunta haka ta dinga juya zancen duk lokacin da zataji an saka rana ko kuma anyi aure, tana kara hankali tana mamakin yanda za'a daura maka aure da mutumin da baka taba gani ba Ta ina zaku fara zaman? Ya zakuyi a haduwar farko? Me zakace masa? Shi ma kuma fa? Idan ita akayiwa irin auren nan ya zatayi To wai idanma aka daura sai ta ganshi baki kato irin mazan da basa burgeta sai yaya kenan? Dan ita duk a cikin abubuwan data dinga tunani, mafi muninsu shine ace namijin ya kasance baki, haka kawai bakaken maza basa burgeta, watakila dan mazan farko-farko da ta farajin sun kwanta mata a rai farare ne, fararen ma indiyawa, tunda gidansu mayun kallon indian films dinne harma da series. Duk sanda zata ga manyan matan gidan na zance in taga saurayin baki saita tabe baki, inta ganshi fari kuwa ta dinga fara'a kenan kamar wajenta akazo. Shisa a yau da ta hangi Adda Maimunatu da Yasir sai take jin inda ace yafi haka haske da anyi namiji mai kyau, da Addanta ta more miji, to wanda ya auri fari ai shiya more, ko wajen hotunan biki saima sunfi haskawa. Ace dai farine kamar Hamma Ishaq din Baba Murtala, murmushi ya kwacewa Maryama, duka shekara daya da wani abu kenan da Ishaq din ya samu gurbin karatu a Zaria, taji ance Injiniya zai zama, da yake ba zata tuna fuskarshi ba sosai, Khairi dai bata cika hasken fata ba, kusan ita Maryam dinma ta fita haske, sai gashi ya biyo 'yan gidan da suke ABU din suma sunzo hutun karshen mako, Ishaq farine har wani dorawa-dorawa yakeyi, da gashin kanshi kamar ya kara tirawa, dogone amman bashi da jiki, 'yan gidansu sunce wai Khairi tafishi kyau, duk gidan Baba Murtala ma babu wanda aka tarawa muni irin Ishaq, saboda shi guntun hanci gare shi, sai wasu jajayen labba shi ba bature ba. Haka ta dinga kallonsu kamar basu san abinda sukeyi ba. Ta ina za'a hada Khairi da Hamma Ishaq? Anya a wankan farko na jarirantaka an wanke musu idanuwansu da kyau kuwa? To ai a idanuwan Maryam duk wanda yazo a fari, musamman namiji, to cikin kaso dari na kyau dai ya tafi da tis'in, sauran goman kuwa ai ba wani abu bane ba, ballantana shifa ga gayu, ga kamshi, ga labbanshi irin na indiyawan da take gani a fina-finai. A zuwanshi na karshe gidansu, wajen satar kallonshi duk ana zaune a falo, ta dibo kunun aya, tayi tuntube tana shekawa Adnan shi a saman kai, ya kuwa kai mata wani duka da Ishaq ya tare mata yana fadin "Ya za'ayi ka kaiwa mace irin wannan dukan Adnan? Ai sai kaji mata ciwo" Shikuma Adnan din yaja tsaki yana mikewa, baiko ce musu komai ba "Dawo nan kinji kanwata..." Ta kalle shi, yanda ya ajiye kalmar kanwata din na zauna mata a wasu sassa na jikinta, shine abinda ya kashe mata jiki ya hanata mayarwa da Adnan maganar da tasan babu abinda zata janyo mata a wajenshi sai duka, a wannan ranar inda ace Maryam tasan cikakkiyar ma'anar kalmar da bature yake kira da "crush" da tace abinda ya faru da ita kenan akan Ishaq Ya samu wani waje da yafi ko'ina laushi a zuciyarta yayi zaune batare dama ya sani ba... #LubnaSufyan ✨ #WomenOfWords #09035723778 (WhatsApp) Littafin nan na kudine akan #1k kacal, zaizo a manhajar Telegram ne kawai 20/06/2025 In Shaa Allaah, bayan mun kammala shafukan dandano. Zaku iya biya ta: 9035723778 Opay, Lubabatu Sufyan. NAGODE. * LABULE...Asirin mai daki 2 Yau Alhaji Sa'id yaje makarantar yaran ne ya biya musu kudi, wannan aikine da mazan gidan sukaso sauke masa tunda jimawa, amman yaki, har yau duk wani PTA da za'ayi, in ba uzuri na rashin lafiya ba da kanshi yake zuwa musu makaranta. Haka yakan ware wasu ranaku ya dauke su da safe ya sauke kowa a tashi motar, ko kuma yayi musu bazata ta hanyar zuwa ya daukosu, wani abu da baya gajiya da jin dadin yi, ko dan irin farin cikin da yake gani a fuskokin yaran nashi. Kowane da nagari baya bukatar dalilin da zaiso iyayenshi, da ace ana da bukatar wannan dalilin, Alhaji Sa'id zai kasance cikin iyayen da ba zasu taba gajiyawa ba. Tun yana makarantar yake ganin kiran Hajiya Rumana, yasan ba zai wuce kara ta kawo masa ba, a lokutta da dama har mamakinta yakeyi, yasan inda zata iya rabashi da Alhaji Mustafa, data jima da yin hakan, sannan kuma bashi da wata daraja da kima a idanuwanta, ko yaranta in dai zasu hadu haka suke gaishe dashi kamar an cusa musu tsumma a baki, da yake sunyi gadon dagawa da jin kai irin nata. Amman kuma duk randa Alhaji Mustafa ya murde mata, bata da wanda zata kira sai shi. Saida ya gama abinda yakeyi, niyyarshi ma saiya koma gida ya karya, amman yanda ta dinga jera masa kira bayan kira ya tabbatar matsalar babba ce, shisa ya daga, aikuwa kuka takeyi kamar anyi mutuwa, har saida gabanshi ya fadi, bai ma fahimci abinda take fada ba, ya daiji Haris ya kuma ji Mustafa, sai yace mata gashi nan zuwa gidan. Ya kuwa karya mota yana nufar hanyar Tudun Wada, da yake akwai 'yar tafiya, makarantar yaran na wajen Rabah Road. Yana isa, baima shigar da motarshi ciki ba, ya dai juyata yanda in yazo tafiya ba sai yayi hakan ba, kanshi tsaye bayan ya shiga gidan ya wuce bangaren Alhaji Mustafa, ya kwankwasa da sallama a bakinshi, da kanshi ya taso ya bude masa kofar yana dariya "Yanzun nake zancenka a raina fa" Cewar Alhaji Mustafa, sukayi musabaha, suna kara gaisawa kamar wadanda sukayi shekaru basu hadu da juna ba, kallo daya zakayi musu ka fuskanci irin shakuwar da take tsakaninsu "Yanzun dinma kararka aka kawomun" Alhaji Mustafa yaja tsaki mai karfi "Karma ka fara shiga maganar nan Sa'idu, na riga na rantse saiya koma inda ya fito, in taga ba zata zauna ba itama zata iya tattara nata kayan ta bishi" Ya karashe maganar yana haki saboda yanda ranshi ya kara baci lokaci daya "Azumi uku dai, ai bansanka da raki ba" Hararashi Alhaji Mustafa yayi "Bafa wasa nakeyi ba..." Ido ya dauka ya sakawa Hajiya Rumanan, daman jiranta yakeyi daga ita har Haris din. Tun lokacin da ya aureta ya fara gane halinta na jin kai da nuna isa, sannan da ace shi din namiji ne mai sanyi, ba karamin raini zatayi masa ba. Halinshi na kin daukar da yawa daga dabi'unta yasa ta dinga kokarin sauke kadan daga ciki, musamman akan danginshi da take ganin basu kai su rabesu ba. Duk da haka in sunzo din ba dadinta sukeji ba, akace shimfidar fuska ma wani abune, to harsu tafi in ba magana takeyi ba, babu wanda zaiga hakoranta. 'Yan uwanshi basu fara jin dadin kawo masa ziyara ba sai bayan daya kara aure, sai kuma ta tsiro da wani abu na kai masa korafi cewa yanzun duk wani nashi ya juya mata baya, basa ma sauka bangarenta saboda ya auro tasu, kuma suna ganin ita bata haihu ba, wani zubin ma kuka take sakashi a gaba ta dingayi, ai sunzo gidan taga sunayi mata dariya akan rashin haihuwarta, bai huta da wannan fitinar ba sai da ta samu cikin Munira, sai kuma bayan ta haihu ya zamana hankalinta kacokan ya koma kan yarinyar, kamar shi dinma bata da wani lokacinshi saina yarinyar, da yake yana samun duk wani abu da yake bukata a tare da Fadime sai bai wani damu ba. Gwarne tayi tsakanin Munira da Anisa, duka shekara daya da wata hudu ne tsakaninsu, har a danginta saida aka nuna a dauke mata Munirar sai taji da rainon Anisa, in yaso idan tayi kwari sai a dawo da ita, tace bata bukata duk zata iya hadasu tayi rainonsu. Sun fara samun matsala da ita ne akan yaran, lokacin Munira na da shekara biyar, ta dauki kofin shayin data gama sha tana bugawa a jikin TV, yana zaune sai yayi mata tsawa, yanda Hajiya Rumana ta karaso ta dauke yarinyar da ta fashe da kuka, idan wani ya hango daga nesa zaiyi zaton makami ne a hannun Alhaji Mustafa "Ya za'ayi kayiwa yarinya karama irin wannan tsawar? Ai saika firgitata" Kallon mamaki kawai ya dinga binta dashi a lokacin saboda yama rasa abinda zaice mata, a hankali kuma saiya kula da itafa akan yaran nan harshi bai isa ba, baisan abinda ya kamata dasu ba sai ita, kowanne irin hukuncine akansu in dai ba ita ta yanke ba to baiyi ba. Cikin danginta ma kafarta kafarsu, haka gidan iyayenshi, in dai ba tare da itaba, to yaran basa zuwa, yaran Fadime ma da yake tsoranta sukeji basa shiga bangarenta sam, saiya zamana tashin hankalin da Alhaji Mustafa ya dingayi akan ganin yaran sun shaku ya tashi a banza, shi dai ba wuni yakeyi dasu ba, wani zubinma sai yafi satika biyu baya garin. Sannan akan yaran Hajiya Rumana dai duk wata tufka da zaiyi yana barin gidan zatabi ta warware. Da ta haifi Haris kuma sai abin ya kara ninkuwa, saboda soyayyar da take nunawa yaron ya wuce yanda za'a misalta. Haka aka cigaba da rayuwar, ya rasa yanda zaiyi da ita akan yaran, ga abin yana damunshi sosai, ko yanda su Munira suke mu'amala da danginshi a darare kadai ya isa abin takaici a wajenshi. A hankali kuma ya yarda Hajiya Rumana na daga cikin kaddararshi ne da babu yanda zaiyi da ita, abinda ya faru gaban idonshi dai zai tsawatar, shisa babu ma wata shakuwa a tsakaninshi da yaran, da yawan lokutta in suka gaishe dashi duk sai su bar falon, musamman Haris da yafisu sangarta, sai rashin jituwarsu yafi yawa da Alhaji Mustafa, tunda su Munira in fada yayi musu zasuyi shiru, harma su bashi hakuri. Amman Haris sai yayi magana, sai yayi kokarin yin bayani ko dai ya fadi wani abin, duk zafin Alhaji Mustafa akan Haris ya fara dukan yaranshi, sukayi wata rigima da Hajiya Rumana har tayi yaji ta kwashi yaran ta tafi Maiduguri, rigima akayi sosai, tunda danginta sun goya mata bayane a fadan, dakyar Alhaji Sa'id yayi ruwa yayi tsaki ya shawo kan aminin nashi sannan aka samu dai-daito. Da yake a lokacin ma Haris din ya kammala primary dinshi, sai kawai ta nuna masa wata makarantar kwana ta kudi take so Haris din ya tafi, makaranta ce mai tsadar gaske da take a garin Kano. Da yaki amincewa dan yana ganin alamar kangara a tare da Haris din. Yana gudun idan yayi nisa da idanuwanshi abin zai iya fin haka, da taga alamar kamar yana neman yaki amincewa, ya tafi Abuja, ya dawo ya samu Haris baya gidan, taje da kanta tayi masa duk wani abu daya kamata ta kuma biya kudin. Suka sake wani rikicin kamar zai saketa, nan ma dai Alhaji Sa'id ta samu, ya lallaba mata shi, sai dai har kasan ranshi bayason wannan makarantar kwanan da aka kai Haris, tunda ga 'yan uwanshi nan a Kaduna suke karatunsu, Mukhtar da Haris din ya ba shekara biyu, alamu sun nuna ma lokaci daya zai hada da gama primary din da kuma haddar Al-Qur'ani. Kuma yawan misalin da Alhaji Mustafa yake yiwa Haris da Mukhtar idan yanayi masa fada ko yayi laifine abinda yasa Haris din baya kaunar ya bude ido yaga Mukhtar, saiya zamana in zai hadu dashi sau goma saiya kwade shi sau goma, ko da kuwa Alhaji Mustafa zai karyashi ne, Mukhtar dinma daya hangoshi yake neman maboya, babu jituwa ko kadan a tsakaninsu. Mukhtar bai samu salama ba sai bayan tafiyar Haris makarantar kwanan nan. Kuma duk wani tsoro da Alhaji Mustafa yake dashi akan nisan Haris shine yake faruwa acan makarantar. Tun satin da aka kaishi, maganar da Hausawa sukayi na sai hali yazo daya ake abota ta tabbata akan Haris, da yake aji dayane su dukansu sababbin dalibai ne, lokacin ake kokarin fahimtar juna. A satin ya hadu da, Idris, Sulaiman da Yakub, kuma sai aka hadasy daki daya, haka suka samu sukayi musayar gadaje da wasu a cikin dakin yanda suka koma makotaka da juna. Basu hada wata a makarantar ba duk wani Malami daya kwana ya tashi saida ya sansu, shugaban makaranta ya haddace fuskokinsu, suka kafa tarihin kasancewa 'yan aji daya da suka gagari seniors dinsu. Idan wani laifin suka aikata, makaranta bata da contact din kowa saina Hajiya Rumana, idan ma aka nemi ganin mahaifinshi sai tace baya kasar. Ita kuma ba fada take iya yiwa Haris din ba, duka yaran bakar fatarta suka biyo, gara Munira ita kai tsaye ba zaka kirata da baka ba, sannan fuskarta sak irin ta Alhaji Mustafa ce, hakama Anisa duk da bakinta dashi take kama, Haris ne duk yanda ake cewa ba'a gane kamannin jariri, a asibiti ma Nurses suka fara maganar yanda yake kama da ita. Hasken fatar da jarirai sukanyi Haris baiyi ba, da duhunshi ta haifoshi, kunnuwanshi bakikirin, aikuwa kafin ma ayi arba'in yayi baki, irin wannan duhun fatar Hajiya Rumana daya hadu da hutu yasa take wani irin kyalli, da yake tana da cikar gashin gira, sannan gashin kanta ma duk da bamai tsayi bane sosai a cike yake, ya kwanta luf har gaban goshinta, haka gashin idanuwanta ma, tana da irin kyawun da idan wasu manyan fashion houses din zasu ganta zasu kafa mata nacin zame musu model. Wannan kalar fatar Haris ya biyo, cikar gashin da kuma kyan daga kallon farko. Yanda idanuwanta suke haka nashi suke, kamar da ruwa a cikinsu, in yayi dariya zaka ga ta isa har cikinsu, haka idan ranshi ya baci zaka ga kyallin bacin ran nan a cikin idanuwanshi, yana da irin idanuwan nan na kalilan mutane, idanuwa masu tonon asiri, wanda zasu haska maka har kasan zuciyarshi inka natsu a cikinsu. Shisa ko yayi kokarin kama bakinshi sai su fada maka duk wata kalma da bai furta ba. Wani irin so Hajiya Rumana takeyi masa da ita kanta bata san iyakarshi ba. Sone daya makantar da ita daga ganin laifukanshi, a wajenta kome Haris zaiyi kuruciya ce, zai bari idan yayi hankali. A wannan bigiren ya kammala ajinshi uku, ya kuma shiga aji daya inda ya zabi bangaren Art, tunda bason karatun yakeyi ba, yama fara kokartawa ne tun wani zagi da aka hadu akayi musu a staff room. Wata Malama ta kirasu da "Dakikai" Kalmar nan tayi masa ciwo matuka, da yayiwa su Sulaiman magana kan ya kamata su fara maida hankali sai abin ya basu dariya, shi dai ya kyalesu ne tunda ba'a dole, ya dai fara canzawa ta bangaren karatun, shisa ya zabi Art din, a tunaninshi zaifi mishi sauki tunda akwai saukin lissafi a duka subjects din. Wannan shekarar itace tazo musu da sauyi daga shi har abokanshi, Idris duk yafisu girma, suna kiranshi da Barde, sai Yakub da soyayyar da yakeyiwa wani sanannen mawaki 2Pac yasa lakabinshi ya koma haka. Sulaiman daman ana kiranshi Lalaye ne tun suna aji daya. A lokacin Haris ne bashi da wani sunan banza. Lokacin da suka dawo hutun first term na aji hudu a Sakandiri ne suka ga canji mai yawa tare da 2Pac, da yake su mahaifiyarsu bata tare da Babansu, tun suna primary suka rabu, gallazawar da mahaifinsu ya kula suna fuskanta ne ma yasa duk ya daukesu yana rarrabasu a makarantun kwana, sai dai babban wanshi da aka tura kasar Amurka, haka ya dawo ya zama rikakken dan shaye-shaye, yanzun haka wannan komawa hutun da 2Pac yayi ma an kai yayan Rehab saboda kwakwalwarshi ta fara samun matsala. Wani abu da iyayen 2Pac da ma abokanshi basu sani ba tun yana aji daya ya fara sha, daga maganin tari, saiya koma sato kwayoyin daya ke gani wajen yayan nashi, kuma sai kowa yayi bacci yake dauko daya ya rabata wajen gida takwas, saiya totse kashi daya yake iya samun bacci. Kamar yanda dabi'ar masu shaye-shaye take, suna girma abin yana gaba, saiya zamana a hankali yake kara dosage din, wannan hutun daya koma kuma ya hadu da wasu abokan da suka girmi kanshi sai suka koya masa shan wiwi, da yake Baban 2Pac na tunanin zai cike musu gurbin rashinshi da na mahaifiyarsu hadi da gallazawar matarshi sai yake sakar musu kudi sosai da sosai, harma baisan abinda zaiyi da kudadenshi ba lokutta da dama, sai yanzun daya fara amfani dasu yana siyan wiwi. Itace yayi sneaking dinta da yawa, da yake abokan sun koya masa yanda ake boyonta, kasan takalman makarantarshi. Sai dare ya raba in ya nada saiya boye da lighter dinshi ya tafi bandakin makaranta ya zuqa. Haris shiya fara kamashi, da farko ya tsorata, har saida sukayi fada da 2Pac din, amman abu na kuruciya, sai yanda 2Pac din yake nada wiwin ya kuma kunnata yana zuqa ya fara burge Haris, harya gwada shima, ranar farko kara daya ya zuqe bayan tarin daya dingayi a zuka wajen biyar kamar zai shide amman yaki hakura, sai dai maimakon cajin da yake ta kwadaita masa, sai yaji kamar kawai wani abune yake dan yawo a kanshi, bai bugu yanda ya kamata ace yayi ba. Kafin term ya kare saiya zamana sun janyo Barde da Lalaye sun fara wannan muguwar ta'adar. Waje suka gano ma cikin makarantar inda suke zuwa susha kayansu, data kare sai 2Pac ya kwanta ciwon karya, ya dingayi kamar wanda jinnu suka shafa, dole aka mayar dashi gida da permit na kwana uku zuwa sati daya in har bai samu sauki ba. Kwananshi uku yayo musu kayanta ya dawo musu da ita makaranta, har shayi idan aka basu sai Haris ya faki ido ya marmasa ganyen a ciki, lokacin ne ya samu sunanshi na Ganja, dan ba karamin burge abokanshi yakeyi ba, sunce babban kai yake dashi. Kuma Hajiya Rumana ta kara kankaro masa mutunci data siya masa wata tsadaddiyar waya, haka yayi sneaking dinta zuwa makaranta, aikam ranar ko wani dan sarki ba zai nuna ma Haris jin kai ba. Inda ace Hajiya Rumana ta nutsu ta saka idanuwa akan Haris, data kula da canjin da ya samu, a lokacin kuma data ga duhun da labbanshi sukayi fiye da sauran fatarshi saboda yawan hayakin da yake bankawa cikinshi. A lokacin yazo hutu, wanda daga shine zasu shiga aji shidda, Alhaji Mustafa ya jima bai saka shi a ido ba, kamar boye masa Haris din yakeyi, sannan Hajiya Rumana ma tana tayashi wannan boyon. Idan da yamma ya dawo gidan sai tace masa Haris na Islamiyya inya tambaya, idan da daddare ne kuma ace ya tafi sallar isha'i, ko kuma ya riga ya kwanta, shi dai bai karyata ba, amman basu taba haduwa da Haris a masallaci ba, duk da unguwar cike take da masallatai, amman ai na kusa shi duk suke zuwa. Sannan yaushe rabon Haris da wata Islamiyya? Ya kan leka dai in ance ya kwanta, har dakinshi, kuma yana samunshi a kwance din, ya dan tsaya sai yayi masa addu'ar shiriya da neman kariya kawai yaja masa kofar. Sai ya yanke hukunci sai yaga Haris a ranar zai ma fita daga gidan, da yake girkin Hajiya Rumana ne, yayi zamanshi a falo, fushi take tayi masa da baima san dalili ba, yara ne suke yawan hadasu fada, kuma ai ya gaji ya hakura, ya yarda tafi karfinshi akansu, tunda da yace ba zai biyawa su Munira su tafi kasar waje ba, sai tace ita zata biya, nan ne ma ya nuna bata isa ba, sai dai in ya yafe mata su gabaki daya, dole ta hakura, amman yanaji yana gani duk sukayi applying Jami'ar Maiduguri, suka koma wajen danginta, sai dai suzo hutu, a lokacin ma ana maganar auren Munira dinne da wani abokin wasanta na bangaren Hajiya Rumana din, wanda haihuwar kasar Ingila ne, kasancewar mahaifinshi yana aiki acan, akwai 'yan uwan Hajiya Rumana da yawa a kasashen waje. Yaron yanzun haka Likita ne, yana aiki a Birmingham ta kasar Ingila, can dinma zasu tafi, itama sai ta cigaba da karatunta dan ta kusan kammalawa inda take karantar fannin magunguna wato Pharmacy. Lokacin da Haris ya shigo falon, wando ne dogo a jikinshi, ruwan toka mai cizawa, sai farar t-shirt, sumar da ya dan tara kadan bakikirin da ita, tasha gyara sai daukar ido takeyi, kallo daya Alhaji Mustafa yayi masa yaji gabanshi yayi mummunar faduwa, ya kafe shi da ido bayan sun gaisa yana dorawa da "Zo nan Haris" Bai musa ba ya karasa, da yake akan doguwar kujera Alhaji Mustafa yake, shi Haris saiya zauna akan hannun kujerar "Ya makarantar?" Ya tsinci kanshi da tambaya "Alhamdulillah" Cewar Haris, wata irin rashin natsuwa ce take ta shigar Alhaji Mustafa game da Haris din, bai kawo wani abu guda daya a ranshi ba, ya dai tabbatar akwai wani abu da ba dai-dai ba a tare da yaron nashi, anya kuwa Allaah ba zai kamashi akan sakaci da 'ya'yan Hajiya Rumana ba? Ya kamata ma ace ya gaji ya hakura ya bar mata su? To ta ina ma zai fara yanzun, inda Mukhtar ne ko wani a cikin yaran Fadime da yanzun sun zagaye shi kowa nason bashi labari, amman kalli yanzun yanda kalamai sukayi musu karanci tsakaninshi da Haris, kamar wasu bakin juna. "Yaushe zaka koma makaranta?" Haris din ya dan numfasa "Ranar Monday" Saiya jinjina kai, kudi yake sakawa Hajiya Rumana na duk wata hidima data danganci yaran, amman yau sai yace "To ka shirya gobe sai muje muyi siyayyar komawa makarantar ko?" Cike da mamaki Haris ya kalle shi, saboda abune da bai saba ba, "Mami ma ta gama saimun komai da nake bukata" Sukayi shiru na wani lokaci "Karfe nawa zaku wuce ran Monday din?" Haris yasan basa wuce karfe goma, direba ne yake kaisu shi da Hajiya Rumana "Wajen tara da rabi zuwa goma haka muke fita" Kafin ma Alhaji Mustafa yace wani abu Haris din ya mike "Ina dan shirya kayana ne Baba, saida safe" Bai kuma jira amsar shi ba ya wuce abinshi, Alhaji Mustafa yaji wani abu ya takure a cikin kirjinshi, haka ya kwanta da wannan rashin natsuwar, itace kuma ta zame masa wata abokiya a kwanakin har zuwa Monday, da saida su Haris din suka ganshi a shirye tsaf, kallo daya zakayiwa Hajiya Rumana kagane bataji dadin wannan bazata na mijin nata ba. Akan dole akayi tafiyar dashi, har makarantarsu Haris, duk wani report card dinshi da take fada masa wai a makaranta ake ajiyewa sun dai fada mata grade dinshi yasa aka dauko, yaji dan sauki ganin Haris din ya fara kokari, ko a term din da aka fita na bakwai yazo. Ya dai kalli Hajiya Rumana da yaji cewa duk sanda za'a nemeshi yana kasar waje, da alama shugaban makarantar yaji dadin zuwanshi. Sukayi musayar Lamba, Hajiya Rumana na sakawa a ranta, suna koma gida zata faki idon Alhaji Sa'id ta rufe lambar ta yanda shugaban makarantar ba zai iya kira ba, shikuma ta sauya lamba daya a ciki yanda inya kira ma sai daiya samu wani. Ba zata bari Haris na gab da gama makarantar nan sujawo mata wata fitina da Alhaji Mustafa ba, so takeyi akan Haris ta shawo kanshi ya fitar da yaron kasar waje, a gaban idonta yake maganar watakila Mukhtar na da rabon komawa Madina, tunda su kananun duk sunje Umra, manyan kuma sun hadane harda Hajj, acan zaiyi karatunshi, da tayi magana sai yace mata "Bafa ni zan kaishi ba, kwakwalwarshi ce zatayi masa sanadi" Wai ita zai ninke a bai-bai, ta dauki idone ta saka masa, dan ba karamin tashin hankali za'ayi ba ace wani a cikin yaran Fadime ya tsallaka wata kasa da sunan karatu, in har ya nuna mata ba zai fitar da Haris ba, sannan ta riga tayi rantsuwa sai dai yayi abinda zaiyi, amman ko da yardashi ko babu, Haris ba zaiyi karatu a Najeriya ba, haka suka dawo gida. Aikuwa abinda tayi niyya shi tayi data samu ta dauki wayar Alhaji Mustafa. Sai dai har ranta bataso a kirashi ne akan irin rashin ji da rigimar da Haris yakeyi Ko a mugun tunani batayi hasashen kiran da za'ayi ma Alhaji Mustafa har akan Haris har ita saiya girgiza... #LubnaSufyan ✨ #WomenOfWords #09035723778 (WhatsApp) Littafin nan na kudine akan #1k kacal, zaizo a manhajar Telegram ne kawai 20/06/2025 In Shaa Allaah, bayan mun kammala shafukan dandano. Zaku iya biya ta: 9035723778 Opay, Lubabatu Sufyan. NAGODE. * LABULE...Asirin mai daki 3 Wata tafiya ce mai matukar muhimmanci ta kamashi zuwa jihar Lagos, saboda dole sai yana wajen komai zai tafi dai-dai, da ya sake komawa makarantarsu Haris tunda ya kira lambar da Shugaban makarantar tasu ya bashi sai wata mace ta dauka, haka ya bata hakuri yana rayawa a ranshi cewar an samu kuskure wajen shigar da lambar, wannan rashin natsuwar da yaji tun ranar da yaga Haris ne yake kara girma duk rana, yana darsa masa wata irin fargaba da tafi karfin fassara. Wani abu na fada masa cewar danshi na bukatarshi, yana bukatar yaja shi a jiki ya gano menene matsalarshi. Satinshi biyu a Lagos kafin ya gama ya dawo Kaduna, sai ya sake shiga wata sabgar bayan ya tambayi Hajiya Rumana ta bashi lambar da take da ita na daya daga cikin Malaman Haris din tace masa babu. Ranar ta kama Lahadi ce, ya kamata ace kuma ya wuni a gida, ko da ba zaiyi bacci ba yana hutawa, sai ya fita wata dubiya, a hanyar dawowa nema kira ya dinga shigowa wayarshi da wata bakuwar lamba, da yake bai cika daga lambar da bai sani ba, amman yanda ake kiran babu kakkautawa yasa shi ya daga hadi dayin sallama. "Alhaji Mustafa ne?" Aka tambaya daga dayan bangaren bayan gajeruwar gaisuwa, ya amsa, sannan aka sanar dashi daga makarantarsu Haris ne, haka kawai yaji zuciyarshi ta buga, musamman da aka sanar dashi ana nemansu ne da gaggawa washegari da zata kama Litinin, jiki da murya a sanyaye ya amsa, tunda ance idan yaje din zaiji koma menene, haka kawai daya koma gida, duk da ba dakin Hajiya Rumana yake ba, sai daya sake shiga ya fada mata kiran da akace anayi masa, taji ranta yayi mugun baci, akan me zasu kirashi? Ai kam dole ne zata kora musu kashedi idan taje "Ba zai wuce kare-karen kudinsu da suka saba bafa, ko kuma kan maganar jarabawar da zasu zana, meye zasu wahalar dakai kai da kake da hidindimu a gabanka, kabarsu kawai goben sai in shirya akaini inji menene" Ya girgiza mata kai, yanajin ya daina bar mata yaran da hidimarsu, koya ne zai dinga kokarin shiga rayuwarsu da sanin me take ciki "Zanje din tunda har suka bukaci hakan, banajin akan karamin dalili ne" Tasan shi, yanayin da yake fuskarshi kuma ya nuna mata babu abinda zata fada da zai sauya masa ra'ayi "Sai in shirya muje tare" Wannan ba laifi bane, shisa ya amsata, suka dan kara taba hira kafin ya fice. Baiyi wani baccin kirki ba saboda tunanin daya cunkushe masa, washegari kuwa tun karfe bakwai na safe daga shi har Hajiya Rumana sun gama shiryawa tunda direbanshi ne zai kaisu. Kuma bayaso ace tara na safiya tayi basu karasa ba shisa yayi mata magana ta shirya da wuri, ta fara janshi da hira taga yana amsata dai-dai, sai kawai ta kama danna wayarta ta kyaleshi. Haka suka karasa makarantar kamar wasu bakin juna, a tunanin Hajiya Rumana ba zai wuce Haris yayi fadan daya saba bane, ya kama wani abokin karatun nashi ya jibga. Ko daya wuce aji daya, babu ruwanshi da duk wani yaro na kasa dashi, wannan seniority din da akeyi a makarantar kwana baya cikin lissafin Haris. Yanda yaran basa shiga hanyarshi haka baya shiga tasu, a aji ma inka cire abokanshi sauran in zasu fita sabgarshi zaiso haka, to fadanshi a tsakanin sa'anninshi ne, sune zai kama ya jibga in wani abin ya hadosu, ya taba jibgar wani Malaminsu dan bautar kasa, ko da yake yace ma ba Malaminshi bane dan Junior section yake koyarwa, shisa baiga dalilin da zaisa ya daga bulala da sunan dukanshi ba, da yake ance matsalar da kudi basa magancewa kalilan ce, dasu Hajiya Rumana ta kashe wannan case din, aka ja masa kunne da suspension din sati biyu kacal. Yau ma ta tabbata Alhaji Mustafa ne zai kwafsa mata, haka suka shiga ofishin shugaban makarantar hancinta a sama, fuskar nan kamar bata taba fara'a ba. Ko gaisuwar da yayi musu ma, a shaqe ta amsa, tanajin shi yanata koro bayani da wani turancin shi da yake kara shakar da ita, sai ga kunnuwanta sun jiyo mata abinda yake neman sakata fadowa daga kujerar da take zaune "Ina mai dana sanin fada maka cewa yaranka na daya daga cikin wanda muka kama suna shaye-shaye a cikin makaranta, ansha kawo mana kara, sai dai abune da yake bukatar bincike shisa bamu dauki wani mataki ba mukayi amfani da wasu hanyoyi wajen zurfafa bincike yanda zamu kamasu da laifin..." Cikin tashin hankali Hajiya Rumana ta katse shi da fadin "Karya ne, ba dai Haris dina ba, shaye-shaye? Karya ne" Ai dan shaye-shaye baya boyuwa ko? Ba haka zaka gansu ko a labarai firgai-firgai ba? Duqu-duqu dasu, Haris dinta da zai shigo dakinta ya fita yana bar mata kamshin  turarenshi na Addictive ambergris, Haris din da yake tsaf-tsaf dashi ko da yaushe, sau nawa suna wuni a gidan bata taba ganinshi yana marisa ba? Ko ana nufin har yayi hutu ya gama baya sha saiya koma makaranta? "Karyane wallahi" Ta sake fadi, Alhaji Mustafa banda "Inalillahi wa ina ilaihi raji'un" Babu abinda yake furtawa cikin zuciyarshi, Shugaban makarantar yayi wani guntun murmushi mai ciwo "Kuyi hakuri, amman wannan laifine daya taka dokar makaranta, kuma hukuncinshi korane, duk daya kamata mu hadasu da hukuma ne tunda an kamasu da tabar wiwi mai yawan gaske a cikin kayayyakinsu, sannan harda kwayoyi ma, sai dai ba zamuyi hakan ba, zamu tsaya iya korar ne kawai gudun karsu gurbata mana sauran daliban..." Ya karasa yana tura wata takarda gaban Alhaji Mustafa, sannan ya daga wayarshi yayi kira, sai ga Haris ya shigo cikin ofishin, kayan gidane a jikinshi dan tun jiya da aka tabbatar musu da korace, da safen akace su sauya kaya su cire uniform din makaranta, su dukansu babu wata razana a fuskokinsu, koshi Haris din baiji wani tashin hankali ba tunda dai yasan ai Hajiya Rumana ce zatazo, kuma korarshi daga wannan makarantar ba wani abu bane, da sun fita ya narke mata yace "Abokaina ne suke sha, muna tare aka kamamu Mami, ke kinsan ba zansha irin abubuwan nan ba" Zance ya kare, ba zata sake tayar da maganar ba ko a tsakaninsu balle har wani yaji, wata makarantar zata samu ta kaishi, tunda shekararce ma kawai ta rage masa, amman ganin Alhaji Mustafa da yanda ya juyo ya kalleshi sai yaji kamar zuciyarshi ta dunkule waje dayane ta kuma gunguro zuwa tafukan kafarshi da sukayi masa nauyi har yana kasa karasawa ciki, ya tsaya a wajen kawai yana sauke kanshi kasa, duk wani abu da ake fada baya karasawa kunnuwan Haris, bayajin komai banda bugun zuciyarshi da yake amsawa a kowacce gaba ta jikinshi. Yaga mikewar Alhaji Mustafa, ya raba ta gefenshi ya wuce, kafin Hajiya Rumana da itace ma ta rike hannunshi tana janshi suka fita daga ofishin "Jakunkunan kayana Mami" Haris ya fadi yanajin yanda harshenshi yake a bushe, direban daya kawosu tasa yazo ya kwashi kayan Haris din ya saka a mota, ita da Alhaji Mustafa suka sake shiga gidan baya, Haris din ya zauna a gaba, data mika hannunta ta riko na Alhaji Mustafa cikin sigar lallashi saboda shirun motar ya fara isarta zarewa yayi kamar ta dora masa garwashin wuta. So take kawai ta gansu a cikin gida, a bangarenta ko nashi su hadu ita da Haris su tabbatar masa da ba zai taba aikata abinda aka fada ba, sai dai in an samu wani akasin. Suna karasawa gidan kuwa shiya fara fita daga motar ya zagaya yana kama hannun Haris da kanshi zuwa nashi bangaren, ta rufa musu baya tana masa magana ganin irin fisgar da yakeyiwa Haris din, ko juyowa baiyi ba. A tsakiyar falonshi ya tsayar da Haris "Ka kalleni Haris, ka fadamun gaskiya, an kamaka da wiwi ko ba'a kamaka da ita ba?" Haris ya kasa dago da idanuwanshi, yasan babu wata shakuwa a tsakaninsu tun tasowarshi, to sau nawa ma suke haduwa da Baban nashi a shekara? Ko lokacin bukukuwan sallah sunfi yin abinsu a Maiduguri wajen dangin Maminsu amman akwai kaunar nan ta 'da da mahaifi, yana kishin shakuwar da take tsakaninshi da Mukhtar, ko da asuba tare suke fita masallaci, inma an taso shi to yanda suke labari sai dai ya koma baya yana binsu kawai, a gaban Alhaji Mustafa, Haris najinshi kamar wata inuwa da sai bayan wani lokaci in ya juya yake tunawa da ita. "Wai wacce irin tambaya ce wannan? Yama za'ayi ace an kama Haris da irin wannan laifin ka yarda" Juyawa Alhaji Mustafa yayi yana mata wani kallo da yasa ta rufe bakinta, dan a karo na farko a zamansu ta tsorata da abinda ta gani "Haris..." Sai lokacin ya iya dago da kanshi, ya kalli Alhaji Mustafa, ya hadiye wani abu daya tokare masa wuya "Da gaske ne Baba...kayi..." Bai karasa ba yaji wata irin iska ta gifta masa da bai taba jin makamanciyarta ba, dan saida ta dauke masa jinshi na wasu dakika, wani irin haske ya gifta masa, yana bude idanuwanshi kuma ya sake jin wata iskar data tabbatar masa da marine, marukane Alhaji Mustafa ya sauke masa guda biyu a jere, yana sake kai masa wani da saida yayi kasa saboda karfinshi "Shaye-shaye? Haris shaye-shaye? Jinina?" Tunda yake bai taba tsintar kanshi cikin matsanancin bacin rai irin na yau ba, yara nawa ya dauke a unguwar iyayenshi zuwa rehabilitation centre, ya dauki dawainiyarsu dan ganin rayuwarsu ta inganta sun fita daga muguwar dabi'ar shaye-shaye, ko sau daya bai taba aibatasu ba saboda gudun kar Allaah ya jarabce shi, ko a hanya yaga giccin irinsu zaiyi musu fatan shiriya ne, to me yasa Haris zaiyi masa haka? Ko dan ya sakarwa Hajiya Rumana su? Baisan irin dukan da yakeyiwa Haris din ba, tunda shi mutum ne da bai iya fushi ba tun asali, saida yaga Hajiya Rumana tana tureshi tana kuka, duk da haka bai dawo hayyacinshi ba saida ya sake kaiwa Haris din wani dukan da Hajiya Rumana ta tare ta sameta a gefen fuska "Ka hadamu kawai ka kashe Mustafa, ai baka da asara tunda kana da wasu yaran maza, in kayi masa lahani ni zaka cutar..." Take maganar cikin hargowa kamar zata bangajeshi, kallonsu kawai yakeyi wani irin duhu na lullube sashi da yawa na zuciyarshi, neman wani zunubi daya aikata Allaah Ya jarabce shi da wannan lamarin yakeyi, kafin ya fara jero neman yafiya da tsari daga mummunan tunani, yana kallo ta janye Haris din suka fice daga dakin baiko motsa ba, dan hakan ma yafi masa, in yana ganinsu zuciyarshi zata cigaba dayi masa bakine, gara su bashi waje ya samu ya saisaita kanshi. Ita kuwa Hajiya Rumana bangaren Haris ta nufa dashi "Ka hada iya abinda zaka iya bukata, zamu wuce Maiduguri" Ya kalleta da idanuwanshi da suka kada, amman babu ko kyallin hawaye a cikinsu duk kuwa irin dukan da yasha, asalima abinda yakeji bashi da fassara sam, kawai dai yana bukatar yaga wani katon nadi na wiwi a hannunshi ne yana busawa, da ita kadai zai raba wannan yanayin ya samu sauki, shisa baiga abinda zai tafi Maiduguri yayi ba a halin yanzun "Mami..." Ta katse shi da "Dan ubanka kayi abinda nace, so kake ka zauna yana ganinka ya illata mun kai a banza?" Hawayen daya ga sun sake zubo mata saboda yanda ranta yake suya da dukan da Alhaji Mustafa yayiwa Haris sai kace ya kama dan fashi. Ficewa tayi tabar masa dakin. Kaya kala hudu kawai ta dauka, saida ta sake watsa ruwa, sannan ta canza kayanta, tanajin gefen fuskarta ya tashi na dukan da ta tarewa Haris, tayi kwafa zuciyarta na wani irin zafi, bacin ran dukan da yayiwa Haris ya shafe mata komai. Ta riga ta gama tunanin matakin da zata dauka, ai sai yaga Haris dinne zai dakar mata shi. Shikuwa data bari a daki saiya rasa abinda zai dauka, wayarshi dai tana cikin kayanshi daya dawo dasu daga makaranta, sai kawai ya samu wata karamar jaka ya zuba kayan da basu wuce kala bakwai ba, ya fita yana sa direban Alhaji Mustafa ya bude masa motarshi ya fito masa da kayayyakinshi duka ya kai masa daki, abinda yake bukata a cikin kayan ya dauka, lokacin daya sake fitowa har direban Hajiya Rumana ya juya musu motarta suka shiga, data fada masa Kano zasu je sai subi jirgi ta can, saida ya fita ya sake daukar wasu 'yan abubuwan da zai bukata. * Alhaji Jibril shine babba a dakinsu Hajiya Rumana, kuma tun bayan rasuwar iyayensu saiya dauki wannan girman nashi da muhimmanci ta yanda in har zai iya to ko quda ba zai gifta ta gefen kannenshi ba ballantana kuma wani abu na cutarwa, su daman zuri'arsu mutanene da suka gaji arziki na dukiya tun sale-sale saboda tsatsonsu na daga cikin kalilan da suka fara harkar siye da siyar da zinari tun a zamanin baya, 'yan kasuwa ne da 'yan boko da wasu a cikinsu suka rike mukamai, suke kuma rike dashi yanzun a mabanbanta wajaje a cikin gwamnati, wasu ma suna kasashen waje da iyalansu can suke zaune. A soyayya irin ta Alhaji Jibril da kannenshi, basa laifi, abinda duk suke so shima shi yake so ko da akwai rashin kyautawa a cikin wannan abin, soyayyarsu ta shafe hakan a idanuwanshi, wani irin ahaline da sangarta da wayewa ta samu wajen zama a cikinsu, kuma yawancinsu kaf irin wannan soyayyar da suka tashi a ciki, itace suke kamantawa akan yaransu, ko da yaji abinda ya faru sai yafi ta harzuqa "Wanne irin duka kuma? Wai har yanzun ba'a daina wannan gidadancin dukan yaran ba, ko da gaske shaye-shayen yakeyi ai janshi za'ayi a jiki a kara nuna masa soyayya aji meye matsalarshi shine zai daina" Itama dai abinda tayi tunani kenan, sai dai duk wani kira da Alhaji Jibril ya dinga yiwa Alhaji Mustafa bai daga ba, bai biyo bayan kiran ba. Da yake sunsan Haris na ajin karshe ne, sai kawai aka kaishi daya daga cikin makarantun da yaran gidan Alhaji Jibril din sukeyi a matsayin external student, dan jarabawa kawai zaiyi. Shi tuni ma ya sake cikin 'yan uwa anata yawo a gari kamar babu abinda ya faru, musamman da yaji abokanshi ma suna cikin koshin lafiya harma sukayi masa alkawarin saka lokaci su kai masa ziyara har Maidugurin. A wannan yawon garin ne ya fita shi kadai ya samu abinda jiki da zuciyarshi suke bukata, kuma ba'a hada sati biyu ba ya gane cikin cousins dinshi ma akwai wanda suke busa hayakin, sai kawai suka hade abinsu, nasu idanuwan ma sunfi nashi budewa tunda sun fishi yawo, basa gida Nigeria basa kasashen ketare, bayan bushe-bushen ma harda mata suke hadawa, saiya zamana Hajiya Rumana da hannunta ta raboshi da Kano ta kawoshi inda zai kara lalacewa. Ita kanta saida tayi sati uku a garin Maiduguri, amman ko data huce ta gwada neman Alhaji Mustafa bai daga mata waya ba, bai amsa tarin sakkoninta ba, yanda ta dauki kafarta ta tafi Maiduguri haka ta tattara ta koma Kaduna duk dama 'yan uwanta da yawa basu so hakan ba. Sai dai ya shayar da ita mamaki, baice mata komai ba, nunawa ma yayi kamar babu abinda ya faru a tsakaninsu, sai itama ta fuske, a gefe daya tanata shiri da Yayanta Modu wanda shi takebi, yana zaune ne a kasar Italy tare da iyalanshi duka, akan yanda za'a fara ma Haris processing samun makaranta a kasar da jarabawarshi ta WAEC ta fito Wannan shine tsarinta Kuma shi din ta aikata a lokacin batare da tunanin komai ba Asalima wani irin sanyi taji ranar da Haris ya sauka kasar Italy, a gefe daya kuma Alhaji Mustafa yayi matukar kokari wajen danne zuciyarshi baice mata komai ba, duk da yasan abinda yake faruwa, yaga Hajiya Rumana ta rantse ta sake rantsewa saita shiga tsakaninshi da danshi kamar ita kadai ta haifeshi, so yake yaga iya gudun ruwanta, shisa ranar da Haris din ya tako yazo da sunan hutu ya birkice mata ta sigar da bata taba gani ba, dan kallo daya yayi musu ita da Haris din da yayi wata irin murjewa saboda hutu da canjin yanayi, sai dai bakinshi yayi duhu fiye da sauran fatarshi, sannan kuma idanuwanshi sunyi wata irin lumshewa da batayi kama data shaye-shaye ba sai ta kara masa wani irin kyau, ya jefesu da tambayar abinda Haris yazo yi masa a gida. Bata kara shiga tashin hankali ba saida taji ya rantse sai Haris ya koma inda ya fito ba zai kwanar masa a gida ba, itama kuma bai hanata ba, zata iya daukar jaka tabi danta tunda daman ai ta jima da nuna masa ita kadai ta haifeshi, suje kawai ya sallama mata shi "Nifa kukanki kara batamun rai yakeyi wallahi, uba fa kika sake masa tun kafin in mutu, to meye a ciki? Nayi miki magana? Nace miki wani abu? Bar muku shi nayi yanda kike bukata, shisa ba zai kwanar mun a gida ba wallahi, kuma daga ke harshi babu wanda ya isa yasa inyi azumin kaffara" Shisa ma ta tsorata matuka, musamman da Haris dinma ya dauki jakarshi duk da hanashin da takeyi "To zaman me zanyi masa Mami? Kinajin yace ya bar miki ni, duk da daman nidin nakine, to ba sai in bar masa gidanshi ba?" Kuma bai saurareta ba ya fice tunda ai akace dan gado saiya dara, gadon zuciya yayita a wajen Alhaji Mustafa, jin kai da Izza kuwa daga wajenta ne, tafiyarshi yayi, ta danji sanyine ma daya dauki motarta ya fita da ita, hotel ya kama abinshi. Kuma ko bayan da Alhaji Sa'id din da take tunanin zai shawo mata kanshi yazo sai taga ma kamar ya sake birkicewa ne, dole ya ce mata suyi hakuri su barshi ya dan huce kwana biyu, amman hankalinta a tashe yake, dan yanayine da bata taba ganin mijin nata a ciki ba. Hukunci ne ta riga ta yanke da take tunanin mafita ne a wajenta da Haris din a wancen lokacin A yanzun shima Alhaji Mustafa gani yakeyi abinda yayi wata hanya ce da zai nunama Hajiya Rumana kuskuren data yi masa Kowa ta bangarenshi gani yakeyi ya duba Haris din a yayin yanke hukunci, amman shikuma Haris din fa Haris ne a tsakiyarsu Daya na gabanshi Daya na bayanshi Amman babu abinda yakeji sai kadaici, kadaici da rashin tsayayye a cikin rayuwarshi Tangal-tangal yakeyi, Babu inda yake samun dai-daito sai ya rike wiwi a hannunshi ko yaji mace a tare dashi... #LubnaSufyan ✨ #WomenOfWords #09035723778 (WhatsApp) Littafin nan na kudine akan #1k kacal, zaizo a manhajar Telegram ne kawai 20/06/2025 In Shaa Allaah, bayan mun kammala shafukan dandano. Zaku iya biya ta: 9035723778 Opay, Lubabatu Sufyan. NAGODE. * LABULE...Asirin mai daki 4 HARIS Dakinshi aka bashi a gidan Alhaji Jibril, daki babba sosai tunda hade ma yake da dan karamin falo harda irin kitchenette din nan, duk dakunan yaran gidan haka suke, shi da ko ruwan zafi bai taba dorawa ba a rayuwarshi, haka yayi dariya da yaga kitchenette din. Lokacin daya zabi bangaren Art, yayi hakan ne saboda yasan akwai saukin darasin lissafi a wannan bangaren, baisan ko yana da kokari ko bashi dashi ba tunda ba wani dagewa karatu yakeyi ba. Yasan da yawan matasa, ko yace yara suna da abinda suke so su zama tun kafin su girma, wasu tun suna primary school, shisa da sun shiga ss1 sai su zabi bangare tunda sunsan abinda sukeso su zama, shi dai yasan yana son harkar motoci irin wadda ya taso yaga mahaifinshi yanayi, amman baya sha'awar siye da siyarwa, bayason duk wani abu da zai dinga daukarshi zuwa wasu garuruwa ko wasu kasashe da sunan aiki, yana so in har ya bar garin da yayi settling to ya zamana hutu ya tafi. Shisa yake so yayi harkar transportation, ya mallaki manyan motoci dama kanana a dinga yi masa aiki dasu, yana kwance a gida yaji alert batare daya fita ko'ina ba. Wannan shine mafarkinshi, sai dai ana karantar harkar transportation a makaranta ne? Har bincike yakanyi idan ya zauna baya komai, bai taba maganar da kowa bane ba, zaiso ace suna irin zaman nan shi da Alhaji Mustafa suyi hira kamar yanda yaga sunayi da Mukhtar, da saiya bashi labarin abinda yake buri, yasan ba zai rasa wasu shawarwari da zai bashi akai ba, ko mutanen da zai hada shi dasu, to gashi a Maiduguri, wata tazara ta kara samuwa a tsakaninsu. Dakin Salim ya shiga, yaron Alhaji Jibril ne shima, ya zauna akan kujerar dakin saiya hango wata karamar camera, haka kawai ya tashi yaje ya dauka yana juyata a hannunshi, sai yakejin wani abu na shigarshi da bai tabaji ba "Ta Aise ce fa ta manta zuwan da sukayi" Salim yace masa, baisan komai game da camera da yanda take aiki ba "Kana amfani da itane?" Salim ya girgiza masa kai "All yours in kana so" Daukar yayi kuwa ya tafi da ita dakinshi, sai gashi yana bincika yanar gizo yana neman yanda ake amfani da camera din bayan yaga sunanta a jiki, sai gashi ya dauki lokacin da baiyi tunani ba akai, tun azahar har yamma liqis, sallar la'asar ma a daki yayi kayarshi wajen biyar da wani abu. Ya dinga amfani da camera din yana daukar duk wani abu da zai iya a cikin dakin, rabon da wani abu da ba wiwi ba ya sakashi nishadi haka harya manta, ko randa su Salim suka matsa masa ya biyewa wata yarinya bata sakashi nishadi irin wannan ba, wani abune na daban ya cika masa zuciya ya samu waje yayi zaune. Sai 'yar camera din nan ta zame masa kamar wata abokiya daya jima yana nema, jinta a cikin hannunshi kadai na sama masa natsuwar da baisan yana bukata ba. Lokacin daya gama jarabawarshi yasan abubuwa da yawan gaske da suka danganci daukar hoto saboda binciken da yakeyi akai, kuma a karo na farko ya saka daukar hoton a cikin abinda yake so yayi tare da harkar transportation dinshi. Shisa ko da sukayi waya da Hajiya Rumana tana tambayarshi ko me yake so ya karanta dan ta fara magana da Alhaji Modu a lokacin sai yace "Photography..." Yasan shirunta na mamaki ne shisa ya tsinci kanshi da dorawa da "Akwai abinda nake so inyi Mami, wannan din yana daga ciki, wancen banajin yana bukatar wani karatu mai yawa, banaso in fada miki yanzun" Abinda yake so shi take so kamar sauran 'yan uwanshi, bayan tayi magana da Alhaji Modu, shima saida ta bashi lambarshi saiya zamana ma dashi suke magana suna shirya yanda komai zai kasance. Saida jarabawarsu ta fito, bashi da wata matsalar komai sannan kuma hankalinshi ya sake rarrabuwa kashi-kashi, shifa daukar hoto ne a ranshi, amman yaga Kawun nashi ya tura masa da wasu courses sama da kala goma wai ya zabi daya. Haka ya zauna ya dinga tunani, kafin ya natsu akan guda daya "Documentary and photojournalism" Akwai wani abu da ya tsaya masa a tattare da course din. A lokacin bashi kadai zai tafi makaranta ba, a tsakanin cousins dinshi maza da mata su 8 ne, kuma duk watannin nan daya shafe a Maiduguri, duk shirye-shiryen da akeyi ko sau daya basuyi magana da Alhaji Mustafa ba, baisan sau nawa ya dauki waya ya danna lambarshi yana kasa kira ba, me zaice to? Inya kirashi me zaice masa? Ko kafin ma yayi masa laifi ba waya sukeyi ba, da wahala ma idan yasan cewa ya mallaki wayar balle harya samu lambarshi, shi dai ya jima da haddaceta tun kafin ma Hajiya Rumana ta sai masa waya. Da lokacin tafiya yayi, mutum biyu zuwa uku zakaga zasuje kasa daya, shi kadaine zai tafi kasar Italy, kuma shi kadaine babu kowa nashi banda Anisa, Munira taje Kano saboda a lokacin ma ana shirye-shiryen bikinta ne, sannan Hajiya Rumana ma tace masa Alhaji Mustafa ya hanata zuwa Maidugurin, sai waya suka dingayi, tana masa alkawarin zata san yanda zatayi taje har Italy din ta dubashi, kasancewar Anisa a wajen bai ragewa Haris nauyin da zuciyarshi tayi na rashin iyayenshi ba, saima inya juya yaga kowa da mahaifinshi, shi da Alhaji Mustafa ba zaizo ba sai ya hana masa Hajiya Rumana zuwa itama, abin yayi masa ciwo na gaske. Ya dinga fadawa kanshi inya tsallaka ya bar kasar sai dai ita Hajiya Rumanan ta dinga zuwa masa. Duk wasu hotunan kasar Italy daya gani a yanar gizo basu shirya zuciyarshi ba ashe, kasar na da kyau, tunda suka bar airport yake kalle-kalle kamar wani dan kauye, ya dinga jin hannunshi yanayi masa kaikayi da son ace akwai camera a jikinshi da zai dauki hotunan duk wani gini da yayi masa kyau, sai dai 'yar karamar camera din da akace masa ta Aise ce tana cikin jakarshi, kuma jakar na bayan mota. Fushin daya hau jirgi dashi ya nema ya rasa a tsakanin kyawun gine-ginen kasar Italy da kuma yanayin komai da yayi masa kyau. Tarba mai kyau ya samu wajen matar Alhaji Modu, Binta, amman tun kafin yazo ma yaji ana kiranta da Mamma. Haka aka nuna masa dakinshi inda ya shiga yayi wanka dan ya gaji, ya sake kaya tukunna ya fito, gidan nasu ne yakejin shi shiru, yasan yaran gidan su uku, Khamis da suke kira da Khaam yana India, sai na biyun baima rike sunanshi ba ance a Madina yake karatu, sai Aise itace Auta, baidai san a tsarin Binta da mijinta yara biyu bane ba, Aise kawai sun samu cikinta ne lokacin da basuyi tsammani ba. Bai tsaya wani bata lokaci ba da tace masa abincinshi na dining, inda ta nuna masa ya nufa, yunwa yakeji duk da abinci ba damunshi yayi ba sosai. Amman banda ruwa babu abinda yaci a jirgi, yana zaune ne ma Aise ta fito, a yanda aka fada masa bata wuce shekaru goma sha uku ba, sai dai yarinyar da ta kalle shi tace masa "Ciao" Cikin alamar gaisuwa batayi masa kama da 'yar shekara sha uku ba, akwai braces a bakinta, sannan gashinta data kama ta daure da wani ribbon, anyi masa irin kananun twisting din nan ne, kuma ba baki bane ba, kamar ta rina shi ya koma ruwan kasa mai dan duhu, bakace bacan ba, da wani sanyi a tare da ita da yasa Haris kasa dauke idanuwanshi daga kanta harta bace ma ganinshi, yana dai juyo maganarta da yake kokarin fahimta tunda cikin yaren kasar Italy din takeyi, kuma saida ya fara koyonshi online tunda yana cikin abinda ya zame masa dole in har zaiyi karatu a kasar, amman saurin da takeyi wajen maganar yasa kalmomi kadan ya tsinta, haka ta sake dawowa ta wuce shi da robar ruwa a hannunta. A wannan lokacin, da Haris yake da shekaru goma sha takwas a duniya, Aise ta wuce shi tana tafiya da wani kaso mai girma na zuciyarshi da baisan ya mika mata ba... Makarantar daya samu, kasa dayane, amman kuma ba cikin gari daya da gidan Alhaji Modu ba, shisa daman harda daki aka biya masa, kwananshi shida a gidan Alhaji Modu kafin yazo dan yayi wata tafiya ne wai, dashi da Binta da Aise da a wannan 'yan kwanakin suka shaku matuka aka tafi rakashi, haka suke ta cakuda hira da Aise din da take gane Hausa kadan-kadan, amman batajin turanci, sannan yaren Kanurin ma kalmomin da take tsinta basu da yawa, shikuma duk yanda ya kara dagewa ya tabbatar dai baya cikin mutanen da suke da kokari, ba karamar wahala yaren Italian din bashi ba, wai danma Aise ta zame masa kamar wani tsani na kara son ya koyi yaren saboda hirarsu ta dinga tsayi. Saida suka rakashi har dakinshi yanajin shi wani sama-sama, suka kuma gaisa da roommate dinshi mai suna Logan dan dan kasar Amurka ne, Alhaji Modu ya tabbatar Haris din zai iya karasa komai da kanshi, sannan akwai wadatattun kudi a wajenshi tukunna suka tafi, bayan Binta da kanta ta kara masa wasu kudin tana kuma jaddada masa da in yana bukatar wani abin kiransu kawai zaiyi, inma ya kama wani yazo har makarantar ne zasu zo. Suka tafi suna barinshi da kewar Aise da tace ya rike camera dinta bayan ya bata, a cewarta ko yanda shi ya fassara abinda ta fada "Banaso ka mantani da wuri..." Yayi dariya, yana fatan ta gane lokacin da yace mata "Ni da nake kasarku Aise, ko inaso ba zan iya mantawa dake ba" Zamanshi na shekara daya a kasar Italy wata shekara ce da ta zame masa mafarin abubuwa masu yawan gaske, tana daga cikin shekarun da zaiso ace sune mafarin rayuwarshi gabaki daya saboda yanda tayi masa dadi. Ya zai manta da Aise? Ta ina? Bayan itace mafarin komai, da bata manta camera din nan ba watakila da yanzun yana nan yana bulayi, watakila da baima san me yake da rayuwarshi ba Kuma a shekarar ya gane samun wiwi a Nigeria yafi wahala akan nan, kusan duk wadanda ya sani a makaranta suna sha, sai dai shan ya bambanta, da yawansu ba irin wanda yakeyi mata sukeyi ba, lokaci zuwa lokaci ne, dan nishadi, sunfi shan giyarsu akan komai, ko Logan bai taba shan wiwi ba, haka ma sigari, bayama shan ko giya, yace masa babanshi mashayi ne na gaske, giya ita ta ruguza gidansu, ta rusa musu farin cikinsu, saboda giyar Mamanshi tabar Babanshi ta kuma kwashe su shida kanwarshi ta tafi dasu, yanzun ma baya magana da Baban nashi. Duk da giya bata taba burge Haris ba, asalima shi bayan wiwi din bashida ra'ayin karawa da komai, ya dai ji tsoron gwada shan giyar ya kara shigarshi, yaso yayi mamaki da Logan yace yanzun baya magana da Babanshi, sai ya tuna ai shima baya magana da nashi Baban, ko kuma haka zaice nashi Baban baya magana dashi baisani ba, bambancin dai ba wani mai yawa bane, kawai dai yaga Logan bai damu da rashin nashi Baban a rayuwarshi ba, shikuma ya damu, ya damu sosai, har yanajin wani fili da rashin Alhaji Mustafa ya bar masa, filin da ko tarin tarkacen kayan daukar hotunanshi bai maye masa gurbinshi ba balle kuma wiwi, ko azo maganar matan daya rasa dalilinsu na like masa da binshi duk inda zaiyi. Tun zuwanshi yaga yanda mata suke sonshi, basa kuma gajiya da fada masa yana da kyau, musamman idanuwanshi. Idanuwan ya sani, tunda shima ai yana ganin kyawunsu, amman fuskarshi koshi din gabaki daya baya tunanin yana da wani abu da zasu dinga binshi har haka. Bawai sonsu bane bayayi, mata sunyi masa, sosai, tun a Maiduguri ya gano wannan bangaren nashi, ya kuma tabbatar da abinda yasa akace mata sune abokan rayuwa, akwai wani abu mai laushi da yake so a tare dasu, ko rauni zai kirashi bai sani ba, ko hannun mace ya rike a cikin nashi saiya dinga kallon bambancinsu yatsunsu, yanda na matan yake kasancewa sirara, da wani laushi na musamman yana masa kyau, shisa baya taba gajiya da rikewa, balle nan din da suke ba jikinsu muhimmanci, ansa farata da suka sha kwalliya, duk da bayason ya gansu dogayen nan, ya fison ganinsu gajeru. Ko da akayi musu hutun lokacin yayi shekara daya harda wani abu, ya mayi kwana biyar a gidan Alhaji Modu, da Hajiya Rumana tayi masa tayin komawa gida yayi hutun saiya tsinci kanshi da amsa gayyatarta, yana so yaje yaga Alhaji Mustafa, suyi magana, saboda yana so ya dinga kiranshi a waya suna gaisawa ko da ba kullum ba. Sai gashi duk wani doki da yakeyi yabi iska lokacin da Alhaji Mustafa ya kare masa kallo daga shi har Hajiya Rumana ya furta kalmomin da yakejin zafinsu a kowanne sassa na jikinshi har yanzun "Me yakeyi mun a daki? Me yakeyi mun cikin gida?" Da tayi kokarin magana ma saiya kara da "Ya koma inda ya fito Rumana, kema in kinaso zaki iya tattara kayanki kibishi, amman wallahi ba zai kwananmu a gida ba!" Shi daya dauko kafafuwanshi tun daga Italy kawai saboda ya zauna a kusa da Alhaji Mustafa ko da gaisuwar da suka sabace suyi, shaf ya manta a wajenshi bashi da wani uban, Alhaji Mustafa ne kawai, kowa zai gwada, komin kokarinshi ba zai maye masa wannan gurbin ba, amman a wajen Alhaji Mustafa shi din wani dane cikin yaran daya haifa, dan da ko dashi ko babu shi zaiyi rayuwarshi hankali kwance, tunda ai daman idan namiji ne babba ya jima da gane shi din bakomai bane in dai Mukhtar yana nan, kamar dama can Alhaji Mustafa na neman maraba dashine yanzun kuma ya samu. Shisa hankali kwance yace wai ya barwa Hajiya Rumana shi, kamar wani abu marar muhimmancin da za'a iya kyautarshi hankali kwance. Saboda Hajiya Rumana ne kawai bai nemi tikitin komawa inda ya fito ba, shisa ya kama hotel ya zauna abinshi. Kuma 2Pac na gari, daman sunyi waya, sai yazo suka shiga gari yawo abinsu. Kwananshi bakwai a hotel din nan, yana raba bacin ranshi da wiwi da mata. Baima san ana can ana rikici a gidansu da Alhaji Mustafa ba, dan saida Alhaji Sa'id da kanshi ya taka har gidan iyayen Alhaji Mustafa da mahaifinshi ya jima da rasuwa, ya samu 'yar tsohuwar nan ya fada mata abinda yake faruwa ganin aminin nashi ya botsare. Da shi da Hajiya Rumanan ta kira ta hadasu tayi musu nasiha sosai ta kuma ce masa in dai ta isa dashi tana so ya bar Haris ya janye kalamanshi, yama hakura da maganar gabaki daya tunda dai yaro ya fara karatu, kuma Hajiya Rumanan tace ta gane kuskuren da tayi harta bashi hakuri. Da gaske ranshi ya baci irin wanda bai taba ba game da Hajiya Rumana, amman ai karya yakeyi yace baya kewar danshi, baya son ace yana cikin rayuwarshi. Daga gidan nasu ya tambayi Hajiya Rumana inda Haris yake ta fada masa, text tayiwa Haris tana sanar dashi cewar Alhaji Mustafa zaizo daukarshi, dan kawai jikinta ne ya dinga bata zai iya kasancewa Haris din na tare da wasu abokai da ba zaiso ace Alhaji Mustafa ya ganshi dasu ba. Aikuwa bama abokai bane ba, macece, macen daya sallama yana mika mata kudaden da baisan adadinsu ba tunda so yake ta tattara tayi gaba batare data ishe shi da wasu tambayoyi ba, a gurguje ya harhada jakarshi daya baje kamar ya samu dakin gidansu, ya shiga ya sake watsa ruwa, yayi brush, saida ya kusan karar da kwalaben turare biyu a jikinshi, har tari ya dingayi. Sai yaba kanshi dariya, to me yake boyewa ne? Warin wiwin? Ko kuma kamshin matan da yake tunanin ya like masa? Me yasa yake boyewar? Alhaji Mustafa ne fa, daya nuna baya bukatarshi kwanaki kadan da suka wuce, amman yanzun daga ance zaizo ya daukeshi ya rikice, zuciyarshi har wani bugawa takeyi, kamar abinda yake ta jira kenan. Tare da Alhaji Mustafa suka koma, shi ya karbar masa jakarshi ya saka a bayan mota, sai direban daya kawo Alhaji ya dauki motar Haris din "Da ka kawo mukullin na tuka Baba" Haris ya furta a dan darare, Alhaji Mustafa ya kalle shi "Ni Haris? Zan baka mukulli ka tukani salon ka janyowa matana takabar da basu shirya ba" Sai yayi dariya, shima Alhajin dariyar yayi, suka shiga motar ya jasu zuwa gida, a hanya ne Alhajin yace masa "Me kake karantawa?" Haris yaji zuciyarshi ta matse a kirjinshi, shekara daya amman Alhaji Mustafa baima san abinda yakeyi a Italy ba, so yake ya bashi hakuri, sai dai bayar da hakurin ya zama wani abu da bai saba ba, baima san ta inda zai fara ba, muryarshi a hankali ta fito lokacin da yace masa "Documentary and photojournalism" Alhaji Mustafa yayi shiru yana juya ma'anar course din cikin kanshi, jin yayi shiru yasa Haris cigaba da magana "Ni hoto kawai nake so in dauka, amman dana fara karatun kuma inaso inyi abubuwa da yawa, inaso duk hoton da zan dauka ya zamana yana isar da wani sako ne, irin hotunan da tarihi ba zai manta dasu ba, watakila idan nayi sa'a har dani din" Yanajin shi, duk wata kalma da ta fito daga bakin Haris, Alhaji Mustafa yaji ta, a karo na farko yau danshi ya bude baki yana bashi labarin wani sashi na rayuwarshi, sai kuma ya zamana yana kokawa da fahimtarshi akan wannan sashin "Wanne irin hotuna ne wannan Haris?" Haris ya dan daga kafadunshi "Nima bangama sani ba har yanzun, idan nazo nace maka inaso in zama war photographer zaka barni?" Zuciyar Alhaji Mustafa ta buga daya hango danshi da ba soja ba, tsaye a filin yaki da camera a hannu, amman saiya tsinci kanshi da fadin "Zanyi maka addu'a, Allaah Ya tsareka ya baka sa'a a duk inda zaka shiga akan kuma duk abinda zakayi" Haris ya lumshe idanuwanshi, ya budesu wani sanyi da bashida alaka da AC din cikin motar na ratsa shi "Ina kuma so inyi harkar transportation..." Alhaji Mustafa ya sauke wani numfashi "Wannan dinma yafi kwantamun, na kasa hangoka a filin yaki da camera a hannu Haris" Dariya Haris din yayi mai sauti "Allaah dama bindiga ce da sauki" Haka suka dinga hira har Haris baiso suka karasa gida ba, da suka fita daga motar suka jera zuwa ciki saiya dinga jin inama ace Mukhtar zai leko, yau ya ganshi shine ya jero da Alhaji Mustafa suna hira Ranar ta zama mafari Ta kuma budewa Haris wata kofa da yake tunanin bashi da hanyar samun mukullinta a tare da mahaifinshi... #LubnaSufyan ✨ #WomenOfWords #09035723778 (WhatsApp) Littafin nan na kudine akan #1k kacal, zaizo a manhajar Telegram ne kawai 20/06/2025 In Shaa Allaah, bayan mun kammala shafukan dandano. Zaku iya biya ta: 9035723778 Opay, Lubabatu Sufyan. NAGODE. * LABULE...Asirin mai daki (Shafin karshe na dandano) 5 MARYAM Ba wani haske na azo a gani Maryam take dashi ba, mutane da yawa ma in suka kalleta kai tsaye ba zasu kirata da fara ba, tana da kalar fatar da yawancin duka yaran gidan Alhaji Sa'id suke da ita. Sai dai babu siririya kamarta, rashin jikin natane yasa ake ganin kamar wani tsayi take dashi, sannan ita din ma'abociyar son dogayen takalma ce, suma suna taimakawa wajen kara mata tsayin da bata dashi. Yau dai duk wanda yasanta kallo daya zaiyi mata ya gane tana cikin bacin rai, haka inka matsa kusa da ita, rashin haskenta ba zai hanaka ganin shatin yatsun Hajja akan kumatunta na haggu ba. Hijabinta a hannu ta dawo dashi yau daga makaranta saboda an yagashi tun daga wuya har kasa, uniform dinta da rigar ruwan madara, wandon kuma ruwan kasa, biji-biji kamar wadda tayi hakar rijiya, dambe ne kwasa a makaranta, tana da kawaye, ko tace 'yan ajinsu da suke shishige mata, ita bata cika shiga shirgin kowa bane saboda bata da hakuri, yau dinma wata 'yar aji biyar ce ta bangajeta da gangan, tayi magana ta zageta, ita kuma ta wanka mata mari, daman suna jin haushinta tunda tayi fada da kanwar yarinyar, da suke aji daya, shine su biyu sukayi mata taron dangi, a garin rabon fadan nema aka yaga mata hijabi. Dukan da akayi musu a makaranta na hukunci bai wani dadarata da kasa ba, inda sabo wannan ba komai bane ba. Hajja ce da bata tsaya tambayarta abinda ya faru ba ta hauta da zagi yayi mata ciwo, kuma dan tace "Ko gobe suka kara shiga shirgina sai sunji a jikinsu" Shine ta mareta, danma wai Khairi tana wajen tanata bawa Hajjan hakuri kamar harshenta zai tsinke, haka sauran 'yan gidan da suke nan suka janye Maryam din suna kara tausar Hajja, mai hakuri bai iya bacin rai ba, ga Maryam da kafiya, shisa in takai Hajjon bango ba karamin duka takeyi mata ba, fadan saiya nemi komawa kan 'yan gidan, wanda duk yayi mata magana a zafafe take mayarwa, duk suka tattara suka fita harkarta, ta samu waje can kan kujera mai zaman mutum daya ta takure jikinta, abincin daren da suketa hada-hadar shiga kicin suna zubowa ana dawowa falon kamar yanda aka saba ita bata tashi ba "Maryam in zubo mana?" Khairi ta tambayeta "Banaci" Ta fadi can kasan makoshi, AbdulKarim da yake jinsu, yake kuma ganin yanda Khairi din ta kasa sukuni tun shigowarshi yaja karamin tsaki "Ki wuce ki zubo abincinki kizo ki zauna kici kafin in kwadeki kema da kayan takaici, tun dazun kike binta tana shareki, ba saiki kyaleta ba da shegiyar zuciyarta ta banza da wofi" Murguda baki Maryam tayi, shigowar Alhaji Sa'id ta hanata maganar da ta bude bakinta zata fada, anata yi masa sannu da zuwa yana amsawa, itama can kasan makoshi tayi masa sannun, yayi dariya yana zama tare da fadin "Waya taba mun Auta ne yau?" Akasa dariya, lokacin kuma Hajja data fito da babban farantin data hado masa abincinshi ta karaso, Abdulkarim harya tayata ta hanyar janyo teburin da aka saba dora masa abincinshi akai ya ajiye, ita kuma ta dora farantin "Halan ke kika tabamun Auta yau" Tayi murmushi, Alhaji Sa'id ya sake cewa "Taho nan kinji Mairama, zo muci abinci tare, kina zaune duk zasu nemoki allura ai" Maryam din ta saki fuska tana murmushi "Waye zatayiwa allura? Wai Abba ka yarda yarinyar nan na da hakurin zama Nurse?" Asiya tayi maganar da mamaki "Ita ai ba Nurse take so ba, midwife tace...ko Mairama?" Da sauri ta daga kanta tana murmushi, ta kuma baro kujerar da take zaune ta koma kasa gefen kafafuwan Alhaji Sa'id "Midwife? Tafdin..." Sagir yace yana kashewa da dariya hadi da dorawa da "Irinsu ne masu marin mai nakuda" Aikuwa akasa dariya "Abba kana jinsu ko?" Shima dariyar yakeyi "Kyalesu, shima Sagir din kina zaune zai kiraki kizo ki taimakawa matarshi, zaki rama" Wannan maganar da Alhaji Sa'id tayi saita rufe bakin Sagir din da yaji kunya, tare dashi Maryama taci abinci sunata hira kamar ba ita bace take ta fushi, a cikin hirar ne da dabara yayi mata nasiha kan muhimmancin hakuri da kuma rage fada "Bakomai akayi maka zakace saika maida martani ba..." Tayi shiru tana amsawa da "In Shaa Allaah Abba" Kamar da gaske taji maganganun, bayan duk wanda yake falon yasan ta bayan kunnenta nasihar take shiga in dai Maryama ce. Washegari kuwa da sanyi-sanyi take shirinta, kunun gyada akayi musu da fanke, an kuma yi kosai ga wadanda fanken bai damesu ba, ita duka biyun tanaso, dan in akayi fanke har diba takeyi ta tafi dashi, amman yau ko surutun da take damun kowa dashi batayi, tunda taga yanda garin yayi bakikirin alamun hadari taji komai ya fice mata daga rai "Season din mutuniyar fa ya kama, yanzun bakin kowa zai huta" Tanajin Asiya, bata da lokacinta, tunda har daki ta samu Hajja tace mata tana zazzabi, ko zata samu dalilin da zata fasa zuwa makaranta, sai tace mata "Allaah Ya saukaka, saiki nemi paracetamol kisha, ki jefa wani a jakar makarantarki ki tafi dashi" Ita Hajjan abin mamaki yake bata, tana tunanin tun Maryam na da shekaru biyu a duniya duk lokacin da za'a fara ruwan sama taji kararshi zata firgice ta saka ihu, har saida akayi zaton ko akwai shafar jinni a lamarin nata, haka aka dinga kawowa Hajjan hayakai da rubutu iri-iri, musamman dangin Alhaji Sa'id da suke neman fada a wajenta, harda garukan magani, ta karba da godiya, rubutun tasa aje a juye cikin kasa, magungunan kuma ta watsar. Tana girma suna gane kara tabbatar da babu wani Jinnu da suka shafeta, ruwan saman ne kawai take tsoro, koma ace duk wani ruwa da Maryam take ganin ba zata iya controlling ba. Da hankalinta sau daya ta taba zuwa saloon, shima haka ta kullo kan da kumfar da komai ta dawo gida ta karasa wankewa. Dan suna kwara mata ruwan farko taji tana neman shidewa saboda yanda ta firgita. Ruwa ko a cikin fina-finai za'a nuno teku sai taji hankalinta ya tashi, tsoro ya shigeta, su basa tsoron su fada su mutu? Khairi ta taba ce mata "Ruwan teku, su kogi da sauran ruwa daban fa Maryam, shi ruwan sama in ba Allaah Ya kawo annobar ambaliya ba ina kika tabajin wani ya nutse a cikinshi?" Saita harari Khairin "Idan kuma na santsi ya kwasheni na fadi, na buga kai, ruwan ya dinga sauka akaina ina shaqewa harna mutu fa?" Dariya Khairi tayi ba 'yar kadan ba ranar "Nifa gabaki daya na rasa me yasa bakwa tsoron ruwan sama" Cikin dariyar Khairi tace "Ke dai zance na rasa dalilin da zaisa ruwan sama ya dinga baki tsoro" Ta jinjina kai "Ai dalilin tsoronshi ya ninka rashin dalilin, ko kin manta tazarar tafiyar shekara nawa Mu'allim yace tana tsakanin sama da kasa ne? To ace tun daga can ruwan yake saukowa harmu samu, shi kadai ba abin aji tsoro bane ba? A karajin tsoron Allaah, balle kuma ace ruwan ya taho da iska, tsawa da cida, idan ina tsaye a fili akayi tsawar ta fado kaina na soye kuma fa? Ko ke kukan kwana daya zakiyi, a ranar ma kina iya cin amanata in dai za'a kawo shinkafa da miya, tsaf zaki share hawayenki ki saka plate a gaba" Dariyar dai Khairi ta cigaba dayi, abubuwan da Maryam take tsoro a duniya, tasan ba masu yawa bane ba, in aka daga yatsun hannu ma za'a iya kirgasu, sai dai tsoron da take yiwa ruwan sama har tausayi take bata, saboda in akace damuna tayi to kusan ko da yaushe idanuwan Maryam din cike suke da firgici mai yawa, inda Khairi na da iko to zatace a dinga kyaleta tanayin zamanta a gida kamar ranaku irin na yau da duk wata alama ta nuna cewar ruwan sama za'a sheka, in dai zaka zauna da Maryam na yini daya a lokacin damuna saika fuskancin tsoron nan a tare da ita, ko fada bata cika yi ba, bata dama kuzari ne ko kadan. In akace ruwan dare akeyi ko baccin kirki bata iyawa, farkawa goma Khairi zatayi zasu hada ido tunda kunna fitilar dakin takeyi ta koma can karshen gadonta ta takure kamar wadda take tsammanin shigowar 'yan fashi. Yanzun ma haka ta saka uniform kamar an zare mata lakka, tana ta kallon kowa ne zuciyarta batayi mata dadi. Adnan ne zai kaisu makaranta, saiga Alhaji Sa'id yama rigashi fitowa yace shi zai kaisu "Abba ni zazzabi nakeyi" Maryam ta fada kamar mai shirin yin kuka, daman hannunta a cikin na Khairi suka fito "Zazzabi dai, ko na ruwan sama?" Khairi ta danne dariyarta, idanuwan Maryam suka ciko da kwalla "Babu abinda zai faru kinji, baki ga nine zan kaiku makarantar ba yau..." Ita dai inda za'a barta zatayi zamanta a gidane "Abba kaine zaka kaisu makarantar bayan duk gamu nan?" Muryarshi ta fara isa kunnuwanta, wani dumi ya lullube ilahirin jikinta kamar an rufa mata bargo, ta tsinci kanta da sake dumtsa hannun Khairi da take rike dashi kafin ta daga kai a hankali, bakar rigace mai laushi a jikinshi data kara haska farar fatarshi "Ai duk na hutar daku Ishaq, yau ni zan kaisu" Murmushi ya danyi, ko tace labbanshi ne kawai suka motsa, kuma sai ya zabi ya saka idanuwanshi cikin nata "Ina kwana" Ta furta akan labbanta dan ko sauti ya fito ita bataji shi cikin kunnuwanta ba, sai ya kara fadada murmushin shi har hakoranshi na bayyana "A dawo lafiya" Yayi mata maganar irin yanda tayi masa, a karo na farko sai taji yau inda ruwan sama zai balle, kuma ace daga ita saishine a filin tsakar gidan nan, in dai har zai tsaya yanayi mata murmushi haka to zata tsaya a kasan ruwan nan tare dashi. Haka ta shiga mota, shikuma yana tsaye a tsakar gidan har sai dai motarsu ta fice, yana barin Maryam da tunanin ko yaushe yazo gidan? Ita dai harta kwanta jiya bata ganshi ba, a gefe daya kuma tana fatan Allaah Yasa harta dawo makaranta bai tafi ba, dan haka kawai tana so ta kara ganinshi. * Tasan ana biki gidan Alhaji Mustafa, bikin Munira,a bakin Hajja ma ta fara ji, kafin ta dinga ganin katikan bikin na watangaririya har a falon gidan, alamun an badasu da yawa, harda irin gate pass din nan na dinner din da za'ayi da kuma na wajen kamu. Da ta gani saita tabe baki, a ranta tana raya "Waye zaije bikin wannan bakar yarinyar mai bakar zuciya" Ai taga kokarin Hajja da take ta faman zarya tun ranar laraba, har wani anko akayi musu, yau ranta baya mata dadi tunda akace za'aje wajen bikin dasu, ita da tayi niyyar kwanciya tabi lafiyar gado tunda babu Islamiyya, wani littafin Hausa ne ta sato a dakinsu Adda Maimunatu, tasan cikin tsofin na Adda Zahra ne kafin bikinta, dan itace mayyar karatu, da yake Hajja bata hanasu, kawai dai wani lokacin zatayi ta fadane in karatun ya hanasu tashi suyi aikin da yake gabansu. Sai dai kusan duk yayyensu maza basa son ganinsu da littafin Hausa, Yaa Khalifa ma yagawa yakeyi, in bakayi wasa ba saiya kwadeka kafin ya kwace littafin, shisa inta dauko saita shige dakinsu ta kwanta ta karanta. Karatunma saita rasa abinyi takeyi dan ba damunta yayi ba, inta cika kallon takardar sai taji idanuwanta sunayi mata yaji. Duk da haka gara suyi yajin da taje wajen bikin nan, bata da yanda zatayi, haka suka shirya, duk surutun da Khairi ta dingayi bai hanata daukar wani farin hijabi ta zunduma ba, ita da saka hijabi bai dameta ba, cikin wadanda ta ware ne na sallah, sai dogon takalminta. Ko Hajja data ganta saita girgiza kai kawai batare da tace mata komai ba. Mota biyu aka daukesu a ciki har Tudun Wada, taji Hajja na cewa in sunje can sai a daukesu tare da yaran gidan a wuce dasu inda ake kamun bikin. Ita dai Maryam lokaci zuwa lokaci saita tabe baki. A bangaren Umma Fadime suka yada zango kamar yanda suka saba, har mamakin yanda su Kubra suketa dokin bikin takeyi, zaka rantse wani muhimmancin suke dashi wajen Hajiya Rumanan dama yaran nata. Ita dai ido ma take ta binsu dashi, gara da Adda Aliya ta shigo, itace babbar 'yar Umma Fadime, kuma jininsu ya hadu matuka da Maryam, tayi aure, bata haihu da wuri ba, yarinyarta daya, Huda, duka shekarar yarinyar biyu "Wai ke nan kikazo kika wani takure" Tayi dariya har hakoranta suka bayyana "Tunda naganki dan Allaah taso ki shiryamun Huda, makotana ne suka zo inaso in zuba musu abinci" Sai ta tashi kuwa, ta cire hijabinta ta ninke, tana bin bayan Adda Aliya, duk wannan dacin ran da takeyi yabi iska, da Khairi ta ganta dariya ta dingayi, Maryam din na mata kama da wadda ba zata rasa iskokai ba, su hau su sauka. Kuma saboda Adda Aliya da ta dauko mata mayafi ta bata sanda za'a tafi wajen kamun, ta ninke hijabin ta saka a jaka ta karba "Haba ko kefa, kamar ba 'yan mata ba, inace kun shiga ss1 yanzun, ke da nake so nan da shekara biyu ace mun naki bikin zamu sha..." Maryam ta sunkuyar da kai tana dariya a kunyace "Kai Adda..." Adda Aliya ma dariya tayi "Ko kema karatun zaki tsaya? Yarinya kiyi aurenki, ba gamu ba, auren ya hanamu karatun ne? Allaah dai ya fito muku da mazaje nagari" Sai ga Maryam ta tafi wajen kamun da tunanin maganganun Aliya fal a ranta. Wai itace zatayi aure? Su duk bikin da akayi a gidansu babu wanda akayi party, harna matan, amman ana shirya Kamu, wannan Abba baya hanawa tunda taron mata ne, ko 'yan uwansu maza basa zuwa wajen. Kuma yana kayatar da ita, sai dai haka kawai taji inda ace za'ayi partyn ma tanaso, ko irin wannan kamun da sukazo, akwai maza da mata a wajen, sannan ita Munira din tasha shigarsu ta gargajiya ta Kanuri, a karo na farko tayiwa Maryam kyau, ga angon daya riko hannunta shima ya hadu, bakine kamarta, dogo sosai, dan duk da takalman da Munira tasa kanta bai karasa kafadarshi ba. Itama ace haka zasu shigo wajen taro da nata angon, kuma wai saiga tunaninta ya hasko mata Ishaq, zuciyarta tayi wata irin bugawa, musamman data hangeshi da farar shadda kal, ya zaiyi a cikin fararen kaya? Tama taba ganinshi da fararen kaya kuwa? Zata so ta ganshi da fararen kaya, ta tabbata zaiyi kyau. "Yau sai Munira tayi mun kama da Haris" Wata da suke zaune a teburi daya ta fada, dan Maryam ta zauna inda Adda Aliya take ne "Kai haba dai? Aisu suna kama da Baba ne kamar mu, shikuma Haris kamarshi daya da Mami..." Cewar Adda Aliya, maganganunsu na kutsawa cikin tunanin Maryam, sai ta sake kallon Munira, ta kuma kalli Adda Aliya da take jajur kamar ka taba jini ya fito, dariya ta kusan kwace mata, taya ma za'ayi ace suna kama da juna? Ko kuma ita Munira na kama da Baba, ko dai ba Baban Tudun Wada take nufi ba? Kawai dai tace daga Munirar har sauran 'yan uwan nata, dashi Haris din na kama da Mamin shine abinda zaifi kama hankali. "Wai baizo ba Haris din?" Adda Aliya ta girgiza kai "Ba zai samu damar zuwa ba, yana Italy" Tunda Mami bata gajiya da fadawa duk wanda zai saurara cewa Haris baya kasar tun da ya tafi, har sun gaji, musamman da aka fara taron nan, zakaji tana "Dan kiramun lambar Haris, ta Italy din" Abinma dariya zai baka, in kaga yanda takeyi sai kayi zaton akwai bakon ketare Najeriya a cikinsu, musamman ita Hajiya Rumanan da karatunta ma kacokan a kasar waje tayi, ko dan Haris din ya zamana mutum na farko daya bar kasar da sunan karatu shisa abin yakeyi mata dadi oho. Maryam dai baki ta tabe, in ba dole ba ko maganarsu batason ji, tasan matar ba wani sonsu takeyi ba, koma tace ba son kowa takeyi ba, itama kuma batare da wani dalili ba tun asali batayi mata ba, daga ita har bakaken 'ya'yanta. 6 HARIS "Hello Babaa" Kalmomi biyu ne kacal, amman a wajen Haris suna da nauyin kalmomi dubu da doriya, har so yakeyi inya furta wani ya juyo ya kalle shi, shikuma ya fadada murmushin da baya barin fuskarshi, kamar yace "Babana ne, Babana ne ya kirani, da Babana nake magana" Shi baisan adadin son da yakeyiwa Alhaji Mustafa yana da yawa har haka ba sai yanzun, bambancin awa dayane tsakanin lokacin kasar Italy da kuma nan Najeriya, sunfi waya da daddare, a lokacin bayan isha'i a wajen Alhaji Mustafa, a wajen Haris kuma karfe tara ne da wasu 'yan mintina "Ya makarantar? Ba dai ka bukatar komai ko?" Haka zasu kusan awa suna waya Haris na bashi labaran darussan da akayi musu a ranar batare daya tabbatar ya fahimci duka abinda yake fada din ba, shekaru biyu ake neman hadawa yanzun, amman harshen shi ya riga ya fara sauyawa ta yanda ko waya yakeyi da 'yan gidansu saiya dinga tsintar kanshi da jefo kalmomi da yawa da yaren kasar, tunda ko turanci ba sosai yake shiga tsakaninshi da Logan bama, shima yaren yakeyi masa kamar kowa na kasar. Idan gidan Alhaji Modu yaje can dinma bata sauya zani, mafi akasarin zuwanshi saboda Aise ne. Tun randa ya fara ganinta batayi masa kama da 'yar shekara sha uku ba, yanayin jikinta, maganganunta da wayonta duka, yanzun kuma a shekaru goma sha biyar, Aise tasan me take so tayi da rayuwarta, tana da wani irin wayau da baisan ko halittarta bane ko kuma yana da alaka da tashin da tayi a kasar waje. Soyayyar daya sani ba wata mai yawa bace ba, shisa ya tabbatar da abinda yakeji akan Aise soyayya ce, irin soyayyar nan da bata bukatar a zurfafa tunani a cikinta, ko wata mace ta burgeshi saiya tsinci kanshi da hasaso Aise yana hadata da wannan, yana kuma tsince bambancin da yake tsakaninsu. Yanda suke kiran Binta da Mamma shima haka yake cewa, Alhaji Modu ne kawai yake kira Uncle saboda ya riga ya saba haka yake ce masa. Sun hadu da Kham, haduwa marar adadi, shima bashi da wata matsala. Da yake ma ba hayaniya yake da ita ba, ba miskili bane ko wani abu, kalmomin shine ba masu yawa ba, zaku iya wuni tare da Kham yana danna waya baice maka komai ba. Shisa ranar da ya fita wani dan lambu da Mamma take dashi a bayan gidan, yana busar hayakinshi, ko da Kham ya same shi a wajen baiji dar ba, shima kallo daya yayi masa ya dauke kai yana cigaba da wayar da yakeyi, harkar duk da bata shafi Kham ba baya shigarta. Da yake Mamma na aiki, itama tana wuni bata gidan, in yazo sai dai ta barsu su kadai shi da Aise inta dawo makaranta, yasha ganinsu Haris na zaune akan kujera, Aise tana kwance tayi pillow da cinyarshi, ko kuma tana zaune amman ta nade jikinta ta kwantar a nashi, sai anyi sa'a ma yake musu magana in ba wani a cikinsu ya gaishe dashi ba. Har a zuciyar Haris babu wani abu banda tarin soyayyar Aise da burikan da yake dasu a kanta, in zai rike hannunta sau hamsin wani tunani bai taba gifta masa ba, kawai tana cikin matan da yakejin yana son karewa daga wani abu da bai kamata ba, ciki kuwa harda shi kanshi da gurbataccen tunanin da zai iyayi, sonta yake, so na gaske. Amman ranar da Mu'adh din daya manta sunanshi ya diro kasar Italy, bama a jikinshi yaga Aise ba, a tsaye suke, da tufa a hannun Aise din da take ci, sai yake kokarin karba, ya kwace ita kuma ta riko masa hannu, wani irin kallo ya watsa mata daya sata sakin hannun Haris babu shiri, kafin ya fara mata fada cikin harshen larabci, ta wuce da sauri idanuwanta cike taf da hawaye "Haris?" Cewar Mu'adh yanayi masa wani kallo mai cike da fassara kala-kala, sai Haris din ya harde hannayenshi a kirji shima yana zuba masa nasa idanuwan batare daya amsa tambayar da yaji a muryar Mu'adh din ba "Karka sake riketa, ina nufin karka sake tabata, ina fada maka ne saboda ita ba zata sake ba, kai ya kamata ace ka zama mai hankalin..." Da yaren Italian yayi masa maganar, yana kuma wucewa batare daya jira amsar Haris din ba. A wannan ranar Mu'adh ya shiga cikin jerin mutanen da Haris baya so, kamar yanda ya shiga jerin na Mu'adh din. A shekaru biyun nan da baizo gida ba, babu wani labari na Haris da baiji ba a bakin Aise, a yanayin yanda take bashi labaran ne kuma ya karanci cewar Haris ya wuce matsayin dan uwa a wajen Aise, Haris yana burgeta, shikuma hakan bai kwanta masa ba, yanzun daya dora idonshi akan Haris dinma sai ya kara fita daga ranshi. Daya gama shiryawa yayi wanka ya sake kaya, yaso ya dan fita ne ya nemi abinda zaici, amman bayason barin Aise ita kadai a gidan, kar Haris daya fita ya sake dawowa. Ita yaje ya samu tayi masa order din abinda zataci, yasan wacece kanwarshi, wata nasiha ko lallami baya aiki a kanta, shisa ya fito mata sak, yaja mata kunne sosai akan zasu raba hanya, zai bata da ita idan ya kara ganin ko da dan yatsanta ne ya kai jikin Haris, harda hawayenta ta dinga bashi hakuri, dan sunfi shakuwa dashi akan Kham. Da Mamma ta dawo ma da fara'arta shi Mu'adh ranshi a bace yake "Mamma Aise takai shekarun da komu 'yan uwanta idan ba lalurar data zama dole ba, bai kamata ace ana barinta a gida daga ita saimu ba balle wani wanda ba Muharraminta ba..." Tayi murmushi, a kasar Italy ta haifi duka yaranta, sunyi kokari wajen saka su a Islamiyyar da suka samu, sai Mu'adh yafi kowa maida hankali akan addini, tun tasowarshi yake da son addini matuka, haka yake yawan fada musu cewa shi burinshi ya zama daga cikin manyan Malaman da za'a bada labarinsu wata rana na cewar sunyiwa addini hidima, haka zai dinga saka su a gaba da wa'azi in yaga sunyi wani abu daya sabawa addini, ita kanta Mamma din, kudi da wayewa yayi tasiri a kanta kamar dai mijinta, Mu'adh ne yayi tsaye wajen ganin tana suturta jikinta yanda ya kamata, hakama ya hanata karin farce, da yake macece mai son yaranta kuma mai saukin fahimta da karbar kuskure idan an gyara mata "Za'a kiyaye Ustaz Mu'adh, kaga shi Haris dinma bawai yana zaune anan din bane ko yaushe, yana makaranta abinshi, sai yayi watanni baizo ba, in yazo dinma baya wuce kwana biyu" Ya dan saki fuska "Ko yini yakeyi bana sonshi su kadai a gida, dan Allaah Mamma" Ta sake fadada murmushinta "Ai nace za'a kiyaye, zo nan, kanata mita ko gaisawa ba muyi ba" Shima murmushin yayi ya karasa yana rungumarta hadi da sumbatar goshinta da kunci tukunna ya zauna a gefenta. * Washegari da yamma Haris yayi musu sallama ya dauki jakarshi, wani coffee shop suka samu shi da Aise da sun riga sunyi magana zasu hadu a wajen saboda Mu'adh, ta kasa hakuri saida ta rungume shi kafin suka zauna "Nasan dukanmu muna da tarin abubuwan da suke gabanmu, ban taba furta miki ba, amman banajin ina bukatar ince miki ina sonki Aise, ba so bane da nake so mu fara shi batare da ya kaimu ko ina ba, ina miki son da duk wani plan da nake dashi saina hango ki a ciki...amman bamu da lokacin wannan soyayyar a yanzun, duk mun sani..." Ta daga masa kai, zatayi karya idan tace bata taba son wani, ko wani ya burgeta ba, aiko a ajinsu ma tayi samari wajen hudu suna batawa, hakama wanda suka wuceta aji, duka ma babu musulmi ko daya a ciki, sai dai wannan soyayyar shiririta ce akan abinda takeji kan Haris, idan taga biki, idan ana maganar biki, ita dashi take hangowa tare anayin nasu, kamar yanda yace tana cikin plans dinshi itama yana cikin nata, tana ji a jikinta soyayyarsu bata bukatar gaggawa, a hankali za subi komai, yanzun ne zata gama high school dinta tunda tana finals nema, kuma fannin data zaba na lafiya fanni ne da tasan yana bukatar duka natsuwarta, ba zata samu lokacin rabashi da wata soyayya ba "Ina so insan cewa Mu'adh baya cikin abinda zai bani matsala dake Aise, ina so in san wannan" Idanuwanta ta saka cikin nashi "A yanzun, ko a gaba, ko da Mu'adh baya sonka in dai ni ina sonka baka da matsala" Haris ya sauke numfashin da baima san yana rike dashi ba, wannan maganganun da tayi zasu rikeshi, sunma isheshi a yanzun. Ta ina ita dashi zasu hango suna bukatar Mu'adh din? Sunfi awa daya suna ta hirarsu da bata taba karewa, tukunna yayi suka fito kowa ya kama hanyarshi tunda daman makaranta zai koma, ita kuma zatayi gidane. A halin yanzun dai, a wajen Haris bayajin yana da wata matsala ko guda daya, zasuyi waya da Alhaji Mustafa kullum, zasu hira, haka ma Hajiya Rumana. A cikin hirarrakin nasu nema Alhaji Mustafa yake yawan nuna masa yanda yake son ace yana magana da sauran 'yan uwanshi kamar yanda yakeyi dasu Munira. Yaji wani yanayi ya saukar masa, shifa in suna da wayoyi ma to bashi da lambarsu "Bani da lambar kowa a cikinsu Baba" Suna gama wayar ya aika masa da lambar Aliya, sai dai yaji nauyin ya kirata, ya tura mata da sakon text yana gaya mata shine tayi saving lambarshi, kamar kuma a lokacin wayar na hannunta ta maida masa da reply harda godiyar nemanta da yayi, saida murmushi ya kwace masa. Daman haka mutum yakeji a lokacin da baya hangowa kanshi kowacce irin matsala? To daga matan har wiwin shi babu wanda yakeyi masa wahalar samu in bukatarsu ta taso, gashi abinda ranshi yake so shine yake karanta, duk sanda zaiji camera a hannunshi nishadin da yake shiga ba dan karami bane ba. Sannan a gefe guda, nan da wasu 'yan shekaru in yaso ya natsu waje daya, da mace daya, ya samu nashi iyalin juyawa kawai zaiyi ya mikawa Aise hannun shi. Ko kadan baiyi hasashen akwai yiwuwar idan ya mika hannun wata daban ta saka nata a ciki ba... Yanda Haris yake a kasar Italy yana hango filin rayuwarshi sambal batare da komai da zai iya cin karo da mafarkanshi ba, haka Maryam take nan gida Najeriya, garin Kaduna da nata mafarkan da take tattaunawa da 'yar uwa kuma mutum daya tilo da zata bugi kirji ta kira da kawarta, wato Khairi "Nifa idan zan samu gurbin karatu a BUK zanfi son hakan, kinga sai inyi BSc dina a Midwifery ba saina wahala ba..." Khairi ta jinjina mata kai "Nifa irin wahalar da naga su Adda sunci wajen neman BUK yasa gwiwata tayi sanyi, sannan banason in tsaya jiran wata university bansan ko ina da kaddarar auren wuri ba, kaje karatu ya hade maka da hidimar gida ko mijin ma ya hanaka karatun, yar diplomar nan ta gagareka hadawa" Sai kawai Maryam ta kwashe da dariya "Meye abin dariya yanzun?" Cewar Khairi "To ai wani zancen naji kinayi, wai miji ya hanaka karatu..." Muryar Khairi da damuwa tace "Wallahi anayi fa, kinsan Mansura ta ajinmu ai? To yayarta da tayi aure haka mijin yace ba zata kara zuwa makarantar ba, gashi tana level 2" Da madaukakin mamaki Maryam take kallon Khairi "Wai da gaske? To ita kuma sai ta daina zuwan? Saboda bata da hankali...lallai ma, tafdin, ya latsa yaji da laushine shisa..." Khairi ta kalleta kawai "In yace ba zataje ba sai tayi yaya? Ai dole ta hakura, mijinta ne fa" "Mijinta ubanta ne? Ko shine yake biya mata kudin makarantar da zaice ya hanata karatun? Ai na gaya miki, raini ne kawai ba wani abu ba, Astagfirullah waye ya isa yayi mun wannan latsin..." Tunda duk matan gidan nasu da sukayi aure batare da sun karasa karatunsu ba, har yanzun Alhaji Sa'id ne yake daukar duk wata dawainiya tasu data shafi makarantar, ko da kuwa mazajen sun nemi zasuyi baya yarda, kowa a gidan ya sani, shisa ita Maryam tayi tunanin duk wata mace da take cigaba da karatunta bayan aure kawai iyayenta ne suke daukar dawainiyar karatun nata. "Ke dai kiyi shiru da bakinki, kuma karki tsaya jiran wata university...duk inda kika samu kawai ki karba kiyi karatun shine mafi muhimmanci" Maryam ta tabe baki "Aiko dai ban samu university ba kinsan ba zan fada ko ina ba saboda inaso inyi karatu ko in fara kafin inyi wani aure..." Asiya data shigo kitchen din ta samesu ta katse maganar ta hanyar kaiwa Maryam din mangari,fere dankali Hajja ta sakasu, suna zaune dirshan a kitchen din "Firar dankalin kenan, wato ku 'yan tsigi-tsigi daku har kunsan wani zancen aure" Maryam ta makawa Asiya harara kamar idanuwanta zasu fado "Kinga Adda banason irin abin nan, na gaya miki, Abba ma yace ki daina mun, yanzun idan nace zan rama sai kuma kice nayi miki rashin kunya" Wani mangarin Asiyar ta sake kai mata tana kaucewa hadi dayin maganganu kasa-kasa "Zagina kike ko? Sai naci kaniyarki ai, marar kunya, ke kuma Khairi harda ke kuke hirar aure ko? Saina fadawa Hajja" A tsorace Khairi tace "Wallahi ba wani abu marar kyau mukace ba Adda, muna hirar makaranta ne nake ce mata gara duk inda muka samu mu tafi..." Nan Khairi ta kwashe maganganun da sukeyi din ta fada mata "To ku ko auren ne yazo meye zai dameku? Waye kuka taba ganin a gidan nan anyi masa aure bai cigaba da karatunshi ba? Ai kunsan Abba ba zaiyi muku haka ba, ke Maryam ma ai baki da wata matsala tunda na gidane" Su duka suka daga ido suna kallon Asiya saboda yanayin yanda ta karasa maganar da wata dariya "Bangane bani da matsala ba? Meye na gida?" Dariyar dai Asiya ta karayi "Ba Yaya Ishaq bane ba? Ai kinsan babu yanda za'ayi ya hanaki karatu" Zuciyar Maryam ta buga, ta kara bugawa, ta tsaya cak da firar dankalin dan a yanda jikinta ya amsa da maganar Asiya tsaf zata iya fere yatsa a maimakon dankalin "Shi Yaya Ishaq dinne yace ni zai aura?" Ta tsinci kanta da tambaya cikin wata karamar murya "Kunji dashi dai, inya gama zagaye-zagayen saiya fada miki da bakinshi, ai inajin kowa ma yasan zaryar da yakeyi tsakanin Zaria da Kaduna taki ce a gidan nan, wani zuwa yakeyi da?" Asiya ta karasa tana daukar saka hannu cikin robar da suke zuba dankalin hausar ta tsami guda biyu manya ta fice daga kitchen din, Khairi data kasa daina murmushi tace "To kinga saiki fara girmamani kina yimun biyayya yanzun tunda zamu zama surukai" Duk da maganar ta saukarwa da Maryam din wani irin sanyi, har saida ta kasa boye murmushinta, sai tace "Ko ba surukai ba? Kema yarda zakiyi da maganar Adda? Yaushe Yayan yace zai aureni? Kuma ko da mun zama surukai ai kece zaki dinga ce mun Anty ma tunda zan zama matar yayanki" Khairi ta dibi ruwan dankalin da hannu tana watsawa Maryam da take dariya, haka kawai farin ciki ya gama mamayeta, tasan da gaske ne yanzun Ishaq na yawan zuwa gidansu, ko da kwana daya ne kuwa, kuma haka zaizo falo yayita janta da magana, tun tanajin nauyinshi saboda abinda takeji in yana mata maganar har yanzun ta fara sabawa dashi, amman aiko da alama bai taba nuna mata wata soyayya ba? Ko dai itace batasan soyayyar ba? In dai irin wadda akeyi a littafi ce bata ga alamarta a tare da Ishaq ba, haka ta film ma, yafi kulata akan Khairi tabbas, amman ai a cikin littafi haka saurayi zai dinga shakaro siyayya iri-iri yana kawowa budurwar da yake so ko da bai furta mata ba. Shikuwa me ya taba siyo mata? Sai wata zuciyar ta saka mata ai shidin dan makaranta ne, yanzun nema zai shiga aji uku, meye zai siyo ya kawo mata tunda bashi da aiki, har Hajja ma ta ga idan yazo tana bashi abubuwa, watakila sai nan gaba kadan idan ya samu kudinshi zai fara yi mata irin wannan siye-siyen, harma ya bude bakinshi yace mata "Maryam ina sonki" Ta karayin wani murmushin mai cike da nishadi, aikuwa da kowa bai huta ba, da tayi kawaye masu tarin yawa dan suzo wajen bikinta suga irin mijin da zata aura, ta karayin wani murmushin kawai. Kuma kamar Ishaq ya hangi zuciyar Maryam a wannan ranar, daya sake zuwa sai gashi da wata babbar leda shakare da kayan marmari, falon nasu a cike yake, amman haka ya karasa ya mikawa Maryam yana fadin "Kanwata ki cire duka guava din dake ciki taki ce, nason kina sonta saiki basu sauran" A kasa ta ajiye ledar bayan ta karba saboda wani irin nauyi na musamman da tayi mata, duk wani surutu da akeyiwa Ishaq din baya karasawa kunnenta, saima da Khairi taso karbar ledar ne ta janye, haka ta saka hannu tayi abinda yace cikin sanyin jiki, idanuwan Hajja yasa ta raba guava din nan gida biyu ta ba 'yan gidan rabi, tanajin kamar ta raba wata kulawace da Ishaq din ya wareta ita kadai ya damka mata tare dasu, zuciyarta tayi mata nauyi matuqa, data kwashi sauran sai tayi daki, bata ma ko tuna ya kamata ace ta wanke ba, ta daga guda daya takai bakinta ta gutsira, irin manyan nan ce koraye da ba zakayi tunanin zasuyi zaki ba, idan ma babu zakin Maryam bataci ba Asalima tunda take bata tabacin guava da tayi mata dadin wannan ba Ishaq ne ya kawo mata, da tunaninta ya siya Akwai wani zaki da take bukata bayan na kulawarshi? 7 Kaso mafi yawa na iyaye, tun kafin amsa sunan suke da tarin burika akan yaransu, a cikin wadannan burikan bai wuce ace a taron yara dubunnai nasu su kasance sune taurarin da haskensu zai dishe na kowa. Musamman uwa da in tayi aure, sai aka wayi gari tasan da shigar ciki a jikinta, duka rayuwarta take tsaya, a wannan lokacin ko faduwa tazo yi ko wani abu na cutarwa ya tunkarota, zuciyarta zata fara sanar da kwakwalwarta, abu na farko da zata farayi shine kare cikinta da hannayenta, cike da fatan koma menene ya tsaya akanta ita kadai, karya taba abinda yake cikinta, sanda zai fito duniya kuma saiya zama kamar bata taba wata rayuwa kafin zama uwa ba. Idan ma ta zauna tana tunanin rayuwarta kafin ta haihuwa, takanji kamar wani lokaci ne mai tsayi, wani lokaci daya shude yake neman bacewa har a cikin tunaninta. A wajen iyaye irin Hajiya Rumana, wanda suka samu haihuwar a lokacin da suka fara karaya, suka fara hangen zasu mutu batare da dacewa da irin wannan rabon ba, ba iya rayuwarsu suke mikawa yaransu ba, da yawansu harda wani kaso na ruhinsu, ita dai wannan kason ne yafi yawa akan Haris, Munira tayi aurenta, tasan ko da yaushe Anisa ma ko da yaushe miji yazo aurenta zatayi, ana cewa 'ya'ya mata sune na iyayensu har abada, ita batajin haka. Da wayonta ta rasa iyayenta, kuma ko suna da rai, a halin yanzun, a yanda takeji ita din ta iyalanta ce, mijinta da yaranta, ko da iyayenta na da rai kyautatawa ce a tsakaninsu da ziyara lokaci zuwa lokaci, mata ai rayuwarsu tare da iyaye tana farawa ne daga haihuwa, ta kuma kare daga ranar da aka damkawa mijinsu, suna kara nisanta da wata rayuwa ne duk rana, balle idan sun fara tara yara, to a tsakanin hidimar yara data miji sun nemi kansu sun rasa, ita tanajin babu ma wani abu da yayi saura, me ake tsammanin zata ba wani? Ai a wajen Hajiya Rumana, a kuma tunaninta, Haris shine nata, shine nata har abada, ko aure yayi matarshi ta haihu yaranshi sune zata bugi kirji tayi iko dasu batare da wani ya daga mata hankali akan hakan ba. Shisa take da tarin burika akan Haris din, ita kadai idan ta zauna sai ta dinga tsare-tsare akan yanda take fatan bikinshi zai kasance, shagulgulan da zatayi, yanda zata tayashi zabin gidan da zai zauna, a yanda tasan Haris ma da son da yakeyi mata, idan ta nemi su zauna a Kaduna, kusa da ita ba zaiyi mata musu ba "Anya Mami?" Shine abinda yakan fadi idan ta nemi yayi wani abin da bayaso "Haka nake so ayi Haris, ko ba zan samu ba?" Wannan maganar, kalmomi goma kacal, wata rana sai yayi mata murmushi ya kada kai kawai, wata rana kuma fuskarshi babu walwala zaice "To Mami" Amman dai ko da bayaso, ko da yayi mata musu, karshe abinda take so dinne zaiyi. To haka zatayi masa magana akan zaman Kaduna, idan ma aikinshi wani gari ne ko wata kasa, iyalin ya bar matasu anan Kaduna shi saiya dinga zuwa, ikon da ya kwace mata akan Munira da wanda tasan zai kwace mata akan Anisa ko wanne lokaci, batayi wani yunkuri akai bane saboda tasan tana da Haris, zatayi yanda take so akan Haris. Wani abu da yake kara sanyaya mata zuciya shine kusancin da take gani tsakanin Alhaji Mustafa da Haris, shisa lokacin da yake fada mata Mukhtar zai tafi Madina sai ma tayi murmushi tana fadin "Ma Shaa Allaah, abin ya tabbata kenan, Allaah Yasa albarka, yaushe zai tafi?" A karo na farko a rayuwarta, da yayi mata tayin rakiyar Mukhtar din bataki ba, kuma bata damu da yanda zuwan nata yasa Fadime da yaranta duk suka sha jinin jikinsu ba, kamar ta takurasu, kamar ta tare musu wani kaso na walwalar da ya kamata ace sunayi, murmushi ma tayi, to aiko Fadimen ma tun da aka aurota take kiyayarta balle kuma yaranta da suka taso da tsoronta fal ransu, tunda ita tazo ta aure mata miji rana daya. Ita kam yanzun duniyar dadinta takeji, abunuwan da suke damunta kuma basu da wani yawa, watakila shisa ma kwanakin dake ta hadewa suna tashin wata, zuwa shekaru ba suyi mata wani tsayi na azo a gani ba. Musamman da a cikin shekarun ta mika Anisa dakin mijinta, taso ace itama ta auri dan uwa kamar yanda Munira tayi, tunda akwai da yawa da suka nuna suna sonta daga bangaren Hajiya Rumanan, a wannan gabar ma har dan Kanwar Alhaji Mustafa da ya nuna yana so, inda Anisa ta maida hankali ba zataki ba, tunda yaron yana tashen kudi sosai, Anisa tayi tsalle ta dire kan cewa bata son auren zumunci, wanda sukayi Allaah Ya kara musu zaman lafiya, wanda suke shirin yi ma Allaah Yasa albarka, ita dai in ba kaddara ba, bata taba hango kanta a cikinshi ba, haka kawai baya burgeta. Bata kuma yin ba, Abuja aka kaita. Haris ne ya roki a saita bikin lokacin da zaiyi hutu saboda yana so yazo, yanda yaga album din bikin hoton Munira babu shi a ciki abin baiyi masa dadi ba. Yazo din, shi ya kama hannun Anisa a wajen dinner dinta yana shigar da ita ciki, yaje ya zaunar da ita kusa da angonta. Yaji dadin zuwan, yaji dadin bikin. Shisa ma da Hajiya Rumana tace masa "Allaah Ya nuna mun naka haka Haris..." Yayi dariya mai cike da nishadi "Allaah Yasa karka kwaso mana ta waje irin yanda Anisa tayi" Ya jinjina kanshi "Ba ta waje bace Mami" Da sauri ta kalle shi, ya karayin dariya "Aise ce, Aisen Uncle Modu" Batasan lokacin data fadada murmushinta ba "Waye zaice Haris zaiyi hankali haka? Kinsan maganar business mukayi jiya? Duk da ma mun kwana biyu da yayi mun maganar, amman yanzun yana cemun ya fara tsara business plan dinshi, Haris fa, da nace masa akwai kudin da nake ware masa tunda yayi mun maganar kinsan me yace mun?" Alhaji Mustafa ya fadi cike da wani alfahari a muryarshi, kafin ma ta amsa ya cigaba da magana "Shekarar karshe nake yanzun Abba, akwai ayyukan da nayi applying, idan na samu kudin babu laifi, ciki nake so inyi tarin shekara biyu inga idan zasu fara siyamun manyan motoci daya ko biyu, ko babba da kananu, inaso in fara daga wani waje, kamar yanda ka bani labarin yanda ka fara naka, ina so in fara da kudina ko da zaka bani wani abu inaso ya zamana a gaba ne, idan na kafu, sai mu zauna muyi magana..." Ai ita duk wannan labaran na yanda Haris yayi hankali bataji dadinsu ba ashe, bata maga hankalin ba sai yanzun daya nuna mata shi, a cikin 'yan uwanta kaf, shakuwar da take tsakaninsu da Modu lokacin da suke tasowa ba 'yar karama bace ba, barin kasar da yayi da auren da tayi itama shine abinda ya fara disashe wannan shakuwar, amman yanzun, Haris zai dawo da ita sabuwa "Aise fa Haris" Ta fadi farin ciki fal muryarta, da kuma wani alfahari da ta kasa boyewa "In Shaa Allaah Mami, itama tana makaranta ne yanzun, sanda dai zan zama stable sai ayi maganar komai In Shaa Allaah..." Da saurinta tace "Wanne stability kake magana? Kufa sai kun dauko abin hankali saiku rushe shi, ai ba wani wasa ko shiriritarku za'a biyewa ba, da wuri ya kamata manya su shiga maganar" A lokacin zumudinta ma dariya ya bawa Haris, kafin ya koma sai da ta karbi lambar Binta a wajenshi, haka ta kirata suka gaisa bayan Haris din ya tafi, sai dai taji wata kunya da batasan daga inda ta taso mata ba, duka gani nawa tayiwa matar ta yanke hukuncin batayi mata ba, taso tun a wayar tasu ta farko ta kwaso mata maganar Haris da Aise, amman saita kasa, zata bari su kara gaggaisawa, watakila ma ita Bintar ta fara yi mata. Kuma kamar yanda Hajiya Rumana tasan da maganar, ko ace Haris ya fada mata, haka ya kasance a wajen Binta. Ita Binta ranar da ta sani, tana kitchen ne, sai take juyo dariyar Aise din da tazo daga makaranta, tunda itama kamar Haris, tata makarantar tafiyar awanni biyar ce da inda iyayen nata suke, da tayi niyyar barin Italy ne, tana yawan maganar, rana daya kuma ta canza shawara, babu wanda yasan cewa tazara ce batason ta kara samarwa tsakaninta da Haris shisa ta zabi kusa da gida. A wayar, Binta taji kalamai da yawa da suke alamta soyayya, shisa ta tambayi Aise kai tsaye, batare data musa ba ta tabbatar mata, tunda ma basu saba irin wannan boye-boyen da iyayensu ba, a wajensu ba wani abu bane na tashin hankali dan wani ya burgeta ma tazo tana labarin da Binta, da mahaifinta ma hirar samari takeyi hankali a kwance. "Ban fada miki bane ba saboda ba sauri mukeyi ba Mamma, inaji a jikina na samu miji ne, shisa, ba abin sauri bane ba" Binta ta fahimta, duk wani bayani da Aise tayi mata, kuma har ranta, a lokacin bataji cewar tana da wata matsala da hadin Aise din da Haris ba, tana sonshi, kuma a lokacin ne ta kula da yanda in dai Haris yazo, idanuwanshi na kan duk wani motsi na Aise, cike da tarin kulawa da wani taushi cikin idanuwan nashi da ya kwantawa Binta a rai, Haris na son 'yarta, irin soyayyar nan mai wahalar samu. Ko da sukayi waya da Mu'adh yake kara jaddada mata maganar da tun wancen zuwan nashi har yau ya kasa natsuwa da ita, wato Haris, sai tayi dariya tana gaya masa ya kwantar da hankalinshi, Haris na son Aise ne, itama kuma tana sonshi, idan har komai ya tafar musu yanda suka tsara ma aure zasuyi. Shirun da Mu'adh yayi daga bangarenshi sai da tayi tunanin ko kiran ya katse ne, data duba taga yana tafiya ta sake masa magana "Inaji Mamma..." Ya furta cikin karamar murya, duk wani labarin Aise da Haris data bashi haka yace mata "To" Yana ma yi mata sallama da uzurin cewa ana masa magana zai sake kiranta. Kuma tun daga ranar bai kara yi mata zancen Haris ba, sai tayi tunanin ya fahimta ne, ya gane abinda itama ta gane, Haris ba zai taba cutar da Aise ba tunda soyayya ce a tsakaninsu ba wani abu ba. Wata goma akayi a tsakani kafin Mu'adh ya diro kasar Italy, kuma kwana daya da zuwanshi, ya fita, ya dawo da wata envelope a babba a hannunshi, envelope din daya ajiye a gaban Binta, idanuwanshi a cikin nata yace "Bana son Haris Mamma, bana son Haris da Aise, tun kafin in samu dalili baiyi mun ba..." Ko da ta dauki envelope din ta bude, hotuna ne masu yawan gaske, hotunan da a tashin farko ta rasa ma me take kallo, Haris cikin abokai, Haris cikin mata, Haris a club, Haris rike da mata kala-kala, Haris a tsaye da wani abu mai kama da sigari a hannunshi, hotuna ne sun kai guda dari "Haris na shan wiwi, Haris na bin mata, Haris baiyi kama da mijin da nakewa Aise mafarki ba, ba anan ya fara ba, tun a can Nigeria, nasan ba zan iya hana Aise abinda take so tayi da rayuwarta ba, amman a matsayina ma dan uwanta, nayi abinda nake tunanin zan iya, na fara fada miki gaskiya, itama kuma zan fada mata, abinda zatayi da gaskiyar zabinta ne" Ita shan wiwin ma bai wani dameta ba, aiko sanda ta auri Modu yana shan sigari, yana ta cewa zai bari, bai daina ba sai ranar data haifi Khamis, ranar, a asibitin yace mata ba zai kara ba, saboda lafiyarshi, saboda a ranar yaji yana da bukatar wannan lafiyar iya tsayin shekarun da Allaah Ya kadarta masa. Kuma har yau, shekaru ashirin da tara, Alhaji Modu bai sake kunna sigari ba, tasan idan har Haris yaso ya daina shan wiwi, zai bari, ai itama kamar sigari din ce a tunanin Binta. Amman mata? Wannan cuta ce da taga maza da yawa na fama da ita, neman mata cuta ce data ruguza aure da yawa har anan kasar Italy, tayi sanadin broken homes da batasan adadinsu ba, kuma yana daga cikin abinda yake bawa Binta tsoro. Abinda har a sallarta in zatayi addu'a saita roki Allaah Ya kara mata mijinta da yaranta da duk wani da zai rabesu daga fadawa cutar neman mata. Sai kuma ta dauki 'yarta kwara daya tilo ta mikawa Haris bayan tasan abinda yakeyi? Haka ta wuni zaune batare da tasan takaimaiman abinda takeji ba. Sai dai kafin ta tashi abu daya ta sani In dai tana numfashi, in dai karfi irin na uwa zai iya tasiri akan 'yarta, to ba zata taba barin Aise ta auri Haris ba... Yanda Mu'adh ya fadawa Binta, haka ya kara daukar dayar envelope din ya samu Aise har cikin dakinta ya mika mata guda daya "Kiyi hakuri, shine kawai abinda zan iya miki a matsayina na dan uwanki...kome zakiyi dashi, kome kika zaba, kowanne hukunci kika yanke, ina tare dake, kinaji?" Ta kalle shi idanuwanta cike da tsoro "Ina tare dake, kome zaki yanke" Kai kawai ta daga masa batare da ta iya cewa komai ba, tunda yace mata yana so suyi magana taji gabanta yana faduwa, take ta jan kafa kuma, saboda yanayin muryarshi tasan ko meye zasu tattauna abune mai muhimmanci, sannan haka kawai zuciyarta ta dinga gaya mata abune daya shafeta, sai gashi yanzun yazo ya tabbatar mata da cewa da gaske maganar ta shafeta, wacce gaskiya? Hannunta har rawa yakeyi lokacin data zazzage abinda yake cikin envelope din nan, sai zuciyarta ta taya hannuwan nata data fara duba hotunan nan, daya bayan daya, kowanne yana samun wajen daya zauna a tare da ita Haris ne, Haris dinta... Fuskarshi ce, shigarshi ce daya saba, shigar da bakaken kaya sunfi yawa a cikinta, kalolin kayanshi da ta taba gani gabaki daya basu wuce guda hudu ba, baki, ruwan toka mai cizawa, koraye masu cizawa, sai ruwan kasa da batasan ma ko zata kirasu da wannan sunan ba saboda da duhunsu "Me yasa baka son kaya masu haske?" Ta taba tambayarshi, da mamaki ya kalleta "Masu haske?" Ya maimaita kamar bai gama fahimta ba "Farare, ja, kala mai haske, ba baki ba, ko irin wannan na jikinka" Sai yayi yar karamar dariya "Inji wa? Ina sakawa mana, ko yanzun singlet dina fara ce, ko in daga rigata kigani?" Itama dariyar tayi "Baka amsa mun tambayar da nayi bafa, me yasa?" Saiya numfasa "Nima ban sani ba, watakila na jima inajin kamar babu mai ganina ne, sai wani sashi tare dani yake son kara boyewa, in zama iri daya da inuwata, sai ka matso kusa, sai kasa hankali zaka ganni" Batajin ta gane inda kalamanshi suka dosa a lokacin, batama san me yasa wannan hirar ta dawo mata yanzun ba, tunda ai bata da alaka da tarin matan da suke tare dashi a hotunan nan, ko suna dashi? Ita Haris din data sani kama kawai yakeyi da wannan, Haris din data sani bata taba jin warin hayaki a jikinshi ba, kuma ai ta rungumeshi har in za'ace ta lissafa zata bace lissafi, duk matan nan, inda hannuwan Haris suke a jikin wasu ko da wasa basu taba kaiwa a nata jikin ba, Haris ne zata nanike masa, cikin dariya zai rabata da jikinshi yana fada mata "Boundaries Aise, ba zaki so ki kunnamun abinda baki san kokawar da nakeyi don kashe shi a gabanki ba..." Haris fa... Haka Mu'adh yace kome zatayi da wannan gaskiyar yana tare da ita, data kai hannu ta share hawayen da babu komai a cikinsu sai wani irin kishi mai rufe idanuwa, sai soyayyar da take tabbatar da girmanta a yau, hukuncin da ta yanke shine Tana son Haris Zata cigaba da son Haris Zata so shi har sai sonta yasa ya rike hannunta ya saki na kowacce mace...yanda take jinta ta Haris, to zata tabbatar da Haris ya kasance nata ita kadai... 8 HARIS Tun tasowarshi, a labarai kawai yake jin menene rashi, kalmar a nesa ko kusa bata taba shafarshi ba, tunda sau nawa ma ya taba tunkarar Alhaji Mustafa da wata bukata tashi ballantana yace masa a'a? Watakila da yana yaro, lokacin kuruciyar da lokaci ya shafe masa daga kwakwalwarshi, shifa ko mutuwa, da girmanshi dai Kakarshi ce ta rasu, yana ma nan Italy aka kira aka fada masa, ko Alhaji Mustafa a waya yayi masa ta'aziyya, haka shine ya tura masa lambobin duk wadanda ya kamata yayiwa gaisuwa, kuma mutuwar ba shigarshi tayi ba, tunda ba sabawa yayi da ita ba, tun da aka fada masa yayi mata addu'a haka ya cigaba da sabgoginshi na ranar kamar babu abinda ya faru. In dai yana son abu, to yana sonshi ne da duk zuciyarshi, sannan kuma idan ba zai yiwu ya sameshi a wannan lokacin ba, tabbas zai fara tsare-tsaren yanda zai cimmasa ne. Tun ranar da yaji yana sha'awar ya ganshi a tsakiyar filin yaki yana daukar hotunan abinda yake da muhimmanci a game da yakin yana nunawa sauran mutanen duniya ya fara bin duk wata hanya data dace da zata saukaka masa hakan, a yanzun haka idan zai fadi adadin mutanen dake bibiyar blog dinshi da yake dora hotuna sai a zata idan akwai yiwuwar kudi su siya maka wannan mutanen abinda yayi kenan, workshops kuwa na sanannu a wannan fannin baisan adadin daya halarta ba, haka adadin mutanen da yayiwa email, wasu suka bashi hakuri cewa ba zasu iya taimaka masa da wani abu daya wuce 'yan shawarwari ba, wasu kuma suka yarda suka hadu har suka duba portfolio dinshi. Burinshi ya samu manyan mentors ko guda biyune da zasu zame masa tsani wajen cimma wannan burin nashi. Ba wai rashi bane kawai Haris bai sani ba a rayuwarshi, harda tashin hankali, ranar farko da ya fara gane ma'anar kalmar shine randa Aise ta kirashi a waya tace masa tana cikin makarantarsu, da dokinshi ya fito, zuciyarshi shimfide akan fuskarshi saboda wannan ziyarar bazatan, amman kallo daya yayiwa rinannun idanuwanta da fuskarta da take a kumbure wani abu ya kulle a kasan cikinshi da baisan abinda zai kirashi ba. Kuma ko da ta mika masa wasu hotuna yasa hannu ya karba, yanayin shi bai canza ba, tunda fuskarta ta sanar dashi ba lafiya ba daman "Ni ne" Ya fadi, yana cigaba da amsa duk wata tambayarta da "Eh" Tunda meye amfanin yayi mata musu? Aise ce fa, sonta yakeyi, son da yake fatan su kare rayuwarsu a karkashin inuwa daya, ko ta binne shi koya binneta, ai ya riga yasan dole zata sani wata rana, daman kuma bashi da niyyar boye mata cewa yana shan wiwi, matan dai, matan ma saboda wannan wutar da yake gani tana kara ruruwa cikin idanuwanta ne kawai zaisa ya boye mata, idan fatanshi ya kai mizani ma, da sunyi aure saiya daina, inya sameta me ya rage masa? Ai matan da zasu burgeshi bayan ta zama mallakinshi yana da yakinin ba masu yawa bane ba. "Me yasa?" Ta tambaya, yayi shiru kamar ba zai amsa ba, kafin ya dan daga mata kafadunshi duka biyun "Ban sani ba Aise, haka kawai..." To meye zaice dalilin da yake dashi? Rana daya ya kalli 2Pac yaji yana so ya zuki abinda yake zuka kawai dan yaji ya yake ji, wannan kuma zai iya zama dalilin da zaiyi amfani dashi ne? Matan kuma lokacin da zai gane amfaninsu a rayuwar kowanne namiji ne ya faru dashi da wuri, kuma tun lokacin saiya kasa dauke kai, ko da ba zaiyi komai da mace ba, shikam yana son yaji laushin jikinta a kusa dashi. Ba zaiki ace duk mirginar da zaiyi a wajen kwanciya su mirgina tare da mace kwance a kirjinshi ba, adadin soyayyar da ya keyiwa mata mai yawa ne, shisa yake so ya mallaketa ai, ta zama tashi, bai ko motsa ba ganin hawayen da suke zubar mata tana saka hannu tana gogesu "Idan nace kabarsu duka ka zauna dani kadai zaka iya?" Ya saka idanuwanshi cikin nata, saboda yana so taga gaskiyarshi, in zata iya ta leka zuciyarshi ko zai samu saukin harhada kalaman da zaiyi amfani dasu "Sai kin taimaka mun" Ta kalle shi tana son gane abinda yake nufi "Saikin taimaka mun kin zama tawa Aise, zanyi kokarin bari idan kin zama tawa" Da alama abinda take kokawa dashi mai nauyine, sai ajiyar zuciya takeyi "Yanzun ba zaka iya ba ko? Ba zaka iya barin matan nan ba sai na zama taka" Ya zabi yayi shirune tunda bayason kara mata ciwo akan wanda takeji, shima zuciyarshi zafi takeyi masa "Shikenan..." Ta furta tana goge fuskarta hadi da mikewa "Shikenan zaki zama tawa?" Ya tambaya da saurinshi shima yana mikewa, saita daga masa kai da wani irin rauni da bai taba gani a tare da ita ba, tunda in zai lissafa jaruman mutanen daya sani zai kira sunan Aise a farko-farko, ya kama hannunta, ta fisge, ya sake kama ta sake fisgewa "Dan Allaah, zuciyata na ciwo" Saiya kyaleta "Tafiya zakiyi?" Ta daga masa kai "In rakaki?" Ta girgiza masa kai, haka ya tsaya ya kalleta harta bacewa ganinshi, ko da yayi magana da ita yaji ta koma makaranta lafiya saiya dan samu natsuwa, baiyi zaton abin ya dameshi sosai ba sai lokacin da yaje kwanciya bacci, ya dinga juye-juye, duk hayakin daya bankada baiyi masa amfanin komai ba. Yana son Aise, kuma Aise tana sonshi, to soyayyarsu kadai zata isa kuwa? Shi ta bangarenshi yasan babu wanda zaiyi fada dashi akan samunta, Hajiya Rumana tana son abin, ko da Alhaji Mustafa bayaso yasan tasirin hakan ba wani mai yawa bane balle ya daga masa hankali, in yaja, ya turje zai barshi da zabinshi ne kamar yanda yasan yayiwa Munira, tunda kamar Hajiya Rumana a lokacin akwai wanda yaso ta aura, ita da take mace ma ba'ayi mata auren dole ba balle kuma shi namiji. Amman Aise fa? Ina ma ta samu hotunan nan? Ya kamata ace ya tambayeta tunda yasan ba zata taba sakawa a bishi ayi masa bincike ba, sai ya kasa hakuri ya tashi zaune daga kwancen da yake ya dauki wayarshi, sako ya fara tura mata Kinyi bacci? Kamar itama shi take jira ta dawo masa da amsa Na kasa... Ya sauke ajiyar zuciya Waya baki hotunan nan? Amsa daya ta bashi Mu'adh Yaji wani abu ya hautsina a cikinshi Ya bani, ya ba Mamma. Sai yakejin kamar zaiyi amai, amman babu komai a cikinshi duk yinin ranar banda hayaki da black tea, da yake baya daga cikin mutanen da suka damu da abinci, in dai zai samu shayi saiya wuni yana gararambarshi "To ya za'ayi kayi kiba Haris? Ka zauna kaci abinci ba zaka zauna ba? Jika dan Allaah sai tsayin" Haka Hajiya Rumana take yawan yi masa mita, sai dai yayi dariya, shi dogo ne tabbas, amman yana da kirar jikin da bature yake kira da lean, ba rama yake da ita ba, kawai dai ba zaka kirashi da mai jiki bane ba, kuma da yake baya wani abu na motsa jiki daya wuce zirga-zirgar da ta zame masa dole, babu wani kwanjin daya tara, sau nawa yabi Logan gudun da yake masa tayi duk safiya yaji yana neman shekawa barzahu, ya kuma gane cewa huhunshi bashi da lafiyar da zaiyi wannan iyayin, ya tattara ya watsar. Kamar yanda yasan a lokacin ko tashi yayi ya shiga bayi babu abinda zai amayar, ko dan ruwan shayin ma ya jima dayin fitsarin wanda baibi jikinshi ba. Meya tarewa Mu'adh da zaiyi masa haka, ina ruwan Mamma da wannan maganar, idan akwai wanda ya kamata ya sani ai Aise ce, tunda itace za tayiwa kanta zabi, a karo na farko da yaji an taba masa mutuncinshi a idanuwan da bayaso hakan ya faru, to ta ina zai fara zuwa gidansu Aise yanzun? Duk da zagi baya cikin dabi'arshi saida ya lalubo wani ya makawa Mu'adh a zuciyarshi. Sosai abin ya dinga damunshi na kwanaki, bai fara samun sauki a ranshi ba saida yaga Aise ta warware, sun fara hira kamar yanda suka saba, sai dai akwai abinda ya canza, a da ko muryar mace Aise taji tayi masa magana bata damuwa, za dai tace masa "Ka fada mata kana da budurwa ko? Ka fada mata kai din na mace daya ne? Naji kamar tana makale maka murya" In yayi dariya sai itama tayi dariya, tunda sai suyi watanni, banda kalmar ina sonka, ina sonki da suke rufe duk wata wayarsu dashi, haka in sun hadu, wani zancen soyayya baya hadasu, hirarsu sukeyi cike da shakuwa, son yana nan, duk sun sani, meye amfanin ayita magana akan abinda babu inda yaje? Amman yanzun da wahala su kare waya lafiya in dai zataji muryar mace a background, ko da bashi tayiwa magana ba, ya dinga jadda mata kenan, har saida ya biye mata sukayi fadansu na farko "Ina sonki Aise, hakan baya nufin zaki dinga tsaramun abinda zanyi ko yanda zanyi da rayuwata, ban zama naki ba balle kice ba zan kula mata ba, idan na kulasu zanji tsoron gaya miki ne? Na taba miki karya?" Itama cikin hargowa tace "Amman gaskiya nawa ka boyemun?!" Ranshi yayi kololuwar baci, yaja tsaki ya kashe wayar kawai, bata sake kiranshi ba, kuma lokacin daya huce ya dinga jera mata kirama bata daga ba, duk sakon daya dinga tura mata na lallashi dama barazana babu wanda ta amsa, daga baya ma saita kashe wayar gabaki daya, sai gashi da bada uzurin karya na rashin lafiya dan akwai wani assignment da zaiyi submitting, ya kama hanya yana nufar makarantarsu. Ya dinga yawon nemanta, tunda wayarta a kashe take, yafi awa daya da wani abu, kawai ya hangota cikin abokanta, maza guda biyu sai mace daya, su hudu, sunata dariya alamar shi kadaine hankalinshi yake a tashe, nata a kwance yake, ko da ya hangi abokinta daya ya kaiwa kafadarta duka cikin wasa, ta bangaje shi da rabin jikinta, sai duhu ya gilma masa, jiri ya nemi ya tikashi da kasa saboda wani irin kishi daya taso masa. Tunda yazo kasar wani abu bai taba hadashi da jami'an tsaro ba, idan ya tsaya yau tabbas babu abinda zai hanashi kwana cell, in su Aise suka karaso zai jibgi abokinta, zai dake shi irin dukan da rabonshi da yayiwa wani shi tun yana makarantar kwana, saiya juya ya koma inda ya fito. Wannan shine sanadin da suka ba juna iska na wata daya shi da Aise, baisan daga bangarenta ba, amman a nashi bangaren kwanaki ne daya san irin girman son da yakeyi mata, kwanaki ne da yayi karamin hauka a cikinsu, har saida ya kasa hakuri ya kara komawa makarantarsu, daya kirata saiya sameta kuma ta daga, ya fada mata inda yake. Tana zuwa tayi tsaye tana kallonshi, idanuwanta cike taf da hawaye "Mi manchi tanto...(Nayi kewarki, sosai...)" Yayi maganar yana jin kamar zuciyarshi zata bude, inta bude kuma ace Aise da take tsaye a gabanshi zai dauka ya kara duba mata wani sabon wajen ya zaunar da ita, hawayen da suka zubo mata yasa shi karasawa inda take ya tallabi fuskarta da hannuwanshi duka biyun "Ni zaka fadawa kai ba nawa bane ba? Ni?" Ta karasa tana ture shi, ya sake rikota, ta kai masa duka tana kukan da yake fitowa tun daga kasan zuciyarta, sai kawai yasa karfi ya rungumeta yanda duk mutsu-mutsun data dingayi ta kasa kwacewa, sai kawai ta kara fashewa da wani kukan, ji yake kamar ace yau Aise ta zama tashi, akwai lallashin da yakejin su duka biyun suke bukata. Numfashi kawai yake saukewa yana maimaita mata kalmomin ban hakuri da kuma yana sonta. A ranar suka shirya, sai kuma labarai yayi musu yawa, kowa nason ya fadawa dayan abinda ya faru a wannan wata dayan da sukayi basa tare. Shi ta bangarenshi ba wani abu bane daya wuce cigaban daya samu a karatu da burinshi, a nata bangaren ne yaji wani abu da yake neman kara birkita masa lissafi, Mamma tace mata ta rabu dashi "Bata sona dake ko? Mu'adh ya batani a wajenta" Ya fada cikin wata karamar murya kamar ba tashi ba "Zanyi magana da Papa, zaiyi mata magana, abinda nake so shi Papa yake so..." Ya kalleta da idanuwan nan nashi da yau suke haskawa da kyallin tashin hankali "Idan ya hanani aurenki fa?" Ta girgiza masa kai "Ka daina irin maganar nan" Numfashi ya sauke "Ya zanyi idan shima yace baya sona? Ba zan iya hakura dake ba Aise" Idanuwanta suka sake cika da hawaye, yanzun haka dakyar Mamma take magana da ita akan Haris din "Ba zai hana ba, ko kana tunanin ni zan iya hakura dakai?" Ya dumtsa hannunta da yake cikin nashi wani abu na dukan zuciyarshi, duk wani tsari da lallashi da takeyi masa da karfafarshi akan cewa babu abinda zai samesu, ita dashi, sunki zauna musu, haka suka rabu bashi da wata walwalar kirki. Ga jarabawarshi ta karshe da yake shirin rubutawa a cikin watanni hudu masu zuwa amman hankalinshi fiye da rabi yana tare da Aise, kuma jarabawar na da matukar muhimmanci a wajenshi, yana bukatar fita da sakamako mai kyau, in son samunshine ma ya zamana yana daga cikin mutum biyar din farko a shekararsu, ko dan kara samun chances na cikar burinshi tunda shi ba dan kasa bane ba, visar shima in ba aiki ya samu ba, ko ya kara dora karatunshi ta fara lissafa masa lokacin karewa. A karo na farko hanyar shi daya hango babu komai ta cika da tarin tudu da gangaren da yake neman afkawa. Ya tabbata akwai abinda yake faruwa lokacin da yake tsakiyar jarabawa da Aise ta kirashi tana ce masa "Akwai biki, a Maiduguri, bansan wanne biki bane ba, Papa zaije, ka aika a same shi ayi masa maganarmu..." Yanda ta sauke duka maganganun nata kusan a numfashi daya yace mata "Wani abu ya faru ko? Wani abu ya faru..." Yayi tambayar yana ba kanshi amsa, tayi shiru "Zan ba Baba lambar Uncle din ya kirashi" Da sauri tace "A'a maganar waya ba zaiyi ba, yaje ya same shi, dan Allaah yaje ya same shi, ba zan iya rasaka ba, amman bani da wani karfi mai yawa tunda Mamma na tsakiya" Saiya daga mata kai kamar tana ganinshi, sai da ya tabbatar mata da zaiyi masa magana, tukunna yaji hankalinta ya fara kwanciya, tambayar duk da yayi mata akan ko me yake faruwa, sai tace masa bashi da wani amfani, in dai Alhaji Mustafa zaije yayi maganarsu da Alhaji Modu shikenan. Kyaleta yayi, a lokacin da suka gama waya dare ya riga yayi sosai, shi damuwa da fargaba ma ita ta hanashi baccin kirki, sai kawai ya tashi ya cigaba da rage wasu abubuwan da suke gabanshi ko zai ragewa kanshi damuwa. Da safe kuwa ya kira Hajiya Rumana yake fada mata yana so ayi maganarsu shi da Aise, yanda ta dinga murna saida murmushi ya kwace mata "Ba wai mun shirya bane mu duka Mami, akwai 'yar matsala ne, shisa nake so a tambayar mun auren, manya su shiga maganar" Da mamaki tace "Wacce irin matsala?" Yayi shiru yana tunanin ta inda zai fara, to haka zaice mata Mamma ta san yana shan wiwi yana neman mata, bata sonshi da 'yarta? "Matsalar me, kayi shiru ina tambayarka" A raunane yace "Mu'adh baya sona da Aise din, haka kawai tun randa ya fara ganinmu nagani a fuskarshi, to yanzun Mamma ma bataso" Hajiya Rumana taja wani tsaki "Shi Mu'adh din ubanta ne? Ko ita Bintar ce zata bada auren Aise din, harta isa tace bata sonka da 'yarta, dadin abin ai ba itace take da iko da ita ba, wannan ma zancen banza ne da bai kamata ya dameka ba, kabar komai a hannu na kawai, kamar ka auri Aise ne kagama tunda dai kana sonta" Ya sauke wata irin ajiyar zuciya, to sau nawa Hajiya Rumana nayi masa alkawari tana cikawa? Tama taba ce masa zata sama masa abu ta saba kuwa? Me yasa tuntuni bai fada mata ba ya tsaya yana ta damuwa? Tun ranar da Aise ta gaya masa Mamma bata sonsu tare bai samu natsuwa ba sai yau, wani abu daya kulle a cikinshi bai saki ba sai yanzun nan "Shisa nake sonki Mami Na" Tayi dariya. Hajiya Rumana uwa ce, Kuma uwa zatayi duk wani kokarin da zata iya wajen samawa yaranta abinda take so, Amman duk karfi da tasiri irin nata babu yanda zatayi da kaddara... 9 A tunanin Hajiya Rumana, yanda labarin soyayyar Haris da Aise ya cika zuciyarta da farin ciki, haka abin zai yiwa dan uwanta dadi, to matarshi ta isa ta hanasu karfafa zumunci ne? Ko kuwa ikon bada auren Aise a hannunta yake? Rashin son da take yiwa Haris babu abinda zai tare. Shisa da karsashinta ta kirashi, haka kawai lokacin kuruciyarsu ya dinga dawo mata "Modu..." Take kiranshi kai tsaye, cikin tsokana, shikuma zai rankwasheta "Ni sa'anki ne kike gatsa sunana haka babu rissinawa" Lokacin da tayi aure ma, haduwarsu ta farko, haka ta kirashi, daya kawo hannu zai rankwasheta, da yake a gaban Alhaji Mustafa ne saiya rike masa hannu yana fadin "Ayi hakuri a yafe mata" Kamar karamar yarinya sai tayi masa gwalo, akwai shakuwa mai karfi a tsakaninsu a wancen lokacin, kuma tasan ba barinshi Najeriya bane silar nakasun da alakarsu ta samu, harda ita da ta fara janye jikinta tana rike Alhaji Mustafa, tana kuma fifita lamarinshi akan na kowa a rayuwarta "Yayana" Ta furta yau, tare sukayi dariya "Ni kuma? Yaushe kika fara ganin girmana Rumana? Ai nasan kina daga cikin mutanen da ko furfura zata lullube duk jikina ba zaki bani girman da na dace dashi ba..." Dariyar dai tayi "Inji wa? Ni din? Ai tunda ma ina girmamaka, kawai ka raina adadin girmamawar ne ba wani abu ba" Ya girgiza kanshi daga dayan bangaren kamar tana ganinshi "Kuma kaga yanzun nice zan koma babbar ka koma karami" Yayi murmushi mai sauti "Amman dai ba anan duniya ba ko?" Saida suka gama zolayar juna sannan suka gaisa sosai, lokacin ne kuma ta kara gyara muryarta saboda tana son ya dauki duk wani abu da zata sake furtawa da muhimmanci "Ashe yara zasu kara mana zumunci Modu?" Abinda bata sani ba shine, Binta ta fada masa komai, babu abinda ta boye masa dangane da dalilinta na kyamatar Haris din, kuma yama fita jin tsanar abin, ai son yaransu a jini ne, kuma shima bai hada nashi da komai ba a halin yanzun, bashi da sama da yaran nan uku rak da Allaah Ya bashi, sonsu yakeyi da gabaki dayan zuciyarshi, abinda kuwa zai cutar dasu in dai akan idanuwanshi ne sai inda karfin shi ya kare balle kuma ace wai shine zai daukesu ya mika inda zasu cutu, musamman Aise, yarinyarshi, yarinyar nan tashi da tafi kowa shakuwa dashi tun tasowarta, yarinyar da tun tana da shekaru biyar a duniya inya kalleta ya tuna wata rana zai mika kulawarta karkashin wani sai zuciyarshi tayi wata irin dokawa. Data tasa sosai kuwa, labaran abokanta maza, da mazan da suke burgeta, inda ta numfasa ta kalleshi watakila da ta godewa Allaah da yasa bashi da lasisin mallakar bindiga duk ya harbesu ya huta da fargaba, a yanzun kuwa, kullum cikin tsara irin mijin da yakeyi mata fatan samu yakeyi, kuma Haris yasha bamban da wannan mijin, shisa yanzun ya nunawa Hajiya Rumana kamar bai gane abinda take nufi ba ta hanyar fadin "To gashi dai Haris yana nan sunata zumunci abinsu, sai kiga sun taso basu watsar da nasu zumunci ya samu rauni irin yanda mukayi ba, balle su zamani ya saukaka musu komai" Ta fadada murmushin da takeyi "Ai wannan zumuncin na musamman ne, halan baka san yaran naka sun shirya kansu ba" Shima murmushin yayi mai sautin da yake tattare da ma'anoni da dama "Nifa har mamakin yanda Hausa ta zauna miki nakeyi, kinga yanzun magana kikayi mun, naji ki amman bangane abinda kike nufi ba" Yayi mata maganar da yaren Kanuri, itama kuma saita juya harshe "Aise da Haris nake nufi, dazun nan yake cemun zaka zo Maiduguri a karshen watan nan da muke ciki, nace ba zai wuce bikinsu Khalisa ba..." Shiru yayi kamar mai jiran karin bayani, itama bata tsaya ba ta cigaba "Shine yake cemun suma yanaso ayi maganarsu" Da mamaki a muryarshi yace "Ikon Allaah, magana kuma? Wacce irin magana? Kinsan har yanzun na kasa fahimtarki fa" Ta kara tabbatar da baisan komai ba "Ai sun jima da shirya kansu...maganar aurensu, dan shiririta irinta Haris wai manya yake so su shiga asan da zancen, ni kuwa nace zamu zuba musu ido ne, ai azo a tsayar da magana asa rana kawai" Ko a yanda ta karashe maganar zaka tsinci tsantsar doki da farin ciki a muryarta, farin cikin da maganganun Alhaji Modu suka barbadar mata dashi "Anya kuwa Rumana? Gaskiya ni bansan da zancen ba, duka Aise din nawa take da zata yanke irin wannan hukuncin? Kuma ma akwai yaron abokina da yake sonta tun bata kai haka ba, yana England yanzun haka, nine na dakatar dasu nace ya nutsu yayi karatunshi, itama ya barta ta nutsu, shiririta ce kawai irin ta Aise nasan shisa ni bata ma tunkareni da maganar ba" Ta cire wayar daga kunnenta kamar mai neman tantance wata kira, ta mayar, ta gyara zamanta "Dan abokinka Modu? Har dan abokinka zaifi Haris ne ko da ma rana aka saka masa da Aise balle magana ce kawai, ya za'ayi na gida yana so ace za'a dauka aba wani bare can" Jin yanda ta harzuka lokaci daya yace "Ke kam kin cika rigima, dan Allaah mu bar wannan maganar, kuruciya ce irin tasu daga shi har Aise din, amman ni ban shirya bada aurenta nan kurkusa ba, kuma ko da zan bayar din tunda akwai maganar wancen yaron babu yanda za'ayi in karbi ta Haris, ai sai in zubarwa da kaina mutunci, a daukeni karamin mutum" Tabbas wannan aikin Binta ne, ita tayi nasarar rabata da dan uwanta harma ya samu damar gaya mata irin wannan maganar, ta numfasa kuma yayi saurin katseta da "Zan kiraki, ana mun magana" Ya kashe kiran daga nashi bangaren, idan ran Hajiya Rumana yayi dubu to kowannensu a bace yake "Lallai Modu" Ta furta a fili, haka ta wuni da wannan bacin ran har tanaji a ranta ai ko 'yar gwal ce shima Haris din ya hakura, sai dai sanda sukayi waya take nuna masa ya hakura da Aise tunda iyayenta basa so, ta wayar tana jin yanda ya birkice mata gabaki daya kamar zai biyo ta ciki ya dira a gabanta, dakyar ta shawo kanshi da alkawarin ba zata bari Aise ta kubce masa ba, ya bar komai a hannunta. Ta tsorata da kalamanshi matuka "Na tambayeki abubuwa da yawa Mami, tun tasowata, kusan kullum ma cikin tambayarki nake, wannan karin roko nakeyi, dan Allaah ki taimaka mun, karki bari Aise ta subuce mun, wallahi idan na rasata zaki iya rasani" Sai gata bayan sallar isha'i a ranar, tayi nafilar da rabonta da ita tun watan azumin daya wuce, wacce irin bakar magana Haris ya fada mata, zata rasa shifa? To ita kuwa ta zauna tayi me a filin duniyar da za'ace ta wayi gari babu shi a cikinta. In dai Aise ce zata lallaba Modu har sai taci galaba akanshi, watakila ya manta naci irin nata ne akan abinda take so, wannan nacin da Alhaji Mustafa zai shafe kwanaki yana bada labarinshi. Aikuwa babinshi ta budewa masa, kiran safe daban, na yamma daban da magana daya "Wai ya za'ayi ka zabi wani a kaini Modu? Ko dan kaga iyayenmu basa nan ne? Shisa kake son fifita bare akan jininka? Ko dai Binta ce ta hana? Ashe mace zata shiga tsakanina da dan uwana" Abinda ta mantane kawai bata gwada ba, kiran karshe da tayi masa ana gobe zai baro Italy ne, kuma ranar ne ya fito mata a mutum "Dan Allaah kibari Rumana, banaso, Haris bai cika sharuddan da shari'a ma tace a bashi auren yarinya kimtsatsiya irin Aise ba..." Aikuwa sai ta birkice masa, dan maganar tayi mata ciwon da batayi zato ba "Yaran nawa kake neman jifa da muguwar kalma saboda yana son 'yarka? Abin naku har yakai da sharri?" Tanajin numfashin daya sauke a gajiye ta cikin wayar "Nifa ba sharri nayi masa ba, Allaah Ya shirya mana su, amman aiko ke ina ce dalilin da yasa kika nemi ya bar kasar nan saboda abinda yayi ne, abinda kika kira da karya akayi masa saboda ya shirya miki zance kin dauka, to gaskiya anan dinma bai daina ba, idan baki sani ba na fada miki, ni ba zan dauki 'yata in bashi alhalin nasan abinda yake aikatawa ba" Ta share hawayen da suka zubo mata, zuciyarta nayi mata zafi, bawai dan ta yarda cewar Haris bai daina abinda yakeyi ba, a'a sai dan yanda Modu baiji kunyarta ba yake jifar mata yaro da abinda tayi kuskuren furtawa, Haris din da ko da ace a wancen lokacin da gaske ne yana shan wani abu, yanzun kallo daya zakayi masa ka tabbatar da natsuwa da kamalarshi, kullum Alhaji Mustafa cikin alfahari da hankalin da Haris yayi yake, fada sukayi sosai ita da Alhaji Modu, dan tun yana kwantar da murya harya biye mata, suka farfadawa juna maganganu marassa dadi, ya kashe wayarshi bayan yaja mata wani dogon tsaki. Haka ta dinga share hawaye cikin takaici, tasan shi kanshi makircin Binta ya hadu dashi bakomai ba, saboda tsabar yanda bata son Haris da Aise, shine ta nemi sharri ta kakaba masa. Kuskurenta na farko kin sake yiwa Haris alkawarin sama masa Aise Kuskure na biyu da tayi shine samun Alhaji Mustafa ta fada masa maganar "Ikon Allaah, wai Haris din da kanshi? Yanzun fa muka gama waya amman yaron nan baiyi mun zancen ba" Tayi dariya ganin yanda yaketa farin ciki, lallai addu'arshi taci, Allaah Ya amsa rokon daya jima yanayi akan Haris, wai yau Haris ne da kanshi yakeso aje a nema masa aure, shikuwa ina zai tsoma ranshi don farin ciki? Alhaji Jibril da kanshi ya tura masa da katin gayyatar auren yara shida da zasuyi a family din nasu, kuma ganin wannan aringizon aure yasa yake ta kokarin rage duk wani aikin gaggawa da zai iya taso masa, yayi niyyar halartar bikin daman, ko da kwana dayane, dan harya gayyaci amininshi Alhaji Sa'id, to amman yanzun dole ma tafiyar ta sake shiri, tunda bayan daurin auren ai zasuyi tambayar aure ne, kuma dai ba sun tafi su biyu ba. "Kikace shi Modun zaizo wajen ko?" Ta jinjina masa kai "Duk da kasan Yayaa Jibril ne yake daurawa duk yaran aure, amman tunda shima yana wajen kaga abin zaifi tafiya dai-dai" Ya sake jinjina kai, duk farin ciki ya lullubeshi "Ki bani lambarshi to..." Zuciyarta ta buga, tasan ko lokacin aurenta da Alhaji Mustafa, Modu yafi kowa murna, tare ya gansu a wancen lokacin, a wajenshi kuma ya fara neman izinin magana da ita, akwai wani girma na musamman da Alhaji Modu yake bawa Alhaji Mustafa, surukantaka yakeyi dashi ta gaske. Yace ba'a taba mutuntashi yanda yayi ba a wancen lokacin, kuma ya jima baiga mutum mai nagartarshi ba. Idan ita baya ganinta da gashi, ai zata ga yanda zai kalli idanuwan Alhaji Mustafa yace masa ba zai ba Haris auren Aise ba idan ya tambaya, musamman da ta tabbata ba su kadai bane a wajen, akwai mutane da yawa da idanuwansu zai hanashi wulakanta mata miji ta hanyar hanawa. "Ka tabbatar ita yarinyar tana sonka?" Shine abinda ta tambayi Haris "Ita tace mun in aika a tambayarmun aurenta Mami, ina sonta sosai, ina sonta fiye da yanda kalamai zasu misalta, amman da bata sona zan hakura, kinsan zan hakura, jininki ne fa yake yawo a jikina" Ya karashe maganar cike da alfaharin da itama ya rufar mata, to tunda suna son juna ai angama magana. "Kasan ya kamo hanya, to lambarshi ta can bata shiga, mun riga munyi magana, yasan da zancen" Sai ya jinjina kai "To bari zan kira Muttaka da kuma Alhaji Kabir sai mu hadu mu hudu da Sa'idu muje" Muttaka din Kaninshi ne uwa daya uba daya, Alhaji Kabir kuma yana daga cikin abokanshi da yake ji dasu bayan Alhaji Sa'id "Allaah Ya tabbatar mana da alkhairi" Ta furta tana fatan addu'arta ta amsu, ita taso a sauya wata maganar ne, amman shi Alhaji Mustafa din babu abinda yakeyi sai maganar bikin da yanda zai kasance idan an tashi, wannan karin shine ya koma ita, saika rantse bai taba aurar da wani ba, akan Haris din zai fara "Kayan daki fa? Kamar nawa kike ganin za'a kashe" Itace maganar da yayi, da tasa ta dinga tuntsira masa dariya har tana mantawa da fargabar kar a samu matsala, shima kuma da ya gane baranbaramar da yayi sai kawai ya tayata dariyar. Haka suka kwanta cike da nishadin da suka jima ba suyi irin shi ba, da yake ranar ta kama juma'a ne, kuma a lokacin sauran kwanaki takwas bikin da za'ayi a Maidugurin. Haka ya wayi gari da wannan farin cikin daya dinga kiran danginshi yana rabawa dasu "Danku fa ya jawo muku rikici, saiku fara shiri dan zamuje masa tambayar aure" Kuma kowa ma tayashi farin cikin ya dingayi, musamman ma Alhaji Sa'id da yasan yanda aminin nashi ya damu da yaga rayuwar dan nashi ta dawo kamar yanda kowanne mahaifi yake fata. Tunda a wancen lokacin shiya fara kira, kuma bayan Hajiya Rumana da aka fada musu abinda Haris yayi, babu wanda ya gayawa sai Alhaji Sa'id "To ni me nayi? Ina na kuskure?" Shine ma ya kwabe shi "Karkayi sabo Mustafa, ai ita jarabawa fuskokin da take dauke dasu masu yawa ne, akan yara kuma dukkanmu in zamu zauna muyi magana a tsorace muke, kuma tsoronmu bashi bane abinda zai hana yaran nan ture duk wani kokari da muke wajen ganin rayuwarsu ta inganta, abinda muke iya gani shine wanda muke tsawatarwa, sauran kuma idan babu idanuwanmu sune muke tsananta addu'a akai, muke rokon Allaah Ya dafa mana, Ya kare mana su...ai abin yazo da sauki tunda har aka sani, yanzun ba sai a dauki matakin daya dace ba? Kaddara ce shima ta fada masa, tunda har yayi kokarin boyewa kaga akwai kyakkyawan zaton yasan abinda yakeyi ba mai kyau bane, kuma yana tsoro da gudun bacin ranku..." Amman kafin ma yayi wani yunkurin aiwatar da shawarwarin Alhaji Sa'idu, Hajiya Rumana ta dauke masa Haris din, shisa yanzun ya kasa hakura saida ya cewa Alhaji Sa'id "Kaga danka ko? Allaah Ya amsa addu'ar mu" Shima murmushin yake tayi, Alhaji Mustafa da iyayenshi sunyi masa halaccin da bayason yaga wani abu na rashin dai-daito ya rabi duk ahalinsu, komin kankantarshi, kuma tun kafin ma yasan wannan maganar ta an kama Haris na shaye-shaye a makaranta, Allaah ne shaidarshi, a duk sallar da zaiyi, yanda zai kira sunayen yaranshi da wanda suke karkashin kulawarshi daya bayan daya yanayi musu addu'a haka yake kiran sunayen yaran Alhaji Mustafan, da yasan matsalar Haris kuma tare suka raba ciwon da damuwar da amininshi, dan daya samu damar sadaka, addu'ar da zaiyi bayan yayi sadakar saiya hada da Haris "Allaah ga dan aminina Haris, Allaah Ka shiryeshi, Allaah Ka shiga al'amarinshi, Allaah Karka jarabci iyayenshi ta sanadinshi" Duka sau nawa ya taba saka Haris dinma a ido? Ba dan yanda Alhaji Mustafa yake da muhimmanci a wajenshi ba, ai zai iya cewa ma fuskar Haris ta bace masa "Nama yankar mana tikitin zuwa dana dawowa, saika shirya" Haka Alhaji Mustafan ya fada masa, shima kuma tun a ranar ya gayawa matarshi zancen tafiyar, take tayi musu fatan alkhairi, da alama ta ga farin cikin da yake ciki shisa take tayashi "Kaga sai mamaki nakeyi, gaskiya tsufa ya kamamu, inata kauda kai daga kirga maka furfura..." Yayi dariya "Ai kanki ma yafi nawa in dai furfura ce, in kuma da ita za'a auna shekaru matso kusa a kirga aga ni dake waye tsufan zaifi dannewa" Dariyar tayi itama "Nifa ba haka nake nufi ba, meye na tone-tone? Kawai dai gani nake Haris din nawa yake? Kamar fa jiya ne mukaje sunanshi..." Alhaji Sa'id ya numfasa kamar mai nazari "Yaran ne muna ganinsu a gabansu, shekarun kuma nata ja, amman mun kasa ganin girmansu, kullum fata muke mu kara samun aron lokaci, su dan kara zama a matsayin yaran nan namu, amman Haris fa yanzun in dai lissafina zai tafi dai-dai ya kusan shekaru ashirin da bakwai" Ta girgiza masa kai "Anya kuwa? Da bakwai? Ni sai nake ganin kamar baifi da biyar ba, shisa ma ashe nake ta juya lamarin, kuruciyarshi nake gani, to duka Haris din nawa yake? In bama dai makaranta da ake sakasu da wuri ba, dama shi din daya bar kasar, tunda karatunsu na can da namu ba daya bane ba, babu ruwansu da wannan yajin aikin na fama..." Alhaji Sa'id ya kalleta "Shekara ashirin da biyar dinne auren wuri? Muna da nawa akayi mana mu?" Ya kuwa bata dariya "Ai zamanin ba daya ba" Ta fadi "Kice ke kike zugamun yaran nan, shisa suke kara mike kafa kowa ya tara kasumba, suna ganin har yanzun yara ne su ko? To kuwa zan tarasu inyi musu zancen aure tunda sun fara gane dadin samun na kansu...ai nima da auren na karasa karatuna" Ta dingayi masa dariya kamar bashi bane ya gama maganar samun karin lokaci tare dasu. Yanda suke wannan lissafin, haka Alhaji Mustafa yayi, duk juyin da zaiyi, sai kawai ya girgiza kai, ko babu komai suna ganin tagomashin auren wurin, ga yaransu nan duk sun tasa, harma wani zai iya jinjinawa in sukace nasu ne. A ranar da zasu tafi Kano, daga nan Kaduna, dan ta can zasu bi jirgi zuwa Maidugurin, yana shirinshi Haris ya kirashi a waya "Shiryawa nakeyi Haris" Sai Haris din yayi dariyar da Alhaji Mustafa yaji kunya a ciki "Abu fa zan gaya maka Baba" Ya kuwa ce "Ba wani nan, so kake kaji na shirya, ko mun kama hanya. Yanzun nan zan karasa sai mu biya mu dauki Kawunka dasu Alhaji Kabiru, yau zamu nema maka auren Aise Haris" Babu abinda kunnuwan Haris suka tace suka adana masa sai "...Yau zamu nema maka auren Aise" Zasu isa Maiduguri lafiya, Abinda Alhaji Mustafa bai taba hangowa ba shine alfaharin shi zai sashi nemawa Haris aure har sau biyu a rana daya, Za'a hana shi daya, Za'a bashi daya... 10 Karfe goma na safe akayi daura duka auren, kuma daga can kai tsaye gidan Alhaji Jibril aka kwaso su, dan anan za'ayi 'yar karamar Walima, duk girman falon nashi, inda duk ka kalla mutane ne anata hada-hada, da hira irin tasu ta manya, kowa ya cire babbar riga an ajiye saboda abinci da ake taci, duk hirar nan da ake ana dariya banda Alhaji Sa'id da yake zaune cikin kujerarshi, abincin ma kadan yaci, saboda akwai tuwon shinkafa da miyar ganye da yasha naman kaji, kuma yana daga cikin abincin da yake so, haka kawai bayajin yunwa, shi tafiyar ma tun jiya jikinshi yake a sanyaye da ita, haka suka iso suka sauka hotel din da suka kwana. To yau daya tashi ma komai nashi a sanyaye yake, da Alhaji Mustafa yayi masa magana sai yace "Kilan zaman jirgine, kasan abinka da wanda bai saba ba" Sosai yaba Alhaji Mustafan dariya "Ka kyauta Sa'idu, ni zaka gayawa bakar magana" Shima sai yayi dariya, dan ya bar maganar ne daman ya sako raha a ciki, shima baisan abinda yake damunshi ba. Jin hayaniyar da ake tayi ta ragu yasa shi maida hankali kan abinda yake faruwa a cikin falon, sai yaji neman aure ne, akwai yarinyar da Alhaji Jibril yake rikewa, yar 'dan uwansu ce daya rasu, to shine wakilan yaron da yake sonta da yake suma sanannu ne anan garin Maidugurin suke neman auren "Ma Shaa Allaah, ai da kunzo da wuri ma da an hada gabaki daya..." Cewar wani cikin Kawunan yarinyar "A shirye muke, a yanka mana sadaki kawai a daura, in yaso sai a hada sauran walimar ta mata da zasuyi ayi tare, da sauran al'adu In Shaa Allaah..." Cewar daya cikin wakilan yaron, nan da nan aka yanka musu sadakin da suka fito dashi aka kirga aka bayar, sai ga wani auren an daura, anata addu'a da fatan alkhairi, Alhaji Mustafa ne zaune a kusa da Alhaji Modu, da yake cikin farin ciki yake, sai abin ya kayatar dashi, ya kuwa juya ya cewa Alhaji Modu "To ai muma a shiryen mukazo, wajenka za'a nemi auren Aise ko gurin Alhaji Babban Yayaa zamu mika kokon barar mu" Kallo kuwa ya koma kansu, Alhaji Modu da sanyin dakin bai hanashi hada zufa lokaci daya ba, ya gyara zamanshi, wani irin bacin rai yana dirar masa lokaci daya, babu wanda yayi masa wannan abin sai Hajiya Rumana, ko rantsuwa yayi ba zaiyi kaffara ba, itace ta hada abin nan, saboda tasan akwai kunya a tsakaninsu da Alhaji Mustafa, ga mutane nata kallonshi "Auren Aise?" Alhaji Jibril ya katse shirun, sai kuwa Alhaji Mustafa ya daga masa kai "Yaronka muke nemawa Auren, Haris" Ganin yanda Alhaji Jibril ya fadada murmushin da yakeyi yasa Alhaji Modu saurin fadin "Na dauka ma ai kunyi magana da Rumana..." Dan ya shirya bata mamaki, kamar batasan girman son da yake yiwa yaranshi, idan duk idanuwan duniya ne zasu tarar masa, ba zai taba mikata inda zata cutu yana cikin hayyacinshi ba, kunya da nauyin Alhaji Mustafa bakomai bane, wasu abubuwa ne da a yau ya turesu gefe daya kamar basu taba wanzuwa ba "Na fada mata akwai yaron da yake neman Aise din, kaga ba'a nema cikin nema" Lokacin dasu Alhaji Mustafa suke yara, idan akaji shiru irin wannan sai manya suce "Mutuwa ta gifta" To kwatankwacin wannan shirun ne ya ziyarci falon, a tare dashi wata irin iska mai sanyin gaske data lullube Alhaji Mustafa, lokaci daya kwakwalwarshi take son fahimtar abinda yake faruwa, kamar in yaji dai-dai auren Aise dinne Alhaji Modu ba zai basu ba "Subhanallah...to ya akayi haka?" Maganar Alhaji Jibril ta kutsa cikin rudanin da Alhaji Mustafa yake ciki "Wallahi ban sani ba, dan ni ba muyi magana dashi ba, ita dai Rumana tayi mun zancen na gaya mata akwai yaron da yake nemanta, karatun shi yake karasawa itama tana karasa nata, ba zai yiwu ayi karanta ace za'a shigo da zancen Haris ba" Kenan Hajiya Rumana ce ta wulakanta shi haka? Ta sakashi ya kwaso har mutum uku suka taho neman auren da an riga an gaya mata ba za'a basu ba? Kuma cikin taro irin wannan? Wanne irin muzanci ne wannan ta janyo masa? A yanda ma yaji Alhaji Modun na magana da bacin rai, kamar Haris din bai kai namijin da zai iya daukar 'ya ya bashi ba, da ya duba sai idanuwanshi suka sauka akan na Alhaji Sa'id, saiya tsinci kanshi da furta kalmomin da zai shafe shekaru masu yawa yana dana saninsu "Ma Shaa Allaah, ai a musulunci ma shari'a ta hana nema cikin nema, da tayi mun bayanin nan, ko nayi magana da kai Alhaji Modu da ba'a samu akasi ba, amman tunda neman aure mukazo, ai ba za'a fasa ba, Sa'idu ina nemawa Haris auren daya daga cikin yaranka..." Ya karashe maganar idanuwanshi cikin na Alhaji Sa'id da yaji zuciyarshi ta buga, ta sake bugawa sanin kowa shi yake jira ya amsa, ya kalli Alhaji Mustafa, yanajin nauyin idanuwan mutanen dake dakin, amman babu abinda yake hangowa sai lokuttan da yayi tuntube da rayuwa, Alhaji Mustafa ya tare shi yana jingina shi da jikinshi batare daya bari ya kai kasa ba, sai yanda tun yana da shekaru kasa da goma a duniya, babu wani shafi na rayuwarshi da za'a bude batare da sunan Alhaji Mustafa ya fito a ciki ba, sau nawa yake rokon Allaah Ya nuna masa ranar da zai kamanta masa wani halacci badan ya rama wanda yayi masa ba, sai dan ya nuna masa shi din dan halal ne wanda baya manta alkhairi komin kankantarshi Sa'idu kaine fa zaka kulamun da abin nan Sa'idu ga kudi nan nasa a sakamun a account dinka in sun shigo ka fadamun Sa'idu cikin kudin nan na wajenka ka dauki kaso kaza Sa'idu Sa'idu Sa'idu Muryoyin Alhaji Mustafa suka dinga dawo masa, wasu na ture wasu, kuma dukkansu na wani alkhairi ne da adadin nauyin shi zai danne shi da ahalinshi gabaki daya, yau a karo na farko wannan muryar ta Alhaji Mustafa da wasu zasu fassara cike da iko da izza, tayi laushi, ta cika da rokon da bai taba giftawa a tsakaninsu ba, ta ina zai fara tankwabeta? Ai aminantaka zatayi Allaah wadai dashi, zaman tare zai tsine masa, ya tabbata duniya duka zasuce "Sa'idu baka san halacci ba" Sai dai cikin yaranshi da suka rage wa zai bawa Haris? Sauran su uku, Asiya yasan akwai yaran da yake zuwa wajenta, tana level 2 a yanzun, sai Khairiyya data gama rubuta jarabawarta ta aji shida, in ba irin yanzun ba, mantawa yakeyi bashi ya haifeta ba, yar kaninshi ce, yana da cikakken ikon bayar da aurenta batare da mahaifinta ya daga masa kai ba, amman anya yayi adalci idan ya tsallake Maryama ya bayar da Khairi? Inda ace daga Asiya sai Khairi ne, to saiya bayar da Khairin da hujjar Asiya na da wanda take so "Maryama, na ba Haris auren Maryama" Yayi maganar yanajin wani nauyi ya danne masa zuciya ya kara sanyaya masa jiki "Da alama dai yau aure bakwai za'a daura kafin taron nan ya tashi" Fadin Alhaji Kabir, sai kuwa Alhaji Jibril ya karbe zancen da "Alhamdulillah, Ma Shaa Allaah, ni zan bada sadaki kuwa..." Ya mike kafin ma wani ya fadi wata kalma, baiyi mintina goma ba ya dawo, a shekarar 2013 ce, kowa yasan darajar dubu dari, haka Alhaji Jibril ya dauko, ya kuma karasa ya kama hannun Alhaji Sa'id ya damka a ciki "Ga sadakin Maryama..." Cikin kasa da mintina goma aka daura auren Haris da Maryama, Auren da kaddara ta rantse akanshi, Auren da kowa zaice rabo ne kawai, Auren da zai canza rayuwar mutane da dama... * Lokacin da suka tafi, tun daga Kaduna har Kano hira sukeyi, wajen dawowa kuwa daga filin jirgi da aka dauke su, hirar tafi yawa ne tsakanin su Alhaji Kabiru, daga Alhaji Mustafa har Alhaji Sa'id kamar an liqe musu bakuna, kowa da abinda yake sakawa a ranshi. Alhaji Kabiru aka fara saukewa, sannan aka sauke sauran, tukunna suka direban ya nufi gida da Alhaji Mustafa, wani abu da Hajiya Rumana ta jima batayi masa ba, ko yace tunda ya kara aure, shine ta tareshi a harabar gida da taji motarshi inya dawo daga tafiya, tasha kwalliya cikin wata doguwar riga ta leshi kalar ruwan toka daya amshi bakar fatarta, tayi shar da ita, daya fito daga motar, murmushinta da kuma tarbar da ta fito tayi masa ya tabbata saboda tasan abinda tayi ne, tun azahar take kiranshi tana tambayar ya ake ciki, yayi wani murmushin takaici yana cewa "Saurin me kikeyi ne Rumana? Ba gidan zan dawo ba" Watakila murmushin ne yasa tayi dariya, ta kuma dauka anyi nasara, ramin data hakawa Alhaji Modu bata bar masa wani zabi daya wuce fadawa ba, aikuwa itace mutum na farko da zata fara kiran Haris ta gaya masa, tayi masa albishir din da take fatan har karshen rayuwarshi karya manta dashi "Sannu da zuwa..." Ta fadi tana kokarin kama hannunshi, bai bata kunya ba, shima nata hannun ya kama suka karasa har bangarenshi "Amman kunyi sauri..." Yayi murmushi kawai, ya zauna kan kujera, ita kuma ta shiga cikin dakin sosai, in dai karamin fridge dinshi yake ta dauko ruwa, ta dauki kofi a wajen da ake ajiyewa tana kawo masa ruwa, ya sha har saida ya nemi kari, ita ta karbi kofin ta ajiye, ta zauna a gefenshi, ya kamata ace tana Maidugurin tasani, sai kiranta sukeyi ta langabe tayi musu karyar bata da lafiya, in taji dadin jikinta, a yanda ta fada washegari zata isa Maidugurin, ranar Lahadi kenan, tunda akwai sauran shagulgulan da za'a gabatar, kuma ba wani abu ya hana mata dokin bikin ba duk kaunarta da hidimar biki, sai gujewa Alhaji Modu da takeyi, bataso su hadu sai ta tabbatar an gama wannan maganar, ita dashi sai dai su bada labarin halayen juna. Kuma ko da shekaru suka ja a tsakaninsu, ai ance hali zanen dutse, akwai halayen da ko lokaci baya raba mutum dasu, daga cikin wannan halayen tasan Alhaji Modu ya bita har cikin gida ya damko hannunta zuwa inda zasu sake suyi fada ba wani abu bane ba, inma taki hankalinshi kwance zaiyi fada da ita a gaban kowa, su biyun anyi musu shaidar rigima a kaf ahalinsu, tun tasowa, kuma wannan rigimar shekaru basu raba kowanne a cikinsu da ita ba. Ta numfasa da niyyar tambayarshi yasa hannu a aljihunshi ya zaro goro, irin goron da tasan ana rabawa ne a lokacin daurin aure, manya-manya, ja da kuma fari, guda biyune ya mika mata, ta karba idanuwanta cike da tambayoyi "Ga goron auren Haris..." Ta dan zaro idanuwa, ta bude baki, ta rufe, ta sake budewa amman duk wasu kalamai nata kamar sunbi iska haka takeji, ta rasa abinda ya kamata ta fada, sai kawai ta kai goron nan bakinta ta gutsira ta tauna "Alhamdulillah, Allaah Yasa an daura alkhairi..." Ya amsa da "Amin thumma amin" Da yake kafin su juyo, Alhaji Modu da kallo daya zakayi masa kaga yanda kunya tayi masa dabai-bayi ya rantse ba zasu bar Maidugurin ba sai anyi duk wata siyayya daya kamata ace bangaren maza sunyi dangane da aure, babu inda zasu dauko wannan kayan su taho dasu, sai goron yasa hannu ya diba ya mimmika musu, harda Alhaji Sa'id "Kayan nan zasu biyo bayanku zuwa Kaduna In Shaa Allaah..." Ya kuma san idan basu iso cikin daren yau ba, to gobe suna hanya "Me yasa kikayi mun karya Rumana?" Ya tambaya idanuwanshi fes cikin nata. "Me yasa zaki turani neman auren da aka riga aka gaya miki ba za'a bayar ba? Saboda ki wulakantani a cikin taron danginki?" Komai nata yayi tsaye cak da tambayoyinshi, harda hakoranta da suke kokarin tauna mata katon goron data gutsira "Har yanzun ba zaki daina halin nan na aikata duk abinda zuciyarki ta saka miki ba ko? To Alhamdulillah, burinki bai cika ba Rumana, ban kunyata ba, na nemawa Haris auren Aise an hanani, amman bamu baro Maiduguri ba saida aka daura masa aure da Maryama" Kuma a duk maganganun da taji, sai ta zabi tayi tsokaci akan kalmarshi ta karshe "Wacce Maryaman?" Yayi mata wani kallo kafin ya amsa da "Maryaman Sa'idu" Goron da yake bakinta ta furzo dashi waje har a jikin Alhaji Mustafa kuwa, batasan ta mike ba sai da taji ta akan kafafuwanta, zuciyarta na kadawa gangar jikinta wata ganga da ta kasa tantance ta bacin raice ko tsananin firgici Haris din aka daurawa aure da 'yar gidan Alhaji Sa'idu? Haris dinta? Babu abinda kwakwalwarta take hada mata sai jininta da na Alhaji Sa'idu a waje daya, sai danta mafi soyuwa a cikin zuciyarta da jinin Alhaji Sa'idu, almajirin nan da mijinta ya dauka da muhimmancin da ta kasa gane tushen shi, wacce irin bakar rana ce "Haris din? Haris din ka dauka kaba Sa'idu? Dana Mustafa?" Tayi maganar wasu hawayen bakin cikin na wanke fuskarta "Ko dai shi Sa'idun ya rufamun asiri ya dauki auren Maryama ya ba Haris ba" Wasu hawayen ne suka sake zubo mata "Allaah Ya tsinewa wannan rufin asirin Mustafa, in dai na Sa'idu ne Allaah Ya tsine masa...na rantse da Allaah ba'a isa ba, babu wanda ya isa yayi mun haka, akan me? Kai ka haifa mun dan ko shi Sa'idun?" Da wani irin bacin rai yake kallonta "Ke kika haifi abinki, amman ni nake da iko dashi a matsayina na ubanshi, kuma a karo na farko a rayuwarshi zan ga idan na isa in amsa wannan matsayin a wajenshi ko zaki hana ne Rumana" Ta kai hannu ta share hawayenta tanajin yanda zuciyarta take zafi kamar zata kama da wuta "To baka isa ba, kana jina? Kaima baka isa ba balle Sa'idu...zan kira Haris ya sakar masa 'yarshi a yau din nan ba sai gobe ba..." Tayi maganar tana juyawa da saurinta, ta kai kofa kalamanshi suka tsayar da ita cak "Idan kikasa Haris ya saki Maryama a bakin aurenki, idan maganar auren nan ta isa kunnen Haris daga bakinki a bakin naki auren Rumana..." Kafafuwanta taji suna neman kasa daukarta, ta juyo da idanuwanta da suka sake launi "Akan Sa'idu? Ni kakewa barazanar saki akan Sa'idu? Akan 'yar shi?" Nashi idanuwan shima sun rine da bacin rai "Eh akan Sa'idu da 'yar shi" Ta jinjina kai, batare data furta komai ba ta fice daga dakin, yanajin yanda bugun zuciyarshi ya karu saboda bacin rai, akan wannan auren da sai bayan an daura shi yaji fargaba ta dirar masa, a shirye yake daya nunawa Rumana iyakarta, ya kawo karshen duk wani kauda kai da yakeyi mata akan yanda ta dauki Alhaji Sa'id, da bakinshi ya nemarwa Haris auren Maryama, kuma zaiyi tsaye wajen ganin ya sauke wannan amanar da ko dogon tunanin Alhaji Sa'idun baiyi ba ya mika masa ita. Ai daman yasan dole za su kwashi 'yan kallo da ita, tunda ta saba ita take iko da yankewa yaran hukunci, shi bai isa ba, wannan karin ya shirya mata tsaf tun da aka daura auren. Sai dai shi Alhaji Sa'id din baiyi wannan shirin ba, asalima bayan kafafuwanshi da yake ja dakyar lokacin da su Alhaji Mustafa suka sauke shi gida. Aljihunshi ma rinjayarshi yakeyi, duka biyun, daya goro ne, dayan kuma sadakin Maryama ne. Haka ya shiga cikin gidan nashi da sallama cikin muryarshi da yaran suka dauka ta gajiya ce, ganin kuma yanda yake ta amsa sannunsu da kai kafin cikin irin muryar yace wa Khairi "Ina Hajjanku?" Ta mike da saurinta, bai ga Maryama ba, amman kafin Hajjan tazo ma duk yaran sun watse, sai kace sunga alamun magana yake so yayi da matarshi, magana mai muhimmancin gaske, dan itama Khairin dakinsu ta wuce, sai gata kuwa tana yi masa sannu, tasan yana hanya, yaran shinkafa da miya sukayi, shine bata sa kowa ba, ta shiga da kanta take soya masa funkason da taki karbar tayin kowa wajen yin aikinshi, tama gama ta hada komai, tana dauraye hannunta ne Khairi ta fada mata gashi nan ya shigo, kallo daya tayi masa tasan ba gajiya bace kamar yanda yaranshi suke tunani, damuwa ce kwance akan fuskarshi, ta zauna akan doguwar kujerar da shima yake zaune, bayan tayi masa sannu da zuwa ya amsa, yaja numfashi yana saukewa, ya kalleta na wasu dakika. Hannu yasa a cikin aljihunshi ya fara dauko goro guda daya daga ciki, baima san guda nawa bane Alhaji Mustafa ya danka masa, ya kamo hannunta ya saka a ciki, duk da bata tare da ma'abota cin goro, amman ai ta ganshi sau babu adadi a rayuwarta, yau dai ne ganin wannan din da yake hannunta ya haifar mata da faduwar gaba mai tsananin gaske, kafin kuma tayi wani yunkuri ya sake saka hannunshi a aljihu ya zaro damin kudi ya kara kama hannunta ya dora akai "Kudin menene wannan? Goron menene?" Tayi tambayar cikin rawar murya, daga farko, kafin taga kudin sai zuciyarta take saka mata ko aure ya kara? Lokaci daya taji tana so ta fashe da kuka, ta kuma ji tanaso tayiwa kanta dariya "Sadakin Mairama ne, goron daurin aurenta ne da akayi da Haris dazun a garin Maiduguri" Ta zuba masa ido na dakikun da suka bace daga lissafinta, kallonshi takeyi kamar wani bakonta "Nayi muku laifi ko? Na bayar da auren 'yarki batare da shawararki ba" Hawaye ne taji sun zubo mata da watakila da tana da ikon hango kaddarorin da suke jiran Maryam din sai tace wasu a cikine ta hango, tausayin 'yarta ne ya kamata shisa, amman a yanzun kam ba zatace ga dalilin hawayen ba "Ya zanyi in kalli Mustafa ince ba zan ba Haris auren 'yata ba?" Ta ajiye kudin akan kujerar, ta kamo hannunshi da yake rawa "Allaah Ubangiji Yasa albarka a auren, Allaah Yasa duka mu hadu wata rana muce gara da akayi, Allaah Ya basu zaman lafiya da fahimta irin wanda za'a bada labari a tsakanin jikokinsu wata rana" Ya dumtsa hannunta cikin godiyar da ya kasa furtawa, duk da kalamanta sun nutsar dashi, amman ai ita yasan macece da baya gajiya da godewa Allaah da samunta, macece da bata taba bata fuska akan hukuncin da zai zartar ba, macece fa da ya kwaso mata yaran 'yan uwanshi ya cika mata gida dasu, ta karba ta rike kamar nata, bai tabajin korafinta akan yanda danginshi suke mata zarya akai akai ba "Ina take? Ina Mairama?" Ya tambaya, sai a lokacin ne kuma zuciyar Hajja ta buga, ita ta karbi auren da zuciyarta daya kamar yanda tasan Alhaji Sa'id ya bayar da auren da tashi zuciyar a wanke, amman ai daga ita harshi babu wanda zai taya Maryam din zaman auren. Sannan ita tasan abinda shi bai sani ba, Tasan Maryam na son Ishaq... Da farko bata maida hankali ba, sai da taji yanda 'yan gidan gabaki daya, ciki harda mazan kuwa suke saka Maryam a gaba in Ishaq yazo "Mutumin naki fa yazo..." Har ta fara saka ido, tana ganin yanda idanuwan Maryam yake cika da kunya da wani abu da yayi mata kama da fuskarta a cikin mudubi a lokuttan da take tsakiyar soyayyar Alhaji Sa'id. A zuciyarta, a lokacin tayi musu addu'a, idan akwai alkhairi a tsakaninsu Allaah Ya tabbatar, idan babu kuma yayi musu musaya da mafi alkhairi, dan kuwa Ishaq din yaro ne nutsatse, bata taba ganin yayi wani abu akasin haka ba, sannan mahaifiyarshi tana mutuntata, in zasu zo gidan nan, a kwanakin da zasuyi tare suke shiga kitchen, haka duk wani aiki da zata ga anayi ko ance tabarshi saita sa hannu anyi da ita. Gashi basu da fargabar tsayawa bincike tunda ai na gidane. Kawai ta cigaba da saka ido ne akan motsin Maryam din dama na Ishaq din idan yazo gidan, da yake bashi da rawar kai, bata taba ganin sun kebe wani waje ba, duk hirar da zasuyi anan falo ne, wani lokacin ma tare da kowa da kowa, sai dai yanayinsu ya nuna maka akwai soyayya, irin soyayyar nan mai sanyi da ake ginata a hankali, soyayyar da babu wata gaggawa a ciki, ashe kaddara zata yayyafa musu ruwa kafin ma itacen nasu su gama bushewa balle suyi tunanin kunna wuta. Sai tausayin Maryam din ya danne zuciyar Hajja, a cikin yaran gidan kaf ma babu wanda akayiwa aure batare daya kammala sakandiri ba, kai Zahra mace kawai tana gamawa akayi bikinta, kuma a lokacin ko ita ta samu admission, sai ta cigaba da karatun a dakinta. "Ke zakiyi magana da ita koni?" Da sauri ta girgiza masa kai, ita uwace, kamar yanda ya kasance irin uban da kowanne yaro zaiyi alfahari dashi, amman a rayuwar yaransu, itace mai zafi, itace mai fada, itace take duka, itace in an tambayi abu takan hana a lokutta da dama, akwai damuwar yaran da yawa da sai dai taji labari a wajenshi, sunfi sakewa dashi da dukkan lamurransu fiye da ita, kamar dai akwai wani abu mai taushi a tsakaninshi dasu, abinda yake sakasu fada masa komai batare da fargaba ba, a gidaje da yawa, ko tsayayyen saurayi yara sukayi suke son mahaifinsu ya sani, mahaifiya suke tunkara sai ita kuma ta sanar, amman haka suke zagayeta suje wajenshi kai tsaye. "Hajja zatayi fada, Hajja zata hana" Haka suke cewa, batama jin tana da wasu kalamai da zatayiwa Maryam bayani, me zatace mata? Ta ina zata fara? Babanki ya bada aurenki? Yanzun ke matar aure ce? Ta inda duk ta kamo zaren sai taji ya tsinke mata "Ki taimaka ki kiramun ita to" Alhaji Sa'id yayi maganar muryarshi cike da rauni, sai ta mike, a wannan yammacin ma, ita Maryam din tana dakinsu, da wuri suka tashi Islamiyya, ko tace ma basu hada mintina talatin ba aka tashi, anyi rasuwa anan kusa da Islamiyyar, babban mutum ne, sai aka tashe su da wuri saboda Janaza, unguwar ma harta fara cika, haka suka ratso mutane suka dawo, bata ma damu dasu Asiya da suke tsokanarta ba, haka ta tashi da wani irin sanyin jiki, ko magana bataso tun safen, su kuma basu ga lokacin da zasu uzzura mata ba sai a wannan yanayin. Suna mata tsiya ne kan wasu turaruka da Ishaq ya kawo mata, guda hudu ne, tayi niyyar basu dai-dai saita fasa, tunda Asiya tace "Na tabbata shekara yayi yana tara kudin turarukan nan, dan daga ganinsu zasuyi tsada, shima da iyayi..." Ita kuma Khairi tayi dariya "Haba ba zai shekara ba Adda, ai kinsan in yazo dole Abba zai bashi kudi idan zai koma..." To ta fasa basu, gara ta fesa guminshi da hakurin da yayi da abubuwan dadi ya kashe mata kudin, tattalasu ma zatayi, ta boye inda tasan daga Asiyar har Khairi duk bincikensu ba zasu iya ganowa ba balle su dauka. Yanzun ma maganar turaren sukeyi, suna ja mata Hadith din da ya haramtawa mata fesa turaren da wani zaiji kamshin shi idan zasu fita "Ke saurayi ya kawo miki, shine kika shanshara kika fito" Cewar Asiya, har sukazo gida, ta tafasa batace musu ba, meatpie dinma da aka gaji dayi mata kwalele aka bata, gutsira daya tayi masa dakyar ya wuce makoshinta, saita ajiye ta kwanta, a ranta take fatan Allaah Yasa ba zazzabi zatayi ba, ta kasa gane yanayin jikinta gabaki daya. Batasan bacci ya dauketa ba saida taji ana tashinta "Baccin yamma Maryam, sai kinyi zazzabi...ke Khairi kina ganinta maimakon ki tasheta" Cewar Hajja, Maryam din ta tashi tanajin kanta yayi mata nauyi "Kije ki wanke fuskarki kizo Abbanku yana kira, yana falo" Kai ta daga, kamar ma bata gama fahimtar abinda tace ba, haka ta shiga bandaki ta wanke fuskarta, ta fito tana nufar falon "Abba sannu da zuwa" Ta fadi da murmushi a fuskarta, ya kalleta yana ganin yanda fuskarta ta kumbura saboda baccin da tayi "Me ya sameki?" Tasa hannuwanta duka biyun tana taba fuskarta, wani abu daya fito masa da kuruciyarta, shekarunta sha shida suka haska a idanuwanshi kamar jiya ya riketa yayi mata huduba. Sai yake jin rauni na kara dirar masa "Bacci nayi, anyi rasuwa shine aka tashi da wuri a Islamiyya, da muka dawo sai nayi bacci, Abba ka kawo mana dublan?" Maganarta tasa shi yin gajeran murmushi "Dublan dai Mairama?" Ta daga kai "Na bikin da kukaje fa" Tayi maganar tana karasawa cikin falon ta zauna a kasan kujerar da yake zaune, kusa da kafafuwanshi, yanda ta saba, ko wani ne ya zauna a wajen nan in tazo saita saka rigimar da zatasa Alhaji Sa'id yace a tashi a bata wajenta "Ai wajen daurin aure ba'a bada dublan, sai dai goro, gashi nan in kinaci" Ta girgiza kai da sauri "Bana cin gori ni kam Abba, bansan me yasa mutane suke cinshi ba duk dacin shi, naga kun kwana ne shisa na dauka an baku dublan" Shine ya girgiza mata kai wannan karin, ya kalleta "Mairama" Ya kira, daman in yana waje kacokan hankalinta akanshi yake, yanzun ma kara natsuwa tayi tana kallonshi kafin ta amsa, shikuma ya cigaba da magana "Kinsan waye Alhaji Mustafa a wajena?" Ta daga masa kai "Abokinka ne, babban abokinka, ka bamu labarin yanda kuka hadu dashi" Ya numfasa, kalamanshi yake ta tattarawa suna neman bajewa "Yau ya rokeni alfarma Mairama, bai taba rokona komai ba tunda na sanshi..." Ta kalli yanayin Abban nata, zuciyarta na neman karyewa, saita tsinci kanta da furta "Kayi masa mana Abba" Cikin karamar murya "Nayi masa, alfarmar ce mai nauyi, yanzun kuma nake kara jin nauyinta dan ta hada dake" Ya kamata ace zuciyarta ta buga, amman bataji komai ba, kallon Alhaji Sa'id kawai takeyi "Yau na bayar da aurenki Mairama, ina ba duka yarana zabine, ina ba kowa dama ya kawo mun mijin daya nutsu dashi, haka kuma nayi addu'ar kuma inyi muku, shisa na rasa ta inda zan baki hakuri Mairama, ban baki wannan zabin ba" Ko kadan bugun zuciyarta bai canza ba, batama san hawaye takeyi ba saida taji duminsu akan kuncinta, ta kuma gane ta fahimci duk abinda yace saboda labbanta da suka furta "To Abba..." Irin kallon da yakeyi mata ne yasa tayi saurin saka hannu ta share hawayen da kamar ta bawa wasu kofar zubowa ne "Kingane me nake fada?" Ta daga masa kai "Ba auren kawai na bada ba, an daura, an daura aurenki da Haris yau...ga sadakinki nan" Ya karasa yana daukar kudin da Hajja ta ajiye masa ya mika mata, batasan ya akayi tasa hannuwa biyu ta karba ba, sai shima ya tsinci kanshi da mayar da hannunshi cikin nashi aljihun ya dauko mata goro guda biyu ya sake mika mata "Goron ne...kiyi hakuri ban baki zabi ba" Ta girgiza masa kai tana kasa cewa komai, sukayi shiru su duka "Nagode, Allaah Yayi miki albarka" Muryarta na rawa ta amsa da "Amin Abba..." Kuma sai ta mike, da kudin, da goron, harta tafi ta dawo tace "Me zanyi dasu Abba? Kudin? Da goron?" Yaso ya kakaro murmushi, hawayen da take tayi ne suke kara karya masa zuciya "Naki ne duka" Saita mika masa da hannuwanta biyu "Ka ajiyemun to" Baiyi musu ba ya karba, saita juya ta nufi hanyar dakinsu, ta tura ta shiga, ta karasa, amman akan gadon Khairi ta zauna batare da tasan tayi hakan ba, yanayinta yasa Khairin tashi zaune "Maryama? Lafiya? Kuka kikeyi...meya faru?" Ta share hawayenta, ta kalli Khairi, wasu hawayen suka sake zubo mata "Zazzabi nakeyi...jikina zafi yakeyi mun" Data taba jikin Maryam din sai kuwa taji akwai zazzabin "Kiyi hakuri, bari in kira Hajja sai ta baki magani, in kuma asibiti zamuje saimu tafi, amman kece kike yiwa ciwo kuka Maryam..." Khairi ta karashe da damuwa a muryarta, saida ta kai kofa sannan Maryam tace "An daura aure na yau, Abba ya fadamun ya bada aurena, wai ya ba Haris" Sai khairi tayi saurin dafa kofar saboda kanta da taji ya sara, babu shiri ta koma cikin dakin tana kama kafadar Maryam din ta girgizata "Bangane an daura aurenki yau ba" Ta saka idanuwanta da suke cike da sababbin hawaye cikin na Khairi da suke cike da firgici, dan tunda take bata tabajin wani abu da yake neman birkita mata tunani lokaci daya ba irin wannan "Haka Abba yace, ya bani kudi da goro sai nace ya ajiyemun" Cikin Khairi ya murda "Wai wanne irin aure? Aure fa kikace, kinsan meye aure?" Maryam taji dariya ta kwace mata "Aure yace mun" Khairi tayi tsaki tana sakin kafadar Maryam din ta wuce ta fita daga dakin, kanta tsaye ta wuce dakin Hajja ta kwankwasa, saida ta bata izinin shiga tukunna ta tura da sallama a bakinta "Hajja kizo, Maryam bata da lafiya, tana zazzabi, gashi tana wasu surutai wai an daura mata aure...kizo a kaita asibiti, kuka takeyi ma" Sai Hajjan ta mike "Ina Asiya?" Khairi ta amsa da "Tana dakinta inajin, bari in kirata, tare zamu tafi mu duka?" Batama jira amsar Hajjan ba ta juya ta fita, sanda suka koma dakinsu ita da Asiyar sun samu Hajja acan, tana zaune, ta rike Maryam a jikinta da take wani irin kuka har jikinta na bari, a cikinsu babu wanda zaice ya taba ganinta tana kuka haka "Wai zazzabin ne Hajja?" Asiya ta fadi cikin rawar murya "Ku zauna" Cewar Hajja, babu wanda yayi musu, a kasa suka zauna "Yau an daura auren 'yar uwarku, Abbanku ya bada aurenta a Maiduguri da sukaje, ya ba Haris din Babanku na Tudun Wada..." Hajjan suke kallo kamar tayi musu wani yare "Aure kuma Hajja? Maryam din? To saboda me?" Asiya ta tsinci kanta da tambaya "Saboda ya isa...ko idan ya daurawa wata a cikinku zatayi masa musu ne?" Hajjan ta fadi tanayi mata wani kallo da yasa ta sadda kanta kasa, hawaye na balle mata, zuciyarta sai bugawa takeyi, ta rasa ta inda zata fara daukar wannan abin, anfa daurawa Maryam aure ake ce mata, da Haris din da a cikinsu babu wanda ya taba ganinshi, to yaushe ma aka fara haka? Yaushe Abban nasu ya fara haka? Wa aka taba yiwa irin wannan auren? Ishaq din fa? Ita kanta Maryam din ta ina zata fara? Tana jin yanda hawayenta suke zuba, Khairi ma kukan takeyi, 'yar uwarta take tayawa kuka, dan ita ko dukan Maryam akayi tare suke kukansu, kome ya samu Maryam tare suke rabawa, a yau dai tanajin wani abu ya samu Maryam wanda ba zasu iya rabawa ba, wani abu da Maryam din ita kadai zata dauki abinta. "Yanzun za'a kira sallah nasan, ke Asiya ki bata paracetamol tasha, sai kuyi sallah...bance ku zauna kuna kuka kamar anyi mutuwa ba, ku kula da 'yar uwarku" Suka daga mata kai, tasan lallashinsu ya kamata ta zauna tayi, amman inta kara mintina biyu kukan zata tayasu, batason suga rauninta akan wannan auren, sai ta fice tana barinsu. Suka kuwa tashi suka koma kan gadon inda Maryam take kwance, ita fa in zasu tambayeta a halin yanzun bata ma san kukan me takeyi ba, gabaki daya batama san me takeji ba, kukan ne yake ta zuwa da kanshi, ta kasa tsayar dashi, batayi gardama ba tasha paracetamol din da Asiya ta bata, ta kuma yi alwala, amman sallar takeyi tana kuka, harta idar bata daina ba "Kar kanki yayi ciwo Maryam, dan Allaah kiyi hakuri haka, ai nasan Abba zai kara yi mana bayani...kuma ba wani abu bane In Shaa Allaah, ba zaiyi abinda yasan zai cutar dake ba" Asiya ta fadi a tausashe tana share hawayen itama "Na sani" Maryam tace cikin shesheka "To ki daina kuka" Saita kalleta "Na kasa" Aikuwa da gasken ta kasa, a haka sukayi isha'i, sun karbi abincin da Hajja ta zuba musu, babu wanda yaci na kirki, Maryam da suka matsa mata loma daya tayi ta fara yunkurin amai, haka suka tattara abincin Khairi ta mayar kitchen ta dawo, yau a gadonta suka kwanta ita da Maryama, Asiya kuma ta kwanta akan na Maryam din, suka kwana anan gabaki dayansu, bayan wani baccin wahala ya dauki Maryam din, dan zazzabine a jikinta ga kuma ciwon kai saboda kukan da tayi. Sai dai su sun samu bacci, ita kuwa Hajiya Rumana yanda taga dare haka taga rana, musamman da a karo na farko bayan ta kira Alhaji Jibril da kukanta riris ya kware mata baya "Haba dai Rumana, kinsan muna da halaye da yawa, za'ayi mana shaida akan abubuwa kala-kala, harda son kanmu da muke dashi, amman kowa zaice dattako halin gidan nan ne, a jininmu yake, iyayenmu da kakanni ba kananun mutane bane, sannan munsan halacci, to abinda Alhaji Sa'id yayiwa mijinki kenan, halaccin daukar 'yarshi ya ba Haris batare da wani dar ba, bayan naki dan uwan, uwa daya uba daya yace hana..." Kuma ya cigaba da fadin "Mun zauna ni da Modu, saboda zancen shi bai zauna mun ba, ni na rutsa shi da tambayar dalilin da zaisa ya hana Haris auren Aise ya gayamun, a ganinki a irin amincin da yake tsakaninsu da kike yawan korafi akanshi shi Alhaji Sa'id din zai rasa sanin halin Haris din? Ina kaunarku, kinsan bana shakkar nunawa, ina kuma kaunarku da duk ahalinku, amman koni ba zai wahala in dauki 'yata in ba Haris, ki karbi auren nan da rufin asirin da nake hangowa tare dashi..." Bata jira ya kara dora kowacce kalma akai ba ta kashe kiran tana kara rushewa da kukan bakin ciki, wanne so Alhaji Jibril yake magana yanayi mata? Aita dauka ko a gidan gala ta tsinci Haris din ta dauke shi tace ya zama nata su masu yi mata kara ne, masu rufa mata asiri ne. Sannan ko da gaske ne Haris nayin abinda Modu ya lika masa, suna nufin ba zasu iya daukar 'ya su bashi ba? Ta share hawayenta, tana kissima shikenan, zatayi shiru, ai ba zata bari Alhaji Sa'id yayi nasara biyu akanta ba, tana da yakinin ba wani abu bane yasa ya dauki Maryam ya ba Haris sai kwadayin abinda zai kara samu sanadin hakan, abinda 'yarshi zata yago musu. Zatayi shiru taga abinda Alhaji Mustafa zaiyi, Haris dai bayan dakon cikinshi da tayi babu wanda ya tayata nishin fito dashi, Gasu gata, zata ga ta inda za'ayi wannan zaman auren in dai jininta na yawo a jikin Haris... 12 Idan ya daga yatsunshi zai kirga abubuwan da ya damu dasu, dama wanda ya taba sakawa a ranshi, tunda baya lissafawa da iyayenshi balle kuma 'yan uwa, su wannan babu wanda ya bashi zabi akansu, sai sauran abubuwan suka zamana yan kadan, idan kuma auna 'yan kadan din zaiyi akan sikeli, a yanda yakeji a halin yanzun, Aise ce zata zamana a saman komai, tunda in ya duba gaba, yayi tunanin inda yake fatan rayuwa ta kaishi sai yaganshi tare da Aise din, hannunta cikin nashi, ko hannunshi cikin nata, idan kuma ya hangi rayuwar, baiga Aise din a ciki ba sai yaji komai ya hargitse masa, kamar wani gini da ba rushewa yayi ba kawai balle yayi tunanin tsintar wani abu da zai harhada, murmushewa yayi, iskar da batayi niyya bama zata iya kadar da abinda yayi ragowa. Shisa daya amsa wayar Alhaji Mustafa, suka gaisa yace masa "Ina so muyi magana Haris, ba zai yiwu ta waya ba, inaso inzo..." Sai yace masa "Zanzo Baba, ni zanzo, nan da kwana biyu In Shaa Allaah" Ya gama exams, akwai mentor dinshi, asalinshi bature ne amman kuma haihuwar nan kasar Italy din, ba alkawari yayi masa ba, ya dai fada masa akwai yiwuwar ya sama masa clearance ya bishi aikin sati biyu a kasar Syria, dan yana daga cikin tawagar masu kawo labaran kai tsaye game da yakin da ake tayi tun shekarar 2011, in yaso sai Haris din ya zama cikin wanda zasu dauki hotuna, dama ce da zata bude masa kofofi masu yawa in har ya samu, sai gashi a karo na biyu yana addu'a akan wani abu bayan Aise, to yana da hutu kafin aikin dama wasu abubuwan da yake ta processing, haka kawai bayason wata hayaniya shisa yayi shiru yaki fadawa kowa ranar graduation dinshi, yasan daga Hajiya Rumana har Alhaji Mustafan zasu zo, haka ma 'yan uwanshi, Aise kadai ta sani. Hajiya Rumana zatayi fada ya sani, amman zata hakura, ai ba iya nan zai tsaya ba, dorawa zaiyi da karatun, zai lallabata ne kawai. Dan haka Aise ce kawai a wajen, ganinta yasa shi jin yanda da gaske baya bukatar kowa bayan ita, bayama cikin yanayin kamar yanda itama ya kula babu wata walwalar kirki a tare da ita "Ya zanyi wata kusan uku banganka ba? Ya zanyi?" Ta tambaya muryarta na karyewa "Zamuyi waya kullum Aise, zamuyi video call" Ta girgiza masa kai, hawayenta na zubowa "Ya mun kadan, komai zai iya faruwa a wata uku" Ya tsinci kanshi dayin murmushi mai sauti "Me zai faru? Sonki zan kara? Ko sona zaki kara?" Ta juya idanuwanta da suke cike da hawaye, ya kama hannunta ya dora a kirjinshi "Kina nan, tare dake zan tafi" Tayi dariya ta kama hannun nata da yake rike dashi ta canza musu waje "Ga inda zuciyar take nan fa" Shima dariyar yayi "Idan tawa ba irin ta kowa bace fa? Tawa a dayan bangaren take, shisa son da nake miki ma nakejin shi daban, kamar babu irinshi, kamar yayi yawa..." Ya fadi yana saka idanuwanshi cikin nata "Son da nakeyi miki baiyi yawa ba kuwa Aise?" Da dukkan zuciyarshi yayi mata tambayar, saboda abin ya fara bashi tsoro, yanda tunanin rasata kawai yake birkita masa komai, yanda yake kasa samun natsuwa a tare da duk wata mace in yana cikin wannan yanayi, yanda har wiwin shi bata batar masa da damuwar Aise, kiris ya hanashi kwankwadar giya daren jiya, wai ko zai samu saukin nauyin da kanshi yayi masa, har zubawa yayi a kofi, sai dai aman da yake ganin masu shanta na shekawa bayan tambelen da take sakasu na daga cikin abinda yake kara masa kyamarta, bayason irin wannan kwamacalar. "Ina so ka kara sona, kayi mun son da zaka rabu da kowacce mace saini kadai" Ya sakeyin dariya, kuma a ranar da zasuyi sallama ya kasa hana kanshi yin abinda zuciyarshi da gangar jikinshi sukaso, ya sumbaceta, hawayen daya zubo mata yasa shi saurin fadin "Kiyi hakuri, na kasa ne, na kasa sarrafa kaina" Ta girgiza masa kai wasu hawayen na kara zubo mata "Bashi bane, ba kai bane ba, bansan me yasa ba, tsoro naji ya kamani Haris, kamar kana mun bankwana ne, kamar...ban sani ba" Sai ya sake sumbatarta, fiye da na farkon, har saida jikinta ya fara kakkarwa a cikin nashi "Wannan yayi miki kama da bankwana?" Yayi tambayar yana rike fuskarta cikin hannayenshi "Babu inda zani babu ke, kina jina, inda duk zanje ina tare dake, a komai nawa" Ta daga masa kai, amman idanuwanta cike suke da shakkun da baisan ya zai goge mata shi ba, sai kawai ya kara riketa a jikinshi, kewarta na dirar masa. Dakyar sukayi sallama kamar zata sakeyi masa kuka, har mamakinta yakeyi, yanda kuka bayayi mata wahala, a wajen Aise, abin murna ma kuka takeyi masa, ko abune yayi mata kyau zata iya fara hawaye, komai nata yayi masa, ko motsi tayi sai yaji ta burge shi. Haka ya hada duk wani abu nashi tunda makarantar dai ko ya kara dawowa dora karatunshi yasan wani dakin za'a bashi daban. Jirginshi na safe ne, haka ya kwanta babu wani karsashi balle dokin zuwan safiyar. Ko kadan baisan ruhinshi bane yake yiwa zuciyarshi alamar abinda yake jiransu a Najeriya. * Kallon Alhaji Mustafa yakeyi kamar yaune rana ta farko daya taba ganinshi a rayuwarshi, kamar kuma akwai wani bakon al'amari da yake faruwa da fuskarshi gabaki daya, ko sabon kai ya kara fitowa kusa da wanda yake dashi sun zama biyu, amman ba anan matsalar take ba, bawai shi bane, abinda yake fada ne, ai Haris yasan bashi da wata matsala data danganci lafiyar kwakwalwa, kuma cutar da bature yake kira da "Amnesia" babu yanda za'ayi ace ta dirarwa mutum yana zaune, bayan ya gama cin abinci har da ruwa, maganar da sukayi a ranar Asabar din na daga cikin maganganunsu da ba zai taba mantawa ba "...Yau zamu nema maka auren Aise" Haka yace masa, da yace zasuyi magana, ya kawo abubuwa da dama a ranshi, ciki harda hana masa auren Aise, kuma ko daya zauna a dakin Alhaji Mustafa din, abinda ya tsammaci ji kenan, shisa yake ta gayawa zuciyarshi wannan bakomai bane ba, son da suke yiwa juna shida Aise wani abune da suka shirya nunawa duniya bama iyayensu ba, dole zasu hakura, dole zasu barsu da juna in suka ga da gaske ba zasu rabu ba, to meye hadin maganarshi da Aise da abinda yaji Alhaji Mustafa ya fada a karshen zancen shi "A gaban mutane Alhaji Modu ya nuna mun ba zai baka Aise ba Haris, cikin taron mutane...tun tasowarka ban taba yanke maka hukunci ba, banajin ma akwai lokacin dana nuna maka matsayina na uba, yau ina so ka bude zuciyarka ka karbi abinda nayi, alfarma nake nema" Alfarma yace "Na nema maka aure, na karba maka auren a wannan ranar, na karba maka auren Maryama yar aminina Sa'idu...ina fatan zata maye maka gurbin Aise" To daman anawa neman aure alfarma ne? Yasan ana bada labaran da akayiwa mata auren dole, duk da abin bai taba kama hankalinshi ba sam, to su suna me za'ayi musu auren dole? Basu san 'yancinsu bane ba? Ko iyayensu basu san me sukeyi ba da kawai zasu kakaba musu aure daga sama sai kace wani kaya da in sun ga dama zasu wurgar, to shi baima tabajin inda akayiwa namiji abinda yaji Alhaji Mustafa yana fadin yayi masa ba "Kana jina Haris?" Cewar Alhaji Mustafan yana jin yanda jikinshi ya karayin sanyi da yanayin Haris din. Bai ga girman abinda ya aikata ba sai da aka kwana aka yini, fushin abinda Alhaji Modu yayi masa dana Rumana ya rissina, shisa ma ya yanke shawarar zuwa yayi magana da Haris din baki da baki, bawai ta waya ba dan yasan muhimmancin maganar, dan karya bashi kunya a idon mutumin da yake gani da daraja matuka. Da yace zaizo kuma sai zaman jiran nashi ya kara saukar masa da zullumi, ga shirun Hajiya Rumana a gefe, wani abu da bai saba ba, wani abu da ba halinta bane, ya tabbata akwai abinda take shiryawa, da kanshi yaje ya dauko Haris daga Airport bayan sun sauka, kuma baiga alamar tayi wata magana da Haris ba, itama ta kawo musu abinci anan bangarenshi bayan Haris din ya huta, tana ajiyewa tayi tafiyarta, inda lafiya zata zauna ne "Haris" Ya sake kira, kuma a duk maganganun da yaji saiya zabi ya mayar da amsa da tambaya "Waye yace akwai macen da zata maye mun gurbin Aise Baba?" Ya karasa maganar idanuwanshi fes a cikin na Alhaji Mustafa "Ai addu'a nayi, nake fatan ta maye maka din, kasan ba zanyi maka zabin abinda zai cutar da kai ba" Shifa so yake ya fahimci Alhaji Mustafa da maganganun shi yau, kamar yanda yake so shima ya fahimce shi, shekararshi hudu da dan wani abu a kasar Italy balle yace Hausa ta fara bace masa duk da yana dadewa baiyi ba in ba waya yakeyi da 'yan gida ba "Ni kuma nawa zabin ya zanyi dashi?" Ya sake tambaya yana kallon hannunshi wannan karin, yatsanshi karami, na haggun, daga ciki, ta gefe, tattoo ne da aka rubuta Aise, tare sukaje akayi musu, itama akwai nashi sunan a jiki, ita ta zabar musu inda zasuyi saboda tana tsoron fadan Binta, ta jima tana son yin tattoo ko da karami ne duk da a lokacin wasu taurari ne taso a zana mata a bayan wuyanta, amman Bintar tayi mata barazana da cewa in ma tayi, a ranar zata sakata a gaba har inda ake cire shi, kuma taji wanda akayiwa tattoo removal na fadin yafi ayi maka azaba, ninkin ba ninkin, saita hakura, har saida ta samu wannan dabarar, ranar haka ta dinga kama hannunshi tana gani kamar bata taba cin karo da wani abu da take so kamar yatsan nashi ba. Shima in ya kalla yana mamakin kanshi, amman zai kara rubutawa a duk inda ta zaba in dai zai sake ganin wannan kyallin farin cikin a idanuwanta "In Shaa Allaah ka samu mafi alkhairi...saboda..." Kallon Alhaji Mustafa yakeyi, amman kalamanshi sunki karasawa cikin kunnuwanshi sam, kamar an dauke masa jinshi na wucin gadi saboda hutun rabin lokacin da kwakwalwarshi ta tabbar zuciyarshi na bukata shisa ta taimaka masa ta rufe kanta Ya zaiyi da Aise Ya zai tsaya a gaban Aise da auren wata "Kasan me yasa nake karajin dadi da muka zo a musulmai?" Ta taba tambayarshi, ya girgiza mata kai "Saboda zan aureka, saboda aurenka zai bani abinda wasu mata ba zasu taba samu a tare da kai ba, saboda na fara addu'a tunda na fara sonka, kar Allaah Yasa ka kara auren wata bayan ni, ina maka son da zan iya hakuri har ka cire wasu mata daga rayuwarka, amman inajin zan mutu in ka ba wata mace kanka ta hanyar hada matsayinmu, ka soni, ka aureni, itama kaso ta ka aureta, mutuwa kawai zanyi" Dariya yayi mata, shi ina zai iya aure sau biyu? Me zai kaishi? Abin bai taba burgeshi ba, har kallon Alhaji Mustafa yakeyi a wasu ranakun yana tunanin abinda yasa shi ya kara aure, duk da Hajiya Rumana ta taba ce musu 'yan uwanshi ne suka sakashi a gaba saboda bata haihuwa ba, amman ai ba yaro bane da za'ace anyi masa dole, a ganin Haris yaso ya kara aurenshi ne shisa kawai "Zan iya tafiya Baba? Zan iya zuwa inyi tunani?" Sai kawai Alhaji Mustafa ya daga masa kai, daya mike ya fice daga bangaren Alhaji Mustafa, bai nufi nashi ba, wajen Hajiya Rumana ya tafi kai tsaye, ya sameta tsaye a falonta kamar wadda take jiranshi, sai ya karasa kawai ya rungumeta yanajin wani abu na karyewa a tare dashi, maganganun Alhaji Mustafa na dawo masa, ya kusan minti biyu kafin ya dago ya kalleta "Me yasa Mami? Me yasa kikayi mun alkawarin da kikasan ba zaki cikamun ba?" Kafin ta amsa ya kara cewa "Me yasa zaki bari Baba yayi mun haka? Yaro ne ni Mami? Zuciyata da abinda nake so basu da wani muhimmanci haka? Kawai sai a daura mun aure da wata batare da an tambayeni ba kamar bani da wani 'yanci?" Ya karasa maganar yanajin zuciyarshi kamar zata kama da wuta, ta sauke numfashi, ya fada masa kenan? Zata iya magana da danta yanzun, hawayen bakin cikin da suke neman zubo mata take ta mayarwa "Ni bansan zaiyi haka ba Haris, ai kasan babu yanda za'ayi a hadu dani ayi maka abinda bakaso, ko da kanaso ma ba zan taba bari ka auri 'yar Sa'idu ba, shima kwadayin abin duniya ne yasa ya yarda da wannan auren ba wani abu ba" Haris ya kalleta yana so ya fahimci abinda take fada "Kwadayi?" Ta jinjina masa kai "Ni nasan wallahi kwadayine, yana tunanin abinda zai samu a wajen Babanka, dama abinda 'yarshi zata samu inta aureka, shisa ya amince" Kai tsaye yace "Bana sonta, koma meyasa aka auramun ita" Amman kuma a kasan zuciyarshi yanajin wani abu na kullewa, yanajin kamar tun tashinshi alakarsu da Alhaji Mustafa hoto ce kawai, kamar baya ma ganinshi ne a cikin jerin yaranshi saita kama, sai yayi wani abu da zaiyi masa fada koya zage shi, duka ba'a shekara hudu ba daya fara jin yana da mahaifi kamar kowa ba, kuma wannan auren zai iya rusa musu komai, zai iya rusa masa wani abu da yake tattalawa, wani abu da bai taba tunanin zai samu ba, sai dai wannan bacin ran ina zai kaishi? Abinda yakeji wa zai saukewa? "Zama zakayi mu tsara yanda zaka rabu da wannan alaqaqai din a tsanake, dan sakinta zakayi Haris, ba zaka zauna da Maryam ba, ba zaka zauna da jinin Sa'idu ba" Maryam Ya maimaita cikin kanshi "Wanne tsautsayi ya sakaki fadowa rayuwata?" Yayi maganar cikin zuciyarshi "Kana jina?" Ta tambaya, yana jinta, kamar yanda yaji Alhaji Mustafa, amman ai ita ta karya masa alkawarin da tayi masa, shikuma ya kakaba masa auren da baiyi shawara dashi ba, su duka sunyi abinda suke so batare dashi sun duba ko sunyi tunanin abinda yake so ba Me yasa suke tunanin zaiyi abinda suke so yanzun? "Sakinta zakayi" Hajiya Rumana ta fadi, wata dariyar takaici mai sauti ta kwace masa "Saboda me?" Ya tambaya, cikin rashin fahimta ta kalle shi "Ba ya daura auren ba Mami? Baba ya daura mun auren da baiyi shawara dani ba, kin karyamun alkawarin da kikayi mun, ke kika cemun kar in damu, ke kika cemun ba zaki bari Aise ta kwace mun ba Mami, to me yasa yanzun zanyi abinda kuke keso?" Tasan Haris dama duka yaranta basu saba tauna magana kafin su fada mata ba, duk abinda suke so shi suke fada tunda tabarsu, ita ta basu fuska, amman ta saba sakasu itama suyi mata abinda take so, sau babu adadi, kuma haka ta shiryawa zuciyarta zai faru akan wannan auren ma, murkushe shi zatayi kafin yaje ko ina, dan ta rantse ta kara rantsewa ba zata zauna da jinin Sa'idu ba, bama zata bari ta rabar mata yaro ba, amman tana ganin wannan gardamar da taurin kan na Haris na haskawa cikin idanuwanshi "Ban fada masa ba, zan fara fada miki, na karbi auren nan Mami..." Yayi maganar wani abu na rabewa a cikin kirjinshi daya tabbata ba zuciyarshi bace ba, tunda ai ita ance dukanta tsokace, abinda ya rabe kuwa yaji kararshi, yaji kamar ya kira masa sunan Aise, juyawa yayi yanaji tana kiranshi bai juyo ba, ya koma bangaren Alhaji Mustafa, yana nan zaune inda ya barshi "Na karbi auren Baba..." Ya furta, yana ganin wani numfashi mai nauyi da Alhaji Mustafa ya sauke, daya juya har ya taka kafarshi daya waje ya kirashi "Haris..." Sai ya juya kanshi "Allaah Yayi maka albarka, Allaah Yasa auren nan yazo maka da alkhairai masu yawa" Ya kamata ko bai amsa addu'a ta biyu ba ya amsa ta farkon, yana bukatar albarkar nan ko ba'a fada masa ba, amman ya zaice amin Mala'iku su dauka yana nufin duka biyun ne? Shisa ya juya kawai ya fice Ba zai taba bari Aise ta subuce masa ba, kome zai faru, alkawari ne yayiwa kanshi, kamar yanda yayi alkawarin duk wani mai hannu a auren nan sai yayi dana sani Amman alkawurra nawa kaddara take karyawa? Akwai wani lilo mai circle lokacin suna yara, a hanyar Islamiyyarsu, duk zagaye uku kwandala lokacin, idan aka tashi haka zata kwasa da gudu ta bacewa sauran 'yan gidansu, lokacin da zasu cimmata har ta hau an zagaya da ita, akwai sanda Adda Zahra ta riketa kuwa, ta dauka zata kwada mata mari, sai tace mata "Karki kara gudu kije kiji ciwo, ki dinga jiranmu saimu tsayaki ki hau lilon" Watakila karancin shekaru ne ya hanata fahimtar muguntar da take kwance bayan murmushin Adda Zahran, dan a wannan ranar ne lilon ya fita daga ranta gabaki daya, ko wucewa sukayi ta ganshi sai taji kanta ya juya, dan Nairarta biyu ta Islamiyyar ta mika tunda ba sauri takeyi ba, sai dai tana hawa Adda Zahra ta karawa mai lilon Naira biyar, haka aka dinga wulwulawa da ita akai tun tana nishadi har taji jiri, ta fara ihu, lokacin da aka tsayar da lilon nan ko gani batayi, ta hada gumi da hawaye, ga kai da cikinta na juyawa kamar wadda zatayi amai, haka Khairi ta kamata suka nufi gida tana jerawa Addan Allaah Ya isa a cikin ranta. Irin wannan yanayin take ji yau kwana biyu, kamar an koma baya da ita an dorata akan lilon nan ne anata juyawa, ta kuma kasayin ko da ihu ne balle wani ya fuskanci halin da take ciki ya kawo mata dauki, tunda a washegari data tashi ta shirya, ta saka uniform sai kawai Hajja tace banda ita za'aje makaranta, sai ta koma kan gado ta kwanta batare da cire kayan makarantar ba, kuma wata murya a cikin kanta ta hana mata samun natsuwa a cikin shirun dakin ta hanyar maimaita mata "Ke matar aurece yanzun Maryam, ke matar Haris ce" Haka ta dinga juyi batare da tasan yanda lokaci yake tafiya ba, kuma anan Adda Zahra ta sameta, ta mika mata kofin shayi tana fadin "Tashi kisha Maryam" Ta amsa da "To" A yinin ranar, duk wani shige da fice da Yayyenta mata dama mazan sukeyi akan idonta ne, abinda duk akace tayi saita amsa da "To" Idan ma nasiha sukayi mata da hakan take amsa musu, tana jin Adda Maimunatu taja wani tsaki tana fadin "Allaah Ya kyauta, dan Allaah jiba yanda yarinyar nan tayi firgai-firgai a kwana daya kawai, ni na kasa daukar maganar ma gabaki daya, haka kawai nakejin inda wani ne can ba zai dameni kamar Haris din ba, ko ace shi din dan Umma Fadime ne, amman kinga wannan isashiyar matar hmmm" Adda Zahra ta kada kai itama "Ni kaina shine damuwata, dangin miji in ba tsananin dace kayi ba, basa ratsa matsalar da zasu dinga baka, balle kuma ace ita kanta uwar mijin ce baka dace da ita ba, Maryam tayi kankanta da ayi mata irin wannan, dama Asiya ya basu" Ita dai bata ko motsa daga kwanciyar da tayi ba, basu bar gidan ba sai dare, washegari kuma suka sake dawowa, sai dai Adda Zahra tasa suka shirya ita da Khairi da bataje makaranta ba itama, dan ance za'a kawo lefe wai, suma din da suka fita a motar Addan, kasuwa ta wuce dasu, haka ta dinga yawo dasu tsakanin shaguna da wani list a hannunta da take ta faman siyayyar kayan kitchen, da zasu koma a gidan gaba suka zauna daga ita har Khairi saboda an cika motar da kaya, ba iya booth ba har baya. Da yake lokacin da direban da Alhaji Jibril ya aiko ya kirawo Alhaji Mustafa sai ya fada masa inda zai tsaya ya jirashi, kai tsaye yayi masa jagora gidan kanwarshi Safina da take aure anan garin Kadunan, ya dinga mamakin irin kayan da aka aiko dasu, tun daga kan goro da biskit katan katan, harda lemuka da ruwan roba kamar za'a bude shago. Anan gidan direban yaci abinci, yace shi juyawa zaiyi, Alhaji Mustafa ya cikashi da abin arziki kuwa, da yake duk sunsan da zuwa neman auren da kuma yanda al'amari ya juye. Itace take tuna masa da batun lefe, yasan cewa Hajiya Rumana ba zata bashi hadin kai ba, yanda ta nuna tsanar auren karara. A matakin da yake bayason wani abinda zai zubar masa da kima a wajen ahalin Alhaji Sa'id gabaki daya, bayaso ko dana yini daya yayi dana sanin bama Haris auren Maryam. Shisa ya cire kudi masu nauyin gaske ya tura mata dan ayi siyayyar lefen dasu, kuma daya fadawa Alhaji Sa'id za'azo kawo lefe sai yace masa "Lefe kuma Mustafa? Wanne irin lefe?" Dariya yayi "Lefe dai da akeyi mana" Kuma sanin zai iya fara musu dashi yasa shi dorawa da "Ni dai ka fada ma Hajiya Asma'u, ranar litinin din nan zasu zo..." Kuma daya fada mata sai tace masa "Allaah Ya nuna mana lafiya" Lokacin ne kuma ta kira 'yan uwanta da suke nan ta fada musu, shima tayi masa magana ya fadawa nashi 'yan uwan. Batayi mamakin ganin yanda sukayo gangami kamar ance za'ayi yinin biki ba, saboda haka gidan cike yake da mutane ko ina ka wulga idanuwanka, sanda su Maryam suka dawo ma sai taji daman ta cewa Adda Zahra ta sauke su gidanta suyi zamansu acan. Haka suka shige dakinsu, nan ma da wasu 'yan uwansu a ciki, sun baje zaka rantse da Allaah a gidan suke rayuwa, suka saka Maryam a gaba da tsokana har wata tana "Kinga yanda kike ta kyalli, mu dai muna nan sai kin kira mana angon mun gaisa dashi" Batace musu komai ba, Khairi ce ta dan dinga biye musu duk da itama bata cikin walwala. Tun daga nan dakin kuma suna jiyo gudar da wata ta rangada tana fadin "Yarinya tayi goshi" Dan kuwa lefe ne aka kawo irin wanda in aka bada labarinshi wani ma zai kwashe da dariya yace anyi masa karya, akwatina ne saiti uku, kowanne shakare yake da kaya, ga kuma sauran tarkace kama daga lemuka da biscuit. Ita kanta Hajja saida lefen ya bata tsoro, zuciyarta ta dinga bugawa, musamman bayan sun tafi, an kwaso komai an kawo dakinta, su Adda Zahra nata dagawa, tunda take bata taba ganin lefe irin wannan ba, kuma ko ba'a fada ba daga gani kayane masu tsadar gaske. Yanda take jinjina lamarin haka Khairi da taga lefen ta samu Maryam da take rakube can karshen gado tana ce mata "Kinga lefen da suka kawo kuwa?" Ta kalleta kamar bata gane abinda take fada ba "Yanda kikasan za'a bude babban shago" Bata dai ce komai ba "Bari in zubo mana abinci, baki ci komai bafa tunda muka dawo" Cewar Khairi tana mikewa, tana shiga kitchen din kuma, Saifullahi na turo kofar baya "Yawwa, dan Allaah Khairi ki kawo mana abinci mana...ki hado da lemo" Ta amsa shi, batasan ko su nawa bane ba, sai kawai ta samu wata babbar kula da Hajja kan zuba musu abinci wani zubin sai akai musu bangarensu, duk wani abu da aka dafa ta hada musu a ciki, meatpie dinne ma ta samu wata leda ta zuba, ta kinkima, sai taci karo da Saifullahin da yayi niyyar dawowa ya dubata, ya karba, ita kuma ta sake komawa ta dibi lemukan taje ta mika musu, tana dawowa ne taji an kirata, ta juya, sai da zuciyarta ta buga ganin Ishaq a tsaye "Khairi" Ya sake kira "Yayaa" Ta furta da mamaki "Ki kiramun Maryam dan Allaah..." Ta numfasa yayi saurin katseta "Dan Allaah, dan Allaah ki kiramun ita" Ya karasa da wani yanayi da ta kasa musa masa, ko da ta koma dakinma saida ta fara daukar hijabin da tayi sallar Magriba dashi, sannan ta kama hannun Maryam din tana janyota, akayi sa'a bata musa ba ta bita, ta kofar kitchen din sukabi, ta bata hijabin tana ce mata "Yaya Ishaq ne" Tasan ya kamata ace taji hawaye sun cika mata idanuwa, amman bataji ko alamarsu ba, ko takalma babu a kafarta suka taka har inda Ishaq din yake tsaye jikin bango, fitilun da suka haske harabar gidan tar a kanshi, tunda tasan shi "Karki dade, kar wani ya ganku, zan jiraki a bakin kofa mu koma, dan Allaah karki dade" Kai ta iya daga mata, a hankali take takawa saboda yanda takejin wani iri, tana taka kananun tsakuwa, kamar yaji takun tafiyarta kuwa ya dago daga jinginar da yayi, ba zata tuna lokacin da ta ganshi babu tulun sumar nan ba, watakila kuma rashin sumar ne yasa ta ga ya rame a idanuwanta, kamar ma yayi duhu, wani abu da bata taba danganta shi dashi ba, tunda Ishaq farine har wani yellow yakeyi saboda haske, kamar yasan gashin nashi ne abinda ta fara lura dashi sai yasa hannu ya shafi kanshi, lectures ya fito yau karfe sha daya na safe, sai ya wuce da niyyar siyan lemo, shine yaci karo da AbdulKarim, daman satin can da yaje Kaduna yaji yana cewa zai shiga makarantar, da yake ya kammala Masters dinshi, project yakeyi, wai zaiga supervisor dinshi "Yau zaka juya ne?" Tunda AbdulKarim ya kasance mutanen da basa kaunar zaman makaranta in ba dole ba, tunda ko lokacin ma da yake karatu yana hanya ne kusan kullum "Kaman zan kwana, bana son komawa, gidan cike yake da mutane" Da mamaki Ishaq yace "Mutane kuma? Wani abu akeyi ne?" Cikin halin ko in kula, yana surbar lemonshi amsa "Kaman za'a kawo lefen Maryama naji Hajja tana fadi" Ishaq yaji kamar wata guguwa ta gifta tana neman dagashi sama ta tiqa da kasa "Lefe? Maryam?" Ya daga masa kai "Yep, an daura aurenta ran Asabar din nan, shine wai zasu kawo lefe, wani irin aure nema a hargitse" Tunda shi da Alhaji Sa'id ya fada musu abin mamaki ya bashi, har yanzun dinma mamaki abin yake bashi, shi kadai idan ya tuna wai Maryam ce aka daurawa aure sai yaji kamar zai kwashe da dariya. Ya dauka itace mace ta karshe da zatayi aure a gidan nasu, lokacin da ta kammala makarantarta, watakila ta rage rigima, ta danyi hankali, sai su hadu har sadaka su bayar Allaah Yasa mijin ya kasance mai tsananin hakuri karya dinga koro musu ita saboda rigima da taurin kanta. Shi ji yakeyi kamar ace ya hadata da wata na'ura ko na rana dayane a hasko masa diramar da yake hasashen zasu kwasa da wannan mijin. Ishaq bayajin yayiwa AbdulKarim sallama, dan iska yaji yana nema, jikinshi ya dauki dumi, daga wajen shagon aski ya nufa ya zauna yana ce masa ya aske masa kan, da ya tambayeshi kowanne iri zaiyi masa sai kawai yace "Ka rabani da sumar nan kawai...banajin iska ne, ka aske komai" Amman saiya kasa aske komai din, ya dai rage masa, yayi mai askin da ake kira da low-cut, amman kuma baiji ya samu iskar da yake nema ba, ya dai bashi kudin ya fice, tafiya yakeyi har saida kafafuwanshi sukayi masa alamar idan ya kara taku daya tabbas zasu kunyatashi tukunna ya tsaya, ya samu mai mashin ya hau zuwa tasha, ya kuma shiga motar Kaduna, shine fasinja na farko a cikin motar shisa ma ya dade a motar, da ya karasa Kaduna yana fatan ya samu labari akasin wanda yaji a bakin AbdulKarim sai suka tabbatar masa da gaske an daurawa Maryam aure, da gaske an gina katanga a tsakaninsu. Kwanciya kawai ya samu waje yayi yanajin zazzabi ya rufe shi. Ashe haka yake sonta da yawa bai sani ba? Yaso ya tashi ya juya inda ya fito ya kasa, aiko babu komai ya kamata yayi mata sallama, ya rasa wa zaisa ya kira masa itane sanda ya taso "Kanwata" Ya kira muryarshi na karyewa, saboda yau da take tsaye a gabanshi sai yake ganin wannan katangar da ta rabasu, bakinshi har daci yakeyi "Ina wuni" Ta tsinci kanta da furtawa, yaji murmushi mai sauti ya kwace masa "Wanne wunin? Wunin da nayi a hargitse? Nayi kwauron baki ko Maryam? Ban furta da wuri ba, ko dama can akwai shi? Nine ban sani ba" Ta rasa abinda zatace masa, tayi tsaye kanta a kasa, dan abubuwan da takeji basu da yawa, kanta yayi nauyi, duka jikinta yayi nauyi, kamar ruhinta ne a gajiye, saiya kwanta yana neman jan gangar jikinta su hadu su kwanta tare "Daman zan ganki ne, zanyi miki fatan alkhairi" Cikin karamar murya tace masa "Nagode..." Yaja wani numfashi da Maryam takejin ya samu waje ya zauna mata, haka kawai ta kasa kallonshi, duk da tanajin nashi idanuwanta a kanta "Maryamm..." Tsautsayi yasa ta daga kai, idanuwanta suka sauka cikin nashi, kuma tunda take jin labarai akan karaya, ta kuma ganta lokacin da Anas yayi hatsari ya karye a kafa, bata taba tunanin zata ganta a cikin idanuwan wani dan adam ba, tunda ai ko zuciyar da ake ikirarin tana karyewa kowa ya yarda bata da kashi, sai idanuwa? Murmushin da yayi mata ma a karye yake "Allaah Yasa ki samu ninkin abinda nake tunanin zaki samu a tare dani" Bai jira amsarta ba ya juya, sai Maryam take tunanin to ko dai idanuwanta ne sukeyi mata wasa? Tafiyarshi ma a karyen take ganinta, ko kuma kalmomi ne sukayi mata karanci shisa ta rasa guda daya da zata samu ta jinginata da abinda take gani a tare da Ishaq din? Ko kuma itace wani abu ya karye a tare da ita? Anan tsaye Khairi tazo ta sameta tana kama hannunta "Dan Allaah Adda kina ganin karaya a jikina?" Da mamaki Khairi ta kalleta "Karaya?" Maryam ta daga mata kai "Ko a idanuwa na, basu karye ba? Ko jikina?" Muryar Khairi na rawa tace "Dan Allaah ki bari Maryam, dan Allaah ki daina..." Ta karashe maganar idanuwanta cike da hawaye, yanda Maryam din ta koma kamar wata 'yar tsana sai yanda akayi da ita yana nukurkusar Khairin daman, ji takeyi kamar taje ta samu Alhaji Sa'id tace masa a warware auren da Maryam a mayar kanta, tunda ita babu wanda take so, batama tabayin wani saurayi ba, tana ganin abin ya taba Maryam ne saboda Ishaq, inda ba Ishaq zatayi mamaki ne an daura mata aure lokaci daya, da yanzun ma kila suna ta dariyar abin, ta ishi kowa da cewa anyi mata irin auren da, irin auren da tunda aka basu labarin shi saida ta shafe watanni tana damun Khairi da zancenshi, wata tambayar ma idan tayi mata sai dai ta girgiza kai tace "Kina da matsala" Ita kuma tayi dariya "Allaah abinne yake bani mamaki, ko su Abba ma irin auren da sukayi kenan oho" Nan nema tace "Allaah Yasa Hajja taji ki" Ta kama bakinta tana dariya. Ko ruwan sama bai taba firgita Maryam haka ba, bata taba ganinta a gigice irin na kwanakin nan ba. Haka tajata suka koma ciki, kuma daga ita har Maryam din abincin da basu ciba kenan a wannan daren. Haka suka kwanta kowa da abinda yake sakawa a zuciyarshi. * Daga Alhaji Sa'id har Hajjan hidima suke haikan, zaka rantse daga kan Maryam sun gama aure, tunda Alhaji Mustafa ya fada masa ranar da Haris zai dawo yake maganar kayan dakin Maryam, kar suje ayi maganar tarewarta, sai gashi a karo na farko Hajjan ta ajiye kawaici a gefe ana shiga kasuwa da ita, kowa ya kallesu a cikin yaran yasan shi yana bada kudine da fatan su wanke masa abinda yakejin yayiwa Maryam, ita kuma Hajjan tayi tsaye ne tana so ta dauki duk wata kala da tasan Maryam naso dama wani abu da zata tuna ta nuna sha'awarshi a daya daga cikin bukukuwan 'yan uwanta, ko babu soyayyar mijinta a ranta, to tanaso inta fito dakinta taci karo da wani abu da zai sanyaya mata zuciya, kafin fatansu da addu'arsu ta karbu. Kullum Khairi saita matse hawaye in taga sun shirya zasu tafi Islamiyya banda Maryam, ita ta gama jarabawarta ta aji shidda tana jiran result ne da kuma lokacin da zatayi jamb, saboda haka tana zuwa wata makarantar koyon computer anan kasan unguwarsu, babu nisa da kafa take zuwa, sai dai tunda akayi zancen auren nan bataje ba ko sau daya, Islamiyyar ma dan tasan Hajja ba zata barta ba shisa take shiryawa suna tafiya da Asiya, kwanakin ma zuwa suke suna wuce musu babu wani sabon abu a ciki. Sabon abin ya faru ne ranar da suka tsinkayi muryar Adda Zahra na fadin "Kano kuma? Kano za'a kaita? To wai akan me?" Khairi taji kamar wani abu ya rushe a cikin kirjinta, ai ko da ba'a kama sunan ita din ba tasan Maryam ce, Kano kuma? Akan me za'a dauke mata 'yar uwa a kaita har wata Kano? Shi Haris dinne ma yace Kano zai zauna kome? Yau dai taji wani abu da bataji ba tunda aka fada musu maganar auren nan, taji tana so tayi ido biyu da Haris din nan, ta kalle shi ta tambaye shi Dame yake takama? 14 Tun tasowarshi abu daya ya sani, yasha jin bashi da kowa banda Hajiya Rumana, ita dinma yasan saboda shi dolenta ne, son da takeyi masa ba zabi bane a wajenta tunda ita ta haifeshi, bashi da kowa da ya taba sonshi ko ya damu dashi haka kawai batare da wani dalili ba sai abokan da yake haduwa dasu a makaranta, a cikin abokan nan ma su Barde sune mutanen farko da yasan sun soshi haka kawai, yana son su Munira da Anisa, amman ba wata shakuwa bace a tsakaninshi dasu, ya taso yaga suna da juna ita da Anisa, kusan komai tare sukeyi kamar 'yan biyu, fadan da akeyi tsakanin sako da sako ma su suna jimawa bai gifta musu ba, tunda Anisan wata irin makauniyar kauna take yiwa Munira kamar bata da kowa sai ita, shisa take kaffa-kaffa da bacin ranta. Yaran Umma Fadime basa shigowa bangarensu, makaranta daya suke, amman ba tare ake kaisu ba, su yawanci ma Hajiya Rumana tafi kaisu da kanta, taje ta daukosu kuma. In dai yana cikin gidansu, zagaye yake da mutane, amman kullum cikin kadaici yake, shisa da Munira ta kirashi zatayi masa wasu maganganu yaja mata tsaki ya kashe wayarshi, ba zai tuna rana daya daya taba mata shisshigi a rayuwarta ba, to inama ta sakashi a ciki? Sai yanzun zatace masa "Haris kaine zaka biyewa Baba ku kashe mana Mami ko? Me yasa ba zaka saurareta ba?" Ta kyaleshi yaji da abinda yake damunshi, kowa ma ya kyaleshi, harda ita Mamin "Nifa tunda can bani da ra'ayin zama a Kaduna Mami, bamu taba maganar bane ba, a Kano zan zauna na riga na fadawa Baba, har an samu gidan da yayi mun kuma na biya kudin" Akwai kudadenshi da yake tarawa, na aikace-aikacen daya dingayi a Italy, bai taba kashe ko naira goma a ciki ba tunda masu bashi kudin kashewar suna da yawa, harma baisan abinda zaiyi dasu ba wani lokacin, daman niyyarshi in suka kai wani adadi ya fara gina kasuwancinshi dasu, kowanne yaro na gidan Alhaji Mustafa yana da gidan daya siya da sunan shi, wasu anan Kaduna, wasu a Abuja, kamar yanda kullum cikin ware wani kaso na dukiyarshi yake yana adanawa da sunayensu, shisa yaso Haris din yayi hakuri ya zauna anan Kaduna, amman yaki, da yake bayason matsa masa akan komai kuma tunda ya karbi auren nan saiya kyaleshi. Ta wata fuskar ma sai yake ganin kamar zaman Kanon sai yafi musu alkhairi akan Kaduna, saboda Hajiya Rumana, shirun da tayi yana da tabbacin bana alkhairi bane ba, kuma dan ta dinga wanke kafa tana musu zarya a gida ta matsawa 'yar mutane batare da izininshi ba, ba komai bane a wajenta. Ya dai yiwa Alhaji Sa'id maganar Kano zasu zauna da kuma lokacin da suka yanke zata tare din shi da Haris, haka yace "Allaah Ya kaimu lokacin Yasa alkhairinsu na tare da zaman Kanon" Yaji dadi, ko da Haris bai gani ba a yanzun, yana da yakinin wata rana saiya gode masa da zabin nan, ita kanta Hajiya Rumanan sai lokaci ya nuna mata cewar ba zata taba samu surukai nagartattu kamar Alhaji Sa'id da matarshi ba, saita rissina tayi dana sanin kiyayyar da take nunawa auren, tunda ba karamin tashin hankali tayi masa ba akan maganar zaman Haris a Kano, saboda kin gaskiya ma haka tace shine ya kitsawa Haris maganar "Ai wallahi baku isa ku rabani da dana ba, baku isa ba tunda babu wanda yayi mun dakon cikinshi" Saima ta bashi dariyar daya kasa boyewa saida ta fito, ta kuwa kara haukacewa tana wani irin kuka da bai taba ganin tayi ba a tsayin zamansu, amman ya gaji, yayi lallashin duniya taki, shisa ya fice ma yana barinta a dakin. Abinda yake kara yi mata zafi shine kaf 'yan uwanta babu wanda ya goya mata baya, tasan tunda Alhaji Jibril yaga farin auren ba zai taba bari wani yaga bakin shi ba, ga bakin cikin lefen da taji ance an kaiwa Maryam din, tunda danginshi dan neman fitina da suka dawo daga wajen kai lefen sai suka biya tanan gidan wai zasuyi mata Allaah Yasa alkhairi, ta kasa danne zuciyarta "Idan ma gulma ce ta kawoku dan kuyimun dariya sai dai ta kare a kanku wallahi, dane babu wanda ya isa ya rabani dashi, kuma wannan auren da yardar Allaah babu inda zaije" Da yake darajar Alhaji Mustafa kawai takeci a wajen kaf danginshi, dukansu haushinta sukeji na yanda bata kaunar ganin sun rabeshi suka kuwa biye mata, dakyar wata Gwaggonshi ta tsawatar musu, suka fice suka koma bangaren Umma Fadime. Tunda Hajiya Rumana take bata taba sanin cewa akwai wani abu da zai daga mata hankali fiye da lokacin da Alhaji Mustafa ya kara aure, kuma matar ta fara haifa masa yara kafin ita ba sai yanzun. Dan nata namiji tilo ne take kallo ana kokarin kwacewa, ita ko da Aise ce Haris ya aura ba zataso ace ya tafi Kano da ita ba, yayiwa idanuwanta nisa, balle kuma wata Maryama. Yanda taci burin bikin Haris, irin shagulgulan data dinga hangowa zatayi shikenan? Sunbi ruwa ake nufi fa, inda hawaye na karewa da tuni nata sun kare saboda yawan data zubar daga daura auren nan zuwa yanzun da take ganin da gaske babu yanda zatayi da Haris, da gaske yaki saurarenta, dan kar yaga fushin da tayi ma saiya dauke kafarshi daga shigowa sashin nata gabaki daya. Batasan yana can yana fama da zuciyarshi da kuma Aise ba, tunda ya siyi sabon layi, ya saka kudi a ciki sosai ya kirata, tanajin shine kuma ta fara dariya tana fadin "Kiranka nake ta jira..." Tana cigaba da dariya, wai Binta ta zuga Alhaji Modu, tun jiya daya dawo ya fada mata wata magana da ta kasa daina dariya "Basu san da gaske babu wani abu da zasuyi da zai rabamu ba ko?" Ya numfasa, kai tsaye yace mata "Ba karya bane Aise, Baba yaje Maiduguri nema mun aurenki Uncle Modu ya hanashi, shine ya dauramun aure da 'yar abokinshi...amman da gaske ne, babu wani abu da zasuyi da zai rabamu, ni dake mun san hakan" Sai ta sake kwashewa da dariya "Saboda na gaya maka inka auri wata bayan ni zan iya mutuwa shine kaima abin ya zame maka wanda zakayi amfani dashi ka tsokane ni ko? Zaka dawo...zaka san ka fadamun maganar nan Allaah" Cikin wata sabuwar damuwar yace "Ba wasa nakeyi ba, ba wasa nakeyi miki ba, an daura aurena" Kawai saita kashe masa waya, ya sake kira wajen sau biyar tana kashewa, saiya kyaleta, da kanta ta kirashi da daddare ya sake tabbatar mata da ba wasa yakeyi ba, an daura masa aure "Ka sake ta" Ta fadi cikin wata irin murya data sa kirjinshi bugawa "Ba zan iya ba" Ya furta kai tsaye "Me yasa?" Itama ta tambayeshi "Saboda Baba...ba zan iya ba saboda shi Aise, dan Allaah ki fahimce ni" Cikin ihu tace masa "Taya zan fahimceka? Baban ne zai zauna da ita ko kai?" Shima da hargowar ya amsa "Karki fara, Babana nace, karki fara Aise" Yanda take sauke numfashi yasan kuka takeyi "Ka zaba, ni ko ita, wallahi sai dai ka zabi daya a yau din nan" Duk wasu kalmomi da ya furta abu daya Aise ta dinga maimaitawa "Ni ko ita?" Daya kashe wayar ganin ba zata saurare shi ba saita dinga jera masa sako iri daya, tambaya daya amman ta tura masa ita tafi sau hamsin, har email dinshi tabi. Kuma tun ranar in ya kirata tana dagawa abinda zata furta kenan, ba zata taba bari suyi wata magana ba, kirjinshi yayi masa nauyin da baisan ya zaiyi dashi ba, ko baccin kirki baya samu, a wannan lokacin ba zaice ga adadin wiwin daya bankadawa cikinshi ba, abinda yake fitar dashi daga gidan kenan a wannan lokacin, saboda bayajin ma fita sam, duk yanayin da yake ciki ba zai taba yarda yasha wani abu a cikin gida ba. Wai kuma a wannan yanayin ne Alhaji Mustafa ya kalle shi yace masa "Sa'idu yayi mun magana kan karatun Maryam, kasan aji shida ta shiga, shekarar nan ne ya kamata ta zana WAEC dinta..." Shikuwa ina zai sani, yarinyar da baima san ya take ba, ta ina zai san wani matakin karatunta, to wai akan me ma su duka suke tunanin abinda suke so zaiyi bayan shi suna neman yi masa katanga da abinda yake so? "Kaga da anan ne saita cigaba da zuwa makarantarta, amman tunda Kano zaku zauna sai dai ka nema mata wata makarantar acan" Ya amsa da "To Baba" Kuma shima Alhaji Sa'id din, Hajja ce tayi masa maganar bayan ya gaya mata suyi kokarin kammala duk wata siyayya da zasuyi, Kano za'a kai Maryam "Kayi musu maganar karatunta, dan Allaah karya zamana karatunta ya tsaya, tunda kaga auren nata yazo daban dana 'yan uwanta" Yanata juya abin a ranshi daman, sai suka samu natsuwa su duka da Alhaji Mustafa yace "Haba wannan ai ba abin damuwa bane ba, In Shaa Allaah zata cigaba da karatunta, abinda shima Haris din yace mun yanaso ya dora Masters dinshi" Yanda dai Hajjan taso su Zahra suyi fatan alkhairi, amman kowa saiya nuna mata hankalinshi ya tashi da maganar kai Maryam Kano, saida tayi musu jan ido tukunna sukayi shiru, kuma yanda akaje akayi jere aka dawo anata koda gidan su bata gani ba ko a fuskokinsu, ta kara dagewa, ta kara rage bacci tana ta kaiwa Allaah kukanta, bata san me yaran suke jiwa 'yar uwarsu tsoro ba, amman tana addu'a koma menene ya juye ta zame mata alkhairi, ita nata hankalin bai tashi ba saida aka shirya Maryaman cikin wani laffaya da Zahra ce ta siye shi da kudinta, ita tayi tsaye har kunshi saida akayiwa Maryam, kuma tun kwanaki uku data mayar da hankali akanta, kallo daya zakayi mata kaga ta fito a amaryarta. "Allaah Yasa kije gidanki cikin aminci Maryama, Allaah Yasa auren nan ya zame miki alkhairi kinji ko? Allaah Yayi miki albarka..." Ta karashe tana jin muryarta na karyewa, da aka daga Maryam din tsaye, saita karbe hannunta taje ta fada jikin Hajjan "Dan Allaah Hajja...dan Allaah" Take furtawa cikin wata karamar murya da kuka ya zuke, kukan da ta kasa ne a cikin kwanakin ya taso mata gabaki daya, tsoro da firgici na lullubeta, da gaske dai auren akayi mata, da gaske rabata za'ayi da gidansu akaita ta zauna da mutumin da bata taba gani ba, har garin Kano da tunda take a rayuwarta sau biyu suka taba zuwa, kuma da yake tana da kulafacin gida, hutun data taba cewa zata raka Khairi gidansu, kwananta daya ta makale aka juya Kaduna da ita. Gata yau zata bar gidan gabaki daya "Ki tashi Maryama, ki tashi ku tafi" Sai ta kara rike Hajjan gam, dole ta mike da ita, ta kuma riketa har dakin Alhaji Sa'id da yake tsaye ya rasa inda zaisa kanshi, wani irin rashin natsuwa ne yake ta ratsa shi, a kasa Maryam din ta durkushe, har gwiwoyinta na taba kafarshi "Abbaa..." Ta kira cikin karyayyar murya, tunda can shi mutum ne mai matukar rauni akan lamarin yaranshi, bashi da wasu kalmomi da zaice "Allaah Yayi miki albarka Mairamata, Allaah Ya kula dake da al'amuranki, Nagode. Ki daina kukan nan, ga Yayyenki can a waje sunce sune zasu wakilceni yau, sune zasu rakamun ke har cikin gidanki..." Ta daga masa kai, watakila akwai wani abu a tare da kalamanshi shisa wannan karin batayi wani gardama ba da taji an kamata ta mike, nan Hajja ta tsaya bangaren Alhaji Sa'id, sai ajiyar zuciya takeyi kuwa, idanuwanta na mata yaji, ta cikin mayafin da aka ja mata ya rufe mata fuska take hangensu, da yake ba mai kauri bane, wani abu ya daki zuciyarta, duka mazan gidansu ne. Ahmad, Khalifa, AbdulKarim, Yazid, Sagir, Adnan, sai kuma Saifullah. Fararen shaddojine a jikinsu, kowa yasha babbar riga da hula, kukan da takeyi bai hanata jin yanda kamshin mabanbanta turarukansu ya cika wajen ba, sai taji an saketa, Ahmad ya karaso ya kama hannunta yana janta a hankali, duk mutanen da sukazo ana tsaye ana kallonsu. Babu irin surutun da ba'ayi ba lokacin da Alhaji Sa'id yace, iya yaran nashi ne maza da mata zasu raka Maryam dakinta, duk wanda yake son zuwa yaga gida yabi masu kai jere, kuma suma ba zasu kwana ba, ya toshe kunnuwanshi, yaran ne sukayi masa wannan rokon da kansu, duk da yace motocin da suke gidan sun isa, sai da aka aiko da motocin da duk wanda ya gani ya shaida sana'ar Alhaji Mustafa, shima mota daya ce ta 'yan uwanshi da zasu dauki amarya, suma gefe suka koma ganin Yayyenta maza tsaye bakin motar da suka ajiye, dan direban ma da ya kawo motar AbdulKarim ne ya karbi mukullinta yace masa yaje abinshi basa bukatar wani direba. Su suka saka Maryam a mota suka zaunar da ita, Ahmad da kanshi ya koma yanda ya kama hannunta ya ratsa cikin mutane yaje gefen Adda Maimunatu ya kamo hannun Khairi da fuskarta harta kumbure saboda kukan da tasha, ya jata ya sakata a motar da Maryam take zaune, ya mayar da murfin ya rufe, shi kuma ya zagaya ya shiga gaban ya zauna dan shine zai tukasu, shi da Khalifa da tun kafin ma a hau titi ya juya ya cewa su Khairi "Muna shiga daji zansa Ahmad ya tsayar da motar nan inci ubanku idan kuka cikamun kunne da wannan koke-koken kamar wanda akayiwa mutuwa, musamman ke Khairi tun safe naji ana fama dake...Zahra tace mun ko abinci bakici ba duk yau, to idan auren ne a ranki in muka dawo sai in yiwa Abba magana kema ayi miki yanda aka yiwa Maryam din" Sanin halinshi yasa su hadiye kukan nasu babu shiri "Karbi nan" Ya cewa Khairi yana mika mata wata leda da tajita da sanyi "Kema ki bude wannan uban lullubin ki shaki iska, ku kuma cinye komai ku mikomun ledar..." Saida Khairi ta bude taga yoghurt ne masu sanyi roba biyu, sai tsire da gurasa, gefe Zahra ta jashi tace masa yasan yanda zaiyi yasa daga Khairin har Maryam din su sa wani abu a cikinsu dan basu ci komai ba. "Ya banji kun bude bane? Ahmad ko zaka samu waje ka dan tsaya in koma baya?" Da sauri Maryam tace masa "Ci zamuyi Yayaa" Yafi kowa wasa da dariya a gidan, shine zaka samu yasa hannu a cikin kwanon abincinsu yana ci tare, kuma shine irin Yayyen nan da kowa yake tunkara da maganar a bashi kudi, ko a siya masa wani abu, amman kuma sunfi tsoronshi akan kowa, saboda a karkashin wannan wasa da dariyar, Khalifa na da zafi idan sukayi masa kuskure, sannan ba kamar sauran da zasuyi hargagi da zagi ba, ko su kai duka inka kauce ko ka ruga shikenan, Khalifa zai rikeka, zai saka bulala ya zane maka jikinka, inya fita saiya dawo maka da wani abu daka tambaye shi, kuma baka isa kace zakayi masa fushi saboda ya dakeka ba, saiya kara maka, yasa ka zauna a wajen ka gama kuka kuyi labari. Ita Maryam dinma ta manta rabon da taci abinci irin wannan, batama san tana jin yunwa ba saida tsire da gurasar suka fara sauka a cikinta, sai gashi jikinta har rawa yakeyi, ta kuma shanye tata yoghurt din tas, tukunna ta karbi tissue din daya basu ta goge hannunta, data gyara zamanta ta jingina jikinta da motar sosai ta rufe idanuwanta, tsakanin sanyin AC din, kamshin turaren daya cika motar mai kwantar da hankali, da kuma karatun Qur'ani cikin muryar Qaari Abdullahi Abba Zaria, sai koshin da tayi ya tattaro mata gajiya da rashin wadataccen baccin da bata samu ba na tsayin kwanaki. Zuciyarta ta nemi salama da kanta ta hanyar barin bacci ya dauketa... 15 Har yanzun Haris bashi da wasu abokai sama da 2Pac, Barde da kuma Lalaye, sauran kawai a hadune ayi sharholiya a wuce wajen. Barde a halin yanzun yana kasar Ingila, 2Pac kuma yana India, a cikinsu Lalaye ne da mahaifinshi ya fitar dashi kasar waje sai yaki karatun gabaki daya, haka ya tattaro ya dawo, da yake dan kasuwa ne babba, saima ya tattara Lalayen ya mayar dashi Kano, ya hadashi da kula da wani babban shagonshi a kasuwar singa, inda suke bada sarin kayan masarufi, ya hadashi da wasu amintattun yaranshi. Ga mamakin kowa sai kasuwancin ya karbi Lalaye, yanda akayi tunanin zai kadar da katafaren shagon yayi shaye-shayen shi da bin mata, sai ya basu mamaki, wani abu daya sanyaya ran mahaifinshi yasa yace ya mallaka masa shagon, shima ya tsaya da kafafuwanshi. Sai dai babu abinda Lalaye ya fasa, tunda gida gareshi a cikin garin Kanon inda yake cin karenshi babu babbaka, kuma shine mutum na farko da Haris ya fadawa an daura masa aure, ya kuwa sheke da dariya yana fadin "Wasa kake amman ko?" Da yake waya sukeyi sai shima Haris din yayi gajeriyar dariya "In ban manta ba na baka wata kusan takwas Lalaye, ni kuma wanne tsautsayi ne zai sani wasa da kai in jawa kaina raini" Ashar din da Lalayen ya maka masa sai da yasa shi yin dariya mai sauti "Da gaske an daura aurena yau kwana goma, ina tunanin kaman a Kano zamu zauna ma, ban dai gama yanke hukunci ba" Gabaki daya lamarin ne yake ta bawa Lalaye dariya "Ashe Ganja zaka rigamu shiga daga ciki...nan fa da wata tara sai dai muji eya ne" Haris yaja tsaki, baisan ya Maryam take ba, amman haka kawai tunanin ma hada shimfida da ita sai yaji yasa kanshi ya hautsina "Kana da matsala..." Ya iya fadi kawai, kuma lokacin daya tabbatar da Kanon zai zauna, aka gama komai aka tsayar da ranar da za'a kai Maryam, Lalayen ya kira "Dole fa a fitar dakai kunya" Cewar Lalaye, Haris baija zancen ba, ya dai hada abinda yake tunanin zai bukata tun sauran kwana biyu yayi tafiyarshi garin Kanon, kuma daya isa gidan, maigadin da aka samar musu nata jera masa barka da zuwa har saida yaji babu dadi saboda babban mutum ne, amman kamar zai durkusa masa, tunda ya fito daga motar ya karasa matattakalar da zata hadashi da falon wani kamshi mai sanyin gaske ya daki hancinshi, Maminshi na son turaren wuta, har saida yayi zaton babu wanda yake amfani dashi kamar ita, dan ya taba jin Anisa nace mata "Mami inda zamuje asibiti ace huhunmu ya samu matsala wallahi ba zan musa ba, na tabbatar hayakin turaren wutarki ne da muke shaka tun muna jarirai" Shi dai yana son irin kamshin turarukan, shisa ya fada mata ake saka masa har a daki, wannan din yayi masa dadi, wani irin kamshine da zakaji kanaso ka samawa kanka hutu a cikinshi, daya bude gidan kuma sai yaji ashe baiji komai ba, saida ya sauke numfashi. Abinda Haris baisani ba, shine wannan aikin Adda Zahra ne, ko kudi ta baka sai kaji suna kamshin turarukanta, 'yan gidansu na yawan yi mata mitar duk garin Kano, saita tsallaka har Bauchi ta siyi turarukan wuta, sai dai tayi dariya abinta "Nifa turare indai ba Meens incense ba akai kasuwa (08036387204)" Tunda itama kawarta da suke makaranta lokacin itace 'yar Bauchi, ita ta bata shi a gudummuwar biki, sai gashi ta zama babbar customer, suma suna mata mitar, duk zuwan da zasuyi gidan sai sun roqeta ta dibar musu, ko suce in za'a kawo mata suna so a hado dasu. Shisa ta siyawa Maryam itama, kuma kafin subar gidan bayan sunyi jere saida ta saka a kusurwoyin kowanne daki na gidan, harda bayi a kasko-kasko, sannan suka rufe gidan, har window duk suka datse dan so takeyi ya kama ko ina, yanda in anzo kawota kafin ma su maimaita kowa zaisan ya shigo gidan amarya. Jeren da akayiwa falon ba mai hayaniya bane ba, komai ya dace da mazaunin da aka ajiye shi, daya daga cikin bedrooms din ya bude, da yake 3 bedroom flat ne, ya ajiye jakarshi, sai yaji kamar bai kamata ya kwana a gidan ba, ya dauki abinda zai bukata a wata karamar jakar, ya fice yana mayar da kofar ya rufe. Hotel ya samu ya biya kwana uku, saboda Aise ne ya kasa kashe wayarshi a kwanakin biyun, yanda Hajiya Rumana take jera masa kira kan kira saida ya daga wayar dan dole "Ni zan dinga kira kana kin dagawa Haris? Ashe akwai ranar da zaka zabi wata mace akan uwarka" Ya dafe goshinshi "Nifa babu macen dana zaba akanki Mami, kece kika kasa fahimtata" Saita kara tunzura kuwa "Taya zan fahimceka bayan ka biyewa ubanka zaku kasheni da raina...auren da nake hango rabashi kafin yayi nisa ashe kai zaka kwaremun baya" Cikin gajiya da maganar raba wannan auren da takeyi masa ita da Aise yace "Nifa ba zan rabu da ita ba, bansan sau nawa zan fada muku ba, ba zan rabu da ita ba" Ta kuwa kwaso salati muryarta na rawa, yasan kuka zata saka masa "Ko dai asirin da ake yawan magana akai bana yarda dashi ne tsautsayi ya fado kaina yau? Ko sun shanyemun kai Haris" Dariyar takaici ta nemi kwace masa "Kaina na ciwo Mami, dan Allaah ki huta, nima kibarni in huta akan maganar auren nan, an riga an daura, kema da bake aka kakabawa auren ba kinajin kin kasa samun abinda kike so, nikuma fa? Dan Allaah kibarni akan maganar nan..." Ya karasa a gajiye, kafin kuma tace wani abu ya kashe wayar gabaki daya, daman da safiyar sukayi tashin hankali da Aise "Sonta kakeyi?" Ta tambaya, gabaki daya ya gaji, ya gaji da komai "Ko kalarta ban sani ba Aise, sau nawa zan maimaita miki?" Taja numfashi "To akan me ba zaka saketa ba, karka kace mun saboda Baba" Ya kuwa fada din yana dorawa da "A cikin taro Uncle Modu ya kunyata mun Babana, ya hanani aurenki, so kike nima in bashi kunya, ni da yakejin ya isa yayi iko dani? Saboda ke?" Cikin wani irin kuka da yakejin sautinshi har kasan zuciyarshi tace "Ban isa ba ko? Ni ban isa ka rabu da ita saboda ni ba" A gajiye yace "Baki isa ba, ke baki isa in watsawa Babana kasa a ido saboda ke ba, na gaya miki bana sonta, banma san ya take ba, dame kike so inji? Rashinki da tunanin ranar da zan sameki? Idan kika sake cemun in zaba ko ke ko ita zan baki mamaki wallahi" Itama cikin hargowar tace "Ka zaba, wallahi sai dai ka zaba, koni ko ita, ba zan cigaba da sonka kana rayuwa da wata a matsayin matarka ba, ba zan aureka a mace ta biyu ba, ba zan iya ba" Ya numfasa, yaji kamar iskar tayi masa kadan, wani abu ya qulle a cikin kirjinshi yana kare matse masa iskar da yake shaka "Ke zaki kashe wayar koni? Bansan ya zan miki sallama ba" Baisan dakikun daya dauka yanajin sautin kukanta ba, kafin ta iya cewa "Me kake nufi?" Wani abu na ratsa gabobin jikinshi yace "Na zabeta..." Sai ta kashe wayar, tana hadawa da wani haske da yakeji kuwa, duhu ya maye masa gurbinshi. Haka ya wuni banda hayaki babu abinda yake shiga cikinshi. Shisa duk abinda Lalaye yace masa sai yace "Duk yanda kaga ya kamata" Haka ya samu wasu abokanshi daya hadu dasu anan Kano din, da yake kuma kudi ba matsala bane, sai dai Lalaye yaja shi sukaje wani shago, a cewarshi ango babu manyan kaya ai bai amsa sunanshi ango ba, wasu tsadaddun shaddoji ne suka siya harda huluna da takalma, ya dinga kallon kayan, shi tunda yake tsakaninshi da manyan kaya sai sallah in zasuje idi, suna dawowa inya cire aka wanko sai yazo daukar wasu kayan yake ganinsu, sababbin kayan da yake dasu manya da bai taba sakawa ba kuwa kilan in suna da expiring date daya dauko zasuyi gari ne a hannunshi saboda ajiya. Yaji dariya na neman kamashi da yake tunanin zai saka babbar riga. Washegari kuwa da yake yana tunanin zuwan nasu, kuma Alhaji Mustafa ya bashi lambar wani Ahmad yace Yayan Maryam dinne, zai kirashi. Yana ganin kiranshi yace masa sun kusan karasawa suka shirya shi dasu Lalaye cikin manyan kayansu, sai baza kamshi sukeyi, inka kallesu zakayi tunanin sunfi shekarunsu, kwarjinin nan na farar shadda da manyan kaya da suke suturta halayya sunyi musu wannan adalcin. Shi kanshi sai yakejin shi daban, ko dan da gaske daban din yakeji ne oho, kamar wanda yake yawo a cikin mafarki, saida Lalaye yasa sukayi tsaye-tsaye, yanata mamakin kayayyakin da aketa lodawa a bayan motocinsu, tun daga kan lemuka harda abinci "Me za'ayi da duk wannan abincin Lalaye?" Ya kalle shi kaman baiga dalilin da zaisa yayi masa tambayar nan ba "Na tarbar baki mana, ko haka za'a jewa mutane sun taho tun daga Kaduna, kaifa Ganja baka da kai wani lokaci, shisa Barde yace in tsaya inga komai ya tafi dai-dai karka ja mana abin kunya" Haris yayi shiru, yanajin su sunata masa tsiya kala-kala da Lalaye ya kira ya fada musu, shi 2Pac ma haka yace daya sani da wuri, daya zo, amman zasu ware lokaci dan dole ne suyi qara'i, shagalin da ba'ayi musu bane zasu zo su huce takaici. Lokacin da suka isa kuwa saida Haris yayi mamakin ganin zaratan mazan da suke tsaitsaye a jikin motoci sunata hirarrakinsu, haka suka karasa aka dinga gaisawa kamar ansan juna, tunda matan sun shiga ciki da Maryam tun isarsu, da suka fada musu akwai abinci, sai daya a cikinsu yayi waya aka fito aka dauka, kuma Lalaye ne yace su fita su suci nasu abincin a waje. Sai dai wanda suka kai da yawa, da AbdulKarim ya fadawa Zahra saiya hana tace su shiga falon suci anan, a gyara mata komai tunda juyawa zasuyi a ranar ba zasu kwana ba, haka akayi harsu Haris din, shi dai su Lalaye da wasu a cikin Yayyen Maryam din nata tsokanarshi da cewar karya ji kunya ya saki jiki ya kwashi abinci, amman sai yake yake yi musu, Maltina kawai yasha, AbdulKarim ne yace "Nifa na kasa natsuwa da yanda kaqi cin abincin nan, duk wani warning da nake shirin doka maka kan Kanwata ai sai kasa jikina yayi sanyi..." Yayi dan murmushi kawai, amman duk da haka, yaji su, yaji duk wasu maganganu da suke fada masa a wasa da dariya, zai iya cewa gargadinsu ko karamin yaro ne shi yaji shi, dauka ce dai wani abu na daban, kuma tare suka fita suka tsaya a harabar gidan ana dan taba hira. Su Zahra kuma suka gyara komai, ta kirasu tace a kwashe sauran abincin a bayar dashi tunda ko sun barshi nan tasan lalacewa zaiyi, su Haris din baci zasuyi ba, su juyawa zasuyi kar dare yayi musu a hanya, sallar la'asar kawai suka tsaya sukayi. Tashin hankalin yana cikin dakin da suka ajiye Maryam, ita kanta sama-sama take jinta, da yake baccin da tasha a mota data tashi sai taji nauyin da kanta yayi ya rage. Komai ya washe mata, shisa kuka tayi ba dan kadan ba, wani irin kuka da saida su Adda Maimunatu suka tayata lokacin da suka iso, aka riketa akace tayi addu'a, sannan ta shiga gidan da kafar dama bayan tayi sallama, nan bakin kofa ta durkusa tanajin kamar kirjinta zai rabe biyu, zuciyarta sai bugawa takeyi "Kirjina Adda, ciwo, komai ciwo yakeyi..." Suka kamata suna shiga daki da ita, akan gadon ta kwanta ta dunkule jikinta tana sakin wani kuka da yake fitowa tun daga zuciyarta, da akace ta hada kayanta da take so a tafi dasu jiya, sai Khairi ce tayi mata, ita dai sanda ta mike kananun abubuwa ta dauka, harda brush dinta, suka dinga mata dariya "Me zakiyi da tsohon Brush ke da kike da sababbi" Inji Asiya, Adda Maimuna ta shigar mata "Ku ina ruwanku? Brush dinku ne? Dauki kayanki Maryam ki rabu dasu kinji" Daman batayi niyyar musu magana ba, ta fito da turarukan nan da take ta boyo, wanda Ishaq ya bata, ta hada hardasu tanajin zuciyarta kamar an dora mata dutse. Ko yanzun dinma tunanin wannan turarukan takeyi, tunanin shikenan, rayuwarta ta tsaya anan, ita da Ishaq har sun kare tun kafin ma su faru? Tunanin me yasa duk a gidansu sai ita kaddara zata zaba haka? Yanzun da suka kawota gidan nan suna nufin tafiya zasuyi su barta a cikinshi? Babu wanda ya bata hakuri, batasan waye ya dagota ya cire mata laffayar jikinta ba saboda kukan da takeyi, haka batasan waya riketa a jikinshi cikinsu ba tayi kukanta har saida taji ya isheta, da kanta ta mike tana tambayar bayi cikin disashiyar murya. Data shiga tayi nufin wanke fuskarta ne kawai, amman sai taji jikinta nayi mata kaikayi kamar tayi kwanaki batayi wanka ba, sai gata tana cire kayanta, akwai komai daga kan soso zuwa sabulu harda shower gel a cikin bayin an jera a mazauninsu, da a hayyacinta take watakila da tsarin bandakin yayi mata kyau, ita mai son abubuwa masu kyau. Da ta fara wankan kuma sai taji kamar akwai abinda take so ta wanke, kamar tana so ta wanke wani kaso na rayuwarta, bata dai san wanne ba, kafin auren ko auren, ko kuma yanzun, ta dai wanke wani kaso yabi ruwan nan ya shiga rariya. Ko zafin da jikinta yakeyi bataji ma, saida aka kwankwasa kofar bayin tukunna ta hakura, ta dauraye jikinta, ta mayar da kayanta, sai tayi alwala. Batason musu ne, shisa ta dan tsakuri abincin da aka shigo musu dashi, da yake haduwa sukayi a waje daya sukaci tare, kuma batayi musu ba da suka zaro mata wata doguwar rigar atamfa suka bata ta saka, tayi sallah, Adda Zahra ta kara gyara mata fuskarta, harda wani jambaki aka shafa mata, jambakin da batasan ina ya goge ba, ko a jikin Khairi ne da ta kankame lokacin da sukeyi mata sallama, duk wata nasiha da hudubar Addan ma bata wani fahimta ba, babu abinda takeji sai tafiyar da zasuyi su barta. Tun suna tayata alhini ita da Khairi akan irin kukan da sukeyi, har saida Adda Zahra ta watsa musu zagi, baisa sun daina ba, balle ma su saki juna "Wallahi zan kira Khalifa yazo yaci ubanku tunda bata mana lokaci zakuyi..." Ita Maryam dince ta fara janye jikinta daga na Khairi, bata daina kukan da takeyi ba, Asiya da take ta sauke ajiyar zuciya ta ja hannun Khairi suka fice, aka bar Maryam da Adda Zahra, ta kamata ta mayar da ita kan gadon ta zaunar da ita "Ki kwantar da hankalinki dan Allaah, kinji duk abinda na fada miki ai ko?" Ta daga mata kai kawai badan ta tuna me tace ba "Wayar da na gaya miki tana nan cikin jakarki, zan dinga kiranki muna magana" Ta sake daga kai tana kai hannu tana share hawayen da sukaqi tsaya mata, tana kallon Adda Zahra ta fice daga dakin taja kofar ta rufe, karar na dirarwa Maryam har cikin ruhi, kamar an rufe da wani bangare na rayuwarta haka takeji, sai ta koma kan gadon ta kwanta kawai, tana jin tashin motocinsu, kuka takeyi har sautinta ya dishe, akan idonta dakin yayi duhu, ta kuma jiyo kiran sallar Magriba, shine ma ya tasheta, ta wanke fuskarta, ta dauro alwala, inda tayi la'asar, dardumar dama hijabin suna nan, dankwalin da aka kinkima matane ta kwance ta jefar anan kasa, tai sallar, tayi kwanciyarta a wajen har aka kira isha'i tayi, ta mayar da Shafi'i da Wutr da ya zame mata jiki saboda tunda suka taso suka ga Hajja nayi, itama duk ta saka musu sha'awar hakan. Ta ga gaske ya gauraye dakin, a hankali kuma kunnuwanta suke jiyo mata karar generator kadan-kadan, ta sauke ajiyar zuciya, kishin ruwa ma takeji, dole ta mike badan tana so ba, fuskarta tayi fayau, hawaye ya wanke mata komai, tama manta babu ko hijabi a jikinta, data bude kofar dakin saita leka kanta kamar mai tsoron wani abu, zuciyarta sai bugawa takeyi, to idan ta ganshi fa? Suka hadu? Ya zatayi? Tasan dole zata ganshi, amman kuma tanajin kamar bata shirya ba, kamar ba yanzun take so su hadu ba, saita yanke shawarar dubawa zatayi ta dauko abubuwan bukata, ruwan ma da yawa saita koma dakin nan ta rufe da mukulli yanda zatayi kwanaki bata fito ba. Amman dole saita dudduba tunda inma akwai ruwan batasan ina yake ba, taje tsakiyar falon kenan taji motsi, a tsorace ta daga kanta, ta kuwa saka idanuwanta cikin na Haris, da yake su Lalaye suka hana ya bisu, a cewarsu zasu raka su Adda Zahra har wajen gari, ya zauna da amarya, wasu ledoji ne suka bashi, daya karba haka yaje ya samu fridge din kwance da aka ajiye a kitchen ya bude ya saka su a ciki, daya fita sallar isha'i ya dawone yaga babu wuta yasa aka kunna generator, so yakeyi ya kwanta, kanshi yayi wani irin nauyi, harma ya kwantan yaji cikinshi na neman agaji, yasan zai iyayin aman da zai bashi wahala in ya kara bankar hayaqi baici komai ba. Shayi yaso ya samu, amman baisan ta ina zai fara ba, tunda baiga lipton ba balle kettle din da zai dora ruwan zafin, sai kawai ya dauki lemo da wani cake, anan kitchen din ya tsaya ya ci badon sunyi masa dadi ba, ya dauko ruwa ya fito kenan ya ganta, ko yace kanta, kitson da yake kanta, kananun kitsonta shiya fara gani, sannan ta dago kai, idanuwanta tar akanshi cikin hasken dakin, abu na farko daya fara gani shine sirantarta, rashin kibarta, amman yaga fuskar nan tata a cikin ta 'yan uwanta dazun, ko yace wasu abubuwa na fuskar a tare da kowannensu, kafin ma ya gama kare mata kallo ta kwashe da wata irin dariya. Farin kwaine a falon, kuma a yanayin hasken zaka san ba guda daya bane, kwayayena dan ko allura ka yadda zaka dauki kayanka, sai taga Haris yafi duka 'yan uwanshi data gani baki, yamafi ita Hajiya Rumanan baki, ita da tafi su Anisa kenan, kawai irin kukan da ta gamayi dazun ne yake dawo mata, tana jin wai daman akan wannan danduqununun ne ta zauna take ta asarar hawayenta? Ai da ta sani da ta sauya akalar kukanta, tayi kukan yanda ta tabbata an gama kashe mata rayuwa tunda aka hadata dashi, ta jingine komai a gefe, idan akwai abinda Haris bayaso shine yaga ana dariyar da baisan dalilinta ba, balle kuma dariyar da aka kalleshi aka tuntsire da ita "Lafiya?" Ya tsinci kanshi da tambaya, kuma data samu ta tsagaita, yayi magana ta sake kallonshi sai kawai ta kara kwashewa da dariya, bakar tshirt ce a jikinshi da wani bakin wando da ya dan wuce gwiwarshi kadan, saboda tsabar karfin hali a tunanin Maryam kenan "Maimakon kasa kayan da zaka dan haska, kai Subhanallahi..." Ta fada batare data shirya ba, ya kankance mata idanuwanshi cikin rashin fahimta, ta numfasa, ita ta manta rabon da tayi dariya irin wannan "Yi hakuri, ganinka nayi baqiqirin..." Tace masa tana sake kwashewa da dariya... 16 Saida ya kwanta maganarta ta dawo masa, dan rabawa yayi ya wuce yana barinta a wajen "Yi hakuri, ganinka nayi baqiqirin..." Lokacin da yake Italy, mata da yawa suna yawan magana akan kalar fatarshi, suce bakinshi nayi musu kyau, duk da anfi yaba idanuwanshi fiye da komai, ko Aise tana ce masa idanuwanshi nayi mata kyau, sai dai yayi dariya, bai taba maida hankali akan irin kyan da ake fadar yana dashi ba, amman yau ba don gajiyar da yakeji ta zuciya da ruhi ba zai tashi ne yaje ya duba mudubi yaga abinda zaisa wancen yarinyar mai kama da sandar raken ta kalleshi ta kwashe da dariya, to wai mema ya samu bakin nashi? Baqiqirin tace, a cikin kan Haris abinda za'a danganta da wannan kalar sai dai gawayi ko bakar leda. Ya dago da hannunshi ya kalla, to bakin nashi ya shahara har hakane? Yaja karamin tsaki kawai yana rasa abinda ya kamata yaji, ya kalli wayarshi da take ajiye can nesa, sai yaji kewar Aise na nukurkusarshi, ya kara jan wani tsakin, ya rufe idanuwanshi kawai, bacci ya dauke shi, sai dai ko sha biyun dare batayi ba ya farka saboda mafarkin Aise da yayi tana tsaye tana kallon shi, tashi yayi yaje ya watsa ruwa ko zai samu sauki, daya fito ya samu t-shirt ya dora akan gajeran wandon da yake jikinshi, ya dauko laptop dinshi da charger, ya saka a jikin socket din kusa da gado ya janyota zuwa kan gadon ya saka laptop din a caji, sannan ya zauna ya budeta ya kunna, akwai wasu hotuna da zaiyi aikinsu, duk da yana da sauran kwanaki uku kafin ranar daya bayar na aikawa dasu ya cika, amman yana bukatar distraction din, aikin zai rage masa tunani. Abinda yayi kenan har safe, tunda a gida yayi sallar asuba duk da yanaji anayi a masallaci, kuma yaga gida baifi bakwai bane tsakanin gidanshi da masallaci a unguwar, shi daman tun yana gida sallah a masallaci bata dame shi ba, Hajiya Rumanan da zatayi masa magana itama bata damu da zuwanshi masallaci ko akasin haka ba, a Italy kuwa wasu ranakun ma hada wasu sallolin yakeyi abinshi. Alhaji Mustafa ne kawai in yana gari yakanyi masa maganar zuwa wasu ranakun, amman shi a karan kanshi sai sa'a, in ba juma'a ba. Yau da yayi sallar saiya kwanta, lokacin ne kuma ya samu bacci. Yanda ya kusan kwana a zaune, itama Maryama abinda ya faru da ita kenan, ta dauki ruwan ta koma daki, data kwanta sai Haris ya dinga dawo mata, ko ido ta rufe saita ganshi baqiqirin cikin bakaken kaya, tasan wasu in suna dariyar da ta kai dariya zakaga idonsu har hawaye yakeyi, amman ita dariyar da takeyi hawayenta bana nishadi bane sam, hawayenta na yanda duk tarin fararen mazan da suke duniya, ace babu mijinta a ciki, sai wannan bakin katon, ga baki ga muni, kamar ma hancinshi yayiwa fuskarshi tsayi ko itace bata gani ba sosai, kuma ta ga alama yanda baiyi mata ba, shima wannan auren kamar na dole ne a wajen shi, tunda taga idanuwanshi kamar cike suke da hawaye. Allaah Ya taimake shi su farare ne, koya hakoranshi suke? Zata so ta gansu. Wannan tunane-tunanen shine abinda ya hana mata samun bacci, ko ya zata juya al'amarin sai taji shi babba a wajenta, mijinta fa, mijinta ne danduqununun nan, sai kawai ta girgiza kai hawaye su zubo mata, ashe da gaske ne ana kasheka da ranka? To da me yasa ma take tunanin zata kulle kofarta, shi da yake bakima bai boye mata ba, itace zata boye masa? Gara ta fita tayi harkar gabanta, ba zai yiwu ace ga auren bakin ciki ga takura ba, gara taji da abu daya. Da ta gaji da saka wasikar jaki ma, saita mike cikin daren ta binciko jakar da Adda Zahra tace mata akwai waya, ta kuwa ganta, Nokia, kirar C3 da ake yayi a shekarar, kamar zata fasa ihu saboda murna, nan da nan ta kunna, ta dauko cajar wayar ta ajiye akan gado, ta koma ta kwanta tunda taga a cike take. Ta shiga nan ta fita can tana jinta kamar a gajimare, ita da take ta lissafin a siyawa Khairi wayar ta zama tata, tunda sai sun gama secondary harsun samu admission sannan Alhaji Sa'id yace zai sai musu wayoyi, to tasan Khairi zata rigata, kuma ita bata damu da waya yanda Maryaman take nacinta ba, ta tabbata bar mata zatayi, ashe zata mallaki tata a kurkusa, taga an saka mata lambar duka 'yan gidansu dake da waya, data duba taga ta Alhaji Sa'id da akayi saving da Abba, sai taji kamar ta kirashi, a lokacin karfe uku da mintina arba'in, amman ai zaiyi tunanin ba lafiya ba, zata bari sai da safe dan taga kudi a wayar, tabi kowa ta kira su gaisa. Sai gashi da karsashi tayi sallar asuba, ta zauna tayi azkar kafin tasa wayar caji ta kwanta, bacci tayi kamar bata da wata matsala a rayuwarta. Yunwa ce ta tasheta wajen karfe goma da rabi, bayi ta shiga ta wanke fuskarta tayi brush, ta fito tana nufar kitchen kanta tsaye, haka ta dinga bin tsarin kitchen din da kallo dan jiya batashi takeyi ba, yayi kyau, ba wani babba bane ba, amman an kawata shi da kayayyaki da kalarsu take da sanyin kallo a idanuwa, tasan Adda Zahra batason kala mai hayaniya tunda canma, ko atamfofinta zaka gan kalar jikinsu bata taba wuce uku, wasu ma kala biyu ne, shisa kitchen din baiyi hayaniya ba. Taga kwan a kunne, kuma bata jiyo karar generator ba, alamar wutace aka dawo da ita. Yunwa take ji ta gaske, amman batasan ta inda zata fara ba, kome zata dafa, taga wata kofa a cikin kitchen din, data shiga sai taga dan karamin store ne, kuma akwai kayan abinci a ciki daga kan shinkafa har zuwa indomie, sai ta shiga ta fasa kwalin indomie din, kananu ne, ta dauko kwara biyu, ta fito ta ajiye, manyan bokatan dai tasan su dublan ne, tana sonsu, amman ta rasa dalilin da yasa su basa sonta, duk sanda zata saki jiki taci sai cikinta ya dingayi mata ciwo, akwai albasa da aka zuba a wani kwando cikin kitchen din, saita dauko ta kara dawowa, tana ta faman bude-bude, bata ga ashana ba, kuma ta kunna gas din taga ba irin na gidan Adda Maimunatu bane, dole sai tasa ashana. Gashi duka gida hudun burners ne babu electric. Tayi tsaye cikin kitchen din ta rasa mafita, to ko dai zuwa zatayi ta duba ta ga idan yana nan ta tambayeshi ko shi yasan inda ashana take? Sai kuma taga ai dukansu bakine a gidan, sai dai tace masa ya siyo mata, tunda ba zata zauna yunwa ta kasheta ba. Ta fito da wannan niyyar kenan taga Haris din shima ya fito, bakar rigace dai a jikinshi, ya dai sake wando zuwa jeans ba irin wandon jiya ba, amman shima bakine, ita ta sake kayan jikinta dan batason takura in zata kwanta, wani material ta saka natane na gida, dinkin bubu ne kuma yadin bashi da nauyi, dashi ta kwanta, shine a jikinta yanzun. Bakin shi dai yana nan yanda tagani jiya, yau dai kamar ya shafa mai tunda har wani sheki-sheki taga yanayi. Abinda bata gani ba jiya shine Haris na da tsayi, duk da bashi da wata cikar jiki, dan itama din ba gajera bace ba tana da matsakaicin tsayi, shisa daga inda take tana tunanin kanta zai kai kafadar Haris inda zasu jera, wayace a hannunshi yana dannawa, ya kalleta sau daya, saiya maida kanshi kan wayar yana cigaba da tafiya, da alama ficewa zaiyi ya bar gidan "Harisu..." Ta tsinci kanta da furtawa, sai kuma taji sunan ya danyi mata nauyi, ko dan basu saba kiran sunan wanda ya girmesu gatsau haka ba, yaji ta, shisa ya tsaya, kuma yanda ta kira sunan nashi ne yasa shi juyawa yana kallonta "Harisu kuma?" Ya maimaita cikin wani yanayi, yana kuma kara maimaitawa cikin kanshi, wanne irin Harisu? Kallonta yakeyi yana so ya gane matsalarta, dan tabbas tana da matsala, babu yanda za'ayi ta rasa matsala "Ina as...ina kwana" Tayi saurin canza akalar tambayar ganin yanda yake kallonta, bai amsa ba sai girarshi daya daya daga sama "Daman...daman..." Ta rasa me yasa taji kallon da yake mata yana neman daburta mata lissafi "Ashana zaka siyomun" Taga lokacin daya dage dayar girar "Ashana? Ni zan siyo miki ashana?" Idan bashi zai siyo mata ba waye zai siyo mata to? Ita bata da ko sisi ma balle tayi tunanin fita ta siya, kuma in tana da kudin ai batasan ina zata nufa ba "Yunwa nakeji, babu ashana da zan kunna gas...bani da kudi, kuma bansan inda zanje in siyo ba ko ina da kudi" Shifa yanda take tsaye a gabanshi tana masa magana kamar wanda suka saba da juna mamaki yake bashi, babu wani alamar bakunta a tare da ita, kamar ta sanshi, abinda bai sani ba, Maryama na daga cikin mutanen da basa bakunta, in yau ta fara ganinka to zata gaya maka abinda yake ranta batare da wani dar ba, duk gidansu ita da Khalifa ne suke da wannan halin, shisa suka fi jituwa, ta kuma fi cin dukanshi fiye da kowa saboda yanda yake gatse-gatse itama haka take, zasu zauna amman da wahala a watse bai kai mata duka ba saboda wata maganar da zata yaba masa "In kuma akwai goma a wajenka saika nuna mun wajen dan Allaah, cikina sai kullewa yakeyi" Ya numfasa "Wai wacce irin goma kuma? Ina zan nuna miki?" Kanta tsaye tace "Wacce irin goma zan tambaya dan Allaah, Naira goma mana, shagon da ake saida ashana zamu fita ka nuna mun, tunda kaga ni ba sanin waje nayi ba" Idan ya tsaya, ba mamaki bane abinda zai sandarar dashi, ciwon kan da ya tashi babu shine wannan yarinyar zata dawo masa dashi, shisa yasa hannu a aljihunshi, yana da lighter, ya riga ya saba ma tana daga cikin abinda yake dauka ya saka a aljihu duk idan zai fita, kuma da yabar kasar sai ta zamana wani abu da saiya duba mai kyau zai cire kudi ya siya, wannan dinma wata irice ta silver, in ba budewa yayi ba, ba zakayi zaton lighter bace ba. "Ga lighter" Ta karba, amman bakinta da bai saba shiru bane yace masa "Lighter? Wannan lighter ce? To kai me kakeyi da lighter?" A iya saninta ba haka lighter take ba, kuma babu masu amfani da ita sai masu shan sigari, taji gabanta ya yanke ya fadi, ta kalli labbanshi da suke da duhu suma kamar sauran jikinshi, tunda ai masu shan sigari zakaga bakinsu bakikirin haka tafukan hannuwansu "Ban sani ba" Haris ya tsinci kanshi da amsa mata "Ki kunna ki bani fita zanyi" Ta kuwa wuce, amman da taje saita rasa yanda zatayi ta kunna, daga kitchen din ta bude murya tana fadin "Nifa na kasa kunnawa..." Ya jita, ya numfasa "Inalillahi wa ina ilaihi raji'un" Haris ya furta kasan numfashinshi, fita yayi niyyar yi, akwai wani tea joint da sukaje da Lalaye, can yayi niyyar zuwa ya zauna ya sha shayin saiya dawo ya cigaba da aikin gyara hotunan da yakeyi, amman yaga alamar ita ciwon kai take son hadashi dashi "Kaji?" Ta sake fadi, bai motsa ba "Harisu!" Yaji kamar ta kwada masa sanda, yanda yakejin dadin sunanshi, amman yau tana neman ta fitar masa dashi daga rai, baisan ya tsohon wake yake ba, amman da tace Harisun nan shine abinda ya fara hangowa, kitchen din ya nufa "Karki kara cemun Harisu, sunana Haris, bani?" Ya karasa maganar yana fisge lighter din daga hannunshi, ta kalle shi ya hade girar sama da ta kasa ya tsuke bakar fuskar nan, ta matsa gefe, daya kunna lighter din saiya rasa me zai murda kuma, ya juya ya kalleta ta zuba masa ido "Ina zan kunna miki?" Kamar tace masa "Ai bari nayi inga gudun ruwanka" Saita cije rike bakinta "Kinsan Allaah zan tafiyata" Da sauri tace "Yi hakuri, saika matsa ai" Ya matsa din, yaga tana kikiniyar murdawa "In baki iya ba karki hada mana gobara ki babbake mun gida, ki bari fita zanyi sai in taho miki da wani abin" Ta karbi lighter din tunda taga yanda ya kunna, ta murda gas din ta kunna, tana mika masa, kuma da yake rowa ba halinta bace sai tace masa "Indomie zan dafa inyi da kai?" Da saurinshi ya girgiza mata kai "Jagwalgwala kayanki, aci lafiya" Yayi maganar yana takawa ya fice daga kitchen din, kafin tace wani abu ya riga ya fita, ta jinjina kai, ai daya tsaya ta gama dafawa yasha mamaki, ita zaice zatayi jagwalgwalo, ita da take dafa abubuwa, danma ba son girki takeyi ba, ko sakasu akayi zatayi gyaran kayan miya, da kananun abubuwa ta bar Khairi da sauran aikin, tana son abinci, amman tafi fahimtar ta aikashi cikinta fiye da ta sarrafashi, duk da haka babu yanda za'ayi a kira girkinta da jagwalgwalo "Kayiwa bakin cikinka" Tayi maganar a fili, tasan yanda wajenshi yake bakikirin haka cikinshi ma yake. Tukunya ta samu karama ta tari ruwa ta daurayeta, ta zuba wanda take tunanin zai isheta ta dora. Shi Haris daya fita, joint din bashi da nisa sosai da unguwar tasu, saiya ga wajen a rufe, ya kira Lalaye yake fada masa "Ai basa budewa da safe sai karfe takwas na dare" Takaici ya kamashi, saiya juyo kawai yana fatan Maryama na kitchen ko ta shige dakinta, bayason wata magana, sai dai shayin yake bukata sosai, daya shiga bata falon, ya juyo maganarta a kitchen din dai, da alama waya takeyi cikin nishadi hadi da shagwaba kuma "Kai Hajja, ni da Abba yace yanzun nama kusa in fi su Adda Asiya hankali..." Wani numfashi mai dan sauti ya subucewa Haris, wai hankali, kamar ya leka kitchen din, sai kuma ya wuce dakinshi, ya sake fitowa, ko ita zaice ta dafa masa shayin? Bayason saka wani abu mai sanyi a cikin nashi daya hakura ya dauki lemo, haka kuma bayason yin wata doguwar magana da ita, da yake hankalinta na kan wayar da takeyi da aka ba Khairi, batason indomie dinta ta dafe, shisa ma ta gama da wuri, ta samu plate ta juye anan kitchen din, ta dauki lemo tana wayar tana cin abinta daga tsaye, yau babu mai ganinta balle ayi mata fadan cin abinci a tsaye. Yunwa takeji, nan da nan ta gama cinye indomien tana kurbar lemonta a cikin roba, sosai zuciyarta takeyi mata sanyi, har yanzun murnar wayar taki sakinta, yanda kuma har Adda Asiya take ta mata hira sai take jinta wata daban, har Hajja mafa haka ta juyo tana cewa "Maryama ce? Bani wayar mu gaisa" Itace aketa nunawa kulawa haka, ana nan nan da ita kamar wadda suka shekara basu gani ba, dadi ya cika mata rai fal, ta shanye lemon tana wasa da murfin tukunyar da ta dafa indomie dinta saboda yanda wayar takeyi mata dadi tasan Haris fita yayi, ko kadan bata tsammaci dawowarshi ba, shikuma daya shiga kitchen din ba magana takeyi ba, ta dai juya masa baya saiya dan taba kafadarta yana fadin "In ba zan takura miki ba ko..." Bai karasa ba saboda yanda ta kwala kara jin an tabata, tana cilli da wayar, data juyo saita juyo da murfin tukunyar nan tana kwada shi da dukkan karfinta, duk da shima yayi kokarin yin baya amman yanajin yanda ta sameshi a kafada harda karar da kashin wajen yayi na haduwa da murfin tukunyar, wani irin radadi ya shigeshi, ita kuma Maryama da zuciyarta ke bugawa ta kula dashine, "Dan Allaah ya za'ayi ka shigo waje ba zakayi sallama ba kuma ka taba mutun? Bakaji yanda zuciyata take bugawa ba" Zuciyarta ce take bugawa yaji tace, shikuma kafadarshi fa? "Meye kika bugamun?" Ya tambaya yana murza wajen dan zafi yakeyi masa sosai, hannunta yake kallo, siririn hannunta, amman ko Barde ne ya kawo masa duka iya karfin da zai sauka dashi kenan "Yi hakuri, dan murfin tukunya ne a hannuna, gaskiya ka dinga sallama, inda wukace kuma fa?" Ya jinjina kai Ko da Alhaji Mustafa ya fada masa ya karbar masa aure, daya hango Aise, ya hango zata iya juya masa baya, kafin ta aikata sai ya dinga hango rayuwarshi zata fara ne ta kare idan ta barshi. Bayan ta barshi kuma sai yaga ashe ita din ba duka rayuwarshi bace, wani sashine mai haske, babu abinda ya same shi, ta dai tafi da wannan hasken ne. Ashe rayuwarshi ba a hannun Aise zata kare ba A hannun wannan mahaukaciyar ce da aka kakaba masa... 17 Duk wani dokin sabon waya a sati dayan nan Maryama tayi shi ta gama, data tashi da safe zata kira 'yan gidansu daya bayan daya tana gaishe dasu, Khalifa mane tunda ya watsa mata zagi sau daya ta kirashi wajen karfe bakwai da rabi bata kara ba. Sannan kuma kowa ya tashi yana saka mata kati, sunfi shan waya da Khairi, anan katin nata yake karewa tas, sai da Khairi tace mata ta bude Facebook sai su dinga hirar ta can, amman ta gaya mata tana bukatar eMail, ita duk abubuwan nan ba gane musu takeyi ba, nacin wayarta ya kare akan camera, tana son daukar hoto, sai game, sai kallo idan akwai film a wayar, to wannan babu film ko daya, ko radio data shiga sai taga takiyi wai saita saka earpiece tukunna. Kadaici ya fara damunta sosai, sai dai ta shiga wannan dakin ta fita, jiya har dakin Haris saida taje ta murda, taji dakin a kulle, ga tv amman ta kasa hadawa, haka abincin da take dafawa duk sun isheta, banda albasa da timatir din gwangwani da aka kawo ta dasu, babu wani kayan cefane, nama kuwa wasu kajine gasassu da aka zuba a fridge, guda hudune, dasu ta dinga amfani sun kare suma. Komai bayayi mata dadi, duk kuwa da "Lafiya kalau, babu wata matsala Adda" Da take amsawa Adda Zahra duk idan ta ta tambayeta, amman batajin alamar lafiyar a wannan zaman kadaicin da yake damunta, saima ta kwanta da daddare, jiya haka ta dinga share hawayen da in za'a tsireta bama zatace ga dalilinsu ba. Haris in ta fito da safe neman abinda zataci, bata ganinshi, tana gane ya fitane lokacin da zata ga babu motarshi inta leqa, sai dare sosai yake dawowa, inta duba agogonta zata ga karfe goma wani lokacin sha daya na dare, batama son jin karar motar shi inya shigo, sai kirjinta ya kulle waje daya, su biyu aka yiwa auren, amman ita take fama da kadaici, tunda shi zai fita duk inda yake so, haka kuma zaici abinda yake so, ita kuma zataci abinda ya samu. Tana son indomie, amman bawai iri daya ba kullum, ta fita daga ranta, yau data tashi kujera kawai takebi, yunwa sai laliqarta takeyi, inda zata samu shayi da madara, ace da wani biredi mai laushi ga wainar kwai a tsakiya ba karamin farin ciki zatayi ba, amman ina zata same su? Hawaye suka cika mata ido, ta tsinci kanta da yiwa Abbanta addu'a, yanda yake tsaye akansu, duk yawansu basu taba neman wani abu suka rasa ba, dai-dai gwargwado rayuwa sukeyi cikin wadata, amman gata nan kwance yau tana neman abinda wata rana sai taga dama zataci, da yake gidan akwai maza, da yawansu kuma shayi da biredin baya rikesu, in shi za'a sha dole sai an hada da wani abin, su da zasuyi aikin, koma tace ita da baifi tayi abinda ba za'a rasa ba, bakinta kamar zai taba bango. Idan ba Hajja ta gani a kitchen din ba haka zata dinga mitar anja musu aiki, ga kewa, ga yunwa, abin ya hade mata, sai share hawaye takeyi daga kwanciyar da tayi, a haka taji wayarta na ringing, kamar ba zata dauka ba, ganin Khairi yasa ta daga wayar ta amsa cikin karamar murya "Lafiya? Me ya faru? Kuka kike ko?" Cewar Khairi ta dayan bangaren, sai taji ta kasa daurewa, kukan ya kwace mata sosai "Me yayi miki?" Khairi ta sake tambayarta "Ba komai" Ta amsa tana kuka har lokacin "Babu komai kike kukan nan Maryam? Ki fadamun menene? Ko in kira Hajja?" Kamar tana ganinta tayi saurin girgiza kai "Ba abinda yayi mun, yunwa nakeji, kuma nagaji, nagaji da zama ni kadai..." A nutse tayiwa Khairi bayanin komai "Shine zakiyi shiru, ai bawai zama zakiyi ba, magana zakiyi masa, ki fada masa yayi miki cefane, haka akace miki ana zaman aure? Ke baki ga komai ya kare a gida Abba ne yake siyowa ba" Maryama tayi shiru "Nafa ce miki ba ganinshi nakeyi ba yanzun, baya zama a gidan, sanda yake dawowa kuma karfe goma ta wuce..." Khairi taja karamin tsaki "Ko ki jirashi da safen, ko da asuba kije ki buga masa kofa, ko kuma da daddaren inya dawo kije kiyi masa magana, in kuma ulcer kike cigiya to Allaah Ya bada sa'a, ni banma san sanda kika koma haka ba da zaki kasa tunkarar wani da wata magana" Ita tunanin ta sami Haris ne baizo mata ba, bawai dan tana tsoronshi ba, sun dan kara taba hira da Khairi, itace take gaya mata ta duba sosai a cikin kayan ta tabbata akwai sikari, a kwali yake dan cube ne, da suka gama wayar kuwa ta duba sai gashi ta gani, ta fasa ta dauko kwali daya. Da yake akwai kayan shayi, ta dafa, sai gashi yanata kamshi, indomie din da ta fita daga ranta ita ta dafa ta hada da shayin, ganyayyakine kala-kala aka harhada mata, yayi wani dandano da batasan lokacin data cinye indomie din nan tana korawa da shayin ba. Da ta gama saida ta karo rabin kofi tasha, sai taji dadin jikinta. Taje tayi wanka, ta kara share gidan da baiyi wani datti ba, ta koma kan kujera ta kwanta tana dan buga game a wayarta. Wajen karfe sha biyu taji motar Haris yau, da sauri ta mike zaune daga kwanciyar da take, idonta akan kofa ya murda ya shigo, wandone mai laushi a jikinshi da kuma riga, amman bakake ne, gani nawa tayi masa kenan? Duka ganin bakaken kayane a jikinshi, ko meye hadinshi da bakin kaya oho? Bambancin kalarshi da ta kayan bamai yawa bace, shi yana wani kyalli-kyalli ne kamar yasha mai, ya kalleta, sai ya dauke kanshi, har yanzun yanajin ciwo kadan a kafardarshi, wajen data kwantara masa murfin tukunya. A ranar ne ma da daddare Lalaye ya addabeshi da kira, wai za'a bude wani restaurant washegari, dan Allaah ya fita suje tunda za'a dauki hotuna sai suyi hotunan, wajen na abokin baban Lalayen ne "Waye yace maka irin wannan hotunan nakeyi Lalaye? Kawai sai in kwaso kayan aikina inzo daukar hoton bude restaurant?" A wajen Haris wannan abune marar muhimmanci, bai fara daga camera dan ya dinga daukar abubuwan da yake ganin ba zasu amfani mutane ba, duk da akwai wasu 'yan ayyukan da yakanyi a Italy da yasan zasu kawo masa kudi, kamar hotunan biki da makamantansu, amman restaurant fa? Sai dai Lalaye mutum ne mai naci, daya fara jera masa kira sai gashi ya tafi wajen, ashe mutumin ma babban dan siyasa ne, bashi da wani mukami a wannan lokacin, amman ana damawa dashi a gwamnatin da take ciki, bayan kwana biyu yaga aikin da Haris din yayi, sai gashi yasa Lalaye ya nemo masa shi zasuyi wani taro, kudine masu dan dama. A satin ya samu ayyukan da ya kula suna rage masa damuwa, suna hana masa tunanin Aise da ya tabbata blocking dinshi tayi shisa baya samunta ta ko ina. So yakeyi ya yaji ya take, ya danji muryarta ko kadan, a gefe daya kuma yanaso ya yakice ta, ya nuna mata bata isa ta bashi zabi ba tsakaninta da Maryama, tunda ai Maryaman zabin mahaifinshi ce, kamar tana cewa ya zabeta koya zabi Alhaji Mustafa ne, shikuma idan zai rayu sau goma, to tabbas a kowacce rayuwa zai zabi Alhaji Mustafa. Wanda ba zai rike hannunshi ya tayashi karbar wannan zabinba zai hakura dashine. To kuma idan ya gama aikin sai su tafi yawonsu ya kara ragewa kanshi damuwa da matan da suketa rububinshi, matan da Lalaye yake ta hadashi dasu. "Kaji..." Maryama tace masa, taga bayason Harisun, kuma yanzun ba neman magana takeyi ba "Dan Allaah, abu zan fada maka" Sai ya tako cikin falon sosai, tabi kafarshi da kallo, takalmin daya karaso dashi har yana taka mata kafet din da yake shimfide, ta daga ido ta kalle shi, shima kallonta yakeyi da nashi idanuwan da take ganin kamar hawaye ne kwance a ciki "Me akayi maka?" Tambayar ta subuce mata, cikin rashin fahimta yake kallonta "Kullum kamar zakayi kuka, idonka da hawaye a ciki" Ta karasa "Kullum?" Ya tambaya "Tun rannan nagani, randa na fara ganinka, na dauka saboda an aura maka nine shisa kayi kuka, ko zakayi kuka" Dariya mai sauti ta kwacewa Haris, irin dariyar daya kwana biyu baiyi irinta ba "Kawai sai inyi kuka dan an auramun ke?" Ta jinjina masa kai "Eh mana, ai baka son auren, nima nayi kuka tunda banaso, dana ganka baki ma na karayin kuka" Cike da mamaki Haris yace "Bakin nawa ne ya saki kuka?" Batare da wani bata lokaci ba ta daga masa kai "Bana son bakin namiji" Dariyar da yayi bata da alaka da nishadi, mamakinta yakeyi, ko dai da gaske bakin nashi yakai wani mataki ne ba'a taba samun wani ya gaya masa gaskiya ba? Ya kalleta, itama ba wata fara bace ba, tana dai da haske, ba zaka kirata baka kai tsaye ba, shi ba zaice ga kalar da yake so a tare da mace ba, abubuwan da yake so a jikin mace basu da alaka da kalarta, ko babu wadannan abubuwan ma in bukatarta ta taso masa zai iya hakura dasu, ita dai da take tsaye a gabanshi yanzun baiga wadannan abubuwan ba, siririya ce da zaka ga hakan a kallon farko, shisa yayi mamakin irin karfinta data kwada masa murfin nan, daga baya ya daina mamakin ya barshi a cewar tsoro ne ya kara mata karfi ba wani abu ba "Daman kin tsayar dani ne dan ki fadamun bakya son bakin namiji?" Da sauri ta girgiza masa kai "Yi hakuri, zan fada maka bani da cefane ne ka siyomun, jiya ma fa taliya da mai da maggi naci, bansan ko an kawomun yaji ba, na duba bangani ba, dan Allaah kayi mun cefane dan in dinga girki, harda biredi ma da kayan shayi" Cikin kanshi ya maimaita taliya da mai da maggi, yana kuma so ya hada hotonta, wani abu marar dadi ya dirar masa, shi abinci bai dame shi ba, in dai zai sha tea, ko da babu madara, to zai iya wuni bai saka wani abu ba, amman taliya da mai? Abin baiyi masa dadi ba sam "Me kike bukata?" Ta fara yi masa wani lissafi daya sashi fadin "Ki shirya in fito muje tare kawai, sai ki duba abinda kike bukata" Murmushi ya kwace mata "Dan Allaah da gaske kake? In shirya? Zakaje dani?" Akwai wani abu a tare da farin cikin nata da yaji yana so yasa murmushi ya kwace masa shima "In na fito baki shirya ba tafiyata zanyi" Da gudunta tabar falon, atamfa ce a jikinta dinkin doguwar riga, saita samu hula ta saka. Da taje dakin kuma saita rasa kayan da zata dauka, kawai saita dauki hijabi ta fesa turare a jiki ta dora a saman kayan ta samu takalmi ta saka ta fito tayi tsaye tana jiran Haris. Daman zaman kadaicin ya isheta, ko babu komai zata sha iska, iya harabar da suka fita sai da taji dadi. Balle kuma da suka shiga motar, haka ta dinga kallon hanya sai kace ta shekara bata fito ba. Wani babban shago suka shiga, ya dinga zagayawa da ita inta dauki abu guda daya saiya kara biyu, shisa siyayyar tasu tayi yawa, haka ta waro ido lokacin da aka lissafa taji kudin da zasu bayar, kuma Haris din ya bayar babu wani dar. Cefanen nema taji yana waya da wani Lalaye yana tambayarshi inda zasu samu "Sai dai ki rubuta list na abubuwan da kike so idan mun koma gida, sai in bayar a siyo" Ya fada bayan ya sauke wayar, ta jinjina masa kai kawai farin ciki ya isheta "Insa harda nama da kifi?" Ya dan kalleta, kafin ya cigaba da tukinshi "Kisa duk abinda kike bukata, komai da komai, karki zo ki dameni babu wani abu, ki saka komai" Abinda yaji dazun, yanayine da bayason ya sake jin irinshi sam, gara ya ajiye mata komai saita karata ita da gidan. Da suka karasa gida, suka fito daga motar saita zagaya ganin ya bude bayan ya fara fito da siyayyar da sukayi, ta kinkimi wata katuwar leda "Ki ajiye ki wuce, sai kin karya wannan siririn hannun naki" Cewar Haris yana bata dariya "Tafdin, ba zai karye ba, zan iya dauka, kasan abubuwan da nake dauka kuwa? Karfine dani, ko a makaranta ma ba'a kayar dani wajen dambe" Ya juya yana harararta "Ke dince kike dambe a makaranta?" Ya karasa maganar da dan karamin tsaki, shi dai ba zai kirga damben da yayi a makaranta ba, tun daga Primary harma secondary, wani lokacin idan ya zauna sai ya dinga mamakin kanshi, kamar yayi sanyi yanzun, ya rage zafin rai da saurin fushi, ko kuma masu harzuqashi dinne babu? Amman da fa kallon da bai gamsar dashi ba in ka dinga aika masa zai iya ja maka duka a wajenshi, shine yanzun wannan siririyar yarinyar zatace masa tana dambe, saboda cika baki "Wallahi kuwa, babu wanda yake rainani, harma 'yan ss3" Murmushi mai sauti yayi yana girgiza kai "Ki ajiye ledar nan kafin in kwada miki gwangwanin madarar nan" Kamar bata jishi ba, ta tallabi kasan ledar bayan ta dagata tana wucewa da saurinta "Ke..." Haris ya fara, saima ta kara sauri kamar zata ruga da gudu, ya sauke numfashi yana girgiza kanshi kawai, ba zai iya surutu ba, data kara dawowa baice mata komai ba ya kyaleta kawai, suka shigar da komai tare "Nagode sosai, Allaah Ya karo kudi masu yawa da albarka, dan Allaah ka hadamun tv dina kuma, idan ka fita kaga zan dinga yin kallo tunda ana barin wuta sosai" Ya daga mata kai "Allaah Yayi maka albarka" Wannan kalmomi ne da suka saba da fada a tsakaninsu, in dai wani zaiyiwa dan uwanshi abinda yaji dadi, kalmomi ne da suka sa Haris kallonta, saboda kalmomi ne da yake jinsu a bakin Alhaji Mustafa, kalmomin da sukayi karanci a tsakaninsu a shekarun baya, sai dai yaji ya furtawa Mukhtar, kalmomi ne da har yanzun da yake yawan furta masa su bai daina yunwarsu ba, haka kawai yaji yace mata "Nagode" Kafin ya fice daga kitchen din yanajin a yau din nan ma zai kirawo azo a hada mata tv din, tunda baisan me dame za'a bukata ba, shi dai ya taso yagani a dakinshi, da yake kallon bai dame shi ba, sai yayi kwanaki bai kalla ba, da suna makaranta kuma su Barde na janshi suje in ana wani wasan ball, to tunda canma ball din bata dame shi ba, yanzun kuma da babu wanda zai jashi suje kallo sai ya hutawa ranshi, da yaje kallon wata ball ma ai gara yayi bacci. Sai da ya kara yin wanka ya sake kaya tukunna ya fita daga gidan da list din da Maryama ta bashi bayan tazo ta kwankwasa masa daki ta tambayeshi ko yana da biro da takarda, ya dauka ya bata, yana tukin kuma yaji yana so ya warware takardar data linke gida biyu, ya duba, rubutunta yayi masa kyau a ido. Ya sake linkewa ya cigaba da tukinshi, yana tunanin abinda zatayi da tattasan daya ga ta rubuta, dan a iya tunaninshi ya kasa hango gurbin tattasai a cikin abinci, ko dan babu wanda ya tabayin girkin a gabanshi? Idan ma zaici sai dai ya gani a girke... 18 Tunda tafiyar da zasuyi zuwa Syria ta tabbata yakejin shi cikin nishadi marar misaltuwa, sati biyu zasuyi, amman yasan sati biyu ne da zasu iya bude masa kofofin wasu satukan a kasashen da ake fama da hargitsi irin na Syria, sannan kuma mataki ne na farko da zai taka akan turbar da yake buri. Sai gashi su Barde kuma sun kara masa wannan nishadin ta hanyar dira a garin Kano shi da 2Pac "Daman surprising dinka mukace zamuyi" Cewar Barde, aikuwa sun bashi mamakin, dan ya kasa rufe bakinshi, da yake lokacin da suka shiga Kanon da yamma ne, sanda ya karasa wajensu ma ana kiran sallar Magriba, dan haka da sukayi sallah sai suka wuce gidan Lalaye suka baje kolinsu acan, wajen karfe takwas 2Pac yace wa Haris "Tashi fa zakayi ka wuce gida, ka bar 'yar mutane ita kadai" Su duka suka kwashe da dariya, Lalaye na zaginshi "Kaman baku san ba'a cin mutuncin aure a gabana ba ko?" Shi ko kishiyar mahaifiyarshi da ta basu wahala baya fatan ace ga ranar da mahaifinsu zaiyi mata wani abu na rashin jin dadi, kawai yana da wani rauni ne akan mata, kuma a yanzun a cikin su hudun shine baya bin mata, zai sha komai, amman wannan harkar bata taba burgeshi ba, su Haris dinma inda zasu ji maganarshi da sun daina, ko yau akwai matan da Lalaye ya kira musu shi da Barde, daya daga cikinsu da ta tunkari Haris shi yayi mata wani irin kallo da yasa ta natsu waje daya, kuma da suka fito zai raka Haris din saida yace masa "Kayi hakuri da matarka ta gida, idan tayi maka kadan ka kara, ka cike hudun tunda kana da halin rike su, amman kayi hakuri da biye-biyen nan Ganja bashi da amfani" Murmushi Haris yayi "Wai wa'azi zakayi mun Pac?" Ya girgiza masa kai "Ni da Malami ha ya zanyi maka wa'azi, gaskiya na fada maka, in kaga damar dauka kenan" Haris din yayi gajeriyar dariya kawai, sukayi sallama tunda sunce masa washegari zasuje su gaisa da amarya, kuma ya amsa musu. Ba zakace Haris mutum bane da baya magana, inka kalle shi sai kayi zaton zaiyi miskilanci, yana da wahalar sabo, sannan bashi da saurin sakewa da mutane, amman yana magana, yana hira sosai da sosai. Sannan abubuwan da suke boyewa juna shi da abokanshi ba masu yawa bane ba, tunda su duka sunsan a shekarun baya bashi da wata kyakkyawar fahimta da Alhaji Mustafa, sai dai banda 2Pac din babu wanda yasan yana tare da Aise "Ba abu bane na sauri Pac, ina sonta, tana sona, banajin son zaije ko ina, so zamubi a hankali ne, tunda duk muna da inda muke da burin kaiwa kafin muyi tunanin wani aure..." Kuma yana da yakinin 2Pac ba zai taba zancen da wani ba, shi mutum ne mai matukar sirri, shisa Haris zai iya cewa abotar da take tsakaninsu tafi ta sauran, saboda yana iya maganar da yake kasawa da su Barde da 2Pac, ya fada masa Alhaji Mustafa ya karba masa auren Maryama, kafin yace wani abu ya dora da "Bana son yin maganar, ya daura auren, na karba, iya abinda na sani kenan" 2Pac saiya sauya akalar hirar tasu a ranar daya gaya masa din, kuma bai sake tayar masa da zancen ba, yasan in bashi da kanshi ya sameshi ba, haka zasu cigaba kamar bai fada masa ba. Tunanin shi yanda zai gayawa Maryama cewa abokanshi zasu zo su gaisa da ita, tunanin da ya dingayi kenan da yake tuki, har ya karasa gidan, ya sameta zaune a falo tana kallon wani Indian, da yake DStv yasa aka saka mata, duk sanda zai ga tana kallo India ne, idan ma ta taba canzawa zuwa wata tashar shi dai baigani ba "Nagode sosai sosai, naga DStv aka sakamun, zan cigaba da kallon films dina" Haka tace masa ranar hakoranta a waje, dan zai rantse har turamenta saida suka bayyana, kuma yanzun daya shigo gidan in dai zata ganshi sai tace masa "Sannu da zuwa..." Ko ta gaishe dashi, jiya ma daya dawo da daddare data gaishe shi kafin ya amsa ta dora da "Farfesun nama nayi, na hada da shayi, yayi dadi shine na rage maka tunda naga kaima kayi mun kirki... harda biredi na ajiye maka, amman na kusan cinye biredin fa saura guda uku...kanaci dashi ko in cinye kayana?" Ya girgiza mata kai, shi kuwa me zaiyi da biredi yanka uku? Taso ma ta bashi dariya "Na koshi duka...ki dai bani shayin" Ta mike da saurinta "Insa maka madara sosai?" Ya daga mata kai "Kisa komai sosai banda sugar, shi kadan" Har ta kusan kofar kitchen din ta juyo "Da yawa shayin?" Kai ya sake daga mata. Ta hado masa, kuma baisan dame-dame ta saka ba, yanata kamshin daya wuce ace na madara da milo ne kawai, yayi masa dadi sosai, sai gashi kofin da ta kusan cikawa yake tunanin inda zai kaishi ya shanye duka. Yau ma ya ce mata "A bani shayi, irin na jiya" Data tashi ta shiga kitchen din, saita hada masa harda cin-cin din kayan gararta a wani dan karamin bowl, ta tsaya ta kwankwasa masa kofa, ta dauka zaice bayacin cin-cin din saiya karba duka yace mata "Nagode" Ya mayar da kofar ya rufe, zataso ta shiga dakinshi, taga yanda yake duka, bawai iya inda idanuwanta suka hango mata jiya da yau ba, wannan laptops din nashi da wasu abubuwa da ta gani baje kan gadon dakin take so ta ga menene, ta kuma tambayeshi duk abinda bata gane ba. Amman zatace masa ya bar mata mukulli ta share masa dakin wata rana, sai ta karayi masa kirki tukunna dan kar yayi zaton wani abu. Ba karamin dadin DStv din nan tayi ba, kuma tasan Haris dinne ya fadawa maigadi da an dauke wuta a kunna generator, saboda haka kallo saita gaji, babu maice mata ta tashi, babu zuwa makarantar boko balle ta Islamiyya, abincinta inta dafa sau daya har dare, ta rage kadaicin nan, in sukayi waya da Khairi ta dinga bata labarin wani film data gani kenan. Da dai tace mata "Ke ba zakiyi girki ba kika zauna kallo ko? Saiya dawo baki gama abinci ba" Shine ta amsata da "Abinci na nakeyi ni kadai fa, da nace in dafa indomie dashi rannan haka yace baya cin jagwalgwalo" Khairi tace mata "In dai kin dafa ki dingayi masa tayi, ko ba zaici ba, kiyi masa tayi Maryama, wata rana sai kiga yace ki zuba masa, hakane zai gane ba jagwalgwalo bane, kinga babu dadi ace mutum yayi cefane kuma ba za'ayi girki dashi ba" Cikin kare kai Maryama take fadin "Nifa ban hanashi ba nace miki Adda, shine yace ba zaici ba daman" Kuma shawarar Khairin ta dauka takeyi masa tayi, sai gashi taji dadi daya karbi shayin jiya, yau ya nema da kanshi, ya kuma karbi cin-cin din bai gwasaleta ba. Ta koma ta kwanta akan doguwar kujera tana cigaba da kallonta. Haris kuma shayin yasha, ya dauki cin-cin din daya ya gutsira, sai yayi masa dadi, duk ranar shine abu na farko mai kama da abinci da ya saka a cikin nashi, ko da su Barde suka tsaya siyayyar abubuwan da zasuci dazun ba'a siya dashi ba tunda sunsan hali, kuma duk tarin lemukan nan ruwa yasa hannu ya dauka ya bude ya sha rabi. Yana gama shanye shayin yaji gajiya ta saukar masa, jikinshi duk ya mutu. Aise ta fado masa a rai "Ya jikinka ba zai mutu ba in kaci abinci bayan ka wuni da yunwa? Yanda ciwo baya kamaka ma abin mamaki ne" Dariya yayi a wancen lokacin, yanzun kuma yayi murmushi yana jin kewarta kamar ace tana gabanshi, ganin tunani zaiyi masa yawa yasa ya mike yana fitowa da kofin da dan bowl din zuwa kitchen, ya riga ya saba in yayi amfani da kofi haka saiya wanke yake ajiyewa, yanzun ma abinda yayi kenan tukunna ya fito falon ya sameta a kwance tana kallo "In karo maka shayin ne?" Ta tambaya data ga ya tsaya jikin kujerar da take kwance akai ta baya "Ya isheni, Nagode" Ta jinjina kai "Abokaina zasu zo ku gaisa gobe...." Ita ta karasa masa da "Idan Allaah Ya kaimu" Dan tanajin wani iri duk lokacin da zataji wani yace, anjima zanyi kaza, gobe zanyi kaza, batare da ya hada da idan Allaah Ya bashi iko koma Ya nuna masa lokacin ba, sai ta dingajin kamar ya aikata babban sabo, kamar rashin fadar zaisa yaki ganin goben, abin da zaiyi din yaki yiwuwa ko da yaga goben ma tunda ai komai na Allaah Ne. "Me za'a dafa musu? Su nawa ne?" Haris ya dan tattare girarshi duk biyun, yana tunanin abinci kuma? "Zaku gaisa ne kawai" Ta tashi zaune tana kallonshi "A'a fa anayin girki, ko Adda Maimunatu ma da akayi bikinta sanda abokan mijinta zasu zo mune mukaje muka tayata aiki ta dafa musu abinci" Ya girgiza mata kai "Ba abinda za'a dafa fa, zasu sha ruwa da lemo su tafi in kun gaisa" Itama abin bai zauna mata ba, dan yana ganin gardamar da take so tayi masa "Maryamm" Ya kira da wani yanayi da yasa kalamanta bacewa "Ba abinda za'a dafa, ke ina zaki iya wani girki, ki basu ruwa da lemo. Akwai cin-cin din da kika bani dazun?" Ta daga masa kai "Tam ki basu dashi, shikenan ya isa" Kafin tace wani abu kuma ya wuce ya koma dakinshi, amman dai tasan anayin girki, haka ma ake cewa za'aje gidan amarya aci taliyar amarya. Sai ita zaice ba zata dafa komai ba, ta kuwa yiwa Khairi text tana fada mata "Saiki hada musu harda dublan dasu alkakin ki basu lemon da ruwa kamar yanda yace, idan basu ci bama in zasu tafi kiyi masa magana a zuba musu a ledoji su tafi dashi, in kina da kaza kiyi peppering irin yanda Abba yake so din nan, wanda Hajja ta koya mana sai kawai ki hada musu dashi" Sai lokacin taji ta dan samu natsuwa, kamar taje ta kwankwasa masa daki ta tambayeshi su nawa ne, sai kawai ta kyale shi. Jin idanuwanta sun fara yaji yasa ta hakura da kallon ta kashe komai taje ta kwanta. Washegari kuwa tun wajen karfe tara ta kara share ko ina, ta dauko gawayinta ta kunna ta saka turaren wutarta a ko ina na gidan, tama manta dashi, amman da yake mai kyaune tun wanda aka turara gidan kana jin alamar kamshin nashi har lokacin, sai taji ko ina yayi mata dadi sosai. Lallai shisa Adda Zahra ta nacewa wannan Meens Incense din (08036387204). Da yake bata zauna kallo ba, kuma farar shinkafa ta dafa wadda zataci, zuwa azahar ta gama komai, tayi wanke-wanke, kaji biyu ne tayi amfani dasu. Ta zuba abincinta taci ta koshi, ta riga tayi wanka, kuma ruwa dai ba wani shiri takeyi dashi ba, in ba tsananin zafi akeyi ba, ko ta kwaso gajiyar da takeji har kasusuwanta, wanka biyu sai dai taga su Khairi na wannan fi'ilin yanda take kiranshi. Ita ko Novel take karantawa taga ance wai matar tayi wanka kafin miji ya fita aiki, ta cancada kwalliya sai kawai ta sheke da dariya, dan bata hango kanta a wannan lamarin ba, to dame zataji, tsakanin share-sharen gidan da akace tayi da girki kala biyar duk kafin mijin ya fita, sannan kafin ya dawo ta sakeyin wasu girke-girken, wani wankan da wata kwalliyar. Kenan ba zatayi baccin rana ba? Ba zatayi komai da rayuwarta ba, yaushe zatayi kallo duk ta gama barbadewa tsakanin kitchen da bandaki. Inda ma taga ina aka zuba mata abayoyinta da ita zata saka, sai kawai ta samu riga da skirt na lace marar nauyi tasa, harta fito da mayafi saita fasa ta dauko hijabi ta ajiye a hannun kujera, kafin ma ayi la'asar ta cire dankwalin data kima, dan ya isheta, tanayin sallah kuma saita daura shi simple ta ajiye hijabin tana sauraren ta inda su Haris din zasu bullo, da zai fita yace mata da yamma zasu zo. Ta dauka da anyi la'asar zata gansu. Amman basu shigo gidan ba sai wajen biyar da wani abu, haka suka gaisa a mutunce, sunayi mata Allaah Yasa alkhairi, sai taji kunya ta kamata, ta kasa daga kanta, ta mike kawai tayi hanyar kitchen "Shege ashe 'yar jinjira ka aura, wannan yarinyar ma ta wuce sha biyar?" Lalaye ya fada yana wata dariya, kawai wannan maganar tasa wani abu ya tsirgawa Haris, kallo Lalaye ya karewa Maryaman kenan? To akan me? Kafin yayi magana 2Pac ya rigashi da furta "Lalaye..." Saiya daga hannyenshi biyu alamar surrender "Nayi shiru Pac...kafin ka sakani a gaba" Sai Haris din ya mike yana rufawa Maryama baya, ya sameta tanata kiciniya da kwanuka da fillatai, yabi siraran hannayenta da kallo, idanuwanshi suka dira kan yatsunta da ke da alamar jan lalle har lokacin, sauran lallenta na biki, babu a jikin faratanta da suke farare qal kamar bata da wadataccen jini, yatsun nata suma sirara ne, amman dogaye, sai sukayi masa kyau, sai yaji yana auna laushinsu a idanuwanshi, yanda basu da tsokar nan ko inya rike zaiji alamar kasusuwanta jiki? Yanda ta daga wata kula yaga kamar sun lauye yasa shi karasawa da sauri ya karba "Saikin karya wannan hannuwan naki hankalinki zai kwanta" Ya bata dariya "Na fada maka ina da karfi fa, Allaah kuwa, kaki yadda ne kawai" Ya tabe bakinshi "Ki tsaya anan inzo in dauki sauran" Kuma gudun kar tayi masa gardama yanda tayi randa suka dawo daga siyayya yasa yace mata "Ki tsaya anan" Cikin umarnin da ta tsinci kanta da daga masa kai, tsayuwae tayi, shi yazo ya karasa kwashe duk abubuwan data hada "Ki koma daki abinki tunda kun gaisa" Ta sake daga masa kai "In basu cinye ba ka juye musu su tafi dashi dan Allaah, ga ledojin dana fito dasu nan" Ya dan kalleta, da yake an zuba mata irin ledojin nan da zaka iya sakawa mutum kayan gara, wai ko da zata ba wani, to tunanin yanda zatayi da wannan bokatan ma takeyi, tunda ita dai ba kawaye ne da ita da zasu zo ba, shima kuma sai yau ya kawo abokanshi, amman zatayi masa magana taji ko akwai wanda yake so yaba, kuma zata dibarwa mai gadi da yawa in yana da iyalai sai ya kai musu. "Kaji, kafa juye musu komai...kaji" Ya daga mata kai kawai, dan bayaso ta koma falon nan Lalaye ya kara ganinta. Sanda dai shiya koma duk sun sauko kasa suna cin dublan din, ga kular daya kinkimo an bude, nama ne yake ta tashin kamshi, dan shi Barde da yake abinda yake sone naman yake ci "Wallahi naman nan yayi dadi sosai" Yake fadi yana dorawa da "Anya ba zanyi auren nan ba in dai za'a dinga mun irin wannan? Ko zaka tambayar mun Madam in akwai kanwarta da ba'ayi wa miji ba" Sukayi dariya su duka, Lalaye yace "Kanwarta fa kace? Amman Barde tabbas rashin imaninka ya shahara, irinku ne kuke shan kunun marar lafiya...kanwar wannan ai ko wanka ba'a daina yi mata ba" Barde ya harareshi "Ina ruwanka, kaine zakayi mun hanya ko Ganja?" Haris kai kawai ya girgiza, duk maganganun da sukeyi bai tanka musu ba, da yaji zasu ishe shine ma yayi zagi. Sun gama ci, 2Pac yace su tashi ana kiran sallah "Ka kira Madam muyi mata sallama..." Kamar ba zai kirata din ba, amman ganin 2Pac ne yayi maganar sai yaje ya kwankwasawa Maryama kofa yace tazo suyi sallama data fito, ta sake dauko hijabinta, sunata yi mata godiya "Komai yayi dadi" Ta kalli Haris ganin ko rabin abubuwan basuci ba "Bari in kawo ledoji a juye musu" Bata tsaya yace wani abu ba ta juya, saida ta karasu dublan din a ledojin tukunna ta fito, Haris ya karba ya juye sauran, ya karbi wata roba mai kyau data bashi tace ya juye musu naman a ciki, tana da murfi "Ganja wato so kayi kai mana bakin hali, ashe gara da Madam ta fito, mikomun naman in rike" Cewar Barde "Ganja" Maryama ta maimaita a cikin kanta tana kallon Haris da baisan ya akayi shima ya kalleta ba, kuma wani abu ya gaya masa tunda taji sunan sai tayi magana, a karo na farko kuma yaji cewa zata bashi dalilin da zai kama wannan siraran yatsun nata ya lankwasa yaji sautin karar da zasuyi, dan tun dazun sukeyi masa yawo a kai, in hannun Aise na cikin nashi haka zai ta lankwasa yatsun yanaji suna qaras-qaras, sai ta kai masa duka tukunna, so yake yaji bambancin wannan sautin, shisa ya fita raka su Barde da fata daya a ranshi, tsautsayi ya aiki Maryama ta kirashi da "Ganja..." 19 Gidan bai taba yi mata girma ba duba da irin wanda ta taso cikin shi, amman duk girman gidansu ba'a taba rabashi da mutane, bayan su 'yan gidan kusan ko yaushe cikin baki suke, kuma kaso mai yawa na bakin nan kwana sukeyi. Shisa bata san ko tana tsoron zama waje ita kadai ba ko akasin hakan. Haris ba wuni yakeyi ba, sai sa'a suke haduwa sau daya a rana, danma yanzun ya mayar dashi dabi'a yasa ta bashi shayi kullum, ranar da abokanshi suka zo, bayan ya rakasu ya dawo. Washegari kuma daya fita da yamma ya shigo gidan, tana kitchen ma dan tashi tayi tana marmarin tuwo amman ta dinga mirgina akan kafet din falonta sai bayan tayi sallar la'asar tukunna ta shiga kitchen din, taga harda shinkafar tuwo a cikin kayan gararta, sannan tana da busashiyar kubewa ma dasu kuka da aka zuba mata a wasu containers. Cikin nishadi take aikinta, tana kuma karanta Surah An Naml cikin Qira'ar Qaari Bilal Darbali, dan yana daga cikin mutanen da take matukar son karatunsu, musamman mashi, wata mp3 ce da Yayanta Ahmad ya bar mata, haka taje ta kafa masa naci saida yasan yanda ya samo mata karatun shi ya saka mata a mp3 din nan, ruwa ta subuce ta fada, har hawaye tayi lokacin saboda takaicin da taji. Duk yanda ake fada mata irin muryar da take da ita in tana karanta Al-Qur'ani bata taba yarda ba sai da Adda Maimuna tayi recording dinta batare data sani ba, ta wuni tana farin ciki, tana fatan ace wata rana ta samu damar recording muryarta, ta dinga kunnawa yara sunaji, kar girma ya kwace mata dadin muryar. Tun da ya shigo daga falon yaji muryarta, wani abu ya tsirga masa, in ba randa yaje masallaci ba, ba zaice ga ranar karshe daya kunna karatun Qur'ani ya saurara ba, koma shi ya bude ya karanta. Daya matsa kusa da kitchen din kuwa zai rantse har yanayin numfashin shi saida yaji ya canza, kafafuwanshi kamar rawa sukeyi, tsikar jikinshi sai tashi takeyi, anya akwai abinda ya taba saurara da yaji ya ratsa har ruhinshi? Ita kuma Maryama ji tayi kamar ana kallonta, saita juyo, ta ganshi tsaye "La tua voce e musica per le mia orecchie..." Ya furta da yaren Italian cikin wata murya kamar yana jin bacci, ta jishi, duk wata kalma da yanda ya lankwasa harshen shi wajen furtawa "Yare kayi ko? Wanne yare ne?" Kowanne irin yare ne yayi mata dadi, ko tace yanda yayi shi yayi mata dadi "Me kace?" Ta sake tambaya, sai yayi gajeran murmushi, shima maganar ce kawai yaji ta subuce masa, amman ta ina zai fassara mata? Ya za'ayi ya gaya mata haka yace muryarta tayi kama da kida mai dadi cikin kunnuwanshi? Ko sauti ne ma, ko waka zaice, kamar ba kowacce kalma bace inka fadeta da wani yare zaka iya fassarata da wani yaren kaji fassarar tayi dai-dai da abinda kake nufi "Me kikeyi?" Ta kankance idanuwanta akanshi "Ba zaka fadamun abinda kace ba ko?" Ya daga mata girarshi "To saboda me?" Ya kara gyara tsayuwar shi yana jingina bayanshi da kofar kitchen din sosai, yasa hannunshi a aljihu ya zaro wasu kudi, yan dari biyar-biyar ne, watakila dan ba sababbi bane shisa ta gansu masu yawan gaske "Ga kudinki" Ta zaro idanuwa, jiyan su Barde suka saka masa su a account, dubu dari ne cif, wai su duka ukun ne suka harhada a bata, shikuma daya fita yau saiya tsaya banki ya cirosu gabaki daya "Kudina? Ni? Yaushe?" Tayi masa tambayar a rikice "Su Lalaye ne suka baki" Kai take girgiza masa "Me yasa? Kudin ai sunyi yawa, Hajja ma sai ta iya mun duka idan ta sani...dan Allaah ka mayar musu da kudinsu kace nagode" Maganar ta bashi dariya "Wacece Hajja?" Ya tsinci kanshi da tambaya "Mamana" Ta amsa masa, ya girgiza kai kawai "Ya za'ayi ta dakeki? Ke da kina Kano ita tana Kaduna, yama za'ayi ta sani" Cike da tsoro Maryama take kallonshi "Hmm bakasan Hajja bane shisa...kuma ai dole zan fada mata idan aka bani abu" Baisan shekararta nawa ba, yana bata sha shida zuwa sha bakwai, amman da tayi magana sai yaji anya kuwa? Anya ta kai wannan shekarun? Saboda shi dai ba zaice yaga kuruciyar kowa ba, yasan Aise tana karama, amman ba zaice akwai rana daya da yaga tayi wani abu na yarinta ba, sai dai ma ta saka tunanin anya bata girmi shekarunta da aka fada maka ba. "Sai kice mata abokaina ne suka baki da suka zo, ba zatayi fada ba" Ta girgiza masa kai "Kinga ba zasuji dadi ba idan aka mayar musu" Da saurinta tace "To na bar maka, ka dauka" Shima ya girgiza mata nashi kan "Nima Mami zatayi mun fada ai, tace na karbe miki kudinki" Ita dai bata ga wanda zaisa ta karbi wannan tulin kudin da suke hannunshi ba "Ka ajiyemun zan dinga karba" Yayi murmushi "Ni zaki yiwa wayau? Ki karba ki ajiye a dakinki" Itama murmushin tayi "Da gaske zan dinga karba, ko yanzun ma bani dari biyar...sai ka ajiyemun sauran" Dariyar da yayi mai sauti ce "Me zaki siya da dari biyar?" Batare da tunanin komai ba tace masa "Flour" Ganin yanda yayi da fuska yasa ta dorawa da "Tayin cin-cin, meatpie zanyi" Dan dazun sukayi maganar meatpie din da Khairi, tace mata taje gidan Adda Zahra ta tayata aikinshi da yawa, sai itama tayi tunanin inda tana da flour din da tayi, saita saka a fridge, ta dinga soyawa in zata hada masa shayi ta dinga bashi, da wani abin ma, tunda ta kula abincinta ne bayaci, rannan da ta zuba masa jalof din shinkafa da tayi a dan karamin bowl, jin tayi mata dadi, saiya dauki kofin shayin yace mata "Na koshi, Nagode" Abinda Maryama bata sani ba, ba abincinta din bane bayason ci, abincin ne gabaki daya bai dameshi ba, in dai zai samu irin cin-cin din da ta bashi ko kuma wani abin dai banda abinci, zaifi masa "Ki rike kudinki, in dai flour ce zan kira Lalaye sai a kawo, suna siyarwa a shagon shi" Da fara'a a fuskarta tace "Dan Allaah? Yaushe za'a kawo?" Ya raba bayanshi da jikin kofar "Ko anjima ma idan na fita sai in taho miki da ita, flour kadai?" Tana son doya ma inda zata samu, da dankali, bataso yaga kamar bata da hankali ne "Bana so kaga kamar bani da hankali ne fa, tun rannan ina so ince ka siyo mun doya da dankali" Kallonta yayi sosai, kallo ne na rasa abin cewa, ita kuma saita fassara shi da kallon rashin hankalin kamar yanda tayi tunani "Ka dauka cikin kudin nan to" Saiya taka har inda take tsaye, yayi abinda yake ta masa yawo cikin kanshi tun jiya, ya kamo hannunta, ya jishi da sanyi a cikin nashi, dan ta gama aiki da ruwa ne, nama ma ta wanke, kuma naman na da kankara a jiki, ya kalli yatsunta, kamar yanda itama ta kalli hannun nata daya rike, zuciyarta na bugawa kamar zata fito waje, yasa dan yatsanshi daya yana taba jan lallen da yake farcenta kamar mai son dangwalo shi, a hankali kuma ya dumtsa hannun nata cikin nashi, kuma a wannan lokacin sai yaji bai taba rike hannun macen daya ga kamar an halitta mata nata hannun ne saboda yayi dai-dai rikewarshi. Gashi hannun nata yayi masa laushi ba kamar yanda yayi tsammani ba, ya bude yatsun nata yana murza yatsanta manuniya da yaga kamar yanka ne a jiki "Dame kikaji ciwo?" Yayi mata tambayar kamar baiji bugun zuciyarta ba, kamar kuma baiga yanda jikinta yake kyarma ba, sai ta ganshi babba a gabanta, taga yana da tsayi tun a ganinta na farko dashi, amman yanzun da yake tsaye a gabanta, sai taga ba tsayi kadai yake dashi ba, babbane, babba sosai, ta yanda ta tabbatar inda wani zai shigo kitchen din a wannan lokacin ba zaisan tana tsaye a gabanshi ba "Ya akayi kikaji ciwo?" Ya kara tambaya yana murza wajen, yana kuma murza wani abu a cikin kirjinta daya kara gudun zuciyarta "Da wuka..ina yanka albasa" Ta iya furtawa cikin rawar murya, daya kalli idanuwanta kuma, yau sai taga wannan ruwan da take gani cikin idanuwanshi kamar hawaye yau sun sauya launi, sunyi wata kala da bata da suna a iya hasashen Maryama, tana jin da zata jure, da batayi saurin sauke nata idanuwan ba, da zata iya ganin fuskarta a cikin wannan maiqon da idanuwanshi sukeyi, ya hadiye wani abu daya taso masa, sai kawai yasa kudin nan a cikin hannunta "Bari in dawo" Yace mata, kafin tayi wani yunkuri harya saki hannunta ya juya ya fice da sauri, yana barinta da nauyin kudin nan da kuma nauyin da dumin hannunshi ya bar mata, ta dafa kantar kitchen din tana jinta wata iri. Haris daya fita motar shi ya bude ya zauna, ya kwana biyu rabonshi da mace, yasan shine dalili, dalilin da yasa rike siririn hannun Maryama ya hautsina masa kai, in ba haka ba wannan 'yar yarinyar? To akan wanne dalili ma? Kuma daya ja motar tashi ya nufi kasuwar singa, har shagon su Lalaye, duk yanda Lalayen yayi na ya bada kudi a aiki daya daga cikin yaran shagon su siyo masa doya da dankalin kiyawa yayi, dole suka fita tare da Lalayen, ji yayi yana so ya siyo da kanshi. In yaga ta soya tana ci kamar zaiji dadi, Lalaye ne ya hana shi kwasar komai da yawa yace masa tunda su kadaine zai lalace, inya kare sai a kara siya, flour dinma da yace a bashi buhu daya sai da Lalaye ya kwashe da dariya "Wai kai Ganja me yasa baka da hankali ne? Ko kai zaka kwanta ta dinga barbadewa da filawar sai tayi kwari bata kare ba...". Saiya dibar masa, baima karbi kudin ba "Maza ka karya shagon" Cewar Haris, Lalaye yayi dariya kawai "Ya akeyi idan mutum zai yanka albasa idan ba'a so ya yanke hannu?" Haris din ya tambaya, dan har yanzun yanajin shatin yankan da yake yatsan Maryaman cikin kanshi "Bangane ba" Ya numfasa "Ta yanke hannu wajen yanka albasa, ba yanda akeyi kar a yanke?" Lalaye ya girgiza kanshi cikin alamar tunani, gidansu akwai mata sosai, kuma yasha shiga kitchen ya gansu suna aikace-aikacensu, amman shi kam ba zaice yasan yanda za'ayi a yanka albasa batare da an yanke hannu ba in tsautsayin yankan yazo "Ni kam ban sani bafa, in ba dai akwai wani abu da ake yanka albasa dashi ba" Da sauri Haris yace "Menene? Dame ake yankawa?" Lalayen ya zageshi "Wai ina zan sani ne Ganja? Ba saika karba ka dinga yanka mata ba, tunda daman ka auri wannan jinjirar ai raino ya ganka" Cikin bacin rai Haris yace "Wai dan uwarka Lalaye kare mata kallo kayi?" Aikuwa me Lalaye zaiyi banda dariya, yayi dariya ba kadan ba "Kwantar abokina, kai kasan ko mace kabi na hakura da ita, balle matarka, musulmin kallo ne wallahi" Yanda Haris ya bishi da ido kamar zai kai masa naushi yasa shi sake kwashewa da dariya "Bari in kira Raliya in tambayeta" Raliya, kanwarshi ita ta fada musu a siyi chopping board, kuma da sukaje wani shago da ake siyar da kayan kitchen sukace a basu, mai shagon ya tambaya guda nawa kuma wanne iri, sai Haris yace "Me kyau, wanda yafi kowanne kyau, guda shida" A tunanin shi idan daya ya lalace sai ta dauko wani, kuma guda shidan ya siya, saita saka masa uku na katako, ukun kuma na roba. Haka ya koma gida da tarin siyayyar nan, da yake Lalaye yasa shi har kwai ya siya mata, shima ya fara shigarwa yana bata. Tana ta binshi da kallon mamaki da wani abu da bashi da fassara a wajenta, sai gashi da wannan chopping boards din ya kwaso ya zube a gabanta "Abin yanka albasa, ki dinga yankawa akai karki sake yanke hannunki" Harya wuce ya shige dakinshi ta kasa cewa komai, ta kalli yatsan nata, ba wani yanka bane mai girma, dan jinin ma kadan ya zuba, tunda tayi wanke-wanke a shekaranjiyan ta tsoma shi a omo ta nemi zafin ta rasa. Batasan me yasa ba, sai taji kamar kuka na neman kwace mata... * Kuma tunda ya kawo doyar da dankalin, ta soya doyar da kwai, ta hada masa da shayi saiya girgiza mata kai "Banyi jagwalgwalo ba wallahi, saida na wanke har hannu na tukunna, dan Allaah kaci kaji" Maryama ta fadi tanajin babu dadi, har kayan kamshi ta saka a cikin kwan yanda taga Hajja nayi, duk yanda tattasai yakeyi mata zafi a hannu haka ta daure ta yayyanka ta watsa cikin kwan saboda yaga suyar tayi kyau yaci, yanda yayi mata kirki, itama tana so tayi masa kirki koya ne "Bana son doya, tana mun nauyi a ciki, bana son abinci masu nauyi, basa narke mun da wuri, cikina zai kumbura" Duk da Anisa ta taba ce masa "Ai injinan da ake markada maka abinci dasune duk sun dakushe, sunyi tatsa, saboda yanda baka son cin abinci, shisa baya narkewa da wuri kake kumburin ciki, in baka maida hankali ba nan gaba kai da su shinkafa sai dai ayi blending ka kurba" Ya dinga dariya kawai, in dai akan abinci ne duk wani da zai rabe shi haka zaiyi fama ya gaji ya kyaleshi "Ba dan kinyi jagwalgwalo bane ba zanci ba" Taji sanyi kuwa, data soya dankali ma ta hada masa harda kwai, haka ya fito mata da plate din ya cinye dankalin tas, amman kwan bata ga alamar ya taba shi bama. Da ta gane yana son dankalin, sai ta soya masa, meatpie din da tayi kuwa, hudu ta saka masa, amman rabi yaci, ita mamaki yake bata, yanda tasan mazan gidansu da kafirin ci, haka akeyin rawun ana kara abinci, randa akayi rana ba'a gama abinci da wuri ba kuwa duk wani dan cin-cin da biredi da yake gidan sai sunga bayanshi. Idan lissafi bai bacewa Maryama ba, to kwanansu talatin harda biyar da aure, kuma a ranar ne Haris din ya sameta zaune kan kafet, ta jingina bayanta da gadon doguwar kujera, da remote a gefenta tana kallo, sai wani filet da ta zuba shinkafa da miya tana ci, sai kamshi abincin yakeyi, kuma daya tashi saiya zauna a gefenta shima yana sakata kusan shakewa da shinkafar da take bakinta, tunda ya zauna gab da itane har kafadarshi na gugar jikinta, a kwanaki talatin da biyar din nan ya shiga Kaduna sau hudu, sai dai bai kwana ba "Ba zan daina zuwa in ganki ba Mami, amman ba zan saketa ba kamar yanda na fada miki, sannan in dai zanzo ki sake tayar mun da maganar nan kona zauna zan tafi abuna..." Haka ya cewa Hajiya Rumana a zuwanshi na karshe ko zata hakura ta daina yi masa wannan maganar, ko zai samu ya kawo karshen wannan tashin hankalin nata akan aurenshi da Maryama, shi yanda ta daga hankalinta ma sai da ya dinga tunanin ko yarinyar na da wani nakasu ne, sai ya ganta lafiya kalau, banda shirme da yarinta baiga wani abu a tare da ita ba, kuma har kasan ranshi yanajin babu wani abu da zaisa ya saketa, tunda ya iya jure rashin Aise, yake kan jurewa saboda auren, me kuma ya rage masa da ba zai jure ba. Daman sallama zaiyi mata saboda tafiyar da zaiyi Syria, amman saita waya yayi mata sallamar tanata bambamin fada, baice komai ba ya kashe wayarshi, ya gama shirya komai, washegari da yamma zai wuce, shisa yake so ya fadawa Maryaman, sati biyu zasuyi "Wai bakya gajiya da kallon Indian?" Ya tambayeta a maimakon amsar gaisuwar da tayi masa "Yana da dadine, wannan tun ina gida ma muke kallonshi" Ya jinjina kai "Bai kare ba kuma?" Ta danyi dabarar gyara zamanta dan ta matsa daga jikinshi, dan ji tayi kamar yana fitar da tiriri, dumin shi na ratsata har cikin ciki, kuma zuciyarta taki daina bugawa "Ai yana da yawa sosai, ance ma ko rabi ba'ayi ba..." Shikuwa ina zai iya wannan kokarin "Tafiya zanyi daman, gobe" Da saurinta ta kalle shi "Tafiya? Ina zakaje?" Ta karasa maganar tana ajiye cokalin da yake hannunta "Syria" Ta maimaita Syria cikin kanta babu adadi, kamar maison gano yankin da Syria din take "Ba dadewa zanyi ba, sati biyu zanyi In Shaa Allaah, amman zan iya biyawa wani wajen, ban dai sani ba, kaman dai ba zan wuce sati hudu ba" Abinda taji ya taso mata sai yayi mata tsaye cikin makoshi, sati hudu? Ita kadai zata dinga kwana kenan? "Nikuma fa?" Ta tambayeshi muryarta na fitowa a karye kamar mai shirin fashewa da kuka, shine tunanin da Haris baiyi ba, ita din, saboda tunanin nashi ya tsayane zata zauna anan, tunda ma inya yawata da tunanin nashi ai babu yanda za'ayi ya dauketa, shima da yaya aka sama masa clearance din tafiyar? "Ni kadai zan zauna?" Cewar Maryama idanuwanta cike taf da hawayen da Haris yaga kyallinsu tar ta cikin hasken dakin, raunin mace na daya daga cikin abu na farko a jerin abubuwan da yake so a tare da mata, in suna tare dashi yana son ganin rauninsu, yana son ganin wannan fragility din da suke tattare dashi, yanayi ne da yake tabashi har zuciya, shisa kukansu ma burgeshi yakeyi, kyau yake ganin sun kara yi masa, yana so yaga fuskar Aise in ta gama kuka, yaga gashin idanuwanta jiqe da hawaye, mascara din da baka raba fuskarta dashi ta sauko kasan idanuwanta da kuma gefe tanayi masa kama da panda, yana so yaji yanda jikinta ke amsawa da kukanta a lokacin da ya riketa a nashi jikin, yana so ya goge mata fuskarta yanajin sanyin hawayenta. Amman yau, a karo na farko a rayuwarshi yaji bayason hawayen dake cike da idanuwan Maryama su zubo Yau bayason ganin hawayen mace... 20 Haka tace masa "Ka maidani Kaduna, ka kaini gidanmu inka dawo sai kaje ka daukeni mu taho nan" Daya kalleta, yaga hawayen da take ta sharewa saiya girgiza kai, yarintarta ta kara fitowa, sai yaji babu wani abu da yake so irin yasan tana cikin gidan nan nashi, sai ya girgiza mata kai "Ba zaki koma Kaduna ba" Ta sake share hawayen daya zubo mata, hawayen da yakeji har cikin ranshi "Ni kadai zan zauna? Dan Allaah karka barni ni kadai" Ya sauke numfashi "Akwai wanda zai iya zuwa ya zauna dake?" Khairi ta fara fado mata a rai, sai dai tasan da wahalar gaske Abbansu ya yarda da wannan lamarin, ba zata manta lokacin da Adda Zahra ta samu cikinta na farko ba, ta dinga fama da wani irin laulayi mai tsanani, ita da mijin sukazo suka roki Abban akan ya bari wani a cikinsu ya koma a dinga tayata zama da aikace-aikace, sai yace musu a nema mata 'yar aiki, ko cikin danginshi wani yaje ya zauna tare da ita, babu yanda ba'ayi ba amman yaki amincewa, da Hajja tayi masa magana sai yace "Bani da natsuwar irin wannan gwamutsin zaman, inda matar su Khalifa ce, sai su tafi hankalina a kwance, ai akwai mata a gidansu, ya daukar mata guda daya" Sai mai aikin aka samar mata kuwa "Adda Khairi ce, kuma Abba ba zai bari ba" Haris ya jinjina mata kai "In dai Abba ne zan hadashi da Baba, zai barta tazo idan yayi masa magana...ki daina kukan nan, bana so" Ta daga masa kai tana jan hanci, ita dai ko mai aikin ce a samo mata, dan ba zata zauna gidan nan ita kadai ba, idan Abban bai bar Khairi tazo ba, in ya tafi akayi ruwan sama fa? Ya zatayi? Dan tama manta ba lokacin damuna bane ba. Data mike sai yace mata "Ina zakije?" Ta sake jan hanci "Fuskata zan wanke in kwanta" Kai kawai Haris ya jinjina, yana kallo ta shiga dakinta, sai lokacin ya kula ko rabin abincinta bataci ba, ya dauke plate din, ya kashe kayan kallon, ya kai kitchen, da yake su can in anyi sauran abinci ba almajiri suke dashi ba, a shara kawai ake zubawa, haka ya juye a shara, ya wanke plate din ya kife shi inda yaga wasu irin shi, sannan ya wuce dakin nashi yana kiran Alhaji Mustafa, da yake sunyi waya ma da yamma, bugu biyu ya daga, suka kara gaisawa "Baba daman tafiyar da zanyi ne, bana so in barta ita kadai, nace ko zakayiwa Abba magana, tace akwai 'yar uwarta Khairi sai tazo su zauna kafin in dawo" Daga yanayin yanda Alhaji Mustafa ya amsa yasan yaji dadine, kafin ya kashe wayar kuwa saida yace "Allaah Yayi maka albarka Haris" Haka ya kwanta kalmomin na zagayawa cikin kanshi suna sanyaya masa zuciya har bacci ya dauke shi. Da safen kuwa Alhaji Mustafa ya sake kiranshi ya gaya masa Khairin zata zo, za'a kawota, daya samu Maryama a kitchen ya gaya mata sai tayi masa murmushi tana dorawa da "Nagode. Karfe nawa zaka tafi?" Ya duba wayarshi, lokacin takwas da rabi ne "Karfe tara da dan wani abu" Lalaye ya kira dan ya kaishi filin jirgi, tunda anan gida zai bar motarshi "Zan bar miki mukullin motata, idan Adda Khairin tazo sai ki bata ko da kina son wani abin saita fita ta siyo miki, ke dai karkije ko ina kina jina? In ba rashin lafiya ba, karki fita ko ina" Ta daga masa kai dariya na kwace mata da jin wai zai bar mata mukullin mota dan Khairi tayi amfani da ita "Ai bata iya ba... motar, bata iya tuki ba" Ya dan nuna alamar mamaki a fuskarshi, shi ba zai tuna ma tun yana da shekara nawa ya fara koyon tuki, ya kuma fara daukar mota yana fita ba, haka ma sauran 'yan gidansu duka, har matan, ko yaran Umma Fadime ma yana ganin suna fita da mota, to idan yaran Alhaji Mustafa ma basu iya tuki ba ai sai a diga musu ayar tambaya, tunda dai mota ba matsala bace a wajensu. Kusan ko yaushe ma cikin sake motocin gidan ake, dan kamar Alhaji Mustafa baya gajiya da hawan kalolin motoci, ba kuma ya gajiya da son ganin suma ya sabunta musu. "To sai ki fadamun idan kina son wani abin kawai" Wannan dai ba zaiyi wahala ba, ta daga masa kai batare dama tayi tunanin basu da lambar juna ba, haka shima Haris din "Ana tafiya da abinci ne? In dafa maka wani abin? Zaka iya jin yunwa kafin ka sauka, awa nawa ne?" Ya girgiza mata kai "Ki dai hadamun tea in sha kafin in fitan, awa biyar ne da wani abu" Yayi wanka, kayan jikinshi kawai zai canza, anan kitchen din yayi tsaye yana kallonta harta dafa shayin, ta hada masa yace ta kara, sai da kofin ya kusan cika, ta mika masa kofin da cokalin a ciki, ya sake juyawa ya kurba, sai yaji zakin yayi masa kadan "Saikin kara mun sugar kadan..baiji ba, kinji" Yayi maganar yana dibo shayin a cokali ya hura da bakinshi ya mika mata saitin nata bakin, saita kurba kadan batare da ta gane komai ba, kuma sauran daya dan rage a cokalin sai kawai Haris ya karasa shanye shi kafin ya saka cokalin cikin kofin ya mika mata, inda ya kalleta sosai watakila daya ga yanda bugun zuciyarta yake kada sauran gangar jikinta, ko ita kadaice takejin hakan na faruwa? Sikarin ta dan kara masa ta mika masa, ya karba, daya kurba saiya daga mata kai alamar yayi, ya fice daga kitchen din ya koma falo ya zauna yana kurba a hankali, ya bar Maryama tsaye da yanayoyi mabanbanta, ta fi mintina biyar cikin kitchen din kamar ta manta abinda zatayi, dankaline ta dan dibo zata fere ta soya, amman kuma cikinta ya cika taf da wani abu da batasan menene ba, ta tabbata ko ta soya bata da wajen zuba shi yanzun, gashi tafi son dankalin turawa daga kasko sai faranti, sai cikinta, ta tsani ya huce, ta kuma tsani a saka shi a cikin kula, zufa ya koma masa. Shisa ta fito daga kitchen din, lokacin Haris harya kusan shanye shayin shi, ta samu waje daga can nesa da kujerar da yake ta zauna. Tana danna wayarta, harya karasa ya tashi, tana nan zaunen ya shiga dakinshi ya fito da jakunkuna guda biyu, daya na da girma dan nan ya zuba duka cameras dinshi da ma abinda zai bukata na aikin. Karamar itace take dauke da kayan sakawarshi, ya canza kayan daya saka dazun, in ba kula kayi ba sai ka dauka kaya daya Haris yake dashi, sai kasa ido ne zaka dinga bambance da yawa daga cikin bakaken wandunan shi, dazun jeans ne, yanzun kuma ba jeans bane ba, wani wandone mai laushi, sannan a karo na farko yau ta ganshi da riga ruwan toka, duk da mai duhu ce kalar, ta kalli fuskarshi, rigar dai bata haska shi kamar yanda take hasashe cikin kanta zai faru inya saka wasu kalar kayan banda bakake, bakin shi yana nan, sai taga wani lokacin na kamar kara baki yakeyi, kila kuma idanuwanta ne, maikon fuskar shi ya hadu dana idanuwanshi yayi mata wani iri yau, ita in kayi fari to kafi rabin kyau a wajenta. Bakaken harda danginta dama wasu a gidansu ba kare musu kallo takeyi ba balle taga wani kyau da suke dashi ko muni, in ba wani bane yace mata wane na da kyau a cikinsu, shine in ta koma gida ranar zata tai kallo tana neman wannan kyan, kamar abinda takeyi yanzun akan Haris, a idanuwanta matashin saurayine, dogo, bakikirin, shikenan, babu ragi babu kari, tasan da zai matso kusa da ita zataji kamshin turarenshi mai sanyi. Babu yanda za'ayi kaji turaren Haris in ba yazo gab da kai ba, kamar daga kayan shi har turaren yana amfani dasune wajen ragewa kanshi attention din mutane, har wanda yake tare dasu. Ya ajiye komai, ya taka zuwa inda take zaune, sai lokacin ma taga ba dogon hannu kadai rigar jikinshi take da ita ba, harda hula a hade. Mukulli ne ya bata guda daya, a jikin wata key-holder mai kyau "Akwai kudi a cikin drawer din gefen gadona...kome kike bukata ki dauka a ciki, ko nawa ne..." Ta jinjina masa kai, saboda wani abu da yayi mata tsaye a makoshi, ita bataso taga wanda ta sani zai tafi wani wajen, ta tsani bankwana, shisa zai wahala kaga anyi rakiya da ita, ko da kofar gidane kuwa. Ko wata Umrah dasu Hajja suka tafi bata bisu airport ba, batama fito daga dakinsu ba, babu wanda ya matsa mata tunda sun san halinta, kafin ma tace wani abu su duka sunji hon din da ake dannawa da alama a kofar gidan ne, Haris yasan Lalaye ne, ba zai shigo da motar ba, sai dai shi ya fita ya same shi, wayarshi da tayi kara ya ciro daga aljihu ya daga da fadin "Gani nan fitowa" Ya sauke yana kallon Maryama data sadda kanta kasa "Zan tafi" Ta sake jinjina kai, cikin karamar murya tace masa "Allaah Ya tsare Ya bada sa'a, Allaah Yasa maka albarka a abinda zakaje yi Ya dawo da kai lafiya" Addu'ar tayi masa dadi matuka, sai kawai ya taka ya kama hannunta ya dagota, kafin tayi wani yunkuri ya rungumeta a jikinshi, ya sumbaci saman kanta "Amin thumma amin, Nagode. Ki kula da kanki sosai, karkije ko ina kinaji?" Kai ta daga masa, duminshi da kamshin shi nayi mata rumfa, daya saketa sai taji wani irin sanyi ya tsirga mata, tana kallonshi ya juya ya dauki jakunkunan shi, ya fice daga gidan, ta koma ta zauna tana goge hawayen daya zubo mata. Kan one sitter din taja jikinta ta kwanta da mukullin nan rike a hannunta, sai wani abu yace mata ta tashi ta shiga dakin Haris din yau taga ya yake. Da saurinta ta mike, harda hadawa da gudu, taje ta bude dakin. Ta shiga da sallama a bakinta, sai taji dariya na kwace mata, zanin gadon da yake shimfide akan gadonshi bakine, sai duvet dinma daya linke ya ajiye a gefe, filallika ne a saman gadon sun kusan guda takwas a iya ganinta tunda ba kirgawa tayi ba, sune ma rigar jiki wasu bakake, wasu kuma ruwan toka, har karamin kafet din da yake gefen gadonshi baki ne. Dakin qal-qal, dan ko nata bai kaishi kimtsuwa ba, babu wani abu a wani waje da bai dace ba, ga kamshin shi nan mai sanyi a cikin dakin da saika natsu zakaji shi, kawai saita karasa cikin dakin, kafet din nashi mai laushine sosai, ta dauko pillow daya ta sauke a kasan ta kwanta. Ta rufe idanuwanta, kuma bata jima ba bacci ya dauketa. Bacci tayi sosai, baccin da bata samu tayi sosai ba da daddare saboda tanata sakawa da warwarewa akan tafiyar Haris din da yanda zatayi idan Abba bai bar Khairi ba. Ringing din wayarta ne abinda ya tasheta daga baccin da takeyi "Bacci ma kikeyi? Ni ki dafamun wani abu gamu nan mun kusan karasowa cikin Kano, yunwa nakeji ban karya ba na fito" Cewar Khairi bayan ta daga wayar, da saurinta ta mike "Me kike so? Zakici dankali? Ko indomie? Ko in soya miki doya?" Dan ji tayi ta wartsake gabaki daya, sai yanzun murnar zuwan Khairin ma ta dirar mata "Ni dai koma me" Tana sauke wayar ta mike, ta dauki pillow din ta mayar masa kan gadon, saida ta kulle dakin da mukullin taje ta ajiye shi a nata dakin, ta wanke fuskarta sannan ta koma kitchen din, cefane ta gyara, tasan Khairin nason stir fry indomie, sai ta soya dankalin, tasan direba ne ya kawo Khairin, shima sai ta zuba masa, shisa ma ta saka da yawa, ta fara aikinta cikin nishadi, burner din gas biyu ta kunna dan aikin yayi mata sauri, ashe ma su Khairin na gab, dan ba'a rufa mintina talatin ba taji sallamarta, da gudu ta fita daga kitchen din suka rungume juna suna tsalle-tsalle kamar yara "Wallahi nayi kewarku, kowa da kowa a gida" Cewar Maryama, tana jan akwatin Khairin ta kaishi dakinta, ta dawo tana ce mata "Bari in duba kar abincina ya kone, sai inzo in shigar miki da jakar" Hijabinta Khairi ta cire, sai suka nufi kitchen din tare, suka karasa komai sunata hirar har kowa na rasa abinda zai ba dan uwanshi labari, saika rantse basa waya har katikansu ya kare, da aka zubawa direban, Khairi ta daukar masa ruwa da lemo ta fita ta kai masa, sukayi sallama dan juyawa zaiyi. Ta dawo ta zauna suka ci nasu ita da Maryaman sunata hira. A ranar kuma ta fahimci akwai wani a rayuwar Khairin, saboda tana yawan daukar wayarta ta danna, sai tayi murmushi ta ajiye "Waye baki bani labarinshi ba?" Murmushin kawai tayi mata batare da tace komai ba, aikenta ma Hajja tayi gidan Adda Maimunatu, daga can ta fita tayi mata cefane sai ta hadu dashi, ba yaro bane ba a idon Khairi da take da sauran 'yan watanni ta rufa shekara goma sha takwas, dan a hasashenta zaiyi shekara talatin da biyu, yace mata yana da mata da yaro daya, sai kuma cikin na biyu. Ma'aikaci ne shi yace mata a FIRS yake aiki, sunanshi Ibrahim Bakori, dan asalin garin Katsina, ita ko kadan babu wani maganar aure a ranta, tana so tayi karatu ne, shima ta gaya masa yace mata "Matata ni na mayar da ita makaranta, yanzun haka tana aji uku a Bayero, inta gama degree dinta kuma zatayi Master's In Shaa Allaah...bani da matsala da karatunki, sai kince mun kingaji da kanki tukunna" Ita ba zatace ma ga abinda takeji akan Ibrahim din ba, bata da dogon buri akan namiji, wanda duk ta samu in zasu zauna lafiya ya mutuntata da iyayenta bata da wani abu da take nema bayan wannan. Duka satinsu biyu kenan da haduwa, ta bashi lambar Yaya Ahmad, dan yaje yayi masa jagora wajen Abba saiya fara zuwa, akwai kasuwancin da yace mata yake shigo dashi Kaduna duk wata daya zuwa biyu, tunda iyalinshi suna Kano, haka iyaye da 'yan uwa. Wannan ne abinda yafi komai jan hankalinta harta ji ta amince ta fara kula shi su fahimci juna, a Kano yake, idan da rabon ya aureta a Kano zai ajiyeta, kusa da 'yar uwata, kusa da Maryama. "Ba zaki bani labari ba" Ta karayin dariya "Sunan shi Ibrahim, kuma baiyi magana da Abba ba shisa ban baki labari ba, babu wani labari a yanzun har sai Abba ya amince" Duk da haka saida Maryama ta kafa mata naci wai sai taga hotonshi "Allaah Ya duba miki, Allaah Yasa ki aure shi, kinga da hasken shi, ba kamarni ba" Khairi ta kwashe da dariya "Wallahi kina da matsala Maryama, to wai uwarme hasken zaiyi miki? Saiki samawa Haris din man bleaching ai" Maryama tayi shiru tana hasaso ta inda zai fara shafa man bleaching, dariya ta kubce mata, irin bakinsu ne mai wahalar sha'ani in ance za'a shafa masa mai, dan tana ganin 'yan bleaching din, sai yayi musu dabbare-dabbare "Wa yaga Ganja yayi dabbare-dabbare" Khairi ta kalleta "Bana ce ki kiyayi kanki karkice masa Ganjan nan ba?" Tayi dariya "To ai yanzun baya nan" Dan ranar da taji an kirashi da sunan, saida ta kasa hakuri da daddare take ba Khairi labari, suka dinga dariya tare "Ganjaa fa,anya kinji dai-dai kuwa? Wanne irin suna ne wannan" Ta rantse ta maya haka taji ance, kuma sau nawa tun ranar take tauna harshenta in ta kusan subutar baki ta kirashi da Ganjan. Ba karamin dadi zuwan Khairi yayi mata ba, dan a washegari ne take ce mata ta kira Haris taji koya sauka lafiya, sai taji wani abu ya fado daga kirjinta zuwa cikinta "Bamu da lambar juna ai" Khairi tayi mata wani kallo "Mantawa nayi bance ya bani ba" Ta kara fada cikin rashin jin dadi da tunanin ko ya sauka, ko me yakeyi yanzun? Ko ya hada shayi? In bai hada ba ya fita ya siya? "Inama kikace mun yaje?" Da sauri ta amsa, Khairi tayi jim "Anya ba Syria bace aketa yakin nan da Abba yake kallo a BBC?" Maryama ta girgiza kai, saboda yanda taji daga zuciyarta har gangar jikinta basu aminta da karbar Haris na wata kasa da ake yaki ba, akan me to? Me zaije yayi acan din shida ba soja ba? Sai kuma ta tuna in wuka za'a saka a yankata a tambayeta aikin da yake sai dai a cire har kan, dan batasani ba, batasan aikin da yakeyi ba, babu wanda taji ya fada, kuma ita bata tambaye shi ba, idan kuma sojan ne bata sani bafa? Shisa yake ta fama da bakaken kaya "Can ne fa Maryama, wallahi can ne ake yaki" Khairi ta fadi dan ta dubane a wayarta ta gani, sukayi shiru na wani lokaci "In Shaa Allaah babu abinda zai faru, ya sauka lafiya, kuma zai dawo lafiya" Batayi magana ba, batace komai ba, jikinta abu daya ya bata Haris ya sauka lafiya, Zai kuma dawo mata, kawai dai batasan zai bar wani kaso na rayuwarshi a kasar Syria ba... 21 Khairi na wanka lokacin da aka kwankwasa kofa, ita kadaice a falon tana kallo, sai ta tashi kawai, ta murza mukullin kafin ta bude kofar, idanuwanta suka sauka kan bakar leather jacket dinshi da bai zage zif din ba, dan haka tana ganin t-shirt din ciki da itama bakace, da saurin gaske ta daga kanta tana kallon fuskarshi "Ba dadewa zanyi ba, sati biyu zanyi In Shaa Allaah, amman zan iya biyawa wani wajen, ban dai sani ba, kaman dai ba zan wuce sati hudu ba" Haka yace mata, kuma abinda ta dinga juya kenan cikin kanta babu dare babu rana, musamman da daddare da take tsintar kanta da kirga kwanakin da yatsunta, addu'ar da tayi ta bacci tana zame mata abu na biyu da takanyi kafin baccin ya dauketa, sati hudu, ba zai wuce sati hudu ba yace, kuma data lissafa bakwai sau hudun nan kwanaki ashirin da takwas ne a ciki, yau kwanan Haris hamsin da tafiya, karyar da Khairi tace mata tayi na fadin "An kara musu lokacin aikin ne" In 'yan gidansu sun tambaya, ita ta dinga maimaitawa kamar mai son ita ta yarda da karyar fiye dasu Abban ma "To in dai bai dawo satin nan ba sai a samo miki wata da zata zauna dake dan su Khairi har an fara registration a makaranta" Abban yace musu a jiya da sukayi magana, haka a jiyan Khairi ta sakata a gaba da zancen Haris na dawowa tayi masa maganar makarantarta, karta yadda ta zauna haka, ko kwalin sakandiri bata dashi, ta dinga amsawa da "In Shaa Allaah" Amman makarantar ce karshen abinda yake cikin kanta, ya dai dawo, ta ganshi, ta ga yana lafiya, babu abinda ya same shi. Tunda kara dagawa kanta hankali ta dingayi ta hanyar kaiwa labaran BBC tayi kur tana jiran ayi magana akan abinda yake faruwa a Syria, itace har tashar Al-Jazeera. Ranar da aka hasko din kuwa, wani babban gini ne aka jefawa bomb ya rushe, ance makaranta ce, dan ginin zaiyi hawa goma ko takwas, masu bada taimakon gaggawa da yan kwana-kwana nata aikinsu, ana daga fasassun ginin nan ana zaqulo gawarwakin yara da manya a kasan shi, wasu kuma masu rai, ita kadaice a dakin lokacin, Khairi taje gidansu, hawaye kawai take sharewa wasu na sake zubowa. Da an daga ginin nan ana kokarin zaqulo mutum daga kasanshi sai taji zuciyarta tayi wata irin tsinkewa, har daga kai takeyi tanajin kamar ta shiga ta cikin tv din ta tayasu, kuma a tarin mutanen da suke wajen nan haka ta dinga baza ido, karshe da taga wani ya gifta da bakin wando a jikinshi sai gata a gaban tv din tana lekawa ta gefe ko zai dawo, ko Haris ne, da ita aka dinga daga ginin nan, ita da masu taimakon kowa da abinda yake nema har aka dauke labaran aka fada wani, ko abinci kasaci tayi don tashin hankali, Khairi ta dinga yi mata fada "To ke waye ma yace miki bangaren da ake yakin yaje?" Sai ta dinga gayawa kanta ba nan Haris yaje ba, wani aikin ne daban ya kaishi, wani sashi na Syria inda hatsaniyar bata kai musu ba, watakila ma ya bar kasar ya wuce wata kamar yanda ya gaya mata. Amman meya tsayar dashi? Me yasa ya dade haka? Bata da mai amsa mata wadannan tambayoyin, sai Haris din da yake tsaye a gabanta yanzun, Haris din da a kallon farko ta ga ya kara yin baki a idanuwanta, sannan ya rame, duka fuskarshi ta rame, da ta saka idanuwanta cikin nashi kuwa sai taji kafafuwanta na rawa, sai taji irin yanayin nan da takanji duk lokacin da take kallo a tv aka hasko teku, ta hasasota a gefen tekun nan, kuma watakila da bata sauke idanuwanta daga cikin na Haris ba da ta gane me bature yake kira da drowning, data nutse a cikin abinda take gani a idanuwan nashi. Sauran jikinshi take kallo batare da tasan abinda take nema ba, da jaka a goye a bayanshi, jakar nan tashi daya tafi da ita, sai dayar daya rike a hannunshi, dayan hannun nashi irin Stanley cup din nan ne "Sono così stanco..." Ya fadi cikin wata murya, kafin ya dan runtsa idanuwanshi ya bude su a hankali yace "Nagaji sosai Maryama, nagaji...kin tare mun hanya" Sai lokacin ta tuna tana tsaye ne a bakin kofa, ta kuma kasa ce masa komai, ta dai matsa. Ya shigo yana rabata ya wuce. Da yake kullum sai ta share masa dakinshi, ita ta cire babban abin rufar da taimakon Khairi suka ninke shi suka saka a wardrobe dinshi dan kar yayi kura "Wai shi komai nashi baki ne? Sai kace jemage" Khairin ta fada ranar, ganin kayan da suke cikin wardrobe din, kuma yau kwana hudu da sukai wanki ta shiga ta cire zanin gadonshi, da rigunan filallikan aka wanke su tas a injin wanki, da suka bushe saita ninke su suma, ta koma dakinta ta dauki wardrobe balls din da take dasu, taji suna da kamshi, kuma kamshine mai sanyi irin wanda takeji a dakin Haris din, tana fatan ba zai dame shi ba, duk ta jefa masa a cikin kayanshi, harda zanin gado. Yau taso tabi Khairi gidansu, gargadin Haris ne ya zaunar da ita, shi yace in ba rashin lafiya ba kar taje ko ina, duk da Mummy din tazo gidan sau biyu tana dubasu. Macece mai kokari da son kyautatawa duk wanda yake tare da ita. Haka tazo da poly bag dinta cike dasu busashen kifi, cryfish, da duk wani abu da take tunanin Maryaman zata iya rasawa harda busashen zogale mai yawa da dakakken quli, dawowa ta biyu ma saida ta siyo mata kayan ganye, danginsu lettuce, kabeji harda su karas ta taho mata dashi, itama Maryaman cikin kudin da aka bata ta kirgi dubu goman ta bawa Mummy, dakyar ta karba, tana godiya da addu'o'i, to fitar Khairin ne taji kadaici ya dameta, da yake da safen duk maimaicin episodes din jiya da suke kalla akeyi, saita shiga dakin Haris din ta gyara masa gadon, ta shimfida zanin gado, ta kara share dakin duk da babu wata kura da yayi, rashin abinyi ne da tunanin halin da yake ciki da yake ta nukurkusarta, har turaren wutar da sukayiwa gidan sai da takai dakinshi, ta saka har bayi, daga baya ta koma ta dauko kaskon ta rufo kofar. Kuma wuni takeyi da mukullin dakin nashi a hannunta tana wasa dashi, rannan da ta fito daga bayi da mukullin a hannunta, Khairi ta gani ta jinjina kai "Kin manta kina da tsautsayin mukulli ko? Bari ki batar masa ya dawo ya niqaki" Ta dinga dariya, kuma bata ajiye ba, ko yanzun da taga ya nufi hanyar dakin nashi, da saurinta ta karasa cikin falo ta dauki mukullin da yake ajiye a kasa, kan kafet inda take zaune ta samu Haris din tana mika masa "Ga mukullin dakin..." Ya karba, tayi tsaye har saida taga ya bude, sai dai daya shiga, kofin hannunshi ya fara ajiyewa ya juyo ya zare mukullin batare daya kalleta ba, ya kuma rufe kofar, tana jinshi ya saka mukullin daga ciki. Ta danyi tsaye jim, sannan ta juya, saita wuce nata dakin inda ta samu Khairi a zaune gefen gado, tasa kaya, tana murza mai a jikinta. "Ya dawo, yanzun ya dawo" Ta fadi da farin cikin da zaka iya ganin kyallin shi cikin idanuwanta "Wa?" Khairi ta tambaya dan bata kawowa ranta Haris ba "Haris din, yanzun ya dawo" Kai Khairi ta jinjina "Na fada miki ki daina gatsa sunanshi haka, ke baya miki nauyin fada a baki?" Itafa a rayuwarta shine mutum na farko daya girmeta kuma taji tana kiran sunanshi duk nauyin da yakeyi mata "Ko Yaya ne ba zaki kara masa dashi ba" Tayi dariya mai sauti "Haka kawai? Mijina ne fa, sai in kama ce masa Yaya ana zaune lafiya" Ita abin baya burgeta, ko dan tana da Yayye da yawa ne? Khairi ta sauke numfashi kawai "To kuma surutun me kika tsaya kinayi anan? Ba zakije ki same shi ko ruwa ki kai masa ba?" Akan kunnenta ya murzawa dakinshi mukulli "Yafa murza mukulli a dakin daya shiga, kuma ni banma taba kai masa ruwa ba" Khairi saita rasa amfanin da karatu da kuma kallon Maryama yakeyi mata, tunda anayi ne dan a karu, ko babu komai zaka tsinci abu daya zuwa biyu dangane da zamantakewa, musamman ta aure. Marubuta na wannan kokarin cikin hikima "Tam saiki samu waje ki zauna ko ki koma ki cigaba da kallonki, dan ni idan na karasa shafa mai na kayana zan harhada, in kira Abba in gaya masa dan ya aiko gobe idan Allaah Ya kaimu azo a daukeni" So tayi taima Khairin magiya akan ta kara wasu 'yan kwanaki, amman tasan abinda yake gabanta, kuma saita zauna a gefen gadon har Khairi ta karasa shiryawarta "Ke me yasa baki da hankaline baki san ayi miki gatse ba, ki tashi kije wajen mijinki kafin in kira Adda Zahra in fada mata shirmen da kikeyi bayan duk naji nasihar data dinga miki tunda aka daura auren" Mikewa Maryama tayi tana ficewa daga dakin, kuma maimakon ta nufi kitchen sai tayi dakin Haris ta tsaya ta kwankwasa sau biyu, tafi mintina hudu, kamar ba zai bude ba, sai gashi ya taso, ya rage kayan jikinshi, dan yanzun din gajeran wando ne sai riga baka, sannan idanuwanshi sun sauya launi, bawai ja kawai sukayi ba, launin jan wani irine da bata taba gani ba, sannan tana jin wani irin kauri da ta rasa daga dakin nashi ne yake fitowa ko daga jikinshi "Ruwa daman, nace zaka sha ruwa? Ko tea? Ko abinci?" Kanshi kawai ya girgiza mata, ya mayar da kofar ya rufe, taji ta kasa juyawa ta tafi, akwai wani abu a tare da Haris din daya sauya, ba haka ya tafi ba, saida taji kafafuwanta sun fara mata barazana sannan taja su, sai dai falo ta koma ta zauna akan kujera batare da tasan takaimaiman abinda take tunani ba. Sunyi abincinsu ne tazarce, kudin da Haris ya bar mata data ga yawansu saida taji tsoro, bata ma taba yafi dubu biyar ba, duk abinda zasu siya cikin kudin hannunta ne sukeyi, Khairi taje musu kasuwa ta karo musu doya da kuma irish, harda dankalin hausa data gani, cikin kudin Haris dinne ta bayar aka siyo madara da kuma Milo, kar yazo ya duba yace bataji maganarshi tayi amfani da kudin ba. "Ki tashi ki samu wani abin ki dafa masa" Cikin sanyin jiki ta cewa Khairi "Bafa zaici ba, abubuwan da naga yana ci basu da yawa..." Lokacin da Khairin tayi mata magana ma takwas saura "Allaah Ya kyauta muku to" Shine abinda ta iya furtawa, saima ta shige daki da wayarta tayi kara, itama Maryaman taji tana son sake komawa ta tambayi Haris ko zata hada masa shayi, wannan karin bai bude kofar ba, cikin wata irin murya kamar wanda ya tashi daga bacci ya tambayeta menene, kuma ta hakan yace mata ba zai sha ba "To dan Allaah ka fito ku gaisa da Adda Khairi, gobe idan Allaah Ya kaimu Abba zai aiko a dauketa...ko ba yanzun ba, zuwa safen kafin ta tafi, dan Allaah, kaji" Saida ya amsa da "Ok" Sannan ta tafi, zuciyarta nayi mata babu dadi. Da tunani iri-iri ta kwanta. Ta dai ware dubu goma daga cikin abinda yayi mata saura ta sakawa Khairi cikin akwatinta tunda inta bata ba zata taba karba ba, da wani abinne ba kudi ba. Haris bai bata kunya ba da safen ya fito, suka gaisa da Khairi, sai dai fuskarshi babu digon fara'a ko kadan, ya dai ce mata "Na dauka zaki kara yi mana wasu 'yan kwanaki kafin ki tafi" Khairi ta girgiza masa kai, tana masa bayanin zatayi registration ne, envelope ya mika mata "Banyi zaton da wuri zaki tafi ba haka" Ta bude baki, kafin tace wani abu ya rigata da "Ba zanji dadi ba in kikace wani abu, ki karba dan Allaah" Saita karba din tanayi masa godiya, tunda direban sammako yayi, karfe takwas ma a Kanon tayi masa "Allaah Ya tsare hanya, mungode sosai, akwai aikin da nakeyi, zan shiga in karasa" Itama tayi masa fatan alkhairi, Maryama harda hawayenta lokacin data raka Khairin, ita kanta karfin haline "A garin nan zanyi aure In Shaa Allaah, saboda ke, zamu zauna kusa da juna Maryama" Kai ta daga ma Khairi tana share hawayenta, haka ta koma tana jin gidan yayi mata wani fadi na daban. Ta kwanta a falo, ko karyawa Khairi bata tsaya tayi ba, ita bata iya cin abinci tunda sassafe, ko ranakun makaranta zai wahala kaga ta saka wani abu a cikin kafin ta fita, sai dai ta tafi dashi. Bacci ne ma ya dauketa anan kan kujera, sanda ta tashi kamar anyi mata sata a cikinta, jikinta har rawa yakeyi, shayi ta hada, tana da sauran biredi, ko kwai bata tsaya soyawa ba, dan anan Kitchen din ma ta tsaya ta karya tanajin ta dawo hayyacinta, bata da jimirin yunwa sam, da azumi ba karamin galabaita takeyi ba. Ta wuce dakinta, tayi wanka ta canza kaya, duk ta rasa abinda zatayi yau din da zai rage mata lokaci da shirun da gidan yayi na rashin Khairi. Ta nufi dakin Haris ta kwankwasa "In kawo maka shayi?" Ta tambaya daga bakin kofar "A'a" Ya amsa mata, ta dawo falo kawai, tana jin babu wani girkin da zatayi, dankalinta zata soya ta kara shan shayin ko taci shi kadai.  Bawai zama sukeyi suna shan hira da Haris ba, amman ba haka yake ba kafin ya tafi, ko dan bata taba zuwa haka kawai ta same shi a daki bane ba? Ta dauka zai fito ya fita kamar yanda ya saba, shisa ta wuni a falon, har sallah anan tayi, da bayin falon ma tayi amfani, hijabinta kawai ta shiga daki ta dauko. Bata ga fitowarshi ba, bacci biyu tayi tana farkawa, tasan bata da nauyin bacci, kuma kofar dakin nasu tana yin kara idan za'a fita, yanda ta murza mukulli ma dole zataji idan akayi kokarin budewa. Kwana hudu sukayi Haris bai fito daga dakinshi ba, jiya a falon ma bacci ya dauki Maryama saboda damuwar da ta tsinci kanta, dan yinin jiya tun safe da tayi masa magana ya amsata, muryarshi na fitowa kamar wanda aka shake zuciyarta ke ta bugawa, da rana ma sai taje ta dinga kwankwasawa, taji shiru "Dan Allaah kasa wani abu a cikinka...ko kadan ne in kawo maka shayin, in baka so ka fito in ajiye maka a bakin kofa sai kazo ka dauka in na tafi...kaji?" Baiyi magana ba, taje ta hado shayin ta kawo, amman haka ta koma ta dauke shi da daddare, maganar duniya bataji an amsaba, ta jijjiga kofar shiru, da yake ba wani bacci tayi mai natsuwa ba, sai gashi akan kunnenta akayi kiran sallar farko, ta tashi tayi alwala tazo tana gabatar da sallolin nafila kafin aka kira asuba ta gabatar da sallar, ko azkar ta kasa, ita kanta duk kaunar da takeyiwa abinci jiya kadan ta saka a cikinta, ko karfin kirki bataji, ta kwanta akan kafet din falon inda tayi sallah tana komawa wani wahalallen bacci data tashi karfe takwas da wani abu, taje dakinta tayi brush ta wanke fuska, ta fito ta nufi dakin Haris, bugawar duniya tayi amman shiru, ta kara kunnenta ko da zataji motsinshi. Saita tuna littafin data taba karantawa da kanin jarumin ya mutu a daki babu wanda ya sani saida aka wuni, anma dauka ya fice ne. Zuciyarta tayi wani irin tsalle daya sa ta mike daga zaman da tayi a bakin kofar, idanuwanta cike taf da hawaye ta koma falo ta dauko wayarta tana dannawa Khairi kira har biyu, ana ukun ne ta daga "Zan kiraki Maryam, ina zuwa" Kafin ta amsa Khairi harta kashe wayar, tabarta da sauketa daga kunnenta tana tunanin wanda zata kira kuma, sai kawai ta tsinci kanta da danna lambar Abba, shi kam a bugun farko ma ya daga, kamar mai jiran kiranta "Mairama" Shine abinda ya fadi taji kuka ya kwace mata "Subhanallahi...Mairama? Me yake faruwa? Ya akayi?" Cikin sheshheka tace "Abba...yana daki...bai bude ba...baya amsawa..." Tayi maganar a rarrabe cikin kuka "Ki natsu ki fadamun abinda yake faruwa kinji ko?" Ta daga kai tana kokarin danne kukan da yake ta kara taso mata, dakyar ta fada masa yau kwana hudu Haris na dakinshi a kulle, kuma tun jiya baya amsawa ko ta kirashi "Inalillahi wa ina ilaihi raji'un...ina maigadinku?" Ta maimaita maigadi cikin kanta "Ki kirashi yazo yaga ko zai iya balla kofar a dubashi..." Duk da tanata daga kai, sai tace "To zaku zo Abba? Zaku taho dan Allaah?" Cikin sanyin murya yace mata "In Shaa Allaah...yanzun kije ki kira maigadin" Sauke wayar tayi, sai Alhaji Sa'id dinne ya bude daga nashi bangaren, ta fita da saurinta tana kiran maigadin, dan dattijon ya wullar da radio dinshi da yake ta murza yana biyo bayanta cikin barin jiki, sai dai koface da tunda ya ganta yasan ko a zamanin kuruciyarshi bai isa ya karyata ba "Bari in kirawo taimako Hajiya, wannan kofar ba zan iya karyata ba" Sai gashi sai da mutum kusan biyar suka hadu sannan aka iya karya kofar nan, lokacin wayar Maryama nata ruri, ta daga ganin Alhaji Sa'id ne "An bude Abba..." Ta fadi tana karasawa cikin dakin, zuciyarta ta rikito, ta koma mazauninta ta sake rikitowa kamar zasu fadi a tare ganin Haris shimfide akan gadonshi, dakin kauri yakeyi har lokacin daya cakudu da turaren wutar data kunna duk da an kwana biyu, saiya bada wani irin kamshi marar dadi, idanuwanshi ba rufe suke gabaki daya ba, amman bakar fuskar nan tashi tayi fayau kamar takarda, labbanshi a bushe kamar yana wani motsi dasu zasu iya tsagewa, ga guntayen takardu nan har akan gadon, ba karshen sigari bane ba, dan Maryama tasan ya yake, suna gani ai a hanya. "Ya rasu ne?" Muryar wani cikin mutanen da suka karya kofar ya tambaya "Ya rasu..." Ta maimaita a hankali, a kunnen Alhaji Sa'id "Mairama? Waye ya rasu?" Sai kawai kuka ya kwace mata, yau ta fara shaida menene tashin hankali "Mairama!" Kuka takeyi da yake fitowa tun daga kasan zuciyarta, wayar ta subuce daga hannunta ganin yanda aka dago Haris din ya subuce ya koma luu kan gadon, suka sake dagoshi Bata taba ganin gawa ba tunda take Amman yanayin Haris yayi mata kama da gawa "Wannan fa sai dai a samo dan sahu a kaishi asibiti...Hajiya ko kin iya mota?" Ta girgiza kai "Ina mukullin?" Wani ya sake fadi, jikinta nata rawa ta karasa ta bude inda taga mukullin ta dauka ta mika masa "Kizo mu tafi asibitin Hajiya, ki kira gida ki sanar, inda kudi kuma saiki dauko kinsan ba lallai su dubashi ba" Kudin dake wardrobe din iya wanda hannunta zai iya damkar mata ta dauka tana bin bayansu, ta koma da sauri ta dauki wayarta, saida aka saka shi a motar, itama bayan ta shiga, maigadinsu daya rufe gate din gidan kuma ya shiga gaba, asibitin Aminu Kano suka wuce kai tsaye, ganin halin da suke ciki ne yasa aka kawo gadon marassa lafiya aka dora Haris din aka shiga dashi ciki, Maryama ta bisu, tanajin yanda take taka tsakuwoyi, haka sanyin tiles din daya ratsa kafafuwanta yana sanar mata da babu takalmi a kafarta balle kuma wata hijabi, wata Nurse ce ma ganin yanda take a firgice, ga wayarta sai qara takeyi yasa ta kamata ta zaunar da ita akan wata kujera, ta karbi kudin da take rungume dasu ta gyara mata hargitsinsu ta sake damka mata "Ki daga wayarki anata kira..." Ta daga wayar, fuskarta duk busashen hawaye sai ajiyar zuciya take saukewa "Muna asibiti Abba...muna asibitin..." Ta kalli Nurse din da ta danyi mata murmushi "Aminu Kano..." Ta dayan bangaren Alhaji Sa'id yace "Gamu nan zamu kamo hanya In Shaa Allaah...ke da waye a asibitin?" Ta hango maigadinsu "Ni da maigadi" Ta amsa cikin karamar murya "Bari in kira Murtaka, ki rike wayarki a kusa kinji, yanzun za'a zo a sameki kafin mu karaso" Kai ta daga tanajin sababbin hawaye na zubo mata, kafin ta sauke wayar daga kunnenta, haka tayi zaune tana kallon reception din emergency din, kafin wannan Nurse din mai kirki tazo ta tabata "Ki taso ana nemanki" Ta mike, tana jin kamar jiri na dibarta, bata san cewa yau din za'a yaye mata wani Labule guda daya daga cikin Labulayen da suke lullube da sirrikan Haris, Kamar yanda batasan cewa idan an daga mata Labulen nan zata kamashi ta sauke suyi tsaye ita da Haris a bayanshi ba... 22 Tambayoyi ne likitan yayi mata, shekarun Haris, kalar jininshi, duka kai kawai take girgizawa, dan tana jin idan ta bude bakinta to zata iya fashewa da kuka "Ina iyayenku? Ko wani babba?" Tana sauke ajiyar zuciya tace "Basu karaso ba, mu kadai ne sai maigadinmu daya taimaka mun muka kawoshi asibiti" Likitan ya kalleta, kallon da yasa taji rashin hijabin da bata saka ba, balle kuma ayi tunanin takalmi "Yayanki ne?" Ta girgiza masa kai, cikin karamar murya tace "Mijina ne" Kallonta dai ya sakeyi, sai takejin ko da bai bude bakinshi yace wani abu ba, ta karanci kalaman shi, kallon yarinta ne yayi mata yanzun "He's extremely dehydrated, jininshi ya hau sosai..." Ta gyada kai tunda ta fahimci abinda yace "Kinsan yana shan wani abu ne?" Taji anyi maganar daga bayanta, saita juya, wani mutum ne, gajere ne sosai, duk da a zaune yake kan daya daga cikin gadajen marassa lafiya na ward din da babu kowa akai, yanda kafafuwanshi suke lilo ne yasa ta gaje gajartarshi, Psychiatrists ne, dan yana aikine a wani private rehabilitation centre, ya shigo wajen abokinshi ne, likitan da yake duba Haris, tunda aka shimfide shi kan gadon nan, kallo daya yayi masa ya gane cewa yana shaye-shaye "Ko kwaya haka ko taba" Mutumin nan ya kara fadi, Maryama taji kamar an dauraye mata kanta da ruwan omo, bata jin komai sai wannan kalmomin daya furta, kwaya da kuma taba, a iya sani da fahimtarta 'yan kwaya kullum a buge suke, wasu ma ance bambancin da yake tsakaninsu da mahaukata kalilan ne, ita dai Haris bai tabayi mata kama da wanda yayi nisa da hankalinshi ba, tabar dai yanzun taga wani abu ya haska cikin kanta, wannan guntattakin abubuwan da ta gani birjik a dakin Haris dazun, ko itace tabar? Ita ba sigari bace ba? "Tun yaushe yake haka?" Likitan ne yayi mata wannan tambayar yanzun yana sa ta mayar da hankalinta kanshi "Ban sani ba...kaman tun jiya" Ta karasa fada da rashin tabbas a muryarta, tana kallon likitan ya dago da Haris din yana cire masa bakar rigar da take jikinshi mai dogon hannu, tana da dan kauri, lokacin da yayi kokarin ajiyeta ne wani abu ya fado daga ciki, a cikin irin ledar nan da ake dura magani a asibiti, sai dai abin yayi mata kama da ganyen shayi, kamar wani hayaqi da aka taba ba Adda Zahra a islamic chemist, lokacin tana fama da wani irin ciwon kai, akayi zaton ko shafar aljanu ne. Likitan nan ya tsugunna ya dauka, saiya dagawa gajeran mutumin nan "Weed" Cewar mutumin yana girgiza kanshi "Amman kasan wannan babban case ne ko?" Da harshen turanci likitan yayi maganar, kuma dashi mutumin ya amsa masa "Ka bashi taimakon daya ke bukata kawai, kayi kamar baka gani ba, a kasar nan dai babu wani amfani, in iyayensu suka zo sai kayi magana dasu a nemar masa taimako ta hanyar daya kamata" Likitan ya kalli Maryama da take tsaye tana jinsu, watakila yanayinta da tayi firgai-firgai ne yasa su duka biyun sukayi zaton ba zataji turanci ba "Ki kira mun wata Nurse, zan rubuta abubuwan da ake bukata, aje a siyo yanzun, kice su nuna miki pharmacy..." Sai ta juya din, tayi hanyar data shigo da ita dakin. Lokacin da ya gama rubutun, suka nufi hanyar pharmacy da Nurse din nan ne kiran Mummy ya shigo wayarta, dan Maryama ta kwance dankwalin kanta ta ninka tayi mayafi dashi ko zai kare mata wani abin, ta daga kiran, sai Nurse din data kula da yanda take tafiya ta karbi kudin hannunta tace mata ta koma bakin emergency din ta jira, dan haka nan ta gayawa Mummy ta sameta, tana ganinta taji hawaye na neman sake balle mata, ta daure "Sannu Maryama, ya jikin nashi? Kawunku ne ya kirani dan shi baya gari ma" A hankali tace "Da sauki..." Mummy ta jinjina kai cike da jimamin yanda taga Maryaman "Akwai shago dana gani anan waje, ki zauna bari inga ko silipas ne in za'a samu in siyo kisa a kafarki" Cikin emergency din ta koma ta zauna, sai taga daga Nurse din har Mummy duk sun dade, Nurse din ta riga dawowa, saida ta fara bata sauran kudadenta da taga sun rage da yawa, tukunna ta shige ciki, sai Mummy din itama, ta dawo da silipas harma da ruwan roba guda biyu "Duk babu karamar lamba, har tsallakawa nayi ban samu ba, sai na siyo wannan din kawai" Ta karba ta saka, babbar lamba ce, siraran kafafunta sunyi wani iri a ciki, ruwanma ta kwance ta kurba, sai taji ashe tana tare da kishi, dan haka tasha sosai, sauran kudin hannunta ta mikawa Mummy, ta karba ta saka a jakar hannunta batare da tace komai ba, kuma da Maryama ta jingina da jikinta sai ta kara gyara zamanta yanda zataji dadin jinginar, maganganun likita da gajeran mutumin nan ne suke ta dawo mata, kamar tana so ta kara fassara su yanda zata fi fahimta, ai taji ya kira abinda ya fado daga aljihun Haris da "Weed". Kalmar ce dai take ta zagayawa da ita daga wannan sashin zuwa wancan a cikin kanta kamar mai tsoron fassarar da zata tarar. Bugun da zuciyarta ta tsagaita dashi ya dawo sabo, taya za'ayi ace Wiwi ce, sha yakeyi kenan? Kaurin da taji yana fitowa daga dakinshi na wiwin ne? Dan wiwi aka aura mata? Abba ya sani? Baban Tudun Wada ya sani? Ko shisa aka aura mata shi saboda yana shaye-shaye? Tunda ai tasan ko duniya yake kwankwada za'a hadu tare da Alhaji Sa'id a rufa masa asiri, Abbanta zai iya sadaukarwa da Baban Tudun wada komai daya mallaka in ya bukaci hakan. Amman idan basu sani ba kuma fa? Sai taji tsoro ya shigeta, taji idan basu sani ba tana so ta kare ma Haris wannan sirrin, ta tayashi boyonshi kar wanda yaji ballantana ya dingayi masa kallon dan shaye-shaye. Itama hadashi a jimla daya da kalmar hautsina wani abu yakeyi a cikinta. Ba zatace ga adadin lokacin da suka dauka a wajen ba, Mummy ta tambayeta ko tana jin yunwa yafi sau babu adadi, tasan dai tun tana zaune harta gaji da zaman ta mike, ta sake dawowa ta zauna, ta kara mikewa tsaye, haka Mummy ma. Sai kuma can wayarta tayi kara, data duba sai taga Alhaji Sa'id ne, ta dauka tana amsa sallamar da yayi mata cikin karamar murya "Eh muna asibitin" Ta jinjina kai kamar Abban na gabanta, sannan ta sauke wayar daga kunnenta, kuma ba'a kara mintina ashirin ba ya sake kira, lokacin data fita ta tsaya bakin kofar emergency din nan, ta hango shi, saita manta da wani aure, ta manta da tarin jama'ar da suke kaiwa da kawowa a harabar asibitin ta ruga da gudu, irin gudun da takeyi lokacin tana kasa da shekaru biyar idan taji shigowarshi, ta kuma fada jikinshi kamar yanda bai kunyatata ba ya riketa, sai dai ta dauka zata fashe da kukane, zatayi yanda ta saba duk sanda take da wata damuwa inta ganshi, amman banda yaji babu abinda idanuwanta sukeyi, babu ko digon hawaye "Inata murna ina gayawa kowa Mairama ta girma yanzun, ashe da mun taho tare da sunyi mana dariya" Murmushi ya kwace mata, data dago daga jikinshi sai suka hada ido da Baban Tudun Wada, taji wata kunya ta lullubeta, da sauri taja dankwalinta daya sauka daga saman kanta ta rufe, cikin karamar murya ta gaishe dashi, ya amsa yana mata murmushi, yana gida lokacin da Alhaji Sa'id ya kira shi yake fada masa Haris bashi da lafiya, yaso yayi kawaici jin Alhaji Sa'id din yace masa ya shirya zaije Kanon, sai kuma ya kara masa da "Bansan ko zaka samu sarari ba sai mu tafi tare" Haka kuma Hajiya Rumana tayi tsalle tace sai an taho da ita, yasan ko yayi hargagi, koya tafi ya barta saita biyo bayanshi, shisa ma yace ta shirya kawai, sai direbanshi ya biya dasu gidan Alhaji Sa'id din suka taho tare, dan Maryama bata kula da ita bama sai lokacin, dan tana bayan Alhaji Mustafa ne "Ina wuni" Ta fadi da wani yanayi a muryarta, saida ta watsa mata wani kallo sannan ta amsa kamar mai ciwon makoshi, ba karamin kokari Maryama tayi ba na ganin bata tabe bakinta ba, shisa tayi saurin juyawa suna rufa mata baya, tana kallon Abbansu da Baban suka nufi wajen receptionist din, ita kuma ta koma wajen Mummy data taso ganinsu, ta gaishe da Hajiya Rumana, amman da yake babu idon Alhaji Mustafa, sai tayi watsi da ita bayan ta jefa mata wani kallo a wulakance, da Maryama ta kalli Mummyn sai tayi mata murmushi, duk da fuskarta ta nuna bataji dadin abinda Hajiya Rumana tayi mata ba, ita matar burgeta tayi yanda ta shigo cikin kasaita, masu kudi suna burgeta, sunayi mata kyau, amman kuma bata son wulakanci, inda duk taga za'a wulakantata tana kiyayewa sosai ta kuma kama kanta. Shisa ta cewa Maryama "Bari in karo ruwa" Ita kuma lokacin hankalinta gabaki daya ma yana kan su Abba, dan taga likitan nan na dazun ya fito, kuma sunbi wani lungu tare, zuciyarta ta buga kamar tana son fitowa daga kirjinta ta bisu ko zata ga abinda zasu fada "Uban me kika bashi? Wato kin aure shi kuna so ku kashe mun shi ke da ubanki ko?" Hajiya Rumana tayi maganar data ratsa cikin tunanin Maryama kamar ta saka lasifika, zuciyarta tafasa kawai takeyi tunda suka kamo hanyar Kano, Alhaji Sa'id ya zauna a gidan gaba, ita da Alhaji Mustafa suna baya, ji takeyi kaman ta shaqo shi kowa ya huta, kamar kuma motar ta bugi wani abu, shi din ya fita ta gilas. Babu kalar tunanin da batayi ba, tunda akayi auren nan ta rasa gane kan Haris, ya botsare mata kamar bashi ba, kamar wanda aka juyawa kwakwalwa, yanzun kuma anzo ance bashi da lafiya har an kwantar dashi asibiti, Haris dinta? Yaron tun tasowarshi sai yayi shekara baiyi ko zazzabin rana daya ba, hakori ma Haris sai dai kanshi yayi zafi, haka ta dinga ganinsu a bakinshi. Ai ta riga tasan wannan auren bana Allaah bane, auren jari ne Alhaji Sa'id yayi da 'yarshi. Maryama taji ta tar, taji abinda ta fada, ita tuntuni bata son matar, batayi mata ba kamar yanda tasan Abbanta ma da yayi sanadiyar haduwa kaddararsu waje daya ba abakin komai yake a wajenta ba, balle kuma su karan kada miya "Magana nakeyi miki kika tsareni da ido kamar wata sa'arki, fitsararriya marar tarbiya" Wani abu yazo wuyan Maryama yayi tsaye, kalaman Hajja suka dawo mata, lokacin da suke kallon wata tashar Hausa sunata rakadin surutu akan rashin tarbiya da kuma rashin kunya irinta 'yan fim, tunda ance maza ne suke cika danqam a wajen, harda 'yan kallo, amman haka zasu kwanta basuji komai ba, suyi rawa su markade can su juya can, sai Adda Maimunatu tace "Iyayensu ne basuyi musu tarbiya ba" Dai-dai shigowar Hajja "Ki roki gafarar Allaah, su kuma ki roka musu shiriya, a duniya babu wata uwa da take so taga danta ya lalace, komin sakacin da zatayi da tarbiyarshi kuwa, fatanta ace yafi kowanne yaro tarbiya, yafi kowanne yaro nagarta, duk yaron da kuka ga yana wani abu, kar bakinku ya sake daukar alhakin iyayenshi, bakusan iya baccin da suka rasa akan wannan abin da yake aikatawa ba" Kuma a ranar ta kara gane dalilin da yasa ko dambe ta kwasa a makaranta take fargabar ace Hajja taji, ko intayi wani abu data hanata, saboda ba bacin rai kadai take gani a fuskar Hajjan ba, harda fargaba mai yawan gaske, shisa da taji tana so ta kuntatawa Hajiya Rumana, musamman da babu idon kowa a wajen tayi wani guntun murmushi tace "Kiyi hakuri Hajja, babu abinda na bashi wallahi, wiwi ce yasha tayi masa yawa..." Kuma akan idanuwan Maryaman Hajiya Rumana tayi wani tangadi kamar tana shirin faduwa, ta kara gyara tsayuwarta, amman girman jikinta yaki taimaka mata wajen boye irin kaduwar da tayi, maganar ta daketa, dukan da ya sanyaya ran Maryaman yana sa abinda ya taso yayi mata tsaye a wuya ya sauka "Shine fa muka kawo shi asibiti, amman naga likitan mane yaja su Abba, kilan bayani zaiyi musu tunda ya tambayeni me ya faru na gaya masa, baki ga yanda muka shigo asibitin nan ba Hajja, kinsan Allaah ba zaki..." Cikin wata murya da izzarta ta sauka Hajiya Rumana ta katse Maryama "Zaki rufe mun baki ko saina kwadeki a wajen nan? Bayanin ubanki zaiyi musu? Ke waye ya aikeki gaya masa? Waye yace miki abinda ya saka shi rashin lafiya kenan?" Ita tunda akayi wannan case din na makaranta ta cire abin daga ranta, Haris bai daina ba? Bai daina sha ba? Allaah Ne shaida ba karamin alfahari take ciki ba ganin yanda alakarsu ta gyaru shi da Alhaji Mustafa, yanda duk hira saiya sako zancen Haris din, saiya dinga bata labari akan Haris kamar ita bata magana dashi, auren nan nema da yake tana fushi har yanzun ta janye jikinta, shima kuma ya shareta, tasan yaji dadin yanda Haris bai watsa masa kasa a ido ba, yanzun idan yaji cewa yana shan wiwi me zai faru? Hanjinta sai kadawa yakeyi, tabi hanyar da taga sunyi tana barin Maryama data samu waje ta zauna "Haka kawai saiki zageni banyi miki komai ba, mata sai bakar fuska da bakar zuciya" Ta fadi a ranta, a gefe daya tana fatan Allaah Yasa kar a fadawa su Abban wani abu. Sai dai fatanta bai karbu ba sam, dan babu wani abu da likitan nan bai warware musu ba, ya nuna musu hoton da akayiwa Haris din "Inaso ku sani ne tunda kune iyayenshi, yaronku na bukatar taimako dan ya rabu da abinda yake sha...inaso inyi muku bayani yanda hankulanku ba zasu tashi ba, huhunshi na gab da samun matsala in har bai tsagaita da shan abin nan ba, musamman irin yanda yayi din nan babu komai a cikinshi, yanzun haka jininshi muke kokarin ganin ya sauka daga hawan da yayi, sannan bugun zuciyarshi ma yayi stabilizing..." Alhaji Sa'id shine mai tarin tambayoyi, saboda Alhaji Mustafa kamar an liqe masa baki, kanshi ma a kasa yake ya kasa dagowa dan baisan ta inda zai fara hada ido da Alhaji Sa'id ba, idan yayi zaton ya nemi alfarmar a hada auren Maryama da Haris ne saboda wannan dalilin fa? Bayan shi babu abinda yake gani a tare da Haris din sai natsuwa da hankalin da yayi, Haris din da waya goma zasuyi, to takwas daga ciki sai sun tattauna akan kasuwanci da kuma plans dinshi, sai yayi masa wasu kalamai da suke nuna irin zurfin da tunanin shi yayi, irin yanda hankali ya fara zauna masa, ashe a gefe wiwinshi yake sha har yanzun, bai daina ba, ba bari yayi ba. Ko ma shine dalilin da yasa Alhaji Modu ya hanashi auren Aise? Sanda suka fito daga ofishin likitan kuwa sai da Alhaji Sa'id ya tabashi tukunna, kafafuwanshi ma hardewa sukayi ya kusan yanke jiki ya fadi badan Alhaji Sa'id ya rike shi ba "Haba Mustafa? Wanne irin abune wannan?" Saiya jingina bayanshi da bangon wajen, cikin rauni ya kalli Alhaji Sa'id "Wallahi Sa'idu bansan ya cigaba ba, kasan lokacin da akayi case din ai...wallahi na dauka ya bari, na dauka ya daina shisa harna nema masa auren nan, wallahi...." Kallon da Alhaji Sa'id yayi masa yasa shi kasa karasa maganar "Ashe Haris din nakane kai kadai Mustafa, ashe akwai abinda yake bukatar rantsuwa a tsakaninmu? Ashe Maryaman dana mika ma Haris babu taradaddi sanin cewa taka ce itama kai ba haka bane a wajenka?" Kai yake girgizawa ya kasa magana "To me yasa kake mun wadannan maganganun kamar wanda yayi mun wani laifi? Ba zaka barni inji da abinda yake damun yarona ba saika batamun rai?" Kamar a lokacin kuruciyarsu, idan Alhaji Mustafan yayi halin shi na zuciya an kasa tankwara shi, yaki jin maganar kowa sai an kirawo Alhaji Sa'id sai yace "Kayi hakuri to Sa'idu" Alhaji Sa'id din ya girgiza kai, har ranshi ciwon Haris din yafi damunshi fiye da shaye-shayen da akace yayi, wannan ai yana daga cikin kaddararshi, yana kuma yi masa addu'a, zai kara da wannan ne yanzun, in suka hadu su duka sai Allaah Ya yaye masa, tare suka koma reception din, tunda ance da Haris din yayi stabilizing zasu canza masa daki ne su cigaba da monitoring dinshi na kwana biyu, kafin daga nan asan mataki na gaba, sunje suka karasa duk wani cike-cike da ake bukata, Hajiya Rumana na mayar da kafarta inda Alhaji Mustafa ya cire tashi, tunda taje ta rasa ina suke dole ta dawo, baiyi mata magana ba "Amman dai ba zama zamuyi mu kwana ba ai, tunda ga matarshi, kuma akwai 'yan uwa anan din" Alhaji Mustafa ya fada "Ni dai zan zauna saiya warware gaskiya" Cewar Hajiya Rumana, ya juya yayi mata wani kallo batare da yace komai ba, Alhaji Sa'id yasan Mummy zata zauna da Maryama idan kwana ya kama, sannan zatayi tsaye akan duk wani abu ma, matar har tafi Murtala zumunci, shi kanshi yanda take kira tana gaishe dashi, haka yaranta Murtala baya kira. Amman yana so yayi magana da Maryama, ya zauna da ita kona mintina ne "Babu laifi, mu dai jira zuwa yamman mugani, in aka canza masa daki sai mu tafi...bari inyi magana da Maryama" Dan yaga kamar Hajiya Rumana ma tana bukatar kebewa da mijinta, har lokacin Mummy bata dawo cikin wajen ba, dan can kasan wata bishiya ta samu ta saka takalmanta tayi zamanta a wajen. Alhaji Sa'id ya samu ya zauna kusa da Maryaman da take ta wasa da wayar hannunta "Mairaman Abbanta, midwife din gidana, da kin gama karatun ma ai da yanzun kece zaki duba Haris din kiyi masa allura" Tayi murmushi mai sauti tana hango zatayiwa Haris allura, to zaima yarda? Shi din da take ganin rashin yadda da abubuwa da dama game da ita, zai yarda tasan abinda takeyi ya mika mata jikinshi? "Kai Abba...ni da zan dinga karbar haihuwa, ai ba za'a kawoni irin wajen nan ba" Shima dariyar yayi, ya dan sauke numfashi "Ya kuke Mairama? Ba lafiya lau din da kike cemun a waya ba, ya kuke?" Ya karasa maganar a hankali, cike da fatan ta fahimci abinda yake nufi, saida ta kalle shi tukunna tace "Lafiya lau Abba, wallahi lafiya lau, yana mun kirki sosai, tunda ya dawo ne bayajin dadi, amman muna lafiya" Ya sauke wani numfashin da baisan yana rike da iskar shi ba "Kinsan me yake damunshi?" Ta daga kai a hankali "Likita yayi mana bayani, nasan zai karayi miki kema, yanda zaki taimaka masa ya kula da lafiyarshi, nasan zaki iya ko?" Ta sake daga kai "Yawwa 'yan matana, nasan ba zaki bani kunya ba daman, Allaah Yayi miki albarka" Dadi ya ratsata, daman tasan Abban nata mutum ne mai yawan uzuri, mai yawan fahimta, ko da an fada masa hankalinshi ba zai tashi ba, watakila daman ya sani "Amman Abba ai babu kyau shaye-shaye" Ya jinjina mata kai "Shisa nake so ki fara yi masa addu'a idan kinyi sallah, Allaah zai yaye masa, zai bari, sai kin dage sosai, kin tayashi kula da kanshi" Ta danyi shiru "Amman Adda Zahra tace shine zai kula dani, tunda shine babba" Alhaji Sa'id yayi shiru, sai can yace "Kin tuna sanda nayi hawan jini? Aka bani magunguna?" Ta daga kai da sauri, tunda lokacin faduwa yayi, sukaita kuka kuwa, akace jininshi ne ya hau, amman gajiya ce, ba wani abu bane da zasu daga hankalinsu, ita dai nata bai kwanta ba "Ke na nada mai bani magungunana idan lokacin sha yayi, ke kika kula dani harna shanye dan kar in dinga mantawa" Kai ta sake dagawa, dan wannan abin da yayi mata a lokacin ya sama mata da natsuwa ne "To kwatankwacin wannan kulawar ake nufi, shine babba, amman a wajen kula da lafiyarshi kece babbar" Ta gane sosai, ta fahimta, zata kuma yi duk wani kokari da zata iya. Su Abban ne suka fita suka siyo musu abinci, da abubuwan da ma yake tunanin zasu bukata, harda maigadinsu da bai tafi ba ya samu waje ne ya zauna, sai Alhaji Mustafa yace direbanshi yaja motar Haris din, ya kaisu gida harda Maryama da Mummy dan Maryaman ta dauko abubuwan da suke bukata tunda zata kwana a asibiti. Haka akayi, wajen karfe biyar da rabi aka sakewa Haris daki, dan sunce bacci yakeyi, alluran da akayi basu sake shi ba, sunata dai canza masa karin ruwa, ba karamin rikici Alhaji Mustafa sukayi da Hajiya Rumana ba, saida ya rantse ba zata kwana ba tukunna ta hakura, tanata share hawaye, musamman irin ramar da taga Haris din yayi kamar wanda yayi wata yana ciwo. A ranta tayi niyyar washegari ma saita dawo, ko Alhaji Mustafa bai barta ta kwana ba, haka zataita zarya tsakanin Kaduna da Kano duk rana sai taga ya warke ras, bayan tafiyarsu ne Mummy ta cewa Maryama ta zauna wajen Haris din itama zataje gida tayi musu abincin dare saita dawo. Kafin ta tafine da likita ya sake shigowa ake fada musu mutum dayane kawai zai kwana wajen Haris din, Mummy taso anyi wannan maganar kafin tafiyar su Alhaji Sa'id, dan suyi musu magana su barta ta kwana itama "Akwai Nurses da zasu kula dashi ko da babu kowa ma, mu munfi son hakan..." Dole taje ta dawo ma da Maryama da abinci, wajen karfe takwas da rabi ta tashi da niyyar tafiya tana tanajin kamar karta tafi saboda tausayin da Maryaman ta bata "Zaki iya kwana babu wata matsala kuma Maryama? Tun da sassafe zanzo In Shaa Allaah...ko da Abbanki zai kira kice masa muna tare kar hankalinsu ya tashi..." Dan murmushi Maryama tayi "Babu wata matsala Mummy, ai kinga sunce qila ma sai goben zai farka saboda alluran da sukeyi masa, da nayi sallar isha'i nima kwanciya zanyi..." Haka sukayi sallama, ta koma cikin dakin, tayi sallar isha'i data idar saita ja kujera saitin gadon da Haris din yake kwance ta zauna tana kare masa kallo "Ya rame, ya rame sosai" Haka Hajiya Rumana ta dinga maimaitawa, kuma yanzun data nutsu taga wannan ramar a fuskarshi, bata dai kai yanda ita din ta dinga fada ba. Tabi hannunshi da babu karin ruwa a jiki da kallo, dan shine a saitinta, bakin hannunshi, yatsunshi take kallo, ance zakaga hannun yan shaye-shaye yayi baki, toshi nashi bakin ne, in ba dai karawa yayi ba, sai dai faratanshi farare ne kal, sai kace bashi da jini saboda haskensu, kamar rubutu take gani a jikin karamin yatsanshi, kafin kwakwalwarta ta hana zuciyarta harta kamo hannunshi, da nata duka biyun, taji hannun nashi yayi sanyi, ta duba yatsan nashi, rubutune kamar anyi shi da bakin fenti ko tawada zatace, ta karanta sunan jiki "Aise" Ta sake kallo tana tsintar kanta da shafa rubutun taji ko akwai alamar shi, ko kuma zai goge, yana nan, kuma babu alamar shi a jikin nata yatsan "Aise..." Wacece Aise? Wanne irin suna ne Aise? 23 Kaman wanda yasha kasa haka yaji makoshin shi ya bushe, ga idanuwanshi sunyi masa nauyi sosai, da yake kokarin budesu ma sai yaji kanshi ya sara, ya dan sake runtsa idanuwan, ya kuma sake kokarin budewa, farin bango ya fara gani, ya dago hannunshi da nufin ya murza gefen fuskarshi da yaji yana kaikayi, amman sai yaji wani abu ya soke shi da ya sashi furta "Ouch" A hankali yana duba hannun, karin ruwane a jiki, dayan hannun kuma da yaja sai ya kalli gefenshi da saurin gaske, kwan dakin a kunne yake, tana zaune ta kife kanta a jikin gadon da alama bacci takeyi, hannunta yana rike da yatsanshi guda daya, karamin yatsanshi, yabi hannun nata da kallo kanshi yayi masa nauyi kamar an dora masa dutse, asibiti yake ya sani, ya kuma san itace ta kawoshi dole da taimakon wasu, shisa bai wahalar da kanshi wajen zurfafa tunanin suwa ba, balle kuma tayaya yazo asibitin. Saiya mayar da idanuwanshi ya lumshe, sai yake ganinshi a tsakiyar rusassun gine-ginen nan na Syria kamar an dauke shi an cilla can. Ranar farko daya gane yana son yara, yana sonsu sosai, yana aji hudu ne a sakandiri, sunzo hutu, sai sukaje duba Barde da bashi da lafiya har an kwantar dashi a asibiti, lokacin da sukaje asibiti akwai yayarshi da tazo itama, da yaranta guda uku, dukansu mata ne, dayar ce jaririya da baisan ko 'yar wata nawa ba, su 'yan matan anyi musu wani kitso da aka jerawa beads, babbar daya fara hada ido da ita, sai tayi masa dariya, babu hakori guda daya a bakinta, baisan lokacin da murmushi ya kwace masa ba shima "Zo mu gaisa" Ya tsinci kanshi yana fada, sai kuma yarinyar bata bashi kunya ba, taje din tana rike hannunshi hadi da gaishe dashi cikin karamar muryarta, kanwarce dai taki zuwa ta sake makalewa a jikin Mamanta "Wannan sarkin tsoron mutane ce" Inji Maman, amman itama ta burgeshi sosai, kafin su tafi saida yarinyar nan da taje wajenshi ta bashi bead guda daya, yasan daya daga cikin na kanta ne data cire, haka suka bar asibiti da wannan bead din da yake ta wasa dashi a cikin hannunshi, a ranar, a karo na farko yaji cewa idan wata rana zai samu nashi yaran, to yana son mata ne, ko guda goma ne yana son duka su kasance mata ne. Kuma kamar wani hadin baki, daga wannan ranar zai wahala ya fita bai hadu da yara ba, har saida ya fara tunanin ko dai kula dasune bayayi da din shisa baya ganinsu haka, wata rana yana zaune a mota zai hangesu suna wucewa, wasu da uniform din makaranta da yan jakunkunansu, wasu ma ledace rike a hannunsu a maimakon jakar, uniform din nan yayi cuducudu da dauda kamar sun shekara basu ga ruwa ba, wasu kuma almajirai ne, 'yan kanana. Akwai wani da yana tsaye wajen mai saida kayan marmari zai siyi Pear, dan yana son abin sosai, in dai zai gani saiya tsaya ya siya. Yaji an rike masa kafar wando "Dan Allaah ka saimun abinci yunwa nakeji" Yaron da Haris baya tunanin ya haura shekaru biyar ya fada, dayan hannunshi rike da wani katon kwanon silva, idanuwanshi da alamun sabon hawaye banda wanda suka bushe a idanuwanshi "Ina mamanka?" Shine tambayar da ta subuce masa, saboda a ganinshi wannan yarone da bai kamata ace yana waje a dai-dai wannan lokacin ba, kamata yayi ace yana gida, kusa da Mamanshi, anyi masa wanka, bashi da wata matsala banda ta wasanni "Ance ta mutu ba zata dawo ba shine Baba ya kawoni nan na zama almajiri" Wani abu ya takure a kirjin Haris har ya nawa fitar numfashin shi barazana, kudin da baiko kirga ba ya ciro ya bashi yana kasa cewa komai, wannan pear din daya siya a ranar a falon Hajiya Rumana ya barshi, akan kujera, saboda cikinshi ya cunkushe fal da kwashewa Baban yaron nan dama Malamin daya karbe shi a matsayin almajiri. Inda shi wani babbane a gwamnati a ranar nan da kwana zaiyi sintiri tsakanin makarantun alluna ana kama masa Malaman, ana kwashe wannan kananun yaran zuwa garuruwansu, saima an rufe masa iyayen a matsayin jan kunne. Ya jima abin na damunshi, in dai zaizo hutu ya fita ya dinga raba ido kenan akan tituna ko zaiga irin yaron nan ya basu kudi. Shisa da tunani daya ya sauka kasar Syria, tunanin ya haskawa duniya wannan kananun yaran daya kamata ace sun hadu sun ba kariya, wannan kananun yaran da basu yiwa kowa laifi ba, yaran da basu ma san me duniyar take ciki ba, yaran da abinda wannan yakin yakeyi musu, album dinshi harya sama masa tittle tun tuni (Innocence in the face of war). Kuma a sati biyun nan babu abinda bai gani ba, jinsu yayi kamar shekara biyu saboda nauyinsu da kuma dadewar da kowacce rana takeyi masa, dare ma tsayi ya dingayi masa, saboda daga inda suka sauka baisan sau nawa yaji fashewar bomb ba, fashewar da take hadawa da wani sashi na zuciyarshi "Yara nawa bomb din nan ya taba yau?" Shine tambayarshi, idan ya kalli yaran nan da idanuwanshi sai ya gansu a matsayin yara, kyawawan yara, farare qal dasu, wasu cikin matan ma da mayafai an nada musu, sai yaga yanayi musu murmushi, saboda yanajin bashi da wani abu da yake dashi da zai ba wannan yaran banda murmushin shi, wasu su mayar masa, wasu har hannu suke daga masa, wasu kuma zasu kalle shine kawai. Idan ya daga camera dinshi, ya hangosu ta ciki sai yaga wani abu da baigani ba kafin ya daga camera din nan, sai ya ga wani firgici a cikin idanuwansu, wani tsoro da yake da yakinin har karshen rayuwarsu ba zai taba barinsu ba. Lokacin ne yake kula da kurar da take jikinsu, wasu har a fuskarsu, wari da warin takalmin da yake kafar wasu, hujin da yake jikin na wasu, wasu ma 'yan kafafuwan nasu babu ko takalmin, busassun labbansu, yanda kashin kumatunsu ya fito alamar rashin wadatar abinci ko abubuwan gina jiki, busassun hawaye dama sababbi, ranar da sukayi kwana shida ne suka tsallaka wani waje da aka cilla bomb a safiyar ranar anata tono mutane da suka jikkata, wasu ma gawarwaki ne, ranar ne camera dinshi ta daukar masa kafa, 'yar karamar kafa da farin takalmin daya baci da jini, iya kafar, babu sauran jikin, kafar daya dauka yana ganinta dishi-dishi a tsakanin hawayen daya cika masa idanuwa taf. Tun daga ranar har suka bar Syria da hawaye a idanuwanshi yake daukar duk wani hoto, batare da yasan nashi Ogan yayi masa hotuna da yawa a wannan yanayin ba, saida ya nuna masa, ya ganshi shima ranar kanshi da hannayenshi duk kura, haka bakaken kayanshi, saboda anyi tonon nan dashi, an kama gawarwakin da baisan adadinsu ba tare dashi, ya taya an daga gini an zaqulo uba, an zaqulo da, an zaqulo uwa, da hannunshi ya mikawa wani tsoho gawar saurayin danshi. "Kamar ince maka zaka daina, wannan hawayen na idanuwanka zaka nemosu ka rasa, amman bana maka fatan nan, bana maka fatan ranar da zaka nemi hawayen nan naka ka rasa, ranar da zaka ganka a war zone amman babu inda zakaji wani abu yana zuba sai anan..." Ya karasa yana dafa kirjinshi, Haris numfashi kawai ya iya saukewa, numfashin da har jiragensu suka daga, dan sun hau mabanbanta ne, kowa akwai inda zai nufa, shi Haris yayi Italy ne, saboda makarantar da yake shirin sake komawa dama wasu abubuwan da zaiyi, sannan zasu hadu da ogan nashi bayan sati biyu, akwai yiwuwar ya samu aiki a wajen yada labaran da ogan nashi yayi recommending dinshi. Gabaki daya bayajin dadin duniyar, kanshi yayi nauyi na gaske, tunda sukaje a sati biyun nan inya kwanta, jikinshi har rawa yakeyi yana neman abinda ya saba, yana neman wiwinshi ko zai samu natsuwar data kwace masa, shisa yana sauka Italy ya samu hotel ya ajiye kayanshi abinda ya fara nema kenan. Daman tun kwanansu biyu da zuwa abinci ya daina zauna masa a ciki, ko yaci sai yayi amanshi. Kwana biyar din farko da yayi a Italy yana hidindimunshi abubuwa masu ruwane kawai suka dinga shiga cikinshi, suma dakyar yake iya hadiyesu tunda yasan jikinshi ba zai taba bashi hadin kai ba in har bai saka wani abu a cikin nashi ba. Ranar na shidan ne ya taka kafarshi zuwa makarantarsu Aise, inda yasan zai sameta, ya nemi waje yayi zamanshi da kofin ice tea a hannunshi da yake dan zuqa a hankali, har saida ya hangota, ita kadaice, da wani baggy din wandon jeans, crazy ne amman sai dai ba'a ganin jikinta a duk inda ya yayyanka din, sai riga da itama bata matseta ba, dankwaline ta daura akanta, dankwalin da Haris yake iya ganin santsinshi daga inda yake tsaye, dan itama ya zame mata, rabin gashinta a waje yake, gashin data rina, kala biyu brown da kuma baki, kamar kalbace kanana akan nata ko meye bai gane ba sosai, ta dai gyara edges din, da kwalliyarta ta sabo a fuskarta, ya tashi da sauri yana karasawa inda take "Amore" Ya furta muryarshi na fitowa a dishe, yanzun da take tsaye a gabanshi, zuciyarshi na kadawa da tarin soyayyar da yakeyi mata, da kuma kewarta, so yakeyi ya hade wannan yar tazarar ya riketa a jikinshi, idanuwanta ne suka dakatar dashi, abinda yake gani a ciki "A'a!" Ta fadi cikin daga murya, ta sake girgiza kanta "Akan me zaka zabeta kuma kazo ka tsaya a gabana haka? Me yasa?" Ya karasa da sauri yana riko hannunta ta fisge, tana tureshi da hannun nata, dan daya rike yake da takardun data daga masa "Kaga takardun transfer dina?" Ita yake kallo ba takardun ba, ta kuma juya masa hannunta na haggu, yana ganin zoben da yake yatsanta "An samun rana, aure zanyi kamar yanda kayi aure, kace mun Babanka ne yayi maka aure, sai dai nima Babana yana nan, kuma nima auren zaiyi mun..." Haris yaji dariya ta kwace masa, dariyar hasaso Aise da auren wani bashi ba, a wajenshi abin dariya ne saboda tunda yasan yana sonta yake hangota a gefenshi, yake hangota da igiyoyin aurenshi, ya za'ayi hankalinshi ya dauki cewar zata auri wani bashi ba? "Baki da hankali ko? Ni zaki gayawa zaki auri wani?" Tayi masa wani kallo daya kasa gane fassararshi "Kai daka fadamun ka auri wata meya faru?" Yayi kokarin sake kama hannunta ta matsa baya da sauri "Kabari, bana so, na fada maka, bana so! Aurena zanyi nima" Sai ya girgiza kanshi kawai yana sake fadin "Baki da hankali" Ya juya yayi tafiyarshi, duk karshen sati Aise din na zuwa gida, kamar ka'idace a wajenta, shisa ya rabu da ita, daya tashi saiya bita gidan, ya samu har Alhaji Modu na gida kuwa, yanda bata kula shi ba data ganshi shima saiya shareta, to tambotsan Aise sai dai ya bada labari, wannan fushin nata ya sanshi, ya saba dashi. Bai bata dalili bama tanayi masa rikici balle kuma yanzun da take da dalilin. Ko a wajen cin abincin anata hira, shi dai shayine daman ya hada, yace musu baya jin yunwa "Ya wajen matarka? Amman dai karatun nan da zaka dawo tare da ita zaka taho ko? Kaga itama sai ta cigaba da karatunta anan" Idanuwanshi suka sauka kan Aise data kware, ta dauki kofin ruwa tana kwankwada, su duka suka hadu suna tayi mata sannu, hakan ya ba Haris damar zillewa tambayoyin Alhaji Modu din da bazai so ya amsa ko daya ba a halin yanzun, a gaban Aise "Kanwar taka ta gaya maka an sa mata rana ko baku kai dayin maganar ba?" Wani abu yayi tsaye a tare dashi gabaki daya da kalaman Binta, yasan ya ajiye kofin hannunshi, ya kuma daga kanshi ya kalli matar "Ba kuyi maganar ba kenan, karshen watan nan za'a daura auren" Sanyi yaji yanaji, kamar an watsa masa ruwan kankara "Allaah Ya kaimu" Ya furta muryarshi na komawa cikin kunnenshi kamar ba tashi ba, ya kalli Aise amman kanta na kasa. Sai kuma ya dauki kofin shayin nashi yana cigaba da kurba, saida ya shanye shi duka sannan yayi musu sallama, har suna cewa sun dauka kwana zaiyi ya girgiza musu kai, har ya taka kafarshi daya wajen gidan saiya koma, ya wuce su Alhaji Modu da suka rakoshi bakin kofar ya koma dining area din nan, inda Aise take zaune har lokacin "Bracelet dina" Ya fadi yana mika mata hannu, data dago hawayen da suke idanuwanta ne suka zubo "Bani tafiya zanyi" Ta kalli hannunta da bracelet din yake, na azurfa ne, customized ne yasa akayi mata daga gida Najeriya ya tafi dashi, shima gani yayi a hannun 2Pac yace masa a wajen wani Nakore ne ya biya akayi masa, daya duba akwai na mata kuwa, saiya bayar, da haruffan sunayensu yayi tunanin a saka, sai kuma ya tambayeta in zaiyi mata customized bracelet me take so a rubuta a jiki "Haris" Ta bashi amsa kai tsaye, bai tambayeta dalili ba yasa aka rubuta mata hakan, harda wani dan heart a gefe, daya kawo shine ya daura mata chain din da yake adjustable. Ya zauna a hannun nata yayi kyau "Na tsaneki adadin lokuttan daya rike hannunki alhalin kina tawa" Ya dora yanajin wani irin tiriri na taso masa "Yanzun da kika zabe shi, kije Aise, na bar masa ke, amman ki bani abuna" Tasa hannu ta share hawayenta, hannunta har rawa yakeyi lokacin data kwance bracelet din ta mika masa "Zaki iya zuwa ki zama tashi, ina muku fatan alkhairi" Ya fada yana juyawa, sai lokacin ma yaga su Alhaji Modu a tsaye, baibi ta kansu ba ya wuce ya fice daga gidan. Tunda baisan me suka tsaya kallo ba, abinda suke sone ya faru, sunyi nasara, sun karasa rabashi da Aise din, kuma ko itace mahadin numfashin shi ya bar musu 'yarsu. Har kasar ma duka zai bar musu, ya fasa komawa makarantar anan. Jirgin yamma yabi zuwa kasar New York City, ya samu Oganshi acan. Kuma ko daya gama abinda zaiyi din, sai ya tsaya yana duba makarantar Parsons School of Design, kafin ma ya zurfafa tunaninshi ya riga ya tsinci kanshi yana applying. Saida ya gama sannan ya tattara kayayyakinshi yayo gida. Daya shiga daki, ko kwan dakin bai kunna ba, yanda yayi wani duhu-duhu sai yaji abinda yake bukata kenan, kamar bayason ganin haske, kamar duk wani karfi da ya bar Syria dashi ya gama karewa ne daga lokacin daya shigo cikin gidan, banda nauyi babu abinda kanshi yayi, babu komai a ciki, bayajin komai sai wani irin kadaici daya lullube har ruhinshi. Kadaicin daya saukar masa da gajiya yaji bayason ganin kowa, bayason yin komai banda kwanciya, sai kuma wiwin da take tayashi hira, wayarshi ma kashewa yayi tunda bayajin yin magana. Saida ya kwana ya yini, tukunna ya sauka daga kan gadonshi dakyar, ya hada sallolin da ake binshi yayi, bashi da karfin bude kofa shisa ya amsa Maryama daga nan inda yake. Da ta kira masa shayi ma ji yayi amai na taso masa, bayason yasa komai a cikinshi. So kawai yakeyi ya kwanta, ya cigaba da kwanciya, in zai iyama ya bace cikin duhun da yakeji ya zame masa aboki a cikin dakin. Tun yana gane gari ya waye, yana bacci ya farka ya tashi ya shiga bayi, ko wanka baiyi ba a kwanakin nan, bayajin karfin yin wanka, dakyar yake sallah, shima harhada wasu da wasu yakeyi, har yaji komai yayi shiru, shirun da yake bukata, shirun da yasan a cikinshine suka dauko shi zuwa asibitin nan. So yake ya tashi yanzun, yasha ruwa, yana bukatar ruwa, amman ko daya zare yatsanshi daga hannun Maryama sai yaji jiri na dibarshi da yayi yunkurin tashi, dole ya koma ya kwanta, a hankali ya dan bubbuga gefen gadon da hannunshi, ta kuwa tashi da saurinta "Ka tashi? Sannu...bari in kirasu in fada musu ka tashi" Shigowar likita uku, taje ta kira Nurses yafi sau bakwai har saida baccin nan ya dauketa, tana cewa suzo su duba sugani, me yasa bai tashi ba har yanzun tunda likitan karshe yace mata zai iya farkawa kowanne lokaci, tana ganin yanda suka gaji da kiran da takeyi musu, bai dameta ba, ai aikin da aka biyasu suyi kenan, taji ya riko hannunta ya dan murza "Ki bani ruwa in sha..." Ta daga masa kai, taje ta dauko ruwan ta bude robar ta mika masa, sannan ta fita, ko ta kira Nurse din tazo ba wani abu tayi masa ba, ruwan da saura kiris ya kare ta cire da nufin canza wani Haris yace mata "Nagaji, kibarni in huta" Ita kuma tana wani lankwasa murya kamar ba ita bace ta ware makoshinta kamar bututu ta amsa Maryaman da taje kiranta ta amsa Haris din "Da kayi hakuri an saka maka tunda saura guda biyu, sai kaga kafin gari ya waye angama" Maryama Haris ya kalla, da take tsaye tana kallonshi itama, tana jiran taji abinda zaice "Ki fada mata, ko ta sakamun zan cire ne" Sai kuwa ta kalleta "Kibarshi tunda bayaso" Akan dole ta fita bayan ta gimtse fuska, kamar gani Maryama tayi ta harareta kafin ta fitan. Ta tabe baki ta koma kan kujerar data tashi ta zauna "Kaina yayi mun nauyi" Yayi maganar a hankali, da bata kusa dashi ma ba lallai taji ba, ta kalleshi, ta tuna yanda ta dinga kwankwasa masa kofar nan shiru, wani abu ya taso ya tokare mata wuya "Kan ba tsoranka yakeyi ba da zaka kulle daki kwana hudu bakaci komai ba kace ba zaiyi maka nauyi ba, ai so kayi ma kan ya gutsire ya fadi" Baisan yanayin yanda tayi maganar bane ko hararar data maka masa cikin takaicin da yake gani a fuskarta koma maganarce ta saka dariya kwace masa ba, dariya tun daga zuciyarshi "Taya kai zai gutsire ya fadi?" Yayi tambayar yana dariya "Ni ina na sani, ba abinda kaso kayi ba kenan? Ka kashe kanka?" Ya dan girgiza kai kawai, har lokacin fuskarshi da alamar fara'a, bayani likita yayi mata sosai, dalla-dalla akan hadarin da Haris yake ciki, duk wani abu da bata gane ba haka ta dinga jera masa tambayoyi kala-kala yana amsata. "Me yasa kake shan wiwi?" Ta tambayeshi kai tsaye, idanuwanta fes akanshi, tambayar da yaji kamar ta sake mayar dashi ta kwantar saboda dukan da tayi masa, tunda a mafarki ma baiyi hasashenta ba "Nasan ka jini" Cewar Maryama ganin yayi wajen mintina uku, kamar bashi da shirin amsa mata, saiya juyo da kanshi yanda zai kalleta sosai "Me zance miki?" Ta dan daga kafadunta "Gayamun zakayi me yasa kake sha bayan bakayi kama da wanda zai sha wani abu ba" Yayi wani gajeran murmushi da bata ga alamun nishadi a cikinshi ba, asalima wani abune ya gilma ta cikin idanuwanshi "Masu shan wani abu suna da wasu kamanni ne?" Ta danyi shiru, ba zatace suna da kama ba, amman ai in an gansu ana ganesu, da yawa a iya tunaninta sun taso ne basu da tarbiya, sun taso a kangare babu wanda ya isa dasu shisa sukeyin shaye-shayen, shikuma bata ga alamar rashin ji a tare dashi ba "Ban sani ba, kawai dai bakayi kama dasu ba, shisa nake so in san me yasa kake sha" Yaja numfashi ya fitar a hankali "Haka kawai" Ya amsa da dukkan gaskiyarshi, rana daya ya kalli 2Pac yaji yana so ya busa hayaqin, yana so yaji abinda yakeji da baya gajiya da bankadawa cikinshi, shikenan kuma, daya fara sai ya kasa bari, ko dan ya taba gwada barin ma? Yana so ya bari kuwa? To me zai maye masa gurbin wannan buzz din da yakeji cikin kanshi? "Sannunka...huhun naka ne baka so kenan?" Ya nanata huhu yafi sau biyar a jere amman ya kasa gane menene shi "Huhu? Menene huhu?" Dariya ta kusan kwacewa Maryama da yanayin yanda yayi tambayar, saita fada masa da turanci "Oh shine huhu daman?" Ta jinjina masa kai "Likita yace naka yayi bakikirin, saida ma na tambaye shi daman ba baki bane ba yace mun wai a'a..." Idanuwanshi akanta yace "Ke naki baki ne?" Ta girgiza kai "To akan me nawa zai zama baki" Saita kalle shi kawai "Wai wanne irin baki nake dashi a idonki Maryamm?" Tayi dariya "Ki amsani wanne irin bakina kike gani" Ta makale kafada, ya kamo hannunta yana janyota ta kuwa rankwafa gabaki dayanta kamar zata fada masa, dan saida jikinta ya daga daga kujerar, ta soma kiciniyar kwacewa amman riko yayi mata bana wasa ba, baima san akwai wannan karfin a jikinshi a yanayin da yakeji ba, amman so yakeyi ya jata kan gadon, ya matseta saita bashi amsa "Yi hakuri...tsaya in fada maka to, ka sakeni" Saiya kara karfin rikon da yayi mata "Allaah zan fadawa Hajjanka, ai tace zata dawo da safe" Wani abu ya haska cikin idanuwan Haris din "Hajja? Hajja tazo?" Ta daga masa kai tana kiciniyar kwace hannunta, saiya sassauta mata rikon harta koma ta zauna, amman bai saki hannun nata gabaki daya ba "Eh da Baban Tudun Wada, harda Abbana sukazo" Yaji wani irin yanayi na shigarshi "Ya akayi sukazo? Ke kika kirasu? Me yasa zaki kirasu?" Ta girgiza masa kai, a hankali ta fada masa abinda ya faru tun daga farko "Sunyi magana da Doctor dina? Yayi musu magana?" Ta daga masa kai a hankali, ya saki hannunta, ta rike shi da dayan tana murza inda ya riketa "Damn" Ya fadi kasan numfashinshi yana shafa sumarshi, karshen abinda zaiso a halin yanzun shine abinda zai taba alakarshi da Alhaji Mustafa, kuma tace harda Alhaji Sa'id akazo, kuma yana da tabbacin tare za'a hadu a fada musu komai, ya sake kallon Maryama, haka kawai yaji koda kowa ya sani, ko da kowa zai sani, yaso ace an tsame Alhaji Sa'id daga jerin wadannan mutanen, itama da ta sani babu abinda yaji, abinne yazo masa a bazata da kuma yanayin da tayi musu maganar "Karka damu, naga fa duk ransu bai baci ba, kawai dai kowa hankalinshi ya tashi, kuma nasan saboda ance huhunka na gab da samun matsala ne" Kallonta dai yakeyi, yanda take fadar duk wani abu da take so kanta tsaye "Huhun naka ne yake da muhimmancin a wajen mutane da yawa, sai ka hakura da wiwin tunda babu wani dalili da yasa kake sha" In ta cigaba da magana, zai jawota, zai matseta a jikinshi, saboda abinda yake so yayi kenan "Kiyi mun shiru in koma bacci Maryamm" Ta dan gyara zamanta, ita batajin baccin, tama manta tsakiyar dare ne "Dan ina fada maka gaskiya? Hajja zata dawo ai, babu ruwana" Tasan matar, amman jiya da ta matso kusa da ita, sai wannan micijin da akeyiwa lakabi da kububuwa ya dawo mata, duk da bawai ta taba ganin kububuwar bane, Hajiya Rumanan ce tayi mata kama dashi a cikin kanta, bata dai bata tsoro bane ko kadan, amman aishi mamanshi ce, dole zata bashi tsoro "Ai kasan halinta" Yanda ya juyo da jikinshi gabaki daya yasa tayi baya da kujerarta da sauri, ya kalleta, da idanuwan nan nashi, idanuwanshi da take ganin wannan ruwan a kwance cikinsu kullum, zuwa yanzun tasan ba hawaye bane, amman kuma akwai wani abu dangane da hayaqa Haris din da yakeyi mata dadi, yana mata yanayi da Khalifa, ita da yake tana da saurin shaqa, sai Alhaji Sa'id yace ta daina tsokanar kowa yanda itama babu wanda zai tsokaneta, sai ta kiyaye kuwa, Khalifan ne kawai take dan tabowa lokaci zuwa lokaci ta bakinshi yakan ce "Jikinki ne yake miki kaikayi ko Maryama?" Shisa tace "Kuka zakayi? Dan Hajja zatazo? Karta zaneka?" Cikin wata irin murya yace "Zo nan" Tayi dariya "Ga idonka nan da hawaye" "Zo Maryamm, zo kiji" Ya sake fadi, ta karayin dariya tana jan kujerarta baya, idanuwan nashi take kallo, da wannan abin kwance a cikinsu, yanda idanuwan sukayi fari qal, kwayar ciki baka, sai take ganin maiqon cikinsu kamar ya karu ne Wata rana, Wata rana zata saka yatsantsa a ciki taga ko zata iya dangwalo maiqon nan, Wata rana... 24 Kwana biyu ya kara a asibitin kafin su sallame shi, a kwana biyun nan kuma ya saka halayen Maryama cikin jerin abubuwan da ba zasu taba gajiyawa da bashi mamaki ba. A daren daya farka, daga shi har ita basu koma bacci ba sai bayan da sukayi sallar asuba, lokacin ne ta kira wani Nurse, namiji, yazo ya saka masa wani karin ruwan, kuma yanda ya fara jin idanuwanshi na rufewa da kansu, ya tabbata akwai allurar bacci cikin wanda yaga sun matsa a ruwan kafin su saka masa. Lokacin daya tashi ba zaice ko karfe nawa ba, amman yaga Maryama a zaune, ta canza kayan jikinta, ba zai tuna kalar kayan jiya ba, amman yasan basu bane a jikinta, yanzun wani material ne, mai dogon hannu da ya matse daga tsintsiyar hannunta, sai kuma hula data saka ja, saboda akwai ja a jikin filawar da akayiwa material din kwalliya dashi. Plate ne a gabanta da take ta yayyanka wani abu a ciki da cokalin da take rike dashi, sai kuma kofi a ajiye, kallonta yakeyi, yanayinta, idanuwan shi sukayi tsaye akan wuyanta, siririn wuyanta da kamar ba zai dauki nauyin kanta ba, a wannan lokacin, sai yaji hannuwanshi nayi masa kaikayi, yana son ace akwai camera dinshi a hannunshi, yana so ya dauketa hoto, yana son ya ganta, a wannan zaman da tayi yasan dole akwai abubuwan da camera dinshi ce kawai zata daukar mishi, kuma kallon da yakeyi matane yasa ta daga kai, suka hada ido "Ka tashi? In kirasu?" Ya girgiza mata kai, yaga sun cire masa ruwan ma "Zan shiga bayi, inaso inyi wanka, amman bani da kaya" Ta kara gyara zamanta "Na dauko maka jiya dana koma gida, harda brush dinka ma duk yana can..." Ta karasa maganar tana nuna masa wata karamar jaka, baice komai ba ya sauko daga kan gadon zuwa inda jakar take, ya bude ya fito da duk wani abu da yake tunanin zai bukata, harda karamin towel data gani ta dauko masa. Sai dai towel din da kuma gajeran wando taga ya dauka sai su brush da kuma yar ziplock din data sako masa soso da sabulunshi a ciki. Kawai ta maida hankalinta kan alalenta da take jira ya huce, Mummy wajen karfe tara saura minti goma ta shigo da basket a hannunta "Inata kiran wayarki bata shiga tun safe..." Tace bayan sun gaisa "Kar dai bai farka ba har yanzun" Ta gaya mata ya tashi "Inata sauri wallahi, da yake Kawunki ya dawo da daddare, sai yace ayi alale da kunun gyada da safen, aikin saiya hade mun, na dibo miki nasan kina son alale, shi dai bansan me zaici ba, ga shayi nan na dafo muku sai na soya masa dankali da kwai" Cikin kudin da Alhaji Sa'id ya batane ma ta aika aka siyo mata dankalin, dakyar aka samu saboda safiya ce, dan aiken nata yace duk ba'a fito ba. Har kwan ma ciki ta siya, madara da milo suna dashi saita samu fararen ledoji ta diba ta qullo a ciki, tana fatan karsu Maryaman su raina "Sannu da aiki Mummy, ni kam zanci alalen nan, kunun gyadar fa?" Ta tambaya "Na dibo miki, sikarin na nan a leda, dan kar in zuba a ciki ya tsinke...in dai bakwa bukatar wani abu inaso in koma dan in karasa aikace-aikace in dora abincin rana, me kike so? Shi me kike tunanin zaici" Maryama tayi "Ai wallahi Mummy karki wahalar da kanki, duk abinda kika dafa kawai ki zubomun iya cikina, ba abinci yake ci ba ko sanda yake da lafiya" Itama dariyar tayi "Sai mutum ya zauna haka kaman ganga" Duk yanda zatayi ma Mummy bayani tasan ba zata gane ba, sai bayan ta rakata, ta dawo, tayi wanka ta sauya kaya, maine ma batayi tunanin ta dauko ba, gashi tanajin kamar jikinta ya bushe, tukunna ta zauna ta zuba alalenta da take ta faman tururi, irin kulolin nan ne nada masu rike zafi, saika rantse lokacin aka sauketa. Ta fara ci sanda taji Haris ya bude kofar bayin, ta daga kai, ta sauke shi da saurin gaske, daga shi sai gajeran wando, sai kuma wannan karamin towel din daya dora shi akan wuya. Taji kamar alalen zata shaketa, dakin ya matse mata sai kace suna cikin keji. "Me kike ci?" Haris ya tambayeta, cikinshi yakejin kamar an kwashe komai, harda hanjin, a zatonta ya saka kayane shisa yayi mata magana, amman da ta daga kai lokacin ma yake jan zip din dogon wandonshi hankali a kwance, bai saka riga ba "Wai kai dan Allaah sai ka kama saka kaya a gabana, maimakon ka shiga dasu bandaki ka saka kafin ka fito?" Tayi maganar muryarta na rawa, cikin rashin fahimta yake kallonta "Me yasa zan shiga da kaya bayi? In ajiyesu ina?" Idanuwanta kamar zasu fado saboda hararar data maka masa, sau nawa ake musu wa'azin kallon tsiraici da irin abubuwan da hakan suke janyowa "Inda na ajiye nawa dana shiga mana, kawai saika fito sanqare-sanqare dakai a gabana, kuma daga shigarka har kayi wanka ka fito? Ka gurje kafarka ta fita sosai? Da kuma hamm...." Sai ta cije lebenta, lokacin da ta fara wanka da kanta, fadan Hajja kenan intayi jiqa-jiqa "Wannan kafar bata fita ba, ki koma ki dirjeta tas, ki kuma wanke hammata, ki daga hannun sama ki wanke, in ba haka ba zakiyi warin dauda..." Abinda taso tace masa kenan, sai taga kamar bai kamata ba, kamar kalmar tayi nauyi ta gifta a tsakaninsu "Bangane na gurje kafata ba..." Cewar Haris da madaukakin mamaki, ya tabbatar Maryama ba zata wuce shekara goma sha shidda ba, hakan na nufin ya bata shekara goma sha, lokacin daya fara wanka da kanshi da wahala in ta gama hakora, amman wai ta kalle shi tana tambayar shi koya dirje kafa "Kafa dame kuma?" Ya kara tambaya ganin ta sauke kanta kasa, shiru tayi, ya kuwa taka har inda take, sai ganin kafafuwanshi tayi a gabanta "Ki amsani inaji" Ta kasa dago kanta, zuciyarta sai bugawa takeyi, saiya tsugunna, kuma taga bai saka riga ba har lokacin "Kinsan Allaah saikin karasa maganar nan" Cikin rawar murya tace "To kasa riga dan Allaah..." Ya maqale kafadarshi "Saikin gayamun" So take ya tashi, dan tayi yunkurin matsawa baya, amman jikinta yayi mata wani irin nauyi "Hammata...kafa da hammata" Tayi maganar, sai ya mike, ya kuma kamo hannunta ya mikar da ita, da tayi kokarin togewa saiya saka mata karfi yana dagota, bata da nauyi kamar yanda yayi zato "Ai zuwa zamuyi ki dirjemun kafar da hammatar, kinga sai inga yanda ya kamata in dingayi" Cikin wani irin yanayi tace "Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..." Tashin hankali na rikito mata, idanuwanta kamar zasu fado waje "Wasa nake maka fa, dan girman Allaah kayi hakuri" Dariya ta kusan kwace masa ganin yanda ta firgice gabaki daya, sai firgicin ya haska masa wani abu a kanshi, yaji ilahirin jikinshi ya amsa, sai kawai yayi mata daukar da akeyiwa yara, irin ta gefen nan, salati Maryama takeyi tana karawa da karfinta, kar dai da gaske bayi zai jata, ita kuwa ta ina zata fara wankewa gardi kafa da hammata, gardin ma bakin gardi "Na rantse da Allaah ka saukeni, kasan zan fadaka da Hajja" Dariya yayi mai sauti "Kice mata me? Kince ban iya wanka ba, nace muje kiyi mun ingani? Ai gode miki zatayi...kinsan irin son da Hajja takeyi mun?" Ya sake gyara mata zama a kugunshi, dan jikinta gabaki daya ya mutu, ko kacaniyar kwacewa ta kasayi, idanuwanta ma cike suke da hawaye "Dan Allaah kayi hakuri, dan Allaah fa nace maka Ganja" Sunan ya kwace mata batare data shirya ba, dariyar da Haris yayi mai sauti ce "Ai wankan ma zakiyi mun gabaki daya kawai..." A dai-dai wannan lokacin ne aka kwankwasa kofar, kafin shi da yake tsaye yayi wani yunkuri Hajiya Rumana ta turo kofar, ta kuma shigo, ta kalle su, ta sake kallonsu, sai tayi tunanin kilan ta kifta idanuwanta shisa sukayi mata ganin abinda ko a mugun tunani bai kamata ace ta gani ba, saita kare ware idanuwanta, Haris ne dai, tsaye, babu riga a jikinshi, rike da yarinyar da a halin yanzun ta tsana fiye da komai, tana can tunanin ciwonshi ya hana mata wataccen bacci, ashe shi yana nan yana rungumeni in rungumeki da kaddararshi "Sauketa dan ubanka" Kalaman suka kwace mata batare da tama sani ba, to akan me zai dauketa ma? Akan wanne dalili? Anya wannan auren ba zai dasa mata ciwon ajali a irin tsanar da tayi masa ba, kuma batasan menene abinda ta fada na nishadi da yasa Haris din dariya ba, ya daiji ta, ya sauke Maryaman da ba tayi tunanin akwai ranar da zataji dadin ganin Hajiya Rumana ba, sai yau, tanajin ya direta kan kafafuwanta da suke rawa tayi saurin takawa ta koma kan kafet din da take zaune tana mayar da numfashi, takai hannu ta share kwallar data taru cikin idanuwanta "Mami" Cewar Haris da murmushi kwance akan fuskarshi, ta harareshi, saiya sakeyin dariya, ya taka zuwa inda take yana hugging dinta, ta ture shi hadi da kai masa rankwashin daya kaucewa da sauri "Ina can ina tunanin ciwonka, ashe kai ka warke ma kana abinda bai kamata ba, saboda rashin hankali ko?" Baiyi magana ba, ya dai taka zuwa kan gadon dakin, ya dauki rigarshi da take ta kamshin wani turare da yaji duk dadinshi yayi masa karfi, ya saka a jikinshi "Sannu da hanya" Ya fadi bayan ya saka rigar, ta karasa shiga cikin dakin, sai kuma da ta ajiye katon kwandon hannunta tukunna ya kula dashi "Ina kwana" Maryama tayi maganar cikin karamar murya "Lafiya" Kawai Hajiya Rumana ta fada tana jan kujera ta zauna "Kaci abinci?" Ya girgiza mata kai yana cewa "Yanzun Maryamm zata hadamun shayi" Saita kalli Maryama da idonta yake kan alalen da yanzun ta fita daga ranta duk zumudin cin da takeyi, tana ta kissima yanda zata rama abinda Haris yayi mata ne kawai "Tunda bakaci ba, ga abinci nan na taho maka dashi" Ya zauna gefen gadon, yasan Hajiya Rumana da nama, yanzun haka duk tarin kulolin nan data jibgo idan aka budesu nama ne da aka sarrafa shi kala-kala, da wahala idan akwai wani abinci, shisa ya girgiza mata kai "Ba zanci nama bafa Mami, bari ta hadamun shayin" Wani abu yazo wuyan Hajiya Rumana yayi tsaye, Maryama na jinsu, kuma data dago sai yanayin dake fuskar Hajiya Rumanan yayi mata dadi, shine ma abinda yasa ta fito da kofi da kayan shayin data gani a ledoji "Meye wannan a ledoji?" Hajiya Rumana ta tambaya "Madara ce da Milo" Madara da Milo a leda? Saboda tsiya kome? "Baku da kayan shayine za'a qullo madara a leda? Wacce irin tsiya ce wannan? Haka kukeyi a gidanku daman?" Maganar tayi ma Maryama zafi, amman sai tayi murmushi tace "A'a Mami, muna da kayan shayi fa, kinsan suna gida tunda an taho asibitin a hargitse, wannan ma taimakawa akayi aka sammana shisa kika gansu a leda" Ran Hajiya Rumana ya kara baci "Sammuku akayi? Rokowa kikayi kenan kome?" Murmushin ta sake fadadawa, kafin ta amsa Haris ya rigata "Mami mana" Ta juya ta harareshi "Kai yanzun abinda aka roko din zaka sha? Sai kace wani almajiri? Idan ita tasha ba wani abu bane ba tunda ubanta yayi yawon bara, amman kai akan wanne dalili" Haka kawai daya janye idanuwanshi daga kan Hajiya Rumana saiya kalli Maryama, maganganun ne sukayi masa wani iri, shisa yake so yaga ita da aka fadawa me sukayi mata "Mami please" Ya sake fadi, sai taja wani irin tsaki, ita duk fadan da tayi tashen yi da mutane a makaranta, koya zaka zageta bata taba ramawa, gara ta kamaka ta jibga, saboda ance wanda ya zagi wani kamar ya zagi kanshi ne, to idan kuma iyaye ne, ta ina bakinta zai fara budewa ta zagi su Abba? In wani ya zagesu ma ba zai wanye lafiya a wajenta ba, amman gashi yau, haka kawai, babu wani dalili Hajiya Rumana ta zauna tana zagar matashi, tana kiranshi da almajiri, ai ya fada musu tabbas, an kawoshi almajiranta, amman yanda tayi maganar da izgili, a kunnuwan Maryama dai-dai yake da zagi, kuma tarbiyar Hajja ce ba zata taba watsarwa ba duk runtsi da ta gaya mata abinda zai hanata bacci, sannan ga Haris da takejin idanuwanshi na yawo a kanta, shisa ma ta cigaba da hada shayin, saida ta kurba taji yayi yanda ta saba hada masa tukunna, sai ta bude yar karamar kular nan, ta samu plate ta juye masa dankalin da wainar kwan da tasha yankakkun kayan miya sai kamshi ke tashi, ta saka cokali a ciki tace masa "Ga shayin" Dan bata yarda da kanta ba, karta mike kai masa ta watsawa Hajiya Rumana shi "Nan zaizo ya karba saboda baki da tarbiya? Ba zaki taso ki kawo masa ba?" Kafin tace wani abu Haris dinma ya mike, da ya karasa kan kafet din kawai saiya samu waje a gefenta ya zauna, ya sake juya shayin ya kurba, bashi da zafi ma can, dan haka ya dauki kofin kawai ya cigaba da kurba "Meye wannan kika zuba?" Ya tambaya a hankali, itama a hankalin tace masa "Alale" Ya sake kallon plate din, da yake 'yar sauce din manja ce Mummyn tayi, ta zuba a gefe, tunani yakeyi idan ya taba ganin alale, ya dai san bata taba zuwa bakinshi ba, amman su Anisa na yawan maganar alalen, ko sun tabayi sun zubo a gabanshi ma ba zai tuna ba "To kici, ko muci dankalin?" Ta girgiza masa kai kawai, ta dauki nata filet din ta fara tura alalar da ta kasa gane dandanonta, kunun ya jima da hucewa, ba zata iya shanshi ba, dan batason kunu yayi sanyi. Hajiya Rumana kuwa kallonsu kawai takeyi tanajin kamar ana watsa mata ruwan zafi. Yanda Haris din ya tattara hankalinshi kan Maryama take kallo, da yanda itama Maryaman take amsa shi, batama jin me suke cewa daga inda take, sai tajita kamar bakuwa yau, bakuwa a rayuwar tilon danta, kamar wata da tazo ta tureta sai kawai ta zauna a wajen. Wani abu ya dinga tasowa yanayi mata rumfa, makoshinta ma daci yakeyi mata, da Maryama ta gama tura iya abinda zai shiga, sai ta mike tabar filet din a wajen. Ganin ta dauki hijabinta da yake gefe yasa Haris fadin "Ina zakije?" A hankali tace masa "Coke zan siya, akwai shago a wajen asibitin, daga tsallake" Kai yake girgiza mata "Kece zaki tsallaka titi? Koma ki zauna" Ta tura bakinta gaba "Zan iya fa, ai zan kalli gefe da gefe" Kai tsaye yace "Ki samu wajen zama" Sai kawai ta tafi inda ta ajiye ruwan dasu Alhaji Sa'id suka siyo musu jiya, ta dauki roba daya, akwai katan din holandia, amman ba sanyi,  akwai dan karamin fridge a dakin, ta saka fruits din da suka siyo ne dan karya lalace. Ta kuma karasa gefen Hajiya Rumana da take ta binsu da ido dan yau ne ta gane asalin abinda ake kira da "Naga abinda yafi zare tsayi" Wayarta da ta saka a caji ta cire tana nufar kofa "Me nace miki?" Muryar Haris ta fito cike da kashedi, ta juyo harda buga kafa "Bafa zuwa zanyi ba, anan waje zan zauna zan kira Abba ne ba muyi magana ba" Tayi tsaye tana kallonshi, ta kasa fita saida ya dan daga mata kai tukunna ta fice daga dakin. Shikuma ya mayar da hankalinshi akan shayin da yake sha, dankalin ma yaci kusan rabi, kwan ne bai taba ba "Haris..." Hajiya Rumana ta kira muryarta can kasan makoshi, wani abune mai kama da tsoro yake neman saukar mata "Mami dan Allaah, idan kina da matsala da Maryamm kiyi mun magana, kiyi mun fada, saboda ba ita ta saka kanta a rayuwata ba, Baba ne ya daukota ya kawo, nikuma nayi masa alkawari cewa na karba...ko ba zaki karbeta bake, to hakan ya tsaya tsakanin ni dake, bana so ki dinga abinda zaisa mutuncinki ya ragu a idanuwanta, bana so ta raina ki" Ta furzar da numfashi "Idan ni banyi abinda zata rainani ba ai kai ka riga ka girma yanzun Haris, ka nuna mata ni din ba komai bace a wajenka, shisa zan dauko kafa inzo dubaka, in kawo maka abinci kaqi ci, sai wanda ta roko muku, sannan a gabanta nayi magana ta kawo maka nan, ka tashi kaje ka sameta kuka zauna waje daya, a gabana..." Yayi shiru, tunda ya riga yasan halinta, yasan kuma yanda ranta yake a bace ba zatayi shiru ba, fadan ta cigaba dayi kamar zata taso ta rufeshi da duka, baiko motsa ba, data mike tana fadin "Ai banga zaman da zan zauna inyi maka ba, gara in barka da wannan kaddararriyar yarinyar, daman saida Babanka yace inyi zamana ashe rabon inga abinda zai dasamun ciwone" Cikin karamar murya yace "Allaah Ya tsare hanya Mami, wayata na gida, amman zan kiraki da tata kafin mu koma in dauka dan inji ya kika sauka" A hasale tace "Inka kirani da wayarta sai naci ubanka Haris" Ya kurbe sauran shayin shi yana ajiye kofin "Zansa ta dauko mun wayar inta koma gida to sai in kiraki da tawa, I love you, Allaah Ya saukeku lafiya" Taja tsaki tana ficewa abinta, yanda ta banko kofar saida kunnuwanshi suka amsa, ta kalli Maryama dake zaune a kujerun karfe da suke corridor din tana waya ta nata dariya, taji kamar ta karasa ta shaketa, ta wuce kawai, Maryama ta ganta, tun data ja kofar ta ganta, shisa ta kara waya a kunne tana dariya, ta kuma yi kamar bata ga fitowarta ba, data wuce tana tayar da iska Maryaman taja siririn tsaki "Allaah Ya raka taki gona" Ta fadi a ranta tana mikewa ta koma cikin dakin, ta samu Haris a zaune inda ta barshi "Naga harta tafi, zataje ta dawo ne?" Ya girgiza mata kai kawai, kafin kuma a hankali yace "Mami tana da fada, haka take, amman ba duka abinda ta fada bane yake fitowa daga zuciyarta, banaso ki dinga rike maganganunta" Cikin ido ta kalle shi "Abinda ta fada daga zuciyarta ya fito, kuma gaskiya ta fada, Abba yayi yawon bara" Yanda tayi maganar yaji baiyi masa dadi ba sam, shisa ya rasa abinda zai kara cewa, sai yayi shiru, ta wuce dan tana so ta maida cajin wayarta, tunda da safen ta saka daman, a wajen dai ta tsaya ta kira Mummy tace mata karta saka abinci dasu, ta gaya mata Hajiya Rumana tazo kuma ta kawo abinci da yawa. Babu wata hira mai yawa da ta sake giftawa a tsakaninsu, shi yanaso yayi mata magana, amman baisan me zaice ba, ita kuma zafin maganganun da bata mayarwa Hajiya Rumana ba shine ya rufe mata baki, da suka sakeyi masa allurai yayi bacci, itama saita samu ta kwanta. Mummy bata dawo ba sai la'asar, Haris nata bacci, ita ta sake raka Maryama gida, ta tafi da wannan kayayyakin da Hajiya Rumana tazo dasu, ta saka a fridge, ta ajiye kayan da suka cire harda na Haris din, ta sake dauko musu kala dai-dai, suka dawo tare har asibitin, sannan sukayi sallama ta tafi. Ba'a sallamesu ba sai washegari wajen karfe sha biyu, batasan waya kai motar Haris gida ba, dan Mummy ta dawo, tana nan akayi sallamar, suka karbi magungunan da aka bashi na kwana bakwai, dan ance su sake dawowa bayan kwana bakwai din idan ya gama shanye magungunan. Haka suka fito Haris na mamakin abinda sukeyi tsaye a bakin titi, yaga Mummy ta tare musu adaidaita sahu, anata zabga ciniki. Shi dai mamaki yakeyi, yaga Maryama ta shiga, sai aka loda kayayyakinsu a baya, kwandon da Mummyn ta kawo musu, basu ko taba ba, sai aka saka shi anan kusa da Maryama, da sauran wasu tarkace ma "Ka shiga Haris, Allaah Ya kara sauki" A hankali ya amsa da "Amin. Mungode sosai" Yana kallo ta zagaya gefen da Maryama take, shikuma ya shiga a darare, haka kawai zuciyarshi sai bugawa takeyi, shifa tunda yake ko mashin bai taba hawa ba, keke ma da yara sukeyi bai hau ba, daga mota sai jirgi, ko a sauran kasashe taxi ce. Dan shi bayason gudu da mota, shisa duk yawon da zasuyi in dai Barde ne zaiyi tuqi sai dai ya hakura da tafiyar, saboda Barde bashi da hankali inya rike mota, to yau gashi mai adaidaitar nan dan ta kife ne, dan yanda ya fisgeta saida Haris yayi gaba har kirjinshi na dukan karfen wajen "Subhanallahi..." Maryama ta fadi dan taga yanda Haris din ya bugu "Ka shigar da jikinka ciki ka zauna sosai, wanne irin zamane kayi haka, sai kaje ka fada" Ya kalleta "Wanne irin zama zanyi, kina ganin gudun da yakeyi, gashi seat din yana da santsi, shine yake zamo dani" Kallon da tayi masa bashi da fassara, tunda yayi mata magana ne kamar wanda bai taba hawa adaidaita ba "Shikenan, karka zauna da kyau ka rike karfen wajen, inka sulmiya ka cire hakori babu ruwana" Maganar ta shigeshi sosai, ya rike karfen da yaga hannunta yana kai da dukkan karfinshi "Ka rage gudun nan fa" Ya cewa mai adaidaita sahun, yanajin wata tsakuwa ta taso ta fada masa a ido "Oga bafa gudu nake ba, dan naga na daukeku a asibiti shisa nake lallabawa" Haris baima ji me yace ba yana ta faman murza idonshi da tsakuwa ta fada, daya kara bude bakinshi sai yaji kamar kasa ta shiga ciki, dole ya rufe, baisan me ya samu motarshi ba, amman ya tuna cewa Maryama bata iya tuki ba "Wai a wannan abin kuka kawoni asibiti?" Ya kasa hakuri saida ya tambaya, ta kalle shi da idonshi daya daya rine, dan akwai alamun danshin hawayen da idon yayi har lokacin "Me ya samu idonka?" Ya dan gyara zamanshi "Wani abune ya shigo daga waje ya fada mun, anan kuka kawoni?" Ya sake tambaya, sai kawai ta daga masa kai "Baya muka sakaka" Da saurin gaske yace "Baya ina?" Ta gimtse dariyarta "Baya fa inda akasa kayan nan, to sai kafafuwanka sunyi tsayi, shine fa aka samu igiya aka kulleka a saman adaidaitar, da yake ba gudu yayi ba ya lallaba tunda da mutum akai, Allaah dai ya sauke mu lafiya" Yaga tashin hankali kala-kala a Syria, amman saida yaji cikinshi ya hautsina, sama? Shi aka kulle a saman wannan abin aka kawo asibiti? Daya sulmiyo fa? Dariyar da yaji Maryaman ta kwashe da ita yasa shi sanin karya takeyi, ya mika hannun shi yana ja mata kunne, amman dariya takeyi har lokacin "Zamuje gidane Maryamm" Dariyar dai takeyi masa... Abu dayane a ranshi har suka sauka, ba za'a rufe satin nan Maryama bata fara koyon mota ba, saboda ba zai kara hawa adaidaita sahu ba, yayi na farko, ya kuma yi na karshe, haka ya fadawa kanshi... 25 Wani abinci ne ta ga maigadinsu yana ci ranar da suka koma daga asibiti, dan da robar a hannunshi ya bude gate din, jikinshi har bari yakeyi lokacin daya gansu, yanata faman jera musu sannu, tana bashi abinci idan ta ga ba zata iya cinyewa ba, amman tunanin ta dinga bashi kullum bai taba zuwa ranta ba sai ranar, tunda su dai ba maigadi suke dashi a gidansu ba. Shiya tayasu shiga da kayayyakinsu ciki yanata yiwa Haris addu'o'in karin lafiya kafin ya koma bakin aikinshi. Daga ita har Haris din kowa nashi dakin ya wuce, dan ita kwanciya ma tayi tanajin gajiya na saukar mata, akan kafet take karasa baccinta a asibitin, tunda tana fara shine akan kujera, da kanta da take dorawa a jikin gadon Haris. Yanzun da taji ta baje sai wani bacci-bacci yake neman kamata, amman dole ta tashi tayi sallar azahar. Data idar, tayi zamanta a dakin har karfe biyu tukunna ta fita dan Haris zai sha magani karfe biyun, saida ta dauki magungunan, tayi kitchen ta dauki robar ruwa da kofi ta samu tray ta dora akai taje ta kwankwasa masa daki, ya bude mata "Karfe biyu, zaka sha magani" Tana ganin yanda wani abu ya tattare a goshin shi, sannan ya yamutsa gabaki daya fuskarshi "Magani?" Kai ta daga masa "Kala uku ne, karfe biyu akace zaka sha yau, sai kuma na dare, sai gobe idan Allaah Ya kaimu zaka sha sau uku a rana, harda na safe" Shifa baya kaunar magani, da yake ma Allaah Ya taimake shi saiya dade baiyi rashin lafiya ba, yanzun tunanin shine zai hadiye wannan magungunan har kala uku kawai amai ke neman taso masa "Bana sha, banajin wani ciwo a jikina" Maryama tayi masa wani kallo "Likitan daya rubutu maka yasan dalilin ai, ka dauki ruwan in ballo maka" Ya girgiza mata kai "Ke nifa ba zan sha wani magani ba" Sai ta jinjina masa kai "Ba matsala, in hado maka shayi? Kaga ance ka daina zama da yunwa" Wannan dai zai sha "Eh, amman ba da yawa ba, rabin kofi haka" Ta daga masa kai sannan ta wuce kitchen din, ta gama hada shayin kenan Haris ya shigo, sai ta mika masa "Nagode" Ya furta yana gasa tafin hannunshi da yaji yayi sanyi a jikin kofin shayin, wanka yayi ya sake kaya. Sai ya kara jin karfin jikinshi sosai, Maryama batace komai ba ta bude fridge ta shiga fito da wasu manyan robobi, ta dinga bubbudesu, nama ne na rago da kuma kaji da baisan sanda ta dafasu ba, yaga ta dibi naman ragon ta saka a wata karamar tukunya, sannan ta dauko wata shinkafa da ta sha kayan lambu ta zuba a wata tukunyar daban. Ta rurrufe ta mayar tana janyo wata robar, kallonta kawai yakeyi tanata hidimarta, ya fara kurbar shayin shi a hankali, kamshin abincin da take dumamawa ya cika kitchen din "Shayin nan yayi wani iri" Ya fadi, tun a kurbar farko yaji haka "Bakinka ne, kasan kayi rashin lafiya, bakinka bai gama dawowa dai-dai ba" Cewar Maryama batare data juya ta kalle shi ba, ya sake kurba, yasan in mutum yayi rashin lafiya yana jin bakinshi ba dadi, amman ai jiya ma sau nawa ta hada masa shayi a asibiti "Amman jiya lafiya kalau fa naji shi dana sha" Kaman ba zata amsa ba sai kuma tace "Wani lokacin saika dawo gida ai yake haka" Bai sake magana ba ya cigaba da kurbar shayin, bama zaice ga abinda yakeyi a kitchen din ba da yayi tsaye, saida ta gama hada komai, harda meatpie yagani guda uku. Ta kuma hada abincin ne waje biyu, wanda shinkafar tafi yawa shi ta bashi tana fadin "Dan Allaah ka mikawa maigadi mana" Ya karasa kurbe shayin, ya dan yamutsa fuska saboda wani taste da yaji a karshen, ya ajiye kofin ya karbi babban bowl din data bashi taba dora murfinshi. Fita yayi ya mikawa maigadin, daya dawo saiya sameta a falo tana zaune kan kafet ta kuma kunna kallo, ga abincin nan a gabanta sai kuma lemon kwali data dauko, cikin wanda ma suka dawo dashine daga asibiti, ya zauna kan kujera, saita mika masa kwanon abincin, ya girgiza mata kai "Zakayi loma daya ne ai, ka kuma ci nama guda daya, saika gutsiri meatpie din...ba abinda zai sameka dan kaci abinci" Ya sake girgiza mata kai "Wanda Mami ta kawo ne, abincin da na tabbata itace ta bata lokacinta ta shirya maka shi kala-kala, ta kuma dauko tun daga Kaduna zuwa Kano ka kalli idonta kace mata ba zakaci ba...bakaji komai ba kace mata ba zakaci ba, ai da saika bude ko cokali dayane kayi zataji dadi" Kallonta yakeyi, yanda take maganar, kamar yayi wani gagarumin laifin da bai sani ba sai yanzun da ta sakashi a gaba tana zayyana masa su daya bayan daya "Ka karba kaci kaji, saika kirata a waya ka gaya mata yanda komai yayi dadi" Dan abincin yayi mata dadi, musamman ma meatpie din, shiya shigar mata ido ta fara gutsira, har yanzun tana jin dandanon shi akan harshenta, tun a asibitin bataji dadin yanda yaki cin abincin nan ba, saita dinga hango yanda hankalin Hajja baya taba kwanciya in basu da lafiya, yanda zatayi tsaye a kitchen da kanta ta dafa musu abinda suka fiso tazo ta sakasu a gaba da lallashi har sai sunci sannan hankalinta zai kwanta, ai taso Hajiya Rumanan ta dauki murfin daya daga cikin tsadaddun kulolin nata ta kwada masa. Ya karbi abincin, yayi loma daya kamar yanda tace, ya gutsiri meatpie din "Bakaci naman ba" Tace masa "Nakoshi ne, kuma nama bai dameni ba" Ta karbe kwanon abincinta "Daman meye ma ya dameka kai? In dai abinci ne. Ka tashi kaje ka kirata" Ga mamakin Haris saiya tashi din, ita kuma ta girgiza kanta kawai, inda dantane ai saita zane masa jikinshi akan abinci. Daya tafi dakin, ya dauki wayarshi ya kunna, Hajiya Rumanan ya fara kira, sai kace tana jiranshi bugun farko ta daga "Mami...yanzun muka dawo babu dadewa" Ya fadi "Harka warware sosai? Kaji saukin da zasu sallameka? Naga shekaranjiya kamar jikin naka baiyi kwari bafa" Ya danyi murmushi "Naji sauki sosai, gashi har naci shinkafar da kika kawomun..." Yanda tayi dariya yasan bata yarda ba "Allaah naci, harda meatpie ma, yayi dadi, amman banci naman ba...zuwa anjima dai zan kara meatpie din da shayi" Dariya tayi mai cike da nishadi, a yanda har suka karasa wayar batayi masa fada ko mitar komai ba yasan taji dadi "Zamu sake dawowa duba jikinka... harda Babanka zamu zo shisa kaga ban dawo ba" Ya jinjina mata kai, suka karayin hira ta fada masa Anisa ma tayi bari, baiji dadin labarin ba ko kadan, yace zai kirata. Daya sauke wayar saiya kira Alhaji Mustafa, suka gaisa yana karfin jikin, ya amsa yana dorawa da "Ciniki nakeso muyi Baba" Cikin alamun dariya Alhaji Mustafa yace "Ciniki dai Haris?" Ya daga kanshi kamar yana tare dashi "Motata, dayar motata da take nan gida nake so in siyar maka" Dariyar da Alhaji Mustafa yayi mai sauti ce "Motar da na dauka na baka itace zaka siyar mun yau kuma?" Shima dariyar yayi "Har takardun fa ka bani Baba, kaga ta zama tawa, banaso cinikin ya wuceka ne shisa zan siyar maka" Sukayi dariya a tare "To kudin zan tura maka yanzun ko ya za'ayi" Ya girgiza kai "Inaso a samo mun wata motar ne, mai kyau, karama, ta mata, bansan ko kudin zai isa ba ko sai nayi ciko" Jin shirun da Alhaji Mustafa yayi ne yasa Haris din cewa "Zan siyawa Maryamm ne, inaso zata fara koyon tuki cikin satin nan In Shaa Allaah" Shirun dai Alhaji Mustafa ya sakeyi, badan yanayin numfashin da yake saukewa ba sai Haris yayi zaton kiran ya yanke ne "Na sake applying makaranta, na fada maka daman tun kwanaki, sai dai ba a Italy bane ba, banaso in barta ko da wani abu zai taso babu mota a hannunta ko saita jira wani yazo ya kaita" Numfashi mai nauyi Alhaji Mustafa ya sauke "Ba zaka tafi da ita ba Haris?" A hankali ya amsa "Sai na fara samun makarantar, idan naje nagama komai, na danyi settling, kafin nan anyi mata passport bansan ko tana dashi ba, sai inga yanda za'ayi ta bini ko in dawo mu tafi tare" Da alama zancen ya zauna ma Alhaji Mustafa "Zamu zo sake dubaka daman, sai a taho mata da motar" Haris ya girgiza kanshi "A'a Baba, ka siyi tawa din dai sai muga wadda aka samu ko zanyi ciko" Dan haka kawai yaji bayaso Alhaji Mustafa yace zai bata motar kyauta, tashin dai yake so ya siyar ya sai mata da kudin "Kar in ba 'yata mota kome kake nufi?" Murmushi yayi "Sai dai in zaka kara mata, amman nafison dai ka siyi tawan" Bai ja maganar ba, yace duk yanda ake ciki zai kirashi su sake magana "Dazun Abbanka Sa'idu yake tambayar jikinka, zan tura maka lambarshi saika kira ku gaisa" Ya amsa da "To" Yanajin wani nauyi da baisan daga inda ya taso ba yana danne shi. Ya ajiye wayar akan gado ya shiga bandaki ya dauro alwala dan baiyi sallar azahar ba, kuma yana so ya dan fita yasha iska. Saida ya fara yin sallar, ya tattare dakin nashi ya gyara ko ina, tukunna ya dauki mukullin motarshi da maigadi ya bashi tun dawowarsu, Maryama na inda ya barta a zaune "Fita zanyi, akwai abinda zan taho miki dashi?" Tayi masa kallon mamaki tukunna ta girgiza kanta a hankali tana dorawa da "A dawo lafiya" Shi da ya fito daga asibiti, batasan inda zai dauki kafa ya tafi ba da tsakar ranar, maimakon ya kwanta ko bacci ne yayi ya hutawa ranshi. Tana da sauran dankali tunda ta kula yanaso, shi zata fere ta soya masa da daddare, ai zai sha mamaki, babu surutun da zata zauna tanayi akan garjejen kato kamarshi, maganin da ba zai sha bane zata dinga zuba masa a shayi yana kwankwadewa sai ya kare. Kuma kamar yanda tace ne, da daddare ma haka ta sake hada masa shayin nan da magungunan shi a ciki "Kinsan Allaah ba bakina bane ba, ko madarar ce ta lalace, kisha kiji yayi wani iri" Ta kalle shi, da yake daki ta mika masa komai, yanzun ne ya fito mata daga shi sai gajeran wando da riga mai guntun hannu, dogayen kafafuwanshi na tuna mata da wani tseren gudu da ta taba samu mazan gidansu na kallo, da wani santalelen baki da akace shine wanda yayi na daya "Dan kenya ne, kasan kaman aljanu haka suke da gudun tsiya, nifa dana gansu a wasa nake basu ci" Bambancin shi wancen nashi kafafuwan sunfi na Haris kauri ne, amman haka ta gansu diqildiqil kamar wanda baya wanka da kyau, ta kula bayajin kunyar ta ganshi da gajeran wando "Babu abinda ya samu madara, nima na sha shayin ai, tare na hada mana kuma lafiya lau najita, nace maka bakinka ne" Kai ya girgiza "To kisha kiji mana" Ya mika mata kofin, haka kawai ana zaune lafiya ba zata kurbi wannan shayin ba, ta makale kafada, ya zuba mata wannan idanuwan nashi da batasan ya akayi tace "Maganin da kaqi shane na zuba maka a ciki, kuma in baka sha a shayi ba zaka sha a ruwa, zan narka a duk inda zan iya in baka kasha, idan kaqiya zan kira su Baban Tudun Wada in fada musu maganin da aka baka a asibiti kace ba zaka sha ba" Cikin wani yanayi yace "Maganin ne kika zuba mun a tea Maryamm? Magani?" Ta kuwa daga masa kai "Zan zauna muna jan magana ne dan Allaah? Tunda ba iya danneka zanyi in matse bakinka in dura maka ba" Ya rasa abinda zaiyi sai kawai ya sauke numfashi yace "Ki hadamun wani shayin" Ta kara gyara zamanta "Maganin kuma asararshi za'ayi koya?" Cikin kashedi yace "Maryamm" Ta tura labbanta gaba "To in ballo maka maganin kasha sai in hada maka wani shayin" Da sauri yace "Bana sha" Bai jirata ba ya nufi kitchen, da gudunta ta rufa masa baya, ta tare wajen sink din "Allaah ka shanye shi, kaga zan kira Baba, da gaske nake" Ya harareta "Matsa daga nan, tunda ba zaki hada mun wani ba, zan hada da kaina, dankalina yana hucewa, kuma kaina ya mun nauyi, bana son surutu" Da gaske yake, shayin yake so ya gama sha, ya dan busa wiwin shi ko nadi biyu ne saiya kwanta yaga ko zai samu bacci ya dauke shi. Tazo tana zuba masa magani a cikin shayi saboda karfin hali irin nata, ganin taki matsawa yasa ya kamo hannunta da nufin ya janyeta daga wajen, sai kawai ta bude kafafuwanta tana tirjewa, dayan hannunta ta rike abin sink din, dariya ta kusan kwacewa Haris, gani takeyi tana da karfin da ba zai iya janyeta ba, saiya samu waje ya ajiye kofin shayin, ya saki hannunta ya kamata cancakat yana ajiyeta a gefe. Tana kallon shi ya dauki kofin yana kokarin juye shayin, tayi wuf ta rike masa hannu da nata duka biyun, Abba yace mata sai tayi jarumta, ta kula da Haris, itace babba idan akazo batun lafiyarshi, to da alama Abba gaskiya ya fada, sai tayiwa Haris jan ido yaga da gaske take tukunna. "Bafa zaka zubar dashi ba, sai dai ko ka shanye, ko kuma in ballo maka magungunan ka hadiya..." Mamaki ya kara kama Haris, yayi karamin tsaki yana amfani da karfinshi ya juye shayin "Allaah sai kasha magani zaka hada wani" Cewar Maryama, tana ture duk wani abu da takeji saboda rikon da tayi masa da yanda jikinsu yake ta haduwa, tureta yayi yana nufar inda flask yake da kuma kayan shayin daya gani, dan bata ma mayar dasu wajensu ba, ta bishi, ya juyo yana mata kallon kashedi, bataji ba ta rufa masa baya "In ballo maka maganin?" Yana bude gwangwanin madara yace "Ba zan sha ba" Duk surutun da take ta masa tana fadin "Kaji, dan Allaah, kaji, haba Ganja, minti biyu fa harka hadiye, minti daya ma, ina da iloka wallahi zan sammaka, Mummy ce ta kawomun kuma tayi dadi" Banza yayi yana kyaleta, akwai yanda take furta Ganjan da yake bashi dariya, itama sunan dariya kawai yake bata "Wai meye Ganja dan Allaah? Ni ban taba jin sunan ba" Ta furta, haka kawai takejin dadi data kirashi da Ganja, tun da taji sunan bakinta yake mata kaikayi, kuma yafi tace masa Haris din aiko? Tunda batasan me zata kirashi ba, Ganjan kuma yayi mata dadi, ya rufe gwangwanin daya bude, ya ajiye ya zuba Milo "Maganin fa, kaji...in dauko maka? Kaji? Kana jina fa" Bakinta baiyi shiru ba harya gama hada shayin nashi, da taga yana motsawa saita ruga ta tare kofar kitchen din, saida murmushi ya kwace masa, da jikinshi yayi amfani ya bangajeta yana wucewa, sai yayi tsaye, cak, ba jikinshi kadai ba harda wani abu a cikin kanshi da baisan menene ba, saboda Maryama data zagaya hannuwanta, siraran hannuwanta a kugunshi tana rike shi gam "Allaah ba zaka shiga daki ba sai kasha magani" Muryarshi can kasan makoshi yace "Sakeni" Ta kara karfin matsar da tayi masa tana jan jikinta baya a kokarinta na jan Haris din "Wai meye haka? Ki sakeni nace" Dan shayin hannunshi ya cika kofin ne, kuma yanda yakeji hannuwanshi sun fara rawa, saida shayin ma ya dan zubar masa "Sai kinsa na kone" Da sauri tace "Zaka sha maganin?" Baisan lokacin daya furta "Inalillahi wa ina ilaihi raji'un" Rike shi takeyi tana janshi baya, baiyi tunanin tana da wannan karfin ba, ko jikinshi ne da yakeji kamar ba nashi ba shisa ta samu damar janshi haka "Dawo nan kasha maganinka saika tafi" Bayajin ya taba ganin mai karfin halinta "Jeki kawo" Ta zagaya da kanta batare da ta kalle shi ba tace "Da gaske? In kawo dan Allaah?" Ya harareta "Zan watsa miki shayin nan, ki wuce ki kawomun maganin kafin in fasa" Sakin nashi tayi, tana juyawa ya kurbi shayin da sauri-sauri kaman sau biyar a lokaci daya, kafin ya ruga da gudu zuwa hanyar dakinshi dan bayaso ya zubar a kasa, yaji ta, ta biyo shi, amman kafafuwanshi ai sunfi nata tsayi, yana shiga daki ya rufo kofar ya murza key. Sai dai bai samu ya kurbi shayin nan cikin dadin rai ba, saboda yanda Maryama tayi tsaye bakin kofar tana kwankwasawa tana fadin "Kazo ka bude, Ganja, kaji..." Ya dauka zata gaji da tsayuwa ta tafi, amman bata tafi ba "Allaah anan zan zauna ko zamu kwana saika bude kofar" Haka kawai zuciyarshi ta fada masa zata iya, daya bude kofar sai ya ganta zaune, da magungunan da robar ruwa, tama saka daya daga cikin filon kujerun falonta hankalinta a kwance  kamar tana tsakiyar gado, sai tayi masa murmushi hakoranta a waje "Ga maganin" Ta fadi tana mikewa, karba yayi "Anan zaka tsaya kasha, inaso ingani, wallahi inka koma ciki zama zanyi inta kwankwasawa" Saiya bata ta ballo masa duka magungunan, ya daga kai ya watsa su a baki,  yana jin tsikar kanshi na tashi, yabi da ruwa ya mika mata robar "Haaa mugani" Saida ya bude mata bakin, ta dinga daddashe da kafafuwanta tana so ta hango "Bangani ba, kayi tsayi, ka sunkuyo" Ya biye mata, ta leka ko ina cikin bakinshi "Ko kaifa, saida safe. Allaah Ya kara lafiya" Tana gama maganar ta juya abinta, sai wata kalma da bature yake yawan amfani da ita tazo wa Haris "pest" Maryama is a pest... 26 Yau take cika shekaru goma sha bakwai, a yau dinne kuma tayi wata shida babu wasu 'yan kwanaki a gidan Haris. Wasu watanni da sukazo suka wuce mata da abubuwa mabanbanta, abubuwan da bata taba zato ba. Dan washegarin ranar da aka sallami Haris, Hajiya Rumana sukazo ita da Alhaji Mustafa, Haris bai fada mata zuwan nasu ba, shima yace mata baisan zasu zo ba, haka ta rikice ta rasa abinda zata basu, sai taliya tayi stir fry, Alhaji Mustafa yaci sosai, ya dinga saka mata albarka, amman Hajiya Rumana ko taba abincin batayi ba, ruwa ma da kayanta ta shigo gidan rike a hannu, bata sha wanda Maryaman ta ajiye musu ba, balle kuma ayi tunanin zataci wani abin. Ta hakimce akan kujera tana ta faman hura hanci kamar wadda kunama ta ciza, Haris ne ya zauna kusa da kafarta akan kafet, shima da alama ranar haushin Maryama ne ya shafeshi tunda haka ta dinga amsa shi dai-dai. Suka zo suka wuce, kwana hudu tsakani kuma Haris yace mata Alhaji Mustafa zasu sake zuwa shi da Umma Fadime, su da yake tasan da zuwan nasu, tun ranar tayi wa Haris magana suka fita tare akayo cefane, shinkafa zatayi da miyar kaji sai ta hada salad, tayi tunanin tayi musu wani dan lemo na gida, sai kuma ta fasa ko ba zasu so shi ba. Tun da daddare ta rage aiki, ta dafa namanta, kayan miyar ma ta dafasu, duk saita saka a fridge. "Nace miki ayi order din abinci, kinqi" Cewar Haris daya shiga kitchen din ya dauki ruwa da daddaren "Abincin gida yafi albarka, yanzun sai kaga kudin cefanen nan da mukayo ya shige a order din abincin, kuma ba lallai yayi dadi kamar wanda zakayi a gida ba, ni da zaka taimaka ma ka yanka mun albasa" Yayi wata dariya mai sauti "Ni zan yanka albasa? Ban iya ba..." Kafin ma tace wani abu ya fice ya bar mata kitchen din, sai dai tayi mamaki sosai ganin ba iyasu Umma Fadime bane ba, harda duka yaranta guda shida, Mukhtar ne kawai banda shi, saboda baya kasar, kuma shima sai da ya kira Haris, baya ma kusa da wayar, da yazo yaga lambar kasar waje ya dinga mamakin waye tunda ba lambar Italy bace ko wata kasa da yake da wani, sai yaga text din Mukhtar "Mukhtar ne Hamma, na kira inji ya jikinka ne daman, Baba ya fadamun baka da lafiya, Allaah Yasa kaffara ne" Ya dinga juya sakon nan, da yazo reply ma saiya rasa abinda zaice, yaushe rabon daya sa Mukhtar din a ido balle ma har ace sunyi wata magana, gara ma su Adda Halima tunda Baba ya bashi lambobinsu, sukan kira shi a gaisa. Yanajin dadi, danma maganganun nasu basa tsayi, babu wata shakuwa a tsakani. Sai gashi sunzo su duka, harda yaransu, ita kanta Maryama taji dadi, Haris nata kallon yanda suke rungume juna kamar sun santa tuntuni, saboda baisan akwai shakuwa a tsakaninsu haka ba, lissafin girkinta ne ya sauya tunda sun kara yawa, danma dai tayi miyar ne da niyyar ta ajiye ragowar. Da ta koma kitchen din sai Shatu ta bita, suka kara dora girki, haka suka cika falon nan Maryama najin kewar gidansu na danneta, sosai wani lokacin shirun gidan yake mata yawa, ta riga ta saba da kullum gidansu cikin mutane yake, duk da ba yawo sukeyi ba, banda makaranta fita sai ta zama dole, amman ko fitar za'ayi ma, ita da Khairi ne, wani lokacin ma su da yawa haka za'aje a dawo. Nan kuwa data gama 'yan aikace-aikacenta sai dai tayi kallo, babu inda take zuwa, a ranar sai taji gidan yayi dadi, kamar karsu tafi, kamar ace kwanaki suka zo suyi musu. Tana kallon Alhaji Mustafa da Haris suka fita sallar azahar tare, da suka dawo kuma sai suka tsaya a waje "Ga motar nan an taho mata da ita, takardun da komai suna ciki, ina binka cikon dubu dari biyu da saba'in" Haris yayi murmushi yana kallon motar, kalar ja ce, tayi masa kyau, yasan da bakar kala ma aka daukar mata sai tafi haka kyau "To Baba zan cika, tayi kyau sosai motar" Alhaji Mustafa ya jinjina kai, shiru ya dan gifta a tsakaninsu kafin yace masa "Likitanka ya bamu shawarar kana bukatar rehab, banji dadi ba Haris, saboda kullum mukayi magana ina kara jin yanda hankali yake zauna maka, sai nake kyautata maka zato matuka, nace Haris dina ya girma, babu kalar fargabar da banyi ba bayan na karba maka auren Maryama, da kace mun a Kano zaku zauna zuciyata cike take da tsoro, kullum ina jiran inji ko zaka bani kunya ne..." Haris ya jingina bayanshi da motar da suke tsaye kusa da ita saboda yanda yaji jikinshi ya dauki rawa, zuciyarshi har bugawa takeyi, abu na karshe da yake so ya faru a tsakaninshi da Babanshi a yanzun shine alakar nan tasu da yake riritawa ta samu matsala "Sai naji shiru, sai baka kunyatani ba, dan iya damuwar da take fuskar yarinyar nan randa mukaje asibiti nasan baka bani kunya ba Haris, kuma na yarda ka karbi auren nan da zuciyarka daya...me yasa zakayi mun haka? Idan baka duba yanda zanji ba mahaifiyarka fa? Baka tattalin lafiyarka? Ko bakasan tana da muhimmanci wajen mutane da yawa ba?" Kan Haris a kasa, ai kamar Maryama tayi masa maganganu masu shigen wannan "Bansan ya Rehab suke ba, amman nasan wajene da ake taimakawa mutane masu fama da irin abinda kake fama dashi, haka kuma nasan wajene da babu wanda zai iya taimaka maka in har baka shirya taimakon kanka ba, kome zasuyi maka in baka shirya bari ba inaji ba zasuyi nasara ba..." Batare daya dago ba yace "Kayi hakuri....dan Allaah kayi hakuri" Saboda ya rasa abinda ya kamata ya fada bayan wannan, tsayin rayuwarshi yana jin kamar bai cika ba a idanuwan Alhaji Mustafa, musamman inya gansu shi da Mukhtar, yana da yakinin yanajin cewa Mukhtar kawai ya ishe shi, daya matso kusa yanzun, ya samu irin abinda yayi tunanin Mukhtar ne kadai yake dashi bayaso ya rasa, wannan kusancin da kaunar bayaso ya rasasu. Amman kuma a gefe daya har yanzun baiji yana so ya daina shan wiwi dinshi ba, saboda abubuwa nawa ake sha anaci da suke da illa ga lafiyar jiki kuma sanin hakan baisa an daina ba? Kawai suyi hakuri su fahimce shi, suyi hakuri karsu yi fushi, suyi hakuri karsu canza masa "Banji dadi bane ba, saboda kana cutar da lafiyarka, bawai nace kayi mun wani abu bane" Haris ya sauke wani gajeran numfashi "In kun koma asibitin saiku sake magana da likitan kaji matakan daya kamata, bansan ko zaka so muje tare ba" Sai lokacin ya dago kai da saurin shi "Zanyi magana dashi Baba" Alhaji Mustafa ya jinjina kai, idanuwanshi cike da damuwa "Dan Allaah ka kokarta Haris, a halin yanzun wannan ne kawai nakasunka" Ya jinjina kai, bayaso ya bude bakinshi yayi magana, bayaso yayi karya, bayaso ya fadi abinda baya hango yiwuwarshi, yaji dadi da suka koma cikin gidan, cikin 'yan uwanshi yau da suke ta tsokanar shi, har Aliya na cewa taga yayi haske, girkin Maryama ne ya karbeshi, kuma da Maryaman ta daga kai suka hada ido, baisan meye yasa ta dinga tuntsira dariya tana karawa ba. Tare dashi suka rakasu har saida suka fice daga gidan, kafin su koma cikine kuma Haris ya bata mamaki na farko a aurensu "Motar nan tayi kyau?" Ta sake kallon motar, dan tanata mamakin me yasa basu tafi da ita ba, har hannu ta dan saka ta shafa motar, sabuwa ce dal, daga gani "Tayi kyau sosai, tun dazun nake ta kallo, mota ka kara siye?" Saiya girgiza mata kai "Taki ce, bana ce miki zaki fara koyon tuki ba? Ranar asabar zaki fara zuwa ba" Kallonshi kawai takeyi tana so tagane abinda yace "Ga mukullin? Baba yace takardun suna ciki" Idanuwanta suka dan fito waje alamar mamaki, sai kuma tayi dariya ta girgiza kanta "Ni zaka tsokana da mota Ganja" Shima dariyar yayi "Ba zaki daina kirana da Ganja ba ko?" Ta makale kafadarta tana shigewa cikin gida, saida ya tsaya ya dauki takardun motar, sannan yabi ta cikin gidan, da yake har wanke-wanke saida suka tsaya sukayi tare sannan suka tafi, gidan a gyare yake kamar batayi baki ba. Tana zaune kan kujera, anan ya ajiye mata takardun da mukullin motar ya shige daki abinshi. Sai da ta duba taga sunanta baro-baro a jiki, da mukullin a hannunta, zuciyarta na bugawa ta dira daga kujerar tana nufar dakinshi, bata ko tsaya kwankwasawa ba, ta tura kofar "Wai dan Allaah da gaske kake? Dan Allaah motata ce? Kai ka siyamun?" Ya daga mata kai, ya numfasa ihun da tayi ya hanashi magana, kafin ma yayi wani yunkuri ta ruqunqume shi tana jijjigawa, ta sake shi ta fice daga dakin da gudu, ko a mafarki bata taba hangowa kanta mota ba, mota fa, ita Maryama da mota, ta rasa inda zata saka ranta dan farin ciki, ta sake rugawa cikin gida ta dauko wayarta, kuma sai taga babu wanda ya kamata ya sani sai Alhaji Sa'id, shine mutum na farko da ta kira ta fadawa, sannan ta dinga bin 'yan gidansu daya bayan daya tana gaya musu Haris ya siya mata mota. Sukace mata zasu hadu su saka lokaci suzo suyi mata Allaah Yasa alkhairi. Ranar yanda batayi bacci da kyau ba, shima bata barshi yayi baccin ba, haka zata fito falo saita leka ta window taga ko motar na nan, daga falon kuma dakin shi zatayi ta kwankwasa "Ganja...kayi bacci? Motata na leka inga ko tana nan" Saida ya bude kofar ya rankwasheta saboda wani bacci mai dadi daya fara yaji ta kwankwasa "Idan kika kara kwankwasa mun kofa saina cire miki kunne Maryamm, idan ma kika kara fitowa baki kwanta kinyi bacci ba da asuba zan kira azo a dauke motar" Tana sosa kanta inda ya rankwasheta ta wuce bakinta data tura a gaba, dakyar ta samu tayi bacci, shima asubar fari ta bude ido. Mayar da hankali tayi ta koyi tukin, dan taba Haris mamaki, yanda yake ganinta da rawar kai, baiyi zaton zatayi tukin hankali ba, sai gashi bata yi wata biyu ba ya fara bari tana hawa babban titi, tunda sun fita tare kuma yaga yanda takeyin tukin. Danma bata da wajajen zuwa ne banda gidan Mummy, ko can dinma sau biyu Haris ya barta, na biyun ma Mummyn ce batajin dadi, tayi zazzabi. Da cefanensu ya kare tayi masa magana "Kabani kudin sai inje kasuwa in siyo" Kallonta yayi kaman bata da hankali "Kece zakije kasuwa yin cefane? Salon wani ya tunkudeki ki fadi ki karye ko?" Mamaki ya kamata "To me yasa ka saimun mota idan ba zan dinga zuwa wajeje da ita ba" Batare daya kalleta ba, dan yana aiki a laptop dinshi ne lokacin yace mata "Ki dinga kallo kina jin dadi, randa kike bukatar motar kiyi amfani da ita" Ta rasa gane kanshi da kuma matsalar da yake da ita akan fitarta, da kanshi yace ya yarda da tukinta, rannan da yace mata "Zo muje yawo, kina shan ice cream?" Ita ya bari ta tukasu, yana nuna mata inda zatabi, amman ta fita ita kadai shine matsalarshi "Ya zanyi da cefanen to" Har lokacin hankalinshi na kan aikin da yakeyi yace mata "Zamuje tare, akwai aikin da zanje gobe, ko kawai kiyi list din abubuwan da kike bukata zan taho dashi" Saboda takaici ranar fice masa tayi daga dakin. Haka Khairi tace mata "Allaah Yasa ba irin mazan nan bane masu kullen tsiya Maryama" Itama kuma ta dinga jujjuyawa maganar a ranta, gashi in zasuyi waya sau goma da Khairi zatace mata tayi masa maganar komawa makaranta. Suna hira, ko tace tana masa hira sosai, tunda yakan zauna a falo inya ganta a zaune, wata rana ma da kanshi zaice ta bashi labarin film din da take kallo, ko in yasa hankali yana kallon ya dinga mata tambayoyi. Zancen makarantar ne saita rasa ta inda zatayi masa shi, kuma haka ta dinga bude baki tana mayarwa ta rufe har akayi kusan wata uku da aurensu, kafin wani yammaci sun fita sun dawo, shima gajiya tayi da zama ita kadai ta roke shi su fita ya sai mata ice cream, kuma baiyi musu ba yace mata to. "Inaso in koma makaranta, inyi WAEC dina" Yayi shiru kamar baiji taba, kafin a hankali yace "Me zakiyi da ita? WAEC din?" Ta dan gyara zamanta "Zan koma makaranta mana, idan nayi sai inyi jamb, sai in cigaba da karatuna, inaso in karanta Midwifery" Taga sanda wani abu ya gilma ta cikin idanuwanshi, kafin ya kalleta da idanuwan nan nashi tar yace mata "Aure akayi miki Maryamm, muyi zaman auren kawai" Itama tayi shiru, tanajin yanda idanuwanta suka tara hawaye, tana son karatunta, inta tuna yanda Abba yake alfahari da cewa zata karanta Midwifery tanajin dadi, tana so taga ranar da zata gama karatun nan ta mika masa shaidar gamawa "Me yasa? Me yasa ba zanyi karatun ba" A hankali yace "Haka kawai" Tunda bashi da wani dalili, ko fita yayi akwai wani abu da yakejin ya natsu a kirjinshi da sanin cewa tana can gida, a zaune, ko a kwance, koma dai a yayane tana gidanshi, tunda yake a rayuwarshi aurenta ne abu na farko da aka bashi batare daya nema ba, itace aka miko masa batare da yace yana so ba, kuma akanta yaji yana so ya mallaki abu da dukkan wata ma'ana ta kalmar, a hankali, da duk ranar da zatayi wani abu, maganarta, surutun nan nata da bata gajiya dayi masa, inta hada masa shayi, in tayi masa tayin wani abu da baisan dashi ba, inta kalle shi tace "Ganja..." Cikin murya da yanayin da ita kadai take fada yaji dariya ta kamashi, idan ya siyo mata wani abu yaga idanuwanta sun haska da farin ciki, ko tayi tsallen nan kamar yar karamar yarinya, yanzun da ta fara sabawa dashi, ta saki jiki da yanda yake riketa a duk wata dama da zai samu, takan riko hannunshi, ko in zatayi masa magana, ko tana masa magiya ya dandana wani abu da tayi, kuma ko da zai rantse to ba zaiyi kaffara ba, da taimakon matan waje ne kawai yake danne abinda yakan taso masa akanta, amman duk sanda zai kalli Maryamm He wants to own her! Haka yakeji, batare da wani dalili ba, yana son ya mallaketa shi kadai, ta zamana a karkashin ikonshi shi kadai, kuma watakila da sanda ta bude bakinta tace masa tana son cigaba da karatu ta zabi wani abu ba Midwifery ba, watakila daya mayar da ita makaranta "Duk courses din dake karkashin health line, me yasa midwifery" Ya tambayi Aise "Saboda ina so in taimaki matan da zan iya a tsayin rayuwata, ina so ina wajen ingansu da yaransu rike a hannu, saboda banajin zan rike nawa" Yayi murmushi "Me yasa? Bakyason yara ne" Ta kalle shi "Ina sonsu, amman banajin ina musu son da nake fatan ni in same su" A lokacin baima dauki maganarta da wani muhimmanci ba, kawai gani yakeyi wahalar da kanta zatayi a yanda take da kwakwalwa, ai gara ta tafi inda albashinsu yake da tsoka. Ko danshi duk wani hange da shirye-shiryenshi na yanda manyan kudi zasu dinga shigo masa ne shisa yake yiwa kowa irin wannan fatan? Ko kadan baiji wata matsala akan karatu ko aikin Aise ba. Amman Maryama bayaso yaji tace masa zata fita, to idan yana da matsala da fitarta unguwa wanda bama kullum bane, zai juri fitarta makaranta? Ita kadai? Babu shi? Sannan ma yanda inya kalleta baya ganin abu ko daya da yayi masa kama da Aise yana sama masa natsuwa, ko kayanshi na waje in sukayi yanayi da ita hakura yake dasu, duk yarinyar da zatayi masa yanayi da Aise ko ta yatsun hannuwanta ne baya iya tabata, wani abu ne yakeji yana taso masa, waji abu da yake tokare masa wuya ya hana masa numfashi. Maryama ta zauna a gida, yana da kudin da zai kula da dukkan bukatunta, yanzun haka ba zaune yake ba, aikin daukar hoto yake samu har ma saiya zabi wanda yake so yayi da wanda bayaso, kudi na shigo masa, dan da Alhaji Mustafa ya tura masa da kudi watanshi na farko da auren Maryama ya kirashi yayi masa godiya sannan ya dora da "Baba ka daina turamun kudi, ina samun ayyuka da yawa, ka daina turamun kudi, kasan account daya nake amfani dashi, suna hargitsewa bana gane lissafin abinda nake samu da kuma adadin bukatuna, inaso in fara yin dukkansu da kudin da suke shigo mun, ina so in fara gane kan samu na" Kuma tun daga ranar bai sake tura masa da kudi ba, in ya koma makaranta ma, ba zama zaiyi ba ya tsaya iya karatun, aikin duk daya samu zaiyi kayanshi, zai kula da Maryama, idan akwai wani ma da take so ta kula dashi zaiyi mata wannan. Ta zauna, A karkashin shi, Ya mallaketa shine kawai abinda yake so. Data fadawa Khairi sai tace ta gayawa Abbansu, tasan zai yiwa Haris din magana, tunda a tunanin Khairi idan ma baiyiwa Haris magana ba, zasuyi maganar da Alhaji Mustafa, shikuma zaisa Haris ya barta ta koma makaranta, duk matan gidansu suna makaranta, sai Abban yayi yarjejeniyar za'a barsu su koma makaranta ko da ba zasuyi aiki ba. Wannan kwarin gwiwar shi Maryama ta samu tayi masa magana dashi, yayi shiru har tayi tunanin kiran ya yanke sannan yace mata "Haris dinne yace kuyi zaman aurenku?" Ta daga kai saboda bataso ta bude baki kuka ya kwace mata "To Mairama kiyi hakuri kinji, kiyi wa mijinki biyayya, inda rabo sai kiga ya barki kin koma makarantar" Aikuwa hawayen ne ya zubo mata "Ba zanyi karatun bani Abba? Ba zakayi masa magana ba" Ta karashe kuka na kwace mata "Kiyi hakuri..." Kuka tayima Abban ba dan kadan ba, ya dinga lallashinta da tausasan kalamai yana tuna mata ladan da yake cikin biyayyar aure da kuma biyayyar maganar miji "Ke da zaki samu lahira in kika hakura, wa yake batun wata duniya Mairama?" Tayi shiru tana ajiyar zuciya "Ko bakyaso ki dinga karbar haihuwar matan aljanna?" Maganar ta bata dariya, bai bari ta kashe wayar ba saida ya tabbatar ta warware, ta saki ranta, kuma ta hakuran da gaske, ko da Khairi ma tace ta kwantar da kai tayi dinga masa biyayya tayi dabara kilan ya barta sai ta amsa da "In Shaa Allaah" Amman a kasan ranta tanajin ta hakura da karatun, in ba Haris din bane yazo da kanshi yayi mata maganar, yanda Abbanta yace ta hakura, to ta hakura din. Kawai dai yanzun in ta kai masa shayi dakinshi tana tsayawa ta dinga kallon shi yana aiki da laptop "Wanne irin aikine kakeyi?" Ta taba tambayarshi "Hotunan dana daukane nake gyarawa" Cikin rashin fahimta tace "Wanne irin gyara? Ba da an dauka ba shikenan" Ya girgiza mata kai, yana mata bayani yanda yake tunanin zata fahimta "Naga wajen laptop dinka hudu..." Yace mata "Daya ta lalace, sai an gyara" Kai ta jinjina masa "Da na iya ai da ka barmun daya sai in dinga tayaka" Ya kalleta "Da kin ragemun aiki kuwa, irin wannan hotunan, ba irin wanda nake so in dinga dauka bane ba, kawai aikine, kuma ina son kudin shisa, banajin dadin editing dinsu kwata-kwata" Da sauri tace "Ka koyamun, zan iya Allaah, ko akwai wahala zan iya in ka koyamun" Da taga yana kallonta sai tace masa "Da gaske fa, ka gwada kagani" Ta karasa maganar tana yi masa murmushin nan da dukkan hakoranta suke bayyana, murmushin da ko baya cikin nishadi sai ya sakashi murmusawa shima. Sai ya matsa mata yana fadin "Zauna to" Ta kuwa zauna a gefenshi cike da tarin doki, dan batayi zaton zai yarda ya koya mata ba A wannan ranar, A wannan daren, suka bude wani sabon shafi daya kara shakuwa a tsakaninsu Da yake bata gajiya da bashi mamaki, sai take fahimtar komai, harda wani littafi data dauka a dakinshi take yin rubutu a ciki na abubuwan da yake koya mata, wanda take tunanin zata manta. Ta maida hankali sosai, har yana ce mata "Kinga in kika kware sosai saiki zama editor dina, mu zauna in tsara miki albashi" Tayi masa murmushin nan "Dan Allaah, irin wanda ake ba ma'aikata? Nima idan zan siyi wani abu sai in dinga cewa ina jiran salary ne, kagane irin yanda masu aiki sukeyi" Ya girgiza kai kawai yana dariya. Tana jin dadin abinda yake koya mata din, yana rage mata kadaici, ta samu karin abinyi bayan kallo. Laptop daya yake bar mata in zai fita, sai taita gwada duk wani abu daya nuna mata, inda take da tambaya wata rana rubutawa takeyi dan karma ta manta, Haris baya gajiya da amsa mata wadannan tarin tambayoyin da basa karewa duk rana. A cikin watanni shiddan nan, A cikin abubuwan da suka faru, sunyi fada sau biyu, Kuma in aka tambayi Maryama zatace duka fadan biyu itace da gaskiya, sannan kuma zata kara da fadin itace ta ja fadan... 27 Fada na farko... Kasuwa ya shiga, da list din da tayi masa a hannu, kusan komai ya gama siya, sai dai ta rubuta masa da dankalin hausa, da yaje gurin siyarwar sai suka nuna masa kala biyu, ja da fari "Ai Alhaji jan nan yafi dadi, ya dai danfi farin tsada ne kawai" Mai siyarwar yace masa, ya sake duba list din, bata ce ga kalar wanda take so ba, baya kuma son surutun Maryama, da zai siyi kala biyun, gaba ta saka shi ta dinga masa fada waccen siyayyar "Kai ba komai kake ci ba, ni kadaice fa a gidan, saika kwaso doya mai yawa haka? Yaushe zai kare?" To yanzun sai take rubuta masa adadin yawan da zai siyo mata komai, kuma kwano daya tace na dankalin, ya laluba a aljihunshi ya zaro wayarshi, lokacin ne ya tuna cewa a tsayin watannin da sukayi aure, bashi da lambar wayarta, kuma ya kamata ace yana da lambarta, da yanzun zai kirata ya tambayeta ne kawai, sai ya bar siyan dankalin, ya siyi albasa a wajen mutumin yace masa zai sake dawowa kawai, har sauran abinda bai karasa bama ya barshi ya nufi gida, bayan ya gama shiga da kayayyakin ne ya mikawa Maryama da take tsaye tana jera masa sannu wayarshi "Ki sakamun lambarki" Da ta saka lambar sai ta mika masa, tana kallonshi yana dannawa alamar saving yakeyi, kafin ta jiyo karar wayarta a falo "Kaine ka kira?" Ya daga mata kai kawai, ta wuce zuwa falon ta dauki wayar, data tashi da murmushi a fuskarta tayi saving din lambarshi da Ganja. "Wanne irin dankalin hausa? Sun nuna mun guda biyu, ja da fari, bansan wanne kike so ba shisa ban siya ba nace sai nazo" Taji maganar shi a bayanta, hakan yasa ta juya ta kalle shi "Ja? Dankalin hausan?" Dan bata taba gani ba, batama tabajin akwai shi ba sai yau "Kuma dankalin hausa kace musu kuwa?" Ya kankance idanuwanshi akanta, wani abu data kula yakeyi idan yana so yace mata "Da gaske? Tambayata kikeyi?" Batare da yayi magana ba "To aini ban tabajin jan dankalin hausa bane ba...in dauko hijabina muje tare in ganshi? Kaji? Dan Allaah" Ya girgiza mata kai "Dan Allaah fa, kaji...dan Allaah, kwana nawa banje ko ina ba, kuma rannan kace zan rakaka saika fasa" Ta karasa kamar zatayi kuka "Ni na fasa ko kece baki shirya ba zaki batamun lokaci?" Da yake so takeyi ta bishi sai ta kara marairaicewa "Ai yanzun na shirya, hijabi fa kawai zansa, dan Allaah" Yaja numfashi, shi baima yi niyyar komawa kasuwar a lokacin ba, amman saiya daga mata kai yana kallon yanda ta ruga da gudu zuwa daki, wayarta ma anan kan kujera ta ajiyeta bayan ta fito, hijabin kalar pink ne mai laushi, yayi masa kyau, ya haska fuskarta da take fayau sai vaseline din data shafa a labbanta, ga alamar murmushi nan a fuskar, shine yasa yaga tayi masa kyau, abubuwa irin wannan, kananun abubuwa a tare da ita. Da sukaje kasuwar kuwa sai tace a saka mata jan dankalin rabin kwano, farin ma rabi, tana ta addu'a a ranta Allaah Yasa kar taji jan wani iri tayiwa Haris asarar kudinshi. Shiya rike musu ledojin, tunda taga salak tace tana so, suka siya da yawa, Mummy ta bata dakakken kuli, tunda ta bata shi tazo gida ta juye take hango kwado, kamar ta kirata tace mata ina zata samu zogale saita fasa kuma. Haris ba wani barinta yakeyi tana fita ba, ba zuwa takeyi gidan ta gaishe da ita ba, sai kawai ta dinga dora mata dawainiya? Sun kusa wajen motarsu ne, daga tsallake ta hango mai saida gawasa da ita a saman kai "Gawasa, kaga gawasa..." Ta fadi tana nunawa Haris "Ka saimun dan Allaah" Ya kalli inda take nunawa, ya kalleta "Mai gawasa!" Baisan lokacin da ya kama hannunta yana janyowa ba, ganin wasu maza sun waigo "Meye haka?" Ya tambaya ranshi a bace, yana kuma kallon wannan mazan hadi da watsa musu harara "Kawai saiki yage baki akan hanya wasu suna kallonki" Ya fadi itama yana watsa mata nata kason hararar, ga mai gawasar kuwa yanata waige-waigen neman wanda ya kirashi, kayan ya fara sakawa a mota "Ki shiga mota gani nan zuwa" Sai kuwa tayi yanda yace, da kanshi ya tsallaka ya siya mata gawasar da ko a ido batayi masa kyau ba, tayi wani kaushi kaushi, danma ita zata fere abinta, tunanin da yazo masa kenan, yana karawa da tambayar ko meye ma gawasar? Ko me zatayi da ita oho, yanda Maryama bata wuni zawo a irin abubuwan da yake gani tana gabzawa cikinta yana bashi mamaki. Da ya dawo leda bakace ya mika mata "Ya isa ko a karo" Ta ganta da yawa, gashi ya saka mata manya "A'a, kai ai da yawa ma sosai, nagode. Allaah Ya kara budi" Bai amsa mata ba, kamshin gawasar ya dinga dukanta, ta kasa hakuri ta dauki robar ruwan data gani a motar, ta dibi guda biyu ta wanke ta gilas ta dan kara sama da gilas din, ta gutsira, ga zaqi "Kaji zaqin wannan kuwa? Allaah Yasa sauran ma haka suke, ungo..." Tayi maganar tana mika masa "Banaci, haka zakici da bawon? Ba zaki fere ba?" Ya tambaya da mamaki a muryarshi "Gawasar zan fere?" Ya dan daga mata kafadunshi, sai kawai ta girgiza kanta, abubuwan da Haris bai sani ba suna da yawa, ta gaji da lissafawa, ta dai kara da gawasar. Parking yayi zai siyi fruit, da yake ya samu wajen mutum hudu, shisa ya tsaya a gefe, Maryama da take cin gawasarta a tsanake tana kallon dayan gefen, ta ga wani Balarabe cikin doguwar rigarshi fara qal, gashi nan nashi daya aske yayi low cut baqiqirin, ya kwanta luf, da Maltina a hannunshi yana tsaye a gefen titin, daga cikin motar tana ganin yanda yake wani dorawa-dorawa saboda haske, kamar an ciroshi daga tv an ajiye shi a wajen, ga hancin nan dogo. Kuma da Haris ya shigo motar, taji shigowarshi saita juyo take ce masa "Kalli wancen balaraben, su dai farare sunji dadinsu da kyau...ji hancin shifa" Hannun Haris ya murda mukullin mota a lokacin, amman karar tashin motar bai karasa kunnuwanshi ba bayan maganar da Maryama tayi, tsikar jikinshi yaji ta tashi, wani abu yana tsirga masa, daya kalleta sai yaga ta sake juyawa, inda take kallo shima ya kalla, gayen ne a tsaye, waya ma yakeyi yana murmushi, a idanuwan Haris wasu irin manyan hakora yaga yana dasu na gaba da sukafi na zomo girma, kamar ma nashi a yanda Haris ya gani suna gab da taba habarshi, tunda yake bai taba ganin mummuna irin wannan gayen da yake tsaye ba "Anya akwai munana a cikin farare kuwa?" Maryama ta sake fadi batare data juyo ba, Haris yaji zuciyarshi na bugawa da sauri-sauri kamar zata fito daga kirjinshi, kamar inta fito zatayi hannaye da kafafuwa ta samu wannan gayen da jibga, sai gangar jikinshi ta jibgi Maryama da take cikin motar, sai kawai ya figi motar dan saida Maryama tayi baya, inya tsaya a wajen, a yanda yakeji zai tsaya a wajen ne ya jibgi dan mutane. Kallonshi takeyi da irin gudun da yakeyi da motar, wani abu da ba dabi'arshi ba "Gudu kakeyi fa, kana gudu..." Baiyi mata magana ba, baiko kalleta ba duk yanda ta dinga masa magana a tsorace dan saida ya kusa bugawa wani mai mota kafin Allaah Ya kaisu gida lafiya, ko gama kashe motar baiyi ba ta fito daga ciki tana maida numfashi, ledar gawasarta a hannu, ya bude bayan motar ya kwashi sauran kayan yayi cikin gida ta rufa masa baya, ta samu ya ajiye mata komai anan cikin falo "Lafiyarka kuwa? Niyya kayi ka kashemu kome?" Yanda ya juyo yasa ta matsa baya kadan, dan ta tsorata "Bansani ba, ashe idan kika fita wasu kartin banza kike karewa kallo har kina ganin tsayin hancinsu?" Kuma batasan me yasa ta zabi wannan yanayin tayi dariya ba "Dariya na baki? Dariya zakiyi Maryamm? Kin saka kato a gaba kina kallo shine abin yake baki dariya? Saboda baki da hankali?" Ta girgiza masa kai "Nifa babu wanda nake kallo wallahi, to ina ruwana dasu, shima dan naga farine" Yayi mata wani irin kallo da ba zatace ga fassararshi ba "Fararen maza kadai kike kallo kenan?" Da yake akwai tarin kuruciya da kuma wauta a tare da ita sai ta daga masa kai, ita fararen ne sukeyi mata kyau, in basu ba me zai kaita kallon wasu? "Fararen ai sune masu kyau..." Yaja numfashi, a hankali, ya kuma sauke a hankali "Idan baki tashi daga gabana ba saina kwada miki mari" Kuma da gaske yake, dukan mace na daga cikin abinda bai taba hangowa kanshi ba, to ka daketa kaji dadin me, amman yau, yanajin in taci gaba da magana tsaf zai kwada mata mari, farare take so ashe, shisa bata gajiya da ganin bakinshi, shisa bata taba nuna alamar yayi mata kyau ba, wani zafi yakeji a duka jikinshi, shi bama bakin nashi da take gani bane matsala, yanda take karewa wasu mazan kallo shine yake sakawa yanajin kamar kirjinshi zai rabe biyu. "Sai ka mareni? Haka kawai? To ni me nayi" Ya jinjina kai "Karki tashi daga gabana, kar kuma ki rufe mun baki" Yanda yake kallonta ne yasa ta matsa, yaja tsaki yana rabata ya wuce, to ita me tayi masa? Me tayi zaice zai mareta? Saita cire hijabinta kawai, ta kwashe komai takai kitchen tana ajiyewa inda ya kamata, ta fito zuwa dakinta, alwala tayi tana gabatar da sallar Magriba, data idar kuma sai tayi zamanta a wajen tana danne-danne a waya har akayi isha'i, saida tayi ta fita zuwa kitchen, salak dinta ta dibi rabi, ta yanka ta wanke tas, ta yanka timatiri harda su koren tattasai, tayi kwadon, ta zuba sauran taliyar da tayi da miya, ta dawo falo ta zauna taci kayanta a tsanake. Sai wajen karfe tara, lokacin da tasan Haris na shan shayin shi tukunna ta tashi ta shiga kitchen din, ta dauki kofi kenan taji shigowarshi, baiyi mata magana ba ya dauki wani kofin, ta kalle shi, sai taga shayin yake kokarin hadawa "Yanzun zan hada maka" Ta fadi, amman ko kallonta baiyi ba, ya gama hadawa ya fice daga kitchen din "Ikon Allaah" Tace a fili, amman bataji dadi ba har ranta, dan da sanyin jiki ta fita daga kitchen din, abu kamar wasa, Haris ya daina mata magana, editing dinma in taje dakinshi a rufe yake, gashi baya fitowa falon, haka zata kwankwasa ba zai koyi magana ba balle ya bude mata, kwanansu hudu a haka, taji gidan ya isheta, komai baya mata dadi, ta kuma rasa yanda zatayi, da safe har hawaye tayi tunda yanajin tanata masa magana amman ya wuce ya fita abinshi, ta kasa hakuri, Khairi na kiranta sai hawaye suka balle mata, dan dakyar ta iya ce mata "Baya mun magana, haka kawai ya daina mun magana" Ta karasa cikin sheshheka "Haka kawai ba zai daina miki magana ba Maryama, me kikayi masa? Kunyi fada ne?" Harta girgiza kai, sai ta tuna tun randa suka dawo daga kasuwa ne bai sake kulata ba, ta kwashe komai ta fadawa Khairi "In bashi ba, babu abinda ya faru, banyi masa komai ba" Khairi taja tsaki "Ai nasan baki da hankali daman, amman ban zata zaki iyayin irin haukan nan ba, taya za'ayi ki fadawa mijinki kina kallon fararen maza? Ki kuma nuna masa wani kice yayi miki kyau? Ke yanzun in kuka fita tare sai ya kalli wata ya tabaki yace miki Maryama kinga waccen hadaddiyar ya zakiji?" Sai da ta zabura daga zaman da takeyi, taji zuciyarta ta lailayo wani zagi da bakinta ba zai iya furtawa ba, wani duhu-duhu na neman rufe mata ido "Ashe zan dirza kan yarinya cikin kasa" Khairi tayi murmushi, tana tuna kishi irin na Maryama, kishin nan da Hajja take yawan damuwa akanshi "Na rantse da Allaah sai nayi mata dukan da ba zata sake giftawa ta kusa dashi ba, kafin muyi tashin hankali dashi" Dariya mai sauti Khairi tayi "Dan yaga hadaddiya ya fada miki? To ina ruwanki? Sonshi kikeyi?" Ta girgiza kai, ba sonshi takeyi ba, ai Khairi tafi kowa sanin bason bakaken maza takeyi ba, amman ai ya aureta, mijinta ne, kuma bata hango zama da wani namijin bayanshi ba tun ranar data tako kafarta cikin gidan, kenan an bata Haris, Haris ya riga ya zama nata, ita kuma sanin kowane duk wani abu da yake nata bata son rabashi da kowa, 'yan uwanta ma tana bakin cikin ta bude ido taga suna son wani daban, yanzun kuwa zuciyarta har zafi takeyi "Ni ba sonshi nakeyi ba, amman babu wata banza da zatayi masa kyau muna tare bataji kanta cikin kasa ba" Cikin dariya sosai Khairi tace "Sai kece zaki ga kyan wasu mazan ki gaya masa kuma kiyi tunanin za'a zauna lafiya ko?" Ita dai har yanzun bata ga wani abu ba "Balarabe ne fa, kuma gaskiya na fada ni, meye dan na fadi gaskiya dan Allaah? Shima in zai fadi gaskiya ai ba zaice balarabe bashi da kyau ba, kuma iya kyan nagani, ko magana yayi mun ba kulashi zanyi ba ni da nake da aure..." Fada Khairi tayi mata sosai, tace mata ta dinga kiyaye bakinta kan fadar irin wannan maganganun a gaban Haris, kuma inya dawo taje ta bashi hakuri. Sai dai a maimakon ta bashi hakurin, tunda tasan ko ta kulashi ba amsata zaiyi ba, sai kawai tayi timing din shigarshi kitchen, taje ta fisge kofin daya dauka, tasha gabanshi "Wallahi saika kulani, ka kulani in baka hakuri" Kallon nan da bataso yayi mata "Dan Allaah, kayi hakurin, ai ba zan kara ba, kaji, ka daina fushi dani, dan Allaah nace, ba zan kara ba" Ya girgiza mata kai, dan ko idanuwanshi ya rufe saiya dinga ganinta a motar nan tana karewa wani tiqeqen banza kallo "Ni me zakice mun? Muna tare, ina zaune a gefe kike kallon wani? Da aurena akanki kike kallon wani katon banza?" Da sauri tace "Na daina, ba zan kara ba" Kai ya sake girgizawa "Ai kin daina fita, babu inda zan kara zuwa dake, kema kina cikin gida, ba sai kin fita bane zakije kina kallon maza" Jin maganarshi yasa ta rude, tasan zai iya hanata fitar gabaki daya, kuma babu yanda zatayi "A'a dan Allaah, wallahi ba zan kara ba, dan Allaah kayi hakuri...dan Allaah, ai kaga ban tabayi maka laifi ba sai yanzun, kuma na baka hakuri" Yana ganin hawaye sun cika mata ido, amman takaicin da ya shaka ya kasa barin shi "Dan Allaah kayi hakuri, kaji....dan Allaah fa nace" Ta karasa maganar tana riko hannunshi da nata duka biyun "Ba zan kara ba, dan Allaah kayi hakuri Wani abu ya hargitsa cikin kanshi da yanda ta rike hannuwan nashi, kuma batasan ma tana kara dumtsa yatsunshi ba, ya dan kwana biyu rabonshi da mace, kusan sati biyu, hannuwan Maryama da suka rike nashi sai yaji yana neman susucewa, baisan lokacin daya daga dayan hannun nashi ya sake rike hannunta ba, yanajin laushinsu, yanajin layukan da suke jikin kowanne yatsa, a hankali ya dagasu yana sumbatar bayan hannunta "Me yasa? Me yasa zaki kalli wasu mazan? Saboda ni ba fari bane?" Ya tsinci kanshi da fadi yana saka idanuwanshi cikin nata, kuma kamar wadda ya rike, kamar wadda ya rike da wannan abin na cikin idanuwanshi saita kasa ko kwakkwaran motsi "Ba zan sake ba, na daina, kayi hakuri" Ta fadi kowacce kalma da dukkan zuciyarta, kila abinda ya gani kenan, saiya daga mata kai "Zaki daina fita daga gidan Maryamm, zan iya hanaki daina zuwa ko ina idan na sake gani" Ta daga masa kai da sauri, sai ya jata yana riketa a jikinshi hadi da sauke numfashi, ba kuma karamin kokari yayi ba lokacin daya rabata da jikin nashi, ya kai hannu yana ja mata kunne saida tayi 'yar kara "Ai saina cire kunnen" Ta tura lebenta na kasa, har lokacin akwai alamar hawaye a idanuwanta "Ki hadamun shayi" Murmushi tayi masa, murmushin daya kasa dannewa saida ya mayar mata, yanajin kewarta kamar ya shekara bai ganta ba, kamar bata gabanshi, baima taba sanin zaka iya kewar mutumin da kake gani kullum ba sai yau, sai yanzun da take tsaye tana ta kokarin hada masa shayi, kuma ta zuba komai, ta ajiye kofin zata dauki flask ne, ta bude wani dan bowl tana saka hannu ta dauki dankalin data soya ta mika masa "Ci kaji, jan dankalin ne, iri dayane fa da wancen, kawai wannan yafi zaki" Ganin ya kalleta yasa tace "Dan Allaah kaci kaji, dankaline fa, bashi da nauyi" Saiya karba, yaci, yayi masa dadi, tunda data kwashe saita kara mai, ta barbada maggi da dan yaji, ta yanka albasa ta rufe shi, sai kamshi yakeyi, bata ko tambayeshi ba bayan ta hada shayin ta zuba masa dankalin, yau ya zauna a falon, ya sha shayin suna kallo tare. Kuma da ya gama ci haka ya sauko kasa suka zauna da laptop din da bama karba yakeyi ba yanzun, ko yaushe tana wajenta. Fada na biyu... Da daddare ne ranar, wajen karfe takwas, ta gama maimaita duk wani abu da ya koya mata a satin kan wasu hotuna, sai kawai taji tana so tayi abinda bata tabayi ba, bude tarin folders din dake cikin laptop din tana kallon hotunan cikin kowacce folder, ta bude wajen guda hudu, sai kawai tayi scrolling can kasa, idanuwanta suka tsaya kan wata folder da aka rubuta "Vita Mia" a jiki, sai taji tana so ta bude, hotuna ne a ciki sunfi guda dari, ta bude na farko, zuciyarta tayi wata irin bugawa, ita bakake ba kyau suke mata ba, amman wannan bakar tayi mata kyau, a kallon farko da tayi mata tsaye cikin shigar riga da wando, ta saka hannunta a kumatu tayi dariya har fararen hakoranta sun bayyana tayi mata kyau. Data danna na gaba ma itace, kusan hotuna ashirin, sai kace anyi mata dole, a na gaban ne tayi zaton ma mikewa tayi tsaye, saboda ita da Haris ne, tana kwance a jikinshi suka dauka, ta ga hotuna sunfi guda goma sha duka babu inda bata manne da Haris, ko ita bata tana ruqunqume shi haka ba, sai numfarfashi takeyi, lokacin data bude wani hoto tayi tsaye a kanshi, Haris dinne rike da hannuwan Aise, irin rikon da yayiwa nata hannun, haka kuma ya kai bayan hannunta ya sumbata irin yanda yayi mata, ta tabbata tiririn da takeji inda wani na tsaye kusa da ita watakila da yaga hayakin da take fitarwa, a lokacin ne Haris yayi sallama ya shigo gidan dan ya fita ne, kuma saiya zagayo, yanda ta dago ta kalle shi da idanuwanta da suka canza kala yasa shi kallon screen din laptop din. Wani yanayi ya saukar masa, wani abu da yaketa dannewa, wani abu da bayaso ko a mugun mafarki ya gani, a tunanin shima dannewa yakeyi, Aise da wani kato, Aise a yanda suke a hoton nan da wani "Wacece wannan?" Ta tambaya muryarta na fitowa kamar anja kwano a kasa "Aise" Ya amsa a hankali, sai wani abu ya gilmawa Maryama, itace taga sunanta a jikin yatsanshi a asibiti, Aise, itace kuma suke ta qaqamar juna, itace yake ta dakon hotunanta kala-kala "Wacece Aise?" Ta sake tambaya batare da ta kalle shi ba, yayi shiru, kamar ba zai amsa ba, sai kuma a hankali yace "My ex" Da wani irin yanayi, wai yau shine yake kiran Aise da Ex dinshi, tsohuwar budurwarshi, har sun faru sun kare, ashe zasu kare shi da ita? "Tsohuwar budurwarka, ba tsohuwar matarka ba? Tsohuwar budurwarka itace kuke aikata wannan zunubin kuma harka adana? Akan me? Saboda me?" Ta karasa tana kallonshi kamar zata rufe shi da duka, takai bayan hannunta tana dirje shi a jikin skirt dinta, tana so ta goge sumbar da yayi mata da wannan bakin nashi da yaje ya sumbaci Aise, da bakin bakinshi, kuma kan idonshi tayi baya ta rufe folder din kafin ya hangi zata danna delete, baisa lokacin daya karaso yana rike hannunta ba "Ka sakeni, ajiyar me kakeyi musu to? Ka sakeni in goge..." Take fadi tana kiciniyar kwace hannunta, sai ya dauke lapton din daga cinyarta yana rufeta, ta kuwa mike tana kai mata wawura itama, daya janye hannunshi sai kawai ta saka nata biyun ta hankade shi, abin yazo masa a bazata saida yayi baya, kuma ga madaukakin mamakinshi sai kawai ta dan ware kafarta tana dunkule hannuwanta kamar wadda take a filin dambe "Maryamm" Ya kira da murmushi, kafin dariya ta kwace masa "Dambe zakiyi dani?" Cikin harzuqar da tayi, hawayen bakin cikin yanda ya hadata da kirjin da Aise ta gama kwanciya a jiki tace masa "Eh din, kuma ko da kake ganin ka fini girma ba anan abin yake ba" Ya girgiza kanshi kawai mamakinta na kara kamashi, sai kawai ya juya da niyyar tafiya da lapton din a hannunshi, yaji ta kawowa kafafuwanshi wawura "Na rantse sai an goge hotunan nan... duka sai an goge su" Ya kasa daina dariya yake fadin "Ki sakeni Maryamm, wai saikin kayar damu, meye haka? Ina ruwanki da hotuna na? Me yasa zan goge" Tana kaima kafafuwanshi duka take fadin "Da ruwana, ka aikata Haram, wallahi Mu'allim dinmu in da zai ganka sai yayi maka wa'azin 'yan wuta kala-kala..." Kokarin bambareta yakeyi amman takiya, sai kara rikeshi takayi tana so ta kayar dashi, shisa yasa karfi yaja baya, ya ajiye lapton din da ta sakeshi da sauri zata dauka, ya kamata yana janyota baya, data juya sai kawai ta kamashi da dambe na gaske, da duka karfinta "Me yasa ma zaka sumbaci hannuna da bakin bakinka?" Cewar Maryama wasu sababbin hawayen bakin cikin na zubo mata, yaji abinda tace, sai yayi mata wani irin riko data kasa ko motsin kirki, lokacin ne kuma yayi wani abu da ya kashewa Maryama jiki, ya sumbaceta, ko tace yayi iya bakin kokarinshi wajen ganin sunyi musayar labban ma gabaki daya, yanda duk taso ta kasa kwacewa, sai da ya gaji ya saketa da kanshi "Inalillahi wa ina ilaihi raji'un, ni? Ni? Ganja ni? Ni kayiwa haka?" Take fadi tana maida numfashi, bakin nan fa taganshi dazun, wajen kunnen Aise, dai-dai bayan kunnenta, bakinshi, watakila ma da sauran dauda a wajen tunda ba gane daudar bakaken mutane akeyi ba, nan ya dankara labbanshi ya kwaso dauda kala biyu, ta Aise din da kuma ta zunubi, sannan yazo ya manna mata a nata bakin "Ni Ganja..." Ta sake fadi wani abu na tsirga mata, tabbas ya gama cutarta, batajin yayi Istigfar, balle ya wanke masa dauda daya, shine ya dankara mata akan nata leben "Wannan baqin bakin kasa akan nawa?" Ya daga mata kai yana murmushi "Ki kular dani, kiga adadin wajajen da bakin nawa zai taba yau, da baqin nashi da komai..." Taji hawaye sun zubo mata, sai kuwa ya tako yana rikota "Ka sakeni, wallahi ka sakeni, ka daina tabani da hannuwanka" Jikinshi ya jata sosai "Ganja bana so, bana so" Dan haka kawai yaji yana so ya sake sumbatarta, baisan me taci ba kafin ya dawo, ko menene yana da yaji, akwai sauran dandanon a bakinta, dandanon da ya saka shi jin son cin koma menene, sai dai inya sake komawa ba lallai ya iya mallakar kanshi ba, kawai saiya sumbaci gefen wuyanta yana sakinta "Ni ko?" Ta sake fadi cikin yanayin nan da yakeji yana saka wasu notina kwancewa a bayan kanshi, ya girgiza kai, yana kallon yanda take goge wuyan nata, yayi dariya, ta jinjina kai tana sake matso hawaye, sai kawai ya dauki laptop din ya wuce yana barinta a wajen da tarin takaicinshi, a ranshi yana fadin Wai duk akan taga hotunanshi da Aise? Akan ya sumbaci Aise? Tasan iya inda bakinshi yaje kuwa? 28 Fridge ta bude ta yanko cake dinta ta dora a plate, da ta koma falon ta zauna, tunda kallo take daman, sai ta dinga kallon cake din, Khairi ce ta aiko mata dashi har guda uku, idan kuma akace tun wancen birthday din nata take tara kudin ba zata musa ba, tunda ita dai Khairi tafi gane ta siyi kowanne irin cake a wajen Zainab Kerau (09057866631) kuma sai yayi watanni koya fridge yake da sanyi bai lalace ba, gashi babu ha'inci. Haris kanshi tayi mamaki daya kusan cinye guda daya shi kadai, da kanshi yake zuwa ya diba, kuma da yake taga wanda yafi so din, chocolate cake ne, itama shi tafi so, fushin da takeyi bai hanata bar masa shi ba. Da yake shi yaje tasha ya karbo mata sakon, ko da Khairi ta kirata ranar tace mata "Ki bani lambar mijinki" Babu wani tunani ta tura mata, daya kawo saida yace mata "Yaune birthday dinki? May 3rd, ban sani ba, me yasa baki fadamun ba?" Saita harare shi tana fadin "Tunda kasan na Aise ai lafiya lau" Ya girgiza kanshi batare da yace mata komai ba ya wuce ya kyaleta. Kawai ta rasa yanda zatayi ne, ko zuwa yayi ya gifta ta gabanta sai ta dinga hango shi Aise a jikinshi, idan hannunta ya rike ma sai taji kamar akwai sauran wani abu na Aise a jikin nashi hannun daya hada ya riketa dashi yana shafa mata, ranar daya sumbaceta, batasan adadin brush nawa tayi ba, saida dadashinta ya dinga zafi. Ko baccin kirki kasawa tayi ranar, data rufe idanuwanta sai ta hangoshi da Aise, sai wani abu mai kama da zazzabi ya rufeta. To Khairi da taga ta kwallafa rai akan wannan saurayin nata bayan tace yana da mata ya zatayi? Anya ita zata iya auren mai mata kuwa? Watakila idan itace zata shiga zata samu sauki, amman tunanin ace wata zata shigo mata gidan miji sai takejin jiri daga kwancen da take. Ko da Hajja take yawan magana akan kishinta tana ce mata "Maryama idan kinyi sallah ki dinga addu'a kinji, kice Allaah Ya sassauta miki kishin da kike dashi, Allaah Yasa karya zame miki halaka, Allaah Karya jarabceki ta sanadin shi" Tanayi din, duk da bata gane dalilin da yasa Hajjan take yawan ce mata ta dingayi ba, ita wanne kishine da ita? Dan batason wasu su kwace mata 'yan uwa? Bataso taga suna fifita soyayayar wasu akan tata? Ko dan gabaki daya ma so takeyi su tattara duk wani so da suke dashi akanta ita kadai? Laifi ne? Amman a ranar da taga hotunan nan ta gane daya daga cikin dalilan da yasa Hajja ke sakata yin addu'ar. A hakanma tanajin dan ba auren soyayya sukayi da Haris ba, ita ba sonshi takeyi ba, amman ai mijinta ne, nata ne, batason kowacce mace a kusa dashi tunda nata ne. Babban abinda yayi mata tsaye ma da yaki goge hotunan, me yakeyi dasu? Me zaiyi dasu? Sakasu yakeyi a gaba ya dinga kallo yana debewa kanshi kewarta mana, wani tunanin ya bata amsa, yana sakata tashi zaune daga kwanciyar da takeyi. Ko randa ya shigo gidanma ya ganta tana cin cake din, tasan dan tayi magana ne yasa shi daukar plate din yana kuma gutsira da cokalin da yake ciki, saima ya shige dashi daki, to tasan dadi yayi masa shisa yake ta kara diba "Wai Maryamm ni kika daina yiwa magana?" Tambayar da yayi mata kenan da safe "Ba kaqi goge hotunan ba? Kafi so zunubinka na karuwa duk kallon da kayi, to ni me kake so ince maka?" Shine amsar da ta bashi kamar zata tashi da mauje shi saboda takaicin daya cika mata ciki. Ficewa yayi batare da ya kara cewa komai ba, bai dawo gidan ba sai bayan Magriba, yana ta shige da fice yana daukar wasu manyan abubuwa da sukayi mata kama da frames, amman an nade kowannensu da takarda ta yanda ba zakasan menene a ciki ba. Ita dai sallar isha'i ta gabatar, taxi abincinta tayi zamanta a falo, duk da kallon ba sosai take fahimtarshi ba, kunnuwanta da hankalinta kacokan yana dakon fitowar Haris ne, tasan zaizo ya hada shayin da ta daina hada masa. Tana jin bude kofarshi, daya fito ba kitchen yayi ba, nan falon yazo ya sameta kan kujera ya kama hannunta, tayi kokarin fisgewa, amman rikon da yayi mata bana wasa bane shisa ta hakura ta mike kamar yanda yake so, janta yayi har dakinshi. Da farko dariya ta bashi, harya kwanta ma ranar dariya ya dingayi, na karfin halin Maryama da kuma rikicinta. A gefe daya akwai wani abu mai nauyin gaske da ya danne masa zuciya da wannan hotunan nasu da Aise, kuma sai da ya bisu dayan bayan daya ya kalla, abinda tun ranar daya baro Italy bai kara barin kanshi yayi ba, ya kuwa kasa bacci, saboda yana tunanin zata kwanta a jikin wani bashi ba, wani daban zai riketa, hannuwanshi zaije har inda nashi a mafarkai kawai suka taba kaiwa. Amman wannan shirun na Maryama da ta tsiri yi masa sai ya dame shi, ya hana masa sukunin kirki, da ya fito take tsuke girarta da take a wargatse, kamar da gangan take saka hannu tana hargitsata, dan inya kalla ya dinga lissafin yanda zaisa hannunshi ya gyara mata gashin. Wani lokacin kuma baki take murgudawa, inda tasan yanda yake kokari wajen rike kanshi intayi hakan data taimaka musu ta daina. Ko ta harareshi kamar idanuwanta zasu fado "Ki hadamun shayi" Yace mata, ta murguda bakinta tana gyara kwanciya, kuma ya jira yakai na minti talatin, daya fito ma bata falon, sai shi ya hada da kanshi. To tun shekaranjiya ma ruwan zafine a flask din, zallan ruwan zafin babu komai, babu wannan spices din masu kamshi da ta saba masa da dandanonsu. Yau kam ya gaji da fushin, ya gaji da rikicinta. Har dakinshi ya jata, ya dauko laptop din da take a kunne, ya zaunar da ita gefen gadonshi yanajin yanda take maida numfashi, kan cinyarta ya dora laptop din, data duba sai taga yana kan wannan folder din, folder din hotunansu shi da Aise "Ki goge da kanki, ki goge ki daina mun rigima Maryamm" Tayi masa wani kallo "Bayan ka gama yin copying a wani wajen" Shima kallon nata yakeyi, tunanin yayi copying ko kusa baizo masa ba, yaso ya goge da kanshi ne ya kasa, shisa ma yaje ya janyota, ganin hotunan wahalar masa da zuciya sukeyi ba kadan ba. Inta goge din zata taimaka masa "Me yasa zanyi haka?" Ta janye idanuwanta daga cikin nashi "Su kadaine, babu wasu a ko ina" A yanayin muryarshi ta karanci gaskiyarshi, yatsanta har rawa yakeyi lokacin da ta goge, ta koma recycling bin kamar yanda ya nuna mata, tabi ta goge acan "Shikenan?" Ya tambaya, ta tsinci kanta da daga masa kai, dan wani abu daya danne mata kirji ya daga, tana gogewa taji kamar iska na shiga kofofin jikinta da batasan lokacin da suka toshe ba "Zan samu shayin yau?" A kunyace tayi murmushi "Bari in hado maka" Ya sauke numfashi mai sauti "Da sauran cake din nan in akwai dan Allaah, zan kira Adda Khairi saimu kara siya ko ina ta siye shi, ayi mana da yawa ko?" Kai ta daga masa tana rufe laptop din ta ajiye hadi da mikewa, kitchen ta nufa, ta dan dauki lokaci saboda saida ta dafa shayin sannan, data kawo masa ya karba, ya sake juyawa, kamshin ya dake shi "Dan Allaah ko munyi fada ki dinga hadamun shayi, ko ki dafamun irin wannan sai in hada da kaina" Yanda yayi maganar saiya bata dariya "Kinji" Ta daga masa kai, ta kama hannun kofar yace mata "Ina zakije?" Da mamaki ta kalle shi "Kallo nakeyi" Da sigar umarni yace "No...ki zauna, anan, ki zauna in sha shayina sai muyi editing wasu hotuna" Ganin tana kallonshi yasa shi dan kankance mata idanuwanshi yana dorawa da "Please..." Batayi musu ba, tasan kan gadonshi zai zauna, ita saita zauna a kasa, kan kafet din dakin, yanda ta saba in dai ta shiga, sai dai shima ya biyota kasan yanda yayi yanzun. Ya gaji dayi mata tayin ta zauna akan gadon. Yana shan shayin yana nuna mata hotunan a dayar laptop dinshi, na bikine, daga ganin bikin kuma kasan na masu hannu da shuni ne, sai kallo takeyi, su dai masu kudi komai nasu ya fita daban, komai nasu a tsare, dinner ce, kaf babu wani da yayi kamar bai kamata ace yana wajen ba, haka shigar kowa ta burge "Su masu kudi sai kaga dinner dinsu tayi kyau, tunda basu da dangi 'yan kauye da zasu zo su bata wajen" Dariya Haris yayi "Suka ce miki? Akwai wanda basu da kauye ne" Ta dan kalle shi "Kuma kuna da kauye ne?" Idanma suna dashi bai sanshi ba, bai taba zuwa ba, rayuwarshi duka tsakanin Kaduna, Abuja sai Maiduguri ne, sai kuma Kano yanzun, shisa ya zabi ya amsa da wata tambayar "Ke baku dasu?" Aikuwa da sauri tace "Muna dasu fa, da yawa sosai, sai dai suna da kirki, in zasu zo gida zaka ga sun kawo mana abubuwan kauye da yawa, harda su goruba ma suna kawo mana" Yayi shiru yana tunanin yanda ita gorubar take, yanajinta, amman bayajin ya taba gani, daya gama shanye shayin, saiya tashi ya fita da komai da kanshi ya bar Maryama a dakin, lokacin daya dawo ya zauna sai yace mata "Kinata fushi dani, baki bari na tayaki murnar birthday ba, shekara nawa kika cika?" Ta gyara zamanta "Sha bakwai" Ya kalleta kamar bai yarda ba "Anya? Ba sha biyar ba?" Da sauri tace "Sha biyar kuma, haba dai, ni da na wuce rabin talatin yanzun, inafa kusa da ashirin ne" Lissafin nata ya bashi dariya "Da zan baki gift, amman na fasa, ladan dafamun tsuran ruwan zafi da kikayi jiya da shekaranjiya" Ashe ya kula, tayine dan yayi mata magana, ganin shima din ya shareta yanda ta shareshi a kwana biyun, har cake din taso ta cinye, mai chocolate din, saita kasa. "Yi hakuri, ai mun shirya yanzun, ina gift din? Menene?" Dan kuwa tana son kyauta, tana son kyautar bazata matuka "Aina fasa" Wannan magiyar yake so yaji tayi, kamar yarinya yar shekaru hudu in tana so ayi mata abu, kyau takeyi masa, yaso ta riko hannunshi, da kanta, yanda takeyi in tana rokonshi abu, amman batayi ba, ya kasa cigaba da hakuri yace mata "Gasu can, tashi ki dauko" Wannan frames dinne daya shigo dasu yau, guda goma ne a yanda Maryama ta lissafa su bayan ya nuna mata, sai dai manya ne, duk ya jingina su da bangon dakin, taji da nauyi, maimakon ta dauka takai inda yake, sai kawai ta tsugunna a wajen, ta janyo daya ta fara yage takardar da aka nade shi da ita. Hotonta ne, da kanta da babu kitso, ta kwance ranar, taji kwiyar zuwa saloon su wanke mata acan suyi mata wani kitson yanda takeyi, sai kawai ta wanke shi a gida, da yake a cike yake sosai, ta kasa tajewa da kyau, daya bushe sai yayi mata tudu, abaya ce a jikinta baka, dankwalin abayar ne ta daura ya zame, saita barshi kawai ta nemi wata farar hula da itama ta dinga zame mata saboda mai santsi ce, ga gashin nata a cike. Haris ya dawo daga aikine, ya zauna a falon, ita waya take dannawa tana amsa sakon Khairi, ko kadan bata ga lokacin daya daga camera din daya fito da ita yanata wasa da ita ba balle sanda yayi mata hoton, yayi kusa dai ta yanda kafadunta ne zuwa sama kawai, gashi da girma, har tana iya ganin kwallin da ta saka na ranar ya fito radau dashi, duk da ya saka shi a black and white, batajin ta taba yin wani hoto da yayi mata kyan wannan, itace dai a jiki, amman ta kasa daina kallo. Dakyar ta ajiyeshi a gefe a hankali, kamar mai tsoron wani abu ya same shi, saita dauko wani ta bude, a kwance take, akan kujera one sitter, ta saka hannunta ta rufe idanuwanta dashi cikin son ragewa kanta hasken dakin dan bacci takeyi, dayan hannun ma ta dorashi akan wannan din. Shi kana ganin alamun kanta, da wani sashi na fuskarta, amman hannuwanta su suka cika hoton, kuma ta kula da muhimmancin daya bayar wajen editing din hannuwan nata, kamar maison fito mata da abinda bata taba gani ba, haka ta bisu daya bayan daya, tana budewa, tana kallo, tana son karantar labarin da taga kamar kowanne hoto yana son bata, amman ta kasa, Haris kuma ita yake kallo, yanayinta nayi masa dadi har zuciyarshi. Ranar farko daya dauketa hoto, tana bacci ne, washegarin ranar da taje gidan Mummy, anyi mata lalle a yatsunta duka goman, jan lalle, ya shigo harya wuce ya dawo ya dauka. Haka ya saka hoton a gaba bayan yayi editing yana son gane meye a jikin wannan siraran yatsun nata, wannan siraran hannayen da bai saba gani a jikin na sauran mata ba, ko faratan ne, farare dasu, dogaye, ko kuma yanda suke a yanke ko da yaushe ne sabanin sauran da ko ba suyi fixing ba to sun tara oho? Bayajin ya taba aikin wasu hotuna da suka sakashi nishadi kwatankwacin na Maryama, yanajin kuma yanda yake so ya kara daukar wasu, masu yawa, ya adana wannan kananun abubuwan da camera dinshi ce kawai take nuna masa, 'yan details din nan, scars din da suke son bacewa tare da lokacin a jikin hannuwanta, wani a gefen wuyanta, kananun abubuwa da inya kalleta saiya tsinci kanshi da yawatawa da idanuwanshi yana nemansu. Yanda ta dauki frames biyu tana mikewa yasa shi fadin "Ina zakije?" Ta dan juyo "Dakina zan kai...ka tayani mu kwashe duka...sunyi kyau, duka zan jera" Sai taga ya girgiza kanshi "Ai gift din naki iya kigani ne ki ajiyemun kayana, waye yace zaki iya dauke su daga dakin nan?" Da mamaki take kallonshi, dan bata gane ta ajiye masa kayanshi ba, hotunan nata ne suka zama kayanshi? Kuma saiya kara sakata kallonshi daya taso ya karbe na hannunta, ya sama ma kowanne waje a cikin dakin, a kasa ya ajiye yana jingina su da bangwayen dakin, cikin wani irin tsari da yayi mata kyau "Kingani, kowanne yana da wajenshi..." Wani abu da bashi da suna ya saukar mata "Haka ake bada gift? Hotunana ne fa" Ya hade space din da yake tsakaninsu, ta bayanta ya zagaya hannuwanshi yana riketa, kanshi a kafadarta, tanajin yanda yayi mata rumfa kamar mai shirin mayar da ita cikinshi "Ke din gabaki daya ta wacece?" Ya tambaya a hankali, amman sautin ya karade ko ina na jikinta saboda kamar cikin kunnenta yayi maganar "An bani ke ko kin manta? Ke din duka tawa ce, sai hotunanki ne zasu kasa zama mallakina Maryamm?" Tsikar jikinta ta tashi, tanajin shige da ficen numfashinshi, haka yake so, haka jikinshi gabaki daya yake muradi, ya riketa, yaji cewa tashi ce, rikon ya sake tabbatar masa da cewa an bashi ita His to own Wannan kalmomin uku da yake neman fassararsu ta bace masa bat "Anan zaki kwana, anan zamu kwana" Kuma yanda jikinta ya mutu gabaki daya saita kasa wani yunkuri, ji takeyi kamar ma daukarta yayi gabaki daya ya ajiyeta akan gadonshi, ya kuma bita kan gadon yana kwanciya, ko tace shi akan gadon tunda ita dai hannunta da wani sashi na hakarkarinta ne taji ya hadu da katifar, amman gabaki dayanta a jikin Haris take, yayi mata wani irin riko kamar ya kama barauniya, kamar yana tunanin inya sassauta zata subuce masa "Ka matseni, ya zanyi bacci a haka" Tayi karfin halin furtawa, yama zatayi bacci gabaki dayanta a jikin Haris? A daki daya dashi? Akan gado daya dashi? "Zaki saba" Ya furta a hankali saboda kamshin humrar data shafa a wuyanta da ya kara cika masa hanci yana saukar masa da wata irin natsuwa, ya rasa yanda za'ayi ace riketa kawai yana neman saka shi bacci a lokaci daya kuma yana masa barazana da wannan baccin? Ya za'ayi yarinya kamar Maryama ace itace take sakashi jin emotions fiye da kala daya haka? Me yasa ma tuntuni ya saka mata ido? Me yake jira? Me yasa tuntuni bai daukota ya kawota dakinshi ba? Mutsu-mutsu takeyi, tana son zamewa, ya sake riketa gam "Stop...stop moving" A hankali yayi maganar, muryarshi na karasawa kunnuwanta kamar yayi mata magana daga nesa, amman akwai wani yanayi a cikinta mai kama da kashedi, mai kama da roko da yasa ta daina kiciniyar da takeyi "Allaah ka matseni" Ta sake fadi, gabaki daya a takure take, banda bugun zuciyarta babu wani abu da take jinshi a sake a irin rikon da Haris yayi mata "Zaki saba" Ya sake maimaitawa "Zaki saba Maryamm" Kuma kamar yana duba, Kwana nawa ya dauketa? Bata lissafa ba, amman anya an dade da yawa? An dade kafin ta saba din kamar yanda yace...! 29 Ya dauka ta hakura, tun jiyan, tunda har tayi bacci yanajin yanda take sauke ajiyar zuciya, kuka tayi har saida yaji tsoro "To me yasa ba zamu tafi tare ba? Ni kadai zan zauna?" Yanajin tayi masa tambayar nan yafi a kirga, duk da tunda ya tsaida ranar tafiya, kuma daga bangarenta babu wanda zaizo ya zauna da ita, aka yanke shawarar samo mata mai aiki. Babbace aka samo, dan zatayi shekara talatin da kusan bakwai, mijinta ne ya rasu ya barta da yara har biyar. Daga ganin matar da tace sunanta Sadiya, tun a jiyan da tazo kuma Maryama ta lankaya mata Mama Sadiya, dan tana tunanin zata iya haifarta. Haris ya dauka shikenan ta hakura, kukan ya kare, ya fada mata za'ayi mata passport, kuma za'a fara cuku-cukun yanda za'ayi ta bishi. Sai dai fa a wajen Maryama ba haka abin yake ba, wani irin sabone Haris yayi mata da kanshi a watanni biyun nan da suka kara ya tashi takwas da aurensu. A jikinshi take kwana, sannan haka kawai ma in yana gidan duk wata dama da zai riketa baya bari ta subuce masa, shima har mamakin kanshi yakeyi, na irin yanda ya saba da ita haka, yanda yakejin kamar ya sakata a daya daga cikin jakunkunanshi su tafi tare. Yanzun da ya dauki jaka ta rike masa hannu tana kuka sai yakejin daman bai hakura da ita ba da safen nan, da ya bata dalili fiye dana tafiyarshi da zatayi kukan, amman saura mintina talatin jirginsu ya tashi, tun dazun ya kamata ya tafi, ta dagula masa lissafi "Zamuyi waya kullum fa Maryamm, dan Allaah, ya zan tafi kina wannan kukan? Ni ya kike so inyi" Taja hanci, ita ina ta sani? Ya fasa tafiyar kawai, ko ya jirata ko suyi zamansu, fuskarta ya rike cikin hannuwanshi, ya kara sumbatarta a karo na babu adadi daga wayewar gari zuwa lokacin, ya dauki dayar jakarshi, tunda ya saka sauran a motar Lalaye da yake jiranshi a waje, haka ya kauda kai ya bambare hannun Maryama ya fice batare da ta sake juyowa ba, inya tsaya tabbas zai rasa jirgin, zai kasa tafiya ne ya tsaya lallashinta. Dankwalin da babu a kanta ne ya hanata binshi waje, duk da tun da yake kai jakunkuna da zata fita ya hanata "Bana ce miki Lalaye bane zai kaini airport? Yana waje cikin mota, ya za'ayi ki fita" Ta fita ya ganta, yanda fuskarta din nan take cike da rauni, ga hawaye ne sababbi da wanda suka bushe, taya wani namiji zai ganar masa ita a haka? Maryama kuwa tunda ta koma dakinta, ko abinci bataci ba, da Mama Sadiya ma ta kwankwasa mata kofa haka tace kanta ne yake ciwo babu abinda zataci, bata fito ba sai bayan da tayi sallar isha'i. Agogo kawai take dubawa, tunda Haris yace mata kusan kwana daya ne daga nan Kano, dole saiya sauka zai kirata. A daren bacci barawo ne ya iya daukarta, dakinta ta kwanta, tanajin in taje dakinshi kewarshi ce zata sake danneta. Amman da yake komin yanda zai qure musu AC, dumin jikinshi yana hana mata wani tasiri a wajen Maryama, yau duk inda ta juya sai taji shi karara, bargonta kuma ba dumi daya suke fitarwa da Haris ba. Washegari kuwa karar wayarta ce ta tasheta daga baccin data koma bayan sallar asuba "Ganja" Ta fadi tana kara rike wayar kamar zai fito ya rungumeta yanda ya saba "Na sauka Maryamm, nagaji sosai, nagaji, yunwa nakeji" Da sauri tace masa "Baka siyi shayi ba?" Ya amsa da "Babu dadi, ba naki bane ba" Ta saka masa tea spice din, taji hawaye ya cika mata idanuwa "Ka dafa to, na saka maka tea spice din a cikin kayan, ka manta?" Zata rantse kai Haris ya girgiza "Na sani, ai hotel na kama, sai na gama hidimar makaranta duka zan samu waje" Ta sauke numfashi "To ka daure kasha a haka, ba shayi kadai ba kuma, kaci wani abu" Kai ya daga, bai amsa ba, shisa tasan kai ya daga "Kuma karka sha wiwi, dan Allaah, kaji? Nasan kana fita kasha kullum, kana sha har a bandaki, ban maka magana ba tunda naga kana boyemun, kuma Mu'allim yace wanda suke boyewa in suna aikata abinda bai kamata ba ana saka musu ran zasu bari, saboda suna jin kunya, dan Allaah karka sha" Ta karasa muryarta na rawa "Maryamm..." Ya kira a hankali "Dan Allaah" Ta sakeyin maganar cikin sigar roko, babu yanda batayi dashi ba su koma asibiti kamar yanda akace yace mata ba zaije ba, kamar takai kararshi saita kasa, saboda batasan ta inda zata fara ba, kar ayi masa fada. "Kaji...dan Allaah" Ya sauke numfashi "Banyi alkawari ba, amman zan rage, zanyi kokari in rage" Da sanyi a muryarta tace "Hakanma nagode, in kana ragewa a hankali zaka daina...kaje kasha shayin saika huta sosai" Tanajin gajiya har a muryarshi "To, amman zan kara kiranki, mu nan dare ne ma, zan kara jin muryarki sai in kwanta" Itace ta daga masa kan wannan karin, muryarshi ta bata karfin gwiwar tashi tayi wanka, taji dadin jikinta, ta fita falon suka gaisa da Mama Sadiya, data bita kitchen bayan ta shiga, tana kokarin karbar doyar data dauko, nan suka dinga musu dan Maryama taki bata, bata ga ta inda zata iya sakar mata aiki alhalin lafiyarta kalau ba, ita kunya ma taji "Dan Allaah Mama kibari zan fere" Haka ta hakura dole sukayi aikin tare, ta kara nuna mata komai da cewar ko da bata tashi da wuri ba sai ta karya abinta. Matar ta kwanta mata a rai, daga gani ba zatayi matsala ba, kuma bata da matsalar, dan sosai suke zamansu da Maryama, kafin ta fito ta gyara ko ina, tare suke girki, suyita hira tana ba Maryama labarin kauyen da sukayi rayuwa ita da mijinta, wani kauye ne na Inyamurai can yankin Calabar, kauyen mai cike da abubuwan mamaki, haka Maryama zata dinga tunani. Wata rana taji tsoro ya shigeta ainun. Akwai tashin hankali ace kana zaune da mijinka sai mutuwa tazo ta rabaku, har tausayin Mama Sadiya takeyi, ta dinga tunanin to kewarshi bata hanata sukuni? Ko dan Allaah Yana saukarwa da bayinShi Rahma ta hanyar mantuwa da kuma dangana. Kullum sai suyi waya babu adadi ita da Haris, amman kewarshi nukurkusarta takeyi ba kadan ba. Ya dai saka anzo har gida, ita da Mama Sadiya suka tafi ma akaje inda za'ayi mata passport din, Haris babu kashedin da baiyi mata ba "Duk wanda yayi miki wata magana data wuce ta abinda kikaje yi ki kirani, karki kalli kowa, in aka cika kallonki kibar wajen ki sake wani, ki zauna kusa da Mama Sadiya kinji?" Ita dai da to ta dinga amsa shi. Haka a wajenma ya dinga faman kiranta, dakyar suka gama abinda zasuyi suka dawo gida tukunna ya barta ta numfasa. A wannan tsakanin ne kuma Minal ta haihu, yayar Khairi. Haihuwar tayiwa Maryama dadi, tunda tasan duk su Adda Zahra zasu zo suna, harda Khairi. Tun ranar take fadawa Haris anyi haihuwa "Yarinyar Mummy ce itama...inaso inje barka, inga baby" Ta fada masa, sai yace mata "Ba za'ayi suna ba?" Tunda yasan ana taron suna idan anyi haihuwa, ta daga kai "Eh za'ayi, su Adda Zahra ma duk zasuzo" Ta karasa cike da zumudi "Me zaki kai? Mace ta haifa ko?" Haris din ya tambaya, ita tunanin abinda zata kai ma baizo mata ba "Nima ban sani ba, banyi tunanin ba, gashi gobe idan Allaah Ya kaimu nake so inje barkar, daman Mama Sadiya tace zataje gida ta duba yaranta, ko kawai in kwana gidan Mummy?" Da saurin shi yace "Saboda baki da hankali? Sai kawai kije wani gida ki kwana, ga gidanki, sau daya zaki fita gaskiya, sai dai ko kije barkar, ko kije sunan, zansa a kawo miki kayan da zaki kai musu" Ta dauka wasa Haris yakeyi, da gaske hanata yayi, har kuka tayi masa tunda tasan bai kamata ace ya hanata zuwa abu irin wannan ba, sai kawai ya kashe kiranma gabaki daya, kuma daya kira zata dasa masa magiya sai ya sake kashe wayar, haka ya dingayi saida ta hakura bayan ta gayawa Khairi tana share hawaye "Sai kiyi hakuri tunda inda Allaah Ya kaiki kenan, muma ana gobe suna zamu taho In Shaa Allaah" Ta dingajin kunyar Mummy, da yake sun saba waya, tana yawan kira ta duba lafiyarta, itama kuma tana kira ta gaishe da ita. Danma haihuwa ta uku ce Minal din tayi, duk da haka taji babu dadi, an kawo kaya, saida tayi mamakin yawansu da kuma tarin tarkacen da ta dinga budewa tanata kallo, komai ya burgeta, kayan jarirai akwai kyau, batasan.ya akayi bata taba ganin hakan ba sai yau, ko dan basu taba zuwa hannunta haka bane ba? Anan gidanta su Adda Zahra suka sauka, ta rasa inda zata sakasu don farin ciki, komai da take dashi ta dinga kwasowa tana kawo musu "Wallahi nayi kewarku Adda, kamar na shekara irin biyar banganku....ashe haka nake sonku da yawa bansani ba?" Suka dingayi mata dariya, kuma basu tashi gaya mata da Hajja akazo ba sai da daddare "Kai dan Allaah, kai dan Allaah Adda" Ta kira Hajjan harda kukanta "Yanzun Hajja ba zakizo kinganni ba, ba zaki zo gidana ba" Tasan bata bakinta takeyi, dan zaka rantse Hajja irin fulanin dajin nan ce saboda kunya da kawaicinta, gidajensu Adda Zahra ma zasu iya kirga sau nawa ta taka, shima a bisa lalura, ko haihuwa sukayi sai dai a biyota da yaran nan tazo ta gansu. Taji kamar ba zata iya hakuri gari ya waye ba, Haris na kiranta tace masa "Ashe da Hajja akazo, tana gidan Mummy, dan Allaah inje in ganta tun yau? Ba zan dade ba wallahi, sai muje ni da wani cikinsu Adda" Ya danyi shiru kafin ya amsa da "Dare ne yanzun anan Maryamm, dare yayi kiyi hakuri sai gobe, sai ki fita da wuri, kuma saiki wuni sai yamma wajen karfe hudu haka ki dawo" Ta fara gane akwai yanayin da idan yayi magana cikinshi komin roqon da zatayi masa ba zai canza ba, shisa tayi masa saida safe, kafin ya amsa ta kashe wayarta gabaki daya. Kuma washegarin haka ta jefata a jaka batare data kunna ba, yau tana cikin 'yan uwanta, balle kewarshi tasa ta kunna wayar batare data shirya ba, sannan ba zata koma gidan da yamma ba, sai dare, tare zasu koma dasu Adda Zahra tunda sai washegari su zasu koma, Hajja dai wajen azahar ita direban da ya kawota ya dauketa, Maryama najin kamar tabita, sai rungumeta takeyi tana tureta. Wajen karfe tara da rabi, lokacin ma suka shiga mota zasu koma, kuma wayarta bata kunna ba, Khairi da ta lallaba zata bita gidanta, tunda jiya ta sauka gidan Minal ne ta mika mata wayar data daga "Mijinki ne" Haka kawai taji gabanta ya fadi, kamar karta saka wayar a kunnenta, ganin yanda Khairi take kallonta yasa ta kara wayar a kunneta tanayin sallama cikin karamar murya, sallamar da Haris bai amsa ba yace "Ina wayarki?" Ta dan tura bakinta gaba "Tana cikin jaka" Tambayoyi ya jero mata "Me yasa kika kashe? Kina ina? Baki koma gida ba?" Sai kawai ta zabi amsa guda daya cikin rawar murya jin yanayinshi "Bani da caji" Kai tsaye yace "Karyane. Karfe nawa nace ki koma gida?" "Da yamma" Ta bashi amsa "Da yamma karfe nawa?" Tayi shiru "Karfe nawa?" Ya sake maimaitawa "Hudu" Ta amsa kamar an saka mata tsumma a baki "Yayi kyau" Ya furta yana kashe kiran, ta cire daga kunne tabi wayar da kallo, wani abu na danne mata makoshi. Kuma daga wannan sunan, saida Maryama ta lissafa watanni uku bata leka ko kofar gate dinsu ba "Ni zance ga lokacin da zaki koma gida, ki kashe waya kiyi zamanki sai dare Maryamm? Saboda muna wasa da juna ne inaga, ni na barki kika fita shisa" Ta jera masa magiya da ban hakuri kamar zata ari baki, a wata ukunma zazzabi tayi, sukaje asibiti, ta dinga kallon gari kamar wata bakuwa, haka ta karbo alluran da aka rubuta mata tas, kuma tayi su saboda kullum zasu fita suje ayi mata, ko babu komai taga gari. Sai dai ta dauka a yanda tayi kewarshi, zataji wani doki na daban idan yace mata ga lokacin da zata bishi, amman sai zuciyarta ta buga, har tana ce masa "Yaushe zanzo ganin gida to idan na taho? Kuma ni kadai zan hawo jirgi? Ba zaka dawo mu tafi tare ba?" Dan fargaba ce ta lullubeta, sai tabar kasar? Duka? Shi yanzun watanshi nawa da tafiya baizo ba, in kuma ta bishi sukaqi zuwa da wuri ya zatayi? Daga ita saishi a wata kasa mai nisa haka. Dokin tafiya kasar wajen yanzun daya tabbata zataje sai ta neme shi ta rasa, turawan ma da zata gani kala-kala taji duk sun fice mata daga rai. Satikan uku suka dinga mata wani irin sauri. Ba karamin dadi taji ba da Haris yace mata zataje Kaduna tayi kwana biyu, sai da tayi hawaye da sukayi sallama da Mama Sadiya, sun saba, matar na da kirki, shisa Maryama bataji komai ba, duk wani kayan abinci da suke dashi raba musu tayi da maigadin gidan da kamar zai tsugunna saboda godiya, ita kanta Mama Sadiyan harda hawayenta. Lokacin da Maryama ta shiga gida, Alhaji Sa'id na nan, daga mota da gudu ta nufi bangarenshi, yanda tayi kewarshi "Abba na" Ta dinga fada duk wani motsi da zatayi a cikin gidan "Abbanki a ina? Sai kace naki ke kadai" Cewar Khalifa da ta fada yana wajen, ai ba karamin dadin saka masa biki da akayi taji ba, duk da bata gidan ta taya yan gidan murna, kowa sai taji sakat, inama wata uku akasa ba shida ba. Sai kuma taji babu dadi data tuna ba lallai ayi bikin tana nan ba. Abubuwa nawa zata rasa? Muhimman abubuwa nawa za'ayi bata nan? Aure ya dauketa ya mikawa Haris, shikuma zai dauketa ya bar kasar da ita. Wata sabuwar nasihar aka bude babin yi mata, kowa da akwai kalar shawarar da zai bata, da yake zuciyarta a karye take sai kuka, duk abinda suka dinga fada sai taji hawaye ya balle mata. Hajja ce tasa ta tambayi Haris din zataje ta gaishe da Hajiya Rumana, akasa direba ya kaita ita da Khairi da tayi mata rakiya, yaji dadi har a muryarshi "Da gaske zakije ki gaishemun da Mami na?" Har saida taga wautarta da batayi tunanin yi masa kara ba, kuma wannan murnar itace ta takaita mata bakin cikin wulakancin da Hajiya Rumana tayi musu, tunda suka shiga falon, taga sune, ta amsa gaisuwarsu da "Lafiya" Ta tashi ta shige ciki, haka suka karaci zamansu, turarukan wutar da Hajja tayi asarar kudinta ta siya ma anan suka gaji da zama suka bar mata kan kujera "Ni dana sani ma na dauko turarukan wutar wallahi, kilanma ta zubar a bola tayiwa Hajja asara" Duk da Khairi ta fita jin zafin abinda akayi musu din, dannewa tayi tace "Ita ta sani, ai dai an samu ladan kyautata mata, ke dai nasanki da kaikayin baki, kamar ba'a gasa miki shi da kyau ba, saura ki gaya masa ga abinda ya faru, kawai kice masa mun gaisheta" Kuma har ran Maryama tayi niyyar gayawa Haris abinda ya faru, yanda in gaba bataje gaisheta ba, ba zaiji haushi ba, sai dai ko Hajjan ma saida ta kara ce mata karta fada masa "Kiyi hakuri, kiyi kokarin tayashi ya zauna lafiya da mahaifiyarshi Maryama. Itace fitilarshi, kuma a yanzun shine naki fitilar, idan baya tare da haskenta, tare zaku hadu ku dishe, ki koyi hakuri, tunda ba sosai zaku dinga haduwa ba, ko da kasar kuka dawo ba gari daya kuke ba" Haka dai ta daga kai, Alhaji Sa'id ma ya kara mata da tashi nasihar, har saida ta fara tunanin yaushe zata fara yin hakurin nan da ake ta kira mata? Shin bayan hakuri sai kuma wanne abu akeyi ne a zaman auren? Kamar dai hakurin fa yafi komai rinjaye shisa aketa jaddada shi har haka. Taci kuka da zasu koma Kano, da duka yayyenta mata suka tafi, aka kara share gidan, aka nade komai, kujerunta ma kira akayi akayi musu leda da duk wani furnitures, dakin da suka kwana ne sai washegari da sassafe akazo akayi masa kamar sauran daku nan. Jirgin karfe goma sha daya ne zata hau, abinci daga gidan Mummy aka kawo musu na safen, tunda duk sun tattare komai, ita ruwan shayi ta iya sha, cikinta ya cika fal da fargaba. Saida su Adda Zahra suka rakata har airport, suma sai gasu suna hawayen duk kuwa da tsokanar da suka kwana sunayi mata, haka suka dinga rungumeta daya bayan daya kamar masu bankwana. Ita dai idanuwanta har yaji sukeyi mata saboda kukan da tayi, daga ita sai akwatinta guda daya, akwatin da Khairi ce ta hada mata shi saboda ta kasa, ta rasa abinda zata dauka, tunda duk wani abu da take so ta dauka ba zai yiwuwa ya shiga akwatin nan da takeja ba, sai karamar jakarta. Ta juya ta daga musu hannu, haka ta dinga juyawa har ta bace musu, tukunna ta sauke numfashi mai nauyi, tana tunkarar rayuwar da take jiranta batare da tasan cewa yanzun ne asalin labarinta zai fara ba Ita da Haris... 30 Yasan ko karfe nawa jirginsu zai tashi, saboda haka a lissafe yake da lokacin daya kamata su sauka, amman baisan me yakeyi a airport awa biyu da kusan rabi kafin lokacin saukar jirgin ba, kuma a zaune yake sai earpiece din daya saka a kunnenshi yana sauraren wani podcast da akeyi akan yakin duniya na biyu, yana sauraren ne yana kuma duba lokacin da yaga kamar da gayya yaki yi masa sauri, kwakwalwarshi ma ta kasune waje uku, daya na duba masa lokaci, daya na kokarin fahimtar abinda yake saurare, dayar kuma tana masa tunanin Maryama, yanda zai ganta bayan watannin nan, ta kara kiba? Ko tana nan da wannan sirantakar tata? Ta kara haske? Duk da dai kai tsaye mutane da yawa ba zasu kirata da fara ba, amman in zata tsaya kusa dashi yasan farar za'a kirata. Wanne kaya ta sako? Ko tasan a wannan watan na January a kasar ta New York lokacine na tsananin sanyi? Ba suyi maganar ba, bai fada mata ba, yace mata ko da bata saka rigar sanyi ba lokacin da zasu taho to ta riketa a hannu saboda zata bukaceta, shi bakin wando ne a jikinshi, takalminshi ma da yake sneakers bakine, sai ya dora leather jacket akan farar tshirt din da ya ganta sabuwa cikin kayanshi, bama zai tuna lokacin daya siyeta ba, kuma yau ya sakane saboda yanaso Maryama taga yana saka wasu kaya da ba bakake ba, har hasashen mamakin da zai cika fuskarta yakeyi, ya saka hular sanyi baka da ya danja baya, gashin shi da yake bakikirin fiye da sauran jikinshi na bayyana, da yake ba tarawa yakeyi ba, yayi ma sabon askine, kana iya ganin yanda edges din suka nuna alamar kwarewar wanda yayi askin. Lokacin kuma da agogo ya buga karfe sha daya da kwata na safe agogon New York, sai gashi ya mike tsaye, ya zare earpiece din dake kunnenshi, ya hada har wayar ya saka a aljihunshi, zuciyarshi na tafiya tare da agogon yana jiran sauran mintina sha biyar din da zasu cika, idanuwanshi kafe a hanyar da yasan Maryama zata bullo, zuciyarshi cike da fatan shine mutum na farko da idanuwanta zasu tsame mata a cikin tarin mutanen da suke wajen. A wannan lokacin, da Haris yake jiran Maryama, a lokacin ne kuma jirgin nasu ya sauka. Wani sanyi ya daki fuskarta tun da kafarta ta taka matattakalar farko ta sauka daga jirgin, kafin kuma sanyin ya ratsa ko ina na jikinta, riga da wando ne a jikinta ruwan kwai, a cikin lefe ta gansu, wandon irin pallazo din nan ne, haka rigar ma bata kamata ba, sannan ta sauka har kusan gwiwarta, kayan ba cutton bane, amman yadin da akayi su dashi mai laushi ne, hannun rigar dogo, shisa sai ta saka jersey scarf da kuma mayafin farare, wata iska taji tana kadata har hanji, ga kamshin iskar cakude yake da wani abu mai kama da kofi da kuma sabuwar rayuwar da Maryama tasan ta shigo, duk ya cakude waje daya, tasan yanayin safiya ce ko tace ma rana zatayi, akwai fitilu sosai a filin jirgin na John F. Kennedy International Airport, ga kuma wani abu nan kaman allo da aka rubuta Welcome to new york da manyan baki. Ta tsaya tana kallon rubutun, zuciyarta na harbawa da sauri, hannunta na rike da jakar da ta dauko tun daga gida, jakar da kuma ko a cikin jirgi tana makale a kafadarta. Sai kuma katon akwatinta da take rike dashi a dayan hannun tana ja a hankali. Maryama ta lumshe ido na wasu dakika. Wata irin fargaba ce ta tsaya mata a kirji da ba zatace takamaimai ta mecece ba, a gefe daya kuma akwai tsoro dokin ganin fuskar da ta shafe watanni tana tunanin canzawarta, fuskar Haris, labbanshi sun kara duhu ko suna nan a wannan kalar mai yanayi da ruwan toka mai cizawa da kuma zanen layukan baki da watakila ita kadai take gani, a hankali take takawa inda taga mutane nabi da tasan zata sadata da inda Haris yake tsaye yana jiranta, ko da ta karasa wajen kuma sai taji ta diririce, bakunta da rashin sabo na shiga ko ina ita kadai ya dirar mata, ta fara waige-waigen nemanshi "Maryamm…" Muryarshi ta shiga kunnenta, ta zarce cikin zuciyarta da wani irin karfi, duk da a hankali yayi maganar, ta juya, da saurinta, tsaye a cikin shigarshi, sanyin daya ratsata wannan karin bashi da alaka da kayan jikinta, kuma Haris yaga yanda jikinta ya kada, daya matsa gab da itama zai rantse yaga wasu kananun goosebumps a kan goshinta, wani abu da bai taba gani ba "Sanyi ko?" Ya tambaya yana kallonta, idanuwanshi cike fal da kulawa, wannan maikon na cikinsu yayo kasa kamar zai zubo, a wannan lokacin Maryama taji ta manta da gajiya, ta manta da hayaniyar mutanen dake wajen, shi kawai take kallo, ta ga lokacin daya cire jacket din jikinshi, farar rigarshi ta bayyana, farinta na shiga idanuwan Maryama tana kuma kara haska mata bakin Haris da har kyalli yakeyi "Farar riga, kasa farar riga yau" Ta tsinci kanta da furtawa, sai kawai yayi dariya yana zagaya da rigar kan kafadunta ya gyara mata zamanta sosai, kamar tace masa ya karayin dariyar, kewar sautin dariyar tashi ya saukar mata da kuma dumin da jacket din tayi, dumin da tasan na jikinshi ne, jakar hannunta ya karba, ya kuma sake mika dayan hannunshi ya karbi akwatin, yana mamakin yanda ya iya rike kanshi bai rungumeta ba har yanzun, ya dai hada jakar da akwatin waje daya, ya riko hannunta da yaji yatsun sunyi sanyi karara, ya kuma dan murzasu a hankali, kafin ya rike shi sosai yana janta, kafafuwanta suka bashi hadin kai, suka fara takawa, da suka fita daga airport din, sai taga yana rike da ita sun wuce sun dan tsaya kafin suka tsallaka titi, wani dan karamin waje ya nufa da ita, ya tura kofar gilas din suka shiga, taji yayi magana, yayi turanci, amman accent din da kuma saurin da yayi maganar baisa ta fahimci komai ba. Kofi aka miko masa, ya karba yana mika mata, saita karba taji duminshi a hannunta, da sauri ta dago dayan hannun ma da yatsunta da suka kandare saboda sanyi, ya biya kudi suka sake fitowa "Kisha, zaki danji dumi kafin mu karasa, mantawa nayi ince miki ki dauko rigar sanyi saboda in kin sauka" Da straw din ta fara zuqa, taji gardin har cikin kunnenta "Hot chocolate ne" Yace mata, ta jinjina masa kai kawai, koma menene dai, tabbas kudadenshi zasu dinga ji a jikinsu wajen siya mata shi, dan yayi mata dadi matuka. Taxi taga ya tare musu, aka saka akwatinta a baya, jakar kuma suka shiga da ita bayan Haris ya bude mata bayan motar, hot chocolate dinta take ta kurba "Daman guda biyu ka siyamun" Ta fadi jin nauyin kofin na raguwa "Ba kici komai ba, yayi zaki da yawa, cikinki zai iyayin ciwo" Da sauri tace "Inji wa?" Ya dan gyara zamanshi "Inji ni" Sai tayi shiru kawai, ko dai zai sakata ciwon ciki ai bakinta ya more dadin, balle tasan babu abinda cikinta zaiyi banda gode mata. Tafiya sukayi da Maryama take kula da nisanta saboda abinda take sha din ya kare, tana ta juya dan kofin ne a hannunta, yunwar da takeji tana dawowa sabuwa, ita duk abinda aka basu cikin jirgin wani orange juice da dan biskit kadai ta iya sakawa a cikin nata, sai kuma ruwa, zuciyarta ta dinga gaya mata data sani ta dafa wani abinma ta jeho a jaka. Ba karamin dadi taji ba lokacin da taxi din nan ta tsaya a wata unguwa mai dauke da gidaje masu matukar tsari, haka bishiyoyin ma ba'a hargitse suke ba, ga babban titi, sai dai babu wata zirga-zirga akanshi. Tanata kallon yanayin unguwar ne da ta fito, sai ganin mai taxi din tayi yaja motarshi baya yayi reverse, har Haris kuma ya fito da akwatinta. "Barka da zuwa New York Maryamm...muje" Ta danyi murmushi tana binshi a baya, suka taka matattakala guda biyu na dan matsakaicin gidan, ba mukulli ya saka bama, wasu yan abubuwane taga ya daddana sai kofar ta bude, ya shiga ta rufa masa baya, dan lungune a wajen karami, sai inda taga ya cire takalminshi ya ajiye, itama ta ajiye nata, ya sauka step daya, saiga falon ya bayyana, tsarinshi yayiwa Maryama kyau sosai, irin gidajen da take gani a fina-finai, tunda daga gefen falon ga kitchen din nan, babu wata kofa ko katanga da ta rabasu da falon, kawai a gefe akayi shi. "Zakiyi wanka ne?" Ta kalle shi tana cire jacket din jikinta ta ajiye kan kujerar da take tsaye a gefenta, dan taji dakin da dumi sosai, alamar akwai na'urar da take dumama waje "Wanka? Yunwa nakeji, kuma idan naci abinci ma saina fara rama sallolina" Baice komai ba taga ya nufi kitchen din nan, ya kuma bude fridge din yana fito da abubuwa, ita dai guri ta samu ta zauna, kafafuwanta duk sunyi tsami. Duk abubuwan da ya riga yayi order ne yake microwaving, abubuwan da yake tunanin zataci, kaza, dankali, taliya sai kuma pizza. Tana zaune tana kallonshi harya gama komai ya kwaso ya kawo ya ajiye mata anan kan kafet din falon. Ta cire gyalenta ta ajiyeshi, saima kawai ta mike taje kitchen din ta wanko hannunta ta dawo ta zauna kasa, da yake Haris yasan nan zata zauna daman, shima akan kafet din yake zaune. Taliyar a wani kwali take, haka ma kazar da chips din, sai Pizza dinma "A ina zan juye? Kabani plate" Ya kalleta, sai kuma ya mike ya dubo mata plate din ya dauraye shi ya kawo mata, ta juye da taliyar da dankalin da kazar, tayi Bismillah ta fara aikawa cikinta, taliyar tayi mata dadi sosai, akwai wani zaki-zaki dama tsami da bata taba tunanin zai hadu waje daya ba a dandanon, ganin yanda Haris yake kallonta yasa ta fadin "Nasan ba ci zakayi ba...ko zakaci?" Ya girgiza mata kai, yayi kewar kallonta tana cin abinci, yanda kuma bata kiba duk tarin abincin da takeci har mamaki abin yake bashi, kamar ya fadawa Mami, ya gaya mata ba abinci bane yake saka wasu mutanen kiba kamar yanda take tunani, amman a halin yanzun ma tafi sati bata daga wayarshi, duk akan zuwan Maryama, rigima akayi da ita da Alhaji Mustafa ba 'yar kadan ba, rigimar da taso ta saka shi a tsakiyarta ta hanyar saka shi yace ya fasa dauko Maryama ta biyoshi "Ubanka zatayi maka inta zo nan? Wato kai Haris duk abinda nake hango maka ka rufe ido ko? Ka rantse da Allaah sai naga abinda banaso, saika likamun jinin Sa'idu a cikin zuri'a fiye da yanda nake fama dashi a yanzun" So yake ta kwantar da hankalinta, ta nutsar da zuciyarta akan zamanshi da Maryama, saboda bai karbi aurenta dan ya sake shi ba "Kiyi hakuri Mami, ki karbi auren nan kamar yanda nayi...saboda..." Katse shi tayi a hasale "Ba zan karba ba din, kana jina, akan me? Ga mata nan kala-kala" Cikin wata irin murya yace "Wadda kikayi mun alkawarin zaki sama mun din kin cikamun ne Mami? A danginki fa na nema aka hanani, kina kallo baki iyayin komai akai ba, bayan kinmun alkawari, ke da kanki kikayi mun alkawari, sai Baba ya miko mun wata matar a madadin wadda nace inaso kika kasa samamun inki karba? Mami so kike in kunyata shi yanda dan uwanki yayi masa?" Yaji shirunta, shiru tayi mai yawa kafin ta kashe kiran batare da tace komai ba, kuma shine har yau bata dagawa, bai fasa kiranta ba, fushine zatayi ta gama, a hankali kuma zata gane babu wani abu da zai rabashi da Maryama in ba mutuwa ba Haka tunanin shi ya fada masa, A gefe kuma kaddara ta girgiza masa kai cikin yanayin rashin tabbaci "Nifa wannan abin ba lallai in iya cinshi ba" Maganar Maryama ta kutsa ta cikin tunaninshi tana saka shi kallon Pizza din data nuna, a fina-finai kawai ta taba ganinshi, kuma baiyi mata kama da abinda take so taci ba, ko abinda in taci zaiyi mata dadi "Akwai dadi" Ya fadi, ta kalle shi kamar bata yarda ba "Baki yarda bane" Ta dan numfasa "Inda wani ya fada, da harshenshi ya saba da dandanon abubuwa da sai in yarda, amman kai...sau nawa ma ya taba zuwa bakinka da zakace akwai dadi" Da gaske yayi kewarta, sosai "Kici kiji mana saiki yanke hukunci" Ta makale kafada, cikinta ma ya cika, data fara gani takeyi abincin duka yayi mata kadan, amman ko rabinshi bata cinye ba. "Nifa na koshi ma, na koshi kuma bacci nakeji" Ta karasa maganar tana mikewa, hannu taje ta wanke "Ina zanyi alwala? Ina ne gabas kuma? Ni bana ganewa idan naje waje, ko can gidan su Adda ne suka nuna mun ranar da aka kaini" Da kanshi Haris ya mike ya nuna mata bedroom din da bayan ta shiga ta nufi bandaki kanta tsaye, ta gama duk uzurin da zatayi ta fito, akwatinta ta dawo ta dauka ta bude, akwai hijabi a ciki ta dauka sannan ta rufe shi ta koma bedroom din ta gabatar da salolinta, dakyar take daga idanuwanta lokacin data idar, a haka take karewa dakin kallon, idanuwanta suka sauka daga can gefen gadon dakin, ta wani lungu, zuciyarta ta buga, hotonta ne, frame din hotonta, daya daga cikin hotunan nan da yace na birthday dinta, kanta babu dankwali, tshirt ce ma a jikinta ranar, wata jar tshirt saita saka wando, kuma a tsaye take da kofin da ba zama ta tuna menene a cikinshi ba, da alama kuma hankalinta kacokan yana kan tv ne, iya cikinta ne zuwa kanta aka dauki hoton, ta rasa hadinshi da black and white, tunda wannan dinma anan yake, da bata tuna rigar ba, babu yanda za'ayi ta gane kalarta. "Baccin yazo ne?" Haris daya leko kanshi ya tambayeta, ta danyi murmushi "Kwanciya zanyi dai..." Shima murmushin yayi "Inzo mu kwanta?" Taji kunya ta dirar mata, ta rasa amsar data kamata ta bashi, shisa ta zabi tayi shiru kawai, ita zataso ma ta rage kayan jikinta ne, amman inta kwanta, yanda Haris ya gayyaci kanshi din nan zuwa zaiyi ya kwanta shima, gashi ba dare bane balle tace duhun zai boyeta daga idanuwanshi ko da yabar masa gangar jikinta. Sai kawai ta mike ta hau gadon, tana kallonshi ya shiga cikin dakin, ya nayar da kofar ya rufe, shima ya zagaya ya hau gadon, lokacin daya saka hannunshi ya jata yana hadawa da jikinshi, taji wani irin numfashi daya sauke "Nayi kewarki Maryamm, har bansan adadin sau nawa na kwanta akan gadon nan ina tunaninki a jikina ba" Tayi luf tanajin duminshi da maganar da yayi sun hadar mata "Amman da alama ni kadai nayi kewarki ko?" Wannan karin ya fada cikin kunnenta, tayi shiru, ya dan kara karfin rikon da yayi mata saida ta motsa "Bakiyi kewata ba Maryamm?" Muryarta a hankali, tana rawa ta fito "Nayi" A hankali yace "Karyane" Yaune karo na biyu daya furta mata kalmar, ya karyatata kai tsaye, amman kuma ta rasa menene a yanayin yanda yayi maganar da maimakon haushi saita sakata murmushi "Da gaske" Sai ya sa karfi yana juyo da ita ta fuskance shi, idanuwanshi cikin nata sukayi mata nauyi ainun, dole ta sauke nata, amman saiya saka hannunshi ya dago da fuskarta "Ban yarda ba Maryamm, ni kadai nayi kewarki" Idanuwanta ta kara saukewa, ba zuciyarta kadai ke harbawa ba, duka jikinta bari yakeyi, sau nawa yake rungumeta suyi bacci, amman na yau yayi mata daban, batasan ko dan ya juyata ta fuskance shi bane ba, ko dan hasken da yake cike da dakin, ko kuma dumin numfashin shi da takeji akan fuskarta "Barka da zuwa New York, duk da na fada miki dazun, yanzun inaso ince miki barka da shigowa rayuwata" Saboda tun daya dora idanuwanshi akanta a airport din nan yaji yanda ta shigo rayuwarshi a yau din nan, kamar wancen karin, ranar da aka kawota, ya karbeta ne kawai, amman baijita ba, amman a yau wani abu ya canza, wani abu a tsakaninsu, koshi kadai yaji hakan ma ba matsala bane ba, amman Maryama ta shigo rayuwarshi, ya kuma bude hannuwanshi ya karbeta, itace dai yake so yanzun ta bude tata rayuwar ta karbeshi, Rayuwarta Jikinta Zuciyarta, harma da ruhinta idan zai samu So yake ta karbeshi yanda zata zama mallakinshi gabaki daya, amman ba yanzun nan ba, ba yanzun da yakejin bugun zuciyarta a kirjinshi ba, ba yanzun da jikinta ke kyarma haka ba "Ba yanzun ba Maryamm, muna da lokaci mai yawa, ina da lokaci, ki huta yanzun, kiyi bacci" Ta daga masa kai kawai dan ko ta bude bakinta ma ba zata iya magana ba, ya sumbaci goshinta, da saman idanuwanta data lumshe. Baccin tayi, da yanda numfashinta ya canza yasan bacci tayi, shima kuma nashi idanuwanta sun fara lumshewa alamar bacci, wata gajiya ta saukar masa, ya kara gyara mata kwanciya a jikinshi, ya rufa musu katon bargon da yake kan gadon, ya rufe nashi idanuwan wani irin bacci mai nauyin daya kwana biyu baiyi irinshi ba yayi gaba dashi. Maryama ta rigashi tashi, na yan dakika ta manta inda take, ta dauka ma mafarki takeyi data bude idanuwanta akan fuskar Haris, kafin komai ya dawo mata, kaddara kenan, wai itace yau a wata kasa, itace ta hawo jirgi har wata kasa, Haris din take kallo, batajin ta taba samun damar kare masa kallo haka, wani haske ya ratso ta gilashin window din, shine ma ya shigar mata ido yana tashinta, da yake labulen window din ba'a jashi ba, kamar wata fitila ce dan baiyi kama da hasken rana ba, kuma yanayin nauyin jikinta ma tasan bacci tayi sosai, hasken ya haska wuyan Haris da bayan kanshi. Ta tsinci kanta da kai yatsa ta dan dangwali kumatunshi, ta kalli yatsan nata, sai kuma dariya taso kwace mata, to ai inda bakin nashi mai zuba ne da ita zai fara batawa, kawai gani tayi yana wani kyalli-kyalli, fuskarshi da yanda yake baccin kamar an jikata cikin wani mai da yake da saukin maiko, ko haka duk bakar fata inta hadu da hutu takeyi? Kuma kilan kallon ne yaji yayi masa yawa yasa shi bude idanuwanshi da suka sauka cikin nata "Me kike nema?" Ya tambaya, tun da ta motsa ya tashi, bai bude idanuwanshi ba "A ina?" Ta tambaya a diririce "A jikin fuskata, me kika shafamun a kumatu?" Ta girgiza kai da sauri, yaji kenan? Idonshi biyu? Allaah ne ya rufa mata asiri da bata dangwalar masa lebe ba kenan "Bakomai ba, ban gani bane nazo gyara kwanciya, ka matseni" Ya danyi murmushi yana sauke numfashi, sai kawai ya saketa ya mirgina gefe, tunda kokarin mallakar kanshi yakeyi, yanda ta diririce din nan so yake ya kara cika wannan idanuwan nata da bacci ya canzawa launi da wani abu na daban. Bandaki ya shige, yabarta kwance zuciyarta nata bugawa, daya fito sai itama ta tashi, yanzun wankan da batayi ba ta samu tayi, ta fito taga Haris ya janyo akwatinta ya shigo dashi dakin, ya kuma bude yana fito da kayayyakinta daya bayan daya, da saurinta ta karaso ganin abinda yake shirin daukowa "Dan Allaah..." Ta fadi da sauri, ita batama san me zaiyi da kayan ba "Zan jera miki ne a wardrobe" Ya amsa kamar yaji me tace "Baga ta can ba, zan jera, kawai saika budewa mutum kayanshi, dan Allaah kabari, karka fito da komai, waye yake taba akwatin mace?" Yayi murmushi "Meye a ciki da bakya so ingani" Ya fada yana kallon akwatin, takai hannu zata janye ya rigata ta hanyar daga abinda bataso ya dauka din, kuma saiya kwashe da dariya "Size nawa ne wannan?" Ya tambaya yana kokarin juyawa ya duba, ta fisge tanajin wani abu bayan tsananin kunya na dirar mata "Wallahi banaso, kabari, ina ruwanka? Me yasa zaka daukar mun?" Ta karasa da rawar murya, taji kunya irin wadda bata taba sani ba tunda take a rayuwarta, kuma saiya kara yin dariya, mai sauti, yanda idanuwanshi ke yawatawa a jikinta sai kawai taga ma waje daya suka tsaya, taja akwatin gefe tana juya masa baya, ya girgiza kanshi kawai yana murmushi, in dai ita dashine, su kadai a kasar nan, a hankali zata gane bata da wani abu da zata boye masa Ita da komai nata nashi ne... Duk da shi kanshi bai hango tazarar faruwar hakan bata da yawa ba...Maryaman zata zama tashi, zata zama tashi ta yanda kowa ma zai shaida hakan... 31 "Dan Allaah ka matsa" Maryama tayi maganar muryarta na rawa, hawayen da take ta rikewa suka zubo mata, komai ya isheta, duniyar duka batajin dadinta, inda ace mutum ya san ranar mutuwarshi, to da sai tace watakila watan nata mutuwar ne ya tsaya, shisa komai ya hargitse mata haka. Dazun da safe sai da ta kara lissafawa, kwananta hamsin da hudu da zuwa, kuma a kwanaki hamsin din nan, ita dai zatace hudun farko ne tayi su cikin jin dadi da walwala. Saboda a daren kwana na biyar dinne daga irin rikon da Haris yayi mata da yawon da hannuwanshi sukeyi a jikinta tasan cewa zaman zurun da yakeyi mata ya kare. Jiki da zuciyarta na rawa ta rike hannun nashi da ya kwace "Dan Allaah, Ganja, dan Allaah, ba muyi sallah ba, ba muyi sallah ba" Ta furta tana kara maimaitawa "Nayi har isha'i" Ya amsa mata da muryarshi da ta dishe "Sallar Nafila, ba muyi Salatul Shukr ba..." Taji yanda ya dakata da komai na wasu dakiku, kamar mai nazarin maganar da tayi, zaice rabonshi da cikakkiyar Islamiyya tunda ya gama primary, a boarding din da yayi kuwa ko an korasu ba wani maida hankali yakeyi ba, yana da haddar izu goma daga kasa, shima albarkacin jajircewar Malamansu ne lokacin kuruciya, itama haddar idan aka tsare shi yasan ba zai iya kawota gabaki daya ba. A secondary kuma, a ranakun da ya zauna a Islamiyyar dan abinda yake tsinta ba wani mai yawa bane ba, ya gane Shukr, ai godiya kenan, Sallar godiya take nufi "Farilla ce? Salatul Shukr din?" Ta girgiza masa kai, asalima Malamai da yawa sun sakata a jerin Mustahabbi ne, amman abune mai kyau, tunda har Salatul Hajah ma saida Adda Maimunatu ta saka tayi ana gobe daurin aure "In kin idar ki roki Allaah Ya saka miki salama a auren nan, Allaah Yasa komai na cikinshi yazo miki da sauki" Tayi sallar dai, saboda a lokacin bataso ta dameta da wani wa'azi, amman data idar ta zauna babu addu'ar da tayi. Watakila yanzun dinma tsoron daya cika kirjinta ne ya tuna mata da ba suyi sallar da duk da ba farilla bace ta zamewa kowanne sababbin ma'aurata farilla "Dan Allaah..." Tayi maganar cike da roko, bakin da take magana dashi ya rufe mata da nashi, data lumshe idanuwanta sai ta dora hannunta saman kanshi a hankali tana furta "Allahumma inni as’aluka khairahu, wa khaira ma jabaltahu ‘alayhi, wa a’udhu bika min sharrihi, wa sharri ma jabaltahu ‘alayhi" A wannan daren ne Haris yayi hannun riga da duk wani kirki data dade tana dangantashi dashi. Idan yaji kukanta bai nuna alama ba, idan yaji magiyarta to ya zabi ya share ne, shisa ta daina magiyar, ta koma karanto duk wata addu'a da tazo cikin kanta, saboda taga alama rayuwarta Haris ya nema a wannan daren. Kuma washegari haka ya sake maimaita mata fiye dana farkon, sai gashi ta tashi da zazzabin da bai taba zauna mata a kai ba inta karanta a littafinta, to zazzabin menene zakayi? Su marubuta karyarsu ba sallah takeyi ba, ashe a wannan karin ainahin gaskiya ce basu haskawa 'yan mata irinta ba, kamata yayi ace babu wani sakaye-sakaye sun fito fili sunci rayuwarka namiji zai nema, saika san irin shirin da zakayi. "Allaah Ganja kabari karfina ya dawo, ba yarda zanyi ba, dan kaga karfina ya tafi shisa" Ta fadi cikin kukan da takeyi, saida ta saka murmushi ya kwace masa, amman da safen ba karamin rikicewa yayi ba jin yanda jikinta yayi zafi rau, danma Allaah Ya rufa masa asiri ko da ta kama ya kaita asibiti ne babu mai garqame shi tunda abinda yaja jinkirin samun izininta na biyoshi shine shekarun nata, kasar New York suna da tsauri matuka akan maganar Legal age, ko da kuwa ga bakine, zasu girmama auren da yake tsakanin Haris da Maryama ne, su kuma yarda dashi idan shekarunta suka kai sha takwas. To dan after care dinma Maryama taki barinshi ya nuna mata, daya riketa a jikinshi zata gartsa masa cizo, ko yanzun ma yayi tunanin zatayi masa musu daya bata magani da ruwa, sai ta karba tasha. Yanda tayi laushi ne kadai yasa ta yarda Haris ya taimaka mata tayi wanka, ta sake kaya, daga zaune tayi sallar asuba, dan kafafuwanta rawa sukeyi, ga jiri-jiri da take gani, kwana biyu tayi tana fama da zazzabin nan kafin ta samu kanta. Bata tabajin dadin kadaici irin na kwana hudun da Haris yayi a makaranta ya barta ita kadai ba. Sai dai tayi kallo, ta dafa duk abinda ya samu, ta kuma kwanta. Da sukayi waya da Adda Zahra ne ma taji yanayinta, duk da ba wasu tambayoyi tayi mata ba tace "Kiyi farfesu Maryama, ki shanye romon duka, ki dinga yawan yi kinji?" Ta daga kai "Kuna samun zuma anan?" Kai ta girgiza tana dorawa da "Bansani ba sai dai in tambayeshi" Tunda dai komai ma shine ya fita yaje ya siyo musu "Tam kice ya siyo miki, ya hado miki da lemon zaki ma, in ana samun kanamfari saiya hado miki, ki matse ruwan lemon da abin ciki, fatar da kwallayen kawai zaki zubar, kanamfarin 'yan pieces, ko hudu haka ki daka sosai ki zuba ki saka zumar sai kisha da daddare, in kin samu dama kullum kiyi kinji? Ko yana nan ko baya nan....ki kuma dinga shiga ruwan zafi, zan tura miki wasu abubuwan ta text" Da ta wuni tana shiga ruwan zafi, tasha farfesun da shayi, sai gashi taji dadin jikinta. Randa Haris ya dawo zuciyarta har makoshinta, kuma shi ta bangarenshi bai dawo gidan da niyyar yayi mata komai ba, shisa ma yayi kokarin sauke duk wani abu da yakeji akan wasu matan, sai dai yana ganinta, yana ganin yanda idanuwanta suka kara girma da tsoronshi sai yaji babu abinda yake so irin ya rabata da wannan tsoron, ta saba dashi. Ta kuma gane shifa wannan harkar na daga cikin abubuwan da yake so, shisa ya ba kanshi mamaki matuka na yanda ya daga mata kafa, wai shine aka ajiyewa mace, kuma ya dinga kwana yana tashi daki daya da ita batare daya tabata ba, baima san yana da wannan self-control din ba sai akan Maryama. Yanzun kuma daya rasa shi, baisan ta yanda zai sake dawo dashi ba, to ta ina ma zai fara idan tana nuna masa wannan raunin? Ya zai hakura da ita bayan zama kusa da ita kawai idan yayi sai yanayin fitar numfashinta ya canza? To shi da yake so ya mallaketa dukanta, taya zai iya rike kanshi? Ko da ta kalle shi tace masa "Daman kasa na biyoka ne saboda ka kashewa iyayena ni?" Saiya girgiza mata kai "To me yasa ba zaka kyaleni ba kona roke ka?" Ya riko hannunta, bata hanashi ba kuma "Saboda ki saba, ina so ki saba dani Maryamm..." Zaiso ace ya kara mata da "Saboda ina son mata, saboda kin hada duk wani abu da banyi zaton zanso a jikin mace ba" Amman sai yayi shiru "Kome zance ba zaka kyaleni ba ko?" Ya daga mata kai "Da kin saba shikenan, kilanma kece zaki dinga damuna" Batace komai ba, bata jinma ta gane me yake nufi, amman bata sake kokarin kwatar kanta a hannunshi ba "Smettila di resistermi..." Haka yace mata, kamar ya tuna ba zata gane ba ya dora da "Stop fighting me, kibari Maryamm, kar inji miki ciwo" To ya daina wahalar da kanshi, taji, ta daina kokarin kwatar kanta, ta daina gudunshi, gabaki daya tayi wani irin sanyi saboda fitinar Haris, shisa randa yace mata zasu fita batama yi wata murna ba, sai bayan sun fitan ne sauyin yanayin data samu yayi mata dadi, wani coffee place ne sukaje, wajen yayi mata kyau, daga kamshin shi zuwa yanayin setting din, shi yayi musu order din komai, kuma taji dadin abinda yayi mata order "Ya sunan abin nan?" Maryama ta tambayeshi tana kara zuka "Frappuccino....a karo ne?" Da sauri ta daga masa kai, yayi mata dadi sosai, sai da tasha kofi hudu, har mamakin kanta tayi, da zasu tafi ma ya sake siya mata kofi daya suka tafi tana rike dashi a hannunta "Mu koma gida ko muje wani wajen?" Gajiya takeji, kwana biyun jikinta nayi mata ciwo fiye da misali, shisa ta girgiza masa "Muje gida kawai, ni jikina ciwo yakeyi mun, kullum ma jikina ciwo yakeyi saboda kai" Dariya yayi "Ni kuma? Ni dai yanzun bana gajiya da yi miki laifi, komai sai kice ni" Ta harareshi "Kaine mana" Ya tsareta da idanuwa "Me nayi? Ki fadi me nayi da bakinki inji" Ta dan murguda bakinta "Komai da komai, meye da meye ma bakayi ba?" Ya karayin dariya, komai nata yayi masa, komai, musamman kananun abubuwa kamar yanda tayi maganar nan yanzun, yanda muryarta take canzawa da abubuwan da takeji, idan ranta ya baci, in tana cikin nishadi, in taji dadi, kowanne yanayi yana zuwa mata da canjin murya. Sai kawai yakai hannunshi yana matsa mata kumatu, ta janye fuskarta tana harararshi "Wannan Maryamm din, nayi kewarta" Shisa yace su fito, ko zata dan warware, ko surutun nan bata cikayi masa ba kwana biyu "Bawani nan, ai kaine" Ya sakeyin dariya, aifa ba zai huta ba, tunda ya tabata ta, daman yasan da ta gama mashau-mashau din ta warware sai yasha surutu, to ta fara, danma yana da abubuwan da shima zai tsokaneta dasu, abubuwan da zaisa ta rufe bakinta ta kyaleshi. Ashe surutun da zaisha da rikicin da zai kwasa na abu daban ne, dan a satin yanda take ce masa jikinta na ciwo saida ya fara bashi tsoro "Dai-dai ina Maryamm?" Ya tambaya "Ko ina, har fatar kaina ma ciwo takeyi" Kuma da gaske takeyi, ko ina ciwo yakeyi mata, wani irin ciwon jikine da bata taba sanin akwai irinshi a duniya ba, batama taba jin labarinshi ba "Ki tashi, bari in kira uber sai mu tafi asibiti" Ita ba son asibiti takeyi ba, amman dai a yanda take jin jikinta tana bukatar taimako, ta dauka asibitocin Najeriya ne kawai za'a iya samun layi irin wanda suka samu, shima kuma ma gwammati, tunda na kudi ai ba zakayi wannan jiran ba "Wai layi baizo kanmu ba har yanzun?" Ta tambayi Haris, dan ta jingina da kafadarshi ne, sai kawai ya gyara mata zamanta yanda ta kwanta a jikinshi, tunda ta kula babu wanda ya damu da harkar wani balle taji kunya. "Ai su nan ba layi bane bafa, suna duba wanda yafi wani jigata ne" Abin ya bata mamaki, tunda itama a jigacen take jinta, ko dai jikinta bai nuna irin wahalar da takeji bane ba? Kawai dai tayi mamaki ne matuka, yanda taga Haris nata cike form din da aka basu, ita bata masan menene rukunin jininta ba, an daiyi mata aune-aune kafin tahowarta, sai taga ya rubuta O+, haka ya gama cikewa batare da yayi mata tambaya ko guda daya ba. Tana ta kallonshi, harya kamata suka shiga wajen likitar, macece ma, kuma tunda aka gama mata duk wani gwaji da aka rubuta, saita tsinci kanta da kasa kallon dan karamin screen din abin gwajin da ake kira da scanner, saboda ta daina gane komai bayan kalmar "Ina tayaku murna, tana da ciki..." Kalmar ciki ce take ta amsawa tana sake maimaitawa a kunnuwan Maryama, lokacin da Haris ya zagayo kuma ya rike hannunta saita kalle shi "Ciki kayi mun Ganja" Ta furta a hankali, kamar mai son tabbatarwa da kanta maganar "Cikina ne a jikinki Maryamm" Yace yana kara dumtsa hannunta da yake rike dashi, a wannan lokacin daga ita harshi ba zasuce ga yanayin da suke ciki ba, amman mamaki ya rinjayi komai. A hanyarsu ta komawa hannunshi na cikin na Maryamm, da suka karasa gida kuwa haka ya riketa gam kamar mai gudun ta taka kasa, sannu kuwa tun tana iya amsashi har tayi shiru kawai "Me kike so kici?" Ta kalle shi "Zaka dafamun ne?" Ya ware mata idanuwan nan nashi da suketa maiko "Ban iya ba ai, kin manta banda shayi ban iya dafa komai ba" Cikin son ta tsokane shi tace "Idan girkin naka nake so inci fa?" Ya kara tausasa yanayin shi "Sai in baki hakuri, ki zabi duk abinda kike so, idan akwai shi a NY, zan bazama komin nisan wajen in nemo miki" Ta danyi murmushi "Abin rannan, wanda ka saimun, mai dadin nan" Ta bashi dariya "Frappuccino?" Ta daga kanta "Shi, shi nake so" In dai wannan ne ai ba zaiyi wahala ba. Kofi shida yayi mata order, duk da bai manta ba, akwai budurwar wani dan ajinsu lokacin da take da ciki, anan yasan ba'a son mai ciki ta yawaita shan Caffeine, dan haka decaf ne duka. Data kurba sai ta kalleshi "Ba irin wancen bane ba, dandanon" A hankali ya amsa da "Akwai Caffeine a wancen, ba zaki iya shanshi ba saboda...saboda Babyn" Ya karasa muryarshi na sauka kasa sosai, tare da idanuwanshi da suka tsaya kan cikinta, ta tura baki "Wancen yafi dadi, ni wancen nake so" Har lokacin idanuwan Haris na kan cikinta yace "A'a" Kalma daya, cikin yanayin da tasan duk wani abu da zata fada bayanta ba zaiyi tasiri ba. Haka tasha, tana gama kofin farko tasha na biyu, wani irin amai ya taso mata, da gudunta tayi bandaki, tayi amai kamar hanjinta zasu fito. Aman daya bude mata kofar wani irin laulayi mai zafin gaske. Laulayin da take cikinshi a halin yanzun, duk ta kara figewa tayi haske, idan Haris zai fita sai dai ya kwankwasawa makotansu guda biyu, dayar matar tsohuwace da zata kai shekaru 50 da karnukanta har hudu, dayan kuma ma'aurata ne da yaransu biyu yace musu dan Allaah matarshi tana ciki, su taimake shi su dan dinga dubata. Komai da zata bukata yake ajiye mata, ya dinga jaddada mata ta kira lambobin taimakon gaggawa da taji ba dai-dai ba, ta fara kiransu karta kirashi, kafin yazo idan wani abinne sun rigashi karaso su. Ita duk ba burgeta yakeyi ba, tunda waye yaja mata wannan wahalar? Ji takeyi kamar mutuwa zatayi, shisa randa sukayi waya da Hajja, tana jin muryarta kawai ta fashe da kuka, aikuwa ba karamin dagawa Hajjan hankali tayi ba "Wai dan ubanki ba zaki bude baki kiyi mun magana bane? Meye? Me yake faruwa" Cewar Hajja cikin kosawa, Maryama na jan hanci da sauke ajiyar zuciya tace "Bani da lafiya Hajja, dan Allaah kizo" Hajjan ta dan sassauta murya daga can bangaren "Subhanallah? Meya sameki? Kunje asibiti" Tasa hannu ta share hawayen daya zubo mata "Eh munje tun rannan, mun kara komawa, amman fa Hajja magani daya suka bani, kuma bani da lafiya sosai....dan Allaah kizo kar in mutu anan ni kadai, shi nace ya dawo dani gida yakiya..." Maryama ta karasa wasu sababbin hawayen na kara balle mata "Basu ce ga abinda yake damunki ba" Batare da tunanin komai ba tace "Ciki sukace fa Hajja, amman nace masa muje a kara dubawa ma jiya, tunda bani da lafiya, komai ciwo yake mun, har fatar kaina ma ciwo takeyi...idan cikine ai ba zan dinga ciwo haka ba ko? Dan Allaah kuzo" Wani irin shiru Hajja tayi daga can bangaren, saida Maryama tayi tunanin kiran ya yanke ne tukunna taji tace "Yanzun Maryama saboda baki da hankali sai ki bude baki ki fadamun kina da ciki?" Maryama taji ta dan diririce, amman ta rasa abinda tayi na rashin hankalin, dan ta gaya mata? Hajja fa, in bata gaya mata ba wa zata fadawa? "Zaki zo?" Ta tambaya "Tunda kasuwar bacci ne da zan dauki hijabi a kaini, kinga Maryama ki fita idona, Addanki zata kiraki" Kafin tace wani abu ta yanke kiran, data kara kira bata daga ba, tasan Adda Zahra take nufi, sai kawai ta kirata da kanta, itace tace mata "Zakiji sauki, In Shaa Allaah, da ya shiga wata na hudu zaki samu sauki...." Duk wasu shawarwari ba wani shigar Maryama sukeyi ba, yanda ta saka Haris a gaba kuwa saida suka koma aka sake dubawa aka nuna mata, ta ware ido, ta sake warewa, harda kunnuwa dan ta fahimci turancin da likitar take tayi, da kuma abinda take nuna mata din, sai bayan sun koma gida, da daddare suna kwance ne ta cewa Haris "Ganja..." Tare da zame hannunshi daga rikon da yayi mata ta juya kwanciyarta tana kokarin ganin fuskarshi ta cikin duhun dakin "Kayi bacci?" Da muryarshi da tayi kasa saboda gajiya da kuma baccin daya dan fara yace mata "Menene? Kina son wani abune? Ko jikin ne?" Ta girgiza masa kai "Dazun, kai kaga babyn? Da ake nuna mana, babyn cikina" Ya dan numfasa "Nagani...meya faru?" Inda tama san yanda ya ajiye karatun daya kamata ace yanayi ya maida hankali akan karatun mai ciki da irin taimakon da take bukata zata sha mamaki, duk wani motsi da zaiyi zuciyarshi na kara tuna masa da cewar akwai cikinshi a jikin Maryama, shima yana gab da amsa sunan uba, kuma har lokacin abinda yakeji bashi da suna. "Me yasa ni banga komai ba?" Tana jinshi ya karasa sakinta, sai kuma taji ya mike, ya kunna kwan dakin, akwai hoton da aka kara basu, shiya sauka daga kan gadon yake falo ya dauko "Tashi kigani" Ya fadi, batayi musu ba ta tashi, yayi amfani da dan yatsanshi yana nuna mata "Gashi nan...dai-dai nan" Ta kura ido, ta karbi hoton ta sake dubawa "Dai-dai ina dan Allaah? To ni me yasa bana gani" Ya sake nuna mata "Wannan farin abin mai kamar wake?" Yaso ya danne, dariyar data taso masa, ko dan yanayin damuwar da yaga tayi, amman saiya kasa, dariya yakeyi ba 'yar kadan ba, itama kuma sai abin ya bata dariya "Allaah ni na kasa gani, to ina kan? Da kafafuwan? Ina hannuwan?" So yake yayi mata bayanin da sauran lokaci kafin duk wannan abubuwan su bayyana amman dariya ta hanashi, sai kara duba hoton hannunta takeyi tana son ganin alamar kai, ko hannuwa "Ai shikenan, ni kam dai banda wannan wake-waken babu abinda nagani..." Da alamar dariya a muryarshi yace "Karki damu, zaki gani...ke da ma zaki ga babyn gabaki daya, ki rike a hannunki" Tayi shiru, maganar ta shigeta, ita da yaro ko yarinya? Kuma ace nata ne duka, itace zata kula dasu, zatayi musu komai, babu wanda zaizo ya kwace mata, yaranta, ko yarinyarta Allaah Kenan... Mai kyauta da kari, Sai dai kuma ai yanzun ne ta fara, kaddarar rabon da yake tsakaninsu. 32 "Ganjaa!!!" Maryama take kira, kuma kusan duk wanda yake taku ashirin daga dakin naqudar da take, yaji yanda ta kira sunan nan harya bace lissafi, wani ma sai yayi zaton ko addu'a ce ta samu ta rike, ko kuma Haris din baya dakin tare da ita, hannunshi cikin nata yana jera mata sannu "Ina ganin girmanka, banaso in zageka, ka daina mun sannu kamar bakai kaja mun ba" Ta fadi tana karayin wani nishi da yaji har cikin ruhinshi, yana makaranta makociyarsu Chloe ta kirashi akan yazo, dan suna tsaye ne a kofar gida suna dan hira lokacin da Maryama taji wani abu mai dumin gaske nabin kafafuwanta, ta dauka ma fitsarin da tunda cikinta ya shiga wata bakwai bata iya rikewa sosai ne ya kubce mata, sai dai ai bataji alamar fitsari ba, kafin ta bude baki tayi magana wani abu ya soketa a gadon baya daya sakata rike karfen da akayi ado dashi a kofar gidan nata "Her water just broke..." Haka Chloe tace masa, kuma bai taba sanin mintina ashirin wasu mintina bane masu tsayin gaske sai a ranar, gani yakeyi kamar zata iya haihuwa kafin yaje. Sai dai ko asibiti ma basu tafi ba harya karasa, yana ta yiwa Chloe data zauna da Maryaman godiya, tukunna suka dauki akwatin da sun jima da hadashi, tunda duk wata siyayya tare sukayi da Haris, da yake sunce basa son sanin gender, sai suka dinga daukar unisex a komai, kayan da kullum sai Haris ya budesu ya kalla sau nawa, ya daga wancen ya ajiye ya daga wannan ya ajiye "Ko dai mu karo set of socks din nan? Kinsan akwai sanyi" Abubuwa da yawa ita ta dinga hanashi kwasarsu, tunda Adda Zahra tace mata su siyia 0-3 months su jira, wasu yaran saurin girma sukeyi, kayan ma sai suyi musu kadan kafin suyi watannin. Ita dai a tsakanin azabar da take sha ma dokin da take ciki ya bace, ji takeyi kamar ta shako Haris su kacame da dambe. Amman bari dai ta haihu, ai ko riga ta gama yarda ya cire a gabanta balle wani abin ya hadasu, daki ma zasu raba, wannan azabar? Ba zata taba yarda ya kara sakata a cikinta ba. Amman kamar anyi ruwa an dauke, haka taji bayan babyn ya fito, kukan jariri ya karade kunnuwanta, kuma batasan meye yasa hawayenta ballewa a dai-dai wannan lokacin ba, da aka mika mata babyn, maimakon ta karba sai ta kalli Haris, idanuwan Haris "Macece ko namiji?" Cikin wata irin murya yace mata "Namiji..." Ta jinjina kanta wasu hawayen na sake zubo mata "Ka fara daukarshi" Yaso ya girgiza mata kai, ita da tasha wannan wahalar? Tayi dakon cikin? Sai shi ya fara dauka? Amman tun kafin tayi magana zuciyarshi ta jima sa barin kirjinshi ta lullube yaron dake hannun likitar nan, hannuwanshi na gaya masa ba zasu yafe masa ba idan ya kara dakika bai karba ba, shisa baiyi musu ba, ya karbi yaron, ya matsa kusa da Maryama, ya sakashi a jikinta, ta sauke ajiyar zuciya, kuka yakeyi har lokacin, ta rankwafo tana kai bakinta saitin kunnenshi "Barka da zuwa, ina rokar maka kariyar Ubangiji daga sharrin da yake cikin duniya da kuma rudinta, Allaah Yayi maka albarka Ya hada rayuwarka da alkhairi daga yau har karshen numfashinka, Allaah Yasa raino da tarbiyarka suzo mana da sauki, Allaah Yasa mu sauke amanarka, Allaah Yasa ka zame mana daya daga cikin hanyoyin shiga aljanna" Bata manta ba, bata taba mantawa ba, yanda ake jaddada musu tasirin addu'ar uwa a Islamiyya, yanda ake fada musu su roki yara nagartattu ba sai sunyi aure ba, su rokama yaransu tsari tun kafin su samesu, kuma addu'ar ma ta zame mata jiki, shisa yanzun data rike shi a hannunta tunanin daya fara zuwa mata kenan. Ta mikawa Haris shi "Kayi masa addu'a" Shima bai manta ba "Kiran sallah a kunnen dama, Iqama a kunnen haggu...karfa ka manta da an miko maka babyn" Ta fada masa baisan adadi ba, hakan yayi yanzun, tana kallonshi, amman gajiya takeji tana saukar mata sosai, idanuwanta ma sun fara mata nauyi, bacci takeji, akace Haris ya mika mata babyn dan ta bashi yasha. Ya mika mata, yaki barin dakin har aka karasa yi musu duk wani abu daya kamata, daga ita har Babyn bacci sukayi. Ya samu waje ya zauna, sai kallon yaron yakeyi, zaiso ya dauke shi daga inda aka kwantar dashi, amman kuma bayason ya tashe shi, yayi kuka ya tashi Maryama, tana bukatar ta huta ko da ba'a fada masa ba. Dakyar ya iya fita ya barsu, shima dan yana so yayi waya ne. Alhaji Mustafa ya fara kira ya gaya masa, ta cikin wayar yakeji irin farin cikin da labarin ya sakashi, sai addu'a yakeyi yana karawa. Inda lafiya, zai fara kiran Hajiya Rumana ne, amman gabaki daya ta canza masa tun tahowarshi da Maryama, ko da ta gama fushin, saida tace masa "Ba zan taba karbar auren nan naka ba Haris, banga ranar da zuciyata zata amince da 'yar Sa'idu a matsayin surika ba, tunda kafi karfina yanzun, babu wani abu da zan fada yayi tasiri akanka, inaso in zamuyi magana muyi maganar data shafemu, karka sakko mun matarka a ciki, bana son ji" Amman haka ta kirashi ta balbale da taji labarin cikin a wajen Munira "To meye na boyemun? Kamar wani abin arziki" A hankali yace "Ke kikace bakyason jin Mami, duk wani abu in dai ya hada da Maryamm, shisa ban fada miki ba" Tsakin da tayi ya tabashi har kasan zuciya, shisa ko haihuwar nan ma ya riga yayiwa kanshi alkawari sai dai taji a bakin ko Alhaji Mustafa din kosu Munira. Dan ya kirasu daya bayan daya ya gaya musu, harda su Mukhtar kuwa, addu'o'in da suke tayi na kara sanyaya masa zuciya. Sanda ya gama wayoyin ya koma basu tashi daga baccin ba, saiya sake fita ya nemi abinci yaci. Saida suka kwana a asibitin tukunna aka sallamesu. Wani sabon kukan ya kwacewa Maryama bayan sun koma gida, taga daga ita sai Haris, shiya karbi Babyn, ita ta shiga wanka, wankan data saka towel tayi shi sosai kamar yanda Adda Zahra ta kwatanta mata. Wai yau itace ta haihu a wata kasar, daga ita sai miji, babu wani dan uwanta ko guda daya, ta tuna irin taron dangin da akeyi a asibiti idan wani na gidansu na nakuda, Hajja ce kawai bata zuwa, amman ko haihuwar farko ta Adda Zahra, ba zata manta ba harda Alhaji Sa'id a wajen "Yanzun kai sai ka bisu asibiti? Dan Allaah sai kaje kayi tsaye 'yarka na nakuda?" Hajja tace masa "Ai idan na samu waje zan zauna, in ban samu ba kuma haka zamuyita tsayuwa tare har Allaah Ya sauketa lafiya" Kuma Hajjan data dauka da wasa yakeyi ta kwashi mamaki, dan tare da yaranshi kaf da suke nan suka dunguma zuwa asibitin, suka cika, danma na kudine, duk da haka saida aka korasu waje, dan sunki yin shiru, kuma duk bayan mintina sai wani cikin mazan yaje ya samu Nurses da duk wani likita da zai gani ya addabeshi da tarin tambayoyi. Da ta haihu kuwa, tunda mijin yace ba zataje gida wankan jego ba, haka dangi suka cika gidanta anata kai kawo. Amman ita nata yaron ma batasan ranar da zasu ganshi ba "Adda Munira tace zata zo, kilan gobe ko jibi...zata zo ta ganku" Kai kawai ta daga masa da yake fada mata a hanyarsu ta komawa gida, kuma kukan da ta dingayi a bandaki ne yasa ta dade, har saida Haris ya kwankwasa mata kofar tukunna, ta fito, ta samu doguwar riga ta zira a jikinta, ko mai bata shafa bama, ta dai murza turare, shima saboda sabone, ta kwanta, Haris yazo ya kwantar da jaririn a tsakiyarsu, shima ya kwanta "Sannu..." Ya fadi a hankali, idanuwanta yake kallo "Me ya sakaki kuka?" Ya tambaya "Ba kuka nayi ba" Ta amsa "Karya ne..." Saita sauke kanta saboda wasu hawayen da taji suna neman balle mata "Me ya sakaki kuka?" Ya sake tambaya "Mu kadai, babu kowa, mu kadai, inka tafi kabarni ya zanyi?" Ya dan sauke numfashi "We will figure it out, ni da ke, bama bukatar kowa, bakya bukatar kowa Maryamm, ina nan, ni kadai na isheki" Tayi shiru, ganin ba zata amsa ba yasa shi cewa "Baki tambayi sunan babyn ba" Har mamakinta ya dingayi da cikin yana girma bata tabayi masa maganar sunaye ba, da yayi mata ma saita dan daga masa kafada "Kowanne suna yayi maka fa" Dan ita dai bata ma taba wannan tunanin ba, kuma a ganinta abu mafi wahala dai ka samu yaran, dan suna, ai ba zaka taba rasawa ba "Ya sunanshi? Kayi masa huduba daman?" Ya daga mata kai, ya gyara kwanciyarshi yanda zai kalleta sosai "Sa'id, sunanshi Sa'id" Kuma shirun daya lullube dakin bayan maganarshi, irin shirun nan ne da yafi duk wata tarin hayaniya tasiri, shiru ne da zaka iya karanta, shirune mai cike da abubuwa masu yawan gaske, idan aka tambayi Haris kai tsaye zaice Ba saboda Maryamm bane, Ba saboda ita bane, Zai kara da Sabo da Baba ne Saboda shi kawai. Ko da ba Maryamm yake aure ba, wannan sunan shine yakeyi masa yawo duk lokacin da yayi hasashen samun yaro namiji tunda alakarsu ta gyaru da Alhaji Mustafa, idan macece kuma zai saka mata Rumana, zai saka sunan Maminshi. Amman namiji kam Sa'id ne, daya duba abinda sunan yake nufi saiya kara kwanta amsa a rai Sa'id Aminin mahaifinshi Dan uwan da kaddara taba mahaifinshi. Mutumin da ya tabbatar Alhaji Mustafa yana kauna fiye da 'yan uwanshi na jini ko da bai taba bude baki ya fadi hakan ba "Sunan Abba na?" Cewar Maryama tana so ta tabbatar "Sunan abokin Babana" Ya amsa mata, sai tayi dariya, tayi dariya hawaye na kwace mata "To me zamu kira shi? Takwaran Baban Tudun Wadan?" Da dukkan zuciyarshi yace mata "Ke zaki zaba, kome kika zaba zaiyi mun" Ta dan numfasa, duk wani hali da take fatan jaririn da yake tsakiyarsu ya dauka na Alhaji Sa'id na gifta mata "Awwab, zance masa Awwab" Maryama ta fadi zuciyarta na budewa waje-waje da tarin soyayyar Awwab din "Zamu ce masa, zamu kira shi da Awwab, yaronmu Awwab" Haris ya gyara mata, yana kara maimaita sunan a kasan numfashin shi, yayi masa dadi "Awwab" Maryama ta maimaita kamar tasan abinda Haris din zai fadi, sukayi dariya a tare. Kuma da Alhaji Mustafa ya kira yana tambaya "Ina bakon duniya? Ni banma tambayi sunan abokin nawa ba" Cikin farin ciki Haris yace "Sa'id, sunanshi Sa'id Baba" Alhaji Mustafa ya danyi jim, kafin yace "Nagode Haris, Allaah Yayi maka albarka, Allaah Ya karramaka ninkin karamcin da kayi mun, Allaah Yayiwa abokina albarka, zuwa New York ya kamani, dole inzo inga Aminina" Haris yayi dariya "Maryamm tace zamu kira shi da Awwab" Alhaji Mustafa ya jinjina kai daga dayan bangaren "Mai yawan ibada, aikuwa abokina ma'abocin ibada ne, Allaah Ya tabbatar dashi akan ma'anar sunanshi da kuma sunan da kuka zabi kuyi masa alkunya dashi. Allaah Yayi muku albarka Haris" Wannan kalmomin, na Alhaji Mustafa, sune suka rike shi, su ya dinga jujjuyawa a cikin kanshi yana amfani dasu wajen goge bacin ran da Hajiya Rumana ta saka shi a ciki "Sa'idu? Haris ubanka ko mutuwa yayi ai banyi zaton idan sunanshi baiyi maka dadi ka sakawa danka ba zaka tsallake dangina da nashi ka dauko sunan bare ka maka, to wai ni daman Sa'idu da 'yarshi na haifawa kai? So kakeyi aga na yanke jiki na fadi? Bakin cikinku kai da ubanka ya kassarani?" Abinda bata sani ba, abinda inda ta nutsu zata gane ya faru, yanda Haris yayi shiru yana shanye duk abinda take fada batare daya kashe wayarshi ba, ai tasan ko fada takeyi masa zai kashe wayarshi gabaki daya, idan ma a gabanta yake zai fadi abinda yake ranshi ne, koya tashi ya bar mata dakin. Amman sai da ta gama tas tukunna yace mata "Kiyi hakuri..." Cikin sanyin murya kafin ya kashe kiran. Zuciyarshi na bugawa saboda bacin rai, dan saida ya shiga gidan, yaji dadin ganin Maryama da Awwab na bacci, ya duba inda yayi ajiyarshi ya nada wiwin ya busa tukunna ya dan samu kanshi ya fara sauka. Shifa Maryama ce tasa ya daina kashewa Hajiya Rumana waya, shima ranar irin ihun da takeyi har Maryaman da take gefenshi saida taji, daya kashe saita bishi da kallo "Kashe mata waya kayi Ganja? Mamin? Tana magana ka kashe wayar?" Ya kalleta shima "To me zanyi idan ban kashe ba?" Tace masa "Bakomai" Amman ga mamakinshi saita dauke masa wuta, sosai ya kasa gane kanta, saida sukayi rigima sosai tukunna tace "Me zance maka to? Kasan hakkokin uwa akan yaranta? Kana kashe mata waya so kakeyi ka jefamu a matsala? Ko bakasan yanzun rayuwarmu hade take ba? Abinda zai sameka zai sameni?" Hajja ma haka tace mata, idan bata tayashi yayiwa Mamin biyayya ba su dukane zasu sha wahala, rayuwarsu ta riga ta hade waje daya, dole ta saka shi yayi mata alkawarin ba zai sake kashe wayar Hajiya Rumana ba duk fadan da zata dingayi, kuma zai dinga yin shiru in tagama ya bata hakuri. Wani abin ma mamaki yake bashi idan yaga wai shine Maryama take sakawa a gaba tana balbalewa da fada, gashi in tana cikin irin wannan yanayin sai dai duk abinda zaiyi mata yayi, ba zatayi shiru ba, har tsalle takeyi kamar zata kama shi da kokawa, yar yarinyar da zai iya rabawa gida biyu. Kamar yanda Munira tace masa zataje, kwana uku da haihuwar Maryama ta sauka a kasar New York, da akwatinta shakare da siyayya, amman ko kadan baiji dadin yanda tayiwa Maryama dibar karan mahaukaciya ta watsar ba, muryarta can kasan makoshi ta amsa gaisuwar da Maryaman tayi mata, dan cikakken kallo ma baiga tayi mata ba, data dauki yaron sai ta wani sauke numfashi "Kasan addu'ar da muka dingayi da Anisa, Allaah abinda za'a haifa karya yo mana kwashe-kwashen wasu kamanni can, sai gashi yayi kama da kai" Shi dai Haris daya kalli Awwab baiga kamannin da tace ba, da alama dai yaron zaiyi baki, amman fuskar Maryama yake gani a tare dashi "Nikuwa fuskar Mamanshi nake gani fa" Ya amsa kanshi tsaye, Maryama tana jinsu "Allaah Ya kiyaye...inji wa? Kai kasan kamanni ne" Taso tayi shiru, amman zuciyarta tafasa kawai takeyi, ai daman itama bawai sunyi mata ba, Haris dinma sai da tasan shi, ya fara mata kirki tukunna ta tsame shi daga jerin masu bakar zuciya kamar bakaken fuskokinsu "Ai ba sai yayi kama dani ba, tunda ba zai canza cewa daga jikina ya fito ba, to Alhamdulillah, fatana dai ya dan haska, kar yayi bakikirin din nan...shine bana so" Haris yayi murmushi mai sauti "In Shaa Allaah baki zaiyi, duka yaranmu bakake zamu haifo, tunda kike mun wulakanci" Munira taji ta shake har makoshi "Dariya maganar ta baka? Wannan ai zagi ne" Kuma wannan fadan da Haris ya biyewa Munira sukayi ne yasa tace ba zata kwana a gidan ba, ta tafi ta kama hotel, dan ta daga akan Maryama ta zagesu, shikuma yace baiji sanda tayi zagi ba yana dorawa da "Babu fa yanda za'ayi kizo gidanta kice zakiyi mata hayaniya, ba zan dauka ba" Ta kara harzuka, Maryama tayi zaune, dan Haris ya gama wanke mata bakin cikin Munira, sai dai ko awa biyu da tafiya batayi ba sai ga Hajiya Rumana ta kirashi ta rufe shi da zagi "Yar uwarka zaka wulakanta? Ai bansan ka gama mallakuwa ba sai yau Haris, wallahi ban yarda ba, da bana yarda da abubuwan nan..." Sai kawai ya zabi ya karya alkawarin da yayiwa Maryama, ya kashe wayarshi, dukanta, Munira bata dawo gidan ba, daga can ta wuce, bai kuma nemeta ba, kamar yanda ya fadane, in ma Anisa da tace masa tare da Alhaji Mustafa zasu zo in zaizo niyyarta kenan, tazo tace zatayi wa matarshi hayaniya, yana fatan Munira ta gaya mata, zasu kwashi 'yan kallo "Na karba Baba, na karbi auren" Haka yace, kuma yana nufin kowacce kalma, a cikin wannan karbar akwai mallakar Maryama, a cikin karbar aurenta akwai kareta daga dukkan abinda zai iya, ko da abubuwan nan sun hada da 'yan uwanshi Hajiya Rumana ce kawai zai cire daga wannan lissafin, ita kadaice zaiyi hakurin dole da ita, tunda wadda zaiyiwa fadan ma in taji ba zasu kwashe da dadi ba Hajiya Rumana ya cire, Ya manta da kanshi, a jerin abubuwan da ba zai iya kare Maryama daga su ba... Haris ya manta bai cire kanshi ba! 33 Da sunyi waya da 'yan gidansu sai suce mata "Ya New York?" Ba zatace ga adadin sau nawa akayi mata wannan tambayar ba, amman duk sanda za'a tambayeta sai ta dauki wasu yan dakika tukunna take iya amsawa da "Alhamdulillah" Tunda tasan abinda suke fatan suji kenan, kuma shi take fada musu, a shekarunta biyu yanzun a kasar, wani lokacin inta na kwance tare da Awwab su kadai a gidan, Haris baya nan, sai tambayar ta fado mata a rai, to ya zata amsata idan zata fadi dukkan gaskiyarta? Ta ina zata fara? Da kanta zata fara? Babu inda take zuwa saita kama dole, daga cikin dolen kuwa asibiti ne, yawanci ma Awwab ne, kuma bata taba zuwa ita kadai batare da Haris ba, sai kuma wani lokaci idan kadaicin ya isheta saita fito waje, a hakane ma suka saba da Chloe sosai, dan har yaranta tana barwa Maryama ta danje siyayya ta dawo. Sai kuma wata rana sukan dan zagaya cikin unguwar, daga can kasa ma akwai wani dan park da zaka iya kai yara, to dansu motsa jiki sai suke takawa da ita da Chloe, ba karamin tashin hankali sukayi da Haris ba kafin yake barinta wannan fitar, sau daya a sati, tunda tsautsayi yasa sun fita tare take ce masa "Nifa tunda nazo kasar nan banda kai banga baki ba, mazansu duk farare ne" Kalar kallon da yayi matane ta gane cewa tayi kuskure, sai kuma da suka koma gida baiyi mata magana ba, lokacin ta fara ganeshi, ta fara karantar abinda ya zabi yayi mata shiru akai ta cikin idanuwanshi dama yanayin shi. Gabaki daya ta kasa sukuni, zuciyarta ta dinga bugawa, tana taradaddin zuwan dare, tunda wani hali data kula ya dauka idan yayi mata shiru haka shine ya huce haushin nashi akanta, ya gayawa jikinta abinda bakinshi bai furta ba, bataso, batasan wannan horon da yakeyi mata, tayi masa magana harta fara gajiya ma, sai kuma ya bude drawer din dakin nasu, batasan me yaje yi ta bangaren kayanta ba ya juyo yana ce mata "Waisu wannan turarukan da kika zo dasu, meye amfaninsu idan ba zakiyi amfani dasu ba?" Tunda bayan kayan sakawarta, spices din shayi, bata dauko komai ba sai turarukan da kuma turaren wutarta na Meens_incense, cancana shi takeyi sosai, tasan ita da sake samunshi sai dai in sunje ganin gida. Ta kalli daya daga cikin kwalaben daya daga, turarukan nan ne, wanda Ishaq ya bata, tun daga Kaduna ta dauki abinta har Kano, kuma bata taba fesasu ba, duk sanda zata bude wardrobe din kayanta zata ganshi, saiya zama wani abu data mallaka, wani abu nata. In zakace mata me yasa ta jefasu cikin kayan da zata taho dashi bata sani ba, kuma har kasan zuciyarta ta manta rabon da ko a tunani Ishaq yazo ranta, ko da kuwa taga turarukan nan ne. Yaushe ma ta samu lokaci? Tsakanin hidimar Awwab da bata karewa, danma Allaah Ya taimaketa bashi da rigima ko kadan. Ga kuma hidimar Haris din in dai yana nan, naniqar da yakeyi mata ma bata barinta wani tunani, kusan ma zatace gabaki daya ita yanzun tanajin babu kowa a rayuwarta sai shi kadai, bata da wanda zata juya ta kira da nata sai shi da Awwab "Zanyi amfani dasu" Ta amsa shi cikin sanyi murya, sai kuma ya fesa a bayan hannunshi "Karya ne" Ya fadi yana dorawa da "A ina kika siya?" Dan kamshin wanda ya fesa din yayi masa dadi "Bani akayi" Bata taba son ace ta iya karya ko boye-boye ba sai da Haris ya kalleta yace mata "Waya baki?" Muryarta can kasa tace "Hamma Na" Kuma batasan ko wani yanayi ta nuna da ya saka shi tsayar da hankalinshi kacokan akanta ba "Wanne a ciki?" Taji muryarshi, tayi kasa, yanda takanyi idan wani abu na gab da bata masa rai "Baka sanshi ba, gidansu daya da Adda Khairi..." Cewar Maryama cikin rawar murya, da yake kallonshi takeyi, tana ganin lissafin da yakeyi, yanda yasan kowa da kowa na gidansu, wanda suke uwa daya uba daya dama wanda suke abokan wasanta har mamakinshi takeyi "Hammanki....kikace Hammanki Maryamm?" Ta sauke idanuwanta "Turaren wani kato kika dauko tun daga Nigeria har New York? To ajiyar me kikeyi musu ma tun daga farko? Akan me zaki ajiyesu? Yaushe ya baki? Ko Khairin ya aiko dasu bansani ba?" Da saurinta ta girgiza masa kai "A'a, sun dade, tun kafin aurenmu" Sauran turarukan ya kwaso, tana kallonshi ya kama hanyar kofa, idanuwanta suka cika taf da hawaye, daga inda take tanajin karar fashewar kwalaben nan, kafin kuma shiru ya biyo baya. Ranar ya dauki mintina kusan talatin kafin ya dawo dakin, daya hawo gadon inda take, taji kaurin wiwi dinshi, sai dai bataso tace masa komai, ita numfashi mai karfi ma bataso tayi saboda dare ne, saboda a yanayi irin wannan Haris yana bata tsoro. Sai dai a karo na farko ya saka tazara a tsakaninsu, sai hakan ma yafi bata tsoro "Kiyi mun shiru Maryamm, ni banyi kuka ba kece zakiyi kuka?" Ya fadi saboda sheshekar da takeyi, kirjinshi zafi yakeyi, yasan yana da kishi, amman baisan cewa kishin nashi ya wuce misali ba haka, sai da yaso buga mata daya daga cikin kwalaben turaren nan "Ya sunanshi?" Tambayar ta kwace masa, taji shi, saida ya sake maimaitawa tukunna "Ishaq" Ta fadane saboda tasan tunda ya tambaya dole saiya samu amsar zai kyaleta Ta fadane saboda bata hango hakan zai zame mata wata gagarumar matsala a shekarun da zasu zo ba "Saurayinki ne?" Ta girgiza kanta, ita ai batama tabayin saurayi ba, duk da 'yan gidansu sun sha kiran Ishaq din da saurayinta, amman tunda babu wata kalmar so data gifta a tsakaninsu ba zata kirashi da saurayinta ba "To me yasa? Zaki ajiyemun abinda ya baki a daki? Me yasa ma zaki ajiye duk tsahon lokacin nan?" Shiru tayi tunda bata da amsar da zata bashi, shima bai sake ce mata wani abu ba, washegari data gaishe dashi bai amsa ba, baiyi mata magana ba sai da ya gama shiryawarshi, tukunna yace mata "Ki duba kiga babu abinda kuke bukata?" Ta girgiza masa kai kawai, idan ma akwai tayi order din abinta a kawo mata har kofar gida "Karki fita ko ina, ina nufin ko ina" Kan dai ta sake daga masa tana kokarin kar hawaye ya balle mata tunda in bata fita ba ai ba zata mutu ba, karshen dai abinda zaiyi mata kenan ya kulleta cikin gida "You are mine Maryamm" Haka yasha fada yana maimaita mata, idan wani yaji yanda yake fadar kalmomin, sai yace zai tayata murna, saiya zata wata zazzafar soyayya ce taja hakan, kamar yanda itama tayi tsammani ranar daya fara furta mata, dan wani irin abune ya taso yayi mata rumfa, tayi kwanaki tana jujjuya kalaman suna kuma yi mata dadi, amman yanzun ta fara gane ba kalaman soyayya bane ba, na nuna iko ne, na mallaka ne, ita din tashi ce, yayi yanda yake so da ita. Shisa in wani abu ya hadasu saiya zabi ya kulleta cikin gida da kalamanshi, dan yasan baya bukatar amfani da mukulli dan yin hakan, bata isa ta fita babu izininshi ba. Idan ya zauna gidan saiya kara janye mata kanshi, Awwab din da zaiga ta shiririce ta biye masa, saiya zo ya dauke shi yayi daki dashi, ko in suna dakin su fiti falo, ko suma fita su bar mata gidan. Wata rana mamaki ya kamata, in ta kyaleshi. Zata so ace zata iya ba Hajja labari inta tambayi ya suke, labarin Haris da taurin kanshi, in ta kare bada labarin ta rufe shi da fadin "Hajja kinga wanda ya fini taurin kai ko?" Tunda ita fadanta ma yafi kafiyarta, to fadan kanshi hayaniya kawai zata nunawa Haris, shima ranar daya zabi yayi mata, yana daga muryarshi tata take dishewa babu shiri. Ita duk fadanta bata da riko, da tayi magana shikenan, amman banda Haris, bata dogon fushi, Haris na iya sati biyu akan dan karamin abu, sai ta bashi hakuri kamar harshenta zai tsinke, tunda in bata lallabashi ba, tana finshi shan wahala, zai fice ya barta, zai iya dauke Awwab su fice abinsu. Sai da yayi kusan wata maganar  nan ta Ishaq bata wuce masa ba "Na fada maka yanzun bana son tashin hankali, ba zaka daina mun fushi ba? Nace ka dinga mun fada a wuce wajen, ka daina mun fushin nan banaso.." Amman yayi biris da ita kamar ko yaushe, sai da tayi masa kuka na gaske tukunna ya sauko, ya riketa yana fadin "Bansan sau nawa zan gaya miki ba, ke tawa ce, ni kadai, in zan iya zan koma baya kafin ki sanni, in goge duk wani namiji da ba muharraminki ba Maryamm, yanzun, yanzun da kike tawa..." Bai karasa ba, amman taji kashedin, tama kanta alkawarin kiyayewa. Tunda sukazo New York babu wanda taji dadin zuwanshi irin Alhaji Mustafa, kamar taga Alhaji Sa'id haka ta dingaji, kwananshi daya ya juya, harda hawayenta, kamar ta bishi lokacin, sai Anisa ma tazo dan batasan me yasa basu zo tare da Alhaji Mustafa kamar yanda Haris ya gaya mata ba, ita dai satinta daya, wasu kwanaki da Maryama tayi su cikin takura matuka, bawai Anisa na shiga harkarta bane ba, amman a lokacin duk abinda zatayiwa Awwab to saita kushe, saita fadi maganar da zata saka Maryama taji cewa ta gaza a matsayinta na uwa. Kuma tana maganar ne cikin sigar da babu yanda za'ayi kace da wata manufa tayi "Sannu Maryam, gaskiya yaron nan ina tausaya masa, tunda naga babu abinda kika iya, kalli yanda kika matse masa ciki da diaper din nan, kila shisa yaita kuka dazun, saifa kin kula, kinsan kowa zai iya haihuwa, amman ba kowa bane zai iya kula da yaro" Saita dinga kallon Haris, taga ko ita kadai ce taji kamar Anisa ta gaya mata magana, amman sai dai in tana kusa dashi ya kara riketa, abinda bayajin kunyar yi a gaban kowa, wani lokacin kuma zaice "Ai zata iya hankali" Idan abinci ne ta dafa Anisa zatayi order din wani abu "Ki dauke kayanki fa, da baki wahala bama, ba kowanne abu nakeci ba, miyar ma kamar mai yaso ya kwace miki" Komai, karamin abu da babba saita samu maganar da zata fada, ba karamin dadi taji ba lokacin da Anisar ta tafi. Ta dinga addu'a kar Allaah Ya sake saka wani cikinsu yazo mata gida, tunda ba zata iya ganin nata 'yan uwan ba, ta yafe nashi, kowa ya zauna inda yake, ita dashi su zauna inda ya kawota. Kadaici nema in ya dameta zata saka shi a gaba da roko "Dan Allaah mu dan fita, kaji Ganja, dan Allaah...nima in sha iska" Saiya girgiza kanshi "Ki bude window, ni ina zan fita dake kije kina kallon wasu garada...ai kiyi zamanki a gida yafi samamun natsuwa" Akwai randa ta gaji tace masa "Ganja" Ya kalleta batare daya amsa ba "Gida nake so in koma, nagaji, ka mayar dani gida..." Sai yayi murmushi "Wallahi nagaji, Allaah nagaji, in baka mayar dani ba zan koma" Dariya yayi, mai sauti, taji hawayen bakin ciki na neman zubo mata, da ma ta saka masa rikici saiya kamata yayi mata rikon da ko motsin kirki ba zata iya ba "Kije ina? In kika bar New York da sunan zuwa gida to tare dani ne, muje mu dawo...ai yanzun ke banajin akwai inda zan iya barinki kije batare dani ba Maryamm, kije wani ya ganki? Ko ke ki ganshi? Kinaso zuciyata ta buga?" Ita wannan ma duka abune da ta fara sabawa dashi, kadaicin, da kuma da yawa daga cikin halayen Haris, dashi dinma gabaki daya. Tashin hankalin farko data fara fuskanta shine wani irin tari da Haris din yakeyi da sassafe, da asuba idan ta tashe shi sallah, haka in yana dariya. Sai takai ta kawo idan zai dauki Awwab su fita to haka zai shigo yana numfarfashi "Mura ce tayi maka wannan kamun haka? Anya ba zaka ga likita ba?" Ta tambaye shi cike da damuwa da taji yana tarin cikin dare, dan sai da ta dafe masa kirjinshi jin yanda yake dagawa, kusan sati yana fama, ita har alamun zazzabi takeji a jikinshi, amman yaki bari suje asibiti "Tari ne kawai, zai daina, kilan sanyin dana kwasa ne a wajen aiki rannan dana fita ban wani saka kaya masu kauri ba sosai" Dole ta kyaleshi, sai ranar wata alhamis, tana kitchen tana hadawa kanta cereal dan taji kamar alamun yunwa ne, kuma batajin yin wani girki, yunwar yamma dai, ita ko kafin ta yaye Awwab yunwa bata damunta haka, yanzun kuwa kamar gara, daga ta ci abinci sai taji kamar an kwashe mata shi, anan ta tsaya ma tana sha, tana kallon yanda Haris ya biyewa Awwab yana binshi da gudu suna ta zagaye falon, shi in za'a wuni ana wasa baya gajiya, sai dai kai ya barka da ciwon jiki, tarin nan Haris ya fara, ta ajiye bowl din hannunta tana jera masa sannu, ruwa take kokarin dauko masa taga ya durkushe ya rike kirjinshi, batasan lokacin data bar fridge din a bude ba ta karasa wajenshi. Numfashi yake fitarwa kamar mai ciwon asthma, ga hannunshi da ya dafe kirjinshi dashi, a durkushe yake amman yanda yake fitar da numfashin a wahalce dole ya karasa kwanciya kawai, gabaki daya Maryama ta rikice, dakyar dabarar kiran 911 tazo mata, ta rike Haris, ta dago masa kanshi ta kwantar a cinyarta kamar yanda sukace tayi ko kofofin iskar shi zasu bude, kuka kawai takeyi, Awwab da baisan meke faruwa ba, ganin dai tana kuka shima ya fara, lokacin da suka karaso kuwa suka janye shi daga jikinta, suka saka masa abin numfashi a hanci, suka dorashi kan gadon daukar marar lafiya, wasu suka wuce dashi zuwa wajen motar asibiti, ita kuma daya a cikinsu yake tambayarta ko akwai wanda zasu kira mata. Ta girgiza masa kai tanata kuka, da Awwab data dauka, haka taja kofar gidan suka shiga motar asibitin, suka wuce da Haris. Allaah Ya taimaketa kafin su fitan taja wani babban showel da take goya Awwab dashi, dan bacci yayi mata a waiting area din nan, ta kuwa goyashi, tana ganin yanda har Nurses din suke ta kallonta, wasu suyi mata murmushi, daman ko Chloe sai ta dinga ce mata ta koya mata yanda akeyin goyo, haka zasu shiririce wani lokacin ana abu daya, kamar goyon ne da basu saba gani ba yake basu mamaki. Ita dai banda ajiyar zuciya babu abinda take saukewa, ko waya ma bata dauko ba, tunda babu amfanin da zatayi mata. Inta dauko wa zata kira? Nan ba kamar Kaduna zuwa Kano bane, tasan sai dai ta daga musu hankali kawai, watakila kuma ta janyo musu 'yan uwan Haris suzo su kara dagula mata lissafi. Hankalinta bai kwanta ba sai da taga Haris, duk da har lokacin akwai abin da yake taimaka masa wajen yin numfashi, taji dadi da suka barta ta ganshi. Abinda akace yana damunshi ne bata tabajin ko sunanshi ba, saida ta tambaya sau biyu, ta kara sa cewa likitan ko zai rubuta mata tagani "Chronic bronchitis" Ta karanta tana haddace kowacce kalma, bayani yayi mata gamsashe, ta dinga goge hawaye, ta rasa ya zatayi da Haris, ya zatayi dashi da wannan Wiwi din da yaki ya taimaki kanshi ya kuma taimaketa a yanzun da rayuwarsu take waje daya ya daina sha, so yake ya kashe kanshi. Wasu hawaye suka sake balle mata jin cewa cutar ba wadda za'a iya warkewa gabaki daya bace ba, asalima in har bai daina bankawa cikinshi hayaki ba zata iya kai matakin da ba'a fata, ta hangota da Awwab, babu Haris, irin kadaicin da take shiga in ya tafi makaranta da aikinshi, to ace babu shi gabaki daya fa? Wani abu ya rufza cikin kirjinta, tashin hankali nayi mata dirar mikiya, kamar itama nata numfashin zai dauke. Tayi sanyi da yawa, itama ta sani, Haris yasa tayi sanyi da yawa, a halin yanzun kuma ba wannan Maryaman yake bukata ba, dole ta bude ido daga rufewar da suka fara, kamar yanda yake fada ne, daga ita sai shi a kasar New York, yana bukatarta kamar yanda take bukatarshi Watakila kaddara ta hadasu ne dan ta taimake shi Amman ai kaddara na da fuskoki da yawa, kuma a tata rayuwar, kaddara tazo mata ne da fuskar Haris Ganja... 34 Kwanansu tara a asibiti, ba zatace ga sau nawa ta kalli kanta a mudubi ba a cikin wadannan kwanakin, amman tasan ta kara ramewa, tayi haske sosai, amman ta rame, kuma abinci take ci da har mamakin kanta takeyi, sai dai idan akayiwa Adda Maimunatu maganar kibar da takeyi sai tace "Ku rabu dani, bafa abinci bane kawai, abincin ne ya hadu da kwanciyar hankali, inda hankalina ba'a kwance yake ba yaushe abinci zai bi mun jiki harku isheni da magana" To Maryama tasan abinda yake faruwa da ita kenan, rashin kwanciyar hankali, ciwon Haris yayi mata tsaye, ba'a asibitin take kwana ba, wannan zirga-zirgar kadai ba karamin jigata takeyi ba, danma Chloe ta taimaka mata ta samu babysitter, sai take bar mata Awwab, saukin data samu kenan. Kawai inta kalli Haris sai ta dinga tunanin tarin dokokin da suke tattare da wannan ciwon da shine ya jawa kanshi, dokokin da take ta tunanin hanyar da zatayi amfani da ita wajen ganin ya bisu. A wannan kwanakin, a rana ta biyar da aka cire masa abin taimakon numfashi, ya koma yi da kanshi, daya tashi daga bacci, idanuwanshi akanta, wandon jeans ne a jikinta, sai riga mai dogon hannu, daga yanda take zaune ma yana ganin girman rigar, dan ta sanyi ce mai laushi, kalar yellow, sai ta saka karamin hijabi, tayi masa kyau. "Ka tashi? Ya jikin?" Ta tambaya muryarta cike da gajiyar da takeji "Kin rame, zo, matso in ganki sosai" Batayi masa musu ba, taja kujerar da take kai har gab da gadon, dan ta matsa ne tana dan kallo a laptop din da take zuwa da ita asibitin, ya mika mata hannunshi da yatsanshi guda daya yake makale da wata na'ura. Saita saka nata hannun a ciki, ta kuma kama karamin yatsanshi "Bana son ganin sunan nan" Ta fadi a hankali, batasan sau nawa taso ta gaya masa ba, ta tsani ganin sunan Aise a jikin yatsanshi, kamar ta saka reza ta kankare haka takeji, idan ma ya jita ya zabi yaki amsawa ne "Kin rame, anya ba zasu dubamun ke ba" Numfashi ta sauke "Zirga-zirgar da nakeyi ne kullum, ga damuwarka" Idanuwanshi cikin nata yace "Kiyi hakuri" Ta sauke nata idanuwan "Inyi hakuri dame? Kokarin kashe kanka da kakeyi? Inyi hakuri in fara shirin yi maka takaba? Inyi hakuri ni kadai zan raini Awwab? Inyi hakuri wata rana inya tambayeni meya kashe Babanshi in masa bayani? Inyi..." Yayi saurin katseta "Maryamm" Ta kalle shi "Meye? Kar in fada masa? Ince wiwi ka zaba akan ka zauna damu?" Sunanta ya sake kira, amman ya kasa kara wata kalma akai, saboda yasan gaskiya ta fada "Kashe kanka kakeyi, kana kashe kanka Ganja, kuma rayuwarka ba taka bace kai kadai yanzun" Karo na farko daya fara jin yana so ya bari, amman inya hanga cikin kanshi sai yaji kamar abune da ba zai iya ba "Zan fadawa Baba, zan kira Mami, watakila in sukaji har yanzun baka daina yunkurin kashe kanka ba su zasu maka magana kaji" Ya danyi murmushi, da dukkan zuciyarshi yasan ba zata iya ba, Maryama ba zata taba kai kararshi ba "Yunwa nakeji" Yace mata "Ki siyomun tea" Bata kara cewa komai ba ta mike, ta juya zata tafi ya kirata "Maryamm" Ta kalle shi "Karki kalli kowa" Sai yaso ya bata dariya ma, ita a kwanakin nan da yake kwance, inda zata iya ai da tasha yawonta ma ta huce takaicin kullen da yakeyi mata, to inta kira uber har kofar gida, zai kawota asibiti, in zata koma haka takeyi, duk wani abu da zata siya naci kuma akwai wajaje a kusa-kusa da asibitin dan ba saita hau abin hawa ba. Kawai sake juyawa tayi ta fice abinta, tunda itama yunwar takeji. Kuma tunda ya tashin dai, duk sanda zata fita saiya dinga jaddada mata karta kalli kowa, yanda ya addabeta da maganar "In kinga an cika kallonki kawai ki bar wajen Maryamm, kinji" Sai kawai take saka facemask, amman bata tsira ba "Me yasa kika saka kwallin nan kika fito? Kinga yanda idanuwanki sukai kyau" Gajiyar da ita yakeyi da irin abubuwan nan "Kin rame da yawa, Allaah sai an dubamun ke zamu bar asibitin nan, kilan wani abin ne daban yake damunki" Batace komai ba, sai kuma yace mata "Ya kamata kina period, yau tara ga wata" Tasani, ita bata kawo komai a ranta ba, ta dauka ko wannan stress dinne yasa ta samu delay "Maryamm" Haris ya kira yana wani irin murmushi "A'a" Tace tana girgiza kanta, ba dai ciki ba, to duka yaushe ta yaye Awwab? Kuma ita da ko numfasawa batayi ba sai ace harta kara samun wani cikin? Haka akeyi? Ita da suke shirin zuwa ganin gida ma kamar yanda Haris yayi mata alkawari nan da watanni uku "Yes" Shikuma yace cike da zumudi, wani cikin? Wani yaron ko yarinyar? Yana so, yana so sosai. Allaah Yasa wannan yayi kama dashi, saboda kowa ya kalli Awwab yanzun zaiga yanda yaron yake juyewa zuwa fuskar Maryamm duk da kuwa bakine, amman baya kama dashi, kalar kawai ya dauko. Haka sukaje ana dubawa kuwa ciki gareta, in tace tayi murna karya takeyi, asalima wani abune ya danne mata kirji, yanzun anan zata kara haihuwa? A wannan kasar ita kadai "Banaso in kara haihuwa anan Ganja, dan Allaah ka mayar dani gida in haihu acan, in yaso sai in dawo" Yanda yaga yanayinta yasa shi yin shiru, bayaso tayi masa kuka ta dagula masa lissafi, amman shi ina zai bari ta tafi batare dashi ba? Taje gida ta haihu, wata nawa kenan? Ba zai iya ba, ya kamata ta fara gane cewa ba zai iya bari tayi nisa dashi ba yanzun. "Zamu san yanda zamuyi, karki damu" Hawaye ya cika mata idanuwa, amman batayi masa gardama ba, asalima ta yiwa kanta alkawarin ba zata sake tayar masa da zancen ba, kyaleshi zatayi, suje gidan, sai taga idan a saman kai zai dauketa yasa ta sake binshi. Ko bayan an sallame shi suka koma gida, babu wanda ta fadawa maganar cikin, harda Khairi kuwa. Tunda batajin tama san me takeji, ta dai san batayi farin ciki ba, kuma tanajin bata shirya kara haihuwa da wuri haka ba. A wannan watan ne ta samu labarin da yayi mata dadi da dukkan zuciyarta, saka ranar Khairi, da Ibrahim Bakori. "Ikon Allaah Adda...Ibrahim din dai" Tace cikin mamaki tana dorawa da "Bakya tsoro Adda? Bakyajin kishi? Yana da wata matar fa" Khairi tayi dariya "To akanta zan zauna Maryama? Ni ina ruwana da matarshi? A Kano fa zamu zauna, kinga Abba ma yanata mun kokari in samu transfer tunda nan da wata uku zamu gama level 2, kuma kinga bikin wata ukun aka saka" Dadi ya kara kama Maryamm "Aikuwa zan yiwa Ganja magana sai kawai mubari ma sai watan bikin mu taho, inaso ayi komai a gabana, komai da komai" Khairi ta sakeyin dariya "A Kano din zaku zauna?" Maryama ta tambaya "Ai shine dalilina na aurenshi, saboda zai ajiyeni kusa dake" Wata kewar Khairin ta danneta, bawai saboda su Mummy ba, ko sauran 'yan uwanta, saboda ita "Ko kun fasa dawowa?" Maryama ta girgiza kanta kamar Khairi tana ganinta, Haris bashi da burin zama a wata kasar da ba tashi ba, ta sani, ya fada mata da bakinshi "Kimun addu'a, na siya truck dita ta farko" Haka yace yana dorawa da "Ta farkon da nake fatan ta budemun hanyar siyan wasu da yawa, ina son inyi kudi Maryamm, manyan kudi, irin kudin da ke da yaranmu ba zaku nemi wani abu ku rasa ba, kudin da idan na mutu na bar musu su cigaba da kula dasu suma subarwa nasu yaran" Duk wani plan dinshi, akan wannan business dinne da baya gajiya dayi mata hirarshi, ko fada mata yanda ake ciki, shi ba kamar Alhaji Mustafa ba, ba motocin yake so ya dinga siye yana siyarwa ba, haya yake so a dingayi da motocin, manyan ana daukar kaya daga gari zuwa gari. Mafarkinshi babba ne, kuma tana yawan tunanin wannan mafarkin nashi, tana ganin wanne kudi yake nema banda wanda yake samu yanzun, ko ita idan ta tayashi aikin hotunanshi yana bata kudi, suna nan tana tarawa, a wata 'yar karamar jaka take sakawa tunda dalolin yake bata cash. "To abubuwan hotonka fa? Zaka daina ne" Ya girgiza mata kai "Wancen business din, ina sonshi ne saboda ina hango tarin kudin da yake ciki, saboda kudinne kawai, hoto kuma, saboda ina so" Ita dai ba zatace ta gane abinda yake nufi ba, ta gane bambanci, tunda hoton ma ai ba kyauta yakeyi ba, kudi yake samu, kudi masu yawa a wajen Maryama, tunda bata taba cewa ga abinda take so yayi korafi ba, abinda ma batace ba kwasowa yakeyi. Inya bata kudi duk sanda zai koma makaranta, baya taba tambayarta koya rage, itace ma in zai sake tafiya ya kara mata zatace "Akwai fa, wancen bai kare ba" Sai yayi dariya "To duk ki hada, kici duk abinda kike so, kiyi order za'a kawo miki, kawai dai karki fita ko ina" Yanzun da dukkan zuciyarta ta cewa Khairi "Zamu dawo, daya gama karatunshi, zamu dawo In Shaa Allaah" Tanajin Khairi ta sauke numfashi "Alhamdulillah, Allaah Ya kaimu lokacin" Suka cigaba da hirarsu, hirar ranar ma duk Maryama ce da take ta tsara abubuwan da zasuyi na biki, harda cewa kar Khairi ta sake ta bari wasu su zabi anko, sai tazo zasu je kasuwa su zabo tare, tanata mata dariya. Kuma ko bayan da suka gama wayar haka ta kalli Awwab tace "Amminka ce, Ammi Khairi, kaima kana so kaje kaganta ko?" Da tayi maganar sai taji kamar zatayi kuka, kewar gida da kowa ta kara danneta, wai ace ta haihu, yaronta har ya shekara biyu amman ko su Hajja basu ganshi ba sai a hoto, shekararta uku fa harda wasu yan watanni yanzun rabonta da gida, inda wani ma yace mata zatayi wata uku batare da taga kowa nata ba dariya zatayi. Dariya mai yawa dan tasan sai dai in mutuwa tayi, kuma ko da mutuwar tayi ai ba za'ace ba zata gansu ba, sune dai ba zasu ganta ba, amman zata kasance tare dasu a duk wata addu'a da zasuyi mata, tasan mazan gidansu zasu dinga ware lokacin da zasuje har kabarinta suyi mata addu'a. Tun a waya take fadawa Haris maganar bikin "Aikuwa zan kirata, yanzun ma dan nasan dare yayi su acan, Allaah Ya kaimu lokacin, gaskiya bikin nan na musamman ne, kibari idan na dawo mu zauna mu fara tsara gudummuwar da zamu bayar ko?" Anya tunda tazo kasar New York tayi farin ciki irin na ranar? Da Haris yazo kuwa da gudunta ta tarbeshi da runguma, dan ta riga Awwab din da yake ta kiran "Appa..." Ya kuwa ji dadi, dan saida ya dan cirata sama ya sumbaci fuskarta sannan ya sauketa ya dauki Awwab "Nayi kewarku, sosai..." Kwananshi biyar "Muma haka, gidan yayi shiru" Da Awwab din a hannunshi ya dan rage tsayi ya sumbaci cikinta yana dagowa ya shafa shi, ta danyi tumbi haihuwar Awwab, tunda Adda Zahra tace mata inta gasa sosai da ruwan zafi wajen wanka ta dinga daurewa, yanda taga anyiwa Adda Maimunatu lokacin data haihu, akwai zafi dai, haka ta daure "In dai ba so kike kiyi dirkeken ciki ba, kuma ki kiyayi abubuwan sanyi aqalla har kiyi arba'in" Sai batayi dirkeken cikin da take tsoro ba "Har yanzun bai fara nunawa ba, wannan ba kamar na Awwab ba" Dan shi ya nuna da wuri, ta danyi murmushi tana shafa dan tumbin nata ta cikin rigar da take sanye da ita, watakila yau farin cikin da takeji ne yasa taji kaunar abinda yake cikin yana ratsata a hankali "Zan sha shayi" Ya fadi, babu bata lokaci kuma ta hada masa shayin "Muna da zuwa asibiti jibi" Kai ya daga mata, yanata kokari, wannan karin, duk wani follow up da aka nemi suje baya kiyawa, bayajin dadin yanda in dai zai jijijjiga jikinshi tari yake kamashi. Haka kuma tun fitowarshi asibiti bai sake shan wiwi a cikin gidan ba, ba dainawa yayi ba, ko ragewa, kawai yana boyewa Maryama ne. Saida suka kwanta tukunna take ce masa "Kaga tafiyar da zamuyi cikin May ne, bikin Adda Khairi kuma June akasa karshe, sai mu bari sai cikin June din" Ya gyara mata kwanciya a jikinshi "June, lokacin cikinki wata shida, ina zakije da tsohon ciki Maryamm? Ai daman nabari saikin haihu ne, dan nima zaifi mun dai-dai, akwai tafiyar da zanyi October, lokacin kin haihu, idan mukaje na ajiyeku sai in wuce, sanda zan gama komai ba sai in dawo mu tafi ba, watakila sati uku haka zanyi, kinga kowa, kowa ya ganku ko?" Wani abune takejin yana tasowa tun daga bangarorin jikinta yana haduwa a cikin kirjinta inda yayi dunqule yake tokare mata numfashi "Bangane ba, kana nufin ba zamuje ba?" Ya girgiza mata kai "Zamuje mana, amman saikin haihu" Cewar Haris "Bikin Adda Khairin fa? Kana nufin ba zanje ba? Kana nufin saina kara kusan wata bakwai a kasar nan banje gida ba...shekara hudu fa kenan, banga kowa nawa ba? Shekara hudu Ganja..." Ta karasa tana zame jikinta ta tashi zaune "Shisa nace ai zan kaiku sai in wuce, Japan zanje" Cikin bacin rai tace "Ina ruwana ko China zakaje, ni kawai gida nake so, ka mayar dani gida, duk inda zakaje sai kaje" Batare daya tashi ba shi, dan kara gyara kwanciya ma yayi yace mata "Zan kaiki, zamuje, da kin haihu" Aikuwa ta birkice masa "Nawa ne kudin jirgi? Ina da kudina, tafiya zanyi, kasan Allaah ba zan zauna ba, ya zan siyi ticket?" Taso ta bashi dariya "Ke kadai zaki tafi amman dai ko? Dan babu inda zakije mun da yara" Ta daga kai tana kokarin shanye hawayen da saida suka zubo mata "Saiku zauna" In dai Awwab ne, ai Allaah bai dora mata qulafacinshi ba, ko dan yanda ya mayar da dauke yaran ya fice dashi wata hanya ta kuntata mata, saita samawa kanta sauki, inta tafinma sai tayi zamanta, sanda ya gama karatun sai su tattaro su taho shi da Awwab din "Hakanma yayi, ga Awwab, saiki zauna ki haifi na cikinki ki hada kibarmun su" Da wani yanayi a muryarta tace "Ganjaa" Shima ya amsa da "Na'am Maryamm" Kawai saita fashe da kuka ganin yana murmushi, ta tashi ta fice daga dakin ta koma falo, ya kuwa bita falon, batare da yayi mata magana ba ya sungumeta, yakushi, kai duka babu wanda batayi ba, amman ya sake saka karfi ya riketa har dakin "Ni zaki tashi ki barwa daki Maryamm? Ni zakiyiwa fushi, ina ruwan kwanciyarmu daki daya da fushinki?" Tayi kuka ba dan kadan ba a daren nan, da safe ba zatace ga abinda taje dauka ba, a cikin drawer din da passport dinta yake, tun zuwanta yana wajen, amman da safiyar ranar baya nan, ta girgiza kai, hawayenta sunma kafe saboda yawan kukan da tayi jiya, Haris ne ya dauke, shi ya canza masa waje kamar mai tsoron da gaske zata hada kaya ya nemeta ya rasa, inda zata iya hakan, ai da ta jima da guduwa gida. Yanda duk yayi mata magana bata kula shi ba, daya gama abinda zaiyi ya fita, ta kira Khairi sai kawai ta rushe mata da kuka "Wai ba zamu zo ba, ba zanzo bikinki ba Adda Khairi, ni duk wani biki da na rasa da wanda ma zan rasa wallahi in dai nazo naki ba zai dameni ba, wai saina haihu zamu zo, mun fasa...." Kamar Khairi bataji komai ba sai maganar haihuwar tace "Ciki gareki Maryama? Wani cikin?" Jin dokin da yake muryar Khairi yasa Maryama kara rushewa da kuka "Wai bakiji me nace ba? Bafa zanzo bikinki ba" Amman sai Khairin tayi dariya "Bikine fa kawai, kinsan banda kamu babu abinda za'ayi, zan saka a dinga turo miki hotuna da video sai kinji kamar kina nan, zan kuma ajiye miki ankonki, da kayan da zamu saka tare, ba zansa ba saikin zo, sai ayi mana sabon lalle da make up, muyi walimar haihuwar Awwab, muyi walimar bikina mu kuma yi walimar sabon baby..." Duk yanda Khairi taso ta kwantar mata da hankali fur taki, saima ta kashe wayar kawai, ita ba bikin bane kadai, haihuwar da zata sakeyi ita kadai a kasar nan, yanda zata kara wasu watanni da take hangowa kamar shekaru batare da taga kowa nata ba shine damuwar. Wani abune ya taru a kirjinta ya danne, ta rasa yanda zatayi masa, kuma duk kokarin da Haris yayi wajen ganin ta sake ta kasa, duk maganar da zaiyi mata zata amsa da "Eh..." Ko kuma "A'a" Haka a shimfida duk abinda zaiyi mata ko motsin kirki batayi "Dan Allaah meye haka Maryamm? Wai duk akan zuwa gidan ne? Na fada miki zamuje fa, Allaah zamuje, sai in barki ma kiyi wata daya..." Amman batace masa komai ba, bata ko motsa ba, ita da zaiyi abinda zaiyi ya kyaleta ya fiye mata surutun da yakeyi mata, ba zai gane yanda takeji bane ba, ba zai gane yanda komai ma ya fice mata a rai ba, ciki harda zuwa gidan, su cigaba da zama kawai har randa zai gama su tattara su tafi gabaki daya, me wata daya zaiyi mata? Tun Haris na lallashinta har shima ya dauki fushi, sai zaman gidan nasu ya koma wani iri, Awwab ma a zuwan da yayi ya samu tana kwance akan kujera yayi bacci a kasa, kan kafet, ga sanyi anayi shikuma babu wani kayan sanyi a jikinshi baiyi mata magana ba, baice mata komai ba, ya dauke shi yayi daki dashi. Washegari ya sama masa wani day care centre nan kusa da unguwar da suke, sai bayan ya dawo yake fada mata, da yamma ya sakata a gaba saida ta tashi sukaje suka dauko Awwab din "Zaki dinga kaishi da safe, sai kije ki dauko shi da yamma, watakila zaki samu ko kanki ne ki kula dashi na wani lokaci" Ya fadi wani abu na masa tsaye a wuya. Ya dauka zata iya zama dashi, ko da shekara goma zasuyi a kasar New York kuwa, amman kalli yanda ta birkice gabaki daya dan ya daga lokacin tafiyarsu, in ya zauna yana ganinta ranshi yakeji yana baci, kamar kawai yace mata sun fasa zuwa, in sun taka Nigeria to ya gama duk wani abu da zaiyi ne a New York sai yaga yanda zatayi, amman cikin jikinta, da yanda akace jininta ya danyi sama a zuwansu asibiti shine yake danne shi, kuma inda zai iya, inya tafiyarshi sai yayi satika bata ganshi ba, to kasawa yakeyi, duk wasu mata, duk girman nadin wiwin da zaiyi tana nan makale a kanshi, ya take, ta tashi taci abinci? Ya zaiyi ta dawo masa dai-dai, ko gida zai kira ya fada musu suyi mata magana, tunda ai suna waya da Alhaji Sa'id, yana kira ya gaishe dashi. Gabaki daya ya rasa yanda zaiyi da Maryama, sai dai bashi bane ya fadawa Alhaji Sa'id, Khairi ce, kuma ranar duk wani kokari da Maryama takeyi in tana magana dasu sai ya barbade yabi iska lokacin da Alhaji Sa'id yace "Haba Mairaman Abba, kin manta girman da nace ya hau kanki yanzun ne? Kin manta maganar da mukayi? Bayanin da nayi miki? In ba auren ba meye zai rabamu dake, balle har ya kaiki wata kasar?" Kuka takeyi, irin kukan nan mai sauti, kukan da takejin yana warware wannan abin mai kama da ball da yake tokare a cikin kirjinta. "Zanzo, In Shaa Allaah zanzo in ganki, kiyi hakuri kinji" Ta daga kanta "Ai nafiso ki bude bakinki inji da gaske kin hakura, maganar ta wuce" Cikin kuka tace "Na hakura Abba, na hakura" Tanajin ya sauke ajiyar zuciya "Allaah Yayi miki albarka" Tana share hawayenta da hannu tace "Yaushe zaka zo" Ya amsa da "Zanyi kokari inzo a kafin watan nan ya kare, In Shaa Allaah...." Sai lokacin taji wani sanyi ya ratsata, lokacin da ta sauke wayar kuma, kuka ta sakeyi sosai, taji ta sakayau, nauyin nan ya warware, ta tashi taje ta wanke fuskarta, an kusan yin azahar, da ta dauro alwala saita dauki Qur'aninta, ta zauna akan dardumar, abinda ta kwana biyu batayi ba, ba karamin sanyi ta karaji ba. Bayan ta idar da sallah ne ta kira Khairi, sukayi hira kamar yanda suka saba, sai gata tana ta dariya "Ko kefa, Allaah Ya kara miki hakuri kanwata ta kaina" Maryama ta kwashe da dariya "Ai yanzun nice babba ingaya miki, harda ni a masu yi miki nasiha in aka daura miki aure" Ba karamar dariya Khairi tasha ba "Ina mijinki? Yama kirani fa yake mun Allaah Yasa alkhairi, yake cewa kinata rigima saboda zakuyi missing din biki" Taji zuciyarta ta dan doka, ita yau kira nawa ma Haris din ya jera mata bata dauka ba, kwana nawa yana kiranta bata dagawa "Bama fa magana mukeyi ba sosai, Allaah naji haushin rashin zuwan..." Cikin sanyin murya Khairi tace "Shine kikayi masa halin, kika saka shi a gaba da rigima" Kai ta girgiza, ta fadama Khairi iya abinda zata iya, abinda take ganin ya kamata "Ai ba'a haka, fadan da kikasan zakiyi nasara shi zakiyi Maryama, dake wata ce ma da ba sai in baki shawara ba" Tana 'yar dariya tace "Shawarar me" Maryama ta dinga tuntsira dariya tana karawa "A wanne film kika ga anyi haka?" Haka tace wai tabi Haris makarantarsu, ta dafa abubuwa kala-kala taje ta kai masa, tayi surprising dinshi "Ke banza ce wallahi, ana koya miki 'yar soyayyar nan, ba kinsan inda yake zaune ba..." Ta sani, bata taba zuwa ba amman har lambar gidan da Haris yake a kusa da makarantar ta sani, in ma ba zatayi karya ba zatace a cikin kanta ta hasaso yanda dakin nan nashi yake yafi a kirga, yace mata su hudu ne suke zaune a gidan, har sunan layin da komai ta sani, amman Haris da abinci bai dame shi ba, me zata dafa ta kai masa? Ita da suke fada ma, sai ta kwashi kafa taje? Ita da kafin ya tafi saida yayi mata kashedin banda kai Awwab day care da dauko shi karta je ko ina. "Bafa abinci yake ci ba, na fada miki kaman aljani haka yake, baya shiri da abinci ko kadan, sannan ni da nace miki muna fada, yama kirani yau sau nawa ban dauka ba..." Amman Khairi ta dinga tsarata, ta dinga fada mata dalilan da yasa zataje, tasan yanzun da zuciyarta tayi sanyi, yanzun da takejin kamar tayi masa abubuwan da basu kamata ba, yanzun ne in ya kula da ta huce zai tisa nashi, watakila zaiyi mata tashin hankalin da bata taba tunani ba, haka ta cewa Khairi zatayi shawara, a yanda Haris yace mata, tafiyar awa uku da rabi ce take kaishi makaranta, batasan dalilin da yasa ya kama musu gida a wannan unguwar ba inda nisa haka, bata tambaya ba tunda tasan babu amfanin da amsar zatayi mata, kuma ba zata canza masa ra'ayi ba tunda nan din yake so su zauna. Da yamma da ta dauko Awwab, sai suka tsaya da Chloe, take ce mata ko zata dauko mata Awwab gobe daga day care, tana so tayi surprising din Haris ne, ta gandara mata karya kan cewa anniversary dinsu ne ranar, tunda tasan turawa da girmama irin abubuwan nan, aikuwa ta dinga washe baki tana musu fatan alkhairi, tace mata zata dauko shi, inma kwana zatayi babu damuwa zata kula da Awwab din. Haka ta koma gida ta kwanta da wani irin bugun zuciya, washegari da safe da Haris ya kira ta daga "Kina neman rigima dani Maryamm, bakya ganin kokarin da nakeyi nakin biye miki ko?" A hankali tace "Kayi hakuri, inaso zan fita" Ya danyi wani murmushi da ta tabbatar da sautin shi na takaici ne "Shisa kika daga kirana, to ba zakije ba, karki fita ko'ina" Jin kamar zai kashe kiran yasa ta fadin "Dan Allaah, dan Allaah, karka kashe, dan Allaah yau daya dai, kayi mun alfarma" Yayi shiru sosai "Karki dade, kisaka facemask dinki...dan Allaah ki kula sosai" Da sauri tace "In Shaa Allaah..." Sai kuma yace "Wai ina ma zakije?" Ita kuma ta amsa da wata tambayar "Kuna da lectures da yawa yau? Ko kun fara exams din? Kamar kace zaku fara exams ko?" Ya danyi shiru "Yeah, bamu fara ba tukunna, ina gidama all day, zan dan rage aiki, sannan ina da assignments da yawa, duk zanyi su..." Dan biye masa tayi sukayi hira, sai ta karajin kwarin gwiwar zuwa, tunda yana gida, haka ta shirya, tayi kwalliya mai sauki, humrar da take so tayi amfani da ita, saita jefa a jaka, ta kara extra kaya, in taje caj saita shafa kafin ta shiga gidan, tunda tana da karfi sosai, kuma tasan haramcin dake cikin ta tana baza kamshi. Zuciyarta sai bugawa takeyi, ta dauka doki ne, ko kuma taradaddin fita ita kadai Bata san bugun na kashedi bane, Nason kareta daga dayan Labulen da yake lullube da rayuwar Haris da zuwanta zai daga mata... 35 Lokacin data kwankwasa kofar nan, bugunta ya koma kunnuwanta ne tare dana zuciyarta, tayi sau daya, sau biyu, saita dagata jin alamun taku, wani matashin saurayine da kai tsaye ba zata auna yawan shekarunshi ba ya bude mata kofar, fari tas dashi harda wani caki-caki a fuskarshi, ya dan runtsa idanuwanshi, alamar hasken yayi masa yawa, Maryama taga yanda ya dafe kanshi yana furta "Damn..." Sannan ya dan bude idanuwanshi kadan yana kallonta "Haris, I'm looking for Haris please" Ta fadi, da kunyar yin turanci takeyi inta fita, sai taga kamar yanda suke lankwasa harshe inta bude baki tayi nata na 'yan Nigeria za'a sheke da dariya, sai a hankali taga babu wanda ma ya damu da yanda take turancinta, itace ma kafin ta saba, ta dinga tattara duka hankalinta ne wajen ganin ta fahimci abinda suke fada, da hannunshi ya nuna mata alamar ciki, sannan ya matsa mata, ta shiga da sallama a hankali, taga inda suke cire takalma, sai kawai ta cire nata anan, falone matsakaici, ya danfi na gidansu girma, ganin ta dan daburce yasa ya nuna mata kofar dakin Haris din, ya koma kan doguwar kujerar da take da fadi sosai, ya kwanta ruf da ciki da alamar bacci zai koma. Takun da ya sadata da kofar dakin daga inda take bai wuce guda takwas zuwa tara ba, bugun zuciyarta ya dan tsagaita mata jin wani irin sauti da kamar daga dakin yake fitowa, ta daga hannu zata kwankwasa ne, taji ta kasa, ta kara matsawa kamar mai shirin shigewa cikin kofar, data dora hannunta jikin handle din ta murda, sai taji kofar ta bude, alamar babu mukulli daga ciki, ita har fentin dakin nan tasa hasashen bakine, tunda dakin Haris ne, inda suke ma kamar wallpaper ne ba fenti ba, in fentinne to an danyi masa wani ratsin kwalliyane ma golden mai kamar walqiya, yayi mata kyau shisa ma batayi masa mitar bakin ba. Baki na da abinda bature yake kira da shade, akwai baki mai haske, akwai baki mai ratsi-ratsi, ko a bakaken mutane sun rabune kashi-kashi, sannan ko a cikin duhun dare, bakin yakan bambanta ne da yanayin lokaci, amman tunda Maryama take a duniya bata taba sanin akwai abinda inta kira da baki kamar batayiwa kalmar adalci ba sai da ta tura kofar nan, ta taka kafarta tana shiga da sallama, ta kalli Haris, kwance akan gadonshi, kwance cikin yanayin da in tace zata lissafa sau nawa ta ganshi a ciki ba zata iya ba, jikinshin nan, bakar fatarshi da inta hadu da wani kalar zanin gadon da take shimfidawa sai ta jima tana kallonta, farin zanin gado saiya kara masa baki, sai kuma ta dinga mamaki idan yanayin yayi mata kyau, ruwan toka kuma saiya hadu da kalar jikin nashi ya bada wani launi da Maryama take maraba dashi duk safiya. Haris dai, amman yau kalar tashi ce ta hade mata da ta farar baturiyar da take samanshi dare-dare, samanshi, babu komai a jikinta, hannuwanta duka biyun dafe da kirjinshi, nashi kuma akanta kamar mai bata tallafi, yanayine da yake so, yanayi ne da tasan ta gaza masa a darare da yawa saboda yanda yake gajiyar da ita. Batasan me sukaji ba, karar budewar kofar? Takunta? Ko karar wani abu da ya rushe a cikin kirjinta takejin duminshi yana bin kafafuwanta, idanuwanshi Haris ya fara sakawa cikin nata, idanuwanshi da suka sake launi, kuma yanda yayi motsine yasa ta kalli abinda yakeyi, yarinyar dake kanshi ya ture "Maryamm" Sai sautin ya shiga kunnenta kamar mashi, ya kuma yi nasarar toshe mata karasawar wani sautin bayan wannan kiran da yayi mata, ta daiso ace yanda jin nata ya dauke ganinta ma yayi mata wannan taimakon, bata ga sanda ya maida kayanshi ba, sanda yayi wa budurwar nan magana, taga tayi mata wani kallo, sannan ta dauki rigar da Haris ya jefa mata ta saka a jikinta, ta kuma saka wani dan karamin wando, Maryama ta kalli rigar, ruwan tokace mai duhu, rigar Haris ce, rigarshi ce da ta zaba da hannunta, rigar da ta zaba da ya bude baki da nufin magana tace masa "Ni zaka dinga sakawa, dan Allaah tunda kai ba jemage bane ba, in muna tare kasa in ganka a wata kalar kayan bayan bakake" Ya karbi rigar yana juyawa "Meye jemage?" Ya tambaya "Bat" Ta bashi amsa, yayi dariya "Jemagenki ne, I'm your batman" Itama dariyar ya bata, ta gefenta budurwar tazo wucewa, tunda tana jikin kofar ne, ba zatace ga yanda abin ya faru ba, a girman jiki, da tsayi duka budurwar nan ta fi Maryama, haka jakar da take rike da ita ma batasan ina ta bulla ba, ta daisan gangar jikinta ta motsa, ta kuma ji hannunta cike da gashin budurwar da ta janyo dashi, taga karasowar Haris da kiciniyar da yakeyi da ita, amman batajinsu, batajin duk abinda suke fada "Ta cire, wallahi saita cire rigar nan" Dakyar Haris ya karbeta, fuskarta duk tayi ja, koma me take fada bai damu Maryama ba, haka shima abinda yake fada, ita da batama jinsu "Kace mata ta cire" Tayi maganar idanuwanta cikin nashi, kuma haka akayi, da ta cire rigar saita wullowa Maryama a fuska, ta cireta ta rike a hannunta, sannan ta juya, tana shirin rigan budurwar ficewa daga dakin, da Haris ya riko mata hannu yanda tayi amfani da duka karfinta ta hankada shi saida yayi baya kamar zai fadi "Karka tabani, da zunubinka, karka tabani da daudar da take jikinka..." Satin da Maryama zata taho New York ya fara duba inda zata zauna, gidan da zai ajiyeta, haka kawai yaji yana bukatar tazara mai yawa a tsakaninsu, nan din, inda yake, wajene da yakeyi masa dadi, wajene da yakeyin duk abinda yaga dama babu wata fargaba, to duk wanda ya sani anan suka hadu, sannan babu ruwan wani da abinda zakayi, itace mutum ta farko da zatazo inda yake, ta farko da bayaso taga wannan bangaren nashi. Shisa ya kaita can unguwar, shisa ya zabi ya dinga zirga-zirgar tsakanin nan din da can. Kuma sau nawa yake so ya dauko Maryama yazo da ita makarantar nan amman yake fasawa? Akwai wajeje da yawa da idan ya wuce sai yaso ace tana zaune a wajen, shikuma ya haskata da camera dinshi, amman kuma yana daga cikin sanannun mutane a makaranta, saboda yanda yake a wajen mata, yanda suke bibiyarshi, yanda kuma yayi kaurin suna wajen kin saurarar kowa da sunan soyayya "Mr no strings attached" Haka yaji ana masa lakabi, in kinyi masa, inya kulaki to karki tsammaci wani abu daya wuce neman juna, koya yaga kina neman wuce hakan ba zai sake kulaki bama. Akwai tarin matan da suke kullace dashi, suke jin haushin shi, ko ba'a fada ba ya sani, kawo Maryama ba karamar barazana bace ga Labulen dayake lullube da wannan sirrin nashi. Idan aka tambaye shi zai rantse kai tsaye, abinda wannan matan kawai zasu nunawa Maryama shine kwarewa, shine jure ma yanayin shi, amman haka yake tsintar kanshi da hasashenta, ace dandanonta ne ya hadu da gogewarsu, kuma ita taki bari ya gogar da itan, taki sakin jikinta gabaki daya dashi har yanzun. Jiya, wayar da sukayi, ya samu sukunin daya kwana biyu bai samu ba, da safen ma sunyi magana, kafin ta fita da Awwab, washegari yayi niyyar zuwa, shisa ya tsara clearing din duk wani abu da yake kanshi a yau din, amman akwai wani yanayi a muryar Maryaman daya hautsina masa lissafi, ta sake, yana zaunen ya dinga hasaso duk wani abu da zai gifta a tsakaninsu, cikin yanayin daya kwana biyu rabonshi dashi saboda fadan da sukeyi, yana kwancen ya kasa tashi yayi komai saiga Autumn, yarinya daya daya san tana sonshi, amman da yake bata fito da maitarta fili ba sai alakar tasu ta jima, kuma a yanayin da yake sai kawai ya biye mata. A mugun tunani, a mummunan mafarki bai taba hango Maryama zata tako inda yake ba, kuma inta tako din tazo ta bude kofa ta shigo ta samu wata a samanshi, a tsayin shekarunshi na duniya, yaune ya fahimci kalmar nan ta "Humiliation" Yau yaji ya muzanta ta sigar da baisani ba, yaji kunya irin wadda baisan da ita ba a rayuwarshi, kuma kamar abubuwan basu isa ba, sai ya kara da wani irin tsoro da firgicin ganin yanayin dake fuskar Maryama, da ta riko Autumn kuwa wannan yanayin na cikin idanuwanta ya bala'in firgita shi, haka na yanzun "Maryamm" Ya kara kira, cike da roko, da wani abu na daban, kuma kamar yanda kiran nata ya rufe mata jinta, haka ya sake dawo mata dashi yanzun, ta kalle shi, itafa wani abun nan daya tarwatse a cikin kirjinta ne takeji yana bin kafafuwanta, kuma kamar shine yake sakata jiri, saita kalli kafafuwan nata, suka kalla tare da Haris da yabi abinda take kallo shima, zuciyarshi ta buga, ta sake bugawa "Jini...jini kike zubarwa" Tasan ta dago, ta kuma ga labbanshi sun motsa, sai fatanta na dazun ya samu karbuwa, ganinta ya dauke tare da jinta...! * So takeyi ta tashi, ta bude idonta, saboda yanzun da yake rufe babu abinda take gani sai Haris da budurwar nan akanshi, kuma kirjinta zafi yakeyi, zafi na gaske, kamar an kara mata garwashi, shi ta fara kai hannu ta murza batare da ta bude idanuwan nata ba "Maryamm" Haris ya kira, duk da saida yayiwa likitanta alkawarin ba zaiyi ko kwakkwaran motsi ba bayan sun kawota asibiti anyi nasarar tseratar da cikin jikinta da yake barazanar zubewa, haka suka sakashi a gaba da tambayar abinda ya firgitata, daya san ba zasu kyaleshi ba sai yace musu an kirasu daga gidane aka fada musu mutuwa. Sannan suka sama masa lafiya. Yau kwananta biyu ko motsi batayi ba, da kanta take numfashi babu taimakon kowacce na'ura, amman taki tashi, kallo daya zaka yiwa Haris kaga yanda ya kara duhu, yake kuma a firgice "Maryamm" Ya sake kira a hankali, sai kuwa ta bude idanuwanta, akanshi, kallonshi takeyi kamar tana neman wani abu a jikinshi, sai kuma ta shafa cikinta "Babu abinda ya same shi" Ya fada da sauri, inda cikin nan ya zube bayajin zai iya dauka, zai iya yafewa kanshi "Kema babu abinda zai sameki" Sai taji dariya ta kamata, amman kuma bata da karfi ko kadan "Ganjaa" Ta kira da karamar murya, ya matsa kusa da saurinshi "Awwab...yarona fa?" Sai yace mata "Yana daycare dinshi, zanje in dauko shi in lokacin tashi yayi..." Ta danyi kokarin daga masa kai, lokacin ne kuma likitanta da wani Nurse suka shigo, dole Haris ya fita, suka sake duba Maryamm, wata allurar baccin suka karayi mata, a cewarsu jininta da yayi sama har yanzun baiyi saukar da suke fata ba, ga jinin da ta zidda, daga ita har abinda yake cikinta basu gama fita daga hadari ba. Yaji hankalinshi ya kara tashi, dakyar ya tafi dauko Awwab, saiya samu ya mikashi wajen da ake kula da yara kanana na cikin asibitin ya koma wajen Maryama. Lokacin data sake farkawa kiranshi ta karayi, ya amsa "Ba mafarki nayi ba ko?" A hankali ya daga mata kai "Kaine, kaine da wata..." Ya sake daga mata kai "Me yasa?" Yayi shiru, bashi da amsar wannan tambayar, ko yayi kokarin amsawa bashi da amsa, yama kasa hada idanuwa da itane saboda abinda yakeji "Tun yaushe?" Da sauri yace "Maryamm" Ta sake maimaitawa "Tun yaushe?" Dan tana tambayar ne tsikar jikinta na tashi, wata irin dauda takeji tana rufar mata, daudar da Haris ya dade yana goga mata, datti, dattin zina, tana so ta san ko tun yaushe, watakila ta iya hasaso irin wankin da zatayiwa jikinta, to inta wanke jikinta ya zatayi da zuciyarta, ita tafi jin daudar a ciki fiye ma da gangar jikinta, ko dai tunda tana asibiti yanzun magana zatayi musu, su bude kirjinta su ciro zuciyar su tsomata a ruwan hydrogen, in tayi wannan kumfar da ciwo yakeyi in an zuba masa, sai su bita da clean da hypo? Ta dan kalli jikinta, wai ko zata ga yana fitar da hayaqi, ko tiririn da takeji ya fito har waje. "Zafi nakeji Ganja, babu AC a dakin nan?" Ta tsinci kanta da amsa masa "Zafi?" Ta daga masa kai "Zafi nakeji, ka kunna mun AC, ka qureta duka, zafi nakeji har cikin kirjina" Ya mika hannu da niyyar taba jikinta, yanda ta mirgina inda babu makangi a jikin gadon ya tabbata saita fada kasa, har saida ta cire karin ruwan da akeyi mata "Karka tabani, dan Allaah karka tabani" Ta karasa cikin wata 'yar karamar murya, dole ya mike ya kira mata Nurse, aka goge mata hannunta da yake jini, sukace masa zazzabine mai zafi a jikinta, dan a gabanshi akayi mata allurar da ta sake komawa bacci, a karo na farko a rayuwarshi da wani abu ya same shi yaji ya furta "Inalillahi wa ina ilaihi raji'un" Kalmomin sukayi masa nauyi a harshe, nauyi na gaske, nauyi na rashin sabo, ya saka fuskarshi cikin tafukan hannunshi, ya sake furtawa, ya cigaba da furtawa wani irin abu yana ratsa shi, kuma a lokacin ne wayarshi da ya dauko tayi kara a cikin aljihunshi, daya fito da ita sai da yaji ta nemi subucewa ganin Alhaji Sa'id ne, ya kasa dagawa saida kiran ya yanke, wani ya kara shigowa, tukunna ya dauka yana kasa cewa komai, sai daga can Alhaji Sa'id yayi masa sallama, ya amsa a hankali "Haris, kuna lafiya dai ko? Inata kiran wayar Mairama ba'a dagawa, daga bayama sai najita a kashe" A hankali yace "Muna asibiti ne Abba, bata da lafiya, amman da sauki..." A cikin addu'o'in Alhaji Sa'id yakejin tsananin damuwa, shisa yace "Zazzabine Abba, sunyi mata allura dan ta samu bacci sosai, idan ta tashi zan kira saiku gaisa" Ya amsa da "A'a kabarta ta huta sosai, in ta kara warwarewa saimu gaisa. Allaah yayi muku albarka, nagode kwarai" Rabon da yaji alamun kuka harya manta, lokacin kuruciya ma anya zai tuna sanda yayi kukan karshe? Amman yanda Alhaji Sa'id ya ajiye kalmar godiyar nan saida yaji yana so ya fashe da kuka, to me yayi da zaiyi masa godiya? Ko godiyar neman kashe masa yarinya? To yama akayi komai ya jagule masa lokaci daya? Me zai kawo Maryama inda yake? Me yasa zataje? Ga abinda zuwan nata ya janyo musu. Ko da sukayi masa suggesting rike Maryama dan tana bukatar absolute bed rest da gudunshi ya yarda, data tashi dai haka tace masa "Ka kaini gida Ganja, ka mayar dani gida" Cikin taushin murya yace mata "Sun baki bed rest ne, kiyi hakuri tukunna, ko da inaso in kaiki ba za suyi clearing dinki fit to fly ba" Ashar ne dankare da makoshinta, ashar din da tarbiya ta nade harshenta daga furtashi, ashar din da tasan in Hajja tasan ta taba jinshi ma saita san yanda tayi ko ta kunnenta ne ta dura ruwan sabulu ta daurayo mata shi tas, so takeyi ta hada shi fit to fly din da bed rest din a waje daya ta maka musu shi "Gida nake so in tafi" Ta kara maimaitawa "Zamu iya rasa Babynmu Maryamm, dan Allaah ki kwantar da hankalinki, zan kaiki gida, I promise" Sai taji taja tsaki "Inya bare ai ya huta, nima na huta, duk mun huta" To me zaizo yayi a duniyar? Rabon ya fito yaga zabin da kaddara tayi mata, tayi musu? Na auren dan wiwi, mazinaci, wai itace tayi zaman aure da mazinaci, itace Haris ya birkida da matan waje yazo ya birkida da ita, suka hadu cikin daudarshi, ita fa, wannan tiririn takeji yana kara gauraye mata jikinta, daman biyya tayi ai, ta aureshi. Ba ita ta zaboshi ba, zabo mata akayi, ta karba, bata nemi wani dalili da zaisa a zabo mata shi ba ta karbeshi, yanzun kuma zata mayar dashine, kuma tana fatan kar wanda ya tambayeta dalili, suyi mata wannan adalcin Sai dai wata kaddarar ai bata ma fara ba... 36 Haris ba zaice ga ranar daya zauna yayi addu'a akan wani abu ba, tunda in ya idar da sallah ma mikewa yakeyi ya kama harkokinshi, gara ma bayan zuwan Maryama, ko da baije masallaci ba, in yayi sallah a gabanta yana kokarin mikewa zatace masa "Bakayi addu'a ba, dan azkar din nan na bayan Sallah, wallahi randa wata bukata ta taso maka zaka sha mamaki, sai ka tsinci kanka da kunyar Allaah..." Dariya take bashi duk inta fadi hakan, wata rana dai yanayin Azkar din bayan sallar tunda ba mai yawa bane ba, da yatsun hannunshi ma saiya kirga talatin da uku sau nawa, amman bayan hakan bayajin yana da wani abu da yake so ya roka, a tunanin shi komai yana tafiyar masa lafiya kalau. Sai gashi washegarin kawo Maryama asibiti daya idar da sallar asuba ya daga hannayenshi sama, bakinshi yayi masa nauyi, wani irin nauyi da bai taba sanin akwaishi ba a duniya, to me ya kamata yace? Ta ina zai fara? "Allaah nine Haris..." Sai kuma yayi shiru, tunda haka Maryama tace "Randa zakaje da bukatarka sai kaba Mala'ikun mika addu'a mamaki, zasuce wannan kuma daga ina? Yau kuma?" Amman akwai ranar da tace masa "Sai dai Allaah Mai Yawan Rahma ne, sai kaga Ya karba maka rokonka, amman da kunya gaskiya" Shisa ya kara gyara zamanshi "Allaah Ka ba Maryamm lafiya, Allaah cikin jikinta, babynmu...Babyn daka bamu, Allaah Karkasa Ya zube, Dan Allaah karya zube, nine nayi laifi, batayi komai ba" Hankalinshi bai kara tashi ba sai da tayi kwana uku bata bude idanuwanta ba, ga Awwab sai yake ganin kamar wani irin kallo yaron yakeyi masa, kallon "Ina ka kaimun Ammi na? Me kayi mata?" Gabaki daya a firgice yakejin shi, kallo daya zakayi masa kagane wannan firgicin, duk kuwa da yana komawa gida yayi wanka, ya sake kayanshi, amman bashi da natsuwa, ko lokacin da suka rabu da Aise bai tsinci kanshi cikin irin wannan rashin sanin abinyi din ba. Yau kwanansu takwas, ta tashi, ta kalle shi tace masa "Gida zan tafi Ganja, ina barin asibitin nan gida zan tafi, bansan taya ba, amman ba zan zauna ba, ba zan zauna da kai ba...ka dauko mun wayata" Wayar na jikinshi, yaje ya dauko mata acan gidan, amman bai sakata a caji ba, da ita yaketa yawo, kuma duk da babu cajin saiya kasa bata, haka kawai yakejin tsoron bata, abinci ma daya ya samu take karba "Ka taba, hannunka da dauda, ka tabamun abinda zan kai cikina da hannunka" Baisan sau nawa ya dirje hannuwan nashi a bandaki ba, har sanitizer saida ya saka jiya yazo ya daga mata "Na wanke Maryamm, dan Allaah" Wani irin kallo tayi masa "Waye ya gaya maka kaf kasar nan akwai sabulun da zai wanke dattin da kake yawo dashi? Dattin daka cuceni ka goga mun" Ya rasa yanda zaiyi da ita, har dadi yakeji idan yaga ta koma bacci, fata yakeyi su cigaba da riketa a asibitin nan harta haihu, watakila kafin nan ya samu zuciyarta tayi sanyi, dan a yanda take din nan tsoron ace an sallamesu sun koma gida yakeyi. Ko yanzun ma bacci takeyi, wayarshi ce taketa vibrating da wata lamba da baisanta ba, an jera masa kira har hudu, shisa ma ana biyar din ya yanke hukuncin dagawa yaji waye zai dameshi haka, sai gashi yanda zuciyarshi ta buga a kirjinshi da yaji muryar mai kiran saida ya tashi tsaye "Ba...Baba" Ya furta da madaukakin mamaki "Ina zamuce a kawomu? Ga Uber mun samu, ina zamuce?" Shi zamuce dinne ya kasa fahimta, bashi kadai ba kenan? Kuma bai gane sun samu Uber ba, zuwa ina? Uber a ina? "Haris muna tsaye fa, kuma mun tsayar da mutum, kuna asibitin har yanzun?" Da harshenshi da yakejin ya bushe lokaci daya har makoshi ya amsa dakyar. "Asibiti Baba, muna asibiti..." Kuma a hankali, cikin wani sabon bugun zuciyar ya fada masa sunan asibitin. Sai gashi a kofar asibitin yana raba idanuwa cikin jiran ganin ta inda zasu bullo, Baban da wa? Me yasa yanzun? Me yasa zasu zo yanzun? Me sukazo yi? Duk lokacin daya kamata, lokacin da suke lafiya kalau daga shi har Maryamm din, kamar dai bayan haihuwar Awwab da Alhaji Mustafa yazo, ai haka ya dinga yi musu addu'a harma bayan daya koma saida yace masa "Naji dadin yanda na ganku Haris, naji dadi sosai" Yanzun kuwa ko da bai kalli mudubi ba, ya tabbata bashi da natsuwa, sannan kallo daya zakayiwa Maryama ma kasan ciwon daya kwantar da ita ciwone da ba dukanshi asibitin nan suke da maganinshi ba. A karo na farko yaji yana so ya ruga da gudu, ya boye, ya boyewa Alhaji Sa'id daya fito daga motar nan cikin fararen kaya da suka kara haska tarin kamala da dattakonshi, wani mutum guda daya da ko a waya Haris yake tsintar kanshi da jin nauyi, dakyar ya iya tsayawa suka karaso, yana fatan abinda yake saman fuskarshi murmushi ne "Haris, sannu da kokari" Cewar Alhaji Sa'id bayan sun gaisa, Haris da kafafuwanshi har rawa sukeyi yayi gaba suna binshi a baya, dan a barsu su shiga ya fada musu cewa 'family' ne. Lokacin Maryama bacci takeyi, sai suka sake fitowa waiting area din, Alhaji Mustafa yake ce ma Haris "Ina Awwab?" Ya fada musu yana daycare, amman anjima zaije ya dauko shi "Bafa muci wani abu ba, dan nikam yunwa nakeji" Cewar Alhaji Mustafa, sai kuwa Haris yayi saurin cewa "To ko zamu fita ne, in sama muku wajen kwana nan kusa, sai kuci abinci ku huta, kafin lokacin ma Maryamm din ta tashi" Alhaji Sa'id ya jinjina kanshi cikin amincewa, kafafuwanshi duk sunyi dayi saboda zaman jirgi, kuma yanda yaga Maryaman na bacci saiya samu natsuwa, zuciyarshi tayi masa sanyi, yana so ya dan kebe ya kira Hajja ya fada mata ko itama zata samu kwanciyar hankali, kwanakin nan duk ba'a nutse suke ba, ita Hajjan ma harta fishi damuwa duk kauda kai da kawaicinta akan yaran "Da Maryama nake kwana da ita nake tashi, tun kafin kace mun bata da lafiya din nan take yawan fadomun fiye da misali...dan Allaah kaje ka dubota" Daman yayi niyya, sai kuma ta kara masa karfin gwiwar zuwan, kafin dai yayi magana ne Alhaji Mustafa ya kirashi yana ce masa "Ka shirya fa muje mu duba yaran nan, wannan baccin da ake cemun Maryama nayi kullum bai kwanta mun ba" Ba karamin dadi yaji ba, tunda dole shi zai yiwa magana daman, yana da passport dinshi, amman yana bukatar processing visa, gabaki daya baisan ta inda zai fara ba, sai gashi da yake idan kudi suna maka abubuwa da yawa, to sanayya ma tana aiki, sun samu visa cikin kankanin lokaci "Kuje kai da Abbanka, ni kam zan jira har Maryamm din ta tashi, kawai ka fara samo mun abinda zanci" Yanda yayi maganar Haris yasan babu wajen yi masa musu, sai kawai ya fara fita shi kadai, abinda yake tunanin Alhaji Mustafa zai iyaci shi ya siyo, sannan suka dauki jakunkunan shi da Alhaji Sa'id suka sake ficewa badan yaso hakan ba. Lokacin da Haris yayi wata dawowa daga makarantar kwana, ya ganshi, lokacin farko daya fara kai ziyara makarantarsu, akwai wani abu tattare da Haris din da bai kwanta masa a rai ba, wani abu daya dinga damunshi, irin wannan abin yake gani yau. A kasan yanayin kamar akwai firgici kwance cikin idanuwan Haris, ko meye yake gani yasa shi son yin magana da Maryama. Shisa bayan sun fita ya samu inda ya kara wanke hannuwanshi, yazo ya zauna yaci iya abinda zai iya, ya zubar da sauran a shara. Cikin sa'a lokacin daya leka ta window din dakin da Maryama take sai yaga ta tashi, kafin ma wani cikin sarakan iyayin Nurses din nan ko likita suzo da wata tsirfar tasu ta kasar waje da zasu hanashi shiga wajenta ya murda hannun kofar da sallama dauke a bakinshi, idan ma Maryama data amsa sallamar a hankali tayi mamakin ganinshi to ko a fuskarta bata nuna hakan ba. Ya shiga ciki sosai, yaja kujera ya zauna "Maryama" Ya kira cikin taushin murya "Baba...sannu da zuwa" Ta tsinci kanta da furtawa tata muryar na fitowa a hankali "Ya jikin naki?" Ciwon da takeji yanzun kawai a zuciyarta ne da kwakwalwarta da koya zata rufe ido babu abinda take gani sai Haris da Autumn, ko alluran baccin da suke ta dankara mata, tana baccin tana ganin wannan kazantar, duk wani bayanshi mai saukine, inda zata goge hoton nan, inda zata samu hanyar da zata cire shi daga kwakwalwarta, watakila da ta fara samun salama "Alhamdulillah" Ta amsa sauran kalaman na makale mata "Tare da Sa'idu mukazo, sun fita shi da Haris, na zauna ne saboda ina so inyi magana dake" Kallonshi takeyi, sai taji gabanta yana faduwa "Lafiya kuke? Karkice mun bakomai Maryama, yanayin Haris, yanayinki yanzun, baiyi mun kama da babu komai ba" Tasan tayi shiru, shiru mai yawa, kuma magana ce ake cewa kana cikin yi ko zakayi an katse maka, Alhaji Mustafa baiyi wani yunkurin katse mata wannan shirun ba, ya barta, kamar mai bata lokaci ta tattara kalamanta, ko ta zabi iya abinda take so ya sani. Maryama ta bude bakinta yafi a kirga tana sake rufewa ta rasa ta inda zata fara, ta rasa me zatace, ta daisan ko meye zai fito ba zata taba iya kallon Alhaji Mustafa da yake zaune ta gaya masa matsalar nan ba, ko kirjinta za'a tsaga masa saita samu hanyar data rufe wannan abin, kafin a hankali tace "Ni dashi ne Baba, matsalar, ni dashine kawai" Alhaji Mustafa ya kalleta, sai tayi saurin karawa da "Inaso inje gida dai, bana so in kara haihuwa anan, kuma ina so in dan huta, ina so inje gida Baba, dan Allaah, idan na zauna ciwon nan banajin zai warkemun, ina so inje gida" Ta karasa maganar cikin karyewar murya, hawayen da batasan tana rike dasu ba suka zubo mata, ganinsu ya saukarwa da Alhaji Mustafa wani abu mai nauyi a cikin zuciyarshi "Dan Allaah, kawai gida nake so" Cewar Maryama ganin yanda yanayin Alhaji Mustafa ya canza gabaki daya, da saurinta kafin yayi magana ta kara da "Idan na fadawa Abba zai bani hakuri, nasan hakuri zai bani yace in zauna, wallahi ba zan iya zama ba, kirjina yana mun zafi sosai Baba, duka zuciyata ciwo takeyi, ka tafi dani gida in huta" Kai Alhaji Mustafa ya jinjina mata "Yace wai ba zasu barni ba, asibiti ba zasuyi clearing dina fit to fly ba, kayi musu magana" Kai ya sake daga mata, ya kasa magana, to me zaice mata? Me zai fada bayan ciwon da yake gani kwance cikin idanuwanta, ciwon da yake ganin ya girmi shekarun da take dashi, meye Haris din yayi mata? Me yakeyi mata? Daman ba lafiya suke zaune ba? Yanda yakejin su a waya ba haka abin yake ba? Ai idan Munira yazo ya samu tana wannan hawayen, ko batace masa komai ba yasan da 'yarshi zai tafi, kai tun ranar da sukaje duba Haris a asibiti yaji kalar ciwon daya kwantar dashi, bayajin zai iya barwa dan wiwi 'yarshi ya cigaba da aure, idan kuma ya dinga numfashi a kusa da ita ya goga mata wani ciwon fa? Ko ya dinga busa hayakin a cikin gidan itama tana shakewa, shisa har yau cikin kunyar Alhaji Sa'id yake, nauyin shine ya ninku a idanuwan Alhaji Mustafa, nauyi mai yawa kuwa. A gefe daya duk addu'ar da zaiyi baya taba tashi bai roki Allaah Yafiya akan son kan da yakejin yayi ba, yana fatan auren Maryama da Haris yakeyi ya cigaba da zame masa rufin asiri, nagartar yarinyar da ta gada wajen mahaifinta ta shafi danshi, kuma akwai abubuwa da yawa na canji game da Haris din da yasan cewa sanadin zama da Maryama ne. To taya zai so su rabu? Bashi da wannan kawaicin irin na Alhaji Sa'id, bashi da wannan karar, kamar yanda yasan yaran Hajiya Rumana sune rauninta, to shima soyayyar da yakeyi musu itace rauninta. Abu daya dai zai iya wanda Alhaji Sa'id ba zai taba kamantawa ba, shine karbar rokon Maryama, wannan karon zaiyi ma Alhaji Sa'id abinda yasan zai tsaya yayiwa Haris ninkinshi. "Tare zamu tafi...dake zamu koma" Kai kawai Maryama ta iya daga masa saboda kukan da taji yana neman kwace mata, kuka ne da bataso tayi, kuka ne da inta fara batasan ko zata iya tsayawa ba, saboda tunda abin nan ya faru batayi kuka ba, kawai dai taji kamar amincewar da Alhaji Mustafa yayi ya daga mata wani abune mai nauyi da yake danne da kirjinta, zataje gida, zataje gida, shine kawai abinda yake mata yawo cikin kanta, abinda yake rufa mata wani bargon Rahma a duka ilahirin jikinta "Nagode, nagode Baba" Ta furta cikin rawar murya, nashi kan ya daga mata "Bari in barki ki huta" Wani irin tausayinta ne yake dukan zuciyarshi, watakila idan ya zauna anan tsaf zata saka shi hawayen da ya manta rabon da yayi su. Daya fita saiya kira Haris yake tambayarshi inda suke, ya fada masa, ya fita ya samu taxi ya hau yana samunsu a wajen, Alhaji Sa'id harya shiga wanka dan Haris ya kama musu daki "Bari in koma asibitin Baba, karta tashi ko zata bukaci wani abin" Haris ya fadi da saurinshi, wani kallo ne Alhaji Mustafa yakeyi masa da baigane ba "Me kayi mata?" Tambayar ta dake shi kamar ya kwada masa wani abu "Kafin kayi tunanin bude bakinka kayi mun karya nasan kayi mata wani abu Haris, nayi magana da ita kafin in taho" Haris ya sauke idanuwanshi zuciyarshi na bugawa kamar tana son fita ta gudu tabarshi da abinda yakeji shi kadai "Me kayi mata?" Alhaji Mustafa ya sake maimaitawa, yana saka Haris juya yanayin tambayar, yace yayi magana da Maryama, to in yayi magana da ita me yasa yake tambayar shi? "Saboda bata fada masa ba" Wani sashi na zuciyarshi ya bashi amsa, amsar ta sama masa natsuwa kadan "Baba..." Ya kira sai kuma ya rasa abinda zaice "Na dauka kuna zaune lafiya, hankalins a kwance yake sanin kana rike da amanar dana karba maka da hannu na, ashe ba haka bane Haris? Ashe ka shirya kunyata ni? Ka shirya ka watsamun kasa a ido?" Kai Haris yake girgizawa, shi duk yaushe yayi hakan? "A'a Baba, na karba, aina fada maka na karbi auren" Alhaji Mustafa ya jinjina kai "Eh ka karba, ka fadamun ka karba, kuma ka nuna mun da gaske ka karba din, sai dai baka cemun zaka riqe da kyau ba, daka karba, shisa kayi mata abinda ya kwantar da ita, wannan 'yar yarinyar Haris, da karancin shekarunta yau a zaune naga bakin ciki a idanuwanta, bakin cikin da na tabbata kai kayi mata sanadinshi" Ya kasa cewa komai, yasan abinda yayi ba dai-dai bane ba, amman a wannan lokacin bawai yana kallon abin ma ta fuskar addini bane ba, yana kallonshi ne ta fuskar zamantakewa "He cheated on his wife" Shine abinda ya sani, bai kyauta mata ba, sai dai har ranshi ai baiyi tunanin zata sani ba, yabi duk wasu matakai daya kamata wajen kareta daga sanin, ita ta dauko kafafuwanta taje har inda yake tagani, ya bata hakuri, zai kara bata hakuri, zaita bata hakuri har saita yafe masa, yanda Alhaji Mustafa yake maganar yana saka shi jin kamar abinda yayi wani gingimemen laifine da bai kamata a yafe masa ba "Zamuyi magana Baba, komai zaiyi dai-dai, matsala ce muka samu, shima duka ba'a dade ba sai tazo bata da lafiya...ka daina cewa haka, kana magana kamar tunda mukayi auren nakeyi mata wani abu" Hararashi Alhaji Mustafa yayi "Yaushe zasu sallameta? Da ita zamu wuce? Dan zan zauna ne sai sun sallameta mu tafi" Haris ya kalle shi da sauri "Eh, tare zamu tafi da Maryam" Kai ya girgiza "Zamu zo ai, ta sani, idan ta haihu daman zamu zo" Shima nashi kan Alhaji Mustafa ya girgiza "Gida take son zuwa, kuma gida zan tafi da ita" Wannan karin ba bugawa zuciyar Haris takeyi ba, ji yake tana kada masa da wani abu da baisan menene ba "To me yasa? Saboda munyi fada? Baba ba'a fadane a tsakanin ma'aurata? Kuna fada da Mami, amman babu wanda yake zuwa ya dauketa sai dai ko idan itace ta tafi da kanta" Bai cika sakin baki a gaban Alhaji Mustafa ba, ko yace ya manta rabon da yayi, tun lokacin kuruciya, da wannan sakin bakin ne abinda yasa duka ya fara giftawa a tsakaninsu, sai dai yanzun in yayi shiru zai cutu ne, ya za'ayi kawai ace za'a tafar masa da mata? Haka akeyi? Ina ake haka "Waya baka Maryama?" Cewar Alhaji Mustafa, bai kuma jira amsar Haris ba ya dora da "Inace ni na nema maka aurenta ko? Inaso kasan yanda na nema maka shi cikin sauki zan iya kashe shi cikin sauki idan naga akwai cutarwa a ciki. Maryama tace mun tana so taje gida, da alama tana bukatar break, daga koma menene yake faruwa tsakaninku da bataso ta fada, saboda haka zata tafi gida" Kai dai Haris yake ta girgizawa "Ai ba tambayarka nakeyi ba, umarni ne nake baka" Da yake dakin hotel din ciki da falo ne Haris ya kama musu, sai lokacin Alhaji Sa'id ya fito, ya sauya kaya, yaji dadin jikinshi, cikinshi nema a cushe, watakila gajiya ce ta hanashi cin abin kirki, Haris ya kalle shi, ya tsinci kanshi da fadin "Abba kayiwa Baba magana" Cikin rashin fahimta Alhaji Sa'id yake kallon su biyun "Wai sai an tafi da Maryamm gida, kuma na gaya masa zamu zo, idan ta haihu zamu zo gida tare" Alhaji Sa'id ya danyi murmushi yana kallon abokinshi, duk da ba wai ya gama fahimtar abinda yake faruwa bane, sai yace "To ina ake haka kuwa? Yarinya ga mijinta ace za'ayi masa iko" Shima nashi kason kallon ya samu a wajen Alhaji Mustafa "Wallahi kafata kafar Maryama zamu bar kasar nan Haris, kuma tunda ba tsoronka nakeyi ba, ba zaka sakani azumin kaffara ba" Da sauri Alhaji Sa'id yace "Subhanallahi...haba Mustafa...kai Haris tafi abinka, kabarshi zamuyi magana kafin muzo asibitin anjima In Shaa Allaah" Kamar Haris zaiyi gardama, saiya tuna ai a lokutta da dama idan Baban nashi ya murde, ita kanta Hajiya Rumana bata da wanda take kira ya shawo mata kanshi sai Alhaji Sa'id din, amman fa a yanda yakeji babu inda Maryama zata taka batare dashi ba, babu mai tafar masa da mata ko ina. Yayi shiru ne yabi maganar Alhaji Sa'id ya tafi. Haka kawai yaji ranshi yana baci, maimakon ya wuce asibitin, sai kawai ya fara yin gida, yana bukatar ya dan busa hayaki ko kanshi zai rage nauyin da yakeji yayi. Daya gama sai yayi wanka, ya kara sake kaya ya balbala turare saboda ya rasa irin hancin da Maryama take dashi wajen jin warin hayakin wiwi a jikinshi. Biyawa yayi ya bada uzurin da ya dauki Awwab tunda lokacin daukar baiyi ba, ya wuce asibitin tare dashi. Mamaki ya dingayi, ganin Maryama a zaune, alamunta sun nuna tayi wanka, ta canza kaya, kuma da murmushi ta mikawa Awwab daya ruga da gudu hannu "Dan albarka, ya kake?" Ita Hausa takeyi masa, haka kawai kuma sai Haris yake yi masa Italian, gashi yanzun da yake cakuduwa da turawa, turanci akeyi, bakin yaron yayi nauyi, watakila kuma yana rasa yaren da zai farayi ne, yarukan sunyi masa yawa a cikin kwakwalwa, ya jima sosai kafin ya fara furta wasu abubuwan, wani abinma inya fada Maryama bata ganewa saboda zai fadane da yaren Italian, ita kuma bataji. Ko yanzun ma labari yake bata, yanata cakuda yarukan uku, tayi 'yar dariya, rabon da tajita sakat haka tun data farka a asibitin nan, yanzun bata da wani fata saina suzo su sallameta, taje gida ta fara hada kayanta. Dan in yau ma aka sallameta ba zataki ace yau zasu bi jirgin da suka samu zuwa Nigeria ba. "Ya jikin?" Muryar Haris ta ratso cikin surutun da Awwab yakeyi mata, yanda ta shareshi, kamar baya dakin, sai abin yakeyi masa wani iri "Da sauki Alhamdulillah" Ta amsa masa, zaiso ace yayi mata wata maganar daban, amman daya sake bude bakinshi sai yace "Me yasa kika cewa Baba kinaso kije gida? Na fada miki zamuje tare, idan kin haihu" Ta dago kai idanuwanta tar cikin nashi "Saboda gida nake so in tafi, na gaya maka ba zan zauna ba ai" Yayi shiru yana kallonta har saida ta kasa jurewa ta sauke idanuwanta "Idan nace ba zakije bafa?" Tasa hannuwanta biyu tana toshewa Awwab kunnuwa "Ai baka isa bane ba Ganja, isar nan ta kare tun randa naga wata a samanka..." Zaiyi magana ta saki kunnuwan Awwab tana cigaba dayi masa wasa kamar bata fada masa magana ba "Maryamm" Cike da kosawa tace "Ni da zaka tafi kayi abinda ka sabama ya fiye mun wannan zaman da kakemun, dan ba son ganinka nakeyi ba" Ta karasa maganar da dukkan gaskiyarta, wani irin tiririn bakin cikine yake taso mata data ganshi, data kalle shi saita ga komai yana dawo mata, kamar ta tashi ta shakare shi "Maryamm" Karamin tsaki taja, wani abu da ta gwada sau biyu kacal a iya zamansu basu kwasheta da dadi ba, bata sake giginyi masa tsaki ba sai yau, kuma taja shi irin da tsayin nan dan so takeyi yajita, aikuwa yaji, tagani a yanda yanayin fuskarshi ya canza zuwa bacin rai, bayason tsaki, tun tasowarshi yana cikin abinda bayaso, inya taba kwatanta yi to ya manta, saboda bayaso, ko sanda yake secondary abinda tsaki na daga cikin abinda zaija yayi maka dukan tsiya. Na farko data fara yi masa ya dalle mata bakine, na biyun ma haka, bayan yayi mata riqon da saida ta bashi hakuri jin kamar zai karyata, kuma fushi ya dauka sosai, ba karamin lallashi tayi ba kafin ya hakura da kashedi sosai, ta kuma dauka, amman yau raini yake gani karara a cikin idanuwanta, rainin da yake so ya dauke Awwab ya maidashi inda ya dauko shi, ya dawo ya murzawa dakin mukulli ya goge shi tas a tare da ita. Babu daya a ciki da zai iya, dan Alhaji Mustafa ne ma yake kiranshi, dole ya daga wayar, tambaya yayi ko zasu iya zuwa, ya amsa musu a takaice. Ba'a kara mintina ashirin ba sai gasu, Maryama da gudunta taje ta fada jikin Alhaji Sa'id kamar ba ita bace bata da lafiya "Mairama kice so kikeyi in taho babu shiri, shisa kuka hada baki da mijinki kukayi mun karyar ciwo" Dariya tayi, daga zuciyarta "Kai Abba" Shima dariyar yayi, yaji dadin ganinta matuka, dan yayiwa Alhaji Mustafa maganar duniya bayan tafiyar Haris bai kulashi ba, bayan sun kara gaisawa da Alhaji Mustafa, sai yayi wa Haris ido, kan dole ya tashi yabi bayanshi suka bar Maryaman da Alhaji Sa'id "Yanzun me yake ciwo?" Kai ta girgiza masa, abinda ya rage da yake mata ciwo ba zata iya fada masa ba "Babu komai, naji sauki sosai" Ya sauke numfashi "Alhamdulillah. Allaah Ya kara miki lafiya yayi miki albarka" Ta amsa a hankali "Babanki yace dake zamu koma, mijinki kuma yace saikin haihu, na dauka nima maganar da muka gama kenan, akwai matsala ne Mairama?" Ta danyi jim, tana tauna abinda zata fada "Eh Abba, fada mukayi, kuma inajin idan ba muba juna tazara ba zata iya yin girma" Shima shiru yayi na dan lokaci "Babu auren da ba'a samun matsala a cikinshi, amman ba ko da yaushe bane in an samu matsalar za'a guje mata maimakon a fuskance ta" Sai taji kamar hawaye na shirin balle mata "Ba gudu zanyi ba, ina bukatar hutun ne Abba..." Suka sakeyin shiru, yasan Maryama na da kafiya, har Hajja takan kawo masa kararta, amman shi batayi masa, in yaja saki takeyi, shisa ya rasa abinda zaice saboda bayaso ya tauyeta, ba kuma yaso ace ya goyi bayanta ta fara gujema matsalolin aurenta, tunda har tayi shiru, itama tasan cewa matsala ce da sirrantawar yafi bayyanawar zama maslaha, kuma tana sa ran ita da Haris din zasu iya samun dai-daito batare da an shiga ciki ba. "Kiyi hakuri Mairama" Ya furta a hankali, taji hawaye ya balle mata "Karkace baka isa dani ba Abba, dan Allaah kayi hakuri" Sai kawai yace mata "Na hakura, Allaah Yayi miki albarka" Tasa hannu ta share hawayenta tana amsawa da "Amin Abba" Cike da wani irin rauni da yake shigarshi a hankali, duk wani kokarin hira da yake janta dashi ta kasa sakewa gabaki daya, ta kuma kasa daina kai hannu tana share hawayenta. Har sanda su Alhaji Mustafa suka dawo dakin kuwa bata daina share hawaye ba, zuciyar Haris har wani tsalle takeyi, ya kasa daga ido ya kalli Alhaji Sa'id, kamar ya zama gari yabi iska haka yakejin shi, taya Maryama zata dinga wannan kukan a gabanshi? Me take so yayi tunani? Bayaso ko kadan mutuncinshi ya zube a idanuwan Alhaji Sa'id din. Sanda zasu tafi kuwa dakyar ya rakasu. Yazo ya dauki Awwab suka koma gida dan yasan koya tsaya magana da Maryama ma ba zata kulashi ba, inta kulashi kuwa maganganun da zata fada masa zata bata masa raine. Washegari da safe aka sallameta da sharadin ta huta sosai, kar ta jijjiga jikinta, kuma suna komawa gida ta fara hada akwatinta kamar bataji kashedin da akayi mata na hutawa ba. "Wai me kikeyi haka Maryamm?" Haris ya tambaya, bata kulashi ba, duk maganar daya tsaya yanayi mata bata kula shi ba, sannan iya kayanta yaga ta hada, ta zage akwatin ta koma falo tana barinshi a bedroom din cikin rashin sanin abinyi. Kuma a ranar da yamma da su Alhaji Mustafa sukazo gidan take ce masa "Baba harna hada kayana, passport dina yana wajenshi..." Alhaji Mustafa ya daga mata kai yana kallon Haris "Saika dauko mun, dan so nake mu samu mu juya, ina da abubuwan yi a gabana, Awwab na da passport ne?" Kafin Haris ya amsa ta rigashi da cewa "Eh" Dan anje anyi masa, saboda lokacin suna saka ran yin tafiya kafin tazo ta samu wani ciki "To Alhamdulillah" Wani murmushin takaici ne yake neman kwacewa Haris "Baba babu fa inda zataje" Kallonshi Alhaji Mustafa yayi "Ni ka tashi ka dauko mun passport dinsu ita da Awwab din kafin ranka ya baci" Alhaji Sa'id ne ya saka baki "Daka tsaya anbi abin nan a hankali Mustafa" Cikin bacin rai yace masa "Nasan kai ka haifi Maryama, amman daga randa ka na karbawa Haris aurenta na karbeta ne duka daga hannunka, saboda haka babu ruwanka, kafata kafar 'yata zamu bar New York, ba kuma shawarar wani nake nema ba" Haris daya mike tsaye yace "Amman dai gaskiya Baba idan akayi mun haka ba'a kyauta mun ba, saboda nima bana ce ba zataje gida bane ba" Kokari yakeyi karya fadi duka abinda yake ranshi, saboda Alhaji Sa'id "Ba zan sake maka magana ba, kaje ka daukomun passport dinsu, idan kuma ban isa ba saika nuna mun" Yayi tsaye, kusan mintina uku, saida yaga Alhaji Sa'id ya daga ido ya kalle shi, wani kallo da baisan ya akayi yaji kafafuwanshi sun motsa ba, sai gashi a daki, inda ya adana duka passport din biyu, ya dauko yazo ya mikawa Alhaji Mustafa, zuciyarshi na tafasa kamar zata kama da wuta "Ma Shaa Allaah, bari muzo mu koma masaukinmu, ki karasa shirya komai dai, dan zan duba mana yiwuwar mu samu tikitin safe" Cike da murmushi take daga kai tana kuma amsawa da "To Baba, ai kayan Awwab ne ma kawai, nagode, Allaah Ya kara lafiya" Wannan karin itace ta rakasu har kofar gida, data dawo kuma sai ta samu Haris a tsaye inda suka barshi "In dai a karkashina kike ban yarda ki taka ko ina ba Maryamm" Ko inda yake bata kalla ba, ta koma ciki abinta, kuma tun yana hargagi, harya koma lallashi, amman Maryama taki tayi masa magana, da daddare da ta kwanta a falo kan kujera yazo yayi yunkurin mayar da ita daki saita saka masa ihu tana kokarin ja makota su kirawo musu 'yan sanda "Meye haka? Meye haka wai Maryamm" Ta watsa masa harara "Wallahi inka sake ka hadamun jikina da wannan bakin jikin naka mai dauda saina maka ihun da makota zasu kira maka 'yan sanda, in bakayi wasa ba kana police custody zamu bar kasar nan, dan ba zan fadawa kowa kana hannun 'yan sanda ba" Yayi tsaye yana kallonta, ta murguda baki ta sake watsa masa harara "Yanzun ba zaki nutsu muyi magana ba, ashe zaki iya tafiya kibarni, ashe zan miki laifin da ba zaki bari in baki hakuri ba balle ki yafemun" Ta kwanta kawai tana juya masa baya, hakurin me zai bata? Wanne irin hakuri? To inya bata hakuri zai goge mata abinda ta gani ne? Ko zai wanke mata cutar da yayi na gauraya mata jiki da nashi da yake cike da daudar zina? Ganin ta juya masa bayane yasa shi karasawa ya zauna a kujerar, cikin zafin nama kuma yasa hannunshi yana toshe mata baki, ta kuwa gartsa masa cizon daya sakashi sakinta babu shiri, filon kujera ta dauka ta shiga maka masa duk inda hannunta yakai, kuka takeyi, irin kukan nan mai gunji "Dan Allaah Maryamm" Yake fadi cikin karyewar murya, duk da baya wani yunkuri na kare kanshi daga dukan da take kai masa, in dai zata huce "Dan Allaah karki barni, karki bari Baba ya tafarmun dake, bansan ya zanyi ba" Da kanta tagaji ta jefar da pillow din, ta sauka daga kujerar tana komawa kasa kan kafet ta kwanta, har lokacin kuka takeyi sosai, wani irin zafi kirjinta yakeyi mata, ita batama taba sanin wani ciwo makamancin wannan ba. Daya sauko kasan karfinta ya riga ya kare, shisa ta kasa hanashi ya dagata ya hada da jikinshi "I'm sorry, dan Allaah kiyi hakuri" Shine abinda yake furtawa yana sake maimaitawa, yana rocking dinta a jikinshi, har baccin wahala ya dauketa, ya mike da ita yaje ya kwantar a gefen Awwab, shima ya hau gadon ya kwanta, yana fatan gari ya waye musu da sauyawar zuciyarta. Sai kawai ta karya masa tashi da safen data shirya, ta kuma shirya Awwab ta fito musu da akwatina guda biyu matsakaita, nata dana Awwab, ta kuma sake karya masa zuciya lokacin data mikawa Alhaji Mustafa akwatinan bayan sunzo da mai taxi "Maryamm" Ta juya, ta kalle shi, idanuwanta cike da hawaye, sannan kuma ta sake juyawa ta murda handle din kofar, dan Alhaji Mustafa ya dauki Awwab ne ya barsu "Ga wayarki" Ya fadi cikin wata murya data kasa ganewa, saita tsaya ta sake juyawa ta karbi wayar, ya karasa hade takun da baifi uku ba daya rage a tsakaninsu, ya sumbaci gefen fuskarta "Kiyi mun alfarma ki zauna a gida, a gidanmu, dan Allaah, zan taho dana gama exams dina...ki kulamun da kanki, karkije ko ina" Harta bude kofar saita sake juyowa, hawayenta suka zubo, tasa hannu ta gogesu, zuciyarta zafi takeyi, zuciyar nan dai da akace guda daya kowa yake da ita, amman kuma a yanzun ba ko ina bane taji yana mata tururin, akwai wani sashi da yayi sanyi da yanayin Haris, da abinda take gani cikin idanuwanshi "Zanje gida, Kaduna" Ta tsinci kanta da furtawa cikin rawar murya, ya daga mata kai "Karki dade, dan Allaah Maryamm, karki dade acan" Batace masa komai ba ta taka kafarta waje "Maryamm" Ta juyo "Ti amo..." Tasan batajin yaren Italian, amman wannan matsala ce data shafi kwakwalwarta, dan kuwa zuciyarta a bude ta karbi abinda ya fada, ta kuma fassara mata "Ina sonki" Ya dan dafe kirjinshi da hannu, ya bubbuga a hankali "Da yawa...." Ya sake fadi, a karo na farko, yana ba kanshi mamaki, saboda kalma ce da bata taba giftawa a tsakaninsu ba a shekaru hudun nan Sai yau Sai yanzun... Kamar kuma zuciyarshi ce bata gama tabbatarwa ba din sai yau, da ta bi bayan Maryama data shiga taxi din nan, kuma ko da suka bacewa ganinshi, ya riga yasan ta tafar masa da kanta ne, a yanda yakejin kamar bashi da komai a kasar New York, yasan ba iya zuciyarshi Maryama ta tafi da ita ba... Harda wani sashi da Haris baisan sunanshi ba! 37 KADUNA Tasan daga zuwanta, a cikin kwana biyun nan inda akwai wani adadi na hawaye da ake warewa kowanne dan adam a cikin kowacce rana, ace in bakayi amfani dashi ba shikenan, to tabbas da ta gama karar da nata, Hajja ta fara gani lokacin da suka isa gidan, tana dora idanuwanta akanta, taji shekaru goma sha daga cikin nata sun murmushe sunbi iska, a wannan lokacin, ta manta da wani abu wai girma, ta manta da auren da yake kanta, ta manta da ta haihu, ta manta tana shirin sake zama uwa a karo na biyu "Sufa iyaye ba'a girma da bukatarsu Maryama, ko shekara 100 zakayi a duniya babu wata rana da zaka wayi gari a cikinta kaji baka bukatar iyayenka" Haka Khairi ta taba fada mata lokacin da suka jewa Malaminsu na Islamiyya gaisuwa taga idanuwanshi duk sun kode, kamar wanda yayi kuka, take mamaki, tunda shi kanshi zaiyi shekara arba'in da wani abu, kuma akwai wanda tagani a wajen da ta sukayi kama dashi, kuma tasan sun girmeshi, to a ganinta kukan me zaiyi? Shi da ba yaro ba? Sai yanzun ta gane, kana kara hankali ne kana kara gane muhimmanci iyayenka da rawar da suke takawa a cikin rayuwarka, dan a ranar so tayi ta ruga, da gudunta ta fada jikin Hajjan, amman nauyin kewarta daya danneta sai ya sauka har cikin kafafuwanta yana hana mata yin wannan gudun, kuma nauyin ne ya tunkudo hawayenta wani na biye da wani. Ta dinga kallon 'yan uwanta da yanda suka cika gidan washegari, masu auren, yara daga makaranta duk an kawosu nan, kuma wai saboda su ganta, suyi mata barka da zuwane sukayi wannan taron, itafa, Maryama, karamar kanwarsu da a cikinsu babu wanda baya gajiya da gaya mata rashin hankalinta a lokutta mabanbanta, amman yau sune suka jingine komai na rayuwarsu suka zo don ita, kowa kuma da abinda ya riko naci ya taho mata dashi, harda mazan kuwa, ta dinga fakar idanuwansu tana share hawayenta, tarin kaunarsu na sake samun sababbin wajaje a cikin zuciyarta Cikinta rabon da taji shi ya cika irin na ranar harta manta, saboda kowa mika mata wani abu yake "Meatpie din nan yayi dadi Maryama, kinji kuwa?" Saita karba, kome suka bata, saita karba ta saka a bakinta, Awwab kuwa ba zatace waye ya fice dashi a cikin mazan gidan ba. Ko kadan baiyi musu kwiya ba. Duk basu fara barin gidan ba sai bayan isha'i, ita dai sun zauna a falo suna cigaba da hira har wajen goman dare, kafin ta yiwa Hajja sallama, suka shige nasu dakin ita da Khairi, da suna shiga ta rufe kofar ta juyo tace mata "Ki fara magana yanzun nan" Abinma sai yaso ya bata dariya, duk da wani abu daya taso mata, wani abu da ganin kowa ya danne "Adda Khairi..." Ta kira sunan muryarta na karyewa, wannan tiririn da ta taho dashi tun daga New York yana tasowa ya sake rufar mata, sai Khairi tazo ta kama hannunta ta jata suka zauna a gefen gadonsu, wasu hawaye masu zafin gaske suka tasowa Maryama "Bansan ta inda zan fara ba, inajin kamar maganganun da nake ta adanawa in cigaba da rike su..." A hankali Khairi ta jinjina mata kai "Idan kina so ki rike, kinsan zan fahimta, ko a tsakaninmu, ni da ke, dole zai zamana muna da sirrikan da zamu adana, amman nice Maryama, sirrinki har abada nawa ne duk lokacin da kika zabi ki rabashi dani" Nata kan Maryama take jinjinawa, ta sani, data kalli Khairi sai tace mata "Kinsan me yasa ake cewa Haris Ganja?" Khairi ta girgiza mata kai, itama zuwansu New York ne ta saka shi a gaba da tambaya "Me yasa ake ce maka Ganja? Kaji? Dan Allaah" Yayi murmushi "Kin tabbata kina so ki sani?" Da saurinta ta daga masa kai "Eh mana, sunan yana mun dadin fada, dariya yake bani kuma" Sai shima ta bashi dariya, yana son wannan barin zancen nata, yanda take fadar duk wani abu da yake zuciyarta batare da ta tsaya ta juyashi ba "Lokacin da na fara...dana fara shan weed, mu duka muna sha, Ni, Barde, Lalaye, 2Pac...saiya zamana babu wanda yake shan yawan da ni nake iya sha batare da yasa sun zama high sosai ba, yawan wanda zan sha inyi hidimata batare da kowa ya gane nasha wani abu, in su suka sha tsaf za'a gane harma ya iya zame musu matsala, shisa suke ce mun Ganja..." Haka ta maimaitawa Khairi, abinda Haris ya fada mata, tana dorawa da "Sai dai na dauka shine kawai matsalarshi, wiwin, tunda yace mun wani abu daban na maye bai taba burgeshi ba...kuma na yarda, ko da zai boyemun, dana tambaya, tunda ya bude bakinshi ko ba zaimun dadi ba zai gayamun gaskiya" Ta numfasa saboda zafin da zuciyarta takeyi, saboda abinda ya dawo mata "Bashi kadai bane Adda, harda mata.." Khairi tayi mata wani dogon kallo "Tarayyar namiji da mata kala-kala ce Maryama, dan kinga wani chatting, ko kiran waya zai yiwu wayar ce kawai, chatting dinne kawai, ba zaki taba raba rayuwar kowanne namiji da wasu matan ba" Maryama tayi wani murmushi mai ciwon gaske "Kince inyi surprising dinshi, in bashi mamaki, inyi masa ziyarar bazata, naje, nayi masa ziyarar Adda amman nice na sha mamaki, bazatan da zanyi sai akayi mun, naga abinda nasan mutuwa ce kawai zata goge mun shi...ba chatting nagani ba, kafin kuma kice wani abu, a samanta naganshi, kuma baiyi musu ba, a karo na farko da naso ko karyace ya kalleni ya fadamun, bai musa ba Adda....mijina mazinaci ne....mijina" Ta karasa hawaye na sake balle mata, wai kalmar da ko kiranta bata so ayi, ko a Islamiyya ake musu karatu da aka tabo zina da hukunce hukuncenta sai taji kamar kasa ta tsage ta shige ciki, in aka gama sai ta bude ta fito da ita saboda yanda take jin munin kalmar a kunnuwanta, littafi kuwa duk dadinshi ficewa yakeyi daga ranta in dai za'ace akwai mazinaci a ciki, saboda bataso ma ace yana da mata, balle kuma akai ga ranar da zata gane irin mijin da take aure, sai ta dinga jin kamar ita, ta dinga jin kamar numfashinta zai iya tsayawa, haka ma take hasashe cikin kanta, inta auri mazinaci ta gane, zuciyarta bugawa kawai zatayi ta sama mata hutun mutuwar da ta tabbatar zata bukata. Ashe wani abin hasashe ne kawai, wani abin baka sanin me zakayi saiya faru da kai. Gata nan zaune, harma ta bude bakinta tana bada labarin cewar bawai zina kawai mijinta yakeyi ba, ita da kanta ta ganshi, ta ga wata akanshi a zaune. Kuma wai bata mutu ba har yanzun, numfashi takeyi, dazun ma da ita aka dinga tuntsira dariya a tsakanin 'yan uwanta, a cikinsu, da suka kalleta babu wanda ya gane tayi birkidedeniya da mazinaci, babu wanda yaga ko wata alama na cewa igiyoyin da suke kanta na aure, auren daya sama mata wannan datajar a wajensu yau, darajar da tasa suka taso tun daga gidajensu da sunan yi mata sannu da zuwa, daure suke gam da mazinaci, dan wiwi. Lallai ne da akace aure sirri ne dashi. Har masu azancin magana ma sai suce ai shi auren Labule ne, labule kuma asirin mai daki ne, duk da a zahiri, kowa in yazo kofar dakin nan, ko babu neman izini zai iya saka hannu ya daga Labulen nan, amman kuma akwai wani Labulen na daban, wanda hannuwan da ba mammalakan dakin nan ba basu isa su iya daga shi ba, shine sirrin, sirrin mai dakin da ake cewa, babu kuma wata mace da zatace bata da wannan Labulen a gidanta na aure, ai yau da gobe babu wani abu data bari, ko da kuwa in ta zabi ta daga Labulen nan babu zina balle wiwi a cikinshi, amman akwai hakuri, hakurin yau da gobe mai zuwa da tarin sadaukarwa, hakurin nan da kowacce mace take kamanta shi a ranaku mabanbanta a zamantakewar aurenta. "Maryama..." Muryar Khairi ta kurda cikin kanta "Nasani, baiyi kama da ko daya ba? Mazinacin, dama dan wiwi" Sunanta dai Khairi ta sake kira, itama hawaye na zubo mata "Kibari, ki daina...dan Allaah, mijinki ne har yanzun, ki daina jingina masa wannan kalmomin" Takai hannu ta share hawayenta, duk da wasu sun sake maye gurbin wanda ta goge din "Bani na jingina masa ba Adda Khairi, da abinshi na same shi daman, ban dai gansu bane ba sai daga baya...saboda siffarshi ta iya adana masa su" A zaune Maryama take, amman ji takeyi kamar bakin cikin da yake taso mata zai iya kayar da ita "Haka yace yana sona, da zamu taho, yace yana sona, bai taba fadamun ba, me yasa sai da naganshi da wata tukunna zai gayamun? Toni me zanyi da wannan son yanzun? Ya zanyi dashi Adda? Ya zanyi da zuciyata da ta karbarmun shi duk da bana so? Me yasa tunda ya fadamun muryarshi take ta dawomun? Ya zanyi? Na fada masa ba zan zauna ba, shisa nayiwa ba Baban Tudun Wada magana sai suka taho dani, tun dana fito daga gidan nake jin kamar ba gabaki dayana na fito ba, kamar akwai wani abu dana bari a wajenshi..." Maryama take fada a numfashi daya, da Khairi ta riko hannunta sai ta kalleta, cikin idanuwa tace "Na haukace ko Adda? Ganjaa ya haukata ni" Kai Khairi take girgiza mata, idanuwanta cike taf da wasu sababbin hawayen, akwai kalmar da bature zaiyi amfani da ita a yanzun in da zaiga Maryama "Broken" Amman kuma a shimfide a kasan wannan kalmar, a dacin da yake fita a sautinta akwai soyayya, soyayyar Haris, irin soyayyar nan da maiyinta baisan da zamanta ba balle kuma girman wajen da ta mamaye a tare dashi "To me na bar masa? Na taho da Awwab, ga cikina na taho dashi, kuma babu abinda nake so irin inyi nisa dashi, inyi nisa da New York, gani na samu abinda nake so amman bai nutsar dani ba, inajina a firgice tun jiya, bansan ya akayi nayi bacci ba saboda inajin ban taho gabaki dayana ba Adda, kirjina ciwo yakeyi mun, I don't feel whole, shisa nace miki na haukace, ya zan bar abinda ban san menene ba?" Khairi ta goge tata fuskar, ta danyi gyaran murya saboda makoshinta da takeji a tokare da tausayin Maryaman "Kinyi magana dashi? Kunyi waya tunda kika sauka" Ta girgizawa Khairi kanta "Ina wayar taki?" Tana cikin jakarta, a kashe take ma, ko kunnawa batayi ba "Tana cikin jakata, ban kunna ba...tunda mukazo ban kunna ba" Jakar tana nan dakin nasu, Khairi da kanta ta tashi ta bude, tana kuma dauko mata wayar ta koma kan gadon ta mika mata "Ki kunna yaji kin sauka lafiya" Ta karbi wayar, tayi shiru tana kallonta, a hankali ta kunna, sau nawa a zuwanta Haris ya sauya mata waya, haka kawai ba dan tayi wani abu ba, inya bushi iska saiya karba ya sai mata sabuwa, kuma wayar tana gama loading, sai taga babu network, ta kuma tuna ba layin Nigeria bane a ciki "Sai dai ki aramun wayarki inyi masa text" Cewar Maryama a hankali, cikin muryar da zaka gane yawan kukan da tayi duk da bashi da sauti, wayar Khairi ta dauko ta bata, akwai ma lambar Haris din a ciki, dan haka ta tura masa gajeran sako "Mun sauka, muna lafiya mu duka ukun" Sai ta rubuta sunanta daga kasa, kuma sakon yana shiga kamar Haris yana jiranshi ne sai ga kiranshi na shigowa, taji zuciyarta ta mulmule tayi wata mirgina kamar tana neman hanyar guduwa, wayar tayi mata nauyi a hannu "Kira yakeyi, shine yake kira" Khairi ta danyi murmushi "Ki daga" Tayi maganar tana mikewa ta fice daga dakin, lokacin kiran ya yanke, amman harya wani ya kara shigowa, ta daga tana saka wayar a kunne kamar mai tsoron zata cijeta "Maryamm" Haris ya kira, a yanayin da sautinshi ya fita, numfashin daya sauke mata cikin kunne, da tarin tazarar da take tsakaninsu bata hanata jin gajiyar da take tare da muryar ba, bata hanata fahimtar abubuwan daya fada batare daya furta ba "Nayi kewarku, nagaji, babu abinda ya shiga cikina banda hayaki, me yasa kika tafi? Me yasa zaki tafi? Ki dawo" Duk wannan, dama wasu masu yawa, taji su, ta kara kankame wayar "Me yasa bakaci abinci ba? Ba zaka daina bankawa cikinka hayakin nan ba ko Ganjaa? Ka manta me likita yace?" Ya sake sauke numfashi "Maryamm" Ta girgiza kanta "Bacci zanyi ni, dare yayi mu anan, kwanciya zanyi, kaje ka samu wani abu kaci, ba shayi kawai ba, shayi da wani abu..." Kamar baiji abinda tace ba "Ni kadai ne, gidan yayi shiru, ni kadai ne Maryamm, ya zanyi? Ina so in biyoku" Kai ta sake girgizawa duk da baya ganinta "A'a, dan Allaah kaje kaci wani abu" Bata ganinshi, amman tabbas yana tsaye, ko a zaune, maikon da idanuwanshi sukeyi kuma na gardama ne "Tafiya kikayi, kika barni, banajin cin abinci, ina so in biyoku" Haka kawai taji ta nemi komai ta rasa, kamar bata da wani emotions daya wuce ta ganta tsaye a gabanshi, da kofin shayi da wani abin da zai hada ta mika masa, saboda zaman nan nashi da yunwa, ta tabbata komai zai iya faruwa, bata manta gargadin likitanshi ba, da yayi wani tari sai gata ta mike tsaye "Kaga ka fara tari, dan Allaah kaje kaci abinci Ganjaa, sai muyi maganar zuwan naka, kaje kaci abinci" A hankali ya amsa da "Bacci kikace zakiyi, ki kwanta, in kika tashi ki kirani" Da sauri tace "Kaci wani abu" Ya amsa da "Si..." Tasan zaici amman sai ta kara da "Dan Allaah, kaji" Ya sake amsawa da "Si..." Yana dorawa da "Maryamm" Kafin ta amsa kuma ya sake cewa "Kiyi bacci" Kai kawai ta daga masa, ita ta kashe kiran daga nan, ta sauke daga kunnenta, tanajin kamar zazzabi zai rufeta, sai kawai ta kwanta, idan ma tayi addu'a to saboda ta sabane, amman baccin ne ta dauketa, mai nauyin gaske. Bata san lokacin da Khairi ta dawo dakin ba. * Washegari kuwa sai bayan tayi wanka ma sannan ta fita suka gaisa da Hajja, abin karinsu ma daki suka kwaso ita da Khairi, Awwab ko magana baiyi mata ba, yana makale da Hajja, duk inda ta cire kafarta nan yake mayar da tashi, da yake Allaah Ya amsawa Maryama addu'ar data dingayi karta haifi irin Haris, ba zata iya ta dinga fama dasu biyun akan abinci ba, Awwab baya wasa da cikinshi, ko yanzun ma batasan me yake ta tauna ba, amman batajin tun zuwansu bakinshi ya huta "Dan Allaah kar cikin yaron nan ya baci, kila bai saba da wadannan ciye-ciyen abubuwan da kuke ta dirka masa ba" Tanajin Hajja tayi magana, amman Awwab dinne yake binsu daya bayan daya yana mika hannu. Kuma suna karyawar suna maganar bikin Khairi din, sai lokacin ma Maryama ta kula da ba ita kadai bace take da damuwa "Me yake faruwa?" Khairi ta sauke numfashi "Ke kinsan zaman da zanyi a Kano yana daga cikin manyan dalilin da yasa na zabi auren mutumin nan, wai sai yanzun yake gayamun transfer ta dawo dashi Kaduna, kuma shi ba zai yiwu ace yana da mata biyu duka sun tare a Kano shi yana nan shi kadai ba, kuma ita matar tashi ba zai yiwu ta baro Kano ba saboda nata karatun, sai nice zanyi hakuri in zauna anan din, ni kosu Hajja ban fadawa ba har yanzun saboda ba zan zauna a Kaduna ba, ba haka mukayi dashi ba" Murmushi Maryama tayi, tasan Khairi tana da hakuri, amman in har ta kafe akan ra'ayinta tana da wahalar sha'ani "Yafa fiki gaskiya, kuma kinyi shiru ne saboda kinsan su Hajja ma haka zasuce" Khairi ta kalleta "To ke kuma fa? Haka zamuyi nisa da juna? Kilan ba lallai bane shima ya dinga barina ina zuwa sanda nake so, balle kuma wannan mijin naki mai kullen tsiya...ke bama zai yiwu bane ba, hakuri zaiyi ya ajiyeni inda mukayi dashi" Har kasan zuciyar Maryama dadi takeji, duk saboda ita, Khairi take so ta zauna a Kano, saboda itane take ta wannan bacin ran, ita dai tana so a damu da ita, tana so taga tana da muhimmanci mai yawa har haka "Dan Allaah ki daina musu dashi, kibari wani tunani nakeyi...idan nagama zamuyi magana" Harararta Khairi tayi tana hadawa da karamin tsaki "Wanne tunani kuma? Nan zan zauna ina jiran tunaninki?" Sosai Maryama taji dariya ta kamata, kuma dariyar saita sake kule Khairi, ta kara jan wani tsakin. Tare sukayi wanke-wanke da Khairi, suka dora girkin rana sunata hira, fitsarin da taji ya sakata komawa dakinsu, taji wayar Khairi nata ruri, da ta karasa ta dauka sai taga Haris ne, taji wani abu mai kama da fargaba ya saukar mata, tace zata kirashi, harga Allaah mantawa tayi saboda ta tashi da saukin zuciya yau din nan, kamar fadawa Khairi da tayi ya rage mata wani kaso mai girma na zafin da takeji a ranta, ta daga "Maryamm" Kafin ya kara da wani abu tace "Zan kiraka daman" Dan tasan fada zasuyi "Karya ne" Murmushi yaso kwace mata "Idan na tuna, mantawa nayi, na manta ne Ganjaa" Yayi shiru na wasu dakika "Da me? Dame kika manta Maryamm? Ni ko kirana?" Akwai yanayin da yayi maganar da yasa ta amsawa da "Kiran, mantawa nayi zan kiraka" Ya sakeyin shiru "Kaci abincin?" A takaice ya amsa "Burger" Ta jinjina kanta tana rasa abinda zatace masa "Zanyi exams, amman ina so in biyoku" Tasan daman maganar ya biyosu ba zata kare ba "Kabari kagama exams dinka" Ya dan numfasa "To ki koma Kano...kinji, ki koma Kano, idan nasan kina Kano zanfi samun natsuwa, bansan ya zanyi da tunanina ba Maryamm, kina Kaduna ina nan, kina gidanku fa, nasan muna fada, kina fada dani, ki koma Kano in na dawo sai mu cigaba" Kai take girgizawa tunda ya fara magana, kamar ya sani ya cigaba da magana "Dan Allaah, ki kara wasu kwanaki yanda zaku gaisa dasu sosai saiki koma" Taji kamar hawaye zasu balle mata, ita dashi, a karkashin inuwa daya, ya zata kalli Haris batare da taga Autumn ba? Ita dashi, daban-daban, numfashinta neman daukewa yakeyi da wannan tunanin ya dirar mata, amman kuma bata shirya ba, komawa Kano, ta zauna ita kadai, tana bukatar ta zauna cikin 'yan uwanta "Dan Allaah" Ya sake fada, tasan naci dabi'arta ne, ashe ta shafa masa, ta koya masa irin magiyarta akan abu "Kinji Maryamm" Hawayenta suka zubo, murmushi na kwace mata a lokaci daya "Nifa saboda ke na zabi mutumin nan, saboda zai ajiyeni a Kano, zamu zauna gari daya" Sai kawai taji tana furta "Nagaji da Kano Ganjaa, bana son Kano, kadaici yana damuna a Kano, dan Allaah nagaji da Kano" Yayi shiru, wani irin shiru har saida tayi zaton kiran ya yanke tukunna yace "Idan na siyi gida a Kaduna kuma fa? Zaki bar gidanku ki koma nawan?" Da saurinta take daga masa kai tana share hawayen da suke zubo mata "Maryamm" Ya kira, muryarta a dakushe ta amsa "Ko kina Kaduna kinsan banda hakurin kina yawan yawo" Kai ta sake dagawa, ko ita bai barta ta fita yanda take so ba, babu yanda za'a rufa sati biyu batare da taga wani nata ba "Ina so ki bude baki ki amsani ne" A hankali tace "Banma san ko inaso in sake zama da kai ba Ganjaa" Sai taji yayi dariya mai sauti "Ni ina so in zauna dake, zai ishemu kafin ki dawo da son zama dani, ya ishemu Maryamm" Tayi shiru kawai "Zan siya mana gida a Kaduna" Shirun ta sakeyi masa "Ki siyi layi, karmu damu Adda Khairi, ki siyi layi saiki kirani" Ta daga masa kai "Zan fita, karkije ko ina kinji" Itace tayi dariya tana girgiza kanta kawai, saita tuna da wani littafi na Aisha Shafi'i, Zanen dutse, da gaske ne hali zanen dutse. Ta ajiye wayar kawai tana sake fita, kuma ta gane wani abu daya Ba wani abu ta manta a New York ba, Ba wani abu bane na daban tabari take jin rashin shi, Haris ne, shi tabari tare da wani kaso mai girma na zuciyarta. Kuma satinta daya a garin Kaduna, Hajja tace mata ta tambayi Haris su shirya suje su gaishe da Hajiya Rumana "Naga yanda baki da hankali, shima kamar baisan abinda ya kamata ba, wannan shirmen naku bansan sanda zaku gyara shi ba" Daga ita har Khairin haka suka hadu suka dinga mitar zuwan tun kafin ma suje, gashi Hajja tace sai sun tafi da Awwab, kuma ta sakasu kwasar wasu manyan ledoji guda biyu, daya na Hajiya Rumana, dayar kuma ta na Umma Fadime, Khairi ta dinga dariya da suke hanya Maryama tace mata su bar ledar Hajiya Rumana a mota, in suka gama abinda sukeyi su biya su kaiwa Adda Zahra su fada mata "Ba ruwana wallahi, ke kinsan Adda tsaf zata iya gayawa Hajja, kilan ke aure yasa ki wuce duka yanzun, amman ni bani da wannan kariyar" Itama sai abin ya bata dariya "Hajjan? Lallai, ai kema kinsan sai in banyi abin dukan ba, ina ruwan Hajja da wani aure na" Sake kama kawunansu sukayi lokacin da suka shiga gidan, Khairi na sabe da Awwab har bangaren Hajiya Rumanan, dukansu Hijabai ne a jikinsu, dan hijabin Khairi ce ma Maryama ta saka, da yake mai hannu ce saita bayyana dan karamin cikin da yake jikinta daya fara nunawa. Da sallamarsu suka shiga gidan, wani kamshin gayu nayi musu maraba. Dole fa ka jinjinawa Hajiya Rumana, ko da yake kamshin ai yana tare da al'adarsu ne ta mutanen Maiduguri. Tana hakimce cikin wata atamfa, ta nade kafafuwanta duka saman kujera tana danna waya, haka ta dago da kanta bayan ta amsa sallamar tana sauke musu fararen idanuwanta da Maryama taga kamar na Haris. Maikon nan ne kawai babu, a maimakonshi sai tarin izza da isar da takeji da ita, kuma ko da suka shiga cikin falon sosai, kan kujera Maryama tayi niyyar zama, Khairi taja mata hijabi sai suka zauna akan lallausan kafet din dakin suna jera mata gaisuwa, bata amsa ba, idanuwanta na kan Awwab, shi take kallo, ta ganshi a hoto, sau biyu, Haris ne ya tura mata, kuma a duka biyun batace komai ba, sai bai kara ba, tana so tace masa ina Awwab, amman sai taji kamar inta tambaya ta hadane ta tambaya harda Maryama. "Awwab" Ta tsinci kanta da fadi tana mika masa hannunta, saiya koma baya ta wajen kafadar Khairi yana makalewa, yanda yayi din, yasa taji zuciyarta ta takure waje daya, ya tuna mata da kuruciyar Haris, yanda yake makalewa a bayanta duk lokacin da wani yaso ya dauke shi, kuma har girmanshi in zasu fita tare to yana daga gefenta, ko da zai rike hannunta zata dinga jinshi ne a bayanta, ta gefenta, amman daga bayanta yana saka kafarshi inda ta daga tata, kamar wanda yake bukatar dukkan kariyar da zata iya bashi, Haris da a yanzun take jin ya matsa daga bayanta ya koma na Maryama shisa a duniya babu wanda ta tsana a halin yanzun sama da yarinyar nan, ta rabata da 'danta, tasa yayi mata nisa. Awwab din take ta kallo, shima ita yake kallo "Yana kwiya ne?" Ta tambaya tana sauko kafafuwanta daga kujerar "Zo mu gaisa" Tayi maganar cikin yaren Kanuri, saiya kalli Maryama, kamar mai jiran umarni "Kaje Awwab, kaje ka gaisheta" Kuma saiya tafi din, duk wani taku da yake da kananun kafafuwanshi da suke sanye da takalmi Hajiya Rumana naji kamar a cikin zuciyarta yakeyin shi, daya karasa ta kama shi, kamshin turaren da yakeyi ya cika mata hanci saita manta anyi masa takwara da sunan babban makiyinta, ta manta daga jikin Maryama ya fito, ta rike jikanta, yaron danta mafi soyuwa a ranta, tana jin kofofin da batasan dasu ba suna budewa da tarin soyayyarshi, ta manta dasu Maryama suna zaune a wajen nan, ta manta da komai sai yaron da take yiwa magana da yaren Kanuri a hankali. Ganin sun kusan shafe mintina sha biyar a zaune, yasa Maryama cewa "Bari mu gaishe da Umma" Bata ko kallesu ba, saida suka mike, Awwab ya nemi ya zame daga jikinta yana shirin saka kuka tukunna ta lura dasu "Tafiya zakuyi?" Ta fadi da saurinta, dan bata gaji da ganin Awwab ba, to duka ma yaushe ta rike shi a hannunta? Dan Haris fa, shine take rikewa a karo na farko yau bayan shekaru biyu da wani abu, to wai me ma ya hanata zuwa New York din ta ganshi? Duk da Maryama ce ta haifeshi ai dan Haris ne, kuma Haris da duk wani abu nashi nata ne "Eh Mami, daman munzo gaishe dake ne, kuma in kawo Awwab" Hajiya Rumana ta jinjina kanta "Gashi naga kuka zaiyi in kuka tafi, yaushe za'a kara kawo shi?" Maryama ta dan kalli Khairi da tayi mata alamar "Ba ruwana" Da nata idanuwan "Ko yaushe ma kikace Mami" Hajiya Rumana ta jinjina kai "Zan dinga aikowa ana daukar mun shi" Har bakin kofa ta taka musu batare data sani ba, saboda Awwab din, dukansu kamar su tunstire da dariya yanda takeyi kamar ta kwace shi daga hannun Khairi, saida ta shafa kanshi, ta rike hannunshi, Khairi da taji ta fara gajiya da tsayuwar dan Maryama harta fice abinta sai kawai tayi dabarar zakuda Awwab din tana fige hannunshi daga rikon da Hajiya Rumana tayi masa tana ficewa itama "Mata sai gulmar tsiya, ashe zaki so abinda Maryama ta haifa, karyar kiyayya kikeyi ai, zanga inda za'a dinga daukar shi ana kawo miki" Cewar Khairi cikin zuciyarta tana makawa Hajiya Rumana hararar da ba gani zatayi ba, ba karamar dariya ta bawa Maryama ba da take mata zancen "Inta aiko a dauke shi ai dole a bata shi" Nata kason hararar ta samu "Babu inda zaije a goga masa bakin hali" Maryama ta kada kai kawai tana fadin "Kayya Adda" Tana jin wani abu mai nauyin gaske na danne mata zuciya, to bakin hali na nawa kuma? Idan har Awwab zai goga a wajen Hajiya Rumana, to tabbas ya fara bin Haris ne, ta kalli yaron, kallo na sosai, sai taji wani abu mai kama da tsoro ya tsirga mata. "Allaah ka karemun Awwab, Allaah Ka karemun yarana" Take furtawa cikin zuciyarta tana dafe cikinta da hannunta guda daya "Allaah Karka kamasu da laifukan da mu iyayensu zamu aikata, Allaah Karka duba ayyukanmu, Allaah cikin tarin Rahmarka Ka karemun yarana. Allaah Ka shirya mahaifinsu..." Saboda ta sani, babu wani abu da zai kwaceta a wannan gabar, bata da wata dabara, bata da inda zata juya sai wajen wanda Ya hada kaddararta da Haris waje daya...! 38 "Yanzun ya zakiyi?" Shine tambayar da Khairi tayi mata, kuma tambaya ce da ta yiwa kanta sau babu adadi, amman wasu tambayoyin anayin sune ba don suna da amsa ba, a wajen Maryama wannan na daya daga cikin irin tambayoyin nan. Gashi dai kalmomi uku ne, amman kuma tambaya ce da inta zauna sai taji tana samar da wasu tambayoyin a karkashinta Ya zatayi da Haris? Ya zatayi da abinda ta gani? Ya zatayi da abinda ta sani? Ya zatayi... A cikin duka tambayoyin, amsar da take da ita, amsa ce ta tambayar da babu wanda yayi mata, ba zata kara bin Haris wata kasa ba, kome zai faru ba zata kara binshi ko ina ba, wannan kadaicin, ba zata kara fuskantarshi ba, amman inta zauna a Kaduna, dole zata fuskanci Haris, shima kuma wani abune da bata shirya masa ba. Satinta uku kenan da dawowa, a kwanaki goma sha na satikan nan suna waya da Haris da ba zata iya kirga sau nawa ba a rana, har tunani takeyi yaushe yake samun lokacin yin wani abu a tsanake a yanda yake jera mata kira haka, tarin da yakeyi na damunta. "Kaci abinci? Yaushe rabonka da abinci?" Saboda wiwi ce, tasan ita yake ta bankadawa cikinshi, daga nan Kaduna kuwa bata da abinda zata fada masa ya rage ma ballantana kuma ya daina, amman in zaici abinci, ko yane zai taimaka masa wajen rage tasirin hadarin da yake kara jefa kanshi a ciki kullum. "Ba zaka daina shan wiwi din nan ba ko?" Tayi masa tambayar kwanaki biyu da suka wuce, yayi shiru, kuma a maimakon ya amsa sai yace "Na siya mana gida, na cewa Baba 3 bedroom yace yayi mana kadan, saboda mun fara haihuwan namiji, zamu iya haifar mace, dole lokaci zaizo mu raba musu daki...daya daga cikin gidajen shine ya siyarmun, an gama gyarawa da komai, yanzun za'a zuba kayane a ciki" Ta numfasa "Sai a kwasomun kayana na Kano" Yayi dariya "Wannan kayan ai sun tsufa yanzun Maryamm, za'a sake komai ne kawai, zamu kyautar dasu kawai. Zan tura miki hotuna saiki duba abinda baiyi miki ba a canza, ina so a gama komai a satin nan" Ita kam bata hango abinda kayanta sukayi ba, amman babu amfanin musu da Haris, kome zata fada ba zai canza masa ra'ayi ba, daya tura mata hotunan, komai ya burgeta, suka dai dinga dariya ita da Khairi, saboda kayan bakake ne "Wai yanzun sai kawai mutum yasa bakaken kujeru, sai kace gidan mayu" Inji Khairi, Maryama tayi dariya, in dai Haris ne to ba zaiki har fentin gidan ayi shi baki ba, ita dai ta zabi ruwan tokane mai duhu, sai yace mata ai falo biyu ne, saboda haka za'a saka ruwan tokan da take so, zaku ma a saka wancen bakaken dan sunyi masa kyau. Wani abinma bata san me yasa ya turo mata ba inya riga da ya yanke hukunci, ko dadin suyita musu yakeji bata sani ba. Yau dai da yamma ne yace mata "Angama komai, zan tura miki kudi ko zaki kara siyan wani abin, kizo ki koma gidanmu" Da yayi wannan maganar sai taji wani abu ya fada mata a ciki kamar dutse, yanayinta ya canza gabaki daya, hirar tasu ma batayi wani tsayi ba, ta zauna a daki kawai batare data san tunanin da takeyi ba. Awwab tun wajen karfe tara na safe Hajiya Rumana ta aiko direba ya dauke shi, haka takeyi tun washegarin zuwansu gidanta, kullum sai anzo an dauke shi, sai yamma likis za'a dawo dashi da tarin tarkacen da take ta tarawa, tasan dai kayan wasan nan har kannenshi sai sun samu a irin yanda Hajiya Rumana take siya masa su, shi Awwab din da wasa bai dame shi ba, wani jirgin kasane tun a New York, ta dauko masa kayanshi, kuma ko yanzun in dai zaiga jirgin babu wani abu na wasa da yake burgeshi. A wannan yanayin Khairi ta sameta "To meye matsalar?" A hankali tace "Nima ban sani ba..." Suka danyi shiru, kafin Khairi tace "Bari muyi maganar gaskiya Maryama, abinda kika gani, wani abune da har abada ba zai taba gogewa daga tunaninki ba, options din da kike dasu basu da yawa, bake kika zabi Haris ba, amman kuma cigaba da zama dashi a yanzun, wannan zabinki ne, zabin da babu wanda zai tayaki yinshi, zaki iya zama dashi bayan abinda kika gani? Zaki iya zama dashi bayan abinda kika sani?" Taji hawaye sun ciko mata "Inajin kamar ba zan iya ba, idan na tuna zuciyata zafi takeyi, idan kuma nayi tunanin rabuwa dashi ma zuciyar tawa zafi takeyi, kuma wani abu na fadamun zaifi mun sauki idan zuciyar namun zafi tare dashi akan ace bana tare dashi...to ya zanyi?" Shirun suka sakeyi "Ko kishiya bana so Adda, duk murnar da nakeyi ta bikinki dana tuna kina da kishiya sai inji murnata ta ragu, wannan fa abinda Allaah Ya halatta ne, yana mun wahalar karba...ya zanyi da na waje? Ba guda daya ba Adda...ko matan da suke auren mazinata zan samu in tambayesu yanda ake suke zaune tare dasu zuciyarsu bata buga ba?" Maryama ta karasa maganar muryarta na karyewa, hawayen da take ta rikewa suna zubowa "Hakuri, hakuri sukeyi Maryama, hakurin da suka zabarwa kansu, wasu su hada hakurin da addu'a har Allaah Yasa su dace" Ta daga ido ta kalli Khairi "Anya wannan hakurin baifi na mutuwa wahala ba?" Tunda hakuri a yayin rashi abune daya zama dole, har mamakin dalilin da zaisa a dinga tambayar mutanen da akayiwa rashin ya hakuri takeyi, ko a dinga jaddada musu suyi hakuri, kamar dai akwai wani abin da zasuyi bayan hakuri. Wannan hakurin da zatayi, hakurine da take da zabi a cikinshi "Kina son mijinki Maryama, kina sonshi" Kallon Khairin dai takeyi, tana kuma maimaita abinda ta fada cikin kanta, kamar wadda take laluben inda son yake "Wannan shine son daman?" Ta tambaya tana kallon tafukan hannayenta yanzun, kamar wadda zata ganshi a rubuce a jiki, ita dai tasan an aura mata Haris, kuma ta jima da karbarshi a matsayin mijinta, amman in ba ranar da zata taho ba, bai taba cewa yana sonta ba, itama kuma bata taba tunanin ta furta masa ba, duk yanda take jin kalmar "I love you" Tana tashi a kasar New York kamar gaisuwa, ita tunanin amfani da ita tsakaninta da Haris ma bata taba gifta mata ba, ko ranar daya furta mata din kuwa, zuciyarta ta dinga bugawa tana sake maimaita mata kalaman Khairi "Maryama kina son mijinki, kuma alamunki sun nuna ko kusa bakya tunanin rabuwa dashi, saboda haka dogon bacci ba naki bane ba, dole zaki kara rike addu'a..." Ai ta jima da sanin dogon bacci ba nata bane, tunda ta kalli Awwab tayi tunanin wayar gari ta riski yana aikata kwatankwacin abinda Haris yakeyi ta rage bacci, ina zatayi bacci bayan wannan amanar da Allaah Ya bata ba zata iya sauketa batare da taimakonShi ba? "Ki fara komawa, kafin ya dawo zamu san ta inda zamu bullowa lamarin In Shaa Allaah" Wannan shawarar ita Maryama ta dauka, ta fara shirye-shiryenta na komawa gidansu da yake cikin wata unguwa can gaban Millennium City, Dan honu, ita duk zamanta a Kaduna ma bata tabajin sunan unguwar ba sai wannan lokacin. Ana gobe zata koma dinne Hajja ta biyota har dakinsu, tana kwance ne tana danna waya, ganin shigowar Hajjan yasa ta tashi zaune, saita zauna gefen gadon "Maryama" Daga yanayin yanda Hajja ta kirata sai taji wani rauni ya fara shigarta "Nasan kina da damuwa, tun kafin ki dawo kasar nan, nakeji a jikina kina da damuwa, kina shigowa kuma na ga wannan damuwar da dukkan wani motsi naki, kowanne aure baya rasa matsala ko da guda daya ce kuwa, sannan a cikin kowanne aure akwai sirri, kuma naji dadin ganin yanda kika zabi ki rike sirrin naki auren..." Hajja ta numfasa "Musulunci yayi mana gata mai yawa, babu wani abu dangane da rayuwa da bai koyar damu yanda zamu gudanar dashi ba, cikin tsarukan da zamuji dadin duniyarmu da lahirarmu, shi kanshi auren ba'a barmu haka ba, sai da aka koya mana matakai na zama a cikinshi" Ta kalli Maryama da ta tattara hankalinta tana saurarenta "Anason idan sabani ya gifta tsakanin ma'aurata to suyi kokarin ganin sun sasanta kansu batare da wani ya shiga ciki ba, amman Maryama akwai sabanin da sakko iyaye a ciki shine maslaha, kamar yanda musulunci ya samar da rabuwa a matsayin maslaha. A zamanku da Haris akwai abinda ya kamata ace mu iyayenki mun sani?" Maryama taji kirjinta na wani irin rugugi, sai kyafta ido takeyi tana kokarin maida hawaye, cikin rawar murya tace "Ba...ba...babu komai Hajja, 'yar matsala ce kuma In Shaa Allaah ma komai ya wuce" Hajjan ta zuba mata ido na wasu dakika, kafin ta numfasa tana fadin "Allaah Yasa hakan, Allaah Ya kara dai-daita tsakaninku Ya kade muku fitina, karkiyi wasa da addu'a kinji ko?" Da kai ta amsa saboda tanata danne hawayenta. Aikuwa Hajjan na fita ta koma ta kwanta tabarsu sunata zuba, su suka zame mata abokan hira har bacci ya dauketa. Daman sunyi magana da Haris dan tana so a samar mata mai aiki da zata dinga kwana, Hajja ce ta bada shawarar a duba a cikin dangin Alhaji Sa'id da suke kauye "Nifa wani lokacin gara a dauko mun bare, yanda in wani abin yayi mun zan saita masa hanya, akan ace 'dan uwa ne, inka kore shi dangi su nemi wutar jefaka" Adda Zahra ta fadi lokacin da ake maganar, ta bawa Hajja dariya kuwa "Ku duk masu aikinku ba kwana sukeyi ba, zuwa sukeyi su kama muku abinda zasu iya su tafi, ita kuwa wannan tare zasu kwana su tashi, ina ganin komin lalacewar da bama fata, gara ace 'yar uwarta ce take zaune da ita, ansan daga inda ta fito, ta kuma san wa take zaune da ita, sannan fargabar dawa zata dinga barin yaranta in bukatar hakan ta taso ma zai ragu" Dan Hajjan a tsorace take da lamarin masu aiki, tasan maita batazo a musulunci ba, sai dai kambun baka, sai dai akwai tsoratarwa, nan makotan su Hajiya Sahura kawarta akace ta dauko mai aiki mayya, ta cinye mata yara har uku, ta kama karamar ta hudun ne asirinta ya tonu, kuma ance tana tsallaka yarinyar sai gata ta mike. Sai ta kara tsorata da batun masu aikin nan. In dai ba'a samu a 'yan uwan Alhaji Sa'id din ba, to ba zata bari Maryama ta dauki kowacce yarinya suna kwana gida daya ba, bayan ba'a san irin abinda zatazo dashi ba. Kuma da yake yawa ne da dangin Alhaji Sa'id din, gashi kowa so yakeyi ace nashi sun rabesu, ba'a sha wahala ba aka samo Fa'iza. Duka shekarunta sha biyu, wai da aure ma zasuyi mata, sai mijin da akayi baikon dashi yayi jinya ya rasu, to jin Kaduna za'a taho da ita yasa babu wani dogon tunani suka tattara mata kayanta. Tunda Maryama ta ganta taji yarinyar ta shiga ranta, dan batayi mata kama da mai rawar kai ba, haka kowa yakeyi mata fatan ace zaman ya dore, kuma Fa'izar tayi musu bazatan zamarwa Maryama alkhairi. Washegari da zugar 'yan uwanta suka rakata, da ta saka rikici ma sai dai Alhaji Sa'id ya kaita "Abba bafa ka taba zuwa gidana na Kano ba, ai yanzun kai ya kamata ace ka kaini" Ya dinga dariya "Zanzo Mairama, idan nazo kuma har girki zakiyi mun in zauna inci abincin gidanki" Saida tayi masa tsaye tasa shi yayi alkawarin zuwa tukunna suka tafi, yanda su Adda Zahra da suka fara zuwa gidan suka kai mata kayan kitchen sukaita zancen tsaruwar gidan, sai taga yafi haka ma, mazan gidansu ma sunje, tunda Alhaji Sa'id ne da kanshi yace suje suyi mata addu'a a gidan. Komai ya burgeta, basu tafi ba sai yamma, aka barta daga ita sai Fa'iza da kuma Awwab da dan kwana biyun da yake ganin Fa'iza acan gidan Hajja ya saba da ita. Tana da duk wani na'u'in kayan miya da zata bukata a cikin fridge din kitchen dinta, zata kwana biyu tasan bata bukaci wani abu ba. "Za'a kawo miki mota Maryama" Tunda bata jima da binshi New York ba yace mata an siyar da motocinsu, kudin na account dinshi, sai sun koma saiya siya musu wasu, in kuma tanaso ya saka mata nata kudin a account dinta ne kuma sai yayi hakan, to da ya saka mata ma dai tasan babu abinda zatayi dasu, yanzun kuma gashi ta dawo, ko da tasan motar haka zata dinga daukar kura taji dadi, kamar wata babbar alama ce na sake samun waje ta mike kafa a Kaduna. Washegari kuwa tunda sukayi sallar asuba, duk bacci suka koma harda Fa'iza, dan gidan ma yana nan a gyarenshi sai dan abinda ba za'a rasa ba. Ringing din wayar Maryama ne ya katse mata baccin da yakeyi mata dadi, ta ga bakuwar lambace, sai dai abinda yasa ma ta daga shine sanin babu wani da yake da lambar banda 'yan uwanta, duka yaushe ta siyi layin? Mamaki tayi matuka jin muryar namiji, saida ya fada mata Hajiya Rumana ce ta bashi lambar zai dauki Awwab ne, yana so tayi masa kwatancen gidan. Ta girgiza kanta kawai, ta kuwa yi masa, har kofar gidan yazo, ta saka hijabinta ta fita tana bude gate din din ta mika masa Awwab da saida yayi mata rigima sosai na tashin shi da tayi, fuskar nan a hade ma suka fitan, ya gane direban shine ma ya ruga wajenshi yana dariya. Data koma ta kwanta, bacci tayi niyyar komawa, sai kuma Haris ya kira, kamar karta daga "Bacci kikeyi?" Ya tambaya jin muryarta can kasa "Eh, Mami ce ma ta aiko aka daukar mata Awwab, kiran direban nema ya tasheni" Da mamaki da wani abu daban a muryar Haris yace "Direba kuma? Direban ne ya kiraki?" Dan shi Hajiya Rumana ta kira tace ya bata lambar Maryama zatayi mata kwatancen gidan za'a dauko Awwab, to akan me zata dauki lambar Maryaman taba wani gardi "Eh ya kirane nayi masa kwatance" Tayi maganar kanta tsaye "Shi direban ne ya kira, kika dauki wayarshi da wannan muryar taki da take cike da bacci Maryamm?" Yanda yayi maganar ne ta gane abin nashi ne ya motsa masa "To akan me da kikaji namiji ne ba zaki kashe ba? Ita Mami me yasa zaya ba wani kato lambarki, ni haka tace mun zata kiraki...ina zuwa bari in kirata" Sanin zai aikata yasa ta saurin ce masa "Ka kirata kace mata me? Dan Allaah, bafa wani magana mukayi ba banda kwatancen gidan da nayi masa, kuma yanzun tunda yaga wajen ai kaga babu wata magana da zata sake hadamu" Yayi shiru "Ganjaa" Shirun dai ya sakeyi mata "Zanyi blocking dinshi" Ta fadi "Better" Murmushi yaso kwace mata "Karka kira Mami dan Allaah, kar kuma kayi mata maganar ko da kiranka tayi" Ya amsa da "Hmmm" Kuma kafin ta kara magana yace "Kiyi baccinki" Ya kashe wayar, ta girgiza kanta kawai, fushi yayi ta sani, wannan rigimar kuma ba zata iya mata ba a yanzun. Baccin ma ya riga ya bar idonta, sai kawai ta tashi ta shiga wanka. Ta fita falon ta ga Fa'iza ma ta tashi, tana goge tv stand, ta gaishe da Maryaman cikin ladabi da kuma sanyin muryarta na halitta, ko kitchen ma tare suka shiga, tana so Fa'iza ta dinga ganin yanda takeyin abubuwa, sannan kuma zata samu Islamiyya ma ta sakata, bataji dadin yanda taga tayi sallar isha'i ba jiya, ta kudirta a ranta, da kanta zata fara koya mata yanda zatayi sallah kafin ma ta shiga Islamiyyar. An riga an saba duk sanda za'a dauki Awwab, to duk inda karfe biyar tayi zuwa shida na yamma an dawo dashi, amman yau har an idar da sallar Magriba shiru, abin yana ran Maryama, danma batajin dadin jikinta, wannan cikin babu wani laulayi da takeyi banda cin abinci kamar gara, sai abinda ba'a rasa ba, kamar dai yau da ba wani aiki tayi ba amman jikinta ko ina ciwo yakeyi sai kace wadda tayi surfe. Da tayi isha'i kuwa taci abinci saita shige dakinta tabar Fa'iza da take kallo a falo. Data kwanta sai zuciyarta ta dingayi mata zillo da tunanin Awwab, haka sukayi waya da Haris da saida ya karanci rashin walwalarta, ya dinga tambayarta ko wani abu ya faru tana ce masa "Babu komai fa" Daya matsa mata ne tace masa "Ciki fa gareni Ganjaa, ba kullum yanayin yakeyi mun dadi ba, yau irin ranakun nan ne" Kuma wannan yasa ya daina tambayarta, saima yayi mata sallama yace ta kwanta ta huta, tayi masa kissing din Awwab, ta amsa da "To" Haka ta kwanta tanajin kewar Awwab din da take turewa gefe idan ya nanike mata wani lokacin, amman yau gadon ma yayi mata fadi sosai. Abin kamar wasa, kwana biyu Awwab shiru, kamar tayiwa Haris maganar saita kasa, saida kanshi da yace ta bashi Awwab din a waya tace masa "Bafa a dawo dashi ba, yana gidan Mami" Bai jira abinda zatace ba ya kashe wayar, ya dauki kusan mintina ashirin kafin ya sake kiranta "Kinga rigimar Mami ko? Ashe wai Maiduguri suka tafi da Awwab din, sai sati mai zuwa zasu dawo" Maryama taji kamar ya kifa mata mari, Maiduguri? Da Awwab din? Kuma harna sati? Ita bawai tafiyar bane matsalarta, kenan bata da darajar da Hajiya Rumanan zata gaya mata? Ba dan ta isa ta hana ba, amman dai ai sai a gaya mata "Uhm, to madalla" Ta iya cewa wani abu yayi mata tsaye a makoshi "Bama a daukar masa kayanshi ba" Haris ya danyi dariya "Haba, kaya dai, ai nasan zata siya masa duk abinda yake bukata, wai taje kaishi ya gaisa da 'yan Maiduguri, Allaah Yasa kar yayi mata rigima sosai" Da alama shi kanshi Haris din baiji cewar ba'a kyauta mata ba kenan? "Nifa bawai banyi murna da zaki zauna a Kaduna ba, kawai ina jiye miki waccen bakar matar da fitinarta ne, kar tazo ta dinga tsiro da wasu abubuwan, Allaah Kanon saita fiye mana" Khairi tace mata kamar mai duba, ita a lokacin bata hango wani abu ba sam "Karta dinga zuwa miki gida kamar wadda ta samu aikin sintiri" Abin dariya ya bata, ko kadan bata hango Hajiya Rumana zata dinga zarya a gidanta babu wani kwakkwaran dalili ba, tunda ta kula in ba dole ba, kamar ko ganinta Hajiya Rumanan batason yi. Ashe ba sai tazo bane zata samu hanyoyin da zata dinga cusguna mata, ita kadai tasan wahalar da tasha lokacin da take koyon saka Awwab din kan schedule, musamman ma na bacci, da suka dawo din nan ne baccin ya dan hargitse masa, amman a hankali a satin ya fara dai-daita, tana ta jin dadi, yanzun kuwa in suka dawo ta tabbata sai abinda ta gani "Akwai aikin da zan karasa, in danyi karatu kuma, muyi magana anjima?" Ta daga kai tana amsa shi da "Allaah Ya kaimu" Sauke wayar tayi a hankali, ba zatayi karya ba, taji zafin abinda Hajiya Rumana tayi mata, in ta fadawa Khairi ko da tayi mita, zata bata hakuri ne, ita kuma bataso a bata hakuri, a wannan auren nata da Haris, hakuri daya takejin zata iya,ko kadan bata hango tayi hakurin zama da Haris, sannan ta hada dana danginshi ba Ai ko kaddara ce sai dai ta zabar mata daya... 39 Shirin bikin Khairi sukeyi, ko tace akeyi saboda yanda Haris ya takureta a gida, ya hanata fita yanda ya kamata. Su Adda Zahra ne tsaye akan komai kamar yanda suka saba, amman Maryama zataso ace da ita ake yawon zuwa kasuwa siyayya, ko ace tana yawan zuwa gida yanda take so "Me zakije kiyi ne wai? Kece zakije musu kasuwar? Bana son fitar nan Maryamm, kin sani kuma, bana so ko kadan" Haka zaice, inta matsa masa suyi fada, koya kashe wayarshi gabaki daya. Ko kai Fa'iza Islamiyya ma haka yace a bari sai ya dawo idan babu wanda Maryaman zata samu ya kaita, ranta ba karamin baci yayi ba, sai dai babu yanda zatayi da Haris tasani tunda babu yanda zatayi dashi, cikin mazan gidansu ta samu akazo aka kai Fa'izar, da yake makarantar ma anan kusa dasu take, karfe uku na rana suke shiga, su tashi karfe biyar da rabi. Ya dameta akan me zasu ba Khairi gudummuwa, ita dai tasan abinda take so ta bata, Khairi na son tukwane, ko gidanta tazo ta dinga sauko kwalayen tukwanen da bata bude ba kenan tana budewa tana kallonsu, a waya ma haka zata dinga nunawa Maryaman "Ki kalli tukunyar nan, in ina da ita ai a kitchen zan wuni, ko ba zan dafa komai ba, in jerasu ina kallo ina jin dadi" Akwai Chef Maryam da take following a manhajar Instagram, dan zatace ma ita kadai takebi tunda bata jima da bude Instagram din ba, tana saka recipe na girke-girke kala-kala kuma Maryaman na karuwa da wasu abubuwan, a wajenta take ganin tallar tukwanen kamfanin Caraway, tun tana New York taso ta siya tunda Chef Maryam din a America take sai kuma tahowar da tayi bata natsuwa bace ba, amman ta dauki lambarta (+13177018261) sunyi magana, tana aikawa kowacce kasa kake, sannan farashin shipping din baiyi mata tsada ba, farkon zuwanta New York, kome suka siya saita tambayi Haris, nawa kenan a kudin Nigeria, inya fada mata saita dinga ganin yayi tsada matuka. "Ki daina lissafi da kudin Nigeria, saboda ba dasu ake biyana albashin duk wani aiki da zanyi ba, da dollar ne, shine zaki dinga ganin saukin komai" Haris ta turawa account din Chef Maryam ya saka mata kudin "Sai kuma me?" Tace masa babu komai, tana da kudinta, zata bayar ayo mata canji tayi duk wata hidima a ciki "Ni me zan bata?" Dariya ta dingayi masa "Kaima kayi tunani da kanka..." Saiya kyaleta, daya tashi kudine ya turawa Khairin wai ta siyi abinda take so, kudine da yawansu a har Hajja saida tasa aka kirawo shi tana masa fadan kudin yayi yawa "Dan Allaah Hajja ki daina cewa haka...ko bana auren Maryamm, Adda Khairi ai kanwata ce da zanyi hidima a bikinta" Dole Hajjan tayi masa addu'a sosai tare da godiya. Itama Maryaman ta karayi masa godiya, dan tayi mamakin yawan kudin. Saura kwana takwas bikin Khairi, Haris ya iso Nigeria, da yake Kano ya sauka, ya riga ya fadawa Alhaji Mustafa, aka aika da direba daya dauko shi zuwa Kaduna. Tun safiyar Maryama take tunanin abinda zata dafa, in da ace Haris kamar sauran mutane ne, ta tabbatar tana nan tana ta girke-girke, abubuwan da yafi so, to abincin ma ba damunshi yayi ba ballantana a samu abinda yafi so a ciki. Duk yanda Khairi ta matsa mata akan tayi kunshi kiyawa tayi "Wallahi ba zanyi kunshi ba, kinsan ba fita zaiyi kafin biki ba" Rantsuwar da tayi ne yasa Khairin ta kyaleta, ta dai dibo mata wasu abubuwa cikin magungunan gyaran da Adda Zahra take bata, har gida tazo ta kawo mata, ta dinga kallon ledar kayan, data bude ma ta duba sticker din jiki ta girgiza kai, wani abin saika rasa inda Adda Zahra take samo shi tana nan garin Kaduna, dan taga ansa Zee Herbal a jiki, kuma taga matar a garin Katsina take, gumbar da aka rubuta chocolate gumba ce ta dinga shigar mata ido, data gutsira ta saka a baki, sai gata ta sake duba lambar 08109343492. Abin yayi mata dadi sosai, ga kwakwa. A ranta ta raya wannan ai ba maganin mata bane ba, kayan kwadayine kawai aka hada, bata iya hakura ba saida taci kusan rabin robar, gudun karya saka mata ciwon ciki yasa ta tattara taje ta adana. Ta dafa ma Haris shayi, ta dai saka Fa'iza ta fere mata dankali tabarshi a cikin ruwa, in dai Haris ne sai yayi wanka inya sauka ta sani, to inya shiga wankan saita soya masa kafin ya fito. Su dai ta dafa musu shinkafa da miyar kifi da taji tana marmari. Sai salad, sai da Fa'iza taci tukunna ta wuce Islamiyya, gidan yayiwa Maryama shiru fiye da kowanne lokaci, batasan ko dan kirjinta da yake ta bugawa da dawowar Haris bane, tunda Awwab na wajen Hajiya Rumana, yanzun in ta dauke shi sai yayi kwana biyu, ido ta dauka ta saka musu, so take ta gama hidimar bikin nan, ta kuma sauka lafiya, makarantar Islamiyya take so a fara saka Awwab din, idan ya samu ko shekara dayane sai a hada masa da boko, dan wannan Islamiyyar ta kusa dasu taga suna da kokari matuka. Tana nan kwance kan kujera, cikin kwalliya mai sauki, lace ne irin marar nauyin nan, ja da aka dan yiwa adon golden, dinkin doguwar riga bubu, hula ce ja ta saka dan dankwalin zai dameta, ta dan goga jambaki, sai ta murza hoda, tayi kyau dan kalar lace din ta kara mata haske, danma cikin nan taga pimples ya fito mata, fasawa takeyi, sun bar mata dark spots waje-waje kuwa. Tana nan kwancen taji ana horn, duka ba'a dade da samo musu maigadi ba, ta dai ganshi sarkin shiririta ne, can yake tafiya wata majalissa da suka samar ta masu gadin unguwar su zauna sunata labari, haka ta mike ta leka ta window din falon, sai taga anci sa'a yana nan, ya bude gate din. Luguden da kirjinta yakeyi ta karu, taje ta bude kofar da take da mukulli a jiki, ta dawo ta zauna kan kujera, har abinda ke cikinta ma motsi yakeyi kamar yana tayata taradaddin da ta shiga. Kwankwasawa Haris yayi sau biyu, kafin ta numfasa tayi magana ya murda kofar dakin ya shigo da sallama a bakinshi, sallamar da saida tayi da gaske sannan ya saba da yinta in zai shigo gida, yanzun kuwa har bedroom wani lokacin sai taji yayi in zai shiga ko da kuwa babu kowa a ciki, ta daga ido, ta sauke cikin nashi, zuciyarta ta buga. Rigace mai dogon hannu a jikinshi, ruwan toka mai duhu, in bata manta ba ita ta daukar masa rigar, sai bakin wando, bata kalli kafarshi ba, tasan bakin takalmi ne, sneakers. Taji sautin numfashin daya sauke kamar matafiyin daya wuni gararamba sai yaci karo da ruwan sanyi, a hankali ya tako har inda take, ya kama hannayenta yana mikar da ita tsaye, bai damu da cikinta daya fito ba kawai ya rungumeta a jikinshi, Maryama taji kanta ya hautsina, tsikar jikinta ta tashi, data lumshe ido ta shaki kamshin turarenshi mai sanyi kuwa sai hoton nan ya dawo mata "Sau nawa nace miki nayi kewarki?" Ya fada yana dagota daga jikinshi, ya sumbaci kumatunta, idanuwanta taji sun cika da hawaye, zuciyarta ta takure waje daya tana mata zafi, tayi addu'a, tayi kuka, ta kara addu'a ta nemi Allaah Ya sassauta mata, ko da hoton nan ba zai goge ba, to tasirinshi ya rage, kuma a hankali tana samun saukin zuciya, sai dai ganin Haris, hadata da yayi da jikinshi yana neman warware mata komai "Nayi kewarki, da yawa" Ya kara fadi yana sake rungumeta, ta dan motsa cikin kokarin danne zuciyarta dan karta hankade shi, kar suyi fada daga dawowarshi. A hankali ta zame jikinta "Sannu da zuwa" Ta furta muryarta na dan rawa, bai amsa ba, sai idanuwanta daya kalla, ta danyi murmushin karfin hali, yatsanshi yasa yana taba goshinta, ba waje daya ba, waje waje "Meye wannan yayi miki spots" A hankali ta amsa da "Pimples" Ya sake saka yatsan nashi yana taba kumatunta "Sunyi miki kyau...kinyi kyau...zo nan" Ya karasa maganar yana shirin sake rungumeta, ta matsa baya tana dan ware masa ido "Kai ko" Yayi dariya "Nayi kewarki da yawa ne" Dan matsawa ta karayi "Ina kayan?" Ta tambaya "Suna mota fa...ina zan tsaya dauko wasu kaya banganki ba" Tunda direban ya riga ya bashi mukullin motar ya tafi, sai kawai yabar kayan a ciki, harda gudunshi ya hada wajen shigowa cikin gidan, ganinta da yayi kawai zuciyarshi ta samu wata natsuwa ta daban. Da ya riketa a jikinshi kuwa sai yakejin komai daya hargitse masa yana dai-daita. Gajiyar ma ya nemeta ya rasa, yanajin yunwa dai "Yunwa nakeji fa...amman ina so inyi wanka" A hankali Maryama tace masa "Akwai shinkafa da miyar kifi" Ya dan hade rai "Shinkafa? Ba wani abin?" Kallonshi takeyi "Saika hada da shayi" Yayi shiru na wasu dakika "Shayin dai da wani abu, kinsan ba son kifi nakeyi ba" Yanda yayi maganar ne yasa ta fadin "Sai in zuba maka shinkafar da mai da yaji ai, ka hada da shayin" Ya kalleta da wani firgici cikin idanuwanshi, kwakwalwarshi na harhada masa shinkafa da mai da yajin data kira, yunwa yakeji da gaske, yunwar kwana biyu, tun washegarin tahowar shi, abinda ya saka a cikin nashi ba wani mai yawa bane ba, yasan shayi kadai ba zai ishe shi ba "To kiyi mun order din wani abu mana, ko cake din nan ne wajen Kerau din nan, tunda kinga muna Kadunan" Nauyin da kirjinta yayi ne yake ta sauka a hankali, shi dai ya kasa manta wannan cake din, ita ta manta dashi ma, amman yanzun kam dole zata lalubo lambarta 09057866631. "Zan mata magana inji idan akwai, kaje kayi wankan" Ya daga mata kai, hankalinshi yana dan kwanciya, amman shinkafa da mai da yaji, shi abinma ya kasa haduwa a cikin kanshi. Harya wuce saiya dan dawo "Ina ne dakinmu?" Da hannu ta nuna masa inda ta ware a matsayin nashi, nata daban, dayan bedroom din Fa'iza ce take kwana a ciki, duk da sai tayi bacci a falo sau nawa saboda kallo. Kitchen ta wuce, tana jin Haris ya sake fitowa yaje ya bude mota ya dauko kayanshi. Kafin ya gama wankan ta soya masa dankalin, haka kawai dai ta soya masa kwai da tayi scrambling, yasha yankakken tattasai da albasa, tasan ba lallai ya burgeshi ba duk yanda ita yayi mata kyau a ido, fata takeyi dai yaci. * Tunda ta tabbatar babu wani abu da zai bukata ta tafi dakinta, amman saiya kwashi komai ya bita can din, batayi masa magana ba, ta cigaba da danna wayarta, dan kuwa ko ba tayi chatting ba, tana samun abubuwan da suke debe mata kewa a Instagram dinta, sannan taci karo da wani shafi, Hausaroom, inda mutane suke tura labarin matsalolin rayuwarsu sai ayi musu posting ana bada shawarwari, zatace taji tsoro matuka, ganin yawan matan da suke fama da maza mazinata, amman kuma ta wani fannin sai hakan ya dan sama mata natsuwa, sanin ba ita kadai bace ba, ta karanta, wasu ma bayan zinar mazan harda tarin wulakanci, wasu ga talauci, ga mazan ma ba dadin zama dasu sukeji ba, tarin matsaloli birjik, ta dinga jinjina lamarin aure. Wato kowacce mace dai kaganta da mijinta, abinda take fuskanta in bata bude baki ta fada ba, ba zaka sani ba, kuma abin da ya kara bata mamaki, yanda kowanne case akayi posting da yake da alaka da neman matan da maza sukeyi sai kaga mata da suke magana da sunan bada shawara suna fadin "Yar uwa kina gyara kuwa? Kinsan mazan yanzun sai dai gyara" Haka zaka ga wasu ma na dorawa da "Ai zagewa zakiyi ki dinga yi masa bajinta a yayin mu'amalar aure, ki koyi abubuwan da zai dauke masa hankali daga matan waje, kinsan suma karuwan da abinda suke janye su kenan" Kamar a kowanne comment da zata gani, a yanayin maganganunsu, sun manta cewa haka tace mijinta na bin mata, mijinta na aikata daya daga cikin manyan laifukan da aka fada a musulunci, shisa ma har suke hango cewa matsalar daga itane, laifin daya zabi ya aikata, shine aka juya aka mayar kan matar data kawo kara, aka nuna gazawarta ce ta janyo haka,dan ko jiya da daddare da Maryam taga wani, saida masu comment din nan suka sakata dogon tunani, to ko dai itama itace take da matsalar? Ko da gaske in kana yawaita gyaran yana hana mazan biye-biye? Tunda acan New York ina ma taga wasu kayan mata? Tun wanda Adda Zahra ta batane, wasu ma zubarwa tayi saboda taga sun dade sosai, ko sun lalace, sannan tasan Haris na da yawan bukata, tana iya kokarinta, amman wani lokacin yana kureta ne. Yanzun ma data dago ta kalli Haris din sai da abin ya fado mata a rai, wani sashi na zuciyarta kuma yana fada mata, ai koma me tayi ba uzuri bane da zai saka shi bin wasu matan, a karo na farko da taji gara ace aure ya kara, da kazantar zina gara ace auren yayi, sai yafi mata sauki. Addu'a ta dingayi duk wadda tazo ranta, tana fatan Allaah Ya saukaka mata abinda takeji, Allaah Ya dubata ya shirya mata mijinta. Hira suka danyi sama-sama, saida taji dawowar Fa'iza daga islamiyya ne ma ya fita, ta kuma sake komawa dakin. Da aka kira sallar Magriba ta kalli Haris da yake kwance akan gadonta "Ana kiran sallah fa" Ya dan kalleta "Zan tashi, nagaji ne, da naci abinci kuma sai naji na kara gajiya" Ta jinjina masa kai "Ka dai tashi ka tafi masallaci kar a tayar da sallar, in ka samu kayi, ka koma isha'i shikenan sai ka kwanta gabaki daya" Saida ta fara ganin musun da zaiyi a yanayin fuskarshi kafin yace "Zanyi a gida ai, idan na mike zan hada da Magribar da isha'in" Bayi ta wuce, dan fitsari ma na damunta, ta farayi sannan ta dauro alwala, Haris yana kwance inda ta barshi. Ta shimfida darduma tayi sallar wani abu tsaye a makoshinta, ko azkar dinta bata iyayi ba, ta sake kallonshi, uzurinshi lokacin da suke New York shine babu masallaci a kusa dasu ko guda daya, to ita in ba lokacin sallah ba da sukaje idi dashi, saida tayi tunanin ko babu masallacin nema gabaki daya, kamar zasu wani gari haka suka sha tafiya. "Ganjaa" Ta kira, bai amsa ba, ya dai kalleta "Kasan meye abu na farko da ake fara dubawa idan mutum ya mutu?" Bata jira amsashi ba taci gaba "Sallah...sallar mutum itace abu na farko a cikin ayyukanshi da ake fara dubawa, shisa zakaga a islamiyya ana fada mana cewa idan sallar nan ta gyaru, to akwai kyakkyawan yakinin cewa sauran ayyukan ma sun gyaru..." A kasalance yace mata "Ai inayin sallar nima" Tunda komin gajiyar da zaiyi, ko da baiyi kowacce akan lokaci ba, baya yarda yayi bacci bai rama duka sallolin nashi ba "Kanayi sanda kaga dama, bawai lokacin da akace kayi ba" Ya sauke numfashi "Maryamm...zanyi fa, ba sai kinmun wa'azin nan naki da baya karewa ba, barin tashi" Ta girgiza kai kawai, to taya za'ace mutum zai tsallake tarkon shaidan? Ita sallah ga mace da namiji in dai zasu tsareta akan lokuttanta, to shaidan zai sha wahalar yin galaba akansu. Anan dakin yayi sallah, tanata kallon shi, kuma yanayin kallon ne yasa lokacin da aka kira isha'i sai ya fita, tare da maigadin gidan sukaje masallaci, baiyi wani nisa dasu ba, layi biyu ne sai a karya kwana. Daya dawo yace mata "Naje masallacin, shikenan? Ki daina kallona kamar na aikata miki wani abu" Batayi masa magana ba, ta fita ta zuba abincinta taci, abincin da bai barta ba saida ya bita har kitchen din, tayi masa tayi, kamar yanda ta tsammata kai ya girgiza mata. Data gama cin abinci ta zauna anan, dan Fa'iza tunda ta fito ta gaishe da Haris, saita koma dakinta ta zauna, dakin da take din akwai tv, amman dai basu taba kunnawa ba, sai taje dakin ta hada mata kayan kallon da yake ciki, dan tasan zaman kadaici ga babbama bashi da dadi, balle kuma yarinya mai shekarunta. Bataso ta koma dakinta, amman bayanta ya gaji, bata jure zaman kujerar ko kwanciya akai yanzun da tayi nauyi, in kuma ta zauna akan kafet to tashin saiya zame mata wani babban aiki. Haka babu yanda zatayi ta tashi "Zamuje mu kwanta ne? Nagaji sosai" Cewar Haris, bata amsa shi ba, data nufi daki dai tanajin yanda yake binta a baya, tana kwanciya kuma shima ya cire dogon wandon jikinshi ya bar boxers din, ya kuma cire rigar, sannan ya hau gadon. Yanda tsikar jikin Maryama take tashi har wani amai takeji yana mata barazana, ta rufe idonta lokacin da taji Haris ya rikota a jikinshi, sai gashi ta fashe masa da kuka, ya kuwa rikice yana dagota gabaki daya "Maryamm...menene? Meya faru? Wani abu na miki ciwo ne?" Yana tambayar ne yana tattaba jikinta ko zaiji alamar zazzabi, ba karamin tsoron kukan nata ya bashi ba "Me yasa? Akan me? Me yasa? Ya zanyi hotonka da yarinyar nan ya gogemun?" Yayi tsam, bawai ya manta da ta gansu bane bane ba, tunda duk sanda zai rike wata macen bayan data tafi saiya tuna Maryama tasan wannan sirrin nashi, tasan cewa he's cheating on her, kawai ganin yanda suke waya lafiya kalau duk watannin nan, saiya dauka komai ya wuce mata, ta hakura, ta yafe masa, tunda ma ai zai kara yin taka-tsantsan ne "Maryamm" Ta kalle shi da rinannun idanuwanta "Menene bana maka? Me zan gyara da zaisa kabari? Tun yaushe kakeyi? Wai me yasa ma?" Baisan taya zai amsa mata tambayoyin nan ba, tanayi masa komai dai-dai gwargwado, kuma zaice natsuwar da yake samu a wajenta baya samunta a waje, bambancin shine bata iya dauke masa duk bukatarshi, ji yakeyi tayi masa kadan, wannan rashin kunyar ta sauran matan da yake bi, yanda zai rikesu yayi yanda yake so babu wani tausayi ko soyayya, ita ko da zata barshi bayajin zai iya mata haka. Babu wani abu da zata gyara, tunda daman ba ita tasa ya fara ba "Kiyi hakuri, dan Allaah kiyi hakuri" Yake fadi yana kara riketa jin irin kukan da takeyi, gefen kanta kuwa da duk inda bakinshi zai samu haka ya dinga sumbata yana bata hakuri, kuka tayi, irin kukan nan da mai yinshi yake neman rage damuwa, tayi kuka har bacci ya dauketa, Haris najin ajiyar zuciyarta har kasan tashi zuciyar. Ya sake riketa da kyau, yana sumbatar idanuwanta da suka kumbura har kana ganin jan da sukayi saboda kukan da tasha, bayason haske mai yawa haka in zaiyi bacci, amman bayaso kuma ya cika motsi ya tasheta, dole ya hakura ya rufe nashi idanuwan har bacci ya dauke shi. Karfe uku da rabi ta bude ido, ta dinga mamaki yanda fitsari bai dameta ba yau, tana tashin alarm din wayarta ma na fara bugawa, tayi saurin latse shi, ta yunkura ta mike ta nufi bayi. Har dogayen riguna guda uku da hijabai uku ta ware nayin sallar dare, da kanta take wanke su ta goge, ta feshe su da turare, tana jin dadin zuwa da bukatunta wajen Ubangiji jikinta tsaf-tsaf, tunda fatanta wadannan ibadun Allaah Ya karbesu ya wanke mata zuciyarta da ruhinta, amman yau a maimakon addu'o'in ma kuka ta dingayi a sujjadar ta, data idar ma hawayen ta zauna tayi saida taji ta wasai, ta mayar da raka'atanil fajr, sannan ta cigaba da Istigfar kafin aka kira sallar asuba, saida ta fara tashin Haris, taga ya shiga bandaki tukunna ta tayar da sallar asuba, kawai batayi zaton dayan dakin Haris ya koma yayi tashi sallar acan ba maimakon ya tafi masallaci. Kuma da yake taji ta hakura, har kasan ranta ta karbi wannan kaddarar ta Haris, daya dawo dakin ya nemeta bata hanashi ba, bata da wani karsashi yanda ya kamata, amman bata hanashi ba, kuma kukan da tayi zaton zatayi ma batayi ba. * A ranar yaje gidansu, yana fada mata da Awwab zai dawo, da yake bata saka rai ba, daya dawo shi kadai ko tambayarshi batayi ba, shima baiyi mata maganar ba. Da tayi waya da Hajja ne take fada mata Haris din yaje ya gaishesu, ba zatayi karya ba, taji dadin hakan da yayi har ranta. Zata lallabashi, so takeyi tun saura kwana uku bikin Khairi, ko da ba zai barta ta kwana ba, to tun safe inta tafi sai dare zata dawo. Ta dan farayi masa maganar yayi wata gajeriyar dariya. Sai ta kyaleshi, tunda ya fita yaje gidansu din nan bai sake fita ko ina ba, tare suke wuni dashi a gida, ya dawo da ayyukane masu yawa, aikin da take ta kama masa yana rage yawansu. Anan dakinta ya yada zango, yana shiga dayan ya ajiye abubuwanshi, amman dai a nata din suke wuni. Yanda ya shigo daga sallar asuba daya fita yana tari ya tabbatarwa da Maryama wiwi dinshi yasha, gashi nan ma ya sake kaya, ba wannan kayan ya fita dasu ba, rigar daya fita da ita bata da collar, kuma yana saka turaren da inya giftaka zaka jishi farat dayane in yanaso ya boyewa hancinta shakar hayakin wiwi dinshi, yanda ma yake ta kokarin danne tarin yana kallonta ya gama tona masa asiri. Ta rasa dalilin da yasa Haris ya rantse saiya kashe kanshi, wasu hawayen takaicine takejin suna neman balle mata, data mike daga dardumar batace masa komai ba. Fita tayi daga dakin, ta nufi dayan, wani abu da bai sani ba shine ta riga ta gane duk wani sako da lungu da yake boyonshi, ai yau da gobe bata bar komai ba. Kuma tana daddaga inda take zato din ta ga abinda take nema, wasu ma ya nannadasu a jikin takarda, wanda ya nannada din wajen guda hudu, su ta kwasa, ta dauki lighter guda daya cikin wadanda tagani, ta kuma kwashi wasu daga cikin wiwi din da suke a kananun ziplock ta koma dakinta. Yana nan kwance, har lokacin tari yakeyi kasa-kasa, tana ganin yanayin idanuwanshi daya canza alamar tarin na damunshi, dan wiwi ta kula komin yawan da zaisha sai dai idanuwanshi su rage girma, basa canza launi, sai ace idon 'yan shaye-shaye in sunyi shaye-shayensu yayi jajur, banda na Haris, in baka san yanayi ba zaka dauka ko bacci ne bai wadace shi ba. Kan gadon ta ajiye abinda ta kwaso, banda lighter da kuma karan wiwi din guda daya, yanda ta kyasta lighter dinne yasa Haris ya kalleta da sauri, mamaki ya hanashi mikewa. Kunnawa tayi, ta ajiye lighter din akan gado, sannan takai wiwi din bakinta tana zuqa, hayaqin ya karasa kirjinta yana rarrabuwa cikin kanta hadi da qulle wasu abubuwa da yasa ta fara tari, amman saboda karfin hali saita kara kaiwa bakinta, Haris da bai taba ganin abinda ya bashi tsoro irin wannan ba, ya yunkuro har yana hadawa da rarrafe daga kan gadon da niyyar kwacewa, ta matsa baya "So nake inji abinda kakeji ne da ka kasa bari..." Ta fadi da wiwi din rike a hannunta, yasha ganinta a hannun mata a kasashen da yake zuwa, kai a cikin matan da yake bi ma anan gida Nigeria ba zaice yaga masu sha ba, amman yaga masu shan shisha sosai, kuma abin bai taba saka shi yaji dar ba, wiwin nan a hannun Maryama, wani abune da baya fata Allaah Ya sake nuna masa makamancinshi "Maryamm..." Tayi wata dariya da yaji sautinta ya hargitsa masa ciki "Wai mu hadu mu kashe kanmu tare, tunda na karbi kaddarar aurenka, naji zan zauna da kai da abinda kake aikatawa, kuma baka shirya bari ba, gara kawai mu dingayi tare, randa abin ya isheka sai kayi mun magana mu bari tare, in kuma kayi nasarar kashe mu gabaki daya shikenan duk mun huta" Daya kara takawa saita daga wiwin tana kaiwa bakinta "Dan Allaah..." Cewar Haris muryarshi na rawa "Cikine a jikinki" Ta dan daga masa kafadunta "Ka damu da cikin ne? Cikin da kake shirin mayar da abin cikinshi maraya?" Cikin saurin da baisan yana dashi ba ya karasa ya fisge wiwin, bai damu da zafin daya ratsa masa har tsakiyar kai ba saboda ya murje wutar ne sa yatsunshi biyu, ya rike Maryama da ta kamashi da kokawa tana kokarin karbar wiwi, da ta fisge jikinta saita nufi kan gadon inda ta zube wadancen, ya rufa mata baya, yanda suke kiciniya yana fadin "Kibari, Dan Allaah, kar in buge miki ciki, Maryamm cikine a jikinki" Amman taki saurarawa, dambe takeyi sosai dashi, saida yasa karfi ya kwantar da ita a gadon, kamar wadda batajin nauyin cikinta, ko ta manta dashi haka tayi yunkurin hantsilawa, ya rikota shima yana hawa gadon, sai kawai tabi ta zauna a cikinshi, ta kuma janyo pillow daga kan gadon tana fara maka masa, hawayenta na zubowa, kokarin karewa yakeyi, yaji ta danne masa kai da pillow din "Bari kawai in karasa ka da kaina Ganjaa..." Yasan Maryama bata da hankali, yasan in tana jin rigima batada hankali, amman yau ya kara tabbatar da wannan rashin hankalin nata jin tana neman toshe masa malumfasa da gaske, dakyar ya iya janye pillow din nan ya wullar dashi gefe yana maida numfashi, tayi masa wani irin kallo "Kana tsoron mutuwa daman? Kana tsoronta kake so ka kashe kanka?" Numfashin dai yake mayarwa ga tarin da yakeyi da bashida alaka da danne masa kai da Maryama tayi, jijjiga jikinshi da yayine tunda huhunshi yana da rauni, da kanta ta tashi daga jikinshi, sauka daga gadon tayi niyyar yi, ya riko hannunta "Maryamm" Ta fisge, ya sake rikowa "Wallahi in dai zaka sha wiwi a cikin gidan nan, zamu sha tare ne Ganjaa, idan kuma zaka fita ka dawo inji warinta a jikinka, zan nemi inda ake siyarwa ko ina ne in fara siya nima" Ko bata rantse ba yasan zata aikata "Maryamm" Ta watsa masa harara, hawaye na zubo mata "Ban zabi zama da kai in ganka kana kashe kanka duk rana ba Ganjaa, ba zan kalleka kana kashe kanka ba, ko mu sha tare ko kabari...saika zabar mana wanda kake ganin yafi dacewa damu" Ta karasa tana fisge hannunta, a zatonshi sauka zatayi daga gadon ta fice daga dakin, sai yaga ta matsa gefe ta kwanta, ya dafe kanshi da hannuwanshi biyu, wani abune yake kai kawo a cikin kirjinshi Baisan ta inda zai fara ba, Ya dai san yaune ranar farko, kuma rana ta karshe da zai kara ganin wiwi a hannun Maryama, kome zai faru kuwa! 40 Bata taba sanin mutum zai iya yana zufa yana jin sanyi a lokaci daya ba sai a kwanakin nan, AC din dakin a kure take, haka fankar da tunda sukazo gidan bata ma tababi ta kanta ba ballantana ta kunna, yau ta hada masa "Ina jin zafi Maryamm" Ya fadi daga kasan barguna biyun data jibga masa, ta kai hannu tana goge hawayen daya zubo mata "Dan Allaah mu tafi asibiti Ganjaa...kabari muje asibiti ko in kira wani yazo ya taimaka mana" Idanuwanshi ma basa buduwa da kyau, a haka yayi mata wata dariya da ta kara mata tsoron da take tare dashi "Ke kikace in zabar mana, me yasa zamu saka wani a tsakiya?" Haka yake ta ce mata tun shekaranjiya, tasani, abune data bude bakinta ta fada, ko da sukayi fadan ranar, ko tace tayi fadan dashi, dauke masa wuta tayi, ta danyi mamaki data tambayeshi shi zuwa gida yace mata "Ki gaishe dasu, kibi a hankali, karkiyi gudu, kuma daga gida karkije ko ina" Ta duba wayarta yafi babu adadi, musamman da taga anyi la'asar, amman bata ga kiran Haris ba, sai taji ta kasa samun sukuni, sakewar da take tunanin zatayi cikin 'yan uwanta ma bata samu ba, wajen karfe shida ta kirashi, saida ta kusan yankewa tukunna ya daga hadi da kiran sunanta "Da anyi Magriba zan dawo fa" Ta tsinci kanta da fadi "Alright, kiyi kula da tuki" Ya karasa maganar cikin yaren Italian, bai dora da komai ba ya kashe kiran, tasan itace ta fara shareshi tun shekaranjiya, amman komin fadan da sukeyi, in zata fita, Haris na iyayi mata kira goma. Shisa data koma gidan, ta dinga kallonshi, shayi ma bai bukata ba, itace ta hada masa, ya karba yana furta "Nagode" A hankali, ta kalle shi, tagan shi yana rashin lafiya sau babu adadi, ta ga Haris ma a lokuttan da baya iya numfashi da kanshi, amman bata taba ganinshi a irin wannan yanayin ba, batama san akwai wani kyalli cikin maikon da idonshi yakeyi ba sai yanzun da bata ga wannan kyallin ba "Me yake damunka?" Ta tambaya, saiya daga mata kafadunshi kawai batare da yace komai ba, ta kyaleshi duk da zuciyarta batayi mata dadi. Haka suka kwanta, baiko matso kusa da ita ba. Washegari ya kama ranar alhamis ne, kuma ranar ne za'ayi kunshin bikin Khairi, juma'a za'ayi kamu anan cikin gidansu kamar yanda aka saba, washegari asabar a daura aure. Lokacin da ta gama shiryawa Haris na bacci, ta tabashi a hankali, ganin har tara da rabi "Inaso in tafi gida, kasan yaune akeyin kunshi dan a gama mun nawa da wuri" Kai kawai ya jinjina mata batare da yace komai ba, ta dan tsaya jim, sai taga ya sake rufe idanuwanshi, dole ta tafi cikin sanyin jiki, har Khairi saida ta tambayeta me yake damunta "Ganjaa ne Adda Khairi, amman ba wani abu bane na tashin hankali" Khairin bata matsa ba, to ko da taso ma ina take da lokaci anata hidimar bikinta? Ga dai yanda take so ta samu, kar Haris ya hanata zuwa gidansu ayi shagali da ita yanda ya kamata, musamman ma da Awwab na gidan Hajiya Rumana, sai ita da katon cikinta da takejin shine kawai abinda zai rage ma bikin armashi, ashe harda yanayin Haris. Haka akayi kunshin nan, yamma likis ta kama hanya, dan ana kiraye-kirayen sallar Magriba ne, har Fa'iza nace mata "Anty dama mun tsaya munyi sallah sannan" Ta amsa da "Ai kam, sai muyi idan munje gida" Tana kallon Fa'izar tana hura inda bai bushe ba a kunshin da akayi mata na bakin lalle da bakinta. Ta dibo musu abinci daga gida, yanda bayanta yake a riqen nan batajin zata iya dafa wani abu. Haris na daki a kwance, da tayi masa maganar sallah ya tashi yayo alwala, anan cikin daki yazo ya kabbara. Ta hadiye wani yanayi da yake taso mata, saida tayi isha'i tukunna tayi karfin halin hada masa shayi, ta zubo masa da samosa din da sukayi order wajen Zainab Kerau, amman shayin ma rabin kofi yasha, ya ajiye sauran, ba'ayi mintina biyar ba ya mike ya nufi bayi, jin yana amai yasa ta tashi da sauri ta same shi a bayin tana jera masa sannu "Baka da lafiya?" Ta tambaya, ya kalleta da wannan abin da batason gani a cikin idanuwanshi, wannan disashen abin "Lafiyata kalau" Ya amsa yana rabata ya wuce bayan yayi brush, ta biyoshi tana karayi masa sannun da bai amsa ba, a daren ne kuma taji yanda yake zabura, da farko ta dauka ma mugun mafarki yakeyi sanin in bata tsaya akanshi ba, ba addu'a yakeyi ba in zai kwanta, yau kuma da kanta ta tofa masa kawai. Data kunna kwan dakin sai taganshi ya hade jikinshi waje daya, akwai wani yanayi da ake fassara farar fata dashi, ace fuskarshi tayi fari tas, ya dashe kamar wanda bashi da jini, to a madadin wannan farin sai taga fuskar Haris tayi mata kamar ya kwaba toka da mai ya shafa, zuciyarta tayi wata irin bugawa. Data girgiza shi a hankali ya motsa, ko tace ya kara zabura ne, fuskarshi ta taba, tayi sanyi, ga zufa yana hadawa, wannan daren yana daga cikin darare masu tsayi a wajen Maryama, tunda ko daya bude idanuwanshi ma ta tambayeshi ko wani abu nayi masa ciwo haka yace "A'a, ki kyaleni dan Allaah" Yana janye hannunta daga jikinshi ya juya mata baya. Washegari kuwa har karfe goma da rabi ta kasa fita daga gidan, sai da taga ya shiga yayi wanka ya fito wajen sha daya lokacin, tukunna ta tafi. Ta ari karfin hali tun a hanya ta sakawa fuskarta, ta dinga murmushin da takejin har kumatunta na amsawa, anyi mata kwalliya mai sauki, tace bayanta ya riqe saboda batajin zata iya wani kai kawo, waje daya ta samu tayi zamanta. Hajja ce ma tasa aka kirata wajen biyar da rabi "Kinga kina fama da kanki, gara kizo ki tafi gidanki ki huta, Addarku tace kina waje daya a zaune tun dazun, kuma yanayinki ya nuna bakyajin dadi" Bata tafin ba saida suka karayin hotuna sannan, ta nemo Fa'iza data shige cikin 'yan uwanta da suka zo biki, silalewa sukayi, motarta daman tana waje, akwai wanda sukace zasu bita gidanta su kwana, sai dai gidan nata na cikin yanayin da bata bukatar wani bako, Fa'izar ma dan tayi mata shara ne da wanke-wanke data kyaleta ta kwana anan gidan nasu. Karfe 11 na safe ne daurin auren Khairi, kuma ko a mafarki Maryama bata hango wai tana garin Kaduna, amman ace bata gefen Khairi a zaune ba a wannan ranar da take da dimbin tarihi a rayuwarta. 'yan gidanma sai kiranta sukeyi a waya "Haris ne bashi da lafiya Adda" Ta tsinci kanta da fadawa Adda Zahra da ta sake kiranta "Wallahi kinganmu haka muka kwana, tun shekaranjiya ma..." Tayi maganar muryarta na rawa "Subhanallah, shine kuma kikayi shiru saboda baki da hankali, ki tashi ku tafi asibiti dashi, in kina bukatar wani ya biyo bayanku saiki kirani, Allaah Ya bashi lafiya" Asibitin itama take so su tafi, amman Haris yaki "Babu inda zanje fa, kuma wallahi karki kiramun wani" Ita babban tashin hankalinta ma batasan abinda yake damunshi ba. Bata iya taje gidansu ba ranar asabar sai karfe biyu, lokacin da za'a tafi kai Khairi gidanta da yake unguwar dosa, kuka biyu Maryama tayi, dana Haris da kuma wanda ta taya Khairi, tare suka tafi aka kaita bayan sallar la'asar. Ta danji sauki da Adda Zahra tace mata ta tashi ta tafi gida wajen karfe shida. Haka ta koma ta samu Haris yanda ta barshi, suka sake kwana lahadi, ga yau likitinin, inta mike itama jiri take gani. Dan haka ta samu ta dafa bango ta fita falo da wayar Haris din a hannunta, tunani takeyi Alhaji Mustafa zata kira ko Hajiya Rumana, ko su biyun zata hada dansu hadu su saka Haris din zuwa asibiti. Tana shirin kiran Alhaji Mustafa ne taji shigowar mota cikin gidan, inda zata iya data tashi ta leka ta hango waye, sai dai batajin zata iya mikewa. Da aka kwankwasa tace waye, bata gane muryar ba, ta kwalawa Fa'iza kira, ita tazo ta bude, ta gaishe da Hajiya Rumana sannan ta koma daki abinta, Maryama kuwa tayi mamakin ganin Hajiya Rumana matuka, Awwab ya rugo yana fado mata, ta dan runtsa idanuwanta tana kokarin dagashi daga jikinta dan ya buge mata ciki. "Sannu da zuwa" Maryama ta furta a hankali, muryarta cike da bacci da gajiya, Hajiya Rumana tayi mata wani irin kallo "Ina Haris?" Dan yau kwana hudu biyar kenan bai kirata ba, idan ta kirashi ma baya dagawa, jikinta ne ya bata ba lafiya ba, musamman da Alhaji Mustafa ma yace mata ya kirashi bai daga ba "Bashi da lafiya, yana ciki" Daman bata zauna ba "Bashi da lafiya? Shine saboda rashin hankali ba zakiyi tunanin kira ki sanar ba?" A yanda Maryama takeji, hayaniya ma bataso, sai kawai ta koma cikin kujerar ta lafe batare da tace komai ba, tana kallon Hajiya Rumanan ta wuce dakin da Maryaman ta nuna mata, ta tura a hankali da sallama, ai batasan lokacin da kafafuwanta suka karasa da ita cikin dakin babu shiri ba. Kuma maganar duniya da tayiwa Haris banda hakoranshi dake haduwa babu abinda yace mata, ta taba jikinshi a maimakon zazzabin da tayi tunani sanyi yayi kalau, ta yaye bargunan da yake rufe dasu tana kokarin dagoshi, ya kwace, ta sake kamoshi tana watsa masa zagi "Bari zakayi ka mutu matarka da ubanta su samu abinda suke so..." Da taga ya sake komawa ya kwanta, duk abinda ta fada ba tasiri yakeyi ba, saita fito falon tana cewa Maryama "Wai meye ya same shi? Sannan kunje asibiti" A takaice tace "Nima bansani ba, ba muje ba" Hajiya Rumana taja wani tsaki mai karfin gaske, ta sake komawa dakin "Wai dan ubanka Haris ba zaka tashi mu tafi asibiti ba?" Zuciyarshi bata masa dadi, duniyar ma duka batayi masa dadi, kamar wanda wani abin firgici ya biyo ya kasa gudu haka yakeji, ga wasu abubuwa sunayi masa yawo cikin kai, maganar da Hajiya Rumana takeyi ma bayaso, bayason komai sai a barshi yaji da abinda yakeji, kuma babu asibitin da zaije, haka Maryama take so ta ganshi, to kowa ya fita ya barsu ta zauna tana kallonshi haka din. Ganin da gaske yake ba zai tashi ba, sannan ita ba zata iya dagashi ba yasa ta zauna a gefen gadon kamar zata rusa kuka, ta kirawo Alhaji Mustafa tana fada masa abinda yake faruwa. Duk da yace mata gashi nan, kuma bata san daga inda yake tahowa din ba, agogo ta dinga dubawa tana jan kananun tsaki, ya kusan mintina arba'in tsakanin wayarsu kafin ya shigo, kuma tana jiyo shi ya tsaya magana da Maryama kamar bata fada masa halin da danshi yake ciki ba. Da taimakon Alhaji Mustafa, da Haris ya kasa yiwa gardama suka dunguma zuwa asibiti, Maryama hijabi ta zirawa jikinta, Fa'iza ta dauki Awwab, suka zauna a tata motar. Tashin farko aka karbeshi aka soma bashi taimakon gaggawa, ita kanta Maryama yanayinta da likitan ya gani yasa shi tirsasa mata kwanciya aka daura mata ruwa, da yake akwai gajiya sosai a jikinta, sai bacci ya dauketa. Bata san abinda yake faruwa ba sam, irin zirga-zirgar da Alhaji Mustafa da Hajiya Rumana sukeyi ganin likitocin kansu kamar canki-canka sukeyi da abinda yake damun Haris din, saida suka jira wani specialist da yake zuwa asibitin daga Shika, sunci sa'a ranar na daga cikin ranakun da yake zuwa. Shine bayan ganin Haris kanshi tsaye ya cewa Alhaji Mustafa "Danku yana shaye-shaye?" Hajiya Rumana ta kalle shi da sauri, zuciyarta na wani irin bugawa, wanne irin shaye-shaye. Wai me yasa duk lokacin da zata ga Haris a nutse, sai a nemi dawo da wannan maganar? "Eh gaskiya nasan yana shan wiwi, amman bayan ita bansan ko yana hadawa da wani abu ba, sannan bansan koya bari ko bai bari ba" Cewar Alhaji Mustafa cikin wata irin murya. A karo na farko da Hajiya Rumana taji idanuwanta sun cika da kwalla akan wannan matsalar ta Haris, shikenan? Ya dai tabbata, duk yanda take gudun wannan gaskiya gata nan a gaban idonta, danta shaye-shaye yakeyi. Haris dinta, kuma abinda take ta gudu da karbar gaskiyar shine inda ya koyi shaye-shayen, tasan a Boarding ne, can zuciyarta ta dauketa ta wulla, ranar da aka gaya musu a ofishin shugaban makarantarsu, ta rufe idonta da zuciyarta taki yarda. Ko meya faru daga wannan makarantar ne, makarantar da Alhaji Mustafa ya nuna mata bayaso, amman tayi fatali da bukatarshi ta dauki Haris din ta kai, kenan in aka zagaya aka zagayo itace sanadi, ita ta jefashi a wannan mummunar dabi'ar. Yaron da yanzun yake da iyali, Haris din da kowa ya kalle shi zaiga kimtsatsen mutum da natsuwa ta saukarwa, duk da batajin dadin yanda ya kasance tare da Maryama ne ya samu wannan natsuwar. Amman idan wani yaji, tasan abune da zai zubar masa da mutunci "Yaronku yana fama da abinda ake kira withdrawal effects ne, da alamu dai iya wiwi din yake ta'ammali da ita, dan da akwai wani abin zaifi haka shiga yanayi" Alhaji Mustafa ya sauke wani numfashi da baisan yana rike dashi ba, har saida ya dafa bangon da yake gefenshi "Kana nufin ya daina sha kenan?" Hajiya Rumana ta tambaya da saurinta "Bai shaba kwana biyu shisa yake wannan abubuwan, muna fatan kuma ya dore da hakan, sai dai yana bukatar taimakon duk wani na kusa dashi, saboda abu dan kadan zai iya sake mayar dashi..." Bayanai yayi musu sosai, bayan ya fita Haris ya motsa, ya sake motsawa. Hajiya Rumana ta karasa wajen shi "Maryamm" Ya kira, ya kuma sake maimaitawa duk da idanuwanshi a rufe suke "Me yake cewa?" Alhaji Mustafa ya tambaya, fuska a hade Hajiya Rumana tace "Wai wata Maryama" Ya dan girgiza kai kawai, shi wannan kiyayyar marar tushe da Hajiya Rumana take yiwa Alhaji Sa'id da ahalinshi ta daina bashi mamaki ma, ya karasa wajen Haris din ya zauna a gefen gadon, ya kuma riko hannunshi a hankali duk da karin ruwan "Maryamm" Ya sake fadi a hankali, sai Hajiya Rumana taja kujera ta zauna, ta matsa jikin gadon sosai, wajen kan Haris "Haris, ga Maminka" Dariya taso kwacewa Alhaji Mustafa "Maryamm" Yace yana dan bude idanuwanshi, sambatu yakeyi, yawanci duk cikin yaren Italian ne, banda sunan Maryamm din da yake kira yana maimaitawa kamar karatu babu abinda Hajiya Rumana take ganewa, saida yace "Ina so in sha, amman na kasa, saboda ke, na kasa Maryamm" Wani irin kishin Maryama da Hajiya Rumana batayi zato bane ya taso mata "Kai Alhamdulillah, Madallah da Maryaman Sa'idu, madallah da 'yar albarka, ashe itace zata zame maka haske Haris" Alhaji Mustafa ya fada da biyu "Ruma kinga abin Allaah ko, kinajin me yake fada?" Ta kauda kai gefe, cikin dabara tana dauke kwallar da take shirin zubo mata, batace komai ba. Alhaji Mustafa dinne ma ya mike ya nufi dakin da aka kwantar da Maryama, bacci takeyi har lokacin, sai Fa'iza da take zaune, ta rungume Awwab da shima yayi bacci "Bata tashi ba?" Ya tambayi Fa'iza "A'a bacci takeyi, amman wata mai farin kaya tazo ta duba ta" Ya jinjina kai yana ficewa, abubuwan da yake tunanin zasu bukata yaje ya sissiyo, tun daga kan ruwa da lemo, har da kayan marmari ya hado, ya kuma yo musu takeaway na abinci. Da yake Fa'iza ba yunwa takeji ba, saita ajiye abinda ya bata din, ta dai dauki ruwa roba daya ta fasa ta sha. Har dare suna asibitin, saida Alhaji Mustafa ya ga Maryama ta farka, tukunna yace ma Hajiya Rumana su tafi gida "Ita da bata da lafiya, ku dai tafi, ku barni in kwana dashi" Har ran Maryama taso ta kwana, taji dadin jikinta, daman rashin bacci ne yake dawainiya da ita, shima kuma Alhaji Mustafa sai yaga maganar Hajiya Rumanan akan gaskiya take, dan hakane ma ya saka su a gaba, bayan ya kwashe musu duk abinda ya siyo ya kai musu motar Maryaman "Zaki iya tuki kuwa?" Ta danyi murmushi "Eh Baba, daman gajiya ce kawai, kuma ina samu nayi bacci na tashi shikenan" Shima murmushin ya danyi mata "Allaah Ya kara lafiya" Ta amsa a hankali, harta bude murfin motar da su Fa'iza sun shiga baya ita da Awwab ya kira sunanta, ta juyo cike da ladabi a yanayinta "Allaah Yayi miki albarka Maryama, sannu da kokari kinji, Nagode, bansan irin yanda zan furta godiyar dan ki gane girmanta kamar yanda nake nufi ba" Tayi kasa da kanta kadan, kunya na lullubeta "Allaah Ya kara muku zaman lafiya da kwanciyar hankali, Allaah Kuma ya shirya muku zuri'a. Allaah Ya kara miki hakuri da juriya" Tanata amsawa a zuciyarta "Ku tafi gida, dare yana karayi, a kula da hanya sosai kinji ko" Kai ta jinjina "In Shaa Allaah Baba. Allaah Ya kara lafiya" Ya kara fadada murmushin shi "Kiyi kwanciyarki tunda kinga shima da sauki, Doctor din yace withdrawal effects ne na abinda bai sha ba kwana biyu, ba wani abu bane ba, zai sake shi a hankali" Zuciyar Maryama tayi wani tsallen murna, abinda bai sha ba, wiwi kenan, Haris bai sha ba na kwanakin nan shine abinda ya kwantar dashi, kamar hawayen farin ciki zasu zubo mata haka takeji "In Shaa Allaah" Ta fadi, tayi masa sallama ta shiga motar, bata gudu da mota, amman yau yanayin nishadin da takeji yasa ta dan taba, musamman da titin yake da saukin hada-hada saboda daren da yayi. Da suka karasa gida ta karbi Awwab taje ta kwantar dashi, Fa'iza ma sai da safe tayi mata, duk sunyi isha'i a asibiti, itama saita kwanta kawai, tanajin abinda ke cikinta nata motsi, ta dafa cikin tana murmushi "Addu'a kake tayani? Allaah Ya shirya mahaifinku ko? Allaha Ya kara shirya shi Yasa ya daina duk abinda yakeyi" Ya kuwa kara motsawa, sai tayi dariya mai sauti, kafin kuma ta furta "Thank you" Kamar Haris din yana gabanta, a karon farko ta dora da "I love you" Tanajin kalaman daban akan harshenta, kamar wasu baki, kamar wani abu da bata taba hasashen zata furta nan kusa ba, zata jira, har Haris ya dawo gida, zata rike shi a jikinta ta furta masa wadannan kalmomin, saboda zuwa yanzun itama tasan tana son Haris! 41 A LEAP A kace lokaci na tafiya da komai, a wajen Maryama, zatace lokaci ya tafar mata da abubuwa masu tarin yawa, a cikin abubuwan nan akwai kuruciyarta, da yanzun inta kalli kanta sai tayita mamaki, itace fa, Mairaman Abba Sa'idu, ba kiba tayi ba, jikinta ya murje, irin murjewar nan da haihuwa inta hadu da hutu yake samarwa, kuma ko a yanzun idan zata kwana tana rantsewa wasu cewa shekarunta talatin da biyu, to haka wasu zasu rantse suna karyata cewar bata kai ba, musamman kuma ace an ganta tare da yaranta. Yaran da ake dauka biyu daga cikin hudun nan ne kawai nata, Awwab (Sa'id), Rauda (Rumana), Naadir (Mustafa), sai Aalim (Aminullah). Haihuwar Rauda tazo mata da tarin alkhairi, tasan ra'ayin Haris ne ya barta a Najeriya, ya koma New York, kuma daya kammala karatunshi, lokacin business dinshi ya fara kafuwa, an fara gane motocin (HM Wheels), dan irin buses din nan ne masu kyau ake daukar fasinja tsakanin garuruwa, sannan yana da manyan motoci suma, a hankali yake tafiyar da HM Wheels, babu gaggawa a cikin lamarin, sannan duk wani aiki daya samu dangane da abinda ya karanta, kowacce kasa ce, yana tafiya "Lokaci zai zo da in kika ganni a wata kasa, tare dakune gabaki daya da sunan hutu" Tasan tazarar shekaru hudun data samu tsakanin Rauda da Naadir, Allaah Ne yaso ta da samun hutun, da kuma rashin zaman Haris din, yawanci lokacin da zaizo bama ta cikin abinda ake kira ovulation window dinta, bata kuma damu ba. Ta kula duk yanda take son yaranta, to Haris ya linkata sau babu adadi, a wadannan shekarun kallo daya zakayi masa kaga yanda sukazo masa da cigaba, bata fannin samu ba kawai, harda ma zama babban mutum. Kamar su duka suka hadu sukayi murjewar samun kwanciyar hankali, shi harda ma lafiya, kullum zata kalle shi sai taji kamar ta sake ce masa ta gode, ta gode daya watsar da wiwi, ta gode da yayi hakan kacokan saboda ita. Dan wannan yana daya daga cikin abinda yayi mata da take yawan dubawa "Kanshi fa ya taimakawa, ko da kece kikayi sanadi ya bari, kanshi ya taimakawa" Haka Khairi tace mata, sai tayi murmushi kawai, to taya Khairi zata gane girman abin tunda babu soyayyar Haris cike fal da zuciyarta? Ita tasan ba kanshi kawai ya taimakawa ba a lokacin daya hakura da wiwi, harda ita, saboda bata shiryawa yin takaba ba, a cire batun doguwar jinyarshi a asibiti, bata shirya kallonshi cikin radadin ciwo ba, zuciyarta ba zata dauka ba. Sannan idan aka cireta, aka cire Haris a cikin lissafin nan, to ya taimakawa yaransu, ko babu komai yanzun bata da fargabar wata rana Awwab zai ga Haris da nadin wiwi a hannu, tunda ma yau da goben da ake cewa bata bar komai ba tana iya faruwa dasu. Duk wanda zai shigo gidanta, ko bai furta ba, tana ganin yanda rayuwarta take burgeshi, wasu ma suna kasa hakuri, balle kuma idan sukayi katarin samun Haris a gidan, Haris da ko a wannan shekarun bayajin nauyin nuna mata kulawa, ko a gaban wanene, kuma ta tabbatar wannan kulawar na daya daga cikin dalilin da tarin shekarun nan ya kasa goge kiyayyar da Hajiya Rumana takeyi mata. Har zaunar dashi tayi tai masa magana sai ya kalleta kamar wanda tayiwa wani yare na daban "Wacce irin kulawa?" Dan da gaske ba zaice ya gane wacce irin kulawa take maganar ya rage nuna mata a gaban 'yan uwanshi ba "Missing step kikayi, da kin fadi kin ji ciwo fa?" Sunje gaishe da Hajiya Rumanan ne, wajen tashi saita take doguwar rigarta data sauka sosai, ta lankwashe yatsanta na kafa shisa ma ta runtsa ido tana kiran sunan Allaah, zafin ya ratsata har kwanya, batasan ya akayi ta ga Haris a gabanta ba, ya kama hannunta yana zaunar da ita akan kujera, ya kuma tsugunna ya kama rigar ya daga sama yana dora kafarta akan cinyarshi tare da dubawa "Saida nace miki ki canza riga saboda sau biyu kina take wannan din, amman kikaqi ji" Watakila Haris baiji tsakin da Hajiya Rumana ta zabga ba, amman akan kunnen Maryama, kuma hankalinshi duka yana kanta shisa baiga tashin da tayi ta bar musu falon ba, saboda yanda yake bin kafarta yanata latsewa "Ban fadin ba, amman kaga ko babu komai akwai kunya a gaban Mami ace ka kama kafata kana murzawa" Sai abin ya bashi dariya sosai "Kafarki na murza fa, kafa, bawai..." Duka takai masa a kafada ya kauce yana cigaba da dariya, in dai zatayi masa magana akan irin wannan, to a haka zai shiriritar da abin, har saida ta gaji ta dauki ido ta saka masa, ta kuma hakurewa zuciyarta akan tsanar da Hajiya Rumana tayi mata, haka su Munira, ko haihuwa sukayi idan ta kira da nufin musu barka basa daga wayarta, sai ta daina kira, in Haris ya kira dai yakan saka a speaker suyi gaisuwar jeka nayi ka, haka kuma duk haihuwa zataje har gida tayiwa Hajiya Rumana barka ko da bata samun tarbar arziki "Ko naman jikinki zaki yanka ki dinga mata farfesu wannan bakar matar ba zata soki ba Maryama, ki tattarata kawai ki watsar, ke dai kyautatawa iya wadda zaki iya, yanda ba zaki takura ba, kiyi, saboda har abada, duk lalacewarta, mahaifiyar mijinki ce, karki manta Hajja bata gajiya da jadda mana taya mazajenmu kula da iyayensu, amman cikin bakaken yayyenshi, duk wadda ta gaya miki marar dadi kikaji ba zaki iya dauka ba ki rama" Haka takeyi da, maganar duk da zasu fada mata in sunyi haduwa goma tana da amsa, idan a gaban Haris ne kuwa kafin ta amsa ma ya rigata, tare mata fada yakeyi kamar itace 'yar uwarshi basu ba, tasan wannan ma ya kara rura wutar tsanarta a cikin zukatansu, har mamakin yanda suka tsaneta amman kamar su lashe su Awwab takeyi. Tana zumuncinta da yaran Umma Fadime, har hutu yaransu na zuwa mata, kuma tayi kokari matuka a shekarun nan wajen ganin ta kara gyara alakar Haris dasu, hakama dangin mahaifinshi, lokaci bayan lokaci take saka shi suyi siyayya niki-niki su zagaya su gaishe su daya bayan daya, wani abu da ranar farko da sukayi, har gida Alhaji Mustafa yazo ya dinga saka mata albarka dayi mata godiya sai da taji kamar zata nutse don kunya. Tana da karamin cikin Naadir ne ta fara zuwa Maiduguri, za'ayi taron 'yan uwane, na bangaren Hajiya Rumana, taron da shine na farko da ake fatan ya dorar da zumunci da ma wasu abubuwan masu yawa, dan haka har wadanda basa kasar sun halarta, taso tayi gardama, amman Haris yabi duk wata kofa da zata kawo yana toshewa "Inaso inje tare dake Maryamm, dama su Awwab, inaso in akace ina matata, in amsa tare da nunaki..." Cikin rauni tace masa "Kasan har yau, Mami bata karbeni ba Ganja..." Ya daga yatsunshi, ta matsa baya da sauri tana yin murmushi, tasan bakinta zai dille "Ba zaki daina ba ko? Kirana da sunan nan" Tace masa Baban Rauda ko Baban Awwab ya zabi daya, a lokacin suna kan gadone, dan haka ya kaita can karshe yana matseta tare da fadin "Ni? Maryamm nine zaki kira wannan sunayen?" Yanda yayi maganar hankalinshi a tashe ya bata dariya ba kadan ba, yaran Papa suke ce masa, ita kuma suna kiranta da Ammi, Papan ma sai yaji shi kamar wani tsoho. Babu tunanin da batayi ba, kafin a wani film din 'yan kasar Turkiyya da take kallo taji "Saheb" Sai yayi mata dadi, data duba ma'anar ma saita zauna mata, amman lokacin ta kasa sabawa, Ganja ya kama bakinta, lokaci zuwa lokaci sai taji ya subuce "Muyi maganar gaskiya, Mami bata karbeni ba, kana zaton danginta zasu karbeni ne alhalin tana qina?" Ya riko hannunta "Shisa nake so inje dake, in nuna ma kowa cewar in zasu tara mutanen Maiduguri da kewayenta ba zasu canzani daga karbar da nayi miki ba..." Kafin tace wani abin kuma ya rigata "Kina tare dani, tsoron me kikeji Maryamm? Ko kina tunanin akwai wanda ya isa yayi miki ko da kallon da bai kwanta mun bane balle kuma ya fada miki wata magana in barshi?" Abinda take tsoro kenan, Haris yaje yana fada da 'yan uwanshi akanta. Tasan abune da mata da yawa zasu dauka soyayya ce da kuma samun gata a wajen miji, sai dai bakowanne fada bane idan miji ya tare maka yake zame maka maslaha, babu abinda wannan halin na Haris yake ja mata sai karin tsana, kuma ko zasu kwana tanayi masa bayani ba zai taba fahimtarta ba "Tunda sai jibi zamu tafi, zanje gidan Khairi gobe idan Allaah Ya kaimu" Yaja girar sama data kasa ya hade waje daya. AnO abinda baya kauna, fita idan bashine ya kirkirar musu ba, sai ankai ruwa rana yake barinta. Har yau din nan 'yan uwanta gani sukeyi itace batason makaranta shisa bata koma ba, itace taki yin dabarun mata tasa Haris ya barta ta cigaba da karatunta. Amman ita da take zaune dashi tasan cewa sai dai in anayi a Aljanna, ko Islamiyyar matan aure da taso shiga, sai yaje har makarantar ya samo Malama da zata dinga zuwa gida tana karantar da ita, da yake tasan muhimmancin karatun haka ta hakura, Malama Fatima take zuwa sau biyu a sati. Bata ma san ta yanda zatayiwa kowa bayanin tsananin Haris akan fita ba, sai dai ko idan matan da suke auren mazaje masu kulle irinshi ne zasu zauna su tattauna, su kadai tasan zasu fuskance ta. Tunda Hajja ma ta kasa hakuri ta taba ce mata "Saifa kin dage Maryama, sai kin nunawa mijinki muhimmancin 'yan uwanki, saikin nuna masa ba kowanne abu bane kudi zaiyi maka, ko baya gari ko da yaushe, ai ba zai rasa ganin yanda 'yan uwanki suke tsayawa akan duk wani abu naki da zai taso ba, sai kice ke ba zaki kamanta musu ba saboda ya hanaki zuwa? In hidimar nashi dangin ne na tabbata da rawar jiki yake barinki kije ai" Haka tace "In Shaa Allaah zan kara kokartawa Hajja, kiyi hakuri" Dan ko ta tsaya bayani ma batasan kalaman da zatayi amfani dasu ba, me zatace? In ta gayawa Hajja a sha'anin nashi 'yan uwan ma haka yakeyi mata zata yarda? To yama zatayi da Haris tunda ya fita taurin kai, kuma ko da ta gwada masa nata taurin kan zata fitane bada izininshi ba? Hankalinta ya dan kwantane, dan tasan Hajja tayiwa Alhaji Sa'id maganar ne shisa ya kirata ya kwantar mata da hankali cikin tausasan kalamanshi "Tsakaninmu dake yanzun kyautatawa ce, amman babu mai cikakken iko akanki sama da mijinki, kuma bin umarninshi in har bai sabawa shari'a ba, kiyi hakuri akai kinji ko? In ya barki kije sha'anin 'yan uwanki, idan bai barki ba kiyi hakuri" Suka kara wayar yanata saka mata albarka. Koya zata shiga wani matsi na rayuwa in dai zatayi magana da Abbanta sai taji ta samu sauki da salama, kamar babu wani wanda yake da kalaman da suke nutsar da ita kamarshi, shisa bata gauraya soyayyar da takeyi masa da komai ba, kuma tana alfahari da biyayyar da tayi masa akan auren Haris. * Haka suka isa Maiduguri, daga Awwab har Rauda suna ganin Hajiya Rumana suka tafi wajenta, daga nan ita batama kara sakasu a ido ba, ta dinga jin wani iri ganin daki daya suka sauka da Haris a wani irin katafaren gida "Wai nan zan kwana nima? Daki daya da kai?" Da mamaki ya kalleta "Ina zaki kwana to in ba tare dani ba?" Har ranta taji hankalinta ya tashi, so take yanda suka sauka lafiya su koma lafiya. Saida Haris din yayi mata bayanin cewa ai kowa in dai da matarshi yazo to daki daya ake basu tukunna hankalinta ya dan kwanta, a fuska dai babu wanda ya nuna mata wani abu, amman a darare take, tunda bayan gaisawar data dingayi da mutanen da bata koyi kokarin kiyasta yawansu ba, yara da manya, maganar da suke tayi da yarensu na Kanuri sukeyi, sai dai taga ana dariya, Haris ma da bai cika mayarwa ba, ranar idan sukayi masa mayar musu yakeyi, su Awwab ma zama da Hajiya Rumana yasa sunaji sosai, ga Awwab dai zaune kusa da ita, amman bai hanata jinta daban a cikinsu ba. Ko da wasu ba 'yan uwa bane ba, sai taga kowa najin yaren, ko koya sukayi bayan auren bata sani ba, amman dai tabbas a ranar taji babu dadi. Karshe ta mayar da hankalinta kan wayarta kawai, da yake Haris da Awwab tsakiya suka sakata, sai da aka kawo abincine Awwab yabar wajenta, yanayin gyara zaman Haris taji, sai kuma hannunta daya kama ya rike, riko bana wasa ba. Ta daga ido dan taga abinda ya sauya masa yanayi lokaci daya, kirjinta ya buga, ya sake bugawa, kafin ya kwaso wasu ganguna da ba zatace ga kalar kidan daya farayi mata ba, aiko a mafarkinta akayi taron mata, fuskar Aise ba zata bace mata ba. Wannan bakar fuskar ta Aise da take sheki a wancen lokacin, yanzun dinma take shekin cikin kwalliyar da ta zauna mata das ba zata taba bace mata ba. Aise da har yanzun in dai zata riko hannun Haris sai taji wani abu ya daki zuciyarta, saboda sunanta da yake rubuce jikin karamin dan yatsanshi, cikin jikinta daya nuna cikin shigar riga da wandon da tayi na wani material pink mai duhu bai hanata yin kyau ba, sai kuma daurin da tayi ta dan turashi baya har kana ganin gyaran gashinta, da wasu manyan dankunne masu circle na silver da suka kara haska kwalliyar da tayi. Wani abu ya daki zuciyar Maryama lokacin da Aise ta karaso inda suke zaune tana budewa Haris abinda Maryama take tunanin shi kadaine mai haske a tare da ita, wato hakoranta "Kai baka zumunci da mutane ko?" Ta fadi cikin yaren Kanuri, batasan ya gawa take ba, amman yanda hannun Haris yayi mata kamar katako a cikin nata sai taji kamar ta rike hannun gawa, ta dan kalle shi, sai taga yayi karamin murmushi "Aise" Ya kira, kalma daya, kalma daya tak, amman yanayin yanda ya furta kalmar sai ya tuno mata da wani scene a wani series film da ta kalla mai suna the originals, anan ne taji ance jini na tafasa, to duk wani jini da yake yawo a jikinta ne yake tafasa "Maryamm...matata Maryamm" Ya fadi yana nuna mata Maryaman, kafin ya dan kalli Maryama yana cewa "Aise...my cousin" Saida tayi kokari matuka sannan ta cewa Aise din "Sannu" Ta kasa mika hannu ta karbi na Aise din data miko mata, dan gani tayi kamar da gayya ta ware mata yatsanta taga sunan Haris da yake ciki, kuma zuciyarta nace mata meye wani aure Maryama? Meye auren balle kuma yara biyu da cikin na uku? Kinsan babu abinda wannan garun budus din zata diba a jikinki, kafin wani cikin 'yan uwanta yayi wani yunkuri kin kaita kasa kin tsige yatsan kin jefa a jaka. Watakila Haris yaji sautin duk wani tunani nata shisa ya gyara zamanshi yana kara dumtsa hannunta, lokacin ne kuma Awwab ya dawo wajen hannunshi rike da plates guda biyu "Ammi karbi dan Allaah akwai zafi" Yake fadi yana mika mata guda daya, dan baima kula da Aise ba sai bayan ya zauna, lokacin ta sauke hannunta data mikawa Maryaman "Dan ka?" Ta tambayi Haris, ya amsa yana nunawa Awwab ita hadi da fada masa wacece, Awwab ya gaisheta a takaice, kuma shiya daukewa Maryama hankali da abinda yake bata labari wanda bama ganewa takeyi ba, ta dai biye masan ne dan batason tunaninta yayi tasiri akanta. Daren dai basu kwasheta dadi da Haris ba "Cikine da ita Maryamm, ko baki gani ba, da auren wani akanta, wani ta aura, ni me zanyi da ita bayan ta auri wani?" Harara ta watsa masa kamar idonta zai fado "Saboda ta auri wani kenan shisa ko? Inda zata fito tsab zaka kara da ita, har yanzun kana nacinta kamar yanda naga tana naka, tunda ku duka kuna makale da sunayen juna a yatsa, to bari kaji wallahi duka biyu zaka sha Ganja" Ya zauna a gefen gadon yana kallonta "Ga dukan sabawa Allaah nayin tattoo, ga kuma dukan sunan matar wani da kake dako, na tabbata bayan an kumburawa Mala'iku kai dai-dai yanda zasuji dadin duka, yatsan nan ma sai an hura shi sau dubu saba'in sannan mala'iku dubu saba'in su zagaye shi kowa ya samu inda zai jibga..." Yayi dana sanin dariyar daya kwashe da ita, dan itace tasa Maryaman ta fashe masa da kukan da tasan yana rikita masa lissafi, kusan raba dare sukayi yana aikin lallashi "Ni wallahi rabona da ganinta harna manta, tun a Italy, sai yau...kuma ai a gabanki, kinsan inda nayi magana da ita ko ba zatayi miki dadi ba zan gaya miki yanzun da kika tambaya" Dakyar ya lallabata, su da sukazo da niyyar yin sati daya kamar sauran, saboda yanda taki kwantar da hankalinta, kwanansu hudu, ya cewa Hajiya Rumana anyi masa kiran gaggawa zaiyi clearing wasu kaya da aka kawo masa, dole sai yana wajen, suka barta da Awwab da Rauda, ya dauki Maryaman suka koma Kaduna. Kuma ya kara faranta mata bayan ya bar kasar ya dawo, abu na farko daya farayi a bakin kofa data tare shi shine mika mata hannunshi, daga farko bata kula ba, sai daya ware mata yatsunshi, ta duba, ta kara dubawa, ta daga kai ta kalle shi "Na cire Maryamm...na cire kuma nayi Istigfar kamar yanda kike cewa inyi idan banyi sallah a masallaci ba saboda Allaah Ya yafe mun ya duba lamarina" Batayi magana ba, hannun ta sumbata, ta juya bayanma ta sumbata, sannan ta rungumeshi duk da katon cikinta kuwa "Zaki latsemun yarinya" Tayi dariya tana sake rikeshi, tana maida numfashi saboda da gaske ta matse cikin nata, dole ta dago ta sake kama hannun tana kallo "Nagode" Saiya kashe mata ido daya "Ban yarda da wannan godiyar ba Maryamm, kibari inyi wanka in natsu sai kiyi mun godiyar sosai" Ta nuna masa cikinta da hannu "Karki bari yarinyar da bakiyi wata bakwai da sani ba ta shiga tsakaninmu" Tayi dariya, a lokacin tana jin kamar babu wata mace da ta kaita farin ciki, kamar babu wata mace da tayi dacen miji kamarta, mijin da yake barin komai saboda farin cikinta. Ko kadan bata san a wannan lokacin kaddara nayi mata lissafi bane ba Wata bakwai Haris yace, Kaddara kuma ta kara mata uku akai daya rage komai ya birkice musu 42 Har gobe Maryama ba zata taba bace lissafi ba, idan ranar ta fado mata, sai ta tuna cewa kwananta talatin da daya da haihuwar Naadir. Tana zaune akan gadon dakinta, ko tace dakinsu ita da Haris, dan dole suka mayar dashi nasu, sai daya ya koma na Awwab, dayan kuma Fa'iza da Rauda. Yanzun dinma Fa'izar ce tayi sallama, saida ta bata izini tukunna ta shigo, inka kalli sanyinta, yanda take komai a nutse zaka iya cewa zatayi san jiki, kuma hutun da take samu ya fito da hasken fatarta sosai. Yarinya ce da Maryama take kara godewa iyayenta da suka basu rikonta, a shekarun nan ba iya islamiyya ba, har boko saida ta tsaya aka mayar da Fa'iza, aka daukar mata lesson teacher, da yake itama tana son karatun kuma saita maida hankali sosai. Yanzun haka tana ss2 ne, sai dai iyayenta aure suke so tayi, karfin hali na Haris harda zuwa ya samesu yace suyi hakuri ta kammala ko da ssce dinta ne, Maryama ta dinga kallonshi tana kasa hadiye mamakinta a lokacin. Sai kuma ta ga daga duk wani abu da Haris zai karba, to yana karbane da dukkan gaskiyarshi "Kanwarmu ce kanan?" Ya tambayi Maryama, ta dan jinjina masa kai "Ta wanni fannin kuma 'ya ba, tunda rikonta aka bamu" Nashi kan ya jinjina mata a lokacin, sai a hankali ta kula da rikon 'ya yakeyiwa Fa'iza, yanda su Awwab suke ce masa Papa, haka ya hanawa Fa'iza kiransa Kawun data nemi kakaba masa itama take kiranshi haka. Sanda ta fara tsayawa da Auwal da yanzun iyaye suka shiga maganarsu, kamar Haris zai daketa, ya dakatar da zuwan Auwal gidan sai bayan da yayi bincike ya gamsu da tarbiya da kuma inda Auwal din ya fito, asalinshi dan zamfara ne, zama ya dawo da iyayenshi nan Kaduna, sai dai shi din jami'in tsaro ne masu yaki da fataucin miyagun kwayoyi wato NDLEA. An tsayar da magana sai ta gama zana jarabawarta sannan za'ayi bikin, haka kuma Haris yake jadda masa ko bayan auren Fa'iza zata cigaba da karatunta. A maimakon haushi ma sai abin ya dinga ba Maryama dariya, yanda ya rufe ido ita ya hanata tayi nata, gashi yanata hakilo akan Fa'iza, ai addu'a takeyi Allaah Yayi mata tsahon rai dan taga yanda za'a kwashe dashi akan Rauda. Yau ma Auwal dinne da yake aiki a Minna yanzun yazo Kaduna, to baiga Naadir ba, shine Fa'iza tazo zata daukar masa shi. Itama ganin yayi bacci da ta cewa Maryama a barshi "Ammi banaso ya farka ya dinga kwala ihu, kyau kema ki dan kwanta ki huta fa" Maryama tayi dariya, Naadir ba dai kuka ba, ita babu ma wanda yayi rigimarshi, kuma da alama zaiyi qwiya, dan tun yanzun duk wanda ya dauke shi saiya dinga kure masa kallo kamar yana so ya gane wanene kafin ya yage baki, kuma shi da alama ba zaiyi duhun fata kamarsu Rauda ba, ta ganshi har yanzun da haskenshi, su kam kafin ayi arba'in duk sun rine. "Kinsan Naadir dai inya tashi rigimarshi zaiyi ne, ki dauke shi ki kai masa shi ya ganshi" Bayan Fa'izar ta dauki Naadir ne ta fita, sai kawai ta kishingida, tasan ko zancen suka gama ma, Fa'iza goyashi zatayi, ta dauki wayarta ta tafi open diaries tana karanta matsalolin mutane, a gefe daya tana godewa Allaah da nata matsalolin, wani abin inka gani dole ma ka godewa Allaah, dan sai kaga taka matsalar na matsala bace ba, iya wannan rufin asirin da take ciki abin ta duba ne, tafi karfin komai na bukatar rayuwa, harma tayiwa wasu batare data takura ba. Tana cikin dubawa ne kuma taci karo da wani abu daya sakata tashi zaune. Ta sake karantawa daga farko "Malama yau kwana hudu da mutuwar mijina, wayarshi na hannuna tun rasuwar, bukatar kudi ta taso da yasa na bude wayar tunda nasan pin dinshi, aka cire kudin, wallahi Malama na yarda da mijina, akwai yarda sosai a tsakaninmu da soyayya da in zan bada labarinta sai wasu sunce karya nakeyi, lokacin da aka kawomun gawarshi da yake hatsari sukayi sumana hudu, har aka rufoshi bansan inda kaina yake ba, amman kinganni yanzun haka naci na koshi harma na hau social media. Kewa ta sakani bude social medias dinshi harna fada Snapchat, na gano abinda ya tsaida mun hawayena ya busar mun da zuciyata. Allaah Ya isa tsakanina da mutumin nan, wallahi ko darajar yara banajin zan iya karayi masa addu'ar samun Rahma, maha'inci, makaryaci..." Kasa karasawa Maryama tayi saboda jikinta da taji yana rawa, wanne irin masifa ce wannan taje ta ganowa kanta? Anya wannan matar tasan mutuwa kuwa? Anya ba dimuwar mutuwar bace ta sakata wadannan maganganun? Ta ajiye wayar ta kwanta, sai kuma ta dauka wani irin tsoro na ratsata, saboda yara take sakawa wayarta Pin, musamman ma Rauda, tayi fadan harta duka ta hada dashi, amman data ajiye wayar saita dauka taje tanayi mata game, yanzun nema ta huta da Haris ya siyawa Rauda din wasu irin games tunda ya kula abinda tafi so kenan. Ta kalli wayar, tasan bata da wani abu da zatace tana gudun a gani. In ba hirarsu da Khairi ba, shima kuma sirrikane da suka shafesu, sune zatace bataso wani ya karanta saboda sirrinsu ne, abune daya shafesu, kuma ko gulmace bata da abokiyar yinta sai Khairin. Yanzun idan itama mutuwa tayi fa haka za'a samu wani cikin 'yan uwanta koma Haris ya iya zama ya bude chat din nan ya karanta ko? Ta karewa dakin kallo, da gaske ne da akace mutuwa mai tonon silili, har dakin ma haka za'azo ayi masa filla-filla, idan akwai wani abu da take boyewa ma sai an bankado shi, tunda mutuwar ita ba sallama takeyi ba balle ace zata baka lokaci kasan ya zakayi da duk wani abu da bakaso a gani. A zamanin da muke kuma, wayoyinmu sune wani abu guda daya da yake dauke da sirrikanmu fiye da komai, fiye ma da kowa namu. Suma ba zasu tsira ba, koyane za'a samu mutum daya da yasan mabudin sirrin wayar, idan an bude, iya inda za'a tsaya da bincikenta Allaah ne kawai zai sani "Inalillahi wa ina ilaihi raji'un" Maryama ta furta a fili, sai gashi tana goge chatting dinsu da Khairi, tana tanin kamar itama mutuwar na iya yi mata dirar mikiya. Haka ta dinga juyi tana tuna mutumin nan kamar ta sanshi, sai take hasashen idan iyayenshi basu da rai kuma fa? Yaranshi ko sunyi girman da zasuyi masa addu'a? Su roka masa yafiyar Allaah a cikin koma menene matar tashi ta binciko daya sakata yi masa wannan tonon sililin? Ko zata huce wata rana ta yafe masa? Kai in akace mutuwa ma ya kamata fa ta kori komai, wanda ya mutu meye ya rage masa? Tashi ta kare fa kenan, komai ma daya aikata anan ya tafi can inda zai tarar dashi, ya kamata a tausayawa mamaci a nata tunanin. Wannan abin ya tsaya mata matuka, dan har Haris saida ya kula da rashin kazarniyarta a ranar, yayi mata magana tace masa babu komai, sai bai dameta ba, yasan takan shiga irin wannan yanayin in tana jego, yana dai saka mata ido sosai saboda ko zaiga alamomin postpartum depression da mata da yawa kanyi fama dashi. Washegari da safe yana sauri ya fita, ya ajiye su Fa'iza a makaranta, sai lokacin ne ta kula daya bar wayarshi a gida, yana barinta sau babu adadi, amman yau dai tasan mantawa yayi. Wayarshi ko password babu, yanda ta kada Haris ta rayashi yaki harkokin social media din nan. Instagram ma ita ta bude shi a wayarshi sai take tayashi posting din wasu cikin ayyukan hotunanshi. Daga karshema ta mayar da account din kan tata wayar, dan yafi mata saukin managing, yake cewa dole ne ya dinga bata albashin wannan aikin suna dariya. WhatsApp kuwa batasan me yasa ya bude ba, tunda sai kayi masa magana hamsin baiko duba ba balle kayi tunanin zai baka amsa, yafi sauki kayi masa text ma. Yau da ta dauki wayar sai abinda ta gani jiya ya fado mata, sai taji zuciyarta tayi wata irin bugawa kamar zata fado daga kirjinta, hannunta har rawa yakeyi lokacin da taga Snapchat din a wayarshi, duk wayoyi suna zuwa dashi, itama akwai a tata, tana ma dan shiga taita gwada filters din kai, amman bayan nan bata komai dashi. Tana budewa sai taga alamar Haris ya bude account ne, duk wani gargadi da kwakwalwarta takeyi mata, saita bar zuciyarta tayi mata fatali dashi, jikinta ya dauki dumi alamar zazzabi na kwankwasa mata kofa. Sakkonni, sakonni da zatace sunfi dari, mata, dukka sakkonin sunayen matane, wasu asalin sunansu, wasu kuma wani suna ne daban, tasan zuwa yanzun ba iya jikinta da kayan cikinta bane suke kadawa, har ruhinta ma rangaji yakeyi, ta bude na farkon, maganganun karshen ta duba, maganar yarinyar ce da tayiwa kanta lakabi da "Lush" "See you 4pm din" Daga sama kuma maganar Haris dince, sunan hotel ne da kuma lambar daki. Ta fice daga chat din, bata san iya awannin data dauka ba, amman saida ta duba duk wani chat da yake kan Snapchat din Haris, zazzabi mai zafi ya rufeta, sai kawai hotonshi da Autumn ya fado mata, sai ta dinga harhada kwatankwacin wannan hoton da wannan kwamacalar da ta gama gani yanzun, tana kuma ajiye Haris a cikin kowanne, sai taji jiri na dibarta daga zaunen, data kwanta ma dakin wulwula mata yakeyi "Ke dai babu ruwanki da wayarshi, ai in kina nemawa kanki zaman lafiya ki kiyayi wayar miji" Haka tasha gani ana ba mata shawara, har karamin tsaki takeja idan tagani, musamman idan Haris ya bar wayarshi a gida. Ashe itace sakaran, basu da takewa kallon basu yarda da mazansu bane ba, ita data yarda Haris zai iya barin mata kamar yanda ya bar wiwi, zai barsu saboda ita, ya barsu saboda ita, haka take tunani, musamman da bai bar mata wata kofa da zatayi wannan tunanin ba. Tana nan kwance ko sallar azahar ta kasa tashi tayi taji alamar shigowar Haris din, da sauri taja jikinta ta shige bandaki, ta saka mukulli daga ciki, tana jinshi ya shigo dakin "Maryamm zan fita, sai bayan Magriba zan dawo..." Yayi maganar bayan ya jinjina kofar bayin nata yaji ta saka mukulli, saita bude famfo dan yayi tunanin wanka takeyi "Sauri nakeyi" Ya sake fadi, a zaune take kan sink, sai taji hawayen da taketa rikewa sun balle mata, tana nan zaune har aka kira la'asar, ta mike tayi alwala, data fito ma ta fara gabatar da azahar, harta idar da duka sallolin bata daina hawaye ba, dakyar ta samu ta tsayar dasu bayan ta saka hijabinta ta dauki mukullin mota, tunda Fa'iza ita ta dawo tun dazun, kuma alhamis ce ba Islamiyya ke akwai ba, su Awwab ma ta tabbata suna gidan Hajiya Rumana ne sai kuma Asabar zasu dawo saboda islamiyyar da sukeyi nan cikin unguwar ne, sai bayan ta shiga mota ta fice ne ta kira Fa'iza a waya tace mata in Naadir ya tashi ta hada masa madararshi, wani irin tsotso gareshi, ita kuma wannan haihuwar bata da ruwan nono sosai, dole tasa suke hada masa da madarar. Babu wani tunani, da tambaya ta ganta a kofar hotel din nan, ta fito daga motarta da tayi parking daga tsallake, idanuwanta har sun kankance saboda kuka da tashin hankalin, inda ma za'ace me takeji ko kasheta za'ayi ba zata iya misaltashi ba. Tana ganin yanda yamma take karayi, ga kuma kafafuwanta da suke mata barazanar kasa daukarta har lokacin, amman haka ta cigaba da tsayuwa, sai ga abinda take jira din ta tabbatar, motar Haris ta danno kai ta fito daga hotel din, duk da gilasan a sama suke, kuma irin wanda na waje baya iya ganin na cikine "Motar marassa gaskiya kenan" Haka 'yan gidansu suke yiwa masu wannan gilashin lakabi, suyita dariyar abin, yanzun kuwa ko daya babu nishadi a ciki data tuno, tata motar ta shiga tana binshi a baya, hanyar gida ya nufa, itama kuma gidan tayi daman, tana kallon yanda ya kara rage gudun da yakeyi yanayi mata fitila alamar ya gane tata motar, sai kawai tayi overtaking dinshi ta wuce da wani irin gudu kamar zata tashi sama, batayi mintina goma da shiga gida ba shima Haris din da yake tunanin abinda zai fitar da ita batare da ta sani ba, kuma ta ganshi ta wuce tana sharara wannan gudun yana kara hauhawar bacin ranshi. Har kiranta yayi a waya ta karaci ringing bata daga ba. Jikinshi har bari yakeyi sanda ya shiga cikin gidan, ya karasa har dakinsu inda ya samu tana birkito kaya, duk wanda hannunta yakai sama, daukowa takeyi tana jefawa kan gado, wasu na faduwa kasa batare data damu ba "Maryamm...." Ya kira, mamakin abinda takeyi din na danne bacin ran da ya shigo dashi, ya sake kiran sunanta amman bata kulashi ba "Magana nakeyi miki fa, meye haka? Me kike? Kuma daga ina kike?" Dan akwai hijabi a jikinta har lokacin, sai ta kalle shi da idanuwanta da suka rine, wasu hawayen na sake zubo mata "Daga inda kake" Ta amsa, da wani sabon mamakin yace mata "Daga inda nake kuma?" Bayan ta kara watso wasu kayan ta jinjina masa kai "Eh daga inda kake, hotel din da kake, dakin dai daka shiga room 305 shine na kasa karasawa" Yaji wani abu ya tsirga masa, musamman yanda ta tsura masa ido "Maryamm" Kayan data dibo shi ta watsawa wannan karin, ya taka har inda take yana kokarin kamata, ta hankade shi "Karka tabani, wallahi zan iya maka illa inka tabani...mazinaci...mazinaci kawai...ashe baka daina ba? Da yaranmu, da girmanka, ni ina nan na killace kaina, inata tattalinka, ashe kana waje kana zubar mana da mutunci...." Take fadi numfashinta na harhadewa saboda maganar takeyi cikin kokarin daga murya da shanye kukan da takejin kamar ta rusa hadi da ihu. Wani akwati ta juya ta janyo, batare data zuba kayan nan data fito dasu ba taja akwatin zuwa falo, Haris yayi yunkuri rikewa, ta juyo ta wulwula akwatin nan tana maka masa shi, ko yanzun daya biyota rike yake da hannunshi na haggu da ko bai karye ba to tabbas ya samu matsala, dan ya sage masa nan take, azaba yakeji har tsakiyar kanshi, tashin hankaline yasa yake biye da ita "Dan Allaah Maryamm, ki tsaya muyi magana" Ta juyo tana sake daga akwatin, ita kanta data janyo shi ba zata tuna meye a cikinshi bama, babu shiri ya matsa baya "Dan Allaah" Wani irin kallo takeyi masa hawaye na zubo mata, lokacin ne kuma akayi sallama, Hajiya Rumana ta daga labulen da yake kofar ta shigo, sabe da Rauda a kafadarta, ta kalle su, yanda suke tsayen, gidan ba bakonta bane ba, shisa ta wuce dakin Fa'iza ta sameta tsaye da goyon Naadir tana dan danna waya, bata ko amsa gaisuwarta ba ta kwantar da Rauda da take bacci. Tunda suka koma ta ganta tana ta kwanciya, saida ta tabata taji zazzabi a jikinta, dole ta dauketa zuwa asibiti, inda akace malaria ce amman babu yawa, saidai wata Nurse ta taimaka mata ta rike Raudan akayi mata allura, tasan ba zata iya sakata tasha magani ba, dan allurar ma kukan da Rauda tayi har yanzun tana jinshi har tsakar kanta, sai kawai ta dawo da ita. Falon ta koma ta samu Maryama ta daga akwatin nan tana shirin sake kwantarawa Haris saboda takai kofa ya riko mata Hijabi "Kashe shi zakiyi Maryama?" Tayi maganar da madaukakin mamaki "Wallahi ka sake tabani saina buga maka shi, ka kyaleni, gidanmu zan tafi" Cewar Maryama da hawayenta ke zuba kamar an bude famfo, ganin Haris din na shirin sake riketa yasa Hajiya Rumana ta karasa da sauri tana watsa masa zagi "Dan ubanka saita kwala maka ta kasheka tayi mana asara ko?" Ta karasa tana hararar Maryama "Ka rabu da ita ta tafi gidan nasu mana, sai me? In bama tsinannen naci irin naka ba, sai kace ita kadaice mace a fadin duniyar nan, daka dauki shawarara tuni har zata tsaya tana maka wannan barazanar ne" Cikin wani yanayi yace "Dan Allaah Mami, nine nayi mata laifi" Hajiya Rumana taja tsaki kamar harshenta zai rabe biyu "Dan Allaah ki bata hakuri, kice ta tsaya muyi magana" Tsakin ta sake ja tana masa kallon takaici kamar tana gab da kwada masa mari, badan tana gudun kar Maryama ta kassara matashi ba, data matsa ai ta barta ta kwantara masa akwatin nan "Laifin me kayi mata? Ko laifin kayi mata saita nemi kasheka?" Wannan maganar tasa wata dariya da kuka suka kwacewa Maryama a lokaci daya, tsaye take waje daya, amman ji takeyi dakin na zagayawa da ita "Me kayi mun? Ka fada mata" Idanuwanshi ya saka cikin nata, wannan maikon yau na roko ne, ta kai hannu ta share hawayenta da sauri, wasu na kara zubowa "Ka gaya mata Ganjaa, wallahi inka bude bakinka ka fada mata abinda kayi mun zan zauna muyi magana..." Wani irin shiru ya ratsa dakin, irin shirun nan da akewa lakabi da kwatankwacin na ratsen mutuwa, kafin karar akwatin da Maryama taja ya kawo karshen shi "Maryamm" Ya kira muryarshi na rawa, ganin harta daga labulen dakin yasa shi fadin "Hotel naje..." Da sauri idanuwanshi akan Maryama da tayi tsaye, sai kuma ta juyo, kallonshi ta sakeyi, shima ita yake kallo, Hajiya Rumana kuma tana kallon su duka biyun "Kaje kayi me?" Cewar Maryama cikin wani irin rauni da yayi barazanar kayar da Haris din "Mami hotel naje...I....I cheated on her" Tayi wata dariya mai sauti, wai yaushe ne aka fara yiwa zina kwaskwarima? "Fassaramun I cheated on her" Cewar Hajiya Rumana cikin tashin hankali, inda ma sun saurara da sunji yanda cikinta ya kwaso wata kara, ya kalli Maryama, yasan kafiyarta, ya dawo da idanuwanshi kan Hajiya Rumana, Maminshi, Maminshi da laifukanshi kullum masu saukine a wajenta, Maminshi da ko zai muzanta a idon kowa yasan in yaje wajenta zai samu mafaka, zata lulluba masa bargon suttura "I...I slept with someone" Yayi maganar yana jin nauyinta bayan ya furta, kuma nauyin ne ya danne Maryama har saida ta dafa bangon da ke kusa da ita tana dan runtsa idanuwanta, ji take kamar zata yanke jiki ta fadi, karar da taji ce tasa ta bude idonta tar, mari ne, marine Hajiya Rumana ta wanke Haris dashi, da alama kuma mamakin marin yakeyi shi kanshi da aka wankawa balle kuma Maryama da take jinta kamar tana yawo a mafarkine "Ai dama shaye-shayen yakeyi da sauki, amman kinsan girman daudar zina Rumana? Shine zan dauki 'yata in bashi" Maganganun Alhaji Modu suka dawo mata ranar da sukayi abinda zata kira da uwar-watsi. Kuma maganar tayi mata zafi matuka, harta kwanta tana share hawayenta ranar, ashe Modu zaiqi jininta haka? Harya danganta mata Haris da mafi daudar aiki, saboda baya son bashi Aise. Ita kuwa meye zai hada jininta da zina? Ba'a shaidar mutum amman ko Qur'ani aka bata zata dafa kan cewa Alhaji Mustafa bai taba ko da kusantar zina ba, balle kuma ita, duk yawan kasashen da tayi ko gaisawa bata tabayi da wani da ba muharraminta ba, haka tayi aurenta cikin mutunci, to meye zai hada zuri'arta da wannan daudar? Dan a lokacin ta manta da wata kaddara balle kuma jarabawar da babu mahalukin da yafi karfinta, ta dai san babu wani abu da zai taba wanke mata wannan abin da Modu ya fada mata. Dan ko a yanzun zumuncinsu yaja baya matuka, sai abu ya zama dole ne yake hadasu, tun yana kokarin shi harya hakura. Kenan gaskiya ya fada mata? To wai laifukan Haris guda nawa ne da soyayyarshi ta rufe mata ido daga gani, ta gabansu Maryama da take cira kafa dakyar tazo ta wuce ta shige dakinsu, ai ta rantse masa, duk da batayi zaton zai bude bakinshi ya furta wannan maganar a gaban Hajiya Rumana ba, kuma marin da tayi masa taji shi har zuciyarta, muzancin da take gani ya mamaye ilahirin jikinshi kafin ta shige daki, irin shine sak ya mamaye ta Wai fa wannan Labulen da Haris yaja musu yayewarshi a gaban mahaifiyarshi ne... A gaban matar da take da yakinin idan da mutane zasu taru su nemi kalle mata Haris a wannan halin tsiraicin zata cire mayafin jikinta ne ta rufa masa, su raba tereren tare... To ina ga ace a idon sauran mutane ne? Anya akwai kaddara mai nauyi irin Allaah Ya jarabeka da zama da mazinaci? 43 MARYAMA Tun ranar da abin ya faru, tasan lokacin da Haris ya shiga dakin dare yayi sosai, duk kuwa da bata duba lokaci ba. Daya hawo gadon sai ta mike daga kai ta dauki pillow dinta "Maryamm" Batare data kalle shi ba tace masa "Ba zan iya kwana waje daya da kai ba, dan Allaah, kabarni, yau kabarni dan Allaah" Kuma a taurin kai irin na Haris, musamman idan fada takeyi dashi, a wannan ranar ba zatace ga abinda yayi aiki ba, yanayin muryarta, ko yanayin fuskarta, sai da ta kalle shi ta kara kallonshi lokacin da yace mata "Ki dawo ki kwanta" Sai shi ya dauki pillow din, tana kallonshi ya bude cikin wardrobe dinta inda take ajiye zannuwan gado, ya dauko guda daya, ya shimfida a kasa, ya ajiye pillow din, sannan ya kara dauko wani ya kwanta. Sai dai duk yanda tayi kokarin ganin tayi bacci, abin saiya gagareta. Akance kuka shi yakeyin kanshi, in yazo baka sanin sanda zakayi, to ita dai yau tanajin alamar kukan, tun daga kasan zuciyarta inda wani abu yake ta kaiwa da kawowa, amman idanuwanta sunki ba wannan abin hadin kai balle ta samu tayi kukan. Da yake ba bacci tayi ba, akan kunnenta aka kira sallah, saida ta tashi ta shiga bandaki ta gama abinda zatayi ta dauro alwala ta fito tukunna ta tashi Haris "Lokacin sallah yayi" Ya jima a kwance, tanajin dai idanuwanshi na mata yawo a jiki, wannan idanuwan nashi. Sannan ya tashi, da yayi alwalar fita yayi. Tana idar da sallolinta da duk wani azkar da zatayi saita fita zuwa kitchen. Kwanansu tara a haka, ya gwada yayi mata magana babu adadi amman batace masa komai, bawai bataso tayi magana dashi bane, kawai ko ta bude bakinta babu abinda zata iya cewa, kanta yayi nauyi, wani irin nauyi na ban mamaki, amman duk nauyin da yayi batajin komai a cikinshi, bata iya wani baccin kirki, zata tashi da safe, tayi duk wani abu data saba, har wanka zatayi sai dai batajin karfin yin wasu abubuwan bayan wadannan, ko yaran sun san wani abu yana damunta, dan haka Fa'iza saita janye su, su bata space din da suke tunanin tana bukata. Wata safiya ta tashi saiga kiran Alhaji Sa'id, ta saba kullum saita kirashi ta gaishe dashi, suyi hira sosai, amman kwana wajen nawa, wayar ma ba dauka takeyi ba "Abba..." Ta furta bayan ta daga "Mairaman Abba, kina lafiya dai ko?" Tayi shiru, so take ta amsa, tace masa tana lafiya, amman labbanta sunyi mata nauyi da wannan karyar tun kafin ta furta "Banajin dadine Abba, amman bansan me ya sameni ba" Shima shirun yayi na wasu dakika, kafin a hankali yace "Kina addu'a Mairama?" Ta daga kai "Inayi, kullum inayi" Dan babu wani abu da ta fasa ko a kwanakin, duk wata addu'a da nafila da takeyi bata fasa ba "Zan fito ba jimawa, zan biyo in dubaki In Shaa Allaah" Ya kuwa biya din, kamar yanda yayi alkawari, dakyar ma ya shiga cikin falon, duk abubuwan da ta kawo ta jera masa, ruwa kawai yasha, tanajin yanda yake ta kallonta, kuma a tunanin Maryama ta aro murmushi ta dora saman fuskarta, sai dai idanuwanta fayau suke, sai kace wadda bata da wadataccen jini. "Allaah Yayi miki albarka Ya sanyaya miki Mairama" Cewar Alhaji Sa'id cike da damuwa, zuciyarshi ta takure waje daya, a karo na farko da yayi dana sanin wannan sadaukarwar da yayi, a karo na farko da soyayya hadi da tausayin Maryaman ya danne girman abotarshi da Alhaji Mustafa, a yau bayaji baya kuma tunanin komai sai 'yarshi. Har bakin mota Maryama ta rakashi yanata tsokanarta sai dai ta kasa mayar masa yanda ta saba, kamar an sauya masa ita haka yake gani, ya shiga mota, harya kunna, ita kuma ta juya da nufin ta koma cikin gida, sai kawai taga wani duhu ya gifta mata, batasan takai kasa ba, duhu ne daya gifta, bai bata damar sake bude idanuwanta ba balle tasan cewa yanke jiki tayi ta fadi, balle kuma ihun Alhaji Sa'id da fitowarshi daga mota. Shiya dauketa ya saka a bayan motar, ya manta da cewa tana da aure balle kuma yayi tunanin akwai jaririn da bai rufa watanni hudu da haihuwa ba a cikin gidan, baya ganin komai sai 'yarshi da tsoron ta rasa rayuwarta. Su Maryama Dialogue suke zuwa, can suke da kati, amman shi Alhaji Sa'id da nashi iyalan a 44 da kuma Frontiers suke da kati, sai kawai ya nufi 44 din da ita. Sai bayan yaje an karbeta dan bata taimakon gaggawa tukunna ya samu ya kira Hajja yana fada mata abinda yake faruwa "Inalillahi wa ina ilaihi raji'un, meya sameta?" Cike da damuwa ya girgiza kanshi "Bansani ba, faduwarta kawai nagani, tana numfashi, naga kirjinta na dagawa, amman duk da haka...na kashe 'yata ko Asma'u? Me yasa na aura mata yaron nan? Na kashe 'yata na raya dan wani ko?" Bata amsa tambayoyin shi ba, sai tace masa "Ina Naadir din?" Cikin rashin fahimta yace "Naadir?" Da sauri tace "Eh..." Har lokacin dai bai gane me take nufi ba "Bansani ba, dauko ta kawai nayi muka taho" Sai yaji ta sake yin wani salatin kafin ta kashe wayar. Ya dade a tsaye a wajen, dan sai bayan ita Hajjan sun iso asibitin harda Khairi da take goye da Naadir din da itace ta biya ta dauko shi, dan har sanda taje yanata bacci ne. "Ina Maryaman?" Khairi da har fuskarta ta kumbura da alamun kuka tasha ta tambaya "Tana ciki" Alhaji Sa'id ya amsa, sun kuma sake kwashe wajen awanni biyu a asibitin nan, banda jinin Maryama da yayi wani irin hawa, sai kuma yanayin bugun zuciyarta da suka kira da palpitation, su kansu ba zasuce ga abinda yake damunta bayan wannan ba, dan ko motsi batayi ba, sun kara mata da alluran bacci a cewarsu tana bukatar hutun. "An gayawa mijinta kuwa?" Hajja tayi tambayar "A fada masa yazo yayi mata me? Ko ta farka ta ganshi ya karasamun ita?" A tsayin shekarun aurensu, in ta daga hannunta zata kirga adadin lokuttan da taga bacin ran Alhaji Sa'id, kuma kullum sai tayi addu'ar Allaah Ya kara masa hakuri, saboda mutum ne shi da bai iya bacin rai ba, ko dan ance daman haka mutane masu hakuri suke "A'a karkace haka, tunda ita dai batace sunyi fada ko makamancin haka ba" Wani irin kallo yayi mata "Saiki fadamun wata matsala da zata sakawa Mairama hawan jini banda kaddararren auren nan dana dora mata..." Shiru tayi, sai ta kalli Khairi da ta dan daga mata kai a hankali, itama kuma da yake tasan halin Abban nasu, sai da tabar wajen tukunna ta kira Haris "Muna asibiti da Maryama bata da lafiya" Ya danyi shiru kafin ya tambayeta wanne asibiti, ta fada masa, saiya kashe wayar. Fa'iza ya barwa message tunda akwai waya a hannunta, yasan direbansu zaije ya daukesu daga makaranta, karsu koma gidan suga babu kowa. Tukunna ya nufi asibitin, zuciyarshi ta buga, ta sake bugawa da yanda Alhaji Sa'id ya kalleshi, kuma rudanin daya shiga bai hanashi gane bai amsa gaisuwar da yayi masa ba. A cikin wannan tsoron ne ya kira Alhaji Mustafa ya fada masa suna asibiti da Maryama, duk kuwa da a ranar Alhaji Mustafan yana Abuja, haka ya jerawa Alhaji Sa'id kira har hudu bai daga ba. "Na kira Sa'idu har sau hudu bai daga ba...lafiya kuwa Haris? Ko dai jikin nata yayi tsanani ne?" Akan idon shi Alhaji Sa'id ya amsa kira dazun da suka fito sallar la'asar daga masallacin da yake wajen asibitin, sai gashi yana shirgawa Alhaji Mustafa karyar da baisan daga inda tazo masa ba "Kilan wayar bata jikinshi ne Baba, ko tana mota, ko bai fito da ita ba...nasan da yaga kiran zai sake kiranka, nima na fito siyan wata allura ne da aka rubuta, jikin da sauki bacci take tayi" Duk da haka akwai yanayin damuwa a muryar Alhaji Mustafan har sukayi sallama, ko a wanne irin yanayi, tun bayan shigowar wayar hannu, bai taba jerawa Alhaji Sa'id kira har hudu bai daga ba, anya yama taba katarin kiranshi baya kusa da wayar kuwa? Haka kawai abin yake ta damunshi. Washegari kuwa sai gashi a garin Kaduna, kuma har lokacin Maryama bata tashi ba, su kansu likitocin sun fara damuwa, dan duk wani kokari da zasuyi wajen ganin sun farkar da ita ya gagara, ga jinin nata ya fara sauka ba kamar sanda aka kawota ba, haka babu zazzabi a jikinta, amman taki tashi. Abu kamar wasa, kwanan Maryama hudu a cikin wannan yanayin, 'yan uwanta mata kuwa babu mai lallashin wani, har Hajja duk karfin halinta sai gashi tana share hawaye. Kallo daya zakayiwa Haris kasan kwanciya ce kawai baiyi a asibitin da sunan marar lafiya ba, amman tare suke wannan jinyar da Maryama, ya fita hayyacinshi gabaki daya, musamman yanda kowa yake masa wani kallo, kallon da yasan duk da basu da cikakkiyar hujjar yi masa, kallo ne daya dace dashi, kallo ne na tuhumar laifin da yasan ya aikata, duk yanda za'a zagaya a zagayo shine sanadin wannan kwanciyar ta Maryama "Kayi mata wani abinne Haris?" Alhaji Mustafa ya tambayeshi a safiyar ranar "Tunda nake da Sa'idu irin wannan shirun bai taba gifta mana ba, ko fadan kuruciya Sa'idu bai taba biyemun munyi ba, ko matana basa hakuri dani yanda yakeyi...me kayi Haris?" Kanshi kawai ya sake saddawa kasa, to me zaice? Aiko hauka yake yana buge-buge yasan ba zai taba bude bakinshi yace wa Alhaji Mustafa ga abinda yayi ba, shirun nashi ne yasa shi fadin "Inalillahi wa ina ilaihi raji'un...me kayi haka Haris? Wanne abu mai girma kayi da ya kure kawaicin mutum irin Sa'idu?" Shirun dai ya sakeyi, Alhaji Mustafa ya sauke wani numfashi cike da damuwa "In Shaa Allaah ba zaka zama sanadin raba alakar da ta kullu tun kafin in san zan sameka ba, ba zaka rabani da abokina ba Haris, In Shaa Allaah ba zaka rabani da abokina ba" Kuka Haris yake so ya fashe dashi, irin kukan nan da 'yan yara sukeyi idan sun fara gane yawo suka ga an fita an barsu, kukan da sai yayi juyi sannan ya tumu da kasa, ya mirgina daga farko zuwa karshen bango, kukan da kararshi zata kidima duk wani mutum daya damu dashi, yanda zasu rugo su rufu akanshi ana turereniya wajen dagoshi a lallashe shi. Sai dai a yanda kowa yake kallonshi din nan yasan babu wanda zai lallashe shi inma kukan yayi. Yana ganin irin kallon da Awwab yake binshi dashi a kwanakin nan "Meya sameta?" Haka yace masa "Bata da lafiya ne Awwab" Kai ya jinjina masa "Eh nasani, meya sameta?" Ya sake tambaya, kafadu kawai yadan daga masa tunda babu damar ya amsa da "Ni, nine na sameta" Ranar kwana na shida a asibitin Maryama ta bude idanuwanta, Hajja, Khairi da sai anyi da gaske take barin asibitin nan kullum, kuma da kuka itama tana dakin, sai Haris da a wajen Hajja ne kawai yake ganin sassauci, itace take amsa gaisuwarshi da fara'a, kuma take kulashi. Kuma yana ganin saita kalli Alhaji Sa'id yake amsa shi da "Lafiya" A halin yanzun ma Alhaji Mustafa fushi yake dashi, ko dan tunda Hajiya Rumana ta dauki wani irin fushi da bai taba gani ba, waye ma ba zaiyi fushi dashi ba? Yau ya tabbata inda akwai wiwi a jikinshi ba zai san lokacin da zai busa ba, ya manta rabon da ko tunaninta ya gifta masa sai da safiyar yau din. Sai kuma yanzun da Maryama ta kare musu kallo su dukansu, Hajja ta kira sunanta, ta kalleta tace mata "Ina nake? Wacece ke?" Da ta fita da nufin kiran likita Haris ya tashi ya riko hannun Maryama data fisge da sauri tana fadin "Subhanallahi, meye haka? Waye kai? Me yasa zaka rikemun hannu?" Wani abune mai kama da aradu yaji ya rikito masa yana neman danne masa numfashi, saima da likitoci biyu suka shigo suka korasu waje "Ina Abbana? Ku kiramun Abbana" Shine abinda Maryama take fadawa likitocin tana sake maimaitawa, babu shiri aka kira Alhaji Sa'id. Ta kuwa rikeshi tana sakin wani irin kuka daya kidima shi "Kinganni nan Mairama...gani nazo" Cikin kukan tace "Wasu ne suke tamun magana tun dazun Abba, ban sansu ba" Dakyar ya samu ya lallasheta, ranar ne kuma aka maida case dinta wajen wani babban likitan kwakwalwa saboda sai a ranar suka gane abinda yake damunta ciwo ne da yake da alaka da kwakwalwarta "Maryamm bata ganeni ba Hajja, bata sanni ba tace" Haris yake fadi cikin tashin hankalin da yake ciki yasa Hajja ta riko hannunshi "Ba kai kadai bane bata gane ba Haris, baka ga harda ni ba" Sai ya girgiza mata kai, kukan daya kwana biyu yana nema ya taho masa, hawaye wasu na ture wasu "Haka tace waye ni Hajja, baki ga idanuwanta ba? Bata gane ni ba har idanuwanta sun nuna haka, riketa fa nayi ta tsorata..." Yake fada cikin fitar hayyaci, gashi ya kasa tsaida hawayenshi, ita kanta Hajjan hawaye taji sun zubo mata, ta sharesu cikin dabara tana sake riko hannun Haris, sai kawai ya zame ya durkushe a wajen, ta tsugunna itama tana masa rikon da uwa zatayiwa danta, kuka yake har jikinshi na amsawa "Kowa fushi yakeyi dani, muna fadanmu Hajja, mun saba fadanmu mu shirya, Maryamm ce, ta saba yafemun...amman kowa fushi yake dani, nina ja mata ciwon ko?" Hajja batace komai ba, dan bubbuga bayanshi takeyi kawai, sun dauki kusan mintina ashirin kafin ya samu ya natsu "Kaje gida kayi wanka Haris, saika kara samu natsuwa ka dawo...tunda kaga sun hana kowa ya kara shiga wajenta" Ba karamin fama Hajja tayi ba kafin ya yarda ya tafi gidan. Duk wani bayani da likita yayiwa Alhaji Sa'id shi yayiwa Hajja "Sunce postpartum depression ne, amman basu gama tabbatarwa ba..." Hajja ta jinjina kai "Shi yaja ta kasa gane mu?" Wannan sunce masa ta samu short term memory loss ne, amman bana komai da komai ba, tunda ta gane shi, ta kuma gane kanta, duk da bakomai ba, ta manta tana da aure, balle wasu yara. A hankali komai zai dawo mata, amman basu san yaushe hakan zai faru ba. Kai Hajja ta jinjina, cikin tarin karfin hali tace "Allaah Ya dafa mana" Tunda tasan babu abinda Yafi karfin Ubangiji daya dorawa Maryama wannan ciwon kowanne irine. Ciwon da zaka kasa gane mahaifiyarka, ka kasa gane yaranka? Ai ba karamin ciwo bane ba, tunda ita bata tabajin irinshi ba sam, tasan dai akwai hauka, amman wani ciwo daban na kwakwalwa bayan wannan, sabon abune a wajenta. Sabon abinda zata dukufa gaban Ubangiji akanshi. Aikuwa sai gashi dakyar aka samu Maryama take shayar da Naadir. Duk kuma yanda aka hana Haris shiga wajenta sai da ya rokesu suka barshi yake tsayawa ta window din dakin yana ganinta "Ba zan shiga ba, Allaah ba zan shiga ba, kubarni anan ina ganinta, dan Allaah kubarni..." Barinshi sukayi kuwa, wasu kwanakin bakwai Maryama ta sakeyi a asibitin kafin aka sallamesu da kashedi kala-kala dan har lokacin Alhaji Sa'id kawai take ganewa. Ko da akayi sallamar shiya kamata ya saka a motarshi, Haris na biye dasu a tashi, yanata mamakin dalilin da zaisa Alhaji Sa'id ya nufi hanyar gidanshi da Maryama, haka dai ya cigaba da binsu har suka isa. Ko inda yake Alhaji Sa'id bai kalla ba, ya sake kama hannun Maryama suka shiga ciki. Shima Haris ya rufa musu baya, nan falon suka zauna su duka, Haris nata kallon agogo, ganin har ana shirin yin azahar yasa shi fadin "Abba zamu wuce gida..." Alhaji Sa'id yayi masa wani kallo mai tarin ma'anoni kafin yace "To madalla, ka gaida gida" Yayi tsam yana rasa abinda zaice, dan likita da kanshi yayiwa Maryama bayani, ga Haris, shine mijinta, haka su Hajja, dama su Awwab, duk da bawai ta ganesu bane saita daga kai, ta rasa yanda zatace duk da bata gane Haris ba inta kalle shi sai taji kirjinta yana mata zafi. Mikewa Haris din yayi "Maryamm muje" Kafin ma ta amsa Alhaji Sa'id ya rigata da fadin "Taje ina? Ai ita ta dawo gida kenan, kai dai ka tafi abinka" Haris ya kalli Alhaji Sa'id, ya kalli Maryama data kara matsawa jikinshi, ya kuma kalli Hajja cikin neman taimako, data kalli Alhaji Sa'id sai yace mata "Wallahi babu inda zataje" Kuma yanda yayi maganar su duka sunsan ba zaiyi kaffara saboda su ba "Kaje Haris zamuyi magana" Haris ya daga mata kai batare da yace komai ba, ya dai dan kara tsayawa jim, ya kalli Maryaman da ta dauke idanuwanta. Sannan ya juya ya fice daga dakin. Sai dai daga nan gidan, makarantar yara yaje ya bada uzurin da yasa aka bashisu, ya biya ya dauki Fa'iza itama. Ya kaisu gida yana ce musu "Fa'iza ki hada muku kayanku, Maryamm tana gida, an sallameta zan kaiku can wajenta" Kayan nasu Fa'iza ta hada musu, harda extra uniform duk ta daukar musu. Sai dai ta tsaya ta dafa musu indomie, daga ita sai Awwab sukaci, Rauda sai anyi fada da ita, in ba Maryama ta zare mata ido ba, wata rana harda duka sannan zata yagi abinci, Fa'iza tasan ba zata iya sakata taci abinci ba, dan haka ma ta samar mata yoghurt a fridge ta bata, shima tanata jujjuyashine a hannunta batare data bude robar ba. Haka Haris ya fito ya samesu "Kungama?" Awwab yace "Eh amman as usual, Rauda bataci komai ba, da safe ma da zamu fita black tea kawai tasha" Rauda tayi saurin cewa "Banajin yunwa...in munje zansha Tea a wajen Hajja" Haris baya iya matsa mata, musamman akan abinci tunda Maryama na cewa ya bata mata yarinya gata nan kaman tsinke saboda batason cin abinci "Tam" Kawai ya iya cewa, yau bayama jin yin magana mai tsayi. Ya sakasu a gaba suka fice daga gidan, ba karamin mamaki Hajja tayi ba data gansu gabaki daya "Hajja ina Abba?" Haris ya tambaya "Yanzun ya fita, sai dai bansan ko zai dawo da wuri ba, Maryama kuma tasha magungunanta ta samu bacci" Kai Haris ya jinjina "Zan jirashi" Zaman yayi, anan gidan yayi sallar magriba da isha'i, kuma daga shi har Rauda duk wani tayin abinci da Hajja tayi musu basuci ba, shayin suka sha, shi da madara da komai, ita kuma tasha bakin ruwan shayi sai wani cracker biscuit da Hajjan ta matsa mata taci kwara hudu. Ta tashi taje ta kwanta, tunda sun san inda suke sauka in zasu kwana gidan Hajjan. Alhaji Sa'id bai shigo gidan ba sai tara saura, ya amsa gaisuwar Haris a daqile. Ganin bashi da niyyar saurarenshi yasa Haris din mikewa yabi bayan Alhaji Sa'id daya fito daga duha Maryama, tare suka taka har sashinshi, Haris ya samu waje kan kafet din dakin ya zauna yana fadin "Abba yaushe zamu tafi gida da Maryama?" Alhaji Sa'id ya kalleshi "Sai ta warke" Ya amsa a takaice, Haris ya jinjina kai "Allaah Ya bata lafiya. Ni a ina zan zauna to?" Kallonshi dai Alhaji Sa'id din ya sakeyi "Baka da gidane Haris?" Batare da wani shakku ba ya amsa da "Bani da gida yanzun Abba, in da babu Maryamm ba gida bane a wajena" Shirune ya ratsa dakin, shiru na wasu sakanni masu yawan gaske, shirun da Haris ya kora ta hanyar cewa "Duka zamu zauna anan, inta warke saimu koma gida tare" In dai dakuna ne akwaisu a gidan, tunda kullum cikin baki suke, sannan akwai samari har lokacin, wasu dakunan kuma a rufe suke a bangarensu, sai dai ana gyarawa kullum, a mayar a sake rufewa, na samarin gidan ne da sukayi aure. Sannan wani abu daya da Alhaji Sa'id ya sani shine, har yanzun matsayin Alhaji Mustafa bai canza ba a wajenshi, kawai dai zuciyarshi taje wani gejine daya daina fifita farin cikin Haris akan na Maryama, kuma kamar yanda ya rantse, sai Maryama ta warke tas ta dawo hayyacinta, sannan sai ta bude bakinta da kanta tace ta zabi cigaba da zama da Haris ne zai bashi ita, amman muddin ta kalle shi tace ta gaji da wannan auren, zai saka ma tarin biyayyar da tayi masa albarka, zai tsaya ya karbar mata takardar sakinta a hannun Haris. Hakan kuma ba zai hana duk randa Haris yazo gidan a bude masa kofa kamar yanda za'ayiwa duk wani ahali na Alhaji Mustafa, kuma ko daga ina Haris ya fito to idan yana bukatar wajen zama, za'a share masa daki guda a bashi ya zauna "Ai gidan nan nakune Haris, ko daga ina kake kana da masauki a cikinshi" Magana ce daya kamata ta sanyayawa Haris rai, sai yaji zuciyarshi ta sake kuntata, sai yaji kamar yau Alhaji Sa'id nayi masa kallo dayane, kallon cewar danshi ne, dan wajen Alhaji Mustafa, bayan hakan babu wata alaka data sake hadasu, hakan kuma ba karamin tashin hankali bane a wajenshi. Dakin aka bashi, daya shiga ya kwanta sai ya karajin wani kunci ya lullubeshi, ya dauki waya ya kira Alhaji Mustafa, sai dai bayan sun gaisa saiya rasa me zaice masa. "Muna nan gidan Abba tare da Maryamm" Ya furta a hankali, Alhaji Mustafa yayi shiru, sai kuma sautin dariyarshi da yaba Haris matukar mamaki "Da aka sallameta can kuka tafi? Yaran fa?" Cewar Alhaji Mustafa "Abba yace saita warke zata dawo gida, shine na daukosu muka dawo nan din, inta warke duka saimu tafi tare" Dariya Alhaji Mustafa yayi ba 'yar kadan ba "To madalla, Allaah Ya baku lafiya ku duka" Ya fadi, dan da alama har Haris din yana bukatar yaga likitan kwakwalwa, daman yayiwa kanshi alkawari ba zai yiwa Alhaji Sa'id katsalandan ba, bama zaije ba balle yaji kunyarshi, yanata addu'a dai, ya kasa hana zuciyarshi yin wannan son kan, yana ma Haris addu'a karya rasa nagartacciyar mace kamar Maryama. * Kwananshi biyu gidan Alhaji Sa'id, duk kiran da Hajiya Rumana tayi masa a kwanakin nan biyu tana bankada masa zagi baije ba, sai rana ta biyun, shima daga wani aikine daya fita saiya biya ta gidan, yana shiga kuwa ta dora daga inda ta tsaya "Ai bansan Sa'idu na haifawa kai ba sai yanzun Haris, saboda lalacewa sai ka koma gidansu mace ku tare, saboda abin kunya..." Fadan takeyi kamar zata hadiye harshenta, har haki takeyi, saida ta gama tas, yana zaune yana kallonta, da ledar peanut a hannunshi, Awwab ne ya bashi, kuma tafi wata a cikin mota, sai yau ya dauka ya fasa, ita yake taci batare da yana gane dadinta ba, haka kawai yake taci, yanzun ma wata ya kara jefawa a bakinshi ya tauna, sai ya ajiye ledar a gefenshi, ya kalleta sosai "Mami kinsan ya nakeji?" Itama kallonshi takeyi, bai jira amsarta ba ya cigaba da magana "Lokacin da Baba ya auramun Maryamm, na karbi aurenta ne da zuciyata duka, kuma ban taba hango ranar da zan rabu da ita ba, saboda Baba, amman yanzun inajin ba zan iya rabuwa da ita ba saboda ni Mami, saboda ina sonta..." Yaja numfashi "Saboda tana sona, tana sona Mami, Maryamm tana sona, Maryamm ta ganni da mace kuma ta cigaba da zama dani, randa kika zo gida, bashi bane na farko, kuma bansan ko shi bane na karshe, amman nasan Maryamm zata sake hakuri, zata dawo wajena...Mami inke ce zaki hakura? In Baba nine zaki...." Da sauri tace "Haris!" Yayi shiru yana cigaba da kallonta "Na hakura Mami, tuntuni na hakura ba zaki taba son Maryamm ba, ina so kema ki hakurane saboda ba zan taba rabuwa da ita ba..." Sai bayan ya mike ne yaga Alhaji Mustafa tsaye a bakin kofa, ya karasa ya gaishe shi, sannan ya rabashi ya fice daga gidan "Yau kinji abinda kike nema ko Rumana? Ai da kin amsa shi, wallahi nasan ba zanyi kaffara ba, idan nine nake da rabin halayyar danki ba zaki zauna dani ba, ba kuma zaki rufamun asiri irin yanda Maryama ta rufa masa ba...in da zaki zauna, ki ture wannan kiyayyar taki marar tushe, ki kalli danki, ki duba Rahmar daya samu ta sanadin auren Maryama, da zakice madalla da wannan auren Rumana. Ina miki addu'a Allaah Ya yaye miki abinda yake damunki..." Yana gama maganar ya fice shima, sai wasu hawaye masu zafi suka zubo mata. Da gaske ne kiyayyarta bata da tushe? To in bata da tushe ya zatayi ta raba kanta da ita? Ya zatayi ta budema Maryama waje ko dan karami ne a zuciyarta? Tunda ta sani, gaskiya Alhaji Mustafa ya fada mata, gaskiya mai ciwo, Maryama matar rufin asiri ce, tun ranar da Haris ya bude bakinshi ya gaya mata meya aikata tasan Maryama rufin asiri ce da batayi masa terere ba, da zazzabi ta kwana saboda kaduwa da tashin hankali, amman girman kai irin nata ya hana ta saduda, ya hana ta rissina. Amman ko taso ta hakura sai taji ta kasa, musamman idan taga yanda Haris yake fifita lamarin Maryaman akanta. In ba wanda aka shanye ba, ya za'ayi yaje gidansu Maryama ya tare? Taya zata ga farin Sa'idu da ahalinshi bayan sun maida mata da soko? Ita ko yau wannan auren ya qare zatayi murna da hakan Sai dai kaddara ta riga fata... Ya zatayi da sauran rabon da yake tsakanin Haris da Maryama? 44 HARIS Kwananshi sittin da hudu, ko yace kwanansu sittin da hudu a gidan Alhaji Sa'id, shi da yaran da Maryama, a lissafe yake saboda kowacce rana jinta yakeyi kamar ba zata wuce masa ba. Kuma tun a kwana na 20 ya kalli Maryama data fito babban falon nasu, yana zaune da kofin shayi a hannunshi, yasan cewa ta dawo hayyacinta, sai dai yanda bata nuna masa ba, shima bai nuna mata ba. Tunda kafatalin 'yan gidansu, masu aure da marassa aure suka daina mamakin zaman da yakeyi a gidan, suka ma fara mantawa cewar shima ba dan gidan bane ba ya kyale Maryama, randa duk taji cewar ta gaji da zaman nasu, sai su tattara su koma. Sai dai a duk wani mafarki da tunani da yakeyi, Maryama zata same shi, zasuyi rigima kamar yanda suka saba, za kuma su shirya, sannan zasu tattara kayansu su koma gida. Ko a mugun mafarki bai hango Maryama zatayi masa wannan gangamin ba, shisa tunda ya samu waje daga can nesa akan kafet a cikin falon da yake bangaren Alhaji Sa'id,  yake kokarin ya hada ido da ita amman taki kallonshi, tana zaune ne daga kasa, kusa da kafafuwan Alhaji Sa'id din, Alhaji Mustafa na gefenshi, sai Hajja, sai kuma Hajiya Rumana da taketa hura hanci ta samu kujera mai zaman mutum daya. Ita inda tasan nan gidan zasu zo, babu yanda za'ayi ta biyo Alhaji Mustafa. Haka kawai yace mata ta shirya zasuje unguwa. Shima kuma Alhaji Mustafa din, da daddare Alhaji Sa'id ya kirashi a waya, bayan Maryama ta sameshi a daki sun gaisa "Mairama da magana a bakin nan naki" Tayi murmushi, tare suke zaryar asibiti, shi yake daukarta a motarshi, sai dai Haris ya bisu a baya da tashi motar, kuma ya zauna ya jirasu a waje saboda Maryama ta nuna bata bukatar shiga ganin likita tare dashi. Tunda ko Alhaji Sa'id din idan yaje barinta yakeyi ita da likitan nata su tattauna. Kuma tunda suke zuwa duk wata dabara da zaiyi amfani da ita wajen ganin Maryama ta bude bakinta sunyi magana, yaji matsalarta saboda yafi gane yanda zai bullowa ciwon damuwar da take fama dashi abu ya faskara, daya hadata da Alhaji Sa'id ma sai tayi dariya tana ce masa "Abba nifa na samu sauki, babu wani abu da yake damuna da zan gaya masa" Da yake baya son matsa mata saiya kyaleta, ko data same shi a daki da kanta dinma maganar da tayi masa bata da yawa "Zan koma gidana Abba, amman inaso mu zauna, dani dakai da Hajja, da kuma su Baban Tudun wada, da shi" Bai tsaya yi mata doguwar tambaya ba ya amsa mata. Ta tashi ta koma cikin gida, kuma har daki Hajja ta sameta bayan Alhaji Sa'id ya gaya mata abinda Maryaman tace "Inayi miki addu'a ko da yaushe Maryama, zan iya cewa addu'ar da nakeyi miki tafi ta kowa a cikin 'yan uwanki, bawai dan nafi sonki akansu ba, sai dan inaji a jikina taki jarabawar tafi tasu yawa, bana so in matsa miki Maryama, bana tambayarki ne saboda ina jiran ranar da zaki bude baki ki fadamun matsalarki, watakila ba zan rasa shawarar da zan baki ba" Tunda abin nan ya faru, sai a lokacin ne Maryama taji hawaye masu dumi sun zubo mata, hawayen da in dai akan Haris ne ya kamata ace bata da saura "Hajja..." Ta kira cikin rawar murya, sai Hajjan ta riko hannunta "Maryama zan cigaba dayi miki addu'a, ko da bansan ainahin abinda yake faruwa dake ba" Ba gayawa Hajja bane bataso tayi, ta rasa ta inda zata bude bakinta ne ta kalli mahaifiyarta tace mata mijinta yana bin mata? Sunyi magana da Khairi, tasan duk abinda yake faruwa d Khairi kinsan ko Kaduna da kewayenta zasu taru Mami ba zata bari in rike yarana ba, Abba kuma nasan ba zai goyamun baya ya tayani karbarsu ba, wa zan barwa tarbiyarsu? Mamin? Ko shi Baban nasu? Ni idan na bar auren ta ina zan fara?" Ita kanta akwai matsalolin da inta gansu, ko da a social media ne, ko taji labarinsu sai ta ga auren ma in za'a tsaya a haska masa ka'idojin musulunci da wahalar gaske ace akwai shi, wani auren kuma sai ya sakata dinga tunanin to meye amfanin shi? Zaman me matan sukeyi? Sai a hankali da matsaloli suka fara kunnowa a nata gidan ne ta gane cewa, shifa lamarin aure abune mai cike da tarin sarkakiya, mata da yawa in zaka saka musu bindiga ba zasu ce maka ga dalili kwara daya da yake rike dasu a gidajen aurensu ba, wasu kuma in suka fada maka nasu dalilin sai kaji nauyinshi ya rinjayi matsalar da suke ciki. Babban abinda Maryama zatace ta fahimta shine, daura aure yafi rabuwar shi sauki a lokutta da dama. Rabuwar aure ba abu bane mai sauki, da gaske ne aure yana da rai, ta yadda, dan duk yawan mutanen da zasu taru dan su kashe shi, idan lokacin shi baiyi ba, idan akwai sauran rabo, ko da rabon wahala ne haka za'a hakura. Ita dai inta duba, yaranta sune dalilinta na farko a yanzun, sannan inta hanga, bata iya ganin wata rayuwa da babu Haris a cikinta. To gani takeyi ma me ya rage mata? Duka kuruciyarta fa aka dauka aka mika masa, ta iya shanye halayenshi a lokacin da batasan inda yakeyi mata ciwo ba sai yanzun? "Wannan son da kikeyi masa Allaah Yasa wata rana kiga ribar shi Maryama...Allaah Ya taqaita miki wahala" Inama zata iya yiwa Khairi musu? Tace halayen Haris sun fitar mata dashi daga rai tas, sai dai ai ko harshenta ba zai bata hadin kai ta furta wannan gingimemiyar karyar ba, tana son Haris, son ne ma yasa damuwarshi tayi mata yawa, watakila wannan son ne yake kara rufe mata baki daga furta halinshi da tasan zai zubar masa da mutunci a idanuwan mutane, watakila shine yasa ta cewa Hajja "Hajja ke kike yawan gaya mana zamu iya samun matsala da mazajenmu, mu yafi juna, harma mu manta, amman idan mun fadawa makusantanmun wannan fadan, zai wahala su manta...abinda nake gujewa kenan, bawai fada miki bane bana so inyi..." Sai kuwa Hajjan tayi mata dan gajeran murmushi, irin murmushin nan na iyaye "Allaah Yayi miki albarka Ya kara miki hakuri da juriya. Allaah kuma Ya dai-daita miki komai" Kuma a yau da Alhaji Sa'id yayi mata yanda ta roka, sai takejin hawaye na neman balle mata, musamman yanda taji idanuwan Haris nata yawo a jikinta, sai ta zabi ta kalli Hajiya Rumana da idanuwan iyayenta bai hanata binta da kallon tsana ba, batasan me yasa Alhaji Mustafa ya kwasota suka zo gidan nan ba, to taron na menene? Bayan duk irin zagin da ta dinga yiwa Haris baiji ba balle yasa ya bar gidansu Maryaman. Da tayiwa Alhaji Mustafa magana sai yace mata "Ko Haris baya auren Maryama ai gidan Sa'idu kamar nawa ne a wajenshi..." Bakin ciki ya hanata magana, inta biye musu, zasu kassarama sauran yaranta da suke sonta itane, gara ta dauki ido ta saka musu "Zan koma gidan Haris..." Maryama ta fadi tana korar shirun da dakin ya dauka, ta cigaba "Amman ina so ku zama shaidane, zan koma gidanshi idan ya yarda zai koma Islamiyya ko zai samu Malamin da zai dinga zuwa gida kullum yana karantar dashi, ko shi ya dinga zuwa..." Haris ya kalleta, sanda ya shigo dakin, duk da zuciyarshi ba karamin bugawa tayi ba, haka kawai yake da yakinin Maryama ba zata taba tona m"asa asiri ba, yasan wata rigimar ce zata janyo musu a gaban iyaye, amman wacce irin Islamiyya kuma? Shine zai koma Islamiyyar? Sai kace dai wani karamin yaro, yau kuma ta nan rigimar ta taso kenan, sun tabayin maganar kusan shekaru bakwai da suka wuce, shi in zai tuna ma banda dariyar daya kwashe da ita baice mata komai ba. "Duk wanda zaifi masa sauki, zan koma ne in har ya yarda..." Cewar Maryama muryarta na rawa "Kuyi hakuri Baba...dan Allaah ku yafemun, amman idan ba zai zabi abu daya cikin biyun nan ba, ina so ku karbar mun takardata a wajenshi" Ta karasa maganar tana kokawa da nauyin da kirjinta yayi, ita Haris yake kallo har lokacin, yana so ya fahimci abinda take nufi da maganganunta "Allaah Yayi miki albarka Maryama..." Cewar Alhaji Mustafa, dan ya rasa irin addu'ar da zaiyiwa Maryama, ko ta yanda zai fahimtar da ita yanda yake alfahari da kasancewarta surukarshi a tsayin shekarun nan, amman yau, a wannan zaman akwai tarin kunyar Maryaman a tare dashi bayan jin abinda Haris ya aikata mata. Ya tabajin wani wa'azi inda Malamin yake magana kan zamantakewar aure, ya dinga mamaki yana jinjina maganganun da Malamin yayi "Iyayenka zasu bugi kirji suce sun haifeka, sun sanka, sunsan halinka, abokanka ma zasu iya wannan ikirarin, watakila harda 'yan uwanka, amman babu wanda ya sanka kamar matarka, saboda babu wanda ka raina kamar ita, duk wani halinka marar kyau da ba zaka bari wani ya gani ba, sai kaga ka nunawa matarka shi batare da wata fargaba ba, dan wani abu na fada maka ko da ta sani dole zata cigaba da zama da kai, inma bata zauna ba, ba zai hana ka nemi wani auren a baka ba..." A lokacin da Alhaji Mustafa yaji, bai yarda da duka maganganun ba, yau kam ya aminta dasu dari bisa dari, dan babu wanda zai fadi halayen Haris sai Maryama, babu wanda ya sanshi kamar yanda ta sanshi, shi dai ya haifi Haris ne, yana sonshi saboda shi ya haifeshi, soyayya ce da bata zuwa da wani zabi, amman yana tir da halayenshi, kuma har kasan zuciyarshi yakejin inda Maryama ya haifa, sai inda karfinshi ya kare wajen ganin ya guntule wannan auren, yau dinma ba zaiyi son zuciya da yawa ba, in har Haris bai amince ba zai tsayawa Maryama. Sai dai abinda bai sani ba shine, Alhaji Sa'id dinma kawaicinshi ya kare, dan shi gani yakeyi bayan Islamiyya a duba wata makaranta da ake koya al'adu da kuma dabi'ar Malam Bahaushe a saka Haris din. Farkon dawowarshi gidan, har ranshi haushi Haris yake bashi, kuma cike yake da dana sanin aura masa Maryama da yayi yake, amman kuma da duk ranar da zata wuce da yake ganin Haris a gidan da kuma yanayin yanda yake mu'amalantar kowa sai zuciyarshi ta dinga sanyaya, akwai wani hali na saukin kai da yake gani tare da Haris din, babu ruwanshi da matsayinka ko nashi, yana mu'amalantar kowane da fuska daya, ciki kuwa harda masu gadin gidan gonar Alhaji Mustafa da Alhaji Sa'id din yaja shi sukaje, zama yayi cikinsu sunata hira yana tambayarsu abubuwa. Sun fita yafi a kirga kafin Alhaji Sa'id ya fahimci bawai Haris nayin sadaka kamar baisan zafin kudinshi bane dan ya burgeshi koya nuna masa yana shi din na kirkine, yana sadakar ne saboda ta zame masa jiki, musamman almajirai kanana, da kuma yara masu saida abubuwa a titina "Inda ina da wani mukami dana hana wannan barar Abba, dana hana kawo yara kanana haka suna yawo a titi babu mai kula dasu...banajin dadin ganinsu, zuciyata namun zafi idan nagansu..." Haris na da halaye masu kyau da sai ka zauna dashi zaka gane, sai dai babu digon al'ada da dabi'ar Malam Bahaushe a tare dashi, duk da ba bahaushen bane ba, tunda mahaifinshi bafullatani ne, mahaifiyarta Kanuri, amman duk da haka, , Alhaji Sa'id yaga dabi'un Haris din irin na turawa ne, duk kawaici da kunya irinta Hajja saida Haris yasa ta sauko. Babu ruwanshi da wata surukantaka, dan saida Alhaji Sa'id yayi da gaske ya iya riqe dariyarshi randa suke zaune a falo Haris din ya shigo, da karamin kwano a hannun Hajja ta zubo dabinon da taketa yiwa kowa rowarshi, Haris ya tsallaka yaje ya saka hannu a kwanon ya tsinta kuma yana mata magana kamar babu abinda ya faru, saima ya zauna akan kujerar da take yana kara fadin "Wanne irin dabino ne wannan Hajja? Wani mai taurine Maryamm take siya kaman zai balla hakori, inaji dan karta sammun ne take siyo shi..." Haka Alhaji Sa'id ya dinga tsokanarta "Sai gaki kuna cin dabino a kwano daya da suruki" Daya matsa matane ma tace "Ai ba surukina bane, dana ne shisa" Yanzun ma cike da wannan halin da a al'adar bahaushe za'a kira wauta Haris yace "Islamiyya fa? Nine zan dinka uniform in koma Islamiyya kamar karamin yaro Maryamm?" Dan yaga da gaske take, kuma kamar Alhaji Mustafa ya kama zancen dan yaji yana saka mata albarka, Hajiya Rumana ta tabe baki tana kauda kai gefe, in ita tayi magana babu abinda zataja mata sai tijarar Alhaji Mustafa, kilanma ya kunyatata a gabansu Alhaji Sa'id "Waye yace maka zaka dinga uniform? Ai akwai islamiyyar manya, in kuma bakaso sai a samu Malamin da zaizo ya dinga karantar da kai a gida..." Kai yake girgizawa tunda Alhaji Mustafa ya fara magana "To shikenan, ai daman zabi ta baka, saika bata takardarta in ba zaka iya ba" Cike da rashin fahimta yace "Wacce takarda kuma Baba? Ni ai babu wata takardarta da take hannu na" Hajiya Rumana da takejin kamar ta tashi ta rufeshi da duka tace "Takardar saki, ka saketa kawai kowa ya huta" Ya dan ware ido yana kallon Maryama da sai lokacin ta kalle shi "Saki? Akan Islamiyya? Akan Islamiyya zaki rabu dani Maryamm?" Haris ya karasa da wani irin rauni a muryarshi kamar ta zageshi, duk abubuwan da suka faru, duk tarin laifukan da yayi mata, akan Islamiyya ne zata tattara iyayensu tace ya saketa? Wanne irin abune wannan? To ko dai postpartum dinne bai gama sakinta ba? Ko da ta dawo hayyacinta ya bar mata wani ciwo ne? Daman ya shirya in sun koma gida zasu bar kasar dan a kara dubata sosai, bawai ya yarda da wannan likitocin bane in akazo maganar mental health. "Abba kanajinta ko?" Alhaji Sa'id ya numfasa zaiyi magana Maryama ta rigashi da fadin "Dan Allaah Abba, muna bukatar komawarshi Islamiyyar ne...in dai bai yarda ba...dan Allaah kayi hakuri ka rabani da auren nan..." Matsawa Haris yayi, ko yace rarrafawa har gaban Alhaji Sa'id "Kara fada takeyi fa Abba, kayi mata magana..." Hajiya Rumana taja wani tsaki da sai da dakin ya kusan amsawa da kararshi, Hajja tayi murmushi kawai, dan zuwa yanzun matar ta daina bata haushi, dan bata mata kallon mai cikakken hankali "Ni dai wannan shari'a taku na barwa Babanku" Haris ya girgiza kai "Kasani Abba, Baba zai goyi bayanta ne..dan Allaah karka barmu dashi" Alhaji Mustafa yayi masa dakuwa "Gidanku Haris, aini bayan gaskiya nake, kuma banga aibun komawarka Islamiyya ba, in kaga ba zaka koma ba, babu dole...Maryama" Ta kuwa amsa "Na'am Baba" Da dan murmushi a fuskarshi yace "Ki hado kayanki mu tafi gidana, sai ya biyoni da takardarki daga baya" Haris ya kalli Maryama data mike, gidansu zata koma, sai dai yasan ko Hajiya Rumana bata isa ta bashi dakin zama a cikin gidan yanda Alhaji Sa'id yayi batare da izinin Alhaji Mustafan ba "A samo mun Malamin...da zamu dinga karatu, a samo Malamin Baba" Maryama ta lumshe idanuwanta hadi da sauke wani numfashi da takejin kamar ya fito ne da dan sauran karfin daya rage mata. Wannan zaman, shine sanadin komawarta gidan Haris, dan batason taja magana dashi a gaban iyayensu, daga dakin Alhaji Sa'id da suka sha addu'o'i daga bakin kowa banda na Hajiya Rumana da ta kara hade girar sama data kasa, Haris ya nemi su wuce gidansu. Hajja ta kara mata kwarin gwiwar cewa "Kuje kinji Maryama, ki dauki Naadir, in kun kwana biyu yaran zasu taho da Fa'iza da sauran kayanki" Tasa hannu ta goge hawayen daya zubo mata "To Hajja" Addu'a ta sakeyi mata, har mota ta rakasu, suka shiga suka tafi. Saima da sukayi parking cikin gidan nasu take tunanin ta inda zata fara, ta tabbatar gidan ya hada qura ba 'yar kadan ba, da ta sani ta taho da Fa'iza sai su hadu su gyara. Ba karamin mamaki tayi ba lokacin da ta shiga taji harda kamshin turaren wuta, ga ko ina fes, mamakin ne ya nuna har akan fuskarta, shisa Haris yace "Ina dawowa in share, sai inyi mopping yanda naga kunayi kullum, in kunna miki turaren wuta..." Ta kalle shi, kallo na sosai, yayi zuru-zuru, idanuwanshi sun shige ciki, bata lura ba saboda ba kare masa kallo takeyi ba "Ina zama ne, idan na gama gyarawa, kamshin da ganin ko ina a haka, yana ragemun kewarki" Batace komai ba, batasan me zatace ba, shisa ta zabi karasawa dakinsu, ta kwantar da Naadir da yaketa harba kafafuwa abinshi. Ta zauna daga gefen gadon bayan ta cire hijabin jikinta ta ajiye. Shima Haris zaman yayi, taji tsikar jikinta na tashi da tunanin zai riketa ne ya hadata da jikinshi, sai baiyi hakan ba, ta kuma san abinda yake so yayine, amman baiyi ba "Maryamm..." Ya kira sunanta, ta kalle shi "Kiyi hakuri" Kalmomi biyu, kalmomi masu nauyin gaske, kalmomi masu dauke da tarin ma'anoni, sai kawai taji hawaye ya balle mata, kafin wani irin kuka ya kwace mata, Haris bai motsa ba, kokari yakeyi da dukkan zuciyarshi, barinta yayi tai kukanta da yakejin kamar kwanaki ta dauka tanayin shi ba mintina ba, saida ta goge hawayenta sannan yace "Zan iya hugging dinki?" Tayi jim "Dan Allaah..." Shirun dai ta sakeyi "Maryamm" Harararshi tayi da idanuwanta da suka kode saboda kukan da tayi, sai kawai ya rungumota ta gefe, sai gata tana sauke ajiyar zuciya, duminshi da kamshin turarenshi sukayi mata maraba, sai takejinta kamar wadda taketa gararamba, ba don ta rasa wajen zama ba, sai dan ko ina baiyi mata kama da gida ba "Nayi kewarki...da yawa" Wasu hawayen suka sake zubo mata, tana ta addu'a, Allaah Yasa Haris ya daina neman mata, sai dai tanajin kamar kamata yayi ace ta roka masa Allaah Ya darsa masa tsoron saba masa, in har zaiji tsoro, zai guji fushin Ubangiji, zai bar neman mata, saboda ta gane abu daya, har yanzun Haris baya kallon abinda yakeyi a matsayin gagarumin zunubi, yana kallon neman matanshi ta fuska dayane, cewar ita yakeyiwa laifi, shisa yayiwa zinar kwaskwarima da kalmar 'cheating'. Gani yakeyi ita kadai yake yiwa laifi, ita kuma zuwa yanzun tasan zuciyarta zata cigaba da yafewa Haris ne, yanzun a cikin zuciyar tace "Allaah Kasa masa tsoronKa, Allaah Ka nuna masa abinda zai tuna da girman ikonKa..." Saita lumshe idanuwanta, kamar zata iya ganin yanda addu'ata ta karbu, kamar kuma zata tsallaka cikin shafukan littafin kaddararsu da Haris, ta wuce kwanaki, watanni, ta kai shekarar da zata ga yanda addu'arta ta karbu...! 45 A yanda Haris ya dauki Fa'iza kamar 'yar daya haifa, Maryama tasan dole ne kowa zaiyi mamakin irin bajintar da zai nuna wajen bikinta. Abinda batayi zato ba, shine yanda Haris yake ta gayyatar mutane, da kanshi yake tura katin gayyata, harda 'yan uwanshi na Maiduguri, dangin Hajiya Rumana, abin ya dinga bata dariya, tasan dai dangin Alhaji Mustafa kowa zaizo, yanda suke sonta, sai wani yayi zaton itace 'yar dan uwan nasu ba Haris ba, dan kuwa zumunci sukeyi da ita bana wasa ba. Amman dai dangin Hajiya Rumana, inda ma ace bikin Rauda ne ya tashi, amman bikin Fa'iza, kanwarta, abin da kamar wuya. "Kin duba store din nan kuwa Maryamm? Lemukan zasu isa?" Tayi dariya, ta kama hannunshi, baiyi mata musu ba, ya zauna a gefenta, yau daya rage saura kwana uku bikin, shiga goma Haris zaiyi, saiya tambaya ko akwai abinda za'a karo, ko an mantawa Fa'iza wani abu, gidan Fa'iza two bedroom flat ne ya kama haya anan cikin Kaduna, unguwar dosa. Gidan yayi kyau, saima da aka tsarashi da tsadaddun kayan dakin da Haris ya siya, wasu cikin kayan kitchen dinta ma sai dawowa akayi dasu saboda kitchen din bashi da wani girma, Maryama tasan inda Hajiya Rumana zataje taga abinda danta ya kashe, saita hadasu ta tsine musu sunbi duniya "Ka huta, dan Allaah..." Sai yayi mata murmushi "Ina naga hutu zan aurar da 'ya?" Dariya Maryamm tayi mai sauti. Ba zatace komai na tafiyar mata babu wata tangarda ba, babu wani aure da za'ace yau babu matsala guda daya a cikinshi, babu wata mace da zatace bata da wani abu da take hakuri ko kauda kai akanshi game da mijinta koma auren gabaki daya. Ita ko kullen Haris aka barta dashi ya isheta jarabawa. Balle kuma ace an hada mata da kiyayyar mahaifiyarshi da 'yan uwanshi da har yanzun basa mata kallon arziki. Amman akwai abubuwan da tasan tana dashi a nata gidan auren da wasu matan suka rasa, kamar yanda tasan akwai abinda wasu matan suke dashi da ita ta rasa, mata da yawa in suka kalleta zasu fara duba sutturar jikinta, watakila da zobunan gwal din da suke hannunta. Kilan ta burge da yawa a cikinsu in sukaji kasashen da ta zagaya da sunan hutu ko yawon shakatawa, Hajj nawa taje, Umrah kuwa duk sanda take so magana kawai zatayi Haris zai biya mata, zasu ga daular da take ciki, to ma sau nawa mutane nace mata "Allaah Ya gama miki komai Maryama" Wasu kuma suce "Ke da kike da miji kamar Haris, baki da matsalar komai" Murmushi take binsu dashi, to sirrikan gidan aure ai labule ne dasu, in ba ka daga ba, babu wanda zaisan dasu. A cikin masu yi mata irin wadannan maganganun, akwai wadda duk hidimar danginta idan ta tashi, mijin ne zai dauketa ya kaita da kanshi, akwai wadda mijinta yake da ilimin addinin da yake aiki dashi, mijin da zai tasheta sallar asuba, ya kuma tashi yaranshi ya sakasu a gaba su tafi masallaci, a cikinsu akwai wadda in zatayi alwala a gaban mijinta tayi kuskure daya zai gani ya gyara mata, akwai wadda zasu zauna da surukarta suyi hira suyi dariya, ta shiga cikin 'yan uwan mijinta su mu'amalanceta da girmamawa. Akwai wadda mijinta ya mayar da ita makaranta, akwai wadda duk fitar da mijinta zaiyi bata da wata fargaba, tasan ko da zai kula wasu matan, to ba zai ketare iyakokin Ubangiji ba, a wajen Maryama babu wani kudi ko daular duniya da zatafi hakan kwanciyar hankali, mijinka ya taka ko ina kana da yakinin zai kare mutuncin kanshi da naku baki daya. Abubuwa da yawa, manya da kanana, in kuma kowacce mace zata nutsu ta duba irin tarin ni'imar da Allaah Yayi mata a nata gidan, watakila sai ta dauki wasu kwanaki masu yawa tana neman gafarar Ubangiji akan hange-hangen da ta dingayi tare da godiya da irin ni'imar da take ciki. Shisa tunda aka shiga satin bikin nan, daga jiya da gidanta ya fara daukar baki, danginsu na bangaren Alhaji Sa'id, 'yan matan nan masu rawar kai, duk wadda tace "Allaah Ya sakani a danshinki Anty Maryama, Allaah Ya bani miji irin naki" Saita kwabesu da "Kiyi addu'a Allaah Ya baki miji nagari, wanda zai zame miki alkhairi" Tana kuma ganin wautarsu a gefe daya. Daga ganin mata da mijinta saiki fara rokon Allaah daya baki irinshi, dan kawai kinganshi a wanke fes, cikin suttura da rufin asirin da Ubangiji yakeyiwa kowanne bawa ta hanyar lullube aibunshi. Bakisan ainahin waye shi ba, me matarshi take shanyewa a zamantakewarsu, idan aka daga Labulen dake lullube da auren, watakila abinda zaki gani saiya kayar dake. Sai dai da gidan ya kara cika, kuma kamar ko da yaushe a shekarun, Haris baya kunyar nuna mata kulawa, ko a gaban waye, ai saiya kara rikita 'yan matan nan, ta dinga girgiza kanta ganin yanda wasu suke lankwasa harshe wajen gaishe dashi. Tabbas addu'a inka jure, ka tsarkake zuciyarka, ka kyautatawa Allaah Zato, sai dai ka jira lokaci kawai, amman a wannan hidimar bikin tasan Allaah Ya amsa addu'arta Ya saukaka mata azababben kishin da yake dawainiya da ita. Sannan kuma a nutse take, ta tabbatar duk biye-biyen matan Haris, ba zai taba kusantar wata da yasan ta san wadda ta santa bama, balle kuma cikin 'yan uwanta. Tunanin dai ya sosa mata zuciya matuka, saboda bawai tana zaton ya daina bane ba, a'a yakini take dashi zaiyi duk wani abu da zai iya wajen boye mata. Ranar asabar za'a daura aure, ranar juma'a zasuyi sword crossing, wannan ma tun daga wajen da aka kama zuwa duk wani abu da za'ayi Haris ne ya dauki nauyi, wasu abubuwan sai da Maryama ta dinga taka masa burki "Kabar yaron nan yayi nashi kokarin, karya ga kamar an raina masa ne, dan Allaah...kaji" Amman duk da haka in dai zai gani sai yayi magana, tasan idan Allaah Ya tsawaita musu rayuwa za'a kwashi kallo akan Rauda. Ita kanta Fa'izar inka kalleta zaka ga yanda take alfahari da iyayen rikon nata, saima Haris ya shigo, cikin taron 'yan uwanta yace mata "Stellina..." Wato tauraruwa da yaren Italian, ko yace "Amore mio..." Duk yana kiransu hakan ita da Rauda, ta amsa da "Si Papa" Yau da gobe yasa tana jin kusan komai zasu fada da yaren, sai dai bakomai take iya mayarwa ba, haka za'a bita da ido, wasu najin kamar suyi musayar matsayi da Fa'izar. Yanda duk Maryama taso suki zuwa wannan sword crossing din, Haris yaki amincewa, ganin ranta zai iya baci inta ja musun yasa ta shirya itama. A maimakon ango da zasu jera su shiga hall din tare, Haris ne ya riko hannun Fa'iza, Tuxedo ma yaso sakawa, da magiya harda guntun hawayenta Maryama ta samu ya saka manyan kaya, shadda harda babbar riga. Abinda dai ya bawa Maryama mamaki shine ganin 'yan uwan Haris, motoci sukayo, harda su Munira, tare suka taho da Rauda, tun satin bikin ta koma gidan Hajiya Rumana, saboda bata son hayaniyar mutane, Awwab ne duk inda ka gilma zaka ganshi, anata hidima dashi, yana tayawa da abinda zai iya ko aka saka shi, don shi din na mutane ne. Ko bai sansu ba kuwa, haka zai zauna yana musu labari da tambayar su din su waye, meye dangantakarsu, Maryama tayi fadan, tayi dukan akan wannan halin nashi ta gaji tabarshi, ta daiyi kokari tana kanyi wajen ganin ya saka ladabi a yanayin tambayoyin da zai saka babba a gaba yana tsareshi dasu. Haka ta dinga kallonsu da irin kwalliyar da suka tsantsara, Haris sai murmushi yakeyi daya gansu. Maryama na gaisawa da Shatun Umma Fadime, ta wuceta zuwa wani teburi data hango wata kanwar Alhaji Mustafa dan ta gaisheta, Maryama ta dago kai, tayi mummunan gani, dan ba zata kirashi da kyakkyawa ba. Tana nan, yanda take, a cikin jerin halittun da Maryama ta sani, ko tace ta gani daga fina-finai, vampires sune basa tsufa, idan a jariri ka zama vampire, to zakaita zama ne a jaririn nan ko da zaka shekara dubu a duniya. Batasan ko idanuwanta bane ba, amman yanda taga Aise a wannan hotunan nata da Haris, haka ta ganta a Maiduguri, haka kuma ta ganta a yau din nan, cikin wani leshi da bature kewa kalarshi lakabi da wine daya karbi bakar fatarta, dinkin bubu ne, sai tayi daurin data dan turo gaban goshinta kadan, tayi kwalliya mai sauki, haka dan kunne da siririyar sarkarta, tsinin takalminta kuwa ko a mafarki Maryama tasan sai anyi yawo da ita tsakanin asibitocin kashi na Nigeria kafin a samu inda zasu iya gyaran karayar da zatayi in tace zatayi amfani dashi. Haka ta karaso har inda suke, inda Haris yake zaune, hannu ta mika masa "Ciao..." Da wani murmushi daya bayyana fararen hakoranta, hannu shima ya mika mata, sai dai a maimakon normal handshake da zama dasu yasa Maryama fahimtar ba wani abu bane, basu ma san zunubi bane tunda su din ba muharraman juna bane, balle kuma runguma da sumbatar kumatun juna, sai kawai duk wadannan shekarun da suka shafe, shekarun da ya saka tazara a tsakaninsu ya bace, sukayi wata gaisuwa da suka kirkira a tsakaninsu, da suka gaisa din, sai suka zame hannayen nasu a hankali, ta dan mari nashi ta baya, yayi mata, sai kuma suka dunkule hannuwan, kowa ya buga akan na kowo, bugun daya fada har zuciyar Maryama, musamman da Aise din tayi wata dariya mai sauti tana fadin "Mi manchi..." Maryama bata bukatar fassara, tasan ma'anar kalmomin, kuma dariyar da Haris din yayi shima, sai kawai ta dira a kunnuwan Maryama da fassarar "Nima nayi kewarki" Ba zatace ga abinda ya cigaba da faruwa ba, bayan Aise taja kujera a teburinsu ta zauna tana gaishe da Maryama da kalmar "Sannu" Wadda ta amsa mata da yin wani guntun murmushi kawai. Kuma kafin a tashi daga wannan sword crossing din, kamar lokacin ma da ake hotuna ne, tunda sunyi da Haris ba zasu zauna har a tashi ba, zasu dai zo yanda yake so, taji wata tana cewa Anisa "Ba Aise bace waccen? Yaushe tazo Kaduna?" Taji Anisan ta amsa da "Suna Abuja ai..." Waccen tayi saurin katse Anisa "Nasani, nasan Uncle Modu ya dawo, ita daice nayi mamakin zuwanta" Anisan ta danyi dariya "Ai itama ta dan dade fa, kinsan bata tare da mijin, sun rabu, tam shine ta dawo...kaman dai tana so ta bude asibiti ne a Kaduna ko wani abu mai kama da wannan" Maryama ta dafa matar dake kusa da ita saboda jirin da taji ya kwasheta, hall dinma juya mata yakeyi "Kaji wata kakkaurar masifa" Sarar 'yan ajinsu ce lokacin da take Islamiyya, idan anyi abu suce lukutar masifa, ita randa ta furta hakan, tayiwa nata ado da kakkaura, haka Hajja ta watsa mata wani kakkauran mari da saida bakinta yayi jini, ko wani ya fada a kusa da ita sai taga kamar hannun Hajja zaiyo fuffuke ya samesu, amman yau sai abin ya fado mata a rai, ashe kishinta yana nan, babu inda yaje. Dan har baki baki take gani, hannun da taji a bayanta, hannun Haris, hannun daya gama tuna tsohuwar soyayya ta hanyar rukunkume na Aise, ta kuwa matsa gaba tana janye jikinta, amman ya sake matsowa yana nanike mata, a daddafe suka gama hotunan suka bar wajen. Lokacin data karasa gida, Khairi na mata kallo daya ta rufa mata baya, dan ita bataje sword crossing din ba, wani irin laulayi take fama dashi mai yawan amai, kamshin turaren da baiyi mata bama inta shaka sai ta dinga amai kamar hanjinta zai fito. "Menene? Meya faru?" Da wani irin yanayi Maryama tace "Gaisawa yayi da Aise...hannunshi cikin nata Adda...aurenta ya mutu, ta dawo, aurenta ya mutu" Cikin rudani da rashin fahimta Khairi tace "Bangane ba, wacce Aise" Maryama taji wasu hawaye sun zubo mata, takai hannu ta gogesu da sauri tana jan hanci "Shikenan ba zan huta ba ko Adda? Aurenshi ya zame mun kamar wani tseren gudun da duk sanda na samu inuwa na fara numfasawa sai wani abin ya sake biyoni..." Kamata Khairi tayi ta zaunar "Na kasa fahimtarki Maryama, wai me yake faruwa" Saida ta dauki wasu dakika sannan ta tattaro natsuwarta tana yiwa Khairi bayani, Khairi taja tsaki "To shine me? Dan sun gaisa? Kinsan fa ba kintsi ne dasu ba, basu dauki wannan abubuwan wani abu ba, sannan aurenta daya mutu ke ina ruwanki? Kinga ki nutsu ki cire wani tunani daga ranki, kika san ko tun yaushe auren nata ya mutu? Tun yaushe ya sani?" Maryama taji ta mike tsaye, tun yaushe ya sani to? Kenan suna magana kome? "Maryama..." Khairi ta kira a tausashe "Babu abinda zai faru, In Shaa Allaah, ki natsu dan Allaah, ki natsu a gama hidimar nan, karki dagawa kanki hankali" Ta daga mata kaine kawai, amman idan hankalinta yayi dubu, to kowanne a tashe yake. Aise fa Aise ce... Koya zatayiwa Khairi bayani ba zata gane ba, a rashin Aise dinne aka aura masa ita. Bashi bane ya gaya mata, Anisa ce ta dankara mata, in bata manta ba haka tace "Kinsan babu wanda ya dauka aurenku zaije wani waje, da yake Aise yaso kamar rai, da aka samu 'yar matsala shine Baba da garajen shi ya nema masa aurenki, yanda ya tubure ya nuna bayaso sai kiyi zaton ana kawoki zai koraki gida" Kalaman sunyi mata ciwo harta rasa martani, ta kuma yi kuka da Anisan ta tafi, Haris ya rutsata da tambaya saida ta gaya masa abinda ya faru "Karya takeyi..." Ya fadi kanshi tsaye "Baba ya nemar mun aurenki, kuma yana fadamun an daura na karbi auren da duka zuciyata, ko sanda na amsa, ban ganki ba, na dai san na karba, kuma babu abinda zaisani rabuwa dake, ko da Baban ne da kanshi kuwa..." Da jajayen idanuwanta tace "Aise din fa?" Ya daga mata girarshi guda daya "Maryamm" Sai kawai tayi shiru tana karbar lallashin da yakeyi mata, inta matsa ba zaiyi mata karya ba, zai fada mata abinda tasan kunnuwanta ba zasu so ba balle kuma zuciyarta. A ranar batasan me yasa data bar dakin saita nufi bangarenshi, da yake gab da bikin suka dawo wannan gidan, gidan da ta dinga yi masa mitar yayi musu girma "Mu da zamu rage yawa?" Saiya ja hannunta, zuwa wani bangare, dakine babba, babba sosai irin mai hade da dan karamin falo da bedroom, kayan ciki ruwan kasa mai duhu, kalar da Fa'iza tafi so "Ga dakinta nan" Dariya tayi "Kwana nawa zatayi a ciki..." Ya daga kafadunshi "Dakinta ne ko da Auwal zaiyi mata wani abu, saita dawo a share mata tayi zamanta...ita da Rauda, suna da dakunansu a duk wani gida da zanyi, yanda na kamokin nan na nuna miki haka zan riko Auwal in nuna masa, in fada masa ban bashi ita dan nagaji da ita ba, ko dan bata da waje a gidansu, ko da zaiyi tunanin yi mata wani abu, sai mun birkice garin Kaduna ni dashi kafin in dauko 'yata" Haka ta dinga kallonshi tana rasa abinda zatace masa. Kamar dai yanzun data shigo dakin ta same shi harya kwanta "Ke zan kira yanzun" Ya fada shi, ta karasa ta zauna gefen gadon, tayi shiru "Me ya faru?" Ya tambaya yana tashi zaune shima, hadi da kunna kwai mai haske, dan da ya rage hasken dakin ne ya barshi dim "Kuka kikayi? Meya faru? Menene?" Tar ta saka idanuwanta cikin nashi "Aise..." Ta kira, ya dan kankance idanuwanshi, tana ganin wannan maikon na cikinsu kamar ya sauya launi, yana son boye mata wani abu "Tun yaushe ka sani?" Ya numfasa ta tare shi "Inaso in sani, dan Allaah..." Dan kamar sanin zai nutsar dashi "Idan dawowarta Nigeria ne, an dade da naji Mami tayi maganar... mutuwar aurenta, lokacin da nasan ta dawo lokacin naji, zuwanta Kaduna...dazun, sanda tazo hall din nan" Saiya riko hannunta, tabi hannuwan nasu da kallo, hannunshi ne na dama, wanda ya rike na Aise, ta zame hannunta tana gogewa a jikin kayanta "Na wanke, na wanke hannuna, wanka nayi" Yayi maganar da wani yanayi a muryarshi sanin abinda take tunani "Babu komai Maryamm, banda gaisawar da mukayi, babu komai...in akwai kinsan zan fada miki" Ya kamata kalamanshi su nutsar mata da zuciya, amman sai zuciyar tayi mata tambayar data subuce harta furtata "Har zuwa yaushe? Babu komai har zuwa yaushe Ganja?" Kai yake girgizawa "Maryamm..." Hawayen da suka cika mata ido suka zubo, haka kawai wani irin tsoro yake shigarta "Dan Allaah karki daga mana hankalin akan abinda bai faru ba, abinda ba zai taba faruwa ba" So take tace yayi mata alkawari, babu abinda zai faru, tsakaninshi da Aise, amman tana tsoro, wani abu yana fada mata Ko yayi mata alkawarin nan zai karya... 46 "Harrasment" Kalma ce da bature yake amfani da ita, kalma ce da in za'a rutsa Haris da bindiga ace ya fassarata sai dai ya lumshe idanuwanshi yayi fatan cikawa da imani, kalma ce da ita kadai tazo cikin kanshi wajen misalta abinda Aise takeyi masa. Ya rasa tsakanin Anisa da Munira waye ya bata address din HM Wheels, ranar da tazo haka ta wuce sakatarenshi da yake mata magana, ta bankada kofar ta shiga ciki, lokacin yana zaune yana sake duba lissafin kudin da suka shigar musu a watan da kuma wanda suka fita wajen yin gyare-gyaren wasu daga cikin motocinsu da suke bukatar service. Har taja kujerar ta zauna bai daina abinda yakeyi ba "Ban dauka akwai ranar da nice zan dinga binka inda kake kana mun wulakanci ba...saboda ina tuna lokacin da kaine kake biyoni kuma na rana daya ban taba wulakantaka ba" Saida ya fara sauke numfashi tukunna ya daga kanshi yana kallonta "Me kike so dani Aise? Me zanyi miki? Sau nawa zan fada miki ni da ke ya kare ne, koma menene muka taba sharing ya kare daga ranar da kika zabi ki auri wani a kaina!" Itama kallonshi takeyi, wanne aure yake magana akai? Baiyi karya ba, tayi aure, amman kuma ba don ta zabi wani a kanshi ba, tana so tayi masa wannan bayanin, bakin kishinshi da takeyi ne yasa ta karbi zabin Alhaji Modu, ido rufe ta karbi auren nan, kuma idanuwanta basu bude ba sai bayan auren. Sai bayan komai ya faru, tana kwance a jikin Abdul, tukunna wani irin kuka ya kwace mata, kukan da yake ta lallashinta dan ya dauka shine sanadinshi, ko kadan baiyi tunanin kukan dana sani da nadama bane suka saukar mata. Dan data kalleshi duk hasken fatar nan tashi sai ta ganshi bakikirin, baki fiye da duhun daya lullube zuciyarta. A ranar ta gane tayi kuskure, ta cuci kanta, ta cuci zuciyarta "Aure kayi kaima" Ta furta a hankali, muryarta na fitowa a karye "Auren da kinsan yanda ya faru, sai kika kasa yimun uzuri..." Kai take girgizawa, hawayenta na zubowa wannan karin "Nace ka saketa ka aureni, na baka zabi Haris, saika zabeta" Yayi shiru, da alama bashi da niyyar magana "Kayi aure, nayi aure...yanzun na shirya, ka nemi aurena, babu wanda zai hanamu aure yanzun..." Tasan Alhaji Modu a yanzun da gudu zai karbi Haris idan yazo neman aurenta, dan da kunnenta taji yana maganar yanda yaga Haris ya zama babban mutum. Kuma akwai dana sani mai yawa a tare dashi lokacin da aurenta ya kare ita da Abdul, yana ganin kamar shine yaja mata komai, dan idonshi ya rufe ya kasa tuna cewa ya kamata ya barwa Allaah zabi, duk da shine mahaifinta, ko da zai duba nagarta da cancanta to ya hada da nemar mata mafi alkhairi bawai shi ya yanke mata hukunci kai tsaye ba, bakowacce nagarta bace take tare da alkhairi, musamman a lokacin da ba'a nemi zabin Allaah a ciki ba. Tabbas zai dauki wani kaso na laifin, amman mafi yawa itace da laifi, babu wani kokari da Abdul baiyi ba na ganin ya kyautata mata, zuciyarta ce bata tare dashi shisa batama ganin wannan kyautatawar, shisa suka dinga samun matsala, gashi yanda takeji da rawar kai, shima kan nashi rawa yakeyi, in suna fada har makota ke kira musu 'yan sanda saboda hayaniyarsu tana yawa, zata jawo abubuwa tana fasawa, shima kuma zai biye mata, akwai randa ya hankadata ta fada kan mudubin data fasa. Ba zatace ga takaimaiman abinda ya hanata pressing charges ba lokacin da sukaje gaban 'yan sanda, amman ta tafi gida, kuma bayyanar cikinta ne yasa suka dan samu dai-daito ta koma. Yaransu biyu da Abdul, duka maza, yaran ma suna wajenshi, zamansu baiyi dadi ba ko kadan, haka ba rabuwar dadi akayi ba, tunda har saida akayi fadama da Alhaji Modu da abokin nashi, kuma ita batayi fada dashi ba akan full custody na yaranshi daya nema, ita yara ba wani sakasu tayi a rai ba, cikinta na biyunma kusan zatace accident ne, tana shan kwayoyin planning, mantawa tayi na rana daya bata sha akan lokaci ba, babu wata shakuwa ta kirki tsakaninta da yaran, tafi bawa aikinta muhimmanci, tasan suma ba zasu so su zauna da ita ba. Ko sanda su Alhaji Modu suka dawo Nigeria, ba nan take ta biyosu ba, zamanta tayi acan Italy tana cigaba da aikinta, sai dai inta samu sarari ta shigo ta sake komawa, a shekaru biyar din nan bayan mutuwar aurenta, Haris ya fado mata sau babu adadi, ko yatsanta ta kalla da har lokacin ta kasa goge sunanshi daga jiki, duk irin tashin hankalin da suka dinga kwasa da Abdul akan sunan kuwa, data tuno yanda ya kalleta a haduwarsu ta Maiduguri, yanda ta ganshi da matarshi, da kuma yanda kafin su Haris din su bar Maiduguri, babu wanda baya maganar irin son da akaga Haris nayiwa Maryaman, son da baya boyewa a gaban kowa, sai taji zuciyarta ta takure waje daya, tsoro da fargaba su dirar mata. Sai dai a shekarar nan da tazo Najeriya, da niyyar sati hudu tazo, sai dai batason zama haka kawai bata komai sai fita yawo, kusan jikinta ya riga ya saba da aiki. Saita fara duba hanyoyin da zata taimaka, akwai kungiyoyin da tayi aiki dasu a kasar Italy, da yake tasan kan komai sai gashi ta fara magana da wasu NGO's masu zaman kansu, sai kawai abin ya shiga ranta sosai, ganin irin wahalar da mata suke ciki, musamman a kauyuka anan Nigeria, wani kauyen Abuja da sukaje sai da tayi hawaye ganin macen da bata rufa shekaru ashirin da biyar ba da yara shida, shi kanshi na farkon bukatar goyo yakeyi, ita kuwa kamar ta shekara arba'in saboda wahala, babu ko wutar nepa a garin, ta dinga kallonsu tana mamakin yanda suke jin dadin zaman duniya. Inda za'ace mata akwai mutanen da tunda suke a rayuwarsu basu taba shan iskar fanka ba, balle ayi maganar sauran jin dadin rayuwa sai ta karyata, sai gashi ta gani da idanuwanta. Data koma gida sai kawai ta rubuta takardar ajiye aiki ta tura ma asibitin da take aiki dasu a can Italy, ta yanke hukuncin zama anan Nigeria na wani lokaci. A cikin irin wannan ayyukan da sukeyi ne sukazo Kaduna, a hotel suka sauka kamar ko da yaushe ita da abokan aikin nata, tunanin ma ta nemi gidan 'yan uwa ko da a gaisa ne bai gifta mata ba, sai bayan sun fita, sun sha yawo, a mota suke amman zafin da akeyi yasa ta gaji likis, da suka koma hotel akwai wasu takardu da suka manta a wani waje, sai abokiyar aikinta Nana tace zata saka aje a karbo a kawo musu anan hotel din da suke. "Wannan masu karbo sakon naku na Nigeria da bata lokaci, da mu muka fita kawai, inaso inyi scanning takardun nan in aika dasu dan zan kwanta da wuri" Ranar da tayi order din abinci saida ranta ya baci a Abuja, sau nawa ma tayi order amman suna samun matsala da masu delivery, karshe abinma saiya fita daga ranta, gara ta dauki mota taje ta siyo abinda take so ta dawo "A'a fa, banda masu delivery din HM Wheels...in dai nazo Kaduna su nake kira, ko da bana Kaduna inaso a karbo mun wani abu a aikomun dashi su nake kira, randa aka samu matsala, mai HM Wheels din da kanshi ya bani hakuri, ni muryarshi ma tasa na kara sonsu, balle kuma da naga hotonshi...har gwada kiran lambar nayi amman naji ta kamfanin ce bawai tashi ba..." Dariya Aise tayi sosai "Kina da karfin hali" Nanan bazawara ce, mijinta ya rasu tun shekararsu ta farko da aure, kuma bata sake wani ba "Daga ganin hoton mutum" Sai kuwa Nanan tace "Bari kiga me nake nufi" Lokacin data mika mata wayar saida taji zuciyarta ta tsaya na wucin gadi, Haris ne, amman ba Haris dinta ba, Haris dinta babu komai a fuskarshi, wannan mutumin akwai saje ko tace kasumba da tasha gyara tana kara masa kyau, bakar fatar nan tashi har wani sheki takeyi saboda hutu, shekaru sun nuna a jikinshi, kamar kuma jikin nashi yayi maraba mai kyau da wannan shekarun, da gaske ne ya zama babban mutum, baiyi kiba ba, jikinshi ya murje dai, babu rama ko kadan a tare dashi. Sai kawai ma'anar HM Wheels ta haska mata da Haris Maryamm, yanda yake furtawa yana jan karshen sunan kamar an radashi ne dan ya gyarashi ya dinga furtawa ta sigar da zai kara dadi, ya kuma bakanta mata zuciya. Batasan cewa soyayyar Haris waje ta samu ta kwanta tanata kara mirgina a zuciyarta ba sai da taje kwanciya, duk juyin da zatayi sai kawai ta dinga hangoshi, zuciyarta tace batasan wani abu su hadu suyi hakuri da Haris ba. Tunda dai tayi aure, to zata ari bakin bature tace "We are even now Amore" Sai dai harta bar Kaduna bata ga Haris ba, taje gidansu sau biyu, bata samu tarbar da tayi zato a wajen Hajiya Rumana ba, yi tayi kamar basu da wata dangantaka, a zuwan farko ma da ta rungumeta sai tayi dabara ta banbareta daga jikinta "Ya Haris kuwa?" Ta tambaya data kasa hakuri "Yana lafiya, tare da matarshi, suna zamansu lafiya..." Ta bata amsar da taji kamar ta kwada mata mari, haka ta shanye da murmushin da bai kai zuciyarta ba. Data sake komawa kuma ko ruwa Hajiya Rumana batayi mata tayi ba, asalima haka tace mata zata kwanta saboda kanta yana ciwo tasha magani. Data tambayi lambar Anisa, kamar ba zata bata ba, sai kuma ta bata lambar sannan ta tafi, sai gashi kuma tasu tazo daya da Anisar matuka "Kamar in miki karya, ince saboda muyi zumunci na karbi lambarki ba saboda Haris ba..." Dariya Anisa tayi sosai "You messed him up Aise, sosai...zanyi entertaining wannan maganar takine kawai saboda bana son wannan matar tashi" A wajen Anisa ta samu lambar Haris, amman kamar layin nashi yana kan tsarin da in dai bashi da lambarka ba zaka iya kiranshi ka samu ba, saita dinga tura masa sakon text, ta dubashi baya kan kowanne social media, har Facebook saida ta duba, banda kamfaninshi da ta tabbatar bashi yake kula da accounts din ba, a Snapchat dai ta ganshi, tayi adding amman baiyi adding dinta back ba, sannan profile dinshi hoton Maryama ne, duk da ba fuskarta bace gabaki daya, rabin fuska ne, itace, a black and white, zuciyarta ta dinga bugawa da wani irin yanayi mai wahala. Ta dinga tunanin inda tayi hakuri a wancen lokacin, data bashi lokaci kamar yanda ya bukata, da ta basu chance, watakila da Maryama bata samu wannan matsayin ba, kilanma da inta shiga zata samu ta fitar da ita. Kawai batasan Haris yaga duka sakonnin da take tura masa ba, tunda ya bude na farkon yaga itace sai yake gogewa batare daya karanta bama, daga karshe ma sai yayi blocking lambarta, ko data tura sakon ba zaije masa ba. Ba karamin mamaki tayi na yanda ya tarbeta wajen bikin Fa'iza ba, taji dadi, ta dinga murna, su Anisa na tayata, duk kuwa da zagin da suka sha a wajen Hajiya Rumana tana kara jaddada musu "Aiko babu mata a duniyar nan Haris ba zai auri Aise ba, wallahi daya aureta gara inta ganinshi da Maryama zuciyata nayi mun baki, abinda Modu ya manta ne kawai bai fadamun ba sai kace 'yar gwal, ya dauketa ya bawa wani, sai yanzun data zama saura ne zata dawo? To me zaiyi da ita? Me ma zaiyi da wata macen tunda bai saki waccen yarinyar ba sanda naso, ai sai suje suyita zama" Amman abinda su Anisa suka yanke shine, Hajiya Rumana ta rissina akan auren Haris da Maryama, ba zata taba fada bane ba, su kuma zukatansu sun kasa hakura, musamman yanda suke tunanin Maryaman nayi musu wani gani gani, shisa gara su hadu da Aise din su kunsa mata bakin ciki. "Ina sonka Haris...ina so ka sake bamu dama" Haka ta fada masa, sai kawai ya kwashe da dariya yana girgiza kanshi, saima ya mike ya fice yana barinta a office din, ganin ya shafe wajen mintina talatin tasan cewa ba dawowa zaiyi ba. Dan motarshi ya shiga ya kama hanyar gida, inda Aise tasan yanda ranshi yake baci duk ganin da zaiyi mata data daina nuna masa fuskarta. Duk wani bacin rai da bai samu ya amayar bane a tsayin shekarun yake taso masa inya ganta. Yara biyu ta haifawa wani, wani daban, shine zata dawo masa? Sai yanzun? To yayi mata me? "Kinsan ya akayi na samu na raba kaina dake Aise? Saida na rasa kaina a wajen kokarin mantaki da tunanin kina tare da wani...ki taimaka mana ki daina zuwa wajena, ki daina damuna...ba zan iya ba, ko meye kike so dani ba zan iya ba" Ya fada mata satika biyu da suka wuce, da yake a tsaye yake a cikin ofishinshi, saita mike itama, da murmushi a fuskarta "Ka fadi abubuwa da yawa, amman babu inda kace ka daina sona, baka sona..." Ya girgiza mata kai "Aise..." Ya furta a hankali, ko giya yake sha ba zaice baya son Aise ba, ganinta da yake yawanyi na tasar masa da kwantattun abubuwa ne da yakeji a game da ita, son da yayiwa Aise, yakeyi mata irin soyayyar nan ce da zuciya take budar ido da ita, soyayyar da bata bukatar wani dalili, rana daya ta gifta ta gabanshi, wani kaso na zuciyarshi ya kwace ya bita, sai ace so so ne, amman kuma shi gashi son da yakeyi wa Aise, idan ya kalli Maryama ba irinshi yakeji ba. A ranar da yake kallon Aise yana iya hango sanda ya fara sonta da lokacin da ya sakawa soyayyar burki, yana iya tuna yanayin da zuciyarshi ta karye, halin daya shiga, duk babu abinda ya manta. Maryama, soyayyar da yakeyi mata tana da dalilai da yawa, dalilan da in aka tsareshi ba zai iya lissafosu ba, yasan dai ba lokaci daya yaji yana sonta ba, soyayya ce da lokaci yake samarwa, irin soyayyar nan mai hade da shakuwa, soyayyar da yanayi yake kara mata yawa, soyayyar da yaji kamar tana hade ne da zaman lafiyarshi lokacin da ta barshi a Ingila, soyayyar da yake hango tsayawar rayuwarshi cak idan ya rasata. Soyayyar da tasa Maryama ta dinga gifta masa a ranar, ranar da Aise ta taka gab dashi har yanajin dumin numfashinta saman fuskarshi saboda dogayen takalma ne a kafarta "Na rabani da kai, dan Allaah....dan Allaah karka rabani da kanka a karo na biyu...ban jure ba daga farko, ba zan iya ba yanzun ma" Ta karasa maganar muryarta na rawa, tana kuma daga hannayenta ta dora akan kafadunshi. Idan akwai wani abu daya da Haris yake jinjinawa kanshi akai shine irin yanda yake iya mallakar kanshi akan mata, duk kuwa da soyayyar da yakeyi musu, komai nasu kyau yakeyi masa, yana kuma so yaji su a jikinshi, amman ba kowacce mace yakebi ba, yanzun da yake ta kokarin bari ma ya kara takaita yawan wadannan matan, sannan in bashi da kanshi yayo ra'ayin yabi mace ba, babu wani abu da zatayi ta ja hankalinshi, ko da zata cire kayanta ne tayi tsaye kuwa zai iya mallakar kanshi, amman Aise ba kowacce mace ba, Aise ko a baya ba karamin kokari yakeyi na ganin baiyi losing control dinshi akanta ba, a lokacin yana hango koma menene zai iya jira, shi da zai kare sauran rayuwarshi da ita, saurin me yakeyi. Amman yanzun ko idanuwanshi ya rufe baya hango wajen zamanta a cikin rayuwarshi, yana sonta, amman ba zai iya ba "Ganjaa..." Maryama tace masa "Idan aure kake so, ka kara aurenka, ba zan baka matsala ba In Shaa Allaah, zanyi kokari, zanyi kokari sosai, kawai kayi mun alfarma karka hadamu gida daya, da matar, ko matan, amman banda Aise, ka auro kowa zanyi kokarin jurewa banda ita" Duk da hawayen da suka zubo mata lokacin da take rokonshi, sai da yace mata "Me yasa?" Ta sake goge wasu hawayen "Saboda irin son da naga kayi mata" Kallonta yayi sosai, na wasu dakika "Ina sonki kema ai" Murmushin da tayi bai karasa cikin idanuwanta ba, asalima wasu hawayen ne suka sake tarar mata "Kagani, wani dalilin, kana sona nima kace Ganja...saboda itama kana sonta har yanzun...ka auro kowa banda ita, inda zan iyama sai ince inka aureta ni zan hakura da kai..." Sai ya girgiza kai yana riketa a jikinshi kawai batare daya sake cewa komai ba. A ranar da Aise ta hade bakinta da nashi, ya kuma zagaya hannuwanshi a kugunta yana mayar mata da martanin abinda take so har saida tsayuwar ta nemi ta gagaresu, shi ya fara sakinta, ya kuma zameta daga jikinshi yana maida numfashi, tayi murmushi "Karka hanamu abinda mu duka muke so" Daya koma gida, sau hudu yanayin brush, yana kara kurkure bakinshi da mouthwash, haka kawai, a karo na farko, yakejin kamar yana hada bakinshi dana Maryama zata iyajin dandanon Aise a jiki, kirjinshi ya dinga dukan uku-uku da yaga ta kure shi da kallo, sai kawai ya dinga nanike mata, tunda a lokacin ma akwai tsohon cikin Aalim a jikinta, sai dai wannan third trimester din yazo mata da yawan kasala, duk bata da wani kazar-kazar, sannan abu dan kadan ne yake sata kuka, ba zai iya tashin hankali ba balle rigima da Maryama akan Aise a wannan phase din da take ciki. Hakan ne ma yasa da ta rokeshi yayi unblocking dinta saboda yayi adding dinta a Snapchat shima, saiya share kamar baigani ba, ba wani sosai yake amsa maganganunta ba, saita wuni tana ajiye masa sako, zai karanta, amman saiya zabi wanda zai amsa, wani abune yake fisgarshi game da Aise din, wani abu da ya kasa controlling, zuciyarshi ce kawai take gaya masa ya biye mata, su watse yanda yaga tana so, yanda yaga ta shirya tayi komai in dai zata sake samun waje a rayuwarshi. Zai iya cewa Maryama da maganganun Malamin da yanzun shine yake zuwa masallacin nan kusa dasu inda Malamin yake limanci yana daukar karatun, bama shi kadai bane ba, suna da yawa tunda makaranta ce ta manya da akeyi bayan isha'i zuwa karfe tara, maimakon farko da Malamin ne yake zuwa har gida. "Sai kaita aikata zunubi kana ganin komai naka na tafiya dai-dai, dukiyarka na karuwa, baka wata rashin lafiya, amman in da zaka zauna ka nutsu tabbas da tsoro mai girma ya shigeka, saboda zakaga Allaah Ya kwace maka abubuwane da zasu zamarwa zaman lafiyarka a kabari, da kuma jefa wasi-wasi a samun aljannarka in harka mutu akan wannan turbar..." Malamin ya cigaba da fada musu "Zakaga sai a kira sallah kayita lakainiya ba zakayita akan lokacinta ba, idan kai namiji ne baka damuwa da yin sallah a cikin jam'i, sannan sai kayi watanni baka bude Qur'ani ba, balle ayi maganar wasu azkar da zasu taimakawa ruhinka..." Haka kawai yana zaune ma wani lokaci sai maganganun Malam AbdulHadi su dinga dawo masa, ko idan yaje yabi wasu matan, shisa ma yake ta kokari wajen ganin ya bari, abinne ya zame masa jiki, kuma har yanzun yanajin kamar ba wani gagarumin zunubi bane, musamman da a wani karatun Malam da kanshi yace musu "Allaah Mai Yawan Rahma ne...idan ka aikata laifi ka tuba, cikin tarin Rahmar Ubangiji saiya yafe maka" Kuma yana gamawa yake tuba, sai dai su kansu sharridan tuban fa? Takesu yakeyi duk sanda zai sake komawa zunubin daya nemi yafiyar Allaah a kai, yana ganin amfanin dagewar da Maryama tayi akan Islamiyyar su Awwab, watakila da yasan abubuwan nan da karancin shekaru, ya maida hankali akansu, sun zauna a zuciyarshi, ba zasu dinga kokawa dasu ba a yanzun. Saiya kara hadawa da cewar ya jima rabonshi da mace, Maryama cikinta ya tsufa sosai, dan a halin yanzun ma Aise kadai yake magana da ita, itama ya kwana biyu basu hadu ba, ya yanka mata warning randa ta gwada shi akan zata kawo musu ziyara a gida, wajen sati ya dauka bai kulata ba, sai da taita bashi hakuri tana gaya masa wasa takeyi. Baije HM Wheels ba a kwanakin, ya karbi wasu ayyukan daukar hoto ne da suke cinye masa lokaci, gashi bayason yayi nisa da Maryama kar nakuda ta kamata. Ita tace masa sunyi waya da Fa'iza tace mata zatazo ta wuni a gidan ranar Asabar, shisa ya amsa Aise da ta matsa tana so ta ganshi da "Zamu hadu ranar asabar..." Shi ya rubuta sakon, amman saiya dinga karantashi yana sakewa wani irin yanayi marar dadi na saukar masa, wani abu da baisan kaddarar da ta rantse tsakaninshi da Aise bace na danne shi... 47 Ranar juma'a... Ko kadan Haris baiyi niyyar fita ba, sai ga kiran Barde, yace masa yana Kaduna, da yake ya dawo daga kasar India, yayi karatunshi har zuwa matakin Masters, babu wani abu daya basu mamaki sai daya samu aikin lecturing "Nifa na kasa hango Barde da dalibai a aji..." Cewar Lalaye yana sheka dariya, sai dai bai hada shekaru biyar yana aikin ba sai ya koma aiki da wani NGO, aikinne ma yasa baya zama sosai, dan yawo sukeyi gari-gari, a halin yanzun yana da mata daya da yara uku. A cikinsu Lalaye ne yayi mata har biyu, kuma maganar kara ta uku ma yakeyi, yaranshi bakwai. 2Pac kuma shekararshi daya kenan da dawowa Nigeria, dan duk shekarun nan yana zaune a kasar Ingila ne da matarshi, yaranshi biyu duka mata, yanzun suna zaune a garin Abuja. Lokacin da Haris ya fita, zuwa inda Barden yace masa zasu hadu, sai bakinshi yaki rufuwa ganin tare suke da 2Pac "Bakace mun tare da Pac kuke ba" Barde yayi dariya "Nace masa zan shigo Kaduna nefa, shine yace bari ya shigo shima..." Da yake eatery ne, sai sukayi order din abinci, Haris dai ruwan kawai ya bude, sai dai anata kiran Barde a waya dan ana jiranshi, hakan yasa yayi musu sallama ya tafi, suna dan hira wayar Haris take ta vibrating ya dauketa yana duba mai kiran, yaja karamin tsaki ya kifeta saman teburin wajen. Yau da safe yayi unblocking din Aise, amman harta isheshi da kira, abinda bayaso kenan, abinda kuma yake gujewa, dole ya saka wayar a silent, sai da zai fito din nan nema ya cire ya mayar vibration dan kar Maryama ta kirashi bai sani ba, wajen kira na biyar ne daya daga ya sake kife wayar, 2Pac ya daga masa gira daya, sai yayi dariya mai sauti "Har yanzun? Har yanzun Ganja?" Cikin son kare kai Haris yayi saurin amsawa da "Duka yaushe ka daina shaye-shaye?" Wani abu ya gifta ta idanuwan 2Pac, wani abu mai ciwon gaske da yasa Haris yin dana sanin maganar daya fada "Kayi hakuri" Murmushi yayi mai ciwo "Gaskiya ka fada ai, duka yaushe na daina, amman na daina, saboda nasan abune daya kamata, ina kuma kokarin ganin nayi ayyukan alkhairi da nake fatan Allaah Ya aramun rayuwa mai tsayi saboda in samu su danne shekarun dana shafe in aikata abinda bai kamata ba, amman ban taba rike hannun macen da ba muharramata ba Haris, ko a lokacin kuruciya balle yanzun da nake kallon yara mata a gabana, nake kallon matar da ba zan taba yin abinda mutuncina zai ragu a idanuwanta ba..." Shiru Haris yayi "Inaso ince maka kabari saboda Rauda, sai dai ina da yakini akan Rahmar Ubangiji, zai kare mana yaranmu, In Shaa Allaah kuskurenmu ba zai shafesu ba...ina maka addu'a, ban cire rai zaka bari ba tunda Lalaye da Barde suka daina..." Muryar Haris can kasan makoshi yace "Aise ce...ba wasu mata bane, Aise ce" 2Pac yasa hannuwanshi duka biyu ya dafe fuskarshi kafin ya bude yana kallon Haris "You are going to destroy your family Man...Maryama ba zata yafe maka ba...saboda Aise ce" A cikin abokanshi kaf 2Pac ne ya san dukkan sirrikanshi, duk wani fada da suka tabayi da Maryama, yasan komai akan Aise "Nasani..." Kai 2Pac din ya daga "Kaima ba zaka yafewa kanka ba inka rasata...ka kyale Aise inda take Ganja...koma menene wannan kuke kokarin yi, ka tsayar dashi" Sai dai ai anan matsalar take, shima Haris din baisan abinda suke kokarin yi din ba, balle yasan ta yanda zai tsayar dashi "Ganjaa..." Kai ya daga da wani yanayi akan fuskarshi, sai 2Pac yayi murmushin takaici yana girgiza nashi kan "Ka jini, amman baka dauka ba ko?" Shirun ya sakeyi, sai kawai 2Pac ya canza maganar suka dauko wata hirar bayan Haris ya turawa Aise gajeran sakon cewar yana wani abune, itama saita dawo masa da sakon da bai bude ba sai bayan sun rabu da 2Pac tukunna, yaji zuciyarshi ta buga ganin adireshin hotel ne da kuma lambar daki, yasan ma hotel din, ya sha zuwa, amman wannan karin wani irin yanayi ne marar dadi ya rufar masa. Ya goge sakon nata da kuma wanda ya tura mata shima, sannan ya koma gida inda ya samu Maryama a kitchen tana gyara zogale zata dafa "Kin cika rigima Maryamm...ba saiki bari su Awwab su dawo makaranta ba ya dafa miki" Tunda yayi mata magana ko za'a kawo mata mai aiki tace masa a'a "Su Awwab zasu wuce gidan Mami, ka manta yau juma'a..." Dan Naadir ma tunda safe Hajiya Rumanan ta aiko aka daukar mata shi, lokacin Haris ko tashi daga bacci baiyi ba. Hannu ya saka yana tayata tsige zogalen "Kafata ta gaji fa, kizo mu koma falo" Tayi dariya "Babu mai gyaramun zogale a falo...kabarmun abuna yanzun zan karasa gyarawa aina kusan gamawa" Bai tafin ba, tsayawa yayi suka karasa gyarawa sai dai yanata mata mitar da bata kulashi ba, itafa wannan cikin ko dogon surutu gajiya yake kara mata. Batasan yara nawa Haris yake so ba, basu taba maganar ba, amman ita dai har kasan ranta tanajin wannan hudun sun isheta, tana fatan Allaah Ya raya mata su, zata tsayar ta numfasa, da take maganar da Khairi saita dingayi mata dariya "Haba mana, aina dauka sai kinyi kamar takwas haka..." Duk da Khairin bata ganinta saida ta watsa mata harara ta wayar "A'a sha biyu ne ba takwas ba" Khairi ta sakeyin dariya "To ai naga kuna da kudin, saiki samu masu tayaki kula dasu...kikasan ko shi Haris din da yawa yake so?" Da wani daci a kasan makoshinta tace "Inya auro Aise ai saita karasa masa sauran" Idanuwanta na cikowa da hawayen da basu zubo ba, a gabanta Anisa ta cewa Haris "Nifa na fara shiri Haris, tunda Aise ta fito nasan rabon zama da kaine ya fito da ita, gara kazo kayi abinda ya kamata kaima dai auren soyayyar nan kayi shi" Duk da cike da kashedi Haris din ya kira sunanta bai hanata yin dariya tana kallon Maryama da cewa "Ai kinsani ko Maryama? Kanina mijin mace hudu ne, kuma bai tara kudin nan dan ya zauna dake ke kadai ba..." Itama murmushi ta dora a fuskarta duk da kirjinta bugawa yakeyi da wani irin abu mai ciwon gaske "Wai meye haka Anee?" Haris ya fadi ranshi a bace, Maryama ta sake fadada murmushinta "Gaskiya ta fada fa, ga gidan nan ma ya ishemu" Anisa dake wata dariya tace "Zata takura, kinsan yanayin gidan da ta taso ba daya bane da naku..." Haris zaiyi magana Maryama ta rigashi "Eh mu gidanmu ma ban taso naga kishiya ba, amman na dauka ba zai zama matsala ba, tunda duk abu dayane dasu Mami, kuma banga sun takura juna ita da Umma Fadime ba da Baba ya hadasu" Kuma sai Anisan taji haushi "Zagina zakiyi Maryama?" Haris yace "Idanma dukanki tayi ai cikin gidanta kikazo kike nema ki daga mata hankali..." Sai fadan ya koma kanshi, Maryama ta bar musu falon ma, batasan sanda Anisa ta shigo ba, shima daya zo ya fara jaddada mata ba auren Aise zaiyi ba, bata kulashi ba. Tunda suka fara maganar ai tasan sai abinda ta gani, ba tun yanzun suke neman hanyar da zasu quntata mata ba, sai su zuba ruwa a kasa susha, dan kuwa sun samu yanzun. Ba zata fara aro jarumtar da tasan bata da ita ba in dai akan Haris da Aise ne, saboda bayan kaddarar auren Haris, Allaah Ya kara jarabata da soyayyarshi, so takeyi masa da dukkan zuciyarta, irin soyayyar nan da zuciya zata dinga yiwa wanda take so uzuri batare da gajiyawa ba, amman akan Aise dai har zuciyar ma ta nuna mata ba zata iya dauka ba. "Waike baya fada miki ba zai aureta ba? Me yasa ba zaki cire tunanin nan daga zuciyarki ba?" Khairi ta fadi a hankali, Maryama ta share hawayen da sai lokacin suka zubo mata "Na kasane Adda Khairi, yana sonta, ko musu baiyi mun akan yana sonta ba har yanzun...a rashinta ne fa aka bashini ya karba saboda babu yanda zaiyi...ni din da ba auren soyayya mukayi ba ki kalli yanda yake zaune dani, kuma da kuke 'yan uwana kalli yanda yakeyi muku...idan kuma yau akace wadda yake so ce ya auro fa? Kingane abinda nakw tsoro Adda? Kingane fargabata yanzun?" Shiru Khairi tayi cikin rasa abin fadi "Ganja ya iya kula da abinda yake so Adda, yanzun nake gane ko da na kamashi da wata, na hakura ne saboda ina da tabbacin ba soyayya ce ta hadasu ba, inajin mutuwa zanyi idan ya auro Aise, in ban mutu ba kam zai wahala ban hakura na bar mata shi ba tunda daman kaddara ce tayi musu katsalandan" A tausashe Khairi tace "Duk ma hakan ba zai faru ba In Shaa Allaah, ki cigaba da addu'a, kuma kiyi kokarin cire tunanin daga ranki, kinsan dai ba'a son masu ciki da yawan tunani" Da "Hmmm" Maryama ta amsa, amman har ranar juma'ar nan inta kalli Haris ta hangoshi da Aise sai taji komai ya fice mata a rai, shima sai taji haushinshi ya turnuketa kamar ta shakareshi ta huta. Haka suka kwanta, amman tun cikin daren takejin bayanta ya riqe, tana tashi zaune Haris na bude idanuwa shima ya kuma kunna kwan dakin haske ya gauraye ko ina "Ya akayi? Bayan ne?" Ya tambaya tunda a satin ma gabaki daya ciwon bayan ya dameta, ta wuce Edd dinta na farko da kwana takwas, kai ta daga masa, a asibiti likitarta ta nuna masa yanda zai dinga taimakawa yana yi mata tausar bayan in yana mata ciwo. Haka suka kwana, basu koma bacci ba sai bayan da sukayi sallar asuba. Ta riga Haris tashi, lokacin karfe tara da wani abu, ta lallaba tayi wanka, ta saka wata doguwar rigar material dinkin bubu, kitsone, zanen hausa a kanta guda shida, yau kwana uku ma dayi mata shi, wata budurwa ce, kabila, amman musulma a saloon din da take zuwa, yarinyar ta iya kitso sosai, shisa ta karbi lambarta, sai take zuwa gida tanayi mata, kusan wuni sukayi ana abu daya, dan sai anayi ana tsayawa saboda ciwon bayan daya dami Maryama "Gaskiya a hakura da kitson nan" Haris ya fada daya dawo ya sameta tana zagayen daki, lokacin guda biyu akayi "Haka zan shiga dakin nakuda da kai babu kitso? Salon azaba ta isheni inta cisgar kan in rasa na parking ko? Kazo kace zaka karo aure tunda ni bani da gashi" Dariya yayi sosai ganin yanda take maganar da dukkan gaskiyarta, dakyar aka gama kitson data kira na shiga labour room. Kitchen ta shiga, yunwa takeji sosai, kwai kawai ta soya ta hada shayi ta dauko biredi, tana cikin karyawa Haris ya fito, shima yayi wankan, da gajeran wando baki a jikinshi sai singlet baka, sanin su kadaine a gidan. Da kanshi yaje ya hado shayi ya dawo falon ya zauna yana sha, tama daina wahalar da kanta wajen yi masa magana kan abinci, takaicinta daya, yanda a cikin yaran Rauda ce take gudun abinci kamarshi, gata nan sai kace tsinke, lokacin data yayeta haka suka sha fama, ta dinga bushewa saboda sai an matseta ake dura mata kunun alkama, shima ganin yanda take sharara amai yasa Maryama ta hakura ta kyaleta, duk wani multi-vitamin ta karbo mata a asibiti, amman tana nan tsigai-tsigai sai kace bulala. Sai dogon hanci irin na Haris din, amman ita bata kai su Awwab baki ba. Har dariya take yiwa kanta idan ta tuna wai itace take auren bakin namiji kamar Haris, ta kuma goya bakaken yaranshi, balle kuma inta tuno yanda take tunanin babu namiji me kyan Ishaq a zamanin kuruciyarta saboda farinshi, shima yayi aure suna zaune a Lagos da matarshi saboda acan yake aiki, ta ganshi wajen sau biyar, suka gaisa tanata mamakin abinda ma taso a tare dashi, musamman yanda ya narka wata irin kiba harda tumbi, ganin da tayi masa na farko bayan aurenta ne ranar data fara ganin kyan Haris, ta dinga kallonshi bayan ta dawo gida, shafaffen cikinshi tana addu'ar Allaah Yasa kar yayi tumbi irin na Ishaq, ashe bama bakin namiji bane bataso, mai tumbi ne. A yau kuwa in tumbinshi zai kai tulelen cikin da yake gabanta, in har ba zai auro mata Aise ta gansu tare ba, ba zata damu ba, data gama karyawa ne take ce masa "Kana ganin Fa'iza ko? Haka fa tace tunda sassafe zata zo" Yayi dariya "Ai banyi magana bane, amman yaushe Fa'iza ta gama baccin safe balle ta tashi ta shirya ta fito?" Gashi cikinta harya fara fitowa, da yake bata same shi da wuri ba, saida ta fara nuna damuwarta ma tukunna, cikinne yasa Haris siya mata mota, a cewarshi ba zai yiwu ta dinga yawon zuwa makaranta a napep ba "Amman baka ganin mijinta zaiga kamar ana nuna masa iyakarshi akan Fa'iza? Tunda a tsaye yake, bafa zai yiwu daka ga bata da wani abu kace zakayi mata ba..." Sai ya kalleta da wani yanayi yana fadin "Dan na bata mota? Ba wata babba bace bafa, nasan zakiyi magana shisa na siya mata karama, sai in sai ma Auwal din wadda ta fita" Dariya tayi tana girgiza masa kai, tunda a lokacin Auwal bashi da mota, hadari yayi da tashin, baiji ciwo ba, amman sai gwangwan din motar akayi, bai mayar ba har yanzun, da mashin yake hawa "Ba ca nayi ka sai masa mota bafa" Ya sauke numfashi "To me kike cewa? Koshi zai kaita unguwa dai ai babu yanda za'ayi ta hau mashin da ciki ko? Balle kinsan ni bana son napep din nan da suke figa gudu kamar mutum zai fado..." Kyaleshi tayi, in dai akan yaranshi ne da kashe musu kudi, Haris ba zai daina ba, ya daina shawara da ita, sai dai inta ga wani abin ta kwace kawai, to Fa'iza ma da yake mata rikon 'ya haka yakeyi, dakyar ta samu ya daina jibgar kayan abinci yana zuwa yana kai musu kamar Fa'iza tace masa Auwal na barinta da yunwa, yaron tsaye yake, wani abinma in yayi mata kamar yafi karfin samunshi, yanayi ne saboda Haris na sakashi jin kamar ya gaza akan iyalinshi, tausayi yake bata, tunda Allaah Ya hadashi da surukin zamani. "Nima fita zanyi, amman zan jira Fa'iza tazo, bana son inyi nisa in barki ke kadai" Yayi maganar a hankali, dan saida ta daga kai ta kalleshi "Ina zakaje?" Ta tsinci kanta da tambaya, ya danyi jim, karya na cikin abinda yakeyi masa wahala matuka, zai gujewa fadin gaskiya ta hanyar yin shiru in ba tambayarshi akayi kai tsaye ba "I'm meeting someone..." Ya fadi, akwai wani abu da bai zauna mata ba, taso ta kara tambayarshi sai taji mararta ta daure, ta kuwa riko hannunshi tana kiran sunan Allaah "Menene? Bayan ne?" Ya tambaya a rude yana saukowa, kai take girgiza masa jin ciwon ya taso mata gabaki daya, dumin da taji a jikinta kuma ya tabbatar mata da faya ce ta fashe mata "Maryamm...muje asibiti, bari in dauko mukullin mota" Haris yake fada a rude jinshi zaune cikin lema shima, kuma haihuwa uku ba wasa ba, ya riga yasan ruwan nakuda ne, kai take girgizawa tana kara rike shi "Nishi nakeji Ganjaa...haihuwa zanyi" Ya zaro idanuwa kamar zasu fado "Nishi kikeji? Nishin ne haihuwar?" Yake tambaya muryarshi da jikinshi gabaki daya yana rawa tare dana Maryaman "Dan Allaah karkiyi nishin to, ki rufamun asiri ki rike nishin sai munje asibiti..." Wani irin yunkuri tayi tana cigaba da kiran sunan Allaah, haihuwar ta taho mata gabaki daya "Kan ya fara tahowa, leka...lekamun kagani" Cikin wani irin tashin hankali da bai taba sanin akwaishi ba yace "In leka me? Inga me? Wanne kan? Maryamm, Maryamm kar kiyi mun haka" Ya karasa maganar yana kokarin mikewa amman saita sake damtse hannunshi kamar zata karya masa yatsu, inma wasu basu karye ba a karar da yaji sunyi, sallamar Fa'iza ta cika falon "Fa'iza zo kiga abinda Maryamm zatayi mun, so takeyi ta haihu anan, ki kama mun ita mu tafi asibiti" Da gudunta Fa'iza ta karasa falon, ita Mass communication take karanta, yanzun take shekararta ta biyu, bata taba ganin haihuwa ba tunda ba'a tabayi a gabanta ba, amman yanda Maryama ta damketa, rikone tayi mata daya tabbatar mata da in ba wanda yake cikin ciwon nakuda ba, babu wanda zai iya rikeka haka, saita tuno kauyensu, ta tuno mahaifiyarta, lokacin da kishiyarta take nakuda, kafin a koresu daga dakin, taji tace mata "Ramatu rike mun hannuna" Babarta ta matsa tana fadin "A'a wallahi, rabani da rike mai nakuda ki karyani, rike karfen gadonki Abule" Tabbas karfen ne ya kamaci masu nakuda su rike ba mutum ba, karfen ma mai kwari, a wannan asabar din, a cikin dakinta, a tsakanin Fa'iza da Haris, da taimakon Ubangiji Maryama ta haifo danta da kukanshi ya karade dakin, Fa'iza ce ta dauko mata jakar data hada kayan haihuwarta a ciki ta yanke cibin da kanta, sannan Fa'izar ta nadeshi cikin showel tana kallon Haris da fuskarshi tayi wani irin fayau "Bani da lafiya Fa'iza..." Kuma yayi kama da marar lafiyar "Meya sameka?" Maryama da takejin kamar an sauke mata nauyin duniya daga kanta ta tambaya "Bansani ba, kamar mahaifata ce ta koma" Daga Fa'iza har Maryama dariya sukeyi, yanda yayi maganar da dukkan gaskiyarshi, har suka tattara sukaje asibiti dan a tabbatar da lafiyarsu data jaririn, bayan Fa'iza ta gyara falon, ta nade kafet din da tasan zai wahala ya fita, basu daina yiwa Haris dariya ba, shi dai kallo daya zakayi masa kasan a firgice yake, ko da yake bin Maryama dakin nakuda, bai taba ganin tashin hankali irin na yau ba, koya hankalinshi a kwance yake tunda likitoci sun zagayeta, amman a gida, sai kawai ta haihu a gida? Ya kasa daina tunanin inda an samu wata matsalar da ya zaiyi? Da gaske kamar bashi da lafiya haka yakeji, dan bakar jallabiya ya saka a jikinshi da zasu fito asibitin, aka dubasu aka tabbatar musu da komai lafiya, sai bayan sun dawo gidane sannan aka fara kiran mutane ana sanar dasu haihuwar da tayiwa kowa bazata. Lokacin ne kuma Haris ya samu kanshi ya dauki wayarshi da take a silent, missed call din Aise ya gani har guda goma sha daya, sai yaji cikinshi ya hautsina, shayin daya sha yana taso masa, babu shiri ya nufi bandaki yana yin aman har ruwan daya sha a ranar, su Fa'iza nayi masa dariya, yasan ya rude ne, bashi da mahaifa, amman da gaske yakeyi bashi da lafiya, wani abu nayi masa ciwo, daya daga hannayenshi ma sai yaga suna rawa, wani yanayi yakeji da bature yake kira uneasiness, ga zuciyarshi nata bugawa batare da wani dalili ba, sai ya cire kayanshi ya watsama jikinshi ruwa, ya fito ya samu kaya ya saka, amman yanayin nan bai barshi ba, ya dauki wayar tashi da mukullin mota ya fito, yanajin  hayaniyar mutane daga babban falon gidan, yasan 'yan uwan Maryama ne da suka zo, ya gaisa dasu Adda Maimunatu, kilan wasune suka kara zuwa shiga hayaniyar ta karu. Akwai wata kofar fita tanan bangaren nashi da yake mantawa da itama saboda ba amfani yakeyi da ita ba, yau ta nan ya fita, ya saka mukullin motar ya bude kenan zai shiga saiya tuna ya bar wallet dinshi, babu kudi a jikinshi sannan katikan bakinshi duka suna ciki, ya danja tsaki yana juyawa ya koma, daya dauka saiya manta ya taka yana bi ta babban falon, haka ya dinga bude hakora suna kara gaisawa da mutane saboda yanayin da yake jinshi, lokacin wayarshi ta hau kara dan ya cireta daga silent, ya nemi idon Maryama a cikin dakin, sai tayi masa murmushin daya kasa mayar mata, ya taka yana juyawa zuwa hanyar fita, kiran harya yanke, yana kaiwa bakin kofa aka sake kira, Aise ce dai, saiya daga muryarshi na rawa kamar wanda akayiwa dole yace "Hello..." 48 Aise Modu Aisha Muhammad shine cikakken sunanta, haka kuma mahaifinta ya saka mata a makaranta lokacin daya kaita, ta dade inta kalli sunan a takarda sai taga kamar ba nata ba, lokacin da tayi girma sosai ma sai takejin inama ta canza, tafison Aise, tana kuma jin dadin yanda yanda ake kiran mahaifin nata, musamman idan sukaje Maiduguri, yanda 'yan uwanshi suke furta sunan da harshensu daya fara karyewa da yaren Kanuri, akwai wani yanayi da suke fadin sunan dashi da a bakunansu ne kawai takeji. Kamar kowanne dan adam, ta taso da burika masu yawa, tasani tana daga cikin mutane masu sa'a, saboda bakowa bane yake samun cikar kaso mai yawa na daga wadannan burikan, ita Aise tun tana da shekaru bakwai a duniya tasan cewa tana so ta zama likita, tana girmane komai na kara fito mata tar, tana kuma fahimtar abinda zuciyarta take so, kafin a hankali ta tsaya kan abu daya, saboda haihuwa da duk wani abu daya danganceta suna burgeta, duk lokacin da wata mai ciki zata shiga ofishinta sai abin yayi mata kamar sabo, kalmar ciki abu dayane, kuma hanyar samunshi ma da nature yazo dashi iri daya ce kafin zamani ya samar da wasu hanyoyin, amman kowanne ciki ya bambanta ne a tsakanin mata, kowa da yanayin laulayinta, wahalhalunta da makamantansu. Tana rike duk wani jariri da zata taimaka wajen karbar haihuwarshi ne da sabon shafi a zuciyarta, shisa mutane sukeyi mamaki idan tace batason yara "Inaso in taimaki duk wanda yake son yara da duk abinda zan iya har sai na mika musu yaransu sun rike a hannunsu, hakan baya nufin ni inaso a taimakamun in rike nawa..." Amsar data bawa Mu'adh kenan lokacin daya tambayeta, saiya girgiza kai kawai. Shisa rashin yaranta baya wani damunta, bata da emotional attachment sosai dasu. Burinta na biyu bayan wannan shine irin mijin da zata aura, tana da tsare-tsare masu yawa a cikin kanta, da tarin hasashe na yanda zai kasance, ba zata tuna ko ya wannan tsarin nata yake ba bayan ta hadu da Haris, idan ma baiyi kama da abinda take hasashe ba, zuciyarta ta karbeshi, tayi masa karbar da ko wani namiji ne ya gifta ta gabanta sai Haris ya gifta a cikin zuciyarta. Ko a mugun mafarki bata hango wai zatayi rayuwa da wani namiji ba shi ba, Haris kuma zai rayu da wata mace ba ita ba, haka wannan burin nata ya zama gari ya barbade yabi iska, to abinda yabi iska zai dawo ne? Haka tayi zato, ko bayan da ta rabu da tsohon mijinta. Sai da ta sake saka Haris a idanuwanta sannan, sai kuma data ganshi a gabanta, ta sake jinta a jikinshi. Haris, Haris dinta, taya ma zatayi tunanin hakura dashi bayan ta sake samun wannan damar? Sai dai abinda batayi zato ba shine zata dinga bin Haris yana zame mata, Haris fa da in bata daga wayarshi ba yake baro makarantarshi zuwa tasu batare da tunanin tazara ba, akwai ranar da yace mata "Kina lafiya, abinda nazo gani kenan" Kuma bai jira tace komai ba ya juya ya tafi abinshi, Haris yasan darajar abinda yake so kuma baya wasa dashi, ashe a baya karyar soyayya tayi tunda ta hakura dashi, yanzun ne ma taji ta fara sonshi, saboda a shirye take da tayi komai dan ta mallake shi, in tace komai, to tana nufin komai. A irin yanda take ganin taurin kan Haris kan sake basu wata dama, raunin shi akan mata kawai zatayi amfani dashi yazo hannunta, har mamaki takeyi, yanda itace take bin namiji haka, kuma wai har take shirin yin komai dan ta sameshi, a baya tana daga cikin mutanen da suke kallon mata masu irin abinda takeyi da ballagazai, ko a Italy in taga mace na bibiyar namiji yana yankwanata sai taja tsaki tana fadin "Shashasha" Sai gata cikin shashancin da take ganin tafi karfin ta aikata shi, a Abuja, akwai cousin dinta, 'yar kanwar Mamanta ce, tazo gidansu ta kwana, suna kwance suna duba abu a wayar Kariman, sai taga wani post a daya daga cikin blogs din da take bi na wata yarinya data ba saurayi kanta kuma yazo ya gujeta "Wasu matan fa wawaye ne, me take tsammani zai faru to? Ya zakayi ma kana musulmi, da hankalinka kaje ka aikata wannan shirmen..." Sai Karima ta kalleta, kallo na sosai "Idan kikaga abu irin wannan, to kiyi addu'ar shiriya kawai, ki kuma nemawa kanki kariyar Allaah daga aikata abu makamancin shi, dan bakiyi ba, baya nufin kinfi karfin kiyine, Allaah Ne kawai ya kareki bai jarabeki ba...babu kyau" Sai taja tsaki kawai, shisa ta tsani shiga dangin Mamanta, abu kadan zakayi su fara yi maka wa'azi, suna so su jingina maka kafurci, ita da hankalinta wanne namiji zata biyewa, ko data taso a kasar waje tasan darajar kanta, sai gata yau da booking hotel da hannunta saboda tana so ta samu kan Haris, saboda a halin yanzun bata da wani buri daya wuce ta ganta a matsayin matar Haris. Motarta ta dauka daga hotel din da suka sauka da abokan aikinta, ta riga ta gane hanyar da zata mayar da ita hotel din da taje ta kama jiya, sunyi da Haris zasu hadu wajen karfe daya na rana ne, shisa ta dinga jera masa kira tun wajen sha biyu kafin ma ta fita, sai dai bai daga ba, kawai ta shiga mota ta fice, tana ganin kiran Mamanta lokacin da take hanya, saita danne wayar tana kashe kiran, ta tura mata gajeran sako cewar tana busy zata kirata. Batason duk wani abu da zaisa taji ta fasa kudurin da yake ranta, traffic ya tsayar da ita tare da wasu jerin motocin a gabanta da bayanta, yau hutun karshen mako, amman batasan ya akayi titin yake a cike haka da kwallin ranar da akeyi ba, turare ta janyo ta kara fesawa, data ajiye sai tayi atishawa, ta sakeyin wata, ta jera atishawa wajen biyar a lokaci daya, hakan yasa ta sauke gilasan motar, wasu turarukan suna saka mata mura, amman wannan lafiya kalau takeyin amfani dashi, sai tayi tunanin ta fesa shi da yawa ne, dan kamar har kirjinta da ya kulle ya shiga, ta danyi tari tana dan murza kirjin nata, wayarta tayi haske, saita kalli wayar, ta daga ido ta kalli traffic din, wasu motocin na gabanta sun fara wucewa, amman ganin sakone ta Snapchat saita daga wayar da sauri, tana fatan Haris ne. Ta daga wayar, ta kalli wayar, kirjinta ya sake daurewa ganinta na daukewa, a shekarun da tayi a asibiti, ba zata kirga adadin mutuwar da ta gani ba, a farko-farko abin yake damunta, amman sai tazo ta saba, zuciyarta ta kekashe, sai dai in akayi mutuwar, taga an dauke gawar, an nade zannuwan gadon, ta kuma san zuwa za'ayi a wankesu, inta zauna shiru saita dinga tunani, to me ake so a wanke? Cutar? Daudar? Ko kuma mutuwar? Idan mutuwar ce taya za'a wanke mutuwa ta fita? Wanda aka sake kawowa aka dora akan wannan zanin gadon ko ya sukeji? Ko suna ganewa? Ko sunaji a jikinsu wani ya mutu akai? Ko yana warin gawa idan gawa nada wani wari a ranar da ruhi yabar gangar jiki kenan, tambayoyin da bata da amsarsu, taga mutuwa a yanayi daban-daban, amman batasan mutuwa ba sai yau data risketa, sai da ta sameta a cikin motarta, ta bude bakinta da niyyar neman yafiyar Allaah sai dai "Ast..." Shine sautin daya fito, lokaci yayi abinda ya saba, ya cika akanta Rai baya jiran buri! Mutane nawa ne irin Aise? Mutane nawa ne suka fita daga gida da niyyar marar kyau lokaci ya kare musu kafin su aiwatar? Inama inama? Inama ace mutuwa sallama takeyi, saboda ka shirya, ka samu wannan dan taqin, ko da bai isheka furta shahada ba, kalmarka ta karshe a harshe da zuciya ya zama neman yafiyar Ubangiji ce... Haka mutanen da suke cikin motocin da suke bayan Aise suka dinga danna mata hon, harda masu leko kai suna hadawa da zagi, wasu ma nayi cikin zukatansu, yayin da wasu suka dinga rabewa suna wucewa da tunanin karfen nasara ne da akace bashi da tabbas yayi mata halin, motar ce ta samu matsala, haka aka dinga rabewa ana wuce Aise, har saida wasu masu POS a tsallaken titin da masu saide-saide suka kula da matar da take ciki kamar bata motsi, sanann kanta ya langabo tunda tana daure ne da seatbelt, aka taso aka tsallako ana dubawa, mai POS din nan shiya fara zira hannunshi ya dauko wayar Aise din da akaci sa'a babu mukulli a jiki, dan yasan a yanayi irin wannan wasu sun zagaye motar ne saboda su samu abinda zasu sace. Lambar karshe da aka kira, ita ya kira, sau biyu ba'a daga ba, sai ana ukun daya saka ranshi in ba'a daga ba zai sake duba wata lambar ne tukunna aka daga kiran kusan a tare sukayi magana, shi sallama yayi, Haris kuma ta dayan bangaren yace "Aisee...." Yana jan sunan da yanayi na kosawa a cikin muryarshi, jin ba ita bace yasa shi tsayawa cak, ya sauke wayar daga kunnenshi ya duba, lambarta ce, ya sake mayarwa yana fadin "Hello..." Aka sake maimaita sallamar, bai amsa ba "Waye?" Ya furta, baisan dalili ba, muryarshi yaji tana rawa "Sunana Isa, munga wannan ce lamba ta karshe da mai wayar ta kira...Allaah Yayi mata rasuwa...t...." Duk wani abu da ya cigaba da fada baya karasawa kunnuwan Haris da sukayi kamar an tashi bomb a cikinsu da kalmomin "Allaah Yayi mata rasuwa" Sune suke juya kansu cikin kwakwalwarshi, suna samun waje a zuciyarshi da take wani irin bugawa da sauri-sauri, wayar da take hannunshi ta subuce ta fadi kasa, yasan ya koma cikin falon nan da kafafuwanshi da sukayi masa kama da taliya saboda rawar da sukeyi, baiga tarin matan da suke falon nan ba, baiga kowa ba sai Maryama da itama take kallonshi ganin yanda jikinshi yake rawa "Maryamm..." Ya furta kalaman na komawa cikin kunnuwanshi da wani irin sauti, saboda yanda yakejin makoshinshi ya bushe kamar wanda yasha bokitin kasa, ya kuma ga tasowar Maryaman, amman zuciyarshi da take bugawa tasa wani irin duhu gilma masa, sama-sama yakejin kamar hannuwan Maryama na girgiza shi, amman dan hasken da yake gani ma saiya dauke masa. Abinda ya sake gani shine bude idonshi da yayi a asibiti, rudewa  sukayi lokacin da suka ga ya fadi, banda Adda Zahra data karasa bakin kofar ta dauko wayarshi da take ta kara, ita ta daga kiran duk da babu suna a jiki. "Wata ce ta rasu, cikin 'yan uwanshi waye a Kaduna?" Kai Maryama ta girgiza musu, dukansu sai in sunzo Kadunan ne, kuma baice mata wani yazo ba, zuciyarta sai bugawa takeyi kamar zata fito daga kirjinta, ta nemi hawayenta ta rasa, abinda yake nutsar da ita shine jin bugun zuciyar Haris a tafin hannunta da yake kan kirjinshi, tasan yana da rai, koma waye ya rasu a wannan lokacin, mai saukine a wajenta, tunda ba Haris bane ba. Su hudu suka hadu amman da yake duk taron matane sai suka kasa daga shi, saida suka nemo taimakon maigadinsu da ya kira wasu mutum biyu sannan aka saka Haris din a mota, Khairi ta goya Aalim, Adda Maimunatu itace ta tuka motar bayan Adda Zahra ta ba Maryama wayar tana fada mata tayi kokari ta kira wani a gidansu Haris din ta sanar musu da abinda yake faruwa. Da wayar Haris din tayi amfani ta kira Hajiya Rumana, sai lokacin ne hawaye ya balle mata "Rasuwa kuma? Waye ya rasu to?" Ta tambaya a kidime, tana kashe wayar kafin ma Maryaman ta samu damar amsawa, sanda suka karya kwanar da zata hadasu da asibitin Frontiers saiga kiran Anisa "Babu suna a jikin lambar?" Ta tambaya, Maryama tace mata "Babu..." Ca tayi ta tura mata, ta kuwa yi copy ta aikata mata, bataji ta samu natsuwa ba saida aka karbi Haris, aka duba shi, likitan yace musu babu wata damuwa, sunyi masa allura da zai dai-daita bugun zuciyarshi, shock ne kawai ya shiga. A asibitin Hajiya Rumana tazo ta samesu, daga gani a kidime take, idanuwanta sunyi kozai-kozai, karo na farko da Maryama zatace taganta babu ko alamar hoda fuskarta, dan a shekarunta, yar gayuce ta kwatance, da alama kuka tasha, cikin wata irin murya mai sanyin gaske ta cewa Maryama "Ya Haris din?" Maryama ta amsa da "Bacci yakeyi, sunce babu wata matsala...waye ya rasu Mami?" Hawaye suka cika idanuwan Hajiya Rumanan "Aise ce..." Ta amsa tana kai hannu ta share hawayen, mutuwar ba karamin gigitata tayi ba, dan ta goge duk wani shekaru na rashin jituwar da take tsakaninta da dan uwanta, da yake bayan sunga kamar ba'a dauki maganar da muhimmanci ba sai suka duba lambar da akasa Mummy a jiki suka kira mahaifiyar Aise suka sanar mata, dan haka kafin ta fito daga gidanma Alhaji Modu ya kirata "Na kira Alhaji Mustafa ban sameshi ba, kuje ku dauko mun ita Rumana...zamu taho yanzun" Yanayin muryarshi ya tuno mata yarintarsu, shakuwarsu, ya dawo mata da komai, a muryar dan uwanta takejin yanda zuciyarshi take a rarrabe da rashin da yayi, tayi kokarin saka kanta a halin da yake ciki amman ta kasa, hankalinta yaki daukar rashi irin wannan, ace Munira ce ko Anisa, ko Haris, watakila ba zata iya dangana ba, zuciyarta ce zata buga a hada a binnesu a tare "Yana gida, yanzun zan fada masa, zamu tafi sai mu wuce da ita asibiti..." A hankali yace "Ta rasu Rumana, Aise ta rasu, naji a zuciyata, 'yata ta rasu, ku dauko mun gawarta kawai" Sai kuka ya kwace mata, kukan da  ya kara dawo mata yanzun, da Alhaji Mustafa yace ba za'a tafi da ita ba, shine tace masa zata taho nan wajen Haris, mutuwar saida ta daki Maryama yanda batayi zato ba "Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..." Take fada tana maimaita, rai bakon duniya, tana nan gefe ta hana kanta da zuciyarta zaman lafiya akan Aise, ashe ma taqin daya rage mata a duniyar ba mai yawa bane, wani irin tsoro ya tsirgawa Maryama yana saka hawaye suka zubo mata, shikenan fa ko? Yanda suke tsayen nan suna jimanta rasuwar Aise, suma babu tabbas anjima ba za'a jimanta ta wani a cikinsu ba "Astagfirullah" Ta furta tana cigaba da maimaitawa "Bari in tafi gida Maryama, tunda jikin nashi da sauki..." Tafiyar tayi, Adda Maimunatu ma bar musu mukullin motar tayi ta samu napep ta koma gidan Maryaman dan ta dauki motarta, aka barta ita da Khairi "Kinga rayuwa ko Adda? Kai La hawla wala quwwata illa billah..." Ita kanta Khairi jikinta yayi sanyi sosai, haka suka dinga jimanta abin, har Haris ya tashi, Khairi ta fice tana basu waje, ya dade yana kallon bangon dakin, yanajin tsikar jikinshi na tashi, ba don sanyin dakin ba, wani abune yake shigarshi da ba zaice menene ba "Allaah Yayiwa mata rasuwa" Shine abinda yakeji cikin kunnuwanshi, ya kalli Maryama da yaji ya rike hannunshi "Allaah Yayi mata rasuwa akace Maryamm, mutuwa kenan ko? Ta mutu ake nufi, Aise ta mutu..." Ya karasa maganar yana tambaya yana kuma amsawa kanshi wannan tambayar, ta sake dumtse hannunshi kafin ta daga masa kai a hankali "Inalillahi wa ina ilaihi raji'un, kace Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..." Ya kuwa fada din, kalmomin da ma'anarsu na danneshi, tun yana fada a hankali harya fara fitowa fili "Inalillahi wa ina ilaihi raji'un" Aise ta rasu Aise ta mutu Da haihuwa batazo ma Maryama ba, da a tare dashi zata rasu, a dakin hotel din da ita ta kama musu, da shine zai kira waya bashi za'a kira ba, yace musu ta rasu! Yanzun kam wani abune yake mikewa a bayan kanshi "Me kuke a hotel tare?" Haka fa za'a tambaya ko? Me sukeyi tare? Ta ina zai fara yi musu bayani "Kowanne sakan da kayi a doron kasa sai an tambayeka akanshi, sai kayi bayanin abinda ka aikata da lafiyar da Allaah Ya ara maka da damar daka samu" Maganganun Malam suka dawo masa "Ai yi musu bayani mai saukine, babban tashin hankalinka bayanin da zakayiwa Allaah" Zuciyarshi ta fada masa "Inalillahi wa ina ilaihi raji'un" Ya furta a firgice yana tashi zaune har yana fisge karin ruwan da aka saka masa, ya riko Maryama a jikinshi, wani yaro ya rasu kwanaki anan unguwar, ya dawo masallaci aka fada masa, sai suka wuce akayiwa yaron sallah, karamine ance baifi shekara uku ba, suka tafi makabarta aka kaishi, sai yanzun yanayin kabarin yake dawo masa, yanda aka hakashi na kasan karami inda aka zira yaron, saina saman, sannan akabi da kasa harda wasu tukwane aka rufe ko ina, can za'a kai Aise itama ko? Cikin kasar nan, a barota ita kadai, to wai daman mutuwar haka take? Da wayonshi dai bai taba rasa wani makusanci ba, sai yanzun, lafiyarta kalau fa, sai kawai ace ta rasu? To me yafi wannan tashin hankali? "Idan nima na mutu fa Maryamm?" Ya tambaya cikin firgici yana kara riketa kamar maison komawa cikinta dan ya boyewa mutuwar "Dan Allaah... Inalillahi wa ina ilaihi raji'un, to ya zanyi? Idan na mutu ya zanyi? Idan Allaah Ya tambayeni zunubaina ya zanyi Maryamm? Idan na tuba komawa nakeyi, komawa nakeyi, Allaah Zai yafe mun kuwa? Ina cikin mutanen da suka shiga uku ko? Mutanen da zasuyi ihu suce Allaah Ya dawo dasu duniya, mutanen da Malam ya bamu labari a makaranta..." Jin yanda muryarshi take rawa yasa ta kara rikeshi itama, tana rasa abinda zatace masa "Kace Astagfirullah, Allaah Mai Rahma ne...dan Allaah ka nutsu" Ya daga mata kai, amman a wannan ranar shi da nutsuwa sunyi hannun riga, saboda a ranar ne addu'ar Maryama ta amsu, Allaah Ya nunama Haris girman IkonShi, Aise ta dawo rayuwarshi ne don ta zame masa silar shiriya "Astagfirullah, ba zan kara ba, na daina, Astagfirullah..." Ya kara fada, a karo na farko idanuwanshi suka cika taf da hawaye, hawayen tsoron Allaah, hawayen tsoron mutuwa, hawayen tsoron kwanciyar kabari, hawayen tarin zunubanshi da sai yanzun yake hangosu, maganganinshi kuma a gefe guda suna tsorata Maryama, sai ta lumshe idanuwanta, hawaye na zubo mata, a cikin zuciyarta ta furta "Allaah Kayi mana Rahma da kyakkyawan karshe, Allaah Kasa in mun mutu mu huta..." Wani abu mai sanyi ya saukar mata a zuciya, kamar taji lokacin da kaddara tace mata A duniya dai, akan auren Haris, ki huta haka Maryama...! Epilogue A shekaru talatin da biyu, shekaru goma sha biyar harda doriya da aure, bayan ni'imar yara har hudu, zata kara godewa Allaah da sauran ni'imomin daya cika rayuwarta dasu. In zata daga Labulen da yake lullube da aurenta daga farkonshi zuwa yau, mata da yawa zasu samu abin fada, wasu zasu bude baki ne suyi mamaki, harma ba za'a rasa wanda zasu tambayeta "Kuma kika zauna da dan wiwi?" To mata nawa ne suke zaune da 'yan shaye-shaye? Babu alamar zasu bari, sannan a gefen wannan shaye-shayen ba dadin auren sukeji ba, babu abinci balle suttura, babu kulawar miji. Ita kuwa zatace taga ribar biyayyar da tayiwa mahaifinta, taga wannan ribar a irin kulawar da Haris yake bata, watakila da auren soyayya tayi, da zabin zuciyarta ta samu, ba lallai wannan zabin nata yazo da irin wannan kulawar ba. Sannan akwai macen da zatace babu wani kalubale da take fuskanta a gidan aurenta? Wasu kuma zasuce ina su Anisa da Munira? Ya alakarta da Hajiya Rumana? Ta saduda? Yau da gobe ta tafiyar da ita? In akayi mata wannan tambayar, dariya zatayi, tunda ai tsanar da sukayi mata bata da wani dalili, to me yasa za'ayi tunanin zasu samu dalilin da zasu daina? Har yau din nan Hajiya Rumana bata sonta, har yau bata maraba da ita in taje gaisheta, in taga hakoranta a waje to jikokinta take yiwa dariya, tun yaranta basu da wayon da zasu fahimci cewa babu jituwa a tsakaninsu har Awwab da Rauda sun gane "Me yasa Mami bata sonki? Kin mata laifi ne?" Rauda ta taba tambayarta, ta rasa abinda zatace mata "Waye yace miki bata sona?" Sai ta daga mata kafadu, da yake ba surutu take dashi ba "Akwai kunya a al'adarmu, tsakanin surukai, shisa zaki ga kaman bata sona" Batasan ko Rauda ta gane bayanin da tayi mata ba ballantana ta rike shi a ranta, kamar yanda bata sake tambayarta ba, amman in dai zasu shirya zuwa gidan, kuma harda Maryama sai tace mata "Dama kiyi zamanki" Bata dai kulata ne, tsakanin Rauda da Anisa kuwa basa wani shiri ko tace Rauda bata shiri da Anisa, duk yanda Anisan take zuwa mata da tarkace kala-kala in zata zo, ko in su sunje take hadota dashi, da kuka take zuwa gidanta, sai Maryama tayi mata jan ido tukunna, kuma hakan ba zai rasa nasaba da yanda Anisa take gwaba mata magana har a gaban yaran ba "Duk tsanarmu da zaki cusawa yaran nan fa ba zai canza matsayinmu a wajensu ba wallahi" Haka Anisan ta taba ce mata, sai tayi dariya kawai. Inda a littafi ne, sai ace su Anisa sun girbi abinda suka shuka yanzun da shekaru suka ja, yanda suka so su hadu ayi mata kishiya, anyiwa daya daga cikinsu, yanda suka dora mata karan tsana to suma dangin miji suna gallazawa wani a cikinsu, za'a dai samu wani abune a lika musu da zaisa su saduda su kuma yi nadamar abinda suka aikata. Amman babu daya a ciki, saboda ba haka rayuwar take tafiya ba, wata shari'ar sai a lahira. In dai itace ma, a yanda ta samu Rahmar Ubangiji Ya shirya mata mijinta, idan akwai wani hakki tsakaninta dasu, to har ranta takejin ta yafe musu. Duk wanda yayi mata wani laifi ma ta yafe masa, bata fatan tsayawa da kowa a gaban Ubangiji da sunan shari'a, taji da kanta ma da tsayuwar nata zunuban. Cikin 'yan uwanta mata kuwa, musamman Adda Zahra, in dai zasu hadu gabaki daya a gida sai tayi mata zancen makaranta yanzun "Bafa ki makara ba Maryama, ko yanzun zaki iya komawa makaranta, shi ilimi bawai sai zakayi aiki ba, dadine dashi, gara ace ki janyo drawer kiga takardunki, ki dauko ki kakkabe kura ki sake mayarwa, inajin takaicin yanda a cikinmu ke kadaice ko kwalin sakandiri baki dashi" Sai dai tayi murmushi, tasan lokaci bai kure mata ba, shi ilimi ba'a girma da nemanshi, amman ta riga ta hakura da karatun boko, tun da Alhaji Sa'id da kanshi yace mata tayi hakuri, ta cire abin a ranta gabaki daya, amman da inta kafawa Haris naci saiya san yanda zaiyi da ita. A yanzun haka tana zuwa Islamiyya, shekaru hudu kenan data fara zuwa, tana yaye Aalim ta samu Haris ya barta, daga karfe goma na safe ne zuwa karfe daya na rana. Gashi nan tana shirin hada haddar Al-Qur'ani, dan sun wuce rabi, da yake hadda sukeyi ta gaske, ga sauran litattafai wanda da yawa ma ta gama wasu, wasu ta haddace su tun lokacin da Haris ya daukar mata Malamar da take zuwa tana karantar da ita a gida. "Ni idan ma ba zatayi karatun ba, to ta samu wata sana'ar ta fara" Inji Adda Maimunatu kenan, murmushin dai Maryama takanyi musu. Har yanzun Haris na daukar hoto, har kasar wannan bangaren na aikin shi yake daukarshi, kuma yanda komai yake tafiya da zamani, haka shima yake tafiyar da ita ta hanyar koya mata, saboda in zai samu aiki, to itama zai bata aikin tayashi editing koma wani abin da ta iya, sannan zai biyata, bayan biyan zai dauki kudi haka kawai ya bata. A shekarun nan da kudinta ta kai Alhaji Sa'id Umrah, ta kuma kai Hajja. Ko da tana so tayi wani business batasan ta inda zata fara ba, banda yan uwanta, kawarta Khairi ce, sai wasu tsirarun da suka hadu a Islamiyya, sai kuma makota anan unguwarsu da suke mutunci, to ta ina zata fara? Me ma zata siyar? Me zatayi da kudin bayan wanda suke shakare a cikin asusun bankunanta? In dai ta wannen bangaren ne, ko su da suke aiki suke kuma kasuwanci, babu abinda zasu nuna mata, idan ma aka tsaya filla-filla to ta fisu kudi, bata san yanda zatayi musu bayanin cewa kamar yanda suke tunanin ta rasa abubuwa da yawa a aurenta da Haris, haka kuma ta samu abubuwan da mata da yawa basu samu ba, ciki kuwa harda su, bama zasu fahimceta ba, Khairi ce kawai take fahimtarta, saboda ita tata jarabawar shine miji mai son abin hannunshi, mijin Khairi komai nashi a kididdige yake, yana da halin da zai wadatasu, sufi karfin bukatun yau da gobe, amman saboda idonshi nakan kasuwancin da takeyi na kayan yara, da kuma kayan kitchen tunda ya nuna bashi da ra'ayin tayi aiki, sai yake kara matse bakin aljihunshi. Ita kuwa wanda suka rabeta ma sunsan cewa hannun mijinta a bude yake, kyautar Haris 'yan uwa na nesa dana kusa ma tana isar musu. Yanzun ma Haris dinne ya shigo yana katse mata tunanin da ta fada ta hanyar rungumeta ta baya, ya sumbaci gefen fuskarta sannan ya saketa yana fadin "An kara samo mun inda za'ayi borehole, can wani kauyene a garin Katsina, na daisa aje a duba a tabbatar tukunna..." Ta kalleshi, tun rasuwar Aise, shekaru shidda kenan, Haris ya kasa samun cikakkiyar natsuwa. A ranar data rasu, duk yanda 'yan uwa sukaso ayi janaizar zuwa washegari saboda kowa ya samu yazo daga Maiduguri, haka ma 'yan uwan Aise din su Mu'adh, Alhaji Modu yaki "Tun wajen karfe biyu ta rasu, sai a barta har gobe? Saboda me? A kaita yau, ta samu ta wuce kwanan yau ko zata samu salama itama, addu'a ce kowa idan yayi mata ko da baizo ba In Shaa Allaah zata risketa" Hakan akayi kuwa, sai dai shi kanshi Alhaji Modu yayi mamakin irin jama'ar da suka halarci Janaizar Aise, saboda Alhaji Mustafa ya sanar, anan gidanshi akayi mata wanka, wajen karfe biyar aka kaita, lokacin Haris ya baro asibiti yazo gidan, dashi aka kama munkarar da akasa Aise, dashi aka zirata cikin kabarinta aka mayar da kasa aka rufe. A ranar ne ya tabbatar da maganar da ake fada ta dan adam ba a bakin komai yake ba. Muna tafiya ne batare da sanin mutuwa na zagaya fuskokinmu ba. Sai gashi ya kasa tsaida hawayenshi, inya gogesu sai wasu su kara zubowa, zazzabi yayi na wajen sati saboda tashin hankali, amman bayan sadakar ukun Aise haka ya lallaba yaje makaranta, saboda yana so yayi magana da Malam, kamar kuma Malam yasan abinda yake ranshi wa'azin ranar akan mutuwa ne, akan shiriya da ba kowanne yake samun Rahmarta ba. "A kowanne hali anaso ka zagaye rayuwarka da mutanen kirki, mutanen da zasu dinga tuna maka da Ubangijinka, ba mutanen da zasu shagaltar dakai ba, a irin wannan ne zakaga kana cikin shagala Allaah Ya dauki ranka, sai anje filin qiyama kaga abokanka sunzo sun wuce aljanna sun barka, ka dinga mamaki, sai daga baya kaji ashe shiriya ce tazo musu bayan mutuwarka ta zame musu wa'azi..." Wannan maganar ta tsorata Haris matuka, sai maganganunsu da Aise suka dinga dawo masa, duk lokacin daya dinga biye mata inta rike shi, lokacin daya amsa zai sameta a hotel kafin mutuwa ta gifta musu. Shi gashi nan yayima kanshi alkawari, ya dauki alkawari tsakaninshi da Allaah ba zai sake kusantar zina ba, Malam kamar yana misali ne dashi da Aise da mutuwarta ce ta zame masa wa'azi, to da kuma tashi mutuwar ce ta zame mata wa'azi fa? Dashi kenan ko? Ya shiga ukunshi ko? To Aise ce a ukun yanzun? "Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..." Ya furta zufa na keto masa, saida kowa ya watse tukunna ya samu Malam da tarin tambayoyinshi, haka kuma bai boye masa komai ba, ya fada masa "Allaah zai yafe mun kuwa? Ina da sauran rabo Malam? Ita kuma fa? Aise fa? Ya zanyi?" Anan Malam ya dinga kafa masa hujjoji da Ayoyin Rahmar Allaah, ya dan sama masa natsuwa da cewar zunubin Aise tsakaninta ne da Ubangiji, Ubangiji kuma mai yawan Rahma ne "Zan iyayi mata sadaka? Ladan zai sameta?" Ya kuma kara jin dadin da aka fada masa ayyukan alkhairi da ko bayan mutuwarka ladansu zai cigaba da samunka har kabari, saboda a cikin irin wadannan ayyukan alkhairin Aise tayi wasu daga ciki, ya san tayi, akwai kauyukan da tayi musu rijiyoyi saboda yanda matan suke shan wahalar zuwa dibar ruwa da kuma rashin samun ruwa mai tsafta alhalin suna da ciki, kar ayi maganar matan data taimakawa da magunguna da kudaden asibiti da makamantan wannan, kuma duk wanda ya samu lafiya ta sanadin taimakonta, yayi amfani da lafiyar wajen aikata alkhairi saita samu lada, haka wanda ta samawa tallafin sana'a don su dogara da kansu ma ba zasu kirgu ba. Sai Haris yace a ranshi "Watakila, daya daga cikin wadannan ayyukan alkhairin na Aise ga bayin Allaah sune suka hana musu haduwa a ranar data rasu, watakila sune sukayi musu Katanga da jin kunyar duniya da lahira..." Shisa ya daura damarar amfani da dukiyar da Allaah Ya bashi wajen nemawa kanshi da ma iyalinshi lahirarsu ba iya duniya kawai ba. Yanajin kamar zunubanshi suna da yawan da yake bukatar aikin alkhairan da yake fatan Allaah Ya karba Yayi masa Rahma ta sanadinsu "Allaah Ya karba daga gareka..." Maryama ta ce masa tana fadada murmushinta, har tausayi yake bata "Akan mata, In Shaa Allaah na daina Maryamm, nagode da baki gaji dani ba, nagode da baki rabu dani ba, dan Allaah ki tayani, kiyi mun addu'a Allaah Ya karbi tubana, kiyi mun addu'a Allaah karya kara jarabani da kusantar zina, na dade a cikinta inajin tsoron sake komawa..." Haka yace mata, saita rike hannunshi, tanajin wani sanyi na ratsa zuciyarta "In Shaa Allaah, ba zaka sake ba, In Shaa Allaah, Allaah zai tsareka, ka kyautata tubanka, in ka kyautata tubanka Allaah Zai duba zuciyarka Ya kareka" Ya dinga jinjina mata kai cikin yarda da kalamanta, yanzun kam sai yace "Amin thumma amin... nagode" Ta karasa tasa hannunta cikin nashi daya mika mata "Da nayi me kuma?" Saiya jata suka zauna gefen gadon "Da kikayi komai ma" Dariya tayi "Kamar me da me?" Ya daga mata girarshi guda daya "Kamar dai auren baki irina bayan ke bakya son bakake ko?" Dariya Maryama tayi sosai "Ai ka karyatani Ganja...ka nuna mun bansan me nake so ba sai bayan na aureka, sai gani ba bakin namiji kawai nake zaune dashi ba, na goya bakaken 'yayanshi Ya dan murda hannunta da yake rike dashi, tayi dariya, shima dariyar yayi "Ba zaki daina ba ko..." Dan kafin Aalim yayi wayau, haka yake binshi yana kiran Ganja Ganja, ta dinga tuntsira dariya "Yanzun dan sunan soyayyar nan ma da mata take kiran mijinta ni na kasa samu" Ta dan daga masa kafadunta "Nafison Ganja dinne, dadi yake mun" Sai kawai ya girgiza kanshi yana murmushi, dan shima inta ce Ganja din yanayi masa dadi, a gefe daya kuma yana tuna masa abubuwa da yawa da kullum ya kalleta suke zamar masa dalilin da zaice mata "Nagode Maryamm, madalla da aurenki" Haka kuma dalilai masu yawa da zasu hadu ita dashi suce "Alhamdulillah..." #LABULE...Asirin mai daki #LubnaSufyan