_*RASHIN SANI.......*_ *HAUWA A USMAN* _JIDDARH_ ```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh``` 1⃣ Alhaji GANEZ HARD'O cikekken bafulatani ne usul gaba da baya, dan kallo d'aya zakayi mishi ka fuskanci hakan, mutum ne kamili mai cikekkiyar nutsuwa da kamala, d'an asalin garin Adamawa ne, yana da matar aure d'aya NISAH, mace mai hak'uri da dattako, 'yar wan mahaifinsa ce akayi musu auren zumunci, kuma cikin ikon Allah suna zaune lafiya, bayan anyi auren su canjin aiki ya kai shi karin Kano, kasancewarsa Police, a kwalli police barrack aka bashi gida, amma yak'i zama ya nemi gida a jan bulo (BUK road) ya siya, ya shirya musu gidan dai-dai gwargwadon k'arfinsa, gidan yayi kyau ba laifi, suka zauna da matarshi, mak'ofcinsa DANISH, mutum ne nutsatse mai cikekkiyar nagarta, shima yana da matarsa d'aya ERUM, mace mai mutunci da karamci, su 'yan asalin garin Kano ne, a k'aramar hukumar Yakasai zama ne ya kai su jan bulo, lokacin da Ganez ya sauka a garin Kano ta tabo, bai san kowa ba, balle kuma matarsa Nisah, a masallaci Ganez da Danish suka fara had'uwa, inda Ganez ya gabatarwa da mak'ocin nasa kansa a matsayinsa na bak'o, hannu bibbiyu Danish ya karb'e shi, cikin karramawa, tun daga wannan rana zumunci da alak'a mai k'arfi ta shiga tsakanin su, haka ma matan su Erum da Nisah, harta kasance basu da kamar junansu a duniya, kowa yana tsananin k'aunar kowa, babu wanda zayyi abu batare da sanin d'ayan ba. Shi Danish d'an kasuwa ne, ba aikin gwamnati yake ba, a kantin kwari yake da shagon atamfofi, sosai alak'ar Danish da Ganez tayi k'arfi ta wuce tunanin mai tunanin dan jama'a da yawa suna tsammanin 'yan uwane, bayan shekara d'aya da zuwan Ganez Kano, Nisah da Erum suka haihu rana d'aya, duka yara maza suka haifa, sosai Danish da Erum sukayi farin ciki, ranar suna d'an Ganez da Nisah yaci sunan HAMRAZ, d'an Danish da Erum yaci sunan RAWAN, yara suka taso cikin so da k'aunar iyayen su, duk bin kwakkwafin mutum bai isa ya gane ga d'an Danish ko Ganez a tsakanin Rawan da Hamraz ba, yadda suka ga iyayen su suna matuk'ar k'aunar junan su haka suma suka taso da san junan su, babu wanda ya isa ya tab'a d'aya, komai nasu tare sukeyi dai-dai da kayan sawa iri d'aya suke yi, kan Rawan da Hamraz a had'e yake sosai fiye da tunani, idan d'aya na kuka shima d'aya sai yayi, ko rashin lafiya d'aya ya kwanta d'ayan ma sai yayi, abin nasu har mamaki yake bawa mutane. Haka suka girma har suka kai munzalin samari, a lokacin Ganez yayi ritaya, dan girma ya d'an fara kama su, Hamraz ya karanci medicine ya zama cikekken Doctor, Rawan kuma ya karanci Low ya zama cikekken Barrister, a lokacin ragamar gidajen su ta koma hannunsu, babban fili suka siya suka ginawa iyayen su da su kansu katafaren gida wanda shine zai zama HARD'O FAMILY HOUSE, sunyi tsarin gidan mai kyau, part d'in Ganez da Nisah, daban, haka ma Danish da Erum daban, sai suma sukayi part d'in su daban-daban, da kuma wasu part d'in wad'anda babu kowa a ciki a k'alla zasu kai 7, rana d'aya Hamraz da Rawan sukayi aure, suka auri 'yan biyu uwarsu d'aya uban su d'aya, Hamraz ya auri Hassana Rawan ya auri Usaina. Rawan da Usaina yara uku suka haifa, ZAFRAN shine babba sai k'aninsa AARIB, da k'anwar su mace AROOS, Hamraz da Hassana yaran su biyu, IDRAK da k'aninsa ZIYAD, har sun cire ran k'ara samun haihuwa , saboda a k'alla sunyi 7yrs, rabon su da haihuwa, Allah ya kuma bawa Hassana da Usaina ciki a lokaci d'aya, a rana d'aya suka haifo yaran su mata, kyawawan gaske san kowa k'in wanda ya rasa, Ganez da Danish suka ce tarihi ya maimaita kansa, ranar suna aka sakawa 'yar Hamraz *SANAH* 'yar Rawan *KHULUD*. Yaran suka taso cikin matsananacin so da k'aunar junansu, fiye da yadda iyayen su suka taso dashi, babu abinda Sanah tafi so a rayuwarta sama da Khulud, haka itama Khulud d'in bata san komai sama da Sanah, basa had'a san da suke yiwa junan su da komai a duniya, suna k'aunar junan su fiye da komai da kowa, tun suna yara k'anana bambamcin halayya da d'abi'u suka bayyana, a tsakanin su dan ita Sanah tana da zafinzuciya gata da tsiwa da fad'a, had'i tsokana da rawar kai, ita kuma Khulud she's so silent, kwata-kwata bata san yawan hayaniya da rigima, dan ita magana ma ba damunta tayi sosai ba, sab'anin Sanah dake da shegen surutu kamar me, idan har kaji surutun Khulud to da Sanarta ne dan muskilar gaske ce, indai bada Sanah ba, ko a gidan su sai a yi tayi mata magana bata amsawa, ita Khulud ko irin b'arnar nan ta yara bata yi, amma oga Sanah akwai b'arna da k'iriniya gata bata jin magana, makarantarsu da ajin su d'aya haka ma desk d'in su d'aya. Duk duniya babu wanda ya isa ya tab'a Khulud a gaban Sanah, koda kuwa su kan su iyayen nasu ne, haka ko'a makaranta malamansu basu isa su tab'a ta ba, muddin kuwa aka yi kuskuren tab'a ta to ranar ba zaman lafiya, itama Khulud duk da rashin fad'a da san hayaniyarta, idan aka sake aka tab'a Sanah yanzu zata fututtuke ta rufe ido tayi ta ruwan bala'i, komai nasu iri d'aya ne sak, har pant da ribbon, ko color basa yarda a bambanta musu. Ko laifi Khulud tayi sai Sanah tayi saurin cewa ita tayi, haka zasuyi ta jayayya wannan na cewa shi yayi wannan ma na cewa shi yayi, har wanda akayiwa laifin ya gaji ya hak'ura. Sanah da Khulud suna wasa a tsakiyar compound d'in gidan su, Sanah ta kalli Khulud tace " Ulud (dayake haka take kiranta, dan da wuya ta fad'i full name d'inta), idan mun girma mun gama secondary me zaki karanta? Dariya Khulud tayi had'i da cewa " tab ai ni ban sha'awar karatu mai zurfi, dana gama Secondary school shikenan na gama karatu har abada, kallanta Sanah tayi kana tace " tab ai ni ko sai naga k'arshen biro da takarda, inasan nayi karatu mai zurfi sosai, Khulud tace " ai dama ke kin saba banbanta mana ra'ayi, tayi maganar tana zumb'uro baki, Rawan da Hamraz na tsaye suna kallansu suna jin abinda suke cewa, Hamraz yace " da alama 'yata Khulud gado zatayi, kallansa Rawan yayi yace " gadon me? Dariya Hamraz yayi yace " gadon Aure da wuri mana, dariya shima yayi yace " amma ni tawa 'yar boko zatayi, "a'a karkace haka dan muna iya sauya muku ra'ayi, Rawan yace " a'a ba wannan maganar, kasan komai ra'ayin mu kuke bi, dariya Sanah tayi tace " shikenan karkiyi kuka my Ulud na daina, Ulud ta kalle ta da sauri tace " da gaske? "Sosai ma, da gaske nake, "yauwa har kinsa naji dad'i cewar Khulud, mik'ewa Sanah tayi tana cewa Khulud ni fa yunwa nake ji, dariya Khulud tayi tace " acici kawai, muje na raka ki kici abincin, " a'a muje na raka ki gida tukunna sai na tafi, " a'a ni zan fara raka ki, tukunna, "to muje cewar Khulud, har k'ofar part d'in su Khulud Sanah ta raka ta, sannan Sanah tace " to kema muje na raka ki, suka koma part d'in su Khulud, itama tace " muje na raka ki, haka sukayi ta zarya suna rakiyar kura, iyayen na kallan su suna dariya, Rawan yace " k'uruci gangin hauka. Yau su Sanah da Khulud suka kammala zana jarabawar fita daga primary school, (Common in trace Exam), cikin farin ciki suka dawo gida, driver nayin parking suka fito da gudu suka nufi inda iyayen ke zaune, da gudu suka fad'a jikin su, Sanah tace " Abbu sun gama exam yau, murmushi yayi had'i da shafa kansu yace " masha Allah, Ubangiji ya bada sa'a, Hamraz yace " da fatan dai anyi k'ok'ari sosai? Khulud tace " mun dage sosai Dide, "Rawan yace to yanzu wacce school kuke san zuwa? Cikin mud'i Khulud tace " Boarding Abbu, da sauri Sanah ta kalle ta tace " boarding kuma Ulud? "Eh mana ko baki san boarding? Shiru Sanah tayi tana kallan yadda Khulud ke farin ciki, gashi ita kwata-kwata bata so ko sha'awar boarding school, asalima ita ta tsani boarding school, kallanta Khulud ta kuma tayi tace " ai boarding zamu ko? Murmushin yak'e Sanah tayi kana tace " eh boarding zamu, Abbu da Dide sun lura da Sanah bata san boarding, dan haka Abbu ya rik'ota yace " Auta kodai day zakiyi? "No Abbu nima boarding d'in zani, tunda Ulud can take so, bana san abinda zai raba ni da Ulud d'ina, ajiyar zuciya Dide ya sauke a hankali yana kallansu had'i jinjina irin k'aunar da suke yiwa junansu, shafa kansu Abbu yayi yana murmushi yace " Allah ya albarkaci rayuwarku, Ubangiji ya sanya haske da lumana a duniyarku, ya k'arfafa dangantarku, ya inganta alak'arku har abada, duk wanda zai zama sanadin rabuwar kanku, ko kawo matsala da sab'ani Allah ya kawar muku dashi daga rayuwarku, gaba d'aya suka amsa da Amin. A gida bayan sun gama cin abinci sunyi wanka, Sanah ta d'auko wayar Mamu, (Mahaifiyarta) tace " Khulud zo muyi game, "a'a kiyi kawai ni bacci zanyi, Sanah ta zumb'uri baki tace " nima banyi to, dariya Khulud tayi had'i da cewa " yi hak'uri kawo muyi, na fasa baccin, ta fad'a tana mik'a mata hannu, garin Sanah ta mik'a mata wayar, akayi rashin sa'a wayar IPhone X ta fad'i ta fashe, ido duk suka zaro dan sun san Mamu bata san wasa, Mamu dake shigowa parlor ta kalle su taga yadda duk sukayi tsuru-tsuru, tace " lafiyarku? Ido Khulud tayi rau-rau kana tace " Mamu kiyi hak'uri ban sani bane wayar ta fad'o ta fashe, ido Mamu ta zaro, a d'an tsawace tace " wacce wayar, badai wacce na siyo jiya ba? "Cikin tsoro Khulud tace " ita, dan Allah kiyi...... tsawa ta daka musu tace " uban waye yace ku tab'amin waya? Da sauri Sanah tace " Mamu nice na d'auko zamuyi game shine ta sub'uce daga hannuna, Khulud tace " a'a Mamu nice na d'auko ba ita ba, Sanah ta kalli Khulud tace " ba kyau k'arya fa, ta juya ta kalli Mamu tace " Allah ni ce ki doke ni amma please karki tab'a Khulud, itama Khulud tace " Mamu ni ce ba ita bace ni zaki daka ba ita ba, tsawa ta daka musu, cikin b'acin rai tace " wato ni zaku rainawa hankali ko? " Dukkan ku sai jikinku ya gaya muku, kuka Khulud ta saka tana cewa " Allah Mamu nice nayi laifin please karki dakar min Sanah, itama Sanah kukan ta saka tana cewa " Mamu ni ce ba itaba, karki doke ta, kai ta dafe dan nema suke su saka mata ciwon kai, ta kalle su a hasale tace " ku b'ace min da gani, dan tasan ko dukan nasu tayi ba hucewa zatayi ba, da gudu suka fita. Computer Girls Sondary School Roni, aka nemarwa su Sanah, Khulud nata murna da d'oki, amma Sanah ko'a jikinta dan banda Khulud babu abinda zai kaita boarding school , Abbu ne ya gama musu duk wani shirye-shiryen su na tafiya, ranar Sunday kusan gaba d'aya Hard'o Family's ne suka raka su, dayake makarantar akwai islamiyya Dide yayi magana aka sanya su, sosai Sanah tayi kukan rabuwa da gida. MOMYN ZARAH _*RASHIN SANI.......*_ *HAUWA A USMAN* _JIDDARH_ ```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh``` 2⃣ Ganin yadda Sanah ke kuka ne yasa itama Khulud yin kukan, Vice principal na office yaji yo sheshshekar kukan su, a hankali ya d'an tsaya da abinda yake yi had'i da kasa kunne, dan ya tabbatar, jin sautin kukan su Sanah yasashi mik'ewa a hankali, ya lek'a ta window dan yaga wad'anda ke kukan, ganin new comers d'in da aka kawo yanzu ne yasa shi,,, takawa zuwa inda suke, sai da yayi a k'allah wajen minti 8 yana kallan su, kafin yace " ku zo nan, ba musu duk suka mik'e suka nufe shi, durk'usawa yayi dai-dai tsawon su yace " ku daina kukan, kar kuyi rashin lafiya kunji? Kai suka d'aga masa batare da sunce komai ba, hannunsa yasa yana goge musu hawayen had'i da cewa, " yauwa good girls, ina san yara irin ku masu jin magana, da biyya, ku kasance masu haka har girmanku, kai suka k'ara d'aga masa alamar to, yace " idan kuna jin magana kuma kuna karatu sosai zan rink'a baku sweet, kuma zamu zama friends, amma idan bakuyi b'atawa zamuyi, na rink'a yi muku bulala, "to Khulud tace, cikin sanyin murya, kansu ya shafa yace " sunanku? Sanah tace " ni sunana SANAH RAWAN, ita kuma KHULUD HAMRAZ, " nice name Malam Jeeb yace, sannan ya mik'e had'i da rik'e hannuwansu, ya nufi Office d'in Dispeeling Master dasu, shiga yayi dasu bakin sa d'auke da sallama, bayan sun gama gaisawa ne ya nuna masa su yace " they're new comers, so please ka basu hostel & class, "Ok sir cewar Malamin da suka iske a office d'in, Malam Jeeb ya mayar da kallansa ga su Khulud yace " yanzu za'a kai ku d'aki, ku ci abinci ku huta kunji, thank you Sir, Khulud tace, har cikin zuciyarsa yaji dad'in maganar Khulud, dan haka yayi murmushi batare daya k'ara cewa komai ba ya fita. Kallan su Malam Moli yayi yace " ya sunanku? Cikin sanyin murya Khulud tace " ni sunana KHULUD HAMRAZ, ita kuma SANAH RAWAN tayi maganar tana nuna masa Sanah, bai k'ara cewa komai ba, har ya gama 'yan rubuce-rubucen sa a wasu file, kana ya d'ago kai yana dube-duben student d'in da zai aika, amma babu kasancewar weekend duk suna Hostel Area, wata d'aliba ya hanga ta fito daga staff room, yayi saurin kiranta, cikin ladabi tazo ta durk'usa a gabansa, cikin sanyin murya ta gaida shi, amsawa yayi had'i da bata umarnin ta kira masa House Captain d'in Turaki House data Lamid'o House, had'i da head girl, da sauri ta mik'e jikinta na rawa ta fita, dan duk makarantar tsoran Sir Moli ake yi, kasancewar baya wasa,akwai shi da zafi, magana d'aya tak yake yi, sallama sukayi daga bakin k'ofar office d'in, had'i da d'an dakatawa, sun kai wajen a k'alla minti 3 kafin ya amsa ya basu izinin shigowa, zubewa sukayi a gaban table d'insa suka ce " good evening Sir, ko kallan inda suke bayyi yace " fine, a tak'aice, batare daya kalle su ba yace " new comers ne , ku aje d'aya a Turaki, d'aya a Lamid'o House, Sanah dake tsugunne a gefe tana kallan iko da miskilancinsa, tayi saurin cewa " raba mu za'ayi? Bai kalleta ba balle yayi magana, Khulud tasa kuka tana cewa " ni dai a'a please kar a raba mu a barmu tare, k'afa d'aya ya d'ora kan d'aya had'i da kishingid'a ya rufe idansa, sosai Khulud da Sanah suke kukan kar a raba su a barsu tare, amma ko kallansu bayyi ba, jin kukan su na neman saka mishi ciwon kai yasa shi bud'e idansa dole, ido kawai ya zuba musu batare dayace komai ba, kafin ya mayar da kallansa ga House Captains d'in, jikinsu na rawa suka rik'o hannayen Sanah da Khulud dan sun fahimci irin kallan da MOLI yake yi musu, fizge hannayensu sukayi had'i da cigaba da kukan su harda bubbuga k'afa, gigitacciyar tsawa ya daka musu, had'i da cewa " get loose a hasale yayi maganar, a tsorace Khulud tayi hanyar fita, dan tsabar ba k'aramin gigitata tayi ba amma fur Sanah tak'i ko motsi, balle ta fara k'ok'arin fita, sauran students d'in jikinsu sai rawa yake, saboda tsabar tsoro, ganin bata da shirin fita ne yasa shi mik'ewa ya hankad'o su waje had'i da cewa " ko uban ku ne yazo nan bai isa yasani abinda banyi niyya ba,sakarkaru kawai, kuka suke yi sosai kamar ransu zai fita, har Sir Jeeb ya jiyo kukan su, yasan Moli ne yasa su kukan, dan kowa yasan halin miskilancinsa, fitowa yayi yana kallan su kafin yace " oh friends har kunyi saurin sab'a alk'awarin mu? Cikin kuka Sanah tace " no Sir, yace " gashi kuwa kuna kuka, Khulud tace " wai hostel za'a raba mana, shiyasa muke kuka, dariya Jeeb yayi yace " karku damu ai zaku rink'a had'uwa kullum, da sauri suka had'a baki wajen cewa " please Sir kar a rabamu dan girman Allah, yadda sukayi maganar ne sukayi masifar bashi tausayi, ya d'anyi shiru yana tunanin kafin ya kalli House Captain d'in yace " ku kai su d'aki d'aya, ku kuma basu kwana d'aya, and please ku kula dasu, Ok Sir suka ce, da sauri Sanah da Khulud suka fad'a jikinsa suna cewa " thank you so much Sir, a Lamid'o House aka ajiye su, aka basu gado da kwana, Halan itace House Captain d'in Lamid'o House, sai da ta nunnuna musu komai da ko'ina sannan tace musu " daga yau na zama Auntyn ku, duk abinda kuke so ku tambaye ni kai tsaye, kunji ko? "Eh suka ce had'i dayi mata godiya, washe gari Monday da wuri Halan ta shirya su Sanah da Khulud, suka tafi assembly gudun kar suyi late, bayan an gama assembly an watse, Halan ta kama hannun su ta nufi b'angaren JSS Classes, a hanya suka had'u da Moli, Halan tayi saurin zubewa tana gaidashi, ko kallanta bayyi ba balle ya amsa, sai ma uwar harara daya watsawa su Khulud, Sanah tace " wai Aunty Halan dole sai mun gaida wannan miskilin mutumin mai taurin kan tsiya ne? Baki Halan tayi saurin toshe mata, had'i da cewa " rufa mana asiri Sanah kar yanzu ki ja mana bak'ar wahala, baki Sanah ta turo had'i da cewa " Allah Aunty ganin kuna tsoransa ne yasa shi yake yi muku haka, Halan tace " ni dai please kiyi shiru dan jine dashi kamar zomo, Sanah tayi tsaki had'i da juyawa, aiko karaf idanta ya sauka cikin nashi, yayi tsaye hard'e da hannu a k'irji yana kallanta cike da mamaki, ji tayi gabanta yayi muguwar fad'uwa, kwafa yayi had'i da girgiza kai ya zubga mata uwar harara, ya juya yayi tafiyarsa, batare dayace mata komai ba. JSS 1A suka shiga, halan tayi sallama, Class master suka iske a cikin class d'in yana kiran suna, cikin girmamawa suka gaida shi, ya amsa cikin fara'a kana halan tace " Sir new comers ne akace na kawo su, "Ok amma sai dai a aje d'aya anan akai d'aya 1B, ai baima k'arasa ba, Khulud ta soma tab'a baki zatayi kuka, yayi saurin cewa " meye na kuka? Halan tace " please Sir karka raba su, zayyi magana Sanah da Khulud sukayi saurin durk'usawa a gabansa had'i da langwab'ar da kai suka ce " please Sir don't separate us, we bag you in the of almighty God, jikinsa yayi sanyi tausayinsu ya kama shi, ya d'ago su a hankali yana murmushi yace " ok, cikin farin ciki suka ce thank you Sir, kansu ya shafa yace " then promise me you will read harder, " We hope so Sir, cewar Sanah "not hope so, promise! murmushi sukayi had'i da cewa " we promises you Sir, yayi dariya sannan ya nuna musu sit, suka zauna. Bayan an tashi daga class direct masallaci suka wuce, tare da sauran students dan haka al'adar makarantar take, sai an ja su sallar adhur jam'i kafin su shiga hostel area, sai bayan sun fito daga masjid suka yi dinning hall, abincin rana aka basu, sannan kowa ya wuce hostel,, Halan tasa sukayi wanka suka shirya cikin islamiyya uniform tun kafin time d'in islamiyyar yayi, gudun kar suyi late Sir Moli ya samu damar cin uban Sanah, dan ta tabbatarwa kanta yaji abubuwan datace d'azu a kansa. Suna kan hanyarsu ta komawa hostel daga islamiyya wata senior ta kira su, "ku kuzo nan, tayi maganar tana watsa musu kallan banza, d'an tsayawa sukayi had'i da juya bayansu dan sunga alamar bada su take ba, ganin sunk'i zuwa ne ya hasala senior d'in ta danna musu ashar, had'i da daka musu tsawa " ku banzaye bazaku zo bane ni nazo, Sanah zatayi magana, Khulud tayi saurin rik'e ta had'i da girgiza mata kai alamar a'a, had'iye yawo Sanah tayi saboda takaici batare datace komai ba, Khulud taja hannunta zuwa inda senior d'in ke tsaye, kasancewar basu san al'adar boarding school ba yasa suka tsaya a tsaye had'i da zuba mata ido, " baku da hankali ne dazaku tsaya min k'erere akai na, dalla ku rage tsayin ku, tayi maganar cikin fad'a tana yi musu wulak'antaccen kallo, ganin still suna tsaye yasata mik'ewa a hasale tace " bazaku durk'usan bane? Da sauri Khulud ta kama hannun Sanah suka durk'usa a gabanta, bokitin k'arfe ta jefa musu tace " kuje tanker ku ciko min shi, cikin rashin fahimtar abinda take nufi Khulud tace " me zamu yi miki? " Ni keke tambaya abinda zakuyi man? Tayi maganar tana nuna kanta, kai tsaye Khulud tace " eh mana, ai bamu gane abinda kike nufi b............ tasssssssss senior d'in ta d'auke Khulud da wani gigitaccen mari, har sai da ta hantsila, a gigice Khulud ta fashe da mahaukacin kuka tasa duka hannayenta ta dafe kuncinta,, tab abinka da mafad'acin mutum da bak'ar zuciya, Sanah tayi fad'an banza ma balle mai dalili, ita da kamar jiran fad'a take, dan ita kad'ai ma yi take, sai dai ka ganta tana jijjige-jijgen jiki, tana magana ita kad'ai, aiko zuciya tazowa Sanah har wuya, cikin b'acin rai da zafin zuciya, Sanah ta wawuri bokitin k'arfen ta shiga kwad'awa senior d'in a jikinta da kanta a haukace, idanta gaba d'aya sun gama rufewa ruf saboda bak'ar zuciyar ta, take jini ya fara zubowa Senior d'in kanta ya fashe, saboda azaba bata san sanda ta shiga kwarara ihuuuuun a taimake ta za'a kashe ta ba, kafin kacame dandanzon students sun cika wajen mak'il, duk Junior d'in da suka zo suka ga ERA ake yiwa duka sai tsoro da farin cikin ya kamasu, tsoron da suke yi na sun san sum shiga uku ne, saboda kwata-kwata Era bata da imani ko tausayi, gata bak'ar muguwa azzaluma, duk wanda ya sake ya shiga track d'inta ya shiga uku dan bata yafiya balle wani abu hak'uri, mutum d'aya ne zayyi mata laifi amma saita had'a gaba d'aya students ta zane saboda zalunci, wannan dalilin ne yasa suke tsoro da murna. Dakyar SS3 suka taru suka kwace Era daga hannun Sanah, suka rik'e Sanah dan sai kici-kici take tana san kwacewa, babu yadda ba'ayi Sanah ta hak'ura ba amma tak'i hak'ura, sai dai Khulud ta mik'e daga inda take durk'ushe taje ta rik'e, had'i da ta rungume ta, sannan Sanah ta hak'ura ta bari, itama ta rungume ta duk suka saka kuka, wasu daga cikin Juniors suka fara magana k'asa-k'asa, "yau dai Allah ya kawo mana k'arshen wannan shegiyar mara imani, wata tace " wallahi kedai bari kawai, ai yau saboda tsabar farin cikin sai na zuba ruwa a k'asa na nasha, d'ayar tace " aini yau wanka zanyi da k'asa, wata daga gefe cikin sanyin murya tace " wallahi ni tausayin yaran nake ji kar ayi musu rufdugu, "Hhhhhhh tab ke yanzu kinga alamar waccen zata daku? Tayi maganar cikin dariya taci gaba " baki hango ruwan bala'i da masifa a kwayar idanta ba? "Ke da ganin wannan kinsan zatayi taurin kai da bak'ar zuciya, jifa yadda bakinta yake kumfa, idanta yayi jajir, saboda tsabar fitina da ruwan fad'a, gaskiya wannan bazata tab'a dakuwa ba, sai dai duk abinda za'ayi ayi, kuma tana da taurin zuciya, kuma da ganin kwayar idanta bata da tsoro ko kunya, kuma zatayi tsiwa, d'ayar tace " kamar ma new comers ne ko? "Eh, jiya bana baki labarin wad'anda sukayiwa Sir Moli taurin kai ba? "Eh, kar dai kice man su ne, tayi maganar tana zaro ido, murmushi d'ayar tayi kana tace " wallahi sune, k'ara kallan su tayi tana girgiza kai, ganin abin ya girmama yasa head girl zuwa staff room ta sanarwa da Dispeeling Master, yana daga kishingid'en idansa a rufe, ya bud'e baki dakyar yace " je ki kira su, yayi maganar a tak'aice, dan shi mutum ne wanda kwata-kwata baya san yawan magana, ko hayaniya dan zai iya irga yawan maganar dayake yi a wata d'aya, gashi miskilin gaske, Service yazo(bautar k'asa), ainahin Dispeeling Master ne ya tafi Malaysia k'arin karatu shiyasa aka bashi rik'on kwarya, saboda yadda students d'in ke bala'in jin tsoransa, kai bama iyakacin students ba har Malamai da Principal shakkarsa suke ji, saboda yana da bak'ar zuciya, kuma bai shiga harkar kowa, saboda kyansa da gwarjininsa yasa 'yan mata da yawa haukacewa da mutuwa a haukan sansa, amma shi ko kallo basu isheshi ba, dan ko gaisuwarsu dakyar yake amsawa , wani lokacin ko amsawar bayyi. Jikin Head Girls na rawa ta koma ta kira su Sanah, Khulud da Era, sauran student najin ance Sir Moli na kiransu jikinsu ya d'auki tsuma, saboda tsananin tsoransa da suke ji, take tausayin su Sanah ya gauraye zukatan students d'in, Halan na Hostel wata Junior ta ruga ta sanar da ita abinda ke faruwa, dan Halan bata san abinda ke wakana ba, sosai hankalinta yayi masifar tashi tsoro da fargaba suka dirar mata, dan ta tabbatar yau sai buzun su Sanah, tana san zuwa taga halin da suke ciki amma ba dama dan tasan waye Sir Moli, dan yana fasa dukan su ma ya jibge ta, saboda baya san tsurku, dole ta hak'ura ta zauna tana jiran dawowar su. Office d'insa suka shiga suka tsugunna a gaban table d'insa, sun kai a k'alla 10 minutes batare daya motsa koya bud'e idansa ba balle su saka ran zayyi musu magana, jin sheshshekar kukan Era yasa shi bud'e idansa a hankali, had'i dabin inda yake jiyo sautin kukan da kallo, wata irin muguwar zamura Sir Moli yayi had'i da mik'ewa zambur, saboda tsoratar dayayi naganin ciwo da uban jinin dake zuba daga kan Era, cikin zaro ya kalli Era had'i da cewa wannan had'arin mota tayi? Shi tsakaninsa da Allah yayi tambayar, saboda yawan jinin dake zuba, cikin kuka Era tace " ba had'ari nayi ba Sir, wannan ce ta dake ni, tayi maganar tana nuna masa Sanah, bin inda Era ta nuna masa yayi da kallo, ganin baiga kowa ba yasa shi yin waige-waige had'i da cewa " ni banga kowa ba, wa kike nufi? Cikin kuka ta kuma nuna Sanah tace " wannan Sir, kallan ta yayi had'i da nuna ta yace " wai wa? A hankali Era ta mik'e taje har inda Sanah take ta dafa ta, had'i da cewa " Sir wannan yarinyar, cike da tsoro gami da mamaki Moli ya zaro ido yana kallan Sanah, had'i nufarta gadan-gadan yana yi mata wani irin kallo. MOMYN ZARAH _*RASHIN SANI.......*_ *HAUWA A USMAN* _JIDDARH_ ```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh``` 3⃣ _A PAGE 2 NAYI MISTAKE WAJEN SUNAYEN SANAH & KHULUD_ _RAWAN SHINE BABAN KHULUD_ _HAMRAZ KUMA BABAN SANAH_ *KHULUD RAWAN* *SANAH HAMRAZ* Yana isa wajen Sanah yasa hannu ya d'ago ta yana kallan Era yace " kina nufin wannan yarinyar itace ta ji miki wannan ciwon? Kai tsaye Era tace " eh Sir, shiru Sir Moli yayi had'i da k'urawa Sanah ido, ganin yadda idonta yayi jajir ne ya tabbatar masa da zafin zuciyar da take da ita, shiru yayi yana nazarinta na wani lokaci, yaga kwata-kwata babu alamar nadama ko danasani a tattare da ita, sai ma cika take tana matsewa had'i da jefawa Era kallan banza tana cije leb'e da alama idan ta samu dama k'ara jibgar Eran zatayi, a cikin kwayar idanta ya hango bak'ar zuciya da zafin ran dake gareta, yadda take motsa bakinta tana magana ciki-ciki ne yasa shi fahimtar tsagwaron masifa da tsiwar dake cinta,,,, mayar da kallansa yayi ga Khulud yaga yadda jikinta ke rawa, tsoro ya bayyana k'arara a fuskarta, kamar zaka ce mata k'et ta ruga, ya kalli idanta yaga alamar tausayawa Era a tattare da ita, kallo d'aya yayi mata ya fahimci kwata-kwata bata san fitina da hayani balle fad'a, sab'anin Sanah dako a jikinta yadda kasan ma bata yi komai ba. Kallansa ya maida ga Era ya ganta jibgegiya, k'atuwa mai k'irar k'atti, dan ko namiji Era tana iya yi masa mugun duka balle mace, ya kalli yadda jini ke zuba daga jikinta, ya kuma kallan Sanah, wacce a haihuwar kaji Era ta haife ta, ya dubi girma da tazarar dake tsakanin Era da Sanah, dan bambamcin a bayyane yake, yadda kasan rak'umi da zakara, haka bambamcin Sanah da Era yake, shi abinda ma yafi d'aure mai kai shine, yadda Sanah ta iya tunkarar Era kai tsaye batare da wani tsoro ko fargabar komai ba, bayan a k'alla Era tayi goman Sanah, abu na biyu daya k'ara bashi mamaki shine dame Sanah ta daki haka? Kuma ya akayi JSS 1 ta iya dambe da SS 3 kuma LABOUR PREFECT, shi abimma dariya ya bashi, dan tunda Era tace Sanah ce ta dake ta yake kanne dariyar dake neman kufce masa, Head Girl ya kalla yace " ku kai ta sick bay ayi mata treatment,, yayi maganar kamar baya so, "to ta amsa had'i da mik'ewa suka fita, komawa kan sofar dake office d'in ya kishingid'a had'i da rufe idansa, batare daya k'ara furta koda kalma d'aya ba, shiri-shiru har akayi 1hr, amma bai ko kalli inda su Sanah suke ba, har aka kira Sallar Magrib bai kalli inda suke ba, jin an kira sallah ne ya sashi mik'ewa a hankali yayi hanyar fita, da sauri Sanah tace " Sir ka manta da mu ne? Ko ta kanta bai bi ba, balle ya juyo , Sir Moli yana yin sallar Magrib ya wuce gida batare daya k'ara bi takan su ba, babu abinda yake tunani sai halayyar yarinyar, wacce bazata wuce 10yrs ba, yana tuno ruwan bala'i da rashin kunyar daya hango a kwayar idanta, ya tuno yadda ya hango bak'ar zuciya a tattare da ita, a hankali ya gyara kwanciyarsa had'i da furta " girman yarinyar nan da kallo, mijinta da iyayenta suna shirin ganin ikon Allah, yayi maganar can k'asan mak'ogwaronsa. Har akayi sallar ishsha shiru Sir Moli bai dawo ba, cikin tsiwa Sanah tace " wai wannan d'an iskan ya manta ya ajiye mutane ne? " Ko yana tsammanin gumaka ya ajiye marasa jini a jikinsu? Da sauri Khulud ta rufe mata baki ta zaro ido cike da tsoro, tace " kai Sanah idan ya kawo kai yaji abinda kike cewa fa? Baki Sanah ta zumb'uro had'i da cewa " to ya jin mana idan yaji sai me, mai zayyi? "Ai dai bai isa ya d'auki ran mu ba, iyakacinsa ya dake mu ko ya bamu wuya, wuya kam bata kisa, sai dai ma ta k'ara hora mu, Khulud tace " ni dai dan Allah kiyi hak'uri kiyi shiru kar yaji, dama muna cikin wani case d'in bamu san makomar mu ba har yanzu, Sanah tace " ke kin cika tsoro wallahi, duk irin ku aka tara a makarantar shiyasa yake jin kansa wani shege, Khulud zatayi magana Sanah ta mik'e tana karkab'e jikinta tace " tashi mu tafi Hostel, ido waje Khulud tace " Hostel? Batare data kalle ba tace " amma dai kin san yanzu dare yayi sosai ko? "Dan nasan a k'alla yanzu 9:00pm na dare yayi, kuma muma musulmai ne ya kamata muyi sallar Magrib da Ishsha, kuma koba komai ai mutane ne mu zamu buk'aci hutu, bacci da abinci, dan nasan shima mugun daya aje mu ya tafi, Khulud zatayi magana Sanah ta ja hannunta, tana tafiya da ita " gobe kice ni nace mu tafi Hostel, ni kuma zan bashi amsa dai-dai shi, suna tafiya Sanah na mitar ajiye sun da Sir Moli yayi " tsabar ya rai nawa mutane hankali, ya jibge mu a waje batare daya furta mata ko kalma d'aya ba, shege miskilin banza mai girman kai, wannan matarsa ta shiga uku, har suka k'arasa Hostel Sanah na mitar Sir Moli da tsoran Khulud da yayi yawa, ita dai Khulud kallanta kawai take yi batare data ce mata komai ba. _Ni ko nace hmmmmm shima haka yace mijinki yana shorin ganin ikon Allah_ Washe gari bayan sun shirya zasu tafi class Halan ta kalle su tace " ku tabbatar baku tafi class kai tsaye ba, ku wuce office d'in Sir Moli, dan baya san irin haka, ko kallanta Sanah batayi ba ta wuce abinta, sai Khulud ce amsa mata da "to, kana tabi bayan Sanah ganin tayi hanyar classes area yasa Khulud kallanta cike da mamaki, tace " Sanah ina zaki? Batare data kalle ta ba, ta bata amsa kai tsaye " abinda iyayen mu suka kawo mu muyi, Khulud ta kuma kallanta cikin rashin fahintar abinda tace, tace " kamar ya? "Ban gane abinda kike nufi ba, tana ci gaba da tafiya tace " karatu mana, ko ba karatu iyayen mu suka kawo yi ba? "Ai ba yawon zuwa staff room da teachers office aka kawo mu yi ba, dan haka ni class zani, shi daya matsu yazo ya same mu, ace mutum babu abinda ya iya sai wulak'anci da wulak'anta mutane, sai wani jijji da kai yake kamar yafi kowa, babu abinda ya sani sai muskilanci da girman ka......, idanta daya sauka akan nashi ne ya hana ta k'arasa abinda tayi niyyar fad'a, gabanta yayi muguwar fad'uwa tsoransa a karo na farko ya shige ta, tsaye yake sanye da sky blue na material yard, takalmi da hularsa, da agogonsa duk blue black ne, yayi masifar kyau, tun da suka taho yana tsaye hard'e da hannayensa a k'irji yana kallansu, ya kuma ji duk abinda suka fad'a, sosai Sanah tayi muguwar tsorata amma ta dage, bata bari tsoran yayi tasirin dazai bayyana a fuskarta ko jikinta ba, Khulud kuwa tunda ta ganshi jinkinta ya d'auki rawa, saboda tsoro da fargaba, a hankali Sanah ta saci kallansa, irin kallan daye mata ne yasa gabanta bugawa da k'arfi, dakewa tayi ta kama hannun Khulud taja tana k'ok'arin rab'awa ta gefensa ta wuce, shiko in banda tsabar mamakin hali da k'ok'arin ta, had'i da rashin tsoranta babu abinda yake yi, bajintar yarinyar da halayyarta ma shi tsoro suke bashi, ace tun tana k'arama take haka, ina kuma ga idan ta girma, ta zama cikekkiyar mace? Yayiwa kansa tambayar, kallan yadda ta had'e rai, ta murtuke fuska yayi, tana k'ok'arin bi ta gefensa ma ta wuce, a ransa yace " ikon Allah, lalle yarinyar nan ta cika cikekkiyar mara kunya da fitsara, amma zan nuna mata ni kakanta ne a wannan fagen,,, tana zuwa daf dashi zata wuce ya fisgo ta baya had'i dayin cilli da ita, ta fad'a, sosai taji fad'uwar har cikin ranta, saboda da k'arfi ya wullata, cikin tashin hankali Khulud ta isa inda take ta d'ago ta had'i da saka kuka, tana tambayarta idan taji ciwo, daurewa Sanah tayi ta mik'e tana murmushi tace " ke meye na kuka kuma? Ba fa wani babban abu bane 'yar fad'uwa nayi, da mamaki ya kuma kallanta a ransa yana cewa " lalle yarinyar nan wato bayan tsiwa, zuciya da fad'a, rashin kunya da fitsara ta had'a har da taurin kai da dakewar zuciya, shi kansa yasan tayi muguwar buguwa amma ta daure ta tashi kamar babu wani abu, a fili ya maimaita 'yar fad'uwa yana murmushin mugunta, fuska cike da tausayawa idanta yana zubar da hawaye, tace " kai Sanah wallahi kin mugu da yawa, hannu Sanah tasa tana goge mata hawayen dake zubo mata, tace " zafin buguwar danayi bai kai zafin hawayen nan da kike zubarwa ba, dan ji nake kamar zuciya ta zata fashe, Please ki daina kukan kinji Uludi nah, tayi maganar tana dariya, shikam tsaye kawai yake yana kallan ikon Allah, abinda ya kuma d'aure mishi kai, shine kalaman da Sanah tayi akan Khulud, yadda take maganar ya tabbatar masa daga zuciyarta kalaman ke fitowa, daga irin kallan da sukewa juna ya tabbatar suna matuk'ar k'aunar junan su. _Kamar ni da my Zainab Shagumba_ 💘💘💘 A dak'ile Sir Moli yace " ke! tasan sarai dasu yake amma tayi kamar ma bata san Allah yayi ruwansa a wajen ba, sai da ya runtse ido saboda tsabar takaicin yadda yariya k'arama take neman gwara kansa ta bashi Headache, ya tabbatar idan yayi sake kafin yabar makarantar sai ta karya masa alk'adari tasa sauran students sun rai na shi, da k'arfi ya daka mata tsawa had'i da cewa " ke dan ubanki badake nake ba? Yayi maganar cikin fad'a zata kuma share shi, Khulud ta juyo cikin tsoro tace " Sir damu kake? Yaso Sanah ce tayi magana, ba Khulud d'in ba, amma dayake ranshi a b'ace yake, cikin fushi ya bata amsa da cewa " a'a da ubanki nake, jin ya zaki Khulud yasa ta juyowa a fusace, cikin b'acin rai, amma yadda taga ya birkice ne yasata kasa yin magana saboda tsoransa data ji, yadda ta jiyo a fusace saboda ya zagi Khulud ne yasa shi fara fahimtar wani abu, saboda ko daya zage ta bata kalle inda yake ba, balle ta nuna b'acin ranta sai daya zagi Khulud, kallan Khulud yayi yace " ku je ku kira Head Girl da wacce kika fasawa kai jiya, yayi maganar yana tafiya, bata tanka masa ba, tayi wucewarta class abinta, babu yadda Khulud batayi akan kar suje class ba, amma fir Sanah tak'i. Ana tashi daga class suka wuce masjid daga nan sukayi dinning hall, duk Khulud a tsorace take amma Sanah ko'a jinkinta sai harkokinta take, babu abinda ya dameta, duk da ta lura da yadda Khulud take a tsorace, daga dinning Hostel suka koma, dole Khulud ta bi bayan Sanah dan babu yadda ta iya, bata san taje wajen Sir Moli ita kad'ai ta kuma jawowa Sanah wata matsalar, gwara ko kashe ta za'ayi a kashe su tare, hakan ne ya hanata zuwa, take bin Sanah dole badan ranta ya so ba, Sir Moli class d'in daya ke d'auka ya wuce direct, bai k'ara bi takan Sanah ba, dan shi a tunaninsa su can suna zaman jiranshi, shiyasa koda akayi break bai koma office d'insa ba ya wuce staff room, sai da aka tashi sannan ya nufi office, yadda ya bar office d'in haka ya dawo ya same shi, kwara-kwata babu alamun shigowar mutum, cike da mamaki ya lek'a ta window ya tambayi leburan dayake gyara musu office, " please wasu yara basu zo nan ba? Shiru leburan yayi na wani lokaci yana tunnani, sannan ya d'ago kai yace " gaskiya Sir tunda ka fita babu wanda ya shigo nan, ko a cikin malamai ma, ko wucewa tanan babu d'alibar data yi, "nagode kawai yace, yana jinjina kai cike da takaici, cikin matsanancin b'acin rai da zafin zuciya Sir Moli ya kwanta akan sofa had'i da rufe idanta, yana tunanin wanne irin hukunci zayyiwa yarinyar nan ya wuce, a fili yace " tab lalle ma, ni wannan shigiyar kwailar yarinyar ke rainawa hankali? "Aiko sai naci ubanta sai na nuna mata nawa iskancin yaci uwar nata, sai naga uban daya d'aure mata gindi, yayi maganar cikin zafin rai yana furzar da iskar bakinsa. Bayan sun gama shiryawa zasu tafi islamiyya, Khulud ta kalli Halan tace " please Aunty Halan kiyiwa Sanah magana muje kiran Sir Moli,,, ido Halan ta zaro had'i da cewa "au baku je ba dana ce kuje? Labarin duk abinda ya faru tsakanin su da Sir Moli Khulud ta bawa Halan tun daga farko har k'arshe, shiru Halan tayi tana mamakin yadda Sir Moli ya d'agawa Sanah k'afa tun daga jiya zuwa yau, tasan da wata daga cikin students ce da tuni jikinta ya gaya mata, kallan Sanah tayi taga babu abinda ya dame ta sai harkokinta take yi hankalinta a kwance, a ranta Halan tace " lalle wannan yarinyar da abun mamaki take, tana da taurin kai, ita gata ba babba ba balle ace ko santa Sir Moli yake shiyasa baya iyayi mata komai, da sauri tace " kai ina badai Sir Moli ba, that's impossible,, abinda ma bazai tab'a yiyu bane, ace wannan kwailar yarinyar yake so, yarinyar dako Nono bata fara ba, manyan 'yan mata, masu ji da kyau, class, kud'in, gayu sunyi sun bari akan Sir Moli,,, kawai dai Allah ne yake d'ora ta akan shi ta k'arasa maganar cikin ranta tana sauke ajiyar zuciya, a hankali Halan tace " Sanah! murtuke fuska Sanah tayi had'i da cewa " na'am, murmushi Halan tayi, dayake ita mai sauk'in kai ce kana ta cigaba da cewa" ni dai ina baki shawara a matsayin 'yar uwa ba senior ba, Sanah fad'a da malami ba naki bane, dan ke ce bazaki tab'a cin riba ba, sai dai fad'uwa, taurin kai da zafin zuciya suma ba nake bane a boarding school in ba haka ba zaki sha bak'ar wuya, ko badan kanki ba, kodan Khulud ya kamata ace kunje kiran nashi kunji mai zai ce muku, wallahi even principal tsoran Sir Moli take balle sauran teachers da students, ki dubi Khulud tana san zuwa kiran, amma saboda dake tak'i zuwa tana bin ra'ayinki, ta gwamamaci duk abinda zayyi muku yayi muku tare data je ita kad'ai, kallan Khulud Sanah tayi, taga yadda duk ta marairaice fuska, murmushi Sanah tayi tace " shikenan zanje hankalinku ya kwanta, ajiyar zuciya Halan da Khulud suka sauke a tare, kallansu tayi had'i da d'age gira d'aya, tana yi musu alamar tambaya da idanta, dariya Halan tayi tace " ni dai tashi ku tafi, tayi magana tana jan su, had'i da mik'a musu hijabansu, karb'ar hijaban sukayi suna dariya suka tafi. MOMYN ZARAH _*RASHIN SANI.......*_ *HAUWA A USMAN* _JIDDARH_ ```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh``` 4⃣ Suna isa k'ofar office d'in gabanta yayi muguwar fad'uwa, amma ta dake dan kar Khulud ta fahimci halin datake ciki, Sanah na niyyar danna kai, Khulud tayi saurin rik'o ta had'i da cewa " ke wai meyasa kike haka ne? Baki Sanah ta zumb'uro had'i da cewa " me kuma nayi? Khulud tace " amma sanin kanki ne ba'a shigar masa office kai tsaye ko? "Tunda a gabanki ko head girl ce tazo tsayawa take a bakin k'ofa, ta fara yin sallama kafin ta shiga , sannan ta tsaya har sai ya bata izinin shiga, kuma ma ko ba haka ba ai bai dace ace kin shigar masa office kai tsaye ba, Sanah tace " to amma kema ai kina ganin yadda yake shanya mutane a cikin rana, sai ya mula ya mulmule kafin ya bawa mutane damar shiga office d'in, kuma ni gaskiya kin san ban iya jira a rana saboda tana iya sani ciwon kai, ta k'arasa maganar tana zumb'uro baki, "ko ma dai miye ai sai mubi doka da k'a'idarsa dan mu zauna lafiya dashi, tunda haka muka ga sauran students nayi, ba kuma fin su mukayi ba, rolling idanta tayi sama had'i da dafe goshinta, tace " to naji yanzu dai sai kiyi masa sallamar, mu kuma muyi ta zama anan har sai sanda yaga damar damu izinin shiga, duk abinda ke faruwa tsakanin Sanah da Khulud Sir Moli na jinsu, murmushin takaici yayi cike da mamakinta, girgiza kai kawai Khulud tayi batare data kuma cewa komai ba ta k'arasa gaf da k'ofar tayi sallama, ga mamkin Sanah sai ji tayi ya amsa had'i da bada izinin shiga, kallanta Khulud tayi tana yi mata alamar kinga ni ko, da idanta. "Assalamu Alaikuma Khulud ta kuma fad'a lokacin da suke shiga, batare daya d'ago ya kalle su ba ya amsa, baki Sanah ta tab'e a ranta tace " majhulil hali, duk abinda take yana kallanta, dakyar ya bud'e baki yace " meya hana ku zuwa d'azu? Kai tsaye Sanah tace " gani nayi during class hrs ne shiyasa nace kar muzo, batare daya bud'e idansa ba ya kuma cewa " uban wa ya ku izinin tafiya jiya? Nan ma kai tsaye Sanah tace " ni ce!" saboda me? ya tambaye ta a tak'aice, "Lokacin salla ne yayi, shiyasa nace, ya kamata ace muje muyi sallah, sannan munci abinci,, ta k'arishe maganar kanta a k'asa. A hankali ya bud'e idansa ya zuba mata batare daya ce komai ba, leb'e ya cije saboda yadda take bashi amsa kai tsaye, wani irin tsanarta yakeji na ratsashi, dan ya tsani rashin tarbiya, ya kuma lura yarinyar bata da kunya, cikin isa ya mik'e zaune daga kishingid'en dayake ya kalle ta, yace " ke 'yar iska ce ? Ido itama ta zuba masa batare data ce komai ba, ya kuma cewa " ke wacce iriyar fitsarerriya ce? a gidan ku babu manya ne?ko suma iyayen naku basu iya magana da manya ba? balle su koyar daku tarbiyyar iya magana da manya?" Fuska ya kumatsukewa tare da cewa: "Amma ina ganin kamar a gidan ku kowa zaman kansa yake yi ba babba ba yaro ko!?" yayi maganar duka a lokaci d'aya, ba Sanah mai bak'ar zuciya da zafin rai ba, dai-dai da Khulud mai sanyin rai sai da maganganunsa suka saukar mata bak'in ciki da b'acin rai, take idanuwan Sanah suka canja launin su daga fari zuwa jajaye, ya kuma kallanta yace " fool an idiot, stupid girl kawai, ke har wata shegiya kike d'aukar kanki ko?, to bari kiji ba gagarerre sai barerre, ke a cikinfitsararrun ma wacece ke? 'yar tatsitsiya dake sai fitsara, shigiya empty head, kanki ba komai sai rawar kan banza, daman k'anan yaran nan kunfi manyan 'yan mata iya iskanci, 'yar iska ko majinar hancinki baki gama iya cireta ba, amma har kin fara zubdawa wasu jini a jiki, woto ke gaki yar sara suka, zaki b'ata mana tarbiyar yaran makaranta daga zuwanki ko, wannan iyayenki idan basu da gaske ba, Uwar yan daba zaki zama, jacakar banza". iya bak'in ciki da takaici Sanah ta k'unsa, saboda tsabar yadda take jin zuciyarta na tafasa, jikinta har tsuma yake, mak'ogwaronta ya bushe rak'ayau, idanuwanta suka koma asalin red, ta kafe shi da ido cike da tsantsar fitsara bata ko k'ifta idanta, ya kalli Khulud dake durk'ushe tana hawaye, yace " Jeki kira min head girl, da Era, cikin sanyin jiki ta mik'e ta fita, ya mayar da kallansa ga Sanah yaga har lokacin kallansa take yi kurrrr ko k'iftawa batayi, ganin yadda lokaci d'aya ta birkice, kamanninta suka sauya ne ya d'aure masa kai,, a ransa yace " lalle yarinyar nan nada bak'ar zuciya. Yace " ke daina kallo na mayya kawai, karki cinye ni, ni ba d'an daba irinki bane" yayi maganar yana kowa kishingid'ar, yana daga kishingid'en yace, "Kinci sa'a banadabanci irin naki,da wallahi sai na sauke miki rawar kan nan naki to sai dai kici kanki witch!". Sallamar su Khulud ce ta katse shi, a dak'ile ya basu izinin shigowa, daga gefe suka rakub'e ya kalli Khulud yace " meya had'a ku? Yayi maganar a tak'aice, su Era da suka shigo da suka ga yanayin Sanah, suka kuma ga Khulud na kuka sai sukayi zaton dukan su Sir Moli yayi, aiko take mugun farin ciki ya lullub'e Era, cikin sanyin murya Khulud ta shiga bashi labarin duk abinda ya faru tun daga farko har k'arshe, shiru yayi na wani d'an lokaci yana nazari, murmushi yayi a cikin ransa dan ya gano logon Sanah yanzu, a ransa yace " Era Khulud ta tab'a shiyasa zuciyar Sanah tayi zafi har idanta ya rufe ta dake ta, wato daka tab'a Khulud gwara a tab'a ta kenan? Murmushin gefe baki yayi, wato wannan dalilin ne yasa d'azo dana zage ta bataji haushi ba amma dana zagi Khulud take yanayinta ya canja? Kai ya girgiza cike da matsanancin farin cikin gano lagwanta, ya kalli Khulud yace " ke idan na bincika naga kinyi min k'arya sai naci uwarki, yayi maganar yana satar kallan Sanah, aiko ido ta runtse da k'arfi, ya kuma yin murmushin mugunta, ya kalli su Era yace " haka akayi? Kanta a k'asa tace " eh Sir, yace " ba'an hana ku aiken JSS ba? Shiru Era tayi kanta a k'asa, ya kalli Head Girl yace " ba an hana ku dueling ba? Itama shiru tayi had'i da sadda kanta k'asa, ya cigaba da cewa " ina tunanin kamar principal ta hana ku koda aiken 'yan JSS musamman JSS1 ko? Duk sukayi shiru, a fusace ya daka musu gigitacciyar tsawa " bada ku nake magana ba? Yayi maganar cikin b'acin rai, take cikin su ya d'auki kerrrma yana b'ari, a tsorace Head Girl tace " wallahi Sir ban san hakan ta faru ba, ina class ina karatun test, aka kira ni, ita kuma Era tace " am so sorry Sir, cikin b'acin rai ya daka musu tsawa " get out!, zanyi bincike akan mate d'inku, wallahi matuk'ar na gano kuna zaluntar na k'asa daku sai kun raina kanku, jiki na b'ari suka fita, Era na cewa " na shiga uku, kashi na bushe, dan nasan muddin Sir Moli yayi bincike akan mu sai buzuna, Head Girl tace " kuma kin san shi magana d'aya yake yi, muddin yace " zayyi abu to sai yayi babu kuma uban daya isa ya hana shi sai Allah. Sir Moli ya mayar da kallansa ga Khulud yace " ke ku 'yan daba ne? "A'a ta bashi amsa cikin sanyin magana, idansa nakan Khulud ya kuma cewa shaye-shaye kuke yi? Ta kuma cewa a'a, yace " abinda kuka taso kuga ana yi a gidan ku kenan, ko shi iyyen na ku suka koya muku fad'a da makami har da fasa kai? Kai ta girgiza masa tana kanne kukan ta, ganin halin da Khulud ke ciki yayi masifar d'agawa Sanah hankali duk abinda take yi Sir Moli yana lura da ita, ya kuma cewa " to amma gidan ku akwai 'yan daba masu sare-sare da yanka mutane da wuk'a ko? Kukan da Khulud take dannewa ne ya kufce mata, tana k'ok'arin yin magana Sanah tayi saurin cewa, " ni ce nayi laifi ba ita ba, dan haka ni zaka yiwa hukunci ko ka tsare da tambayoyi ba ita ba, Khulud tayi saurin cewa " a'a Sir tare mukayi komai dan haka duk hukuncin da zakayi kayi mana tare, Sanah tace " wai meyasa kike haka ne Ulud, please ki bari ni danayi laifi ya hukunta ni dai-dai da abinda nayi, Khulud tace " kin fara ko? "Amma ai sanin kanki ne tare mukayi amma shine kike san zamewa, Sir Moli ido ya zuba musu yana ganin ikon Allah, kowacce na k'ok'arin kare 'yar uwarta, Sir Moli ya kalli Khulud yace " ashe kema 'yar iskarce, da k'arfi Khulud ta saka kukan bak'in ciki, aiko zuciyar Sanah ta hasala, a tsawace cike da tsantsar masifa tace " don't say it again, haba kai wanne irin d'an Ada....... Kafin ta k'arasa Sir Moli ya d'auke ta gigitaccen mari, tassssssssssssssss a razane Khulud ta d'ago kanta, ganin Sanah aka mara yasata fita daga hayyacinta ta nufi Sanah d'in da sauri Sanah ta fad'o jikinta, bak'in ciki ne yasa Khulud durk'ushewa had'i da saka gigitaccen kuka, a hankali Sanah ta durk'usa a gabanta tasa hannu ta d'ago kanta, hannu Sanah tasa hana gogewa Khulud hawayen dake zubawa daga idanta tace " Uludi na ki daina kuka please, kai Khulud ta girgiza mata alamar a'a, ido Sanah ta zaro tace " meyasa? Cikin rawa murya tana danne kukan bak'in cikin dake cinta, Khulud tace " marinki fa akayi a gaba amma bani da yadda zanyi, please barni nayi kukan kona samu sassaucin abinda nake ji, murmushin bak'in ciki Sanah tayi tace " wallahi marin da akayi min bai kai kwatankwacin zafin zubar hawayenki a cikin rai na ba,, da sauri Khulud ta share hawayenta had'i da yin murmushi tace " na dai na kukan to, Sanah na murmushi tace " kinyi alk'awari? Dariya Khulud tayi had'i da cewa " eh nayi alk'awarin daga nan har k'arshen rayuwar mu duk abinda kika ce na bari zan bari, duk kuma abinda kikace nayi zanyi, in sha Allahu, Sanah ta kuma yin dariya tace " ni kuma nayi miki alk'awarin daga nan har mutuwar mu bazan tab'a bari kiyi kuka ba, ba kuma zan tab'a barin ki cikin damuwa da matsala ba in sha Allah, dariya sukayi a tare had'i cewa alk'awari, Sir Moli na gefe yana kallan yadda yara k'anana ke k'aunar junansu, ashe ba Sanah ce kad'ai ke san Khulud d'in ba, itama tana santa, yayi maganar cikin ransa, dan yadda ta taso a haukace badan Sanah ta rik'e ta ba, tana iya fad'a masa, can k'asan mak'ogwaro yace "aiko da kinci ubanki yarinya da kinga ne shayi ruwa ne. Jin an shiga Sallar Magrib ne yasa shi fita da sauri dan ko kiran sallar bai ji ba, sai da ya tsaya yayi sallar ishsha kafin ya tafi gida, kwance yake rufe da ido amma ba bacci yake ba, tunani da mamakin yaran yake yi, babu abinda yafi d'aure masa kai sai tarin so da k'aunar da suke yiwa junan su, ya kuma san ba uwarsu d'aya uban su d'aya ba, saboda ita SANAH GANEZ sunanta, ita kuma KHULUD HAMRAZ,,, a fili yace " so halitta ne dan ko uwa d'aya uwa bazasu yi wa junan su irin wannan mugun son ba, yasan k'aunar da suke yiwa juna daga Allah ne, ido ya runtse yana tunanin shi yaushe ne zai san so? Yaushe zai san zafin so, zai san abinda ake ji a cikin so, dan shi a iya tsayin rayuwarsa bai tab'a yin soyayya ko ya so wata 'ya mace ba, asalima bai san abinda ake kira da so ba, tunda aka haife shi har zuwa yanzu da yake da 22yrs, yana da 3yrs aka saka shi a primary school, ya gama yana da 10yrs saboda yayi nursery 1&2, yana da 16yrs ya gama secondary school, sai yanzu dayake service, amma idan ka ganshi sai ka rantse ya haura 30yrs, saboda tsabar kwarjini da kamalarsa, had'i da nutsuwarsa, yana cikin tunani bacci yayi awon gaba dashi batare daya sani ba. Su Khulud ganin ya fita yasa Sanah rik'o hannun Khulud tace " tashi mu tafi hostel, Khulud bata ko motsa ba, ta kafe Sanah da ido, kana tace " muje ina Sanah? " Salan ya dawo bai iske mu ba ya samu abinda yake so, ya kuma samun damar zagin iyayen mu da ahalin mu, ya kuma ci mana fuska da mutunci, yanzu ke zagin da yayiwa iyayen mu da ahalin mu damu kanmu kinji dad'insa? Shiru Sanah tayi bata furta kalma ko d'aya ba, Khulud ta cigaba " ke yake zaga amma ni nake jin k'unar abin a zuciya ta, ke yake jifa da munanan kalaman amma ni nake jin zafi da bak'i ciki a rai na, dan girman Allah my Sanah ki daina shiga sabgar mutumin nan, mu lallab'a mu rabu dashi lafiya, ido Sanah ta zaro had'i da cewa " wacce sabgar tasa nake shiga? "Wacce idan yace kiyi abu kike k'inyi, please daga yau duk abinda ya saki ko ya umarce dayi muddin bai sab'awa shari'a ba kiyi, idan kina yin abinda yace ai sai yaci kansa, muga kuma ta inda zai b'ollo ganin yadda Khulud ke magana ne yasa cikin sanyin jiki Sanah tace " to in sha Allah zanyi k'ok'arin kiyaye duk abinda zai kawo sab'ani a tsakani na dashi, saboda ke kodan hankalinki ya kwanta ki samu nutsuwa. Amma wallahi badan ke ba da sai dai ya kashe ni, idan shi k'aramin d'an iska ne, da sai na nuna masa ni babba ce, shege d'an iska mai girman kan tsiya, muskilin banza, wai harshi zai cewa wani d'an iska bayan shine cikkekken kwarto, ja'irin yaro kullum bashi da aiki sai ya kwanta haka, ta kwanta akan sofa tana kwaikwayon yadda yake kishingid'a, ta kwaikwayi maganar sa tace " ke kina shaye-shaye ne? Tayi maganar kamar yadda yake yi, tace kaji munafuki shida yayi kama da masu shaye-shayen ma ba'a ce yana yi ba sai shine zai cewa wani yana yi, wama ya sani ko irin sune masu lab'ewa a uncompleted buildings suna 'yan kurb'e-kurb'e da zuk'e-zuk'e, zata kuma magana Khulud ta rok'o hannunta tana nuna mata agogon bangon dake manne a office d'in, tace kalli har 10:05pm na dare, zo mu tafi nasan shima ya tafi, Sanah tace " mugu azzalumi kawa ya ajiye mu kamar ba mutane ya jibge ba, ba ci ba sha balle bacci, sai gobe yazo yana tare late comers, shi yana can saki baki yana bacci har da munshari, Khulud taja hannunta tana cewa " mu tafi ni dai yunwa da bacci nake ji, kuma nasan hankalin Aunty Halan nacan a tashe. Washe gari bayan an kad'a break Sir Moli ya tafi office, har ya kishingid'a ya tuna da voice recorder daya kunna ya aje ye dazai fita yabar su Sanah a office d'in sa, dan ya tabbatar da sai sunyi wata magana a kansa, d'aukowa yayi daga inda ya b'oyeta a gefen table d'insa yana murmushi ya koma kan sofa had'i da kunnawa. MOMYN ZARAH_*RASHIN SANI.......*_ *HAUWA A USMAN* _JIDDARH_ ```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh``` 4⃣ Suna isa k'ofar office d'in gabanta yayi muguwar fad'uwa, amma ta dake dan kar Khulud ta fahimci halin datake ciki, Sanah na niyyar danna kai, Khulud tayi saurin rik'o ta had'i da cewa " ke wai meyasa kike haka ne? Baki Sanah ta zumb'uro had'i da cewa " me kuma nayi? Khulud tace " amma sanin kanki ne ba'a shigar masa office kai tsaye ko? "Tunda a gabanki ko head girl ce tazo tsayawa take a bakin k'ofa, ta fara yin sallama kafin ta shiga , sannan ta tsaya har sai ya bata izinin shiga, kuma ma ko ba haka ba ai bai dace ace kin shigar masa office kai tsaye ba, Sanah tace " to amma kema ai kina ganin yadda yake shanya mutane a cikin rana, sai ya mula ya mulmule kafin ya bawa mutane damar shiga office d'in, kuma ni gaskiya kin san ban iya jira a rana saboda tana iya sani ciwon kai, ta k'arasa maganar tana zumb'uro baki, "ko ma dai miye ai sai mubi doka da k'a'idarsa dan mu zauna lafiya dashi, tunda haka muka ga sauran students nayi, ba kuma fin su mukayi ba, rolling idanta tayi sama had'i da dafe goshinta, tace " to naji yanzu dai sai kiyi masa sallamar, mu kuma muyi ta zama anan har sai sanda yaga damar damu izinin shiga, duk abinda ke faruwa tsakanin Sanah da Khulud Sir Moli na jinsu, murmushin takaici yayi cike da mamakinta, girgiza kai kawai Khulud tayi batare data kuma cewa komai ba ta k'arasa gaf da k'ofar tayi sallama, ga mamkin Sanah sai ji tayi ya amsa had'i da bada izinin shiga, kallanta Khulud tayi tana yi mata alamar kinga ni ko, da idanta. "Assalamu Alaikuma Khulud ta kuma fad'a lokacin da suke shiga, batare daya d'ago ya kalle su ba ya amsa, baki Sanah ta tab'e a ranta tace " majhulil hali, duk abinda take yana kallanta, dakyar ya bud'e baki yace " meya hana ku zuwa d'azu? Kai tsaye Sanah tace " gani nayi during class hrs ne shiyasa nace kar muzo, batare daya bud'e idansa ba ya kuma cewa " uban wa ya ku izinin tafiya jiya? Nan ma kai tsaye Sanah tace " ni ce, saboda me? ya tambaye ta a tak'aice, "saboda muma mutane ne kuma musulmai ya kamata ace munyi sallah munci abinci,, a hankali ya bud'e idansa ya zuba masa batare daya ce komai ba, leb'e ya cije saboda yadda take bashi amsa kai tsaye, cikin isa ya mik'e zaune daga kishingid'en dayake ya kalle ta, yace " ke 'yar iska ce ? Ido itama ta zuba masa batare data ce komai ba, ya kuma cewa " ke wacce irin dabba jaka ce? "A gidan ku babu manya ne, ko suma iyayen naku basu iya magana da manya ba? Balle su koyar daku tarbiyyar iya magana da manya, amma ina ganin kamar a gidan ku kowa zaman kansa yake yi ba babba ba yaro ko? yayi maganar duka a lokaci d'aya, ba Sanah mai bak'ar zuciya da zafin rai ba, dai-dai da Khulud mai sanyin rai sai da maganganunsa suka saukar mata bak'in ciki da b'acin rai, take idanuwan Sanah suka canja launin su daga fari zuwa jajaye, ya kuma kallanta yace " fool an idiot, stupid girl kawai, ke har wata shegiya kike d'aukar kanki? "Ke a cikin matan ma wacece ke? "Tatsitsiya kwaila kawai, shigiya empty head, kanki ba komai sai rawar kan banza, dama kwailayen nan kunfi manyan 'yan mata iya iskanci da san masa, 'yar iska ko irgen dangi baki fara ba amma har kin fara zak'ewa maza, wannan iyayenki idan basu da gaske ba, KARUWA za'ayi anan, ajacakar banza, iya bak'in ciki da takaici Sanah ta k'unsa, saboda tsabar yadda take jin zuciyarta na tafasa, jikinta har tsuma yake, mak'ogwaronta ya bushe rak'ayau, idanuwanta suka koma asalin red, ta kafe shi da ido cike da tsantsar tsana bata ko k'ifta idanta, ya kalli Khulud dake durk'ushe tana hawaye, yace " jeki kira min head girl, da Era, cikin sanyin jiki ta mik'e ta fita, ya mayar da kallansa ga Sanah yaga har lokacin kallansa take yi tarrrr ko k'iftawa batayi, ganin yadda lokaci d'aya ta birkice, kamanninta suka sauya ne ya d'aure masa kai,, a ransa yace " lalle yarinyar nan nada bak'ar zuciya. Yace " ke daina kallo na mayya kawai, karki cinye ni, ni ba d'an iska bane, yayi maganar yana kowa kishingid'ar, yana daga kishingid'en yace " kinci sa'a bana zina da wallahi sai sauke miki rawar kan nan taki, oh! na manta ashe cewa zanyi kinyi rashin sa'a ni ba d'an iska bane bana zina, balle ki samu abinda kike so dan nasan babu abinda ke d'awainiya dake sai feelings d'ina, to sai dai kici kanki witch, sallamar su Khulud ce ta katse shi, a dak'ile ya basu izinin shigowa, daga gefe suka rakub'e ya kalli Khulud yace " meya had'a ku? Yayi maganar a tak'aice, su Era da suka shigo da suka ga yanayin Sanah, suka kuma ga Khulud na kuka sai sukayi zaton dukan su Sir Moli yayi, aiko take mugun farin ciki ya lullub'e Era, cikin sanyin murya Khulud ta shiga bashi labarin duk abinda ya faru tun daga farko har k'arshe, shiru yayi na wani d'an lokaci yana nazari, murmushi yayi a cikin ransa dan ya gano logon Sanah yanzu, a ransa yace " Era Khulud ta tab'a shiyasa zuciyar Sanah tayi zafi har idanta ya rufe ta dake ta, wato daka tab'a Khulud gwara a tab'a ta kenan? Murmushin gefe baki yayi, wato wannan dalilin ne yasa d'azo dana zage ta bataji haushi ba amma dana zagi Khulud take yanayinta ya canja? Kai ya girgiza cike da matsanancin farin cikin gano lagwanta, ya kalli Khulud yace " ke idan na bincika naga kinyi min k'arya sai naci uwarki, yayi maganar yana satar kallan Sanah, aiko ido ta runtse da k'arfi, ya kuma yin murmushin mugunta, ya kalli su Era yace " haka akayi? Kanta a k'asa tace " eh Sir, yace " ba'an hana ku aiken JSS ba? Shiru Era tayi kanta a k'asa, ya kalli Head Girl yace " ba an hana ku dueling ba? Itama shiru tayi had'i da sadda kanta k'asa, ya cigaba da cewa " ina tunanin kamar principal ta hana ku koda aiken 'yan JSS musamman JSS1 ko? Duk sukayi shiru, a fusace ya daka musu gigitacciyar tsawa " bada ku nake magana ba? Yayi maganar cikin b'acin rai, take cikin su ya d'auki kerrrma yana b'ari, a tsorace Head Girl tace " wallahi Sir ban san hakan ta faru ba, ina class ina karatun test, aka kira ni, ita kuma Era tace " am so sorry Sir, cikin b'acin rai ya daka musu tsawa " get out!, zanyi bincike akan mate d'inku, wallahi matuk'ar na gano kuna zaluntar na k'asa daku sai kun raina kanku, jiki na b'ari suka fita, Era na cewa " na shiga uku, kashi na bushe, dan nasan muddin Sir Moli yayi bincike akan mu sai buzuna, Head Girl tace " kuma kin san shi magana d'aya yake yi, muddin yace " zayyi abu to sai yayi babu kuma uban daya isa ya hana shi sai Allah. Sir Moli ya mayar da kallansa ga Khulud yace " ke ku 'yan daba ne? "A'a ta bashi amsa cikin sanyin magana, idansa nakan Khulud ya kuma cewa shaye-shaye kuke yi? Ta kuma cewa a'a, yace " abinda kuka taso kuga ana yi a gidan ku kenan, ko shi iyyen na ku suka koya muku fad'a da makami har da fasa kai? Kai ta girgiza masa tana kanne kukan ta, ganin halin da Khulud ke ciki yayi masifar d'agawa Sanah hankali, tasa hannunta ta dafe sai saitin zuciyarta kota samu sauk'in abinda take ji, duk abinda take yi Sir Moli yana lura da ita, ya kuma cewa " to amma gidan su akwai 'yan daba masu sare-sare da yanka mutane da wuk'a ko? Kukan da Khulud take dannewa ne ya kufce mata, tana k'ok'arin yin magana Sanah tayi saurin cewa, " ni ce nayi laifi ba ita ba, dan haka ni zaka yiwa hukunci ko ka tsare da tambayoyi ba ita ba, Khulud tayi saurin cewa " a'a Sir tare mukayi komai dan haka duk hukuncin da zakayi kayi mana tare, Sanah tace " wai meyasa kike haka ne Ulud, please ki bari ni danayi laifi ya hukunta ni dai-dai da abinda nayi, Khulud tace " kin fara ko? "Amma ai sanin kanki ne tare mukayi amma shine kike san zamewa, Sir Moli ido ya zuba musu yana ganin ikon Allah, kowacce na k'ok'arin kare 'yar uwarta, Sir Moli ya kalli Khulud yace " ashe kema 'yar iskarce, da k'arfi Khulud ta saka kukan bak'in ciki, aiko zuciyar Sanah ta hasala, a tsawace cike da tsantsar masifa tace " don't say it again, haba kai wanne irin d'an Ada....... Kafin ta k'arasa Sir Moli ya d'auke ta gigitaccen mari, tassssssssssssssss a razane Khulud ta d'ago kanta, ganin Sanah aka mara yasata fita daga hayyacinta ta nufi Sir Moli gadan-gadan,,, da sauri Sanah ta rok'ota, bak'in ciki ne yasa Khulud durk'ushewa had'i da saka gigitaccen kuka, a hankali Sanah ta durk'usa a gabanta tasa hannu ta d'ago kanta, hannu Sanah tasa hana gogewa Khulud hawayen dake zubawa daga idanta tace " Uludi na ki daina kuka please, kai Khulud ta girgiza mata alamar a'a, ido Sanah ta zaro tace " meyasa? Cikin rawa murya tana danne kukan bak'in cikin dake cinta, Khulud tace " marinki fa akayi a gaba amma bani da yadda zanyi, please barni nayi kukan kona samu sassaucin abinda nake ji, murmushin bak'in ciki Sanah tayi tace " wallahi marin da akayi min bai kai kwatankwacin zafin zubar hawayenki a cikin rai na ba,, da sauri Khulud ta share hawayenta had'i da yin murmushi tace " na dai na kukan to, Sanah na murmushi tace " kinyi alk'awari? Dariya Khulud tayi had'i da cewa " eh nayi alk'awarin daga nan har k'arshen rayuwar mu duk abinda kika ce na bari zan bari, duk kuma abinda kikace nayi zanyi, in sha Allahu, Sanah ta kuma yin dariya tace " ni kuma nayi miki alk'awarin daga nan har mutuwar mu bazan tab'a bari kiyi kuka ba, ba kuma zan tab'a barin ki cikin damuwa da matsala ba in sha Allah, dariya sukayi a tare had'i cewa alk'awari, Sir Moli na gefe yana kallan yadda yara k'anana ke k'aunar junansu, ashe ba Sanah ce kad'ai ke san Khulud d'in ba, itama tana santa, yayi maganar cikin ransa, dan yadda ta taso a haukace badan Sanah ta rik'e ta ba, tana iya fad'a masa, can k'asan mak'ogwaro yace "aiko da kinci ubanki yarinya da kinga ne shayi ruwa ne. Jin an shiga Sallar Magrib ne yasa shi fita da sauri dan ko kiran sallar bai ji ba, sai da ya tsaya yayi sallar ishsha kafin ya tafi gida, kwance yake rufe da ido amma ba bacci yake ba, tunani da mamakin yaran yake yi, babu abinda yafi d'aure masa kai sai tarin so da k'aunar da suke yiwa junan su, ya kuma san ba uwarsu d'aya uban su d'aya ba, saboda ita SANAH GANEZ sunanta, ita kuma KHULUD HAMRAZ,,, a fili yace " so halitta ne dan ko uwa d'aya uwa bazasu yi wa junan su irin wannan mugun son ba, yasan k'aunar da suke yiwa juna daga Allah ne, ido ya runtse yana tunanin shi yaushe ne zai san so? Yaushe zai san zafin so, zai san abinda ake ji a cikin so, dan shi a iya tsayin rayuwarsa bai tab'a yin soyayya ko ya so wata 'ya mace ba, asalima bai san abinda ake kira da so ba, tunda aka haife shi har zuwa yanzu da yake da 22yrs, yana da 3yrs aka saka shi a primary school, ya gama yana da 10yrs saboda yayi nursery 1&2, yana da 16yrs ya gama secondary school, sai yanzu dayake service, amma idan ka ganshi sai ka rantse ya haura 30yrs, saboda tsabar kwarjini da kamalarsa, had'i da nutsuwarsa, yana cikin tunani bacci yayi awon gaba dashi batare daya sani ba. Su Khulud ganin ya fita yasa Sanah rik'o hannun Khulud tace " tashi mu tafi hostel, Khulud bata ko motsa ba, ta kafe Sanah da ido, kana tace " muje ina Sanah? " Salan ya dawo bai iske mu ba ya samu abinda yake so, ya kuma samun damar zagin iyayen mu da ahalin mu, ya kuma ci mana fuska da mutunci, yanzu ke zagin da yayiwa iyayen mu da ahalin mu damu kanmu kinji dad'insa? Shiru Sanah tayi bata furta kalma ko d'aya ba, Khulud ta cigaba " ke yake zaga amma ni nake jin k'unar abin a zuciya ta, ke yake jifa da munanan kalaman amma ni nake jin zafi da bak'i ciki a rai na, dan girman Allah my Sanah ki daina shiga sabgar mutumin nan, mu lallab'a mu rabu dashi lafiya, ido Sanah ta zaro had'i da cewa " wacce sabgar tasa nake shiga? "Wacce idan yace kiyi abu kike k'inyi, please daga yau duk abinda ya saki ko ya umarce dayi muddin bai sab'awa shari'a ba kiyi, idan kina yin abinda yace ai sai yaci kansa, muga kuma ta inda zai b'ollo ganin yadda Khulud ke magana ne yasa cikin sanyin jiki Sanah tace " to in sha Allah zanyi k'ok'arin kiyaye duk abinda zai kawo sab'ani a tsakani na dashi, saboda ke kodan hankalinki ya kwanta ki samu nutsuwa. Amma wallahi badan ke ba da sai dai ya kashe ni, idan shi k'aramin d'an iska ne, da sai na nuna masa ni babba ce, shege d'an iska mai girman kan tsiya, muskilin banza, wai harshi zai cewa wani d'an iska bayan shine cikkekken kwarto, ja'irin yaro kullum bashi da aiki sai ya kwanta haka, ta kwanta akan sofa tana kwaikwayon yadda yake kishingid'a, ta kwaikwayi maganar sa tace " ke kina shaye-shaye ne? Tayi maganar kamar yadda yake yi, tace kaji munafuki shida yayi kama da masu shaye-shayen ma ba'a ce yana yi ba sai shine zai cewa wani yana yi, wama ya sani ko irin sune masu lab'ewa a uncompleted buildings suna 'yan kurb'e-kurb'e da zuk'e-zuk'e, zata kuma magana Khulud ta rok'o hannunta tana nuna mata agogon bangon dake manne a office d'in, tace kalli har 10:05pm na dare, zo mu tafi nasan shima ya tafi, Sanah tace " mugu azzalumi kawa ya ajiye mu kamar ba mutane ya jibge ba, ba ci ba sha balle bacci, sai gobe yazo yana tare late comers, shi yana can saki baki yana bacci har da munshari, Khulud taja hannunta tana cewa " mu tafi ni dai yunwa da bacci nake ji, kuma nasan hankalin Aunty Halan nacan a tashe. Washe gari bayan an kad'a break Sir Moli ya tafi office, har ya kishingid'a ya tuna da voice recorder daya kunna ya aje ye dazai fita yabar su Sanah a office d'in sa, dan ya tabbatar da sai sunyi wata magana a kansa, d'aukowa yayi daga inda ya b'oyeta a gefen table d'insa yana murmushi ya koma kan sofa had'i da kunnawa. MOMYN ZARAH_*RASHIN SANI.......*_ *HAUWA A USMAN* _JIDDARH_ ```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh``` 4⃣ Suna isa k'ofar office d'in gabanta yayi muguwar fad'uwa, amma ta dake dan kar Khulud ta fahimci halin datake ciki, Sanah na niyyar danna kai, Khulud tayi saurin rik'o ta had'i da cewa " ke wai meyasa kike haka ne? Baki Sanah ta zumb'uro had'i da cewa " me kuma nayi? Khulud tace " amma sanin kanki ne ba'a shigar masa office kai tsaye ko? "Tunda a gabanki ko head girl ce tazo tsayawa take a bakin k'ofa, ta fara yin sallama kafin ta shiga , sannan ta tsaya har sai ya bata izinin shiga, kuma ma ko ba haka ba ai bai dace ace kin shigar masa office kai tsaye ba, Sanah tace " to amma kema ai kina ganin yadda yake shanya mutane a cikin rana, sai ya mula ya mulmule kafin ya bawa mutane damar shiga office d'in, kuma ni gaskiya kin san ban iya jira a rana saboda tana iya sani ciwon kai, ta k'arasa maganar tana zumb'uro baki, "ko ma dai miye ai sai mubi doka da k'a'idarsa dan mu zauna lafiya dashi, tunda haka muka ga sauran students nayi, ba kuma fin su mukayi ba, rolling idanta tayi sama had'i da dafe goshinta, tace " to naji yanzu dai sai kiyi masa sallamar, mu kuma muyi ta zama anan har sai sanda yaga damar damu izinin shiga, duk abinda ke faruwa tsakanin Sanah da Khulud Sir Moli na jinsu, murmushin takaici yayi cike da mamakinta, girgiza kai kawai Khulud tayi batare data kuma cewa komai ba ta k'arasa gaf da k'ofar tayi sallama, ga mamkin Sanah sai ji tayi ya amsa had'i da bada izinin shiga, kallanta Khulud tayi tana yi mata alamar kinga ni ko, da idanta. "Assalamu Alaikuma Khulud ta kuma fad'a lokacin da suke shiga, batare daya d'ago ya kalle su ba ya amsa, baki Sanah ta tab'e a ranta tace " majhulil hali, duk abinda take yana kallanta, dakyar ya bud'e baki yace " meya hana ku zuwa d'azu? Kai tsaye Sanah tace " gani nayi during class hrs ne shiyasa nace kar muzo, batare daya bud'e idansa ba ya kuma cewa " uban wa ya ku izinin tafiya jiya? Nan ma kai tsaye Sanah tace " ni ce!" saboda me? ya tambaye ta a tak'aice, "Lokacin salla ne yayi, shiyasa nace, ya kamata ace muje muyi sallah, sannan munci abinci,, ta k'arishe maganar kanta a k'asa. A hankali ya bud'e idansa ya zuba mata batare daya ce komai ba, leb'e ya cije saboda yadda take bashi amsa kai tsaye, wani irin tsanarta yakeji na ratsashi, dan ya tsani rashin tarbiya, ya kuma lura yarinyar bata da kunya, cikin isa ya mik'e zaune daga kishingid'en dayake ya kalle ta, yace " ke 'yar iska ce ? Ido itama ta zuba masa batare data ce komai ba, ya kuma cewa " ke wacce iriyar fitsarerriya ce? a gidan ku babu manya ne?ko suma iyayen naku basu iya magana da manya ba? balle su koyar daku tarbiyyar iya magana da manya?" Fuska ya kumatsukewa tare da cewa: "Amma ina ganin kamar a gidan ku kowa zaman kansa yake yi ba babba ba yaro ko!?" yayi maganar duka a lokaci d'aya, ba Sanah mai bak'ar zuciya da zafin rai ba, dai-dai da Khulud mai sanyin rai sai da maganganunsa suka saukar mata bak'in ciki da b'acin rai, take idanuwan Sanah suka canja launin su daga fari zuwa jajaye, ya kuma kallanta yace " fool an idiot, stupid girl kawai, ke har wata shegiya kike d'aukar kanki ko?, to bari kiji ba gagarerre sai barerre, ke a cikinfitsararrun ma wacece ke? 'yar tatsitsiya dake sai fitsara, shigiya empty head, kanki ba komai sai rawar kan banza, daman k'anan yaran nan kunfi manyan 'yan mata iya iskanci, 'yar iska ko majinar hancinki baki gama iya cireta ba, amma har kin fara zubdawa wasu jini a jiki, woto ke gaki yar sara suka, zaki b'ata mana tarbiyar yaran makaranta daga zuwanki ko, wannan iyayenki idan basu da gaske ba, Uwar yan daba zaki zama, jacakar banza". iya bak'in ciki da takaici Sanah ta k'unsa, saboda tsabar yadda take jin zuciyarta na tafasa, jikinta har tsuma yake, mak'ogwaronta ya bushe rak'ayau, idanuwanta suka koma asalin red, ta kafe shi da ido cike da tsantsar fitsara bata ko k'ifta idanta, ya kalli Khulud dake durk'ushe tana hawaye, yace " Jeki kira min head girl, da Era, cikin sanyin jiki ta mik'e ta fita, ya mayar da kallansa ga Sanah yaga har lokacin kallansa take yi kurrrr ko k'iftawa batayi, ganin yadda lokaci d'aya ta birkice, kamanninta suka sauya ne ya d'aure masa kai,, a ransa yace " lalle yarinyar nan nada bak'ar zuciya. Yace " ke daina kallo na mayya kawai, karki cinye ni, ni ba d'an daba irinki bane" yayi maganar yana kowa kishingid'ar, yana daga kishingid'en yace, "Kinci sa'a banadabanci irin naki,da wallahi sai na sauke miki rawar kan nan naki to sai dai kici kanki witch!". Sallamar su Khulud ce ta katse shi, a dak'ile ya basu izinin shigowa, daga gefe suka rakub'e ya kalli Khulud yace " meya had'a ku? Yayi maganar a tak'aice, su Era da suka shigo da suka ga yanayin Sanah, suka kuma ga Khulud na kuka sai sukayi zaton dukan su Sir Moli yayi, aiko take mugun farin ciki ya lullub'e Era, cikin sanyin murya Khulud ta shiga bashi labarin duk abinda ya faru tun daga farko har k'arshe, shiru yayi na wani d'an lokaci yana nazari, murmushi yayi a cikin ransa dan ya gano logon Sanah yanzu, a ransa yace " Era Khulud ta tab'a shiyasa zuciyar Sanah tayi zafi har idanta ya rufe ta dake ta, wato daka tab'a Khulud gwara a tab'a ta kenan? Murmushin gefe baki yayi, wato wannan dalilin ne yasa d'azo dana zage ta bataji haushi ba amma dana zagi Khulud take yanayinta ya canja? Kai ya girgiza cike da matsanancin farin cikin gano lagwanta, ya kalli Khulud yace " ke idan na bincika naga kinyi min k'arya sai naci uwarki, yayi maganar yana satar kallan Sanah, aiko ido ta runtse da k'arfi, ya kuma yin murmushin mugunta, ya kalli su Era yace " haka akayi? Kanta a k'asa tace " eh Sir, yace " ba'an hana ku aiken JSS ba? Shiru Era tayi kanta a k'asa, ya kalli Head Girl yace " ba an hana ku dueling ba? Itama shiru tayi had'i da sadda kanta k'asa, ya cigaba da cewa " ina tunanin kamar principal ta hana ku koda aiken 'yan JSS musamman JSS1 ko? Duk sukayi shiru, a fusace ya daka musu gigitacciyar tsawa " bada ku nake magana ba? Yayi maganar cikin b'acin rai, take cikin su ya d'auki kerrrma yana b'ari, a tsorace Head Girl tace " wallahi Sir ban san hakan ta faru ba, ina class ina karatun test, aka kira ni, ita kuma Era tace " am so sorry Sir, cikin b'acin rai ya daka musu tsawa " get out!, zanyi bincike akan mate d'inku, wallahi matuk'ar na gano kuna zaluntar na k'asa daku sai kun raina kanku, jiki na b'ari suka fita, Era na cewa " na shiga uku, kashi na bushe, dan nasan muddin Sir Moli yayi bincike akan mu sai buzuna, Head Girl tace " kuma kin san shi magana d'aya yake yi, muddin yace " zayyi abu to sai yayi babu kuma uban daya isa ya hana shi sai Allah. Sir Moli ya mayar da kallansa ga Khulud yace " ke ku 'yan daba ne? "A'a ta bashi amsa cikin sanyin magana, idansa nakan Khulud ya kuma cewa shaye-shaye kuke yi? Ta kuma cewa a'a, yace " abinda kuka taso kuga ana yi a gidan ku kenan, ko shi iyyen na ku suka koya muku fad'a da makami har da fasa kai? Kai ta girgiza masa tana kanne kukan ta, ganin halin da Khulud ke ciki yayi masifar d'agawa Sanah hankali duk abinda take yi Sir Moli yana lura da ita, ya kuma cewa " to amma gidan ku akwai 'yan daba masu sare-sare da yanka mutane da wuk'a ko? Kukan da Khulud take dannewa ne ya kufce mata, tana k'ok'arin yin magana Sanah tayi saurin cewa, " ni ce nayi laifi ba ita ba, dan haka ni zaka yiwa hukunci ko ka tsare da tambayoyi ba ita ba, Khulud tayi saurin cewa " a'a Sir tare mukayi komai dan haka duk hukuncin da zakayi kayi mana tare, Sanah tace " wai meyasa kike haka ne Ulud, please ki bari ni danayi laifi ya hukunta ni dai-dai da abinda nayi, Khulud tace " kin fara ko? "Amma ai sanin kanki ne tare mukayi amma shine kike san zamewa, Sir Moli ido ya zuba musu yana ganin ikon Allah, kowacce na k'ok'arin kare 'yar uwarta, Sir Moli ya kalli Khulud yace " ashe kema 'yar iskarce, da k'arfi Khulud ta saka kukan bak'in ciki, aiko zuciyar Sanah ta hasala, a tsawace cike da tsantsar masifa tace " don't say it again, haba kai wanne irin d'an Ada....... Kafin ta k'arasa Sir Moli ya d'auke ta gigitaccen mari, tassssssssssssssss a razane Khulud ta d'ago kanta, ganin Sanah aka mara yasata fita daga hayyacinta ta nufi Sanah d'in da sauri Sanah ta fad'o jikinta, bak'in ciki ne yasa Khulud durk'ushewa had'i da saka gigitaccen kuka, a hankali Sanah ta durk'usa a gabanta tasa hannu ta d'ago kanta, hannu Sanah tasa hana gogewa Khulud hawayen dake zubawa daga idanta tace " Uludi na ki daina kuka please, kai Khulud ta girgiza mata alamar a'a, ido Sanah ta zaro tace " meyasa? Cikin rawa murya tana danne kukan bak'in cikin dake cinta, Khulud tace " marinki fa akayi a gaba amma bani da yadda zanyi, please barni nayi kukan kona samu sassaucin abinda nake ji, murmushin bak'in ciki Sanah tayi tace " wallahi marin da akayi min bai kai kwatankwacin zafin zubar hawayenki a cikin rai na ba,, da sauri Khulud ta share hawayenta had'i da yin murmushi tace " na dai na kukan to, Sanah na murmushi tace " kinyi alk'awari? Dariya Khulud tayi had'i da cewa " eh nayi alk'awarin daga nan har k'arshen rayuwar mu duk abinda kika ce na bari zan bari, duk kuma abinda kikace nayi zanyi, in sha Allahu, Sanah ta kuma yin dariya tace " ni kuma nayi miki alk'awarin daga nan har mutuwar mu bazan tab'a bari kiyi kuka ba, ba kuma zan tab'a barin ki cikin damuwa da matsala ba in sha Allah, dariya sukayi a tare had'i cewa alk'awari, Sir Moli na gefe yana kallan yadda yara k'anana ke k'aunar junansu, ashe ba Sanah ce kad'ai ke san Khulud d'in ba, itama tana santa, yayi maganar cikin ransa, dan yadda ta taso a haukace badan Sanah ta rik'e ta ba, tana iya fad'a masa, can k'asan mak'ogwaro yace "aiko da kinci ubanki yarinya da kinga ne shayi ruwa ne. Jin an shiga Sallar Magrib ne yasa shi fita da sauri dan ko kiran sallar bai ji ba, sai da ya tsaya yayi sallar ishsha kafin ya tafi gida, kwance yake rufe da ido amma ba bacci yake ba, tunani da mamakin yaran yake yi, babu abinda yafi d'aure masa kai sai tarin so da k'aunar da suke yiwa junan su, ya kuma san ba uwarsu d'aya uban su d'aya ba, saboda ita SANAH GANEZ sunanta, ita kuma KHULUD HAMRAZ,,, a fili yace " so halitta ne dan ko uwa d'aya uwa bazasu yi wa junan su irin wannan mugun son ba, yasan k'aunar da suke yiwa juna daga Allah ne, ido ya runtse yana tunanin shi yaushe ne zai san so? Yaushe zai san zafin so, zai san abinda ake ji a cikin so, dan shi a iya tsayin rayuwarsa bai tab'a yin soyayya ko ya so wata 'ya mace ba, asalima bai san abinda ake kira da so ba, tunda aka haife shi har zuwa yanzu da yake da 22yrs, yana da 3yrs aka saka shi a primary school, ya gama yana da 10yrs saboda yayi nursery 1&2, yana da 16yrs ya gama secondary school, sai yanzu dayake service, amma idan ka ganshi sai ka rantse ya haura 30yrs, saboda tsabar kwarjini da kamalarsa, had'i da nutsuwarsa, yana cikin tunani bacci yayi awon gaba dashi batare daya sani ba. Su Khulud ganin ya fita yasa Sanah rik'o hannun Khulud tace " tashi mu tafi hostel, Khulud bata ko motsa ba, ta kafe Sanah da ido, kana tace " muje ina Sanah? " Salan ya dawo bai iske mu ba ya samu abinda yake so, ya kuma samun damar zagin iyayen mu da ahalin mu, ya kuma ci mana fuska da mutunci, yanzu ke zagin da yayiwa iyayen mu da ahalin mu damu kanmu kinji dad'insa? Shiru Sanah tayi bata furta kalma ko d'aya ba, Khulud ta cigaba " ke yake zaga amma ni nake jin k'unar abin a zuciya ta, ke yake jifa da munanan kalaman amma ni nake jin zafi da bak'i ciki a rai na, dan girman Allah my Sanah ki daina shiga sabgar mutumin nan, mu lallab'a mu rabu dashi lafiya, ido Sanah ta zaro had'i da cewa " wacce sabgar tasa nake shiga? "Wacce idan yace kiyi abu kike k'inyi, please daga yau duk abinda ya saki ko ya umarce dayi muddin bai sab'awa shari'a ba kiyi, idan kina yin abinda yace ai sai yaci kansa, muga kuma ta inda zai b'ollo ganin yadda Khulud ke magana ne yasa cikin sanyin jiki Sanah tace " to in sha Allah zanyi k'ok'arin kiyaye duk abinda zai kawo sab'ani a tsakani na dashi, saboda ke kodan hankalinki ya kwanta ki samu nutsuwa. Amma wallahi badan ke ba da sai dai ya kashe ni, idan shi k'aramin d'an iska ne, da sai na nuna masa ni babba ce, shege d'an iska mai girman kan tsiya, muskilin banza, wai harshi zai cewa wani d'an iska bayan shine cikkekken kwarto, ja'irin yaro kullum bashi da aiki sai ya kwanta haka, ta kwanta akan sofa tana kwaikwayon yadda yake kishingid'a, ta kwaikwayi maganar sa tace " ke kina shaye-shaye ne? Tayi maganar kamar yadda yake yi, tace kaji munafuki shida yayi kama da masu shaye-shayen ma ba'a ce yana yi ba sai shine zai cewa wani yana yi, wama ya sani ko irin sune masu lab'ewa a uncompleted buildings suna 'yan kurb'e-kurb'e da zuk'e-zuk'e, zata kuma magana Khulud ta rok'o hannunta tana nuna mata agogon bangon dake manne a office d'in, tace kalli har 10:05pm na dare, zo mu tafi nasan shima ya tafi, Sanah tace " mugu azzalumi kawa ya ajiye mu kamar ba mutane ya jibge ba, ba ci ba sha balle bacci, sai gobe yazo yana tare late comers, shi yana can saki baki yana bacci har da munshari, Khulud taja hannunta tana cewa " mu tafi ni dai yunwa da bacci nake ji, kuma nasan hankalin Aunty Halan nacan a tashe. Washe gari bayan an kad'a break Sir Moli ya tafi office, har ya kishingid'a ya tuna da voice recorder daya kunna ya aje ye dazai fita yabar su Sanah a office d'in sa, dan ya tabbatar da sai sunyi wata magana a kansa, d'aukowa yayi daga inda ya b'oyeta a gefen table d'insa yana murmushi ya koma kan sofa had'i da kunnawa. MOMYN ZARAH_*RASHIN SANI.......*_ *HAUWA A USMAN* _JIDDARH_ ```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh``` 4⃣ Suna isa k'ofar office d'in gabanta yayi muguwar fad'uwa, amma ta dake dan kar Khulud ta fahimci halin datake ciki, Sanah na niyyar danna kai, Khulud tayi saurin rik'o ta had'i da cewa " ke wai meyasa kike haka ne? Baki Sanah ta zumb'uro had'i da cewa " me kuma nayi? Khulud tace " amma sanin kanki ne ba'a shigar masa office kai tsaye ko? "Tunda a gabanki ko head girl ce tazo tsayawa take a bakin k'ofa, ta fara yin sallama kafin ta shiga , sannan ta tsaya har sai ya bata izinin shiga, kuma ma ko ba haka ba ai bai dace ace kin shigar masa office kai tsaye ba, Sanah tace " to amma kema ai kina ganin yadda yake shanya mutane a cikin rana, sai ya mula ya mulmule kafin ya bawa mutane damar shiga office d'in, kuma ni gaskiya kin san ban iya jira a rana saboda tana iya sani ciwon kai, ta k'arasa maganar tana zumb'uro baki, "ko ma dai miye ai sai mubi doka da k'a'idarsa dan mu zauna lafiya dashi, tunda haka muka ga sauran students nayi, ba kuma fin su mukayi ba, rolling idanta tayi sama had'i da dafe goshinta, tace " to naji yanzu dai sai kiyi masa sallamar, mu kuma muyi ta zama anan har sai sanda yaga damar damu izinin shiga, duk abinda ke faruwa tsakanin Sanah da Khulud Sir Moli na jinsu, murmushin takaici yayi cike da mamakinta, girgiza kai kawai Khulud tayi batare data kuma cewa komai ba ta k'arasa gaf da k'ofar tayi sallama, ga mamkin Sanah sai ji tayi ya amsa had'i da bada izinin shiga, kallanta Khulud tayi tana yi mata alamar kinga ni ko, da idanta. "Assalamu Alaikuma Khulud ta kuma fad'a lokacin da suke shiga, batare daya d'ago ya kalle su ba ya amsa, baki Sanah ta tab'e a ranta tace " majhulil hali, duk abinda take yana kallanta, dakyar ya bud'e baki yace " meya hana ku zuwa d'azu? Kai tsaye Sanah tace " gani nayi during class hrs ne shiyasa nace kar muzo, batare daya bud'e idansa ba ya kuma cewa " uban wa ya ku izinin tafiya jiya? Nan ma kai tsaye Sanah tace " ni ce, saboda me? ya tambaye ta a tak'aice, "saboda muma mutane ne kuma musulmai ya kamata ace munyi sallah munci abinci,, a hankali ya bud'e idansa ya zuba masa batare daya ce komai ba, leb'e ya cije saboda yadda take bashi amsa kai tsaye, cikin isa ya mik'e zaune daga kishingid'en dayake ya kalle ta, yace " ke 'yar iska ce ? Ido itama ta zuba masa batare data ce komai ba, ya kuma cewa " ke wacce irin dabba jaka ce? "A gidan ku babu manya ne, ko suma iyayen naku basu iya magana da manya ba? Balle su koyar daku tarbiyyar iya magana da manya, amma ina ganin kamar a gidan ku kowa zaman kansa yake yi ba babba ba yaro ko? yayi maganar duka a lokaci d'aya, ba Sanah mai bak'ar zuciya da zafin rai ba, dai-dai da Khulud mai sanyin rai sai da maganganunsa suka saukar mata bak'in ciki da b'acin rai, take idanuwan Sanah suka canja launin su daga fari zuwa jajaye, ya kuma kallanta yace " fool an idiot, stupid girl kawai, ke har wata shegiya kike d'aukar kanki? "Ke a cikin matan ma wacece ke? "Tatsitsiya kwaila kawai, shigiya empty head, kanki ba komai sai rawar kan banza, dama kwailayen nan kunfi manyan 'yan mata iya iskanci da san masa, 'yar iska ko irgen dangi baki fara ba amma har kin fara zak'ewa maza, wannan iyayenki idan basu da gaske ba, KARUWA za'ayi anan, ajacakar banza, iya bak'in ciki da takaici Sanah ta k'unsa, saboda tsabar yadda take jin zuciyarta na tafasa, jikinta har tsuma yake, mak'ogwaronta ya bushe rak'ayau, idanuwanta suka koma asalin red, ta kafe shi da ido cike da tsantsar tsana bata ko k'ifta idanta, ya kalli Khulud dake durk'ushe tana hawaye, yace " jeki kira min head girl, da Era, cikin sanyin jiki ta mik'e ta fita, ya mayar da kallansa ga Sanah yaga har lokacin kallansa take yi tarrrr ko k'iftawa batayi, ganin yadda lokaci d'aya ta birkice, kamanninta suka sauya ne ya d'aure masa kai,, a ransa yace " lalle yarinyar nan nada bak'ar zuciya. Yace " ke daina kallo na mayya kawai, karki cinye ni, ni ba d'an iska bane, yayi maganar yana kowa kishingid'ar, yana daga kishingid'en yace " kinci sa'a bana zina da wallahi sai sauke miki rawar kan nan taki, oh! na manta ashe cewa zanyi kinyi rashin sa'a ni ba d'an iska bane bana zina, balle ki samu abinda kike so dan nasan babu abinda ke d'awainiya dake sai feelings d'ina, to sai dai kici kanki witch, sallamar su Khulud ce ta katse shi, a dak'ile ya basu izinin shigowa, daga gefe suka rakub'e ya kalli Khulud yace " meya had'a ku? Yayi maganar a tak'aice, su Era da suka shigo da suka ga yanayin Sanah, suka kuma ga Khulud na kuka sai sukayi zaton dukan su Sir Moli yayi, aiko take mugun farin ciki ya lullub'e Era, cikin sanyin murya Khulud ta shiga bashi labarin duk abinda ya faru tun daga farko har k'arshe, shiru yayi na wani d'an lokaci yana nazari, murmushi yayi a cikin ransa dan ya gano logon Sanah yanzu, a ransa yace " Era Khulud ta tab'a shiyasa zuciyar Sanah tayi zafi har idanta ya rufe ta dake ta, wato daka tab'a Khulud gwara a tab'a ta kenan? Murmushin gefe baki yayi, wato wannan dalilin ne yasa d'azo dana zage ta bataji haushi ba amma dana zagi Khulud take yanayinta ya canja? Kai ya girgiza cike da matsanancin farin cikin gano lagwanta, ya kalli Khulud yace " ke idan na bincika naga kinyi min k'arya sai naci uwarki, yayi maganar yana satar kallan Sanah, aiko ido ta runtse da k'arfi, ya kuma yin murmushin mugunta, ya kalli su Era yace " haka akayi? Kanta a k'asa tace " eh Sir, yace " ba'an hana ku aiken JSS ba? Shiru Era tayi kanta a k'asa, ya kalli Head Girl yace " ba an hana ku dueling ba? Itama shiru tayi had'i da sadda kanta k'asa, ya cigaba da cewa " ina tunanin kamar principal ta hana ku koda aiken 'yan JSS musamman JSS1 ko? Duk sukayi shiru, a fusace ya daka musu gigitacciyar tsawa " bada ku nake magana ba? Yayi maganar cikin b'acin rai, take cikin su ya d'auki kerrrma yana b'ari, a tsorace Head Girl tace " wallahi Sir ban san hakan ta faru ba, ina class ina karatun test, aka kira ni, ita kuma Era tace " am so sorry Sir, cikin b'acin rai ya daka musu tsawa " get out!, zanyi bincike akan mate d'inku, wallahi matuk'ar na gano kuna zaluntar na k'asa daku sai kun raina kanku, jiki na b'ari suka fita, Era na cewa " na shiga uku, kashi na bushe, dan nasan muddin Sir Moli yayi bincike akan mu sai buzuna, Head Girl tace " kuma kin san shi magana d'aya yake yi, muddin yace " zayyi abu to sai yayi babu kuma uban daya isa ya hana shi sai Allah. Sir Moli ya mayar da kallansa ga Khulud yace " ke ku 'yan daba ne? "A'a ta bashi amsa cikin sanyin magana, idansa nakan Khulud ya kuma cewa shaye-shaye kuke yi? Ta kuma cewa a'a, yace " abinda kuka taso kuga ana yi a gidan ku kenan, ko shi iyyen na ku suka koya muku fad'a da makami har da fasa kai? Kai ta girgiza masa tana kanne kukan ta, ganin halin da Khulud ke ciki yayi masifar d'agawa Sanah hankali, tasa hannunta ta dafe sai saitin zuciyarta kota samu sauk'in abinda take ji, duk abinda take yi Sir Moli yana lura da ita, ya kuma cewa " to amma gidan su akwai 'yan daba masu sare-sare da yanka mutane da wuk'a ko? Kukan da Khulud take dannewa ne ya kufce mata, tana k'ok'arin yin magana Sanah tayi saurin cewa, " ni ce nayi laifi ba ita ba, dan haka ni zaka yiwa hukunci ko ka tsare da tambayoyi ba ita ba, Khulud tayi saurin cewa " a'a Sir tare mukayi komai dan haka duk hukuncin da zakayi kayi mana tare, Sanah tace " wai meyasa kike haka ne Ulud, please ki bari ni danayi laifi ya hukunta ni dai-dai da abinda nayi, Khulud tace " kin fara ko? "Amma ai sanin kanki ne tare mukayi amma shine kike san zamewa, Sir Moli ido ya zuba musu yana ganin ikon Allah, kowacce na k'ok'arin kare 'yar uwarta, Sir Moli ya kalli Khulud yace " ashe kema 'yar iskarce, da k'arfi Khulud ta saka kukan bak'in ciki, aiko zuciyar Sanah ta hasala, a tsawace cike da tsantsar masifa tace " don't say it again, haba kai wanne irin d'an Ada....... Kafin ta k'arasa Sir Moli ya d'auke ta gigitaccen mari, tassssssssssssssss a razane Khulud ta d'ago kanta, ganin Sanah aka mara yasata fita daga hayyacinta ta nufi Sir Moli gadan-gadan,,, da sauri Sanah ta rok'ota, bak'in ciki ne yasa Khulud durk'ushewa had'i da saka gigitaccen kuka, a hankali Sanah ta durk'usa a gabanta tasa hannu ta d'ago kanta, hannu Sanah tasa hana gogewa Khulud hawayen dake zubawa daga idanta tace " Uludi na ki daina kuka please, kai Khulud ta girgiza mata alamar a'a, ido Sanah ta zaro tace " meyasa? Cikin rawa murya tana danne kukan bak'in cikin dake cinta, Khulud tace " marinki fa akayi a gaba amma bani da yadda zanyi, please barni nayi kukan kona samu sassaucin abinda nake ji, murmushin bak'in ciki Sanah tayi tace " wallahi marin da akayi min bai kai kwatankwacin zafin zubar hawayenki a cikin rai na ba,, da sauri Khulud ta share hawayenta had'i da yin murmushi tace " na dai na kukan to, Sanah na murmushi tace " kinyi alk'awari? Dariya Khulud tayi had'i da cewa " eh nayi alk'awarin daga nan har k'arshen rayuwar mu duk abinda kika ce na bari zan bari, duk kuma abinda kikace nayi zanyi, in sha Allahu, Sanah ta kuma yin dariya tace " ni kuma nayi miki alk'awarin daga nan har mutuwar mu bazan tab'a bari kiyi kuka ba, ba kuma zan tab'a barin ki cikin damuwa da matsala ba in sha Allah, dariya sukayi a tare had'i cewa alk'awari, Sir Moli na gefe yana kallan yadda yara k'anana ke k'aunar junansu, ashe ba Sanah ce kad'ai ke san Khulud d'in ba, itama tana santa, yayi maganar cikin ransa, dan yadda ta taso a haukace badan Sanah ta rik'e ta ba, tana iya fad'a masa, can k'asan mak'ogwaro yace "aiko da kinci ubanki yarinya da kinga ne shayi ruwa ne. Jin an shiga Sallar Magrib ne yasa shi fita da sauri dan ko kiran sallar bai ji ba, sai da ya tsaya yayi sallar ishsha kafin ya tafi gida, kwance yake rufe da ido amma ba bacci yake ba, tunani da mamakin yaran yake yi, babu abinda yafi d'aure masa kai sai tarin so da k'aunar da suke yiwa junan su, ya kuma san ba uwarsu d'aya uban su d'aya ba, saboda ita SANAH RAWAN sunanta, ita kuma KHULUD HAMRAZ,,, a fili yace " so halitta ne dan ko uwa d'aya uwa bazasu yi wa junan su irin wannan mugun son ba, yasan k'aunar da suke yiwa juna daga Allah ne, ido ya runtse yana tunanin shi yaushe ne zai san so? Yaushe zai san zafin so, zai san abinda ake ji a cikin so, dan shi a iya tsayin rayuwarsa bai tab'a yin soyayya ko ya so wata 'ya mace ba, asalima bai san abinda ake kira da so ba, tunda aka haife shi har zuwa yanzu da yake da 22yrs, yana da 3yrs aka saka shi a primary school, ya gama yana da 10yrs saboda yayi nursery 1&2, yana da 16yrs ya gama secondary school, sai yanzu dayake service, amma idan ka ganshi sai ka rantse ya haura 30yrs, saboda tsabar kwarjini da kamalarsa, had'i da nutsuwarsa, yana cikin tunani bacci yayi awon gaba dashi batare daya sani ba. Su Khulud ganin ya fita yasa Sanah rik'o hannun Khulud tace " tashi mu tafi hostel, Khulud bata ko motsa ba, ta kafe Sanah da ido, kana tace " muje ina Sanah? " Salan ya dawo bai iske mu ba ya samu abinda yake so, ya kuma samun damar zagin iyayen mu da ahalin mu, ya kuma ci mana fuska da mutunci, yanzu ke zagin da yayiwa iyayen mu da ahalin mu damu kanmu kinji dad'insa? Shiru Sanah tayi bata furta kalma ko d'aya ba, Khulud ta cigaba " ke yake zaga amma ni nake jin k'unar abin a zuciya ta, ke yake jifa da munanan kalaman amma ni nake jin zafi da bak'i ciki a rai na, dan girman Allah my Sanah ki daina shiga sabgar mutumin nan, mu lallab'a mu rabu dashi lafiya, ido Sanah ta zaro had'i da cewa " wacce sabgar tasa nake shiga? "Wacce idan yace kiyi abu kike k'inyi, please daga yau duk abinda ya saki ko ya umarce dayi muddin bai sab'awa shari'a ba kiyi, idan kina yin abinda yace ai sai yaci kansa, muga kuma ta inda zai b'ollo ganin yadda Khulud ke magana ne yasa cikin sanyin jiki Sanah tace " to in sha Allah zanyi k'ok'arin kiyaye duk abinda zai kawo sab'ani a tsakani na dashi, saboda ke kodan hankalinki ya kwanta ki samu nutsuwa. Amma wallahi badan ke ba da sai dai ya kashe ni, idan shi k'aramin d'an iska ne, da sai na nuna masa ni babba ce, shege d'an iska mai girman kan tsiya, muskilin banza, wai harshi zai cewa wani d'an iska bayan shine cikkekken kwarto, ja'irin yaro kullum bashi da aiki sai ya kwanta haka, ta kwanta akan sofa tana kwaikwayon yadda yake kishingid'a, ta kwaikwayi maganar sa tace " ke kina shaye-shaye ne? Tayi maganar kamar yadda yake yi, tace kaji munafuki shida yayi kama da masu shaye-shayen ma ba'a ce yana yi ba sai shine zai cewa wani yana yi, wama ya sani ko irin sune masu lab'ewa a uncompleted buildings suna 'yan kurb'e-kurb'e da zuk'e-zuk'e, zata kuma magana Khulud ta rok'o hannunta tana nuna mata agogon bangon dake manne a office d'in, tace kalli har 10:05pm na dare, zo mu tafi nasan shima ya tafi, Sanah tace " mugu azzalumi kawa ya ajiye mu kamar ba mutane ya jibge ba, ba ci ba sha balle bacci, sai gobe yazo yana tare late comers, shi yana can saki baki yana bacci har da munshari, Khulud taja hannunta tana cewa " mu tafi ni dai yunwa da bacci nake ji, kuma nasan hankalin Aunty Halan nacan a tashe. Washe gari bayan an kad'a break Sir Moli ya tafi office, har ya kishingid'a ya tuna da voice recorder daya kunna ya aje ye dazai fita yabar su Sanah a office d'in sa, dan ya tabbatar da sai sunyi wata magana a kansa, d'aukowa yayi daga inda ya b'oyeta a gefen table d'insa yana murmushi ya koma kan sofa had'i da kunnawa. MOMYN ZARAH _*RASHIN SANI.......*_ *HAUWA A USMAN* _JIDDARH_ ```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh``` 5⃣ Playing yayi zai fara ji, Vice Principal ya shigo office d'in,, cikin sallama, Sir Moli yayi saurin kashe record d'in, ya tattara hankalinsa kan VP batare daya mik'e daga inda yake ba, dayake VP ya riga da yasan halin Sir Moli bai wani ji haushin abin ba, dan idan da sabo sun sabawa baud'add'an halinsa, VP yace " Malam Moli dama wata alfarma nake nema a wajenka idan ba damuwa, ido Moli ya zuba masa had'i da cewa " kamar ta me fa? "Please dama wasu students za'akai Hospital, saboda ciwon zu yafi k'arfin sick bay d'in mu, dole sai an kai su babban asibiti, cikekken Doctor ya duba su, to kuma ni ina da aiki a office, shine nake san ka taimaka ka tayani aikin ko kuma ka kai yaran Hospital, d'an gutun murmushi yayi kana yace " ok badamuwa Sir, ka zab'i wanda kake ganin zaka iya ni sai nayi kowanne ne, murmushi shima Sir Jeeb yayi kana yace " no choose anyone kawai, ni bani da damuwa zan iyayin kowanne, dan yasan halin Moli idan yace zayyi mai gatse-gatse sai yak'i yi, sai dai duk abinda zai faru ya faru, shi kuma Moli saboda baya san yawan magana yasa shi cewa " ok zan kai su asibitin,, yayi maganar yana mik'ewa, "thank you, cewar Sir Jeeb, Moli bayyi mishi magana ba sai murmushi kawai da yayi. Private Hospital dake cikin garin Roni ya kai su, batare da wani b'ata lokaci ba aka karb'e su aka shigar dasu da hanzari, a gaggace aka shiga duba su, ba'a shima ba likitan ya fito, a wajen jira ya iske Sir Moli zaune ya jingina kansa da bayan kujerar dayake zaune had'i da rufe idanuwansa, sallamar Doctor d'in ce tasa shi bud'e idansa, ganin Doctor tsaye akansa yasa shi mik'ewa a hankali had'i da mik'a masa hannu, bayan sun gaisa ne Doctor yace " d'aya hawan jini ke damunta, ido Sir Moli ya zaro waje, cikin kid'ima yace " what! hawan jini fa kace? "Yes abinda ke damunta kenan kuma yayi mata mugun kamu, yama zama dole mu d'ora ta akan magani yanzu, cikin sanyin jiki Sir Moli yace " d'ayar fa? "Malaria ke damunta, "wannan is normal cewa Moli, magunguna Doctor ya rubuta musu, sannan ya sallame su, sai da Moli ya biya ta Pharmacy ya siya kafin ya wuce school, kallan yarinyar da Doctor yace tana d'auke da hawan jini yake ta mirror, babu abinda yake bashi mamaki sai k'arancin shekarunta, dan ya tabbata bazata wuce 14yrs zuwa 15yrs ba, kuma tun fitowar su daga makaranta take kuka har suka je asibiti kukan take, har zuwa yanzu kukan take bata daina ba, kanta na k'asa tana wasa da fingers d'inta tana zubar da hawaye, tausayi yarinyar ta bashi dan haka Moli yace " ajinki nawa? Yayi maganar batare daya kalli inda take ba, bata motsa ba tana yadda take ta bashi amsa cikin rawar murya " JSS3, sake kallanta yayi ta cikin mirror kana yace " shekarunki nawa? "Sha hud'u (14yrs) ta bashi amsa, har a lokacin kanta na k'asa tana cigaba da kukan ta, a ransa ya maimaita "sha hud'u, amma harta kamu da hawan jini? "To meye damuwarta haka? yayi maganar cikin ransa, a fili yace " kin san me likita yace yana damunki? D'an murmushi tayi kana tace " nasan bazai wuce hypo tension ba, tayi maganar tana goge hawayen dake k'ara zubo mata, sake kallanta yayi ta cikin mirror cike da mamaki, yace " kin san abinda ke damunki kenan!? "A'a ban sani ba, kawai dai nasan halin danake ciki yakan iya haifar min da hakan, shiru yayi batare dayace komai ba, taci gaba " ainahin cewon dake damuna yana cin zuciya ta, da ruhi na, yana kuma wargaza duk wani farin ciki da walwalata bashi da magani, har gwara hypo tension ma yana da magani, tayi maganar sabon hawaye na zubo mata, bai kuma cewa komai har suka isa makaranta, direct office d'in Sir Jeeb ya wuce yayi masa bayanin abinda ke faruwa a tak'aice, sosai hankalin Sir Jeeb yayi mugun tashi ya kalli Sir Moli yace, "kaga yara kenan ma, ina kuma ga mu manya? Sir Moli yace " al'amarin sai dai addu'a kawai, Sir Jeeb yace " tab yara k'anana na hawan jini lalle zamani ya lallace, Sir Jeeb ya d'an dafa kafad'ar Sir Moli yace " please idan ka samu dama ka kira ta ka bincike ta abinda yake damunta, kodan mu sauke hakk'i, amana da nauyin da iyayen su suka d'ora mana, abinda yasa nace kai ka tambaye ta matsalarta saboda yaran suna jin tsoranka, tana iya sanar dakai damuwarta kai tsaye batare da an sha wahala ba, kodan tsoranka da suke ji, amma idan wani ne sab'anin kai, tana iya yi masa yawo da hankali, ajiyar zuciya Sir Moli yayi, badan yaso ba, dole tasa shi amsawa Sir Jeeb " ok badamuwa i will try my best in sha Allah, amma har ga Allah bai so hakan ba, dan shi a nashi ganin wannan abinda ya shafi rayuwarta da sirrin ta ne, bai kamata a matsa mata akan lalle sai ta fad'i ba, yana ganin hakan kamar takura ce, kuma idan akayi mata an shiga hakk'inta. Area classes ya nufa saboda yana da ajin da zai d'auka a lokacin, a hanya ya hangi Sanah da Khulud na tahowa amma su kwata-kwata basu kula dashi ba, hakan yasa Sanah bangazar sa batare data sani ba, da k'arfi ya hankad'a ta had'i da saurin ja baya, dan kar jikinta ya tab'a nashi, tafiya Sanah tayi taga-taga zata fad'i Khulud tayi saurin tare ta, a hasale ta juyo cike da tsiwa tana shirin zazzage ruwan bala'i, hard'e hannayensa yayi a k'irji yana jiran jin abinda zata ce masa, bisa mamakinsa tana sauke ido a kansa tayi saurin ja da baya, had'i da d'an rusunawa tace " am sorry Sir ban gani ba ne, tayi maganar kanta na k'asa, tsaki yayi mtswwwwww had'i da cewa " fool yayi gaba, bayansa tafi da kallo cike da takaici tace "wicked & stingy man. Tsawa yayi cak a inda yake had'i da juyowa ya zuba mata idansa, Khulud tace " mun shiga uku wallahi yaji abinda kika ce, tayi maganar tana zaro ido waje, kanta ta duk'ar k'asa batare datace komai ba, sai da yad'an d'auki lokaci yana kallanta kafin ya girgiza kansa, ya juya yaci gaba da tafiyarsa, har ya kai bakin k'ofar class d'in dazai shiga ya juyo, aiko karaf suka had'a ido cikin na juna, k'in kawar da idanta tayi shima haka, a hankali ya motsa bakinsa yace " jackass, ido ta rufe tana jin k'onar abin har cikin zuciyarta, Khulud tace " sai mu tafi ko? Tayi maganar tana rik'o hannunta, ba musu ta bita kamar rak'umi da akala, har Sir Moli ya gama koyar da class d'in hankalinsa yana kan kalmar da Sanah ta fad'a masa, bayan an tashi daga class direct masallaci ya wuce yayi sallar zhur, kafin ya wuce office d'insa, ya kwanta akan sofa yana tuna kalmar wicked & stingy man, kai ya girgiza had'i da furta kalmar a fili " wicked & stingy man, a fili yace " yarinya dole ki biya da kanki, yayi maganar yana mik'ewa had'i da had'a kayansa, ya fita daga office ya nufi gida dan kwata-kwata school d'in ma ta fice masa a rai. Su Sanah kam babu abinda ya dame su, hankalinsu kwance suke harkokin su, dan sun san da zai d'au mataki da tun d'azun da akayi abin ya d'auka, bayan sun tashi daga class, sunje maasjid & dinning hall,, Hostel suka nufa, Aunty Halan suka iske tana gyara musu kwana, da sauri suka k'arasa inda take, Khulud tace " kai Aunty maimakon ki bari muzo mu gyara da kan mu? "Lah bakomai ai ku k'annena ne, dan na gyara muku ba fad'uwa nayi ba, nima k'aruwar kai na ce, tunda lada zan samu, murmushi Sanah tayi hannuwanta sark'e a k'irjinta tace " Aunty Halan tun da nake a rayuwa ta ban tab'a ganin mutum mai sauk'in kanki da sanyin zuciya irin ki ba, dariya tayi tace " sai Uludin ki, dan nasan itama zata iyayin fiye da abinda nayi, Sanah tace " kai Aunty Halan ni fa? Tayi maganar cikin shagwab'a tana zumb'uro baki, Halan tace " ai duk ku biyun nake nufi, amma fa idan mutum ya daina zafin rai da tsiwa, dariya Sanah tayi had'i cewa " ai na daina, naji fad'an ku ke da Uludina, Khulud tace " ina fa kika daina tunda yauma kin kuma, " na kuma me? "Ni dai duk abinda nayi aban iya nake ba, kullum nice cikin laifi, Halan tace " hala yauma ta kuma tsokanar tasa? Tayi maganar tana cigaba da gyara kwanar, Sanah tace " au tsokanarsa ma nake yi? "Sosai ma cewar Khulud, Halan tace " ni ina mamakin yadda Sir Moli yake bala'in d'aga miki k'afa haka, abin har d'aure min kai yake, gaskiya kina cin sa'arsa, Allah kuma yana d'ora ki a kansa, dan Sir Moli asalin mugu ne ga bak'ar magana, dan idan ya fad'awa mutum wata maganar wallahi har gwara ya dake ka, Khulud tace " ai jiya taga ni da idanta, ta kuma ji da kunnanta, amma yau tsabar rashin ji ta kuma ce masa wicked & stingy man, ido Halan ta zaro a tsorace tace " ya kuma ji ta? "Sosai ma tunda har juyowa yayi ya kalle ta, dan yama dad'e yana kallan nata, ido Halan ta zuba mata na wani lokaci, sannan ta sauke nannauyen ajiyar zuciya had'i da cewa " Allah ya kyauta, Khulud tace " Amin, cikin sanyin murya Sanah tace " Aunty Halan badai fushi kikayi da ni ba ko? Murmushi Halan tayi had'i da shafa kanta tace " a'a ko d'aya, kawai dai ina tunanin abubuwa da dama ne, ina kuma tausaya miki ranar dazaki shiga hannunsa, dan nasan ranar da kika cika shi, idan ya damk'ek'i kika shiga hannunsa, wallahi sai an tausaya miki sai buzunki, baki Sanah ta zumb'uro had'i da cewa " a tausaya mana dai, Halan zata kuma yin magana Khulud tace " dan Allah Aunty Halan ki kyale ta ki daina wahalar da kanki a banza, Halan tace " wallahi kuwa, ku tashi kuyi wanka dan yau game za'ayi, cikin rashin fahimta suka kalle had'i da cewa " game kuma? "Opss sorry ban sanar daku ba, duk ranar Friday around 4:00pm na yamma lacture akeyi ta addinin musulunci (wa'azi) ,, kamar dai yadda kuka gani jiya anyi, haka duk Saturday & Sunday (weekend), around 4:00pm na yamma game akeyi, kamar su basketball, football, handball & basket ball, ya danganta da ra'ayin mutum, Club d'in da yake so nan zai shiga sai yaje wajen shugabar club d'in ta bashi team & group ta kuma sanya sunansa, baki Sanah ta tab'e kana tace " kuma dole kowanne student sai yayi koda bai ra'ayin yin hakan? Kallanta Halan tayi cike da mamaki dan tunda take bata tab'a ji ko ganin wanda yace baida ra'ayin yin game ba sai Sanah, a ranta tace " wannan wace irin yarinya ce mai shegen iyayi da kwainane? Ta tambayi kanta, taci gaba da gama a cikin ran nata, wannan yarinya da baud'add'en hali take, mijinta ya shiga uku yaga ta kansa, kamar ba yarinya k'arama ba, kwata-kwata bata yin wani abu na yara, sai na manya kamar rainon tsuhuwa kowacce takai 100yrs a duniya, cikin murna Khulud tace " kai amma naji mugun dad'i wallahi, nayi farin ciki, ko ba komai mutum ya motsa jikinsa, Sanah ta kuma tab'e baki, tace " ni dai bazanyi ba gaskiya, Halan tace " aiko dole kiyi dan doka ce mai k'arfi yin game a makarantar nan, Khulud tace " ni dai ko ba doka bace ina son yi, kuma tsarin ya burge ni sosai, Halan tasa su sukayi wanka suka shirya, jikin Khulud sai rawa yake saboda murna da d'oki yayinda oganniya keta kumbure-kumbure ita a dole an takura mata, dan in banda Khulud da dole babu abinda zai kaita wajen wani game, kansewar basu da club & team yasa basu da kayan game, sai yau idan sun zab'a shugabar team d'in zata basu kayan, haka suka fita suka nufi babban filin da aka tanada dan yin wasannin, Khulud nata murna da farin ciki, Oga Sanah kam an sha murr an had'e rai murtuk. Filin wasan ne ya k'ara burge Khulud sosai, fuskarta cike da murmushi ta kalli Halan tace " wooow masha Allah, amma gurin yayi bala'in kyau, an shirya wajen sosai, ga kayan game d'in ma masu kyau, Halan tayi murmushi tana shafa kanta tace " ai sai ma kin fara wasan, zaki ji wani nishad'i na shigar ki tako ina, Halan ta kalli Sanah dake ta ciccin magani, tayi murmushi had'i da cewa " Oganniya wanne wasan zaki yi? Had'a idan da sukayi da Khulud ne yasa ta sakin murmushin dole, tace " anyone ni bani da choice, kowanne ma yi zanyi, Khulud tace " wasa d'aya zamuyi? Sanah ta kalle ta cike da mamaki tace " ke da a tunanin ki daban-danan zamuyi? "Ko kina tunanin wasa zai raba mu ne? "Ai team & club d'aya zamu yi, Khulud tayi murmushi, dama tsokace tasa ta tambayar Sanah, dan ko cewa akayi dole sai an raba musu team sai dai su hak'ura da wasan, amma matuk'ar suna raye babu abinda zai iya raba ta da Sanarta, koya shiga tsakanin su koma meye shi, Khulud tayi maganar cikin ranta, Halan ta kalle su tace " to kunga dai nau'ikan wasan sai ku zab'i wanda yayi muku, Sanah ta kalli Khulud tace " zab'ar mana Ronaldo tayi maganar cikin tsokana, Khulud tace " baki da ra'ayinki ne Ozil? Murmushi Sanah tayi tace " ni fa nace kowanne ma yi zanyi, tunda matsa min akayi dole badan rai na yaso ba, Khulud tace " to ni dai a tunani na Ronaldo & Ozil football suke yi ko? Tayi maganar tana juya idanta, Sanah ta tab'a baki had'i cewa " oho ni na sani, Khulud zatayi magana Halan tayi saurin cewa " na gaji da jiran ku fa, ku zab'a na kai ku, ni ma na wuce nawa team d'in, Sanah tace " Aunty Halan ke wanne wasan kike yi? "Football, ta bata amsa a tak'aice, Khulud tace " to Aunty Hakan wanda kike yi muma shi zamuyi, Halan tace " no ba wai abinda wani yake yi lalle shi zaku yi ba, abinda ran su ke so shi zaku yi, Ku dai na bin san zuciya ko ra'ayin wani, ku zama masu ra'ayin kan ku a koda yaushe kun ji ko? Duka suka amsa da "tom, Hakan ta kuma cewa " to yanzu ku fad'a min wanne kuke so? Khulud tace " muma football d'in muke so, tayi maganar cikin sanyin murya, Halan ta d'an k'ura mata ido had'i da cewa kun tabbata? Kai suka d'aga mata alamar eh, b'angaren da akeyin football d'in ta kai su, dayake itama tana d'aya daga cikin shuwagabannin team d'in, babu wani b'ata lokaci aka yiwa su Khulud duk abinda ya dace, aka basu team & game ware, suka fara wasan, sosai Sanah taji dad'in wasan dan sai yanzu abin ya fara burgeta yana bata sha'awa, ba'a kad'a bell ba sai 6:00pm na yamma, kowacce students ta nufi hostel dan yin alwalar sallar Magrib, dan makarantar ana koyar da yara addini da ibada sosai, cikin farin ciki sosai Sanah take tsalle tana cewa Khulud da Halan, "kai gaskiya tunda nazo makarantar ban tab'a tsintar kai na a farin ciki irin na yau ba, wasan yayi masifar burge ni, naji dad'in wasan sosai, tayi maganar tana dariya cike da annushuwa. Ranar Monday tunda sassafe suka shirya suka nufi assembly, dan tsoran kar Sir Moli ya tare su dan har yau bai tab'a tare su a late comers ba, bayan an tashi daga class Sir Moli na office d'insa, Sir Jeeb ya shigo, hannu Jeeb ya mik'ewa Moli suka gaisa, bayan sun gama gaisawa ne Sir Jeeb yace " ka tambayi yarinyar nan abin da ke damunta kuwa? Shaf Sir Moli yama manta da maganar kwata-kwata dayake shi ba mai damuwa da harkokin jama'a bane, kai ya dafe yana cewa " oh! na shafa'a ne, amma kayi hak'uri bari na tura a kira ta yanzu, murmushi Sir Jeeb yayi kana yace " ok badamuwa dama mahaifinta ne ya kira ni shiyasa nima na tuna, yayi maganar yana niyyar fita, Moli yayi saurin cewa " yama sunanta? "SIYAH ya bashi amsa, "ok bari na aika a kira ta yanzu yayi maganar yana k'ok'arin fita, Jeeb yace " no ka zauna bari zansa a kira maka ita, "nagode, Moli yace. Yana daga kwance akan sofa idanuwansa a rufe, tayi sallama daga bakin k'ofar office d'in, a dak'ile ya amsa, tare da bata izinin shigowa, a hankali ta shigo ta durk'usa cikin nutsu ta gaidashi, ciki-ciki ya amsa gaisuwar, murmushi tayi dan idan da sabo sun saba da halin sa, har a lokacin idansa a rufe yake, a k'alla takai wajen 5 minutes batare daya ko motsa ba balle yayi mata magana, cikin sanyin murya tace " cewa akayi kana kira na, tayi maganar kanta a k'asa,, shi ko rasa ta inda zai fara tambayarta abinda ke damunta yayi, shiyasa yayi shiru baice komai ba, a hankali ya mik'e ya zauna, gami da zuba mata ido, ganin yadda take sissine kanta cikin hijab yasa cewa " munafuka, a cikin ransa, a hankali yace " ke!, ta d'ago idanta karaf idansu suka sark'e cikin na juna, tayi saurin kawar da idanta, ya cigaba da magana " Vice Principal ne yace na kira na tambaye abinda yake damunki, a hankali ta d'ago kai ta kuma kallansa, ganin ita yake kallo yasata saurin duk'ar da kanta, ganin tayi shiru bata ce komai ba yasa shi cewa " ke nake jira fa, wasu zafafan siraran hawaye ne suka shiga zubo mata, tasa hannu tana gogewa amma still k'ara zubo mata suke yi, d'an guntun tsaki yayi kana yace " ke ni fa ba kuka na kira kiyi min ba, idan kuka zakiyi tashi ki fitar min daga office yayi magana a d'an zafafe, d'ago idanta tayi da suka gama rinewa ta zuba masa su, tsaki ya kuma gami da mik'ewa yana shirin barin office d'in, har ya kai bakin k'ofa yaji tace " zan fad'a maka damuwa ta, saboda kai ne wanda yafi kowa cancanta daya san halin dake ciki, a hannunka maganin cutar dake damun ruhi da zuciya ta yake, amma da farko kayi min alk'awarin babu wanda zaka sanarwa, tayi maganar cikin sanyin murya, tsayawa yayi cak yana mamakin kalamanta, cikin ransa yace " ni ne wanda maganin cutar ta ke hannunsa kamar ya? "Ni ne wanda yafi kowa cancanta yasan halin data ciki akan wanne dalili? " Me hakan yake nufi? Yayi maganar cikin ransa......... MOMYN ZARAH _*RASHIN SANI.......*_ *HAUWA A USMAN* _JIDDARH_ ```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh``` 6⃣ Ido ya k'ura mata na tsayin lokaci kafin yace " ina jinki, cikin rawar murya tace " ka zauna, ba musu Sir Moli ya koma kan sofa ya zauna, ya karkata gaba d'aya hankali da nutsuwarsa gare ta, yana sauraren abinda zata ce masa, hawayenta ta kuma gogewa tare da d'ago kanta a hankali ta zuba masa ido, cikin muryar kuka tace " ba ni da matsalar komai a rayuwa ta, tun daga kan ci da sha, da kuma gata, duk ina dasu, bansan wata matsalar rayuwa ba sai a wannan shekarar da k'addara ta, ta soma, mahaifana nayi min mugun so kasancewar mu uku suka haifa a duniya, biyun duk maza ne ni kad'ai ce mace, hakan ne yasa iyaye na suka d'auki so da k'auna had'i da duk wani burin duniya suka d'ora a kai na, iyaye na ba talakawa bane, mahaifina yana da kud'i sosai, shekarar sa takwas (8yrs) yana d'an majalisar tarayya, kuma.......... Katseta yayi ta hanyar d'aga mata hannu yace " ni duk ban tambaye ki wannan ba, abinda na tambaye shine meye damuwar data haifar miki da hawan jini? Yayi maganar cike da k'osawa, murmushin gefen baki tayi gami da jefa idanta cikin nashi, kai tsaye tace " SOYAYYA ita ce damuwa ta, cikin mamaki ya kalle ta gami da cewa " what!? "Wai kina nufin so shine silar gamuwa da cutarki? Ya tambaye a k'agauce, murmushi ta kuma yi kana tace " eh, so shine ya jefa ni cikin mawuyacin halin danake ciki, ina san mutumin da bai ma san ina yi ba, bai san a wane hali nake ba, bana kuma san sanar dashi ina san shi da kai na, saboda bana san zubar da mutunci da k'ima, had'i da darajar da Allah yayi man a matsayi na, na d'iya mace, tasa hannu ta goge hawayen dake zubowa daga idanuwanta, cike da tausayawa halin datake ciki yace " waye shi wanda kike san? D'ago kai tayi tana kallan sa eyeball to eyeball, ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi tare da cewa " KAI NE WANDA NAKE SO, wata mahaukaciyar zabura Moli yayi gami da mik'ewa a tsorace, "what!? Ya furta a zafafe, kana yaci gaba " ke ni abokin wasan ki ne? "Ko kinga nayi miki kama da wanda ban san me nake yi ba? D'an shiru yayi yana yarfa hannu kana yace " ni zaki rainawa hankali? Yayi maganar yana nuna kansa, fashewa da kuka Siyah tayi tana cewa " wallahi Allah da gaske nake maka, KAI KAD'AI NE DAMUWA TA, kai me wanda tunda na d'ora ido na a kansa na haukace a san sa, tun daga kallo d'aya a kuma ranar farko, kai ne farkon wanda na fara so a rayuwa ta, a kanka ne na fara sanin meye so, na kuma fara sanin zafi, k'unci da bala'in so, akan ka nasha kwana na yini da yunwa, sanka ya sha hana ni bacci da walwala, sanka ne yaja na zama kamar mahaukaciya, dan Allah ka taimake ni kayi min gurbi a zuciyarka. "Ka taimake ni ka so ni, ko da kwatankwacin irin san da nake yi maka ne, ka taimaki rayuwa ta, ka cece ni daga fad'awa halaka da musiba, kai kad'ai zan so har k'arshen rayuwa ta, kai kad'ai zan iya mallakawa zuciya ta, kai ne kad'ai wanda nake iya gani nayi murmushi da dariya, koda ina cikin matsanancin k'unci, kai kad'ai nake gani naji ni cikin farin ciki da walwala, ko da ina cikin damuwa da b'acin rai, kai me hasske na, kai ne ji da gani na, idan babu kai babu ni, wallahi idan kace baka so na mutuwa zanyi, dan nasan k'arshen numfashi da rayuwa ta sun zo, ta k'arasa maganar cikin matsanancin kuka mai k'ona zuciya. Ido kawai Moli ya zuba mata cike da tsantsar mamakinta,, a hankali ta rarrafo ta rik'e k'afarsa, gami daci gaba da magana cikin kuka, " ka dubi girman Allah ka so ni, ka tausayawa rayuwata, wallahi ina cikin mawuyacin hali, halin da a koyaushe jiran mutuwa ta nake yi, INA SANKA, dan Allah kai ma ka so ni, ta k'arasa maganar cikin mahaukacin kuka had'i da kifa kanta akan k'afarsa, please Sir Moli ka tausayin ka ceci rayuwa ta, I really love you more & more much, wallahi kai ne rayuwa ta, dan girman ka so ni, ta k'ara fashewa da kuka tana rik'e k'afarsa. Da sauri ya ja baya had'i da zuba mata ido kawai batare daya iya furta koda kalma d'aya ba, ganin tana k'ara rarrafowa gare shi ne, yasa shi daka mata gigitacciyar tsawa " ke!!! dalla tsaya anan, amma ina bata ma san yayi ba, dan ta gama makancewa idanta ya rufe ruf, cigaba da nufarsa tayi, a hasale ya kuma ja baya tare da cewa karki kuskura kizo inda nake, bama ta saurare shi ba harta k'arasa inda yake ta kuma mik'a hannu zata rik'o k'afarsa,, cikin b'acin rai yayi ball da ita, ta fad'a ta baya kanta ya bugi bango, kanta fashe jini ya fara zuba, kwata-kwata bata damu da ciwon data ji ba, dan bama tasan taji ciwon ba, cikin kuka tace " dan girman Allah kayi min gurbi a zuciyarka, wallahi idan kace a'a mutuwa zanyi, please ta had'e hannayenta biyu tana rok'onsa. Shiru kawai yayi yana kallan ikon Allah, yarinya k'arama har ta san so? Ta san ta haukace akan son d'a namiji haka? Mik'ewa ta tayi ta nufe ta shi kanta na zubar da jini, amma kwata-kwata bata damu da yadda jinin ke zuba daga jikin nata ba, tana zuwa kusa dashi ta fad'a jikinsa ta rungume shi gami da k'ara saka kuka, cikin matsanancin b'acin rai da zafin zuciya, Moli yayi wurgi da ita gefe, kanta ya kuma bugar bango k'ummm, goshinta ya kuma fashewa, a haukace ta taso tana sake k'ok'arin rungume shi, wasu kyawawan marika ya shiga zuba mata a jere har guda shida 6, had'i dayin ball da ita yayi mata k'afa a bayanta, ta fad'a kan table d'in dake tsakiyar office, cikinta ya bugu sosai, ta sulale k'asa cikin mawuyacin hali, a kanta ya tsaya yana kallanta cike da tsantsar tsana yace, "ni kuma bana sanki, na tsane ki, ban zan tab'a sanki ba, bazan kuma tab'a jin ina sanki ba daga nan har k'arshen rayuwa ta, wallahi ko mata sun k'are a duniya babu abinda zanyi dake, shegiya 'yar iska fasik'a, kina shiga jikin nawa zaki ce naso ki? "Nasan iya adadin mazan da kika yiwa haka, kenan 'yar k'aramar yarinya dake har kin san so? Kina da 14yrs kin san ki d'orwa kanki cuta mai girma akan d'a namiji, to ki bud'e kunnenki da kyau ki saurare ni da idan basira,, ni Moli bana sanki, bazan tab'a sanki ba, bazan kuma aure ki, da in aure ki gwara na mutu banyi aure ba, useless girl kawai, k'ananan yara daku amma kun san ku so maza, shegu, jakai, k'idahumai, lusaran banza, Allah ya tsare ni da aure ki, ko laifi nayiwa Allah ya hukunta ni da sonki ko aurarki nasan nayi laifi mafi girman gaske. Murmushin bak'in ciki tayi cike da takaicin zuciyarta na fad'awa san wanda bai san daraja da mutuncin d'an Adam kwata-kwata ba, ta kalle shi ido cikin ido tace " bakomai nagode matuk'a, amma ka jira sakayyar Allah,, a bisa wulak'anci da cin zarafin daka yi min akan abinda bani da d'orawa kai na ba, nima da ina da yadda zanyi da tuni nayiwa kai na magani, amma in sha Allah kai ma sai Allah ya d'and'ana maka irin ciwon danake ji, sai Allah ya jarrabeka da soyayya mai rad'ad'i da zafin gaske fiye da yadda nake ciki, in sha Allah kai ma bazaka tab'a samun macen dake so ba, bazaka tab'a mallakarta a matsayin mata ba, kuma in Allah ya yarda akan idanka kana ji kana gani za'a raba ka da ita, bawai kuma dan an fi k'arfin ka ba, sai dan Allah ya d'and'ana maka zafin rabuwa da masoyi da abinda zuciya ke so, take mararin samu, kamar yadda nima naji, da k'unar rashin mallakar masoyi, kai ma sai kayi zafin rabuwa da abinda zuciya ke so, da yarda Allah sai kayi kuka akan so, kamar yadda nima nayi, sai ka rasa tausayawar kowa, kamar yadda nima na rasa tausayawa daga gareka, in sha Allah sai kayi son maso wani, sai soyayya ta gwara kanka, ta wahalar dakai da wannan bak'ar zuciyar taka, sai ka d'and'ani zafin rabuwa da masoyi, ka d'anani zafin da ake ji idan ka cewa mutum kana sanshi yace maka baya sanka, In Allah ya yarda sai mace ta kalli tsabar idan ka tace maka bata sanka, bayan ka sanar da ita kana santa, sai an wulak'anta ka an k'ask'antar dakai, daga lokacin ne zaka fuskanci meye rayuwa, meye duniya, ina mai tausayawa rayuwarka a lokacin. Kum......... Saukar gigitattun marikan, dataji ne ya hanata k'arasa maganarta, tassssssss kauuuuuuu ya fara janta a k'asa, saboda magaganun data fad'a masa,, sun kawo shi har wuya, zuciyarsa ta hasala iya hasala, jin k'irjinsa yake kamar zai kama da wuta saboda tsananin b'acin rai, duk ilahirin jikinsa kerrrma yake, yana tsuma, yayinda gumi keto masa yake tako'ina, mak'ogwaransa nayi masa zafi, yawon bakinsa nayi masa d'aci, a k'asa ya fara janta yana nufar k'ofar fita daga staff room, dai-dai lokacin Sanah da Khulud sunzo shigowa staffroom, ganin yadda gaba d'aya kamanninsa suka sauya ne yasa Sanah da Khulud saurin ja da baya, idanuwansa sun koma pure red, a haukace ya fara dukan ta ba ji ba gani, ganin yadda yake dukan ta ga jini na fita daga jikinta yasa Sanah da Khulud rud'ewa jikinsu ya d'auki muguwar kerrrma, dan duk iskancin Sanah bata san abinda zai tab'a lafiyarsa, sosai Moli yake ball da ita yana surfa mata ruwan ashar, sosai tsoro yayi bala'in kama su Sanah, har Khulud ta saki fitsari a wando batare data sani ba, itako Sanah saboda tsabar rud'ewa hannu ta d'ora aka had'i da fasa kuka, daga Sanah har Khulud duk sun rud'e matuk'a sun fita daga hayyacinsu. Da sauri Malamai suka taso suka rik'e shi, dakyar suka iya kwatar Siyah daga hannunsa, komawa yayi ya zauna akan step d'in shiga staffroom gami da dafe kansa da duka hannayensa, kasancewar Sanah bata cikin hayyacinta yasa har lokacin kuka take jikinta na b'ari, Khulud kam saboda tsabar tsoratar data yi ma kasa kukan tayi ita, sai jikinta dake kerrrma, fitsarin datayi duk ya b'ata mata kaya, kukan Sanah ne ya fara hawar mishi kai, a hankali ya d'ago red eyes d'insa ya kalli inda yake jiyo kukan, karaf idansu suka sark'e cikin na juna shi da Sanah, ganin yadda idanuwansa suka koma red ya k'ara tsorata Sanah, tsawa ya daka mata " shut up, ai tun kan ya k'arasa Sanah da Khulud suka zunduma a guje, basu tsaya a ko'ina ba sai a hostel d'in su, cikin kwanar su, Halan na kwance suka shigo da gudu, duk sun firgice sun fita daga hankalin su, "Lafiya na ganku haka? Cewar Halan, magana suke san suyi mata amma dukkan su sun kasa koda furta kalma d'aya ce, kama su tayi ta zaunar dasu, sannan ta mik'e ta d'auko pure water ta mik'a musu da sauri suka amsa, jiki nata b'ari suka sha, sai da ta bari a k'alla sunyi 15 minutes, ta zabbatar sun dawo cikin hayyacinsu, nutsuwar su ta dawo normal kana ta kuma tambayarsu, "wai me ya faru na ganku kun dawo a kid'ime, kamar wad'anda suka ga mutuwa? Cikin kid'ima Sanah tace " Sir Moli ne zai kashe wata, ido Halan ta zaro cike da tsoro, tace " ince dai baku mishi komai ba ko? Cikin rawar murya Sanah tace " ai har abada babu abinda zamuyi mishi, Halan ta tuntse da dariya tana cewa " tab yau Sir Moli ya furgita wasu, ashe fa baku tab'a ganin b'acin ransa ba ko? "Baku tab'a ganin yana duka ba ne shiyasa wannan ya d'aga muku hankali, ai duk wacce ta sake ta kawo mishi wurgi ko ta shiga track d'insa, ta kad'e daga ita har buzunta, dan kwata-kwata bashi da tausayi idan ranshi ya b'aci, bak'ar zuciya ce dashi, wannan dalilin me yasa nake matuk'ar mamakin yadda kike masa abubuwa da dama, amma yake sharewa yana d'aga miki legs ta k'arasa maganar tana dariya, Khulud da har yanzu jikinta ke kerrrma yake saboda tsananin tsoro da firgici, tace " yanzu Aunty muma zai iya yi mana irin wannan mugun dukan? "Ku a wa da idan kuka cika shi zai kasa jibgar ku? Tsoro ne ya k'ara mugun kama su, cikin rawar murya Sanah tace " ai bama zamu cika shin ba, in sha Allah daga yau na daina yi mishi duk abinda nake yi, bazan k'ara yi masa fitsara da rashin kunya ba, daga yau duk abinda yace nayi zanyi, bazan kuma yi mishi musu da rawar kai ba, wai idan mu yayiwa wannan jahilin dukan ai mutuwa zamuyi, Khulud da jikinta har lokacin kerrrma yake ta kasa cewa komai sai ido kawai datake bin Sanah dashi, cikin sanyin murya Khulud tace " Allah Aunty Halan sai yayi mana irin wannan dukan? Halan tace " wallahi har fiye da haka ma yana iya yi muku, muddin kuka kai shi bango, hak'urin dayake yi a kanku ya k'are, dan idan ransa ya b'aci, idansa rufewa yake yi ruf, bashi d..... fitsarin data gani a jikin Khulud ne ya hana ta k'arasa fad'ar abinda tayi niyya, ta kalle ta cike da mamaki tace "Khulud fitsari kikayi? Da sauri Khulud ta kalli jikinta, dan ita bama tasan tayi fitsarin ba, Sanah ta kalle ta cike da mamaki tace " Uludi na ya haka? Khulud tace " wallahi ni bamma san nayi ba, tayi maganar cikin sanyin murya, Sanah da Halan suka saka mata dariya, haushin dariya da suke yi mata yasa ta fashew da kuka, Sanah tayi saurin mik'ewa taje inda take tsaye ta rungume ta, tana cewa " yi hak'uri Uludina, ni ce ko? "Na dai na ban k'arawa, muje na rakaki kiyi wanka, kuma mun b'ata da Aunty Halan bamu kuma yi mata magana. Hakan tayi dariya tace " Auntyn guda za'a daina yiwa magana? "Anya kuwa Auntyn ce? Basu bata amsa ba suka yi hanyar Bathroom suna dariya, Siyah bayan Malamai sun kwace ta dakyar a hannun Moli, zubewa tayi a k'asa had'i da fasa fininannan kukan bak'in ciki, bawai kukan dukan da Moli yayi mata take ba, kuka takaicin zuciyarta take yi, da har yanzu tak'i ganin koda laifin Moli ne, balle ta rage ko ta daina san shi, sai da tayi mai isarta sannan ta mik'e, ta zuba mishi ido tana kallansa, tare da cewa " ita zuciya bata san rashin cancanta ko cancantar abinda ya kamata koya dace da ita ba, haka k'unci da k'untatawa, muzantawa, wulak'anci, duk basa hana ta cigaba da san abinda take so, wallahi nasan koda zaka rink'a kashe ni a kullum ina dawowa, zuciya ta bazata tab'a koda rage kad'an daga cikin azababban son da take maka ba, harta juya zata tafi, ta kuma juyowa tace " ka sani Siyah nayi maka mugun mahaukacin so, kuma zata cigaba dayi maka wannan son har k'arshen rayuwarta, nayiwa kai na alk'awarin matuk'ar bakai zan aura ba, babu ni babu yin aure har abada, idanko har zanyi aure a duniya to ka tabbatar da kai ne wanda zan aura, idan ba kai bane wallahi Allah bazan tab'a yin aure ba, har abada har in koma ga mahalicci na, zan kasance mai jiranka a koyaushe, a wanne lokaci na rayuwa ta da fitar numfashi na, kowanne hours, minutes & seconds, zan kasance mai dakon jirank..... A harzuke Moli ya nufe ta.... MOMYN ZARAH _*RASHIN SANI.......*_ *HAUWA A USMAN* _JIDDARH_ ```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh``` 7⃣ Da sauri Malaman suka kuma tare shi, d'aya daga cikin Malaman ne ya buga mata tsawa "oya get loose, da sauri tabar wajen jikinta na kerrrma, dan yadda Moli ya taso ba k'aramin tsotsata ta yayi ba, a harzuk'e Moli ya koma office d'insa, ya zauna akan sofa gami da rafka uban tagumi yana tanani, ji yayi gaba d'aya duniyar tayi masa bak'in k'irin komai ya fita a ransa, ya kuma fara jin haushin kansa, dan gani yake kamar rai ni ne yasa Siyah yi mishi haka, ransa a matuk'ar b'ace ya mik'e ya rufe office d'in ya fita ya bar makarantar gaba d'aya, kalaman da Siyah tayi na k'arshe su suka bawa sauran malaman damar fahimtar abinda ya faru, a tsakanin su, Sir Jeeb shiru kawai yayi yana nazarin abubuwa da dama, shi yanzu yaran ma sun fara bashi tsoro, duba da abinda ya faru da Siyah, wato dai idan ya fahimta son Moli take yi, kuma hakan ne ya haifar mata da hawan jini, a fili Jeeb ya furta "Ya Salam. Kwance yake a kan k'atuwar katifarsa, daga shi sai boxer, gaba d'aya duniyar tayi masa zafi, k'irjinsa sai tafasa yake yi yayinda zuciyar keyi masa k'una, a hankali ya runtse idanuwansa, yana tuna abubuwan da suka faru, gami da kalaman Siyah, guntun murmushi yayi, bayan ya tuna wai sai yayi kuka akan soyayya, sai ya durk'usawa mace, kuma sai ya ruk'i a soshi, a fili yace " God forbid, ni har akwai macen data isa nayi duk wannan abin akan ta? "Ina babu ita, dan ko uwarta ma ba'a haifa ba, tsoki yaja mtsssssss had'i da cewa " shegiya banlagaza, tsoki ya kuma ja lokacin daya tuno rungumshin datayi, yana bin jikinsa da kallan k'ama , "yar iska ya fad'a yana furza iskar saman leb'ensa, tunowa da su Sanah yayi da yadda tsoro yasa Khulud sakin gitsari a wando, da yadda yaga idan Sanah, ya tuna yadda take kuka jikinsu na kerrmar tsoro duk sun furgice, dariya yayi tare da cewa " k'aramar 'yar iska, shegiya mara kunyar k'arya, ashe iya nan fitsarar taki ta tsaya yayi maganar yana dariya. Washe gari da kamar bazai zo office ba, amma kasancewar ya tashi yaji shi so fresh babu wani abinda ke damunsa, ya sashi shiryawa ya tafi makarantar, bayan ya shiga staff yayi signing, ya fito ya nufi area classes, daga bakin Hostel get ya hangi su Sanah na tahowa, agogon hannunsa ya duba yaga 8:40am na safe, komawa yayi ya tsaya had'i da sark'e hannunsa, Khulud ce ta fara hango shi tsaye ya kafe su da ido, ai cikin tashin hankali ta tab'a Sanah, ganin yadda hankalin Khulud yayi masifar tashi lokaci d'aya yasa Sanah cewa, "Ulud lafiya naga duk kin birkice? Kasa magana Khulud tayi saboda yadda Moli ya kafe su da ido, sai da hannun ta shiga nunawa Sanah Moli, rolling idanuwanta tayi kana ta kalli inda Khulud ke nuna mata, karaf idanuwansu suka sark'e cikin na juna, saboda tsabar tashin hankali da firgicin da Sanah ta shiga baya tayi zata fad'i, da sauri Khulud ta tare ta cikin k'arfin hali tace " my Sanah ki kula karki ji ciwo, Sanah tace " please tayani duba gaban mu, kamar Sir Moli nake gani ko? "Ba kama bace shine, cewar Khulud tana k'ifk'ifta idon tsoro, k'irji Sanah ta dafe had'i da cewa " wayyo yau mun shiga uku, Khulud tayi kiyi shiru please kar yayi tunanin ko wani mugun abun muke cewa a kansa, d'if Sanah ta d'auke wuta jin abinda Khulud tace, har suka k'arasa wajensa, kansu a k'asa suna k'ok'arin wuce shi, tsawa ya daka musu kana cikin fad'a yace, " ke dan uban ku zo nan, sumi-sumi suka nufi inda yake tsaye kan su duk'e, bisa mamakin Moli yaga Sanah tayi saurin duk'awa bisa gwiwowinta, duk ilahirin jikin su kerrrrma yake, ganin yadda jikinsu ke kerrma cike da tsoro ne ya kusa bashi dariya, amma dayake muskili ne sai ya dake ya k'ara had'e ransa murtuk, "ku dan uwarku yanzu ne lokacin zuwa class? Cikin rawar murya Sanah tace " we are sorry Sir, "cewa nayi yanzu ne lokacin fitowa class? Ba hak'uri nace ki ba ni ba, amsa nake so, yayi maganar a tsawa ce, jikin Khulud na kerrrma tace " a'a, ba yanzu bane, "ok wato iskanci da fitsara ce tasa ku k'in fitowa da wuri kenan? Muryar Sanah na rawa tace " a'a ba haka bane, wallahi muna fitowa akan lokaci, yaune rana ta farko da muka tab'a zuwa class late, tabbas Moli yasan basa makara dan bai tab'a tare su a cikin late comers ba, "uban me tsaida daku yau? Khulud tace " school bag d'ina na manta shine muka koma muka d'auko, "lalle baki d'auki karatun da mahimmanci ba tunda har kike manta school bag kacokan a hostel, shiru sukayi babu wanda yace wani abu, yaja dogon tsoki mtswwwww bastard girls, yayi maganar yana wucewa, ajiyar zuciya suka sauke da k'arfi, Sanah tace " Allah yayi mana gyad'ar doguwa, Khulud tace " yau dai Allah ya kub'utar da mu, waigowa yayi yaga har lokacin suna inda ya barsu a durk'ushe, tsawa yayi musu a fusace " dan uban ku bazaku shiga class ba? Tun kafin ya gama rufe bakinsa sun kwasa a guje sunyi cikin class, sai da ya gama koyar da duk classes d'insa kana ya koma staff, office d'insa ya wuce direct ya kwanta akan sofa, bai dad'e da shigowa ba Sanah ta shigo, staff d'in d'iban chock, jin taku ya sashi bud'e idansa dayake a lumshe, ganin Sanah na sand'a a hankali yasa shi mik'ewa ya fita a hankali dan yaga me zata yi, lek'awa ta fara yi ta window taga ba kowa a staff d'in, kowanne malami yana class, ganin haka yasa Sanah sakinF tsoki, ta shiga staff d'in kai tsaye da takalmi, har ta d'ebo chock d'in zata fito, idanta ya sauka akan hular Sir Moli, dashi kansa ya manta da ita, daya shigo da safe d'azu gaisawa da sauran Malamai ne ya manta ta, komawa tayi ta aje chock d'in, akan table kana ta d'auki hular ta saka a kanta, zuruf hular ta shige, "wai wannan mutumin badai ra'asun ba, ashe k'aton kai gare shi yake yiwa mutane d'agawar banza, saita hular tayi akanta sosai kana ta tsaya yadda yake tsayawa, had'i da hard'e hannayenta a k'irjinta kamar yadda yake yi, ta kwaikwayi maganarsa tace " ku 'yan daba ne? Ta kuma gyara tsaiwar sosai taci gaba " ku yanzu ne lokacin fitowa class? Tayi maganar tana duba hannunta kamar yadda yayi a lokacin, duk abinda Sanah keyi Sir Moli na bayanta yana kallan ikon Allah, tuntsewa tayi da dariya sosai ja'irin yaro mai girman kai da fad'in rai, ta kuma gyara zaman hular akanta, ta saka dariya , tana cikin dariyar ta d'ago kai, aiko d'ago kan da zatayi karaf sai cikin nashi, a fili Sanah ta furta " innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, iya rud'ewa da firgice Sanah ta shige shi, hankalin ta yayi mak'urar tashi, tsoro yayi masifar kamata, lokaci d'aya duk ilahirin jikinta ya d'auki kerrrrma, ganin babu sarki sai Allah yasa Sanah fara kuka, tana ja baya zata cire hular kanta. Sosai Sanah take kuka kamar ranta zai fita shiko yayi shiru gami da tsura mata ido batare dayace komai ba, durk'usawa Sanah tayi a k'asa bisa gwiwowinta ta shiga bashi hak'uri had'i da rok'onsa tana kuka, "dan Allah kayi hak'uri ban k'arawa, Allah yauma tsautaayi da k'addara ne, ka tausaya min idan ka dake ni mutuwa zanyi, baya ya ja a hankali had'i da cewa kina so na kyaleki? Da sauri Sanah ta d'aga kai had'i da cewa "eh, "to sai kin maimaita duk abinda kikayi da abinda kika fad'a kana na rabu dake ki fita salin alin, ido Sanah ta zazzaro waje cikin tashin hankali, yace " eh, inba haka ba sai nayi miki irin dukan da kikaga nayiwa Siyah, ai Sanah najin yace zayyi mata irin dukan da yayiwa Siyah tsoro ya k'ara kamata, kerrrmar jikinta ta k'aru, jikinta na rawa ta d'auki hular ta mayar kanta ta gyara tsayiwarta, ya kalle ta yace " oh! dama haka nake tsaiwa? Tayi shiru, yace "cigaba, hannayenta da sark'e a k'irjinta, yace " uhnnn ashe haka nake yi? "Dama k'are min kallo kike yi? "Duk abinda nake yi idanki na kai na ashe ni ban san sani ba, kanta ta duk'ar k'asa, tana kuka, yace " cigaba, jikita na kerrrma ta soma maimaita duk abinda tayi, da tazo wajen data ce ja'irin yaro sai tayi shiru, ta sunkuyar da kanta, yace "cigaba mana ke nake jira, cikin sanyin murya tace " dan girman Allah kayi hak'uri, yace " ashe rashin kunyar taki babbace? Da ina tunanin k'arama ce ashe ta wuce tunani da sani na, tun da harta kai daki d'auki suturar Malaminki ki saka kina kwaikwayonsa, yanzu Sanah ni kike kira da ja'irin yaro? "Fitsarar ki har ta haka? "Gaskiya duk da ban san daga irin gidan da kina fito ba, nasan gidan ku babu tarbiya, babu ganin girman na sama, babu bawa babba daraja da k'imarsa, saboda charity's begin at home, tarbiyya tana farawa ne daga gida, idan kana san sanin hali da tarbiyyar gida, Bahaushe yace ka kalli d'an gidan, gaskiya iyayenki sun cuce ki da suka kasa baki ingantacciyar tarbiyya, duk mijin daya aureki ya shiga uku yaga ta kansa, mijinki ya banu, yana shirin ganin ikon Allah, dan nasan sai ya kwana yana la'antar iyayenki, kukan bak'in ciki da takaicin cin fuskar da Moli yake yiwa iyayenta da ahalinta kawai take yi, dan da wad'annan maganganun har kwara ya kashe ta, amma k'iri-k'iri ba kunya babu kara da kawaici yana jefan iyayenta da munanan maganganu, kodan ba laifin shi bane laifinta ne data zama d'an kuka, mai jawa uwarsa jefa, sosai Moli ya zage ya rink'a gasawa Sanah maganganu masu zafi san ranshi, har ya gaji, sai da ya gama kana ya kalle ta yace " jeki kira min Era, yanzu, jikinta a sanyaye ta fita, yabita da kallo, bata jima ba suka dawo tare da Era, a office d'insa suka iske shi kwance, idansa rufe, batare daya bud'e ido ba, yace " kije da yarinyar nan ki bata hora mai tsanani, cike da mamaki Era ta kalle shi, ta kalli Sanah dake duk'e sunkuye da kai, bai bud'e idan ba, yace " ba magana nake yi miki ba? Jiki na rawa Era tace " ok Sir, I will by God grace, tayi maganar tana mik'ewa cikin murna da matsanannacin farin ciki, saboda tsabar murna jikin Era har rawa yake, dan tasan dole zata fanshe abinda Sanah tayi mata, itace mutum ta farko data fara karya mata alk'adari, ta zubar mata da mutunci, dan da a baya har mate d'inta tsorarta suke ji, amma banda yanzu, dan haka take ganin kamar wannan wata dama ce da Allah ya kawo mata, da zatayi amfani da ita wajen dawo da martabarta data rasa, ta kuma ganawa Sanah azaba mai matuk'ar rad'ad'i,, jikin Sanah a sanyaye ta mik'e babu wani alamar tashin hankali ko tsorata a tattare da ita, har sun kai bakin k'ofa suka ji yace " karki sake ki tab'a lafiyarta, dan bance ki dake ta ba, kuma duk huran da zaki ba ta iya nayau ne kad'ai, daga yau naji kin kuma bata huro...... shiru yayi had'i da cije leb'ensa na k'asa, jikin Era a sanyaye ta fita dan ba haka taso ba, shi kuma dama yace Era ne dan yasan har yanzu da haushin Sanah a ranta yasan zata bata bak'ar wuya. Direct toilet Era ta wuce da Sanah ta kalle ta a Wulak'ance, tace " na baki nan da 15 minutes ki tabbatar kin wanke su tass, Sanah ta kalli Era tace " to ruwa da omo fa? Hannu ta d'aga da niyyar kifawa Sanah mari, Sanah tayi saurin rik'e hannunta, had'i da cewa " la la ina tunanin a cikin jerin horon babu duka ko? "Kuma in ba mantawa nayi ba kamar har kashedi yayi miki akan karki sake ki tab'a lafiya ta ko? Tayi maganar idanta tarr cikin na Era, had'i da yarfar da hannun Era da k'arfi gefe, a fusace Era ta juya zata tafi Sanah tayi saurin cewa " bafa ki ban ruwa da omo ba, dan haka kina iya dawowa ki ta tadda so yadda kika barsu, kamar Era bazata jiyo ba, sai kuma ta tuni da halin Sir Moli, dakyar Era tace " ruwa yana famfo, omo kuma kiyi amfani da toka, duk abinda ke faruwa tsakanin Sanah da Era Moli na kallan su ta window, kai ya girgiza had'i da cewa " majahulil hali. _ni ko nace kamar dai yadda tace maka itama_ Kallan tazarar dake tsakanin toilet d'in da famfon tayi, taga tazarar rayi ta rabin 1km, kuma kowanne toilet zai ci ruwa bucket 10, ga toilet d'in a k'alla sun kai 50, ajiyar zuciya ta sauke kana ta d'auki bucket ta nufi tanker, har aka tashi daga class Sanah bata gama wanke toilets d'in ba, sai kusan 3:00pm na rana kana ta gama wanke su, Khulud na can tana ta bulayin neman Sanah, lungu da sak'o amma ta rasata, hankali tashe taje wajen Halan ta sanar da ita halin da ake ciki, itama hankalinta yayi masifar tashi matuk'a, Halan ta kalli Khulud tace " ina tace miki zata je? Khulud tace " Uncle d'in mu ne ya aike ta staff d'iban chock tun daga nan ne nata dawo ba, cikin kid'ima Halan tace " Allah dai yasa ba wani abun ta kuma yiwa Sir Moli ba, ido Khulud ta zaro a tsoro ce, tare da cewa " please Aunty muje mu gani to, ba musu Halan ta zari hijab suka fita, staff suka shiga suka duba amma babu ita babu alamarta, Halan tace " zo mu zagaya ta bayan staff mu gani ko tana nan, aiko suna zagayawa Khulud ta hango ta zaune kan bucket, tana 'yan wak'e-wak'enta na fitsara tana yiwa Era habaici cikin wak'ar, da sauri Khulud ta nufe ta tana cewa " lafiya meya faru my Sanah? Halan ma da sauri ta nufe ta, suka shiga tambayarta abinda ya faru, bata b'oye musu komai ba, ta fad'a musu duk abinda ya faru, tun daga farko har k'arshe, kuka Khulud ta saka tana cewa " dama sai da nace miki ki fita harkar mutumin nan amma kika k'i ai ga irinta nan, Sanah tace " kinga tunda akayi abin nan hankali na a kwance yake, amma yanzu kinzo zaki d'aga min hankali da kukan ki, Khulud zatayi magana Eta ta k'araso wajen tana hura hanci, da sauri Halan da Khulud suka tare ta, suka shiga bata hak'uri suna rok'onta akan ta kyale Sanah amma fur tak'i, daga k'arshe ma noma ta kuma saka Sanah da hannu, Khulud zata taya ta Era ta hana ta taya ta, tace " wallahi idan kika tayata sai na kuma k'ara mata wata azabar, Sanah tayi dariya had'i da cewa " wai azaba, ai babu wanda ya isa ya azabtar da d'an Adam face Ubangijin daya halicci abinsa, Era bata kula ta ba ta juya tayi tafiyarta, Khulud da Halan suka bi bayan Era, babu irin hak'uri da rok'o gami da ban bakin da basu bawa Era ba, amma tak'i hak'ura. Sosai Era ta bawa Sanah wuya da duk taurin kanta sai da tayi laushi, Era bata kyale Sanah ba sai 10:30pm na dare, jikin Sanah duk yayi la'asar saboda bak'ar wuya amma har a lokacin bakinta bai mutu ba. Bayan sati d'aya da faruwa al'amarin, Sir Jeeb ya aiki Sanah dataje office d'in Sir Moli ta kira masa shi, tunda aka yi abun daga Sanah har Moli babu wanda ya k'ara ganin wani, da sallama ta shiga office d'in kanta a k'asa kamar mumi na, Sir Moli nakan sofa yana kallanta amma yak'i yin magana, jin shiru ba'a amsa sallamar ba yasa Sanah tad'o kanta, ganin ba kowa yasa ta ware ido ta shiga dube-dube ko zata ganshi, amma kwata-kwata hankalinta bai kai kansa ba, takalminsa data hango a bakin gefe tasa hannu ta jawo, ta d'aga su sama tana kallo gami da cewa " fasa zurmi badai kofatai ba, idanta ne ya sauka akan hularsa da agogonsa dake kan table, da sauri ta mik'e ta k'arasa inda suke, ta d'auki hular tace " wai akan wannan banzar abar aka ban bak'ar wuya ko? Ta tambayi kanta, tsoki tayi tasa hular akan ta, jin hular ta shige zuruf cikin kanta ne, yasa ta cewa dad'i na dashi badai ra'ason ba, ta saka hular sosai akan ta, ta zura takalmi da gogonsa, ta gyara tsaiwarta sosai tace " ranar nan hula kawai na saka aka kusa aika ni k'iyama, aka zage ni tassss aka jefi iyaye da ahali na da bak'ak'en maganganu, to yau nasaka har da takalmi da agogo sai a kashe ni idan an tashi, wai harda cewa mijikin ya shiga uku, yana shirin ganin ikon Allah tayi maganar tana kwaikwayon sa, kai ba'ace maka matarka ta shiga uba sai kai zakace mijin wani, ya shiga uku yaga ta kansa, wallahi duk matar data auri wannan taga bani da arkani, taga izajar rayuwa, mai baud'add'en hali kawai, majhulil hali, duk abinda Sanah keyi akan idan Moli, dan tashi ma yayi daga kwancen ya zauna dangwar-gwar yana kallan abinda yafi k'arfinsa, ya girmewa saninsa da tunaninsa, cike da tsantsar mamaki da al'ajabi, a hankali ta cire hula da agogon ta mayar dasu yadda suke, kamar babu wanda ya tab'a, haka ma takalmin ta juya zata fita, jiyo muryarsa tayi yana cewa " har kin gama iskancin da fitsarar? Cak ta tsaya a inda take had'i da runtse idanta ta cije hak'oranta........ MOMYN ZARAH _*RASHIN SANI.......*_ *HAUWA A USMAN* _JIDDARH_ ```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh``` 8⃣ Cak ta tsaya a inda take had'i da runtse idanta ta cije hak'oranta, a hankali tace " Subhanallah yauma rana ta b'aci, murmushin takaicin halayyar yarinyar yayi kana yace " zo nan! a slow ta juyo kanta a duk'e a k'asa tana murza hannayenta, "zo nan nace, yayi maganar a d'an hasale, a hankali Sanah ta d'ago kanta, ta kalle shi, ganin yadda launin idansa ya canja kala zuwa red, ne yasa jikinta d'aukar kerrrrma, gaba d'aya yanayinsa da kamanninsa sun sauya, take tsoro yayi masifar kamata, jikinta ya d'auki rawa da tsuma, a tsawa ce yace " ba magana nake miki ba dan ubanki? Cikin kerrrmar jiki Sanah taje gabansa ta tsuguna had'i da fasa kuka, dan tasan yau kashinta ya bushe, takai a k'alla 10 minutes durk'ushe a gabansa ya zuba mata ido batare dayace mata komai ba, kallanta kawai yake cike da tsantsar mamaki da al'ajabin halinta, na taurin kai da dakewar zuciya, tunda yake a duniya bai tab'a yarinya irinta mai shegen rawar kan tsiya da rashin jin magana irin ta ba, ashe matar da zan aura taga bani da arkani? Cigaba tayi da kukanta batare datace komai ba, "me ma kikace d'ayan? "Yauwa taga izajar rayuwa ko? Ya kuma tambayar ta, k'ara k'asa tayi da kanta, tana cigaba da kuka, "mai baud'add'en hali, ya maimaita yana girgiza kansa, idansa na kanta yace " wanne irin baud'add'en hali ne dani? Bai bari tayi magana ba yaci gaba, meye ma'anar majhulil hali? yayi maganar cike da rainin hankali, Ya kuma tambayarta, to yanzu dai da farko meye ma'anar bani da arkani, da izajar rayuwa? Shiru tayi batace komai ba, ganin bata da niyyar yin magana ne, yasa shi daka mata tsawa had'i da cewa " ke dan kan uwarki badake nake ba? Yayi maganar cikin zafin rai, yadda yayi maganar ya k'ara firgitata sosai, jikinta ya k'ara cigaba da kerrrmar da yake yi, a tsorace tace " bani da arkani yana nufin bala'i da masifa, "a wanne yaren? Ya kuma tambayar ta, cikin kuka tace " Sokkotanci, "ke basakkwaciya ce? Kai ta girgiza masa alamar a'a, "magana zakiyi min dan ubanki kamar yadda nake yi miki magana nima, ko finki bakin magana nayi? " A'a, yace " shegiya mara kunya fitsarariya, kin iya zagewa kiyi rashin kunya da tsiwa san ranki, amma da kin shiga hannu sai ki fara kuka, ga rok'o da ban hak'uri kamar a bakin ki aka saukar dasu, kince ke ba Basakkwaciya bace, to gidan uban wa kika iya sakkwatanci? "Ko wajen rawar kai da fitsarartaki kika iya? Yayi magana duk a lokaci d'aya, cikin muryar kuka tace " a'a nima ji nayi ana fad'a, " wajen ubanki kika ji yana fad'a? Tace "a'a bakin wata 'yar ajin mu, ita 'yar Sokota ce, zama ne ya su Kano, "ke 'yar Kano ce? Ya kuma tambayar ta, "eh tace, "ok meye ma'anar izajar rayuwa? "Taskun rayuwa, ta kuma bashi amsa, " shi kuma wannan a wanne yaren ne? "Larabci tace masa, "oh dama ke Balarabiya ce? "A'a tace cikin sanyin murya, ya kuma cewa " wanne yare ce ke? Fulani ta bashi amsa, ido ya zaro had'i da cewa " what!? Tace " eh kakana har yanzu baijin Hausa sosai, koyaya yayi magana saika gane ba cikekken Bahaushe bane, yace " haba no wander kike irin wannan iskancin, ai dama duk wani mugun hali Fulani sun had'a shi, sune Kidnappings, Robbery, mugunta da k'eta, ba mamaki dan kinyi irin wad'annan k'ananan halayen, da wuya a kama Kidnapers ko Army Robbers babu ku a ciki, kallansa tayi tana mamakin yadda yake d'ebewa fulani albarka, dan ita a tunaninta shima Bafulati ne, musamman data ganshi fari sol ga gashin kansa, a kwance luf kamar na Larabawa, tace " kai ba Bafulata ni bane? "Allah ya kike yace da sauri, ya d'ora da, Allah ya tsare ni da zama Fulani, ko kinga nayi miki kama da Fulani? "Eh tace, yace "dayake kinganni fari ko? "Ku dayake babu fari mai kyau a duniya sai ku, "ai munfi yawa ne shiyasa da an ganka fari mai kyau ake cewa Bafulatani ne, kuma kasan abinda yafi.... shiru tayi ganin irin kallan dayake mata, kallanta yayi yace " shegiya kuna bayin mu amma kina min fitsara, da sauri ta kalle shi, yace " eh ko Fulani ba bayin Barebari bane? Sai yanzu ta gane shi Bababbare ne, cike da mamaki ta kalle shi tace " kuma ya na ganka fari? "Au dama Barebari babu farare? "Eh Kakana yace min duk bak'ak'e ne, kuma masu k'aton kai da balle, duk abi a cika musu fuska da tsagu tun suna yara, gasu da san girma da fad'in rai, kuma yace min Barebari bayin Fulani ne, "tab Moli yace, amma ko zanso naga Kakan nan ki, "saboda me? Ta tamabaye shi, yace " saboda ba gaskiya ya gaya maki ba, tunda gashi kema yanzu kinga tabbas da idanki, tunda kin ganni fari kuma babu tsagu, murmushi tayi tana goge hawayenta, danta gano d'an adawa ne yanzu, dama Ganez yasha fad'a mata akwai zolaya da tsokana, tare da wasa da dariya a tsakanin Fulani da Barebari, tace " ai my Ulud ma..... da sauri ya kalle, ido ya zuba mata na wani lokaci yana tunani had'i da sak'a abubuwa da dama a ranshi, Allah kad'ai yasan meyake tunanin, a hankali ya sauke ajiyar zuciya ya murtuke fuska sosai kamar bai tab'a dariya ba, fuskarsa kwata-kwata babu annuri, Sanah na ganin haka jikinta ya soma kerrma, tsoranta ya dawo sabo fil, dan tasan andawo maganar laifinta, tunda taga ya koma asalin Moli, ya kalleta yace " yauwa dama kince kin saka hular kawai an kusa kashe ki, ta yanzu kin saka har da takalmi da agogo a kashe ki ko? Yayi maganar yana kallan kwayar idanta, kuka ta saka sosai had'i da cewa " dan girman Allah kayi hak'uri, Allah ban k'arawa, kayiwa darajar Annabi Muhammad S.A.W, ka dubi darajar iyayenka dan Allah da Annabi, dan darajar mahaifiyar ka kayi hak'uri , tayi maganar tana ci gaba da rikitaccen kuka, ido ya runtse da k'arfi had'i da komawa kan sofa ya kwanta, dan ko kashe shi aka ayi, aka had'a shi da girman Allah, darajar Annabi da mahaifiyar sa, sai ya hak'ura, duk girman laifin da akayi masa, muddin aka yi masa wannan magiyar dole ya hak'ura, amma da yaso ya d'and'ana mata kud'arta, yaso tayi kuka har sai ta gaji da kuka, amma taci darajar Allah da Annabi da mahaifiyar sa data had'a shi da su, taje idan halinta ne zata k'ara, yayi maganar cikin ransa, cikin kuka Sanah ta kuma cewa, " wallahi Allah nayi maka alk'awarin ban k'ara yin wani laifin har in bar makarantar nan, in sha Allah, Allah bama kai ba ko wani Malamin ka kama ni na kuma yi masa laifi, kayi min duk abinda kaka dama, a hankali ya bud'e idansa ya sauke su a kanta yace " kin tabbata? Da sauri tace " Allah, ya kuma cewa " ke da kanki kika ce duk abinda naga dama nayi miki ko? Ta d'aga kanta, yace " to ki rik'e wannan a ranki, tace " to, in sha Allah ma bazan kuma ba, yace " tashi kije, da sauri jikinta na rawa ta mik'e ta fita har tana tuntub'e, yabi bayanta da kallo, had'i da cewa " evil girl, sarai Sanah taji abinda yace amma ko juyowa bata yi ba. Sir Jeeb gajiya yayi da jira yayi tafiyarsa, dama cikin garin Roni zasu siyan abinci, shiyasa yasa a kira Moli ko yana da sautu, sanda ta koma class har an tashi, dan haka ta wuce hostel, a tsaye ta iske Khulud tana safa da marwa, idan Halan ne ya fara sauka a kanta, da sauri Halan tace " Sanah daga ina kike, ina kika je? Da sauri Khulud ta juya ta kalli inda Halan ke kallo, ido kawai ta zubawa Sanah tana kallanta, a hankali Sanah ta duk'ar da kanta k'asa, tana wasa da 'yan yatsunta, Khulud tace " yauma laifin kika kuka yi masa ko? Tayi maganar idanta na kanta, cikin sanyin jiki Sanah ta d'aga kanta, alamar eh, Halan tace " yau kuma me kika yi masa? Cikin sanyin murya tace " irin na last week, ido Khulud ta zaro a tsorace tace " yauma hular tasa kika kuma sawa? "Na yau yafi haka ma, Halan tace " yafi haka ma kamar ya? "Yau har da takalmi da agogonsa na saka bayan hular, Khulud da Halan suka zaro ido had'i da cewa " me!? A lokaci d'aya sukayi maganar, cikin sanyi Sanah ce " eh Allah, Halan tace " yau kuma dawa ya had'aki ta baki punishment d'in? Khulud tace " wanne irin punishment aka baki yau? " Dan nasan na yau sai yafi na last week, shiru Sanah tayi kanta a k'asa, cikin tashin hankali Halan da Khulud suka ce " mai matuk'ar wuya aka baki yau ma ko? Baki ta tab'e kamar zatayi, Khulud ta runtse idanta da k'arfi, Sanah ta buga tsalle had'i dayin ihuuuu, tace " yau kam naci mubus, Halan da Khulud suka had'a baki wajen cewa " bulus kamar? "Tana dariya ta fad'a musu duk abinda ya faru a tsakanin su, Halan cike da mamaki ta tsaya tana kallan Sanah, cikin ranta tace " yau Sir Moli ne ya tsaya da wata d'aliba sukayi magana haka? Bayan tayi mishi laifi mai girma irin haka, har ya tsaya yana fad'a mata yare da jinsa sa? Rasa abin cewa tayi saboda tsananin mamaki, shiru kawai tayi ta k'urawa Sanah ido, Sanah tayi murmushi kana tace " Aunty Halan lafiya, wannan kallan fa? Tayi maganar cikin shagwab'a, Halan tayi dariya had'i da cewa " wallahi ina mamakin wannan abu ne kawai, gaki yarinya k'arama ba babba ba balle ace ko sanki yake, Khulud da Sanah suka had'a baki tare suka ce " SO!!!? Murmushi Halan tayi had'i cewa " eh mana, zasu kuma yin magana Halan tace " ban san yawan surutu ku tashi kuje kuyi wanka, kuci abinci ku tafi karatu kun san dai ranar Monday za'a fara exam ko? "Eh duk suka ce, kana suka mik'e suka fita, sosai Sanah da Khulud suka dage da karatu baji ba gani, ko baccin kirki basu samu har sai da aka gama Exam kana Halan ta sarara musu, dan hana su sakat tayi da karatu, Sanah ta d'auki 1st result Khulud ta d'auki na 2rd, dama haka abin yake tun suna primary school, Sanah ke d'aukar na d'aya Khulud na biyu, Ranar Friday ta kama ranar hutu duk d'alibar daka gani cikin murna da matsanannacin farin cike take, kasancewar ranar duk wani d'an boarding school zai samu 'yan cin kai, ranar zasu koma gida su sadu da dangi da iyayensu, ana gama assembly bankwana, students d'in suka fara watsewa dan komawa hostel , dan makarantar akwai tsaro sosai basu sakin yara sakaka, kamar dabbobi su fita ranar hutu, dole sai anzo d'aukar d'aliba sannan zata fita, koda a cikin garin Roni kike wanda gangarawa kawai zasu yi, amma doka ce dole sai an zo d'aukar d'aliba, wanda yazo d'aukar yaje ya bada sunanta da sunanshi, yayi signing, an kira d'alibar dayazo d'auka an tambaye ta sanshi, an tabbatar akwai dangantaka a tsakanin su sannan za'a bashi ita, idan Sir Moli ya sauka akan Sanah da Khulud, "ke ku zo nan, ya kira su, jiki na rawa suka k'araso suka zube a gabansa, hannu ya mik'a musu alamar su bashi result d'in su, dake rik'e a hannunsu, ba musu suka mik'a mishi ya amsa ya bud'e yana dubawa, na Sanah ya fara gani ya d'ago kai ya kalle ta yace, "ashe dai ba laifi, ba iskancin kad'ai bane, ana fahimtar karatu, sunkuyar da kanta tayi k'asa batare datace komai ba. Na Khulud ya bud'e, ganin na biyu yasa shi had'e fuska yana kallan Khulud, kanta ta sunkuyar k'asa, "ke ya akayi wannan ta fiki k'ok'ari? Cikin sanyin murya Khulud tace " dama haka muke d'auka tun daga primary, rai ya k'ara had'ewa kana yace " to nan ba Primary school bane, Secondary school ne, dan haka ki dage sosai, kema ki fita, dan so nake ki zarce ta komai a rayuwa kinji ko? Shiru tayi batare data ce komai ba, tsawa ya daka mata had'i da cewa "ba magana nake da ke ba? Jikinta na rawa tace " bana fatan Allah ya bani abinda zanfi Sanah a rayuwa, duk abinda zaizo mana na cigaba da k'aruwa ina fatan Allah ya bamu tare, ina addu'a ina rok'on Allah, kada ya bani ikon mallakar abinda Sanah bazata tab'a samun abinda ya fishi ba, idan ko har zan samu ina addu'ar Allah ya sanwantar dashi, daga gare ni ya bata, a d'an tsorace Moli yace " ke kina da hankali kuwa? "Sosai tace had'i da d'aga kanta sama ta kalli al'arshe tace " ina fata Allah da Mala'iku su zama shaida, akan abinda na fad'a yanzu, koma miye a duniya muddin na samu abinda Sanah bazata samu mafificinsa ba, Allah ka kwace shi daga gare ni ka bata, ka mallaka mata shi mallakawa ta har abada, koda tare da rai na da rayuwa ta ne, shiru Moli kawai yayi yana kallan su cike da mamaki, dakyar ya iya mik'a musu result d'in tare da cewa " ku tashi ku je, suka mik'e a tare suka bar wajen, ya bi bayan su da kallo yana jinjina abin a ransa. Hango Yayyan su Zafran da Ziyad da sukayi tsaye, yasa rugawa a guje suka fad'a jikin su, kowa ya d'aga d'aya sama suna dariya, batare da b'ata lokaci ba aka sallami su Sanah, a Hard'o Family kowa ka gani cike yake da murna da farin cikin ganin Sanah da Khulud, an shirya musu abinci kala-kala na tarbar su, Sanah sai zuba surutu take tana bada labarin boarding school, yayinda Khulud tayi shiru tana tunani, wanda ita kanta bata san tunanin me take yi ba, haka nan kawai ta tsinci kanta a cikin k'unci da kewar dabata na meye ba, Sanah ta kalli Khulud tace " muje na raka ki, ki kwanta, kasancewar a gidan su Sanah suka sauka, Khulud tayi dariya tace " a boarding school ma bamu rabu ba balle a gida, daga yau har muyi AURE a part d'aya bedroom d'aya zamu rink'a kwana, daga yau bedroom d'in mu ya dawo d'aya, cikin murna Sanah ta kalli Abbu da Mamu (iyayenta Hamraz & Hassana) tace " Abbu kaji wai Khulud ta dawo nan, dariya yayi yace " sai aji dad'in k'iriniya ba, Mamu tayi murmushi tana jawo su jikinta ta rungume tace " Allah ya barku tare, Ubangiji ya k'ara had'e mana kanku, duk suka ce Amin, Khulud tace " raka ni na kwaso kaya na daga part d'in Juju da Dide (iyayenta Rawan & Usaina), Mamu tace " ku bari mana sai gobe da safe, "a'a suka ce tare, Abbu yayi dariya had'i da cewa " maza a dawo lafiya. A parlor suka iske Juju da Dide, da gudu suka fad'a jikinsu Sanah tace " albishirinku, Dide da Juju suka amsa da "goro suna dariya, kasancewarsu masu sauk'in kai da wasa da dariya, Sanah tace " my Ulud yau zata bar part d'in nan, Dide da Juju suka cewa " zuwa ina? Sanah tace " zuwa part d'in Abbu da Mamu, dariya sukayi, Juju tace " Allah ya raka taki gona, kuje can ku k'arata kuda Mamunku, ni nama huta, Sanah tace " au dama an gaji damu? Dariya suka kuma yi, Abbu yace " ku dai da Mamu kusan halinta, suka yi dariya suna shiga d'akin Khulud, Dide da Juju suka ce "Allah kabar min kan yaran nan a had'e har abada, Ubangiji karka kawo sab'ani a tsakanin su, suka amsa da "Amin lokacin da suke fitowa, ko tsinkenta basu bari ba, sai da suka kwashe komai, suka mayar dashi d'akin Sanah, tun daga wannan rana Khulud ta koma part d'in su Sanah, suka koma bedroom d'aya kansu ya k'ara had'ewa shak'uwa da sabo mai k'arfi ya k'ara shiga tsakanin su. MOMYN ZARAH _*RASHIN SANI.......*_ *HAUWA A USMAN* _JIDDARH_ ```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh``` 9⃣ Washe gari da safe da wuri su Sanah suka tashi, suka gyara gidan ko'ina yayi fesss, koda Mamu ta fito k'anshin bonar turaren wuta ne ya daki hancinta, da sauri ta k'araso parlor'n dan ganin meke wakana, ganin ko'ina tsaf ya sata tsayawa cak, cike da mamaki take bin ko'ina da kallo, "good morning Mamu, suka fad'a tare suna dariya, juyowa bayanta tayi inda taji yo muryarsu, fesss suma ta gansu sunyi wanka, cike tsantsar mamaki Mamu tace " wa yayi duk wannan aikin? Suna dariya suka amsa da mune Mamu, " ku ne? Tace, cikin mamakin, "yes Mamu, mu mukayi komai, dan ma bamu iya had'a breakfast ba, da sai dai ki tashi ki ganshi jere a dinning table, cikin mamaki Mamu tace "ikon Allah, ku ce yanzu dai kun girma kunyi hankali, kun san meya kamata? " Sosai ma Mamu, cewar Khulud, "waya koya muku duk wannan aikin? "Aunty Halan, cewar Sanah, shiru Mamu tayi na wani lokaci kafin tace " wacece kuma Aunty Halan? "Wacce muke wajenta ce a makaranta, ita keyi mana komai, bata barin kowa ya tab'a mu, "kai amma baku da kirki, amma shine da muka je visiting baku kirata mun gaisa ba? Sanah tace " murnar ganin ku tasa muka manta, itama sai da tace meyasa bamu kirata ta gaida ku ba, Mamu tace " gaskiya dai bamu kyauta ba kam, "masha Allah cewar Abbu yana saukowa daga samansa, da gudu Khulud da Sanah suka fad'a jikinsa, "good morning Abbu, shafa kansu yayi yana murmushi yace " Alhamdulalillah, how was your night? Ya tambaye su, "Alhamdulalillah suka bashi amsa, Mamu dake tsaye tace " ka ganni nan cike da mamakin yarana, Abbu yace " mamakin me? "Mamakin canzawar su mana, kalli gidan fa gaka yadda suka gyara ko'ina yayi fesss, parlor'n yabi da kallo yana mamaki shima yace " wai su suka yi duk wannan? "Eh Mamu tace, kansu ya kuma shafawa yace " Alhamdulalillah yara na sun girma ko? Sanah tace "eh Abbu, damma bamu iya girki ba da har breakfast sai dai ku tashi ku iske mun gama, "wannan aikin Mamunku ne ta koyar da hazik'an yaranta girki, Abbu yayi maganar yana kallan Mamu, dariya tayi tace " ai dole ma na fara koya musu girki daga yau, dan nan gaba kad'an duk masu aikin gidan nan sallamar su za'ayi, Abbu yace " idan aka sallame su suwaye zasu aikin? "Ina fatan dai ba yara na za'a d'orawa hidimar kula da gidan ba? Mamu tace " to in ba su ba suwa? Abbu yace " aiko tun wuri ma ki nemi masu yi miki aiki dan baza'a mayar min da yara bayi ba, yayi maganar yana dariya, Mamu tace " gani da 'yan mata har biyu zan tsaya ina d'aukar masu aiki, suna samin ciwon kai? "Duk abinda nake so nasan 'yan mata na zasuyi min ko? Ta k'arasa maganar tana kallan su, da sauri suka ce " yes Mamummu, dariya Abbu yayi yace " wato kun gwale ni, kun bi bayan Mamun ki ko? Khulud tace " haba wane mu, mu gwale Abbun mu guda, kawai dai muma muna san mu taimaka muku ne, dai-dai gwargwadon k'arfin, Aunty Halan tasha ce mana duk d'an dabaya tausayi da taimakon iyayensa, bazai tab'a cin nasara a rayuwarsa ba, kullum yana cikin wulak'anta da tab'ewa, ajiyar zuciya Abbu ya sauke yana kallan Mumu yace " gaskiya ya kamata muga Halan d'in nan, Mamu tace " gaskiya kam, hanyar fita Abbu yayi Mamu tabi bayan tana cewa " bazaka tsaya kayi breakfast ba? "Inda anyi niyyar bani da antashi anyi da wuri, kin dai ga hazik'an yara na, na neman koya miki yadda akeyi idan ke baki iya ba, yayi maganar yana murmushi cike da wasa, dariya tayi tace " oh! abin gori ya samu fa yanzu, har bakin motarsa ta raka shi kana ta dawo gida, tare dasu Sanah suka shiga kitchen suka had'a breakfast, ta nunnuna musu duk abinda ya kamata, da rana ma daza'a girka abincin rana, tare suka shiga kitchen tana koya musu, bayan sallar la'asur suka tafi islamiyya. A islamiyya sosai k'awayen su sukayi murnar ganin su, dan duk cikin su babu wad'anda aka kai boarding school sai su, yara suka zagaye Oga Sanah tana basu labarin boarding, sai zuba take, yayinda Khulud tayi shiru kawai ta zuba mata ido, dan ita bamai san yawan magana bace, ranar dai kam haka suka taso babu wani karatu da sukayi sai labarin boarding school kawai da Sanah tayi ta basu, suna komawa gida suka iske Mamu a parlor, da murna ta tare su, suka fad'a jikinta, tace " maza aje a cire uniform, a huta, kuje ku gaida Jujunku kuzo mu d'ora abincin dare, Khulud tace " ba wani hutu da zamuyi, bari kawai mu cire uniform mu gaido Juju sai muzo muyi girkin, "to maza yaran kirki cewar Mumu, bedroom d'in su suka shiga suka shire uniform d'in, "Mamu mun cire bari mu gaido Juju mu dawo yanzu, "sai kun dawo, tace. A kitchen suka iske Juju na aikin abincin dare, da sallama suka shiga, fuskarta d'auke da fara'a ta amsa musu, tana cewa " 'yan boarding sai yanzu aka tashi? "A'a Juju mun tashi tun safe, munje islamiyya ne, tayi murmushi tace " masha Allah, ana dai karatun sosai ko? "Eh, Juju muna yi sosai, cewar Sanah, kana ta cigaba da cewa " Juju bari mu tayaki girkin, "a'a na yafe kuje ku taya Mamu, Khulud tace " ai tare muke yin girki da ita, yauma tare mukayi breakfast & lunch, dariya Juju tayi tace " oh su Mamu manya, wato harta fara mayar da yaran ta 'yan mata? Didi dake zaune a parlor yana karatun jarida yace " ai gwamma hakan kinga sai tayi musu aure da wuri, dayake basu kula dashi ba, suka juya da sauri suna cewa " lah Didi dama kana zaune a parlor, muka wuce bamu kula da kai ba? "Ina fa zaku kula dani hankalin ku nakan Jujunku, dariya sukayi suna fad'awa jikinsa, suka ce " ina yini Didi? Kansu ya shafa, kana yace lafiya lau, yaran Abbu, ya Abbun naku da Mamu? "Duk muna lafiya, Khulud tace " bari mu tafi gida, Mamu nacan na jiran mu, girki zamuyi, tunda nan baza'a barmu muyi ba, tayi maganar tana kallan Juju tana dariya, Juju tace " ita da taga zata iya cin jagwalgwalanku sai taci, amma ni da mijina bamu iyawa, dariya sukayi Khulud ta rik'o hannun Sanah tana cewa " zo mu tafi kinji my Sanah, tunda basu iya cin girkin mu, dariya Didi da Juju sukayi suna bin bayansu da kallo. Da daddare bayan sun gama girki sun jere a dinning table, Idrak da Aarib, Ziyad da Zafran suka shigo tare duk su hud'un, zama sukayi akan sofa, Sanah da Khulud suka fad'a jikin su, cike da shagwab'a Sanah tace " Yaya kace fa zaka kai mu yawo ni da my Ulud, murmushi yayi yana k'ara kwantar da kanta ajikinsa yace " sorry Auta na manta ne, amma ku shirya gobe zan kai ku in sha Allah, tsalle suka farayi cike da murna, Abbu da Mamu suka fito tare fukarsu d'auke da murmushi, gaba d'ayan samarin suka zube suna gaida iyayen nasu, suka amsa cikin walwala, Abbu ya kalli Sanah da Khulud yace " murnar me 'yan matan naki suke yi haka? Yayi maganar yana kallan Mamu, tace " ina zan sani ne, tayi maganar cikin sanyi tana kallan su, cike da tsantsar so da k'auna, kana ta kalle su tace " 'yan matan Mamu murnar me akeyi haka? Khulud tace " Yaya Aarib da Idrak ne zasu kai mu yawo gobe, Abbu yace " uhnmmm 'yan gatan Yayyan su, zama sukayi suka duka akan dinning table, suna cin abincin cikin farin ciki, Abbu ya kai spoon d'aya bakin sa yace " uh uhn uhn carkwad'i wayayi girkin nan? Da sauri Sanah da Khulud suka ce mune Abbu, Abbu yace " wai badai dad'i ba, tunda nake ban tab'a cin abincin mai dad'in na yau da Yara na suka girka ba, Mamu ta kalle su tace " oh! kuji k'arfin hali, daga koyo kuma sai ku zak'e kuce ku kukuyi? Sanah ta kalli Khulud tace " my Ulud, waya gyara kayan miya? Khulud tace " mu ne mana, Sanah ta kuma cewa " waya yanka albasa, ya wanke shinkafa, ya zuba maggi da gishiri? Khulud tace " mu ne, tana dariya, " waya rink'a kula da girkin? "Mu me, " waya kwashe ya zuba food flask, ya kuma shirya dinning table? Khulud tace " duk mune my Sanah, Khulud ta kalli Abbu da Mamu da Yayyansu tace " to yayi girki? Duk sukayi kana suka ce " Sanah da Uludinta, bayan sun gama cin abincin Sanah ta kama hannun Khulud zasu fita, Mamu tace " ina kuma zaku? Sanah tace " wajen wad'ancan tsofaffin da suka k'i mutuwa har yanzu, Abbu ya zaro ido had'i da cewa " uwaku! yana yi musu dak'uwa, " iyayen namu ne tsofaffin da suka k'i mutuwa? Khulud tace " Abbu ko sun mutunne bamu sani ba? "Uwaku cewar Mamu tana dariya, Sanah tace " ina fa zasu mutu my Ulud, bayan suna jin dad'in duniyar dan na lura ma jin kansu suke yi kamar samari sa'annin su Yaya, Abbu yayi kwafa yana dariya yace " Ziyad muk'o min yaran can, da gudu suka fita suna dariya, washe gari sosai yakai su Sanah yawo, har da su shopride ya kai su kallo, daga nan ya wuce dasu gidan zoo da rockzy, da zasu dawo ya kai su cin shawarma da bugger da ice cream, sosai suka ji dad'in fitar su, haka hutun su Sanah ya k'are, Mamu tana koya musu abubuwa da dama, musamman a b'angaren girki, da kwalliya, kasancewar Didi d'an k'aida yasa dole sai da aka mayar da su Khulud ranar Sunday da aka koma school, Sanah manne a jikin Aarib tana ta kuka had'i da zuba masa shagwab'a, dayake duk cikin mazan sunfi d'asawa dashi sosai, Khulud ko babu ruwanta, sai Zafran daya rik'e hannunta. Sir Moli nakan staffroom step zaune, ya hango su Sanah, yaga yadda ta mannewa Yayanta tana kukan shagwab'a, shi kuma sai wani lallab'ata yake yi, yaga Khulud ba ruwanta babu abinda ya dame ta ma,, aiko Sir Moli ya k'ulu, yazo har wuya, tsoki yaja ya mik'e ya shige cikin staff yana mita, "ashe dole yarinyar tayi fitsara da rashin kunya, tunda an riga an gama sangartata a gida, shiyasa take rawar kai, shegiya! ya fad'a yana kuma jan tsoki mtswwwww, Zafran ya kalli Khulud yace " ina Auntyn taku take? "Saboda Abbu yace mu tabbatar mun ganta, " Allah yasa dai ta dawo, amma bari naje na kira ta cewar Khulud, ta juya zata tafi taji muryar Halan na kwala kira dai-dai lokacin dasu ma motar su take shigowa cikin makarantar, da hanzari Halan ta bud'e motar ta fito, da gudu Khulud ta nufe ta had'i da fad'awa jikinta, cikin murna Halan ta rungume ta, a hankali ta zame jikinta had'i da cewa " ina our Sanah? Khulud tace " gata can tana ta kuka, "kuka kuma cewar Halan? Tana bin inda Khulud ta nuna mada kallo, mik'ewa tayi had'i da rik'e hannun Khulud ta nufi inda Sanah take, suna k'arasawa Khulud tace " Aunty Halan ga Yayyanmu ku gaisa, sai lokacin Halan ta kula da su, dan kwata-kwata hankakinta baika kansu ba, tana murnar ganin su Sanah, cikin nutsuwa da sanyin murya tace, " please kuyi hak'uri ban kula daku ba, sun d'auke min hankali, ina yinin ku? Tayi maganar tana murmushi, duk suka amsa banda Ziyad daya kafeta da ido tun ganinta, ta kalle shi tace " ina wuni? Gaba d'aya hankalinsa ya tafi dan haka baiji ta ba, ta kuma cewa " ina wuni? Had'i da sunkuyar da kanta saboda kallan da yake mata, ganin ana nema aji kunya yasa Zafran saurin tab'a shi,,, da sauri yayi firgit, had'i da cewa " kun kira ta ne? Gaba d'aya suka saka dariya, amma banda shi daya kula da abinda yayi, a hankali ya shafa kansa yana murmushi, ta kuma gaida shi ya amsa fuska a sake, Yayan Halan ya k'araso wajen fuskarsa d'auke da murmushi, yace " ganin su Sanah yasa kin manta da ni? "Lah ba haka bane, "to yaya ne? Cewarsa yana dariya, fuska Ziyad ya had'e danshi a tsammaninsa ko saurayinta, Halan tace " ga Brother na ku gaisa, da sauri Ziyad ya saki fuska yana murmushi, ya mik'a masa hannu suka gaisa, su Khulud ma suka gaidashi, ganin har lokacin Sanah na jikin Aarib yasa Halan cewa " Oga rigima sauko, Zafran yace " ashe kuma ana d'an tab'a muku halin? Murmushi tayi batare datace komai ba, Sir Moli ya lek'o ta window ganin har lokacin Sanah na mak'ale a jikin Aarib, yasa shi jan tsoki had'i da cewa " shegiya, exchanging phone numbers sukayi tsakanin Yayan Halan dasu Ziyad, Ziyad ya ciro bandir d'in 2 hundred naira na 20k, ya mik'awa Halan, kai ta girgiza tace " ka barshi na gode, yace " meyasa? Tace " haka nan bakomai, yace "ba kyau mayar da hannun kyauta baya ba fa, murmushi tayi kana tace " ai nima ba mayarwa nayi ba, tayi maganar kanta a k'asa, yace " to me kikayi idan ba mayarwa kikayi ba? Murmushi kawai tayi batare datayi magana ba, yace " wannan kyautar ba daga ni bane, balle kik'i k'arb'a daga Abbu ne, murmushi tace " to na karb'a tunda daga Abbu ne, amma gashi nan ka je min, zan karb'a wata rana, babu yadda basuyi da ita ba amma tak'i amsa fur, hakan ya k'ara tabbatar musu daga gidan mutunci da tarbiyya take, suka kuma k'ara ganin k'imarta, kana suka taf, bayan sunyi sallama. Bayan sun koma gida Abbu ya tambaye su sunga Halan, Ziyad yayi saurin cewa " eh Abbu yarinyar nada hankali da tarbiyya, Zafran yace "ai kayi saurin bada amsa mana, Abbu yace " ya aka yi ne? Aarib yace " ai inaga dai Abbu surukar ku ma zata zama, Ziyad yayi saurin kai masa duka, ya goce yana dariya, Didi yace " kai karku damar man d'a, Juju tace " kai masha Allah, amma gaskiya naji dad'in hakan, dan daga jin yarinyar 'yar mutunci ce, duba da yadda ta canja su Sanah a term d'aya kawai, "ai damma baku ganta ba, wallahi ta had'u sosai gata da nutsuwa, cewar Aarib, hannun Zafran Ziyad ya rik'o suka fita, iyayen nayi mishi dariya, bayan sum fita Ziyad yace " wallahi ina san yarinyar nan, dan haka ma duk week sai naje visiting, Zafran yace "kai mutuna irin wannan rik'e wuta haka, Ziyad yace " ai dole. Washe gari Monday, bayan anyi assembly kowacce students ta koma class, bayan an tashi daga class Sir Moli ya koma office d'insa, yana k'ok'arin kwanciya idansa ya sauka akan voice recorder d'insa, wacce shi yama manta da ita, da sauri ya mik'e ya d'auko had'i da kunnawa yana saurara, ai tun kan Sir Moli ya gama saurara duk ilahrinsa jikinsa ya d'auki kerrrma da b'ari, idansa suka koma pure red, sai da ya gama ji kaf, jikinsa na b'ari saboda tsananin b'acin rai, zuciya ta kawo shi har wuya, ransa ya kai k'ololuwar b'aci, zuciyarsa na tafasa gami da azalzala......... MOMYN ZARAH _*RASHIN SANI.......*_ *HAUWA A USMAN* _JIDDARH_ ```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh``` 🔟 Da sauri ya fito daga office d'insa, har yana tuntub'e, akan step ya tsaya yana hanga yarinyar da zai samu ya aika kiran su Sanah, daga can nesa ya hango wata yarinyar tana k'ok'arin shiga Hostel get, da k'arfi ya d'aga murya yace " hey, yarinyar ta juyo a d'an tsorace, ganin Sir Moli tsaye yasa jikinta d'aukar kerrrrma, da sauri ta k'araso ta tsuguna a gabansa, gaidashi take amma bai iya amsawa ba, saboda yadda zuciyarsa ta gama jagulewa, yace " ke ajinki nawa? Jikinta na tsuma tace " JSS2, yace " kin san Sanah Hamraz? Ya tambaye ta idanshi na kanta, cikin kerrrmar jiki tace " eh, mamaki ne ya kama shi sosai jin ta santa, kamar zai share sai kuma yace " ya akayi kika san su, bayan ba class mate d'inki bane? Jikinta na rawa tace " kowa ai ya san su a makarantar nan, " saboda me? Ya kuma tambayar ta a tak'aice, yana yi mata tambayar ne dan yana san samun k'arin hujjar cin uban Sanah, "tun ranar da suka daki Aunty Era suka zama popular's, "Ok, maza jeki kira min su yanzu, yayi maganar yana komawa cikin office d'insa, da sauri yarinyar ta mik'e jiki na rawa tayi hanyar hostel, a zaune ta iske su suna hira da Halan, yarinyar tayi sallama, kana ta kalli su Sanah tace " Sir Moli na kiranku, k'irjinta ta dafe had'i da zaro idanuwa waje, tace " mu kuma? Yarinyar tace " eh ku yace, Halan ta kalli yarinyar tace " waya ce ku kira masa? "Sanah Hamraz ta bata amsa, ido Sanah ta kuma zarowa tace " na shiga uku me kuma nayi masa? Ta tambayi yarinyar, tace " ban sani ba, ya dai ce kawai na kira masa ku, Halan tace " ya kika ga yanayinsa? Yarinyar tace " ban kula da fuskarsa ba dan kai na duk'e yake har ya gama yi man magana, Yarinyar ta fad'i haka ne saboda gudun abinda zai je ya dawo, dan tasan halin Sir Moli sarai, Halan tagai dubanta ga Khulud , da jikinta ya fara rawa tun jin kiran da Sir Moli yake yi musu, tace " me kuma kuka kuma yi masa? A tsorace Khulud tace " wacce ni, mai kai ba gashi, ai sai dai ki tambayi Oga, Halan ta kalli Sanah tace " yau kuma mai kika tarowa kanki? Kamar zatayi kuka tace " wallahi Aunty Halan tunda muka dawo ban sashi a ido na ba, balle nayi masa wani laifin, idon Halan na kanta tace " kin tabbatar? Kai Sanah ta gyad'a mata, cikin sanyin jiki suka mik'e had'i da zarar hijabansu, Halan tace " Allah dai yasa alkhairi ne, Sanah tace " kayya Aunty Halan kema kin san a kira mutumin nan babu alkhairi, Halan tayi murmushi, tace " ku irink'a maimaita " innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, ku kuma d'auke numfashinku, ku karanta, Qulhuwallahu Ahad, sannan ku maido da numfashinku ku karanta Nasi da Falak'i, da لا حول ولا قوه الا بالله العلي العظيم, har ku isa gare shi, in sha Allah duk girman laifin da kuka yi masa Allah zai d'ora ku a kansa, cikin sanyin murya Khulud tace " to Aunty Halan mun gode, kamar zata fasa ihu Sanah tace " wai ni meye dalilin kiran dayake mana? Halan tace " o! o! ni da nake nan tare daku ina zan sani? " Idan kinje can sai ki tambaye shi, ko idanki ya gane miki, batare dasun kuma cewa komai ba suka fita, addu'o'in da Halan ta gaya musu suke ta maimaktawa, Moli nacan zaune kamar zai fashe saboda tsananin zugin da zuciyarsa keyi masa, minta d'aya minti biyu sai da duba agogo had'i da jan tsoki, kishingid'a yayi ya rufe idanta, yana sauraren yadda zuciya ke azalzalarsa gami da bugawa da sauri, a k'ofar office d'in suka ci burgi, kowa yana kallan kowa still they're praying, Sanah tace " kiyi sallama, Khulud tace " inyi sallama kamar yaya? Tayi maganar cikin rad'a gudun kar ya ji, Sanah tace " amma dai kin san idan ni nayi bazai amsa ba ko? "Sanin kanki ne shanya mu zayyi, batare datace komai ba ta matsa kusa da k'ofar tayi sallama, batare daya amsa sallamar ba yace " in, a tak'aice, Sanah ta tab'e baki had'i da cewa " sai kace karifi ayi maka sallama kak'i amsawa, mstwwwwww taja tsoki can k'asan ranta, durk'usawa sukayi a gabansa, Khulud tace " Sir ina wuni? Batare daya bud'e ido ba yace " Alhamdulalillah, Oga Sanah ko kwata-kwata bata da niyyar gaidashi, Khulud ta d'an tab'a ta da hannunta tace " ki gaida shi, baki ta turo ta kau da kanta gefe, hakan ya tabbatarwa Khulud bata gaida shi, sun kai 7 minutes batare daya, motsa ba balle ya bud'e idansa ko yayi musu magana, Sanah na k'ok'arin yin magana taga ya mik'a hannunsa ya d'auko voice recorder, yayi playing, still idansa na rufe, suna fara saurara Sanah tayi baya zata fad'i tana daga tsugunnan, dab'assss ta zauna a k'asa jiki ba kwari, tun kafin su gama sauraran voice d'in suka fara gurzar kuka, kamar ransu zai fita, while duk ilahirin jikin su na kerrrrma, da tsuma yake, tsoro da firgici ya gama kama su, dan sun san babu mai kwatar su yau a hannun Sir Moli sai Allah, har record d'in ya k'are Moli bai motsa ba, yana yadda yake, idanshi rufe, yana daga hakan yace " that's good, "hmmmmmm yace yana sauke ajiyar zuciya, "ashe ni k'aramin d'an iska ne kice babbar? Yayi maganar still his eyes closed, "shege d'an iska mai girman kan tsiya, miskilin banza, ya maimaita under his breath, "please ina san nasan girman kai da muskilnaci, iskanci da ja'iranci, kwartancin danayi Malama Sanah? "Ina san sani kiyi man bayani in briefly, yayi maganar still bai bud'e idan shi ba, batayi magana ba sai sautin kukan su dake tashi, "ashe ni munafuki ne, kuma shege, marar aikin yi sai kwanciya? Ya kuma tambayarta, mai lab'ewa a uncompleted building, yana kurb'e-kurb'e da zuk'e-zuk'e ko? " Mugu azzalumi still ko? "wallahi idan har kina san na kyale ki sai kin yi man bayanin wad'annan halayen da kika danganta ni dasu, bayan na tabbatar bani da alak'a da ko d'aya daga cikin su, ina saurarenki yi min bayanin, kwartanci, iskanci, ja'iranci, muskilnaci, munafurci, girman kai da zaluncin nadayi miki, kafin mu zo kan shege, shaye-shaye, zuk'e-zuk'e da kurb'e-kurb'e, shiru duk suka yi, babu abinda suke yi sai kuka, jin shiru yasa shi bud'e idansa a hasale ya zabura ya daka musu gigitacciyar tsawa, " ke dan kan uwarku bada ku nake ba? Idonsu duk suka d'ago suka kalle shi, cikin matsanancin tashin hankali da tsoro, suna had'a ido da yaran yaji tausayin su ya saukar mishi a rai, musamman dayaga yadda suke kukan mutuwa, ji yayi zuciyarsa da ransa sunyi masa sanyi, duk wannan zafi da k'unar ran dayake ji sun gushe, sai ma matsanancin tausayin su daya mamaye ruhi da gangar jikinsa, ajiyar zuciya ya sauke yace " shut up!, duk sukayi shiru saboda tsoro, ido ya k'ura musu na tsayin lokaci kafin yace "ku tashi kuje, cike da mamaki suka d'ago suna kallansa, yace " badaku nake ba? Da hanzari suka mik'e jiki na rawa zasu fita har sun kai bakin k'ofar fita yace " don't be a greedy girls, you know greedy pupils will pay for their sins, jiki na rawa suka amsa da " to!, bai k'ara bi ta kansu ba ya koma ya kwanta, yana mamakin abinda yaji yanzu, ya kuma kasa koda yi musu kallan banza. _K'ARFI DA TASIRIN ADDU'A KENAN, DUK MAI YINTA BAI TAB'EWA KO WULAK'ANTA,_ _MUSAMMAN DAGA BAKIN YARAN DA BASU BALAGA BA, SABODA ALLAH YACE " DAN YARA K'ANANA DA DABBOBI AKE YI MANA RUWAN SAMA,_ _SANNAN ADDU'AR YARA BATA DA HIJABI GA UBANGIJI, SHIYASA WASU SUKE TARA YARA SUNA YI MUSU ADDU'A_ A bakin hotel get suka iske Halan tana jiransu, suna ganinta suka fad'a jikinta suna sakin kuka, a kid'ime ta d'ago su tace " lafiya, dukan ku yayi? Kai suka gyad'a mata a tare, tace " me kuka yi masa? Cikin kuka Khulud ta zayyane mata duk abinda ya faru tun daga farko har k'arshe, ajiyar zuciya ta sauke jin bai dake su ba, ta mayar dasu jikinta ta rungume, Sir Moli sai juyi yake cikin dare ya kasa bacci, babu abinda yake tunani sai irin words d'in da Sanah ta jefe shi da su, shi abinda yafi d'aure mishi kai k'arfin halin yarinyar da dakewar zuciyarta, murmushi yayi lokacin daya tuno, wai irin su ne masu lab'ewa a uncompleted building suna kurb'e-kurb'e, da zuk'e-zuk'e, murmushi ya kuma yi had'i da girgiza kansa. A week later Ziyad ya dawo visiting, Sir Moli ya tarar akan staff zaune, Ziyad ya mik'a masa hannu suka gaisa suna yiwa juna murmushi, a nutse Moli ya tambayi Ziyad wad'anda ya zo gani, Ziyad yace " Sanah Hamraz da Khulud Rawan, & Halan murmushi Sir Moli yayi yace " Bother su ne? Ziyad yace " same Mom & Dad, ka san su ko? Cewar Ziyad, "sosai, Moli ya bashi amsa yana murmushi, Ziyad yace " ah Sanah ana tab'a halin anan ma kenan? Ya fad'a yana murmushi, Moli ya zuba mishi ido, "hmmm wato haka take kenan har a gida, shegiya 'yar iska, ya fad'a cikin ranshi, Ziyad yace " nasan dama za'a rina ai dama mai hali baya tab'a fasa halinsa, murmushi Moli kawai yayi batare dayace komai ba, head girl ya aika ta kira su, shi kuma ya shige cikin staff yana mamakin nutsuwa da kamalar Ziyad. Da gudu Sanah da Khulud suka k'araso, suka fad'a jikinsa, a nutse Halan ta k'araso, tana murmushi, sai da ya gama magana da wasa dasu Khulud kana yace " maza ku d'auki kayan kukai hostel, kuma idan kun tafi karku dawo, sai da aka sha daru da Sanah kana ta tafi tana kuka, shima sai da yace mata idan bata daina rigima ba bai k'ara zuwa, kana ta tafi, bayan sun tafi ya karkata gaba d'aya hankalinsa ga Halan, har k'asa ta duk'a ta gaidashi, ya amsa cike da fara'a da tsantsar farin cikin tarbiyyarta, a hankali ya kira sunanta " Halan!, cikin nutsuwa ta amsa "na'am, yace " zan tambaye amma please ki sanar da ni gaskiya, tace " in sha Allah, sai da ya nisa kafin yace " anyi miki miji? Kanta ta duk'ar kanta k'asa kana tace "a'a, yace " kina da wanda kike so? Ta kuma cewa "a'a, da k'arfi ya sauke ajiyar zuciya, "Alhamdulillah yace, kana yaci gaba " magana ta gaskiya Halan, tunda na d'ora ido na kanki naji kin kwanta min, na kuma samu nutsuwa dake, abinda yasa ban zurfafa sosai ba, sai dan gudun ko kina da wanda kike so, ko wanda zaki aura, kuma nasan nema cikin nema haramun ne, magana ta gaskiya ina sanki ya fad'a kan shi tsaye, tunda ya fara magana ta duk'ar da kanta k'asa bata d'ago ba, har ya dasa aya, shiru yayi had'i da kafe ta da idonsa dan ganin reaction d'inta, ganin tana murmushi ne yasa shi fahimtar ya samu karb'uwa, hira yayi ta zuba mata, ita sai dai ta bishi da eh ko a'a, kud'i ya bata amma tak'i karb'a, babu yadda bayyi ba, dole ya hak'ura. A kwana a tashi ba wuya wajen Allah, kamar yaune su Sanah suka dawo hutun first term gashi yanzu har sun kusa gama second term exam, while Ziyad ya zo a term d'in waje 10 tyms, sosai soyayya mai k'arfi ta shiga tsakanin Halan da Ziyad, har maganar takai ga iyaye, an tsaida magana akan data gama secondary school za'ayi bikin su, ranar hutu Sanah da Khulud da Halan sun sha kuka sosai, kasancewar zasu bar Halan a makaranta, zaman vocation, koda suka koma gida hutu Mamu d'orawa tayi daga inda ta tsaya wajen koyar dasu girki da sauran abubuwa, ranar da hutu ya k'are sosai Sanah tayi ta mak'alewa Aarib, sai da kyar aka raba su, tana risgar kuka, washe Monday first week na third term, akayi assembly kamar yadda aka saba, kowacce students ta kama hanyar class d'in su, class d'in su Sanah yayi shiru dan basu da yawa wad'anda suka dawo, dukkan su sunyi shiru cike da tsantsar kewar gida, ganin haka yasa Sanah tashi ta cire hijab d'inta taci d'an mara dashi a k'ugunta, ta hau saman seat ta fara kid'a, abinka da wad'anda ke cikin kewa, ga kuma k'uruciya na damunsu, ai ko suka zage suka shiga tik'ar rawa da wak'a, while Sanah naci gaba da kid'an tana rawa daga zaune saman seat, Khulud na zaune bata ko motsa ba, tana ta dariya, Sir Moli na SS2 yana teaching, yaji kid'a na tashi, his face with surprise, saboda yaune first time daya soma jin maka makamancin haka a school d'in, a hankali tako ya biyo inda yake jin sautin na tashi, jin sautin na fitowa daga JSS side, yasa mamkinsa k'aruwa sosai, bai tsinke ba sai da ya ganshi a k'ofar JSS1 class, a hankali ya shiga, ganin Sanah ta tara yara tana yi musu kid'a da wak'a, yasa shi tsayawa cike da tsantsar mamaki yana kallan ikon Allah, a ransa kuma yana mamakin wannan wacce irin yarinya ce? Sosai kid'a da wak'a ya d'auki zafi, kwata-kwata hankakin su Sanah bai kai gare shi ba, ya kai a k'alla wajen 15 minutes a tsaye yana kallan yadda Sanah ke zazzaga fitsara, while Khulud na zaune a nutse tana bin su da kallo tana murmushi, juyowar da Sanah zata yi idanta ya sauka akan Sir Moli dake tsaye hard'e da hannuwasa a k'irji, cikin wani irin mugun zafin nama ta yunk'ura da niyyar guduwa, yayi wuf ya rik'e ta, sai lokacin hankakin sauran ya kai ga Sir Moli, kowacce ta koma seat d'inta ta zaune a matuk'ar tsorace jikinsu sai kerrrrma yake, ajin yayi tsit, tsawa ya daka musu " ku dan kan uwarku tun da kuka zo makarantar nan kun tab'a ganin anyi kid'a? Duk suka ce " a'a, " wa yasa ku kid'a da rawa yanzu dan ubanku? Jikinsu na kerrrrma suka ce SANAH HAMRAZ, "Idan tace ku shiga wuta zaku shiga? "A'a, " wallahi daga yau kuka kuma yi mana kid'a school sai naci kan uwarku, yayi maganar while yana rik'e da Sanah gam a hannunsa, tuni Sanah ta soma kuka, jikinta sai kerrrrma yake, gaba d'aya tsoro ya gama cika mata ciki, ji take kamar ta saki fitsari, Khulud na zaune inda take cikin matsanancin tashin hankali da matsananciyar fargaba, kuka kawai take dan tasan yau Sanah ta shiga ukku, a fisace ya fita da Sanah, Khulud tayi saurin mik'ewa tabi bayan su, jin taku a bayansa yashi juyowa, tsayawa yayi cak ya zubawa Khulud ido, " ke koma, yayi commanding nata, shiru tayi tana kuka batare data motsa ba, ya daka mata tsawa "ke dan uw..... kasa k'arasawa gazin ta yayi, idansa ya runtse da k'arfi, kana ya bud'e yace " ki koma, cikin kuka Khulud tace " please Sir kayi hak'uri, tare mukayi laifin ni da ita, ba ita kad'ai ce tayi ba, Sanah tayi saurin cewa " no Sir banda ita, ni kad'ai ce nayi laifin, kafewa Khulud tayi akan harda ita, while itama Sanah ta kafe banda ita, kallan Khulud yayi yace " this is the last time da zance ki koma class, Sanah tace " my Ulud idan baki san nayi fushi dake to ki koma, tsawa ya daka mata "ke dan ubanki ubanwa yasa bakin ki, shegiya 'yar iska fitsararriya, yayi maganar yana matse hannunta dake cikin nashi, kamar zai karyata, tsananin azaba ne yasa Sanah sakin gigitaccen kuka,, tana tsallen wuya, cigaba da tafiya Sir Moli yayi rik'e da Sanah a hannunshi, Khulud ta tsaya a inda suka barta tana kuka, dan yadda taga idanshi, da yadda yake jan Sanah kamar zai b'alla ta, yana tafiya a zafafe kamar mahaukaci tasan yau sai buzun Sanahrta..................... . MOMYN ZARAH _*RASHIN SANI.......*_ *HAUWA A USMAN* _JIDDARH_ ```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh``` 1⃣1⃣ Har cikin office d'insa ya shigar da ita, "kneeling down, ya fad'a a tak'aice, jikinta na rawa ta d'urk'usa bisa gwiwowinta, zama yayi akan sofa, had'i da k'ura mata ido kusa 10 minutes batare dayace komai ba, a hankali ya sauke ajiyar zuciya, yace " ke wacce irin yarinya ce, mai taurin kai? Shiru tayi bata ce komai ba, "na dad'e ina tunanin halayya da d'abi'unki, me yasa baki jin magana? "Dan ubanki ke 'yar bidi'a ce? Kai ta girgiza masa, yace " ida kika kuma girgiza man kai sai na kifa miki mari, shegiya bakin magana nafiki? Da sauri tace " a'a, "ah gidan ku akwai club, ko kuna zuwa yawan club? "A'a tace, tana cigaba da kuka, "to shaid'aniya ce ke, ko shad'aici yasa ki yin kid'a? "A'a ta bashi amsa tana kuka, ganin yadda take kuka yasa shi cewa " dukanki nayi? "A'a, " to uban me kike yi ma kuka? "Bakomai ta fad'a tana goge hawayenta, "yanzu dan ubanki bidi'a kika san kawo mana makarantar, ko so kike ki lalata mana yara, ki kangarar dasu kamar yadda kike kangarariya, ko irin taki fitsarar kike san koya musu? "A'a, dan Allah kayi hak'uri ban k'arawa, "shegiya kullum maganar ki kenan, "Allah da gaske nake, ban k'arawa, " 'a'a ai dole kema ki d'and'ana dukan Moli, ya fad'a yana mik'ewa, direct kan table ya nufa ya d'auki dorinar da yake duka da ita, (bulala), Sanah na ganin ya d'auki bulala ta mik'e tsaye a kid'eme tana yarfa hannunta, kuka ta fasa masa sosai, "please kayi hak'uri Allah ban k'arawa, tayi maganar still tana kuka. Nufo ta yayi gadan-gadan rik'e da zafgegeyar bular a hannunsa, baya tayi tana yarfa hannu, dan gani take idan ya dake da bulalar hannunsa, mutuwa zatayi,, cikin kuka tace " Allah ban san duka, idan ka dokeni mutuwa zanyi, "baki san bugu amma kike iskanci da fitsara? Yayi maganar while yana takowa gare ta, "Allah na daina ban k'arawa, "k'arya kike, "Allah da gaske ban kumawa, dan Allah karka dokeni, tayi maganar tana shaking head d'inta, "ke kima yi min shiru dan wallahi sai na dake ki, gwara ma ki motsu na dake ki huta, jin ya rantse yasata increasing cry volume d'inta, cikin sanyin murya tace " yanzu duka na zakayi? Yace " kwarai kuwa ko zaki hana ne? "A'a, amma dan Allah kayi min a hankali ba mai zafi ba, "tab yau nake ganin zunzurutun rainin wayo, wato sai ma kin ban instruction d'in yadda zan dake ki? A'a, zata kuma yin magana taji saukar bulala ajikinta, da k'arfi ta saka gigitaccen kuka, lokaci d'aya ta rud'e ta kid'ime ta fita fita daga hayyacinta, ta zama kamar mahaukaciya sabon kamu, saboda tsabar tud'ewa ta cire hijabin jikinta tayi cilli dashi gefe, bata gama hucewa ba, ya k'ara zuba mata d'aya, zillo ta fara yi tana tsalle, ya kuma zuba mata biyu a jere, durk'ushewa tayi a k'arasa tana murk'usu da juye-juye, dan kwata-kwata Sanah bata k'aunar abinda zai tab'a lafiyar jikinta koyaya ne, bata san duka, duk abinda tasan muddin tayi za'a dake taba yi, idan ko taji ciwo kota yanke, duk k'ank'antar ciwon an shiga uku ranar a gidan, dan ta rink'a tsalle da ihuun kuka kenan, gata da shegen san jiki kamar mage, yanzu zata lafe a jikin mutum, a gida shiyasa tafi shiri da Aarib dan kullum tana jikinsa, idan kaga Sanah ta zauna ita kad'ai to babu mutum ne a kusa da ita, amma muddin akwai mutum duk k'ank'antarsa koda ta girmeshi sai ta lafe a jikinsa, Sanah kam akwai san jiki da shegiyar shagwab'a, tasan darajar jiki da lafiyarta sosai, sai dai akwai bakin tsiwa da fitsara, gata masifaffiya dan mafad'aciya sosai, uwa uba kuma bak'ar zuciya,, jikinta tabi da kallo taga duk inda bulalar ta sauka yayi ja, wajen duk yayi rud'u-rud'u, yayi jajir kamar garwashin wuta, shima jikin nata ya kalla, yaga wajen yayi mugun yin jajir, ganin ya d'aga hannunsa zai k'ara zuba mata, yasa ta mik'ewa da sauri ta rik'e hannunsa da k'arfi, tana tsalle "dan Allah kayi hak'uri Allah ban k'arawa, tayi maganar cikin gigitaccen kuka, bin jikinsa da ta rirrik'e shi yayi da kallo, hannunta d'aya na rik'e da hannunsa wanda ya rik'e bulalar, d'aya hannun nata kuma ta cukuikuye shi ta rik'e shi gam, ta shige jikinta ta rungume shi yadda bazai iya dukan ta ba. K'ok'arin kwace kansa ya fara yi, amma ina Sanah tayi mishi mugun rik'o, jin zai kwace kansa yasa Sanah zubewa k'asa had'i dayin ihuuuu, da k'arfi kamar yadda taga masu aljanu nayi, ta zub'e k'asa wanwar, tana k'ifk'ifta idanu, kamar gaske, idan ka ganta saika rantse da Allah aljannun gaske ta tayar, da sauri Sir Moli ya ja baya, amma babu alamar tsoro ko firgice a tattare dashi, ganin yadda take harba k'afa tana yarfa hannu kamar mai farfard'iya ya sashi fita da sauri yayi waje, Sanah na ganin ya fita ta mik'e da sauri ta dira ta window tayi hostel, anan ma tabar hijabinta, yarinya Sir Moli ya aika kira masa Halan da Khulud, sannan yayi alwala ya shiga Masjid ya d'auko Qur'an, at the same time Halan da Khulud suka k'arso, "ku biyo ni, yace a tak'aice, jikin su kerrrrma suka bi bayansa, office d'insa ya shiga kai tsaye rik'e da Qur'an, ganin babu Sanah babu dalilinta, yashi yin tsaye sororo, kan sofa ya zaune gami da dafe kansa, cikin ransa yana mamakin yadda tayi yanzu kamar gaske, dan shi tsakanin sa da Allah ya yarda da gaske ta, a hankali suka shigo, suka tsuguna gefe jikinsu na rawa, zaton su ko Sanah ta jawo musu wani abun kuma, kallan su yayi kana, yace " zan tambaye ku tabbatar kun gaya man gaskiya, dan idan na bincika naga k'arya kuka gaya man, wallahi sai naci ubanku, "to suka ce cikin fad'uwar gaba, " Sanah nada aljanu? Ya tambaye su gami da kafe su da ido dan yaga reaction d'in su, kallan juna Halan da Khulud sukayi cike da mamaki, baki suka had'a wajen cewa "aljanu kuma wanne iri? " Tambayar ku nayi, ku ban amsa bawai ku maido min tambaya akan tambaya ba, Halan data gane abinda ya faru, tayi k'asa fakai tana b'oye dariyarta, Khulud zatayi magana Halan tayi saurin cewa " a'a, gaskiya tunda muke da ita bata tab'a tada aljanu ba, amma bamu sani ba ko tana da su ko kum....... " Ba doguwar magana na tambaye ku ba, abinda na tambaye ku Sanah tana da aljanu eh ko a'a? K'asa Khulud tayi da kanta tace " a'a gaskiya bata dasu, duk wanda ya gaya kama k'arya yake ba gaskiya ya fad'a maka ba, "good yace, yana mik'ewa ya fita batare daya ce komai ba, yana fita Halan ta kalli Khulud tace " me kuma ya faru? Tass Khulud ta fad'awa Halan duk abinda ya faru tun daga farko har k'arshe, ajiyar zuciya Halan tayi tana kallan Khulud tace, "inaga fa k'aryar aljanu tayi masa danta kwaci kanta, ido Khulud ta zaro tace " what! aljanun k'arya ta tayar mishi? Halan tace " bani da tabbas amma ina tunanin hakan, dan nasan halin kayana, ajiyar zuciya Khulud ta sauke cike da tsoro, Sir Moli na fita direct Hostel get yaje da kansa ya tsaya k'ofar shiga, ya tura wata yarinyar kiran head girl, bata jima ba suka dawo tare, a tak'aice yace " duk inda Sanah Hamraz take ki nemo min ita yanzu, yayi maganar yana gyara tsaiwar shi, "Ok Sir, ta amsa, tana mik'ewa ta koma cikin hostel, Sanah na dirawa ta window tayi hostel dan tasan ba damar Sir Moli ya shigo hostel kai tsaye, tun daga k'ofar room ta fara kwalawa Halan da Khulud kira, taji shiru, tana k'ok'arin jiyawa head girl ta isa, batayi mata magana ba ta rik'e hannunta, Sanah tace " Malama lafiya, zaki zo ki rik'e ni kina ja ba wani bayani? "Kallanta Head Girl tayi cike da mamakin irin maganar da Sanah ta fad'a mata, amma sai ta dake tace " in munje can kya gani, tana jin haka ta gane sak'on Sir Moli ne, dan haka ta fara k'ok'arin turjewa, juyowa Head Girl tayi tace " wallahi zansa a d'aukar man ke aka kaiki idan baki tsaya ba, baki ta turo had'i tana cewa " sai kace wata dabba ko wani kaya, bata kula ta ba ta cigaba da janta, HG na mamakin irin halin Sanah, na rashin jin magana da taurin kai, a ranta tace " hmmmm tun tana yarinya kafin ta balaga ta zama cikekkiyar mace ma kenan, ina ga kuma idan ta girma, zan so ganin 'yan matancin yarinyar nan, dan nasa akwai ganin ikon Allah, suna isa Sir Moli ya damk'i hannunta yayi office da ita, kwata-kwata babu alamar tsoro ko firgice a tattare da ita, sai ma baki da taka buro tana harare-harare, gami da gunguni, k'asa-k'asa,, suna shiga office d'in ya saki hannunta ya zauna kan sofa,, ganin Halan da Khulud a office d'in, yasa ta runtse idanta da k'arfi, ya kalle ta yace " sakin aljanun ne ya zo? Ta bud'e ido tarr cikin nashi, ya mik'e yana d'aukar bulalar shi, dan ya fahinci tana mugun tsoron duka, tana ganin ya d'auki bulala ta zub'e k'asa tana tab'a baki zatayi kuka, hannun ya d'ora akan lips d'insa, yace " shhhhhhhhhhhh, da sauri ta had'iye kukanta, yace " kin san Allah idan baki san na doke ki toki kiran aljanunki suzo, kuka ta soma tana cewa " Allah bani da aljanu dama k'arya nayi maka danna kwaci kai na, dan Allah kayi hak'uri ban k'arawa, "shegiya ga tsoro ga iskanci da fitsara, ai 'yan iska fitsararru masu taurin kai da zafin zuciya basu saurin saduda, ban hak'uri wuya yake yi musu, "ni dai dan Allah kayi man hak'ura, Allah na daina, "ba yanzu kika gama bada wani hak'urin ba? "Amma few minutes tsakani kika kuma yin wani laifin, cikin kuka tace " please kaban last chance yanzu, idan na kuma yin laifi kayi man koma miye, wallahi I promise ban k'ara yin laifi harna ban makarantar nan, " are you sure you promise? "Yes Sir, Allah idan na kuma kayi min komai kaga dama, na yarda na d'auka, duk abinda kaga damanyi man kayi man, murmushi yayi had'i da cewa " good, and keep it in your mind,, I know one day you will pay for your promise, kai ta gyad'a masa, k'ura mata ido yayi wajen 10 minutes yana kallanta, kana yace " tashi kije while idansa na kanta, har ta kai bakin k'ofa, yace "Sanah cikin sanyin murya ya kira sunnan nata, cak ta tsaya jin karo na farko a rayuwarta ya kira ta da real name d'inta, a hankali ta juyo tana kallanshi ido cikin ido, yace " kada ki tab'a raina matsayin tsoro, lalle ki martaba matsayin tsoro, wad'anda basa jin tsoro rashin tsoron su yakan jawo musu walaha da masifa, a rayuwa, murmushi tayi tace " ya zaka ce bana jin tsoro Sir? " Bayan yanzu ma ka gani da idanta, yace " ni dai na fad'a maki, shawara ce na baki, nasan kuma ko gaba zata yi maki amfani, murmushi ta kumayi tace " thank you Sir, ido kawai ya zuba mata har suka fita, while Halan na kallan su, deep down kuma tana cike tsantsar mamaki, tana sak'e-sak'e kala-kala a ranta, komawa kan sofa yayi ya kwanta had'i da lumshe idansa, Bayan sun koma hostel sosai Halan tayi musu fad'a akan shiga case d'in teachers, ta k'ara da basu shawarwari,,, sosai jikin su yayi sanyi, Khulud ta kalli Sanah tace " please ki dai na kinji? "Allah kwata-kwata ban san yadda yake yi miki, tayi maganar wahaye na gangaro mata, da sauri Sanah ta tashi daga inda take zaune ta koma kusa da Khulud, tasa hannu tana goge mata tears d'inta, itama kwalla na taruwa a idanta, Khulud tace " please my Sanah karkiyi kuka,, kukanta ta had'iye kana tace " to please kema karkiyi kukan kinji my Ulud, wallahi bana san kukanki, bana k'aunar na ganki cikin damuwa, ido Khulud ta zuba mata tana kallan yadda duk ta marairaice saboda tana kuka kawai, cikin sanyin jiki da murya Khulud tace " my Sanah idan na mutu ya zakiyi? Sosai Sanah ta zazzaro ido waje kamar zasu fad'o k'asa,, tace " please ki bar wannan maganar, inba so kike ki tada min hankali ba, cikin sanyi Khulud tace " my Sanah kin san dukkan mai rai mamaci ne, dole dukkan mu sai mun mutu, sai mun d'and'ani zafin da rad'ad'in mutuwa, ni dai abinda nake so idan na mutu ki rink'a yi man addu'a koyaushe, ki zama mai sanyin hali, mai hak'uri da kawar da kai please, a d'an zafafe Sanah tace " kina san tada min hankali ne? Khulud tayi nodding kanta, Sanah tace " ki na san na kafa miki kuka tun daga yanzu har safe? Khulud tayi dariya tace " a'a Oga rigama, tace " to kibar maganar nan please, Khulud na dariya tace " na bari, kasancewar wannan shine 3rth term, a wannan term d'in ana mugun repeating, dan daga shi sai 1st term JSS2, yasa Sanah da Khulud dagewa da karatu sosai baji ba gani, Sanah da Khulud na tafiya, zasu koma hostel, daga area class's, Khulud ta kalli Sanah tana zaro ido had'i da ja baya, Sanah ta kalle ta tace " lafiya? Tayi maganar tana matsawa jikin Khulud, da sauri Khulud ta ja baya tana kallan Sanah a tsoroce tana nuna mata kanta, cikin tsoro Sanah tace " me? Khulud tace "k'adangare, a razane Sanah ta saki k'ara tana cire hijabin jikinta, tayi cilli dashi, sosai Sanah ke tsalle tana ihuuuuuu, Khulud ta kalle tana dariya while tana ja baya, tace " wasa nake yi, da gudu Sanah ta bita, tana dariya, itama ta kwasa da gudu tana dariya, suka shiga zage wajen, cikin matsanancin farin ciki, sai da suka gaji da zagaye wajen kana Sanah ta rik'e Khulud, rungume juna sukayi suna dariya cire da so da k'aunar junansu, abin sha'awa. _MAFARIN K'ADDARA_ Ranar Saturday dukkan su sanye cikin game were, suka nufi filin game suna tafe suna wasa da dariya, Sanah ta kalli Khulud tace " haka nan naji gaba na, na fad'uwa, Halan tace " kiyi ta maimaita innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, cikin sanyin jiki Sanah tace " to, amma wallahi sosai gaba na ke fad'uwa fa, Khulud ta dafa ta had'i cewa " karki damu kinji my Sanah? "In sha Allah babu abinda zai faru, kuma ma baga ni ba, tayi maganar tana dariya, kai Sanah ta d'aga mata cikin sanyin jiki batare datace komai ba, suna isa clubs d'in su Sanah ta koma gefe ta zauna tare da rafka tagumi hannu bibbiyu, hango ta Khulud tayi, a zaune a hankali ta nufe ta had'i da durk'usawa a gabanta tasa hannunta ta zame tagumin da Sanah tayi, tace " my Sanah meke damunki ne? "Nima ban sani ba haka nan nake ji na wani iri, tayi maganar kamar zatayi kuka, Khulud tace " in Allah ya yarda babu abinda zai faru sai alkhairi, karki damu kinji my Sanah? "To Sanah tace, Khulud ta rik'o hannunta tace " to taso muje muyi fara wasan ko, Sanah tace " a'a ban jin zan iya buga ball d'innan, ido Khulud ta zaro had'i cewa " tab! kema kin san baki isa ba, Allah sai kinyi kinji ma na rantse, salan a cinye mu yau, Sanah ta d'aga kai ta kalli Khulud tace " kiyi hak'uri amma yau banyin ball, baki Khulud ta zumb'uro had'i da zama a gefen Sanah tana tab'a baki zatayi kuka, Sanah tace " ke meye kuma na kuka? Khulud tace " Allah idan baki san nayi kuka to ki taso muje muyi ball, idan ba haka ba yau na kwana ina kuka, Sanah tayi dariya tana kamo hannun Khulud tace " shikenan tashi muje mu fara, dariya Khulud tayi tace " thank you so much my Sanah, sosai wasa ya d'auki zafi, sai buga ball suke yi, har lokacin babu 'yan b'angaren da suka ci, ganin haka ya zuciya Sanah dan haka ball d'in na shigowa hannunta, ta bugata da k'arfi, da hannu 'yar d'aya b'angaren ta tare ball d'in dan haka akayi musu fanaret, duk suka tsaya cak aka saka Sanah ta sake buga ball d'in. _Wayyo tsautsayi da k'addara_ *RASHIN SANI* yasa Sanah buga ball d'in da iyakacin k'arfinta, bisa tsautsayi sai ball d'in ta daki Khulud sosai a ciki, garin Sanah ta juya ta kuma yiwa Khulud k'afa a cikin ta, Khulud ta k'urawa Sanah ido tana daga tsaye tace " my Sana.... Bata k'arasa ba ta zube k'asa, a kid'ime Sanah ta nufi Khulud da gudu tana kiran sunanta da k'arfi Khulud!!!! saboda tsabar rud'ewa yasa Sanah mantawa ta kuma taka cikin Khulud da takalmin 'yan ball akan ruwan cikin ta, tsananin azaba ne yasa Khulud sakin mahaukaciyar k'ara, kana idanuwanta suka kakkafe numfashinta ya d'auke cak, da k'arfi Sanah ta shiga jijigata tana kiran sunanta da k'arfi cikin matsanannacin kuka, ganin bata motsi yasa Halan tafiya staffroom da gudu ta kira Malamai, da gudu su Sir Moli suka k'araso a kid'ime Moli ya kalli Khulud, yaga kwata-kwata bata numfashi, da sauri ya sunkuya kusa da ita yana tab'a k'irjinta, gami da kunnensa a hancinta, jin yayi shiru yasa Sanah sakin mahaukacin kuka ta rirrik'e shi kamar zararariya tace " meya same ta? Rik'e hannunta yayi yana kallan Sir Jeeb tare da girgiza masa kai yace " bata numfashi ina ganin kamar fa ta mut.......... Bai k'arasa ba yaji Sanah ta fad'o jikinsa, bata numfashi idanuwanta sun kakkafe............ MOMYN ZARAH _*RASHIN SANI.......*_ *HAUWA A USMAN* _JIDDARH_ ```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh``` 1⃣2⃣ A gigitacce Sir Moli ya mik'e rik'e da Sanah a hannunsa, yana jijjiga ta had'i da kiran sunanta da k'arfi, Sanah! Sanah!! Sanah!!!, duk ya rud'e ya fita hayyacinsa, jikinsa sai kerrrrma yake, yana rungume da ita, ya nufi fanfo da gudu, duk Malamai da students dake wajen tsayawa sukayi kallan ikon Allah, kanta ya tara a bakin fanfon yana jijjigata, while yana cigaba da kiran sunnata da k'arfi, ajiyar zuciya ta sauke da k'arfi ta bud'e idanta a hankali, shima ajiyar zuciyar ya sauke had'i da runtse idansa, da sauri Sanah ta mik'e daga jikin Sir Moli, dakyar tace " ina my Ulud? Sai lokacin hankalin Sir Moli ya koma ga Khulud, da sauri ya mik'e daga durk'ushen dayake, ya nufi inda Khulud ke kwance ya sungume ta yayi sick bay da ita, Sanah da Halan suka bi bayansa suna cigaba da kuka, da sauri aka kwantar da ita akan patient bed, school doctor d'in su ya fara dubata, Sir Jeeb da sauri ya fita yayi dialing number Abbu, dayake kowacce students akwai number parent ko guardians d'inta, bugu d'aya Abbu yayi picking ganin VP Roni ke kiransa, hankalin Sir Jeeb a tashe yace " Assalamu Alaikum,,, "Amin wa'alaikassalam Abbu ya amsa, bayan sun gama gaisawa, Sir Jeeb yace " Sir please kuzo makarantar yanzu, gaban Abbu yayi muguwar fad'uwa, a hankali yace " innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, lafiya dai ko? Abbu ya tambaya a k'agauce, VP yace " lafiya, amma ba lau ba, a kid'eme Abbu yace " meya faru? "Khulud Rawan ce ba lafiya, da sauri Abbu ya mik'e yana cewa " meke damunta? "Wallahi bamu sani ba amma doctor yana duba ta, "ok to gamu nan, Abbu ya fad'a yana fita, hankali tashe ya kira Didi, " hello Dide yace, cikin rawar murya Abbu yace " ka shirya yanzu zamu je Roni, a firgice Didi yace " lafiya, meke faruwa? Abbu yace " wallahi nima ban sani ba, yanzu Vice Principal d'in su ya kira ni, yace Khulud bata da lafiya, tsaki Didi yayi yana komawa kan sofa ya zauna, " yanzu dan Khulud bata da lafiya sai mun kwasa rid'i-rid'i har mu biyu munje? Yayi maganar cikin dauriya yana danne abinda yake ji, Abbu yace " please karka yi min irin halin naka nako in kula, ya za'ayi akira daga makaranta a sanar damu 'yar mu bata da lafiya amma ko a jikinka, Didi yace " to ai kai ne da wata magana, saboda bamu da aikin yi sai mu tafi Roni har mu biyu dan Khulud bata da lafiya, kai ma da zaka ji tani da bazaka je ba, Abbu yace " idan ban je ba waye zaije? Didi yayi shiru, Abbu yace " ai bama ni kad'ai zani ba, " kai da wa zaka je? " Ina ruwanka tunda kai dai baka zuwa shikenan, Abbu ya kashe wayarsa yana mamakin kara da kawaici irinna Rawan, Didi ko yana jin Hamraz ya kashe waya, ya kwantar da kansa akan sofa had'i da runtse idansa, dan Allah ya sani yana mugun san Khulud, duk cikin yaransa babu kamarta, yafi santa fiye da kowa, kawai dai yana kara da kawaici ne saboda tsakaninsu da Hamraz, kuma Hamraz yana iyakar bakin k'ok'arin sa wajen tsayawa iyalin su akan komai, ko kayan abinci da school fees kafin shi ya biya sau d'aya, Hamraz ya biya sau goma, haka ma a b'angaren cefane, da kula da iyayen su komai Hamraz keyi bai jiransa, saboda akwai so, k'auna, sabo da matsananciyar shak'uwa a tsakanin su, tun suna yara suka taso da san junun su, kamar yadda suka ga Ganez da Danish na san junan su har yau har gobe. Juju dake kitchen tana girkin abinci, ta fito da sauri,yadda taga yanayin Didi ya canja ne ya tabbatar mata ba lafiya, a hankali tace " lafiya Dide? Shiru yayi bayyi magana ba, komawa tayi kitchen ta rage wutar girkinta sosai, kana ta dawo, ta zauna a kusa dashi, cikin sanyin jiki ta dafa kafad'arshi, tace " lafiya, meke faruwa? Ta kuma tambayarshi a karo na biyu, ganin bashi da niyyar yin magana ne, yasa ta tausasa muryata k'asa-k'asa tace, koma me ke damunka kayi addu'a, sai Allah ya sausauta maka shi, ya kuma yi maka maganin matsala da damuwarka, ko kayi ta maimaita, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, tana kaiwa nan ta mik'e cikin sanyin jiki zata bar wajen, tausayinta ne ya kama shi, dan haka yayi saurin rik'o hannunta, yace " Khulud ce bata da lafiya, yanzu Abbu ke sanar dani Vice Principal d'in su ya kira shi, " meke damunta? Ta tambaye shi, " ban sani ba, dan ni ko tambayar Abbun ma ban tsaya yi ba, shiru tayi had'i da k'ura masa ido, kana tace " Allah ya sauke, Ubangiji ya bata lafiya, "Amin yace yana kallan kwayar idanta, murmushi tayi masa kana tace " kasan dai yanzu ba 'yar mu bace, sai dai muyiwa Abbu da Mamu jaje, dan nasan yanzu haka ma suna cikin tension, tayi maganar tana dariya, danta kwantarwa da Didi hankalinsa, dariya yayi shima kana yace " kamar ko kin sani, ke kinji yadda Abbun ya kira ni a kid'ime wai in shirya zamu Roni, dariya tayi, zatayi magana sai kuma tayi shiru, cikin alamun jimami tace " Sanah fa? Dide yace " me? Tace " Allah sarki 'yata Sanah, Allah kad'ai yasan cikin mawuyacin halin datake ciki yanzu, cikin jimamin shima Dide yace " wallahi kuwa, nasan yanzu tana can cikin tashin hankali da kuka, ni nama fi jin tausayin Sanar akan Khulud, murmushi Juju tayi ta mik'e tace " bari na dubo abinci, Mamu dake tsaye bakin k'ofa, ta share hawayenta, ta juya ta koma part d'in su. Abbu na kashe waya ya kira Ziyad, Zafran ya sanar da su, batare da wani b'ata lokaci ba, suka d'au hanyan Roni, Ziyad na driving, Zafran na gefensa, Abbu yana baya, sai da suka hau hanya sannan Abbu ya kira Mamu ya sanar da ita, sosai hankalinta yayi masifar tashi, ta nuna masa kamar bata sani ba. A makaranta ana ta faman k'ok'arin maido da numfashin Khulud, amma kwata-kwata babu alamar dawowarsa, wata irin gigitacciyar k'ara Sanah ta saka, had'i da fasa kuka ta fad'a jikin Khulud ta rungume ta tana ihuuun kuka, " please my Ulud ki tashi, kinyi man alk'awarin duk abinda nasaki zakiyi, idan kuma na hana ki zaki bari, dan Allah ki tashi, wallahi idan kika mutu nima mutuwa zanyi, bazan tab'a rayuwa cikin farin ciki da walwala ba, matuk'ar baki tare dani, a hankali tasa hannu tana marin kuncin Khulud a hankali, tana cewa " ki tashi kince bazaki ta tab'a rabuwa dani ba, kince tare zamu girma muyi aure, dan Allah ki tashi my Ulud, nayi miki alk'awarin bazan tab'a barinki cikin k'unci da matsalar rayuwa ba, nayi miki alk'awarin bazan tab'a barinki cikin damuwa da masifa ba, nayi miki alk'awarin zan zame miki garkuwa daga dukkan matsalolinki, zan zame miki maganin dukkan damuwa da k'uncinki, dan Allah ki tashi ta k'arasa maganar cikin rikitaccen kuka tana d'ora kanta akan k'irjin Khulud, duk wanda yaga yadda Sanah ke kuka tana magana tana jijjiga Khulud abin sai ya bashi tausayi komai rashin imanin mutum, sai yaji zuciyarsa ta karyae, Halan na gefe na aikin kuka, Sir Jeeb zaune kan sofa ya zuba musu ido cike da tausayin Sanah. A hankali Sir Moli ya d'ago pure red eyes d'insa ya kalli Doctor yace " wai ya ake ciki ne har yanzu shiru? Doctor yace " hmmm gaskiya ciwon babba ne dan ko numfashi batayi, Sanah ta k'ara sakin rikitaccen kuka, Sir Moli yace " kamar ya? " gaskiya koma me ke damun yarinyar babban ciwo ne, Sir Jeeb yace " wai har yanzu baka gano ciwon ba? " Eh, ban san takaimaiman abinda ke damunta ba, ni fa ina ganin mutuwa zatay........ gigitacciyar k'arar da Sanah ta kwalla ce ta hana Doctor k'arasa abin da yayi niyyar fad'a, a gigice ta mik'e tsaye had'i da d'ora hannu aka tana rikitaccen kuka mai ban tausayi, " a'a wallahi na tabbatar Khulud bazata tab'a mutuwa ta barni ba, ko ita kanta mutuwar zataji kunyar d'aukar Khulud a gaban ido na, kuma koda mutuwar ce da gaske tazo nasan Khulud zatayi iya k'ok'arin ta na ganin bata tafi na barni ni kad'ai ba, tayi maganar a matuk'ar rud'e, gaba d'aya ta fita hayyacinta, ta kid'ime ta fita fit daga hayyaci da nutsuwarta, jikinta sai rawa da kerrrrma yake, ganin yadda ta rud'e ne yasa Sir Moli dakawa Doctor tsawa " kai baka da hankali ne, baka san aikin ba ne? Yayi maganar a tsawace, da sauri Doctor da Sir Jeeb suka kalle shi cike da mamaki, da saurinsa ya rik'e Sanah ya sunya hannu a hankali yana goge mata hawayenta, cikin sanyin murya yace " kiyi hak'uri Khulud bazata mutu ta barki ba kinji? Kai ta d'aga masa, " ki rink'a yi mata add'u, ki dai na kuka, tunda kinga bata san kukan ko? Ta kuma d'aga masa kanta a hankali, " magana zakiyi kinji ban san nodding kai, da sauri tace " na dai na, ban k'arawa, ya shafa kanta yace " yawwa good girl, cikin sanyin murya ta kuma cewa " bazata mutu ba ko? Tayi maganar hawaye na gangaro mata, cike da tausayinta ya d'aga kai, " ka tabbatar zata tashi? Ta kuma tambayarsa, " in sha Allah, ya bata amsa, bazato yaji ta fad'a jikinsa tana cewa " thank you so much Sir, tayi maganar tana k'ara shegewa jikinsa, murmushi yayi yana k'ok'arin zame jikinsa daga nata, da sauri ta k'ara matseshi, tana cewa " I will never forget you in my life, yayi murmushi kana yace " are sure? " Yes , tace tana cigaba da kukanta, a hankali ya zame jikinsa, duk da tana k'ok'arin k'ara shigewa jikin nasa, ya mik'e yana kallan Sir Jeeb,, da mamaki ya gama kashe shi a tsaye, ba Sir Jeeb kad'ai ba, duk wanda ke wajen yana cike da tsantsar mamaki da al'ajabi, ya lura sarai da reactions d'in su amma ya basar, ya tamke face yace, " ka kira gidan nasu kuwa? "Eh na kira su tun d'azu ma, Sir Moli ya kuma cewa " tun yaushe ka kira su? " Tun wajen 2 hours back, yaci ace sun iso ma, yayi maganar yana duba agogon hannunsa, " ka k'ara kiran su please, asan abinyi tun da wuri, "ok yace yana ciro wayarsa daga aljihu, yana k'ok'arin kiran su, kiran Abbu ya shigo, da sauri Sir Jeeb ya d'aga, Abbu yace " gamu mun k'araso muna bakin get, kana ina? Da sauri Sir Jeeb yace " gani nan zuwa, ya kashe wayar yana kallan Sir Moli, yace " sun k'araso fa, Sanah dake zaune bakin gadon da Khulud ke kwance ta d'ora kanta saman chest d'inta, ta k'ara runtse idanta hawaye na zubowa. Da sauri Sir Jeeb ya fita ya tari su Abbu, hannu Sir Jeeb ya mik'awa Abbu had'i da d'an risinawa, "Assalamu Alaikum, sir Jeeb yace, fuskar Abbu d'auke da murmushi ya amsa, Sir Jeeb yace " muje office, "Ok cewar Abbu yayi gaba, Ziyad da Zafran na bin su a baya, zama Abbu yayi a kan kujerar dake fuskantar Sir Jeeb, ajiyar zuciyar ya sauke kana yace " please Sir kuyi hak'uri bamu san meya faru ba, muna staffroom Halan ta zo ta kira mu, saboda yadda hankalin mu yake a tashe bamu tsaya tambayar abinda ya faru ba, Abbu yace meya same ta? " Har yanzu Doctor yana kanta, ba'a gano takaimaiman abinda ke damunta ba, "tana ina yanzu? Mik'ewa Sir Jeeb yayi yace " muje, duk suka mik'e suka bi bayansa, da sallama Abbu ya shiga cikin sick bay, duk Malaman dake wajen suka amsa, ganin yadda idanuwan Khulud yayi fari fat, babu alamar bak'in kwayar ido, ga idan ya kakkafe yayi masifar d'agawa su Abbu hankali, da sauri suka nife ta, Abbu na cewa " Subhanallah, hannun sa na rawa ya d'ago Khulud yana jijjiga ta had'i da kiran sunanta, Ziyad da Zafran kasa motasawa suka yi daga inda suke tsaye, zuciyar su ta karye sosai, sun shiga rud'u da tashin hankali, Abbu ya d'ago ya kalli Doctor da idanuwansa da suka gama zama yin jajir, muryarsa na creaking yace " please Doctor meke damunta? "Nayi iyakar bakin k'ok'arina wajen gano abinda ke damunta amma na kasa, Doctor ya fad'a cikin sanyin murya, a hankali Abbu yasa hannu ya d'ago kan Sanah dake ta kuka kamar ranta zai fita, d'agowa tayi ta kalle shi had'i da k'ara fashewa da rikitaccen kuka, tace " Abbu na kashe my Ulud da kai na, ni da kai na buga ball, na kuma naushe ta a cikinta, sannan na taka ta da takarmin 'yan ball a cikinta, dan Allah ka bata hak'uri kace mata tashi ban k'arawa,, *_RASHIN SANI_* ne yasa ni yin hakan, wallahi Allah Abbu ban sani ba na buge ta na kuma taka ta, ni da kai na yiwa kai ma illa, ni da kai na, na kashe my Ulud, ni da kai na, na illata rayuwa ta da zuciya ta, bazan tab'a yafewa kai na ba, bazan tab'a sake tsintar kai na cikin farin ciki da walwala ba, bazan tab'a sake dariya da murmushi ba, har na mutu, duk wani abu na jin dad'in duniya da walwala na haramtawa kai na har abada, ko aure bazan tab'a yi ba Abbu, ta d'ago hannunta da k'afarta tana yi musu wani irin kallo, kana tace " bazan tab'a yafe muku ba, mutuk'ar my Ulud ta mutu sai na azabtar daku, sai na azabtar da kai na rayuwa ta, azabtarwa mai rad'ad'i, ta k'arasa maganar cikin matsanancin kuka, mai cin rai. Kanta Abbu ya shafa, kwalla na taruwa a idansa, kana yace " ba laifinki bane Sanah, da sauri ta d'ago kanta ta kalle shi, tace " Abbu laifin waye idan ba laifi ba? "Wallahi Abbu ni da kai na, na buge ta na kuma taka ta, a kan ruwan cikinta, tayi maganar kamar zararriya, " k'addara ce tasa faruwar hakan, karki d'orawa kanki laifiin kinji Sanah? Zata yi magana Abbu yayi saurin mik'ewa had'i da sungumar Khulud, da sauri su Ziyad da sukayi mutuwar tsaye suka tare shi, jikin Zafran na rawa ya karb'i Khulud daga hannun Abbu, jikin Sanah na rawa ta mik'e tabi bayan su, saboda sauri har tana tuntub'e, cike da tsantsar tausayinta Sir Moli ya bita da kallo har suka fita, kishingid'a yayi akan sofa had'i da lumshe idanuwansa,, kafin su fito har Halan tasa Juniors sun fito musu da kayan su kaf, babu abinda ta bari, ko tsinke, Ziyad ya bud'e bayan boot ya saka gaba d'aya kayan. A baya Sanah ta ke bin su Abbu tana sauri harda tuntub'e, Sanah na zuwa dai-dai flowers, dake zagaye da staffroom taji wani abu ya fad'o mata a jikinta, d'aga idan da zatayi taga............ MOMYN ZARAH _*RASHIN SANI.......*_ *HAUWA A USMAN* _JIDDARH_ ```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh``` 1⃣3⃣ D'aga idan da zatayi taga k'aton k'adangare (jangwali gwada), ai kota tayi muguwar tsorata, a rud'e ta nufi Zafran tana tsalle had'i da ihuuu, ganin katon koren k'adangaren dake jikinta yasa shi yin baya, shima a rud'e, saboda shima yana mugun tsoron k'adangare, a kid'ime take binsa yana yin baya shima, ga k'adangaren ya mak'ale mata, da rud'e ta cire hijabinta tayi wurgi dashi, tana cigaba da kukanta da tsalle, ganin Zafran na ja da baya ga k'adangaren na neman shigewa cikin rigarta, ya sata d'aga murya da k'arfi a matuk'ar rud'e tace " SIR MOLI! SIR MOLI!! SIR MOLI!!!, dan girman Allah ka taimakeni zan mutu, Sir Moli na kishingid'e lumshe da ido akan sofa cikin office d'inta, ya jiyo muryarta tana kwala mishi kira, da sauri ya bud'e idannasa, had'i da kasa kunne dan jin da gaske ko gizo muryarta ta keyi masa, da k'arfi ya kuma jin Sanah tace " please Sir Moli zai shiga cikin riga ta kazo da sauri, a mugun kid'ime ya mik'e ya fita ko takalmi bai sanya ba,,,, lokacin daya isa tana gaf da cire rigar jikinta, wani irin wawan tsalle Sir Moli yayi, wanda shi kansa bai tab'a tsammanin zai iya yin irinsa ba, bisa gwiwowinsa ya isa gabansa a durk'ushe ita kuma tana tsaye, tana kuka da tsalle, tana yarfa hannuwanta idanta sunyi jajir duk ilahirin jikinta kerrrrma yake, gami da tsuma, a zabure yasa hannu yayi saurin gyara mata rigar jikinta, gudun karta k'arasa cireta a gaban mutane, sannan ya fusge k'adangaren yayi jifa dashi, kai da ganin yadda yayi jefa dashi kasan yana mutuk'ar jin haushin shi, yana daga durk'ushen a gabanta ya d'auko d'ankwallinta, ya d'aura mata, ya maida mata hijabinta jikinta, kumatunta ya d'an tab'a a hankali yana murmushi yace " karki k'ara k'ok'arin cire kaya a gaban mutane kinji ko? Ta d'aga kai a hankali hawaye faca-faca a fuskarta,,, tunowa da tayi baya san d'aga kai yasa cewa " to ai tsoro nake ji tayi maganar a hankali, idansa na kanta, while yana murmushi yace " ki zama d'aya daga cikin matan da ko kashe su za'ayi bazasu tab'a bayyanar da tsiraicin su ba, bazasu tab'a zubar da k'ima da mutuncin su ba, idansu sark'e cikin na juna tace " meye k'ima? Murmushi yayi yana shafa kanta yace " k'ima da mutunci duk abu d'aya ne, kuma abu ne daya fi komai mahimmanci a rayuwar d'an Adam, muddin akace mutum bashi da k'ima da mutunci dashi da dabba duk d'aya suke ba zai tab'a zama cikekken mutum ba, cikin sanyin murya tace " to ya za'ayi ni ma na zama mai mutunci? "Kina san ki zama mai mutunci? Ya tambaye ta idansa na kanta, "Eh tace, yace " meyasa? "Saboda naji kace duk wanda bai da su, dashi da dabba duk d'aya, murmushi yayi kana yace " ki zama mace mai kunya, daraja, tausayi da jin k'ai, mai jin magana da d'aukar gyara, ki zama mai k'an-k'an da kai, mai karrama mutane, mai gaskiya da amana, mai tsoran Allah, mai addini, mai suturta jikinta wacce tasan darajar kanta da jikinta, ki zama salihar mace, wacce iyaye, ahalinta da 'yan uwanta zasu yi alfahari da ita, su kuma samu kwanciyar hankali da nutsuwa a duk inda take, ido kawai ta zuba masa bata ko k'iftawa, har ya kai aya sannan tace " ya za'ayi na iya duk wad'annan? " Kiyi yak'ini a zuciyarki cewar zaki iya, karki tab'a zama mutum marar kwarin gwiwa, ki sawa ranki da zuciyarki, zaki iya cimma duka burikanki, duk abinda kikaga mutum bai yi ko ya iya ba, bashi da yak'ini ne, a hankali tace " yak'ini? "Meye kuma yak'ini? Murmushi ya kuma yi kana yace " gaskatawa, yarda da tabbatarwa duk suna cikin yak'ini, shiru tayi tana kallansa kana tace " duk wad'annan abubuwan d'aya suke nufi? "Eh yace yana kallan kwayar idonta, Abbu, Ziyad da Zafran suna tsaye cike da tsantsar mamaki suna kallan ikon Allah, shi Abbu mamaki d'aya yake yi, yadda duk jama'a da Malaman su dake wajen bata nemi taimakon kowa ba, sai na wanda baya wajen, bayan a wajen har da shi kansa mahaifinta, ga Ziyad, da Sir Jeeb, amma babu sunan wanda ta kira sai na MOLI, kanta Sir Moli ya shafa yace " bye, juyawa tayi ta nufi mota, har ta d'ora k'afarta zata shiga motar, ta juyo bisa mamakin kowa sai akaga tayi murmushi akaro na farko tun bayan faruwar abun tayi murmushi,, cikin sanyin murya tace " nagode sosai, bazan tab'a mantawa da alkhairin daka yi min ba, thank you so much, tayi maganar tana murmushi, murmushi kawai yayi mata batare dayace komai ba, motar ta shiga ta zauna, ta d'auki kan Khulud ta d'ora akan cinyarta, Abbu na gaba Zafran na driving, Ziyad na baya yana rik'e da hannun Sanah, Halan bata bar wajen ba har sai da motar su tabar harajar makarantar, shima Sir Moli yana nan durk'ushe bai motsa ba har suka fita daga get, a hankali ya d'aga kansa sama had'i da lumshe ido, duk Malaman suka yi jugum-jugum suna kallan ikon Rabbi. A mota babu wanda yake cewa komai, kowa da abinda yake sak'awa a ransa, shi dai Abbu Sir Moli ne ya tsaya masa a ransa, musamman yadda ya lura akwai sabo tsakaninsa da Khulud da Sanah, dan yadda Sanah ta kira sunanshi ta nemi taimakonsa shi kad'ai bayan tarin mutanen dake wajen ya tabbatar masa da hakan, kuma tunda suka je baiga yayi magana da kowa ba sai Sanah, kuma kallo d'aya zaka yi masa kasan yana cikin tension, saboda ya hango wani abu a cikin kwayar idansa, a hankali Abbu yace " Sanah waye wannan? Cikin muryar kuka tace " wa Abbu? Yace " Sir Moli, hawayen dake zubo mata ta goge kana tace, "Malami ne a makarantar amma mu baya d'aukar mu,, ba permanent teacher bane service yazo, Abbu yace " daga gani yana da sauk'in kai da tausayi, gashi nutsatstse, shiru Sanah tayi bata kuma cewa komai ba, dan ita kad'ai tasan me take ji a ranta, ita kad'ai tasan irin zafi da k'unar da zuciyar ta keyi mata. A harabar Aminu Kano Teaching Hospital suka yi parking, dan Abbu yace wannan babban case ne yafi k'arfin private Hospital, dole sai babban asibiti inda manyan Doctors zasu duba ta, sai dai idan matsalar ta wuce nan su tafi Germany 🇩🇪, suna yin parking Abbu ya fito da sauri ya shiga ciki, bai shima ba ya fito tare da Doctors biyu da Nurse's hud'u, d'auke da gadon d'aukar marasa lafiya, da sauri aka d'auki Khulud, Sanah tayi saurin fitowa tabi bayansu hannunta cikin na Khulud tana cigaba da kukanta, suna isa k'ofar Emergency room, Doctor ya kalli Sanah yana dariya yace " Mrs Cry sake ta zamu shiga ciki, jin abinda Doctor d'in yace ya sata sakin gigitaccen kuka, " ni Allah ban rabuwa da Khulud sai dai mu shiga tare, Doctor ya kalle yana murmushi yace " ina ai ba zai yiyu ba, tana kukan ta fara buga k'afa " Allah ba mai raba ni da Khulud, salan a fito ace man ta mutu, Doctor yace " a'a ba wanda zai ce miki ta mutu in sha Allah, sai dai ayi miki albishirin ta warke, " ni dai a'a tace kana cigaba da kuka, dai-dai lokacin su Abbu suka k'araso, jin yadda ake ta fama da Sanah ya sashi hasala ya daka mata tsawa " ke badake ake ba? Sosai Sanah ta rikice jin tsawar Abbu ta saka rikitaccen kuku, kallan Abbu Doctor yayi yana girgiza masa kai yace " no Alhaji, ba haka ake yiwa yaran dake cikin matsala da damuwa ba, a hankali Doctor ya durk'usa a gabanta kana yace " kina san Khulud d'inki ta samu lafiya? Da sauri ta d'aga kanta, yace " kin tabbatar? Ya kuma tambayar ta, ta d'aga masa kanta a karo na biyu, yace " to matuk'ar kina san ta samu lafiya ku cigaba da wasa tare ki bari a duba ta, cikin rawar murya tace " to na bari, murmushi Doctor yayi had'i da goge mata hawayenta yace " ki dai na kuka kiyi mata addu'a kinji? " To tace, mik'ewa yayi yana k'ok'arin shiga emergency room, da sauri Sanah ta rik'o hannunsa tace " ka tabbatar My Ulud zata tashi bazata mutu ba? Tayi maganar cikin wani irin yanayi mai ban tausayi hawaye na zubo mata, wanda hakan yayi masifar saukarwa da duk jama'ar dake wajen tsananin tausayinta, a hankali Abbu ya goge hawayen dake k'ok'arin zubo masa, ido kawai Doctor ya zuba mata batare daya iya furta koda kalma d'aya ba, ta kuma cewa " dan Allah kayi k'ok'arin ceto min rayuwarta idan ba haka ba nima mutuwa zanyi, kai ya jinjina yana shafa kanta yace, "da yardar Allah nayi miki alk'awarin zanyi iyakar bakin k'ok'arina, murmushi tayi masa hawaye na zubo mata tace " nagode. Gefe ta koma ta rakub'e a k'asa tana cigaba da kuka, abin gwanin ban tausayi, Abbu ya ciro waya ya kira Mamu bugu d'aya tayi picking, bayan sun gama gaisawa Abbu yace " muna Aminu Kano b'angaren accident and Emergency, kuma nasan kwantar da mu za'ayi, da sauri tace " ok ganin zuwa yanzu, me za'a kawo muku? A tak'aice Abbu yace " duk abinda ya kamata, "ok tace tana mik'ewa da sauri, Abbu yana kashe wayar Mamu ya kira Didi, bugu d'aya yayi picking yana dariya yace " Abbun patient, fuska Abbu ya b'ata kana yace " muna Aminu Kano b'angaren accident and emergency idan kana iya zuwa, Abbu na fad'ar haka ya kashe wayar, murmushi Didi yayi yabi phone d'in da kallo, kana ya kira wayar Juju, yace ta shirya yanzu zasu je Hospital, tace " aiko yanzu Mamu ta kira ni tace na shirya zamu tafi, yace " ok to mu had'u acan. Da sauri Didi ya k'araso inda Abbu yake, duk fushin da Abbu yake yi da Didi yana ganin shi yaji zuciyarsa tayi sanyi, yaji duk zafin ransa ya gushe, yaji bai iya yi masa komai, Abbu ya kalli Didi yace " wato dan kaga bana iya yin dogon fushi dakai shiyasa kake man san ranka ko? Didi yayi dariya yace " ai ni ban ma iya fushin dakai koda wada ne, bama dogo ko gajere ba, kuma nasan ai zakayi fiye da abinda ni zanyi, Abbu zayyi magana Mamu da Juju suka shigo, da sauri Mamu ta k'arasa tana tambayar ina Khulud, Abbu yace "tana Emergency room, shiru Mamu tayi tana safa da marma, Juju ta kalle Abbu tace " Sanah fa? Murmushi yayi kana ya nuna mata inda Sanah ke rakub'e a k'asa tana kuka, har ta fara fita daga hayyacinta, " Subhanallah Juju ta fad'a tana nufar Sanah, d'ago Sanah Juju tayi ta rungume had'i da bubbuga bayanta, Sanah ta saka gigitaccen kuka, jikinta sai kerrrrma yake yana tsuma, tace " Juju na kashe my Ulud da kai na, Juju dan girman Allah kice mata ta tashi karta tafi ta barni, idan ta tafi ta barni bazan tab'a jin dad'in rayuwar duniya ba, tayi maganar a matuk'ar firgice, a hankali Didi ya k'araso wajen, ya zauna kusa da Sanah, shida Juju suka saka ta a tsakiya, ta kalle shi bakinta na rawa tace " Did..... bai bari ta k'arasa ba ya jawo ta jikinsa ya rungumeta, yana shafa kanta, batare dayace komai ba. An kai wajen 3grs kana Doctors suka fito, da sauri Abbu da Mamu suka nufe su, Sanah ma tayi sauri kwace kanta daga jikin Didi duk da yana k'ok'arin k'ara matseta a jikinsa, Doctor bai kalli su Abbu ba, gaba d'aya hankalinsa nakan Sanah, dan koda yana duba Khulud gaba d'aya hankalinsa na wajen Sanah, dan mugun tausayin ta yaji ya kama shi, a hankali ya durk'usa kusa da ita yana murmushi, ido kawai Sanah ta zuba mishi ta kasa cewa komai, yace " Alhamdulillah babu abinda ya samu Uludin ki, gogon suma ne kawai tayi, sai numfashinta dayake sneezing, amma munyi mata allura mun saka mata Oxygen dan numfashinta ya dawo normal, jikin Doctor d'in Sanah ta fad'a ta lumshe idanta hawaye na zubo mata, "thank you so much Doctor, dariya yayi yace " ki godewa Allah, tace " Alhamdulillah, a gadon tura marasa lafiya aka fito da Khulud d'aure da k'arin ruwa da Oxygen, d'aki aka kaita, d'akin mai kyau akwai bed, sofa toilet & bathroom, wardrobe, da sauri Sanah ta zauna a bakin gadon ta d'ora kanta akan k'irjin Khulud tana cigaba da kuka, abin tausayi, Mamu ce ta zauna ta kwana dasu. Har washe gari Khulud bata farfad'o ba, al'amarin dayayi masifar d'agawa Sanah hankali kenan, ta rink'a kuka tana jijjigata Khulud tana kiran sunanta, "please my Ulud ki tashi, dan Allah ki tashi, karki mutu dan Allah, tana maganar cikin matsanancin kuka, Mamu dake gefe zaune akan sofa cike da tausayin 'ya'yan nata, ta mik'e a hankali ta nufi inda Sanah take kwance akan Khulud tana kuka tana kiran sunanta, Mamu ta rungume su duka, kana tacewa " Sanah jeki alwala kiyi sallah ki rok'i Allah yabawa Khulud lafiya, da sauri Sanah ta d'ago fuskarta dake cike da hawaye tace " Mamu idan nayi addu'a zata warke? Mamu tace " Addu'a ai maganin komai da komai ce Sanah, duk abinda ya damu musulmi koya shige masa duhu, ko mutum ya shiga matsala da damuwa idan yayi addu'a ya rok'i Allah, sai Ubangiji yayi masa maganin matsalarsa, ya kuma yaye masa damuwarsa, ya kawo masa mafita, baki ganin 'yan kowanne addini suna addu'a wa abinda suke bautawa, dan haka ki rik'e addu'a Sanah aduk halin da kike ciki, idan kika dage da addu'a sai Allah ya kawo miki d'auki, ya shiga cikin lamuranki, ki zama mutum mai zafin addu'a da addini, wallahi sai kinfi k'arfin komai da kowa dake duniya, sai kin zama gagara badau, sai kin zama murucin kan dutse, ko aljani da mugayen mutane sai kin gagare su, Annabi (S.A.W) yace " الدعاء سيف المؤمنين, Allah maji rok'on bayinsa ne, mai kuma amsa addu'ar su, musamman addu'a daga bakin yara k'anana wad'anda basu balaga ba, cikin sanyin jiki Sanah ta mik'e tace " Mamu zanje nayi alwala nayi ta Sallah da addu'a bazan daina ba har sai my Ulud ta farfad'o, murmushi Mamu tayi mata kana tace " yauwa good girl. Alwala Sanah tayi ta d'auko prayer mat & Qur'an, hislin muslim a inda Mamu ta aje, sallah tayi raka goma sallama biyar, kana ta bud'e hislin muslim tayi addu'a sosai, ta aje ta d'auki Qur'an ta fara karanwa a fili muryarta na rawa irin ta masu kuka, Abbu, Didi da Juju suka shigo tare d'auke da food flask na breakfast, tun daga bakin k'ofar shiga d'akin suka jiyo muryar Sanah tana karatun Qur'an cikin kuka, akan Sofa Abbu da Didi suka zauna Mamu na zaune a bakin gadon Khulud, bayan sun gama gaisawa, Didi ya kalli Sanah yace " aje karantun kizo kiyi breakfast, bata ko kalli inda yake ba taci gaba da karatunta, babu yadda Didi da Juju basu yi ta aje ta karya ba amma bata ko kalle su ba, Didi da Abbu suka fita tare suka bar Juju da Mamu, tun asuba Sanah ke karatu tana addu'a har akayi sallar azhur, alwala kawai ta tashi tayi, ta dawo ta cigaba da karatun Qur'an da addu'a, haka ma da akayi sallar alasur, sau biyu Doctors na shigowa suna ganinta, duk wanda yayi mata magana bata kallansa balle ta amsa, sosai Sanah ta burge Doctors da Nurses d'in dake shigowa ta kuma k'ara basu tausayi. Da daddare Abbu da Didi suka shigo d'auke da basket na abinci, lokacin Doctor da Nurses sun shigo duba Khulud, da sauri Didi ya turje ganin yadda suka bar Sanah tun safe haka suka dawo suka same ta, Didi yace " Sanah lafiyarki kuwa? Bata kalle shi ba ta cigaba da karatunta tana kuka, Doctor ya kalli Dide da Abbu, Juju & Mamu yayi murmushi yace " wallahi duk inda kayi yau a cikin Hospital d'in nan maganar Sanah kawai akeyi, Abbu yace " ikon Allah, Juju tace " duk yau fa ko ruwa bata sha ba, duk suka yi jugum-jugum, Doctor yayi musu sallama ya fita cike da sha'awar halayyar Sanah, _Ni ko nace hmmmm Doctor baka san Oga Sanah bane, ruwa ne ya k'arewa d'an kada, kaje ka tambayi Sir Moli wacece Sanah Hamraz_ Allah maji k'oron bayinsa, wajen 11:00pm na dare, Doctor ya shigo ya duba Khulud, bayan ya gama dubata ya kalli inda Sanah ke zaune har lokacin tana addu'a, yayi murmushi ya bud'e baki zayyi magana, suka ji muryar Khulud na salati, sai da tayi salati sau uku a jere, kana ta kira sunan Allah, sai kuma tad'anyi shiru, duk d'akin aka rasa wanda zayyi magana balle kwakkwaran motsi, har shi kanshi Doctor d'in, da k'arfi suka ji Khulud tace............... MOMYN ZARAH _*RASHIN SANI.......*_ *HAUWA A USMAN* _JIDDARH_ ```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh``` 1⃣4⃣ Da k'arfi suka ji Khulud tace " My Sanah!!!!, Sanah dake ta faman karatu bata san wainar da ake toyawa ba, sai jin muryar Khulud datayi tana kiranta, da sauri ta juyo da kanta ta kalli inda Khulud ke kwance, dan ta tabbatarwa da kanta abinda kunnawanta suka ji ye mata, ganin da gaske Khulud d'ince yasa ta yin sujdul shukru , tana hawaye ta shiga gode ma Allah, da sauri Mamu ta nufe ta tana kiran sunnata, "Khulud kin tashi? Taba ko kalli inda Mamu take ba, gaba d'aya hankalinta yana wajen Sanah, Doctor tsaye yayi yana kallan ikon Allah, yadda suka yi ta faman k'ok'arin ganin Khulud ta farfad'o amma abu ya gagara, amma sai gashi lokaci d'aya ta farka, Abbu ya k'arasa inda Khulud ke kwance tana kallan Sanah , ya shafa kanta yana murmushin jin dad'i yace " Alhamdulillah Khulud kin tashi? Kwata-kwata hankalinta baya kan gaba d'aya jama'ar dake wajen, balle ma tasan abinda suke yi, gaba d'aya hankalinta yana kan Sanah, a hankalinta Sanah ta d'ago daga sujdar , ta tako inda Khulud take,hawaye na cigaba da zubowa daga idanta, ta k'urawa Khulud ido, da k'arfi ta fashe da kuka gami da fad'awa jikinta, itama Khulud kukan ta saka a hankali tace " my Sanah ki daina kuka, tayi maganar dakyar, murmushi Doctor yayi kana ya k'araso bakin gadon, idansa nakan su, yace " Mrs Cry zan duba ta, yayi maganar cikin tsokana, baki Sanah ta turo kana tace " tafa warke, cikin dariya yace " to fa Doctor Sanah, wato ke har kin san ta warke ko? Bata bashi amsa ba,ta kalli Khulud tace " ai kin warke ko my Ulud ? Dariya itama tayi tace " eh my Sanah babu abinda ke damuna, Doctor ya kalli Sanah yace " naga alamar dai baki san ta warke sosai yadda zaku koma gida da wuri ko? " Ina so mana ta fad'a cike da k'uruciya, yace " to idan kina so ki bari a duba ta, batare data ce komai ba,ta matsa ta koma gefe , aune-aune da d'an gwaje-gwaje yayi, kana ya d'ago kai ya kalli Khulud yace " akwai inda ke miki ciwo? A'a, ta bashi amsa, "babu inda ke miki ciwo ko zafi, ya kuma tambayarta idansa na kanta , dan ya tabbatar da abinda zata fad'a, " eh ta fad'a itama tana kallanshi, yace " kiyi tunani dai kinji our Khulud yayi maganar cikin wasa, dariya tayi,kana ta d'anyi shiru alamar tunani, "babu ,ta kuma bashi amsa, yace " kin tabbatar da gaske babu abinda ke damunta ko inda ke yi miki ciwo? "Karki fa kiyi amfani da maganar our Sanah datace babu abinda ke damunki, murmushi tayi kana tace " Allah babu abinda ke damuna, sai baki na danake jin babu dad'i, sai kuma jiki na dayake man ciwo, idan shi na kanta yace " bakin ki rashin apartheid ne, jikin ki kuma dad'ewar da kikayi a kwance ne yasa shi yin tsami, da our Sanah tayi miki wanka da ruwan zafi zaki warware, yayi maganar cikin tsoka na, dariya duk sukayi batare da sunce komai ba, yace bayan nan fa? Tace " babu komai, juyawa yayi wajen su Abbu dake tsaye suna kallan su fuskokin su d'auke da murmushi, yace " Alhamdulillah, Allah maji rok'on bayin sa ne, abinda muka kasa yi acikin 48hrs , gashi Sanah tayi a cikin yini d'aya kawai, Allah ya amsa addu'arta, gaskiya ko ni anan na k'aru, k'aramar yarinya ta tunatar dani fahimmanci da amfanin addu'a, ta nusarshe ni komawa ga Allah, da kai kuka ga Ubangijin talik'ai mai kowa da komai, gaskiya ne babu abinda ya gagari addu'a koya fi k'arfin Ubangiji, wannan kad'ai ya isa ya nunuwa mutum akwai Ubangiji, ya isa ya nunuwa wad'anda basu yarda akwai Ubangiji ba,, cewar akwai mak'agin kowa da komai. Ya k'arasa maganar yana kallan Abbu ido cikin ido, murmushi Abbu yayi kana yace " Alhamdulillah mun godewa Allah, Doctor yayi murmushi yace " kuma da gani akwai so da k'auna mai k'arfi a tsakanin yaran, musamman yadda Sanah ta d'aga hankalinta, tak'i ci da sha , da kuma yadda itama Khulud tana farfad'owa babu sunan wanda ta fara ambata sai na Sanah, kad'ai ya isa ya tabbatarwa mutum suna mugun san junan su, yayi maganar idansa na kan Khulud da Sanah, cike da sha'awar su, murmushi Didi yayi cikin jin dad'in yabon da Doctor yake yiwa yaran su, yace " mun gode sosai Doctor, Allah ya saka da alkhairi Ubangiji yabar zumunci, Allah ya albarkaci iyali, " amin ya Allah,ya amsa kana ya d'ora da cewa " ai babu iyalin har yanzu, muna dai nema ya k'arasa maganar yana shafa kai idansa nakan Sanah, murmushi Abbu yayi yace " to madalla Allah ya bada nagari, "Amin, ya kuma cewa idansa nakan Sanah, har ya juya zai fita Mamu ta kira sunanshi " Doctor, a hanlaki ya juyo yana kallanta had'i da amsawa "na'am, cikin murmushi Mamu tace " zuwa yaushe za'a sallame 'yar ta wa? Dariya yayi kana yace " ko zuwa gobe ma in sha Allah, dan babu sauran abinda yake damunta, "Allah ya kai mu,Mamu tace, ya amsa da "Amin, ya d'ora hannunsa akan handle d'in k'ofa , Sanah tace " thank you so much Doctor, juyowa yayi yana murmushi yace " don't mention it, murmushi tayi a tak'aice tace " ai dole nagode , "saboda me? Yace idansa na kanta, " besouse you fulfilled your promise , dariya yayi kana yace " it's my pleasure, suka yi dariya su duka,batare da sun ce komai ba, Sanah ta mayar da kallanta ga Khulud tace " hankalina ya tashi sosai, tayi masa cikin sanyi da karaya, "karki damu muna tare har rai da mutuwa in sha Allah, Khulud ta fad'a tana dariya, Sanah tayi rau-rau da ido alamar tana san yin kuka tace " Allah nayi mugun tsora ta fa, na gama sawa rai na..., sai kuma tayi shiru had'i da k'urawa Khulud ido hawaye na zubo mata, Khulud tayi rolling idonta " please my Sanah ki dai na kukan kinji? Idan ba so kike na koma jinyar ba, tayi fad'a tana gogewa Sanah hawayen dake zubo mata, murmushi Sanah tayi tace " ke kyama so ma komawa, Khulud tayi dariya, d'an shiru Khulud tayi na wajen 5 minutes kana tace " my Sanah Sir Moli, tayi maganar can k'asan mak'ogwaranta, baki Sanah ta d'an tab'a kana tace " kamar ya Sir Moli? A hankali Khulud tace " yana ina? Cikin masifa Sanah tace " bangane yana ina ba? "Ko an fad'a maki yawo nake dashi ko kuma shi d'an gidan mu ne , dazaki tambaye ni inda yake? Cikin sanyin murya Khulud tace " kawai na tambaye ki ne, saboda....... sai kuma tayi shiru had'i da sunkuyar da kanta k'asa, ido Sanah ta k'ura mata bata ko k'iftawa, zatayi magana Mamu tace " hala an manta damu ko? Da sauri Khulud ta d'ago ido tana mik'awa Mamu hannu tace " lah ba haka bane Mamu My Sanah ce ta d'auke man hankali, Mamu tayi murmushi tana cewa " ai naga alama, tayi maganar tana zama kusa dasu، cikin sanyin murya Khulud ta gaida Mamu,Juju,Didi da Abbu duk suka amsa Abbu yana shafa kanta , cikin so da k'auna, Abbu ya tambaye ta abinda take san ci , ta kalli Sanah tace " My Sanah me zamu ci? Sanah da har lokacin idanta yana kan Khulud ta k'ura mata ido, tun tambayarta Sir Moli datayi, ta d'anyi guntun murmushi kana tace " anything, tayi maganar a tak'aice, Khulud ta kalli Abbu tace " nasan babu abinda my Sanah tafi so kamar shawarma da gashashshan kifi karfasa, da kuma ice cream, Abbu ka siyo kana su, "to yanzu kuwa, Abbu yace ya fita, Mamu ta mik'e ta had'awa Khulud ruwan wanka mai d'umi, tayi wanka da brush,ta kuma rama sallolin da ake binta, tana idarwa Abbu ya shigo ya mik'awa Sanah ledojin su , ya mik'awa Mamu nata, kana ya mik'awa Didi da Juju nasu, suka amsa suna godiya ,Didi yace " wannan sauran ledoji ukun fa ,ko na amaryar ne? Yayi maganar cikin zolaya, " wacce amarya na iyayen mu ne, Abbu ya fad'a yana dariya, Didi yace " kai dai ka fad'i gaskiya ko kana tsoro ne? Yayi maganar yana kallan Mamu, murmushi Mamu tayi tace " tsoran wa zaiji? Duk suka saka dariya, hankalin Sanah da Khulud nakan Ice cream, shawarma da gashashshen kifin su, Abbu yace " to ni fa zan tafi naga 12:20 ya fad'a yana kallan agogon hannunsa, Didi yace " muna ai tafiyar zamu yi, sukayiwa su Mamu sallah suka fice. Washe gari da safe k'arfe 8:30am na safe Doctor ya shigo sanye cikin cot , fuskarsa d'auke da fara'a , ya kalli Sanah yace " good morning Mrs Cry, "no ka bari na gaida ka, tunda nice k'arama , murmushi yayi yana k'ara jin yaran na burge shi, saboda hankali da nutsuwar su, har k'asa Sanah da Khulud suka durk'usa, had'i da cewa ina kwana? " Lafiya lau, ya amsa yana murmushi, "an tashi lafiya? " Alhamdulillah ya basu amsa، duba Khulud yayi sosai yaga she is normal , babu abinda yake damunta, dan haka ya basu sallama, sosai Khulud da Sanah sukayi mishi godiya, Mamu ta kira Juju ta sanar da ita an sallame su, kar ta sha wahalar kawo breakfast, Juju tace " ok badamuwa zanyi na naje muku idan kun k'araso sai kuyi break d'in a gida, Mamu ta amsa mata da " to, tana kashe wayar ta kira Abbu, yayi picking bayan Mamu ta gaidashi , ta sanar da shi an basu sallama , yace " ok dama ganin nan na kusa k'arasowa, "ok Mamu tace ,kana ta kashe wayar, Abbu na k'arasowa ya nemi Doctor ya kuma yi mishi godiya sosai, kana ya kwashi su Khulud suka yi gida, kafin suje gidan har Mamu tasa 'yan aiki sun shirya breakfast akan dinning table , sai da suka karya kana suka shiga part d'in kakanin su, saboda dakyar Abbu ya basu hak'uri suka zauna a gida , yayi ta kwantar musu da hankali yana lallashin su, sannan suka hak'ura, dan tuburewa sukayi sai an kai su Hospital d'in su duka, bayan sun dawo suka shiga bedroom yin bacci. _BAYAN SATI BIYU_ Sosai Khulud ta warke garau , dan har sun koma islamiyya, ganin haka yasa Abbu kiran su parlor, bayan sun zo ya kalle su yace " to yaushe za'a koma makaranta? Kafin Khulud tayi magana Sanah tayi saurin cewa " Allah ni dai Abbu ban san boarding school, a samar mana day school kawai mu koma, amma ni ban k'ara yin boarding, na gama yin boarding har abada, Khulud tayi saurin kallanta dan ba haka taso ba, dan ita taso su koma Computer Girls Secondary School Roni, amma dole ta hak'ura tunda My Sanarta bata so, ita kuma duk abinda Sanah bata so ta barshi har abada,, saboda bata k'aunar duk abinda zai shiga tsakanin su ko ya raba su, shiru tayi batare data ce komai ba, ganin yadda tayi shiru yasa Abbu cewa " Khulud ko kinfi san boarding d'in ne? Yayi maganar idanshi na kanta, murmushin yak'e tayi tace " a'a Abbu nima ban san boarding d'in a canja mana kawai, " wacce kuke so? Abbu ya tambaye su, duk suka ce " babu,kawai ka zab'a mana kowacce, "ok ku tashi kuje, Abbu ya fad'a, washe gari Abbu ya aika Aarib da Ziyad suka amso musu transfer, bayan kwana uku Abbu ya samu musu admission a Momy speed international School, makarantar private School ce mai shegen kyau, ranar Monday suka fara zuwa, Ziyad ne yake shaidawa su Sanah Halan sunyi candy tun last week, aiko suka addabe shi akan sai ya kai su wajenta sun ganta, dole tasa ya kai su dan itama ta dame shi da maganar su, yana yin parking suka fito da gudu suka shiga gidan, Halan na zaune a parlor tana yankan salad taga su Sanah, cike da murna da farin ciki ta rungume su, dan kwata-kwata Ziyad bai sanar da ita zuwansu ba, Halan ta kalle su tace " I really misses you so much my dears , dariya suka yi kana suka ce " we miss you too ,our Aunty , Sanah tace " Allah Aunty Halan kullum sai munce Yaya ya kawo sai yak'i, yau ma dakyar ya kawo mu, Halan tayi dariya tace " ni ma haka,har cewa nayi ya kai ni na gano ku amma ya k'i, baki Sanah ta turo tace " aiko bamu komawa sai dai ya tafi shi kad'ai, "yauwa My Sanah ku zauna anan, Khulud tace " muna nan har sai randa zaki koma gidan mu sai mu tafi tare, mahaifiyar Halan dake zaune kan sofa tace " aiko baku isa ba, idan kuka zo kun zo kenan ban barin ku, ku koma,tayi maganar cikin fara'a da sakin fuska, kwata-kwata basu lura da ita ba, sai da tayi magana, cikin nutsuwa suka durk'usa har k'asa suka gaida ita, ta amsa tana d'ago su, wayar Halan ta fara ringing tayi saurin picking , yace " wato anga su Khulud an manta da ni ko? " Lahhhh yi hak'uri Allah sun d'auke man hankali ne, tayi maganar cikin shagwab'a, mahafiyarta ta jefa mata uwar harara wanda tasa ta saurin mik'ewa tana dariya ta nufi bedroom d'inta, tana shiga tace " ka sani na manta nayi picking gaban Nanan mu, dariya yayi yace " ni dai ki fito ina waje, "to tace ,fuskarta ta d'an gyara kana ta fesa perfumes masu sanyin k'amshi, anan ya bar Sanah da Khulud, sai dare ya dawo d'aukar su, koda ya dawo k'in fitowa sukayi, suka cewa Halan tace masa su sunzo kenan, da Halan ta fad'a masa cewa yayi taje tazo dasu, Sanah tace " Allah ko naje haka zan fad'a masa tayi maganar tana murgud'a baki, daga bakin k'ofar sit room suka tsaya, ya had'e fuska yace " muje ko? Ya fad'a batare daya kalle su ba, Khulud tayi gaba sumi-sumi ganin ya had'e rai, dan har tsoro ya kamata , amma Oga Sanah sai ta shiga bubbuga k'afa tace " please Yaya ka barmu nan, ido ya zaro yace " exam d'in da zaku fara next week fa? Sanah tace " daga nan zamu rink'a zuwa ai, yace " wazai rink'a kai ku? Sanah tace " Aunty Halan mana, ya zaro ido sosai ,kana yace " wacce Halan d'in,amma badai tawa ba ko? Sanah tace " taka kuma Yaya ko ta mu,ko harka kwace mana ita? Dariya yayi yace " a'a ,dan ya lura Sanah bata tsoran zare ido, sai dakyar Sanah tabi Ziyad shima sai da yayi musu alk'awarin dasun gama exam zai kawo su,su zauna har ayi biki, bayan sati uku da fara zuwan su Khulud school , aka fara 3thr term exam, duk da a k'urarran lokaci su Khulud suka shiga school d'in su, sai da suka yi matuk'ar bada mamaki dan Sanah ta d'auki 1st position Khulud second , a islmaiyya kuma Khulud ta d'auki 1st position Sanah second , dan dama Khulud tafi Sanah k'ok'ari a ismiyya, suna dawowa gida suka tarar da duk 'yan gidan a parlor, da gudu Sanah ta fad'a jikin Aarib , Zarfan kuma ya mashi result d'in su, yana dubawa, Ziyad yace " meye kuma na dubawa kai da ka san na yadda suke zuwa? " Ai dole a duba saboda sabuwar makaranta ce, Mamu tace " to yanzu na nawa suka zo? "Yadda dai suke,tayi murmushin jin dad'i tace " ai har abada ba'a canjawa tuwo suna, Sanah ta kalli Ziyad tace " Yaya ya alk'awarin mu? "Na me fa? Ya tambaye ta, baki ta turo tana buga k'afa tace " Yaya zaka fara ko? " To ikon Allah,kin tab'a ganin an kama mutum da laifin dabai sani ba? Khulud tace " Yaya kai fa kayi mana alk'awarin damun gama exam zaka kai mu gidan su Aunty Halan har a gama biki, dariya yayi yace " yara ai yanzu an shiga Inconclusive, dan haka kuma kun shiga inconclusive, Sanah ta tab'a baki zatayi kuka Khulud tace " no please karki yi kuka ki bari muje idan yace bai kai mu nima sai ma tayaki kukan, Sanah tayi saurin mai da kukan , duk suka zuba mishi ido suna jiran suji abinda zai ce su fara kuka, "kambuuuu Ziyad yace yana dariya, " wato tsabar rai nin hankali har mai da kuka ake yi ana jiran mai zance ko? Duk sukayi shiru babu wanda yace masa k'ala, ganin yadda duk suka kafe shi da ido, yasa shi cewa " to ban kai ku, aiko suka had'a baki suka saki kuka lokaci d'aya, Aarib yayi saurin cewa " kuyi shiru please ni zan kai ku, kamar d'aukewar ruwan sama suka yi tsit, Ziyad ya kuma yin dariya, Mamu tace " naga nan gidan ma bikin za'ayi, kuma ai kamata yayi ku tsaya wajen Aroos (yayar Khulud wacce take bi), Sanah ta zumb'uro baki, Idrak angon Aroos (dayake auren zumunci za'ayi musu), yace " au wato baku tsayawa ku taya tawa amaryar hidimar biki ko? Sanah tace " ita ai bata san mutane, tafi san komai nata tayi ita kad'ai, Mamu tace " uwaki,Yayarki kike cewa haka? Khulud tace " Allah Mamu haka take , shiyasa muma muke ja baya,bata da kirki gata da saurin dukan mutane da zagi, Idrak yace " aiko sai na fad'a mata, Sanah tace " ai halinta ne,ta juya ta kalli Aarib tace " Yaya kai yaushe zakayi auren? Ido kawai ya kafe ta da shi batare dayace komai ba, dole tasa su Khulud hak'ura da zuwa gidan su Halan dan biki uku za'ayi a gidan, bikin Ziyad & Halan, sai bikin Aroos & Idrak da bikin Zafran & Seenah, Seenah 'yar mak'otan su,ce yarinyar mai hankali da nutsuwa kamar Aroos & Halan, itama iyayenta mutanen kwarai ne,masu mutunci da kamala, kamar na Halan. satin biki na zagayowa aka shiga hidimar biki kowa ba zama yayi busy musamman Juju da Mamu, ba wata bidi'a akayi sosai ba, anyi yinin biki normal sai walima da wa'azi, ranar Friday a babban masallacin juma'ar gidan sarkin kano bayan an idar da sallar juma'a millions mutane suka d'aura auren, Halan & Ziyad Aroos & Idrak Seenah & Zafran, a ranar kowacce ta tare a gidan ta dake Hard'o Family estate, sosai mugun sabo da shak'uwa ta k'ura shiga tsakanin Halan da su Sanah, suka kuma mai da hankali sosai akan karatun su. _BAYAN SHEKARU 5_ MOMYN ZARAH _*RASHIN SANI.......*_ *HAUWA A USMAN* _JIDDARH_ ```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh``` 1⃣5⃣ _BAYAN SHEKARU 5_ Tafiya suke sannu a hankali cikin nutsuwa kamar basu san taka k'asa, sanye suke da uniform mai kalar peach color , da guntun hijab wanda k'irjinsu kawai ya rufe, 'yan mata guda biyu santala'sanatala, san kowa k'in wanda ya rasa, gaba d'ayan su kyawawan gaske ne ajin farko, irin mata nan da zakaji ana kira da full option, wato komai yaji, babu abinda zai k'ara d'aukar hankalinka a ajikinsu sai kalar fatar jikinsu, wacce ita ba fara ba ba kuma bak'a ba, wato chocolate color,kalar su tafi ta fararen mata kyau da tsada, saboda fatar su tafi laushi da tsantsi, duba nakai kan k'irjinsu naga na fulanin su tantsan-tantsan, a hankali ya gangaro da ido na zuwa k'ugun su, "masha Allah kawai na iya furtawa, saboda sun wuce iya kar kyau da had'uwa, matasan 'yan mata masu ji da kyau da k'uciya 'yan 16yrs, daga bedroom d'in su suka fito, cikin sauri da alama sauri suke yi, cornflake naga d'aya daga cikin su ta d'eba takai bakinta , tana sauri ta kurb'i ruwan madarar dake gefe ajeye cikin glass cup, wata dadtijiwar mata naji tace" SANAH bazaku tsaya kuyi breakfast bane? Wacce aka kira da Sanah ta jiyo a hankali tana murmushin dayasa dimples d'in dake kumatunta lutsawa, jerarrun fararen hak'uranta masu d'auke da siririyar wushirya suka bayyana, hakan ne ya bani damar k'arewa faffad'ar fuskarta kallo mai d'auke da dogon hanci , da dara-daran idanu farare tass, kalar kwayar idanta blue color, badan a Nigeria na ganta ba da sai na rantse Pretty Zinta ce , domin babu abinda ya raba su , sai kalar fatar jikinta da lulu eyeball d'inta, sai daga k'ugu tafi Pretty Zinta hip da fad'in k'ugu da cikar booms nesa ba kusa ba, rolling lulu eyes d'inta tayi masu kamar tana jin bacci tace " no Mamu munyi late ,saura 2hr kawai mu shiga final exam, Mamu tace " to kuma shine bazaku tsaya ku karya ba? "Bayan naga kuna da sauran lokaci, Mamu ta fad'a tana kallan Sanah, d'an tsukakken bakinta mai d'auke pink lips ta turo tace " Mamu yau ne ranar Graduation's d'in mu, shiyasa bana san muje a late, Mamu tayi murmushi kana tace " au to cewa zakiyi duk murnar kammala karatun Secondary ne yau, Sanah tayi dariya tace " ashe dai kin gane our Mamu, daga yau bamu da fama da uniform, Mamu tace " Khulud kema bazaki k'arya ba? Wacce aka kira da Khulud na kalla , can k'asan mak'ogwaro na ,na furta masha Allahu, Ubangiji yayi halitta anan, dan itama kyakkyawa ce ta gaban kwatance, siririya dogowa mai doguwar fuska , abu d'aya Sanah zata nuna mata shine wushirya da dimples, sai kuma bam-bamcin halitta, ita Sanah 'yar duma-duma ce irin jikin Jennifer Lopez, ita kuma Khulud siririya ce mai irin jikin Thamanna Batia, Sanah tad'an fi Khulud jiki da k'ira, ita Sanah dirarriyar mace ce, Khulud kuma irin matan nan ne da ake kira American Lady, saboda irin jiki da shape d'in turawa ne da ita, silent smile tayi tace " no Mamu ba sai mun karya ba, idan muka je maci abincin, baki Mamu ta tab'e tace " kwaji dashi dai, ai dama nasan tunda Sanah tace " a'a kema a'an zaki ce, Khulud ta kuma yin murmushi tace " eh mana Mamu ai ba'a tab'a raba d'aya biyu, Mamu tace " ku dai kuka sani, idan zaku wuce ku d'auki Mash su mik'awa Halan d'anta ya dame ni da k'iniya, baki Sanah ta turo tace " yanzu sai an samu d'aukar yaro Mamu? Mamu zatayi magana Khulud tace " bakomai Mamu bari sai mu mik'a shi tayi maganar cikin sanyinta, a hankali Khulud ta d'auki Mash dake ta wasa, har sun kai bakin k'ofa Mamu tace" Khulud idan kunje kucewa Halan ta turo man da Maheen tazo, "to Khulud tace kana suka fita, direct part d'in Halan suka shiga, a bakin k'ofa suka iske ta rako Ziyad , suna tura k'ofa Halan takai bakinta tayi masa kiss, Sanah ta zumb'uri baki had'i da cewa " 'yan iska kawai, tayi maganar cikin ranta, Khulud ko kauda kanta tayi gefe , Halan tayi dariya tana cewa " ah ah kaga 'yan candy yau, Sanah bata kulata ba, sai Khulud ce tace " Allah Aunty Halan yau ji nake kamar anyi man bushara da aljanna, Halan tayi dariya tana cewa " ai haka ne dama , musamman kuna ganin zaku shiga sawon'yan mata, Sanah tace " au yanzu mu ba 'yan matan bane? Dariya Halan tayi tace " kwailaye dai, Sanah ta turo baki " haba Aunty Halan we are 16yrs now and you call us kwailaye? Halan zatayi magana Ziyad yace " dan ubanku baku iya gaisuwa bane? Sanah ta kawar da kanta tana turo baki, Khulud tace " yi hak'uri Yaya bamu lura da kai bane, ina kwana? Ta fad'a cikin girmamawa, lafiya lau ya amsa mata fuskarshi a sake, kallansa ya maida kan Sanah yace " ke zanci uwarki fa, shegiya mai fad'in ran tsiya,mai bak'in hali, Halan tace " a'a Abban Maheen karka kuma ce mata mai bak'in hali ba kyau, a fusace yace " ai daman ke ke d'aure mata gindi take zubawa mutane iskaci da fitsara san ranta,,, Khulud tace " please Yaya kayi hak'uri, Halan ta kalli Sanah taga ko ajikinta yadda kasan bada ita yake magana ba, idan Halan na kanta tace " Sanah!, Sanah ta juyo ta kalle ta, Halan ta nuna mata ta gaida shi da ido, Sanah tace " oh! wai dama dani ake? "Ai ban sani ba, tayi maganar tana mik'ewa tace " sorry Yaya good morning, ko kallanta bayyi ba yayi tsaki yayi ficewarsa,, ta bi bayan sa da harara, Khulud ta kafe ta da ido had'i da cewa " it's not good my Sanah, bai kamata ba, Sanah tace " to shi abinda yayi yanzu ya kamata? Halan tace " mai yayi? "Ai ke dama bazaki ga abinda yayi ba, Halan tace " oh ni Halan shi yace bana ganin laifinki ko ban san laifinki, kema kice ban ganin laifin sa ko ban san laifinsa, ni dai kun sani a tsakiya , ta fad'a tana dafe kanta, Sanah tace " ina Maheen? "Tana kitchen wai breakfast zata koyi had'awa, Sanah ta zaro tana cewa " she's 4yrs fa, Halan tace " a to na sani kotayi gadan rawar kai wajen k'aramar uwarta, "wajen wacce uwar tata? Halan tayi dariya tace " ni dai ai ban ambaci sunan kowa ba balle a kama ni da laifi, "hmmmm kima ji da tsohon cikin ki, bada tsokanar mutane ba, " ai dole naji dashi tunda a jiki na yake, Sanah ta mik'e had'i da dafe bayanta, tana gwada irin tafiyar Halan tace " to mu zamu tafi, Halan takai mata duka tana dariya, itama ta goce tana dariyar, Halan tace " rai dai ,ni ma zan rama, wama yasan irin naki cikin ke, Sanah tace " aiko bazaki rama ba, dan ni ba anan k'asar zanyi goyan ciki na ba, balle har ki gami, Halan tace " ai in dai nan cikin duniyar zakiyi ciki sai na bi ki, ko'ina ne na gano, Sanah na shirin fita Halan ta kalli bayanta, ta zaro ido tace " Sanah bleeding kike ne? A d'an tsorace Sanah tace " bleeding d'in me? Halan tace " period mana, "ina period d'in yake? Sanah tayi maganar tana zaro ido, Halan tace " gashi nan ya b'ata ki, dariya Sanah tayi tace " wai ni zaki ma wayou dan ki kama ni ko? Halan tace " Allah da gaske nake yi maki, jin Halan ta rantse yasa Sanah zaro ido tace " please seriously da gaske kike? Halan ta kuma cewa " Allah da gaske , ta kalli Khulud tace " zo ki gani sai ki fad'a mata, cikin sanyinta Khulud ta mik'e ta zo tana duba bayan Sanah, kallanta kawai Khulud tayi ,Sanah ta gane da gaske ne, ta marairaice fuska kamar zatayi kuka tace " just 2 weeks back ba nayi wanka, Halan tace " ai tun kuna SS 1 nace miki kije kiga Doctor kika a'a is normal, amma bleeding d'in yayi yawa ,kuma duk after 2 weeks period ya dawo ai da matsala idan kikayi aure, a tsorace Sanah ta kalli Halan idanuwanta duk waje tace " wacce irin matsala kuma? Dan kwata-kwata bata fahimci abinda Halan ke nufi ba, murmushi Halan tayi kana tace " ke is not so serious issue , "are you sure? Sanah tayi maganar cikin sanyin jiki, Halan tayi dariya kana tace " yes Ma'am, Khulud tayi murmushi tace " oh! ni dai na huta da wannan jidalin, "wanne jidali? Halan ta tambaye ta, Khulud tace " na period mana, Halan tace " kamar ya kin huta bayan kowacce mace bata da hutu akan shi? Khulud tace " aiko ni Allah ya hutashe ni, Halan tace " wai kamar ya Allah ya hutashshe ki? Kai tsaye Khulud tace " ai ni ban fara ba , a kid'ime Halan ta zaro ido "what!? Tace a razane, murmushi Khulud tayi kana tace " yes mana, a firgice Halan tace " wai kina nufin baki fara period har yanzu ba? Ta tambaye ta cikin tension , Sanah tace " eh bata fara ba, akwai damuwa ne? "Innalillihi wa'inna ilaihirraji'un, Halan tace ,Sanah da Khulud suka kalli juna cike da tsantsar mamaki,, cikin tsoro Sanah tace " meye Aunty Halan? Halan tace " tunda kika fara 2yrs back dama ita bata fara ba? Cikin sanyin jiki Sanah ta d'aga kanta, a sanyaye Khulud tace " lafiya Aunty? Halan tace " amma shine baku fad'a anje hospital ba? "Hospital kuma? Khulud tace, " eh man ai dole aje hospital dan aji meke faruwa, mace 16yrs bata fara period ba ai akwai damuwa, ta kalle su tace " uban me ya hana ku fad'a? Cikin sanyin murya Sanah tace " bakomai ,ai mun d'auka there's no problem ne, "ubanwa yace muku babu problem? Halan ta fad'a a tsawace, tunda suke da Halan bata tab'a yi musu ko kallan banza ba, balle har ya kai ga tsawa ba yau sai yau,, gasu yanzu a k'alla sun kai wajen 6yrs da ita, saboda yadda take nuna musu so da k'auna take kuma jan su ajikinta sosai, yasa suma suka fi sabawa da sakin jiki da ita sosai akan Seenah da Aroos, tunda sun fahimci halin Seenah da Aroos kusan d'aya ne, shiyasa ta su ma tafi zuwa d'aya akan Halan, duk da babu wani rashin jituwa ko matsala a tsakanin su , su duka ukun,suna zaune lafiya babu wata damuwa, tare suke yin komai,kan su a had'e yake sosai sai dai d'an abinda ba'a rasa na yau da kullum ba, ko yaran su kan su a had'e yake suma sosai, komai na su iri d'aya ne, dan Danish da Ganez suna iya bakin k'ok'arin su wajen ganin sun had'e kan zuri'ar su, ta yadda ko bayan babu su,sun san basu tafi sun bar baya da k'ura ba, kuma Alhamdulillah family'n su yana zaune lafiya cike da so da k'aunar juna, basa tare da wata matsala ko rashin jituwa a tsakanin su, haka ma Rawan da Hamraz suna iya yin su dan ganin sun kafawa zuri'arsu zumunci mai k'arko da dank'o, shiyasa kullum suke k'ara nusar da yaransu mahimmanci, amfani da k'arfin zumunci, suna koyar dasu su zama tsintsiya mad'aurin su d'aya , kuma cikin ikon Allah sunyi narasar kafa hakan a zukutan ahalinsu, kowa cike yake da san d'an uwansa babu wani nuna bambamci ko ware-ware, duk sun d'auki kansu d'aya,babu abinda wani zai zartar batare da sani ko shawarar junansu ba, dan k'ara k'arfafa zumuncin su yasa every last Saturday ta k'arshen wata suke family meeting, yaran Halan biyu mace da namji Maheen itace babba sai k'aninta mash, sai yanzu data ke tsohon ciki haihuwa yau ko gobe, Aroos kuma yaranta biyu duk mata Aabish ce babba sai Aairah bata kuma da ciki, dan tace sai ta huta, Seenah yaranta d'aya namiji Ejaz itama tana da ciki....... Duk sukayi shiru cikin sanyin jiki ta kalle su tace " saura awa nawa ku shiga last exam? "1hr 40 minutes Khulud ta bata amsa cikin sanyin jiki, dan tunda suke da ita basu tab'a ganin b'acin ranta irin na yau ba, ta kalli Sanah tace " na baki just 10 minutes kije ki gyara jikinki kizo yanzu mu tafi holital, Hospital ? Sukace cike da mamaki, batare data kalle su ba , ta d'auki wayarta tayi hanyar bedroom tana dialing number Ziyad, duk suka bi bayanta da kallo, Khulud tace " kiyi sauri ki shirya naga alamar yau ranta yayi masifar b'aci, "ok kawai Sanah tace tana barin wajen, a parlor ta tarar da Mamu zaune akan sofa da remote a hannunta tana canja channel, cikin mamaki Mamu ta kalle ta tace" au dama baku tafi ba? Sanah tace " eh jiki na zan gyara tayi maganar tana shiga d'aki da sauri, cikin gaggawa Sanah ta shirya, ta fito da gudu zata fita, Mamu tace " kin d'ibi pad & pant spare? Kanta ta dafa alamar mantuwa kana ta juya ta kalli Mamu tace " thank you, ta koma d'akin da gudu ta d'ebo ta watsa cikin school bag d'inta , ta fita da gudu, a harabar gidan ta iske Khulud da Halan tsaye , suna ganinta suka shiga bayan mota , driver ya ja motar, a harabar Nasarawa Hospital sukayi parking, batare data kalli inda suke ba ta fita suka bi bayanta, bayan ta gama yiwa Doctor bayanin matsalar data kawo su,kana ya kalli Khulud yace " kina jin ciwo ko wani abun ne? Tace " a'a , yace " baki jin wani sigh a mararki ko cikin ki? Tace " eh ban jin komai, a hankali ya mik'e yaje bakin gadon dake cikin office d'in, ya kalle ta yace " Bismillah, ba musu ta mik'e taje inda yake tsaye, yace " kwanta, gyara mata kwaciyar yayi , sannan ya d'an d'aga rigarta yayi k'asa da wondon uniform d'in dake jikinta, yasa hannu a hankali yasa d'an danna mararta, yace " duk inda na tab'a kikaji zafi ko wani emotions kiyi man magana, tace "tom, yakai wajen 10 minutes yana tab'awa amma batayi magana ba,, ya kalle ta yace " baki ji komai ba? Tace "eh, " sakko yace mata,yana barin wajen, 'yan rubuce-rubuce yayi kana ,ya kira nurse yace " kije da ita, ki kaita Scanning room, za'ayi mata Scanning kala biyu, na mara dana mahaifa, sannan ki kaita lap a d'ebi jininta, "Ok Sir tace cikin girmamawa, sai da suka yi wajen 1hr a hospital d'in ana gwaje-gwaje da aune-aune, sannan Doctor ya dawo , ya karkata gaba d'aya hankalinsa ga Halan, yace " gaskiya munyi mata duk abinda ya kama, munyi mata Scanning & tests amma bamu ga komai, asalima lafiyarta k'alau tana cikin k'oshin lafiya, babu wata matsala ko damuwa, kana ya d'ora da cewa " kowanne mutum da kika gani akwai irin nau'in halittarsa, da kuma kwayayensa,da organs & cell d'in jikinsa, dama ana iya samun irin haka, sai kiga wata macen ma takai 22yrs bata fara period ba, ko kuma kiga mace bata da ciki , asalima bata da auren amma sai kiga tayi wajen 5monts batayi period ba, muna kiran abun a likitance Hormonal imbalances, kuma abubuwan dake haifar da haka suna da yawa akwai, Birth Control, Thyroid irregularity ,Polycystic ovary syndrome (PCOS), Early peri menopause, Stress ,weight loss and Breastfeeding, wad'annan abubuwan suke iya haifar da dad'ewa ba'a fara period ba, ko mace ta dad'e bata ga yazo ba, amma ita Khulud lafiyarta k'alau kawai Allah ne yasa bai zo ba, ajiyar zuciyar Halan ta sauke,kana tayi masa godiya suka fice, ana saura 15 minutes su shiga exam suka isa makaranta, d'alibai na ganin Sanah suka saki ihuuu , dan Sanah popular student ce,Halan taita dariya had'i dayi musu addu'ar sa'a. Suna fitowa daga exam hall suka fara sakin ihuuu, wasu daga cikin students d'in na yayyaga uniform d'in su, duk d'alibin daka kalla a ranar kasan yana cikin tsananin farin ciki, assembly principal da teachers sukayi musu as usual sukayi musu nasiha mai ratsa jiki da jijiya, aka basu shawarwari akan rayuwar duniya, daga wajen assembly wajen bikin murnar yaye d'alibai suka nufa ,kowa yaci yasha cikin tsantsar farin ciki, kana aka sallami kowanne students d'auke da kyautar da yasamu, kasancewar Khulud itace mosque prefect yasa aka bata kyaututtuka masu tarin yawa, harda Qur'an da litattafan addini, itama Sanah dayake itace Labour prefect itama tasha kyauta sosai, dan principal naji da ita sosai, dama su Sanah sunce kar azo d'aukar su daga gida dan zasu biya wajan saloon da henna, saboda Abbu ya shirya musu walima a gida saboda tare sukayi Candy da saukar Al Qur'an mai girma, fita sukayi daga cikin get d'in makarantar suka nufi bakin titi dan shiga napep. Sanah ta kalli Khulud cikin tsananin farin ciki tace " my Ulud ya kike ji yau? Khulud tayi murmushi kana tace " wallahi ji nake kamar na zuba ruwa a k'asa nasha dan murna, muma yau mun girma mun zama 'yan mata Classy & big Beb , "ke ya kike ji yau my Sanah? Tayi maganar tana kallan Sanah, Sanah tayi gaba had'i da juya bayanta tana tafiya tana fuskantar Khulud, tace " ni kuma yau ji nake kamar nayi ta burgima a k'asa ina ihuuuun dad'i, Khulud tace " my Sanah kin juyawa titi baya fa, kuma kina tafiya da baya-baya bayan kin san ba kyau, Sanah ta d'aga hannayenta sama cikin farin ciki tana tsalle tace " barni my Ulud yau d'aya nad'an sha iska na wataya, ta fad'a tana dariya, d'aga idan da Khulud zatayi taga wata sabuwar mota dalleliya kirar Kia 2019 , ta nufo Sanah gadan-gadan, a kid'ime Khulud ta saki k'ara had'i da d'ora hannu aka, ganin haka yasa Sanah juyawa a firgice, shima matuk'in motar kwata-kwata bai lura ba sai da yaji ihuuun Khulud, a gigice ya taka burki da k'arfi k'uuuuuu, duk da haka sai da motar ta gogi Sanah, ta fad'a cikin ruwan dake tare gefen hanya kasancewar kwana akayi ana ruwan sama jiya, hijab d'inta da d'ankwalinta suka fad'i gefe, kwantaccen gashin kanta ya zubo ya rufe mata fuskarta, hannunta ta saka ta kawar da gashin gefe, bakin bud'e take bin jikinta da kallo , taga yadda duk ruwan ya gama b'ata ta, taga mai motar kwata-kwata bashi da alamar fitowa da alama ma jira yake ta tashi ta bashi hanya ya wuce, cikin tashin hankali Khulud ta k'araso tasa hannu tana k'ok'arin d'ago Sanah, tace " my Sanah baki ji ciwo ba dai ko? Sanah tace " babu abinda ya same ni, ki koma gefe ga guri can ki zauna yau zanga k'aryar iskanci, ta fad'a tana kallan motar, Khulud tayi dariya kana tace " a'a my Sanah ki tashi mu tafi, zamanta ta gyara sosai a cikin ruwan kana tacewa Khulud " kin san Allah ban tashi, sai dai mu kwana anan naga k'aryar taurin kai, d'an gutun tsaki yaja had'i da gyara zansa a cikin motar ya k'ara k'arfin ac, kana ya kwantar da kujerar motar baya, ya kishingid'a gami da lumshe idonsa, sun kai wajen 30 minutes a haka Khulud na tayiwa Sanah magiyar ta tashi su tafi amma tak'i, idansa ya d'an bud'e gami da kallan agogon hannunsa k'irar Gucci, ya ja tsaki ganin tana niyyar b'ata masa lokaci, cikin isa da tak'ama gami da aji ya zuro k'afarsa d'aya k'asan motar , sanye da takalmin Gucci sau ciki, wacce kallo d'aya zakayi mata kasan k'afar d'an hutu da jin dad'in duniya ce, sai da akayi 2 minutes kafin ya k'ara fito da d'aya k'afar tasa, nan ma sai da yayi wajen 2 minutes kafin ya fito gaba d'ayansa, ya taka k'asa kamar baya so, dai-dai lokacin idan Sanah ya sauka akan................. MOMYN ZARAH _*RASHIN SANI.......*_ *HAUWA A USMAN* _JIDDARH_ ```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh``` 1⃣6⃣ Idon Sanah ya sauka akan pant & pad d'inta da suka watse a k'asa, kallanta ta mayar kan matashin saurin daya fito daga cikin motar,, wanda bazai wuce 30yrs ba, hannayensa ya hard'e a k'irjinsa, kwata-kwata fuskarsa babu alamar annuri, cikin izza yace " hey common from here , yayi maganar cikin zazzak'ar muryarsa, wani irin wulak'antaccen kallo Sanah ta watsa mishi, kana tace " baka iya bada hak'uri bane? "Ko ba'a koyar da kai sanin darajar 'ya mace ba? Tayi maganar cikin tsiwa, a k'ufule yace " ina macen take anan? Ya fad'a yana yi mata kallan banza,, "ok tunda baka ga mace ba,ai kaga mutum kuma 'yar Adam ko? Tsaki yayi kana yace " ni banga komai ba sai dabba, "oh! kai kuma naka salan rainin wayan kenan, tayi maganar tana mik'ewa tsaye, tsawa ya daka mata " dalla can bani hanya ko na bi ta kanki ta taka banza, Sanah tayi murmushi had'i tattare hannun rigar ta , ta hard'e hannunta a k'irji had'i da zuba masa lulu eyes d'in ta, kana tace " Bismillah, tayi maganar cikin tsiwa , "Ok yace yana komawa cikin motar had'i da cije leb'ensa, Khulud tayi saurin cewa " a'a dan Allah kayi hak'uri , tayi maganar cikin sanyinta, sai lokacin idansa ya sauka akan Khulud, kallanta ta mayar kan Sanah tace " My Sanah please bashi hanya, kinsan ban san rigima da tashin hankali ko? Sanah tace " barni dashi idan kanshi hayak'i yake ni nawa wuta yake ci, barni naga iya inda tashi rashin kunyar ya tsaya, ta fad'a tana kallan shi ido cikin ido, takowa yayi a hankali har zuwa gabanta, yayi guntun murmushi kana yace " kinci sa'a, wallahi badan darajar wannan 'yar uwar taki ba, da sai na koya miki hankali, ki kuma godewa Allah sai bayan na ganta kika ce kina san ganin kalar tawa rashin kunyar, da sai na nuna miki bambamcin fitsara ta da taki, idonta na cikin nashi tace " ok to mai zai hana yanzu ma nuna min, tunda na fuskanci mara tarbiyya ne kai, a fusace ya d'aga hannu zai wanka mata mari , tayi saurin rik'e hannunsa, tayi guntun murmushin gefen baki tace " hey! karka kuskura ka soma, dan ba kunyar ramawa zanji ba, nonsense kawai, cike da tsantsar mamakin rashin kunya da fitsarar ta yake kallanta, a ranta ya maimaita nonsense, ya bud'e baki zayyi magana, Khulud tayi saurin shiga tsakiya tana kallan Sanah tace " wai me yasa kike haka ne My Sanah? " Na fad'a miki ban san hayaniya, baki Sanah ta turo tace " bakiga abinda yayi man ba? " Amma shine dan iskanci ba zai iya bani hak'uri ba, a ransa yace " tab ,yana jinjina rashin kunya da tsoranta, Khulud tace " to sai me dan bai baki hak'uri ba? "Ko kuma sai akace kin ragu da wani abun, sai ki bashi girmansa a matsayinsa na babba kuma namiji, ki barshi da halinsa yaje, idan ma bazaki iya yafewa ba , sai ki barshi da Allah, dan sakayyar Ubangiji tafi ta kowa, gwamma shi ya saka miki akan hak'urin da zai baki, amma fitsara da rashin kunya babu inda zasu kai mutum , Khulud tayi maganar a hasale, kana ta juya wajensa dake tsaye ya kafe Khulud da dara-daran idanuwansa, tace " we are very sorry, lokaci d'aya haji halayyar yarinyar da d'abi'unta sun burge shi, tasan shine bai da gaskiya amma take yiwa sister ta fad'a, take kuma bashi hak'uri akan laifin daba nata ba, murmushi yayi wanda ya bayyanar da tsantsar kyawunsa, jerarrun fararen hak'oransa suka bayyana, ya kuma kafe ta shu'uma idanunsa masu kamar dana mashaya, yace " bakomai ,kema kiyi hak'uri, yayi maganar cikin zazzak'ar muryarsa mai icon , martanin murmushin shi ta mayar masa batare datace komai ba, dogon tsaki Sanah taja mtswwwww gami da kauda kanta gefe, kallanta yayi cike da jin haushinta, danji yake kamar ya rufe ta duka , har zayyi magana sai kuma ya fasa ya juya ya shiga motarsa, Khulud bata kalli Sanah ba ta durk'usa ta kwashe kayan su dake zube a k'asa , kana ta tsaida mai napep sukayi gida. A harabar wani katafaren gida yayi parking, tsayawa fad'ar had'uwa ko girman gidan b'atawa kai lokaci ne, dan irin gidajen turawa ne da muke gani a films , cikin isa da tak'ama yayi parking ,ya d'auki lokaci kafin ya fito yana taka k'asa kamar baya so,, wata k'ofa naga ya shiga dan haka nayi saurin bin bayansa, dan na kashe kwarkwatar ido na,, "woww nace,saboda had'uwar parlor'n, iya kud'i kam an kashe su wajen tsara parlor'n, akan sofa naga ya zauna had'i da d'ora k'afa d'aya kan d'aya, masu aikin gidan suka fito sun kai biyar suka jiru daga gefensa kansu k'asa , suka ce " me za'a kawo Sir, a tak'aice yace " babu, batare da sun k'ara cewa komai ba suka bar wajen, dan haka al'adarsa take baya san yawan hayaniya , ko gadarma, wata hamshak'iyar mace naga tana sakkowa daga kan steps, fuskarta d'auke da farin glass, dagani medical ne, murmushin fuskarta ta fad'ad'a ganinsa zaune a parlor'n, yana ganinta ya mik'e tsaye yana murmushin jin dad'in ganin mahaifiyar tasa, dan duk tarin bak'i ciki da damuwarsa muddin ya ganta sai ya ji duk sun gushe,, ta bud'e masa hannayenta alamar yazo , aiko da sauri ya fad'a jikinta ya rungume, kansa ta shafa kana tace " what's wrong with you my son? Dan kallo d'aya tayi masa ta fuskanci ran d'an nata a b'ace yake, murmushi yayi yana kwantar da kansa akan kafad'arta, a shagwab'e yace " nothing so serious, "nothing so serious amma shine naga ranka a b'ace? " MIMMEE (sunan da suke kiran mahaifiyarsu dashi) yace yana k'ara shegewa jikinta, dariya tayi ta shafa kansa, tace " HANASH kaci abinci? "No Mimmee ba yanzu ba ,bari nayi wanka tukunna, d'ago shi tayi daga jikinta tana facing d'inshi tace " zaka fara ko? Dan tasan Hanash baya san cin abinci, a shagwab'e yace " Allah Mimmee wanka zanyi kawai, " to yi sauri ina jiranka ta fad'a tana zama akan sofa, yace " ok Mimmee gv me just 20 minutes، ya wuce part d'insa da sauri. Alhaji WASEEF DIKKO sanannan d'an kasuwa ne Nigeria, harma da k'asashen k'etare,yana da matar aure d'aya tak AFROOZ, wacce sukayi auren soyayya ,duk da ta kasance 'yar k'anwar mahaifiyar sa ce, yana da yara uku mata biyu namiji d'aya, HANASH shine babba ,sai da yayi wajen 13yrs sannan Mimmee ta k'ara haihuwar twins duk mata ZOHAL & WAJNAH, mahaifin su wanda suke kira da PAPU, mutum ne adili mai tausayi da j'in k'an talawa, yana da kyauta sosai shiyasa mutane keyi masa lak'abi da DIKKO RUWAN SAMA NA KOWA, saboda tak'aice sunan ake kiransa da DIKKO RUWA, duk inda yaji ana buk'atar taimako da gudu yake yakaiwa, mutum ne shi mai imani da tsananin tsoran Allah, kwata-kwata bashi k'aunar yaga wani acikin matsalar rayuwa, burinshi kullum taimakon mutane koda duk abinda ya mallaka zai k'are bai damu ba,, gashi da san zumunci, mutum ne shi mai san raha da barkwanci, mai kyautatawa na k'asa dashi, zuciyarsa a tsarkake take matuk'a, bai san wani abu fushi ko b'acin rai da fad'a ba, duk iya shekarun da zaka d'iba dashi, bazaka tab'a ganin yayi fushi ko yana fad'a ba, kullum fuskarsa da ransa a sake suke cikin fara'a, haka ma matarsa Hajiya AFROOZ, mutunyar kirki ce, kwata-kwata ba ruwan ta rayuwar duniya ko kyalele, macece kamilar gaske nutsatstsiya ,mai hak'uri da tausayi, Hanash yaro ne Classic, handsome and ajebota guy, d'an gayu mai ji hutu, mai tsananin biyayyar iyaye , da duk wanda ya girmeshi, yana da matuk'ar hak'uri da kauda kai, duk tarin dukiyar mahaifinsa hakan bai saukar masa da girman kai ba, sai dai bai d'aukar raini daga wajen koma waye, yaro ne mai tausayi da jin k'ai, kwata-kwata bashi da girman kai ko raini da wulak'anci, ko irin jijji da kan nan irin na yaran masu kud'i bashi dashi, yana zaune da kowa lafiya,gashi da san wasa da dariya, yana da d'an surutu amma ba sosai ba, kuma ba koyaushe ne yake san magana ba, dan akwai randa zai iya kwana ya tashi batare da yayiwa kowa magana ba, Allah yayi shi mutum mai sanyin rai da zuciya, amma bai iya b'acin rai ba, dan idan ranshi ya b'aci zai iya yin komai, zai kuma iya taka kowa , kusan mutum mai hak'uri bai iya fushi ba, babu abinda yafi tsana a rayuwar sa kamar raini da wulak'anci, muddin kace zaka raina shi koka wulak'anta shi, bazaku tab'a shiryawa dashi ba, balle ku zauna inuwa d'aya, muddin kana san ganin b'acin ran Hanash to ka nemi kawo masa raini da wulak'anci, anan zakaga fuskanci tantirancin rashin mutuncinsa, baya san mutum bai tsiwa da rashin kunya, da mutum bai yawan hayaniya da surutu, muddin kana san kaga b'acin ransa, to ka nemi kawo masa rai ni, ko ka wulak'anshi, anan zaka fuskanci tantirancin rashin mutuncinsa. Hanash nutsatstse ne kamili, mai aji da izza gami da tsafta dan kallo d'aya zaka yi mishi kasan cikekken d'an gayu ne, duk abinda zakaga yayi amfani dashi to mai tsada ne (designer),,, yana da muguwa tsafta da gayu kamar mace, dan idan kaga yadda yake gyara d'akin shi zaga sha mamaki, gaban mirror d'insa kuwa jere yake da kayan shafa iri-iri da perfumes,, yayi mugun tsanar mace marar kamun kai, da fitsara, ko tsiwa, muddin yaga mace da irin wad'annan d'abi'un yanzu zaiji ya tsane ta, sai dai duk sanyin ran Hanash yana da fushi dan idan ransa ya b'aci idansa rufewa yake yi, sai dai kaga yana ta faman huci kamar mesa, Hanash bai iya k'iyayya ba ,dan idan ya tsani abu ya tsane shi kenan har abada, ko ganinsa bai san yi, duk duniya babu abinda yafi so kamar iyayensa da k'annansa , akan su babu abinda bai iya yi, mahaifiyar Waseef Papu wacce suke kira da JADDA, tana nan a raye, macece mai tsananin iko da mulki, duk Family tsoranta ake ji, dan haka sai abinda tace akeyi a gaba d'aya Familyn, muddin Jadda ta zartar da hukunci toya zartu babu makawa, idan ko tace eh, duk duniya babu wanda ya isa yace a'a, hakama idan tace a'a babu wanda ya isa yace eh, sai Allah, babu wanda ya isa tayi magana kota zartar da hukunci yace ba haka ba, kwata-kwata bata san rai ni, duk duniya babu abinda Mimmee da Jadda suka fi kamar suga Hanash yayi aure, gashi shi ko buduwar bai da ita, dan gani yake kamar har yanzu bai samu kalar macen zai so ko zai iya zama da ita ba. Su Sanah na shiga gida ta wuce part d'in Halan , Khulud tabi bayanta, a zaune suka iske Halan tana shan fruits, da sauri Maheen ta tare su tana cewa " oyoyo Aunty's, ko kallanta Sanah batayi ba ta wuce bathroom, Halan tabi bayanta da kallo, kana ta mayar da kallanta ga Khulud data d'auki Mash, tace " waya tab'a ne? Khulud tayi dariya kana ta bawa Halan labarin duk abinda ya faru,,, Halan ta saka dariya harda hawaye,, tana cikin dariyar Sanah ta fito,d'aure da towel ta kalli Maheen tace " jeki bedroom d'in mu ki d'auko man kaya da pant, batare data kalli inda Halan take ba ta wuce kan dinning table danta lura da dariyar da Halan ke kannewa, tuwon semota miyar agushi ta zuba ta fara ci, Khulud tace " my Sanah laifin me nayi ne? Batare data kalle ta ba tace " me kika gani? Khulud tace " gani nayi ana cin abinci bako tayi, Sanah tace " da tayi nake yi miki inzamu ci ? Ta kuma yin maganar batare data kalli inda take ba, Khulud tayi murmushi kana tace " a'a, Sanah bata kuma cewa komai ba ta cigaba da cin abincinta, Halan tace " lalle yau ran 'yan maza ya b'aci, tunda ba'a kyale Ulud bama waza'a kyale, bari muyi ta kammu mu shafawa kammu ruwa, Sanah tayi kwafa kana tace " kuma dai, Maheen ta shigo da gudu ta mik'awa Sanah kayan, ta amsa ta shige ciki, Halan da Khulud suka saka dariya, Halan tace " badai mu muka kar zamon ba, bata juyo ba tayi ciki fuuuuu, Khulud ta kalli Halan tace " uhmm bari inbi kaya na in lallab'a ta, bazan bari ki had'a mu ba, tayi maganar tana bin bayan Sanah, Halan tayi dariya tace " ki tsaya kici abincinki dan ya fiye miki, Khulud bata kuma magana ba ta shige ciki wajen sanah, tsaye ta iske ta agaban mirror tana zipping doguwar rigarta, Khulud ta shiga ta zauna a bakin gado had'i da zubawa Sanah ido, taga bata kwata-kwata Sanah bata bi ta kanta ba balle ta kalli inda take zaune, 'yar ajiyar zuciya Khulud ta sauke a hankali kana tace " me nayi miki my Sanah? Batare data kalle ta ba tace " wani abun kika gani ne? Khulud tayi rau-rau da ido zata fara kuka, cikin rawar murya tace " idan wani abun nayi miki kiyi hak'uri please, tayi maganar tana kama kunnanta, alamar sorry, ganin Khulud nasan yin kuka yasa Sanah rolling sexy eye's d'inta, had'i da zama kusa da ita tace " meye kuma na kukan? Khulud tace " ba ke ba ce, ta fad'a a shagwab'e, Sanah tace " to yi hak'uri na daina ban k'arawa, kema ai kece kika zab'i wani can bare a kaina, sannan kuka yi man dariya ke da Aunty Halan , Khulud tayi murmushi tace " I'm sorry ban k'arawa, Sanah tayi murmushi tana rik'o hannunta, "ta so muje kici abinci nasan kina jin yunwa , tayi maganar tana rik'e da hannun Khulud zuwa dinning table, Halan tayi gutun murmushi tace " hmmm kudai kuka sani, ai _*RASHIN SANI*_ ne zai saka mutum shiga tsakanin ku, basu kula ba ta,Sanah ta zubawa Khulud abincin tace " kici sai mu shiga mu gai da Juju da Mamu, "to Khulud tace tana saka hannunta cikin abincin. Cikin sauri yayi wankan ya shirya cikin 3 quarter da t shirt max, ya shafa lotion olay kana ya feshe jikinsa da perfumes kala-kala, da sauri ya fita dan ya tabbatar Mimmeensa nacan na jiransa, kamar yadda yayi tsammani haka ya tarar da ita zaune akan sofa kamar yadda ya barta , tana zaman jiransa, da sauri ya k'arasa yana cewa " I'm so sorry Mimmee na, na barki kina jira na, mik'ewa tana murmushi ta rik'e hannunsa tayi dinning table dashi, da kanta ta shiga bashi jollop couscous daya sha vegetables & dry fish, dan kwata-kwata Hanash baya san cin abinci tun yana yaro sai an sha fama dashi kafin yaci abinci, dakyar yaci rabin plate shima saida Mimmee ta matsa masa sannan, a hankali ya mik'e cikin takunsa na isa da tak'ama, dan duk da Hanash bashi girman kai , akwai shi da takun isa,tak'ama da izza, idan yana tafiya sai ka rantse baya san taka k'asa, haka ma duk da kasancewar shi mai sauk'in kai baya barin takwana, akwai shi da bak'ar magana, dan idan ya yab'awa mutum bak'ar magana sai kaji kamar kabar garin, sai dai mutum ne shi mai yawan murmushi da fara'a, ko ransa ne ya b'aci wani lokacin sai dai yayi murmushi kawai, Mimmee ta kalle shi tace " ina kuma zuwa? Yace " zan shiga wajen Jadda mu gaisa daga nan kuma zanje ball, "Ok Allah ya tsare, Mimmee tace tana murmushi. Bayan Khulud ta gama cin abinci Sanah ta mik'e tace " muje , ba musu Khulud ta mik'e tabi bayanta, har sun kai bakin k'ofa Sanah ta dawo ta d'auki Mash, dayake ta faman kukan sai ya bita, Khulud kuma ta rik'e hannun Maheen suka fita, Halan ta bi su da dariya, part d'in Juju suka fara shiga suka iske bata nan dan haka suka koma part d'in Mamu nan bata nan, Sanah ta kalli Khulud tace " ina kuma suka je? Khulud tace " kin manta gobe ne walima wata k'ila sunje siyayya ne, Sanah ta zaro ido ,tace " wallahi na manta yi sauri kiyi wanka , muje sallon & henna d'in, kinga har wajen 2:00pm na rana yanzu, "ok kawai Khulud tace , batafi 20 minutes ba ta fito sanye da irin doguwar rigar jikin Sanah sak, ta material purple color, takalmin su vine plate shoe mayafan su ma duk iri d'aya, black color, sukayi rolling da mayafan su, suka fita, suna fita driver ya taso yana murmushi yace " 'yan matan hajiya ina zuwa? Dariya sukayi masa, kana Sanah tace gyaran kai da k'unshi, yana murmushi yace " inda na saba kai ku dai? Khulud ta amsa masa da "eh, a bakin wani babban wajen saloon da wankin k'afa & henna dake Lamid'o crescent yayi parking, suka fito, cikin girmamawa suka ce " mun gode, yayi murmushi yace " injira ku ne manyan gobe? Cikin girmamawa Sanah tace " a'a Baba ka tafi kawai idan mun gama ma hau napep, dayake duk halinta tana ganin mutuncin ma'aikatan gidan su, babu wani abu na rashin mutumci ko fitsara daya tab'a shiga tsakanin su, tana basu girma da mutuncinsu, yace " manyan gobe, bazan barku ku hau napep ba, meye amfani na, ku dai kira ni idan kun kammala, Sanah tace " to mun gode Baba, yayi murmushin jin dad'in, kana yaja motar ya tafi su kuma suka shiga ciki, dayake wajen babba ne sosai akwai ma'aikata da yawa yasa babu layi, ba'a jima ba aka fara yi musu bibbiyu, wata na gyara musu kai,wata kuma na wanke musu k'afa, kafin daga baya aka fara yi musu k'unshi mai 2 colors red & black, wajen 5:30pm na yamma aka kammala musu komai suka fito, sunyi masifar yin kyau sai kace amare, kamar mutum ya sace su ya gudu, Khulud ta kalli Sanah tace " oh! kinga mun manta bamu sanarda da Baba driver bamu da phone ba, Sanah taja d'an gutun tsaki " mtswwwww, yanzu irin haka ne ko matsala mutum ya shiga babu yadda zayyi ya sanar a gida, Khulud tace " gaskiya nima dai rashin wayar nan ya fara damuna, Sanah tace " ai dai ance da mun gama Secondary School za'a bamu ko? "To ai yanzu mun gama, Khulud tace " sai mu tsaya muga iya gudun ruwan su, suna tafiya suna maganar, Khulud tace " ga wajen nan shiru , yanzu ko a ina zamu samu napep? Sanah ta kuma jan dogon tsaki " mtswwwwww, ga magrib ta kawo kai ba, _*RASHIN SANI*_ ne yasa Khulud cewa " muyi trekking zuwa bakin titi, Sanah ta kuma jan tsaki mtswwwwww, cike da haushi tana turo baki,, hand bag d'in dake hannun Khulud ta sub'uce mata ta fad'i k'asa, d'an tsaki taja "mtswwwww kana ta sunkuya k'asa zata d'auka, Sanah na cigaba da tafiya, dan bata san Khulud ta duk'a d'aukar jaka ba tace " wa...............! bata k'arasa ba sakamakon jin wani irin ruwa a fuskarta da bakinta, a razane ta d'ago kanta da niyyar kallan wanda ya watsa mata ruwan amma sai me....................!!! MOMYN ZARAH _*RASHIN SANI.......*_ *HAUWA A USMAN* _JIDDARH_ ```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh``` 1⃣7⃣ Amma sai me? wanda ya jefa ta cikin ruwan kwata d'azu, taga irin motarsa sak, jikinta tabi da kallo taga gaba d'aya ya b'ata mata jikinta ruwan kwatar, har fuskarta da bakinta, Hanash na d'ago kansa yaga 'yan matan d'azu, still ya kuma b'atawa da ruwan kwata, a hankali ya furta " ya salam , had'i da runtse idansa, Khulud ta d'ago tana cewa " jakar m........, tsaida maganarta tayi ganin abinda ya faru, Khulud ta kalli Sanah kana ta mayar da kallonta ga motar, Sanah na tsaye takai iya wuya, ta k'ufula sosai, Khulud tace " my San..... dakatar da ita Sanah tayi ta hanyar d'aga mata hannu, muryarta na cracking saboda tsananin b'acin rai tace " ai yanzu kinga ni ko? " So sai ki barni dashi naga dame yake tak'ama, ta fad'a idanta nakan motar, Khulud ta sauke ajiyar zuciya had'i da zubawa motar ido, ganin bashi da niyyar fitowa ne yasa Sanah takawa zuwa bakin motar, Khulud tayi saurin rik'o ta ,ta fisge , cikin zafin rai ta fara dukan glass d'in motar da k'arfi, a hankali ya bud'e idansa had'i da sauke su a kanta, yayi mugun mamakin ganin yadda eye color d'inta suka canja , saboda tsabar masifa da ruwa bala'i, bata tsoran koshi irin mugayen mutanan nan ne, gaba d'aya idanta ya rufe saboda tsiwa, murmushin takaici yayi kana yace " bari na bud'e naga mai zata iya yi, cikin isa yayi k'asa da glass d'in, ga mamakinsa yaga ta kalle ido cikin ido tace " fito, tayi maganar cikin fad'a, Khulud ta k'araso wajen da sauri tana cewa " wai meye haka ne My Sanah? Bata kalle ta ba ,ta kuma cewa " fito, "my Sanah meyasa baki da hak'uri da kau dai kai ne a rayuwa? Cikin masifa ta kalli Khulud tace " ko? Khulud batayi magana ba ta fara k'ok'arin rik'o hannun Sanah, ta kuma fisgewa, tace " Allah ban tafiya sai na d'auki mataki, murmushi ya kuma yi a karo na biyu, kana cikin isa da tak'ama ya ziro k'afafunsa k'asa ya fito, had'i da sark'e hannuwansa a k'irji ya jingina da jikin motar yana kallanta, yana san yaga mai zai zata iya yi, Khulud tace " dan Allah my Sanah kizo mu tafi gida, Sanah tace " idan ban rama ba bazan huce ba, d'azu ma haka yazo har inda nake ya b'ata man jiki , yanzu ma shine ya kuma biyo ni ya b'ata man jiki, Khulud tace " ki rama me? " Shifa Namiji ne Sanah, ina ke ina fad'a da Namiji, ko kina tunanin idan kinyi akwai ribar da zaki samu? " Kuma da kike cewa yana bimmu, baki tunanin hanya ke had'a mu? " Hanya ai ta kowa da kowa ce, shi dai ba sanin mu yayi ba ,balle muce ko yana bibiyar mu ne, da d'azu da yanzu duk Allah ne ya had'u mu hanya d'aya dashi, batare da sanin mu ko sanin shi ba, please my Sanah ina baki shawarar duk mutumin da Allah ya had'aki dashi kiyi k'ok'arin zama da rabuwa dashi lafiya, saboda babu wanda yasan gobe sai Allah, Sanah tace " gobe akan wa kenan? " Wai kina nufin wannan? Tayi maganar tana nuna shi a wulak'ance, kana ta cigaba " kin san Allah sai na rama na koya mishi hankali, murmushi takaici yayi yace " wazaki koyawa hankalin? Tace " kai! a fad'ace, yace " ok Bismillah ina jira, ya fad'a yana gyara tsaiwarshi, batayi magana ba ta fara dube-dube, da sauri Khulud ta k'arasa gabansa tace " please dan girman Allah kayi hak'uri ka tafi, tattausan murmushi yayi mata yace " no badamuwa ki barta naga abinda zata iya, Khulud tace " ni dai please ka tafi, ta fad'a kamar zatayi kuka, ya bud'e baki zayyi magana yaji saukar ruwan kwata a fuskarshi da jikinshi, a hankali ya kalli jikinsa ya maiyar da kallansa ga Sanah, da sauri Khulud tasa hannuwanta ta tushe bakinta, had'i da zaro idanta waje cikin tsoro, kafin yayi aune ta kuma d'ebo ruwan kwatar ta k'ara zuba masa, har a jikin motarsa, abinka da mai hak'urin dabai iya fushi ba, mutumin da bai san raini da wulak'anci, take zuciyarsa tayi sama jikinsa ya d'auki kerrrma saboda tsabar b'acin rai, kalar idansa ta koma pure red, cikin tsuma Khulud tace " my Sanah meye haka? Tace " oho ban sani ba abinda yayi ne akayi masa, tayi maganar tana kallansa shek'ek'e, cikin zafin rai ya kalle ta yace " ke ni kika watsawa ruwan kwata? Tace " idan baka gani bane kake tambayata bari na tabbatar maka, tayi maganar tana k'ok'arin k'ara d'ebo ruwan kwatar, batayi aune ba sai jin saukar gigitattun marika kyawawa guda biyu tayi a jere, yana shirin finciko ta Khulud tayi saurin shiga tsakiyarsu, bata san sanda ta d'ora hannunta akan k'irjinsa dai-dai saitin zuciyarsa tana tura shi baya ba, wata irin muguwar fad'uwa gaban Hanash yayi, jin sabon al'amarin dabai tab'a ji ko tsintar kansa a ciki ba, da sauri yaja baya while zuciyarsa na k'ara beating so past, saboda tsabar rud'ewa Khulud ta k'ara binsa tana k'ok'arin k'ara d'ora hannunta akan k'irjinsa, da sauri ya rik'e hannunta, gudun karta sake haifar masa da abinda yaji, hannunshi daya tab'a nata yasa shi jin mugun shock, saurin sakin hannun nata yayi yana ja baya, a haukace Sanah ta fara neman abinda zata bugawa Hanash, sanin halin Sanah yasa a kid'ime Khulud ta kuma d'ora masa hannunta akan k'irjinsa tana tura shi baya, sororo Hanash yayi kamar wanda aka cirewa laka, saboda yadda yake jin gaba d'aya mode d'in jikinsa ya canja, shu'uman idonuwansa kawai ya zubawa Khulud yana kallan yadda ta kid'ime gaba d'aya, sai da ta kai shi har bakin motarsa ta tura shi ciki kana ta koma wajen Sanah dake ta faman neman abun duka, kasa tuk'in motar Hanash yayi dan wani iri yake jin jikinsa, da sauri Khulud ta rik'e Sanah gam ta rik'e k'ugunta ta baya, murya Khulud ta d'aga tana ce masa " ka tafi! ka tafi , jin muryarta yasa shi dawo hayyacinsa, cikin mutuwar jiki yayiwa motar key yaja while idansa nakan Khulud. Da sauri Khulud ta tare mai napep ta danna Sanah sukayi gida, tun a harabar gidan Sanah tayi cilli da talami da mayafinta , batayi part d'in Halan ba, tayi part d'in Mamu direct bedroom d'insu ta wuce, Mamu na tambayarta lafiya amma bata tsaya ba, kai Khulud ta girgiza tana bin bayan Sanah da kallo, kana ta sunkuya cikin nutsuwa ta kwashe kayan da Sanah tayi watsi dasu a harabar gidan, tabi bayanta, a parlor ta iske Mamu tana kallan k'ofar bedroom d'in su, "Assalamu Alaikum, Khulud tace tana shiga parlorn , Mamu ta d'aga kai ta kalle ta tana amsa sallamar tata, Khulud na niyyar shigewa Mamu tace " ita kuma wancan ita da wa? Khulud tace " ita da wata mata ne, tayiwa Mamu k'arya dan tasan muddin Mamu ta san Sanah tayi fad'a da Namiji sai ta ci ubanta, Mamu tace " wata mata kamar ya? Khulud tace " ban san sunnanta ba, a wajen saloon muka had'u,tayi maganar cikin alamun rashin gaskiya, Mamu tace " to da kuka had'u a wajen saloon sai akayi yaya? Tayi maganar idanta nakan Khulud danta hango rashin gaskiya k'arara a tattare da ita, " budurwa ce fa kamar mu Mamu, Khulud ta fad'a danta kawar da wancan maganar, Mamu ta bud'e baki tace " oh ashe fa ku 'yan mata ne ko? Khulud tayi saurin rufe fuska tana niyyar shigewa, Mamu tace " shiyasa kenan ake san yiwa Mamu wayo ko? Mamu ta fad'a tana kallan yanayinta, kana ta cigaba " meya had'a ku da matar? Khulud tace " nothing but serious, Mamu ta tab'a baki, kana tace " Allah ya kyauta, kuma Allah idan na bincika na gano baku da gaskiya kun shiga uku, Khulud tayi murmushi tabare datace komai ba, ta shige ciki wajen Sanah'rta,, a kan bed ta iske Sanah ta had'a kai da gwiwa tana sharar kukan bak'in cikin an mare ta bata rama ba, da hanzari Khulud ta k'arasa gare ta tana d'ago kanta tace " my Sanah meye kuma abin kuka? Tayi maganar muryarta na rawa, kwace jikinta tayi ta d'an matsa gefe, while tana cigaba da kukanta, cikin sanyin murya Khulud tace " ni ce na b'ata maki rai? Sanah tayi mata banza, Khulud tace " kina san nima nayi kukan? Tayi maganar muryarta na cracking, jin yadda muryar Khulud ke rawa alamar tana san yin kuka ne yasa ta d'ago kanta, had'i da zuba mata jajayen idanuwanta, Khulud tace " wannan duk akan shine? Ta fad'a tana nuna mata hawayen dake cigaba da zubowa, cikin muryar kuka Sanah tace " I hate him , I really hate him more & more most, I never hate someone like him, murmushi Khulud tayi tace " har Sir Moli? Sanah ta juya jajayen idanuwanta tace " ashe ke har tuna shi ma kike yi? Khulud tace " ai naji kince before ne, ni kuma nasan kin fad'i wannan kalmar akan Sir Moli yafi a k'irga, Sanah ta zumb'uro baki tana cewa " Allah nafi tsanar wannan akan Sir Moli, shi ai bai tab'a mari na ba, kuma koma ya tab'a shi ai malami na ne, amma shi wannan k'atilan mak'atulan ya kama ni ya mara haka nan a banza, wallahi ban tab'a kyale shi sai na rama, Khulud tace " ki rama me? Sanah tace " marin dayayi man mana, Khulud tace " ina zaki kuma ganin shi balle har ki rama? Sanah tace " in dai kere na yawo zabo na yawo wata rana za'a had'u, "hmmm wato har kina saka ran sake ganin shi kenan? Sanah tace " sosai ma, kodan bashin marin daya d'auka nasan wata rana dole zamu had'u, kuma wallahi a duk inda na ganshi sai na rama kuma duk yawan shekarun daza'a d'auka, Khulud tace " alk'awari fa kika d'aukarwa kanki kenan,, Sanah tace " sosai ma kuwa, ki kuma aje wannan a ranki, Khulud tace " ni dai tashi muje mu ji ya shirye-shiryen walimar mu, Sanah tace " bari nayi wanka na canja kaya tukunna, ta fad'a tana shiga bathroom,, bata jima ba ta fito ta canja kaya, kana suka fita, a parlor suka iske Mamu kamar yadda suka barta, Mamu ta bisu da kallo tana tab'a baki tace " ikon Allah har anje an lallaso ta kenan? Sukayi dariya suna zama akan sofa, "wato duk fushin da d'aya tayi da d'aya ta bata hak'uri take hak'ura, Sanah tace " ai dole a hak'ura Mamu, Aarib ya shigo sanye da jallabiya, Sanah na ganin shi ta zumb'uri baki had'i da kauda kanta gefe, dariya yayi yace " me aka yiwa amaryar mu ne naga tana ta kumbure-kumbure? Sanah ta kuma turo baki tana kauda kai gefe, batare da tace komai ba, hannayensa daya b'oye a bayansa ya ciro ya mik'awa Khulud walin sabuwar waya k'irar IPhone 10, ihuuu Khulud tayi had'i da buga tsalle ta rungume shi, light kiss tayi masa a chicks d'inshi , "nagode sosai Big Bro, ta fad'a tana bud'e kwalin wayar, hannunta na rawa ta ciro red color iPhone 10 d'in daga kwalinta, Sanah na ganin wayar ta rud'e ta mik'e da sauri, tace " Yaya ina tawa? " Ke da kike fushi dani Matar mu, baki ta turo tace " Yaya ai na fad'a maka ban san sunan da kake fad'a man, yace " wanne sunan? "Matar mu ko amaryar mu mana, kuma kak'i fad'a man ma'anar sunanyen, Mamu tayi dariya tace " bake kad'ai ba, nima nayi-nayi ya fad'a man amanar sunayen yak'i, kai ya shafa, had'i da fiddo kwalin wayar ya d'aga sama,, dan ya kawayar da maganar, cike da murna Sanah ta fara tsalle tana rirrik'eshi tana k'ok'arin kamo hannunsa danta karb'i wayar, k'irjinsa na gogar nata, jin tana neman canja masa emotions yasa shi saurin mik'a mata wayar yana dariya, da sauri ta bud'e kwalin taga irin ta Khulud sak har color, tsalle tayi had'i da fad'awa jikinsa ta rumgume shi, tayi mishi light kiss itama a kumatunsa, " Yaya nagode sosai tace cike da farin ciki, da sauri ya raba ta da jikinsa yana dariyar yak'e, fita tayi da gudu kanta ba ko d'an kwali tace " na tafi na nunawa Aunty Halan, ta daina mana gori, Khulud ma tabi bayanta, Aarib yayi saurin bin bayanta danya rik'o ta ganin gidan akwai ma'aikata maza, amma kafin ya rik'o ta harta kai farfajiyar gidan, Khulud na biye da ita a baya, ganin yadda ma'aikatan ke kalla Sanah , ga kanta bako d'an kwalli ya saukar mishi da bak'in ciki,, ya runtse idansa da k'arfi, da gudu suka shiga parlorn Halan suka iske bata nan tana kitchen, da gudu suka bita kitchen ta baya suka rungumo ta a tare, suna cewa " muma yanzu mun wuce gori, sukayi maganar suna nuna mata phone d'in, "woow Halan tace " tana karb'ar wayoyin daga hannunsu, waya saya muku? Cikin zumud'i suka " Yaya Aarib, Halan tace " kai masha Allah, amma shine ko yayi kara ya had'o da Auntyn taku, tayi maganar cikin tsokana, Sanah tace " ke da mijinki ya tashi siya miki wani yayiwa karar? Daga bayan su suka ji muryar Ziyad na cewa " zanci ubanki Sanah, da sauri ta juya bayanta, taganshi zaune a parlor yana kallan labarai, da alama ma anan suka wuce shi basu kula dashi ba,, Sanah ta kulli Halan ta tab'a baki kana tace " ashe yana nan? Halan tayi murmushi batare da tace komai ba, ta mayar da hankalinta kan wayoyin tace " to yanzu daya siyo muku iri d'aya sak har color ya zaku rink'a bambamce ta kowa? Sanah tace " wannan ai ba damuwa bace, tunda kayanta nawa ne, kaya na ma nata ne, kuma ba yau muka fara abu iri d'aya ba, dai-dai da reborn, pand & bra iri d'aya ne damu sak, Halan tace " to sarkin bada amsa, ta fad'a tana mik'a musu wayoyinsu, da sauri Khulud tace " lah ashe harda sim card? Sanah tace " da gaske? Tana duba wayar, aiko da gaske MTN nema a ciki, Sanah ta fad'a, Khulud tace " aiko yanzu zamu bud'e Facebook, WhatsApp, Instagram, Twitter and Snap chart, Halan tace " to fa ba'a samunba, ai dama yanzu mun shiga uku kuma cewar Seenah tana dariya, "lahh ashe kina nan Aunty? Suka ce, tace " eh , yanzu zan koma gida dama shigowa nayi naga ya jiki-jikin nata, Sanah "oh bamu kula dake ba, Seenah tace " dama ya za'ayi ku kula dani, hankalinku nagan waya, duk sukayi dariya. Hanash na komawa gida direct ya wuce part d'in shi, abinda bai tab'a yi kenan a rayuwarshi ba, ya shigo gida ya wuce part d'in sa kai tsaye batare dayaje yaga Mimmeensa ba,, kayansa ya cire yayi niked kana ya shiga bathroom ya sakarwa kansa shower, ko wankan kasa yi yayi ya fito d'aure da towel a k'ugunsa , ya fad'a kan bed ta baya, gaba d'aya ya rasa meke damunsa, wani irin bak'on al'amari yake ji yana ratsa ruhi da gangar jikinsa, gaba d'aya jikinsa babu dad'i wani iri yake jinsa kamar rashin lafiya ke san kama shi, jikinsa duk yayi sanyi, babu abinda yake gani sai yarinyar tsaye a gabansa, haka ma zuciyarsa ta hana shi sakat, da tunaninta, daya rufe ido ita yake gani tsaye a gabansa, ko da daddare kasa shiga part d'in Mimmee yayi, haka ya kwanta baici komai ba. Washe gari tunda safe su Sanah suka fara shirye-shiryen walima har wajen 2:40pm, suna aikin had'a coslow Halan tace " wai ni kun karb'o d'inku nan ne banga kun nuna min ba? Tayi maganar tana cigaba da goga carrot, ido duk suka zaro waje Khulud tace " Subhanallah wallahi Anuty Halan mun manta bamu amso ba, da sauri Halan ta kalle su tace " what!? Wai kuna nufin baku amso d'inkin kayan dazaku sanya ba ko me? Sukayi tsilli-tsilli da ido, Halan tace " to uban me zaku saka? Ta kuma tambayar su, a k'ufule, duk sukayi shiru, cikin fad'a Halan tace " wai ba tambayar ku nake yi bane? Cikin sanyin ta Khulud tace " we are sorry our Aunty Allah mun manta ne, Sanah tace " sorry bari muje mu amsa yanzu, ta fad'a tana mik'ewa, tsaki Halan tayi kana tace " duk ku biyun zaku tafi amso d'inkin ko me? Sanah tace " eh mana, " a' a d'aya taje ta amso muku d'inkin, d'aya kuma ta zauna anan ta shirya tunda lokaci ya fara k'urewa, tayi maganar batare data kalli inda suke ba, tsayawa sukayi cirko-cirko akanta su basu tafi ba, ba kuma su zauna ba, ta kalle su tace " uban me kuke jira kuma? Khulud tace " dan Allah Aunty ki barmu mu tafi tare please, " mstwwwwwww sai ku tafi, kuma wallahi kuyi sauri ku dawo, karku sake ku b'ata man lokaci, Halan ta fad'a tana cigaba da aikin gabanta, "to suka ce, kana suka koma part d'in Mamu suka jira simple dogayen riguna bak'ak'e suka sanya, sukayi rolling kan su da mayafi, Baba driver na hango su ya taso da sauri ya nufo yana murmushi, yace " manyan gobe fita za'ayi ne? Murmushi sukayi su duka biyun, kana Khulud tace " eh Baba shagon Barrister mai d'inkin mu zaka kai mu, yace " na sallari gidan bulo? Suka ce " eh, " manyan gobe ku shiga mu tafi, yayi maganar yana k'ok'arin bud'e musu mota, Sanah tayi tare shi tana murmushi tace " ka barshi Baba ka bari zamu bud'e da kanmu, idan mu bamu bud'e maka ba, ai bazamu bari kai ka bud'e mana ba, ta k'arasa maganar tana zama a cikin motar, yayi murmushi batare dayace komai ba yaja motar. Gaba d'aya jikin Hanash a mace yake kwata-kwata ya rasa abinda yake damunsa, jinshi yake kamar mara lafiya, dan ko dad'in bakinsa ma baya ji, dan haka tun jiya bai iya cin komai ba, yadda ya kwanta tun dare daga shi sai towel haka ya kwana, sai asuba kana ya mik'e yayi alwala ya zura jallabiyya yayi sallah, ya dad'e sosai akan prayer mat yana azkhar da addu'o'i akan sabon yanayin daya tsinci kanshi, anan kan sallayar ya kwanta, bacci mai nauyi yayi awon gaba dashi, dan bai wani samun ishashshan baccin dare ba, Mimmee ta kasa zaune ko tsaye, hankalinta yayi mugun tashi ganin har azhur bata saka Hanash a idonta ba, abinda bai tab'a faruwa ba, dan muddin Hanash yana k'asar bai iya kwana batare daya ganta ko yaji lafiyarta ba, tun jiya ta tambayi mai gadi ya shaida mata ya dawo ya shege part d'insa ne, tun jiya taso ta bishi taji ko lafiya amma sai tayi tunanin bari ta bashi privacy, a hankali ta d'aga kanta taga har wajen 1:50pm, Hanash bai fito ba, jikinta a sanyaye ta fita ta nufi part d'in shi, cikin sanyin jiki ta fara knocking k'ofar, cikin baccinsa mai cike da mafarkinta yaji sama-sama ana buga k'ofar, firgigit ya farka, cikin sanyin sa ya mik'e zauna yana cusa hannu cikin kwantaccen gashin kansa, jin an k'ara buga k'ofar ne yasa shi d'aga kansa ya kalli k'ofar, ya tabbatar Mimmee ce , dan ya san babu mai zuwa part d'insa balle har yayi masa knocking, saboda yana da privacy ya hana duk masu aikin gidan zuwa part d'insa su gyara masa, shi da kanshi yake gyara kayansa, k'ara buga k'ofar Mimmee tayi, da sauri ya mik'e a hankali yana cigaba da cusa hannunsa cikin kwantacciyar sumarsa, a hankali ya bud'e mata k'ofar ta shigo, idanta na kansa tace " lafiya Son najika shiru tun jiya? Kansa ya kuma shafawa yace " lafiya lau Mimmee, ido ta k'ura masa tace " amma shine baka zo ka ganni ba? Yace " kai na ke ciwo nasha magani, ban san sanda bacci ya d'auke ni ba, ya fad'a cikin sassanyar muryarsa mai dad'in sauraro, ido ta k'ura masa na wani lokaci kana tace "are you sure? Yace " yes Mimmee yana kyataccen murmushinsa mai tsada, hannunta ya kama yana cewa " muje ki bani breakfast Mimmee yunwa nake ji, ya fad'a danya kawar mata da hankalinsa daga gano abinda shi kansa bai san takamaimansa ba, dan yasan muddin Mimmee ta gano yana cikin damuwa koyaya take tada hankalinta zatayi sosai, dariya Mimmee tayi tace " breakfast ko lunch? Tayi maganar tana zaunar dashi akan sofa, yace " ni dai abani koma meye yunwa nake ji, Mimmee tayi mamakin yadda yau Hanash da ke kansa ke cewa a bashi abinci yunwa yake ji, a bowl ta zubo mishi farfesun kan naman rago, ta had'o masa da plantain & chips , ta kawo mishi da sauri ya amsa ya fara ci, yana sanya lomar farko a bakinsa yaji kamar ya sanya mad'aci, gudun kar Mimmee ta gane yasa shi cusa abincin kad'an badan yaso ba, a hankali ya cire hannunsa daga cikin abincin, yace " Alhamdulillah, thank you so much Mimmee, Mimmee ta kalli d'an abincin daya yakusa kana ta mayar da kallanta gare shi tace " har kayi me? Murmushi yayi daya fito da kyanshi sosai yace " na k'oshi Mimmee ya fad'a cikin shagwab'a, Mimmee tace " ni dama nasan ba wani cin abincin zakayi ba, yace " Mimmee naci sosai fa duba ki nani, yayi magana yana nuna mata cikinsa, dariya tayi tace " to Son, yanzu kuma ina zuwa? Yace " kai Mimmee duk inda zaki sai kin tambaye ni, yanzu fa na girma, yayi maganar a shagwab'e, Mimmee tace " oh! k'ato a dawo lafiya Allah ya tsare, yace " amin ya Allah, my Mimmee thank you, kana ya fita, bedroom d'insa ya koma ya watsa ruwa, ya sanya simple t-shirt (red tag), da 3 quarter shima na company red tag, ya sanya takalmi boot Nike, kallo d'aya zaka yi mishi kasan anci uwar kud'i wajen siyan kayan cikinsa, kayan sunyi mugun yi mishi kyau da amsar cikekkiyar surar jikinsa mai zati, kana ya feshe jikinsa da manyan perfumes, kyan sura dana fuskarsa ya fito sosai, idan ka ganshi sai ka rantse ba d'an Nigeria bahaushe bane, idan ba Hausa yayi ba, zakayi tunanin he's Indian man, ya d'auki key ya fita, har zai hau motar jiya KIA, ya fasa ya hau Ferrari, ya fita, yana driving idansa ya sauka akan wasu yara k'anana dake ta faman k'ok'arin tsallaka titi, amma motoci sun hana su, abinka da mutum mai kyakkyawar zuciya, ya koma gefen titi yayi parking ya fito ya rik'e hannun yaran ya tsallakar dasu titin, yaran sukayi masa godiya sosai, har ya shiga mota suna d'agawa juna hannu, ya shiga mota zayyi mata key, ya hango wata tsohuwa tana bara a bakin titi, kasancewar Hanash mai tsananin tausayi da taimako yasa shi fitowa ya nufi inda tsohuwar ke zaune niyyar ya bata sadaka. Su Sanah na tafiya a mota kanta na jikin window tana kallan gefen titi, karaf idanta ya sauka akan Hanash, da sauri tace " Baba driver dan Allah d'an tsaya, yace " to manyan gobe, yayi maganar yana gangarawa gefen hanya, Khulud ta kalle ta tace " ina kuma zaki? Sanah bata bata amsa ba, jikinta har rawa yake ta fita daga motar, Khulud tace " wai my Sanah me zakiyi ne? "Kina fa jin abinda Aunty Halan tace mana ko? Sanah tace " eh cewa tayi muyi sauyi, amma hakan bazai hanani cika buri na na minti 2 kawi ba na dawo ba, " to Khulud tace tana gyara zamanta acikin motar tana bin Sanah da kallo, idan Khulud ne ya sanka akan Hanash, tayi saurin maida kanta k'asa saboda yadda taji gabanta yayi mugun fad'uwa,, tunowa da alwashin da Sanah tayi ne, yasata d'ago kanta cikin tashin hankali, ta kalli inda Sanah ta nufa, gani tayi ta nufi shi gadan-gadan, a kid'ime Khulud ta bud'e motar ta fito da gudu, amma ina kafin ta k'arasa har Sanah ta cimmasa, Hanash ya mik'awa tsohuwar kud'i ya juyo da niyyar komawa cikin mota yaji saukar gigitattatun maruka tassssssss a jere har guda biyu................... MOMYN ZARAH _*RASHIN SANI.......*_ *HAUWA A USMAN* _JIDDARH_ ```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh``` 1⃣8⃣ Tsayawa cak Khulud tayi jin aikin gama ya gama, babu abinda jikin Khulud keyi sai kerrrma da tsananin tsuma, tsoro da fargaba sun cika mata cikinta fal, dan bata tab'a tsammanin fitsara da rashin kunyar Sanah yakai ta iya d'aga hannu ta mari zafgagen namiji kamar Hanash ba, Hanash wanda ya gama gigicewa, saboda kwata-kwata bazato ba tsammani yaji saukar mari, shu'uman idanuwansa da suka gama rinewa zuwa jajaye ya zuba mata, jin zuciyar shi yake kamar zata fashe, k'irjin ko yadda kasan an zazzaga fetur an kunna wuta, haka yake ji, dan tunda Hanash yake a duniya ba'a tab'a koda mangarinsa ba, balle har ya kai ga ammare shi, sai yau, da k'aramar yarinyar da yasan ya kusa haihuwarta a haihuwar kaji, dan ya tabbatar ya bata kyakyawar 15yrs, tunowa yayi da yadda k'annansa keyi masa biyayya kamar zasuyi masa sujjada, ya tuno shi dai a iya sani da wayonsa Mimmee ko Papu babu wanda ya tab'a koda yi mishi kallan banza, saboda kasancewar shi mai biyayya da sanyin rai, had'i da sauk'in kai gashi da girmama na gaba dashi. Ido kawai ya zuba mata batare daya ce komai mata komai ko yayi yunk'urin yi mata wani abu ba, Sanah ta murgud'a baki tana kallanshi ido cikin ido, tace " an fad'a maka ana cin bashin na batare da an biya ba? Kallanta kawai yake, bai iya koda furta kalma d'aya ba, ta cigaba " ko an fad'a maka banza marar galihu ka mara? "To idan ma kana tunaninka haka, ka gaggauta canjawa dan Sanah ta wuce sani da tunninka, haka kawai k'aton banza dakai ka kamani ka mara batare da nayi maka komai ba, sannan kayi tunanin kaci bulus, a hankali Hanash ya d'aga kansa ya kalli yadda jama'ar dake wajen ke kallan su cike da tsantsar mamaki, suna nuna su had'i dayin magana k'asa-k'asa, nazarin su Hanash yayi sosai ya fahimci da alama basu gane wanda aka mara ba, kawai dai sunji k'arar marin ne, dan haka ya gyara tsayyuwarshi had'i dayin murmushi yace " am I your mate? Yayi maganar while idanshi cikin nata, murmushi itama tayi idanta nakan shi tace " oho maka ban sani ba, a hankali ya kuma satar jama'ar dake wajen yaga still hankalin su na kansu, yayi guntun murmushi mugunta, yace " dan ubanki daga yau kya kuma, gashi nan kin cajawa kanki a banza na mare ki, gobe ma ki koma, shegiya 'yar iska , k'aramar yarinya dake sai iskanci da san maza, wallahi daga yau duk ranar da kika koma tare ni a hanya ko kika nuna kin sanni sai nayi miki abinda yafi na yanzu, dan zagewa zanyi nayi miki mugun duka, shegiya 'yar iska fitsararriya, ko dole ne, haba kin fiye nacin jaraba, ance ba'a sanki amma kin nace man duk inda nayi sai kin bini, wallahi daga yau kika kuma bibiyata sai nayi miki abinda harki mutu baki mantawa dani, yayi maganar azafafe cikin d'aga murya dan jama'ar dake wajen su ji sosai, cike da tsantsar mamaki Sanah ta bud'e baki, zatayi magana ya d'auke ta da gigitaccen mari yace " shut up idiot kawai, idan kika kuma bud'e baki zakiyi magana sai na nad'a miki na jaki, ya fad'a yana nunata da yatsa, kumatunta ta dafe danjin fuskarta tayi kamar an maka mata rodi, saboda da iya k'arfinsa ya mare ta, abinka dame ciwo a zuciyarsa, Sanah dafe da kuncinta ta d'ago kai a hankali ta kalli jama'ar wajen, taga gaba d'aya hankalinsu na kanta, sai nuna ta suke suna magana a hankali, karaf taji wani yace " halan irin banzayen 'yan matan nan ne marasa kamun kai, da aji, shiyasa ya bugeta, kinga yanzu kinjawa kanki marika har uku a banza, d'aya kuma yace " ai ni ya burge ni wallahi, d'ayan yace " nima dai yayi man dai-dai, daga ganinta fitsararriyar yarinya ce, mara kunya, shegiya in banda ballagar mace wake bin namiji yana masa naci, " gata masha Allah, a fuskarta da jikinta kamar ita tayi kanta, amma a zuciya babu kyau, wani mai saida lemo da ayaba ya fad'a idanshi kan Sanah, " waya gaya maka mata masu kyau abin so ne yanzu? "Ai yanzu babu abinda yakai mace mai kyau had'ari, dan koda kayi dace ka same ta da kyan hali mazan waje basu tab'a barinka ka zauna da ita lafiya, haka zakayi ta fad'a maza da mata, baga mazan ba baga matan ba, haka zakayi ta fama, kuma yawancin su kud'i kawai suke so, babu abinda ke gabansu sai duniya, amma sai kaga wasu mazan saboda tsabar rashin hankali da tunani, burin su kawai su auri mace mai kyau ko bata da hali, har kaji suna cewa Allah ya basu farar mace ko mayya ce, basu san hali, taribiyya da addinin mace sune farkon abin dubawa ba, amma burin wasu mazan a samu farar mace kyakkyawa ta sawa a gaban mota, ana fashion ana burga da bagu, ana bud'awa ana nunuwa abokanai, duk kyan mace idan ka aure ta babu hali kayi a banza, saboda sai an wayi gari kaji ka tsaneta ka tsani kanka da ma duniyar gaba d'ayanta, idan ko ba kayi sa'a ba haka zakayi ta sharing d'inta da wasu mazan banza, ana kwaso 'yayan wasu na zina ana kawo maka gidanka da sunan naka ne, batare daka sani ba, ko da fita mace 'yar uwanta tazo ta danne maka mata har cikin gidanka, mai sai da rake ya fad'a, d'ayan yace " ai ba duka suka taru suka zama d'aya ba, dan a cikin kyawawan akwai na Allah, kamar yadda kace haka akan kyawawan mata, haka ma munanan suma da nasu, dan sai kaga wata macen kamar a yanka b'oye wuk'a amma tana yin fiye da abinda kyawawan keyi, baka san wasu matan 'yan fashi bane? Wasu 'yan cult, (matsafa) wasu sun aure kane dan su kashe ka, wasu dan abun hannunka, suka aure ka su raba ka da kowa da komai naka, sannan su zama maka alak'ak'ai, daga k'arshe idan sun gama cin moriyarka su aunaka lahira su fad'awa wani, tsautsayin kuma, wasu kuma setup ne ma, abokinka ko mak'iyinka zayyi maka da mace, kai dai muyi addu'a kawai, Allah ya taimake mu ya rufa mana asiri, Ubangiji ya iya mana maganin abinda bazamu iya ba, duk abinda zaifi k'arfin mu koya wahalar damu Allah yayi mana maganinsa, duk suka amsa da "amin. A hankali Khulud ta runtse ido tana hawayen bak'in ciki da takaici, ita bak'in cikinta d'aya yadda aka muzanta mata Sanarta a bainar jama'a, Hanash hard'e hannuwansa yayi yana murmushi, while idanshi na kanta, deep down kuma shi kad'ai yasan me yake ji, a cikin ransa da zuciyarsa, idanshi cikin nata ya d'age mata gira d'aya, yana nuna mata jama'ar dake wajen yana murmushin gefen baki, gigitaccen kuka Sanah ta saki na takaici, ta nufi Hanash gadan-gadan, cikin zafin nama Khulud tayi saurin shiga tsakiyar su Sanah nagaf da isa ga Hanash, batare da Khulud ta kula ba, k'irjinta dana Hanash suka had'u , k'ijinta da nashi suna gogar na juna, lips d'inta da kumatunta suma suka had'u da nashi, tsaye kawai Hanash yayi idanshi na kanta, ya kafe ta da shu'uman lulu eyes d'inshi, bugun zuciyar shi ya k'aru yana bugawa da tsananin sauri, gaba d'aya jikinsa ya d'auki rawa yana kerrrma, still Khulud ta na k'ok'arin rik'e Sanan ta bayansa ta zura duka hannayenta, ta rumgume shi suka saka shi a tsakiyarsu, Khulud ta rik'e duka hannayen Sanah da nata hannun, har lokacin k'irjinta na kan nashi, booms d'inta na gogar k'irjinshi, hab'arta na kan kafad'arshi,kumatunta na gogar nashi, hawayenta na sauka akan kafad'arshi, Hanash na nan tsaye yayi sororo ya kasa yin koda gwaggwaran motsi, babu abinda yake ji sai mugun shock a duk ilahirin jikinsa, gaba d'aya jikinsa tsuma yake yi. A hankali Khulud ta d'aga hannunta sama ta zagaye Hanash, ta rik'e Sanah gam, cikin nutsuwa ta juyo ta fuskance shi while hawaye na cigaba da gangaro mata, cikin muryar kuka tace " bani da baki ko kalmar da zan iya baka hak'uri dasu, but dan girman Allah kayi hak'uri, duk mumunin kwarai an sanshi da hak'uri, yafiya, afuwa ga mutane, please if it's possible forgive us, tayi maganar tana duk'ar da kanta k'asa, hawaye na cigaba da zubowa daga idanta, while tana rik'e gam da Sanah, Hanash bai san sanda his cutie smile d'inshi ya kwace masa ba, martanin murmushin ta mayar mishi, tana goge hawayenta, kana ta juya ta nufi mota da Sanah, Baba driver da duk wainar da ake toyawa bai sani ba ya ja motar, zuwa gida dan sun amso d'inkin, sosai Khulud ke kuka har suka k'arasa gida, suna isa haraba gidan Khulud ta d'auki kayan tayi part d'in Halan batare data ko kalli insa Sanah take ba, baki Sanah ta zumb'ura kana tabi bayan Khulud, a porlor Khulud ta zube tana cigaba da kukanta, zama Sanah tayi kusa da Khulud had'i da dafa ta, Khulud tayi saurin ture hannun Sanah daga jikinta, cike da tsantsar mamaki Sanah tace " wai meye haka? " Kike ta kuka kamar wacce aka daka, batare da Khulud tace mata komai ba, ta cigaba da kukanta, Sanah ta zumb'uri baki kana tace " menayi miki kuma? Khulud tayi banza da ita, Sanah ta kai hannunta tana k'ok'arin dafa Khulud, Khulud tayi saurin gocewa , a tsorace Sanah ta zaro ido tana cewa " wannan duk na meye? Shiru Sanah tayi kana tace " ko dai akan shi ne? Tayi maganar batare data kalli inda Khulud take ba, shiru Khulud bata kulata ba, Sanah ta ciji leb'enta had'i da runtse idonta tace " I hate him, I really hate him madly, tunda muke dake baki tab'a yin fushi da ni ba, sai akan shi, sai a kuma dalilinsa, wallahi na tsane shi ba kuma zan tab'a san shi ba har abada, tunda a dalilin shi ne kika fara yin fishi dani a iya tsawon rayuwarmu, Sanah tayi maganar kanta gefe, jin Khulud tayi shiru bata da niyyar yin magana yasata yin tsaki " mtswwwww ta mik'e zata bar wajen, Khulud tayi saurin rik'o hannunta tana goge hawayenta tace " ba akan shi bane, akan gaskiya ne, ni ina ma ruwa na dashi,da har zanyi fushi dake akan shi, ni da bamma san shi ba, ban kuma san daga inda ya fito ba, Sanah ta koma ta zauna tana cewa " to idan ba akan shi bane akan meye kike fishi dani? Khulud tace " ke yanzu abinda kikayi kina ganin kinyi dai-dai kin kyauta? Sanah ta zumb'uri baki tace " me kuma nayi? " Auke yanzu kina ganin bakiyi komai ba kenan? Sanah batace komai ba, ta cigaba da zumb'urar baki abinta, " Ai kowa ya b'ata ya sani kowa kuma ya gyara ya sani,, wallahi ban tab'a zaton zaki iya saka hannu ki mari zabgagen namiji saurayi ba, idan gaya man akayi bada ido na, na gani ba , sai na rantse k'arya ne, ba gaskiya bs, in banda yana da hankali, hak'uri da tunani da yasanin akamata me kike tsammanin zai iya faruwa? Sanah tace " oho shiya sani, ai dama nace maki sai na rama, dan ban tab'a yafewa in bari ina ji ina gani wani k'aton banza ya mari ni a wofi, Khulud tace " ok yanzu baki ganin kinyi abinda ba dai-dai ba kenan? Sanah ta kuma zumb'uro baki kana tace " naji kiyi hak'uri ban k'arawa, Khulud tace " idan kina san na hak'ura kiyi man alk'awarin duk abinda yayi maki baki kuma ramawa, Sanah tayi dariya kana tace " ina zan kuma ganin shi? " Ai kuma shikenan target d'in mu ya k'are, Khulud tace " k'addara , Sanah ta juyo a hankali tana kallanta kana tace " k'addara, k'addara kamar yaya? Khulud tace " k'addara mace ce marar tabbas, da akoyaushe tana iya canjawa, da kin san zaku tab'a had'uwa ke da shi a rayuwa? Sanah tace " a'a ,ba kuma na fatan sake had'uwa dashi har abada, Khulud tace " k'addarar data had'amu dashi a baya ita zata sake had'amu dashi a gaba, so ni dai dan Allah kiyi man alk'awarin baki kuma rama duk abinda yayi maki, Sanah tayi dariya tace " ai akwai sauran marin daya kuma yi man ban rama ba, ki bari idan na rama sai nayi miki alk'awarin, Khulud ta zaro ido tana mik'ewa tsaye tace " ke yanzu sai ki kuma iya sake marin shi? Cikin dariya Sanah tace " da gudu ma, tayi maganar tana ja da baya, Khulud ta d'auki pillow ta jefa mata tana binta da gudu suka shiga zageye parlor'n, jin hayaniyar su tasa Halan fitowa da sauri tace " kun shir...... ganin su tsaye suna wasan jefe-jefen pillow yasata tsayawa sororo tana kallansu kana tace " au baku shirya ba, shine kuka tsaya kuna wasa? "Lalle ta kai muku karo, duniyar tayi muku dad'i, sukayi dariya su duka cike da tsantsar farin ciki, Halan tace " to oya maza aje a shirya, kunga lokaci na niyyar k'urewa, suka amsa da "to kana sukayi cikin gidan da gudu Halan tabi bayan su da kallo tana dariya cike so, basu d'auki lokaci ba suka shirya cikin riga da siket na atamfa, d'inkin yayi bala'in yi masu kyau, ya amshi jikinsu, irin d'inkunan da zaka gani ana talla a Facebook & Instagram, dayake sunyi masifar iya make up kamar me, suka tsarawa kansu fitacciyar kwalliya irin wanda kuke ganin celebrities nayi, dan sun kai 2yrs a makarantar koyar make up & food training centre, shiyasa sukayi masifar iya make up, da girkin abinci, dan babu irin girkin da basu iya ba, kafin su fito an gama komai na shirya wajen, har k'awayen su sun fara hallara. Hanash yakai wajen 10 minutes tsaye a inda suka barshi, still jikinsa bai bar kyarma, sai dakyar ya jan k'afarsa ya shiga mota, a cikin motar ma yakai a k'alla 6 minutes kafin ya iya jan motar, fasa zuwa inda yayi niyya yayi, dole ya karya kan motarsa ya nufi gida, yanayin parking a harabar gidan ya fito, ko tsayawa zare key da rufe motar bayyi ba, direct part d'insa ya nufa tun a parlor ya cire kayan jikinsa yayi naked, ya fad'a bathroom ya sakarwa kansa shower, dan haka Hanash yake tun yana yaro k'arami muddin ransa ya b'aci ko yana cikin damuwa, naked yake yi ya shaga bathroom ya sakarwa kansa ruwa na tsayin lokaci, sai da Hanash ya d'auki lokaci a bathroom kana ya fito d'aure da towel, kan sofa ya zube yana tunani biyu, na farko tsabar rashin kunyar Sanah da fitsararta, yayinda lokaci d'aya yaji tsanarta da k'iyayyarta ta dira a zuciyarsa, dan dama shi haka yake yayi bala'in tsanar mace mai fitsara da rashin kunya a rayuwarsa, ji yayi kwata-kwata yayi masifar tsanarta ko san sake ganin fuskarta ba yayi a rayuwarsa, daga b'angare d'aya kuma shi kansa bai san tunanin dayake yi ba, bai kuma san meke shirin faruwa dashi ba, shi dai still yana jin shock a jikinsa, haka duk lokacin daya tuno ta yana jin yarrrrr a jikinsa, yana jin duk tsikar jikinsa ta mik'e, gaba d'aya ya rasa samun sukunin ransa, ya rasa nutswarsa, babu abinda ke k'ara burge shi da yarinyar sai sanyin halinta, gata da hankali, hak'uri, nutsuwa da sanin ya kamata,, da gani tana da ingantacciyar tarbiyya, ba ita ke yin laifin ba, amma ita ke kuka tana bada hak'uri, da gani tana da sanyin hali kamar shi, dama ya dad'e yana addu'ar Allah ya bashi mace mai sanyin hali da zuciya irin shi, mai tausayi da sanin ya kamata, mai cikekkiyar nutsuwa da tarbiyya, yasan muddin ya same ta matsayin matar aure yayi sa'ar mace, yasan ya shiga sahun wad'anda Manzan Allah (S.A.W) yace sun samu farin cikin duniya, domin Annabi S.A.W. yace mace ta gari itace jin dad'in duniya, duk namijin dayayi sa'ar mallakar mace ta gari, ya gama samun fari ciki da kwanciya hankali, murmushi Hanash yayi batare daya sani ba, had'i da cusa hannunsa a cikin kwantacciyar sumar kansa, while yana cigaba da murmushi. K'annan Hanash Zohal da Wajnah, suka shirya tsaf domin zuwa wajen walimar k'awayen su da suka gama Secondary School tare, tun a makaranta suka gayyace su, fitowa sukayi suka iske Mimmee a parlor zaune tana shan fruits salad, ta kalle su cike da kulawa tace " har kun shirya? Suna zauna kusa da ita suka amsa da " yes our Mimmee, tayi murmushi kana tace " me zaku kai musu gift? Zohal tace " perfumes & bangles, Mimmee tace " eh yayi, to kuyi maza ku tafi karku makara, kuma ku tabbatar kun dawo da wuri karkuyi dare, suka amsa mata da " in sha Allah Mimmee, light kisses sukayi mata a kumatu kana suka fita, basu dad'e da fita ba suka dawo, cikin shagwab'a Wajnah tace " Mimmee duka drivers d'in basu nan, wai Jadda ta aiki d'aya kasuwa, ta kuma aiki d'ayan Pharmacy, d'ayan kuma ke kika aike shi gidan k'awarki, ta fad'a tana turo baki, Mimmee ta dafe goshinta alamar mantuwa tace " ops na manta, duk suka shiga diddira k'afa had'i da kukan shagwab'a, "a'a yau me akayiwa 'yan lelan Mimmee? Papu dake shigowa yayi maganar yana dariya, da gudu suka fad'a jikinsa, kana cikin shagwab'a suka shiga fad'a masa abinda ke faruwa, " naga kamar Yayanku yana nan, kuje ya kai ku mana, in yaso sai ya tsaya ayi walimar dashi ya dawo da ku, Papu yayi maganar yana zama akan sofa, Zohal tace " Papu kasan fa ba kai mu zayyi ba, " kun tab'a ganin na sashi abu yak'i yi? Cewar Papu yana kallansu, suka ce "a'a , yace " tom kuje kuce Papu yace ya kai ku, ya kuma zauna ayi walimar dashi sannan ya maida ku, cikin murna suka fita da gudu suka nufi part d'in Hanash, yana kwance akan sofa abun duniya ya dame shi, yaji knocking dakyar ya iya cewa " waye? Wajnah tace " mune Yaya, yace " ya akayi? Yayi maganar cikin sanyinsa idanuwanshi a rufe, Zohal tace " Papu ne yace " wai ka kaimu walimar k'awayen mu, ka kuma tsaya ayi walimar da kai sannan ka maido mu gida, " sai da yayi d'an shiru kana yace " ku je ina zuwa, basu kuma yin magana ba, suka juya, suka koma part d'in su, Papu ya kalle su yace " ya akayi? Sukayi dariya kana suka ce " shiryawa zayyi ya fito, Mimmee tace " sai kuyi koyi wajensa, dakyar Hanash ya mik'e ya sanya d'anyan boyel sky blue, ya sanya takalimi da hula da agogo duk black colors, ya feshe jikinsa da arnan perfumes, kana ya fito cikin takunsa na izza, a parlor ya iske Mimmee da Papu da su Wajnah, har k'asa ya durk'usa ya gaida iyayen nashi, suka amsa cikin kulawa, kana yacewa su Zohal su fito, suka mik'e suka bi bayanshi, bayan su Sanah sun shirya sun fito kamar wasu taurari sai shek'i suke, duk inda suka juta walk'iya sukeyi, Khulud ta kalli Sanah tace " bafa kiyi man alk'awarin ba, Sanah tace " alk'awarin me? Khulud tace " na bazaki kuma rama duk abinda yayi maki ba, Sanah tayi rolling lulu eyes d'inta, tace " wai ke meye na damuwa dashi ne? Khulud tace " badashi na damu ba, dake da mutunci da kuma k'imarki na damu, ba wai dashi na damuwa ba, ke kinfi kowa sanin ban san fitina da tashin hankali, Sanah tace " ok zanyi miki amma sai bayan na rama guda d'ayan dayayi man sannan, kema kin san Sanah bata barin bashi, so ki bari sai munyi equal sannan, Khulud ta zaro waje tace " what! yanzu idan kika kuma ganinshi sai ki iya sake marinshi? Sanah tace " mai zai hana? " Wallahi da gudu ma, ai ko a cikin taron walimar nan na ganshi sai na rama sai dai a kashe ni daga baya, bayan na rama d'in.............. MOMYN ZARAH _*RASHIN SANI.......*_ *HAUWA A USMAN* _JIDDARH_ ```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh``` 1⃣9⃣ Khulud ta kuma zaro idonta waje tace " kai my Sanah, cikin dariya Sanah tace " eh mana, " ni dai please kiyi man alk'awarin baki kuma ramawa please, tayi maganar cikin sanyinta, Sanah ta kuma yin dariya had'i da dafa kafad'ar Khulud tana kallanta ido cikin ido, cikin marairaicewa Khulud tace " please tana langwab'ar da kanta gefe, Sanah ta d'an k'ura mata ido kana ta sauke ajiyar zuciya had'i da cewa " nayi miki alk'awarin daga yau har abada duk abinda zai man ban kuma ramawa, cikin jin dad'i Khulud ta rungume ta tana cewa " yawwa my Sanah thank you so much, murmushi Sanah tayi kawai batare datace komai ba, ta rok'o hannun suka nufi part d'in kakannin su. Fitowa Hanash yayi zuwa harabar gidan, su Wajnah na biye dashi a baya, Papu yace " au kinga na manta Hanash zai fita batare dana aike shi bank d'in bako? Yayi maganar yana kallan Mimmee, tace " kaga kuma yau Friday ba, da idan ya aje su sai ya biya bank d'in, kafin su gama walimar shi yaje yayi abinda zayyi, Mimmee ta fad'a idanta kan Papu, " kuma daga yau ba bank har sai Monday, ga time na tafiya naga yanzu wajen 4:30pm, yayi maganar yana mikewa had'i da kallan agogon hannunsa, da sauri ya fita daga parlor'n yabi bayan su Hanash, Hanash na niyyar yiwa mota key, yaga Papu ya nufo su da sauri, a hankali Hanash ya fita ya nufi Papu, check Papu ya mik'ewa Hanash yana cewa " idan ka aje su a gidan walimar ka biya banki ka amshi wad'annan kud'in, sai ka saka su a account d'ina ko naka, Hanash yayi murmushi yana kallan Papu zayyi magana drivers biyu suka shigo gidan a lokaci d'aya, Papu yace " yauwa ga drivers nan sun dawo, bari na saka d'aya daga cikin su ya kai su gidan walimar, kai kuma sai ga je bank d'in, Papu yayi maganar yana nufar wajen drivers d'in, cikin taushi Papu ya fad'a musu, sannan ya sanar dasu Zohal su fito su shiga motar driver shi zai kai su, kana ya koma wajen Hanash dake tsaye inda ya barshi, Papu ya lura da yadda yanayin Hanash ya canja sosai, sannan walwalarsa da sakin fuskarsa ba kamar da ba, kallan Papu Hanash yayi kana yace " Papu wannan kallan fa? Ya fad'a yana dariya, shima Papun dariya yayi yana dafa kad'afar Hanash yace " bakomai kawai ina kallan d'ana ne, in kuma za'a hana ni ne to, yayi maganar cikin barkwanci, Hanash yayi dariya batare dayace komai ba, Papu yace " kaje maza ka dawo zamuyi magana da kai, Hanash yayi dariya kana yace " hala Papu ya manta yau Saturday? Papu ya zaro ido had'i da cewa " what! haba dai? Hanash yayi murmushi yace " Allah kuwa Papu yau Saturday, hala ka shafa'a ne? " Ka manta jiya mukaje sallar juma'a? Papu yace " na manta, kasan tsufa ya fara kamamu , abinka da tsoho, Hanash kuma yin dariya yace " kai Papu wanne irin tsufa kuma? "Bayan gaka nan kamar matashin sauryi kamar mu,, Hanash ya fad'a cikin tsokana, dayake sun saba wasa da dariya sosai da Papu, dan wani lokacin idan ka gansu sai ka rantse abokanai ne, Papu yace " kayya wanne matashin sauriya, muda samartaka ai sai dai a lahira a aljanna, jiya ai ba yau ba , tunda na haifi k'aton saurayi kamarka ai na tsufa, ko yanzu Alhamdulillah dan na mori k'uriciya ta, kai ma sai kayi k'ok'ari ka mori taka k'uruciyar, sanda nake kamar shekarunka na haifeka, amma kai gaka nan har yanzu 30yrs baka da ko budurwar, ko rowa kake man dan karna ga 'ya'yanka oho, inaga sai na mutu sannan zakayi aure ka haihu, Jadda dake jiyo su ta window ta, suka jiyo muryarta tana cewa " kyale ja'iri wallahi idan na gaji sai dai ya shigo gidan ya iske matarsa a b'angarensa, imma bak'in ciki kake man dan kar naga yaranka ehe, daga Papu har Hanash duk suka sanya dariya, Hanash ya shafa kansa yana kallan Jadda, Papu dake tsaye a wajen shiya hana shi ce mata komai, sai murmushi da yayi tayi shi kad'ai yana shafa kai, kallansa Papu yayi yana nazarin yanayinsa ya tabbatar akwai abinda yake damunsa, amma sai ya sabar yace " ka rik'e check d'in a hannunka, ranar Monday sai kayi kamar yadda na saka ka, "tom Papu ba damuwa Allah ya kai mu Monday, Papu ya amsa da " amin yana komawa part d'in Mimmee, iske ta yayi tana k'ok'arin shigewa bedroom d'inta, ganinsa yasa ta jiyowa tana kallan shi, yace " wai meke damunsa ne? Tace " wa? Yace " Hanash mana, naga kwana biyu yanayinsa duk ya canja, Mimmee tace " nima dai haka nagani kwana biyun nan, kamar yana cikin damuwa, Papu yace " kin tambaye shi ne? Tace " eh, "Ok meya ce maki? " Wai bai jin dad'in jikin sa ne, Papu yace " ok mu barshi zuwa nan da kwana biyu mu gani, Mimmee tace " Allah ya kai mu, muje ciki kayi wanka ko? Bayanta yabi yana cewa " kamar ko kinsan zafi nake ji, Hanash na komawa b'angarensa ya kuma zubewa kan sofa, had'i da runtse idannuwansa, shi har yanzu bai san so da soyayyar Khulud ke d'awainiya dashi ba, ta hana shi sakat, ta hana shi walwala da farin ciki, haka nan kullum yake jin damuwarsa na k'aruwa, babban burinsa a rayuwa yanzu bai wuce na sake ganinta ko sau d'aya ne a rayuwarsa ba. part d'in Ganez suka fara shiga suka iske Nisah zaune kusa dashi, Sanah tace " oh! ashe dai har yanzu ana tsinkar korawayen fure? Duk sukayi dariya kana Ganez yace " a'a aini idan bada ku zan tsinki korayan fure ba, ai a banza, Khulud tace " kinji shi zayyi mana wayo kullum yayi ta cewa idan ba mu ba sai rijiya, Sanah tace " kuma yana tsoran matarsa ba, Nisah tayi dariya kana tace " oh! kuji man yara, wato kun saka mana ido, ai irin haka ake so, Khulud tace " mijin ya rink'a jin tsoran matarsa? Nisah tace " eh mana, Sanah tace " ina fa dad'i miji ya zama mijin tace, an dai mayar mana da kakanmu tace kawai, Nisah tace " wannan ai kan tace ne ma, duk sukayi dariya kana suka fita suka nufi part d'in Danish, ganin Erum tayi kwalliya yasa su yin dariya, Khulud tace " wato ke har yanzu baki dai na kwalliyya bako? Erum tace " ina ni ina daina kwalliya, Sanah tace " kici zamaninki kici na wasu ko? "Sosai ma kuwa cewar Erum, " a'a kace yau amare nane a gidan, cewar Danish dake fitowa daga bedroom d'insa, Sanah tace " mune, munzo a bamu abinda akaci aka rage,, Danish yace " ku da kuke amare ina ku ina raguwa, ai sai dai sabuwar dahuwa, Khulud tace " ai dama kun saba yi mana wayo, bayan duk tsoron matan ku kukeji, Erum tace " ai irin wannan k'arshen ake so ayi yara, ku ma kuyi addu'ar Allah ya baku ita mu, Sanah tace " wai ma duk ba wannan ba, ina zaku na ganku duk kunyi kwalliya? " Mu da muke da walima yau har a tambaye mu inda zamu dan munyi kwalliya, Erum tayi maganar tana dariya, Khulud tace " a she walima ce daku, a ina kuma? Erum tace " sosai ma, kuma a nan gidan, Sanah tace " tab wai wacce walimar kuke nufi? Badai tamu ba ko? Tayi maganar a lokaci d'aya, Erum tace " walimar ku ko tamu? "Ai muke da walima kuwa, tunda mune manyan k'awaye, tayi maganar tana dariya, Khulud tace " mu dai bamu gayyace ku ba, kuma bamu san gayyar sod'i ehe, duk sukayi dariya kana suka fita, part d'in Juju sukayi, da sallama suka shiga, Didi ya amsa musu cikin fara'a, kana yace " 'yan candy ne yau a gidan namu? Sanah tace " mu ne, Didi ya kalli Juju yace " ina kika b'oye mana su ne? Juju tace " wacce ni? " Ai sai dai ka tambaye Mamun su, ni tunda sukayi candy ban sa su ido na ba, sai yau, ko irin kayan kayan candy nan ba'a kawo mana ba, balle muce mu shaida anyi candy, muce Allah ya sanya alkhairi, Khulud tace " kai Juju Allah bamu zauna bane, mu ta yawan zuwa saloon da k'unshi, Sanah tayi dariya kana tace " Juju ku da zaku bawa wasu ma, kayan candy kuma ga walima nan kun shirya ku da kanku, sai ku shaida anyi candy kuyi addu'ar Allah ya sanya alk'airi, Didi yayi dariya yace " wai Sanah baki abin magana, ke dai ba'a tab'a k'ure ki ta wajen magana, Juju tayi dariya tace " ai ni nayi shiru tunda an fini baki,,, dama hausawa sunce dokin mai baki yafi gudu, Didi ya kuma yin murmushi kana yace " Sanah yaushe jamb d'inku zata fito? Sanah tace " naji ance this coming Monday, Juju tace " wacce university kika cike? "First choice BUK second kuma ABU Zaria, Didi yace " masha Allah Ubangiji ya taimaka, Allah ya bada sa'a, duk suka amsa da Amin, har Khulud dabata zana jamb d'inba, dan cewa tayi ita ta gama karatun boko har abada, Juju ta kalli Khulud kana ta mayar da kallan ta ga Didi tace " 'yar Abbu da Mamu ita aure take so, Khulud ta d'ago kanta da sauri suka had'a ido Juju tayi saurin sadda kanta k'asa tace " Allah Juju ba haka bane, tayi maganar a shagwab'e, Juju tace " idan ba haka bane to yaya ne? Khulud tace " Allah ni ban san cigaba da karatun ne kawai, ni kwata-kwata ban tab'a sha'awar yin karatun boko mai zurfi ba, Juju zata kuma yin magana, Didi yayi saurin cewa " haka ne ai kowanne mutum yana da nashi ra'ayin, hakan ma da kikayi dai-dai ne dabaki yaudare iyayenki kin shiga jami'ar ba, kana kik'i yin karatun ko wata matsala ta faru, so ni ina ganin kinyiwa kanki da Abbunki adalci, Allah ya zab'a maku abinda yafi alkhairi a rayuwarku, ya haskaka rayuwarku ya sanya albarka acikinta, duk suka amsa da Amin, fita sukayi suka nufi wajen da aka tanada dan yin walimar da tuni k'awayensu sun fara zuwa, sosai walima ta kankama haik'an, aka ci aka sha sosai dan sosai Abbu ya saki bakin aljihunsa dan nuna tsantsar farin cikinsa na kammala karatun yaransa lafiya, sosai aka rarraba kyaututtuka, kana kowa ya watse cikin farin ciki aka gama walimar lafiya. Sannu a hankali matsanannaciyar soyayyar Khulud tayi mugun kama Hanash, ta addabi ruhi da gangar jikinsa, kwata-kwata ya rasa sukuni da walwalarsa, ya rame sosai dan raban dayaci ishashshen abinci ko ya samun bacci har ya manta, kullum yana cikin bedroom ko parlor'nsa, dan ko fituwa sosai ya dainayi sai dai ya fito ya gaida iyayshi ya koma, yauma kamar kullum kwance yake a d'akinsa ya tsunduma duniyar tunaninta, idanshi rufe babu abinda yake gani sai ita tsaye a gabansa, tana sakar mishi k'ayataccen murmushinta, jin knocking yasa shi bud'e shu'uman idanuwansa, k'ofar ya zubawa ido na tsayin lokaci, batare da yayi wani yunk'uri ba, sake knocking akayi a karo na biyu, dakyar ya iya cewa " waye? Muryar Papu yaji yace " mu ne, dan sun kasa jurewa ganinsa cikin wannan mawuyacin yanayin, da sauri ya mik'e ya bud'e musu k'ofar suka shigo, akan sofa duk suka zauna, a hankali Mimmee ta d'ora hannunta akan kafad'arsa, had'i da zubawa d'an nata ido, Papu ma ya zauna kusa dashi ya zuba masa ido, kansa ya duk'ar dan ya san kwanan zancen, muddin akace bashi da lafiya ko yana cikin damuwa to gaba d'aya gidan babu mai yin walwala, a hankali Papu ma ya d'ora hannunsa akansa kana ya kira sunansa, " Hanash, "na'am, Hanash ya amsa cikin ladabi, " meke damunka? Cewar Papu a tak'aice, murmushin k'arfin hali Hanash yayi kana yace " babu abinda ke damuna Papu, yayi maganar while kanshi k'asa, Mimmee ta shafa kansa kana tace " Hanash please karka b'oye mana abinda yake damunka, ka daure ka sanar damu koda babu wani abu da zamu iya yi akai, sai mu tayaka da addu'a, ta fad'a cikin damuwa, murmushi Hanash ya kuma yi kana yace " ba ni da lafiya ne, Mimmee zazzab'i da ciwon kai ke damuna, ido Mimmee ta zuba mishi tana nazarinsa dan ita kwata-kwata bata yarda da abinda yace ba, Papu yace " kaje hospital? Hanash yace " eh Papu, "me sukace yana damunka? Papu ya kuma tambayarsa, d'an shiru Hanash yayi kafin yace " Malaria, " to ikon Allah kai ko ina kaga sauron daya cije ka? Mimmee ta fad'a tana kallan kwayar idansa, murmushi yayi kana yace " Mimmee, cikin shagwab'a, Papu yace " shi ciwo ai daga Allah ne, ba ta inda baya shiga jikin mutum ko son? Yayi maganar cikin tsokana, dan shima yadai ji Hanash ne kawai, amma bai yarda da abinda ya fad'a ba, babu yadda Papu da Mimmee basu yi akan Hanash ya sanar da su damuwarshi ba, amma yak'i yace babu abinda yake damunsa, Papu yace " Allah ya sauwak'e, ya amsa da " Amin, kana suka fita, suna fita Hanash ya koma ya kwanta, had'i da rufe idansa. Ranar Monday jamb ta fito, Sanah cikin murna da d'oki suka je ita da Aarib & Khulud suka duba, a cafe, aiko taci sosai dan ta samu 251, tsalle ta buga ta rumgume Khulud da Aarib cikin matsananciyar murna, motar su nayin parking a harabar gidan ta fito, ta shiga kwalawa Halan kira, da gudu ta shiga part d'in Halan, ta iske ta parlor zaune ita da Ziyad, cikin murna ta fad'a kanta, ta ma manta da tsohon cikin dake jikin Halan, Ziyad ya daka mata tsawa had'i da cewa " ke baki da hankali ne ko baki ganin abinda ke jikinta? Bata kula da tsawar daya daka mata ba, sai ma kiss datayi mishi a kumatu, cikin murna tace " Yaya naci jamb, ta fad'a tana tsalle, dariya Halan tayi tace " kai masha Allah gaskiya nima nayi murna, badan kayan dake gaba na ba, da har dani za'ayi tsallan, Ziyad yayi dariya yace " bani abu na inyaso sai kije kiyi tsallanki, Halan ta kalleshi had'i da zumb'uro baki tace " Allah da ana bayarwa ai bama sai ka tambaya ba, Sanah da Khulud suka fita da gudu suka nufi part d'in Mamu, suna zuwa Sanah ta fad'a kan Abbu, yace " kai Sanah ke dai baki girma, naga alamar so kike ki karya ni tunda baki ganin na tsufa yanzu, Sanah tayi mishi kiss tace " Abbu albishirinka, yana dariya yace " goro, tace " fari ko ja? Yace " fari tass, tace " Abbu na ci jamb, Abbu yace " wai dole ayi murna, Mamu tace " masha Allah, saura waec & neco, Abbu yace " suma duka za'a cinye su, in sha Allah, fita sukayi suka nufi part d'in Juju, nan ma aka sanar mata anci jamb, murna kam ba'a magana, a week d'in waec ta fito, Sanah ta samu result mai kyau, result d'inta yayi mugun kyau, bayan two weeks BUK ta kira su first UME, bayan week nan ma result ya fito, ta samu taci, suka bata Admission letter na BSC COMPUTER SCIENCE. Kullum Hanash bashi da wani aiki sai mafarkin Khulud, da tunaninta ko idansa ya rufe ita yake gani, koyaya ya rufe idansa ita yake ya gani, abun duniya duk ya dame shi, ba shi da wani burin daya ce na sake ganinta a yanzu, ko da sau d'aya ne a rayuwarsa. Yau itace rana ta farko da Sanah zata fara hallartar BUK, ta gama shirinta tsaf cikin riga da siket na material red color d'inkin yayi masifar yi mata kyau, ya amshi jikinta sosai, ta saka high hill shoe ta yafa mayafinta mai kyau kalar flowers dake jikin material d'in black, sosai Sanah tayi shegen kyau, duk da ba wani make up tayi ba, ta dayyi simple make up abinta, wanda ya bayyanar da tsantsar kyauta, har cikin makarantar Aarib ya kaita, sai da yayi mata fad'a sosai kana ya tafi, sannu a hankali take tafiya harta isa department d'insu, tambaya tayi, aka nuna mata, inda zasuyi lectures yau, dayake tana da time table na duka courses & time d'in su, a hannunta tasan Computer lectures zata fara attending, zama tayi a inda taga students na zama, zamanta ke da wuya ta fara jiyo hirar students, " yau fa Sir Aryan ne damu, kasan ko ba sauk'i, d'ayan yace " wallahi ko ni gaba na ma sai fad'uwa yake yi, tun jiya dana duba naga shine damu hankali na yake a mugun tashe, wani daga gefe yace " kai ai Malamin nan bai da kyau, d'ayan yace " kaga fito sak a mutum kai tsaye kace bai da mutunci, d'ayan yace " ni fa yana mugun ban mamaki shi ko irin na sauran lectures d'in nan bayyi, d'aya yace " me? " San mata mana, d'ayan yace " kai tanan wajen ai Sir Aryan yayi wallahi, ba ruwanshi da mata, duk kyanki yanzu zai yarfa ki, ba kamar sauran lectures d'in ba, shegu da sunga mata sai suyi ta rawar jiki, idan mune 'yan uwansu maza tsakanimu dasu ba mutunci, sai su rufe ido su karta mana, amma shi kwata-kwata mace bata isheshi kallo ba, naga 'yan mata dayawa sunyi mugun matuwa akansa, d'ayan yace " aiya had'u ne ga kyau ga kud'i, kaga kuwa ai dole mata su matu, tunda ready mate ne, d'ayan yayi dariya yace " aiko suna shan dizgi da wulak'anci a wajensa ba, dan yanzu zai kartawa mutum rashin m, idan ta kama ma ya yarfa maka mari ba ruwanshi, shege ga girman kai da d'agawa da jan aji dan sai kayi mishi magana goma amma dakyar idan yaga dama zai amsa maka d'aya , d'ayan yace " kai ai ya iya d'aukar wanka dacin uwar sutura, yana zagin gizna ta asalimma, ni na rasa uban me yake yi a makarantar wallahi, "hmmmm ga babu ruwanshi da ke wai mace ce, shi hukunci d'aya yake yi tsakanin mace da namiji, idan ya riga ka shiga class ko waye ubanka kuma ko uban ya tsaya maka ya d'aure maka gindi baka shiga, d'ayan ya duba agogo yace " sauran just 5 minutes ya shiga fa, kusan kuma baya African time, d'an tsaki Sanah tayi a hankali kana ta mik'e tabar gurin, saboda duk gurin wajen mutum 100, maganar mutum d'aya suke tayi Sir Aryan, duk inda students sukayi d'an group, maganar shi kawai sukeyi mata da maza, daga maganar had'uwarsa kyansa, gayu, ajinsa, sai ta wulak'anci da dizginsa da kuma girman kansa, da yadda mata suka mato akansa yake wulak'antasu, shiyasa duk randa yake da lectures dasu suke kaffa-kaffa. Can gefe ta koma ita kad'ai ta zauna, ita kad'ai kasancewar yaune farkon zuwanta bata san kowa ba, tana daga zaune taga wata matsiyaciyar had'add'iyar mota ta danno kai cikin makarantar, students na ganin motar suka kai duba zuwa number motar dan su tabbatar idan shi, saboda baya hawa motar d'aya, duk nacinka baka isa kace ga yawan motocinsa ba, ta number motarsa kad'ai suke gane shi ne, saboda sunan family d'in su ne a duka number motacinsa,, ai students na tabbatarwa shine, suka fara gudu maza da mata ana rige-rigen shiga class. Yana yin parking, ya zare key d'in tare da komawa ya kishink'id'a jikin kujerar, ido ya lumshe tare da fesar da numfashi mai sanyi, a hankali ya kuma bud'e idon tare da sauk'e ajiyan zuciya, yana mai shak'ar k'amshin jikinsa dana mortar, a hankali ya sa hannun damanshi ya dafe saitin k'ahon zuciyarshi dan jin gabansa yana muguwar fad'uwa da k'arfi, bugun zuciyarsa ya k'aru sosai, zuciyarsa ta rink'a bugawa so past, idansa ya kuma lumshe yana k'ara d'an kishingid'a akan kujerar motar, a hankali ya furta " innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, saboda yadda yake jin duk ilahirin jikinsa ya mutu, gabansa na mugun fad'uwa zuciyarsa na bugawa da tsananin k'arfi, addu'ar yayi ta maimaitawa dan baya son ayi mishi African time shiyasa shima baya son yayiwa d'alibanshi, bere daga inda yayi parking yana iya hango yadda suke sassarfan shiga class, sharshesa ya fitar tare da d'an laso lips nashi, hadi da d'an cizawa dan kauda kasalar dake saukar mai a jiki, a hankali ya b'alle marfin motar tare da zuro k'afarshi d'aya woje, baki ya d'an tab'e ganin yadda wasu matasa suka wuceshi da sassarfa, gudun karya rigasu shiga class, ya hanasu shiga, fitowa daga cikin motar tare da jawo laptop nashi, ya bud'eta tare da dorata kan hannunshi daya mik'ar, yana kuma d'an lallatsashi cikin k'orewa, ajiyan zuciya ya sauk'e tare da fara takawa zuwa class d'in yana mai jin dad'in iskar dake busawa sirrai da fawowi suna shawagi tsuntsaye na kai komo ga k'amshin furanni dake ratsashi. Cikin takunsa na isassun maza masu haiba da kamala ga tarin nagarta yake tafiya cap-cap sautin takalminshi ke ratsa wurin in dalibai sun hangoshi sai suna rusunawa tare da ratse mishi. Ganin yadda students ke gudu yasa Sanah kai idanta kan motar dataga kamar an saka MOLI'S 15, amma data duba so sai taga kamar ba haka bane, baki tad'an tab'e kana ta mik'e cikin takunta mai daukar hankali tabi bayanshi, ta nufi class itama, daga bayansa ya rink'a jin kamar takun mutum a bayansa k'at-k'at, Fuska ya kuma had'ewa dan ya gane mace ce, daga k'asa ya kalli k'afarta data sha kunshi mai ja da bak'in lalle yayi masifar yi mata kyau, gabansa ne yayi muguwar fad'uwa lokacin daya d'ora idansa akan k'afarta, sake had'e rai yayi , kana ya cigaba da tafiya, yana tafiya tana binsa a baya, har suka zo gaf da isa class d'in, Kai ya d'an jinjina tabbatarwa da yayi class d'in sa zata shiga , hankalin shi na kan laptop d'inshi, hannunshi mai yin typing d'in ya d'an d'aga shi saman kafadarshi ta yadda zata gani, sanan ya had'e doguwar yatsarsa ta tsakiya da babbar yatsarsa ya kettasu sau d'aya ta yadda ya bada sauti, sannan ya had'e yatsunsa biyu ya kad'asu kamar mai buga fiyano ya mata nuni data tsaya inda take karta biyoshi, batare daya juyo ya kalle ta ba bai kuma tsayaba yaci gaba da takunshi zuwa cikin class, Itako Sanah bata gane abinda yake nufi ba, dan haka taci gaba da binsa a baya, Kai ya jinjina tare da yin gutun murmushi, mai dauke da alamar zaki gane kurenki, kana ya cigaba da tafiya har suka k'arasa cikin class d'in, Sanah tazo zata wuce mazaunin d'aliban, *"Keeh"* kamar daga sama sautin muryarsa ya ratsa shirun daya ratsa ajin,sai sautin takalminta dake amsakuwa, shirune ya sake ratsa ajin duk sunsha jinin jikin su, ita kuwa Sanah kai ta d'ago ta kalleshi ,Amman bata ga fuskarsa ba dan baya ya bata, sai gashin k'eyarsa da ta tsurawa ido ganin shi a kwance lub sai wani lauyewa a yayi ya bi k'eyan nashi yana Shek'i, tana cikin nazarin da me tayi mishi ta kuma jiyo muryarshi na ratsa ajin baki d'aya taji tajiyo muryarsa nacewa yana cewa, *"kneeling down,"* ya fad'a still bai jiyo ya kalle ta ba, juyawa tayi bayanta taga babu kowa sai ita kad'ai, cikin mamaki ta kalli bayansa dan ita a iya saninta tasan ba'a saka Patick a jami'a. Cikin mamaki ta kuma kallan bayansa, batare daya jiyo ba taji yace *"ko bazaki kiyi bane?"* Muryar dataji ta daki dodon kunnenta, tasa gabanta mugun fad'uwa a razane ta kuma kallan bayansa, babu damar taga fuskarsa saboda ya juya mata baya, a hankali Sanah ta d'an zumb'uri baki kana tayi kneeling down d'in, gaba d'aya students mamaki ya gama cika su, duk da sun san halinsa, sun tabbatar zai iyin abinda ma yafi hakan, dan sun san mari ko dizgi abu ne mai matuk'ar sauk'i a wajensa, amma basu tab'a ganin yasa wata ko wani kneeling down ba, sai yau kuma daganinta new comer ce, students suka rink'a yin dogon wuya suna l'eka ta, jin muryarsa ta fara explanations yasa duk suka shiga hankalinsu. Sanah na nan har ya gama lecture tana ta zumb'ure-zumb'uren baki, Cikin k'asaita ya fito zai tafi , ganin ya wuce ta gabanta amma bashi da niyyar ce mata komai, yasa ta cewa *"Sir to ni wuni zanyi a nan ne? "* Tsayawa yayi cak a inda yake, kana ya juyo da fuskarsa a hankali ya zuba mata ido, had'i da hard'e hannayensa a k'irji, mik'ewa Sanah tayi batare daya bata umarnin tashi daga kneeling d'in ba, kanta durk'ushe tana kakkab'e siket d'inta, tana yin magana k'asa-k'asa, "eh wato kai zaka fece gidanku ni kuwa in zauna a nan, sai kace baiwar gidan ku ko, hegen k'eya! da nad'edd'en gashi." dan ita a tunaninta ya tafi shiyasa ta d'anyi halin, baki ta murgud'a tare da mik'ewa tsaye, d'ago kan da zatayi, keda wuya sexy eyes d'inta, suka sark'e cikin na *SIR MOLI* dayake tsaye hard'e da hannuwa yana kallan ta.................. _Aunty AISHA ALIYU GARKUWA_ _kina tambayar inda nakai miki Sir Molinki to gashi nan na maido miki abinki_ ~To fans masu tambayar ina nakai Sir Moli na b'oye har tsayin six years, gashi nan ya dawo~ ~sai a cigaba da gashi a d'ora daga inda aka tsaya~ MOMYN ZARAH_*RASHIN SANI.......*_ *HAUWA A USMAN* _JIDDARH_ ```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh``` 1⃣9⃣ Khulud ta kuma zaro idonta waje tace " kai my Sanah, cikin dariya Sanah tace " eh mana, " ni dai please kiyi man alk'awarin baki kuma ramawa please, tayi maganar cikin sanyinta, Sanah ta kuma yin dariya had'i da dafa kafad'ar Khulud tana kallanta ido cikin ido, cikin marairaicewa Khulud tace " please tana langwab'ar da kanta gefe, Sanah ta d'an k'ura mata ido kana ta sauke ajiyar zuciya had'i da cewa " nayi miki alk'awarin daga yau har abada duk abinda zai man ban kuma ramawa, cikin jin dad'i Khulud ta rungume ta tana cewa " yawwa my Sanah thank you so much, murmushi Sanah tayi kawai batare datace komai ba, ta rok'o hannun suka nufi part d'in kakannin su. Fitowa Hanash yayi zuwa harabar gidan, su Wajnah na biye dashi a baya, Papu yace " au kinga na manta Hanash zai fita batare dana aike shi bank d'in bako? Yayi maganar yana kallan Mimmee, tace " kaga kuma yau Friday ba, da idan ya aje su sai ya biya bank d'in, kafin su gama walimar shi yaje yayi abinda zayyi, Mimmee ta fad'a idanta kan Papu, " kuma daga yau ba bank har sai Monday, ga time na tafiya naga yanzu wajen 4:30pm, yayi maganar yana mikewa had'i da kallan agogon hannunsa, da sauri ya fita daga parlor'n yabi bayan su Hanash, Hanash na niyyar yiwa mota key, yaga Papu ya nufo su da sauri, a hankali Hanash ya fita ya nufi Papu, check Papu ya mik'ewa Hanash yana cewa " idan ka aje su a gidan walimar ka biya banki ka amshi wad'annan kud'in, sai ka saka su a account d'ina ko naka, Hanash yayi murmushi yana kallan Papu zayyi magana drivers biyu suka shigo gidan a lokaci d'aya, Papu yace " yauwa ga drivers nan sun dawo, bari na saka d'aya daga cikin su ya kai su gidan walimar, kai kuma sai ga je bank d'in, Papu yayi maganar yana nufar wajen drivers d'in, cikin taushi Papu ya fad'a musu, sannan ya sanar dasu Zohal su fito su shiga motar driver shi zai kai su, kana ya koma wajen Hanash dake tsaye inda ya barshi, Papu ya lura da yadda yanayin Hanash ya canja sosai, sannan walwalarsa da sakin fuskarsa ba kamar da ba, kallan Papu Hanash yayi kana yace " Papu wannan kallan fa? Ya fad'a yana dariya, shima Papun dariya yayi yana dafa kad'afar Hanash yace " bakomai kawai ina kallan d'ana ne, in kuma za'a hana ni ne to, yayi maganar cikin barkwanci, Hanash yayi dariya batare dayace komai ba, Papu yace " kaje maza ka dawo zamuyi magana da kai, Hanash yayi dariya kana yace " hala Papu ya manta yau Saturday? Papu ya zaro ido had'i da cewa " what! haba dai? Hanash yayi murmushi yace " Allah kuwa Papu yau Saturday, hala ka shafa'a ne? " Ka manta jiya mukaje sallar juma'a? Papu yace " na manta, kasan tsufa ya fara kamamu , abinka da tsoho, Hanash kuma yin dariya yace " kai Papu wanne irin tsufa kuma? "Bayan gaka nan kamar matashin sauryi kamar mu,, Hanash ya fad'a cikin tsokana, dayake sun saba wasa da dariya sosai da Papu, dan wani lokacin idan ka gansu sai ka rantse abokanai ne, Papu yace " kayya wanne matashin sauriya, muda samartaka ai sai dai a lahira a aljanna, jiya ai ba yau ba , tunda na haifi k'aton saurayi kamarka ai na tsufa, ko yanzu Alhamdulillah dan na mori k'uriciya ta, kai ma sai kayi k'ok'ari ka mori taka k'uruciyar, sanda nake kamar shekarunka na haifeka, amma kai gaka nan har yanzu 30yrs baka da ko budurwar, ko rowa kake man dan karna ga 'ya'yanka oho, inaga sai na mutu sannan zakayi aure ka haihu, Jadda dake jiyo su ta window ta, suka jiyo muryarta tana cewa " kyale ja'iri wallahi idan na gaji sai dai ya shigo gidan ya iske matarsa a b'angarensa, imma bak'in ciki kake man dan kar naga yaranka ehe, daga Papu har Hanash duk suka sanya dariya, Hanash ya shafa kansa yana kallan Jadda, Papu dake tsaye a wajen shiya hana shi ce mata komai, sai murmushi da yayi tayi shi kad'ai yana shafa kai, kallansa Papu yayi yana nazarin yanayinsa ya tabbatar akwai abinda yake damunsa, amma sai ya sabar yace " ka rik'e check d'in a hannunka, ranar Monday sai kayi kamar yadda na saka ka, "tom Papu ba damuwa Allah ya kai mu Monday, Papu ya amsa da " amin yana komawa part d'in Mimmee, iske ta yayi tana k'ok'arin shigewa bedroom d'inta, ganinsa yasa ta jiyowa tana kallan shi, yace " wai meke damunsa ne? Tace " wa? Yace " Hanash mana, naga kwana biyu yanayinsa duk ya canja, Mimmee tace " nima dai haka nagani kwana biyun nan, kamar yana cikin damuwa, Papu yace " kin tambaye shi ne? Tace " eh, "Ok meya ce maki? " Wai bai jin dad'in jikin sa ne, Papu yace " ok mu barshi zuwa nan da kwana biyu mu gani, Mimmee tace " Allah ya kai mu, muje ciki kayi wanka ko? Bayanta yabi yana cewa " kamar ko kinsan zafi nake ji, Hanash na komawa b'angarensa ya kuma zubewa kan sofa, had'i da runtse idannuwansa, shi har yanzu bai san so da soyayyar Khulud ke d'awainiya dashi ba, ta hana shi sakat, ta hana shi walwala da farin ciki, haka nan kullum yake jin damuwarsa na k'aruwa, babban burinsa a rayuwa yanzu bai wuce na sake ganinta ko sau d'aya ne a rayuwarsa ba. part d'in Ganez suka fara shiga suka iske Nisah zaune kusa dashi, Sanah tace " oh! ashe dai har yanzu ana tsinkar korawayen fure? Duk sukayi dariya kana Ganez yace " a'a aini idan bada ku zan tsinki korayan fure ba, ai a banza, Khulud tace " kinji shi zayyi mana wayo kullum yayi ta cewa idan ba mu ba sai rijiya, Sanah tace " kuma yana tsoran matarsa ba, Nisah tayi dariya kana tace " oh! kuji man yara, wato kun saka mana ido, ai irin haka ake so, Khulud tace " mijin ya rink'a jin tsoran matarsa? Nisah tace " eh mana, Sanah tace " ina fa dad'i miji ya zama mijin tace, an dai mayar mana da kakanmu tace kawai, Nisah tace " wannan ai kan tace ne ma, duk sukayi dariya kana suka fita suka nufi part d'in Danish, ganin Erum tayi kwalliya yasa su yin dariya, Khulud tace " wato ke har yanzu baki dai na kwalliyya bako? Erum tace " ina ni ina daina kwalliya, Sanah tace " kici zamaninki kici na wasu ko? "Sosai ma kuwa cewar Erum, " a'a kace yau amare nane a gidan, cewar Danish dake fitowa daga bedroom d'insa, Sanah tace " mune, munzo a bamu abinda akaci aka rage,, Danish yace " ku da kuke amare ina ku ina raguwa, ai sai dai sabuwar dahuwa, Khulud tace " ai dama kun saba yi mana wayo, bayan duk tsoron matan ku kukeji, Erum tace " ai irin wannan k'arshen ake so ayi yara, ku ma kuyi addu'ar Allah ya baku ita mu, Sanah tace " wai ma duk ba wannan ba, ina zaku na ganku duk kunyi kwalliya? " Mu da muke da walima yau har a tambaye mu inda zamu dan munyi kwalliya, Erum tayi maganar tana dariya, Khulud tace " a she walima ce daku, a ina kuma? Erum tace " sosai ma, kuma a nan gidan, Sanah tace " tab wai wacce walimar kuke nufi? Badai tamu ba ko? Tayi maganar a lokaci d'aya, Erum tace " walimar ku ko tamu? "Ai muke da walima kuwa, tunda mune manyan k'awaye, tayi maganar tana dariya, Khulud tace " mu dai bamu gayyace ku ba, kuma bamu san gayyar sod'i ehe, duk sukayi dariya kana suka fita, part d'in Juju sukayi, da sallama suka shiga, Didi ya amsa musu cikin fara'a, kana yace " 'yan candy ne yau a gidan namu? Sanah tace " mu ne, Didi ya kalli Juju yace " ina kika b'oye mana su ne? Juju tace " wacce ni? " Ai sai dai ka tambaye Mamun su, ni tunda sukayi candy ban sa su ido na ba, sai yau, ko irin kayan kayan candy nan ba'a kawo mana ba, balle muce mu shaida anyi candy, muce Allah ya sanya alkhairi, Khulud tace " kai Juju Allah bamu zauna bane, mu ta yawan zuwa saloon da k'unshi, Sanah tayi dariya kana tace " Juju ku da zaku bawa wasu ma, kayan candy kuma ga walima nan kun shirya ku da kanku, sai ku shaida anyi candy kuyi addu'ar Allah ya sanya alk'airi, Didi yayi dariya yace " wai Sanah baki abin magana, ke dai ba'a tab'a k'ure ki ta wajen magana, Juju tayi dariya tace " ai ni nayi shiru tunda an fini baki,,, dama hausawa sunce dokin mai baki yafi gudu, Didi ya kuma yin murmushi kana yace " Sanah yaushe jamb d'inku zata fito? Sanah tace " naji ance this coming Monday, Juju tace " wacce university kika cike? "First choice BUK second kuma ABU Zaria, Didi yace " masha Allah Ubangiji ya taimaka, Allah ya bada sa'a, duk suka amsa da Amin, har Khulud dabata zana jamb d'inba, dan cewa tayi ita ta gama karatun boko har abada, Juju ta kalli Khulud kana ta mayar da kallan ta ga Didi tace " 'yar Abbu da Mamu ita aure take so, Khulud ta d'ago kanta da sauri suka had'a ido Juju tayi saurin sadda kanta k'asa tace " Allah Juju ba haka bane, tayi maganar a shagwab'e, Juju tace " idan ba haka bane to yaya ne? Khulud tace " Allah ni ban san cigaba da karatun ne kawai, ni kwata-kwata ban tab'a sha'awar yin karatun boko mai zurfi ba, Juju zata kuma yin magana, Didi yayi saurin cewa " haka ne ai kowanne mutum yana da nashi ra'ayin, hakan ma da kikayi dai-dai ne dabaki yaudare iyayenki kin shiga jami'ar ba, kana kik'i yin karatun ko wata matsala ta faru, so ni ina ganin kinyiwa kanki da Abbunki adalci, Allah ya zab'a maku abinda yafi alkhairi a rayuwarku, ya haskaka rayuwarku ya sanya albarka acikinta, duk suka amsa da Amin, fita sukayi suka nufi wajen da aka tanada dan yin walimar da tuni k'awayensu sun fara zuwa, sosai walima ta kankama haik'an, aka ci aka sha sosai dan sosai Abbu ya saki bakin aljihunsa dan nuna tsantsar farin cikinsa na kammala karatun yaransa lafiya, sosai aka rarraba kyaututtuka, kana kowa ya watse cikin farin ciki aka gama walimar lafiya. Sannu a hankali matsanannaciyar soyayyar Khulud tayi mugun kama Hanash, ta addabi ruhi da gangar jikinsa, kwata-kwata ya rasa sukuni da walwalarsa, ya rame sosai dan raban dayaci ishashshen abinci ko ya samun bacci har ya manta, kullum yana cikin bedroom ko parlor'nsa, dan ko fituwa sosai ya dainayi sai dai ya fito ya gaida iyayshi ya koma, yauma kamar kullum kwance yake a d'akinsa ya tsunduma duniyar tunaninta, idanshi rufe babu abinda yake gani sai ita tsaye a gabansa, tana sakar mishi k'ayataccen murmushinta, jin knocking yasa shi bud'e shu'uman idanuwansa, k'ofar ya zubawa ido na tsayin lokaci, batare da yayi wani yunk'uri ba, sake knocking akayi a karo na biyu, dakyar ya iya cewa " waye? Muryar Papu yaji yace " mu ne, dan sun kasa jurewa ganinsa cikin wannan mawuyacin yanayin, da sauri ya mik'e ya bud'e musu k'ofar suka shigo, akan sofa duk suka zauna, a hankali Mimmee ta d'ora hannunta akan kafad'arsa, had'i da zubawa d'an nata ido, Papu ma ya zauna kusa dashi ya zuba masa ido, kansa ya duk'ar dan ya san kwanan zancen, muddin akace bashi da lafiya ko yana cikin damuwa to gaba d'aya gidan babu mai yin walwala, a hankali Papu ma ya d'ora hannunsa akansa kana ya kira sunansa, " Hanash, "na'am, Hanash ya amsa cikin ladabi, " meke damunka? Cewar Papu a tak'aice, murmushin k'arfin hali Hanash yayi kana yace " babu abinda ke damuna Papu, yayi maganar while kanshi k'asa, Mimmee ta shafa kansa kana tace " Hanash please karka b'oye mana abinda yake damunka, ka daure ka sanar damu koda babu wani abu da zamu iya yi akai, sai mu tayaka da addu'a, ta fad'a cikin damuwa, murmushi Hanash ya kuma yi kana yace " ba ni da lafiya ne, Mimmee zazzab'i da ciwon kai ke damuna, ido Mimmee ta zuba mishi tana nazarinsa dan ita kwata-kwata bata yarda da abinda yace ba, Papu yace " kaje hospital? Hanash yace " eh Papu, "me sukace yana damunka? Papu ya kuma tambayarsa, d'an shiru Hanash yayi kafin yace " Malaria, " to ikon Allah kai ko ina kaga sauron daya cije ka? Mimmee ta fad'a tana kallan kwayar idansa, murmushi yayi kana yace " Mimmee, cikin shagwab'a, Papu yace " shi ciwo ai daga Allah ne, ba ta inda baya shiga jikin mutum ko son? Yayi maganar cikin tsokana, dan shima yadai ji Hanash ne kawai, amma bai yarda da abinda ya fad'a ba, babu yadda Papu da Mimmee basu yi akan Hanash ya sanar da su damuwarshi ba, amma yak'i yace babu abinda yake damunsa, Papu yace " Allah ya sauwak'e, ya amsa da " Amin, kana suka fita, suna fita Hanash ya koma ya kwanta, had'i da rufe idansa. Ranar Monday jamb ta fito, Sanah cikin murna da d'oki suka je ita da Aarib & Khulud suka duba, a cafe, aiko taci sosai dan ta samu 251, tsalle ta buga ta rumgume Khulud da Aarib cikin matsananciyar murna, motar su nayin parking a harabar gidan ta fito, ta shiga kwalawa Halan kira, da gudu ta shiga part d'in Halan, ta iske ta parlor zaune ita da Ziyad, cikin murna ta fad'a kanta, ta ma manta da tsohon cikin dake jikin Halan, Ziyad ya daka mata tsawa had'i da cewa " ke baki da hankali ne ko baki ganin abinda ke jikinta? Bata kula da tsawar daya daka mata ba, sai ma kiss datayi mishi a kumatu, cikin murna tace " Yaya naci jamb, ta fad'a tana tsalle, dariya Halan tayi tace " kai masha Allah gaskiya nima nayi murna, badan kayan dake gaba na ba, da har dani za'ayi tsallan, Ziyad yayi dariya yace " bani abu na inyaso sai kije kiyi tsallanki, Halan ta kalleshi had'i da zumb'uro baki tace " Allah da ana bayarwa ai bama sai ka tambaya ba, Sanah da Khulud suka fita da gudu suka nufi part d'in Mamu, suna zuwa Sanah ta fad'a kan Abbu, yace " kai Sanah ke dai baki girma, naga alamar so kike ki karya ni tunda baki ganin na tsufa yanzu, Sanah tayi mishi kiss tace " Abbu albishirinka, yana dariya yace " goro, tace " fari ko ja? Yace " fari tass, tace " Abbu na ci jamb, Abbu yace " wai dole ayi murna, Mamu tace " masha Allah, saura waec & neco, Abbu yace " suma duka za'a cinye su, in sha Allah, fita sukayi suka nufi part d'in Juju, nan ma aka sanar mata anci jamb, murna kam ba'a magana, a week d'in waec ta fito, Sanah ta samu result mai kyau, result d'inta yayi mugun kyau, bayan two weeks BUK ta kira su first UME, bayan week nan ma result ya fito, ta samu taci, suka bata Admission letter na BSC COMPUTER SCIENCE. Kullum Hanash bashi da wani aiki sai mafarkin Khulud, da tunaninta ko idansa ya rufe ita yake gani, koyaya ya rufe idansa ita yake ya gani, abun duniya duk ya dame shi, ba shi da wani burin daya ce na sake ganinta a yanzu, ko da sau d'aya ne a rayuwarsa. Yau itace rana ta farko da Sanah zata fara hallartar BUK, ta gama shirinta tsaf cikin riga da siket na material red color d'inkin yayi masifar yi mata kyau, ya amshi jikinta sosai, ta saka high hill shoe ta yafa mayafinta mai kyau kalar flowers dake jikin material d'in black, sosai Sanah tayi shegen kyau, duk da ba wani make up tayi ba, ta dayyi simple make up abinta, wanda ya bayyanar da tsantsar kyauta, har cikin makarantar Aarib ya kaita, sai da yayi mata fad'a sosai kana ya tafi, sannu a hankali take tafiya harta isa department d'insu, tambaya tayi, aka nuna mata, inda zasuyi lectures yau, dayake tana da time table na duka courses & time d'in su, a hannunta tasan Computer lectures zata fara attending, zama tayi a inda taga students na zama, zamanta ke da wuya ta fara jiyo hirar students, " yau fa Sir Aryan ne damu, kasan ko ba sauk'i, d'ayan yace " wallahi ko ni gaba na ma sai fad'uwa yake yi, tun jiya dana duba naga shine damu hankali na yake a mugun tashe, wani daga gefe yace " kai ai Malamin nan bai da kyau, d'ayan yace " kaga fito sak a mutum kai tsaye kace bai da mutunci, d'ayan yace " ni fa yana mugun ban mamaki shi ko irin na sauran lectures d'in nan bayyi, d'aya yace " me? " San mata mana, d'ayan yace " kai tanan wajen ai Sir Aryan yayi wallahi, ba ruwanshi da mata, duk kyanki yanzu zai yarfa ki, ba kamar sauran lectures d'in ba, shegu da sunga mata sai suyi ta rawar jiki, idan mune 'yan uwansu maza tsakanimu dasu ba mutunci, sai su rufe ido su karta mana, amma shi kwata-kwata mace bata isheshi kallo ba, naga 'yan mata dayawa sunyi mugun matuwa akansa, d'ayan yace " aiya had'u ne ga kyau ga kud'i, kaga kuwa ai dole mata su matu, tunda ready mate ne, d'ayan yayi dariya yace " aiko suna shan dizgi da wulak'anci a wajensa ba, dan yanzu zai kartawa mutum rashin m, idan ta kama ma ya yarfa maka mari ba ruwanshi, shege ga girman kai da d'agawa da jan aji dan sai kayi mishi magana goma amma dakyar idan yaga dama zai amsa maka d'aya , d'ayan yace " kai ai ya iya d'aukar wanka dacin uwar sutura, yana zagin gizna ta asalimma, ni na rasa uban me yake yi a makarantar wallahi, "hmmmm ga babu ruwanshi da ke wai mace ce, shi hukunci d'aya yake yi tsakanin mace da namiji, idan ya riga ka shiga class ko waye ubanka kuma ko uban ya tsaya maka ya d'aure maka gindi baka shiga, d'ayan ya duba agogo yace " sauran just 5 minutes ya shiga fa, kusan kuma baya African time, d'an tsaki Sanah tayi a hankali kana ta mik'e tabar gurin, saboda duk gurin wajen mutum 100, maganar mutum d'aya suke tayi Sir Aryan, duk inda students sukayi d'an group, maganar shi kawai sukeyi mata da maza, daga maganar had'uwarsa kyansa, gayu, ajinsa, sai ta wulak'anci da dizginsa da kuma girman kansa, da yadda mata suka mato akansa yake wulak'antasu, shiyasa duk randa yake da lectures dasu suke kaffa-kaffa. Can gefe ta koma ita kad'ai ta zauna, ita kad'ai kasancewar yaune farkon zuwanta bata san kowa ba, tana daga zaune taga wata matsiyaciyar had'add'iyar mota ta danno kai cikin makarantar, students na ganin motar suka kai duba zuwa number motar dan su tabbatar idan shi, saboda baya hawa motar d'aya, duk nacinka baka isa kace ga yawan motocinsa ba, ta number motarsa kad'ai suke gane shi ne, saboda sunan family d'in su ne a duka number motacinsa,, ai students na tabbatarwa shine, suka fara gudu maza da mata ana rige-rigen shiga class. Yana yin parking, ya zare key d'in tare da komawa ya kishink'id'a jikin kujerar, ido ya lumshe tare da fesar da numfashi mai sanyi, a hankali ya kuma bud'e idon tare da sauk'e ajiyan zuciya, yana mai shak'ar k'amshin jikinsa dana mortar, a hankali ya sa hannun damanshi ya dafe saitin k'ahon zuciyarshi dan jin gabansa yana muguwar fad'uwa da k'arfi, bugun zuciyarsa ya k'aru sosai, zuciyarsa ta rink'a bugawa so past, idansa ya kuma lumshe yana k'ara d'an kishingid'a akan kujerar motar, a hankali ya furta " innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, saboda yadda yake jin duk ilahirin jikinsa ya mutu, gabansa na mugun fad'uwa zuciyarsa na bugawa da tsananin k'arfi, addu'ar yayi ta maimaitawa dan baya son ayi mishi African time shiyasa shima baya son yayiwa d'alibanshi, bere daga inda yayi parking yana iya hango yadda suke sassarfan shiga class, sharshesa ya fitar tare da d'an laso lips nashi, hadi da d'an cizawa dan kauda kasalar dake saukar mai a jiki, a hankali ya b'alle marfin motar tare da zuro k'afarshi d'aya woje, baki ya d'an tab'e ganin yadda wasu matasa suka wuceshi da sassarfa, gudun karya rigasu shiga class, ya hanasu shiga, fitowa daga cikin motar tare da jawo laptop nashi, ya bud'eta tare da dorata kan hannunshi daya mik'ar, yana kuma d'an lallatsashi cikin k'orewa, ajiyan zuciya ya sauk'e tare da fara takawa zuwa class d'in yana mai jin dad'in iskar dake busawa sirrai da fawowi suna shawagi tsuntsaye na kai komo ga k'amshin furanni dake ratsashi. Cikin takunsa na isassun maza masu haiba da kamala ga tarin nagarta yake tafiya cap-cap sautin takalminshi ke ratsa wurin in dalibai sun hangoshi sai suna rusunawa tare da ratse mishi. Ganin yadda students ke gudu yasa Sanah kai idanta kan motar dataga kamar an saka MOLI'S 15, amma data duba so sai taga kamar ba haka bane, baki tad'an tab'e kana ta mik'e cikin takunta mai daukar hankali tabi bayanshi, ta nufi class itama, daga bayansa ya rink'a jin kamar takun mutum a bayansa k'at-k'at, Fuska ya kuma had'ewa dan ya gane mace ce, daga k'asa ya kalli k'afarta data sha kunshi mai ja da bak'in lalle yayi masifar yi mata kyau, gabansa ne yayi muguwar fad'uwa lokacin daya d'ora idansa akan k'afarta, sake had'e rai yayi , kana ya cigaba da tafiya, yana tafiya tana binsa a baya, har suka zo gaf da isa class d'in, Kai ya d'an jinjina tabbatarwa da yayi class d'in sa zata shiga , hankalin shi na kan laptop d'inshi, hannunshi mai yin typing d'in ya d'an d'aga shi saman kafadarshi ta yadda zata gani, sanan ya had'e doguwar yatsarsa ta tsakiya da babbar yatsarsa ya kettasu sau d'aya ta yadda ya bada sauti, sannan ya had'e yatsunsa biyu ya kad'asu kamar mai buga fiyano ya mata nuni data tsaya inda take karta biyoshi, batare daya juyo ya kalle ta ba bai kuma tsayaba yaci gaba da takunshi zuwa cikin class, Itako Sanah bata gane abinda yake nufi ba, dan haka taci gaba da binsa a baya, Kai ya jinjina tare da yin gutun murmushi, mai dauke da alamar zaki gane kurenki, kana ya cigaba da tafiya har suka k'arasa cikin class d'in, Sanah tazo zata wuce mazaunin d'aliban, *"Keeh"* kamar daga sama sautin muryarsa ya ratsa shirun daya ratsa ajin,sai sautin takalminta dake amsakuwa, shirune ya sake ratsa ajin duk sunsha jinin jikin su, ita kuwa Sanah kai ta d'ago ta kalleshi ,Amman bata ga fuskarsa ba dan baya ya bata, sai gashin k'eyarsa da ta tsurawa ido ganin shi a kwance lub sai wani lauyewa a yayi ya bi k'eyan nashi yana Shek'i, tana cikin nazarin da me tayi mishi ta kuma jiyo muryarshi na ratsa ajin baki d'aya taji tajiyo muryarsa nacewa yana cewa, *"kneeling down,"* ya fad'a still bai jiyo ya kalle ta ba, juyawa tayi bayanta taga babu kowa sai ita kad'ai, cikin mamaki ta kalli bayansa dan ita a iya saninta tasan ba'a saka Patick a jami'a. Cikin mamaki ta kuma kallan bayansa, batare daya jiyo ba taji yace *"ko bazaki kiyi bane?"* Muryar dataji ta daki dodon kunnenta, tasa gabanta mugun fad'uwa a razane ta kuma kallan bayansa, babu damar taga fuskarsa saboda ya juya mata baya, a hankali Sanah ta d'an zumb'uri baki kana tayi kneeling down d'in, gaba d'aya students mamaki ya gama cika su, duk da sun san halinsa, sun tabbatar zai iyin abinda ma yafi hakan, dan sun san mari ko dizgi abu ne mai matuk'ar sauk'i a wajensa, amma basu tab'a ganin yasa wata ko wani kneeling down ba, sai yau kuma daganinta new comer ce, students suka rink'a yin dogon wuya suna l'eka ta, jin muryarsa ta fara explanations yasa duk suka shiga hankalinsu. Sanah na nan har ya gama lecture tana ta zumb'ure-zumb'uren baki, Cikin k'asaita ya fito zai tafi , ganin ya wuce ta gabanta amma bashi da niyyar ce mata komai, yasa ta cewa *"Sir to ni wuni zanyi a nan ne? "* Tsayawa yayi cak a inda yake, kana ya juyo da fuskarsa a hankali ya zuba mata ido, had'i da hard'e hannayensa a k'irji, mik'ewa Sanah tayi batare daya bata umarnin tashi daga kneeling d'in ba, kanta a sunkuye tana kakkab'e siket d'inta, tana yin magana k'asa-k'asa, "eh wato kai zaka fece gidanku ko, ni kuwa in zauna a nan, sai kace baiwar gidan ku ka samu ko, hegen k'eya! da nad'edd'en gashi , hege mugu kawai , d'an masu k'aton kai." dan ita a tunaninta ya tafi shiyasa ta d'anyi halin, baki ta murgud'a tare da mik'ewa tsaye, d'ago kan da zatayi, keda wuya sexy eyes d'inta, suka sark'e cikin na *SIR MOLI* dayake tsaye hard'e da hannuwa yana kallan ta.................. *_Aunty AISHA ALIYU GARKUWA_* _kina tambayar inda nakai miki Sir Molinki to gashi nan na maido miki abinki_ ~To fans masu tambayar ina nakai Sir Moli na b'oye har tsayin six years, gashi nan ya dawo~ ~sai a cigaba da gashi a! d'ora daga inda aka tsaya~ MOMYN ZARAH _*RASHIN SANI.......*_ *HAUWA A USMAN* _JIDDARH_ ```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh``` 2⃣0⃣ Ido ya d'an tsura mata na wani d'an lokaci, yana mamakin yadda akayi har yanzu bata canja hali ba, halinta yana nan babu abinda ta canza ko ya ragu, sai ma abinda ya k'aru, dan tuni Sir Moli ya gane Sanah, tunda ya kalli k'afarta ya gane itace, basarwa kawai yayi saboda halin muskilancinsa, amma tuntuni ya dad'e da gane itace SANAH HAMRAZ, itama Sanah ta gane shi tunda ta d'ora idanta akansa ta gane shine, kallansa itama take yi ido cikin ido, bata ko k'iftawa tana mamakin yadda ya canja, kyansa, kwarji da haibarsa ta kuma k'aruwa fiye da da, fuska ya kuma tsukewa tare da cewa " Zo nan". ya fad'a had'i da juyawa ya nufi office nashi, baki ta turo kana tabi bayansa, har suka isa office d'insa bai jiyu ya kalle ta ba, shiga ciki yayi ya zauna akan kujerar zamansa, ya d'ora laptop d'insa akan table d'in dake gabansa sannan ya maida hankalinshi kaco kam bisa laptop d'in yana sarrafata cikin k'warewa da, shiru ya ratsa office d'in sai sautin yatsunshi dake kan pins din system d'in yana typing, Ita kuwa tana tsaye a gefenshi, ta k'ura masa ido tana kallan yadda hutu da k'udi suka nuna k'arara a jikinsa, da gani ba sai an fad'awa mutum ba kasan yana cikin jin dad'i da more rayuwa, dogayen yatsunsa ta d'an saci kallon su, ido ta d'an juya ganin yadda skin d'inshi ya murje tsananin farinshi ya k'ara bayana, kana ta kai duba zuwa kwantaccen gashin kansa, wanda ya gangaro gefen fuskarsa zuwa hab'arsa yayi masa saje, komai a fuskarshi mai kyau ne, musamman idonsa da d'an k'aramin bakinsa mai d'auke da zayen tattausan suma da yayi mashi k'awanya sai jajayen lips d'inshi dake ta shek'i a tsakiyar kota million d'inshi,ga hak'ora farare tass, ga dogon hancinsa, idan ka ganshi sai ka rantse ba indiyene, musamman ma daya kasance fari tasss dashi dogo, tun suna Roni yake mugun yi mata kama da Hiritik Roshan, bata gama tantancewa da tsananin kamarsa da Hiritik ba sai yanzu, dan idan aka jera maka Sir Moli da Hiritik baka isa ka banbance d'aya daga cikinsu ba, dan har k'asunbar da Hiritik ya tara shima Sir Moli yana da ita, har eye color d'in Hiritik datake brown color, shima Sir Moli haka tashi eye color d'in take. " har yanzu dai halin muskilanci da wulak'anci da girman kai d'in yana nan! hmmm mai hali dai baya tab'a canja halinsa" ta fad'a cikin ranta. Shiko Sir Moli ya lura sarai da irin kallan mamakin da Sanah keyi masa, wanda shima mamakin mugun kyau da girmanta yake yi, musamman skin color & dimples da wushiryarta, sunyi bala'in burge shi, amma babu abinda yafi d'aukar hankalinsa a jikinta kamar sexy eyes d'inta, da kuma structure d'inta, girmanta ba k'aramin mamaki ya bashi ba, duk da dama can tun tana yarinya tana da kyau, amma dayake yanzu ta girma mak'erin 'yan matanci ya k'era ta sai yaga ta k'ara kyau, sai ta zama kamar hurul'in (matan aljanna), Idanshi nakan system d'insa yace " wannan kallan fa? Ko na miki sata ne ,kikaga abunki a guna da zaki tsareni da ido, ko ajiyan wani abunki kika bani yanzu kike so in maida miki?". Da sauri ta d'auke idanta daga kansa, "ko kin sanni ne?". Ya kuma tambayarta batare daya d'ago kansa ba, mamakin tambayar da yayi mata ne ya kamata, danta tabbatarwa kanta ya gane ta sarai, " halin za'a tab'a kenan, tayi maganar cikin ranta, a fili kuma cikin muryarta mai d'an tsiwa tace " a'a ban sanka ba, ina zan sanka?". Sosai shima yayi mamakin amsarta, dan shima ya tambatar ta gane shi, amma dayake yasan halinta sai ya basar, yace: " To meyasa zaki tsareni da kallon maita, cinyeni zakiyi ko?". Shiru tayi dan ta gane tijara zai mata , shi kuwa ganin tayi shiru yasashi ce mata, "Me sunanki?". Still bai d'ago ya kalle ta ba, tace " SANAH HAMRAZ, "wacce school kikayi?". Ya kuma tambayarta idan shi nakan system, tace " primary ko secondary?". "Both, ya bata amsa a tak'aice, tare da tab'e baki, A hankali tace: " primary gate way nayi, secondary school kuma Computer Girls Secondary school Roni na fara, daga baya na koma Momy Speed na k'arasa a can" "ba'a Roni kika gama ba kenan? " Eh". ta bashi amsa, "To meyasa?". Ya kuma tambayarta, rolling lulu eyes d'inta tayi kana tace " kawai haka nan". yadda ta juya idanta yasa shi d'an d'agowa ya d'an kalleta a dai'ile, kana ya mayar da idansa ga abinda yake yi, yace " wanne gari kike?". "Kano, ta bashi amsa kai tsaye, " wacce unguwa? Ya kuma tambayarta while bai kalli inda take ba, idanta na kansa tace " duk wannan tambayoyin fa na meye ne, ko cinye wani nai ake neman gidan mu?". Ba tare daya kalle ta ba, yace " out!!!". a tak'aice da sauri ta fita yadda kasan jira take, a hankali ya d'ago kansa yabi bayanta da kallo, still yana cigaba da mamakinta ,dogon tsaki yaja tare da rufe system d'in ya jingina da kurar tare da lumshe idonsa, yana fesa numfashi a hankali. Sosai kewar Sanah ta dami Khulud kasancewar yau ne karo na farko, kuma rana ta farko a duk tsayin rayuwarsu, da suka yi nesa da juna har na tsayin hrs bama minutes ba, dan tunda suke a rayuwarsu basu tab'a yin nesa da juna na tsayin lokaci haka ba sai yau, dan haka Khulud taji gaba d'aya gidan yayi mata bak'i k'irin, yayi mata mugun duhu, da girma, ji take kamar gidan babu mutane, gane take kamar ita kad'ai ce a gidan, tunda Sanah ta tafi nata ko fito daga bedroom d'insu ba, tana ciki k'unshe kamar mai taka ba, ko part d'in Halan da Juju yau bata iya shiga ba, dan tasan tsokarta zasu tayi har suka ta kuka daga k'arshe, karo na farko a duniya dataji sha'awar cigaba da karatun itama, dan sai da ta gwammaci dama itama ta shiga jami'ar koba komai tasan bazatayi nisa da Sanarta ba, tasan zata kasance da ita, duk bayan 2 to 3 minutes sai ta kalli agogo taja dogon tsaki, dan ji take kamar Sanah tayi 1yr bata gidan, gaba d'aya kewa da kad'aici ya dame ta ya addabi rayuwarta. Zohal Mimmee ta aika ta kira mata Hanash bayan ta gama jera lunch a dinning table, yana kwance akan sofa ya samu bacci ya d'auke shi, cikin baccinsa yaji sama-sama ana knocking, idansa cike da bacci ya bud'e su dakyar, yace " waye? Cikin muyar bacci, Zohal tace " nice Yaya, Mimmee ce tace a kira za'ayi lunch, idansa ya murtsuke kana ya kalli agogo, a hankali ya mik'e zaune yace " jeki ce ina zuwa sallah zanyi, "Ok tace " kana ta koma part d'in su ta sanar da Mimmee, Mimmee tace " koma kice masa ina jiransa sai ya zo zanci abinci, dan tare dashi nake san ci yau, Zohal ta koma ta Sanar dashi, mik'ewa yayi tsaye yana cewa " tom, da sauri ya shiga bathroom ya watsa ruwa, yayi brush kana ya d'auro alwala, da sauri ya shirya yayi sallah ya fita, kamar yadda Mimmee tace hakan ya gani, tana zaune tana jiransa, fuskarta d'auke da murmushi ta tare shi tace " son yau da kaina girka maka best food d'inka, murmushi yayi yace " Mimmee me? Fuska ta b'ata kana tace " bangane me ba? Yace " sorry Mimmee tambaya fa nayi, tace " lalle yaro na yana cikin damuwa tunda har ya manta abincin daya fi so, kansa ya d'ora akan kafad'arta kana yace " no Mimmee ba mantawa nayi ba fa, kawai dai na tambaya ne, tace " traditional food mana, murmushi yayi had'i dayi mata light kiss a kumatu yace " thanks best Mimmee of the whole world, kansa ta d'an buga tana murmushi, kana ta rik'o hannunsa taja shi zuwa dinning, da kanta tayi serving d'insa tuwon shinkafa miyar taushe da naman rago ga man shanu da kunun aya a gefe, "wow! Mimmee thank you so much, yace yana dariya, da sauri ya jawo abincin gabansa ya sanya hannu ya fara ci, yana kai lomar farko bakinsa yaji babu dad'i, a hankali ya d'an yamutsa fuska, duk abinda yake Mimmee na kallansa, abincin itama ta zuba ta fara ci, ganin yana ta juya spoon d'in tun daga lomar farko bai k'ara ci ba, yasa Mimmee cewa " wacece ita? Ta fad'a batare data kalle shi ba, ta jefa masa tambayar bazata, da sauri ya d'ago kansa ya zubawa Mimmee shu'uman idanuwansa, dan bai tab'a tsammanin wannan tambayar daga gare ta ba, shiru Hanash yayi , yayi kamar bai ji abinda Mimmee tace ba, Mimmee ta kuma cewa " wacece ita? Ta kuma tambayarsa, Hanash yace " wa kuma Mimmee? Batare data kalle shi ba ta kuma cewa " nace wacece yarinyar da kake so? Cikin shagwab'a Hanash yace " Mimmee, Mimmee ta ture abincin da take ci gefe, ta tattara dukkan hankali da nutsuwarta ga Hanash, tace " Hanash babu wani hali dazaka shiga a duniya wanda zan kasa fahimta, wanda bazan gane kona lura ba, ka tuna nice mahaifiyarka ni na tsuguna na haife da kai na, ni nayi goyon cikinka wata tara da kwana tara, na shayar dakai daga gare ni,, na raine ka, kayi wasa dani ka kuma yi kuka a jikina, na sanka tun kafin kai kanka kasan kanka, nasan damuwrka da matsalarka tun kafin kai kanka kansan damuwa da matsalar taka, dan haka zan tambaye a karo na k'arshe wacece yarinyar da kake so? Shiru Hanash yayi had'i da k'urawa Mimmee ido, yana tsananin mamaki bai tab'a yarda da maganar da bahaushe ke fad'a akan uwa ba sai yau, duk duniya babu wanda ya gane damuwarsa koya fahimci matsalarsa sai ita, lalle uwa dabance rayuwa duk wanda ya rasa uwa yayi kuka, "uhnnmmm ina sauranka Mimmee ta fad'a, idanta yana kan Hanash, 'yar ajiyar zuciya Hanash ya sauke kana yace " Mimmee ni ma ban santa ba, ya fad'a cikin sanyinsa, "kamar yaya baka santa ba? Mimmee ta fad'a cike da mamaki, yace " Allah Mimmee ban santa ba, "amma kake santa? " So kuma Mimmee? " Ba wani so kawai dai...... sai kuma yayi shiru, Mimmee bana tunnin sonta nake yi, "saboda me kace haka? Ta tambashi idanta na kanshi, Mimmee haka nan, kawai dai ina yawan ganinta a cikin mafarki na ko tunanina, sannan tana yawan hana ni suku ni, murmushi Mimmee tayi irin na manya kana tace " Hanash wannan ai shine san, a hankali ya d'ora idansa akan Mimmee, ta cigaba "Hanash kana santa, kai ne dai har yanzu baka yarda kana santa nata ba, ka yarda koda na rana d'aya ne ka bawa zuciyarka dama akanta, ka saurari bugun zuciyarka a tun sanda ka ganta, ko tazo maka, daga yau zuwa gobe kawai zaka gane abinda nake fad'a maka, yayi murmushi kawai, Mimmee tace " tashi kaje, amma gobe ka dawo bayan 24hrs. Su Sanah basu gama lecture's ba sai wajen 6:30, tayi muguwar gajiya, tana fitowa ta hango Aarib zaune akan mota yana jiranta, murmushi kawai tayi masa dan bazata iya magana ba, saboda tsabar gajiyar data yi,, Aarib da kansa ya bud'e mata motar ta shiga, kana ya zagaya ya shiga ya ja motar, duk abinda sukeyi akan idan Sir Moli, baki ya tab'a kana yaja motarsa shima yayi waje, Khulud na jiyo k'arar parking d'in mota ta lek'o ta window, dama abinda take yi kenan tunda taga 4:00pm tayi, ganin Sanah yasa ta fita da gudu ta tare ta, tana zuwa ta fad'a jikin Sanah ta saka kuka, Sanah tayi rolling sexy eyes d'inta, tace " kai my Ulud daga dawowa ta, sai kuka, so kike nima nayi kukan? Khulud ta girgiza kanta kana goge hawayenta, Sanah tayi murmushi itama tasa hannu tana gogewa Khulud hawaye, parlor suka shiga tare Khulud rik'e da jakar Sanah, sai da Sanah tayi wanka ta canja suka ci abinci tare sannan ta kwanta bacci mai nauyi yayi gaba da ita. Aryan Rayyan cikekken Bababbare ne na asali, d'an garin Maiduguri, wato k'asar barno, suna zaune a unguwar polo dake garin Maiduguri, General Rayyan Moli shine mahaifinsa, mutum mai adalci da sanin ya kamata, mai tsoran Allah, tausayi da taimakon talawa, mutum kamili nutsatstse mai dattako, General Rayyan Moli shine shugaban sojojin Nigeria har yau har gobe yana nan akan muk'aminsa bayyi retaya ba, mutum ne daya samu lambobin yabo dama, tau daga kan halayyarsa har zuwa nasoririn dayasamu a wajen aikinsa, dan yana kan yiwa k'asarta aiki irin na mazajen jiya, duk Nigeria babu wanda bai san MOLI'S FAMILY ba, dan ko jika ne kai a gidan saikayi amfani da MOLI, matarsa Hinah ba 'yar asalin Nigeria bace balarabiyar k'asar Kuwait ce, suna da yara 9 mata 6 maza 3 Sir moli shine dansu na 5 yana da babban yayanshi wanda shine d'an farinsu sunashi Aliyu suna kiranshi Haiydar, Haiydar yanada mata har biyu da yara 6, sannan Sir moli yanada yayu mata 3 mai bin Haiydar Anty Kubra itace sai Anty Nina ta uku sai Anty Ayyam ta hudu, sannan shalelensun dan daga kan Haiydar basu kuma samun d'ana mijiba sai kan, ARYAN RAYYAN MOLI (SIR MOLI), sai k'annenshi masu binshi MEELAH, da NAJMAH, sai d'an auta Jabeer mai tsananin kama dashi, dan suna muguwar kama dashi, gidan su gida ne daya ginu akan turbar addinin musulunci, da tarbiyyar da kuma wayewar boko dai-dai musali, dan mahaifinsu da suke kira da HILWA da kuma mahaifiyar su da suke kira da NAINAH, mutane ne masu matuk'ar sauk'in kai, Allah yayi mugun jarrabarsu da mugun san yaransu musamman ma Aryan, duk family nasu anfi ji dashi, yayunshi da k'annenshi suna mishi wani irin so na musamman, duk da halin miskilancin shi, suna mishi matsanaicin so sabida tsananin kamanshi da mahaifinsu, shi kuwa wani irin so yakewa yaran yayun nashi, suma yaran komai nasu zakaji suna Uncle Moli, dan shi kusan yafi gadar sunan inkiyar mahaifin nasu Meelah da Najmah suna gama secondary school akayi usu aure, mazansun suma barebari ne suna zaune a cikin garin Maiduguri, a anguwar low cost. Duk wata mota da zaka gani da sunan MOLI'S ta gidan suce, Allah yayiwa MOLI'S tarin arziki, wanda su kansu basu isa suce ga abinda suka mallaka a duniya ba, yana da estate manya-manya a nan gida Nigeria dama sauran k'asashen duniya, duk k'asar kaje kaga estates ko malls, da sauraran abubuwa da sunan MOLI'S na General Rayyan ne, Aryan Moli (Sir Milo) yayi karatun degree & master da PHD d'insa duka a Oxford University dake America, bayan ya gama degree ne ya dawo Nigeria yayi service dan haka dokar k'asar take, duk inda kaje kayi karatu dole ka dawo gida kayi bautar k'asa, bayan ya gama service ne ya koma yayi master & PHD duka a America, Aryan ya kasance mutum ne mai bin ra'ayin kansa, shi kwata-kwata bai damu da tarin dukiyar da mahaifinsa keda da ita ba, Aryan tun yana yaro yake mugun so da sha'awar yin aikin government, musamman koyarwa, mahaifinsa bai hana shi ba, ya barshi dan shi mutum ne mai matuk'ar sauk'in kai, bai san koyaya ne ya tauyewa mutum hakk'in shi. Washe gari da safe bayan Sanah ta shirya dakyar Khulud ta barta ta tafi school, dan harda kukanta, tare Aarib da Sir Aryan sukayi parking, Sanah ta d'an jima a cikin motar kafin ta fito, Hanash yayi kamar yadda Mimmee ta sashi, ya kuma tabbatarwa kansa san Khulud yake yi, a parlor ya iske Mimmee zaune, tana ganinshi ta sakar masa murmushi, har k'asa ya durk'usa ya gaida ita, tana murmushi tasa hannun ta d'ago shi, ta zaunar dashi a kusa da ita , tace " son ya ake ciki? Murmushi yayi yana kallanta batare daya iya cewa komai ba, "Son! ta kira sunanshi cikin sanyin murya, kansa k'asa ya amsa amsa mata " na'am, tace " ya kaji yau d'in? Ya kuma yin shiru, tace " Son kayi man bayani mana, murmushi yayi yana kallanta had'i da d'aga mata kai alamar "eh, murmushin jin dad'i tayi tana shafa kansa tace " Alhamdulillah abinda muka dad'e muna jira yau yazo kusa, to yanzu ina ne gidansu? "Ban sani ba Mimmee ya fad'a kamar zayyi kuka, kansa ta kuma shafa kana tace " ina kuka had'u? Bayanin komai yayi mata tun daga farkon had'uwar su har zuwa last had'uwar da sukayi, abu d'aya kawai ya b'oye mata, marin da Sanah tayi mishi, kai ta jinjina kana tace " babu wani abu da zaka iya tunawa akanta wanda zai baka damar gane ta? Shiru yayi na wani lokaci kana ya d'ago ya kalle ta cikin alamun karaya ya girgiza mata, yace " no Mimmee, tace " try please, ya k'ara shiru can yace " I can't, "try ta kuma fad'a tana shafa kansa, Mimmee ban iya tuna komai fa, ta kalle shi cike da tausayawa, tace " bakomai karka damu kaji Son idan har Allah yayi ita matarka ce babu makawa sai kun had'u, so karka d'aga hankalinka kaji, kansa ya d'aga mata cikin sanyin jiki, kana yayi mata sallama ya mik'e zai fita, har ya kai bakin k'ofa ya tuno ranar daya fara ganinsu,, da irin uniform d'in makarantar su Zohal ya gansu, da sauri ya dawo kusa da Mimmee yace " Mimmee na tuna wani abu, tace " meka tuna? "Ranar dana fara ganin su da irin school uniform d'in su Wajnah na gansu, " yauwa Mimmee tace, kana ta shiga kwalawa Zohal da Wajnah kira, da sauri suka fito daga bedroom d'insu, Mimmee ta kalle su tace " yayanku ke nemanku, suka mayar da kallansu kansa, ido ya zaro yana kallan Mimmee yace " ni kuma Mimmee? Mimmee tayi mishi alama da ido da yayi magana, kana ta kauda kanta gefe, ajiyar zuciya ya sauke had'i dayin gyaran murya yace " akwai wasu yara a school d'in ku, d'aya tafi d'aya fari, wacce tafi farin tafi jiki, sannan d'ayar doguwa ce sirirya, tafi d'ayar tsayi, d'ayar tana da dimples da wushiya, kun san su? Duk shiru sukayi suna tunnani, kana suka ce " gaskiya Yaya bamu gane su ba, kuma kai baka san sunan su ba? Shiru yayi yana tunanin, ya jima sosai yana tunanin kafin ya tuno sanda Khulud tacewa Sanah, "wai my Sanah meye haka ne, lokacin daya watsa mata ruwan kwata, tana yi mishi rashin kunya, a hankali yace " sunan d'ayar SANAH, da sauri suka zauna kusa dashi suna dariya, kana sukace " oh! Sanah Hamraz & Khulud Rawan kake nufi ashe, Mimmee dashi sukayi dariya, Mimmee tayi saurin cewa " yaya halayyar su take? Zohal tace " suna da kirki basu da wani munin hali, sai dai ita Sanah tana da tsiwa da bak'ar zuciya, sab'anin Khulud da babu ruwanta, nan suka kwashe halayyarsu suka fad'awa Mimmee, Mimmee taji dad'i sosai jin daga Sanah har Khulud basu da wani mugun hali na kyama wanda uwa zata hana d'ansu auren su, Wajnah tace " ai ranar nan gidan su mukaje walima ma, sune suka gayyace mu walimar, class d'in mu d'aya, Zohal tace " amma fa suna matuk'ar so da k'aunar junan su, dan tunda nake a duniya ban tab'a ganin wad'anda suke san junansu kamar su ba, wallahi idan d'aya bata san abu, to duk sanda d'ayar keyiwa abun ta hak'ura dashi, haka ma komai nasu iri d'aya ne, hatta reborn ko color basu canjawa, idan d'aya na kuka d'ayar ma sai tayi, nan suka kwashe irin so da muguwar shak'uwar dake tsakanin Sanah da Khulud suka fad'awa Mimmee da Hanash, har labarin abinda ya faru a Roni sai da suka basu labari, dan sun samu labarin komai, Mimmee ta jinjina kai tana mamakin irin wannan mugun son dake tsakanin su, Hanash yayi shiru dan yaga tabbas da idansa yaga zahiri,, amma duk da haka shi kansa sai da yayi mamakin son da suke yiwa junansu, Zohal tace " bari na d'auko waya ta na nuna maka pictures d'in mu dasu a wajen walimar, ta shiga bedroom d'insu ta d'auko wayar, mik'a mishi wayar tayi ya amsa hannunsa yana kerrma. Ido sosai ya k'urawa Khulud yana kallan yadda take murmushi da dariya, kayan da kwalliyar sunyi mata kyau sosai, kyanta ya fito, take yaji shi cikin matsananin farin ciki da walwalar daya dad'e bai tsinci kansa a ciki ba, amma yana d'ora idansa akan Sanah lokaci d'aya yaji mugun bak'in cikin ya saukar masa, ya nemi gaba d'aya walwalarsa ya rasa, danba k'aramar tsana yayiwa Sanah ba, yana jin tsanar ta har cikin ransa da zuciyarsa, sosai Hanash yake jin k'iyayyar Sanah a cikin jinin jikinsa da tsokarsa, tunowa da maganar su Wajnah yasa jikinsa yin sanyi yaji gabansa yayi muguwar fad'uwa, lura da yanayin daya shiga yasa Mimmee cewa su Zohal "ku mik'oman wayar nima naga pics d'in walimar ku shiga ciki, ba musu suka bata wayar, su kuma suka koma bedroom d'insu, Mimmee ta kalli pics d'insu, sosai taji tana matuk'ar k'aunar su gaba d'aya duk da bata san ainahin wacce Hanash yake san ba, ta kalle shi tace " waccece a ciki? Murmushi yayi kana ya mik'e ya koma kusa da ita, ya nuna mata Khulud, tace " wow! masha Allah she's so beautiful as so mush as I think bf, yayi murmushi, ta kalle shi tace " meye naga duk yanayinka ya canja, bayyi niyyar b'oye mata komai ba, dan haka yace " Mimmee wallahi kwata-kwata ban san sister nan tata, bata da kunya sosai, kinji ma su Zohal sun fad'a, murmushi tayi kana tace " eh kamar yadda naji sun fad'i rashin jinta haka naji sun fad'i so da k'aunar dake tsakanin su, dan haka muddin kana san Khulud dole ka b'oye k'iyayyar abinda tafi so a duniya, inba haka ba ka rasa ta, dole ka daure ka rink'a pretending na kana santa, murmushi ya kumayi kana yace " nagode Mimmee a ransa kuma yana tabbatarwa kansa muddin ya samu soyyayar Khulud har ya kai ga ya aure ta dole ne ya raba ta Sanah, dan bai ko k'aunar ganinta, kuma muddin ya bar Khulud tana mu'amula da Sanah yasan sai ta lalata ta, ta watsa mata tarbiyyarta. _Ni ko nace kuji man mutum da k'afin hali ka same su tare tsawon rayuwarsa kace zaka raba su, dacan bata lalata ko ta canja mata tarbiyyarta ta ba sai yanzu, tare fa gansu_ Mimmee tace " yaushe zaka je ka sanarta da ita? Dariya yayi yace " da wuri haka Mimmee? Tace " idan baka je yanzu ba sai yaushe zaka? "Kasan bahaushe yace " a bari ya huce shike kawo rabon wani, ka tabbatar yau ka shirya kaje ka sanar da ita, yayi dariya kana yace " in sha Allah yau zani wajen 4:30pm, "Allah ya taimaka ,Ubangiji ya kuma baka sa'a ya zama muku abinda yafi alkhairi a tsakaninku, ya amsa da " Amin, kana mik'e ya fita cike da farin ciki, barin ma daya tura duka pictures d'in a wayarsa, part d'in sa ya koma ya zauna a parlor yayi editing pics d'in, ya cire Sanah, duk inda ta fito ya yanke ta, yabar Khulud d'insa ita kad'ai, 4:00pm nayi ya tashi ya shiga wanka, ya shirya cikin shiga ta alfarma, kyansa da haibarsa suka fito, sai da ya biya yayiwa Mimmee sallama tayi masa addu'a sosai, kana ya fito, driven daya kai su Zohal gidan walimar yasa shi raka shi gidan, ya saka shi gaba yana binsa a baya har suka isa gida, kana ya sallame shi, shi kuma ya shiga get d'in gidan, get man ya aika akayi masa sallama da Khulud, tana zaune kusa da Mamu cike da cewar Sanarta, mai gadin yayi sallama a bakin k'ofa, Mamu ta amsa kana ta bashi izinin shigowa, bayan sun gaisa da Mamu kana yakai dubansa ga Khulud yace " manyan gobe ana sallama dake, ido Khulud zaro had'i da cewa " ni? Ya bata amsa da "eh ke yace, " kai badai ni ba, dan ban kowa ba, ka dai koma ka k'ara tamyarsa, yace " ke yace manyan gobe, zata kuma yin magana, Mamu tace " jeka ce tana zuwa, ya fita, kana ta mayar da kallanta ga Khulud tace" tashi kije, Khulud tace " Mamu ni fa ban san kowa ba, Mamu tace " ai da haka ake sanin kowan, tunda kikaga yazo gidan ku, ya kuma ambaci sunanki, ai ya sanki kenan, dan haka tashi kije, tayi shiru bata da alamar mik'ewa, Mamu ta daka mata tsawa tace " dan ubanki ba magana nake yi maki ba? Ta mik'e ta zari mayafi zata fita, Mamu tace " haka zaki fita baki gyara fuskarki ba bakiyi komai ba? "Dalla koma ciki ki canja kaya ki gyara fuskarki ki fesa turare, Khulud ta d'an turo baki kana ta nufi bedroom d'insu, shiru bata fito ba, Mamu ta d'aga murya tace " zaki fito ko sai nazo na iske ki a d'akin nan? Khulud ta fita, zata wuce Mamu tace " sakaran yara kawai, kince bazakiyi karatu ba, so kike mu tasaku gaba muna kallo bayan kun isa aure, har ita mai karatun idan ta samu miji aure zatayi, duk mu aurar daku mu huta fargaba da tsoran mu ya k'are, baku san duk mai 'ya mace cikekken bacci ma bai iya yi ba, da ido d'aya yake bacci, har sai ya kawar da ita ya huta kana, Khulud ta fita batare data ce komai ba. A gajiye lik'is su Sanah suka fito daga second to the last lectures d'in su, in badon lectures d'in Sir Moli ce next lactures d'insu ba, da dalibai da yawa zasu tafi gida, dan yadda suka gaji, ga yunwa ga yanayin garin da ya fara sauyawa, hadari ne daga k'asa ya fara shatawa sai iska dake dan busawa a hankali tana ratsa, illahirin bani adam dake wurin, sai d'aga kai students d'in suke yi, wasu suce "ruwafa za'ayi, wasu kuwa suce, hadarin zai fa watse, bakuji iska mai sanyi ke kadawa ba". haka dai suke ta hasashen su, gudun dai kar su taka k'aidar Sir Aryan (Sir Mili) shima ya tattakesu yasa dole, suke ,tsumayin lokacin zuwansa, A hankali Sanah, ta d'an ja tsaki, dan yunwar da taji tana k'wak'wularta, hannu tasa ta d'an dank'i cikin nata, gyara zamanta tayi akan kujerun SUG, dake a tsakiyar shuke-shuken dake zageye da department d'in nasu, shiru tayi dan ita kadai keta green, kasan cewar har yau batayi k'awaba, jin shirun ya mata yawa yasa ta zaro woyarta, ta fara lallatsawa, dan ta d'an d'ebe mata kewa kafin yazo, tana cikin danne-dannen taji, motsi a saman bishiyar ayaban da take zaune cikin inuwarsa, ido ta lumshe, dan k'amshi da wurin yakeyi gaba d'aya, sabida bananan da ke zagaye da wurin, gasu sunyi sutu-sutu, dai-dai ci, Amman ba damar tab'awa, kamar dai irin dokar dibinon dake cikin G,S,U duk d'alibin daya tab'a ya tab'owa kanshi C/O. da sauri ta d'ago kanta jin motsin yayi yawa sosai, ido ta zazzaro woje, dan ganin wasu k'attin k'adangaru, suna hard'e da juna suna fad'a, cizo juna sukeyi harda jini, a firgice ta mik'e ,dan tsoron karsu rikito a kanta, har ta juya zata tafi, sai kuma taji gyalenta ya sule ya fad'in cikin tsoron, ta sunkuyo da sauri ta d'auke mayafin, tana mik'ewa tare da yafawa a jikinta, tana gama mik'e tsawonta kenan, suka rikito kanta, wani irin tsalle tayi tare da k'am-k'ame jikinta, ta bud'e hannayenta duka buying, tuni ta cilla woyarta gefe, ihu ta saki da iya k'arfinta tare da furta, "innalillahi". k'ara ta kuma cillarawa jin d'aya k'adangaren yabi wuyan rigarta ya shiga jikinta, tuni yabi tsakiyar k'irjinta yana neman wurin b'uya a jikinta, dan d'ayan ya fishi k'arfi duk ya jikkatashi, shiko d'aya k'aton sai huci yake yana kumbura kai, ya shimfid'e a fuskarta, kanshi na k'atsan idonta, ganin haka ya k'ara firgi tata tare da gigicewa, cikin tsananin razane ta saki gigitacciyar k'ara, wanda yajo hankalin students d'in dake zaune wajen, gaba d'aya, sukayo kanta suka zagaye ta, suna zuwa kusa da ita kuma, sai suka fara ja baya-baya harda mazan, ganin abunda yake jikinta, dan ana iya hango, bindin wanda ke cikin rigarta d'inma a saman k'irjinta sai jujjuya bind'in yakeyi, tuni students suka fara tayata sowa, mata kam harda ihu, wasu har cewa suke "Wayyo Allah macizai nefa a jikinta, ku mazan ku taimaka mata mana, wayyo zasu sareta fa". su kuwa mazan da ake gani kamar sune jaruman sai cemata suke, "Kiyi tsalle zasu fad'i". suna fad'in hakan suna kuma k'ara matsawa baya-baya, duk sun cika wurin, sun kuma gaza taimaka mata, ita kuma, sai ihu takeyi da kururuwa da Andd'ar neman taimakon Allah. Tun daga parking lord, yake jiyo yadda wurin ya rud'e, a hankali ya bud'e motarshi ya fito, tare da d'aga kanshi sama yana hago yadda dalibanshi sukayi dandanzo sunata ife-ife, ga kuma sikiwritis d'in makarantar ke tsaya sunyi cirko-cirko, baki ya d'an tab'e dan a zatonsa maciji ne suka gani suka gaza kashewa, tsaki ya d'an ja tare da yin kansu yana tafiya cikin takunsa na isa da cikar haiba, hango dandanzon students d'in nashi yayi a waje d'aya sun zageye juna, Ita kuwa Sanah sosai take kukan fitar hankali tana ihuuu da tsalle, karaf idanta ya sauka akan na Sir Moli daya iso wurin yanzu a rud'e ta fara kwala masa kira tana kiran sunansa da iya k'arfinta da karaji, Sir Moli! Sir Moli!! Sir Moli!!! please kazo k'adangaru zasu kasheni, wayyo Allah na!, ganin yadda duk ta rud'e tana kuka yasa Sir Moli ya nufi inda take, students suna ta bud'a mishi hanya, tare da rusunawa suna gaidashi, Gabanta ya tsaya ya tsura mata ido ganin yadda taketa tsalle da ihu da kururuwa, fuska ya tsuke tare da kauda kanshi gefe, A hankali yasa ............ *-Am so sorry Fans, kunjini shiru kwana biyu, abubuwane suka dan min yawa, Amman in sha Allah yanzu zamuci gaba, har sai in watan Ramadan ya kama zamu ajiye kuma sai bayan Salla-* MOMYN ZARAH _*RASHIN SANI.......*_ *HAUWA A USMAN* _JIDDARH_ ```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh``` 2⃣1⃣ Tana fita harabar gidan ta hango Hanash tsaye, tsayawa tayi daga nesa kad'an yadda bazai ganta ba, tana mamakin abinda ya kawo shi gidan su, da yadda akayi ma har ya san gida, a fili tace " ko dai k'arar my Sanah kawo? Tayiwa kanta tambayar, da sauri ta k'arasa gare shi, tunda ya hango ta ya kafe ta da idansa, baya ko k'iftawa, d'an gutun murmushi ya sakar masa, ta mayar masa da martanin murmushin, cikin nutsuwa tace " ina wuni? " Lafiya Alhamdulillah, ya fad'a still idanshi yana kanta, ganin yadda ya k'ura mata ido, baiko blinking yasa ta yin k'asa da kanta, jin shirun yayi yawa yasa ta d'ago kanta, aiko karaf idanuwansu suka sark'e cikin na juna, tayi saurin mayar da kanta k'asa, murmushi yayi mai sauti kana yace " ina san kunyar nan taki, bata d'ago kanta ba, bare tace masa wani abu, "magana nake sanyi dake please, hope zaki ban dama? Kanta k'asa tace " ok muje ciki, gaba tayi yana binta a baya har suka k'arasa set room, d'akin da aka tanada dan bak'i, cikin sanyin murya tace " Bismillah ka zauna, cikin nutsuwa ya zauna a d'aya daga cikin kujerun, itama ta zauna, zai fara magana suka ji sallamar mai aiki, Khulud ta bata izinin shigowa, ta shigo d'auke da tray fal da drinks ta ajiye a gaban Hanash kana ta fita, zai kuma yin magana Khulud tace " kasha wani abun tukunna, ta fad'a tana tsugunnawa agaban tray d'in, rasa wanda zata bashi tayi dan haka tace " wanne zan baka? Tayi maganar kanta k'asa, murmushi yayi yace " any one, d'aukar d'aya daga cikin drinks d'in tayi ta mik'a masa, wajen amsar drinks d'in ya had'a da hannunta batare daya sani ba, daga shi har ita wani mugun shock suka ji, da sauri ta zame hannunta, shima yayi saurin sakin hannun nata da leman, cikin nutsuwa ta aje masa drink d'in a gefensa, kana ta koma ta zauna, d'aukar drink d'in yayi ya kurb'a kana ya ajeye a gefe, ya tattara dukkan nutsuwa da hankalinsa gare ta, cikin sanyin murya ya kira sunanta " Khulud! yana yin yadda ya kira sunan nata ne yasa ta kasa amsawa, a hankali ta d'ago kanta ta zuba masa idanta dan jin abinda zaice, d'an shiru yayi kana ya sauke numfashi ya soma magana, " kin san komai yin Allah ne, kuma Allah shike had'a mutum da mutum, kowa yasan farkon alak'a amma babu wanda ya isa yasan k'arshenta, kamar yadda kika fad'awa 'yar uwarki dukkanin mu bamu san zamu had'u ba, amma Allah da kuma k'addara ta had'a mu, d'an shiru yayi, ya kasa cigaba da magana, sai da ya sauke ajiyar zuciya kafin yace, tun ranar dana fara ganinki naji abu a raina game dake, amma sai ban damu ba, amma daga baya saina gane SO!!!ne, cikin wata irin murya mai wuyar fassarawa yace " I love you, ya fad'a cikin harshen turanci dan bai iya fad'a da Hausa. Da sauri Khulud ta d'ago kanta ta kalle shi, marairaice fuska yayi kamar zayyi kuka yace " please Khulud don't say no, murmushi Khulud tayi tana kallanshi, tace " ina ni ina amincewa wanda Sanah ta bata so, ta kuma fi tsana sama da komai, ban tab'a amincewa wanda baya shiri da My Sanah, duk namijin dakaga na amincewa kona aura to ka tabbatar da my Sanah ce ta zab'ar min shi a matsayin abokin rayuwa ta, duk sanda nakeyiwa abu muddin my Sanah bata sanshi nima ban sanshi, kamar yadda nasan bazan tab'a san abinda bata so ba har abada, zayyi magana tayi saurin d'aga masa hannu tace " kaje ka fara neman izinin yarda ta daga gare ta, kaje wajenta ka nemo soyayyata, muddin ta yarda ta kuma amince koda ban sanka nayi maka alk'awarin zan aure ka, wani irin abu Hanash yaji tun daga tafin k'afarsa har zuwa cikin kwakwalwarsa, k'ululun bak'in ciki ya takare masa zuciya da mak'ogwaransa, take ya kuma jin sabuwar tsanar Sanah ta dirarmasa a ransa, yaji ya tsane ta fiye da komai da kowa, yaji tunda yake a duniya bai tab'a tsanar wani abu kamar yadda ya ji ya tsane ta ba, leb'ensa na k'asa ya cija da k'arfe, had'i da runtse shu'uman idanuwansa, a ransa yake jin koda zai rasa Khulud, kuma koda ciwon santa da k'aunarta zai zama ajalinsa bazai tab'a neman alfarma a wajen Sanah ba, a hankali ya bud'e idansa da suka canja launi ya sauke su akanta, ya jima yana kallanta yana jin mugun so da k'aunarta na k'ara ratsa duk wani b'argo, jini da jijiya dake jikin sa, cikin sanyin murya yace " please Khulud wallahi ina iya mutuwa idan kika k'i amince man, murmushi tayi tace " maganin cutar zuciyarka da mutuwarka, yana hannunka, sai kayi maganin matsalarka da kanka, zayyi magana tayi saurin cewa " please zan shiga gida, my Sanah na hanyar dawowa ban san ta dawo ta iske ka, dan nasan ranta zayyi mugun b'aci, ni kuma duk abinda zan sanya ta cikin b'acin rai da damuwa ban san shi, kullum bani da burin daya wuce na ganta cikin farin ciki da walwala, tayi maganar tana mik'ewa, shima jiki a sanyaye ya mik'e yabi bayanta, sallama tayi masa kana ta koma cikin gida, bayanta yabi da kallo harta shige cikin gidan, cikin motarsa ya shiga cike da bak'in ciki da damuwa, har yayi hanyar gida ya tuna sak'on Papu daya aike shi BUK tun last week, na yaje kan maganar Admission d'insu Zohal, direct BUK ya nufa. Sir Moli yace " cire mayafinki ki yar, kanta ta girgirza masa alamar a'a, yace " idan baki cire mayafinki ba, na kan fuskar taki ma zai shige miki cikin rigarki fa, kallan taran jama'ar dake wajen tayi, taga gaba d'aya hankalinsu na kanta, kanta ta kuma girgiza masa cikin matsanancin kuka tace "ban iyawa, tsawa ya daka mata cikin fad'a yace " wai badake nake magana bane? "Dalla can cire mayafinki ki yar, cikin kuka tace " I can't, Sir Moli tsare ta da idansa yayi yana tunanin abinyi, " kiyi tsalle da k'arfi zai fad'i, ya fad'a while idanshi na kanta, ba musu Sanah ta buga tsalle da k'arfi, maimakon k'adangaren dake kan fuskarta ya fad'i k'asa sai ya shige cikin rigarta, Sanah naji ya shige cikin jikinta ta kuma sakin gigitacciyar k'ara, daga cikin jikinta taji k'adangaren yasa farcensa yana kartar fatar cikinta, tsalle ta farayi sosai tana kuka, gaba d'aya fuskarta tayi jajir,, hawaye da majina sun had'e sun yiwa fuskarta faca-faca, tsallan datake yi yasa k'adangaren yin k'asa yana neman hanyar shiga cikin siket d'inta, tana jin yana neman hangar guduwa, saboda shima a takure yake , farce ya saka yana kartar fatarta sosai, tsoran da yayiwa Sanah yawa ne yasa, numfashinta ya d'auke tayi luuuuuuu zata fad'i k'asa, cikin zafin nama Sir Moli yayi wuf ya tare ta, ta fad'a jikinsa a some, jikinsa na kerrma da tsuma, kansa ya kawar gefe had'i da runtse idanuwansa, kana ya d'aga rigarta kad'an ya zura hannunsa ciki, ya cire k'adangaren yayi jefa dashi, jijjigata ya shiga yi had'i da kiran sunanta, Sanah! Sanah!. Amma batako motsa ba, controlling kansa yayi ganin agaban students yake, dan haka ya had'e face ya sungume ta yayi office d'insa da ita, students suka bi bayansa da kallo cike da mugun mamakinsa, akan table d'in dake office d'insa ya kwantar da ita, da sauri ya nufi fridge d'in dake cikin office d'insa, ya d'auko robar faro, hannunsa na rawa ya b'alle murfin ya zuba mata ruwan,, ajiyar zuciya ta sauke da k'arfi, had'i da rirrik'e shi gam,tana cigaba da kuka, ganin har lokacin bata dawo hayyacinta ba, yasa shi cewa " ke dalla bud'e idanki, yayi maganar a dak'ile, jin muryarsa yasa ta saurin bud'e idanta, ta zuba su cikin nasa tana kallan cikin kwayar idansa, hannunta data rik'e shi yabi da kallo, tayi saurin sakin shi, baya ya ja ita kuma ta mik'e zaune had'i da sanya hannunta tana shafa cikinsa, jin wet yasa ta saurin ciro hannun ta kalli hannun, ganin jini yasata zaro idanta, jikinta na rawa ta d'aga rigar jikinta. Kuka ta saka ganin sosai k'adangaren ya karce mata cikin ta da faratansa, kallanta yayi yana mamakin yadda kuka bai mata wuya, d'an tab'a baki yayi kana ya nufi inda yake ajiye first aid box, ya d'auko, direct ya nufe inda take zaune tana kuka, " kwanta, yace a tak'aice, kallansa tayi cike da mamaki, taga ya kauda fuskarsa gefe, banza tayi dashi tayi kamar bata ji ba, ya kuma cewa " kwanta, " in kwanta kuma? Ta fad'a tana kallan fuskarshi, ganin ya had'e rai yadda kasan bai tab'a yin dariya ba, yasa ta kwanciya kamar yadda ya umarce ta, "d'aga rigar ce, yayi maganar yana bud'e box d'in, da sauri ta kalle shi, tace " kamar ya na d'aga riga ta mezakayi man? Bai kulata ba " ya kuma cewa " nace ki bud'e rigarki ko? Ya daka mata tsawa, mik'ewa tayi zaune, while idanta nakan shi, tsaki yayi "mtswwwww kana yasa hannunsa ya maida ita kwancen, ya d'aga rigarta d'an sama kad'an, kamar baya so ya fara yi mata dressing, yana cewa " banza kawai zan za'a taimaka miki uban me zan gani? "Kwaila dake har kina wani b'oye-b'oye, ko uban me zan gani ajikinki oho, yayi maganar cikin nutsuwa, Sanah zatayi magana taji an turo k'ofar an shigo, da sauri ta mik'e tana gyara rigarta, tsawaye cak Hanash yayi had'i da k'ura mata ido na tsayin lokaci, a ransa yace " wato wannan yarinyar bayan fitsara da rashin kunya, ashe ta had'a harda iskanci? Ya tambayi kansa, "haba ba mamaki shiyasa kwata-kwata bata jin tsoro ko kunyar uban kowa, ya fad'a cikin ransa, d'an kwallinta da mayafinta dake k'asa yabi da kallo, wanda itama sai lokacin ta lura dasu, tasan kuma kanta babu d'an kwali, hannun Sir Moli dake kan cikin Sanah yabi da kallo, da sauri Sanah ta lura da hannun tayi saurin ture hunnun nasa gefe, cikin sanyinsa Hanash yace " I'm sorry na katse muku hanzari ko? Bai jira abinda zasu ce ba, ya fita, Sanah ta runtse idanta da k'arfi had'i da dafe goshinta, Aryan ya kalle ta yace " kin san shine? "Eh tace, yace " waye shi? Ya kuma tambayarta idanshi na kanta, baki tad'an tab'e kana tace " ba wani saninsa fa nayi sosai ba, ta fad'a tana mik'ewa, mayafinta da d'an kwallinta ta d'auka, jingina yayi da table d'in, had'i da hard'e hannayensa a k'ijinsa, ya zuba mata ido, yace " d'azu sunanwa kika kira? Tana d'aura d'an kwalinta tace " Sir Moli, ta batare data kalle shi ba, yace " waye shi, meye alak'arki dashi da kike kiran sunanshi? Ido ta zaba masa tana mamakin tsantsar rainin wayonsa, kana ta tab'a baki tace " bani da alak'ar komai dashi, yace " kin san shi kenan? Ya fad'a idansa na kanta, "eh na sanahi wani mugun secondary school teacher d'in mu, kwata-kwata bai da tausayi da imani, ba ruwanshi da yarinta ko k'ank'antar shekarun yarinya, ta fad'a idanta tarrr cikin nashi, mamaki ne ya hana Sir Moli cewa komai, " lalle yarinyar nan bata da kunya da tsoro, ya fad'a cikin ransa, a fili kuma yace " amma duk da wannan mugayen halayen nashi meyasa baki kira sunan kowa ba sai nashi? " Bayan nasan kina da wad'anda suka fishi kusanci dake, kallan shi tayi na wani lokaci, kafin tayi rolling sexy eyes d'inta tace " hakan ya tab'a faruwa ne, bawai saboda mahimci ko kusancinsa dani bane yasa ni kiran sunansa, dan kwata-kwata bashi da wani kusanci ko alak'a dani, dan ni na maanta dashi da rayuwarsa, kawai dai naji sunansa yazo baki na ne, ido ya zuba mata na tsayin lokaci kana yace, "meyasa dance ki cire mayafinki kika k'i cirewa? Sai da ta yamutsa fuska kana tace " Wani Malamin mu ne ya bani shawara, still idanshi na kanta yace "Akan me? Ya kuma tambayarta, sai da ta juya idanta kana tace " yace na zama d'aya daga matan dako kashe su za'ayi basu tab'a bayyanar da tsiraicinsu ba, bazasu tab'a zubar da k'ima da mutuncin su ba, saboda yace man duk d'an Adam d'in, daya rasa k'ima da mutunci dashi da dabba duk d'aya suke, sassanyar ajiyar zuciya ya sauke yace "waya fad'a miki duk wannan? Air Moli ya fad'a yana kallanta, murmushi tayi kana tace " wannan mugun Malamin namu ne dai, murmushin takaici yayi kana yace " zaki iya tafiya, tayi masa murmushin rainin wayo kana ta fita, Sanah na fita taga garin da hadari sosai, sai iske akeyi mai k'arfi, ganin duk malamai da d'alibai nata tafiya gida, masu yin hostal nayi, yasa Sanah kiran Aarib a waya, tambayarshi yana ina tayi, ya amsa mata da yana office aiki yayi mishi yawa, idan sun gama lecture's ne tahau adaidaita sahu. Get ta nufa iska na neman kada ita, tana ta fama da mayafinta, shima ganin hadari yasa shi d'aukar brief case d'insa yayi hanyar fita daga office, ya d'ora hannunsa akan handle ya bud'e k'ofar, sukayi karo da Leem dake k'ok'arin shigowa cikin office d'in, fuska Sir Moli ya tsuke had'i da jan tsoki, yace " mtswwwww banza kawai ka wani shigo da k'arfi ka buge ni, " dalla kai baka canja halinka, koyaushe aka kanga rai a had'e kamar wanda akayiwa sammacin mutuwa, kullum kai fuskarka babu fara'a da murmushi, Leem ya fad'a yana dariya had'i da d'an dukan kafad'ar Aryan, Sir Moli ya d'an basar, Leem yace " to mu shiga mota mana, kabarni yayyafi yana dukana, murmushi Sir Moli yayi yace dalla matsoraci kawai, ashe dai har yanzu baka daina shegen tsoran nan naka ba, sai shegen tsoro kamar wata mace, ko uban me ruwan sama zayyi maka oho, " ba wani tsoro kaima ai kasan ban san ruwan sama zazzab'i da ciwon kai yake sani,, muddin na bari ya dake ni ko yayane, Leem yayi maganar suna shiga mota, Leem na cewa " dama yanzun nan nazo gunka fa, kwana da yawa bamu had'u ba, kayi wuyar gani, yau na shigo kano shine nace yau dai bari na shigo mu gaisa ko'a tsaitsaya ne, a gida ma nabar mota ta. Sir Moli na driving, Leem yace " kai dai ka nacewa kano, kwata-kwata kak'i zaman Maiduguri, wallahi kai dai banza ne, ko uban me kake samu a kanon oho, na rasa me ka gani a makarantar nan ka mak'alewa makaratar, ko dai 'yan matan makarantar ke d'auke maka hankali kake san kayi ta kallansu? Tsaki Sir Moli yayi had'i da tsuke fuska ya tab'e baki, " to meye abin kallo ajikin 'yan mata? " 'Yan matan har wasu ababen kallo ne? " Bayan duk yawancin su tatsitsan yara k'anane, duk kwalaye ne, ku mata suka dama suke kuma gabanku da har kuke maganarsu, Sir Moli yayi maganar kamar bayaso, cikin dariya Leem yace " ah lalle kam ba ababan gani bane, ai dama kai d'an banza ne, nasan dama baka tab'a d'aukar mace abar kallo ba, mu dai da Allah ya jarrabe mu da san mata ya kuma bamu lafiya sai muyi tayi, hankalin Sir Moli nakan tuk'in dayake yi yace " kamar ya ku da Allah ya bawa lafiya? " Eh mana, in ba mara lafiya ba ya za'ayi cikekken namiji kamar ka ya tsani mata har ya rink'a cewa shi baiga abin kallo ajikin mata ba, wallahi gwara kaje kaga likita tun kan kayi aure azo aji kunya, a d'an gak'ile Sir Moli yace " haka kake gani? "Sosai ma kuwa, dan ni na dad'e ina maka kallan mara cikekkiyar lafiya, dan Allah kaje kaga Doctor karkayi aure ka rink'a cutar 'yar mutane, murmushi Sir Moli yayi batare dayace komai ba, sai wasa sukeyi suna dariya, Sir Moli na gaf da fita get ya ganta sai sauri take yi, iska na neman d'aukarta, ido ya zuba mata tun daga nesa har suka zo zasu wuce, Leem nata magana yaji shiru, inda Aryan ke kallo yabi da kallo, Sanah ya gani sai faman sauri take yi, Leem yace " yanzu fa kace baka kallan mata, kuma a yanzun ka tsare wata da ido kamar tsohon maye, ko ita wannan ba mace bace, namiji ne? A tak'aice Sir Moli yace " wannan d'in har wata macece? Kallan Sanah Leem yayi cike tsantsar mamaki, yaga duk inda mace mai tak'ama da kyau da body takai Sanah ta wuce nan, dariya Leem yayi yace " au wannan ba mace bace namiji ne, yayi maganar cike da rainin hankali, Sir Moli yace " ni a waje na babu wani banbanci tsakanin mace da namiji duk d'aya nake d'aukarsu, dan ni ban jin wani emotions ko feelings, itama haka nake kallanta kamar namiji, kuma ina da yak'inin lafiya ta lau, Leem yace " shiyasa nace ai baka da lafiya wallahi, kaje kaga Doctor, guntun murmushi Sir Moli yayi kawai batare dayace komai ba, Leem yace " to yanzu dai ita wannan d'in wacece danaka ka k'ura mata ido kana ta kallanta? Sir Moli yayi dariya kana yace " she's my student tun daga Jss1, sosai Leem yayi mamaki kana yace " ikon Allah, kuma harka iya gane ta, abokina kodai ka kamu ne? Moli ya kuma yin dariya yace " kamuwa kuma? "Da wa d'in? " Lalle duniya ta lalace tunda aka fara kiran su Sanah mata, kuma wacce zan so, tab that's impossible, " to ya akayi baka mantata ba? Leem ya kuma tambayarshi, " she's very stubborn, bata da kunya, fitsararriya ce no 1, gata tsaurin ido da taurin zuciya, ko ka tab'a ganin an manta d'alibin marar jin magana? Dariya Leem yayi yace " ta shiga cases d'inka kenan? Moli yace " sosai ma, kana ya d'an bashi labarin Sanah in briefly, sosai Leem yayi dariya kana yace " please mu koma kayi mata lift, tunda abokiyar dramarka ce, ko ni ma Allah ya ci da ni ayi a gaba na, nima in gani in shaida dan ba mamaki sharri kake yi mata, batare daya kalli Leem ba yace " aiko indai wannan yarinyar ce tana iyayi a gabanka, dan fitsararta ta wuce da saninka, " naji yanzu dai mu koma kayi mata lift, " wa zan bawa lift d'in? Moli ya tambaya, " dalla ban sani ba, wa muke magana yanzu? " Dan Allah Malam ka tsaya ka rage mata hanya, Moli yayi kamar baiji abinda Leem me fad'a ba, "please mana abokina kaga macece ,, kuma ga hadari a garin gashi har an fara yayyafi, ba lalle ta samu abun hawan da zai kaita gida ba, saboda idan ana ruwa yawancin masu abin hawan haya basu yin aiki, still Sir Moli yayi banza da Leem, " please Aryan, Leem ya fad'a, a d'an fad'ace Sir Moli yace " kai banfa tsayawa d'aukar yarinyar nan, wai ina ma ruwanka da zaka damu da ita ne? "Ina ko ruwa na tare fa na ganku, Leem yayi tayi masa magiya amma Sir Moli yayi kamar bai jin shi, ganin haka yasa Leem jan hand break d'in motar, motar tayi wata irin k'ara k'uuuuuu, Sir Moli ya zaro ido yana kallan Leem yace " dan ubanka kashe mu kake sanyi? " Dan Allah ka koma ka taimake ta mana, tsaki Sir Moli yaja had'i da yiwa motar key, Leem ya kuma cewa " please mana, bayyiwa Leem magana ba ya juya kan motar dan yasan muddin yana san zaman lafiya dole ya koma ya d'auko ta, inko ba haka ba, yasan ya shiga uku wajen Leem, dan gaba sai saka shi yayi tayi masa naci da magiya, a gabanta yayi parking, d'an tsayawa tayi kasancewar motar tintak ce, bata ganin wanda ke ciki, baki ta murgud'a had'i da watsawa motar harara ta zakagaye zata wuce, Leem yayi dariya yace " lalle kam, kai kaga yadda take hararar mota, Moli yace " bakaga komai ba indai wannan yarinyar ce, shiru Sir Moli yayi had'i da kauda kansa gefe batare dayace komai ba, bai kulata ba saima uwar harara daya zuba mata, Leem yayi k'asa da glass d'in motar ta yadda Sanah zata iya ganin Sir Moli, kana yayi murmushi yace " k'anwata shigo mu kai ki gida, kaita girgiza masa tana murmushi tace " no nagode, Leem yace " ki shigo muyi miki lift kinga an fara ruwa fa, cikin sanyin murya tace " a'a ka barshi nagode, Leem zai kuma yin magana Sir Moli yayi sama da glass d'in motar, yana cewa Leem " d'an iska idan so kake ka bata lift kaje ka d'auki motarka ka d'auke ta kayi mata lift d'in, yana niyyar jan motar aka kece da ruwan sama mai k'arfi,, walk'iya akayi had'i tsawa mai k'arfi, da sauri ta bud'e motar batare datace komai ba ta shiga baya, tana haki jikinta sai kerrrma yake yi, tana addu'ar da bama tasan me take cewa ba, duk addu'ar data zo bakinta kawai take yi، dan Allah yayiwa Sanah mugun tsoran ruwan sama tun tana yarinya, Leem yaso yin dariya amma ba dama, sosai Sanah ta bawa Sir Moli dariya, amma saboda tsabar muskilancinsa sai ya tab'e baki had'i da kauda kansa gefe yayiwa motar key, Leem ya kalli Sanah yace " sannu naga kin tsorata sosai,, ashe manya irinku ma na tsoro? Murmushi kawai tayi masa batare datace komai ba, Leem ya maida hankalinsa ga Sir Moli yace " wai yaushe zakayi aure ne Aryan? Banza Sir Moli yayi masa, Leem ya kuma cewa " wallahi na matsu naga wacece matar da zaka aura, naga kalarta naga had'uwa da kyanta, shiru still Sir Moli yayi saboda Sanah dake cikin motar, " hmmm ashe wannan muskilancinsa nasa babu wanda baya yiwa, ta fad'a cikin ranta had'i da tab'e bakinta, duk abin takeyi idan Sir Moli na kanta ta cikin mirror, Leem yace " please kayi koda soyayya ne, a dak'ile Sir Moli yace " aini soyayya wahala da b'ata lokaci nake d'aukarta, kawai dan rashin abin yi sai na tsaya ina wani soyayya, ku ma gani kukayi zaku iya, dan haka sai kuyi ta fama, Leem yace " hmmm kasan me Aryan? Sir Moli yayi masa banza, Leem ya cigaba" a wani tak'i na rayuwar mutum dole zai fuskanci soyayya, nasan a yau ba lalle ka fahimci hakan ba, amma wata rana zaka fahimci bakai ne kake yanke shawarar fad'awa a soyayya ba, ita soyayyar ce take yanke lokacin faruwar hakan, " akwai lokaci, Sir Moli ya fad'a kamar baya so, Leem yayi dariya kana yace " to ai ita soyayya bakai ne kake yanke lokacin da zakayi ta ba, faruwa kawai take yi, Sir Moli ya kauda kansa gefe kana yace " to ai ni bana san ta faru dani, Sanah sake zaune bayan mota tana jin hirar su, ta tab'e baki cikin ranta tace " ka bata lokaci tabbas wata rana zata faru dakai, ko dan girman kanka da halin wulak'ancinka, nasan wata rana sai ka fad'a soyayya mai zafi, wacce zata wahalar dakai kamar yadda ka wahalar da wasu, cike da mamaki Leem ya juya ya kalleta, Sir Moli ko ta cikin mirror ya k'ura mata ido, sai a lokacin Sanah ta fuskanci a zahiri tayi maganarta, ba acikin ranta tayi ta ba, kuma ta fito fili sunji, ido ta zaro had'i dasa hannu ta rufe bakinta, cike da alamun tsoro,murmushi Sir Moli yayi batare daya ce mata komai ba, ya mayar da hankalinsa ga tuk'insa, Leem yace " yauwa k'anwa ta fad'a masa dai, batare da Sir Moli ya tambayi Sanah kwantacen gidansu ko unguwarsu ba, ya kaita har k'ofar gidansu, a bakin get yayi parking batare dayace mata komai ba, cikin matsanancin mamaki ta fito, ta kalli Leem tayi masa guntun murmushi tace masa " nagode, shima murmushin yayi mata yace " bakomai k'anwata, harta juya zata shiga gida ta juya ta kalle shi tace " ya akayi kasan gidan mu? Bai bata amsar tambayarta ba, ya ja motarsa yayi gaba, Sanah ta tab'e bakinta tace " Allah ya kyauta maka, kana tayi shigewarta gida, a parlor ta tarar da Khulud tana chart, Khulud na ganinta tayi cilli da wayar gefe, ta mik'e da sauri ta rungume ta, kasancewar a matuk'ar gajiye Sanah, take dawowa kullum yasa bata tab'a bawa Khulud labarin taga Sir Moli ba, bugu da k'ari kuma bata damu dashi ba, data bar makaranta take mantawa da Allah yayi ruwansa, bata sake tunawa dashi sai idan ta ganshi. Hanash na zaune Papu ya shigo parlor'n, da sauri Hanash ya durk'usa ya gaida Papu, Papu ya amsa cike da fara'a kana yace " Hanash kako je BUK wajen maganar Admission d'in Zohal? Hanash yayi shiru ya shiga tunanin yadda yaga Sanah kwance wani k'ato na yadda yaga dama da jikinta, ido ya runtse dan yayi masifar tsanar mace marar kamun kai, mai sakarwa namiji jikinta anyhow, Papu yace " yadai naga kayi shiru, baka je ba ko? Ya fad'a idanshi na kansa, murmushi yak'e Hanash yayi kana yace " naje, amma banga mutumin ba, Papu yace " kuma ka tabbata office d'in kaje? Hanash yace " eh, Papu yace " ka koma gobe, Hanash yace" tom Papu Allah yakai mu, Papu yayi murmushin jin dad'in biyayyar Hanash kana ya shafa kansa. Washe gari wajen 4:30pm na yamma, Sanah na zaune a cafeteria bayan sun fito daga lectures taje cin abinci, drinks & snacks taci kasancewar Sanah tafi san heavy food, a hankali ta bud'e hand bag d'inta ta d'auko table ta duba, ganin Sir Moli ne dasu 4:30pm yasata kallan agogon hannunta, ganin har 4:30pm d'in tayi ya sata mik'ewa da sauri had'i da cewa " oh! sheet!, anan tabar abincin datake ci ta nufi class, jikinta sai rawa da tsuma yake, dan kwata-kwata bata san shiga track d'insa, duk saurin da Sanah take dan kar Sir Moli ya rigata shiga class sai da ya rigada, hango yadda take sauri yayi, dakewa tayi ta saita kanta kana ta danna kanta ta shiga class d'in kai tsaye, batare daya kalli inda take ba yace " kneeling down ya fad'a tak'aice, idanta ta runtse dama tasan za'ayi hakan, dan tasan kamar kad'an yake jira akanta, a hankali tasa gwiwarta a k'asa tayi kamar yadda yace tayi, yana fitowa daga lectures yace " ki same ni office, yayi maganar batare daya kalli inda take ba, Mik'ewa tayi ta kakkab'e jikinta ta shiga class, tayi attending lectures. Wanka Hanash yayi ya shirya cikin manyan kaya, ya nufi BUK..... Office d'insa ta nufa, a hankali ta shiga bakinta d'auke da sallama, iskewa tayi baya nan, harta juya zata fita karaf idanta ya sauka akan talkami, agogo, da kuma rigarsa ta sama(cut) daya aje ya rataye a saman kujerar zamansa, dariya Sanah tayi had'i da nufar kayan tasa hannunta ta d'auka tace " rayuwa kenan, komai na duniya yana da lokacinsa, babu wani abu dayake da da tabbas a rayuwa, Allah karka kawo abinda bazai wuce ba, d'an lek'awa tayi ta window taga bai taho ta, dariya ta kuma yi kana ta nufi inda kayan ke aje a hankali sad'af- sad'af ta nufi inda ta hango hularsa dake aje a gefe, da alama ba ranar ya shigo da ita ba, dan yau cut ya saka a jikinsa, ta d'auki hularsa ta saka a kanta d'an kwalinta ya zame ya fad'i k'asa, kwantaccen gashin kanta bak'i ya zuba har gadan bayanta, tace " ah wannan fa ya shanye k'aton kansa, yanzu kansa ya k'ank'ance, hannunta takai ta d'auki cut d'insa ta saka a saman kayan jikinta, taga tayi mata zulum har kusan gwiwarta, tace " kai yaron nan ya k'ara girma da tsawo ashe, cire takalmin k'afarta tayi ta zura nashi, tace " to mazurmi kenan, dama shi fa akwai k'afa, k'afar nan dai tana nan har yau yadda take ada, ita bata k'aru ba bata kuma ragu ba, ta saka agogon a hannunta, tana dariya sosai, show glass d'in dayake aje perfume's & book ta nufa, ta tsaya a gabanta had'i da sanya hannunta a hab'arta tana kallan yadda show glass d'in ke shak'e da turarurruka kala-kala, kowanne turare da akwai lokacin saka shi, dan taga an rubuta ranar sanya kowanne a jikin turarurrukan, Friday to Thursday & na safe daban ya rana daban na yamma daban, k'ara kallan turin littatafansa tayi tana mamaki, tace " eh! yaran nan hancinsa kam yasan k'amshi, bud'ewa tayi a hankali ta shiga fesa kowanne turare a jikinta, sosai Sanah tayiwa jikinta b'arin turarurrukan Aryan, tayi masa b'arnar Perfume's sosai, gaba d'aya office d'in ya gauraye da k'anshin perfumes yadda kasan company had'a turaren, k'amshin turarurrukan ya had'u da sanyin Ac ya bada wani irin yanayi mai wuyar fad'a. K'afarta ta d'aya ta d'ora akan set d'in zamansa, ta kwaikwayi maganarsa tace " kneeling down, ta fad'a tana dariya, juwayar da zatayi ta ganshi tsaye ya fito daga bathroom, ya zuba mata rikitattun idanuwansa masu kamar yana jin bacci, hannunta ta saka ta rufe bakinta............ MOMYN ZARAH _*RASHIN SANI.......*_ *HAUWA A USMAN* _JIDDARH_ ```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh``` 2⃣2⃣ Hannunta ta saka ta rufe bakinta, had'i da zaro sexy eyes d'inta waje, a hankali cikin takunsa na cikakkun maza ya fara takowa gareta, cikin tsoro Sanah ta fara ja baya tana yarfe hannu, yana biyo ta ita kuma tana cigaba da yin baya har suka isa bango, hannayensa ya saka ya dafe bango, ya saka ta a tsakiyar hannayensa, gaban rigarsa inda ya b'alle bottles d'in jikin rigar kyakkyawan k'irjinsa mai d'auke da yalwataccen kwantaccen gashi, ta kalla, take taji gabanta yayi muguwar fad'uwa da k'arfi, da sauri ta runtse idanta yayinda da k'irjinta keyin sama da k'asa da sauri-sauri, lulu eyes d'insa ya zuba mata yana kallan yadda k'irjinta ke bugawa yana up an down da sauri, yanayin k'amshin da sanyin Ac dake office d'inne suka saukar masa da wani irin yanayi a gaba d'aya ilahirin jikinsa, yaji kasala ta saukarwa duk wata gaba ta jikinsa, abinka kuma da yanayin damuna, k'ara matseta yayi sosai a jikin bangon, ta yadda k'irjinsu na gogar na juna, da sauri Sanah ta bud'e idanta, ta zuba cikin nashi, ganin yadda lokaci d'aya gaba d'aya yanayinsa da kuma kamanninsa suka canja yasa zuciyarta ta shiga bugawa, dayake ya fita tsayi yasa idan zata kalle shi sai dai ta d'aga idanta sama, kanta na k'asa, idanta kawai ta d'aga tana kallanshi, cikin wata irin kasalalliyar murya Sir Moli yace " kin tuna? D'an kawar da kanta tayi gefe, muryarta can k'asa tace " me? Yace " alk'awarin da kikayiwa wannan mugun secondary teacher d'in naku, muryarta na rawa tace " na manta, "Ok bari na tuna miki, ya fad'a yana k'ara shegewa jikinta, " please kaban last chance, idan na kuma yin laifi kayi man koma meye, wallahi I promise ban k'ara yi maka laifi, Allah idan na kuma kayi man komai kaga dama na yarda na d'auka, duk abinda kaga damanyi kayi man, ya fad'a bakinsa saitin kunnenta, had'i da hura mata iskar cikin bakinsa a kunnenta, kana yace " kin tuna yanzu? Idanta na kansa ta d'aga masa kanta, muryarsa can k'asan mak'ogwaro yace " kin san ban san d'aga kai ko? Bakinta na rawa tace " eh!, yace " good, muryarsa bata fitowa sosai yace " shi kuma a lokacin mai yace miki? Ya fad'a yana shinshinar wuyanta, had'i da goga hancinsa a wuyanta, kamar zatayi kuka saboda yadda duk yabi ya shege mata jiki, tace " keep it in your mind, I know one day you will pay for your promised, "good yace , yana goga hancinsa a wuyanta, " kince duk abinda naga dama nayi miki ko? Ya fad'a muryarsa bata fita sosai, "dan Allah kayi hak'uri Allah ban k'arawa, yadda take maganar yasa shi k'urawa cutie lips d'inta ido, still hannayensa na jikin bongon, ita kuma tana tsakiyar hannayensa, ya sanya fuskarsa a wuyanta yana goga mata, kana a hankali ya fara goga mata fuskarsa akan tata fuskar, sajensa yana gogar kumatunta, k'irjinta na gogar na shi, yadda k'irjinta ke yin sama da k'asa ya fara sa Aryan yin loosing control, itako Sanah tsaron yanayin data ganshi ciki ne ya hanata yin koda kwakkwaran motsi, idanshi na kanta yana karantar yanayin data shiga, yasa hannu ya zame hularsa dake kanta, ya cusa hunnunsa cikin gashin kanta, bakinsa yakai cikin kunnenta ya rad'a mata, kin shirya karb'ar punishment d'inki yanzu? Ya fad'a muryarsa na creaking, " kayi hak'uri tace , kuka na neman kwace mata, yadda tayi maganar tana turo bakinta, yasa Sir Moli had'e bakinsu waje d'aya batare daya sani ba, ido Sanah ta zaro waje cike da tsoro jin abinda Sir Moli keyi mata, gaba d'aya jikinsu ya d'auki rawa da tsuma, kasancewar jin su a cikin wani irin yanayi da basu tab'a tsintar kansu ciki ba, duk ilahirin jikinsu kerrrrrma yake, musamman Sanah, da har hawaye ya fara zubowa daga idanuwanta, a hankali ya zagayo da hannunsa ya tallafe kanta yadda zaiji dad'in shan bakinta sosai, had'i da cusa hannunsa cikin gashin kanta, yana ya mutsuwa, still bakinsa na cikin nata, d'aya hannun yakai yana shafa duk ilahirin jikinta, hannu Sanah ta sanya a k'irjinsa tana k'ok'arin ture shi, a hankali hannunta ya shege cikin rigarsa inda yake ya bud'e, Sir Moli yana jin tattausan hannunta akan fatar k'irjinsa ya k'ara fita saga hayyacinsa, jikinsa na kerrrma ya fara k'ok'arin neman zip d'in rigarta. Hanash dake ta faman knocking a bakin k'ofar amma ba'a amsa ba, ya d'an ja tsoki kana ya juya a hankali zai tafi, bakinshi cikin nata tace " uhmm innnn amma ba damar yin magana, saboda da gaske yake tsotsar bakin nata, Hanash dake waje jin ance innnnn, sai ya zata cewa akayi ya shigo dan haka ya danna kai cikin office d'in kai tsaye, tsawa yayi cak ganin yanayin da suke ciki, bakin Hanash na rawa yace " innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, ya fad'a batare daya sani ba, jin maganar Hanash ya sanya Sir Moli dawowa cikin hayyacinsa, a matuk'ar kid'ime ya saki Sanah yayi baya, cike da tsoro da kuma tsantsar mamaki Sir Moli yake bin Sanah da wani irin kallo, yana tambayar kansa me yayi mata, ido Hanash ya k'ura musu na tsayin lokaci, yana kallan Sanah sanye da kayan Aryan a jikinta, a hankali yabi cut da agogo da takalmin k'arfarta da kallo, ya kuma kalli yadda gashin kanta ya barbaje, kana ya mayar da kallansa ga Aryan dake dafe da kansa kwalla na neman gangarowa daga idansa, yaga gaba d'aya jan bakin Sanah ya dame masa fuskarsa, murmushin bak'in ciki Hanash yayi kana ya juya ya fita batare dayace musu komai, durk'ushewa Sanah tayi had'i da fashewa da wani irin rikitaccen kuka, kansa ya dafe dake barazanar tarwatsewa had'i da zuba mata idanuwansa da suka koma pure red color,, muryarsa na rawa Sir Moli yace " me nayi? " Meke shirin faruwa dani ne? Yayi maganar idansa na kanta, yana kallan yadda take ta faman kuka, sai da taci kukanta ta k'oshi kana ta mik'e cikin sanyin jiki, ta cire agogonsa ta d'ora masa akan table, kana ta durk'usa ta d'auki hularsa dake yade a k'asa itama ta d'ora masa akan table, ta cire takalmin ta aje a gefe, kana ta d'auki d'an kwalinta ta d'aura, ta yafa mayafinta, ta saita kanta sosai kana ta fita, duk abinda take yi idansa na kanta, tana fita ya naushi bango da k'arfi, "oh! sheet! ya akayi nayi loosing control? " Na aikata abinda ban tab'a yi ba, zama yayi akan sofa dake cikin office d'insa yayi tagumi hannu bibbiyu yana san ya tuna abinda ya faru yanzu, tana fita ta nufi get, ko ta kan lectures bata bi ba, tafe take kawai batare data san inda take jefa k'afarta ba, gaba d'aya hankalinta baya tare da ita, ta fad'a duniyar tunnani, a fili tace " shin da gaske ne abinda ya faru dani yanzu koko mafarki nake yi? "Da gaske Sir Moli ne yayi abinda yayi man yanzu? " Ashe dama d'an iska ne, mazinaci, fasik'i? " Allah kad'ai yasan yawan matan dayayiwa abinda yayi man yanzu, tana fita bakin get ta samu mai adai-dai sahu, babu b'ata lokaci ta shiga ya kaita gida, a harabar gidan ta iske Aarib yana k'ok'arin shiga mota, yana hangota ya fasa ya tsaya yana jiran ta k'araso idanshi kanta yana yi mata murmushi, "meyasa baki kira ni nazo na d'aukeki ba? Ya tambaye ta, kwata-kwata hankalin Sanah baya jikinta, dan bama ta lura da wani Aarib ba, kallanta yayi cike da mamaki kana yace " Sanah!, amma shiru bata amsa masa ba, tafiya kawai take yi, direct part d'in Halan ta nufa, Aarib yabi bayanta da kallo, har yayi yunk'urin binta sai kuma ya fasa, ya shiga mota yayi waje, parlor ta shiga ta zauna akan sofa had'i da runtse idanta da k'arfi, Halan na durk'ushe ciwon nak'uda ya dameta, ji take kamar zata mutu, dakyar ta kira sunan Sanah, amma shiru bata amsa ba, cikin muryarta da bata fita sosai ta kuma cewa " Sanah!, amma shiru bata amsa ba, dakyar Halan ta rarrafo tazo inda take tasa hannu ta tab'a ta, firgigit Sanah tayi ta farka daga hang d'in da brain d'inta tayi, ajiyar zuciya ta sauk'e da k'arfi kana ta kalli Halan dake ta faman cije baki tace " Aunty lafiya dai ko? Dakyar Halan tace " kira yayanku, Sanah najin muryarta tasan tana cikin mawuyacin hali, da sauri ta mik'e jikinta ta kerrrma, tayi kan Halan tana dialing number Ziyad, sai da ta kusa yin cutting kana yayi picking, bata jira taji abinda zaice ba tace " Yaya kazo gida yanzu Aunty Halan ba lafiya, a kid'ime ya mik'e yana cewa gani nan, wayar Khulud tayi dialing tana yin picking tace " ki zo part d'in Aunty Halan, ina nan bata da lafiya, da sauri Khulud ta mik'e tana cewa Mamu " Aunty Halan ba lafiya inaga haihuwa ce, Mamu ta mik'e itama tace " Allah ya raba lafiya ki biya ki sanar da Juju, kasancewar mutanen da akwai kara, ita Mamu bata iya binsu hospital saboda ita ta haifi Ziyad, dole zatayi kara, Khulud na fad'awa Juju ta mik'e da sauri ta zari hijab sukayi part d'in Halan, suna shiga Ziyad na shigowa bai wani ji kunyar Juju ba ya sab'i Halan yayi cikin mota da ita, yana cewa " Khulud d'auko akwatin kayan haihuwa, da sauri ta nufi d'akin ta d'auko, Family Hospital d'in su ya kaita suna isa aka karb'eta aka shigar da ita labour room, Sanah da Khulud suka yi cirko-cirko, Juju da Ziyad na gefe. A hankali ya mik'e ya sanya agogonsa da cut, kana ya zira takalminsa ya zari brief case d'insa ya fita, kasancewar yau Friday yasa Aryan nufar masallacin juma direct, ana idar da sallah ya koma mota ya zauna, dayake a yanayin damuna ne yana zaune cikin mota yaji an fara yayyafi, ji yayi gaba d'aya hankalinsa yayi gida Maiduguri, dama ya kai wajen 4 weeks baije weekend ba, a hankali ya d'ago hannunsa ya kalli agogo yaga 1:30pm na rana, ido ya lumshe yana jin sha'awar yin long journey a mota, ya san kuma muddin Hilwa yasani bai barinsa ya tuk'o mota tun daga Kano har Maiduguri, cewa zayyi dole sai yabi jirgi ko a aiko masa da Army Jet a d'auke shi, kuma a ransa bai wani san tafiya a jirgi sosai, musamman ma idan anan gidan Nigeria ne, baya kuma san driver yafi san yayi tuk'i da kansa, dan haka ya yanke shawarar tafiya kawai batare daya sanar da kowa ba, sai dai yayi musu zuwan bazata, a hankali yayiwa motar key ya d'auki hanyar Barno, ya sakarwa motar wuta, dan Aryan akwai gudu da mota. Halan takai 3hrs tana labour kana ta haifo yaronta, mai kyau, nurse ta fito d'auke da baby Sanah tayi saurin amsar Baby tana murna, Khulud ta kalli nurse d'in tace " ya Maman Babyn? Nurse tayi murmushi kana tace " tana lafiya, ai kaita d'akin hutu tana bacci, nan da d'an wani lokaci zaku ganta, a ranar da dare aka sallami su Halan kasancewar ta haihuwa lafiya babu wata matsala, suka koma gida cikin murna da farin ciki. Hanash na fita daga office d'in Sir Moli ya shiga mota, ya kai wajen 10 minutes yana tunanin da bai san kona meye bane, ji yayi ya k'ara jin tsanarta fiye da koyaushe a rayuwarsa, tsoki yaja kana jiki a sanyaye yayiwa motar key yayi gida, a parlor ya iske Mimmee zaune tana cin kwad'an Salad, kusa da ita ya zauna, jikinsa duk ba dad'i, kallo d'aya tayi masa tasan akwai abinda ke cikin ransa, kallansa tayi tace " Son meke damunka? Murmushi yayi kana yace " bakomai Mimmee, d'an shiru tayi had'i da zuba masa ido kana tace " kamar ya bakomai? Shiru yayi baice mata komai ba, dan shi kansa bai san meke damunsa ba, " ya kukayi da Khulud d'in? Ajiyar zuciya ya sauke kana ya sanar da ita duk yadda sukayi, bai b'oye mata komai ba, shiru tayi na wani lokaci kana tace " kayi hak'uri, in sha Allah I will pray for you kaji, zan nemar maka zab'in Allah, a sanyaye ya d'aga mata kansa, tace " karka karaya kaji Son, ka cigaba da zuwa, haba kai kamar ba namiji ba, kai fa cikekken namiji ne, kayi amfani da basirarka da kuma wayonka, ka sanya mata sanka, "how!? yace, " ban sani ba Mimmee ta fad'a a d'an hasale, tana ture shi, murmushi yayi kana yace " I promise you Mimmee I will try my best, tayi murmushi kana tace masa good Son. Aryan na shiga garin Maiduguri aka tsuge da ruwan sama kamar da bakin kwarya, wani mahaukacin katafaren gida, wanda tun daga waje naga sojoji sunfi a k'irga suna kaikawo, automatic get d'in naga ya bud'e kansa, bayan yayi snapping number motar Sir Moli, gaba d'aya habarar gidan babu komai sai dandazon sojoji dake kai kawo, gidan yana da haukacin girma, dan da gani filin da akayi gidan 300 by 300 ne, gaba d'aya gidan zagaye yake da shukoki iri-iri, a harabar gidan yayi parking batare daya fita ba ya kishingid'a, Yara na gani a k'alla sun kai 7 suna wasa da ruwan sama a cikin farfajiyar gidan, yayinda na hangi wasu yaran rakub'e cikin baranda, da alama suma suna san yin wasan ruwa, tsoro ne ya hana su, d'aya daga cikin yaran dake tsaye a cikin baranda yace " Yaya kun fa san Uncle Aryan ya hana mu wasa a cikin ruwa ko? D'ayan yace " kai zaka fad'a masa munyi wasan ruwan? D'aya yaron yace " a'a amma kasan fa yace " idan mukayi zai gani, kuma yace duk abinda muke yi yana ganin mu, a duk inda yake, d'ayan yace ba wani nan wayo yake yi mana, kazo muyi ai babu wanda zai fad'a masa, d'ayan yace " a'a ni banyi ni dai tsoro nake ji, d'ayan zayyi magana Sir Moli ya bud'e mota ya fito, gaba d'aya jikin yaran ya d'auki kerrrma da tsuma, suka shiga rige-rigen guduwa, wasu na take wasu, yadda kasan sunga dodo ko aljani, wad'anda ke kan barandar suna ganin shi suka fito da gudu, suka nufe shi suna cewa " ga Uncle Aryan ga Uncle Aryan, oyoyo Uncle Aryan, yaran naga ya kalla farare tass dasu, masu kama da yaran turawa, suna sanye da kaya na alfarma da gani kasan masu tsada ne, murmushi yayi musu kana sunkuyo dai-dai tsayin su, da gudu suka fad'a jikinsa, d'ayan yaron ya zagayo ta bayansa ya sak'alo wuyansa, ya d'auki cutie Baby's d'in a hannunsa, yayi hanyar part d'in Hilwa ya, kasancewar yau ana suna a gidan yasan part d'in Nainah akwai mutane, matar Yayanshi Haidar ta ce haihu, yau ake suna, a parlor'n Hilwa ya iske babban Yayanshi da auta Jabeer, zaune suna hira, Hilwa na ganinsa yayi saurin mik'ewa zaune daga kishingid'en dayake, ya mik'e masa hannu alamar yazo, yana dariya yadda kasan anyi masa bushara da aljanna, annurin fuskarsa ya fad'ad'a ganin Sir Moli, shima yana murmushi ya nufi mahaifin nasa mai tsananin so da k'aunarsa fiye da duk 'ya'yan daya haifa, kwata-kwata Hilwa da Nainah basu iya b'oye tsananin son da suke yi Aryan a cikin yaransu, yadda kasan shi kad'ai suka haifa a duniya, kusa da Hilwa Aryan ya zauna yana fad'ad'a murmushinsa, Hilwa ya shafa kansa yace " Soul shine kazo bako announcement, dariya Sir Moli yayi yace " nasan baka bari na nayi driving ne, ido Hilwa ya zaro yace " kai ka tuk'o motar tun daga Kano har Maiduguri? Aryan yayi dariya yace " eh Love, Hilwa yace " Moli (dayake haka yake kiransa wani lokacin saboda tsananin kamar dayake da shi, shiyasa yake ganin kamar shine magajinsa), "please ka daina wasa da rayuwarka kasan bazan iya jure rashinka ba ko? Murmushi Haidar yayi kana yace " Hilwa ka hana mu gaisawa da d'an uwanmu ma, Aryan yayi dariya yace " Big Bro ina wuni? " Lafiya lau,yace yana dariya, kana yace " ya aiki? Sir Moli yace " aiki Alhamdulillah, babban d'an Haidar ya shigo wanda zayyi sa'an Jabeer, tare Jabeer da Noor suka gaida Sir Moli, ya amsa fuska a sake, hira sosai Hilwa da Aliyu & Aryan suka shiga, yaran da suka tsorata sukayi cikin gida, gidan suka shiga da suna cewa " Nainah, Ummi Uncle Aryan ya dawo, "Uncle Moli ya zo (duk gidan suna kiransa da Moli) Nainah tayi murmushi tace " zakin d'ana ya dawo, dama indai na ganku kun shigo a firgice nasan shine, manyan Yayyansa mata duk suka mik'e suna tambayar " ina yake! ina yake!? Aunty Kubra ta d'auki wayarta tayi dialing number sa, wayar na fara ringing Sir Moli ya kalli wayar, kana yayi murmushi, Hilwa da Haidar suka kai dubansu ga wayar, Hilwa yace " hala har an kai musu labarin zuwanka, murmushi ya kuma yi kana yayi picking wayar, Aunty Kubrah tace " yanzu Mudah suka sanar mana ka zo, kuma har yanzu bamu ganka ba, "dariya yayi yace " ina part d'in Hilwa ni da Yaya, "au ashe ko da gaske suke? " Sannu kasha hanya bari yanzu na dawo maka ruwa, "nagode yace had'i da yin dropping wayar, gaba d'aya gida aka shiga munar dawowarsa saboda tsananin so da k'aunar da suke yi masa, abinci Aunty Nina da Aunty Kubra suka shirya masa kala-kala, Nainah, da Aunty Ayyam suka nufi part d'in Hilwa, Jiya ta shigo da gudu a gabansa ta tsaya tana hakki tace " Uncle Aryan ina alk'awarin mu? Jabeer yace " wallahi nima shi nake jira tun d'azu, Sir Moli ya tsuke fuska had'i da cewa " bako gaisuwa, balle ya hanya kinzo kin tsare kina tambayata alk'awarinki kamar wacce taban ajiya, baki ta tab'a ta fara diddira k'afarta, cike da shagwab'a tasan yin kuka, tsawa ya daka mata had'i da cewa " karki soma dan ubanki, sanin halinsa yasa jiya had'iye kukanta, ta fad'a jikinsa tana dariya tace " I'm sorry Uncle, ina wuni? "Alhamdulillah, ya amsa yana d'agata sama, dai-dai lokacin Nainah, Aunty Kubra, Aunty Nina da Aunty Ayyam, suka shigo, gaba d'ayansu suka zauna kusa da shi, suka zagaye shi suka sanya shi tsakiya, Nainah ta jawo shi jikinta ta rungume tana shafa kansa tace " Life kasha hanya, sannu Life, Hilwa yace " kuma a mota yazo shine ma yayi driving, Nainah ta zaro ido, tace " Life meyasa? Kansa ya k'ara kwantarwa a jikinta, yace " sorry Nainah ban k'arawa, tayi dariya tana d'ago shi tace " tashi kaci abinci, nasan halinka da rashin san cin abinci, mik'ewa yayi zaune yace " ai dole naci abincin gidan Nainah da Hilwa na yau dan nayi missing d'inshi sosai, Aunty Ayyam ta jawo tray d'in abinci, ta fara zuba masa, Aunty Nina na zuba masa drink a glass cup, Haidar yace " uhmmm kaga d'an gatan Aunty's d'insa da Nainah, ni dayake yau matana suna can wajen hidimar suna babu wanda ya kula dani ai, aka barni da yunwa, Nainah na ta hidimar da Hilwanta, ni kun manta da ni, ashe rabon naci da Brother na ne, ya fad'a yana dariya, had'i da matsowa suka fara cin abincin tare, Hilwa dayake soja ne bai san yaji, abincin shima daban ake girka masa yace " ni ban iya ci da ku, Jabeer da Jiya suka zauna kusa dashi a hankali suka ce " Uncle! ya juya ya kalle su yace " meye kuma? "Alk'awarin na mu, kansa ya dafe had'i da cewa " oh my God, Haidar yace " wai alk'awarin me kayi musu ne? Aryan yace " Jiya laptop take so, Jabeer kuma iPhone X yake so, Hilwa yace " meyasa baku fad'a man na siya muku ba zaku damar man yaro? Aryan yace " ai nama siyo musu suna mota, Jiya da Jabeer suka shiga tsalle suna murna jin an siyo musu, Jabeer yace " Yaya suna ina? Sir Moli yace " suna mota, ungo key d'in ku d'auko ku barni na huta, har ya basu key d'in ya tuna ana ruwan sama, da sauri yace " yanzu ana ruwa ku bari sai an d'auke ruwan sannan, ya fad'a yana amsar key d'in, suna hira cikin so da k'auna, sai da suka gama kana Sir Moli ya nufi part d'insa, wanka yayi jikinsa duk a sanyaye, ya rasa meke damunsa a duniya, abinda yayiwa Sanah ya tsaya masa a ransa, shi kunyarta ma yake ji, ji yake kamar bazai iya sake had'a ido da ita ba, shi tsoransa d'aya ma karta d'aukeshi d'an iska tayi tunanin ko haka yake yiwa wasu matan, wanka yayi ya shirya ya fita ya zagaya baya, gani nayi ya b'ullo bakin swimming pool, mai kyau da kayan k'awa, gadon dake gaban swimming d'in ya hau ya kishingid'a, wata 'yar kwararrawa ya danna naga wasu sojoji sun fito sanye da uniform iri d'aya a jikinsa, batare daya d'aga kansa ba yace " a bani abu mai sanyi, kai suka risina cikin girmamawa kana suka juya, basu jima ba suka dawo d'auke da drinks kala-kala, ya kai good 1hr anan kana ya mik'e ya nufi gym, wata k'ararrawar ya danna sojoji suka fito, a tak'aice yace " green tea, sosai ya motsa jikinsa kana ya fita ya koma garden mai d'auke da flowers masu k'amshi da kyau, ga tsuntsaye kala-kala suna kukan su mai dad'in sauraro, tsayawa fad'ar had'uwar gidan Moli's b'ata lokaci ne, saboda an kashe kud'i kamar ba gobe wajen tsara gidan, duk wani abu na more rayuwar duniya akwai shi a cikin gidan, abun da yafi ban mamaki shine, duk wani ma'aikaci dake gidan soja ne, dai-dai da masu aiki da wanki da guga duk they're sojan. Aryan na kwance a bedroom d'insa, Nainah ta shigo d'auke da fruits salad, sallama tayi a k'alla takai sau uku, amma Sir Moli baiji ba, a hankali ta ajeye tray d'in akan glass, kana ta zauna kusa da shi, hannun tasa ta kwantar da kansa akan cinyarta, tana shafa kansa, ajiyar zuciya ya sauke a hankali, Nainah ta kira sunansa " Aryan! a hankali ya amsa " na'am, tace " meke damunka? Tunda na d'ora idona akanka kasan kana cikin damuwa, shiru yayi baice komai ba, Nainah ta k'ara cewa " meke damunka Aryan? "Bakomai heartbeat, ya amsa mata, " ya zakace bakomai bayan ga damuwar nan k'arara ta bayyana a tattare dakai, murmushi yayi kana yace " nayi exercise da yawa na gaji ne, murmushi tayi ta k'ara shafa kansa duk da bata yarda da abinda yace ba, mik'ewa tayi a hankali ta d'auko fruits salad d'in ta shiga bashi a baki, bata barshi ba sai da ya shanye tass, dan tasan halin Aryan bai san cin abinci, kansa nakan cinyarta tana shafa masa har yayi bacci, a hankali ta mik'e ta d'auko Italian blanket ta rufe shi, tayi masa kiss a kumatu kana ta fita, sosai Moli's Family ke mugun so da tsananin k'aunar Aryan kamar ransu, kowa yana nan-nan dashi kamar k'aramin yaron goye. Washe gari da safe wajen k'arfe 11:30am na safe, ya fito ya nufi part d'in Nainah, dayake yasan 'yan taran suna duk sun tafi, yasan babu sauran bare sai Moli's Family, har ya kusa shiga part d'in ya tuna da alk'awarin su Jabeer, komawa yayi ya d'auko sabuwar laptop da wayar duk a cikin kwalayen su, kana ya nufi part d'in, ganin ba kowa a parlor yasa shi nufar bedroom d'inta, a can ya iske ta zaune tsakiyar Aunty's d'insa, ana ta hira, Aunty Nina da Aunty Kubra na kan gado, yayinda sauran ke zaune akan carpet, kan gadon shima ya zauna had'i da tankwashe k'afarsa, kana ya shiga gaida su, Nainah ta k'urawa Aryan ido tana karantar yanayinsa batare datace komai ba, Jabeer da Jiya suka zuba masa ido, suna tsoron sake tambayarsa, lura da irin kallan da su yi masa ne yasa shi mik'a musu, cikin murna suka amsa suna da tsalle, had'i dayi masa kiss a kumatunsa, kana sukayi waje da gudu, Aunty Ayyam tace " brother bari na kawu maka breakfast d'inka nan, dariya yayi kana yace " thank you sister, kunun gyad'a da zazzafan k'osai dayaji hanta da kwai ta kawo mishi, " woww gaskiya nagode sosai Nainah, ya fad'a yana kallan Nainah, Aunty Nina tace " oh! mai yin wahalar daban wanda ake yiwa godiya daban, yayi dariya yace " sorry Aunty, nagode sosai kema, hira suka shiga yi sosai, dan Moli's Family suna matuk'ar so da k'aunar junnansu, gasu da had'in kai sosai kamar tsintsiya, fuska ya d'an b'ata kana yace " wai Aunty me kuke har yanzu baku koma gidajenku ba? Aunty Ayyam tace " kai kaga matsalarka ko, kai sai ka juya fuska kamar kai ne babba akan mu, fuska ya k'ara tsukewa yace " kowacce ta tashi ta shirya ta koma gidan mijinta, miye dan suna kawai zaku zo ku zaune har ku sake kwana, maza ku shirya yanzu ku tafi, dayake Sir Moli akwai san girma idan yana wani abun sai ka rantse shine babba a gidan, kuma dukda yana k'aramin su dukkan su suna jin shayinsa, dan basa tab'a gigin kawo mishi rai, shiyasa Hilwa yake ganin Aryan shine magajinsa, Nainah tace " gaskiya kam nima tun jiya nake cewa su shirya su tafi, suka k'i tafiya, kai yanzu dayake kai ne daka tasasu a gaba ai dolansu su tafi, Hilwa ma bai san suna nan sun k'ara kwana ba, Sir Moli bai bar part d'in Nainah ba, sai da ya tabbatar kowacce ta kwashi yaranta ta koma gidanta, da daddare Sir Moli zaune kusa Hilwa a part d'insa, Hilwa nayi fad'a akan rayuwa, kan yaji tsoron Allah ya rik'e gaskiya da amana aduk inda yake, Sir Moli yace " Hilwa gobe zan koma, Hilwa yace " au gobe fa Sunday ko? " Ni nama manta, amma bazaka koma a mota ba, ba zaka koma gobe ba, ka bari sai Monday, sai jet ya kai ka da asuba, ya amsa da to. ranar Monday ana yin Sallar Asuba jet ya d'auki Moli yayi kano, gidan yayi shiru kowa yana cike da kewarshi. Ranar suna yaron Halan yaci sunan Didi Rawan, suna kiranahi da Khair, yau tunda Khulud ta tashi ta tashi da matsanancin ciwon mara kamar zata mutu, dan ko kanta bata iya d'agawa, gashi ta kasa tashi balle taje tayi wanka, Sanah kuma tun 7:00am ta tafi school kasancewar tana da lectures 8:00am, tana kwance kamar zata mutu tayi shiru, Hanash yau ma ya shirya cikin shiga ta alfarma, yayi masifar kyau ya nufi gidan su Khulud, yauma mai gadi yaje yayi sallama da ita, sai lokacin Mamu ta shiga d'akin dubota, dan tunda Sanah ta fara school, ita kuma ta koma zaman bedroom, shiyasa yau koda Mamu taga bata fito ba batayi tunanin wani abu ba, ganin Khulud kwance tana ta murk'ususu, yasa Mamu k'arasawa da sauri, " ya Salam, Mamu ta fad'a tana d'agota, " meke damunki? Mamu ta tambaye ta, dakyar tace " ciki na ne, tana fad'ar haka Mamu ta gane period zatayi, cikin tausayawa Mamu tace " dama yana yi maki ne? Dayake su Mamu basu san Khulud bata fara ba, shiru Khulud tayi bata bawa Mamu amsa ba, kwantar da ita Mamu tayi ta mik'e ta shiga bathroom d'insu, ta had'a mata ruwan wanka, kana ta fito ta umarce data shiga dakyar Khulud ta mik'e ta shiga, kafin ta fito Mamu ta fiddo mata kaya harda pad, pant & bra, kana ta fita, cikin sanyi Khulud ta fito, kayan da Mamu ta fiddo mata tabi da kallo, kayan ta saka ta shirya sosai , ta d'auke pad d'in ta maidata cikin wardrobe, bata jima da shiryawa ba, Mamu ta shigo d'auke da tray na abinci, tea ta fara bata tasha dakyar, Mamu ta matsa mata ta shanye tea d'in tsaf, kana ta bata chips & miyar hanta, ta d'anci kad'an kana Mamu ta bata magani tasha, sosai Khulud taji ciwon ya lafa mata, Mamu na zaune kusa da Khulud taji sallamar get man, kai Mamu ta dafe tace " tab na manta tun d'azu kikayi bak'o fa, Khulud ta d'an zumb'uro baki tace " Mamu ban jin dad'i ban iya fita, Mamu tace " mutumin yazo tun d'azu yakai wajen awa d'aya da rab'i yana zaman jiranki amma ki k'i fita? "Mamu please ki aika ace masa ban jin dad'i, ta fad'a a shagwab'e, Mamu tace " ki fita da kanki kije kiyi masa bayani, zata kuma yin magana Mamu tace " no argument, jiki a sanyaye Khulud ta fita, iskewa tayi har an kai shi set room, koda ta shiga taga kayan drinks & snacks jere a gabansa, tana shigowa ya mik'e da sauri had'i da zubawa fuskarta ido, a hankali ta zauna tana cije lips, cikin sanyin murya tace " ina wuni? " Alhamdulillah ya bata amsa yana kallanta, ganin yadda take cije lips yasa shi cewa " meke damunki? Muryarta na rawa tace " ciki na ke ciwo, " innalillahi wa'inna ilaihirrajji'un yace, cikin tashin hankali yace " tun yaushe? " Tun safe ta bashi amsa, cike da tension ya shiga jera mata sannu, yadda kasan zayyi kuka yake magana muryarsa na rawa, ido kawai Khulud ta zuba masa ganin yadda lokaci d'aya yanayinsa ya canja, duk ya shiga cikin tashin hankali ya rud'e, sosai Hanash yayi mugun bata mamaki, yadda ya nuna damuwa k'arara a fuskarsa, murmushi Khulud tayi tace "karka damu fa, naji sauk'i ai, kamar zayyi kuka yace " kamar ya karna damu? Bayan kin san dole na damu, kin san abinda rai ke so ne ai, shiru tayi bata kuma yin magana ba, ganin haka yasa shi cewa " tashi ki ciki, gobe na dawo naji ya jikin, murmushi tayi kana tace" nagode, yace " bakomai, ya mik'e zai fita idansa ya sauka akan wayarta data manta, da sauri ya koma ya zauna ya d'auki wayar, to his lucky wayar babu pin, pic d'in Sanah ya gani a screen sever, in capital letter an saka my Happiness, theme d'in wayar ma na pic d'in Sanah ne, murmushin bak'in ciki yayi yana jin matsanancin kishin Sanah na shigarsa, contacts d'inta ya shiga, my heartbeat yaga tayi saving number Sanah, tsaki yayi kana ya saka number sa a wayarta yayi saving da MY LIFE, kana yayi dialing dan ya samu number ta, kiran ya shiga yayi saving number ta da My love, kana ya bawa mai gadin wayar ya kai mata, tun a motar ya kira ta, tana zaune taga My life na kira, cikin mamaki ta d'auki wayar tana mamakin waye, har kiran tsinke aka kuma kira, tana yin picking taji shine, a ranar Hanash ya kira Khulud yaji ya jikinta yakai 10×, Khulud na waya da Hanash taji k'arar parking, da sauri cikin murna tace masa " my Sanah ta dawo, bata jira amsarsa ba kashe wayar. A ranar da daddare matsanancin ciwon mara ya hana Khulud sakat, amma gudu karta tashi Sanah daga bacci yasa ta daurewa dan tasan da sassafe take fita, sai wajen 3:00am period d'in Khulud yazo kana ciwon ya lafa mata, sosai Hanash ya nunawa Khulud so da kulawa a rashin lafiyarta, tun tana basar dashi harta fara sakin jiki dashi suna hira sosai, sai dai duk rabin hirar labarin Sanah take bashi, bata da wata magana ko labari daya wuce na Sanah, bata san duk lokacin data ambaci sunan Sanah a kunnen Hanash daurewa kawai yake yi ba, amma ji yake kamar tana watsa mishi wuta, lokacin da Khulud ta sanar da Sanah da Halan ta fara period sosai sukayi murna da farin ciki, satinta d'aya tana period tayi wanka, Hanash ko kullum sai ya zo ba fashi, dan ya dage sai ya sakawa Khulud matsananciyar soyayyar shi a zuciyarta, kasancewar babu Sanah babu mai d'ebewa Khulud kewa, yasata fara kula Hanash, tun tana shashshare har dai ta fara kula shi, sai dai ko zancen yazo hirar dai d'aya ce ta Sanarta, daga my Sanah kaza sai my Sanah kaza, sosai Hanash ya rink'a d'ebewa Khulud kewa, yana bala'in kula da ita sosai, saboda yadda ya nuna damuwa da kulawa a gareta, musamman ma da bata da lafiya, ko kuma da tace abu yake yi babu musu, duk abinda zayyi ya faranta mata shi yake yi, yana kuma gudun duk abinda zai b'ata mata rai, sosai yake nuna mata so da soyayyarta a zahiri, sannu a hankali soyayya mai k'arfi ta shiga tsakanin Hanash da Khulud, suna yiwa junansu mugun so, 24hrs suna tare a waya, ko chart, kasancewar Sanah da sassafe take fita school bata dawowa sai gaf da magrib, idan kuma ta dawo bata da lokaci sosai datayi wanka taci abinci tayi sallah sai bacci ko karatu, yasa kwata-kwata bata lura da abinda ke faruwa tsakanin Hanash da Khulud ba, bata san komai ba, ita kuma Khulud ba b'oye mata tayi ba, dan bata samun lokaci ne yasa bata sanarda ita abinda ke faruwa ba, sosai tsantsar soyayya mai k'arfi ta shiga tsakanin Hanash da Khulud, fiye da tunanin mai karatu, ta yadda babu abinda d'aya zayyi batare da d'ayan sa ni ba, kullum kuma ko yaushe suna manne da juna a waya, sunyi masifar bawa junansu mahimanci fiye da tunani. Tun bayan faruwar wannan al'amarin babu wanda ya k'ara ganin wani tsakanin Sir Moli da Sanah, sosai suka shiga wasan b'uya, a gajiye lik'is Sanah ta koma gida yau ma, Khulud na waya da Hanash taji shigowar Sanah tayi saurin mik'ewa, had'i dayin cilli da wayar, Sanah ta zube akan sofa, had'i da cewa " wassh Allah na gaji da yawa, cikin tausayawa Khulud tace sannu My Sanah, Hanash dake ta faman hello hello, jin shiru, ya jiyo muryar Sanah, tsaki yayi had'e da kashe wayar, Khulud ta rik'e hannun Sanah tace " muje kiyi wanka, ba musu Sanah tabi Khulud zaunar da Sanah Khulud tayi a bakin bed, kana ta shiga bathroom ta had'a mata ruwanka, ta fito tace " my Sanah shiga kiyi wankan, Sanah ta mik'e ta cire kayan jikinta ta d'aura towel, ta shiga tayi wankan ta d'auro alwala, kafin ta fito Khulud ta fiddo mata kaya marasa nauyi da pant ta aje mata akan bed, Sanah ta fito ta zauna gaban mirror tana shafa lotion, cikin matsananciyar gajiya, Khulud tayi dariya tace " ko inzo na shafa maki man? Ta fad'a cikin tsokana, Sanah tayi dariya tace " dako kin taimaka da yawa, mai kawai Sanah ta shafa ta zura doguwar rigar bacci, ta saka pant kawai bata saka bra ba dan bata bacci da bra, perfume's ta fesa, kana ta fara k'ok'arin hawa bed, Khulud ta kalle ta tace " abinci fa? Naga kina k'ok'arin yin bacci, Sanah tace " kai bar abincin nan kawai, Khulud ta turo baki kana tace " Allah sai kinci kefa nake jira ki damo mu ci, Sanah tayi murmushi tace " sorry jeki d'auko mana muci, Khulud ta mik'e ta fita tana cewa " yauwa ko ke fa, wayar Khulud dake gefe ta ringing, Sanah bata kula wayar ba harta katse, aka sake kira, nan ma bata yi picking ba, sai da kira na 5 ya shigo kana ta mik'a hannunta daga inda take kwance ta lalubo wayar, sunan ta kalla taga anyi saving da My Life, cikin mamaki ta tace " my life kuma, waye kuma my life? Ta tambayi kanta, jin wayar na neman katsewa yasa ta saurin yin picking, "hello my happiness ina ta kira shine ba'ayi picking ba, yayi maganar zazzak'ar muryarsa, gaban Sanah yayi muguwar fad'uwa, a hankali ta zame wayar daga kunnenta ta k'ara kallan screen d'in, taga tabbas ba wrong number bace, tunda gashi anyi saving, cikin mamaki ta k'ara mayar da wayar kunnenta, muryarta na rawa tace " bata nan, jin muryarta ya sashi sakin tsoki had'i da kashe wayar, wayar Sanah ta k'urawa ido cike da mamaki, Khulud ta shigo d'auke da tray d'in abinci, ganin yadda Sanah ta k'urawa wayar ido tanaR juyata, ya sata zama kusa da ita, " lafiya? Khulud tace, cikin sanyin jiki Sanah tace " waye my life? Murmushi Khulud tayi tace " he's my love, "your love? Sanah ta maimata cikin mamaki, Khulud tace " eh!, ban baki labarinsa bane saboda baki zama, da kin dawo kike kwanciya bacci, Sanah tace " yanzu dama Khulud har akwai wani abu da zamu b'oyewa junanmu, har akwai abunda zamuyi batare da sanin juna ba? Khulud tace " My Sanah baki zama fa, Sanah tace " saboda bana zama shine ya hana ki fad'a min, wannan ai ba dalili bane, tunda ba mutuwa nayi ba, ba kuma garin na bari ba, cikin sanyin murya Khulud tace " I'm so sorry, ban san na hana ki bacci ne, shiyasa kika ga ban sanar dake ba, Sanah " ok yanzu ai ina jinki, Khulud ta mik'e tsaye had'i da d'aga murya cikin farin ciki tace " I love him, I really love him so much, I love him more & more most my Sanah, ke kad'ai nafi so a duniya sama da Hanash, ganin yadda Khulud ke farin ciki yasa Sanah yin murmushi tace " who is he? Khulud tace " Hanash Waseef, Sanah tayi rolling sexy eye d'inta tace " taya za'ayi na sanshi, description d'insa gaki man yadda zan gane, Khulud tace " ai kin san shi ma, Sanah tace " na sanshi, a ina? Khulud tace " wannan wanda kukayi fad'a, Sanah tace " wai wa? Khulud tace " wanda ya watsa maki ruwan kwata har sau biyu, ke kuma kika mare shi, a firgice ta mik'e tana kallan Khulud had'i da ja baya.............. _Banyi editing ba, so nasan akwai typing errors_ MOMYN ZARAH _*RASHIN SANI.......*_ *HAUWA A USMAN* _JIDDARH_ ```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh``` 2⃣2⃣ Hannunta ta saka ta rufe bakinta, had'i da zaro sexy eyes d'inta waje, a hankali cikin takunsa na cikakkun maza ya fara takowa gareta, cikin tsoro Sanah ta fara ja baya tana yarfe hannu, yana biyo ta ita kuma tana cigaba da yin baya har suka isa bango, hannayensa ya saka ya dafe bango, ya saka ta a tsakiyar hannayensa, gaban rigarsa inda ya b'alle bottles d'in jikin rigar kyakkyawan k'irjinsa mai d'auke da yalwataccen kwantaccen gashi, ta kalla, take taji gabanta yayi muguwar fad'uwa da k'arfi, da sauri ta runtse idanta yayinda da k'irjinta keyin sama da k'asa da sauri-sauri, lulu eyes d'insa ya zuba mata yana kallan yadda k'irjinta ke bugawa yana up an down da sauri, yanayin k'amshin da sanyin Ac dake office d'inne suka saukar masa da wani irin yanayi a gaba d'aya ilahirin jikinsa, yaji kasala ta saukarwa duk wata gaba ta jikinsa, abinka kuma da yanayin damuna, k'ara matseta yayi sosai a jikin bangon, ta yadda k'irjinsu na gogar na juna, da sauri Sanah ta bud'e idanta, ta zuba cikin nashi, ganin yadda lokaci d'aya gaba d'aya yanayinsa da kuma kamanninsa suka canja yasa zuciyarta ta shiga bugawa, dayake ya fita tsayi yasa idan zata kalle shi sai dai ta d'aga idanta sama, kanta na k'asa, idanta kawai ta d'aga tana kallanshi, cikin wata irin kasalalliyar murya Sir Moli yace " kin tuna? D'an kawar da kanta tayi gefe, muryarta can k'asa tace " me? Yace " alk'awarin da kikayiwa wannan mugun secondary teacher d'in naku, muryarta na rawa tace " na manta, "Ok bari na tuna miki, ya fad'a yana k'ara shegewa jikinta, " please kaban last chance, idan na kuma yin laifi kayi man koma meye, wallahi I promise ban k'ara yi maka laifi, Allah idan na kuma kayi man komai kaga dama na yarda na d'auka, duk abinda kaga damanyi kayi man, ya fad'a bakinsa saitin kunnenta, had'i da hura mata iskar cikin bakinsa a kunnenta, kana yace " kin tuna yanzu? Idanta na kansa ta d'aga masa kanta, muryarsa can k'asan mak'ogwaro yace " kin san ban san d'aga kai ko? Bakinta na rawa tace " eh!, yace " good, muryarsa bata fitowa sosai yace " shi kuma a lokacin mai yace miki? Ya fad'a yana shinshinar wuyanta, had'i da goga hancinsa a wuyanta, kamar zatayi kuka saboda yadda duk yabi ya shege mata jiki, tace " keep it in your mind, I know one day you will pay for your promised, "good yace , yana goga hancinsa a wuyanta, " kince duk abinda naga dama nayi miki ko? Ya fad'a muryarsa bata fita sosai, "dan Allah kayi hak'uri Allah ban k'arawa, yadda take maganar yasa shi k'urawa cutie lips d'inta ido, still hannayensa na jikin bongon, ita kuma tana tsakiyar hannayensa, ya sanya fuskarsa a wuyanta yana goga mata, kana a hankali ya fara goga mata fuskarsa akan tata fuskar, sajensa yana gogar kumatunta, k'irjinta na gogar na shi, yadda k'irjinta ke yin sama da k'asa ya fara sa Aryan yin loosing control, itako Sanah tsaron yanayin data ganshi ciki ne ya hanata yin koda kwakkwaran motsi, idanshi na kanta yana karantar yanayin data shiga, yasa hannu ya zame hularsa dake kanta, ya cusa hunnunsa cikin gashin kanta, bakinsa yakai cikin kunnenta ya rad'a mata, kin shirya karb'ar punishment d'inki yanzu? Ya fad'a muryarsa na creaking, " kayi hak'uri tace , kuka na neman kwace mata, yadda tayi maganar tana turo bakinta, yasa Sir Moli had'e bakinsu waje d'aya batare daya sani ba, ido Sanah ta zaro waje cike da tsoro jin abinda Sir Moli keyi mata, gaba d'aya jikinsu ya d'auki rawa da tsuma, kasancewar jin su a cikin wani irin yanayi da basu tab'a tsintar kansu ciki ba, duk ilahirin jikinsu kerrrrrma yake, musamman Sanah, da har hawaye ya fara zubowa daga idanuwanta, a hankali ya zagayo da hannunsa ya tallafe kanta yadda zaiji dad'in shan bakinta sosai, had'i da cusa hannunsa cikin gashin kanta, yana ya mutsuwa, still bakinsa na cikin nata, d'aya hannun yakai yana shafa duk ilahirin jikinta, hannu Sanah ta sanya a k'irjinsa tana k'ok'arin ture shi, a hankali hannunta ya shege cikin rigarsa inda yake ya bud'e, Sir Moli yana jin tattausan hannunta akan fatar k'irjinsa ya k'ara fita saga hayyacinsa, jikinsa na kerrrma ya fara k'ok'arin neman zip d'in rigarta. Hanash dake ta faman knocking a bakin k'ofar amma ba'a amsa ba, ya d'an ja tsoki kana ya juya a hankali zai tafi, bakinshi cikin nata tace " uhmm innnn amma ba damar yin magana, saboda da gaske yake tsotsar bakin nata, Hanash dake waje jin ance innnnn, sai ya zata cewa akayi ya shigo dan haka ya danna kai cikin office d'in kai tsaye, tsawa yayi cak ganin yanayin da suke ciki, bakin Hanash na rawa yace " innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, ya fad'a batare daya sani ba, jin maganar Hanash ya sanya Sir Moli dawowa cikin hayyacinsa, a matuk'ar kid'ime ya saki Sanah yayi baya, cike da tsoro da kuma tsantsar mamaki Sir Moli yake bin Sanah da wani irin kallo, yana tambayar kansa me yayi mata, ido Hanash ya k'ura musu na tsayin lokaci, yana kallan Sanah sanye da kayan Aryan a jikinta, a hankali yabi cut da agogo da takalmin k'arfarta da kallo, ya kuma kalli yadda gashin kanta ya barbaje, kana ya mayar da kallansa ga Aryan dake dafe da kansa kwalla na neman gangarowa daga idansa, yaga gaba d'aya jan bakin Sanah ya dame masa fuskarsa, murmushin bak'in ciki Hanash yayi kana ya juya ya fita batare dayace musu komai, durk'ushewa Sanah tayi had'i da fashewa da wani irin rikitaccen kuka, kansa ya dafe dake barazanar tarwatsewa had'i da zuba mata idanuwansa da suka koma pure red color,, muryarsa na rawa Sir Moli yace " me nayi? " Meke shirin faruwa dani ne? Yayi maganar idansa na kanta, yana kallan yadda take ta faman kuka, sai da taci kukanta ta k'oshi kana ta mik'e cikin sanyin jiki, ta cire agogonsa ta d'ora masa akan table, kana ta durk'usa ta d'auki hularsa dake yade a k'asa itama ta d'ora masa akan table, ta cire takalmin ta aje a gefe, kana ta d'auki d'an kwalinta ta d'aura, ta yafa mayafinta, ta saita kanta sosai kana ta fita, duk abinda take yi idansa na kanta, tana fita ya naushi bango da k'arfi, "oh! sheet! ya akayi nayi loosing control? " Na aikata abinda ban tab'a yi ba, zama yayi akan sofa dake cikin office d'insa yayi tagumi hannu bibbiyu yana san ya tuna abinda ya faru yanzu, tana fita ta nufi get, ko ta kan lectures bata bi ba, tafe take kawai batare data san inda take jefa k'afarta ba, gaba d'aya hankalinta baya tare da ita, ta fad'a duniyar tunnani, a fili tace " shin da gaske ne abinda ya faru dani yanzu koko mafarki nake yi? "Da gaske Sir Moli ne yayi abinda yayi man yanzu? " Ashe dama d'an iska ne, mazinaci, fasik'i? " Allah kad'ai yasan yawan matan dayayiwa abinda yayi man yanzu, tana fita bakin get ta samu mai adai-dai sahu, babu b'ata lokaci ta shiga ya kaita gida, a harabar gidan ta iske Aarib yana k'ok'arin shiga mota, yana hangota ya fasa ya tsaya yana jiran ta k'araso idanshi kanta yana yi mata murmushi, "meyasa baki kira ni nazo na d'aukeki ba? Ya tambaye ta, kwata-kwata hankalin Sanah baya jikinta, dan bama ta lura da wani Aarib ba, kallanta yayi cike da mamaki kana yace " Sanah!, amma shiru bata amsa masa ba, tafiya kawai take yi, direct part d'in Halan ta nufa, Aarib yabi bayanta da kallo, har yayi yunk'urin binta sai kuma ya fasa, ya shiga mota yayi waje, parlor ta shiga ta zauna akan sofa had'i da runtse idanta da k'arfi, Halan na durk'ushe ciwon nak'uda ya dameta, ji take kamar zata mutu, dakyar ta kira sunan Sanah, amma shiru bata amsa ba, cikin muryarta da bata fita sosai ta kuma cewa " Sanah!, amma shiru bata amsa ba, dakyar Halan ta rarrafo tazo inda take tasa hannu ta tab'a ta, firgigit Sanah tayi ta farka daga hang d'in da brain d'inta tayi, ajiyar zuciya ta sauk'e da k'arfi kana ta kalli Halan dake ta faman cije baki tace " Aunty lafiya dai ko? Dakyar Halan tace " kira yayanku, Sanah najin muryarta tasan tana cikin mawuyacin hali, da sauri ta mik'e jikinta ta kerrrma, tayi kan Halan tana dialing number Ziyad, sai da ta kusa yin cutting kana yayi picking, bata jira taji abinda zaice ba tace " Yaya kazo gida yanzu Aunty Halan ba lafiya, a kid'ime ya mik'e yana cewa gani nan, wayar Khulud tayi dialing tana yin picking tace " ki zo part d'in Aunty Halan, ina nan bata da lafiya, da sauri Khulud ta mik'e tana cewa Mamu " Aunty Halan ba lafiya inaga haihuwa ce, Mamu ta mik'e itama tace " Allah ya raba lafiya ki biya ki sanar da Juju, kasancewar mutanen da akwai kara, ita Mamu bata iya binsu hospital saboda ita ta haifi Ziyad, dole zatayi kara, Khulud na fad'awa Juju ta mik'e da sauri ta zari hijab sukayi part d'in Halan, suna shiga Ziyad na shigowa bai wani ji kunyar Juju ba ya sab'i Halan yayi cikin mota da ita, yana cewa " Khulud d'auko akwatin kayan haihuwa, da sauri ta nufi d'akin ta d'auko, Family Hospital d'in su ya kaita suna isa aka karb'eta aka shigar da ita labour room, Sanah da Khulud suka yi cirko-cirko, Juju da Ziyad na gefe. A hankali ya mik'e ya sanya agogonsa da cut, kana ya zira takalminsa ya zari brief case d'insa ya fita, kasancewar yau Friday yasa Aryan nufar masallacin juma direct, ana idar da sallah ya koma mota ya zauna, dayake a yanayin damuna ne yana zaune cikin mota yaji an fara yayyafi, ji yayi gaba d'aya hankalinsa yayi gida Maiduguri, dama ya kai wajen 4 weeks baije weekend ba, a hankali ya d'ago hannunsa ya kalli agogo yaga 1:30pm na rana, ido ya lumshe yana jin sha'awar yin long journey a mota, ya san kuma muddin Hilwa yasani bai barinsa ya tuk'o mota tun daga Kano har Maiduguri, cewa zayyi dole sai yabi jirgi ko a aiko masa da Army Jet a d'auke shi, kuma a ransa bai wani san tafiya a jirgi sosai, musamman ma idan anan gidan Nigeria ne, baya kuma san driver yafi san yayi tuk'i da kansa, dan haka ya yanke shawarar tafiya kawai batare daya sanar da kowa ba, sai dai yayi musu zuwan bazata, a hankali yayiwa motar key ya d'auki hanyar Barno, ya sakarwa motar wuta, dan Aryan akwai gudu da mota. Halan takai 3hrs tana labour kana ta haifo yaronta, mai kyau, nurse ta fito d'auke da baby Sanah tayi saurin amsar Baby tana murna, Khulud ta kalli nurse d'in tace " ya Maman Babyn? Nurse tayi murmushi kana tace " tana lafiya, ai kaita d'akin hutu tana bacci, nan da d'an wani lokaci zaku ganta, a ranar da dare aka sallami su Halan kasancewar ta haihuwa lafiya babu wata matsala, suka koma gida cikin murna da farin ciki. Hanash na fita daga office d'in Sir Moli ya shiga mota, ya kai wajen 10 minutes yana tunanin da bai san kona meye bane, ji yayi ya k'ara jin tsanarta fiye da koyaushe a rayuwarsa, tsoki yaja kana jiki a sanyaye yayiwa motar key yayi gida, a parlor ya iske Mimmee zaune tana cin kwad'an Salad, kusa da ita ya zauna, jikinsa duk ba dad'i, kallo d'aya tayi masa tasan akwai abinda ke cikin ransa, kallansa tayi tace " Son meke damunka? Murmushi yayi kana yace " bakomai Mimmee, d'an shiru tayi had'i da zuba masa ido kana tace " kamar ya bakomai? Shiru yayi baice mata komai ba, dan shi kansa bai san meke damunsa ba, " ya kukayi da Khulud d'in? Ajiyar zuciya ya sauke kana ya sanar da ita duk yadda sukayi, bai b'oye mata komai ba, shiru tayi na wani lokaci kana tace " kayi hak'uri, in sha Allah I will pray for you kaji, zan nemar maka zab'in Allah, a sanyaye ya d'aga mata kansa, tace " karka karaya kaji Son, ka cigaba da zuwa, haba kai kamar ba namiji ba, kai fa cikekken namiji ne, kayi amfani da basirarka da kuma wayonka, ka sanya mata sanka, "how!? yace, " ban sani ba Mimmee ta fad'a a d'an hasale, tana ture shi, murmushi yayi kana yace " I promise you Mimmee I will try my best, tayi murmushi kana tace masa good Son. Aryan na shiga garin Maiduguri aka tsuge da ruwan sama kamar da bakin kwarya, wani mahaukacin katafaren gida, wanda tun daga waje naga sojoji sunfi a k'irga suna kaikawo, automatic get d'in naga ya bud'e kansa, bayan yayi snapping number motar Sir Moli, gaba d'aya habarar gidan babu komai sai dandazon sojoji dake kai kawo, gidan yana da haukacin girma, dan da gani filin da akayi gidan 300 by 300 ne, gaba d'aya gidan zagaye yake da shukoki iri-iri, a harabar gidan yayi parking batare daya fita ba ya kishingid'a, Yara na gani a k'alla sun kai 7 suna wasa da ruwan sama a cikin farfajiyar gidan, yayinda na hangi wasu yaran rakub'e cikin baranda, da alama suma suna san yin wasan ruwa, tsoro ne ya hana su, d'aya daga cikin yaran dake tsaye a cikin baranda yace " Yaya kun fa san Uncle Aryan ya hana mu wasa a cikin ruwa ko? D'ayan yace " kai zaka fad'a masa munyi wasan ruwan? D'aya yaron yace " a'a amma kasan fa yace " idan mukayi zai gani, kuma yace duk abinda muke yi yana ganin mu, a duk inda yake, d'ayan yace ba wani nan wayo yake yi mana, kazo muyi ai babu wanda zai fad'a masa, d'ayan yace " a'a ni banyi ni dai tsoro nake ji, d'ayan zayyi magana Sir Moli ya bud'e mota ya fito, gaba d'aya jikin yaran ya d'auki kerrrma da tsuma, suka shiga rige-rigen guduwa, wasu na take wasu, yadda kasan sunga dodo ko aljani, wad'anda ke kan barandar suna ganin shi suka fito da gudu, suka nufe shi suna cewa " ga Uncle Aryan ga Uncle Aryan, oyoyo Uncle Aryan, yaran naga ya kalla farare tass dasu, masu kama da yaran turawa, suna sanye da kaya na alfarma da gani kasan masu tsada ne, murmushi yayi musu kana sunkuyo dai-dai tsayin su, da gudu suka fad'a jikinsa, d'ayan yaron ya zagayo ta bayansa ya sak'alo wuyansa, ya d'auki cutie Baby's d'in a hannunsa, yayi hanyar part d'in Hilwa ya, kasancewar yau ana suna a gidan yasan part d'in Nainah akwai mutane, matar Yayanshi Haidar ta ce haihu, yau ake suna, a parlor'n Hilwa ya iske babban Yayanshi da auta Jabeer, zaune suna hira, Hilwa na ganinsa yayi saurin mik'ewa zaune daga kishingid'en dayake, ya mik'e masa hannu alamar yazo, yana dariya yadda kasan anyi masa bushara da aljanna, annurin fuskarsa ya fad'ad'a ganin Sir Moli, shima yana murmushi ya nufi mahaifin nasa mai tsananin so da k'aunarsa fiye da duk 'ya'yan daya haifa, kwata-kwata Hilwa da Nainah basu iya b'oye tsananin son da suke yi Aryan a cikin yaransu, yadda kasan shi kad'ai suka haifa a duniya, kusa da Hilwa Aryan ya zauna yana fad'ad'a murmushinsa, Hilwa ya shafa kansa yace " Soul shine kazo bako announcement, dariya Sir Moli yayi yace " nasan baka bari na nayi driving ne, ido Hilwa ya zaro yace " kai ka tuk'o motar tun daga Kano har Maiduguri? Aryan yayi dariya yace " eh Love, Hilwa yace " Moli (dayake haka yake kiransa wani lokacin saboda tsananin kamar dayake da shi, shiyasa yake ganin kamar shine magajinsa), "please ka daina wasa da rayuwarka kasan bazan iya jure rashinka ba ko? Murmushi Haidar yayi kana yace " Hilwa ka hana mu gaisawa da d'an uwanmu ma, Aryan yayi dariya yace " Big Bro ina wuni? " Lafiya lau,yace yana dariya, kana yace " ya aiki? Sir Moli yace " aiki Alhamdulillah, babban d'an Haidar ya shigo wanda zayyi sa'an Jabeer, tare Jabeer da Noor suka gaida Sir Moli, ya amsa fuska a sake, hira sosai Hilwa da Aliyu & Aryan suka shiga, yaran da suka tsorata sukayi cikin gida, gidan suka shiga da suna cewa " Nainah, Ummi Uncle Aryan ya dawo, "Uncle Moli ya zo (duk gidan suna kiransa da Moli) Nainah tayi murmushi tace " zakin d'ana ya dawo, dama indai na ganku kun shigo a firgice nasan shine, manyan Yayyansa mata duk suka mik'e suna tambayar " ina yake! ina yake!? Aunty Kubra ta d'auki wayarta tayi dialing number sa, wayar na fara ringing Sir Moli ya kalli wayar, kana yayi murmushi, Hilwa da Haidar suka kai dubansu ga wayar, Hilwa yace " hala har an kai musu labarin zuwanka, murmushi ya kuma yi kana yayi picking wayar, Aunty Kubrah tace " yanzu Mudah suka sanar mana ka zo, kuma har yanzu bamu ganka ba, "dariya yayi yace " ina part d'in Hilwa ni da Yaya, "au ashe ko da gaske suke? " Sannu kasha hanya bari yanzu na dawo maka ruwa, "nagode yace had'i da yin dropping wayar, gaba d'aya gida aka shiga munar dawowarsa saboda tsananin so da k'aunar da suke yi masa, abinci Aunty Nina da Aunty Kubra suka shirya masa kala-kala, Nainah, da Aunty Ayyam suka nufi part d'in Hilwa, Jiya ta shigo da gudu a gabansa ta tsaya tana hakki tace " Uncle Aryan ina alk'awarin mu? Jabeer yace " wallahi nima shi nake jira tun d'azu, Sir Moli ya tsuke fuska had'i da cewa " bako gaisuwa, balle ya hanya kinzo kin tsare kina tambayata alk'awarinki kamar wacce taban ajiya, baki ta tab'a ta fara diddira k'afarta, cike da shagwab'a tasan yin kuka, tsawa ya daka mata had'i da cewa " karki soma dan ubanki, sanin halinsa yasa jiya had'iye kukanta, ta fad'a jikinsa tana dariya tace " I'm sorry Uncle, ina wuni? "Alhamdulillah, ya amsa yana d'agata sama, dai-dai lokacin Nainah, Aunty Kubra, Aunty Nina da Aunty Ayyam, suka shigo, gaba d'ayansu suka zauna kusa da shi, suka zagaye shi suka sanya shi tsakiya, Nainah ta jawo shi jikinta ta rungume tana shafa kansa tace " Life kasha hanya, sannu Life, Hilwa yace " kuma a mota yazo shine ma yayi driving, Nainah ta zaro ido, tace " Life meyasa? Kansa ya k'ara kwantarwa a jikinta, yace " sorry Nainah ban k'arawa, tayi dariya tana d'ago shi tace " tashi kaci abinci, nasan halinka da rashin san cin abinci, mik'ewa yayi zaune yace " ai dole naci abincin gidan Nainah da Hilwa na yau dan nayi missing d'inshi sosai, Aunty Ayyam ta jawo tray d'in abinci, ta fara zuba masa, Aunty Nina na zuba masa drink a glass cup, Haidar yace " uhmmm kaga d'an gatan Aunty's d'insa da Nainah, ni dayake yau matana suna can wajen hidimar suna babu wanda ya kula dani ai, aka barni da yunwa, Nainah na ta hidimar da Hilwanta, ni kun manta da ni, ashe rabon naci da Brother na ne, ya fad'a yana dariya, had'i da matsowa suka fara cin abincin tare, Hilwa dayake soja ne bai san yaji, abincin shima daban ake girka masa yace " ni ban iya ci da ku, Jabeer da Jiya suka zauna kusa dashi a hankali suka ce " Uncle! ya juya ya kalle su yace " meye kuma? "Alk'awarin na mu, kansa ya dafe had'i da cewa " oh my God, Haidar yace " wai alk'awarin me kayi musu ne? Aryan yace " Jiya laptop take so, Jabeer kuma iPhone X yake so, Hilwa yace " meyasa baku fad'a man na siya muku ba zaku damar man yaro? Aryan yace " ai nama siyo musu suna mota, Jiya da Jabeer suka shiga tsalle suna murna jin an siyo musu, Jabeer yace " Yaya suna ina? Sir Moli yace " suna mota, ungo key d'in ku d'auko ku barni na huta, har ya basu key d'in ya tuna ana ruwan sama, da sauri yace " yanzu ana ruwa ku bari sai an d'auke ruwan sannan, ya fad'a yana amsar key d'in, suna hira cikin so da k'auna, sai da suka gama kana Sir Moli ya nufi part d'insa, wanka yayi jikinsa duk a sanyaye, ya rasa meke damunsa a duniya, abinda yayiwa Sanah ya tsaya masa a ransa, shi kunyarta ma yake ji, ji yake kamar bazai iya sake had'a ido da ita ba, shi tsoransa d'aya ma karta d'aukeshi d'an iska tayi tunanin ko haka yake yiwa wasu matan, wanka yayi ya shirya ya fita ya zagaya baya, gani nayi ya b'ullo bakin swimming pool, mai kyau da kayan k'awa, gadon dake gaban swimming d'in ya hau ya kishingid'a, wata 'yar kwararrawa ya danna naga wasu sojoji sun fito sanye da uniform iri d'aya a jikinsa, batare daya d'aga kansa ba yace " a bani abu mai sanyi, kai suka risina cikin girmamawa kana suka juya, basu jima ba suka dawo d'auke da drinks kala-kala, ya kai good 1hr anan kana ya mik'e ya nufi gym, wata k'ararrawar ya danna sojoji suka fito, a tak'aice yace " green tea, sosai ya motsa jikinsa kana ya fita ya koma garden mai d'auke da flowers masu k'amshi da kyau, ga tsuntsaye kala-kala suna kukan su mai dad'in sauraro, tsayawa fad'ar had'uwar gidan Moli's b'ata lokaci ne, saboda an kashe kud'i kamar ba gobe wajen tsara gidan, duk wani abu na more rayuwar duniya akwai shi a cikin gidan, abun da yafi ban mamaki shine, duk wani ma'aikaci dake gidan soja ne, dai-dai da masu aiki da wanki da guga duk they're sojan. Aryan na kwance a bedroom d'insa, Nainah ta shigo d'auke da fruits salad, sallama tayi a k'alla takai sau uku, amma Sir Moli baiji ba, a hankali ta ajeye tray d'in akan glass, kana ta zauna kusa da shi, hannun tasa ta kwantar da kansa akan cinyarta, tana shafa kansa, ajiyar zuciya ya sauke a hankali, Nainah ta kira sunansa " Aryan! a hankali ya amsa " na'am, tace " meke damunka? Tunda na d'ora idona akanka kasan kana cikin damuwa, shiru yayi baice komai ba, Nainah ta k'ara cewa " meke damunka Aryan? "Bakomai heartbeat, ya amsa mata, " ya zakace bakomai bayan ga damuwar nan k'arara ta bayyana a tattare dakai, murmushi yayi kana yace " nayi exercise da yawa na gaji ne, murmushi tayi ta k'ara shafa kansa duk da bata yarda da abinda yace ba, mik'ewa tayi a hankali ta d'auko fruits salad d'in ta shiga bashi a baki, bata barshi ba sai da ya shanye tass, dan tasan halin Aryan bai san cin abinci, kansa nakan cinyarta tana shafa masa har yayi bacci, a hankali ta mik'e ta d'auko Italian blanket ta rufe shi, tayi masa kiss a kumatu kana ta fita, sosai Moli's Family ke mugun so da tsananin k'aunar Aryan kamar ransu, kowa yana nan-nan dashi kamar k'aramin yaron goye. Washe gari da safe wajen k'arfe 11:30am na safe, ya fito ya nufi part d'in Nainah, dayake yasan 'yan taran suna duk sun tafi, yasan babu sauran bare sai Moli's Family, har ya kusa shiga part d'in ya tuna da alk'awarin su Jabeer, komawa yayi ya d'auko sabuwar laptop da wayar duk a cikin kwalayen su, kana ya nufi part d'in, ganin ba kowa a parlor yasa shi nufar bedroom d'inta, a can ya iske ta zaune tsakiyar Aunty's d'insa, ana ta hira, Aunty Nina da Aunty Kubra na kan gado, yayinda sauran ke zaune akan carpet, kan gadon shima ya zauna had'i da tankwashe k'afarsa, kana ya shiga gaida su, Nainah ta k'urawa Aryan ido tana karantar yanayinsa batare datace komai ba, Jabeer da Jiya suka zuba masa ido, suna tsoron sake tambayarsa, lura da irin kallan da su yi masa ne yasa shi mik'a musu, cikin murna suka amsa suna da tsalle, had'i dayi masa kiss a kumatunsa, kana sukayi waje da gudu, Aunty Ayyam tace " brother bari na kawu maka breakfast d'inka nan, dariya yayi kana yace " thank you sister, kunun gyad'a da zazzafan k'osai dayaji hanta da kwai ta kawo mishi, " woww gaskiya nagode sosai Nainah, ya fad'a yana kallan Nainah, Aunty Nina tace " oh! mai yin wahalar daban wanda ake yiwa godiya daban, yayi dariya yace " sorry Aunty, nagode sosai kema, hira suka shiga yi sosai, dan Moli's Family suna matuk'ar so da k'aunar junnansu, gasu da had'in kai sosai kamar tsintsiya, fuska ya d'an b'ata kana yace " wai Aunty me kuke har yanzu baku koma gidajenku ba? Aunty Ayyam tace " kai kaga matsalarka ko, kai sai ka juya fuska kamar kai ne babba akan mu, fuska ya k'ara tsukewa yace " kowacce ta tashi ta shirya ta koma gidan mijinta, miye dan suna kawai zaku zo ku zaune har ku sake kwana, maza ku shirya yanzu ku tafi, dayake Sir Moli akwai san girma idan yana wani abun sai ka rantse shine babba a gidan, kuma dukda yana k'aramin su dukkan su suna jin shayinsa, dan basa tab'a gigin kawo mishi rai, shiyasa Hilwa yake ganin Aryan shine magajinsa, Nainah tace " gaskiya kam nima tun jiya nake cewa su shirya su tafi, suka k'i tafiya, kai yanzu dayake kai ne daka tasasu a gaba ai dolansu su tafi, Hilwa ma bai san suna nan sun k'ara kwana ba, Sir Moli bai bar part d'in Nainah ba, sai da ya tabbatar kowacce ta kwashi yaranta ta koma gidanta, da daddare Sir Moli zaune kusa Hilwa a part d'insa, Hilwa nayi fad'a akan rayuwa, kan yaji tsoron Allah ya rik'e gaskiya da amana aduk inda yake, Sir Moli yace " Hilwa gobe zan koma, Hilwa yace " au gobe fa Sunday ko? " Ni nama manta, amma bazaka koma a mota ba, ba zaka koma gobe ba, ka bari sai Monday, sai jet ya kai ka da asuba, ya amsa da to. ranar Monday ana yin Sallar Asuba jet ya d'auki Moli yayi kano, gidan yayi shiru kowa yana cike da kewarshi. Ranar suna yaron Halan yaci sunan Didi Rawan, suna kiranahi da Khair, yau tunda Khulud ta tashi ta tashi da matsanancin ciwon mara kamar zata mutu, dan ko kanta bata iya d'agawa, gashi ta kasa tashi balle taje tayi wanka, Sanah kuma tun 7:00am ta tafi school kasancewar tana da lectures 8:00am, tana kwance kamar zata mutu tayi shiru, Hanash yau ma ya shirya cikin shiga ta alfarma, yayi masifar kyau ya nufi gidan su Khulud, yauma mai gadi yaje yayi sallama da ita, sai lokacin Mamu ta shiga d'akin dubota, dan tunda Sanah ta fara school, ita kuma ta koma zaman bedroom, shiyasa yau koda Mamu taga bata fito ba batayi tunanin wani abu ba, ganin Khulud kwance tana ta murk'ususu, yasa Mamu k'arasawa da sauri, " ya Salam, Mamu ta fad'a tana d'agota, " meke damunki? Mamu ta tambaye ta, dakyar tace " ciki na ne, tana fad'ar haka Mamu ta gane period zatayi, cikin tausayawa Mamu tace " dama yana yi maki ne? Dayake su Mamu basu san Khulud bata fara ba, shiru Khulud tayi bata bawa Mamu amsa ba, kwantar da ita Mamu tayi ta mik'e ta shiga bathroom d'insu, ta had'a mata ruwan wanka, kana ta fito ta umarce data shiga dakyar Khulud ta mik'e ta shiga, kafin ta fito Mamu ta fiddo mata kaya harda pad, pant & bra, kana ta fita, cikin sanyi Khulud ta fito, kayan da Mamu ta fiddo mata tabi da kallo, kayan ta saka ta shirya sosai , ta d'auke pad d'in ta maidata cikin wardrobe, bata jima da shiryawa ba, Mamu ta shigo d'auke da tray na abinci, tea ta fara bata tasha dakyar, Mamu ta matsa mata ta shanye tea d'in tsaf, kana ta bata chips & miyar hanta, ta d'anci kad'an kana Mamu ta bata magani tasha, sosai Khulud taji ciwon ya lafa mata, Mamu na zaune kusa da Khulud taji sallamar get man, kai Mamu ta dafe tace " tab na manta tun d'azu kikayi bak'o fa, Khulud ta d'an zumb'uro baki tace " Mamu ban jin dad'i ban iya fita, Mamu tace " mutumin yazo tun d'azu yakai wajen awa d'aya da rab'i yana zaman jiranki amma ki k'i fita? "Mamu please ki aika ace masa ban jin dad'i, ta fad'a a shagwab'e, Mamu tace " ki fita da kanki kije kiyi masa bayani, zata kuma yin magana Mamu tace " no argument, jiki a sanyaye Khulud ta fita, iskewa tayi har an kai shi set room, koda ta shiga taga kayan drinks & snacks jere a gabansa, tana shigowa ya mik'e da sauri had'i da zubawa fuskarta ido, a hankali ta zauna tana cije lips, cikin sanyin murya tace " ina wuni? " Alhamdulillah ya bata amsa yana kallanta, ganin yadda take cije lips yasa shi cewa " meke damunki? Muryarta na rawa tace " ciki na ke ciwo, " innalillahi wa'inna ilaihirrajji'un yace, cikin tashin hankali yace " tun yaushe? " Tun safe ta bashi amsa, cike da tension ya shiga jera mata sannu, yadda kasan zayyi kuka yake magana muryarsa na rawa, ido kawai Khulud ta zuba masa ganin yadda lokaci d'aya yanayinsa ya canja, duk ya shiga cikin tashin hankali ya rud'e, sosai Hanash yayi mugun bata mamaki, yadda ya nuna damuwa k'arara a fuskarsa, murmushi Khulud tayi tace "karka damu fa, naji sauk'i ai, kamar zayyi kuka yace " kamar ya karna damu? Bayan kin san dole na damu, kin san abinda rai ke so ne ai, shiru tayi bata kuma yin magana ba, ganin haka yasa shi cewa " tashi ki ciki, gobe na dawo naji ya jikin, murmushi tayi kana tace" nagode, yace " bakomai, ya mik'e zai fita idansa ya sauka akan wayarta data manta, da sauri ya koma ya zauna ya d'auki wayar, to his lucky wayar babu pin, pic d'in Sanah ya gani a screen sever, in capital letter an saka my Happiness, theme d'in wayar ma na pic d'in Sanah ne, murmushin bak'in ciki yayi yana jin matsanancin kishin Sanah na shigarsa, contacts d'inta ya shiga, my heartbeat yaga tayi saving number Sanah, tsaki yayi kana ya saka number sa a wayarta yayi saving da MY LIFE, kana yayi dialing dan ya samu number ta, kiran ya shiga yayi saving number ta da My love, kana ya bawa mai gadin wayar ya kai mata, tun a motar ya kira ta, tana zaune taga My life na kira, cikin mamaki ta d'auki wayar tana mamakin waye, har kiran tsinke aka kuma kira, tana yin picking taji shine, a ranar Hanash ya kira Khulud yaji ya jikinta yakai 10×, Khulud na waya da Hanash taji k'arar parking, da sauri cikin murna tace masa " my Sanah ta dawo, bata jira amsarsa ba kashe wayar. A ranar da daddare matsanancin ciwon mara ya hana Khulud sakat, amma gudu karta tashi Sanah daga bacci yasa ta daurewa dan tasan da sassafe take fita, sai wajen 3:00am period d'in Khulud yazo kana ciwon ya lafa mata, sosai Hanash ya nunawa Khulud so da kulawa a rashin lafiyarta, tun tana basar dashi harta fara sakin jiki dashi suna hira sosai, sai dai duk rabin hirar labarin Sanah take bashi, bata da wata magana ko labari daya wuce na Sanah, bata san duk lokacin data ambaci sunan Sanah a kunnen Hanash daurewa kawai yake yi ba, amma ji yake kamar tana watsa mishi wuta, lokacin da Khulud ta sanar da Sanah da Halan ta fara period sosai sukayi murna da farin ciki, satinta d'aya tana period tayi wanka, Hanash ko kullum sai ya zo ba fashi, dan ya dage sai ya sakawa Khulud matsananciyar soyayyar shi a zuciyarta, kasancewar babu Sanah babu mai d'ebewa Khulud kewa, yasata fara kula Hanash, tun tana shashshare har dai ta fara kula shi, sai dai ko zancen yazo hirar dai d'aya ce ta Sanarta, daga my Sanah kaza sai my Sanah kaza, sosai Hanash ya rink'a d'ebewa Khulud kewa, yana bala'in kula da ita sosai, saboda yadda ya nuna damuwa da kulawa a gareta, musamman ma da bata da lafiya, ko kuma da tace abu yake yi babu musu, duk abinda zayyi ya faranta mata shi yake yi, yana kuma gudun duk abinda zai b'ata mata rai, sosai yake nuna mata so da soyayyarta a zahiri, sannu a hankali soyayya mai k'arfi ta shiga tsakanin Hanash da Khulud, suna yiwa junansu mugun so, 24hrs suna tare a waya, ko chart, kasancewar Sanah da sassafe take fita school bata dawowa sai gaf da magrib, idan kuma ta dawo bata da lokaci sosai datayi wanka taci abinci tayi sallah sai bacci ko karatu, yasa kwata-kwata bata lura da abinda ke faruwa tsakanin Hanash da Khulud ba, bata san komai ba, ita kuma Khulud ba b'oye mata tayi ba, dan bata samun lokaci ne yasa bata sanarda ita abinda ke faruwa ba, sosai tsantsar soyayya mai k'arfi ta shiga tsakanin Hanash da Khulud, fiye da tunanin mai karatu, ta yadda babu abinda d'aya zayyi batare da d'ayan sa ni ba, kullum kuma ko yaushe suna manne da juna a waya, sunyi masifar bawa junansu mahimanci fiye da tunani. Tun bayan faruwar wannan al'amarin babu wanda ya k'ara ganin wani tsakanin Sir Moli da Sanah, sosai suka shiga wasan b'uya, a gajiye lik'is Sanah ta koma gida yau ma, Khulud na waya da Hanash taji shigowar Sanah tayi saurin mik'ewa, had'i dayin cilli da wayar, Sanah ta zube akan sofa, had'i da cewa " wassh Allah na gaji da yawa, cikin tausayawa Khulud tace sannu My Sanah, Hanash dake ta faman hello hello, jin shiru, ya jiyo muryar Sanah, tsaki yayi had'e da kashe wayar, Khulud ta rik'e hannun Sanah tace " muje kiyi wanka, ba musu Sanah tabi Khulud zaunar da Sanah Khulud tayi a bakin bed, kana ta shiga bathroom ta had'a mata ruwanka, ta fito tace " my Sanah shiga kiyi wankan, Sanah ta mik'e ta cire kayan jikinta ta d'aura towel, ta shiga tayi wankan ta d'auro alwala, kafin ta fito Khulud ta fiddo mata kaya marasa nauyi da pant ta aje mata akan bed, Sanah ta fito ta zauna gaban mirror tana shafa lotion, cikin matsananciyar gajiya, Khulud tayi dariya tace " ko inzo na shafa maki man? Ta fad'a cikin tsokana, Sanah tayi dariya tace " dako kin taimaka da yawa, mai kawai Sanah ta shafa ta zura doguwar rigar bacci, ta saka pant kawai bata saka bra ba dan bata bacci da bra, perfume's ta fesa, kana ta fara k'ok'arin hawa bed, Khulud ta kalle ta tace " abinci fa? Naga kina k'ok'arin yin bacci, Sanah tace " kai bar abincin nan kawai, Khulud ta turo baki kana tace " Allah sai kinci kefa nake jira ki damo mu ci, Sanah tayi murmushi tace " sorry jeki d'auko mana muci, Khulud ta mik'e ta fita tana cewa " yauwa ko ke fa, wayar Khulud dake gefe ta ringing, Sanah bata kula wayar ba harta katse, aka sake kira, nan ma bata yi picking ba, sai da kira na 5 ya shigo kana ta mik'a hannunta daga inda take kwance ta lalubo wayar, sunan ta kalla taga anyi saving da My Life, cikin mamaki ta tace " my life kuma, waye kuma my life? Ta tambayi kanta, jin wayar na neman katsewa yasa ta saurin yin picking, "hello my happiness ina ta kira shine ba'ayi picking ba, yayi maganar zazzak'ar muryarsa, gaban Sanah yayi muguwar fad'uwa, a hankali ta zame wayar daga kunnenta ta k'ara kallan screen d'in, taga tabbas ba wrong number bace, tunda gashi anyi saving, cikin mamaki ta k'ara mayar da wayar kunnenta, muryarta na rawa tace " bata nan, jin muryarta ya sashi sakin tsoki had'i da kashe wayar, wayar Sanah ta k'urawa ido cike da mamaki, Khulud ta shigo d'auke da tray d'in abinci, ganin yadda Sanah ta k'urawa wayar ido tanaR juyata, ya sata zama kusa da ita, " lafiya? Khulud tace, cikin sanyin jiki Sanah tace " waye my life? Murmushi Khulud tayi tace " he's my love, "your love? Sanah ta maimata cikin mamaki, Khulud tace " eh!, ban baki labarinsa bane saboda baki zama, da kin dawo kike kwanciya bacci, Sanah tace " yanzu dama Khulud har akwai wani abu da zamu b'oyewa junanmu, har akwai abunda zamuyi batare da sanin juna ba? Khulud tace " My Sanah baki zama fa, Sanah tace " saboda bana zama shine ya hana ki fad'a min, wannan ai ba dalili bane, tunda ba mutuwa nayi ba, ba kuma garin na bari ba, cikin sanyin murya Khulud tace " I'm so sorry, ban san na hana ki bacci ne, shiyasa kika ga ban sanar dake ba, Sanah " ok yanzu ai ina jinki, Khulud ta mik'e tsaye had'i da d'aga murya cikin farin ciki tace " I love him, I really love him so much, I love him more & more most my Sanah, ke kad'ai nafi so a duniya sama da Hanash, ganin yadda Khulud ke farin ciki yasa Sanah yin murmushi tace " who is he? Khulud tace " Hanash Waseef, Sanah tayi rolling sexy eye d'inta tace " taya za'ayi na sanshi, description d'insa gaki man yadda zan gane, Khulud tace " ai kin san shi ma, Sanah tace " na sanshi, a ina? Khulud tace " wannan wanda kukayi fad'a, Sanah tace " wai wa? Khulud tace " wanda ya watsa maki ruwan kwata har sau biyu, ke kuma kika mare shi, a firgice ta mik'e tana kallan Khulud had'i da ja baya.............. _Banyi editing ba, so nasan akwai typing errors_ MOMYN ZARAH _*RASHIN SANI.......*_ *HAUWA A USMAN* _JIDDARH_ ```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh``` 2⃣3⃣ Tace " wannan kike nufi? Khulud tace " eh shi My Sanah, Allah ina sanshi dayawa, Sanah tayi shiru tana karantar yanayin Khulud, taga yadda take cikin farin ciki, tana murna da tsalle, take fad'in she love him so much, Sanah tayi shiru tana tunanin yadda akayi yasan gidansu, da yadda akayi har soyayyar su da Khulud tayi zurfi haka batare data sani ba, Khulud ta fad'a jikin Sanah tace " nasan kema zaki soshi saboda nima ina sanshi, shima yana sanki sosai, ya manta da duk abunda ya faru tsananin ku a baya, kullum bamu da wata hira sai taki, ko ban yi mishi maganarki ba, shi sai yayi man taki, murmushin yak'e Sanah tayi, cikin sanyin jiki tace " wow! My Khulud gaskiya nayi murna, da farin ciki da jin wannan labarin, kice kun dad'e kuna shan love? Ta fad'a tana kallanta, Khulud tace " ba wani dad'ewa mukayi sosai ba, da bani da lafiya ne ya nuna kulawarsa sosai akaina, kuma shine yake d'ebe man kewarki, taja hannun Sanah suka zauna a bakin gado, kana Khulud ta shiga bata labarin mafarin soyayyarta da Hanash tun daga farko har k'arshe, " kai amma abin ya burge ni, Sanah ta fad'a tana b'oye damuwarta, saboda yadda ta hango soyayyar shi a cikin kwayar idon Khulud, tasan kuma muddin ta nunawa Khulud bata sanshi, bata kuma kula shi, sai dai idan tayi mata haka bata yi mata adalci ba, musamman ma data fahimci shima yana bala'in san Khulud d'in, kuma yana kula da ita sosai, dan haka bazata tab'a b'ata musu farin cikin su saboda wani banzan dalilinta ba, ta kuma yiwa kanta alk'awarin daga yau har abada bazata k'ara k'insa ba, saboda soyayyar da yake yiwa Uludinta, da kuma yadda itama Khulud take sanshi, ta kuma d'aukarwa ranta komai zayyi mata, bazata tab'a ramawa ba, zaici arzikin soyayyar Khulud, zata kuma ta danne komai a ranta, ta kawar da komai, ta rink'a kula shi tana bashi girma da mutuncinsa, saboda Khulud, kuma koba komai, ai yana d'ebewa Khulud kewa, yana kuma sanyata cikin farin ciki da walwala, jin shiru yasa Khulud tab'a tace " My Sanah lafiya naji kinyi shiru? Sanah tayi saurin k'ak'aro murmushi tana girgiza kanta tace " bakomai My Ulud, kawai ina jin dad'i da farin ciki ne, Khulud ta kalle ta k'ura mata ido na wani lokaci kana cikin sanyin murya, tace " My Sanah ko baki san alak'a ta da Hanash ne? Sanah ta zaro idonta, tace " kai injiwa? Khulud tace " My Sanah nafi kowa saninki, nafi kowa sanin wacece ke, nafi kowa halayenki da d'abi'unki, dan girman Allah ki sanar dani gaskiyar abunda ke ranki gami da Hanash please, Sanah ta kuma yin dariya tana rik'o hannun Khulud cikin nata, tace " my Ulud ki kwantar da hankali, babu abinda ke raina, kawai dai ina mamaki ne, "mamakin me? Khulud ta tambaye ta idanta na kanta, Sanah tace " yadda akayi my Uludina ta fad'a tarkon love, Khulud tayi dariya tace " kai my Sanah, Allah nima ban san yadda akayi na fara ba, haka nan kawai na ji ni..... d'an shiru tayi, Sanah tace " kika ji me? Khulud ta turo bakinta, tace " nima ban sani ba, Sanah tace " a'a ina za'ayi haka ai dolanki ki fad'a man abinda kika ji, Khulud ta lura akwai abinda Sanah ke k'ok'arin b'oyewa dan haka cikin sanyin jiki tace " my Sanah! Sanah ta kalle ta, taga Khulud ta k'ura mata ido, rolling idanta Sanah tayi kana tace " me? Khulud tace " please kin ban damar cigaba da kula da Hanash, Sanah ta d'an yamutsa fuska tace " sai yanzu za'a nemi izinina bayan aikin gama ya gama, Khulud tayi dariya tace " ni dai please ni yes or no? Sanah tace " hmmmm sai bayan kin gama yanke hukuncin fad'awa a soyayyar sa? Khulud tace " my Sanah ba mutum ne ke yanke hukuncin fad'awa a soyayya ba, ita soyayyar ce take lokacin faruwar hakan, shiru Sanah tayi tana san tuna inda ta tab'a jin irin wad'annan kalaman, Khulud tace " nasan ba lalle ne yanzu ki fahimci hakan ba, amma akwai lokacin da ke da kanki zaki fad'awa wasu, Sanah ta shafa fuskar Khulud tace " karki damu kinji My Ulud, nayi farin ciki sosai da jin wannan labarin, Allah ya sanya alkhairi, Ubangiji yabar ku tare, ya kuma albarci soyayyarku, ya baku zuria ta gari, Khulud ta amsa da Amin, idanta yana kan Sanah, Khulud tace " Yayan su Zohal & Wajnah Waseef ne, Sabah tace " kai haba? Khulud tace " Allah da gaske uwarsu d'aya ubansu d'aya su uku ne kawai a wajen iyayensu, Sanah tayi dariya kana tace " kin san me? Khulud tayi saurin cewa " a'a, Sanah tace " naga Sir Moli fa, cikin zumud'i Khulud tace " kai a ina? Sanah tace " a makarantar mu, lecturer ne a department d'in mu, Khulud tace " kuma ya gane ki? Sanah tace " ya gane ni ko na gane shi? " D'an rainin hankali, Khulud tace " zaki fara ko? Sanah tayi dariya kana ta shiga bawa Khulud labarin had'uwarta da Sir Moli tun daga farko har k'arshe, amma ta kasa sanar da ita abinda ya shiga tsakaninsu, karo na farko a rayuwarta data b'oyewa Khulud wani abu, haka nan kawai taji bata san sanar da ita, Khulud tayi dariya kana tace " kai wallahi drmarku na birgeni, ashe an d'ora daga inda aka tsaya, dama ina nan dana sha kallo wallahi, Sanah ta tab'e baki, tace " rabu da rainin sense shi so yake ni na fara nuna na sanshi ko na gane shi, yadda zai samu damar wulak'anta ni, ya farfad'a man bak'ak'en maganganu san ranshi, cikin dariya Khulud tace " durk'usawa wada ai ba gajiyawa bane, my Sanah in kin nuna kin sanshi sai me, wani abun ne zai ragu daga jikinki? Sanah ta nuna kanta tana tab'e bakinta, had'i da yin rolling sexy eye d'inta, tace " ni na zan nuna na sanshi God forbid, ta fad'a tana nuna kanta, Khulud tayi dariya kana tace " Sir Moli witch kawai, Sanah ta zaro ido had'i da mik'ewa tsaye tace " what! ni? Khulud tace " eh mana in ba ke ba da wa!? Sanah ta d'auki pillow tana bin Khulud, Khulud tayi baya tana dariya tace " Sir Moli witch, Sanah ta bita da gudu tana jefa mata pillows, Khulud ta hau kan bed tana yiwa Sanah kwalo, had'i da tare pillows d'in, wayar Khulud ta soma ringing, Sanah tayi saurin d'aukar wayar tace " sake fad'a inba tsoro ba, Allah yanzu na taro miki March, Khulud ta rik'e kunnuwanta had'i da d'an girgiza kanta tace " I'm so sorry, ban k'arawa, Sanah tayi dariya kana ta mik'e mata wayar, da sauri ta amshi wayar had'i dayin picking, " hello my life, ya kike? "Lafiya lau, Alhamdulillah, an u, yace " ina lafiya kamar yadda kike, kin ci abinci? "Eh, kai fa, murmushi yayi mai sauti har dimples d'insa suka lotsa kana yace " yanzu Mimmee ta gama bani, Khulud tace " dear wai meyasa baka san cin abinci? Dariya yayi yace " ni ma ban sani ba, Mimmee dai tace haka nake tun ina Baby, idan kika zo sai ki wakilci Mimmee ki rink'a baki ko? Ya fad'a cikin shagwab'a, fuskarta ta rufe kamar yana ganinta, tace " hmmmm, yace " Papu yace nayi miki magana kan zasu zo wajen Abbu, tun last week na sanar dake amma kink'i cewa komai, murmushi tayi kana tace " dama jira nake ayi approving d'in mu kuma anyi, cike da mamaki yace " approving!? Tace " yes! Yace " waye zayyi approving d'in? Tace " My Sanah mana, ji yayi kamar ta watsa masa wuta, amma sai ya kanne yace " to tayi yanzu? Tace " eh tayi, dama ai na fad'a maka bata tab'a kin amincewa da abinda nake so, Allah baka ga yadda taji dad'i tayi murna da farin ciki ba, " shegiya karuwa 'yar iska ba, ai dole ta yarda saboda tana tsoran kar na tuna mata asirin iskancin da take yi, ya fad'a cikin ransa, a fili kuma yace " masha Allah, kana yace " yanzu if she's saying no , shikenan our true love has been cancel, da sauri tace " wallahi capital latter YES!, dan ban ko k'ara kallan inda kake balle nayi maka magana, so put it your mind albarkacin My Sanah kaci, ido Hanash ya runtse da k'arfi yana jin kamar zai mutu, yana jin yadda zuciyarsa ke k'una had'i da tafasa, in banda yana mugun san Khulud da tuni ya rabu da ita, amma rabuwa da ita dai-dai yake da fitar numfashinsa, daurewa yayi yace " ok any way, yanzu yaushe su Papu zasu zo? " Bari na nemi izini wajen my Sanah, zayyi magana yaji ta kashe wayar, wayar kawai Hanash yabi da kallo yana sak'e-sak'e da tunani a ransa, Khulud ta juya ta kalli Sanah tace " my Sanah! "na'am Sanah ta amsa, Khulud tace " wai iyayen su Hanash ne zasu zo, Sanah tayi saurin mik'ewa zaune tace " kai haba, yaushe? " Ai shine nace bari na tambaye ki, Sanah tace " ok bari naje na sanar da Mamu, in yaso sai ta sanarwa da Abbu ko? Khulud tace " ni dai a'a kunya nake ji, Sanah tace " to mu sanar da Aunty Halan inyaso saita sanarwa da Yaya Ziyad shi sai ya sanarwa Abbu da Didi, Khulud tace " ni dai kunya nake ji, Sanah tace " to za'ayi idan ba'a sanar da su ba? "Ko haka nan kawai zasu ga mutane da ka? Khulud zatayi magana Sanah ta mik'e, Khulud ma tayi saurin mik'ewa , Sanah zata fita Khulud ta rik'o tace " no, Sanah ta fisge ta fita da gudu, Khulud tayi saurin bin bayan ta, da gudu suka yi parlor, Abbu da Mamu na zaune suka gansu da gudu, Abbu yace " lafiya!? Sanah zatayi magana Khulud tayi saurin rufe mata baki, tana yak'e tace " bakomai Abbu, Sanah na k'ok'arin kwace bakinta ta d'aga hannunta alamar k'arya take, Mamu tace " wai ku meye haka? "Kun girma amma baku san kun girma ba, kuna abu irin na yaran goye, Sanah ta kwace bakinta tana hak'i, Khulud na k'ok'arin sake rufe mata bakin tace " iyayen Hanash zasu zasu zo, Khulud na jin Sanah ta fad'a ta saka kuka, Abbu yace " to ikon Allah meye abin kuka kuma? "Zonan kinji d'iyata ya fad'a yana mik'awa Khulud hunnu,, ba musu Khulud ta nufi wajen Abbu ta zauna kusa da shi, cikin rashin fahimta Mamu tace " waye Hanash? Sanah tace " saurayin Khulud ne, shine iyayensa suka ce suna san zuwa, shine tace wai kar a gaya maku kunya take ji, da gudu Khulud tayi bedroom d'insu cike da kunya, cikin mamaki Abbu ya kalli Mamu yace " dama kin san da maganar ne? Mamu tace " eh! Abbu ya kalli Sanah yana murmushin jin dad'i cikin murna yace " zanyi magana da Didi, sai na sanar daku ranar da zasu zo, Sanah tace " tom, kana ta nufi bedroom, ta iske Khulud, Khulud na ganinta mik'e tana dukan Sanah cikin wasa, Sanah tayi dariya tace " wannan duk murnar ce, uhnnn amaryar Hanash, Khulud ta kuma kaiwa Sanah duka, wayar Khulud ta soma ringing, Khulud tayi banza da wayar cike da murna Sanah tayi picking, tace " hello! jin muryarta yasa shi jin zafi har cikin ransa, " hello ta kuma cewa, sai da ya runtse idonsa kana yace " ina mai wayar? Sanah bata d'auki wani abu ba, tace " gata nan kusa dani, a dak'ile yace " bata, jikin Sanah a sanyaye ta mik'awa Khulud wayar tana yak'e, cikin ranta kuma tana mamakinsa, Khulud ta amshi wayar kana tayi masa bayanin komai, guntun murmushi yayi kana yace " kiyi mata godiya, Khulud tace " gata kayi mata da kanka, yace " no ba sai kin bani ba, kiyi mata kawai, nima sallah zanyi, shiru Khulud tayi batare data ce komai ba, yace " I love you, good night, bata bashi amsa ba, ta kashe wayar, kana ta tura masa text, _Ka sani ban tab'a auren mutumin da baya san my Sanah baya kuma shiri da ita duk son danake yi masa,_ _wallahi koda sanka zai zama ajalina muddin baka san my Sànàh ko babu good understanding tsakaninku zan iya hak'ura da kai,_ _na barka har abada na kuma manta da kai da rayuwarka_ _so gwara ma ka sani ka kuma lura,_ _muddin kana so na kana kuma san aure na ka kasance da ni har rai da mutuwa to ka fara koyar yadda zakayi kà so Sanah ka kuma yi mu'amula da ita,_ _dan ko a ranar d'aurin auren mu Sanah ta nuna bata amince da kai bà wallahi sai na fasa,_ Murmushin takaci Hanash yayi bayan ya gama karanta text d'in, yana jin inama zai iya rabuwa da Khulud da ya rabu da ita ya hutawa ransa da rayuwarsa, sai dai bai iya rabuwa da ita a yadda yake jin mugun santa har cikin kwakwalwarshi, text ya tura mata shima, _I'm so sorry if I hurt you_ _ba da wata manufa nayi hakan ba, amma kiyi hak'uri please,_ _gobe zanzo na baku hak'uri ke da our Sanah, I love you so much_ Murmushi tayi kana tayi cilli da wayar ta kwanta. Washe gari da wuri Sanah ta shirya kasancewar suna da lectures da Sir Moli 8:30am na safe, tun da wannan abun ya faru Sanah ta shiga taka tsantsan dashi, data ga suna da lectures dashi take sauri ta shiga class ta samu can baya lungu ta zauna, a hankali Sanah ta shiga cikin class d'in tana takawa a hankali, ta samu wajen a baya ta zauna tana jiran lokaci yayi ya shigo, kan motarsa ya danno cikin makarantar, a parking space yayi parking, ya kai wajen 15 minutes kana ya zuro k'afarsa d'aya waje, kai da kanin k'afar sanye cikin takalmin Nike, kasan mamallakin k'afar yana cin duniyarsa da tsinke، a hankali ya zuro d'aya k'afar kana ya fito gaba d'ayan sa, sanye yake cikin arnan Man material, mai laushi, color blue black, takalmi, agogo da hularsa black color, cikin nutsuwa ya d'auki laptop & brief case d'insa, ya fara takawa a hankali ya nufi class d'insu. Sir Moli na gaf da shigà yà fara jiyo hirar su rose, dan haka ya d'an tsaya kad'an, Sanah na zaune a baya taji wasu Christians suna hira, d'ayar mai suna Rose tace " ni fa ina mamakin Muslim, d'ayar tace " mamakin me? Rose tace " yadda suke bautawa wanda basu sani ba, ba kuma su tab'a ganinsa ba, d'ayar ta tab'e baki tace " nima abin nan yana bani mamaki fa, yanzu da zaka tambaya su ina Allah su yake shiru zasuyi suyi tsuru-tsuru, a zafafe Sanah ta mik'e ta nufi inda suke zaune, tana zuwa bata jira wata-wata ba ta kifawa kowacce mari bibbiyu, Sir Moli dake tsaye jikin window yayi saurin kallan Sanah cike da mamakin rashin tsoranta, dan dukkannin su gidiga-gidiga ne, masu k'irar k'atti babu wacce bazata iya sab'ar Sanah ta zagaye garin Kano kaf da ita ba, Rose da d'ayar suka mik'e da sauri cike da mamaki, suna kallan Sanah Rose dafe da kuncinta tace " kika mare mu? Sanah ta zaro idanta kamar gaske tace " ni yaushe na mare ku? Sir Moli ya gyara tsaiwarsa yana kallan ikon Allah, Rose tace " yanzu fa kika mare mu, Sanah tace " idan har da gaske kuke yi na mare ku, ku nuna min marin, Rose ta nuna kuncinta tace " gashi, Sanah ta kalli kuncin had'i da sanya hannunta ta rik'e fuskokinsu tana duddubawa kamar gaske, tace " ni fa banga komai ba, gaba d'aya ajin akayi tsit kowa ya maida hankalinsa kansu, Rose tace " kamar ya baki ga komai ba? Sanah tace " eh banga marin ba, amma ke tunda kina ganinsa kina iya nuna min shi na ganshi, d'ayar tace " ke karki raina mana wàyo, Sanah ta sanya hannunta ta rik'e hab'arta had'i yin sautin da bakinta, tana kallansu cike da rainin hankali, " in banda rainin hankali dama ana ganin mari ne? D'ayar ta fad'a, Sanah tayi murmushi kana tace " au dama ba'a ganin mari? Rose tace " tayaya za'a ga mari? Sanah tace " to yaya kika san na mare ki? Rose tace " naji shi ne, Sanah tace " yauwa anzo wajen, kin tabbata ba'a ganin mari, amma ana jinsa, dana mareki baki ganshi ba amma kinji shi har cikin kwakwalwarki da zuciyarki, to kamar yadda bakiga marin nan ba, amma kika yarda akwai shi, zuciyarki da kwakwalwarki suka amince suka kuma gaskata shi gaskiya ne, haka Allah Ubangijin mu mai komai da kowa yake, shi dayake shine Ubangijin gaskiya shiyasa ba'a ganinsa, amma zuciya, rai ,ruhi , kwakwalwa, duk suka yarda suka kuma amince akwai shi, zati da k'udurar Ubangijinmu tafi k'arfin ido ya ganshi, yafi k'arfin zuciya ta siffatanshi, yafi k'arfin rai ya misaltashi, kana ta kalli jakarta tace " yanzu Rose idan kika shigo ajin nan kika ga ba kowa sai wannan jakar kad'ai, kin san akwai mai ita, akwai kuma wanda yake mallakinsa ce, sannan kin tabbatar akwai wanda ya k'era ta ko? Rose tace " haka ne, duk wani da kika gani akwai meshi, Sanah tace " good, to kamar haka be akan duniya, Rose ko kwano kika gani ajiye kin san akwai meshi, balle kuma duniya da abinta ke cikinta, ke kanki kin san akwai mai ita, saboda babu abinda yake halittar kansa komai kika gani a duniya yinsa akayi, idan kika kalli shuke-shuke da ruwa, jini da mutum kad'ai ya isa ya tabbatar miki akwai Ubangijin gaskiya, so please ku bar irin wad'annan maganganun a cikin al'umma saboda hakan yana iya haifar da fitina, ayi ta kashe rayukan da basu ji ba, basu gani ba, ba su Rose kad'ai ba, duk wanda ke wajen sai da jikinsa da zuciyarsa tayi sanyi, Sanah ta koma inda take zaune ta zauna kamar babu abinda ya faru, Rose ta kalli Sanah tace " I'm sorry, then thank you so much, Sir Moli dake tsaye yayi guntun murmushi, yau karo na farko da Sanah tayi abu a rayuwarsa yaji ta burge shi, sosai yayi mugun mamakin basira da hikimarta, a hankali ya taka ya shiga class d'in, sai da ya gama koyar da su as usual kana ya fita. Hanash sai da ya tabbatar Sanah ta tafi makaranta kana ya shirya cikin Man lace, ash color, takalmi, agogonsa gucci, hularsa kalar aikin jikin kayan yayi masifar kyau, idan ka ganshi sai ka rantse bai san Hausa ba, dama abinka da bafulatani usul back and front, duk inda kake tunanin had'uwa ko kyan namiji Hanash ya kai koma in ce ya wuce, yana da bala'in kyau kamar aljani, dan da yawa wad'anda sukayi karatu tare basu yarda d'an Nigeria bane, waya ya ciro daga aljihunsa ya sanar da ita yazo yana set room, itama tayi kwalliya cikin riga da skirt na atamfa tayi simple make up, bakinta d'auke da sallama ta shiga, har k'asa ta durk'usa ta gaida shi, ya amsa fuska cike da fara'a, a hankali ta zauna akan sofa had'i da satar kallanshi, karaf suka had'a ido, tayi saurin sunkuyar da kanta k'asa, yayi murmushi cikin nutsuwa yace " ya dai ake satar kallo na, a fito kai tsaye a kalle ni mana, kiga angon naki sosai, kar sai daga baya kice nahi, tayi murmushi, yace " ina our Sanah, tana ji yace " our Sanah, tayi saurin d'ago kanta ta kalle shi cikin jin dad'i, tace " tana makarata, kansa ya d'an dafe yace " oh! zuwa fa nayi na bada hak'uri, ance jiya nayi laifi, dariya tayi had'i da saka hannu ta rufe face d'inta, yace " ya kukayi da Abbu yau? Tace " ai my Sanah bata dawo ba, dole sai idan ta dawo zamu ji komai, sannan koma meye kayi magana da ita kawai, duk abinda tace is okey to me, murmushi yayi yana danne abinda ke ransa, sosai sukayi hira kana da zai tafi ya mik'o mata laida, k'in amsa tayi, dan dama sun saba haka duk lokacin da zai mata kyauta sai ya sha fama kafin ta amsa, yace " to zaki fara ko? "Wannan ai ba naki bane ke kad'ai, ke da our Sanah ne, jin yace harda Sanah ta amsa had'i dayi masa godiya, har bakin mota ta raka shi ya fita, tana shiga gida ta aje kyautar tak'i b'ud'ewa tana jiran Sanah ta dawo. Ko da Abbu yajewa da Didi da maganar masu neman auren Khulud zasu zo, cewa yayi shi ina ruwansa ai shine ubanta yayi duk abinda ya dace kawai, hakan da Didi yayiwa Abbu yasa Abbu yaji dad'i sosai, Didi yana komawa gida ya sanar da Juju, jikinta a sanyaye tace " to ita Sanah fa? Didi yace " itama Allah zai kawo mata, mu dai addu'a ce tamu, Abbu ya sanar da Mamu ta fad'awa su Sanah cewa su zo ranar Friday, kana Abbu ya Sanar da Ziyad da Zafran, ko da Ziyad ya sanar da Halan itama cewa tàyi Sanah fa, Sanah yau da wuri ta dawo daga school, wanka tayi kana tayi sallah taci abinci, sai data gama komai kana Khulud ta d'auko ledar da Hanash ya kawo musu, tace " My Sanah Hanash yazo ganinki baki nan, amma yabar sak'o, Sanah tayi dariya kana tace " ayya dan Allah ki bashi hak'uri, Khulud tace " ai badamuwa ya fahimta yace zai dawo da weekend sai ku gaisa, Sanah ta amshi ledar ta bud'e wasu arnan perfumes suka gani masu shegen kyau da k'amshi, da gani kasan masu shegiyar tsada ne, Sanah tace " wow! amma gaskiya naji dad'in kyautar nan, please kice masa nagode sosai, Khulud tace " in ce masa kodai ki kira shi kiyi masa godiya da kanki, Sanah zatayi magana Mamu ta shigo, a bakin bed ta zauna kana ta kallesu tace " to ku sanar da su suzo ranar juma'a, Khulud tasa hannu ta rufe fuskarta, Mamu tace " kwaji dashi dai 'yan nema, ta fita tana dariya, Sanah tace " kira shi a fad'a masa, ba musu Khulud tayi dialing number sa, kashewa yayi ya kira ta, tayi picking sai da ta gaida shi kana tace " magana zakuyi da my Sanah, yayi murmushin k'arfin hali yace " ok bata, Sanah ta amsa tana murmushi ta gaida shi, ya amsa ba yabo babu fallasa, godiyar perfumes ta fara yi masa, kana ta sanar dashi sak'on Abbu, yayi d'an murmushi yace " nagode, a tak'aice, itama murmushin tayi kana ta mik'awa Khulud wayar, suka shiga shan love, suna gama wayar Hanash ya nufi part d'insu Mimmee, a parlor ya tararda su, har k'asa ya durk'usa ya gaida su, suka amsa cikin so da k'auna, zayyi magana Papu yace " ya kukayi a BUK? Kansa ya shafa kana yace " Papu ban samu ganin shi ba, Papu yace " kamar ya baka ganshi ba? Hanash yace " naje har sau biyu amma ban samu ganinshi ba, kana yace " wai Papu dole ne sai su Zohal sun cigaba da karatu? " Mai zai hana ayi musu aure kawai, Allah yawancin malaman jami'a 'yan iska ne, basu da wani aiki sai lalata yaran mutane, a d'an hasale Papu yace " saboda baka san suyi karatun shiyasa kak'i maida hankali? A hankali Hanash yace " kayi hak'uri Papu ban san magana ta zata b'ata maka rai ba, kayi hak'uri in sha Allah ranar Monday zan koma, zan kuma yi iya bakin k'ok'ari na, zuciyar Papu tayi sanyi jin kalaman Hanash, cikin sanyi Papu yace " yauwa nagode Allah yayi maka albarka, Ubangiji ya baka zuri'a ta gari, Allah ya albarkaci rayuwarka, Hanash da Mimmee suka amsa da Amin, Papu ya kalle shi yace " naga kamar da magana a bakinka ko? Hanash ya d'an shafa kansa kana yace " eh!, Papu ya karkata hankalinsa gaba d'aya gare shi, yace " ina jinka, baki Hanash ya d'an turo kana yace " to ka daina kallo na Papu, yayi maganar cike da shagwab'a, Papu yayi dariya yace " nama rufe ido na, Hanash yace " iyayen Khulud ne suka ce ku je ranar juma'a, Papu da Mimmee suka bud'e baki cikin matsananciyar murna, Papu yace " kai masha Allah, rabon danaji labari mai dad'i irin wannan har na manta, Hanash yasa hannu ya rufe fuskarsa wai shi kunya, Papu yace " kayi min text d'in details na gidan, Hanash yace " tom, Mimmee ta mik'e zata fita, Papu yace " ina zaki? Tace " wajen Jadda mana a sanar mata abin farin ciki, abinda ta dad'e tana jira, Zohal da Wajnah dake lab'e suka fito da gudu suka yi waje suna dariya, sukace " Mimmee mu zamuyi mata albishirin, koda suka sanar da ita bata yarda ba, sai da tazo har part d'in Mimmee, suka fad'a mata da kansu kana ta yarda, dan murna har rawa ta taka. Kamar yadda aka tsara ranar Friday iyayen Hanash suka je, Yayyan Papu biyu da abokinsa ne suka je, an karb'e su hannu bibbiyu, cikin mutunci da girmamawa, suka gabatar da kansu, ashema sun san juna sosai, Papu abokin Didi da Abbu ne tare sukayi primary da secondary, set d'in su d'aya, sosai sukayi farin cikin sake ganin juna rayuwarsu, dan sun nemi juna har sun gaji da neman junansu har sun hak'ura, dayake an san juna Abbu yace karsu damu zai sanar dasu duk halin da ake ciki, a cikin kwana biyu Abbu yayi bincike sosai akan Hanash dama gidansu, babu wani abun k'i a tattare dasu, sai ma yabo da suka samu daga wajen mutane, sosai Abbu da Didi sukayi farin cikin jin yabon da al'umma keyiwa Wassef, duk da dama sun san halayyarsa, Abbu ne ya kira a waya cewar sun gama duk abinda ya kamata, mutanen da suka zo da farko su suka k'ara dawowa, duk abinda ya kamata sunyi, sun kawo goro da alawa da kud'in neman aure, goro da alawa kad'ai Abbu ya amsa shima dakyar, yace " sadaki kawai zasu kawo shima sai ranar d'aurin aure, aka sanya bikin wata biyu kad'ai, shima dan Mamu ta dage ne, saboda tanasan shirya 'yarta sosai, amma da wata d'aya aka saka. Tafiya kawai take a matuk'ar gajiye lik'is, dan dakyar take iya d'aga k'afarta, ga yauma Aarib yana busy bazai samu damar zuwa d'aukarta ba, fita tayi daga get tana neman mai adai-daita, daga gefenta taji haushin kare, a hankali ta juya taga wasu tik'a-tik'an karnuka guda biyu, suna lasar harshe, da k'arfi gabanta ya fad'i, jikinta ya d'auki kerrrma, saurin tafiyarta ta k'ara, taga karnukan sun mik'e daga kwancen da suke, suna kallanta, juyawa tayi taga lungun babu kowa, dan haka tsoro ya k'ara kama ta, ta fara gudu-gudu sauri-sauri, ganin yadda jikinta ke tsuma yasa karnukan zaton ko bata da gaskiya, san haka suma suka fara binta a hankali suna haushi, jin haushinsu yayi masifar gigita ta, dan haka ta tattare doguwar rigar material dake jikinta, ta zage iya k'arfinta ta soma gudu, aiko karnukan suka ce dawa Allah ya had'a mu, suka bi bayanta a guje, ganin sun biyota yasata yin cilli da mayafinta datayi rolling dashi, gaba d'aya gashinta kanta ya zubo bayanta ya barbaje, ya hargitse, tayi kuma yin cilli da takalmi da jakarta, tana gudun tana kuka, tana kuma juyawa baya tana kallan yadda karnukan ke binta, direct baya Sanah ta koma ta nufi cikin makarantar, karnukan suka bi ta, a hankali ya fito daga office d'insa, ya nufi motarsa cikin takunsa na izza, cikin nutsuwa ya bud'e d'ayan b'angaren ya ajiye laptop da brief case d'insa, kana ya zagayo zai shiga motar, hangota yayi tayiyo kansa gadan-gadan, American dogs na biye da ita, bako d'an kwalli bare takalmi da mayafi, sai iska dake faman kad'awa tana yin baya da rigar jikinta, had'i da d'aukar gashin kanta yayi sama ya barbazu, ganin direct shi ta nufo yasa shi zaro ido, had'i da girgiza mata kansa alamar no, saboda yadda compound d'in ke cike da students, ganin bata fasa nufo shi ba, yasa shi ce mata " a'a fa, amma kafin yayi aune ta fad'a kansa, daga shi har ita sukayi baya, suka fad'i k'asa, shiya fad'i a k'asa ita kuma ta kansa, gashinta ya bazu ya rufe musu fuska, fuskarta kan tashi, bakinta kan nashi, hancinta na gogar nashi, hannayenta duka akan k'irjinsa, ita kuma gaba d'ayanta akan jikinsa................ MOMYN ZARAH _*RASHIN SANI.......*_ *HAUWA A USMAN* _JIDDARH_ ```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh``` 2⃣4⃣ Gaba d'aya Malamai da students dake wajen, suka tsaya cak had'i da sanya hannu suka rufe bakin su, cikin tsantsar mamaki, suna tunanin wanne irin hukunci Sir Aryan zai yiwa Sanah, gashin Sanah ya rufe musu fuskarsu ta yadda babu mai iya ganin fuskokin su, eyeball to eyeball suke kallan junansu, dukkan su sun shagala suna kallan juna, daga shi har ita babu wanda yayi motsi balle suyi k'ok'arin tashi, karnukan kuwa yadda kasan anyi musu magana suka juya suka koma, bakin Sanah nakan na Sir Moli, sun k'urawa juna ido basu ko blinking, Leem dake tsaye ya zuba musu ido fuskarsa d'auke da murmushi, d'an gyaran murya Leem yayi had'i da cewa " a compound dai ake, da saurin Sanah ta mik'ewa tsaye had'i da duk'ar da kanta k'asa cike da kunya, shima mik'ewa yayi had'i da tsuke fuskarta, ya had'e rai tamau, yadda kasan bai tab'a yin dariya ba, a hankali ta d'ago kanta cikin rawar murya tace " kayi hak'uri, ta fad'a tana gyara gashin kanta, daya zubo mata, tasa hannu ta mayar dashi baya, harara ya watsa mata batare dayace mata komai ba ya shiga motar, gaba d'aya mutanen dake wajen tsananin mamaki ne ya hana su yin koda kwakkwaran motsi ne, Leem ya kalli Sanah yace " shiga mu tafi, kai ta girgiza masa alamar a'a, Sir Moli ya kalleta cikin takaici yaga yadda jama'a ke kallanta, wasu ma sun shagala da kallanta, sun k'ura mata ido kamar mayu, gata jikinta babu ko d'an kwali babbe mayafi, jajayen idansa, dasuka gama komawa pure red saboda tsabar b'acin rai, ya d'ago ya kalle ta dasu kawai, ta gane abinda yake nufi, jikinta na kerrrma ta bud'e bayan motar zata shiga, cikin masifa yace " driver ki ne ni? Da sauri ta rufe k'ofar baya ta bud'e ta gaba ta shiga, Leem zayyi magana Sir Moli ya figi motar cikin b'acin rai, batare daya kalli inda take ba yace " ina kika zubar da kayanki? Cikin rawar murya tace " waccen lungun ta fad'a tana nuna masa lungun da hannunta, bai kuma magana ba, yayi hanyar data nuna masa, parking yayi a inda yaga jakarta da mayafinta, bayyi mata magana ba ta fita da sauri, jikinta na rawa ta d'auki mayafinta ta yafa, kana ta d'auki takalmi da jakarta, ta bud'e motar ta shiga, kanta a k'asa, dan tayi mugun tsorata dashi, musamman yadda kalar idansa ta canja kala in few sec, a k'ofar gidan su yayi parking batare dayace mata komai ba, ya kauda kansa gefe, jikinta a sanyaye ta bud'e motar ta fita, zatayi magana ya bugi motar yayi gaba, bayan motar tabi kallo kana ta shiga gida. Tana shiga cikin harabar gidan, ta iske motar Hanash, daga bayanta taji Khulud na kiranta, da sauri ta juya bayanta, Khulud ta nufo ta cikin fara'a, tsayawa tayi cak tana bin jikin Sanah da kallo, kana tace " my Sanah lafiya? Ta fad'a tana bin jikin Sanah da kallo, itama jikinta tabi da kallo kana tayi dariya tace " karnuka ne suka kusa murmushe ni, Khulud ta zaro ido tace " wayyo a ina? Sanah ta bata labarin duk abinda ya faru, Khulud tayi dariya tace " baki tashi sanin Sir Moli sai kinga bala'i, wallahi in nine shi banko kallanki, Sanah ta tab'a bakinta tace " shi ya sani, Khulud ta rik'o hannun Sanah tace " Hanash tun d'azu yake jiranki kan maganar shirye-shiryen biki, Sanah tace " ayya to muje, tabi bayanta, tare suka shiga set room d'in, hannunsu sark'e cikin na juna, Sanah tayi dariya tace " ango kasha k'amshi, ayi man afuwa na bar ango da kansa yana zaman jira, yayi murmushi yana bin kayan jikinta da kallo, " iskancin yarinyar nan fa ya wuce tunanin, wato har a k'asa take kwanciya wannan shegen d'an iskan ya hau kanta, a fili kuma yace " ah ai girmanki ne, ba damuwa, kuma naga yanzu kika dawo, kamar ma a gajiye kike ko? Tayi murmushi tana zama akan sofa, tace " badamuwa our groom manta da gajiya, ya kuma yin murmushi mai sauti wanda har sai da dimple d'insa suka lutsa, yace " badamuwa our Sanah kije ki huta, tunda yau Friday kinga gobe weekend ne muna da free time sosai, sai in dawo muyi magana ko? Khulud na tsaye gafe ta k'ura masa ido, tana jin sansa da k'aunarsa yana ratsa duk wata gab'a da jijiya dake jikinta, tana jin zata iya bada rayuwarta akansa, ta rasa meyasa yake yi mata bala'in kama da Seif Ali Khan, ido kawai zai fi Saif Ali Khan, da yake Hanash akwai manyan ido dara-dara, shi kuma Saif abu d'aya zaifi Hanash d'inta, shine fari, da yake Hanash ba fari bane sosai, skin color d'insa chocolate color ne, mai shegen kyau, wanda wasu mutanen ma suke ganin kamar sunfi fararen fata kyau, fakaitar idan Sanah yayi, ya kashewa Khulud ido d'aya dan ya lura da irin kallan datake yi masa, da sauri ta kawar da kanta gefe tana murmushi, Sanah tace " to in baku waje ne? Dan ta lura da abinda ke faruwa a tsakaninsu, Khulud tayi saurin cewa " me akayi my Sanah? Sanah ta kalle ta tana dariya tace " oho maki ban sani ba, karki raina man wayo, Hanash yace " a'a our Sanah karki tafi, Sanah tace " to ai gani nayi an kira ni an zaunar dani ana shan love, ba'a ko jin kunya ta balle ayi man kara da kawaici, " hmmm kaji shigiya wai ita 'yar duniya, kowa zata nunawa ita ta Allah ce, fasik'a kawai shegiya, ya fad'a cikin ransa, a fili kuma yace " ayi mana afuwa kin san abun ne ba'a iya b'oye shi, wad'anda suke yin haramtacciyar soyayya ma suke bainawa duniya, ba kunya ba tsoran Allah, balle mu tamu mai tsarki, daga Sanah har Khulud babu wanda ya fuskanci abinda yake nufi, duk sukayi dariya, saboda Sanah tabar wajen ya kuma cewa " our Sanah kije kiyi wanka ciki abinci goben sai na dawo muyi magana, " badamuwa in dai hakan yayi maka, yak'e Hanash ya kuma dan ya gaji da ganinta da kuma magana da ita, Allah Allah yake yi tabar wajen, yace " badamuwa kije, tayi dariya kana ta mik'e tayi mishi sallama tayi cikin gida. Direct part d'in Halan ta nufa, ta iske su zaune a parlor ita da yaran Khair sai rigima yake yi, Sanah tace " kai dai wannan yaro anyi jarababbe, kai ke nan kullum bakinka baya shiru? Halan dariya tace " ya za'ayi bakinsa yayi shiru bayan jinin Sanah na yawo a jikinsa, Sanah ta d'an turo baki tace " kwaji dashi, kowacce yaronta yake kuka sai kuce ni ya biyo, sai kace ni kad'ai keda bakin magana, Halan tace " ai dole muce ke suke biyowa, tunda kinfi kowa bakin mai da magana, Sanah ta mik'e tayi hanayar bathroom tana cewa " ku ai ta kunne kuke magana, Halan tayi dariya, wanka Sanah tayi ta zura doguwar riga mara nauyi, taci abinci ta kwanta. Washe gari Hanash bayyi niyyar zuwa ba, amma saboda kar ya b'atawa Khulud rai yasashi zuwa, cikin shadda brown color yazo, yayi masifar kyau, a waya ya kira Khulud ya sanar da ita yazo, ta kalli Sanah tace " to oganniyya tashi ki shirya Hanash yana waje, ba musu Sanah ta mik'e ta zura dogon hijab, suka fita a set room suka iske shi zaune as usual gabansa an jera masa kayan motsa baki, Khulud ta durk'usa har k'asa ta gaida shi, Sanah ta kalle shi cikin mamaki, baki tad'an tab'e batare dasun ganta ba, kana ta zauna akan sofa, tace " ango ina yini? Fuskarsa a sake ya amsa da lafiya lau, amma deep down yana jin kamar ya shak'eta, yace " ya kike? ta amsa da " Alhamdulillah, yace " dama kan shirye-shiryen biki ne, nace ko kuna da wasu abun da kuke san kuyi? D'an kallan Khulud Sanah tayi, Khulud tayi mata alama da tayi magana, Sanah ta d'anyi gyaran murya kana tace " to mu dai har yanzu bamuyi wani plan ba, amma ina ganin kar muyi bidi'a a bikin, saboda neman albarkar aure da kuma zuria ta gari, duk auren da zakaga an zage anyi bad'ala baya albarka saboda duk an gama janye tallafi da albarkar auren tun daga waje, so ina ganin muyi walima da wa'azi kawai zaifi ko? "Shegiya munafuka uwar tsari, a fuska da baki kamar ta Allah, amma a zuciya da bad'iri ko fir'auna albarka, ya fad'a cikin ransa, yak'e yayi kana yace " Alhamdulillah da ra'ayin mu yazo d'aya, dama nima bani da ra'ayin bidi'a a biki, saboda duk abinda Allah yace kar ayi, to bashin shi shine abinda yafi a'ala da masalaha (alkhairi), amma idan aka k'iji aka k'i bin dokar Allah, aka kauce hanya saboda ra'ayin mu, to za'aga ba dai-dai, shiyasa auren yanzu yawanci baya albarka, daga wannan sai wannan, miji na fama, mata na fama suma iyayen ba'a barsu sun zauna lafiya hankalinsu ya kwanta ba, so nima dai ina ganin muyi bikin mu cikin bin dokin Allah, muyi walima kawai kamar yadda addini ya tanadar, mu kuma yi wa'azi dan fad'akar da al'umma. Sanah tace " gaskiya dai nima ina ganin hakan zai fi, yace " to maganar lefe fa? " Shi kuma ya kuke ganin za'ayi dashi? Sanah tace " duk yadda kukayi dai-dai ne, mu bamu da matsala, yace " ok zanyi magana da Mimmee sai muji ta bakinta, Sanah tace " hakan ma yayi, yace " maganar hidimomin biki nawa ne zai isheku? Sanah tace " no karka damu Abbu yace " kar mu karb'i komai daga gareka, dan kaima d'ansa ne, ko ba gidan nan kake neman aure ba, shi zai tsaya maka, dan haka duk abinda muke so mu tambaye shi, Hanash yayi murmushin jin dad'i, a ransa yace " kowa a gidan mutum kirki ne, amma banda wannan shegiyar, kodan dama ance a duk zuri'a sai an samu zakka, a fili kuma yace " ai hakk'i nane dan haka dole nima nayi wani abun, Sanah zatayi magana yayi cewa " please! ku barni nima nayi iya yina, "Ok tace kana suka cigaba da maganar shirye-shiryen biki. Bayan Hanash ya tafi direct part d'in Halan suka nufa, tana kitchen tana aikin abincin dare, suka shiga, amsar aikin sukayi sunayi Sanah na sanar da ita yadda sukayi da Hanash, itama Halan sosai ta goyi bayan tsarin da sukayi, sai da suka gama girkin kana sukayi part d'in Mamu suka sanar da ita komai, itama taji dad'in hakan, dan haka ta tashi ta nufi part d'in Juju ta sanar da ita, ita dayake bata cewa komai, sai dai tabi su da addu'a, shima Hanash yana komawa gida ya sanar da Mimmee da Papu yadda sukayi, tace " eh gaskiya wannan tsarin yayi, waye ya kawo tsarin, baki ya tab'a kana yace " Sanah, yana fad'a ta gane wacce basa shiri ce, tayi dariya tace " kai amma yarinyar tana da hankali da tunani, wallahi har naji ta burge ni, Hanash yace " hmmmmm Mimmee baki san wacece Sanah bane, tayi murmushi batare datace komai ba, yace " Mimmee ya maganar laifi? Tayi murmushi tace " in sha next week za'aka kai, kaga saura 3 weeks kenan lokacin, ya amsa da Allah ya kaimu, tace " Amin ya Allah. Sannu bata hana zuwa sai dai a dad'e ba'aje ba, rana bata k'arya sai dai uwar d'iya taji kunya, duk abinda aka sakawa lokaci komai daren dad'ewa zai zo koda shekara dubu ne, yau gaba d'aya gidan Hard'o ya kacame da girke-girken tarbar 'yan kawo lefe, kasancewar yau ne ranar kawo lefen, sosai ake ta aikin girki, an shirya abinci da snacks kala-kala, manya-manyan tray aka shirya wajen guda 30 d'auke da samosa, spring grl, pepper chicken, donut, meat pie cincin, duk anyi raping d'insu da foil papers, an ajiyesu a gefe wad'anda za'a bawa masu kawo lefen ne idan sun tashi tafiya, su tafi dashi as tukwici, a part d'in Mamu aka shirya amsa lefen, dan haka su Khulud suna part d'in Halan, yayinda gaba d'aya mutanen gidan suka hallara a part d'in Mamu ana jiran su, wajen k'arfe 5:00pm na yamma lumtsuma-lumtsuma motoci suka fara parking, a harabar gidan, had'add'un mata 'yan boko suka fito, su Halan ne sukayi musu iso har part d'in Mamu, aka tare su hannu bibbiyu cikin sakin fuska, saitin akwatuna biyu na company Victoria Secret, k'irar 2019, new design aka shigar dasu part d'in Mamu, jama'a 'yan amsar lefe suka shiga bud'awa, komai na cikin akwatin dozin biyu ne 24, har da key d'in Range Rover da tikect na d'in America & Dubai, na zuwa honeymoon, kowa ya yaba da lefen sosai, bayan an gama ganin lefen kana aka shiga cin abinci da shaye-shayen drinks, da suka tashi tafiya aka basu tray d'auke da snacks. Sosai ta kowanne b'angare aka shiga shirye-shiryen biki haik'an, Mamu ta dake sosai wajen shirya d'iyarta, ta shiga tsumata da magunguna kala-kala, aka fara yi musu gyaran jiki dilka da halawa, daga Sudan Mamu ta d'auko mai gyaran jikin Sanah da Khulud musamman, aiko nan da nan suka shiga shek'i suna k'alli, kyansu ya k'ara fitowa sosai, tunda biki ya taho gadan-gadan Sanah ta daina zuwa makaranta, saboda sunyi busy da yawa kullum suna faman yawan kasuwa, har Halan bata zama kullum tana nan da can, bayan an bugo invitation card, Khulud ta mik'awa Sanah tace " gasu nan ko kina da wanda zaki gayyata d'aurin aure, Sanah tace " bani da wanda zan gayyata, Khulud tace " har Sir Moli, tayi maganar idanta yana kan wayarta, Sanah ta zaro ido waje tace " wa kika ce? Khulud tace " Sir Moli nace, tayi maganar idanta yana kan phone, Sanah ta jefa mata pillow tace " kinyi magana kinyi kamar bake kikayi ba, Khulud tace " eh meye a ciki? "Cewa nayi ki gayyato Sir Moli yazo d'aurin aure, in kuma baki gayyatarsa ni zan kai mishi IV da kaina, Sanah tace " tab so kike ya samu damar cimin mutunci kenan, Khulud tace " dan Allah ki gayyace shi, Sanah tace " ke! wai meye haka ne, Allah ban gayyatarsa, Khulud tace " shikenan ni zan gayyace shi, kuma Allah sai kin raka ni har office d'insa gobe na kai masa, Sanah tace " indai wannan ne ba damuwa muje zan raka ki Allah ya kaimu goben,, Khulud ta amsa da " amin. Washe gari wajen 10:30am suka shirya suka nufi BUK, har cikin makarantar Aarib ya kai su, yace " na tafi kona jira ku? Sanah tace " no ba dad'ewa zamuyi ba, yace " ok badamuwa ina jiranku, Sanah na sanye da riga da skirt na atamfa, d'inki yayi masifar yi mata kyau, yabi jikinta, ta yafa mayafi a kafad'arta, sai shek'i suke abinka dama da amsu kyau, balle kuma yanzu an k'ara da gyaran jiki har kala-kala, sai shek'e suke suna d'aukar ido, a k'ofar office d'insa suka tsaya, Sanah ta kalli Khulud tace " sai kiyi knocking ko? Khulud tayi murmushi tace " tarihi ya maimaita kansa kenan, Sanah tace " me? Khulud tace " kin manta a Roni mun tab'a yin irin haka, Sanah tayi dariya tace " haka ne, ranar da kika matsa sai muje ko? Khulud tayi murmushi kana tayi knocking had'i dayin sallama, tunda suka tsaya Sir Moli na hango su ta cikin glass, yana kuma yijo hirarsu, sosai ya k'ura musu ido yana kallansu, muryarsa a dak'ile yace " waye? Still idanshi na kansu na cikin glass, rolling sexy eye d'inta tayi had'i da tab'e baki, Khulud tayi murmushi had'i da girgiza kanta tace " Sanah ce Sir, Sanah ta zaro ido waje, tace " meyasa zaki ce ni bazaki ce ke ba? Khulud tace " yadda zaifi ganewa mana, idan nace mishi Khulud ce sai yayi dogon nazari kafin ya gane, amma danace Sanah zaifi saurin ganewa, duk abinda suke yana jinsu, cikin izza yace " wacece Sanah? Sanah ta kalli Khulud had'i da zare mata ido, tana yi mata alamar kin gani ko? Khulud tace " Sir nice Khulud Rawan your student, " in.. yace a tak'aice, zaune suka iske shi akan sofa, Khulud ta durk'usa har k'asa ta gaidashi, ya amsa fuskarsa a sake, yace " masha Allah su Khulud an girma, tayi murmushi, Sanah na daga tsayen tace " ina wuni? Banza yayi da ita baiko kalli inda take ba, Khulud ta kalli Sanah tace " ki bashi to, Sanah " au to kana ta ciro IV daga cikin jaka ta mik'a masa, ya amsa batare daya kalli inda take ba, Khulud tace " katin d'aurin mu ne, shine nace kai zamu fara gayyata, katin ya sub'uce daga hannunsa, yayi saurin d'auka cikin fara'a yace " masha Allah, na tayaki murna Ubangiji ya sanya alkhairi, Khulud ta kasa amsawa sai Sanah ce tace " Amin, baiko kalli inda take ba, Khulud tace " Sir kullum sai na tambayeka, yayi murmushi yace " ayya ni ma ina sane dake, naso na tambaye ki, sai dai babu wanda zan tambaya, Sanah ta gane abinda yake nufi, da ita yake, wato girman kanshi bazai barshi ya iya tambayarta ba, Khulud tayi murmushi tace " Sir dan Allah kazo, yace " in sha Allah zanzo, waye ango? Sanah tace " wannan wanda ya shigo office d'inka 2 times unexpected, of head, with out your permission, ya gane wanda take nufi, wanda ya shigo ya ganshi yana goge mata cikinta, da lokacin daya shigo ya kamasu yana shan bakinta, amma sai yayi kamar bai ji ta ba, ya kalli Khulud ya kuma cewa " waye angon? Khulud tayi murmushi tace " sunanshi Hanash Waseef, Sir Moli yace " Allah ya kaimu lokacin, suka amsa da amin, Sanah na tsaye ji take kamar zata fashe saboda dizgin da yayi mata, Sanah ta kalli Khulud tace " sai ki tashi mu tafi ko? Khulud ta kuma yin murmushi kana tayiwa Sir Moli sallama suka tafi, suna fita ya bud'e IV d'in yaga saura just 4 dayas d'aurin auren, Sanah ko masifa taitayiwa Khulud wai ta kawo ta an wulak'anta, bayan kwana biyu ana saura kwana biyu d'aurin aure 'yar Sudan ta zana musu arnan k'unshi mai matsiyacin kyau, mai black and golden color, aka gyara musu gashin kansu, suka fito d'asss dasu kamar amaren indiyawa, ranar alhamis akayi walima ana gobe d'aurin aure, Hanash k'in zama gida d'aya dasu Mimmee yayi, d'aya daga cikin gidajen Papu dake Nasarawa GRA Kano, aka gyara, gidan yayi masifar had'uwa kamar gidan film d'in hate story 3, sosai gidan ya had'u, Abbu yayi bajibta dan zagewa yayi sosai ya fitar da 'yarsa kunya, daga China yayi oder komai, even spoon daga China aka shigo masa dashi, Royal bed d'aya aka saka sai Dubai bed d'aya, da Italian bed d'aya, ya kama 3 bedroom, 2 parlor, including kitchen daya gaji da had'uwa shima and dinning table, gidan kam ya had'u iya had'uwa, ranar juma'a aka shirya za'a d'aura aure da safe da yamma ayi wa'azi then akai amarya. Ranar Friday da misalin k'arfe 10:30am na safe, dubbun mutane suka shaida d'aurin auren Khulud Rawan & Hanash Waseef, akan sadaki 1 million naira, dakyar Abbu ya karb'i sadakin, dan shammatarsa ma sukayi, ango Hanash sanye cikin matsiyar shadda wacce a k'alla kud'inta zai kai 300k, takalmi da agogonsa duk designer, sai gaisawa yake yi da mutane, idanshi ya sauka akan Sir Aryan Moli, dake tsaye yana gaisawa da mutane shima fuskarsa d'auke da fara'a, ji yayi ransa ya b'aci, " wato sai da wannan shegiyar yarinyar ta gayyato min abokin fasik'ancinta wajen d'aurin aure, ya fad'a cikin ranshi, Sir Moli na sanye cikin normal yard, fari tasss kana hango har singlet d'in jikinsa, yayi masifar yin kyau sosai, yana niyyar shiga mota Aarib ya hangoshi, ya k'arasa wajensa da sauri, hannun Aarib ya mik'a masa suka gaisa kana yace " malaminsu Sanah ko? Dan ya sanshi tun a Roni ya kuma gane shi, murmushi Aryan yayi kana yace " eh, Aarib yace " mu shiga ciki mana, Sir Moli yace " no ba sai na shiga ciki ba, tafiya zanyi, Aarib yace " no please ka shiga ciki na turo maka su ku gaisa, dakyar Sir Moli ya yarda ya shiga ciki, part d'in Seeya ne bakowa, dan haka can Aarib ya nufa da Sir Moli, a parlor ya zaunar dashi kana yace " bari naje na turo maka su, Sir Moli ya amsa da "to, Sanah data shiga wanka a part d'in, kasancewar sauran part d'in ciki yake da jama ta fito d'auke da gutun towel, hannunta rik'e da wani towel d'in tana tsane ruwan kanta, gashin kanta duk ya mammanne mata a jiki, tana wak'ar Celine Dion new day has come, tana wak'ar tana rawa tana kad'a boom-boom d'insa, kwata-kwata bata lura da Sir Moli ba, shi ko tunda ta fito daga bathroom idansa yake kanta, hand drear ta d'auko ta gyara gashin kanta yayi masifar kyau,, kana ta fara shafa lotion a jikinta, tana shafa man tana rawa da d'an tsalle, tana yarfa gashin kanta, tana cigaba da yin wak'ar, sai da ta fesa body spray a jikinta, kana ta d'auko pant zata saka, tana k'ok'arin sakin towel d'in dake jikinta, taji muryarshi can k'asan mak'ogwaro yace " no please, ya fad'a kamar mai koyan magana, a firgice ta juyo danta tabbatarwa kanta gaskiyar abinda taji, zaune ta ganshi akan sofa idanuwansa sunyi canja kala , sunyi masifar yin jajir, kamar gauta, wata mahaukaciyar gigitacciyar k'ara ta saki da gaba d'aya gidan sai da ya amsa, dai-dai lokacin Hanash ya shigo parlor'n............. MOMYN ZARAH _*RASHIN SANI.......*_ *HAUWA A USMAN* _JIDDARH_ ```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh``` 2⃣5⃣ Sir Moli gyara zamansa yayi ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya, yana bin dukkan su dan kallo, Hanash dubansa yakai kan pant da bra d'in Sanah dake zube a k'asa, kana ya bita da kallo tun daga sama har k'asa, kansa ya girgiza kana yace " Allah ya kyauta, ya juya ya fita, yana tunnanin why Khulud ta kirashi tace su had'u a part d'in, kiran Khulud ya shigo wayar Hanash, sai da ya d'an saita kansa kana yace " hello Mrs Hanash Waseef, murmushi tayi kana tace " please ka d'an jira in ina zuwa yanzu part d'in, da sauri yace " no ni ma banje ba, ina cikin mutane ki bani nan da 20 minutes idan na gama zan kira ki, ya fad'i hakan ne dan kwara-kwata baya san b'ata musu wannan mahimmiyar ranar, mai cike da tarihi gami da farin ciki, dan yasan muddin Khulud taga abinda ya gani yau sai Allah, yasan zata kasance bak'ar rana kuma mummunar rana a gareta, wanda shi bazai tab'a san ranar auren su ta zame mata bak'ar rana ba, ni ko nace hmmm Hanash wannan a naka tunanin kenan, tsakanin Khulud da Sanah sun wuce haka, "ok Khulud tace, kana ta rufe wayarta. Hanash na fita Aryan Moli ya mik'e cikin takunsa na isa da tak'ama ya nufe ta, tsaye take cak ta kasa koda motsi, ganin ya nufo ta direct yasa ta saurin juyawa da gudu zata shiga bedroom, cikin zafin nama yayi wuf ya rik'o ta, baki ta bud'e tana da niyyar yin ihuuuu, yayi saurin sanya hannunsa ya rufe mata bakinta, had'i da tura ta jikin bango ya matse ta, still hannunshi nakan bakinta, ido suka zubawa juna na tsayin lokaci, yayinda gaba d'aya jikin Sanah ke kerrrma ga ba damar yin magana dan ya rufe mata baki, matseta ya k'ara yi sosai a jikin bangon, while yana kallanta ido cikin ido, muryarsa can k'asa yace " meyasa baki da kunya? Da ido tayi mishi alamar me nayi? Yace " abinda kikayi yanzu, da idanta ta kuma bashi amsar " a gidan mu nake, "ok anyway, yace had'i d'age kafad'arsa, irin I don't care, sakinta yayi ya juya zai tafi, tsoki taja had'i da rolling sexy eyes d'inta, ta girgiza kanta ta juya da niyyar shiga bedroom da sauri, santsin tails ne ya kwashe ta tayi baya zata fad'i, cikin zafin nama Sir Moli yayi saurin tare ta ta fad'a jikinsa, tana niyyar sakin ihuuuu ya had'e bakinsu waje guda, ido Sanah ta zazzaro waje had'i k'ok'arin hankad'a shi baya, amma ina bata iyawa namiji da mace ba d'aya suke ba, yadda take kallansa ido cikin ido, idanuwanta duk waje yasa shi sanya d'ayan hannunsa ya rufe mata ido, a hankali shima ya lumshe idanuwansa yana cigaba da tsotsar lips d'inta, sai da yasha bakinta san ransa, ya gaji dan kansa kana ya saki bakin nata, had'i da zame hannunsa daya rufe mata ido, ya k'ura mata ido na tsayin lokaci, suka kallan juna ido cikin ido, gaba d'aya kammaninsa sun gama sauyawa, idanuwansa sun rikid'e sun koma asalin jajaye, duk da sanyin Ac dake parlor'n gume karyo masa yake tako'ina, itama ido ta k'ura mishi tana mamakinsa, yadda lokaci d'aya yanayinsa ya sauya, ganin yadda yake kallanta yasa tabi idanshi, taga inda yake kallo, jikinta ya k'urawa ido musamman slink skin d'inta, a tsorace ta zaro ido waje, dan ita tama manta daga ita sai towel, nuna shi da yatsanta tayi had'i da yin kwafa batare datace komai ta shige bedroom, murmushi yayi had'i da girgiza kansa ya cusa hannunsa cikin kwantaccen gashin kansa, kana yayi hanyar fita. Sir Moli yana niyyar fita Khulud ta shigo, fuskarta d'auke da murmushi, baya ya d'an ja dan ya bata hanyar shigowa, Khulud ta shigo ciki tana murmushi tace " Sir da tafiya zakayi baka gammu ba? Murmushi yayi kana ya koma ya zauna batare dayace komai ba, itama Khulud d'in zama tayi akan sofa, Khulud zatayi magana Aarib ya shigo tare da 'yar aiki d'auke da tray, agaban Sir Moli ya umarce ta data aje, kana ya zauna kusa da Sir Moli, Aarib ya kalli Khulud yace " ina Sanah? Khulud ta juya tana d'an dube-dube kana tace " ni ma ita nake nema, rabo na da ita nakai 1hr, Aarib yana k'ok'arin yin magana Sanah ta fito cikin arniyar kwalliya, sanye take cikin riga da skirt na material lace, yayi masifar yi mata kyau, d'inkin yayi d'assss a jikin ta, fuskarta tasha make up, da sauri Aarib ya mik'e had'i da zuba mata ido, cikin ransa yace " love of rest of my life, a hankali Sir Moli ya d'aga kansa ya kalle shi, dan yaji abinda Aarib yace, tana murmushi ta k'araso ta zauna kusa da Khulud, Khulud tayi murmushi tace " kinyi kyau sosai my Sanah, Aarib yace " ai dama ita mai kyau ce ko ba make up, Sir Moli ya tab'e bakinsa had'i da kansa gefe, Sanah tayi murmushi tace " da gaske Yaya? Aarib yayi dariya yace " kina da kyau sosai ma, gaki da manyan ido farare tass, masu d'aukar hankali, ga dimple both side, then wushirya da farare hak'ora a jere, ga dogon bak'in gashi har gadon baya, ga........ d'an tari Sir Moli yayi dan kwata-kwata ba san hirar yake yi ba, Sanah tayi murmushi tace " thank Yaya, karaf idan Khulud ya sauka akan pant & bra d'in Sanah, ido ta zaro had'i da kallan Sanah, da ido Sanah tayi mata alama da meye? Itama Khulud da ido ta nuna mata pant & bra d'in, ido Sanah ta zaro had'i da satar kallan Aarib da Sir Moli, wanda duk abinda suke yi yana kallansu, Sanah tayi yak'e kana ta sanya k'afa zata ture su, Khulud ta zaro ido had'i da girgiza mata kai, Sanah ta cije hak'ora had'i da zaro ido, ta motsa lips d'inta ta yadda babu wanda zai gane abinda tace, tace " ya kike san ayi to? Khulud tace " kina tab'awa zasu gani, Aarib yace " me? Dan ya ji abinda Khulud d'in ta fad'a, da sauri sukayi murmushin yak'e kana sukace bakomai, Sanah ta kuma cije hak'oranta alamar kin gani ko? Khulud tace " me? Aarib yace " a ina? Suka kuma yin yak'e had'i da cewa " bakomai, Sanah tayi rolling sexy eye d'inta tace " ki kwashe, ta fad'a yadda babu wanda zai ji ta, da k'arfi Khulud tace " tabb! ni? Aarib ya kalle su tare cikin alamar tambaya, Sir Moli yana sane da duk abinda suke yi basarwa kawai yayi had'i da kauda kansa gefe, ganin yadda duk sukayi tsuru-tsuru yasa Sir Moli yin murmushin gefen baki kana ya mik'e, da sauri Aarib ma ya mik'e Sanah na ganin sun mik'e tayi saurin sa k'afa ta tura su k'ark'ashin sofa, ajiyar zuciya suka sauke a tare, kana suma suka mik'e, hannu Sir Moli ya mik'awa Aarib sukayi musabaha kana yace " zan tafi, Aarib yayi dariya yace " ok mun gode sosai, kana ya kalli su Khulud yace " my Sanah ku raka shi, Sanah turo baki kana tace " Yaya shifa ba yaro bane, ai yasan hanya, Khulud tace " Sanah! Sanah ta kalleta kana tayi gaba, Aryan yayi murmushi kana ya fita, Khulud tabi bayansa, suka jera da Sanah suka bi bayansa, sun kusa isa bakin motarsa Halan ta kira Khulud, Khulud ta kalle shi tace " Sir mun gode sosai, Allah ya nuna mana naka, Allah ya maida kai gida lafiya, murmushi yayi mata kana yace " amin, Khulud ta juya zata tafi Sanah na k'ok'arin bin bayanta, Khulud tace " kije ki raka shi mana, Sanah ta turo baki tace " ni dai a'a, Khulud ta k'ura mata ido had'i da cewa " Sanah! Sanah ta kuma turo baki kana tabi bayansa, yana sane da tana biye dashi amma bai ko juya ba, ya shiga motarsa ya fige ta, kamar zai taka ta, tabi motar da harara kana ta ja tsoki ta juya ta koma cikin gida, Hanash na tsaye yana kallan duk abinda suke yi, yaja tsoki kana yace " dan daraba ba'a iya hak'uri na yau kad'ai, sai an zo har gida anyi, iskancin ma yanzu ya wuce ayi a makaranta. Bayan sallar la'asur Malamar addini tazo tayi wa'azi akan zamantewar aure, tayi musu nasiha sosai mai ratsa jiki da jijiya, sosai nasihar ta shiga jikin duk wanda ya halarci wajen, tun daga wajen wa'azin Sanah da Khulud ke ta faman kuka kamar ransu zai fita, dama mutane sun san za'ayi haka, dan kowa yasan rabuwar Khulud da Sanah akwai ganin ikon Allah, d'akinsu suka shiga suka rufe suna ta faman cin uban kuka, ana yin sallar Magrib Abbu ya aiko a kira masa Khulud da Sanah, babban parlor'n gidan Halan ta shiga dasu, India suka iske kowa da kowa harda kakanninsu ciki, fad'a aka yiwa Khulud sosai kan zamantakewar aure, kusan kowa sai da yayi mata fad'a, inda zuciyar kowa ke cike da tsantsar tausayin su, musamman ma Sanah, Abbu ya kalli su Mamu yace " a fad'awa mutane babu kai amarya, sunna zanyi ni da kaina zan kai 'yata, daga ni sai Mamu, Halan da Sanah, duk mai san zuwa yaje daga baya, Didi yayi murmushi yace " wama zaije? "Uba da kansa zai kai 'ya d'akin miji? Abbu yayi murmushi yace" eh sunna zamu raya, kana ya kalli Halan yace " kuje ku shirya nan da 10 minutes zamu tafi, Khulud da Sanah najin haka suka k'ara fashewa da sabon kuka, Halan ta mik'e rik'e dasu ta fita, basu fi 10 minutes d'inba suka fito rik'e da juna gam, suna ta kuka, har suka sanya zuciyar mutane karyewa, motar Abbu suka shiga, Sanah da Halan suka saka Khulud a tsakiyarsu, Abbu da Mamu na gaba, tunda suka shiga cikin motar baka jiyo komai sai sautin kukan su, sun rirrik'e juna kamar za'a raba su har abada, a harabar gidan Khulud Abbu yayi parking suka fito, Abbu da kansa ya rik'e hannun Khulud ya shigar da ita cikin gidan, da suka zo shiga main cikin gidan Abbu ya tsaya a bakin k'ofar shiga, ya shiga biya mata addu'a Khulud na maimaitawa kana yace " ki shiga da k'afar dama, bismillah tayi kana ta shiga da right leg d'inta, zama Abbu da Mamu sukayi akan sofa, yayinda Khulud, Sanah da Halan ke zaune akan Italian carpet, addu'o'i Abbu ya kuma yi kana ya sake yi mata fad'a sosai, sai da ya gama ya kalli su Halan yace " ku tashi muje, Mamu da Halan suka mik'e amma banda Sanah, Khulud ta rirrik'e ta gam suna cigaba da kuka, Abbu ya kalli Sanah cike da tausayawa yace " tashi mu tafi, cikin muryar kuka Sanah tace " Abbu zan tsaya saboda siyan baki, tunda bamu da wasu k'awaye dole ni zan jira, shiru Abbu yayi kana yace " ok tom, har ya kai bakin k'ofa ya juyo yace " karki sake ki kwana, dan wallahi idan kika kwana sai ranki ya b'aci, yayi commanding d'inta, cikin muryar kuka ta amsa da " tom, kana su Abbu suka fita, shiru kawai Abbu yayi yana driving amma a k'ark'ashin zuciyarsa yana mugun tausayawa Sanah, while itama Mamu da Halan tunanin da suke yi kenan har suka isa gida. Su Abbu na fita Sanah ta kalli Khulud cikin muryar kuka tace " yanzu shikenan bazamu k'ara kwana tare ba, bazamu kuma cin abinci, muyi wasa tare ba? Khulud tace " meyasa? Ta fad'a still crying, Sanah tace " gashi kuwa aure ya raba mu, daga yau ni kad'ai zan rink'a kwana, ni kad'ai zan rink'a yin komai a rayuwata, Khulud tace " mutuwa nayi? Sanah tace " ai ko baki mutu ba aure ya raba mu, shikenan munyi nesa da juna, ta fad'a cikin matsanancin kuka, Khulud tace " dan Allah my Sanah ki daina kukan, ta fad'a itama tana kukan, Sanah tace " dole nayi kuka, daga yau zan kasance komai nawa ni kad'ai, gwara ke kina da mijinki ma, zai rink'a d'ebe maki kewa ta, amma ni babu kowa, Khulud tace " duk duniya babu mai d'ebe min kewarki my Sanah, you still alone in my heart baki da kishiya a zuciya ta, har yau har gobe ke kad'aice, murmushi Sanah tayi tana gogewa Khulud hawaye tace " thank you so much, Khulud tace " nayi miki alk'awarin har abada babu abinda zai raba mu koya shiga tsakanin mu, Sanah tace " ni ma nayi miki alk'awarin bazan tab'a barinki kiyi kuka ba, Khulud tayi dariya tana goge mata hawaye, Hanash bai shigo gidan ba sai around 9:00pm na dare, dan yayi tsammanin 'yan kawo amarya ne suka kawo ta, shi kad'ai ya shigo kasancewar shima ba wasu abokai ne dashi ba, rik'e da ledoji, fuskarsa d'auke da murmushi, ganin Sanah yasa shi yin turus, kana ya k'ak'aro murmushin dole, yace " ana nan ana ta faman kukan ko? "Ni dai a taimaka man kar ayi ciwon kai, Khulud ta d'ago red eye d'inta ta kalle shi, ganin ya shigo shi kad'ai yasa Sanah cewa " Ango ina 'yan siyan bakin? Murmushi yayi kana yace " bana da abokanai ai, tana mik'ewa tsaye tana goge fuskarta tace " aiko na tsaya ne saboda kar 'yan siyan baki su zo su iske babu kowa, yace " ok shikenan sai ki kwana anan, Sanah ta zaro ido tace " in kwana a ina? Abbu yace " kar in sake in kwana, Hanash ya d'anyi shiru kana yace " Ok shikenan muje na maidake gida, Khulud najin ance za'a mayar da Sanah gida ta k'ara fashewa da matsanancin kuka, jikinsa ya jawota ya rungume ta yasa harshe yana lashe mata hawayen, babu wani jin kunyar Sanah na tsaye, cike da mamaki Sanah ta kawar da kanta gefe, Khulud tayi saurin kwace jikinta, ta ruga ta rungume Sanah gam, sai dakyar Hanash ya sa Khulud ta saki Sanah, dukkan su suna ta faman kuka kamar zasu mutu, da gudu Sanah ta fita daga parlor'n tana cigaba da kuka, a harabar gidan ta tsaya had'i da jingina jikin motarsa, a hankali ya tako wajen cikin takunsa na izza, ya zuba mata ido, yace " do you think zan d'aukeki a motata ne? Ya fad'a yana yi mata wani irin kallo mai cike da kyama, " so idan ma kina tunanin hakan ki daina, dan ban tab'a d'aukar mazinaciya fasik'a cikin motata, wallahi kin ban mamaki duk irin tarbiyyar gidanku, da halin mutumci da kirkinsu ke kin fita zakka, saboda tsabar ke kwararriyar karuwa ce, duk iskanci da kike yi cikin makaranta bai isheki ba, sai kin kawo k'ato har cikin gidan ubanki, ranar d'aurin aurin 'yar uwarki, haba ashe shiyasa baki da kunya kwata-kwata, nayi mamakin yadda kika iya d'aga hannu kika mari cikekken namiji kamata, a kan titi a cikin bainar jama'a, ina 'yar mutumci zata iya irinka, ai dama idan kaga haka sai rikakk'un karuwai, banza 'yar iska kawai, wallahi dana d'aukeki a motata gwara a sace gaba d'aya motocin dana mallaka, kuma baki kwanar min a cikin gida tunda ba gidan ubanki bane, sai kira shi abokin fasik'ancin naki ya maidaki gida, kinga kun sake samun wata damar kuna iya yin abunku cikin mota, ya k'arasa maganar yana kallanta, cike da kyama, " innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, dama kallan da Hanash yake yi mata kenan? Ta fad'a cikin ranta, wato kallan karuwa, mazinaciya, fasik'a yake mata, a hankali ta shiga tunani, tabbasa ya ganta da Sir Moli har sau uku, na farko ya ganta kwance kan table a office d'insa, babu d'an kwali, ya kuma d'age mata riga, na biyu ya gansu cikin wani yanayi, har Sir Moli na shan bakinta, kuma tana sanye da kayansa, na uku ya ganta d'aure da towel a gabansa, tabbas dole yayi zargin wani abun, tunda su ba ma'asumai bane, dole yayi tunanin akwai wani abu tsakaninsu, tunda shima d'an Adam ne kamar kowa, yana da zuciya kamar ta kowa mai sak'a alkhairi da sharri, dole zayyi musu mummunan zato, tunda shi ba daban yake da kowa ba, saboda ko ita ce ta kanshi da mace kamar yadda ya ganta da Sir Moli dole tayi masa mugun kallo, kuma ko shi Sir Moli ya ganta da wani kamar yadda Hanash ya ganta dole zayyi zargi, musamman ma har sau uku, d'aya daga ciki kuma yana shan bakinta, kuma su ba waliyyay bane, sai lokacin wasu abubuwa da dama suka shiga dawo mata cikin kanta, ashe dayace wad'anda suke yin haramtacciyar soyayya ma basu b'oyewa ko jin kunya da ita yake? Ashe saboda wannan dalilin ne ya rungume Khulud a gabanta, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, ta fad'a had'i da rutse idanta, dan tasan bata da bakin wanke kanta, tasan duk duniya duk wanta ya ganta haka dole yayi tunanin wani abu, tasan ko Mamu da Abbu da suka haife ta , suka fi kowa sanin halinta da ciwonta, suka ganta kamar yadda Hanash ya ganta dole suyi zargin akwai wani abu, " tab! tace a ranta, tana jin zafin abun, tana jin tuk'ok'in bak'in ciki a zuciyarta, " ya Salam! ta kuma fad'a idanta ta runtse hawayen bak'in ciki da takaici na zubo mata, a hankali ta bud'e idanta ta ganshi still yana tsaye hard'e da hannuwa yana kallanta, hawayenta ta goge ta kalle shi ido cikin ido tarrr, had'i da nuna shi da yatsa, cikin rashin tsoro da tsiwa ta bud'e baki zatayi magana, alk'awarin datayiwa Khulud ta tuna, " _nayi miki alk'awarin daga yau har abada duk abinda zai yi man ban kuma ramawa,_ a hankali ta sauke hannunta data nuna shi da shi, kana ta juya zata tafi, murmushi Hanash yayi mai sauti kana yace " iskanci da fitsarar naki da kika saba zaki kuma yi man, batare data jiyo ko tayi magana ba, ta fice daga gidan, murmushin jin dad'i yayi kana ya juya ya koma cikin gidan. A parlor ya iske Khulud kamar yadda ya barta tana ta faman kuka, a hankali ya zauna kusa da ita had'i da jawo ta jikinsa ya rungume, cikin muryar kuka tace " My Sanah! fa? Ya gane abinda take nufi dan haka yace " nasa driver ya maida ta gida, shiru tayi tana jin gabanta na fad'uwa, haka nan taji tsoro da fargaba sun shigeta, cikin nutsuwa Hanash ya mik'e ya shiga kitchen ya d'auko plate da cup, a hankali ya jawo ledojin daya jigo dasu, ya bud'e su, ya kalle ta yace " my queen me zaki ci? Cikin kuka tace " my Sanah! Shiru yayi had'i da k'ura mata ido yana nazarin yanayinta, a cikin idanuwanta ya hango rashin yarda, da kuma rashin kwanciyar hankali k'arara, wato idan ya fahimta jikinta ya bata akwai wani abu, mamakin tsananin soyayyar dake tsakanin su yake, murmushi yayi kana yace " me? Shiru tayi batare data amsa ba, a hankali ya kuma jawo ta jikinsa, ya manne ta da k'irjinsa ya shiga lallashinsa, sosai Hanash ya lallashi Khulud kana ya bata abinci taci kad'an, sai fresh milk data d'an sha, mik'ewa yayi da ita a hannunsa ya nufi bathroom, ganin ya nufi bathroom yasa Khulud fara mutsu-mutsun sakkowa daga jikinsa, k'in ajeta yayi sai da ya kaita har cikin bathroom d'in, kana ya dire ta cikin tub bath, yana yi mata wani irin kallo yace " wanka zamuyi, cikin tsoro Khulud ta zaro ido waje tace " kai da wa? Yayi murmushi kana yace " with my wife, murmushi tayi tace " ok tom, ta fad'a tana k'ok'arin fitowa, dariya yayi mai sauti kana ya mayar da ita cikin tub bath d'in, Khulud ta kwab'e fuska tana san soma kuka, tace " please ka barni nayi, yana dariya yace " wannan duk tsoron mijin ne haka? Kuka ta soma yi cike da shagwab'a, yayi dariya yace " sorry bari na fita, kiyi wanka ki d'auro alwala, ya fad'a yana fita, direct bedroom d'insa ya shiga ya shiga wanka, ya fito ya shafa lotion & body spray kana ya fesa perfumes kala-kala, ya shirya cikin arnan kayan bacci ya nufi bedroom d'inta, itama tuni tayi wankan ta d'auro alwala, ta shirya cikin kayan bacci so slink, doguwar rigar har k'asa, ta shafa turaruruka da body spray kala-kala, ta d'auki k'amshi ta ko'ina, ta zura hijab har k'asa, tana gama shiryawa ya shigo, bakin gado ya zauna yasata ta shinfid'a musu prayer mat, ya ja su Sallah bayan sun idar ya dafa kanta ya shiga kwararo addu'o'i kamar yadda sunnah ta koyar. Suna idarwa ta fara hamma, ya kalle ta yace " bacci ko? Kanta ta d'aga masa tace " eh! "ok yace kana ya mik'e ya d'auke ta cak ya nufi kan bed da ita, kwantar da ita yayi kana shima ya kwanta ya jawo ta jikinsa, yana shigewa jikinta mata kamar wani k'aramin yaro, a hankali ya sanya hannunsa yana shafa jikinta, cikin wayo ya fara k'ok'arin cire rigar jikinta, da sauri ta rik'e masa hannu, duk ilahirin jikinta kerrrma yake yana tsuma, yadda kasan ana kad'a mata gangi, cikin wani irin salo yakai bakinsa saitin kunnenta, muryarsa na rawa yace " please ki bari muraya daren yau, ya k'arasa maganar yana hura masa iska cikin kunnenta, da sauri ta runtse idanta, while jikinta na cigaba da rawa, bakinsa da nata ya had'e ya shiga tsotsar bakinta, yayinda hannunsa ke yawo a jikinta yana shafa ko'ina, a hankali Hanash yayi sama da hannunsa zuwa k'irjinta, ya shiga wasa da k'irjinsa, still bakinshi na cikin nata, a hankali ya zame rigar jikinta ya mayar da ita naked, kana shima ya cire kayan jikinsa, duk abinda yake yi bakinsu manne, cikin nutsuwa ya gangaro da bakinsa zuwa k'irjinta, had'i da cusa hannunsa cikin gashin kanta, yayinda d'aya hannun keta faman shafa ta, ganin gaba d'aya ya rud'e ya gama fita daga hayyacinsa, duk ilahirin jikinsa kerrrma yake, yanayinsa da kamanninsa sun sauya, yasa Khulud k'ara rud'ewa tsoronta ya k'ara k'aruwa, taga kamar ba Hanash d'inta ba, cikin muryar kuka tace " no please, muryarsa na rawa yace " dan Allah, still bai bar abinda yake yi ba, sai da yayi romancing d'inta sosai, ya tsotse tass in an out kana, a hankali ya burkitata, ya hawaye kanta, ya fara k'ok'arin neman hanyar shiga, azaba tasa Khulud fashewa sa matsanancin kuka tana tureshi da iya k'arfinta amma ina, ya sakar mata gaba d'aya nauyinsa, a hankali ya bita harya samu k'ofar shiga, Hanash jinshi a duniyar dabai tab'a ziyara ba, yasa shi zagewa iya k'arfinsa yana kashe arna, bai sarara mata mata ba, sai da ya samu nutsuwa, kana ya d'agata ya koma gefe, had'i da jawota jikinsa ya rungume ta tsam, itako sai ajiyar zuciya take saukewa cikin wahala. Kasancewar unguwar su Hanash unguwar manyace, layukan duk kusan iri d'aya ne, yasa Sanah kid'imewa ta kasa gane takamaiman hanyar fita bakin titi, tafiya kawai take tana waige-waige cike da tsoro da fargaba, gashi dare yayi sosai, dan yanzu 11:00pm na dare, awa biyu kenan tana ta tafiya tana neman abun hawa, amma ta rasa, tunda ta fito ko mota d'aya bata gani ba, ga Sanah ba saba tafiyar k'afa tayi ba, ga dare yayi sosai, duk ta rud'e tsoro ya cika ta fall, tana tafe tana kuka, da zarar ta shiga wannan layin sai taga kamar ta koma baya, haka idan ta kuma shiga wani layin sai taga kamar ta kuma komawa baya, haka taitayi tana bulayi ita kad'ai cikin unguwar, kowanne gida rufe, sai faman haushin karnuka da take jiyowa daga cikin makamakan gidajen, sauk'inta d'aya dayake unguwar manyan mutane ce,, ko'ina a haskake yake da wuta, babu duhu kwata-kwata, wajen so silent, k'arar motar taji tazo wucewa shuuuuuu, d'agowar da zatayi hasken motar ya dalle mata ido, ta yadda bata iya ganin komai, kafin ta ankara sai taga motar tsaye a gabanta, a tsorace Sanah ta d'ago kanta fuskarta cike da hawaye, fuskar tayi jajir, a kid'ime ta mik'e tayi baya da aguje, ta fara gudu iya k'arfinta, a hankali matuk'an motar suka bi bayanta da motar cikin wani irin gudu, da gudu aka sha gabanta da motar, ganin da gaske gudu take yasa matuk'in motar fitowa، da sauri ya rufe mata bakinta, had'i da d'aukarta cak ya dannata cikin motar ya rufe.................... MOMYN ZARAH _*RASHIN SANI.......*_ *HAUWA A USMAN* _JIDDARH_ ```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh``` 2⃣6⃣ Da k'arfi ya rufe motar kana ya zagaya ya shiga mazaunin driver, da k'arfi Sanah ta shiga dukan glass d'in motar tana ihuuun kuka, had'i da neman ceto, " Keeh! ni ne, taji muryarsa ta daki dodan kunnenta, ajiyar zyciya ta sauke da k'arfi kana ta cigaba da kukanta, da gudu yake jan motar dan dama shi baya tuk'in mota a hankali, jin har lokacin batayi shiru ba, yasa shi ganganrawa gefen titi yayi parking, ya kashe motar, had'i da kishingid'a ya lumshe idansa, ita kuwa sai kukan take cikin disashewar murya, ido ta zura mushi tana me k'ara sautin kukanta ciki, tsananin rauni tace,, "Ka kaini gida Abbuna zaimin fada dere yayi, meyasa zaka tsaya?. " muryarsa can k'asan mak'ogwaro yace " idan kin gama kukan sai mu cigaba da tafiyar, ya fad'a kamar baya san yin magana, shiru tayi masa batare data ce masa komai ba ta cigaba da kukanta, cike da tsantsar bak'in ciki da takaici, shiru motar tayi babu abinda ke tashi sai sautin kukan Sanah da takeyi sosai kamar ranta zai fita, idonsa lumshe yana sauraran kukanta babu abinda ya dame shi, a hasale Sir Moli ya juyo yace " wai baki gama bane? Ganin yadda take kukan yasa shi yin tsaki had'i da bud'e motar da k'arfi ya fito, a fusace ya bud'e bayan motar inda Sanah ke zaune kamar zai b'alla murfin, ya fisgota waje, yayi wurgi da ita gefe , kana ya bud'e motar cikin zafin zuciya ya shiga yayi mata key, ya fige motar yadda kasan zai tashi sama, yayi tafiyarshi, durk'ushewa Sanah tayi wajen had'i k'ara fashewa da rikitaccen kuka, takai wajen 10 minutes durk'ushe a wajen tana ta faman kuka, ta hangi motarsa na dawowa, a gabanta yayi parking batare daya fito ba, ya kai wajen 5 minutes tsaye gabanta cikin motar, amma ko alamar motsi bata dashi, ganin haka yasa shi fitowa ya taka a hankali zuwa inda take durk'ushen, yasa hannu ya d'ago ta kana ya nufi motar ya bud'e ya saka ta a baya, shima ya shiga bayan kusa da ita ya zauna, yakai wajen 6 minutes zaune kusa da ita babu wanda yayiwa wani magana, while tana cigaba da kukanta, ido kawai ya k'ura mata yana kallan yadda take kuka kamar ranta zai fita, a hankali ya jawota jikinsa ya rungume ta tsam had'i da d'ora kanta a saitin zuciyarsa, batayi musu ba, saboda itama tana neman wanda zai lallasheta, dan haka ta lafe a jikinsa, tana sauraran bugun da zyciyarsa keyi da sauri da sauri, while bata daina kukan da take yi ba, sun dad'e a haka kana cikin rawar murya yace " meye? Cikin sheshshekar kuka ta d'ago kanta tana kallansa, tace " ARYAN! mun shiga uku! ta fad'a cikin kuka, cikin tsantsar mamaki Sir Moli yake kallanta, jin yau rana ta farko Sanah ta kira sunansa, dan shi a iya saninsa bata tab'a ambatar sunansa ba, sai idan taga bala'i ko tana neman taimako, amma haka nan bata tab'a kiranshi ba, amma yau sai gashi ta kira shi da real name d'insa, bai nuna mata mamakinsa a fili ba, yace " kamar ya mun shiga uku!? Ya tambaye ta, cikin kuka tace " ni dai kai wallahi mun shiga uka, da k'arfi k'irjinsa ya buga, amma ya dake kamar bakomai yace " meyasa!? Ya tambaye ta a tak'aice, cikin matsanancin kuka jikinta gaba d'aya na kerrrma gami da tsuma still tana kukanta tace " zargin mu akeyi, "zargin me? Ya fad'a idanshi na kanta, jikinta na rawa tace " zargin mu yakeyi, Hanash mijin Khulud zargin mu yake yi, yana yi mana mummunan zato, wani irin kallo yake yi mana, ta k'arasa cikin matsanancin kuka, cikin rawar murya yace " zargi akan me!? Kuka ta k'ara fashewa da shi kana tace " wai muna.... shiru tayi ta kasa k'arasawa, Sir Moli ya gane abinda take san fad'a, amma yayi kamar bai gane ba ya kuma cewa " muna me? " Wai muna.... kukan dayaci k'arfinta ne ya hana ta k'arasawa, fuska ya tsuke kamar bai gane abinda take san fad'a ba, yace " wai meye, muna me!? Kin dame ni da muna! muna! kawai, idanta ta rutse da k'arfi tana cigaba da kuka, tace " wai muna ZINA!!!, ta fad'a cikin mahaukacin kuka na fitar hankali, yayinda gaba d'aya jikinta rawa yake, ta gama rud'ewa sosai ta fita daga hayyacinta, jin yayi shiru yasa ta d'ago kanta ta kalle shi, gani tayi ya zuba mata ido kawai yana kallanta, babu alamar damuwa ko razana a tattare dashi, ganin yadda ta rud'e sosai jikinta nata faman kerrrma, yasa shi maida ita jikinsa ya rungume, Sir Moli daurewa kawai yayi bai nunawa Sanah yaji maganar ba, amma maganar tayi masifar shigarsa har cikin kansa, ya daure ne kawai saboda karya k'ara d'aga mata hankali, dan yasan muddin taga wani reaction a tattare dashi sai ta k'ara tsorata, amma deep down ji yake kamar an watsa masa wuta, jin zuciyarsa yake kamar ana dafata da narkarkiyar dalma, sosai ransa yayi masifar b'aci, k'irjinsa nayi masa zafi kamar ana zuba masa ruwan zafi, mak'ogwaronsa nayi masa k'ona da zafi, gaba d'aya yawon bakinsa ya koma masa tamkar mad'aci, ji yake kamar ya mutu, amma a zahiri dayake namijin gaske ne kai baka isa ka gane halin dayake ciki ba, shiru yayi batare dayayi magana ba, ya sanya hannu yana shafa kanta had'i da bubbuga bayanta, sun kai a k'alla 5 minutes a haka kana yayi controlling temper sa, "meya ce miki? Jikinta na rawa ta shiga bashi labarin abinda ya faru tsakaninta da Hanash tun daga farko har k'arshe, idanta ya runtse da k'arfi yace " kiyi hak'uri, ita dama rayuwa ta gaji haka, wata rana fari wata rana bak'i, wata rana zuma wata rana mad'aci, yayinda wata rana zakayi kuka wata rana kuma kayi dariya, so karki tab'a yin abu dan mutane su gani su yabeki, komai zakiyi kiyi shi kanki tsaye, saboda baka tab'a iyawa mutanen duniya, duk yadda kakai da kyan hali, da kyawawan d'abi'u sai wani ya kusheka, koda kullum karatun Qur'an kake yi, kana kwana fatawa, sai ka samu masu ya aibataka, suna zaginka, so kibi rayuwa da mutane a sannu, karki tab'a yin komai dan kowa, duk abinda zakiyi kiyi dan Allah, ki kuma saka tsoran Allah a ranki, ki kyautatawa mutane zato, ya fad'a idansa lumshe, kanta ta girgiza masa alamar to, idansa lumshe yasa hannunsa dayake bubbuga mata baya, yana shafa jikinta a hankali da niyyar lallashi, d'aya hannun kuma yana shafa kanta, a hankali Sanah ta d'ago kanta had'i da kafe shi da sexy eyes d'inta bata ko blinking, shima ido ya k'ura mata while yana cigaba da abinda yake yi. Sun juma suna kallan juna kana a hankali ya sanya hannunsa ya zame mata d'an kwallinta, cikin wani irin salo ya sanya hannunsa ta k'ark'ashin wuyanta, ya zame reborn d'in data d'aure gashin kanta dashi, ya saki gashin ya zuba gadan bayanta, while idansu na cikin na juna, cikin nutsuwa ya zura duka hannunsa ta k'ark'arshen wuyanta, ya tallafe fuskarta, a hankali yayi k'asa da kansa, ya had'e bakinsu, ya shiga tsotsar bakinta, yana shan harshensa had'i da tsotsar lips d'inta, idanuwansu duka lumshe daga shi har ita, a hankali yanayinsu ya fara sauyawa, suka fara mance a duniyar da suke, hannunsa ya sanya yana shafa jikinta ta ko'ina a gaggauce kamar wani mara hankali, while d'aya hannun yana cikin gashin kanta yana aikin yamutsawa, k'asa yayi da hannunsa ya d'aga rigarta ta k'asa ya zura hannunsa, yana shafa shafaffen jikinsa, kana cikin salo yayi baya da hannunsa yana shafawa a hankali, bayanta ya shiga shafawa ya sanya yatsansa cikin kwarmin bayanta, yana yi mata tafiyar tsotsa had'i da shafawa, still bakinsu na manne dana juna suna aikin tsotsar lips da harshen junansu, idansu duk rufe suna sauke nauyayyan numfashi, had'i da ajiyar zuciya kamar wad'anda sukayi tsare, gaba d'aya basa cikin hayyacinsu, sun dad'e da shigewa cikin wata duniya ta musamman, hannunsa ya ciro daga cikin rigarta, ya zaya yana neman zip zai zuge, a hankali ya fara yin k'asa da zip d'in, while baibar abinda yake yi ba, hannunsa d'aya na cikin gashin kanta, bakinsa kuma yana tsotsar nata, hannunsa ya zura ta cikin zip d'in, yana shafa gadan bayanta cikin salo mai mantar da mutum duniyar da yake, bakinsa ya zame daga cikin nata, ya mayar wuyanta ya shiga tsotsar wuyanta zuwa saman k'irjinta, yayinda d'aya hannun ke aikin shafa gadon bayanta zuwa cikinta da cibiyarta, babu abinda suke fitarwa sai nishi, da wani irin sauti, sama Sir Moli yayi da hannunsa ta bayanta cikin salo yana k'ok'arin b'alle bra d'in jikinta, dan gaba d'ayansu basu cikin nutsuwarsu, daga waje akayi knocking glass d'in motar, daga shi har ita babu wanda yaji, k'ara kwankwansa glass d'in akayi a karo na biyu da d'an k'arfi, wanda yasa Sanah dawowa cikin hayyacinta, aiko a zabure tayi saurin yin baya, had'i da d'ora hannunta akan bakinta ta rufe cikin tsoro, k'ara biyota Sir Moli yayi yana k'ok'arin sake had'e bakinsu, hannunta ta saka a k'irjinsa ta tura shi baya, idanuwanta duk waje saboda tsoro da fargaba, yana k'ok'arin sake matsowa kasancewar har lokacin bai dawo cikin hayyacinsa ba, yaji an kuma buga k'ofar da k'arfi, wanda yasa shi dawowa cikin nutsuwarsa, red eyes d'insa ya d'ago ya kalleta, ganin irin kallan datake yi masa a tsorace ne yasa shi, d'an matsawa baya kana ya gyara jikinsa, ya saita kansa da nutsuwarsa. Muryarsa na rawa yace " koma gaba, ya fad'a a tak'aice, da sauri ta mayar da ribbon d'inta ta d'aure gashinta, kana ta d'aura d'an kwalinta had'i da yafa mayafinta, jikinta na kerrrma kamar mazari ta fita ta koma gaba kamar yadda ya umarce ta, sai ta zauna kana ya bud'e bayan ya fito, sojoji ya gani tsaye, suna ganinshi yasa sukayi saurin sara masa had'i da cewa " sorry Sir bamu san kai ban......... hannu ya d'aga musu kawai batare dayace komai ba, yayi shigewarsa cikin mota yaja, kasancewar motar tint ce yasa basu ganshi ba, a hankali Sanah ta saci kallansa tana mamakin dalilin dayasa shi fitowa yanzu cikin daren nan, dan taga dare yayi sosai, tana mamakin meyasa duk sanda ta shiga cikin matsala Allah yake turo mata shi dan ya ceceta, tunani taitayi cikin ranta tana yiwa kanta tambayoyi ganin babu mai bata amsa yasata tab'e bakinta had'i da cewa " anyway komai dai yaya ne shi kamar GARKUWA ta ne, saboda Allah yana kawo shi gare ni a lokacin daya dace, ta fad'a cikin ranta, " kinci abinci! ya tambaye ta, kanta ta d'aga ta kalle shi taga kamar bashi yayi maganar ba, dan haka itama ta share, bai kuma yi mata magana ba, yayi parking a k'ofar USA restaurant, batare dayace mata komai ba ya fita, oder ya bayar kana ya tsaya yana amsa wayar, tana daga cikin motar ta k'ura mishi ido, duk da bata jiyo abinda yake cewa, wani mutum taga ya zo batare da yayi mishi magana ba, ya mik'a mishi wani abu, kamar splash disk kamar memory card, dayake tana daga nesa yasa bata ga ko meye sosai ba, shima Sir Moli taga ya amsa batare da yayiwa mutumin magana ba, mutumin ya juya da sauri yabar wajen, shi kuma Sir Moli ya nufo motar, tambayar kanta tayi waye wannan mutumin? "Me ya bashi? " Ko shine dalilin fitowarsa cikin dare? tambayoyi taitayiwa kanta, wanda babu mai bata amsarsu, motar ya bud'e ya shiga ya zaune had'i da lumshe idanuwansa yace " ke bakiga inda nazo bane? Kanta ta d'aga kana tace " na gani, yace " meya hanaki fitowa ko ni kike so na zab'ar mike abinda zaki ci? Ya fad'a still idanshi rufe, banza tayi dashi bata bashi amsa ba, can wajen 5 minutes dayin maganar yace " daga yau idan kikaga na fita kema ki fita dan ban san yawan magana, idanta na kanshi ta amsa masa da " to! bai kuma cewa komai ba, har aka kawo masa oder da yayi, baya bud'ewa wanda ya kawo ya aje a bayan motar, kana yaja motar, a k'ofar gidansu yayi parking, baiko d'aga kanshi ya kalle ba, " nagode tace, cikin sanyin murya, bai kalle ta ba, yace " ki d'auka ya fad'a a tak'aice, tace " me!? Bayyi mata magana ba, ya kalle ta, baki ta tura had'i da cewa " ni fa ban gane abinda kake nufi ba, " gasu nan a baya, ya fad'a yana kallanta, " kabarshi nagode, ta fad'a, tsawa ya daka mata a zafafe yace " ke! ni sa'anki ne, ko abokin wasanki ne? Jikinta na rawa ta bud'e bayan ta d'auka, kana ta shiga gida, part d'in Mamu Sanah tayi direct ta shiga bedroom d'insu, taga yayi mata girma sosai, take kewar Khulud ta dawo mata sabuwa fil, kan bed ta fad'a had'i da fashewa da kuka ta jawo pillow ta rungume, sai da tayi kuka mai isarta kana ta mik'e ta shiga bathroom tayi wanka ta sanya kaya mara nauyi, ji tayi duk jikinta ba dad'i dan haka kwanciya tayi batare databi takan abincin ba. Sir Moli yayi parking a makeken harabar gidansa, ya fito da nufin shiga cikin gida, daga bayan motar yaji waya na ringing, cike da mamaki ya koma ya d'auki wayar, wayar ya zubawa ido yana kallanta, har kiran ya tsinke aka sake kira, sunan wanda ke kiran wayar ya kalla yaga Yaya Aarib, baki ya tab'e kana ya shiga gida, shima wanka yayi ya shafa lotion ya sanya boxer ya kwanta kan makeken royal bed d'insa, har ya kwanta ya tuna da wayar Sanah, a hankali ya mik'e ya d'auko wayar ya dawo ya kwanta, pictures ya shiga, yana kallan pictures, dariya yayi sosai ganin irin tab'arar datake tsulawa, wasu daga ita sai bra, wani saga ita sai bom short da half best, wasu daga ita sai towel, wasu 3 quarter, wasu sleep dress nema kad'ai a jikinta, videos ya shiga nan ma yaga yadda take tsula tsiyarta san ranta, yayi dariya sosai. Tsakar dare yunwa ya tashi Sanah, ta farka a gigice kasancewar duk yinin ranar bata ci komai ba, da sauri tayi bathroom ta wanke bakinta, ta dawo fresh milk d'in ta fara sha sosai kana taci gashashshan naman daya siyo mata, sosai yayi mata dad'i, tana gama ci ta baje ta cigaba da bacci, da safe da Sir Moli zai fita ya biya ya kaiwa me gadin su Sanah wayarta, karb'a yayi ya kai mata cikin gida, ya bawa Mamu, tayi mamaki amma bata tambayeshi ya akayi wayar tazo hannunsa, takai mata cikin bedroom, koda Sanah ta tashi daga bacci taga wayarta kusa da ita batayi tunanin komai ba. Rungume da Khulud Hanash ya kwana a kirjinsa yana ta faman lallashi, da tarairayarta, da asuba da kanshi ya tashi ya had'a mata ruwa, ya gasa ta sosai kana yayi mata wanka sukayi sallah, da gari ya waye daga gidan Mimmee aka kawo musu breakfast, mai rai da lafiya sai da suka sake wanka suka shirya cikin shiga ta alfarma, kana sukayi breakfast, kasancewar Hanash ya gasata sosai yasa ta warke, tare suka yini Hanash yana lallab'a ta, yana nan da nan da ita kamar ransa, da yamma ya shirya zai fita zaije gaida su Mimmee, ya kalleta yace " my zanje gaida su Mimmee, fuska ta kwab'e kana cikin shagwab'a Khulud tace " nima zani, ido ya zaro waje yace " da wannan tafiyar taki? " Kamar kina koyan tafiya, kin rufa mana asiri kar su Mimmee su gane, baki ta d'an tura tace " ni dai zan je please, ido ya zuba mata kana yace " to tafiyarki taki fa? Baki ta kuma turowa had'i da sanya hannunta ta rufe fuskarta tana murmushi, shima murmushin yayi kana ya shiga bedroom ya d'auko mata hijab, da kanshi ya saka mata kana d'auketa cak, bai aje ta ako'ina ba sai sai cikin mota, kana yayiwa motar key, bai tsaya ko'ina ba sai harabar gidansu, tana k'ok'arin fitowa yayi saurin dakatar da ita, kana ya zagayo tana ganin yana niyyar d'aukarta, tayi saurin girgiza mishi kanta, bai saurare ta ya sungume ta cak, tana ta mutsu-mutsu had'i da waige-waige, Jaddah na kallansu ta window, murmushi tayi had'i da cewa " yaran zamani babu kunya, tana ganin yana k'ok'arin shiga main parlor da ita tayi saurin direwa tana dariya, dariya shima yayi suka shiga ciki, a parlor suka iske Mimmee tana ganinsu tayi saurin mik'ewa, had'i da nufar Khulud tayi hugging d'inta, cike da murna tace " you are welcome dear, murmushi Khulud tayi kana ta zame har k'asa ta gaida ita, Mimmee na murmushi ta d'agota had'i da zaunar da ita akan sofa, kana ta kwalawa su Zohal kira, da dugu suka fito suna ganin Khulud sukayi wajenta suna murmushi had'i da cewa " Khulud Rawan, tsawa Mimmee ta daka musu had'i da cewa " kul! karna sake ji, Anuty sunanta daga yau, jikinsu a sanyaye suka amsa da " to, kana ta umarce su dasu akawo mata abinci, kana Mimmee ta mik'e ta nufi sama wajen Papu, Hanash na ganin Mimmee ta tabar wajen ya dawo kusa da Khulud ya zauna, ya mik'a hannunsa zai jawo ta jikinsa, tayi saurin zaro ido had'i da d'an matsawa, tace " please ka koma can ka zauna kar Mimmee ta dawo ta ganka anan, " to sai me? " Ba kusa da matata na zauna ba? Zatayi magana Papu da Mimmee suka sauko, a hankali ta fara k'ok'arin mik'ewa Mimmee data gane halin datake ciki tayi saurin dakatar da ita, " a'a ba saikin mik'e ba, kiyi zamanki, ta fad'a suna zama ita da Papu kan sofa, har k'asa Khulud ta durk'usa ta gaida Papu, ya amsa cikin fara'a yana tambayarta ya bak'unci, ta amsa da Alhamdulillah, Papu ya kalle ta yace " Khulud! ta d'ago kanta a hankali ta kalle shi, " na'am ta amsa, yace " ki d'auke ni tambakar Abbu da Didi, saboda duk d'aya ne ni da su, abokaina ne tun na yarinta, tare muka taso dasu, ki d'auke ni kamar su, ni ma zan d'aukeke ki tamkar Zohal da Wajnah bawai surukata ba, ki tambaye ni duk abinda kike so, nayi miki alk'awarin zan yi miki duk abinda kike so in sha Allah, a hankali ta amsa " to Papu in sha Allah zanyi yadda kace, yayi murmushin jin dad'i, Mimmee zatayi magana Jaddah ta shigo, " to daba'a je an gaidani ko ankai min amaryar ba, ni nazo ganinta da kaita, Hanash yayi saurin mik'ewa had'i da zuwa inda take ya rik'o hannunta, yana dariya yace " yi hak'uri na d'auka kina bacci ne, shiyasa ban shiga ba, kema kin san ai bazan tab'a wuce ki nazo nan ba, kece fa ta k'arfen, ya fad'a yana dariya, dariya itama tayi kana tace " kaji sarkin wayo, nice ta k'arfen ka d'auko matarka, da sauri Khulud ta rufe fuskarta, cikin jin kunya, Papu ya mik'e yana dariya yabar wajen, Jaddah ta zauna kusa da Khulud ta dafata kana tace " amarya Allah ya sanya alkhairi, Ubangiji ya bada rabo mai amfani, fuska Khulud ta sunne, cikin jin kunya, Jadda tace " ai kima daina jin kunya dan nayi miki maganar haihuwa, dan babu abinda nake san gani kamar yaran Hanash a duniya, dan haka ki shirya haihuwa duk shekara, Hanash yayi dariya kana yace " Jadda itama tasan muna san yara dan tasan babban burin Hanash shine yaga yaransa, Jaddah ta mik'e had'i da cewa " atoh! kama gaya mata ta shirya dan in sha Allah ban mutuwa sai na ga yaran Hanash, ta fad'a tana k'ok'arin fita, har takai bakin k'ofa ta juyo tana dariya, tace " yanzu ma sai ka d'auke ta, Hanash ya mik'e yana dariya yace " tom Jaddah yanzu kuwa, ya fad'a yana k'ok'arin d'aukar Khulud, ido Khulud ta zaro had'i da girgiza mishi kanta, fuskarta kamar zatayi kuka, Jaddah tace " jama'a kuji man yaro mara kunya, cikin dariya Hanash yace " kefa kika ce na d'auke ta, sai dare su Hanash suka koma gidan su, ranar ma Hanash bai sararawa Khulud ba sai da yayi, sai da akayi sati biyu kullum daga gidan Mimmee ake kawo musu abinci, kana bayan 2 weeks Khulud ta fara girki, yayinda kullum suna cikin waya da Sanah ko chart, a rana sai suyi waya fiye da goma. Tuni Sanah ta koma makaranta ta cigaba da attending lectures, dan ta yanzu tafi san zaman makarantar fiye da gidan, danma yanzu ta fara sabawa, yau basu gama lectures ba sai magrib, suna fitowa ana kiran sallar magrib, ga hadari ya had'o sosai garin yayi bak'i k'irin, saboda hadarin daya had'o, a matuk'ar gajiye ta nufi get tana tafiya tana hard'ewa kamar zata fad'i saboda tsananin gajiya, ga bak'ar yunwa data addabeta, matarsa ce ta tsaya a gabanta batare daya kalleta ko yayi mata magana ba, yayi parking, idanta tayi rolling kana ta zagaya ta bud'e gaban motar a hankali, ta shiga batare da sunyiwa juna magana ba ya ja matar yayi waje, yayyafi aka farayi mai d'an k'arfi, hannunsa rik'e da drinks yana sha, mik'a mata lemun yayi batare daya kalleta ba, yace " sha! a tak'aice, kallansa tayi kana ta kalli sauran lemon dayake sha wanda ya mik'o mata, tace " me!? "Sha! ya kuma fad'a mata, still bai kalli inda take ba, kallanshi tayi cike da mamaki kana tace " me d'in zan sha? Kallanta yayi kana ya kalli lemon batare da yayi magana, " na koshi tace, bai kalle ta bai kuma janye hannunsa daga mik'a mata sauran lemon ba, idanta ta juya kana tasa hannu ta amshi robar lemon MIWADI, (drink d'in dayafi kowanne lemo tsada a duniya) bakinta takai ta kurba, taga har lokacin bai janye hannunsa ba, kallansa tayi tace " me! kuma? "Bani! yace a tak'aice, " oh! God tace kana ta mik'a masa lemon, bakinsa taga ya mayar ya cigaba da sha cikin nutsuwa kamar bashi yayi ba, ruwa aka kece dashi mai k'arfi, kamar da bakin kwarya harda k'ank'ara, da gudu yake jan motar, yana gaf da wuce danja, danjar ta tsaidasu, gudun karya taka doka ya sashi saurin taka burki da k'arfi k'uuuuu, sosai Sanah ta tsorata tayi saurin fad'awa jikinsa had'i da rirrik'e shi, lemon hannunsa ya kufce ya zube masa jikinsa, ya b'ata masa gaba d'aya jikinsa, gashi farin yadi ne a jikinsa, jikinsa yabi da kallo, yaga gaba d'aya ya gaba b'aci, d'an tsoki yaja, wanda yasa Sanah d'agowa daga jikinsa, amma still bata sake shi ba, inda ta rik'e shi yabi da kallo, itama wajen ta kalla, da sauri ta sake shi had'i da komawa mazauninta, kanta k'asa tace " kayi hak'uri, bai amsa mata ba, ya karya kan motarshi ya nufi gidansa, gatafaren gidansa dake Lamid'o Crescent, ya nufa, gani tayi get d'in ya bud'e kansa da kansa bayan yayi snapping number motarsa, tun daga waje taga sojoji na kai kawo a k'ofar gidan, take tsoro ya kamata yayi masifar cika mata ciki, a hankali ta d'ago kanta ta kalle shi, da niyyar tambayarsa inane nan, taga ya had'e ranshi sosai kamar bai tab'a yin dariya ba, ganin ba fuska yasata sadda kanta k'asa jikinta na kerrrma, sosai ake yin ruwan saman kamar da bakin kwarya, parking yayi harabar gidan wanda ke d'auke da motoci kusan 15, kowacce mota private number ce a jikinta, *MOLI'S!*, a hankali ya zuro k'afarsa k'asa, kana ya fito gaba d'ayansa, sojojin dake harabar gidan suka nufo shi jikinsu na rawa, dakatar dasu yayi ta hanyar d'aga musu hannu, zamanta ta gyara cikin motar da niyyar cigaba da zama, tunowa da gargad'in da yayi mata kan duk sanda taga ya fita itama ta fita tabi bayansa, ya sata saurin fita tabi bayansa, Sanah na fitowa daga mota k'arfin ruwan saman dakeyi ya k'aru kamar me, ta shiga inda taga ya shiga, Sir Moli na shiga cikin gidan ya cire kayan jikinsa tun a parlor ya shiga bathroom, a hankali ta shigo tana sand'a kamar b'arauniya, girma da had'uwa parlor sunyi masifar bata mamaki, yadda kasan irin gidajen nan na turawa ko manyan masu kud'in indiyawa, duk wani abu na jin dad'i da more duniya akwai shi a parlor, sofa ma set 3 ne a parlor'n b'angare d'aya, royal, b'angare d'aya American, d'aya b'angaren kuma Paris chairs, sai makeken dinning, ga wani irin bed daga gefe cikin parlor'n, dabata tab'a ganin irinsa a rayuwarta ba, da gani daga turai yake, duk da kallo d'aya zakayiwa gidan kasan komai daga k'asar waje akayi oder sa, even tails dan glops & sucket na waje ne, gidan a gyare tsaf dashi yadda kasan a turai, k'amshe kawai ke tashi a hankali wayarsa dake cikin aljihun rigarsa ta soma ringing, kasancewar yasan babu kowa a gidan sai shi d'aya kuma yasan ya barta a mota, jin wayarsa na rori yasa shi fitowa daga shi sai d'aure da towel a k'ugunsa, turus yayi ganinta zaune a parlor'n, a hankali ya juya yana k'ok'arin komawa bedroom da sauri, jin taku ya sata d'agowa a hankali, ganin yadda yake yasata saurin mayar da kanta k'asa ta sunyar, gaba d'aya jikinta ya d'auki rawa da kerrrma, wani irin gigitacciyar tsawa akayi da k'arfi gami da walk'iya mai hasken gaske, kana ruwan yayi wani irin kece shaaaaaa kamar da da bakin kwarya ya b'alle, cikin tsananin firgici da kid'ima ta mik'e ta nufi shi, jikinta na tsuma ta fad'a jikinsa had'i da rirrik'e shi gam................ *Al'bishirinku fans ku tsumayi page 27 nanda awa biyu* MOMYN ZARAH _*RASHIN SANI.......*_ *HAUWA A USMAN* _JIDDARH_ ```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh``` 2⃣7⃣ Fatar jikinsa na had'uwa da tata yaji wani irin abu dabai tab'a jin irinsa ba a rayuwarsa, tsikar jikinsa ta tashi had'i da yin yarrrr gaba d'aya k'ofofin gashin jikinsa, suka rink'a buduwa, suna shigarmai da wani bak'on yanayi, sandarewa yayi a wajen batare daya iyayin koda kwakkwaran motsi ba, gaba d'aya jikinsa ya d'auki kerrrma, jin k'afafunshi na rawa, bazasu iya daukar nauyin jikinshi da nataba yasashi, tattaro sauran k'arfin shi ya fara motsawa, a hankali ya zagayo da ita gabansa, saboda ta bayansa ta rungume shi, ido ya k'ura mata yaga gaba d'aya a mugun tsorace take, sai kerma take ta rufe idonta gam, sai k'ara k'wak'umarsa takeyi, a hankali yaja hannunta ya nufi kan sofa da ita, tafiya yake kamar yau yake koyan takawa da k'afafunshi, cikin kasala ya zame bisa sofar, zama yayi ya jingina da kujerar, kana ya zaunar da ita saman cinyarsa, had'i da rungume ta tsan a jikinsa, kamar wani zai kwace ta, sai da ya d'auki tsawon lokaci a haka, ba abinda yakeyi sai sauk'e nannauyan ajiyan zuciya tare da shak'an k'amshin furannin dake zagaye da gidan, kana ya d'ago kanta dake saman k'irjinsa, ya kalleta da jajayen idansa, har a lokacin a tsorace take, jikinta sai kerrrma yake ta tsuke d'an bakinta ta cinnoshi sama, yayinda lips dinta sukayi jazir, in slowly Sir Moli ya lumshe idansa, sai kuma ya sake bud'esu da sauri ya zubasu kan Red lips d'inta, cikin Rashin sani da wani irin fisga da shauqi keyi masa, ya ajiyan zuciya had'i da kai bakinsa kan nata, ya had'e su ya ya lik'a lips enshi da nata ya shiga tsotsar leb'enta da harshenta, ita kuwa idanta ta rufe da k'arfi dan tsananin bugawa da k'irjinta keyi, wani irin kasala ya rufeta ya hana ta k'ok'arin hana shi abinda yakeyi matan, ta rasa meyasa bata iya dakatar dashi daga tab'a mata jikinta, ta rasa dalilin dayasa bata kwace kanta ko yi mishi gardama aduk lokacin dayake yi mata makamanta irin wad'annan abubuwan, tasha zama tayi tunanin why , danganta abin tayi da rudun shaidan ,kamar yadda annabi yace, matuk'ar mace da namiji da ba muharramaiba suka keb'e to cikon na ukunsu shaid'an ne, dan haka take ji wannan hudubar shaid'an ne, tana son tureshi Amman ta gaza ko yanayin yadda yake komawa a duk lokacin dayake cikin irin yanayin ne yake sawa yake fin k'arfinta, dan gaba d'aya yake juyewa kamar ba Sir molin da ta sani bane, Shi kuwa cikin zuciyarshi, fargaba yakeji da tsananin kunyar mahaliccinshi da tsoron laifin da yake shirin kusanta kanshi da aikatawa, amman ya kasa tsaida hannunshi, a hankali yakai hannunsa ya zame d'an kwallinta, had'i da baza gashin kanta kana ya cusa hannunsa ciki, while yana cigaba da shan bakinta, d'aya hannunsa ya saka a muyanta yana shafa duk ilahirin jikinta, jikinsa na kerrrma ya d'ago hannunsa ya d'ora saman k'irjinsa, a hankali ya zame bakinsa daga cikin nata, muryarsa na rawa yake cewa, "Ma. Maatsa, ta. ta tashi a jikina". ya k'arishe maganar cikin fizgo numfashi tare da k'ara matsota jikinshi, ikon Allah sai kallo, yana ta tashi a jikinshi yana kuma k'ara matseta, cikin k'arfi da ficewar numfashi ya sake cewa, "Tashi. " ya fad'a a tak'aice, ba musu saboda a tsorace take ta dashi dan haka ta shiga yunk'urin kwace kanta daga matsar da ya mata, kici-kicin da takeyi dan k'wace kanta , shi kuma sai yakejin kamar shafa faffad'an k'irjinsa mai kwantaccen gashi takeyi, d'aya hannunta ya rik'o ya sanya cikin suman kansa kana cikin muryar raunieyace " Ki tashi", ya fad'a kamar mai koyan magana, nan ma Sanah ta fara yin yadda yace, cikin salo ya kai bakinsa wuyanta yana tsotsa had'i lasar kunnenta yana hura mata iska ciki, had'i da gogo k'asumbarsa a saman fuskarta, a hankali Sanah ta lumshe idanta, tana yunk'uri had'i da cusa hannunta cikin sumar kansa, tana cigaba da mik'ewa, wuyanta ya sank'alo tare da jawota jikinshi, yana kuma Allah wadaran abinda yakeyi a cikin zuciyarsa, manneta yayi da jikinshi, take jikinsu duka ya d'auki rawa da kerrrma, daga ita har shi tsuma sukeyi kamar mazari, idansa yayi masifar yin jajir, duk da sanyin Ac da ruwan saman da akeyi gumi Sir Moli yake yi, dukkansu sun fita daga cikin hayyacinsu, baka jin komai sai sautin fitar numfashinsu, dake fita da sauri da sauri, a hankali ya zura hannunsa ta k'asan rigarta, ya shiga yin wasa da cibiyarta, had'i da zura hannunsa cikin kwarmin cibiyar yana shafawa, d'ayan hannunsa ya zagaya dashi bayanta, yana shafa tsakiyar bayanta, zuwa cikinta, a hankali yayi sama da hannunsa zuwa k'irjinta, jin hannunsa saman booms d'inta, yasa gabansa muguwar fad'uwa da k'arfi, yana mai zubda k'ollar bak'in ciki, yana tuna ayoyin dake hani da kusanta zina, hawaye yake zubdawa sosai daga idonshi yana tuno ayoyin forko-forkon suratul Noor, amman duk da haka ya gaza control din kanshi abinka da wanda bai tab'a ba, itama tana jin hannunsa saman booms d'inta ta saki naunauyan nishi, a hankali ya mik'e had'i da d'aukarta cak ya nufi kan bed d'in dake parlor'n, kwantar da ita yayi idanuwanta lumshe tana fitar da numfashi da sauri k'irjinta nayi sama da k'asa. A hankali ya birkita bayanta ya zuge zip d'in rigar, bayanta ya bayyana, sai da ya rumtse idansa da k'arfi kana a hankali ya yasa harshe yana lasar gadon bayanta, yayinda hannunsa ke faman yawo a sassan jikinta, cikin salo yasa hannunsa ya ya sab'ule rigar jikinta, kana a hankali ya b'alle bra d'in jikinta, ya d'ora hannunsa saman booms d'inta, batare daya zame bra d'in ba, a hankali yasa harshensa yana lasar saman booms da k'irjinta zuwa wuyanta, while hannunsa bai bar yawo a jikinta ba, zame towel d'in jikinsa yayi ya rage daga shi sai boxer, a hankali ya ya kwanta ya d'orata saman jikinsa, k'irjinta saman nashi, booms d'inta na gogar k'irjinsa, tana daga saman nashi ya cigaba da shafa yana shan bakinta, had'i da tsotsar harshenta, sosai Aryan ya gigice ya d'imauce sosai, ya fita sosai daga hayyaci da nutsuwa, gaba d'aya jikinsa kerrrma da tsuma, joy stick d'inshi ta mik'e samb'al, kamar taci babu dan yunwa da azabtuwa da take tsawon shekaru tana dakon abincinta. Parlor'n yayi tsit baka jin komai sau k'arar ruwan sama, da gurnaninsu, a hankali Sir Moli yakai hauununsa yana k'ok'arin cire bra d'in jikinta gaba d'aya. wayarsa ce ta d'auki rori ta cika parlor'n gaba d'aya!, jin k'arar wayar ya dawo da Sanah cikin hayyacinta, da sauri ta yunk'ura ta fara k'ok'arin tashi, da k'arfi Sir Moli ya mayar da ita kwance, had'i da juyewa ya mayar da ita k'asanshi, ya danne ta, saboda har lokacin ya kid'ime yake, kana ya zura hannunsa k'asan skirt d'inta yana shafa cinyoyinta, k'ara yunk'urawa Sanah tayi had'i da sanya hannunta da niyyar ture shi, sakar mata gaba d'aya nauyinsa yayi, had'i da zame bakinsa daga cikin nata, yakai bakinsa saitin kunenta muryarsa na creaking, yace "Wa iyazubillah! ya fad'a yana lasar kunnenta, kanta ta fara girgiza mishi had'i da saka kuka, tace " ni dai a'a dan Allah, ta fad'a cikin kuka, " Sakeni". ya kuma fad'a, kamar mai koyan magana muryarsa can k'asan mak'ogawaro, kana mayar da bakinsa cikin nata, yana cigaba da shafa saman booms d'inta, ido Sanah ta bud'e ta bishi da kallo taga daga shi sai boxer, abinda bata tab'a ganin a rayuwarta ba, tsiraicin babba, kana tabi jikinta da kallo taga jikinsa babu riga an zame ta k'asa, wajen k'ugunta, skirt d'in dake jikinta ma an tattare shi sama, da k'arfi ta saki gigitaccen kuka, wanda ya dawo da Sir Moli duniyarsa ta ainahi, da sauri ya d'agata had'i da hantsilawa baya a gigice, a kid'ime ya dafe kansa yana bin jikinshi da kallo kamar mai tabbayar kansa me yayi, ido ya rumtse da k'arfi yana furta, LA'ilaha'illa anta subahaka innikuntu minazzalumin, azubullahi minashaidani rajin," jikinsa ya kuma kalla yaga yadda yake,, hannu yasa ya dafe kansa da tsananin k'arfi, yana mamakin kansa da abubuwan da yake yi a cikin kwanakin nan, ya rasa meyasa daya ganta koya keb'e da ita yake loosing control, cikin tsananin dana sanin abinda yayi , ya mik'e da da sauri ya d'auki towel d'insa ya d'aura, kana cikin sauri da maimaita addu'o'in ya shiga toilet ya sakarwa kanshi ruwa, tare da rumtse idonshi yana mai zubda zazzafan hawaye da jin kunyar kanshi da mahaliccinsa, bedroom ya fito tare da shirya. A kunyace ya fito, koda ya fito ganinta yayi yadda ya barta, a durk'ushe tana ta faman kuka, Ido ya kawar tare da tsuke fuska da neman tsari daga sharrin shaid'an yace, "Keeeh wai a nan zaki kwana nane?". Kallonshi tayi tana cigaba da kukan, " Tashi in meda ke gida, ya fad'a muryarsa na rawa kamar kuka zai kwabce mai, bata ko kalli inda yake ba ta cigaba sa kukanta, murya can k'asa cike da madame yace, *" kiyi hak'uri!* red eyes d'inta ta d'aga ta kalle shi cike da hawaye tace " hak'uri!? Kansa ya kawar gefe cikin tsananin jin haushin kanshi da nadama, kana yace " Wallahi ni ma ban san yadda akeyi hakan na faruwa ba, Wallahi Allah ba halina bane". batayi mishi magana ba, ta mik'e dan gani take hankali yake san kuma raina mata,, gyara rigarta da skirt d'inta, tayi hanyar fita bata ko kalli inda yake ba, ganin k'ofar akwai password yasata tsayawa cak, batare data juya ko tayi mishi magana ba, mik'ewa yayi ya nufi inda take, ganin ya nufo ta gadan-gadan yasa ta matsawa had'i da kauda kanta gefe, bayyi mata magana ba, tissue ya d'auka a gefe ya mik'a mata batare dayace mata komai ba, kanta ta kuma kawarwa gefe , fuska ya tsuke ya kuma tare da d'aga kafad'arsa, alamar i don't care, kana ya tab'e bakinsa ya zauna akan sofa had'i da d'ora k'afarsa d'aya kan d'aya, yace " anyway! ni bazaki kwananmin a gida ba." kallansa tayi taga kwata-kwata babu abinda ya dame shi, sai ma yadda yake wani reacting kamar itace mai laifin, cikin rawar murya tace " amma dai kasan kallo da zargin da akeyi mana ko? " Ko so kake mu tabbatar da mummunan zato da zagin da ake yi mana? " So kake ni in zama karuwa, fasik'a mazinaciyar daya ambace ni dasu? " Ko so kake yi mu zama MAZINATAN da gaske? Take launin idansa ya canja, ya dawo asalin Sir Aryan Moli, fuskarta tayi jajir yadda kasan ta watsa mishi wuta, idansa ya runtse batare dayayi magana ba, " dan Allah ka tashi mu tafi, ko ka bud'e min k'ofar na tafi, kaga dare yayi har anyi sallar ishshsha, idansa ya bud'e da suka koma pure red, ya zuba mata su, batare daya motsa daga inda yake zaune ba, kallansa ya mayar ga tissue d'in, yayi alama da idansa data d'auka ta goge fuskarta, sanin matuk'ar bata d'auka tayi abinda yace ba, sai dai su ta zama anan, yasata d'aukar tissue d'in ta goge fuskarta, bayyi mata magana ba ya mik'e ya bud'e k'ofar, da sauri ta fita yadda kasan ana hankad'a ta, bayanta yabi da kallo yayi wani irin ajiyar numfashj had'i girgiza kansa kana yabi bayan ta. K'ofar gidan su yayi parking batare daya bud'e k'ofar motar ba, k'ok'arin bud'e k'ofar motar ta shiga yi, taji ta a kulle, kallansa tayi had'i da zuba masa ido batare datace masa komai ba, kansa ya kauda gefe yana kallan waje, muryarsa can k'asa yace *kiyi hak'uri,"* yayi maganar kamar bashi ya fad'a ba, kallansa tayi cikin mamaki kana tace " akan me? "Ki yi hak'uri, ya kuma fad'a yana kallan waje, murmushin yak'e tayi dan tasan idan ta tsaya zasu iya kwana nan, tace " bakomai, Allah ya yafe mana gaba d'aya, bayyi magana ba, yayi unlocking k'ofar, fita tayi da sauri tana mamakin yau Sir Moli da kanshi ya bata hak'uri, kallanta yayi yaga yadda take sauri kana yaja motar yabar wajen. Duk duniya yanzu babu abinda ya damu Khulud kamar kewar Sanahrta, wayarta dake gefe ta d'auka tayi dialing number Sanah, wayar na fara ringing Sanah ta d'aga, tana dariya tace " uhmm kaga amarya Hanash Waseef, Khulud ta turo baki kamar Sanah tana kallanta tace " my Sanah Allah nayi fushi, Sanah ta zaro ido tace " me kuma nayi? Khulud tace " oho ban sani ba, Sanah tace " please mana, Khulud " amma yau fa 2 weeks nake dashi a gidan nan baki zo ba, Sanah tayi dariya tace " ai barinki nayi kici amarci, Khulud tace " amarcin banza, ni dai yaushe zaki zo, Sanah tace " ki bari sai weekend sai nazo na yini, Khulud tace " a'a ni dai kizo yau, Sanah tace " yau yamma tayi ki dai bari sai gobe, Khulud tace " are you sure zaki zo goben? Sanah tace " in sha Allah, hira sukayi sosai kana sukayi sallama, washe gari ta shirya ta nufi gidan Khulud, tana shiga harabar gidan taga Hanash na k'ok'arin shiga mota, yana ganinta ya fasa shiga ya tsaya had'i da hard'e hannunsa a k'irji, ya kafe ta idansa, nufarshi tayi tana dariya kamar wani abu bai faru, cikin fara'a tace " ango! " ke! uban me ya kawo ki gida na? Shiru tayi batayi masa magana, yace " ko gidan ubanki ne? Still shiru tayi, ya kuma cewa " kina da gado cikin gidan? Ido kawai Sanah ta zuba masa batare datace masa k'ala ba, yace " ni gida na ba gidan 'yan iska da karuwai bane, dan haka karki kuma zuwanmin gidan, in ba haka ba, wallahi duk abinda nayi miki ke kika ja, ba musu Sanah ta juya ta fita zuciyarta tayi mata k'ona kamar zata fashe, sai da Sanah ta koma gida kana ta kira Khulud, tayi mata k'aryar suna da test, tayi hak'uri next week zata zo. Yau kimanin wata d'aya da sati biyu kenan da zuwan Sanah gidan Sir moli har wannan zuwan ya zama sanadin da yayi romancing da ita, tun daga wannan ranar har yau Sir moli azumi yakeyi da isiqfari da neman yardar Allah, yayi niyar bazai bar yin azumin nanba har sai yaji a jikinsa ubangijinmu ya yafe mishi, ya kuma k'ara dagewa da azumin da addu'o'in Allah ya sassauta mishi wani abun da yake yawan ji matuk'ar yana tare da Sanah, Sir moli bawan Allah ne tsarkakekke bai taba kusanta kanshi da zina ba ko saudaya a rayuwarsa duk da zama cikin turawa da yayi, shiyasa yanzu da haka ta faru yake matuk'ar jin kunyar kanshi da tsoron abinda ya aikata, shiyasa kullum yake azumi sai ran jumma'a-jumma'a yake hutawa. Khulud na kitchen tare da Hanash tana girki yana taya ta, ya motsa jikinta ya rungume ta baya yace " Allah yasa nan da 8 months mu samu baby, ido ta zaro tace " 8 months kuma? Yace " eh! man, ai nasan zuwa yanzu na saka kwai na, ya fad'a yana shafa cikinta, dariya tayi tace " da wuri haka? " To me zamu jira!? Tace " wai meyasa kai kullum baka da wata magana sai ta haihuwa da yara, kab'arsa ya d'ora bisa kafard'arta yace " wallahi Khulud bani da burin daya wuce naga yara na a duniya, ina mugun san yara da yawa Allah, kinga ma Jadda kullum bata da wata magana sai ta samun yara, kullum tambayarta matarta nada ciki, murmushi tayi kana tace " Allah ya bamu masu albarka ya amsa da " Amin, girgikin ta gama ta zuba a food flask, ta juyo ta kalle shi tace " to ga na my Papu, dariya yayi yace " shiyasa kullum babu bashi da wata magana sai taki, dariya tayi tace " ai haka ake so, to mu gama cin abincin sai mu kai musu ko? Cikin zumud'i tace " da ni zakaje, "eh! yace , yana fita da abincin, sai da suka gama kintsawa kana sukayi gidan Mimmee, part d'in Jaddah suka fara shiga saboda kar tayi musu k'orafi, zaune suka iske ta a parlor, tana ganinsu ta mik'e idanta nakan cikin Khulud, tayi murmushi tace " mai ciki da kanki, meyakun kiyi mana waya mu muzo? Dariya Khulud tayi tana sunne kanta, Jadda tayi murmushi tace " kin ganni nan harna fara siyan kayan haihuwa ta fad'a jawo wata leda, bud'ewa ledar tayi ta shiga ciro kayan jarirai kala-kala, Hanash yayi dariya yace " kai Jadda wannan ai har kin fimu zamud'in haihuwar, tana dariya tace " ai dole d'an Hanash guda, ai duk ranar da aka haife yaron nan zaiga gata, ji nake kamar na jawo watannin haihuwar, murmushi sukayi kana sukayi mata sallama, suka shiga part d'in Mimmee, babu kowa a parlor'n, dan haka Hanash yayi sallama da k'arfi, Papu ya fito daga gyms room, yana murmushi cike da so da jin dad'in ganinsu, dan harga Allah Papu yana mugun san Khulud, yana jinta har cikin ransa, yana jin babu abinda bazai iya yi mata ba, kullum cikin tambayarta abinda take so yake, amma amsar d'aya ce babu, har jiran ranar dazata nemi wani abu daga gare shi, har k'asa suka durk'usa dukkansu suka gaidashi, ya amsa cikin fara'a, Hanash yace " Mimmee fa? Papu yace " sun tafi kasuwa dasu Wajnah, Hanash yace " dama 'yar gaban goshinka ce tayi maka girki, Papu yayi murmushi yace " masha Allah, a zubo min naci, Khulud ta mik'e ta shiga kitchen ta d'auko plate da serving spoon ta zuba masa sakwara da miyar agushi data gashi dajin dry dish da sukunbiya had'i da ganda, Papu yace " kai masha Allah gaskiya nagode sosai, Papu ya zage yaci abincin sosai ya k'oshi, ganin har yamma su Mimmee basu dawowa yasa su Hanash tafiya. Su Khulud na tafiya kiran Sanah ya shigo, da sauri tayi picking amma batayi mata magana ba, Sanah tace " hello my Ulud! Khulud tayi mata banza, Sanah tace " kiyi hak'uri idan laifi nayi, still Khulud batayi mata magana ba, Sanah tace " kiyi man magana please, fashewa da kuka Khulud tayi wanda yasa Hanash saurin yin parking, yace " lafiya my wife, bata kalle shi ba, tace " haba my Sanah ace har shiga wata na biyu amma baki zo kin ganni ba, d'an tsoki Hanash yaja jin dailin kukanta kana yaja motar, Sanah tace " kiyi hak'uri gobe zan zo na yinar miki kinji my Ulud, cikin murna Khulud tace " Allah da gaske goben zaki zo? Sanah tace " Allah nayi miki alk'awarin zanzo na yini ma, cikin zumud'i Khulud tace " me zan dafa miki? Sanah tace " no karki bawa kanki wahala, ki bari idan nazo sai mu girka tare Khulud tace " OK badamuwa, har suka isa gida Sanah da Khulud na waya. Washe gari da wuri Sanah ta shirya, driver ne ya kaita a k'ofar gidan ta sauka ta shiga cikin gidan, tsaye ta ganshe sanye da jallabiya, da gani yasan da zuwan nata ita yake jira, "sannu da zuwa mayya makwawaciya, uwar naci da jaraba, an kore ki an kore amma dan tsabar jaraba da naci kin dage sai kin zo, wannan wanne irin naci da jaraba ce, bata kula shi ba, ta rab'e ta gefensa zata wuce, da k'arfi Hanash yasa hannunsa ya fisgo ta ya dawo da ita baya, kana yace " ke! ni sa'an uban ki ne da ina yi maki magana zaki wuce? " Ko gidan da kike k'ok'arin shiga gidan uwarki ne? Idanuwan Sanah sukayi jajir saboda tsabar ruwan bala'i, amma ba damar yin magana, ga abun gudu sai da ba gurin zuwa, a cikin kwayar idanta ya hango tsantsar b'acin rai da ruwan masifar dake cinta, murmushi yayi yace " oh! na manta da tantiriyar fitsararriya mara kunya nake magana, idanta ta runtse a hankali, sannan ta bud'e had'i da had'iye abinda take ji , ta zagaye shi zata wuce, da k'arfi ya kuma jawo ta had'i da kifa gigitaccen mari, kana ya hankad'a baya ta fad'i k'asa, nunata yayi da yatsa yace " wallahi kika kuma k'ok'arin shiga cikin gidan nan sai nayi miki jahilin bugu dan ubanki, shegiya kamar gidan ubanta ko da gadanta cikin gidan, still batayi mishi magana ba ta mik'e ta kakkab'a jikinta, ta kalle shi ido cikin ido tace " kaci darajar masu daraja, kaje kaci albarkacin alk'awarin daya yiwa Khulud, kuma duk d'an halak cikekken mutum baya karya alk'awari, k'ara d'auke ta yayi da mari, sai da ta kifa saboda k'arfin marin, kana yace " lalle 'iskanci da rashin kunyarki sun rik'a in banda haka kizo har cikin gida na ki nemi gaya mana magana, to bari kiji matuk'ar san da kikewa Khulud gaskiya ne, matuk'ar kina san farin ciki da walwalarta su d'ore kiyi nesa da ita da gidanta, zatayi magana yasa hannunsa ya rik'o hannunta ya soma janta a da k'arfi har tana fad'uwa yana fizgota sai da ya kaita har waje kana yacewa mai gadi " duk ranar daka k'ara barin wannan ta shigo a bakin aikinka, Ita kuwa Khulud na parlor zaune tana zaman jiran Sanah, haka kawai taji gabanta na fad'uwa, a hankali ta mik'e ta shiga bedroom wajen Hanash, ganin baya nan yasa ta lek'awa bathroom nan ba baya nan, a hankali ta juya zata fito, karaf idanta ya sauka akan Hanash dake tsaye bakin get yana zazzaga ruwan bala'i, a kamar mutun ta hango a durk'ushe a gabansa, a hankali ta k'ara lek'awa dan taga wanda ke durk'ushen amma bata gane ba, bata wani damu data gani ba, dan haka tayi komawarta parlor ta zauna, d'an tsoki taja had'i da kallan agogo, a hankali tace " kodai my Sanah bazata zo ba? Ta tambayi kanta, baki ta tab'e kana tace " Hanash ko shida wa oho! yake ta bambami, gabanta ne yayi muguwar fad'uwa tunowa da tayi Sanah, da sauri ta mik'e ta koma bedroom d'insa ta kuma l'ek'awa ta window, ganin still bata ganin wanda ke durk'ushen yasa juyawa ta fita da gudu ta nufi harabar gidan................... *Alhamdulillah wata ya tsaya, inai mana fatan muyi azumin Ramadan lfy, Allah kuma ya amsa mana ibadunmu* MOMYN ZARAH _*RASHIN SANI.......*_ *HAUWA A USMAN* _JIDDARH_ ```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh``` _DIDECATED TO_ *MY AUNTY AYSHA ALIYU GARKUWA* (```GARKUWAR MARUBUTA```) ~MY UWAR ROOM~ 2⃣8⃣ Khulud ba ko takalmi ta k'arasa harabar gidan, shi kuma dai-dai lokacin ya juyo yana niyyar shiga cikin gidan, a tsakiyar compound suka had'u, kallanta yayi kana yace " lafiya? " Lafiya ta bashi amsa tana hangawa bayansa, bayan nasa shima ya juya ya kalla kana ya mayar da idansa kanta, yace " me kike dubawa? " My Sanah ta bashi amsa, " oh!, yace yana rik'o hannunta, da nufin shigar da ita cikin gidan, k'in binsa tayi ta tsaya cak, tana kallansa a marairaice, yace " me kuma? " Ina My Sanah ta tambaye shi, wata muguwar fad'uwa gabansa yayi, amma ya dake kamar babu komai yace " kamar ya? Tace " bada ita na ganku yanzu kuna magana ba? Murmushi yayi had'i da sungumarta cak, yayi cikin gidan da ita, cikin sanyin murya tace " please my Sanah!, murmushi ya kuma yi yace " oh! wannan duk d'okin ganin our Sanah ne? Zata kuma yin magana yayi saurin had'e bakinsu, yana cewa muje na gaisa da baby na, dan nasan idan our Sanah tazo ba'a da lokaci na, ya fad'a yana tura k'ofar bedroom da k'afarsa, dole tasa Khulud yin shiru amma badan taso ba, dan gaba d'aya hankalinta yana kan Sanahrta, kwantar da ita yayi a kan bed yana cigaba da shan bakinta, had'i da shafa jikinta, a hankali ya rabata da kayan jikinta, kana ya kashe arna, Hanash bai wani samu yadda yake so ba, dan Khulud bata sakar mishi jikinta yadda ya kamata ba, bata kuma taimaka mishi wajen bashi hakk'in nasa ba, dan kwata-kwata bata cikin hankali da nutsuwarta, dama ko ba yanzu ba, yana fuskantar irin wannan matsalar daga wajen Khulud, dan kwata-kwata bata da wayewa a wajen sex, kwanciya takeyi kamar ruwa sai dai shi ya sarrafa ta, amma even romance Khulud bata iya yi mishi, farko-farko ya d'auka kunya da rashin sanin, da kuma rashin sabo da abun ne ke damunta, amma yanzu gashi kusan 3 months da auren su, amma still bata san komai ba, gashi shi ba abokanai ba balle ya kaita wajen matan su suyi mata bayani, kuma shi kunyarta yake ji bai iya yi mata bayani da kansa, dan gani yake kamar cin fuska da wulak'anci ne, shi yadda ake fad'ar ana mugun jin dad'in sex shi bai wani ji, dan wani lokacin ma sai yayi da gaske yake yin releasing, tun abun bai damunshi har abun ya fara damunshi sosai, wani lokacin koda yana cikin buk'ata hak'ura yake yi, dan bai san shan wahala a banza, bayan komai ya lafa tsakanin Hanash da Khulud ya jawo ta jikinsa ya rungume ta tsam a k'irjinsa. Yana shafa kanta, deep down kuma yana sak'e-sak'e a ransa, yana jin inama zai iya fitowa ya fad'a mata gaskiyar abinda ke ranshi, sun kai 15 minutes a haka kana ta mik'e ta shiga bathroom, tayi wankan tsarki ta shirya, wayarta ta d'auka da nufin kiran number Sanah, Hanash yayi saurin cewa " my love yunwa nake ji bani abinci naci, ido ta zaro waje tace " yanzu fa kaci abincin, yayi kyakkyawan murmushinsa kana yace " bakiga uban aikin danayi yanzu ba? " Ai dole naji yunwa tunda kin zuk'e abincin dana ci, bata kuma cewa komai ba saboda kunyar abinda ya fad'a, ta juya da sauri ta nufi kitchen, tana fita yayi saurin d'aukar wayarta ya sanya number Sanah a black list, bata jima da fita ba ta dawo d'auke da tray, sai da yaci abincin sosai kana ya shiga wanka. Sai da Sanah ta tsaya a bakin get d'in da Hanash ya hankad'o ta, taci uban kukanta sosai, kana ta share hawayenta, ta mik'e ta nufi bakin titi, tana tafe hawayen bak'in ciki na sake zubo mata, Allah ya taimake ta tun kafin ta k'arasa bakin titin ta samu mai napep, da sauri ta tsaida shi ta shiga ta zauna, sai da ta zauna kana ta fad'a masa inda zai kaita, sai da ta tsaya a bakin get d'in shiga gidan su, ta saita kanta kana ta shiga, dan bata san kowa ya fuskanci abinda ke faruwa tsakaninta da Hanash, bata tsaya shiga part d'in Halan ba tayi shigewarta part d'in Mamu kai tsaye, a parlor ta iske Mamu tana jera abinci a dinning, kallo d'aya Mamu tayi mata ta fuskanci da akwai matsala, da sauri Mamu ta nufe ta tana cewa " ke lafiyarki? Murmushin k'arfin hali Sanah ta k'ak'aro kana tace " meye Mamu? Mamu ta kalle ta cike da mamaki tace " ban gane me ba? " Bayan ga fuskarki nan da idanki sun nuna kinyi kuka, rolling sexy eyes d'inta tayi kana tace " kuka kuma Mamu? Mamu tace " ke ban san rainin hankali, zanci ubanki wallahi, ni kike san yiwa yawo da hankali dan gidan ku? Sanah ta zumb'uro baki kana tace " ni fa babu komai Mamu, Mamu tace " wai tsaya ma, ba gidan Khulud kika tafi ba? Sanah tace " ni kuma? Ta fad'a tana zaro idanta waje, " ni bance zani gidan Khulud ba, Mamu tace " kan uba!, ke ni kike san maidawa mahaukaciya ko me? " Idan ba gidan Khulud kika ce zaki ba, gidan ubanki kika ce zaki? Sanah tace " a'a ni test naje nayi, Mamu tace " oh! ni Allah na, Ubangiji ya kawo mu wannan lokacin, yanzu Sanah ni zaki yiwa yawo da hankali dan ubanki yanzu kina nufin har kinje BUK, kinyi test kin dawo ko me kike nufi? Ta fad'a tana kallan Sanah a k'ufule, Sanah tace " kai Mamu dan Allah kiyi hak'uri ki kwantar da hankalinki mana, cikin fad'a Mamu tace " a gidan ubanki zan kwantar da hankalin nawa, kin fita kin kuma dawo min gida kina kuka, sannan kina neman raina man hankali, amma ina zuwa, ta fad'a tana nufar inda ta ajeye wayarta, ta d'auka had'i dayin dialing number Khulud, da sauri Sanah ta k'arasa inda Mamu ke tsaye fuskarta d'auke da tsoro tace " me zakiyi Mamu? Mamu bata kula ta ba, ta maida hankalinta ga abinda take yi, Khulud na zaune kusa da Hanash taji wayarta na ringing, bai wani damu ba saboda ya san ya saka number Sanah a black list, da sauri Khulud tayi picking ganin number Mamu, cikin girmamawa Khulud ta gaida Mamu, Mamu ta amsa kana tace " Khulud ba gidanki Sanah tazo yanzu ba? Sanah najin Khulud Mamu ta kira tayi saurin zaro ido, Khulud tayi shiru ta rasa amsar da zata bayar, a hankali tace " lafiya Mamu? Mamu tace " 30 minutes back tayi man sallama tace " ta tafi gidanki, amma yanzu ta dawo cikin damuwa kuma da gani taci uban kuka sosai, ido Sanah tayi rolling, itako Khulud idanta ta zaro tana yiwa Hanash kallan zargi، kana ta cewa Mamu bani Sanahr, Mamu tace " kamar ya na baki Sanah? " Karku had'u kuyi min yawo da hankali, tambayarki nayi dan haka ki bani amsa, cikin sanyin murya Khulud tace " eh nan tazo, Mamu tace " meya faru da har tayi kuka? Khulud tayi shiru na d'an wani lokaci kana tace " wai cikinta ke ciwo, Mamu tayi tsaki kana tace " Allah ya shiryeku, cikin sanyin Khulud tace " Mamu bani ita please, Mamu tace " ai kina da phone number ta ki kira ta mana, Khulud zata kuma yin magana Mamu ta kashe wayarta, bata k'ara bi takansu ba ta cigaba da subgoginta, cikin sanyin jiki Khulud tabi wayar da kallo na wani d'an lokaci, kana ta k'urawa Hanash ido tana karantar yanayinsa, " me!? Yace, yana kallanta, yayinda gabansa ke fad'uwa, idanta na kansa tace " me kayiwa My Sanah? Da sauri ya mik'e zaune kana yace " kamar ya menayi mata? Idan Khulud na kansa still tana karantarsa tace " please me kayi mata? " Wani abun tace nayi mata? Ido ta kafe shi dashi batare data kuma cewa komai ba, shima shirun yayi bai ce komai ba, wayarta ta d'auka, tayi dialing number Sanah amma sai taji not reachable, bata kawo komai a ranta ba ta aje wayar, itama Sanah nacan na faman neman layin Khulud amma busy yake nuna mata. Tunda Sir Moli ya lura matuk'ar ya keb'e da Sanah yana loosing control, yasa shi yin nesa sosai da ita, ya gujewa duk wani abu da zai keb'anta shi da ita, dan shi kansa yana mugun mamakin kansa, ya rasa meyasa yake shiga wani yanayi idan yana tare da ita, ya rasa meyasa yake mance kansa idan yana tare da ita, shi dai yasan a iya tsayin rayuwarsa bai tab'a kusantar zina ba, ya zauna da turawa, larabawa, indiya da sauran jinsunan duniya, amma bai tab'a tsintar kansa da irin haka ba, sai akanta, sosai ya dage da yin azumin nafila da istigfari, saboda neman tsira dan gani yake kamar ya aikata babban laifi. Yauma bayan sun gama attending lectures, bata fito ba sai gab da magariba, ganin yanayin garin na damuna ga kuma dare na neman kawo kai, yasa Sanah yin sauri sosai, tun daga nesa ya hangota, yayinda dashi ke zaune cikin motarsa k'irar ferrari, yana driving, idansa ya lumshe lokacin dayazo zai wuce ta dai-dai ita, yana san taimaka mata ya d'auke ta, amma baijin zai iya yin haka, dan gudu da kaucewa duk abinda zai kai shi ga keb'ewa da ita, balle har a samu sab'anin da zai iya kawo shigar wani abun a tsakaninsu, motar Sanah tabi da kallo had'i da tab'a bakinta tace " kai dai ka sani. Hanash kwance akan k'ayataccen royal bed d'insa, ya fad'a duniyar tunani, idan da abunda yafi damunsa yanzu a duniya bai wuce na rashin gamsuwa da jin dad'in sex da bayayi ba, saboda kwata-kwata baya samun ishashshiyar gamsuwa, ba wai dad'i ko ruwan ni'ima ne Khulud bata dashi ba, tana da ni'ima sosai kamar me, dan ruwan ni'imarta har mamaki yake bashi wani lokacin idan yaga yadda take b'ulb'ulo da ruwa daga k'asanta, shi abinda ke damunsa kwata-kwata bata iya sex ba, bama tasan yadda zata yi sex d'in ba, ga rashin samun had'in kanta wajen sex, da rashin taya shi, kwata-kwata bata iya komai ba, ba kuma tasan komai, shi kad'ai yake kid'ansa yake rawarsa, ko romance bata iya ba, gashi bata iya sex styles and irin kukan kissa da nuna irin tana enjoying sosai ba, sai dai ta kwanta kawai kamar ruwa, shi zayyi komai ya sauka, wannan abun yana matuk'ar damunsa, dan tun abin baya damunsa yanzu har abun yazo ya zame mishi babban matsala, dan wasu lokutan ma yana bala'in jin haushinta, dan ji yake kamar ya rufe ta da duka, ita ko irin shigewa jikin miji, da nanik'ar miji batayi, ko irin zama akan cinyarsa batayi, kwata-kwata ba romantic girl bace, shi kuma gashi so hot romantic, yana bala'in san irin rayuwa da soyayyar turawa, yana san koyaushe ya kasance matarsa tana nanik'e dashi, yana bala'in san mace mai san jiki, da iya love, & romancing, sosai yake cikin damuwa, ya rasa ta inda zai b'ullo mata, ya rasa ta hanyar da zai bi yayi mata bayani, yana tsaka da tunaninsa ta shigo, zama tayi a bakin bed d'in fuskarta d'auke da murmushi tace " breakfast is ready Sir, idanshi na kanta yace " ji babu ko d'an sexy abu balle romantic, babu even kiss, just breakfast is ready, ya fad'a cikin ransa, a fili kuma yayi mata guntun murmushi, kana ya mik'e ya shiga bathroom batare dayace mata komai ba, mik'ewa tayi ta fita ta koma parlor, yana jin fitarta ya tab'e baki had'i da cewa " even wanka da miji bazata iya ba, dan duk wad'annan abubuwa babu yadda bayyi ya koya mata ba amma tak'i ta d'auka, sai da yayi wanka ya shirya kana ya fita parlor'n, a parlor ya same ta zaune, tana ganinshi tayi saurin mik'ewa tana murmushi, shima murmushin yayi mata kana suka zauna a dinning table, serving d'inshi farfesun kayan ciki da soyayyar doya da miyar kwai tayi, sama-sama ya d'an tsakuri abincin ya mik'e, da sauri ta kalle shi ta kalli abincin tace " wai kana nufin har kayi me? Murmushi yayi mata yace " Alhamdulillah na k'oshi, bata kuma yin magana ba ta mik'e rik'e da brief case d'insa, " ba ko tarairayar miji, ko irin ta saka ni gaba tana yi man shagwab'a tana tarairayata akan dole sai naci abincin babu, ina cewa nak'o shi shikenan, bayan tasan ba iya abinda na saba ci kenan ba, ya fad'a cikin ranshi, har bakin mota Khulud ta raka shi ya shiga kana ta koma cikin gida. Kullum sai Khulud tayi ta faman kiran number Sanah amma not reachable, haka itama Sanah kullum cikin kiran number Khulud take amma busy, dukkansu basu kawo komai a ransu, dan haka suka cigaba da harkokinsu, haka ma sau uku Sanah na zuwa gidan Khulud mai gadi yana hanata shiga, daga k'arshe ma rok'arta yayi akan dan Allah karta k'ara zuwa saboda mai gidan yace zayyi asarar aikinsa, dole Sanah ta hak'ura ta daina zuwa gidan Khulud, haka duk sanda Hanash zai kai Khulud gida, sai ya tabbatar da Sanah bata gidan, sannan zai kaita, kafin ta dawo kuma sun bar gida, haka suka cigaba da rayuwa lokaci na tafiya har Khulud tayi wata hud'u da aure, amma ko sau d'aya basu tab'a had'uwa da Sanah ba, tun bayan aurenta, su dukkansu basu tab'a tsammanin zasuyi kwana d'aya a rayuwarsu batare da sunga juna ba. Su Khulud na zaune a parlor'n Mimmee ita dasu Zohal, Mimmee ma na zaune gefensu, Zohal ta kalli agogo tace " kinga har 3:30pm na rana tayi, muyi sauri mu fita kafin Yaya ya dawo, yanzu daya dawo sai yace yamma tayi babu inda zamu mu bari sai gobe, Khulud tace " gaskiya kam muyi sauri dan nima ina san zuwa saloon d'in nan wallahi, Mimmee tace " ta ku tashi kuyi sauri ku shirya mana, kun tsaya kuna surutu, Khulud tace " mu ai mun shirya Wajnah kawai muke jira, Mimmee tace " ina Wajnah nan? Zohal tace " tana bedroom tana ta faman k'ak'ale-k'ak'ale kema ai kinsan halin shirinta, Mimmee tace " ikon Allah ta kuje ku kirata mana, kafin suyi magana Wajnah ta fito tana cewa " gani ma na fito ai, babu wanda yayi magana duk suka mik'e Mimmee ta bisu da kallo d'aya bayan d'aya, suna k'ok'arin fita Jaddah ta shigo, tana binsu da kallo, kana tace " ina zuwa? "Saloon cewar Zohal, kallan Khulud Jaddah tayi kana tace " wajenki fa nazo, Mimmee ta kalli Jaddah cikin mamaki batare da tace komai ba, Khulud ta durk'usa har k'asa tace " ina yini? Jaddah bata amsa gaisuwarta ba, tace " ke wai har yanzu ba wani labari ne? Khulud ta kalleta cikin rashin fahimta, tace " me Jaddah!? Jaddah tace " watan ku hud'u kenan da aure amma har yanzu banji kin fara 'yan amaye-amaye, da rashin lafiyar laulayi ba, ko har yanzu babu komai, ni fa kin san babu abinda nafi so sama da ganin yaran Hanash ato kima dage, Khulud durk'ushe agaban Jaddah kanta na k'asa, daga Mimmee har su Wajnah babu wanda yace k'ala, dan sanin halin Jaddah sarai, Papu dake sakkowa daga samansa yace " Jaddah ba sai Allah ya kawo ba tukunna, ai basu isa su bawa kansu ba, sai idan Allah yaga dama ya basu tukunna, kallan Papu tayi cike da mamaki dan hakan bata tab'a faruwa ba, tunda take dashi bai tab'a mayar mata da magana ba sai yau akan Khulud, Khulud ta kalla kana ta juya zata fita, harta kai bakin k'ofar fita ta kuma juyowa tace " ni dai na fad'a miki, kana tasa kai tayi ficewarta, Papu ya k'arasa shigowa cikin parlor'n, a hankali Khulud ta juya tana gaida Papu, cike da fara'a ya amsa kana yace " kiyi hak'uri kinji? Murmushi tayi tace " lah bakomai Papu, yayi murmushi shima, kana suka fita. Washe gari Sanah bata shiga makaranta ba sai around 10:30am na safe, saboda bata da lafiya zazzab'i da ciwon kai ke damunta sosai, a hankali take tafiya dan ji take kamar zata fad'i saboda jirin dake d'ibarta, in banda suna da test da Sir Moli babu abinda zai kawo ta makarantar, tana shiga class Rose ta nufo ta da sauri ganin yanayin datake ciki, dan tun da suka samu d'an sab'anin nan suke shiri, Rose tace " meke damunki, murmushi Sanah tayi kana tace fever & headache, cike da tausaywa Rose tace " ayya sorry, gashi har anyi test baki nan, da sauri Sanah ta d'ago kanta tace " Sir Aryan har yayi test d'in!!? Rose tace " yes! tun around 9:30am na safe, kai Sanah ta dafe had'i da cewa " ya salam! shiru tayi na wani lokaci kana ta kalli Rose tace " please ki raka ni office d'insa, Rose ta zaro ido waje cike da tsoro tace " am sorry sister babu abinda zaki tambaye ni na kasa yi maki, amma ban iya rakaki office d'insa, shiru Sanah ta kuma yi, batare data kuma cewa Rose komai ba, ta nufi office d'insa, sallama tayi ya bata izinin shigo, a hankali ta tura k'ofar ta shiga, yana kishingid'e akan sofa, idanuwansa lumshe, ta durk'usa a gabansa, saboda ji take kamar zata fad'i, cikin muryar marasa lafiya tace " Sir!, bai ko motsa ba balle ya bud'e idansa ko yayi mata magana, muryarta na rawa ta kuma cewa " Sir! a dak'ile yace " fad'i, "Sir banyi test ba, " sai akayi yaya? Ya fad'a bai motsa daga inda yake ba, " bani da lafiya ne, ta fad'a muryarta ba creaking, " me zanyi miki to? Ya kuma fad'a bai motsa ba, "dan Allah kayi man tawa! ta fad'a tana kallanshi, shiru yayi baice komai ba, Khulud na kwance a parlor Hanash na gefenta zaune, tayi saurin mik'ewa ta, a hankali Hanash ya d'ago kansa ya kalleta, yace " lafiya naga kin zabura!? "Ki rink'a bi a hankali saboda unborn d'ina, dariya tayi tace " kai komai Baby, shima dariyar yayi kana yace " shine babban buri na a duniya, wallahi komai za'a bani bai kai na samu Baby ba, bani da wani sauran buri ko muradi daya wuce na ganni da d'a ko 'ya nawa na kaina, idan naga Baby na bani da sauran buk'ata a duniya, murmushi tayi had'i da cewa " Allah ya bamu basu albarka, ta fad'a tana nufar bedroom d'inta, wayarta ta d'auko ta dawo parlor ta zauna had'i da kunna data ta shiga WhatsApp, ta shiga sunan Sanah jikinta na rawa dan basirar yi mata voice note bai tab'a zo mata ba sai yau, muryarta na rawa tace " My Sanah kina kusa please? "Idan kina kusa kiyi man magana, Sanah na durk'ushe gaban Sir Moli taji notification na WhatsApp, kamar bazata duba ba, sai kuma ta duba, ganin Khulud ce yasa ta saurin kunnawa a speaker, Sanah tayi murmushi kana tace " ina kusa my Khulud, Khulud na rik'e da waya tana jiran amsa, taji k'arar shigowar sak'o, da sauri ta duba, kuka Khulud ta saka had'i cewa " me nayi miki My Sanah? Sanah tayi playing, a hankali ta lumshe idanta jin Khulud tana kuka, kana tace " meye my Ulud? Khulud tace " au meye ko? Sanah tace " eh mana, cikin kuka Khulud tace " haba my Sanah yanzu fa na shiga 5 months da aure amma baki tab'a zuwa inda nake ba, tunda nayi aure bamu sake had'uwa ba, wallahi ko a mafarki aka fad'a min zamuyi 5 months bamu had'u ba ban yarda, matuk'ar muna raye a duniya, musamman ma a cikin gari d'aya, dan Allah idan wani laifin nayi miki ki fito ki sanar dani sai na gyara, na kuma baki hak'uri, idan kuma akwai abinda ke faruwa please ki sanar da ni, dan Allah hukuncin nan yayi man tsauri, Sanah na danne kukanta tace " kiyi hak'uri kinji my ulud, komai na duniya muk'addari ne kuma yana da iyaka, Khulud tace " dan Allah kizo yau please, Sanah ta lumshe idonta hawaye na zuba, tace " kiyi hak'uri my Ulud ban iya zuwa dan bani da lafiya, Khulud ta tura mata amsa cikin tashin hanakali " subhanallah meke damunki? Sanah tace" fever & headache, Khulud tace " kina ina yanzu? Sanah tace " ina makaranta, Khulud tace " yaushe zaki dawo gida? " Sai dare, Sanah ta fad'a while hawayen bai bar fita ba, Khulud tace " to dan Allah gobe karki je ko'ina zanzo, Sanah tace " tom zan jira ki in sha Allah, sai da sukayi hira kana sukayi sallama, Hanash na jinsu, suna gama wayar ya jawo ta jikinsa ya rungume batare dayace komai ba, suna gama chart d'in Sanah ta saka kukan da take dannewa, Sir Moli yana nan yadda yake baiko matsa ba, idanuwanshi lumshe, sai da taci kukanta ta k'oshi kana ta mik'e zata fita, har takai bakin k'ofar fita, yace " meke faruwa tsaninku ku ukun? Cak ta tsaya had'i da juyowa a hankali, red eyes d'inta ta d'aga ta kalle shi, taga yana nan yadda yake, batayi niyyar b'oye masa komai ba, dan haka ta fad'a masa tun daga zuwanta na farko gidan har zuwanta na k'arshe bata b'oye masa komai ba, idansa rufe yace " yanzu kina san zuwa ganin Khulud d'in? Ido ta k'ura masa batare datace komai ba, a hankali ya bud'e idansa had'i da mik'ewa zaune, yana kallanta yace " tambayarki nake, cikin sanyin jiki ta d'aga masa kai, yace " amma kin san ban san nodding kai ko? Cikin sanyin murya tace " sorry، ya kuma cewa " kina san zuwa ganin Khulud? "Eh! tace tana kallanshi, a hankali ya mik'e batare daya kuma kallanta ba, ya zura talmi da hularsa, kana yace " muje, da sauri ta kalle shi tace " ina? " Ban sani ba, yace yana fita daga office d'in, bayansa tabi a hankali kasancewar jikinta babu kwari, office d'in ya rufe kana yayi gaba batare daya kalle ta ba، binsa tayi a baya har suka isa motarsa, bayyi mata magana ba ya bud'e ya shiga, tsaye tayi bakin motar tana kallanshi, harara ya watsa mata, ganin hararar dayiyi mata yasa ta zumb'urar baki kana ta bud'e motar ta shiga, Sir Moli bai tsaya ko'ina ba sai a unguwar su Khulud, dai-dai inda yaga Sanah da daddare, batare daya kalle ta ba yace " ina ne gidan? Nuna masa ta shiga yi har suka k'arasa bakin get, sosai gaban Sanah ke muguwar fad'uwa saboda bata san abinda zai jawowa Khulud matsala a zamantakewar aurenta, dandai babu yadda zatayi da Sir Moli ne, yasa ta biyo shi, musamman ma da irin zargin da Hanash yake yi musu, horn yayi mai gadin ya lek'o, kasancewar motar tine tac ce yasa bai ga Sanah ba, kuma daya ga motar babbar motace d'auke da private number yasa shi, tsayawa yana tunani dan shi ba'a sanar dashi akwai bak'i ba, ganin haka yasa Sir Moli zuge glass d'in motar a hankali, ya lek'o da kansa yace " bud'e, ya fad'a a tak'aice, ba musu mai gadin ya hangame get d'in, Sir Moli ya danna motarsa cikin gidan kanshi tsaye, lura da yadda Sanah take yasa shi cewa " fita، fuska ta kwab'e kamar zatayi kuka tace " please mu koma, bai kalle ta ba, yace " nace ki fita ko!? Yayi maganar a d'an hasale, a hankali Sanah ta kwab'e fuska had'i da cewa " to dan Allah karka tafi ka jira ni, bai amsa bata ba, ya kawar da kanshi gefe, a hankali Sanah ta bud'e motar ta fito, mai gadi na ganin Sanah, ya nufo ta da sauri, jikinsa na kerrma, yace " Hajiya dan girman Allah ki taimaka min karki shiga, Yallab'ai yana nan, kuma a gabanki yayi min gargad'i, Sanah zatayi magana Sir Moli ya bud'e motar ya fito, ya jingina da jikin motar had'i da hard'e hannayensa a k'irjinsa, yace " gargad'in me yayi maka? Muryar mai gadin na rawa yace " Yallab'ai ne yace muddin na kuma barinta ta shiga cikin gidan a bakin aiki na, "Ok Sir Moli yace kana ya mayar da kallansa ga Sanah yace " shiga, fuska ta kwab'e kamar zatayi kuka tace " please! mai gadin yayi saurin cewa " dan Allah ku taimaka min، ina da yara k'anana, da mata, sannan ga iyaye na, ga yaran d'an uwana daya mutu, duk a k'ark'ashi na suke, ni kuma da wannan aikin kad'ai na dogara, Sir Moli yace " idan ya koreka kazo zan baka aiki mai kyau, ya fad'a batare daya kalli inda mai gadin yake ba, mai gadin yace " ni dai dan Al........., hannu Sir Moli ya d'aga masa, yace " please Baba kayi shiru nace idan ya kure ka zan baka aiki, kuma dama matsalarka bata aikin bace, idan kuma aikin ne baka so zan baka jari mai kyau, shiru mai gadin yayi saboda kwarjinin da Sir Moli yayi masa, karaf idan Sir Moli ya sauka akan Hanash dake nufar d'aya daga cikin motocin dake jere a harabar gidan, da alama bai lura da su ba, daga Sanah har mai gadin babu wanda ya lura dashi, Sir Moli ya kalle ta yace " karna sake miki magana, da sauri ta nufi hanyar shiga part d'in, Sir Moli ya tsaya jikin motarsa had'i da hard'e hannuwansa a k'irjinsa, ya zubawa Hanash ido, yana nazarinsa, shi dai a fuska baiga wani mugun hali ko alamar munana d'abi'u a tattare dashi ba, sai nutsuwa da kalama had'i da suffar nagartattun mutane, daya gani tattare da Hanash d'in, abinda da marar lafiya Sanah na fara takawa tayi taku na uku, k'afarta ta gurd'e kasancewar takalmin k'afarta mai tudu ne, jiri ya d'ebeta tayi baya luuuuuu zata fad'i, cikin matsanancin zafin nama Sir Moli yayi saurin tare ta, ta fad'a jikinsa, a tsorace Sanah ta saki 'yar k'ara, saboda ta gama sadak'arwa ta fad'i, k'arar da Sanah tayi ce tajawo hankalin Hanash kansu, ya sauke idansa a kansu dai-dai lokacin da Sanah ta fad'a jikin Sir Moli. A hasale Hanash ya juyo yana kallansu cikin matsanancin b'akin rai yace " hey! nan ba hotel ko club bane, ba kuma gidan karuwai da 'yan iska bane, idan zakuyi iskancinku kuje can kuyi, tsabar rainin hankali kuzo man har cikin gidana kuna iskancin da kuka sabo yi, ko an gaya maku nan gidan 'yan iska ne? Da sauri Sanah ta fara k'oka'rin kwace jikinta daga na Sir Moli, amma Sir Moli ya k'ara manneta da jikinsa, idansa akan Hanash yana kallan cikin kwayar idansa, yana karantar yanayinsa, had'i da san fassara abinda yake hangowa cikin kwayar idan nasa, ran Hanash ya kuma mugun b'aci cikin mugun takaici yace " get out from my house, kwaratan banza, 'yan iska fasik'ai kawai, guntun murmushi Sir Moli yayi yana k'ara shigewa jikin Sanah, had'i da shinshinar wuyanta yana goga hancinsa a kumatunta, ita ko Sanah sai k'ok'arin kwace kanta take yi, amma ta kasa sai nuk'u-nuk'u take, tana k'ifk'ifta idanuwa, ido Hanash ya runtse cike da tsantsar bak'in cikin ganin abinda Sir Moli yake da mace kuma har cikin gidansa, cikin b'acin rai Hanash yace " I said get out from my house, nan ba hotel bane, gidan ma'aurata ne, Sir Moli yayi dariya kana ya saki Sanah ya maida kallansa ga Hanash yacewa Sanah " jeki shiga, tsayawa Sanah tayi bata ko iya d'aga k'afarta ba, idan Sir Moli nakan Hanash ya had'e rai sosai, yadda kasan bai tab'a yin dariya ba yace " nace ki shige ko, Hanash tsaiwarsa ya gyara yana kallan Sanah, yace " tazo ta wucen inta isa ita tacacciyar mara kunya ce, cikin kuka Sanah ta kalli Sir Moli tace " please mu koma na hak'ura da ganin Khulud d'in, gigitacciyar tsawa Sir Moli ya daka mata cikin b'acin rai yace " nace ki shiga ko!? Jikin Sanah na kerrrrma saboda tsawar da Sir Moli ya daka mata bawai saboda tsoran Hanash ba, ta nufi hanyar shiga gidan, Khulud dake zaune a parlor ta mik'e ta fito da sauri kasancewar gigitacciyar tsawar dataji Sir Moli ya daka, dama tun d'azu take jiyo maganganu k'asa-k'asa, Khulud na fitowa harabar gidan dai-dai lokacin Sanah ta rab'a ta gefen Hanash zata wuce, a k'ufule Hanash ya maka mata kyawawan marika gudu biyu a jere, wad'anda sukata zubewa k'asa ba shiri, karaf akan idan Khulud........ cikin tsananin b'acin rai da zafin zuciya Sir Moli ya......... Ya azumi da ibada? Ubangiji ya amshi ibadun mu, Allah yayi mana rahama da rahamarsa, yaji k'anmu da jin k'ansa, Allah yasa muna daga cikin wad'anda za'a yafewa a wannan watan mai albarka. MOMYN ZARAH _*RASHIN SANI.......*_ *HAUWA A USMAN* _JIDDARH_ ```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh``` 2⃣9⃣ Take duk ilahirin jikin Sir Moli ya d'auki kerrrma da b'ari, zuciyarsa ta shiga tafasa tana yi masa k'una, cikin matsanancin zafin rai da k'unar zuciya Sir Moli ya makawa Hanash kyawawan marika guda hud'u a jere, had'i da sakar masa gigitaccen naushi a cikinsa, zafin naushin ne yasa Hanash dafe cikinsa had'i da durk'ushewa ya saki k'ara, Khulud tsaye tayi cak ta kasa koda motsa k'afarta, ta k'ame a tsaye, saboda tsantsar mamaki, Sir Moli ya sunkuya ya d'ago Sanah had'i da manna ta da k'irjinsa, kallo d'aya zakayiwa Sir Moli kasan ransa yakai k'ololuwar b'aci, idanuwansa sunyi masifar yin jajir dasu, ya kalli Hanash yace " kayi gangancin tab'a ta a gaba na, how dare you da hannunka zai tab'a jikinta? "Ko an gaya maka ita irin matan nan ce da kowanne Tom and Jerry yake tab'a su, kaje kaci darajar masu daraja, amma badan haka ba da sainayi maganinka, Sir Moli ya fad'a cikin matsanancin zafin rai a hankali Hanash ya d'ago had'i da nufar Sir Moli gadan-gadan, cikin zafin nama Khulud tayi saurin shan gaban Hanash, cikin bak'in ciki da suyar zuciya ta jefa idanta cikin nashi, yayinda hawaye ke rubdugun zubo mata, ta kallanshi idanta tarr cikin nashi tace " ashe dama haka kake? " Wannan itace true color ka? "Dama na dad'e ina zargin akwai wani abu k'asa, dan nasan haka nan banza bazai tab'a yiyiwa Sanah ta iya jura getting to 5 months batare data zo ta ganni ba, Hanash ka ban mamaki, ashe duk abinda kake fad'a k'arya ne? Baki ta bud'e zatayi magana amma kukan dayaci k'arfinta ya hanata cigaba da magana, da gudu Baba mai gadi ya rugu ya zabe a gaban Hanash, had'i da cewa " Yallab'ai kayi min rai, wallahi ba laifi na bane, sai da nayi musu bayani amma suka k'i ji, tazo wajen sau biyar ina hanata shigowa, cike da mamaki Khulud ta tsaida kukanta, ta maida kallanta ga mai gadin tace " meye Baba? Cikin rawar murya mai gidan yayi mata bayanin komai, had'i da cewa " dan girman Allah kayi hak'uri, ido Khulud ta runtse cike da bak'in ciki, kana ta nufi Sanah, Sanah da har lokacin tana manne jikin Sir Moli, saboda rashin kwarin jikin data ke fama dashi ya hanata kwace jikinta daga gare shi, duk ilahirin jikinta kerrrma yake, ganin Khulud ta nufo ta yasa ta saurin barin jikin Sir Moli, cikin kukan bak'in ciki Khulud ta rungume Sanah tana kuka, tace " please my Sanah kiyi hak'uri wallahi kwata-kwata ban san abinda ke faruwa ba, nayi sake da sakaci dana kasa tsayawa na maida hankalina na lura da abinda ke faruwa, ta k'arasa maganar tana k'ara fashewa da gigitaccen kuka, Sanah ma tana zubar hawaye dan bata da k'arfin yin kuka mai k'arfi ta shiga girgiza mata kai, cikin bak'in ciki Hanash yace " ni ka daka ko!? Ya fad'a yana nuna kansa, cikin isa da tak'ama Sir Moli yace " an dake ka d'in, kayi duk abinda zakayi, kaci sa'a ma daban illata kaba, akanta babu abinda zaban iya yi ba, a hankali Sanah ta d'ago kanta ta kalli Sir Moli jin abinda yace, Hanash yace " saboda tsabar rainin hankali da rashin sanin shari'a da hakk'in d'an Adam shine zaka shigo har cikin gidan ka dake ni? Gyara Tsaiwarsa Sir Moli yayi kana yace " ko kana buk'atar k'ari ne? Hanash yace " wallahi sai naga uban waye ubanka, sai naga uban da ya d'aure maka gindi, shege d'an iska fasik'i karuwan namiji kawai, Sir Moli yayi guntun murmushi kana yace " kai inda kasan waye uban nawa, da baka soma yin marmarin cewa zaka ganshi ta wannan hanyar ba, kuma da kake maganar shari'a, da sanin hakk'in d'an Adam kai abinda kake yi dai-dai ne? "In banda rashin sanin daraja da k'imar mace, har zaka iya saka hannu ka mareta, har kana wani fiffik'a kana nuna k'arfi, waya fad'a maka ana nuna k'arfi akan mace? " Idan k'arfi kake da buk'atar nunawa kaje ka tari maza 'yan uwanka mana, amma saboda kai lusarin namiji ne, wanda ya rako maza duniya, wanda bai san mutunci da k'imar kansa ba, bai kuma san darajar da Allah yayiwa 'ya mace ba, shine har kake fiffik'ar dukan mace, Hanash yace " au kai har maganar k'ima da sanin darajar kake yi? "Kai yanzu inda kasan kunya har zaka kalle ni kayi man maganar sanin mutuncin kai, lalle kamm! kodan dama ance 'yan iska basu data ido, banzaye 'yan iska fasik'ai kawai, wad'anda basu da aikin yi sai yad'a b'arna a doran k'asa, then da kake cewa inda nasan waye ubanka banzanyi marmarin ganinsa ba, waye shi!? Kana ya mayar da kallansa ga Sanah yace " karuwa! fasik'a kawai, Sir Moli ya matso daf dashi ta yadda har suna iya juyo mumfashin juna, had'i da kallansa ido cikin ido, ya nuna masa yatsansa yace " kul karka sake ci mata karuwa, inba haka ba... ya cije lips d'insa da k'arfi had'i dayin kwafa, sannan idan kana san sanin waye ubana sai ka nemi ganin nashi kamar yadda kace, kana Sir Moli ya juya cikin takunsa na isa ya nufi mota, Khulud ta kalli Hanash tace " karka kuma ce mata karuwa, dan ba karuwa bace, ido Hanash ya runtse da k'arfi kana ya kalli Khulud yace " please karki saka kanki cikin wannan maganar, a hankali Khulud ta saki Sanah ta nufi Hanash, Sanah tayi saurin rik'o ta, amma ta fizge, ta taka har gabansa ta kalli cikin kwayar idansa tace " ban gane kar na saka kaina cikin wannan maganar ba, me kake nufi Hanash? "Yama za'ayi a gaba na kuma ina tsaye ka rink'a kiran Sanah da karuwa fasik'a, wallahi in banda arzikin aure da kuma matsayinka na mijina, had'i da girman igiyoyinka dake kaina, dana nuna maka mai hak'uri bai iya fitina ba, kai da kake da k'anne mata, kuma kake neman haihuwa har kake aibata 'ya'yan wasu, kamar yadda k'annanka suke mutane haka Sanah da Sir Moli suka mutane, masu cikekken gata, Hanash kabi a hankali dan haihuwa zakayi, kuma shi ciki mai haife-haife ne, ba'a san abinda zai haifu ba, ka daina zagi kana aibata 'ya'ayan wasu, dan baka san kaima abinda zaka haifa ba, ina jiye maka tsoran kada Ubangiji yayi maka jarawar da zata fi k'arfinka, jarabawar da zara gigitaka, Hanash ka kiyayi duniya da rayuwa, dan ita duniya tamkar mace mai ciki ce ba'a san abinda zata haifa ba, haka kuma k'addara mace ce mara tabbas da akoyaushe tana iya canjawa, hannu Hanash ya yarfe cike da takaici ya kalli Khulud, yace " idan ba karuwar bace mecece? " Ko kin san sau nawa ina kama su da ido na, suna aikata masha'a? " Sau hud'u ina ganin su, biyu a office d'in abokin karuwancin nata, d'aya ranar d'aurin mu, sannan da ido na naga ya kaita gidansa, lokacin Papu ya aiki ni gidan abokinsa a unguwar, tsaiwarsa ya gyara kana ya kuma cewa " sai ki fad'a man yanzu duk macen da take bin namiji har zuwa gidansa mecece? Shiru Khulud tayi tana kallan Hanash cikin takaicinsa, murmushi yayi yace " baki da amsar bani ko? " To idan baki da amsa ni ina da amsa, sunan macen dake bin namiji har zuwa gidansa KARUWA!, FASIK'A!!, MAZINACIYA!!!, dan haka wad'annan sunayen duk sunanta ne ya fad'a yana nuna Sanah, cikin zafin rai Khulud ta d'aga hannu da niyyar kifawa Hanash mari, tsaida hannun nata tayi a dai-dai fuskarsa, ta kasa k'arasa abinda tayi niyya, hannunta dake kerrrrma Hanash yabi da kallo, cikin tsantsar mamaki, yace " what! Khulud da marina zakiyi danna fad'i gaskiya? Hannunta ta yarfe had'i da durk'ushewa kasa, ta fasa gigitaccen kuka mai cin rai, a hankali Sanah ta tako inda Khulud ke durk'ushe tana kuka tasa hannu ta d'ago ta, tana zubda hawaye itama, a hankali Khulud ta d'ago kanta ta kalli Hanash tace " Allah ya isar musu, ya kuma saka musu a bisa zargin da kake yi musu, Hanash yace " wai baki yarda ba kome? "Kina nufin sharri da k'arya nayi musu? " Ko kina nufin k'age nayi musu? " Ko so kike kice ba karuwar bace? A fusace Sir Moli ya juyo cikin k'araji yace " i said don't dare you call her karuwa! ya fad'a yadda kasan anyi masa sammacin mutuwa, cikin sanyin jiki Khulud da Sanah suka mik'e tsaye rungume da junansu, Hanash ya kuma gyara tsaiwarshi, cike da dagara yace " if i repeat it again what will you do!? Tsaiwa Sir Moli ya gyara had'i da tattare hannun rigarsa, kana ya zuba hannunsa cikin aljihun wandansa, had'i da jefa idansa cikin na Hanash yace " ok k'ara fad'a inka isa kai cikken mara kunya ne, Hanash yace " I said it in capital letter she's *KARUWA!!!*, yadda kasan mahaukacin zaki Sir Moli ya nufi Hanash gadan-gadan, yana wani irin takun k'arfin, had'i da fitar da huci mai zafin gaske, kai da ganinsa kasan ransa yazo iya wuya, ran 'yan maza yayi mugun b'aci, shima Hanash nannad'e hannunsa rigarsa, yayi yana jiran k'arasowarsa, ganin abinda ke shirin faruwa yasa Sanah saurin shan gaban Sir Moli tana kuka kamar ranta zai fita kana tace " please no! a harzuk'e Sir Moli ya zagaye ta yana k'ok'arin k'ara nufar Hanash, da sauri ta kuma shan gabansa, had'i da sanya hannunta a saman k'irjinsa tana k'ok'arin dakatar dashi, cikin kuka tace " a'a dan Allah, jajayen idansa ya zuba cikin nata, na tsayin lokaci, batare dayace komai ba, ya dad'e yana kallanta ido cikin ido, kana cikin zafin rai ya furzar da iskar bakinsa, had'i da naushi motar dake kusa dashi ta Hanash, inda ya daka a jikin motar ya lotsa, hannunsa daya naushi motar yaji ciwo, ya shiga zuwar da jini, cikin furgici Sanah ta zaro ido had'i da saurin rik'o hannun, tace " kana bleeding, ta fad'a cikin tashin hankali, ganin yadda ta kid'ime yasa shi kafe ta da shanyayyun idanuwansa, da sauri ta zame d'an kwalin kanta, ta d'aure mishi hannun while tana cigaba da kukanta, a hankali Sanah ta rik'e hannun Sir Moli ta jashi cikin mota, ta bud'e mishi ya shiga, Sanah ta zagaya zata shiga cikin motar Khulud tace " my Sanah jira ni na d'auko hijab mu tafi gidan tare, murmushi Sanah tayi kana tace " ok maza jeki d'auko, a hankali Khulud ta juya ta shiga cikin gidan, Sanah na ganin ta shige tayi saurin bud'e motarta ta shiga, cikin muryar kuka tace " zaka iya driving d'in? Baice mata komai ba yayiwa motar key, jikin Baba mai gadi na rawa ya bud'e get, Sir Moli yazo zai fita ya tsaya ya d'auko card d'inshi ya mik'awa mai gidan, yace " ka kira ni letter, cikin rawar jiki Baba mai gidi ya amsa, had'i da yin godiya, Sir Moli bai kuma yin magana ba yaja motar, sai da ya fita daga gaba d'aya unguwar kana yayi parking a gefen hanya, had'i da kwantar da kujerar motar ya kishingid'a gami da lumshe idansa, yana fitar da huci had'i sauke ajiyar zuciya akai-akai, ido Sanah ta k'ura mishi tana mamakin abubuwa da dama, abu na farko daya tsaya mata yadda yayi akanta, da yadda gaba d'aya yayi loosing control, akan ance mata karuwa, dan taga yadda kalar idansa ta canja, ta kuma hango tsananin b'acin rai acikin kwayar idansa, ta tabbatar in banda tayi gaggawar shiga tsakiyarsu da Allah ne kad'ai yasan me zai faru, can k'asan mak'ogwaranta ta maimata, kalmarsa _akanta babu abinda bazan iya yi ba_, sake kallan yadda yake ta faman huci tayi، yana fitar da numfashi had'i da sauke ajiyar zuciya, a ranta tace " yanzu wannan duk akai na ne? "Idan akai na ne yayi wannan abun me hakan ke nufi? " Idan dan ance man karuwa ya shiga cikin wannan matsanancin halin, yanayinsa ya canja haka, to meye manufar yin hakan!? Tana cikin yin zancan zuci taji yace " meyasa idan yayi maki abu baki iya ramawa!? Yayi maganar batare daya motsa ba, idanta na kansa cikin muryar kuka tace " nayiwa my Ulud alk'awarin duk abinda yayi man ban kuma ramawa, "Ok tasan yana yi miki hakan kenan? " A'a bata sani ba! ta fad'a still idanta na kanshi, " idan bata sani ba ya akayi kikayi mata alk'awarin? Cikin sanyin jiki Sanah ta bashi labarin komai, tun daga farkon had'uwarsu a ranar da sukayi graduated har zuwa ranar data yiwa Khulud alk'awarin bata kuma yi mishi komai har abada, " ashe rashin kunyarki ce ta ja maki? Ya fad'a yana bud'e idansa a hankali, " yanzu in banda tsabar rashin kunya ina ke ina marin namiji? " Duk abinda yayi maki ma dai-dai ne wallahi, damma yana da sauk'in kai da sauyin zuciya, inda irin mu ne hmmm ya k'arasa maganar yana yin murmushin gefen baki, ido cikin ido Sanah ke kallan Sir Moli, tana kallan cikin kwayar idansa, wani irin abu take gani daga cikin kwayar idan nasa, mai kamar brown color, idan kuma ta kalli farin cikin idansa sai taga yayi mata wani iri, kwata-kwata ta kasa fassara abinda take hangowa cikin kwayar idansa, shima cikin kwayar idanta yake kallo, jin yanayinsa ya fara canjawa yasa shi saurin kauda idansa, daga kallanta ya mayar da kansa gefe, ajiyar zuciya ta sauke da k'arfi, kana ta kalli hannunsa, a kid'ime tace " har yanzu yana bleeding fa, dan Allah muje hospital, ta fad'a tana k'ok'arin rik'o hannun, saurin janye hannunsa Sir Moli yayi had'i da tsuke fuska, " please muje hospital kaga still yana bleeding, a hankali ya kalle ta, yaga duk ta marairaice masa, ta zama wata kalar tausayi, key yayiwa motar batare dayace mata komai ba, suna fara tafiya Sanah tace " amai nake ji, bayyi mata magana ba ya gangara gefen hanya yayi parking, yana tsaida motar ta fito da sauri tun kafin ta tsugunna ta fara shek'a aman, a hankali ya bud'e motar ya fito, ya zagoyo inda take, a hankali ya tallafo ta cike da tausayi ya shiga mata sannu, sai da ta gama yin aman kana, ya bud'e mota ya d'auko ruwa ya zuba mata ta wanke jikinta, jikinta sai kerrrrma yake yana rawar sanyi, a hankali ta mik'e tsaye jiri na rib'arta, ganin tana neman fad'uwa yasa shi d'aukarta cak ya sakata cikin mota, kana shima ya zagaya ya shiga, kwantar mata da kujerar motar yayi, kana ya kashe Ac saboda yadda take rawar sanyi. Direct standard hospital ya nufa da ita, yayi parking a harabar asibitin bayyi mata magana ba, ya zagayo ya bud'e motar ya tallafo ta, a hankali Sanah ta zuro k'afafunta waje, cikin sanyin jiki ta shiga takawa zuwa cikin asibitin, while Sir Moli yana tallafe da ita, da sauri nurses suka tare su, suka amshi Sanah daga hannun Sir Moli, but bai sake ta gaba d'aya ba, yana rik'e sa ita ta d'aya b'arin, office d'in Doctor aka nufa dasu, a hankali suka zaunar da ita akan kujera, Doctor ya mik'e da sauri yana murmushi yace " sannu! kai kawai ta d'aga masa, Doctor yana shirin fara dubata ta kalli Sir Moli tace " please kaje ayi maka dressing hannunka, kallanta yayi batare dayace mata komai ba, ta k'ara marairaicewa tace " please! yace " bari a fara dubaki tukunna sai inje, Sanah zatayi magana, Doctor tace " wow! amazing lovers gaskiya kun burgeni, da yadda kuke bala'in so da kula da junanku, Sir Moli zayyi magana Nurse d'in tayi tayi dariya tace " bari kaidai Doctor they're wonderful and best couples of the whole world wallahi, sunyi masifar dacewa da junansu, d'aya nurse d'in tace " saboda yab'ar yadda yake caring da san matarshi yama bari mu rik'e ta k'i yayi, Doctor yace " Allah yasa dai Baby ne, inyi maka babban albishir, dan da ganinku sabon aure ne, kuma akwai soyayya a wajen, kaga idan Baby ne amarci yayi kyau, d'aya nurse d'in tace " aiko da gani ma laulayin ne, d'ayar tace " aiko da kaya na zan kwaso na dawo gidanku ganin ikon Allah, dan nasan akwai abu a goyon cikin nan. Tunda suka fara magana idan Sir Moli yana kan Sanah yana karantar yanayinta, bai iya gane yanayinta ba saboda halin rashin lafiyar datake ciki, kallansa ya maida ga Doctor da nurses d'in, yayi musu murmushi batare dayace komai ba, kana ya fita ya nufi dressing room. Da gudu Khulud ta fito hannunta rik'e da trolley, ganin babu motar su Sanah yasa ta fashewa da kuka ta nufi hanyar fita, Hanash dake tsaye yadda tabarshi, baiko motsa ba, cike da tsantsar bak'in ciki da takaici, yayi saurin shan gaban Khulud, ya marairaice face yace " please kiyi hak'uri, ban k'arawa, bata ko kalli inda yake ba ta cigaba da nufar get tana kuka, rik'eta yayi tayi saurin fisge jikinta, tace " karka kuma tab'a ni, da sauri ya janye hannunsa had'i da cewa " na bari, dan Allah kiyi hak'uri kinji, kallansa tayi tace " wallahi kaban mamaki Hanash, na yarda dakai 100%, idan wani ne ya fad'a man zaka yi duk wannan wallahi ban tab'a yarda, na d'auka kai mai gaskiya ne, na zata kai daban ne a cikin millions of millions na maza, ban tab'a k'in yarda ko gaskata ka ba, ban tab'a yin kokonto akanka da magarka ba, Hanash na yarda dakai sosai, meyasa zakayi haka!? "Meyasa zaka tarwatsa duk yardar danayi maka? " Meyasa zaka kawo kokwanto da zargi a zamantakewar mu? "Mai yasa zaka zama mai fuska biyu? " Why kake k'ok'arin raba ni da Sanaha, why Hanash! ta k'arasa maganar cikin matsanancin kuka, muryarsa na rawa yace " wallahi Khulud nima ban san meyasa nake yin haka ba, amma dan Allah kiyi hak'uri, kallansa tayi tace " ina ai ba maganar hak'uri Hanash, idan baka manta ba tun farkon alak'armu na fad'a maka, cewar Sanah itace komai nawa, ina matuk'ar santa fiye da komai da kuma kowa, na fad'a maka bana k'aunar duk wani abu dazai shiga tsakani na da Sanah, dan haka rabuwa dakai ta zama dole Hanash, ta fad'a tana jan trolley d'inta, da sauri Hanash ya fara k'ok'arin karb'ar trolley'n hannunta, cikin tsawa tace " live me alone, da sauri ya sake ta ya d'aga murya yacewa " Baba mai gadi " karka sake ka bud'e mata get, kar bari ta fita, jin abinda yace yasa Khulud durk'ushewa a wajen ta saki gigitaccen kuka, a hankali Hanash ya durk'usa a kusa da ita, cikin rawar murya yace " dan Allah kiyi hak'uri, ki tashi mu shiga cikin gida, red eyes d'inta ta d'ago ta kalle shi, tace " wallahi ko yunwa da rana zasu kashe ni ban shiga cikin gidan da aka haramtawa my Sanah shigarsa, sosai Hanash ya shiga lallab'a ta yana bata hak'uri, amma fafur tak'i ko sauraronsa, sosai Hanash yayi mugun mamakin taurin kan Khulud, a ransa yace " dama ance masu hak'uri basu iya fushi ba, ganin tak'i sauraronsa yasa shi mik'ewa cikin sanyin jiki yace " tashi muje na kaiki gidan da kaina, babu musu Khulud ta mik'e, da kanshi ya bud'e mata gaban mota, amma tak'i shiga ta bud'e bayan motar ta shiga ta zauna, murmushi yayi had'i da girgiza kansa, kana ya zagaya ya shiga motar yayi mata key, tunda ya fara tuk'i yake kallanta ta mirror yana bata hak'uri had'i da rarrashinta, amma tayi masa banza, ta cigaba da kukanta, har suka k'arasa gidan yana ta faman bata hak'uri, a harabar gidan yayi parking, da sauri ya fito jikinsa na rawa ya zagaya b'angarenta, fitowa tayi itama tana jan trolley, dai-dai lokacin Abbu da Didi suka fito, turus sukayi a harabar gidan suna kallan ikon Allah, cikin nutsuwa Hanash ya k'arasa inda suke had'i da durk'usawa har k'asa ya gaidasu cikin girmamawa, cikin fara'a suka amsa masa, Khulud ta k'araso inda su Abbu ke tsaye ta durk'usa ta gaida su, Abbu bai amsa gaisuwar ba yace " lafiya na ganki da akwati? Shiru Khulud tayi had'i da sunkuyar da kanta k'asa, Abbu yace " tambayarki nake yi, lafiya na ganki da akwati, me kikazo yi gidan harda zuwa da akwati? Abbu yace " biki ake yi ko suna a gidan? Kan Khulud na k'asa tace " a'a, Abbu yace " to uban me ya kawo gidan? Cikin kuka Khulud tace " Abbu na dawo gida ne? Abbu yace " ban gane kin dawo gida ba? "Me kika dawo yi? Shiru Khulud tayi batace komai ba, Abbu yace " magana nake yi miki, cikin kuka Khulud tace " ban kuma zama dashi, Abbu yace " shiwa? Khulud tace " Hanash! Abbu yace " akan wanne dalilin? Khulud tayi shiru, Abbu yace " ci da sha ne baya baki ko hakk'ink'i na auratayya ne baya biya miki? "Ko mutuncinki ya kasa karewa, ko kuma nauyinki dake kansa ne bai saukesu!? Cikin sanyin murya Khulud tace " a' a! Abbu yace " Allah yake sab'awa, ko kuma mashiriki ne? "A'a Khulud tace, " giya yake sha ko lud'u yake yi? " A'a! Abbu yace " a cikin sharadd'an rabuwar aure da Allah ya gindaya akwai d'aya a tsakaninku? A hankali Khulud tace " a'a! Abbu yace " auren dole mukayi miki ko mu muka kawo miki shi muka matsa maki kika aure shi? "A'a tace tana zubar da hawaye, Abbu yace " mu muka had'aki dashi? Nan ma Khulud tace " a'a, Abbu yace " ke kika wo kayanki kikace kina so ko? Tace " eh! " To shine dan iskanci daga yin auren dududu wata biyar zaki kwaso kaya kice kin dawo gida? " Ni dai dan Allah Abbu ku raba ni das....... gigitaccen marika Abbu ya maka mata guda biyu a jere, cikin fad'a yace " dan ubanki mu zaki maida k'ananan mutane, daga yin auren zaki dawo, ki dawo gidan kiyi uban me? " Tunda kike cikin gidan nan kin tab'a ganin anyi yaji? "Ko tunda kuke dasu Mamu kin tab'a ganin sun kwashe kayansu sunce sun koma gidansu? " Kin tab'a ganin su Halan sun fita ko k'afar gida da sunan yaji, ko so kike yi ke ki fita zaka kibar tarihi? " Idan baki sani ba, gwara ki sani haka dokar Hard'o family take, idan suka aura ko aka aure su babu saki ko yaji sai dai mutuwa ta raba da yardar Allah, ki bud'e kunne dakyau kiji ni daga yau duk ranar da kika sake d'auko k'afa da sunan yaji to ki nemi wani gidan da kuma uban ba ni ba, zan cire ki daga jerin yara na, kinji ko baki ji ba, cikin kuka ta amsa " naji! dan Allah kayi hak'uri ban k'arawa, ajiyar zuciya ya sauke kana yace " yauwa good girl, Allan yayi miki albarka kinji aje ayi ta hak'uri, duk wacce kika gani gidan mijinta zaman hak'uri da juriya takeyi, duk matar datace maki bata da matsala gidan mijinta k'arya take yi, da zarar anyi aure so da soyayya sun k'are sai dai ayi zaman hak'uri, idan kika bar mijinki na yanzu saboda wani dalilin, kin san wanda zaki sake aura? "Ko shi kin san halinsa, kin san nashi d'abi'un? " Kinga baki san hannun wanda zaki kuma fad'awa ba, dan haka kiyi hak'uri kinji my daughter, nasanki da hak'uri da juriya had'i da kawar sa kai da saurin yafiya fa, Abbu ya fad'a cikin tsokana, kanta ta kuma sunkuyarwa k'asa, Abbu yace " maza tashi ki koma d'akinki kinji, mik'ewa tayi a hankali kana ta kalli Abbu tace " bari na gaida su Mamu, Abbu yace " a'a ba sai kinje ba, suma zaune suke a gidajen mazajensu suna hak'uri, dan haka kema ki koma naki gidan mijin, kyazo ki gaida su daga baya cikin dad'in rai, ba musu Khulud taja trolley d'inta ta koma mota, Hanash ya mik'e tsaye had'i dayiwa su Abbu godiya sosai, Abbu yace " kai ma kayi hak'uri, kasan mata 'yan a lallab'a ne, sai anyi hak'uri dasu, muma duk abinda mukeyi kenan har yanzu, shiyasa kaga ankawo har tsayin wannan lokacin ana tare, kansa ya sunkuyar had'i da cewa " in sha Allah Abbu, sallama sukayi kana suka tafi, Didi dake tsaye bayyi magana ba, har su Khulud suka tafi kana ya sauke ajiyar zuciya yace " oh! yaran zamani dai ba hak'uri daga yin auren har an kwaso rigid'i-rigid'i, an taho yaji gidan, Abbu yace " kadai bari, Didi yayi murmushi yace " uban 'ya anyi fad'a an dawo kuma ana rarrashi, Abbu yace " yaran yanzu ne sai da hakan milkin soja zalla ba yayi musu, dole sai an had'a mulkin farar hula anyi musu siyasa kana, ina murna na kusa gama aurar da yara na lafiya, tana neman d'aga min hankali, ta tada man zaune tsaye, Didi yayi dariya, kana suka nufi part d'in iyayensu dan dama can suka fito zasu. Sai da aka gamawa Sir Moli treatment kana ya koma inda ya bar Sanah, Doctor na ganin shi yayi dariya yace " master of love, murmushi Sir Moli yayi had'i da cewa " how is she? Doctor yace " gaskiya bata da lafiya sosai, Sir Moli yace " meke damunta!? Doctor yayi murmushi had'i da mik'ewa Sir Moli takardar batare da kawo komai aranshi ba ya amshi takardar, karaf idansa ya sauka akan abinda Doctor ya rubuta da sauri Sir Moli ya mik'e had'i da cewa " what!, Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un.................! MOMYN ZARAH