[3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: 🖋🖋 *ALKALI NE* 🖋🖋 (A book of law case) An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT __ Nah Marubuciyar Zamani NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) Email..... nabilalady5@gmail.com Facebook...Nabeela Ladeey Wattpad.... Nabeelertlady 0⃣1⃣ *Bismillahir Rahmanirrahim*. Ina mik'a godiya ga dukkanin masoyana. Wannan littafin k'irk'irarre ne, banyishi dan cin zarafin wani ba, ina fatan Allah yasa kowa ya amfana da abinda yake ciki amin. *LAGOS* Cike babbar kotun garin Lagos take da jama'a, wasu basu da alak'a da wannan shari'ar, amma yanda ake fad'in yanayin shari'ar da kuma wanda aka maida shari'ar wajensa yasa kowa yake so yaje domin yaji yanda zata kasance. Kasancewar lauyen da aka maida shari'ar wajensa sabon zuwa ne hakan yasa kowa yake son ya ganshi, domin an sanar cewa wannan zaman shine zama na k'arshe, saboda tsohon lauya ya kasa kawo kwararan shedu hakan yasa shari'ar ta gamsu da shedun abokin karawarsa. Tsaye mutane suke a bakin kotun suna jiran abasu izinin shiga kafin Alkali ya iso. Wasu Matasa ne da suke gefe guda suke magana akan wannan shari'ar. 'Daya daga cikinsu yake fad'in abokina ko kasan nima ban gamsu cewar gaskiya ce wannan lauyen yake fad'a ba, taya za'ace bayan mutum ya mutu da wata biyar sannan ace matarsa tana da ciki har na wata ukku, kai da gaji ma kasan rainin hankali ne har sai sunzo wata kotu. 'Dayen yace kuma wannan shari'ar kotun musulunci yakamata ace an kaita ba wannan kotun ba, gashinan yau zuwa na ukku ne amma an kasa tsaida mafita, da kotun musulunci ce tuni an wuce wajen amma hada wani sake lauya, ai zaizo muji tashi basirar. Murmushi wanda yake gefensu yayi yana fad'in wallahi kuna bani dariya, kunsan fa ance shari'a sab'anin hankali, abinda wani yayi ya kasa sai kuga wani yayi, koshi Alkalin sai ya kasa gano abinda wani lauyen zai gano, duk da ance sabon lauya ne babu wanda yasan basirar da Allah ya bashi, kuma ba jiya bane ya amshi shari'ar kusan sati guda kenan rabon mu da nan, kunga kuwa acikin sati d'aya zai iya had'a shedu masu kyau idan yana da basira, koda kotun musulunci aka kai wannan shari'ar ai dole sai da shedu, dan haka muyi masu fatan alkhairi shine zaifi, danni wallahi tausayin matar nakeyi, itace k'arama acikin matan Alhajin, kuma itace ta ukku fa, kasan unguwar mu d'aya dasu babu abinda ban sani ba akan irin zaman da sukeyi da abokan zamanta, kasan halin mata, akan kishi babu abinda bazasu iya ba, kuma nasan halin matar, duk da basu dad'e da Alhaji ba amma mutane suna fad'ar kyan halinta, shiyasa jikina be yarda da wancan lauyen ba, domin ina yawan ganinshi a unguwar mu yazo wajen sauran matan. Jinjina kai sauran sukayi suna fad'in to Allah ya bayyana gaskiya. Yace amin. Tashi sukayi ganin an fara shiga ciki. Kowa ya sami waje ya zauna ana jiran shigowar Alkali. Wani Matashin yaro ne wanda bazai wuce shekara 32 zuwa da 33 ba yashigo kotun yana sanye da kayan aikinshi, idanuwansa suna b'oye cikin farin gilashi hannunsa d'auke da k'aramar jaka. Yanayin takunsa yaja hankulan mutanan da suke zaune a kotun, koda ganinshi kowa ya gane shine sabon lauyen da ake magana akanshi. Wasu da yawa suna mamakin ganinshi a haka, sun d'auka zasu ga wani babban mutum sai gashi sunga Matashi mai jini ajika. Yana k'arasowa wajen da aka tanadar masu domin zama ya fara mik'a hannu ga sauran 'yan uwansa lauyoyi suna gaisawa. Ko da yazo kan mutum na k'arshe bayan ya bashi hannu sai yaji bai sakeshi ba, d'ago kai yayi yana kallonshi. Babban mutum ne, yasan ya girme mashi a shekaru. Kallon hannunshi ya sakeyi ganin har lokacin bai sakeshi ba kuma murmushi bai b'ace daga fuskar mutumin ba. Murmushi shima ya sakar mashi yana kauda kai. Sunana *Brr. Nuhu Bajinta*, amma amfi kirana da *Brr. Bajinta*, nine wanda yake jagorantar wannan shari'a, wato abokin karawar ka. Murmushi yayi yana fad'in sunana *Brr. RA'EEZ HAMZA MWD*, nine sabon lauyen daya amshi wannan shari'a. Jinjina kai Brr. Bajinta yayi yana fad'in muna maka maraba da shigowa wannan babbar kotu mai albarka, Allah ya baka sa'a a wannan aikin namu mai had'ari da wahala. Brr. Ra'eez yace amin nagode. Zama sukayi suna jiran k'arasowar Alkali. Wanda yake kusa da Brr. Ra'eez ya sake bashi hannu yana fad'in sunana *Brr. JABEER USMAN*, ina aiki a wannan kotun kusan shekara d'aya da farawata kenan, ina maka fatan alkhairi da zuwa wannan kotu. Murmushi Brr. Ra'eez yayi yana fad'in nagode Jabeer Allah ya bamu zaman lafiya. Yace amin. Shigowar Alkali yasa kowa ya tashi. Bayan ya zauna kowa ya zauna tare da natsuwa. Bayan da Alkali ya gama 'yan rubuce-rubucensa sannan ya bada izinin acigaba da gabatar da shari'ar. Tashi magatakarda yayi yana fad'in, a yau sha hud'u ga watan oktoba shekara ta 2019, wannan kotu zata cigaba da sauraron k'arar da akeyi akan iyalan gidan Alhaji Bala wanda matanshi guda biyu suke k'arar amaryarsa Amina akan fitowar ciki a jikinta bayan mutuwar mijinsu wanda suka tabbatar ba nashi bane, wannan shari'ar da ake gabatarwa ta tashi daga hannun lauyen da yake kare wacce ake k'ara ta koma wajen sabon lauya mai suna Brr. Ra'eez Mai Wada wanda aka yimasa canjin aiki zuwa wannan kotu. Risnawa yayi yana mik'ama Alkali takarda. Bayan daya gama dubawa yace ina sabon lauya kotu tana so ka gabatar da kanka. Fitowa yayi yana fad'in sunana Brr. Ra'eez Hamza MWD, kuma nine lauyen daya amshi wannan shari'a a wajen abokin aikina. Jinjina kai Alkali yayi yana fad'in lauyen da zai fara bismillah. Komawa Brr. Ra'eez yayi ya zauna dan beyi niyar farawa ba, yafiso ya zauna yaga kamun Brr.. Bajinta. Fitowa Brr. Bajinta yayi yana fad'in ya mai shari'a, har yanzu Amina bata amsa laifin da ake zarginta ba, haka kuma taki furta sunan wanda yayi mata wannan cikin, duk da matanshi sun tabbatar da Alhaji bai tab'a haihuwa ba a duk zaman da suke dashi, kuma sun dad'e atare dashi bai haihu ba, dalilin rashin haihuwar ne yasa ya k'aro aure, har sukayi zaman kusan shekara Amina bata tab'a b'atan wata ba sai gashi bayan mutuwar Alhaji ciki ya bayyana a jikinta har na wata ukku wanda likita ya tabbatar Alhaji baya haihuwa, kuma kowa ya sheda bayan mutuwar Alhaji sannan cikin ya bayyana wanda Alhaji ya riga cikin barin duniya kafin ya bayyana. Takowa yayi wajen da Amina take tsaye yana fad'in Malama Amina ya kamata zuwa yanzu ki bud'e baki ki fad'a mana gaskiyar wannan al'amari, be kamata kicigaba da wahalar da kotu ba, agabanki aka gabatar da manyan hujjoji, kowa ya aminta da hujjojin yakamata kema ki bayyana wanda yayi wannan cikin domin ki sauk'ak'a ma kotu wahala. Tashi Brr. Ra'eez yayi yana fad'in ya mai shari'a, bai kamata lauya yarik'a takura wadda ake zargi ba, Amina tana da ikon ta fad'i gaskiya akan abinda ta sani, bai zaima dole dan kowa ya amince da abinda wani ya fad'a ba ace itama dole ta amince. Nagode ya mai shari'a. Kallon Brr. Barjinta Alkali yayi yana fad'in ka gyara kalamanka. Risnawa yayi yana fad'in za'a kiyaye ya mai shari'a. Iya kar abinda zan fad'a kenan, ina rokon wannan kotu data yanke wannan hukunci domin magada su san halin da suke ciki. Nagode ya mai shari'a. Tashi Brr. Ra'eez yayi yana fad'in ya mai shari'a inaso nayima Alhaji Kabir babban aminin marigayi wasu tambayoyi. Da sauri Brr. Bajinta ya kalli Brr. Ra'eez jin wata magana da yazo da ita, shi tunda aka fara shari'a beyi tunanin sako aminin Marigayi ba domin yasan beda wani amfani a shari'ar, sai gashi Ra'eez ya gayyatosa a cikin shari'ar. Alhaji Kabir ya fito gaban kotu. Brr. Ra'eez... Kotu zata so tasan alak'ar ka da Marigayi. Alh. Kabir... E to, kowa dai yasan Alhaji bai da amini daya wuce ni, atare muka taso, abotar mu ta wuce abota ta koma ta 'yan uwantaka, sirrina na Alhaji ne, haka shima nashi nawa ne, babu abinda muke b'oyema juna. Brr. Ra'eez.... A tsawon zamanka dashi ko ya tab'a fad'a maka yana da matsalar rashin haihuwa? Brr. Bajinta... Ina da ja ya mai shari'a, be kamata Brr. Ra'eez ya maido mana da hannun agogo baya ba, kowa yasan munyi nisa a wannan shari'ar, dan yazo daga baya bai kamata ya maido da komai farko ba. Alkali... K'orafi bai karb'u ba, Brr. Ra'eez yana da ikon sako wannan shari'a daga farko matuk'ar yana da tabbacin ya kawo hujjojin da zasu gamsar da kotu. Brr. Ra'eez.. Murmushi yayi yana fad'in nagode ya mai shari'a. Ina jinka Alhaji. Alh. Kabir... Gaskiya tunda muke da Alhaji be tab'a fad'a mani yana da matsalar rashin haihuwa ba, asali ma duk lokacin da zaije wajen duba lafiyarsa tare muke zuwa, duk lokacin daya tashi zuwa asibiti baya yarda ya tafi da direba, ko bana gari yana hak'ura har na dawo domin muje tare, abu d'aya na sani shine yana fama da damuwa akan rashin haihuwa da Allah be basa ba, wannan dalilin ne yasa shi aure har mata ukku, domin munsha zuwa wajen likitoci daban -daban suna tabbatar mana lafiyarsa kalau kawai lokaci ne beyi ba, wannan dalilin ne yasa na bashi shawarar ya k'ara aure kila adace, sai gashi har Allah yayi masa rasuwa bai samu haihuwa ba, a daren ranar da zai rasu bana gari ina hanyar dawowa ya kirani, tabbas alokacin muryarsa cike take da farin ciki, duk da yana cikin hali na rashin lafiya hakan bai hana farin cikinsa bayyana ba, bayan mungaisa nake tambayarsa dalilin farin cikinsa, jin hayaniya ya gane ina tafiya hakan yasa ya kashe wayar yana fad'in idan na sauka zamuyi waya, bamuyi wayar ba har Allah ya d'auki ransa. Brr. Ra'eez... Jinjina kai yayi yana fad'in mungode zaka iya tafiya. Juyowa yayi yana fad'in ina so nayima Hajiya Binta uwar gida ga marigayi tambaya. Hajiya Binta ta fito gaban kotu. Brr. Ra'eez.... Hajiya ko kin tab'a zuwa asibiti aka gwadaki domin a tabbatar da lafiyar ki? Hajiya Binta... Kwarai kuwa, ni da Alhaji munsha zuwa asibitin nan garin har ma da k'asar waje, duk inda mukaje amsar d'aya ce, matsalar tana wajen Alhaji, sun tabbatar mana bazai tab'a haihuwa ba, alokacin yaso mu rabu amma nace masa ban yarda ba, aurena dashi na saurayi da budurwa ne, ban damu da haihuwa ba matuk'ar muna tare dashi, alokacin na fad'a masa kada ya yarda da maganar likitoci domin ba maganar Allah bace, nice nayi ta bashi kwarin guiwa akan yayi aure kila adace, nayi mamaki da Alhaji Kabir yace wai sunje asibiti ance lafiyarsa kalau, kuma so da yawa Alhaji yana zuwa asibiti shida direba, dan haka maganar Alhaji Kabir ba gaskiya bace. Brr. Ra'eez. Mungode zaki iya tafiya. Ina so nayima likitan daya tabbatar da awon cikin Amina tambayoyi. Likita ya fito gaban kotu. Brr. Ra'eez.... Kai ne likitan Alhaji ko? Likita... E nine. Brr. Ra'eez.. Amatsayin ka na likitanshi ya akayi baka tab'a fad'a mashi bazai iya haihuwa ba tun yana da ranshi sai bayan mutuwarsa ne kayi rubutu sannan ka kawo kotu? Sannan ya akayi alokacin da ka auna Amina iya cikin kawai ka gani baka gano komai ba? Likita... Hannu yasa yana goge zufar data zubo mashi kafin ya furta, iya abinda aka umarceni na auna kenan a kotu, kuma dana auna na kawo sakamakon a kotu. Maganar Alhaji kuma kasan ana son a b'oye sharri a bayyana alkhairi, Alhaji ya manyanta, bazaiji dad'i yaji cewar bazai tab'a haihuwa ba, yana matuk'ar son haihuwa har hakan ya jawo yayi aure har so ukku, ganin haka yasa na kasa fad'a mashi gaskiya har sai da buk'atar hakan ta taso a kotu. Brr. Ra'eez... Amma gashi Babban aminin Alhaji ya tabbatar da sunje asibiti an tabbatar da lafiyarsa kalau. Likita... E to, ai kasan ko wane likita da yanayin aikinsa, kowa yasan yanda muka dad'e da Alhaji, kuma Alhaji ya yarda da aikina, to bazanyi mamaki ba dan wani likitan yace lafiyar Alhaji kalau ba, domin koni abinda na fad'a masa kenan, kasan mu likitoci masu ceto ne, muna iya b'oye gaskiya domin farin cikin marar lafiyar mu, wannan dalilin ne yasa na b'oye masa gaskiya. Brr. Ra'eez... Mungode likita zaka iya tafiya. Ya mai shari'a zan so nayima *IYA* mai aikin gidan Alhaji wasu tambayoyi. A firgice Hajiya Binta ta mik'e tana fad'in ya mai shari'a Iya ta dad'e da barin gidan mu, tun kafin ya rasu muka nemeta muka rasa acikin gidan wai bazata iya cigaba da aiki agidan ba, yau kusan wata bakwai kenan da barin ta gidan. Bubbuga tebur Alkali yayi yana fad'in ki kama bakin ki nan kotu ce ba kasuwa ba, dan haka kada ki sake magana idan ba kiranki akayi ba. Zama Hajiya Binta tayi tana goge zufa, kallon kishiryata Zainab kawai take, ita kuma ta kasa fahimtar halin da Hajiyar tashiga dan ankira Iya bayan tasan babu abinda ta sani Iyar tayi. Brr. Ra'eez.... Iya ko zaki fad'ama kotu tsawon shekarun da kikayi agidan marigayi kina aiki? Iya.... Gaskiya na dad'e ina aiki agidan Alhaji, tun bayan da Hajiya Binta ta cika shekara d'aya agidanshi tasa k'awarta ta samo mata mai aiki amma tafison Babbar mace, kuma bata son 'yar birni ta fison wacce za'a nemo a kauye, hakan yasa k'awarta taje har k'auyen mu da yake katsina wato 'Danja ta samo ni, tun daga lokacin na fara aiki agidan, sosai Hajiya take mani kirki, na d'auketa 'yar uwa, duk da na girmeta amma haka nake bauta mata, itama kuma tana bani hakki na sosai. Brr. Ra'eez... Amma ya akayi aka wayi gari ba'a sameki agidan ba? Iya.... Hannu tasa tana goge hawayen da suka zubo mata, kafin tace tabbas na cutar da Amina da Alhaji, nayi kuka wanda beda amfani, naso na nemi yafiyar Alhaji amma Allah be bani iko ba, abu d'aya nasan nayi mashi wanda idan na tunashi nake jin sauki. Kamar yanda na fad'a maka aiki nake ma Hajiya Binta, bayan shekara ukku sai Alhaji ya sake aure, sosai hankalin Hajiya Binta ya tashi, domin likita ya tabbatar mata bazata iya haihuwa ba, alokacin atare mukaje da ita, domin Hajiya ta aminta dani, lokacin da ta fad'a mani abinda likita ya fad'a sai tace na rufe maganar bata so kowa yaji. Bayan da aka kawo amarya Hajiya Zainab sai tazo ba kamar yanda mukayi zato ba, ta kasance mace mai kwantar da kai awajen Hajiya Binta, ganin haka sai Hajiya Binta taji dad'i. K'awarta ce ta kawo shawarar kada ta bari Zainab ta haihu agidan, hakan yasa mukaje wajen wani k'asurgumin Boka ya bada maganin hana d'aukar ciki. Bayan da muka dawo na rik'a zubama Zainab magani a abinci tana ci, kuma Allah ya taimaka bata d'auki cikin ba. Bayan shekara biyu da aurenta Alhaji ya sake aure inda ya auri Amina, itama mace ce mai hakuri da kwantar da kai, hakan yasa Hajiya Binta taji dad'in zuwanta, anan itama mukayi kokarin bata magani a cikin abinci. Jin shiru bata d'auki ciki ba yasa hankalin mu ya kwanta, sai dai abinda bamu sani ba ashe ciki ya shiga jikin Amina, nice na fara sanin tana da ciki, a hankali da wayau da dabara irin tamu ta manya na tambayeta rabon data ga al'adarta, a yanda tayi mani bayani yasa na gano cikin watanshi d'aya da kwanaki, anan nayi mata dabara nace kada ta fad'ama Alhaji zaiga rashin kunyarta, ta bari na fad'ama Hajiya Binta ita zata masa albishir hakan zaisa yafi ganin darajarta. A ranar muka koma wajen Boka, anan ya bamu maganin da za'a rufe mata baki bazata fad'ama kowa tana da ciki ba, zata manta da wani ciki ma ajikinta, sannan Boka ya bamu maganin zubar da cikin, sai Hajiya tace tana tsoron yaki fita, gara dai a kwantar dashi zata san abinyi. Anan Boka yayi mana aiki muka dawo gida. Tun daga ranar maganar cikin Amina tasha ruwa, bata sake maganar ba, har gwada ta nayi amma ta nuna ita bata san da maganar ba bata da wani ciki. Muna cikin haka Hajiya Binta ta samo maganin da zai kwantar da Alhaji ta bani na zuba mashi a abinci, tunda yaci bai sake lafiya ba. Wata rana na dawo daga cikin gari kai tsaye na wuce d'akin Hajiya Binta, abinda naji ya firgitani, magana suke da k'awarta akan ta kashe ni, domin ita bata yarda da kowa ba, tunda ina da son kud'i wata rana zan iya juya mata baya idan na samu wasu kud'in. Nan take ta amince akan washe gari zata kashe ni, sannan Alhaji yana mutuwa zata koma wajen Boka ya tashi cikin domin ta jama Amina sharri kuma aki amincewa da cikin jikinta, ita kuma Zainab zata nuna mata soyayya domin ta bata dama su kwarema Amina baya, idan komai ya kammala itama tasa akasheta sai taci dukiyar ita kad'ai. Cike da firgici Hajiya Binta ta mike tana fad'in wallahi k'arya take, Zainab kada ki yarda da abinda tace makirar tsohuwa ce. Bubbuga tebur Alkali ya buga hakan yasa ta natsu. Kallon tuhum kawai Zainab take binta dashi. Brr. Ra'eez... Iya cigaba da bayaninki muna sauraron ki. Iya... Aranar hankalina ya tashi, cikin sand'a na shige d'akina na had'a kayana na bar gidan, ko mai gadi be ganni ba dan yashiga sallah, kafin na bar garin sai da na samu wani yaro da nake mutunci dashi na sashi ya rubuta mani wasik'a, anan na sheda ma Alhaji Amina tana da ciki, alokacin zai kai wata biyu, ban iya fad'ama Yaron komai ba dan bana son ya gano ni, kawai nace masa ina jin kunyar Alhaji nafiso ya karanta a rubuce. Bayan ya gama nace ya taimaka muje ya bama maigadi kuma ya tabbatar mashi Alhaji zai bamawa. Ina tsaye har Yaron ya bama Mai gadi takardar, bayan ya dawo ya fad'a mani Mai gadin yace zai bama Alhaji duk da baya fitowa amma zaiyi kok'arin kai mashi. Godiya nayi mashi na bashi kud'i na bar garin, a ranar cikin dare na isa Funtua, a tasha na kwana sai washe gari na isa kauyen mu, ban sake sanin abinda yake faruwa ba sai lokacin da kaje gidana, nayi mamakin ganinka da bayanin da kazo mani dashi, nayi kukan mutuwar Alhaji domin hada ni aka kashe shi, naso na nemi yafiyarsa babu dama saboda banyi ilimin boko ba dana rubuta mashi a wannan wasikar, zuwanka yasa naji kwarin guiwa kuma na amince zanzo na bada sheda akan abinda na sani domin duniyar ta juya mani baya. Brr. Ra'eez... Zaki iya tafiya mungode. Ya mai shari'a iya kar mutanan da zanyi ma tambaya kenan, wannan takarda ce dana samu a d'akin marigayi alokacin da mukaje gidan bincike nida 'Dan sandan da yayi mani jagora. Takarda ce mai d'auke da rubutun Marigayi tare da sa hannunshi, tun daga ranar daya samu labarin cikin Amina ya rubuta kwanan watan, ya nuna farin cikinsa, har yayi fatan Allah ya tashi kafad'arsa domin yaga jininshi, atare da takardar da Iya ta aika masa ya had'esu ya b'oye a cikin dirowarsa, Allah ne ya bani ikon ganinta, domin gaba d'aya takardun dirowar an kwashe su, itama daga k'asan dirowar akwai wajen da yake b'oye abubuwan sirrinsa anan ya aje ta. Mik'ama Magatakarda yayi yana fad'in ya mai shari'a, iya abinda zan fad'a kenan, ina rokon wannan kotu mai alfarma data yanke hukunci ga mutanan da suka zalunci Amina da Marigayi, sannan ta hukunta Likita daya goyi bayan k'arya. Nagode ya Mai shari'a. Gaba d'aya kotun ta d'auki hayaniya, mutane da yawa Brr. Ra'eez ya burge su, acikin sati d'aya ya gano gaskiya, abinda akayi wata anayi sai gashi acikin sati guda ya gama komai. Bayan da kowa ya natsu Alkali ya d'ago yana fad'in kotu tana son ganin Hajiya Binta, Iya da Likita agabanta. Haka suka fito jiki a sanyaye, Hajiya Binta sai kuka take dan tasan ta k'are mata. Kallon Hajiya Binta Alkali yayi yana fad'in kinji shedun da aka kabartar ma kotu, ko kina da ja akan abinda aka fad'a? Girgiza kai tayi tana goge hawaye tace na amince da abinda aka fad'a, amma wallahi sharrin shed'an ne, son zuciya da neman duniya yasa na aikata abinda ban tab'a yi ba, ina rokon wannan kotu da ta mani sassauci. Alkali yace Likita kana da ja akan abinda aka fad'a? Girgiza kai yayi yana goge zufa yana fad'in na amince, amma wallahi Hajiya Binta ce ta bani mak'udan kud'i akan nayi rubutu akan k'arya kuma nazo na bada sheda, dan Allah arufa mani asiri. Alkali yace kotu wajen adalci ne, duk wanda kaga yazo kotu to yazo ne domin abi masa hakkinsa, babu batun wani rufin asiri a kotu domin wajen tonon asiri ne, dan haka kowa ya tsaya yaji hukuncinsa. Hajiya Binta.... Kinfi kowa laifi anan, dan haka kotu ta yanke maki hukuncin d'aurin rai da rai agidan yari, sannan zaki biya Amina tarar dubu d'ari biyar abisa kok'arin ki na b'ata mata suna da kikayi. Iya.... Kema kotu ta yanke maki d'aurin rai da rai agidan yari, amma kin samu sassaucin aikin wahala abisa kokarin da kikayi na warware gaskiya da kikayi. Likita..... Kaci amanar aikin ka, an had'a baki da kai anyi rashin gaskiya, dan haka kotu ta yanke maka d'aurin wata biyar agidan yari, kuma zaka biya Amina tarar dubu d'ari biyu abisa b'ata mata suna da kayi. Wannan kotu tana yima Brr. Ra'eez jinjina akan namijin kok'arin da yayi wajen gano gaskiya, da fatan kowa zai d'auki darasi akan wad'annan mutanan, sannan kotu ta wanke Amina daga zargin da ake mata, ciki na mijinta ne, kuma dole yaci gadon mahaifinsa.... Kotttttt!!!! Gaba d'aya mutanan mik'ewa sukayi suna ma Alkali tafi, sosai mutane suke son Alkalin su, domin suna ganin shi d'in adali ne, yana kokarin zartar da hukunci akan duk wanda aka kama da laifi. Hannu Brr. Bajinta ya mik'a ma Brr. Ra'eez yana fad'in ina taya ka murna akan wannan nasara da kayi, ba'a tab'a samun wanda ya kada ni a shari'a ba, sai gashi sabon zuwa yayi mani warwas, duk da ba yaune ka fara aiki ba, anyi maka canjin wajen aiki ne amma duk da haka kayi kok'ari, sai mun had'e wani lokacin. Murmushi Brr. Ra'eez yayi yana fad'in nagode. Har kusa da Brr. Ra'eez dangin Amina suka zo suna masa godiya. Brr. Ra'eez yace haba ai bakomai ku godema Allah. Sallama yayi masu suka fita shida Jabeer. Bayan sunyi sallama da Jabeer ya zo shiga mota yaji ana masa magana, yana juyowa yaga *ALKALI NE,* murmushi yayi yana masa sannu. Alkali yace kaine da sannu, gobe idan kashigo ina son ganinka a ofis. Jinjina kai yayi yana fad'in to yallab'ai. Sallama yayi mashi ya tafi. Da kallo Alkali ya bishi yana sakin murmushi, a zuciyarsa yana nanata sunanshi (Brr. Ra'eez Hamza MWD), kamar ya san mai shigen sunansa sheru da yawa, sai dai kuma wancan ba haka sunansa yake ba, to me MWD take nufi kuma? Kafad'a ya d'aga yayi gaba. **** **** Kai tsaye babbar gidan yari ya nufa, bayan sun gama gaisawa da masu gadin yashiga ciki ya zauna yana jiran akira masa wanda yazo wajensa. Wani babban mutum ne ya fito yana sanye da kayan gidan yari ajikinsa, da ganinsa daga aiki yake. Yana zuwa Brr. Ra'eez ya mik'e ya bashi wajen zama. Bayan sun gaisa Brr. Ra'eez yace *KAWU* nayi nasara, yanzu aka gama yanke hukunci anjima za'a kawo masu laifin nan. Murmushi wanda aka kira da Kawu yayi yana fad'in nasan zakayi nasara Ra'eez, an haifeka ne domin Nasara, yanzu kam hankalina ya kwanta, nasan k'arfin ka ya kawo, zaka iya gogawa da kowa, nayi farin ciki da aka maidoka wannan kotu da aiki, nasan aikin *Alhaji Mansur* ne, yana matuk'ar kok'ari akan ka, yarik'e amana, shima Allah bazai barshi ahaka ba. Brr. Ra'eez yace ai Kawu ban tab'a kukan rashin Mahaifina ba, Abba Mansur ya gama mani komai arayuwa, fatana Allah ya bani ikon saka masa. Kawu yace Allah yasa, kai dai kacigaba da hak'uri arayuwa zaka cigaba da samun nasara, kaje wajen Umman ka kuwa? Brr. Ra'eez yace yanzu dai zan biya. Kawu yace ka dubata da jiki, sannan ka kiyaye da wannan Alk'alin, zuwa gaba zaka gane nufina, nasan Alhaji Mansur ya fad'a maka wasu abubuwa amma dole kasan komai domin ka shirya yakin kwato 'yanci tare da d'aukar fansar Mahaifinka, kada ka sake ka fad'ama kowa abinda MWD yake nufi har sai burinka ya cika, shiyasa naji dad'i da akafi sanin mahaifinka da sunansa na biyu. Ra'eez yace insha Allahu zan kiyaye. Tashi yayi ya mik'a masa kud'i yana fad'in sai na sake dawowa. Kawu yace Allah yayi maka albarka. *** *PSYCHIATRIC HOSPITAL* (ASIBITIN MAHAUKATA) Zaune Brr. Ra'eez yake akusa da wata babbar mace, duk wanda ya ganta yasan tana cikin yanayi na hauka, zaune take tana kallon 'Danta wanda ya bud'e ledar da yazo da ita wadda take d'auke da kayan motsa baki. Lemu ya d'auko yana kok'arin bud'e mata, da sauri ta warce tana kok'arin fasa kwalin. Murmushi yayi ya mik'a hannu yana fad'in Ummu na bani na bud'e maki kinji. Kallonshi tayi kafin ta mik'a masa kwalin. Bud'e mata yayi ya zuba mata akofi ya bata. Amsa tayi ta shanye tana mik'a hannu. Aiba ya b'are mata ya bata. Rabi taci kafin ta mik'a masa rabin abaki, amsa yayi ya gutsura hawaye suna zubo mashi. Hannu tasa ta goge masa hawayen tana fad'in Likita yace adena kuka, yace Alhaji zai dawo, ba dai sun kashe shi ba? Idan na fito zamuje mu kashe su dukan su, ai dai zaka siyo mani wuk'ar Makka ko? Kasan ita kad'ai ce zata iya kashe su. Murmushi yayi yana fad'in Ummu bazan kyale jinin Abbu ya tafi abanza ba, zanyi kwakkwaran bincike, akwai rud'u acikin wannan lamarin, dole sai nasa natsuwa kafin na gano su, bazaki dawwama ahaka ba, Allah zai baki lafiya. Dariya tasa ta kamo hannunshi tana fad'in nima binshi zanyi, kai kad'ai zamu bari ai, sai kaje makka kasiyo wuk'a ka kashe su. Wani likita ne ya k'ara so. Bayan sun gaisa Brr. Ra'eez yace nagode likita, kana kok'ari akan Ummu na. Likita yace haba bakomai, tana samun kulawa sosai, yanzu ma lokacin shan maganinta ne, kasan tana sha take bacci. Jinjina kai Brr. Ra'eez yayi yana fad'in nima tafiya zanyi, nagode sosai likita. Hannu ya bashi yana fad'in Allah ya baka lada Brr. Ra'eez, hakika da wuya asamu irin ka da yawa aduniya, kana kok'ari akan Mahaifiyarka. Hawaye Brr. Ra'eez ya goge yana fad'in dole nayi Likita, duk wanda yasan darajar *UWA* zaiyi fiye da abinda nakeyi, Uwa ba abun wasa bace. Likita yace haka ne gaskiya, Allah yayi mana jagora. Brr. Ra'eez yace amin. Sallama sukayi ya wuce yana kallon Ummunsa. Kai tsaye gidanshi yawuce da yake unguwar ( *APAPA*). Kwance yayi a falo hawayen da suka zamar masa jiki suna kwaranyo masa, gaba d'aya baya jin dad'in ranshi, duk lokacin da ya kai ziyara wajen Ummunsa haka yake kasancewa, kuma duk da haka baya iya faashi wajen zuwa ganinta, can ne kad'ai yake zuwa yaji dad'i aranshi. Runtse ido yayi yana fad'in Allah gani gare ka, Allah kayi mani jagora akan wannan al'amari, bani da gata sai kai ya Allah, kashige mani gaba wajen gano gaskiyar wannan al'amari, Allah ka tona asirin wad'an da suka aikata ma Mahaifina wannan abun, Allah ka tona asirinsu ta yanda bazasu iya k'aryatawa ba. Juyi yayi yana sakin kuka marar sauti. *GA DUK WANDA YAKE SON CIGABAN WANNAN LABARI ZAI TURO NAIRA 200 KACAL, MTN CARD TA WANNAN LAMBAR.. 08147669770, SAI KAYI SCREEN SHOT KA TURA TA WHATSAPP A LAMBAR K'ASA, IDAN KUMA BANK TRANSFER NE, KA TUNTUBE NI TA WHATSAPP NO 08028525263 ZA'A SAKA GROUP DIN DA ZA'A RIKA POSTING. NAGODE. SAI KUYI HAKURI DA YANDA LITTAFIN YAZO.* Ur's. NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) 08028525263 [3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne. naira 200 kacal, MTN card ta wannan lambar.. 08147669770, kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a lambar k'asa, idan kuma bank transfer zakayi sai ka tuntube ni a whatsapp ta wannan lambar. 08028525263* 0⃣2⃣ Da kyar ya tashi yayi wanka, bayan yayi sallah ya fita zuwa gidan Kawu dan can ne waje na biyu da yake d'ebe masa kewa, duk da Kawu ya so ya koma can da zama amma yaki komawa, acewarsa yafi son kad'aici. Da sallama yashiga cikin gidan, a tsakar gida ya iske matar gidan tana kok'arin kauda kayan da suke a tsakar gidan. Amsa sallamarsa tayi tana fad'in Ra'eez sannu da zuwa. Zama yayi yana fad'in yauwa sannu da aiki Mama, ina *RUMAISA* kike aiki ke kad'ai? Murmushi Mama tayi tana fad'in na aiketa siyen kayan miya ne shiyasa nake rage aikin kafin ta dawo. Jinjina kai yayi yana fad'in Kawu yana gaishe ku. Mama tace ka je kenan? Ra'eez yace naje na sanar dashi yanda shari'ar tamu ta kasance ne. Mama tace ikon Allah, ashe fa yau ka fara shiga babbar kotu ko? Ina fatan dai komai yayi dai-dai? Ra'eez yace Alhamdulillahi Allah ya amsa addu'ata, komai ya tafi yanda ya kamata, domin nine nayi nasara. Mama tace kai amma naji dad'i, Ubangiji Allah ya baka ikon yin nasara akan shari'ar da zaka fara nan gaba domin kwato hakkin mu da aka danne. Ra'eez yace amin Mama. Hannu tasa ta goge kwallar data zubo mata tana fad'in ina Kawun naka babu dai abinda yake damunsa ko? Ra'eez yace lafiyarsa lau yace agaishe ku ma. Mama tace amma yana cikin wahala ko? Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in Mama ki daina damuwa, sam basa sashi aikin wahala domin akwai mutane na acikinsu, muna mutunci sosai hakan yasa suke sauk'ak'a masa, addu'a itace abinda zamuyi masa. Mama tace haka ne, shiyasa fa bana son zuwa wajensa, duk lokacin da naje ina dad'ewa kafin na warware, ya jikin Ummun ka? Duk'ar da kai Ra'eez yayi yana fad'in kamar kullum Mama. Girgiza kai tayi tana fad'in Allah ya bi mana hakkin mu, an zalince mu an tauye mana hakkin mu, Allah ne kad'ai zai iya saka mana, Allah ya baka ikon jure wannan jarabawa Ra'eez, hakika an zalince ka, an rabaka da Mahaifinka, ga halin da Mahaifiyarka take ciki, Allah ya baka ikon gano gaskiya kuma ya baka sa'a akan kosu waye suka aikata hakan, babu abinda zamuce da kai sai godiya, Allah ya saka maka da alkhairin abinda kake mana, karike mu amana tamkar jininka. Ra'eez yace amin Mama, amma bana so kina mani wata godiya, kun wuce duk yanda kuke tunani a waje na, bani da kowa a garin Lagos sai ku, duk da bamu had'a komai da ku ba amma Allah ya had'a mu, ku da Abba Mansur kun zame mani 'Yan uwa na jini, ku kad'ai nake kallo naji dad'i arayuwata, ta silar Mahaifina Kawu yashiga halin da yake ciki, tunda babu Abbu dole na maye gurbinsa awajen ku, domin nasan da yana raye shi mai rik'e ragamar gidan ku ne, dan haka kada ki sake mani godiya, ke Uwace agare ni. Jinjina kai Mama tayi tana goge hawayen idonta tace haka ne Ra'eez, hakika kai 'Dah nagari ne, ko wace Uwa zatayi alfahari da samun ka, kada ka sake cewa ta silar Mahaifinka Malan yashiga wannan halin, dama can Allah ya rubuto masa K'addararsa a haka, fatan mu Allah ya bashi ikon cinye wannan jarabawar. Ra'eez yace amin. Sallamar Rumaisa ce ta katse su, amsawa sukayi. Da sauri ta k'araso tana fad'in Yayana sannu da zuwa. Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in Rumaisa ya gidan? Tace lafiya lau, an gama shari'a lafiya? Ra'eez yace lafiya lau nayi nasara. Tashi tayi tana murmushi tace naji dad'i Allah ya k'ara d'oraka akan makiya. Ra'eez yace amin 'Yar K'anwata. Mama tace an samo komai ko? Rumaisa tace an samo. Tashi Mama tayi tana fad'in bara na tayaki naga lokaci ya kure. Da sauri Ra'eez yace aa Mama kinyi aikin ki, yanzu mune zamu shiga ofis. Dariya sukasa, Mama tace ai shikenan ayi aiki lafiya bara naje na gyara cikin kafin Abdallah ya dawo makaranta. Ra'eez yace ina ruwan Autan Mama, ina fatan dai yana karatun sosai? Rumaisa tace ai Abdallah ba wasa, dana fad'a masa zaka zo sai kaga ya dage. Ra'eez yace saura ke, tunda kin gama makaranta. Turo baki Rumaisa tayi tana fad'in Yaya kaima dai ka san ra'ayina ai. Harara ya wurga mata yana fad'in wannan tsohuwar magana ce, dan haka dole kiyi karatu. Duk'awa tayi tana hawaye tace dan Allah Yaya bana son karatu. Murmushi yayi yana fad'in Rumaisa kina nan da ra'ayinki, da ace baki da kok'ari da bazan takura maki ba, kada ki manta kece zakara a makarantar ku fa, tun kafin kishiga makaranta fa kike da kok'ari, meyasa baza kiyi amfani da iliminki ba? Kece babba agidan nan, kina ganin halin da Mahaifinki yake ciki, ga Abdallah k'aninki yana makaranta, baki so yayi koyi da ke? Idan yaga baki karatu shima sai abun ya fice masa arai ai. Hawaye ne suka zubo ma Rumaisa. Ra'eez yace ba kuka nasa kimun ba, gaskiya nake fad'a maki, a zamanin nan kowa yana son auren mace mai ilimi, ko ba dan kanki ba zaki taimaki yaranki, Rumaisa duk kok'arin ki matuk'ar baki wuce karatu ba wata rana zaki nemi ma'anar kalma d'aya ki rasa, domin shi ilimi sai ana tilawarsa yake zama, duk da kinayin islamiya amma zakisha wahala matukar bakiyi karatun boko ba, bance dole kiyi aiki ba, amma idan kikayi karatun wata rana kwalin zaiyi maki amfani, kin ganni nan bazan iya auren macen da iyakarta sakandire ba. Da sauri Rumaisa ta d'ago tana kallonshi. Jinjina kai yayi yana fad'in da gaske nake, nafison na auri mai ilimi kodan saboda yaran mu, idan kuma auren kike so badamuwa ki fito da wanda kike so ni zan maki aure. Mama ce ta fito tana fad'in gara dai kayi mata fad'a, kullum maganar da nake mata kenan amma ta toshe kunnanta, tunda Rumaisa ta taso take fad'in baza tayi karatu ba bayan ta gama sakandire, ada na d'auka yarinta ce ashe har zuciyarta abun yake, ko auren da kake magana ai bata kula kowa, na rasa inda tasa gaba. Ra'eez yace barni da ita Mama, kada ki sake mata maganar karatu, nima bazan sake mata ba, kuma dole tayi aure. Murmushi Mama tayi ta shige tana fad'in aiko zan fara shirin biki. Da sauri Rumaisa ta tashi tana dire-dire ta nufi kicin tana gungunai. Dariya Ra'eez yasa yana rufe baki. Tashi yayi yana fad'in bani alaiyahun na yanka maki. Baki ta murgud'a tana fad'in bana so. Dariyar da yake b'oyewa ce ta kwace masa, sosai yake dariya. Kayan miyar ta d'auka ta cigaba da aikinta tayi banza dashi. Tashi yayi yana fad'in bara na d'auko maki tsarabar ki amota na manta. Bata kulashi ba yayi waje. Bayanshi tabi da kallo hawaye suna zubo mata, dole ma ta amince tayi karatu matuk'ar tana son Yayanta, da sauri ta d'auko wayarta ta rubuta mashi ya samo mata makarantar aikin lafiya ta unguwar zoma (Mid-Wife) zatayi karatun. Tun a zaure Ra'eez yake dariya, sai da yasha dariyarsa kafin yashigo ciki, dama yasan idan ba haka yayi mata ba baza tayi karatun ba, yana matuk'ar son Rumaisa amma yafi so ya auri mai ilimi, kamar tasan yana son mace tayi aikin asibiti ta zab'i haka. Ciki yashiga ya fara taya ta aiki be nuna mata yaga sakon ta ba. **** **** Kwankwasa k'ofar ofis d'in Alkali yayi kusan sau biyu kafin daga ciki aka bashi izinin shiga. Tare da Brr. Bajinta ya iske Alkali. Murmushi Alkali yayi yana fad'in kaga d'an halak d'in ma, yanzu muke maganar ka ashe kana hanya. Hannu Ra'eez ya mika masu suka gaisa cike da girmamawa. Kujera Brr. Bajinta ya nuna mashi yana fad'in bismillah. Zama yayi Alkali yace ba dai yanzu kashigo ba? Ra'eez yace tun d'azu nazo nasan baka shigo ba shiyasa na zauna a ofis. Alkali yace ya gajiyar aikin jiya kuma? Ra'eez yace Alhamdulillahi. Brr. Bajinta yace ai jiya Brr. Ra'eez ya caza mana kwakwalwa, na rasa yanda akayi ya iya had'a wannan aikin acikin sati d'aya. Alkali yace shiyasa nace ya sameni domin naji yanda akayi yayi wannan kok'arin, gaskiya ban tab'a samun mutum irinka mai hazaka ba, shiyasa tun ajiyan nayi masa jinjina. Brr. Ra'eez ko zaka fad'a mana yanda akayi kayi wannan aikin haka? Kada ka damu nasan ba hurumi na bane nayi maka wannan tambayar, kawai dai naga kok'arin ka ne shiyasa zan so naji daga gareka. Murmushi Ra'eez yayi ya kauda kai bece komai ba. Tashi Brr. Bajinta yayi yana fad'in Yallab'ai zanje ana jira na a ofis. Alkali yace to badamuwa nagode. Bayan ya fita Ra'eez ya d'ago kai, dama saboda Brr. Bajinta yaki yin magana, taya Alkali zai tambayeshi agaban abokin aikinsa bayan yasan tare suka kara. Alkali yace yi hak'uri nayi maka tambayar da bata dace ba. Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in haba ba komai. Alkali yace kawai ina so naji yanda akayi ka iya gano gaskiya ne dan gaskiya ka burgeni, zan so ka saki jiki dani, ka d'auke ni tamkar d'an uwanka dan gaskiya ka burge ni, da alama ba'a garin nan kake ba ko? Kai Ra'eez ya girgiza yana fad'in a garin nan nake, sai dai ba anan nayi karatu ba shiyasa, nayi aiki a babbar kotu da take kano na kusa shekara d'aya kafin na nemi canjin wajen aiki aka maido ni nan. Alkali yace zuwanka alkhairi ne a kotu ta, domin ina da buk'atar mutane irin ku, domin tunda na saurari bayaninka na gano kana da gaskiya, dan haka kacigaba da rik'e gaskiya dan ita ce cikar darajar mutum. Ra'eez yace nagode da wannan karamcin daga gare ka, kuma insha Allahu ba zaka sameni da rashin gaskiya ba. Hakika lokacin da nazo wannan kotun na kawo takardar canjin aikin da akayi mani aranar na iske wannan shari'ar, zaman da nayi ina jiranka alokacin na tsinci kad'an daga cikin shari'ar, alokacin Lauyen da yake kare Amina naji yana fad'in bazai iya cigaba da shari'ar ba, domin yayi iya bincikensa ya kasa gano komai, gashi Brr. Bajinta ya fishi sanin makamar aiki bazai iya gogawa dashi ba, yaso ya taimaka ma Amina amma dole ya hakura har ya fad'a mata ta samu wani lauyen kafin lokaci ya kure mata. Bayan dana gama jin firarsu bayan da kazo nashiga muka gama komai kasa a nuna mani ofis d'in mu shine naje nayi masa sallama na gabatar masa da kaina na nuna masa naji firarshi ko zai iya bani dama na amshi shari'ar da yakeyi? A lokacin da nayi masa magana sosai farin ciki ya bayyana a fuskarshi, babu b'ata lokaci yashiga warware mani komai akan shari'ar. Aranar bayan na koma gida banyi bacci ba, yanda ya bani labarin na zauna na fitar da komai, washe gari na nufi gidan marigayi nida lauyen, bayan munje muka samu Amina ya fad'a mata nine zan karb'esa. Sosai tayi farin ciki anan tashiga bani labarin gaskiyar abinda ta sani, bayan nayi mata tambayoyi anan na gano mai aikinsu bata gidan da dad'ewa, shine nace mata ina so ta fad'a mani inda zan samu Iya, shine ta fad'a mani 'yar asalin 'Danja ce, sai dai bata san gidanta ba, amma ta tab'a fad'a mata gidanta yana bayan kasuwa wata rana da suke fira. Bayan na gama jin labarin Iya sai na nemi da ta fad'a mani aminin Alhaji data sani, shine ta fad'a mani sunan Alhaji Kabeer, nan nace mata zan tafi tunda babu lokaci, ina so naje can garin su Iya. Haka mukayi sallama da ita muka tafi. A ranar nabi jirgi zuwa kano, washe gari na nufi funtua sai da na huta daga can naje garin su Iya, cikin ikon Allah bansha wata wahala ba na gano gidanta, alokacin da naje mata da bayanin daga Lagos nake nasan tayi aiki agidan Alhaji k'ark'ashin Hajiya Binta. Fad'ar sunan Hajiya Binta yasa Iya ta fara kuka tana fad'in ba laifinta bane, tun anan na gano akwai wata ak'asa, hakan yasa na lallab'ata nace ta bani labarin abinda ta sani domin Alhajin ya rasu. Haka ta warware mani komai tana kuka, na tausaya mata domin naga nadama a idanuwanta, nan na roketa akan ta biyoni idan har ta yarda tayi nadama kuma tana so ayi mata hukunci a duniya. Babu b'ata lokaci ta amince, domin ta fad'a mani gara a yanke mata hukunci akan rayuwar da takeyi agarinsu, duniyar tayi mata zafi koda banje ba ta yanke shawarar barin garin ta koma wani gari ko zata samu sauki. Naji dad'in maganarta, aranar muka nufi Funtua da ita, dole ta mota muka dawo saboda naga zamu b'ata lokaci. Bayan da muka dawo naje na samu 'Dan sanda yayi mani jagora zuwa gidan Alhaji domin a bayanin Iya ta fad'a mani ta aika masa da takarda, bayan munje na tambayi Amina ko an samu wata takarda a d'akin Alhajin wadda aka fad'a masa tana da ciki? Sai tace gaskiya bata sani ba, ganin haka yasa muka nemi izinin Hajiya Binta muka shiga d'akin, cikin sa'a na samu wannan takardar dana gabatar. Haka muka tafi na nuna masu ban samu komai ba. Bayan nan naje na samu Alhaji Kabeer, shima mun dad'e muna tattaunawa dashi kafin muka rabu, ana saura kwana d'aya a koma kotu na kammala had'a shedu na, cikin ikon Allah nazo na gabatar dasu kuma nayi nasara. Kaji yanda akayi na gano komai cikin lokaci. Jinjina kai Alkali yayi yana fad'in gaskiya Brr. Ra'eez kai na daban ne, basirar ka daga Allah take, kayi aiki da ilimi, sai kwararren lauye ne zai iya abinda kayi, sai gashi baka dad'e da aikin ba amma ka tafiyar da wannan shari'ar mai rikitarwa, gaskiya dole na yaba maka, kayi abinda ya kamata, kuma daga yau ka zama babban lauya a wajena, insha Allahu zan rik'a aiki da kai, domin ra'ayin mu iri d'aya ne, ina son mutum mai son zakulo gaskiya a duk inda take. Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in nagode Yallab'ai. Alkali yace karik'a kirana da Abba kamar yanda Yarana suke kirana zanfi jin dad'in hakan domin nasan zakayi sa'an 'Dana na biyu, duk da banyi aure da wuri ba da nasan sai dai kazo ana ukku ma. Ra'eez yace to Abba nagode. Alkali yace a ina kake da zama ne? Yace a Apapa nake. Alkali yace kayi aure ne ko kana zaune da Iyayen ka? Murmushi yayi yana fad'in banyi aure ba ni kad'ai nake zaune. Alkali yace Allah sarki, Iyayenka ba anan suke ba ne? Baki Ra'eez ya bud'e zai bashi labarinsa sai kuma ya tuna da maganar Kawu ( *Ra'eez ka koyi b'oye sirrin ka, a ciki hada labarin zuri'ar ka, kasan dai yanda kake kok'arin gano wad'an da suka aikata ma Iyayenka wannan abun, kuma nasan dole asan Mahaifinka agarin nan tunda babban mutum ne, kuma ana da tabbacin akwai sa hannun manyan mutane a kisanshi, a ciki hada lauyen da nake zargi domin Mahaifinka ne ya hanasu sakewa hakan yasa suke kokarin ganin bayansa, bani da sheda a hannu amma ina zarginsu domin sune abokan fad'an mahaifinka, dole ka b'oye labarinka har sai komai ya kammala domin gujema matsala, bana son kowa yasan ko kai waye, dan haka bana son ka fad'ama kowa labarin ka.*) Gyara zama yayi yana fad'in Iyaye na suna Gombe ni kad'ai ne anan. Alkali yace Allah sarki, lallai kayi nisa da gida, bakomai ka d'auke ni tamkar Mahaifinka, idan ka tashi kajira ni sai muje na gabatar da kai a wajen Iyalina domin karik'a zuwa kuna gaisawa, ina zaune a *SURELERE*. Ra'eez yace bakomai zan jira ka. Alkali yace nagode zaka iya tafiya. Wayar Alkali ce tayi k'ara, sallama Ra'eez yayi masa ya fita. Bayan ya d'auka suka gaisa, alamu sun nuna abokinsa ne ya kira. Shiru yayi yana jin bayanin da yake masa. Kai ya jinjina yana fad'in haba *Alhaji Marusa* wannan ai ba abun tada hankali bane, shikenan na gane bayanin ka, insha Allahu bamu da sauran matsala, na kammala shari'ar da nake fad'a maka kuma an gano gaskiya, sabon lauya ne ma ya gano komai, ai ina fad'a maka yanzu ya bar ofis d'ina, gaskiya yaron yana da hazak'a, dan haka abinda ya kamata zan rik'a bashi, sauran kuma sai aba Brr. Bajinta saboda kasan shine namu bazamuyi saurin nuna fuskar mu a wajen sabon zuwa ba. To shikenan sai kazo. Wayar ya aje yana murmushi. Tunda Ra'eez ya shiga ofis ya gama duba takardun da suke akan teburinsa ya janwo hoton da sukayi shida Iyayenshi, alokacin bai wuce shekara takwas ba, yana tsakiyarsu suna dariya aka d'auki hoton. Koda yaushe yana tare da wannan hoto dan shine yake d'ebe masa kewar Mahaifinsa. Zaroshi yayi daga cikin jakar da yake ajeshi (wallet) aranshi yana fad'in dole ya maidashi gida ko dan gudun b'acin rana, tunda Kawu yace ya kikaye barin duk wata alama da zata nuna koshi waye har sai ranar da burinshi ya cika. A hankali yasa hannu cikin dabara ya goge hawayen da suka kusa gangaro masa ta gefen gilashinsa, tashi yayi yasa hoton a aljihu ya d'auki mukullin mota domin yaje ya aje hoton agida dan hankalinsa yaki kwanciya akan ya kara ko mintuna biyu a wajenshi, hakan yasa ya fita domin yaje gida ya adana hoton. A waje suka had'u da Brr. Bajinta ya rako wasu manyan mutane, da ganinsu ba sai an fad'a maka naira ta zauna masu ba, har sun gaji da kud'i a yanayin jikinsu, motar da suke tsaye ajiki kad'ai abun kallo ce bare kuma suturar da take jikinsu. Yanda yaga Brr. Bajinta yana wani risna masu ya k'ara tabbatar masa da su d'in wasu ne. Kai tsaye wajen daya aje motarsa ya nufa ba tare daya sake kallon su ba, maganar Kawu ce take masa yawo akan tsohon ma'aikacin wannan kotu mai suna *Brr. Barau*, akoda yaushe yafi tsayama masu hannu da shuni akan talakawa, hakan ya nuna masa yana danne gaskiya akan k'arya, tunda ya kasance shine ya tsaya har aka yanke ma Kawu hukunci amatsayin ya kare hakkin Mahaifinsa wannan ya nuna akwai wata ak'asa, duk da hakkin mahaifinsa ya kare amma kuma ai ba Kawu bane ya aikata laifin meyasa ya tsaya har sai da yaga an yanke masa hukunci? Gaskiya dole ya fara bincikensa akan Brr. Barau, to wai ma yana ina? Yasan dai zuwa yanzu kila ya aje aiki ko kuma ya zama shugaba, gashi kuma Kawu bai fad'a masa komai akansa ba, ko hotonsa bai sani ba bare idan ya ganshi ya ganeshi, amma zai tambayi Kawu inda yake. Haka ya isa gida da wannan tunanin. Bayan ya adana hoton ya zauna yana tunanin hanyar da zai fara bibiyar Brr. Barau domin ya gano hakikanin gaskiya, dole ta kanshi ne zai fara aiki hakan zaisa ya gano komai, domin lokacin da aka kashe mahaifinsa bai bari kowa ya kai k'ara kotu ba yayi saurin amsar shari'ar Mahaifinsa yayi tsaye har sai da yaga an gama komai cikin k'ank'anin lokaci. Saurin tashi yayi ya d'auko wani k'aramin littafinsa, sunan Brr. Barau ya fara rubutawa aciki kafin ya b'oye littafin ya kwanta yana kallon sama. Dole ya gano masu hannu akisan Mahaifinsa kodan ya sama ma Mahaifiyarsa lafiya domin ta silar mutuwarsa ta samu kanta acikin wannan hali. Ta ina ya kamata ya fara kenan? Dole yaje wajen aikin Mahaifinsa yasan zai samu wani abu, sannan lokaci yayi da Kawu zai bashi labarin Mahaifinsa, saboda Abba Mansur ya fad'a masa Kawu ne kawai zai iya bashi labarin komai. A zabure ya tashi ya d'auki mukullin motarsa ya nufi gidan Yari, bazai iya jira a k'ara kwana ba tare da yasan labarin Iyayensa ba. Yaci sa'a alokacin da yaje suna hutawa, hakan yasa akayi kiran Kawu suka samu waje suka zauna. Kawu ya kalleshi cike da mamaki yana fad'in Ra'eez lafiya? Wannan zuwan fa? Kuka Ra'eez yasa yana fad'in daga wajen Alkali nake, yace mani yana son yarika aiki dani, gashi na gama duba sunayen ma'aikatan wajen banga sunan Brr. Barau ba, dan Allah Kawu ka bani labarin komai. Murmushi Kawu yayi yana fad'in wannan Alkalin ai shine Brr. Barau, na fad'a maka ne saboda kasan ta yanda zaka cigaba da tarayya dashi, kuma tunda yanzu ka kawo girma dole na baka labarin komai saboda ka fara shiryama doguwar shari'a, yanzu zakaji komai...... *ASALIN LABARIN* Ur's. Nabeelert Lady🖋 [3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kudi ne, naira 200 kacal, MTN card ta wannan lambar.. 08147669770, kayi screen shoot ka turo a whatsapp ta lambar k'asa, idan kuma bank transfer zakayi ka tuntub'e ni a whatsapp ta wannan lambar 08028525263* 0⃣3⃣ *ALHAJI HAMZA MAI WADA* shine cikekken sunansa, asalinsa d'an *MAIDUGURI* ne, aiki ne ya fito dashi daga garinsu, ma'aikacin *KWASTAM* ne, yayi aiki a garuruwa da yawa, tun yana a k'aramin matsayi har Allah ya d'agashi, mutum ne mai gaskiya da amana, kowa yasan yanda halin masu irin aikinsu yake a wannan zamani, duk wanda aka ce maka yana aikin Kwastam da wuya ka sameshi mai gaskiya, zaka sameshi mai dukiyar gaske musamman idan akace ya kai babban matsayi, kafin ka samu mutane masu irin wannan aikin da gaskiya a wannan zamani zaka sha wahala, akwaisu sai dai basu da yawa. Alhaji Mai Wada ya kasance acikin mutane masu riko da gaskiya da amana, wanda hakan ya jawo masa bakin jini a wajen manyansa da kuma manya a najeriya, yayin da ya jawo masa farin jini a wajen masu k'aramin k'arfi musamman masu shigo da kayansu ta hanya mai kyau. Saboda halinsa yasa ake yawan canza masa wajen aiki, wannan dalilin ne yasa yayi zama garuruwa da yawa, hakan ne ya jawo masa rashin yin aure da wuri, domin yana ganin akwai zalinci yayi aure ya bar matar ya tafi wajen aikinsa. Sai da 'yan uwansa suka matsa masa kafin ya amince su zab'a masa wata daga cikin danginsa dan baya son yaje wani waje ya samo mata. Kasancewar zuri'arsu akwai had'in kai, dan zaune suke a waje d'aya, katafaren gida ne mai b'angarori da yawa hakan yasa duk 'yan uwan suke zaune awaje d'aya, dama basu da wani yawa a zuri'arsu. Cikin lokaci k'ank'ani aka sama masa mata mai suna *BILKISU*, mace ce mai hakuri da juriya, masaniya ce a karatun addini, iya karta diploma a fannin girke-girke, lokacin da aka mata maganar anyi mata miji babu b'ata lokaci ta amince dan dama yana burgeta. Bayan anyi bikinsu da wata d'aya aka sake masa canjin wajen aiki zuwa Kano. Haka ya tafi ya kwashi kusan wata biyu kafin ya dawo, da zai koma Mahaifinsa yace daga yanzu duk inda aka maidashi ya d'auki matarsa su tafi, be amince masa yarik'a barinta ba, da ace tare suka tafi kila da yanzu ta samu rabonta, amma ya tafi har wata ukku taya zai tara zuri'a a haka. Haka ya d'auki matarsa sukayi sallama da 'yan uwa sai kuka Bilkisu take kamar kada ta bishi. Haka suka tafi cike da kewar gida. A wannan karon ya dad'e a Kano ba'ayi masa canjin wajen aiki ba. Har Bilkisu ta haifi d'anta namiji suka koma gida domin ayi suna acan. 'Yan uwa sunyi matuk'ar farin ciki, domin Alhaji Mai Wada shine babban 'Dah a zuri'arsu, kuma gashi Allah ya bashi magaji. Anyi taron suna na gani na fad'a, anyi hotuna kowa yayi farin ciki, inda aka sama yaron *RA'EEZ*. Bayan suna haka ya tafi ya barta anan sai bayan tayi arba'in kafin ta koma. Kwanan su talatin da biyar Mahaifinsa yayi masa waya akan yazo ya d'auki matarsa. A washe gari ya taho. Bilkisu kuka tasa da taji zasu tafi dan asonta tayi kwana hamsin, sauran matan ma hakuri suka bama Mahaifin Alhaji Mai Wada amma yace sai sun tafi baiga amfanin zamanta ba ta bar mijinta shi kad'ai. Haka suka tafi sai kuka takeyi. Tafiya suke Alhaji Mai Wada yana tunanin maganganun da sukayi da Mahaifinsa adaren da zasu taho, haka kawai yake jin jikinsa yana sanyi. Bayan komawarsu da sati biyu fad'a ya kaure a Maiduguri, gaba d'aya babu wanda ya tsira a gidansu. Lokacin da suka samu labari sumewa Alhaji Mai Wada yayi, kwanansa biyu a asibiti kafin ya farfad'o. Bilkisu ma duk ta fita hayyacinta. Babban aminin Alhaji Mai Wada wato *ALHAJI MANSUR*, shine wanda yake tsaye akansu, shima d'an Kano ne babban d'an kasuwa ne, tunda Alhaji Mai Wada ya dawo Kano ya tab'a taimakonsa akan wasu kayansa da wasu suka so dannewa, tun daga lokacin suka kulla abota, sun zama tamkar 'yan uwa, matarsa *AISHA* suna zumunci da Bilkisu sosai, dan halinsu yazo d'aya. Bayan da aka sallamesu Alhaji Mai Wada yaso su tafi can garinsu amma Alhaji Mansur ya hanashi dan garin a hargitse yake. Sai da aka rik'a had'a masu da rokon Allah kafin suka samu natsuwa. Sai da akayi watanni da faruwar abun kafin suka je domin su duba ko akwai wad'an da suka rayu. Haka sukaje ofishin 'yan sanda anan suka samu labarin yanda abun ya kasance. Lokacin da sukaje unguwar su sunsha kuka, dan kamar ba'a tab'a gini a wajen ba. Sun sha kuka haka akayita basu hakuri. Kasa zama agarin sukayi aranar suka koma Kano. Tun daga lokacin Maiduguri ta fitar masa arai, bai sake tunanin zuwanta ba, domin babu abinda zeyi bayan zuri'arsu sun mutu babu kowa, be tab'a tunanin yaje ko Allah zaisa wasu sun tsira ba, dan har lokacin ance ba'aga gawar wasu ba kuma ba'aji labarinsu ba kawai yacigaba da rayuwarsa da matarsa da d'ansa. Lokacin da Ra'eez ya isa sawa makaranta haka aka sashi tare da d'iyar Alhaji Mansur *LABIBA*, tare ake kaisu a maidosu tare. A lokacin ne kuma Alhaji Mai Wada ya samu k'arin matsayi inda aka maidashi Lagos aka bashi matsayin shugaban Kwastam acan. Alhaji Mansur yafi kowa shiga damuwa shida matarsa, domin sun shaku dasu Alhaji Mai Wada, Bilkisu hada kukanta, duk da ta rasa danginta sai Allah ya had'ata da Aisha, tana jinta tamkar 'yar uwarta, sai gashi kuma yanzu zasu rabu. Ganin halin da suka shiga ita da Aisha har ma da Alhaji Mansur sai Alhaji Mai Wada ya yanke shawarar barin Bilkisu anan domin Ra'eez ya k'arasa makarantarsa. Lokacin da sukaji haka sosai sukayi farin ciki, duk da Alhaji Mansur yaji dad'i amma kuma zaiyi rashin amini nagari. Haka Alhaji Mai Wada ya tafi cike da fatan nasara, duk lokacin da akayi masa canjin wajen aiki yana sawa ayi masa sauka da addu'oi saboda neman tsari daga mahassada. Tun farkon zuwanshi Lagos ya fara gano ta'asar da akeyi a wajen aikinsu, baiyi yunkurin hanawa ba duk da ya kasance shugaba, domin abinda ya sani shine ba'a saurin nuna ma mai laifi kuskurensa musamman idan kana bakon waje, ba kamar gari irin Lagos, domin ya dad'e da sanin garin, babu labarin da bai sani ba a hukumar Kwastam ta Lagos, tun kafin yazo garin yake da labari hakan yasa yayi masu kwanciyar b'auna domin ya gano komai cikin sauki ta yanda zai san yanda zai b'ullo masu. Kowa yasan yanda aikin Kwastam yake, kowa baya da buri wanda ya wuce ya tara abin duniya. Haka ya kasance a wajen da Alhaji Mai Wada yake, akwai mataimakinsa mai suna *ADEBAYO*, d'an *kudu* ne, Allah yayi masa son kud'i ga karb'ar cin hanci kamar me, yana harka da manyan mutane na garin Lagos har ma dana waje, duk wani wanda ake shigo masa da kaya yasan da zaman Adebayo, kafin a canza ma shugabansu wajen aiki shima jirgi d'aya ne ya kwaso su, shiyasa alokacin masu kaya basa jin dad'in abinda ake masu, domin ana karb'ar kud'i awajensu sosai, idan bakaci sa'a ba wani lokacin a kama kayan ka, sai ka saki kud'i masu yawa kafin a sakar maka su. Da yawa ma'aikatan da suke aiki ak'ansan su basa jin dad'insu, domin idan suka samu sai abinda sukaga damar yaga masu, wasu suna fatan a kawo masu canji yayin da wasu sunfi buk'atar abar masu su kodan samun na cefane da sukeyi. Tun bayan zuwan Alhaji Mai Wada ya amshi komai a rubuce daga wajen Adebayo, sai rawar jiki yake dan yana so ya samu shiga awajenshi. Bayan da Alhaji Mai Wada yayi wata guda a wajen sai ya canza wanda yake kula da karb'ar haraji domin ya gano ta wajenshi ana babbar b'arna, haka ya canza wanda yake kula da shigowar kaya da saukesu, haka duk ya tarwatsa kowa Adebayo kuma yace ya tsaya a matsayinsa baya so yana shiga abinda ba aikinsa ba. Tun daga wannan rana daya tarwatsa kowa mutane da dama sunji zafinsa, yayin da wasu sukaji dad'i, wasu daga cikin wad'an da ake shigo masu da kayansu sunyi farin ciki da zuwan Alhaji Mai Wada, yayin da wasu suke bakin ciki. Hatta da direban da ya iske wanda yake tuk'ashi sai da ya canza, domin Alhaji Mai Wada bashi da saurin yarda da mutane, tunda ya lura direban yana da kusanci sosai da Adebayo yaji bai kwanta masa ba, domin yasan wasu daga cikin halayyar Adebayo. Ya dad'e yana tuk'a kanshi kafin ya samu direba mai suna *MALAN SANI*. Ya had'u da Malan Sani wata rana bayan ya dawo daga ofis da dare wajen k'arfe goma da rabi, ya tsaya domin ya sayi biredi sai kawai ya hango Malan Sani ya fito daga wani lungu da gudu sai waige -waige yakeyi, yana tsaye har yazo ya wuceshi sai yaga ya b'oye a bayan motarsa yana lekowa yana kallon hanyar daya fito. Bayan daya gama siyen biredin sai ya zagayo domin yashiga mota, sam baiji tsoron komai ba ya dafa Malan Sani, a firgice ya jiyo jikinsa yana rawa. Alhaji Mai Wada yace kwantar da hankalin ka babu abinda zanyi maka, zan tafi ne kuma naganka ajikin mota ta shine na tab'o ka. Hannu Malan Sani yasa ya goge zufar data keto mashi kafin yace na rokeka da Allah ka taimaka mani na fita daga wajen nan, wallahi kashe ni zasuyi. Cike da mamaki Alhaji Mai Wada ya kalleshi, har zai masa tambaya sai kuma yayi saurin bud'e bayan motarsa yana fad'in shiga amma ka duk'e kada aganka. Yana shiga yaja motar suka bar wajen, babu wanda yayi magana har sai da suka iso unguwar da Alhaji Mai Wada yake kafin ya tsaya agefen hanya ya juyo yana fad'in Malan anan nake da zama kai ina zakaje? Tashi Malan Sani yayi yana kallon inda suke, ajiyar zuciya ya saki yana fad'in ai nazo gida Alhaji, nima anan unguwar nake gidana yana can layin baya. Alhaji Mai Wada yace nima ga gidana can idan bazaka damu ba mu k'arasa akwai abinda nake son na tambayeka. Malan Sani yace Alhaji yanzu dare yayi, kaga har goma ta wuce, nasan Iyalina suna can cikin damuwa dan bana wuce goma awaje, amma muje ka nuna mani gidan ka ni kuma nayi maka alk'awarin gobe da safe zanzo na sameka. Kallon Malan Sani Alhaji Mai Wada yayi na wani lokaci, tabbas haka kawai yake jin ya yarda dashi, domin beyi kala da macuci ba, magidanci ne sosai yana da fuskar kamala. Ajiyar zuciya yayi yana fad'in kana da gaskiya, nima bani da iyali shiyasa banyi tunanin dare yayi ba, badamuwa muje kaga gidan nawa. Har bakin gate suka isa kafin suka fito. Kallon Malan Sani yayi yana fad'in sunana Alhaji Hamza Mai Wada, kuma ni mutumin Maiduguri ne, sai dai Iyalina suna zaune akano, banfi wata d'aya dana dawo nan ba dan anyi mani canjin wajen aiki nine shugaban Kwastam na wannan garin. Jinjina kai Malan Sani yayi yana fad'in ikon Allah, dama kaine naji ana ta magana a wajen aikin mu? Wallahi ko d'azu naji ana maganar sabon shugaban da aka kawo a wajen da naje. Ni sunana Malan Sani, d'an Katsina ne ni, neman kud'i ya kawo ni Lagos nafi shekara goma sha biyu anan, tun ina k'aramun aiki har Allah ya bud'a mani na samu aikin tuki a kamfanin Fanta, da buga-buga har Allah yasa nayi gidan kaina. Murmushi Alhaji Mai Wada yayi yana fad'in lallai Malan Sani ka zama d'an Lagos, bara na barka kada ashiga hakkin Iyali, tunda gobe asabar babu inda zanje zanyi jiranka dan akwai abinda nake son ji daga gareka. Malan Sani yace insha Allahu wajen k'arfe goma zanzo nasan zuwa lokacin ka tashi. Dubu biyu Alhaji Mai Wada ya mik'a mashi yana fad'in ga wannan kayi cefane. Malan Sani yace haba Alhaji ka bar su nagode da wannan taimakon ma da kayi mani. Alhaji Mai Wada yace bafa roko na kayi ba, dan haka ka amsa dan Allah. Amsa yayi yana fad'in nagode sosai Allah ya k'ara bud'i. Sallama yayi masa ya tafi cike da farin ciki, har sai da kwallar farin ciki ta fito masa. Allah mai jink'ai kenan, ko sisi be tashi dasu ba yau, haka ya fita domin neman aiki har dare be samo komai ba sai rayuwarsa da akaso illatawa, gashi yayima matarsa laifi, ya b'oye mata sallamarsa da akayi daga aiki kusan kwana ukku kenan, a nufinsa idan Allah yasa ya samu aiki yau sai kawai ya fad'a mata ya canza wajen aiki, sai gashi bai samu ba kuma ko kud'in abincin safe bedasu, sai gashi Allah ya kawo masa wannan Alhajin ya bashi har dubu biyu bayan taimakonsa da yayi. Lallai mutanan kirki basa k'arewa duniya. Haka ya nufi gida cike da farin ciki, yaji dad'in samun kud'in nan domin yana tausayin matarsa saboda tana da tsohon ciki. Ur's. Nabeelert Lady🖋[3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kudi ne, naira 200 kacal, MTN card ta wannan lambar.. 08147669770 kayi screen shoot ka tura a whatsapp ta lambar k'asa, idan kuma bank transfer ne ka tuntube ni a whatsapp ta wannan lambar 08028525263* 0⃣4⃣ Da sallama Malan Sani ya shiga gidanshi fuskarsa d'auke da fara'a. Matarsa tana zaune a tsakar gida tana hutawa bayan ta gama shan fatan tsakin da tayi, amsa masa sallamar tayi tana kok'arin tashi tana fad'in sannu da zuwa Malan. Saurin k'arasowa yayi ya kamata suka zauna yana fad'in haba *HALIMA* kada ki wahalar da kanki kina fama da jikin ki. Murmushi tayi tana fad'in ai bana jin komai. Malan Sani yace ai dai kinyi nauyi kidena yunkurin tashi da sauri haka. Halima tace Malan hankalina yau ya tashi ganin ka dad'e a waje na d'auka ma ko kunyi tafiya waje mai nisa ne. Murmushi yayi yana fad'in wallahi nima hankalina yana wajenki musamman da nasan ke d'aya ce agidan, yau nayi wani aiki ne shiyasa ban dawo da wuri ba, a hanyar dawowa ta kuma na had'u da wani Alhaji har ya rago mani hanya, layin gaban mu yake da zama shine sabon shugaban Kwastam d'in da aka kawo, to shine fa na tsaya dashi mukayi fira kamar mun san juna. Halima tace Allah sarki, wallahi har hankalina ya kwanta na d'auka wani abun ne ya faru da kai, musamman da naga yanayin daka fita da safe, baka tab'a barina babu kud'in cefane ba sai yau, acikin kwanakin nan sai nake gani kamar akwai abinda yake damun ka. Murmushi yayi yana fad'in babu abinda yake damuna kawai kicigaba dayi mani addu'a ina so na canza wannan aikin da nakeyi. Da sauri ta kalleshi tana fad'in ba dai korarka sukayi ba? Murmushi yayi yana fad'in basu kore ni ba kawai nagaji dayi masu aiki ne saboda basu da lokacin tashi, kina ganin kullum idan na fita sai dare nake dawowa, gashi yanzu kinyi nauyi bana son ki haihu ace ina barin ki ke kad'ai, gara na canza aiki kema kirik'a samun kulawa keda abinda zaki haifa. Halima mun dad'e da aure Allah be babu haihuwa ba, yau gashi Allah ya amshi addu'ar mu kinga dole na tsaya na rik'a kula daku, duk da kince d'iyar yayarki zata zo cikin sati mai kamawa amma nafison ace nima ina kusa da ke. Murmushi tayi tana fad'in to Allah ya zab'a maka wanda yafi wancan alkhairi, Allah ya kareka daga sharrin ko wane aiki da zaka samu. Hannunta ya kamo yana fad'in amin Halimatus Sa'adiya. Tashi tayi tana fad'in bara na kawo maka abinci yau dai faten tsaki nayi da wake sai nasa alaiyahu. Malan Sani yace baiwar Allah, ubangiji Allah ya biyaki da aljanna, nasan dai akwai abinci agidan, amma ban bar na cefane ba ashe kin samu kinyi? Halima tace d'azu ne *JAMILA* ta aiko mani da d'ari biyun dana ara mata shine nayo mana cefane dasu. Malan Sani yace Allah yayi maki albarka, kinga nima wannan Alhajin ya bani dubu biyu yace nayi cefane, kuma gobe da safe yana nemana. Halima tace amma mungode masa Allah ya biyashi da alkhairi. Malan Sani yace amin. Wucewa ciki tayi ya bita da kallon tausayi, baya so ya fad'a mata halin da yake ciki yasan halinta da damuwa, ga tsohon ciki tana dashi idan taji an koresa a aiki zata shiga damuwa, haka idan ya fad'a mata wasu sun biyoshi d'azu hankalinta bazai kwanta ba. Gara ya cigaba da b'oye mata har Allah yasa ya samu wani aikin. *WAYE MALAN SANI?* *MALAN SANI HASSAN*, shine cikekken sunanshi, d'an asalin garin Katsina ne, neman kud'i ne ya kawosa Lagos, tun yana kwana a k'asan gada har ya koma kwana a shago, yasha wahala sosai arayuwarsa kafin ya samu na kanshi, kasancewarsa mutum mai gaskiya da amana yasa duk inda yayi aiki ake sonshi, a hankali yarik'a tara kud'i har Allah ya bashi ikon siyen fili a unguwar *AGEGE*. Da kad'an -kad'an ya fara gini, da a kasuwa yake aiki sai kuma ya fara aiki da masu had'a buhun da ake rufe saman babbar mota dashi (TAMPOL) . Da wannan sana'ar sosai yake samu, yana aikinsa kuma yana cigaba da gininshi, ya dad'e beyi aure ba sai daga baya yayi aure inda ya auri matarsa Halima, itama 'yar Katsina, gidansu gidan rufin asiri ne, mahaifinta d'an kasuwa ne, hakan yasa ta taso cikin tarbiya da sanin rayuwa. Bayan da yayi aure sai ya barta a gidan Mahaifiyarsa shi kuma ya koma Lagos, sai ya samu lokaci yake zuwa wajenta, sai dai duk wata yana yi mata aike. Da haka Allah ya bashi ikon kammala gininshi, inda yayi d'akuna biyu ciki da falo sai band'aki da kicin sai tsakar gida, daga gefen tsakar gidan kuma an fitar da wani d'aki sai dai bai fara ginashi ba ya fitar dashi ne saboda zuwa gaba idan ya samu hali ya gina d'akinshi sai ya bar ma Halima wancan koda ta haihu. Bayan daya gama komai yaje ya d'auko matarsa suka dawo nan da zama. Sun dad'e basu samu haihuwa ba har Allah ya taimakeshi kamfanin Fanta suka d'aukeshi aikin direba. Sosai yayi farin ciki da wannan aikin daya samu musamman daya maido da Iyalinsa Lagos nauyi ya k'aru sai gashi kuma Allah ya taimakeshi da aiki mai kyau. Haka suka cigaba da zaman rufin asirin su yayin da Halima ta fara sana'ar saide-saide a cikin gida har Allah ya basu k'aruwa. *Wannan shine labarin Malan Sani.* ***** **** Washe gari bayan sun gama karyawa wajen k'arfe goma Malan Sani ya fita domin ya cika alk'awarin da yayi ma Alhaji Mai Wada. Tafiya yake yana tunanin dalilin da yasa Alhaji yake zaune a wannan unguwar, yasan dai duk wanda aka kawo aiki na Kwastam ana bashi wajen zama bare kuma shi da ya kasance shugaba, sai gashi yazo wannan unguwar ya zauna. Da wannan tunanin ya isa k'ofar gidan Alhaji Mai Wada. Yana kwankwasawa Maigadi ya bud'e. Bayan sun gaisa ya fad'a masa yazo wajen Alhaji ne. Murmushi Maigadin yayi yana fad'in Malan Sani ko? Kai ya d'aga yana mamakin yanda akayi har Alhaji ya fad'ama Maigadi zuwanshi. Wajen zama ya nuna mashi yana fad'in ai tun jiya Alhaji ya sanar dani zuwanka, shiyasa kana zuwa nayi tsammanin kaine, domin babu wanda yake ma Alhaji sallama da safe haka musamman irin wannan ranar da baya fita aiki da wuri. Malan Sani yace Allah sarki, ai da yake yau asabar ma'aikata kowa yana hutawa ba aiki. Maigadi yace gaskiya banda Alhaji, gobe ne kawai nasan baya fita wajen aiki, amma asabar yana fita sai dai bada wuri ba, sannan baya wuce magriba ya dawo gida sai ya wuce masallaci wajen da suke d'aukar karatun asabar da lahadi. Gyara zama Malan Sani yayi yana fad'in gaskiya ban tab'a ganin mutum irin Alhaji ba, a sanina duk wanda ya kai matsayi irin nashi musamman a aikin Kwastam gidan kud'i da wuya kaga yana rayuwa makamanciyar tashi, unguwar da yake zaune kad'ai abun mamaki ne, sai irin yanda yake rayuwa kuma. Maigadi yace indai Alhaji ne yanzu ka fara ganin abubuwan mamaki a wajensa, sam be d'auki duniya da zafi ba, mutum ne shi mai saukin kai, ga addini, kana ganin yawancin masu irin aikinsu yanda suke kasancewa musamman idan akace su kad'ai suka zonan ba tare da Iyalin su ba, sai kaga sun aikata abinda suka ga dama. Ka ganni nan tun farkon zuwan Alhaji garin nan Allah ya had'ani dashi, yazo unguwar nan yana neman gidan haya mai kyau shine naji wasu suna neman damfararsa, ina gefe sai banyi magana ba, asalima sai na tashi nabar wajen dan bana so su fahimci ina wajen kasan yanda rayuwar Lagos take yanzu zasu far maka. Bayan da suka gama shima kamar ya san mai suke nufi sai yace masu bara yaje ya dawo, ganin basu samu nasara ba sai suka wuce suka kyaleshi. Har yashiga mota yayi hanyar fita na tarbeshi, bayan ya fito na fad'a masa gaskiya abinda wad'an can mutanan suke da niyar yi masa. Murmushi yayi yace mani ai ya fahimcesu shiyasa ya kyalesu. Anan yake fad'a mani abinda yakeso, an bashi gida acan wajen aikinsu amma yafiso ya shigo cikin mutane ya zauna kafin ya gama gane komai na garin sai ya canza wajen zama. Jin haka yasa nayi masa jagora wajen mai wannan gidan, domin wani ne ya zauna daya tashi kuma bakowa ciki. Tunda ya samu gidan nine na tsaya aka gyara komai. Bayan da aka gama sai yake tambayata aikin da nakeyi, shine nake fad'a masa ina 'yar buga-buga ne dan bani da iyali, tunda nayi aure mata ta rasu wajen haihuwa acan garin mu shikenan na taho Lagos da zama saboda ban aje kowa ba. Jin haka yace kawai hankalinsa ya kwanta dani, idan na amince zanyi masa gadi zai rik'a biya na, amma da sharad'in duk ranar daya kamani da cin amanarsa saiyasa an kulle ni. Jin abinda yace jiki na rawa na amince, domin na samu wajen zama mai kyau, da zakaga inda nake rayuwa ada zaka tausaya mani, bacci kawai yake kaini wajen, da nayi asuba zan fice, sai gashi Allah ya kawo mani Alhaji ya taimakeni, shiyasa nake zaune dashi da gaskiya, yana da dad'in zama sosai, sam beda mugunta, yana kyautata mani, kullum sai ya bani kud'in siyen abinci kuma k'arshen wata ya bani albashi, hatta da mukullin cikin gidan ina dashi, domin duk bayan kwana biyu ina shiga ina gyarawa, d'akinshi ne kawai banda mukullinshi, kalli d'akin da nake zaune yanzu. Jinjina kai Malan Sani yayi yana fad'in gaskiya ka godema Allah, kuma kacigaba da rik'e gaskiya arayuwar ka, domin itace tasa ka kawo matsayin da kake ayanzu, shiyasa ake so duk inda mutum yake ya kasance mai gaskiya. Sai dai baka fad'a mani sunanka ba. Maigadi yace sunana *AMADU* amma anfi kirana da *MADU*. Malan Sani yace sannu Amadu suna mai dad'i. Fitowar Alhaji Mai Wada yasa sukayi saurin tashi. K'arasowa yayi da sauri yana murmushi. Bayan sun gama gaisawa yace lallai Malan Sani kana da cika alk'awari, shiyasa nace bara na leko naga ko kazo nasan Madu bazai kirani ba zaiyi tunanin ko ban tashi ba. Malan Sani yace ai tunda nace zan zo bazan sab'a alk'awari ba, gashi nazo muna ta fira da Madu ma. Alhaji yace bismilla kashigo. Kallon Madu yayi yana fad'in ina fatan dai ka karya? Madu yace ai tun d'azu naci k'osai da koko. Alhaji yace haka ake so, Malan Sani kashigo. Bayan sun sake gaisawa Alhaji ya kawo masa shayi da kyar Malam Sani yasha. Kallonshi Alhaji Mai Wada yayi yana fad'in Malan Sani nasan zakayi mamakin kiran da nake maka, ba wani abu bane yasa nace kazo illa abinda na gani jiya, tunda na ganka kawai naji ka kwanta mani, hakan yasa naji ina so nasan kad'an daga cikin labarin ka, domin ajiya naga wasu mutane sun biyo ka da kyar kasha. Jinjina kai Malan Sani yayi yana fad'in Alhaji wannan labarin ko Mata ta ban fad'amawa ba, domin tana da tsohon ciki, hakika ina cikin damuwa, kuma naji na yarda da kai zan iya fad'a maka koni waye...... Bayan ya gama bashi labarin asalinsa ya d'ora da fad'in, nayi kusan shekara ina aiki da kamfanin yin Fanta, kuma har lokacin nine nake tuk'a motarsu, da farko ban fahimci komai ba, a hankali na fara gano wani abu da suke aikatawa a kamfanin, kuma manajen wajen shine yake da alhakin yin komai, wata rana bayan na tashi daga aiki har nayi masu sallama na tafi sai na manta na sayi biredi na had'a da lemun da ake bamu na aje a mota ban d'auko ba, hakan yasa nayi saurin komawa domin na d'auko. Kasancewar kullum acan nake barin su Manaja da wasu daga cikin manyan yaranshi, sai su kai sha biyun dare basu tafi ba, ban tsaya bin ta wajen su ba kawai na wuce wajen mota domin na d'auki abinda na manta. Muryar d'aya daga cikinsu naji yana fad'in akwai kayan da aka kawo masu daga wajen John d'azu, wai daga waje ya shigo dasu kuma lafiya lau aka dubasu a bakin ruwa kuma aka wuto dasu, domin ya saki kud'i sosai shiyasa Kwastam d'in wajen basu binciki kayan ba, yanda naji yana fad'i wasu maganin shaye-shaye ne irin na kwalba kamar dai maganin tari, to irinsu ne ya shigo dasu sai dai kwalinsu na lemu ne irin na waje, idan ba an bud'e ba baza'a tab'a sanin ba lemun bane aciki, yana fad'in zasu samu kud'i sosai da kayan. Bayan ya gama fad'a masa sai naji Manaja yana fad'in ai sunyi magana da John zasu rik'a siyar da kayan ab'oye tunda kowa yasan harkar lemu sukeyi yan drugs bazasu saka idonsu akan kayan ba, yace zasu rik'a d'ora kayan had'e da katan d'in Fantar da muke d'auka muna kaiwa wajen da ake sara. Jin wannan abun sai hankalina ya tashi, domin nasan zanyi aiki ne da haramtacciyar abu aciki, alokaci sai na kasa rik'e firgici na har suka jiyo motsi, ganin sun taho zasu duba yasa nayi saurin bud'e mota na d'auko leda ta na fito ina kok'arin b'oye damuwata na fad'a masu mantuwa nayi. Ganin Manajan ya tsura mani ido yasa na d'an daburce, gashi dama Inyamuri ne, sai kawai ya matso kusa dani yana fad'in tun yaushe nake awajen? Ganin yanda hankalinsa ya tashi yasa nace zuwana kenan. Matsowa d'ayan yayi yana fad'in Manaja nima yanzu naji motsinshi da alama yanzu yazo. Kallona yayi yana fad'in ka tabbata babu abinda kaji? Kai na d'aga mashi ina fad'in babu abinda naji dan hankalina yana wajen kayana. Kai ya jinjina yace zaka iya tafiya. Bayan tafiya ta bansan abinda suka tattauna ba, ni dai haka na isa gida jikina babu kwari, rayuwata ina tsoron cin dukiyar data fito da haramun acikinta, musamman ace kasan abinda ake kullawa amma kacigaba da aiki a haka, nasan kona je na fad'ama 'yan drugs za'a iya samun masu karb'ar cin hanci a rufe maganar ni kuma na jawo ma kaina, hakan yasa na yanke shawarar barin aikin na nemi wani, duk da Matata tana da tsohon ciki amma naji aikin ya fitar mani, nasan yanda aiki yake da wahalar samu a Lagos, amma ya fiye mani na bar aikin da dai arik'a aikata b'arna dani kuma nasan komai. A waccan shekaran jiyar ina zuwa wajen aiki na samu takarda daga wajen Manaja ta sallamar aiki wai na manyanta da yawa sunfi son Matasa, gaba d'aya kud'in da suka bani na sallamata dubu talatin ne, ganin haka yasa nayi hamdala ga Allah, ban nuna masu komai ba mukayi sallama dasu, haka naje na siyo komai na abinci, domin nafison na aje abinci da na rike kud'i ahannu na, nasan har Matata ta haihu bamu da matsalar abinci, kud'i ne dai bani dasu a hannu, domin acikin kud'in nayi biyan bashi dan nasan banda aiki bare nace sai na kwashi albashi kafin na biyasu, hakan yasa na biya duk mai bina bashi saura nayi cefanan gida. Wallahi Alhaji ajiya da muka had'u bana maganin naira biyar a aljihu na, haka na bar gida ko kud'in cefane ban bayar ba, nasan dai akwai abinci shiyasa ban damu ba, sai gashi Allah yasa ka bani wad'an nan kud'in. Jinjina kai Alhaji yayi yana fad'in to amma su waye suka biyoka jiya? Malan Sani yace wallahi ban san su ba, kawai ina zaune bayan na gama neman aikin yi na rasa sai na zauna bayan nayi sallar isha'i ina jiran wani Alhaji da naji ance yana neman direba, na dad'e a wajen ina jiranshi amma bai dawo ba, ganin dare yayi nace bara na tafi yau na koma kozan dace. Kawai na taho sai had'uwa nayi da wasu Matasa suna kok'arin yin Lalata da wata yarinya sai ihu take yi, cikin azama nayi kansu ina kok'arin ceton ta, da kyar na kwaceta daga wajen su nasa ta gudu, ganin ta tafi yasa sukayo kaina d'auke da adduna, shine fa na gudo har Allah yasa muka had'u, sauki na d'aya akwai duhu babu wanda ya sheda fuskata bare naji tsoron sake had'uwa dasu. Kaji dalilin da yasa suka biyo ni. Jinjina kai Alhaji Mai Wada yayi yana fad'in lallai Malan Sani ka had'u da jarabawa, tabbas kai mutumin kirki ne, ba kowa ne namiji bane zaka samu wanda yake gudun tashin hankalin Iyalinsa ba, kayi kok'ari daka iya b'oye mata halin da kake ciki, kuma wannan abun da kayi shine akeson mutane surik'a aikatawa, matuk'ar ka gano ana aikata haramtaccen abu a wajen da kake samun na abinci abinda zai fi maka kayi kok'arin barin wajen, musamman idan kasan cewar ko ka fad'i gaskiya baza tayi aiki ba. Ina mai tabbatar maka da ace wad'annan mutanan sun gano cewar kaji su bazasu barka ba, dole su nemi rayuwar ka domin gudun kada ka tona masu asiri, da yawa yanzu ana aikata kasuwanci had'e da haramtacciyar harka, tun zuwana garin nan na gano abubuwan da suke gudana, kasan yanayin aikin mu, duk kayan da za'a shigo dasu hakkin mu ne mu tabbatar da nagartarsu kafin a wuce dasu, kasancewar gaskiya tayi k'aranci yasa mutanan mu suke son karb'ar cin hanci, domin mutane da yawa suna shigo da kaya ba bisa k'aida ba, wannan dalilin ne yasa suke sakin kud'i ga masu matattar zuciya acikin mu domin su samu kayansu su fito lafiya, tabbas k'asar mu bazata cigaba ba matuk'ar muna da irin wad'annan mutanen, nasan ni d'aya bazan iya gyara su ba, amma ga Allah na dogara, kamar yanda nayi rantsuwa zanyi aikina bisa gaskiya da amana to bazan gajiya ba, zanyi kok'ari wajen ganin na kare hakkin aikina, naci ta hanyar halak d'ina, kuma insha Allahu zanyi kok'ari wajen gano b'ara gurbi acikin yankina. Malan Sani yace hakika Alhaji kai d'in mai gaskiya ne, tun bayan zuwanka na fara jin labarin ka, duk da baka fara aikata komai ba amma naji wasu daga cikin manya sun fara tsoron kada ace kazo da wani abu daban ba kamar wanda ka canza ba, domin sun riga sun saba dashi, sam basu da wata matsala tun alokacin tsohon shugaban kwastam, tun lokacin da na fara jin magana akan ka nake tunanin ko dai Allah ya kawo mai gaskiya ne, duk wanda kaji ana yawan magana akanshi to akwai wani abu na daban agareshi. Alhaji Mai Wada yace wannan haka yake, hakika ina tsoron kaidin mutane, wannan aikin da nake son tabbatarwa yana da matuk'ar had'ari, domin duk wanda ya fito a zamanin nan yace yana son ya kauda b'arna to yasa aranshi zai iya mutuwa a kowane lokaci, domin su dai masu aikata b'arnar bazasu so wani ya dakatar dasu ba, domin ayanzu mutane sunfi sha'awar aikata haramun akan aikin halak, domin shed'an yariga ya gama da zuciyarsu, ya nuna masu hanyar haramun tafi kawo kud'i, shiyasa zaka iske kowa yanzu wannan hanyar yake bi sai dai fatan shiriya kawai. Ajiyar zuciya yayi ya kalli Malan Sani yana fad'in, naji labarin ka Malan Sani, kuma na yarda da kai sosai, zuciyata ta aminta da kai har naji dad'i daka fad'a mani mutumin da yake neman direba baka sameshi ba, ina ganin nine wanda Allah yayi ma zab'in ka shiyasa baka sameshi ba. Murmushi Malan Sani yayi domin yaji dad'in kalaman Alhaji Mai Wada, saboda tunda yaji labarinsa yaji yana son kasancewa dashi. Kamar daga sama yaji Alhaji Mai Wada yana fad'in idan bazaka damu ba Malan Sani inason ka kasance direba na, domin na yarda da kai, na dad'e ina neman wanda zai rik'a tuk'ani amma tsoro yasa na kasa samu har yanzu, kasan yanayin yanzu amana tayi k'aranci, amma samun ka ayanzu yasa zuciyata ta aminta da kai. Hamdala Malan Sani yayi yana fad'in ina matuk'ar godiya Alhaji, Allah maji rok'on bawansa, cikin rufin asirinsa ya kawo mani mafita tun kafin mai d'akina tasan halin da nake ciki, hakika naji dad'in samun wannan aikin, domin Mai d'akina zata iya haihuwa a kowa ne hali, ko yanzu akace ta haihu baza ayi gardama ba. Murmushi Alhaji yayi yana fad'in babu komai Malan Sani, abinda nake so kawai shine amana, Allah ya had'ani da maigadi nagari, na roki direba nagari gashi Allah ya bani, babu abinda zanyima Allah sai godiya. Dan haka inaso ranar litinin kazo ka fara aiki, kud'in albashinka ayanzu naira dubu talatin ne awata kafin zuwa gaba muga abinda za'a k'ara maka. Zaro ido Malan Sani yayi cike da farin ciki yake godiya, kallon Alhaji yayi yana fad'in na rasa bakin magana, ina d'aukar dubu sha biyar ada sai gashi yanzu Allah ya juya mani, ina dab da samun zuri'a sai gashi Allah ya kawo mani cigaba, nagode sosai Allah ya k'ara bud'i ya kuma bamu zaman lafiya. Alhaji zaiyi magana wayar Malan Sani tayi k'ara. Saurin d'auka yayi ganin sunan makwabcinsa ne. Bayan sun gaisa ya fad'a masa suna asibiti da matarsa tana nakuda shine matarsa tashiga ta fito da ita ya kaisu a motarsa. Saurin tashi yayi yana fad'in ganinan zuwa. Kallonshi Alhaji yayi yana fad'in ko haihuwar ce? Kai Malan Sani ya d'aga jiki asanyaye. Tashi Alhaji yayi yana fad'in bara na d'auko mukullin mota mu tafi tare. Sakin baki Malan Sani yayi yana kallonshi jin irin karamcin da yayi masa. Yana tsaye har ya fito suka nufi waje. Hannu Malan Sani ya mik'a yana fad'in Alhaji kawo na tuk'a mu. Murmushi Alhaji yayi yana fad'in haba yanzu ai baka cikin natsuwar ka, ka bari na tuk'a mu. Madu ne ya k'araso yana tambayarsu lafiya? Alhaji ne yayi masa bayani. Murmushi yayi yana masu fatan alkhairi. Haka suka fice Malan Sani sai addu'a yake Allah ya sauketa lafiya shima yaga kwanshi a duniya. Ur's. Nabeelert Lady🖋 [3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kudi ne, naira 200 kacal, MTN Card a wannan lambar... 08147669770, kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a lambar k'asa, idan kuma bank transfer ne ka tuntube ni a whatsapp ta wannan lambar 08028525263.* 0⃣5⃣ Tsaye suke a cikin asibitin, Malan Sani ya kasa zama duk yashiga damuwa, tsoronshi d'aya kada ya rasa Matarsa, gashi tun kafin suzo aka kawota tana nakuda har sunzo da kusan mintuna ashirin amma shiru. Alhaji Mai Wada ne ya dafashi yana fad'in addu'a zakayi mata Malan Sani, wannan damuwar bazata amfanar da komai ba, kai namiji ne ya kamata kasa dauriya aranka. Jinjina kai Malan Sani yayi yana fad'in nagode Alhaji. Fitowar wata ma'akaciyar asibitin ne yasa sukayi saurin matsawa wajenta. Bakinta a washe take tambayarsu sune suka kawo Halima? Da sauri Malan Sani ya amsa mata. Murmushi tayi tana fad'in Halima ta sauka lafiya Allah ya azurta ta da 'Diya mace, tasha wahala sakamakon dad'ewar da tayi bata haihu ba kuma gashi haihuwar faari, wannan shine ya jawo mata doguwar nakuda amma yanzu suna lafiya. Hamdala Malan Sani yayi yana mata godiya. Murmushi tayi tace ai bakomai, yanzu ana gyara ta idan aka kaita d'akin hutu zaku iya ganin ta. Hannu Alhaji Mai Wada yasa a aljihu ya ciro kud'i masu yawa ya bata yana fad'in ga tukuicin ki. Amsa tayi tana masa godiya ta wuce tana fad'in idan kun gama kuje wajen likita akwai maganar da zakuyi. Bayan da aka maida Halima d'akin hutu Malan Sani yaja Alhaji Mai Wada suka nufi d'akin. Sai murmushi yake yana kallon matarsa. Alhaji kuwa yarinyar ya d'auka ya tsura mata ido domin Allah yayi mata kyau tun tana jaririyarta, yana matuk'ar son mace amma Allah be bashi ba. Mika ma Malan Sani ita yayi yana fad'i kayi mata hud'u ba. Murmushi yayi yana fad'in Alhaji wannan yarinyar da namiji ne sunanka zan saka, domin had'uwata da kai akwai alkhairi acikinta. Murmushi Alhaji yayi yana fad'in bakomai a hakan ma nagode. Amsarta yayi nan take yayi mata hud'uba da *RUMAISA*, suna ne da Halima take matuk'ar so, tasha fad'in duk ranar data haifi mace wannan sunan za'asa. Ajeta yayi akusa da Halima yana fad'in Allah ya amsa addu'arki ya baki mace kuma ansa mata sunan da kike so wato *RUMAISA.* Murmushi tayi tana duk'ar da kai dan kunyar Alhaji take ji. Tare da Alhaji suka fita yace ya mik'ashi wajen aiki sai ya dawo da motar saboda d'aukar matarsa da Rumaisa. Sosai wannan abun yayi ma Malan Sani dad'i, haka yayi ta jera masa godiya kamar zaiyi kuka. Bayan ya kaishi Alhaji ya miko masa dubu goma yana fad'in ga wannan kasa a aljihun ka nasan zaka buk'ace su. Har k'asa Malan Sank yazo duk'awa da sauri Alhaji ya rik'osa yana fad'in daga yau kada ka sake yunkurin aikata hakan, ni ba kowa bane dan haka ka d'aukeni tamkar d'an uwanka. Jinjina kai Malan Sani yayi yana goge hawayen farin ciki yayi masa godiya yana fad'in anjima zan dawo na d'auke ka. Alhaji yace kada ka damu zan hau motar haya ka aje motar a wajenka saboda zirga-zirga, idan ka gama zuwa dare sai ka kawo mani. Rasa bakin magana Malan Sani yayi sai kawai ya fashe da kuka. Murmushi Alhaji yayi ya dafashi yana girgiza masa kai kafin ya shige ofis d'insa. Wannan abu da Alhaji yayi ma Malan Sani ba k'aramun dad'i yayi masa ba, yanaji aransa duk duniya baya da kamar Alhaji ayanzu, yasa aranshi zai iya bada ranshi akan Alhaji. Haka ya nufi kasuwa domin sayen abubuwan buk'ata kafin a sallame su. A ranar Malan Sani ya kira gidan su ya fad'a masu haihuwar, sosai sukaji dad'i domin abinda kowa yake fata ne. Nan aka turo wata Gwoggonta da 'Diyar Kawunta suka taho. Sai k'arfe d'aya kafin Malan Sani yaje amsar sallama. Anan likita yayi masa bayanin kada ya bari Halima ta sake d'aukar ciki yanzu saboda mahaifarta ta wahala akan wannan haihuwar, idan samu ne su bari kamar nan da shekara biyar kafin ta sake d'aukar ciki. Malan Sani yace to mungode likita, sai ku aunata domin abata abinda zaiyi dai-dai da jininta wanda zai hanata d'aukar cikin. Murmushi likita yayi yana fad'in ina son mutane irin ku masu saurin fahimta, bara na had'aka da wata ma'aikaciyar mu itace take kula da wannan b'angaren, Allah ya bada lafiya. Sallama Malan Sani yayi masa yana masa godiya. Haka suka tafi gida cike da farin ciki. Lokacin da suka isa har Jamila makwabciyarsu ta sauke ruwan wanka ta kammala girki. Sosai Halima taji dad'i, dama irin abinda take gudu kenan ace ta haihu babu kowa nata, sai gashi Allah ya bata makwabciya tagari. Sai dare Malan Sani ya maida ma Alhaji motarsa yana sake masa godiya. Alhaji Mai Wada yace haba bakomai, zuwa gobe kazo akwai abinda zaka amsa. Malan Sani yace nagode Allah ya kaimu. Sai tsakiyar dare Gwoggon Halima suka iso saboda basu taso da wuri ba, Malan Sani ne yaje ya d'auko su. Halima baki yaki rufuwa yau 'yan uwanta sunzo. Washe gari haka 'yan barka sukayi ta shigowa wad'an da suke mutunci dasu kasancewar unguwar ba laifi akwai hausawa, yaren ma akwai wad'an da suke mutunci. Sai da akayi azahar Malan Sani yaje gidan Alhaji dan baya so yaje ya tashesa. Malan Sani ya cika da mamakin kayan abinci da Alhaji ya bashi, sannan ya kawo kud'in rago ya bashi hada na cefanan suna wanda zasu ishe sa ya saya ma Halima kayan fitar suna. Yana hawayen farin ciki yashiga yimasa godiya. Tare da Madu suka d'auki kayan a mota shima yaje ganin jaririya. Bayan ya ganta sukayi sallama Malan Sani ya nufi kasuwa domin ya siyo ma Halima kaya ya k'aro ma Rumaisa kaya duk da sun sayi wasu sai da lokacin basu san abinda zasu haifa ba hakan yasa suka sayi na jinsi d'aya wanda mace da namiji duk zasu iya sawa. **** Ranar litinin tunda wuri Malan Sani ya isa gidan Alhaji bayan daya gama aje masu komai na buk'ata. Zama yayi wajen Madu suka shiga fira kafin Alhaji ya fito. Alhaji yana fitowa ya cika da mamakin ganin Malan Sani ganin har yazo shida yake da hidima. Tasowa sukayi gaba d'aya suna gaishe shi. Alhaji yace lafiya lau, Malan Sani ina masu jego? Malan Sani yace suna lafiya. Alhaji yace ai da ka bari sai gobe ka fara zuwa. Malan Sani yace haba Alhaji nida ba mace ba, na gama masu komai shiyasa na fito, nima bazanji dad'in zama agidan ba, nagode Allah da yasa na samu wannan aikin da yanzu haka zanyi ta gararan ba. Murmushi Alhaji yayi ya mik'a masa mukullin yana fad'in haka ne, gashi muje. Sallama suka yima Madu suka tafi. Malan Sani yayi mamaki ganin Alhaji ya zauna agaba, kasa daurewa yayi ya kalleshi yana fad'in Alhaji ai daka zauna a baya. Murmushi Alhaji yayi yana fad'in hakan ma yayi nafi buk'atar na zauna agaba. Murmushi Malan Sani yayi yana fad'in Alhaji kai na daban ne. Beyi magana ba yacigaba da duba wasu takardu. Lokacin da suka isa ofis mutane sunyi mamaki ganin Alhaji Mai Wada tare da wani, sai dai basuyi tunanin direba bane saboda sun ganshi agaban mota. Sai bayan da suka tsaya Malan Sani ya fito ya d'auko masa takardunsa yabi bayansa sukayi tunanin direba ne. Haka yayi ta gaisawa da mutanan wajen anan ya gabatar masu da Malan Sani amatsayin direbansa. Sunyi mamaki da jin haka domin sunyi tunanin acikin masu aikin wajen zai d'auki direba. Kai tsaye suka wuce ofis d'inshi, bayan ya aje masa takardu Alhaji yace Malan sani zaka iya tafiya idan ina da buk'atar wani abu zanyi maka waya tunda kana da hidima. Risnawa Malan Sani yayi yana fad'in nagode, mukullin motar ya d'ora masa saman teburi yana niyar barin ofis d'in. Sunanshi Alhaji yakira yana fad'in idan ka bar motar anan ai babu abinda zanyi da ita, kawai ka tafi da ita kayi abinda ya dace. Dawowa yayi ya d'auki mukullin yana sake masa godiya. Murmushi Alhaji yayi yana fad'in agaishe da Maijego. Fiya yayi yana murmushi yace zataji. Kwankwasa k'ofar akayi hakan yasa Alhaji ya bada izinin shigowa. Masinjansa ne yashigo yana gaishe sa. Alhaji yace *Malan Bala* katashi lafiya? Nashigo ban ganka ba nazo da sabon direbana naso in had'aku amma ya tafi. Risnawa Malan Bala yayi yana gaishe shi kafin yace na zagaya baya ina d'auraye tsumman dana goge ofis d'in ne, amma ai zai dawo ko? Alhaji yace zai dawo yaje gida ne matarsa ce ta haihu. Malan Bala yace masha Allah, Allah ya raya, gaskiya naji dad'i daka samu direba, domin wasu suna tunanin baka son ka d'auki direba saboda karik'a cinye kud'in da ake fidda masu. Murmushi Alhaji yayi yana fad'in hada kai acikin masu fad'in haka kenan? Zaro ido Malan Bala yayi yana fad'in haba dai Alhaji, kaima zaka mani shedar kirki ai, wallahi ko d'aya bana maka mugun zato, domin tun bayan zuwanka nan rayuwata ta canza, mezaisa na shiga cikin masu zagin ka? Jinjina kai Alhaji yayi yana fad'in wasa nake ma Malan Bala, kada ka damu da duk abinda mutane zasu fad'a akaina, domin idan kana biye ta mutane bazaka tab'a yin gaba ba, kai dai kasa Allah aranka. Malan Bala yace insha Allahu. A had'o maka shayin ne? Alhaji yace sai zuwa anjima nasha agida. Risnawa yayi yana fad'in ahuta lafiya. Yana kok'arin fita sai ga mataimakin Alhaji yashigo ofis d'in, gaishe sa Malan Bala yayi kafin ya fita. Hannu Adebayo ya mik'a ma Alhaji yana fad'in barka da safiya Sir, murmushi Alhaji yayi yana fad'in yauwa Mr. Adebayo ka tashi lafiya? Cikin harshen turanci ya maida mashi da lafiya lau, saboda Adebayo yafi son magana da turanci duk da yana jin hausa sosai, amma saboda bata zauna abakinsa ba yasa yafison yayi magana da turanci koda kuwa abokin maganarsa da hausa yake masa magana saboda yana jin hausa maidawarce take masa wahala. Zama yayi yana mik'a ma Alhaji wata takarda yana fad'in *Alhaji Marusa* babban mutumin nan mai shigo da kayan na'urori da sauran kayan masarufi na k'asar waje shine ya aiko da wannan takardar akan yana son sa hannunka saboda yana samun matsala da ma'aikatan mu akan kayansa, duk da kowa yasanshi yasan matsayinsa amma ana samun wasu daga cikin ma'aikatan mu suna rik'e masa kaya, wani lokacin kuma suna bincikar masa kaya suna b'ata masa lokaci har hakan ya kan jawo masa asara, kafin zuwanka Oga ne ya tsaya masa, domin kowa yasan irin matsayin daya taka ak'asar nan, to bayan tafiyar Oga sai ya fara samun matsala da mutane, duk da akwai wad'an da suke kular masa da kayanshi amma wannan karon sai da ya kira Oga yayi masa magana, shine ma Oga yakirani akan nazo kasa hannu domin ya zama sheda akan duk wasu kaya da za'a shigo dasu nashi ba sai an bincike su ba tunda ansan abinda yake shigowa dasu. Tunda ya fara magana Alhaji ya had'e hannu ya jingina da kujera yana kallonshi murmushi kwance a fuskarsa. Jin Alhaji yayi shiru bece komai ba yasa Adebayo yacigaba da fad'in Alhaji akwai babbar sallamar da muke samu daga Alhaji Marusa, sam beda rowa, yasan yanda muke masa mutunci shiyasa yake sakar mana kud'i, kuma munyi bincike babu abinda yake shigowa dashi wanda ya sab'a doka hakan yasa muka aminta dashi. Wannan karon k'aramar dariya Alhaji yayi ya gyara zamanshi yana fad'in Mr. Adebayo taya kasan cewar baya shigo da kayan da suka karya doka? Saurin kallon Alhaji Adebayo yayi yana motsa baki. Takardar Alhaji ya amsa yana fad'in idan har zamu iya sa hannu akan wasu surik'a shigo da kaya ba tare da an bincike su ba ina ganin babu amfanin gwamnati ta ajemu tana biyan mu anan, idan muka kyale wasu wad'an da muke kamawa kuma su basu da hakki akan mu? Mr. Adebayo ina so ka fahimci wani abu guda, duk abubuwan da suke faruwa ak'asar nan mune muke haifar dasu, idan muka rik'e aikin mu babu yanda za'ayi arik'a shigo mana da haramtattun kaya a k'asar mu, kana ganin k'asashen da suka cigaba sai dai ashigo da kaya marasa kyau ta b'arauniyar hanya, domin ma'aikatansu sun rike gaskiya, mu kuma sai muka banzatar da aikin mu muka rik'a barin ana shigo mana da kaya ta hanyar daya kamata ace mun tsare ta, sam masu aikata hakan basu da damuwar bin b'arauniyar hanya domin sun san mud'in kwad'ayayyu ne, da sun watsa mana tsaba sai mu saki hanya mu koma muna tsintar abinda suka watsa, su kuma sai su koma suna abinda suka ga dama, duk abubuwan da suke faruwa anan babu wanda ban sani ba, wasu tun kafin nazo wajen nan nake da masaniya akan su, wasu kuma bayan zuwa na na karance su, wannan dalilin ne yasa tunda nazo bance komai akan aiki ba, na zuba ido domin na gama karantar kowa, kuma daga yau ne aikina zai fara, wannan dalilin ne yasa na cireka daga bakin boarder domin ba aikin daya kamata kayi ba kakeyi. Wata takarda ya d'auko yana fad'in wannan sune sabon tsarin dana kawo, kuma yanzu nake jiran kashigo na fad'a maka k'arfe goma akwai taro domin kowa yaji sabon tsari, sai kuma gashi kazo mani da wannan maganar, dan haka ka fad'ama sauran ma'aikata sakona, ina fatan ka fahimce ni? Kai Adebayo ya jinjina zuciyarsa tana masa zafi, dama shi tunda Alhaji Mai Wada yazo haka kawai yaji baya sonshi, shiyasa yafi son akawo masu yaran su sunfi jin dad'in aiki dasu, amma idan aka kawo bahaushe musulmi da wuya ya basu goyon baya musamman idan mutumin bashida had'ama. Tashi yayi ya d'auki takardar da ya bama Alhaji yana fad'in shikenan zan koma ofis sai zuwa anjiman. Murmushi Alhaji yayi yana d'aga masa kai. Haka ya fita cike da jin haushi. Murmushi kawai Alhaji yayi yacigaba da aikin da yake gabansa. *** Cike d'akin taron yake da ma'aikatan wajen tun daga masu gadi, masinjoji har zuwa manyan ma'aikata. Bayan an bud'e taro da addu'a Alhaji Mai Wada ya bama Adebayo izinin yayi ma sauran 'yan uwansa jagoranci suyi tasu addu'ar. Bayan sun gama Alhaji ya bama Adebayo takardar yace yarik'a karantowa sai shi yayi bayani. Zuciyar Adebayo a cunkushe ya mik'e, sai dai da yake d'an duniya ne babu wanda zai iya fassara abinda yake a fuskarsa. Haka ya fara karanto sabon tsarin Alhaji yana bayani d'aya bayan d'aya. Gaba d'aya wajen kowa yayi shiru, masu jin dad'i sunayi masu jin haushi sunayi. Bayanin da Alhaji yayi na k'arshe yafi d'aga ma wasu hankali, musamman masu aikata irin laifin. Kallon mutanan wajen Alhaji Mai Wada yayi yana fad'in wannan dokar itace doka ta k'arshe acikin jerin dokokin dana rubuta, shiyasa na barta a k'arshe domin ba abu bane na wasa. Kamar yanda na fad'a zan sake maimaitawa, duk wanda aka kama da laifin karb'ar cin hanci daga wajen masu kaya za'a dakatar dashi har na wata ukku ba tare da albashi ba, idan aka maidoshi ya sake aikata hakan to kora ce, ba haka dokar take ba, nine na sassautata domin bana fatan na zamo wanda zaiyi silar korar wani daga wajen nan, domin bazanji dad'i ace nine silar katse mashi hanyar abincinsa ba, amma abinda nakeso daku shine ku daure ku bani had'in kai domin mu gyara tare, kowa yasan yanda yankin mu na nan garin Lagos yayi suna, domin mune manya, inaso na kawo cigaba, ba dole sai mun amshi cin hanci zamu samu kud'i ba, akwai mutanan da suke bada kyauta saboda kawai an tsare masu kaya sun sauka lafiya, dan haka kowa yayi kok'arin kiyayewa, insha Allahu zaku sameni mai adalci agare ku. Sai magana ta biyu, kowa ya tsaya a inda aka ajeshi, duk wanda kayansa suka iso zamu tsaya muyi binciken daya kamata kafin mu badasu, babu wani dalili da zaisa ace baza'a binciki kayan wani ba, komin matsayinsa, komin ikonsa matuk'ar kayansa suka iso dole a tabbatar da ingancinsu kafin a sake su, duk wanda muka kama da wannan laifin zai fuskanci hukunci, ku daure ku tsaya a binciki kaya, gara su dad'e ba'a sake su ba da muyi sauri mu saki kaya bayan akwai haramtattu aciki. Wannan shine iya sabon tsarin dana kawo, ina fatan kowa zai fahimceni, nasan wasu zasuji haushi, dama haka abun yake, dole sai anyi b'arna kafin ayi gyara, kuma sai an daure kafin a tsaida gaskiya, dan haka wanda beji dad'in wannan sabon tsarin ba ina mai bashi hak'uri haka aikin kwastam yake. Gaba d'aya wajen ya d'auki tafi, masu jin haushi ma haka suka daure suka tafa masa, Adebayo bazaka tab'a gane yanayin da yake ciki ba. Haka taro ya tashi kowa ya koma wajen aikinsa. Tsaye Adebayo da Umar suke a jikin mota, gaba d'aya fuskar Adebayo ta canza kala daga fari zuwa ja, zuk'ar sigari kawai yake kamar wanda zai hadi'ye bakinsa saboda b'acin rai. Dafashi Umar yayi cikin harshen hausa yake fad'in haba abokina kadena damun kanka akan wannan abun, kada kamanta an kawo wad'an da suka fishi tsanani ma amma cikin ruwan sanyi manyan k'asar suka sa aka canza masu wajen aiki, kasan dai wajen aikin mu babba ne, duk wani maiji da kud'i bazai so ace an kawo wanda zai rik'a bincikar kayansa ba, hakan yasa ba'a barin irin su Alhaji su dad'e anan, to ka kwantar da hankalin ka, babu wanda ya isa yazo ya kawo mana wani sabon tsari, yanda muka saba facaka da kud'i taya za'a zo lokaci guda akawo mana wani tsarin banza, kuyi magana da Alhaji Marusa koshi kad'ai ya isa yasa acanza masa wajen aiki. K'arasa zuk'e sigarinshi yayi kafin ya fara magana cikin harshen turanci"Haba Omar kaima kasan hankalina bazai tab'a kwanciya ba matuk'ar wannan mutumin yana wajen nan, gobe ne kayan Alhaji Marusa zasu iso, kuma kaima kasan akwai abinda za'a sako aciki, gashi wannan Alhajin ya kawo wannan dokar, ya kake tunanin idan ya kama wani abu acikin kayan? Gaskiya akwai matsala, zan kira Alhaji na fad'a masa kada kayan nan su taho gobe, ya jira zuwa nan da kwana biyu kafin su taho. Jinjina kai Umar yayi yana fad'in haka ne, kawai ka kirashi yanzu. Waya Adebayo ya ciro ya kira Alhaji Marusa, bayan ya d'aga Adebayo yace masa kada kayan nan su taho gobe. Alhaji Marusa yace yanzu nake da niyar kiran ka ai, d'azu muka gama magana da mutanan sunce cikin daren yau kayan zasu iso Lagos, kasan akwai kaya masu muhimmanci da tsada aciki, shiyasa nace zan kiraka naji ko Alhaji Mai Wada yasa hannu a wannan takardar? Adebayo yace akwai matsala fa Alhaji, komai ya b'aci, sabon tsari ya fito, wannan mutumin yazo da sabon tsari, yaki saka hannu a takardar, kuma yace dole a binciki kayan kowa, ina tsoron kada ace ya tsaya da dare idan ya samu labarin kaya zasu iso. Cike da tashin hankali Alhaji Marusa yace mene? Haba Adebayo, ya zakayi mani haka, kai da nace kayi kok'ari cikin dabara ka shawo mani kansa sai ka fad'a mani bai amince ba, yanzu gashi kaya sun taho, dole nasan abunyi. Umar ne ya amshi wayar yana fad'in Alhaji kawai kayi waya daga can sama kasa ayi kiranshi da dare, idan yaje sai su rik'eshi da magana har kayan su iso idan yaso sai acire abinda ya kamata abar sauran zuwa safiya idan yazo sai yasa hannu a amshi kayan. Shiru Alhaji Marusa yayi kafin yace maganar ka abun dubawa ce, ka kyaleshi bai isa ya sani cikin tashin hankali ba, zanyi magana da Mr. Kallah. Kashe wayar yayi yana fad'in ai na fad'a maka Alhaji Marusa bazai bari yayi asara ba. Ajiyar zuciya Adebayo yayi yana fad'in dole ma mutumin nan ya bar wajen nan. *** Bayan sallar magriba Alhaji Mai Wada ya samu sakon kayan Alhaji Marusa da suka taso. Bayan ya gama aikinsa saiga waya daga Mr. kallah akan yana nemansa k'arfe tara na dare. Cike da girmamawa Alhaji yace zai zo. Yana aje wayar yayi murmushi, tabbas hasashensa yayi dai-dai, dama irin wannan ranar yake jira. Dirowa ya jawo ya d'auko wani abu ya tashi yabar ofis d'in aranshi yana fad'in zanyi maganin ku. Ur's. Nabeelert Lady🖋[3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kudi ne, naira 200 kacal, MTN Card ta wannan lambar... 08147669770, kayi screen shoot ka tura a whatsapp ta lambar k'asa, idan kuma bank transfer ne ka tuntube ni a whatsapp ta wannan lambar. 08028525263.* 0⃣6⃣ Wata k'aramar kemara ya saka ta yanda zata d'aukar masa komai kafin ya koma ofis ya had'a kayansa ya fito. Da Adebayo yaci karo shima ya fito zai tafi. K'arasowa Adebayo yayi da sauri yana fad'in Sir, tafiya zakayi ne? Alhaji yace e na tashi. Adebayo yace amma ai direban bezo ba. Alhaji yace zan hau mota ne. Amsar takardun hannunshi Adebayo yayi yana fad'in haba Sir muje na ajeka. Alhaji yace ka barshi ba gida zanje ba Mr. Kallah ne yake nemana. Adebayo yace muje na ajeka kawai. Murmushi kawai Alhaji yayi ya bishi yana fad'in kaima har ka tashi ko? Adebayo yace bana jin dad'i zanje na kwanta. Mota suka shiga Alhaji yace amma dai ka duba masu aiki yau saboda ance kaya zasu zo. Adebayo yace munyi magana dasu kila cikin dare kayan zasu zo. Alhaji yace da kyau. Shiru sukayi har suka isa ya ajeshi yayi masa sallama. Sai wajen k'arfe shad'aya Mr. Kallah ya bar Alhaji Mai Wada domin yasan zuwa lokacin bazai iya komawa wajen aiki ba dole ya nufi gida, duk da yawancin firar labarin yanda tsarin aikin yake yake ta fad'a masa, tun Alhaji yana ganewa har ya gaji, sosai yake jin bacci. Direba Mr. Kallah yasa ya mik'a Alhaji gida, beyi musu ba domin shima baya buk'atar hawan motar haya. Kai tsaye gida yawuce, godiya yayi ma direba hada kud'i ya bashi kafin ya shige ciki. **** **** Washe gari da safe Malan Sani ya iso, alokacin har Alhaji ya shirya dan ya k'osa yaje yaga abinda ya faru. Bayan sun gaisa ya tambayi mai jego. Malan Sani yace lafiya lau ya gajiyar aiki? Alhaji yace akwai ta fa. Kud'i ya bama Madu kafin sukayi masa sallama suka tafi. Lokacin da suka isa Alhaji yace ya tafi da motar idan ya gama zai kirashi. Malan Sani yace Alhaji da ka barni na zauna anan ai. Murmushi Alhaji yayi yana fad'in nima zanso zamanka anan, amma saboda hidimar da take gaban ka gara ka tafi, idan akayi suna sai ka fara zama a wajen aiki. Murmushi Malan Sani yayi yana fad'in nagode. Kayansa ya d'auka ya bishi abaya zuwa ofis. Bayan sun gaisa da Malan Bala Alhaji ya gabatar da Malan Sani a wajenshi. Malan Bala yace gaskiya nayi farin ciki da zuwan ka, ya masu jego? Malan Sani yace lafiya lau suke ya aiki? Malan Bala yace gashinan munayi. Malan Sani yace Allah ya taimaka ni zan wuce. Alhaji yace shikenan sai kaji ni. Bayan da ma'aikata suka gama shigowa suka gaisa da Alhaji sai ga *Peter* wanda shine shugaban masu kula da kayan da ake saukewa. Bayan sun gaisa ya mik'a ma Alhaji takarda yana fad'in jiya wajen k'arfe 2:00 kayan Alhaji Marusa suka iso, na duba abinda ya samu sai muka sallame su kafin kazo ka gama dubawa. Jinjina kai Alhaji yayi yana fad'in bara na kammala aiki sai nazo na duba. Risnawa yayi ya juya ya fita. Shiru Alhaji yayi yana nazarin yanda zai b'ulloma Alhaji Marusa idan har ya kamashi da laifi acikin kayansa, domin yasan babban mutum ne, karo dashi bazaiyi kyau ba, amma dole ya tsaya domin ya tabbatar da gaskiya. Bayan daya gama komai yasa aka kira masa Adebayo, bayan ya iso suka fita tare da wasu ma'aikatan. Tunda suka isa Alhaji yasan an tab'a kayan, haka yasa aka fara bincika kayan, sai dai abun mamaki babu komai na laifi aciki. Adebayo yace ai na fad'a maka Alhaji Marusa baya shigo da kaya masara kyau. Murmushi Alhaji yayi yana fad'in bazan tabbatar ba sai na gama bincike. Adenayo yace bincike kuma? Na d'auka za agama komai abasu kayan su ai. Alhaji yace ka sani ko akwai haramtattun kaya aciki kafin muzo aka cire? Da sauri ya kalli Alhaji yana had'iyar miyau. Dafashi Alhaji yayi yana fad'in wasa nake maka, bayan yanzu muka gama dubawa kuma babu komai, amma dai zan sake bincike idan na tabbatar da komai lafiya sai abasu kayansu bayan sun gama biyan komai kamar yanda doka ta tanadar. Adebayo yace ai Alhaji Marusa baya kin biyan kud'in kaya, domin yasan yanda dokar take. Alhaji yace haka akeso ai. Cikin dabara Alhaji ya ciro abinda yasa kafin ya nufi ofis, mukulli yasa ya kulle ya fad'ama Malan Bala duk wanda yazo yajirashi zai shiga band'aki ne. Malan Bala yace angama Alhaji. Zaune yayi yana kallon abun mamaki, faskar Adebayo ya gani shida wasu ma'aikata hada Peter da yaran Alhaji Marusa suna ta aikin jidar wasu kwalaye wanda besan meye aciki ba. Lokaci ya duba yaga k'arfe 3:30 na dare. Mamaki yayi ganin duk saboda su cire wad'an nan kaya ne suke tsaye a cikin dare. Gaskiya duniya ba gaskiya. Bayan ya gama gani ya kashe dan ya baro (flash) d'insa agida bare ya tura aciki, dirowa ya jawo ya saka kemarar acikin jakarta kafin ya tashi tafiya. Tashi yayi ya bud'e k'ofar yana tambayar Malan Bala ko akwai wad'an da suka zo nemansa? Malan Bala yace Oga Adebayo yazo shida Umar. Alhaji yace kaje ka kirasu. Bayan sunzo Adebayo yace dama Alhaji Marusa ne yakira waya idan angama duba kayan yana buk'atar su. Alhaji yace bana tunanin bada kayan nan yanzu domin bangama yarda dasu ba. Kallonshi sukayi cike da mamaki. Alhaji yace akwai fararen kwalaye guda bakwai da akazo dasu wanda nasan da zuwansu sai gashi kuma ban gansu ba, kaga dole mu gano inda suke domin amana Alhaji Marusa ya bamu akan kayansa, yanzu idan yaji acikin kayan babu wasu bayan kuma anzo dasu har nan ai dole yashiga damuwa, kuma tunda naga sun b'ace na tabbatar suna da tsada da muhimmanci shiyasa akayi kokarin sace su, dan haka dole muyi bincike mu gano komai tun kafin Alhaji Marusa yasan da maganar, domin hakan zai iya tab'a aikin mu. Zufa ce ta fara keto masu jin abinda Alhaji ya fad'a. Adebayo ne yayi kok'arin fad'in gaskiya Sir, babu wasu kaya da suka b'ace, domin Alhaji ya fad'a mani duk abinda yake ciki, kuma na d'auki hoto na tura mashi yace komai haka yake, kila dai ba'a fad'a maka da kyau bane. Murmushi Alhaji yayi yana fad'in sai da na tabbatar kafin na fad'i haka, dan haka ka fad'ama Alhaji Marusa yayi hak'uri kayansa zasu iso zuwa wani lokaci akwai abinda ba'a gama ba. Umar yace Alhaji ni ina ganin tunda shi Alhajin yace haka kayansa suke kawai mu bashi, idan ba haka ba zamu jawo ma kan mu wajen son bincike. Alhaji yace tunda nine nace zanyi binciken kawai kuje. Fita sukayi jiki a sanyaye. Bayan sun koma ofis Adebayo yace ya akayi Sir, yasan da kwalayen da muka cire? Umar yace nima nayi mamaki, kodai wani munafukin ya fad'a masa ko cikin wad'an da mukayi aikin tare akwai wanda ya turo? Adebayo yace bana tunanin haka, dole akwai abinda yayi, domin duk cikin mutanan da mukayi aiki dasu kowa yana da amana, kuma kafin mu fara sai da na tabbatar babu kowa, dole akwai abinda yayi dai. Umar yace to yanzu ya za'ayi, kada fa ya tona ma Alhaji Marusa asiri ba k'aramun kunya zaiji ba domin kasan kayan da suke cikin kwalin, gashi babban mutum. Adebayo yace Omar bari nashiga tunani dole na gano abinda Sir, yayi, idan yana tunanin zai iya kama mu zamu gani, domin na buga da wanda yafishi. Dariya Umar yayi yana fad'in dad'ina da kai akwai basira, duk yanda aka k'ulle abu kana iya warwareshi, shikenan bara na barka kayi nazari. Bayan ya fita Adebayo ya kira Alhaji Marusa ya fad'a masa halin da ake ciki. Sosai hankalinsa ya tashi, nan yace ma Adebayo duk yanda zasuyi kada su bari asirinsa ya tonu, akwai kyauta mai tsoka matuk'ar suka kashe maganar. Adebayo yace angama Alhaji, kasanni akan kud'i bani da wasa, zan iya yin komai. **** Bayan la'asar Alhaji Mai Wada ya samu kira daga sama, Mr. Kallah ne ya kirashi yana tambayarsa abinda yasa basu sakar ma Alhaji Marusa kaya ba har yanzu? Alhaji yace Mr. Kallah akwai abinda na gani ne shiyasa nakeso ayi bincike kada mu bashi kayan bayan akwai cuta aciki. Mr. Kallah yace wace irin cuta? Ka ce da kai aka duba kayan kuma babu komai aciki taya yanzu zaka kawo wata magana, tsaya kaji Alhaji Mai Wada, baza kazo ka kawo mana matsala ba, kowa yasan yanda aikin nan yake, matuk'ar aka duba kaya babu matsala, kuma mai kaya ya biya komai abisa k'aida to dole ne abashi kayansa, dan haka na baka nan da awa d'aya ka sakar masa kayansa. Dafe kai Alhaji yayi yana fad'in Mr. Kallah ka tsaya nayi maka bayani, ana aikata binda bai dace ba, ana shigowa da kaya haramtattu idan bamu tsaya muka gyara ba tofa kan mu cutar zata dawo, domin idan ta tab'a yaran mu kamar ta tab'a mune, Allah kad'ai yasan abinda aka shigo dashi, ina da shedar da zan nuna maka ka tabbatar ina da gaskiya, kuma wallahi kaji na rantse komin girman Alhaji Marusa dole hukuma ta hukuntashi kuma sai tacisa tara, domin ya karya doka. Ajiyar zuciya Mr. Kallah yayi yana fad'in wace irin sheda kake da ita fad'a mani? Alhaji yace bazan fad'a maka yanzu ba, amma zan kawo maka ka gani da kan ka, kuma ba kai kad'ai zaka gani ba dole sai an had'a taron manya kafin na fito da shedar. Mr. Kallah yace shikenan Alhaji bazan hanaka aikin ka ba, wannan abun da kayi yana da kyau, nima na d'auka babu wata matsala a kayan shiyasa nashiga maganar bayan da Alhaji Marusa ya fad'a mani, amma tunda kaine shugaba a wajen bazamu hanaka aikin ka ba, domin irin ku k'asa take nema, bakomai Allah ya taimaka kayi aikin ka a natse. Murmushi Alhaji yayi yana fad'in nagode Yallab'ai. Bayan ya kashe wayar yayi shiru yana tunanin ashe dai Mr. Kallah mutumin kirki ne, ya d'auka shima yana goyan bayan su ne, tunda har ya bashi goyon baya dole a gobe ya mik'a abinda ya d'auka manya su gani kafin a mik'a Alhaji Marusa kotu domin acan ne za'a yanke masa hukunci dai-dai laifinsa, kuma dole ya fito da kayan da aka b'oye domin asan abinda yake ciki. Haka ya wuni yana aiki sallah kawai take fitar dashi, abinci ma anan Malan Bala ya kawo masa yaci. Har sukayi magriba kafin Malan Sani yazo ya d'aukeshi, sai da ya d'auki komai nashi hada kemarar kafin suka tafi. **** Washe gari tunda safe ya kira Adebayo akan ya kula da ofis bazai samu zuwa da wuri ba zaije wajen taro. Murmushi Adebayo yayi yace sai ka dawo Sir. Koda suka isa can babbar hedikwata haka Malan Sani ya koma gefe yana jiran Alhaji, kai tsaye Alhaji ya nufi hanyar shiga, yana dab da shiga wayarsa tayi k'ara. Yana dubawa yaga Mr. Kallah ne, saurin d'auka yayi. Bayan sun gaisa Mr. Kallah yace Alhaji Mai Wada ka sameni a ofis d'ina yanzu, akwai maganar da nakeso muyi dan ban fad'a masu zakazo a zauna ba. Alhaji yace shikenan gani nan zuwa. Mota yashiga suka nufi ofis d'in Mr. Kallah. Kallonshi Mr. Kallah yayi yana fad'in Alhaji Mai Wada nasan ka dad'e kana wannan aikin, kasan kuma yanda halin k'asar mu take, k'ananan mutane ma ka kalli yanda ake gogawa dasu bare kuma manya, nasan kasan kad'an daga cikin labarin Alhaji Marusa, babban mutum ne shi, bana so kaje kayi abinda zaisa mutuncinka ya ragu, kome zakayi ka tabbatar kana da kwakkwarar sheda kafin kayishi, ko kotu kaje idan baka da sheda kwakkwara kotu tana watsi da k'ara, ajiya ka fad'a mani kana da sheda akan abinda ka fad'a, nace ka fada mani amma kace sai kazo, gashi kuma baka fad'a mani ba amma kake kok'arin kai shedar gaban Manyan mu, wannan dalilin ne yasa ko ajiya daka kirani kace na fad'a masu zaka zo na amsa maka kawai, amma babu wanda na fad'ama wannan maganar, koshi Alhaji Marusan besan kana da wata sheda akanshi ba, shiyasa kaji nace kazo domin mu fara gano komai kafin mu mik'a maganar sama. Jinjina kai Alhaji yayi yana fad'in wannan gaskiya ne, ya kamata ace mun zauna mun had'a komai kafin afitar da maganar, domin ance idan baka iya kama b'arawo ba shi sai ya kamaka. Hannu yasa ya ciro kemara yana fad'in ajiya ma naso na tura a (flash) sai kuma bacci ya d'auke ni, da safe kuma na manta kawai na taho da ita. Kunnawa yayi ya mik'a ma Mr. Kallah yana fad'in tun lokacin dana samu labarin kayan zasu iso cikin dare nayi niyar tsayawa ayi komai agabana, sai kawai na samu kira daga wajenka, hakan ya b'ata mani rai, har nayi tunanin wani abu, to da zan tafi sai na mak'ala wannan kemarar domin ina zargin wani abu, washe gari dana zo aka duba kaya babu komai na laifi aciki, bayan dana koma na duba kemarar sai na gano ajiyan an cire wasu kaya kusan kwalaye bakwai wanda bansan abinda yake ciki ba, kuma na tabbata kaya ne marasa kyau aciki, gashinan ka duba zakaga abinda na gani. Murmushi Mr. Kallah yayi yana fad'in Alhaji ai banga komai aciki ba, duhu kawai nake gani babu komai aciki. Da sauri Alhaji ya mik'e ya amshi kemarar yana dubawa, ya duba ko ina amma babu abinda ya d'auka aciki sai wata d'auka da akayi ta kusan mintuna talatin amma kuma duhu ne aciki, lokaci ya duba sai yaga k'arfe 1:30 ne lokacin sallar azahar. Komawa yayi ya zauna jiki a sanyaye kamar an zare masa lakka. Kallonsa Mr. Kallah yayi yana fad'in kaga abinda nake fad'a maka ko? Yanzu da ace kaje agaban mutane ka gama wannan bayanin kazo kunna masu sukaga wannan abun ai zasuce kayi wasa da tunanin su ne, babu wanda ya tab'a kawo k'arar Alhaji Marusa, yanzu idan kaje ka kai kuma ka kasa kawo sheda me kake tunanin za'ace? Tun daga ranar za'a dena gazgataka, ko wata rana kazo da wata maganar bazasu d'auketa da muhimmanci ba. Jinjina kai Alhaji yayi yana fad'in nagode da wannan taimakon da kayi mani, insha Allahu dana koma zan sakar masa kayanshi. Mr. Kallah yace bakomai ka k'ara kiyayewa, aikin kwastam akwai had'i acikinsa. Tashi yayi ya bashi hannu kafin ya fita. Tunda suke tafiya yayi shiru, gaba d'aya kanshi ya d'aure, tabbas wani ne yashiga ofis d'insa ya goge abinda ya d'auka aka d'aukar masa wannan abun, amma *WAYE NE* (tsohon littafi na) yayi masa wannan abun? Babu wanda yasan ya d'auki wannan abun amma gashi an goge masa, da ace ya fad'ama Mr. Kallah yayi d'auka da sai ya zargeshi. Hannu yasa ya dafe kanshi. Tabbas maganar Mr. Kallah gaskiya ce, aikin kwastam akwai had'ari acikinsa, kuma ya godema Allah da bai kai wannan shedar ba, dole ya sake sabon taku, domin Lagos tasha ban-ban da sauran wajen da yayi aiki, Lagos shu'umin gari ne, k'aramin yaron daya taso acikinta ma sai yayi maka wayau. Malan Sani ne yace Alhaji kamar akwai abinda yake damun ka ko? Ajiyar zuciya yayi yana fad'in Malan Sani duniya babu gaskiya, son kud'i ya rufema mutane ido, zasu iya aikata komai akan kud'i, wani babban al'amari ne ya faru ajiya zuwa yau, amma na faad'i, domin ban samu damar aiwatar da aikina ba. Ai kasan Alhaji Marusa ko? Malan sani yace sosai kuwa, a Lagos waye bai sanshi ba........ Labarin abinda ya faru Alhaji ya bashi. Sosai Malan Sani ya tausaya mashi, kallonsa yayi yana fad'in Alhaji haka Lagos take, shiyasa nake tausayin bakon daya zo cikinta, mutane da yawa suna shan wahala idan suka zo Lagos kafin su waye da ita, haka idan aiki ya kawo ka nan matuk'ar baka da masaniya akan komai kana shan wahala, wasu sun sha rasa ransu akan aikin su, a tunani na dad'ewar da kayi kana aiki zaka iya aiki a Lagos, domin nasan ka zagaya garuruwa da yawa. Murmushi Alhaji yayi yana fad'in nima haka nayi tunani Malan Sani, ashe abun ba haka yake ba, duk yanda na d'auki Lagos ta wuce tunani na, shiyasa tunda nazo nake taka tsan-tsan da mutane, domin nasan yanda cin amana yayi yawa. Malan Sani yace Alhaji maganar gaskiya kada ka sake yarda da kowa, ni jikina ma be yarda da Mr. Kallah ba, tunda kace mani yace kaje nasan akwai wani abu, dole akwai abinda ya sani shiyasa ya kira ka domin baya so kaji kunya, sai yayi amfani da wannan damar domin yasa ka yarda dashi. Kallon Malan Sani Alhaji yayi cike da nazari. Kai Malan Sani ya jinjina kafin yacigaba da tuk'i yana fad'in Adebayo shu'umin mutum ne, kasan yaren mutum da kud'i, duk da bansanshi ba, amma labarinsa daka bani yanzu yasa na fahimceshi, bazan ce ga wanda nake zargi ya bada damar shiga ofis d'inka ba, domin nasan idan zakaje sallah dole ka rufe odis d'in ka, amma dole sai ka sake lura Alhaji. Jinjina kai Alhaji yayi yana fad'in nagose sosai Malan Sani, hakika Allah ya had'a ni da abokin shawara, na yarda da kai, kuma daga yau bani da abokin shawara sai kai, insha Allahu zanyi kamar yanda kace, da sannu sai na gano gaskiya kuma sai na tabbatar da ita, wallahi kaji na rantse maka sai na tabbatar da ainihin fuskar Alhaji Marusa, domin fuska biyu yake da ita, amma zan kwantar da kai domin na samu damar aiwatar da komai cikin sanyi. Malan Sani yace wannan haka yake, idan mage zata kama b'era kwantar da kai takeyi har sai ta cika burinta, dole sai kayi hak'uri kafin ka tabbatar da gaskiya. Alhaji yace nagode sosai. Bayan da ya ajeshi ya wuce ofis, sam be nuna komai ba, haka yakira Adebayo yace a saki kayan Alhaji Marusa. Risnawa yayi yana fad'in angama Sir. Bayan da ya dawo sallar azahar ya iske wasu mutane suna jiranshi. Izinin shiga ya basu. Bayan sun gama gaisawa d'aya daga cikinsu yace sunana Brr. Barau daga babbar kotu, wannan abokin aikina ne Brr. Hamza. Alhaji yace madalla sannun ku da zuwa, akwai wani abu da kuke buk'ata ne? Brr. Barau yace wani mutumi ne ya shigar da k'ara a kotu saboda wani zalunci da akayi masa, ya kasance yana shigo da taliya dasu makaroni da sabulai daga waje, yau kusan sati d'aya kenan kayansa suka iso, yace ya biya komai amma kuma da aka tashi sakar masa kayan sai aka bashi ba yanda suke ba, wanda hakan ya jawo masa asara sosai, shine yashigar da k'ara, da muka duba sai naga a wajen ku ne, kuma ni ina mutunci da ma'aikatan wajen nan, wanda ya bar wajen ma nine Lauya d'inshi, hakan yasa nace zanzo domin naji yanda gaskiyar abun take, domin mutumin ya d'auko lauya, ni kuma ina giramama ofis d'in ku shiyasa nace zan tsaya maku domin a wanke ku daga zargi, dan idan har akayi shari'ar aka tabbatar daga cikin ku wasu sun danne masa kaya tabbas mutuncin ku zai zube, gashi kai sabon zuwa ne a nan baka gama sanin komai ba, idan akace ma baka da labarin abinda ya faru baza'ayi gardama ba, domin an fad'a mani ajiya ne ka fara sabon tsari. Cike da mamaki Alhaji yake kallonsu, ak'asan ranshi yana fad'in kaji wata sabuwa kuma. Murmushi Brr. Barau yayi yana fad'in kada ka damu Alhaji, ni da ku babu wani shamaki domin akwai taimakekeniya atsakanin mu, tsofaffin ma'aikatan wajen sun san da haka, domin kowa ya sanni, dan kana sabon zuwa ne, amma shi Adebayo mutumina ne sosai, dan haka kada ka damu a shigar farko zan kada su, domin ni shari'a cin abinci ma yafi mani wahala akanta, domin ni haka nake, wasu ma da *MAI NASARA* suke kirana. (Tsohon littafina,) Murmushi Alhaji yayi danshi ya ma rasa bakin magana. Tashi Brr. Barau yayi yana fad'in kada ka damu, wannan itace takardar sammaci daga kotu, zuwa ranar litinin za'a shiga, sai kayi kokarin gano wad'an da suka aikata hakan idan baka da masaniya domin kaja masu kunne, zanyi magana da Adebayo sai mu k'arasa komai dan naga baka gama warware wa da wajen ba, gashi lokaci ya k'ure dole muyi sauri domin mu kare mutuncin ku, saboda kai d'in sabon zuwa ne bazamu so ka fara da haka ba. Kai Alhaji ya jinjina danshi gaba d'aya kanshi ya k'ulle, beda masaniya akan komai, bazai iya shiga abinda bai sani ba, dole ya zuba masu ido yaga abinda zasuyi dan shi yanzu yanda zai b'ullo ma Alhaji Marusa kawai yake damunsa. Hannu Brr. Barau ya bashi yana fad'in sai ka jini mungode da lokacin daka bamu. Alhaji yace bakomai nagode. Bayan sun fita Alhaji yashiga dogon tunani, tabbas lokacin da aka aikata wannan abun beda masaniya, yanzu shikenan haka za'a danne ma bawan Allah kayansa kuma kotu ta bashi rashin gaskiya? To idan ma yace zai taimaka mashi ta yaya? Dole wannan karon ya aikata laifi kodan kare mutuncin aikin su, amma matukar aka gama da kotu saiya gano wad'an da suka aikata wannan abun kuma sai ya d'auki mataki, dole yajira litinin yaje kotu yaji komai. Ur's. Nabeelert Lady🖋 [3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kudi ne, naira 200 kacal, MTN Card ta wannan lambar... 08147669770, kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a lambar k'asa, idan kuma bank transfer ne ka tuntube ni a whatsapp ta wannan lambar 08028525263.* 0⃣7⃣ Tafe suke a mota ya kalli Malan Sani yana fad'in wato Malan Sani idan kana da rai zakayi ta ganin abubuwan al'ajabi. Malan Sani yace wani abun akayi maka ko Alhaji? Murmushin gefen baki yayi yana fad'in maganar da mukayi da kai jiya itace ta rushe, an duba kemarar babu komai aciki, an samu wani mai wayon ya goge abinda ta d'auka. Kallonshi Malan Sani yayi cike da mamaki yana fad'in amma Alhaji ya akayi haka ta faru? Alhaji yace mai son abunka yafika dabara ai, naje sallar azahar lokacin ne aka shiga ofis d'ina. Malan Sani yace ina Malan Bala to? Alhaji yace atare muka je masallaci dashi kum na rufe ofis d'in. Jinjina kai Malan Sani yayi yana fad'in lallai ko waye ya san takan ofis d'in. Alhaji yace ko waye yayima kansa, kuma insha Allahu matuk'ar ina raye sai na kawo k'arshen zaluncin da akeyi. Yanzu haka ranar litinin kotu zamuje, d'azu wani Brr. Barau yazo ya kawo mani takardar sammaci wai an zalunci wani ya shigar da k'ara, kayansa ne sukazo sai aka rik'e, bayan daya amsa sai ya samu abubuwa da yawa sun b'ata, yayi asara sosai shine yashigar da k'ara, abinda na lura dashi Brr. Barau ya dad'e yana ma ofis d'in mu aiki, da alama shid'in marar gaskiya ne. Murmushi Malan Sani yayi yana fad'in Alhaji waye besan Brr. Barau ba, wannan mutumin idan beyi wasa ba sai yaci wutar Allah, duk wata k'ara da aka kaita babbar kotu matuk'ar mutum ya saki kud'i Brr. Barau zai tsaya masa, kafin a kadashi a shari'a da wuya, shi kuma Alkali kwakkwarar sheda yake nema, matuk'ar ya sameta shikenan zai yanke hukunci, wannan adalci da Alkali yakeyi shine yasa mutane suke sonshi, duk da wani lokacin ba akan gaskiya yake yanke hukuncin ba amma babu yanda ya iya, domin abinda ya gani dashi yake aiki, kuma baya yanke hukunci sai kowa ya sheda gaskiyar abinda aka gabatar, shiyasa nake fad'a maka Brr. Barau shine babban azzalumi. Alhaji yace abinda yake fad'a mani kenan da yazo, wai ni sabon zuwa ne shiyasa yazo da kanshi dan baya so daga zuwana na samu matsala, shiyasa yake so ya wanke mu. Girgiza kai yayi yana fad'in Malan Sani a wannan karon bani da zab'i, domin lokaci ya kure mani, idan nace bazan bi yanda yace ba tabbas nine a k'asa, domin bansan da wannan maganar ba sai zuwanshi. Tausayi Alhaji ya ba Malan Sani, domin yasan yana son tabbatar da gaskiya amma be gama sanin kan wajen ba. Kallonsa yayi yana fad'in Alhaji kada ka karaya domin Allah yana tare da mai gaskiya, bakomai kaje kotun kaji yanda komai yake Allah yaga zuciyar ka, idan yaso daga baya sai kayi bincike. Murmushin jin dad'i Alhaji yayi yana fad'in nagode Malan Sani, ina matuk'ar jin dad'in zamanka akusa dani, insha Allahu zanyi kok'arin bincike domin na gano gaskiya, kila ta wannan hanyar ne Allah zai haska mani komai. Malan Sani yace in Allah ya yarda. ***** **** Ranar litinin haka babbar kotu ta cika, *Alhaji Usman* wanda shine ya shigar da k'ara yana daga gefe shida sauran abokansa tare da lauyen daya d'auko. Alhaji Maiwada yana isowa Brr. Barau da Adebayo suka tarbeshi. Bayan sun gaisa Brr. Barau yace Alhaji komai ya kammala insha Allahu zamuyi nasara. Murmushin takaici Alhaji yayi yace Brr. Allah ya shige mana gaba. Brr. Barau yace amin. Cikin lokaci k'ank'ani aka kammala shari'ar wanda Brr. Barau ne yayi nasara, domin ya gabatar da shedun bogi wanda kowa ya d'auka da gaske ne. Alhaji Usman kusan zubewa yayi lokacin da Alkali ya yanke hukunci, zama yayi ana ta yimasa fifitu. Alhaji Maiwada yana zaune kamar wanda aka dasa, besan lokacin da idonshi ya cika da kwalla ba, lallai duniya babu gaskiya, yanzu shikenan an cuci wannan mutumin? Kallon Brr. Barau yayi yaga suna kashewa da su Umar da Adebayo. Murmushin takaici kawai yayi ya bar kotun ko ta kan Brr. Barau bebi ba suka tafi ranshi a b'ace. **** Ranar Talata tunda safe Alhaji yaje ofis. Malan Sani shima be tafi ba saboda anyi suna, tunda yazo suke zaune da Malan Bala suna ta fira, a hankali Malan Sani yake tambayar Malan Bala yanda wajen yake. Haka Malan Bala yayi ta bashi labari. Har zuwa azahar Alhaji yana bincike akan abinda ya faru, wasu daga cikin ma'aikatan da ya yarda dasu yarik'a kira yana masu tambayoyi tun daga ranar da abun ya faru. Mutum d'aya ya samu mai suna *Abubakar*, shine mataimakin mai kula da kaya, kasancewar shima yana kwatanta gaskiya yasa ake maidashi baya tun lokacin tsohon shugabansu, musamman idan akace kaya masu tsoka sunzo. Kallon shi Alhaji yayi yana fad'in Abubakar aranar da kayan Alhaji Usman suka zo ya akayi da aka rike masa wasu daga ciki suka b'ace? Gyara zama Abubakar yayi yana fad'in wallahi Alhaji aranar da abun zai faru Adebayo da Umar ne suka karb'i kayan, ina wajen amma sai Adebayo ya bani sako na kaima Alhaji Marusa, ban dawo ba saboda dare yayi sai kawai na wuce gida. Jinjina kai Alhaji yayi yana fad'in dole sune suka d'auki kayan Alhaji Usman. Abubakar yace kuma sun amshi kud'i da yawa awajenshi kafin suka sakar masa kaya, kuma ina tunanin kayan nan basu raba su ba, dole akwai inda suka aje su, akwai *Moses* abokina ne yasan sirrinsu domin suna yaga masa wani abu saboda sun san halinsa, ina ganin zai iya sanin yanda akayi da kayan. Alhaji yace Abubakar kira mani shi Allah yasa ya bamu had'in kai. Abubakar yace kada ka damu nasan waye Moses, mutumina ne sosai. Waya ya dauka ya kirashi. Beyi mintuna biyar ba sai gashi. Risnawa yayi ya gaishe da Alhaji. Wajen zama Alhaji ya nuna masa, bayan ya zauna Abubakar yayi masa bayanin abinda Alhaji yake buk'ata. Murmushi Moses yayi yana fad'in Sir, wannan abu ai ya dad'e yana faruwa a wajen nan, tun lokacin da nazo Oga John yake abinda yaga dama shida su Oga Adebayo, Omar shima baya da gaskiya, saboda sun san nasan komai yasa suke yaga mani kasona, Sir kasan zuciya da kud'i shiyasa nima nake amsa, amma wancan ranar da suka sace kayan Alaji Osman ni nasan inda suka b'oyesu, sunce sai anyi kamar wata d'aya ko biyu komai ya wuce sai suzo cikin dare su kwashe abunsu su raba, acikinsu akwai wasu ma'aikatan da suke bin bayan su. Sir ina fad'a maka a wajen nan fa akwai b'arayi, ni dai bana sata, amma idan aka bani ina amsa Alhaji yace yanzu Moses a ina suka aje kayan? Moses yace Sir, zan fad'a maka amma du Allah kada ka beri su gano nine na fad'a maka, ina son kud'i kuma idan suka gano bazasu rik'a bani ba. Murmushi Alhaji yayi yana fad'in zan rubuta sunanka acikin wad'an da zan dakatar har na tsawon watanni biyu kuwa, domin kana amsar cin hanci wata rana zaka fara d'aukar kayan wasu. Zubewa Moses yayi yana fad'in du Allah Alaji ka rufa mani asiri, wallayi daga yau zan zama kamar Abubakar, zan rikayin gaskiya. Alhaji yace naji, amma idan na gano kacigaba da karb'ar cin hanci sai na dakatar da kai. Tashi Moses yayi yana murza hannu yace na yarda. Nan ya fad'a masu inda kayan suke. Jinjina kai Alhaji yayi yace suje. Bayan sun fita yayi shiru yana tunanin yanda zai b'ullo ma al'amarin, baya so ya watsa ma Brr. Barau k'asa a ido, domin idan yace zai bayyanar da gaskiya tamkar yaci masa fuska ne, amma dole ya hukunta duk wanda yake dasa hannu a cikin wannan abun. Waya ya d'auka yakira Adebayo. Ba'afi mintuna biyar ba sai gashi ya shigo yana ladabin munafurci. Murmushi Alhaji yayi yana fad'in Adebayo na samo inda kayan Alhaji Usman suke, kuma za'a mayar masa da abunsa. A zabure Adebayo ya mik'e yana fad'in Sir, waye ya fad'a maka inda suke? Alhaji yace kasan b'oyesu akayi kenan? Zama yayi jiki a sanyaye yana fad'in Sir, ba haka bane, naga an gama komai a kotu be kamata amaido maganar baya ba. Tashi Alhaji yayi yana fad'in na baka nan da anjima ka rubuto mani sunayen wad'an da suke dasa hannu a abinda kukayi, a sunan farko kasa naka dana Umar. Hannu Adebayo yasa yana goge zufa, hannuwa yahad'e yana fad'in Sir, kayi hak'uri, shikenan zan fito da kayan amma kada a koma kotu domin zamu iya rasa aikin mu kuma za'a iya kaimu gidan yari. Alhaji yace abu d'aya zakayi, matuk'ar ka rubuta mani sunayen wad'an da suke dasa hannu a abinda kukayi to bazan kai ku kotu ba, amma ina da sharad'i wanda dole ne ku bishi. Da sauri Adebayo yace yanzu zan fad'a maka, mu biyar ne hada Omar, kuma zamubi sharad'in ka. Jinjina kai Alhaji yayi yana fad'in doka zata fara aiki daga kanku, sai dai zan maku sauki zan dakatar da ku na wata d'aya kawai, sannan zanyi magana da Alhaji Usman, idan ya yafe maku shikenan, idan kuma yace sai an koma kotu bani da zab'i. Cike da damuwa Adebayo yace ka bashi hak'uri kayansa suna nan babu abinda muka tab'a amma kada a koma kotu. Alhaji yace tashi kaje zamuyi magana dashi. Jiki a sanyaye Adebayo ya fita. Bayan ya fita Alhaji ya d'auki waya ya kira Alhaji Usman domin ya samo lambarsa. Koda ya d'auki wayar ya gane har lokacin yana cikin damuwa. Bayan sun gaisa yayi masa bayanin kansa, cike da masifa Alhaji Usman ya fara magana, sai da ya gama Alhaji yace idan zaka yarda ina son ganinka amma agida, domin maganace akan kayanka dana gano, amma inaso kayi shiru kada ka fad'ama kowa. Cike da farin ciki Alhaji Usman yace kayi hakuri ban fahimceka daga farko ba, shikenan zaka iya zuwa anjima bayan sallar isha'i. Alhaji yace shikenan ka turo mani da kwatancen gidan ka. Sallama sukayi ya kashe wayar. *** Bayan sallar la'asar su Umar da sauran mutane ukkun da Adebayo ya rubuta sunan su suka hallara ofis d'in Alhaji. Bayan ya gama masu bayani duk suka shiga bashi hak'uri. Alhaji yace bana magana biyu, kunci sa'a da na rage maku wata biyu, sannan zanyi kok'arin kare mutuncin aikin ku, amma daga yau idan na sake kama ku da aikata makamancin wannan abun to maganar sai taje sama. Idan kunso zaku iya tona asirin ku, amma ni dai babu wanda zan fad'a mawa, kuma bazan dakatar da albashin ku ba domin daga banki yake zuwa, matuk'ar nace zanje adakatar dashi dole sai manya sun san da maganar, amma ni zan yanka ma kowa abinda zai bayar a bama Alhaji Usman amatsayin tara, domin wannan shine adalci, kuma baza ku zo aiki ba har sai nan da wata d'aya, sannan kowa acikin ku zai bayar da dubu hamsin ga Alhaji Usman domin kun jawo masa asara, ko ya amshi kayanshi wasu kud'in bazasu dawo ba, idan kuma kuna ganin wannan abun beyi maku ba, shikenan sai muje kotu ta yanke maku hukunci. Gaba d'aya suka had'a baki wajen fad'in sun amince. Murmushi Alhaji yayi yana fad'in da kyau, daga yau ba sai kun sake zuwa aiki ba, kowa yaje ya huta. Adebayo yace Sir, ka barmu muzo aiki wasu zasu iya gano wani abu. Umar yace dan Allah Alhaji ka rufa mana asiri abarmu muyi aiki sannan zamu bayar da kud'in. Jinjina kai Alhaji yayi yana fad'in shikenan, tunda wannan shine karo na farko dana fara kama ku da laifi zanyi maku uzuri, amma akan biyan kud'i babu uzuri, sannan zan rubuta na ba kowa yasa hannu akan duk lokacin da aka sake kamaku da irin haka babu sauran uzuri. Gaba d'ayansu suka amsa da sun amince. Bayan da suka gama sa hannu akan kowa zai bayar da kud'in kuma sun amince da lifin da aka kamasu dashi. Haka kowa ya fita jiki a sanyaye. Adebayo da Umar waje suka samu kowa da abinda yake fad'a. Adebayo yace Omar wannan mutumin sai yasan yayi mana haka, Brr. Barau zan kira na fad'a masa komai. Umar yace kada ka fad'a masa, kasan Brr. Barau da surutu zai iya fitar da maganar, tunda dai Allah yaso Alhaji zai rufa mana asiri to mu bar maganar. Adebayo yace shikenan, amma wallayi sai na rama kasanni ai. Umar yace ba yanzu ba, dole mu kwantar da kai har zuwa wani lokaci. Adebayo yace shikenan. *** Bayan da akayi sallar isha'i Alhaji ya tashi domin yana son zuwa wajen Alhaji Usman. Haka suka nufi gidanshi suna bin kwatancen da ya turo masa. Malan Sani yayi mamakin abinda Alhaji ya fad'a masa, kuma ya jinjina adalcin da Alhaji yayi masu. Zaune suke a cikin rumfar da take a harabar gidan. Bayan sun gama gaisawa Alhaji ya sake bama Alhaji Usman hak'uri akan rashin adalcin da akayi masa. Alhaji Usman yace bakomai, nima ina baka hak'uri akan abinda nayi maka awaya, duk da nasan kai d'in sabon zuwa ne amma nayi tunanin kaima irin halin tsohon shugaba gare ka, domin daga zuwanka har na fara asarar kaya. Alhaji yace bakomai, domin ni bansan da maganar ba sai da Brr. Barau yazo mani da maganar, alokacin bani da abinda zanyi hakan yasa nayi shiru da niyar nayi bincike bayan an gama komai. Alhamdulillahi kayan ka suna nan babu wanda ya b'ace, kuma na gano wad'an da suka aikata hakan. Alhaji Usman yace acikin su akwai Adebayo. Murmushi Alhaji yayi yana fad'in kaima kasan halinsa kenan? Alhaji Usman yace waye besan Adebayo ba, dashi da Mr. John halinsu d'aya, shegu arnan banza, babu Allah aransu sai cuta. Alhaji yace nazo neman wata alfarma awajenka ne Alhaji, nasan zeyi wuya kayi mani ita, amma ina rokon ka da ka dubi girman Allah ka amince da abinda zan fad'a maka. Alhaji Usman yace babu abinda zaka nema awajena banyi maka shi ba, domin kayi mani abinda Kotu ta kasa tayi mani, dan haka kayi maganar ka kawai..... Bayanin abinda yake so yayi masa. Shiru Alhaji Usman yayi kafin can yayi murmushi yace saboda kai zanyi masu wannan alfarmar, domin ko alahira wani yana cin arzik'in wani, bakomai, ka d'auka baka fad'a mani komai ba, nayi maka alk'awarin babu wanda zaisan da faruwar haka, zan nuna cewar wasu kayan ne sukazo. Murmushi Alhaji yayi yana fad'in nagode sosai Alhaji Usman Allah ya k'ara girma. Alhaji Usman yace amin nagode, kuma acikin kud'in da zasu had'a dubu d'ari biyu da hamsin ka d'auki dubu d'ari na baka kyauta. Girgiza kai Alhaji yayi yana fad'in hakkina ne nayi maka hakan, bana buk'atar komai. Alhaji Usman yace nima kyauta ce nayi maka ai. Alhaji yace Allah bazan amsa ba. Alhaji Usman yace shikenan na bama direban ka, domin nasan irin halinka gareshi. Alhaji yace to mungode sosai, anjima kad'an kayanka zasu iso. Alhaji Usman yace nagode. **** Tun daga wannan rana Alhaji Maiwada yake aikinsa hankali kwance, kowa yashiga hankalinsa domin sun san Alhaji Maiwada ba wasa. Adebayo da Umar sun natsu tamkar babu su a wajen, su kad'ai sukasan abinda suke kullawa. A yanzu duk wani wanda yake samun matsala da ma'aikatan kwastam na wajen su Adebayo yanzu hankalinsa akwance yake, domin idan kaya suka iso cikin lokaci k'ank'ani za'a duba a cike komai bisa tsari a sakar maka kayanka idan babu haramtattun kaya aciki. Duk wanda aka kama da haramtattun kaya aciki babu batun ya bada cin hanci asakar masa, idan aka kama shikenan baza'a badasu ba. Alhaji Marusa yanzu ya dakatar da shigo da kayan da yake shigowa dasu, domin sun tattauna akan Alhaji Maiwada, sun yanke shawarar su d'aga masa k'afa zuwa wani lokaci ya gama zafin kanshi. Kafin wani lokaci Alhaji Maiwada yayi suna a Lagos musamman a wajen wad'an da suke jin dad'in zuwansa. Duk bayan wata yake zuwa Kano ganin iyalinsa. Alokacin Ra'eez yana aji ukku a primary, Alhaji yace zai maidasu Lagos saboda ya kusa kammala gininsa. Nan Ummun Ra'eez ta nuna ya bari Ra'eez ya kammala firmare kada a lalata masa karatu. Alhaji yace shikenan Allah ya kaimu, kafin lokacin ma na kammala gini na, bara naje muyi maganar da Alhaji Mansur kada yaji maganar daga sama. Lokacin daya fad'ama Alhaji Mansur yana so ya mai da Iyalinsa Lagos sai Alhaji Mansur yace wannan yana da kyau, bazai yuwu kayi ta zama babu mata akusa da kai ba, kasan yanda zuciya take, duk yanda muka kai da sabawa dole muyi hak'uri, amma kuma zumuncin mu yana nan, amma nafi so Ra'eez yayi makarantar kwana anan Kano, haka kawai bana so yaje yashiga cikin arnan nan, kaga anan akwai karatun addini a makarantar da nakeso na samar masu shida Labiba. Murmushi Alhaji yayi yana fad'in wannan ai bakomai, Ra'eez 'Danka ne, duk abinda ka yanke akanshi yayi, nima ina masa kwad'ayin samun ilimin addini mai zurfi domin Kano dabance a wajen ilimin addini. Alhaji Mansur yace to nagode. **** *** Kwanci tashi ba wuya a wajen Allah Alhaji ya kammala gininshi, yayin da yasa Malan Sani ya sayar da gidanshi ya cika masa ya sayi wani gidan ya canza unguwa, yaso ya sama masa gida a unguwar da yayi gini amma babu gida mai k'aramin kud'i, hakan yasa ya saya masa a unguwa dai-dai kud'insa, sai dai tafi waccan unguwar da suke. Sosai Malan Sani yaji dad'in abinda Alhaji yayi masa. Matarsa Halima tafishi jin dad'i, domin tunda taga Rumaisa tayi wayau kyanta sai fitowa yake ta fara tsorata da unguwarsu, domin unguwace ta marasa tarbiya, shiyasa har lokacin shigarta makaranta yayi Halima bata yarda ansata ba, lokacin da taji zasu tashi hada kukan farin ciki tayi, duk da zata rabu da makwabciyarta mai kirki. Yanzu tsakanin Malan Sani da Alhaji yanda kasan 'yan uwa, d'aya baya zartar da abu ba tare da shawarar d'aya ba, akwai girmamawa sosai atsakaninsu, Malan Sani bai tab'a tsallake maganar Alhaji ba amatsayinsa na direbanshi, duk da Alhaji ya sakar masa komai amma baya masa almubazzaranci. Haka Alhaji da kanshi ya saka Rumaisa makarantar kud'i mai sauki, kuma shine ya d'auki nauyin karatun ta. A wajen aikinsa kuwa yana kokarin adalci ga na k'asa dashi, sai dai yana samun damuwa daga na sama dashi, yasha kama kaya amma ya samu sako akan ya sake su, wani lokacin kuma a hanashi ya duba kayan, sosai wannan abun yake damunsa. *** Bayan shekaru biyu Ra'eez ya kammala makaranta, haka Alhaji yaje akayi taron yayesu. Bayan kwana biyu sukayi sallama dasu Alhaji Mansur zasu tafi hada Ra'eez kafin jarabawarsu ta fito. Ummun Ra'eez da Matar Alhaji Mansur hada kukan rabuwa. Haka suka d'aga zuwa Lagos cike da kewar babbar aminiyarta. Ur's. Nabeelert Lady🖋[3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kudi ne, naira 200 kacal, MTN Card ta wannan lambar... 08147669770, kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a lambar k'asa, idan kuma bank transfer zakayi ka tuntube ni a whatsapp ta wannan lambar. 08028525263.* 0⃣8⃣ *SURELERE* itace unguwar da suka koma, gida ne mai kyan gaske, domin Alhaji ya dad'e yana ginashi ta yanda zaiji dad'in rayuwa da Iyalinsa, acewarsa beda wasu dangi da suka wuce Iyalinsa, shiyasa ya tsara gida mai kyau saboda suji dad'in rayuwa aciki. Tunda Ummun Ra'eez taga gidan taji ya burgeta, sosai tayi farin ciki da wannan gida. Ra'eez sai murna yake sun dawo gida mai kyau. 'Dakinshi daban babu abinda ba'asa mashi ba. Haka d'akin Ummunsa komai akwai aciki, jitake kamar wata sabuwar amarya, saboda farin ciki rungume Alhaji tayi hada kukan farin ciki. Murmushi yayi yana shafa bayanta yace haba Ummun Ra'eez, meyasa zaki rik'a kuka haka? Hannu tasa ta share hawayenta tana fad'in Abbun Ra'eez dole nayi kukan farin ciki, ban tab'a tunanin kasancewa a irin wannan gidan ba, duk da gidan ka na Kano yana da kyau amma wannan daban ne, ginin zamani ne had'e da kayan zamani aciki, unguwar kad'ai abun kallo ce, bansan da wane baki zan gode maka ba. Rungumeta ya sakeyi yana fad'in bana buk'atar godiyar ki Bilkisu, addu'arki kad'ai nake buk'ata, domin kinsan halin irin aikina, addu'a kad'ai zaki bini da ita, Allah ya albarkaci Ra'eez ya kuma kawo wasu masu albarka a sabon gida. Guduwa tayi d'akinta tana murmushi. Dariya yayi yana fad'in yau kuma an tuno da daren amarci ne? Tana jinshi ta shige tana dariya. Madu ne ya danna kararrawa hakan yasa Alhaji yaje ya bud'e. Kwando ya gani mai d'auke da kuloli aciki sai babbar roba wadda aka cikata da zob'o. Kallonsa Alhaji yayi cike da mamaki yana fad'in Madu wannan kuma daga ina? Madu yace Malan Sani ne ya bani yace na kawo maku. Murmushin jin dad'i Alhaji ya saki yana fad'in ikon Allah!, ina shi Malan Sanin yake? Madu yace yana bani ya tafi yace baya son a taso ka kana hutawa. Amsar kwandon Alhaji yayi yana fad'in gaskiya naji dad'i sosai, yanzu nake shirin na fito na aike ka ka samo mana abinda zamuci saboda Ummun Ra'eez ta gaji bazata iya girki ba, ashe Malan Sani yayi mana tanadi, Allah ya saka masa da alkhairi. Madu yace amin. Alhaji yace bara nashiga ciki sai na miko maka naka. Ciki yashiga yana kiran Ummu, fitowa tayi tana amsawa. Alhaji yace kinga Malan Sani ya kawo mana abinci, matarsa ce ta dafa. Murmushi Ummu tayi tana fad'in kai amma naji dad'i sosai, wallahi dama yunwa nakeji ina tunanin abincin siyarwa. Ra'eez ne ya fito yana fad'in Abbu nima zanci. Murmushi Alhaji yayi yana fad'in ashe dai kowa yunwa yakeji? Taho kaci Kawun ka ne ya kawo mana. Ra'eez yace Abbu anjima zamuje naga Rumaisa ko? Dariya sukasa Ummu tace daga yau dai andena baka labarin Rumaisa zaka rik'a ganinta tunda mun dawo garin su. Alhaji yace anjima muna hutawa zamuje ka ganta. Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in yauwa nagode Abbu. *** Bayan sallar la'asar suna shirin zuwa gidan Malan Sani sai k'arar kararrawa sukaji, Alhaji ne yaje ya duba, saurin bud'ewa yayi yana fad'in ikon Allah, Malan Sani kune haka? Yanzu muke shirin zuwa Ra'eez ya matsa mana sai munje yaga Rumaisa. Matsawa yayi yana fad'in kushigo, kamo hannun Rumaisa yayi yana fad'in kema kinzo ganin Ra'eez ko? Kai ta d'aga tana murmushi. Malan Sani yace ai mune ya kamata muzo muyi maku sannu da zuwa. Ciki suka shiga Alhaji yashiga kiran Ummu. Kallon Malan Sani Halima tayi tana fad'in lallai Malan idan kana raye zakasha kallo, ashe haka gidan nan yayi kyau? Ai baka fad'a mani komai ba. Malan Sani yace dama ai gani da ido ya kori ji, duk yanda zan baki labarin gidan be kai yanda kika ganshi yanzu ba. Rumaisa tace Baba ni dai anan zan kwana yau. Malan Sani ya d'aure fuska yana fad'in idan na sake jin wannan maganar abakin ki saina zaneki kina ji na? Kai ta d'aga cike da tsoro. Halima tace nima zaneki zanyi idan kika sake fad'ar haka, idan ma ance kizauna bance ki amince ba, nasha fad'a maki duk abinda zakiyi arayuwa kada ki hangi na wani, ban tab'a duba da k'arancin shekarun ki ba kullum nake fad'a maki haka saboda ya zauna a kanki, kwad'ayi bashi da amfani kinji Rumaisa? Kai ta d'aga tana fad'in bazan sake ba. Murmushi Malan Sani yayi ya jawota yana shafa mata kai yace yauwa Rumaisar Baban ta, haka akeson yaron kirki ya kasance. Sallamar su Ummu sukaji hakan yasa suka maida hankalinsu wajen su suna amsawa. Zama sukayi nan suka shiga gaisawa. Ummu tace Maman Rumaisa yau dai Allah yayi mun had'u, koda yaushe sai dai muyi waya yau gashi mun dawo garin ku. Halima tace wallahi kuwa, tunda Alhaji yace zaku dawo nake cike da farin ciki, Allah ya kare ki daga sharrin mahassada. Ummu tace amin. Hannu ta mik'a ta kamo Rumaisa tana fad'in zonan 'Diyata. Duk'awa Rumaisa tayi har k'asa tana gaishe da ita. Dariya Ummu ta saki don sosai Rumaisa ta burgeta, gaba d'aya shekarunta bazasu wuce biyar ba amma tana da tarbiya. Shafa kanta tayi tana fad'in lafiya lau Rumaisa ya karatu ana zuwa ko? Kai ta d'aga tana fad'in duka biyu duk ina zuwa. Ummu tace da kyau, ki dage kiyi karatu kinji? Kai ta d'aga tana murmushi. Ra'eez ne ya sauko daga sama sai sauri yakeyi dan lokacin da suka zo yana band'aki. Yana isowa falon ya dai-daita tafiyarsa, dan Ra'eez akwai natsuwa, ya samu tarbiya mai kyau. Da sallama ya shigo, gaba d'ayansu suka amsa suna murmushi. Har k'asa ya duk'a ya gaishe da su. Malan Sani yace matsonan mugaisa abokina. K'arasawa yayi ya bashi hannu yana mai masa sallama. Dariya sukasa Malan Sani yace lallai Malaman Kano sun karantar da kai da kyau, to ya hanya, kazo lafiya ko? Ra'eez yace lafiya lau Kawu. Sosai Malan Sani yaji dad'in yanda Ra'eez ya kirashi da Kawu. Halima tace Ra'eez ya karatu ka gama firamare sai ta gaba ko? Ra'eez yace na gama. Matsawa yayi ya kamo hannun Rumaisa yana murmushi yace yau baza kiyi mani magana ba bayan a waya muna gaisawa? Dariya tasa tana fad'in sannu da zuwa Yaya. Gaba d'aya sai da sukayi dariya. Ummu tace ta waya ta k'are ai tunda ka dawo garin su, sai karik'a koya mata karatu. Ra'eez yace to Ummu kice ma Kawu ya barta nan. Kafin Ummu tayi magana Rumaisa ta kwace hannunta tana fad'in ni dai wajen Mama zan zauna. Dariya sukasa Ummu tace nima ai Mamanki ce. Rumaisa tace ni dai gidan mu zan kwana. Alhaji yace nan ma gidan ku ne ai. Kafad'a ta mak'ale tana kwanciya saman cinyar Mamanta. Ra'eez yace Ummu kinji abinda tace wai. Ummu tace kada ka damu zata rik'a zuwa, kaga itama ita kad'aice a wajen Mamanta, idan ta dawo nan za'a bar Mama ita kad'ai. Jinjina kai yayi yana fad'in to nima zan rik'a zuwa gidansu. Dariya suka sa. Tashi Malan Sani yayi yana fad'in bari mu koma yamma tayi kada mu hana ku aiki. Alhaji yace ba wani aiki da mukeyi kuyi zaman ku. Malan Sani yace zamu dawo wani lokacin akwai gajiya ai. Tashi Ummu tayi tana fad'in ina zuwa. Tsarabar data kawo masu ta d'auko tana fad'in Rumaisa ga tsarabar ki. Kin amsa Rumaisa tayi tana nok'e kafad'a. Murmushi Ummu tayi tana fad'in Rumaisa da wayau kike, gaskiya Maman Rumaisa kin bata tarbiya me kyau, a garin nan dama idan yaronka be samu tarbiya mai kyau ba abun tsoro ne. Alhaji yace indai Rumaisa ce zakisha mamaki, wayonta har ya wuce shekarunta. Dariya sukasa Malan Sani yace ai Hajiya Lagos abun tsoro ce, addu'a kad'ai zamu rik'e. Ummu tace haka ne. Mik'ama Halima ledar tayi tana fad'in ga tsarabar kanawa. Amsa tayi tana fad'in mungode sosai. Ummu tace haba bakomai, munci abinci yayi dad'i angode. Haka suka rakasu har bakin mota, sai da suka tafi sannan suka dawo. Ra'eez sai fushi yakeyi. Kamoshi Ummu tayi tana fad'in haba Ra'eez ai zaka rik'a ganinta tunda gari d'aya kuke. Alhaji yace ka bari zan kai ka wuni acan kaji. Ummu tace wallahi dama su dawo wancan b'agaren na waje. Murmushi Alhaji yayi yana fad'in nayi tunanin haka tun farkon da aka fara zanen gidan, amma abinda nayi tunani ya hanani aikata hakan, akoda yaushe idan zaka taimaki mutum to kayi kok'arin d'orashi a hanyar da zai samu ba hanyar da zaka rik'a bashi ba, hakan yana kashe zuciya, hausawa suna fad'in daka d'auki abinci kaba mutum gara ka nuna masa hanyar gona, koba komai zai dogara da kanshi kuma zaifi tattala abinda ya samu, na duba naga gara na canza masa unguwa na cika masa ya sayi gida akan na kawoshi gidana ya zauna, domin kawoshi gidana da zama zai kashe masa zuciya ya kasa mallakar nasa, kuma zumuncin mu zaifi kwari idan akace muna nesa da juna, kinji dalilin da yasa ban maidosu nan ba. Ummu tace kana da gaskiya kuma, shikenan Allah ya karemu daga sharrin mahassada kuma ya bamu zama lafiya. Alhaji yace amin. Ra'eez yace Abbu a wace islamiyar za'a sani? Abbu yace Ra'eez zamanka Lagos ba mai dad'ewa bane, bana son ma ka saba da ita har sai bayan ka mallaki hankalin kan ka, dan haka babu makarantar da zan saka, jarabawarku tana fitowa zaka tafi Kano, ko hutu akayi sati biyu kawai zaka zo kayi ka koma saboda islamiya, nafi buk'atar kayi ilimi mai zurfi dana zauna da kai anan, duk lokacin daka kammala karatun ka sai kazo mu zauna tare, domin wancan filin dana bari gidan ka ne za'a gina idan kayi aure ka zauna da matar ka. Hannu Ra'eez yasa ya rufe fuskarsa ya bar wajen da gudu. Dariya sukayi Ummu tace Yarona fa akwai kunya. Alhaji yace ashe Yaron ki, Yarona dai. Murmushi Ummu tayi tace Yaron mu dai. Alhaji yace idan kina son naki to ki haifo Mamana. Murmushi tayi tana fad'in Allah ya kawo masu albarka, yace amin Ummun Ra'eez. **** *** Tunda suka dawo Lagos Alhaji ya k'ara samun natsuwa, aikinsa yake sosai, yayin da Ummu suke zumunci da Maman Rumaisa sosai, Ra'eez yana zuwa gidan su yayita koya mata karatu, itama ana kawota idan ba makaranta, sai dai babu wanda yake kwana gidan kowa, Malan Sani shine yake kaita kuma ya d'aukota koda tayi bacci, haka ma Ra'eez shine yake maidashi. A wajen aikin su Alhaji Maiwada babu wanda yasan yana da 'Da, domin babu wanda ya fad'ama ya maido iyalinsa, ko walimar shiga sabon gida beyi ba, yayi addu'a kamar yanda addini ya koyar, shiyasa babu wanda yasan ya tare a sabon gida, asalima babu wanda yasan yana gini, dan Alhaji mutum ne mai son sirri, duk yanda kuke dashi baya bari ka sameshi agida musamman akan maganar data shafi wajen aiki. *** Zuwa yanzu Boda d'insu ta samu lafiya, domin aiki ake sosai, duk wanda aka kama da laifi nan take ake yanke masa hukunci, shiyasa kowa yake kaffa-kaffa da aikinsa. Manyan masu kud'i wad'an da suke kasuwancin shigo da kaya sam basa son Alhaji Maiwada, sunyi-sunyi a canza shi sai dai abun yaki tasiri, domin har yanzu ba'a canzashi ba, ganin haka yasa suka fara shirya masa mugunta, sai dai har yanzu basuci galaba akansa ba. ***** Jarabawar su Ra'eez ta fito kuma ya samu makarantar kwana shida Labiba, inda suka samu *FGC DAURA*, yayin da aka canza masu islamiya mai kyau idan suka dawo hutu surik'ayi. Sosai yayi farin ciki da samun makarantar kwana, saboda yana son makarantar kwana. Haka aka kammala masa komai, lokacin da zai tafi hada kukan rabuwa da Rumaisa, Ummu tace tare da ita zata tafi domin tayi masa rakiya. Haka suka shirya kasancewar ta jirgi zasu bi hakan yasa basu tafi dasu Malan Sani ba. Kwanansu biyu sai da suka kaisu har makaranta kafin suka koma Lagos. Rumaisa sai kuka take Ummu tana lallashinta. Bayan komawarsu ne Ummu tace gidan yayi mata shiru tana son ta samu mai aiki. Alhaji yace ina tsoron mutanan garin nan, wane aiki ne agidan da sai kin samu mai aiki? Ummu tace kawai ina so na samu abokiyar fira ne, kaga idan ka tafi baka dawowa sai dare, wani lokacin ma har sai nayi bacci kake shigowa, bazan iya zama ni d'aya ba. Alhaji yace ga Madu nan ai babu abinda zai sameki, wallahi ina tsoron mu kawo abinda zai halaka mu. Marairaice fuska tayi tana fad'i kayi magana da Malan Sani kila ya samo mana tagari. Jinjina kai Alhaji yayi yana fad'in shikenan, tunda kince Malan Sani nasan bazai tab'a kawo mana abinda zai cutar damu ba. *** Koda ya samu Malan Sani da maganar sai yace akwai wata mata mai suna *Ladi*, makwabtansu ne acan tsohuwar anguwarsu, ta iya aiki dan tayi aiki sosai agidajen mutane, yawanci abinda yake sa tana barin gidan aikinta wulakancin mutane, wasu kuma idan taga ana aikata wani abu marar kyau bakinta baya iya shiru sai tayi magana, wannan ne yake sa a koreta, ko kuma idan aka so had'a baki da ita ayi cuta sai taki yarda to sai su rabu, aikin da tayi na k'arshe wanda dagashi tace ta daina aikatau, dalilin barinta gidan aikinta shine, matar gidan tasa ta zuba ma kishiyarta guba a abinci, data ki amincewa sai matar taso taja mata sharri ta zuba abincin a b'oye kuma ta kai maganin cikin kayanta, gashi dama itace take dafa masu abinci, sai akaci sa'a matar bata ci ba, ta zuba zataci ta tashi ta shiga d'aki, da yake suna da mage sai tazo ta saci nama taci, tana gamaci ta fara shure-shure sai gawarta aka iske ga kumfa abakinta. Tunda aka ga haka akace guba ce a abinda taci, da aka duba sai akaga abincin matar ne taci, nan aka fara bincike sai ga magani an samu akayan Ladi, da yake Allah yana tare da mai gaskiya sai tayi sa'a mai gidan ya yarda da rantsuwar ta ya sallame ta da kud'i yace ta bar aikin. Mutuncin da Mai gidan yayi mata yasa ta sameshi ab'oye ta fad'a masa gaskiya, kuma ya yarda domin yasan halin matarsa. Tun daga lokacin ta dawo gidanta tace bazata sake aiki ba, domin wata rana za'a jawo mata d'auri, a bayan gidan mu take, ita kad'ai take zama a k'aramin gidanta mai d'aki d'aya, na mijinta ne daya mutu taci gado, da ba anan suke ba cirani ya kawo su har ya samu ya gina gida suke zaune shekara da shekaru, da ya rasu sai ta cigaba da zama dan tace bata da kowa, hakan yasa take aikatau. To yanzu sana'ar k'osai takeyi. Jinjina kai Alhaji yayi cike da gamsuwa yace Malan Sani abun mamaki baya k'arewa a duniya, gaskiya naji tausayinta, kuma tunda ka yabeta nasan tana da hali mai kyau, dan haka kayi mata magana sai muji yanda kukayi. Malan Sani yace insha Allahu bazaku samu matsala da ita ba. Alhaji yace amma ka fad'a mata gidan mu zata dawo da zama, idan yaso sai ta bada hayar nata. Malan Sani yace angama. **** Cikin sa'a Malan Sani ya samu Ladi da maganar, kasancewar Ladi tasan Malan Sani sosai, kuma taji shima a gidan yake aiki hakan yasa ta amince. Sosai tayi farin cikin samun wannan aikin, domin sana'ar babu kasuwa yanzu, hakan yasa ta fara addu'ar samun aiki sai gashi Allah ya kawo mata. Babu b'ata lokaci ta amince tace zuwa jibi yazo suje gidan kafin ta samu wanda zai tsare mata gidan kafin a samu mai haya. Malan Sani yace Ladi haya a Lagos ai bata wahala, ayau idan aka tallata gidan zaki samu wanda zai kama. Ladi tace yauwa dan Allah ka taya ni tallata gidan. Malan Sani yace insha Allahu, abinda nake so da ke ki k'ara kok'ari akan wanda na sanki dashi, domin nasan kina da Amana da gaskiya. Ladi tace insha Allahu zan kiyaye. Sallama yayi mata yana fad'in sai nazo jibin, idan kuma na samu wanda zai kama gidan zaki ganni. Ladi tace nagode sosai Malan Sani. Ur's. Nabeelert Lady🖋 [3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, MTN Card ta wannan lambar... 08147669770, kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a lambar k'asa, idan kuma bank transfer zakayi ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.* 0⃣9⃣ Cikin kankanin lokaci Ladi ta fara aiki agidan su Ra'eez, d'aki guda mai had'e da band'aki aka bata wanda yake a k'asa kusa da kicin, basu dade ba suka saba da Ummun Ra'eez saboda Ladi mace ce mai tsafta, kirki da natsuwa, rayuwar Lagos ta ratsata shiyasa take a waye, idan ka ganta sai kace bata manyanta ba, domin sam jikinta baya nuna shekarunta, yanda kasan tayi boko haka take, gata da ilimin addini. Itace take shara, guga da wanke-wanke, sannan tana yima Ummun Ra'eez wanki da guga, duk da a injin wanki ne takeyi, abinci kuma Ummun Ra'eez ce takeyi duk da Ladi tana tayata wani abun, haka idan tana da sako a kasuwa itace take zuwar mata saboda tasan ta kan kasuwa sosai. Ummun Ra'eez tana jin dad'in zama da Ladi sosai, sam bata jin kad'aici yanzu. **** *** Adebayo ne da Umar zaune a ofis d'in Alhaji Marusa, bayan sun gama gaisawa Alhaji Marusa yace Adebayo maganar gaskiya hak'urina ya k'are, jiya mukayi magana da Brr. Barau akan wannan mutumin Alhaji Maiwada, duk wata dabara da zamuyi akan a d'aukeshi daga nan munyi amma abun yaki aiki, Mr. Kallah ya fad'a mani bazai yuwu a canzashi yanzu ba, da ace ba amatsayin shugaban kwastam aka kawoshi nan ba da tuni an canzashi, amma yanzu dole sai nan gaba kafin a canzashi. Saboda haka jiya na yanke shawara ina ganin idan muka bita zamu samu mafita. Adebayo yace Alaji wace shawara ka yanke? Murmushi yayi yana fad'in mai zai hana idan kayana suka shigo musan yanda zamuyi a b'oye wasu idan yaso sai muce shine ya kwashe su. Gyara zama Umar yayi yana fad'in Alhaji akwai abinda nake zargi a wajen Alhaji Maiwada, ina tunanin kamar ya samu wani canji mai tsoka, domin da alama ya maido Iyalinsa nan garin, ada nasan agidan haya yake zaune, domin lokacin da yazo aka nemi abashi gida yace baya so, to sai yaje ya kama haya, abinci ma direbanshi yake siyo masa alokacin na gane Iyalinsa basa nan, to a kwanan nan naga canji sosai, da alamu ya maido Iyalinsa nan, domin ina ganin Malan Sani yana kawo masa abinci da azahar tayi, kulolin da ake zubo abincin sun sha bamban da abinda yake kawo masa abinci da, sannan alamu sun nuna ya tashi daga tsohon gidanshi, domin shekaran jiya ina bayansu naga ba hanyar tsohon gidanshi suka bi ba, kuma alokacin ya tashi gida zaije. Alhaji Marusa yace ko dai yayi sabon gini ne? Umar yace da alama, domin hanyar da naga yabi wajen Surelere ne. Jinjina kai Alhaji yayi yana fad'in kasa mashi ido, idan har zargin mu ya zama gaskiya ina mai tabbatar maku Alhaji Maiwada ya shigo hannu. Murmushi Adebayo ya saki yana tambayar Umar abinda suka fad'a dan be fahimta duka ba. Bayani Umar yayi masa. Saurin tashi yayi yana fad'in idan ya kasance gaskiya yayi gini Alaji kabarni dashi, zan kulla masa sharrin da zaiyi kuka. Dariya Alhaji Marusa yasa yana fad'in nasanka Adebayo baka da kyau, idan kana nan bani da sauran damuwa, dan haka na baka wuka da nama. Jinjina kai Adebayo yayi. Kud'i masu yawa Alhaji Marusa ya basu kafin suka tafi. **** *** Lab'e su Umar suke a wani waje suna kallo motar Alhaji Maiwada ta tsaya a bakin gate suna jira a bud'e masu. Mamaki ne ya kamasu ganin irin tsalelen gidan da zasu shiga. Basu gama mamaki ba sai da aka bud'e k'ofar gidan, k'ara matsowa sukayi domin su gane ma idanuwan su. Bayan da suka shiga Madu ya rufe k'ofa. Umar yace Adebayo ka gani ko? Adebayo yace tunda naga sun shigo wannan unguwar nasan Sir ba k'aramin sata yayi ba, kalli yanda gidan yake kamar na shugaban k'asa. Umar yace ka bari yashiga dole muje wajen maigadin muji ko gidansa ne ko kuma haya yakeyi. Suna nan sai ga Malan Sani ya fito daga gidan shi kad'ai suna sallama da Madu, dan anan yake barin motar yana hawa ta haya, duk da Alhaji yace yarik'a tafiya da ita amma Malan Sani yace nan yafi tsaro acan yana tsoron b'arayi. Har suka gama sallama da Madu yazo ya wuce su be gansu ba. Bayan 'yan mintuna suka fito suka nufi gidan. Umar yace Adebayo ka tsaya anan, bana so maigadin yayi saurin gane mu, kaga idan ya fad'ama Alhaji akwai wanda baya jin hausa zai iya d'agowa, dan haka ka tsaya naje. Murmushi Adebayo yayi yace shikenan kaje. Madu yana zaune yaji alamun sallama daga waje. Lek'awa yayi sai yaga Umar atsaye. Fitowa yayi ya bashi hannu suka gaisa. Umar yace sannu da aiki kayi hakuri na tadoka kana zaune. Madu yace haba ai bakomai, dama aikina ne na kula da k'ofar ai. Umar yace ni bako ne, akwai gidan da akayi mani kwatance anan unguwar gashi nazo kuma wayata ta mutu bare nakira azo a d'auke ni kuma kwatancen ya b'ace mani shine nace bara nayi tambaya. Madu yace ka kyauta kuwa, domin matambayi baya b'ata, ya sunan Maigidan da kazo wajenshi? Murmushi Umar yayi yace ina neman gidan Alhaji Hamza mai naira ne. Murmushi Madu ya saki yana fad'in duk da sabon zuwa ne ni nasan Alhaji Hamza, muma ba mufi wata biyar da muka dawo nan ba, maigidana ne ya gina wannan gidan shine muka dawo kasan shine shugaban kwastam. Umar yace lallai kace agidan shugaban kwastam kake aiki, lallai kaja kaya abokina. Madu yace sosai kuwa, domin Alhaji ba ruwansa, yana da kirki sosai, yafi shekara biyu da rabi yana gina wannan gidan sai wannan shekarar muka dawo bayan ya d'auko Iyalinsa. Umar yace kaji dad'in ka, ina ne gidan Alhaji Hamzan? Madu yace da ka shiga wancan layin zakaga gida mai babbar katanka fitilu sun haske layin, gidanshi yafi na kowa tsawo a layin zaka ga hada sojoji a k'ofar gidan. Umar yace nagode sosai. Madu yace bakomai agaida gida. Har ya k'arasa wajen Adebayo yana mamakin irin kud'in da Alhaji Maiwada ya kashe a wannan gidan. Yana zuwa yaja Adebayo suka nufi wajen da suka aje motar su. Sai da suka bar unguwar sannan Umar ya fad'a ma Adebayo komai. Hannu Adebayo ya tafa yana fad'in da kyau, anzo wajen, wallayi sai Sir, yasan yayi mana rashin mutunci, wannan gidan daya gina sai yayi danasani, ya hana mu jin dad'i ya tsare komai ashe kanshi yake tarama kud'i, kalli gidanshi kamar na babban d'an siyasa, Umar ka bani zuwa gobe zan nemo shawara. Dariya Umar yayi yace bana jinka Adebayo. *** Tun da safe Malan Sani yazo domin yau da wuri zasu fita. Ummun Ra'eez ce ta fito daga kicin hannunta rik'e da kwandon abincin data zuba masa. Kallonta Alhaji yayi yana fad'in sannu Ummun Ra'eez. Murmushi tayi tana fad'in sai kace nayi wani aiki babba. Alhaji yace aiki ne mana, yanda kike faranta mani Allah ya faranta maki kema. Murmushi tayi tace amin Abbun Ra'eez. Amsa yayi yana fad'in yau zamu kai dare saboda wasu kaya za'a kawo kuma dole na tsaya a gama duba su domin kayan Alhaji Marusa ne kuma kinsan na fad'a maki yana shigo da kaya marasa kyau yanzu ne abun yayi sauki dana saka ido, amma duk da haka idan aka kawo kayan manyan mutane dole sai na tsaya na duba duk da yanzu komai yayi sauki. Ummun Ra'eez tace to Allah ya tsare mun kai, ya kareka daga sharrin mahassada, domin wannan aikin naku akwai had'ari, domin mutane basa son gaskiya gashi kai mutum ne mai gaskiya. Murmushi Alhaji yayi yana fad'in kome zai faru dani bazan bari a aikata b'arna ba sai dai kawai addu'a. Ummun Ra'eez tace to Allah ya tsare. Yace amin, yauwa na manta ban fad'a maki ba su Ra'eez zasuyi hutu amma nace ma Alhaji Mansur kada akawoshi ya zauna tunda sabuwar islamiya aka maidasu idan muka samu lokaci sai muje, wani hutun sai yazo ko sati daya yayi. Ummu tace bakomai nima nafison ya zauna yayi karatu ai. Har bakin k'ofa ta rakoshi tana masa addu'a, sai da ya fita kafin ta koma ciki. Malan Sani yana ganin Alhaji ya fito yayi saurin tasowa ya amshi kwandon hannunsa yasa a mota. Bayan sun gaisa da Madu suka fita. A mota ma labarin kayan da za'a kawo Alhaji yake bama Malan Sani har suka isa ofis. *** Yau har karfe biyun dare Alhaji yana ofis ana duba kaya, aciki kuma sai da aka samu abinda aka fitar kafin yasa hannu suka gama biyan komai ya sallame su, sauran kayan kuma yace sai zuwa gobe za'a duba, acikinsu akwai sauran na Alhaji Marusa aciki. Haka sukayi sallama suka tafi hadasu Adebayo. Aranar dole Alhaji yasa Malan Sani ya tafi da mota saboda dare yayi. Bayan ya ajeshi yashiga ciki shi kuma ya wuce. Gaiswa sukayi da Madu wanda har yayi bacci, bayan ya shiga ya rufe k'ofar shima yashiga d'akinsa domin Alhaji yace yarika shiga d'aki yana baccinsa idan ya dawo Allah ne mai tsarewa tunda suna addu'a. Hakan yasa da Alhaji ya dawo Madu yake kulle k'ofa yashiga ciki. *** Washe gari kasancewar asabar ce yasa Alhaji bai fita da wuri ba, duk da yasan yana da aiki akwai kayan da zaije ya duba yasa hannu kafin a d'auka amma ya kwanta domin jiya agajiye ya dawo yace sai zuwa goma sai ya fita. Tunda ya tashi kawai yake jin kasala da fad'uwar gaba, wanka yayi sai yayi nafila ya zauna yana karatun kur'ani. Sai k'arfe tara da rabi ya fito domin ya karya. Zaune suke yana cin abinci, kallonshi Ummun Ra'eez tayi tana fad'in Abbun Ra'eez yau sai naga kamar kana cikin damuwa ko? Murmushi yayi yace kawai na tashi da mutuwar jiki da fad'uwar gaba ne. Hannunshi ta kamo tana fad'in kacigaba da addu'a nima ina taya ka, insha Allahu babu abinda zai faru da kai, Allah yana tare da kai domin kana rike da gaskiyar ka. Alhaji yace nagode kicigaba da yi mani addu'a kinsan aikin mu. Murmushi tayi tana mika masa abinci abaki. Amsa yayi yana sakar mata murmushi, da haka tacigaba da bashi abaki tana masa fira har yaji damuwar ta tafi. Bayan ya gama Malan Sani yazo ta rakashi tana ta masa addu'a suka tafi. Bayan da sukaje ofis suka kammala duba sauran kayan yasa hannu kafin aka d'auka. Aranar haka ya wuni baya jin dad'i, ko la'asar beyi ba ya tashi suka dawo gida. **** Washe gari tunda safe wayar Mr. Kallah ta tadashi, yana ganin sunan sai da gabanshi ya faad'i, d'auka yayi tare da yin sallama. Bayan sun gaisa Mr. Kallah yace Alhaji jiya na samu waya daga Alhaji Marusa wai kayansa sunzo amma babu rabi acikin kayan kuma masu tsadar ne aka cire masa, ya fad'a mani abubuwan da babu kuma naji babu abinda ya sab'a doka bare ace an ciresu. Ajiyar zuciya Alhaji ya saki yana fad'in Alhaji gaskiya babu wasu kaya da aka cire na Alhaji Marusa, wani kwali guda biyu ne kawai aka cire acikin kayansa domin akwai abinda ya karya doka, kuma agabana aka gama komai nasa hannu aka d'auki kayan kafin nabar wajen. Mr. Kallah yace Alhaji Marusa yace bazaiyi asara ba dole a nemo masa kayansa ko kuma yashigar da k'ara domin yana da hoton komai kuma an kawo masa kaya babu wasu aciki, shiyasa nace bara na kira ka domin kayi bincike kafin yashigar da k'ara. Alhaji yace shikenan zan bincika tunda kace ayi haka. Sallama sukayi ya kashe wayar. Kai Alhaji ya dafe yana fad'in innalillahi wa inna ilaihirraji'un. Da sauri Ummun Ra'eez ta tashi dan tunda aka kirashi ta farka. Dafashi tayi tana fad'in lafiya Alhaji? Labarin abinda ya faru ya bata. Jinjina kai tayi tana fad'in kayi binciken kamar yanda ya fad'a, gaskiya Mr. Kallah yana sonka da har ya iya kiranka ya fad'a maka, kila dai bayan daka gama duba kayan aka samu matsala bayan ka bar wajen. Alhaji yace Ummun Ra'eez matuk'ar ba'a gano inda kayan suke ba akwai matsala, domin kayan da suka b'ace na miliyoyin kud'i ne, dole Alhaji Marusa bazai kyale ba domin hakan zai jawo masa babbar asara, dole ma yashigar da k'ara saboda kayan suna da tsada. Ummun Ra'eez tace yanzu idan ba'a gano inda suke ba mai zai faru kuma? Alhaji yace Allah kad'ai ya sani, domin sai abun ya shafemu duk wani wanda yake wajen alokacin da aka duba kayan. Ajiyar zuciya ta saki tana fad'in insha Allahu haka bazata faru ba. Tashi yayi yana fad'in bara nayi wanka na fita. Ummun Ra'eez tace yau fa lahadi taya zaka fita da wuri haka. Alhaji yace dole na fita domin wannan babbar matsala ce. Waya ya d'auka ya latso Adebayo. Bayan ya d'auka ya fad'a masa su had'u ofis ya kira sauran wad'an da sukayi aiki ajiya da shekaran jiya. Adebayo yace Sir, zanje coci anjima sai dai idan mun dawo. Alhaji yace na manta, shikenan zan jira ku a ofis. Kashe wayar yayi ya kira Umar, yana dauka yace su had'u a ofis. Kashe wayar yayi yashige band'aki. **** Zaune suke a d'akin taro kowa yayi shiru yana jimamin abinda ya faru. Alhaji ya rasa abinda yake masa dad'i, tun d'azu da yazo yake bincike amma be samo komai ba, har sauran ma'aikatan sukazo aka cigaba da bincike. Adebayo yashiga damuwa yanda kasan kayanshi ne. Sallah kad'ai take fitar dasu. Har yamma suna bincike amma basu gano komai ba, sun duba komai gashinan kayan sunzo, kuma an duba su amma gashi ba'a kaisu ba, hatta da wad'an da suka d'auki kayan sun tabbatar iya abinda suka kai sune abinda aka basu. Sosai abun ya d'aure ma kowa kai, haka suka gaji kowa ya tafi. Alhaji kuwa wajen Mr. Kallah ya wuce, alokacin suna tare da Alhaji Marusa, acan ma maganar d'aya ce Alhaji Marusa yace k'ara zai shigar, gaba d'aya ya tashi hankalinsa saboda kaya ne na makudan kud'i suka b'ace. Mr. Kallah sai hakuri yake bashi amma yaki hakura, yaki bari ma a cigaba da binciken yace yayi magana da lauyenshi gobe za'a shigar da k'ara. Ganin Alhaji ya damu yasa Mr. Kallah yace ya kwantar da hankalinsa gara aje kotu za'afi saurin gano wanda ya d'auki kayan domin hukuma zata shigo ciki. Jin haka yasa Alhaji yaji hankalinsa ya kwanta domin shima yafi buk'atar hukuma tashigo ciki. Haka sukayi sallama ya tafi. Yana barin wajen suka kwashe da dariya. Alhaji Marusa yace ai na fad'a maka, bani da kyau Mr. Kallah, dama can kyaleshi nayi amma yanzu yashigo hannu na, sai na sashi yayi dana sanin zuwanshi Lagos, haka kawai muna zaune lafiya wani yazo ya nemi tada mana hankali, wallahi rabon dana shiga damuwa har na manta sai zuwan wannan mutumin. Mr. Kallah yace baka da kyau mutumina, wallahi banji tausayinsa ba, domin tun farko naso na d'orashi a hanya ya nuna mani shi mai gaskiya ne, yo yanzu waye yake wani aiki da gaskiya, ai yanda kazo kaga kowa da bindi kaima nemi ko tsumma ne ka d'aura domin agudu tare a tsira tare, wannan matsayin fa ba daga gidanku kazo dashi ba, anan ka sameshi kuma nan zaka barshi, ka bari kaci wasu ma suci amma ya tsaya yana nuna mana shi mai gaskiya ne, zaiga gaskiya kuwa Allah ya kaimu aje kotu gobe zai gane baida wayau. Alhaji Marusa yace baka ga gidan daya gina bane, yasan beda gaskiya shiyasa ko walimar tarewa beyi ba. Mr. Kallah yace ai tunda kace mani a surelere yayi gidan nasan akwai wata ak'asa. Alhaji Marusa yace ka barshi da gidan zamu kamashi ai, yau da dare su *Peter* zasuyi aikinsu. Mr. Kallah yace kai dan Allah? Alhaji Marusa yace wallahi kuwa, ai kaidai kasa ido kayi kallo. Dariya suka kwashe da ita. Ur's. Nabeelert Lady[3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, MTN Card ta wannan lambar... 08147669770, kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a lambar k'asa, idan kuma bank transfer zakayi ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.* 1⃣0⃣ A daren ranar Alhaji Maiwada kasa runtsawa yayi, Ummun Ra'eez ce take kwantar masa da hankali, sosai hankalinsa ya tashi domin jikinsa yayi sanyi, yana ji aransa kamar wani mugun abu ne zai faru, yayi mamaki da akace wai masu d'aukar kaya basu dauka duka ba, bayan yasan sai da aka gama komai suka tafi kafin ya bar wajen. Haka yayo alwala ya fara nafila yana neman tsarin Allah daga kowane sharri da yake tunkaroshi. Bayan ya idar ya bud'e kur'ani ya fara karatu har sai da aka kira sallar farko kafin ya tashi ya yo alwala yayi nafila sannan ya fita zuwa masallaci. Beshigo gida ba sai da gari yayi haske, yana shigowa wanka kawai yayi ya kwanta anan bacci ya d'aukeshi saboda gajiya. Sai k'arfe takwas ya farka dalilin wayarsa da aka kira. Sunan Adebayo ya gani, yana d'auka bayan sun gaisa Adebayo ya fad'a masa an aiko da takardar sammaci daga kotu k'arfe goma za'a shiga. Alhaji yace shikenan sai na fito. Band'aki yashi bayan ya fito ya shirya sannan ya fito falo. Bayan sun gaisa da Ladi ta shige ciki yayin da Ummu ta zuba masa abinci. Ruwan shayi kawai ya sha yace ya koshi. Zama Ummu tayi tana fad'in haba Abbun Ra'eez, ka sani damuwa bata haifar da komai sai ciwo, ka yi addu'a Allah bazai barka haka ba, idan kuma kaga wani abu ya faru da kai kada kace addu'ar ka bata karb'u ba, kasa aranka Allah yana so ya jarabceka ne kawai, kuma kasan muhimmancin yadda da k'addara. Ajiyar zuciya ya saki yana fad'in naji dad'in maganarki, kuma tasa zuciyata tayi sanyi haka kuma kin k'ara mani kwarin guiwa, bakomai, duk abinda ya faru zan d'aukeshi amatsayin k'addarata, domin bawa baya zama haka dole sai da jarabawa. Murmushi Ummu tayi ta zuba masa abinci ta fara bashi abaki tana kwantar masa da hankali, a haka yarika amsa har yaci sosai, yaji dad'in yanda Ummu tayi masa, shiyasa akoda yaushe yake k'ara sonta domin tasan yanda ake kula da miji. Bayan ya gama ta rakashi har k'ofar gida inda suka gaisa da Malan Sani kafin tayi masa fatan alkhairi ta koma ciki. Amsar jakarsa Malan Sani yayi yana fad'in Alhaji yau ka makara. Murmushi yayi ya shiga mota bece komai ba. Bayan sun fita ya kalli Malan Sani yana fad'in babbar kotu zamuje. Da sauri Malan Sani ya kalleshi yana fad'in maganar ta tabbata kenan?........ ....... Labarin abinda ya faru Alhaji ya bashi. Malan Sani yace ikon Allah, Alhaji wannan abu akwai alamar tambaya fa. Alhaji yace Malan Sani kawai mu barma Allah komai, jikina yana bani akwai abinda suka shirya, dan haka zan d'auki duk wani abu da zai taso. Tausayin Alhaji ne ya kama Malan Sani, yasan wani kullin ne suke so suyi mashi. Malan Sani yace Allah ya saukaka koma menene. Alhaji yace amin. **** Bayan sun isa kotu da Mr. Kallah ya fara had'uwa, wucewa yayi wajensa suka gaisa kafin ya jashi suka nufi wajen motarsa. Kallon Alhaji yayi yana fad'in kayi hak'uri da duk abinda zai faru, nayi magana da kwamishinan 'yan sanda yace zasuyi bincike dole a gano inda aka b'oye kayan, dan haka zasuzo suyi bincike duk inda ya kamata, Adebayo ya bani sunayen mutanan da suka tsaya akan kaya tun daga kanka har k'asa, kuma kowa za'a bincikesa, dan haka kada ka damu idan suka zo bincike, hakan ne kawai zaisa a gano gaskiya. Jinjina kai Alhaji yayi yana fad'in babu damuwa, suzo zan basu damar yin bincike duk inda suke so, nima nafison hukuma suyi bincike domin na kasa gano komai. Ganin motar Alkali yasa sukayi saurin nufar cikin kotun. Haka kowa yashiga ciki ya samu waje ya zauna suna jiran shigowar Alkali. Brr. Barau ne yashigo bayansa Alhaji Marusa yana bayansa suna magana a hankali, wajen zamansa ya wuce Alhaji Marusa ya zauna gefen Mr. Kallah. Alkali yana shigowa kowa ya tashi, bayan ya zauna kowa ya zauna. Gaba d'aya kotun tayi shiru ana jiran a fara. Magatakarda ne ya tashi ya fara karanto k'ara kamar haka.... *Yau sha biyu ga watan janairu shekara ta dubu biyu, (12/1/2000), wannan kotu zata saurari k'arar da Alhaji Marusa ya shigar akan tuhumar hukumar Kwastam da salwantar masa da kayansa na mukudan kud'i bayan sun iso a jirgin ruwa, wanda aka rik'esu har tsawon kwana d'aya da yini guda kafin aka sake su, sai dai aciki babu wasu daga cikin kayan da suka iso wanda ya tabbatar da zuwan su kuma an dubasu kafin a kaisu wajenshi aka cire wasu daga ciki. Alhaji Marusa yana rokon wannan kotu mai alfarma data kwato masa hakkinsa a wajen hukumar kwastam*. Risnawa yayi ya mik'a takardar wajen Alkali. Bayan daya gama dubawa yace lauyoyin da zasu gabatar da shari'ar su fara. Brr. Barau ne ya tashi yana fad'in sunana Brr. Nuhu Barau, nine lauyen da yake kare wanda yake k'ara. Alkali yace ina lauyen da zai kare wad'an da ake k'ara? Tashi Alhaji Maiwada yayi yana fad'in bamu d'auki lauya ba domin yau da safe takardar sammacin ta same mu, nine zan kare hukumar mu. Jinjina kai Alkali yayi yana fad'in Brr. Barau zaka iya farawa. Risnawa yayi kafin ya fito yana fad'in ina so nayima shugaban kwanstam wasu tambayoyi. Alkali yace an baka dama. Bayan Alhaji ya fito Brr. Barau yace kotu zata so taji sunanka da kuma matsayin ka. Sunana Alhaji Hamza Maiwada, nine shugaban kwastam. Brr. Barau yace kaji bayanin da aka karanta yanzu, shin ko zaka iya yima kotu k'arin haske akan abinda ake tuhumar hukumar ku dashi? Gyara tsayuwa Alhaji yayi yana fad'in tabbas nine wanda ya duba kayan Alhaji Marusa, kuma sai da na tabbatar da komai lafiya kafin nasa hannu aka gama komai sannan muka sakar masu kayan suka d'auka, agaban mu suka d'auki kayan babu abinda aka rage kafin muka bar wajen. Brr. Barau.. Amma Alhaji Marusa yace kafitar da kwalaye biyu acikin kayansa kace sun sab'a doka, kuma gashi kai kace ba'afitar da komai ba? Alhaji yace ina nufin acikin kayansa da aka duba wanda nasa hannu babu abinda aka rage, wad'an da aka fitar kuma dama bandasu acikin wad'an da nasa hannu, haka ne nasa acire kwalaye biyu acikin kayansa domin sun sab'a doka. Murmushi Brr. Barau yayi yana fad'in tun bayan zuwanka garin nan Alhaji Marusa ya fara fuskantar matsala da hukumar ku, kuma kowa yasan irin dad'ewar da yayi yana kasuwanci a k'ashashen waje, akwanakin baya ma sai da kayansa suka samu matsala, shin ko akwai wata matsala da take tsakanin ku ne? Girgiza kai Alhaji yayi yana fad'in nifa ma'aikacin al'umma ne, su nake ma aiki tare da k'asata, bani da wata matsala tsakanina da Alhaji Marusa, kamar yanda kowa yake shigo da kaya muke dubawa shima haka muke duba nashi, sai dai kawai kasan kowa da tsarin aikinsa, to nima haka nawa tsarin yake, matuk'ar kaya suka iso dole sai mun tabbatar da ingancin su kafin musa hannu a sake su, matuk'ar muka kama kayan da suka sab'a k'a'ida dole ne mu ciresu, bayan wannan ni banida wata matsala da kowa. Brr. Barau... Amma yace kayan kwannasu d'aya da yini guda, baka tunanin kafin ku kammala duba kayan aka samu wani ya d'auke wad'an da suka b'ace? Alhaji yace babu wanda ya tsaya akan kayan, bayan da muka duba na farko haka kowa ya tafi sai washe gari aka k'arasa duba sauran, sai dai kasan zuciya bata da k'ashi, Allah ne kad'ai yasan gaskiya, tun bayan da aka fad'a mani wannan matsalar na tara duk wad'an da sukayi aiki aranar muka tattauna, sai dai maganar d'aya ce, babu wanda yasan inda suke, dan haka ina rokon wannan kotu mai albarka data bada izini hukuma tayi bincike akan wannan matsalar hakan zaifi mana sauki. Jinjina kai Brr. Barau yayi ya juya yana fad'in ya mai shari'a, ina rokon wannna kotu mai albakar, kamar yanda Alhaji Maiwada ya nemi alfarma a d'aga wannan shari'a domin hukuma ta samu damar yin bincike hakan zaisa a samu cikakkar sheda. Nagode. Bayan da Alkali ya gama rubutu ya d'ago yana fad'in wannan kotu ta bama hukumar 'yan sanda dama da su tsananta bincike zuwa nan da kwana biyu za'a dawo kotu domin acigaba da gabatar da wannan shari'a. Tebur ya buga gaba d'aya akace kottttt . Gaba d'aya kowa ya fita yana jajanta abinda ya faru, yayin da wasu suke tausayin Alhaji Maiwada domin sun san halinsa. Bayan da suka fito Mr. Kallah yaja Alhaji Maiwada suka nufi wajen motar kwamishinan 'yan sanda wanda be dad'e da zuwa ba saboda wayar da sukayi da Mr. Kallah. Bayan sun gama gaisawa Mr. Kallah yayi masa bayanin halin da ake ciki akan abinda Alkali yace. Kwamishina yace kada ka damu Alhaji zansa yarana suyi bincike, ina so ku bamu had'in kai ta haka ne zamu ji dad'in yin aikin. Alhaji yace insha Allahu bazaka samu matsala da mu ba. Haka suka gama tattaunawa kafin sukayi sallama ya shiga mota suka nufi ofis. A hanya Malan Sani sai kwantar ma Alhaji da hankaki yakeyi har suka isa. *** A can ofis kuwa hankalinsa atashe yake, Adebayo da Umar ne kawai hankalinsu yake kwance domin sun san bakin zaren, Alhaji ya sake tara kowa ya rokesu akan idan akwai wanda yake dasa hannu akan wannan abun ya taimaki mutane ya fito da kanshi kafin hukuma ta ganoshi, domin duk wanda aka gano shi kad'ai za'a kama. Nan kowa yace beda masaniya akan abun. Haka dai taron ya tashi babu wani labari. Haka Alhaji ya wuce ofis jiki a sanyaye. Yinin ranar haka yayishi jiki babu kwari. Bayan anyi sallar azahar sai ga DPO da yaranshi sun iso. Haka suka fara nasu binciken cikin kwanciyar hankali. Duk ma'aikatan da sukayi aiki aranar sai da aka d'auki komai nasu tun daga kwatancen gidansu da bayanin bankinsu. Bayan da suka gama sukayi sallama da Alhaji sukace akowane lokaci za'a iya ganinsu a gidan mutum. Godiya Alhaji yayi masu suka tafi. Sunayin la'asar ya tafi gida domin baya jin dad'in jikinsa. Malan Sani bayan ya ajeshi yace zaisa Malamin unguwarsu ayi addu'a. Alhaji yace nagode sosai Malan Sani, bara na baka kudin da za'a basu sadaka. Malan Sani yace wallahi bazan amshi ko sisi ba, nine nayi niya dan haka ka barni kawai. Murmushi Alhaji yayi yace nagode agaishe da Rumaisa. **** Ana gobe za'a koma kotu da misalin k'arfe bakwai bayan anyi sallar magriba Alhaji yana zaune a tsakar gida shida Malan Sani da Madu suna fira kawai sukaji k'ararrawa. Da sauri Madu ya tashi ya nufi k'ofa, sai da ya lek'a kafin yayi saurin bud'ewa. Tashi Alhaji yayi tsaye ganin 'yan sanda, lokaci guda yaji gabanshi ya faad'i, duk da yasan suna zuwa gidaje suna bincike amma haka kawai yaji gabansa ya faad'i. Bayan sun gama gaisawa DPO yace Alhaji sai dai kayi hak'uri yau gamu munzo bincike yazo kan ka. Murmushi Alhaji yayi yana fad'in haba ai bakomai, ai haka mukeso domin ta haka ne za'a gano gaskiya. Bismilla ku shigo, bara nayima Iyalina magana. DPO yace bakomai kayi masu magana. Suna tsaye suna k'arema gidan Alhaji kallo ya fito yana fad'a masu su shigo. Suna shiga suka iske Ummu da Ladi a falo sanye da hijabi suna zaune. Gaishe dasu sukayi Alhaji ya samu waje ya zauna yana fad'in DPO kushiga ko ina abud'e yake. Jinjina kai yayi kafin yasa yaranshi suka fara bincike. Tunda suka haura sama Ummu tasa kuka, rungumeta Alhaji yayi yana fad'in kidena kuka, ina da gaskiya ta dan haka su shiga duk inda suke so. Ummu tace yanzu har d'akin kwanan mu sai sun bincika mana? Alhaji yace daga binciken fa shikenan, bana so kisa damuwa aranki. Suna nan zaune kusan mintuna goma sai gasu sun sauko, DPO yace zamu shiga kicin Alhaji. Jinjina kai yayi ya nuna masu hanyar kicin d'in. Bayan sun gama duba komai suka fito. DPO yace Alhaji babu abinda muka samu acikin gidan ka, sai dai zamu duba can waje zuwa bayan gidan ka dan kamar naga akwai ginin da kakeyi acan baya wanda ba'a kammala ba. Alhaji yace akwaishi muje ku duba. Cire Ummu yayi ajikinshi yabi bayansu. Suna fita Malan Sani yace Alhaji mujirasu anan kada suga kamar muna binsu. Kai Alhaji ya jinjina ya samu waje ya zauna. Kusan mintuna ashirin sai ga wani d'an sanda ya fito da gudu, Alhaji yana ganinshi yayi saurin tashi tsaye. Yana zuwa yace Alhaji Oga yana son ganinka. Jiki a sanyaye Alhaji da Malan Sani hada Madu suka bi bayan shi. Tun kafin su k'arasa suke hango kaya daga cikin wani d'aki da aka bud'e. Da sassarfa Alhaji ya k'arasa wajen. Turus ya tsaya yana kallon DPO. Girgiza kai DPO yayi yana fad'in meyasa haka Alhaji? Meyasa ka zab'i ka bamu wahala bayan kasan komai? Salati kawai Alhaji yakeyi jikinsa yana rawa, idan ba gizo idanuwansa suke masa ba kaya yake gani a cikin d'akin da yake gabanshi kuma kayan da ake tuhumarsu akansu, sai dai kayan da suke wajen basu kai rabin wanda akace sun b'ace ba, da alamu ba duka bane a d'akin. Da sauri Malan Sani ya rik'e Alhaji yana fad'in wallahi Yallab'ai bamu da masaniya akan wannan kayan, sai dai idan wani ne ya shigo dasu. Murmushi DPO yayi yana fad'in meye matsayinka awajen Alhaji? Malan Sani yace direbansa ne. Dafashi DPO yayi yana fad'in Malan Direba ka tsaya amatsayinka, wannan mune muke da ikon yin bincike, dan haka kaja bakinka kayi shiru domin duk abinda zaka fad'a zai iya zama hujja akan ka. Kallon Alhaji yayi yana fad'in bincike ya k'are Alhaji, dan haka zamu tafi da kai kafin gobe akoma kotu, sai dai na lura kamar kayi amfani da wasu kayan saboda yanda na samu labari kayan sunfi haka yawa, amma dai koma meye zamuji daga bakin ka gobe. Shiru Alhaji yayi ya kasa magana. DPO yasa mai d'aukar hoto ya d'auki komai kafin su tafi. Kallon yaransa yayi yana fad'in ku taho dashi. Alhaji yace zan iya sallama da Iyali na? Wani d'an sanda yace babu inda zakaje. DPO yace barshi ka rakashi yaje yayi magana dasu. Bayansa Malan Sani yabi suka wuce jiki a sanyaye. Tunda Ummun Ra'eez taga Alhaji taji gabanta ya faad'i, saurin k'arasowa tayi tana kuka. Rungumeta Alhaji yayi shima ya saki kuka. Sun dad'e ahaka kafin ya goge idonshi yana fad'in kiyi mani addu'a Ummun Ra'eez, abinda nake tsoro ya tabbata, Allah ne kad'ai zai fitar dani, sun samu kayan a ginin Ra'eez wanda bansan da suba. Hannu tasa ta goge masa fuskarsa tana fad'in wallahi nasan k'arya ne, nafi kowa saninka, baka tab'a ciyar damu da haram ba, kuma Allah zai fitar da kai. Gyaran murya d'an sandan yayi yana fad'in Alhaji kana b'ata mana lokaci. Cireta yayi daga jikinsa yana fad'in kada kiyi kuka, kiyi mani addu'a gobe zan dawo. Kai ta jinjina tana hawaye tace Allah ya tsare mani kai. Ladi ma kuka takeyi tana masa addu'a. Haka suka tasa keyarsa Malan Sani da Madu sai kuka sukeyi. Suna kallo suka tafi dashi yayin da aka sa kayan amota aka tafi dasu. **** *Washe gari a kotu.* Ur's. Nabeelert Lady [3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, MTN Card ta wannan lambar... 08147669770, kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a lambar k'asa, idan kuma bank transfer zakayi ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.* 1⃣1⃣ Zaune Alhaji Marusa da Mr. Kallah suke a ofis d'in Brr. Barau. Dariya Alhaji Marusa yayi yana fad'in Mr. Kallah ai na fad'a maka bani da kyau, yanzu Alhaji Maiwada zai san ya ja dani, babu wanda ya isa yazo ya kawo mani matsala akan kasuwancina, domin bana had'a kud'i da komai, saboda ina samun had'in kai da ma'aikatan Lagos yasa ban damu da shigo da kaya ta bodar portcourt ba, amma saboda shi sai da na koma ina shigo da wasu kayan ta can saboda ya kasa ya tsare, duk da ba huruminsa bane diba kaya amma sai yayi hakan, ya tsaya ofis yayi aikinsa bazeyi ba ya koma shine yake duba duk kayan da aka shigo dasu, wanda yake kula da b'angaren duba kaya ya zama hoto, kuma saboda raini yafi tsayawa ya duba kayana fiye dana kowa, amma ai yanzu nayi maganinsa, Mr. Kallah kayi mana wannan taimakon a saukeshi daga wannan matsayin, naji dad'i da ya kasance kana hutu abun ya faru, tunda litinin zaka koma Abuja idan kaje ofis inaso a aiko masa da takardar rage matsayi saboda an kamasa da babban laifi. Murmushi Mr. Kallah yayi yana fad'in Alhaji Marusa baka da kyau, kasan nine shugaban kwastam na k'asa baki d'aya, duk da ina goyon bayanka dole wani abun sai an duba saboda idanuwan mutane, ba kai kad'ai ba, manya da yawa nine nake tsaya masu saboda nidai inason kud'i, duk wanda zai yaga mani dole na bashi goyon baya, amma duk da haka muna kimantawa saboda mu kauda hankulan mutane, hutun dana d'auka litinin yake k'arewa, tunda yau za'a yanke hukunci bayan na koma zamu tattauna akan abinda yayi. Brr. Barau yace rankaidad'e ai ko da abinda kotu zata yanka masa aka barshi ya isheshi ya tsani aikin kwastam, domin miliyoyin kud'i zai biya, inaji ma kila ya saida gidanshi saboda Kwamishna yace da suka binciki bankinsa babu wasu kud'i da yawa aciki duk ya zuba su a gini, domin wannan binciken sai da suka had'a da EFCC saboda babban abu ne, kaga kuwa dole ya sayar da wannan makeken gidan ya biya kud'in da kotu zata yanka masa. Murmushi Alhaji Marusa yayi yana fad'in kuma nine nan zan sayi gidan, sai dai banzan bari yasan haka ba, zan aika wani yaje ya siya mani shi. Dariya sukasa gaba d'aya. Brr. Barau yace ina ganin lokacin shiga yayi. Mr. Kallah yace bara na fara fita kada azargi wani abu. *** Duk girman kotun sai da ta cika da jama'a, domin tun jiya ake fad'ar an kama shugaban kwastam na Lagos da laifin satar kayan Alhaji Marusa, wannan dalilin ne yaja hankulan mutane da yawa suka kawo ziyara a kotun, hada manyan mutane sai da suka ziyarci kotun saboda suji abinda za'ayi, 'yan jarida kuwa sun cika kotun kowa yana jira ya samu abun k'araswa. Bayan da Alkali yashigo kowa ya natsu. 'Yan sanda ne suka shigo da Alhaji Maiwada, kowa kallonsa yakeyi yayin da Alhaji Maiwada yake ta addu'a, gaba d'aya jikinsa rawa yake masa, idanuwansa a k'asa ko kallon mutanan bayayi. Ummun Ra'eez kasa zuwa kotun tayi, domin bazata iya ganin ana cima mijinta mutunci ba. Malan Sani da Madu sai Alhaji Mansur kawai suka zo kotun, shima a safiyar yau ya biyo jirgi saboda tun a jiya Ummun Ra'eez tayi masa waya. Maman Rumaisa da Ladi sune suke ta bama Ummun Ra'eez hakuri. Ma'aikatan ofis d'insu Alhaji Maiwada da yawa sun zubar masa da kwallah musamnan wad'an da suke jin dad'insa. Adebayo, Umar da sauran mabiyansu sunfi kowa murna, sai dai a fuskarsu suna nuna jimami. Bayan da Magatakarda ya sake karanto k'arar Alkali yace a fara gabatar da shari'ar. Tashi Brr. Barau yayi yana fad'in inaso kotu ta bani izini na kira Alhaji Maiwada domin nayi masa wasu tambayoyi. Alkali yace kotu ta baka dama. Bayan ya fito Brr. Barau ya k'arasa wajensa yana fad'in Alhaji inaso kayima kotu cikekken bayani akan yanda aka samu kayan Alhaji Marusa wanda ake tuhumar hukumar ku dasu a gidan ka. Ajiyar zuciya Alhaji yayi yana fad'in tabbas an samu kayansa a gida na, amma maganar gaskiya bani da masaniyar zamansu agida na, sai dai idan saka mani akayi, domin duka kwali ukku ne aka samu a gidana. Murmushi Brr. Barau yayi yana fad'in Alhaji kada ka bama kotu wahala, 'Yan sanda sun tabbatar mana a cikin d'akin da yake bayan gidanka aka samesu, kuma tambayar anan itace, Alhaji Marusa ya bamu iya yawan kayansa da suka b'ace hada kud'ad'en su, sai dai kuma kayan da aka samu a wajenka basu kai kwatar kud'insa ba, haka kuma ko rabin wad'an da suka b'ace basu kai ba, domin lokacin da aka duba gidanka an iske saura kad'an ka rage, shine muke so muji ina ka kai sauran? Idan kuma siyarwa kayi to ina kud'in suke, domin a binciken asusunka da akayi kud'in da suke ciki ba wasu masu yawa bane, shine muke so kayi mana bayani. Wani lauya ne ya tashi yana fad'in ya Mai shari'a nine lauyen da nake kare wanda ake k'ara. Sunana Brr. *Kamal Auwal*. Kai Alkali ya jinjina yana fad'in Brr. Kamal akwai maganar da kake da ita ne? Risnawa yayi yana fad'in ya mai shari'a ya kamata lauyen da yake kare wanda yake k'ara ya sassauta maganarsa akan wanda ake k'ara, be kamata yarik'a masa wasu tambayoyin ba. Nagode. Jinjina kai Alkali yayi yana fad'in wanda ake tuhuma ba zarginsa ake ba domin anga zahiri a gidanshi, dan haka dole ya amsa tambayar da akayi masa saboda shi kad'ai ne zai iya warware mana wannan matsalar. Murmushi Brr. Barau yayi yana fad'in Alhaji kotu tana sauraron ka. Gyara tsayuwa Alhaji yayi yana fad'in kamar yanda nace bansan da zaman kayan Alhaji Marusa agidana ba, haka zalika bansan ina sauran suke ba, kuma ni ban siyar da komai ba saboda ban tab'a zaluntar kowa akan kayansa ba, iyakar abinda na sani kenan. Juyowa Brr. Barau yayi yana fad'in ya mai shari'a inaso wannan kotu tayi duba da abubuwa guda biyu da zan gabatar mata yanzu, wanda sun isa su tabbatar ma kotu lallai Alhaji Maiwada shine ya d'auki wad'annan kaya. Na farko Alhaji Maiwada ya gina katafaren gida na makudan kud'i, kuma babu wanda yasan lokacin daya fara ginin da lokacin da aka gama, sannan be gayyaci kowa ba alokacin da zai tare agidansa, haka zalika Alhaji Maiwada baya son kowa yasan inda gidansa yake acikin ma'aikatansa gaba d'aya, duk wanda yake son ganinsa sai dai su had'u a ofis, domin baya bari aje gidansa. Abu na biyu alokacin da aka kawo kayan Alhaji Marusa bayan Alhaji da ma'aikatan da suke aiki aranar sun gama duba kayan aka barshi akan sai washe gari zasu k'arasa, bayan da kowa ya tafi Alhaji Maiwada shine wanda aka bari na k'arshen tafiya, wanda maigadi ya tabbatar mana da cewar ya dad'e kafin ya tafi, kuma kafin ya tafi sai da ya aikeshi ya d'auko masa wasu takardu wanda hakan ya d'aukeshi kusan mintuna ashirin kafin ya dawo, da wannan ne Alhaji Maiwada yayi amfani domin ya fitar da abinda yakeso wanda shine yasan ta yanda ya fitar da kayan a cikin lokaci k'ankani. Da wannan nake rokon kotu data kwatoma Alhaji Marusa hakkinsa. Nagode. Bayan Alkali ya gama rubutu yace lauyen da yake kare wanda ake k'ara ko kana da abinda zakace? Tashi Brr. Kamal yayi yana fad'in ina dashi ya mai shari'a, ina so zanyima Mai gadin da yayi aiki aranar da aka kawo kayan Alhaji Marusa tambaya. Kotu ta baka dama. Matsowa yayi kusa da Maigadin bayan ya fito yana fad'in ko zaka iya fad'a ma kotu wajen da Alhaji ya aike ka d'auko takardun da kace? Maigadi yace a cikin ofis d'in da ake aje kaya ne inda suka zauna shine ya mantasu acan sai yace na d'auko masa. Brr. Kamal... Idan na fahimceka Kenan shi Alhaji ya fito wajen motarsa, daya tuna yayi mantuwa shine ya aike ka? Kai Maigadi ya jinjina yana fad'in yashiga mota ma sai ya aike ni, to kafin na d'auko masa na d'an jima saboda ban gansu a inda ya fad'a mani ba. Jinjina kai Brr. Kamal yayi yana fad'in ya mai shari'a inaso kotu tayi duba da abinda Maigadi ya fad'a, Brr. Barau ya ce Maigadi ya fad'a masu Alhaji ya aikesa bayan kuma Alhaji yana cikin mota, hakan zai nuna mana cewar Alhaji baya cikin d'akin da kayan suke taya zai d'aukosu ya fita dasu bayan Maigadi yana cikin d'akin? Inaso wannan kotu mai albarka da tayi duba da wannan sheda da aka gabatar, duk da an samu kaya a gidan Alhaji ba shine yake nuna Alhaji ne ya d'aukesu ba, nagode. Tashi Brr. Barau yayi yana fad'in ya mai shari'a wannan hujja da abokin aikina ya kawo bata isa ta kare wanda ake k'ara ba, domin kowa ya sheda an samu wad'an nan kaya agidan Alhaji, idan akace yana cikin mota ya aiki mai gadi mai yasa da Maigadin yashiga baiga takardun a inda Alhaji yayi masa kwatance ba? Dama yana da wata manufa shiyasa ya barosu kuma ya aiki Maigadi domin yasan kafin ya gansu ya gama abinda yakeyi. Ina rokon wannan kotu data yi amfani da shedun da aka gabatar mata domin ta kwatoma Alhaji Marusa hakkinsa, domin ga kwararun hujjoji nan mun gabatar. Nagode. Bayan da Alkali ya gama rubutu ya d'ago kai yana fad'in Alhaji Maiwada kana da ja akan abinda aka gabatar? Girgiza kai Alhaji yayi wasu hawayen bakin ciki suka zubo masa, hannu yasa ya goge idonshi yana fad'in iya gaskiyata na fad'a, bani da sauran ja akan abinda aka gabatar ma kotu Allah ne kad'ai yasan gaskiya. Gaba d'aya kotun akayi shiru, mutane da yawa jikinsu yayi sanyi akan maganar Alhaji, su Malan Sani sai kuka sukeyi. Bayan Alkali ya gama rubutu ya d'ago yana fad'in abisa kwararun shedu da aka gabatar ma kotu, kuma wanda ake tuhuma ya kasa kare kanshi a gaban kotu, wannan ya tabbatar mana cewar Alhaji Hamza Maiwada yana dasa hannu acikin b'acewar wad'annan kaya, inda wasu daga ciki suka salwanta. Abisa adalci irin na wannan kotu Alhaji Maiwada zai biya Alhaji Marusa duk abinda ya kashe akan kayan da suka b'ace, tun daga siyosu, kud'in kawosu zuwa nan, sauran da suka rage kuma za'a mik'asu ga Alhaji Marusa, 'Yan sanda da hukumar bincike zaku tsaya a kammala komai, domin a tabbatar Alhaji Maiwada ya biya komai daya b'ace, hukumar kwastam sai ku d'auki mataki domin akiyaye sake faruwar irin wannan. Tebur ya buga gaba d'aya akace kotttt!. Duk'awa Alhaji yayi ya d'ora kanshi saman katakon da yake tsaye wasu zafafan hawaye suna zubo masa. Malan Sani da Madu sai Alhaji Mansur ne kad'ai suka k'araso wajenshi. Kamoshi Alhaji Mansur yayi yana lallashinsa. Haka suka fito 'yan sanda suna binsu abaya. Mr. Kallah ne yayi magana da DPO tare da mai jagorantar cibiyar bincike akan su bar Alhaji ya koma gida zasuyi magana da Kwamishna dan ayi komai cikin hankali kwance tunda Alhaji babban mutum ne. Haka Mr. Kallah ya samu su Alhaji Mansur yayi masu bayani, sosai sukaji dad'in abinda yayi masu, godiya sukayi mashi sannan suka k'arasa wajen Brr. Kamal sukayi masa godiya akan abinda yayi masu domin sun san basu d'aukeshi ba amma ya tashi domin ya kare Alhaji. Brr. Kamal yace haba bakomai, wallahi naji tausayinsa hakan yasa na tashi domin na kareshi, rashin hujjoji yasa aka kadamu, amma bakomai Allah yana gani. Godiya sukayi masa suka wuce gida. Duk yanda 'yan jarida suka so suyima Alhaji tambaya hakan be samu ba dole suka hakura. *** Zaune suke a falo Alhaji yana kwance saman doguwar kujera zazzab'i ya rufeshi. Alhaji Mansur ne yasa Ladi ta had'o masa shayi dan Ummu tana zaune kusa dashi sai kuka takeyi, sosai hankalinta ya tashi da abinda aka fad'a mata. Malan Sani yana gefe ya kalli Alhaji Mansur yana fad'in Alhaji yanzu shikenan haka zamu kyalesu an yanke ma Alhaji hukuncin zalunci? Alhaji Mansur yace Malan Sani najeriyar kenan, gashi dai munsan sharri ne aka kulla masa amma babu yanda zamuyi, domin sun fimu hujja, kasan ita kotu da hujja take amfani, duk wasu hujjoji da zasu tabbatar Alhaji ne ya d'auki kayan Alhaji Marusa sun gabatar dasu, babban abinda yasa suka k'ara cin galaba akan Alhaji shine samun kayan a gidanshi, amma dan sun gabatar da irin ginin da yayi wannan ba hujja bace, sunyi amfani da hakan ne dan su k'ara ma hujjarsu girma, amma bakomai, akwai Allah, kuma shi kad'ai ne zai bayyana gaskiya. Ummun Ra'eez tace wallahi na tsani garin nan, bana son wannan aikin na Abbun Ra'eez, tunda abun ya fara zuwa da haka dan Allah Abban Labiba kasa baki ya aje masu aikin su yazo mu koma Kano mucigaba da rayuwar mu, sun fara neman kassarashi ta hanyar dukiyarsa da goga masa bakin fenti, nan gaba wallahi rayuwarsa zasu nema, bani da kowa saishi, idan suka rabani dashi ina zansa kaina. Rungumeta Maman Rumaisa tayi itama tana kuka. Alhaji Mansur da jikinsa yayi sanyi ya kamo Alhaji Maiwada yana mik'a masa kofin shayin. Amsa yayi ya shanye dan yunwa yakeji saboda beci komai ba. Komawa yayi ya kwanta yana runtse idonshi. Alhaji Mansur ne ya kamashi suka mik'e tsaye, kallon su Malan Sani yayi yana fad'in bara nashigar dashi ciki nayi waya da likitansa zaizo ya dubashi yana buk'atar hutu saboda jininsa yana iya hawa. Tashi Ummu tayi tana fad'in ko zaiyi wanka? Alhaji Mansur yace aa abarsa yayi bacci. Ciki suka nufa wani d'aki da yake ak'asa. Bayan sun kwantar dashi wayar Alhaji tayi k'ara, Alhaji Mansur ne ya duba sai ya ga likitan ne, fita yayi yana fad'in bara nashigo dashi. Bayan ya gama dubashi ya bashi magunguna yayi masa allurar bacci, cikin lokaci kad'an bacci ya d'aukeshi. Fitowa sukayi likita yana fad'in jininsa ya hau, dole ya samu bacci mai yawa hakan zai taimaka masa. Godiya sukayi masa ya tafi. Kallon Ummu Alhaji Mansur yayi yana fad'in ki kwantar da hankalin ki babu abinda zai faru, abarshi ya samu hutu zuwa gobe zamuyi maganar. Ummu tace mungode Abban Labiba, kashiga ga d'akin baki can ka huta Ladi ta kai maka abinci. Jinjina kai yayi ya nufi wajen Malan Sani. Bayan yayi masa bayanin da likita yayi masa Malan Sani yace shikenan abari zuwa goben sai muji abinda za'a yanke. Sallama sukayi masu suka tafi. Alhaji Mansur ya nufi d'akin da aka saukeshi. *** Dariya ce take fitowa daga harabar gidan Alhaji Marusa inda suke hutawa, Mr. Kallah ne sai Brr. Barau, Adebayo, Umar sai Alhaji Marusa a zaune, daga gefe guda wasu manyan maza ne sunci sun k'oshi, fuskarsu babu alamun fara'a, d'aya daga cikinsu Peter ne, sai abokinsa na hannun damarsa. Lemu Mr. Kallah ya kurb'a yana fad'in gaskiya Alhaji Marusa wannan karon bansan dame zan saka maka ba, rabon da muyi irin wannan samun har na manta, kodan an dad'e ba'a samu masu irin halin Alhaji Maiwada ba? Dariya Alhaji Marusa yasa yana fad'in ai dama haka irinsu suke k'arewa, yanzu gashinan ya rasa kimarsa, zai rasa dukiyarsa abanza, kaga mu gaba ta kaimu, wata kilama hukumar ku ta dakatar dashi. Mr. Kallah yace baza'ayi haka ba, kasan dan an kama mutum da laifi so d'aya ba'a saurin dakatar dashi, tunda dai nasan abinda ya faru bazan bada goyon baya a dakatar dashi ba domin ya bani tausayi zafin zaiyi masa yawa, amma ranar litinin zan koma aiki hutuna ya k'are, zamu tattauna dole aja masa kunne kuma ya tsaya a aikinsa ya bar masu kula da sauran wajen suyi nasu aikin, idan ya kama dole saiya duba abu sai yaje amma ya tsaya a inda ya kamata. Adebayo yace Wallayi Sir da an canza manashi kawai. Mr. Kallah yace kada ka damu da kanshi zai nemi canjin wajen aiki, yana nema kuma zamu masa sai mu kawo wanda mukeso. Umar yace shikenan ma mun huta. Alhaji Marusa yace idan komai ya kammala kowa zaiji sak'o a asusunsa, Peter kunyi kok'ari dole wannan karon ku samu k'ari. Murmushi Peter yayi yana fad'in mungode Oga. Haka suka cigaba da tattaunawa suna shagalinsu. *** *Alhaji Marusa da Mr. Kallah*, *menene labarin asalin su*? Ur's. Nabeelert Lady🖋[3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.* 1⃣2⃣ *Alhaji Job'e Marusa* d'an asalin garin *Mayo Barwa* ne, cikekken bafullata ni ne, duk cikin zuri'arsu shi kad'ai ne yayi karatun boko, shima wani Yayan Mahaifinsa *Bukar* ne ya d'aukeshi ya koma wajensa da zama a kudu, sana'ar Yayan Mahaifinsa shine siyar da Fata, babban dila ne kuma hamshakin mai kud'i ne, be tab'a haihuwa ba hakan yasa ya d'auki Alhaji Marusa ya koma dashi gidansa. Baffa Bukar yana da mugun son kanshi, daga matansa sai masu masa fadanci kawai yake sakar ma bakin aljihunsa, sannan mugun mutum ne, sam baya so yaga wani ya fishi, zai iya kashe rai akan abun duniya, kuma be yarda da asara ba, zamansa a kudu ya k'ara masa rashin imani, yana da babban matsafi wanda yake masa aiki, yafiso akoda yaushe ya kasance shine a sama. Haka Alhaji Marusa ya taso duk wani bakin hali na Baffansa ya d'aukeshi, a k'asar waje yayi karatunsa acan ya kara koyo mugayen halaye, sam ibada bata dameshi ba sai yaga dama, hatta da azumi ciyarwa yakeyi wai ulcer yake da ita. Bayan daya kafu da kanshi sai Baffansa ya basa babban jari ya fara shigo da kaya daga k'asashen waje, cikin lokaci k'ank'ani Allah ya bashi abinda yake nema, hakan yasa ya tashi ya koma Lagos da zama, gidan da yake zaune kanshi abun kallo ne, domin shine ake kira da Aljannar duniya, dan Alhaji Marusa mutum ne mai son jin dad'i. Wani zuwa da yayi k'asar waje acan ya had'u da wani abokinsa da sukayi karatu mai suna *Herry*, bature ne, sana'arsa siyar da miyagun k'wayoyi, bayan daya samu labarin Alhaji Marusa yana kasuwancin kai kaya k'asar najeriya sai ya bashi shawarar ya fara siyar da kwayoyi zaici riba sosai. Jin harkar k'aruwa yasa Alhaji Marusa ya amince, nan ya fara saka miyagun kwayoyi acikin kayan da yake shigo dasu, yana shigo da shaddodi, su taliya da sauran kayan masarufi, acikin kwalayen ake saka miyagun kwayoyin ta yanda za'aga kamar kayan gaskiya ne a ciki, hakan yasa da wuya a kama kayan Alhaji Marusa da laifi, musamman da yake saye manyan kwastam da k'ananan su. Sam beda matsala da bodar Lagos shiyasa yafi son shigo da kaya tanan, matarsa d'aya da yaransa biyu yasa aka cire mata mahaifa dan baya son haihuwa, ko kauyensu baya zuwa sai dai yayi masu aike, haka baya son wani nashi yazo inda yake, danshi be yarda da jininsa ba yafi son mutanan gari, acewarsa besan su ba idan sukayi masa abu zai iya masu rashin mutunci. Brr. Barau tun yana k'aramin lauya yake masa aiki har ya zama babba, ya kware a harkar aikinsa, domin Allah yayi masa wata baiwa, ya iya tsara zance, idan yaso maida k'arya gaskiya babu wanda zai iya gano gaskiya, hakan yasa yayi saurin d'aukaka domin lauyen manyan mutane ne. Zuwan Alhaji Maiwada bodar Lagos yasa Alhaji Marusa ya fara sanin meye damuwa akan shigo da kaya, gashi Baffansa ya jima da rasuwa da tuni ya kai sunan Alhaji an d'aure bakinsa, ganin zai caza masa kai yasa ya had'a masa wannan sharrin. Shi da Mr. Kallah aminan juna ne, sunfi shekara goma sha atare, kowa yasan sirrin kowa, kuma Mr. Kallah shine yake goya masa baya a duk wani abu da zaiyi. *** *Garba Bala* shine asalin sunansa, bamaguje ne daya fito daga garin *Malumfashi* cikin kauyen *K'afur*, yayi karatun boko sosai, yana da masifar kok'ari, ya rik'e muk'amai da yawa daga baya ne ya maida sunansa *Mr. Kallah*, idan ka ganshi bazaka tab'a cewa bamaguje bane, zaka masa d'aukar cikekkan musulmi, hausa abakinsa dama gadonsa ce, domin kowa yasan yanda maguzawa suke jin hausa, rashin hasken musulunci daya rasa shine ya banbantasa da musulmai, amma acikinsu yake komai, shigarsa da mu'amalarsa duk irin na musulmai ne. Mr. Kallah yana da son kud'i, matuk'ar zaka yaga masa zai iya tsaya maka, sai dai yana da matuk'ar wayau, domin shi mutum ne mai aiki da kwakwalwa, duk yanda zaiyi abu baya bari aganosa, shiyasa a zahiri mutane suke masa kallon mai gaskiya da amana, wannan halin nasa yaja masa k'arin matsayi sosai, wanda a yanzu haka shine shugaban kwastam na k'asa, a Abuja yake zaune da matarsa ta farko, matarsa ta biyu kuma tana Lagos, gidansa na Lagos babban gida ne, waje guda ya ware ya gina katafaren ofis, idan yazo hutu anan yake aikinsa danshi mutum ne wanda baya son zaman banza. Duk wani mai kasuwanci matuk'ar yana shigo da miyagun kaya to yana da alak'a da Mr. Kallah, saboda yana goya masu baya yasa suke cin karensu babu babbaka, sai wanda yaso yake ma k'arin matsayi, idan kuma yaga baka binsa yanzu zai canza ka da wani. Alokacin da aka kawo sunan Alhaji Maiwada akan abashi shugaban kwastam na lagos yaso ya hana saboda yasan halinshi, amma gudun maganar mutane yasa ya amince dashi, sai gashi yazo yana caza masu kai. Wannan shine labarin *Mr. Kallah* da *Alhaji Marusa* ***** ***** Washe gari Alhaji Maiwada ya tashi da k'arfinsa, domin yaji sauki sosai, zugin da yake ji a zuciyarsa ma yayi sauki sai damuwar da baza'a rasa ba, bayan da likita yazo ya aunashi yaga jinin ya sauka. Zaune suke a falo bayan sun gama karyawa. Alhaji Mansur ne ya kalli Alhaji yana fad'in naji dad'i dana ganka katashi ahaka yau, dama kuma haka akeson bawa ya kasance mai tawakkali da yarda da K'addara, Alhaji nafi kowa saninka, nasan abinda zakayi da wanda baza kayi ba, kada ka damu da kallon da mutane zasuyi maka, Allah yasan baka aikata abinda akace ba, kuma shine zai saka maka akan zaluncin da akayi maka, dan haka kada kasa damuwar komai aranka, ka d'auka wannan dukiyar Allah ne ya baka kuma gashi zai amshe abunsa, dan haka kada kaji komai zamu biyasu abinda kotu tace, insha Allahu sanadiyar wannan kud'i da zaka basu sune zasu zamo silar lalacewar tasu dukiyar. Hannu yasa a aljihu ya ciro wata takarda, bud'eta yayi yana fad'in d'azu aka aikota daga hannun kwamishna, sunzo sai suka ba Madu, iya yawan kud'in da za'a biyasu ne aka rubuta aciki, kuma wata guda suka bada idan yacika ba'a basu ba zasu amsa da kansu. Naira miliyan saba'in yace ya kashe akayan da suka b'ace hada kud'in daya kashe na zuwansu nan. Aje takardar yayi yana dafe kai. Murmushi Alhaji Maiwada yayi yasa hannu ya d'auki takardar yana kallo. Kuka kawai Ummun Ra'eez takeyi jin makudan kud'in da zasu biya. Gyara zama Alhaji yayi yana fad'in Alhaji Mansur zansa wannan gidan nawa akasuwa. Da sauri Alhaji Mansur ya kalleshi jin abinda ya fad'a. Jinjina kai yayi yana fad'in wallahi gidan nan ya fitar mani arai, da nasan gina gidan nan zai jawo mani irin wannan zargin bazan tab'a ginashi ba, dama na ginashi ne saboda muji dad'in rayuwa nida iyali na, sai gashi hakan ya jawo mana tashin hankali, da zan samu wanda zai bani kud'in gidan nan ayanzu wallahi bazan sake kwana aciki ba. Girgiza kai Alhaji Mansur yayi yana fad'in baza'ayi haka ba, dama abinda suke so kenan su rabaka da wannan gidan, idan sukaga kasa shi akasuwa burinsu zai cika, dan haka bazaka siyar dashi ba, zamusan yanda za'ayi. Murmushin takaici Alhaji Maiwada yayi yana fad'in kayi hakuri Alhaji Mansur, ina d'aukar shawarar ka, amma a wannan karon ko Alhajina ne yace kada na siyar da gidan nan bazan jishi ba, kwanciyar hankalina shine nabar gidan nan, na ciresa araina hakan zaisa na samu natsuwa. Cikin kuka Ummun Ra'eez tace dan Allah Abban Labiba ka barsa ya siyar dashi, kasashi ya aje har aikin mu koma kano da zama wallahi bana son garin nan. Hannu Alhaji yasa ya kamo hannunta yana fad'in kada ki sake fad'ar haka Bilkisu, idan na aje aikina kamar ban yarda da k'addara bane, kuma zuciyarsu zatayi sanyi tunda sun sa na aje aikina, idan kinga na bar aikina to takardar sallama aka bani, amma matuk'ar basu bani ba to mutuwa ce zatasa nabar aikina sai kuma idan lokacin aje aikin yayi, dan haka matuk'ar kina sona ki tayani cin wannan jarabawar da Allah ya d'ora mani. Jinjina kai tayi tana goge ido tace shikenan Abbun Ra'eez, na amince ka siyar da gidan, ina maka addu'a akan Allah yayi maka sakayya akan zaluncin da akayi maka, kuma ya baka ikon cigaba da aikin ka. Alhaji Mansur yace amin, nima na amince da abinda kace, bakomai Allah ya shige mana gaba. Alhaji Maiwada yace amin, ka kira DPO ka sanar masa zan siyar da gidana, nasan Alhaji Marusa ne zai siyeshi kaga sai ya fad'a masa, akira dillalai suzo suyima gidan kud'i, idan na biyasu zan sayi wani gidan sai mu koma can da zama. Kwalla Alhaji Mansur ya goge yana fad'in Allah ya saka maka. Alhaji yace amin. **** **** Cikin kwana biyu aka gama komai, dillalai suka yima gida kud'i akan naira miliyon d'ari biyu, tayin farko wanda Alhaji Marusa ya aiko yace ya siya, haka aka gama komai aka mik'a masa takardun gida shedu suka sheda, dama acikin kwana biyun Alhaji ya kwashe kayansa, a unguwar *APAPA* ya samu wani gida mai kyau kuma aka sayar masa akan naira miliyon tamanin, nan take ya amince. Bayan da aka mik'a masa kud'insa agaban 'yan sanda da hukumar bincike sukaje shida Alhaji Mansur da Malan Sani suka biya Alhaji Marusa naira miliyon saba'in da biyar da ya buk'ata, bayan da aka gama cike-cike suka bar wajen. Kud'in gidansa ya biya sauran kud'in yasa a banki. Alhaji Mansur gudummuwar milayan d'aya ya bashi amma da kyar ya amsa, haka abokinsa Alhaji Usman wanda ya tab'a kwatoma kayansa shima sai da ya bashi dubu d'ari biyar, haka mutanan da suke mutunci suka rik'a kawo masa gudummuwa. Bayan sun maida kayansu zuwa sabon gidansu suka gyara ko ina, gida ne mai kyau, sai dai ba me bene bane, bangare biyu ne, wanda d'ayan bangaren yake kamar d'akunan maza, sai babban b'arin mai d'auke da babban falo, sai kicin mai had'e da sito, sai wani d'aki akusa da kicin mai d'auke da band'aki wanda yake amatsayin na masu aiki, daga can kuma zaka shiga wata hanya mai d'auke da d'akuna biyu dukkansu da band'aki aciki, wannan shine b'angaren matar gidan, daga gefen falo akwai d'aki wanda shine na maigida, sai wajen teburin cin abinci. Daga waje kuma akwai d'akin mai gadi sai harabar gida da wajen aje motoci sai rumfa. Sosai Ummun Ra'eez taji dad'in gidan dan ya burgeta, haka kawai ta tsinci kanta cikin farin ciki duk damuwar da take ciki sai ta tafi. Haka suka gyara komai dama gidan besha wahala ba, Ladi tasa kayanta a d'akin ta, kayan Ra'eez kuma aka aje masa a d'akin da yake na kusa da Ummunsa. ** Bayan kwana biyu Alhaji Mansur yayi masu sallama ya koma yana mai sake kwantar ma Alhaji Maiwada da hankali, haka ya tafi cike da tausayin abokinsa. Malan Sani yaji dad'i da suka samu gida a wannan unguwar saboda baya so ace sun bar unguwa mai kyau sun koma marar kyau, sai gashi itama wannan d'in tana da kyau. Tunda wannan abu ya faru Alhaji be lek'a ofis ba, yana jiran yaji halin da yake ciki, babu inda yake zuwa sai masallaci, sosai hankalinsa ya kwanta dan ya dage da addu'a hakan yasa Allah ya yaye masa damuwar da take ransa yasa masa dangana, duk yanda yake tunanin mutanen gari zasu yaya tashi sai Allah ya kwantar da abun, wanda ba haka su Alhaji Marusa suka so ba. Suna kwance ad'aki ya samu kira daga Mr. Kallah, bayan sun gaisa ya sake jajenta masa akan abinda ya faru, anan yake fad'a masa gobe ana nemansa a can abuja. Alhaji Maiwada yace nagode kuma zan zo akan lokaci. Sallama sukayi ya kashe wayar. Ajiyar zuciya ya sauke yana fad'in ya Allah ka zab'a mani abinda yafi alkhairi akan wannan aikin. Hannunsa Ummu ta kamo tana fad'in nemanka ake ko? Kai ya d'aga mata. Murmushi tayi tana fad'in nasan mijina mai tawakkali ne, kuma nasan zaka amshi duk abinda yazo maka da hannu biyu, dan haka kada ka damu da kiran da suke maka, idan su basa tare da kai ni da Ra'eez muna tare da kai har abada. Murmushi ya saki wanda har hak'oransa sai da suka fito, sake matseta yayi yana fad'in nagode Uwar gidana, ina mai tabbatar maki matuk'ar suka barni akan aikina sai na zaluko gaskiya, ko bayan raina sai duniya tasan cewar bani da laifi, sai Allah ya haska su kowa ya gansu. Ummu tace amma kayi komai a hankali kada su sake maka wani sharrin. Alhaji yace kada ki damu, wannan abun da ya faru alkhairi ne a wajena, domin ya k'ara haska mani duhun da nake ciki, ayanzu zasu gane basu da wayau, domin zanyi aiki ta k'ark'ashin k'asa. Murmushi tayi tana fad'in nasan zakayi fiye da haka. **** **** Cike babban d'akin taron yake da manyan mutane masu babban matsayi, bayan da aka gama tattaunawa kowa ya fad'i ra'ayinsa akan Alhaji Maiwada, wasu suna ganin ayi masa canjin wajen aiki tare da rage masa matsayi, wasu suna ganin takardar sallama ce ta dace dashi domin yaci amanar aikinsa, idan aka barshi hakan zai bama wasu dama su aikata irin abinda yayi ko fiye da haka, wasu suna ganin a bashi takardar jan kunne. Bayan da kowa ya gama kawo tasa shawarar Mr. Kallah ya mik'e yana fad'in naji duk abinda kuka fad'a, kuma a dokar tsarin aiki idan aka kama mutum da laifi abu na farko da akeyi ana duba file d'insa, idan har ba'a tab'a samunsa da wani laifi ba to ana masa uzuri, acikin mu nan babu wanda bai san irin tsarin aiki na Alhaji Maiwada ba, tun yana k'aramin ma'aikaci ake yabon iya aikinsa, yarik'e matsayi kala-kala ba'a tab'a samunsa da karb'ar cin hanci ko so d'aya ba, har kawo warsa wannan matsayin ba'a tab'a kamasa da wani laifi daya sab'a ma doka ba, kuma wannan abu daya faru ina ganin kamar akwai lauje cikin nad'i, koma menene Allah ne yasan gaskiya, be kamata ace mun rufe ido munyi masa haka ba, idan mutum yayi ba dai-dai ba sai ajuya a kalli aikin kwarai nashi sai ayi masa hukunci dashi, dan haka ni dai a tawa shawarar ina ganin aja masa kunne a bashi dama ta biyu, kuma ya tsaya a aikinsa, kada yarik'a shiga aikin wasu, idan ya kiyaye shikenan, idan kuma aka sake kamashi sai ayi masa hukuncin daya dace. Bayanin Mr. Kallah yayi ma mutane da dama dad'i, kuma sun gamsu da bayaninsa, nan take aka amince da shawararsa. Bayan sun gama rubutu aka rufe taro. Alokacin Alhaji Maiwada yana zaune a inda aka tanadar ma baki dan ba dashi akayi taron ba, bayan sun fito Mr. Kallah yayi kiransa suka shiga ofis, su ukku ne a ofis d'in. Bayan ya gama karanto masa abinda suka yanke anan kowa yayi masa tashi nasihar. Bayan sun fita ya rage su biyu Mr. Kallah ya dubeshi yana fad'in kayi hak'uri haka aikin kwastam ya gada, kafin nazo wannan matsayin nasha wahala sosai, matuk'ar kace zakayi gaskiya dole karik'a had'uwa da sharrin mutane, shawarar da zan baka ka tsaya akan aikin ka, kuma duk abinda zakayi karika tanadar kwakkwarar sheda, sannan ka rage shiga harkar Alhaji Marusa dan zai iya b'atar da kai. Alhaji Maiwada yace bakomai zan kiyaye, nagose sosai. Mr. Kallah yace bakomai. Kud'i ya d'auko dubu d'ari biyar ya mik'a masa yana fad'in ga tawa gudummuwar. Alhaji yace kabarshi Mr. Kallah nagode. Murmushi Mr. Kallah yayi yana fad'in sunyi kad'an ko? Girgiza kai Alhaji yayi. Mr. Kallah yace to ka amsa. Amsa yayi yana masa godiya, haka sukayi sallama ya fito yana jinjina kirki irin na Mr. Kallah. Mr. Kallah kuwa yana fita yayi murmushi, ya rasa ya akayi duk cikin ma'aikatansa yake jin nauyin Alhaji Maiwada, sosai yake masa kwarjini, duk da abinda yayi masa yayi ne dan ya k'arama kansa yarda awajen mutane amma ya rasa dalilin da yasa baya so Alhaji Marusa ya cutar dashi. Wayarsa ce tayi k'ara hakan yasa ya dawo daga tunanin da ya keyi. **** *** Haka Alhaji Maiwada ya koma bakin aikinsa, sosai ya canza daga yanda suka sanshi, babu ruwansa da kowa, abinda ya kamata shi yakeyi, kowa ya raba masa wajen aikinsa, kuma idan kayi aiki dole ka kawo rahoto ya duba, duk abinda ya faru sai anzo an sanar dashi, haka duk wad'an da zasu duba kaya dole su duba su da kyau, kuma dokar amsar cin hanci tana nan, sai dai ba ruwansa da kayan Alhaji Marusa, idan sunzo ma ba shine yake dubasu ba, amma duk da haka ana bincikasu yanda ya kamata, idan akwai abinda aka samu ana cirewa, shima Alhaji Marusan ya rage shigo da miyagun kwayoyi ta bodar Lagos, yace sai abun ya lafa. Adebayo da Umar kowa yaga sun canza, domin hada sabbin motoci suka sake, sosai suke fantamawa, saboda suna cikin kud'i yasa basu damuwa da dokar ansar cin hanci ba. A b'oye Alhaji yasa Abubakar da Moses suna bincika masa abinda yake faruwa, dan wannan abun daya faru yasa Moses yaji tausayin Alhaji, domin yasan wani abun daga cikin abinda su Adebayo sukayi, kawai yayi shiru ne saboda beda sheda, kuma yasan halin Alhaji Marusa matuk'ar ya ganoshi zai iya kashe shi, hakan yasa yaja bakinsa yayi shiru, amma yayi alk'awarin sai ya taya Alhaji sun gano gaskiya koma me zai faru, hakan yasa ya had'e da Abubakar. Ur's. Nabeelert Lady🖋 [3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.* 1⃣3⃣ *Bayan dogon lokaci* Wajen wani abokinsa mai suna *Tayo* Moses yaje domin ya taimaka masa, dan wannan hanyar ita kad'ai zasubi domin su gano gaskiyar komai, dan Moses yayi alk'awarin sai ya taimaki Alhaji saboda yasan abubuwa da yawa a wajen su Adebayo kawai beda sheda a hannu ne. Tayo gurun kamfuta ne, kuma abinda ya karanta kenan. Babu b'ata lokaci ya bama Moses abinda zaiyi amfani dashi, wasu na'urori ya bashi sai yayi masa saitin da wayarsa hada kamfutarsa ta hannu duk ya had'a masa ya nuna masa yanda zaiyi amfani dasu. Godiya Moses yayi masa ya tafi. A ofis d'in Adebayo ya fara zuwa yasa d'aya daga cikin na'urorin da aka bashi, sai yayi kok'ari yasa a cikin motarsa, daga nan yaje wajen da ake duba kaya nan ma yasa guda d'aya, saura d'aya ta rage kuma yana so ya sata a gidan Alhaji Marusa musamman inda yaga yana ganawa da mutane, duk da yana zuwa gidanshi ada yanzu ya rasa ta yanda zaije yasa wannan na'urar, kuma duk tafi sauran muhimmanci saboda yasan a wajen Alhaji Marusa za'afi sanin komai. Shiru yayi yana tunanin abunyi sai ga Abubakar yazo, nan yayi masa bayanin abinda yake kok'arinyi. Abubakar yace gaskiya Moses ka kyauta, tun jiya nake tunanin hanyar da zamubi mu taimaki Alhaji, ashe har ka rigani. Moses yace abinda nakeso shine yanda zan had'a wannan abun agidan Alhaji Marusa. Shiru Abubakar yayi kafin yace akwai maigadin gidansa nasanshi, mai zai hana mu je masa da maganar kila ya amince. Moses yace kasan halin mutane da son kud'i, kada muje muna tunanin yasa yaki sakawa yaje ya fad'ama Alaji kasan dai bazai barmu ba. Abubakar yace kai dai muje, inaji yau ba shine keda aikin kwana ba, idan mun tashi daga nan mu biya ta wajen da yake zama insha Allahu zai amince. Moses yace shikenan. *** Bayan da suka tashi suka nufi wajen da Maigadin Alhaji Marusa yake zama. Yana ganin Abubakar ya saki murmushi yana fad'in kaga kwastam masu gidan kud'i, murmushi Abubakar yayi yana fad'in *Malan Hassan* bazaka dena fad'a mani wannan abun ba ko, ai ma'aikatan banki sune masu gidan kud'i. Malan Hassan yace ai dole na fad'a, kowa yasan kwastam kuna morewar ku domin kunfi masu banki 'yanci. Murmushi yayi anan suka gaishe shi. Malan Hassan yace wannan abokin aikin ka ne? Abubakar yace aikuwa dai Malan Hassan. Zama sukayi Malan Hassan yana fad'in ina shugaban ku bawan Allah? Abubakar yace yanzu muka rabu ya wuce gida, ashe kaima kana tausaya masa? Malan Hassan yace ai dole na tausaya masa domin kowa yasan sharri akayi masa. Moses yace Baba kaima kasan sharri akayi masa kenan? Malan Hassan yace ni ganau ne ba jiyau ba. Dariya Moses yayi yana fad'in Baba me kake nufi haka? Shima dariya yayi yana fad'in Abubakar ya fahimci abinda nake nufi ai. Murmushi Abubakar yayi yana ma Moses bayani. Dariya Moses yayi yana fad'in Baba nima na fahimta yanzu. Abubakar yace wallahi Malan Hassan Alhaji mutumin kirki ne, kawai ya had'u da sharrin su Alhaji ne. Gyara zama Malan Hassan yayi yana fad'in nan wajen babu tsaro ko zamuje cikin motar ku? Da sauri suka tashi domin abinda suke nema kenan. Bayan sun zauna Moses ya kunna wayarsa saboda kada Malan Hassan yazo ya k'aryatasu idan lokacin hakan ya taso. Malan Hassan yace Abubakar Alhaji Marusa da kake gani mugun mutum ne, Allah dai yasa a k'ark'ashinsa zanci abinci shiyasa nake zaune a gidansa har yanzu, duk abinda kukaji ance Alhaji Maiwada yayi wallahi k'arya ne, abu ne wanda aka shiryashi, hatta da kayan da sukace sun b'ace ina tunanin k'arya ne, domin akwai abinda nake gani. Abubakar yace Malan Hassan kaima baka da tabbaci kenan? Malan Hassan yace tunda ban gani da idona ba bazan ce ba, amma akwai abubuwan da nake gani agidanshi. Mr. Kallah da kuke gani abokin Alhaji ne sosai, domin yana yawan zuwa gidansa idan yazo Lagos, sannan akwai wasu mutane biyu suma irin aikin ku sukeyi ina yawan ganinsu, d'aya bahaushe ne, d'ayan ko hausa bayaji sosai, sai wasu manyan mutane da ganinsu kasan mugaye ne, tunda nake ganinsu hankalina bai kwanta ba, babu yanda za'ayi naje naji abinda suke fad'a saboda acan wajen hutawarsa suke zama, amma tabbas sune suka k'ullama Alhaji Maiwada wannan sharrin. Abubakar yace muma abinda muke tunani kenan, akwai abinda mukeso asa mana a wajen hutawarsa, babu wanda zaiyi mana wanan aikin idan ba kai ba Malan Hassan, shine nace muzo ko zaka taimaka mana domin Allah. Malan Hassan yace kome kuke so zanyi maku domin nima nayi aikin lada. Na'urar Moses ya fiddo yana masa bayanin inda suke so yasa. Malan Hassan yace dan wannan ai mai sauki ne, kawai ku koya mani yanda zan sata. Nan Moses yashiga koya masa yanda zaisa ta, bayan sun gama Malan Hassan yace gobe nine zanyi aikin kwana, kuma agoben zanje na saka kada ku damu, Allah zai taimaka mana, idan na gama zan fad'a maka Abubakar. Sosai sukaji dad'in abinda yayi masu, kud'i Abubakar ya ciro ya mik'a masa. Malan Hassan yace haba Abubakar, dan zanyi maka aiki sai ka bani kud'i? Abubakar yace ba biyanka nayi ba kawai kyautace. Amsa Malan Hassan yayi yana fad'in nagode sosai. Sallama sukayi masa suka tafi. *** Washe gari suka samu Alhaji a ofis sukayi masa bayanin abinda ake ciki. Shiru Alhaji yayi yana tunanin sunan Mr. Kallah da aka fad'a, girgiza kai yayi yana fad'in gaskiya ban yarda akwai sa hannun Mr. Kallah aciki ba, nasan dai abokin Alhaji Marusa ne, kila wani abun yake kaishi gidan amma bana tunanin zai iya aikata mani haka. Moses yace Sir, kada kayi saurin yanke hukunci, mujira ai gaskiya zata nuna kanta. Jinjina kai Alhaji yayi yana fad'in nagode sosai. Abubakar yace haba Alhaji wannan ba wani abu bane, insha Allahu gaskiya zata fito. Alhaji yace wallahi ba saboda kud'ina su dawo nakeso a gano gaskiya ba, ina so na wanke kaina awajen mutane, sannan kowa yasan abinda Alhaji Marusa yake aikatawa. Moses yace zamu kamasu ne zasuci Ubansu. Murmushi Alhaji yayi yana fad'in nagode. A daren ranar Malan Hassan ya kira Abubakar ya fad'a masa ya gama komai. Abubakar yace nagode Malan Hassan Allah ya bamu sa'a. Yace amin. **** **** Haka rayuwa tacigaba da tafiya kowa yana aikinsa, duk hutu Ra'eez yana zuwa yayi sati d'aya ya koma saboda islamiya, alokacin da yazo sai da yayita tambayar dalilin da yasa suka canza gida. Ummunsa ce tayi masa dabara tace b'arayi suka matsa masu shiyasa suka tashi. Da wannan suka rufe bakinsa. Tun bayan da Alhaji Marusa yayi ma Alhaji Maiwada wannan abun sai ya fara samun matsala a kasuwancinsa, cinikin da yakeyi sosai ya fara raguwa, ga yawan asara da yakeyi a wajen kawo masa kaya, amma da yake ya tara hakan yasa dukiyarsa bata girgiza ba, sai dai duk wacce ya fitar aka saro kaya da wuya ta dawo fiye da yanda take. Haka su Umar da Adebayo komai ya fara lalace masu, mata da shaye-shaye ne suke cinye masu kud'i, duk yawan kud'in da suke samu basa masu afki. Alhaji Maiwada kuwa tamkar anasa ma dukiyarsa taki, sosai yake samun bud'i, sai dai duk bud'in da yake samu sai yaji tsoron ya sayi kadara a Lagos, hakan yasa ya turama Alhaji Mansur kud'i ya saya masa gidaje a kano ya zuba masa haya, sannan ya bud'ema Ra'eez asusu a banki yana zuba masa kud'i a ciki dan baya son yarik'a tara kud'i a bankinsa dan ya tsorata da abinda ya faru. **** **** Dogon hutu su Ra'eez suka samu saboda sun zana jarabawa ta aji ukku zasu shiga babban aji idan sun koma, hakan yasa ya rok'i Abbunsa akan ya barshi yazo ko wata d'aya yayi tunda hutun dogo ne. Alhaji yace Ra'eez wata d'aya yayi maka yawa, Labiba zata wuceka a islamiya da sauran 'yan ajinku, kuma kaga shirye-shiryen sauka kukeyi. Kuka Ra'eez yasa mashi yana rokonsa. Ummu ce tasa baki tana fad'in tunda Ra'eez ya taso baka tab'a zaman sati biyu dashi ba, baka tsoron rashin mu ya tab'a karantunsa? kabarshi tunda har ya fito ya rok'a yakamata muyi masa wannan alfarmar, karatu ba wani abu bane tunda yana da kok'ari zai iske su, idan yazo nan bazai rik'a fita yawo ba sai yarik'a karatu. Murmushi Alhaji yayi yana fad'in shikenan Uwargida na amince, nima inaso ya zauna akusa dani, rayuwar Lagos d'ince take bani tsoro shiyasa bana son yazo yayi rayuwa acikinta, nafiso sai ya kammala karatunsa yayi hankali kafin yazo muzauna. Murmushi tayi tana fad'in nagode. Alhaji yace Ummun Ra'eez nifa ban yarda dake ba, naga kamar kin canza kwana biyu anya babu ajiyata kuwa? Dariya tasa ta rufe fuskarta. Alhaji yace wallahi bazan iya hakura ba tashi muje asibiti aduba idan ma babu komai duk zan gani. Dariya tayi tace dan Allah ka barni bana son tashi. Mikewa yayi yana fad'in abu mai sauki bara na d'auke ki. Rik'eshi tayi tana fad'in zan fad'a maka. Zama yayi yana fad'in to inajinki. Duk'ar da kai tayi tana fad'in maganarka gaskiya ce, Ra'eez zai samu K'anwa ko K'ani. Wani irin farin ciki ne ya lullub'e Alhaji, rungumeta yayi yana fad'in narasa bakin magana, Allah yayi maki albarka Bilkisu, tashi muje a duba aga ko wata nawa ne. Tashi tayi tana fad'in tunda kace sai anje muje. Suna zuwa asibiti aka gano cikin watansa ukku, sosai yayi murna nan suka koma gida. Waya ya d'auka ya kira Alhaji Mansur yana masa albishir. Sosai sukayi farin ciki, anan Alhaji yake fad'ama Alhaji Mansur Ra'eez zeyi hutun wata d'aya anan idan yazo. Alhaji Mansur yace wannan yayi dai-dai, amma idan yazo yarik'a karatu bana son a wuceshi. Alhaji yace insha Allah. **** *** Tunda Ra'eez yazo baya zuwa ko ina, iyakar yawansa Malan Sani ya kaishi gidansa wajen Rumaisa wacce yanzu tayi wayau tana a aji ukku firamare, duk lokacin da yaje yana koya mata karatu, idan suka gama Malan Sani ya maidashi. Sosai yake karatunsa, inda bai gane ba ya tambayi Ummunsa ko Abbunsa, zuwansa hutu suka k'ara shakuwa da Abbunsa, koda yaushe suna tare, yana dawowa ofis suke zama suyi ta fira, wasu abubuwan haka nan Alhaji yake fad'a masa duk da yasan wayonsa bazai d'aukesu ba, amma sanin natsuwar Ra'eez yasa Alhaji yake fad'a masa komai nasa. Lokacin da hutu ya k'are haka suka had'a masa komai shida Labiba, alokacin Alhaji ya samu hutu sai suka tafi gaba d'aya kano. Sosai Maman Labiba taji dad'in zuwansu ita da Mijinta. Satinsu biyu a Kano sannan suka koma Lagos cike da kewar juna. Haka Ummun Ra'eez ta aika ma Maman Rumaisa da tsaraba mai yawa, sannan ta aika Malan Sani yaje ya d'auko Ladi, itama ta samu tsaraba sai godiya takeyi. **** *** Dube-dube Malan Hassan yakeyi a wajen daya aje na'urar da su Abubakar suka bashi amma be gani ba, mamaki ne ya kamashi ganin inda ya aje abun babu komai a wajen. Motsin da yaji ne yasa shi saurin juyawa, Alhaji Marusa ya gani da wani mai aikinsa inyamuri. Jikin Malan Hassan ne ya fara rawa ya fara kok'arin barin wajen. Alhaji Marusa yace Malan Hassan a iya sanina aikin ka agidan nan shine gadi, ko mai kula da tsaftar wajen nan baya aiki da dare, sai gashi kai kuma kazo wajen da dare bayan nasan bakwa zuwar mani cikin gida, ko dai wani abu ka aje kake nema? Jikin Malan Hassan yana rawa ya fara matsawa da baya. Kallon wanda suke tare Alhaji Marusa yayi hakan yasa kawai yaje ya damko Malan Hassan, juyawa Alhaji Marusa yayi ya nufi wani b'angarenashi da yake gefe, haka mutumin ya d'auki Malan Hassan suka nufi wajen. *** *** Mamaki ne yayi ma Alhaji Maiwada yawa ya kasa furta komai saboda abinda idanuwansa suke gani da abinda kunnuwansa suke ji. Zaune suke a ofis d'in Alhaji bayan an tashi daga ofis, Moses ne da Abubakar da Alhaji suke kallon abinda Moses ya tara a kamfutarsa wanda ya d'auka. *** Abinda yafi basu mamaki d'aukar da akayi wajen da ake duba kaya, wani kwali ne aka bud'e na taliya amma ba taliyar bace aciki duka, rabin kayan miyagun kwayoyi ne aciki hada hodar ibilis. Adebayo ne yake waya da Alhaji Marusa yana fad'in kayan sunzo komai lafiya, bayan ya gama ya kalli Umar yana fad'in Alhaji Marusa yace a fitar da kayan yanzu kada abari Sir, ya dubasu tunda anci sa'a bayanan. Umar yace ai tunda Alhaji Marusa yayi ma Alhaji hankali yanzu ya sakar masa mara, kai ko mutum ya rasa katafaren gida irin wannan ai dole ya tsorata, gaskiya Alhaji Marusa bai da imani, gashi dai ya kulla masa sharri kowa ya yarda ya shashi asarar gida, kuma ya saye gidan sannan ya cabke kud'insa ga kayansa babu wanda yayi ciwon kai muma an raba damu. Adebayo yace Yanzu wannan motar kad'ai ta rage mani acikin kud'in da aka bamu na sallama, kason Mr. Kallah dana Brr. Barau sunfi yawa gashinan har yanzu suna cin abunsu. Umar yace baka san kason wanda yake da yawa ba, Mr. Kallah da Brr. Barau ba sune masu kaso mai yawa ba, Babban Yallab'ai nashi yafi nasu yawa ai, domin kasan shi baya wahala amma ana bashi kasonshi a duk lokacin da akayi irin wannan harkar. Adebayo yace wai Alhaji Marusa kake nufi? Umar yace bashi ba, wannan ai shine Oga kwata-kwata, babban Yallab'ai nake nufi. Dariya Adebayo yayi yana fad'in wallayi Umar baka da kyau, har na manta dashi ai, kasan shi baya son asan dashi sai dai yaji kud'i kawai. Umar yace gaskiya muje mu samu Alhaji Marusa ya k'ara mana wani abu asusuna yayi k'asa, kaga dai yanzu bama samun cin hanci. Adebayo yace idan aka d'auki kayan kawai muje. Hannu Alhaji Maiwada yasa yana goge zufar da ta zuba masa, *** canza wata d'aukar Moses yayi sai ga Adebayo zaune a mota yana waya da Mr. Kallah.... Yallab'ai wallayi Alhaji Marusa ne yace a fad'a maka anjima kayansa zasu iso kuma wannan karon yace rabin kayan ba wanda ya saba kawowa bane, gashi ta bodar mu yace ashigo dasu kuma yau Sir, yana ofis gashi Abubakar ne yake da aiki yau, d'azu yakira baka d'auka ba shine yace idan na sameka na fad'a maka saboda kayan wannan karon masu tsada ne sosai kuma za'a samu riba, shine yace ka d'auke Abubakar daga wajen shida Sir, hakan ne zaisa a tafi da kayan ba tare da an duba ba.... E, yauwa, sauran ma'aikatan nasan basu da matsala. Toshikenan mun gode. Murmushin takaici Alhaji Maiwada yayi domin ya tuna ranar da Mr. Kallah yayi masa waya akan suje Abuja shida Abubakar akwai abinda zasuyi, ashe dama wannan harkar zasuyi. Runtse ido yayi yana jin takaici da kayan suka samu wucewa, ya tabbata yanzu sun gama rabar dasu ga dilolinsu. *** 'Dayan d'aukar Moses ya kunna wadda take a gidan Alhaji Marusa. Fitowar farko Alhaji Marusa ne da Brr. Barau, Mr. Kallah sai wani babban mutum wanda ya juya baya ba'a ganin fuskarsa. Zaune suke a saman kujeru gabansu cike da kayan motsa baki. Yanda yaga suna nutsuwa suna nuna ladabi ga wannan babban mutumin ya tabbatar masa koma waye mai babban matsayi ne. Muryar Alhaji Marusa sukaji yana fad'in Brr. Ina kara maka godiya akan kok'arin da kayi mana a wancan karon na shari'ata da Alhaji Maiwada, wannan karon ma akwai wata shari'a nida wani abokin kasuwancina, kayansa na cinye kuma ya biyani, to nawa ne bansan ya akayi suka salwanta ba shine naji bazan iya biyansa kud'insa ba sai kawai nace ai rabin kud'in ya bani yace idan na bashi kaya zai cika mani, shine yanzu yake fad'in zai shigar da k'ara, kuma gaskiya kud'in da yawa, ina dasu kawai bana jin zan iya biyansa shiyasa nake son a juya maganar, domin jiya na bashi rabin kud'in kuma na d'auka lokacin da nake bashi. Muryar babban mutumin sukaji yana fad'in wannan ba wani abu bane na tada hankali, nasan Brr. Barau zai iya da wannan matsalar kawai ka bar masa komai. Brr. Barau yace Yallab'ai duk abinda kace angama ai. Mr. Kallah yace Alhaji Marusa baka da kyau akan kud'i. Alhaji Marusa yace kud'i ai dole muso su, nifa duk yawan kud'ina banki su linka so goma ba, shiyasa nake so ka d'auke mana wancan jarababben Maiwadan ko harka zata k'ara bud'ewa. Mr. Kallah yace kwantar da hankalin ka k'arshen shekarar nan zan canza masa wajen aiki, gara ya dawo kusa dani kaga hankalin mu zai kwanta. Dariya sukasa gaba d'aya. *** Wuce wajen Moses yayi, sauran d'aukar duk bata da amfani, wucewa yayi tayi har yazo wani waje, sai kawai sukaga wani babban mutum da ganinsa mai gadin Alhaji Marusa ne, tsaye yake a wajen yana ta dube-dube yana kallon agogon hannunsa wanda suke jin k'arar harbawarsa, da alama wani abu yake nunawa, can kuma sukaji yana fad'in kemera kuma anan? Nasan dai ba Alhaji bane yasata domin da ya sanar dani, hannu sukaga yasa a wajen sai kawai sukaga hoton ya d'auke. Hannu Moses ya tafa yana fad'in kassh! Wannan banzan ya lalata mana. Zama yayi yana cije baki. Abubakar yace bakomai mun samu abinda muke so, domin ko wannan kad'ai ya ishe mu sheda. Ajiyar zuciya Alhaji yayi yana fad'in kwashe su duka ka had'a mani a (Flash) in tafi dasu akwai abinda nakeso nayi, dole sai ancire abubuwa marasa amfani abar masu amfani kafin mu gabatar dasu, bana so na bar maka kayi aikin kada tsautsayi yasa wani ya gani, amma idan naje dashi gida nasan acan yafi tsaro domin ni kad'ai ne zanyi aikin. Moses yace yanzu kuwa Sir, nima bana son su zauna a wajena saboda wallayi tsoro nakeji, zan turasu duka sai na goge komai. Dariya Abubakar yayi yana fad'in kai dama ai sarkin tsoro ne. Kallonsu Alhaji yayi yana fad'in muryar wannan babban mutumin tayi mun kama da ta wani, naso an d'auko fuskarsa domin koma waye babba ne a k'asar nan, lallai duniya babu gaskiya, amma koma waye idan aka mik'asu kotu zasu fad'esa. Tabbas na tuna shari'ar da Alhaji Marusa yayi da abokin kasuwancinsa har akace shine yayi nasara, ashe dai shine beda gaskiya, lallai Brr. Barau mutumin banza ne, insha Allahu k'arshen su yazo. Bayan Moses ya gama ya mik'a ma Alhaji sannan ya goge komai, haka suka fito, sallama yayi masu Malan Sani ya tuk'a suka nufi gida, a hanya Alhaji yake bashi labarin abubuwan da suka faru, sosai Malan Sani yayi mamakin abinda Alhaji ya fad'a masa, dama shi yana zargin Mr. Kallah kawai Alhaji ne ya yarda dashi. haka suka nufi gida Malan Sani yana bashi shawara akan abinda ya kamata. **** *** A cikin wani d'aki mai duhu aka jefa Malan Hassan, Alhaji Marusa yace ka barsa nan zuwa safiya zamu bincikesa, wannan babban al'amari ne, yanzu zanyi waya dasu Brr. Barau dole suzo asan abunyi domin ina da tabbacin Alhaji Maiwada ne ya aikosa, kuma tabbas ya kalli wannan d'aukar, idan har ya fito da ita ya gama damu, zan iya yin komai domin na kare mutuncin kai na koda ya had'a da wani ya rasa ransa ne. Rufe k'ofar da Malan Hassan yake ciki akayi da makulli kafin Alhaji Marusa ya wuce ciki hankali atashe yana neman wayar Mr. Kallah. Ur's. Nabeelert Lady🖋 [3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.* 1⃣4⃣ A daren wannan rana Alhaji Maiwada bai samu bacci ba, sai da ya gyara komai ya had'ashi kamar a lokaci guda akayi komai, bayan daya gama ya b'oye wani a cikin kamfutarsa dan guda biyu yayi saboda tsaro, cire flash d'in yayi wanda shine zai kai a kotu, k'asan gadonshi ya b'oyeshi saboda washe gari juma'a yafiso sai litinin sannan yashigar da k'ara kotu dan Brr. Kamal yakeso gobe ya samu suyi maganar kafin litinin. ** Malan Hassan kuwa gaba d'aya ya tsure, hankalinsa a tashe yake dan yasan halin Alhaji Marusa, akan dukiyarsa babu abinda bazai iya ba, haka ya zauna yana ta fargabar wayewar safiya dan yana tsoron abinda zai faru, babban tashin hankalinsa Iyalinsa, duk da d'azu yayi masu sallama amma besani ba ko zai koma garesu da rai. Haka yayi ta tunani har barci b'arawo yayi gaba dashi. *** Kasancewar akwai band'aki a cikin d'akin hakan yasa yashiga yayi alwalar asuba, bayan yayi sallah ya zauna yana ta addu'a. K'arar bud'e k'ofa yaji hakan yasa cikinsa ya d'auki k'ara, ga yunwa dama yanaji dan ko abincin dare beci ba. Alhaji Marusa, Brr. Barau, sai wasu majiya k'arfi guda biyu ne suka shigo d'akin. Da sauri Malan Hassan yaja da baya yana cira ido, k'ofar suka jawo sannan Alhaji Marusa ya kunna wuta hakan yasa haske ya gauraye d'akin. Waje suka samu shida Brr. Barau suka zauna, sauran mazan kuma suna tsaye sun hard'e hannuwa akirji. Brr. Barau ne yace yanzu kai tsoho da kai amma ka iya munafurci, da Lucky be gano abinda kayi ba shikenan a jiya kake tunanin d'auke abinda kasa kaje ka kai masu ko? Lallai tsoho ka kira mutuwar ka, dan wallahi bazamu bari ka tarwatsa tamu rayuwar ba tun lokacin mu beyi ba. Cikin rawar murya Malan Hassan yace na roke ku kuyi mani rai, wallahi ina da iyali, basu da kowa sai ni, idan kuka kasheni zasu shiga matsala. Alhaji Marusa yace bakasan darajarsu ba shiyasa ka jefa kanka a cikin matsala, mu da kake shirin tona mana asiri ai bamu da Iyali ko? Wallahi kaji na rantse maka ko Matata na samu da irin wannan laifin sai na kasheta, arayuwata bana had'a dukiyata da komai, kana tunanin idan aka mik'amu kotu bazan rasa komai ba? Dan haka inaso ka fad'a mani *WAYE NE*(Tsohon littafina), ya saka wannan aikin? Shiru Malan Hassan yayi jikinsa na rawa. Brr. Barau yace Alhaji bamu da lokaci, na tabbata wannan abun da sukasa sun riga sun ganshi a can, domin had'awa akeyi, duk abinda yake faruwa anan zasu ganshi a wajensu, muyi abinda yake gaban mu domin muje garesu tun kafin su fitar dashi domin nasan yanzu suna jiran Malan Hassan ya kai masu wannan su had'a dashi. Alhaji Marusa yace Mr. Kallah yana hanya dan munyi waya dashi, kallon Malan Hassan yayi yana fad'in bazaka fad'a ba? Jiki a sanyaye Malan Hassan yace su Abubakar ne da abokinsa Moses, sunyi ne dan su taimaki Alhaji Maiwada, dan Allah kubarni wallahi nayi maku alk'awari zan kwashe Iyalina mu koma garin mu har abada bazan sake dawowa nan ba. Murmushi Alhaji Marusa yayi yana fad'in daga baya kenan, kallon Lucky yayi yana fad'in bana son aji labarin gawarsa. Ficewa sukayi shida Brr. Barau. Malan Hassan duk rokon da yake masu sai da suka kashe shi, nad'eshi sukayi suka d'aukeshi zuwa mota suka nufi bayan gari suka binneshi. *** Abbun Ra'eez ka tasa abinci kana kallo ka kasa ci, kuma na tambayeka kayi mani shiru, anya babu abinda yake faruwa kuwa? Ajiyar zuciya ya saki yana fad'in Bilkisu dole na bar wannan aikin, dole mubar garin nan ina aje aikina, wallahi aikin Kwastam ya fice mani, nayi danasanin fara yinsa. Matsowa tayi tana fad'in haba Abbun Ra'eez ya zaka fad'i haka, tun jiya dama nake ganin ka wani iri, dan Allah ka fad'a mani abinda yake faruwa kila ina da abinda zan taimaka maka dashi. Beyi magana ba ya fara cin abincinsa, sai da yaci rabi sannan ya aje, hannunta ya kama suka nufi d'aki. Bayan sun zauna ya kalleta yana fad'in Bilkisu kicigaba da tayani addu'a domin Allah ya fara haska mani wad'an da suke bibiyata da sharri. Murmushi ta saki tana fad'in kai amma naji dad'i, meya faru? Wayarsa ce tayi k'ara hakan yasa yayi shiru ya d'auka. Alhaji Mansur ne, bayan sun gaisa yake tambayar Alhaji k'arin bayani akan sakon daya tura masa jiya? Gyara zama Alhaji Maiwada yayi yana fad'in wallahi jiya na gama aiki naji bazan iya kwanciya batare dana fad'a maka abun farin cikin da nake ciki ba........ Labarin komai ya fad'ama Alhaji Mansur Ummu tana gefe tayi tagumi tana jin abun al'ajabi. Bayan ya gama Alhaji Mansur yace Allah mungode maka, lallai Allah shine abin godiya, abinda nakeso da kai kada ka bari wannan maganar ta fita, Malan Sani nasanshi beda matsala, sannan kayi magana da Brr. Kamal zuwa litinin zan biyo jirgi domin ayi komai ina nan, wallahi kaji na rantse bazamu yarda ba sai an bi maka hakkin ka, wannan gidan daya anshe maka sai ya maidoshi, sai a maida masa kud'insa. Alhaji yace insha Allahu zanyi yanda kace, Allah ya kaimu litinin d'in. Alhaji yace amin. Sallama sukayi yana fad'in sai ya sake kira. Hannunshi Ummu ta kamo tana fad'in yanzu kam na goyi bayanka akan maganar aje aiki, ana kammala shari'ar nan ka aje masu aikinsu, wannan gidan ma kasayar dashi mu koma Kano da zama, Malan Sani ma nasan zai bimu kawai mutafi dasu bazamu sake waiwayar Lagos ba. Murmushi Alhaji yayi yana fad'in insha Allahu aikina yazo k'arshe, abinda na tara ya ishe ni, Allah ya albarkaci abinda zan samu anan gaba. Ummu tace amin. **** **** Zaune suke su Ukku, Brr. Barau, Mr. Kallah da Alhaji Marusa, magana suke akan yanda zasu b'ulloma wannan abun. Alhaji Marusa ne yace abinda nake gani kawai mu kawar da Alhaji Maiwada. Zaro ido Mr. Kallah yayi yana fad'in kasan abinda kake fad'a kuwa? Brr. Barau yace wannan itace mafita, dole ya mutu kuma mu anshe shedar da take wajensa, hatta da wannan direban nasa bazamu bari ba saboda yasan komai. Girgiza kai Mr. Kallah yayi yana fad'in maganar gaskiya bazan iya aikata kisan kai ba, duk son kud'ina bai kai nayi kisan kai ba, ina laifin mu saceshi tare da matarsa har sai ya kawo mana duk wata sheda da yake da ita. Murmushi Alhaji Marusa yayi yana fad'in Mr. Kallah ka manta waye ni, to Malan Hassan ma da aka ba aikin tuni ya tsufa arami. A zabure Mr. Kallah ya mik'e yana fad'in haba Alhaji Marusa, duk da ban kasance musulmi ba nasan kisa ba abu bane mai kyau, me yayi mana? Sheda ce yake da ita kuma muna da hanyar da zamu karb'eta. Tashi Alhaji Marusa yayi fuska a d'aure yana fad'in Mr. Kallah bana so mu fara haka da kai, kasan yanda muka dad'e da kai muna harka, bana so saboda wannan k'aramun abun mu samu matsala, kasan dai tunda muka san sirrin juna dole mucigaba da tarayya, dan haka ka amince da abinda muka fad'a. Murmushi Mr. Kallah ya saki ya kamo hannun Alhaji Marusa yana fad'in haba abokina ai wannan abun bazai lalata tarayyar mu ta shekara da shekaru ba, ka sani nima bazanso asirin mu ya tonu ba, shikenan ayi abinda kukace. Murmushi Alhaji Marusa ya saki yana fad'in ko kai fa abokina, wannan hanyar ita kad'ai zamubi mu rufe wannan maganar, domin Allah kad'ai yasan iya abinda suka samu akan mu. Brr. Barau yace amma ya zamuyi dasu Abubakar da Moses? Alhaji Marusa yace zasubi wanda sukasa aikin ne. Mr. Kallah yace kisan zaiyi yawa fa, kasan yanda jini yake zai iya binmu, abinda zaifi zanyi masu canjin wajen aiki, kuma zamusa su Lucky suyi masu barazana akan abinda sukayi. Brr. Barau yace shikenan ayi hakan na yarda da kai. Alhaji Marusa yace duk ranar da wani abu ya faru babu ruwana. Mr. Kallah yace babu abinda zai faru ma. Wayar Brr. Barau ce tayi k'ara, yana dubawa ya kallesu yana fad'in babban 'yallab'ai ne bara naji abinda zai fad'a kunsan kiransa samu ne. Saurin tashi yayi yana fad'in shikenan 'Yallab'ai ka kwantar da hankalin ka zanji da wannan abun, wanda ya fishi ma muna rufewa bare kuma yau ya had'o da kai, shikenan zamuzo anjima akwai wata magana da zamuyi dama. Kashe wayar yayi ya zauna yana fad'in wata sabuwa. Alhaji Marusa yace meya faru kuma? Brr. Barau yace kunsan akwai Yaron wajen 'Yallab'ai na biyu mai suna Fawwaz ko? Kai suka jinjina. Brr. Barau yace wallahi wani tsautsayi ne ya faru dashi, yaron yana makarantar *King's collage* ne, kunsan yaran zamani akwai wauta, tsautsayi yasa sukayi fad'a da wani abokinsa akan mace shine fa ya yankeshi da wuk'a a wuya ajali yana kusa yaron ya mutu, 'Yallab'ai yace agaban mutum biyu akayi abun yanzu haka sun wurgar da gawar a wani waje, to sauran mutum biyun manyan abokansa ne nasan bazasu tab'a tona masa asiri ba, to amma d'aya daga cikinsu yace yaga wani d'an ajinsu kamar yana d'aukarsu alokacin da akayi abun, domin yaga lokacin daya fito ya ruga, shine hankalin 'Yallab'ai ya tashi, domin idan wannan maganar ta fito zai rasa kimarsa, toshine yace naje yana nemana. Jinjina kai Mr. Kallah yayi yana fad'in lallai wannan babbar magana ce, abinda ya sameshi ai ya same mu ne, dan haka kutashi muje yanzu sai mu gama komai kawai. **** *** *Naseer* ne ya fito daga gidansu hankali atashe, ya rasa wanda zai nuna ma wannan abun daya d'auka, haka Allah yayishi da tsoro gashi yaje ya gano abinda yafi k'arfinsa har ya d'auko saboda ya nuna sheda, domin yaron da aka kashe abokinsa ne suna gaisawa. Kallon wayarsa yayi yana tunanin wanda ya kamata ya nuna ma wannan abun, ko a gidansu babu wanda yasani, shiyasa ya fito kada Mamansa ta ganoshi. Tunani yayi ko dai ya kaima Baban Fawwaz tunda babban mutum ne yasan dole ya d'auki mataki akanshi. Jinjina kai yayi cike da gamsuwa, wayarsa yasa aljihu yana fad'in bara yayi sallah yaje ya kaimasa shima ya huta. (Allah sarki Naseer yarinta ta hana ka gane tsakanin Uba da 'Dahsai Allah🤦🏻‍♀) . *** Lokacin da yaje gidansu Fawwaz Maigadin gidan ya samu, bayan sun gaisa ya fad'a masa d'an makarantar su Fawwaz ne malaminsu ya aikoshi wajen Babansu. Murmushi maigadi yayi yace aikuwa Alhajin yayi baki suna lambu suna ganawa, amma tunda sako zaka bayar kaje ka fad'a masa kada na tsaida ka bansan lokacin da zasu gama ba. Godiya Naseer yayi masa yashiga, babu wanda ya ganshi har ya d'auki hanyar lambu, yana dab da zai isa wajensu yaji muryar Brr. Barau yana fad'in 'Yallab'ai ba ance sunan yaron daya d'auki kisan Naseer ba? Abinda zaifi anemoshi a daren yau a kashe shi kawai. Hannu Naseer yasa ya dafe kirjinsa jin abinda aka fad'a, har ya juya zai gudu sai kuma jarumta tazo masa, wayarsa ya d'auko ya kamo wajen ya matsa kusa dasu yanda zai d'auka da kyau ya b'oye yana d'aukar su. Mr. Kallah yace wai Brr. Barau meyasa fad'in kisa baya maka wahala ne, kace akashe Alhaji Maiwada, sannan kuma k'aramin yaro kace akashe shi Allah fa zai kama ka. Alhaji Marusa yace Mr. Kallah yanzu idan yaron ka ne aka ce ya aikata haka zaka bari a yanke masa hukuncin kisa bayan be gama more rayuwarsa ba? Brr. Barau yace Fawwaz shekararsa 19 ya isa ya d'auki kowane hukunci, tunda aji shidda yake yanzu gab suke da gamawa domin jarabawa suke zanawa, Mr. Kallah kayi tunani mana, mu da 'Yallab'ai mun saba tonawa mu rufe domin zaman lafiyar mu, idan asirin wani ya tonu acikin mu gaba d'ayan mu ya shafa. Jinjina kai Mr. Kallah yayi yana fad'in haka ne, yanzu ya kuke gani za'ayi? Alhaji Marusa yace ayau za'a kashe su duka, Abubakar da Moses na tura su Lucky tun d'azu ina da tabbacin sun kamasu yanzu, zanyi magana da Peter 'Yallab'ai ka tambayar mana kwatancen gidan su Naseer zaije ya d'aukoshi za'a shafe babinsa, shi kuma Alhaji Maiwada su Lucky zasu kaddamar masa anjima bayan ya taso daga wajen aiki. Dariya Brr. Barau yasa yana fad'in shugaban kwastam ake fad'a maka, daga yau bamu da sauran tashin hankali, Alhaji zaka cigaba da tafiyar da kasuwancinka yanda kakeso, muma zamu k'ara hannun jari domin ya bunk'asa. 'Yallab'ai yace wannan haka yake, dama dole kasa rigar mutunci ka b'oye zahirin ka idan kana so ka zauna lafiya da mutane, domin yanzu mutum ake kiwo ba dabba ba, nafi son mutuncina so dubu. Mr. Kallah yace amma akwai abokan Fawwaz da kace sun san komai, baka tunanin yanayi yasa su tona? Brr. Barau yace bazasu iya tona komai ba, kawai zanyi magana dasu akan su manta da komai, 'Yallab'ai dole a fitar da Fawwaz waje yayi karatu hakan zaisa hankalinsa ya kwanta. Jinjina kai 'Yallab'ai yayi yana fad'in nagode sosai, kuma zanyi hakan, abinda nakeso mu k'ara rik'e sirrin junan mu, Brr. Barau kayi mani alkhairi da yawa arayuwa, abu d'aya zanyi maka wanda zan saka maka, kaine zaka zamto *ALKALIN GOBE* na babbar kotun ku. Murmushi Brr. Barau yayi yana fad'in nagode Allah ya saka, ashe zan kai wannan matsayin. Jiki na rawa Naseer ya baro wajen, gaba d'aya zufa ta gama rufeshi, ko takan Maigadi bebi ba yayi hanyar waje, Maigadi yana tambayarsa ya bada sakon amma be saurareshi ba yayi waje da gudu. Kai tsaye d'akinsa ya shige ya saki kuka, ya dad'e yana kuka kafin ya d'auko Flash ya jona da wayarsa, gaba d'aya abinda ya d'auka ya tura, kayan jikinsa ya canza ya b'oye Flash d'in a aljihu ya fito. Mamansa ce ta kalleshi tana fad'in Naseer wai yau lafiyar ka kuwa? Murmushi yayi yana fad'in lafiya lau Mama. Dama zanje gidansu Mannir na amso littafina saboda muna da jarabawa da safe ranar litinin a makaranta na mantoshi a ajakarsa. Jinjina kai tayi tana fad'in yanzu za'ayi kiran sallar magriba ka biya masallaci kayi sallah kafin ka wuce, kuma kasan yanda unguwarsu take da ka bari ma sai da safe. Naseer yace bazan dad'e ba Mama. Murmushi tayi tace shikenan kaje kayi sallah. Naseer yace to Mama yanzu zanyi. Har ya kai bakin k'ofa Mamansa ta kirashi, dawowa yayi yana fad'in gani. Ido ta tsura masa kafin tace Naseer kamar akwai abinda kake b'oye mani ko? Saurin girgiza kai yayi yana fad'in bakomai Mama. Murmushi tayi tana fad'in shikenan ai nasan baka mani k'arya, Allah ya tsare ka gaishe da Mannir d'in. *** Risnawa Maigadi yayi yana fad'in barkan ku da fitowa, hannu Alhaji Marusa yasa aljihu ya ciro kud'i yana fad'in ga wannan anci goro ko. Amsa yayi yana masa godiya. Har sun kai bakin k'ofa Maigadi yace 'Yallab'ai wannan yaron ya samu ganin ka kuwa? Cak suka tsaya jin abinda yace. 'Yallab'ai yace wane yaro kenan? Maigadi yace d'azu wani yaro yazo yace yana nemanka shine nace kana da baki, sai yace sako zai baka inji malaminsu, shine nace kuna lambu yaje ya sameka, to bayan wani lokaci ina zaune sai kawai naga yaron ya fito a firgice, yanayin yanda naganshi yasa na taso ina tambayarsa ya ganka, amma be tsaya saurarata ba yayi waje a guje, to da yake bansan yanda kukayi ba shiyasa na kyaleshi na zauna. Gaba d'ayansu hankalinsu ne ya tashi jin binda Maigadi ya fad'a. Brr. Barau ne yace a ina Yaron yace maka yake? Maigadi yace ni dai yace mun d'an ajinsu Fawwaz ne. Dam... Gabansu ya sake fad'uwa. Da sauri suka fita waje hankali tashe. Da kallon mamaki Maigadi ya bisu ganin yanda hankalinsu ya tashi. Dafe kai 'Yallab'ai yayi yana fad'in duk yanda akayi wannan yaron turoshi akayi. Brr. Barau yace ba lallai turosa akayi ba, nafi tunanin yazo wajenka domin ya fad'a maka abinda ya faru, sai kuma yaci sa'ar sauraron abinda muke tattaunawa wanda ya tada hankalinsa ya kasa ganinka ya fita da sauri, abin tambayar anan shine, ya d'auki abinda muke tattaunawa akai ko kuwa saurara kawai yayi? Alhaji Marusa yace koma menene bazamu barshi ba, dole anemoshi kuma a amso wannan shedar daya d'auka. Waya ya ciro yana fad'in bara nakira Lucky. Bayan ya d'auka Alhaji Marusa ya bashi umarnin su nemo Naseer a duk inda yake, su kashe shi kuma su amso wayarsa. Peter ya kira anan yake fad'a masa ya baza yaranshi su jiran Alhaji Maiwada ya fito su k'addamar masa. Godiya yayi masu ya kashe wayar. Fawwaz ne yazo wucewa shida abokansa, risnawa sukayi suka gayar dasu Alhaji, duk sai Fawwaz ya tsargu ganin fuskokinsu d'auke da damuwa. Dadynsa ne yayi kiransa, bayan yazo ya tambayesa unguwar su Naseer. Fad'a masa yayi, Brr. Barau yace baka da hotonsa? Fawwaz yace akwai, wayarsa ya d'auko ya nuna masu, amsa Alhaji Marusa yayi nan take ya tura awayarsa, bayan sun shiga Alhaji Marusa ya turama Lucky had'e da kwatancen unguwar. Brr. Barau yace zamu wuce 'Yallab'ai ka kwantar da hankalinka babu abinda zai faru, anjima zan dawo domin in gana da abokan Fawwaz hada shima. Godiya yayi masu yana fad'in ab'atar da duk wata sheda. Alhaji Marusa yace wannan ba matsala bane nasan yarana. **** Bayan an gama sallar magriba kafin Naseer ya fito yaji ana sanarwar mutuwar abokinsa wanda aka tsinci gawarsa a cikin daji saboda unguwarsu d'aya. Runtse ido Naseer yayi hawaye suka zubo masa, da sauri yazo fita sai yaji an dafashi, yana juyowa yaga wani abokinsa ne makwafcinsu. Hannu yasa ya goge idonshi yana fad'in Saddik ya gidan? Saddik yace lafiya lau Naseer, naji wanda aka fad'a ya rasu a makarantar ku yake ko? Kai Naseer ya jinjina masa. Saddik yace Allah yajik'ansa, cike da k'osawa Naseer yace amin kafin ya fice. Wayarsa ya d'auka ya kirawo abokinsa Mannir, yana d'auka Naseer yace Mannir kana gida? Mannir yace ina gida lafiya naji muryarka wani iri? Naseer yace akwai wata magana da nakeso na fad'a maka akan mutuwar abokin mu amma ka jirani agida yanzu zanzo. Mannir yace shikenan sai kazo. Mota ya tare ya hau yana fad'in dan Allah Malan ofis d'in shugaban kwastam zaka kaini, jiyowa mai motar yayi yana fad'in sai dai na ajeka bakin titi domin bana son harka da kwastam. Naseer yace bakomai muje. Tafiya suke sai mai motar yaga kamar ana binsu, kallon Naseer yayi yana fad'in nifa jikina yana bani wani abu, sai nake ganin kamar ana binka, kodai ka d'auko wasu kud'i ne? Naseer yace ba wasu kud'i kawai ka tsargu ne. Lucky ne ya kira Alhaji Marusa ya fad'a masa sun samu yaron mma sunga kamar ya d'auki hanyar ofis d'in Kwastam. Alhaji Marusa yace kuyi a hankali kunga dai dare beyi ba sosai, bana so kuzo ba tare da kungama komai ba. Tsayawa direban yayi yana fad'in iya nan zan tsaya sai ka k'arasa. Kud'i Naseer ya bashi yana fad'in nagode. Tafiya ya fara gabanshi yana fad'uwa, yanaso yaje ya tambaya a nuna masa shugaban Kwastam dan shine yaji su Alhaji suna maganar za'a kashe, gara yaje ya fad'a masa yasan kila shima ya samu kariya, gashi ko ganinshi bai tab'ayi ba ballantana ya ganeshi, dole sai yayi tambaya. *** Alhaji Maiwada bayan ya gama aikinsa ya fito, sallama sukayi da Malan Bala yana fad'in gobe bazan shigo aiki ba sai litinin, a gyara ofis d'in da kyau. Malan Bala yace insha Allahu. Kud'i Alhaji ya ciro ya mik'a masa yana fad'in gashi kayi kud'in mota kayi cefane naga wata ya raba tsakiya. Godiya sosai Malan Bala yayi masa, har bakin mota ya rakoshi. Ganin su Abubakar da Moses yasa ya tsaya, k'arasowa sukayi suna fad'in har yanzu basu samu wayar Malan Hassan ba, kuma agidanshi ance bai koma ba. Moses yace ina tunanin wani abu, ko dai sun kamashi ne suka kulle? Alhaji yace insha Allahu babu abinda zasuyi masa, gobe zamuje can gidanshi muji. Godiya saukayi tare da masu sallama yashiga mota Malan Sani yaja suka tafi. Su Moses suna barin wajen kasancewar a motar Abubakar suke, bayan sunyi nisa yaran Peter suka tare su, nan take suka shiga motar suka bar wajen dasu bayan sun watsa masu wata hoda. ** A hanya Alhaji yana gyara wasu aiyuka a cikin kamfutarsa yake fad'ama Malan Sani yanda sukayi da Alhaji Mansur. Malan Sani yace Alhaji ni har wannan kamfutar ma da kadena fitowa da ita kasan akwai abu mai muhimmanci aciki. Alhaji yace ai babu wanda yasan yanda ake bud'eta, kuma natura shedar a Flash saboda tsaro. Malan Sani yace hakan dai yafi. *** Jikin Naseer ne ya fara rawa ganin kamar ana binsa, nan take tsoro ya kamashi sai ya baza da gudu yana tunanin ya koma gida kada garin neman shugaban kwastam akamashi, haka kawai ma yaje garin tambaya wani yace shine sai ya fad'a masa gaskiya a kamashi tunda duniyar babu gaskiya, gudu yake aranshi yana fad'in babu wanda zan tambaya gara naje na fara saninshi a hoto kafin naje wajensa. *** Birki Malan Sani ya taka da sauri ganin mutum ya faad'o masa. Alhaji yace lafiya dai Malan Sani? Bud'e motar Naseer yayi ya shige sai haki yake yana fad'in dan Allah ku taimaka mani wasu ne suka biyo ni. Alhaji yace ikon Allah! Kai ko yaro meya had'aka dasu? Naseer yace kawai 'yan iskan gari ne. Malan Sani yace ka tabbata abinda ka fad'a gaskiya ne? Naseer yace wallahi da gaske nakeyi. Alhaji yace tuk'a muje. Malan Sani yace Alhaji... Hannu ya d'aga mashi hakan yasa yaja suka tafi. Naseer yayi masu kwatancen unguwar su Mannir, kasancewar hanyar gidansu bata da kyau Malan Sani yace sai dai mu ajeka bakin hanya dan yasan unguwar bata da kyau. Naseer yace hakan ma yayi nagode. *** Waya Lucky yakira Alhaji Marusa yana fad'a masa yaron yashiga motar su Alhaji Maiwada. A firgice Alhaji Marusa ya mik'e yana fad'in mene? Wallahi idan kuka bari ya sha sai na kashe ku, inaso kushiga gabansu yaron yana fita ku gama dashi, shima Alhaji bazai sha ba yana barin wajen su Peter zasu k'addamar masa. ** Malan Sani ne yace Alhaji kaji labarin wani yaro da aka kashe ko? Alhaji yace wallahi d'azu nakejin labari, kai zamanin nan ran mutum ba abakin komai yake ba. Naseer yace ai abokin mu ne makarantar mu d'aya. Alhaji yace Allah sarki, Allah yajikansa ya tona asirin wad'an da suka kashe shi. Naseer yace amin. Yana so ya fad'a masu gaskiya yana jin tsoro hakan yasa yaja bakinsa yayi shiru. Suna zuwa bakin hanya Malan Sani ya tsaya yana fad'in kayi sauri ka wuce kasan dai wannan hanyar bata da kyau. Godiya Naseer yayi masu, jiyowa yayi yana fad'in Abba nagode. Murmushi Alhaji yayi masa yace bakomai ka kiyaye ka daina kaiwa dare a waje kaji. Kud'i ya bashi yana fad'in ga wannan kasa kati. Godiya Naseer yayi masa, haka kawai yaji ya yarda da mutumin, sai yayi tunanin ya b'oye Flash d'in amotarsa yasan zai gani, idan ya gani zai taimaka. Hannu yasa ya zaro Flash d'in, a hankali ya turashi k'asan kujerar baya ya fita. Kan motar Malan Sani ya juya yana fad'in wallahi shiyasa nake jin dad'i da Ra'eez baya zama agarin nan, kallifa ko isha'i ba'ayi ba amma an fara bin mutane. Alhaji yace kai dai sai addu'a, shiyasa nace maka muna gama wannan shari'ar zan aje aikina na bar garin nan. Malan Sani yace ai k'afarka k'afata Alhaji, domin bazanji dad'in zaman garin nan ba idan bakanan. Alhaji zaiyi magana kenan sukaji motarsu tana rawa alamun taya ta samu matsala. Malan Sani yace kila kuwa mun taka k'usa, Alhaji yace tsaya mugani. Malan Sani yace gara mu tuk'ata ahaka wajen nan beda kyau kuma babu mutane. Alhaji yace Malan Sani kaci ka tsoro, dare fa beyi ba gara mu canza wata tayar zaifi. *** Taku ukku Naseer yayi yaji an damkoshi, baki ya bud'e zeyi ihu aka rufe bakin, d'aukarshi sukayi zuwa cikin motarsu. Kasancewar motar bakin gilashi ne yasa ba'aganin na ciki. Mari Lucky ya d'auke Naseer dashi yana fad'in mai ka fad'ama Alhaji Maiwada? Cikin firgici Naseer ya kallesu yana fad'in waye haka kuma? Lucky yace motar data ajeka yanzu ai shugaban kwastam ne aciki meya had'a ka dashi? Farin ciki ne ya kama Naseer jin ya aje shedarsa a inda ta dace, kuma ko zasu kashe shi bazai fad'a masu abinda ya aje ba. Dukan da akayi masa yasa ya dawo daga tunanin da yakeyi. Cikin wahala yace wallahi babu abinda na fad'a masa ni bamma sanshi ba kawai ragemun hanya sukayi dama wajen shugaban kwastam zanje sai kuma tsoro ya hanani k'arasawa shine na dawo sai muka had'u suka d'aukoni. Amsar wayarsa Lucky yayi, yana dubawa yaga abinda ya d'auka duka suna nan, waya ya kira Alhaji Marusa ya fad'a mashi, murmushi yayi yace ku gama dashi kuma ku jefar da gawarsa, banaso ku rifeta ku barta domin Iyayensa su masa sallah. Duk magiyar da Naseer yake masu haka suka kashe shi suka ja motar zuwa inda zasu yarda shi sukayi tafiyarsu da wayarsa bayan sun cire layin sun yona rami sun rufe. *** Cike da tsoro Alhaji yake kallon mutanan da suke tun karosu, Malan Sani yace Alhaji kana ganin abinda nake gani kuwa? Alhaji yace dama tunda su Moses sukace Malan Hassan ya b'ace jikina ya bani kamashi akayi, sun gano komai shine suka turo akashe mu. Abinda nakeso da kai Malan Sano ka fita da gudu kai ka tsira. Malan Sani yace ka daina fad'ar haka, bazan barka anan ba. Alhaji yace dole wani ya tsira acikin mu, Bilkisu da Ra'eez basu da kowa sai ni, idan suka kasheni zasu iya zuwa su kashe ta, Ra'eez zai taso cikin maraici, inaso kaje ka fitar da ita daga gidan nan, inaso ka kula mani dasu domin rayuwata suke nema ba taka ba, idan ka tsaya zasu had'a da kai. Kuka Malan Sani yasa yana mai rik'e da hannun Alhaji.Kamfutarsa ya miko masa yana fad'in jeka da ita, ka tabbatar ka fitar da Bilkisu, kace ta yafe mun kuma tayi hakuri da rayuwa, Allah ya albarkaci abinda zata haifa, kuma kuyi kok'arin barin garin nan kada kuzauna aciki dan Allah, ka shafa mani kan Rumaisa da Ra'eez. Kuka kawai Malan Sani yake haka ya fita daga motar, kasancewar bata b'angaren da suke taho yake ba hakan yasa ya gangare basu ganshi ba, wani daga cikinsu ne ya hango giccensa nan ya fad'ama Peter. Kafin su k'arasa ya kira Alhaji Marusa ya fad'a masa direban ya gudu hada jakar kamfuta a hannunsa. Alhaji yace nasan gidan Alhaii Maiwada zaije domin ya ceci matarsa, kuji da Alhajin zain tira su Lucky gidan yanzu, nasan zasu rigashi zuwa tunda da mota hannunsu shima zasu kasheshi. Fito da Alhaji sukayi, yana rok'on su amma basu saurareshi ba, wani kyalle sukasa suka nad'e mashi wuya dashi har sai da yadena numfashi. Wurgashi cikin motar sukayi suka bar wajen. ** Brr. Barau ne yayi kiransu Lucky ya basu umarnin kada su kashe Malan Sani su barshi sun canza shawara, kawai sujirashi agidan yazo su amso kamfutar su fito. Ur's. Nabeelert Lady🖋[3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.* 1⃣5⃣ Tsayawa Malan Sani yayi yana hutawa sai dube-dube yake, hawaye kawai suke zubo masa, shikenan yanzu sun kashe Alhaji, kai duniya. Hannu yasa ya ciro wayarsa, Alhaji Mansur ya kira, yana d'auka ya sake fashewa da kuka. Hankali tashe Alhaji Mansur yake tambayarsa abinda yake faruwa. Tsagaita kukansa yayi ya fad'a masa abinda ya faru. Salati Alhaji Mansur yasa jikinsa yana rawa. Malan Sani yace yanzu haka ina hanya inaso na k'arasa can gidansa na tafi da Hajiya. Alhaji Mansur yace kaga tana d'auke ta juna biyu, kayi yanda hankalinta bazai tashi ba dan Allah, kuma shima Alhajin insha Allahu babu abinda zasuyi masa, gobe da wuri zan iso, Allah ya tsare ku gaba d'aya. Mota Malan Sani ya tare yana saka wayarsa aljihu. Gani yake kamar mai motar baya gudu, addu'a kawai yake Allah yasa basu yima Alhaji komai ba. *** Ta bayan gidan suka shiga dan Alhaji Marusa yace baya so Maigadi yasan da zuwan su saboda Brr. Barau ya had'a wani shiri ta yanda zasu fita daga zargi. Ummun Ra'eez tana zaune a falo sai gwada kiran wayar Alhaji take amma taki shiga, duk da tasan yana wuce haka bedawo ba amma kafin ya baro ofis sunyi waya yace ta dafa masa kwai guda ukku zaici abinci dasu. Gashi Ladi bata nan taje Kauyensu ana biki sai litinin ma zata dawo. Wayar ta aje tana mai jin wani irin sanyi yana shigarta, rufe ido tayi tana karanto duk addu'ar data zo mata. ** Madu ne ya bud'e k'ofa jin k'arar bugawa, mamaki yayi ganin Malan Sani shi kad'ai ga idanuwansa duk sun kumbura. Shigowa Malan Sani yayi yana fad'in Madu akwai matsala fa. Madu yace matsalar me ina Alhajin? Malan Sani yace ina zuwa bara na fito. Be jira abinda zai fad'a ba yayi gaba. Zama Madu yayi yana fad'in ikon Allah, wace matsala ce kuma wannan? Taya Malan Sani zai dawo shi kad'ai kuma, ga jaka a hannunsa kamar ta kud'i, sannan idanuwanshi duk sunyi ja kamar wanda ya shawu, ko dai Alhajin ne ya aikosa? Amma da mamaki, Redionsa ya jawo yana fad'in bari ya fito muji. Bayan Ummu ta bud'e k'ofar sai taji gabanta ya fad'i ganin Malan Sani d'auke da bak'ar jaka ta kamfutar Alhaji. Batayi magana ba ta shiga ciki tana fad'in shigo mana. Shiga yayi ba tare daya rufe k'ofar ba. Zama Ummu tayi tana fad'in Malan Sani Abbun Ra'eez ko aiki ya rik'esa ne? Duk'ar da kai yayi hawaye suna cika masa ido yace shine ya aiko ni na d'auke ki mu tafi can gidana gobe kuma zamu wuce kano. Zatayi magana kenan sukaji alamun motsin shigowa, dama zaman jiran Malan Sani sukeyi kuma aka ci sa'a be rufe k'ofar ba. Saurin mik'ewa sukayi ganin manyan mutane a cikin gidan. Hannu Ummu tasa ta dafe cikinta tana fad'in Malan Sani kace mun sun kashe Alhaji kawai, gashinan kaima kuka kakeyi, meyasa zasuyi mani haka, ina gawarsa take dan Allah? Kuka Malan Sani yasa yana kallon su yace narok'e ku da girman Allah kada ku kashe ta, ku kasheni amma kubarta ita da abinda yake cikinta. Zuciya ce ta ciyo Ummun Ra'eez ta rarumi flask d'in ruwan zafi da yake kusa da ita ta wurga ma Lucky, saurin kaucewa yayi cikin zafin nama ya kwad'a mata sandar da take hannunsa akai. K'ara Ummu ta saki ta fad'i da k'arfi saman cikinta, nan take jini ya b'alle mata. Salati Malan Sani yasa yayi kanta da sauri, kamota yayi yana jijjigata amma babu alamun rai ajikinta, ga kanta yana fitar da jini k'asanta ma jini na fita. Kuka yake yana fad'in baku da imani, me wannan matar tayi maku. Tsaki Lucky yayi danshi baya b'ata lokaci a aikinsa. Wata hoda ya fesama Malan Sani nan take yaji kanshi yayi nauyi, hannu yasa ya dafe kanshi yana jin yanda falon yake juya masa. Duk'awa Lucky yayi ya kama hannun Malan Sani ya kamo na Ummun Ra'eez, Malan Sani yana kallonsa amma jikinsa ba kwari, hannun Ummun Ra'eez yasa a wuyan Malan Sani ya karceshi da faratan ta da bata yanke ba, nan take sahu ya fito harda jini. D'aukar jakar kamfutar sukayi suka kamo Malan Sani suka fito dashi sai layi yake dan sam baya cikin hankalinsa. Turashi sukayi hanyar gate, sai da sukaga ya kama hanya yana tafiya yana layi kafin suka fice ta bayan gidan. Saurin tasowa Madu yayi ganin Malan Sani yana tangad'i, kamoshi yayi yana fad'in lafi... Tsayawa maganar tayi ganin jini a jikinsa, zeyi magana Malan Sani ya tureshi har sai da ya faad'i yayi tafiyarsa ya fice daga gidan. Yana fita su Lucky suna jiransa bakin k'ofa, saurin kamashi sukayi sukasa a mota suka tafi. Koda Madu ya lek'a sai kurar motar ya iske. Mamaki ne ya kamashi, me yasamu Malan Sani haka? Me ya aikata acikin gida tunda yasan Ladi bata nan? Ga jini ajikinsa, ko dai wani abu yayima Hajiya? Ai kuma yaso yaji ihu, Saurin komawa Madu yayi, cikin gidan ya nufa jikinsa sai rawa yakeyi. Yana shiga falo yayi mutuwar tsaye, da sauri ya fito yana gudu yayi wajen gidan yana neman taimako. Makwabcin su ya gani shida abokinsa, da sauri ya k'arasa wajensu jikinsa na kyarma. Tsayawa sukayi ganin Madu. Makwabcinsu mai suna *Alhaji Musa* yace Madu lafiya kuwa? Kuka Madu yasa yana nuna masu cikin gidan. Mamaki ne ya kamasu sukace meya faru? Madu yace ya kasheta wallahi gata can a kwance cikin jini Alhaji. Wanda aka kira da Alhaji yace waye ya kashe ta kuma wa aka kashe? Madu yace Hajiya ce, Malan Sani ne yashigo kuma shi kad'ai ya dawo ba tare da Alhaji ba, hannunsa d'auke da jaka kamar ta kud'i, yana shiga cikin gidan sai ihun Hajiya naji, band'au ka wani abu bane ina zaune sai gashi ya fito jikinsa duk jini, dana rik'esa saiya tureni ya fito, kafin na fito wata b'akar mota ta d'aukeshi sun bar wajen. Abokin Alhaji yace tabbas naga bak'ar mota har nake maka magana nace mai motar can yana tukin hauka ashe da abinda suke ma sauri. Ajiyar zuciya Alhaji yayi yana fad'in lallai duniya babu gaskiya, yanzu bazamu shiga gidan ba, bara nayi waya a turo 'yan sanda idan suka zo sai mushiga saboda tsaro. *** Sai da suka d'auki yaron daya gano masu gidan Malan Sani sannan suka wuce unguwarsu, har k'ofar gida suka kaishi, kuma sukaci sa'a ba mutane a wajen, ajeshi sukayi suka kama gabansu. Cikin layi Malan Sani ya k'arasa cikin gidansa yana rik'e da kanshi. Halima da Rumaisa suna zaune tsakar gida suka ga Malan Sani yashigo ko sallama babu. Da sauri Halima ta tashi tana fad'in Malan lafiya kuwa? Hannu ya d'aga mata, beyi magana ba yayi hanyar d'akinsa, bayansa tabi cike da damuwa ga jini ajikinsa duk sai hankalinta ya sake tashi. Yana shiga ya rufe k'ofar yasa mukulli, zubewa yayi saman gadonsa nan take nannauyen bacci ya d'aukeshi. Kamo Rumaisa Halima tayi suka zauna nan take hawaye suka wanke mata fuska, gaba d'aya jikinta yayi sanyi ganin Malan Sani a cikin wani yanayi wanda betab'a shiga ciki ba. *** Bayan 'yan sanda sun gama bincike motar asibiti ta d'auketa aka nufi asibiti da ita dan sunce ba mutuwa tayi ba. Gaba d'aya unguwar hankalinsu atashe yake saboda abinda ya faru. Madu kuwa kamar wanda aka watsama ruwan zafi, gashi yakira Alhaji wayar bata shiga. Ana shirin rufe gidan sai ga wata motar 'yan sandan sunzo. Bayan sun shigo suka tambayi maigadin gidan. Madu ya taso yana fad'in gani nan. Tambayarsa sukayi nan ne gidan Alhaji Maiwada shugaban kwastam? Jiki a sanyaye Madu yace nan ne. Hannu babban cikinsu ya mik'ama d'an sandan da suka samu, Alhaji Musa makwabcin su Alhaji ya matso yana tambayar lafiya? 'Dan sandan yace mun samu gawar Alhaji Maiwada ne a motarsa shine akayi mana kwatancen gidansa, yanzu haka gawarsa tana asibiti an wuce da ita domin ayi bincike, tare ma muka kaita data wani yaro da muka tsinta itama anjefar, gaba d'aya de suna asibiti kafin mu samu Iyayen yaron. Wani irin kuka Madu yasa yana fad'in shikenan shima ya kashe shi, kai Malan Sani ina zaka kai alhakin wad'an nan mutanan? Mutum ya d'auko ka cikin talauci ya taimake ka amma kazo kayi masa butulci. Alhaji Musa ne ya kamo Madu yana fad'in ya isa haka, tunda hukuma tashigo ciki za'ayi bincike. 'Dan Sandan yace kasan gidan Malan Sanin? Kai Madu ya d'aga yana fad'in sosai ma. Kallon Alhaji Musa yayi yana fad'in Alhaji zamuje can gidan domin mutafi da Malan Sanin, idan akwai wani d'an uwan Alhaji Maiwada asanar masa domin dole a rufe gidan nan kafin su zo. Alhaji Musa yace gaskiya danginsa ba anan suke ba, kuma bani da lambar kowa. Madu yace ina da lambar Alhaji Mansur a kano yake. Alhaji Musa yace kawo lambar asanar masa idan yaso sai arufe gidan ku tafi da mukullin wajen ku kafin yazo. Bugu biyu Alhaji Mansur ya d'auka, ganin bak'uwar lamba yasa gabanshi ya sake fad'uwa. Bayan sun gaisa Alhaji Musa ya fad'a masa halin da ake ciki. Salati kawai Alhaji Mansur yakeyi jikinsa yana rawa, ya dad'e kafin yace gobe zai taho da wuri, sannan ya roki alfarmar Alhaji Musa ya kula da Ummun Ra'eez kafin yazo da matarsa. Alhaji Musa yace bakomai sai kazo. Haka aka kulle cikin gidan Madu yace zai cigaba da zama kafin ya tafi dan shima bazai iya cigaba da zama ba. Haka ya kulle gate d'in yashiga motar 'yan sanda suka nufi gidan Malan Sani, sauran 'yan unguwa sai jimamin abinda ya faru sukeyi. *** Har sun rufe gida taja Rumaisa d'akinta sun kwanta dan Rumaisa har tayi bacci, ita ko ta kasa baccin, tunanin halin da Malan Sani yake ciki kawai takeyi. Jin k'arar buga gida yasa tayi saurin tashi tana lallubar fitila, hijabi tasa kafin ta nufi waje jiki a sanyaye. Tsayawa tayi tana tambayar waye? Daga waje akace 'yan sanda ne ki bud'e. Jikinta ne ya tsananta rawa, da kyar ta iya bud'e k'ofar. Madu ta fara gani hakan yasa taji sanyi, kallonshi tayi duk idanuwanshi sunyi ja. 'Daya daga cikinsu ne yace ina maigidan ki? Halima tace yana ciki ina jin beda lafiya dan ya kule k'ofar d'akinsa kuma ya dawo cikin wani yanayi. 'Dan sandan yace muje ki nuna mana d'akin munzo tafiya dashi ne. Gabanta ne ya faad'i ta kalli Madu tana fad'in wai meye yake faruwa dan Allah? Matsawa Madu yayi gefe yana goge kwalla ya kasa magana. Kuka Halima tasa tare da komawa ciki ta fara bubbuga d'akin Malan Sani. Shiru babu alamun motsi hakan yasan d'an sandan yace zamu b'alle k'ofar tunda bai bud'e ba. Abun buge k'ofa suka samo haka suka bud'eta da k'arfi. Mamaki ne ya kamasu ganinshi kwance kamar gawa, da sauri Halima tayi ciki tana fad'in Malan na shiga ukku me yasame ka haka? Ciki suka shiga suna tsoron kada dai ace shima ya mutu shirin da Brr. Barau yayi ya rushe. Komawa baya d'aya daga cikinsu yayi ya d'ebo ruwa, yana zuwa ya watsa mashi, a firgice ya tashi sai dai jikinsa babu kwari. Rungumoshi Halima tayi tana kuka tace Malan me yasame ka? Kallonta yayi idanuwansa suna rufewa amma ya kasa magana. 'Dan Sandan yace Malama ki matsa muyi aikin mu kina b'ata mana lokaci, idan kina son sanin abinda ya aikata zaki iya zuwa ofis d'in mu gobe da safe amma yanzu dashi zamu tafi. Kuka Halima tasa tana fad'in wallahi mijina ba me laifi bane, dan Allah kada ku tafi dashi. Murmushi d'an sandan yayi yana fad'in idan baki sani ba to mijinki makashi ne, domin ya kashe uban gidansa kuma ya nemi matarsa da alfasha yanzu haka tana asibiti. A zabure Halima tayi baya tana binsu da wani irin kallo, hannu tasa ta rik'e cikinta jin yanda ya murd'a mata, ganin halin da take ciki yasa wani daga cikin 'yan sandan yaji tausayinta, duk'awa yayi yana fad'in ki kwantar da hankalin ki, idan akayi bincike beda laifi babu abinda za'ayi masa. Ajiyar zuciya Halima ta saki tare da sakin wani irin kuka. Tana ji tana gani suka rik'e Malan Sani dan bema iya tafiya saboda mutuwar jiki, sai kallonta yakeyi, yana so yayi magana amma ya kasa, hawaye ne suka zubo mashi, haka sukayi waje Halima tana zaune ta kasa tashi. Jin k'arar motarsu yasa tayi saurin tashi, mararta ce ta murd'a hakan yasa ta duk'e tana cije baki, ta jima ahaka kafin ta dafa bango har ta kai k'ofa, tsayawa tayi tana kallon kurar motarsu hawaye suna wanke mata fuska. A hankali ta maida k'ofar ta rufe kafin ta koma d'aki ta fashe da kuka. *** Wai Baffan Naseer har yanzu baka samu wayar tashi ba? Ajiyar zuciya Baffa yayi yana fad'in duk kiran da nakeyi wayarsa akashe take, gaba d'aya hankalina ya tashi domin Naseer baya kai dare awaje. Mama tace kuma fa gidansu Mannir yace zaije a masallacin unguwar nan ma yayi sallar magriba. Baffa yace ba agida nayi sallah ba da bazan barsa yaje ba, idan ma yace dole yaje sai dai na kaishi da kaina, kinsani sarai bana son yawon dare. Mama tace kayi hakuri gani nayi yace littafinsa zai amso. Baffa yace wai baki da lambar shi Mannir d'in? Mama tace ina da ita dan Naseer ne ma ya ajeta saboda wata rana yana kiransa da wayata. Baffa yace bani lambar. Bugu biyu Mannir ya d'auka, bayan sun gaisa suka tambayeshi Naseer. Shiru Mannir yayi yana mamakin Naseer baya gida, yace masa zaizo da yaga shiru ya d'auka ko agida aka hanashi.... Labarin yanda sukayi da Naseer ya fad'a masu. Jiki asanyaye suka masa godiya. Hawaye ne suka zuboma Mama tana fad'in kada dai ace saceshi akayi. Baffa yace banga ta zama ba bara na kira DPO gara mushigar da k'ara da wuri. Suna gama waya da DPO yace yajirashi zaisa yaranshi suje su duba. Zama sukayi gaba dayansu jiki amace. Can wajen sha biyun dare DPO yakira Baffa, yana d'auka yace masa ya tura yaranshi zasuyi bincike, amma wani yace an kai wasu gawawwaki guda biyu d'azu asibiti data babban mutum data yaro, ko zasuje su duba? A zabure Baffa ya tashi yana fad'in yanzu zan fito DPO mu had'u a asibtin. Da sauri DPO ya amsa saboda Baffa babban mutum ne akwai naira. Tare suka tafi hada Mama sai kuka takeyi domin Naseer shine autan ta, yaranta biyu babban yana can abuja yana karatu. *** Kuka kawai sukeyi asaman gawar Naseer, Mama tana fad'in su waye ne suka maka haka Naseer? Ya Allah ka saka ma bawanka. DPO yace Alhaji kuyi hak'uri insha Allahu zamuyi bincike, idan muka gano wad'an da suka aikata haka dole ashigar da k'ara kotu. Jinjina kai Baffa yayai kafin suka wuce domin su amshi gawar. Likita yace zasuyi bincike dole su bari zuwa safiya tunda ba yau za'a rufeta ba. Baffa yace ayanzu zakayi binciken ka bani gawar Yarona, gara naje na kwana ina masa karatu daya kwana anan. Jikin likita yana rawa yace angama. Ur's. Nabeelert Lady🖋 [3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.* 1⃣6⃣ Washe gari ko da Malan Sani ya farka sai ya dawo cikin hankalinsa, tashi yayi yana dafe kanshi da yake masa ciwo, a hankali abubuwan da suka faru jiya suka fara dawo masa, tun daga shigarsa gidan Alhaji har abinda ya faru ya fito ya shiga mota har zuwanshi gida, iya nan kawai ya iya tunawa sai kuma yau daya tashi. Da sauri ya d'aga kai yana sake kallon inda yake, mamaki abun ya bashi, yasan dai yashiga d'akinsa amma gashi a wajen 'yan sanda. Runtse ido yayi yana salati tunawa da abinda ya faru, kada dai sun kashe Ummun Ra'eez? Saurin sa hannu yayi a wuyansa, zafi yaji a wajen dan har yayi fushi saboda yakushin da sukasa Ummun Ra'eez tayi masa, a hannunsa yana jin shatin faratan ta. Girgiza kai yashigayi hawaye suna zubo masa, tabbas yasan yashiga tsaka mai wuya Allah ne kad'ai zai iya fitar dashi, domin wannan abun daya faru yasan duk shirin su Alhaji Marusa ne. Dafe kai yayi yana kuka, ko a wane hali Halima take ciki yanzu? Jin motsi yasashi saurin d'agowa. Wani d'an sanda ne yazo wajenshi dan yaga beyi sallah ba kuma shi zai tafi shine ya matso yaji ko yana da buk'atar yayi sallah, dan tunda aka kawoshi jiya yana zaune a ofis kawai yaji ya tausaya mashi, yanayin da aka kawoshi yasan akwai abinda ya sha ko kuma akasa mashi. Saurin tashi Malan Sani yayi yana fad'in dan Allah inaso nayi sallah kaga har gari yayi haske sosai. Murmushi d'an sandan yayi yana fad'in ai tun d'azu naga kana bacci shiyasa ban tasheka ba, fito ga wajen sallah can. *** Mota ce ta sauke Alhaji Mansur da Matarsa a k'ofar gidan Alhaji Maiwada saboda ta jirgi suka zo. Idanuwan Maman Labiba har sun kumbura saboda kuka, shikanshi Alhaji Mansur idanuwansa sunyi ja saboda ba k'aramin tashin hnkali yashiga ajiya ba. Isowar Alhaji Musa ne yasa suka k'arasa cikin gidan saboda da suka zo basu shiga ba. Da sauri Madu ya taso yana masu sannu da zuwa, shima duk jikinsa a sanyaye yasha kuka. Bayan sun gama gaisawa suka jajanta abinda ya faru, anan Alhaji Mansur yayima Alhaji Musa godiya sannan yace su wuce asibitin domin a gama komai a basu gawar Alhaji ayi masa sutura. Alhaji Musa yace shikenan bara na d'auko mota ta sai mutafi, zansa a kawo tabarmi saboda zaman gaisuwa, Madu sai ka gyara cikin rumfar can idan suka kawo sai a shimfid'a. Kai Madu ya d'aga yana share kwallah. *** Sosai Abubakar da Moses suka tsorata da abinda sukaji, gashi su Peter basu kyalesu haka ba sai da suka basu wahala sosai, domin a wajensu suka kwana, sun jigata sosai, haka kuma sunyi kukan mutuwar Alhaji Maiwada da Malan Hassan, Abubakar yanaji kamar laifinsa ne, da be sako Malan Hassan a cikin wannan abun ba da haka bata faru dashi ba, gashi babu halin yaje ya sanar da Iyalinsa yanzu za'a tsareshi ya nuna gawarsa kuma besan inda take ba, hakan kuma zai sashi cikin matsala,, dole ya bar abun sai dai Allah ya basu hak'uri. Shigowar Lucky da Peter ne yasa sukayi saurin kallon su. Matsowa Lucky yayi fuska babu annuri yana fad'in kunci sa'a ba'a bamu umarnin kashe ku ba, kashedi kawai akace muyi maku, nasan zuwa yanzu jikin ku ya fad'a maku abinda muke nufi, dan haka zaku samu takardar canjin wajen aikin ku da zaran litinin tayi, matuk'ar kuka sake nuna kan ku ko kuma wani yaje neman wata sheda akan ku zamu kashe kowa naku. Cike da tsoro Moses yace wallayi aboki bazaka sake gani na a lagos ba, tsautsayi ne yasa nayi haka, amma na goge komai bani da wata sheda kada ku kashe ni. Abubakar yace insha Allahu bazaku sake ganina a lagos ba koda da yawo, kuma babu abinda zan fad'a, bazan barima asan nasan wani abuba, dama bani da iyali anan suna can dan haka ayau zan bar garin. Murmushi Lucky da Peter sukayi kafin suka kwance su, hannu suka rik'e saboda tsamin da yayi masu, ga kansu da yake ciwo saboda abinda suka shak'a masu. Haka suka d'aure masu fuska suka fita da su. *** Kuka kawai Maman Labiba takeyi alokacin da taga gawar Alhaji Maiwada, Alhaji Mansur kanshi kasa daurewa yayi, juya baya yayi ya saki wani irin kuka, Alhaji Musa ne yayi ta bashi baki. Gaba d'aya gawar Alhaji ta canza kama, fuskarsa duk da kumbura, wuyansa yayi wani irin ja gwanin tausayi. Brr. Barau ne tare da d'an sandan da yake kula da case d'in Alhaji suka shigo. Hannu suka bama su Alhaji suka gaisa, kallon Alhaji Mansur yayi yana fad'in sunana Brr. Barau, kuma nine lauyen da zan kula da wannan shari'ar ta Alhaji Maiwada, domin nine lauyensu na wajen aiki, bazamu tab'a bari jininsa ya zuba abanza ba, duk wanda yake dasa hannu akisanshi sai mun kamashi, to abun yazo da sauki domin an kama direbansa da ake zargin shine ya kashe shi, saboda an kamashi da laifin yima matar Alhaji fyad'e har yayi sanadiyar zubewar cikinta, yanzu haka yana kulle. Tunda ya fara magana Alhaji Mansur ya zuba masa ido har sai da Brr. Barau ya tsargu da kallon da yake masa. Gyaran murya yayi yana fad'in kada ka damu Alhaji zanyi aiki sosai akan mutuwar Alhaji Maiwada. Kauda kai Alhaji Mansur yayi yana jin wani irin tukukin bakin ciki, yasan komai akan Brr. Barau, domin babu abinda Alhaji Maiwada ya b'oye masa, amma kaji saboda rainin hankali wai shine zai tsayama Alhaji, gashi sun kullama Malan Sani sharrin da babu mai fitar dashi sai Allah, tabbas yasan sune suka aikata hakan, amma iya abinda ya sani a baki ya tsaya beda sheda ko kad'an a hannu, ita kuma kotu da sheda take amfani, dole yasa ido yaga yanda komai zai kasance, idan aka cutar da Malan Sani sai dai Allah ya saka masa. Muryar Alhaji Musa yaji yana fad'in bakomai Brr, mungode sosai, gaskiya ka kyauta da zaka tsaya domin a kwatoma Iyalan Alhaji Maiwada hakkinsu, domin har yanzu ita Hajiyar bata farfad'o ba, shi kuma wannan direba ayi masa hukunci dai-dai dashi domin hakan ya zama darasi a wajen 'yan baya. Brr. Barau yace insha Allahu babu abinda zai gagara. Alhaji Mansur yace yanzu dai muna so a bamu gawar Alhaji muje mu suturta ta. Brr. Barau yace nima abinda yasa nazo kenan saboda nasan Alhaji Maiwada beda kowa a garinnan shiyasa nazo domin an fad'ama wajen aikinsu suna jira suji lokacin jana'izar domin suzo a suturtashi. Dan sandan yace ai duk wani bincike mungamashi, duk wani abun daya kamata anyi dan haka zakuje wajen likita ku gama dashi sai abaku gawar, sannan motarsa nasa yarana su kaita gidanshi yanzu. Jinjina kai sukayi kafin suka nufi ofis d'in likita. Haka aka gama komai aka basu gawar Alhaji Maiwada, acikin motar asibiti aka d'aukeshi saboda babban mutum ne, a motar Alhaji Musa suka tafi. *** Kafin wani lokaci mutuwar Alhaji Maiwada ta yad'u, manyan mutane duk sun halarci k'ofar gidansa domin ayi masa sallah, 'yan wajen aikinsu gaba d'aya sun halarci wajen, Malan Bala sai kuka yakeyi yana tuna rabuwarsu da Alhaji jiya, ko kud'in daya bashi bai gama kashe su ba amma wai ya rasu. Kafin wani lokaci an gama shirya Alhaji, haka mak'udan mutane suka taru aka sallaceshi, kafin Alhaji Marusa ya iso har an sallame, yana zuwa sai dai ya juya domin rakiyar kai gawa. Mr. Kallah kuwa yana gida sai sun dawo zai zo masu gaisuwa, gaba d'aya hankalinsa tashe yake, tunda Alhaji Marusa ya kirashi ya fad'a masa an kashe Alhaji yake jin babu dad'i aransa, amma babu yanda ya iya dole ya bar komai aransa tunda mai faruwa ta faru. Hatta da Abubakar sai da yazo jana'izar Alhaji, duk da baya jin dad'in jikinsa amma haka yazo saboda yana tsoron rashin zuwanshi yasa a zargeshi musamman da mutane suka san suna shiri da Alhaji. Bayan an dawo daga binneshi aka shiga yima juna gaisuwa, sauran abokan aikinshi wad'an da ba musulmai ba haka suka fara zuwa suna gaisuwa, Mr. Kallah ma yazo gaisuwa kuma ya zauna a kusa da Alhaji Marusa anan aka cigaba da zaman gaisuwa dasu. Cikin gida kuwa Maman Labiba itace Uwar amsar gaisuwa, matan unguwa duk sunzo suna tayata zaman makoki, abinci kuwa azahar tanayi aka fara shigo dashi kuloli, abunka da birni sai dai akawo abinci daga waje, *sab'anin wani wajen da zaka iske masu mutuwa sune suke ciyar da 'yan zaman makoki, d'an abincin da suka samu sadaka kafin a share makoki mutane sun cinye wasu hada guzirin na gida*. *** Sai da Ummu tayi kwana d'aya da yini kafin ta farka, Hajiya Amina matar Alhaji Musa tana zaune a gefenta tayi saurin tashi ganin tana motsi, hannu Ummu tasa ta dafe kanta, da k'arfi ta saki ihu tana kiran Abbu. Saurin matsawa Hajiya Amina tayi tana rik'eta. Shigowar wata ma'aikaciya ne yasa Hajiya Amina ta matsa domin ta bata waje, ganin yanayin da Ummu take ciki yasa ma'aikaciyar tayi saurin danna wata alama, kafin wani lokaci sai ga likitoci sun shigo. Fita Hajiya Amina tayi cike damuwa. Haka suka shiga duba Ummu, ganin ta kasa natsuwa yasa dole sukayi mata allurar bacci kafin suka gungurata zuwa wani d'akin gwaji. *** Alhaji Mansur ne da Alhaji Musa suka iso da sassarfa dan Hajiya Amina ta kirashi shine suka taho, Alhaji Mansur yaso ya taho da matarsa amma baya so abar gidan abud'e saboda basu san halin wasu ba. ** Zaune suke a ofis d'in babban likita. Bayan ya gama 'yan rubuce-rubuce ya d'ago kai yana fad'in agaskiya Hajiya ta had'u da lalurar tab'in hankali sakamakon dukan da akayi mata akai da kuma abinda yashiga zuciyarta na tsorata, sannan cikin jikinta ya zube, yanzu haka munyi mata allurar bacci saboda jikinta babu kwari muna buk'atar ta samu hutu shiyasa mukayi mata allura, idan ta samu saukin ciwon jikinta dole zamu maidata asibitin mahaukata wanda nine zan mayar da ita can saboda takasance matar Alhaji Maiwada, tunda na fahimci tana d'auke da wannan lalurar nayi alk'awarin zan kula da ita. Salati Alhaji Mansur yayi yana fad'in Allah mungode maka da wannan jarabawa taka, ya Allah ga baiwarka nan Allah kada ka mayar da Ra'eez Maraya gaba da baya, ya Allah ka bata lafiya. Gaba d'ayansu sukace amin. Alhaji Mansur yace amma likita ina da magana, inaso idan ta samu sauki zamu maidata Kano domin zatafi samun kulawa akusa damu, kuma haka ne kawai zanyi na kyautata ma Alhaji Maiwada, domin yanzu bani da burin daya wuce na rike iyalinsa, kuma na cika masa burinsa na barin garin nan da yayi niya. Gyara zama likita yayi yana fad'in ban tari numfashin ka ba Alhaji, dama tunda naji Alhaji Maiwada beda 'yan uwa agarin nan nake jiran wani nashi yazo domin na nemi wannan alfarmar, naroke ka da girman Allah ka barni na samu wannan ladar, Alhaji Maiwada yana da muhimmanci agaremu, ta silarsa Yayana Alhaji Usman ya samu kayansa da aka sace suka fito tun yana farkon zuwa garin nan, Yayana tunda yaji wannan labari yace shine zai d'auki nauyin kud'in jinyar Matar Alhaji, ayau da muka gano matsalar da take ciki nayi alk'awarin zan kaita wajen abokina da yake kula da masu irin wannan lalurar, kuma acan asibitin zata zauna har Allah ya bata lafiya, sannan idan tana garin nan zatafi saurin dawowa hankalinta tunda anan abun ya sameta. Shiru Alhaji Mansur yayi dan likita ya d'aureshi, ajiyar zuciya ya saki yana fad'in shikenan likita bazan hanaka aikata aikin alkhairi ba, nasan abubuwan alkhairin da Alhaji Maiwada yayi sune suka jawo masa haka, dama ance idan kana aikin alkhairi ko bayan mutuwarka aikinka yana nan, bakomai Allah ya baka lada, kuma zamucigaba da magana ta waya ina jin halin da take ciki. Godiya likita yayi masu, anan sukayi musayar waya Alhaji Mansur yace da anyi sadakar ukku zasu tafi, kafin lokacin yana so su gana da wancan likitan. Murmushi likita yayi yana fad'in babu damuwa. Alhaji Musa yace 'yan sanda sunzo nan kuwa likita? Likita yace sunzo tun a washe garin ranar, sun d'auki hoton shatin hannun Hajiya na dama wanda naga jini acikin k'umbarta, sai sukasa mukayi awon jinin da yake cikin farcanta muka basu sakamakon, sai dai sunce fyad'e akayi mata amma gaskiya babu alamun haka, kila dai garin yin fyad'en ne cikin ya zube, ganin jini yasa sukace fyad'e ne, amma gaskiya babu wani fyad'e. Girgiza kai Alhaji Mansur yayi wani takaici ya turnuk'eshi, gashi dai yasan gaskiyar wasu al'amuran amma beda halin magana. Tashi yayi yana fad'in likita mungode sai mun had'u a kotu ranar litinin dan nasan bazasu ja shari'ar ba, idan angama da wuri zamu wuce saboda ranar ne sadakar ukku. Godiya yayi masu suka fita. Alhaji Mansur yaso Hajiya Amina tazo su koma gida itama ta huta amma Alhaji Musa yace ai babu komai baza'a bar mai jinya ita kad'ai ba. Haka suka tafi bayan sun aje masu abincin da suka zo dashi. Ur's. Nabeelert Lady🖋 [3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.* 1⃣7⃣ Zaune Alhaji Mansur da Maman Labiba suke a tsakar gidan Malan Sani yayin da Halima take jingine da filo Rumaisa tana gefenta gwanin tausayi. Tunda aka tafi da Malan Sani washe gari ta tashi da rashin lafiya, makwabciyarta ce ma tashigo saboda ma'aikaciyar asibiti ce tazo su gaisa dan ta saba kullum sai tashigo sun gaisa kafin ta wuce, bayan ta shigo ta isketa cikin wannan yanayin hakan yasa ta tsaya sai da ta taimaka mata tayi wanka ta had'a mata shayi sannan ta koma gida ta kira mai aikinta suka kama Halima suka nufi asibiti. Bayan anyi mata gwaji aka gano tana da ciki har ya kusa b'arewa sakamakon tashin hankalin data shiga, hakan yasa aka bata magunguna har yamma tana can, sai da matar ta tashi daga aiki kana suka dawo tare kuma ta hanata aikin komai har sai ta warke, taso ta barta a asibiti Halima tace bata so, shiyasa suka dawo, Mai aikinta tasa ta kawo masu abinci dan tace Halima kada tayi aiki. Cike da tausayi Alhaji Mansur yake mata ya jiki tare da kwantar mata da hankali. Hannu tasa ta goge hawayen da suka zubo mata tana fad'in wallahi Alhaji sharri akayima Malan, tunda yashigo na gane ba'a hayyacinsa yake ba, taya za'ace Malan ne zai... Hannu Maman Labiba tasa ta rufe mata baki tana fad'in ya isa haka. Alhaji Mansur yace yanzu kam bamu da wata sheda, duk da nayi magana da Brr. Kamal kuma shima yace sunyi waya da Alhaji akan yana so yaje suyi wata magana mai muhimmanci saboda zai shigar da k'ara, amma yace Alhaji bai riga ya bashi wata sheda da zai iya tsayawa da ita ba, kawai zaije ya tsaya ma Malan Sani idan Allah yasa basu da shedar da zata kada Malan Sani komai zaizo cikin sauki, idan kuma suna da ita sai dai Allah ya bimasa hakkinsa domin kotu da sheda take amfani. Halima tace bakomai nayi imani da k'addara, kuma ina rokon Allah yasa mani juriya akan wannan abun tashin hankalin daya samemu, insha Allahu Allah bazai bar kosu waye suka aikata haka ba. Alhaji Mansur yace haka ake son mutum mai yarda da k'addara, inaso kuma idan komai ya lafa mutafi gaba d'aya Kano tunda Malan Sani yace shima can zai koma. Murmushi Halima tayi tana fad'in matuk'ar aka yanke hukunci mukayi nasara to tare zamu tafi, amma idan sune sukayi nasara zan zauna anan har sai ranar da Malan ya rasu, idan ina raye zan koma Kano da zama, idan kuma nima na tafi to ga Rumaisa nan ku kular mani da ita. Tausayin Halima ne ya kamasu, hannu yasa ya goge idonshi kafin ya mik'e yana fad'in ina so naje naga Malan Sani. Saurin kallonsa tayi tana fad'in dan Allah ka tafi damu. Alhaji Mansur yace shikenan muje. *** Kuka kawai sukeyi Alhaji Mansur ne yake lallashin su. Bayan sunyi shiru Malan Sani yace shikenan yanzu an rufe Alhaji ba tare da nayi rakiyarsa ba? Wallahi an cutar dani, Allah ne kad'ai zai saka mani, yanzu ina Ummun Ra'eez take?.... Labarin halin da take ciki Alhaji Mansur ya bashi. Sosai yake kuka yana fad'in Allah ya isa, Allah ka saka mani. Alhaji Mansur yace bani labarin abinda ya faru.....Komai Malan Sani ya fad'a masa har zuwansa gida ya kwanta. Hannu Alhaji Mansur yasa ya goge kwallar data zubo masa, kallon Malan Sani yayi yana fad'in wad'an nan mutanan shed'anu ne, dalilin barinka araye saboda su d'ora laifin awajenka. Malan Sani yace bakomai Alhaji, zan d'auki kaddarata da hannu biyu, fatana Allah ya albarkaci abinda na bari. Alhaji Mansur yace insha Allahu zaka kara samun wasu zuri'ar ma. Saurin kallon Halima yayi ita ko ta duk'ar da kanta. Tambayarta yayi wata nawa? Da hannu tayi masa nuni wata biyu. Murmushi ne ya sauka akan fuskarshi, itama Halima murmushin takeyi. Malan Sani yace narokeki Halima da ki cire damuwa aranki saboda ki kular mana da zuri'ar mu, kinga dai halin da nake ciki, ke kad'ai zaki cigaba da kula da tarbiyar yaran mu, ki daure kisa juriya aranki dan Allah. Jinjina kai tayi tana hawaye. Alhaji Mansur yace zanga Brr. Kamal insha Allahu zamu san abunyi. Murmushi kawai Malan Sani yayi, dan yasan Alhaji Mansur ya fad'a ne kawai dan ya kwantar masa da hankali, amma yasan dole ayanke masa hukunci. Sallama sukayi masa suka tafi yana kara kwantar ma Halima da hankali. *** Fetur Lucky yasa ma Wayar Naseer da Kamfutar Alhaji bayan sun gama kallon abubuwan da suke ciki, wuta ya kuna nan take suka kama da wuta. Dariya Alhaj Marusa yasa yana fad'in Brr. Barau aiki yayi kyau, saura zuwa kotu, nasan dole a yanke ma Malan Sani hukunci. Brr. Barau yace ai mune da kotu, kuna da ni sannan muna da 'Yallab'ai, dan haka ku kwantar da hankalin ku, wani abu sai ma na zama Alkali. Dariya sukasa gaba daya. **** *** *Safiyar Litinin a kotu*..... Wajen k'arfe tara na safe akayi addu'ar sadakar ukku ta Alhaji Maiwada, bayan an kammala suka nufi kotu saboda k'arfe goma za'a fara shari'a, tare da Halima suka tafi bayan ta mik'a Rumaisa makaranta. Babbar kotu ta cika da al'umma, domin kowa yana so yaji yanda wannan shari'ar zata kasance, hatta da Mr. Kallah sai da yazo, duk da yau litinin yana da aiki a ofis amma haka yazo dan tunda Alhaji ya rasu hankalinsa ba akwance yake ba, gani yake kamar za'a ganosu idan akazo kotu, shiyasa ya tsaya yaga komai ya kammala agabanshi. Brr. Barau yau shiri yayi na musamman, fuskarsa babu alamun far'a dan so yake ya nuna matuk'ar damuwa akan wannan shari'ar saboda kowa ya yarda dashi, koda ya iso bakin kotu be tsaya magana da kowa ba yashiga ciki, dan baya so aganshi tare da kowa ayi tunanin wani abu, shiyasa suka shirya baza suyima juna magana ba har sai sun bar kotu saboda idon mutane ga yan jarida agefe. isowar Alkali yasa kowa ya natsu, bayan ya zauna aka shigo da Malan Sani, gaba d'aya aka bishi da kallo, kwana biyu amma ya canza, Halima kuwa duk'ewa tayi tana kuka. Malan Sani kuwa tunda yashigo yaki kallon kowa. Bayan an natsu Alkali ya bada ikon a karanto k'ara. Tashi Magatakarda yayi yana fad'in *a yau litinin goma ga watan Mayu shekara ta dubu biyu da takwas (10/05/2008), wannan kotu zata saurari k'arar da hukumar kwastam ta shigar akan mutuwar shugabansu Alhaji Hamza Maiwada wanda ake zargin direbansa wajen aikata kisan a daren juma'a da misalin k'arfe bakwai na dare, bayan nan kuma suna zarginsa da hayyek'ema matar Ubangidansa a wannan rana inda sanadiyar haka har cikinta ya zube kuma ta had'u da lalurar tab'in hankali sakamakon dukan da yayi mata akai, yanzu haka tana kwance a asibiti*. Risnawa yayi tare da mik'ama Alkali takardar, komawa yayi ya zauna. Duk'ar da kai Malan Sani yayi hawayen bakin ciki suna zubo masa, addu'a kawai yakeyi. 'Dago kai Alkali yayi yana fad'in ina lauyoyin da zasu gabatar da shari'ar? Tashi sukayi suna risna kai. jinjina kai Alkali yayi kafin ya basu iznin gabatar da kan su. Brr. Barau ne ya fara gabatar da kansa a matsayin wanda zai kare Alhaji, sai Brr. Kamal ya gabatar da kansa amatsayin wanda zai kare Malan Sani. Alkali yace wanda zai fara ya fito. Komawa Brr. Kamal yayi dan ba shine zai fara ba. Matsowa Brr. Barau yayi yana fad'in idan kotu ta bani dama inaso nayima Malan Sani wasu tambayoyi. Kotu ta baka, Malan Sani ya matso gaban kotu. *Brr. Barau*... Kotu zata so taji sunanka da kuma san'ar ka. Sunana *Malan Sani*, kuma sana'ata shine tukin mota. *Brr. Barau*... Malan Sani meye alak'ar ka da Alhaji Maiwada? *Malan Sani*... Bamu da wata alak'a ta jini tsakanin mu, sai dai ina masa aikin tuki, nine direbansa tun farkon daya fara aiki a garin nan. *Brr. Barau*... Zaku kai shekara nawa tare? *Malan Sani*... E to gaskiya mun dad'e dashi, a kalla zamuyi shekara sama da biyar atare. *Brr. Barau*... Idan na fahimceka kun dad'e sosai har kun zama 'yan uwan saboda sabo? *Malan Sani*... Maganar gaskiya Alhaji ba Ubangidana bane kad'ai, ina jinsa tamkar Yayana da muka fito ciki d'aya, domin Alhaji ya gama mani komai arayuwa. *Brr. Barau*... Malan Sani, kotu taji irin yanda ka d'auki Alhaji Maiwada, sai kuma gashi duk irin alkhairin da yayi maka hakan bai hanaka kashe shi ba kuma ka keta ma Iyalinsa haddi... Ina da ja ya mai shari'a, ya kamata abokin aikina ya kula da maganar da yake jifar Malan Sani da ita, har yanzu ba'a tabbatar shine ya aikata kisan ba zarginsa akeyi, be kamata yarik'a masa irin wannan tambayar ba. Nagode. *Alkali*... Brr. Barau ka kiyaye. Risnawa Brr. Barau yayi yana fad'in za'a kiyaye. *Brr. Barau*... Malan Sani aranar juma'a da misalin k'arfe bakwai da 'yan mintuna kana ina? *Malan Sani*... Ina tare da Alhaji a wannan lokacin muna kan hanyar mu ta zuwa gida. *Brr. Barau*... Ko Malan Sani zai fad'ama kotu abinda ya faru a wannan lokacin da suke kan hanyar gida? *Malan Sani*... E to muna cikin tafiya sai tayar motar mu tayi faci, muna kok'arin fita sai ga wasu mutane kamar daga sama, kafin suzo wajen mu sai Alhaji yace na tafi gidansa na tafi ta matarsa gidana saboda yana tsoron wani abu ya faru da ita, shine na tafi ashe kashe shi zasuyi. *Brr. Barau*... Murmushi yayi yana fad'in, Malan Sani kamar yanda ka fada, kace kuna hanyar ku ta zuwa gida ne, wanda mun san cewar Alhaji Maiwada yana zaune a unguwar Apapa ne, sai gashi kun taso daga wajen aikinsa kun canza hanyar da zata sada ku da gida, ko zaka fad'a mana dalilin da yasa bakubi hanyar da kuka saba bi ba. *Brr. Kamal*.... Ina da ja ya mai shari'a, wannan tambayar bata da alak'a da wannan shari'ar, domin kowa yana da ikon bin inda yakeso domin zuwa gida. *Alkali*..... Korafi bai karb'u ba, dole zai amsa wannan tambayar domin tana da alak'a da wannan shari'ar. Brr. Barau kacigaba. *Brr. Barau*.... Risnawa yayi kafin yace kotu tana sauraron ka. *Malan Sani*... Haka ne, bayan fitowar mu daga wajen aiki sai muka had'u da wani yaro yana neman taimako, sai Alhaji yace mu d'aukeshi, bayan ya fad'a mana unguwar da zaije muka tafi, sai dai da muka isa a bakin hanya muka ajeshi saboda nasan layin beda kyau, bayan mun juya zamu koma hanyar mu ta zuwa gida shine mukayi faci har wannan abun ya faru. *Brr. Barau*... Girgiza kai yayi yana fad'in bayan ka isa gida ya akayi ka fito ba tare da Matar Alhajin ba? *Malan sani*.... Bayan na shiga gidan muka gaisa da Madu mai gadin gidan, anan nake fad'a masa zanshiga ciki, bayan na shiga ciki mun gaisa da Hajiya, ina kok'arin na fad'a mata abinda Alhaji yace sai kawai mukaga wasu mutane sun shigo fuskarsu a rufe, Hajiya tana kok'arin magana sai kawai wani ya kwad'a mata sanda, nan take ta fad'i sai ganin jini nayi yana fita daga k'afarta, kafin nayi wani yunku'ri suka hura mani wani abu, tun daga lokacin ban sake sanin abinda yake faruwa ba, domin kaina yayi nauyi, ina kallo suka sa hannunta a wuyana suka yakusheni da farcenta, sai suka turoni waje, bayan na fito wajen gida suka sani a mota muka tafi, suna ajeni k'ofar gidana suka tafi, iya abinda na sani kenan amma wallahi ba nine na kashe Alhaji ba, haka kuma banyima Hajiya abinda ake zargina dashi ba. *Brr. Barau*... Malan Sani zaka iya tafiya. Ya mai shari'a inaso nayima Maigadin gidan Alhaji wasu tambayoyi. Kotu ta baka. *Brr. Barau*... Kotu zata so taji sunan ka da aikin ka. *Sunana Amadu wanda akafi sani da Madu*, kuma aikina shine gadi agidan Alhaji. *Brr. Barau*... Ka kai shekara nawa agidan Alhaji kana masa aiki? *Madu*.... Zanyi shekaru kusan sama da shidda tare dashi. *Brr. Barau*..... Ko akwai wata matsala da kasani wadda take faruwa atsakanin Malan Sani da Alhaji a zaman su? *Madu*... Gaskiya tun had'uwar Alhaji da Malan Sani basu tab'a samun sab'ani ba, asalima Alhaji yana kyautata masa sosai, domin hatta da karatun d'iyarsa shine ya d'auki nauyi, gidan da yake ciki ma Alhaji ne ya cika masa ya sayeshi, gaskiya ban tab'a ganin sun samu matsala ba. *Brr. Barau*.... Aranar juma'a a wane yanayi Malan Sani yashigo gida? *Madu*.... E to gaskiya yashigo ba'a yanayin dana saba ganinsa ba, ina zaune ya buga mani k'ofa, bayan na bud'e sai na ganshi wani iri idanuwansa sunyi ja hannunsa rik'e da wata bak'ar jaka wanda bansan meye aciki ba, sai na tambayeshi ina Alhaji sai yace mani akwai matsala bara ya fito daga ciki, ban tsaya tambayarsa ba na barshi yashiga kasancewar nasan amintaccen Alhaji ne, ina zaune sai naji kamar ihun Hajiya, amma sanin Malan Sani yana ciki sai banyi yunkurin shiga ba, ba'a dad'e ba sai naga Malan Sani ya fito jikinsa duk jini yana tafiya kamar a buge, dana tareshi ina tambayarsa sai kawai ya ture ni har sai da na faad'i, kafin na tashi ya fice, ina lek'awa sai dai kurar mota na iske babu shi, sai nayi saurin shiga ciki, Hajiya na iske a kwance cikin jini hakan yasa nayi saurin fitowa domin na sanar da mutane. Iya abinda na sani kenan. *Brr. Barau*.... Madu mungode zaka iya tafiya. Ina so zanyima Inspector Bello tambaya idan kotu ta bani dama. Kotu ta baka dama. *Brr. Barau*.... Kotu zata so taji sunnanka kuma kayi mata bayanin binciken da kukayi. *Sunana Bello Kabir*, nine d'an sandan da yake kula da case d'in mutuwar Alhaji Maiwada. A ranar juma'a mun samu waya daga wasu daga cikin ma'aikatan mu da suka fito aiki cewar sun samu motar Alhaji Maiwada tare da gawarsa aciki, bamu b'ata lokaci ba mukaje wajen, bayan an d'auke gawarsa daga motar sai muka binciki motar, mun samu sirinji da kwalbar wata allura a ciki, haka muka had'a komai muka nufi asibiti da gawar domin likitoci suyi bincike akai. Bayan munje mun kama Malan Sani sai na koma asibiti, bayanin da likita yamun akan mutuwar Alhaji yasa a jiya na koma gidan Malan Sani domin yin wani bincike, a binciken da mukayi mun samu wata bak'ar jaka b'oye a d'akinsa acan k'asan gado wacce take d'auke da muk'udan kud'i a kalla zasu kai milliyan biyar, a cikin jakar muka samu irin kwalbar allurar da muka samu a motar Alhaji. Wannan sune takardun binciken da akayi ga kuma jakar. Cusa kai Halima tayi cikin k'afafuwanta tare da sake sakin wani irin kuka, tunda 'yan sanda suka zo jiya suka gano wannan jaka a d'akin Malan Sani take cikin tashin hankali, bata san lokacin da aka aje jakar ba, ta tabbata Malan Sani ba zai aje wannan jaka ba, kuma ita tunda aka tafi da Malan Sani bata sake shiga d'akinsa ba sai kawai jiya da aka zo bincike taga an fito da jaka ashe wannan abun ne aciki, shikenan tasan babu wanda zai fitar da Malan Sani sai Allah. *Brr. Barau*... Mungode zaka iya tafiya. Ina so zanyima likitan da yayi binciken gawar Alhaji tambaya idan kotu ta bani dama. Kotu ta baka dama. Likita ya fito gaban kotu. Wani abokin aikin likitan ne ya mike yana fad'in likitan yayi waya yana hanya ya taho motarsa ta samu matsala amma ya kusa k'arasowa. Dafe kai Brr. Barau yayi, kada dai likitan bazai zo ba gashi akwai abubuwa masu muhimmanci awajensa, dole ya nemi hanyar fita yanzu ko hutu ne ya nema. Risnawa yayi yana fad'in ya mai shari'a ina rokon wannan kotu data bada izinin hutu ko na rabin sa'a ne domin akwai abinda za'a kawo mai muhimmanci wanda ya shafi wannan shari'ar. Alkali yace muje ga sheda ta gaba kafin likita ya k'araso. Risnawa Brr. Barau ya sakeyi yana fad'in ina neman alfarmar kotu ta bada wannan hutu saboda wani uzuri daya taso mani yanzu. Jinjina kai Alkali yayi yana fad'in kotu zataje hutun mintuna ashirin, idan be iso ba zamu cigaba da gabatar da shari'a. Buga tebur yayi. Girgiza kai Alhaji Mansur yayi hawaye suka zubo masa, har cikin ranshi yana zargin wannan *ALKALIN*. Tashi yayi ya fita zuciyarsa na zafi, ga tunanin Ra'eez wanda har yanzu besan Mahaifinsa ya rasu ba, tsoro yake kada wani ya fad'a masa tunda Alhaji babban mutum ne mutuwarsa bazata b'oyu ba, dole gobe idan suka koma yaje ya d'aukoshi. Ur's. Nabeelert Lady🖋*Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.* 1⃣8⃣ A waya Brr. Barau ya kira likita, hak'uri ya bashi yace gashinan zuwa. Sosai Brr. Barau ya sake nana ta masa abinda zaice kafin ya kashe wayar. ** Bayan an dawo hutu Alkali ya bada izinin acigaba da gabatar da shari'a, tambaya yayi idan likitan ya iso? Tashi Brr. Barau yayi yana fad'in ya iso ya mai shari'a, inaso nayi masa tambaya idan kotu ta bani dama. Kotu ta baka dama, likita ya fito gaban kotu. *Brr. Barau*... Kotu zata so taji sunan ka da kuma bayanin binciken da kayi. *Sunana Aliyu Sani*, nine likitan da yayi binciken gawar Alhaji Maiwada, a binciken da nayi mun samu shatin hannu wanda akayi amfani dashi wajen shak'e Alhaji kafin aka masa wannan allurar da 'yan sanda suka kawo mana wacce aka samu a motarsa, ita dai wannan allura tana da had'ari sosai, domin tana kisa a cikin lokaci kad'an, Alhaji yaci matuk'ar wahala alokacin da akayi masa allurar, domin alokacin da aka kawosa tuni ya dad'e da rasuwa, haka wuyansa ya kumbura kuma yayi ja, gaba d'aya rahoton dana rubuta yana wajen Inspector Bello na had'a masa. *Brr. Barau*... Jinjina kai yayi yana fad'in ko allurar da aka samu a cikin jakar da take d'akinsa tayi dai-dai da wadda aka samu a motarsa? *Likita*... Kwarai kuwa, dukkansu iri d'aya ne. *Brr. Barau*... Mungode likita zaka iya tafiya. Ina so zanyi tambaya ta k'arshe ga likitan da yake kula da Matar Alhaji Maiwada idan kotu ta bani izini. Kotu ta baka dama. *Brr. Barau*.. Kotu tana so taji sunan ka da kuma bayanin binciken daka gudanar akan matar Alhaji. *Sunana Saddik Mansur*, nine likitan da nake kula da Hajiya Bilkisu matar Alhaji Maiwada, bayan da 'yan sanda suka kawo ta sai muka gano cikin da yake jikinta ya zube sakamakon fad'uwar da tayi asamanshi da k'arfi, haka kuma a rahoton da aka bada na cewar fyad'e ne yayi silar zubewar cikinta maganar gaskiya babu alamun wani fyad'e, sanadiyar bugun da akayi mata akai yasa ta faad'i saman cikin wanda ya jawo zubewarsa, sannan taji abinda ya firgita ta, sannan sakamakon bugun da akayi mata akai ya jawo ta samu tab'in hankali wanda yanzu haka tana kwance tana karb'ar taimako daga gare mu, sai bincike na k'arshe shine mun samu jini a cikin farcenta, bayan da muka auna muka gano sakamakon duk na had'a na bama 'yan sanda. Wannan shine abinda na sani. *Brr. Barau*... Likita mungode zaka iya tafiya. Murmushi yayi yana fad'in ya mai shari'a Malan Sani yayi nasarar kashe Alhaji Maiwada ne ta hanyar daya shirya, tun daga kisan da yayima Alhaji ya tabbatar mana cewar ya dad'e yana shirya yanda hakan zata kasance, domin a daren juma'a bayan sun taso daga wajen aiki sai Malan Sani yayi dabara ya canza masu hanyar da zata sadasu zuwa gida, yayi amfani da faci ya tsayar da motar domin ya fita ya duba, da haka ne ya shiga bayan mota da niyar d'aukar wani abu kasancewar Alhaji baya zama a baya sai gaban mota, ta baya ya shakoshi kafin ya caka masa allura a wuyansa kafin ya d'auki jakar kud'in Alhaji yayi saurin barin wajen. Yayin da yayi kok'arin hayk'ema Matar Alhaji sunyi kokowa da ita domin an samu shatin faratan ta a wuyansa, sannan jinin jikin farcenta yayi dai-dai da jinin Malan Sani, sannan an samu hoton hannunsa a nata, ganin zata tona masa asiri sai ya buga mata abu akai, ganin ta suma ya d'auka mutuwa tayi shiyasa yayi saurin barin wajen yana tunanin ya gama da ita. Wad'annan sune sakamakon da aka samu a wajen likita da duk wata sheda da zata tabbatar ma kotu Malan Sani shine ya aikata wad'an nan laifukan da ake zarginsa dashi. Ina rokon wannan kotu mai albarka da tayi amfani da wad'annan hujjoji domin ta yanke ma Malan Sani hukuncin da yayi dai-dai dashi. Nagode. Gaba d'aya kotu ta d'auki kus-kus kowa da abinda yake fad'a. Brr. Kamal gaba d'aya jikinsa yayi sanyi domin yasan sun fad'i, duk wata sheda Brr. Barau ya gabatar da ita, kuma ko waye dole ya yarda da abinda aka gabatar saboda sheda ce tabbatacciya, amma dole ya tashi yayi wani abu ko dan kada aga gazawarsa. Bubbuga tebur Alkali yayi, bayan anyi shiru Alkali yace Baristan da yake kare wanda ake k'ara ko kana da abinda zaka fad'ama kotu? Tashi Brr. Kamal yayi cike da kwarin guiwa yace ina dashi ya mai shari'a, ina so nayi ma Maigadin gidan Alhaji tambaya idan kotu ta bani dama. Kotu ta baka dama maigadi ya fito. *Brr. Kamal*... Madu a cikin bayanin daka bayar naji kace lokacin da Malan Sani ya shigo gidan ya fad'a maka akwai matsala, sannan kace kaga idanuwansa sunyi ja, sannan kaga bak'ar jaka a wajensa, shin ko waccan jakar da aka gabatar tayi dai-dai da wadda ka gani? Sannan daya shigo kaga yanayin maye atare dashi? Sannan alokacin da kace kaji ihu meyasa bakayi saurin shiga ciki ba amatsayinka na wanda yake kula da mutanan gidan? Kace Malan Sani ya fito da jini a jikinsa, sannan ka ganshi acikin yanayi na maye, amatsayinka na maigadi ya akayi ka barshi har ya fita daga gidan ba tare da ka rik'esa ba? *Madu*.... E to gaskiya lokacin daya shigo babu yanayin Maye a tare dashi, kawai dai baya cikin natsuwarsa, alamu sun nuna kamar yana cikin tashin hankali domin jan da idanuwansa sukayi sun nuna alamun kamar wanda yayi kuka. A lokacin da naji ihu kuma dalilin da yasa ban shigaba saboda nasan Malan Sani yana ciki, kuma nasan amintaccen gidan ne, alokacin da ya fito kuma nayi kok'arin tareshi amma sai ya ture ni, kuma tabbas da yanayin maye ya fito, sai dai kafin na tashi ya fice, saboda gaskiya jikina ne yayi sanyi saboda ganin abinda ban tab'a zato ba, hakan yasa na kasa yunkurin rikeshi da kyau. Sannan kuma wannan jakar tabbas irin tace na gani a hannunsa, kuma nasan ta Alhaji ce domin koni nasha d'aukarta idan ya fito zai fita domin nasan jakarsa ce da yake saka kamfutarsa. *Brr. Kamal*.... Kace jakar kamfutarsa ce, kenan lokacin da Malan Sani ya shigo da ita kamfutarce aciki? sannan kace ya fito cikin yanayin maye, shin ya fito da jakar ko kuma be fito da ita ba? *Brr. Barau*... Ina da ja ya mai shari'a, duk da Madu yace yaga Malan Sani ya shigo da jaka ta kamfutar Alhaji ai be zama dole ace kamfutar bace aciki tunda alokacin be bud'a masa ba, ya kamata abokin aikina yasan irin tambayar da zaiyima mai bada sheda. Nagode. *Alkali*... Brr. Kamal ka gyara yanayin tambayarka. Risnawa yayi yana fad'in zan kiyaye. *Brr. Kamal*... Madu kotu tana sauraronka shin kaga Malan Sani ya fito da wannan jakar? *Madu*.... A gaskiya ban lura da hannunsa ba, saboda yana fitowa naga jini a jikinsa sai hankalina ya tashi hakan yasa bazan iya cewa ya fito da jaka ba. Iya kar abinda na sani kenan. *Brr. Kamal*.. Jinjina kai yayi yana fad'in mungode zaka iya tafiya. Ina so nayima Malan Sani wasu tambayoyi idan kotu ta bani dama. Kotu ta baka dama. *Brr. Kamal*... Malan Sani kace alokacin da aka tare ku Alhaji yace ka tafi domin kaje ka tafi da iyalinshi gidan ka, shin ko zaka fad'ama kotu abinda kuka tattauna da yasa yace kaje ka tafi da matarsa. *Malan Sani*... Tabbas Alhaji shine yace naje na tafi da Hajiya, sannan ya bani jakar kamfutarsa yace na tafi da ita saboda mutanan da suka taremu kada su ansheta dan akwai abubuwa masu muhimmanci aciki. Hannu Brr. Barau yasa yana gyara zaman gilashinsa jin abinda Malan Sani ya fad'a, kada fa aje allura ta tono galma, kada ace Malan Sani ya b'oye wata shedar da zata tabbatar da abinda sukayi. *Brr. Kamal*.... Malan Sani kace akwai abubuwa masu muhimmanci acikin kamfutar Alhaji hakan yasa ya baka ka tafi da ita, shin ko zaka fad'a mana wani abu wanda ka sani idan Alhaji ya sanar da kai. *Malan Sani*... Tabbas akwai masu neman rayuwar Alhaji, kuma hakan ya faru ne saboda sun gano yasan wani sirri nasu akan abubuwan da sukayi mashi, kuma ya shirya komai yana jiran litinin tayi domin ya shigar da k'ara saboda ya samu duk wata sheda da zata tabbatar da abinda sukayi domin shedar bidiyo ce da maganganunsu aciki, wanda suka san duk abinda yayi hakan yasa suka shirya kashe shi. Wannan dalilin ne yasa ya bani kamfutar yace na tafi da ita. *Brr. Kamal*... Ko zaka iya fad'a mana su waye suke kokarin kashe shi? *Malan Sani*... E to wad'an da aka turo ban san su ba, amma mutanan da suke cikin kamfutar 'yan tawagar Alhaji Marusa ne kuma shine babban su domin shine abokin takun sak'ar Alhaji. A zabure Brr. Barau ya tashi yana fad'in ya mai sharia wannan magana da Malan Sani yake fad'a ba gaskiya bane, yariga da yasan komai na Alhaji hakan yasa zeyi amfani da wannan damar ya kare kanshi domin ya ga beda wata hanyar tsira, Malan Sani yasan duk wani sirri na Alhaji, yasan cewar sun samu sab'ani da Alhaji Marusa alokacin baya, hakan yasa zaiyi amfani da wannan damar ya sako Alhaji Marusa a cikin wannan shari'ar, ina so kotu tayi watsi da wannan gurguwar hujjar ta Malan Sani tayi duba da hujjar zahiri da aka gabatar mata domin ta yanke masa hukunci, domin Malan Sani zai b'atama kotu lokaci ne kawai, kuma idan beyi hankali ba Alhaji Marusa yana da damar neman hakkinsa akan b'ata masa suna da yake kok'arin yi. Nagode. *Brr. Kamal*... Ya mai shari'a maganar Malan Sani tana kan hanya, babu wanda besan alak'ar da take tsakanin Alhaji Marusa da Alhaji Maiwada ba, kuma tabbas hakan zata iya kasancewa domin Alhaji Marusa yana takun sak'a da Alhaji Maiwada. Inaso wannan kotu da tayi duba da maganar Malan Sani, kada tayi saurin yanke hukunci, abashi dama domin ya tabbatar da abinda ya fad'a. Nagode ya mai shari'a. Hayaniya ce ta cika kotun. Bubbuga tebur Alkali yayi kafin akayi shiru. Kallon Malan Sani yayi yana fad'in Malan Sani ko kana da shedar da zaka tabbatar ma kotu abinda ka fad'a gaskiya ne? Duk'ar da kai Malan Sani yayi hawaye suna zubo masa yace bani da sheda ya mai shari'a domin mutanan da suka shiga gidan Alhaji sune suka amshe kamfutar da shedar take ciki. Ajiyar zuciya Brr. Barau ya saki jin abinda Malan Sani ya fad'a. Girgiza kai Alkali yayi yana fad'in kowa ce kotu tana amfani ne da kwakkwarar hujja kafin ta yanke hukunci, dan haka wannan kotu baza tayi amfani da abinda ka fad'a ba amatsayin hujja. Brr. Kamal idan kana da sauran tambaya kotu tana sauraronka. Jiki a sanyaye Brr. Kamal yace bani da ita ya mai shari'a. Komawa yayi ya zauna yana jin d'aci aranshi, tabbas yasan akwai munakisa acikin wannan shari'ar, amma saboda basu da hujja dole suyi hakuri Allah zai saka masu. *Alkali*... Brr. Barau kana da sauran abinda zaka fad'ama kotu? Tashi yayi yana fad'in bani da sauran abun fad'a, ina so wannan kotu da tayi gaggawar yanke ma Malan Sani hukunci saboda zaluncin daya aikata. Nagode. Rubutu Alkali yayi kafin yace kotu zataje hutu na rabin sa'a. Bubbuga tebur yayi kowa ya tashi. Zamewa k'asa Malan Sani yayi yana sakin kuka mai tsuma zuciya. Da sauri Alhaji Mansur da su Halima sukayo wajensa. Ur's. Nabeelert Lady[3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.* 1⃣9⃣ Hannu Alhaji Mansur yasa ya kamo Malan Sani yana fad'in kayi hak'uri Malan Sani, Allah yana tare da kai, koda sunyi nasara akan ka yanzu wallahi baza suyi nasara akan ka ba ranar lahira, Allah yasan komai, kuma yana kallon su, shine kad'ai zai saka maka, zuciyata tana mani wani tunani akan wannan Alkalin, sai dai bana so nayi zarginsa kada Allah ya kama ni da laifi, a gaskiya daga farko yanda naga yana yawan goyon bayan Brr. Barau sai nake tunanin ko an bashi cin hanci ne, amma daga baya sai na gano ko wane Alkali hakan zaiyi, domin kotu da sheda take amfani, da yawan Alkalai suna yanke hukunci bisa hujjar da aka gabatar masu, ko da hujjar ta k'aryace matuk'ar aka aminta da ita suna amfani da ita, dan haka kayi hak'uri Allah zai saka maka. Hannu Malan Sani yasa ya goge ido shi yana fad'in bakomai Alhaji, wallahi tun ba yau ba na sadak'as, nasan dole irin wannan hukuncin ya hau kaina, shiyasa tunda farko ban tsaya b'atama kaina lokaci wajen fad'ama Brr. Barau komai ba daya tambaye ni, ai kunga alokacin banyi maganar dalilin da yasa Alhaji ya bani kamfutarsa ba, ban kawo komai na abinda nasan sunyima Alhaji ba, saboda nasan kona kawo bani da hujjar tabbatar da hakan, saboda Brr. Kamal ne yasa na bud'e baki nayi magana, shima bana so yaga yana mani kok'ari amma naki bashi had'in kai, amma kaga yanzu da yasan babu hujja zai hak'ura, wallahi na d'auki k'addarata, fatana Allah ya bani ikon cinyeta. Cike da tausayi Alhaji Mansur yace amin Malan Sani. Cikin kuka Halima tace nikam Malan zan tafi gida, bazan iya tsayawa a yanke maka hukunci ba, ina tsoron binda zai faru dani, bana so muyi asarar abinda yake ciki na. Jinjina kai Malan Sani yayi yana fad'in tunda na ganki naji rashin dad'in zuwanki, kinsan baki da lafiya, kuma nasan matuk'ar aka yanke mani hukunci wani abun zai iya faruwa da ke, dan Allah ki koma gida, kinga an kusa tashin su Rumaisa idan ta koma gida zata iske babu kowa, ki kwantar mata da hankali, bana so tasan abinda yake faruwa har sai ta k'ara hankali. Alhaji Mansur yace bara mu rakata ta tafi hakan zaifi, dama tace tana son zuwa shiyasa muka taho da ita. Malan Sani yace akwai kud'i a inda nake ajewa kiyi amfani dasu, tunda kina sana'ar cikin gida ki k'ara jari nasan Allah bazai tozarta ki ba. Kai kawai ta d'aga tayi waje da sauri. *** Bayan kowa ya dawo Alkali yashigo, nan kowa ya natsu. Zama yayi yana gyara takardu. Kotu tayi tsit tana jiran abinda Alkali zai yanke. *Alkali*... 'Dago kai yayi yana fad'in bayan dogon bincike da kwararan hujjoji da aka gabatar agaban wannan kotu, kotu tayi dogon nazari akansu kuma ta tabbatar da ingancin su, domin duk abinda aka gabatar mata babu wanda yake na bogi, an tabbatar cewar an samu allurar da akayima Alhaji Maiwada agidan Malan Sani, sannan an tabbatar da hoton hannun jikin wuyan Alhaji yayi dai-dai dana Malan Sani, haka zalika an tabbatar da hoton jikin hannun matar Alhaji yayi dai-dai dana Malan Sani, sannan jinin da yake jikin farcenta yayi dai-dai dana Malan Sani, bayan haka Malan Sani ya gaza kawo ma kotu wata hujja da zata tabbatar da abinda ya fad'a gaskiya ne, dan haka kotu zata yanke hukunci. *A k'arkashin penal code sashe na 302,da 201,da 180, da 340 sashen kisa amfani da makami ko wani abu, bisa la'akari da wannan sashe na kundin tsarin mulki na k'asa penal code, wannan kotu ta yanke ma Malan Sani hukuncin d'aurin rai da rai agidan yari, sannan zai biya tarar naira dubu d'ari biyar ga Iyalan Alhaji amatsayin cin zarafinta da yayi na yunk'urin haike mata, haka zalika zai biya diyya ga Iyalan Alhaji idan suna da buk'atar hakan. Kottttt!!!!.* Gaba d'aya mutanan kotun suka mike kowa da abinda yake fad'a, wasu suna yabama Alkali da Brr. Barau abisa kok'arin da sukayi, yayin da wasu suke ganin gaskiyar Malan Sani. Haka kowa ya fita 'yan sanda suka taso Malan Sani wanda hawayen idanshi suka k'afe ya koma yin kukan zuci. Alhaji Mansur kasa motsi yayi daga inda yake, gaba d'aya jiyake kamar amafarki abubuwan suke faruwa. Maman Labiba kuwa kuka kawai takeyi. Alhaji Musa ne da Alhaji Usman suka k'araso wajen Alhaji Mansur, kamoshi Alhaji Musa yayi suka fito waje. Jingina sukayi da mota Alhaji Musa yana fad'in sai hak'uri Alhaji, Allah kad'ai yasan gaskiyar wannan al'amarin, domin har cikin zuciyata na kasa yarda da abinda ya faru, na jima da sanin Malan Sani haka kawai nake jin bazai iya aikata abinda akace yayi ba. Alhaji Usman yace wallahi kaji na rantse maka banyarda da abinda aka gabatar ma kotu ba, kawai babu yanda zamuyi ne, koda zamuje kotun da tafi wannan iya hukuncin da za'a zartar kenan, saboda ko waye aka bama wannan shedun dole ya amince dasu, mu da mukasan hakan bazai yuwu ba mu kad'ai zamu iya k'aryatawa, amma an cutar da Malan Sani, domin nasan waye Alhaji Marusa, zai iya komai akan kud'i, tunda naji sun fara takun sak'a da Alhaji Maiwada nasan ba zai barshi haka ba, domin duk wani ma'aikacin kwastam da za'a kawo nan matuk'ar mai gaskiya ne Alhaji Marusa shine yake silar barinsa garin nan, saboda aminin Mr. Kallah ne shugaban Kwastam na k'asa. Alhaji Musa yace wallahi tunda Malan Sani ya fara bada labarin dalilin da yasa aka kashe Alhaji naji na yarda da abinda ya fad'a, ko Brr. Barau beda gaskiya, domin a lokacin naga yanda yanayinsa ya canza, sai dai kawai mu barma Allah amma sun cutar da Malan Sani. Alhaji Usman yace kasan abinda yafi bani mamaki? Brr. Barau lauyen Alhaji Marusa ne, sai gashi ana fad'in wannan abu ya fito da wuri amatsayin wanda zai kare Alhaji Maiwada, a tunanina Brr. Kamal shine lauyen daya tsayama Alhaji a wancan karon, amma sai gashi an juya abun, tun daga lokacin nasan akwai wani abu. Ajiyar zuciya Alhaji Mansur yayi yana fad'in duk abinda zan fad'a maku bazai canza komai ba, amma kusa aranku Brr. Barau, Mr. kallah, 'Yallab'ai da Alhaji Marusa duk a rumfa d'aya suke, nasan mutane ukku d'ayan ne ban sani ba, amma wallahi su dukansu munafukai ne, babu yanda zamuyi ne dole mu barma Allah, zanje na biya tarar da akasa ma Malan Sani, sannan amatsayina na dangin Alhaji da Matarsa mun yafe diyyar da aka fad'a, kuma insha Allahu yau zamu wuce Kano, kome kenan zamuyi waya saboda Bilkisu. Alhaji Usman yace wannan ba matsala bane, insha Allahu zata samu kulawa kamar tana kusa da ku, su kuma ka barsu, wata rana Allah zai nuna su a lokacin da basuyi zato ba, zasuji kunya tun aduniya, ina rok'on Allah ya k'ara masu tsawon kwana ko dan su girbi abinda suka shuka. Gaba d'aya suka amsa da amin. K'arasawa sukayi wajen Brr. Kamal, anan sukayi masa godiya. Brr. Kamal kam hak'uri yayi ta basu zuciyarsa cike da damuwa. Alhaji Mansur yace haba wallahi bakomai, mun bar ma Allah. Kafin a tafi da Malan Sani Alhaji Mansur ya rok'esu alfarmar su bashi mintuna biyar. Matsawa sukayi daga wajen suna fad'in yayi sauri. Dafa kafad'ar Malan Sani yayi yana fad'in kasa Allah aranka, kuma kacigaba da addu'a Allah maji roko ne, sannan yana saurin amsa addu'ar wanda aka zalunta yayi hak'uri, insha Allahu wata rana zakaga sakamakon hak'urin da kayi, kuma ina tabbatar maka zaka fita daga wajen nan, ta silar Alhaji Maiwada kashigo wajen nan, domin kana aiki a k'asanshi akayi amfani da wannan aka kulla maka wannan abun, insha Allahu jinin Alhaji shine zai kwato maka hakkin ka, da izinin Allah sai Ra'eez ya zama lauya, domin tun yanzu zan fad'a masa irin zaluncin da akayi ma mahaifinsa da kai, zai tashi da burin d'aukar fansa, ta haka ne zai dage ya cimma burinsa. Kai Malan Sani ya jinjina yana fad'in zan so naga wannan ranar, ka dage Alhaji Ra'eez yayi karatu, kada ka barshi a k'asar nan, domin har yanzu acikin makiyan Alhaji babu wanda yasan yana da 'Dah, insha Allahu sai Ra'eez ya basu mamaki. Ayanzu da kayi wannan maganar sai naji wani haske ya ziyarci zuciyata, kuncin da nakeji yayi sauki, inajin zan shiga gidan yari hankali kwance, kuma zan zauna ba tare da wata damuwa ba, domin bazan bari damuwa ta kamani ta kassara lafiyata ba, zan roki Allah ya ara mani rana domin naga wannan rana da kake fad'i, nagode sosai Alhaji. Alhaji Mansur yace haka nake son ji Malan Sani, ayanzu kasa zuciyata tayi dad'i, domin damuwakar zata sa naji babu dad'i, amma ayanzu nasa burin d'aukar fansa, zan tsaya ma Ra'eez har ya kai matsayin da zai tsaya mana, kuma insh Allahu zan kula da matarka da d'iyar ka, Allah ya k'ara maka hak'uri. Malan Sani yace amin. Haka aka tasa Malan Sani suka shiga mota mutane sai kallonshi akeyi, shi ko gaba d'aya yaji damuwarsa ta ragu sosai, haka suka bar kotu. *** Hannu Halima tasa ta goge idonta bayan ta gama jin abinda ya faru, sannan Alhaji Mansur ya fad'a mata yanda sukayi da Malan Sani. Murmushi tayi wanda yafi kuka ciwo tana fad'in daga yau nima zanyi yaki da damuwar da take zuciyata, dole nayi irin ta Malan matuk'ar ina so naga wannan rana, haka idan ina so na raini yaran mu dole na cire komai araina, zan toshe kunnuwana daga jin surutun mutane, zan bama kowa mamaki domin zan kasance jarumar mace wadda tafi wasu mazan, Allah ya shige mana gaba. Alhaji Mansur yace amin Halimatu, hakika kin k'ara sanyaya mani zuciyata da kalamanki, kamar yanda kika d'auki wannan k'addarar ina tabbatar maki Allah bazai barki haka ba, zan tsaya akan al'amuran ku, duk wata matsala bana so ki b'oye mani, ki d'auke ni amatsayin Yayanki, ga Maman Labiba nan ki d'auketa amatsayin 'Yar uwarki, insha Allahu babu abinda zai gagara. Jinjina kai Halima tayi tana masu godiya. Alhaji Mansur yace zamuje can gidan domin a kulleshi, zan aiko da duk wasu kayan abinci da suke gidan saboda idan an barsu zasu lalace, nasan hakkin Ra'eez ne da Bilkisu, kuma zan masa bayani nasan bazai hana a baku ba, ita kuma Bilkisu ga halin da take ciki, saboda haka babu wata matsala dan an baku abinci, sauran kayanta zan aikama Likita dasu saboda arika kula da tsaftar ta, idan akwai wad'an da ya kamata abayar zan fad'a masa ya aika dasu gidan marayu, haka kayan Alhaji duk zan tafi dasu, idan Ra'eez ya d'auki wanda yake so sauran za'a bada sadakarsu dan banga amfanin ajesu ba, sauran abinda yake da amfani duk zamu tafi dasu, kaya masu nauyi ne kawai zamu bari nasan babu abinda zai samesu, domin munyi magana da Alhaji Musa yace zai kawo maigadin da zai zauna agidan sai na rik'a biyanshi saboda Madu yace bazai iya zama ba. Halima tace mungode sosai, Allah ya biyaka da alkhairinsa, kuma insha Allahu zan rik'a zuwa duba Ummun Ra'eez sai ka fad'a mani sunan asibitin. Alhaji Mansur yace sai dai muje tare domin likitan ya ganki, dan na fad'a masa kada ya yarda da kowa, tunda gaki ke kad'aice wadda zata rik'a zuwa wajenta dan ina jin tsoron a illata ta. Maman Labiba tace wannan haka yake. Tashi yayi yana fad'in bara muje mu fara da wuri dole ma sai gobe zamu tafi saboda mu gama komai, tunda ga mota Alhaji Musa ya bani nayi zirga-zirga da ita gara na gama, idan zamu kawo kayan abincin sai ki shirya muje can asibitin. Halima tace shikenan sai kunzo. ** Duk wani abu mai muhimmanci na takardun Alhaji sai da suka had'asu a cikin akwati, kayansa kaf sun had'a, dama shi Alhaji Maiwada baya tara sutura, da yayi d'inki yake bayar da wasu dan baya son tara kaya. Haka kayan Ummu duk sun had'a mata, sai kayan abinci suka had'a komai sukasa amota. Madu sai kuka yakeyi. Suna cikin had'a kaya sai sukaji sallamar Ladi. Bayan tashigo sai tayi turus, kada dai abinda takeji gaskiya ne? Tunda ta shigo Lagos a mota take jin ana wani labari, sai dai bata gazgata ba. Ganin Madu yana kuka yasa tayi saurin matsowa tana tambayarsa. ** Kuka kawai Ladi takeyi bayan da ta gama jin komai. Maman Labiba tace sai hak'uri Ladi, haka Allah ya tsara bamu da hanyar kaucewa. Ladi tace ikon Allah, wannan abu da me yayi kama? Da zan tafi dubu ashirin Alhaji ya bani kud'in gudummuwa Hajiya ta k'ara mani goma ashe shikenan rabuwar kenan, ya Allah kajik'an Alhaji, itama kuma Hajiya Allah ya bata lafiya, Malan Sani kuma Allah ya saka mashi. Gaba d'aya suka amsa da amin. Ladi tace dan Allah kuje dani na gano Hajiya, shikenan yanzu dole na koma gidana amma insha Allahu bazan manta da alkhairinsu ba. Alhaji Mansur yace shikenan bara mu k'arasa sai mu tafi. Ladi tana kuka haka ta tayasu had'a kaya, sun bata wasu kayan abincin hada wasu kayan Ummu Maman Labiba ta bata. Alhaji Mansur yace zaije ya ciri kud'i sai ya basu na sallamarsu. Haka suka rufe ko ina bayan sun zare mahad'ar wutar gidan, dama kuma wutar kati ce. Bayan sun fito suka rufe gate d'in gidan suka tafi hada Madu, Alhaji Mansur yace idan ya dawo anjima sai ya bama Alhaji Musa mukullin gate d'in da motarsa tunda a hotel zasu kwana saboda da wuri zasu tafi. Sai da suka aje kayan sannan suka d'auki Halima suka nufi asibiti. A mota sai jajanta ma Halima Ladi takeyi tana fad'in tunda unguwarsu babu nisa bazata yarda zumunci ba. *** Kallon su kawai Ummu takeyi, domin tunda ta farka bata magana sai kallon mutane. Ganin su Halima da Ladi suna kuka yasa itama ta fashe da kuka. Girgiza kai Dr. Saddik yayi yana fad'in abinda takeyi kenan tunda ta farka, idan ta gama kallon mutum sai kawai ta fashe da kuka. Alhaji Mansur yace yaushe ne za'a maidata can? Dr. Saddik yace nan da kwana biyu idan ta k'arasa warwarewa. Alhaji Mansur yace ga Halima nan itace Matar Malan Sani, idan ba ita ba kada abar kowa yazo wajenta. Dr. Saddik yace wannan ba damuwa, zan amshi lambarta kome kenan zan rik'a mata bayani. Alhaji Mansur yace mungode likita. Haka suka gama ganinta ba tare da tace masu komai ba suka tashi zasu tafi bayan sun aje akwatin kayanta. Har sun kai k'ofa sukaji muryarta tana fad'in Abbun Ra'eez sun kashe shi, akira mani Ra'eez kada su kashe mani shi. Saurin juyowa sukayi gaba d'aya. Shiru tayi sai kuma ta fashe da kuka tana fad'in duk saina kashe su da wuk'ar makka. Hatta da Alhaji Mansur sai da kwalla ta cika masa ido, jiki a sanyaye suka bar d'akin. Dr. Saddik yace kada ku damu, dama fatana ta fara magana, tunda ta fara sai mugodema Allah, insha Allahu zata samu lafiya. Alhaji Mansur yace mungode sosai. Haka sukayi mashi sallama suka tafi. ** Bayan Alhaji Mansur ya ciro kud'i yayi masu sallama mai tsok'a, godiya sukayi mashi Madu yace zai tafi. Alhaji Mansur yace wai Madu yanzu ina zakaje? Madu yace zanje na nemi wajen da zan zauna kuma. Da sauri Halima tace idan zaka yarda ka zauna a shagon waje na gidan mu hakan zai zamar mana tsaro musamman yanzu da babu namiji agidan dan Allah. Jinjina kai Alhaji Mansur yayi yana fad'in maganar ki gaskiyace, abinda zuciyata take tunani kenan. Dan Allah Madu ka zauna hakan zai zame masu kariya, kaga akwai Rumaisa, kuma kana da amana ka zama tamkar d'an uwa agaremu, duk da wanda ya had'amu baya raye be kamata mubar abinda ya had'a ya lalace haka ba. Jinjina kai Madu yayi yana fad'in shikenan zan zauna sai na rik'a biyan kud'in haya. Halima tace wallahi bazamu amsa ba, kayi zamanka har mutuwa ta raba babu wani abu, dama mutanan unguwar sun saba ganinka agidan, dan ka dawo ba wani abu bane, tunda shagunan biyu ne sai ka bud'e shagon saida abubuwa a d'ayan dama Malan Sani yana so ya bada hayarsa, tunda ga yanda komai ya kasance sai kawai kayi amfani dashi saboda kada ka zauna haka, akwai band'aki a cikin d'ayan shagon sai ka d'aukeshi a d'akin ka. Alhaji Mansur yace wannan haka yake, kuma bana so kace a'a. Madu yace shikenan nagode da wannan abu da kukayi mani, wallahi da zan iya zama agidan Alhaji da bazan bari wani ya zauna ba, kawai idan na zauna hankalina bazai kwanta ba, amma nine yafi cancanta na zauna na rik'e amanar gidan, amma duk da haka zan rik'a kula da gidan bazan bari wani abu ya sameshi ba, saboda wanda za'a ba gadin gidan abokina ne agidan Alhaji Musa yake gadi su biyu ne. Alhaji Mansur yace bakomai Madu na fahimceka, kunyi sabo sosai da Alhaii, dama nasan bazaka iya zama agidan ba, hakan ma da zakayi yayi, dan haka zan fad'ama Alhaji Musa kaine zaka rik'a kula da gidan. Madu yace nagode. Bayan sun aje su aka bud'ema Madu shagunan domin ya gyara, katifarsa daya d'auko da kayansa ya shigar dasu ciki kafin ya gama gyara. Ladi kuwa sallama tayi masu tana godiya kafin ta sake zagayowa saboda basu da nisa. Kud'i Alhaji Mansur ya bama Halima masu yawa yana fad'in idan zaiyi aike zai turoma Dr. Saddik sai yarik'a bata tunda bata da account. Godiya tayi masa kafin suka fita. A mota yake fad'ama Maman Labiba zasuje ya kama d'aki sai ya barta ta huta yana so yaje yaga Mr. Kallah yasan gobe zai koma abuja, duk da sune suka kashe Alhaji amma shine shugabansu ta hanyarsa za'a samu kud'in Alhaji su fito cikin sauki, kuma idan yaga yaje wajensa da maganar zaifi maida hankali kodan su fita daga zargi. ** Bayan ya kama d'aki suka shiga, wanka ya farayi kafin yayi sallah yasa aka kawo masu abinci sukaci. Tashi yayi yana fad'in ta kulle zaije ya dawo. Addu'a tayi masa kafin ya nufi wajen Mr. Kallah. Ur's. Nabeelert Lady🖋 [3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.* 2⃣0⃣ Gaba d'aya kunya ce ta rufe Mr. Kallah, ji yake kamar Alhaji Mansur zai gano su, da kyar yasa jarumta aranshi. Canza fuska yayi zuwa kalar tausayi yace yanzu shikenan fa, har yanzu na kasa mantawa da mutuwar Alhaji Maiwada, shiyasa muka tsaya sai da aka yanke ma direbansa hukunci domin munyi zaman amana da Alhaji. Alhaji Mansur yace an dai yanke hukunci, amma wad'an da suke da laifi ai sun san kansu dan wata shari'ar sai alahira. K'warewa Mr. Kallah yayi da sauri ya d'auki ruwa yasha. Murmushi Alhaji Mansur yayi yana fad'in sannu. Kai Mr. Kallah ya d'aga yana fad'in yanzu meke tafe da kai? Alhaji Mansur yace akan maganar kud'in Alhaji Maiwada ne. Jawo takarda Mr. Kallah yayi yana fad'in wannan baka da damuwa, Alhaji Maiwada na mu ne, dole mu tsaya komai nashi ya fito. Yanzu ka bani lambarka kome kenan zamuyi magana, amma ina tabbatar maka kud'inshi bazasu dad'e ba nayi maka alk'awari. Jinjina kai Alhaji Mansur yayi yana fad'in nagode sosai, kawo wayar taka nasa maka lambartawa. Bayan ya gama saka masa yayi masa sallama, har bakin mota Mr. Kallah ya rakoshi. Yana tafiya ya saki ajiyar zuciya. Ciki ya koma yana lalaubar lambar Alhaji Marusa. Yana d'agawa Mr. Kallah ya fad'a masa yanda sukayi da Alhaji Mansur. Alhaji Marusa yace abokina kasan yanda zakayi komai ya fito cikin lokaci, bana son asake tada maganar Alhaji Maiwada, gara a sallamesu nasan bazai sake zuwa garin nan ba. Mr. Kallah yace amma ina tsoron matarsa ta warke ta tona mana asiri. Alhaji Marusa yace ai babu abinda ta sani, iyaka tace Malan Sani beyi mata abinda aka fad'a ba, amma bazata k'aryata kisan da muka d'ora masa ba, idan kuma kana ganin akwai matsala itama tabi bayan mijinta kawai. Da sauri Mr. Kallah yace haba Alhaji, wai wace irin zuciya kake da ita ne haka? Kai kisa baya maka wahala, kada kamanta rayuwaka biyu muka kashe fa, dan Allah kabar wannan maganar, shikenan bani da wata damuwa akan matarsa abarshi ahaka gobe ma zan koma abuja daga can zanje waje nayo sati biyu dan na samu natsuwa. Dariya Alhaji Marusa yasa yana fd'in abokina kacika tsoro, nifa akan dukiyata babu abinda bazan iya ba, dan haka kadena sako mani maganar wata matsala. Mr. Kallah yace shikenan na dena. Sallama sukayi Alhaji Marusa yana ta tsokanarsa. **** Wai Maman Naseer baza kici abincin ba, haba dan Allah, ya kike so nayi ne, ga rashin Naseer ke kuma kina so ki jefa kanki cikin damuwa. Hannu tasa ta goge idonta tana fad'in yanzu shikenan haka zamu bar wad'an da suka kashe Naseer susha banza kenan Baffan Naseer, kana gani wanda aka kashe su a rana d'aya har an yankema makashin hukunci amma mun kasa tab'uka komai sai kace an kashe mana karan gida. Hannunta ya kamo yana fad'in Hajiya Zainabu Abu kenan, wani lokacin mata k'aramin tunani gare ku, shi wanda aka yanke ma hukuncin kinsan irin hujjojin da aka gabatar ma kotu kuwa? To bari kiji, duk da banje kotu ba a labarai naji yanda shari'ar ta kasance, hatta da lauyen da ya tsayama Alhaji Maiwada sai da aka bashi lambar yabo domin ya gabatar da shedu kwarara wanda a kowace kotu akaje dole ta amshe su, kinga kuwa bazamu had'a kanmu da su ba. Ni na barma Allah akan mutuwar Naseer, domin nasan zamusha wahala ne kawai idan mukace zamu nemo wad'an da suka kashe shi, domin babu wata alama da aka bari a mutuwar Naseer, ko Waye ya kashe Naseer ba k'aramin makashi ba ne, abinda nake so da ke kema ki barma Allah sai ya saka mana. Jinjina kai tayi tana fad'in shikenan Baffan Naseer tunda ka fad'i haka, insha Allahu bazan sake d'aga maganar ba, dama su biyu Allah ya bamu koma waye ya aikata hakan zan cigaba da addu'a Allah ya tona asirinsa. Baffa yace amin Zainabu. Murmushi tayi tana goge fuskarta. Sallamar Yayan Naseer ce tasa suka kalli k'ofar tare da amsawa. Zama yayi yana fad'in sannun ku da gida. Baffa yace yauwa sannu *RAFIK*. Maman Naseer tace ga abincinka a kicin ka d'auko kaci ina kaje haka ne? Kallonta yayi yana fad'in Mama kinci naki ko? Baffa yace ina fa taci, yanzu nake mata magana kasan yanda tasa damuwa akan rashin gano wanda ya kashe Naseer aranta. Maman Naseer tace baka bani amsata ba. Rafik yace naje wajen Junaidu ne nayi masa gaisuwa kinsan makarantar mu d'aya shima k'aninsa ne aka tsinci gawarsa an kashe shi da wuk'a kuma d'an makarantar su Naseer ne, shine naje nayi masa gaisuwa kinsa abokina ne abu iri d'aya muke karantawa ma. Baffa yace ikon Allah, dama fa naji ana sanarwa a masallaci an kashe d'an makarantar su Naseer har nake cewa nazo gida naji ko Naseer yasan shi ashe nima bazan iske nawa d'an ba, ya Allah ka tona asirin ko suwa suke aikata wannan mugun abun, ace duk lokaci guda akashe mutum ukku. Maman Naseer tace shiyasa nake damuwa da mutuwar Naseer, ina ma akwai wata sheda da mun shiga kotu. Rafik yace haba Mama mu barshi da Allah kawai, wahala zamusha idan mukace zamu shigar da k'ara domin babu sheda, Allah yajik'an Naseer ya bamu ikon jure rashinsa kawai, gashi yau har anyi sadakar ukku ma. Baffa yace amin dai. Yaushe zaka koma makaranta? Rafik yace sai anyi kwana bakwai sannan, shima saboda mun kusa fara jarabawa ne. Baffa yace wannan karatu naku akwai wahala ko? Rafik yace da sauki Baffa, idan muka dawo sai munyi (IT) kafin mu koma. Baffa yace lallai kace zaka fara karanto labarai. Rafik yace da saura dai, ai yanzu muka fara baza'a bamu karanta labarai ba, zamu dai je muga yanda akeyi. Mama tace ina ruwan Rafik d'an jarida. Dariya sukayi Baffa yace zamusha tambaya dai. Rafik yace Baffa ai sai a wajen aiki ake surutu amma agida wazan ma tambaya. Baffa yace Allah dai ya taimaka ya cika maka burinka ka zama cikekken d'an jarida. Gaba d'aya suka amsa da amin. **** **** Washe gari tunda wuri suka bar kano cike da kewar su Alhaji Maiwada. Alhaji Mansur sai da yayi kwalla lokacin da jirginsu ya tashi saboda tunowa da amininsa kuma d'an uwansa. *** Koda Halima ta gama abincin safe sai ta zuba ma Madu ta bama Rumaisa ta kai masa. Da fara'a Madu ya amsa gaisuwarta yana fad'in hada abinci haka, to kice mata nagode sosai. Bayan ta koma taci abincinta Halima tace Rumaisa ki maida hankali akarantun ki kinji, kinga Babanki yace idan baki karatu zaku b'ata. Rumaisa tace Mama yaushe Baba zai dawo to? Halima tace Babanki yayi tafiya shida Abbun Ra'eez zuwa wata k'asa bazasu dawo ba sai kunyi girma. Dariya Rumaisa tasa tana fad'in zasu kawo mana tsara ko? Halima tace sosai kuwa, ke dai ki maida hankali kiyi karatu, babu ruwanki da k'awa kiyi rayuwarki ke kad'ai domin k'awaye gori garesu, ko tashi akayi kada ki tsaya kowa kiyi tahowarki kinji. Kai ta d'aga tana fad'in ai babu ruwana da kowa idan akayi break ma ni kad'ai nake zama naci abincina, kuma kinga Auntyn mu tace saura sati biyu muyi hutu da mun dawo zamu shiga aji biyar ai kinga mun kusa gamawa. Halima tace sosai ma kuwa, shikenan sai atafi wata makarantar. Rumaisa tace to Mama zan tafi kada amun duka. Halima tace Allah ya ba da sa'a kiyi addu'ar fita daga gida kinji, kuma duk wanda ya tare ki yana maki tambaya akan Babanki ko kallonsa kada kiyi, kome zaice kitafi kada kitsaya duk karya sukeyi kinji. Rumaisa tace to bazan tsaya ba. Bayan Halima ta gama karyawa sai ga Sister Hassana tashigo dan su gaisa. Zama tayi suka gaisa, bayan sun gama gaisawa tace Maman Rumaisa ashe haka abu ya kasance kuma? Duk'ar da kai Halima tayi tana kok'arin maida kwallar data taho mata. Sister Hassana tace Allah ya kyauta gaba, dan Allah Maman Rumaisa kada kisa damuwa aranki, wallahi har cikin raina ban yarda da abinda akace Malan ya aikata ba, kinsan dama haka aikin Kwastam yake, matuk'ar zakayishi da gaskiya dole ka samu makiya musamnan masu kud'i, dan haka kicigaba dayi masa addu'a wata rana gaskiya zata fito, Allah ya baki ikon jurewa. Halima tace amin nagode Sister Allah ya bar zumunci. Sister Hassana tace amin. Ina so duk abinda kike da buk'ata kiyi mani magana matuk'ar befi k'arfina ba zanyi maki, ina fatan kina shan maganin ki? Halima tace ina sha, sister tace yauwa, idan yashiga watan fara zuwa awo sai ki fara insha Allahu babu abinda zai gagara. Halima tace nagode sosai. Dubu biyu Sister Hassana ta aje mata tana fad'in zan wuce sai na dawo. Halima tace nagode sister Allah ya saka da alkhairi tace amin. Har ta juya ta dawo tana fad'in yauwa wannan mutumin da nagani a shagon k'ofar gida kamar ina ganinsa yana zuwa wajen Malan ko? Kai Halima ta d'aga mata kafin ta bata labarin yanda akayi. Murmushi Sister Hassana tayi tana fad'in amma gaskiya ya kyauta, irin wad'annan mutanan ba'a barinsu domin suna da amana, kuma nima naji dad'in zamanshi anan domin kariya ce, a jiya har Dadyn 'yan biyu yana mani magana ko a samo maki maigadi saboda tsaro, to sai kuma daya dawo da dare yake fad'a mani yaga wani mutum a shagon gidan idan nashigo na tambayeki ashe ma na gida ne. Halima tace wallahi kuwa. Sister Hassana tace to Allah ya k'ara tsarewa, ita kuma Allah ya bata lafiya. Halima tace amin. Sallama tayi mata ta fita. Madu ne yayi sallama ya tsaya a zaure. Hijabi Halima ta d'auka ta lek'a. Bayan sun gaisa ya k'ara jajanta mana kafin yace dama kasuwa zaije yayo sarin kaya shine ya leko ko tana da sako. Halima tace ina da sako kuwa, bari na rubuto maka abubuwan da za'a siyo mani, tunda zaka bud'e shago sai na canza wasu abubuwan da nake saidawa a gida. Madu yace baza'ayi haka ba, ki rubuto mani abubuwan da kike saidawa sai asiyo maki a zubasu ashago sai na rik'a saida maki, sauran abinda baza'a aje a shago ba kuma sai ki ajeshi a cikin gida. Murmushi Halima tayi tana fad'in nagode sosai Madu. Yace haba ai bakomai, zan samo littafi sai arik'a rubuta komai. Halima tace haba meye na wani rubutu. Madu yace ko musulunci ya yarda da rubutu ai, dan haka babu komai. Halima tace nagode sosai. **** **** A washe garin ranar da suka dawo Alhaji Mansur ya nufi makarantar su Ra'eez, bayan sun gama gaisawa da shugaban makarantar ya fad'a masa abinda yake faruwa. Shugaban makarantar yace Allah sarki, ashe Alhaji Maiwada yana da yaro a makarantar nan? Alhaji Mansur yace wallahi kuwa, da yake nine na ke zuwa wajensa shiyasa. Jajanta masa yayi kafin yace yanzu jarabawa sukeyi saura sati d'aya suyi hutu, ranar juma'ar nan suke gamawa kaga yau saura kwana biyu kenan tunda yau muna laraba, me zai hana kayi hak'uri zuwa ranar juma'a sai kazo ka tafi dashi. Alhaji Mnsur yace haka ne kuma, idan yasan Mahaifinsa ya rasu zai shiga damuwa wata kilama ya kasa rubuta jarabawar, shikenan, dama ina jin tsoron kada yasan labarin daga sama ne, amma tunda sun kusa gamawa ranar juma'ar zan dawo. Shugaban makarantar yace bakomai Allah yajikansa. Alhaji yace amin. Sallama yayi masa ya tafi. *** A ranar juma'a yazo ya d'auki Ra'eez, duk hankalin Ra'eez ya tashi ganin anzo d'aukarsa ba'ayi butu ba, duk da Alhaji Mansur yace masa bakomai amma hankalinsa yaki kwanciya, saboda sunsha ganin ana zuwa d'aukar wasu idan iyayensu suka rasu. Tun amota Ra'eez ya fara kuka, Alhaji Mansur sai lallashinsa yakeyi shima hawayen suna shirin zubo masa, ganin Ra'eez sai ya sake dawo masa da mutuwar sabuwa. Haka suka isa gida ba tare daya fad'a masa komai ba. Maman Labiba ma tana ganin Ra'eez ta fashe da kuka, saurin juyawa Alhaji Mansur yayi saboda hawayen da suka zubo mashi. Zama Ra'eez yayi yana sakin wani kukan. Ya jima ahaka kafin Alhaji Mansur yafito. Abinci yasa Maman Labiba ta kawo masa, sai dai duk yanda sukayi yaci kinci yayi. Gyara zama Alhaji Mansur yayi ya jawo Ra'eez, cikin kwantar da hankali ya fara bashi labarin abinda ya faru...... Ra'eez yasha kuka bana wasa ba, wanda kukan da yakeyi ya sakar masa zazzafan zazzab'i lokaci guda. Gaba d'ayansu suma kukan sukeyi, jin jikinshi yayi zafi sosai yasa Alhaji Mansur ya kaishi d'akinsa, rigarsa ya cire ya kawo ruwa ya fara goge masa jikinsa. Ya dad'e yana masa haka har sai da jikin yayi sauki, magani yasa Maman Labiba ta kawo masa, tadashi yayi yasha sannan ya kwanta, cikin lokaci kad'an bacci yayi gaba dashi. Fitowa sukayi Maman Labiba tana fad'in irin wannan ranar nake tsoro, dole Ra'eez yashiga damuwa, domin yasan komai akan Iyayensa, Allah ne kawai zai saka masa, bawan Allah gashi dai yaro amma yana da halin manya. Alhaji Mansur yace bazan bari sai nan da shekara biyu kafin ya gama makaranta ba, tunda yana da kok'arinsa idan sun koma makaranta aji biyar zai shiga, zanyi magana da shugaban mkarantar asa sunanshi cikin 'yan aji shidda domin ya zana jarabawa acikinsu, kinga zuwa shekara mai zuwa sune zasu gama sai kawai yaje ya fara karatunshi. Maman Labiba tace hakan yayi dai-dai, Allah ya saka masa kok'ari da hazak'a ya kuma bashi ikon cimma wannan burin da muka d'auka. Alhaji Mansur yace amin. **** **** Tun daga wannan lokacin Ra'eez ya koma shiru-shiru, hatta wasan da sukeyi da Labiba tamkar abokan wasa yanzu sai dai yayi murmushi, gaba d'aya baya dariya sai ta kama dole, a islamiyarsu kuwa sosai yake maida hankali, yanda kasan an bud'e masa kwakwalwa yanzu haka yake karatu, duk abinda ya d'auka sai ya iyashi. Kasancewar dogon hutu ne na canjin aji yasa suka dad'e agida, ana saura sati biyu su koma ya roki Alhaji Mansur akan suje Lagos yaga Ummunsa. Babu b'ata lokaci Alhaji Mansur ya amince, dama saboda kada ya tada masa hankali yasa bece suje ba. Haka suka shirya suka tafi su biyu dan ta jirgi suka bi. **** *** Halima tana zaune tsakar gida ita da Rumaisa suna gyara alaiyahun da zata zuba amiya, sai sauri sukeyi dan Alhaji Mansur yayi mata waya tun jiya yace zasu zo. Rumaisa sai murna take Yayanta zai zo. Bayan ta gama komai suna zaman jiransu sai sallama sukaji, hakan yasa Rumaisa tayi saurin tashi tana murna. Amsa sallamar Halima tayi ta sako hijabi tana fad'in bismilla sannun ku da zuwa. Shigowa sukayi Ra'eez yana goge idonshi, dan tunda suka sauka a Lagos yake kuka. Idanuwan Halima ne suka cika da kwalla ganin Ra'eez. Bayan Rumaisa tayi masu shimfid'a suka zauna. Bayan sun gama gaisawa Halima ta kamo Ra'eez tana shafa kanshi sai hak'uri take bashi. Zama Rumaisa tayi tana fad'in Yayana kadena kuka mana, ai Mama tace da Baba da Abbu sunje unguwa sai na girma zasu dawo kaima kadena kuka kaji. Murmushi Ra'eez ya saki hawaye suna zubo masa jin shirmen Rumaisa. Dad'i Alhaji Mansur yaji ganin Rumaisa tasa Ra'eez murmushi. Tashi Halima tayi zata kawo masu abinci Alhaji yace Halima bar abincin nan sai anjima, yanzu ina so muje wajen Bilkisu ne, ina Madu ko baya nan ne? Halima tace yanzu ya leko yace mun zaije can gidansu Alhaji ya dawo. Alhaji Mansur yace Allah sarki, ya zaman naku yake babu wata matsala ko? Halima tace babu komai wallahi, ai Madu ya zame mani tamkar d'an uwana, dole Alhaji yake rik'eshi, domin mutum ne mai gaskiya da amana, babu abinda bayayi mana, cefane duk bayan kwana biyu sai yayo mana, haka Rumaisa shine yake bata kud'in tara, sannan ya amshi kayan da nake sayarwa anan yasa ashago yana tara mani ribar, gaskiya babu abinda zance sai Allah yasa albarka, amma Alhaji ya tafi ya barmu da masu kula damu, Allah yajik'ansa. Alhaji Mansur yace amin, ai gaskiya Madu mutumin kirki ne, Allah ya saka masa da alkhairi, ina Ladi fa? Halima tace jiya ma tazo nan mun wuni sai yamma ta tafi, gaskiya ta rike alkawari tana zuwa wallahi, gaskiya bana cikin damuwa sai ta rashin Malan, amma Allah ya had'ani da mutanan arziki, ga Sister Hassana da mijinta babu abinda basa mani, wancan satin ma naje naga M..... Shiru tayi ganin Rumaisa tana wajen. Alhaji yace na gane, yana lafiya ko? Halima tace lafiya lau, dan naji dad'in ganinsa a haka, shine ma yasa hankalina ya k'ara kwanciya dan shima ya kwantar da nashi hankalin. Alhaji Mansur yace idan kin gama muje asibitin sai muwuce wajensa, Rumaisa kije gidan Sister ki zauna zamuje mudawo kinji. Kai ta d'aga tana fad'in Yayana taho muje. Alhaji Mansur yace asibiti za'a kaishi yanzu zamu dawo. Rumaisa tace wayyo sannu kaji, idan anyi maka allura da zafi ka fad'a mani zan rama maka. Dariya Ra'eez yasa yana kallonta. Da mamaki Alhaji Mansur yake kallonshi ganin yayi dariya. Gyara wajen Halima tayi suka fita. *** Kasancewar an mayar da Ummu asibitin Mahaukata yasa suka nufi can. Suna zuwa shima Dr. Saddik ya isa dan sunyi waya dashi. Bayan sun biya mai mota kud'insa suka k'arasa ciki. Da fara'a Dr. Saddik ya tarbe su, bayan sun gama gaisawa suka shiga ciki. Ofis d'in *Dr. Najib* suka nufa. Bayan sun gama gaisawa Alhaji yayi masa godiya akan kok'arin da yakeyi. Dr. Najib yace haba bakomai wallahi, ai jikinta da sauki sai dai acigaba da addu'a. Alhaji yace mungode fa. Dr. Saddik yace muje su gaisa ga yaronta nan. Dr. Najib yace ikon Allah, sannu kaji sai hak'uri. Kai kawai Ra'eez ya d'aga yana maida kwallar data taho masa. Suna tura k'ofar d'akin da take Ra'eez yayi saurin shigewa, jikinsa har rawa yakeyi yana so yaga Ummunsa. Kwance take idanuwanta a rufe kamar me bacci. K'arasawa Ra'eez yayi ya kamo hannunta hawaye suna zubo masa, a hankali ya furta Ummunah! Da sauri ta mik'e tsaye, ganin Ra'eez agabanta yasa ta kwala k'ara tana fad'in Ra'eez sun kashe shi, wallahi sun kashe shi, ka samo mani wuk'ar Makka sai na kashe su dukansu. Tashi Ra'eez yayi yana kuka ganin yanda Ummunsa ta koma, su kansu sai da jikinsu yayi sanyi ganin yanda tsigar jikinta ta tashi sai rawa jikinta yakeyi. Hannu tasa ta rik'e kanta tana wani k'ara. Da sauri Dr. Najib yayo kanta, kafin ya k'araso ta tafi zata faad'i, aguje ya tareta ta fad'a jikinsa a sume. Ur's. Nabeelert Lady🖋 [3/10, 8:39 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.* 2⃣1⃣ Sai da aka yi mata allurar bacci kafin suka samu kanta, gaba d'aya yau jikinta ya rikice zuwan Ra'eez. Bayan ta samu bacci Dr. Najib yace suje ofis. Kallon su yayi yana fad'in ayau naga wani canji atare da ita ganin d'anta da tayi, alamu sun nuna bata mance dashi ba, kuma ina ganin idan tana ganinshi zata iya tunawa da wani abun, tunda kace karatu yakeyi mai zai hana duk hutu yarik'a zuwa yana ganinta kila ta haka zamu samu shawo kanta. Gyara zama Alhaji Mansur yayi yana fad'in likita zuwan Ra'eez bazai yuwu ba, domin zai shiga aji shidda, kuma kaga zasu fara karatu mai zurfi ga islamiyya yanayi hakan nema yasa koda Mahaifansa suna nan baya zuwa wajensu, bayan nan kuma gaskiya waje nakeso yayi karatu, akwai wata makaranta *Queen Mary*, law school ce a Landon, tunda nasa ma raina inaso ya karanci fannin shari'a na fara duba makarantu masu kyau, hakan yasa na zab'a masa wannan makarantar, kuma bana so idan ya tafi ya rik'a dawowa, amma tunda akwai wannan lalurar zanyi kok'ari yarik'a zuwa ko so d'aya a shekara ne. Jinjina kai Dr. Najib yayi yana fad'in kaima da naka uzurin, bakomai, tunda zai rik'a zuwa hakan ma yayi, dama bana so ace kwata-kwata bazai rik'a zuwa ba domin yin hakan zai maida mu baya. Alhaji yace insha Allahu zai zo, Allah ya bata lafiya. Gaba d'aya suka amsa da amin. Tashi sukayi suka masa godiya. Ra'eez yace abarsa a wajenta. Alhaji Mansur yace Ra'eez kaga ciwonta yana tashi kana so tarik'a shan wahala? Kai ya grigiza yana goge hawayen idonshi. Alhaji Mansur yace kayi hak'uri zan barka a gidan Maman ku kayi sati d'aya kaga idan zata zo ganin Ummunka sai kuzo tare kaji. Kai ya jinjina. Murmushi Dr. Najib yayi yana fad'in gara kasa juriya azuciyarka hakan zaisa kayi karatu sosai, idan kasa damuwa aranka bazaka gama karatu da wuri kazo ka kwato maku hakkin ku ba. Godiya sukayi masa suka tafi. Dr. Saddik yaso ya kaisu amma Alhaji Mansur yace ya barshi, baya son arik'a ganinsu tare. Haka suka wuce gidan yari wajen Malan Sani. *** Malan Sani yasha kuka, ganin Ra'eez sai ya dawo masa da mutuwar sabuwa, shima Ra'eez d'in kuka yakeyi, duk dauriyar da Halima takeyi sai da tayi kuka, da kyar Alhaji Mansur ya basu hak'uri. Kamo Ra'eez Malan Sani yayi yana fad'in wallahi sharri sukayi mani Ra'eez, ban kashe Alhaji ba, haka kuma ban.... Rufe masa baki Ra'eez yayi yana girgiza kai. Zame hannunsa yayi yana fad'in Kawu kadena fad'ar haka, duk da k'arancin shekaruna nasan abinda zakayi da wanda baza kayi ba, tunda Abbah ya bani labarin abinda ya faru nasan cewar ba gaskiya bane sharri akayi maka, zanje nayi karatu insha Allahu wata rana sai ka fita daga nan, kuma sai gaskiya ta tabbata. Gaba d'ayansu tsayawa sukayi suna kallon Ra'eez jin yanda yake sako magana mai cike da hankali da nutsuwa sai kace wani babba, alokacin gaba d'aya shekarunsa bazasu wuce 17 ba amma yana maganar masu shekaru da yawa. Murmushi Alhaji Mansur yayi aranshi yana fad'in Allah mai iko, Allah mai shirya yanda yaso, gashi dai ya hukunta wannan abun sai kuma ya kawo Ra'eez, yasa masa natsuwa da zurfin tunani. Ya Allah ka tabbatar da ikon ka akan wannan bawan naka. Sun dad'e a wajen Malan Sani suna fira, lokacin da zasu tafi Alhaji Mansur ya samu shugaban ma'aikatan suka gaisa, alheri yayi masa yana rok'onsa akan ya kula da Malan Sani. Murmushi yayi yana fad'in bakomai Alhaji, babu abinda zamuce da wannan k'asa tamu sai addu'a, amma wata shari'ar sai a lahira. Godiya Alhaji Mansur yayi masa suka tafi. *** Bayan sun gama cin abinci sukayi sallah. Zama sukayi da Madu suna ta fira. Madu yake fad'a masa komai lafiya na gidan Alhaji, dan Maigadin yana kula da komai, motar Alhaji ma an rufeta da tampol, sai dai yana ganin gara a cire tayoyin a d'ageta zaifi. Kallon Ra'eez Alhaji Mansur yayi yana fad'in Ra'eez ko dai asiyar da motar asaka maka kud'in a banki tunda nan gaba yayinta zai wuce? Kallonsa Ra'eez yayi yana fad'in Abbah idan aka barta har na girma akwai abinda zai sameta? Kai ya girgiza masa. Ra'eez yace dan Allah Abbah abarta, ina so idan na girma na tuk'ata domin narik'a tunawa da Abbu kaji. Murmushi Alhaji Mansur yayi yana fad'in angama Ra'eez, insha Allahu baza'a sai da ta ba, kuma sai ka tuk'ata da izinin Allah, sai dai ina ganin zamu tafi da ita can kano kaga akwai gareji sai sata ciki kawai. Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in yauwa Abbah. Madu yace shikenan ma, nima hankalina zaifi kwanciya idan aka tafi da ita, domin za'a iya d'auketa, amma idan aka tafi da ita ya rage sai gida kawai shiko babu wanda zai d'aukeshi, shima dan kace abarshi amma da an sayar dashi hankalin kowa ya kwanta. Alhaji Mansur yace akwai dalilin da yasa nace baza'a siyar dashi ba, wata rana Ra'eez zai zo yayi aiki agarin nan, kuma bana so ya zauna a wani waje, dan haka ka barshi babu abinda zai sameshi da izinin Allah, idan ma Maigadin ya gaji sai asamo wani. Madu yace begaji ba, shikenan ayi yanda kace. Rumaisa ce ta shigo tana fad'in Yaya kazo muje kaga takarduna to. Murmushi yayi yana fad'in kilama duk ziro kikaci. Rumaisa tace wallahi duk na cinye, kok'ari fa gareni, kusan kullum sai an bani kyauta a aji. Ra'eez yace to muje na gani. Dariya sukayi Alhaji yana fad'in ina ruwan Ra'eez, tunda yasan mutuwar mahaifinsa ban sake ganinsa cikin annashuwa ba sai da mukazo yaga Rumaisa, shiyasa na yanke shawarar barinsa yayi sati d'aya idan yaso sai ya taho ta jirgi, ni kuma sai na tafi da motar dan bana son na tafi dashi amota kasan hanyar Lagos. Madu yace haka ne, Allah ya tsare mana kai. Alhaji yace amin. **** **** Wshe gari tunda asuba Alhaji Mansur ya tafi bayan ya cika Halima da kud'i ita da Madu. Ra'eez da Rumaisa sai dad'i sukeji zai zauna yayi sati. Sosai Halima take jin dad'in zaman Ra'eez domin koda yaushe yana koyama Rumaisa karatu, haka idan tayi ba dai-dai ba yana tsawatar mata, sai take ji ina ma abar matashi kodan Rumaisa. Tunda sukaje asibiti basu sake komawa ba sai ana saura kwana biyu Ra'eez ya tafi, a wannan rana jikin Ummu bai tashi ba, haka Ra'eez ya wuni a wajenta dan Halima acan ta barosa, duk da ita kad'ai take shirmenta amma shi d'auka yake fira sukeyi, dan ita labarin Abbu kawai take bashi, hakan yasa shima yayita bata labarin Abbun. Idan ka gansu sai ka d'auka mai hankali ce, gaba d'aya masu kula da ita aranar sunyi farin ciki domin kowa yasan Ra'eez yazo, duk wanda yaje sai ta fad'a masa ga Ra'eez shine zaije makka yasiyo mata wuk'ar da zata kashe wad'an da suk kashe mata Abbun Ra'eez, gaba d'aya aranar kowa sai da ya gaji da jin sunan Abbun Ra'eez. Sai da yamma sosai Madu yazo tafiya da Ra'eez, anan fa Ummu tace bata san maganar ba, kuka da ihu tashiga yi za'a sace mata Ra'eez, haka ta rik'eshi tana kuka duk ta yakushe shi, sosai Ra'eez ya tsorata da yanayinta, duk yanda aka so akwace Ra'eez abun ya faskara domin wani irin k'arfi ne yazo mata, ta jima mutane da yawa ciwo hakan yasa dole suka kira Dr. Najib. Koda yazo shima yasha fama, sai da yayi ta maza ya rik'eta da k'arfi akayi mata allura kafin tayi shiru, har bacci ya d'auketa hannunta yana rik'e dana Ra'eez, a hankali aka cireshi daga jikinta. Ra'eez yana waigenta har suka fita daga d'akin suka wuce gida sai kuka yakeyi. A ranar haka ya wuni da kyar Rumaisa tasa yaci abinci. Bayan kwana biyu aka gama mashi komai na tafiya Madu ya d'aukeshi domin ya kaishi inda zai hau jirgi. Daga Rumaisa har Halima sai da sukayi kuka da zai tafi, shima kukan yakeyi da kyar suka rabu. *** *** Lokacin daya sauka Alhaji Mansur hada Labiba sukaje d'aukoshi, Labiba sai murna takeyi abokin firarta ya dawo. Haka suka nufi gida. *** Lokacin da hutunsu ya k'are haka Alhaji Mansur ya had'a masu komai, d'aki yaja Ra'eez ya fad'a masa kud'in mahaifinsa sun fito, kuma ya saka masa abankin da Alhaji Maiwada ya bud'e masa ya saya masa hannun jari domin arik'a juya kud'in. Ra'eez yace Abbah bana so kace bazaka tab'a kud'ina ba, kaga a waje zanyi karatu ina so nayi karatu da kud'in Abbu domin ina so nayi amfani da guminsa nayi karatun da zan kwato masa hakkinsa. Murmushi Alhaji Mansur yayi yace Ra'eez kenan, ko sisi baza'a tab'a maka ba, nine nayi niyar sai kayi karatu a waje kuma zakayi shi komin tsadarsa. Ra'eez yace dan Allah Abbah. Alhaji Mansur yace naji yanzu dai muje kada muyi dare, kuma bana so kasa damuwa aranka idan ba haka ba baza kaje karatun aikin lauya ba kaji. Ra'eez yace zan dage. Haka suka fito suka yima Maman su sallama suka tafi cike da kewar gida, Labiba sai haushi takeji an canza ma Ra'eez aji yanzu saiya rigata gamawa, itama taso amayar da ita ajinsu amma Alhaji Mansur yace bazai maida ta ba dole ta hak'ura. *** Haka rayuwa tacigaba da tafiya, wasu suna jin dad'i wasu suna cikin wahala, tuni Halima ta fawwalama Allah al'amuranta, ta rungumi k'addararta da hannu biyu, cikin ikon Allah take tafiyar da rayuwarta babu abinda ta nema ta rasa, Madu yana kokari akansu sosai, ga Sister Hassana da mijinta. Cikinta sai girma yakeyi tana zuwa awo ba tare da wata matsala ba, damuwarta d'aya idan taje ganin Malan Sani, ganin yanda take damuwa yasa Malan Sani yace ta dena zuwa kawai tacigaba da kulawa da kanta. Su Brr. Barau kuwa rayuwa tayi masu dad'i, domin arzik'in yanzu ya wuce na baya, sun had'a hannu da Alhaji Marusa suna shigo da kaya wad'an da suke so, domin Adebayo shine aka ba kujerar Alhaji Maiwada dama kuma alk'awari aka masa matuk'ar komai yayi dai-dai shi za'a ba yayin da aka bama Umar matsayinsa. Wannan dalilin ne yasa suke cin karen su babu babbaka dan yanzu mutane suna kuka da yanda ake amsar masu kudi. **** Lokacin da cikin Halima ya isa haihuwa safiyar juma'a ta tashi da nakuda, alokacin Rumaisa tayi shirin zuwa makaranta sai fasawa tayi, da gudu taje ta kira Sister Hassana, haka suka d'auketa suka nufi asibiti. Cikin ikon Allah ta haifi d'anta namiji. Bayan an gama komai suka koma gida. Bayan da ta gama gyara jikinta Ladi tayima yaro wanka, kunu ta kawo mata da d'umamen tuwo, kasa ci tayi sai kuka takeyi. Zama Ladi tayi tana fad'in haba Halima, godiya ya kamata kiyima Allah daya sauke ki lafiya, nasan kina tunanin rashin Malan Sani, ki sani bazaiji dad'i ba idan yaji kina cikin damuwa, kinsan yanzu ba'a son kina saka damuwa aranki, ki daure kici abinci dan Allah. Hannu tasa ta goge idonta tana fad'in shikenan Ladi nagode. Amsar kunun tayi ta fara sha tana kwalla. Da wayar shugaban ma'aikatan gidan yari tayi magana da Malan Sani, sosai yaji dad'i haka yayi ta lallashinta kuma yace mata zai zo insha Allahu. Bayan sun gama waya shugaban ma'aikatan yace masa zai kaishi yaje yayi ma yaron hud'u ba. Sosai Malan Sani yaji dad'i yayi ta masa godiya. Sai da dare suka je, alokacin Rumaisa ma tayi bacci. Haka yayi ma yaron hud'uba da *Abdallah*, yaso yasa sunan Alhaji Hamza amma sai ya tuna da maganar Alhaji Hamza da yake fad'a masa.. *idan Ummun Ra'eez ta haihu idan mace ce zai saka sunan mahaifiyarsa, idan kuma namiji ne zaisa sunan mahaifinsa Abdallah, saboda beyi amfani da sunansa a jikin takardunsa ba, sai yayi amfani da sunan da ake kiransa dashi a cikin 'yan uwa wato MAIWADA, hakan yasa yake son yasa sunanshi na gaskiya*. Wannan dalilin ne yasa Malan Sani ya cika ma Alhaji Maiwada burinsa. Ya dad'e yana kallonshi, wajen Rumaisa yaje yayi mata addu'a, sai da yaci abinci shida shugaban sannan suka tafi yana ta yima Madu godiya. *** Dubu hamsin Alhaji Mansur ya aiko mata asayi rago ayi siyayyar kayan yaro. Godiya tayi masa. Haka akayi hidimar suna cike da rufin asiri tamkar Malan Sani yana nan. **** Bayan da Ra'eez ya zana jarabawarsa suka baro su Labiba amakaranta, satinsa biyu a Kano ya taho Lagos yayi hutu kafin jarabawarsu ta fito. Sosai Rumaisa da Halima sukaji dad'in zuwanshi. **** **** Bayan da jarabawarsu ta fito haka aka kammala masa komai, cikin sa'a ya samu gurbin shiga makarantar koyon aikin lauya da take Landon, cike da farin ciki yaje yayi ma Ummunsa sallama, sai dariya takeyi kamar tasan abinda yake fad'a. Haka yayi ma kowa sallama ya tafi cike da fatan nasara. *** *** *Bayan shekaru da dama*, Abubuwa da yawa sun faru, aciki hada kaddamar da Brr. Barau a matsayin sabon Alkali na babbar kotu bayan da tsohon Alkali ya aje aiki, sosai yayi farin ciki da wannan al'amari dan ya dad'e yana jiran wannan rana. Mr. Kallah ma ya dawo Lagos da zama saboda ya aje aiki, gaba d'ayansu girma ya kama su, sai dai naira ta hana aga tsufansu, har zuwa wannan lokaci Alhaji Marusa yana shigo da haramtattun kaya, sai dai yanzu abun nashi na zamani yakeyi dan an samu cigaba. Ummun Ra'eez tana kan amsar magani, zuwa yanzu jikinta da sauki sosai, sai dai bata da yawan magana, idan ka ganta tamkar mai hankali amma bata magana, a koda yaushe maganarta d'aya Abbun Ra'eez sai kuma d'anta. Su Alhaji Mansur suna yawan kawo masu ziyara, haka wajen Malan Sani suna zuwa wajensa. Komai yana tafiya yanda ya kamata. A yanzu haka Rumaisa an girma tana aji ukku a babbar makaranta. Sosai kyanta ya k'ara fitowa, ga natsuwa ga kok'ari, sosai take maida hankali a karatun ta. Abdallah ma yashiga fimare, sosai suke waya da Ra'eez. Labiba kuwa tuni ta kammala makarantar ta, inda tayi karatu a FCE kano har ta kammala dan shekara ukku ne, yanzu haka ana shirin bikinta. **** Bayan da Ra'eez ya kammala karatunsa haka ya dawo gida cike da nasara dan ya fita da first class, sosai Alhaji Mansur yaji dad'in haka. Bayan dawowarsa yaje yaga Ummunsa kafin ya dawo kano, haka Alhaji Mansur ya nema masa (Bar school) da take abuja. Sai da akayi bikin Labiba kafin ya tafi. Shekara d'aya yayi kafin ya kammala, bayan ya dawo yayi service shekara d'aya, alokacin Rumaisa zata jana jarabawar fita daga makaranta. Yana kammala service d'insa ya samu aiki a babbar kotu da take kano. Kasancewar Ra'eez mai natsuwa da hazaka, cikin lokaci kad'an ya saye zuciyar mutane, dan duk abinda yasa agaba sai yaga bayansa, haka duk shari'ar da zaiyi sai yayi nasara, danshi baya amsar shari'ar da yasan babu gaskiya a cikinta, shiyasa mutane suke masa lak'abi da Mai gaskiya. Sai da yayi shekara d'aya a kano kafin Alhaji Mansur yayi nasara aka canza ma Ra'eez wajen aiki zuwa babbar kotu da take lagos. Ranar da takardarsa ta fito sosai sukaji dad'i, haka Alhaji Mansur yayi ta masa nasiha yana bashi shawarar yanda zai tafiyar da komai musamman da yasan cewar Brr. Barau shine Alkali a kotun da Ra'eez zaiyi aiki, kuma yaja kunnansa akan ya b'oye komai nashi, dan baya so kowa yasan yana da alak'a da Alhaji Maiwada har sai komai ya kammala. Cike da d'oki ya shirya ya tafi Lagos yana mai farin cikin zai koma kusa da abun sonshi Rumaisa, dan ya girma ne da soyayyarta, sannan zai koma kusa da Mahaifiyarsa. Sai da sukayi kwana ukku suna gyaren tsohon gidansu dan Alhaji Mansur yace ya zauna acan, alokacin tuni an sake maigadi kusan ukku bayan wancan, haka aka gyara komai kamar alokacin aka zuba su. A d'akin Abbunsa yace zai zauna. Haka ya shirya komai nashi. Yaso Maman Rumaisa su dawo gidan amma tace yayi zamansa tafi son ta zauna acan, duk yanda yayi haka ya hak'ura dan sai da Alhaji Mansur ya shiga maganar sannan. *Wannan shine asalin labarin Alhaji Hamza Maiwada* Ajiyar zuciya Kawu yayi yana goge hawayen da suka zubo masa. Ra'eez kuwa kuka yake sosai kamar k'aramin yaro. Hannunsa Kawu ya kamo yana fad'in kada ka barsu Ra'eez, sun cutar dani sama da shekaru da dama, nayi kuka har na gaji, nayi dauriya har sai da hak'urina ya kusa k'arewa, sun lalata mani rayuwa, sun b'ata mani suna, sunci mutuncin Mahaifiyarka, ta kwashe shekaru tana cikin hali na rashin lafiya. Girgiza kai Ra'eez yayi yana fad'in kada ka damu Kawu, na girma da shirin d'aukar fansa, zan b'ullo masu ata yanda basuyi zato ba, insha Allahu sai asirin su ya tonu, sai Allah ya kawo mani hujja gamshashshiya, kamar yanda sukayi amfani da kwakkwarar hujja suka kada ka nima sai Allah ya bani wannan damar, kacigaba da tayani addu'a Kawu. Murmushi Malan Sani yayi yana fad'in ina kan yi Ra'eez, kaine keda nasara a wannan karon, sai sunyi nadamar abinda suka aikata. Allah yayi maka albarka. Ra'eez yace amin Kawu, zan zo na koma ka k'ara hak'uri Kawu. Malan Sani yace yanzu kam acikin farin ciki nake, fatana Allah ya barni da raina domin nasha kallo. Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in amin. Sallama yayi masa ya tafi cike da damuwa aransa. Ur's. Nabeelert Lady🖋 [3/10, 8:39 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.* 2⃣2⃣ Yana kan hanyarsa ta komawa wajen aiki wayarsa tayi k'ara, yana dubawa yaga *Alkali ne*, saurin d'auka yayi, yana d'agawa ya fara tambayarsa ina yaje? Ra'eez yace na d'an fita na siyo magani ne ganinan dawowa. Kashe wayar akayi. Tsaki Ra'eez yayi yana jin wani b'acin rai, sosai yake jin hushin Alkali Barau, tunda yasan irin muguntar da sukayi ma Abbunsa da Ummunsa ya k'ara tsanarsa. Gudun motar ya k'ara dan yayi sauri ya isa. Inda ake aje motoci ya aje kafin ya fito, kai tsaye ofis d'in Alkali Barau yawuce, sai da ya fara kwankwasawa aka bashi zini kafin yashiga da sallama. Kallonshi Alkali yayi yana fad'in baka jin dad'i ne? Kai Ra'eez ya d'aga yana fad'in kaina ne yake ciwo amma nasha magani yayi sauki. Alkali yace ko dai ka tafi gida kila bacci ne. Ra'eez yace da sauki zan iya zama. Murmushi Alkali yayi yana fad'in shikenan, dama nace idan an tashi ko zaka bini gidana nasa ayi abinci da kai amatsayin ka na sabon ma'aikacina mai kwazo, ina so na gabatar da kai a wajen Iyalina. Kau da kai Ra'eez yayi yana fad'in badamuwa nagode Allah ya kaimu atashi. Alkali yace amin, kuma naji dad'i, dan haka idan an tashi zan maka magana sai mutafi. Ra'eez yace to. Juyawa yayi ya fita. Zaune yake a ofis suna fira shida Brr. Jabeer, sauran ma'aikatan ne suka iso suna ma Ra'eez sannu da zuwa. Da murmushi ya amsa yana basu hannu suna gaisawa. Bayan sun gama Ra'eez ya kalli Jabeer yana fad'in gaskiya naji dad'in zuwa wannan kotun, domin mutanan cikinta suna da kirki musamman 'Yallab'ai. Murmushi Jabeer yayi yana fad'in wai Alhaji Barau kake nufi? Ra'eez yace shi nake nufi. Murmushi Jabeer yayi yana fad'in kayi a hankali dai, domin kura ce rufe da fatar akuya. Ra'eez yace bangane ba? Jabeer yace bakomai manta kawai. Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in tunda nazo muka gaisa da kai sai nake jin kamar kaine kafi cancan ta nayi abota dashi a wajen nan duba da yanayin ka, sai gashi nazo kai kuma kana so ka b'oye mani wani abu, kyakkyawar alak'a ana kullata ne da kyakkyawar zuciya, amma kila ni d'in ne banyi maka da zama aboki ba. Hannunsa Jabeer ya kamo yana fad'in wallahi ba haka bane, kasan ba'a son mutum yarik'a saurin fad'ar mugun abu ga wanda yazo waje amatsayinsa na sabon zuwa, ban sani ba kilama 'yallab'ai d'an uwanka ne haka kawai nayi sara akan gab'a. Ra'eez yace amma na fad'a maka ba'anan nake ba, bani da kowa nan aiki ne ya kawo ni. Jinjina kai Jabeer yayi yana fad'in nima ai ban dad'e anan ba, kawai nasan labarinsa ne a wajen Kawuna, domin sunyi aiki tare dashi alokacin yana lauya, yanzu haka Kawuna yana Babbar Kotu da take garin Abuja, da tare suke anan, sai Kawu na yaje ya k'aro karatu, sukayi wani taro na k'asa da k'asa akan yanda za'a kawo cigaba akan shari'ar k'asarnan, Kawuna ya bada gudummuwa sosai, hakan yasa aka maidashi babbar camber da take abuja, kaji dalilin da yasa yabar wannan kotun domin yanzu yana saman Alhaji Barau. Ra'eez yace lallai ashe dai gadon aikin shari'a kayi. Jabeer yace wallahi kuwa, domin acikin 'ya'yansa ma akwai lauya amma shi yana Jos acan yake aiki, a cikin dangin mu kusan mu biyar ne muke aiki a wannan fannin, da anan garin kake kila da ka san Kawuna, sunansa *Kamal S. Buzu*, alokacin da yake aiki tare da Alhaji Barau yasha wahala, domin bakinsu d'aya da manyan masu kud'i, gashi ya iya tsara magana, shiyasa duk yawancin shari'a shine yake nasara musamman ta masu kud'i, yasan yanda zai maida gaskiya ta koma k'arya, ta yanda babu wanda zai iya ganowa. Ra'eez yace lallai kace yanzu sai ya raina kanshi tunda Kawun ka ne samansa. Jabeer yace ai yanzu yayi sauki sosai, kasan dama idan kaga mutum yana yanda yaso ba'a bashi shugabanci bane, ai tamkar ka d'auki ajiya ne ka bama b'arawo, kaga dole idan kazo amsa ya baka, shiyasa wasu suke ganin da zama da munafuki gara zama da b'arawo. Dariya Ra'eez yayi yana fad'in wallahi Jabeer kana da abun dariya, gashi ka iya karin magana kamar wanda tsofaffi suka yaye, to ni dai ban fahimci abinda kake nufi ba. Murmushi Jabeer yayi yana fad'in ina nufin yanzu shine shugaba, dole abinda lauyoyi suka fad'a shi zaibi, domin yanzu kotu ce take tafiyar dashi ba shine yake tafiyar da kotu ba, kasan duk abinda lauya ya fad'a dashi kotu take zama ta duba kafin ta yanke hukunci, shiyasa nace maka yanzu yayi sauki, dole yake yanke hukuncin gaskiya, shiyasa yanzu mutane suke sara masa, gani suke shid'in mai gaskiya ne, musamman koda yana lauya ba'a tab'a kamashi da laifin cin amanar aikinsa ba, shiyasa yanzu duk inda kaje zakaji ana fad'in Alkalin babbar kotu yafi kowa iya aiki, dan haka mutane suke son kawo k'ara a wannan kotu, damma ana soke wasu amaida su k'ananan kotu. Jinjina kai Ra'eez yayi yana fad'in lallai irin wad'an nan mutanan wahalar sha'ani garesu, domin sun riga sun gama saye zuk'atan mutane, duk yanda wani yaso ya fad'i wani aibunsu mutane bazasu yarda ba har sai an gabatar masu da babbar hujja akansu. Jabeer yace shiyasa ka zuba masu ido yafi, domin fad'a da aljani ba kyau, ko kace zakayi ma kaine a k'asa, domin zaka sa mutane su tsaneka ne kawai, shiyasa duk da nasan shid'in ba mai gaskiya bane dole na had'iye abuna nake binsa a yanda kowa yake kallonsa kafin ranar da Allah zai kamashi, wata kila a duniya wata kila kuma sai anje can. Ra'eez yace irin wad'an nan mutanan asirinsu ya tonu aduniya yafi dad'i, domin mutanan da suka basu gaskiya zasu ga komai da idanuwansu, sannan masu aikata makamancin laifinsu zasu hankalta, idan suna da rabon shiriya sai kaga sun shiryu, amma abarsu sai anje lahira ai sun bar baya da k'ura. Jabeer yace kai da kasan haka kenan, addu'ata d'aya Allah ya bayyana gaskiya, domin Kawuna yasha fad'a mani wata shari'a da sukayi wacce har yanzu bata wuce a zuciyar Kawu ba, saboda tare sukayi ta kuma shine yayi nasara, saboda irin hujjar daya gabatar ma kotu dole ne ta yanke hukunci, kuma Kawu yace ba hujjar gaskiya bace, sai dai shima bai da ikon k'aryatawa, domin an gabatar da ita ne amatsayin ta gaskiya, sune kad'ai suka san cewar ba ta gaskiya bace. Ra'eez yace shari'ar waye haka? Jabeer yace an dad'e fa, shari'ar wani marigayi daya rik'e shugaban Kwastam a garin nan, kaga na manta sunansa wallahi, amma dai naji Kawu na yana fad'in har yanzu direbansa da aka k'ullama sharrin yana nan a gidan yari, kai wallahi wata shari'ar sai alahira kaji, amma mutanan da suke zaune agidan yari masu gaskiya suna da yawa. Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in Allah ya kyauta, mu kuma ya bamu ikon tabbatar da gaskiya, amma aikin mu yana da had'ari sosai, idan mutum yaso zai nemi lahira dashi, idan kuma yaso sai ya tara abun duniya dashi. Jabeer yace wannan haka yake, muje muyi sallah naji an fara kira. *** Bayan da suka tashi Ra'eez yayi sallama da Jabeer, bakin motarsa ya tsaya yana jiran fitowar Alkali. Yana nan tsaye sai gashi ya fito shida Brr. Bajinta suna tafe suna magana sai dariya sukeyi. Da wani irin kallo Ra'eez ya bishi yana jin wani zafi aranshi. K'arasowa sukayi Alkali yana fad'in Ra'eez yi hak'uri na tsayar da kai. Ra'eez yace ai bakomai. Brr. Bajinta yace 'yallab'ai yau kana da babban bako kenan? Alkali yace wallahi kuwa, bara muje sai Allah ya kaimu. Brr. Bajinta yace Allah ya kaimu. Alkali yace Ra'eez bara na shiga gaba sai ka biyoni abaya ko. *** Tunda suka shiga unguwar Surelere idanuwan Ra'eez suka canza kala, gaba d'aya jijiyoyin kansa suka tashi, shigowarsu unguwar sai ya tuna masa da rayuwar Iyayensa. Runtse ido yayi lokaci guda suka kawo ruwa. Tunaninsa ya tsaya ne alokacin da yaga Alhaji Barau ya tsaya a k'ofar gidan da yake tunanin ya tab'a rayuwa acikinsa a shekarun baya, tabbas ko ba'a fad'a masa ba yasan wannan gidan Abbunsa ne daya gina da kud'insa wanda Abbu yayi masa wayau akan baya sonshi hakan yasa ya koma Apapa. Tsayawa yayi har yaga motar Alhaji Barau ta shige ciki, tunani yayi ko dai ya tafi, dan bazai iya shiga gidan ba. Wata zuciyar ta bashi shawara daya daure yashiga, dole ya b'oye komai matuk'ar yana son gano gaskiya. Cike da gamsuwa da shawarar da zuciyarsa ta bashi ya kutsa kan motar cikin gidan, yayin da yake kok'arin saita kanshi. Alhaji Barau ya fito yana jiran fitowar Ra'eez. Sai da ya rufe motar kafin ya nufo wajen Alhaji Barau. Murmushi kwance a fuskarsa ya kalli Ra'eez yana fad'in bsimilla muje. Haka yabi bayansa yana kallon gefen gidan wanda Abbunsa yace b'angarensa ne zai gina idan yayi aure su zauna, tuni an gama gina wajen da alama b'angaren baki ne ko na yaransa maza. Girgiza kai Ra'eez yayi aranshi yana fad'in fenti kawai aka sake ma gidan amma komai nashi yana nan. Tunaninsa ya dawo alokacin da Alhaji Barau yake gaisawa da mai aikin gidan. Risnawa Ra'eez yayi yana gaishe da mai aikin daya fito daga gidan. Har ciki suka shiga bakinsa d'auke da sallama, sai dai babu kowa afalon sai TV da takeyi ita kad'ai. Kallonsa Alhaji Barau yayi yana fad'in zauna Ra'eez bara nayima mutanan gidan magana. Zama yayi yana k'are ma gidan kallo. Da sauri yasa hannu ya goge kwallar data zubo masa, duk yanda yaso ya tsaidata kasawa yayi dole sai da suka zubo, hakan yasa yayi saurin goge su. Motsin da yaji ne yasa shi kallon matattakalar benen, wata mata ce ya gani sun jero da Alhaji Barau sai murmushi take suna magana. Tana k'arasowa falon ta kalli Ra'eez tana fad'in lallai Alhaji yau muna da babban bako, ka kyauta daka kawo manishi, dan tunda ka bani labarin yanda ya tafiyar da shari'ar su Amina naji ya burgeni, sannu da zuwa Ra'eez. Zamewa Ra'eez yayi yana gaisheta. Zama tayi tana amsawa. Alhaji Barau yace ai Ra'eez yana da kirki, jinsa nake tamkar d'ana. Hajiya Hauwa tace nima haka kawai naji ya kwanta mani, shiyasa nace maka naji dad'i daka kawo manashi. Alhaji Barau yace ina *Raheenatu* take? Hajiya tace tana ciki, bara na kirata ta kawo masa abunsha. Ra'eez yace Hajiya kibarshi akoshe nake tafiya ma zanyi. Alhaji Barau yace ai ba haka mukayi da kai ba, dole kaci abinci ko kad'an ne. Duk'ar da kai Ra'eez yayi bece komai ba. Wucewa Hajiya tayi tana fad'in ina ma za'ayi haka ai har abinci sai kaci. Bayan ta kira Raheena ta wuce kicin. Suna zaune Raheena ta fito, tun kafin ta k'arasa shigowa falon k'amshin turarenta ya bud'e falon, a hankali Ra'eez ya d'ago kanshi domin yaga wanda yashigo da k'amshin. Ido suka had'a da Raheena alokacin da ta fito sai kwarkwasa takeyi, wata doguwar rigace ajikinta mai kyan gaske, d'inkin yayi kyau domin tabi jikinta, kanta d'aure da d'ankwali fuskarta tasha kwalliya, sosai kayan suka matseta sai yanga takeyi tana taubar cingam ko mayafi babu. Kicin ta wuce, ta jima kafin ta fito hannunta d'auke da faranti babba. Ra'eez kuwa tunda ya kalleta ya d'auke kai. Alhaji Barau ne ya tashi yana murmushi yace bara nashiga daga ciki ka saki jikinka kaci abinci nan ma gidan ku ne, yanzu zan fito, Raheena ki tayashi fira. 'Daga kai tayi tana murmushi. A tare da Hajiya Hauwa suka haura sama. Zama Raheena tayi tana fad'in barka da zuwa da fatan kazo lafiya? Ra'eez yace lafiya lau. Lemu ta zuba masa ta mik'a masa tana fad'in bismillah. Amsa yayi yana fad'in nagode. Matsowa tayi kusa dashi tana fad'in naji labarin shari'ar daka gudanar gaskiya kayi kok'ari, sosai naji dad'i fa. Ra'eez yace nagode. Shiru tayi ta tsura masa ido, tunda take arayuwarta bata tab'a ganin namiji mai kyansa ba, haka tunda Dadynta yace mata tayi kwalliya zai zo da bako take jin farin ciki, ashe wanda zai zo had'ad'd'an gaye ne, gaskiya dole ma Dady ya aura mata shi don ayanzu kad'ai jitake bazata iya rabuwa dashi ba, idan ko yaki amincewa da ita. zata iya shiga wani hali. Gyaran murya Ra'eez yayi ganin irin kallon da take masa, da sauri ta d'auke idonta tana murmushi. Ra'eez yace zaki iya tafiya nagode. Raheena tace haba Yayana baka son na taya ka firar? Kauda kai yayi yana fad'in kaina yana mani ciwo ne. Murmushi tayi tana fad'in bara na kawo maka magani. Kai ya girgiza yana fad'in bana shan maganin ciwon kai kawai surutu ne bana so. Tashi tayi tana fad'in nayi shiru bara na zauna acan, kallon ka ya fiye mani surutun ma. Zama tayi a saman kujera tana binshi da kallo. Kauda kai yayi yana jan tsaki a zuciyarsa dan har itama haushinta yakeji gashi bata da kamun kai. Fitowar Alhaji Barau ce tasa ya d'an saki fuska. Alhaji Barau yace Ra'eez har ka sha ruwan ko? Ra'eez yace nasha tafiya ma zanyi. Hajiya Hauwa da ta sauko take fad'in ga abinci fa zamuci. Mik'ewa Ra'eez yayi yana fad'in nagode Hajiya ana jirana a gida ne. Da sauri Raheena tace kana da aure ne? Murmushi Alhaji Barau yayi yana fad'in beda aure kila dai abokinsa ne yake jiransa. Ajiyar zuciya ta saki tana fad'in har naji dad'i Dady. Hajiya Hauwa tace Oh! ni Hauwa'u, wallahi Raheena baki da kunya. Alhaji Barau yace nagode Ra'eez, amma wata rana zaka zo muci abinci tare. Ra'eez yace insha Allah. Sallama yayi masu sai godiya suke masa. Alhaji Barau ne ya kalli Raheena yana fad'in bazaki rakasa mota ba. Da sauri tayi gaba tana fad'in na d'auka kai zaka rakashi ai Dady. Hajiya Hauwa tace waye k'arami anan ai dole kece zaki rakashi. Har bakin mota ta rakashi, bayan ya zauna zai rufe tayi saurin rik'e murfin, langwab'ar da kai tayi tana fad'in Yayana sai yaushe kuma? Kau da kai yayi yana fad'in nima ban sani ba. Shagwab'e fuska tayi hada dira k'afa tace kai dan Allah Yayana! Murmushi yayi dan ta basi dariya. Kallonta yayi yana fad'in shikenan zan samu lokaci nazo. Murmushi ta saki tana fad'in nagode Allah ya kaimun kai gida lafiya. Ra'eez yace amin nagode. Rufe masa k'ofar tayi. Sai da ya fita daga gidan kafin ta shige ciki. A mota Ra'eez sai jan tsaki yakeyi akan abinda Raheena takeyi, sai kace ba mace ba, wai nan har karatu tayi. Murmushi yayi yana shafa fuskarsa, a hankali ya furta Alhaji Barau zan bar maka tabo biyu kuwa. *** Da tsalle tashiga gidan ta rungume Hajiya Hauwa tana dariya. Alhaji Barau yace ikon Allah lafiyar ki kuwa? Hajiya Hauwa tace da alama anyi nasara. Alhaji Barau yace ai tunda na ganshi nayi ma Raheena sha'awarsa, domin nasan shine irin zab'inta. Hajiya Hauwa tace wallahi nima ya kwanta mani, yaro sai kace jinin larabawa, jikinsa na hutu ne, da gani kasan ya fito daga babban gida, dan ya tsumu a cikin daula. Raheena tace wallahi Dady ina matuk'ar sonshi dan Allah ka aura mani shi zan iya shiga wani hali idan na rasashi. Saurin rufe mata baki Hajiya Hauwa tayi tana fad'in haba shalele, kima daina fad'ar haka, ke d'aya muke da ita mace, sannan kece ta gaban goshin mu, dole ma ki auresa. Sake rungumeta tayi tana fad'in nagode Momy nah. Ur's. Nabeelert Lady🖋 [3/10, 8:39 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.* 2⃣3⃣ Da gudu Raheena tayi d'akin ta tana mai cike da farin ciki, da kyar tayi sallolinta abinci ma a d'aki taci ta kosa dare yayi sosai ta kira Ra'eez dan ta amshi lambarsa a wajen Dadynta. ** Ra'eez bayan ya kammala abubuwan da yakeyi ya kakkab'e gadonsa ya kwanta, rungume filo yayi yana jin kewar Iyayensa, tun dawowarsa gidan da aka gyara komai ya koma d'akin Abbunsa da zama, domin yana matuk'ar son gadon Abbunsa, babu abinda aka canza hatta da filo da katifar duk sune na kusan shekaru takwas, zanin gadon kawai ya canza shima na Ummunsa ya d'auko yasa, duk lokacin daya kwanta a gadon yana mai jin dad'i, sai yake jin kamar yana tare da Abbunsa ne. K'arar wayarsa ce ta dawo dashi daga tunanin da yakeyi, d'auka yayi yana bin wayar da kallo har ta tsinke, dan besan lambar da ya gani ba, sake kira akayi amma be d'auka ba, sai da aka kira sau ukku kafin ya d'auka. Shiru yayi ba tare da yayi magana ba. Mak'e murya Raheena tayi cikin shagwab'a tana fad'in haba Yayana sai da na kira sau ukku sannan zaka d'auka. Murmushi Ra'eez yayi dan ya fahimci mai magana. Raheena tace koda yake laifina ne da ban baka lambata d'azu ba, amma kuma ya kamata ace ka d'auka tun akira na biyu. Gyara kwanciya yayi yana fad'in kin kira waya sai surutu kikeyi baki fad'i sunanki ba. Cikin shagwab'a tace kai Yayana nasan dai ai ka d'auki muryata? Ra'eez yace ai ni ko wata mukayi da mutum ba lallai bane na rik'e muryarsa ba. Murmushi tayi tana fad'in Raheena ce fa. Ra'eez yace Raheena? Wace Raheena fa? Yanzu kam kukan shagwab'a tasa hada birgima asaman gado, duk yana jiyota sai ma murmushi da yayi. Gyaran murya yayi yana fad'in Malama zan kwanta naga alamar bakida abun cewa. Cikin sauri tafe Raheena da kazo gidan mu d'azu a Surelere fa. Tab'e baki yayi yana fad'in Allah sarki ashe kece? Nasan dai ban baki lambata ba shiyasa nayi mamaki. Raheena tace awajen Dady na amsa ai. Ra'eez yace to yayi kyau ya 'yan gidan ki gaishe mani da su. 'Dif ya kashe waya yana sakin murmushin mugunta. Raheena kuwa saurin cire wayar tayi tana binta da kallo, sake kira tayi amma a kashe. Wurgar da ita gefe tayi tana mai jin haushi, amma bakomai zata jure komai matuk'ar zai amince da ita, tasan ma yana da saukin kai zai amince da ita. Bargo ta jawo tana murmushi. *** Washe gari wayar Raheena ce ta tashesa abacci, dan bayan yayi sallar asuba ya kunna wayar ya kwanta bacci ya d'aukeshi. Saurin tashi yayi yana kallon yanda gari yayi haske sosai, wayar ya kalla yaga lambar jiya ce dan beyi saving ba. Hannu yasa ya d'auka akaro na biyu da ta sake k'ara. Gaishesa tayi tana fad'in Yayana ko bacci kakeyi ne? Murza ido yayi yana fad'in wallahi kuwa gashi har na kusa makara, gaskiya nagode maki. Dad'i ne ya kamata ta sake kank'ame wayar tana fad'in naji dad'i kuma zan rik'a tada ka a koda yaushe dan bana so ka makara. Murmushi yayi yace nagode, bara nashiga wanka. Da sauri tace da ina kusa dana had'a maka ruwan. Ra'eez yace hakan ma nagode. Kashe wayar yayi ya nufi band'aki. Raheena kuwa fad'awa tayi saman gado tana murmushi, saurin tashi tayi ta jawo hijabinta domin tayi sallah, dan alokaci zatayi sallar asuba, ahakan ma saboda suyi waya da Ra'eez yasa ta tashi wajen k'arfe takwas, dan Raheena akwai sallah a makare, wani lokacin sai ta kai k'arfe tara batayi sallar asuba ba. Tashi tayi tana fad'in dole nasa alarm ko dan narik'a tashinsa sallar asuba, da haka zan saye zuciyarsa, idan na tashesa nima zan daure nayi sallar sai na koma bacci kafin alarm d'in 7:30 yayi na sake tadasa yayi wanka. Murmushi tayi tana kabbara sallah. *** Komai beci ba ya rufe gidan ya nufi gidan su Rumaisa dan ya saba saiya fara duba su kafin yawuce wajen aiki. A tsakar gida ya iske su suna karyawa koko da kosai, Rumaisa kuma tana had'awa da shayi dan bata shan koko. Da sallama yashiga. Amsawa sukayi Mama tana fad'in yanzu nake fad'in Rumaisa ta kawo mani wayata na kiraka naga shiru baka shigo ba. Zama yayi yana fad'in wallahi yau makara nayi Allah yaso ma Raheena ta tashe ni da... Kwarewar da Rumaisa tayi ne yasashi yin shiru yana kallonta. Mama tace kiyi ahankali mana Rumaisa. Shayin ta d'auka tasha tana goge hawayen da suka taho mata wanda babu wanda ya gani sai Ra'eez. Murmushi yayi dan ya fahimci dalilin kwarewarta. Juyawa yayi yana gaishe da Mama. Bayan sun gama gaiswa Rumaisa ta gaishe sa. Harara ya buga mata yana fad'in shine ko ki tashe ni ko? Duk'ar da kai tayi fuskarta a d'aure. Mama tace Rumaisa kawo masa kofi ya karya kafin yawuce. Ra'eez yace Mama na kusa makara gara dai na tafi kawai. 'Daure fuska Mama tayi tana fad'in tashi ki kawo masa kofin. Murmushi yayi dan yasan halin Mama bata son ya fita beci komai ba. Tashi Mama tayi ta koma ciki ta barsu a waje. Zuba masa tayi ta mik'a masa kular kosan. Amsa yayi yana kallon yanda tayi kicin-kicin da fuska kamar zatayi kuka. Murmushi yayi yana girgiza kai yace K'anwata waya tab'a mani ke kuma? Zama tayi tana kok'arin maida hawayen idonta. Kosan ya kai baki yana kallonta sai juya kosan hannunta takeyi. Murmushi yayi yana fad'in ke shayi zaki sha ni kuma kin had'ani da koko saboda son kai ko? Kauda kai tayi bata ce komai ba. Ra'eez yace wai bazaki kulani ba ne yau? Turo baki tayi tana fad'in kaje Raheena ta baka. Dariya yayi yana fad'in lallai sunan yayi maki dad'i, daga fad'ar suna so d'aya shikenan har kin haddace, ko kina so na had'aku kawance ne? Tab'e baki tayi tana fad'in Allah ya kyauta. Girgiza kai yayi yana fad'in kada ki sake kiranta da Raheena domin Yayarki ce. A zabure Rumaisa ta tashi tana dira k'afa tayi d'akinta. Dariya yayi sosai yana girgiza kai, abincinsa yacigaba da ci aranshi yana jin wani sanyi yana ratsa masa zuciya ganin yanda Rumaisar sa take nuna kishinta akansa, yana matuk'ar sonta amma har yanzu ya kasa fad'a mata, yana jira ta kammala karatun ta kafin ya fad'a mata amma a yanzu baya jin zai iya jiranta, domin yana buk'atar mai kula dashi, dole ma ya fito mata da abinda yake zuciyarsa shekaru da yawa. Bayan ya kammala yayi ma Mama sallama. Fitowa tayi tana masa addu'a, kud'i ya aje yana fad'in Mama yau sakwara nake son ci. Mama tace badamuwa za'ayi maka, kun gaisa da Madu ko? Ra'eez yace lokacin dana shigo yana band'aki sai dai idan na fita yanzu. Mama tace to Allah ya tsare ya baka sa'a a duk abinda kasa gaba, Allah ya kareka daga sharrin masu sharri. Murmushi yayi cikin jin dad'i yace amin Mama. Mama tace ina Rumaisar fa? Ra'eez yace tana d'aki kila wani abun takeyi. Mama tace to sai ka dawo. Fita yayi yana waiwayen d'akin Rumaisa. Sai da suka gaisa da Madu ya bashi kud'i yana ta masa addu'a kafin ya tafi. Asibiti ya fara biyawa ya duba Ummunsa kafin yawuce wajen aiki, koda yaje ya iske har Alhaji Barau yazo, kai ya jinjina yana fad'in lallai yau na makara da yawa. Ciki yawuce yana gaisawa da mutanan da suke waje. Lokacin daya shiga ofis d'in Alhaji Barau tare da bako ya iskeshi, risnawa yayi ya gaishe su. Alhaji Barau yace Ra'eez ko dai bakayi bacci jiya da dare bane? Murmushi yayi yana fad'in wallahi makara ce kawai nayi. Alhaji Barau yace Mr. Kallah kaga sabon lauyen da nake fad'a maka. Da sauri Ra'eez ya kalli wanda aka kira da Mr. Kallah, domin duka sunayen wad'an da suka zalunci Abbunsa babu wanda bai rik'e ba. Murmushi Mr. Kallah yayi yana fad'in lallai ankawo maka cigaba a ofis d'inka, domin samun lauyoyi masu hazak'a yana k'arama waje kima, sannu Ra'eez kacigaba da dagewa kaji. Kai Ra'eez ya d'aga. Alhaji Barau yace ga wani file nan kaje ka dubashi yanzu aka kawoshi, bana son ka wahalar da kanka domin ba wata babbar shari'a bace kasan wasu mutanan basu da kwakkwarar sheda kawai saboda sun maida kotu wajen wasa komai su kawo k'ara. Ra'eez yace zan duba. Kai Alhaji Barau ya jinjina yana fad'in zaka iya tafiya. Sallama yayi masu ya fita. Mr. Kallah yace gaskiya natsuwar Yaron nan tayi mani sosai, daga ganinsa d'an manyan mutane ne. Alhaji Barau yace shiyasa nake son had'ashi da Yarinyar waje na. Mr. Kallah yace wai Raheena kake magana? Alhaji Barau yace ita fa, ai kasan ita kad'aice mace sauran maza ne. Mr. Kallah yace lallai kayi tunani, kaga nan gaba ko zaka aje aiki zaka iya d'orashi a matsayin ka, kaga shikenan bamu da sauran damuwa kotu ta zama tamu. Alhaji Barau yace kamar kashiga zuciyata. Dariya sukasa suna kashewa. ** K'arfe d'aya dai-dai wayar Ra'eez tayi k'ara, yana dubawa yaga sunan daya sama Rumaisa a saman wayar ( *Cutie*) . Murmushi yayi kafin ya katse kiran, dan baya d'aukar mata waya sai dai ya kashe ya kira. Da kallo Jabeer ya bishi ganin yanda yake sakin murmushi. Wayar yasa a kunne yana jiran ta d'auka. Tana d'agawa suka gaisa, shiru tayi ta kasa magana. Ra'eez yace an gama fushin dani ne? Rumaisa tace dama lokacin sallah ne yayi. Sosai ya saki murmushi dan ya gano manufarta. Rumaisa tace katashi kayi sallah to. Jinjina kai yayi kamar tana gabansa yace yanzu kuwa rankiyadad'e, nagode da wannan kulawa, kinga yau kin riga Rah.... Katse wayar tayi dan bata son ya k'arasa fad'ar sunanta. Dariya yayi yana kallon wayar. Dafashi Jabeer yayi yana fad'in Mr. Love idan ka gama muje kada atayar. Girgiza kai yayi yana fad'in waya fad'a maka soyayya nakeyi K'anwata ce fa. Jabeer yace naga alama, tashi mutafi to. Dariya Ra'eez yayi yana fad'in da gaske fa nakeyi. Jabeer yace kaji kama kai, kaji nace wani abu ne? Muje kada atayar. Sosa kai Ra'eez yayi suka fita. Kasancewar a ofis ya bar wayar suna shigowa ya iske wayarsa tana k'ara, kafin ya d'aga ta katse. Hannu Jabeer yasa ya d'auke wayar yana fad'in yanzu kuma waye ya kira? Ido ya zaro yana fad'in missed call takwas fa. Hannu Ra'eez ya kai zai amshe wayarsa yana murmushi. Jabeer yace sai dai kuma lambar babu suna amma duk mutum d'aya ne. Ra'eez zaiyi magana wayar ta sake k'ara. D'auka Jabeer yayi yasata a speaker, harararsa Ra'eez yayi yana amsar wayar, kafin ya cire a speaker Raheena tace Allah yasa ba laifi nayima Yayan nawa ba, tun d'azu nake kira amma shiru har kasa hankalina ya tashi fa. Saurin cireta yayi yasa a kunne yana kallon Jabeer da yake masa dariya. Zama yayi yana fad'in Raheena ce? Shagwab'e fuska tayi tana fad'in yanzun ma bakayi saving lambar tawa ba? Murmushi yayi yana fad'in ayi hak'uri mantawa nayi. Raheena tace nayi ai baka laifi a wajena, ina fatan dai kaci abinci? Ra'eez yace sallah ya kamata ki fara tambaya ko dai bakiyi ba kema? Rufe baki tayi dan itama batayi sallar ba bare ta tambayi wani, wayancewa tayi tana fad'in ai nasan baka wasa da sallah shiyasa ban tambaya ba, amma nayi tawa. Ra'eez yace to kin kyauta dan bana son mutum mai wasa da sallah. Raheena tace insha Allahu bazan sake wasa da sallah ba tunda baka so. Ra'eez yace da naji dad'i kuwa. Murmushi tayi tana fad'in bazan sake ba, yanzu dai kaci abinci? Ra'eez yace banci ba. Raheena tace gaskiya bazanji dad'i ba ace har yanzu baka ci abinci ba, bani minti talatin yanzu zan kawo maka. Ra'eez yace nasa Mama tamun sakwara kibarshi nagode. Raheena tace kai Yayana dan Allah ka barni nazo. Ra'eez yace kibarshi nagode. Shagwab'e fuska tayi tana fad'in to kamun alk'awari zakazo anjima kaji. Ra'eez yace zan duba nagani. Raheena tace nagode, ka kular mun da kanka. Ra'eez yace nagode. Kashe wayar yayi yana murmushi. Zama Jabeer yayi yana kallonshi hada tagumi. Gira Ra'eez ya d'aga mashi yana fad'in ya dai? Jabeer yace lallai kai d'in azimun ne. Gyara zama Ra'eez yayi yana fad'in kacika sa ido wallahi. Jabeer yace naji amma a bani amsa ta. Ra'eez yace kasa ido kacigaba da kallo kawai. Jabeer yace bazaka fad'a ba kenan? Ra'eez yace ka bari idan na tashi zuwa sai muje tare. Jabeer yace yanzu naji batu. Dariya sukayi suka cigaba da aiki. Suna tashi Ra'eez yace ma Jabeer dole sutafi tare suci abinci a wajen Mama, Jabeer yace shikenan daga can sai mu wuce ko? Ra'eez yace shikenan amma sai munyi magriba. Jabeer yace sai dai mu fara biyawa gidan mu kada Ummana taga na dad'e sai mu wuce. Ra'eez yace shikenan muje. *** Bayan sun biya gidansu Jabeer suka wuce gidan su Rumaisa. Tunda Jabeer yaga yanda Rumaisa take sunne kai ya gano abinda yake tsakanin su, musamnan da yaji Ra'eez yana fad'in ta sako hijabi su biyu ne. Shiru kawai yayi yana dariyarsa. Ra'eez yace kai fa d'ansa ido ne. Jabeer yace me kaji nace kuma? Kwafa Ra'eez yayi ya jawo kwano suka fara cin abinci. Mama tace lallai Jabeer ka ciri tuta, da alama hankalin Ra'eez ya kwanta da kai, ban tab'a ganin Ra'eez da aboki ba sai yau. Murmushi yayi yana fad'in nima nace masa nayi shiyasa ya amince dani Mama. Murmushi tayi tana fad'in gaskiya naji dad'in had'uwar ku, Allah yasa hakan ya zama alkhairi, sai ku kula da aikin ku kunsan yanda yake da had'ari. Gaba d'aya suka amsa da insha Allah. Bayan sun gama suka tashi. Mama tace tafiya zakuyi ne? Jabeer yace zan rakashi wajen... Take masa k'afa Ra'eez yayi hakan yasa yayi shiru. Kallonshi Rumaisa ta tsaya yi. Ra'eez yace yanzu zan dawo Mama. Wayarsa ce tayi k'ara, yana d'agawa yace gamu nan zuwa, kashewa yayi yana fad'in muje. Kallon Rumaisa Jabeer yayi yaga yanda ta had'e fuska, fita sukayi tana mai binsu da kallo cike da bakin ciki. Ur's. Nabeelert Lady🖋 [3/10, 8:39 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.* 2⃣4⃣ Tsaye suke a jikin mota acikin harabar gidan su Raheena, tunda suka shigo anguwar fuskar Ra'eez ta canza, haka kawai yake jin wani d'aci a zuciyarsa, a hanya sai wasa da dariya suke da Jabeer amma suna shigowa anguwar yanayinsa ya canza. Jabeer ya d'auka wani abunne shiyasa yayi shiru, amma a yanzu da suke tsaye suna jiran fitowar Raheena sai yaga abun yayi yawa, domin yana zolayarsa akan ya fad'a masa tsakanin Rumaisa da Raheena wacece yake so aciki amma sai yaga Ra'eez bai san yanayi ba dan hankalinsa yana wajen kallon gidan, musamman ginin da yake can bayan gidan. Hannu Jabeer yasa ya tab'o Ra'eez, da sauri ya juyo jin an dafashi. Ido Jabeer ya tsura mashi ganin yanda idanuwansa sukayi ja. Duk'ar da kai Ra'eez yayi yana kok'arin b'oye b'acin ransa. Jabeer yace Ra'eez lafiyar ka kuwa? Murmushin yake Ra'eez yayi yana fad'in lafiya lau me kagani? Jabeer yace tun shigowar mu anguwar nan naga yanayin ka ya canza, tsayuwar mu anan kuma sai naga abun ya k'aru, gashi kana kallon wani waje har idanuwanka sunyi ja, da alama akwai abinda ya sosa maka zuciya ko? Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in bakomai kawai kai ne kaga haka. Jabeer yace bazaka fad'a mani ba ne kawai, amma har fa magana nake maka hankalin ka yana wani waje har sai da na tab'oka kafin kasan ina magana. Ra'eez yace babu komai kawai ina tunanin dalilin da yasa Raheena take son nazo bayan nasan babu komai atsakanin mu, duka jiya muka fara ganin juna kuma. Jabeer yace kaima kasan soyayya ce kad'ai zatasa ta nemeka, nifa tun wayarku ta d'azu na fahimci komai, sai dai kaine ban gane maka ba, a gida ga Rumaisa sannan kuma anan ga Raheena, ban sani ba ko auren gata zakayi. Ra'eez yace meye kuma auren gata? Jabeer yace auren mata biyu a lokaci guda mana, idan ba gata ba taya zaka had'a mata biyu kana soyayya dasu alokaci guda kuma dukansu wajen kunya ne babu wacce zaka iya ajewa. Murmushi kawai Ra'eez yayi bece komai ba. Jabeer yace duk da bansan komai a labarin ka ba amma na fahimci kana da alak'a mai k'arfi dasu Rumaisa, kaga kuwa bazaka iya yaudararta ba, ga 'Yallab'ai kuma, kaga kana aiki a k'ark'ashin sa bazaka iya yaudarar d'iyarsa ba. Ra'eez yace haka ne, domin Rumaisa ruhin jikina ce, da soyayyarta na girma, domin soyayyarta ta samo asali tun lokacin da naji sunanta, bayan da muka fara gaisawa awaya sai ta k'ara shiga zuciyata, aranar dana fara ganinta duk da muna yara amma najita a jinin jikina, daga lokacin da na mallaki hankalin kaina sai na fahimci ta zama b'argon jikina, in tak'aice maka mutuwace kad'ai zata iya rabani da Rumaisa. Baki Jabeer ya rik'e yana kallon Ra'eez wanda yake zuba bayani har wani lumshe ido yake yayin da hannunsa yake saman kirjinsa yana nuni dashi. Dariya yayi yana fad'in ita kuma Raheena fa? Ra'eez zaiyi magana yaji k'amshin Raheena ya dakar masa hanci. Shiru yayi yana kok'arin d'ago kanshi. Cike da yanga Raheena take taku kamar bata son taka k'asa, kayan jikinta kamar zatayi nishi su yage saboda yanda suka matse ta, k'aramin gyale ta yafa a saman kanta ko d'ankwalin kayan bata sa ba, sai gashin data k'ara data bazo a bayanta. Kallo d'aya yayi mata ya d'auke kanshi cike da takaici, badan akwai abinda yake sak'awa aranshi ba da babu abinda zaisa yazo wajen wannan abar. Fuskarta d'auke da murmushi ta k'araso wajensu tana fad'in sannun ku da zuwa wallahi banyi zaton zaka zo ba. Fuska a had'e Ra'eez yace sallama ya kamata ki farayi ba wannan maganar ba. Saurin dafe bakinta tayi ta juya tana fad'in kayi hak'uri na manta ne amma bazan sake ba. Seda ta koma da baya kafin ta dawo bakinta d'auke da sallama. Gaba d'aynsu suka amsa Jabeer yana fad'in sannu da shanyamu Raheena. Murmushi tayi tana fad'in kuyi hak'uri bansan kun taho ba ne kuma shirina dad'ewa gareshi kusan awata d'aya ina shiryawa. Ra'eez yace idan kika cigaba da haka bazaki sake ganin mu a wajenki ba, domin mu bama jiran da yawuce minti biyu. Hannuwa ta had'e tana fad'in ayi hak'uri, daga yau bazan sake ba, tunda dai baka son jira nima bazan sake dad'ewa ina shiri ba koda baka nan zanyi kok'arin koyon sauri matuk'ar hakan zai saka farin ciki. Murmushin gefen baki Ra'eez yayi ya kauda kai. Jabeer ne yace Hajiya Raheena ina wuni. Murmushi tayi tana fad'in la.... Kallon da Ra'eez yayi mata yasa tayi saurin yin shiru. Ra'eez yace lallai ma, abokin nawa zai gaisheki ki amsa, bayan kinsan daga sallama gaisuwa itace tafi dacewa. Hannu tasa ta d'an bigi kanta tana fad'in dan Allah kuyi hak'uri wallahi ban saba da hakan bane amma zanyi kok'arin gyarawa tunda abinda kake so kenan. Ina wunin ku? Jabeer yace lafiya lau. Raheena tace mushiga ciki bana fira awaje akwai wajen zaman baki acan. Ra'eez yace bana fira a cikin falo nafi son waje saboda nafi buk'atar iskan waje. Murmushi ta saki tana fad'in duk yanda kace, ga kujeru acan muje kuzauna to. Jinjina kai Ra'eez yayi yana fad'in muje. Bayan sun zauna mai aiki ta iso da kayan motsa baki a faranti, har k'asa ta duk'a tana gaishe su, bayan sun amsa ta fara kok'arin zuba masu lemu. Da sauri Ra'eez yace kibarshi kije kawai. Raheena tace haba ka barta mana aikinta ne fa. Kallonta Ra'eez yayi beyi magana ba. Raheena tace shikenan jeki. Kallon Jabeer tayi tana fad'in gashi bansan sunan ka ba. Jabeer yace zakiji a bakin abokina ai. Kallon Ra'eez tayi tana fad'in Yayana kusha ko ruwa ne mana wane zan zuba maku? Ra'eez yace da ace kece kika had'a komai da kanki kuma kika d'auko daga gida kika kawo har nan shine zan sha, amma ni bana cin abinda masu aiki suka had'a. Shagwab'e fuska tayi tana fad'in kayi hak'uri daga yau nice zan rik'a maka hidima, duk da bana shiga kicin amma zan fara akan ka. Tab'e baki Ra'eez yayi yana fad'in amma kin bani kunya, yanzu kamar ki ace bata shiga kicin idan kikayi aure waye zai rik'a maki aikin kuma? Rausayar da kai tayi tana fad'in ai na iya dafa indomie. Ra'eez yace Jabeer kaji fa. Dariya Jabeer yasa yana fad'in aikin kenan, ai yanzu duk wata mace data fito daga gidan hutu indomie kad'ai zaka sameta ta iya girkawa, wasu ma ko ruwan zafi basu iya d'orawa ba, shiyasa ka ganni nan bazan iya auren macen data fito daga gidan masu kud'i ba. Raheena tace kai Jabeer kada ka tunzura Yayana mana, wallahi daga yau zan fara koyon komai matuk'ar zaisa shi farin ciki ni kuma zanyi koda zan cutu ne. Murmushi Jabeer yayi yace lallai Ra'eez ana ji da kai, sai dai kace mani Raheena K'anwar kace amma gashi naji wata maganar kamar... Harara Ra'eez ya sakar masa hakan yasa yayi shiru yana dariya. Raheena tace e Yayana ne amma wanda za'a iya aura, Jabeer ina so ka tayani neman soyayyar abokin ka, tunda Allah yasa na fara jin sunanshi a wajen Dady naji soyayyarsa a zuciyata, aranar dana fara d'ora idanuwana akansa sai naji komai ya kwance mani, maganar gaskiya bazan b'oye maka ba inama abokin ka soyayya mai zafi, wallahi bana ji zan iya rayuwa babushi. Tashi Jabeer yayi yana fad'in lallai wannan maganar babbace, Raheena sai nace Allah ya bada sa'a, amma sai kin dage dan abokina mai zafi ne. Wucewa yayi yana kallon Ra'eez yana dariyar shakiyanci, yana mamakin Raheena yanda take fad'ar magana kamar itace saurayin sam babu aji, gata dai 'yar gayu amma tana kwafsawa. Ko kallonsa Ra'eez beyi ba amma yasan dariya yake masa. Wayarsa ce tayi k'ara alamun sako yashigo hakan yasa ya maida hankalinsa yana dubawa. Rumaisa ce, murmushi yayi kafin ya bud'e *Yayana gaskiya ka dawo gida akwai d'orin da zakamun kuma yanzu nake so kamun.* murmushi yayi ya maida wayar a aljihunsa. Yana d'ago kai suka had'a ido da Raheena da ta langwab'ar da kai tana masa wani irin kallo, saurin d'auke kansa yayi aranshi yana fad'in wannan yarinyar bata da kunya wallahi. Saurin tashi yayi yana fad'in zamu tafi. Da sauri ta mik'e tana fad'in haba My D, shikenan bazaka tsaya muyi fira ba daga zuwa zaka tafi ko amsata baka bani ba fa. Kallonta Ra'eez yayi yana fad'in idan kika gyara halayenki da bana so alokacin zan fad'a maki abinda na yanke wanda nasan kece zai taimaka. Murmushi tayi tana fad'in kasa naji dad'i sosai, kuma daga yau zan fara gyara duk abinda baka so, nan da wata d'aya zan zama macen da ta iya girki sosai. Ra'eez yace zangani ai. Jerowa sukayi zuwa wajen motarsu sai labari take basa kamar zata shige jikinsa, shi kuwa hankalinsa yana wajen Rumaisa ya kosa ya koma. Itace ta bud'e masa k'ofa tana fad'in Jabeer nagode sosai, idan ka sake dawowa girki na zakaci. Jabeer yace lallai naga alamar da wuri zaki d'auki darasin abokina. Murmushi tayi tana duk'ar da kanta cikin motar tace My D, kayi tuki a hankali bana so ka wahala, idan kun isa zankira naji yanda ka isa kaji. Kai ya d'aga yana d'aukar mukullin motar. Tana tsaye har suka fita. Ajiyar zuciya ta saki tana jin wani dad'i na ratsa ta, sam batayi tunanin Ra'eez zaiyi saurin amincewa da buk'atar ta ba, shiyasa zata dage domin ta gyara komai matuk'ar hakan zaisa ta sameshi. Juyawa tayi da niyar kiran mai aiki tazo ta kwashe kayan sai kuma ta tuna abinda Ra'eez yace. Murmushi tayi ta juya zuwa wajen kayan ta fara had'asu tayi cikin gida. Tana shiga Momynta ta fara tambayarta an dace? Kai ta d'aga tana fad'in sosai ma, bara na kai kayan nazo. Tana fitowa tazo ta rungume Momy tana fad'in ai na fad'a maki Ra'eez bazaiki amincewa dani ba, ko awancan ranar baki ga yanda yake bina da wani kallo ba, gaskiya Momy Ra'eez ya had'u. Momy tace amma naji dad'i sosai, kinga nan da wani lokaci sai mu fara shirin biki, lallai zanyi bikin da ba'a tab'ayinsa adangi ba, duniya sai ta sheda bikin ki Raheena, bari Alhaji yazo tun yanzu zamu fara shirya yanda komai zai kasance, ke dole duniya tasan za'ayi bikin ki. Dariya Raheena tasa tana fad'in nagode Momy na, dole na koma group d'in mu dana fita na kawayena, domin ina son su san irin mijin da zan aura kuma inaso na tara mutane da yawa domin kowa ta samu abun fad'a. Momy tace haka nake so 'Diyata. Mai aiki ce tashigo bakinta d'auki da sallama. Da sauri Raheena ta amsa tana fad'in Lawisa ya akayi? Ba Lawisa ba har Momy tayi mamakin abinda Raheena tayi, domin tsakaninta da masu aikin gidan kyara ce, kome zakayi mata baka burgeta, haka kuma bata tab'a kiran sunan ka sai dai tayi amfani da kalmar Ke, ko Kai, sai gashi yau itace hada amsa sallama da kiran suna. Duk'ar da kai Lawisa tayi tana fad'in dama abinda za'a dafa maki da dare nazo tambaya. Tashi Raheena tayi tana murmushi tace ai yau tare zamu shiga kicin d'in nima daga yau zan rik'a tayaki girki domin ina son na kware sosai. Murmushi Momy tayi tana fad'in Raheena anya? Tashi tsaye tayi tana fad'in Lawisa muje, kallon Momy tayi tana fad'in Momy nasan bazaki so kiyima 'Diyarki aure taje gidan miji bata iya komai ba. Kai Momy ta jinjina tana fad'in wannan haka yake d'iyar albarka, amma naji dad'in wannan tunanin naki, ko kuma nace nagode ma Ra'eez domin nasan wannan sabon canjin daga garesa ne. Dariya Raheena tasa tayi kicin tana fad'in kai Momy. **** Tunda suka tafi Jabeer yake damun Ra'eez da tambaya akan yanda zaiyi da Raheena. Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in yanda kowane namiji yakeyi da 'yan matansa nima haka zanyi da ita. Jabeer yace amma dai kai bakayi kama da mayaudara ba. Ra'eez yace ka sani ko zan fara daga yau. Dukansa Jabeer yayi yana fad'in dan Allah muyi maganar gaskiya. Ra'eez yace amma dai a gabanka kaji tace tana sona ko? Kaga kuwa bazaka kirani da mayaudari ba, bata tsaya tayi binciken akwai wacce nake so ba ko babu kawai kanta ta sani, kaga kuwa idan taga na auri wata bazata zargeni ba. Jabeer yace duk da haka, ya kamata ka fad'a mata akwai wacce kake so idan zata iya rayuwa da kai ahaka shikenan, idan kuma bazata iya ba kaga sai ta hakura. Ra'eez yace bazan iyaba, ka sani ma wai ko ina sonta. Dariya Jabeer yasa yana fad'in ai har mata hud'u ma zaka iya aure, to Allah ya bada sa'a, amma wallahi duk ranar da aka rutsa ka kada ka nemeni. Ra'eez yace insha Allahu. Sai da ya fara aje Jabeer gida kana yawuce gidansu Rumaisa, tana jin k'arar motarsa tayi saurin shigewa d'aki ta gyara fuskarta hada fesa turare. Muryarsa tajiyo a tsakar gida shida Mama, kwala mata kira Mama tayi tana fad'in ki d'auko littafin ga Yayan naki nan yazo. Ciki ta shige ta barshi a saman tabarma. Kai ak'asa Rumaisa ta fito, bakinta d'auke da sallama ta k'araso wajenshi. Tunda ta fito yaji k'amshin turarenta, dama shine yake shiya mata saboda yana matuk'ar son k'amshinsa saboda na mata ne. Idanuwa ya tsura mata ganin yanda tayi kwalliya kamar mai shirin fita wani waje hada shafa janbaki ita da bata sonshi. Amsa mata sallamar yayi yana sakin murmushi. Tana zama ta gaisheshi. Amsawa yayi yana fad'in Rumaisa ko dai bako zakiyi ne? Saurin kallonsa tayi tana zaro ido. Murmushi ya saki yana kallonta yanda ta zaro idanuwanta masu matuk'ar burgesa. Maida kanta k'asa tayi tana wasa da hannunta tace ni babu wani bakon da zanyi, waye ma yake zuwa wajena. Ra'eez yace to wannan kwalliya wa akayi mawa? Rufe fuska tayi tana fad'in haka kawai naji ina buk'atar nayi. Ra'eez yace Uhmm! Ke dai ki fad'i gaskiya. Rumaisa tace da gaske mana, yauwa wai Yaya ina kukaje? Ra'eez yace naje fira ne. Saurin kallonsa tayi idanuwanta tuni suka canza, a hankali ta mik'e tana shirin komawa d'aki. Da sauri ya tashi yana fad'in ina zaki ba'ayi k'arin ba? Murya na rawa tace na iya ai. Ra'eez yace dawo ki zauna. Kasa dawowa tayi kawai tashige d'aki da gudu saboda kukan da taji ya taho mata, ashe dama ita kad'ai take haukanta, ta d'auka kulawar da yake bata soyayyace ashe ba haka bane a zuciyarsa, lallai ta cutar da kanta data bari ta girma da soyayyarsa a ranta. Ra'eez kuwa jiyayi jikinsa yayi sanyi, tabbas yasan Rumaisa tana sonshi, meyasa zai fad'a mata haka? Kada garin neman ruwa kwad'o yayi masa k'afa. Lek'awa yayi wajen Mama yayi mata sallama. A mota ya zauna yana tunanin abunyi. Kasa daurewa yayi kawai ya jawo wayarsa ya fara rubuta sako.... *Haba pretty na taya zaki tafi kibar Yayanki bayan kinsan ke kad'ai yake gani yaji dad'i, ina da kamar ki ina zan iya zuwa fira, wasa nake maki fa, Rumaisa ina matuk'ar sonki bazan iya had'a kowa da ke ba, kece rayuwata, da sonki na girma bana jin zan iya rayuwa babu ke, na dad'e ina son na fad'a maki wannan maganar amma ina tsoron kada ki kasa amincewa dani, ina sonki Rumaisa, kuma kisa aranki kece Uwar 'Ya'Yana da yardar Allah, ina so ki maido mani da amsa idan ba haka ba bazan iya bacci ba.* Ya mai-maita sakon daya rubuta yafi so biyar kafin ya tura fuskarsa d'auke da murmushi, yana turawa yayi saurin barin k'ofar gidan. Rumaisa da Mama take tama fad'a akan k'uncin da ta sameta tanayi taji k'arar wayarta, amma saboda Mama tana wajen sai ta share taki dubawa. Mama tace idan kin gama k'uncin ki fito ki kai Abdallah yayi fitsari ya kwanta tunda bazaki fad'a mani abinda yake damunki ba, bansan lokacin da kika fara b'oye mani abu ba Rumaisa. Tashi Rumaisa tayi tana turo baki tace bakomai fa Mama Yaya ne yace dole sai na bashi hadda gobe ko mu b'ata. Murmushi Mama tayi tana fad'in ai gara ku b'ata tunda kina son wasa da karatu. Bayan ta kwantar da Abdallah taje tayi shirin kwanciya ranta a dagule, saman gadonta ta kwanta sai tsaki takeyi, wayarta ta jawo domin ta kunna karatu ko zataji sauki sai taci karo da sakon Ra'eez. Da sauri ta bud'e, tana fara karantawa tayi saurin tashi zaune tana mutstsike ido, bata san lokacin da murmushi ya bayyana a fuskarta ba, filo ta jawo tana sakin dariya. Ta karanta sakon daya turo yafi akirga. Kwanciya tayi tana fad'in ashe ma yana sona shine yake ja mani aji, nima bazan maida amsar ba sai gobe nima sai naja aji. Kwanciya tayi da anjima sai ta jawo wayar ta sake karanta abinda ya rubuta. Can dai ta kasa daurewa, tashi tayi domin ta maida masa amsa... *Yayana nagode da soyayyarka agare ni, insha Allahu zaka sameni amatsayin Uwa tagari a wajen 'Ya'yan mu, amma dan Allah kadena mani wasa da wata mace zuciyata bazata iya d'auka ba. Kayi bacci lafiya nagode.* Tana turawa tayi saurin kashe wayar gaba d'aya tana murmushi. *** Ra'eez daya kasa bacci yana rokon Allah yasa ta amince dashi, k'arar wayarsa yaji alamun shigowar sako, jiki na rawa ya jawota yana fatan Allah yasa yayi farin gani. Ur's. Nabeelert Lady🖋 [3/10, 8:39 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.* 2⃣5⃣ Ra'eez besan lokacin daya tashi zaune ba, filo ya jawo ya rungume yana sakin murmushi, ya dad'e yana jiran irin wannan ranar domin shima yashiga sahun masoya amma sai yau Allah yasa zai shiga. Komawa yayi ya kwanta yana kok'arin kiran Rumaisa, sai dai kiran farko yaji wayar akashe. Murmushi yayi yana fad'in sarkin kunya, dama nasan bazan sameki ba. Lumshe ido yayi yana tunanin ya kamata ya sama mata gurbin shiga makaranta kafin ayi bikinsu. Saurin girgiza kai yayi yana fad'in bana son ta fara karatu garin nan saboda ba lallai zaman mu ya d'ore anan ba, daga ranar da aka gano gaskiya dole zasu koma kano, gara ma ya bari bayan anyi biki a hankali sai tayi karatun ta. Cike da gamsuwa ya jinjina kai. Shiru yayi yana tunanin Raheena. Murmushi yayi yana fad'in kiyi hakuri Mahaifinki ne ya jaza maki, amma dole su d'and'ana illar yaudara da zalunci, koba komai nima zakici moriyata. Haka ya kwanta cike da tunanin masoyiyarsa har bacci ya d'aukesa. *** *** Kiran wayar Raheena ne ya tashesa a bacci da ya makara, saurin tashi yayi ya d'auka. Murmushi Raheena tayi tana fad'in lokacin sallah yayi. Ra'eez yace amma nagode maki, badan ke ba da na makara, amma nasan kema bakya tashi sallar asuba ya akayi har kika tashe ni? Raheena tace wallahi ada ne bana tashi sai da safe nake sallah, amma tun daga ranar da kace kaji dad'i dana tasheka kuma kana son mai sallah da wuri yasa nake tashi, saboda kai har alarm nasa wallahi. Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in Allah yasa ki dawwama a haka, kuma ina so ki rik'a yin komai saboda Allah ba danni ba, hakan zai sa abun ya bi maki jiki ko dani ko bani kicigaba. Raheena tace insha Allahu. Ra'eez yace nagode bara naje masallaci. Raheena tace ka sani cikin addu'ar ka. Murmushi yayi yana fad'in insha Allah. Sauka yayi ya nufi band'aki yana murmushi yayin da k'asan zuciyarsa ya fara tausayin Raheena danshi mutum ne mai tausayi. *** Bayan ya kammala shirinsa na fita aiki ya tsaya yana duba wayarsa, yasan bayan ya fito wanka Jabeer ya kirasa, bayan sun gama waya ya ajeta saman gado yacigaba da shiri. Kugu ya rik'e yana mamakin ina ta shige? K'aranta ya faraji alamun ana kiransa, dubawa ya farayi har ya gano daga k'ark'ashin gado k'aran yake fitowa. Murmushi yayi yana fad'in ashe kina nan. Hannu yasa ta k'asan gadon sai dai tayi ciki hakan yasa ya tashi ya fara d'aga katifar, sai da yasa k'afarsa ya tokare katifar kafin ya duk'a ya d'auko wayar. Bayan ya d'auko wayar har ya d'ago ya koma yana duba jikin gadon ganin kamar wata durowa a jiki, mamaki ne ya kamashi yana tunanin dama anama gado durowa? Murmushi yayi yana fad'in mutanan Da akwai dabara. Hannu ya kai zai bud'e wayarsa tayi k'ara, yana dubawa yaga Mama ce, saurin sakin katifar yayi ya tsinke kiran kafin ya kirata. Tana d'agawa ta fara tambayarsa lafiya be fito ba har yanzu? Ra'eez yace na shirya wayata na tsaya nema amma gani nan. Kashe wayar tayi. Juyawa yayi yana kallon gadon kafin ya d'auki jakarsa da mukulli yayi waje yana tunanin abinda yake cikin durowar. Yana tuki ya kira Alhaji Mansur, bayan sun gama gaisawa yake tambayarsa jikin Ummunsa? Ra'eez yace kamar koda yaushe Abba, kwana biyu banje ba saboda wani aiki da nakeyi amma yau daga ofis zan je na ganta. Alhaji Mansur yace baka kyauta ba gaskiya, kasan dai yanda take jin dad'i idan kaje shine zaka kwana biyu ba tare daka lek'a ba. Ra'eez yace ayi hakuri Abbah zanje yau. Alhaji Mansur yace shikenan, yasu Mamar taku da Rumaisa fa? Ra'eez yace duk suna lafiya ina hanyar zuwa gidan ma. Alhaji Mansur yace ina Kawun ka fa? Ra'eez yace duk yau zan lek'a insha Allahu. Alhaji Mansur yace idan kaje wajensa ka had'amu ina so mugaisa, kaima idan ka samu lokaci akwai maganar da zamuyi, ina fatan kana kula a wajen aikin ka ko? Ra'eez yace sosai ma Abbah. Alhaji Mansur yace haka ake so, da fatan kana kula da yanayin Alkalin ku? Ra'eez yace Abbah shekaran jiya har gidansa ya gayyace ni cin abinci wai yana sona, ashe d'iyarsa yake so ya had'amu, sai da mukaje gidan na samu ashe tsohon gidan Abbu ne. Alhaji Mansur yace ka kula fa, duk yanda zai jaka jikinsa kada ka saki jiki dashi har ya gano wani abu daga gareka, bana so kowa yasan kana da alak'a da Mahaifinka, nasan waye Brr. Barau, yana da matuk'ar wayau, dan haka ka kula sosai. Ra'eez yace insha Allahu. Alhaji Mansur yace ina fatan ba son yarinyar tasa kake ba ko? Zaro ido Ra'eez yayi yana fad'in haba dai Abbah, ai ko d'aura mani ita akayi na kwanceta na gudu. Murmushi Alhaji Mansur yayi yana fad'in ai dole na tambaya kasan ita zuciya ba ruwanta da kiyayyar wasu. Ra'eez yace babu komai a zuciyata Abbah, ni yanzu ma ta Rumaisa nake dan jiya na fad'a mata abinda yake raina. Murmushi Alhaji Mansur yayi yana fad'in ja'iri, ai na d'auka zaka cigaba da b'oyewa ne, ko jiya Ummanku tamun maganar nace ta barka idan ka gaji da ajiyar abunka zaka furta ne, ashema har ka shigar da kan ka. Shafa kai Ra'eez yayi yana fad'in wallahi kuwa Abbah. Alhaji Mansur yace haka akeso, Allah ya tabbatar da alkhairi. Kasa amsawa Ra'eez yayi yana fad'in ina Labiba? Alhaji Mansur yace jiya ma tazo gida da yaranta. Ra'eez yace zan kirata. Alhaji Mansur yace bara na barka gashi ma ka kusa makara, ka gaishe dasu Maman ta ku. Ra'eez yace nagode agaishe da Ummah. **** Koda yaje gidan su Rumaisa bai isketa a tsakar gida ba, tana jinsa tayi saurin shiga band'aki. Bayan sun gaisa da Mama ta kawo masa abinci. Yana ci suna fira yana fad'a mata Abbah yana gaisheta. Mama tace Allah sarki ko jiya munyi waya da Umman ka ai. Ra'eez yace anjima idan na taso zan biya wajen Kawu da Ummu. Mama tace wallahi nima ina son naje na ganshi, Abdallah yana yawan tambayarsa. Ra'eez yace kushirya idan na dawo sai na biyo mutafi gaba d'aya, amma sai dai Abdallah ya hakura da islamiya tunda dawuri zan dawo. Mama tace shikenan. Rumaisa ta kwalama kira amma taji shiru. Tsaki tayi tana fad'in bansan me kike a band'aki ba idan ki kashiga kamar wacce zata canza fata. Ra'eez yace Mama kibarta tayi wankanta atsanake. Rik'e baki Mama tayi tana fad'in goya mata baya zakayi? Dama saboda kai nake kiranta tazo ku gaisa. Tashi yayi yana murmushi yace zamu gaisa a waya ai, idan Abdallah ya dawo agaishe mani dashi sai na dawo. Mama tace to Allah ya bada sa'a ya kare ka daga sharrin mahassada. Ra'eez yace amin. Kud'i ya aje mata yayi waje da sauri dan yasan halinta. Tana tambayarsa abinda zaici amma yayi waje. Madu ne ya taso yana fad'in Ra'eez har ka fito? Ra'eez yace nafito Baba Madu ya kasuwar? Madu yace gatanan Alhamdulillahi sai godiya. Kud'i Ra'eez ya ciro ya mik'a masa yana fad'in ga wannan, anjima idan na dawo ka shirya zamu kaima Kawu da Ummu ziyara. Madu yace gaskiya daka kyauta, angode sosai Allah yayi albarka sai ka dawo. Ra'eez yace amin na tafi. Yana shiga mota ya latso wayar Rumaisa, bugu biyu ta d'auka bakinta d'auke da sallama. Lumshe ido yayi yana amsawa tare da fad'in kin gama gudun? Murmushi tayi mai sauti ta fara gaishe shi. Ra'eez yace bana cin mike, wallahi idan kina mani rowar ganin ki zakisa na rik'a kula wasu. Da sauri Rumaisa tace kayi hak'uri to. Ra'eez yace bazanyi ba, aikinsan bazan iya aikin kirki ba idan ban ganki ba ko. Saurin tashi tayi tayo waje tana bashi hak'uri, kamar ance ya d'aga idonshi sai ganinta yayi a k'ofar gida ta langwab'ar da kai tana kallonshi hannunta rik'e da waya tana murmushi. Da sauri ya kashe wayar ya fito. Yana zuwa tayi saurin duk'ar da kanta k'asa tana sake gaisheshi. Tsura mata ido yayi yana fad'in ashe dai ana tsoron kishiya? Turo baki tayi tana fad'in ni bana tsoro. Dariya yayi yana fad'in gashi daga fad'in magana kin fito, ai dama nasan ba wani abinda kikeyi aband'aki saboda kada Mama ta kira ki kawo mani abinci yasa kika shige band'aki, to daga yau bazan sake cin abinci ba matuk'ar ba kece kika kawo mani ba. Kallonshi tayi tana fad'in shikenan bazan sake ba. Murmushi yayi yana fad'in yauwa Pretty na, ina fatan dai jiya kinyi bacci mai dad'i? Kai ta d'aga a hankali tace sosai ma. Ajiyar zuciya ya saki yana fad'in bara na tafi aiki na kusa makara, idan na dawo zamuje wajen Kawu da Ummu. Murmushi ta saki tana fad'in sai ka dawo ka kular.... Shiru tayi tana sunne kai. Murmushi yayi mai sauti yana fad'in zan kular maki da kaina sosai. Da sauri tashige ciki tana murmushi. Girgiza kai yayi ya juya zuwa mota ya tafi. Da Mama taci karo a tsakar gida. Saurin duk'ar da kai tayi kamar marar gaskiya. Murmushi Mama tayi tana fad'in zaku k'araci gulmar ku dai. Turo baki Rumaisa tayi tace kai Mama me nayi kuma? Mama tace ina zan sani, idan tayi wari dai naji. Dariya Rumaisa tayi tashige ciki. Murmushi Mama tayi tana fad'in Allah ka tabbatar da alkhairi. Idanuwanta ne suka ciko da kwalla tana fad'in Allah ka kawo mana k'arshen wannan masifa da muke ciki, Allah ka fiddo bawanka haka nan, ka bama Hajiya lafiya kuma ka tona asirin munafukai. **** **** Zaune suke a ofis suna ta aiki Ra'eez yana kok'arin had'a aikin da Alhaji Barau ya bashi akan wani case wanda za'ayi da Yaron abokin kasuwancinsu, Alhaji Marusa shine yayi mashi jagora domin yasan matuk'ar akazo kotun su case d'in zai mutu cikin ruwan sanyi. Bayan da aka kawo ma Alhaji Barau sai yace Ra'eez zai bamawa. Alhaji Marusa yace abama Brr. Bajinta domin shine namu, shine yasan yanda muke tafiyar da komai, bana so azo a samu matsala. Murmushi Alhaji Barau yayi yana fad'in ina da dalilin da yasa na bama Ra'eez, domin idan muka bama Brr. Bajinta aikin su wad'an can zasu iya d'aukar Ra'eez ya tsaya masu, na tsora ta da yaron domin yana da wata baiwa, koni da nayi gogayya alokacin ina Barrister bazan nuna masa komai ba, kaga dan ya goga da Brr. Bajinta tuni zai kadashi, wannan dalilin ne yasa na bashi case d'in, domin zamu bashi shedar bogi kuma kaga dole da ita zaiyi amfani, nasan zasu iya d'aukar Brr. Bajinta domin sun san yana kada mutane, kaga shikuma sai yaki zaluko kwararen hujjoji, kaga kuma kotu da kwararen shedu take aiki, shikenan case ya mutu. Tafi Alhaji Marusa yayi yana fad'in Alhaji Barau har yanzu kana nan yanda na sanka, shiyasa akoda yaushe hankalina yake kwance, domin nasan kowace katob'ara nayi ina da mai tsaya mani. Alhaji Barau yace ai baku da matsala, wani abun ma sai ya zama surikina. Dariya sukasa, Alhaji Marusa yace amma duk da haka Brr. Bajinta ya tarbi wad'an da suka kawo k'arar yace zai tsaya masu kada suje su bama wani lauyan. Alhaji Barau yace kaima ka kawo shawara, shikenan hakan za'ayi. Dariya suka sake sawa da haka suka bar zancen akan a bama Ra'eez case d'in, sai gashi kuma an bashi. Shiru Ra'eez yayi yana kallon takardun da masinjan Alhaji Barau ya kawo masa. Sake dubasu yayi yana mamakin irin wannan abu, gashi dai an bashi takardar case, ina ruwanshi da aiko masa da shedu kuma? Ai wannan aikinsa ne yaje ya nemo komai da kanshi, kuma yana so ma ya gana da yaron da zai tsaya mawa. Tsaki yayi yana fad'in bazan biye tasu ba, dole na gano lauyen da zai tsaya ma d'ayan b'angaren domin nasan irin shirin da zanyi, tunda yaga haka ajikinsa yasan abinda aka bashi babu gaskiya aciki, shi kuma yayi alk'awarin bazaiyi aikin rashin gaskiya ba. Jabeer ne ya dafashi yana fad'in Ra'eez lafiya kuwa? Ajiyar zuciya yayi yana fad'in wallahi nashiga tunanin wani rainin hankali da akeso amun ne. Jabeer yace akan mefa? Takardar Ra'eez ya mik'a masa yana fad'in wani k'arfin hali nake gani yanzu, sai kace wanda yake aikin gata, ace ina lauya amma sheduma sai an nemo mani kawai zuwa zanyi na gabatar dasu. Dariya Jabeer yayi yana fad'in da sannu dai zaka fara gano halin mutumin. Tsaki Ra'eez yayi yana fad'in ko kasan wanda zamu kara dashi? Jabeer yace yawuce Brr. Bajinta. Saurin kallonshi Ra'eez yayi cike da alamun tambaya. Jabeer yace nasan dole hakan ne zata kasance, domin farkon zuwana da nayi wani case nayi nasara anyi mani irin haka, sai dai alokacin ban gama gogewa da kowa ba sai nayi yanda suka ce, kuma nida Brr. Bajinta muka kara, abun ya bani mamaki ganin yanda yake ma wanda yake karewa wata irin tambaya, sai ka kad'auka shine yake kare wanda nake karewa, gashi dai abinciken da suka bani nasan akwai alamun tambaya, bangama shan mamaki ba sai da shari'ar tazo k'arshe, ina ji ina gani aka yanke ma wanda Brr. Bajinta yake karewa hukunci, mutane sunyi mamakin yanda sabon zuwa kamata ya iya kada kwararren lauya, kuma a shari'ar da mukayi ya fini baki amma duk da haka nine nayi nasara. Jinjina kai Ra'eez yayi yana sakin murmushi ta gefen baki, kallon Jabeer yayi yana had'a takardu yace ka barni dasu, zanyi wasa dasu, za'aga yanda ake shari'a a wajena domin bazan bari su sani aikata kuskure irin nasu ba. Jabeer yace sai kayi da gaske kam. Ra'eez yace dole inaso na had'u da yaron domin bazan shiga shari'a da abinda suka bani ba. Jabeer yace kayi dai-dai, tashi muje sallah. *** *** Bayan sun tashi daga aiki kowa ya fito ya nufi motarshi, wani dattijo suka gani zaune a gefe ya buga tagumi ya lula tunani, har sun wuceshi sun kai wajen motarsu sukaji alamun motsi. Dattijon suka gani yayo wajensu da d'an sassarfa. Tsayawa sukayi suna kallonshi. Bayan ya k'araso ya matsa kusa da Ra'eez fuskarsa d'auke da damuwa. Ra'eez ne ya fara gaisheshi yana fad'in lafiya dai Baba? Wanda aka kira da Baba yace ba lafiya ba Yaro. Gyara tsayuwa Ra'eez yayi yana fad'in mecece damuwar ka Baba? Hannu Dattijon yasa ya goge kwallar data zubo masa yana fad'in nazo wajen nan dasa ran ganinka domin nasan zaka iya kwato mana hakkin mu, tun ranar dana fara kallon shari'ar ka da akayi ta farko na yaba da kwazon ka, duk da ban tab'a tunanin zan samu kaina a kotu na kawo k'ara ba amma tun a wancan lokacin nake aiyana koda shari'a zata had'oni a kotu tabbas kaine wanda zan nema, sai gashi lokaci yazo shari'a ta kawoni kotun ku, an zalunceni anci mutuncin Auta ta, nazo neman lauya sai na samu ance kaine wanda zai kare Yaron daya lalata rayuwar 'Yata, abun ya bani mamaki alokacin da Brr. Bajinta ya tarbeni kamar dama ni yake jira, kuma anan take yace shine zai tsaya mani, tunda ya fad'i haka jikina ya kasa amincewa dashi, domin nasan shi lauyan manyan mutane ne, narasa inda zansa raina hakan yasa nace dole sai na ganka naji da gaske kaine zaka tsayama wannan Yaron ko kuwa. Ajiyar zuciya Ra'eez yayi cike da tausayin wannan Dattijo, tabbas su Brr. Bajinta sun shirya wani abu, tun daga jin bayanin Baba yasan akwai alamun tambaya. Kallon Dattijon yayi yana fad'in Baba kayi hak'uri, insha Allahu kaine zakayi nasara, tabbas nine wanda 'Yallab'ai ya bama damar kare wanda kake k'ara, amma ina mai tabbatar maka kaine zakayi nasara. Dattijo yace ta yaya Yaro? Nasan irin basirar ka baza'a iya kada ka ba, yanzu kam inaji na hak'ura da wannan shari'ar, cuta ce an cuci Auta ta, zan koma gida muyi hakuri da K'addarar da Allah ya aiko mana, shi kuma mun barsa da Allah, zai biyamu alokacin da beda kowa. Jabeer ne yayi saurin fad'in Baba kada kace haka, tunda abokina yace kaine zakayi nasara to kasa aranka zakayi d'in, bazamu bari a danne maku hakkin ku ba, ka yarda damu. Jinjina kai Dattijon yayi yana fad'in shikenan, na amince da ku, Allah ya bamu sa'a. Ra'eez yace amin Baba, yanzu kashiga mota ina so naje naga Autar taka dan bana so kowa ya gammu tare, kuma kada ka fad'ama kowa munyi magana da kai kawai kayi abinda Brr. Bajinta yace maka. Dattijo yace nagode sosai. Mota suka shiga Ra'eez yana fad'in na makara ma akwai inda zamuje, amma daga can sai na d'auko su Mama mu wuce kawai. Shima Jabeer yashiga tashi motar ya bisu abaya. Ur's. Nabeelert Lady🖋*Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.* 2⃣6⃣ Idanuwan Ra'eez ne suka ciko da kwalla tun daga lokacin da yayi ido biyu da Yarinyar Baba wacce bazata wuce shekara 16 ba amma an lalata mata rayuwa. Hannu yasa ya goge idonshi yana kallon Mahaifiyar Yarinyar yana fad'in Mama kuyi hakuri, insha Allahu zakuyi nasara, duk da ba nine zan tsaya maku ba kusa aranku ku nake ma aiki. Goge idonta tayi tana fad'in na yarda da abinda kace, mungode da wannan taimako. Ra'eez yace bakomai, ya sunanta ne? *Habiba* sunanta, ita kad'ai gare mu mace dama su ukku ne, biyu maza sai ita, babban cikinsu ya rasu yanzu su biyu ne, muna murnar ta kammala babbar makaranta Malan yana cewa za'a sama mata wata makarantar tunda burinta ne ta karanci aikin lafiya sai gashi an lalata mata rayuwa, duk da bamu da k'arfi mun yanke shawarar tsaya mata tayi ilimi domin ta cika burinta, hatta da Yayanda iya karsa babbar makarantar sakandire, ganin bamu da hali yasa bece zai wuce ba haka ya fara sana'a, sai gashi yanzu Allah ya d'aukakashi, ganin haka yace dole Habiba tayi karatu zai tsaya mata, amma yanzu an cutar da ita. Ra'eez yace insha Allahu sai burinta ya cika. Habiba ina so kisa jarumta aranki, kada kiyi kallon an ruguza maki rayuwa ki hakura da karatun ki, da izinin Allah sai kin d'aukaka, kisa aranki zakiyi karatu, domin shi kad'ai zakiyi kijawoma kanki daraja a wajen kowa, idan kika zama wata babu wanda zaifi karfin ki, amma idan kika sare ma rayuwa haka zakiyi ta cikin kunci, saboda ko aure zakiyi babu wanda zai d'auke ki da daraja, amma idan da ilimin ki zakiga yanda za'a daraja ki. Kai Habiba ta jinjina tana share hawayen idonta. Jabeer yace duk yanda za'a maki tambaya a kotu kada ki bari a saki fad'in abinda ba shikenan ba, ki tsaya akan gaskiyar ki kuma kada kiji tsoro, koda Brr. Bajinta ya zo yace ki fad'i abinda zai tsara maki kada kice bazaki amince ba, ki bari sai anje kotu sai ki canza abinda ya fad'a ki fad'i abinda kika sani. Baba yace mungode sosai Allah ya saka maku da alkhairi. Gaba d'aya sukace amin. Amsar lambar wayar Baba Ra'eez yayi yasa masa tashi yana fad'in zamu rik'a magana a waya kafin litinin ashiga kotun. Baba yace nagode sosai. Tashi sukayi Baba ya rakosu sai godiya yake masu. Bayan ya koma gida Ra'eez yace wallahi duniya babu gaskiya, ka duba fa acikin shedun da Alhaji ya bani hada rahoton likitan daya duba Habiba, saboda shima d'an rashawa ne har ya canza abinda ya gani, amma ka barni dashi dole zai zo kotu zamuji komai, nima zan caza masa kai. Jabeer yace ai duniya babu gaskiya, da likita, da 'Yan sanda da Lauyoyi dama ana samun azzalumai, domin kowa kud'i yake so, shiyasa duk inda suke kansu a had'e yake. Ra'eez yace Allah ya kyauta, bara na wuce sai gobe ko. Jabeer yace gobe juma'a bazan fito da wuri ba. Ra'eez yace kaji d'an gayu, dan Allah kazo da wuri bazanji dad'i ba idan bakanan. Dariya Jabeer yayi yana fad'in shikenan Allah ya kaimu. Wayar Ra'eez ce tayi k'ara, yana dubawa yaga Raheena ce, d'agawa yayi. Sallamarta yaji tana mai kwantar da murya, yana amsawa ta fara gaisheshi. Murmushi yayi ya amsa aranshi yana fad'in lallai su Raheena an fara canzawa. Daga can Raheena tace kira nayi naji yanda ka tashi daga aiki. Ra'eez yace lafiya lau gani zan tafi gida ma. 'Dan zaro ido tayi tana fad'in biyar fa ta kusa amma baka koma gida ba? Ra'eez yace naje wani waje ne yanzu zan tafi. Murmushi tayi tana fad'in bara na barka idan kaje mayi waya, ina fatan dai kaci abinci? Ra'eez yace idan naje zanci dai. Raheena tace shikenan kaci dani, amma yaushe zaka zo? Tab'e baki yayi yana fad'in wani aiki zanyi kuma yana buk'atar natsuwa, bazan samu hutu ba har sai na kammalashi. Raheena tace shikenan amma dan Allah ka rik'a kirana hakan zai mun dad'i naga kiranka awayata. Ra'eez yace shikenan. Sallama sukayi ya kashe wayar. Har zaisa aljihu wayar ta sake k'ara. Murmushi ya saki yana mai tsinke kiran domin ya kira. Sakin baki Jabeer yayi yana kallonshi. Pretty na kinga na dad'e ko? Murmushi tayi tana fad'in damuwata rashin cin abincin ka gashi yamma tayi. Ra'eez yace ni kuma damuwata na wuni banji muryaki ba kuma banga fuskarki ba, amma gani nan yanzu zanzo amun kwalliya mai kyau, da nazo na ganki naci abinci sai mu tafi. Murmushi tayi tana fad'in sai kazo, kayi tuk'i a hankali. Ra'eez yace angama Pretty na, ki kula da kanki. Dariya Jabeer yasa yana fad'in dama haka kake? Ra'eez yace namafi haka, ka zauna nan ayi babu kai, wallahi abokina soyayya dad'i gareta, gaskiya an barka abaya. Jabeer yace abinda bangane ba shine, yaushe ka fara soyayyar? Ra'eez yace lokacin kana bacci. Dariya Jabeer yasa yana fad'in Allah da gaske nake, nasan dai kace mun kana son Rumaisa kuma nasan baka fad'a mata ba, amma kuma gashi kuna waya kamar wad'an da suka dad'e suna soyayya. Ra'eez yace kasan duk soyayyar da aka tara, aka jik'ata ta tsimu ba'a sanin lokacin da ake fara ta, idan kuma aka fara ba'a mata bakunta, to haka tamu take, ajiya muka bayyanata gashi kuma har tabi mana jiki. Jinjina kai Jabeer yayi yana fad'in lallai kam, soyayya tayi kam, sai nace Allah ya bada sa'a, ga Raheena kuma a gefe. Ra'eez yace ba ruwanka kasa ido kawai kayi kallo. Jabeer yace hada jiki ma duk zansa, ina jiran ranar da zansha kallon da kyau. Ra'eez yace E naji. Murmushi Jabeer yayi yana fad'in soyayya ko wahala. Ra'eez yace ga wanda bai samu ba ko. Tab'e baki Jabeer yayi yana fad'in kaga Malan sai da safe. Ra'eez yace ai gara katafi ka tsareni da surutu Pretty na jirana. Murmushi Jabeer yayi yana fad'in agaishe da Pretty to. Ra'eez yace wannan sunan ya fita abakin ka wallahi. Baki Jabeer ya kama yana fad'in yanzu kuwa. Dariya sukasa sukayi sallama kowa ya nufi gida. **** Ganin yanda Rumaisa tayi kwalliya sai gyare-gyare takeyi yasa Mama ta koma d'aki tana mata dariya dan tasan Ra'eez yakusa dawowa. Abincinsa ta shirya a falo ta koma d'aki wajen Mama. Zama tayi tana satar kallon Mamar. Murmushi Mama tayi tacigaba da linke kaya. Kallonta Rumaisa tayi tana fad'in wai Mama naji kinyi shiru sai murmushi kikeyi. Mama tace kuka kike son inyi? Turo baki Rumaisa tayi tana fad'in amma ai ba haka kikeyi ba. Mama tace ya kike so nayi bayan kina ta shiri da alama bak'o zakiyi ban sani ba. Rufe fuska Rumaisa tayi tana murmushi tace ba wani bakon da zanyi kawai fa abincin Yaya ne na aje masa yace sauri yakeyi kada mu makara. Mama tace naga alama ai, wannan kwalliyar ta zuwa unguwar ce ko? Tashi Rumaisa tayi tana kwalama Abdallah kira. Dariya Mama tayi tana fad'in kwayi ku gama. Da gudu Abdallah ya shigo hannunsa d'auke da leda yana fad'in Aunty Yaya ya dawo kinga ya siyo mun kayan dad'i. Amshe ledar tayi tana fad'in kawo insha. Abdallah yace kai Aunty yace fa taki tana mota zai baki. Rumaisa tace ya akayi ka sani? Abdallah yace daya bani nace masa ina taki shine yace ai taki ta dabance tana mota. Murmushi Rumaisa tayi ta d'auki alewa d'aya. Muryar Ra'eez taji yana fad'in banda kwad'ai dai. Murmushi tayi tashige falo. Da sallama ya k'arasa shigowa. Mama ce ta fito tana amsawa. Har k'asa ya duk'a yana gaisheta. Amsawa tayi tana masa sannu da aiki. Ra'eez yace kunjini shiru wallahi wani aiki aka bani ranar litinin ma zamu shiga kotu wata shari'a. Mama tace aifa shari'a bata k'arewa, to Allah ya tabbatar da alkhairi kuma ya baka sa'a. Ra'eez yace amin. Hannun Abdallah taja tana fad'in kashiga kaci abincin mutafi ko. Sosa kai yayi ya kasa tashi. Murmushi tayi ta wuce d'aki, cike da kunya ya shiga falo. Rumaisa tana jin Mama ta shiga d'aki ta fito da sauri. Tsayawa tayi a bakin k'ofa tana wasa da hannunta. Ido ya tsura mata yana murmushi, takowa tayi tashigo bakinta d'auke da sallama. Amsawa yayi yana fad'in bazaki dena wannan kunyar ba ko? Saurin zama tayi tana masa sannu da zuwa. Ra'eez yace yunwa nakeji fa. Saurin bud'e abinci tayi ta fara zuba masa. Kallonta yake yana jin sanyi, sosai tayi masa kyau, tasa bak'ar jallabiya ta yane kanta da pink d'in mayafi fuskarta tasha kwalliya mai sauki. Mik'a masa abincin tayi tana shirin tashi. Kallonta yayi yana fad'in ina zaki? Kanta ak'asa tace abinci zan barka kaci. Murmushi yayi yana fad'in aiko bazanci ba. Zama tayi tana murmushi tace to kaci. Cokali ya d'auka yana fad'in damma bance ki bani ba. Saurin cusa kanta tayi a cinyoyinta tana murmushi. Murmushi shima yayi ya fara cin abinci yana mata fira. Bayan ya gama ta kwashe kayan suka fito. Rufe gidan sukayi Madu na jiransu. Shida Ra'eez ne a gaba su kuma suka shiga baya. Suna tafiya Ra'eez yace wai Mama ina Aunty Hassana kullum ina so na tambayeki ita? Mama tace Allah sarki Sister Hassana sarkin kirki, ai sun dad'e da tashi, tunda aka canzama mijinta wajen aiki itama ta nemi canjin wajen aikinta suka tafi suna Abuja. Ra'eez yace lallai kunyi nisa sai dai waya. Mama tace tana kirana muna gaisawa kuwa ai tana da kirki har cewa tayi zata zo ta d'auki Rumaisa taje mata hutu can. A zabure Ra'eez yace ba dai Abuja ba wallahi, waye zai kaita haka kawai mayun garin nan su sa mata ido. Dariyar da Madu yayi ce ta ankarar dashi abinda yayi. Hannu yasa yana sosa kai. Rumaisa kuwa duk'ewa tayi tana murmushi. Mama tace ni kuwa har na amince mata k'arshen wata zata zo su tafi. Kicin-kicin yayi da fuska yana kallon Rumaisa ta madubin motar, be sake magana ba kawai yayi shiru. Murmushi Mama tayi tana kallonshi. Madu yace ai Halima baza'ayi haka ba, Ra'eez shine babba kuma shine namiji, dole sai ya amince zata je ko Ra'eez? Fuska a d'aure yace bazan amince ba ma, dan hadda zata fara babu inda zataje hutu. Dariya Mama tayi, yanda yayi maganar kasan haushi ne yake cinsa. Madu yace angama Alhaji Ra'eez nima ban amince ba. Mama tace ai shikenan tunda kun fini k'arfi. Murmushi Ra'eez yayi yana shafa gefen fuskarshi. Wajen Kawu suka fara zuwa dan kada magriba tayi. Zaune suke a cikin d'akin da ake ganawa da masu laifi. Bayan sun gama gaisawa da ma'aikacin wajen wanda dama sun saba da Ra'eez, shine ya aika akira Malan Sani. Kallon Ra'eez yayi yana fad'in ya aiki kuma? Ra'eez yace aiki muntashi sai gobe kuma. Yace to Allah ya taimaka, bara na baku waje ku gaisa. Godiya Ra'eez yayi masa ya fita. Tunda Malan Sani ya tunkaro wajen idanuwan Mama suka cika da kwallah, da gudu Abdallah yaje ya taroshi, duk ya tsufa saboda wahala, sai dai har yanzu jikinsa akwai jarumta, dan yasa dakiya aranshi hakan yasa zuciyarsa bata raunana ba bare ta shafi lafiyarsa. Yana zuwa Ra'eez ya tashi yana gyara masa wajen da zai zauna. Zama yayi murmushi d'auke a fuskarshi. Hannu ya mik'ama Madu suka gaisa yana tambayarsa rayuwa. Har k'asa Ra'eez da Rumaisa suka duk'a suka gaishe da Malan Sani. Kamosu yayi yana murmushi yace lafiya lau ina fatan ana kula da karatu Rumaisa? Kai ta jinjina tana b'oye hawayen da suka taho mata. Kallon Mama yayi ganin ta kasa magana sai share hawaye. Wani abu ya had'iye yana fad'in Halima kuka dai, shiyasa fa bana so kina zuwa domin kina raunana mani zuciya, bayan kin tafi kuma ina jinyar zuciyata, ina tsoron kada hakan ya fara tab'a lafiyata, idan bazaki rik'a dakewa ba gara ki zauna agida sai murik'a gaisawa ta waya. Hannu tasa ta goge idonta tana fad'in na dena, gaishesa ta farayi. Murmushi yayi yana fad'in lafiya lau ya gidan? Bazan tambayi komai ba domin nasan ina da masu kula da ku, sannan idanuwana sun ga abinda nake son gani, kuma naji dad'i a zuciyata. Ra'eez yace Kawu Abbah yace idan nazo zaku gaisa bara na kirashi. Malan Sani yace Allah sarki ya iyalan nashi? Ra'eez yace lafiya lau. Waya ya d'auka ya kira Abbah. Bayan sun gaisa ya mik'ama Malan Sani. Gaisawa sukayi yana tambayarsa rayuwa. Malan Sani yace lafiya lau Alhaji, ai rayuwar gidan yari tabi jikina, nasa araina nan d'in Muhallina ne, domin ina son naga ranar da Allah zai kawo mani k'arshen zama acikinta, ina son nayi wata rayuwar hakan yasa nasa juriya araina dan gudun damuwa ta kassarani. Alhaji Mansur yace wannan haka yake, kuma naji dad'i sosai, dama abinda nake son na fad'a maka kenan, domin acikin satin nan bani da tunani sai na yanda zamu maido da shari'ar ku baya, domin kwanakin baya na had'u da tsohon ma'aikacin Alhaji Abubakar, dan yanzu a Kano yake aiki shima ya zama babba, Allah ne yasa zamu had'u har labari ya kawo muka zo maganar Alhaji Maiwada, ya tabbatar mani a yanzu baya tsoron kowa, kuma duk lokacin da muke buk'atar taimakonsa ashirye yake, abokinsa da aka canza ma wajen aiki Moses shi ya mutu a had'arin mota, amma yace shi zai zo ya bada sheda. Jinjina kai Malan Sani yayi yana fad'in wallahi nima kwanan nan mafarkin da nake yawanyi kenan, wai an sake shari'a kuma munyi nasara, ina nan ina fad'ama Allah nasan kuma zai shige mana gaba, ko ban fita a nan ba matuk'ar asirin azzalumancen zai tonu burina ya gama cika. Alhaji Mansur yace zaka fita, matuk'ar asirin su ya tonu dole a wanke ka, dan haka kacigaba da daurewa komai zai zo k'arshe. Malan Sani yace insha Allah. Sallama sukayi ya kashe wayar. Sai da yaci abincin da suka kawo masa suna ta fira, bayan ya gama Ra'eez ya bashi ledar da suka kawo masa mai d'auke da kayan bukata, kud'i ya bashi yana fad'in zamuje wajen Ummu. Godiya Malan Sani yayi masa yana fad'in agaisheta. Tashi sukayi kowa jikinsa a sanyaye, duk dauriya irin ta Malan Sani sai da kwalla ta cika masa ido, azuwansu sai yaji damuwarsa ta yaye, yanaji kamar a gida suke zaune, amma yanzu da zasu tafi sai yaji duk babu dad'i. Mama kuwa saurin fita tayi tana kuka, bayanta Rumaisa tabi itama kukan takeyi, kama Abdallah Madu yayi sukayi hanyar fita shima jikinsa a sanyaye. Kallon Malan Sani Abdallah yayi yana fad'in Baba sai yaushe zakazo gidan mu? Saurin juya baya Malan Sani yayi hawayen da yake b'oyewa suka zubo masa, yana jin muryar Abdallah amma ya kasa magana, ganin haka yasa Madu yayi saurin jansa sukayi waje. Hannu Ra'eez yasa ya goge idonshi kafin ya dafa Malan Sani yana fad'in Kawu zamu tafi sai mun sake dawowa. Ajiyar zuciya ya saki yana fad'in Ra'eez kada ka sake kawo su, idan zaka zo kazo kai kad'ai dan Allah. Jinjina kai Ra'eez yayi yana fad'in insha Allah. Tare suka fito suka k'arasa wajen ma'aikacin. Kallonsu yayi cike da tausayi yana fad'in zaku koma? Ra'eez yace magriba ta kusa, mungode sosai. Hannu yasa ya ciro kud'i ya mik'a masa yana sake masa godiya. Amsa yayi yana fad'i ai babu komai nima nagode. Sallama yayi masu Malan Sani ya d'auki kayanshi ko juyowa beyi ba yayi gaba yana kuka. A mota gaba d'ayansu shiru sukayi kowa yana jimami, Abdallah kanshi da yake yaro shiru yayi ya kwanta jikin Rumaisa yana goge mata fuskarta, har suka isa asibiti babu mai magana. Sai da Ra'eez yayi ma Dr. Sadeek waya, dan yanzu ya zama babba baya aiki a asibiti sai dai sune masu kula da wajen, hakan yasa ya damk'a Ummu a hannun babban likitan da yake wajen duk da idan yashigo yana kawo mata ziyara. Bayan sun gama wayar suka fito suka nufi d'akin da Ummu take. A zaune suka isketa tana sanye da hijabi ta kurama tv ido wadda ake shirin addu'ar safe da marece, wata dattijuwa ce zaune a gefe da alama itace take kula da ita. Idan kaga Ummu sai ka d'auka mai hankali ce, domin komai fess a jikinta, fuskarta ta nuna alamun manyanta kad'an saboda tana samun kulawa ga cima mai kyau sai fatar ta tayi kyau sosai, sam yanzu bata komai sai dai wani lokacin idan ta fara kuka tana kiran Abbun Ra'eez sai ta kai wani lokaci ta nayi, wani lokacin dole sai anyi mata allurar bacci kafin suke samun saukinta. Wani lokacin kuma sai tayi sati bata nuna alamun hauka ba, magana ma batayi sai dai mai kula da ita ta rik'a kula da abinda take so tayi mata, dan yanzu kam ta zama shiru-shiru, idanuwanta duk sun canza kala sun rage girma saboda kuka. Da sallama suka shiga d'akin, matar da take zaune tayi saurin amsawa ta mik'e tana masu sannu da zuwa. Har suka shigo Ummu bata kalli inda suke ba, yanda kasan bata cikin d'akin dan yau 'yan miskilancin take. Bayan sun gaisa da matar ta basu waje tayi waje. Ido Ra'eez ya tsura ma Ummu kwalla tana cikowa a idonshi, kusa da ita ya matsa yana mai kamo hannunta. Shiru tayi bata kulashi ba. Zama yayi ya jawota hawaye suna gangarowa a fuskarshi. Mama dasu Rumaisa duk sai sukaji wani sabon kuka, a hankali Ra'eez yace Ummu kiyi hak'uri aiki ne yamun yawa shiyasa banzo ba amma bazan sake ba. Tamkar bada ita yayi magana ba haka ta kyaleshi idanuwanta suna kan Tv tamkar mai fahimtar abinda akeyi. Matsowa Mama tayi ta kamo Ra'eez tana fad'in kayi shiru mu bata lokaci zatayi magana idan ka tursasata kanta zai iya d'aukar zafi. Zama sukayi kowa da abinda yake tunani, Ra'eez kam yana rik'e da hannun Ummu yaki sakinta. Can yayi saurin kallonta yana fad'in Ummu jiya fa nayi mafarkin Abbu ina kwance a kan gadonshi har... Zumbur tayi tana kallonshi, kamoshi tayi tana fad'in Abbun ka? Nima jiya yazo mun anan ma ya kwana, hannu tasa tana buga gadon da take zaune. Murmushi sukayi dukansu, Ra'eez yace Ummu meyasa baki tsaidashi har nazo ba? Dariya tayi tana tafa hannu tace ai yau idan yazo igiya zansa na d'aureshi, jiya nace ya zauna tare dani shine yamun wayau ya gudu, amma ka barshi yau sai na d'aureshi kaga bazai sake barina ba ko. Murmushi Ra'eez yayi ya gyara zama tare da d'ora kanshi saman cinyarta yana fad'in sosai ma Ummu, zan kawo maki igiya ki d'aure manashi kullum murik'a ganinshi. Nan fa Ummu ta saki jiki da Ra'eez sukayi ta firar Abbu, haka ya biye mata yana taya ta shirme duk dan suyi labari, Mama da Madu kuka kawai sukeyi a b'oye ganin yanda Uwa da 'Danta suke fira ta marasa hankali. Cikin firar sai dai Ra'eez yasa hannu ya goge hawayen da suke zubo masa saboda firar tana sakashi shiga cikin yanayi, ita ko Ummu dariya kawai takeyi suna firar Abbu. Da haka Mama ta zuba mata abinci, amsa Ra'eez yayi suna fira yana bata abaki, itama haka tarik'a bashi, duk da akoshe yake haka yake amsa yanaci yana hawaye. Bayan sun gama tacigaba da bashi labarin shirmenta. Har akayi sallah suka fita shida Madu da kyar ma ta yarda suka tafi. Bayan sun dawo ta jawo Ra'eez tana fad'in kaima yau anan zaka kwana idan Abbunka yazo sai muyi fira muci abinci gaba d'aya. Murmushi Ra'eez yayi ya haye saman gadon yana fad'in tabbas anan zan kwana Ummu muga Abbu atare. Wayarsa ce tayi k'ara, yana dubawa yaga Alhaji Barau ne, tsaki yayi kafin ya d'auka. Bayan sun gaisa ya fad'a masa idan anyi sallar isha'i yana nemansa muhummiyar magana ce. Ra'eez yace shikenan sai nazo, kashe wayar yayi yana tsaki. Mama ce ta tambayeshi wanda ya kira? 'Bata fuska yayi yana fad'in Alhaji Barau ne wai yana... K'arar da Ummu tasa ne yasashi saurin yin shiru. Kular abincin da take kusa da ita tayi wurgi da ita tana fad'in sai na kashe shi, wallahi sai na kashe shi, Abbunka baya sonshi, ya takura ma Abbunka. Saurin tashi Ra'eez yayi yana kok'arin rik'eta amma ya kasa, da sauri Madu ya fita domin kiran ma'aikatan, kafin suzo duk ta hargitse wajen tana ihu, hannun Ra'eez kuwa duk taji masa ciwo. Allura akayi mata cikin mintuna biyu bacci ya d'auketa. Zama Ra'eez yayi tare da sakin wani irin kuka mai cin rai. Kamoshi Madu yayi yana lallashinsa. Tashi Mama tayi tana fad'in mutafi tunda ta samu bacci, Ra'eez kada ka sake yin maganar wad'an nan azzaluman agabanta, nima mantawa nayi har na tambayeka. Kai ya d'aga ya tashi yana mai sake kallon Ummunsa, sosai ya k'ara jin kiyayyar su Alhaji Barau. Haka yayi ma ma'aikatan alkhairi da wannan matar kafin suka tafi, a waya ya fad'ama Dr. Saddek halin da take ciki. Dr.. Sadeek yace insha Allahu Ummunka ta kusa samun sauki, tunda har take jin haushin mutanan da take zargi tabbas alamun sauki sun fara bayyana, gobe zan shiga dan a d'auki hoton kwakwalwarta. Godiya Ra'eez yayi mashi ya kashe wayar. Mama tace idan ka ajemu sai kaje kaji kiran da yake maka. Ra'eez yace bazanje ba sai dai mu had'u a ofis gobe. Mama tace a'a, idan bakaje ba zaiyi tunanin wani abu. A fusace Ra'eez yace wallahi bazanje ba, saboda sunanshi kad'ai komai na Ummu ya hargitse, muna firar mu daga jin sunanshi komai ya tsaya, idan naje wallahi zan iya yin wani abu da zaisa na b'ata masa. Jinjina kai Mama tayi tace shikenan ka fad'a masa wani uzuri to. Kai ya d'aga yana goge idonshi. Bayan ya ajesu Mama tace yashigo yaci abincin dare. Ra'eez yace akoshe nake ai munci a asibiti gida zan tafi kaina yana mun ciwo. Mama tace idan kaje kasha magani, kuma bana so kasa wata damuwa aranka wani ciwon ya shige ka. Kai ya d'aga yana masu sai da safe. Har yashiga mota Rumaisa ta fito, jiki a sanyaye ta k'arasa bakin motar. Idanuwa ya tsura mata ganin yanda take kuka. Fitowa yayi ya hard'e hannuwansa a kirji yana kallonta. Kasa magana tayi sai kawai ta juya, da sauri ya kamo hannunta ya maidota baya, sakinta yayi kafin yace ta goge fuskarta. Hannu tasa tana goge fuskarta wasu hawayen suna zubowa. Murmushin k'arfin hali yayi yana fad'in kina so na kasa bacci ne? Kai ta girgiza. Ra'eez yace to bana son kukan ki, idan naje gida zan kiraki kimun fira mai dad'i da zata sakani bacci kinji? Kai ta d'aga tana murmushi. Ra'eez yace da kyau Pretty nah, yanzu kishiga gida sai na kiraki, kuma kici abinci kinji? Kai tazo d'agawa yayi saurin fad'in magana zaki mun Malama. Dariya tasa tana rufe fuskarta. Shima murmushi yayi yana jin sauki a zuciyarsa. Kallon shi tayi tana fad'in kayi tuki a hankali Yaya. Murmushi yayi yashige mota yana fad'in zanyi amma sai kince kina sona idan ba haka ba a 180 zanje gida. Zaro ido tayi tana fad'in kai Yaya. Gira ya d'aga mata yana fad'in sosai kuwa. Murmushi tayi tace to ka rufe idonka zan fad'a. Ra'eez yace Allah beyini makaho ba kuma bazan rufe ba, idan bazaki fad'a mun ba zanje na saurari na wasu Mat... I love you! Kafin ya kallota sai kurar gudunta ya iske tayi cikin gida. Besan lokacin daya saki wata dariya ba. Baki ya rik'e yana fad'in lallai ma Pretty, anya itace ma tayi maganar? Lumshe ido yayi yana mai-maita abinda ta fad'a. Rufe motar yayi ya nufi gida, shi kad'ai sai murmushi yake saki, a hankali ya furta lallai soyayya tana da dad'i, kuma tana taimako sosai, kafin minti goma zuciyata zafi take ina cikin damuwa, amma cikin mintuna biyar na samu canji. Allah nagode maka da ka saka soyayya a zukatan mu. K'aran wayarsa ce ta katse mashi abinda yakeyi, saurin d'auka yayi yana fad'in Abbah ina hanyar gida dana k'arasa zan kira ka. Abbah yace shikenan amma ka kirani fa. Kashe wayar yayi. K'ara gudun motar yayi dan yasan tunda Abbah yace zeyi magana dashi to ba k'aramun abu bane, yaso ma tun d'azu ya kirashi a ofis to yasan Abbah baya son magana a waje shiyasa bai kirashi ba. Ur's. Nabeelert Lady🖋[3/10, 8:39 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.* 2⃣7⃣ Cikin sauri ya kammala abubuwan da ya saba kafin ya kwanta, kallon agogo yayi yaga k'arfe 8:30, wayarsa ya jawo yayi kiran Abbah kirjinsa yana bugawa, tun lokacin da yaji yana son magana dashi yake jin fad'uwar gaba. Bayan sun gaisa Alhaji Mansur yace Ra'eez ya Ummun taka da jiki? Ra'eez yace da sauki sosai Abbah, sai dai sunan Alhaji Barau da Mama ta ambata agabanta ya jefata cikin tashin hankali har sai da akayi mata allurar bacci kafin aka samu kanta. Jinjina kai Abbah yayi yana fad'in da alamu sauki ya fara zuwa. Ra'eez yace haka Dr. Saddek ma ya fad'a, yace zai shigo asibitin gobe domin suyi mata awo. Abbah yace to Allah yasa muji alkhairi. Ra'eez yace amin Abbah. Gyaran murya Abbah yayi yana fad'in Ra'eez ya kamata a birkito da abinda ya faru shekaru 11 da suka wuce. Ajiyar zuciya Ra'eez ya saki jin abinda Abbah ya fad'a. Ya naji kayi shiru Ra'eez? Abbah ya fad'a jiki a sanyaye. Murmushin yake Ra'eez yayi yana fad'in bakomai Abbah, kawai maganar ce naji tazo mun daga sama. Abbah yace ya kamata kasa wannan maganar aranka, ka tuna akowane lokaci zamu iya maidota domin bazamu tab'a barin jinin Alhaji ya tafi abanza ba, idan kaga haka ta faru to bamu da cikakkar hujjar da zamu gabatar ma kotu. Ra'eez yace nima wannan abun yana damuna Abbah, wani lokacin ina ganin kamar bamu da shedar da zamu iya mik'a su Alhaji Barau kotu, duk wata hujja sune suke da ita, koda kotun duniya zamu kaisu sune zasuyi nasara akan mu. Abbah yace kada kayi saurin sarewa Ra'eez, mai gaskiya Allah baya tab'ar dashi, ko alhakin Malan Sani ya isa yasa a wannan karon muyi nasara, domin zalunci baya d'orewa. Jinjina kai Ra'eez yayi yana fad'in insha Allahu muna kammala shari'ar da zamuyi ranar litinin zan fara shirya yanda tamu zata kasance, zanje na lalubo kundin shari'ar su Abbu domin na fara dubashi. Abbah yace haka nake son ji Ra'eez, ai fad'uwar gaba asarar namiji, kasa aranka zamuyi nasara. Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in insha Allahu Abbah. Abbah yace sai kuma maganar waccan motar da take ajiye a gareji, badan kace kana sonta ba da ansayar da ita da ayita ajiyarta bata komai. Ra'eez yace dan Allah Abbah abarta, inaso idan nazo Kano na kaita ayi mata seti dan ita nake son nacigaba da hawa. Murmushi Abbah yayi yana fad'in haba Ra'eez, ai zamaninta yawuce, idan aka ga kana hawanta sai arik'a maka kallon matsolo. Dariya Ra'eez yasa yana fad'in Allah Abbah sai na hauta kona 'yan watanni ne, tun lokacin da Abbu ya siyeta nake cewa idan na girma zai koya mani ita, kuma yace zai ajeta har na girma a cikinta zai fara koya mani mota, kaga tunda ban fara koyo acikinta ba ai gara na hauta. Abbah yace wannan haka yake, bakomai duk lokacin da kazo sai ka kaita a dubata, amma maganar shari'ar da zakuyi ina fatan babu wata matsala? Ra'eez yace akwai Abbah, amma insha Allahu komai zaizo da sauki, idan muka kammala zan baka labari. Abbah yace shikenan Allah ya bada sa'a. Ra'eez yace amin. Sallama yayi mashi ya kashe wayar. Kwanciya yayi yana kallon saman d'akin, tunanin ta yanda zai nemo kundin shari'arsu Abbu kawai yakeyi, dole ya k'ulla alak'a da ma'aikacin d'akin ajiyar kundi. K'arar wayarsa ce ta maido dashi daga tunanin da yakeyi. Raheena ya gani, d'an tsaki yayi kafin ya d'auki wayar. Sallama tayi masa, bayan ya amsa ta gaishe shi tana tambayarsa gajiyar aiki. Ra'eez yace lafiya lau. Raheena tace d'azu Dady yake fad'amun zaka zo ina ta murna sai kuma yace wai wani uzuri ya hana ka zuwa duk banji dad'i ba ko abinci kasa ci nayi, ta fad'a cike da shagwab'a. Murmushi yayi jin abinda ta fad'a. Raheena tace Allah baka san irin son da nake maka bane, saboda kai duk wasu abubuwa da nakeyi marasa kyau na dena, yanzu tsakanina da masu mana aiki sai alkhairi da girmamawa, abinci kuwa tuni na fara iyawa duk saboda kai. Ra'eez yace haka akeso ai, kinga har abada bazaki tab'a mantawa dani ba, domin ta sila ta kin samu rayuwa mai kyau. Murmushi tayi tana fad'in sosai kuwa, kaga nima zan zamo Uwa ta gari, zan kula da yaran mu wad'an da zamu haifa. Dariya Ra'eez yasa wacce besan da zuwanta ba. Raheena tace kadena dariya nasan auren mu bazai ja lokaci ba, dan Momy da Dady duk sun san da maganar, kai kawai nake jira ka amince dani kuma nasan zaka amince tunda gashi kana kula ni. Zeyi magana kiran Rumaisa yashigo wayarsa, dafe kai yayi aranshi yana fad'in ga sarkin kishi nan, amma bari ya gwada ta, sharewa yayi suka cigaba da magana. Rumaisa kuwa ganin call waiting yasa taji ranta ya b'aci, sake gwadawa tayi amma yana waya, haka tayi ta kiranshi kusan mintuna ashirin begama wayar ba, haushi ne ya isheta tayi wurgi da wayar ta kwanta. Hankalin Ra'eez gaba d'aya yana wajen Rumaisa, duk da yayi hakan ne dan ya tsokaneta amma sai yaji babu dad'i. Raheena kuwa sai zuba masa surutu takeyi, ganin yanda yake amsawa yasa tace Dear da alamu bacci kakeji. Ra'eez yace gaskiya kam. Raheena tace shikenan bara na barka bana so na takura maka, ina fatan zakayi bacci mai dad'i. Ra'eez yace sosai kuwa. Raheena tace Dear bazaka ce naci abinci ba? Ya kamata ka lallasheni ko abu marar nauyi ne naci. Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in to kisha tea da biscuit kafin ki kwanta. Murmushi ta saki tana fad'in yanzu kuwa my one. Sallama yayi mata ya kashe wayar. Latso lambar Rumaisa yayi, har ta gama k'ara ba'a d'auka ba. Murmushi yayi ya sake kira amma bata d'aga ba. Sai da ya kira so biyar bata d'aga ba. Sako ya tura mata kafin ya aje wayar yana murmushi. Rumaisa tana kwance ta gama jin wayarta na k'ara amma taki d'agawa wai tayi fushi. Jin alamun sako yasa tayi saurin jawo wayar. *Tunda baki son jin muryata bara na nemo wadda zata taya ni fira kafin nayi bacci.* Saurin tashi tayi tana kok'arin kiranshi. Murmushi ya saki a lokacin da yaga kiranta. Kashewa yayi kafin ya kirata. Tana d'agawa ta fara masa rigima. Dariya yasa yana fad'in ashe dai ana sona? Turo baki tayi tana fad'in Allah Yaya wata rana zakasa zuciyata ta buga. Ido ya zaro kamar tana ganinsa yace rufa mun asiri, idan zuciyarki ta buga nayi rayuwa da wa kuma? Da wacce kuke waya ka share ni mana. Dariya yayi yana fad'in nikam naji dad'i domin an nuna ana kishina yau. Rumaisa tace Yaya... Kinga ni bana son wannan Yayan, ga sunaye nan masu dad'i kinemo kisa mun. Murmushi tayi mai sauti tana fad'in ai bansan su ba. Ra'eez yace shikenan zancigaba da sauraran wacce take kirana da sunaye masu dad'i. Da sauri Rumaisa tace kayi hak'uri *Deel*. Saurin kallon wayar yayi yana sakin murmushi, zeyi magana ta kashe wayar. Kwanciya tayi ta rufe fuskarta tana murmushi. Sake kira yayi amma yaji akashe. Murmushi ya saki yana rungume filo, juyi yayi yana jin wani irin sanyi aranshi, tabbas soyayyar Rumaisa tayi nisa aranshi, baya jin zai iya rayuwa ba tare da ita ba, fatanshi a kammala wannan shari'ar ayi maganar aurensu. Haka yayi ta tunani har bacci ya d'aukeshi. *** A gurguje ya shirya, koda yaje gidansu Rumaisa da kyar yasha tea ya tafi ko had'uwa da Rumaisa basuyi ba dan tunda safe Alhaji Barau yayi masa waya akan maganar jiya hakan yasa yake ta sauri. *** Zaune yake a ofis d'in Alhaji Barau, mamaki yake ganin yau yashigo da wuri ko dan yau juma'a yasa yazo? Bayan sun gama gaisawa Alhaji Barau yace ai tun jiya naso kazo dan dai kace kana da uzuri. Dama akan maganar wannan shari'ar ce da aka baka, maganar gaskiya Ra'eez wannan yaron da zaka kare Yaron abokin kasuwancin mu ne, babban aminin Alhaji Marusa ne, kasan yanda talakwa suke idan suna jin haushin mutum, wannan yarinya 'yan unguwarsu ma sun bata shedar bata da hali mai kyau, amma koma menene ina so ka duba shedun da aka baka da kyau, bana so ashiga kotu a samu matsala, domin wannan kotun kowa yasan yanda take da adalci bazan so ace a wannan karon dana zab'eka ace an samu matsala. Gyara zama Ra'eez yayi yana fad'in insha Allahu Alhaji bazan kasance mai samar da rashin adalci a kotun ka ba, kamar yanda kowa yasan wannan kotu da adalci ina mai tabbatar maka zan tsaya tsayin daka domin a tabbatar da gaskiya a wannan shari'a. Murmushi Alhaji Barau yayi yana fad'in nasan bazaka bani kunya ba, nagode sosai, zaka iya tafiya. Tashi yayi, har ya kai bakin kofa yaji muryar Alhaji Barau yana fad'in Raheena tace na gaishe ka. Murmushi kawai Ra'eez yayi ya d'aga kai kafin ya fice. 'Yar dariya ya saki jin wani rashin kai a wajen Alhaji Barau, wai Uba ne yake bada irin wannan sakon. Tsaki kawai yayi yawuce. Kallon mutumin da suka taho tare da Brr. Bajinta yayi, kauda kai yayi yawuce dan ya gane Mr. Kallah tun wancan zuwan da suka had'u. Bayan sun gaisa da Alhaji Barau Mr. Kallah ya kalli Brr. Bajinta yana fad'in d'an bamu waje zamuyi magana. Gimtse fuska Brr. Bajinta yayi dan beji dad'in abinda yayi masa ba. Kallonshi Alhaji Barau yayi yana fad'in kaje kawai. Kai ya jinjina kafin ya fice fuska a d'aure. Gyara zama Mr. Kallah yayi yana fad'in ka ganni da sammako ko? Murmushi Alhaji Barau yayi yana fad'in mamakin da nakeyi kenan, gashi baka kira kace zaka zo ba. Mr. Kallah yace wani abu ne ya bani haushi siyasa na taso dan nasan baka da masaniyar abun. Alhaji Barau yace menene kuma ya faru? Mr. Kallah yace mutumin ka mana Alhaji Marusa. Cire glass Alhaji Barau yayi yana fad'in wani abun yayi ko? Tab'e baki Mr. Kallah yayi yana fad'in ai nasha fad'a maka Alhaji Marusa beda gwani, tunda ya iya yakice 'yan uwansa nasan cewar kowama zai iya yakicewa. Alhaji Barau yace dan Allah ka bani labari duk kasa kaina ya fara caji. Gyara zama Mr. Kllah yayi yana fad'in ajiya cikin dare ina duba Email d'ina sai ga sako yashigo mani daga *Mark* yana fad'a mani maganar da Alhaji Marusa yayi masa akan wannan kasuwancin da mukace zamu bud'e na shigo da manyan kayan zamani da Mark ya gano mana, kasan harkar akwai k'aruwa sosai, dan matuk'ar muka dace mun gama zama masu kud'i a duniya, kai ina tabbatar maka wannan aikin dole ka ajeshi dan zaman garin nan ma began mu ba. Jinjina kai Alhaji Barau yayi yana fad'in ina jinka. Mr. Kallah yace ashe Alhaji Marusa ya zagaye ya fad'ama Mark shi kad'ai zai sayi kayan saboda shine ya dad'e a harkar kasuwaci daga baya ya jawo mu, ya kyale mu zai yaga mana wani abu idan komai yayi dai-dai, to ahaka suka tsaya, kasan Mark beda munafurci, shine ya turo mani da sako jiya cikin dare yake fad'a mani yayi mamaki da abinda Alhaji Marusa ya fad'a saboda yasan yanda muka aminta da juna, shi kuma baya iya munafurci dan baya so yaga ta silarshi ya raba abokai, hakan yasa ya fad'a mani domin muje mu sasanta kan mu. Dariya Alhaji Barau yasa yana buga tebur. Mr. Kallah yace indai Alhaji Marusa ne kuka ma sai ya saka. Tashi Alhaji Barau yayi yana fad'in wallahi k'aryarsa tasha karya, idan yana tak'ama da jinin fulani ajikinsa zan nuna masa irin namu cin duduniyar, ka barni dashi, cikin ruwan sanyi zan nuna masa rashin wayonsa. Zama yayi yana fad'in kai baka tab'a tunanin dalilin da yasa na rabashi da gidanshi na Surelere ba? Duk da gidan ya kasance da zalunci aka amshe shi amma dai ya biya kud'in gidan, domin nasan da Iyalan Alhaji Maiwada suna nan har abada bazasu manta da wannan gidan ba. Tun lokacin da wannan gidan ya zama mallakinsa na kudira araina sai na rabashi dashi, hakan yasa cikin ruwan sanyi da muka fara gabatar da kasuwanci atare lokacin da muka samu kaya masu kyau bayan an raba ya nuna yana son wasu daga cikin nawa na barmasa babu ja, da wannan na yaudareshi har ya siyar mani da gidan akan kud'i kalilan gashi yanzu ina rayuwata aciki nida iyalina hankali kwance. Dariya Mr. Kallah yasa yana fad'in baka da kyau Alhaji Barau, ai tun alokacin na cika da mamakin yanda akayi ya siyar maka da gidan a wannan kud'i, ashe dai ka nuna masa kafishi sanin kan duniya. Alhaji Barau yace ai karatun lauya ba k'arya bane, cud'anya da mutanen da nayi betashi abanza ba tunda gashi yayi mani amfani. Jinjina kai Mr. Kallah yayi yana fad'in a wannan karon ma baza muyi sanya ba, bana so abotar mu ta tab'u amma kada ka bari yasan munsan komai. Alhaji Barau yace sa ido kayi kallo kai dai. Dariya sukasa suka cigaba da tattaunawa. **** Bayan sun fita sallah Ra'eez be jira Jabeer ba ya sulale yaje ya dubo Ummunsa, sosai yaji dad'in ganinta dan jikinta da sauki, sai dai be samu ganin Dr. Saddek ba saboda yana sauri, hakan yasa yawuce. Lokacin daya koma duk yanda Jabeer yaso yaji inda yaje be fada masa ba yace kawai Mama ce tayi masa kiran gaggawa hakan yasa ya yarda. Bayan sun tashi daga aiki Ra'eez yace Jabeer ya masa rakiya zuwa gidan su Yaron da zai tsaya mawa. Jabeer yace kamar kasan abinda yake raina kenan, gara muje domin kaji ta bakinsa. Ra'eez yace haka ne, sai dai bana so kowa yasan naje wajenshi. Jabeer yace muje akwai abinda zan fad'a masa wanda zai hanashi fad'ama kowa. Mota suka shiga suka tafi. Ur's. Nabeelert Lady🖋 [3/10, 8:39 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.* 2⃣8⃣ Sun dad'e a tsaye jikin mota suna jiran su samu wanda yasan Yaron da suka zo wajenshi. Kallon Jabeer Ra'eez yayi yana fad'in kaga na manta sunan yaron da Baba ya fad'a mana rannan. Jabeer yace anya ya fad'a mana sunansa kuwa? Gaskiya bana jin ya fad'i sunanshi. Waya Ra'eez ya ciro yana fad'in bara na tambayeshi gara musan sunanshi bana so asan wajenshi muka zo. Bugu d'aya Baba ya d'auka, bayan sun gaisa Ra'eez ya tambayeshi sunan Yaron? Bab yace sunanshi *Sameer* gidansu shine na biyu akan layinsu yana nan mai bakin gate. Ra'eez yace shikenan sai munyi waya. Kashewa yayi yana kallon gidan da suke fuskanta. Jabeer yace meye sunansa? Sameer! Ra'eez ya fad'a yana mayar da wayarsa aljihu. Wani matashi ne yazo wucewa, da sauri Ra'eez yayi masa sallama, bayan sun gaisa yake tambayarsa ko yasan Sameer da yake wancan gidan? Murmushi Matashin yayi yana fad'in *B-Boys* zaka ce. Jinjina kai Ra'eez yayi yana fad'in shi nake nufi. Matashin yace yanzu zaka ganshi ya dawo dan lokacin zuwanshi bitch yayi. Jabeer yace lallai babban yaro ne. Matashin yace idan B-Boys ne ai beda wasa akwai son harka da jin dad'i. Ra'eez yace mungode. Sallama yayi masu yawuce. Jabeer yace da ka sallameshi taya zamu iya ganeshi bayan bamu tab'a ganinshi ba? Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in sa ido kawai kayi kallo, mu k'arasa k'ofar gidansu zamufi saurin cimmasa. Basu dad'e a wajen ba sai ga wata rantsatstsiyar mota mai bakin glass ta shigo layin, tun kafin ya iso sauti yake tashi, ganin mutane a bakin gate kuma Matasa ya hana Sameer yin horn, amma a k'aidarsa yana doso gidansu yake horn, kafin ya iso an bud'e gate sai dai kawai ya shige. Sautin motar ya rage kafin yaja burki ya sauke glass d'in motar. Hannu yasa ya cire bakin glass da yake idonshi yana bin su Ra'eez da kallo, ko ba'a fad'a masa ba yasan wad'an nan matasan masu ji da kansu ne, domin su duka kyawawa ne, shigar jikinsu abun kallo ce domin dogayen kaya sukasa kasancewar yau juma'a. Saurin matsawa Ra'eez yayi fuskarshi d'auke da murmushi ya mik'a mashi hannu yana fad'in barka da zuwa Sameer. Jiki a sanyaye Sameer ya bashi hannu suka gaisa. Ra'eez yace idan bazaka damu ba inaso ka juya kan motarka zuwa inda tamu take akwai maganar da nake so muyi. Kallon rashin fahimta Sameer yayi masa. Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in kada ka damu, sunana Brr. Ra'eez, nine wanda zan kareka a kotu ranar litinin. Jinjina kai Sameer yayi yana fad'in am sorry ban ganeka ba, muje. Zaune suke a cikin motar Sameer sun zuge glass ta yanda baza'a gansu ba. Kallon Sameer Ra'eez yayi yana fad'in duk da an bani duk wata sheda dazan kareka nafi son nazo wajenka naji da bakin ka hakan zaisa nasan yanda zanyi na kare ka da kyau. Jiki a sanyaye Sameer ya kalli Ra'eez yana fad'in wallahi Halima sharri take mun fa. Ra'eez yace kasanta kenan? Girgiza kai yayi da sauri yana fad'in haka naji wasu suna kiranta anan nasan sunanta. Jabeer yace anan unguwar take ne? Sameer yace nifa bansan gidan su ba, kawai tana sona nayi mata wulakanci shine tace sai tasa an d'aure ni, bayan kwana biyu har na manta sai ga mahaifinta yazo wai nayima d'iyarsa fyad'e, ni mema zanyi da wannan k'azamar nida nake harka da.... Saurin had'iye abinda zai fad'a yayi. Ra'eez yace dama kana harka da wasu matan ne? Saurin girgiza kai yayi yana fad'in nifa ko lafiyar kirki banda ita hakan ne ma yasa banyi aure ba amma har k'anina yayi aure. Ra'eez yace ashsha, to Allah ya kyauta, shikenan zamu wuce, amma bana so kowa yasan nazo wajen ka idan ba haka ba shirin mu zai rushe. Jabeer yace kana fad'ama Mahaifinka lauyen ka yazo shikenan hankalinsa zai tashi zaiyi tunanin ka fad'i wata magana. Cike da gamsuwa Sameer yace babu wanda zan fad'amawa dan Allah kada ka bari a rufe ni. Ra'eez yace kada ka damu kotun mu wajen adalci ne. Jinjina kai Sameer yayi yana fad'in nagode. Sallama sukayi suka fita zuwa motarsu. Kallon Ra'eez Jabeer yayi yana fad'in meka fahimta agame dashi? Beda gaskiya kawai, Ra'eez ya fad'a. Dariya Jabeer yayi yana fad'in kaifa lauyensa ne ya zaka fad'i haka? Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in su lauya manya, ai kasan Allah baza suyi nasara ba. Jabeer yace sai ka kula fa, bana so su Alhaji Barau su san cewar da gangan ka kadasu. Ra'eez yace kai dai kasa ido zakasha kallo, cikin week end d'in nan zan gama komai. Jabeer yace Allah ya bada sa'a. Hannu Ra'eez ya bashi yana fad'in sai litinin ko? Jabeer yace haba dai, bazaka shigo ba? Ra'eez yace sai dai wani satin, dan wannan satin bazan fita ba inaso na shiryama wannan shari'ar. Jabeer yace shikenan, nima zan kwanta na huta sai munyi waya. Sallama sukayi kowa ya nufi motarsa zuwa gida. **** Wai Raheena har yanzu Ra'eez bece komai ba? Kallon Momy tayi tana fad'in yace mana, uhm! Wallahi Momy D, ya iya soyayya, bakiga yanda yake sona ba, damma suna da shari'a ranar litinin da wannan week end d'in tare zamu yishi anan gidan. Murmushi Momy tayi tana fad'in amma naji dad'i sosai, shiyasa jiya nayi magana da Dadynki akan shirin bikin ki, waje nake so muje a had'o komai. Rungume Momy tayi tana fad'in gaskiya naji dad'i, bakiga yanda k'awayena suke santinshi ba, rannan dana d'ora wani hotonshi dana had'a da nawa bakiga yanda mukayi kyau ba kamar atare muka d'auka, wasu sai cewa suke nayi dace. Momy tace zauna nan su rufe ki da dad'in baki wata ta kwace maki shi. Zaro ido tayi tana fad'in haba dai Momy, ai Ra'eez nawa ne ni kad'ai, idan ban sameshi ba Allah kad'ai yasan halin da.... Saurin rufe mata baki tayi tana fad'in ko da zan rasa komai sai kin aureshi, dan haka ki kwantar da hankalin ki, kisa aranki anyi auren ku, dan yanda na fara fad'ama k'awayena an kusa aurenki bazan bari naji kunya ba. Murmushi Raheena tayi tana fad'in ina sonki Momy na. Mai aikinsu ce ta shigo da sallama. Bayan sun amsa ta kalli Raheena tana fad'in Aunty lokacin shiga kicin yayi. Saurin tashi Raheena tayi tana fad'in amma nagode, muje kada mu makara. Dariya Momy tayi tana fad'in Allah nagode maka, gaskiya naji dad'in zuwan Ra'eez rayuwarki Raheena, ta silarsa gashi kin canza, sallah akan lokaci, ga girmama masu aiki sannan abinci ma kin iya, ai dole ma na dage ki auri Ra'eez. *** *** Cikin kwana biyu Ra'eez ya kammala abubuwan da yakeyi, ko Ummunsa da kyar yake zuwa ya duba ta saboda beda lokaci, sunyi magana da Dr. Saddek yace sai litinin zasuyi mata awon akwai wani likita da suke jira zaizo. Gidan su Rumaisa ma so d'aya yake zuwa da rana yaci abinci, yafiso ya kammala komai ta yanda zai shiga kotu da kwarin guiwa, hatta da wayoyinsa baya d'auka sai idan kiran me muhimmanci ne. *** Safiyar litinin da wuri ya kammala shirinsa, haka ya nufi gidan su Rumaisa, bayan sun gaisa yace zai wuce. Mama tace abinci fa? Ra'eez yace Mama yayi safiya da yawa idan muka kammala zanci. Girgiza kai tayi tana fad'in zauna kasha ko shayi ne. Haka ya zauna Rumaisa ta kawo masa. Zama tayi tana kallonshi harya kammala. Murmushi yayi yana fad'in kimun addu'a Allah ya bani sa'a kinji. Kai ta d'aga tana fad'in inayi maka ai, kuma nasan zakayi nasara. Ra'eez yace nagode, da mun kammala zan maido maki da lokacin ki dana ara. Murmushi tayi ta mik'e. Addu'a sosai Mama tayi masa kafin yawuce wajen aiki. Ofis d'insa ya fara wucewa kafin lokacin shiga kotun yayi. K'arfe goma babbar kotu tacika da mutane suna jiran isowar Alkali. Bayan daya shigo kowa ya samu waje ya zauna ana jiran afara. Bayan ya zauna ya umarci magatakarda daya karanto shari'a. Tashi yayi ya fara karantowa. *A yau litinin goma ga watan oktoba shekara ta dubu biyu da sha tara wannan kotu mai albarka zata saurari k'arar da Malan Haruna ya shigar ta Sameer Aliyu Jabb'ama, wanda yake zarginsa da yima d'iyarsa 'yar shekara sha shidda fyad'e.* Risnawa yayi ya mik'a takardar. Bayan da Alkali ya gama dubawa yace lauyoyin da zasu gabatar da shari'a fa? Tashi sukayi, fitowa Brr. Bajinta yayi yana fad'in sunana Brr. Bajinta, nine wanda yake kare wad'anda suke k'ara. Sunana Brr. Ra'eez, nine nake kare wanda ake k'ara. Jinjina kai Alkali yayi yana fad'in lauyen da zai fara bismilla. Fitowa Brr. Bajinta yayi yana fad'in ya mai shari'a inaso zanyima Sameer wasu tambayoyi idan kotu ta bani dama? Koti ta baka dama, Sameer ya fito gaban kotu. Brr. Bajinta... Kotu zataso taji sunanka. Sunana Sameer Aliyu Jabb'ama. Brr. Bajinta... Malan Aliyu kaji abinda ake tuhumarka dashi, shin ko da gaske ne ka aikata abinda ake zarginka dashi? Sameer... Ban aikata abinda ake zargina dashi ba gaskiya. Brr. Bajinta... Kana nufin baka san Halima ba? Sameer... Tabbas ni bansanta ba idan ba ranar da tazo wajena wai tana sona ba, ni kuma tamun yarinta nayi soyayya da ita sai nace ta tafi ta bani waje, nan fa ta fara mani rashin kunya wai idan tana son abu dole ta sameshi kuma zanga abinda zatayi mani, shine fa kawai naji anzo ana fad'in wai nayi mata fyad'e. Brr. Bajinta... Kana nufin dai baka tab'a kaita gidanku ba? Sameer... Aini banda lafiyar da zan iya kwanciya da mace ma, hakan yasa ko aure banyi ba. Brr. Bajinta... Ko kana da shedar da zaka nuna ma kotu cewar baka da lafiyar kusantar mace? Sameer... Kwarai ina da sheda tana wajen likita na. Brr. Bajinta... Shikenan iya kar abinda ka sani kenan akan wannan abun da ake zargin ka? Sameer.... Iyakar abinda na sani kenan. Brr. Bajinta... Zaka iya tafiya, inaso nayi ma likitan Sameer tambaya idan kotu ta bani dama? Kotu ta baka dama. Brr. Bajinta.... Kotu zata so taji sunanka da aikin ka. Sunana Dr. Sa'eed Jafar, nine likitan da yake kula da lafiyar Sameer kusan shekaru ukku kenan. Brr. Bajinta.... Likita wace irin rashin lafiya Sameer yake da ita da har yake zuwa wajen ka? Dr. Sa'eed.... E to, a shekarun baya sunzo wajena shida Mahaifinsa kasancewar nine likitan gidansu, alokacin Mahaifinsa yake sheda mani wai Sameer har lokacin baya kula mata, daya bincikeshi sai yace masa shi kawai baya sha'awar mace, shine sukazo wajena, alokacin ne na gano Sameer beda lafiyar da zai iya kusantar mace, hakan yasa na d'orashi akan magani, wannan shine sakamakon binciken da akayi masa, ga magungunan da yake sha. Brr. Bajinta... Shikenan zaka iya tafiya. Ina so nayima Dr. Kaseem tambaya. Kotu ta baka dama. Brr. Bajinta.. Kotu zataso taji sunan ka da aikin ka. Sunana Dr. Kaseem Nuhu, nine likitan daya duba Halima alokacin da Iyayenta suka kaita asibiti. Brr. Bajinta... Dr. Kaseem alokacin da aka kai Halima asibiti a wane hali take? Dr. Kaseem.... E to, gaskiya ba wani cikin damuwa sosai aka kaita ba, asalima da k'afafuwanta taje, bayan da Mahaifinta yayi mani bayanin fyad'e akayi mata sai muka shiga da ita d'aki domin mu dubata, to abinda na gani yasa nayi mamaki da akace wai fyad'e ne, domin babu alamun wani ciwo ajikinta, da ganin yanayinta kamar ta saba mu'amula da maza haka, sai kawai na rubuta mata magungunan ciwon jiki na kwantar ma da Mahaifinta da hankali dan gaskiya besan halin da d'iyarsa take ciki ba, na fad'a masa anyi mata d'inki kawai zata kwanta na kwana biyu. Brr. Bajinta... Idan na fahimceka Halima ba fyad'e akayi mata ba kenan? K'arya ne ya mai shari'a, wallahi 'Diyata bata tab'a aikata masha'a ba, wannan likitan k'arya yakeyi, domin shine ya dubata sai dai idan siyeshi akayi kuma..... Bubbuga tebur Alkali yayi hakan yasa Malan Haruna ya koma ya zauna hawaye suna bin fuskarshi, kallon Brr. Barau kawai yakeyi zuciyarsa na masa zafi, yanda yake tafiyar da aikinsa kamar shine yake kare mai laifi. Kallonshi Alkali yayi yana fad'in kada ka sake magana akotu dan nan ba kasuwa bace, idan kana da magana kajira abaka dama, Brr. Bajinta zaka iya cigaba. Risnawa yayi yana fad'in Dr. Kaseem zaka iya tafiya mun gode. Ina so nayima Halima tambaya idan kotu ta bani dama? Kotu ta baka dama. Jiki a sanyaye Halima ta fita gaban kotu, da kyar take iya d'aga k'afarta, kanta ak'asa hawaye ne kawai suke sauka ajikinta. Brr. Bajinta.. Meye cikekken sunan ki? Sunana Halima Haruna. Brr. Barau... Shin ko kinsan wancan? ya nuna Sameer. Kai Halima ta d'aga. Brr. Bajinta... Baki zaki bud'e kiyi magana. Halima na sanshi. Brr. Bajinta... Meye alak'ar ku dashi? Halima... Babu wata alak'a tsakanina dashi, abinda na sani duk lokacin da zanje islamiya yana tare ni da maganganun banza ni kuma bana kulashi, wata rana nayi latti nazo wucewa kawai naga yasha gabana, zanyi magana kawai ya shafa mani wani kyalle a fuskata, daga nan ban sake sanin abinda yake faruwa ba sai bud'e ido nayi na ganni kwance a d'akinsa cikin jini, kuka nasa shine yace ko nayi shiru koya k'aramun, cikin tashin hankali na kama bakina, sani yayi na tashi yace na fice kuma kada na bari kowa yasan daga d'akinsa nake, nasan dai na fita daga gidansu na kama hanyar gida, kafin na kai gida bansan abinda ya faru ba sai dai na bud'e ido a gadon asibiti. Brr. Bajinta... Halima kuma kin tabbata Sameer ne kika gani? Kai ta d'aga tana fad'in wallahi shine. Brr. Bajinta... Shikenan zaki iya tafiya. Ya mai shari'a iya tambayoyin da nake dasu kenan, ina fatan wannan kotu zatayi duba da shedun da aka gabatar domin a kwatar ma me hakki hakkinsa. Nagode. Wasu daga cikin kotun dariya suka farayi k'asa-k'asa dan ganin wata bahaguwar shari'a, domin yanda Brr. Bajinta yayi tamkar ba shine yake kare Halima ba. Ra'eez kuwa yana zaune ya nutsu ya gama had'a duk wasu bayanai da aka gabatar ma kotu. Bayan kowa yayi shiru Alkali yace lauyen da yake kare wanda ake k'ara bismilla. Ra'eez... Ya mai shari'a ina so nayima Dr. Sa'eed tambaya idan kotu ta bani dama. Kotu ta baka dama. Ra'eez... Likita naji bayanin daka bayar yanzu a kotu akan rashin lafiyar Sameer, shin dama har namiji ya girma baya iya gane beda lafiya ne? Dr. Sa'eed..... Yana ganewa mana, ai tun lokacin da namiji ya isa balaga zai iya fahimtar yanayin da yake ciki. Ra'eez... Amma naji kace shekaru ukku da suka wuce aka gano Sameer beda lafiya wanda nasan Sameer zai kai shekaru talatin da hud'u ko da biyar ma, shin kana nufin tun alokacin baya besan cewar beda lafiya ba? Kada fa maganarka ta jawo masa bakin jini yazo ya rasa matar aure nan gaba. Dr. Sa'eed... E to, kasan ba kowane yake maida hankali akan lafiyarsa ba, wasu kuma zaka samu haka suke Mata basa gabansu koda suna da lafiya. Ra'eez.... Mungode likita zaka iya tafiya. Ya mai shari'a ina so nayima Dr. Kaseem tambaya idan kotu ta bani dama. Kotu ta baka dama. Ra'eez... Dr. Kaseem kace lokacin da aka kawo Halima wajenka da k'afarta ta tako ko? Dr. Kaseem... Kwarai kuwa da k'afarta ta tako. Ra'eez.... Kenan lokacin da aka kawota kaine ka amsheta? Dr. Kaseem... Saurin d'ago kai yayi yana kifta idanuwa. Ra'eez yace tambayarka nakeyi. E to ba nine na amsheta ba amma nine na dubata. Ra'eez... Ai ba cewa nayi kaine ka dubata ba, tambayar ka nake kaine ka amsheta? Dr. Kaseem... Ba nine na amsheta ba. Ra'eez... To ya akayi ka gane da k'afarta tazo? Dr. Kaseem... Yanayinta ya nuna bata cikin wahala ai. Ra'eez.... Murmushi yayi yana fad'in amma ai ka kwantar da ita har na kwana biyu kafin ka basu sallama. Dr. Kaseem... Kasan idan marar lafiya ya nuna sauki ajikinsa hakan yake bamu damar sallamarsa, to ita ta nuna rashin kwari a jikinta hakan yasa dole na kwantar da ita. Ra'eez..... Alokacin da aka kawo ta asibiti jikinta duk jini, gashi kai kuma kace babu alamun fyad'e ajikinta saboda ba shine na farko ba, ko zaka fad'a mana jinin na meye? Dr. Kaseem... E to, da yake akwai ciwo a jikin hannunta ina ji jinin ciwon ne. Ra'eez... Shikenan zaka iya tafiya. Ina so nayima sister Asabe tambaya idan kotu ta bani dama. Kotu ta baka dama. Hannu Brr. Bajinta yasa yana gyara wuyan rigarshi, dama yasan Ra'eez bazai tab'a goyon rashin gaskiya ba, gashinan anyi gudun gara an fad'a gidan zago. Haka sauran mutanan kotun duk kansu ya d'aure, gashi dai sunji kowa da lauyenshi amma kuma abun ya juye. Ra'eez... Kotu zata so taji sunanki da aikin ki. Sunana Asabe Habu, kuma ni ma'akaciyace a asibitin Dr. Kaseem wanda ya kasance na kud'i ne. Ra'eez.... Shin ko zaki fad'ama kotu abinda ya faru alokacin da aka kawo Halima asibitin ku? Asabe.... E muna zaune gab da magriba sai ga Mahaifinta ya shigo da ita a hannunsa a rud'e, alokacin ma ko motsi batayi ga jikinta duk jini harya b'ata rigar Mahaifinta, yana kuka ya rok'emu akan mu taimaka masa, alokacin ni d'aya ce nan na nuna masu gado ya kwantar da ita, turata nayi zuwa d'aki domin bata taimakon gaggawa, gaskiya abinda na gani ya tada hankalina, sai dai kafin na fara dubata sai ga Dr. Kaseem ya shigo sai yace mun na tafi zai k'arasa dubata, naso na tsaya na taimaka masa sai yace kawai na tafi, hakan yasa na tafi. Ra'eez.... Jinjina kai yayi yana fad'in kamar meye kika gani ya tashi hankalin ki? Asabe... Yanda aka ci mutuncinta yasa hankalina ya tashi, domin ko waye ya aikata mata haka to da k'arfi ya shigeta. Ra'eez... Mungode zaki iya tafiya. Ina so nayima Sameer tambaya idan kotu ta bani dama. Kotu ta baka dama. Ra'eez... Malan Sameer, kace Halima tace sai tayi maka rashin kirki ko? To dama can kuna takun sak'a ne da ita? Sameer..... Gaskiya ko magana bamayi domin bansanta ba, nasan dai ta k'ofar gidan mu take bi idan zataje makaranta, saboda tana ganina yasa tazo tace mun tana sona ni kuma nayi mata wulak'anci shine tace zan gani. Ra'eez.... Sameer ko kasan wannan zoben? Sameer... Hankali tashe Sameer yake kallon zoben hannun Ra'eez, tabbas tun bayan rabuwarsu da Halima ya nemeshi ya rasa ashe yana jikinta. Wata irin zufa ce ta fara keto masa, kwalla ne suka cika masa ido, kasa magana yayi sai dai ya duk'ar da kai. Ra'eez... Murmushi yayi yana fad'in wannan zoben Malan Haruna ya sameshi ne a jikin gashin Halima alokacin da yake kok'arin kaita asibiti, hakan yasa ya cireshi ya aje, gashi kuma a wannan hoton naka naga irin zoben a hannunka, wata kila ko kama ce kawai. Hawaye ne suka fara zubo ma Sameer, a yanzu kam ya sare domin yasan dole a ganoshi, gara kawai yayi kundunbale ya fad'i gaskiya kamar yanda Ra'eez ya kirashi ya fad'a masa ya gano gaskiya shine ya aikata laifi, idan ya tona kanshi shi zai tsaya masa ayi masa hukunci mai sauki. Ajiyar zuciya ya saki yana sake kallon hoton hannun Ra'eez, ya rasa a in da ma ya samu hoton. Ra'eez... Juyowa yayi yana fad'in ya mai shari'a da alama wannan zoben da Malan Haruna ya bayar bana Sameer bane tunda gashi ya kasa amsawa, ze iya yuwuwa kawai kama ce, domin za'a iya samun irinshi a waje da yawa, kamar yanda Dr. Sa'eed ya sheda ma kotu Sameer beda lafiyar da zai iya hayk'ema mace ina so wannan kotu tayi duba da wannan magana tashi domin ta..... Nine na aikata laifin ya mai shari'a, Sameer ya fad'a da k'arfi cikin muryar kuka. Da sauri kowa ya kalleshi. Murmushi Ra'eez ya saki kafin yayi saurin canza fuska ya juyo. Gaba d'aya wajen ya hargitse da surutu, Brr. Bajinta kuwa kamar wanda aka dasa haka yake kallon Ra'eez, lallai ya tabbatar yafi k'arfin tunanin Alhaji Barau ba shi bama, wannan rainin hankalin yayi yawa, bayan ya gama fito da gaskiya kuma ya koma yana kok'arin kare Sameer. Bubbuga tebur Alkali yayi jiki a sanyaye, gaba d'aya Ra'eez ya kwance masa notin kanshi, daurewa yayi ya tattaro jarumta yasa aranshi. Mahaifin Sameer ne ya tashi yana fad'in k'arya ne wallahi, kowa ya sheda Yarona beda lafiya, ina rokon wannan kotu da ta d'aga wannan shari'ar domin aje ayi binciken kwakwalwar Sameer dan wannan maganar da yayi tayi kama da ta masu tab'in hankali. Da hankalina Dady! Sameer ya fad'a yana kuka, kallon Alkali yayi yana fad'in zan fad'i gaskiya ya mai shari'a. Jinjina kai Alkali yayi kafin yasa akayi shiru. Komawa Ra'eez yayi ya zauna. Sake kallon Sameer Alkali yayi kafin yace muna sauraron ka..... Ur's. Nabeelert Lady🖋 [3/10, 8:39 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.* 2⃣9⃣ Kamar yanda nace nine nayima Halima fyad'e to haka maganar take, tabbas nine na keta mata haddi kuma nine farkon saninta a d'iya mace, hakika na taso cikin rayuwar jin dad'i, nine babba a gidan mu, sam iyayena basu damu da irin rayuwar da mukeyi ba, mun taso cikin jin dad'i, ina da K'ani mai suna Kamal, sam halayyarmu bata zo d'aya dashi ba, domin shi tun lokacin daya taso ya fuskanci yana da k'arfin sha'awa sai ya buk'aci ayi masa aure, Mahaifin mu yaso ya hanashi amma yace shi aure yake so, kasancewar Iyayen mu suna mana abinda muke so yasa ya amince akayi masa aure. Ni kuwa da na kasance mai hali irin na Mahaifinmu wato son more rayuwa sai tamu tazo d'aya, yana matuk'ar sona, duk abinda nake so shi ake mani, ina taka duk wanda naso, kuma yarinya sai idan batayi mani ba amma sai nayi kok'arin lasar zumarta, wasu basa tab'a sanin nine na aikata hakan agaresu, domin wani lokacin yarana nake sawa su sato mani yarinya kuma sai sun gusar mata da hankali kafin su kawota. Har na gama abinda zanyi da ita su maida ta bata tab'a sanin abinda ya faru, hakan yasa nakeyin komai hankali kwance, yayin da wasu matan sune suke kawo kansu gare ni. Tun ranar dana fara ganin Halima na kwad'aitu da ita, duk da itace mafi k'arancin shekaru da nasan na tab'a hayk'emawa, naso na cireta araina saboda ganin k'arancin shekarunta amma hakan beyuwu ba, nafi wata ina fama da kwad'ayinta, nayi yaki sosai da zuciyata amma shed'an yariga ya kwad'aita mani ita, a hankali na fara mata magana sai dai bata tsayawa kula ni, kasancewar ta hanyar gidan mu take wucewa zuwa makaranta yasa duk lokacin da zata wuce ni kuma nake fitowa domin na ganta. Ganin na rasa hanyar da zanbi yasa kawai nayi amfani da abinda nakema sauran matan, Halima itace mace ta farko dana tab'a kaita cikin gidan mu da sunan fyad'e, domin duk abuna banayi agida, sai dai idan sauran 'Yan matana ne su wannan ina kawosu har d'akina, sai gashi na kasa hak'ura akai mani Halima inda nake kai sauran matan. Wata rana da yamma ina zaune na gama had'a komai ina jiran wucewarta, tun ina jiranta har na fara fidda rai saboda aranar ta makara, har na tashi zan koma gida na yanke shawarar zansa a sato mani ita sai kawai na ganta zata wuce, farin ciki nayi, kasancewar unguwar mu bata da hayaniya yasa nayi saurin shan gabanta. A tsorace tayi baya tana neman hanyar guduwa amma nayi saurin saka mata kyallen hannuna, dama na aiki mai gadin gidan mu, saurin d'aukarta nayi muka shige ciki. Ajiyar zuciya ya saki hawaye suna zubo masa, kallon Halima yayi yana fad'in ban tab'a aikata fyad'en da nakasa samun natsuwar zuciya ba sai akanta, sam bana baccin kirki. Bayan da komai ya faru sai gashi ta farka, nayi mamakin farkawarta domin maganin yana da k'arfi, amma sai ta farka kuma ta sheda ni, ganin haka yasa na tsoratar da ita, tashi tayi ta bar gidan, sai da nabi bayanta naga tayi hanyar gidansu, agaban idona ta zube hakan ya tabbatar mani maganin bai saketa ba, komawa nayi gida har lokacin maigadi bai dawo ba. Bayan nashiga d'aki jinin da nagani ya tashi hankali na, saurin shiga wanka nayi amma jikina yana rawa, kasa daurewa nayi na kira d'aya daga cikin yarana nace yayi sauri yaje yaga halin da take ciki kuma ya gano mani asibitin da za'a kaita. Ina tsaye a harabar gidan mu sai ga Dady, ganin da yayi mani cikin tashin hankali yasa ya tambaye ni, bana masa k'arya hakan yasa na fad'a masa komai, nan take yace kada na damu na bari muji asibitin da za'a kaita. Muna nan Gayen ya kirani ya sheda mani yaga Mahaifinta ya samo mota sun nufi asibitin Dr. Kaseem, mamaki ne ya kamani nasan talakawa ne amma suka nufi asibitin kud'i, Dady yace kila baya son ya kaita babban asibiti atsaya b'ata masu lokaci wajen kiran 'yan sanda shiyasa ya kaita can. Nan take Dady yakira Dr. Kaseem ya fad'a masa halin da ake ciki, kuma yace kada a karb'i kud'in su. A lokacin ya fita amma yace zaiyi sauri ya koma asibitin kuma zai rufe komai. Wannan dalilin ne yasa Dr. Kaseem ya kori sister Asabe ya duba Halima kuma ya rubuta bayanin k'arya, domin yace har d'inki yayi mata. Bayan kwana biyu da faruwar haka sai muka samu labarin an kaini kotu, hankalina yayi matuk'ar tashi, kuka nasa Dady yace kada na damu babu abinda zai faru, nan take yakira Dr. Sa'eed ya fad'a masa abinda yake so, babu b'ata lokaci ya shirya sakamakon k'arya akan rashin lafiyata, har gida ya kawo ma Dady suka tattauna yanda komai zai kasance, haka ya cika masa jaka da kud'i ya tafi. Wallahi tun daga lokacin da haka ta faru ban sake samun natsuwa ba, hakan yasa a yanzu naga ya dace na fad'i gaskiya, kuma zan amshi ko wane hukunci aka yanke mun. Shiru kotun tayi ana sauraren kukan Sameer. Dadynsa kuwa zama yayi jiki a sanyaye yana goge zufa, gashi d'an siyasa yana tsoron hakan ya tab'a masa mutuncinsa. Jiki a sanyaye Alkali ya gama rubutu, gaba d'aya kunyar kallon Mahaifin Sameer yakeyi, babu yanda ya iya, Allah ma yaso Sameer ne ya tona komai yasan bazasu zargeshi ba. Bayan ya kammala rubutu ya d'ago yana kallon Sameer...... Bisa hujjojin da aka gabatar ma wannan kotu da kuma samun babbar sheda daga bakin wanda ya aikata laifi cewar ya amince shine ya aikata wannan laifi, wannan kotu mai adalci ta yanke ma Sameer hukuncin daurin wata biyar agidan yari ko kuma tarar naira dubu d'ari biyar, sannan zai biya Halima tarar naira million talatin domin keta mata haddi da yayi, haka kuma zai cigaba da kula da lafiyarta har ta samu sauki, sannan idan rabo yashiga tsakanin su zai kula da ita har ta haihu da bayan ta haihu har zuwa lokacin da zata yaye abinda ta haifa ta bashi abunshi, idan kuma zata rik'e masa to shine yake da alhakin kula dasu. Dr. Kaseem da Dr. Sa'eed zasu biya tarar dubu hamsin-hamsin bisa kamasu da akayi da kawo ma kotu shedar k'arya, idan aka sake kamasu da makamancin irin wannan laifin kotu zata soke lasisin su. Kallon mutane yayi yana fad'in ina fatan wannan hukunci zai zama izna ga sauran mutane. Saurin tashi Brr. Bajinta yayi yana fad'in ina neman alfarmar wannan kotu data k'ara ma Sameer tarar da zai biya Halima saboda ya keta mata haddi, ya rabata da abinda yafi komai muhimmanci agareta. Nagode ya mai shari'a. Jin jina kai Alkali yayi yana fad'in bisa duba da k'orafin lauya mai kare Halima wannan kotu ta amshi rokon ka, dan haka Sameer zai biya Halima tarar naira million hamsin, kuma dole ne ya biyasu akan lokaci... Kotttt.!!!!! Gaba d'aya kowa ya tashi ana jinjina ma Alkali bisa hukuncin adalcin da ya yanke, haka kowa yarik'a masa jinjinar ban girma, wannan adalci da kowa yake samu yasa suke k'ara son Alkalin su. Hannu Brr. Bajinta ya bama Ra'eez yana fad'in a wannan shari'ar dai na kada ka, amma duk da haka kayi kok'ari, nan gaba sai kayi kok'arin kada ni. Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in na tayaka murna, amma nan gaba ka rik'a kok'arin tsayawa akan aikin ka kadena kok'arin juya akalar kariyar ka zuwa ga wani daban, sannan karika aikata abinda ya dace ba sai an fad'a maka ba. Cira idanu ya fara yana yaken dole dan ya tuna d'azu da Ra'eez ya duko yana fad'a masa yayi sauri yatashi ya nemi a k'ara ma Halima kud'i hakan zaisa ya wanke kansa wajen mutane, hannunsa ya cire yana fad'in haka ne, kuma nagode. Jabeer ne yaja Ra'eez suka bar wajen. Kusa da Sameer suka je wanda yake rungume jikin Mahaifiyarsa dan Dadynsa ana gamawa ya sulale ya bar wajen. Dafa Sameer Ra'eez yayi yana fad'in kayi abun kirki, kuma har abada baza kayi danasanin abinda kayi ba, kaci sa'a ba kotun musulunci bace da sai kasha bulala, amma yanzu kana da damar biyan dubu d'ari biyar idan baka son zaman gidan yari. Da sauri Mamansa tace kud'in zamu biya, mungode sosai lauya, idan bazaka damu ba ina son ganin ka idan kana da lokaci. Jinjina kai Ra'eez yayi yana fad'in ayanzu Alhaji ya d'auki zafi, amma zanzo idan na samu lokaci. Haka suka fito ita da Sameer suka wuce gida 'yan jarida sai d'aukarsu hoto sukeyi. Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in wannan itace shari'ar ban dariya. Jabeer yace wallahi yanda kasan a film, ban tab'a ganin irin wannan shari'ar ba, daga kai har Brr. Bajinta kun bani dariya. Ra'eez yace ai shiyasa na barshi ya fara, da yake be iya wasan ba ai kaga kowa ya ganoshi. Jabeer yace amma nayi mamakin yanda Sameer yayi saurin amsa laifinsa. Ra'eez yace kila hakan yafi masa sauki. Kallonsa Jabeer yayi yana fad'in ban yarda da kai ba, anya babu sa hannunka? Dariya Ra'eez yasa yana fad'in muje ofis. Iyayen Halima basu tsaya jiran Ra'eez ba dan ya fad'a masu ana gamawa su wuce gida baya son agansu atare. Duk da sunji haushin Brr. Bajinta amma abinda yayi daga k'arshe yasa sukaji dad'i, hakan yasa sukaje sukayi masa godiya. Murmushi yayi yace haba babu komai, ai dama nace maku mune zamuyi nasara. Malan Haruna yace nawa ne kud'in ka? Brr. Bajinta yace haba kyauta nayi maku. Sosai sukayi masa godiya suka wuce cike da farin ciki. Zagaye kawai Alhaji Barau yake a ofis d'insa, ya rasa taya zai kalli abinda Ra'eez yayi masa, ya akayi ya canza komai beyi amfani da abinda suka bashi ba? Dole ya turkeshi sai ya fad'a masa abinda yake nufi. Waya ya d'auko yana niyar kiransa. K'ofa aka bud'e hakan yasa ya aje wayar. Alhaji Marusa ne yashigo fuskarsa d'auke da murmushi. Bayan ya zauna Alhaji Barau ya mik'a masa hannu suka gaisa dan shima haushinsa yakeji akan abinda yayi masu. Daurewa yayi dan baya so ya gano ya san komai. Alhaji Marusa yace Babban Alkali da girman kujerar ka. Alhaji Barau yace zaka fara ko. Dariya Alhaji Marusa yasa yana fad'in alokacin da nace kada ka bama Ra'eez shari'ar me kace? Na fad'a maku nifa jikina be yarda dashi ba, yaron da yazo a ranar farko ya cinye babbar shari'ar da aka sha wahala akanta taya kake tunanin zai amshi tayin rashin gaskiya? Tun farko na fad'a maku amma bakuji ba, sai kace wai zasu iya d'aukarshi, to ko sun d'aukeshi ba sai yana da hujjar nunawa ba, haba Alhaji Barau ya kake so kabar tsohuwar basirar ka ta gushe ne. Ajiyar zuciya Alhaji Barau ya saki yana fad'in kai dai ka bari kawai Alhaji Marusa, kwanan nan na rasa abinda yake damuna, ganin yana neman yarinyar wajena yasa nayi tunanin zaiyi duk abinda na sashi sai gashi ya watsa mani k'asa a ido, wallahi yanzu daka shigo kiranshi nayi niyar yi naji dalilin da yasa zaiyi mani haka. Dariya Alhaji Marusa yasa yana fad'in shiyasa nace basirar ka ta tsufa, taya kana Alkali zaka kira lauyenka ka titse shi akan shari'ar da yayi bayan kasan gaskiya ce, ai Brr. Bajinta ne kawai ze maka haka ka titse shi a zauna lafiya. Abinda nake so da kai ka nuna baka damu ba, kuma kayi masa jinjinar ban girma ka gode masa akan abinda yayi, kuma ka fad'a masa baka san haka abun yake ba amma kace ka gode da yaje ya sake bincike, ina tabbatar maka idan ka fad'a masa haka zai yarda da kai, gashi ka yanke hukunci yanda ya kamata, domin ko wannan kud'i da za'a bata zai inganta mata rayuwar ta, kaga zaka fita daga zarginsa. Jinjina kai Alhaji Barau yayi yana fad'in nagode da zuwanka Alhaji Marusa da na kwafsa, damuwa ce tamun yawa hakan yasa na kusa rasa dabarata, amma zanyi yanda kace. Tashi Alhaji Marusa yayi yana fad'in zanje na rarrashi Alhaji, ya godema Allah da ba kisa yaron yayi ba, gashima har ka bada zab'i biyu, kuma nasan bazasu barshi ya shiga gidan yari ba. Alhaji Barau yace ka gaishe shi kuma ka bashi hak'uri nagode. Alhaji Marusa yace zaiji. *** Ina jinka Ra'eez, Jabeer ya fad'a yana sunno kanshi a fuskar Ra'eez. Dariya yayi ya tureshi yana fad'in kaga Malan kada ka dameni, taya zaka zo a wajen aiki ka ishe ni na baka labari idan wani yaji fa, kawai ka bari idan muka fita na fad'a maka. Jabeer yace ai gashi can ana kiran sallah muje muyi idan muka fito sai ka bani. Ra'eez yace muna fitowa na tashi dan wallahi na gaji, kasan dama idan nayi shari'a bana son nayi zaman aiki. Jabeer yace aiko sai dai mutafi tare dan bazanji dad'in zama wajen nan baka nan ba. Ra'eez yace idan kuma na bar kotun fa? Da sauri Jabeer ya kalleshi yana fad'in ban gane ba? Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in ina nufin idan aka mana canjin wajen aiki. Jabeer yace insha Allahu hakan bazata faru ba. Ra'eez yace Allah yasa. *** Bayan sun gama sallah yashiga domin ya fad'ama Alhaji Barau zai wuce gida. Cike da jin nauyi Alhaji Barau ya kalleshi yana fad'in Ra'eez na rasa bakin da zan maka godiya, hakika zuwanka wannan kotun alkhairi ne a wajena, so biyu kana ceto ni daga yanke hukuncin danasani, bazan iya biyanka da komai ba wallahi, nagode sosai, sam banyi tunanin haka abun yake ba, shiyasa wanda nasa yaje yayi mani binciken yana kawowa ban tsaya dubawa ba na baka saboda nasan na yarda da kai, ashe abubuwan da suke ciki ba gaskiya bane, nagode sosai da ka sake bincike, duk da kayi kok'ari baka fito fili ka nuna kasan gaskiya ba, amma kayi aikin da yakamata ace Brr. Bajinta ne yayi, tabbas nasan wannan shari'ar ta yau ta juya ma mutane kai, domin ku duka lauyoyin an rasa gane a wane b'angare kuke, gaskiya nagode sosai, shima Brr. Bajinta ya taimaka daya gyara kuskuren da ya kusayi. Murmushi Ra'eez yayi yace ai bakomai duk taimakon kaine, nima nasan bazaka bani abinda za'ayi rashin gaskiya aciki ba, hakan yasa dana duba shedar nasan baka duba ba, shiyasa banyi maka magana ba naje na sake sabon bincike. Alhaji Barau yace naji dad'i sosai tunda kasa bamuji kunya ba. Ra'eez yace ina son zanje gida kaina yamun nauyi ne. Murmushi Alhaji Barau yayi yace haba bakomai kaje kawai nima yau da wuri zan tashi nagaji. Tashi yayi yana masa sallama, da sauri Alhaji Barau yace zaka lek'a wajen mutuniyar ko? Murmushi ne ya kwace ma Ra'eez babu shiri, duk'ar da kai yayi alamun kunya yayi waje da sauri. Dariya Alhaji Barau yasa yana fad'in Allah nagode maka daka zab'a mani suriki nagari, gaskiya Raheena tayi dace, Allah nagode maka da banyi saurin sata ta fiddo da miji ba ashe yana zuwa. Da k'yar Jabeer ya bar Ra'eez dan yace sai ya tsaya ya bashi labarin yanda akayi, shi kuma Ra'eez yace ya gaji sai dai suyi waya anjima. Babu yanda ya iya dole ya kyaleshi ya tafi. Bayan sunyi sallama da Jabeer yana kok'arin shiga mota yaji anyi masa sallama. Juyowa yayi tare da amsawa. Murmushi ya saki ganin kamar yasan fuskar wanda yake tsaye. Hannu ya mik'a masa yana fad'in barka da kok'ari Brr. Ra'eez ina tayaka murna akan wannan nasara da kayi a wannan shari'a. Hannu Ra'eez ya bashi yana fad'in nagode, amma kamar nasan fuskar nan? Murmushi yayi yana fad'in *Rafeek Labaran Zaki*, Ma'aikacin gidan redion *Liberty*. Jinjina kai Ra'eez yayi yana murmushi yace yanzu kam na tuna, nagode Rafeek amma ai ba nine nayi nasara ba. Murmushi Rafeek yayi yana fad'in wanda ka kare dai ya faad'i amma ai kaine hasken shari'ar, gaskiya kayi matuk'ar burge ni, na saurari shari'ar ka ta farko a wannan kotun, duk da alokacin ana gamawa na tafi saboda saurin da nakeyi, naso mu had'u amma wani aiki yasha kaina ga tafiye-tafiye, sai a wannan karon naji labarin wannan shari'ar shine nazo domin naji yanda zata kasance, sai gashi nazo nasha mamaki, gaskiya kai d'in na daban ne. Ra'eez yace nagode. Rafeek yace gaskiya ina so mu kulla abota idan bazaka damu ba, yanzu naga kana sauri amma zan amshi lambarka duk lokacin da kake da lokaci zan iya kawo maka ziyara. Kallonshi Ra'eez yayi, yasan dai ya girme mashi sosai, sai yaji kunya da yace zasu kulla abota. Kamar Rafeek yasan abinda yake tunani yayi saurin fad'in nayi maka tsufa ko? Dariya Ra'eez yasa yana girgiza kai. Rafeek yace ita abota ai ba'a duba girma, idan na yarda da hankalin mutum ina abota dashi koda na haifeshi bare kuma nasan ban haife ka ba, dan haka kada ka damu kawai naji ka kwanta mani ne. Jinjina kai Ra'eez yayi yana fad'in nagode Yayana, kada ka hanani kiranka da haka domin nima naji inaso na kiraka da hakan domin ina buk'atar hakan. Murmushi Rafeek yayi yana fad'in nima ina buk'atar samun K'ani domin na rasa nawa shekaru da yawa, amma tunda na samu wani nafi kowa farin ciki. Wayarsa ya mik'a mashi, amsa yayi yasa masa lambarsa ya kirashi yana fad'in ga tawa nan, sai munyi waya nagode. Ra'eez yace nima nagode. Mota yashiga yana kok'arin kunnawa wayarsa tayi k'ara, yana dubawa yaga lamba ce, yana d'auka yaji muryar Sameer da alamun kuka. Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in lafiya Sameer? Cikin sanyin murya Sameer yace ina so mu had'u ne ko zaka mun kwatancen gidan ka? Ra'eez yace kada ka damu bara nazo Mamanka ma tace tana son gani na. Sameer yace nagode sai kazo. Kashe wayar yayi yana murmushi, yaso yaje gida ya huta anjima yaje wajen Ummunsa amma dole yaje yaji dalilin kiran..... Ur's. Nabeelert Lady🖋[3/10, 8:39 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.* 3⃣0⃣ Cikin kuka Sameer ya rungume Ra'eez yana fad'in nagode sosai Ra'eez da abinda kamun, wallahi yanzu ina jin sanyi araina, gashi dai na girma amma na kasa gane hakan, abinda nake so yanzu naje na nemi yafiyar Halimatu, da zata amince dani wallahi zan aureta ma. Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in bakomai kadena kuka, tunda dai har kayi nadama Allah zai yafe maka, sai dai kaje ka nemi yafiyar Halima, idan da hali zaka iya tuna sauran matan da ka lalata ma rayuwa suma kaje ka basu hak'uri sannan kayi masu alkhairi hakan zaisa ka sake samun nutsuwar zuciya sosai. Zama Sameer yayi yana fad'in zanje, wallahi zanje Ra'eez, duk da nasan ba lallai bane na iya samun wasu amma duk matan da nayi harka dasu nasan su, nagode Allah da basu da yawa kuma zanje na nemi yafiyarsu, amma ni ina son kashige mun gaba muje gidan su Halima. Ra'eez yace kada kadamu zan zo muje, amma shawarar da zan baka ka ajiye kudirin ka na son aurenta a gefe, ina mai tabbatar maka Halima bazata amince da kai ba, duk da hakan taimako ne agareta amma baza ta amince ba, gara ka bata hak'uri idan akwai taimakon da zaka sake mata kayi mata kaje ka cigaba da istigfari ka samu wata mata can daban ka aura hakan zai fi maka kwanciyar hankali. Jinjina kai Sameer yayi yana fad'in shikenan, dama tausayinta ne yasa nace zan aureta badan soyayya ba, saboda dama sha'awarta kawai nakeyi amma zanyi yanda kace. Ra'eez yace kaga tunda baka sonta gara ka hakura, domin shi aure soyayya ce jigonshi, Allah ya k'ara tsare gaba. Sameer yace amin, amma dan Allah a ina ka samu hoto na? Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in tunda komai yawuce ai shikenan ba sai kaji ba. Sameer yace shikenan, ai nasan sirrin ku ne na lauyoyi na barshi. Maman Sameer ce tashigo bakinta d'auke da sallama. Bayan sun gaisa ta kalli Ra'eez tana fad'in nagode sosai, dama godiya nake so nayi maka domin ka taimake mu, sam banyi danasanin fad'uwar mu ba, domin gata kayima Sameer, gara mutum yaji kunyar duniya akan ta lahira, gashi ta silarka Sameer ya natsu, shima Alhaji da yayi fushi na sameshi nayi masa bayani kuma ya fahimce ni yace ayi maka godiya yana jin kunyar ka ba zai iya fitowa ba. Ra'eez yace haba babu komai Allah ya tsare gaba. Sukace amin. Kallon Sameer tayi tana fad'in Alhaji ya tura maka duka kud'in da za'a kai kotu, sai ka shirya gobe kaje Ra'eez yayi maka jagora ka kai kud'in a aika ma su Halimar. Sameer yace nagode Mamy, kuma Ra'eez yace zai rakani wajen Halimatu na bata hak'uri. Mamy tace angode sosai Ra'eez. Tashi Ra'eez yayi yana fad'in nizan tafi, Sameer sai munyi waya kila ko zuwa goben ne sai muje can. Tashi Sameer yayi yana fad'in nagode sosai. Mamy tace ka gaida gida dan Allah karik'a zagayowa muna gaisawa. Ra'eez yace insha Allahu. Sallama yayi mata suka fita shida Sameer. Sai da ya shiga mota kafin Sameer ya rufe masa k'ofar yana masa godiya. Sai da ya b'acema ganinsa kafin ya koma gida cike da farin ciki. *** *** Sai yamma sosai ya isa asibiti, bayan sun gama shiriritar su da Ummunsa ya wuce ofis d'in likita dan Dr. Saddek ma yazo yana jiranshi. Bayan sun gama gaisawa Dr. Saddek yace gaskiya Ra'eez jikin Ummunka yayi sauki sosai, domin a hoton da mukayi mata akwai cigaba sosai, matuk'ar zata cigaba da tunawa da abubuwan da suka faru abaya to zata dawo hankalinta, shiyasa yanzu an canza mata magani kuma akwai cigaba. Ra'eez yace nagode sosai likita Allah ya saka da alkhairi, bansan da abinda zan saka maku ba. Dr. Sadeek yace haba ai babu komai, Allah dai ya bata lafiya. Ra'eez yace amin. Sallama yayi masu yawuce gidan su Rumaisa. Tun a hanya Jabeer ya kirashi akan zaije gidansa sai Ra'eez yace ya sameshi gidan su Rumaisa. Dariya Jabeer yasa ya fara zolayarsa, be kulashi ba ya kashe wayar yana dariya. Yana zaune bayan sun gama gaisawa da Mama tana masa murnar nasarar da yayi Jabeer ya kirashi. Tashi yayi yaje ya shigo dashi. Bayan sun gaisa da Mama tasa Rumaisa ta kawo masu abinci. Ra'eez yace Mama ki barshi an kusa kiran sallah idan mukayi sai muci. Mama tace ai shikenan. Jabeer yace Rumaisa bazaki fito mu gaisa ba? Murmushi Mama tayi tace ai tana jinka. Ra'eez yace ya akayi yau bata je islamiya ba ma? Mama tace kanta ne yake ciwo harta shirya zataje naga yanda jijiyoyin kanta suka tashi shiyasa nace tasha magani ta kwanta sai Abdallah ne kawai yaje nasan shima yanzu yana hanya. Cike da damuwa Ra'eez ya kalli d'akin Rumaisa, badan yana kunyar Mama ba sai yaje ya ganta. Jabeer yace Allah ya bata lafiya ciwon kai beda dad'i. Mama tace amin. Mama tace ya shari'ar taku ta kasance kuma? Zunguro Ra'eez Jabeer yayi yana fad'in ana magana fa. Harara ya buga mashi yana kallon Mama. Murmushi tayi tana fad'in kaje ka duba jikin Rumaisar kafi jin dad'in bamu labarin. Rufe fuska Ra'eez yayi yana fad'in kai Mama! Dariya tasa Jabeer yace Mama ashe dai kin harboshi? Murmushi Mama tayi tana fad'in bara nashiga ciki na kira maka ita. Da sauri Ra'eez yace dan Allah Mama ki zauna dama labarin nazo baki. Dariya Jabeer yasa yana fad'in haka ne Mama kizauna nima labarin zai bani sai ja mani aji yake. Zama tayi tana fad'in ina jinka...... Labarin yanda shari'ar ta kasance ya bata har da zuwanshi gidansu Sameer. Jabeer yace saura bayani akan hoton Sameer da yanda ya amsa laifinsa. Ra'eez yace wallahi idan maye ne kai ka kama mutum sai ka cinyeshi duka. Jabeer yace naji kawai ka fad'a mana. Dariya Ra'eez yayi yana fad'in d'azu ma sai da Sameer ya tambayeni amma naki fad'a masa. A cikin week end da na fad'a maka zan had'a komai, duk iya bincike na na rasa yanda zan samo shedar da zata nuna Sameer ne ya aikata laifin, Baba na kira nake tambayarsa basu da wani abu da zai nuna Sameer ne ya aikata laifin. Sai yake fad'a mani alokacin daya d'aukota zasuje asibiti yana kok'arin gyara mata hijabinta yaji wani abu a akanta, yana dubawa yaga zobe shine ya cireshi ya aje, gashi nan ma zaije ya kaima Brr. Bajinta dan yana tunanin na Sameer ne. Cikin sauri nace masa ya dakata zanje na amsa dan nasan ko ya bama Brr. Bajinta bazaiyi amfani dashi ba, bayan na amso nazo ina tunanin yanda zanyi dashi. Komawa nayi unguwar su Sameer cikin sa'a na samo lambar wayarsa. Bayan na ajeta sai na shiga Whatsapp ina dubawa ko zan ganshi, cikin sa'a sai gashi, ina dubawa naga babu hoto a Dp d'inshi, har zan fita sai kuma na hau status ina cikin dubawa kawai naga ya d'ora wasu hotunanshi, yan dubawa sai naga hannunsa sanye da irin zoben da aka bani, saurin d'aukar hoton nayi. Ban b'ata lokaci ba naje aka wanke mani hoton, sosai naji dad'in wannan hujja, ana gobe za'a shiga kotu nayi wani tunani, sai kawai na daure na kira Sameer, har ya kwanta bacci amma ina fad'a masa nine yayi saurin tashi. Nan nake tambayarsa ya tabbata be bar wata sheda da zata tonashi ba? Sai yace mani yana da wata azurfa kuma tun bayan da abun ya faru be ganta ba, yasan kuma baya rabuwa da ita. Anan na fad'a masa zanyi kok'arin nemota abinda nake so dashi ya fad'a mani gaskiya. Sai yace mun be aikata komai ba. Sai nace masa amma yace mun bayan abun ya faru bega zobensa ba. Ganin na ganoshi babu b'ata lokaci ya tabbatar mani shine ya aikata laifin amma na rufa masa asiri, nan nayi masa nasiha na kuma ce masa ga zoben a hannuna, idan har ya iya fad'in gaskiya a kotu zan taimaka masa, kuma na tabbatar masa baza'a d'aureshi ba dole zab'i biyu za'a bashi nasan kuma Iyayensa bazasu bari a d'aureshi ba. Anan ya amince zeyi abinda nace, amma nace masa kada ya fad'i gaskiya har sai na nuna zoben sannan. Kaji yanda mukayi dashi. Jinjina Jabeer yayi masa yana fad'in gaskiya kai d'an baiwa ne Ra'eez, Allah kad'ai yasan irin baiwar da yayi maka amma ka gode masa. Mama tace gaskiya kayi kok'ari, kaga ka fita daga zargin kowa, Allah dai ya k'ara tsare ka kuma ya baka sa'a akan shari'ar da za.... Saurin tashi Ra'eez yayi dan yasan abinda Mama zata fad'a shi kuma baya son Jabeer yasan komai yanzu. Kallonshi tayi suna had'a ido yayi mata alama, nan take ta gane abinda yake nufi. Murmushi tayi tana fad'in duk son ganin Rumaisar ne baza'a tsaya na k'arasa addu'ar ba. Jabeer yace idan ba ya ganta ba hankalinsa ba zai kwanta ba, ni Allah ma yasa ka bamu labarin dai-dai. Duka Ra'eez ya kai mashi da sauri ya mik'e yana dariya. Tashi Mama tayi tana fad'in ai bakayi kokowa kana yaro ba gara kayi k'ari. Turo baki Ra'eez yayi yana hararar Jabeer da yake masa dariya. Bayan Mama ta tashi ta turo Rumaisa. Fitowa tayi sanye da hijabi dan kanta yayi sauki. Zama tayi tana gaishe su kanta ak'asa. Saurin matsawa Ra'eez yayi yana fad'in Pretty na ya kan naki? Murmushi tayi tana fad'in ya warke ai. Ra'eez yace bana son wasa da lafiyar ki kizo muje asibiti. Jabeer yace kaji mani mutumi, tace ta warke zaka jajibo mata wani asibiti. Ra'eez yace malan ba ruwanka, kai da ko tsuntsu baka kiwo taya zakasan yanda ake kula da mutum ma, dan Allah idan ana maganar Iyali kadena tsoma baki. Baki Jabeer ya rik'e yana kallon Ra'eez. Gwalo yayi masa ya zauna gaban Rumaisa ya juya ma Jabeer baya yana dariya k'asa-k'asa. Tashi Jabeer yayi yana zungurinshi da k'afa yana fad'in ni zan wuce bazan iya tsayawa kallon kayan haushi ba. Dariya Ra'eez yasa yana fad'in kaje kayi fira da Baba Madu yanzu zan fito muje masallaci. Wucewa Jabeer yayi yana murmushi, sai da ya kai k'ofa sannan yace daga masallaci wajen Raheenar ka zamuce ko dan nasan shine dalilin da yasa kace nazo nasan baka iya zuwa kai kad'ai. A zabure Ra'eez yayi kanshi jin Bom d'in da yake had'a masa. Da gudu Jabeer yayi waje yana dariya. Kwafa Ra'eez yayi ya dawo wajen Rumaisa kada ta yarda da abinda yace. **** **** Kai amma Alhaji ka tsallake rijiya da baya, gaskiya Ra'eez d'an albarka ne, shiyasa nace maka gara azo ayi maganar auren su da Raheena tun kafin wata ta kwace matashi. Gyara zama Alhaji Barau yayi yana fad'in abinda nake tunani kenan, jira nake yazo nasa Raheena tayi masa magana na fad'a masa ya turo iyayenshi ayi magana dan bana son aja bikin tunda mu duka kowa yana da halinsa. Momy tace yauwa Alhaji dan Allah kada yawuce wata d'aya, kaga sai ka bani kud'i muje Dubai nida Raheena mu zab'o kayan da take so, idan so samune a cikin sati mai zuwa muje. Alhaji yace haka ne, bakomai ku fara shiri zansa a nema maku Visa zuwa asabar sai ku tafi, dama bani da matsala akan kud'i dan akwai su a account kawai tura maki zanyi. Murmushi Momy tayi tana fad'in dole ayi bikin da zai girgiza mutane, naji dad'i da muka tara yanda kowa zaizo ya dangwali arziki. Alhaji yace ai da wuri zan bugo kati saboda kowa ya samu dan wannan babban biki ne. Momy tace Allah ya k'ara girma. Yace amin. **** **** Washe gari tunda wuri Ra'eez yaje wajen aiki, yana zuwa kai tsaye d'akin ajiyar tsofaffin kundi ya nufa yana addu'ar Allah yasa mai kula da wajen yazo. Cikin sa'a ya sameshi, da sauri ya k'arasa ya fara gaishe shi kasancewar babban mutum ne. Murmushi mutumin yayi yana fad'in Malan Ra'eez ya gajiyar shari'ar jiya kuma? Ra'eez yace lafiya lau gajiya tawuce *Kawu Datti*. Murmushi yayi cikin jin dad'in abinda Ra'eez ya kirashi dashi. Kallonshi Ra'eez yayi yana fad'in dama Kawu Datti akwai wata alfarma da nake son na nema awajenka idan babu damuwa. Kawu Datti yace haba bakomai fad'i koma menene kaji Ra'eez. Cike da fatan nasara Ra'eez yace dama akwai wani kundi da nake son dubawa ne domin jiya Iyalan mutumin suka sameni ganin mun kammala wannan shari'ar suka kawo mani wata magana data girgiza ni, duk da nasan abun akwai wuya amma sun roke ni na tausaya masu kuma na masu alk'awarin zanzo na duba kundin ko bazan iya yin komai akai ba, shine nake son ka taimaka na duba kuma inason abun ya zama sirri dan Allah. Murmushi Kawu Datti yayi yana fad'in kada kaji komai Ra'eez, kasa aranka tamkar da kurma kayi magana, domin bazan iya fidda sirrin makiyina ba bare kuma kai, wallahi Ra'eez tun shari'ar da kayi akan 'Yar uwata nake jinka araina, nasan baka san Amina 'yar uwata bace, idan baka manta ba shari'ar ka ta farko wata Amina daka tsaya mawa, to ita d'in tamkar 'Ya take awajena, kuma mijinta shine silar zamana anan gashi har yanzu ina cin gajiyar aikin, dan haka ka d'auke ni tamkar d'an uwanka bazan tab'a cin amanar ka ba. Jinjina kai Ra'eez yayi cike da farin ciki yace nagode Kawu Datti, shari'ar anyita ne shekarar 2008, kila kana nan lokacin da akayi ta ma. Jinjina kai Kawu Datti yayi yana fad'in tabbas ina nan, domin na fara aiki anan a shekarar 2005, duk wata shari'a da akayi a bayan wannan shekara babu wadda ban sani ba sai dai na manta, matuk'ar na zauna na saurareta kuwa to nasanta, kuma duk wasu kundi suna cikin d'akin nan nida abokin aikina muke kula dasu dan yau ma na amshe shi aiki. Ra'eez yace amma naji dad'i nasan kila kasan shari'ar, dama ina so na samu wanda yasan shari'ar saboda ban tsaya na fahimci abinda suke nufi ba, sunce nayi kok'ari na duba kundin zan fahimci komai. Kawu Datti yace akan me akayi shari'ar? Ra'eez yace akan tsohon shugaban Kwastam Alhaji Hamza Maiwada wadda aka mik'a direbansa Malan Sani gidan yari akan laifin shine ya kashe shi kuma yayi yunkurin yima matar Alhajin fyad'e silar haka ta samu tab'in hankali. Girgiza kai Kawu Datti yayi yana fad'in kace azzalumar shari'a, ai bazan tab'a mantawa da wannan shari'ar ba, domin tunda na fara aiki ban tab'a cin karo da shari'ar da na zubar ma kwalla kamar k'aramin yaro ba irin wannan, kai Ra'eez wata shari'ar sai a lahira, amma Allah bazai bar azzalumai ba, domin wallahi tun a lokacin kawai naji ban yarda da shari'ar ba, dan dai an gabatar da shedu masu kyau, amma tabbas nasan akwai munakisa a shari'ar. Kwalla ne ya ciko ma Ra'eez yayi saurin kauda kai yana kok'arin maidasu. Kawu Datti yace kayi hak'uri yanzu mutane sun fara zuwa, bana son kowa yasan abinda zakayi, domin naji ajikina zaka taimake su, ka bani lambarka zanyi kok'arin nemo maka kundin na kawo maka shi a b'oye ba tare da kowa ya sani ba, idan yaso sai ka kwafeshi ka maido amayar gudun matsala. Murmushin jin dad'i Ra'eez yayi yana masa godiya. Lambarsa ya bashi shima ya bashi kafin yayi masa sallama ya tafi, sosai yaji dad'i da Allah yasa Kawu Datti ya iske dan yafi Malan Salisu fuskar kamala. Wajen k'arfe da'ya Sameer yazo ofis d'in su Ra'eez, waya yayi masa ya fita suka had'u, shine yayi masa jagora ya gama cike komai na shedar biyan kud'in tarar da kotu tayi masa, bayan sun gama yace ma Ra'eez maganar zuwa gidan su Halima. Kallon agogo Ra'eez yayi yana fad'in yanzu lokacin cin abinci ne, ina ganin muyi amfani da wannan damar muje mu dawo. Murmushi Sameer yayi yace nagode Ra'eez, Allah yasa Halima ta yafe mani. Ra'eez yace amin. Jabeer yayima magana yazo suka wuce. Ur's. Nabeelert Lady🖋 [3/10, 8:39 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.* 3⃣1⃣ Jinjina kai Baba Haruna yayi yana goge idonshi yayin da Sameer yake tsugunne akusa dashi shima kukan yake da alamu neman gafara yakeyi. Kallonshi Baba Haruna yayi yana fad'in shikenan Sameer, k'addara ta riga fata, haka Allah ya tsaro ma Halimatu dole sai ta faru kuma, tabbas nasan da ace alokacin da abun ya faru nazo gidan ku na sanar maku bazaku saurare ni ba, da ace kamar yanda kazo ka rok'i yafiya irin hakan ne zai kasance alokacin da zanje gidan ku da farko wallahi bazan tab'a fitar da maganar duniya ta sani ba, amma sanin halin masu kud'i yasa dole sai da kowa yaji wannan maganar, a hakan ma badan wannan bawan Allah Ra'eez ya tsaya mana ba da shikenan ahaka zamu shigar da k'ara amma a tozar tamu kuma a sake b'atama Halima suna, amma duk da haka mungode ma Allah, bakomai, Allah ma muna masa laifi murokesa yafiya kuma ya gafarta mana, ni kama na yafe maka, bara na kira Mahaifiyarta da ita kuyi magana. Bayan sunzo Sameer ya d'ora guiwarsa k'asa ya had'e hannuwansa biyu yana rokon su yafiya. Cikin kuka Maman Halima tace ta yafe masa. Kallon Halima yayi yana sake rok'onta. Jinjina kai tayi tana share hawayen idonta tace na yafe maka, koba komai ta silata Allah ya ganar da kai gaskiya, kuma bazan bijirema Allah ba naki yafe maka ba, ina fatan kamar yanda ka cutar dani kuma ka rokeni yafiya na yafe maka Allah ya d'aukaka rayuwata, yasa ko nan gaba kada na wulak'anta daga ni har zuri'ata. Gaba d'aya suka amsa da amin. Ra'eez yace gaskiya Halima kinyi matuk'ar burge ni, domin kalamanki masu tsada ne sai mai zurfin ilimi ne zai iya amfani dasu, gasu sun fito daga bakin mai k'ananun shekaru, ubangiji Allah ya amsa addu'ar ki amin. Jabeer yace Allah ya k'ara tsare gaba, ga wannan check d'in kud'in ki ne da kotu tace abaki, Baba idan kana da asusu a banki sai muje a ciresu asaka aciki domin zasuyi mata amfani wajen karatun ta. Baba yace gaskiya banda wani asusu a banki, amma inaso aje a bud'e da sunan Halima sai azuba su ciki, hakika badan hakkinta bane babu abinda zaisa na amshi kud'in nan, amma sune zasu taimaka ma rayuwarta wajen inganta, domin burin ta ne karatu musamman a fannin lafiya. Kallonshi Sameer yayi yana fad'in ta kammala makaranta ne Baba? Kai ya d'aga masa yana fad'in sakamakonta ma yayi kyau. Jinjina kai yayi yana fad'in zaka iya barinta taje waje tayi karatun fanin lafiya kamar a Madina? Shiru Baba yayi yana tunani. Ra'eez yace Baba ka barta ta tafi, domin Madina k'asa ce mai kyau, kuma zatayi karatu hankalinta a kwance, sannan zata koyo abubuwa da yawa na addini, a ganina Halima tana da natsuwar da zatayi karatu a waje. Kai Baba ya jinjina ya kalli Halima yana fad'in zaki iya Halimatu? Saurin d'aga kai tayi tana sakin murmushi. Baba yace shikenan na amince, nasan wad'an nan kud'in zasu isheta ta kammala karatun ta. Sameer yace Baba zan bayar da naira million biyar nasan zasu isheta ta kammala karatunta, sannan nine zan sama mata makarantar, wannan itace babbar kyautar da zan bata bisa yafiyarta agare ni, fatana Allah yasa kada mu samu rabo a tsakanin mu. Baba yace nagode sosai, kuma insha Allahu babu rabon da za'a samu, domin tun a asibiti wannan malamar ta kawo mana wani magani tace abata tasha insha Allahu ciki bazai shiga jikinta ba. Sameer yace amma naji dad'i sosai, kuma zanje nayima sister Asabe kyauta domin ta taka rawar gani akan wannan matsala, Allah ya k'ara tsare gaba. Gaba d'aya suka amsa da amin. Ra'eez yace gobe idan Allah ya kaimu ko daga ofis ne zan zo na d'auki Halima muje a bud'e mata asusu a banki. Sameer yace muje na rubuta mata kud'in sai a had'a dasu. Godiya sukayi masu kafin suka masu sallama suka tafi. Bayan sun koma Sameer yace nagode sosai Ra'eez, Allah ya baka abinda kake nema duniya da lahira, ka bani account d'inka ina so nayi maka alheri. Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in ka barshi, badan kud'i nayi maka ba, ko a iya abinda kamun ka biyani. Sameer yace nagode sosai, Jabeer nagode Allah ya huta gajiya. Jabeer yace amin Allah ya k'ara tsare gaba, sai a daure a nemo mata kafin muma muzo mu wuce ka. Dariya suka sa gaba d'aya. Sameer yace insha Allahu zanyi kok'arin haka nima nasan na kusa tsufa damma bani da jikin kiba dan nayi arba'in idan ban wuce ba. Ra'eez yace to Allah ya kawo ta gari. Murmushi Sameer yayi kwalla ta cika idonshi yana fad'in bazan ce maka komai ba domin kace Allah, amma bana tunanin zan samu mace tagari tunda ban kasance nagari ba. Ra'eez yace kada kayi saurin yanke hukunci domin Allah baya duba da haka, abinda yake so ka tsarkake zuciyarka. Sameer yace insha Allahu nagode. Suna shirin sallama wata mota ta tsaya a kusa dasu, kid'an da yake tashi ne a ciki yasa hankalin su ya koma kanta. Wani gaye ne ya fito sanye da k'ananun kaya masu matuk'ar tsada a jikinsa fuskarsa sanye da wani bakin glass mai tsadar gaske. Rufe motar yayi yana taunar cingam. Saurin cire glass d'in yayi yana fad'in Yaya Sameer, saurin k'arasowa yayi yana shafa kai. Murmushi Sameer yayi yana fad'in Fawwaz dama ka dawo k'asar nan? Risnawa yayi yana gaishe shi. Hannu Sameer ya mik'a mashi suka gaisa, juyawa yayi yabama su Ra'eez hannu. Sameer yace lallai Fawwaz ka zama babban yaro da yawa ga abokin ka can hada yara biyu. Fawwaz yace ai bansan meya shiga kan Adnan ba Yaya, ko kai bakayi aure ba sai shi, lokacin muna secondary kamar wayayye amma muna rabuwa shikenan yanemi zama ustaz, bansani ba ko jami'ar da yayi a Nija ne ya sashi komawa haka, shiyasa naji dad'i lokacin da Dad yace waje zai kaini karatu, koda na gama kawai nayi zama na acan sai wancan watan ne na dawo shima Mom ce ta matsa na dawo ta gaji. Sameer yace ai gashi ya zama Baba ya bar ka, ina d'ayan abokin naku? Fawwaz yace Allah sarki Sufwan, har ka tuna mani dashi, ina can Adnan yake fad'a mani mutuwar sa domin kowa yasan mu three stars ne a Kings college amma mutuwa ta rabamu dashi daga zazzab'i na kwana biyu, gaskiya naji mutuwarsa sosai. Sameer yace Allah yajik'ansa, lafiya kazo kotu? Fawwaz yace Dad ne ya aiko ni wajen Abba Barau. Kai Sameer ya jinjina yana fad'in ai kotun taku ce. Murmushi Fawwaz yayi yace kai Yaya. Sameer yace emana, ai na d'auka kaima zaka biyo Dadyn ka ko lauya ka karanta ai yayi. Fawwaz yace Yaya wannan karatun ba irin namu bane. Sameer yace to Allah ya taimaka, ka gaishe da mutanan gidan. Fawwaz yace zasuji agaishe da Adnan amma zanje naga Yaranshi. Sameer yace zasuji. Sallama yayi masu ya wuce yana tafiyar 'yan gayu. Murmushi Sameer yayi yana girgiza kai. Jabeer yace dama wannan shine Fawwaz d'an tsohon Alkalin kotun nan? Sameer yace shine fa, kai duniya babu gaskiya, idan kana da iko da kud'i baka da matsala. Ra'eez yace ai shiyasa mutane suke son kud'i. Sameer yace yaron nan fa alokacin suna makaranta har kisan kai ya tab'ayi amma da yake Mahaifinsa babba ne ko maganar ba'a tada ba, agaban su Adnan yayi kisan sai dai kasancewar su aminan juna ne yasa suka rufa masa asiri, kuma Mahaifinsa ya basu kud'i masu yawa shikenan sukayi shiru alokacin Adnan yana Niga, uhm shikenan maganar ta mutu, yaron ma da sukace ya gansu shima babu labarinsa sai gawarsa aka tsinta, silar haka aka tura Fawwaz waje karatu. Shiru Ra'eez yayi yana tunani, da sauri ya kalli Sameer yana fad'in a wace shekara akayi abun? Sameer yace lokacin dai suna aji shidda dan har sun fara jarabawar fita, ina ganin kamar 2008 ne, E a lokacin Adnan ya kammala makarantarsa. Jikin Ra'eez ne yayi sanyi, tabbas wannan labarin yana da had'aka da yaron da Kawu ya bashi labari, amma zaibi komai a hankali zai had'a kan zaren da sannu. Sameer yace bara na wuce na tsaya ina cinye maku lokaci. Jabeer yace shikenan mungode sai munyi waya. Hannu ya basu yawuce. Dafa Ra'eez Jabeer yayi yana fad'in lafiya kuwa Ra'eez? Ajiyar zuciya Ra'eez yayi yana fad'in me ka gani? Jabeer yace tun lokacin da naji an fad'i mutuwar wannan yaron ka tambayi shekarar da akayi abun naga kamar ka canza. Murmushi Ra'eez yayi yace kawai abun ne ya bani tsoro, dalilin tambayar shekarar ina so nasan shekarunsu har suka iya aikata haka. Jabeer yace to yaran masu kud'i meye basa aikatawa, kai dai kawai ayi sha'ani. Ra'eez yace Allah ya kyauta. Wayarsa ce tayi k'ara, yana dubawa yaga ansa Journalist, murmushi yayi dan ya gane Rafeek ne. Bayan sun gaisa Rafeek yace ko anjima bayan isha'i kana da lokaci na kawo maka ziyara? Ra'eez yace ina nan kuwa, zan turo maka da kwatencen. Rafeek yace to nagode. Kallonshi Jabeer yayi yana fad'in kai da wa? Ra'eez yace wani d'an jarida ne yake son mu had'u bayan isha'i. Jabeer yace sarakan tambaya, sai ka kula kada su saka fad'ar wani abun kasan su da wayon tsiya ga dabara. Ra'eez yace ai tsakanin su da 'Yan sanda da kuma mu ana fafatawa, domin kowa yana da ilimin fasaha da 'yan dabaru, dan haka kada ka damu zan iya bi dashi. Jabeer yace ai nasanka. **** Bayan sun tashi daga aiki sukayi sallama da Jabeer kowa ya shiga motarsa ya tafi. Har Ra'eez ya d'auki hanya wayarsa tayi k'ara, yana dubawa yaga Kawu Datti, saurin tsayawa yayi ya kashe wayar sannan ya kirashi. Cike da farin ciki yace gani nan waje Kawu bara na matso. To shikenan bara na jiraka anan sai ka zo. Kashe wayar yayi cike da farin ciki. Kwankwasa k'ofar da akayi yasa yayi saurin bud'ewa. Shigowa Kawu Datti yayi ya zauna ya rufe k'ofar. Kallon Ra'eez yayi kafin ya d'age rigarsa ya zaro kundu ya mik'a ma Ra'eez yana fad'in ban tsaya dubawa ba kawai na d'auko maka shi kaje ka duba amma ka maidoshi da wuri, Allah yasa kana da abun photo copy dan bana son kaje wani waje ayi maka idan baka dashi gara ka kwafeshi kawai. Ra'eez yace nagode Kawu Datti, kuma babu wanda zai san dashi ina da komai a gidana zanyi na maido maka shi gobe. Kawu Datti yace ina maka fatan nasara. Kud'i Ra'eez ya ciro ya mika masa yana fad'in amin. Girgiza kai Kawu Datti yayi yana fad'in idan na amsa tamkar cin hanci ka bani. Ra'eez yace wallahi Kawu ba cin hanci bane, ai tsakanin mu babu wannan, ka d'auke ni tamkar d'anka dan Allah Kawu. Murmushi yayi ya amsa yana fad'in nagode sosai. Ra'eez yace nima nagode. Sallama yayi masa ya fice daga motar ya koma ofis. Hamdala Ra'eez yayi yawuce gida cike da murna. **** Sai da suga gama firar soyayya da Rumaisar sa kafin yayi masu sallama dan yasan Rafeek ya kusa zuwa. Har bakin mota ta rakashi sai shagwab'a take masa bata so ya tafi. Ra'eez yace kiyi hak'uri ai kullum muna tare, kicigaba damun addu'a domin nakusa fara bincike, dan haka dole ki aramun lokacinki. Rumaisa tace bakomai in dai lokaci nane na baka domin naka ne, kuma ina maka fatan nasara, addu'a kuma kullum ina maka. Murmushi yayi yace nagode Pretty na. Sallama sukayi yawuce. A hanya Raheena ta kirasa, kin d'auka yayi dan baya son damu yasan kuma daya d'auka zata tsaidashi da surutu. Ganin ta cigaba da kira yasa ya d'auka, ko magana batayi ba yace mata yana hanya ta bari wajen 11 zasuyi waya. Kashe wayar yayi yana tsaki ya k'ara gudun motar. *** Lemu da ruwa ya aje masa yana fad'in sannu da zuwa Yaya. Murmushi Rafeek yayi yana fad'in yauwa sannu Ra'eez, yau dai bani da aikin dare nace zan zo mu gaisa sosai. Ra'eez yace ai naji dad'i sosai, naso na fara kai maka ziyara gashi har ka rigani. Rafeek yace ai bakomai, na fad'a maka babu babba a abota. Jinjina kai Ra'eez yayi ya mik'a masa ruwan daya zuba yana fad'in gidan gauro ne babu abinci. Dariya Rafeek yayi yace haba ai babu komai, wata rana idan kayi auren zan zo naci. Kallon Ra'eez yayi yana fad'in gaskiya ka burge ni a shari'ar da kukayi jiya, kuma nayi mamaki da kayi masu haka, sai nake tambayar kaina dama kasan gaskiya ne yasa kace kaine zaka tsaya masu? Girgiza kai Ra'eez yayi yana fad'in Mahaifin yarinyar da ya fad'a mani abinda ya faru yasa nace zan taimaka masu, duk da alokacin na riga na amshi tayin su Sameer. Rafeek yace ai ka kyauta sosai Allah ya biyaka, shima Mahaifin Halima ya burge ni, duk da yana talaka amma ya iya neman hakkinsa, wallahi ina son naga an zalunci mutum ya tsaya akan neman hakkinsa. Ra'eez yace nima ina son irin mutane masu dakakkiyar zuciya haka, shiyasa nace zan taimaka masu sosai. Rafeek yace shiyasa a shekarun baya da aka kashe K'ani na naso mushigar da k'ara amma Baffa yace baya so dole muka hakura, duk da alokacin ina makaranta amma naso ashigar da k'ara. Ra'eez yace Allah sarki, ashe kaima an kashe maka wani, to Allah yaji k'ansa. Rafeek yace amin, har yanzu inajin d'acin mutuwar Naseer, yaro yana shirin kammala secondary d'insa amma aka samu wasu suka kashe shi, kamar marar gata haka aka wurgar da gawarsa. Ra'eez yace wayyo Allah ya saka masa, yana gab da fara sabuwar rayuwa suka katse mashi ita, domin duk wanda ya gama secondary alokacin yake fara shirya burinsa. Rafeek yace wallahi kuwa, a Kings college yake har sun fara jarabawa aka kashe shi, a shekarar su biyu aka kashe a makarantar kuma duk ajinsu d'aya. Saurin kallonshi Ra'eez yayi yana fad'in a wace shekara ne Yaya? Kallonshi Rafeek yayi yace shekarar 2008 ne, ai bazan iya mantawa da wannan shekara ba, alokacin ina jami'a. Shiru Ra'eez yayi jikinsa yana tsuma, runtse ido yayi yana tasbihi ga Allah, tabbas Allah ya fara haska masa akan shari'ar da zai gabatar, domin ayau ya fara had'uwa da abubuwan da sukayi had'aka da rayuwar Abbunsa, tabbas yana buk'atar natsuwa yayi dogon nazari, dole yaje kano yayi shawara da Abbah akan Rafeek, domin yaji ajikinsa shid'in zai taimaka masa da wani abu, yana jin zai iya bari yasan wayeshi da kudirinsa, amma idan Abbah be amince ba shikenan zaiyi yakin shi kad'ai. Dafashi Rafeek yayi yana fad'in Ra'eez lafiya kuwa? Ajiyar zuciya ya saki yana fad'in Yaya abun ne akwai tausayi, wallahi bana so naji an kashe mutum, kawai ina hango yanda mutum zaiji alokacin da ake kashe shi, Allah yajikansu da rahma. Rafeek yace amin. Amma Ra'eez ba anan garin kake ba ko? Ra'eez yace a Kano nake aiki ne ya maido ni nan. Jinjina kai yayi yana shirin jefo masa wata tambayar wayarsa tayi k'ara, yana dubawa yaga Baffansa ne. Bayan ya gama wayar ya kalli Ra'eez yana fad'in Baffa ya katse mana fira, wai yana nemana yanzu. Ra'eez yace kai amma banji dad'i ba muna ta firar mu. Rafeek yace bakomai idan nasamu lokaci zan dawo dan bana so mu had'u a ofis d'in ku ko namu dan kowa yasan su waye mu, da an gammu tare kowa zai fara tunanin wani abu, dan haka idan ka samu lokaci idan zaka kawo mani ziyara a gidana zakaje. Ra'eez yace insha Allahu nagode sosai. Tashi yayi yana fad'in nima nagode. Har bakin mota ya rakashi, sai da ya tafi sannan ya rufe gidan, kundin da Kawu Datti ya bashi ya d'auka ya nufi d'akin kayan aikinsa domin ya fara gamawa da su. Ur's. Nabeelert Lady🖋 [3/10, 8:40 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.* 3⃣2⃣ A wannan dare Ra'eez kashe wayarshi yayi dan baya son damu, sai da ya gama copying komai kafin ya maida komai yanda yake yasa a leda dan kada ya manta, d'akinshi ya koma ya fara duba takardun. A hankali ya gama karanta komai, ya mai-maita yafi so ukku, hawaye ne kawai suke zuba a idonshi, yana kallon abun kamar yana wajen yake faruwa, jiyake ina ma shine lauyen da yayi shari'ar a wancan lokacin, domin ga hujjoji nan da yawa daya kamata akare Kawu dasu amma ba'ayi amfani dasu ba, tabbas yasan lauyen daya kare Kawu sarewa yayi alokacin shiyasa be kula da hujjojin ba. Jin kansa yana ciwo yasa ya tattara komai ya tura k'asan gado dan yasan anan ne kawai zasu b'oyu, duk da shi kad'ai ne agidan dole ya fara b'oye duk wata sheda tashi saboda ayanzu zai fara fuskantar kalubale saboda da manyan mutane zai gwabza, zesa rayuwarsa cikin had'ari, idan yana da tsawon rayuwa shikenan, idan kuma akan kwato ma Mahaifinsa hakkinsa zai rasa ransa a shirye yake daya bada ranshi. Bayan ya adana komai ya kwanta yana tunanin ta yanda komai zai kasance da haka har bacci yayi gaba dashi. **** **** Washe gari tunda wuri ya isa ofis, sai da ya bama Kawu Datti kundin yayi ta masa godiya, sosai Kawu Datti yaji dad'i, hankali kwance yaje ya maida inda ya d'auko su. Bayan ya rage aikin da yake gabanshi ya samu ya fita dan yaje ya d'auko Halima su gama komai da wuri. Babu b'ata lokaci suka kammala komai cikin lokaci. Sai da ya maidata gida sannan ya koma ofis. Yana shiga yayi turus yana kallonta zaune a saman kujera Jabeer ya kawo mata lemu tana sha. Saurin tashi tayi tana sakin murmushi, matsowa tayi tana fad'in D. sannu da dawowa wallahi na kasa hakurin rashinka shiyasa nazo, tun d'azu ma naso nazo Momy tace na bari sai anjima. Murmushi Ra'eez yayi ya ratse ta yawuce ciki. Zama tayi tana fad'in na manta ina kwana? Ra'eez yace lafiya lau, daga shigowata ba gaisuwa kin rufeni da surutu. Hannu tasa abaki tana fad'in wallahi mantawa nayi kewarka ce tamun yawa shiyasa duk na rud'e. Ra'eez yace ai na fad'a maki ina da aiyuka agabana. Raheena tace duk da haka D ko waya ne sai ka kirani, bakasan yanda nake shiga damuwa ba idan banjika ba, dama kai ba kirana kake ba ni kuma na kira kace kana aiki. Ra'eez yace daga yau kada ki sake zuwa wajen aiki na, duk macen da take iya bin namiji to bata da daraja a idon kowa, kuma ni bazan iya auren macen da take bina ba, domin zan rik'a ganin kowama haka kike masa. Saurin tashi tayi tana fad'in Allah ban tab'a bin kowa gidanshi ba, kaima dan ina sonka shiyasa na biyoka amma kayi hakuri bazan sake ba. Kai ya d'aga ya jawo wasu takardu yana fad'in hakan zaifi maki. Jabeer ne yashigo hannunsa d'auke da leda da alamu wani abu ne a ciki. Tsaye yayi yana kallon Ra'eez. Jaka Raheena ta d'auka tana fad'in Jabeer zan wuce. Saurin kallonta yayi yana fad'in ban gane ba, keda kikace mun wuni kikazo mana taya zaki tafi kuma? Murmushi tayi tana kallon Ra'eez tace dama Momy ce tace nazo zata aike ni. Kallon Ra'eez Jabeer yayi yana murmushi. Kauda kai yayi yacigaba da aikinsa. Jabeer yace shikenan ga wannan sai ki tafi dashi. Amsa tayi tana godiya. Jabeer yace ki gaishe da Momy sai mun leko, Yallab'ai sai kaje ka rakata ai. Harara Ra'eez ya aika masa. Raheena tace haba Jabeer ya kake son bama D wahala bayan yanzu ya dawo, ka barshi ya huta, kallon Ra'eez tayi tana fad'in D kayi aiki lafiya amma kada ka matsa ma kanka dan Allah. Murmushi yayi yana kallonta, sai kuma ta bashi tausayi ganin yadda tayi kok'arin kareshi a wajen Jabeer, tabbas yasan zuwa yanzu Raheena ta canza sosai. Tasowa yayi yana fad'in nagode Raheena da ziyara ki gaishe da Momy idan na samu lokaci zan zo nima. Murmushi ta saki tana jin wani dad'i. Iyaka bakin k'ofa ya tsaya dan baya son kowa ya ganshi da ita. Sai da ta tafi kana yashigo ciki. Dariya Jabeer yasa yana fad'in Allah ya shiryeka abokina. Tsaki Ra'eez yayi ya zauna yana fad'in zaka fara ko? Jabeer yace kai d'in ne sai a hankali wallahi kana wahalar da Raheena sosai. Ra'eez yace ai sai ka rama mata. Jabeer yace ni na isa, kawai tausayinta nakeyi, saboda kai duk ta canza, kalli yanayin shigarta komai ya canza, wallahi tausayi take bani, irin su Raheena zasu iya yin komai akan abinda suke so, kuma ko aurensu kayi baka tab'a samun matsala dasu. Tab'e baki Ra'eez yayi yana fad'in kaga malan ina da aiki gara kaje kayi hidimar gabanka. Rik'e baki Jabeer yayi yana fad'in lallai kam, ya Allah ka nuna mani ranar da Ra'eez ze fad'a son Raheena. Tofar ta miyau Ra'eez yayi yana fad'in har abada wallahi, nan take idanuwansa suka canza kala yana b'ata fuska. Shiru Jabeer yayi cikin mutuwar jiki yake kallon Ra'eez. Kasa rubuta komai yayi haka ya rufe takardun da k'arfi yayi saurin barin ofis d'in yana jin wani b'acin rai. Sosai jikin Jabeer yayi sanyi akan abinda ya faru, bai tab'a ganin Ra'eez a irin wannan yanayin ba,daga wannan maganar har zai iya fushi haka, ya d'auka yana son Raheena amma yau ya tabbatar da zahiri, sai dai dole akwai dalili. Ajiyar zuciya ya saki tare da barin ofis d'in. *** Bayan an tashi ya fito ya hangi Jabeer a jikin motarsa yana kok'arin shiga, da sauri ya k'arasa wajensa. Dafashi yayi yana fad'in yau guduwa zakayi babu sallama. Murmushi Jabeer yayi yana fad'in haba Ra'eez, meyasa har yanzu baka d'auke ni kamar yanda na d'auke ka ba? Kasan kuwa yanda na d'auke ka? Wallahi kamar d'an uwana da muka fito ciki d'aya haka nake jinka, amma na lura akwai abubuwan da kake b'oye mani naka, ban gama tabbatarwa ba amma ka sani duk ranar dana tabbatar da hakan aranar zan san matsayina awajenka, domin ni ban b'oye maka komai nawa ba, tun ranar had'uwar mu na sanar da kai komai nawa, amma babu komai bance dole sai ka sanar dani labarin ka ba. Ajiyar zuciya Ra'eez ya saki idanuwansa suka ciko da kwalla, tabbas ya aminta da Jabeer, amma alk'awarin Abbah ne bazai fad'ama kowa labarinsa ba yanzu. Jin motsin Jabeer yashiga mota yasashi saurin shiga yana goge idonshi. Da kallon mamaki Jabeer ya bishi. Hannunsa Ra'eez ya kamo yana fad'in kayi hakuri Jabeer, zanje kano cikin satin nan nayi maka alk'awarin zan sanar da kai labarina idan na dawo. Murmushi Jabeer yayi ya rik'o hannunsa yana fad'in kada kadamu abokina, bana son kana zubar da kwalla, na dad'e da sanin kana da ciwo aranka sai dai bansan komeye ba, amma nasha ganin ka cikin damuwa wani lokacin, dan haka kayi hak'uri da abinda nace maka bazan sake tada maka maganar ba. Murmushi yayi yana fad'in nagode da ka fahimce ni. Jabeer yace bakomai zo mu tafi. Jinjina kai Ra'eez yayi yana fad'in ka gaishe da Mamy. Jabeer yace zataji agaida Rumaisa. **** *** A ranar alhamis ya lek'a gidan su Raheena saboda damunshi da tayi yazo siyi sallama zasuji Dubai ranar asabar. Bayan sun gaisa da Momy Raheena ta shige kicin domin d'auko masa kayan motsa baki. Kallonshi Momy tayi tana fad'in yau dai Raheena hankali zai kwanta kazo, kullum cikin damuwana take kaki zuwa, nace mata ai aikin ku haka yake, shine yau tace zaka zo kuyi sallama. Kai a duk'e Ra'eez yace wallahi kuwa. Momy tace ai gara muje a fara rago siyayyar kayan d'aki dan Alhaji yace baya son bikin yawuce wata guda, shine zamuje Dubai jibi musiyo kayan d'aki, naji tace kaima zaka je kano ko? Kai Ra'eez ya d'aga yana mamakin wannan lamari. Momy tace idan kaje ka gaishe su, ai gara kaje a kammala komai, muma kwana biyu zamuyo kada suzo bamu dawo ba. K'ara duk'ar da kai Ra'eez yayi yana sakin murmushi. Tashi Momy tayi tana fad'in Raheena kuje falon baki nan kada ayita gitta maku. Raheena tace to Momy. Kallon Ra'eez tayi tana fad'in D muje can. Kallonta yayi yana sakin murmushi mai kama da dariya yace ai wucewa zanyi akwai abinda zanyi. Zama tayi tana fad'in kai D zamuyi sallama bazaka tsaya muyi fira ba kuma. Hannu ya mik'a mata alamun ta zuba mashi ruwa. Saurin zuba masa tayi ta mik'a masa tana fad'in yi hakuri ina wuni. Lafiya lau sarkin mantuwa, ya amsa. Murmushi tayi tana rufe fuska. Tashi yayi yana fad'in Allah ya kiyaye hanya zance ko? Murmushi tayi tace nagode kaima ka dawo lafiya, me kake so nasiyo maka? Ra'eez yace dama tambaya akeyi? Girgiza kai tayi tana fad'in shikenan zan kawo maka zab'ina. Kai ya jinjina yana fad'in ki gaida Momy zan wuce. Biyoshi tayi tana fad'in wallahi kamar kada ka tafi. Ra'eez yace dole ko na tafi. Har bakin mota ta rakasa, sai da ya tafi kana ta wuce gida. Daga wajenta wajen Kawu ya wuce, sun dad'e suna tattaunawa kuma ya sanar masa duk kok'arin da yakeyi kana ya fad'a masa zaije kano gobe. Kawu yace agaishe mani da Alhajin kuma insha Allahu zan cigaba da addu'a Allah yashige mana gaba. Ra'eez yace amin, zasuji. Sai da ya fara biyawa wajen Ummunsa kafin yawuce gidansu Rumaisa, daga can bayan ya gama yawuce gida dan yagaji sosai. *** *** Washe gari be tsaya aka tashi dashi wajen aiki ba, bayan yayi ma Alhaji Barau sallama Jabeer ya kaishi filin jirgi dan ta jirgi zai bi. Sun dad'e suna fira kafin lokacin tafiyarsu yayi, haka sukayi sallama ya tafi. *** Jinjina kai kawai Abbah Mansur yake yana kallon takardar da Ra'eez ya kawo mashi hawaye suna fita a idonshi. 'Dago kai yayi yana kallon Ra'eez wanda shima kukan yakeyi bayan ya gama fad'a masa abinda ya faru da kuma wanda ya gani awajen Rafeek da Sameer wanda suka fad'a masa. Hannu Abbah yasa ya goge idonshi yana fad'in tabbas a wannan karon Ra'eez kaine zakayi nasara a kotu, hakika Malan Datti yana da matuk'ar mutunci, sannan na amince maka daka fad'ama Jabeer da Rafeek sirrinka, domin inaji ajikina sune bangon da zaka jingina dasu, sune tsaninka wanda zaka taka zuwa matakin da nakeso kaje, domin na fahimci Jabeer aboki ne nagari, dan haka ka sanar dashi komai saboda duk lokacin daya fahimta da kanshi abotar ku zata iya samun matsala. Ra'eez yace shikenan Abbah zan fad'a masu, dama umarninka nazo nema dan bana so nayi abinda ya kaucema umarnin ka. Murmushi Abbah yayi yana fad'in na sani Ra'eez, nasan bazaka tab'a tsallake umarni na ba, Allah yayi maka albarka. Ra'eez yace amin Abbah. Murmushi yayi yana fad'in zuwa gobe sai ka lek'a wajen Labiba ku gaisa dama tana korafin rashin zuwanka. Ra'eez yace tunda nazo dole naje mu wuni muyi fira. Abbah yace maganar motar fa? Sosa kai Ra'eez yayi yana fad'in Abbah kaga gobe zanje gidan Mamyn Sultan bansan lokacin da zan dawo ba, kuma jibi da wuri nake son tafiya inaga abar motar zan dawo ko nan da wata d'aya sai na kaita gyara. Abbah yace da alamu nakusa sayar da motar nan. Zaro ido Ra'eez yayi yana fad'in kai Abbah, shikenan ko ina can sai ka bama mai gyaranka sai ya duba mani ita kaga ina dawowa sai na tafi da abuna. Murmushi Abbah yayi yana fad'in shikenan zan bashi ya duba maka ita amma yanzu yayi tafiya ni kuma nafi aminta dashi idan ya dawo zan kirashi yazo ya tafi da ita, amma ka sani bazaka je Lagos da ita ba, ko an gyara ta anan za'a barta domin ana kammala wannan shari'ar Kano zaku dawo gaba d'aya sai kacigaba da aikin ka anan. Ra'eez yace haka ne Abbah, nima bani da buk'atar zama a Lagos, muna kammala shari'ar har gidan zan sayar domin nasan Ummu bazata iya komawa gidan nan ba. Abbah yace to Allah yashige mana gaba. Ra'eez yace amin. **** *** Yaji dad'in zuwanshi Kano har yaji kamar kada ya tafi, haka Abbah ya kaishi ya hau jirgi ya tafi cike da kewar juna. Tun kafin ya taso ya sanar ma Jabeer, aikuwa suna sauka ya iskeshi yana jiranshi. Rungume juna sukayi kafin suka shiga mota suka tafi. Jabeer yace wallahi abokina ka canza kwana biyu. Ra'eez yace ba dole ba ina can ana shagwab'ani. Dariya Jabeer yayi yana fad'in naga alama ai. Waya Ra'eez ya ciro ya kira Rafeek. Bayan sun gaisa Ra'eez yace Yaya ko kana wani abu zuwa dare? E dama inaso kazo gida akwai maganar da zamuyi ne. Toshikenan sai kazo nagode. Jabeer yace ina ka samu Yaya kuma? Murmushi Ra'eez yayi yace wannan d'an jaridar da nake fad'a maka ne. Jabeer yace lallai kayi Yaya kuwa. Ra'eez yace idan yazo zan fad'a maku wata magana, dan haka yau muna tare. Jinjina kai Jabeer yayi yace Allah ya kaimu. Ur's. Nabeelert Lady🖋[3/10, 8:40 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.* 3⃣3⃣ Lokacin da Ra'eez ya kammala basu labarinshi babu abinda akeji sai sautin kuka, gaba d'ayansu an rasa mai lallashin wani. A hankali Ra'eez ya zame ya kwanta yana jin wani iri a zuciyarsa, kasancewar shine aka bama labarin da farko shiyasa beji abinda yakeji yanzu ba, dan ayanzu da yake bada labarin abinda ya faru da kanshi sai yakejin wani irin d'aci a ranshi. Sun dad'e a haka kafin Rafeek ya kamo hannun Ra'eez yana fad'in tabbas Yaron da Abbunka ya rage ma hanya Naseer ne k'anina, domin a ranar shima aka tsinci gawarsa, duk da bani da masaniyar haka amma zuciyata ta bani hakan, domin kace Kawunka ya fad'a maka yaron da suka d'auko yace abokinsa ne yaron da suke magana alokacin an kashe a kings college, tabbas ina zargin mutane iri d'aya ne suka aikata kisan Abbunka da Naseer, banbancin shi Abbunka bayan an kashe shi anyi amfani da allura, amma da wuya idan allurar aka fara masa, domin ance akwai sahun hannu na shaka, haka shima Naseer shakeshi akayi har ya rasu. Ajiyar zuciya yayi yana fad'in dole akwai abinda Naseer ya sani agame da mutuwar abokinsu wanda Sameer yace Fawwaz ne ya kashe shi, tabbas wannan yaron da Adanan k'anin Sameer yace ya gansu shima ankashe shi Naseer ne, amma zamu zauna mu zana yanda komai yakasance, dole akwai abinda yake faruwa, Abbunka - Naseer ⬇ *Fawwaz, - tsohon Alkali mahaifin Fawwaz,- Alhaji Barau,- Alhaji Marusa, - Mr. Kallah*. Wad'annan mutanan suna da alak'a da mutuwar Abbunka, idan ko haka ne Alhaji Barau shine abokin tsohon Alkali a wancan lokacin, kunga Fawwaz yaron Alkali yayi kisa dole su san yanda suka shafe maganar, domin wannan dalilin ne yasa aka tura Fawwaz waje karatu. Saurin gyara zama Jabeer yayi yana fad'in, amma ya akayi Naseer yaje wajen aikin Abbun Ra'eez? Domin a cikin labarin Kawu yace sunzo fitowa suka had'u dashi hakan yasa suka taimaka masa, bayan kuma kace aranar yace ma Hajiyar ku zaije wajen abokinsa Mannir, kuma kace ba wajen unguwarsu bane, to meya kaishi wajen aikinsu Abbunka? Rafeek yace yes! Wannan maganar taka tana kan hanya, a yanzu muna cikin damuwa dan haka mu bari bayan kwana biyu muzo anan domin mu bama kanmu tambaya kuma mu nemo amsa, kafin nan dole sai Sameer yashigo, domin ya had'amu da K'aninsa, sai dai bazamu fad'a masu case d'in Abbunka ba, iya abinda ya shafesu kawai zamu sani, case d'in Abbunka ya tsaya iya mu har zuwa lokacin da komai zai kammala, sannan bayan mun fara wannan aikin dole muna buk'atar ganin Uncle d'in ka Jabeer, domin shine lauyen daya tsaya ma Kawu a wancan lokacin, kaga yanzu yana abuja babbar kotu komai zai zo mana da sauki. Jabeer yace babu damuwa, naji Dady yana maganar zasuyi wani taro k'arshen satin nan na family ne kuma maza kad'ai ne zasu zauna, nasan dole Uncle zaizo dan irin wannan taron baya wuceshi, abinda nake gani mu bari yazo zanyi masa maganar, idan yana buk'atar ganin ku sai muje gaba d'aya. Rafeek yace yauwa komai ma zaizo da sauki, insha Allahu wannan shari'ar da zafi zamu d'auketa, a wannan karon zasu gane kuskurensu, domin zasu had'u da 'yan zamani, kamar yanda sukayi amfani da basira haka zamuyi muma, kuma a hankali zan nemo duk mutanan da suka bada gudummuwa wajen aikata laifi, zan amshi sunayen likitocin da suka kula da gawar Abbu, hatta da wanda ya duba Ummunka inaso na ganshi, sai kuma 'yan sandan da suka kula da case d'in dan nasan yanzu duk sun zama manya, amma komin girman mutum bazai ja da shari'a ba, insha Allahu zamu gudanar da komai, Ra'eez kasa aranka tare zamuyi wannan yaki, kuma insha Allahu zamuyi nasara, sai Kawu ya fito kuma sai an d'aure duk wani mai hannu a cikin wannan laifin. Jinjina kai Ra'eez yayi yana hawaye dan ya kasa magana saboda wani sanyi da yakeji. Kamoshi Jabeer yayi sai yaji jikinsa yayi zafi ga rawar sanyi da yakeyi. Saurin kallon Rafeek yayi yana fad'in Yaya Ra'eez fa beda lafiya. Tasowa Rafeek yayi yana fad'in damuwace ta haifar masa da hakan, ai yana ma kok'ari, akwai ciwo arayuwarshi amma haka yake daurewa domin ya sa burin d'aukar fansa aranshi, dole muje asibiti a aunashi saboda asan irin maganin da za'a bashi dan damuwa tayi masa yawa. Jabeer yace Ra'eez tashi muje asibiti. Girgiza kai yayi yana hawaye. Rafeek yace wallahi sai munje, matuk'ar kana son kammala wannan shari'ar to ka bari a duba lafiyar ka, sannan kasa jarumta aranka kamar yanda Kawu yayi, idan ba haka ba ciwo zai kwantar da kai. Jinjina kai yayi yana kok'arin tashi, kamoshi Jabeer yayi tare da gyara masa rigarsa suka fita waje, rufe gidan sukayi suka wuce asibiti. *** Cire glass likitan yayi yana fad'in Rafeek ya akayi Brr, yake barin damuwa aranshi har haka? Jininsa fa ya hau ga zuciyarsa tana samun damuwa saboda yana yauwan tunani, gaskiya dole akula dashi idan ba haka ba zai iya kamuwa da ciwon zuciya. Jinjina kai Rafeek yayi yana fad'in insha Allahu za'a kiyaye likita, kasan yanayin aikinsu, ga rashin hutu gashi dole sai mutum yana zurfafa tunani, amma duk da haka za'a kula insha Allah. Likita yace dama kana da alak'a da hazikin lauyan nan? Murmushi Rafeek yayi yana fad'in cousin d'ina ne a Kano suke da zama. Likita yace lallai kunyi dace da samun hazikin lauya, dan haka ku kula dashi kada al'umma ta rasa mutum mai gaskiya. Murmushi Rafeek yayi yana fad'in zamu kula insha Allah. Likita yace ba sai mun kwantar dashi ba zaku iya maidashi gida tunda nasan zaku kula dashi acan. Rafeek yace likita inaso ka bashi gado ko na kwana biyu ne, domin Ra'eez yana da buk'atar hutu sosai, idan ya koma gida bazai iya hak'ura beje aiki ba, koda munce kada yaje acan wajen aikin bazasu gane beda lafiya ba, amma idan suka san yana kwance a asibiti dole zasu d'aga masa k'afa. Jinjina kai likita yayi yana fad'in shikenan bara a bashi VIP room domin babban mutum ne. Dariya Rafeek yayi yana fad'in lallai kanaji da Ra'eez, ko dai ya tab'a tsaya maka ne? Murmushi likita yayi yana fad'in ko d'aya, ban tab'a zuwa kallon shari'arsa ba ma, kawai dai yanayin aikinsa ne yake burgeni, domin an bani labarin shari'arsa ta farko, sannan an bani labarin wadda yayi wancan satin, tun daga lokacin kawai nake sonshi. Rafeek yace to mungode, akwai magungunan da za'a siyo ne? Likita yace yanzu kam tunda a nan za'a barshi zamuyi masa komai, kuma nine zan biya domin gwarzo na ne. Tashi Rafeek yayi yana fad'in nagode abokina. Likita yace haba bakomai, muje akaishi d'akin saboda akwai allurar da zan saka masa a ruwa wadda zata sashi bacci mai k'arfi. *** Sai da aka gama masa komai kana Rafeek yace ma Jabeer yaje gida ya fad'ama su Momynsa tunda yace anan zai kwana, amma kada ya fad'a ma Maman Rumaisa tunda dare yayi abarsu zuwa gobe. Jabeer yace ai ba sai naje ba sai nayi masu waya kawai. Rafeek yace baza'ayi haka ba, kwanciya asibiti tana buk'atar shiri, kaje ka fad'a masu nasan kaima bazaka rasa abinda zaka d'auko ba. Jabeer yace shikenan bara naje ai kana nan ko? Rafeek yace ina nan har sai ka dawo zan tafi. *** Bayan mintuna Jabeer ya dawo. Haka Rafeek yayi mashi sallama yace zuwa safe zaizo ya kawo masu kayan kari. Godiya Jabeer yayi masa, har bakin mota ya rakashi sannan ya dawo. *** *** Washe gari wajen k'arfe bakwai da rabi Rafeek ya iso asibiti ya kawo masu kayan kari, alokacin Ra'eez ya fito daga wanka yana zaune ya idar da sallah, dan Jabeer be tashe shi da asuba ba ganin yanda baccinsa yayi nauyi. Tashi yayi jiki a sanyaye dan har lokacin baya jin kwarin jikinsa, zama yayi yana gaishe da Rafeek. Matsowa yayi yana fad'in Ra'eez ya jikin? Ra'eez yace da sauki nagode Yaya. Zama yayi yana fad'in kadena gode mani domin duk abinda zanyi maka dan Allah ne nayi, dan haka bana son godiyar ka, kallon Jabeer yayi yana fad'in kaci abinci kaje gida ka shirya sai ka sanar ma su Mama bayan ka shiryo ka taho da ita sai ta zauna dashi kafin mu taso. Tashi Jabeer yayi yana fad'in ka had'a masa abincin idan naje gida zanci ni. Rafeek yace shikenan amma ka biya ka fad'a masu kaga kafin ka shiryo itama ta gama shiryawa. Jabeer yace to. Sallama yayi masu yana fad'in Ra'eez sai na dawo. **** Cike da damuwa Mama ta kalli Jabeer tana fad'in shiyasa nace ya dawo nan da zama yana ganin mu bazai rik'a damuwa ba, amma ya je ya zauna acan dole yarika damuwa, a d'akin Abbunsa fa yake kwana a saman gadonshi, taya bazai d'aura aure da damuwa ba, amma ka barni dashi dole ya dawo nan duk da yafi sabawa da can amma bazan bari wani abu ya sameshi ba. Jabeer yace haka ne Mama, nima tunda wannan abun ya faru nake wani tunani, amma mujira asallamosa sai musan abunyi. Mama tace shikenan kaje ka shiryo zan k'arasa aiki kafin ka dawo, abinci ma Rumaisa zata tsaya tayi idan ta gama sai ta same ni can ai tasan asibitin. Jabeer yace shikenan sai na dawo. Kallon k'ofar d'akin Rumaisa yayi yana murmushi dan tunda ya shigo ya fara magana ya ganta tsaye tana hawaye. Suna had'a ido tayi saurin sakin labulen. Murmushi yayi yana ma Mama sallama ya fice. ** Ko da sukaje alokacin Ra'eez ya koma bacci anyi masa allura bayan yaci abinci yasha magani. A tare da Rafeek suka fito zasu wuce aiki, Mama sai godiya take masu. Bayan sun tafi ta zauna cike da tausayin Ra'eez. *** K'arfe 12:00 Rumaisa ta iso asibitin, waya tayima Mama ta fito suka shiga ciki, a bakin k'ofar shiga suka had'u da likita tare da Alhaji Barau da Brr. Bajinta. A jingine da filo suka iskeshi yana shan lemun da Mama ta bashi kafin ta fita. Da sallama suka shiga. Kallonsu yayi da idanuwanshi da suka fad'a a dare guda. Murmushi yayi yana masu sannu da zuwa. Shigowa sukayi Alhaji Barau yana fad'in kaga ikon Allah ko Brr. Bajinta, jiya fa mukayi waya yace mun ya dawo lafiya ashe a asibiti ma zai kwana. Brr. Bajinta yace aishi ciwo beda lokaci, idan mutuwa ce ma haka zamu jita daga sama. Hannu ya mik'ama Ra'eez yana fad'in sannu ya k'arfin jikin? Ra'eez yace da sauki. Gaishe da Alhaji Barau yayi. Alhaji Barau yace lafiya lau ya jikin? Ra'eez yace da sauki sosai. Su Mama suna gefe tashiga gaishe su. Kallonta Alhaji Barau yayi yana fad'in lafiya lau ya mai jiki? Mama tace da sauki. Tashi sukayi Alhaji Barau ya aje kud'i masu yawa a gefen Ra'eez yana fad'in ban siyo komai ba ga wannan an saya masa lemu Allah ya k'ara lafiya, zuwa anjima da dare zamuzo tare da Hajiya, amma nasan Raheena tanaji zata taho nan. Godiya Ra'eez yayi mashi fuskarsa a d'aure. Brr. Bajinta yace to Allah ya k'ara lafiya. Sallama sukayi ma su Mama suka fice. Tsaki Ra'eez yayi yana jin wani bakin ciki, hannu yasa ya ture kud'in daya aje suka fad'i k'asa. Matsowa Mama tayi tana fad'in munafikin Allah, da yardar Allah k'arshensa bazeyi kyau ba, zezo ya kawo ma mutane kud'in haram. A hankali Ra'eez yace Mama d'auke su nadena ganin su, ki ajesu idan kika fita ki badasu sadaka. Mama tace sai dai sadakar, amma wallahi ko da yunwa nake kwana bazan iya cin kwandalar munafuki ba. Kwashe su tayi ta nemi bak'ar leda tasa sannan tasasu ajaka. Matsowa Rumaisa tayi idanuwanta cike da kwalla, tsaye tayi a gefen gadon tana wasa da yatsunta. Tashi Mama tayi tana fad'in bara naje waje kila na samu mabarata. Har ta fita Rumaisa bata d'ago kai ba sai hawayen da suke sakko mata. Tsura mata ido Ra'eez yayi shima idanuwanshi cike da kwalla, a hankali yasa hannu ya jawota ta fad'o jikinshi, kamar jira take ta kifa kanta tare da sakin kuka. Lumshe ido yayi hawaye masu zafi suka sakko mashi, tabbas daga jiya zuwa yau yana jin wani irin ciwo a rayuwarshi, amma dole yasa jarumta aranshi matuk'ar yana so yabar asibitin nan gobe. Sun dad'e a haka yana bubbuga mata baya, a hankali tayi shiru tana ajiyar zuciya. Duko da kanshi yayi yana fad'in Pretty kinaso ciwo na ya tashi ne, kinsan dai kukan ki yana d'aga mani hankali sosai, gashi jinina ya hau idan kina kuka zai k'ara hawa. Saurin tashi zaune tayi tana goge idonta. Murmushi yayi yana fad'in ashe dai ba'aso na mutu? Turo baki tayi tana fad'in dan Allah Yaya na kadena maganar mutuwa. Waro ido yayi yana fad'in yau kuma na koma Yaya? Kai ta girgiza tana murmushi. Ra'eez yace to afad'amun sunan. Murmushi tayi tace kai Annur! Dariya yasa yana fad'in yanzu naji. Tashi tayi ta zuba masa abinci, gyara masa filo tayi ya gyara zamansa kafin ta mik'a masa filet d'in. Ido ya tsura mata be amsa ba, jin shiru yasa ta kalleshi. Turo baki yayi yana mak'ale hannu a baya. Murmushi tayi ta zauna gefen gadon ta fara bashi abaki. Haka yarik'a amsa idan yaci d'aya sai yace dole sai taci dan yasan bataci komai ba saboda rashin lafiyarsa. Haka suka cinye hada k'ari, abincin da sukaci sunyi mamaki dan basu san sunci ba. Wajen k'arfe 3:00 Jabeer ya iso, a d'akin waje ya iske Mama tana jan carbi Abdallah yana gefenta wanda Rumaisa taje ta d'aukosa a makaranta. Duk'awa yayi suka gaisa yayi mata ya mai jiki. Mama tace yaji sauki sosai suna ciki kashiga. Tashi yayi yana fad'in Allah ya k'ara sauki. Yana tura k'ofar Rumaisa tana kok'arin bama Ra'eez aiba a baki. Cak ta tsaya tare da duk'ar da kai tana murmushi. Da sallama yashigo yana murmushi. Harara Ra'eez ya aika masa yana gyara zamanshi. Zama Jabeer yayi yana fad'in ae dole a tura Mama waje ashe ana nan ana.... Da sauri Rumaisa tayi waje cike da kunya. Dukan wasa Ra'eez ya kaima Jabeer yana fad'in wannan ai wulakanci ne mutum yana jin dad'i da iyalinsa azo a takura masa. Jabeer yace lallai kam Yaro ka samu, banda wukalanci a asibiti zaku zo kuna soyayya saboda rashin kunya kayi wani kwance ana baka abinci abaki. Ra'eez yace wani ma ya samu hakan, kaga malan bana son sa ido. Dariya Jabeer yayi ya bashi hannu suka gaisa yana tambayarsa jiki. Ra'eez yace da sauki sosai, ai Pretty tana zuwa naji na warke gabad'aya. Jabeer yace da alama yau ita zamu bari ta kwana kaga kafin gobe sai ka koma dai-dai. Dariya Ra'eez yasa yana fad'in wallahi baka da kirki, mutumin ka fa yazo shida d'an kazaginsa. Jabeer yace ina zuwa na fad'a mashi shine yace dole yazo ya dubaka. Ra'eez zeyi magana aka turo k'ofa, Raheena ce tashigo bakinta d'auke da sallama. Jabeer ne ya amsa yana mata sannu da zuwa. Wani b'acin rai ne ya ziyarci Ra'eez, shikenan zatasa Pretty cikin damuwa. Cikin sauri ta k'ara so idanuwanta suna kawo ruwa, gefen gadon tazo zama da sauri Ra'eez yasa k'afarsa a wajen yana mata nuni da kujera. Jiki a sanyaye taja kujera ta zauna ta fara gaishe su. Tashi Jabeer yayi yana fad'in matso da kujerar jikin gadon keda kika zo jinya. Murmushi tayi ta matso tana tambayar Ra'eez jiki. Zamewa yayi ya kwanta yana amsawa. Kallonshi tayi tana fad'in sannu Dear, wallahi bakaji yanda hankalina ya tashi da Dady ya fad'a mun ba, tare muke da Momy tana wajen wasu anan da alamu 'yan uwanka ne shine ta tsaya suna gaisawa. Kai Ra'eez ya jinjina yana fad'in nagode. Momy ce tashigo bakinta d'auke da sallama. Jabeer ne ya amsa mata yana mata sannu. Bayan ta zauna suka gaisheta tayima Ra'eez sannu. Kallon Raheena tayi tana fad'in to ke haka ake zuwa jinyar bazaki zuba abinci ki bashi ba? Murmushi Raheena tayi tana fad'in Momy yanzu zan zuba mashi ai. Momy tace yauwa, matsa ki zauna gefen gadon ki bashi ba sai ya wahalar da hannunsa ba. Saurin juyawa Jabeer yayi ya fita saboda dariyar da ta taho mashi. Da sauri Ra'eez yace akoshe nake yanzu naci abinci. Raheena zatayi magana sai ga Rumaisa ta shigo da sauri, tunda taga Raheena hankalinta ya kasa kwanciya musamman da Momy ta fad'a masu daga inda suke. Ganin Raheena akusa da gadon Ra'eez yasa tayi saurin k'arasawa, bata san lokacin data zauna gefen gadon ta kamo hannun Ra'eez tana fad'in Annur baka buk'atar komai ko? Runtse ido Ra'eez yayi ganin Rumaisa zata rusa masa shiri. A firgice Raheena ta kalli Rumaisa jin abinda tace. Ganin Ra'eez ya runtse ido yasa Rumaisa tayi saurin sakin hannunsa tana fad'in Yaya dama fa Mama tace nazo na tambayeka idan akwai abinda kake buk'ata tunda taga surikarta tazo jinya. Murmushi ne ya sauka a fuskar Raheena da Momy wad'an da sukayi zuru suna jiran k'arin bayani. Da sauri Ra'eez ya bud'e idonshi jin abinda Rumaisa tace, a cikin idanuwanta ya sauke nashi, sai dai ganin yanda idanuwanta suka canza yasashi gano tsananin kishi a ciki. Da sauri Raheena tace lallai wannan k'anwar tamu tana ji da Yayanta, kada ki damu ina nan zan bashi duk abinda yake buk'ata, idan kina son zuwa gida ki huta zaki iya tafiya dan sai dare zan bar nan shima dan bazeyuwu na kwana anan ba da zan kwana dashi. Momy tace sosai kuwa, tunda kinzo zasu iya tafiya su huta dan nasan tun safe suke nan. Kai Rumaisa ta jinjina dan bazata iya magana ba tayi saurin barin d'akin. Runtse ido Ra'eez yayi cike da jin haushin Raheena da Momynta, yasan Rumaisa zata shiga damuwa, ko abinda tayi ganin ya rufe ido ne yasa ta fad'i haka kuma ya gano da biyu ta fad'a. Tashi Momy tayi tana fad'in Ra'eez Allah ya k'ara sauki, zan tafi na barku kuyi firar ku, Raheena idan direba ya maidani zai maido maki motar sai ya koma gida saboda idan kin tashi komawa sai kiyi amfani da ita. A hankali Ra'eez yace nagode. Raheena tace Momy sai na dawo. Momy tace ki kula dashi sosai fa. Raheena tace to Momy. Sallama tayi masu Mama ta wuce. Jabeer da yake kok'arin shiga yaji abinda ya faru dan tunda yaga Rumaisa ta fito idanuwanta jawur yasan akwai abinda ta gani. Yana shiga Ra'eez yayi saurin tashi yana fad'in Jabeer kayana akwai matsala fa, kaje ka gyara komai bana so asamu matsala suyi kura. Murmushi Jabeer yayi yana fad'in da alamu ajiyar tayi kura sosai, bara naje na kakkab'e kada k'ura tayi mata illa. Kwanciya Ra'eez yayi yana fad'in kayi sauri dan Allah. Raheena tace Dear meyasa zaka aje kaya baka rufe ba ai dole k'ura ta b'ata su, Allah yasa ba fararen kaya bane nasan dole a sake wanke su🤣. Kasa rik'e dariya Jabeer yayi da sauri ya fita yana fad'in farare ne tass sosai Raheena yanzu zanje na gyara komai. Raheena tace sai ka dawo. Murmushi kawai Ra'eez yayi yana lumshe ido jin abinda Jabeer ya fad'a. Ur's. Nabeelert Lady🖋 [3/10, 8:40 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.* 3⃣4⃣ Saurin b'oye fuska Rumaisa tayi tana kok'arin goge hawayen da suke fuskarta jin labarin da Jabeer ya bata. Murmushi Jabeer yayi yana fad'in a mana afuwa matar lauya, laifin mu ne da bamu fad'a maki shirin mu ba, amma yanzu ina fatan kin fahimci labarin dana baki, sam Ra'eez baya son Raheena, yana so shima ya rama abinda akayi ma Abbunsa ne. Jinjina kai Rumaisa tayi tana fad'in Allah ya so ban kwafsa ba, ai da farko kansu ya d'aure da na kirashi Annur, amma jin na ambaceta amatsayin surikar Mama sai hankalinsu ya kwanta, nima haka kawai naji na fad'i surikar Mama dan naga yanayin fuskar Yaya kamar beji dad'in abinda nayi ba. Jabeer yace ai kin kyauta, ina fatan kuma zaki taya Ra'eez yakin da yake gabansa, ki d'auka Raheena namiji ce kawai, kuma kirik'a kokarin kaucema had'uwar ku waje d'aya hakan zesa zuciyarki ta natsu. Rumaisa tace wallahi bakomai, ni mai iya sadaukar da farin cikina ne matuk'ar Yaya zai cika burinsa, yau ko cewa akayi saiya aureta zan iya amincewa idan har hakan zaisa ya cika burinsa. Jabeer yace hakan ma bazata faru ba, domin yanzu ne zamu fara aiwatar da komai, kinga ana kammala shari'ar sai musha biki. Murmushi tayi ta rufe fuska. Jabeer yace muje na ajeku gida tunda nazo. Rumaisa tace bara nayima Mama magana. Jabeer yace shikenan. Tare da Mama suka shiga d'akin, mamaki Rumaisa tayi ganin Ra'eez a kwance ya rufe ido kamar me bacci ga Raheena a kusa dashi sai kallonshi takeyi. Saurin amsa sallamarsu Raheena tayi tana matsawa hada duk'ar da kai. Bud'e ido Ra'eez yayi jin muryar Mama. Gyara kwanciyarshi yayi yana fad'in sannu Mama. Murmushi tayi tana fad'in kai ne da sannu, ya jikin naka? Da sauki Ra'eez ya amsa. Kallon Rumaisa yayi suna had'a ido ya kashe mata ido d'aya, murmushi tayi itama ta rama. Mama tace zamu koma sai gobe idan Allah ya kaimu tunda ga Jabeer nan yazo. Ra'eez yace kai Mama, ku bari zuwa dare bana son ku tafi. Da sauri Raheena tace haba ka barsu suje su huta ai akwai gajiya, tunda gashi nazo zan zauna da kai har wajen tara sai na tafi. Murmushi Mama tayi tana fad'in sannu da kokari angode. Turo baki Ra'eez yayi yana fad'in to Rumaisa ta zauna sai ya kaiki ke da Abdallah anjima zai maidata. Mama zatayi magana Raheena tace gaskiya baza'a wahalar mun da K'anwa ba, da ganinta ta gaji taya zaka ce ta zauna bayan ko ta zauna sai dai ta koma wancan falon tunda bazata iya zama anan ba dan a takure take. Murmushi Rumaisa tayi tana fad'in maganar ki gaskiya babbar Yaya, nima bazan zauna ba kada na shiga hakkin ki. Raheena tace to ka gani, Mama kawai kuje ku huta zan kula dashi. 'Daure fuska Ra'eez yayi ya koma ya kwanta, jiyake kamar ya kwad'a mata mari saboda haushi, shi sam beso zuwanta ba yaso ace Pretty d'insa ce akusa dashi yau su sha soyayya amma wannan anacin tazo ta zauna. Muryar Mama yaji tana fad'in to sai da safe kaci abinci sosai kafin kasha magani. Kai ya d'aga yana hararar Rumaisa. Dariya tayi ta wuce tana fad'in Yayana Allah ya baka lafiya kaji. Suna fita Raheena ta matso tana fad'in D ashe ba bacci kake ba kawai ka rufe ido ka barni shiru,. Kauda kai yayi bece komai ba. Hannunshi ta kamo tana fad'in idan ina tare da kai tamkar ahalinka ne a kusa da kai, domin zan d'auke maka abinda bazasu iya d'auke maka ba ma. Saurin zare hannunshi yayi yana mata wani kallo. Baki ta rik'e tana fad'in yi hak'uri wallahi mantawa nayi, zamana akusa da kai sai nake ganin kamar agidan mu muke shiyasa na iya rik'e ka amma ba halina bane. Zeyi magana Rafeek ya shigo. Murmushi ya saki yana fad'in Hajiya Raheena kece mai jinyar kenan? Murmushi ta saki tana gaishe shi, sosai taji dad'i, duk da bata sanshi ba amma tasan abokin Ra'eez ne, lallai Ra'eez yana sonta, gashi har abokanshi sun santa. Zama Rafeek yayi yana fad'in Ra'eez ya jikin? Ra'eez yace da sauki Yaya ya aikin? Rafeek yace akwai wahala, sai yanzu fa na tashi, abinci kawai na biya naci agida. Ra'eez yace sannu da aiki. Shigowar Jabeer yasa Ra'eez ya kalli Raheena yana fad'in ki tashi ki wuce gida magriba ta kusa. 'Bata fuska tayi tana fad'in ka barni sai zuwa anjima bazan iya barin ka a..... Kallon da yayi mata yasa tayi saurin tashi tana turo baki. Murmushi Jabeer yayi yana fad'in wai a ina aka tab'a korar d'an jinya? Rafeek yace ai mace ce ga magriba ta kusa kaga babu dad'i ta zauna nan, da ace babu kowa dan ta zauna ba wani abu bane, amma bana son ina ganin mace a waje da dare domin ba mutuncinta bane. Murmushi Raheena ta saki jin abinda Rafeek ya fad'a, sai yanzu ta gane Ra'eez baya son tayi dare a waje, sannan ga abokansa duk maza yana kishi ta zauna a cikinsu. Jaka ta d'auka tana fad'in D kana da gaskiya, tunda akwai maza a d'akin be kamata na zauna acikinsu ba, wasu ma zasu iya zuwa kaga babu dad'i a kalle maka ni, shikenan zan tafi sai zuwa goben. Dariya Jabeer yayi yana fad'in ai kinsan abokina akwai kishi. Harara kawai Ra'eez yake aiko masa, be kulashi ba yacigaba da fad'in nan gaba kila bazai barmu shiga gidansa ba. Raheena tace ai jin dad'i ne ka samu mai kishinka. Jabeer yace sosai kuwa, ai Allah ya nuna ranar biki. Raheena tace amin. Juyawa tayi tana fad'in D kaci abinci da yawa dan Allah. Rafeek yace zaici, ki gaida gida. Fita tayi tana murmushi. Tsaki Ra'eez yaja yana fad'in wallahi Jabeer kashiga hankalin ka. Jabeer yace daga fad'in gaskiya. Ra'eez yace shikenan, insha Allahu kaine zaka aureta. Dariya Jabeer yasa hada rike ciki yana fad'in amma baka ta kirki, yanzu ka rasa da wadda zaka had'ani sai Raheena, haba ai koda bani da budurwa bazan iya aurenta ba. Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in me yasa kake shiga maganarta to? Jabeer yace kawai ina tausayinta ne, duk da bansan zafin so ba amma ina tausaya mata domin ta kamu da sonka, kuma ma ni bazan iya auren wacce take son wani ba, to na aureta nace na auri wa? Ka auri mace, Ra'eez ya fad'a. Dariya Rafeek yayi yana fad'in wallahi idan mutum yana kusa da ku sai kusashi ciwon ciki saboda dariya, yanzu kai Jabeer ai taimakon ka Ra'eez yayi daya baka ita, domin naga ko 'yar tsana baka da ita. Dariya Ra'eez yasa yana fad'in wallahi kuwa Yaya, kaganshi nan kullum yana gida, lokacin bacci haka yake kwanciya babu mai sashi farin ciki, dan na bashi Raheena ai banyi laifi ba. Jabeer yace sai dai ka bani Rumai.... Kamar walkiya Ra'eez ya diro daga gado, dariya Jabeer yasa yayi bayan Rafeek. Nufoshi Ra'eez yayi sai ga likita ya turo k'ofa. Dariya Rafeek yasa yana fad'in likita kaga marar lafiyar ka ko? Murmushi likita yayi yana fad'in da alama yau zan baku sallama. Zama Ra'eez yayi yana fad'in wallahi da yafi. Dariya suka sa Jabeer yace aikuwa sai jibi. Rafeek yace tunda dai ya warke ai shikenan. Matsawa Likita yayi yana fad'in bara na duba na gani. Har likita ya gama dubashi yana hararar Jabeer. Kallon Rafeek likita yayi yana fad'in gaskiya jikin lauya da sauki, ko yanzu zaku iya tafiya gida. Rafeek yace nima naga alamun sauki gara asallameshi mu koma gida. Likita yace shikenan bara ayi sallah. Jabeer yace mungode. Sai da sukayi sallah kafin suka had'a kaya suka wuce. Kai tsaye gidan Ra'eez suka wuce dan Rafeek yace Jabeer ya kwana acan zuwa gobe sai suje wajen Mama aji abinda ta yanke akan zaman Ra'eez. **** **** Washe gari tare da Jabeer suka nufi gidan su Rumaisa, Mama tayi mamakin ganin su dan sauri take ta had'a kayan abinci Rumaisa ta kai masu. Bayan sun gaisa suka fad'a mata sallamar da akayi masu. Murmushi tayi tana fad'in to Allah ya k'ara sauki, kaga yanzu sai kuje a kwaso kayanshi ga d'aki can ya zauna aciki. Jabeer yace Mama ina ganin abar Ra'eez a gidanshi zaifi, domin a ayanzu akwai shirin da zamu fara kuma yana buk'atar natsuwa, tun bayan da ya bani labarinshi na fara tunanin yanda zan taimakeshi, rashin lafiyarsa da sanin abinda yake damunshi yasa na yanke shawarar komawa kusa dashi kafin Allah ya bama Ummu lafiya, hakan yasa na samu Iyaye na nayi masu bayanin zan koma gidanshi mu zauna, kuma sun amince mun. Jinjina kai Mama tayi tana fad'in gaskiya mungode, dama haka Allah yake, idan ka rasa wani jigo sai ya baka madadinsa, hakika kai aboki ne nagari, Allah ya saka maka da mafificin alkhairin sa. Jabeer yace amin. Rungume Jabeer Ra'eez yayi yana hawaye. Murmushi Jabeer yayi yana fad'in meye na kuka kuma, yanzu ka zama d'an uwana. Bayan sun karya Jabeer ya bar Ra'eez anan yawuce gidansu saboda zaije wajen aiki. Shimfid'a Mama tayi masa a falo ya kwanta dan bacci yake ji saboda maganin da yasha. Sai da Rumaisa ta kammala aikinta kafin taje ta zauna a kusa dashi, duk da bacci yake amma haka ta zauna tana gadinshi. Wayarsa ce tayi k'ara, tana dubawa taga ansa Raheena. Tsaki tayi ta maida wayar silent. Ganin an cigaba da kira yasa ta d'auka. Cikin sauri tace bacci yakeyi. Raheena tace Rumaisa ce? Kai ta d'aga tana fad'in itace. Raheena tace dama naje asibiti akace an sallameshi shine nake son naji inda yake nazo. Rumaisa tace ai bacci yakeyi ki bari zuwa anjima da rana sai amaki kwatance kizo. Ba haka Raheena taso ba amma haka ta daure tayi mata godiya tare da kashe wayar. Murgud'a baki tayi tana fad'in jarababbiya kawai, hakanan kin takuwara ma mijina, wallahi badan shiri bane da na nuna maki iya karki dan bazan lamunci had'a Annur da kowa ba. Haka tayi ta masifa tamkar agaban Raheena take. Ra'eez da tun farkon wayar ya tashi ido ya tsura mata sai murmushi yakeyi ganin yanda ta dage tana masifa ita kad'ai. Kamar ance ta juyo, waro ido tayi ganin Ra'eez ya tashi yana kallonta, da sauri ta yunkura zata gudu yayi saurin jawota ta fad'o jikinshi. Tusa kanta tayi tana mashi shagwaba. Dariya yayi ya tashi tare da cire hannunshi ajikinta yana fad'in babu inda zaki sai kin mai-maita abinda kika fad'a. Rufe fuska tayi ta zame gefe tana fad'in nifa bance komai ba. Ra'eez yace shikenan, amma ki sani ina binki bashi. Saurin d'aga kai tayi tana fad'in naji. Wayarsa ce tayi k'ara, yana dubawa yaga Raheena, kallon Rumaisa yayi yana kallon wayar. Tsam ta tashi tayi waje da sauri. Murmushi yayi kafin ya d'aga. D ina kwana ya jikin? Lafiya lau, ya amsa cike da yanga kamar mace. Wayyo D d'azu na kira Rumaisa ta d'auka wai kana bacci, dama ina so nazo na dubaka tunda ance an sallameka. Yatsina fuska yayi yana fad'in ki barshi bana son kina zuwa kunyar Mama nakeji. Murmushi tayi tana fad'in nikam bazanji dad'i ba idan banzo ba, kasan fa har yanzu gajiyar Dubai bata sakeni ba amma tunda naji baka lafiya naji bazan iya zama ba, muma ranar lahadi muka dawo cikin dare, naso na kira alokacin amma naga dare yayi, da safe kawai Dady ya fad'a mana kana asibiti nan take naji gajiyar ta tafi. Murmushi yayi yana fad'in kun dawo lafiya ko? Raheena tace lafiya lau, kayan suna hanya sai zuwa jibi zasu iso, D bakaga zab'en da nayi mana ba, tsarabar ka tana nan idan kazo zan baka. Girgiza kai yayi yana fad'in ki adana mun ita sai nan gaba zan amsa. Kai ta jinjina kamar yana ganinta tace angama Angona, fatana Allah ya baka lafiya. Ra'eez yace ina so na kwanta. Murmushi tayi tana fad'in ka huta lafiya idan ka tashi ka kirani kada na kira kuma baka tashi ba na katse maka bacci. Ra'eez yace angama. Kashe wayar yayi yana sakin murmushi. Hannu yasa yana shafa wuyansa, ta wani gefen yana tausayin Raheena, bayaso Allah ya kamashi da laifin yaudara, Raheena batayi masa komai ba, asalima lokacin da abun ya faru batasan komai ba, mahaifinta ne me laifin shi yakamata ya amshi hukunci ba ita ba, amma dole ya dakatar da komai koda hakan zai ruguza amintakar da Alhaji Barau yayi masa, domin ko yanzu suka b'ata bazai damu ba, domin lokacin fafatawa yayi. Ajiyar zuciya ya saki yana tunanin hanyar da zaibi dan kada ya cutar da zuciyar Raheena, yasan koya rabu da ita yayi mata gata, domin ta silar shi ta canza rayuwar ta wacce duk wanda ya aureta zaiji dad'in hakan. Lumshe ido yayi yana tunani. *** Har la'asar suna tare da Jabeer, tashi sukayi domin suje gidan su Jabeer daga can su wuce gida. A tare suka fito. Mama tace ina kuma zakuje? Jabeer yace ai gara mu fita hakan zeyi masa dad'i, zamuje gidan mu daga can mu wuce. Mama tace to abincin daren fa? Ra'eez yace Mama kinsan bana cin abu mai nauyi da dare. Mama tace to Jabeer fa? Jabeer yace nima hakan take mama. Murmushi tayi tana fad'in haka kawai kun maida kan ku turawa, ai shikenan sai Allah ya kaimu, amma kasha maganin ka. Ra'eez yace to Mama. *** *** Kamar ya saba da 'yan gidan su Jabeer haka sukayi ta fira, har isha'i suna tare, anan suke jin Kawun Jabeer zaizo gobe. Jabeer yace yauwa idan yazo zanyi masa maganar ka, kaga sai muzo musameshi muji yanda zaice. Ra'eez yace Allah ya kaimu. Wayarsa ce tayi k'ara, yana dubawa yaga Yaya Rafeek, bayan sun gaisa yace yana jiransu a gidanshi tare suke da Adnan k'anin Sameer zasuyi magana akan mutuwar Naseer. Ra'eez yace gamu nan zuwa. Tashi sukayi suna masu sallama suka nufi gida cike da farin ciki, koba komai zasu fara samun hujjar shiga kotu. Ur's. Nabeelert Lady🖋 [3/10, 8:40 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.* 3⃣5️⃣ Kamar yanda nace maku mu ukku ne abokai a kings college, tun farkon had'uwar mu muka kulla abota, duk wanda yazo makarantar atare ya sammu, domin kusan arana d'aya mukaje, hakan yasa wasu suke tunanin 'yan uwa ne mu. Duk cikin mu Fawwaz ya fimu wayewa, domin Mahaifinshi yafi namu kud'i, sannan gatan da ake masa ba'ayi mana, sai Sufwan, shima d'an gata ne, a cikin mu ni kad'ai ne nake shakkar Mahaifiyata, duk da Abban mu yana mana gata kuma baya hana mu abinda muke so, amma gaskiya Mamy tana kula da mu sosai. A hankali muka zama manya amakarantar, ajin mu d'aya da Naseer, ganin yana da kok'ari yasa muke kulashi, munso mu jawoshi cikin mu amma yaki amincewa domin yanayin mu da nashi ba d'aya bane, abokinsa d'aya Munnir. Ganin yaki bamu had'in kai yasa muka kyaleshi amma duk da haka muna gaisawa. Zuwan mu aji shidda Fawwaz ya k'ara zama tantiri, wani abun ma muna tsawatar masa amma duk da haka sai abinda yaga dama, akwai wata yarinya *Minal* aji biyar take alokacin, Fawwaz yana matuk'ar sonta, sai dai ita bashi take so ba, wani d'an ajin mu take so *Farouk*, Fawwaz ya dad'e yana jama Farouk kunne akan ya rabu da Minal amma yayi banza dashi, saboda shima akwai zuciya. Ganin abun ya fara koma masu fad'a yasa muka fara bama Fawwaz hakuri akan ya rabu da ita ya nemi wata, amma yace bazai hakura ba. Wata rana da yamma zamu tafi gida yaga Minal da Farouk suna zaune suna shan lemu, takawa yayi har inda suke, yana zuwa ya kwashe Farouk da mari, cikin zafin nama Farouk ya rama, yana marinsa Minal ta k'ara masa hada juye masa lemu a jiki. Saurin rik'e Fawwaz mukayi gudun kada abun yayi tsamari, duk yanda yaso mu sakeshi kiyawa mukayi, haka muka turashi mota naja muka tafi gida. Washe gari koda mukazo makaranta muna zaune sai dai mukaga Fawwaz yana murmushi yana sakin kwafa, da muka tambayeshi lafiya yace bakomai. Aranar mun tsaya lesson har yamma, bayan mun tashi mukaga Fawwaz ya mik'e ya fita da sauri, juyawar da mukayi sai mukaga ashe Farouk ne ya fita zuwa bayan aji da alama band'aki zaije, har mun zauna sai kuma muka tashi muka bi bayansu. Kafin mu k'arasa muka hangosu suna fad'a, kasancewar wajen babu mutane yasa babu wanda yagansu, da sauri muka nufesu, sai dai kafin mu isa Fawwaz ya zaro wuk'a ya yankar masa wuya nan take ya zube. Cike da firgici muka isa tare da rik'e Fawwaz, muna dubawa mukaga Farouk baya numfashi, cike da tashin hankali na fige wuk'ar naje na sata cikin wani k'aton rami da ake kona bola, dawowa nayi mukaja Fawwaz muka wuce, sai dai alokacin naga Naseer ya juya baya da gudu ya bar wajen yana kok'arin maida wayarsa aljihu, tabbas ko ba'a fad'a ba nasan ya d'auki abinda ya faru. Sai alokacin shima hankalinsa ya tashi. Kuka yasa yana fad'in shima kashe shi za'ayi, lallashinsa muka farayi muna fad'in bazamu bari kowa yasan shine ya kashe shi ba, saboda muna son junan mu. Kai tsaye gidansu muka nufa, wajen Dadynshi mukaje, bayan daya gama jin abinda ya faru na d'auka zai shiga tashin hankali ko kuma yayi ma Fawwaz fad'a amma sai naga cikin ko in kula ya kamo kafad'ar Fawwaz yana shafa kanshi yana fad'in Auta ka kwantar da hankalin ka, meye zaka tashi hankalin ka dan d'an wannan abun, ka d'auka kwananshi ne ya k'are, dan haka ba kaine ka kashe shi ba tsautsayi ne ya kai wuk'ar hannunka wuyanshi, amma babu mai kashe wani sai Allah, dan haka ka kwantar da hankalin ka kacigaba da hidimar ka tamkar yau aka haife ka, bana so ka nuna damuwa, ina fatan babu wanda ya ganku? Suka amsa mashi da babu. Saurin kallonshi nayi nace masa naga wani abokin mu Naseer ina tunanin ya d'auki abinda ya faru kuma ya gani da idonshi dan naganshi yana maida waya aljihu. Jinjina kai yayi yana fad'in nine Alkalin babbar kotu, kome na fad'a ya zauna, ko case d'in yaron baza'a kaishi kotu ba bare aje afara bincike, zakuce na fad'a maku babu wanda zai tada maganar kawai gawar yaron za'a d'auka a rufe Iyayenshi suyi hakuri, dan haka kuje kawai, shima waccan yaron zansan yanda zanyi dashi. Kud'i ya bamu masu yawa yana fad'in kuje kusayi wani abu. Anan take Fawwaz ya warware, ni kuwa jikina ne yayi sanyi sosai, ba dan ina son Fawwaz ba babu abinda zai hana na rabu dashi, amma amintakar mu daban take. Haka na wuce gida jiki a sanyaye, aranar da zazzab'i na kwana. Washe gari haka mukaje makaranta abun mamaki babu wanda yaje da sunan bincike, sai nake jin labarin wai an tsinci gawar Farouk a bayan gari an yankashi, koda na tambaya a ina nayi tunanin za'ace a makaranta amma babu wanda yace haka, abun ya bani mamaki, nan Fawwaz yake rad'a mana ai Dadynshi ne yayi komai, muna tafiya yayi magana da shugaban makarantar akaje inda gawar take aka fita da ita ba tare da kowa ya sani ba, wannan dalilin ne yasa babu wanda yasan a cikin makarantar aka kashe shi, sai dai aka buga ajarida amma Iyayenshi basu tada maganar ba saboda basu san wanda zasu tuhuma ba. A ranar mun dawo daga yawo mukazo gidansu Fawwaz kawai muka iske Dadyn Fawwaz yayi bak'i, anan aka kiramu, Brr. Barau shine wanda ya tambaye mu kwatancen gidan su Naseer tare da hotonshi, bayan mun bashi ya sake ja mana kunne akan kada mu fadama kowa, nan muka jaddada masu babu wanda zamu fad'amawa. Kafin mu wuce naji yana waya da wasu yana fad'a masu kada su bar Naseer, su amso abinda ya d'auka kuma su kashe shi. A lokacin nashiga firgici jin za'a kashe Naseer, tun daga lokacin naji Fawwaz ya fice mun arai, nayi danasanin tarayyar mu, haka na wuce gida. Washe gari sai labarin mutuwar Naseer naji, tun daga lokacin zuciyata ta tsinke, haka kuma tarayyata da Fawwaz tayi baya, Allah yaso zamu fara jarabawa babu sauran zama amakaranta, hakan yasa ban cika shiga cikinsu ba, bayan mun kammala jarabawa aka fitar da Fawwaz waje, tun daga nan muka rabu sai dai waya. Shigata makaranta a hankali halayyata ta canza, a hankali na rika shiga damuwa saboda abubuwan da suka faru sun kasa barin zuciyata, shiyasa har yanzu ban mance abinda ya faru ba, duk da an d'auki shekaru na kasa manta koda kalma d'aya ce, wani lokacin inajin kamar ina da laifi, domin nayi tarayya wajen b'oye mai laifi, kuma nine silar tona Naseer, domin nine na fad'a ya gammu. Abinda ya faru da Yaya Sameer da kammala komai har zuwanshi wajena ya fad'a mun Fawwaz ya dawo da abinda yakeso nayi yasa hankalina ya sake tashi, kuma nayi alk'awarin a wannan karon zan tsaya na bada kowace irin sheda ake buk'ata domin a tabbatar da gaskiya, duk abinda ya faru yana nan a zuciyata be goge ba, dan haka ashirye nake domin bada sheda. Jinjina kai Ra'eez yayi yana fad'in tabbas wannan 'Yallab'ai d'in da muke nema ina kyautata zaton tsohon Alkali ne wato mahaifin Fawwaz, domin alokacin da sukaje gidansu Fawwaz su ukku sun had'u, kunga kenan shine na hud'unsu. Rafeek yace babu tantama shine na cikon hud'unsu, kuma dole zamu tabbatar da abinda zai tona asirinsu, ayanzu mu kad'ai ne mukasan gaskiya, kuma mu dukan mu babu wanda yake da tsinken da zai iya rik'ewa a matsayin hujja, kotu bata amfani da hujjar baki, ko shari'ar muka dawo da ita baya sune zasu sake nasara domin sune masu hujja mai kwari, dan haka ba yanzu zamu tado da maganar ba. Jabeer yace wannan haka yake, gobe zan samu Kawu da maganar abinda yace zakuji, Yaya dole mu fara bincike a b'oye, sai mun had'a komai kafin mu fara aiki. Ra'eez yace ina ganin shari'ar su Naseer zamu fara, itace zata tono waccan shari'ar. Rafeek yace haka ne, domin muna da d'an wani abu akan shari'ar Naseer, duk da itama ba mai kwari bace, domin d'ayan abokinsu ya mutu, ko yana nan su biyu bazasu bada sheda ba, ko sun bada baza tayi amfani ba saboda abaki take, kunga anan ma sai mun zurfafa bincike. Jabeer yace Adnan kana da hoton ku alokacin kuna makaranta? Adnan yace ina da su sosai ma. Jabeer yace Fawwaz bazai iya k'aryata abotar ku ba, kana da labarin shugaban makarantar ku? Adnan yace e amma yanzu baya makarantar ya aje aiki, sai dai nasan gidanshi dan d'anshi abokina ne. Rafeek yace turk'ashi, yanzu ya za'ayi musamu ganawa dashi bana so abokin ka yayi tunanin kayi masa rashin mutunci idan yaji kana dasa hannu wajen saka Babanshi cikin masu laifi. Adnan yace a wannan gab'ar babu batun abotaka, tunda har na amince zan tsaya a yanke ma babban aminina na da hukunci babu wanda zan iya rufa ma asiri, domin shi Nabeel jami'a mukayi dashi, shikuwa Fawwaz akwai shakuwa atsakanin mu, dan haka ku bani lokaci insha Allahu Nabeel zai bamu goyon baya, duk da Babanshi ya aikata laifi amma dole a hukuntashi. Rafeek yace mungode sosai, kuma zamu tafiyar da komai yanda ya kamata, idan komai ya kammala zasu san gata mukayi masu domin sun huta amsar hukunci a lahira. Tashi Adnan yayi yana fad'in zan wuce gida dare yayi. Rafeek yace muje na aje ka zamuyi waya. Hannu ya bama su Jabeer suna ta masa godiya. Rafeek yace zuwa gobe zan fara binciken mutanan da sukayi tarayya a waccan shari'ar. Jabeer yace nima a goben zan samu Kawu da maganar. Ra'eez yace Allah ya kaimu, nima gobe zan koma aiki. Tashi sukayi suka rakasu kafin suka dawo. Bayan sun kwanta wayar Ra'eez tayi k'ara, yana dubawa yaga Raheena ce, duba agogo yayi yaga har sha biyu tayi, tsaki yaja yana fad'in bana son rashin hankali wallahi. Murmushi Jabeer yayi yana fad'in bacci ta kasayi shiyasa ta kira ka. Kashe wayar yayi gaba d'aya yana fad'in sai tayi da wani kuma. Jabeer yace Ra'eez na Raheena, wallahi kuna bani dariya, tun farko na fad'a maka ka rabu da ita gashinan tana baka ciwon kai. Tsaki Ra'eez yayi yana fad'in daga ita har Iyayen ta basu da kai, sufa a haukansu jiran yan gidan mu suke suje neman aure, har kayan d'aki fa sun siyo. Gyara kwanciya Jabeer yayi yana fad'in ka bari da Allah? Ra'eez yace wallahi kuwa, ba na fad'a maka zasuje Dubai ba a week end d'in da naje Kano ba. Jabeer yace haka ne. Ra'eez yace wallahi jiya take fad'a mun wai kayan suna hanya, nifa na fara tausaya mata ma. Jabeer yace da nace maka ina tausayinta meka fad'a mun? Nifa aganina bekamata kayi ramuwar gayya akanta ba, duk da an zalunceka amma bata da laifi, idan mukayi haka kamar Allah zai kama mu ko kuma ya hana mu samun wani abun da muke so. Ajiyar zuciya Ra'eez ya saki yana fad'in b'acin rai ne yaso ya jefani cikin damuwa, tabbas Raheena bata cancanci nayi mata haka ba, amma insha Allahu a yanzu zan fad'a mata tayi hakuri kawai. Jabeer yace baza'ayi haka ba, Raheena tana maka so mai yawa, idan ka fito fili ka fad'a mata abinda yake ranka zata iya fad'awa wani hali, ina ganin abi komai a hankali. Ra'eez yace shikenan nasan abinda zan rubuta mata. Wayarsa ya jawo ya kunna ya fara rubutu. Jabeer da yake gefenshi yace kafin ka tura ka bani na gani. Ra'eez yace sa ido. Jabeer yace gaskiya dai. Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in bara na gama to. Mik'a masa wayar yayi yana fad'in bance kamun gyara ba. Amsa yayi yana fad'in sai dai idan baka kwafsaba, dan na lura da kai haushin Mahaifinta yasa ka tsani kowa. Jinjina kai yayi yana fad'in ba laifi kayi amfani da kalamai masu ma'ana, sai muce Allah yasa mata dangana. Ra'eez yace amin. Shuru sukayi gaba d'ayansu bayan sun tura sakon. Jabeer! Ra'eez ya kirashi a hankali, be amsa ba sai juyowa da yayi yana fuskantarshi. Mai zai hana ka nemi auren Ra... Kada ma ka k'arasa, Jabeer ya fad'a. Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in wallahi tausayinta nakeji. To kayi ta biyu da ita mana. Jabeer yace yana harararshi. Dariya Ra'eez yayi yana fad'in haba abokina, yanzu da bakin ka kake fad'in nayima Pretty kishiya. Jabeer yace ai naji kana wani kilibibin kana tausayin ta, idan har bazaka iya aurenta ba damme zaka lak'aba mani ita? Ra'eez yace saboda naga babu soyayyar kowa a zuciyar ka. Tsaki Jabeer yayi yana fad'in to kama dena wannan maganar, babu abinda zanyi da ita, na fad'a maka bazan iya soyayya da wacce ta mutu akan wani ba, wanin ma kai, haka kawai idan na aureta data ganka sai tsohon tsumin soyayyarka ya tasar mata. Dariya Ra'eez yasa yana fad'in kawai kace kishi kake malan, bakomai Allah zai bata wani. Jabeer yace hakan ma yafi, amma kada ka janye mata lokaci guda kamar yanda ka rubuta kaga baka fito fili kace mata baka sonta ba. Ra'eez yace kada ka damu. *** *** *Raheena ina so ki tsaida hankalin ki wajen karanta abinda na rubuta maki, bana so kiyi mani wata fassara, dalilin rubuta maki wannan sakon saboda naga kunyi nisa akan abinda zuciyar ku take tunani shiyasa naga ya dace nayi maki magana dan kada ku zurfafa, a tunanin ku ayi bikin ki nan da wani lokaci, domin naji kina fad'ar kunje siyayyar kayan d'aki, idan baki manta ba na fad'a maki ki jirani zanyi tunani akan soyayyar ki, kuma har yanzu ban gama yanke hukunci akai ba, domin ko Iyayena banyi maganar dasu ba, kuma ni gaskiya ba yanzu zanyi aure ba dan akwai abubuwa masu muhimmanci akaina, kuma bazan tab'a yin aure ba har sai na kammala su, shiyasa nace zan fad'a maki gaskiya dan naga kamar kina son yin aure da wuri, ina fatan zaki fahimce ni dan bana son a takura mani dan ban shirya aure yanzu ba, dan haka kudena maganar yin aure ayanzu. Nagode.* Ta maimaita sakon yafi a kirga, zufa kawai take zubo mata, wasu zafafan hawaye ne suka zubo mata, hannu tasa ta goge tana fad'in me D yake nufi da wannan sakon? Gashi dai bece mani baya sona ba, *Dama can kuma be tab'a fad'a maki kalmar so ba.* wata zuciyar ta kwab'eta. Gyara zama tayi tana zurfafa cikin tunani, tabbas sunyi gaggawa wajen aminta da maganar aurenta dashi, amma tunda yace akwai abinda yake gabansa zata mashi uzuri, kuma bazata fad'ama kowa wannan maganar ba, sai dai zata nuna masu abar maganar aurenta zuwa wani lokaci, idan ya kammala komai tasan zai dawo gareta. Murmushi ta saki tana fad'in zan jiraka, bazan tab'a bari naji kunya a wajen k'awaye na ba, bara naje muyi magana da Momy. Ur's. Nabeelert Lady🖋 [3/10, 8:40 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.* 3⃣6️⃣ Ban gane abar maganar auren ki sai zuwa gaba ba? Matsowa tayi tana fad'in Momy Ra'eez yace beyi magana da Iyayenshi ba saboda akwai wani aiki mai muhimmanci da yakeso ya kammala kuma baya so maganar aurenshi tasa yaki maida hankali akan aikin, kinga babban biki ne za'ayi dole yana buk'atar natsuwa, nima bana so ace za'ayi bikin mu kuma yana wani aikin sai kiga bikin beyi dad'i ba, kuma tunda yace aiki ne mai muhimmanci nasan ba k'aramun abu bane, kinsan kuma yanayin aikinsu dole yana buk'atar natsuwa da zurfafa tunani, shiyasa yace a bari harya kammala aikinsa kafin yazo ayi magana. Murmushi Momy ta saki tana fad'in yanzu naji batu, ai na d'auka ko wata matsala kuka samu, haba dan wannan ai bakomai, kaya ne an riga ansiyo su, idan ma baki son su zuwa lokacin auren za'a iya siyar dasu aje asiyo maki wasu dan bancika son amfani da tsofaffin yayi ba. Murmushi Raheena tayi tana fad'in yanzu Momy zaku iya sake mani wasu kayan? Momy tace to me zamuyi da kud'in? Ke d'aya muke da ita shiyasa muke so muyi maki abinda ko d'iyar shugaban k'asa iya abinda za'a mata kenan, dan haka idan har aikin ya jashi dogon lokaci dole asiyar da kayan idan lokacin bikin yayi asiyo maki wasu. Raheena tace nagode Momy, sai kiyi ma Dady bayani. Babu wani bayani da za'a mun domin naji komai. Alhaji Barau ya fad'a yana sakkowa daga bene. Murmushi Momy tayi tana fad'in ashe har ka gama shiryawa? Zama yayi yana fad'in tunda kin gudu wajen d'iyar ki dole na shirya ni d'aya. Tashi Raheena tayi tana fad'in Dady ayi hak'uri bazata sake ba. Dariya sukasa gaba d'aya. Alhaji Barau yace bakomai naji duk abinda kuka fad'a, tunda dai yana sonta ai babu damuwa, ni dama ban matsa sai Raheena tayi aure da wuri ba dan nima bangaji da ita ba, dan haka zamu jirashi ya kammala abinda yakeyi. Momy tace kila ma kaine ka bashi aiki mai wahala ko? Alhaji Barau yace babu ruwana, kila dai a wani wajen zaiyi aiki amma ni bana bashi aiki mai wahala. Momy tace to Allah ya nuna mana lokacin. Yace amin. **** *** Bayan sun tashi daga aiki Jabeer yace zaije wajen Kawu akan maganar su. Ra'eez yace bakomai zan wuce wajen Kawu daga can na biya wajen Ummu. Jabeer yace ka gaishe su mu had'e gidan Mama. Ra'eez yace ka gaishe dasu Mamy. **** Hannu Kawun Jabeer yasa a hankali ya zare glass d'in idonshi, ido ya kurama Jabeer jin abinda yazo dashi. Kauda kai yayi yana jinjina kai. Shiru Jabeer yayi yana addu'ar Allah yasa Kawun ya amince ya taimaka masu. Gyaran murya Kawu yayi yana fad'in Allah mai iko, lallai duniya da girma take, wai akace d'an hakkin daka raina wata rana zai iya tsone maka ido. Kallon Jabeer yayi yana fad'in wai kana nufin tare kuke aiki da Yaron marigayi Alhaji Maiwada? Jabeer yace kwarai kuwa Kawu, yanzu haka shine babban gwarzo a kotun mu. Kawu yace naga alama daga labarin shari'ar da kace yayi, wannan shine ikon Allah, ashe dama irin wannan ranar zata zo? Ashe jinin Alhaji Maiwada ba zai zuba abanza ba? Ashe Malan Sani zai samu adalci? Ashe wad'an can azzaluman zasu fuskanci hukunci dai-dai dasu? Lallai Jabeer ka zo da magana mai matuk'ar amfani, ayanzu ne zanyi ramuwar abinda na gazayi ashekarun baya, ayanzu ne zan nuna masu Brr. Barau bakomai ne kud'i yake badawa ba, tabbas anzo wajen, dan haka kaje ka fad'ama Ra'eez, da Rafeek ina son ganin su ko zuwa dare ne. Cike da farin ciki Jabeer yace angama Kawu. Kawu yace bana son wannan maganar ta fita, shiyasa daka fara fad'a mani nace maka muzo mota, inaso komai ya tafi yanda ya kamata, insha Allahu zan shirya yanda komai zai kasance, sai Alhaji Barau yaji kunyar da bai tab'a jinta ba, sai ya gwammace k'asa ta tsage ya shige ya huta, kaje ka fad'a masu. Godiya Jabeer yayi ma Kawu ya tashi ya tafi cike da farin ciki, tun alokacin yayi masu waya ya fad'a masu sakon Kawu, sosai sukayi murna. **** Rafeek ne ya fito daga ofishin 'yan sanda tare da wani d'an sanda, har bakin motarshi suka k'arasa. Hannu Rafeek ya bashi yana fad'in nagode *Usman* Allah ya bar zumunci. Murmushi wanda aka kira da Usman yayi yana fad'in haba babu komai, ai wannan taimakon juna ne, duk da baka fad'a mani dalilin da yasa kake neman Alhaji Bello Kabeer ba. Rafeek yace bakomai fa, akwai wani yaro da yake son shiga aikin d'an sanda shine nace masa zan taimaka masa, to da nayi bincike sai na gano a ofis d'in ku yayi aiki harya kai babban matsayin Kwamishina na 'yan sanda ayanzu, shine nace zan fara zuwa wajen ka na fara jin labarinshi kafin nasan ta yanda zanje mashi. Usman yace indai zaka bud'e masa bakin aljihu baka da matsala dan 'Yallab'ai akwai son naira. Rafeek yace babu damuwa tunda dai kayi mani kwatancen gidanshi insha Allahu zan sameshi Allah yasa mudace. Usman yace amin. Sallama sukayi yashiga mota. Tafiya yake yana tunanin ta yanda zai fara b'ulloma Alhaji Bello Kabir, amma tunda ya ganoshi zai shirya masu fira ta haka zai san yanda yayi ya tab'o mashi maganar wannan shari'ar. Agogo ya duba sai yaga lokaci ya tafi, yaso ya biya asibitin da Dr. Aliyu Sani yayi aiki yaji ko yana wajen har yanzu ko kuma ya k'ara matsayi, ajiyar zuciya ya saki, dole ya bari sai gobe saboda neman da Kawu yake masu. *** Daga wajen Ummunsa gidan Mama ya wuce, acan ya iske Jabeer suna ta fira da Mama. Bayan sun gaisa suka wuce masallaci, bayan sun idar da sallah suka zauna Rumaisa ta kawo masu abinci. Kallon Jabeer yayi yana fad'in nifa jinake akoshe nake duk na k'osa muje wajen Kawu, ina son naji ana bani labarin Abbuna. Murmushi Jabeer yayi cike da tausayin Ra'eez. Wayar Rafeek ce tashigo, yana d'auka ya fad'a mashi suna gidan Mama. Rafeek yace dama yanzu na fito bara na k'araso mugaisa da Mama. Ra'eez yace shikenan sai kazo. Jabeer yace gaskiya Yaya yana da kirki. Ra'eez yace shiyasa nace maka tunda muka had'u naji ya kwanta mani, kasan bana saurin yarda da mutane amma akanshi naji na yarda dashi. Jabeer yace wai jiya inaso na tambayeka ka d'auki bayanin Adnan kuwa? Dafe kai Ra'eez yayi yana fad'in wallahi na manta, kuma kasan nace maka daga yanzu duk wata sheda da zamu samu sai mun rik'a d'aukarta gudun yaudarar mutane. Jabeer yace Allah yasa kada ya yaudare mu, duk da naga alamun gaskiya atare dashi amma kasan halin yau, zuciya bata da k'ashi babu ta yanda bazata iya canzawa ba, sai dai muyi fatan Allah yasa ya cika alk'awarinsa. Ra'eez yace amin, amma da ya gama damu idan ya kasa zuwa ya bada shedar abinda ya sani. Jabeer yace kaga sai mu kiyaye. Wayar Ra'eez ce tayi k'ara, saurin tashi yayi ya fita yana fad'in Yaya ne. Sosai Mama taji dad'in bayanin da Rafeek yayi masu akan gano Alhaji Bello Kabir wanda yake inspector a lokacin da akayi shari'ar su Malan Sani, godiya tashiga yimasa tana saka masa albarka. Rafeek yace haba Mama babu komai, insha Allahu wannan karon mune da nasara. Mama tace Allah yasa. Abinci tasa akawo masa yace daga gida yake, kallonsu Jabeer yayi yace muje kada Kawu yajira mu. Sallama sukayi ma Mama suka fita. **** *** Ido Kawu ya tsurama Ra'eez, tabbas ga kamanninsa da Mahaifinsa a fuskarshi, amma sai wanda ya san Alhaji Maiwada zai iya sheda hakan, kuma sai ka k'arema Ra'eez kallo zaka gano kamannin su, lallai Alhaji Barau be yima Ra'eez kallon tsab ba da tuni ya gano kamannin Mahaifinsa. Gyara zama yayi yana fad'in sannu kaji Ra'eez, tabbas kai d'in Kainuwa ne dashen Allah, domin Allah yasan dalilin da yasa ya bar su Alhaji Barau har yanzu araye, haka kuma ya barka kaida Malan Sani da Ummunka araye, domin ya tsara yanda ikonsa zai kasance, hakika Mahaifinka yayi mutuwar cutarwa, domin wad'an da suka kashe shi basu da imani ko kad'an, amma ayanzu zasu gane kuren su. Kayi hak'uri na kasa tsayama Mahaifinka, duk da alokacin nasan su Alhaji Barau suna da sa hannu a kisanshi amma bani da ikon magana saboda bani da hujjar da zan nuna, ita kuma kotu hujja take so, amma ayanzu dana ganka sai naji gashi can mun cinye shari'ar, da izinin Allah zamu samo hujjar da zata ruguzasu gaba d'aya. Hannu Ra'eez yasa ya goge hawayen da suka zubo mashi, duk'ar da kai yayi yana fad'in babu komai Kawu, Allah ya rubuta dole sai hakan ta kasance, ko ka bada hujjar baza tayi tasiri ba alokacin tunda Allah ya tsara haka, amma ayanzu zamu samota Kawu. Jinjina kai yayi yana fad'in dole amaido da shari'ar baya, domin ita shari'a bata tsufa, koda ta kai shekaru hamsin za'a iya maidota, kuma awannan kotu za'a gabatar da ita, dan haka zan shirya yanda komai zai kasance, koda Alkali Barau yace bazai amshi shari'ar ba za'ayi masa magana kuma dole ya amsheta. Rafeek yace mungode Kawu, kuma zamu k'arasa nemo sauran mutanan da suka tsaya a waccan shari'ar matuk'ar suna raye. Kawu yace gashi kusa mani lambar ku, daga yau inaso ku kasance ashirye, domin zaku fara aiki mai had'ari, dan mutanan da zaku kara dasu azzalumai ne, zasu iya komai saboda rufin asirin su. Bayan sun saka mashi lambar sukayi masa sallama suna ta godiya suka tafi. A can suka rabu da Rafeek yayi gida suma suka wuce gida saboda dare yayi. *** Ina jinka Lucky. Gyara tsayuwa Lucky yayi hannunshi nad'e a kirji yana fad'in 'Yallab'ai gobe ne za'a kawo kayan Alhaji Marusan, kuma nasa yarana su ankare baza'a samu matsala ba. Ruwa Alhaji Barau yasha yana fad'in Lucky na sanka da son kud'i, bana so ka fad'ama Alhaji Marusa komai dan nasan zakayi tunanin zai iya k'ara maka kud'i idan ka fad'a masa, mu ba kud'in bane suka dame mu, yaudara da cin amanar da yayi mana muke so mu nuna masa iyakarsa, kasan dai daga ni har Mr. Kallah bamu da zalamar kud'i, wannan aikin idan har ka yishi yanda ya kamata kana da kaso mai tsoka, kaga dai yanzu ka manyanta, aiki da yawa sai dai kasa yaranka suyi, dan haka ina so wannan ya zama sirri, kamar yanda nace ku kwace kayan kuma ku kashe masu d'aukar kayan zakaga abinda zan saka maka dashi. Murmushi Lucky yayi yana fad'in Alhaji baka da matsala, wannan harka mun dad'e muna yinta daku, kuma ka dena tunanin zan koma wajen Alhaji Marusa domin shi d'in ba mai alk'awari bane, kanshi kawai ya sani, kafin ku shi muka sani ni da abokina Peter, amma saboda cin amana da son kud'i irin na Alhaji Marusa daga abokina yayi masa kuskure d'aya yasa aka kashe shi, har yanzu ina da haushin wannan abun, dan haka zanyi maku aiki koda bazaku biya ni ba, domin nasan Alhaji Marusa ya zuba makudan kud'i a wannan harkar, matuk'ar ya rasa wad'an nan kayan zai shiga tashin hankali, sannan hukuncina na farko da zanyi mashi nasa babban yarona yaje cikin dare ya kona mani babban store d'inshi. Dariya Alhaji Barau yasa yana fad'in Mr. Kallah kaji mutumin ka ko? Mr. Kallah yace lallai Lucky ka d'ebo da zafi, ayi masa hakuri yaji da wannan asarar ma. Alhaji Barau yace aifa kai har yanzu bazaka canza hali ba, kada kamanta amanar mu yaci, tare muke kashewa mu rufe amma yau saboda harkar k'aruwa tazo shine yaci amanar mu, dan haka ka bari shima anuna masa iyakarsa, ganin yana da kud'i yasa yake abinda yaga dama, idan ya fara shin-shino karayar arziki kaga dole ya dawo k'asan mu. Mr. Kallah yace shikenan yanda kace babban Alkali. Dariya sukasa Alhaji Barau yace zaka iya tafiya Lucky sai munji daga gareka. Lucky yace nagode Alhaji. Yana fita Mr. Kallah yace yanzu kai ka yarda dashi? Alhaji Barau yace shiyasa ai na zab'eshi saboda nasan yana da haushin Alhaji Marusa akan kisan abokinsa, kaga kuwa bazai tab'a komawa bayanshi ba. Mr. Kallah yace zaiji idan cin amana tana da dad'i, kuma zamu nuna mashi munshiga tashin hankali. Alhaji Barau yace da masu ilimi fa yake tare wad'an da suka goga da mutane, duka nawa iliminshi yake, meya sani a harkar duniya, kabarshi zamu nuna mashi muma munyi asara. Mr. Kallah yace Alhaji Barau a kiyaye ka. Dariya sukasa. **** *** Wai Adnan kayi shiru bayan kuma akwai magana abakin ka. Murmushi Adnan yayi yana fad'in bakomai kawai wani abu na gani d'azu daya tada mani wani tsohon ciwo da yake zuciyata shekaru masu yawa da suka wuce. Nabeel yace lallai agaisheka, taya zan iya aje abu araina har na wasu shekaru masu yawa, kaganni nan ko b'ata mani rai akayi baya wuce kwana biyu yawuce, amma kuma bansan wane irin ciwo bane aranka, kasan wani ciwon sai mutum ya mutu dashi be manta ba. Adnan yace d'azu muka had'u da Yayan wani abokin mu da aka kashe lokacin muna aji shidda a secondary, rabona dashi tunda mukaje masu gaisuwa, saboda yasan nine babban abokinsa yasa da muka had'u d'azu muka zauna muna ta fira hada firar abokina mukayi bakaji yanda jikina ya mutu ba, gaba d'aya sai mutuwar ta dawo mani sabuwa musamman da naga yana kuka, kuma yake fad'a mani har yanzu Mahaifiyarsu bata warke ba akan ciwon daya sameta alokacin da aka kawo mata gawar d'anta, wannan abun shine ya tada mani hankali sosai. Nabeel yace Allah sarki, amma basu shigar da k'ara ba ne? Adnan yace basu shigar ba. Nabeel yace da sun sani sun shigar da k'ara, kasan wani lokacin idan aka kashe maka naka matuk'ar an yanke ma wanda yayi kisan hukunci kana jin sauki a zuciyarka domin ka rage wani abun. Adnan yace taya zasu shigar da k'ara bayan an juyar da abun, kasan fa ita shari'a sai da shedu take amfani, domin kisan a makarantar mu akayi ta amma sai aka gano gawar abokina a wajen gari, alokacin ma Abban ka ne shugaban makarantar. Nabeel yace a kings college ko? Adnan yace nan fa. Nabeel yace tabbas acan Abbah yayi aiki ashe kayi karatu ak'asanshi? Adnan yace sosai kuwa, ai Abbanka beda wasa, nayi mamaki alokacin da aka kashe Farouk da aka fita da gawarsa kuma be tsananta bincike ba. Nabeel yace dan Allah bani labarin abinda ya faru. Adnan yace abinda na sani ance a makaranta aka kashe shi, domin akwai wanda yaga lokacin da akayi kisan kuma har d'auka yayi, sai dai kuma daga baya aka samu gawarsa a wajen gari sannan yaron daya d'auki shedar shima aka kashe shi, kuma shedar ta b'ace, mamakin da nayi duk zafin Abbanka da iya aikinsa amma beyi komai ba, daga baya kuma nayi tunanin kila besan a makaranta aka kashe shi ba. Girgiza kai Nabeel yayi yana fad'in duk da haka Adnan ya kamata ace anyi bincike koda da gaske ba'a makarantar aka kashe shi ba amatsayin Abbah na shugaban makaranta ya kamata ace yayi ruwa da tsaki wajen nemawa Farouk hakkinsa. Murmushi Adnan yayi yana fad'in Nabeel kenan, kaida kayi wannan tunanin zaka fad'i haka, ka rabu da duniya idan akace akwai azzaluman shuwagabanni, talaka beda ikon aiwatar da komai matuk'ar ta had'oshi da mai kud'i, ko d'azu Yayan Farouk ya fad'a mani da zai samu sheda koya take saiya maido da shari'ar Farouk kotu, sai anyi bincike koda wanda ya kashe shi baya duniya. Jinjina kai Nabeel yayi yana fad'in amma Abbah bazai iya taimakawa ba? Adnan yace a wajen me kenan? Gyara zama Nabeel yayi yana fad'in dole yasan duk wasu masu gadi da sukayi aiki dashi a waccan shekarar, ina zargin kamar an had'a baki da masu gadi wajen fitar da gawar Farouk, kaga idan aka tabbatar da haka dole za'a gano wanda yasa suka aikata haka, daga nan kuma zai kai agano wanda yayi kisan, danni ina tunanin kamar a cikin yaran makarantar ne aka samu wani ya kashe shi, kaga makarantar yaran masu kud'i ce dole asan yanda za'a rufe maganar. Adnan yace abu ne me wuya Abbanka ya saurari wannan maganar, domin shekarun da yawa, idan aka tado mashi da maganar zaiga kamar anaso asashi wani babban aiki ne, tunda ya jima da aje aiki kaga abu ne mai wuya ya koma binciken abinda ya faru abaya. Nabeel yace wallahi duk naji jikina yayi sanyi, kasanni Adnan bana son zalunci, haka Allah yayi ni, matukar naga anyi zalunci bana kyalewa, shiyasa a secondary d'in mu nine Ameer dan gaskiya bana goyon bayan zalunci, shiyasa fa ban zab'i makarantar ku ba dan bana son irin makarantun yaran masu kud'i, dan haka ka barni da Abbah zanyi magana dashi cikin sanyi, kuma zamuyi nasara. Adnan yace Nabeel sai kayi ahankali kaga Mahaifinka ne. Nabeel yace koda shine ya aikata laifin bazanji kunyar tonashi ba, domin Allah ya hana zalunci. Ajiyar zuciya Adnan yayi cike da farin ciki, yana masa godiya. Shiru Nabeel yayi can ya kalli Adnan yana fad'in akwai abinda ka b'oye mani Adnan. Saurin kallonshi Adnan yayi yana fad'in kamar mefa? Murmushi Nabeel yayi yana fad'in wasa nake, kome kenan zamuyi magana. Adnan yace nagode sosai abokina. Nabeel yace bakomai. Sallama yayi mashi ya rakoshi. Sai da ya tafi kafin ya nufi d'akin Mahaifinshi cike da fatan dacewa dan yasan yanzu yana kallon news. **** Sai da Adnan ya tsaya wata super market yayi siyayya kafin ya fito zai wuce gida. Adnan Abdurrazak Matawalle! Saurin juyowa yayi jin ankirashi da cikekken sunanshi. Gabanshi ne ya faad'i ganin wanda yake gabanshi. Matsowa Fawwaz yayi yana ware hannu ya rungume Adnan yana dariya. Jiki a sanyaye Adnan ya rungumeshi zuciyarsa tana tsinkewa. Kallonshi Fawwaz yayi yana dariya yace shegen kaya, kaganka kuwa? Lallai na yarda ka zama Baba. Murmushi Adnan yayi yana fad'in Fawwaz dama da gaske ka dawo, Yaya Sameer yake fad'a mani shine ko kaneme ni. Fawwaz yace taya zanki nemanka kawai abubuwa ne sukayi mani yawa, yanzu haka sauri nake zamuje wani party na abokin mu. Adnan yace lallai dole bazaka nemeni ba saboda kazama d'an gayu ga sababbin abokai kayi. Fawwaz yace No ba haka bane, kasan yanzu kai ka girma, kana da Iyali bekamata narik'a sako ka cikin mu ba, gashi gaba d'aya ma naga kacanza daga yanda nasanka, duk da tun kafin mu rabu naga sabon canji daga gare ka. Murmushi Adnan yayi yana fad'in dole nake canzawa, domin mun aikata babban laifin da har mu mutu yana bin mu, naga kamar kai kamanta, duk da ba nine na aikata laifin ba kullum cikin nadama nake da istigfari, amma kai gashinan kana morewar ka yanzu ma party zakaje. Canza fuska Fawwaz yayi yana fad'in bangane ka aikata laifi ba? Adnan yace ka aikata dai, mu kam ai taimaka maka kawai mukayi nida marigayi. Ja da baya Fawwaz yayi yana k'ank'ance idanu yana kallon Adnan. Murmushi Adnan yayi yana fad'in kada ka damu kawai na tuna maka ne saboda inaso ka fara neman yafiyar Allah, amma tabbas har yanzu ina kallon lokacin da ka yanki Farouk da wuk'a. Sosai Fawwaz ya canza fuska tamkar wanda be tab'a dariya ba, jijiyoyin kanshi suka tashi idanuwanshi sukayi ja, hannu yasa aljihu ya ciro kwalin sigari, abaki yasa kafin ya bata wuta, sai da yayi mata kyakkyawar zuk'a ya fesar kafin ya kalli Adnan yana fad'in ban d'auka zaka iya tuna wannan abun ba, kamar yanda kasa ma bakin ka kwad'o a wancan karon to inaso kacigaba da zama ahaka, bazan d'auki wannan maganar ba, idan kuma ka san zaka rik'a mani ita to ka d'auka bamu tab'a sanin juna ba. Jinjina kai Adnan yayi yana murmushi yace haba abokina, kada ka manta da amintakar mu, ada ma banyi magana ba bare yanzu, kawai shawara na baka tunda baka so baza'a sake ba. Murmushi Fawwaz yayi yana fad'in nasanka ai bazaka iya tona asiri na ba, nagode ka gaishe da Yaranka. Adnan yace zasuji tunda babu kara. Fawwaz yace zan wuce. Mota Adnan ya shige ranshi fess, koba komai ya tado mashi da abinda yawuce, idan yana da hankali maganar bazata bar zuciyarshi ba. Fawaaz har ya shiga mota ya d'auki hanyar wajen Partyn yayi saurin canza hanya, tsaki yayi yana zuk'ar sigari ranshi ab'ace, gaba d'aya Adnan ya b'ata masa shirinshi, ya tuno masa abinda ya dad'e da mantawa. Wayarsa ce tayi k'ara, yana dubawa yaga abokinsa ne, d'auka yayi yana fad'in Guy bazan samu zuwa ba gida zanje kaina yana ciwo. Shiru yayi kafin ya kashe wayar, gudun motar ya k'ara zuwa gida. Ur's. Nabeelert Lady🖋 [3/10, 8:40 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.* 3⃣7️⃣ Fawwaz lafiyar ka kuwa? Kauda kai yayi yana fad'in Ammi normal. Zama tayi tana fad'in kace mun zakaje wajen Party amma kuma kadawo kana b'ata fuska ko partyn beyi maka ba? Ammi kawai b'ata mun rai akayi shiyasa. Murmushi tayi tana fad'in Fawwaz nasha fad'a maka ka girma, yakamata karage wannan shirmen da kakeyi, zuwa yanzu yaci ace ka aje Iya.... Ammi dan Allah kada ki k'arasa, duka me nayi a duniyar da zan cutar da kaina ta hanyar aure har da tara wasu Iyali can, kina ganin Dady sai da ya more rayuwarsa kafin yayi aure, bayan aurensa ma sai da kuka dad'e kafin ya yarda kika haihu gashinan yanzu kowa yaganki bazaiyi tunanin kin haifeni ba, da ace kin haihu da yawa ko kinyi aure da wuri da yanzu kila hak'oranki sun fara fita. Duka ta kaimashi yayi saurin kaucewa yana dariya. Dadynshi da yake jinsu ya shigo yana fad'in kada ki dokar mani yaro kinsan tunda ya taso besan me ake kira zafin duka ba. Ammi tace ai duk kaine ka sangartashi, ba damar yaro yayi laifi a tab'ashi sai ka fara fad'a, idan bam manta ba har rabuwa mun tab'ayi akan zan dokeshi. Dady yace sa'a kikaci baki kai ga dukansa ba shiyasa hukuncin ya tsaya a haka kikaje gida kikayo kwana biyu, da ace kin dokesa kila sai nayi babban hukunci. Tab'e baki tayi tana fad'in dad'ina da gobe saurin zuwa, shima gashinan ya girma damma ka hanashi aure ai da yanzu shima ya fara jin yanda naji akan Yara. Zama Dady yayi yana fad'in My Son wai kana son aure yanzu? Saurin girgiza kai yayi yana fad'in bana so Dady, gara abari na k'ara girma. Ammi tace lallai kam zamu mutu bamuga auren ka ba. Dady yace aikuwa da ran mu zaiyi aure, kana ji na, kada ka damu da ita ka kwantar da hankalin ka babu me takura maka akan aure, duk lokacin daka shirya sai kayi abunka. Gyara zama Fawwaz yayi yana fad'in Yawwa Dady d'azu daka aike ni gidan Abbah Barau na ga wata yarinya d'iyarsa ce? Dady yace Raheena kenan, itama waje tayi karatu lafiya? Ya mutsa fuska yayi yana fad'in ko gaishe ni batayi ba tana zaune a wajen lambu duk da taji shigowar mota kuma taji masu aiki suna gaishe ni. Ammi tace dan me zata gaishe ka bayan ba kusa kuke ba, ina ma ruwanka da ita dan batayi maka magana ba? Kika sani ko Yaron nawa ya k'yasa. Dady ya fad'a. Murmushi Ammi tayi tana fad'in to wannan dai anyi mata miji dan Hajiya Binta ta fad'a mani sunje Dubai siyo kayan aurenta kila ma bikin bazai wuce wata d'aya ba. Kallonta Fawwaz yayi yana fad'in d'an bani lambarta mugaisa to. Harara Ammi ta banka masa tana fad'in bana son sakarci, meye zaka amshi wayarta bayan kaji aure zatayi. Dady yace bana son haka fa, da Raheena da Fawwaz duk d'aya ne a wajena, domin Alhaji Barau na hannun dama ta ne, kuma Fawwaz kamar Yaya yake agareta, ko kinji yace maki yana sonta? Girgiza kai Ammi tayi tana fad'in kasan halin zuciya. Dady yace to ki bashi suyi zumunci, yace maki ba aure zeyi yanzu ba damme zakisa zargi akanshi. Murmushi Ammi tayi tace ayi hak'uri baza'a sake ba. Kamo hannun Fawwaz Dady yayi yana fad'in akwai abinda yake damunka dan nasan baka saba dawowa kamar haka ba. Yamutsa fuska Fawwaz yayi yana fad'in Dad babu komai kawai gajiya nayi zan kwanta. Tashi Dadyn yayi yana fad'in shikenan ka kwanta, Ammi muje kada mu hanasa bacci. Tashi tayi tana fad'in Allah ya tashemu lafiya. Fawwaz yace amin. Kwanciya yayi sai dai daya juya maganganun Adnan ne suke dawo masa, tsaki yayi yana fad'in wallahi Adnan ka b'atamun rai, banda jahilci taya zaka tado abinda yawuce shekaru kusan sha biyu, gashi nan nima abun ya dawo mani. Tashi yayi ya d'auko wata kwalba a cikin durowarsa, bud'ewa yayi ya shanye abinda yake ciki duka, wurgar da ita yayi ya haye gado yana jin jikinsa yana saki, a hankali idanuwansa suka fara rufewa tamkar wanda ake yawo dashi asama, da haka bacci yayi gaba dashi. **** Washe gari har wajen k'arfe goma be fito ba, Dady ne ya kalli Ammi yana fad'in wai yau lafiyar Fawwaz kuwa, nasan baya tashi da wuri amma kuma yana fita motsa jiki idan ya gama ya sake kwanciya yau banji motsinshi ba? Ammi tace nima abinda nake tunani kenan. Dady yace muje mu dubashi. Da mamaki Dady yake kallon kwalbar da take hannunshi, kallon Ammi yayi yana fad'in dama Fawwaz yana shan syrup ne? Ammi tace wallahi nima sai yau na gani. Girgiza kai Dady yayi yana fad'in wannan syrup d'in mai k'arfin ne, shiyasa be tashi ba har yanzu, da alama kuma be had'ashi da komai ba haka kawai ya sha dan banga robar lemu ba. Hannu Ammi tasa ta fara tadashi, girgizashi tayi kafin ya farka a firgice yana kiran sunan Farouk. Da mamaki suka bishi da kallo. Zama Dady yayi yana fad'in Fawwaz waye kuma Farouk? Hannu yasa ya dafe kanshi yana goge zufar datake goshinsa. Sake tambayarsa yayi kafin ya kallesu yana fad'in bakowa. Ammi tace banyarda ba, taya zaka farka da sunan mutum abakin ka da alamu mafarkinsa kayi, kuma da tunaninshi ka kwanta. 'Bata fuska yayi yana kokarin sauka yace Ammi nace bakowa wani abokina ne. Dady yace shikenan tashi kaje kayi wanka kayi sallah kazo ina da magana da kai. **** **** Wai Nabeel lafiya kake kuwa? Jiya da dare ina kallo kazo ka zauna kayi shiru kamar da magana abakin ka, na tambayeka kace bakomai ka tafi, yauma gashi kazo mun gaisa kuma kazauna kamar zaka fad'i wata magana amma kayi shiru. Gyara zama Nabeel yayi yana fad'in Abbah dama wata tambaya zanyi maka to jiya naga hankalin ka yana wajen kallon news shiyasa na tafi. Kofin shayin Abbah ya aje yana fad'in ina jinka. Duk'ar da kai Nabeel yayi yana fad'in d'azu ne da ana gyara wancan tsohon d'akin na kaya shine naga wata tsohuwar jarida, har na barta sai kuma naga sunan makarantar da kayi aiki a jiki ga hoton wani yaro a kwance da kayan makarantar jikinsa duk jini, hakan ne yaja hankalina na karanta shafin, kuma hada hotonka na gani a kasan shafin a matsayin ka na shugaban makarantar, to shine labarin yaja hankalina nakeso naji yanda abun ya faru. Saurin zare glass d'in idonshi yayi yana kallon Nabeel, ido Nabeel ya d'ago yana karantar mahaifinsa. Kayi hak'uri Abbah idan maganar ta b'ata maka rai. Ajiyar zuciya Abbah yayi yana fad'in waye ya baka wannan labarin? Nabeel yace a jarida na gani. Jinjina kai Abbah yayi yana fad'in dama ba'a kone duk wasu jaridun d'akin ba? To yaushe ma aka fiddo da kayan d'akin tunda nasan babu abinda za'ayi a d'akin, ko dai kaine kaje kayi mani bincike? Saurin girgiza kai Nabeel yayi yana fad'in da gaske gyaran d'akin nasa ayi, gashi can ma suna k'arasawa. Ina jaridar take? Abbah ya fad'a jiki a sanyaye. Hannu Nabeel yasa a aljihu ya cirota ya mik'a masa. Shiru Abbah yayi yana kallon hoton Farouk da yake kwance cikin jini ga wuyansa da shatin wuka. Wasu hawaye ne suka taho masa, da sauri ya maida glass d'inshi ya aje jaridar. Kallon Nabeel yayi cikin dakiya yana fad'in wannan ai tsohon abu ne, kanaga tun 2008 fa, ni harna manta da abun ma, muma haka muka samu labari dan abun ya faru ne bayan an tashi daga makaranta. Nabeel yace to Abbah bakuyi bincike ba? Girgiza kai yayi yana fad'in duk abinda ya faru bayan makaranta to bamu da hakki akansa, sannan kuma abun ba'a makaranta ya faru ba, kaga bamu da ikon yin wani abu, kayan makarantar da suke jikinsa ne yasa kaga ansa hotona saboda 'Dalibina ne, da ace Iyayenshi sun nuna zasu shigar da k'ara da amatsayin mu na shuwagabannin makarantar Yaron mun taimaka wajen ganin a kwato masa hakkinsa, amma koda mukaje gaisuwa Mahaifin Yaron yace abar maganar. Amma Abbah.... Kaga Nabeel bana son yawan tambaya, kana son jin abinda ya faru kuma na fad'a maka, bansan ta yanda aka kashe shi ba tunda ba'a makaranta ya mutu ba, dan haka bana so ka tado mani da abinda yawuce shekaru da yawa, ka maida hankali wajen aikin ka zaifi maka. Tashi kaje, kuma bana so naji ka sake tada maganar dan nasanka da son kwato ma mutane hakkinsu, shiyasa ma ka zab'i kayi aiki a hukumar kwato ma d'an Adam hakkinsa. Jiki a sanyaye Nabeel ya fice, kai tsaye wajen masu gyaran d'akin ya nufa, yana zuwa ya iske har sun gama sun rufe d'akin an kwashe dattin. Zama yayi yana murmushi, dama yasan za'a iya samun tsohuwar jarida a wannan d'akin, shiyasa tunda Adnan ya fad'a masa an buga labarin ajarida a daren jiya yayi tunanin yazo ya bincika dan yasan Abbanshi akwai aje tsofaffin kaya, hakan yasa yau tunda safe yashiga d'akin, cikin ikon Allah yaga jaridar, shiyasa yasa masu aiki su gyara d'akin gudun kada ya kaima Abbah jaridar yace da niya ya bincikota. Ajiyar zuciya yayi yana tuna yanayin da yaga Abbansa aciki, tabbas akwai wani b'oyayyan lamari, akwai abinda Abbansa ya sani yake b'oyewa, haka ma Adnan ba gaskiyar labarin ya bashi ba. Dole yasan gaskiyar labarin kodan ya taimaki Abbansa kada mutuwa ta riskeshi da hakkin wasu. Waya ya ciro ya kira Adnan, bayan sun gaisa yace mashi yana so su had'u anjima. Adnan yace shikenan. Kashe wayar yayi ya koma cikin gida. **** *** Hello Alhaji Marusa lafiya kuwa naji kamar kana cikin damuwa? Alhaji Barau ya fad'a cikin tashin hankali. Alhaji Marusa yace nima tambayar da zan maka kenan najika cikin tashin hankali, yanzu nake shirin kiranka sai gashi ka kirani. Narke murya Alhaji Barau yayi yana fad'in store d'in kayana akazo cikin dare aka yashe ni, komai basu bar mani ba, da asuba Mr. Kallah yamun waya babban shagonshi na garinsu cikin dare ya kama da wuta ko tsinke ba'a fitar ba, shine nace bara na kiraka na fad'a maka halin da muke ciki. Hawaye ne suka zubo ma Alhaji Marusa yana fad'in naku me sauki ne, tun jiya na kira ku amma wayar ku bata shiga, wallahi jiya banyi bacci ba, gaba d'aya tashin hankali yamun yawa ko abinci na kasaci, shikenan talauci ya fara mani sallama Alhaji Barau. Mekake fad'a ne haka Alhaji Marusa? Sun takaita ni Alhaji Barau, kayan da nayi oda jiya an d'auko mani su cikin dare aka tare masu motar aka kwace sannan aka kashe su, kaya ne masu tsadar gaske, na saka dukiyata mai yawa wajen d'aukosu, sannan babbar ma'ajiyata itama yau da asuba akamun waya ta kone kurmus, shikenan nashiga ukku. Murmushin gefen baki Alhaji Barau yayi kafin ya canza fuska yana fad'in yaushe ka bada odar kaya Alhaji Marusa? Ai na d'auka mun yanke shawarar had'a guiwa mu d'auko wasu kaya gaba d'aya, tun daga lokacin kuma babu wanda ya sake shigo da kaya amma gashi kace an kawo maka kaya jiya? Daburcewa Alhaji Marusa yayi yana fad'in ba su bane, wad'annan wasu ne daban abokin harkallarmu yamun tayinsu shine na tura masa kud'i, dan Allah kazo inaji dole muje asibiti dan numfashina baya tafiya dai-dai. Alhaji Barau yace shikenan kazauna kada ka tashi gani nan. Godiya yayi masa ya kashe wayar. Wata irin dariya Alhaji Barau yasa yana fad'in damu kake magana, Allah yasa ma kasheka mu huta. Jakarsa ya d'auka ya saukko. A falo ya iske su Momy, kallonta yayi yana fad'in direba zaizo ya amsar mani kayan kari sauri nake Alhaji Marusa beda lafiya. Momy tace ikon Allah, meya sameshi kuma? Alhaji Barau yace idan na dawo zakiji amma dai bala'i ne ya afka masa. Momy tace to Allah ya kyauta, ince dai babu komai naka a cikin bala'in? Murmushi yayi yana fad'in babu. Kai ta jinjina tana fad'in to mun gode Allah, sai ka dawo. Yana fita direbanshi yazo ya amshi jakar hannunsa ya bud'e masa mota yashiga suka bar gidan. A hanya aka kirashi da wata lamba, yana d'auka aka fad'a masa babban 'Dan Alhaji Marusa ne. Alhaji Barau yace naji dai, lafiya ko? Daga can aka fad'a masa Alhaji Marusa ne ya fad'i an wuce dashi asibiti. Cike da jimami yace gashinan zuwa.Murmushi yayi ya kalli direba yana fad'a masa su wuce asibitin su. Mr. Kallah ya kira ya fad'a masa yace gashinan zuwa. **** *** Fawwaz meya had'a ka da wannan maganin mai k'arfi haka? Kauda kai yayi yana fad'in Dady mura nakeyi shine nasha. Ammi tace murar ce tasa ka shanye kwalba d'aya? Saurin kallonta yayi yana fad'in Ammi wace irin kwalba d'aya kuma, ya dad'e fa iya yanda akace asha nake sha kawai jiya ne ya k'are. To meya saka dogon bacci haka? Dady yace isa haka Ammi tunda yace ba duka yasha ba abar maganar. Tab'e baki tayi tana fad'in kaje kaci abincin ka. Dady yace sa akawo masa nan. Tashi tayi tana fad'in wallahi Alhaji kana shagwab'ar da yaron nan, ya girma amma ka hanashi ya fahimci haka. Dady yace e naji bakomai. Murmushi Fawwaz yayi yana fad'in Dady da Ammi nah. **** **** Abbah ina kwana ya gidan? Lafiya lau jiki yayi sauki ai. Alhaji Mansur yace to madalla, sai ka k'ara kula, bana so kana saka damuwa aranka, sai jiya Maman ku take fad'a mani baka da lafiya. Ra'eez yace ai na warke Abbah. Alhaji Mansur yace ta fad'a mani kokarin da kukeyi kai da abokan ka, kayi masu godiya, insha Allahu komai ya kusa zuwa k'arshe. Ra'eez ya fad'a masa yanda sukayi da Kawun Jabeer. Alhaji Mansur yace Allah sarki Brr. Kamal, kaga kuwa na rasa lambarshi ka turo mani sai muyi magana dashi, Abubakar ma zan kirashi na fad'a masa shari'ar ta kusa zuwa dan ya shirya. Ra'eez yace yanzu zan turo maka. Alhaji Mansur yace maganar motarka ban manta ba, wannan satin zai dawo zai zo ya dubata. Ra'eez yace to Abbah nagode, agaishe dasu Umma. **** *** Yes, shigo. *Malan Dauda* lafiya dai,,? Risnawa yayi yana fad'in 'Yallab'ai kana da bako. Bako kuma, waye ne? E to ya nuna mani katinshi ma'aikacin gidan babban redion ne. Shikenan kace yashigo. Da sallama Rafeek yashigo ofis d'in Kwamishna, amsawa yayi yana nuna mashi wajen zama. Hannu Kwamishna ya mik'a masa suka gaisa. Murmushi yayi yana fad'in lallai yau muna da manyan baki. Murmushi Rafeek yayi yana fad'in 'Yallab'ai barka da aiki. Kwamishna yace yauwa kaima sannun ka da aiki, ai kune masu aiki domin kuna nishad'antar damu da labaruka masu gamsarwa, musamman kai, dan ina kallon labaranka. Ruwan da masinjan ya aje ya d'auka yasha yana fad'in ai abun ba sauki 'Yallab'ai. Kwamishna yace to Allah yasa mudace. Rafeek yace amin. Wato dama nazo ne ina so naroki alfarmar fira da kai agidan redion mu idan babu damuwa. Murmushi Kwamishna yayi yana fad'in haba babu damuwar komai, ai gidan redion ku babba ne, kunsan abinda kukeyi shiyasa nake matuk'ar son sauraren abinda ya fito daga can, babu komai yaushe ne lokacin firar? Rafeek yace 'Yallab'ai kaine zaka sa mana lokaci ai. Murmushi Kwamishna yayi yana fad'in ko gobe ma yayi. Rafeek yace to mungode Allah ya k'ara girma. Kwamishna yace amin. Kati Rafeek ya mik'a masa shima ya bashi nashi. Godiya yayi masa ya baro ofis d'in cike da farin ciki, kai tsaye asibitin da akayi masa kwatance mallakin Dr. Aliyu Sani ya nufa. Kwamishna kuwa farin ciki ne ya rufeshi jin za'ayi fira dashi a babban gidan redio, yasan tunda suka gayyaceshi sun yaba da aikinsa shiyasa suke son fira dashi, yasan kilama ya samu lambar yabo idan aka ga karramawar da 'yan gidan redion zasuyi mashi. **** **** Adnan maganar daka fad'a mani gaskiya ce kuwa? Kallon Nabeel Adnan yayi yana fad'in baka yarda dani bane? Girgiza kai yayi yana fad'in na yarda da kai, sai dai acikin labarin daka bani baka fad'a mani gaskiyar yanda abun ya faru ba, da alama kasan komai tunda makarantar kuce, kuma Yaron ajinku d'aya, kawai dai kana b'oye mani ne saboda kana jin kunyar ka tona asirin mahaifina. Adnan yace ya kake fad'in haka, waye ya fad'a maka Abbanka yana da hannu acikin abinda ya faru? Idan beda hannu ka fad'a mani waye yake bayanshi to? Ajiyar zuciya Adnan ya saki yana fad'in wai Nabeel lafiya kake kuwa, yanda ka d'auki wannan abun kamar wani naka ne haka ta faru dashi. Murmushi Nabeel yayi yana fad'in kada kamanta aikina ne, Allah ya bani ilimin sanin yanayin da mutum yake ciki, gashi kuma ina aiki a k'arkashin masu kare hakkin d'an Adam (Human right), tun daka fad'a mani wannan labarin nasan dole Abbah yana da alak'a dashi, kaima kana neman wani abu ne shiyasa kazo mani da maganar, domin bani da had'i da labarinka amma gashi kazo mani dashi, shekarar mu nawa tare baka tab'a bani wannan labarin ba sai jiya. Uhmm Adnan ko baka fad'a mani ba dole Abbah yana da masaniya akan wannan abun, kuma ka sani idan baka fad'a mani ba zanje nayi bincike da kaina, domin tunda ka bani labarin nan ya tab'a zuciyata, kuma naji ina da sha'awar taimakawa. Jinjina kai Adnan yayi yana fad'in kayi hak'uri zan baka labari, abun ne babu dad'in ji dan bansan yanda zaka kalleshi ba tunda ya shafi ahalin ka, amma tunda kace na fad'a maka zan fad'a maka, sai dai ina rokon ka koda kaji labarin idan har bazaka taimaka ba saboda Mahaifinka dan Allah kada ka fad'ama kowa. Nabeel yace wallahi koda Abbah ne ya kashe Farouk sai na tabbatar da gaskiya, dan haka ina jinka.... Ur's. Nabeelert Lady🖋 [3/10, 8:40 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.* 3⃣8️⃣ Hannu Nabeel yasa yana share hawayen da suka jik'a masa fuska na tausayin labarin da Adnan ya gama bashi, Adnan ma kukan yakeyi, jiyake kamar ayanzu abun ya faru. Girgiza kai Nabeel yayi yana fad'in na sani dama Abbana yana da masaniya akan wannan abun, tun d'azu da mukayi magana naga halin da yashiga hankalina bai kwanta ba, hakan yasa nace ka fad'a mani gaskiya. Adnan yace wallahi Nabeel tunda Yaya Sameer yazo mani da maganar hankali na yake tashe, duk da abaya ina d'an tuna abun amma ba kamar da Yaya yazo mani da maganar ba, tun daga ranar komai ya canza mani, wallahi jiya har mafarkin Naseer da Farouk nayi, shiyasa na kudirta araina ko zan rasa raina sai na bayar da sheda akan shari'ar da za'a gabatar, gaba d'aya laifin mu ne, da ace mun fad'i gaskiya duk haka bazata faru ba. Nabeel yace dole a tabbatar da wannan gaskiyar, koda ace dasa hannun Abbah akayi kisan wallahi sai an tona komai, sai kuma Allah yasa babushi aciki, laifinsa d'aya daya taimaka ma masu laifi wajen b'oye gaskiya, nasan shima dole ayi masa hukunci. Jinjina kai Adnan yayi yana fad'in nagode Nabeel, hakika kai d'in abokine nagari, na d'auka zansha wahala kafin ka bani had'in kai sai gashi kaima zaka bada taka gudummuwar, tabbas ka dace da yanayin aikin ka, Allah ya saka maka da mafificin alkhairi. Nabeel yace amin, sai dai kuma banso kayima Fawwaz wannan maganar ba, domin nasan duk inda yake maganar tana masa yawo akai, duk lokacin da yaji an shigar da k'ara kaine zaka fad'o masa arai, zai iya yin duk abinda zeyi wajen ganin bakaje kotu ba. Adnan yace ka barshi Allah ya fishi, gara da nayi masa maganar na tabbata bazai sake kwanciyar hankali ba. Nabeel yace haka ne, Allah ya bamu ikon tabbatar da gaskiya. Adnan yace amin. Sallama yayi mashi yawuce cike da farin ciki. **** **** Tsaye Rafeek yake a bakin k'ofar asibitin Dr. Aliyu Sani sai kallon agogo yakeyi, wani ma'aikacin wajen ne yazo wucewa, da sauri Rafeek ya k'arasa yayi masa sallama. Murmushi mutumin yayi yana amsawa dan ya gane Rafeek saboda ba b'oyayye bane kasancewarsa ma'aikacin gidan babbar redio. Hannu Rafeek ya bashi suka gaisa. Mutumin yace yau muna da babban bako, shine kuma kake tsaye a waje Malan Rafeek. Murmushi Rafeek yayi yana fad'in ai ban dad'e da zuwa ba dama ina jiran naga wani ne. Mutumin yace barka da zuwa ni sunana *Dr. Sageer Isah*, kai kam nasan naka domin sananne ne a wajen kowa. Murmushi Rafeek yayi yana fad'in nagode sosai Dr. Sageer. Shiru yayi kafin yace dan Allah Dr. Aliyu fa? Dr. Sageer yace aikuwa yau zaishigo dan yau ranar zuwansa ne, kasan Dr. Ba kasafai yake shigowa ba akwai wasu aiyukan da suke gabansa, amma yau munyi waya yace zaishigo, sai dai ban sani ba ko da wuri zai shigo. Jinjina kai Rafeek yayi yana fad'in ina jin labarinsa gaskiya babban likita ne, gashi har ya bud'e asibitinshi, ga na gwamnati da yake aiki, ga sauran wajaje da yaje gudanar da aiyukansa, hakan yasa nakeso mu d'an gana dashi. Murmushi Dr. Sageer yayi yana fad'in ai Dr. Ba sauki, mutum ne mai matuk'ar son kud'i, shiyasa gaba d'aya rayuwarsa beda lokacin kanshi, duk wani abu indai zai kawo kud'i to Dr. yana gaba wajen nemoshi, shiyasa asibitin nan muke da abubuwa da yawa, ba dai muje waje muyi wani abu ba sai dai ma azo wajen mu ayi. Rafeek yace Allah sarki, gaskiya yasan kanshi, ai duniyar sai da neman kud'i. Dr. Sageer yace muje daga ciki ka jirashi ai bazamu bar babban bako a waje ba. Rafeek yace shikenan muje, amma idan naga bezo ba zan tafi saboda na baro aiki. **** Ra'eez Yaya fa yace mu fara shirya yanda za'a shigar da k'arar su Naseer, dan sunyi waya da Adnan ya fad'a masa an samu Nabeel zai taimaka, tunda ba'a gano Iyayen Farouk ba gara ashigar da shari'ar Naseer hakan ne zai tono ta Farouk. Ajiyar zuciya Ra'eez yayi yana fad'in nima so nake zuwa litinin afara shari'ar dan bana so murasa damar da muke da ita. Jabeer yace sai dai Yaya yace beyi magana da Baffansa ba, yafiso sai anshigar da k'arar kafin yayi masu magana. Ra'eez yace ina tsoron kada suce basu amince ba. Jabeer yace zasu amince, domin babu wanda zaiji labarinka be tausaya maka ba, kuma ta shari'ar su ce za'a tado taka. Ra'eez yace Allah yasa. Jabeer yace amin, wai ina mutuniyar? Tsaki Ra'eez yayi yana fad'in ko jiya tamun waya muka gaisa. Jabeer yace baiwar Allah. Tashi Ra'eez yayi yana fad'in muje ni kada ka fara kawo mani maganar wata Raheena. Dariya Jabeer yayi yana fad'in daga fad'in gaskiya. **** *** Dr. Sageer ya aiki ina fatan komai yana tafiya dai-dai? Jinjina kai Dr. Sageer yayi yana fad'in aiki lafiya lau babu matsalar komai, sai dai kana da babban bako. Glass ya cire yana fad'in bako kuma? Ai babu wada yace mun zai zo. Dr. Sageer yace wannan ma'aikacin babban gidan redion ne *Rafeek Sambo Jarmai*. Jinjina kai yayi yana fad'in meya kawo d'an jarida waje na kuma? Dr. Sageer yace yanda kake cigaba 'Yallab'ai ai dole 'yan jarida surika son ganinka, shima d'azu ya gama yabonka. Murmushi Dr. Aliyu yayi yana fad'in ka shigo dashi to. Dr. Sageer yace yanzu kuwa. Bayan Rafeek yashigo suka gaisa sai Dr. Sageer ya basu waje. Dr. Aliyu yace yau kaine da kan ka? Rafeek yace wallahi kuwa, jiya nashiga babban asibiti wajen wani abokina shine ake maganar irin kwazonka shine nace ni kuma zanzo naga asibitinka kuma mugaisa. Murmushi Dr. Aliyu yayi yana fad'in amma nagode, ai mutum baya zama gwarzo dole saiya jajirce, kafin na kawo wannan matsayin nasha gwagwarmaya sosai, da haka dai ina hak'uri har Allah ya d'aga ni. Rafeek yace wannan haka yake, ai kamar babban Alkali ne Alhaji Barau, duk wanda yasanshi yasan yanda yake da jajircewa awajen aiki, saboda kok'arinsa sai da sunanshi yayi fice a gidan redion mu, sannan ga tsohon Alkali, su duka biyun mutane suna alfahari dasu. Gyara zama Dr. Aliyu yayi yana fad'in Allah sarki Brr. Barau, ai mutumina ne sosai, yanzu ma aiki ne yamun yawa shiyasa muka rage gaisawa, ai ta silarsu na samu alkhairi sosai, zan iya cewa ta silarsu na kai wannan matsayin da nake ayanzu, domin sun taka rawar gani arayuwata. Jinjina kai Rafeek yayi yana fad'in da alama kayi masu abinda sukaji dad'i hakan yasa suka tsaya maka. Dr. Aliyu yace sosai kuwa, domin nine na fara taimaka mashi ya kai wannan matsayin da yake kai kafin shima yasa tsohon Alkali da wasu manya suka dafa mani, tabbas nine na fara taimaka masu. Rafeek yace idan haka ne kaine ka tsaya masu ba sune suka tsaya maka ba, domin duk wanda zai maka wani taimako har kaci nasara arayuwa to baka da kamarsa, duk da bansan abinda kayi masu ba amma nasan amatsayinka na babban likita nasan ka cece rayuwar wani daga cikinsu. Girgiza kai Dr. Aliyu yayi yana fad'in ko d'aya, kawai nayi masu.... Gyaran murya yayi yana fad'in haka ne, kasan mu likitoci akwai mu da taimako, idan kuma mutum yasan alkhairi to baya mantawa damu, wannan shine abinda ya had'ani dasu har muke abota. Rafeek yace gaskiya kai d'in na daban ne, gashi dai kaine mai taimakon amma duk da haka kana ganin sune suka taimaka maka, Allah ne zai iya biyanka. Murmushi Dr. Aliyu ya saki yana fad'in maganar ka gaskiya ce Rafeek, ya kamata ace har yanzu suna bani girma, sai dai kuma nine nake nemansu ba sune suke nemana ba, akwai Alhaji Marusa da Mr. Kallah duk mutane na ne. Rafeek yace saboda ka gama masu amfani shiyasa suka kyale ka, kasan suna hud'd'a da mutane da yawa dole surik'a samun masu yi masu alfarma da yawa shiyasa bazasu rik'a neman wad'an da suka taimakesu ba. Murmushi Dr. Aliyu yayi yana fad'in aiko be kamata ace sun manta dani ba musamman shi Brr. Barau, domin na bada gudummuwa wajen hayewarsa wannan kujera, gaskiya ka sosa mani inda yake mani kaikayi ma, maganar ka gaskiya ce, bekamata ace nine nake binsu ba domin nine nayi masu rana. Murmushi Rafeek yayi ya mik'e yana fad'in 'Yallab'ai zan koma, dama nace zanzo mugaisa ne. Hannu Dr. Aliyu ya bashi yana fad'in nagode Rafeek, ga katina sai murik'a gaisawa ko. Rafeek yace nike da godiya. Sallama yayi mashi ya fice ya barshi yana juyi a kujera cike da tunani. Murmushi ya saki yana fad'in Allah yayi maka albarka Rafeek, ka sosa mani inda yake mani kaikayi, ga babban Lab can zan fara ginawa dama ina tunanin gininshi bara nayi amfani da wannan damar, Allah ma yaso banyi sub'utar baki ba dana fad'a masa tsohon sirrin mu. Waya ya ciro ya fara neman Alhaji Barau. Bugu biyu ya d'auka, bayan sun gaisa Alhaji Barau yace babban likita kwana da yawa, ka ganni nan nazo asibiti an kawo Alhaji Marusa. Dr. Aliyu yace kunki dai dawowa asibitina duk da kunsan nima ina da kayan aiki. Alhaji Barau yace ba haka bane, kasan asibitin mu hada turawa kai kuma naka babu wasu kwararrun likitoci, kasan ni kuma bana son wasa da rayuwa shiyasa na rik'e asibitin Dr. James. Jinjina kai Dr. yayi yana fad'in idan da amana ai ruwa bazaici gwani ba. Alhaji Barau yace me kake nufi? Gyara zama Dr. yayi yana fad'in manta kawai, dama wasu 'yan kud'i nake so zan fara gina parmanent side na Lab d'ina kuma babu kud'i masu yawa a hannuna shine nace bara na maka magana. Shiru Alhaji Barau yayi kafin yace haba likita, taya zaka zo mani da maganar kud'i da rana tsaka haka. Murmushi Dr yayi yana fad'in ko bashi ne ai zan samu ko? Alhaji Barau yace amma kaji nace ankawo Alhaji Marusa asibiti ko? Kuma ni yanzu banida kud'in da zan iya baka aro dan bikin d'iyata za'ayi, wai Likita meyasa kake son tambayata kud'i ne. Dr yace yanzu dan nace ka bani bashi shikenan ya zama laifi, haba Alhaji kada ka mance da alkhairin da nayi maka fa, ko shekaru dubu za'ayi bekamata kamance da abinda nayi maku ba, domin nayi maku babbar rana kaima kasani, kuma har yanzu da bazata kake rawa. Tsaki Alhaji Barau yayi yana fad'in ni bangane abinda kake magana akai ba danni bani da lokacin tunawa da rayuwar baya, koma menene bani da kud'i sai dai kajira Alhaji Marusa ya warke, ka gaishe da iyalin ka sai anjima. Kallon wayar yayi jin an katse. Murmushi yayi yana fad'in maganar ka gaskiya ce Rafeek, dama nayi haka ne dan na gwadasu, lallai Brr. Barau ya cika butulu, amma bakomai indai nine bazan sake nemanshi ba, nagode Allah nima ina da kud'i, ko ba komai naci daga jikinsu da kud'in su ma nayi wannan ginin. *** *** Wai *Marwan* meya faru ne? Wanda aka kira da Marwan ya yamutsa fuska yana fad'in nima bansani ba, nazo zan amshi wasu kud'i ina shiga falon kawai na ganshi ya mik'e daga zaunan da yake, kafin na shiga kawai naga ya zube k'asa, gashi can dai ana dubashi. Alhaji Barau yace shima Alhaji Marusa sai da nace mashi ya zauna nazo amma ya tashi, ba'a son idan tashin hankali ya same ka ka tashi. Marwan yace kamar ya ban gane ba? Labarin abinda ya faru ya fad'a masa. Yamutse fuska yayi yana fad'in amma ai babu abinda zai tab'a dukiyarshi dan ya rasa d'an wannan abun dan nasan Dad yana da mak'udan kud'i, meye nashi nashiga damuwa gashinan zai jama kanshi, da kyar idan bai samu mutuwar b'arin jiki ba, yanzu ko kula dashi ai aiki ne, sai dai ya biya kud'i a fiddashi waje yayi jinyarsa acan danni cikin satin nan zan koma India. Ido Alhaji Barau ya tsura ma Marwan har ya gama maganarshi. Ajiyar zuciya ya saki yana fad'in yanzu ina K'anin naka? Marwan yace kasan baya son zaman k'asar nan, dama kuma Dad baya son muna zuwa gida, Mom kuma taje Dubai sai jibi zata dawo. Alhaji Barau yace to Allah ya kyauta, sai ka tsaida tafiyarka ka kula dashi kafin asan abunyi. Waro ido yayi yana mik'ewa, kallon agogo yayi yana fad'in yanzu ni ina da wajen zuwa, dama kai na tsaya jira da naji kace kana hanya, zanje kafin anjima na dawo. Bai jira amsar Alhaji Barau ba yayi gaba. Baki Alhaji Barau ya saki yana kallon Marwan, a hankali yake fad'in Allah nagode maka da baka bani namiji ba, tabbas yanzu Alhaji Marusa zaiyi nadamar rashin kula da yaranshi da yayi, koba komai ita tarbiya wani abu ce, saboda baka son takura ka tura yara waje sai dai ka aika masu kud'i, lallai Alhaji Marusa taka tazo k'arshe, nima ba zama zanyi ba ina da aikinyi. Fitowar likita yasa yayi saurin binshi zuwa ofis. Bayan sun gaisa yake fad'a masa sanadiyar fad'uwar da yayi ya samu mutuwar b'arin jiki, dole abashi gado saboda za'a fara masa gashi, anci sa'a ma akwai sauran kud'inshi da yawa a asusun asibitin da ya zuba ana juyawa saboda rashin lafiyarshi data iyalinshi, dan haka yanzu kulawa kawai zasu bashi, sannan jininsa ya hau dole ya samu hutu. Alhaji Barau yace lallai tashi ta sameshi, tunda akwai kud'i ai damuwar da sauki, yanzu acigaba da bashi kulawa zamu rik'a waya. Likita yace ba komai zamu kula dashi. Sallama yayi mashi ya fita. **** *** Wai Rafeek lafiya kwana biyu ka canza ba kamar yanda kake ba? Murmushi yayi yana fad'in lafiya lau Baffa kawai wani aiki ne ya tasoni gaba shine yasa bana zama. Gyara zama Baffa yayi yana fad'in bana so kana matsama kanka, nasha fad'a maka aikin ku yana da had'ari, shiyasa kaji ina yawan tambayarka dan bana so kajefa kanka cikin damuwa kazo kaja mana, dan Allah Rafeek kada kajawo mana abinda zamu rasaka kamar yanda muka rasa d'an uwanka, kome zakayi arayuwa yana da kyau karika sanar mana domin addu'ar mu agareka kariya ce. Jinjina kai Rafeek yayi yana fad'in Baffa banyi niyar sanar da ku komai ba har sai na kammala abinda nakeyi, amma wannan maganar da kayi tasa jikina yayi sanyi, tabbas akwai abinda nake shirinyi, kuma ina da niyar sanar daku nan gaba kad'an, amma dole yanzu na fad'a maku. Dama shari'ar marigayi Naseer ce nakeso zan dawo da ita domin abi masa hakkin sa sabo.... Dakata Rafeek! Ummansu ta fad'a cikin karaji, da sauri ya d'ago kai yana kallonta. Hawaye ne suka gangaro a fuskarta tacigaba da fad'in ban amince maka ka tado wannan maganar ba, abinda yawuce shekara da shekaru meye amfanin tadoshi, wato acan baya k'arfin ka be kawo ba shiyasa da mukace abarshi ka hak'ura, yanzu kuma kana ganin kayi kwari ka isa tsayawa da k'afafuwanka shine zaka tado mana da tashin hankalin da muka manta dashi, wallahi Rafeek ka fita a idona, zan sab'a maka akan wannan maganar, babu wanda ya isa ya maido da wannan maganar baya, domin nasan ruhin Naseer yana can cikin salama. Matsowa Rafeek yayi yana had'a hannu, magiya zai fara mata ta daka masa tsawa dole tasa yayi shiru. Girgiza kai Baffa yayi yana fad'in shiyasa jikina be bani ba kaji nayi maka wannan tambayar, yanzu Rafeek so kake kaima mu rasaka kamar yanda muka rasa Naseer? Allah ya fimu sanin wad'an da suka aikata masa haka ka barsu dashi zeyi maganinsu, idan ma ka shigar da k'ara inaso kaje ka soketa, domin babu wanda zai sani shiga kotu, ko kai babu inda zakaje. Hawaye ne suka zuboma Rafeek, kai yashiga girgizawa yana fad'in dan Allah Baffa ku saurare ni, wallahi ba saboda Naseer zanyi wannan abun ba, inaso a tabbatar da gaskiya shiyasa na fara sako maganarshi amma.... Tashi kabar gidan nan Rafeek, kuma kada ka sake shigowa matuk'ar da wannan maganar zaka zo. Umma ta fad'a cikin dakiya. Kallon Baffa yayi yana hawaye. Kai ya jinjina masa hakan yasa ya fice yana share hawayen idonshi, yanzu ya zeyi dasu Ra'eez, duk wani sa ransu akanshi ne, sai da komai yazo k'arshe za'a hanashi. Wayarsa ce tayi k'ara, yana dubawa yaga Ra'eez, saurin seta kanshi yayi kafin ya d'auka. Bayan sun gaisa Ra'eez yace Yaya mun gama rubuta k'arar da za'a shigar, zan kawo maka kagani zuwa gobe juma'a sai ashigar da ita zuwa litinin ashiga kotu. Runtse ido yayi cikin k'arfin hali yace Ra'eez kai da Jabeer ina so anjima kuzo inaso muje wajen su Baffa ne. Ra'eez yace Yaya kamar akwai matsala ko? Murmushi yayi yana fad'in bakomai kawai kuzo. Jiki a sanyaye Ra'eez yace Allah ya kaimu. Kashe wayar yayi yana goge hawayen idonshi, dole ya sako su Ra'eez a wannan maganar idan ba haka ba Umma bazata tab'a amincewa ayi shari'ar ba, shi kuma yana so kowa yasan cewar ba Abbun Ra'eez kad'ai suka kashe ba, yafiso kowa yasan yanda suka aikata mugayen abubuwa. Motarshi ya nufa ya bar gidan. Ur's. Nabeelert Lady🖋 [3/10, 8:40 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.* 3⃣9⃣ Guiwa biyu Ra'eez yasa a k'asa ya had'e hannuwansa biyu yayin da hawaye suke ambaliya a idonshi, matsawa kusa da Baffa yayi bayan daya gama basu labarinshi, cikin kuka mai tab'a zuciya da raunanniyar murya yake fad'in Baffa na roke ku da girman Allah ku bar Yaya ya tayani wannan yakin, zuciyata tana da rauni, Allah shine yasan hakan shiyasa ya had'ani da Yaya tare da Jabeer, tabbas Yaya jigo ne agareni, shid'in tsani ne wanda zai taimaka mani zuwa ga kai matakin da nake fatan kaiwa da dad'ewa, matuk'ar kuka janyeshi acikin wannan shari'ar nasan zuciyata zata raunana, duk wani sa rai da nake dashi zan rasa shi, na amince a janye shari'ar Naseer amma dan Allah ku bar Yaya ya tayani kwatoma Ummu na hakkinta ko hakan zai zamo silar samun lafiyarta. Shiru yayi yana wani irin kuka mai ban tausayi. Gaba d'aya falon shiru yayi babu wanda baya kuka, duk dauriya irin ta Baffa sai da ya zubar da kwalla. Umma ce tayi saurin kamo hannun Ra'eez tana share masa hawaye yayin da nata suke zubowa. Girgiza kai tayi tana fad'in ban tab'a jin labarin daya tab'a zuciyata irin naka ba, ya isa kadena kuka, daga yau ka zama 'Dah na, haka zalika ga Baffansu nan ya zam mahaifinka. Kallon Rafeek tayi tana fad'in na amince maka ka tayashi tabbatar da gaskiya, shari'ar Naseer kuma baza'a fasata ba, kushigar da k'aran aranar litinin za'ayita. Tabbas ayanzu bazan yafema kaina ba idan naki amincewa ayi wannan shari'ar, dan haka na amince maka. Runtse ido Rafeek yayi hawayen farin ciki suna zubo masa. Murmushi Jabeer ya saki yana rungume Rafeek. Hannu Baffa yasa yana goge idonshi yace tabbas duniya babu gaskiya, ashe dama wad'an nan azzaluman sune sukayi silar mutuwar Mahaifinka? Tabbas nasan mahaifinka mutum ne mai gaskiya, duk da bani da alak'a dashi amma zuwanshi ya samar mana kwanciyar hankali, duk wasu masu shigo da haramtattun kaya sai da yayi maganin su, lallai barin irin su Alhaji Barau a duniya babbar illa ne, dan haka nima na amince a tabbar da wannan shari'a. Gaba d'ayansu farin ciki ya rufeso haka suka shiga yi masu godiya. Umma tace babu komai Allah yayi maku albarka, kuma yayi maku jagora akan wannan aiki da zaku fara, insha Allahu sai naga yanda k'arshen azzalumai zai kasance. Bayan sun fito Rafeek ya kallesu yana fad'in yanzu kam hankalina ya kawanta, shiyasa dama nace kuzo nasan zuwan ku ne kad'ai zaisa su Baffa su amince dani, dan haka Ra'eez akai wannan takardar kotu, nasan kana da basira ina so kasan yanda zakayi magana. Ra'eez yace insha Allahu. Sallama sukayi mashi suka wuce cike da farin ciki. Kai tsaye gidan su Jabeer suka wuce, acan suka ci abinci, sai da suka zauna suka huta kafin suka wuce gidan su Rumaisa. *** **** *Liberty Radio* 'Yallab'ai barka da zuwa. Kwamishna yace yauwa sannu Rafeek, amun afuwa aiki yamun yawa shiyasa ban samu zuwa da wuri ba hakan yasa na kira ka nace sai da dare zan samu shigowa. Murmushi Rafeek yayi yana fad'in har na cire ran zaka zo, dama aikin dare nakeyi yau shiyasa tunda nashigo da safe naga baka zo ba kawai na fita sai kuma ga kiranka. Gyara zama yayi yana fad'in ai bana son karya alk'awari, shiyasa nace maka sai zuwa dare nasan lokacin na samu saukin aikin. Rafeek yace barka da zuwa, ruwa ya aje masa tare da zubawa. Amsa yayi yana fad'in nagode. Bayan ya shanye ya kalli Rafeek yana fad'in sai mu fara kada na samu wani kiran. Murmushi Rafeek yayi ya tashi yana fad'in bismilla dama kafin kazo mun shirya komai. 'Yallab'ai gidan redion mu yana maka barka da zuwa. Murmushi Kwamishna yayi yana fad'in yauwa barka dai. Rafeek.. Jama masu sauraron mu barkan mu da sake had'uwa a wannan gidan redion namu mai albarka, ayau muna da babban bako wanda ya kawo mana ziyara kuma zamuyi fira dashi, mai sauraro idan kana biye damu zakuji sunan bakon namu da kuma yanda firar tamu zata kasance, kubiyomu a cikin shirin namu. To 'Yallab'ai mutane zasu so suji cikekken sunan ka da kuma irin matakin da kake ayanzu saboda kowa ya sheda ka. E to, ni dai sunana Bello Kabir, kuma nine kwamishnan 'yan sanda a garin lagos. 'Yallab'ai nasan kafin ka kawo wannan matsayin kasha gwagwarmaya har zuwa lokacin da Allah ya kawo ka wannan matsayin, ko zaka fad'ama masu sauraron mu irin gwagwarmayar daka sha? Kwarai kuwa nasha gwagwarmaya kafin nazo wannan matsayi, kuma dama kowa yasani kafin aji dad'i dole sai ansha wuya, kamar yanda kowa ya sani aikin 'Dansanda aiki ne na jihadi, aiki ne wanda dole sai ka bada k'arfin ka, dukiyar ka da kuma lokacin ka, duk wani d'an sanda yana fuskantar kalubale arayuwarsa, wasu ma suna rasa rayukansu akan wannan aikin, kamar yanda na bada misali da dukiya, tabbas akwai wani abun idan yazo maka dole sai kayi amfani da dukiyar ka kafin kaci nasara akanshi, haka ma lokaci, duk wani d'an sanda beda lokacin kanshi matuk'ar yasa aranshi k'asarshi yakema aiki, wani lokacin koda kana hutu zaka iya samun kira daga sama kuma dole kaje, shiyasa nace maka aikin d'an sanda aiki ne na sadaukarwa, d'an sanda beda lokacin kanshi sai lokacin al'umma domin su yake ma aiki, hakki ne ya rataya akanshi dole ne ya bama kowa tsaro, to da haka dai mukayi ta fafatawa da dad'i ba dad'i har Allah ya kawo ni wannan matsayi. Jinjina kai Rafeek yayi yana fad'in gaskiya dole na sara maka, tabbas aikin d'an sanda babban aiki ne, yakamata mutane su k'ara jinjina ma 'yan sanda kuma su k'ara basu muhimmanci domin suna da muhimmanci arayuwar mu baki d'aya. Kwamishna yace nagode, amma ina ganin mutane kad'an ne suke fahimtar muhimmancin mu, domin kuwa masu zagin mu sunfi yawa. Murmushi Rafeek yayi yana fad'in tabbas nasan akwai masu zagin 'yan sanda da yawa, sai dai kuma wasu suke b'ata wasu, da yawa mutane suna ma 'yan sanda kallon masu cin hanci da rashawa, wannan bakin fentin har yanzu yaki goguwa a wajensu, kuma wasu ne suka jawo wannan abun, duk yanda kuke aiki matuk'ar ana samun masu k'arb'ar cin hanci to al'umma bazata tab'a ganin muhimmancin ku ba, shiyasa ake son arik'a kamanta gaskiya. Kwamishna yace wannan shine babban abinda muke yaki dashi, amma har yanzu an kasa dainawa, saboda mutane suna d'aukar cin hanci shine abinda zai rik'esu. Murmushi Rafeek yayi yana fad'in 'Yallab'ai a matsayin ka na wanda yayi shekaru yana aikin d'an sanda, nasan dole akwai wani babban kalubalen daka fuskanta wanda bazaka iya mantawa dashi ba, ko zaka fad'ama masu sauraron mu irin kalubalen daka fuskanta? Kwarai kuwa akwai kalubale da yawa dana fuskanta, kowa yasan idan kana irin aikin mu akwai kalubale sosai akan mu, kuma nasha wahala sosai, amma juriya da jajircewa irin tawa yasa na kawo wannan matsayin. Jinjina kai Rafeek yayi yana fad'in duk da lokaci ya fara hararar mu amma zanso ka fad'ama masu sauraron mu a shekarun baya lokacin kana aiki a k'aramin ma'aikaci wane case ne yafi baka wahala kuma ya baka tsoro. E to, gaskiya nayi cases da yawa wad'an da bazan iya tunawa da wasu ba, amma ina ganin akwai wani case da na tab'ayi wanda yayi matuk'ar bani wahala da tsoro, idan ban manta ba yau kusan shekaru goma kenan, case ne wanda yake a cukurkud'e hakan yasa nasha wahala kafin na kammala lashi, zan iya cewa a wannan case d'in bayan kammalashi har k'arin matsayi na samu. To 'Yallab'ai tambayata ta k'arshe a wannan shirin ko zaka fad'a mana dalilin zuwanka wannan matakin? Gyara zama yayi kafin ya d'auki ruwa yasha yana gyara glass d'in idonshi. Kofin ya aje yana fad'in E to, gaskiya wannan matsayi dana zo zan iya cewa dalilin taimako ne yasa nazoshi, nasan kuma mutanan da suka taimaka mani nazo wannan matsayin har yanzu suna alfahari dani, bazan iya fad'arsu ba domin ba'a son ka fad'i wanda yayi maka alkhairi tunda dan Allah yayi, amma gaskiya har in mutu bazan iya mantawa dasu ba. Murmushi Rafeek yayi yana fad'in 'Yallab'ai kayi mana halin ku na 'yan sanda, domin baka fito fili ka fad'a mana silar zuwanka wannan matsayin ba. Murmushi Kwamishna yayi yana fad'in wannan kuma sirri ne. Dariya sukasa gaba d'aya. Rafeek yace daga k'arshe wata shawara zaka bama sauran 'yan sanda. E to inaso nayi amfani da wannan damar na k'ara bama sauran yan sanda shawara akan surike gaskiya, dan duk wanda ya rike gaskiya baya tab'ewa, kuma su sani wannan aikin da sukeyi a ciki zasu nemi duniyarsu da lahirar su, Allah yasa mudace amin. Juyowa Rafeek yayi yana fad'in to masu sauraron mu anan muka kawo k'arshen wannan shiri na fira da mukayi da Kwamishnan 'Yan sanda, sai muce mungode Allah yasa aje gida lafiya. Kwamishna yace madallah nima nagode, masu saurare ina maku fatan Alkhairi. **** Bayan da Rafeek ya koma gida duk da dare yayi sai da ya tace shirin da ya gabatar ya adanashi dan yasan zeyi masa amfani kafin ya kwanta. **** **** Alhaji ya jikin Alhaji Marusan? Jiki da sauki za'ace, amma fa yana can yana jin jiki. Momy tace bawan Allah, gaskiya asara bata da dad'i dole yashiga wannan halin, amma ai zaku taimaka masa da wani abun ko zai rage asara ko? Murmushi yayi yana fad'in Hajiya Binta kenan, baki san waye Alhaji Marusa ba, shine fa silar arzikin mu, taya kike tunanin dukiyarsa zata girgiza dan kawai yayi wannan 'yar asarar, kawai shegen son kud'i gareshi shiyasa yashiga wannan halin, amma babu abinda zamu taimaka masa dashi sai kulawa. Jinjina kai tayi tana fad'in to Allah ya kyauta ya kuma tsayar akanshi. Yace amin. Kallonta yayi yana fad'in wai Ra'eez yana zuwa gidan nan kuwa? Girgiza kai tayi tana fad'in rabonsa da gidan nan tunda yazo sukayi sallama da zamuje Dubai, amma tace aiki ne yayi masa yawa shiyasa. Murmushi yayi yana fad'in wallahi na kosa naga Raheena a gidan miji nima ko na samu jika. Momy tace lokacin zai zo, ai anyi mewuyar tunda ta samu mijin aure, Allah dai ya bashi ikon kammala wannan aikin lafiya. Alhaji Barau yace amin ya Allah. 🤣 **** **** Wajen k'arfe goma na safe Ra'eez ya kwankwasa k'ofar ofis d'in Alhaji Barau dan yaga lokacin da yazo, amsa mashi yayi tare da bashi izini hakan yasa ya tura k'ofar bakinsa d'auke da sallama. Amsawa yayi yana fad'in wai Ra'eez kaine shine ka tsaya kwankwasawa? Gaisheshi yayi yana fad'in wallahi kuwa. Kujera ya nuna masa yana tambayarsa k'arfin jiki. Ra'eez yace jiki yayi sauki babu abinda yake damuna yanzu. Alhaji Barau yace nima asibiti na biya shiyasa ban shigo da wuri ba, abokina Alhaji Marusa ne beda lafiya wata asara ce ta sameshi tunda yaji hankalinsa ya tashi ya zube shikenan sai ya samu shanyewar b'arin jiki. A zabure Ra'eez ya kalleshi yana fad'in Alhaji Marusan? Ido ya tsura mashi kafin ya furta kasanshi ne? Duk'ar da kai Ra'eez yayi yana fad'in a wajenka nasanshi shiyasa naji tausayinsa. Murmushi ya saki yana fad'in ai da sauki tunda likita yace jininsa ya sauka saboda har yanzu basu bari ya farka ba, sunfi so sai ya samu hutu zuciyarsa ta natsu sannan, a wajenshi ma na d'an jima saboda babu kowa a gunshi, kasan yaran zamani, akwai babban d'anshi amma saboda be damu dashi ba ko kuma ince shi Alhajin be jawosu ajikinshi suka saba ba shiyasa basu damu dashi ba, ga matarsa taje Dubai sai gobe zata dawo. Ra'eez yace Allah ya kyauta. Alhaji Barau yace amin. Kallonshi yayi yana fad'in kamar akwai magana a bakin ka ko? Jinjina kai Ra'eez yayi yana fad'in dama jiya bayan mun tashi daga aiki wani yazo ya shigar da k'ara, to case d'in kisa ne, kuma nine suka d'auka amatsayin wanda zai tsaya masu, shine nazo inji ko an kawo maka takardar? Gyara zama Alhaji Barau yayi yana fad'in yanzu na shigo gaskiya ban iske takardar komai ba, kila dai ko zuwa anjima, amma case d'in waye? Ra'eez yace e to, gaskiya tsohon case ne, dan abun ya dad'e za'ayi kusan shekaru sha biyu da faruwar abun, to alokacin basu da shedar da zasu gabatar ma kotu shiyasa sukayi hak'uri, amma ayanzu sun samu duk wata sheda shiyasa suke so ayi shari'ar. Tsaki Alhaji Barau yayi yana fad'in kaji wani shirme, ko sababbin cases nawa muke dasu duk basu ishemu ba sai an koma shekarun baya an d'auko mana wata tsohuwar shari'a saboda kawai an maida kotu wajen wasan yara, yanzu haka ko anyi shari'ar bance shedarsu zata wadatar ba, saboda na tabbata da wuya a samu wanda yayi kisan araye, idan ko an sameshi to wasu shedun basa nan, gaskiya banji dad'i daka amshi wannan case d'in ba, kawai ka turasu k'aramar kotu. Gyara zama Ra'eez yayi yana fad'in Alhaji a taimaka masu, kasan kowa yana alfahari da wannan kotun, ba kowa bane kuma yake jawo mata farin jini sai kai, yau idan babu kai a wajennan nasan ba kowa ne zaiso ya kawo shari'arsa nan ba, domin kaine hasken da yake haske kotun, duk wasu mutane da suke zarya nan saboda kai suke zuwa, idan sukaji kayi fatali da case d'insu zaka sare masu sa ran da suke dashi, domin idan basu samu adalci a wajen ka ba sun san babu inda zasuje a amshe su. Murmushi Alhaji Barau yayi yana gyara zaman glass d'inshi yace wannan haka yake, nagode daka tunatar dani, shiyasa nake jin dad'in kasancewar ka akusa dani, domin wani lokacin nakan so na kwafsa amma sai ka maidoni hanya, gaskiya Ra'eez kai d'in na daban ne, shikenan kashirya tsaya masu zuwa litinin za'a fara shari'ar, kuma insha Allahu zan sama masu adalci kodan ta silarka. Turo k'ofar ofis d'in akayi had'e da sallama, amsawa sukayi kafin ya shigo. Alhaji Barau yace Malan Jamilu yau ka makara ko? Wanda aka kira da Malan Jamilu yace wallahi iyalina ne basuji dad'i ba sai da mukaje asibiti amma da sauki. Alhaji Barau yace Allah ya basu lafiya, ai bazaka zauna ba dama yau juma'a sa hannu kawai ka tafi. Mik'a masa takarda yayi yana fad'in jiya aka kawota lokacin ka tafi shiyasa na ajeta, takardar... Katseshi yayi yana fad'in Ra'eez yayi mani bayani, amsa yayi yana fad'in zaka iya tafiya. Godiya yayi mashi Ra'eez ya gaishe shi yana masa ya mai jiki. Kud'i Alhaji Barau ya bashi yana fad'in ga wannan ka siya mata magani. Godiya yayi mashi ya fita yana mamakin yau Alhaji Barau yayi masa kyauta. (Niko nace agaban suriki ai dole yayi gwaninta😉) Tashi Ra'eez yayi yana fad'in zan koma nagode Alhaji. Murmushi yayi yana fad'in babu damuwa Allah ya bada sa'a, idan kana da wata matsala kazo ka fad'a mani, domin bazan bari ka fad'i ba. Godiya yayi masa ya fice. **** Dariya sosai Jabeer yayi jin yanda Ra'eez yayi da Alhaji Barau. Tsaki Ra'eez yayi yana fad'in wallahi wannan mutumin beda kunya, amma ka kyaleshi na kusa koya masa yanda akejin kunya. Jabeer yace gashi kuwa hada maka addu'ar neman sa'a besan akanshi zata k'are ba. Ra'eez yace ai d'azu munyi waya da Yaya yace ayau zai sanar da shari'ar dan yana so tayi mutane. Jabeer yace kasan kuwa duk wanda yaji za'ayi shari'ar shekaru da yawa dole yazo yaji yanda zata kaya, ni kaina ina so litinin tayi kawai naji yanda za'a fafata. Ra'eez yace wallahi ni kaina nakosa akammala komai kona samu natsuwa, gaba d'aya bani da lokacin kaina, Pretty hak'uri kawai take dani damma muna d'an waya. Jabeer yace ai komai ya kusa zuwa k'arshe da izinin Allah. Waya Ra'eez ya d'auka yana fad'in bara naji muryarta ko naji kwarin yin aikin dan gaskiya yau dole na tsaya fira. Murmushi Jabeer yayi ya mik'e yana fad'in nayi nan kada naji kayan haushi. Ra'eez yace idan kaji haushi gobe na ganka da budurwa. Jabeer yace kai dai kasa ido Allah ya kusa kawota. Maganar da yaji yasa ya maida hankalinsa ga wayar. Jabeer kuwa ficewa yayi yana masu dariya. Bayan ta gaishe shi yace Prettyna ki k'ara hakuri kinji, ni kaina ina kewar ki da yawa. Murmushi tayi tana fad'in haba bakomai, ai wannan aikin da kakeyi mu kake mawa, dan haka ina nan ina jiranka kuma ina maka addu'a nasan zakayi nasara. Ra'eez yace nagode sosai ina so yau kimun kwalliya kamar zakije party dan yau fira zamuyi. Murmushi tayi tace shikenan yanda kace, sai kazo. Ra'eez yace me zan taho maki dashi? Duk abinda yayi maka ta fad'a cike da farin ciki dan tayi kewarsa, kwana biyu koya zo baya dad'ewa shima da Mama kawai suke gaisawa. Ra'eez yace shikenan sai nazo ki gaishe da Abdallah da Mama. Zasuji ta fad'a. Kiss yayi mata yana fad'in miss u, da sauri ta kashe wayar. Dariya yayi yana fad'in zan kamaki ne. **** *** Tsaki Fawwaz yaja a karo na ba adadi, zaune yake a cikin lambun gidansu, yau kwana biyu kenan ya kasa samun nutsuwa, tunda Adnan yayi masa maganar Farouk shikenan hankalinsa yaki kwanciya, duk yanda yaso ya cire abun aranshi ya kasa, gashi baya so ya fad'ama Dad d'insa hankalinshi ya tashi, gara kawai yayi shiru ya magance matsalar da kanshi. Kashe sigarin daya gama sha yayi yana kurb'ar giyar da ya zuba a kofi, a 'yan kwanakin nan ko wajen abokansa baya zuwa saboda damuwa, shaye-shayenshi ya k'aru ko zai samu sauki amma abanza. Waya ya d'auka ya kira babban abokinsa, yana d'agawa yace *Milo* mu had'u a gidan shakatawa ta akwai maganar da zamuyi, amma kazo kai d'aya. Shikenan sai kazo Ur's. Nabeelert Lady🖋 [3/10, 8:40 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.* 4⃣0⃣ What? Dude kasan abinda kake fad'a kuwa? Kai Fawwaz ya jinjina yana zuk'ar sigari. Gyara zama Milo yayi yana fad'in lallai kai babba ne Dude, haba shiyasa baka da tsoro ashe tuni tsoron ya bar zuciyar ka, ai duk mutumin da zai iya aikata kisan kai bana tunanin yana da tsoro a ranshi, ka ganni nan ko fad'a bana so saboda nasan yanda halin maza yake akwai bak'ar zuciya, da an fara fad'a yanzu zakaji an yanki wani ko an fitar masa da jini, wannan dalilin ne yasa bana son zama a club. Tsaki Fawwaz yayi yana fad'in kada ka bani kunya mana Milo, ina tunanin na kawo kuka gidan mutuwa sai kazo mani da wannan banzar maganar. Gaskiya na fad'a maka ai, Milo ya fad'a yana kunna sigari. Ajiyar zuciya Fawwaz yayi yana fad'in wallahi tsoro nakeji kada Adnan ya tona abinda ya faru. Murmushi Milo yayi yana fad'in haba kada ka bani kunya, kada kamanta Dadyn ka shine tsohon Alkalin babbar kotu, duk da ya aje aiki har yanzu yana fad'a kuma anaji, sannan kace abun ya faru tun kuna secondary banga dalilin da zaisa ka damu kan ka ba, shima Adnan d'in cewa yayi kawai ya tuna maka ne bawai zai tona asiri yake nufi ba, kaga idan har zaka saka damuwa aranka ina tabbatar maka kaine zaka tona kan ka, kawai ka share kacigaba da chilling. Dariya Fawwaz yasa yana fad'in shiyasa nake sonka abokina, amma wallahi kwana biyu bana baccin kirki. Hannu Milo yasa aljihu yana fad'in ina zuwa, ai nine mai bada maganin bacci, ina tabbatar maka daga yau ka dena rashin bacci. Mik'a masa yayi yana fad'in kaga wannan kwayar ita ake kira da 'yar hutu, nima wani abokina ne ya bani ita d'an gidan Alhaji Marusa. Fawwaz yace ba dai Marwan ba? Shifa, ai kasan Gayen yasan ta kan kayan hutu, shiyasa fa kaga muna d'asawa dashi dan baya harka da kayan Nija dan basu da inganci, jiya mukayi waya dashi yake fad'a mani ranar monday zai koma india kasan baya son zama a Nija. Amsa Fawwaz yayi yana fad'in ai gaskiya Marwan babba ne, shiyasa nima banso su Dad sukace na dawo ba, acan hankalin mu kwance sai abinda mutum yaga damaryi. Milo yace tashi muje Beb d'ina tana jirana d'azu tazo mani week end. Fawwaz yace ai kai kaji dad'inka tunda an ware maka gidanka, ni kuwa basa bari na kwana a wani waje duk da an mallaka mani gida. Tashi Milo yayi yana fad'in ba sai karik'a wuni anan ba wayasan abinda kakeyi, iyaka sai lokacin bacci yayi ka koma. Fawwaz yace ka kawo shawara haka za'ayi, nagode abokina. **** **** Wai Marwan ba magana nake maka ba. Baki ya turo yana fad'in wai meyasa kike son takura mani Mom, ko dan kinga ina zuwa ganin ku, shi *Khalil* da baya zuwa ai bakiyi masa haka. Hannunshi ta kamo tana fad'in yi hakuri ba takura maka nakeyi ba, naji kace mun Alhaji beda lafiya kuma kana maganar zaka tafi bayan kasan yanzu ne Alhaji yake da buk'atar ka tunda kaga halin da yake ciki, ni dai mace ce bazan iya jinyarsa ba, gashi ba wani d'an uwa gareshi ba da an kirashi, dole kaine babba kai zaka tsaya ka kula dashi. Saurin kallonta yayi yana fad'in wallahi Mom bazai yuwu ba, shikenan abubuwan da nake dasu acan sai na hakura dasu, Dad fa yana da kud'i, idan kana da kud'i babu abinda zai gagareka, shi kanshi likitan yace zasu kula dashi tunda akwai kud'inshi da yawa a account d'insu, dan haka ni bazan iya jinya ba. Kai ta jinjina tana fad'in shikenan dena fushin, tunda akwai kud'in za'a samu masu kula dashi, nima ba zama zanje inyi ba saboda kasuwancina, amma zan rik'a lek'awa, kaga yanzu asara ta sameshi idan ban tsaya na kula da tawa dukiyar ba sai nima nabi sahunsa dan shi tsufa ya taho masa ga mutuwar b'arin jiki ai kaga beda sauran amfanuwa matuk'ar be warke ba, yanzu haka kayan dana saro suna hanya jiransu ma nakeyi kafin na lek'a asibitin tunda kace allurar bacci sukayi masa. Tashi yayi yana fad'in zan fita ni. Kallonshi tayi tana fad'in amma Marwan akwatin da naga ka d'auko a d'akin Alhaji na meye? Fuska ya d'aure yana fad'in amma ai ina da gadonshi ko? Kai ta d'aga, kauda kai yayi yana fad'in amfani zanyi dasu to. Be jira amsarta ba yayi waje. Murmushi tayi tana fad'in Marwan manya, da Alhajin yana nan zai baka wad'an da sukafi haka ma. Wayarta ce tayi k'ara hakan yasa tayi saurin d'auka ganin wanda ya kira. A zabure ta mik'e tana fad'in ban gane ba, ka bincinka jirgin da akace ya nutse kuwa? Shiru tayi tana sauraronshi. Salati tasa hawaye suka fara wanke mata fuska, hakuri ya bata ya kashe wayar. Zaman 'yan bori tayi tana kwara ihu, da sauri masu aikin gidan suka fito jin Hajiya na ihu. Kuka suka isketa tanayi kamar k'aramar yarinya, nan suka shiga bata hakuri amma kamar izata sukeyi. **** **** Ido kawai Alhaji Marusa ya tsura ma Matarsa da take zaune a gefenshi tana share hawaye, Alhaji Barau da Mr. Kallah sai hakuri suke bata jin asarar data sameta. Alhaji Barau yace Hajiya hakuri zakiyi, kinga yanayin da yake ciki be kamata arik'a tada masa hankali ba, addu'a zakiyi Allah ya maido maki da wasu kud'in. Goge idonta tayi tana fad'in dole nayi kuka, wannan bala'i kamar wad'anda aka sama hannu, so akeyi asirin mu ya tonu. Mr. Kallah yace Hajiya sai hakuri, yanzu Alhaji kulawa yake buk'ata dole ki daure ki kula dashi hakan zaisa ya samu k'arfin jikinshi tunda likita yace abun beyi yawa ba za'a iya shawo kan matsalar dan yanzu haka zasu fara mashi gashi kinga idan kina kwantar masa da hankali zaifi saurin warkewa. Alhaji Barau yace to Allah ya kyauta, Mr. Kallah muje ko. Tashi sukayi suna fad'in Alhaji Allah ya k'ara sauki. Kai ya jinjina masu yana binsu da kallo har suka fita. Zaune suke a mota suna kwasar dariya. Mr. Kallah yace gaskiya na tausaya masu, ga Hajiya itama asara ta sameta, gashi a kwance ko magana baya iyawa, gaskiya da munsan haka zata faru dashi da bamu aikata masa haka ba. Alhaji Barau yace bamuda laifi, son kud'inshi ne ya jawo masa haka, ita kuma Hajiya kila zakkace aka fitar mata, itama son kud'in gareta ai, kasan kuwa yanda take cin kud'in Alhaji ita da 'Ya'Yanta, ga satar da suke masa, ai alhakinsa ne ya kamata. Mr. Kallah yace duk da haka ya kamata mu tausaya mashi a fitar dashi waje sai kaga cikin kwana ukku ya tashi amma zafin zeyi masa yawa, gaskiya ko bazaka taimaka ba ni zansa afitar dashi. Ganin yanda Mr. Kallah ya dage yasa Alhaji Barau ya amince. Fita sukayi zuwa ofis d'in likita, anan suka masa bayani, nan take ya kira wani abokinsa a America, babu b'ata lokaci suka gama komai, inda za'a tafi dashi gobe saboda litinin a fara masa magani. Sallama sukayi masa suka wuce domin nema masa Visa, dole da Mr. Kallah zasu tafi tunda Marwan yace bazeyi jinya ba. Kasancewarsu manya nan take suka samu jirgin safe na gobe, haka suka rabu. **** **** Washe gari tunda safe jirginsu ya d'aga, Hajiya taso ta bisu dan bata jin dad'in zaman gidan, wayar data samu daga Yaronta zai zo yasa ta fasa binsu asalima taji dad'in tafiyar tunda zata sake wannan karon a gida zasuyi sha'aninsu ba sai taje gidanta da suka saba had'uwa ba tunda Marwan ma yau ya tafi. **** *** Duk wani shirin shiga kotu sun kammalashi, duk inda kaje zakaji ana maganar shari'ar da za'ayi gobe, mutane da yawa suna son suje suji wace irin shari'ace haka bayan shekaru masu yawa kuma za'a maidota baya. Wajen k'arfe sha biyu su Alhaji Mansur da Matarsa suka sauka lagos, Ra'eez da Jabeer suka d'aukosu, kai tsaye gidan Mama suka kaisu inda Alhaji Mansur zai zauna a gidan Ra'eez. Sosai Mama tayi farin ciki da zuwan su, Rumaisa ta kawo masu abincin da zob'o. Zama sukayi aka gama gaisawa kafin suka ci abinci, haka suka cigaba da tattaunawa. Da yamma Alhaji Mansur da su Ra'eez suka nufi wajen Kawu tare dasu Jabeer. Sosai Kawu yayi farin cikin ganinsu. Haka suka zauna suna ta fira. Alhaji Mansur yace sunyi waya da Abubakar yace da zaran za'a fara gabatar da shari'ar su Malan Sani zai zo. Murmushi Kawu yayi yana fad'in wallahi jinake kamar mafarki, bani da abun roko daya wuce Allah ya nuna mani ranar da zan fita daga wajen nan, ranar da zanga lokacin da za'a tona asirin munafukai. Ra'eez yace ai Alhaji Marusa da Mr. Kallah suna America. Alhaji Mansur yace akan ciwon Alhaji Marusan ne? Ra'eez yace wallahi kuwa, nima d'azu Alhaji Barau yake fad'a mani. Alhaji Mansur yace ina rokon Allah ya bashi lafiya domin ya amshi hukuncinsa, bakomai nasan bazasu dad'e ba tunda kace jikin da sauki, kafin a kammala wannan shari'ar zasu dawo da izinin Allah. Wayar Ra'eez ce tayi k'ara, yana dubawa yaga Dr. Saddek ne, d'agawa yayi, bayan sun gaisa Dr, yace masa yazo yana son ganinshi. Ra'eez yace gani nan zuwa. Kashe wayar yayi yana fad'a masu abinda Dr, yace. Alhaji Mansur yace ai sai kutashi muje kila wani abunne. Kawu yace aduba mani Hajiyar. **** *** Zaune suke a ofis d'in Dr. Saddek, bayan sun gama gaisawa Dr, yace dama akan maganar shari'ar da naji za'a gabatar gobe ne, tunda har shari'ar zata kai zuwa gano abinda ya shafi abinda yayi silar jefa Hajiya wannan halin ina ganin zaku tafi da ita, ina so na gwada wani abu ko Allah zaisa a dace, shiyasa nace bara nakira ka. Alhaji Mansur yace likita kana ganin babu matsala atafi da ita? Bana so fa Alhaji Barau ya gano wani abu, sannan kada aje garin gyara ayi b'arna, kana gani kwanaki daga fad'in sunanshi yanda tayi, inaga ace ta ganshi kuma ta san shine Brr. Barau d'in. Likita yace Alhaji jikina yana bani wani abu shiyasa kaji nace aje da ita, kasanfa da yawa irin wannan haukan yana warkewa ne ta silar faruwar wani abu, musamman idan mutum yaga abinda ya tsaya masa arai, ina rokon ka amince aje da ita, idan Allah besa zata warke ba shikenan sai adawo da ita. Hawaye ne suka zubo ma Ra'eez, kallon likitan yayi yana fad'in koda ace Ummu bazata warke ba ana kammala wannan shari'ar zan tafi da ita, tunda dai haukarta bata duka bace ni zan cigaba da zama da ita ahaka. Dafashi Alhaji Mansur yayi yana fad'in insha Allahu Ummunka zata warke, bakomai likita zamuyi yanda kace, amma akwai maganin da zaka bata ko? Kai likita ya jinjina yana fad'in zan bata magani, kuma nima zan halarci wajen tare da wasu daga cikin ma'aikatan mu, kuma zamu kula babu abinda zai faru. Godiya sukayi masa. Sallama sukayi mashi akan gobe zasu taho da ita, sai dai bazasu bari kowa ya gane daga asibiti suka fito ba. Alhaji Mansur yace shikenan mungode, akwai Maman Rumaisa da Hajiya sai su kula da ita goben. **** **** Zaune suke su biyar sai Alhaji Mansur na shida a gidan Ra'eez. Rafeek ne ya kalli Adnan yana fad'in ina fatan ka shirya ma shiga kotu gobe? Jinjina kai Adnan yayi yana fad'in sosai kuwa, domin a wannan karon bazan bari a sake aikata zalunci ba. Rafeek yace Nabeel fa? Nabeel yace ashirye nake Yaya, domin nashirya duk yanda zan shawo kan Abbana, dalilin da yasa banyi masa maganar ba bana so yaje masu Alhaji Barau da maganar shiyasa nace sai yau da dare zanje na rokesa akan ya fad'i gaskiya. Ra'eez yace lallai da ka kwafsa, ai gara da baka fad'a masa ba, kabarshi idan yaje zaiji komai da kunnansa, abinda nakeso kawai kayi kok'arin sashi yazo kotun domin nasan za'a buk'aci ganinsa. Nabeel yace shikenan dana koma gida zansan yanda zan fad'a masa. Rafeek yace insha Allahu babu abinda zai gagara, domin kowa yasan yanda komai ya kasance, shikuwa Fawwaz ku barshi Alkali da kanshi zai bada umarnin a kawoshi. Alhaji Mansur yace ni narasa ma bakin magana, agaskiya nayi farin ciki da wannan had'in kan naku, domin taimako ne zakuyi kuma Allah ne kad'ai zai iya biyanku, dan haka idan kowa ya samu dama kafin ya kwanta yayi nafila ta neman nasara, sai kuga Allah ya taimake mu, Allah yayi mana jagora. Gaba d'aya suka amsa da amin. **** **** Abbah ka kalli labaran jiya na Liberty radio kuwa? Abbah yace labaran da yawa ai, wanne a ciki? Gyara zama Nabeel yayi yana fad'in aikuwa agari naji ana ta maganar shari'ar da akace za'ayi gobe a babbar kotu kuma tsohuwar shari'a ce, naji mutane suna fad'in zasuje suyi kallo. Abbah yace wai wace irin shari'ace haka bayan shekaru kuma za'a maidota? Nabeel yace gaskiya ban sani ba, amma koma menene nasan babbar shari'arce tunda gashi an maido ta. Abbah yace aikuwa nima zanje kodan naji wace shari'ace haka, kasan ina son zuwa saurarar shari'a. Murmushi Nabeel yayi yana fad'in nima nace zanje ai. Abbah yace dama ku ai ba'a barin ku abaya. Murmushi Nabeel yayi yana fad'in ai bana son naga anyi zalunci Abbah. Abbah yace to Allah ya bama masu gaskiya sa'a. Nabeel yace amin. ***** ***** *Safiyar litinin a Kotu* Cike babbar kotu take da mutane, yayin da su Mama da Maman Labiba, Rumaisa sai Ummun Ra'eez da matar da take kula da ita suke zaune a cikin kotun, saboda dawuri sukazo dan kada su rasa wajen zama, sannan basa son sai an shiga su shiga gudun kada Ummu tayi wani abun, duk da jikinta amace yake tun maganin data sha. A hankali mutane suka shige ciki kowa ya zauna ana jiran zuwan Alkali. Shigowar Alkali yasa kowa ya mik'e, bayan ya zauna kowa ya zauna. Shiru kotun tayi ana jiran a fara. Bayan ya kammala abinda yake Magatakarda ya tashi domin ya karanto shari'ar da za'a gabatar. *A yau litinin biyar ga watan december shekera ta dubu biyu da shatara wannan kotu zata saurari k'arar da Iyalan Alhaji Sambo Jarmai suka shigar akan kissan gillan da akayima 'Dansu a shekarar dubu biyu da takwas, wanda aka tsinci gawarsa a ranar juma'a da misalin k'arfe tara da rabi na dare, suna rokon wannan kotu mai albarka data kwato masu hakkinsu.* Mika takardar yayi ya koma ya zauna. Gyara zama Alkali yayi yana fad'in ina lauyoyin da zasu fabatar da shari'ar? Tashi Ra'eez yayi yana fad'in ya mai shari'a nine lauyen da zai k'are wad'anda suke k'ara. Jinjina kai Alkali yayi yana fad'in zaka iya farawa. Fitowa Ra'eez yayi yana fad'in Iyalan Alhaji Sambo Jarmai sun shigar da wannan k'ara ne saboda suna da yakinin a wannan kotun ne kad'ai za'a iya kwato masu hakkin su, duk da wannan case ya dad'e amma dalilin rashin kwakkwarar sheda yasa basu shigar da k'ara ba, haka zalika basu shigar da k'ara a ofishin 'yan sanda ba, sai dai kuma alokacin da abun ya faru akwai shedar sa hannu ta 'yansanda a wancan lokacin, wannan shine rahoton da muka samu a ofishin 'yan sandan da suka kula dashi a wancan lokacin. Amsar takardar Magatakarda yayi ya mik'a ma Alkali. Ra'eez yace a shekarun baya an tsinci gawar Naseer Sambo Jarmai a wajen gari da misalin k'arfe tara da rabi na dare, kuma 'yan sanda ne suka d'auki gawarshi suka mik'ata asibiti, a lokacin inspector Musa shine wanda ya kula da wannan gawa harya d'auketa zuwa asibiti inda ya mik'a case d'in ga abokin aikinsa Inspector Bello Kabir wato Kwamishnan 'yan sanda na yanzu, inaso kotu ta bani dama na kira Alhaji Musa domin muji bayani daga bakinsa. Kotu tana buk'atar Alhaji Musa. Ra'eez.... Kotu zata so taji sunanka da kuma aikin ka. Sunana Alhaji Musa Adam, nayi aikin d'ansanda a shekarun baya, amma ayanzu na aje aiki tun shekaru biyar da suka wuce, ayanzu haka ina kasuwanci ne. Ra'eez... Alhaji Musa ko zaka iya tuna abinda ya faru a shekarar dubu biyu da takwas akan gawar da kuka tsinta ta Naseer Sambo Jarmai? Muna so kayima kotu cikekken bayani. Alhaji Musa.... Kwarai kuwa zan iya tuna wannan case d'in, domin bashi kad'ai muka samu a wannan dare ba, kuma wannan lokacin yana d'aya daga cikin abinda bazan iya mantawa ba, domin a wannan shekarar a wannan kotun anyi zazzafar shari'a, wanda d'aya daga cikin gawar da muka tsinta had'e data Naseer ce akayi shari'a akanta, sai dai ita ta Naseer Iyayenshi basu buk'aci yin shari'a ba, saboda babu wata sheda da muka samu a lokacin da muka tsinceshi. A wannan dare na juma'a mun samu waya cewar an samu gawar tsohon shugaban kwastam wato Alhaji Maiwada, bayan da 'Yallab'ai Bello ya tura mu wajen, da muka d'auko gawarsa mun taho muka sake samun labarin gawar da wasu suka gani, haka muka wuce muka d'auko gawar Naseer, kai tsaye asibiti muka nufa dasu, daga can kuma case d'in ya koma hannun Ogana wato 'Yallab'ai Bello Kabir, iya abinda na sani kenan akan gawar Naseer, sai rahoton dana baka wanda nine na rubutashi da hannuna. Ra'eez... Mungode Alhaji Musa zaka iya tafiya. Ya mai shari'a wannan shine d'an sandan daya d'auki gawar Naseer, ga rahoton mutuwarsa nan, sai dai a binciken da mukayi mungano Naseer yana aji shidda ne a makarantar Kings college a wancan lokacin, kafin mutuwarsa akwai abinda ya faru a makarantar su wanda akan idonshi abun ya faru, yayi kok'arin ya tabbatar da gaskiya sai dai silar wannan abun ya jawo mashi mutuwar wulakanci. A binciken da mukayi akwai abokinshi *Fawwaz Muhammad Sanda* wanda shima d'alibi ne a makarantarsu, bincike ya nuna mana akwai rigima da akayi tsakanin Fawwaz da d'an ajinsu mai suna Farouk, wanda Adnan da Sufwan duk sun san da wannan rigima domin su ukku suke tare abokai ne sosai, kuma bincike ya nuna cewar bayan rigimar Farouk da Fawwaz a ranar aka tsinci gawar Farouk a wajen gari, komenene ya faru alokacin Fawwaz ne zai fad'a mana saboda yasan Naseer, ina neman alfarmar wannan kotu data bada umarnin a kawo Fawwaz Muhammad Sanda domin muji komai daga bakinsa. Nagode. Tashin hankali wanda ba'a samasa rana. Gaba d'aya zufa ce ta lullube Alkali da Abban Nabeel, da wani zaije kusa da Alhaji Barau zaiji yanda zuciyarsa take bugawa, jarumta ya tattaro ya kalli Ra'eez, cikin k'arfin hali yace an d'age wannan shari'ar zuwa gobe, kafin nan kotu tana umartar akawo mata Fawwaz Muhammad Sanda zuwa gobe. Kotttt!!! Gaba d'aya kotun ta d'auki hayaniya, Abban Nabeel kuwa kasa tashi yayi daga inda yake, gaba d'aya hankalinsa ya tashi, abinda ya guda shekarun baya gashi zai faru, Allah ya sani tun bayan daya aikata wannan laifin yayi nadama, bayan da Nabeel yazo masa da maganar kuma be sake samun kwanciyar hankali ba, haka kawai yake jin kamar wani abu zai faru ashe kuwa lokacin jin kunyarsu ne yazo. Cira ido kawai Ummu takeyi saboda gaba d'aya hayaniyar tayi mata yawa, jin kanta tayi yana sara mata. Wasu mutane da suke bayansu taji suna fad'in.... Ai wannan shari'ar da akayi ta shugaban kwastam Alhaji Maiwada a wancan lokacin Brr. Barau ne yayita, gashi kuma yanzu shine Alkali, amma kuma Fawwaz da ake magana ai d'an gidan tsohon Alkali ne, lallai wannan shari'ar akwai lauje cikin nad'i, ga mutuwar Farouk ana magana kuma duk 'yan makaranta d'aya ne, tabbas za'ayi tone-tone a yanda na fuskanci wannan shari'ar babban al'mari ne. Zumbur sukaga Ummu ta mik'e, saurin tashi Mama tayi tana kok'arin kamota amma ina tuni Ummu ta zube k'asa yayin da kanta ya bugu da kujera. Da sauri ma'aikatan da sukazo tare sukayo kanta, hankali tashe Ra'eez ya nufo wajenta, sai dai kafin ya iso Alhaji Mansur yayi saurin rik'eshi yana girgiza mashi kai, dole ya tsaya. Jabeer ne ya jashi sukayi waje. Haka hankalin mutane yayo kanta, sai dai kafin a taru tuni anyi waje da ita ansata mota sun wuce. Da sauri su Alhaji Mansur sukabi bayansu shida Rafeek. Ur's. Nabeelert Lady🖋[3/10, 8:41 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.* 4⃣1⃣ A gado aka turota zuwa d'akinta bayan an gama mata dressing goshinta daya fashe sanadiyar buguwar da tayi da kujera. Hannunta Ra'eez ya rik'e yana kuka. Dafashi Jabeer yayi yana bashi hak'uri. Ra'eez yace dole nayi kuka Jabeer, sai da Abbah yace kada aje da ita gashinan abinda ya faru, yanzu idan ciwonta ya tsananta mai zaice mana. Alhaji Mansur yace Ra'eez kadena fad'ar haka, ni na hango alkhairin da yasa Likita yace aje da ita, kuma insha Allahu hakan ne silar samun saukinta, dan haka mujira farkawarta zamuji alkhairi, yanzu shari'ar da take gabanka zaka fuskanta kuka ba naka bane. Jinjina kai Ra'eez yayi yana goge ido yace shikenan Abbah Allah ya bata lafiya. Abbah yace amin, dan haka kutashi mutafi dan tana buk'atar hutu. Tashi sukayi suka wuce. *** **** Zagaye kawai Alhaji Barau yake a ofis yayin da zufa take zubo masa, duk da ya kure masanyar ofis d'in amma duk da haka zufa yake, shigowarshi ya sha ruwa yafi roba biyu. Jin k'arar wayarsa yasashi saurin nufar inda take dama jiran kiran yake dan ya kira ba'a d'aga ba. Sunan Alhaji M. Sanda ya gani hakan yasa ya zauna yana amsa wayar. Lafiya Babban Alkali nazo na iske kira kusan so goma shine nace babu lafiya. Ajiyar zuciya Alhaji Barau ya saki yana fad'in Alhaji babu lafiya, wani tashin hankali ne yake tunkaromu, wallahi da nasan abinda shari'ar da zan gabatar kenan yau da duk juyin da za'ayi bazan amsheta ba, kuma bazan bari hazikin lauya kamar Ra'eez ya tsaya masu ba. Alhaji M. Sanda yace dakata Alkali, ka fito fili kayi mani bayani yanda zan fahimceka, nasan kace mun kana da shari'a yau wadda naga ana tallar ta a gidan radio amma bansan meta kunsa ba, dan haka kayi mani bayani yanda zan fahimta. Gyara zama yayi yana fad'in Alhaji ina Fawwaz yake? Alhaji M. Sanda yace yana nan lafiya dai? Alhaji Barau yace zaka iya tuna abokansa Naseer Sambo Jarmai da Farouk d'an ajinsu na makarantar kings college? Alhaji M. Sanda yace taya zan iya tuna abokan Fawwaz kuma na secondary ma. Alhaji Barau yace zaka iya tunawa mana, a shekararsu ta k'arshe, fad'an Fawwaz da Farouk wanda yayi sanadin yankarsa da Fawwaz yayi da wuk'a ajali na kusa ya mutu, Naseer shine wanda ya d'auki lokacin da akayi kisan, silar haka muka had'u mu hud'u muka yanke hukunci akanshi, yayin da aka tsinci gawarsa a bayan gari, wanda aka kashe shi tare da Alhaji Maiwada. Wannan shari'ar da ba'ayita ba a shekarar dubu biyu da takwas, itace aka gabatar da ita a kotun mu yau. A zabure Alhaji M. Sanda ya mik'e yayin da zufa tayi masa sallama, ya d'auki mintuna kafin ya furta Alhaji Barau garinya aka tado da wannan shari'ar? To waye ma ya tadota bayan lokacin da akayita shi kanshi lauyen da ya tsaya masu yana k'arami dan nasan dai beda wasu shekaru masu yawa. Alhaji Barau yace wallahi nima abinda ya tsaya mani kenan. Alhaji M. Sanda yace ai nasan mahaifin Naseer ko alokcin da abun ya faru da naje gaisuwa yace bazai b'ata lokacinsa wajen shigar da k'ara ba ya barma Allah, dole akwai wanda yake bayan wannan abun kuma zan bincikoshi. Alhaji Barau yace ka taimaka mana, bani da sauran wata dabara domin na fiku shiga tashin hankali saboda nine Alkalin kotun. Jinjina kai Alhaji M. Sanda yayi yana fad'in wannan maganar bata waya bace, ka sameni agida, shima lauyen dole mu siyeshi. Alhaji Barau yace nagode, amma gobe ana buk'atar Fawwaz yazo Alhaji. A tsawace Alhaji M. Sanda yace kasan abinda kake fad'a kuwa Barau? 'Dan nawa ne zaizo kotu ayimasa tambaya, idan ma mafarki kakeyi to ka farka, duk duniya babu wanda ya isa yasa Fawwaz yaje kotu, ka sani ma daga yanzu zan fara nema masa visa ya koma inda ya fito. Jiki a sanyaye Alhaji Barau yace ayi hak'uri Alhaji sai nazo. Kashe wayar yayi. Hannu Alhaji Barau yasa ya dafe kanshi, wane irin tashin hankali ne haka ya kunno masu kai lokaci guda? Yanzu yazeyi gobe idan akazo babu Fawwaz? Murmushi ya saki yana fad'in nasan Alhaji bazai tab'a bari asirinmu ya tonu ba domin shima yana ciki, bakomai zanje muyi yanda zamuyi, bazan bari ayi saurin gano ni ba, da haka zan shiriritar da shari'ar. Kayansa ya fara had'awa yana kokarin kiran Mr. Kallah. **** **** Fawwaz ina passport d'inka yake? Fawwaz yace wallahi Dady tunda na dawo ban sake bi ta kanshi ba saboda naji kunce bazan sake komawa ba na dawo kenan, Allah yasa ban had'a dashi cikin takardun da nasa akonasu ba. Alhaji yace kana da hankali kuwa Fawwaz? abu mai muhimmanci zakace baka san inda ka ajeshi ba. Zama Ammi tayi tana fad'in yau kuma meya had'o Alhaji da 'Dansa? Tsaki Dady yayi yana fad'in ki barni dashi kawai. Matsowa Fawwaz yayi yana fad'in Dady ka fad'a mani abinda yake faruwa dan Allah. Ido Alhaji ya tsura mashi, wani irin tausayinsa ya kamashi, da sauri ya kamoshi ya rungume. Ammi da jikinta yayi sanyi ta matsa tana fad'in Alhaji akwai abinda yake faruwa, tunda har yau ka iya yima Fawwaz fad'a tabbas nasan akwai abinda yake faruwa. 'Dagowa yayi yana fad'in Fawwaz ka shirya zaka bar k'asar nan cikin satin nan, kuma bana so ka sake dawowa, idan muna buk'atar ganin ka zamu kai maka ziyara, ka zab'i wadda kake so ayi maku aure domin can rayuwar ka zata koma. Farin ciki ne ya cika Fawwaz nan ya hau murna, sai dai ganin damuwa fal a fuskar Dadynsa yasa jikinsa yayi sanyi, hannunshi ya kamo yana fad'in amma Dady wannan canjin na lafiya ne? Kauda kai Dady yayi yana kok'arin cire damuwar da take fuskarshi. Ammi tace dole akwai wani abu, nifa jikina yana bani akwai matsala, dan Allah kayi mana bayani sai kaga an samu mafita. Kallon Fawwaz yayi yana fad'in ina abokan ka da kukayi secondary atare? Fawwaz yace Adnan da Sufwan, ai Sufwan na fad'a maka ya rasu lokacin bana k'asar ma, amma Adnan yana nan har yayi aure ko rannan mun had'u har ya bani haushi dan ya tuno mani da abinda ya faru muna makaranta, shiyasa ni yanzu ba ruwana dashi saboda naga ya canza hali tun bayan gama makarantar mu, ya koma wani ustaz. Da sauri Alhaji yace a ina yake da zama? Fawwaz yace ni bansani ba na fad'a maka ba ruwana dashi fa. Jinjina kai Alhaji yayi yana fad'in wace magana ya tuna maka? Fawwaz yace akan abinda ya faru tsakani na da Farouk ne yake fad'in waishi yana cikin damuwa da abun. Ammi tace ko Farouk d'in da kayi mafarkinsa rannan? Fawwaz yace shifa. Cije baki Alhaji yayi yana gyad'a kai. Ammi tace towai meya faru? Alhaji yace case d'in Fawwaz ne ake kok'arin maidowa ko kuma ince an maido dan yau aka fara shari'ar a kotun Alhaji Barau, kuma ana buk'atar Fawwaz yaje kotu gobe. A zabure Fawwaz ya mik'e yana fad'in Dady mene? Dan Allah Dady kada ka bari a kashe ni, wallahi nasan kashe ni zasuyi dan Allah Dady. Kuka yasa mai ban tausayi. Jikin Ammi ne ya fara rawa jin abinda Fawwaz yace, tashi tayi ta kamoshi tana fad'in babu wanda zai kashe ka Fawwaz, ba dai kace ba kai bane ka kashe shi ba. Zama yayi jiki a sanyaye dan ya tuna lokacin da abun ya faru Dady ya hanashi ya fad'a mata gaskiya saboda sun san halinta bata goyen bayan zalunci, shiyasa suka fad'a mata daga fad'a aka rabasu shikenan aka tsinci gawarsa a wajen gari. Alhaji yace matuk'ar ina numfashi babu wanda zai kaika kotu ma bare har ayanke maka hukunci, dan haka ka fara shiri zaka bar k'asar gaba d'aya. Ammi tace tunda har da gaskiyarshi meye za'a turashi wata k'asa, idan ya tafi kowa zaice beda gaskiya, babu fa wanda zai masa komai tambayarshi kawai za'ayi ya fad'i abinda ya sani. Alhaji yace amma baki da hankali Ammi, yanzu kina ganin zan bari Fawwaz yaje kotu domin bada sheda ne, to wallahi kisama bakin ki linzami akan wannan maganar matuk'ar kina so mushirya dake, babu ruwanki da inda zaije, idan zaki iya kije ki bada sheda tunda ai kinsan abinda ya faru. Tashi yayi yaja Fawwaz suka fita waje. Ajiyar zuciya Ammi tayi tana fad'in ikon Allah, lallai duniya babu gaskiya, na dad'e ina tunanin akwai abinda yake faruwa sai yanzu na k'ara tabbatarwa, yau da ace bani na haifi Fawwaz ba sai nayi kuka akan wannan iko, amma bakomai, koma menene bazan fasa mashi addu'a ba, ya Allah ka tabbatar da abinda yafi alkhairi. A waje Alhaji yace ma Fawwaz ya kake ganin za'ayi da Adnan? Fawwaz yace nasan ko banje ba shi zaije kuma zai bada amsar abinda aka tambayeshi bazai b'oye ba, domin nasan tabbas shine zaisa amaido shari'ar baya domin duk duniya shi kad'ai ne ya rage wanda yasan maganar, ina ganin Dady a hanashi zuwa kotun kawai. Alhaji yace ba kotu zan hanashi zuwa ba, idan yayi wasa zai bi Naseer inda yaje, ashirye nake na kawar da duk wanda zai kawo mana gargada, domin ban shirya jin kunyar duniya ba, matuk'ar wannan abun ya fasu dole muma zamu shiga ciki, dan haka zansa a saceshi. Fawwaz yace hakan yayi Dady, ka bari nasa abokaina su sace manishi. Alhaji yace wannan aikin ba naka bane, bana so ma ka saka wasu abokan ka aciki saboda maganar sirri ce, wad'an da suka fara aikin su zasu k'arsashi. Fawwaz yace nagode Dady, nasan idan kana nan bazan tab'a kuka ba. Murmushi Alhaji yayi yana shafa kanshi. **** **** Abbah kamar akwai abinda yake damun ka, tunda muka taho daga kotu nake ganin damuwa a fuskar ka, gashi kuma dama da kyar ka iya tashi a kotu muka taho. Nabeel nima abinda na fahimta kenan, yau kusan kwana ukku kenan ina ganin canji agurinshi. Nabeel yace wallahi Umma akwai abinda yake damun Abbah kawai bazai fad'a mana ba. Gyara zama Abbah yayi yana zare glass d'in idonshi, kallonsu yayi yana jin wani nauyi aranshi, taya zai kalli Iyalinsa ya fad'a masu irin abinda yayi, wata zuciyar tace ai gara ka fad'a masu da suna zaune a gano ka. Wasu zafafan hawaye ne suka zubo mashi, hannu yasa ya goge idonshi, kallonsu yayi yana fad'in kuyafe mani na ciyar daku haram, son zuciya ya hanani na gane illar abinda na aikata ba dai-dai bane, amma na d'aukeshi a matsayin k'addarata, yanzu zan baku labarin abinda na aikata tsahon shekaru shabiyu da suka wuce, amma ina rokon ku da ku yafe mani.... **** *** *Safiyar Talata a kotu* Tafe suke a hanya zasu isa kotu, Jabeer yace wai har yanzu likita be kiraka ba? Ra'eez yace na kirashi d'azu yace allurar da akayi mata zata d'auketa kwana biyu saboda suna buk'atar ta huta, kaga kafin lokacin mun kammala wannan shari'ar. Jabeer yace nakira Adnan wayarsa a kashe sai ta Nabeel na samu yace mun yana hanya yaje wajen aikinsu. Ra'eez yace kila ko rashin caji ne, amma nasan zaizo dan yasan yau ne zamu buk'aci ganinshi. Lokacin da suka isa kotun sun iske har wasu mutanan sunzo. Jabeer yace dad'ina da mutane akwai sonjin ya akayi. Ra'eez yace har bakin fuska sai ka gani yau, domin duk wanda aka fara shari'ar dashi jiya dole yaso dawowa yau hada k'arin wasu ma. Bayan da kowa yashiga kotu sai ga Alkali ya iso, duk da k'asan zuciyarsa akwai tsoro amma kasancewarsa tsohon lauya yasa yayi kok'arin b'oye damuwarsa, idan kaganshi tamkar besan komai ba, duk da Alhaji M. Sanda ya k'arfafa masa guiwa amma yana shakkar abinda zai iya biyo baya. Bayan da yashigo kowa ya nutsu, zama yayi bayan ya kammala abinda yake ya buk'aci Magatakarda daya maimaita shari'ar da sukeyi. Bayan Magatakarda ya karanto shari'ar Alkali ya kalli mutane yana fad'in ina fatan anzo da Fawwaz M. Sanda gaban kotu? Tashi d'aya daga cikin mutanan da sukaje gidansu Fawwaz yayi yana fad'in ya mai shari'a Fawwaz baya k'asar nan kusan sati biyu. Jinjina kai Alkali yayi yana fad'in ina lauya mai kare wad'anda suke k'ara? Tashi Ra'eez yayi yana risnawa. Alkali yace zaka iya cigaba da gabatar da shari'ar, sai kaje ga sheda ta gaba saboda wanda ake nema kunji baya k'asar, idan har shari'ar dole tana buk'atar zuwanshi dole sai an maido dashi. Murmushi Ra'eez yayi a zuciyarsa jin wani sabon rainin hankali, jinjina kai yayi yana fad'in ya mai shari'a abisa binciken da mukayi tabbas Fawwaz yana k'asar nan sai dai idan a jiya ya barta, amma ko daren lahadi mun had'u dashi a wajen siyayya duk da shi bai sanni ba, nayi mamakin da akace wai yafi sati baya k'asar. Alkali yace ko kana da shedar da zaka tabbatar ma kotu cewar Fawwaz yana k'asar nan? Kai Ra'eez ya girgiza yana fad'in bani da ita ya mai shari'a. Alkali yace wata kila bashi ne ka gani ba, domin nasan mutanan dana aika kiransa bazasu fad'i k'arya ba, shiyasa nace idan har akwai buk'atar zuwansa ko ina yaje kotu tana da ikon da zatasa shi ya dawo, zaka iya cigaba. Gaba d'aya mutane suka jinjina adalci irin na Alkali. Jinjina kai Ra'eez yayi yana fad'in ya mai shari'a zanso kotu ta bani dama domin nayima Alhaji Sulaiman tsohon shugaban makarantar kings college tambaya. Dam!!! Gaban Alkali ya bada wani sauti jin abinda Ra'eez yace, tsura mashi ido yayi aranshi yana jinjina tsabar iya aiki na Ra'eez, wato ya shiryama wannan shari'ar, sam sun manta da Alhaji Sulaiman da tun jiya sun sake rufe mashi baki da kud'i, amma yasan bazai yi kok'arin tona masu asiri ba saboda shima yana da laifi. Ajiyar zuciya ya saki yana fad'in kotu tana buk'atar Alhaji Sulaiman ya fito gabanta. Ido Alkali ya saki yana jiran yaga tashinsa. Juyawa Ra'eez yayi yana kallon inda Nabeel yake zaune dan yasan jiya akusa dashi ya zauna, sai dai abun mamakin babushi a wajen sai kujerarsa wadda Nabeel ne ya kama masa ita tun bayan da yazo dan ya barshi yana shiryawa shi kuma sai da ya biya wajen aikinsu daga can ya wuto. Tashi Jabeer yayi ya isa wajen Nabeel, atare suka fita waje. Alkali yace ko dai shima baizo ba? Kai Ra'eez ya jinjina jiki a mace. Alkali yace da alama ba'a shirya wannan shari'ar ba, sai kaje ga sheda ta gaba. Jiki a sanyaye Ra'eez yace ya mai shari'a sheda ta gabama bai k'araso ba, kuma wayarsa akashe. Murmushin farin ciki Alkali ya saki a zuciyarsa, sai yanzu ya kuma gazgata maganar Alhaji M. Sanda. Kallon mutane yayi yana fad'in da alama wannan shari'a tazo da wani salo, idan har babu kwararan hujjojin da za'a iya gabatar ma kotu babu amfanin a tara mutane kuma ab'atama kotu lokaci, saboda adalci na wannan kotu yasa ta amshi wannan shari'ar, domin case ne tsoho wanda shekarun da akayishi suke da yawa, sai gashi kuma kun kasa tabbatar da abinda zaisa abima mutane hakkinsu, dan haka tunda har kuka kasa gabatar da wata kwakkwarar hujja agaban kotu, kotu ta.... Dan Allah ya mai shari'a ina buk'atar a k'ara mana lokaci, tabbas akwai abinda yake faruwa, domin shedun nan akwaisu, amma gashi anzo kotu basu k'araso ba, ina rokon wannan kotu mai adalci data d'age wannan shari'ar domin mu samu damar gano abinda yake faruwa. Alkali yace wannan kotu mai albarka zata maku lazimin d'age shari'ar nan zuwa jibi alhamis, matuk'ar kuka sake dawowa da irin haka tabbas kotu zatayi watsi da wannan shari'ar, kuma zata soketa baza'a sake amsarta a ko ina ba. Kottt!!!! Cikin hanzari Ra'eez ya had'a kayanshi yayi waje, bayanshi Rafeek yabi shima yana tunanin dalilin da yasa Adnan da Abban Nabeel basu zo ba, bayan kuma ajiya Nabeel ya fad'a masa Abbansa ya amince zai zo ya fad'i gaskiya. Haka kowa ya fito yana jinjina ma Alkali bisa wannan adalci nashi, yayin da wasu suke ganin kamar shari'ar bazata d'ore ba saboda an kasa gabatar da hujja, haka kowa ya watse wasu suna fad'in bazasu sake dawowa ba tunda abun shirme ne. Ur's. Nabeelert Lady🖋 [3/10, 8:41 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.* 4⃣2⃣ Wai me yake faruwa Nabeel? Wallahi nima ban sani ba, domin munyi waya da Abbah yace mun ya fito daga gida ya taho, bayan dana iso naga bai zo ba nakira wayarsa bata shiga na d'auka matsalar network ne shiyasa banyi wani abu ba, ga Adnan ma wayarsa gaba d'aya akashe. Shiru sukayi Ra'eez yace dama nasan da wuya mu kwashe da sauki a wannan shari'ar, domin da manyan mutane abun ya had'o dole sai mun hada' da 'Yan sanda amma amintattu. Rafeek yace tabbas zargin da nakeyi ya tabbata, Ra'eez kaje ka samu Alkali ni nasan suna buk'atar ka, ina so kayi amfani da wannan damar ka k'ara samun wani abu, nasan dole Alhaji M. Sanda yayi wani abu, kuma k'arya ne ace Fawwaz baya k'asar. Ra'eez yace wallahi na ganshi. Jabeer yace yanzu ya zamuyi? Jinjina kai Ra'eez yayi yana fad'in zanyi magana da abokina inspector Hamza nasan zai taimaka mana, kome ake ciki bazamu bari Fawwaz ya bar k'asar nan ba, dan nasan ayanzu suna gab da fitar dashi, dole muyi wani abu matukar muna son a kammala shari'ar cikin sauki. Ra'eez yace haka za'ayi, yanzu bara naje wajen Alkali, Jabeer kai da Nabeel kuje abi maku diddikin layin Abbah da Adnan, kafin nan Yaya yaje wajen Inspector Hamza sai kuyi magana dashi dole muna buk'atar 'yan sanda saboda kada a cutar dasu Abbah. Kai suka jinjina gaba d'ayansu. Wucewa yayi ofis d'in Alkali yayinda Alhaji Mansur suke zaune a mota shida Kawun Jabeer suna tattaunawa. *** Wallahi Alhaji dole na sara maka, sai yanzu na yarda da maganar ka, tabbas kai d'in kwararre ne, amma abinda ban gane ba, gashi dai kace Adnan kawai za'a sace sai kuma gashi Alhaji Sulaiman bezo kotu ba, kuma alamu sun nuna zai zo d'in saboda sunce ya taho. Murmushi Alhaji M. Sanda yayi yana fad'in kana wasa dani Alhaji Barau, na fad'a maka duk wani wanda naga zai kawo mana tasgaru a wannan tafiyar zanyi komai dan na kaudashi. Bayan tafiyarka jiya na zauna ina wani tunani, nasan dole sai an buk'aci ganin shugaban makarantar su Fawwaz, gashi kuma bamuyi wata magana dashi ba hakan yasa zuciyata bata amince abarshi ba, hakan yasa na turama Lucky kwatancen gidanshi nace shima a d'aukemunshi idan ya fito zai taho kotu, yanzu haka suna wajen su Lucky nace sujirani a kammala shari'ar kafin a aiwatar masu, dan yanzu idan aka kashe su wata sabuwar shari'ar ce, kaji yanda nayi dashi. Jinjina kai Alhaji Barau yayi yana fad'in yanzu kam hankali na ya kwanta, abinda ya rage na kira Ra'eez na siyeshi domin yayi watsi da shari'ar. A'a kada kayi haka Alhaji Barau, na fad'a maka zuciyata bata kwanta da wannan yaron ba, k'wazonshi yayi yawa, basirarsa baiwace daga Allah, kuma nasan bazai tab'a amincewa da cin hancinka ba, dan haka ka barshi kada kayi abinda zaisa ya gane ko kai waye, dole sai yana da shedu sannan zai gabatar da shari'ar, kuma jibi ne za'a kammala komai, dan haka ka barshi, idan yazo ma ka k'arfafa masa guiwa. Alhaji Barau yace shikenan nagode. Kwankwasa k'ofar da akayi tasa yayi saurin kashe wayar, izinin shigowa ya bada hakan yasa Ra'eez ya shiga. Bayan ya zauna Alhaji Barau yace sannu da kok'ari Ra'eez, gaskiya kana kokari akan wannan shari'ar, shiyasa ma na kaita zuwa alhamis saboda ka samu damar kammala sauran shedun ka, maganar Fawwaz kuma idan har yana da laifi dole a maidoshi. Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in nagode Alhaji, nasan ai saboda nine kayi haka kuma naji dad'i. Alhaji Barau yace haba ai bakomai, abinda nakeso da kai ka tsaida hankalin ka ka samo cikakkar hujja dan bana so mutane suga gazawarka musamman da shari'ar take tsohuwa, gara ace kayi nasara zaifi. Kai Ra'eez ya jinjina yana fad'in insha Allah. Tashi yayi yana fad'in nagode zan tafi. Alhaji Barau yace ka kula da kanka. **** **** Kada ka damu Rafeek, wannan abu ne mai sauki, ina tabbatar maka ayau zan kama Fawwaz, nasan Iyayen shi sun killace shi agida suna jira lokacin tafiyarsa yayi sannan su fiddoshi ya tafi, nasan dan wasa yanzu bazamu ganshi ba, amma nasan wanda zansa ya fiddo manishi cikin sauki. Rafeek yace nagode Hamza, sai maganar su Adnan, tabbas nasan sune sukasa aka kamasu, amma na tura su Brr. Jabeer suje abi mana diddikin layinsu. Hamza yace bara nakira amintattun ma'aikata na dole wannan aikin yana buk'atar sirri saboda kasan yanzu duniyar babu gaskiya zasu iya siye masu matattar zuciya acikin mu, shiyasa sai amintattuna kad'ai zan d'auka domin na saba fita dasu irin wannan aikin sirrin. Rafeek yace yanzu waye kake tunanin zai iya fito da Fawwaz? Murmushi Hamza yayi yana fad'in akwai babban abokinsa d'an uwan su Maid'akina ne, nasan yanda zanyi ya fito mana dashi. Hamdala Rafeek yayi yana fad'in nagode abokina. Hamza yace haba bakomai, insha Allahu komai zai tafi lafiya lau, kuma zan tsaya har sai an tabbatar da gaskiya. Wayar Rafeek ce tayi k'ara, yana dubawa yaga Jabeer, saurin d'auka yayi. Jabeer yace Yaya gaba d'aya layinsu a waje d'aya ya dena aiki, sai dai kuma alamu sun nuna wajen da yabar aikin waje ne da yayi nuni da b'oyayyan waje dan ba cikin gari bane. Rafeek yace shikenan ku taho zamu san yanda za'ayi. Hamza yace ya dai? Fad'a masa abinda ya faru yayi. Murmushi Hamza yayi yana fad'in sace su akayi, idan kuma har abinda aka duba gaskiya ne to zamu duba daga inda layin ya tsaya dole suna ata wajen. Rafeek yace nagode. Sallama yayi mashi ya tafi. **** **** Dan Allah Sweetheart ki nutsu, idan akabi komai a sannu babu abinda zai faru. Zama Momin su Marwan tayi tana goge idonta, kallon Yaronta tayi tana fad'in wallahi kashe shi zasuyi, kasan kuwa dokar k'asar saudiya? Ni na rasa wannan abu na Marwan, shida yake india bansan ya akayi yaje saudiya ba, duk da nasan yana fad'a mun yana kasuwanci a Madina amma be fad'a mun zeje can ba. Gyara zama saurayin yayi yana fad'in to dama baki san Marwan yana dillacin kwayoyi ba? Momy tace wallahi ban tab'a sani ba, idan nasani taya zan barshi, dan Allah *Nuress* idan kana da mafita ka fad'a mani. Murmushi Nuress yayi yana fad'in gashi kuma gobe zan koma, kuma gaskiya ni bani da wanda na sani a Madina, tunda Alhaji zai dawo gobe ki barshi yazo nasan abun zaizo da sauki tunda sune masu k'asar. Ajiyar zuciya tayi tana jawo wayarta tace bari na turama Khalil kud'i yace mun kud'inshi sunyi k'asa, nima ba kud'in gareni ba tunda duk na kwashe su nayi wannan siyayyar gashi kuma asara ta sameni, jira nake Alhaji ya dawo ya k'ara mani jari dan duka kud'in account d'ina bazasu wuce million goma ba. Matsowa Nuress yayi yana shafa mata baya yace kada ki damu Baby komai zaizo da sauki, tunda Alhaji ya warke daya dawo kud'inshi zasu dawo. Murmushi tayi tana kok'arin tura kud'i, tsaf Nuress ya haddace code d'inta. Bayan ta gama ta mik'e tana cire sark'ar zinarinta dan tunda suka dawo daga unguwa bata samu cire kaya ba ta samu wayar an akama Marwan hakan yasa hankalinta ya tashi. Durowa ta bud'e ta d'auko wani akwati, bud'eshi tayi saiga wasu sarkokin da abun hannu hada zobuna duk na gwal, maida wadda ta cire tayi ta rufe akwatin da mukullinshi ta maida mukullin inda yake. Koda ta juyo sai taga Nuress ya juya mata baya da alamu baisan abinda takeyi ba dan hankalinshi yana kan waya. Abinda bata sani ba ta cikin wayar yake kallonta. Sunanshi ta kira hakan yasa ya juyo. Nuress yace Baby kije kiyi wanka naga jikin ki duk yayi sanyi. Murmushi tayi tana fad'in zanyi amma kad'an zo ka sakani nishad'ani sai nayi wankan da hujja. Murmushi yayi yana fad'in yanzu kuwa, ai gara nayi na bankwana tunda anjima zan bar gidanki zuwa gobe na wuce. **** **** Wai abokina dan zaka koma waje shine ake kullen ka? Fawwaz yace wallahi ba haka bane, kasan na fad'a maka abinda ya faru lokacin muna sacondary, to ashe munafuki Adnan yaje ya fad'ama Iyayen yaron da nake fad'a maka na yanka da wuka, shine fa aka maido shari'ar babbar kotu, yanzu haka nemana akeyi shi ne fa Dady yace komawa zanyi bazan sake zuwa Nija ba. Milo yace yana da gaskiya, domin idan ka tsaya nan dole a kama ka, amma haka zaka zauna har lokacin tafiyar ka yayi bazaka d'an shana da budurwarka ba? Fawwaz yace gobe ne fa tafiyar kuma inaji jirgin safe zanbi. Milo yace gaskiya zanyi kewa, amma ya kamata kazo muje kayi na bankwana. Fawwaz yace gaskiya Dady yace kada naje ko ina, kuma idan na fita dole zai gane. Milo yace motata bakin glass ne, ka fara fita kashige zan biyoka daga baya kaga babu wanda zai san tare muka fita. Fawwaz yace shikenan, amma dole zaka k'ara mani wannan kayan. Milo yace baka da matsala. Dariya sukayi ya tashi, wayarsa ya aje yana fad'in nan zan barta kada Dady ya kira. **** **** Wallaji Oga munyi iya binciken mu bamu samu komai ba, har mun wuce inda wayarsu ta dena aiki amma babu abinda muka samu, kuma bamuga kowa wanda zamu iya zargin wani abu ba, shiyasa muka dawo ko zuwa gobe sai mu canza waje. Gyara zama Hamza yayi yana fad'in ba sai kun canza waje ba, dole suna nan inda kukaje, ba k'ananan b'arayi bane shiyasa basu bar wata alama da za'a iya ganesu ba, dole sai munsa basira a aikin kafin mu kamosu, dan haka ku barshi sai gobe sannan mu koma. Sara mashi yayi kafin yayi waje. Wayarsa ya d'auka yana fad'in ina jinka Milo, toshikenan kayi yanda nace dan bana so ya zargeka, gamu nan zuwa kawai ka nuna baka san komai ba. Nagode. **** *** Ra'eez tashi muci abinci kaji. Tashi Ra'eez yayi yana dafe kai. Jabeer yace jarumta zakasa aranka insha Allahu komai zaizo da sauki, idan suna tunanin wannan abun da sukayi sunyi nasara to hakan zai jawo masu fitina, domin Allah baya barin azzalumai, idan ka bari damuwa ta kaika k'asa shikenan zasuyi galaba akan mu. Kallonshi Ra'eez yayi yana fad'in wallahi aikin shari'a ya fitar mun akai, dama can saboda d'aukar fansa na tsaya na karanceshi, amma ina kammala wannan shari'a to zan kammala ta tare da aikina, wallahi Jabeer bazan iya ba, aikin lauya aikine na halaka. Kada ka sare Ra'eez. Saurin juyowa sukayi jin magana daga bakin k'ofa. Alhaji Mansur ne tsaye yana kallonsu. Duk'ar da kai Ra'eez yayi. Shigowa yayi yana fad'in wannan fa somin tab'i ne, duk da ma shine mai wahalar domin kafin akai k'arshen shari'ar kowa zaisan matsayinsa, dan haka kadena damuwa yanzu haka Fawwaz yana hannun Inspector Hamza. Cike da farin ciki Ra'eez ya d'ago kai yana kallonshi. Kai ya jinjina yana fad'in Rafeek ya kirani ya tabbatar mani da haka, kaga komai zaizo da sauki. Jabeer yace amma naji dad'i, sai ka matso muci abincin yanzu. Murmushi Ra'eez yayi ya matso yana fad'in ko yanzu ma akoma kotu. Dariya Alhaji Mansur yayi yana fad'in banda cika baki fa. Ra'eez yace Allah Abbah naji sauki yanzu, sai dai hankalina yana wajen su Adnan da Abban Nabeel, bana so ta silata su rasa rayukansu. Alhaji Mansur yace Hamza ya tura amintattun yaranshi, duk da sunje basu samu komai ba amma gobe zasu koma, bazasu tab'a kashe su yanzu ba, nasan zasu jira zuwa jibi kafin nan kuma insha Allahu an kwatosu. Ra'eez yace Allah yasa. Wayar Alhaji Mansur ce tayi k'ara, yana dubawa yaga Bala bakanike, murmushi yayi yana fad'in ko har an kammal gyaran motar? 'Daga wayar yayi. Bayan sun gaisa Alhaji Mansur yace Bala an kammala ne? Daga can Bala yace wallahi yanzu haka aikin nakeyi, kasan motar ta dad'e a aje dole sai da na fiddo komai dan tayi kura sosai, amma kuma injinta lafiya lau yake, to bayan da na fito da kujerun motar sai na samu wani tsohon flash, shine nace bara na kiraka na fad'a maka. Alhaji Mansur yace flash kuma? Saurin gyara zama yayi yana fad'in Bala kana ji na ko, ina so ka samu abinda zaka saka mani shi, ka jira ni nan da mintuna zan kira ka, ina so yazo lagos daga nan zuwa gobe. Kashe waya yayi yana fad'in Allah amin. Ra'eez yace Abbah lafiya? Murmushi yayi yana fad'in Ra'eez gaskiya tana ta kok'arin bayyana kanta, kasan Bala ya tafi da motar Alhaji zai dubata, shine yace mun a k'asan kujera ya tsinci wani tsohon flash, duk yanda akayi ajiyar Marigayi ce, Alhamdulillahi Allah mungode maka, dole nayi waya a samu wanda zai taho lagos ya kawo manashi, badan ma bana so wani abu ya faru ba da ko amotar haya sai a d'oroshi, amma bari nayi waya da abokina shine shugana 'yan Union. *** **** Ka kwantar da hankalin ka Mr. Kallah babu abinda zai faru, ina fatan baka fad'ama Alhaji Marusa komai ba dan kaga daga ciwo ya tashi? Mr. Kallah yace ban fad'a masa ba amma dole na damu Alhaji Barau, tsohon sirrin mu da yayi shekara da shekaru fa akeson bankwad'owa taya hankalina zai kwanta. Alhaji Barau yace kada kamanta fa mune kotu, Alhaji M. Sanda bazai tab'a bari asirinmu ya tonu ba, kai tun daga can sama muna da k'afa taya kake tunanin asirin mu zai tonu, kai dai kawai sai kun dawo goben, ka gaishe mani da 'Yallab'ai Marusa. Dariya sukasa ya kashe wayar. **** **** A zabure ta tashi daga kwancen da take ganin sakon daya shigo wayarta, hannu tasa ta murtsike idonta ta d'auka ko bacci takeyi amma tabbas zahiri ne. Gaba d'aya ta rikice, taya aka amsar mata makudan kud'i har haka, gashi kuma acikin bankin aka amshe su, dole tasan a volk room ne kad'ai za'a iya amsar wad'annan kud'in domin tasan acan take amsar kud'i masu yawa. Suman zaune tayi, wasu hawayen tashin hankali ne suka zubo mata lokacin data kalli balance d'inta, ita da take da kusan million takwas dan d'azu ta turama Khalil kud'i amma yanzu itace take da dubu d'ari biyar. K'arar sakon daya shigo mata ne yasa tayi saurin dubawa. Ido ta tsura ma sakon tana karantawa a hankali. *Nasan da ciwo aci amanarka, amma ciwon mai sauki ne idan akayi duba da abinda mutum ya aikata, nasan baki san koni waye ba shiyasa kika fara tarayya dani, ni kuma sanin da nayi maki ne yasa nashigo rayuwar ki, ina fatan hakan zai zama darasi agareki idan kina da sauran Imanin da zaki iya koyon darasin. Nuradden Hambali, 'Dah ga Shehu Hambali Rigacukum zariya, ko ahaka na barki nasan ya isheki ki tuna komai, kinci amanar mahaifina wanda hakan ya jawo ajalinsa, kin wulak'antani akan nazo neman taimakon kud'in da zan kai Mahaifina asibiti, duk da kece silar jefashi halin da yake amma kika tozartani, tun daga ranar na d'auki alk'awarin tozartaki, na tausaya maki shiyasa na rage maki na cefane, kada kiyi tunanin nemana domin zakisha wahala kuma hakan zai kaiki ga mutuwa ma, ki gode Allah daya baki basirar zab'en akwati mai kyau na ajiyar gwalagwalai, na barki lafiya. Ur's Nuress.* Wurgi tayi da wayar cikin tashin hankali ta bud'e durowa, ihu ta saki ta zube tana wani irin kuka, tabbas Nuress ya gama da ita, bayan da ya mayar da ita tamkar matsarsa, ta siya masa gida da mota, duk hakan be ishe shi ba sai da ya aikata mata cin amana. Runtse ido tayi a hankali ta furta *Shehu Hambali* **** Shine saurayinta na farko arayuwarta, tana kaduna yana zariya amma haka yake zuwa wajenta, sunyi soyayya sosai, kasancewarta mai idon cin naira yasa ta tasoshi gaba, shi kuma yana sonta shiyasa baya iya mata gardama, a hankali ta rik'a tatseshi, kafin asa masu rana duk wani abu nashi sai da ta cinye, bayan ansa masu rana akazo had'a lefe tace ga irin wanda takeso, beda kud'i sai gidanshi na gado, dole ta sashi ya raba gidan biyu ya siyar da rabi tace zatayi maleji tasan bayan aure zasuyi kud'i. Ana saura sati d'aya bikinsu ta had'u da Alhaji Marusa, cikin k'ank'anin lokaci labari ya canza, aranar d'aurin aure Shehu da abokansa suna zaune sukaji an d'aura da wani bashi ba. A asibiti ya kwana, kwananshi ukku aka sallamoshi, yana zuwa gida ya iske amaryarsa, domin tun acan Kawunsa yasa aka d'aura da diyarshi, ana dawowa kuma aka siya mata komai ta tare. Yayi kuka har ya gaji, tun daga ranar ya kamu da ciwon zuciya, sau d'aya ya tara da matarsa rabon Nura yashiga, ga talauci, ana haka ya samu labarin inda Karimatu take a Lagos, haka ya wanke kafa yaje, sai dai wulakancin da tayi masa ko kare bazai d'auka ba, tunda ya dawo ya samu littafi ya rubuta tarihinsu, haka yacigaba da rayuwa cikin kunci, duk da matarsa tana kula dashi. Bayan shekaru Nura ya tasa, tunda ya taso haka ya iske Mahaifinsa babu lafiya, zuwa lokacin basu da komai, ga ciwo, ganin zai mutu suka kaishi asibiti, makudan kud'in aikin da za'a mashi ya tada hankalinsu, haka yazo d'akin Mahaifinsa yana duba takardun gidan ya siyar ayi masa magani. Littafin daya iske yaja hankalinsa ya karanta. Yayi kuka har ya gaji, a washe gari yaci bashin kud'i ya nufi Lagos, duk da bayanin da yayi mata besa ta tausaya mashi ba, haka ta wulakantashi tasa masu gadi suka masa duka suka wurgoshi waje. Kafin ya dawo sai zaman makoki ya iske, ta silar haka Mahaifiyarsa ma ziwon zuciya ya kasheta, yasha wahala hakan yasa ya taso da niyar d'aukar fansa. Dole tasa ya siyar da gidan gadonshi yaje ya sayi kaya masu kyau ya koma Lagos da zama. A hankali ya fara bibiyar Karimatu, wata rana ta fito daga wani Mall suka had'e, shine ya amsar mata kayan ya kai mata mota, tunda ta ganshi ta mace akanshi. Wannan ne silar had'uwarsu, yana sane ya maidata kamar matarsa duk da ba hakan yaso ba, zafin dake ranshi yasa ya biye mata, tayi masa hidima a ciki hada gida da mota, a yau daya kammala aikinsa sai yaji duk wani kunci ya bar zuciyarsa, haka yabar Lagos. Ajiyar zuciya ta saki mai k'arfin gaske bayan data gama dogon tunani, wato shiyasa Nuress yashigo jikinta har haka kenan, ta aminta dashi hatta da aiken banki shi take turawa ko nawa ne zai karb'o mata kuma be tab'a mata sata ba, ma'aikatan bankin duk sun sanshi dan tace masu k'aninta ne shiyasa da ta aikeshi da check matuk'ar akwai sa hannunta suke bashi kud'i, to ya akayi ma tasa hannu a check d'in? Dole sai idan satar fasaha yayi mata. Wani sako ne ya sake shigowa wayarta, saurin dubawa tayi... *Nasan zakayi mamakin yanda akayi aka bani kud'i ba tare da sa hannun ki ba, to idan baki sani ba yanda na iya sa hannun ki ko ke bazaki nuna mun iyawa ba, wannan dalilin ne yasa na iya saka hannunki, ada nayi tunanin na cira ta Atm, sai naga bazan ciresu alokaci guda ba, shiyasa na shirya tafiya da rana saboda na samu naje banki, sai kuma naci sa'a aka gama komai na bar bankin kafin kisan anyi, na barki lafiya.* Wani irin ihu ta saki data tuna abinda yayi mata, da sauri Mai aikinta tashigo, ganin halin da take ciki yasa tayi saurin kiran masu aiki maza, kafin suzo ta sume, dole suka d'auketa zuwa asibitin su. *** *** Wai ina Fawwaz yaje ne? Ammi tace tun bayan da abokinsa yazo har ya tafi yana d'aki kwance dan naga lokacin da abokin ya tafi sai dai ban shiga d'akin ba dan nasan baya son takura. Amma ai nakira wayarsa tana k'ara kuma be d'auka ba, jeki duba mani d'akin, ko kuma muje ma. Turuss sukayi ganin baya d'akin, saurin tura k'ofar band'aki yayi amma baya ciki, hankali tashe ya d'auki wayar Fawwaz yana duba sunan Milo, sai dai babu lambarshi babu alamunta. Zama yayi zufa tana keto mashi. Ammi tace wai lafiya Alhaji? Kallonta yayi yana fad'in burinki ya cika kin barshi ya fita saboda akamashi dan bakiso yabar k'asar. Ammi tace mekake fad'a haka, nice zan barshi ya fita? Tomeyayi ma da za'a kamashi? Tsaki yayi yafice daga d'akin. Wayar Lucky ya kira, yana d'agawa yace Lucky Fawwaz ya fito, inaso ka kokarta ka dawo dashi gida tun kafin aganshi, ka duba gidan hutawarsa kuma ka bincika inda yake zuwa bana so asamu matsala. Kashe wayar yayi yana huci. Ur's. Nabeelert Lady🖋[3/10, 8:41 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.* 4⃣3⃣ Haka Alhaji M. Sanda yayi ta zagaye a d'akinshi sam ya kasa kwanciya, duk bayan mintuna sai ya kira Lucky amma amsar d'aya ce ba'a dace ba, dole tasa ya hak'ura ya kwanta ranshi a b'ace. **** **** Milo kaga abinda nake fad'a maka ko, nace maka Dady yace kada na fita amma kace na fito gashinan an kama mu, gara kai nasan sakin ka za'ayi ni ko kamani zasuyi zuwa kotu kuma kashe ni za'ayi. Milo yace yanzu meye amfanin b'oyewar, ko ka tafi idan aka gano kana da laifi ko birnin sin kaje kotu tana da ikon maido ka, shawarar da zan baka kawai kaje ka fad'i iya abinda ka sani zaifi maka. Hawaye ne suka zubo ma Fawwaz yace yanzu Milo kaine kake bani shawarar naje akashe ni? Dafashi Milo yayi yana fad'in ka fahimce ni abokina, wallahi ban tab'a jin na tsani rayuwar da nakeyi ba sai yanzu, tunda ka bani wannan labarin hankalina ya tashi, ayanzu da ka fad'a mani shari'ar da za'ayi sai nayi nadamar abubuwan dana aikata, kuma insha Allahu daga yau na bar shirmen da nakeyi, shaye-shaye kuwa dole zan barshi domin shine yake samu aikata sauran laifukan. Kwanciya Fawwaz yayi yasa kuka. Matsowa Milo yayi yana rarrashinsa tare da kwantar masa da hankali. **** **** Wajen k'arfe goma motar su Alhaji Marusa ta shigo cikin gidanshi, masu aikin gidan ne suka zo suna masa sannu da zuwa, Mr. Kallah ne ya bud'e mashi mota ya fito tare da sandar da yake dogarawa, duk ya rame sai dai yayi haske. Har cikin falonshi suka rakashi shida Alhaji Barau dan shine ya d'auko su. Ruwa Mai aikin gidan ta kawo masu, bayan ta aje ta duk'a tana sake gaishe su tana tambayar mai jiki. Alhaji Marusa yace ina Hajiya fa na kira wayarta akashe? Mai aikin tace ai Hajiya bata da lafiya jiya sai wajen k'arfe d'aya muka dawo daga asibiti dan tace bata son kwana acan shine aka sallameta amma tana can kwance tana cikin ciwo ko magana batayi sai kuka. Alhaji Marusa yace meya sameta ne? Wallahi ina aiki kawai naji ihunta, kafin nazo na iske ta suma, haka na kira sauran muka kaita asibiti, sai dai lokacin data farfad'o tasa kuka tana fad'in wayyo kud'inta tana kuma kiran sunan Nuress. Alhaji Marusa yace to Allah ya kyauta, idan na huta na shiga. Da sauri Alhaji Barau yace ba haka za'ayi ba, kana ji fa tace tana ambaton kud'i hada sunan namiji, ke wanene Nuress? Wiki wiki mai aikin tayi da ido. Alhaji Barau yace magana zakiyi dan musan abinda yake faruwa, domin daga bayanin ki na fara fahimtar bakin zaren gara ma ki fad'i abinda kika sani ko nasa a kulle ki. Mr. Kallah yace wai Alhaji Barau ina ruwanka, wannan fa maganar cikin gida ce. Alhaji Marusa yace barshi yacigaba nima naji ina son naji komai. Mr. Kallah yace kasan fa ba wata lafiya kake da ita ba meyasa zaka damu kanka. Alhaji Marusa yace muna jinki. Kai a k'asa ta fad'a masu waye Nuress har zamanshi a gidan bayan tafiyarsu da irin alak'ar da sukeyi da Hajiya, sai dai batasan abinda ya had'asu ba. Mamaki sosai ya kamasu Alhaji Barau, Alhaji Marusa kuwa murmushi ya saki yana fad'in ashe dai maganganun da ake fad'a mani gaskiya ne nine ban yarda ba, lallai Karimatu kin cika butulu, koda yake dama ai nasan za'a rina dama can butulu ce ita, shikenan tayima kanta domin ni mace bata isa ta sani damuwa ba, abu d'aya ne zan rasa nashiga tashin hankali shine kud'i domin sune nasa araina fiye da komai, ko Marwan da naji yaki tsayawa yayi jinyata banji haushi ba, domin dama can ban sasu araina ba dan nasan zasu iya sani ciwon kai. Mr. Kallah yace baza'ayi haka ba Alhaji, yakamata kaji abinda ya faru domin ka taimaka mata, muna can fa take fada maka kayanta sun salwanta, kaga kila shima yaron yaudararta yayi. Tsaki Alhaji Marusa yayi yana fad'in wallahi babu abinda zan mata, kai na saketa ma saki ukku tazo ta barmin gidana bana buk'atar ta ayanzu. Alhaji Barau zeyi magana sukaji an saki kuka, ganin Hajiya sukayi ta shigo tana takawa da kyar, dama daurewa tayi jin ya dawo tazo tayi masa sannu da zuwa. Cikin sauri ta shigo tana fad'in Alhaji ka rufa mani asiri, wallahi zan shiga damuwa idan ka rabu dani, duk tarin kud'in da kake bani ban tab'a tunanin siyen kadara ba, abu d'aya nasan ina tarawa sune gwalagwalai, sai kuma kud'ad'e da nake ajewa a banki suma na kwashe su na saro kaya gashi nayi asara, sauran kud'in kuma an sace su da gwalagwalai na, ga Marwan jami'an Madina sun kamashi da kayan kwayoyi yana can dama jiran dawowar ka nakeyi, dan Allah ka rufa mani asiri wallahi sharrin shed'an ne, gaba d'aya Nuress ya takaitani. Shiru sukayi suna kallonta da jin irin abinda take fad'a. Alhaji Barau yace to a ina za'a samu shi Nuress d'in? Cikin kuka take fad'in nima ga sakon daya rubuto mani nan, ashe d'aukar fansa ce ta kawoshi waje na...... Tsab ta fad'a masu abinda ya faru. Shiru wajen yayi sai sautin kukanta. Alhaji Marusa ne yayi gyaran murya yana fad'in wallahi da zanga wannan yaron sai nayi masa babbar kyauta, wannan yaro shi ake kira da d'an halak, kuma yayi dai-dai, to bari kiji, wallahi babu wanda zai b'ata lokacinsa wajen tayaki nemoshi, kema yanzu ba anjima ba zaki bar mani gidana, suturarki kad'ai zaki d'auka amma ko mota bazaki d'auka ba wallahi, taimako d'aya zansa direba ya kaiki tasha zan baki kud'in mota kitafi, dama bakizo da komai ba. Ihu tasa tana fad'in Alhaji kodan Yaranmu da suka girma kada kamun haka wallahi zan gyara, idan ma ka sake ni naji ka barni nayi zaman yarana. Tsaki yayi yana fad'in ni yanzu yaro d'aya nake dashi domin nasan Marwan tashi ta k'are dan saudiya hukuncin kisa suke ma duk wanda suka kama yana siyarda miyagun kaya, ni ko wallahi bazan b'ata kwabo na wajen amsoshi ba, shima Khalil idan ya dawo to, idan kuma ya zauna acan zan cigaba da kula dashi. Alhaji Barau zeyi magana yayi saurin tashi yana kwalama direba kira, kallonta yayi yana fad'in na baki mintuna ashirin, idan baki shirya ba zaki tafi haka. Jiki na rawa tayi saurin tashi dan tasan halinshi. Haka taje ta had'a kayanta kusan akwati bakwai, sai kuka takeyi, Nuress ya cuceta, amma tasan alhakin Hambali ne, ashe dama irin wannan rayuwar zata risketa, yau kusan shekaru talatin da wani abu tana cikin jin dad'i amma rana d'aya komai ya tafi, sam bata tab'a tunanin ta gyara gidansu ba, batayi tunanin ta taimaki wani nata ba, asalima bata cika zuwa gida ba, sai tayi shekara bata leka ba, idan taje ma bata wuce kwana biyu, shima har ta baro gidan bata cin komai na gidan, gashi yanzu zata koma can da zama. Haka ta fito masu aiki suka d'aukar mata kaya sai kuka takeyi. Dubu hamsin Alhaji Marusa ya bata, Mr. Kallah ya ciro tubu talatin ya k'ara mata yana bata hakuri, Alhaji Barau kuwa wajen ya bari yana yamutsa fuska. Bayan sun tafi Mr. Kallah yace Alhaji ya za'ayi da Marwan? Alhaji Marusa yace Allah yaji k'ansa, yanzu ta Khalil nake kuma kada ku sake tuna mani dashi. Mr. Kallah yace kada kace haka.... Hannu ya d'aga mashi yana fad'in dan Allah. Kai Mr. Kallah ya jinjina yana fad'in muje ciki kayi wanka ka huta zamu wuce. Hannu ya mik'a masu yana masu godiya. Alhaji Barau yace zan wuce dan tun d'azu Alhaji M. Sanda yamun waya yana nemana sai munyi waya. Godiya yayi masu suka wuce. **** **** Ido awaje Alhaji Barau yake kallon Alhaji M. Sanda jin abinda yake fad'a. Hannu yasa ya goge zufar data zubo mashi yana fad'in Lucky d'in yace basu ganshi ba? Alhaji yace har yanzu babu labari. Gyara zama Alhaji Barau yayi yana fad'in ana wata ga wata, nasan dole su Ra'eez ne zasu sa a d'aukeshi, yanzu ya zamuyi? Alhaji yace nasan Fawwaz bazai tab'a amsa laifinsa ba, kai kuma ina so kayi saurin yanke hukunci da zaran Fawwaz yaki amsa laifinsa shikenan magana ta wuce, domin dole jawabinshi ne kad'ai zai tabbatar da gaskiya, nasan kuma bazai fad'i gaskiya ba, kaga babu Adnan, babu Alhaji Sulaiman, kuma su kad'ai ne suka san gaskiya, kai ko suna nan basu da hujja ahannu iyakarta abaki, kotu kuma da hujjar zahiri take amfani, sannan kuma basu kai su ukku ba. Ajiyar zuciya Alhaji Barau yayi yana fad'in hakan ma yayi kuma yasa naji sauki, gara ma Fawwaz d'in yaje kotun hakan zaisa kowa ya yarda dashi tunda bazai fad'i gaskiya ba. Alhaji yace magana ta wuce, anjima zanje na duba Alhaji Marusa, bazan sake damuwa akan a nemoshi ba, mubarshi yaje kotun ba shikenan ba. Alhaji Barau yace haka ne. Sallama yayi mashi ya fita. **** **** Rumaisa leka naji ana sallama. Fitowa Rumaisa tayi tana amsawa, cike da mamaki take kallonta. Murmushi Raheena tayi tana fad'in K'anwarmu ko na koma? Murmushi Rumaisa ta saki tana fad'in kishigo mana. A falo ta zauna, fita tayi ta kawo mata ruwa tana fad'in sannu da zuwa. Raheena tace kin ganni ko azahar ban bari tayi ba, dole tasani fitowa tun d'azu ma naso zuwa naga safiya tayi da yawa shiyasa na daure har shabiyu tayi. Rumaisa tace amma Yaya besan zaki zo ba ko? Raheena tace shine ma silar zuwana, kwana biyu idan nakirashi baya d'auka, duk da nasan yana kan aiki ne amma ko beje ba ai sai muyi waya ko. Murmushi Rumaisa tayi tana fad'in sosai kuwa. Mama ce tashigo da sallama, saurin risnawa Raheena tayi tana gaisheta. Amsawa Mama tayi cikin sakin fuska, fita tayi ta basu waje. Ganin sunyi shiru Rumaisa tace Aunty bara naje na d'ora abincin rana kada na bar Mama da aiki, kiyi kallo kafin na gama. Tashi Raheena tayi tana murmushi tace haba muje muyi aikin tare. Rumaisa tace ki barshi zanyi. Wucewa tayi tana fad'in Allah tare zamuyi. Fita Rumaisa tayi tana mamkin karfin halin Raheena, dole haka suka had'u sukayi aikin, Mama kuwa tausayin Raheenar ma takeji. **** **** Shiru sukayi suna jiran fitowar likita daga d'akin gwajin da aka shigar da Ummu, Ra'eez addu'a kawai yake Allah yasa Ummunsa ta samu sauki. Jabeer ne ya dafashi yana fad'in insha Allahu zata samu sauki. Fitowar likita yasa su saurin tashi. Hannu ya mik'a ma Alhaji Mansur suka gaisa. Kasa hakuri Ra'eez yayi yana fad'in an dace likita? Zama yayi yana murmushi, gaba d'aya suka zauna suna kallonshi. Takardar da take hannunsa ya kalla yana fad'in da farko zan fara da godema Allah, domin shine mai kwantarwa kuma ya tayar, Alhamdulillahi Allah shine abin godiya, yau kam Allah ya kawo mana saukin al'amauran da suka shige mana gaba, acikin mutane goma da aka d'aukesu a wannan asibitin a shekarar 2008 tare da Hajiya yau Allah ya nufa itama ta samu lafiya kamar yanda biyar daga cikinsu tuni an sallamesu. Cikin farin ciki Ra'eez ya zube k'asa, goshinsa ya kai yana mai sujudar godiya ga ubangiji. Gaba d'ayansu kallonshi sukayi cike da tausayi. 'Dagowa yayi yaje ya rungume likita yana hawaye. Alhaji Mansur yace ai babu sauran kuka kuma sai farin ciki, gaskiya nayi matuk'ar farin ciki, likita babu abinda zamuce maka sai godiya kai da Alhaji Usman, hakika kun bada gudummuwa akan Hajiya Bilkisu, Allah ya saka maku da alkhairi. Zama Ra'eez yayi yana fad'in amin Abbah, wallahi na rasa bakin godiyar ma. Likita yace ai kayi abinda akeso, domin wannan sujadar da kayi ta wadatar, sai kuma aje ayi sadaka. Jabeer yace wannan kam kullun cikin yinta akeyi, amma dole ta yau ta zama ta musamman. Alhaji Mansur yace ya jikin nata yanzu? Likita yace babu abinda yake damunta yanzu sai rashin kwarin jiki, ina ganin nan da juma'a zaku iya tafiya da ita, dalilin da yasa nace zan riketa anan nafison ku kammala wannan shari'a hankalin ku zaifi kwanciya, kafin nan ta k'ara warwarewa. Ra'eez yace yanzu zamu iya ganinta? Kai likita ya d'aga yana fad'in kaje ka ganta idonta biyu. Hannun Jabeer yaja sukayi waje da sauri. Murmushi Alhaji Mansur yayi yana fad'in bawan Allah, koba komai yanzu zaiji sanyi a ziciyarshi. Likita yace sosai ma. A hankali ya tura k'ofar d'akin, Ummu tana kwance tayi saurin tashi tana kallon Ra'eez, cikin sauri yaje ya shige jikinta yana sakin kuka. Rungumeshi tayi itama hawaye suka zubo mata, duk da iya abinda ya faru alokacin da Malan Sani yazo kawai zata iya tunawa amma tasan tabbas wani abu marar dad'i ya faru da Abbun Ra'eez. Shigowar Alhaji Mansur yasa suka nutsu. Zama yayi yana fad'in Ra'eez kai da zaka kwantar mata da hankali shine zakasa mata kuka. Murmushi yayi yana goge idonshi. Kallon Ummu yayi yana fad'in sannu Hajiya Bilkisu, Allah ya k'ara lafiya yasa iya wahalar kenan. Murmushi tayi tana amsawa, tana son ta tambayeshi amma kawaici ya hanata. Kamar yasan abinda take tunani yace abinda nakeso dake kisa aranki kome ya faru muk'addari ne daga Allah, nasan akwai tarin tambayoyi a zuciyar ki, amma ki sani yanzu ne kika warke daga ciwo, kuma ciwonki yana buk'atar natsuwa domin abu ne daya had'a da kwakwalwa, dan haka ki adana tambayoyinki insha Allahu ranar juma'a idan muka koma gida zakiji komai, amma inaso kisa jarumta aranki, sannan ki godema Allah bisa baiwar da yayi maki na baki lafiya da yayi. Kai ta jinjina tana kok'arin maida kwallar idonta. Tashi yayi yana fad'in bara naje Alhaji Kamal yana jira na, Ra'eez ku dawo gida dawuri saboda an kawo wannan sakon na Kano ina so mu bincikeshi. Kai Ra'eez ya d'aga. Tashi Jabeer yayi yana fad'in bara na koma wajen aiki kai ka zauna anan. Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in nagode. Haka suka fita suka barsu, gyara zama Ra'eez yayi yashiga bama Ummu labarin karatunshi. **** **** Yauwa kana ji na ko, kada ka bari su b'ace maka gani nan zuwa, inaso kayi amfani da hankali kasan manyan 'yan fashi ne zasu iya gane kana binsu, shikenan gani nan zuwa. Cikin mintuna ashirin Hamza ya isa bayan gari, da sauri d'an sandan ya fito daga inda ya b'oye. Hamza yace yauwa sannu Hassan ina ne suka shiga? Hassan yace cikin wancan lungun naga sun shige, sai dai su biyu ne kawai. Hamza yace kai da sauran ku biyo ta baya, ni kuma zan shiga ta gaba amma kuyi ahankali. Su ukku suka zagaya ta baya yayin da Hamza yawuce ta gaba. Ruwa suka watsama Adnan wanda yake a sume saboda tsab'ar kishir ruwa da wahalar d'aurin da akayi masa, Abban Nabeel yana d'aure a saman kujera cike da tausayin Adnan, saboda sunfi bashi wahala shi a zaune yake kan kujera yayin da Adnan yake d'aure atsaye, sannan shi Abbah ana bashi abinci da ruwa amma basa bama Adnan. A firgice Adnan ya farka yana sakin ajiyar zuciya. Abbah yace haba bayin Allah wace irin zuciya ce da ku, idanshi Ogan ku beda d'igon Imani da hasken musulunci ai ku musulmai ne, meyasa zaku biye mashi bazaku bama wannan Yaron ruwa yasha ba, ko babu abinci ai zai iya rayuwa da ruwa. Dariya d'aya daga cikinsu yasa yana fad'in idan baka sani ba kome mukeyi Oga Lucky yana kallon mu a gidanshi, ko baya zaune yana zuwa zai kunna yaga abinda ya faru, idan ma mun kashe kemarar zai gane, dan haka bazamu b'ata aikin mu ba saboda kud'i muke so. 'Dayan zeyi magana yaji saukar k'asan bindiga akanshi, k'ara ya saki ya zube a sume, rarumar bindiga d'ayan yayi amma Hamza yarigashi kwad'a masa sanda, fad'uwa yayi yana nishi, saurin shigowa su Hassan sukayi, kama su sukayi suka d'aure suka fita dasu. Saurin kwance Adnan da Abbah Hamza yayi, sai dai tuni Adnan ya faad'i saboda babu kwari ajikinshi. Ruwa Hamza ya d'auko ya kamoshi, saurin amsa yayi ya fara sha, yana gama sha ya fara amai. Abbah yace muyi saurin barin wajen nan domin Ogansu zai iya zuwa dan yana ganin duk abinda akeyi. 'Daukar Adnan Hamza yayi sukayi saurin barin wajen. **** **** Ra'eez goge flash d'in kafin ka saka shi nasan yayi kura, Ra'eez yace Jabeer wurgomun gashinan gefen ka, d'aukowa Jabeer yayi yana fad'in bara muga ka iya kwallo. Murmushi Rafeek yayi yana fad'in duk wanda yayi makaranta ai ya iya buga kwallo sai dai matsoraci. Wurga masa Jabeer yayi yana dariya, hannu Ra'eez yasa zai cab'e sai dai bezo a dai-dai ba sai ya fad'a k'asan gado. Alhaji Mansur yace lallai Ra'eez beyi kwallo ba. Ra'eez yace Allah mugunta yamun. Jabeer zeyi magana wayar Rafeek tayi k'ara, saurin d'auka yayi ganin Hamza. Saurin tashi yayi yana fad'in amma mungode Hamza, shikenan kayi yanda kace, bana so akaishi asibiti subi bayanshi, shikenan nagode sai mun had'u goben. Zama yayi yana fad'in Allah maji rokon bawansa, su Hamza sun samu kama b'arayin da suka sace Adnan da Abban Nabeel, yanzu haka Adnan da Abban suna gidanshi ana bama Adnan taimako dan yaji jiki. Gaba d'ayan su sukayi hamdala. Alhaji Mansur yace Jabeer kira Nabeel ka fad'a mashi dan hankalinsu ya kwanta, kai ma kira Sameer ka fad'a masa. Bayan sun kirasu Rafeek yace d'auko flash d'in mu duba. Lek'awa Ra'eez yayi sai yaga ya shige ciki, tasowa yayi yana fad'in sai kazo ka d'aga katifar a d'auko. Murmushi Jabeer yayi yana fad'in Ra go kawai. Alhaji Mansur yace Rafeek kama masu naga yau shiriritar tasu ta motsa. Tashi Rafeek yayi yana murmushi ya kama mashi suka d'age katifar. Ur's. Nabeelert Lady🖋 [3/10, 8:41 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.* 4⃣4⃣ Bayan ya d'auko flash d'in har za'a maida katifar Ra'eez yace wallahi Abbah mutanan Da akwai su da dabara, tun kwanaki dana d'aga katifar nan naga wata loka a jiki amma ban bud'eta ba. Da sauri Alhaji Mansur ya taso yana fad'in ina lokar take? Ra'eez yace gata nan ajikin gadon hada mukullinta ajiki da gani babu komai ciki tunda ba'a cire makullin ba. Saurin lek'awa Alhaji Mansur yayi yana fad'in ku k'ara d'age katifar. Hannu yasa ya bud'e, jawowa yayi saiga ajiyar da Abbu yayi ta flash daya adana sirrikanshi. Da sauri ya d'auko yana fad'in ikon Allah, lallai yau muna da sa'a, garinya da ka ga lokar baka d'aga ba? Ra'eez yace wallahi lokacin sauri nakeyi shiyasa ban bud'e ba, tun daga lokacin kuma ban sake tunawa da ita ba. Sakin katifar sukayi gaba d'aya suka zo domin ganin abinda yake ciki. Jabeer yace wanne za'a fara sawa? Alhaji Mansur yace ku fara saka mana wanda aka samu yanzu kamar zamufi samun abinda muke so. Sakawa sukayi gaba d'aya suka natsu. *** Ajiyar zuciya suka saki lokacin da ya k'are. Hawaye ne suka saukoma Ra'eez a lokacin daya gama jin bayanin Abbunsa, dan daga k'arshe Abbu ya d'auki kanshi yana fad'in wannan sheda ce ta haramtattun kaya da Alhaji Marusa yake shigowa dasu, ko da bana raye ina fatan wannan sheda zata riski adalin Alkali domin a yanke ma masu laifi hukunci dai-dai da abinda sukayi. Jinjina kai Alhaji Mansur yayi yana fad'in wato wannan shine abinda ya jawo suka kashe Alhaji Maiwada, domin Abubakar ya fad'a mani sun gano abinda Malan Hassan yasa a gidan Alhaji Marusa shine suka kashe shi, jin yace Alhaji Maiwada yaga komai shine dalilin da yasa suka kashe shi suka d'auke kamfutarsa atunaninsu sun b'atar da kowace sheda basu san Allah yafisu ba. Rafeek yace su hud'u ne manyan cikinsu kuma manyan masu laifi, Adebayo da Umar sune k'ananan masu laifi, sai sauran 'yan dabarsu. Jabeer yace wato sun had'a kai an kashe Abbu sai suka d'ora Adebayo amatsayinsa, shi kuma Alhaji Barau bayan tsohon Alkali ya sauka sai ya d'orashi amatsayinsa, shi kuma Umar ya hau matsayin Adebayo, haba shiyasa yanzu ake shigo da abinda akaga dama saboda sune keda abun. Alhaji Mansur yace kunna d'ayan mu gani....... Bayan ya k'are suka kashe, mayar da flash d'in sukayi cikin jaka. Hamdala sukayi Alhaji Mansur yace shari'a tazo k'arshe, wannan karon mune masu matsayi domin mune masu abun nunawa, Allah sarki Naseer, Allah yaji k'ansa ya kyautata makwancinsa, domin yayi abinda akeso, dan wannan shedar tashi tafi komai muhimmanci, ko ita kad'ai muke da ita basu da hanyar da zasu iya k'aryata zargin da ake masu, ko da kotun da tafi kowace kotu shiririta da rashin iya aiki za'a kai shari'arsu ina mai tabbatar maku dole a yanke masu hukunci, haka zalika ko akwai shugaban k'asa acikinsu k'arewar kud'i da matsayi dole hukunci ya hau kansu, dan haka dole muyi magana da Alhaji Kamal a daren nan kafin gobe. Rafeek yace gaskiya Naseer yayi jarumta, amma Abbah a shawarata a fara gabatar da shedar Naseer, bayan da kowa yasan masu laifi idan za'ayi shari'ar su sai agabatar data Abbu. Alhaji Mansur yace wannan haka yake, Ra'eez wannan aikin ka ne, dole ka saka wad'annan shedun a mizanin da kowa zai k'ayatu da shari'ar, dan haka kasa tunani irin naku na lauyoyi ka tafiyar da shari'ar yanda zata k'awatu. Ra'eez yace insha Allahu Abbah. Tashi yayi yana fad'in Malan Sani komai yazo k'arshe, domin daga gobe ya gama kwanan gidan yari insha Allah, zan kwanta Rafeek ka gaishe da mutanan gidan. Tashi Rafeek yayi yana fad'in zasuji Abbah, nima tafiya zanyi ina so naje wajen Hamza kafin nawuce. Alhaji Mansur yace ka masa godiya. Sallama yayi masu ya wuce d'akin da yake kwana. Tashi sukayi suka raka Rafeek, bayan ya tafi suka kulle gidan suka dawo ciki. Wanka Ra'eez yayi kafin ya kwanta, bayan Jabeer ya fito ya kwanta yana kallon Ra'eez da yake waya k'asa-k'asa. Murmushi yayi ya juya baya yana fad'in gulmamme wayar ma baza'ayi da k'arfi ba. Kyaleshi Ra'eez yayi yana fad'in Pretty kikace Raheena tazo? Rumaisa tace ai naji dad'i da kace bazaka zo cin abincin rana ba Yaya Jabeer yazo ya kai maku asibiti kai da Ummu zakuci, bakaga yanda ta b'ata rai ba, abincin ma kasa ci tayi dole ta tafi. Murmushi yayi tana fad'in daga gobe ai zata gane dalilin da yasa naki karb'ar soyayyar ta, idan tana da hankali bazata sake nemana ba. Rumaisa tace wallahi na kosa a gama wannan shari'ar mubar garin nan. Ra'eez yace kinsan gobe Kawu a gida zai kwana fa. Rumaisa tace da gaske? Ra'eez yace insha Allahu, domin a gobe zamu nemi ayi shari'arsa dasu Alhaji Barau. Rumaisa tace Allah ya tabbatar, aikuwa gobe azumi zanyi. Ra'eez yace muna tare kenan, nima azumin zanyi, kinga zamuyi shan ruwa mai dad'i. Murmushi tayi suka cigaba da firar su. Bayan daya kashe wayar ya lek'a fuskar Jabeer yana fad'in kayi hak'uri na hanaka bacci abokina. Tsaki Jabeer yayi ya tureshi yana fad'in dalla matsamun marar kunya. Dariya Ra'eez yasa yana fad'i. Haushi kakeji kai baka da abokiyar fira. Jabeer yace Allah tausayin Raheena nake, ina tunanin yanda zataji idan tasan asalin kalar Mahaifinta. Ra'eez yace hakuri zatayi, shiyasa nace ka aureta hakan zai rage mata zafi, kaga.... Saurin juya masa baya Jabeer yayi ya rufe kunnuwanshi yana fad'in sai da safe. Dariya Ra'eez yasa yana fad'in Allah ya kaimu. ***** ***** *Safiyar alhamis a kotu* Duk da kasancewar shari'ar ta bama mutane haushi amma hakan be hana suka dawo ba domin suji yanda za'a k'are. A sannu kowa ya shiga kotun suna jiran zuwan Alkali. Bayan da Alkali yazo kowa ya samu nutsuwa, sai dai Alkali sam baya cikin natsuwarsa, tunda Lucky ya fad'a masa an kama yaranshi kuma an tafi dasu Adnan hankalinsa yake tashe, gashi Lucky yace bazai zauna ba shima guduwa zaiyi, hakan ne yayi masifar tada mashi hankali, dan ko sauran abokansa bai fad'amawa ba dan yasan suna iya barinshi tunda shine ya zamar ma dole yazo kotu. Magatakarda ne ya tashi ya sake karanto shari'ar da za'a gabatar. Bayan ya zauna Alkali ya d'ago kai yana fad'in Brr. Ra'eez muna jiranka, da fatan wannan karon kazo da cikakkar sheda. Fitowa Ra'eez yayi yana fad'in nazo dasu ya mai shari'a, kamar yanda kowa ya sani a ranar talata an buk'aci kotu da ta kawo Fawwaz M. Sanda domin ya amsa wasu tambayoyi wad'an da suka shafi wannan shari'ar da akeyi, sai dai bayan da aka je kiransa sai akace baya k'asar wanda na ja da hakan sai aka buk'aci dana tabbatar da shedar yana cikin k'asar nan, alokacin bani da wannan shedar, amma ayanzu ina so kotu ta bani dama domin na gabatar da ita.... Kotu ta baka dama. Hamza ne yayi ma su Hassan alamu hakan yasa suka fita, ba'a jima ba sai ga Fawwaz sun taso shi agaba duk ya fita hankalinsa, duk da babu wanda ya tab'ashi amma tashin hankali ya hanashi sakat. Gyara zama Alkali yayi kirjinsa yana dukan ukku-ukku, gaba d'aya zufa ce take zubo masa, amma duk wanda ya kalleshi sai ya d'auka yayi murna da hakan, saboda ba'a gane komai ta fuskarshi. Bayan da Fawwaz ya shiga ya tsaya sai Ra'eez ya tako kusa dashi. Ra'eez... Kotu zata so taji cikekken sunan ka. Sunana Fawwaz Muhammad Sanda. Ra'eez... Malan Fawwaz ko zaka fad'a mana yaushe ka dawo k'asar nan. Fawwaz... Zanyi wata d'aya dana dawo. Ra'eez.... kenan dai baka sake komawa ba? Kai Fawwaz ya d'aga yana fad'in E. Ra'eez... Malan Fawwaz ko zaka iya fad'a mana sunan makarantar da kayi wato secondary da shekarar da ka gama, da kuma abokan ka wad'an da bazaka iya mantawa ba. Fawwaz... Kings college nayi, na kammalata a 2008, manyan abokaina kuma guda biyu ne, Sufwan da Adnan, sai dai Sufwan ya rasu. Ra'eez... A cikin 'yan ajinku ko zaka iya tuna *Farouk Ahmad Ringim*? Fawwaz... Shiru yayi yana mazurai, can kuma yace gaskiya na mantashi domin shekarun da yawa. Ra'eez... Naseer Sambo Jarmai fa? Fawwaz... Nifa mutane biyu kad'ai na iya rik'ewa saboda sune manyan abokai na, sauran kawai ana gaisawa wasu ma ko magana bamayi. Ra'eez... Murmushi yayi yana fad'in shikenan bara na tuna maka su, Farouk shine abokin fad'an ka lokacin kuna aji shidda, a binciken da nayi hakan ta faru ne silar wata yarinya mai suna Minal wacce ta kasance budurwa a wajen Farouk, bayan ka ganta kaji kana sonta hakan yasa ka nemi daya bar maka ita, shi kuma ya nuna besan haka ba, wannan shine silar rikicin ku dashi, shin ko zaka fad'ama kotu abinda ya faru a ranar da kukayi fad'a na k'arshe wanda Adnan ne ya raba ku? Fawwaz... Zufa ce ta fara keto mashi, kallon mutanan kotun ya farayi ko zaiga Dadynsa. Runtse ido yayi yana tuna maganar da sukayi da Dady ana gobe za'a saceshi. *Fawwaz abinda nakeso da kai ka sani, koda Allah yasa dole sai kaje kotu ina so ka tsaya akan maganar da zan fad'a maka, duk yanda za'ayi kada ka sake ka amsa laifinka, domin ita kotu da hujja ukku take amfani, na farko idan aka samu shedu mutum ukku, na biyu idan aka sami hujjar zahiri kamar ace hujja ta vedio, na ukku idan wanda ake zargi ya amsa laifinsa. Ina so ka sani ayanzu Adnan da Alhaji Sulaiman ne kawai suka. san abinda ya faru kaga kuwa su biyu ne, sannan basu da shedar da zasu iya nunawa saboda mun konata, kai ka d'ai ne zaka iya bada k'ofar a kamaka da laifi, dan haka ina so duk yanda Brr. zai maka tambaya ka nuna baka san komai ba.* Ajiyar zuciya Fawwaz ya saki yana kokarin tattaro jarumta, kallon Ra'eez yayi yana fad'in gaskiya ni bani da wani abokin fad'a a makaranta, duk wanda yasan mu yasan mu ukku ne, bama shiga harkar kowa bare har muyi fad'a da wani, kuma ni bana soyayya a makaranta. Ra'eez... Jinjina kai yayi yana fad'in shikenan zaka iya tafiya. Ajiyar zuciya Fawwaz ya saki shida Alkali kafin ya koma ya zauna. Ra'eez... Ya mai shari'ar ina so kotu ta bani dama domin nayima Alhaji Sulaiman tsohon shugaban makarantar kings college tambaya.... Kotu ta baka dama. Ra'eez.... Kotu zata so taji sunan ka da kuma bayani akan tsohuwar makarantar ka. Sunana Alhaji Sulaiman, na rik'e matsayin shugaba amakarantar kings college wanda tuni na aje aiki. Ra'eez... A shekarar 2008 an samu gawar d'aya daga cikin d'alibanka a bayan gari, shin ko zaka iya fad'a ma kotu abinda ka sani. Alhaji Sulaiman.... Ajiyar zuciya yayi yana jin wata irin kunya, kallon yawan mutanan kotun yayi kafin ya duk'ar da kai yana fad'in da farko ina so na fara neman yafiyar Iyayen Farouk Ahmad, domin na aikata masu laifi mai girma, duk da bani da hannu cikin kisan da akayi masa amma ina da sa hannu a wajen lullub'e gaskiya. A shekarar 2008 a ranar alhamis da misalin k'arfe 5:15 na yamma, a ranar ina zaune a ofis na samu waya daga Alhaji Muhammad Sanda wato tsohon Alkalin kotun nan wanda ya kasance Mahaifin Fawwaz, bayan mun gaisa yake fad'a mani yana so nayi masa alfarma, idan har nayi masa haka zai bani mak'udan kud'i, to alokacin kunsan zuciya da kwad'ai, jin yawan kud'in da za'a bani yasa na amince da abinda ya fad'a. Anan yake fad'a mani Yaronshi Fawwaz yayi fad'a da Farouk tsautsayi yasa ya yankeshi da wuk'a har hakan ya jawo ajalinsa, ayanzu haka yana bayan makarantar wajen band'akuna yana so nayi kok'ari kafin kowa yaga gawar a fitar da ita, hakan ne zaisa babu wanda zai zargi komai tunda ba'a makarantar aka ga gawar ba, kuma lokacin tashi yayi. Duk da na jinjina abun amma tuna yawan kud'in yasa banyi tunanin komai ba kawai na amince, haka naje da mota ta dan bana so nasa wani ya tayani aje a tona asiri, koda aka ganni nayi cikin makaranta babu wanda ya damu acikin masu aiki saboda sun san nine sunyi tunani zagaye nakeyi. Haka naje na d'auki gawar nasata a mota na bar makarantar, sai da gari yayi duhu kafin naje na wurgar da ita na bar wajen, tabbas zuciyata taji babu dad'i domin na aikata babban laifi, amma tunda na amshi kud'i a hannu sai na manta da komai, tabbas nayi nadamar abinda na aikata, kuma ina neman alfarmar wannan kotu data sassauta mani akan hukuncina. Ina da ja ya mai shari'a. Brr. Bajinta ne yayi saurin tashi, risnawa yayi yana fad'in ya mai shari'a nine lauyan Alhaji M. Sanda, ina so kotu ta bani dama domin na kareshi abisa sharrin da Alhaji Sulaiman yake son yayi masa. Ajiyar zuciya Alkali ya saki dan besan Alhaji M. Sanda yayi magana da Brr. Bajinta ba. kai ya jin jina yana fad'in kotu ta baka dama, amma zaka iya jira Brr. Ra'eez ya kammala tambayoyinsa. Komawa yayi ya zauna yana fatan nasara. Gaba d'aya kotun ta d'auki hayaniya. Bubbuga tebur Alkali yayi kafin akayi shiru. Hannu yasa yana gyara glass d'insa ganin abinda yake faruwa a cikin kotu. Alhaji Kamal ne ya shigo shida wasu mutane guda biyu, hakan yasa wasu daga cikin kotun suka tashi domin su basu wajen zama. Ajiyar zuciya ya saki yayin da cikinsa ya fara kad'awa, meya kawo Alhaji Kamal kotu kuma bayan shima Alkali ne? Hannu yasa ya d'auki kofin ruwan da yake kusa dashi yasha, gyara zama yayi yana fad'in Brr. Ra'eez kacigaba. Ra'eez... Murmushi yayi yana fad'in Alhaji ko zaka iya fad'ama kotu dalilin da ya hanaka halartar kotu a ranar talata bayan kuma kace zaka zo? Alhaji Sulaiman... Tabbas nayi niyar zuwa kotu domin nazo na fad'i gaskiya, kuma aranar na shirya na fito daga gida domin halartar kotu, sai dai ina barin gida wasu mutane suka tare ni, tunda na tsaya suka fiddo ni ban sake sanin abinda yake faruwa ba sai da na farka na ganni a d'aure ni da wani yaro wanda shima yana da alak'a da wannan shari'ar domin shine abokin Fawwaz da yake magana wato Adnan, tun alokacin na gane dalilin kamo mu, an azabtar da Adnan yanzu haka yana can ana masa magani dan cikin ikon Allah 'Yan sanda suka ceto mu yayin da suka samu sa'ar cafke mutane biyu daga cikin b'arayin. Ra'eez... Mungode Alhaji zaka iya tafiya, ya mai.... Saurin tashi Brr. Bajinta yayi yana fad'in ya mai shari'a ina so kotu ta bani dama domin nayi magana akan abinda Alhaji Sulaiman ya fad'a. Da sauri Alkali yace kotu ta baka dama. Mamaki ne ya kama mutane, gashi dai Brr. Ra'eez be kammala tambayoyinsa ba amma an bama wani dama. Ra'eez kuwa murmushi yayi ya koma gefe yana kallonshi. Matsowa Brr. Bajinta yayi yana fad'in Alhaji Sulaiman naji bayanin ka, sai dai kada ka manta kotu tana amfani ne da hujjar zahiri ba ta baki ba, shin ko zaka iya nuna ma kotu hujja akan cewa Alhaji M. Sanda ne ya saka aikata abinda ka fad'a. Alhaki Sulaiman... Gaskiya bani da wata hujja domin lokaci ne mai tsawo, kuma banyi tunanin d'aukar wata sheda ba saboda nasan bazata mun amfani ba, amma tabbas shine yasani wannan aikin. Brr. Bajinta... Baka da hujja Alhaji Sulaiman, domin duk wanda yake cikin kotun nan da wanda yasan tsohon Alkali da wanda besanshi ba kowa yasan irin adalcinsa, kuma wannan abun daka fad'a zai iya yuwuwa wasu ne suka biyaka domin kazo ka b'ata masa suna tunda gashi ka kasa gabatar da hujjar abinda ka fad'a, ina rokon wannan kotun da kada tayi amfani da abinda Alhaji Sulaiman ya fad'a. Nagode. Matsowa Ra'eez yayi yana fad'in Alhaji zaka iya tafiya, ya mai shari'a ina so kotu ta bani dama domin na gabatar da mutanan da suka sace Adnan da Alhaji domin nayi masu tambayoyi. Dammm gaban Alkali ya fad'i, hannu yasa ya sake d'aukar ruwa yasha, abun goge fuska ya ciro ya goge zufar data sauko masa, da kyar ya sauke ajiyar zuciya yace kotu ta baka dama. Zuwa yanzu mutane sun fara mamakin Alkali, domin gaba d'aya ya fara rasa nutsuwarshi sai gyaren zama yake ga ruwa da yake yawan sha yana goge fuska. Bayan da suka tsaya agaban kotu kowa ya natsu yana kallon su. Ra'eez... Kotu zata so taji sunan ku. Sunana Gali Haruna... Ni kuma sunana Zubairu Garba. Ra'eez... Gali ko zaka iya fad'ama kotu dalilin dayasa kuka kamasu Adnan da Alhaji? Gali... Hakanan muka kamasu domin muna so a bamu kud'i amma babu wanda yasa mu. Ra'eez... Ai ban tambayeka waya saka ba, kawai dalilin sace su na tambayeka, kenan kaine shugaban ku ko? Gali gaskiya ba nine shugaba ba bansan inda yake ba dan babu wanda yasan gidanshi a cikin mu iya abinda na sani kenan. Ra'eez... Zubairu zaka iya fad'ama kotu wanda kuke ma aiki? Zubairu... Babu wanda muke ma aiki kawai muna neman kud'i ne. Ra'eez... Shikenan zaku iya tafiya. Ina so kotu ta bani dama domin na gabatar da sheda ta k'arshe.... Kotu ta baka dama. Jabeer ne ya tashi ya fara had'a kayan da zasu haska domin kowa ya gani. Tunda Alkali ya fahimci abinda suke shirinyi hankalinsa ya tashi, kafin su gama yasha ruwa kusan kofi ukku, sai goge zufa yake yayin da cikinsa yake buk'atar agajin zuwan band'aki, haka ya daure gudun kada ya tona kanshi. Shiru kotun tayi yayin da kowa ya zuba ido yana jiran a kunna. Hannu Ra'eez yasa ya kunna nan take aka hasko fuskar Fawwaz alokacin da suke fad'a da Farouk. A zabure Fawwaz ya mik'e yana shirin barin kotun, da sauri jami'an tsaro suka cafkoshi, ladabtar dashi sukayi kafin yayi shiru. Dede lokacin da ya yanki Farouk da wuka da zuwan su Adnan har suka bar wajen. Hannu Ra'eez yasa ya kashe kallon. Salati akasa gaba d'aya kotun. Wani babban mutum da yake zaune a baya yasa hannu ya goge hawayen da suka zubo masa, tun ranar Talata da yaronshi yaje masa da labarin shari'ar su Farouk yayi alkawarin zuwa domin yaji yanda shari'ar zata kasance danshi ya cire rai da neman adalci a mutuwar Farouk saboda afarko ma beyi niyar neman hakkinsa ba bare kuma yanzu, kawai yazo ne domin yaga wad'an suka tado da wannan shari'ar, sai gashi zuwanshi yayi amfani domin Allah ya nuna mashi wanda ya kashe mashi babban 'Danshi da idonshi. Bayan kowa yayi shiru Ra'eez yace ya mai shari'a iyakar abinda zan gabatar kenan, ba sai nace wani abu ba, domin nasan adalcin wannan kotun ne, saboda duk abinda zan fad'a idanuwan kowa sun gani, ina fatan wannan kotu zata bima Farouk hakkinsa, sai magana ta gaba akan shari'ar Naseer Sambo Jarmai. Nagode. Duk yanda Alkali yaso ya daure kasawa yayi domin jikinsa ya jik'e da zufa, gashi cikinsa yariga ya kad'a bazai iya daurewa ba dole sai yaje band'aki. Cije baki yayi cikin dauriya yace kotu zataje hutun rabin awa, kafin nan kotu tana buk'atar da a killace Fawwaz da sauran masu laifi. Kottt!!! Ur's. Nabeelert Lady🖋 [3/10, 8:41 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.* 4⃣5️⃣ A sanyaye mutumin yabi bayan d'ansa suka fita, kai tsaye wajen Ra'eez wanda yake tare dasu Alhaji Mansur suna magana ya nufa. Sallama yayi tare da mik'a ma Alhaji Mansur hannu suka gaisa. Kallonshi sukayi dan basu fahimceshi ba. Kallon Ra'eez yayi yana fad'in barka dai Brr, nasan baka sanni ba, sunana Alhaji Ahmad Ringim, Asalina d'an kano ne, kuma nine mahaifin marigayi Farouk, agaskiya nayi farin ciki da wannan shari'a, na dad'e da fidda ran nemawa Farouk adalci, sai gashi ranar talata Yaro na yazo mani da maganar shari'ar hakan yasa nace zanzo wajenka domin naji wanda yayi silar tado da shari'ar. Alhaji Mansur yace Allah sarki, ashe dai wad'an da aka zalunta suna da yawa, sannu Alhaji insha Allahu komai yazo k'arshe, kuma ayau zakaga yanda za'a yanke ma azzalumai hukunci, muje can mu zauna na fad'a maka yanda akayi. **** K'arar burkin mota yasa mutane suka maida hankalinsu inda ya fito, tsayawa sukayi suna kallon Alhaji M. Sanda ganin ya fito daga mota tamkar wanda aka wurgo, ganin yanda mutane suke kallonshi yasa yayi kok'arin dai-daita kanshi. 'Yan jarida ne sukayo kanshi hakan yasa yayi saurin shigewa kafin su k'araso, dole tasa suka hakura kowa yana jiran d'aukar rahoto. Alhaji Barau ne ya fito yana sharce zufa yana kok'arin d'aure wandonshi. Cak ya tsaya yana kallon Alhaji M. Sanda yayin da gabanshi yayi wani irin fad'uwa. Jiki a sanyaye ya samu waje ya zauna yana kokarin shan ruwa, sai da ya gama sha kafin ya goge fuskarshi yana fad'in Alhaji sannu da zuwa. Ajiyar zuciya ya saki yana fad'in Alhaji Barau me nake shirin ji haka? Brr. Bajinta ya kirani ya fad'a mani halin da ake ciki, duk yanda naso abun ya kasance amma naji ana niyar kai bango, a jiya na shiryama Brr. Bajinta duk yanda zaiyi sai gashi yana fad'a mani wai an kawo irin shedar da muka k'ona a wayar wannan yaron, Alhaji Barau lokacin mu fa yayi, inaji ajikina bamu da sauran mafita matuk'ar aka samu d'ayar shedar da yaron ya d'auka. Ajiyar zuciya Alhaji Barau ya sauke yana fad'in wallahi Alhaji kaina ya d'aure, yanzu haka saura mintuna a koma kowa yana jiran ayanke hukunci, babban abinda yafi d'aga mani hankali ganin Alhaji Kamal tare da wasu mutane wad'an da nake kyautata zaton daga chamber suke, kasan kuwa abinda yasa Alhaji Kamal ya iya baro ofishinsa kasan babban dalili ne. Gyara zama Alhaji M. Sanda yayi hankali tashe yace ba dai an kai maganar sama ba? Alhaji Barau yace wallahi bansani ba, amma idan zaka tuna Alhaji Kamal shine Baristan Alhaji Maiwada, sannan acikin wannan vedion da muka kona ta wayar Naseer akwai maganar da mukayi ta yanda za'a kashe Alhaji Maiwada, gaskiya jikina yayi sanyi. Ajiyar zuciya Alhaji M. Sanda ya sauke yana fad'in su Alhaji Marusa sun san da wannan maganar? Alhaji Barau yace babu wanda na fad'amawa, sun san dai maganar shari'ar Fawwaz kuma na fad'a masu komai zaiyi dai-dai tunda an kama su Alhaji Sulaiman. Kallon agogo yayi yana fad'in yanzu dai lokaci ya tafi, abinda nakeso da kai kada ka yanke ma Fawwaz hukuncin kisa. Saurin kallo shi yayi. Kai ya jinjina yana fad'in nasan lokacin da yayi kisan shekarunsa sun kai ya amshi hukunci saboda alokacin zeyi shekara 18, kaga kuwa hukunci ya hau kanshi, amma za'a iya juya abun, kace shekarunsa 14 kawai ya shiga makaranta ne da wuri, kaga hukuncinsa bazaiyi dede dana baligin mutum ba, idan kayi mani haka zanji dad'i. Alhaji Barau yace abu d'aya zakayi, sai dai ka b'oye takardar shedar haihuwarsa hakan ne zesa kowa ya yarda. Ajiyar zuciya ya saki yana fad'in babu damuwa dan bazasu tab'a gano inda take ba, kawai kayi yanda nace, su Alhaji Marusa kuma ka barsu a kammala wannan shari'ar sannan. Kai ya jinjina yana fad'in bara na koma lokaci yayi. Alhaji M. Sanda yace zan zauna anan bazan iya fita ba, kome kenan idan kowa yashige zan fice dan bana son had'uwa da 'yan jarida. *** Hannu Alhaji Ahmad yasa ya goge hawayen da suka zubo masa, sosai ya jinjina rashin imani irin nasu Alhaji Barau. Kallon su yayi yana fad'in wannan shi ake cema Allura ta tono galma, lallai wannan shari'ar abun so ce, domin d'aya bayan d'aya za'a warware komai, nagode sosai Alhaji Allah ya biyaku da alkhairinsa. Alhaji Mansur yace amin, ku tashi mu koma gashi can ana shiga. Tashi sukayi suka wuce. Rafeek ne ya fito daga mota, Jabeer yace yauwa gashinan ma ya dawo. Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in kasan abinda nake tunani kenan hakan yasa kaji nayi shiru tun d'azu. Jabeer yace ai tunda Abban Nabeel yace za'a samu nasan za'a samu. Mik'a mashi takardar Rafeek yayi yana fad'in sai da naje na tayasu kafin Allah yasa aka binciko file d'in, ai gaskiya Allah na sammu. Amsa yayi yana fad'in sannu Yaya. Murmushi yayi yace yauwa. Sameer ne da Nabeel suka k'araso wajensu, gaisawa sukayi suna tambayarsu Adnan da jiki. Sameer yace da sauki dan ya farfad'o, muna ta sauri kada a kammala ashema yanzu za'a koma. Jabeer yace muje gashi can Babban Alkali ya shiga. Dariya sukasa kafin suka wuce. *** Tsit kotun tayi kowa yana jiran hukuncin Alkali. Bayan daya gama rubuce-rubucenshi ya d'ago yana fad'in kotu taji duka bayanin da aka gabatar mata, bisa manyan hujjojin da aka gabatar ma wannan kotu ta gamsu da cewa Fawwaz Muhammad Sanda shine ya kashe Farouk Ahmad, wanda yayi amfani da wuk'a wajen kashe shi. Sai dai anan kotu zatayi duba da abubuwa guda biyu, na farko kotu zatayi duba da yanayin shekarun Fawwaz alokacin da yayi kisan kafin ta yanke masa hukunci, na biyu kotu zata kalli yanayin yanda akayi kisan, domin kisa kala-kala ne, akwai kisan da akeyinsa da niya, akwai kuma kisan tsautsayi. Idan akayi duba da yanayin yanda Fawwaz yayi wannan kisan zamuga cewar zuciya ce ta d'ebeshi, domin ba daga zuwanshi ya yankeshi da wuk'a ba, sai da suka fara kokowa kafin tsautsayi ya ratsa har ya yankeshi da wuk'a, sai na biyu, wannan kisan anyishi a shekarar 2008, alokacin Fawwaz yana da shekara 14, idan akayi duba da yanayin shekarunsa zamu ga cewar be kai shekarun girma ba, domin Mahaifinsa ya tabbatar ma kotu an sakashi makaranta da wuri shiyasa ya kammala ta a k'ananun shekaru, dan gaka kotu zata zartar da hukunci. Saurin tashi Ra'eez yayi yana fad'in ya mai shari'a ina neman alfarma, inaso kotu ta bani dama domin akwai abinda zan gabatar ma kotu. Langwab'ar da kai Alkali yayi alamun k'osawa da maganganun Ra'eez, ganin kallon da ake masa yasa yayi saurin amincewa. Murmushi Ra'eez yayi ya fito yana fad'in ya mai shari'a wannan takarda ce ta haihuwar Fawwaz wadda aka samo a cikin file d'insa na makarantar daya kammala secondary d'insa, idan akayi duba da wannan takardar haihuwar za'aga cewar alokacin da Fawwaz yake aji shidda yana da shekaru 18 ne, hakan kuma yayi dai-dai da lokacin daya kashe Farouk, abisa tsarin addinin musulunci duk namiji mai wannan shekarun ya isa ya d'auki hukunci domin yashiga shekarun baligi, sannan kuma ba a wajen da sukayi fad'an ya samu wuk'ar ba, dama can yazo da ita, kunga kenan dama yazo da niyar kashe shi, zamu iya cewa wannan kisa bana ganganci bane, kisa ne da aka shiryashi kafin ayi, bisa wannan hujjar nake so kotu tayi amfani da ita wajen yanke ma Fawwaz hukunci dai-dai da laifinsa. Nagode. Mik'ama Magatakarda yayi shi kuma ya mik'ama Alkali. Jiki a sanyaye ya amshi takardar yana dubawa. Tabbas takardar haihuwar Fawwaz ce, kuma duk wanda ya ganta zai tabbatar cewar bata k'arya bace. Ajiyar zuciya ya sauke, shikenan babu sauran wata hanya domin duk wasu shedu sun tabbata dole ayanke ma Fawwaz hukunci. Kallon gefen dasu Alhaji Kamal suke zaune yayi, ganin shi kad'ai suke kallo dole tasa yayi gyaran murya yana fad'in kotu ta gamsu da wannan shedar, dan haka zata yanke hukunci. Abisa hujjojin da aka gabatar ma kotu kwarara, wanda suka tabbatar da Fawwaz shine wanda ya kashe Farouk, abisa kundin tsarin mulki na k'asa, sashen kisa, amfani da makami ko wani abu, wannan kotu mai albarka ta yanke ma Fawwaz M. Sanda hukuncin d'aurin rai da rai agidan yari, sannan Iyayen shi zasu biya diyyar Farouk ga mahaifansa idan sun buk'aci hakan. Sannan kotu ta yanke ma Alhaji Sulaiman da Alhaji M. Sanda hukuncin d'aurin wata ukku a gidan yari ko kuma tarar naira dubu d'ari biyu saboda an kamasu da laifin taimakawa wajen b'oye gaskiya. Mutanan da aka gabatar ma kotu cewar sun kama su Alhaji Sulaiman kotu bata gamsu da hujjar da aka gabatar mata akansu ba, dan haka take umartar da a koma a sake bincikensu a tabbatar da hujja kafin a sake kawo su. Annan kotu ta kawo k'arshen wannan hukunci, zaku iya d'aukaka k'ara nan da wata ukku idan kuna buk'atar hakan. Ihu Fawwaz yasa yana kuka yana kiran Dady, saurin rik'eshi akayi aka fita dashi. Tashi Ra'eez yayi yana fad'in ya mai shari'a sai shari'a ta gaba akan Naseer Sambo Jarmai. Runtse ido Alkali yayi ya bud'e yana fad'in kotu ta d'age sauraron wannan shari'ar zuwa ranar litinin idan Allah ya kaimu. Kottt!!! Gaba d'aya mutane suka tashi kowa yana fad'in shari'a tayi, haka kowa ya jinjina ma Ra'eez, sannan sun k'ara jinjina adalci irin na Alkali. Alhaji Barau kuwa ta kofar kotun yayi saurin ficewa dan yasan 'yan jarida zasu iya rutsashi. Suna fita Nabeel yaja Abbansa zuwa mota dan yasan 'yan jarida suna iya rufeshi da tambaya, ayanda yaga jikinsa yayi sanyi yasan dole yana buk'atar hutu, hakan yasa yasashi mota suka bar kotun, ko su Ra'eez sai dai yayi masu waya. Brr. Ra'eez wane irin farin ciki kake ciki da Allah ya baka sa'a kayi nasara a wannan shari'ar? Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in ina mai cike da farin ciki domin yau Allah yasa Iyayen Farouk sunga yanda aka yankema wanda yayi silar mutuwar d'ansu hukunci, duk da shari'a ce tsohuwa amma yau Allah yasa an kammala ta, har Allah yasa a cikinta an samo wata hanya da zata kaimu ga samo gaskiyar wata shari'ar. Brr. Ra'eez ya kake gani akan shari'ar da za'ayi ranar litinin? Insha Allahu itama muna saran nasara. Nagode. Saurin wucewa yayi dan a matuk'ar gajiye yake. **** Wai Alhaji wane hali ake ciki naga tunda ka dawo kotu wajen Alhaji Barau kake kwance anan baka sake cewa komai ba. Ajiyar zuciya Alhaji M. Sanda ya sauke yana fad'in ko dai muyi nasara ko kuma suyi nasara, yanzu haka an tabbatar cewa Fawwaz shine ya kashe Farouk. A zabure Ammi ta mik'e tana dafe kirji idanuwanta awaje, kallon Alhaji tayi tana fad'in amma ba haka kuka fad'a mani ba. Runtse idanuwanshi yayi ya bud'e, sosai sukayi ja. Kallonta yayi yana fad'in ban d'auka abun zai kai haka ba shiyasa na b'oye maki, amma yanzu dole kiji komai..... Kuka kawai Ammi takeyi da tagama jin abinda ya faru, kallon Alhaji tayi tana fad'in yanzu shima kashe shi zasuyi? Garinya saboda b'oye laifin Fawwaz zaku kashe wani, haba Alhaji. Saurin tashi zaune yayi yana fad'in saboda irin haka yasa na b'oye maki, ki sani zan iya yin komai domin farin cikin Fawwaz, dan haka ban fad'a maki dan kiyi mani wa'azi ba, na fad'a maki ne dan naga babu amfanin b'oyewar. Tashi yayi ya shige d'aki. Zubewa Ammi tayi hawayen bakin ciki yana zubo mata, ashe dama Alhaji zai iya kisan kai akan son da yake ma Fawwaz? Lallai biri yayi kama da mutum, gashinan Fawwaz yayi kisa an kamashi, idan bincike ya tsananta shima dole akamashi, lallai wannan shine abun kunya Uba da 'Dah sunyi kisan kai. Yana shiga d'aki wayarsa tayi k'ara, saurin d'auka yayi ganin Brr. Bajinta........ Salati kawai Alhaji M. Sanda yake bayan da ya gama jin yanda shari'ar ta kasance, zubewa yayi saman gado jikinsa yana rawa, a sanyaye yace yanzu shikenan an tafi dashi? Brr. Bajinta yace wallahi dole ne tasa Alkali ya yanke wannan hukuncin, domin idon mutane suna kanshi, ga bak'i da nagani a kotun, Alhaji sai dai hakuri kawai, idan kuma zaka d'aukaka k'ara shikenan. Jinjina kai yayi yana fad'in shikenan, amma bazan iya zaman gidan yari kona wuni d'aya bane bare har wata ukku, kawai zan biya tara nagode. Kashe wayar yayi ya fara neman Alhaji Barau, tsaki yayi jin wayar a kashe. Hannu yasa ya dafe kanshi yana jin d'akin yana juya masa, tabbas idan har suka bari aka gabatar da shari'ar Naseer asirin su zai tonu, tunda har suka iya gabatar da wannan vedion dole suna tare da d'ayar. Kwanciya yayi hawayen bakin ciki suka zubo mashi. **** *** Sannu da zuwa Alhaji bansan ka dawo ba sai da Raheena take fad'a mun kana kwance a falo taga kamar baka jin dad'i. Tashi zaune yayi yana fad'in Hajiya ina cikin tashin hankali kawai kitayani da addu'a. Zama tayi tana fad'in menene ya faru kuma? Hukuncin kisa ya tabbata akan Fawwaz, domin an tabbatar da shine yayi kisan da nake fad'a maki, yanzu haka na yanke masa hukuncin d'aurin rai da rai agidan yari, wallahi kunyar Alhaji M. Sanda nakeyi shiyasa ma na kashe wayata domin shima hukunci ya hau kanshi. Jinjina kai Momy tayi tana fad'in gaskiya akwai tausayi, amma kadena damuwa, shima fa tsohon Alkali ne, waya san yawan mutanan daya yanke ma hukuncin kisa, wasu ma ratayesu akeyi wasu a jefesu wasu kuma a harbesu, damme zaka damu kanka kamar ka aikata wani babban laifi, abune a fili, dole sai da kowa yaga hujja kafin ka yanke hukunci, kuma ma wannan hukuncin arabuce yake, kana tunanin da ace shine a matsayinka akace d'anka yayi kisa zaice kai abokinsa ne bazai yanke masa hukunci ba? Kada kamanta nasan awajen hada 'Yan Jarida, da ace baka yanke hukuncin daya dace ba ina mai tabbatar maka da yanzu ka amsa kira daga sama, dan haka ka kwantar da hankalin ka bana so wani abu ya same ka, Allah ya basu hak'urin rashinsa. Murmushin takaici yayi yana kallon Momy, batasan sirrin da yake k'asa ba da bata fad'i haka ba, amma zai bita ahakan dan baya so ya tashi hankalinsu. Jinjina kai yayi yana fad'in nagode Hajiya, muje ki had'a mun ruwan wanka. *** *** Ai na d'auka bazai iya yanke ma Fawwaz hukunci ba, domin naga lokacin da Alhaji M. Sanda yazo wajenshi lokacin da aka fito hutun rabin awa, na tabbata alokacin ya shirya masa abinda ya fad'a. Ra'eez yace ai Abbah shiyasa muka dage sai da aka binciko mana takardar haihuwarsa, domin nasan irin haka zata iya kasancewa, ajiya Yaya yayi magana da Abban Nabeel, shine yayi mana jagora domin samo takardar, duk da ansha wuya saboda shekarun da yawa, amma kasancewar ana adana duk wasu takardu na 'yan makarantar yasa aka sameta. Alhaji Kamal yace dole a gobe zanje Abuja domin ranar litinin za'a k'aro mutane, kafin nan dole asa masu ido gudun karsu gudu, hatta shi shugaban Kwastam d'in da mataimakinsa duk asa masu ido saboda suma sai an hukuntasu. Alhaji Mansur yace ai naso ya tsaya yayi shari'ar Naseer da ayau sai dai suyi kwanan takura dan dole a akamasu, amma bakomai Allah ya kaimu litinin d'in. Alhaji Kamal yace amin. Wato abinda ya bani mamaki da kace mani an samu flash d'in a motar Alhaji Maiwada, abun tambaya nan shin dama Naseer ya kai mashi flash d'in ne ko kuma ya akayi? Alhaji Mansur yace kasan a labarin da Malan Sani ya bamu, a daren da za'a kashe Naseer da Alhaji Maiwada sun had'u da Naseer yana kokarin shiga wajen aikinsu da gudu har suka kusa tureshi, anan ya tsaidasu yace biyoshi akayi, hakan yasa suka taimaka mashi, dalilin da yasa Malan Sani yace wannan yaron shine Naseer saboda ya fad'a masu sunanshi, kuma da suna maganar kisan Farouk da akayi sai Naseer yace masu abokinsa ne, kaji dalilin da yasa Malan Sani yace wannan yaron shine Naseer, kuma da aka samu flash d'in a motar na fad'ama Malan Sani sai yace tabbas aranar da suka d'auki Naseer a kujerar baya ya zauna saboda Alhaji Maiwada baya zama baya. Alhaji Kamal yace bara mugani idan zan iya had'a kan labarin..... A hasashe na, bayan da Naseer yaje gidan su Fawwaz sai ya iske su Alhaji Marusa suna tattaunawa akan kashe Alhaji Maiwada, bayan daya gano shugaban kwastam suke nufi shine dalilin da yasa Naseer ya nufi ofishin su domin ya bashi wannan d'auka da yayi, kafin ya kai sai aka tura mashi mutane kamar yanda Adnan ya baku labari yaji ance aje a kashe shi har an anshi hotonshi, ganin an biyoshi sai tsoro ya kamashi, bayan da suka taimaka mashi sai yayi tunanin kada ya bada flash d'in a inda be kamata ba domin kaga ai dare ne bazaiyuwu ya iya gane Alhaji Maiwada ba, bayan da suka ajeshi sai yaga dacewar ya b'oye flash d'in a motarsu saboda ya tsorata kada abiyo bayanshi bayan tafiyarsu, ina ganin wannan shine dalilin samuwar flash a motar Alhaji Maiwada. Jinjina Alhaji Mansur yayi mashi yana fad'in aiki ga mai k'areka, wani abun sai ku tsofaffin lauyoyi, wannan hasashen naka tamkar kana wajen akayi, domin ya tafi dai-dai, tabbas babu ja hakan ce zata kasance, kuma ba kowa bane yasa hakan ta kasance sai Allah, domin ya riga daya tsara komai, kuma Alhamdulillahi gashi nan yau yayi mana rana. Alhaji Kamal yace Allah yajik'ansu da rahma, mu kuma yasa mucika da imani kuma yasa a kammala wannn shari'ar lafiya, amma fa Alhaji sai kace ma su Ra'eez su kula, domin ayanzu suna gab'ar rikici domin zasu faraucesu tamkar tsohon zakin daya shekara babu abinci, abinda nake gani kada Ra'eez ya aje wannan flash d'in a wajenshi. Hannu Alhaji Mansur yasa ya ciroshi yana fad'in Alhaji ina ganin ka tafi dashi wajenka hakan zaifi, duk da mun rarraba shi a wayoyin mu amma nafison a k'ara samun wani awajen ka. Alhaji Kamal yace shikenan Allah ya bamu ikon tabbatar dashi, ya kuma kare kowa daga sharrinsu. Alhaji Mansur yace amin ya Allah. *** *** Daga duba Adnan wajen Ummu suka wuce, ganin yanda jikinta yayi sauki yasa Ra'eez yace abarshi su tafi da ita, Alhaji Mansur ya kira ya fad'a mawa hakan yasa yace su taho da ita. Sosai sukayima matar da take kula da ita alkhairi da godiya, haka sukabi duk 'yan wajen da akhairi, har bakin mota likita ya rakosu suka tafi cike da murna. Gaba d'aya gidan ya hargitse da murna, Maman Labiba da Mama sun saka Ummu a tsakiya kamar zasu goyata, bayan koke-koke suka zauna akaci abinci, aranar kamar ana biki haka gidan ya kasance. Madu kasa zaman waje yayi haka yashigo ciki akayi murnar dashi. Suna zaune saiga Ladi dan Madu ya aika yaro ya fad'a mata, zama tayi tana ta farin cikin samun lafiyar Uwar d'akinta. Gaba d'aya sai abun ya dawo ma Ummu sabo, sosai tayi kuka. Bayan da suka dawo sallar isha'i suka zauna a falo Ummu tayi wanka tasa kaya sai ta fito tamkar ba itace tayi hauka ba, sosai tayi kyau, sai dai har yanzu akwai damuwa a fuskarta, duk ta kosa a fad'a mata abinda ya faru. Gyara zama Alhaji Mansur yayi yana fad'in Bilkisu inaso ki bani aron hankalinki, na lura idan ba'a sanar dake abubuwan da suka faru ba bazaki tab'a samun nutsuwa ba amma ki dubi girman Allah kada kiyi abinda zai dawo da ciwonki, nasan dai zuwa yanzu kinsan cewar Allah ya amshi Alhaji Maiwada, sai dai bakisan sauran abubuwan ba, dan haka yanzu zan sanar da ke komai...... Ur's. Nabeelert Lady🖋 [3/10, 8:41 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.* 4⃣6️⃣ Kuka kawai Ummu takeyi lokacin da ta gama sauraron labarin abinda ya faru, a hankali Ra'eez ya matso ya rungumeta shima yana kukan, gaba d'aya sai suka bama mutanan wajen tausayi sai mutuwar ta dawo masu farko. Da kyar Alhaji Mansur ya lallashe su kafin sukayi shiru. Ajiyar zuciya Ummu ta sauke tana fad'in Allah yajik'an ka Alhaji Allah ya kai haske kabarinka, hakika bazan tab'a yafema wad'an da suke dasa hannu a mutuwar ka ba, kuma insha Allahu sai sun wulak'anta. Alhaji Mansur yace kiyi hakuri komai yazo k'arshe, idan suna tunanin sun rufe sirrinsu Allah zai haskasu kowa ya gansu, ina so kisa jarumta aranki domin kije kiga yanda azzalumai zasuji kunya agaban idonki. Jinjina kai tayi tana goge ido tace dole nasa jarumta kam, kuma zanje har kotun domin na bada sheda akan zaluncin da akayima Malan Sani, domin duk abinda ya faru alokacin ban mance ba. Murmushi Ra'eez yayi ya rik'o hannunta yana fad'in Ummu ki kwantar da hankalin ki ina nan babu wanda zai sake saka ki zubar da kwalla, kuma zakiga yanda azzalumai zasu wulak'anta. Kanshi ta shafa tana fad'in Allah yasa Ra'eez. **** *** Dan Allah ka cire damuwa aranka, bazan bari kayi zaman gidan yari ba koda ace bani da kud'in da zan biya tarar da aka saka maku wallahi zanje naci bashi, dan haka kadena damun kan ka. Ummah tace mu godema Allah da abun ya tsaya a haka, yau da ace kana dasa hannu a cikin kisan shikenan kaima rayuwar ka acan zata k'are, babu wanda besan k'addara ba, kuma zuciya bata da k'ashi dan haka kadena saka damuwa aranka kaga likita yace jinin ka ya hau. Ajiyar zuciya ya sauke yana fad'in dole na damu Nabeel, ka tunafa ko auren farko bakayi ba, kamar yanda wannan abun ya faru ina mai tabbatar maka daga lokacin da ka fara neman aure sai wannan abun ya shafi auren ka, wallahi nayi nadamar abinda na aikata domin nayi maku bakin fenti, taya zan iya fita na kalli mutane, nasan da zaran na fita za'a rik'a nuna ni. Nabeel yace ni dai bazan damu ba Abbah, damuwata d'aya idan ka kasance acikin damuwa, duk wanda zai nuna mu yaje yayi ta nunawa domin abun kunyar mu mai sauki ne, ina mai tabbatar maka daga nan zuwa litinin za'a mance da labarin ka, domin za'a tono abinda zai girgiza mutane, dan haka kacigaba da neman yafiya awajen Allah, kud'i kuma gobe zanje na kaisu. Murmushi Abbah yayi yana fad'in nagode Nabeel Allah yayi maka albarka kuma ya baka wad'an da zasuyi maka fiye da haka. Gaba d'aya suka amsa da amin. *** *** Washe gari wajen k'arfe goma suka had'u a gidan Alhaji M. Sanda, zaune suke a lambu kowa tashin hankali kwance a fuskarshi. Mr. Kallah yace hakika muna cikin tashin hankali babba, dama irin wannan ranar nake tsoro, wallahi jiya banyi bacci ba bayan da naji wai an yanke maka hukuncin d'aurin wata ukku agidan yari, sannan Fawwaz d'aurin rai da rai, shiyasa nayi saurin kiran kowa nace mu had'u a nan dan muna da buk'atar tattaunawa kafin litinin saboda shari'ar da za'ayi ta shafemu duka. Alhaji Barau yace wallahi jiya kwana nayi ina gudawa, banyi baccin kirki ba saboda tashin hankalin da yake gaban mu, gani nake duk kunfini kwanciyar hankali domin nine wanda zan yanke hukunci da zaran an tabbatar da mai laifi. Alhaji Marusa yace wai an tabbatar da shedar ne? Alhaji Barau yace ai tunda har aka iya samun shedar kisan Fawwaz na tabbata akwai tamu aciki, domin idan baku manta ba alokacin da aka kawo wayar yaron a ciki mukaga duka d'aukar da yayi. Alhaji Marusa yace muna da sauran lokaci, nasan wannan shedar dole tana hannun Brr. Ra'eez, abinda nake gani mai zai hana mu aika Lucky ya sato mana ita ba shikenan ba. Mr. Kallah yace kana wasa da wannan lauyen, taya zai bar irin wannan shedar da ta riga ta fito a waje d'aya, kada kamanta yasan abinda yake ciki, idan ma an sace ta wajenshi ina da tabbacin ya tura a wani waje, kawai a samo wata hanyar. Alhaji Marusa yace bara na kira Lucky naji yanda za'ayi domin ina tsoron yaran can da aka kama idan sukaji duka zasu iya tona komai, kunga idan ma Ra'eez beda wata sheda akan mu sun samu a wajen su. Waya ya d'auko ya kira Lucky. Bayan sun gaisa yace wai Lucky kasan halin da ake ciki kuwa? Lucky yace na sani mana meye abun damuwa aciki dan kawai an kama Yarana, zuwa anjima zakuji labarin mutuwarsu dan yanzu haka sun kusa shek'awa, maganar shedar da akace an samu ta kisan Fawwaz kuma ina mai tabbatar maku ita kad'ai suka samu a flash d'in, idan kukayi duba da lokacin daya d'auki vedion zakuga be isa ace yaje ya tura a flash ba har ya nufi wajen shugaban kwastam, nafi tunanin tun bayan daya d'auki kisan Fawwaz ya adanashi a flash d'in kuma agidansu ya b'oyeshi, sauran na wayarshi kuma an k'onasu, dan haka kudena damun kanku idan ba haka ba zaku tona kan ku kuma wallahi ba ruwana dan zan iya barin garin gaba d'aya kuma babu wanda zai iya gano inda nake. Jinjina kai Alhaji Marusa yayi yana fad'in na fahimce ka, mungode sai munyi waya. Kashewa yayi ya kallesu yana fad'in kunji dai abinda yace, dan haka ku kwantar da hankalin ku yaran ma zai gama dasu, ai nasan Lucky beda wasa, kuma nima na aminta da bayaninsa. Gyara zama Alhaji M. Sanda yayi dan tun d'azu beyi magana ba, kallonsu yayi yana fad'in hankalina ba zai tab'a kwanciya ba matuk'ar ba gani nayi an gama da shari'ar litinin ba, wai meyasa ma acikin mu babu wanda yake hud'd'a da malan tsubbun nan. Alhaji Barau yace haba dai 'Yallab'ai kai da kan ka, ai wannan sai mutane marasa ilimin boko sune suke irin wannan harkar, dama can ban yarda da irin wannan abubuwan na Iyaye da Kakanni ba, nafi gane nasa majiya k'arfi suyi mani aiki, amma ka tsaya a wajen wani tsugunnan nan mutum kace shine zai maka aiki, idan Kura na maganin zawo tama kanta mana, kai tunda kake ka tab'a ganin Malamun tsubbu cikin kyakkyawan yanayi, shegu kullum suna zaune a bukka ko arami kamar mujiya, kawai ka barshi Lucky ma ya ishe mu da sauran basirar da muke da ita. Alhaji Marusa yace baka had'u da manya bane shiyasa, idan kana buk'atar aiki babu b'ata lokaci kaje wajen manyan arna a cikin tsaunuka anan sai abinda kaso. Mr. Kallah yace kudena wannan maganar ta wasu masu tsafi bamu da lokacin yin wannan, kamar yanda Alkali Barau yace aiki ne na marasa ilimin boko nima na goyi bayanshi, muyi amfani da ilimin mu da basirar mu kawai. Alhaji M. Sanda yace shikenan Allah ya kaimu litinin d'in muga da abinda zasuje, amma fa asanar dasu Adebayo domin suma acikin mu suke. Alhaji Barau yace wannan ba matsala bace duk za'a fad'a masu, kuma nasan ma dole suji hukuncin dana yanke a kotu tunda akwai sunan ka, abinda yafi kawai bakin mu ya zamo d'aya. Gaba d'aya suka ce badamuwa. Alhaji Marusa yace ni yanzu babban abinda yake damuna rashin kud'in da yake so ya sameni, domin jarina yayi k'asa sosai, a yanzu haka bani da jarin da zan iya shigo da kaya masu yawa dole sai dai na fara da kad'an-kad'an, gashi dama ni ba gwanin sayen kadara bane duka gidajena basu wuce ukku ba agarin nan, biyu haya ake aciki, gaskiya duk b'arayin da suka mani satar nan ban yafe masu ba wallahi kuma sai Allah ya saka mani. Kauda kai Alhaji Barau yayi yana murmushi a b'oye. Alhaji M. Sanda yace ka kwantar da hankalin ka a kammala wannan matsalar sai asan abunyi. Alhaji Marusa yace shikenan nagode maku. ***** Bayan sun tafi Alhaji M. Sanda yashigo gida, zaune ya iske Ammi tayi tagumi tana tunani. Zama yayi yana fad'in wannan tunanin babu inda zai kai ki, idan zakije ganin Fawwaz kitashi muje. Ajiyar zuciya ta sauke tana fad'in yanzu Alhaji hankalin ka har akwance yake da zakace na bar tunani, gudan jinina fa aka yanke ma hukuncin kisa shine zakace na bar damuwa. Gyara zama yayi yana fad'in kinsan dai baki fini sonshi ba ko? To tunda kika ga na saka hakuri araina kema kisa, domin Fawwaz bazai tab'a wulak'anta ba, da ace yau ratayeshi za'ayi shine hankalina zai tashi, amma zan ganshi a duk lokacin da naso, kuma ni nasan yanda zanyi domin a sama masa kwanciyar hankali a gidan yari domin ina da mutane acan, kuma kinsan babu abinda kud'i basayi, dan haka kitashi muje idan zaki. **** *** Ya isa haka Fawwaz kadena kuka babu abinda za'ayi maka, yanzu daga nan zanje naga shugaban gidan Yarin zamuyi magana dashi har wajen kwana dole asake maka, ina zaka iya kwanciya da manyan katti wad'an da suka gawurta awajen aikata laifuka, ko aiki ma bazan bari kayi ba, sannan abinci zansa arika baka wanda kake so kaji. Kai ya d'aga yana goge idonshi. Ammi tace Fawwaz ka godema Allah da yasa ba kisan lokaci guda za'ayi maka ba, yanzu lokacin da zaka koma ma Allah ne, kaga dai har abada bazaka fita anan ba sai dai a fitar da gawar ka, abinda nakeso da kai ka zama nagari, domin duk wanda yazo gidan yari zai had'u da wad'an da suka fishi komai arashin ji, haka kuma zai had'u da wad'an da yafi, dan haka ina so ka natsu ka koyi darasin rayuwa, kada kace zaka biyema wasu ka lalata rayuwar ka, duk inda aka tara jama'a akwai na banza dana kirki, abinda nakeso da kai kayi kokarin nemo na kirki kayi tarayya dasu, ni dai na yafe maka duk abinda kamun kuma zan cigaba da nema maka shiriya. Shiru tayi tana goge hawayen da suka zubo mata. Matsawa Fawwaz yayi ya rungumeta yana kuka, kasa daurewa Alhaji yayi shima ya juya yana goge kwalla, soyayya tasa ya jefa d'ansa cikin matsala. Wani daga cikin ma'aikatan yazo yana fad'in Alhaji lokaci yayi. Kallonshi Alhaji yayi sai yaga da alamu sabon d'auka ne dan duk ma'aikatan wajen girmamashi sukeyi. Kai ya jinjina yana fad'in naji, wucesu yayi yana fad'in kai ka taso kaje ku faskara wancan iccen. Kuka Fawwaz ya fashe dashi yana fad'in Dady kaji ko, dan Allah kayi wani abu wallahi bazan iya wahala ba, ni gara ma asake mani hukunci arataye ni zaifin mu sauki, kwana d'aya bakaji yanda nakeji ba. Saurin tashi Ammi tayi ta bar wajen tana kuka. Tashi Alhaji yayi yana fad'in kada ka damu zanyi magana yanzu. Kud'i yasa mashi aljihu yana bin kayan da suke jikinsa na gidan yari da kallo, wai yau 'Dansa ne yake sanye a cikin kayan nan, shida yayi shekara da shekaru yana aiko mutane gidan nan, da masu laifi da marasa laifi yau gashi shima an kawo nashi. Juyawa yayi yana fad'in sai mun sake dawowa... Barka dai Alhaji Muhammad Sanda. Saurin jiyowa yayi yana kallon dattijon da yake tsaye kusa da Fawwaz. Ido ya tsura mashi sai dai ya kasa gane waye. Murmushi Malan Sani yayi yana fad'in dama ai bazaka sheda ni ba, domin ka yanke ma mutane da yawa hukunci zuwa gidan nan ba lallai bane ka iya gane kowa musamman wad'an da sukayi shekaru a gidan, sai dai su daka yanke ma hukuncin har abada bazasu tab'a mance fuskar ka ba. Murmushi Alhaji yayi yana fad'in bawan Allah duk wanda kagani agidan nan to abinda ya shuka ne yazo girba. Malan Sani yace sosai kuwa, tunda gashi ma har an fara kawo 'Ya'yanku a gidan, da sannu sauran zasu biyo bayanshi, domin mutanan da sukayi suka agidan nan suna da yawa, lokaci kawai ake jira yayi domin akawo su su girbe shukar su, domin gidannan yana maraba da kowa, mai kud'i ko mulki ko sarauta babu wanda baya d'auka, kuma duk wanda yazo dole ya jeru da sauran mutane. Ajiyar zuciya Alhaji ya sauke yana fad'in kaga Malan ni bansanka ba haka kawai kazo kana gasa mani magana, Fawwaz kaje ciki zanje wajen shugaban gidan nan. Juyawa Fawwaz yayi yana goge idonshi, har Alhaji ya juya Malan Sani yace idan baka sanni ba ai kasan Tsohon shugaban kwastma marigayi Alhaji Maiwada, idan har ka tunashi dole ka tuna da direbanshi da ka yanke ma hukunci zuwa gidan nan. Dammm!!! Gaban Alhaji ya fad'i, saurin jiyowa yayi yana kallon Malan Sani. Murmushi Malan Sani yayi yana fad'in da sannu zaku maye gurbina yayin da Allah zai d'aukeni naje nacigaba da rayuwa cikin Iyalina. Wucewa yayi yana murmushi. Jiki a sanyaye Alhaji yaja k'afarsa zuwa ofishin shugaban gidan Yari, har ya isa yana maimaita maganar Malan Sani. A bakin k'ofar ofishin ya tsaya suna gaisawa da masinjan, magana yayi masa akan yana son ganin shugaban wajen. Masinja yace ai baya gari Alhaji. Kallonshi yayi yana kallon motar mutumin, juyowa yayi yana fad'in amma ai ga motarsa can. Masinja yace ai yau yayi tafiyar bayan yazo nan ya ajeta suka tafi a motar abokinsa. Jinjina kai Alhaji yayi yana fad'in shikenan bani lambarsa. Babu musu Masinja ya bashi, juyawa yayi ya tafi yana masa godiya. Tsaki Masinjan yayi yana fad'in munafukan Allah, a hankali asirin ku zai tonu, shekara nawa kana aiki baka tab'a zuwa gidan nan ba sai yau da aka kawo d'an ka, insha Allahu sai Allah ya toni asirin duk wasu masu zalunci, kun lalata Yara sai abinda sukaga dama sukeyi ba dole surik'a kisan kai ba. Ciki ya shiga, yana shiga yace 'Yallab'ai ya tafi. Tsaki 'Yallab'an yayi yana fad'in ai tunda naji yanda shari'ar ta kasance nasan dole sai yazo shiyasa na shirya masa hakan, su sauran da ake kawowa suna rayuwa ba mutane bane, a yanda hukuncinsa yazo aikin wahala zeyi sosai, kaga hakan zai zama darasi akanshi, kuma wallahi zan jama sauran ma'aikatan kunne duk wanda ya amshi cin hanci akan wannan yaron zai iya rasa aikinsa, domin ni ba tsohon shugaba bane babu maganar cin hanci, duk wanda yazo gidan nan dole yayi aiki, wasu ma basu da alifi amma haka suke aiki, sai kuma ace za'a kare masu laifi, koya kirani ba zai samu ba ma. **** **** Duk wani shirye-shiryen shiga kotu sun kammala shi, sosai Ummu ta sake a cikin su Mama da Umman Labiba, kuma jikinta yayi sauki sosai, sai damuwar rashin Abbu da take damunta. Zaune suke a falon gidan su Sameer sunzo duba Adnan, jingina yayi dan jikinsa da sauki sosai. Nabeel yace abokina kajiyo k'amshin lahira fa. Murmushi Adnan yayi yana fad'in ai azabar kishi bata da dad'i, wallahi mutanan nan basu da Imani, wai shikenan an sake su? Rafeek yace taya za'a sake su, ai tunda Alkali yace acigaba da rik'esu har sai an kawo kwakkwarar sheda akansu dole a rikesu, Hamza ma yace suna nan suna shirya yanda zasu kama Ogansu. Jabeer yace ai wannan Ogan nasu shine babban azzalumi, matuk'ar aka kamashi shikenan komai yazo k'arshe, dan yanda na fahimcesu bazasu tab'a tona asirin junan su ba. Ra'eez yace Adnan baka da wata hanyar da za'a iya kamashi? Adnan yace gaskiya gidanshi ba cikin gari yake ba, domin wani lokacin idan suna waya ina jin yana fad'a masu su sameshi bayan ruwa, ina kyautata zaton kamar yafi zama acan. Rafeek yace shikenan zanyi magana da Hamza saboda su san inda zasu farauceshi. Sameer yace wato a kullum ina k'ara godema Allah da yasa shiryata tazo mani tun ina da sauran kwana, hakika zalunci beyi ba, haka zalika aikata b'arna beda amfani, wallahi ayanxu ne nake jina cikekken mutum. Rafeek yace sai ma kayi aure zaka k'arasa zama cikekken mutum. Dariya sukasa gaba d'aya. Sameer yace ai na kusa nayi auren nan, akwai Hindatu tana d'aya daga cikin matan da na b'atama rayuwa, sai dai ita ba ta hanyar da nakebi na bi da ita ba, anan bayan layin mu take, Iyayenta suna da rufin asiri haka yarinyar akwai natsuwa, tun farkon ganina da ita sai naji ta burgeni, hakan yasa na fara mata magana har muka fara gaisawa, a hankali sai ta fara sona, duk da bata fad'a mani ba amma na fahimci hakan, ni kuma kawai sha'awarta nakeyi, da haka na fara janta jikina, soyayyar da take mun yasa take bin umarni na, da haka har na samu na biya buk'ata ta da ita, tun daga lokacin na dena kulata, lokacin da Iyayenta suka gane abinda nayi mata tasha duka, inda Allah yaso bata d'auki ciki ba, mahaifinta yaso ya tada maganar sai mahaifiyarta tace ya rufa masu asiri yin hakan kamar tona masu asiri ne, dole haka ya hakura, tun Hindatu tana kirana bar na kulleta dole ta hakura dani, shiyasa a lokacin da nace zanbi wad'an da na b'atama rayuwa na basu hakuri naje har gidansu na bama Iyayenta hakuri itama na bata hakuri, cikin sa'a kuma ta yafe mani, tun daga lokacin kawai sai na fara tunaninta, daga baya na fara kiranta, maganar da nake maku yanzu haka soyayyarmu mukesha kuma za'ayi maganar bikin mu. Tafi sukasa suna dariya. Rafeek yace gaskiya naji dad'in hakan, kuma nasan zaka kula da ita, dama kuma haka ake so, Allah ya baku zaman lafiya. Gaba d'aya suka amsa da amin. Wayar Rafeek ce tayi k'ara, yana dubawa yaga Hamza ne, bayan sun gaisa ya fad'a masa mutuwar Yaran Lucky, Rafeek yace shikenan yanzu zan zo. Kashe wayar yayi ya fad'a masu abinda ya faru. Shiru sukayi suna jimamin abun. Rafeek yace kada ku damu hakan bazai tab'a shedunmu ba, domin su kawai hanyar muce da zata sa mu gano inda Ogansu yake, kuma insha Allahu za'a kamashi. Suka ce Allah yasa. **** **** Wai Raheena me yake damunki ne kwana biyu bana ganin ki cikin walwala? Gyara zama tayi tana fad'in Momy haka kawai nakeji kamar bazan samu Ra'eez ba, ada nafi jin zan mallakesa, amma ayanzu zuciyata ta fara tsinkewa, kina gani yaushe rabon da yazo gidan nan, kowane irin aiki yakeyi tunda har muna gari d'aya ai ya kamata ko so d'aya ne ace yana zuwa wajena, idan bezo bama ai akwai waya, wallahi Momy jikina ya fara sanyi. Hannu Momy tasa ta goge mata hawaye tana fad'in ki kwantar da hankalin ki, tunda har yace maki aiki yakeyi kiyi masa uzuri, kina ganin Alhaji ma yaushe rabon daya zauna muyi fira dashi, da alama wata shari'a zasuyi mai zafi, kinga duka shekaran jiya suka kammala shari'ar yaron gidan Alhaji M. Sanda, yanzu kuma gobe suna da wata shari'ar, shiyasa nima nayi ma Alhaji uzuri saboda nasan yanda aikinsu yake. Murmushi Raheena tayi tana fad'in Momy kina ganin da sun kammala shari'ar nan zai dawo gare ni? Sosai kuwa, ai ina ganin suna gama wannan shari'ar za'asa maku rana, shima Alhaji lokacin hankalinsa ya kwanta kinga sai ashirya komai, wad'an nan kayan naki idan bakison su kawai zai siyar dasu. Raheena tace a'a Momy abarsu tukunna. Momy tace shikenan tashi kije kici abinci. **** *** *Safiyar litinin a kotu.* Ur's. Nabeelert Lady🖋[3/10, 8:41 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.* 4⃣7️⃣ *High court Lagos* Cikar kotu ya bama ma'aikatan wajen mamaki, yanda kasan za'ayi wata shari'ar da bata wuce kwana biyu da faruwa ba, wanda yazo da wuri shi ya samu waje. Bayan da aka gama shiga Alkali ya shigo, bayan ya zauna kowa ya samu waje ya zauna. Kallon mutanan kotun yake yana so yaga kosu Alhaji Kamal sun zo, aikuwa caraf suka had'a ido, mamakin da yayi yau sun k'ara yawa, hakan yasa jikinsa yayi sanyi, gashi su Alhaji Marusa basu zo ba. Magatakarda ne ya tashi domin karanto shari'ar da za'a gabatar...... *Kamar yanda aka karanta wannan shari'ar a wancan lokacin kafin a shigo da wadda ta gabaceta, hakan yasa aka d'age wannan shari'ar zuwa yau litinin. A yau litinin 18/12/2019 wannan kotu mai albarka zata saurari k'ararraki guda biyu, ta farko itace wadda zuri'ar Alhaji Sambo Jarmai suka shigar akan mutuwar d'ansu mai suna Naseer Sambo Jarmai, wanda aka tsinci gawarsa a shekaru goma sha biyu da suka wuce a ranar wata juma'a da misalin k'arfe 9:00 na dare a bayan gari, hakan yasa Iyayensa suka shigar da k'ara domin suna buk'atar kotu ta bi masu hakkinsu.* *Shari'a ta biyu itace wadda Iyalan Malan Sani suka shigar, shari'ace tsohuwa wadda akayita a wannan kotun a shekarar 10/5/2008, inda aka yanke ma Malan Sani hukuncin d'aurin rai da rai a gidan yari, shari'a ce data shafi tsohon ma'aikacin Kwastam Alhaji Hamza Maiwada, wanda ake zargin Malan Sani da kasheshi da kuma yunkurin haikema matarsa a matsayinsa na direbansa, Iyalan Malan Sani sun sake dawo da wannan shari'ar baya saboda suna so asake shari'ar dan basu gamsu da hukuncin da kotu ta yanke a shekarun baya ba.* Mik'ama Alkali takardun yayi kafin ya koma ya zauna. gaba d'aya kotun ta d'auki hayaniya dan basu san da wata shari'ar ba bayan ta Naseer. Alkali kuwa tamkar wanda aka sama shokin, gaba d'aya jikinsa rawa yakeyi yayin da zufa ta fara keto masa, duk yanda yaso ya daure sai da zufar ta sauko masa afuska tamkar wanda aka zuba ma ruwa, kyalle yasa ya goge fuskarshi kafin ya shanye ruwa kofi d'aya. Bubbuga tebur Alkali yayi hakan yasa akayi shiru. Jarumtarsa ya tattaro kafin yace lauyen da zai gabatar da shari'a bismilla. Tashi Ra'eez yayi yana gyara zaman farin glass d'insa, sosai yau yayi kyau sai kace zeyi gasar lauyoyi, gaba d'aya mutanan suka bishi da kallo yanda haibarsa ta fito. Risnawa yayi yana fad'in ya mai shari'a kamar yanda muka fara karanto k'arar Naseer Sambo Jarmai a wancan satin yanzu ma zamu cigaba, duk da yanzu shari'ar ta zama biyu kuma duk nine zan gabatar dasu, amma ayanzu zamu fara gabatar data Naseer. Kamar yanda na fad'a an samu gawar Naseer a bayan gari, kuma na gabatar ma kotu da bayanin mutuwarsa da 'yan sanda suka rubuta, inda bincike ya nuna cewar ankashe Naseer ta hanyar shakeshi da akayi har ya mutu, kuma wannan kisa da akayi kisa ne da aka shiryashi domin a toshe wata kafa wacce ake zargin Naseer da kok'arin tona wani b'oyayyen sirri, hakan yasa aka kashe shi wajen b'oye wannan sirri. A cikin sirrin da Naseer ya d'auka akwai wanda aka nuna anan ranar alhamis data wuce inda ya d'auki hoton Fawwaz alokacin da ya yanki Farouk da wuk'a, acikin abokan Fawwaz wani yaga lokacin da Naseer yake d'aukarsu, hakan yasa suka sanar da Mahaifin Fawwaz. Ina so kotu ta bani dama domin na kira Adnan d'aya daga manyana abokan Fawwaz domin yayi mana bayanin yanda komai ya faru...... Ajiyar zuciya mai k'arfi Alkali ya sauke kafin yace kotu ta baka dama. Adnan ne ya fito yana takawa da kyar dan har yanzu jikinsa beyi kwari ba. Ra'eez... Kotu zata so taji sunan ka da kuma alak'ar ka da Fawwaz. Sunana Adnan kuma Fawwaz abokina ne, domin alokacin da mukayi secondary kowa yasan abotar mu saboda mu ukku ne muke tare, duk inda kaga Fawwaz to dole kagan mu nida marigayi Sufwan, abotar mu ta kai har Iyayen mu sun san mu atare. Ra'eez... Kotu tana buk'atar kayi mata cikekken bayani akan abinda ka sani na kisan Farouk da kuma abinda ya shigo da Naseer cikin maganar. Adnan.... E to, kamar yanda kowa ya gani a vedion da aka nuna Fawwaz ya kashe Farouk wanda ba kowa bane ya d'auki wannan vedio sai Naseer, kuma Naseer d'an ajin mu ne muna gaisawa dashi, alokacin da Fawwaz ya kashe Farouk bayan munzo muka iske ta'asar da yayi sai hankalin mu ya tashi, kasancewar mu abokai yasa mukayi kokarin rufama Fawwaz asiri, nine na d'auki wauk'ar na jefata a wani rami da ake tara bola, bayan da muka juyo zamu tafi sai na hangi Naseer yana d'aukar mu, sai dai muna jiyowa shi kuma ya bar wajen da gudu. Bayan da mukaje muka sanar ma Dadyn Fawwaz sai yace kada mu damu, abinda yake so shine kada mu fad'ama kowa yasan yanda zaiji da komai. Washe gari dana tambayi Fawwaz ya naji ance a bayan gari aka samu gawar Farouk, shine yake fad'a mani Mahaifinsa ya had'a baki da shugaban makarantar aka fitar da ita. A ranar da za'a kashe Naseer munzo gidan su Fawwaz sai muka iske Dadynsa da bak'i a waje, bayan mun gaisa sai ya bukaci da mu fad'a masu kwatancen gidansu Naseer kuma mu tura masu hotonshi, haka muka bashi muka tura masu hotonshi. Washe gari sai mutuwar Naseer naji, tabbas na girgiza da mutuwarshi, kuma har gobe ina ganin laifina, domin nine na fad'a cewar ya d'auki vedio, da ban fad'a ba babu yanda za'ayi asan shine, tun daga lokacin na fara janye masu Fawwaz har Allah yasa muka gama kowa ya kama gabansa, ina mai bama Iyayen Naseer hakuri abisa sakarcin da nayi. Jinjina kai Ra'eez yayi yana fad'in mungode Adnan zaka iya tafiya. Ya mai shari'a wannan shine Adnan abokin Fawwaz, kuma kowa yaji wanda yasa aka kashe Naseer saboda kawai a b'oye gaskiya ina.... Saurin tashi Brr. Bajinta yayi yana fad'in ya mai shari'a ai wannan shedar baki ce kawai Adnan ya bayar, kuma shi kad'ai ne ya bada sheda wanda kowa yasan cewar mutum d'aya baya sheda, domin za'a iya biyanshi yazo ya b'ata Alhaji M. Sanda. Miyau Alkali ya had'iye dan ya riga daya sadakas, yasan Brr. Bajinta yana kokarin kare Alhaji M. Sanda ne kawai saboda ba komai ya sani ba. Ruwa yasha kafin yace Brr. Ra'eez kotu tana buk'atar cikakkar sheda domin bazata amshi wannan hujjar da aka bayar ba. Risnawa Ra'eez yayi yana fad'in ya mai shari'a zan so kotu ta bani dama domin na nuna mata hujjata ta k'arshe wadda zata tabbatar da abinda Adnan ya fad'a gaskiya ne... Kotu ta baka dama. Tashi Jabeer yayi ya had'a kayan da za'a kunna. Tunda Jabeer ya tashi Alkali yaji cikinsa ya kad'a, zufa kawai take keto masa ta ko ina, gaba d'aya kyallen dayake goge zufar ya jike. Mutane kuwa mamakin yanda hankalin Alkali ya tashi suke dan zuwa yanzu ya kasa b'oye tashin hankalinsa, zaman kanshi a d'osane yake. Shiru kotun tayi yayin da fuskokin Alhaji Marusa dana Mr. Kallah suka bayyana, sai gefen fuskar Alhaji Barau saboda shi a gefe yake hakan yasa ba'a d'aukoshi duka ba, idan ba wanda yasanshi ba bazai iya shedashi ba, sai kuma bayan Alhaji M. Sanda danshi ya bama mai d'aukar baya. Muryoyinsu ne suka fara cika kotun, muryar Alhaji Barau itace ta tonashi, domin yana magana wasu suka fahimci shine, sai kuma lokacin da aka fara ambatar sunanshi, haka suka cigaba da sauraron shirin da suke akan kashe Alhaji Maiwada da kuma yanda zasu sa akashe Naseer. Babban abinda ya k'ara tabbatar da Alhaji Barau ne awajen alokacin da Alhaji M. Sanda yake fad'in *Brr. Barau idan har kayi mani wannan taimakon ina mai tabbatar maka kaine Alkalin gobe*. Zuwa lokacin mutanan kotun kasa jurewa sukayi dole wajen ya d'auki hayaniya, dama kuma d'aukar tazo k'arshe. Hannu Jabeer yasa ya kashe. Jiyowar da Ra'eez zeyi sai dai yaga wayam a kujerar Alkali domin ya sulale ta kofar da take kusa dashi🤣. Ra'eez besan lokacin da dariya ta kwace masa ba, hannu yasa ya toshe bakinsa yana girgiza kai, ai da mutane suka fahimci abinda yake faruwa sai kotu ta hargitse da dariya tare da surutu. Duk yanda aka so mutane suyi shiru abun ya faskara, dole sai Magatakarda ne ya hau sama ya buga tebur hakan yasa kowa yayi shiru ya juyo sun d'auka Alkali ne ya dawo. 'Daya daga cikin manyan ma'aikatan kotun ne ya mike yana fad'in an d'age wannan shari'a zuwa lokacin da za'a sanar. Haka kowa ya fito daga kotun yana fad'ar yanda akayi, 'Yan jarida kuwa sun cika wajen kowa yana son yaji yanda za'ayi, kamar ance su kalli gefe sai ganin 'Yan sanda sukayi sun saka Alhaji Barau a tsakiya suna shirin barin kotun dashi, ai da gudu 'Yan Jarida sukayi wajen, sai dai kafin su kai sai kurar motar suka iske. Abinda ya faru shine, tun alokacin da hankulan mutane suka raja'a wajen kallon abinda aka kunna hankalin Alkali ya tashi musamman da yaga an hasko hotonsu, tabbas ya tuna da wannan vedion, domin irinshi ne suka kalla a wayar Naseer kuma anan suka konata, ganin beda wata mafita gashi su Mr. Kallah basa wajen hakan yasa ya fakaici idanuwan mutane ya sulale. Sai dai yana fita su Inspector Hamza suka tareshi, domin sun shiryama hakan, gaba d'aya jikinsa ya d'auki rawa a lokacin da suka kamashi, rokonsu ya farayi akan su barshi ya tafi baya son yaji wannan kunyar, har zasu wuce dashi Hamza yace su jira mutane su fito dan yafison kowa yasan an kamashi. Hakan yasa suka tsaya har sai da aka fara fitowa sannan suka taho dashi. Tsaye su Alhaji Kamal suke tare da sauran mutanan da yazo dasu. 'Daya daga cikinsu yace lallai Alhaji Kamal maganar ka gaskiya ce shiyasa kace muzo, wallahi na d'auka ba wata babbar shari'a bace, amma meyasa baka fad'a mana komai ba kafin muzo dan nasan kasan da wannan vedion? Murmushi Alhaji Kamal yayi yana fad'in nafiso ku gani da idon ku. Mutumin yace fad'i gaskiya dai Babban Alkali, kawai kace kasan halin zuciya, kada ka nuna mana asamu wani ya sanar dasu Alhaji Barau kafin muzo. Alhaji Kamal yace kunga laifi na? Gaba d'aya sukace a'a, ai ana son sirri, kuma hakan da kayi yayi dai-dai, dan haka sai asanar da manyan mu saboda wannan babban abu ne dole sai anyi zama. Alhaji Kamal yace tun kafin muzo na sanar da Chief Judge, duk da bansanar dashi komai ba amma na fad'a masa ana zargin babban Alkalin kotun nan tare da wasu manya da aikata babban laifi, kuma na sanar dashi za'a gabatar da shari'ar a yau wanda acikinta ne za'a gano komai, kunsa dai mutum baya yanke ma kanshi hukunci, hakan yasa shima Alkalin ya gudu tun kafin a sauke shi, dan haka nasan zuwa yanzu sun kusa isowa dole muyi zama zuwa anjima dan bana so shari'ar nan ta wuce gobe. *** Wallahi Ra'eez kai mugune, ashe dama ka iya dariyar mugunta, yanzu agaban mutane kasa dariya sai ka tona kan ka. Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in ayanzu bana tsoron kowa yasan waye ni, domin komai yazo k'arshe, kuma tsakani da Allah bazan iya rike dariyata ba alokacin shiyasa nayi abuna domin Alhaji Barau yayi abun kunya Alkali da guduwa. Dariya sukasa gaba d'ayansu. Jabeer yace Allah yaso Raheena da Momynta basa nan da Allah kad'ai yasan halin da zasu tsinci kansu. Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in wallahi Jabeer kana son Raheena kawai dai kana b'oyewa ne saboda ni, kuma kasan dai ni ba aurenta zanyi ba. Tsaki Jabeer yayi yana fad'in wai kai zuciyata kashiga da zaka rik'a fad'ar haka, nifa ba sonta nake ba kawai tausayinta nakeyi. Murmushi Rafeek yayi yana fad'in kai ma Ra'eez da sa ido kake, tun yaushe Jabeer yake fad'a maka ba sonta yake ba kawai tausayinta yakeyi abarshi ahaka. Jinjina kai Ra'eez yayi yana dariya yace an barshi ahaka Yaya, Allah ya kawo masa mai sonshi. Tsaki Jabeer yayi yana fad'in d'ansa ido kawai. Ra'eez zeyi magana wata matashiyar yarinya tayi masu sallama. Amsawa sukayi suna kallonta yayin da Jabeer ya juya baya yana waya. Gaishe su tayi tana fad'in dan Allah Yaya Sameer nake nema munyi waya yace yana kotu kuma nashigo wayarsa bata shiga. Ra'eez yace wane Sameer fa? Tace Yayan Adnan wanda yazo bada sheda. Ra'eez yace oho, K'anwarsu ce ke? Kai ta d'aga tana murmushi. Ra'eez yace kuma bamu sanki ba ya sunan ki? *Husnah!* ta bashi amsa. Ra'eez yace amma dai ba'a nan kike zaune ba ko? Murmushi tayi tace sati na d'aya dana dawo na kammala karatuna a A.b.u zariya. Ra'eez yace masha Allah, na tayaki murna, bara na kira maki shi yanzu na ganshi kila koya zagaya. Kafin ya bar wajen saiga Sameer ya fito daga baya da alama band'aki yaje. Murmushi ya saki yana fad'in Husna ashe kin iso? Kai ta d'aga tana fad'in na kira ka bata shiga ba. Sameer yace kila network ne. Juyowa Jabeer yayi yana maida wayar aljihu yace mu tafi idan ka gama surutun naka. Dariya Ra'eez yayi yana fad'in ai fa yau nashiga ukku, sai fushi kake kamar kaine Alhaji Barau. Dariya sukasa gaba d'ayansu banda Husnah data shagala wajen kallon Jabeer😉. Rafeek yace wallahi Jabeer sai kayi da gaske dan Ra'eez yaga wajen baccin ka. Harara ya buga ma Ra'eez yana fad'in ka barni dashi Yaya nasan tsiyar da zan masa. Kamoshi Ra'eez yayi yana fad'in haba d'an uwana na kaina, yi hakuri muje, kasan akwai sauran abubuwa agaban mu. Sameer yace bara na aje Husna gida zanzo. Rafeek yace shikenan nima ofis zan wuce dan dole ayau mu saki wannan labarin, gidan Tv ma nasan zasu haska dan nasan dole akwai wad'an da suka d'auka kasan mutane ba'a iya masu ko yaya ne sai an samu cikin 'Yan jarida sun d'auka. Sameer yace shikenan Husna muje. Jin shiru yasa suka juyo suna kallonta, ita ko hankalinta yana wajen Jabeer da yayi gaba zuwa wajen motarsu. Hannu Sameer yasa ya mintsinota da sauri ta juyo tana sosa kai. Ra'eez yace K'anwarmu ki gaida gida ko. Murmushi tayi tana jinjina kai. Gaba Ra'eez yayi yana fad'in Yaya sai munyi waya. Murmushi Rafeek yayi yana fad'in tunda kana sauri kayi d'aukar magana ba. Zama cikin motar yayi yana fad'in wai saurin me kake ko sallama dasu Husna bakayi ba bayan kuma kayi kasuwa. Harara ya wurga mashi yana fad'in wallahi Ra'eez kashiga hankalin ka dani, wacece kuma wata Husnah? Kafad'a Ra'eez ya d'age yana fad'in oho, lokacin da ka gama wayar wayace baka tsaida hankalin ka har ka ganta ba. Murmushi Jabeer yayi yana girgiza kai yace naga alama yau ahaka zaka k'are wajen tsokana, ina su Ummu ko sun wuce? Ra'eez yace suna fitowa Abbah ya tafi dasu kasan kotun ta cika. Jabeer yace ina muka nufa? Ra'eez yace muyi gida dan nasan anjima Kawu Kamal zai nememu dan yace akwai zaman da zasuyi gara muje mu huta. **** **** Zaune suke a gidan Alhaji Marusa su ukku suna jiran tsammani, dan tunda sukasan an shiga kotu suka had'u a gidan Alhaji Marusa dan Alhaji M. Sanda ya fad'ama Alhaji Barau da zarar yaga za'a gabatar da shedar data tabbatar suna dasa hannu a kisan Naseer da Alhaji Maiwada yayi kokarin fitowa yazo su gudu tun kafin a kamasu. Sai dai basu san jiran gawar shanu suke ba. Gyara zama Mr. Kallah yayi yana fad'in nifa hankalina ya kasa kwanciya, tun d'azu nake kiran Brr. Bajinta naji ko an gano wani abu amma wayarsa ma akashe take, da farko tana shiga be d'auka ba, nasan lokacin ko yana cikin kotun, amma yanzu a kashe ma take. (Abinda basu sani ba Brr. Bajinta ma yayi takanshi, dan tunda ya tabbatar da mugayen halinsu ya tsorata, danshi duk tarayyarsu dashi iyaka su sashi yayi shari'ar karya su biyashi amma betab'a sanin su d'in makisa bane, hakan yasa asiri yana tonuwa ya kashe wayarsa dan yace bazai fada masu ba kada su gudu, shiyasa ma ya sanar ma Hamza inda suke.) Alhaji Marusa yace nima hankalina ya fara tashi, gashi na kira wayar Lucky itama akashe, da alama shima yayi takanshi, ina ganin fa lokaci yayi da kowa zai nemi hanyar tsira, kawai ku tashi mubar garin nan kafin komai ya kwab'e. Mr. Kallah yace Alhaji Barau fa? Alhaji Marusa yace kai kasanshi, amma wallahi bazan sake mintuna goma awajen nan ba, idan kai zaka tsayashi to ni nayi nan. Tashi Alhaj M. Sanda yayi yana fad'in jirani Alhaji Marusa. Dole Mr. Kallah ya mik'e jiki a sanyaye yabi bayansu. Suna fitowa suka iske 'yan sanda suna jiransu, ai gaba d'aya sai hankalinsu ya tashi, nan fa suka fara kokarin tserewa, da sauri aka cafkesu akasa mota yayin da 'Yan jaridan da Hamza ya taho dasu suke ta d'aukarsu. Yayi haka ne domin a watsasu ayau saboda kowa yasan halin da ake ciki, haka suka tafi dasu sai zare ido suke a mota. Ganin haka gaba d'aya ma'aikatan gidan Alhaji Marusa suka fito domin suyi takansu, sai dai kowa sai da ya kwashi rabonshi kafin yayi gaba. Ur's. Nabeelert Lady🖋 [3/10, 8:41 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.* 4⃣8️⃣ Gaba d'aya gari ya hargitse da labarin abinda ya faru, yayin da 'yan jarida suke ta kok'arin had'a kan labarin da zasu gabatar. Da misalin k'arfe hud'u su Alhaji Kamal suka shiga taron gaggawa. Manya sun fusata akan wannan abun kunyar da aka jawo ma kungiyar su, dan wannan abun ba k'aramun tab'a Kadar su zeyi ba domin sun san dole sai duniya taji wannan abu. Haka suka gama tattaunawa yayin da suka tsaida wanda zaiyi shari'ar a gobe. Haka Alhaji Kamal ya sake kunna masu vedion kowa ya gani, tabbas sunji kunyar wannan abu, babu abinda yafi ciwo irin na Malan Sani, shekaru da yawa an kulleshi ba akan hakkinsa ba. Da haka taron ya tashi. *** **** Rafeek agaskiya yanzu kam naji dad'in wannan shari'ar daka tado, koba komai silar shari'ar Naseer ta jawo za'a tona asirin mutane da yawa, kamar yanda mutane suka aminta da wannan kotu suna fad'in irin adalcinta ashe dama a cikin duhu muke, Allah ya k'ara tona asirin munafukai. Rafeek yace amin Baffa, ai yau jinake kamar nayi kuka saboda farin ciki, hakika Allah yana son bayinsa, kuma shi maji rokone, insha Allahu zuwa gobe kowa zaisan matsayinsa. Ummansu tace nikam ko ba'ayi komai ba zuciyata ta wanke, koba komai duniya tasan waye ya kashe mani Naseer, kuma sun kunyata sai fatan Allah ya kara tona asirinsu. Rafeek yace amin Umma, bara na wuce dama ina wajen aiki naga kiran ku. Baffa yace Allah ya tsare ka. Yace amin. **** **** Ya Allah wannan wace irin bak'ar rana ce haka, yanzu Alhaji ne 'yan sanda suka kama har wajen aikinsa saboda tozarci, ina zansa kaina yau, da wane ido zan kalli K'awayena da sauran mutane? Zubewa Raheena tayi jikinta tana kuka. Dafata Momy tayi tana fad'in wallahi dole kiyi kuka Raheena, mu kam Alhaji ya gama cutar mu, taya zamu iya rayuwa cikin wannan tashin hankalin, ashe dama halin da yake aikatawa kenan ab'oye bamu sani ba? Duk tarin dukiyar nan daya tara mana ta hanyar haram ya tara ta? Kalli wannan uban gida da muke ciki, haba ashe shiyasa Alhaji Marusa ya sayar masa da gidan ashe duk jirgi d'aya ne ya d'ebosu, yanzu gashinan sun kaishi sun baro, meyafi wannan kunya ace kana zaune saman kujera kana shirin yankema wani hukunci sai kuma a nunoka kana cikin masu laifin. Tashi Raheena tayi tana fad'in wallahi Momy nayi dana sanin shiga yanar gizo ayau, domin ina hawa nayi bakin gani, a group d'in da nake kawai naga an turo hoton Dady a kotu hada vedion shi lokacin daya sulale a kotun, dan bala'i hatta da shedar da aka kunna akotu wallahi an samu wad'an da suka d'auketa, ina hawa face book ma abinda nagani kenan, duk wata kafa ta yanar gizo idan kika shiga maganar su Dady akeyi. Goge ido Momy tayi tana fad'in bamu da bakin magana kam, abinda nakeso da ke kawai ki kashe wayarki, idan da hali ma kawai ki kulle account d'inki sannan ki karya layin ki hakan zai fi maki kwanciyar hankali, idan yaso lambobin da kike so ki barsu akan wayar dan nima haka zanyi wallahi Raheena bazan iya wannan abun kunyar ba, dole mubar garin nan, gara na koma asalina dama nayi gini na a kano ina shirin zuba 'yan haya wallahi na fasa garin zamu bari. Raheena tace ya zamuyi da wannan gidan kuma? Waro ido Momy tayi tana fad'in ke yanzu har maganar wata kadara ta Alhaji kikeyi, to ina tabbatar maki sai kotu ta kwace komai nashi dan sai ya biya diyar mutanan da ya kashe, kayan d'akin ki ma zansa azo goben nan a tafi dasu kano, kije ki fara had'a kaya ki da duk wasu abubuwa masu muhimmanci dan wallahi idan masu bincike sukazo bazasu bari mu d'auki komai ba. Kuka Raheena tasa tana fad'in shikenan yanzu kam nasan Ra'eez yafi k'arfina, dan ko rana aka samana sai ya fasa dan yanzu Dady yayi mana bakin fenti. Momy tace ki kwantar da hankalin ki sai kiga kuma yaji tausayinki tunda yasan ba laifinki bane, dole muje kotu domin ayi komai agaban mu, tashi ki kunna mana Tv nasan yanzu zasu nuna komai. Aikuwa Raheena tana kunnawa sai ga masu labarin k'arfe takwas na dare. Kowace tasha ka kunna ko gidan radio duk maganar d'aya ce, nuno su Alhaji Marusa ne ya k'ara d'aga masu hankali, shikenan yanzu an had'a kan masu laifi dole a yanke hukunci. Daga k'arshen labaran aka tabbatar da gobe talata k'arfe goma na safe za'a zartar da hukunci a babbar kotu. Kashewa Momy tayi tana sakin kuka. Masu aikin gidan ne suka shigo jiki asanyaye suna masu jaje. Tashi Momy tayi tana fad'in bazan bari a cuce ku ba, domin nasan gidan nan ya kusa haramta agaremu, dan haka zan sallame ku zuwa gobe kowa ya tafi ina rokon ku daku yafe mana, bara naje d'akin Alhaji dole nayi maku sallama mai tsoka. Farin ciki suka kamayi jin abinda Momy tace. Fitowa tayi da wata k'atuwar jaka wadda kud'i ne kawai aciki, haka tasa suka d'auko bakar leda ta bama kowa kud'i masu yawa, kayan Alhaji ta d'auko duk ta raba ma mazan masu aikin, sannan ta d'ebo wasu daga cikin nata dana Raheena ta bama matan, haka sukayi ta godiya kowa ya nufi wajen kwanansa kafin gobe. Ciki suka shiga suka fara had'a kaya yayin da tayima wani d'an uwanta waya da yake Lagos akan ya taho da motar d'aukar kaya tunda asubar fari zai kai mata kano kafin a kammala shari'ar sai su tafi. **** *** Hawaye ne kawai yake zubo ma Ammi bayan data gama kallon labarai, mai aikinta da take gefenta sai hakuri take bata. Ammi tace dole nayi kuka Inno, Alhaji ya gama zalunta ta, ya b'ata mani tarbiyar yarona, ya lalata mani mahaifa, gashi daga k'arshe ya sani jin kunyar duniya, na farko an yanke ma Fawwaz hukuncin kisa, na biyu an kama Alhaji shima nasan hukuncin kisa ne domin rayuka ya kashe, shikenan na tashi a babu, wannan gidan dole na barshi koda bazai shiga cikin diyar da zai biya ba wallahi bazan zauna aciki ba domin komai na ciki haram ne, sisinsa bazan d'auka ba, haka zan tafi garin mu gara idan naje Iyayena su siya mani sutura da kud'insu amma babu abinda zan iya cigaba da amfani dashi domin duk haramun ne. Inno tace kiyi hakuri Hajiya ai bakisan haramun bane sai yanzu kinga duk abinda kike dashi ya halatta agareki sai idan ya sake baki wani abun ne. Murmushin takaici Ammi tayi tana fad'in Inno bakinsa girman haram ba, matuk'ar ka kasance kana cin haram kuma kasan haram ne wallahi Allah bazai barka ba agobe kiyama, tabbas ada bansan bakin halin Alhaji ba, nasan dai ma'aikaci ne kuma albashinsa muke ci, amma zuwa yanzu na fahimci ya cakud'a kud'insa da haram domin harkar shigo da haramtattun kaya sukeyi, ban tab'a sanin haka ba sai jiya da nayi bincike a d'akinsa naga wasu takardu, kinga kuwa idan har nacigaba da amfani da kayanshi nima nashiga layin halaka, dan haka ki barni, idan kina son kayana gasu can kije ki had'a dan sallamarki zanyi, sauran kud'ina na banki ma asusun marayu zan kaisu, idan baki son kayan zan mik'asu gidan marayu sadaka. Inno tace tunda sadaka kika bani ai ba haram bane zan d'ebi wasu sai akai sauran gidan marayu bazan had'e duka ba, gaskiya wannan abu beyi dad'i ba, amma ai zakije kotun gobe ko? Ammi tace badan inaso na mik'a mukullin gidan nan a gareshi ba kuma ya furta mani saki da babu abinda zai sa rana ta fito ta sameni a Lagos, amma dole naje nayi sallama da Fawwaz kuma na amshi sakina. Inno tace gaskiya zanji babu dad'i, amma Allah yasa haka yafi alkhairi, yama sunan garin ku? Ammi tace Sokoto. Inno tace ikon Allah ashe fa kin tab'a fad'amin wallahi na manta, ai gaskiya garin ku akwai nisa, amma idan da rai wata rana zaki ganni. Ammi tace Allah yasa, kira mani masu gadi su duka. *** **** Umar yanzu ya zamuyi, ni wallahi na manta da wannan maganar, tunda na haye saman kujerar Oga shikenan na manta dashi da abubuwan da mukayi, sai cikin satin nan Alhaji Barau yake fad'a mani an fara bincike akan shari'ar da akayi shekarun baya. Miyau Umar ya had'iye yana fad'in Adebayo wannan shi ake kira ga k'oshi ga kwanan yunwa, muna farin ciki shekaru sun ja an manta da komai ashe abu be wuce ba, kana kallon dai yanda aka kama Alkali a kotu, su Alhaji kuwa har gida aka bisu, taya kake tunanin abun bazai zo kan mu ba, koda ba'a kamma mu yanzu ba idan akaje shari'a gobe dole bincike yazo kan mu. Adebayo yace wallahi tsoro nakeji, da nasan da wannan abun bazan zo aiki yau ba, gashi aiki ya rik'emu mun kai har dare kada mu fita akama mu, da ace ina da mai a motata daga nan hanyar garin mu zan nemo gara na kwana a ahanya tunda ATM d'ina yana mota bani da matsala, to yanzu idan na tafi an kulle gidan Mai sai na masu jarka kuma ina tsoron na siya da yawa ya bani matsala. Umar yace kasan abinda za'ayi? Tunda sai gobe k'arfe goma za'a shiga kotu kuma sai an fara shari'a sannan bincike yazo kanmu kawai yau mu kwana cikin shiri, gobe tunda asuba kowa ya kama gabanshi, lokacin da za'a neme mu nasan munyi nisa, dan haka kawai mu tafi. Adebayo yace haka za'ayi Umar kulle ofis d'in mu tafi. Cak suka tsaya ganin 'yan sanda a gabansu. Tsoro ne ya kamasu gaba d'aya, babu b'ata lokaci suka kamasu suka tafi, motarsu ma sai wasu 'yan sandan ne suka tukasu. *** *** Kafin gari ya waye sai da su Hamza suka had'a kan duk wasu masu laifi, sai dai kowa da wajenshi babu wanda yasan an kamo wani sai wad'an da aka nuna a tv, hatta dasu Kwamishna da Dr Aliyu Sani duk an kamasu, sai dai shi kwamishna basu kawoshi ofishinsu ba wani waje suka ajeshi saboda girmamawa. **** **** *Tuesday 19/12/2019* *High court Lagos* Fad'in cikar da kotun tayi ba abu bane me yuwuwa, domin duk wanda yasan labarin wannan shari'a yasan dole tayi mutane, ko yawan masu d'aukar rahoto ya isa ya cika rabin kotun. Gaba d'aya ma'aikatan kotun k'arfe bakwai suka halarci kotu saboda dole akwai tsare-tsare, manyan jami'an tsaro ne a harabar kotun su duka suna d'auke da manyan makamai, duk wanda zai shiga kotun dole sai an bincikeshi da abun duba mutane, hanyar maza daban ta mata da ban, sosai abun ya k'ayatar domin sun shirya ma shari'ar saboda sun san ana iya samun wani tashin hankali musamman da shari'ar ta kasance ta manyan mutane. Lokacin da kotun ta cika dole sai hakuri sauran mutanan sukayi domin jami'an tsaro sun tare hanyar shiga sai dai masu son jin kwakwaf suka tsaya a harabar kotun. Masu laifi dama da wuri aka kawosu kotun kowa da inda aka ajeshi, kana shiga cikin kotun zaka iske Alkalai ukku zaune asama sai b'angare guda na manyan mutane, yayin da d'ayan b'angaren lauyoyi suke zaune, sai wajen da su Magatakarda suke a zaune, daga wajen zaman mutane kuma duk akwai jami'ai ko wace hanya suna tsaro. Tsit kake jin kotun dan kowa yasan yau babu wasa, iya mutanan da suke zaune agaba kad'ai ya isa yasa mutum ya natsu, ga kuma jami'ai suna zagaye da bindigu. Bayan da kowa ya natsu aka umarci da ashigo dasu Alhaji Barau. Idanuwa kawai mutane suka zuba dan gangar jikinsu ta kasa motsi bare ta jawo hayaniya gudun kada suma suyi laifi. Gaba d'ayansu kawunansu a k'asa suka shigo kotun, Alhaji Barau da aka kamashi yana sanye da kayan aiki zuwa yanzu babu su ajikinshi dan an bashi wata jallabiya yasaka. Haka suka jeru a gefe suna sunnar da kai. Tashi Magatakarda yayi domin ya karanto shari'ar.... *A yau talata 19/12/2019 wannan kotu mai albarka zata cigaba da sauraron shari'ar da aka fara jiya litinin 18/12/2019, an tsaya a inda Brr. Ra'eez ya gabatar da shedar data tabbatar da wad'an da suka had'a baki wajen kashe Naseer Sambo Jarmai.* *Sai shari'a ta biyu itace ta Iyalan Malan Sani, inda suke rokon wannan kotu data sake shari'ar da aka gabatar shekaru sha biyu da suka wuce akan mutuwar tsohon shugaban kwastam Alhaji Hamza Maiwada a wannan kotun domin an samu wasu manyan shedu da zasu tabbatar ma kotu ba Malan Sani bane ya aikata laifin da aka yanke masa hukunci akai.* Risnawa yayi ya mik'ama d'aya daga cikin Alkalan da suke zaune. Bayan da ya gama dubawa ya mik'ama sauran. Na tsakiyar daya kasance shugaba shine ya bama Ra'eez izinin ya cigaba da gabatar da shari'a a inda ya tsaya jiya. Tashi Ra'eez yayi yana risnawa, ganin bakin fuska yasa ya fara da gabatar da kanshi. Gyara riga yayi yana fad'in ya Mai shari'a ni sunana *BARRISTER RA'EEZ HAMZA MAIWADA, 'DAH GA MARIGAYI SHUGABAN KWASTAM NA LAGOS WATO ALHAJI HAMZA MAIWADA.* Nine wanda yake kare wad'an da suke k'arar shari'a ta farko data biyu. Gaba d'ayansu suka d'ago cikin firgici suna kallon Ra'eez, Alhaji Barau yafi kowa girgiza da abinda kunnuwanshi sukaji, tabbas sai yanzu ya gama gano dawa Ra'eez yake kama. Runtse ido yayi yana jin wani irin tashin hankali. Mutane kuwa duk yanda suka natsu jin abinda Ra'eez ya fad'a dole tasa aka fara kus-kus, domin abun ya basu mamaki. Raheena da Momy kuwa suman zaune sukayi. Runtse ido Raheena tayi hawaye suna zubo mata, ayanzu kam tasan Ra'eez ya girmema tunanin ta, dama fansa yazo d'auka kenan. Saman cinyar Momy ta kwanta tana kuka. Bubbuga teburin da akayi ne yasa kowa ya shiga hankalinsa. Gyara tsayuwa Ra'eez yayi yana fad'in, kamar yanda aka gabatar da shedar vedion da aka shirya yanda za'a kashe Naseer a jiya nasan wannan shedar ta tabbatar da wad'an da suka shirya kashe Naseer domin fuskokinsu sun fito yayin da akaji muryoyinsu suna ambatar sunan juna. Ina so kotu ta bani dama domin na yima mutanan da suke gabanta tambayoyi.... Kotu ta baka dama. Matsowa yayi kusa da masu laifin yana sakin murmushi. Alhaji M. Sanda zan fara ta kan ka, duk da fuskar ka bata bayyana a cikin vedion ba amma muryarka ta sheda kai ne, sannan mutane biyu sun tabbatar da cewar kai ne ka bada umarnin aka kashe Naseer, domin duk sauran goya maka baya kawai sukayi, kotu zataso taji daga bakin ka yanda komai ya kasance. Alhaji M. Sanda... Kanshi a k'asa yace maganar gaskiya duk abinda akaji a ciki haka yake, sai dai kuma mun fad'a ne kawai amma ba mune muka aikata ba, domin mun aje akan zamusa ayi sai kuma aka samu wani ya rigamu aikatawa, dan haka ni bansa a kashe kowa ba. Jinjina kai Ra'eez yayi yana fad'in Alhaji Barau me zaka iya cewa agame da wannan vedion? Alhaji Barau... Haka maganar take, kamar yanda Alhaji M. Sanda ya fad'a tabbas mun shirya yanda za'a kashe Naseer saboda a b'oye abinda Fawwaz ya aikata sai kuma wani ya riga mu. Murmushi Ra'eez yayi kafin ya matsa gaba ya tambayi Alhaji Marusa da Mr. Kallah, sai dai duk amsar d'ayace. Murmushi yayi dama yasan za'ayi haka shi kuma yafiso su k'aryata kafin ya tabbatar masu. Juyowa yayi yana fad'in ya mai shari'a inaso kotu ta bani dama domin na kira mutumin da akayi hayarshi ya gabatar da wannan kisa.... Kotu ta baka dama. Kallon k'ofa kawai suke yayin da zufa ta fara keto masu, ji suke kamar su nutse, duk da basu san wanda zai shigo ba amma sun tsorata da murmushin kan fuskar Ra'eez. Ur's. Nabeelert Lady🖋 [3/10, 8:41 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.* 4⃣9⃣ Hannu Mr. Kallah ya d'ora akai ganin anshigo da Lucky, bayansa kuma Dr. Aliyu Sani ne sai Kwamishna Bello kabir wanda duk kunya ta hanashi kallon kowa. Mamaki ne ya cika mutane ganin Kwamishnan 'yan sanda a jerin masu laifi, sai wad'an da suka san Dr. Aliyu suma sunyi mamakin ganinshi. Lucky ne ya fara fitowa zuwa wajen da ake tsayawa. Matsowa Ra'eez yayi yana fad'in kotu zata so taji sunanka da kuma san'ar ka. Sunana Adekulle Isnewa, amma anfi kirana da Lucky, sana'ata itace sata sai kuma ana d'aukata nayi aiki a biyani. Ra'eez... Kamar wane irin aiki kenan? Lucky... Kamar idan wani yana son ajama wani kunne ko kuma a shekeshi to ina irin wannan aikin a biya ni. Ra'eez... Shin Lucky ko kasan wad'an nan mutanan? Lucky... Kallonsu yayi yana sakin murmushi, juyowa yayi yana fad'in sosai kuwa, domin tunda nake harka da mutane ban tab'a harkar da nake jin dad'inta ba kamar harka dasu, zan iya cewa sune Ubayen gidana domin mun dad'e atare musamman Alhaji Marusa dan shine ya nuna masu ni. Ra'eez... Ko zaka iya fad'ama kotu irin aiyukan da suka saka kayi masu. Lucky... Gaskiya sun sani aiyuka da yawa, wasu zan iya tunawa wasu kuma bazan iya tunawa ba, dansu basa jin tsoron a kashe kowa matuk'ar zasu samu biyan buk'ata, hatta da junansu ma basu bari ba, domin ko kwanakin baya Alhaji Barau da Mr. Kallah sun sani nayi masu wani aiki akan Alhaji Marusa, duk da shi na sani amma silar kashe mun aboki da yayi yasa na amshi aikinsu. Ba wani aiki bane sun sakani na kwace kayanshi da yayi odar su masu matuk'ar tsada, sannan na kashe matuk'an motar, ni kuma aikin da nayi mashi na cinna ma babban ma'ajiyarsa wuta kuma duk sun san da haka, wanda silar haka har ya kamu da ciwo. Dalilin da yasa na fara baka wannan labarin saboda kasan cewar suma zaluntar junansu sukeyi, sai kuma kashe yarana da aka kama wancan satin da nayi a ofishin 'yan sanda kuma na fad'a masu duk sun san da haka. Wani irin kallon Mamaki Alhaji Marusa yake bin Alhaji Barau da Mr. Kallah dashi, gaba d'aya takaicinsu ya rufeshi, jiyayi beda sauran wata dabara garama ya amsa laifinsa kowa ya rasa. Ra'eez... To Lucky kotu tana sauraron ka. Lucky... Acikin aikin da suka saka ni wanda bazan manta ba shine kashe tsohon shugaban Kwastam, sai kuma Naseer wanda ake magana amma shi ba nine na kashe shi ba abokina Peter ne ya kashe shi domin aranar aiki biyu mukayi, mune mukaje har gidan Alhaji Maiwada muka bugi matarsa yayin da muka shak'ama direbansa abun kauda hankali sannan muka saka hannun Matar Alhaji ta yakushi wuyanshi, bayan daya koma gidansa nine na kaima Inspector Bello wato Kwamishnan 'yansan na yanzu jakar da aka samu a gidan Malan Sani had'e da allurar da mukayi ma Alhaji, shine ya sakata a d'akin Malan Sani, sannan Dr. Aliyu shine aka had'a baki dashi wajen tabbatar da Malan Sani akan zargin da ake masa. Ra'eez... Hannu yasa a aljihu ya ciro kyalle ya goge kwallar data zubo masa, gyara glass d'inshi yayi yana fad'in bayan wannan sai wane aiki kayi masu? Lucky.... Labarin yanda suka saka kayan Alhaji Marusa a gidan Alhaji Maiwada ya basu wanda akayi shari'a har kotu tasa ya biya Alhaji Marusa makudan kud'i wanda silar haka ya siyar da gidanshi, duk abubuwan dasu Alhaji Marusa suka k'ulla sai da Lucky ya fad'a. Gaba d'aya kotun tayi shiru ana sauraronshi har ya kammala bada labarin. Jinjina kai Ra'eez yayi yana fad'in zaka iya tafiya. Inaso kotu ta bani dama domin nayima Kwamishna da Dr. Aliyu tambaya... Kotu ta baka dama. Dr. Aliyu kaji bayanin da Lucky yayi, shin ko kana da ja akan abinda ya fad'a? Duk'ar da kai Dr yayi dan beda ta cewa, a hankali ya d'ago kai yana fad'in wallahi tsautsayi ne yasa na amshi tayinsu ba halina bane. Kallon Kwamishna Ra'eez yayi yana fad'in 'Yallab'ai akwai abinda Lucky ya fad'a wanda ba haka yake ba? Sunkuyar da kai yayi yana goge zufar data zubo masa. Hannu Ra'eez ya tafa yana fad'in ya mai shari'a inaso kotu ta bani dama domin na gabatar da wasu shedu... Kotu ta baka dama. Flash d'in da suka samu a d'akin Abbu yasa Jabeer ya kunna.... Anan kowa yaga yanda su Alhaji Marusa suka shirya duk wani tuggu akan Alhaji Maiwada, da yanda ake shigo da haramtattun kaya da yanda su Adebayo da Umar suke kulla nasu sharrin har zuwa lokacin da aka cire abinda Malan Hassan yasa a gidan Alhaji Marusa. Kashewa yayi yana fad'in inaso abani dama domin nayima d'aya daga cikin mutanan da sukayi wannan aikin.... Kotu ta baka dama. Cike da mamaki suke kallon Abubukar wanda ya zama babban mutum, haka ya tako har gaban kotu. Ra'eez... Kotu zataso taji sunanka da kuma alak'ar ka da shugaban Kwastam. Sunana Abubakar Sani, kuma ina d'aya daga cikin ma'aikatan da sukayi aiki tare da Marigayi Alhaji Maiwada, hakika shi mutum ne mai son rike gaskiya da amana, be yarda da cin hanci ko zalunci ba, zuwansa garin nan mun samu cigaba, sai dai wannan gaskiyar tashi itace ta jawo ajalinsa, domin duk abinda aka gani ayanzu haka yake, wasuma ba'a d'aukesu ba, amma tabbas Alhaji Marusa shine yasa aka kashe Malan Hassan tsohon maigadinsa kuma yasa aka rufeshi ba tare da iyalinsa sun sani ba, haka yasa aka wahalar damu nida abokin aikina shima ya mutu Moses saboda muna bayan gaskiya, sannan Mr. Kallah yayi mana canjin wajen aiki kuma suka tsorata mu da kada mu sake dawowa garin nan. Tunda na bar garin nan ban sake dawowa ba, sai dai mutuwar Malan Hassan ta tsaya mani arai, domin mune silar jefashi cikin halin daya shiga, hakan yasa na kasa daurewa domin anbar Iyalinsa cikin tashin hankali saboda basu san halin da yake ciki ba, haka na dawo garin nan na fad'a masu abinda ya faru. Sanin bazasu iya komai ba yasa suka sai da d'an gidan da suke ciki suka tattara suka koma garinsu. Tun daga lokacin bansake zuwa garin nan ba, bayan wani lokaci naji aikin kwastam ya faitar mun shine na ajeshi. Ra'eez... Jinjina kai yayi yana fad'in mungode Alhaji zaka iya tafiya. Inaso kotu ta bani dama domin na gabatar da Matar Alhaji Maiwada... Kotu ta baka dama. Fitowa Ummu tayi tana share hawayen da suke fuskarta, tabbas yau mutuwar Abbu ta dawo mata sabuwa. Da kallo su Alhaji Barau suka bita kowa jikinsa yana k'ara sanyi. Ra'eez... Kotu zata so taji sunanki da kuma abinda kika sani akan sharrin da akayima Malan Sani. Sunana Bilkisu kuma nice matar Alhaji Maiwada, tabbas abinda akace Malan Sani ya aikata k'arya ne, domin aranar yashigo yana kuka, bayan na tambayesa abinda ya faru shine kafin ya fad'a mutanan suka shigo, nice nayi yunkurin bugama wani flask sai shi kuma ya kwad'a mani sanda anan na zube, amma tabbas Malan Sani be aikata abinda aka fad'a ba. Girgiza kai Ra'eez yayi, duk yanda yaso b'oye hawayenshi sai da suka zubo, gogewa yayi yana fad'in zaki iya tafiya. Cikin d'aga murya Alhaji Marusa yace ya mai shari'a duk abinda aka gabatar agaban kotu gaskiya ne, gaba d'ayan mu muna dasa hannu a duka laifukan. Shiru yayi yana harararsu Alhaji Barau, dan gara ya fad'i gaskiya kowama akamashi. Ra'eez kuwa shiru yayi har sai da zuciyarsa tayi dai-dai kafin ya kalli Alkali yana fad'in ya mai shari'a anan na kawo k'arshen duk wata sheda da zata tabbatar da wad'an da suke da hannu akan mutuwar Naseer da Alhaji Maiwada, ina rokon wannan kotu data hukunta masu laifi sannan ta bima Malan Sani hakkinsa na d'aureshi da akayi shekara da shekaru bisa zalunci wanda Alhaji Muhammad Sanda tsohon Alkalin kotun nan ne ya yanke wannan hukunci kuma akan sani ya yanke domin dashi ne aka aiwatar da komai, sannan ta hukunta Kwamishna domin ya bada gudummuwa wajen jama Malan Sani sharri akan saka masa jaka a d'akinsa da yayi, haka zalika ta hukunta Dr. Aliyu domin ya bada sakamakon k'arya wanda biyanshi akayi domin yayi hakan, sai Shugaban Kwastam na yanzu Adebayo da mataimakinsa, suma suna cikin wannan b'arna da akayi. Ina fata wannan kotu mai albarka zata bima Mahaifina hakkinsa bisa kisan zaluncin da akayi masa, kuma... Kasa k'arasawa yayi saboda kukan da yaci k'arfinsa. Tashi Jabeer yayi ya kamoshi suka zauna dan shima hawaye yakeyi. Gaba d'aya kotun tayi shiru mutane da yawa sai da suka zubarma da Ra'eez hawaye saboda tausayi. Bayan mintuna Alkalai suka gama duba shedun da aka gabatar, babban cikinsu ne yayi gyaran murya yana fad'in abisa manyan shedun da aka gabatar ma wannan kotu, kotu tayi dogon nazari wanda ta tabbatar da ingancin wad'an nan shedu, dan haka kotu zata yanke hukunci. Da farko ina mai bakin cikin faruwar wannan al'amari, domin an samu manyan mutane wad'an da mutane suka yarda dasu, suka basu amana da hannu dumumu wajen aikata miyagun laifuka. *Tsohon shugaban Kwastam na k'asa, tsohon Alkalin babbar kotu ta lagos, Alkalin babbar kotu na yanzu, Kwamishnan 'yan sanda na Lagos, babban likita, shugaban Kwastam na yansu alagos da mataimakinsa.* Wad'an nan mutane dana lissafo gaba d'ayansu manyan mutane ne wad'an da suke kula da dubban mutane a k'asan su, sai dai sunci amanar k'asa, sunci amanar aikinsu, sun had'a kai wajen dakusar da gaskiya, da kunya ace mutumin da yake kwatoma wasu hakkinsu yau shine aka kama da wad'an nan miyagun aiyukan, shigo da miyagun kaya, kisan kai, gaskiya ina mai tsananin jin kunyar wannan al'amari daya faru a k'asata, amma shari'a bazata barsu ba, domin duk matsayin ka bakafi k'arfin hukunci ba, dan haka kotu zata fara zartar da hukunci daga k'asa. *Adekulle Lucky*... Bisa shedun da suka tabbatar cewar shine yake wannan kisa, da kuma amincewarsa akan laifukansa, bisa kundin tsarin mulki na k'asa k'ark'ashin Penal code shashin kisa, wannan kotu ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya har sai ya mutu. *Dr. Aliyu Sani*... Abisa hujjar da kotu ta samu da kuma amincewarsa bisa laifin bada shedar k'arya, wannan kotu ta soke lasisin aikinsa, sannan ta yanke masa hukuncin d'aurin wata biyar agidan yari tare da tarar naira million d'aya ga Malan Sani. *Kwamishna Bello Kabir,* bisa kamashi da hannu dumudumu wajen taimakawa masu laifi, da kuma aikata laifi wajen sakama Malan Sani jaka a gidanshi, wannan kotu ta soke lasisin aikinsa, sannan ta yanke masa hukuncin d'aurin shekara biyu a gidan yari, sannan zai biya Malan Sani tarar naira million d'aya da rabi. *Shugaban Kwastam Adebayo da Mataimakinsa Umar,* bisa kamasu da akayi wajen k'arba'r cin hanci, taimakama masu aikata laifi, da zaluncin da sukayi ma Alhaji Maiwada wannan kotu ta kwace lasisin aikinsu, sannan ta yanke masu hukuncin d'aurin shekara asirin agidan yari, sannan zasu bada tarar naira million ukku ga iyalan Alhaji Maiwada. Sai hukunci na k'arshe akan mutuwar Naseer Sambo Jarmai da Alhaji Hamza Maiwada. Mutane hud'u ne suka had'u wajen bada gudummuwa akan wannan kisa, dan haka kotu zata yanke masu hukunci. *Alhaji Barau, Alhaji Muhammad Sanda, Alhaji Marusa da Mr. Kallah,* bisa kwararan shedu da aka gabatar ma wannan kotu, da kuma amincewar masu laifi akan laifinsu, kotu ta tabbatar da laifinsu, hakika sunci amanar aikin su, dan haka kotu ta yanke masu hukuncin d'aurin rai da rai agidan yari tare da horo mai tsanani, Alhaji Marusa zai biya diyar kashe Malan Hassan da yayi ga Iyalansa, sannan su duka zasu biya diyar Naseer da Alhaji Maiwada tare da tara mai yawa ga Malan Sani, domin sun zalunceshi. Da wannan ne kotu ta kawo k'arshen wannan shari'a, kuma ta wanke Malan Sani daga zargin da ake masa, haka kuma tana buk'atar masu kula da hakkin d'an Adam da su tsaya wajen tabbatar da biyan duk wata tara da aka d'ora akan masu laifi, had'e da sauran jami'an tsaro, sannan za'a sake d'ora sabon Alkali zuwa wani lokaci. Kottt!!!. Hayaniya ce ta kaure a kotun. 'Yan sanda ne sukayi kok'arin fitar dasu Alhaji Barau dan mutane sai jawosu sukeyi, da kyar aka fitar dasu. Malan Sani kuwa zubewa k'asa yayi yana sujada hawaye suna bin kuncinsa. Alhaji Mansur ne yaje ya kamoshi, rungumeshi yayi yana kuka. Ra'eez ma sai da yayi sujadar godiya ga Allah, kuka kawai yakeyi domin yau itace ranar farin ciki agareshi domin ya cika burinsa. Rungumeshi Jabeer yayi suna murna, haka suka fito waje. Suna fita suka tsaya suna kallon fad'a atsakanin su Alhaji Barau. Alhaji Marusa ne ya cakumo wuyan Alhaji Barau yana fad'in tsakani na daku Allah ya isa, shegu ashe dama kune kuka jefani cikin tashin hankali, duk amanar dana baku sai da kuka cuce ni. Dokeshi Alhaji Barau yayi yana fad'in dalla can azzalumi kawai, waye ya cuce mu idan ba kai ba, mu dukan mu nan kaine silar shigarmu wannan halin ba dan kai ba babu abinda zaisa na aikata wannan abun kunyar, waye ya koya mana kisa. Haka sukayi ta mayar da kalamai yayin da suka fara fad'a suna tona asirin juna, 'Yan sjarida kuwa sai d'aukarsu sukeyi. Da kyar 'yan sanda suka rabasu. Takowa Ra'eez yayi har gaban Alhaji Barau yana murmushi. Ido kawai Alhaji barau ya tsura mashi yana sauke numfashi. Raheena da Momy suna gefe sai kuka sukeyi. Kallonshi Ra'eez yayi yana fad'in ina taya ka murnar samun sabon waje na rayuwa, ina fatan yanzu ka gane komai akaina? Murmushi yayi yana fad'in yau kam zanyi bacci mai dad'i domin karatun da nayi yau ya k'are domin ya biya buk'ata, dama nayi shine saboda ku, tunda naga k'arshen azzalumai Alhamdulillah, Allah shine abun godiya. Takawa yayi har gaban Raheena, ido kawai ya tsura mata yana kallon yanda take kuka ajikin Momy. Kauda kai yayi dan tausayinta ne ya kamashi. Matsowa su Jabeer dasu Nabeel sukayi wajen. Momy ce cikin muryar kuka tace Ra'eez bani da bakin magana, ayanzu kam mun fahimci komai, sai dai laifin wani baya shafar wani, ina rokon ka da girman Allah ka yafe mana domin bamu da sa hannu a cikin mutuwar Mahaifinka. Ra'eez yace bakuyi mani komai ba, dama kuma ban tab'a furta kalmar so ga Raheena ba, hannu yasa ya jawo Rumaisa yana fad'in wannan itace matar da zan aura d'iya ga Malan Sani wanda Mahaifin Raheena yayi sanadiyar zamanshi agidan Yari shekara goma sha biyu, ina fatan bazaku kullace ni ba. Momy ta kalli Alhaji Barau cikin kuka take fad'in ka gani ko, tun kafin aje ko ina abinda bakin halin ka ya jawo mana, shikenan kaji dad'i zaka tafi ka barmu cikin tsangwama da tsana, domin babu wanda zaiso had'a zuri'a damu, ka cucemu, dan haka garin zamu bari ka bani takardar sakina domin kai yanzu gawa ne. Hawayen bakin ciki ne suka zubo ma Alhaji Barau, sunkuyar da kai yayi yana jin tsananin nadama atare dashi, zeyi magana sukaga Nabeel yayi gefen su Momy da gudu, yana zuwa Raheena ta fad'a jikinsa a sume, dan tun zuwanshi wajen ya sauke ido akanta ya kasa d'aukewa, duk bidirin da akeyi besani ba dan hankalinsa yana kanta, hakan yasa da yaga alamun zata fad'i yayi wajenta. Kanta sukayi gaba d'aya, cak Nabeel ya d'auketa Jabeer na gaba sukayi hanyar ofis d'insu da ita. Ammi ce tasha gaban Alhaji M. Sanda idanuwanta jawur alamun taci kuka, hannu ta mik'a masa tana bashi mukullin gidanshi had'e da biro da takarda. Kuka yasa yana girgiza mata kai. Daurewa tayi tana fad'in wallahi bazan tab'a yafe maka ba, ka rubuta mani saki na a hanya nake, Fawwaz kuwa ba laifinsa bane, naje wajensa tunda safe kuma naji dad'in yanda na ganshi, domin alamu sun nuna yayi watsi da shawararka, kai da kake kok'arin sama masa gata kaima zakaje ka iskeshi acan, kuma har na mutu zan cigaba dayi masa addu'a, dan haka ina jiran ka. Zubewa k'asa yayi yana kuka ya riko hannunta yana fad'in kar kimun haka dan Allah, da wanne zanji, idan baki yafe mani ba zan shiga wani hali. Fizge hannunta tayi tana fad'in ina jiranka. Kai ya jinjina yana fad'in bazan sake zaluntar ki ba, domin nasan yanzu banida amfani agareki, na datse igiyar auren mu, amma dan Allah... Wucewa tayi hakan yasa yayi shiru yana kuka. Haka 'yan sanda suka tasa su sukayi gaba, jiyowa Alhaji Barau yayi yana fad'in Ra'eez kace ma Momyn Raheena na yanke igiyar auren mu nasan bazata sake zuwa waje na ba, ka dubi girman Allah ga Raheena nan aduba mani lafiyarta. Kauda kai Ra'eez yayi yana sakin tsaki. Rafeek yace muje muga halin da Raheena take ciki Ra'eez. Goge hawayen idonshi yayi yabi bayan su Rafeek da Sameer hada Husnah da suka shiga wajen su Jabeer. Mama ce ta rik'e Ummu suka nufi mota saboda yanda jikinta yake rawa, haka Alhaji Mansur yayi sallama dasu Alhaji Kamal akan zaije gidanshi anjima, saboda yanzu zai kai su Ummu gida, tare da Malan Sani suka nufi motar. Da sauri wasu 'yan jarida suka sha gaban Malan Sani. 'Daya daga cikinsu yace Malan Sani wane irin farin ciki kake ciki akan wannan 'yanci daka samu yau? Murmushi Malan Sani yayi yana fad'in yau kam bani da bakin magana sai hamdala awajen Allah, domin wannan nasara da muka samu Allah ne yasa muka sameta. To me zakace akan wad'an nan azzalumai da suka jefaka cikin wanan tashin hankali? Babu abinda zance masu domin Allah ya fisu, kuma wannan zaman gidan Yari da nayi dama Allah ya rubutoshi acikin K'addarata, Alhamdulillahi nayi godiya ga Allah daya bani ikon cin wannan jarabawa, domin ba k'aramun alkhairi bane Allah ya jarabceka sannan ya baka ikon cin jarabawar, su kuma sai dai nace Allah shine zeyi maganin su. Zasu sake tambayarsa Alhaji Mansur ya janyeshi yana fad'in sai mu kwana anan. Murmushi yayi ya shiga mota sukayi gida. Sun dad'e suna zubama Raheena ruwa amma ko motsi batayi ba, cike da tashin Hankali Momy tasa kuka tana fad'in ku taimaka mani kada na rasata dan Allah, jikin Ra'eez ne yayi sanyi ganin halin da Raheena take ciki, da sauri Nabeel da Jabeer suka kai hannu domin d'aukarta, tuni Nabeel ya sureta suka nufo waje domin su kaita asibiti. Ur's. Nabeelert Lady🖋 [3/10, 8:41 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.* 5️⃣0⃣ *Last page* Kusan mintuna ashirin suna tsaye babu labarin Raheena, Nabeel da Jabeer sun kasa zaune kowa ya tsaya bakin kofar d'akin kamar zai shiga. Ra'eez da yake gefe guda a zaune sai kallonsu yake, duk da shima yana cikin damuwar halin da take ciki amma k'asan ranshi dariyarsu yakeyi dan tuni ya gama harbo jirginsu. Zama Rafeek yayi kusa dashi yana fad'in wad'an can Romeo's d'in fa? Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in Yaya kaima ka ganosu kenan? Rafeek yace dama can ai Jabeer yana son Raheena, shi kuwa Nabeel shigar sauri Sonta yayi masa. Ra'eez yace ga Husnah kuma a gefe. Murmushi Rafeek yayi yana fad'in abun ai yazo da sauki sai wani yayi hakuri. Wai Husnah lafiyarki kuwa naga duk baki cikin natsuwarki. Ajiyar zuciya ta sauke tare da d'auke idonta daga kan Jabeer, kallon Sameer tayi tana fad'in Yaya. Sai kuma tayi shiru. Murmushi yayi yace Jabeer ko? Hannu tasa ta rufe fuskarta. Girgiza kai yayi yana fad'in ai na fahimceki tun jiya, kada ki damu matuk'ar kina sonshi zanyima Ra'eez magana, ke kuma sai kiyi amfani da dabarun ku na mata ki janyoshi. Murmushi tayi tana fad'in nagode Yayana. Fitowar likita yasa gaba d'aya sukayo kanshi. Ofis ya nufa hakan yasa suka bishi banda Nabeel da yayi saurin shiga wajen Raheena. Ku kwantar da hankalin ku kawai tashiga cikin damuwa ne shiyasa tayi doguwar suma, amma yanzu komai yayi dai-dai munyi mata allurar bacci saboda zuciyarta ta samu natsuwa. Ajiyar zuciya Momy ta sauke tana fad'in mungode likita, idan ta farka zata warke ko? Kai ya d'aga yana murmushi, kallon su yayi yana fad'in sai dai tana buk'atar arik'a kwantar mata da hankali idan ba haka ba zata iya had'uwa da hawan jini saboda akwai damuwa a zuciyarta. Rafeek yace insha Allahu za'a kula likita, yanzu me ake da buk'ata? Takarda ya mik'a masa yana fad'in abiya wad'an nan kud'in zasu bada magungunanta. Amsa yayi suka fita suna masa godiya. A gefenta suka iske Nabeel ya zuba mata ido, komawa da baya Jabeer yayi ganin abinda yake faruwa. Ra'eez yace Momy zamu wuce sai zuwa anjima idan ta farka zamu dawo kila ma asallameta zuwa anjima. Momy tace nagode sosai Ra'eez Allah ya baku abinda kuke nema. Gaba d'aya suka amsa da amin. Rafeek yace Alhaji Nabeel muje ko. Kai ya sosa yana fad'in kuje Yaya anjima zan tafi. Murmushi sukayi Sameer yace ai gara ka tsaya kayi jinya. Sallama sukayi masu suka fita. Suna fitowa suka iske Jabeer saman mota yana latsa waya. Ra'eez ne ya matsa yana fad'in Jabeer ya naga ka fito kuma? Jabeer yace jiran ku nake mu wuce. Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in Jabeer kada ka kwari kan ka fa. Kallonshi yayi yana fad'in wai Raheena kake nufi? Kai ya d'aga masa. Saukowa yayi yana fad'in fatana ta samu wanda zai kula da ita idan ta rasaka, kuma Alhamdulillahi ta samu, sai fatan ta amince dashi, kuma nayi murna daya kasance shine. Hannunsa Ra'eez ya kamo yana fad'in kaine ka santa kuma kaine ya kamata ka kasance da ita, ina maka sha'awar samunta domin nasan wacece Raheena. Murmushi Jabeer yayi yana fad'in wallahi ko son da nake mata zai iya cutar dani gara ya cutar dani da dai na aureta, bare kuma ni tausayinta yafi yawa a zuciyata, koda ina sonta to kad'an ne, kuma ni bazan iya aurenta ba. Ra'eez yace dalili? Ajiyar zuciya ya sauke yana fad'in kaine dalilin, da ace wani ne daban da ban sani ba Raheena take ma irin wannan son to zan iya aurenta kuma na mantar da ita komai na koya mata sona, amma bazan iya aurenta ba bayan tana maka irin wannan son, har bada zuciyata bazata tab'a natsuwa ba, domin koda yaushe muna tare da kai, zaka zo gidana itama zata je gidanka, koda ta mance da kai zuciyata zata cigaba da raya mani tana sonka, kaga kuma shed'an beda gwani zai iya d'arsa wani abu a zuciyata shiyasa kaji nace maka bazan iya aurenta ba, ganin yanda Nabeel ya rikice daya ganta nasan cewar Allah ya kawo mata sauyi, dan haka ina so ka bar wannan maganar anan bana so Nabeel yaji kada wani abu ya tsarga zuciyarsa. Rungumeshi Ra'eez yayi yana fad'in na fahimceka sosai abokina, kuma ko nine haka zanyi, idan ka amince dani zan iya baka mata? Saurin kallonshi Jabeer yayi. Jinjina masa kai Ra'eez yayi. Murmushi Jabeer yayi yana fad'in na amince. Sakinsa Ra'eez yayi yasa hannu ya juya fuskarshi zuwa wajen dasu Sameer suke tsaye shida Rafeek, saitin da Husnah take ta zuba mashi ido ya aje fuskarshi. Murmushi Jabeer ya saki har hak'oransa suka fito, shiru yayi suna kallon juna shida Husnah. Hannu Ra'eez yasa ya kamo hannun Jabeer yana fad'in na baka ita amatsayina na Yayanta. Dariya Jabeer yasa ya tureshi. Wucewa Ra'eez yayi yana fad'in Yaya muje. K'arasowa sukayi Rafeek yace an gama Maths d'in ko? Kai Ra'eez ya d'aga yana fad'in sauran English. Dariya sukasa gaba d'aya. *** *** Lokacin da aka shigar dasu Alhaji Barau wajen da sauran fursunonin suke bayan an basu kayan gidan yari sun saka gaba d'aya mutanan wajen sukayo kansu suka sasu tsakiya. Yanda kasan zasu rufesu da duka haka suka matse su kowa da abinda yake fad'i yayin da wasu suke masu dariya suna nuna su. Kunya da tsoro ne ya kamasu Alhaji Barau sai b'oye fuskarsu sukeyi. Wani daga cikin mutanan wanda da ka ganshi kaga rik'ekken marar ji, shine ya matso tsakiya yana fad'in ansutu jama'a. Kowa yayi shiru suna kallonshi. Takowa yayi kusa dasu Alhaji Barau yana tafa hannu, kallonsu yayi yana fad'in *da d'ina da gobe?*.. Mutane suka amsa gaba d'ayansu da *saurin zuwa.* Murmushi yayi yace *Alhaki?* suka amsa da *Kuikuiyo.*.... *Komin nisan jifa?*... *K'asa zata dawo*... *Idan zaka gina ramin mugunta*?... *Ginashi dai-dai tsawonka*... *NASHIGA BAN 'DAUKA BA?*... *BATA FIDDA 'BARAWO.* Gaba d'ayansu suka d'auki ihu suna dariya. Hannu ya d'aga hakan yasa akayi shiru. Kallonsu yayi yana fad'in barkan ku da shigowa duniyar mu, gashi dai kun turo mu cikinta ashe dama zaku zo ku iske mu, dan haka ku sani kunzo wajen da za'a mulke ku, domin wannan gida Masarauta ta ce, Mazaje kuna ji? Gaba d'aya suka amsa da E muna ji. Kallonsu ya sakeyi yana fad'in yau dai Allah ya fidda Baba Sani daga gidan nan yayin da ya maido azzalumai a cikin gidan, saboda haka bana so kowa ya d'aga masu k'afa domin da yawa wannan tsohon macucin Alkalin shine ya kawo mu nan, sai wannan guntun Lauyan wato Barau shine yayi silar aka yanke mana hukunci, daga yau babu sani babu sabo tsakanin mu dasu, dole cikin kwana biyu su gane shayi ruwa ne, domin hukuncinsu horo ne mai tsanani. Dariya sukasa gaba d'aya yayin da suka sungumesu sama sukayi cikin gidan dasu sai ihu sukeyi. Masu gadi kuwa gefe suka koma suna shan dariya dan sun san basuda yanda zasuyi da su domin Allah ne ya kawo masu azzalumai har gida, hakan yasa kowa ya nufi wajen aikinsa. Fawwaz da yake gefe guda yana kallon abinda yake faruwa hawaye ne kawai suke zubo masa na takaici, tunda Amminsa tazo masa da labarin d'azu da safe yake cikin damuwa, da kunya ace shida mahaifinsa suna zaune waje guda, dole ma ya rik'a nisantarsa dan ba zai iya zama kusa dashi ba, gara kowa yayi hanyarsa danshi ayanzu ilimin addini yasa agaba domin nasihar Amminsa ta shigeshi. Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da yaji an dafashi. Juyowa yayi sai yaga abokinsa ne wanda yake d'aukar karatu a wajensa. Zama yayi yana fad'in Fawwaz na fad'a maka sai kasa jarumta aranka idan ba haka ba ciwon zuciya zai iya kama ka, nasan da ciwo amma haka Allah ya k'addaro maka kayi hakuri kawai. Jinjina kai Fawwaz yayi yana fad'in nagode. **** **** Zaune suke afalo bayan da Malan Sani yayi wanka dama yayo aski, kaya sababbi Alhaji Mansur ya bashi ya saka, sosai ya fito yayi kyau duk da alamun tsufa da wahala sun fito masa amma ya canza. Abdallah yana zaune saman cinyarsa sai shafa kanshi yake yana murmushi, abinci Mama ta zuba masu sai murmushi take kamar amarya. Gyaran murya Alhaji Mansur yayi yana fad'in muna k'ara mik'a godiya ga Allah daya nuna mana wannan rana, hakika Allah shine mai iko mai juya al'amura yanda yaso. Kallon Ra'eez yayi yana fad'in sannu da kok'ari Ra'eez, hakika kayi kok'ari kuma ka bada gudummuwa sosai, duk da ka fad'a mani duk ranar daka sauke wannan nauyi zaka aje aikin ka amma ban sani ba ko kana da sha'awar cigaba da aikin. Saurin girgiza kai Ra'eez yayi yana fad'in wallahi Abbah aikin shari'a ya fitar mun rai, nikam daga yau nagama tsayuwa domin na kare wani, dama saboda haka nayi karatun kuma Alhamdulillahi burina ya cika, takardar aje aikina tana nan na dad'e da rubuta ta kwanan wata kawai zan saka na basu abunsu, nifa na kosa mu bar garin nan ma. Dariya suka sa gaba d'aya. Ummu tace maganar ka gaskiya ce Ra'eez, koni bazan barka kacigaba da wannan aikin ba, haka kuma jina nake kamar ina zaune asaman k'aya domin garin nan ya fitar mun arai. Jinjina kai Abbah yayi yana fad'in tsarin mu yana kan hanya d'aya, dama na tambayeshi ne dan ban sani ba ko ya canza ra'ayi, amma tunda kana kan ra'ayin ka shikenan Allah ya albarkaci aikin da kayi, sai mu koma Kano a sama maka wani aikin, amma wane aiki kafi so? Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in nafi son naganni ina koyawa a jami'a, domin buri na ne, shiyasa ma dana samu aikin nake son na k'aro karatu, dan arayuwata ina son aikin da yake da lokaci, wanda mutum zai iya tsara lokacinsa da kanshi, kuma kowa yasan koyarwa ce kad'ai take da wannan tsarin. Kai Yaya makarantar 'yan mata kuma zakayi aiki? Rumaisa ta fad'a kamar an tsikareta, hannu tasa ta rufe bakinta ganin a inda tayi maganar. Da sauri ta mik'e tayi waje hakan yasa suka kwashe da dariya. Umma tace kina da gaskiya 'Diyata, nima na fara tayaki kishi haka kawai zaije cikin 'yan mata yarik'a bud'e murya yana koya masu. Mama tace ai Yarona beda kalle-kalle kusha kurimin ku babu abinda zai faru. Dariya sukasa Ummu ta duk'ar da kai tana murmushi. Abbah yace tunda dai shine ra'ayinsa zan sama maka, kai ina tabbatar maka wannan shari'ar da kayi zata d'aukaka ka, duk inda ka nemi aiki a fad'in k'asar nan sai ka samu, dan haka mu fara shirin tafiya, Malan Sani gara mu tafi daga baya sai mu dawo asa duk gidajen kasuwa domin mun bar Lagos kenan sai dai muzo da yawo saboda mutanan arziki. Malan Sani yace duk yanda kace Alhaji haka za'ayi, domin banki kada na kwana alagos ba yau dan wallahi ta fitar mun arai. Abbah yace shikenan zuwa nan da kwana biyu sai mu tafi kafin nan an kammala komai. Madu ne ya kalli Malan Sani yana fad'in dan Allah Malan Sani ka yafe mani, har yanzu ina jin kunyar shedar dana bayar akan ka wancan lokacin. Murmushi Malan Sani yayi yana fad'in wai Madu bazaka dena wannan maganar ba, tun yaushe nace na yafe maka, ko nine fa amatsayin ka wallahi shedar da zan bayar kenan, dan haka komai yawuce. Abbah yace ai wannan maganar ma abar tada ta, wad'an da suka assasa fitinar ma suna can nasan mutanan gidan Yarin kad'ai sun ishesu, dan haka kowa yayi nagari kansa, ubangiji Allah ya k'ara tsare mana Imanin mu da zuk'atan mu. Sai magana ta gaba, muna komawa Kano zanyi bikin Yarana dan bazan jira komai ba, ko kuma hada Raheenar zaka had'a? Waro ido Ra'eez yayi yana kallon Abbah da yake kunshe dariya. Umma tace Allah ya kyauta wallahi Yarona bazai had'a zuri'a da wad'annan mutanan ba. Dariya sukasa Abbah yace dama tsokana ce, babu wata amarya agidan Ra'eez sai Rumaisa ta. Malan Sani yace ai duk yaranka ne duk yanda kayi yayi, Allah yasa alkhairi. Gaba d'aya suka amsa da amin. *** *** Maganar ka gaskiya ce Nabeel, dama ka fad'a, zuwa kwana biyu za'a dena labarina, gashi kuma ya tabbata, sai fatan Allah ya yafe mani, dad'in da nakeji yanda Iyayen Farouk suka yafe mani. Nabeel yace ai Abbah dama na fad'a maka, duk abinda mutum ya aikata akwai wanda ya aikata abinda yafi nashi, Allah dai ya k'ara tsare mu baki d'aya. Ummansa tace amin Nabeel, ya jikin Raheenar kuma? Kallonsu Abbah yayi yana fad'in wacece kuma Raheena? Duk'ar da kai Nabeel yayi yana murmushi. Murmushi Abbah yayi yana fad'in to nagane, na samu surika kenan, amma a ina take haka? Sosa kai Nabeel yayi yana fad'in Abbah anan garin take, sai dai zuciyata tana cikin damuwa saboda nasan na d'auko abinda bazaku amince dashi ba, nima wallahi bansan yanda akayi zuciyata ta kamu da sonta ba, domin komai ya faru ne ayau, yanzu hakama daga wajen ta nake tana asibiti bata da lafiya. Hannunsa Abbah ya kamo yana fad'in bana so kasa aranka ni zan iya tauye maka hakkin ka, fad'a mani wacece ita? Kallon Umma yayi yana fad'in 'Yar gidan Alhaji Barau ce Alkali. Ajiyar zuciya Umma ta sauke tayi shiru tana kallonsu. Shiru shima Abbah yayi har Nabeel ya fara tsorata da shirunsu, can Abbah ya saki murmushi yana fad'in Allah mai juya al'amura, nine nake tsoron ranar da zaka kawo mani surika arik'a goranta maka abinda Mahaifinka yayi, sai gashi Allah ya k'ulla alak'a tsakanin ka da wacce laifin Mahaifinta ya take na Mahaifin ka so dubu, matuk'ar ita yarinyar tana da hali mai kyau bazan hana ka aurenta ba, domin laifin wani baya shafar wani, Allah ya tabbatar da alkhairi. Kallon Umma Nabeel yayi yana matse idanu. Hannu tasa ta ja kunnansa tana fad'in amsata kake jira? Kai ya d'aga yana kallonta. Murmushi tayi tace Allah yasa abokiyar rayuwarka kace. Rungume Umma yayi yana fad'in amin Ummana, nagode sosai, yanzu na samu kwarin guiwar tunkararta da maganar dama amincewar ku nake jira sai dai kutayani da addu'a akwai soyayyar wani a zuciyarta, sanin bazata sameshi ba yasa tashiga cikin wannan halin. Abbah yace *WAYE NE*? Nabeel yace Brr. Ra'eez ne. Jinjina kai Umma tayi tana fad'in itama ta d'ebo da zafi, koda yake kowama sai yanzu yasan d'an gidan marigayi ne, babu komai, matuk'ar kana sonta kaje ka gwada sa'ar ka. Abbah yace Allah ya baka sa'a. Yace amin. *** *** Kwance take ajikin Momy tana kuka, hakuri Momy take ta bata. Raheena tace Momy Dady ya cuceni, ba dan wannan abun daya aikata ba nasan dole na samu Ra'eez, amma kina gani sai dai na hakura dashi, gashima har yana da matar aure, shikenan nasan bazanyi aure ba har na mutu domin Dady ya goga mani bakin fenti. Shafa kanta Momy tayi tana fad'in zakiyi aure Raheena, domin a yau da kika rasa Ra'eez Allah ya kawo maki wani, abinda nakeso da ke ki daure ki amshe shi, domin idan kika rasashi zaiyi wuya ki sake samun wani, domin shine yazo maki alokacin daya kamata kowa ya gujeki, dan haka ina mai baki shawara daki amshe shi, tunda kika suma yake tare da ke be jima da tafiya ba yace zai dawo, shima abokin Ra'eez ne, sunanshi Nabeel, d'an gidan tsohon shugaban makarantar kings college ne wanda aka yanke ma Mahaifinsa hukunci wan can satin shida Alhaji M. Sanda, yaron kirki ne ina maki sha'awarsa. Shiru Raheena tayi ta d'ago kai tana kallon Momy, zatayi magana aka turo k'ofa. Nabeel ne dasu Ra'eez suka shigo bakinsu d'auke da sallama. Saurin duk'ar da kai Raheena tayi dan yanzu kunyar Ra'eez takeji. Momy ce ta amsa masu tana masu sannu da zuwa. Zama sukayi suka gaisheta tare da tambayar mai jiki. Momy tace gatanan taji sauki likita ma ya sallame mu dama zaman jiranku nakeyi tunda Nabeel yace mujirashi. Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in K'anwata babu magana. 'Boye fuskarta tayi tana murmushi. Jabeer yace ko saboda Nabeel ai sai a kallemu. Murmushi Nabeel yayi yana fad'in dan Allah kubarta ta huta. Tashi Ra'eez yayi yana fad'in anbarta mai Raheena, Momy kutashi mu wuce. 'Dago kai Raheena tayi zata kalli Nabeel caraf suka had'a ido, da sauri ta kauda kai tana jin fad'uwar gaba. Haka suka tattara suka wuce gida. Bayan sun ajesu Ra'eez ya fad'a masu nan da kwana biyu zasu koma Kano da zama. Momy tace muma ai bazamu zauna ba Kanon zamu koma gobe ma. Ra'eez yace ashe muna kusa, to Allah ya taimaka, na manta Alhaji yace na fad'a maki ya datse igiyar auren ku. Tsaki Momy taja tana fad'in shi ya sani dai, nagode maku, kome kenan zamuyi waya. Ra'eez yace shikenan. Sallama sukayi masu Nabeel yace nima ina nan. Jabeer yace dama kaji munce kaTaho? Ai gara ka zauna kuyi sallama. Fita sujayi suna dariya. Suna shiga mota Jabeer yace wai da gaske garin nan zaku bari? Ra'eez yace wallahi kuwa. Jabeer yace aikuwa wallahi tare zamu tafi nima na rubuta takardar aje aiki na. Waro ido Ra'eez yayi yana fad'in yaushe? Jabeer yace tun lokacin da nasan zaka aje naka. Ra'eez yace su Abbah bazasu barka ba ai. Jabeer yace tuni ma suka amince, da ace mace ce ni ai dole na rabu dasu saboda aure, dan haka sun amince zan koma Kano da zama kuma nima rin aikika zanyi. Rungumeshi Ra'eez yayi hawayen farin ciki suna sakko masa, bayansa ya dafa yana fad'in nagode d'an uwana, hakika tarayyar mu daga Allah take, na dad'e cikin damuwar rabuwar mu, ashe zamu kasance tare, muje dole nayima su Abbah godiya. Dariya Jabeer yasa yana fad'in sai dai zuwa anjima yanzu muje ka rakani na shigar da kaina wajen Husnah kaga muna komawa sai asha bikin mu tare. Dariya Ra'eez yasa yana fad'in yanzu kuwa. *** *** Kafin dare an gama kammala duk wasu labarai, tun daga gidan tv, gidan radio, yanar gizo, kai duk wata kafa ta yad'a labarai sai da aka yad'a maganar shari'ar su Alhaji Barau. Ba iya Lagos ko Nijeriya ba, gaba d'aya duniya labarin wannan shari'a ya watsu, duk inda kasan akwai yanar gizo to dole su samu wanann labari. Mutanan da suka kalli wannan shari'a basa kirguwa domin abune daya tab'a zuk'atan mutane, yayin da wasu suke Allah wadai da halin su Alhaji Barau. Haka Rafeek sai da ya bada firar da suka tab'ayi da Kwamishna a gidan Tv aka kunna, wanda hakan ya jawo karin surutu awajen mutane, kowa yana fad'in ta bakinsa, yanda Kwamishna yake lailaya zance ta kamar mutumin kirki ashe azzalumi ne. *** *** Washe gari wajen k'arfe sha d'aya aka aiko kiran Alhaji Marusa. Koda yazo yayi mamakin wanda ya iske a wajen. Zama yayi jikinsa a sanyaye. Jin shiru anki magana yasa Alhaji Marusa yace Khalil!. Idanuwa kawai Khalil ya tsura mashi ya kasa magana. Matsowa Alhaji Marusa yayi hawaye suna sauko masa, hannu ya kai zai kamo Khalil yayi saurin kwace hannun sa yana fad'in kada ka tab'ani. Alhaji Marusa yace kayi hakuri Khalil, nasan bani da bakin da zan maka magana amma inaso ka d'auka kaddarace ta sameni. Tashi Khalil yayi yana fad'in babu wata K'addara Dady, kai ne ka zab'ama kan ka wannan rayuwar, ko haihuwar mu da kayi Allah ne yasa zamu fito duniya, kud'in ka sune Mahaifanmu domin sune suke kula damu ba kai ba, bakasan komai namu ba, baka san tarbiyar mu ba, kawai ka turamu cikin turawa dan kada muzauna akusa da kai mutakura maka, Alhamdulillahi ina k'ara godiya ga Allah daya shirya ni, haka ina bakin ciki da Yaya ya tsinci kasan a irin halin da kake ciki, dama kuma barewa bazatayi gudu d'anta yayi rarrafe ba, bansan abinda kayima Momy kenan ba sai jiya Yaya yake fad'a mani da mukayi waya bayan daya samu aron waya dan yaga abinda ya faru da kai. Tunda aka kamashi so d'aya bakaje ba, shiyasa ya aiko ni na fad'a maka yana tayaka murnar zaman gidan yari, dalilin zuwana saboda ka fad'a mani inda Momy take naje na nemota domin bazan iya barinta ba, saboda itama bata barmu ba alokacin da baka kula damu. Cikin kuka Alhaji Marusa yace kayi hakuri Khalil, nasan ban kyauta maku ba, kuma naji dad'i dana ganka cikin kamala, dama kuma Allah yana fitar da rayayye a jikin matacce, bakasan abinda Momynku tayi bane amma zan fad'a maka...... Hawayen bakin ciki ne suka zuboma Khalil daya gama jin abinda ya faru. Alhaji Marusa yace bayan tafiyarta da kwana biyu na samu labarin mutuwarta, ashe barin ta nan abinda saurayinta yayi mata ya jawo mata ciwon zuciya, ciwon kwana biyu zuciyarta ta kumbura ta mutu, kayi hakuri da ban fa.... Saurin tashi Khalil yayi yana fad'in ya isa, ba sai ka k'arasa ba, Allah yajik'anta, nima zan koma inda ka koya mani rayuwa, Alhamdulillahi na had'u da Ubangida nagari mai ilimin addini, duk da kasancewarsa farar fata amma musulmi ne, kuma ya samar mani shedar zama d'an k'asa, yanzu haka bikin mu za'ayi da d'iyarsa, dan haka daga yau ni ba d'an najeriya bane na manta da ita zan rik'e surukaina amatsayin iyayena. Rikoshi Alhaji Marusa yayi yana fad'in na amince da haka, kuma naji dad'i, amma inaso kaje gidana cikin d'akina zakaga takardun kadarorina ka d'auka gadonka ne duk... Hannu ya d'aga masa yana fad'in kai da kotu ta bayar da dukiyar ka ina kake da wasu kud'i? Ko kana dasu wallahi bazan sake cin sisin ka ba domin dukansu haram ne, nizan wuce, ina rokon ka da ka yafe mani idan na maka badede ba. Kuka Alhaji Marusa yasa yana kiran Khalil amma ko juyowa beyi ba. Zubewa yayi a wajen yana wani irin kuka. Masu gadi ne sukazo suka korashi ciki. Haka ya koma wajen da suke fasa duwatsu, yana kuka yana cigaba da aiki, su Alhaji Barau ne suke bashi hakuri suma kukan suke, tausayin kansu ne ya kamasu, acikin kwana daya komai ya canza masu, lallai duniya abun tsoro ce. *** *** Duk wata dukiya ta masu laifi sai da jami'an tsaro suka had'a kanta, gidaje da sauran kadarori duk sun had'a takardunsu za'a sasu kasuwa dan sai an fitar da abinda kotu ta yanke idan anyi saura a basu kayansu. Su Momy tuni suka kama hanyar Kano wanda Nabeel ne ya d'auki nauyin kaisu dan yakasa ya tsare dole sai da Raheena ta saurareshi, hakan yasa yace zai kaisu domin ya gano waje. Itama Raheena tana jinsa aranta dan tana kokarin cire Ra'eez dan tasan ta rasashi, gara ta amshi Nabeel koba komai yanzu ta fara sanin dad'in so saboda ta samu mai sonta ba wanda take so ba, domin za'a kirata aji lafiyarta, sab'anin da itace take kira. Lokacin da shugaban kula da hakkin wad'an da kotu ta nema da a damk'ama tarar da ta yanke ya buk'aci ganin Malan Sani da Iyayen Naseer, bayan da yayi masu jawabi sai Malan Sani yace gaba d'aya abinda aka bashi a mik'asu gidan marayu dan bazai iya amfani da kayan haram ba, haka ma Baffa yace. Wannan abu da sukayi bak'aramun burge mutane yayi ba, anan ya fito yasheda ma 'yan jarida komai, su kuma suka shiga rattabawa a labaransu, hakan ya jawo masu d'aukaka da addu'oi a wajen mutane, domin ba kowa bane zai iya tsallake irin wannan dukiya ayanzu. *** *** Aje aikin Ra'eez da Jabeer ya tab'a zuk'atan manyansu da sauran mutane, domin sun san sunyi asarar hazikai, tun daga can sama aka aiko da sakon ban hakuri da neman alfarma akan Ra'eez ya koma bakin aikinsa amma yace ayi hak'uri ya gama aikin lauya, duk yanda Alhaji Kamal yaso amma hakan be samu ba dole sai dai sukayi hakuri. 'Yan jarida kowa so yake yayi fira da Ra'eez amma yaki basu had'in kai, da sun tambayesa dalilin aje aikinsa amsar d'aya ce, dama cikar burinsa yake jira kuma ya cika shiyasa ya aje. Tarin masoyan Ra'eez na garuruwa dama k'asashe basu fad'uwa domin har dena kunna data yayi saboda yawan sako. *** *** A ranar da zasu tafi kasancewar jirgin yamma zasubi hakan yasa Alhaji Mansur ya shirya masu taro a harabar gidansu Ra'eez, duk wasu abokan arziki sai da suka zo wannan taron domin su k'ara tayasu murna. Iyayen Nabeel, Iyayen Sameer, Iyayen Rafeek, Iyayen Jabeer duk sunzo dan sunce zumunci yanzu aka fara. Anci ansha kuma anyi raha, anan Alhaji Mansur ya tashi yana mik'a godiyarsa abisa goyon baya da kuma had'in kan da suka basu wajen ganin an kammala wannans shari'a, haka yayi ma Iyayen Jabeer godiya da suka amince mashi ya bisu, kuma yayi masu alk'awarin kula dashi kamar yanda zai kula da Ra'eez. Anan ya kalli Iyayen Sameer yana fad'in ina nema ma 'Dana Jabeer auren Husnah domin inaso da an koma a had'a bikinsu dana Ra'eez. Dariya akasa nan Dadyn Sameer yace ai duk 'ya'yanka ne, dan haka na bama Jabeer Husnah. Cusa fuska Husnah tayi cikin mayafinta tana sakin murmushi. Dadyn Sameer yace biki biyu zanyi, domin tare za'a had'a dana Sameer. Abban Nabeel yace ashe kuwa za'ayi babban taro, domin shima Nabeel zan had'a nashi da Raheena, kunga kuwa ya kamata ace an tsaida bikin a waje d'aya. Alhaji Kamal yace idan haka ne nine zan bada wannan shawarar, tunda mutanan Kano sunfi yawa kuma a cikin mu babu d'an asalin garin nan duk munfi kusa da can wajajen ina gani zamu maida bikin mu a kano, domin kuwa nasan zata d'auke mu. Tafi akasa gaba d'aya kowa yana fad'in hakan yayi dai-dai. Baffa yace gaskiya naji dad'in wannan zumunci da yaran mu suka had'a, ubangiji Allah ya k'ara k'arfafashi har zuwa jikokin mu da masu zuwa bayansu. Gaba d'aya aka amsa da amin. Alhaji Mansur yace insha Allahu zamu tsara yanda komai zai kasance, sai dai zamu aro al'ada, inaso bikin ya kasance tamkar na Yarbawa, ma'ana ayi komai arana d'aya atashi, a d'aura aure lokaci guda a wuce wajen cin abinci hada matan, ana gamawa amaren kusa akaisu gidajensu, na nesa kuma washe gari atafi dasu. Dariya suka sa kowa yace wannan yayi ba sai an tsaya yin wani dogon biki wanda za'a fara tun daga laraba sai lahadi a gama. Bayan sun kammala suka kulle taron da addu'a. Kowa wajen budurwarsa yawuce domin suyi fira. Jabeer da Husnah tamkar masoyan da suka dad'e, dan Husnah ta iya soyayya, tasan yanda zata sa namiji ya mace akanta ya kuma saba da ita cikin kankanin lokaci, abunka da sabon shiga tuni Jabeer ya zurma har yakusa fin Ra'eez kwarewa. Kallon juna kawai suke fuskarsu d'auke da murmushi. Rumaisa ce ta fara d'auke idonta tana murmushi. Ra'eez yace komai yayi farko zaiyi k'arshe, kinga yanzu sai muje musha biki babu sauran damuwa ko tunanin shiga kotu. Dariya Rumaisa tasa tana fad'in ai wannan kotu taci mana lokaci. Ra'eez yace shiyasa ai na zab'i wannan aikin domin nasamu damar kula dake, kinga kema sai kishiga makarantar ki anatse, ko har yanzu kina akan bakarki na bakison karatu? Murmushi tayi tana fad'in yanzu kam nake da sha'awar karatu koda bazanyi aiki ba, dan haka ashirye nake dana fara karatun aikin lafiya. Tafi yayi mata yana fad'in haka nake son ji, ina matuk'ar son na ganki kina taimakon al'umma, duk da nasan zan baki kulawa amma inaso kema kiyi aiki domin kishiga cikin al'umma kirika sanin rayuwa, Allah ya baki sa'a kuma ya barmu tare. Kallonshi tayi tana fad'in Amin Annur. *** Tsaye suke a tashar jirgin sama suna jiran akirasu, gaba d'ayansu fuskokinsu d'auke suke da farin ciki, acikin matafiyan hada Madu dan shima yace binsu zeyi, duk wanda yaga wannan zuri'a sai sun burgeshi saboda yanda fuskarsu take d'auke da annashuwa. Ra'eez kuwa mutane sai zuwa suke suna gaisawa wasu kuma suna d'aukar hoto. Kiran sunaye da aka fara yasa mutane suka barshi. Murmushi Jabeer yayi yana fad'in kaga angon Rumaisa. Ra'eez yace ga kuma angon Husnah ba, wai ya akayima bata zo rakiya ba? Jabeer yace nine na hanata dan bana so ta sani kuka. Dariya sukasa gaba d'aya hada su Rafeek, Sameer, Adnan da Nabeel. Rafeek yace ai dama fa ance farin shiga sunfi saurin iya abu, yanzu ko kunyar Yayunta bakaji kake fad'in haka. Rufe fuska Jabeer yayi yabar wajen yana fad'in na d'auka bakowa ai. Dariya sukasa Adnan yace gara ka fad'a sai dai kuma baka canka dai-dai ba ka ganta can a baya dan kuka tasa mana sai ta biyo mu hakan yasa Yaya yace ta taho. Jabeer yace Yaya Sameer kai da kan ka? Gira Sameer ya d'aga yana fad'in bana son k'anwata tayi kuka shiyasa na taho da ita, kaje ku k'ara sallama kafin azo kan ka. Ra'eez yace ba sai yaje ba kamar naji an kira sunanshi fa. Da gudu Jabeer yayi wajenta yana fad'in d'an bakin ciki saboda kasan da Rumaisa za'a tafi ai dole ka fad'i haka, to sai naje. Dariya suka sa. ajiyar zuciya Rafeek ya sauke yana fad'in gaskiya zamuyi kewa, amma bakomai ai Kano da Lagos babu nisa musamman da sauki yazo yanzu, insha Allahu zumuncin mu bazai lalace ba zai d'ore a haka. Sameer yace Allah yasa. Haka sukayi ta fira har aka kirasu. Sallama sukayi cike da kewa dan Ra'eez sarkin kuka sai da yayishi, suma duk jikinsu yayi sanyi haka suka rabu cike da kewar juna. Sai da kowa ya gama shiga jirgin kafin jirgi ya d'aga. Hannun Jabeer Ra'eez ya rik'e yana fad'in aiki ya kammala gashi yayi riba tunda ya sama mani babban aboki kuma d'an uwa. Jabeer yace sosai kuwa domin gashi na samu K'ani daga sama. Harara Ra'eez ya watsa mashi yana fad'in kamanta, ai kasan dai na girmeka. Juyawa Jabeer yayi yana fad'in dan Allah Ummu nida Ra'eez waye babba? Murmushi Ummu tayi tana kok'arin maida kwallar idonta ta kewar mijinta kafin tace kaine babba. Dariya sukasa hada mutanan da suke kusa dasu. Gwalo Jabeer yayi ma Ra'eez. Murmushi Ra'eez yayi ya rik'e hannun Jabeer, runtse ido yayi yana fad'in daga k'arshe Allah ya bani Yaya nima. Hawaye ne suka sauko masa. Hannu Jabeer yasa ya jawo kanshi ya kwantar a kafad'arsa yana shafa bayansa. Murmushin farin ciki Alhaji Mansur yayi yana fad'in Allah ya k'ara had'a kanku baki d'aya. Malan Sani da yake gefe yace amin. *ALHAMDULILLAH* Nima anan jirgina ya d'aga zuwa Zango daga Lagos😉. Ina mik'a godiyata ga Allah daya bani ikon kammala wannan littafi nawa mai suna *ALKALI NE,* ina rokon Allah ya yafe mani kuskuren da yake ciki, ya kuma bada ikon d'aukar darasin da yake ciki. Ina mik'a godiyata ga dukkanin masoyana, hakika kun nuna mani soyayya, wad'an da suka karanta da wad'an da basu samu damar biyan kud'in littafin ba da wad'an da suka karanta asama duk ina mik'a godiyata agareku, domin masoyin tsuntsu shike binsa da jifa, sai ana sonka ake iya kallon kayan ka, ina matuk'ar farin ciki dana samu ana yad'a labarina domin soyayyace ta jawo hakan, Allah ya gafarta mana baki d'aya, dama kuma ban kullaci duk wanda ya karanta be biya ba. Nagode nagode sosai da addu'ar ku agare ni Allah yabar zumunci. *ALKALI NE FANS GROUP,*... Jinjinar ku ta dabance, Allah ya biya maku buk'atun ku na alkhairi amin. Sai kunjini asabon littafina mai zuwa insha Allah... *NA SHIGA BAN 'DAUKA BA.* An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT __ Ur's. Nabeelert Lady🖋