An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXTJARUMA YAZILA Littafi na daya Na Abdul'aziz sani madakin gini Created and design by:- Shuraih Usman Publishing shuraih Usman From http://shuraih.waphall.com . A wani zamani can baya mai tsawo da ya shude a kasar kisra an yi wani karamin kauye mai suna himsarul aswad ya wanzu a yammacin birnin kisra kuma shi ne gari na karshe wanda yayi iyaka da birnin rum. mutanen birnin himsarul aswad manomane wadanda suka sami albarkacin kasa domin agaba daya garuruwan dake kar kashin birnin kisra babu inda ake da arzikin noma kamar himsarul aswad acikin wadannan kauye akwai wani mutum da ake kira hukairu wanda asalinsa dan uwan hakimin garinne amma saboda bambancin ra'ayi da halayyarsu sai hukairu yahakura dazama tare dan uwansa hakimi yakoma daji inda yayi gidansa kusa da gonarsa yaci gabada rayuwa a wajen tare da matarsa guda daya jal wacce akekira humaira shidai hakimin kauyen himsarul aswad wanda ake kira da suna barzuk yakasance azzalumi kuma make taci mai danne hakkin talakawa kamar yadda sarkin kisra ya zamo na wannan lokaci dalilin dayasa kenan ma yadade akan mulkin yana tayin abinda yakeso Hukairu da barzuk sun kasance hassan da usaini kuma suna matukar kama da junansu tamkar antsaga kara wani abin mamaki shine matansuma yan'uwan junane kuma suma hassana da usainane. Sunan matar barzuk nuzaira. Humaira da nuzaira sun shaku da juna ainun kuma har aka yimusu aure basu rabuba tunda agidadaya suke zaune lokacan da hukairu da humaira zasuyi hijira subar cikin kauyen himsarul aswad da kyar hukaira da nuzaira suka rabu domin kankame junayi suka fashe da.matsanancin kuka A wannan lokaci shima Hukairu kuka yake koda yakama. Humaira yana kokarin banbareta daga jikin yar uwarta nuzaira saita dubeshi alokacinda Fuskarta ta jike sharkaf da hawaye tace "yakai mijina saboda me zaka rabani da yar uwata alhalin tunda aka haifemu Bamu taba rabuwaba Nikam da dai ka rabamu gwara ka barnina zauna anan gidan koda kuwa zan zama baiwar sune. ". Sa 'adda hukairu yaji wannan batu saiya dada kamuwa da tausayin Humaira "yace yake matata ki sani cewa ba a sonraina zan raba ki da 'yar uwarkiba, sai domin mugayen halayen mijinta Nassey ke magana Tabbas bazan iyaci gaba da kallon irin rashin imani da yake yiwa talakawaba tunda banida IKon Hanashi. Ni a rayuwata bantaba marin wani mutumba bare ma muyi kace nace amma shi dan uwannan nawa ba a kwana ba kwai sai yasa ankewa wani hannu kokafa. Sannan yana kwacewa mutane dukiyarsu ko matansu ya maishesu bayinsu. Kituna cewa ahalin yanzu kina da ciki tsawon wata hudu yaza ayina tafi nabarki acikin wannan hali alhalin ina son nakula da lafiyarki da kaina kuma naga abin dazaki haifa. " Sa adda Hukairu yazo nan azancensa sai hukaira ta kara fashe da matsanancin kuka da kyar tayi shiru sannan tace yakai mijina kasani cewa itama 'yar uwata nuzaira a halin yanzu tana. Dauke da juna biyu tsawon watanni hudu dai dai da nawa. Ita haihuwa abuce mai hadarin gasKe. Zan iya rasa rayuwa yayin haihuwar itama zata iya zata iya rasa rayuwarta saboda haka bana son rabuwa da 'yar uwata awannan lokaci, zan so naga ranar da zata haihu. Don haka ina rokonka daka barni na zauna tare da ita har izuwa ranar haihuwarta" Har Hukairu ya budi zaice wani abu sai nuzaira ta tari numfashinsa ta dubi.humaira taceyake 'yar uwata kada ki guji mijinki saboda ni domin shima ba shi da kowa face ke, idan babu ke akusa dashi zai iyashiga mugun hali. Ina son ki bishikutafi tare, kada kidamu dani naayimiki alkawarin komai rintsi bazan haihu ba sai agabanki." Koda jin wannanbatu sai farinciki ya lullube humaira takara kamkame nuzaira tafashe da kuka. Haka dai ta hakura sukayi bankwana suka rabu. Tun da hukairu da humaira suka koma daji basu kara ganin mutumba daga cikin Himsarul Aswad saboda sunyi nesa da garin kimanin tafiyar sa'a bakwai, saidai suna ganin tafiyar fatake. Wani iko na allah yanzu Hukairu da Humaira sunsami tsawon wata hudu A wannan daji inda shi dakansa yagina musu wani narkeken gida. Harda garken dabbobinsu dasuke kiwo da rumbu na ajiye kayan amfanin gona amma ko sau daya 'yamfashi. Ko 'yan sumame basu taba kawo musu hariba. Dalilikuwa shine akwai layar sihiri da wani boka yabashi. Wadda ya binneta a tsakiyar gidansa. Duk wani mugu idan yazo gidan bazai ganshiba koda daranane tsaka. A ranar da cikin Humaira yacika wata takwas ne laulayi yayi mata yawa har ya zamana takasa yin komai. Ka wai saita zauna. A tsakar gidan tana kallon hukairu alokacin da yake baiwa dabbobi acikin garkensu. Koda ta dan jima tana kallonsu sai idanunta suka ciko da kwalla, Hawaye ya fara zuba. Yayin da Hukairu juyo yaga halin da take ciki sai hankalinsa ya dugunzuma yabar garken da sauri yazo gareta ya tsuguna ya rike hannunta yace matata ina dalilin kukannan naki shin jikin kine yake ciwo. Kokuwa ninayi miki badaidaiba ?"Lokacinda humaira taji wannan tambayar sai ta gyadakai tace Ba wani abubane yasa kaga ina zubar da hawaye ba face tunanin cewa abune mawuyaci na sake ganin ranar dani kaina zanyi I rin wannan aiki dakakeyi yanzu domin ina ji ajikina abune mawuyaci na rayu daga hadarin wannan ciki danake dauke dashi." Kodajin haka sai Hukairu yayi murmushi yace. Ki daina wannan tunanin naki kisani dawowatanan bisa umarnin bokanane domin ya tabbatarmin dacewa idan kika haihu acikin gari zamurasa abinda zaki haifa kuma zamurasa duk abinda muka mallaka. Saboda a shekarar daki haihune za ayi mugun fari da cututtuka acikin garin amma mu damuke anan wannan annoba bazata shafemuba. Koda jin haka sai Humaira tayi murmushi cikin karfin hali tace "idan zancenka ya tabbata haka ina fatan "yar uwata nuzaira tazo ta haihu tare dani domin kada annobar ta shafi abinda zata haifa." Hukairu yayi ajiyar zuciya yace "nima ina fatn haKan tafaru duk da cewa nasan halin "yar uwarki macece maicika alkawari. Lailai zata zonan ta haihu tare dake cikin kowane hali. Da gawannan rana hukairu yaci gaba da kulada humaira har cikinta ya tsufa sosai harma ranar da nakudarta tazo. A wannan ranane hankalin hukairu ya dugunzuma ainun domin basu da makota bare yasamo mace wadda zata karbi aikin ungozoma. Amma dayake dama can Yasami cikakken bayani a wajen wata tsohuwar mace tunkafin subaro cikin gari sai yayi sauri ya shigar da Humaira cikin daki ya kwantar da ita akan shimfida ya shiga taimakamata. A wannan lokacine hadari yagangamo aka fara walkiya da tsawa kafin ajima ruwan sama ya kece kamar da bakin kwarya kuma asannane humaira tafara kwalla ihu sakamakon nakudar data zomata. Duk da cewa Humaira nacikin tsananin shan wahala duk sanda ta kwala ihu tayi shiru saita kuma kirawo sunan "yar uwarta nuzaira. Al'amarin dayayi matukar dugunzuma hankalin Hukairu kenan domin yana tsoron cewa idan nuzaira bata zoba har bayan haihuwar Humaira zata iya shiga cikin wani mugun halin dazata zamo sanadin salwantar Hankalinta ko rayuwarta. Kwazam bazato ba tsammani sai hukairu yajiyo sukuwar doki a wajen gidansa kuma adai dai lokacinne kan jaririn yafito daga jikin humaira. Namfa Hukairu yarude yarasa abinda zaiyi shin zai rabu da humairane. Ya ruga waje yagano ko nu zairace tazo. Kokuwa zai tsayane har sai yaga humaira ta haihu lafiya. Yana cikin wasu wasinne yaji humaira ta damki hannunsa da kyar, tace ya kai mijina maza ka ruga izuwa.kofar gida domin ina ji ajikina 'yar uwata ce ta iso kuma na tabbata kodai ta haihu kukuma tana cikin i rin halin da nake ciki. Karka damu dani zan iya kara sa haihu wa da kaina. Cikin matukar damuwa hukairu yace menene tabbacin hakan? Humaira tace shinna taba maka karyane? Hukairu ya girgi za kai yace baki tababa kuma ina gasgata maganarki kamar yadda nake gasgaga maganar ma haifiyata marigayiya. " Koda gama maganar sai ya mike da sauri yaruga da gudu yana fita ya arba da keken doki. Kwance acikin keken dokin nuzairace kaca-kaca da jinin haihuwa gefe kuma ga jaririn data haifa ko motsi bayayi. Itama a kwai a lamun dogon suma tayi cikin razani hukairu ya ruga gareka ya dauki jaririn ya girgiza shi kuma ya kara shi akunnuwansa yaji ko numfashi bayayi. Sai tausayi yakamashi. Adai dai wannan lokacinne kuma yajiyo kukan jarirai acan dakin da ya baro humaira nantake nuzaira tabude idanunta tayi arba da gawar jaririnta data haifa kuma taga hukairu tsaye akanta. Saita fa she da kukan bakin ciki amma da ta jiyo kukan jariri adakin humaira. Sai ta fashe da dariya cikin hanzari subiyun suka ruga izuwa cikin gidan. Da shigarsu cikin dakin da humaira take kwance saisukayi arba 'yan ta gwayen jariranta mata. Guda biyu suna ta tsala kuka.kuma ita humaira ta kasance cikin Koshin lafiya. Fuskarta cike da murmushi. Koda humaira taga nuzaira babu juna biyu kuma babu komai ahannunta sai ta yunkura donta mike tsaye. Nuzaira ta ruga gareta da cikin hanzari ta kwanta tace "kwanta ki huta tukunna yake yar uwata kiyi sani cewa kin zubarda jini mai yawa ajikinki. Kafin nuzaira ta rufe bakinta humaira tatari numfa shinta tace ina abinda kika haifa nuzaira ta kalli hukairu takasa cewa komai sai humaira tayi murmushi tace "yake 'yar uwata ai baki da damuwa tunda 'ya'ya biyu na haifa saiki dauki daya ki barmin daya. " Koda jin wannan batu sai nuzaira ta cika da tsananin mamaki ta dubi hukairu shima sai yayi murmushi yace "yar uwarki tayi gaskiya domin abinda ta haifa nakine koda kuwa guda dayane zan iya amincewa ta mallaka mikishi domin zakiyimishi komai kamar yadda zata yi mishi da kanta. Nuzaira tayi murmushi ta dauki daya Jaririyar ta zauna ta shayar da ita. Bayan dukkaninsu sunnu tsu sai hukairu ya dubi nuzaira cikin tsananin damuwa yace yaya akai kika baro mijinki kika tahonan ba tare da yasaniba shinkin tabbatar baisa abiyo bayan kiba? Nuzaira ta gyada kai tace aidama kun kafi ranar naku dar nayi kyaky kyawan shiri domin na hada baki da kuyangina tuni suntanadi wancen keken dokin danazo dashi. Acan bayan gari kuma acikin dare muka saci jiki muka sulale muka bargarin banyarda wani daga cikin masu tsaro yagammuba kuma suna dorani akan keken dokin na umarcesu dasu share sahun keken dokin don kada aga alamar komai kafinna baro gida kuwa nabarwa mijina wasikar cewa nibazan haihuba acikin garinsa acikin irin wannan lokaci nafari da annoba tun satin jiya gari ya hargitse da wadannan matsaloli. Saboda haka ninasan cewa mijina bazai biyo sawunaba idan yaga wannan wasika. Nikam na zabi na karasa. Sauran rayuwata tare da ku anan har izuwa karshen rayuwata. Sa'adda nuzaira tazo nan azancenta sai hukairu ya jawo kwauran numfashi ya ajiye sannan yace yake Nuzara kiyi sani nasan halin mijinki fiye da kowa aduniya. Tabbas sai yabiyo bayanki danhaka zamanki anan abune mai hadarin gaske. Aduniya babu abinda mijinki yakeso sama da samun magaji. Hanka linsa bazaitaba kwanciyaba idan baiga abinda kika haifaba idan yazo nan ya iske.cewa abin dakika haifa ya mutu. Zai iya hallakamu nida matata da dukkan abida muka haifa. Yazama dole ki dauki wannan jaririya guda daya ki tafi da ita kikoma wajen mijinki. Nayi imani cewa a halin yanzu ya baro gari yataho nemanki. Idan baki tashi kin tafi tafi yanzuba kintareshi ahanya. Tabbas zaizo har nan ya riskemu abinda nake gudu ya faru sai ya faru. Kodajin wannan batu sai nuzaira ta fashe da kukan bakinciki saboda jin cewa zata sake rabuwa da yar uwarta. Cikin tsananin damuwa Humaira ta dubi hukairu tace yakai mijina shin gidannan na dauke da sihirin mugu bai isa yagan shiba? To ai koda dan uwanka Barzuk yazo.nan bazai ga gidan ba kenan. Hukairu ya gyada kai yace ai shima yanaa da irin wannan sihirin nawa kuma yana da makarinsa domin tunmuna yara boka saibur yabamu shi sa'adda mai haifimmu yakaimu gurinsa. Nuzaira bamu da ishashshan lokaci dan haka dole ne ki tashi kiyi shirin gaggawa ki koma cikin gari. " Koda jin sai Nuzaira da Humaira suka fa she da kukan bakin ciki kamar bazasu dainaba nan dai hukairu da humaira suka raka nuzaira wajen keken dokinta suka bata abinci da kayan marmari. Nuzaira ta goya jaririyar da akabata ta rungume humaira suka sake fashewa da kukan bakinciki suka kamkame juna. Da kyar suka rabu har nuzaira ta sa kafarta guda cikin keken dokin saita waigo ta dubi hukairu tace. "Yakai mijin 'yar uwata shin baka tsammanin wannan farin da annoba bazai shafi wannan jaririyar da kuka baniba". Hukairu yayi murmushi yace karki damu ba abinda zaisameta kuma ina tabbatar miki nan da kwanaki kadan wannan fari da annuba zasu kau. " Nuzaira tace wana suna zan sawa ya rinyar?" Caraf humaira tace "kisamata suna YAZILA mukuma zamu sawa tamu suna DABIRA. " Nantake nuzaira ta shiga cikin keken dokinta ta kada linzamin da wakanta tayi gaba. A can birnin Himsarul Aswad kuwa lokacin.Hadari ya gangamo a ka fara walkiya da tsa warnan sai Barzuk yatafi dakin nuzaira domin ya ga halin da take ciki saboda sanin lokacin haihuwarta yayi a ko yaushe zata iya haihuwa. Da shigar Barzuk cikin haraba bankaren nuzaira saiyaga abin mamaki. Bakomai yaganiba face.dukkanin kuyan ginta akwakw kwance suna ta sharar barci al halin lokacin baccinsu bayyiba. Sannan ya ji warin banju yacika gurin gaba daya. Cikin firgici Barzuk ya toshe hancinsa ya ruga izuwa cikin dakin Nuzaira dazuwa yaga dakin wayam babu Nuzaira babu alamarta. Cikin tsananin fushi ya fita daga dakin da sauri ya kwalawa Dakarunsa kira nan da nan kwa dakarun suka rugo gare shi sai ya dubesu yace "maza kuje ku shirya hawa za afita neman matata lallai anzo an saceta batare da bata lokaciba kuwa barzuk yayi gagarumar shigar yaki mai matukar kwarjini. Daban tsoro ya hauwani farin ingarman doki ya jagoranci dakaru dakaru dari biyu suka fice daga cikin birnin. Babban abinda yatayarwa dasu barzuk hankali shine kokadan ba suga sawon da wakaiba bare su san hanyar dayakamata subi. Koda ganin haka sai barzuk yaja linzamin dokinsa ya tsaya cak, suma dakarun nasa sai suka tsaya a bayansa. Nantake barzuk ya dauko madubin tSafinsa ya shafashi da hannunsa take barzuk yagano hanyar da yakamata yabi amma bisa mamaki saiya kasa ganin hoton komai acikin madubin tsafi face hanya kawai al'amarin daya matukar bashi mamaki kenana domin asaninsa gaba daya kasar kisra inbanda sarki Daksur babu wanda ya fishi karfin sihirin tsafi wanda zai i ya hada kafada da shi sai dai dan uwansa Hukairu. Hukairu kuwa ya dade dayin hijira gabarin gari gaba daya to wane ha tsabibinne haka yazo har cikin garin sa ya sace masa mata. Nan dai barzuk yakada linzamin dokinsa. Yayi gaba, dakaru suka bishi abaya duu aguje sai da su barzuk suka shafe tafiyar wajen sa'a hudu sannan suka hango wani keken doki yanufo garesu aguJe cikin mamaki su barzuk suka yi tur jiya kuma suka zare maka mansu suna jiran isowar keken dokin. Tun daga nesa kadan barzuk ya shaida keken dokin yagane na matar sane Nuzaira dan haka sai jikinsa yayi sanyi ya maida ta kofinsa cikin kube ya sauko da gakan dokinsa ya ruga izuwa keken dokin. A gabansa keken dokin yayi turjiya yayi arba da matarshi Nuzaira rike da linzamin dawakan fuskarta cike da annuri kuma tana dauke da goyan jariri abayanta al'amarinda ya matukar bashi mamaki kenana. Cikin tsananin farin ciki ya kama nuzaira ya sauketa dagakan keken dokin ya rungumeta sannan ya karbi jaririn dake baynta ya kura mata ido yana dariyar farin ciki daga can kuma ya turbune fuskarsa ya dubi nuzaira yace "bani labarinki yake matata wanene yazo ya saceki har cikin gidana, kuma ai na kika haifi wannan tsaleliyar jaririya mai kama dani ainun haka?" Sa'adda Nuzaira taji wannan batu saitayi murmushi tace "yakai mijina kayi sani bansan meya faruba ina cikin turakata sai naji anrufe mini fuska an shaka mini banju ahanci. " Kawai sai farkawa nayi naganni a tsakiyar dokar daji kuma babu kowa a kusa dani sai wasu mutane masu shigar bakaken kaya kuma duk sun rufe fuskokinsu i danunsu kadai ake gani suna rike da muggan makamai. Adadin mutanen yakai dubu. Babban cikinsu ne kawai da Jajayen tufafi bisa jan doki koda naga wadannan mutane sai na firgita abin da jawo tasowar nakudata kenan cikin kankanin lokaci na haifi wannan jaririyar dake hannunka acikin keken doki shugaban wa dannan mutanen ya matso kusa dani yakura min ido sannan ya bushe dadariya. Yace yake matar babban abokin gabata kisani cewa kinyi babbar sa'a da yazamana cewa kina dauke da juna biyu da tuni na hallakaki amma saboda ganin kina dauke da juna biyu shiyasa muka fasa dalili kuwa aduniya bana tausayin kowa sai mace mai juna biyu. Narasa matata ne alokacin da take nakudar haihuwar dana kuma tamutu tabarmin dan, har yau har gobe ina tausayin dan saboda ba shi da uwa. Bisa wannan hujjane zan kyaleki kikoma wajen mijinki wannan karankan kun tsallake harina amma baza ku tsallake na gababa. Koda gama fadin haka sai ya doki daya daaga cikin da wakan keken dokina take suka zabura sukayi tatafiya dani har na hangoku akan hanya wannan shine iyakar abin da zan iya tunawa ya faru gareni ya kai mijina. Lokacin da nuzaira tazo nan azancenta sai barzuk yacika da tsananin mamaki kuma yakamu da matukar farin ciki yace tabbas babban makiyin mune sarki Raihan yaturo aka daukeki domin ya dauki fansar yar uwarsa da na kashe amma bai sami na saraba lallai yazama wajibi naje na sanar wa sarki daksur wannan al'amarin domin mu dauki matakin gaggawa saboda nayi mamakin yadda abokin gabarmu ya shigo har cikin kasarmu ya sace min mata batare da munsaniba yake matata ki sani yau shekara goma dayin auranmu amma bamu taba samun haihuwaba sai yanzu lallai acikin farin ciki nake mara misal tuwa dan haka yanzu da ganan birnin kisra zamu wuce nanunawa sarki wannan kyakykyawar 'ya" dakika haifa mini kuma na gaya masa maganar makiyammu Sarki raihan koda gama fadin haka sai barzuk ya shiga cikin keken dokin ya zauna kusa da nuzaira sannan daya daga cikin yaransa ya hau gaban keken dokin ya fara sarrafa dawakan aka cigaba da tafiya aka nufi hanyar da ta nufi birnin sin. Tunda aka fara wannan tafiya zuciyar nuzaira ta fara bugawa da karfi domin ta tabbatar da cewa da zarar sun isa gaban sarki Daksar asirinta ya tonu bisa karyar data shirgawa mijinta cewa yaran sarki raihanne suka saceta domin shi sarki Daksur ka sur gumin ma tsafine wanda ka iya ganin duk abinda yafaru tun gabannin su isa fadar tasa har aka iso cikin kisra hankalin Nuzaira atashe yake bata da sukuni al'amarin dayasa barzuk ya dubeta kenan yace yake matata lafiya naga kamar kina cikin damuwa? Tunda muka fara wannan tafiya bakice uffanba kuma babu walwala da annu shuwa afuskarki koda jin haka sai nuzaira tayi murmushi tace yakai mijina kasani cewa ban taba shiga fadar sarki Daksur ba da girmanaba saboda tun ina yarinya wata rana sa'adda mahaifina ya je dani naga an sare kan wani mutun a gabana saina firgita ainun na tsandara ihu tun daga wannan rana kullun sai nayi mafarkin wannan abu ina firgita acikin barcina saida ma haifina yanaimi taimako awajen bokansa sannan na daina wannan mugun mafarki yanzu dakace zamu fadar sarki daksur sai mafarkin ya fadomin arai saboda haka nidai bana son shiga fadar sarki Daksur ka samomin masauki agari kafin mu isa fadar. Sa'adda Nuzaira tazo nan azancenta sai barzuk ya bushe dadariya yace kadaki damu yake matata lallai bazanje fadar sarki batare dake. Kamar yadda barzuk yayi alkawari haka abin ya kasance wato da shigarsu birnin kisra sai ya kai nuzaira cikin wani ka sai taccen gida irin na sarakai wan da ke dauke da komai na jin dadin duniya harda baruri da kuyangu masu hidima. Al'amarin daya matukar bata mamaki kenan domin bata ga lokacin da aka biya kudin hayar gidanba kuma da zuwansu kofar gidan ta ga masu gadin gidan sun tsube kasa sun kwashi gaisuwa har nuzaira ta bude baki zata tambaye shi batun wannan gida sai yace saboda me zakiyi mamakin mallakar wannan gida agareni ? Shin kin manta ina daya daga cikin makusan tan sarki? Nuzaira tayi murmushi ta ce bana mamakin mallakar wannan gida agareka amma ina mamakin dalilin da ya hana ka sanar dani labarinsa Barzuk yayi murmushi yace sonake na shamma cekine nabaki mamaki kinga kenana zamu tare a sabon gida nuzaira tace yanzu idan katare anan birnin ya zakayi da wakilcin sarki a kauyen Himsarul Aswad? Barzuk yayi dariya yace aiba tarewa zanyi ananba kece dai zaki tare a cikin birnin nan domin na fison 'yarmu tataso da wayewa ta zama cikakkiyar 'yar birni mai waye war kai in yaso duk kar shen mako nazo nata fi daku tare kubi yun. Bayan barzuk ya nunawa Nuzaira bangarenta a cikin wannan gida harta shiga ciki ta kwanta tana hutawa kuyangi suka fara mata shidima sai barzuk yayi shiri yata fi izuwa fadar sarki daksur. Fadace kasaitacciya wadda aka kawatata da kayan alatu iri iri tamkar aljannar duniya sarki daksur na zaune bisa wata kerarriyar kara gar mulki ta ka saita fadawa sun kewaye shi a tsakiyar fadar ga wasu tsala tsalan 'yammata sai tikar rawa suke cikin mummunar shiga mai baiyana tsaraicinsu. A kaida duk sa'adda sarki ke kallon wadannan 'yammata yayin da suke tikar rawa yana dariya da murmushi amma a yau sai sarki ya tur bune fuska babu annuri atare da shi koka dan kuma tun da ya fito fadar haka ya ka sance cikin rahin walwala da sukuni kallo daya mutum zai masa yasan yana cikin tsananin bacin rai. Al amarin daya matukar dugun zuma hankalin fadawa kenan domin sun sancewa fushin sarki ba karamin ta shin hankali bane agaresu gaba daya. A na cikin wannan haline akaga hakimi barzuk ya shigo fadar cikin farinciki kamar wanda aka yiwa albishir din mulkin duniya cikin sauri har da hardewa barzuk ya isa gaban sarki Daksur ya zube kasa ya kwashi gaisuwa ya dago kai domin yayiwa sarki baya nin abin farin cikin da ya sameshi sai sarki yayi farat ya tashi tsaye kawai sai ya dubi barzuk yace kabiyoni izuwa cikin dakin gani ina son magana dakai a sirrance. Koda gama fadin haka sai sarki Daksur yanu fi dakin gani nanfa Barzuk ya bishi da sauri aka bar fa dawa da jama'ar gari a zazzaune sun yi tsurutsuru da idanuwansu suna mamakin abin da ke faruwa. Yayin da sarki Daksur da Barzuk suka shiga dakin gani sai sarki ya tsaya a tsaye maimakon ya zauna ya juyo suka fuskanci juna shida Barzuk yace kazone kayi mini aibishir bisa cewa matarka ta haifi "ya" mace koba hakaba? Cikin muryar rawar murya burzak yace hakane ya shugabana Daksur yace tokasani kasani wannan "ya" data haifa ba "yar ka bace "yar" dan uwanka ce Hukairu amma ita matarka "da" na miji ta haifa kuma a mace yazo duniya hakika matarka ta yau dareka kuma karya ta shiryama domin ka jaddada magana ta yanzu zan nuna maka duk abubuwan da suka faru azahiri. Kagani da ida nuwanka. Gama fadin hakan ke da wuya sai sarki yayi nuni da hannunsa izuwa ga jikin bango take hoton al'amarin suka rinka gudana tun lokacin da Nuzaira tayiwa 'yar uwarta Humaira alkawarin cewa lallai awajenta zata haihu har lokacin da aka bata jariri yarnan koda ganin wannan al'amari sai barzuk ya kwarara uban i hu cikin tsananin bakin ciki jikinsa gaba daya ya kama tsuma ka wai sai ya zare ta kofi ya juya da nufin yaje ya sare kan Nuzaira amma sai sarki daksur ya daka masa tsawa ya tsaya cak ya juya ya durkusa bisa gui wowinsa a gaban sarki daksur ya mayar ka takofinsa bisa kubenta ya sunku yar da kansa kasa alokacin da hawayen ta kaici yake zubo masa yace ya shugabana yanzu me ya kamata nayi? Sarki dak sur yayi ajiyar numfa shi sannan yace ya kai Barzuk kayi sani bisa bin ciken da nayi idan muka ka bar matarka da wannan "ya da aka bata wannan fari da annoba da muke fama dasu a gari zasu kare nan da sati biyu kacal gari zaiyi lafiya amma inda masifar take shine wannan jaririyar da matrka ta zo da ita idan har ta girma zama gawur tacciyar jaruma kuma maya kiya fiye da sarkin yakinmu sadauki Hauzar bin Mausus duk yakin da muka taro sai ta sami nasara amma fa duk sanda ta san sirrin tsafina mun banu mun lalace sai mulkimmu ya rushe. Kuma sai talakawanmu sun zama shugabanninmu sun dauki fansar zaluncin da muka dade muna yi musu tsawan shekara da shekaru ta han ya daya ce ka dai zamubi kada azo da ita fadata kada abari tayi arba da fuskata kuma kada ka nunawa matarka bacin ranka koka gaya mata abin da muka tattauna anan yanzu A can daji kuwa inda manomi hukairu yayi gidansa suna wayi garine a cikin farin ciki da bakin ciki dalili farinkinsu shine na haihuwa da humaira tayi nayaya tagwaye mata duk da cewa tayi kyautar byar goda ga rayuwarka nuzaira shi kuwa mummuna mafarkin wanda himaira tayi a jiya da daddare da safe sa adda humaira ta farka daga bacci ta fara bawa mijinta hukairu labarin mafarkinda tayi a jiya al amari daya matukar dugunzuma humaira duk hankalinsa kenan dalili kuwa shine a iya saninsa da matarsa humaira duk abin datayi mafarkinsa saiya tabbata a gaske. Bawani abu humaira ta ganiba acikin mafarki ba face saukar wadansu dakaru kamar daga sama wadanda suka bukawa gidan wuta ya kone kurmus babu abin da ya tsira. Lokacin da hukairu yaji labarin mafarkin da humaira tayi sai hankalinsa ya dugunzuma ainun rasa abin dake masa dadiya shiga tunani mai zurfi daga can saiya dubi ita humaira yace yake matata kinsani cewa wajibine a garemu muyi hijra mubar gabadaya yankin wannan kasa tamu idan har muna son mu da abin damuka haifa mutsirada rayuwarmu naji ajikina cewa sarki daksar kasurgumin matsafine don haka na tabbatar da cewa abinda ya faru tsaka nimmu da 'yar uwarki nuzaira ya gani kuma ya nunawa barzuk bisa wannan da lilinne za su turo a hallakamu lokaci yayi da zan gaya miki wani sirri wanda bantaba gaya mikiba. Tun muna yara nida dan uwana barzuk bokan ma haifina wanda muka sami sirrikan tsafi a wajensa yace mana cewa agaba daya kasar nan babu wani mahaluki mai karfin sihirinmu face sarki daksar amma duk 'yar da muka haifa idan tayi arba da idan sarki daksar to zata samu duk irin sihirin da sarki daksar yake da shi a cikin kwana uku harta samu nasarar Hallaka shi ta hau kan kara garsa face ya kasheta kafin cikar kwana uku shi kansa sarki daksar ya san da wannan sirri don haka bazai taba barin abun da muka haifa arayeba dun haka ba zai barmuba yazama wajibi muyi shirin gaggawa yanzu muyi hijira mukara gaba. Sa adda hukairu yazo nan azancensa sai humaira ta ce yanzu ina kake tsammanin zamu shiga mu buya ba tare da sarki daksar yaturo an kashemuba Hukairu yace waje daya ne zamu iya zuwa muyi rayu wa acan kuma mu tsira daga sharrin sarki daksar da dan uwana Barzuk. Bawani waje bane face birnin misra inda sarki Raiyan ke mulki. " Koda jin haka sai idanun Humaira suka zazzaro tace "ya ya za ayi muje birnin misra kuma muyi rayu wa alhalin mutanen can sun kasance musulmai mukuma ma abota tsafine da gunki? Humaira tace "shin ka manta ne sarki daksur bashi da wani makiyi wan da yafi sarki Raiyan na birnin misra? Ai idan sarki raiyan ya fa shinci cewa mu mutanen birnin kisra ne sai yasa anyi mana kisan gilla domin ya dauki fansar ran 'yar uwarsa gimbiya Numaira wacce sarki daksur ya ka she yayin da aka fafata kazamin yaki da su a shekaru uku baya. " Hukairu yayi ajiyar numfashi sannan yace "duk nasan da wannan al'amari amma abinda nake so ki fahimta shi ne abinda ya koro bera yafada cikin wuta ya fi wutar zafi. " Koda gama fadin haka sai hukairu ya mike tsaye yakama hada kayyayyakinsu domin suyi hijira. Bayan ya gama hada hada komai a waje guda ya dora a kan rakumansa wasu kuma akan shanunsa sai yaje tsakiyar filin gidan ya haka rami sai ga shi ya tuno wata laya. Nan take ya rataya layar a wuyansa, sannan yakira Humaira ta fito da ga cikin daki goye da jaririyarta. Ba tare da bata lokaciba suka hau kan ra kumansu biyu sukayi gaba suna janye dabbobinsu. Koda hukairu ya juya ya dubi gonarsa da wannan gida nasa sai idanunsa suka cikoda kwalla saboda takaicin ya tafiya bAr kasa mai albarkar noma wadda abu ne mawuyaci ya sake samun irinta. Bayan kamar sa a hudu da tafiyar hukairu da matarsa humaira sai ga sarkin yaki haizar bin mausus bisa doki tare da dakaru dari biyar suna take masa baya dukkaninsa dauke da muggan makaman yaki tun daga nesa haizar ya dauko wani gilashi na sihiri wanda sArki daksur ya bashi ya ce da shi da wannan gidashi ne kadai zai iya hango gidan hukairu. Haizur yasa gilashin a kan idanunsa amma bai hango komaiba dan haka sai suka kara kaimin gudu bisa da wakansu. Jim kadan da faruwar haka sai suka hango gidan daga can nesa. Daya daga cikin daka runnasane ma ya fara hangowa ya nuna masa al'amarin daya matukar ba shi.mamaki kuma yaba shi tsoro ya fara tunanin duk yadda a kayi su Hukairu basa gidan kuma lallai ya tone wannan laya wacce sarki daksur ya bashi labarin cewa hukairu ya binneta a tsakiyar gidansa. Tun da ga inda suka hango gidan Haizar yabada umarnin a fara harba kibiyar wuta izuwa gidan. Ai kuwa cikin kan kanin lokaci gidan gaba daya ya kama ya kama da wuta yana ci balbal. Su sarkin yaki haizar suka karqso gaban gidan aguje bisa dawakansu suka yiwa gidan kawanya kuma suka dana kwari bisa baka suna jira suga wani abu mairai yayi fitar burgu don ceton ransa su harbeshi amma hargidan yagama konewa kurmus yazama toka ko kyanwa basu ganiba. A sannanne sarkin yaki haizar ya sakko daga dokinsa ya duba tsakiyar gidan nan take kuwa yayi arba da wannan rami wanda hukairu tone ya cire layarsa ta sihiri. Cikin tsananin ta kaici da fushi haizar ya kwarara ihu sannan ya dakko mudubin tsafinsa ya shafeshi sau uku yana mai karanta wadansu dalasiman tsafi guda uku. Faruwar hakan keda wuya sai ga fuskar sarki daksur ta bayyana akan madubin suka dubi juna. Kafin haizar ya budi baki yace wani abu sai sarki daksur ya tari numfa shinsa yace "maza ku ruga gaba domin tuni Hukairu da matarsa sunyi nisa, taza rarku da su ta kai nisan sa'a hudu. Idan kuka yi sakaci suka shiga yankin kasar misra shi ke nan baza ku taba riskar suba. Tun da hukairu na tare da wannan laya baza ku taba ganin koda sawunsuba amma i dan kayi amfani da wannan gilashin sihiri da na baka zaka i yaganin sawayensu. Idan har kana son kariskesu sai kunyi ta fiyar kwana uku bayada zango babu barci. Idan har kasami nasarar cika wannan aiki kana dawo wa birnin kisra zanbaka wazircina kuma zanbaka dukiya ninkin goman abin da ka mallaka a yanzu. Koda gama wannan jawabi sai fuskar sarki daksur ta bace bat, daga cikin madubin sarkin yaki haizar nan take yaji farin ciki ya lullubeshi dan haka sai yaruga kan dokinsa yayi tsalle ya haye kan dokin ya zabure shi cikin matsanancin gudu koda ganin haka sai suma ragowar dakarun suka sakarwa dawakansu linzami suka rufa masa baya. Lokacin da ake wannan mugun artabu tsakanin Hukairu da Zaihar tuni humaira ta isa bakin kofar birnin misra amma sai ta ja linzamin ra kumin ta ta tsaya cak ta kasa shiga birnin ta juyo cikin ta shin hankali tana kallon gumurzun da akeyi tsakanin mijinta da sadauki zaihar. Lokacin da sadauki zaihar yaga wankin hula zai kai shi dare sai ya fusata ya fara amfani da karfin sihiri domin ya hallaka hukairu amma sai ya ga ashe shima hukairu ba kyalle bane abangaren tsafi domin karfi ya zo daya. Haizar yaja da baya yaduru daga kan dokinsa ya tsaya cak a waje daya yana tunanin dabarar da ya kamata yayi. Koda ganin haka sai shima hukairu ya duro daga kan ra kuminsa ya gyara tsayuwa yana mai fuskan tarsa sannan ya kyalkyale da dariya yanuna haizar da dan ya tsa ya ce "ya kai wannan tsohon azzalumi ba wan azzalumai ka sani burin mai gidanka bazai cikaba a kan iyalina domin sun tsira daga sharrinkku a yanzu tunda sun haye iyakar kasarku. Ko a yanzu ka kashe ni bani da na damar komai. Yayin da haizar yaji wannan batu sai shima ya kyalkyale da dariya sannan yace "ai kuwa yanzu zan kasheka sannan nabi iyalinka har bakin kofar birnin misra suma na hallakasu tun dadai sun kasa shiga cikin birnin sun tsaya suna kallo domin suga irin mutuwar dazakayi. " Koda jin wannan batu sai hukairu yajuya da sauri domin ya dubi bakin kofar birnin misra kafin ya juyo da kansa tuni Haizar ya zaro wata wuka siririya mai kaifi da tsini ya wur gamasa take wukar ta cake atsakiyar kirjinsa ya dur kushe bisa guiwowinsa koda humaira ta hango abinda ya faru da sai ta tsandara uban ihu al'amarin da ya janyo hankalin masu gadin kofar birnin misra kenan suka rugo waje da gudu rike da makaman yaki suda yawa. Yayin da sarkin yaki ya hango fito war wadannan mayaka sai ya juyo da sauri ya ruga izuwa kan dokinsa na sihiri ya zabure shi da gudu yanufi baya. Ita kuwa Humaira sai ta diro kasa daga kan ra kuminta ta falfala da gudun tsiya tana kuka izuwa inda mijinta yake durkushe. Koda zuwanta gabansa sai ta tabashi sai taji ya bingire kasa ko motsi baiyiba alamar cewa yamutu ba shi da rai nan fa ta rungume gawarsa tasake fashewa da matsanancin kuka. Tana cikin wannan haline dakarun misra suka zo gareta suka banbareta daga jikin gawar da karfin tsiya suka tafi da ita izuwa cikin birnin misra tana ta iface iface da koke koke tamkar sabuwar mahaukaciya. Wannan shine abin da ya faru ga Humaira matar Hukairu bayan srkin yaki ya riskesu ya kashe hukairu, ita da jaririyar sun tsira A can birnin kisra kuwa lokacin da hakimi barzuk ya koma wannan gida nasa inda ya ajiye matarsa nuzaira sai ya shaida mata duk wadannan dokoki wadanda sarki daksur ya shimfida masa a kan jaririyar data haifa ko da jin wadannan dokoki sai ta cika da tsananin mamaki ta dubeshi tace to wai shin laifin me mukayi harda sarki zai kafawa yarmu irin wadannan dokoki masu tsauri dayawa haka?” Koda jin wannan tambaya sai barzuk ya tumbune fuska yace ” ni kaina bansan daliliba amma babu mamaki akwai babbar hujja data janyo mana hakan saboda haka indai kIna son mu tsira rayuwarmu da mutuncinmu lallai kikiyaye wadannan dokoki ” daga wannan rana kowa nuzaira tacigaba da renon jaririyarta da ranar suna tazo sai aka radawa jaririya suna yazila tunda nuzaira ta acikin wannan gida na mijinta acikin birnin kisra batata bin hanyar gidan sarauta ba bare ma taga sarki da idanunta bare kuma jairiyar datake raino. Tafiya sannu sannu kwana nesa darare na wucewa kwanaki na shudewa sai aka wayi gari yarinya yazila ta cika shekara bakwai a duniya nan da yazila tazama sananniya a birnin kisra saboda kasancewarta tataso da tsananin kyau dakuma jarumantaka domin tun a sannan tana iya daga kato komai girmansa ta rankwalashi da kasa har sai datakai cewa ana shirya mata gasar kokawa da mazaje majiya karfi tana zama zakarar gasar daga nan kuma sai lamari nata kara samun cigaba domin ta fara koyon sarrafa takofi`mashi`kwarida baka. Duk mutumin daya fara koya mata amfanida kayan yaki sai yaga tafi kwarewa acikin kwanaki uku kacal. Tun da yazila ta taso taga wata farar laya a wuyanta bata son abin da zai rabata da layarba dare da rana har kwanciyar barci kuwa. A takaice dai batata cire layarba kuma tana iya tuno lokacin da mahaifiyarta hakimi barzuk ya samata layar sa adda batafi shekara biyarba aduniya. Koda wasa yazila batata bin hanyar gidan sarki ba kuma kojitayi sarki zai shigo cikin gari tobazatataba fita daga cikin gidan domin a rayuwarta babu data tsana tagani ko taji zancensa face sarki. Abinda batasaniba shine. Wannan laya da aka rataya mata awuya itace sanadin dataji batason taga sarki. Ana nan cikin wannan hali har yazila ta cika shekara goma sha takwas. Alokacin ne kyawunta yaruda gaba dayan jama ar birnin kisra ya zaman cewa duk inda mutun yaje saidai yaji ana labarinta. Afagen jaruman taka kuwa al amarin maya wuce tunanin mai tunani domin duk sa adda aka fita yaki da mutanen birnin misra tana ya musu mummunar barna wata jaruma guda daya takeci mata tuwo akwarya wadda itace sarkin yakin mutanen birnin misra a wani lokaci ita dai larziya taji ana yiwa jarumar kirari da basadaukiya dabira babban abin takaita awjen yazila shine batataba ganin fuskar wannan abokiyar gaba tata ba domin duk sa adda zata fito yaki tana rufe fuskarta ne da hular karfe. Akalla yazila da dabira sun fafata kazamin yaki kamar sau hudu amma duk sa adda suka hadu.kare jini biri jini sukeyi. Koda rauni suka yiwa juna sai kaga raunin yazo adadi daya baya gotawa sukansu suna matukar mamakin wannan al amari babu irin kokarin da yazila batayi ba don ganin ta cire hular karfen datake dabira taga fuskarta amma abu ya gagara. Akwai.wata rana da dabira ta tambayi bokanta wanda ake kira mushrid bin affan tace dashi yakai abin dogarona yaza ayina sami nasara akan abokiyar gabata absadaukiyar dabira na kai kasa kuma har na cire hular karfen dake kanta naga fuskarta ?” Koda jin wannan tambaya sai boka mushrid ya kyalkyale da dariya sannan yace ” idan har kina son ki sami wannan nasara sai dai ki cire wannan laya dake wuyanki kije har cikin fadar sarki daksur ku yi arba da juna in dai kikayi haka sai kin nasara akan jaruma yazila har kiyi.mata rauni sama da adadin wanda zatayi miki. Kuma ki kaita kasa ki cire hular karfen dake kanta kiga fuskarta amma ki sani cewa ranar da wannan tashin hankali irin wanda baki tabaga shigarsab” Koda jin wannan babu sai jaruma yazila tasa hannunta ta kama wannan farar laya dake wuyanta da nufin ta cireta amma sai ta ji kamar an soka mata allura guda dubu a sassan jikinta. Ba shiri ta saki layar ta kama ihu kuma ta fadi kasa a matukar galabaice tana haki wadda aka yi yunkuri zare ruhinta. Nan ta jike sharkaf da gumi da kyar ta dago da kanta ta dabi boka mushrid tace ” meya sana kasa cire wannan laya daga wuyana kuma taya ya zan iya rabuwa da ita ?” *WACCE AMSA BOKA MUSHRID ZAI BAIWA JARUMA YAZILA? *YAUSHENE JARUMA YAZILA ZATA YI ARBA DA FUSKAR SARKI DAKSUR? *YAYA AKAYI BASADAUKIYA DABIRA TAZAMO SARKIN YAKIN BIRNIN MISRA? SHIN ITAMA TA ZAMA MUSULMA CE? *I NA LABARIN MAHAIFIYARTA HUMAIRA? *SHIN NUZAIRA DA HUMAIRA ZASU SAKE GANIN JUNA? MUHADU A JARUMA YAZILA NA BIYU DON JINCIGABAN WANNAN LABARI. . JARUMA YAZILA Littafi na daya Na Abdul'aziz sani madakin gini Created and design by:- Shuraih Usman Publishing shuraih Usman From http://shuraih.waphall.comAn dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT