706 650 5625: *👄MUGUN FURUCI*👄 *WRITING BY AMEENATU SANI* *_Wannan labarin kirkirarran labari ne banyarda a juyaman shiba ta kowace siga_* *JIGWAN LABARIN*_:Akan mahaifin da yayi *MUGUN FURUCI* Akan budurwar d'an shi inda kuma tsautsayi ya fada mashi, shikuma d'an yazama lauyan mahaifin yarinyar_. *SADAUKARWA ga my friend DARMA* *NASARA WRITERS ASSOCIATION* {{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }} https://www.facebook.com/103637491942644/ 💫💫 *{{N W A}}* 💫💫 بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم PAGE 1_5 "Haba Habeeb in baka fadaman damuwar kaba waye zaka fadamawa?, kasandai ni mahaifinka ne duk duniya babu Wanda yakaini sanka amma ace Abu na damunka kaki sanar dani haba barrister" daga kwancen da Habeeb yake ya dago ya kalli mahaifin nashi yace "Abba saidai katayani da addu'ah amma ni inaji ajikina mutuwa, zanyi Abba Santa shine zaiyi ajalina Dan Allah kayafeman" da sauri Abba ya matso kusa da Habeeb din yace "my son Dan Allah ka fadaman wacece kake so, kuma kake cewa Santa zai kashe ka itadin yar gidan ubanwa ye agarinnan?" Habeeb yace "Abba zuciyata ta kaini da nisa salma bata sona tace har abada ba zata soni ba!" atsawace Abba yace "Habeeb wacece salma nace" Habeeb yace "y'ar gidan Alhaji Lukuman Wanda kuke Neman kujerar chairman kaida shi". Hular kanshi Alhaji Muhammad yacire yayi fifita da ita kana yaja ajiyar zuciya yace "lallal zuciya batada kashi, Habeeb gaskiya zuciyarka batayi maka adalci ba da har taso diyar abokin karawata, kasani sare koda ace Yarinyar tana sanka Alhaji lukuman bazai taba yarda ka aureta ba, nidai amatsayina na mahaifinka inamai baka shawarar. kayi hakuri da ita kaci gaba da addu'ah Allah yabaka wadda tafita" tashi yayi yafita Yaja mashi kofar, Karo sukaci da Hajiya Fadeela dake kokarin shiga dakin Habeeb da sauri tace "Alhaji lafiya dai, ko jikin Habeeb din ne ya matsa?" Girgiza kai yayi yace "wato Hajiya akwai matsala babba" tire din Lemon da ta dauko ta saki kasa ya tar watse ta buga salati tace "Alhaji Dan Allah karka ceman Habeeb ya mutu, innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!" zata kwasa da gudu zuwa dakin Habeeb din Alhaji Muhammad ya dakatar da ita yace "Hajiya bai mutu ba amma lalle yana dabda mutuwa Wanda nikuma bazanbar hakan ya faruba indai ta sanadiryar yarinyar nan zai mutu". Hajiya tace "wace yarinya kuma Alhaji?" Alhaji Muhammad yace "wato Habeeb duk ciwon nan da yakeyi Ashe saboda yarinyar gidan Alhaji lukuman ne Santa yakeyi ita kuma bata sanshi". Hajiya ta zaro ido tace "Alhaji lukuman dai danasani Wanda kuke Neman kujerar chairman?" Alhaji yace "itafa, kuma kinsan dai yanda Alhaji lukuman ya tsaneni bazai taba bari Habeeb ya auri y'arsa ba". Kan kujera Hajiya Fadeela ta zauna ta dafe kai tana addua akan Allah ya sausautama Dan nata. Bayan kwana biyu Habeeb bayaci baya asha rarrashi na gidan duniya iyayenshi sunyi amma yaki yaci duk yabi ya ramai kullum cikin fadin sunan Salma yake. Yanzu haka Alhaji Muhammad ya dawo daga office yashigo ya sami Hajiya Fadeela sai magiya takema Barrister Habeeb akan ya daure yaci kada ciwuka su tarar mashi. Jin gina kai Alhaji Muhammad yayi ajikin kofa can ya dago yace "Habeeb nalura kana san yarinyar nan dayawa,shikenan bari naje na roki Alhaji lukuman da yataimaka yabaka auranta koda kuwa bata sanka ne, ai ita macece zata soka wata rana" Da sauri Habeeb ya tashi daga kwancen da yake yace "Abba mutafi tare kodan naganta na roketa ta tausayaman ta soni". Kai Abba ya girgiza yace "Habeeb jikinka babu kwari kabari ninaje insha Allah komi zaitafi daidai" Habeeb yace "Abba Dan Allah mutafi tare wlh ko ganin ta nayi nasan zansami sauki". Da sauri Hajiya Fadeela tace "Alhaji kuje tarai din wata kila a dace" Haka kuwa suka tafi tare sai gidan Alhaji lukuman... *_Yawan comment yawan typing, masoya wannan salonshi na da banne👌🏻_* *Ameenatu Sani ce* 08065522770 [4/18, 5:10 PM] +234 706 650 5625: *👄MUGUN FURUCI*👄 *WRITING BY AMEENATU SANI* *_Wannan labarin kirkirarran labari ne banyarda a juyaman shiba ta kowace siga_* *JIGWAN LABARIN*_:Akan mahaifin da yayi *MUGUN FURUCI* Akan budurwar d'an shi inda kuma tsautsayi ya fada mashi, shikuma d'an yazama lauyan mahaifin yarinyar_. *SADAUKARWA ga my friend DARMA* *NASARA WRITERS ASSOCIATION* {{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }} https://www.facebook.com/103637491942644/ 💫💫 *{{N W A}}* 💫💫 بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم PAGE 11_15 Wani kallan ukku saura kwata yayi mashi kana yace "kaga malam tashi kaficeman daga gida please" yafada yana nuna mashi kofa Alhaji Muhammad yace "nifa zuminci nazo mu kulla tsakani na dakai, domin 'Dana yaga y'ar ka yana so". Sai a wannan lokacin Salma ta d'ago ta kalli alhaji Muhammad da Habeeb, dayake tunda suka shigo bata dago kai ta kalli kowa ba. Shiko Habeeb yama shagala da kallanta kacokam hankalinshi na garaita jiyake kamar ya dauketa daga gidan yamaidata gidansu da gashi sai ita yanuna mata tsantsar qaunar da yake mata. Salma idanunta ta tsayar kan Habeeb nan take taji wata wutar tsanarshi taqara ruruwa a zuciyarta da sauri ta taso daga inda take tana nuna shi da yatsa tace "waikai mayan inane?,dady miyakawo wannan marar zuciyar gidammu?nace bana sanshi bana kaunar shi amma dayake wawa ne yaki ya fahimta." Wani shi'umun murmushi alhaji Lukuman yasaki tare ta murza gashin bakinshi haryaji sanyi aranshi daya kasance Salma batasan Habeeb. Yace "kinga daughter yishirunki banni dasu" kallan Alhaji Muhammad yayi da ya daskare a tsaye tun jin irin kalaman da Salma ke jifar d'anshi dasu yace"kai kana tunanin har akwai ranar da zan iya hada jini dakai? To inkana tunanin haka kama daina tun wuri Dan zaren ba irin yadin bane,Dan haka ja d'anka kubarman gida konasa afitarman daku" Alhaji Muhammad yabuda baki zaiyi magana Salma ta qaraso gaban shi tace "dama Kaine mahaifin shi? Haba shiyasa Ashe naji nakara tsanar shi Dan haka kajama d'anka kunne koshi mayene ni nafi karfin shi wlh kuma bazantaba sanshi ba koda zai mut......saukar mari taji akumatunta Alhaji Muhammad ya kasheta da qwararan maruka har biyu ya d'aura da cewa " kedin y'ar gold ce ko lu'ulu'u da Habeebu bazai rabu dake ba?,marar tarbiya kawai" qarar Habeeb yaji ya fadi qasa dafe da zuciyarshi yasa bai qarasa maganar shiba yayi kan Habeeb din ya tallaboshi yace "Habeebu bude idanunka Dan Allah Ashe dama yarinyar batada tarbiyya kaketa wahalar da rayuwar ka a kanta?" Wani tari Habeeb yayi sai gudajin jini yabiyo baya daqyar yabuda baki yace "Abba mutafi gida". Alhaji Lukuman da wani baqin ciki yarufe zuciyar sakamakon marin da akaima y'arsa yace "kaini zakazo har gida kadakarman y'a, aiko wlh sainayi shari'a dakai koda wa kake takama". Afusace Alhaji Muhammad yace "andaka din kaje kayi abunda zakayi" yanuna Salma da hannu yace "ke kuma wlh inbakiyi wasaba sainayi Ajalinki Dan akan 'Da na babu abinda bazan iyaba" kama Habeeb yayi yace "muje habeebu" Fita sukayi daga parlorn Alhaji Lukuman sai bala'i yake yanakiran "Muhammad in baka kashe man Salma ba kaiba Dan sunna bane kuma wlh kajira sammaci akan Marin dakayima y'ata" Afusace Alhaji Muhammad yace ma isah driver yaja motar zuwa hospital aiko batare da bata lokaci ba suka isa medical hospital cikin kankanin lokaci likitoci suka hau duba Habeeb ganin babban 'Dan d'ansiya babu lafiya Kusan awa daya kana likita yafito daga dakin yasamu Alhaji Muhammad dake tsaye sai safa da marwa yake awajan yace " yella6e muje office mana" Alhaji Muhammad yace yajikin habeebun doctor?" Likita yace da "sauki ranka yadad'e muje office" kana yayi gaba Alhaji Muhammad yabi bayan shi Zama sukayi su duka kana doctor Auwal ya cire farin gilas din dake makale ga idanunshi yamiqama Alhaji Muhammad hannu yace "barka ranka shidade" musabaha sukayi kana doctor Auwal yayi gyaran murya yace "wato Alhaji, Habeeb Sam yakasa cire damuwa a zuciyar shi bayan nasheda maku zuciyarshi tanadab da kamuwa da ciwo amma ankasa daukar mataki akai" Zazzafar iska Alhaji Muhammad ya huro kana ya muskuta yace "nidai doctor Dan Allah ayi abinda ake ganin yadace wajan ganin Habeeb yasamu lafiya" To "insha Allahu Alhaji indai za abi dokokin da za'a gindaya masa , kana ayi kokarin ganin ansa dashi da abinda yake so insha Allah zai samu sauki" takarda yajawo yayi Dan rubutu akai kana yamikama Alhaji Muhammad yace "ga wa innan magungunan za'a samosu saiyayi amfani dasu" Karba yayi ya duba kana ya zaro kudi yamiqa mashi yace "doctor ayi amfani dasu wajan siyan duk abinda ake bukata" Karba yayi yayi godiya kana yace "da ruwan da akasa mashi yaqare zaku iya tafiya gida" Shima Alhaji Muhammad godiya yayi kana yabaro office din jama'ar dake bisa barandar sai gaisheshi suke domin sunganeshi dakin da Habeeb yake yashiga, yananan kwance lokaci guda harya qara wata irin rama bacci yake ga qarin ruwan da akasa mashi sai tafiya yake ahankali, wayar shice tayi qara zarota yayi ganin Hajiya Fadeela ce ya daga abangaran Hajiya Fadeela yana dagawa tace "lafiya dai Alhaji inata kira baka daga ba?" Numfashi yaja kana yace "inafa lfy gamu nan hospital Habeeb babu lafiya" arikice Hajiya Fadeela tace wace asibiti Alhaji!?" "Medical hospital" kett ta datse wayar ta nufo asibitin..... *_tofa kunadai ji yanzu akafara wasan,innaga comment yanda nake so zancigaba, gamai bukatar document din YANAR GIZO complete saiya tuntubi number ta👇_* *Ameenatu Sani ce👌* 08065522770 [4/18, 5:10 PM] +234 706 650 5625: *👄MUGUN FURUCI*👄 *WRITING BY AMEENATU SANI* *_Wannan labarin kirkirarran labari ne banyarda a juyaman shiba ta kowace siga_* *JIGWAN LABARIN*_:Akan mahaifin da yayi *MUGUN FURUCI* Akan budurwar d'an shi inda kuma tsautsayi ya fada mashi, shikuma d'an yazama lauyan mahaifin yarinyar_. *SADAUKARWA ga my friend DARMA* *NASARA WRITERS ASSOCIATION* {{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }} https://www.facebook.com/103637491942644/ 💫💫 *{{N W A}}* 💫💫 بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم PAGE 26_30 Wata irin tafiya Isah driver keyi a saman titi kamar yana tsoran kwaltar Alhaji Muhammad dake bayan mota hakimce yana duba jarida yadago yace "wai Isah mike faruwane kakejan motar kamar baka so?" Bai kulashi ba yaci gaba da tukinshi, cike da mamakin shirun da Isah yamashi yakara magana "wai Isah hala bakaji minace ba ne?" Daidai lokacin kuma motar su Salma tawuce ai da sauri Isah driver yace "wlh Alhaji kaina ke ciwo" parking yayi a gefen hanya yace "Dan Allah Alhaji kaja motar nan wlh bazan iya tukinba yanzu juuwa nake gani" dayake Alhaji Muhammad sauri yake batare da wata damuwa ba yafito ya zauna wajan driver shi kuma Isah driver yakoma wajan mai zaman banza Alhaji Muhammad yaja motar da karfi suka tafi Isah driver kamar bashine ya lankabeba yace kanshi na ciwo ba sai baza idanu a titi yake can yaga sunkusa taddo motar su Salma aiko ya fakaici idanun Alhaji Muhammad ya taka giyar motar da karfi jikake kuuuuuuuuuuuuuuuu gammmmm daki motar su Salma cikin minti daya wani mummunan hadari ya afku a titin domin ko motar su Salma tayi wani raga raga mutane suka taru sai sallallami ake ana San fito Dana cikin motar. Alhaji Muhammad salati ya dauka tunda motar ta fizgesu shiko Isah driver kira yake Alhaji zaka kashemu to adaidai wannan lokacin motar ta daki tasu Salma motar na tsayawa Alhaji Muhammad yafito yana salati innalillahi wa'inna'ilaihir raji'un agigice yanufi wajan motar mutane sun taru dayawa aka Ciro Salma da driver ko kadan ba wanda ke motsi da sauri aka sasu motar Alhaji Muhammad akatafi asibiti mutane sai kira suke "masu kudi basuda imani jibafa Dan yana Dan siyasa irin gudun dayake a titi"zagin Alhaji Muhammad kawai ake mutane dayawa suka bi motar zuwa asibiti Isah driver irin cikin irin yarude din nan kira yake "Alhaji saida nace karkayi kisa karkayi" Amma kakijin maganata, innalillahi wa'inna'ilaihir raji'un muyau munbani!" emergency aka shigar dasu cikin yan muntuna likitoci suka taru akansu dayake a kusa da junction abin yafaru akwai yan Sanda a wajan ba asha wahalar ansar suba Alhaji Muhammad duk yarude tunda yake tuki tsautsayi baitafa fada mashi ba sai yau kira yake "Dan Allah doctor's karku bari sumutu wlh bada gangan ba" mutane sai kira suke Alhaji da gangan fa kature su irin gudun da kakeyi kamar titin ka". Shikuwa Isah driver fakar idanun jama'ah yayi yabar wajan,wata number yakira ana dagawa yace "Alhaji mai afkuwa fa ta afku muna medical hospital yanzu haka ketttt" yakashe wayar yadawo cikin jama'ah. Wajan minti goma saiga motocin Alhaji Lukuman sun shigo harabar asibitin cikin sauri ya sauko daga cikin motar yashige emergency din daidai da likita ya fito nan yadakatar da shi cikin hausar dabata ida bin harshenshiba yace "yi hakuri mana muje ana dubasu" kira yake "doctor kataimaka itace diyata kwal a duniya karta barni Dan Allah" da 'kyerdai aka fito dashi daga ciki doctor yace "Kaine mahaifin yarinyar?" Alhaji Lukuman yace "eh wancan kuma driver ne" Da sauri Alhaji Muhammad ya matso yace "doctor ya jikin nasu?" Ai wata irin juyowa Alhaji Lukuman yayi nan suka hada ido da Alhaji Muhammad aiko yakaimashi wata cabka a wuya yace "Ashe Kaine ka bankeman Salma? haba Muhammad minayi maka a rayuwa da kake Neman rayuwar Salma Ashe da gaske kake saikaga bayan ta haba Muhammad". shidai Alhaji Muhammad baiyi tunanin Salma ce ya bankeba sai da yaga Alhaji Lukuman. nan jama'ah sukayo caaaa anaba Alhaji Lukuman hakuri da 'kyardai yasaki Alhaji Muhammad dayaji matsa a hannun Alhaji Lukuman Nan doctor yace "yanzu dai Ku biyoni office nayi maku bayanin abinda ke faruwa" Office din doctor sukaje waje yanuna masu su zauna kamun yafara koro masu bayani "to Alhaji saifa hakuri"..nan take gaban Alhaji Muhammad yafadi da sauri yace "innalillahi wa'inna'ilaihir raji'un don Allah doctor karka ceman sun mutum" shiko Alhaji Lukuman wani shu'umun murmushi yayi cike dajin dadin kudurunshi yakusa cika. Zaman glass din shi doctor ya gyara ganin yanda Alhaji Muhammad ya rude kana yace "cool down Alhaji babufa Wanda ya mutu Duk kanninsu suna numfashi saidai sunji jiki harkarama namijin da sauki buguwa ce yayi akai sai glass daya yanke shi a fuska ita kuma macen gaskiya tabugu sosai domin hannunta na dama yakare glass ya shigarmata a fuska saikuma kananun ciwoka Amma gaskiya bata farfado ba haryanzu mundai yimata allure Wanda zasusa ko tafarka ta farka a cikin hayyacinta shi kuma namijin ya farfado maybe ma zuwa anjima a sallamaishi because jikin shi da sauki. Wata sassanyar ajiyar zuciya Alhaji Muhammad yasaki yace "alhamdulillahi Allah nagodai maka da katsareni da yin kisan kai!". Shi kuwa Alhaji Lukuman kaidagani kasan baiwani ji dadin labarin ba yanayin fuskarshi ta nuna hakan Amma inkagani saikace duk cikin jimami ne. Alhaji Lukuman yanuna Alhaji Muhammadda yatsa yace "kuma wlh inasan kasani jinin diyata bazai tafi abanza ba dama kace saikaga bayanta to shine yanzu kanemi ka aikata ko?, to Wlh sainayi shari'a dakai koda kuwa zanyi yawo tsirara, yo anfada maka siyasa haukace Dazaka nemi kasheman diya?" Cikin kwantar da murya Alhaji Muhammad yace "kayi hakuri Alhaji Lukuman wlh wancanma Dana fada *MUGUN FURUCI* ne nayi wlh bada gangan nabigeta ba tsautsayi ne yafada kaina wlh am...."dakata malam Adana kalaman ka ko kasamu nafada gaban alkali dannan bazasuyi wani tasiri ba" Alhaji Lukuman ne yakatse Alhaji Muhammad da karfi... _gaskiya nakusa daina typing din book din nan_ *Ameenatu Sani ce* 08065522770 [4/18, 5:10 PM] +234 706 650 5625: *👄MUGUN FURUCI*👄 *WRITING BY AMEENATU SANI* *_Wannan labarin kirkirarran labari ne banyarda a juyaman shiba ta kowace siga_* *JIGWAN LABARIN*_:Akan mahaifin da yayi *MUGUN FURUCI* Akan budurwar d'an shi inda kuma tsautsayi ya fada mashi, shikuma d'an yazama lauyan mahaifin yarinyar_. *SADAUKARWA ga my friend DARMA* *NASARA WRITERS ASSOCIATION* {{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }} https://www.facebook.com/103637491942644/ 💫💫 *{{N W A}}* 💫💫 بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم PAGE 16_20 Batare da bata lokaci ba Hajiya Fadeela ta iso hospital din alokacin Habeeb yasamu bacci sakamakon allurar da akayi mashi,cikin kujerun da aka tanada Dan masu dubiya suka samu suka zauna. Bangaran gidan Alhaji Lukuman kuwa koda barin Alhaji Muhammad gidan sai ya koma yanata zagayan parlorn tare da buga hannu Hajiya Mariya ta muskuta daga zaunan da take tace "wai Alhaji wannan abun da yafaru duk miyaka woshi harda yake maganar zaiyi ajalin Salma? Nisawa Alhaji Lukuman yayi kana yace " banni dashi wlh danshi ko zai mutu bazai taba auran ya taba koda kuwa ita Salma tana sanshi bare ma bata sanshi". *______________________________* Napep ce tayi parking gaban wani Dan karamin gida madaidaici mai karamin get wata kyakkawar budurwa ce tafito daga ciki hannu ta rike da jikka sai rigar lauyoyi sallamar mai napep din tayi kana ta fara tafiya cike da natsuwa kauran get din ta tura tashiga gidan bayada hayaniyar komi acikin shi amma gidan yahadu daidai na masu rufin asiri. A parlor tayi sallama wata kyakkawar matace zaune a kan kujera ta fa dada murmushi a fuskarta tace "oyoyo ga *MEENAL* barka da dawowa!". Itama MEENAL murmushi tasaki tace " thanks you Ammi" zama tayi a kan kujera tace washhhhh Ammi nagaji dayawa wlh" Ammi tace ai MEENAL sai kin daure tashi zakiyi ki watsa ruwa ga abinci can na tanadar maki yau abinda kikafi so na girka a gidan" baki MEENAL tawashe tace kai amma wlh naji dadi sosai Ammina Bari naje ciki mikewa tayi ta kwashi jikkarta da kayanta ta shige dakin ta Da kallo Ammi tabita harta shige cikin Dan madaidaicin dakin nata,da shigarta kayanta ta hau cirewa kana ta shige toilet takai 20mint da shiga kana tafito tana tsane ruwan kanta da Dan karamin towel basilin da kwalli kawai ta shafa tasa wata doguwar Riga baka da pink din hula yar yayi parlorn ta shigo a lokacin Ammi harta kawomata Abincin a tsakiyar daki zamatayi kana ta soma cin danwaken tana yima Ammi santi gami da bata labari. ______________________________ Kwanan Habeeb 3 asibiti jiki yayi sauki alhmdlh lillahi domin har ansalla maishi yana dakin shi shida abokin shi Hisham suna fira hisham yace "nikau barrister nabaka shawara mana!" Habeeb yadan muskuta kana yace "Inajinka",Hisham yace " Naga duk ka daura damuwa akan lamarin nan daya faru barrister yakamata kasanya hakuri da dangana a lamarinnan Salma dai ba ita kadai bace mace a duniyar nan ga mata nan k...... "Dakata Hisham shawara kace zaka bani koko umarni ne?" Hisham yace "aikaga matsalar ka Habeeb kai ba'ataba fada maka gaskiya imdai akan wannan yarinyar ne, Salma tafito ta nunama duniya bata sanka ubanta ma ya nuna baya sanka Amma ka like mata why Habeeb?". Tashima Habeeb yayi daga kwancen dayake yashige toilet yace " saikuma kayi da Wanda kagani" Kai kawai Hisham ya girgiza ya haye gadon yayi kwanciyar shi Alhaji Lukuman ne zaune a office din shi murmushi kawai yake saki yana sauraron labarin da Alhaji Bala ke bashi, saida ya gama tsab kana Alhaji Lukuman yace "Bala ka ganni nan wlh komi nasama gaba a rayuwata sainaga nasa maishi barai wata kujerar chairman, taibur din gabanshi ya buga hadi da mikewa tsaye yace kalleni nan Alhaji Bala badai su Alhaji Nabadi da Alhaji Sabo sun yi saranda da Neman kujerar ba? Hmmmm Alhaji Muhammad shi mai kunnen kashi yace ya nanan akan ba kanshi ba nasan zama chairman ba? To albishirinka yau saura sati naya zabe?" Alhaji Bala yace "3" Alhaji Lukuman yayi murmushi hadida zagayowa yafara taku daya bayan daya a office din kana yace "nanda Lokacin saina sanya Alhaji Lukuman nadamar shigowa gonata saina nuna mashi ruwa ba a San kwando bane domin kuwa kila kamun lokacin har mala iku sunyi mashi tambayoyin kabari". Idanu Alhaji Bala ya zaro kana yace "kana nufin kashe shi zakasa ayi kenan?, tonidai banbaka goyon bayan aikata hakaba domin mutane dayawa sai anyi zarginka ka ka daganan kujerar da kake so zaka iya rasata Ku.....hannu yadaga mashi yace " babu Wanda zansa ya kashe shi sai hukuma da kanta". Alhaji bala yace "taya kenan kuma zata kashe shi ?" Alhaji Lukuman yace "wannan tambayar yakamata ace tunfar ko kayiman amma katsaya zaka bataman lokaci,kawo kunanka kaji shirin danayi amma zan fada maka ne saboda nayarda dakai banida wani amini daya wuce kai shiyasa" Kunnanshi Alhaji Bala yakayo,rada Alhaji Lukuman yayi mashi daga bisani suka sheke da dariya Alhaji bala yace "kai Amma wlh dole aji tsoranka Lukuman wato kai akan dukiya babu abinda bazaka iya aikatawa ba ko?" Alhaji Lukuman yakoma mazauninshi yace "kware kuwa Bala ciki ko harda salwantar da rai.......... ________________________________ *TALLA! TALLA!! TALLA!!!* *Assalamu Alaikum* *Ina yan'uwa masu sha'awar shiga kungiya ta online writer? To albishirinku😊 kakar tayanke sa'ka👌 Kuma damace agare Ku sabuwar kungiyarmu mai suna 💫💫NASARA WRITER'S ASSOCIATION💫💫 tana maraba da kowa da kowa duk mai sha awar shiga kungiyar kinada damar shiga bako sisin ki👌* *Ina tsofaffin hannu da sababbin hannu wa inda basuda kungiya? Maza hanzarta domin kasan cewa daya daga cikin members din cikin ta💃💃 domin a dama dake* *Ina masu San gwada basirar su wajen fara fadakar da Al'umma ta hanyar rubutun Hausa novel? Kungiyar mu tana maraba da ke yar uwa indai kina da sha awar zama online writer* *Domin neman Karin bayani saiku tuntubi daya daga cikin number's din nan*👇 08065522770 08104335144 *NASARA WRITER'S ASOCIATION* 💫💫 _*{{Nasara abin so ga kowa ,domin marubuta da cigaban rubutu al'kalaminmu y'ancinmu.}}*_💫💫 *Ameenatu Sani ce* 08065522770 [4/18, 5:10 PM] +234 706 650 5625: *👄MUGUN FURUCI*👄 *Writing by Ameenatu Sani* PAGE 31_35 Bayan komi yadaidaita Alhaji Muhammad yabiya duk wani kudi da aka bukata na asibiti, haryanzu dai hankalin shi baiwani kwanta ba addu'ah kawai yake Allah yatashi kafadunsu lafiya, waya yabugama iyalanshi yasanar dasu halin da ake ciki Amma ba a sanar da Habeeb ba. Shimadai Alhaji Lukuman yasanar da Hajiya Mariya aikuwa ba karamin dadi taji ba jin cewa Salma bata mutu. Asibitin duk suka shiryo suka zo duba su. Alhaji Lukuman ne zaune a motar shi shida Alhaji Bala dubanshi yayi a fusace yace "wlh yanzu haka Isah beyi aikin nan yanda yakamata ba mswwww yanzu yatsira kenan?" Wata dariya Alhaji Bala yayi yace "wlh harka bani dariya Alhaji Lukuman, ainasa duk tantirancin ka ya zarce duk yanda nake zato Ashe baikai ba? Ainasa yanzu wata maganar ake ba wannan ba". Wani kallo Alhaji Lukuman yayi mashi yace "kaga Bala karka tunzurani wlh kasandai halina ko? To shikenan cigaba da dariyar kagani". Alhaji bala yace "aidole nayi dariya, waima jira kai baso kake Salma ta mutu ba kuma laifin ya rataya akan Alhaji Muhammad ba?, Kuma sai aka samu akasi yarinyar bata mutu ba?" Alhaji Lukuman yace "aikasan burina kenan duniya naga an wulakanta Madu an mashi kisan wulakanci kamun kuma yamutu zuciyar shi ta buga,aini wannan shine babban burina wlh". Wani murmushi Alhaji bala yayi yace "to kwantar da hankalin ka burinka zaicika yau basai gobe ba". Alhaji Lukuman yace "tayaya kenan?" Alhaji bala yace "ai ida kasheta za ayi kawai tunda kace haryanzu bata farfado ba kaga daganan kowa yasan shine yakasheta koba haka ba?" Alhaji Lukuman yace good haka ne Amma tayaya zata mutu?" Alhaji bala yace "ta hanyar yimata allurar guba doctor ko nurse kawai zaka cika da kudi kace sokake ta mutu wlh da gudu zasu aika ta bakaga duk arna bane kuma kasandai arna da kudi". Hannu ya miko mashi suka kashe yace "wlh aikin ka nakyau bala kai babban shegene kasan takan duniya wlh, ai kuwa haka za ayi yanzu bari naje komi kenan zamuyi waya" "Ok normal saina Jika" kana ya sauka daga motar Baiyuce ko inaba sai gida Akan daya daga cikin kujerun parlorn ya zauna sai zuba murmushi yake yace "Madu (Muhammad) kabani indai da sharrina ne yanzu wasan yafara wlh sainaga ankashe ka har lahira kana hankalina zai kwanta" Kiran number Hajiya Mariya yayi dayake tanacen asibiti tana d'agawa yace yi sauri dawo gida ina jiranki" yanke wayar yayi ya cigaba da sambatun shi Mintuna kadan saiga motoci sunyo mata rakiya tana shigowa parlorn tace "lafiya kuma?" Wani murmushin yakara yi yace "zauna mana tana zama ya fara fada mata duk yanda sukayi da Alhaji bala saida ya ida fada mata kana ta zubamashi wata uwar harara tace "Amma wlh daga kai har bala bakuda imani ainasa tunda har Salma ta tsallake tarkon Ku nasa tatsira, to bari kaji wlh ko duniya za'abani bazan taba yarda a kashe Salma inaji ina gani ba, ai wannan maganar banza ce wlh karama Ku canza shawara". Wani naushi ya kaima kujera yace "waini miyasa banida sirrine? Miyasa komi zanyi saina fada maki? Da ace ban sanar dake ba aida baki isa kifada man magana ba to bari kiji wlh yanda na tsara shirin nan babu ubanda ya isa ya dakatar dani kuma yau basai gobe ba Salma zata mutu". Hajiya Mariya dataga yanda yake tada jijiyoyin wuya kuma tasan tabbas zai aikata komi yace saita Dan sabko tace "naji Salma zata mutu Alhaji Amma ba mutuwa ta har abada ba zadai ta mutu a idon duniya Amma mu agaremu bata mutu ba". "Kamar ya" cewar Alhaji Lukuman "kamar dai yanda kaji nafada inasan Salma bazan juri rashin ta ba Amma yau dinnan zamu fitar da ita kasar waje sai muhada baki da doctor yasamo wata gawa mai irin jikin Salma sai a rufeta kar mubari kowa ya bude gawar muce Salma ce ta mutu kaga ko yansanda zasuyi bincike basusan Salma ba saidai karmu bari Wanda yasanta yaga gawar ai shikenan ko?" Wani banzan kallo yayi mata yace "Amma wlh Mariya bakida hankali taya hakan zata faru? ke wannan shawarar taki batayi ba ki canzata tun wuri". Nan dai Hajiya Mariya taita kawo mashi misalai harya gamsu da bayabinta yace "to bari naje su hadu da doctor Din". Bayan yaga doctor sunyi magana nan danan doctor ya amince da bukatar Alhaji Lukuman Amma saida ya tura mashi makudan kudi ta account kana yace yanzu cikin dare zasu canza ita salmar Amma lalle yanzu su naimi jirgin da zai tashi zuwa anjima tana fitowa su wuce haka Alhaji Lukuman yabi shawarar doctor yaje ya kammala komi na tafiyar Salma nan da d'ayan dare jirgin zai tashi. 6:00am "Innalillahi wa'inna'ilaihir raji'un wayyo Allah ni Mariya Salma Dan Allah kitashi wlh bazan iya rayuwa babu keba wayyo Allah na!" Doctor kira yake "kiyi hakuri Hajiya kiyi hakuri" Alhaji Muhammad yana shirin zuwa asibiti sai yaji ana buga kofa Hajiya Fadeela tace "daure Alhaji kayi break din bara naduba kowaye" kofar ta bude security din gidan tagani tace "lfy dai office?" Cikin rawar murya yace "Hajiya babu Lfy ga police's can bakin get sun tare ko ina yanzu haka gidannan zagaye yake da police's kowa kaga fuskar shi kasan babu imani Hajiya kum....bai ida maganar ba saiga wasu police din su shigo wajen Hajiya Fadeela tace "yallabe Lfy ko" daya daga cikin police din yace "matsa babu hanya" suka shige ciki Alhaji Muhammad yadago yagansu zaiyi magana suka ce "yu a onda aress" Alhaji Muhammad ya zaro ido yace "Lfy!?" "Alhaji anbamu umarni damuzo mutafi dakai In munje can kaji mikayi" Alhaji Muhammad yace "Toni miye hadina da police? Amma muje" keyarshi suka tusa hajiya Fadeela tace "innalillahi wa'inna'ilaihir raji'un miyayi maku Dan Allah?" Alhaji Muhammad yace "Hajiya nima nan kaina bansan minayi ba Amma in munje naji ai ciki da gaskiya wuka bata hudashi" har ciki mota suka shiga kana sukabar unguwar da jiniyi....... _Turkashi_ *Ameenatu Sani ce*👌 [4/18, 5:10 PM] +234 706 650 5625: *👄MUGUN FURUCI👄* *Writing by Ameenatu Sani* *NASARA WRITER'S ASSOCIATION* 36_40 Alhaji Lukuman ne gaban gawar Salma sai zabga kuka yake da sambatu kamar wani zautacce likitoci da yan sada sai hakuri suke bashi yayinda Hajiya Mariya take a wani gadon kwance wai suma tayi bayan angama duk abinda za ayi aka fito da gawa zuwa gida domin ayi mata sallah akaita makwancinta da kyar suka fito suka shiga mota sukabar harabar asibitin. Ana fita da Alhaji Muhammad sai Hajiya Fadeela tai sauri ta dauko wayar ta kiran number Habeeb tashiga yi Amma Sam bata shiga wayar abokin shi Hisham takira yana dagawa tace "Hisham kuna tare da Habeeb?" Hisham yace "a'a mummy bama tare yanzu dai ya fita". Hajiya Fadeela tace Dan Allah Hisham kace mashi komi yake yi yau ya baro Kaduna yazu gida" "Lafiya dai mummy? Cewar Hisham?". "Hisham babu lafiya" kettt takashe wayar itama tabi bayan su ________________________________________ "MEENAL wai yau bazaki fita bane?" "Ammi wlh yau Sam banajin dadi kuma yau munada wata shari'a banajin fitane kawai". Ammi tace "lalle agajiye kike MEENAL yanda nasanki baki wasa da aiki to 'kara ki huta Amma kitashi kiyi break saiki koma baccin" "to shikenan Ammi". Fitowa daga cikin bargon tayi tashige toilet wanka tayi kana tayi brush ta fito shiryawa tayi kana ta samu Ammi a parlor tana kallo tace "Ammi kallo kike?" "Eh ai kinsan shike debeman kewa da kin tafi aiki" murmushi MEENAL tayi tawuce tana cewa "aiko Ammi yakamata asamo mai tayaki fira because TV tana iya gundurar ki" Kitchen tashiga ta dauko break din ta zauna kusa da Ammi suna kallo. Tace "gaskiya Ammi yakama a nemo mai aiki a gidannan kinga ta tayaki fira ko yakika gani?" Ammi tayi murmushi tace "aa yar albarka nikad'e ai zan iya zama kuma kinga y'ay'an y'an uwa suna zuwa duk suna debe Mani kewa". "Allah Ammi banaso kina kad'eci shiyasa nace haka" "a,a MEENAL to lokacin da kikayi aure fa? Aikin gani dole na saba". Fuska MEENAL tarufe tace kai Ammi". Ammi tace "waike MEENAL miyasa duk lokacin da zanyi maki zancen aure sai kin nuna jin kunya Da alamun baki so? Kuma ni gidannan bantaba ganin inda yau wani saurayi yazo wajen kiba mike faruwa? ya kamata nasani domin yanzu kinkai lokacin da za ace kinyi aure Amma naga Sam baki da ra ayin hakan" MEENAL ta aje cokalin hannunta takalli Ammi tace "wlh Ammi Sam banasan nayi aure nabarki kita wahala ke daya saidai in tare zamu". Baki Ammi tarike tace a ina akataba haka MEENAL?" Baki ta tura gaba tace "abar maganar Dan Allah Ammi,bari nabaki labarin sari'ar da mukayi jiya"..... Alhaji Muhammad zaune a gaban dpo " Dpo yace "Alhaji Muhammad fatan kasan laifin mi kayi aka kawoka nan?" Alhaji Muhammad yace "ranka ya Dade ni bansan mi nayi ba". Dpo yace "yazaka rainama hukuma wayau kace bakasan mikayi ba, to kisan kai kayi" Zaro idanu Alhaji Muhammad yayi yace "kisankai kuma wana kashe". Dpo yace "yanzu dai mu umarni akabamu mu kamoka yanzu kotu za amika ka inkaje cen saikayi bayani" "Innalillahi wa'inna'ilaihir raji'un kisan kai kuma ni? haba yallabe ni din nayi kisa?" Dpo yace "kai sajan" wani Dan Sanda ya shigo Dpo yace "Ku shiga dashi ciki ku rufe" "Yes sir" kana ya cema Alhaji Muhammad "tashi muje". Ankammala hada gawa har an wuce da ita domin sadata da makwancinta Yayin da mata sai rike Hajiya Mariya ake ana bata hakuri nan ko da tashiga cikin hijabi dariya take tayanda shirunsu ke tafiya daidai. A gaggauce Habeeb ya dawo tunda ya duro garin yaji mike faruwa hankali tashe yanufa gida Amma mai gadi yamashi bayanin "ai babu kowa gidan anwuce da Alhaji police station Hajiya ma kila can tanufa".aiko kiran Hajiya yayi ya tambayeta "wace station ce suke" nan tafada mashi ya wuce can shida Hisham.... *Ameenatu Sani ce👌* [4/18, 5:10 PM] +234 706 650 5625: *👄MUGUN FURUCI👄* *WRITTEN BY AMEENATU SANI* *NASARA WRITER'S ASSOCIATION* 41_45 Da isarsu station din yaga Hajiya rakube a bango ta zabga uban tagumi hawaye sai zubar mata a fuska suke da sauri ya karasa gateta yace "mommy miyasa kike kuka ina Daddyn?" Hajiya bata iya cewa komiba illah hawaye da ke zarya akan fuskar ta Hisham ne yace "Habeeb Mommy bazata iya magana ba yakamata muga dpo" aikuwa haka akayi suka nemi aimasu iso wajan dpo batare da bata lokaci ba suka shiga bayan sun gaisa Habeeb yace "ranka yadade Sunana barrister Habeeb Muhammad *HM*". Dpo yace "ai nagane ka" Habeeb yace Ok to nazone akan maganar mahaifina bana garin ne akakirani miyayi yallabe?" Wani murmushin takaici dpo yayi kana yace "gobe case din zaikoma kotu kaji komi ya aikata" Habeeb yace "nidai nasan mahaifina bazai aikata wani mugun abuba yallabe adai sake bincike kamun akai kotu" dpo yace "ai laifin nashi a bayyane yake wannan ma basai an wahalar da shari'ah ba za ayanke mashi kukunci daidai da abinda ya aikata na kisanka" murmushi Habeeb yayi yace "badai mahaifina ba gaskiya" kafad'a dpo ya daga yace "Ok ainaga kai babban lauyane maizaman kanshi kuma ka kware wajan zakulo mai gaskiya da marar gaskiya nasan tabbas zaga gano gaskiya don haka zaka iya fara bincike wajan gano gaskiya kamun alkali ya bukaci hakan" kai Habeeb ya jinjina yace "insha Allahu yanzu don Allah ina bukatar ganin shi" dpo yace "gaskiya barrister kayi hakuri bazaka ganshiba a yanzu" murmushin takaici yayi kana yace "to shikenan". Bayan sun fito ne ya lallashi Hajiya akan sukoma gida komi zaizo da sauki insha Allah haka suka koma gida cike da jimamin abun.. Alhaji Lukuman kuwa bayan an rufo gawar da akakira da sunan Salma yanufo gida jama'ah sai gaisuwa suke mashi shikuwa sai share hawanyen munafurci yake yabukaci ganin dpo akan adaga kai karar kotu harsai an gama zaman gaisuwa amma acigaba da tsare shi. Bayan kwana biyu da mutuwar, Alhaji Lukuman suka haduda Alhaji bala Alhaji Lukuman yace "to Bala kagadai shirina yanata tafiya daidai yanda na tsara babu matsalar da aka samu ko?" Alhaji bala yace "hakane Lukuman nikaina ina mamakin yanda shirin ke tafiya daidai" wani murmushi yayi kana yace "to yanzuma wani shirin zan sake kullawa kuma nasan zaitafi yanda nake so" Alhaji bala yace "to wane kuma shiri zakayi bayan gashi burinka zai cika nasan ganin bayan Alhaji Muhammad?" Wani murmushin Alhaji Lukuman yakara yi yace "ai bazaka gane bane bala nifa wlh har abada bazan so ace Ahalin Alhaji Muhammad sunyi farin ciki ba, wai ko kanada labarin Alhaji Muhammad dan uwa nane ubammu daya dashi?" Idanu Alhaji bala yazaro yace "Dan uwanka kuma? Taya yazama Dan uwanka?" Alhaji Lukuman yace "manta da wannan, ni yanzu burina shine bayan an kashe Alhaji Muhammad sai kuma duniya ta zagi danshi Habeeb uwarsa ta tsine mashi kana daga baya itama uwar nasan yanda zanyi da ita" Alhaji bala yace "taya kuma hakan zata faru?" Alhaji Lukuman yace "ta hanyar yima Habeeb asiri a daran yau yazama shine lauyana kuma yayi tsaye tsayin daka harsai yaga nayi nasara alkali ya yankema Muhammad hukuncin kisa, Kaga duniya zata zageshi akan yana lauya amma yagaza kare mahaifinshi uwar shi zata tsine mashi ta dalilin haka kila intaji za'a kashe Muhammad zuciyar ta ta buga nan take ta mutu kagani nayi nasara shikenan burina na shekara da shekaru yacika". °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°′°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° Shiri take a gagauce tomin ta makara da hanzari tafito daga dakin ta tashiga dakin Ammi zaune ta isketa tana lazimi jiranta tayi hartakai karshe kana tace "Ammi Nina shirya zan wuce" Ammi ta dubeta tace "to ga break din ki can ki dauko ki karya kamun ki tafi" "Aa Ammi wlh banada isasshen time lokaci na kurewa yanzu barrister umar yakirani ni ake jira zamu shiga meeting karfe shabiyu munada wata shari'ah kuma kinga Tara takusa" Ammi tace "waike MEENAL miyasa bakisan karyawa ne inzaki fita? Tun dazufa nake tashinki daga bacci Amma kinki tashi dama nasan karshen ta bazaki karyaba zaki fita" mikewa tayi tace "ayi hakuri Ammi bari natafi dashi can naci" Ammi tace "to hakan yayi" tana kokarin mikewa MEENAL ta dakatar da ita tace "haba Ammi sha zaman ki bari na zuba" Da sauri ta zuba abincin a kula tayima Ammi sallama tafita abakin titi take tsaye tana tsaida mai napep bayan ya tsaya tafada mashi inda zata tashiga suka wuce Da saukarta kawarta jiddah ta iso tace "kai Amma wlh MEENAL nawarki tayi yawa tunfa dazu nake tsaye wajannan ina jiranki Amma sai ceman kike gaki a hanya" dariya MEENAL tayi tace "sorry besty wlh Ammi ce tamatsa sainaci abinci bamma Ciba kinganshinan nazubo" karbar kular tayi tace "kai Amma Allah yasakama Ammi da alkhairi wlh kinsan kuwa yunwa nakeji tunda matsa maki akayi kawonan ninaci" kular MEENAL ta sakarmata tace "aidama ke a cici ce wlh saikita kaya, dazu Brs.Umar yakirani wai ni ake jira naga kuma kamar ba ashiga ba ko?" Jidda tace "to aidai kinsan halin umar burinshi yazo ya ga kema kin iso shiyasa Amma yanzu za'a shiga" kai kawai MEENAL ta girgiza sukaci gaba da tafiya Karfe shadaya suka fito daga meeting din suna zaune Jidda nacin abinci MEENAL ko waya take latsawa umar na gefansu sai surutu yakema MEENAL tana dariya sama sama can umar yace "wai madam ya maganar mu don Allah? haryanzu kinki bani amsa ta" MEENAL tace "ayya Barrister don Allah abar maganar nan kagadai yanzu akwai aiki gabana" Barrister umar yace "to shikenan madam kardai kimanta Ina sonki! koba yanzuba ina jiran amsarki please" Jidda tace "lalle Barrister kaima sai wahalar da kanka kake akan wannan y'ar ba'kar" MEENAL tace "eh aba'kar kuma ya nace ko?" dariya sukayi su duka daidai da lokacin Jidda tagama cin abincin kuka tashi domin gabatar da shari'a *_Ameenatu Sani ce👌_* [4/18, 5:10 PM] +234 706 650 5625: *👄MUGUN FURUCI👄* *Writing by Ameenatu Sani* 51_55 Da sauri ya karasa gareshi jijjigashi ya hauyi yana kiran "Habeeb! Habeeb!!" Amma Sam Habeeb baya motsi da kyar ya fito dashi daga toilet din kan gado ya shimfidar dashi yaciga ba da jijjigashi amma har yanzu shiru da sauri Hisham ya dauko ruwa masu sanyi a firiji ya shafama Habeeb a fuska wani dogon numfashi yaja kana ya sauke ajiyar zuciya amma baibude idanshi ba Hisham yace "Habeeb bude idonka mana" zuciya Habeeb ya dafe murya na rawa yace "ba..ni.....maaa...gaaani na". Hisham yace "to, sannu Habeeb bari naje nakawo maka ko tea ne nasan bakaci komi ba tun jiya". Baijira cewar saba ya bar dakin kasancewar ansan Hisham sosai a gidan shiyasa kai tsaye yanufi parlor mai aiki ya gani tana goge goge nan yamata magana "tayi sauri ta hadoma shi tea mai kauri" da "toh" ta amsa kana ta shige Kitchen mintuna Kad'an ta kawo tea din Hisham ya karba, kwance ya samaishi ya dafe kai da kyar Hisham ya lallabashi yayi kurba ukku da tea din kana ya ballar masa maganin da yake sha dayake akwai maisa bacci cikin kankanin lokaci ya kama bacci. Bargo Hisham ya ja ya rufeshi da shi kana yabar dakin parlor ya fito yaga mai aiki yace "tayi mashi magana da Hajiya", bayan mintuna Kad'an saigata tana saukowa Kaida ganinta kasan tasha kuka zama tayi akan kujera Hisham yace "ina kwana Hajiya?" Hajiya tace "lafiya lau" Hisham ya gyara zama yace "am Hajiya Dan Allah kiyi hakuri akan maganar da Habeeb yayi, wlh baida lafiya wannan abun daya faru duk ya rudar dashi yarasa nutsuwar shi,yanzu haka na ba shi magani harya samu bacci insha Allah daya farka zaidawo normal" Hajiya tadanyi murmushi tace "bakomi Hisham Allah yabasa lafiya" "Amin Hajiya" cewar Hisham kana ya kara da "fadin Hajiya nazone akan maganar daddy to da muyi maganar da Habeeb amma nasamu baida lafiya yanzu ya kike ganin za mu fara bullo da maganar?" Hajiya ta fashe da kuka tace "wlh Hisham Alhaji bai kashe wannan yarinya ba kawai ajalinta ne ya biyo ta hannunshi" nan tacigaba da kuka kamar ranta zaifita Hisham yace "kiyi hakuri Dan Allah Hajiya insha Allah babu abinda zai faru da daddy, yanzu bari na je station din naji ina akatsaya inma takama naje har gidan Alhaji Lukuman din sai naje" Hajiya tace "to Hisham an godai Allah yasaka da alkhari" Hisham yace "amin Hajiya ai duk yima Kaine" Nan yasa kai ya bar gidan.. Dariya suketa shekawa a mota Alhaji bala yace "gaskiya Lukuman kai din bakaramin shu'umi bane hahahahaha" Alhaji Lukuman murza gashin bakinshi yayi yace "waikai Bala haryanzu baka ida Sani naba ko? To bari kaji da wannan hannun nawa na kashe mahaifimmu Dan kawai na mallaki dukiyar sa kaga kuwa ai babu Wanda bazan iya kashewa ba, Muhammad ne kawai bazan iya kashe shi da hannu naba nafiso a yimashi kisan wulakanci a gaban idanu na" Alhaji bala yace "wai to Alhaji Lukuman jiya kace man shi Muhammad din mahaifinku daya to taya hakan ta faru?" Kamun Alhaji Lukuman yayi magana wayarsa tafara ringing dagawa yayi ya amsa wayar kana bayan ya gama yace "Bala taka mota muje"... Ameenatu Sani ce👌 08065522770 [4/18, 5:10 PM] +234 706 650 5625: *👄MUGUN FURUCI👄* *Writing by Ameenatu Sani* 46_50 Da mugun zabure Alhaji Bala ya kalli Alhaji Lukuman yace "wai da gaske kunne na yaji mikace kuwa? Wani muskilin murmushi Alhaji Lukuman yayi yace " wato kana wasa dani ko? To nafada maka sharrina ya wuce duk yanda baka zato, yanzu bari nashiga ciki gobe tunda asuba saimu hadu karakani wajan malamin" Shi dai Alhaji Bala haryanzu yana cike da mamakin Alhaji Lukuman, haka sukayi sallama yatafi. Washe gari tun hudu na Asuba Alhaji Lukuman yayi ma Alhaji Bala waya akan yafito sauri zasuyi tunkamun Jama'ah sufara zuwa . A bangaran Barrister Habeeb kuwa a daran ranar baiyi bacci ba tunani kawai yake taya har mahaifinshi zai iya kashe Salma? Shin da ganganne ko kuwa 'bacin rana ce? Saikuma ya tuna da wani *MUGUN FURUCI* da mahaifin nashi yayi akan Salma _"Ke kuma idan bakiyi wasa ba sainayi ajalinki Dan akan d'ana babu abinda bazan iya ba"_ Da sauri ya Runtse idanuwanshi yace "nooooo daddy!!!, Nasan baka aikata haka ba, bakai bane, ajalinta ne ya biyo ta hannuka". Dafe kai yayi domin yanda yaji yana sassara mashi da 'kyar ya isa kan katafaran bed dinshi ya sulale ya kwanta amma tunani ne cike da kwanyar shi ta gefe daya yanajin zafin mutuwar Salma tunda duk duniya babu Wanda ya kaishi Santa, dayan ban garan kuwa ya kasa gasgata shin tsautsayine ko da gangan ka 'kagare yake gari ya waye ya binciko gaskiya. Yanda yaga dare haka yaga sapiya Tunda gari ya waye Hisham yazo wajan Habeeb daya kasa fitowa Kwance yasa maishi cikin bargo saurin karasawa gareshi yayi yace " Barrister ashedai da gaske baka fito ba?, gashi har tara ta wuce" tashi yayi daga kwancen da yake yace "to ai zuwanka gashi na tashi" Hisham ya zauna bakin gado yace "yakamata ka hanzarta tashi ka shirya muje station din nan domin magana da daddy daga can din sai mu biya gidan shi Alhaji Lukuman din muji" Wani kallo Habeeb yamashi yace "mizamuyi Station kuma?" Batare da wata damuwa ba Hisham yace "muyi magana da daddy mana muji yanda Accident din ya faru". Mikewa Habeeb yayi yace "kaga Hisham ni yanzu banda lafiya, gaskiya babu wata station din da zani tun jiya fa nake tunanin kisan da Daddy yayima Salma kuma a iya binciken da nayi an tabbatar shine ya daki motar ta, baya ga haka a can baya inba zan manta ba akwai wani *MUGUN FURUCI* da daddy yayi akan Salma duk saiyanzu abin ya fadoman a rai wlh" tassssss sukaji saukar fashewar pilet Hajiya Fadeela ce tazo kawoma Habeeb breakfast taji wannan *MUGUN FURUCIN* abakin Habeeb da sauri suka juya suna kallonta Karasowa tayi gabansu da sauri ta wanke Habeeb da maruka harbiyu hannunta na rawa ta nunashi da ya tsa tace "Habeeb bakada hankali ne? Mahaifin naka ka yarda yayi kisan kai?" Kumatun shi ya shafa ya zagayeta ya shige toilet, da shigarshi ya sulale kasa wasu zafafan hawaye na biyo kun cinshi ya rasa miyasa yayi wannan *MUGUN FURUCIN* ga mahaifinshi zuciyarshi ce tafara bugawa da sauri ya dafeta a cikin toilet din ya kwanta yana nishi. Shi kuwa Hisham mutuwar tsaye yayi tunda Habeeb yafara maganar saida Hajiya tashigo kana ya motsa a sanyaye yace "am Hajiya kiyi hakuri Habeeb baida lafiya ne ya damune da tsare daddy da akayi harya fara Sambatu amma aikinsan yanda Habeeb ke kaunar daddy bazai taba aikata haka agare shiba, ki kwantar da hankalinki Dan Allah". Juyawa tayi ta fice daga dakin jin wasu sabbin hawayen na kara sauko mata itama Sam jiya bata iya wani bacci ba. Tana fita Hisham ya isa kofar toilet din ya buga yace "Habeeb yi sauri kafito" jin shiru sai ya saurara jin nishin Habeeb a toilet din da sauri ya murda kofar toilet din ya shiga a kwance shamai shamai ya samu Habeeb..... Ameenatu Sani ce 👌 [4/18, 5:10 PM] +234 706 650 5625: *👄MUGUN FURUCI*👄 *WRITING BY AMEENATU SANI* *_Wannan labarin kirkirarran labari ne banyarda a juyaman shiba ta kowace siga_* *JIGWAN LABARIN*_:Akan mahaifin da yayi *MUGUN FURUCI* Akan budurwar d'an shi inda kuma tsautsayi ya fada mashi, shikuma d'an yazama lauyan mahaifin yarinyar_. *SADAUKARWA ga my friend DARMA* *NASARA WRITERS ASSOCIATION* {{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }} https://www.facebook.com/103637491942644/ 💫💫 *{{N W A}}* 💫💫 بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم PAGE 6_10 Da isarsu gidan parking sukayi abakin get, Alhaji Muhammad yacema Isa driver yaje yayi magana da security's din bakin get din, aiko haka akayi isa yaje yasanar da daya daga cikin security's din nan security din yace "amma koma waye kesan ganin boss baisan yau ranar weekend bane? " Isa yace "to ai inajin baisan da tsarin bane amma Dan Allah kayi mashi iso da Alhajin inaga babbar magana ce ta kawo shi wajanshi". Dan nisawa security din yayi kana yace " to ina zuwa" wajan sauran yace dayake security's ukku ne abakin get din sukayi magana kana daya daga cikinsu ya bude karamar kofar get din yashiga. Gidan katon gidane don ko get din gidan ukku saboda girmanshi ga katan parking space a wajan manyan motoci ne kusan shidda awajan, atakaicedai gidan Alhaji Lukuman ya hadu iya haduwa. Zaune suke a babban falo su ukku ne Alhaji Lukuman sai matar shi Hajiya Mariya sai y'arsu Salma, suduka da ka kalli fuskarsu suna cikin farin ciki, karamin table ne agaban Alhaji Lukuman samanshi da katon plate mai dauke da kayan fruit Hajiya Mariya na yayyanka mashi yana duba jarida, Salma ko katuwar wayace a hannunta ta toshe kunnanta da earpiece tana taunar chin gum. Security din ne ya turo kofar gami dayin sallama acikin su babu Wanda ya amsa mashi to dayake sun saba da hankan baiwani damuba yace "boss kanada bako awaje". Ko kallanshi Alhaji Lukuman baiyiba yace " kaje kace koma waye yakoma " security din yatashi zaije yasanar da sakon sai muryar Hajiya Mariya yaji tace "jeka shigo dashi". Da sauri Alhaji Lukuman ya dago ya kalleta yace " wai Mariya miyasa kike man wannan abun? Kobakiji amsar Dana bada bane zakiyi man eyayi kuma?" Hajiya Mariya tace "haba Alhaji kasan kowayene kesan ganin ka? zakace ace yakoma ai inaga koma waye bakone baisan tsarinka ba shiyasa" Alhaji Lukuman zaiyi magana sai akaturo kofa security din ne agaba sai Alhaji Muhammad sai Habeeb abaya, sanar dasu yayi ga bakinnan kana ya koma. Alhaji Lukuman yakai dubanshi wajan wa inda akakira da bakin idanunshi suka sabka afuskar Alhaji Muhammad Kallashi yayi da alamun mamaki saikuma yayi wata munafukar dariya gani da taba hannuwa ya nuna Alhaji Muhammad yace "aidama nasan zakazo koba yauba nasan da wannan yo Alhaji Muhammad anfada maka siyasa wasane ko anfada maka Lukuman na wasane? To inbaka saniba kasani ni Alhaji Lukuman nafi karfin innemi Abu kuma ace ban samuba balle wata banzar kujerar chairman,yo Allah natuba ko kujerar Governor nanema ai saina samu bare ta chairman Dan haka basai kasanar dani ka janye ba nasan ai dama haka kazo kasanar dani ko? To badamuwa ngd" sai ya nuna mashi kofa yace "bi inda kafuto ba sai anyi wani dogon turanciba hutawa nake" Tunda yafara maganar Alhaji Muhammad da Lukuman dama sauran wa inda ke falon suka bishi da kallo har ya dire maganar kana yace "Haba Alhaji Lukuman nifa bakone a wajanka koba komi kabamu wajan zama" wani irin kallan raini Alhaji Lukuman yayi mashi kana yace "wajan zama kuma? Naga ai mungama magana ko tunda nasan makasudun zuwanka nan Dan haka katashi katafi" Batare da wata damuwa ba Alhaji Muhammad yanemi daya daga cikin kujerun parlorn ya zauna kana yace "Alhaji Lukuman zauna muyi magana ni yanzu ba maganar siyasa takawoni wajanka ba magana ce mai mahimmanci... Manage please👏 *Ameenatu Sani ce*👌 08065522770 [4/18, 5:10 PM] +234 706 650 5625: *👄MUGUN FURUCI*👄 *WRITING BY AMEENATU SANI* *_Wannan labarin kirkirarran labari ne banyarda a juyaman shiba ta kowace siga_* *JIGWAN LABARIN*_:Akan mahaifin da yayi *MUGUN FURUCI* Akan budurwar d'an shi inda kuma tsautsayi ya fada mashi, shikuma d'an yazama lauyan mahaifin yarinyar_. *SADAUKARWA ga my friend DARMA* *NASARA WRITERS ASSOCIATION* {{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }} https://www.facebook.com/103637491942644/ 💫💫 *{{N W A}}* 💫💫 بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم PAGE 21_25 Bala yace "lalle Alhaji Lukuman bakada sauki akan abinda kake so" Alhaji Lukuman yasha mur da fuska yace "Alhaji Bala saurareni nan! kagadai kaikade kasan sirrina to Dan Allah kada naji kada nagani please! " Baki Alhaji Bala ya washe yace "bakada matsala dani kai kasani, to amma miye kasona aciki?" Alhaji Lukuman yace "kada kadamu da wannan yanzu dai zaka iya tafiya ni zan karasa cike wasu takardu nan". "Ok" abinda Alhaji bala yace kenan yabar office din. To bangaran Alhaji Muhammad duk ya bar rarrashin Habeeb tunda yace yarabu da son Salma Amma shi yanace ita yake so shiyasa yanzu ya daina kulashi ya maida hankalinshi a kan aiyikan da suka sha mashi kai ga siyasa ta taho babban abinda ya kara bashi tsoro shine yana zaune a office wasu yan daban yara suka shigo sukayi mashi gargadin ya hanzarta janye kudurinshi nasan kujerar chairman in bahaka ba zasu kawar dashi daga doron duniya, shikuma yanuna masu Sam baya tsoronsu nan suka kira waya suka fad'i yanda sukayi dashi kana sai suka fita d'aya daga cikin su haryana fadin Allah ya tai makeka da yanzu lahira tayi bako. To irere ireren wa innan abubuwan sune suka daukema Alhaji Muhammad hankali daga Habeeb. Shima dai Habeeb momynshi ta lallabashi harya koma aiki Bayan sati daya Zaune suke Hajiya Mariya ta dafe 'kirji tace gaskiya Alhaji banyarda ba wlh saidai kasami wata hanya badai wannan ba" Alhaji Lukuman yace "kinga saurara mana Mariya nagadai Yarinyar nan bake ce kika haifeta ba ko? Kana kuma duk abinda taci ta sha tasa nine nabata ko? To Dan haka bakida hurumin da zaki hanani iko da ita". Hajiya Mariya tace "naji koma mizaka fada to Amma aini naci kashinta da fitsarinta ko? Kuma nice na kula da tarbiyyarta da kake maganar banice na haifeta ba". Ganin Hajiya Mariya ta inda take shiga batanan take fitaba sai ya kwantar da murya kuma a zuciyar shi yana nadamar shigo da ita cikin shirinshi, shi 'kwalwarsama ta dode a lokacin da yake sanar da ita. Cewa yayi "haba my love Mariya kinsan ko wace magana zan fada maki kinsan saida nayi tunani a kanta kana Salma dai matsayin 'ya take a gareki Amma inasan kisani ko itace ta samu wannan damar zata iya rabuwa damu". Da "kyardai Alhaji Lukuman yashawo kan Hajiya Mariya tare da alkawarin kudi masu tsoka to dayake idonta idon kudi ai tuni ta amince da bukatar shi. Amma kuma gefen zuciyar ta na jimamin rabuwa da Salma don ita ko kad'an batajin ba ita ta haifeta ba. A daran yasami Salma yake fada mata gobe in Allah yakaimu ta shirya zataje g.r.a wajan takwas zai aiketa itada driver. To gidan Alhaji Muhammad shima yasamu kira daga wani abokin su yasheda mashi gobe sunada meeting wajan takwas a nan g.r.a batare da bata lokaci ba yace "Allah ya kaimu Lfy" Washe gari 7:30 sauri kawai Alhaji Muhammad yake Dan yakusa makara Hajiya Fadeela tanata taimaka mashi wajan ganin ya kammala shirin ko break fast baiyi nakirki ba ya tafi Isah driver yajashi suka dauki hanya. Salma ce ta shid'o daga kan matattakalar bene taji shashshekar kukan mom dinta da sauri ta je gabanta tace "subuhanallahi mom miyafaru kike kuka?" Hajiya Mariya ta dago idanuwanta jawur tace "please Salma Dan Allah ki yafeman wlh bada niyata hakan zata faruba". Ainan Salma ta rud'e itama sai hawaye ya wanke mata fuska tace "mom mikika yiman? Ni wlh koma minene nayafe maki Dan Allah kidaina kuka please mom". Rungumaita Hajiya Mariya tayi tana "nidai kiya feman kiya feman Dan Allah Salma!" suna cikin wannan yanayin Alhaji Lukuman ya sauko 'kasa ya gansu haka nan ya had'e fuska cikin wata mummunar murya yace "Mariya!!!" A firgice ta dako kai yace "miye haka kike shirin aika tawa? Ke Salma tashi ki tafi lokaci na kurewa tun dazu ya kirani yana wajan yana jiranki". Tashi Salma tayi tashare hawayenta ta fita mota tashiga driver yajata sukabar harabar gidan. Kallan Hajiya Mariya yayi yace " waiku miyasa 'kwalwar kifaye gare Ku? Yanzu Mariya duk yanda mukayi dake sai kin rusaman shiri? Nibanma San gigin dayakaini harna sanar dake abinda na shiryaba wlh". Itama Hajiya Mariya cikin daga murya tace 'wlh Kaine mai 'kwalwar kifi in baccin rashin imani Salma zakasa a kashe? To wlh nima nayi nadamar haduwa da kai a rayuwata Lukuman ". Jin irin maganganun da take fada ya sashi fitar da wayar shi transfer yayi mata ta one million kana yace "duba wayar ki in kingama bala'in". Hawaye shabe shabe a fuskarta ta jawo wayar ganin uban kudin da ya tura mata sai kukan da take ya koma dariya tace " kai Alhajina wlh harkasa naji dadi ngd sosai " Alhaji Lukuman yace "ainan bama sallamarki bace sai komi ya daidaita zan maki alert mai fasa waya" wani ihon dadi tayi ta ma'kal'kalai Alhaji Lukuman... _Shegiya naira😎_ *TALLA! TALLA!! TALLA!!!* *Assalamu Alaikum* *Ina yan'uwa masu sha'awar shiga kungiya ta online writer? To albishirinku😊 kakar tayanke sa'ka👌 Kuma damace agare Ku sabuwar kungiyarmu mai suna 💫💫NASARA WRITER'S ASSOCIATION💫💫 tana maraba da kowa da kowa duk mai sha awar shiga kungiyar kinada damar shiga bako sisin ki👌* *Ina tsofaffin hannu da sababbin hannu wa inda basuda kungiya? Maza hanzarta domin kasan cewa daya daga cikin members din cikin ta💃💃 domin a dama dake* *Ina masu San gwada basirar su wajen fara fadakar da Al'umma ta hanyar rubutun Hausa novel? Kungiyar mu tana maraba da ke yar uwa indai kina da sha awar zama online writer* *Domin neman Karin bayani saiku tuntubi daya daga cikin number's din nan*👇 08065522770 08104335144 *NASARA WRITER'S ASOCIATION* 💫💫 _*{{Nasara abin so ga kowa ,domin marubuta da cigaban rubutu al'kalaminmu y'ancinmu.}}*_💫💫 *Ameenatu Sani ce👌* 08065522770 [4/18, 5:17 PM] +234 706 650 5625: *👄MUGUN FURUCI👄* *Writing by Ameenatu Sani* 56_60 Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR Call 08066268951* Da Isar Hisham police station ya nemi ganin Dpo batare da bata lokaci ba ya ganshi bayan sun gaisa ne dpo ke sanar dashi "ai yanzu haka anjima wajan goma za akaishi gidan yari domin bazasu cigaba da rike mai laifi kamar Alhaji Muhammad ba a wajan su" Da sauri Hisham ya kalleshi "haba yallaba miye na gaggawar kaishi gidan yari? Dan Allah abani bailing shi" Dpo yace "kataba ganin anbada bailing din mai laifin kisa?, kaga gata daya zakuyi mashi kuje Ku binciko bayanan da zaku karaishi duk da yanada kwararran louya amma ina tabbatar maku shari'ar zuwa daya za ayanke mashi hukunci" Ai Hisham ko sauraran shi baiyi ba yabar office din kiran wayar Habeeb yayi amma no answer haka Yakama hanyar zuwa gidan Alhaji Lukuman " Da isarshi security din bakin gate suka tabbatar mashi baya gida, jiki a sanyaye yabar wajan gidansu Habeeb ya koma amma bai iske Habeeb ba da mamaki yabar dakin wajan Hajiya yaje yafada mata duk yanda sukayi da dpo bakaramin rudewa Hajiya tayi ba amma Hisham yashiga kwantar mata da hankali. Shikuwa Habeeb bayan fitar Hisham da Kad'an wayarsa takama ringing wata number ce akakirashi da ita cike da bacci idanunshi ya daga wayar jin an ambaci sunan Alhaji Lukuman yasa ya wartsake daga bacci yace "Ok ganinan zuwa" Bayan mintuna goma saiga Habeeb ya iso a wajan shakatawar Alhaji Lukuman cike da girmamawa ya gaishe su, inda suka bashi wajan zama bayan ya zauna Alhaji Lukuman yaci gaba da koroma shi bayanin dalilin kiran da a kayi mashi.... Daran ranar lahadi Hisham ne yazo wajan Habeeb amma Habeeb Dan nar waya kawai yake a tsawace Hisham yace "waikai Habeeb ya ina maka magana mai mahimmanci amma kayiman banza?" Kunnewa Habeeb ya dade kana yace "wai miye haka Hisham? Kana Neman kasheman dodan kunne" Hisham yace "magana fa nake maka haryanzu bakace komi ba akan kotu da za'a shiga gobe" Habeeb yace "to Dan za a shiga kotu gobe sai akayi yaya malam Hisham?" cike da murmushi a fuskar shi ya ida maganar amma in ka kireshi da ido zakagano hawaye kwance a cikin idanunshi Kai Hisham ya girgiza tare da zama kusa da Habeeb yace "nifa barrister na kasa gane maka kwana biyunnan mike faruwa ne kake wasu abubuwan?" Habeeb yace "hauka kaga inayi komi?" Hisham yace "niba wannan ba ga magana mai mahimmanci danake maka Habeeb kodai bakasan insan ainihin shirin da kakeyi ne gamai da shari'ar?" Habeeb yace "Ashe dai kagane" Hisham yace "Ok ai ba matsala nasan duk cikin aikine na kwararraran barrister bai kamata kabudeman gaskiyar da ka gano saboda ni barene" yana gama fadar haka ya fice daga dakin. Yana fita Habeeb yabishi ya rufe dakin ya dawo zama yayi kan gado yace "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" haka yayta maimai tawa saiga hawaye sun fara zuba a idanuwanshi, shikanshi ya rasa gane mike damunshi miyasa yake aikata wasu abubuwan, haka yaita sambatu a daranma baiyi bacci ba... Washe gari tunsafe Habeeb yabar gidan haka Hajiya tazo bata samaishi ba kiran wayarshi tayi nan ma a kashe tajita Hisham takira ta tambayeshi ko suna tare, ya tabbatar mata basu tare Hajiya tace "to kayi sauri Hisham ina jiranka time na tafiya". Wajan Tara da rabi saiga Hisham bayan sun kara gaisawa tace " wai ina shi Habeeb yace maka zayane?" Hisham yace "wlh Hajiya baifada man ba nima tun safe nake kiranshi wayarshi bata shiga" Hajiya tace " ok to yanzu ina kuka tsaya ina fata Habeeb yasamo cikakkiyar amsar da zaiba alkali har ya saki Alhaji?" boyayyar ajiyar zuciya Hisham yasaki kana yace "ai Hajiya kinsan Habeeb jarumi ne ba a taba kadashi a shari'a ba Dan haka ki kwantar da hankalinki insha Allah yau sai daddy ya dawo gida" Hajiya tace "Allah yasa, ni Habeeb ne naga yanzu gaba daya ya canza wlh" Hisham yace "karki damu komi zaikoma dai dai, Hajiya tashi ki shirya mutafi kar lokaci ya kure" Hajiya na mikewa wasu mata su hudu sukayi sallama sosai Hajiya tayi farin cikin ganinsu, sisters dinta ne yayyenta biyu sai kannanta suma sunzo ganin shari'ar ne... Kotu.... Ameenatu Sani ce👌 08065522770 [4/18, 5:17 PM] +234 706 650 5625: *👄MUGUN FURUCI👄* *Writing by Ameenatu Sani* *NASARA WRITERS ASSOCIATION* _____________________________ {{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }} ________________________________ https://www.facebook.com/103637491942644/ 💫💫 {{N W A}} 💫💫 بِسْـــــمِ ٱاللَّهِ ٱلرَّحْمَنِ ٱلرَّحِــيــمِ 61_65 Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp ORCall 08066268951* Cike kotun take makill da mutane kuma manyan mutane Harta da sugaban jam'iyya yazo, ga lauyoyi ciki harda barrister Habeeb Muhammad *HM*, kotun tayi tsit ana jiran shigowar alkali bayan wasu yan mintuna saiga shi yashigo, gaba daya a ka tashi domin girmama alkali bayan an zazzauna maga takarda ya fara karanto kara kamar haka.. "A yau ishirin da biyar ga watan daya shekara ta dubu biyu da ashrin da biyu Alhaji Lukuman yana karar Alhaji Muhammad da kisan y'arsa ta hanyar banketa da mota". Tsittt kotun ta dauka bayan alkali yagama rubuce rubucen shi ya dago kai yace "kotu na bukatar ganin Alhaji Muhammad a gabanta". Bayan anzo dashi kana yakara fadin " in da kwai lauyoyin mai kara da Wanda ake kara su tashi su gabatar da Kansu". Hajiya da Hisham da sauran magoya bayan Alhaji Muhammad kowa hankalinshi ya karkata zuwa ga Habeeb basu an karaba sukaji yana gabatar da kanshi. "SUNANA BARRISTER HABEEB LAUYEN MAI KARA" Dayawa daga cikin mutanan kotun sunyi mamakin jin furucin Barrister Habeeb musamman magoya banyan Alhaji Muhammad saboda sun San Dan sane Hajiya Fadeela tace "Habeebbbbbb, bakada hankali ne?" Cikin tsawa ta fadi hakan. Alkali ya buga gudumar kotu alamun a saurara amma Hajiya Fadeela taki yin shiru saboda rudewa tama manta gaban alkali take. alkali yace "inbazakiyi mana shiru ba kifita domin nan ba kasuwa bace". Kukan da ta rushe dashi ne yasa alkali bada umarnin a fita da ita waje, kuma kowa yayi shiru. Bayan an sakeyin shiru ne alkali yace "ina lauyan mai kare Wanda ake kara?" Shiru babu Wanda ya Mike Hisham da bakaramin haushin Habeeb yaji ba yana mamakin taya Habeeb ya sauya lokaci daya harya kasa taimakon mahaifinshi? "Allah sarki daddy Allah ya fitar dakai daga wannan iftila'in da yafada maka!". Shikuwa Alhaji Lukuman da Alhaji bala suna daga gefe tare da sakin wani mugun murmushin jin dadi, shikanshi daddy yayi mamakin Habeeb. Alkali yace "barrister Habeeb zaka iya fara tambayar ka ga Alhaji Muhammad" A sanyaye Habeeb ya fito da zaka kurama kwayar idanunshi ido da ka ga kwanciyar hawaye a gurbin idon, agaban Alhaji Muhammad ya tsaya tare da gyara gilashin idanunshi yace " zamuso ka bayyanama kotu cikakken sunanka". Alhaji Muhammad yace " kamar yanda kowa yasani sunana Alhaji Muhammad ". Habeeb yace " zamuso kafada mana alakar da ke tsakanunka da Alhaji Lukuman " Alhaji Muhammad yace "ni babu wata alaka tsakanina dashi". Habeeb yace "inbaku da alaka amma aikuna takara tare ko?" Alhaji Muhammad yace "dan muna naiman kujera a tare ba shine zaisa munada alaka ba" Habeeb yace "Ok to miye Alakarka da ita mariganyiya Salma da harka yi ikirarin saika kashe ta kuma sai gashi ka kasheta da mota" Alhaji Muhammad yace "ni ban kashe taba kuma da ranta na kaita asibiti, kuma ni banta ba wannan ikirarin ba" Habeeb yace " kafadama kotu gaskiya domin wannan laifin naka a bayyane yake" Alhaji Muhammad yace "ni ban kashe ta ba tsautsayine kawai da inya yini baikwana amma ni wlh bada niya na bigeta ba" Habeeb ya kalli alkali yace "yamai girma mai shari'a Alhaji Muhammad yana so ya wahalar da shari'a ne har yanzu yaki amsawa shiya kashe Salma dan haka nake rokon wannan kotu da a bani dama in gabatar da sheduna domin tabbatar da Alhaji Muhammad da gangan ya kashe Salma"... _Tofa ikon Allah muje zuwa🤭_ *Ameenatu Sani ce👌* 08065522770 [4/18, 5:17 PM] +234 706 650 5625: *👄MUGUN FURUCI👄* *Writing by Ameenatu Sani* _Ina godiya da Addu'o'inku sosai kuma masu magana akan bana typing akan lokaci kuyi hakuri Dan Allah ba zaune nake ba amma insha Allah komi zai daidai ta karkuji komi masoya🥰_ 66_70 Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR Call 08066268951* ______________________________ Alkali yace "anbaka dama" Juyawa yayi ya kalli jama'ah yace in Isah driver yana kusa ya fito batare da bata lokaci ba sai gashi ya fito. Habeeb yace "isah zamuso kafadama kotu ko kawai waye d kuma shedar da zaka banda yanzu". Isah driver yace "sunana Isah kuma ni driver ne a gidan Alhaji Muhammad, shedar danazo badawa itace, Lokacin da abun yafaru muna tare da Alhaji ya buge ita yarinyar kuma saida nace mashi kada ya bugeta amma ya bugeta". Alkali yace " kana driver miya hada shi Alhaji da driving?" Nan Isah Yakama zare idanu kana yace "ai ai lokacin ni kaina ke ciwo shiyasa ya amshi tukin". Alkali yayi yan rubucece kana ya kalli Alhaji Muhammad yace " Alhaji Muhammad haka akayi ysakaninka da isah driver?". Alhaji Muhammad yace "kusan hakan mukayi amma lokacin shike driving din wucewar motar yaceman kanshi na ciwo bayan kuma lfy lau muka taho, kuma batun da yace wai yaceman karna kasheta ya mai shari'a inaso ka tambaye shi tsakaninshi da Allah in munyi wannan maganar, kuma ni abunda na lura shine ya takaman Giya da kafarshi wlh". Wata uwar zuface ta shatatowa Isah gabanshi ya kama faduwa nan alkali ya kalli Isah yace "tokai Isah kaji tsakaninka ga Allah kace mashi haka?" Isah yace "wlh munyi haka dashi ya mai shari'a". Nan Alkali ya yi yan rubuce rubuce kana ya dago yace " wannan kotu mai adalci taji bayani daga bakin kowa kuma ta gamsu saidai za'a dage wannan Shari'a harzuwa nan da 5-2-2022 kuma kotu na bukatar lauyan da zaikare shi Alhaji Muhammad din, za acigaba da zare shi babu batun balling shima Isah driver kotu na bukatar yansanda su bincikeshi". Nan ya buga guduma alamun antashi. Alkali ya tattara kayanshi ya fice kotun tacika da hayaniya shikuwa Alhaji Lukuman da Alhaji bala ba haka suka soba sun so ace yau anyanke hukunci amma ai akwana atashi babu wuya, nan suka bar kotun rai bace. Shikuwa barrister Habeeb da sauri yabar kotun danjin yanda mutane suka fara zaginshi hakan yasa kanshi fara jujjuyawa. Hisham a fusace yabi ba yanshi......... *Ameenatu Sani ce👌* [4/18, 5:17 PM] +234 706 650 5625: *👄MUGUN FURUCI👄* *_By Ameenatu Sani_* *_Masoya ina dai dad'a Baku hakuri, kuma inajin dadi da nuna kulawar Ku akan buk dina insha Allah zaku dunga jina ba 'kak'kautawa😂mun kusa 'kar'karewa kuhuta da jirana_* 71_75 Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===150 1GB@=====270 2GB@=====550 3GB@====800 5GB@====1,350 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR Call 08066268951* ____________________________ Koda Habeeb ya hau motar hawaye kawai yake yi wani irin tukuki yakeji a zuciyarshi ga wani zafi da take mashi, da'kyar dai yakai gida wani mahaukacin hon ya dunga dannawa da sauri mai gadi yazo ya bude mashi gate ya danna motar da karfi ko parking din kirki baiyiba ya fito da gudu ya nufi dakin shi kulle kofar yayi ya fada kan gado wani irin kuka ya saki kamar wani karamin yaro yace "innalillahi wa'inna'ilaihir raji'un, wai maike faruwa dani ne?,mai na aikatawa daddy na haka? Why why why haka kakeyi Habeeb?" Ya ida maganar da wani irin kuka. A fusace Hisham ya shigo parlon murda kofar dakin Habeeb yayi yajita a rufe da karfi yace "Habeeb!!! Bude kofar nan" jin shiru ya kara cewa "na fada maka ka bude kofar nan inba so kake na karyata ba!" Y'an uwan Hajiya ne suka shigo gidan 'ban garan dakin Hajiya suka shiga samunta sukayi tana kuka Hajiya badariyya tace "wlh Fadeela bansan asararran da kika Haifa ba sai yanzu wlh Habeeb yayi asara duniya da lahira" Hajiya Saude tace "Kenifa inaga Habeeb ya haukace ne Dan wlh abida yayi ba mai hankali ne zaiyishi ba,ace mutum ya dauki d'awainiyar ka har ka kawo wannan matsayin amma ace ka kasa taimakon shi" Hajiya Umma da tabuga uban tagumi tunda suka shigo tace "Kai jama'ah wai haka Habeeb yakoma?,wlh danasan irin takaicin da zan kwasa kenan da banje ba , ai Fadeela ki godaima Allah dayasa baki kalli shari'ar nan ba inaji da zuciyarki ta fito waje Dan bakin ciki". Hajiya badariyya tace "yo ni kinji yanda zuciyata tayi? Wlh kamar ta fado naji, kaini yau Habeeb yaban mamaki wlh". Kuka Hajiya Fadeela ta kara rushewa dashi tace " Dan Allah ya isa haka kubarni naji da wannan damuwar!". Sallama Hisham yayi dakin Hajiya Umma ce ta amsa mashi Hisham ya samu waje ya zauna yace "Dan Allah Hajiya kuyi hakuri da abinda Habeeb yayi wlh ba acikin hayyacinsa yake ba" Hajiya Fadeela nuna kofa tace "Hisham tashi kabar nan, ai duk halinku daya dashi duk munafurcin tare kuka kullashi zaka wani zoman nan simi simi tashi kaban waje nace" tafada cikin tsawa. Cikin sanyin jiki Hisham yatashi yana kiran "ayi hakuri Dan Allah" yabar dakin Hajiya badariyya taja tsoki tace "aikin banza kawai, kinga Fadeela bawai kuka zaki zauna yiba mafita ya kamata ki nema indai kina san mijinki". Bangaran Alhaji Lukuman kuwa tafiya sukeyi a mota shida Hajiya Mariya da Alhaji bala Allah Lukuman yace " ya kukaga wasan nawa?, duk da dai aikin baitafi yanda ake so ba amma da alama da nasara" Wata dariya Alhaji bala yayi yace "gaskiya Lukuman ka iya lalata, to waini abinda ya keban mamaki rannan kaceman babanku daya da shi Alhaji Muhammad din to taya kuka zama haka?" Wata dariya yayi kana yace "yaudai bari nabaku labari dama itama Hajiya ta isheni da tana so taji". *Baya Kad'an* Alhaji Mukutar shahararran Dan kasuwa ne yana safarar man faitur da fiton shinkafa da man Olga da manja turaila turaila ake fito mashi da su , shidin mazaunin kasar Niger ne, yatara kudinda koshi kanshi baisan iya adadinsu ba, matanshi biyu Hajiya binta da Hajiya Sakina, Hajiya Binta itace uwar gida shekaran su shidda da aure amma ko batan wata bata ta'ba yiba hakan yasa Alhaji Mukutar ya auro Hajiya Sakina shekara guda ta Haifa mashi Da namiji Wanda yaci sunan mahaifinshi Muhammad sosai Alhaji Mukutar ya dauki Son duniya ya daurama Muhammad hakan ba karamin bakanta ran Hajiya Binta yayi ba tana tunanin duk dukiyar Alhaji zata koma ga Hajiya Sakina shiyasa ta shiga yawon bin malamai da bokaye amma duk inta taje ace bata haihuwa tasha wahala sosai da 'kyar tasamu bokan dayace zai taimaketa amma saidai cikin aljani zai turo yasa matashi kuma zata haifi da marar jin magana kuma indai tanaso taci kudin Alhaji to yaran shine zai kashe alhajin da hannunshi, haka Hajiya Binta ta yarda bayan shekara daya Hajiya Binta ta haifi danta yaci sunan Lukuman duk da irin murna da haihuwar da Alhaji Mukutar yayi sam baiji yanasan Dan ba ko Kad'an murnar ma ba wani sosai yayita ba hakan yasa Hajiya Binta kara tsanar Muhammad da uwarsa. Muhammad Nada shekara shidda shikuma Lukuman hudu Allah yayima Hajiya Sakina rasuwa kuma kisan Hajiya Binta ce sularshi bayan shekara daya da mutuwar itama Hajiya Binta ta mutu wajan zuwa wurin boka Dan yakashe Muhammad motar tayi accident ta mutu _(Dama ita rayuwa haka take duniya juyi juyi)_. Haka Muhammad da Lukuman ke rayuwa cike da rashin jituwa Lukuman baya kaunar Muhammad kokadan kuma kullum hudubar Hajiya Binta yake tunawa na indai yana so suji dadin Rayuwa sai sun kashe Alhaji Mukutar da Muhammad to hardai tabar duniya burinta bai cika ba, haka shima Lukuman ya taso da wannan burin yanada shekara sha biyar yafara tunanin yasama Alhaji Mukutar maganin bera ga abinci, haka kuwa akayi ya zuba mashi harya mutu. Da yake Muhammad tun yana karami yarone mai hankali hakan yasa koda yaushe yake Jan Lukuman a jiki yana so su gudu tare su tsira tare tunda basuda iyaye yanzu, amma shi Lukuman Sam hakan baya cikin tsarinshi kullum cutawa Muhammad yakeya yana Dan shekara ishirin cib a duniya yafara biye biyen bokaye har ya samu wani boko yace mashi Muhammad basu da ikon kashe shi yanzu amma indai so yake yaci dukiya shi kade to saidai ayi mashi kurciya yabar garin ko kasar ya manta da kowa da komi da ya sani a rayuwar shi to kuma hakanne ya faru Muhammad da yatashi bai Lula ko inaba sai garin katsina anan ya fara rayuwa yau dadi gobe babu har yazama yaran wani mai shago da ganan har yayi jarin kanshi har yazama Dan kasuwa sosai mai shagon da da Muhammad kema tsaro shiyazama uban gidan shi tunda yaga shi mai rukon amana ne sai ya bashi yarshi Fadeela ya aura daganan arziki ya fara yimashi sallama ta ko ina ga kyaur da da Allah yayi mashi Habeeb harya fada harkar siyasa. Shi kuwa Lukuman bayan barin Muhammad gida sai duniya tazamo mashi sabuwa watayawa kawai yake da kudi y'ammata kawai ke cin kudin da abokan banza cin kudin kawai suke har saida kudi suka fara kasa kana ya Dan fara sana ar saida tabar wiwi da koken da ganan ya dawo Nigeria da zama yana ci gaba da haramtacciyar sa na arshi a boye har yagamu da Hajiya Mariya suka gama tambadewa kana sukayi aure suma nan bayan shekara biyar da auran su suka gane basu haihuwa nan dai ita Hajiya Mariya ta matsa mashi dole saidai suje gidan marayu su dauko yaro Dan ita gaskiya tana San Da ko diya, to dayake yana Santa shiyasa sukaje suka dauko Salma kuma babu Wanda yayi tunanin ba Yar su bace da a Kano suke amma Salma na cika shejara sha biyar suka dawo katsina da zama ana haka ya fara ganin fastocin Alhaji Muhammad na San kujerar chairman ba karamin tashin hankali ya shiga ba domin shi harya manta da wani Muhammad a rayuwa nan yasa akayi mashi binciken komi na gamai da family din Alhaji Muhammad aiko ya lashi takobin a wannan karan saiyaga bayan shi,shima saiya Shiga harkar siyasa, to dama tun farkon da wowarsu katsina Habeeb yaga Salma yaji duk duniya babu wacce yake so inba ita ba, shi kuma Alhaji Muhammad yayi Alkawarin bama danshi kwaya daya tak a duniya farin ciki, wannan dalilin shi ne na zuwa gidan Alhaji Lukuman haryayi *MUGUN FURUCI* ga Salma.. Cigaban labari.... *Ameenatu Sani ce👌* 08065522770 [4/18, 5:17 PM] +234 706 650 5625: *👄MUGUN FURUCI👄* *Writing by Ameenatu Sani* *NASARA WRITERS ASSOCIATION* ___________________________________ {{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }} ___________________________________ https://www.facebook.com/103637491942644/ 💫💫 *{{N W A}}* 💫💫 بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم *Wannan shafin na kune Sister's Fatima Sa'id da Khadija Sa'id sai Darma* *godiya ta musamman gareka Sdeen Allah ya bar zumunci* 76_80 Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===150 1GB@=====270 2GB@=====550 3GB@====800 5GB@====1,350 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR Call 08066268951* Bayan Alhaji Lukuman yagama basu tarihin rayuwar su ya daura da fadin "Aini wlh kiyayyar Muhammad a jinina take a duniya innaga bai numfashi to burina yacika wlh". Ajiyar zuciya Hajiya Mariya tayi tace " Ni kuwa wlh duk jikina yayi sanyi gaskiya Alhaji ina kara jinjinama rashin imaninka". Wani kallo Alhaji Lukuman yabita dashi yace "kinga kefa matsala gareki wlh ba abinda za'ayi dake baki kawo kwafsu aciki ba mstwww" yaja tsoki tare da Jan motar sukayi gaba. Zaune suku suna fira da Ammi meenal tace " kai Ammi wlh duniya ba gaskiya wani posting nake gani dazu wlh wai an kashe wata yarinya da akayi garkuwa da ita, kumafa malamin makarantar sune" Ammi tace "innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un, ke malamin su fa kikace?". Meenal tace "Wlh kuwa Ammi,bakigani ba gwanin ban tausayi". Ammi tace " to Allah ya kyauta,Allah tsare gaba, Allah ya cigaba da tona masu asiri,mukuma Allah ya shiga lamarimmu🤲🏻" "Amin" meenal tace, kana suka cigaba da firar su sakon message ne ya shigo wayar ta dubawa tayi taga sakone batarai da takaranta ba kawai ta aje wayar sai wajan goma saura tayima Ammi saida safe ta shige dakin ta, bayan ta kammala dukkan abinda zatayi ta haye gado tare da kashe glove ta shige a bargo wayarta tafara dubawa sai ta tuna da message din da akayimata dazu, budewa tayi taga bakuwar number ce amma dukda haka rubutun dake ciki yaja ra'ayinta sosai sau ukku tana nanata karanta sakon _Barrister meenal Dan Allah ki taimakeni kamar yanda Allah ya taimakeki kizo ki fitar da bawan Allah nan daga iftilakin da Allah ya daura mashi ni zuciyata takasa hakan, ana tuhumar shi da laifin kisa bayan nasan bazai taba aikata hakan ba_ Dan guntun message din da akayi Mata kenan Wanda ya kasa barin tunanin ta abinda ya bata mamaki shine waye? Miyasa baza'a tunkareta kai tsaye ba? Bata karasa tunanin ba message ya kara shigo wa _Barrister ki dubi girman Allah kada ki maganar da nayi maki wasa ko rainin hankali banida wani zabi da yawuce na fada maki ta message bakina bazai iya fada ba yaman dauyi, za a kara zaman kotu 5-2-2022 a babbar kotun nan jahar katsina nasan kila kinji labarin Alhaji Muhammad Dan takarar kujerar chairman Wanda akace ya kashe diyar gidan Alhaji Lukuman, Dan Allah kitsaya ki binciko asalin gaskiyar please_ Sakon yamatukar girgizata ai kuwa nan take takira number amma ina bata Shiga. Kawarta Jidda takira bayan sungaisa take tambayar ta "ko taji labarin dake faruwa a can garin katsina na kashe diyar gidan Alhaji Lukuman?" Jidda tace "e tabbasa naji labari Dan ke ba hawan media kikeyi sosaiba amma ai kwana biyun nan labarin da aketa yadawa kenan, toke miye hadinki da shari'ar ne? Ai kara a yanke mashi hukunci dai-dai da abinda ya aikata wlh" ajiyar zuciya Meenal ta sauke har aranta taji tana so ta taimaki wannan bawon Allah to amma ta ina zata fara? Jin Jidda nakiran "hello banfa jinki" yasa tayi gyaran murya nan ta fada mata message din da aka turo mata, " Jidda tace tab keji wani rainin hankali ke yanzu saiki kwasa tundaga nan Kaduna har katsina akan shari'ar da bakisan gaskiyar taba" Meenal tace "Jidda wlh zuciyata tana fadaman naje na taimake sa dama gashi kwana biyu ina fama da wani mafarki wani mutum ya duk kusa a gabana yana rokona ke har yakaida banasan na kwanta saboda da zaran na kwanta sainayi wannan mafarkin, Dan haka zan fadama Ammi duk abinda tace haka za ayi" Jidda tace "Ok to Allah yasa muji alkhari" Meenal tace "Amin" Kusan raba dare tayi tana kiran number amma akashe ake ce mata gashi duk bayan minti talatin sai ammata message ance _Please Meenal!!!_ Sai wajan asuba tasamu bacci ya dauketa saboda ta kwana tunanin abun. Washe gari takama week end babu inda zataje shiyasa tasha baccin da batasamu tayi jiya ba sai wajan goma ta farka bayan ta yi wanka ta fito tashiya cikin dinkin doguwar Riga tayi kyau sosai ba karya Dan kuwa meenal kyakkyawace tubarkalla zuwa tayi suka gaisa da Ammi kana ta dauki break din ta bayan ta gama ta fito ta samu Ammi bata boye mata komi ba ta fada mata itama Ammi taji tausayin Alhaji Muhammad ya kamata sai tace ma meenal "aikuwa na baki izinin kije katsina Meenal shi mai gaskiya yana tare da Allah insha Allah indai yanada gaskiya zata fito,kuma nidai kamar kullum shawarar da zan baki itace ki tsaya a matsayinki na marainiya kitsaya a fadar gaskiyar kada wata dukiya ta rudeki ki boye gaskiya domin kuwa ita karya fure take bata y'a'ya kiji tsoran Allah a duk al'amuranki Meenal" sosai jikin meenal yayi sanyi kuma tayima Ammi Alkawarin zata tsaya akan gaskiyar ta kuma zata kare mutuncinta, sai Ammi tace "inkije a katsinar to a ina zaki kwana" nan meenal tayi tunani kana tace akwai wata abokiyar aikimmu da anan take yanzu sukoma katsina kuma gaskiya tanada kirki sosai Dan ba tun yanzu take so mukai mata ziyara ba, kawai zankirata na fada mata zanzo kuma kinga har ta taimaka man tunda zata fini sanin garin" Sosai Ammi ta yarda da batun kuma tayi mata fatan alkhari Meenal tace "gobe tun wajan takwas zata wuce saboda lokaci na ta karatowa" Nan dai suka cigaba da jajanta lamarin kuma ta shiga Facebook da sauran media taga yanda aketa posting din abun jama'ah da yawa suna fadin basu yarda da gangan ya kasheta ba, a ranar Meenal tayi setting din komi tundaga wajan aikinta har sallamar Ammi, kuma ta samo mata mai aikin da zata tayata zama kamun ta dawo. Washe gari tun Tara Meenal ta daga zuwa katsina ta dukko dakin kara...... Muje zuwa *Ameenatu Sani ce*👌🏻 [4/18, 5:17 PM] +234 706 650 5625: *👄MUGUN FURUCI👄* *Writing by Ameenatu Sani* *NASARA WRITERS ASSOCIATION* ___________________________________ {{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }} ___________________________________ https://www.facebook.com/103637491942644/ 💫💫 *{{N W A}}* 💫💫 بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم 86_90 *Masha Allah godiya nake garaiku masoya da irin addu'oinku da kuma yanda kuke nuna jin dadin buk din nan🥰, kuma ina mai baku hakuri da nace zan sakar maku sabon littafina mai suna SHU'UMIN IKO to kuyi hakuri yanzu da na kammala wannan zan ida maku littafin WAYAFI ZURFIN CIKI? saboda yanda naga kuna maganar na ci gaba da rubuta shi amma zan faro daga farko ne kuma zanyi gyare gyare aciki Dan haka zaikoma maku sabo😉😉 harma saiya fi na da sweet in kuma da dama zan hada maku da SHU'UMIN IKO amma banyi Alkawari ba gaskiya* *Thank you for contacting Sdeendtm!* *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===150 1GB@=====270 2GB@=====550 3GB@====800 5GB@====1,350 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR Call 08066268951* Kai su Meenal suka jin ji na tare da yin yan rubuce rubuce kana meenal tace "Yalla6ae wannan shine cikakken abinda yafaru tsakanin ka da Alhaji Lukuman?" "Eh ni wannan shi kadainai abinda nasani" cewar Alhaji Muhammad. Meenal tace "shinkai kanaga gawar ita salmar da idanunka?" Alhaji Muhammad yace " a'a, ni ina gida a lokacin kawai yan Sanda suka zoman wai za su tafi dani" Kai Meenal ta jinjina tace "Ok insha Allah zamuyi nasara a kan shari'ar nan" barrister Halima tace "Allah yasa". Nan Alhaji Muhammad yayi godiya gare su shidai hakanan yaji Allah ya daura mashi San Meenal yaji ta burgeshi so sai gaskiya iyayenta sunyi sa'ar haihuwarta, yana tunowa kuma da Habeeb sai fuskar shi ta canza haryanzu ya kasa tantance miyakeji a gamai da Habeeb so ko kiyayya yake mashi ? Bayada mai bashi wannan amsar. Sosai su Meenal sukayi yawo a garin katsina duk inda suka San zasu ji wani labarin sunje kuma Alhamdulillah suna fatan wannan hujjojin da suka samu suyi tasiri. Cike da gajiya suka dawo gidan bayan sun watsa ruwa sun samu abun da zasu sama cikin su kuma sun huta nan suka kara tattaunawa a kan maganar suna fatan Allah ya kaisu gobe lafiya. Kotu Bayan alkali yashigo anyi gaisuwa gareshi maga ta karda yasake karanto karar da za acigaba da saurare , alkali yace " kotu na bukatar ganin lauyoyin mai kara da Wanda ake kara in akwai" Habeeb ya tashi ya kara gabatar da kanshi a matsayin lauyan mai kara, sosai kotun aketa hayaniya ana zaginshi wannan karanma Hajiya Fadeela saida tayi kuka Hisham ma yayi mamaki sosai saidafa suka aje magana akan bazai kara bin bayan Alhaji Lukuman ba amma ji yanda yayi masu Aida tun farko yasanar dashi bazai iya ba da yasamu wani lauya koda dukiyar shi zata kare wajan nemama daddy yanci, gaskiya Habeeb ya haukace, Alhaji Lukuman kuwa dadi kamar ya kasheshi yanda yaji ana zagin Habeeb yasan yau dole ayanke hukunci, shi kuwa Habeeb saizare idanu yake komi yake nema oho, kusan minti biyu anata hayaniya kana Alkali yace "a saurara,in akwai lauyan Wanda ake kara ya gabatar mana da kan shi" Cike da ladabi da girmamawa Meenal tamike cikin zazzakar muryarta wadda ta rikita kotun gaba daya Dan dadinta tace *SUNANA BARRISTER MEENAL IBRAHIM, NICE LAUYAN WANDA AKE KARA* dib kotun tayi dukda wasu basuyi mamaki ba amma bangaran su Hajiya sunyi mamaki sosai taya Alhaji yasamu lauya? Kodai Hisham ne ya samota amma bai sanar da suba, koba komi sunji dadi da irin wancan zaman baisake faruwa ba na rashin lauya, to shimadai Hisham din yaji dadi sosai kuma yasan barrister Meenal sosai babu wasa a aikinta, ita da Habeeb ba asan waye yafi wani kwarewa ba. Uhmmm baiyana maku irin bakin cikin da Alhaji Lukuman yayi bata lokaci ne Ku kwatanta da kanku🤪 Dukewa sukayi shida Alhaji Bala Allah bala yace "ya kuma naga haka Alhaji?" Alhaji Lukuman yace "to nima bansan mike faruwa ba bayan malam yaceman har agama shari'ar nan babu wani lauyan da zai taimake shi" Alhaji bala yace "to ita kuma wannan daga ina waye ya kirawota?" Alhaji Lukuman yace "tawuci wancan shasha shan abokin Habeeb din Hisham ai barsu sunyi sun gama basucin riba saboda har antsara yanda za'ayi shari'ar nan waccen yarinyar bata isa ta hana ba wlh" Alhaji bala yace "Wannan haka yake in kudinsu ma taci to taci banza" Suduka murmushin mugunta sukayi Alkali yace "ko barrister Habeeb yanada tambaya da zaiyima Alhaji Muhammad?" Kan Habeeb a kasa yace "eh" alkali yace "to muna sauraronka" A hankali Habeeb ya isa gaban Alhaji yace "Alhaji Muhammad haryanzu bazaka fadi gaskiyar Kaine ka kashe salma ba?" Nan Meenal ta tashi tace "up junction ya mai shari'a ya kamata barrister Habeeb yasan irin kalaman da zaiyi amfani dasu wajan tambaya bawai kawai ya yanke mashi kukunci kai tsaye ba because haryanzu zarginshi akeyi". Alkali yace " Barrister Habeeb ka sassauta kalaman ka" "Insha Allah" Cewar Habeeb, ita kuma Meenal ta zauna, Habeeb yace "banida sauran wata tambayar da zanyi mashi" Alkali yace "ko barrister Meenal tanada abin cewa?"..... *Ameenatu Sani CE*👌 [4/18, 5:17 PM] +234 706 650 5625: *👄MUGUN FURUCI👄* *Writing by Ameenatu Sani* *NASARA WRITERS ASSOCIATION* ___________________________________ {{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }} ___________________________________ https://www.facebook.com/103637491942644/ 💫💫 *{{N W A}}* 💫💫 بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم 91_95 Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===150 1GB@=====270 2GB@=====550 3GB@====800 5GB@====1,350 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR Call 08066268951* Meenal tamiƙe tace "eh ya mai shari'ah, inaso abani dama domin nayima Alhaji Lukuman wasu tambayoyi" alƙali yace "Alhaji Lukuman inyana kusa yazo Domin Ya Amsa tambayoyi". Nan ya fito ya tsaya wajan da aka tanadar domin amsa tambaya Meenal ta matsa kusa dashi tace "Alhaji Lukuman bincikyenmu yanuna Salma ƴar hutu ce bata fitowa daga gida sai wajan goma inma takama kenan, to amma kuma abin mamaki sai gashi ta fito wajan takwas na sapiya, hakan yana nufin mikenan?". Aranshi yace "laillema wannan yarinyar!" Kallanta yayi kana yace "baizama dole koda yaushe ace sai wannan time din zata fita ba". Meenal tace "to data fita ina taje?" "Up junction ya mai shari'ah yakamata a tsawar ma barrister domin tana wuce gona da iri na tambayoyinta, wannan ai ba huruminta bane". Cewar Habeeb Alƙali yace "ƙorafi bai karɓu ba barrister, yanada ƙyau ace munji amsar wannan tambaya". Wani irin Murmushi Meenal tayima Habeeb shi kuwa kai ya sun kuyar, yanajin wani iri aranshi, alhaji Lukuman ko harara da matsiyacin kallo yake aika mata batare da kowa ya ankare ba, amma ita Meenal kar take dashi. "Muna sauraranka Alhaji lukuman" meenal ta faɗa tana kafeshi da idanu. Cewa yayi "Tace Tace zata karɓo saƙo a wajan ƙawarta kuma saƙon yanada muhimmanci shiyasa, barrister Nifa wlh Alhaji Muhammad shine ya kasheman ƴa" Meenal tayi saurin cewa "wace shedace kake da ita da zata tabbatar mada kotu cewa shine yakasheta?" Wani murmushi yayi kana yace "ni kuwa keda sheda" hannu yazura a aljihu ya fito da memory yace "wannan memory ɗin idan har an sanyashi an haska shine zai tabbatar maku da cewa shine ya kasheman Salma" wani marayan kuka yasaki wanda da yawan ƴan kallo yabasu tausayi. Shikuwa Alhaji Muhammad idanu kawaiya ƙura mashi yana sauraran ikon Allah . Su Hisham kuwa sun ƙagara suji mike cikin memory ɗin duk dade sunsan duk ƙaryace a ciki. Amsar memory ɗin Meenal tayi tamiƙama Maga takarda shikuma ya miƙama Alƙali Alƙali kuma yabada umarnin a haska a computer dake maƙale a kotun..... Manage please 🙏🏻 [4/18, 5:17 PM] +234 706 650 5625: *👄MUGUN FURUCI👄* *Writing by Ameenatu Sani* *NASARA WRITERS ASSOCIATION* ___________________________________ {{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }} ___________________________________ https://www.facebook.com/103637491942644/ 💫💫 *{{N W A}}* 💫💫 بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم 96-100 Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===150 1GB@=====270 2GB@=====550 3GB@====800 5GB@====1,350 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR Call 08066268951* To bayan anjonata komi ya fara aiki memory ɗin ma ya ɗauka yafara loading tsitt kotun ta ɗauka kowa ya ƙagara yaga mike acikin memory ɗin, to da farkodai fitowar Salma ce daga ɗaki ta zauna akan kujera tana shan kiɗanta kamar yanda tasaba sai kuma fitowar Hajiya Mariya da Alhaji Lukuman duk sun hadu a parlourn suna fira can saiga security ɗin da yazo yima Alhaji Muhammad iso wajan Alhaji Lukuman.....hakadai duk abinda yafaru a parlourn bayan shigowar Alhaji Muhammad da irin daramar da akasha a parlourn har marin da Alhaji Muhammad yayima Salma da kuma MUGUN FURUCIN Da yayi a kanta duk angani a kotun amma iya nan kaɗe aka gani saboda videon tazama guntuwa. Bayan angama gani Alƙali yayi gyaran murya yace "ko barrister Meenal tanada ja akan wannan videon?" Murmushi Meenal tayi tace "ƙware kuwa ya mai shari'a, baikamata ayi saurin yarda da wannan video ba kum".... "ya isa haka barrister Meenal duk wata hujja ta ƙare babu wani sauran bayani da zakiyi saboda a da munji labarin cewa Mugun furuci ne Alhaji Muhammad yayi yanzu kuma gani mukayi da idanuwan mu, dan haka abusa sauraran kowace hujja ta ɓangare biyu da mukayi mun tsaya mun tattare kowace shaida da aka bayar anan, dan haka wannan kotu mai adalci zata bama Lauyan Alhaji Muhammad dama ta ƙarshe daganan suwa 5-3-2022 domin kawo ƙwaƙƙwarar hujjar da zamu gamsu da ita cewa bashi ya aikata wannan kisa ba, in kuma babu wata sheda to tabbas a ranar za'a yanke mashi hukunci daidai da abinda ya aikata" gudumar da ake bugawa yayin tashi daga kotu ita alƙali ya buga akace kotuuuu. Da sauri Habeeb ya bar wajan duk yanda ja'mah da ƴan jarida sukaso su tareshi kauce masu yayi Hisham ne ya ƙara so wajan barrister Meenal dake tsaye kusa da barrister Halima sallama yayi masu kana suka amsa Hisham yace "Sannun ku ba bayin Allah barrister Meenal tace yauwa sannu yace sunana Hisham kuma ni Abokine ga barrister Habeeb ɗan Alhaji Muhammad" meenal tace "wane barrister Habeeb kuma?😳" Hisham yace wanda de kuke shari'ah tare, dan Allah inba zaku damu ba munasan magana da ku kunga a family ɗin Alhaji Muhammad cen in kun kalle so da kyau duk suna buƙatar ƙarin bayani a gamai da ku saboda kunyi mana bazata" Meenal ta kalli barrister Halima barrister Halima tace "ok babu da muwa ku biyoni gidana sai muyi magana" Hisham yaje ya samu su hajiya ya faɗa masu kana duk suka shiga mota sukabi bayan Su Meenal. London Salma tace "wlh joon komi zakayi saina koma Nigeria why za'a kawoni wata ƙasar?" Joon yace " waike salma bakijin magana ne nafa faɗamaki babu inda zaki wlh keda Nigeria har abada Dan haka ki fitar da rai daga zuwa can" Salma tace naji to indai kanaso na bar maganar Nigeria to kafaɗaman miyasa dad ya maidoni nan?" Baki joon ya washe yace "harkinsa naji daɗi kinga sai mu cigaba da rayuwar mu hankali kwance " to dayake Salma a iya zamanta da joon ta karanci mayan mata ne kuma dolo ne akan mace shidai burinshi bai wuce ace koda yaushe yana tare da mace ba, kuma indai mace zaita kasance tare dashi to komi yana iya yimata, ko da ta tuno da haka sai tayi saurin rungumoshi tace "kuma fa hakane sweet joon ni na hakura da Nigeria ai nasan zakji daɗi ko?" Joon yace "sosai ma kuwa" Salma tace "ok to ina saura ranka joon kafaɗaman gaskiya komi karka boyeman kaji?" Joon yace "ok kina nufun komi zan faɗa maki harda koke wacece?" Salma bata damu da wannan maganar da Joon yayi mata ba dan tasan ƙila shir man shi ne kawai sai tace mashi "eh" Joon yace..... *Ameenatu Sani ce👌🏻* *To ga new number na nan nasan zakuyiman saƙo a wancan number to na daina chart da ita 09039556566* [4/18, 5:17 PM] +234 706 650 5625: *👄MUGUN FURUCI👄* *Writing by Ameenatu Sani* *NASARA WRITERS ASSOCIATION* ___________________________________ {{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }} ___________________________________ https://www.facebook.com/103637491942644/ 💫💫 *{{N W A}}* 💫💫 بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم 101-105 Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===150 1GB@=====270 2GB@=====550 3GB@====800 5GB@====1,350 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR Call 08066268951* Joon yace "Aidai kinsan Alhaji Lukuman ko?" Salma tace "kaji joon da wata magana yo ni kuwa nasan dad" murmushi joon yayi yace "to ba dad ɗinki bane" nan yabata labarin matsayin dake gareta wajan Alhaji lukuman wata irin zabura Salma tayi tace "wlh ƙarya kakeyi joon, nafi ƙarfin kakirani da ƴar tsintuwa". Joon yace "Salma natsu mana gaskiya fa nace zan faɗa maki ni nan da kike gani yaran Alhaji Lukuman ne na hannun damarshi babu wani sirrinsa da bansani ba wlh yanzu ma da kika ganni nan ƙasar kisa yasani nayi a Nigeria kuma nemashi akeyi acan shiyasa yace na dawonan dazama kwata kwata duk ranar da yaganni Nigeria saiyasa an kasheni, tokema a Nigeria sunan ki matatta" nan ya bata labarin duk abinda ya faru da kuma duk irin shirin da Alhaji lukuman keyi akan Alhaji Muhammad harta dangan takar dake tsakanin Alhaji Lukuman da Alhaji Muhammad saida ya faɗa mata ya ɗaura da faɗin "to kijinji gaskiyar magana dan haka Alhaji lukuman ya kawoman ke nan yace da inma kasheki hankalinshi ya kwanta nace a'a London bakamar Nigeria ba da ake kisa kamar ankashe dabba kawai ya barmanke kinzama tawa har abada kamar yanda nabaro Nigeria haka kema kin barota kenan yaceman da ansamu nasarar kashe Alhaji Muhammad to zaiban nera million biyar musha shagalimmu" tunda joon yafara magana Salma ke rusar kuka hawaye kuwa kamar anbuɗe famfo zuba kawai suke ba ƙaƙƙautawa. joon ya rungumota yace "sorry my love ni bazan kasheki ba saboda inasonki kinji". ƙwace jikinta tayi daga nashi ta ruga da gudu ɗaki tana kuka wata irin tsanar Alhaji Lukuman taji aranta jitake dama zata ganshi yanzu da ta kasheshi da hannunta dan haka tayima kanta Alƙawarin komi zaifaru saidai yafaru amma bazata taɓa zama a London ba saita koma Nigeria ta tona mashi asiri, daganan tafara tunanin taya zata bar ƙasar gashi babu kuɗi a hannunta kuma babu pasport ɗinta a hannunta komi nata joon ya boye. Joon ya shigo ɗakin ya hau gadon ya mirginota a kanshi yace "please beautiful kidaina kuka miye dan an raboki da Nigeria kawai kimanta kizo muci gaba da rayuwar mu mai daɗi anan" Murmushi tayi ta share hawayanta cike da kissa tace "to shikenan joon nawa maganar tawuce" Shmaɗin murmushi yayi kana ya haɗe bakinshi da nata yana kissing ɗinta.. Nigeria Bayan sun isa gidan barrister Halima tabasu wajan zama da lemo bayan sunsha sun nutsu Hisham yace Mungodai sosai barrister Allah yasaka da alkhari" barrister Halima tace "babu komi" Hisham yace "dan Allah munaso musan ko ku suwaye" barrister Halima tace "Ni sunana barrister Halimatu Usman ni ƴar kaduna ce mijina yadawo nan shiyasa muke anan garin" hajiya Fadeela tace "masha Allah" meenal tace nikuma sunana Barrister Ameenatu Amma amfi sanina da meenal nima ƴar kaduna ce wannan case ɗin yakawoni nan garin" Hisham yace "masha Allah, to amma kina ƴar kaduna taya kikazo katsina saboda case ɗinnan?, Ke bama wannan ba dan Allah waye ya ɗaukeki lauyan Alhaji" Meenal tace "Case ɗin nan ai bana ƙananan mutane bane bare ace anyi mamaki dan ɗan kaduna yaji ba, ɗaukana lauya kuma nikaina ina da buƙatar sanin ko waye ya ɗaukeni dan nima ban sanshi ba" Hisham ya jinjina kai yace "amma da mamaki kice baki sani ba" wayarta ta ɗauko ta nuna mashi messages ɗin da akeyi mata kullum ko yanzu ga shinan an turo mata message kamar haka *Bansan da bakin da zan godai maki ba barrister bakina yaman nauyi wajan gode maki ba dan Allah ki cigaba da kokari harsai kin tabbatar da gaskiya please* Bayan tagama karantawa tamiƙamasu kowa ya gani. Kana tace "kawai hakanan nakeji ajikina saina taimakeshi" Jimamin abin suka dunga yi da mamaki su kansu sun kasa gano waye wannan, nan dai sukaita tattaunawa akan maganar daga ƙarshe suka yimata sallama akan zasu kirata in sunsamu wani bayani. *Ameenatu sani ce 👌🏻* 09039556566 [4/18, 5:17 PM] +234 706 650 5625: *👄MUGUN FURUCI👄* *Writing by Ameenatu Sani* *NASARA WRITERS ASSOCIATION* ___________________________________ {{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }} ___________________________________ https://www.facebook.com/103637491942644/ 💫💫 *{{N W A}}* 💫💫 بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم 106-110 Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE* *I selling MTN data with this cheap price* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===150 1GB@=====270 2GB@=====550 3GB@====800 5GB@====1,350 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo* *also available.* *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR Call 08066268951* Da misalin biyu da rabi na dare kowace halitta na hutawa domin ance dare ma hutar bawa, amma banda Meenal dake zaune kan abin sallah tana lazimi gama sallarta kenan tana addu'ar allah ya basu nasara da sa'ar wannan Sari'ah Allah yabama mai gaskiya gaskiyar shi. Kamar an tsunkulaita haka taji da sauri ta mike ta je jikin tagar da ke fuskantar bakin gate ta tsaya labule ta daga aikuwa idanuwanta suka sauka akan wasu ƙatti dake durowa ta katangar gidan ai da sauri tasaki salati ta ruga da gudu ɗakin Barrister Halima ta tasheta da ƙarfi tace "Anty Halima tashi da Alama ankawo mana harin sumamai tshiii" da sauri tamiƙi tace "hari kuma meenal?" meenal tace "Miye mafita gasucan suna saukowa a katanga" ai da sauri ta duro ta ɗauki hijabinta da wayarta itama meenal ta ɗauka suka fito parlour can meenal ta hango tagar da lafiya lau zasu dire waje aiko tacema Halima "Anty zo mubi ta nan" direwarsu kenan sai gasu sun shigo parloun ogansu yace "Kushiga lungu da saƙo na gidannan ku fito man da ita nan" sukace "toh boss" su meenal kuwa sunajin haka sukatafi a hankali a hankali har sukaje wajan ƙofa suka buɗeta aiko suna fita suka ruga da gudun tsiya gudu suke bana wasa ba saida sukayi nisa da gidan sosai kana Suka tsaya brrs. Halima ta fito da wayarta ta kira mijinta tafaɗa mashi komi ke faruwa yace "karsu koma gidan in suna kusa da gidan da suka sani suje can" aiko tana kashe wayar ta kira wata ƙawarta dake kusa da inda suke saida tayi mata kira biyar kana ta ɗauka Halima tace "Shafa'atu Barrister Halima ce dan Allah ki bude mana gidanki ga munan zuwa muna cikin matsala ne" tace "ok toh sai kunzo" haka suka sake rugawa a guje har suka isa gidan. Bayan sun bincika ko ina na gidan basuga kowa ba harta ƙarƙashin gado saida suka leƙa babu kowa haka suka zo suka sanar da ogansu, shima ya ƙara dubawa da kyau babu kowa haka suka kwashe komi nasu mai hamfani kamar kuɗi tv buhunnan abinci jarkar mai da dai sauransu sata sukayi masu sosai kana suka fito sai a lokacin suka fahimci guduwa sukayi tunda ga ƙofanan a bude suma sai suka shige motar da sukazo da ita suka loda kayan da suka sace aciki ogan ya kira Alhaji Lukuman yashe da mashi ai sun gudu daga gidan nan yaitayi mashi faɗa yace kuma ya tambatar sunnemota duk inda take kamun wayewar gari. Haka sukaita bi lungu da saƙo amma babu su babu alamunsu. London So sai Salma ta kwantar da kai wajan Joon yana ƙara bata sirrin Alhaji lukuman kuma take karɓar kuɗi a wajanshi dukda de bai barinta fita ita kaɗe kuma cikin narasa ta gano inda ya boye mata komi nata na barin ƙasar kuma a koyaushe ce mashi take bata ba Nigeria saboda in ta koma tasan zaikashe tanai da irin wannan tabbatar war da take mashi yasa har ya yarda da itatafara fita ita kaɗe a cikin fitar da takene ta sawo maganin bacci mai mugun ƙarfi haka da safe tasa mashi a cikin lemu yasha bacci ya kwashe shi aiko da sauri ta ɗauki duk abinda take so ta gudu batare da ɓata lokaci ba taje ta yanki visa nan da awa kaɗan jirginsu zai tashi.. Nigeria Washe gari Su meenal dama tunda sukazo basu koma bacci ba haka sukaita jajanta maganar har mijin shafa'atu nacewa a kira police meenal tace a'a amma bazasu koma gidanba sai mijin Halima ya dawo dayake yace ya nanan zuwa garin yau ko gobe. Bayan sunyi breakfast Meenal takira Ammi ta faɗa mata komi yafaru ai kuwa itama tace zatazo garin yau meenal tayi ƙoƙarin hanata amma tace saitazo. Habeeb Saboda damuwa tayi mashi yawa ciwon zuciyarshi ya tashi haka yaita jinya a cikin ɗaki Hajiya dama tace bata ba Habeeb shiyasa ko wajanshi bata zuwa takuma hana kowa zuwa wajanshi, saida yaji zai mutu da ƙyar ya iya ɗaga wayarsa ya kira hisham shima da yaƙi ɗagawa saidaga baya ya ɗauka jin muryar shi yandata koma yasa yazo gidan batare da hajiya ta sani ba cikin irin hali da yaganshi yasa a kiɗimai ya ɗauke shi sai asibiti... Ameenatu Sani ce👌🏻 [4/26, 11:39 AM] 💜Ameenatu Sani💜: *👄MUGUN FURUCI*👄 *writing by Ameenatu Sani* *NASARA WRITERS ASSOCIATION* ___________________________________ {{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }} ___________________________________ https://www.facebook.com/103637491942644/ 💫💫 *{{N W A}}* 💫💫 111-115 tun ƙarfe goma Salma ta duro Nigeria ɗan ƙaramin hotel tasamu ta kama nan take zaune waya tasaya ta sayi layi ta buɗe duk wata social media ai kuwa batare da ɓata lokaci ba taita cin karo da yanda komi ke gudana dan har shoot video anyi na zaman kotun,anan ta ƙudiri aniyar kawo ƙarshen cutar Alhaji lukuman ta hanyar tuna mashi asiri sai dai matsalarta ɗaya batasan inda zataga barrister Meenal ba amma zata cigaba da bibiyar kowa batare da an sani ba . Alhaji Lukuman a tsawace yace "wlh dage kunbani kunya aina ɗauka kuɗin wasu jarumai ne ashe taran shasha shaune ban sani ba ace yarinya ɗaya ta gagareku kamawa!" yafaɗa cikin ƙunar zuciya dage yace "kayi haƙuri mai gida baza a ƙara samun saɓani ba insha Allah kamun gobe sai mun kawo maka ita" "ku kawoman ita taiman uban mi?, ku kasheta kawai" "angama mai gida, kai kutashi mu fasa yau komu ko ita" dage ya faɗa tare ta jan zugarshi. Meenal tace " yanzu ga ammi can tazo tasha bari naje naɗauke ta amma banan zan kawota bazan jena kama mana hotel tunda kinga nan kada a takura bayin Allah" barrister Halima tace "hakane nima ɗazu munyi waya da yallaɓai (mijinta) yace inyi haƙuri yau bazai samu tahowa ba amma kada na takura mutanan gidan naje mu kama hotel cikin sirri kafin ya dawo". meenal tace "ok bari naje zumbulailiyar hijabin matar gidan ta saka da niƙaf ta yanda babu mai ganeta kana ta rataya jikkarta tayi ma barrister sallama tana cewa ta kula fa. bayan ta ɗauko ammi da tasha zaune suke a napap sai bama ammi labarin yada abin yafu take har mai napap nacewa allah ya kyauta. ɗan madaidaicin hotel takama acewarta nan da two days zasu tafi bayan ammi tahuta Meenal ta kira barrister Halima ta bata address ɗin hotel ɗin jimawa kaɗan saigata ta ƙara so. bayan heesham ya kai Habeeb hospital an bashi tai makon daya dace an ɗaura mashi ruwa bacci yake kaida ganin baccin kasan bana daɗi bane idanu heesham yatsura mashi yana kallanshi duk ya ramai yayi baƙi kamar ba HM ɗan gayuba maiji da kan shi ba amma ji yanda ya koma wani iri a ranshi yace alhakin dad ne sai kuma yayi saurin girgiza kai yace waṇnan ba halinshi bane. sanye take cikin baƙar doguwar riga tare da hajabi pink dogo amma baikai har ƙasa ba hakama fuskarta boye cikin niƙaf baƙi kulle ɗakin hotel ɗin tayi ta na tafiya cikin sauri karo sukayi har wayar ɗayar ya faɗi a tare suka duƙa domin ɗauka suna ɗagowa Salma ta nuna Meenal da hannu tace Barrister. *Ameenatu Sani ce👌* [4/26, 1:17 PM] 💜Ameenatu Sani💜: *👄MUGUN FURUCI👄* writting by Ameenatu Sani *NASARA WRITERS ASSOCIATION* ___________________________________ {{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }} ___________________________________ https://www.facebook.com/103637491942644/ 💫💫 *{{N W A}}* 💫💫 116-120 da mamaki Meenal ta kalleta da sauri salma ta ɗaga niƙab ɗinta tace "nice Salma ɗiyar Alhaji lukuman". idanu meenal ta zaro tace "salma!?" hannunta salma taja tace "muje ɗakina" binta meenal tayi har suka ƙarasa ɗakin salma ta rufe kana ta yaye niƙab ɗin tace "nasan kiyi mamaki ko?, to ba abin mamaki bane dan Allah ya nuna ikonsa, zauna mana kinyi tsaye " zama meenal tayi har yanzu bata daina mamaki ba ace wai wannan salma ce salma tace "kamar yanda na faɗa maki nice salma ɗiyar da Alhaji lukuman ke iƙirarin ni ɗiyarsa ce, yanzu haka fitar nan da kikaga nayi nemanki zani yau kwanana biyu ina yawon nemanki saboda nasan gobe za a shiga shari'a ta ƙarshe da harna yanke shawarar in dai ban ganki ba yau to zan baiyana kaina kawai" da ƙar meenal ta tattaro nutsuwarta tace badan naga videon gidan kuma kuma na ganki a ciki ba da bazan taɓa yarda kece salma ba amma abin mamaki keda akace kin mutu taya kike a raye har ina magana da ke?" salma tace ban mutu ba asalima bana ƙasar ina London......nan takwashe komi da joon ya faɗa mata ta faɗama meenal cike da jin matsanan cin farin ciki meenal ke rarrashin salma dake kuka tunawa da abinda lukuman yayi mata. bayan ta nutsu meenal tace gaskiya salma bansan da wane irin baki zanyi maki godiya ba saboda baiyana mana kanki da kikayi kin taimaka sosai wajan wannan shari'a kuma insha Allah sai anyanke ma lukuman hukunci daidai da abinda ya aikata, yanzu ki kwaso kayanki kitaho muje ma sauki mu dan na kula dake kafin gobe dan rayuwarki a nanda matsala. batare dabata lokaci ba suka isa ɗakin su meenal a can ma sunyi mamaki ƙware da gaske da sukaji labari salma nan suka fara sabon shiri da yanda zasu fara. a gurguje jikin habeeb yayi sauki sosai har an sallamoshi har zuwa wannan lokaci babu wata kyakkawar mu a mulla tsakanin habeeb da heesham domin heesham haushin habeeb yakeji sosai koda ya maidashi gida har heesham ya jiyo zai tafi habeeb ya riƙe hannunshi yace haba heesham wai fushi kakeyi dani a tsawace heesham yace sakeni malam karkaga nayi jinyarka daga jiya zuwa yau kayi tunanin ko har yanzu ina tare da kai habeeb yace haba heesham kaida kowa nawa kun ɗauki karan tsana kun ɗaura mani akan wani dalili naku harta momy ta juya man baya why? heesham yace tambaya ma kakeyi?, wlh habeeb ban taɓa ganin wawa sakare daƙiƙi irin kaba kuma bari kaji wlh saikayi nadamar abinnan da kakeyi habeeb yace heesham a kwai abinda ya ɗaure zuciyata nakasa furtashi dan Allah kuyiman addu'ah wani kallan raini heesham yayi mashi ya fice daga gidan, kuka habeeb ya rushe da shi zuciyarshi nasan komawa ciwo. kutu bayan kowa ya hallara anfara karanto ƙara alƙali yace in lawyan mai kare wanda ake ƙara na kusa ya fito domin muji hajjojin ƙarshe domin yaune za ayi zaman ƙarshe. cike da murmushi da farin ciki meenal ta miƙe tace ya mai shari'a inaso a gayyato mani doctor ɗin da ya duba Salma inason yin magana dashi al ƙali yace in yana kusa ya fito nan hanjin cikin alhaji suka kaɗa sai alokacin yayi nadamar gayyato doctor domin yaune suka aje maganar ana kashe alhaji Muhammad zai cika mashi kuɗin shi doctor batare da fargabar komi ba ya fito tunda alhaji ya tabbatar shi babu wata matsala da za asamu cike da ƙasaita meenal ta fito cikin burgewa ga kayan sun yimata kyau sosai ta isa ganban doctor tace doctor ko zaka sanar da kotu ko nawa alhaji lukuman ya biyaka domin kayima salma allurar suma? ba doctor ba harta ja ma'ar dake kotun saida suka girgiza musamman alhaji lukuman da alhaji bala da hajiya mariya cikin sarƙewar numfashi alhaji lukuman yace ƙarya take ya mai shari a sheri zatayi mashi alƙali yace "waya saka bakinka a ciki nan kotu ce ba wajan wasa ba dan haka kakiyaye ba ayin magana sai an bada umarni" wani murmushin zaka gane kuranka meenal tayi mashi kana tace tambayar ka nake doctor cikin hausar da bata ida gamai bakin doctor ba yace ni bai biyani wasu kuɗi ba daughter ɗinshi ta mutu meenal tace ka tabbatar ta mutu? da sauri yace eh meenal ta kalli alƙali tace ya mai shari'a ayiman afuwa za aji ina tayin wasu tambayoyi a ɗauka inasan wasa da shari'a ne, amma bari na ta ƙaita tambayoyina kawai na kawo ƙarshen case ɗin nan saboda a bar bawan Allah ya sha iska, kamar yanda na faɗa Alhaji Muhammad bashi ya kashe salma ba kawai tsautsayi ne da kuma *MUGUN FURUCI* da yayi ya hau kanshi shi kuma Alhaji lukuman yayi amfani da shi domin ganin ya kaishi ƙasa isah driver drivern alhaji Muhammad ne amma kuma alhaji lukuman yake ma aiki, haɗuwar salma da alhaji Muhammad hanya ɗaya duk shirine domin ankira alhaji Muhammad ance mashi ana meeting a g.r.a ƙarfe 8 shi kuma alhaji lukuman yace ma salma ta shirya zai aiketa g.r.a karɓo saƙo, to tanan hanya ta haɗasu batun ciwon kan da isah driver yace yanayi ƙarya ce duk shiri ne dan alhaji muhammad ya amshi tuƙin dan yaga motar da salma take ciki ta taho,kuma shine ya take giyar motar domin tabi takan motar salma saidai allah ya kyauta salma bata mutu ba saidai ta bugu a kai alhaji lukuman ya haɗa baki da doctor dan akashe salma amma ba su samu nasara ba saboda shawarar hajiya mariya anan aka yima salma allurar suma kuma a daran aka fitar da ita daga ƙasar zuwa london doctor ya samo masu gawa mai daidai jikin salma akace salma ta mutu, kuma inaso ka tambayi police ɗin da suka fara cace ɗin ko idan sunga fuskar salma lokacin da akace ta mutu. kowa acikin su suman zaune yayi alhaji lukuman kau saboda tsananin zufar da ta wanke shi kace jarka ɗaya aka sa mashi a jiki alƙali ya sauke a ajiyar zuciya ya dubi meenal yace ke duk a ina kikasan haka? meenal tace ya mai shari'a duk wanda keda hannu a cikin wannan case a tambaye shi in ba haka a kayi ba kamun na bayyana sheda ta ta ƙarshe nan alƙali ya fito dasu su duka kuma duk sunce ƙarya takeyi barrister habeeb kuwa tunda aka fara ya koma kamar gunki nan cece kuce ya tashi a kotun inda alƙali ya tsawatar bayan kowa yayi shiru alƙali ya buƙaci meenal ta bada sheda ta gaba cikin takon ta na isa da nuna ita jaruma ce ta ke tafiya har inda jama'a ke zaune anan tasa hannu ta kamo salma take ƙunshe cikin niƙab ta fito da ita kowa ya ƙagara yaga wacece. Ameenatu Sani ce👌 [4/27, 10:44 AM] 💜Ameenatu Sani💜: *👄MUGUN FURUCI👄* By Ameenatu Sani *NASARA WRITERS ASSOCIATION* ___________________________________ {{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }} ___________________________________ https://www.facebook.com/103637491942644/ 💫💫 *{{N W A}}* 💫💫 🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚 121-125 gaban Alƙali ta kaita gami ta yaye fuskarta nan take fuskar ta bayyana jama a suka buga salati suna tsinema lukuman meenal tace ya mai shari a wannan itace salma da akace ta mutu kamun alƙali yayi magana akaji Alhji lukuma ya buga ihu yace woni kafuri woni lukuman mai ta ɓargaaza woni lukuman mai kashe kashe hahahahaha nine na kashe ubana na kashe uwar muhammad na ɓatar da ɗan uwana muhammad woni makiri nina shirirya komi dannayi dukiya hahahaha, maganganu dai barka tai da akalura ya fita dada hankalinshi nan aka rirriƙeshi ana tsine mashi da faɗin alhakine yake tambayar sa anan dai aka yankema alhaji bala da doctor da isah driver hukunci ɗaurin shekara ashirin da biyar a gidan yari tareda horo mai tsanani hajiya mariya shekara goma ahaji muhammd kuwa kotu ta wanke shi suɓul soso da sabili kuma agaban kowa hajiya mariya ta tona cewa asiri alhaji lukuman yayima habeeb duk dan duniya ta tsane shi ta nemi yafiyar salma kuma ta yafe mata saboda badan ita ba da yanzu sunanta gawa sai anan hankalin alhaji muhammad na ainihi ya dawo habeeb ma hankalinshi yadawo alƙali da kanshi yayima alhaji Muhammad bayanin komi ya faru gami da nasihar ya ɗauki ƙaddara alƙali yace a je da lukuman asibiti a tabbatar da hankalinshi kana a yanke mashi hukunci haka aka kakkamashi zuwa cikin mota amma ya shammace su ya ruga da gudu ƙatuwar motar da ta nufoshi ya afkamata nan tabi ta kanshi koshurawa baiyi ba ya mutu saboda kanshi ya da gargaje. a gurguje bayan wata biyu da faruwar wannan al-amari alhaji Muhammad kowa ya zamai mashi sabo a gidan kowa sai godaima salma da barrister meenal yakeyi soyayyar meenal ta ruru a zuciyar habeeb tunda tasan shine yake mata message ɗin nan kowa yayi farin ciki musamman Hajiya Fadeela da Muhammad da suka dawo da soyayyar su sabuwa dal hakama soyayya ta ƙullu tsakanin salma da heesham amma ita salma habeeb take so dan bayanda zatayi ne shiyasa kuma alhaji Muhammad ya riƙe salma. bisa shawarar da abokai da jamar alhaji Muhammad ya nemi kujerar governor kuma yasa mu saidai fatan allah ya tayashi ruƙo bayan wasu watanni anyi auran meenal da habeeb heesham da salma dukkanin su suna a tantsama tansaman gidajansu suna rayuwar farin ciki dana nnushuwa babu wata damuwa atare dasu har kullum addu a ammi takema meenal akan aikin ta kuma addu arta karɓaɓɓiya ce saboda tana ta samun ciga ba da promotion a wajan aikinta yanzu tare suke aiki da mijinta barristar habeeb arziki sai ƙara samunsu yake, hakama alhaji muhammad jama a sunata san mulkinshi har so suke yazama shugaban ƙasa domin mutumne mai adalci da san talakkawanshi.. *Alhamdulillahi anan na kawo ƙarshen littafina mai suna a sama ina roƙon allah ya ya feman kuskuran da na yi abinda na rubuta daidai allah yasa a amfana dashi👏🏻* *harkullum bazan gaji da godai makuba masoyana tayanda kukayi jimurin jirana kukaita bibiyar littafin nagodai sosai son so fisibidillahi nakema kowa* *sai munhaɗu a sabon littafina bayan sallah insha Allah, ya Allah ya karɓi ibadummu alfarmar watan ramadana allah ya biya kowa buƙatunsa na alkhairi👏🏻* *Ameenatu Sani ce*👌