Compiled By Umar Dalha Funtua. ✍🏽 *~KUNDIN QADDARATA~*✍🏽 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *innama amruhu iza arada shai'an an yaqula lahu kun faya kun* 0⃣1⃣            Falo ne mai matsakaicin girma wanda ke dauke da set din kujeru labulaye carfet wanda dukkansu kalolin ash ne turarre da kuma mai haske,daga bangare daya t.v plasma ce 'yar matsakaiciya reciever da kuma D.V.D  wadanda aka qawata jeransu.      Can daga kowacce kusurwa ta falon flower ce cikin plower vase dake a tsaye masu matsakaicin kudi,sosai falon ya bada sha'awa duk da ba wani uban kudi aka narka masa ba sakamakon yadda komai yake tsare a muhallinsa,bugu da qari kuma yadda ya wadatu da tsafta yake bada qamshin turaren wuta mai sanyi     Mamallakiyar falon ce zaune kan daya daga cikin kujerun falon,matashiya ce wadda ba zata wuce shekara sha takwas ba,fara ce ba irin qal din nan ba,tana da matsakaicin kyau wanda kwalliyar da tayi cikin shadda orange dinkin bubu ya sake fidda kyanta,dan kwalin shaddar na ajjiye gefanta wanda ya zamo sanadiyyar bayyanar kitson dake kanta qananu wadanda aqalla sun doshi guda dari da hamsin,yadda falonta ke qamshi hakama jikinta yake yi.     A hankali ta daga kanta karo na barkatai ta sake aza su kan agogon bangon dake manne saman t.v plasma din dake gabanta maqale jikin bango.      Sauke idanun nata tayi kana ta maida kan dan madaidaicin centre table din dake gabanta,ta miqa hannunta ta dauki wayarta samfurin tecno w3 ta sake lalubo lambar da tun dazun take ta nacin kira,duk da cewa amsa daya ake bata tun dazun cewa lambar da take nema din a kashe take amma hakan bai sanyata ta daina kira ba.    Yanzu ma amsar duka daya ce,bai saba kaiwa war haka bai dawo gida ba,yawancin baya gota qarfe takwas indai ya dade da yawa bai dawo din ba,sau tari idan taga hakan kuma ta tabbatar ba zaya wuce gidan babbar yayarsu ba hajiya yahanasu,saidai yau duk sai taji gidan shiru babu dadi,saboda baki daya 'yan tayata zaman sun tafi gida saura ita daya.     Sauke ajiyar zuciya tayi tare da lumshe idanunta,ta dan zame kadan ta kwanta saman kujerar tana jin kewa na ratsata,kewar yara take sosai,mutum ce ita mai bala'in son yara,saidai Allah bai azurta ta da samun nata na kanta ba tsahon shekara shida da aurenta,kasancewar tayi aure tun tana da shekara goma sha biyu kacal a duniya.      Tayi zurfi kadan cikin tunanin nata taji ana yunqurin bude qofar gidan da muqulli,ta bude idanunta tana duban agogo,qarfe tara har da mintina arba'in da biyar goma saura kenan,zumbur ta miqe ta janyo dankwalinta ta daura kana ta fito a hankali ziwa tsakar gidan nasu wanda yake da yalwa babu laifi,bayan nata dakin ciki da falo akwai dakuna biyu masu ciki dai dai wanda guda daya mallakin mai gidan ne,dayan kuma 'yan karikicen da ba'a rasa ba take ajjiyewa ciki,sai kuma bandaki daga bangare daya gefensa rijiya ce,sai kuma yalwataccen kitchen dake kallon dakuna biyu masu ciki dai dai din wanda yayi girman dakunan nasu,fes tsakar gidan shima yake kamar yadda ilahirin gidan yake,sumuntin tamkar ka zuba abinci a qasa kaci saboda wadatar tsafta.         Tana tsayen har ya kammala bude gidan ya turo babur dinsa(lifan)samfurin companion,a tsakar gidan ya masa matsugunni gefe daya lokacin da take qarasowa gareshi tana ambaton "sannu da zuwa" fuskarta qunshe da murmushi wanda lokaci guda ya soma qoqarin gushewa daga fuskarsa sakamakon ganin fuskarsa sam babu annuri lokacin da yake amsa mata da "yauwa sannu da gida,na barki ke daya na tsaya gidan yaaya yahanasu" "Eh nayi zaton hakan" ta fada tana sanya hannunta ta amshi jaka da ledar hannunsa jikinta a sanyaye tana qara cika da mamakinsa saboda sam ba haka ya sabar mata ba idan ya shigo gidan.       Tana gaba yana biye da ita a baya tare da qare mata kallo,komai na sumayyarsa na burgeshi,har yau baya manta lokacin da ya aureta da qananun shekarunta wanda za'a iya kiranta qwaila,amma a ayanzun sai ka rantse ba sumayyar nan bace wadda ya aureta shekara shida baya da suka wuce.    A falon ta barshi ta dawo tsakar gida tana hada mishi ruwan wanka zuciyarta na sake gaya mata akwai abinda yau ke damun mukhtar dinta,mutumin da ita ke tayashi shigowa da babur dinsa ta hanyar bude masa qofa da rufewa,da ya shigo zai rungume ta yana yaba kwalliyarta,a haka zasu qarasa falo,ko da ruwan wanka wani lokaci tare suke hadawa,bai barin bakinta ya huta idan ya dawo,gwanin tsokana ne da son sanyata dariya.    Falon ta sake dawowa tana tsane ruwan hannunta,yadda ta barshi zaune haka tazo ta tarad da shi,bata ce uffan ba ta qarasa gareshi ta rage masa kayan jikinsa,shima bai tanka ba illa kallo da yake binta da shi har ta kammala ta miqa masa towel,karba yayi ya rataya a wuyansa sannan ya fice.    Kafin ya fito har ta kammala jera abinci zuwa ruwan wanke hannu,dakinsa ya wuce kansa tsaye ya sanya jallabiya kana ya dawo cikin falon.     Dukkaninsu jagula abincin kawai suke da cokulansu,damuwar data lura yana ciki ita ta hana mata sakewa taci abincin,duk da yunwar da take ji saboda bata iya cin abinci sai tare da shi,hakan ya sanya ko da rana ba don albarkacin yaran dake shigo mata ba wanda ta maida tamkar qannenta da ba zata dinga cin abincin rana ba,tana son tambayarsa amma bata son masa katsalandan,saboda shi da kansa yake sanar mata damuwarsa ba tare da ta kai ga tambayarsa ba,kasancewar ya maidata tamkar abokiyar shawara gareshi,sosai zuciyarta tayi ta kasa sukuni.    A hankali ya daga idanunsa ya dora akanta sakamakon tuna a inda yake,sai yaji tausayinta ya kamashi,baiji dadin sanyata a damuwa ba,ga uwa uba yana hasashen nan gaba kadan zata iya shiga damuwar data linka wannan.    Ajjiyr cokalin yayi yana qirqirar murmushi tare da kamo hannayenta ya riqe "Lafiya qalau kuwa yau kike my sumy?" Cikin raunanniyar murya tana qoqarin maida qwallar data taru a idonta kasancewarta mace marason damuwa,kanta ta langabe cike da rauni "Kai zan tambaya yaya mukhtar" ta qarashe fada muryarta na rawa,girarsa ya dage "Me ya faru?" Qoqarin daidaita muryarta tayi "Ban taba ganinka cikin damuwa yaa mukhtar irin haka ba,me ya faru da kai" kai ya girgiza yana sake qirqirar murmushi yana qoqarin azawa fuskarsa,don baisan ta ina zai fara sanar mata damuwarsa ba,ya tabbatar za tayi nauyi a qirjinta fiye da yadda tayi nauyi a nasa qirjin,bai da buqatar fadawarta damuwa ko kusa,sai gashi yaya yahanasu nason jefasu damuwa duka su biyun,sonta da tausayinta wani bangare ne mai girma a rayuwarsa "Sumayyaaaaah" ya dan ja sunan nata yana kallonta "Babu wani abu da yake damu na,gajiya ce kawai,matso maza kici abinci don na tabbata babu abinda kika ci" ya fada yana janyo plate din gabansa tare da zare nata cokalin ya fara juya abincin da iya nasa cokalin da alamu yana nufin ciyar da ita da kansa kamar yadda yake mata wasu lokuta.    Kan ta ta girgiza idanunta cike da qwalla"ya mukhtar kayi haquri amma wlh ban yarda cewa baka da damuwa ba,bazan ci abincin nan ba har sai ka gayamin meke damunka"cokalin ya ajjiye kana ya sauke ajiyar zuciya,baya da nufin fada mata komai amma ya fuskanci idan baiyi wani abu ba zata qi cin abincin ne kuma ta kwana cikin damuwa saboda haka yace da ita "Naji,zan gaya miki amma ba yanzu ba,kinga dare yayi sai gobe idan Allah ya kaimu,yanzun ki matso kici abinci tukun" "Kayi alqawari?" Dariya ta bashi saboda yadda quruciyarta ta fito muraran sanda tayi maganar "Eh nayi" ya fada shima.     Ko da suka zo kwanciya haka ya dinga qoqarin boye damuwarsa,ya dinga qarfin halin aiwatar da duk wani abu da ya saba yi mata su don cire zargi daga zuciyarta da kuma son ganin ta sake,zamu iya cewa barcinsa kadan ne a daren ranar,cikin duhun dakin ya dinga juyi yana sake bitar maganganun da sukayi da yaaya yahanasu a wannin da suka shude dazu,yana cikin wannan tufka da warwarar bacci yayi awon gaba da shi.     Washegarin ranar duk da maganar da sukayi daren jiya na maqale a zuciyarta tana mata yawo wanda ya haddasa mata wata kasala hakanan da mutuwar jiki saboda har wayewar garin damuwar dake fuskar sa bata bace ba,hakan bai mata tasiri ya hanata yin duka wata hidima ta gidan ta ba,wanda ya kama da tsaftace gidan kafin tashin mukhtar daga bacci,shirya abun kari da tanadar masa ruwan wanka.      Yana tsaye bakin gado yana sanya links din hannun rigar shaddarsa,yayin da take gaban madubi tana shirya masa ragowar kudadensa da ya taho da su daga kasuwa da zai fita da su ya kaisu banki,hira suke jefi jefi duk da ba kamar yadda suka saba bane.      Bayan ya kammala ya tako gaban madubin yana gyara zaman hularsa a kanshi,sumayya ta dubeshi cikin zuciyarta tana yaba kyawun da yayi,ya kula da ita saboda haka cikin salon tsokana yace "Ki fito kawai kice na fiki kyau yarinya,sai wani satar kallona kike" sau tari idan ya fadi haka kunya da dariya yake bata,har ma wani lokacin musu ya dan kaure tsakaninsu,yau din ma dariyar tayi,maimakon ta biye masa auyi musun su na ta fishi kyau da iya kwalliya yadda suka saba sai tace "Yaa mukhtar,yau ne fa sunan fiddausin" yanayin fuskarsa taga ya dan sauya,bai ce komai ba yana daura agogon hannunsa,har ta fidda rai tayi zaton ba zaya ce komai din ba sai taji yace "Zaki je dinne?" Murmushi tayi saboda mamaki tambayar ta bata,fiddausi ai kamar diyarsa ce saboda 'yar yaya yahanasu ce,kuma shi da kansa ya bada kudin ankon sunan harda kudin dinkin ma "Me zai hana yaa mukhtar,saidai idan kai ka hana" shiru ya sake yi har ya kammala ya dauki jakarsa ya rataya sannan ya sanya hannu cikin aljihun rigarsa ya fiddo da dari biyar ya miqa mata kudin cefane,sannan ya sake fitar da dubu daya daban yace mata kudin mota,ya sake bata wata dubu biyun yace ta baiwa mai jego barka,hannu biyu ta saka ta amsa tana jera godiya kamar yadda ya zame mata al'ada duk qanqantar alkhairin da zaya yi mata,tako masa tayi ta rakoshi har ya fidda babur dinsa waje tayi masa a dawo lafiya.     Tana shirin mayar da qofar gidan ta rufe taga ya juyo "Idan kika je kada ki dade,ki dawo gida da wuri,kuma bana son ki shiga cikinsu kuyita faman surutu" dan jim tayi saboda bai taba cewa hakan ba idan zata shiga cikinsu sai yau,amma sai ta share ta gyada kai kawai tace "Insha Allahu".     Qarfe sha biyu da arba'in ta kammala shirinta tsaf,tayi kyau cikin ankon sunan duk da cewa qaramar atamfa ce 'yar leda wadda kudinta bai wuce dubu da dari biyar ba,mayafinta takalmi da jakarta har sarqarta duka sun dace da atamfar,yau cikin yaranta ba wanda ya leqo,hakan baya rasa nasaba da ce musu da tayi zata unguwa ne gobe,yaran kusan tarbiyyarta ce,suna da hankali da nutsuwa,tsahon shekara shida suna tare suke debe mata kewa,sanda aka kawota unguwar ita din ma tana qwailarta,yaran basu wuce shekara biyu ba harda masu daya da rabi,ita ta dinga rainonsu,don karbo su take su wuni gurinta,iyayensu sun riqeta tamkar 'yarsu,don haka sabo da shaquwa ne tsakaninsu sosai.    Gidan maman sadiya ta shiga saboda tahowa da nana yarinyar maman sadiya wadda zata rakata,duk cikin yaran yarinyar tafi shiga ranta,a kitchen ta samu maman sadiyan na dora girkin rana,nana anci kwalliya ana tsaye bakin qofar daki,hatta da takalminta na qafarta,cikin barkwanci suka gaisa da maman sadiya kana tac" ga mutuniyar nan,tun dazun ta addaba sai taje taga kin shirya,ni na hanata"dariya sumayya tayi "Ai na gama sai tafiya" fatan dawowa lafiya maman sadiyan tayi musu kana suka fice.      Qarfe daya da wasu mintina ta isa gidan,tuni har ya fara cika da jama'a kasancewar haihuwar fari fiddausin tayi,gaisawa ta dinga yi da duk wanda taci karo har ta dangana da dakin mai jegon,'yan uwan mukhatar ne cike da falo zuwa uwar dakan fiddausin,bata gajiya ba sai data bi ta gaida kowa,yayin da kowa ke amsa mata cikin mabanbantan yanayi,wani ya amsa mata ba yabo ba fallasa,wani ya amsa mata cikin shakulaton bangaro,yayin da wani bai amsawa ma sai an tabo shi ance ana gaidaka,duk hakan bai dameta ba saboda shekaru biyu kenan da fara fuskantar irin hakan daga garesu,mutum ce ita mai qaranta zargi qwarai a kan mutum,babu wani abu da suka taba ce mata face sauyin fuska kawai da take gani daga garesu.     Cikin uwar dakan ta cimma fiddausi tare da yaya bara'atu wadda ita ke bin muktar sai mai bi mata fadima sai kubra 'yar yayan mukhtar,sai babbar 'yar yaaya yahanasu mansura,jaririyar ta dauka fuskarta qunshe da murmushi tana fadin "Kai masha Allah,jariri akwai abun sha'awa" "Hmmm,ku kam ba ruwanku da ita ko?"cewar fadima kafin tace wani abu yaaya bara'atu ta karbe zancen "Nan da wata goma idan Allah yaso gidan mutari zamu suna,wannan karon kam shima Allah ya kusa kawo masa" "Allah yasa"inji fadiman.     Hakanan ta samu kanta da fargaba hadi da faduwar gaba,bata fita daga wannan yanayin ba maganar fiddausi ta katse mata zaren tunanin da ta fara qullawa " au,ciki ne da sumayyan?"tabe baki yaya bara'atu tayi tana fadin "Hmm,ina fa,yaaya yahanasu ke nema masa auren fa'iza" wata matsananciyar faduwar gaba ta saukar mata,jikinta yayi sanyi qalau,ta dinga jin zuciyarta na bugawa da sauri "Alla ya sanya alkhairi" fiddausi ta fada tana kwashe rigunan barka na jaririyar daga kan gadonta tana lodawa cikin sif,hakanan take,baka fiya gane alqiblarta kan lamura ba.     A hankali ta zame yarinyar daga cinyarta cikin kasala sakamakon shigowar 'yan suna cikin dakin,ta budr jakarta ta fito da dubu biyun da mukhtar ya bata ta miqawa fiddausin tana cewa "Gashi,a siyawa baby turare" karba tayi tana fadin "An gode".      Duk yadda zancan ya daketa haka ta dinga dakewa tana yaqe,sam hankalinta ba'a kwance yake ba,qarfe hudu da rabi ta musu sallama don komawa gidan,ba wanda ya damu da tafiyar tata ballantana ya tambaya,sai data miqa nana gida sannan ta bude gidanta ta shigr.     Kan kujerar falonta ta zube tana kiran sunan Allab,tayi a qalla awa guda tana saqa tana warwarewa,tabbas sauyin fuska da ta samu daga garesu yana da nasaba da rashin haihuwarta?,aure kenan mukhtar zai qara?,eh mana,dole mukhtar ya qara aure,'yana da buqatar ganin jininsa kamar yadda danginsa ke da irin wannan buqatar',abinda zuciyarta ta tunasar da ita kenan,ambaton sunan Allah tayi ta runtse idanunta,babu shakka don so tana son mukhtar,amma bata jin zata yarda ta zama silar batawarsa da yayarsa wadda take tamkar mahaifiya a wajensu,tasan halin yaaya yahanasu sarai,duk abinda ta quduri aniya sai ta aiwatar da shi,hana na nufin bashi da amfani tace zatayi adawa da abinda ta umarceshi.     Cikin mutuwar jiki ta miqe don yin sallar la'asar tana istigfari,saboda lokacin ta da ya kusa qwace mata ba tare da ta yita ba,ko da ta idar ta jima zaune saman abun sallar tana addu'o'i sannan ta samu ta miqe,kitchen ta shiga,ta riga da tasan yau ta makara don haka bata da buqatar dora girki mai wuya saboda bata son mukhtar din ya dawo ya buqaci abinci bata kammala ba.     Tana girkin tana saqe saqe,tana ta faman hada daya da daya,sai yanzu ta tabbatar cewa damuwar jiya da mukhtar ya shigo da ita bata rasa nasaba da wannan zancan kenan?,da gaske ne kenan auren mukhtar zai qara?,sai tasa tafin hannunta ta share qwallar da take zubo mata tana addu'ar neman agajin ubangiji,babu shakka qauna ce ta sanya mukhtar ya kasa gaya mata komai.     Jallope din shinkafa tayi da kayan lambu saboda haka ana kiraye kirayen sallar magariba ta kammala,tuni dama tana da lemonta cikin dan qaramim fridge dinta wanda zobo ne da lemon tsamiya saboda mukhtar na sonsu musamman lemon tsamiya saboda maiqo.     A gurguje tayi wanka ta hada da alwala,bayan ta kammala sallah ta shirya tsaf cikin qananun kaya wanda take siya cikin gumama da ake budewa bayan layinsu,sosai kayan suka yi mata kyau,sai ka rantse babu wani abu dake damun zuciyarta.     Tana cikin yin turaren wuta taji bugun qofa,ta ajjiue kaskon ta zira hijabinta kana taje ta bude,Amrah ce 'yar maqotansu daya daga cikin yaran gidanta kenan riqe da kwanon samira a hannunta "Anty yau duk bamu ganki ba,baki dawo daga unguwar da wuri bane?" Yarinyar ta tambaya tana murmushi,murmushin itama sumayya tayi "Da wuri na dawo amrah,banajin dadi ne sosai yau" "Allah sarki anty sannu" yarinyar ta fada cikin nuna alhini,sumayyan ta amsa mata tana karbar kwanon da amrahn ke miqo mata "Gashi,dama mama ce tace na kawo miki dambu ne" murmushi ta sake yi tana cewa "Ayyah ki cewa mama na gode,ashe bata manta da ni ba,jirani ina zuwa" ta fada tana shiga da kwanon ciki,alewa ta ciro guda biyu cikin jakar alawar 'yar dari da hamsin da take badawa ana siyo mata saboda yaran "Ungo ki gaida mama da kyau" hannu biyu tasa ta amsa tana cewa an gode ta juya ta tafi.     Tana shirin maida qofar ta rufe horn din mashin din mukhtar ya dakatar da ita,sai ta zare sakatar gami da bude masa qofar ta raabe daga can bakin qofar tana jiran shigowarsa. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍🏽 *~KUNDIN QADDARATA~*✍🏽 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) _bismilla hir rahmanir rahim_ *_qul ya ibadiyal lazina asrafu ala anfusihim la taqnad'u minr rahmatillah_* _____________________ 0⃣2⃣ Shi din ma a yau kallo daya yayi mata ya tabbar akwai abinda ya mata kutse cikin farinciki da walwalarta,sosai fuska da jikinta baki daya suka nuna gazawa da kasawarta,gabansa ya fadi saboda wani tunani da ya darsu cikin zuciyarsa,a hankali qirjinsa ya dinga bugawa. Yarinya ce amma a dabi'unta sam ba zaka kirata haka ba,tana da halin manya da dattako da sanin ya kamata,sai tayi qoqarin cilla duk wata damuwarta gefe guda ta garbeshi yadda suka saba,a yau din ya sake sosai har ma yana tsokanarta,amma ta nan fannin sai ta samu kanta da gaza amsa masa,duk da murmushin yaqen da take ta qoqarin binsa da shi,wani abu ne cunkushe a qirjinta. Tana ta kai kawon shirya masa abinci yana ta binta da kallo,babu shakka iya kula da miji ba wai mace mai karatun boko kawai ta iya ba,shi ya yadda da wannan,komai na sumayya a nutse yake,ba zaka taba tunanin bata taba shiga aji ba face ajinsa,shi ya koya mata yadda zata yi karatu da rubutu,rainonsa ce shi ya raini abarsa,ko motsi sumayya tayi yasan me yake nufi,hakan ya sanya a yanzu kallon da yake binta da shi karantarta yake,duk wani motsi nata na gaya masa akwai damuwa mai yawa cikin zuciyarta. Hannunsa ya sanya ya ruqota lokacin da take duqe tana shirin zuba mishi abinci,sai ta dago idonta take idanunsu suka gamu,ko baiyi magana ba tasan meke yawo cikin idanunsa,sai ta narke qwalla ta cika idanunta,janyota yayi ta fada jikinsa ya rungumeta da dukka hannayensa,kuka ne ya qwace mata ba tare data shiryawa hakan ba,baice mata komai ba har sai da tayi mai isarta,ya fuskanci zuciyarta ta soma sanyi sannan yace da ita cikin murya mai sanyi "Me ya faru my sumy,me ya sameki?" Cikin muryar kuka maganar na kakkatse mata saboda shishshiqar kukan dake kawo wa muryarta caffa "Yaa mukhtar,yanzu saboda zakayi aure kake boyemin?,me yasa baka gayan ba ya mukhtar saidai na tsincin zancan a waje?" Shiru yayi wuta ta dauke masa lokaci guda,zancan da yake ta faman boye mata kenan,shi kansa cikin awanni kadan maganar ta dagulamasa dukka wata nutsuwa tasa,ina ga sumayyar tasa,ajiyar zuciya ya saki sannan yace "Sumayya,bana son ki tada hankalinki kan wannan maganar,ni mukhtar a yanzu bana sha'awar qara wani aure,ke daya sumayya kin isheni,kuma babu wanda ya isa ya sani dole tunda ni zan zauna da ita". Da sauri ta daga kanta daga qirjinsa tana dubansa tana kada kanta. "Ko ba jima ko ba dade dole ya mukhtar sai ka qara aure,koda baka da muradi 'yan uwanka zasu tursasa ka,tunda na kasa samar musu da abinda suke da buqata,na kasa haihuwa....." Ta qarasa maganar kuka na sake qwace mata. Da sauri ya sanya hannunshi ya rufe bakinta. "Subhanallah,sumayya!,ina ilimin addininki ya tafi?,Allah kadai ke bada haihuwa kin sani na sani kowa ma ya sani saidai klwa ya take saninsa,to saboda haka babu wani sake auren da zanyi,mu barwa Allah lamuranshi har zuwa lokacin da yaga damar bamu". Ta lura da gaske mukhtar yake ba zaya karbi auren da aka bashi ba,wanda hakan dai dai yake ya debo baqin fenti ya yaba mata a idanun 'yan uwanshi,a yanzun ma tana rakawa ne kawai da yanayin dangantaka da alaqarsu,ba zata iya tuna yaushe rabon da ta ga wani da ya jibanceshi a gidansu da zummar ziyara ba,kawaici kara da yakanarta ne kawai yasa bata dauki lamarin a bakin komai ba,ta riga ta sani ta kuma yi imani da shi shine dukkan tsanani yana tare da sauqi. Ji take a jikinta wannan ce kadai dama ta qarshe a gareta da zata dawo da kyakkyawar alaqar da a da can baya take tsakaninsu " ya mukhtar"ta kira sunansa,bata tsumayi jin amsarsa ba ta dora "Don Allah da annabinsa kada ka yimin haka,kada kace ba zaka karbi auren nan ba" "Sumayya,bana so kuma bazan karba ba,bana da buqatar qarin aure a yanzu haka,domin babu abinda na nema na rasa ga mata ta" ya fadi yana dubanta kansa tsaye,rasa me zata ce masa tayi saboda yadda taga ya tunzura kamar ta sokeshi da allura. Qarar wayarsa ce ta sanyashi mai da idanunsa kan wayar,har ra qaraci ringing dinta ta katse bai daga ba,tana katsewa wani kiran ya sake shigowa,sai da ta kusa katsewa sannan ya daga "Hello" aka fada daga can bangaren,ko bata ga sunan mai kiran ba tasan yaya yahanasu ce,tana jiyo muryarta tar kasancewar tana jikinsa "Assalamu alaikum"mukhtar ya fada " sai yanzu kaga damar daga kiran nawa hamshaqi?"ta fada cikin fada "A'ah ba haka bane...." Ta katseshi da sauri ta hanyar fadin "Ba wannan nake so naji daga gareka,munyi maganar yarinyar nan fa'iza,naji shiru baka ce komai ba" ransa ya sake baci fiye da dazu,har yanayin fuskarsa ya sake munana fiye da dazun. "Yaaya,kiyi haquri,inaga gaskiya gwara kawai abar maganar nan,kada in zama silar bata zumuncinku ke da qawarki,domin a gaskiya bani da sha'awar qara aure a yanzu haka,mata ta babu abinda na nema daga gareta na rasa". " iyeeee,ni muntari kake gayawa haka,kai kuwa ka rasa komai daga matarka,shekararku nawa tare,ko dan yatsa ta taba haifa maka?,hala ma haka sumayyan tace ka fadamin kenan?". "Babu ruwanta yaya,hasalima bata san da zancan ba banda yanzu,nine kawai bani da ra'ayi". " muntari ka bini a hankali,idan nayi maka baki fa sai ya kamaka wallahi kai ka sani,aure kuma babu fashi wallahil azim,mu zuba ni da kai da ita kanta qaramar alhakin sumayyar muga wanda zai kai qasa,banza shashasha kawai solobiyo,yarinyar da a haihuwar tumaki ka haifeta zaka tsaya tana juyaka kana tsoronta"qit ta kashe wayar daga fadin hakan. Tuni sumayyan tayi nisa a duniyar kuka,so tayi ma ya saketa ta zauna qasa ko ta kwanta ko zata fi jin dadin yin kukanta son ranta amma yaqi sakin nata. Cikin jarumta ta hadiye kukan nata ta dubeshi "Ya mukhtar,wallahi kaji nima na rantse qarin aure gareka babu fashi matuqar kana qaunata da gaskiya kamar yadda ka fada,wannan kawai ya isheka ishara ka gane kashin kaji kake shirin sake yabamin bayan wanda na goga a baya,saboda haka ya zama dole ka yiwa yaayaa biyayya tunda mazaunin mahaifiya take a gareka" tana gama fadar haka ta miqe daga jikinsa ta shige dakin gadonta. Cikin kwanakin gaba daya ta daina yi da shi,ta tsame hannu daga sabgarsa ba wai don haka ta so ba,tayi amanna auren da zaiyi ne kadai zai sama mata salama cikin rayuwar aurenta,ta tabbata ba zasu barta ba ko ba dade ko ba jima tunda bata haihu ba. Kwanaki uku kenan zaman babu dadi,saidai ta tara yaranta suyita sabgarsu amma na ruwanta da shi. Ranar cikon ta hudun bayan ya dawo daga kasuwa,ya tadda kayan abincinsa ta jera kamar yadda ta saba,tayi shigewarta uwar dakanta babu ita ba alamarta,toilet ya shiga yayi wanka duka tana jinsa bata ko motsa ba balle ta fito,ya gama ya kintsa cikin jallabiya,bai ko kalli abincin ba ya shiga uwar dakan tata,nan ya cimmata saman gado zaune jingine da fuskar gadon,hannunta dauke da qaramin littafin alma'asuraat,ba taka haue bace 'yar gado ce,domin gidansu gidan malamai ne akwai ilimin addini tsantsa wanda hakan ya sanya yara matan gidan basa karatun boko sam sam. Bata dubeshi ba har ya hauro gadon ya sanya hannu ya karbe littafin ya ajjiye gefe guda,ganin tana shirin yi masa bore ya sanyashi saka qarfinsa ya riqeta gam,cikin salo ya soma rarrashinta da neman sulhu daga gareta,cike da tuburewa ta dubeshi "Karbar auren nan ne kadai zaya samo maka kaina yaa mukhatar,idan ba haka ba zaka iya tafiyarka muci gaba da zama a haka,ya fiye min akan danginka su dinga ganin na mallakeka,kullum ban da kwanciyar hankali ko nutsuwa a cikinsu" ta qarashe maganar zuciyarta na sake yin rauni,dama can a raunane take,dakiya da haquri yasa take iya sabgoginta kamar bata da damuwa,tun asali mutumce mai zurfin ciki,bugu da qaari zamanta da mukhtar babu wani abun tur da yake mata don haka bata iya fadar matsala ko kai qara ba. Ya kusan kwashe minti talatin cikin nazari da dogon tunani,har ta fara jan abun rufa zata yi kwanciyarta tana tsammanin yana kan batunsa,ya waiwaya cikin sanyin jiki ya dubeta "Sumayya,ina sonki kin riga da kin sani,babu kuma abinda na nema na rasa daga garekin,ban dauki rashin haibuwarki a wata matsala ba,saboda na riga da na sani cewa bawa bai isa ya tasara kansa *KUNDIN QADDARARSA* ba,tunda kina gani shine buqatarki kuma shine kwanciyar hakalinki na amince". Duk da hakan take buqata saboda tasan shine samun salamarta daga hannunsu yaa yahanasu amma sai da wata 'yar banzar faduwar gaba ta ziyarceta,ta hadiye wani abu sannan tace " shikenan,amma ya kamata gobe kafin ka dawo gida kaje ka sanar da yaayaa yahanasu amincewarka,so nake ta daina zargi ko jin haushina"kallonta ya waiwaya yayi,saboda a yadda tayi maganar shi zai nuna maka akwai ragiwar zallar quruciya a tattare da ita,bai son zuwan saboda haka ya kada kai yace "Bazan je ba saidai idan zaki shirya muje tare". Ido ta dan zaro don har ga Allah batasan ya hafuwarsu zata kasance da ita ba,amma sai dabara ta fado mata,kasancewar babu wani nisa sosai tsakanin gidansu da gidan yaya yahanasun bazai wuce naira talatin ba kudin mota " eh zani,amma saidai ka ajjiiyeni a gida,idan ka dawo kazo ka daukeni mu tafi"baice komai ba ya tire bargon ya shige ciki tare da janyota jikinsa,da sauri ta dubeshi "Abinci fa kaci ne?" Kai ya girgiza mata "Na qoshi" "Amma yaa mukhtar bai......." "Shshshshsh" yace da ita sai tayi shirun tare da komawa ta lafe ajikinsa,ta sani tunda yace bzaici din ba bazai ci ba,ita kuma bata saba musu da shi ba saboda girman da yake da shi a idanunta. Cikin dare ta kasa barci,itadai bata san kishi ba tunda bata taba soyayya ba saboda shekarunta sha biyu a sanda aka aurar da ita,tadai auri yaya mukhatar,kuma tanaji a zuciyarta tana sonsa bata so wani abu ya rabeshi,amma tana jin babu dadi duk sanda ta tuna zai kawo wata gidan ta zauna tare da su,ya dinga kulata kamar yadda yake kulata,da tunanin yaqi qare mata sai ta sauko daga saman gadon,ta sadada ta fita ta daura alwala ta kabbara sallah. Kusan wannan tarbiyyar gidansu ce tun kafin tayi aure,mamarsu tasha gaya musu duk sanda suka kasa barci da kwanciyar banza suyita zaman tunani gwara suyi salla,zasu samu lada kuma daga bisani baccin yazo,a lokacin dariya sumayya take qyalqyalewa da shi saboda tsantsar quruciya,takan ce "Nikuwa mama mai zai hanani bacci?,bacci fa dadi ne da shi wallahi mama,baki ga da qyar nake iya tashi nayi sallar asuba ba,wataran ma sai kin sanya tsumagiya kin dakeni?" Murmushi kawai uwar takeyi kana tace "Sumayya kenan quruciya mai dadi ko" sai ta sake yin dariya tace "Hmmm,mama kenan,nikam babu abinda zai hanani bacci na,ga katifata mai laushi,ga iskar fanka". Washegari tare suka tashi,shi ya dinga taimakata da ayyukan gidan kamar yadda suka saba yi wadansu lokuta,sunayi yana tsokanarta saboda ya fuskanci tamkar bata da walwala,hatta sallar jiya a idanunsa tayi kasancewar shima bai samu isasshen bacci ba,sai goma ya fita yana gaya mata ta shirya bayan sallar magariba idan ya dawo zasu fita. Qarfe shida ta kammala girkinta ta tsaftace gidan,ta hada kan yaranta ta zuba musu abinci cikin kwano daya,sannan ta kwashe na mai gidan ta kai falo ta jera sannan ta shiga wanka tana gaya musu saura ta jiyo su suna fada,duk wanda yayi fada ba ruwanta da shi. Tsaf ta shirya cikin wami swiss lace mai matsakaicin kudi cikin kayan sallarta yake,sanyawarta daya wannan ne na biyu,mukhtar akwai qoqari da zuciyar yiwa iyali,sosai yayi mata kyau,ya sake fidda zallar quruciyarta,tana cikin fesa turare ta jiyo yaran na yi masa sannu da zuwa,bai shigo yau da babur din nashi ba saboda zasu sake fita. Ta fito sanda yake raba musu alewa suna karba suna godiya kana suka yi mata sallama suka fice,haka ta koya musu,da ya dawo ko bata fada ba zasuyi mata sai gobe su tafi saidai idan ita ta tsaidasu,idanunsa a kanta ya bude mata hannayensa ta tako a hankali cikin kunya ta shige cike ya kulleta gam cikin qirjinsa yana fadin " kinyi kyau my sumy ta"siririyar dariya ta saki cike da jin dadin yadda yake yaba kwalliyarta. Wanka ya shiga yayi a gurguje saboda qaratowar lokacin sallah magariba,y hada da alwalarsa ya fice,bayan ya dawo ya shirya cikin shadda ruwan bula mai turuwa(dark blue)wanda yayi shige da lace din jikinta,dariya ta dinga ganin yadda yake waqar(munyi anko da anko)irin ta yara. Gidan yaya yahanasu taga sun nufa,bugawa qirjinta ya dinga yi,bata so ta masa magana yaga kamar tana qin 'yan uwansa,tunda duk tsiya naka naka ne,sai da ya faka babur dinsa qofar gidan sannan yace da ita "Idan mun gama da nan gidan mama zamuje ki gaidasu" hakan ne ya dan sake sa mata nutsuwa,"to"kawai tace da shi. Yana gaba tana biye da shi kamar wadda za'a kama,a tsakar gida suka ci karo da yaron yaya yahanasu wanda bazai wuce shekara goma sha uku ba,ya gaida mukhtar ya amsa yana ce masa "Jeka qofar gida ka kulamin da machine dina kafin na fito" "To kawu" ya fada yana ajjiye modar hannunsa saman randa ya fice. Suna shirin shiga rumfarta tana daga labulen dakin "Au sai yau kaga damar zuwa kenan......shashan yaro ana maka gata kana noqewa" ta fada tana sakin labulen ta juya zuwa ciki. Bata lura tare suke ba sai da suka shiga ciki suka zauna,sumayya ta gaisheta ta amsa sama sama,ganin idonta sam bai hana yaya yahanasu yin duk maganganunta ba,ita dai kam kanta ta sunkuyar,daga bisani ta miqe ta basu guri jin musu nason barkewa tsakanin mukhtar da yaya yahanasu kan lissafin abinda suke da buqatar ya bada,kama daga kudin aure kudin zance lefe har zuwa sadaki,yace zaya bada kudin aure da na sadaki amma shikam bazaya iya yin wani lefe ba,kasuwa babu ciniki,nan ta barsu batasan yanda suka kaya ba yadai fito yace ta tashi su tafi. Ko sallamar da take wa yaya yahanasun bata tanka mata ba har suke wuce,suna kan hanya babu wanda yace da dan uwansa komai har suka qarasa gidansu. Ciki ya shiga suka gaisa da maman nata kasancewar abba malam mahaifinsu kamar yadda suke ce masa baya nan,'yan qannanta duk suna tsakar gida mukhtar ya raba misu biscuite kamar yadda ya saba,ya miqe zai fice yana cewa zai zaga bayansu gun wani abokinsa idan ya dawo zai kirata su wuce tace tom. Gaisawa sosai sukayi da mamanta ta tambayi lafiyarta da ta gidanta ta amsa mata da komai lafiya. Shiru ne ya biyo baya,tunanin abinda ya faru dazun gidan yaya yahanasu yayi nasarar wafce tunaninta ba tare da ta shirya ba,haka maman ta tadda ta,ta ajjiye kwanon dambun data je debo mata "Lafiya dai ko sumayya" murmushin yaqe tayi ta janyo kwanon dambun tana budewa sannan tace "Mama aure yaya mukhtar zai qara" maganar ta dan taba maman,tsakanin da d'a da mahaifi,tausayinta ta dinga ji yana ratsata,babu shakka abu ne mai wuya zama da kishiya a wannan zamanin,abu ne da har yau yaqi dadi a cikin gidajen aurenmu,ga yarinyar tata gwanar haquri da shegen zurfin ciki ce,amma duk da haka ta sani ba duka aka taru aka zama daya ba,duk abinda zata gaya mata a yanzu shi zai zame mata madubin dubawarta. Murmushi maman tayi sannan tace "Babu komai,ai namiji mijin mace hudu ne,Allah ne ya halasta masa,abinda nake son gaya miki kawai shine kada ki soma cewa zaki tada hankalinki ko ki daga hankalin mijinki,ki zauna da ita tsakani da Allah,ki sauke duk wani haqqi nata dake wuyanki,sumayya kada ki sake kice zaki cuceta,idan kika cuceta sumayya ni mahaifiyarki ban yafe miki ba". Kai ta gyada" in sha Allahu mama zanyi duk abinda kika ce,da ikon Allah bazan zama mai sabawa maganarki ba"a hankali maman ta dinga hilatarta tana kwantar mata da hankali har ta kusa cinye dambun baki daya. *mrs muhammad ce* 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍🏽 *~KUNDIN QADDARATA~*✍🏽 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) _bismilla hir rahmanir rahim_ *inna ma'al usri yusrah,fa inna ma'al usri yusrah* ______________________ 0⃣3⃣     Suna cikin hirar mukhatr ya turo qaninta mubarak yayi kiranta ta fito zasu tafi,nan mama ta hada mata su kuka kubaiwa daddawa barkono har da tsakin masara saboda dambu ko dan malele,tana hada mata kayan tana dada kwantar mata da hankali tare da jaddada mata kada ta sake ta tashi hankalin mijinta ko ita kanta,ko tace zata yi wani rashin kyautawa ga daya daga cikin 'yan uwan mukhtar,haihuwa kuwa lokaci ne,idan Allah yaso ma sai taga sanadiyyar shigowar wata ita ma ta samu nata rabon,ta dora da cewa "Bare ma duka duka nawa kike sumayya,mu a da can Allah na tuba ba sai kiyi shekara goma da aure baki haihu ba babu wanda ya damu da ke,haka kema baki damu kanki ba,ci da zuci ne kawai yanzu irin na yaran zamani" maganar sai ta bama sumayya dariya da kunya,har ta sanya tafin hannunta ta rufe fuskarta.        Suna shirin kwanciya bacci lokacin yana zaune gefan gadonsu yana shan ruwan baqin shayi,ita kuma tana taje kanta,ta cikin madubin yake qare mata kallo yadda kullum take sake zama cikakkiyar mace,tamkar ba zata masa magana ba amma abun nata cinta a zuciya,saboda daga shigowarsu gida zuwa shirin kwanciya da sukeyi yanzu yaya yahanasu ta kira shi ya kusa sau biyar,duk da bata kusa amma ta fahimci taqaddamar me suke,maganar lefe ne da yace ba zaya yi ba,ta dan cije lebanta sannan tace "Ya mukhtar" "Ya akayi sumy?" Ya fadi yana saurarenta.     Sai data jawo dressing chair gabansa ta zauna sannan ya dubeshi,cikin nutsuwar nan tata hadi da kaifin hankali da zurfin tunani "Ya mukhtar kayi haquri idan na maka shishshigi,sai nake ganin baka kyauta ba",cikin rashin fahimta ya tambayeta " da akayi me fa?"ta danyi jim kamar ba zata yi magana ba sannan tace "A ganina bai kamata ka dinga sa'insa da yaya yahanasu ba,ko banza ta girmeka,bugu da qari ita ta zame maka tamkar mahaifiyarka ka manta?,ita ta raineka har ka kawo girmanka,ka san cewa dai ba zata taba yin abinda zai cutar da kai ba,a ganina auren nan saboda qaruwarka ne take buqatar kayi,ko babu komai idan fa'iza ta haihu sai an fara cewa danka kafin a ce dan yaya yahanasu ko?" Ta dan sarara da maganar tana hadiye wani abu mai daci wanda bata san meue sanadiyyar tasowarsa ba daga qirjinta.      Ko bata qarasa ba ya fahimci kan me take magana,saboda haka ya bata fuska "Kinga sumayya,babu ruwanki da wannan maganar ki fita a cikinta,lefe ne nace bazanyi ba suyi mata,ai bani nace ina son auren ba ko?,ina zaman zamana haka kawai ina lallaba rayuwata sai su baro min aikin da bani na saka su ba?".        Kai take gyadawa idonta cikin nasa wanda tuni ya tara qwalla shirin zubowa kawai take " na gode ya mukhatar,ina ka taba gani an auri budurwa ba'a yi mata lefe ba?bayan haka kuma ka riga da ka san cewa matuqar bakayi lefe ba to sumayya ce ta hanaka,duk wanda yaga laifina ko ya zageni ya mukhtar kai ka jawomin"sai ta tashi daga saman kujerar ta haye gado ta lulluba har saman kanta kaana ta fashe da kuka.      Har cikin ransa ya dinga jin shigar kukan nata,ya runtse ido yana jin bata can can ci haka ba,da me zata ji cikin abu ukun,sai ya sanya hannayeshi ya dagota baki daya zuwa jikinsa yana goge mata hawayen tare da fadin "Ya isa sumayya,ya isa,me kike so ayi?,gaya min" sai da taja hanci kadan sannan tace "Kayi lefe kamar yadda yaya yahanasu ta buqata" "Shikenan an gama,sunci darajarki" sai ta saki dan qaramin murmushi sannan tace "Na gode".        Washegari yana cikin karyawa kafin ya fita wayarsa ta soma ringing,sumayya ta dauko ta miqa masa da yake tana kan t.v stand tana chargy,daga yanayin maganarsa kawai ya tabbatar mata yaya yahanasu ce,kuma zancan jiya ne bai wuce ba,a gimtse ya amsa cewa zaiyi laifen,amma fa sam shi ba kudi zai bada ba,zaiyi iyakacin abinda zai iya ya kawo musu,daga haka ya kashe wayan ma baki daya,tana gefe tana saurarensu kanta sunkuye tana wasa da yatsun hannunta,ya kammala ta masa rakiya kamar yadda ta saba,dawowa yayi da baya ya rungumeta sannan ya sumbaci goshinta " Allah yayi miki albarka"ya fada yana sakinta "Amin ya mukhtar" ta fada cikin farinciki,saboda tuni maman ta ta gaya mata albarkar miji na bin mace,hakanan fushinsa ko  yardarsa na tare da ta ubangiji.      Cike da farinciki ta koma cikin gidan saboda albarkar da ya sa mata ta faranta mata,taci gaba da kintsa ragowar ayyukan da suka rage mata,bata jima da kammalawa ba ta zauna tana hutawa wayarta ta dauki qara,da sauri ta daga ganin sunan abbanta na yawo bisa screen din wayar.      Cikin girmamawa ta gaidashi ya amsa mata yana tambayarta gida da kuma mukhtar tace ai yama fita. "Mamanki ta gaya min mukhtar zai qara aure" "Eh abba malam" "To ina fata ba zaki watsa mana qasa a ido ba,ba za kiyi watsi da tarbiyyar da muka baki ba" "In sha Allahu malam" "To Allah ubangiji ya albarkaceki ya albarkaci aurenki" daga haka ya dora mata da nasiha cikin hikima da ilimi,cike da fadar Allah da ma'aikinsa,hakan ba qaramin sake kwantar mata da hankali yayi ba,ya qare nasihar tasa da fadin "Babu wani abu da kike buqata?" "Eh babu malam" ta fadi hakan saboda babu abinda mukhtar ya gaza da shi,don hatta kudin kashewa yakan qimanta ya bata,ya danganta da yanayin samun da yayi a kasuwa. "To shikenan,haka ake so,inaga zan duba wajen sati na gaba ko wajejen satin sama,zan aiko abubakar(yayanta ne shine na fari a gidansu,amma baiyi aure ba karatu yake)zaizo. A fidda kayan gadonki da kujerunki a sauya miki wasu" farinciki ya cikata,duk da cewa wadan nan natan ma babu abinda sukayi,don sanda sukayi shekara hudu da aure mukhtar ya fitar da na aurenta na ainihi ya sauya mata su. "Na gode,na gode qwarai malam Allah ya saka da alkhairi,ya qara lafiya da nisan kwana mai amfani,Allah ya qara budi da rufin asiri" "Amin ya Allah,amma abinda zaki biyani da shi kawai kici gaba da zaman aure cikin gidanki" "Da yardar Allah malam" ta amsa masa daga haka sukayi sallama.      Sosai malam yake aon sumayya,don tun tana mitsitsiyarta halayyarta daban take,tana da tarin haquri kawaici da zurfin ciki,shi yasa duk cikin yaransa yafi sonta,duk da cewar dukan yaran nasa maman sumayyan ce ta haifesu,ko a lokacin da suka aura mata mukhtar ma ce mata kawai yayi ga miji yayi mata kuma aure zaiyi mata,bata ce komai ba don ba wayo gareta ba,duk da haka dama kunya gareta,gudu tayi ma ta bar gurin sanda malam din ke gaya mata,ita ce yarinya mace ta farko a gurinsa sai qannenta su hudu.     Mukhtar zamu iya cewa rako wani abokinsa yayi gurin malam din kasancewar malam din yana bada karatu tsakanin sallar magariba da isha'i wa matasa da dattijan unguwa,gani daya ya yiwa sumayya yaji tayi masa kasancewarsa mutum wanda sam baya da sha'awar auren macen da tayi zurfi a karatu,tunda yayi universty shima yaga irin qazamar rayuwar da mafi yawancin 'yammatan keyi duk da ba duka aka taru aka zama daya ba.      To sara ne yazo kan gaba shima malam ba mai son yaransa suyi bokon bane,saboda haka yana bincike kan mukhtar ya tabbatar da nagartar halayyarsa ya basu auren sumayyan.      Da fari 'yan uwansa sun so su turje kan mai zai sa ya auri yarinyar da rainonta kawai zaiyi,musamman yaya yahanasu wadda ita ta riqe mukhtar din,saboda bai wuce shekara biyar a duniya ba Allah ya yiwa mahaifiyarsu rasuwa wanda dama tun mukhtar na da watanni a duniya mahaifinsu ya rasu,to amma daga bisani suka haqura kasancewar sun lura mukhtar din bashi da niyyar fasa aurensa.      Da fari sun karbi sumayyan a matsayin 'ya kuma qanwa,amma daga lokacin da suka lura da gatan da mukhtar ke mata hassada ta soma aiki,duk da ba zaka kirashi mai kudi ba amma mai arziqi ne,iyalansa sunfi qarfin yin kukan rashin wani abu cikin gidansa,shekara uku tayi ta cika shekara sha shida,a lokacin ta zama mace saboda Allah ya mata halitta da jiki mai kyau,sai suka juya akalar hassadarsu kuma zuwa sa mata idon yaushe zata samu ciki?,yaushe zata haihu?,wanda har yau suna bisa wannan bigire basu sauka daga kai ba Wannan kenan.....       Sati hudu suka sanya lokacin aurensu,sunata budirinsu suna shirye shiryensu ango ko oho,kayan lefe ne yace zaiyi kuma bai fasa yi din ba.      A falonta ta tadda shi yana amsa waya bayan ta gama soya masa wainar fulawa da yace yana sha'awa har tana ta masa dariya qai qwalama ce kawai ta dameshi,mai ya hadashi da abincin mata,ya sauke wayar daga kunnensa yana janyo plate din tare da budewa yana fadin "Yauwa amaryata kuma uwargida na" qeya ta juya masa tana turo baki "Um_um,barni a uwar gidan dai,amaren na nan tafe" cikin sigar tsokana ya dan talle mata qeyar data turo masa "Ka jini da yarinyar nan wai itama ta iya kishi?" Duk da tasan wasa yake sai ta juyo tana dubansa zuciyarta na raunana amma ta dake "Don me bazanyi kishinka ba ya mukhtar?" Bai so maganar tayi tsayi don bata masa rai maganar take balle ita saboda haka yace "Haka ne" a taqaice sannan ya hau qirqiro santin waina duk da cewa a zahiri tayi dadin,biye masa tayi tana masa dariya tare da kara masa filo a bayansa.     Sai da yaci kusan rabi sannan tace da shi "Nikam yaya mukhtar banga kana shiri ba" cikin son samun qarin bayani yace "Wanne irin shiri?,name?" "Banga wani sauyi ba agidan nan?" "Kamar wanne iri fa" ya sake tambayarta "Gani nayi kace na kwashe shirgin dake cikin dakin shirgin can nan amarya zata zauna,nace maka ka hada mata da naka dakin itama ta samu falle biyu ka qiya,to a barshi a hakan,amma ya kamata ace daga dakin nata zuwa tsakar gida ko shafen farar qasa ka yi masa don ya haska ko,tunda nawa dakin ba'a jima da yi masa fenti mai tsada ba fes yake kamar yau akayi".     Banza yayi da ita kamar bai ji ba har sai da ta qosa tace masa " kana jina kuwa ya mukhtar?" "Ina jinki kuma bazan yi ba,ke wallahil azim kika sake yimin magana makamanciyar haka sai ranki ya baci,idan zata zo ta zauna haka ta zauna,idan ba zata zauna ba ta qara gaba dama ba ni na gayyatota ba,haba,dame kike so naji?".sai ya miqe a fusace ya fice zuwa dakinsa ya barta da sauran wainarta.      Jikinta ne yayi sanyi,tayi da na sanin yi masa maganar,sai data bashi kusan awa guda sannan ta gyara gurin ta shirya zuwa shigar barci tabi bayansa don ta lallashe shi.      Bata sake masa maganar ba kuwa,sai ranar asabar ranar 'yan yaranta duka suna gida saboda ba ranar karatu bace,ta aika nana tayi mata kiran wani dan saurayi dake maqotansu,tace ya duba mata don Allah farar qasa kwano nawa zai isa dakin zuwa tsakar gidansu ya gaya mata yadda yake zaton zata isa,cikin kudin da take adanawa ta qirgo ta bashi har da kudin mota,cikin minti talatin ya dawo,tasa ya jiqa mata sannan ya tafi ta masa godiya ta bashi dari tace yasha ruwa.       Yaranta ta kalla wadanda sun kai su takwas,akwai bilkisu,fatima,hauwa'u,khadija,aisha,ummi,asma'u sai nana ta gurinta " maza kowa yaje gida ya cire kayan jikinsa ya saka marasa kyau zamuyi fenti"cikin zumudi kuwa har suna rige rige suka fice suna murna.      Kafin su dawo itama har ta sauya nata kayan,saiga yaran kuwa,nan suka zage suka dinga shafen farar qasar,abinka da ba aikinsu bane tun safe har bayan la'asar,nan ta musu girki suka ci,idan sun huta su dora.     Cikin haka sai ga maman nana ta shigo,salati ta saka tare da kama habarta ganin sumayya saman tsani,duk sunyi face face da farar qasa "Ni salma,ai nayi zaton qarya nana take da tace fenti zakuyi ashe da gaske take",dariya ta qyalqyale da ita tana saukowa daga kan tsanin " to ya zanyi maman naana,ya mukhtar yaqi yarda yayi fenti,shi yasa na siyo da kaina mukeyi ni da 'ya'ya na"(da yake ita kadai ta gayawa zancan,saboda yadda take mata tamkar mamanta,tafi shaquwa da ita fiye da sauran iyayen yaran.     kai maman naana ta dafe tana cewa "Lallai sumayya quruciya na damunki,yanzu kishiya kike yiwa fenti da kudinki da jikinki,Allah ya shiryeku" ta fada tana dariya "To sauko hakanan na kira muku jamilu(babban danta) ya qarasa muku,tunda kun rantse sai kunyi" murmushi tayi tana kakkabe jikinta tare da fadin "Ai kuwa mun gode" da kanta maman naanan ta leqa ga nemo jamilun,cikin 'yan qananun mintina ya qarasa musu inda basu qarasa din ba. "Magana ba zata yiwu yau ba sumayya na dawo gobe,tunda yau kun zama 'yan qwadago yinin fenti kukayi" ta fada tana miqa mata ledar data shigo da ita,tana dariya ta amsa tana dubawa,ko bata ce mata komai ba ta fahimci meta kawo mata,magunguna ne masu kyau ingantattu na 'ya'yan itatuwa data saba bata.      Sanda mukhtar ya dawo yaga aikin da sukayi cak ya tsaya,sai kuma yayi gaba ba tare da yace komai ba,qaunarta ke saka ratshi,uwa uba kuma tausayi don yasan har yau da zallar quruciya tattare da ita,inda yasan zata yi da tun sanda yace ba zaiyi ba da tuni ya hada da yimata hannunka mai sanda don kada ma tace zata yi din.     Kamar yadda abba malam ya alqawarta mata,sati biyu da yin maganarsu kuwa saiga motar kaya,irin kayan da sam sumayya bata zata ba,kaya ne 'yan italy masu kyau da tsada har kujerun wanda ko a aurenta ba'a yi mata irinsu ba,har da qarin labulaye masu kyau da door mat,mamam naana da maman ummi ne tare da uaran gidanta suka tayata jerawa,saiga dakinta ya fito fes tamkar ma ita ce amaryar,mukhtar baiyi qasa a gwiwa ba yace har gida yiwa abba godiya,hakanan shima ba'a barshi a baya ba,kayan kitchen baki daya ya sauya mata,kasancewar yanzun an maida kitchen din bangare biyu,hannun hagu da hannun dama,kowacce anyi mata kantarta da drowers dinta,hakanan ya sauya maya plasma wadda tafi waccar girma harda qarin home thierther,sai ta dinga mamaki da yace bashi da kudi da bazaiyi lefe da fenti ba,bata ce masa komai ba tunda ta fuskanci dama ce bai gani ba,godiya ta dinga zuba masa sosai kamar yadda yake al'adarta.      Mamanta ita ta sauya mata showglass da kayan cikinta baki daya,farinciki duk ya cika sumayyan,ta fuskanci ita 'yar gata ce sosai,batasan duk sunyi haka bane don kwantar mata da hankali da sake sa mata nutsuwa,ba qaramin kyau dakinta ya sake yi ba sai ka rantse amarya ce. *mrs muhammad ce* 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍🏽 *~KUNDIN QADDARATA~*✍🏽 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) __________________________ _bismilla hir rahmanir rahim_ _iza qada amran fa innama yaqulu lahu kun fa yakun_ ________________________ 0⃣4⃣       Sati guda da kammala gyara gidan ranar wata litinin mukhtar ke gaya mata ran laraba masu kafin amarya zasu zo,sai da taji wata faduwar gaba da bata san ta mece ba "Allah ya kawo su" ta fada kawai kana tayi shiru tana dubansa yana rubuta lissafin kasuwa cikin wani qaramin excercise book.        Jin shirun yayi yawa ya sanyashi dago kansa ya dubeta,sai yaga littafin take kallo,ya sanya tsinin biron ya dan mintsini cinyarta,sai ga dago tana dubansa fuskarta dauke da murmushi tana sosa gurin "Yadai 'yammata?" Kai ta girgiza tana murmushi "Babu komai.....cewa nayi ai za'a yi musu girki ko,tunda naga ana yi",rai ya bata,don yasan yanzu zata fara soko masa zantukan da baiso,ya tabbatar sumayya danya ce shakaf,domin da wata macen ce aka yi mata zancan kishiya da tuni yanzu gidan ya dade da zama dan qaramin sansanin yaqi,ya tabbatar ba qaramin dauki ba dadi za'a yi ba,duk da quruciyarta ma ya tabbatar da gudun mawar qarin tarbiyya da ta samo daga gida,tunda ko a gidansu bata taso taga mamanta da kishiya ba,da wata ce wannan kadai ya isheta mafaka. " ba da kayan abinci na ba,kuma kema ban lamunce kiyi ba,idan kunne yaji....."sai ta ja bakinta ta tsuke,don bata son yayi fushi da ita irin na baya kan zancan fenti da lefe.      Washe gari ranar talata gefin magariba lokacin dawowarsa,ta gama komai kamar yadda yake al'adarta,gidan nata qamshin turaren tsinke,tana tsakiyar yaranta ta siyo madarar ruwa ta musu iloka ta rarraba musu suna sha,wani yaro dake bayan gidansu yayi sallama dauke da akwati wasu yaran na bayansa. "Wai gashi inji yaya mukhtar" ya fada kamar yadda yaji matar gidan na gaya masa,sai mamaki ya kamata don bata ji alamar  shigowarsa ko qarar babur dinsa ba,tashi tayi ta bude masa labulen falonta suka shiga da su,akwatunane guda shida masu kyau duka iri daya uku set daya uku set daya.     Suna fita ya shigo yana dauke da baqar leda,duka yaran suka masa sannu da zuwa suna qoqarin tafiya gida,ya bibbisu da alawa kamar yadda al'adaraa take sannan suka bi sumayya da "Anty sai da safe.....anty sai gobe" "To Allah ya bamu alheri" ta amsa musu suka fice ta rufe gidan sannan tabi bayan mukhtar da tuni ya shige falon.     Murmushi ta sakar masa kamar yadda ya sakar mata "Kinyi kyau sumayya ta" kanta ta sunkuyar cikin kunya tana murmushi "Na gode yaya na,sannu da zuwa" ta fada tana cire masa hular kansa da bai samu cirewa ba "Ya kasuwar" ta sake fadi tana qoqarin ajjiye masa ruwa mai sanyi "Kasuwa alhamdulillah......kinga ai my sumy abinci zaki kawomin don yunwa nake ji",ta dan zaro ido tana dubansa " da wuri haka yau?,na zaci sai ka dawo daga sallar magariba",shafa cikinsa yayi yana murmushi "Salla bazata yiwu cikin nutsuwa ba ina fama da yunwa,taimakeni ki bani sumayya magaribar da sauran lokaci,idan na kammala ko masallacin sun idar mayi jam'in da ke" "To" ta fada tana miqewa zuwa kitchen.      Bayan ta gabatar masa da komai tuwon semo ne miyar kuka sai qamshin daddawa take duk da babu nama amma tayi dadi qwarai,taasa bismillah sannan ta koma gefansa ta zauna.      Sai da ya kai loma biyu sannan yace "Ga kayanku nan ki duba kiga" ya fada yana mata nuni da akwatunan dake jere gefe,da to ta amsa masa sannan sannan ta sauka qasa ta janyo akwatunan ta soma dubawa.     Tana dubawa yana zuba mata santin tuwo,yayin da itama ke santin kayan,komai yayi kyau,sai data kammala tas,lokacin har ya gama cin twon ya jngina da kujera yana kallonta tana ta daga kayan tana yabawa,ta rurrufesu yadda ta gansu sannan ta dubeshi. "Nayi zaton ma har an kai kayan ne naga lokaci ya qurato" "Um um" ya fada a taqaice "Sunyi kyau sosai ya mukhtar,Allah ya qara budi,saidai komai naga bibbiyu ka saka kala daya,nufina kayan dake cikin akwatin kayan sawa sune a daya akwatin,under wears da mayafai ma" "Eh,akwatin uku naki ne uku nata", idanu ta zaro a firgice tana dubansa " aini yaya ka manta ka yimin lefe na tun sanda zaka aure ni?" "Na fiki sani,kayan fadar kishiya na miki".     Tsoro ne sosai ya kamata,tsoron su yaya yahanasu,ina zata sa kanta idan suka ga wadan nan kayan,komai iri daya ita da amaryarsu,hatta da man lebe iri daya ne?,tabdi lallai ya mukhtar so yake ya janyo mata bayan lallabawa takeyi. " gaskiya ya mukhtar ba'a haka,itafa amarya ce ya zaka hadamu kayi mana abu iri daya?bayan kayan kitchen da kayimin,ka sauya min kayan kallo,kasan su yaya yahanasu sai sunce wani abu idan ma basu ga laifina ba lo sun zargeni ba" "Eh,saboda kin fiye min ita,ke din zabi na ce,kuma raino na ce,tun kan kisan ciwon kanki kike zaune da ni,tun ana ciyar da mu bana daukar nauyinki,ita din ban santa ba,bansan halinta ba bansan ko zata iya irin zaman da kika yi da ni ba,sannan idan su yaya yaha da kike zance ai basu suka yimin ba,da kudina nayi balle a ce don me?,kufi na ne kuma iyali na ne,saboda haka bana buqatar ki sake cewa komai".     Tun asali ita ba mai musu bace da ya mukhtar din ba,girmansa take gani,kallon yaya take masa saboda haka cikin sanyin jiki tsoro da sanyin murya tace " hidimar ce naga kamar taso tayi yawa,na gode Allah ya saka da alheri,Allah ya jiqan magabata ya basu aljanna madawwamiya"cike da jin dadin yadda ta yiwa mahaifansa addu'a yace "Amin,Allah yayi miki albarka" "Amin ya mukhtar na gode sosai".      Tun qarfe takwas washegari ta kammala komai saboda da wuri mukhtar yace zai fita saboda masu jere,qarfe tara ta sallameshi,har ya fita ya dawo ya dubeta " idan kinga babu dadi zaman gidan,na baki izini kina iya tafiya duk inda kike so,idan yaso idan sai kimin waya ki gayan inda kike,idan na taso daga kasuwa sai na biyo na daukeki"murmushin yaqe kawai tayi,don hakanan tunda ta tashi yau take jin fargaba da bacin rai "Babu komai ya mukhtar zan iya zaman ma,me zai hana" "Kada dai ki takura kanki idan ba hali kiyi ficewarki" "To,a dawo lafiya",ya amsa mata da " Allah yasa"ya saka kai ya fice.       Tayi wanka ta shirya tsaf cikin atamfarta da abbanta ya dinka mata ita kwanaki,dark brown ce da adon mint green ajiki,sosai ta mata kyau dinkin ya zauna mata das a jikinta,falo ta koma ta zauna,jikinta a sanyaye bata san dalili ba,gidan ya mata shiru kasancewar 'yan hirar tata duka ana makarantar boko sai sha biyu da rabi suke tashi.      Ganin akwai wuta ya sanyata jona kayan kallo,tashar arewa 24 ta kama,cikin sa'a suna maimaicin shirin agent ragab,tana son film din sosai,kusan shi ya dauke mata hankali har sha daya da rabi.     Gamawarsu yayi dai dai da bugun qofa da ta soma ji,ta miqe ta fito tana tambayar waye tare da nufat soron,tun kafin ta kai ga budewa taji cikin kakkausar murya "Malama ki bude bana son salo kin wani kama qofar gida kin rufe,bayan kinsan akwai wadanda zasu zo,dadin abun saura 'yan kwanaki naga ta iyayi" da sauri ta qarasa bude qofar domin tuni ta dauki muryar wace,yaya bara'atu ce sai fadima tsaye a bayanta,dai sauran da bata san su waye ba,tasan dai ba zasu wuce dangin amaryar ba tunda ita daga amaryar har 'yan uwanta babu wanda ta sani,iyaka dai tasan cewa amaryar 'yar aminiyar yaya yahanasun ce.       Saura kadan yaya bara'atun tayi gaba da ita badan tayi gaggawar matsawa gefe ba ta wuceta saura suka biyo bayanta suka bar mazan da zasu shigo da kayan katakon da kujerun.      Bata qosa ba tabi bayansu zuwa dakin da aka bawa fa'izan wanda tuni yasha fentin farar qasar data siya tayi da kudinta,babu komai a dakin a share yake fes kasancewarta gwanar tsafta ce,tun kafin tace wani abun yaya bara'atun ta galla mata harara yayin da sauran suka mata caa da ido "Uban me kuma kika biyo mu ki mana?" Ta tambayeta tana huci,qasa tayi da kanta saboda yaya bara'atun ta girme mata nesa ba kusa ba cikin ladabi tace "Zuwa nayi mu gaisa ne" "Riqe gaisuwarki bama so" "Uhmm,wallahi kuwa" fatima tayi caraf ta karbi zancan "Allah ya baku haquri" ta fada sannan ta juya ta fice kai tsaye falonta ta shige taci gaba da kallonta.        Miqewa tayi zata dauko wayarta dake uwar daki tana ringing ta hangosu suna kici kicin budw kwadon dake rufe da dakin ya mukhtar wanda da kansa yasa ya rufe ya tafi da abinsa,da taga a kulle yake sai ta saka tana fadin "Lallai,kaddai yaya mukhtar daki daya ya bayar,tabdi lallai,yana nufin ita a falle daya zata zauna waccar tana da ciki da falo....haka ne....mu shirya mata kayan idan muka koma ma sanar da yaya yahan",bata ce uffan ba don ba mas'alarta bace,ko tata din ce ma basu sako da ita ba.       Ya mukhtar ne ya kira yana tambayarta komai lafiya ko tace eh sannan sukayi sallama ya kashe wayar.       Kafin wani lokaci gidan nasu ya cika da 'yan jeren,ko ina sai shewa ke tashi da qananun magan ganu,take tsoro ya cika sumayya,ta dinga kiran lambar maman naana kan ta shigo ta tayata zama amma wayar a kashe take,ta dinga leqe ta window dinta taga ko akwai hanyar da zata ratsasu ta fice.       Bata samu sararin gurin ba sai da suka fara daura alwalar sallar azuhur,tayi hanzarin shiga uwar dakanta ta dauko hijabinta tare da padlock  ta sanyawa qofar dakin nata ta fice.      A qofar gida ta tarad da su naana suna tsaye,suna ganinta suka nufota da sauri,ta dubesu tana cewa " me kuma yau kuke tsaye a qofar gida?"bilkisu ce tace "Hanamu shiga anty akayi?" "Waye ya hana ku shiga?" "Masu jeran amarya"inji nana,take taji ranta ya baci,sam bata son abinda zai taba mata yaran,ba zata juri haka ba sam,bata ce misi komai ba sai " kuzo muje,qila fitina zaku shiga kuyi musu shi yasa suka hanaku shiga don kada ku bata masu kaya" "Wallahi anty a'ah" inji aysha "Shshshshah" sumayya tace da su,sun san me take nufi ko batayi magana ba,bata da son su kawo mata hirar wani dama.       Gidan mamam naana ta shiga,ta taras da ita tana kwashe abinci cikin kula "Ina zaku haka ke da gayyar yaran naki,ina kika baro baqin naki,ai yanzu nake shirin shiga kinga girki ya tsayar da ni ina so na kammala na turasu islamiya sannan na shigo" murmushin yaqe tayi ta ja kujera 'yar tsuguno ta zauna daga bakin qofar falon maman nanan,yaran nata suka zazzauna kusa da ita "Eh wlh,na gaji da zama ni daya nace bari na leqo" "Banda abinki sumayya aiko baki aiko na shigo miki ba kyayi waya a turo miki halima da zainab ko su tayaki zama" "Wallahi maman naana bansan haka akeyi ba ai" murmushi tayi tana tausayawa sumayya da quruciyarta "Ai shikenan,Allah ya bada zaman lafiya,ya kade fitina tsakaninku" "Amin" sumayyan ta fada cikin faduwar gaba.      Duka yaran ta zubawa abinci suka ci sannan ta tura kowa ya gida saboda ganin lokacin tafiya islamiya yayi,ta shirya su naana ma suka tafi sannan suka daura alwala sukayi sallar azahar ita da sumayyan.      Shinkafa da miya har da salad da kifi abinda ta dafa ta zubo musi cikin plate "Sauko sumayya maza muci" kai ta girgiza don a cunkushe take jin cikinta babu space din abinci "Na qoshi maman nana" tausayinta ya kamata amma ta dake tayi murmushi "Sauko muci akwai abinda nakeson gaya miki" bata da jan doguwar magana saboda haka ta sauko ta sanya hannu suka soma ci.       Cikin hikima maman nanan ke kwatantawa sumayya dabarun zama da kishiya,qissa dabara da wayo kala kala,ta dora da yi mata nuni da haquri,kau da kai kara da alkunya,gaskiya da amana,zama na tsakani da Allah,sai gashi sun tashi da abincin tas,har sai da hannayensu ya fara bushewa da miya saboda sun kasa tashi a gun darussan maman naana sunqi su qare,saiga sumayya na kwasar dariya saboda wani abun idan maman nanan na gaya mata kunya ce ke kamata ko mamaki.      Hararta maman nana tayi dariya itama nason qwace mata itama amma ta dake saboda yadda taga sumayya na dariya wani abu da ta gaya mata "Au dariya ma nake baki ko?,zaki ci gidanku wallahi idan baki dauke duk abinda nake gaya miki ba" cikin dariyar ta dafe baki "Yi haquri maman nana,abunne wallahi" ta kuna saka dariya,kada kai maman nana tayi itama dariyar ta qwace mata,ba shakka sumayya danyace har yau,ta miqe ta dauke plate din da suka gama cin abincin ta fice da shi.      Basu ankara ba sukaji ana qwala kiran sallar la'asar,nan suka tashi sukayi,maman nana ta dubeta tace "Ba zaki koma gida kiyi girki wa mukhtar bane" "Ina som in koma maman nana amma ina zaton har yau basu tafi ba,bari na kira ya mukhtar din naji mai zai ce".      Koda ta kirashi cewa yayi tayi zamanta kawai idan ya dawo din ya kirata ta dawo,a nan tayi zamanta suka ci gaba da hirarsu har su nana suka dawo daga islamiya,sai qarfe shida kiran mukhtar ya shigo wayarta,ta yiwa maman nana sallama ta wuce gida.       Kaca-kaca ta tarad da gidan tun daga qofar gidan tamkar bata taba shara ba,kwalaye da ledojin abubuwan da suka jera duja ko ina a gidan,ga kwanukan abinci nan nata har da sabbi da bata taba amfani da su ba,da alama ma girki sukayi saboda kitchen din na bude zasu jerawa amarya nata kayan a ciki,mukhtar na tsaye a tsakar gidan riqe da qugu cikin bacin rai,da alama ransa ya baci da irin abinda sukayi,ga abincin da suka dafa din ma basu iya cinyewa ba sun kuma lalata bare a bawa wani,zai soma sababi ta shige jikinsa ta soma lallabashi,sai da ta sauke masa temper dinsa sannan ya tayata suka fara kintsa gidan fes.      Kafin su kammala anyi kiran sallar magariba,ruwan wanka ta dora musu sannan sukayi alwala sukayi sallah,bayan sun idar ta juye musu ruwan sukayi wankan tare,ta shirya tsaf tayi kwalliya cikin qananun kaya,zata dora musu girki yace ta barshi kawai ya zura jallabiyyarsa ya fita.     Cikin minti a shirin ya dawo da ledoji a hannunsa,ya ajjiye kan kujerar yana cewa "Dauko faranti ki juye mana wannan,ki hado da cups,hala ma yau duka bakici abinci ba" murmushi tayi sanda take fita daga falon tana cewa "Naci mana ya mukhtar a gidan maman naana" ,ta dawo dauke da plates din ta juye abinda ke cikin ledar.      Tsire ne da zafinsa sai zuba qamshi yake,sai rabin gasashshiyar kaza,ta bude dayar ledar,lemon roba ne na fanta sai maltina wanda tasan ta mukhtar din ce tunda ita bata dameta ba.        A nutse suke ci suna hirarsu jifa jifa kamar babu wani abu dake damunsu.       Suna tsaka da ci wayar sa ta dauki qara,sumayya ta miqe ta isa inda take chargy ta ciro masa kana tazo ta miqa masa,baquwar lambace,yayi kamar bazai daga ba amma yadda kiran keta nacin shigowa ya sanyashi dagawa ya kara a kunnensa. *mrs muhammad ce* 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍🏽 *~KUNDIN QADDARATA~*✍🏽 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) _________________________ _Bismillahir rahmanir rahim_ *_la yadillu rabbi wala yansa_* _______________________ *_ina taya maman farida(dan maliki,baya tsami banza,hanyan ruwa)murna sauka lafiya tare sa samun zan kadeden baby boy,Allah ya raya mana shi cikin musulunci,ya albarkaceshi,ya qara musu lafiya ita da babyn,sannan kuma muna kamu tun yanzu,lol_* 0⃣5⃣     Sallama yayi maimakon ya amsa hello da ake faman cewa,yayi jim yana jiran amsa sallamar tukun,fahimtar abinda yake nufi da akayi ya sanya aka sa sallamar "Da wa nake magana?",cikin karyar da murya akace " mukhtar baka ganeni ba,fa'iza ce fa" "Fa'iza?,wacce fa'iza" wani murmushi akayi mai fidda da sauti cikin siga ta nufin jan hankali "Fa'iza amaryarka mana".        Hade rai yayi kana cikin dakiya yace"ok,ya akayi?",sake marairaice murya tayi "Haba mana mukhtar,ai ko gaisawa ka bari muyi tukunna ko?" "Yayi kyau,ina gajiya?" "Gata nan muna fama da ita mun fara shiga sabgogin biki,amma mukhtar ko marmarin sake zuwa guna bakayi,haba" "Wannan ne dalilin da yasa kika kira ni?" Kai ta girgiza kamar tana gabansa,cikin ji haushin yadda yake amsa mata da qyar kamar wanda aka tilastawa "A'ah ba shi bane" "Fadi uzirinki kai tsaye".       Gyara zama tayi sannan cikin salo da kisisina ta fara magana "An ce daki falle daya ka bani,haba mukhtar,ya zaka bani daki falle daya sannan ka bawa uwar gidanka ciki da falo alhalin nice amarya ni nafi cancantar ciki da falo"tana direwa ya dora "Ko?,a wanne hadisin?".      Fara quluwa tayi amma ta dake"haka na ya dace ai" "To ai babu damuwa,sai ki gayan nawa muka hada muka gina gidan sai na fidda miki haqqinki" ya fada cikin jin haushi da sigar gatse,da sauri tayi saurin cewa don kada kwabarta tayi ruwa "Allah ya baka haquri ba nufina kenan ba" tayi saurin katse wayar,cilla wayar yayi gefe yana jan tsaki kana ya tsame hannunshi daga tsiren ya wuce daki.       Itama kasa ci gaba da cin tayi,saboda haka ta tsame nata hannun ta fada wanka,ta gyara jikinta ta sanya kayan bacci sannan ta lullube farantin tsiren ta bishi da shi,cikin kwantar da murya da tausasa harshe ta sanya shi suka cinye tare.       Ranar alhamis ta siyi relexer,nan saloon din dake bayan layinsu ta shiga aka wanke mata kanta aka busar mata cikin drayer,da yake tana da gashi babu laifi sai ya sake kyau ya kwanta sosai,daga nan bata shiga gida ba,gidan maman nana ta shiga wadda ta kwaba su madara ruwan kankana qwai su dilka da kurkur tana jiran dawowarta,ita ta gyare mata jikinta fes,zuwa la'asar ta fito shar,fatarta ta sake wani kyau da haske.     Tsokanarta sosai mukhtar ya dinga yi,yana mata waqa "Uwar gida na,amarya ta,amanata ki damqeta(waqar my habib(muhammad)" dariyar itama ta dinga yi.      Ranar juma'a aka zo aka mata lalle ja da baqi,ta aika halima da zainab suka karbo mata dinkinta data bada kala takwas cikin kayanta,duka sai data gwada babu wanda bai mata kyau ba,a nan su halima suka kwanar mata da anty dije qanwar mamanta saboda washe gari asabar zata yi wuni saboda ranar sukace zasu kawo amarya.        Wuni tayi babu laifi ta dan tara jama'a,sosai mutanen unguwar suka yi mata kara sun shishshigo,maqotanta na kusa da gidan ne suka zauna mata suna jira a kawo amarya su karbeta.        Ana gab da sallar magariba ta shiga tayi wanka,ta sauya wasu kayan cikin kayanta,shadda ce ja wadda aka yiwa baqin stone work,kwalliya tayi mai kyau da tsari,sosai tayi kyau saidai komai da take yi cikin sanyin jiki take yinsa,haka nan take ta fama da fargaba da faduwar gaba,anty dije nata azalzalarta kan ta shirya kada 'yan kawo amarya su iso bata gama shiryawa ba,ta dauki turare ta feshe jikinta sannan ta nemi baqin mayafinta mai kyau da kwalliyar duwatsu ta yafa ta dawo falo.        Tun magariba suke zuba idon ganin amarya har qarfe takwas na darw babu ita babu alamarta,hakan ya sanya maqotam suka fara tafiya da dai dai da dai dai saboda dawowar mazajensu,wasunsu kuma sun bar yara a gida,har tara shiru hakan ne yasa 'yan uwanta suka fara mata sallama suma saboda tafiya nasu gidajen,babu wanda za'a bar mata saboda anty dije tace hakan baiyi tsari ba,sai taji zuciyarta ta raurawa qwalla ta cika mata ido,bata san me zata yi ba batasan ya zata yi ba hakanan bata san yadda akeyi ba,anty dije da maman nana ne suka dinga kwantar mata da hankali tare da bata shawarwari wadanda suka sake sanya mata nutsuwa,sukayi mata sallama suka tafi,maman nana kawai ta rage.        Qarfe goma na dare maman nanan na shirin tafiya itama ganin shirun yayi yawa sai ga hayaniyarsu da ta motocinsu,hakan ya sanyata ta koma ta zauna tana tsumayin isowarsu,saidai ga mamakinta yadda akeyi a al'adance a fara kai amarya ga uwargida su ba hakan bane,dakinta suka bude kai tsaye suka shige da ita suna faman yada kirari tamkar jinin maroqa "Shiga da bismillah uwar 'ya'yan mukhtar".        Da sauri maman nana ta soko ma sumayyan wata hirar don ta hana kunnuwanta jin abinda suke fadin,saidai ko kadan bata cimma nasara ba saboda wani tashin hankali da taji ya ziyarceta,gudun zuciyarta ya qaru,sai ta kalli maman nana " maman naana,qirjina bugawa yake bansan me ya sameni ba"dan murmushin kwantar da hankali tayi mata "Kada ki damu,wannan shi ake kira kishin,kiyita ambaton hasbunallahu wa ni'imal wakeel,ni'imal maula wa ni'iman nasir" kai ta kada hawaye na silalo mata,ta sanya hannunta ta share tana mai bawa kanta qwarin gwiwa tare da hana kanta da kanta kuka.      Labule aka bankade aka shigo,fiddausi cs goye da 'yarta,ta dubi sumayyan sannan tace "Kije dakin amarya,yaya bara'atu na son ganinki",cikin mamaki maman nana ta dubeta " a'ah,ai ba'a haka,amaryar ai ya kamata tazo ko?"duban maman nanan tayi sai ta juya ta fice ba tare da tace komai ba.      Ko minti daya ba'a qara ba saiga yaya bara'atun ta shigo "Baiwar Allah ke a suwa kuma,wacece ke da har zaki hanata zuwa,to bari kiji,idan ma irin masu shige da fice ne gidan kishiyoyi suna hurewa kishiya kunne wahalar da sumayya kawai zakiyi,don zama fa'iza tazo yi ta kuma hayayyafa,ba mun kawota ne don ta tafi ba,saboda haka ke sumayya ina jiranki", wani abu yazo ya tokare maman nana a wuya,tamkar zata tanka sai taga hakan bashi da wani alfanu,tayi qoqarin kai zuciyarta nesa,saboda koda ta tanka din qila qarshe abun ya juye kan sumayyan wanda bazata so hakan ba,sai abun ya mata yawa ta rasa da wanne zata ji.      Itama ta riqe hannun sumayyan cikin kalamai na qarfafa gwiwa ta mara mata baya har zuwa dakin marya,babu laifi dakin ya cinye komai nata kasancewar yana da yalwa,kuma ba wasu uban kaya suka mata ba,tunda gaba daya sun daga hankali ne anyi bikin cikin matsatstsen lokaci ba tare da sun gama shiryawa ba su kansu.            Gefe daya suka samu suka zauna,sumayyan ta gaidasu daidaikum cikinsu suka amsa,maman nana kam babu wanda ta duba cikinsu don dama darajar sumayyan ya sanyata shigowa dakin,wata 'yar tsohuwa ce dake zaune gefan amarya wadda ta lullube fuskarta da mayafi tace " to sumayyatu,ga 'yar uwa nan mun kawo miki,abokiyar zama,Allah ya baku zaman lafiya,muna fata zaku hada kanku ku zauna lafiya" "Kowa ya kwana lafiya ai shi yaso ato,fa'iza dai gata nan zama daram ila yaumut takunu" yaya bara'atu ta karbe zancan daga gun tsohuwar,rai bace maman nana ta daga kai ta dubi yaya bara'atu,mamaki take bata,wai 'yar yarinyar da duka duka take cikin shekaru na sha takwas take zagewa babba da ita tana yadawa wadan nan habaice habaicen da suka girmi kanta,babu lallai ma kan nata ya iya dauka,ina laifi ma ta bar yaranta masu shekara sha hudu sha biyar su gayawa sumayyan?,wata qila ace wadan nan sine dai dai da ita,amma ba ita ba wadda ta kusa linka shekarun sumayyar ba.       Ta tabbatar idan taci gaba da zama cikin dakin tabbas za'ayi batacciya da ita,bata so kuma wani abu na tsiya ya hadasu,tunda duk tsiya tafiya zasuyi ba zasu shekara ba,kuma gidan dan uwansu ta shigo sunci albarkacinsa,tunda mukhtar kowa ya shaidi halinsa,sai ta kama sumayyar ta miqar sannan ta ari bakinta ta ci mata albasa,don ta fuskanci ba zata iya magana ba kuka take qasa qasa kanta duqe "Insha Allahu baba babu wata matsala,don sumayya bata da damuwa mu mun shaideta tun tana tatsitsiyarta muke tare da ita,zaman lpy an sameshi an gama da izinin Allah" "To Allah ya yarda 'yar nan" cewar tsohuwar.        Da sauri ta janye hannun sumayyan suka fice saboda ta soma ganin bakinsu yana motsi suna shirin fara qananun maganganu,sai data tabbatar sumayyan ta samu nutsuwa kana tayi mata sallama ta tafi,zuwa lokacin suma 'yan kawo amaryar suna qofar gida suna shirin tafiya.       Sha daya na dare agogon falon nata ya nuna mata,gidan yayi shiru kowacce na dakinta,sauqinta daya akwai wutar nepa da ta haskake ko ina cikin gidan,ta sauke ajiyar zuciya tana ci gaba da jan hasbunallahu wa ni'imal wakil,har zuwa lokacin da taji an turo qofar gidan an shigo,sai ta miqe tsam a tsorace kasancewar basu taba barin qofar gidan nasu haka ba.       Tana ji aka rufe qofa ta biyu hakan ya alamta mata cewa mai gidan ne,ta aauke ajiyar zuciya duk da cewa tana tsayen bata zauna ba.       Da sallama ya daga labulen dakin idanunsa ya sauka a kanta,ta kowa yayi a hankali ya shigo dakin yana dubanta yadda tayi carko a tsaye,cikin sanyin murya yace "me kikeyi a tsaye haka kamar wadda taga wani abun tsoro" ta saki ajiyar zuciya,muryarta a sanyaye tace "Ji nayi ana taba qofa ne",murmushi yayi yana ajjiye ledojin hannunsa " ke kam farar kura ce sumy"sai tayi murmushin yaqe tana kawar da kai,ta qarasa inda yake tana masa sannu da zuwa ya amsa yana zama kan daya daga cikin kujerun falon "Hada min ruwan wanka sumayya" ta danyi sororo kamar tace wani abu sai kuma ta fasa tace to.     Wanka yayi sannan ya sauya kayansa,falon ya dawo ya zauna yana maida numfashi cike da gajiya,shiru ne ya ratsa tsakaninsu kowa ya rasa abinda zaya cewa dan uwansa har kusan sha daya da rabi.       Motsi suka dinga jiyowa a tsakar gida,kallo juna suke suna sauraron motsin ba tare da kowa ya cewa kowa komai ba,sumayya ce ta fara fahimtar amarya ce,sai ta dubi mukhtar "Ya mukhtar bacci nakeji" "Hala ma korata kike da dabara ko?"kai ta kada zuciyarta a cunkushe " a'ah ya mukhtar ba haka bane"shiru yayi har kusan mintina goma wanda motsin da suke ji na qara qarfi kadan kadan.     Miqewa yayi ya dauki leda biyu cikin ledojin da ya shigo da su ya tura mata daya sannan yace "Tashi muje ki rakani" daga kai tayi kawai ta dubeshi,tamkar tace ba zata ba amma sam bata iya rashin kunya da gardama ba,kuma ba zata fara a kan ya mukhtar din ba da take ganin qimarsa.       Mayafinta ta janyo ta yafa sannan ta miqe,tare suka jero har zuwa qofar dakin.       A tsaye suka sameta a bakin qofar dakin,tana ganinsu tayi hanzarin komawa kan kujerar ta zauna,saidai kallo daya zaka mata ka fuskanci ko kadan babu walwala saman fuskarta.      Mazauni kowanne ya yiwa kansa,shiru ya dan ratsa,sumayya ta gyara zama tayi qoqarin cewa "Sannu amarya" "Uhmmm" kawai ta fadi,shirun suka sakeyi,sai da ta mula don kanta wai ita an mata laifi kana ta gaida mukhtar din,ya amsa sannan ya fara magana,daki daki daga bisani ya gangaro ga rufewa "Daga qarshe ban auroki don ki raina min mata ba,ban auroki saboda sumayya ta gaza ta kowanni fanni ba,ina son mata ta matata tana sona,bana son tashin hankali cikin gidana,na riga da nasan halin sumayya tun tana mitsitsiyarta,saboda haka ku hada kanku ku zauna lafiya.....haka kema sumayya duk da nasan ki tun ba yau ba baki da matsala,inaso ki dore kan halayenki kada kice zaki sauya,saboda bazan lamunci rashin gaskiya ba......akwai wani sauran mai magana?".       Jin shiru ya sanya duka suka gane ba zata yi magana ba,sai cika da take tana batsewa,hakan ya sanya sumayya cewa "In sha Allah ba zaka samemu da matsala ba,zamu zauna lafiya da junanmu,Allah ya baka ikon yin adalci a tsakaninmu" "Amin amin" miqewa sumayyan tayi sai shima ya miqe "Muje na rakaki ko" duk da suyar da ranta yakeyi amma sai da yasa ta dan murmusa,ina dakin fa'izan ina dakinta.        A tsakiyar falon suka tsaitsaya suna kallon juna,hannayenta ya kama a sanyaye yace "Kiyi addu'a ki kulle qofar dakin,kiyi bacci sosai kada ki sa damuwa a ranki,mukhtar naki ne kinji ko" kai ta gyada "Sai da safe" ya fada yana juyawa a sanyaye.        Duk yadda taso danne qwallar data cika mata ido abun ya faskara,duk yadda taso jurewa ta kasa,ashe kishi gaskiya ne haka yake?,ada idan ana zancan shi dariyarta take tuntsirawa abunta,sai ta cafko hannunsa ya waiwayo yana dubanta "Ya mukhtar,ka zama mai adalci tsakaninmu,don Allah kada ka wofantar da ni" kai ya gyada ya janyota jikinsa ya rungumeta yana share mata hawaye yana fadin "In sha Allah" sai da ya tabbata ta hau gadonta ta kwanta sannan ya fice ya rufe mata qofar.       Ta rufe idanunta a hankali tana fata bacci ya dauketa,karo na farko kuma rana ta farko a shekarun aurenta da zata fara kwana ita daya cikin dakinsu kan gadon su. *mrs muhammad ce* 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍🏽 *~KUNDIN QADDARATA~*✍🏽 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *rabbana afrig alaina sabran watawaffana muslimin* 0⃣6⃣        Idonta ta runtse tana jin qarar rufe maga qofar da yayi,ta gefe daya ta kwanta ta sake mirginawa daya gefan,gaba daya take jin gadon yayi mata fadi.         Ganin tana neman cinhe daren idanu biyu ya sanyata runtse idonta,ta damqe filon da take kai tana fadin "Ya rabb,afrig li sabra" tayi ta maimaitawa babu qaqqautawa,Allah maji roqon bawansa,bata san lokacin da wani bacci ya sadado ya sace ta ba.         Qarfe shida ta farka firgigit tana ambaton sunan Allah,tayi mamakin yadda tayi bacci mai nauyi irin haka,cikin mutuwar jiki ta sauko daga kan gadon ta fito.          A hankali ta murda qofar dakin nata kana ta tura ta ta bude,tashin farko idanunta suka sauka kan qofar dakin fa'iza amarya,qofar dakin na kulle gam da alamu ba'a bude ta ba tunda aka rufe,sai taji wani qunci na ziyartar zuciyarta,ta kau da kai tana jan tsaki kana ta wuce bakin fanfo,ta taro ruwa ta shige bandaki ta kama ruwa sannan ta fito ta daura alwala.       Har qarfe takwas na safiya tana saman abun sallar,ta kalli agogo sannan ta janyo rediyonta data kunna wadda ita ta tayata zama ta kashe,ta miqe ta zare hijabin jikinta ta ajjiye ta fito zuwa tsakar gidan,ta saba tun tuni da kammala ayyukanta da wuri saboda ya mukhtar bai wuce goma a gida.          Idanunta suka sake sauka kan qofar dakin karo na biyu,sabanin dazu yanzu an sassauta rufin qofar da alama an budeta ne,sake dauke kanta tayi sannan ta shiga ayyukanta kamar yadda ta saba.           Sai da ta tsabtace ko ina har zuwa dakinta sannan ta shiga tayi wanka,tsab ta shirya cikim daya daga cikin ragowar sabbin dinkunanta,atamfa ce dinkin riga da skert da ta fidda shape din qugunta yayi das,bata sake yarda da kyawun dinkin ba sai da taga yadda yayi mata a jikinta,maman nana ce ta zabar mata shi.           Tsakar gidan ta dawo,kitchen ta shiga,sai yanzu taga jeran da aka ma fa'iza,za'a iya cewa ta fita duk wani kayan aiki na kitchen nesa ba kusa ba,bangaren ta ta nufa ta wanke tukunya ta tara ruwa ta dora ruwan tea wanda ya sha hadin kayan qamshi sannan ta koma gefe ta fara fere dankalin turawa,babu abinda mukhtar din bai siya ba na kayan abinci tun shekaran jiya.        Aikin take amma zuciyarta a cunkushe take,fuskarta kawau zaka kalla ta gaya maka hakan koda bata bude baki ta fada ba,ta gama firar ta wanke sannan ta juye shayin cikin wani sabon tea flask wanda yake seat ne da farantansa da kofuna.          Tana cikin suyar dankalin ta dinga juyo motsi a tsakar gidan,bata fasa abinda take ba kamar yadda bata damu tasan waye cikin su biyun ba,aikinta taci gaba da yi har lokacin da taji hancinta ya cika da qamshin turaren mukhtar,kamar ta waiwaya sai ta fasa,wani haushinsa ta dinga ji tana ji hakanan.      "Sannu da aiki uwar gida na" taji ya ambata yana takowa zuwa cikin kitchen din,ta dan waiwayo hannunta riqe da abun tsame dankalin yana tsaye a bayanta gab da ita,maimakon ta tarad da annuri da qyalli irin na ango sai ta tarad da sabanin hakan,fuskarsa tana nan kamar kullum "Ina kwana" ta fada a taqaice fuskarta a daure ba tare da ta damu da yanayin fuskarsa ba,maimakon ya amsa sai taji ya sanya hannu ya karbe abun tsamewar ya matsa gefanta ya shiga kwashe dankalin wanda shi yayi saura cikin man "Sumy,me yake faruwa?" Ya tambayeta yayin da take jingine da kantocin fa'iza hannunta harde a qirjinta "Kamar me?" Ta tambayeshi tana debo qwan da zata soya tana zubawa cikin kwano,ya bata amsa sanda yake qwace bowl din ya fara fasa qwayayen "Babu fara'ar nan a fuskarki yau ko kadan" shiru tayi masa bata da niyyar fankawa,ganin haka yasa shima ya ja bakinsa ya tsuke har ya kammala suyar.        Nata kayan karin ta diba ta kammale musu nasu a kitchen ta wuce dakinta,tana zaune kan kujera tana kallon mbc yayin da take zarar dankalin da dai dai da dai dai tana ci tamkar bata so mukhtar ya shigo dakin,yayi kyau cikin dinkin shadda ruwan qasa mai turuwa sai qamshi ke tashi "A'aha,ya kike karyawa ke kadai ina namu break din" "Yana kitchen" ta fadi tana ajjiye plate din hannunta,kai ya girgiza yana zama gefanta "Ba haka na tsara ba,ki shirya mana a nan falon naki,gaba daya zamu karya,daga nan ki shiga ki kira fa'izan" bata ce komai ba ta miqe ta fita din ta dinga kwaso kayan tana jerawa har ta kammala.          A qofar dakin ta tsaya ta qwanqwasa mata,tunda tana ganin bai kyautu ta fada mata kai tsaye ba tunda ba falo gareta ba,sai data qwanqwasa kusan sau biyar sannan tace cikin alamun fusata "Wai waye ne?" "Sumayya ce", sai data bata kusan minti biyu sannan tace " shigo"ciki ciki kamar wadda aka cusawa tsumma a baki.         Kan gado ta tarad da ita kwance,ta samu gefan kujera tadan dosana tana qoqarin dora murmushi saman fuskarta "Sannu amarya" cikin shan qamshi da dauke kai tace "Yauwa" ta danyi jim sannan tace "Amm.....dama mukhtar ne yace ki fito mu karya" shiru tayi kamar bata ji ba sannan ta bude baki da qyar tace "Bazan samu fitowa ba,kuna iya karyawa", bata sake cewa komai ba ta miqe ta fice ta isarwa da mukhtar saqon,kai ya kada sannan yace da ita " zauna mu karya"gefan kujera ta zauna tana kada kai "Nikam na qoshi" "Ban son musu kinji ko,oya sauko" ya fada yana hada tea cup biyu,bata sake cewa komai din ba ta sauko ta karbi cup din tea din daga hannunsa ta fara kurba.        Duk yadda yaso janta da hira ta kasa sakin jikinta sama sama take amsa masa shima bai tsawwala ba har suka kammala ya miqe ya ajjiye mata kudin cefane ya fita.        Tattare kwanukan tayi da nufin fita da su ta dauraye,a bakin qofa taga fa'izan a tsaye mukhtar na bakin qofar yana sanya takalminsa,fuskarta a quntace da alama wani maganar take gaya masa "Sai na dawo" ya fada bayan ya kammala sanya takalminsa,bata ce komai ba sai komawa dakinta da tayi rai bace,sumayya ta miqe daga durquson da tayi ta bi bayansa ta bude masa qofa kamar yadda ta saba "A dawo lafiya Allah ya kiyaye ya bada sa'a" "Amin my sumy" ya fada cikin jim dadi.            Bakin famfon ta dawo taci gaba da wanke wankenta,tana iya jiyo qunquni daga dakin fa'izan wanda batasan dawa take ko me take cewa ba.          Tana gab da gama wanke wanken taji ta turo qofar ta fito,qerere tayi a kan sumayyan "Ke" ta fada cikin gadara,dago kanta tayi a hankali tana dubanta,sai yanzu ne zata iya gane kamannin fa'izan,baqa ce sosai mai matsakaicin jiki,bata da qiba bata da rama,tana da dogon hanci mai tsini sai qananun idanu,aqalla ta tasamma shekara a shirin da uku zuwa da hudu zata bata shekaru biyar ko shida kenan "Yana kitchen" ta fada tana ci gaba da wanke wankenta zuciyarta na bugawa,addu'a take cikin zuciyarta kada Allah ya sanya fa'iza na daya daga cikin masifaffun kishiyoyi,indai ko haka ne bata san ta inda zata sanya kanta ba,bata san inda ta inda zata fara tarar wannan bala'in ba,mutum ce ita tun asali da bata son tashin hankali saboda sam bata iya ba,wani tsaki ta ja sannan ta juya zuwa cikin kitchen din.          Sai gata ta fito hannunya dauke da flask din data zuba mata dankalin don kada yayi sanyi,bude flaak din yayi ta sake tsayuwa a kanta cikin hayaniya tace "Wai ke,kina nufin wannan abun zanci da ya sassanqame yayi sanyi?" Sai ta kuma dagowa tana dubanta "Ina zaton kamar baiyi sanyin da zaki kasa ci ba,tunda cikin flask yake ko" tayi shiru tana jira taji ko zata tanka "Shi yasa tun dazun ya mukhtar yace ko fito mu karya din gudun kada yayi sanyin"ta fada tana dan murmushi       Zaro ido tayi cikin masifa "Iyeee,ashe abinda ake fada gaskiya ne lallai yarinya baki san wace fa'iza ba to banyi niyyar karyawar ba alokacin,ko dole ne?,gidan miji na ne fa,saboda haka babu wanda ya isa ya takurani sai abinda naga dama shi zanyi,saboda haka ki kiyayi shiga hurumina" ta juya fuuu ta shige kitchen din.         Ita dai binta kawai tayi da ido abun na bata mamaki,me tayi mata daga yin maganar da bata kai ta kawo ba?,tana tattare kayan zata maida kitchen din sai gata ta fito hannunta dauke sa dan matsakaicin kwandon tace taliya cike da dankali daya hannun wuqa da kujera 'yar tsuguno ta dawo bakin kitchen din ta zauna.         Bata ce mata komai ba ta rabe ta ta shiga kitchen din ta maida kayan wanke wanken muhallinsu ta jera ta sake goge gurin sannan ta fito.         Zamanta kenan taji muryar yaranta na sallama,murmushi tayi tana miqewa,ko banza ta samu anokan debe kewa,don ta lura fa'izar akwai matsala tattare da ita,haka take ko wani abun ke damunta oho Allah masani,miqewa tayi ta fito da tabarma hannunta,da yake wani lokaci idan bata so su bata mata gu a tsakar gida suke zamansu.        Tana shimfida tabarmar yaran na gaida fa'iza da dai dai da dai dai,ta amsa musu babu yabo babu fallasa,suka qaraso gun antyn tasu.          Tana tsakiyarsu tana biyewa surutunsu,fa'iza na kitchen tana fama da suyar uban dankali da qwai wanda a zahiri yafi qarfinta,so take tun daga yau ta fara nunawa sumayya ikonta cikin gidan kafin ta haifo yaran da zasu zama ajalin zamanta cikin gidan,kamar yadda yake cikin KUNDIN BURINSU ita da su yaya yahanasu.         har zuciyarta sumayya take jin dadin hirarta da yaran,duk wani bacin ranta ya gudu,ta miqe ta nufi kitchen don dauko dankalin da fa'izar taqi ci ta rarrabawa yaran don kada ayi asararsa,a nan taga uban dankalin da fa'izar ke soyawa daidai lokacin data kammala ta juye cikin babban bowl da tadauka ta fice,bata tanka ba tunda dazun ta fara mata da jan kunnem fita daga sabgarta.         'Yar carafke yaran keyi musu ya sarqe tsakaninsu kan rinton da aisha tayi musu,sumayya nata qoqarin sulhuntawa,tsawa suka ji wadda ta sanya su yin shiru baki dayansu suka waiwaya suna kallonta "Dalla malamai kun cikawa mutane kunne,ina buqatar nayi ramuwar bacci kun hana mutane aikin banza aikim wofi,to wallahi bazan lamunci takura cikin gida na ba ku kintsa bakinku" ta banko qofar tata ta shige ciki.         Tsuru tsuru yaran sukayi saboda basu taba ganin an musu haka cikin gidan ba,sumayya ce tayi qarfin halin yin murmushi sannan ta miqe cikin son bagarar da abinda tayi musun "Ku zo kuyimin cefane maza" nan suka miqe da hanzarinsu kuwa ta rararba musu aiken suka fice,yayin da ita kuma ta tattare tabarmar ta sake share gun kafin su dawo,sannan ta moma kitchen ta gyara duk inda fa'iza taci ubansa har bangaren fa'izar duka.           Bayan sun dawo ta gyara kayan miyar ta bada suka kai mata markade,suna dawowa ta rarraba musu alewa ta turasu gida ganin qarfe daya na rana tayi saboda zuwa islamiyya.         Shinkafa da miya da wake tayi niyyar dafawa a abincin rana,tunda mukhtar ya aiko da nama daga kasuwa,tana tsakar gida tana yankan salad ta juyo sallama da muryoyin mutane,ta daga kanta tana amsawa,baqi ne su kusan shida "Sannunku da zuwa" ta fada fuskarta a sake,shigewarsu sukayi yayin da uku daga ciki suka juyo suka mata kallon banza kana suka wuce,sanyi sosai jikinta yayi,wai dama haka ake?,haka ake kishin ne wai?,ita kam sam bata sani ba ji take qwaqwalwarta ta kasa jan zaren ko wanne tunani.      Tana nan tana yanka salad din ta soma jiyo tashin maganganunsu gami da shewa "Wai dama wannan ce kishiyar taki? Cab di wannan ai ma'aikaciya kurum kika samu Lallai ai wannan banga abun kishi ba Ke irinsu fa sunfi iya tsiya wallahi,kada ki soma cewa zaki sakar mata fuska balle ta rainaki,ki dasa mata tsoronki,bada umarni ne kawai tsakaninku Wallahi ki bautar da shegiya,ki mori bati" take taji jikinta ya kama rawa gabanta ya shiga faduwa,lallai ba shakka suna iya dukanta,haka zuciyarta ta dinga raya mata,zuciyarta tsoro fal irin na yarinta,su kamsu suna sane suka dinga maganar don ta jisu,saboda su dasa tsoro cikin zuciyarta.         Kitchen din ta tattara ta koma tana ci gaba da ayyukanta,sai dai har yanzu tsoron bai saketa ba,addu'a ta dinga yi cikin zuciyarta hakan ya sanya ta dan samu nutsuwa.        Tana gab da kammala girkin fa'iza ta shigo kitchen din ita da daya daga cikin baqin nata tana fadin "Ga bangare na nan,ki dafa duka abinda kuka ga ya muku yadda zai isheku" sumayya ta waiwayo tana dubanta "Amma amarya har da ku nayi abincin fa zaya ishemu duka,ina ga idan aka dafa wani zaiyi yawa" juyowa itama tayi ta zabga mata wata harara sannan ta nunata da yatsa "Ina cewa ko awa biyu ba'a yi ba da yi miki maganar ki guji shiga sabgata ba ko,ke har kin isa kina sa'ar qanwata ki dinga dafawa kina bani iya limit din da kika ga dama ina ci?,kin shirya cin na jaki kenan,don wallahi jibgarki zanyi a gidan nan banza juya kawai" sai ta dauke kanta daga garesu ta maida kan girkinta,abun mamaki sai kalmar juya yau tayi mata zafi,karo na farko kenan da ta taba jin hakan.       Tana jinta ta gama gayawa baquwar tata abinda za'ayi ta fice,bakin fanfo ta wuce ta tari ruwa ta shiga wanka don sai yanzu ta samu damar yin.       Tana kammala girkin ta zubawa mukhtar nashi,ta zuba nasu fa'izan ta aza a bangaren kantarta ta dibi wanda zata ci ta shige daki abinta,bata sake fitowa ba har suka gama tsiyar da zasuyi suka tafi wajen qarfe biyar na yamma,a sannan ta fito ta shiga kitchen don dora ruwan wanka.       Tamkar ba'a taba guara kitchen din ba haka suka lalatashi,ga uban abinci nan da suka dafa sun kasa cinyeshi cikin tukunya a bude,kwanukan duka vikin sink din fa'iza gaje gaje,hatta wanda ta ajjiye musu sun cakalkala shi sun bar cooler rabi a bude rabi a rufe.          Ranta taji ya baci karo na farko,ta tsani almubazzaranci da abinci,saboda tana da imamin abinda ka raina shi wani ke nema yasa a bakin salatinsa amma ya gagareshi,to don me kai don Allah ya baka zaka wulaqanga,bayan ya baka ne ba don kafi kowa ba.         Bata gaji ba bayan ta dora ruwan ta soma tattara kitchen din,ta gyara ko ina fes,saidai batasan ya zatayi da abincin ba tun kafin mukhtar ya gani yaji babu dadi,ita ba leqe take ba kuma yaro gidan bare ta samu almajiri ta bashi,dole ta jira dan aike yazo.        Ruwanta na zafi ta juye ta shiga wanka,can ma sai da ta tsaya ta gyara,sam bata qaunar taga guri ko yaya ya sauya yanayi.         Taji qarar babur dinsa sanda take maida kaskon turaren wuta kitchen,sanin cewar gidan a bude yake ba kamar sanda tana ita daya ba saboda haka ta toge a tsakar gidan tana jiran shigowarsa.           Cikin mintuna ya qaraso tsakar gidan,tana murmushi ta qarasa inda yake tana niyyar karbar jakarsa,sai ya bude hannayensa ya kai mata runguma sai ta goce tana murmushi tare da kallon qofar dakim fa'iza,qasa qasa da murya tace "Bamu kadai bane fa a gidan" ta miqa hannu ta karbi kayan hannun nasa,sai ya kalleta yana turbune fuska "Haka kawai tun yau an fara shiga haqqina,ai shikenan" yayi maganar yana wucewa dakinsa ta bishi a baya tana masa gwalo.       Har ta kammala kintsa abinda ya shigo da shi babu fa'iza babu alamarta,sai da ta gama zata fita daga dakin sukayi kacibus da fa'izan na shigowa,harara ta balla mata,gefe ta matsa ta raba ta kawai ta wuce.         Tunda ta gabatar musu da abinci tayi alwalar sallar magariba shigewarta daki,bata sake fitowa ba sai da taji mukhtar na qwala mata kira,ta miqe a hankali ta gyara daurin dankwalinta ta amsa tana fitowa.          A kitchen ta tadda shi tsaye ransa bace yana qarewa himilin abincin kallo,gefe guda kuma ga dankali da qwai da fa'izan ta soya a wulaqance cikin cooler ba'a idasa cinye shi ba,ya dago idanunsa daga kallon coolers din ya maida su ga sumayya,da hannu yayi mata nuni "Me wannan?,meye haka sumayya?" A ladabce tace "Nima ban sani ba ya mukhtar saidai ka tambayi amarya" baiyi musun hakan ba tunda a gefanta yaga tarin coolers din,ya daga murya ya qwala mata kira,ta shigo kitchen din sanye da hijab "Gani" ta fada tana kallonshi.       Ya kalli kayan ya kalleta sannan yace "Wannan na waye?" "Na baqin da nayi ne" ya hadiye wani takaici saboda yadda tayi maganar cikin halin ko in kula da nuna rashin muhimmancin laifinta,wacce iriyar yarinya ce ita,yinin farko kenan a gidan mijinta?,yayi qoqarin danne bacin ransa yace "Na lura kamar harda dankali ya akayi aka dafa abinci yayi yawa haka?" *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍🏽 *~KUNDIN QADDARATA~*✍🏽 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) _______________________ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *hasbiyallahu la'ilaha illa huwa,alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azim* _________________________ 0⃣7⃣     Hannunta riqe kan qugunta tace "Dankali ne ta barmin ya huce,ni kuma ban iya ci ba,abinci rana kuma gaskiya bazan zauna qanwar qanwata tana dafa abinci tana bani ba,bayan ba cewa nayi bazan iya ba", shiru yayi yana ci gaba da kallonta zuciyarsa na quna,da qyar ya samu ya hadiye wani abu mai zafi a qirjinsa sannan ya gyada bayan wani tunani da yayi " yayi kyau"kawai ya fada sannan ya ratsa ta tsakaninsu ya fice cikin bacin rai.          Sa kai sumayya tayi itama tana shirin bin bayansa "Banza munafuka,idan ma ke kika nuna masa an gaya miki wani abun zai min" bata kulata ba tayi ficewarta ta koma dakinta,tana kammala sallar isha'i ta tura qofarta tayi kwanciyarta.          Washe gari shi ya shigo ya tada ta sallah,ta miqe tana mutstsuka idanunshi a kanta,sam bata ma ji kiran sallahr ba yau "Ki tashi haka kiyi sallar asuba" ya fada yana qare mata kallo ta cikin rigar baccinta wadda tayi mata kyau "Kinyi kyau sosai my sumy" ya fada sanda take qoqarin saukowa daga kan gadon,sai ta waiwayo ta dubeshi,dan qaramin murmushi ta sakar masa wanda yaso rudashi,ya qarasa inda take tsaye tana zura hijab dinta don fita waje tayi alwala,ya janyota da baya ya rungumeta yana rada mata "Nayi missing dinki sumy ta" sai ta zare daga jikinsa ta waiwayo tana dubanshi idanunta a waje,ta maida su kana ta langabe kai "Kai ya mukhtar,ni ban fafi haka ba sai kai dake da amarya?" Baice komai ba sai wani guntun murmushi da ya saka ya sanya kai yana ficewa tare da ce mata ta fito tayi salla.          Yauma kamar jiya ta fito ta kammala aikinta,saidai sabanin jiyan yau a bude taga dakinsa da alama yana ciki,saidai bata san ko me yake yi ciki ba,tana fitowa daga wanka sukayi kacibus,ya zuba mata ido yana dubanta "Yanzu sumayya ko ruwan wanka ma an daina bani?" Ya fada murya a karye "Ba haka bane ya mukhtar,na dauka aikin amarya ne wannan ko,amma kayi haquri akwai wani da na dora zan zuba a flask bari na juye maka" ta fada tana shigewa zuwa kitchen din da sauri.         Tare suka karya yauma,saidai bai aikata kiran fa'iza ba da kansa ya gaya mata tazo zasu karya ya juya ya fito,saidai har suka gama karyawar bata fito din ba,har ya fita daga gidan.          Tana kwance kan doguwar kujerar falonta tana hutawa taji sallamar anty dije,da sauri ta sauko daga kujerar tana amsawa don ko da wasa fa'iza wadda tafi maqotaka da qofa bata yi kuskuren amsawa ba.        Rungume anty dije qanwar maman nata tayi tana mata sannu da zuwa kana suka wuce dakinta,bayan gaishe gaishe da tambayarta zaman gidan ta gaya mata komai lafiya suka shiga hira,lokaci lokaci ta dinga tashi tana duba girkinta na rana da ta dora.          Kammalawarta yayi dai dai da lokacin sallah,saboda haka anty dije tace sai tayi sallah kafin taci abincin,tare suka fito anty dije tayi bakin famfo ita kuma ta nufi kitchen don gama kwashe abincin.          A bakin qofar kitchen sukayi kacibus da fa'iza na shirin fitowa ita kuma na qoqarin shiga,hannun fa'izar riqe da qatuwar kula da ta gama shaqewa da abincin da ta girka wanda a zahiri ko yara gareta yafi qarfinsu su duka balle cikinta ita daya,harara ta galla mata kana cikin daga murya tace "Gafara malama na wuce,da wani idonta kamar jiqaqqiyar aya" rabe mata tayi tazo ta wuce fuuu tamkar guguwa cike da tsoro sumayya ta bita da kallo.          Duk a idanun anty dijen haka ya faru,ta kada kai cike da takaici ta wuce bandakin ta daura alwalar.           Tana saka hijabin sallarta sumayyan ta shigo dakin dauke da coolers din abincin,tun kafin ta saukesu anty dije ta finciki hannunta tayi bedroom dinta da ita,gefan gado ta zaunar da ita kana ta zauna kusa da ita suna fuskantar juna,cike dabacin rai ta tsareta da ido sannan ta soma magana "Kar dai kice min sumayya tsoron kishiya kike?,kada ki gayan cewa kin fara nuna mata cewa kina tsoronta?" Da idanu sumayyan ke bin anty dijen cikin sanyi jiki.         Cike da zafi tace da ita "Me innarki ta gaya miki sanda za'a kawo miki abokiyar zama" duk sai ta rude saboda tasan cewa anty dijen ba dai zafi ba,tsab ta mareka ba komai bane idan ka bata mata,cikin tsawa ta sake maimaitawa "Dake nake,nace me innarki ta gaya miki?" Cikin rawar murya da in ina wanda tuni idanunta ya fara tara qwalla tace "Tace min na zauna da kowa lafiya,kada na daga hankalin kowa,kada na zalunci kowa kada na cuci kowa idan na cuci abokiyar zama na bata yafemin ba" Kai ta jinjina ta kama hannunta tana matsawa da dan qarfi,cikin kakkausar murya ta sake ce mata "Tace ki zauna a cuce ki?" Kai ta kada,idanunta ta zaro mata "Ki bude bakinki kiyi magana" "A'ah" ta fada qwalla na gangaro mata. "Tace ki zauna a zalunceki ko a rainaki?",nan ma ta amsa "a'ah" kai ta jinjina. "Da kyau......me yasa kika fara bawa fa'iza qofar da zata rainaki?,me yasa kika fara nuna mata kina tsoronta" shiru tayi ta kasa bata amsa don itama bata san dalili ba.       Ganin haka ya sanya anty dije sasaauta fushin fuskarta ta sake matsowa ga sumayya "Bamu lamunci ki zalunci kowa bama balle abokiyar zamanki,amma......bazan lamunci ki zauna ki zama bola ba,bazan lamunci ko zama raguwa matsoraciya ba,kishiyarki ba mai son zaman lafiya bace,bamu ce ki biye mata ba,bamu ce ki zama mai son tashin hankali ba,amma sam bazamu zuba ido ki zama banza ba.....kinsam wace kishiya...kishiya ma irin taki sumayya" kai ta girgiza,anty dije ta soma warware mata komai,dukkanin kunnayenta sumayya ta bata,sosai maganar ke ratsata,sai ta dinga dauko ta maman naana tana hadawa da anty dije,tabbas dukkaninsu gaskiya suke gaya mata.         "Kada ki yarda naga ba haka ba kina jina ko?" Anty dije ta fada tana kama kunnanta da kanta "In sha Allahu" inji sumayya tana dan murmushi,dukansu suka fito any dije ta tada sallarta ita kuma ta je ta daura tata alwalar tayi sallahr sannan suka ci abinci,suna ci anty dijen na bata labaru kala kala na kishiyoyi,wani ya bata dariya wani ya bata mamaki wani ya bata al'ajabi.        Har soro ta rako anty dije sukayi sallama,tana shirin komawa ciki taki qarar machine dinsa,hakan ya sanyata dakatawa ta bude mishi qofar ya shigo tana mamakin dawowarsa yau da wuri haka bayan duka duka biyar da 'yan mintuna ne,saidai bata ce komai ba kamar yadda anty dije ta gaya mata ta koyi yawan dauke kai da yin shiru kam wasu al'amuran da ba cutarwa ne gareta ba,ko ba hiruminta bane,ko kuma bazai cutar ko ya amfaneta ba yin magana akansa duk da cewar dama can ita din ba mai shishshigi bace.             Da murmushi saman fuskarta take masa sannu da zuwa,ya kashe mata ido daya sanda suke shiga cikin gidan "Ko ki tambayeni ma ta akai ka dawo gida da wuri ko?" Murmushi tayi tana rausayar da kai "Ai ba laifi kayi ba,kuma mai gida da gidansa ai yana da hurumin dawowa duk sanda yaga dama"mintsinarta yayi a bayanta har sai da ta sanya dariya yace " sarkin wayo da iya magana,ko yaushe duka kika koyi wannan wayon haka?" "Ka manta rainonka ce?" Ta fada tana kashe masa ido daya "Gaskiya ne" ya fada yana sanya hannunshi cikin alhjihunsa ya fiddo da kwado(key) yana fadin "Muje kitchen ki tayani wani aiki"..... *mrs muhammad ce* 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍🏽 *~KUNDIN QADDARATA~*✍🏽 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) ______________________ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *wa iy yamsaskallahu bi durrin fala khaashifa lahu illahuw,wa iy yuridka bi khairin fala raadda li fadhlih* _____________________ 0⃣9⃣         Ya rantse sai ya hukunta ta,sai ta gane bata da wayo,'yar bariki ce ita ko mai,zai nuna mata bata iya iskanci ba.          Miqewa yayi ya dauki jakarsa zai fice sumayyan ta sha gabansa "Ya mukhtar,bai kamata ka fita cikin wannan halin da kake ba" sai ya tsura mata ido yana kallon yadda ta langabe kamar zata yi kuka,haka kawai ana son shiga tsakaninsu da farincikinsu kam wani dalili can maras tushe,kan wani abu da basu isa su yiwa kansu shi ba sai Allah ya ga dama,sai ya saki murmushi don ya kwantar mata da hankali,ya sanya hannunshi ya shafi gefan fuskarta "Kada ki damu sumayya,ina gane komai" yayi kissing goshinta yana fadin "Sai na dawo" ya juya ya fita a gaggauce don bai son ma yaya yahanasu ta kuma tsaidashi.          Kai ta kada sannan ta fito daga dakin ta ja ta kulle masa ta tafi da key din dakinta,cikin falonta tayi zamanta bayan ta kunna redio tana sauraran labaran rana freedom.           Tana kammala jin labaran ta shiga kitchen ta dora abincin rana,cikin kitchen din ta zauna har ta kammala saboda jallop din shinkafa ta musu,ta zuba cikin cooler ta ajjiye cikin kitchen din kana ta nufi dakin fa'izar,ita daya ta taras da alama yaya yahanasun ta tafi wanda ita sam batasan ta tafin ba "Ga abinci can cikin kitchen na gama" ta fada ta juya ta fice ba tare da ta jira amsarta ba,bata zaci ta ci ba sai da ta shiga dora sanwar dare taga babu komai cikin cooler din tas,mamaki ya kamata saboda batayi tsammamin zata iya cinyewa duka ba,don har da yaya yahanasu ta dafa,ta kada kai ta shiga sabgar dora abincin dare.           Sau biyu suna kacibus da fa'izan na fitowa a kitchen din sanda take tsaka da girkin,tuwon semo tayi miyar kuka wadda ta wadata da man shanu da nama,ta kammala ta jere komai cikin kitchen sannan ta nufi famfo ta tara ruwan wanka tana jira botikin ya cika.           Da sauri taga ta fito daga dakinta ta suri silifas ta fada bandakin ta bame qofa,sai ta bita da ido kana ta dauke kai,tana tsammamin matsuwa fa'izan tayi har haka?,ta kashe fanfon ta koma gefan rijiya ta zauna tana tsumayin fitowarta.       Wasa wasa har ba fa'iza ba alamunta,abun har ya dan bawa sumayyan tsoro,sai ta miqe ta isa ga bakin bandakin ta qwanqwasa qofar,gyaran muryar da taji tayi mata ya tabbatar mata komai lafiya,sai ta koma bakin riniyar ta zauna tana ci gaba da dakon fitowarta.         Ba ita ta fito ba sai da taji shigowar mukhtar gidan,a qalla awa daya kenan ta kwashe cikin makewayin,sumayyan ta miqe tana masa sannu da zhwa tare da jin nauyin zuwa ya taddata babu kwalliya saboda ta riga da ta saba al'adarta ce daya dawo ya sameta tsaf.         Ta miqa hannu zata karbi ledar hannunta taji anyi wuf an karbe,da mamaki ta waiwayo fa'iza ce wadda batasan sanda ta fito daga bayin ba ke tsaye tana ta faman doka masa murmushi tare da yi masa sannu da zuwa,a dake yake sa mata,sai sumayyan ta koma ta dauki botikinta zata shige wankan "Ai wlh ni da ke ne cikin gidan nan,indai ina nan an daina wannan karuwar kwalliyar daren" ta fada bayan da taga mukhtar ya shige dakinsa,waiwayowa tayi ta dubeta sai ta saki murmushi sannan tace "Ko?"cikin qufula da ganin yadda maganar bata da da ta da qasa yadda taso ba tace " eh,ko kina musu ne?"kai ta gyada sannan a taqaice tace mata "Zamu gani" ta shige bandakin abinta,yatsa ta ciza takaici ya kamata,wai dama can yarinyar ba tsoronta take ba basaja take mata ko kuma zugata aka soma yi?,qwafa ta ja domin bata da amsa ta shige dakin angon nata.          Ga mamakinsu suna shirin soma cin abincin dare sai ga fa'izan,tana wani murmushi ta raba gefan mukhtar din ta zauna "Naga ya kamata nima adinga cin abincin da ni don qara donqon zumunci ko?" Ta fada tana wani kashe masa ido,ha fuskanci yau sai wani rawar kai take,amma idan batasan kan garin ba shi zai mata kyakkyawan kwatance,babu wanda ya tankata iyaka aka tura mata kulolin ta debi yadda taga zata iya.       Ita da sumayyan kusan tare kowannensu ya sanya lomar farko a bakinsa,idanu sumayya ta zaro sakamakon wani dan banzan gishiri da ya cika harshenta har zhwa kwanyarta,take qwaqwalwar tata ta tafi tunanin ta yadda akayi hakan ya faru?,a iya saninta lafiyar Allah ta kammala komai ta gyatta shi,amma me ya kawo wannan sauyin?,ko dai harshenta ke shirin samun matsala?,.         "Qundun uban nan" abinda fa'iza ta fada kenan wanda shi ya tsinke zaren tunanin sumayya,kallon mukhtar suke dukkansu kowanne da tasa manufar a zuciya,zaquwar mukhtar yayi magana ta samu filin baje hajarta da kuma mamakin yadda yaqi maida hankali ga kalamanta takeyi,cikinsu babu wadda ya kalla saici gaba da sambada lomarsa yake,yayin da sumayya tayi qas da kanta ta daure duk wani abu da take ji kan harshenta itama taci gaba da kai lomarta tamkar babu wata matsala dake waka na.        Idanu fa'iza ta dinga binsu da shi,to ko dai harshenta ne kadai ke gaya mata tuggunta yayi dai dai?,ganin sunyi uwar watsi da ita ya sanya ta kasa shiru sai da ta magantu "Wai muntari bakaji uban gishirin dake cikin abincin nan ba ne?" Bai amsa maga ba sai da ya sake wata lomar "Wanne abinci fa?" "Na gabanku mana" ta fada tana nuna kwanon da yatsa tare da qanqance idanu "Hala kina da matsalar dan dano ko?" Kafeshi tayi da idanu tana tantama,sai kawai ta miqa hannu ta kwaso miyar gabansa ta kai bakinta,tabbas iri daya ce haka ma dandanon iri daya ne,to tsabar iya asiri ne na sumayya yasa bai fahimta ba ko sun tasamma raina mata wayo ne,fa'iza macace da sam bata da siyasar zamantakewa,hakan ne ya sa ta kasa boye fushinta ta tashi ta fice fuuuu ta bar dakin cike da baqinciki,so tayi yau ya ciwa sumayya mutunci sannan ya janyeshi kuma ta kwana da shi yau ta cusa mata baqinciki.          Idanunta ta dora kan mukhtat fuskarta qunshe da tashin hankali,ta bude baki zatayi magana ya dora yatsansa kan lebansa "Shshshshsh!,kada kice komai,ita ta zuba gishirin kan ido na bayan shigarki wanka,tana zaton bazanci ba,batasan ba maqaryacin so nake miki ba,zan iya cin wanda yafi haka ma,bare ma shekararmu nawa da sumayyaty na santa qwarai wajen iya sarrafa hatsi" yadda ya qare maganar ne ya bata dariya har sai da ta dara din,daga bisani ya wanke mata duk wani damuwa tata suka bige da hira,yace idan ba zata iyaci ba kada ta cuci kanta ta ajjiye ya sama mata wani abu shikam zai iya ci,tace sam tunda har ya iya ci itama sai ta ci,qarshe dai ramun muguntar gun fa'izar ya koma tunda ko banza ta tashi ciki babu komai.          Yau din da kanshi ya mata sai da safe,kishi ya kamata sosai ta dinga rayawa cikin ranta wato zashi yaje yayi abinda anty yahanasun ta umarceshi kenan dazu da safe,ta dinga juyi saman gado ita daya da qyar bacci ya saceta.          Bata jima da fara baccin ba ta dinga jin ihu sama sama cikin barcinta,a sannu ta bude idanunta tarwai,tabbas ba mafarki bane,ihu ne daga dakin fa'izan kuma muryarta ce cike da gunjin kuka,ta kasa kunne sosai ta dinga jin yadda take neman agaji da dauki,runtse idanunta tayi sai kuka ya subuce mata ta sanya hannunta ta toshe dukka kunnuwanta baccin da bata koma ba kenan.          Kiran sallar farko na asuba taji an bude falonta,ta kasa kunne sai kuma taji shuru har akayi kiran sallah na biyu,ta sauko daga san gadon da idanunta wadanda sukayi luhu luhu saboda kuka,ta zira hijabinta ta fito daga dakin jiri da dibarta.         A falon nata taga kamar mutum kwance,gabanta ya fadi da sauri ta koma da baya ta kunna makunni qwan lantarkin falon,haske ya qauraye ko ina,mukhtar ne kwance saman doguwar kujerarta tafin hannunsa dafe da goshinsa.          Dauke kanta tayi tamfar ma bata ganshi ba yayin da shi kuma ya bita da ido har ta fice,sai da ta daura alwala ta dawo sannan ya tashi ya fice,tana kan abun sallarta har gari ya soma haske,sallamarsa taji yana shigowa ta runtse idanunta har ya qaraso gabanta,ya fuskanci me take nufi domin yana da tabbacin mawuyaci ne idan baya jiyo qarajin fa'iza a jiya ba,saboda shi kadai yasan ta'asar da ga tafka mata da gayya.       Muryarsa a tausashe da irin salon dake kwantar da hankali da ratsa sassan jikinta yace "Sumayya,kiyi haquri don Allah,wlh ban shiga dakin fa'iza a jiya don naci fuskarki ko na bata miki rai ba,kiyi haquri idan ranki ya baci,komai nayi nayi ne saboda koya mata saboda ta fice daga rayuwarmu....kiyi haqur....." "Ya isa ya mukhtar" ta fada da sauri tana katseshi "Ka daina bani haquri,matarka ce kamar yadda nake matarka,kuma adalcin kenan" ta fada duk da tana jin daci qasan zuciyarta amma hakan ba zaya hanata fadin gaskiya ba.      Hannunta ya sake kamawa sosai,kana ganin fuskarsa kasan cikin bacin rai tsantsa yake "Duk da haka nayi da na sanin kasancewa ta tare da ita,fa'iza......." Hannunta ta dora saman bakinsa qwalla da digar mata "Matarka ce bana son jin komai,don Allah ka tafi ya mukhtar kaji,ka tafi bacci nakeji" da gaske take fadin maganar saboda haka ya saketa ya miqe a sanyaye ya fice,tun tana kukan bilhaqqi har ta koma yi qasa qasa,da haka bacci ya sureta.         A firgice ta farka sakamakon hasken rana da ya dalle ta wanda ke alamta mata gari ya waye sarai,da sauri ta dubi agogo,har qarfe goma na safe,gabanta ya fadi data tuna cewa babu abinda yau tayi a gidan,a hankali ta miqe ta isa falo ta yaye labulen window dinta ta duba dakinsa,a kulle yake da muqulli tana jin mawuyaci ne idan fita kasuwa ba kenan,dawowa tayi uwar dakin ta tsaya gaban madubi don duba idanunta,bata so ta fita har fa'iza ga fuskanci tayi kuka ko ta fuskanci taji kishi ko ta gane abinda ya faru daren jiya cikin gidan har ta raina ta,hudubar anty dije ce boye duk wani abu da zai sa ta gane logonta,bare ta riqeshi ta dinga musguna mata da shi,fuskarta fayau haka ma idanun sun koma babu kumburin,saima haske da suka dada yi,hijabinta ta cire ta daura dankwali saman kanta ta fice tsakar gidan.          Sai da ta kammala aikinta tas tana bakin rijiya tana diban ruwan wanka sannan taga fitowar fa'izan,ta daga kai ta dubeta,da qyar take iya tafiya tamkar yaron da aka yiwa shayi yanzu yanzu,idanun nan sun kumbura sunji jazur,hatta da fuskarta a kumbure take,da alamu ba qaramar izaya mukhtar din ya ganawa rayuwarta ba a jiyan,har qasan ranta sai da sumayyan taji ta tausaya mata,amma da baqar zuciya irinta fa'izan sai data iya samun sararin wulla mata harara tare da fadin "Baqar manufarki a kanki zata qare,anyi mai wuyar tunda yazo hannu ko,saiki saurari zuwan 'yan dagwai dagwai" ita kanta tasan ta fada ne kawai amma ita daya tasan halin da take ciki,dariya ta qyalqyale da shi sannan tace "Wai.....a hakan,to bamusan gaibu ba" ta juya ta waiwayenta tare da sheqa dariya ta shige daki abinta don bata ga dacewar tsayawa cacar baki da fa'izan ba,ai kuwa ba qaramin qona mata rai dariyar tayi ba,sai ta dinga jin duk ta muzanta,ta dinga jin tamkar mukhtar ya kwashe duka cin kashin da yayi mata daren jiya ya gayawa sumayyar,ta dinga jin kamar ya gaya mata wace ce ita,jiki a sanyaye da jan qafa ta lallaba ta dibi ruwa ta shiga bandakin.         Bata fito ba balle ta biye mata suyi sai da ta kammala ta shiga daki sannan tayi nata wankan,tana daki tana shiryawa taji kamaf motsi cikin falon ta,bata leqo ba sai data kammala shiryawar,ta fito hannunta dauke da dan kwalinta tana daurawa,fa'iza ce tsaye a falon karo na farko tunda tazo gidan,gaba daya ta shagala da kallon yadda aka tsara falon,babu qarya babu fallasa amma yayi kyau matuqa,komai a tsaftace a killace,sosai baqinciki ya rufe ta na yadda dakin sumayya yafi nata kyau tsadar kaya tsafta da tsari bugu da qari ga yalwa dai dai gwargwado.       "Lafiya dai ko?" Sumayya ta fada bayan ta gama kallon yadda take qarewa dakin nata kallo,juyowa tayi cikin jin kunya da bori,ba tare da ta shirya ba abinda ke zuciyarta ta fito "Hmmmm,lallai kam,kaga masu daki,kin tatsi muntari kin gyara kanki shi yasa kikewa kowa kallon banza ko?ayi mu gani naga ta yadda za'a mora" murmushi sumayyan tayi ba tare da nuna damuwa kan batunta ba "Fadi meke tafe da ke nasan dai ba wannan ne ya kawoki ba"cikin qanqance ido fa'izan tace " eh,ina abun karina?"ta tambaya cikin gadara,bata san cewa yau sumayyan jinta take dai dai da yadda tazo mata ba,dariyar nan ta rainin hankali tayi mata sannan ta zauna kan daya daga cikin kujerunta "To idan banda abinki fa'iza amarya wanda yayi aika aikar ma ya tsallake ya tafi don me zaki dinga haushin kaza huce kan dami a kaina,ki roqeni kawai na taimaka ma baki abinda zaki sanyawa cikinki ko?".         Sosai ta hasala har ta fara huci,ba shakka da acw da qwarinta babu abinda zai hanata neman dambacewa da sumayyan,sanin cewa babu qarfin sai ta buge da nuna ta da yatsa " ke baki isa ba wallahi qaramar mara kunya,dududu nawa kike da zan nemi alfarma gunki,na fuskanci kanki ya fara rawa ko bakisan wace fa'iza ba,wallahi sumayya ki kuka da kanki don ke abar tausayi ce nan gaba sai kin zama abarkwatancen wa wasu" "Bakinki ya sari danyan kashi jeki ki duba kitchen ki dauki da'amin tunda duka don shi kike wannan dai ko?" Ta fada tana miqewa tayi komawarta uwar dakanta,nan ta barta tana hauka sannan daga bisani ta fice,abu goma da ashirin ga wani baqinciki da ta taras,dakin sumayyan ya kere nata da take taqama da shi,kuma tana da zaton cewa daga jikin mukhtar din ta yaga,tana jin dole ta dau mataki kafin zuwan yaran da zasu zama silar zamantowar gidan mallakinta. *mrs muhammad ce* 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) ______________________ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *wa ufawwidu amri ilallah,innal laha basirun bil'ibaad* __________________________ 1⃣0⃣          Yau kam da ta dora girkinta zama tayi cikin kitchen din tana kallo cikin wayarta har takammala girkinta,duk da cewa yau din akwai sauqim zirga zirgar fa'izar tana daka tana jinya,yau daga ita har yaranta sun wataya abunsu.          Yau ma tare sukaci abincin dare,saidai babu fa'izan,don tun sumayyan bata jima da kammalawa ba ta fito ta kamfata ta fice,ita kam sumayyan mamakin shege cin abinci irin na fa'izan take.          Abin jiya akaso a maimaita ko kuma nace har ma ya wuce na jiyan,don kusan har da dambe ne yaso kaurewa tsakanin fa'izan da mukhtar din,ba wai don tana burgeshi ko abinta ya dada shi da qasa bane ya sanya shi dagewa kan sai yayi,ko kadan,yana so ne ta bambance tsakanin aya da tsakuwa,yana so ne ya dasa mata qin abun ta yadda ba zata sake marmari ko gigin nemansa ba.        Iya wuya kam ta shata don har taso ta zarta ta jiya,don yau har mikin jiya sai da ya dawo sabo fil baya ga sabon da ta yo guzirinsa,kamar jiya haka yayi fitarsa da asuba,saidai wannan karon a masallaci yayi zamansa har gari ya ida wayewa,shi kadai ya dinga murmushi saboda yasan ya gama koya mata lesson.         Tun daga ranar ta shiga kulle qofarta,dariya ya dinga yi cikin zuciyarsa yana fadin "Ta dauka wani damuwa akayi da abinta,bata san ko giyar wake na sha bazan sake rabarta ba" kewar sumayyansa ce kawai take damunsa sam fa'izan bata a cikin lissafinsa.         Har ta qarasa cinye kwanakinta bata sake yarda ya kwana dakinta ba,haka nan sumayya ma qin yarda take ganin cewa ba kwanakinta bane,bugu da qari kuma maman naana na tsumata,so take ta d'ai d'aita tunanin mukhtar din a duk lokacin da ya dawo hannunta.        Randa zai dawo dakinta tun safe take jin nishadi,ta shiga dakinsa ta masa gyaran tsaf lungu da sak'o ta k'alk'ale ko ina,sai data kammala duk wani abu da ya dace sannan ta zauna tana jiran zuwan yammaci.          Tana kan kujerar falon ta kwance bayan sallar azahar tana hutawa taji sallama qofar gida,saukowa tayi ta sanya hijabinta don ganin waye,don ta sani cewa ko digewa mai yin sallamar zaiyi ba amsawa ko saurarensa fa'iza zata yi ba.         Abdur rahman ne d'a ga qanin mahaifin mukhtar,gefansa qanwarsa ce bahijja wadda zatayi shekaru sha biyar,fuskarta qunshe da fara'a tayi masa iso kan ya shigo ta juya yabi bayanta,dai dai lokacin da fa'iza ke shimfida tabarmarta a tsakar gida da alamu zama zata yi,abinda bata taba ganin fa'izar tayi ba tsawon kwanaki takwas da zuwanta gidan,da kallo ta bisu suna gab da shigewa dakin sumayyan ta rabka salati "Meye haka zaki kama ki shigo mana da gardi cikin gida?" Waiwayowa sukayi dukkaninsu suna dubanta "Gyara maganarki qani yake ga mukhtar,muje bahijja" ta fada tana dage musu labulen suka shige.          Ruwa ta gabatar musu da lemo wanda ta tanada cikin cooler dinta saboda mukhtar,kasancewar ya musu yawa yasa suma suka samu rabonsu "Mutanen misra,kaga ko yadda ka koma abdur rahman,yaushe ka dawo ne?" Sumayya ta tambaya tana murmushi,karatu ya tafiyi qasar misra saboda schoolership da ya samu daga gwamnatin tarayya,kasancewarsa haziqin dalibi cikin daliban dake jahar wanda ke karantar fannin da ya shafi addinin musulunci,shekararsa biyar da tafiya sai yau ya dawo,a lokacin da ya tafi din shekararta daya da aure da mukhtar,da gidansu jikin gidan mukhtar din yake kafin su tashi,wani lokaci idan mukhtar din nason fita kuma baiso ta fita abdur rahman din yake kira ya tayata zama,hakanne yasa suka saba har ya zama kamar wani abokin wasanta,a lokacin duka duka shekararsa sha bakwai shima.        Ruwan da yake sha ya ajjiye yana fadin "Kwana na uku kenan,ashe yaya mukhtar bai gaya miki ba kenan?"kai take girgizawa " bai gayamin ba kam ina ga ya sha'afa" "Ya manta kam,irin wannan mace da ya ajjiye haka a gidansa babu kan gado" cewar bahijja don ita ta qulu da abinda ta musun,murmushi sumayyan kawai tayi,abdur rahman yace "Itace matar da aka ce ya kuma aure?" Kai sumayya ta gyada masa sai yace "Masha Allah,Allah to ya baku zaman lafiya,lokacin ina misra ai munyi waya da alhaji yake gayamin don alokacin anata rikici ya mukhtar ya kai qarar umma yahanasun" kai kawai ta kuma jinjinawa cikin mamaki din ita bata ma san ya kai qarar ba,hira suka sha sosai,suka tuttuna baya sai wajen qarfe uku suka yi mata sallama suka tafi bayan abdur rahman ya bata kyautar abaya har guda biyu masu kyau ta rakosu har soro tana musu godiya tare da bawa bahijja dari biyar tace ta hau mota.          Ko da ta dawo fa'izan na zaune har yanzu a tsakar gidan,duka hirar da sukayi da alama na cikin kunnenta,alwala ta daura tayi sallar la'asar sannan ta shiga kitchen ta soma hidimar dora sanwar dare.            Ta shiga ta fita ta shiga ta fita tayi hakan ya kusa sau biyar,ganin haka ya sanya sumayya tayi zamanta a kitchen din taqi komawa daki saboda gujewa sake afkuwar abinda ya faru ran nan,sai data gama komai ta kwashe nashi zuwa dakinta sannan ta bar kitchen din.           Sam bata nunawa fa'izan wanka zata shiga ba saboda ta gama gane ta tsaf,bata tashi shigewa bayab gidan ta banke qofa sai taga tana shirye shiryen shiga wanka,sai data fito taji fa'izan nata jan qwafa da tsaki,tayi dariya cikin ranta ta shige dakinta ta hau shiryawa.          Kan idanunta ta tarbi mukhtar wanda sai data gwammace tayi komawarta daki,don kuwa yana gama ajjiye babur dinsa ya sungumi abarsa kamar yadda suka saba a da can baya kafin qara aurensa ya dinga juyi da ita yana fadin "Masha Allah my sumy,kyau kenan" duk da kunya ta dan kamata sai ta basar,ta gaban fa'izan ya wuce da ita,bai direta ko ina ba sai kan gado ya bita ya turmushe yana yamutsata tare da cakulkuli.          Duk yadda taso qunshe dariyarta ko don fa'iza amma ina abun ya faskara,haka ya sanyata ta dinga qyaqyatawa tana roqonsa ya bari,da qyar ta samu ta tsaida shi tana goge qwallar da ta hada,kunnanta ya kai bakinsa ya rada mata wata magana da ta sanyata jin kunya har ta rufe fuskarta da tafin hannunta.         Ga mamakinsu sai ga fa'izan tazo cin abincin daren,duk da sumayyan bata so hakan ba amma ta basar saboda kada taga kamar ta wulaqanta ta,shi kuwa yazo iua wuya domin har wata shigar ya sanya sumayyan ta sake masa cikin qananun kaya.             Suna kammala ci ta ja gefe ta sake sabon zama,da ido mukhtar ya bita sannan ya dauke kansa yaci gaba da abinda yake,ba qaramin tsanar falon tayi ba saboda yadda ya kere nata amma ta gwammace tayi ta zama ciki ko banza ta musguna musu ta hanasu sakewa.         Gefansa sumayyan ta dawo ta zauna tana kallon yadda yake shigar da wasu bayanai cikin sabuwar laptop da ya siyo,tana da sha'awarta sosai hakan ya sanya ya saki aikin da yake yana koya mata.         Sosai ta qulu amma hakan baisa ta bar dakin ba,har suka kammala ya miqe ya fita,cikin 'yan mintina ya dawo yana shigowa falon ya sunkuceta kamar dazu,har ya kai bakin qofar dakin gadon ya waiwayo ya dubeta "Ammm,idan kin gama abinda kike yi ki rufe mana qofar,sai da safe" ya fada yana shigewa,da gayya ya dinga takalo sumayyan har sai da ya fuskanci ta fice musu daga falon ta hanyar dukan kujera tare da banko qofar sannan ya saki murmushin mugunta yana saukowa daga gadon don ya rufe dakin.         Riqo hannunsa sumayya tayi tana masa kallo qasa qasa "Kai ko.....ba'a haka ya mukhtar fa,nasan da gayya kake komai" murnushi ya saki har yana fidda sauti sannan yace "Koma me nayi ita ta jama kanta,ta yaya haka kurum zaka dage sai ka cusa kanka inda baka da muhalli?,sai kayi zaman aure a inda ba'a da muradinka?" Ya fada yana sauka daga gadon tare da cewa "Jirani nazo sai muyi hirar sosai" ya fadi yana kashe mata ido daya,dariya ta saka. **********************       Wani irin zama ne yake wakana a tsakaninsu,cikin abinda bai wuce sati uku ba gaba daya fa'iza babu layin da bata karade ba neman qawa,kasancewar duka maqotan nasu mutanan sumayya ne,hakan ba qaramin qona mata rai yayi ba,bilhaqqi bata qaunar sumayya ko wani abu da ya danganceta,hatta da yaran dake shigowa gun sumayyan fa'iza qorafi take a kansu,idan taso tana iya korarsu,wani lokacin idan kan idon sumayyan ne ta hanasu tafiya,tsoronta yaran keji hakan ya sanya wasu daga ciki suka janye shigowa,mutum ce ita ta jama'a hakan ya sanya idan fa'izan nason yawonta saidai tayi uwar tafiga zuwa can bayan layinsu.          Tunda tazo gidan bata taba daukar tsintsiya da sunan shara ba baya ga ta dakinta,koda ran girkinta ne da ta kammala zata bar wajen yadda yake tayi gaba abinta,ko kadan sumayya bata lamunci qazanta ba ita zata killace komai ta gyara,ko banza tasan tana da lada.           Ko kadan mukhtar baya daga mata qafa wannan shi ya rage kaso casa'in cikin dari na rashin mutuncinta,tun da can irin 'yammatan nan ne da basuqi su fito da daurin qirji su dambatu da namiji ba,hakan ne ya bawa yaya yahanasu sha'awa a gajeran tunani irin nata,tana ganin cewa ita daya ce zata iya zama cikin gidan muntari ta take kowa ta kuma kawo musu abinda suke so,duk da cewa fa'izar ta taba shege tuna gida aka zubar amma hakan ba aibu bane a gun yahanasu,tana ganin ma wata dama ce dake nuna zata iya haifawa muntarin d'iyoyin da take tsammatar zasu iya alfahari da su,tarbiyya cancanta kunya asali da cikakkiyar nasaba basu zame mata mizanin ma'auni ba a gareta wajen hada qanin nata da ita.         Ko daya sumayya bata taba shaidawa muntarin fitar barbadar da fa'izan keyi ba,ta azawa ranta cewa idan kere na yawo zabo na yawo dole a hade,abu daya ne da ta tsaya a kansa shine,bata yadda fa'izan ta shiga haqqinta kamar yadda ita bata shiga nata haqqin har ma da hurumi da shirginta baki daya,sai yanzu take sake ganin alfanun shawarar anty dije gareta,tabbas gaskiya ta gaya mata,kuma gata ta mata,ba dan hakan ba da zuwa yanzu Allah ne kadai yasan yadda fa'izan zata maidata.             Duk yadda ya dauki lamarin shigowa gidan muntarin da sauqi ya fice haka,sai ta tadda soyayyar da muntarin kewa sumayyab bairin soyayyar nan bace da tuggu ko makirci ke nasarar wargazata ba,soyayya ce mai azabar danqo da yauqi,amma ta daukarma kanta alqawarin sai ta wargaza zaman lafiyar sumayyar ko ta halin yaya,kafin ta waiwaya ta takawa su yaya yahanasu birki wadanda zuwa yanzu suka soma yi mata lissafin zuwa yaushe zata dauki ciki,bata son takura ko sanya ido cikin lamuranta,basu san wace ainihin fa'izan ba har zuwa yau *A WANI DARE* *_Masu karatu ku biyoni,yanzu aka fara littafin._* *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍✍✍✍ ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) ________________________ *bismillahir rahmanir rahim* *inna ma'al usr yusrah,fa'inna ma'al usr yusrah* _______________________ 1⃣1⃣ *A WANI DARE*      Tun magariba ta shige dakinta kasancewar ba ranar girkinta bane,tun wajejan yammaci take jin ciwon kai da fargaba kadan kadan,hakanne ya sanya tun tana saman abun sallarta bayan ta kammala sallar isha'i bacci yayi awon gaba da ita,ko mukhtar da yazo mata sai da safe haka ya sameta,daukarta yayi cak ya maidata saman gado sannan ya ja mata qofar ya fice.       Kamar cikin mafarki taji ana kiran sunanta,cikin wata iriyar murya ce wadda sam bata ta dadin amo,a hankali ta dinga bude idanunta cikin duhun da ya gauraye dakin nata,tabbas sunanta ake kira cikin wata murya mai kama da amon sautin kukan kare.       Idanunta ta ware sosai saboda wata siffa data dinga hangowa ta tokare bangon dakinta daga inda take fuskanta,wata mummunar faduwar gaba ce ta ziyarce take gumi ya rufeta baki daya,jikinta ya hau rawa "Bismillahil lazi la yadurru ma'as mihi shai'un fil'ardi wala fissama'i wa huwas sami'ul alim" haka ta dinga maimatawa,tun tana yi cikin zuciyarta har ya fito fili,maimakon kiran sunan nata da ake a hankali sai aka koma da sauri sauri,sannu a hankali siffar halittar da take gani jikin bangon ta bace bat.          Cikin wani irin hanzari da kuzari ta diro daga saman gadon nata hannunta dauke sa wayarta,falo tayo tana ci gaba da ambaton sunan Allah,ta kunna qwan dakin tana mai qarewa falon nata kallo,babu abinda ta gani,cikin sanyin jiki ta zauna kan daya daga cikin kujerunta dafe da kanta.            Tsawon mintina ashirin ta dauka a haka sannan ta isa bakin t.v stand dinta,ta dauki ruwan leda guda daya da ya rage wanda tash dazu,dankwalinta ta cira ta ninka ta shimfida ta daura alwala a kai sannan ta fuskanci gabas.           Sallah tayi raka'a hudu sannab daga bisani ta zauna,cikin surorin data haddace ta dinga karantawa daya bayan daya,har zuwa sallar asuba bata samu ta runtsa ba,a nan zaune mukhtar da ya shigo tayar da ita sallah ya sameta,yaso ya danyi mamaki amma sanin cewa wani lokaci takan tashi da wuri ya sanya boye mamakin nasa ya fita ya tafi masallaci.            Sai kusan biyar da rabi ta koma saman kujerarta ta kwanta a nan bacci ya sureta.           Sallamar mukhtar ce ta tasheta,ta miqe tana mutstsike idanunta,a shirye ya shigo da alama kasuwa zaya fita "Lafiya kuwa kike sumayya,wani irin bacci yau kike haka sam ban ji motsinki ba?" Murmushi tayi tana gaida shi ba tare data amsa masa tambayarsa ba "Ni zan fita babu wata matsala ko?" Ya fafa kamar yadda ya saba fadi duk sanda zai fita kasuwa,kai ta girgiza "Babu komai,a dawo lafiya Allah ya bada sa'a" "Amin" ya fada yana kashe mata idanunsa daya tare da cewa "Yau ba rakiya my sumy?" Kai ta kada "Kaima ka sani ba girki na bane,ka kuma san halin fa'iza sarai,ranar girkinta bata son kowa ya rabeka ko?" Kai ya kada "Ba ruwa na da ita,tunda kafin na san ta ke na sani ko,amma tunda kince haka shikenan,sai na dawo" ya fada yana daga mata hannu kana ya fice.             Sai da ya fita da wajen mintina biyar sannan ta miqe,daki ta nufa da nufin shiga,gab da zata shiga din abinda ya faru jiya ya dawo mata tar a kwanyarta,tsayawa tayi jim sannan ta karanto addu'o'i  ta shiga.           Tsayawa tayi tana bin kowanne lungu da saqo da kallo bata ga komai ba saboda haka ta dauki abinda zata dauka ta fito.         Ga mamakinta tsakar gida ta taras da fa'iza zaune saitin window din dakinta zaune,kallon juna sukayi sumayya ta dauke kanta ta nufi bandaki don yin wanka,yayin da fa'izan ta bita da kallo,har ta kammala wankan ta koma daki ta shirya ta fito ta shiga kitchen don samawa kanta abinda zata ci fa'izan na zaune,dim yawanci idan ranar girkinta ne bata baiwa sumayya abin kari,to da yake ita din ma ba gwanar abinci bace hakan baya dada ta da qasa saita hada duk abinda ya samu taci shikenan an wuce gurin.            Yauwa kamar jiya bacci ya dauketa da wuri,kamar jiyan dai cikin bacci taji ana kiran nata,tarwai wannan karon bude idanunta nata cikin gigita,yau kam siffar macizai take gani tsaye ya mamaye bangon "A'uzu bi kalimatillahit taammati min sharri ma khalaq" ta dinga maimaitawa da qarfinta har bata san tana daga murya ba ko kuma ta manta cewa dare ne,bat abun ya bace sama ko qasa,a bakin qofar fita daga dakin sukaci karo,mukhtar ne yana tsaka da bacci ya dinga jiyo muryarta,jikinsa ta fada gabanta na tsananin duka jikinta na rawa,janyeta yayi zuwa falon suka zauna gefan kujerar yana tofa mata addu'a.           Sai da ta samu nutsuwa sannan ya dubeta ba tare da ya tambayeta me ya faru ba "Muje dakina ki kwanta a can" kai ta kada tana zare jikinta daga nashi "Kaje kawai babu komai zan iya kwanciya a nan,mafarki kawai nayi kuma yanzun nayi addu'a" idanu ya zuba mata sai ta kada kanta tana son gamsar da shi kan abinda ta fada din,kan doke saboda yadda ta kafe ya sanya shi barinta tare da sake mata addu'a sannan ya fita.            Qarfe tara na safw tuni tayi wankanta tana zaune a falon cikin rashin kuzari da tunani barkatai,a haka mukhtar din ya taddata,bayan sun gaisa ya samu gefanta ya zauna "Sumayya,meke damunki,na tabbata akwai abinda ke damunki,yanayinki jiya ya tabbatar min da haka,kada kuma ki soma cemin babu komai" qasa tayi da kanta don kada ya ga tsoron dake cikin idonta,sai da ta saisaita kanta sannan ta dago "Ya mukhtar,ina zaton akwai maciji cikin dakin nan" "Maciji?" Ya tambaya cikin mamaki,kai ta gyada masa,sai yayi shiru na wasu daqiqu kana daga bisani ya ajjiye jakar dake hannunsa yana mai miqewa "Ina zuwa" ya fada yana ficewa.           Minti kusan arba'in da biyar sai gashi ya dawo da wani matashin saurayi,wanda aikinsa shine fidda maciji kowanne iri,dakinsa ya bude mata yace ta shiga ciki ta zauna tare da kulle dakin,duk abin nan da ake fa'iza na cikin dakinta tamkar bata cikin gidan,shi da matashin suka shiga cikin dakin nata.               Duk wani salo da dabara irin tasa da ya gada ta fiddo da maciji ko wani mugun qwaro daga bigirensa babu wanda bai gwada ba,saidai ko kusa ko alama babu wani abu da yayi ka da maciji cikin uwar daka da rumfar tata,hayaqi yayi kusan kala uku amma shuru babu maciji,hakan shi ya tabbatar masa babu wani maciji cikin gidan ma baki daya ba dakin ba,yace amma ta sake kula sosai idan ta sake ganin wulgawar wani abu nan da kwanaki uku ta sanar masa zaya dawo,mukhtar ya sallameshi ya tafi.          Shi ya taimaka mata suka maida suka kintsa dakin,suka maida komai muhallinsa,bai samu fita kasuwa ba sai azahar ya fice,ita kuma ta nufi bakin fanfo ta tara ruwa zata yi alwalar sallar azahar din.            Sai lokacin fa'iza ta fito,wani kallo ta yiwa sumayyan kana ta sheqe da dariya "An tara haram an gyara daki dama ta yaya za'aji dadin zama a ciki?,kayan haram ne fa?.......hhhhhh......hmmm kadan ma kenan" ta fada tana jan wani shegen tsaki tare da juyawa ta koma dakinta.            Cikin mamaki take binta da kallo tare da neman tsari cikim zuciyarta,matar da duk artabun da ake cikin gidan tun safe bata fito ba sai yanzu,watsar da tunanin tayi,me yasa dakinta ya tsone mata ido,koda yaushe bata da magana sai nashi,da bata ce Allah ya sawwaqe ba ta ja bakinta tayi shiru mana,itadai tunda ta riga da tasan cewa tayi addu'a koma meye zaizo ko da QADDARARTA ne sai ya sameta din zaya zo mata da sauqi.         Tana kammala sallarta kitchen ta wuce ta soma hidimar dora girki saboda yau girkinta ne ita zata karbi mukhtar din,ita kuwa bata wasa da ranakun girkinta,tana kitcehen taga ficewar fa'iza daga gidan. _kuyi haquri da wannan ina cikin uzururruka_ *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍✍✍✍ ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) ________________________ *bismillahir rahmanir rahim* *inna ma'al usr yusrah,fa'inna ma'al usr yusrah* _______________________ 1⃣1⃣ *A WANI DARE*      Tun magariba ta shige dakinta kasancewar ba ranar girkinta bane,tun wajejan yammaci take jin ciwon kai da fargaba kadan kadan,hakanne ya sanya tun tana saman abun sallarta bayan ta kammala sallar isha'i bacci yayi awon gaba da ita,ko mukhtar da yazo mata sai da safe haka ya sameta,daukarta yayi cak ya maidata saman gado sannan ya ja mata qofar ya fice.       Kamar cikin mafarki taji ana kiran sunanta,cikin wata iriyar murya ce wadda sam bata ta dadin amo,a hankali ta dinga bude idanunta cikin duhun da ya gauraye dakin nata,tabbas sunanta ake kira cikin wata murya mai kama da amon sautin kukan kare.       Idanunta ta ware sosai saboda wata siffa data dinga hangowa ta tokare bangon dakinta daga inda take fuskanta,wata mummunar faduwar gaba ce ta ziyarce take gumi ya rufeta baki daya,jikinta ya hau rawa "Bismillahil lazi la yadurru ma'as mihi shai'un fil'ardi wala fissama'i wa huwas sami'ul alim" haka ta dinga maimatawa,tun tana yi cikin zuciyarta har ya fito fili,maimakon kiran sunan nata da ake a hankali sai aka koma da sauri sauri,sannu a hankali siffar halittar da take gani jikin bangon ta bace bat.          Cikin wani irin hanzari da kuzari ta diro daga saman gadon nata hannunta dauke sa wayarta,falo tayo tana ci gaba da ambaton sunan Allah,ta kunna qwan dakin tana mai qarewa falon nata kallo,babu abinda ta gani,cikin sanyin jiki ta zauna kan daya daga cikin kujerunta dafe da kanta.            Tsawon mintina ashirin ta dauka a haka sannan ta isa bakin t.v stand dinta,ta dauki ruwan leda guda daya da ya rage wanda tash dazu,dankwalinta ta cira ta ninka ta shimfida ta daura alwala a kai sannan ta fuskanci gabas.           Sallah tayi raka'a hudu sannab daga bisani ta zauna,cikin surorin data haddace ta dinga karantawa daya bayan daya,har zuwa sallar asuba bata samu ta runtsa ba,a nan zaune mukhtar da ya shigo tayar da ita sallah ya sameta,yaso ya danyi mamaki amma sanin cewa wani lokaci takan tashi da wuri ya sanya boye mamakin nasa ya fita ya tafi masallaci.            Sai kusan biyar da rabi ta koma saman kujerarta ta kwanta a nan bacci ya sureta.           Sallamar mukhtar ce ta tasheta,ta miqe tana mutstsike idanunta,a shirye ya shigo da alama kasuwa zaya fita "Lafiya kuwa kike sumayya,wani irin bacci yau kike haka sam ban ji motsinki ba?" Murmushi tayi tana gaida shi ba tare data amsa masa tambayarsa ba "Ni zan fita babu wata matsala ko?" Ya fafa kamar yadda ya saba fadi duk sanda zai fita kasuwa,kai ta girgiza "Babu komai,a dawo lafiya Allah ya bada sa'a" "Amin" ya fada yana kashe mata idanunsa daya tare da cewa "Yau ba rakiya my sumy?" Kai ta kada "Kaima ka sani ba girki na bane,ka kuma san halin fa'iza sarai,ranar girkinta bata son kowa ya rabeka ko?" Kai ya kada "Ba ruwa na da ita,tunda kafin na san ta ke na sani ko,amma tunda kince haka shikenan,sai na dawo" ya fada yana daga mata hannu kana ya fice.             Sai da ya fita da wajen mintina biyar sannan ta miqe,daki ta nufa da nufin shiga,gab da zata shiga din abinda ya faru jiya ya dawo mata tar a kwanyarta,tsayawa tayi jim sannan ta karanto addu'o'i  ta shiga.           Tsayawa tayi tana bin kowanne lungu da saqo da kallo bata ga komai ba saboda haka ta dauki abinda zata dauka ta fito.         Ga mamakinta tsakar gida ta taras da fa'iza zaune saitin window din dakinta zaune,kallon juna sukayi sumayya ta dauke kanta ta nufi bandaki don yin wanka,yayin da fa'izan ta bita da kallo,har ta kammala wankan ta koma daki ta shirya ta fito ta shiga kitchen don samawa kanta abinda zata ci fa'izan na zaune,dim yawanci idan ranar girkinta ne bata baiwa sumayya abin kari,to da yake ita din ma ba gwanar abinci bace hakan baya dada ta da qasa saita hada duk abinda ya samu taci shikenan an wuce gurin.            Yauwa kamar jiya bacci ya dauketa da wuri,kamar jiyan dai cikin bacci taji ana kiran nata,tarwai wannan karon bude idanunta nata cikin gigita,yau kam siffar macizai take gani tsaye ya mamaye bangon "A'uzu bi kalimatillahit taammati min sharri ma khalaq" ta dinga maimaitawa da qarfinta har bata san tana daga murya ba ko kuma ta manta cewa dare ne,bat abun ya bace sama ko qasa,a bakin qofar fita daga dakin sukaci karo,mukhtar ne yana tsaka da bacci ya dinga jiyo muryarta,jikinsa ta fada gabanta na tsananin duka jikinta na rawa,janyeta yayi zuwa falon suka zauna gefan kujerar yana tofa mata addu'a.           Sai da ta samu nutsuwa sannan ya dubeta ba tare da ya tambayeta me ya faru ba "Muje dakina ki kwanta a can" kai ta kada tana zare jikinta daga nashi "Kaje kawai babu komai zan iya kwanciya a nan,mafarki kawai nayi kuma yanzun nayi addu'a" idanu ya zuba mata sai ta kada kanta tana son gamsar da shi kan abinda ta fada din,kan doke saboda yadda ta kafe ya sanya shi barinta tare da sake mata addu'a sannan ya fita.            Qarfe tara na safw tuni tayi wankanta tana zaune a falon cikin rashin kuzari da tunani barkatai,a haka mukhtar din ya taddata,bayan sun gaisa ya samu gefanta ya zauna "Sumayya,meke damunki,na tabbata akwai abinda ke damunki,yanayinki jiya ya tabbatar min da haka,kada kuma ki soma cemin babu komai" qasa tayi da kanta don kada ya ga tsoron dake cikin idonta,sai da ta saisaita kanta sannan ta dago "Ya mukhtar,ina zaton akwai maciji cikin dakin nan" "Maciji?" Ya tambaya cikin mamaki,kai ta gyada masa,sai yayi shiru na wasu daqiqu kana daga bisani ya ajjiye jakar dake hannunsa yana mai miqewa "Ina zuwa" ya fada yana ficewa.           Minti kusan arba'in da biyar sai gashi ya dawo da wani matashin saurayi,wanda aikinsa shine fidda maciji kowanne iri,dakinsa ya bude mata yace ta shiga ciki ta zauna tare da kulle dakin,duk abin nan da ake fa'iza na cikin dakinta tamkar bata cikin gidan,shi da matashin suka shiga cikin dakin nata.               Duk wani salo da dabara irin tasa da ya gada ta fiddo da maciji ko wani mugun qwaro daga bigirensa babu wanda bai gwada ba,saidai ko kusa ko alama babu wani abu da yayi ka da maciji cikin uwar daka da rumfar tata,hayaqi yayi kusan kala uku amma shuru babu maciji,hakan shi ya tabbatar masa babu wani maciji cikin gidan ma baki daya ba dakin ba,yace amma ta sake kula sosai idan ta sake ganin wulgawar wani abu nan da kwanaki uku ta sanar masa zaya dawo,mukhtar ya sallameshi ya tafi.          Shi ya taimaka mata suka maida suka kintsa dakin,suka maida komai muhallinsa,bai samu fita kasuwa ba sai azahar ya fice,ita kuma ta nufi bakin fanfo ta tara ruwa zata yi alwalar sallar azahar din.            Sai lokacin fa'iza ta fito,wani kallo ta yiwa sumayyan kana ta sheqe da dariya "An tara haram an gyara daki dama ta yaya za'aji dadin zama a ciki?,kayan haram ne fa?.......hhhhhh......hmmm kadan ma kenan" ta fada tana jan wani shegen tsaki tare da juyawa ta koma dakinta.            Cikin mamaki take binta da kallo tare da neman tsari cikim zuciyarta,matar da duk artabun da ake cikin gidan tun safe bata fito ba sai yanzu,watsar da tunanin tayi,me yasa dakinta ya tsone mata ido,koda yaushe bata da magana sai nashi,da bata ce Allah ya sawwaqe ba ta ja bakinta tayi shiru mana,itadai tunda ta riga da tasan cewa tayi addu'a koma meye zaizo ko da QADDARARTA ne sai ya sameta din zaya zo mata da sauqi.         Tana kammala sallarta kitchen ta wuce ta soma hidimar dora girki saboda yau girkinta ne ita zata karbi mukhtar din,ita kuwa bata wasa da ranakun girkinta,tana kitcehen taga ficewar fa'iza daga gidan. _kuyi haquri da wannan ina cikin uzururruka_ *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍✍✍✍ ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 1⃣2⃣ ________________________ *Bismillahir rahmanir rahim* *qul innal amra kullahu lillah* _________________________           Sallamar fadima ce ta ratsa dodon kunnenta,tana daga kitchen din ta amsa mata,kai tsaye ta nufo kitchen din ta leqo,murmushi sumayya tayi qoqarin sannan tace "Au fadima ce?" Yatsina fuska tayi ta karkace baki tace "Eh.....nice,ana ta kitchen ne anata fama?" Cikin jin dadin jin fitowar kyakkyawan furuci yau daga bakin wanda ya jibanci mukhtar zuwa gareta tace "Wallahi kuwa,kin ganmu muna ta fama da sanwa" bisa ga sabanin tunaninta sai taji tace "A'aha,anan dama aka fi kauri ai,aci a cika mana gida da kashi,sockaway nan da nan ta tumbatsa" sosai maganar ta bata ranta,cin fuskar tana ganin kullum dada gaba yake,me yayi zafi ne haka?,ba aure bane kuma ta bar dan uwansu yayi,tunda a yanzu suna da wadda suke tunanin zata cika muradinsu ai yaci ace sun sakar mata mara tayu fitsari yadda ya kamata,sai ta sake yin wani murmushin idanunta cikin na fatiman "Ayyah,ai kayi auren ma kayi kashi cikin gidan mijinka ma rahama ce,wasu har yau an rasa wanda zai daukesu ya kaisu gidansa ko kashin ne ma suyi" sarai ta fahimci magana ta yaba mata,a fusace ta qarasa shigowa kitchen din tana tunkarar sumayya kamar zata kai mata shaqa "Da uban wa kike?" "Da wanda ya tsargu" ta fada tana bude tukunyar miyarta tana juyawa,wuyanta ta ruqo ta baya,a nutse ta juyo ta sanya hannunta ta zare shi daga wuyan nata tana nunata da yatsa "Kada ki kuskura fati" sumayyan ta fada kana ta ja tsaki ta juya taci gaba da abinda takeyi.         Baki ta saki galala tana dubanta,iya tsawon zamanta da su ko kallon banza babu wanda sumayyar ta taba yiwa duk irin budurin da sukeyi tsakiyar kanta,kafin ta kai ga cewa komai fa'iza ta sanyo kai cikin kitchen din tana cewa "To malama,da kika zo nan kika tsaya kina kalen magana nan aka aikoki?" Ta bude baki tayi da niyyar yin magana fa'izan ta tarbeta "Kinga miqon saqona sai ki dawo kuyita yinta 'yar ayi jikar na saba" waiwayowa fatiman tayi cikin mamakin kalaman fa'izar "Wace 'yar ayi jikar na saba din?,babata da ta haifeni ta haifi mijinki muntari ko innar babarmu?" "Kinga duk wanda kika zaba cikinsu,zaki bani saqon ko kuwa?" Ba yadda ta iya saboda yaya yaha ta jadda da mata saqon,amma ta sake yarda fa'iza ba mutunci gareta ba,tsaf zata iya zagesu su dukan,haka tayi haushin kaza juye kan dami ta zabgawa sumayya harara tare da jan doguwar qwafa "Yar malamai ba'a haifa ba an shanye mana dan uwa" ta fadi tana shirin ficewa tabi bayan fa'iza,dariya tayi "Au ashe na isa ma" tana jin maganar kuma ta bata haushi tare da mamakin budewar bakin sumayya amma haka ta haqura tabi bayan fa'izar.           Qeme me fa'izan ta hanata kudin motar komawar bayan ta bata saqon,juyin duniya tace bata da ai dan uwansu bai bada ba,haka nan ba don taso ba ta shiga wajen sumayyan,a lokacin ta gama aikinta tana kan kujera tana gyaran qumbarta(farce) "Kudin mota nazo ki bani zan koma gida"a nutse ta daga kai ta dubeta " da na aikeki ina?"fuska ta hade don kada ta rasa "Ai na sancewa akwai kudi gurinki" "Wadanda kika bani ajiya kenan dazu" sosai take shan mamakin yadda sumayyan ta zama,amma babu komai komai ya kusa zuwa qarshe saboda haka ta dan sassauto "Ba halinki bane sumayya ba fa,ko dari ce ki bani zata kaini gida" shiru ta danyi sannan ta ajjiye rezar hannunta ta shiga uwar dakanta ta dauko dari biyu ta miqa mata,babu godi bare na gode ta amsa ta juya ta fice,da kallo ta bita sannan ta girgiza kai,ashe guri suka samu suketa shanya yadda suka so?,wato sam wani mutumin baisan alkunya ba kenan,sai ka sauya launi kuke iya zama dai dai da shi?,idan banda sun sayawa kai raini ina ita ina fadiman ina ita?wadda a qalla ta bata shekara kusan shekara hudu ko biyar "Allah ya kyauta ya rufa asiri" ta fada a fili tana ci gaba da abinda take.           Lafiya lau yau tayi barcinta har ta kammala ranakun girkinta ta miqa mukhtar din ga fa'iza.          Kasancewar da safe suje miqa girki ga wadda zata karba ya sanya tana kammala komai ta wanke kanta ta wuce gidan kitso nam qarshen layinsu,sai data fara shiga gidan maman nana ta dauki saboda tana son zuwa gida sannan suka wuce.            Zuwa sha daya na rana aka gama mata kitson ta wuce gidansu.           A kitchen ta tadda innarta ta dora sanwar rana,gidan babu kowa saboda qannen nata duk weekend na zuwa wata islamiya tun tara na safe sai biyar da rabi na yamma suke dawowa.          "Ina fatan lafiya kuke dai ko?" Innar ta tambayeta bayan sun gama gaisawa,murmushi ta saki ta kada kai "Lafiya qalau inna" "To madalla haka akeson ji,aci gaba dai da haquri,zaman aure ko kai kadai ne sai kayi haquri balle kuma da abokiyar zama,Allah yayi miki albarka"cikin jin dadin addu'arta tace " amin inna na gode"suka dan fada wata hirar kafin tace "Wai ni kam inna ina ya abbakar?,ko leqoni fa inna baya yi" ta fada cikin shagwabe fuska "Hmmm,yayanku ai yanzu bai ga ta zama ba,ya dauko aure" cikim zumudi da murna sumayya tace "Allah innarmu?,wace a ina take" "A'ah,sai ki jira shi yazo kuma wannan kyaji daga bakinsa" ta fada innar tana miqewa saboda kasancewar abubakar dan fari a gunta.           Tana nan har abubakar din ya dawo,nan suka sha hirarsu,sai kusan shida saura ya dauketa kan babur dinsa ya kaita har qofar gida,tayi tayi ya shigo yaqi haka ta haqura.           Muqullinta ta sanya ta bude dakin nata ta sanya kai zata shiga,wani dunqulallen abu ya tokareta,tashi daya taji wani azabbaben bacin rai ya kamata,tsanar dakin ta mamayeta,sai ta koma da baya ta janyo kujera 'yar tsuguno bakin qofar dakin ta zauna,duk da uban tarin gajiyar da ta debo amma sam bata sha'awar shiga dakin.            Har qarfe goma na dare tana tsakar gudan zaune,a nan tayi magariba tayi isha'i kasancewar mukhtar baya gari yayi tafiya legos sarin kaya.            Tsakar gidan yayi tsit sai ita daya,fa'iza ta gama kara kainarta ta qule daka tana kyautata zaton ma tayi bacci,gashi babu hasken wutar lantarki don nepa sunyi tsiyar,gidan taje ta rufe sannan ta dawo tsakar gidan,ta jima tsaye a bakin qofar tana nanata addu'a sannan taji salama na saujarwa ruhinta,ta kwashi jakarta ta shiga dakin gabanta na wani irin bugawa,kayanta kawai ta sauya ta haye gado a takure wani tsoro da batasan na meye ba fal ranta.             Cikin baccinta taji kamar ana tashinta,a firgice ta farka tana ambaton Allah,tamkar ana korota daga dakin haka ta dinga ji,a gaggauce ta fito izuwa tsakar gida jikinta na rawa,sulalewa tayi ta zauna dirshan jikin qofar dakin tana ci gaba da kiran sunan Allah a haka asuba ta risketa,a nan ta daura alwala tayi sallar asubar.           Qarfe shida da rabi na safiya taji wani irin qwarin gwiwa na shigarta,ta miqe cikin hanzari ta koma cikin dakin,tamkar ana tafasa zuciyarta da tsanar dakin ta nufi uwar dakanta ta dangana da sif dinta,akwatinta ta jawo tamkar ana umartarta ta shiga loda kayanta tsaf sannan ta sauya na jikinta ta rufe akwatin ta janyo shi waje,sakatar gidan ta zare kana ta fice kai tsaye ta nufi bakin titi.          Ta kusan a qalla awa guda tsaye bakin titin ba tare da ta samu abun hawa ba kasancewar safiya ce babu yawaitar sawaye,sai da ta fara qosawa sa tsaiwar har tana tunanin fara takawa da sawayenta wani mai adaidaita ya nufo inda take,da hanzari ta tsaidashi gudun kada ya wuce ta rasashi,ta gaya masa inda zai kaita shi kuma ya gaya mata abinda zata biya,ba tare da ta tsaya ciniki da shi ba ta hau tare da tura akwatinta ciki shima. *masu karatu muje zuwa,kada kuce komai kowanne dan adam da irin tasa QADDARAR* *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍✍✍✍ [9/25, 12:41 AM] ‪+234 908 222 8222‬: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 1⃣3⃣ ______________________ *wa iyyamsaskallahu bi durrin fala khashifa lahu illa huw,wa iy yuridka bi khairin fala raadda li fadhlih* __________________________            A qofar gidansu mai adidaita sahun ya ajjiyeta,ta biyashi sannan ta ja akwatinta zuwq ciki.          Ta jima a soron tsaye gabanta na faduwa,tana mtuqar shakkar iyayenta,saidai hakanan taji ana ingizata zuwa barin gidan,wani irin qunci take ji idan tana cikin gidan,numfashi ta ja sannan tayi shahada ta shige.            Qannanta na tsakar gida suna karyawa jikinsu sanye da unifoarm din islamiyya,innarta kuma na daga cikin rumfarsu, "Lah sannu da zuwa yaya sumayya" suka fada halima na karbar mata akwatinta tare da shiga da shi cikin rumfar tasu ita kuma tabi bayanta.            "Lafiya sumayya da safiyarnan?" Innar ta tambayeta cikin fuskar mamaki,gefan kujerar ta samu ta zauna sai kawai ta fashe da kuka ba tare da tace komai ba,baki innan ta sake tana kallonta kafin daga bisani ta yiwa halima nuni da hannu kan ta fita ta basu guri,daga qarshe itama da ta gaji da tambayarta sai ta miqe ta fito tsakar guda ta hau ayyukanta ta barta cikin dakin.            Wuni guda innan na tambayarta amma ta gaza cewa komai,to me zata ce mata ya korota daga gidan,ba matsala bace tsakaninta da mijinta ba ballanta na tace,ba wani abu sukayi ba,to meye dalilinta,sosai hankalin innan ya tashi ganin taqiyin maganar,gashi kuma malam din baya gida sun tafi musabaqa ta jaha da ake gudanarwa daga shi har yayan ta abubakar,amsa daya ta iya bata data tambayeta ina mukhtar din ta sanar masa yayi tafiya,sai kan innar ya sake daurewa,har dare tana zuba ido ko zata ga wani kan sumayyar amma shiru haka suka wayi gari.             Mamaki innar ta kuma tashi da shi na ganin washegari sumayyan ta sake sarai,walwalarta take kamar babu wani abu da ya shalleta,wannan damuwar da ta zo da ita jiya duka yau babu ita.            Tunda suka dauko hanya daren jiya yake Allah Allah ya iso gidan nashi don yayi tozali da sumayyar tasa,qarfe uku da minti biyar dan adaidaita sahu ya ajjiyeshu qofar gidan nasa ya sallameshi ya shige gidan bakinsa dauke da sallama fuskarsa qunshe da murmushi don yana da yaqinin samun tarba mai kyau kasancewar ya tafka sa'a cikin ranar girkinta zai dawo din.            Mamaki ne ya maye gurbin doki murmushi da fara'ar da yakeyi ganin yadda tsakar gidan yake a tarwatse babu cikakkiyar tsafta,sallama ya sakeyi karo na biyu saidai shiru babu amsa,a hankali idanunsa suka sauka kan dakin sumayya,take yaci karo da kwad'on da take kulle dakin duk sanda zata fita,mamakinsa ya sake ninkuwa,ko da can sumayya sanda take da qananun shekaru ainun bata taba fita ba tare da uzininsa ba koda kuwa maqota ne,ya maida kallonsa dakin fa'iza ana sakaye,ya qarasa ya tura ya leqa kansa ciki bata nan,ya tura bandakin ya leqa nan ma bata ciki,jikin bango ya koma ya jingina tare da ajjiye jakar bacco din hannunsa,ba fa'iza ce damuwarsa ba sumayya ce,lambarta ya lalubo ya kira saidai an sanar masa da cewa a kashe take,ya maida wayar cikin aljihunsa yana maida ajiyar zuciya tare da shiga tunani.           Maganar fa'iza ta katseshi wanda da alama da wasu dake daga waje take maganar,ya zubawa qofar soron idon har ta qaraso,da fari tayi turus,sai kuma ta qaraso tana dubansa "Au......ashe kai ne.......ashe yanzu zaka dawo.....na dauka sai anjima gashi ban tanada ma komai ba" "Ina sumayya take?" Ya tambaya ba tare da ya kula da surutun da take zuba masa ba,wani abu ya takore wuyanta,wato ta sumayya ma yake ko,zai gane kuransa ne wlh,baki ta tabe sannan tace "Ka bani ajiyarta ne?"idanunsa ya ware baki daya har sai da taji tsoro " ke bana ciki da iskanci,ni kike gayawa haka,zan tattaki ne wallahi naga uban da ya tsaya miki,banza sha sha sha,ina sumayya take nace miki"cikin gunguni tace "Oho,nidai da asussuba naga ta hada kayanta ta fice bansan inda taje ba".         Bai qara bi ta kanta ba ya shige dakinsa ya ajjiye kayan hannunsa,da sauri ya sake zaro wayarsa saboda tunawa da yayi waccan satin sumayyan ta saka maaa lambar wayar innar tata ta gaya masa ya abubakar ne ya siya mata waya.          Bugu biyu zainab ta daga tana fadin " ya mukhtar ga innar can bari a kai mata"da sauri ya katseta "A'ah zainab,ina yayarku" "Gata can a daki a kwance" "Tun yaushe tazo gidan" "Tun jiya" "Ok" ya fada sannan cikin sauri ya ajjiye wayat,kayan jikinsa ya cire sannan ya fito ya nufi tsakar gida,yana jin motsin fa'izan daga kitchen bai bi ta kanta ba ya tara ruwan wanka ya fada bandaki.            Sai da ya rama sallar azahar dake kansa sannan ya shirya cikin wani yadin kufta ruwan toka(ash),ya feshe jikinsa da turare,yayi kyau matuqa,take zatinsa da kwarjininsa suka fito,yana sanya takalminsa sau ciki irin na maza fa'iza ta shigo dakin hannunta dauke da plate data ciko da jallope din taliya wadda keta zuba qauri saboda uwar wutar da ta babbaka mata saboda saurin da take ta kawo masa yaci tun kafin yaje ya maido da sumayya gidan plan dinta ya rushe.        "A'ah,mutari ina zaka daga dawowarka,ga abinci na maka ai ko shi ka tsaya kaci" kallo daya yayi mata ita da taliyar tata yaci gaba da sanya takalmansa yana daga duqen ya jefeta da "Bani da buqata" gabanta ya fadi ganin asara qiri qiri na shirin riskarta,kwana uku tayi tana tattalin kayan tarkacen da ta dafa taliyar da shi sai gashi cikin mintinan da basu gaza biyar yana son janyo mata asara.         Matsowa tayi kusa da shi cikin marairaicewa da tausasa murya irin wadda bai taba riska daga gareta ba ta soma hilatarsa,da sauri ya ja baya tare da jan matsiyacin tsaki ganin tana gab da shafa masa maiqon abincin,maqullin babur dinsa ha zara ya fice ya barta tsaye a nan dafe da kai.             Tana kwance cikin falon yaro yayi sallama ya shigo "Wai mukhtar ke magana a qofar gida" inji yaron,zumbur ta miqe zaune saboda wata muvuwar faduwar gaba data tsinci kanta a ciki,da sauri ta qule uwar daka sanda taji muryar inna na sanya hijabinta tare da cewa yaron ya shigo.            Ta window ta dinga leqensa sanda yake tsugunne gaban innan kansa qasa yana gaidata,sosai ya mata kyau,mukhtar akwai bala'in kwarjini da kyawun siga,sonsa da qaunarsa ke dambarwa cikin zuciyarta,gefe guda kuma  wani mashahurin tsoro fargaba da qin son komawa cikin gidansa ke kai kawo cikin wani irin qarfi cikin qirjinta,sai ta koma gefan gado ta zauna jiki sanyaye tana fidda qwalla.           Tana jin shigowarsu cikin falon shi da innar,ta sa baki tayi kiranta,sai data kirata kusan sau hudu sannan ta samu ta fito,kanta a qasa tana digar qwalla,gefe ta samu ta takure kanta a qasa ta gaidashi,ya amsa yana dubanta,har yanzu mamakin da ya daureshi tun farko shi yaqi sakinsa,me ya samu sumayyar?,me yayi mata ta baro gidansa ba tare da saninsa ba?. "Ka ganta nan,nima hakanan na ganta da sassafe bansan me ya faru ba,kuma juyin duniya meke faruwa taqi cewa komai,to gaka nan dai gata" inna ta fada tana dubansu "Wlh nima inna dawowata ta ras bata nan,amma ki sake tambayarta inna ko wani abu nayi mata"waiwayawa tayi cikin daurewar fuska dake nuna ba'a son wargi tace " ke sumayya......dubeni da kyau banason rashin mutunci da iskancim banza,ki gaya mana me mijnki yayi miki?"cikin muryar kuka tace "Babu inna,babu abinda yayimin wallahi" cikin hargowa da bacin rai innar ta sake cewa "Babu abinda yayi miki don iskanci shine zaki debo qafa ki taho gida,to ki tashi tun muna shaida juna tun kafin mahaifinki ya dawo sawunki a likkafa ki tattara kayanki kibi mijinki" wani irin kuja ta fashe da shi tamkar ana cire ranta ba tare da ta iya cewa komai ba,juyin duniya inna tayi mata ta tashi ta bishi taqi,har duka ta kai mata amma a banza,ganin hakan ya sanya mukhtar tarar innar yace "Inna,ki barta,barta kawai,idan malam din ya dawo ko zuwa gobe ne sai na dawo" bacin rai tsantsa ne cikin ran innan haka mukhtar din ya fita.           Sake qara sautin kukan nata tayi can qasan zuciyarta na mata zafi,ta rasa dalilin da ya sanya ta yiwa mijin nata haka,can qarqashin zuciyarta itama son binsa take,son kebancewa take da shi,tana da buqatarsa,tana buqatar jin duminsa amma tsanar gidan ya taso ta danne komai.         Tun innan na jin haushinta da jin haushin kukan nata har abun ya fara bata tsoro,addu'a ta soma cikin zuciyarta tana fata ba abinda take tunani bane ya afkawa sumayyan.              Tunda ya koma gidan ya qulle kansa cikin dakinsa,fa'iza ta sake dawowa da niyyar bashi taliyar,nacin duniya yaqi bude qofar,da taga haka kuma ta lura bai dawo da sumayyan ba sai ta watsar da shi tayi komawarta daki tare da kwafar da taliyar cikin kwandon shara tunda burinta dai ya cika,dama ba wai damuwa tayi da yunwar cikinsa ba,aikinta dake cikin taliyar take yiwa kuma komai ya tafi dai dai.           Tun a daren da malam din ya dawo ta zayyane masa komai,shiru yayi cikin dogon nazari,innar tayi niyyar taso masa sumayyan ya dakatar da ita yace ta barta zuwa safiya sa hadu.            Qarfe bakwai da rabi na safe ta shigo dakin malam din sanye da hijabi,ga mamakinta sai ta tadda su tare da mukhtar,gabansu kayan kari ne wanda malam din ya gama karyawa kasancewar da wuri yake karyawa ya kuma takura mukhtar wanda shayi kadai ya iya sha.           "Sumayya,me ya hadaki da mai gidanki wanda har ya sanyaki fitowa daga gidanki ba tare da izinin mai gidanki ba?bayan ba haka muka baki tarbiyya ba" Shiru tayi qwalla na taruwa cikin idanunta ta daga kai ta dubi abba malam din,inna da zuciya ta hasalota tace "Tsabar rashin mutunci ne da sakarci kawai ba komai ba" da sauri malam din ya dakatar da inna ta hanyar daga mata hannu sannan ya sake duban sumayyan "Uhmmmm,ina jinki" ya fada yana zuba mata idanunsa,motsa bakinta ta shiga yi sai ya fahimci tamkar bata son yin magana ne saboda haka ya bata qwarin gwiwa "Kada ki ji tsoron komai kada ki kuma damu,ki gayamin ko ma mene,mu iyayenki ne baki da kamar mu,baki da wanda zaki gayawa damuwarki sama da mu kinji ko?"kai ta gyada sannan ta bude bakinta qwalla na ziraro mata " Abba.......bana son gidan,haushin gidan da d'akina nake ji,tsoron dakin ma nake ji,bana iya bacci,wani abu kullum sai ya fito ta bango yana kiran suna na......"shiru ne ya ratsa dakin,kowa da tunaninsa,tausayinta ke yawo cikin ransu.           Bayan dogon nazari da abba malam yayi sannan ya magantu "Kin tabbata kina addu'o'inki kuwa?" Shiru ta danyi sannan cikin karyewar murya tace "Eh inayi amma wani lokaci ina mantawa bana yi" kai ya jinjina "Shikenan babu komai,wani lokaci kuna sakaci da addu'a har shaidanu ke samun damar rabarku su cutar da ku,ba komai ki shirya kibi mai gidanki zan baki qarin wasu addu'o'in ki hada da na gunki,ki tabbata kin dage da yi babu fashi,insha Allah babu abinda zai sameki".            Ga mamakinsu sai ta fashe da kuka kamar wadda ake zarar ranta " Allah abba malam bazan iya komawa ba,tsoro nake ji abba,don Allah ku qyaleni"idanu suka zuba mata baki daya,bayan wani lokaci malam ya maida kansa ga mukhtar ya dafashi "Kayi haquri mukhtari,ka bar min sumayyah anan,bayan kwana uku kacal kazo ka dauketa,kayi haquri kuma kada ka damu,ba zata wuce kwana ukun ba" kansa a qasa cikim girmamawa yace "To malam,na gode" ya miqe ya fice suka bishi da kallo.      Inna ce ta soma cewa cikin laushin murya "Meye hikimar yin hakan din malam?" "Zaki gani habiba,ku shiga ciki ke da ita sai ki dawo ki dauko kin jakar fatar can ta cikim uwar dakina" "To" ta amsa sannan ta miqe ta kama hannun sumayya dake ci gaba da kuka suka koma ciki. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍✍✍✍ [9/25, 12:42 AM] ‪+234 908 222 8222‬: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 1⃣4⃣ ________________________ *A hasiban nasi ay yaquluu amanna wa hum la yuftanun?* _____________________ *Sadaukarwa ne ga* *MAMAN HANIF NOVELS GROUP*👌🏽       Qarfe goma na dare tana saman gadon innar tata,juyi kawai takeyi tare da tuhuma da kuma bincikar kanta kan abinda ta aikata,batasan dalili ba batasan me yasa ba amma ji ta dinga yi kamar ana ingizata barin gidan,wata qauna da kewar mukhtar din suka kamata,halima ce ta shigo dauke da wayar innarsu "Yaya sumayya,yaya mukhtar ne" ta fada tana miqa mata wayar,da sauri ta miqe ta amsa wayar sannan ta kara a kunnenta halima ta juya ta fita,kasa cewa komai tayi har sai da yace "Sumayyah!" Muryarsa a tausashe "Na'am" ta amsa muryarta na rawa "Sumayya......me yasa kike son ki gujemin bayan kinsan zuciyata ba zata juri haka ba?,sumayya ko cikin mafarki banson mu rabu bare a gaske,a zahiri kuma  idanu biyu" tuni ta fara tara qwalla a idanunta,zuciyarta na sake karyewa "Ya mukhtar ban sani ba,nima bansan dalili ba da ya sanya na tsani dakina ba,bansan dalili ba na tsani dakina ma baki daya ba,kayi haquri ya mukhtar........kaji?" Shiru yayi yana mamako,babu shakka gaskiya take gaya masa har cikin zuciyarta,ya riga da yasan sumayyan sosai,koma mene yana jin ya haqura ya bada kwana ukun kamar yadda malam yace yaci gaba da addu'a kamin zuwan kwanakin,ajiyar zuciya ya sauke sannan yace "Shikenan....babu komai kada ki damu kinji,muyi addu'a mu jira kwanakin ukun kamar yadda malam yace" "To" ta fada,sai ya kawar da zancan ya soko wani don son faranta mata rai da kawar da zancan "Yanzu me zan samu my sumy,nayi kewarki sosai,na dawo da kewar taki kuma tarar kin min yaji" ya qarashe cikin sigar shagwaba,dariya sosai ya bata har ta dinga jiyo sautinta ta cikin wayar wanda hakan ya masa dadi sosai,kewarsa taji ya kamata kamar ta bude idanu ta ganta gabanshi,nan ya janyeta da hira har sai da ya qarar da dukka kudin dake cikin wayarsa sannan ya haqura.       Cikin kwanakin duk wani hadi da malam din ya sani na kariya daga shaidanu ya hada ma sumayyan,suratul baqara itace ruwan shanta,ayatush shifa,da ayoyin karya sihiri,hadin ganyan magarya,man habbatus sauda shi take shafawa saboda yana kore duk wani shaidani da zai iya kusantarka,sai turaruka daban daban,azkar na safiya da maraice da wasu qarin addu'o'in kan wanda takeyi          Ita kanta cikin jiki da zuciyarta take jin salama da farinciki,dokin ganin mukhtar da son komawarta dakinta take.          Ranar kwana na biyun da maraice sai ga abdur rahman,sosai tayi mamakin ganinsa yace mata yaje gidan bai tadda ta ba,wannan sabuwar abokiyar zaman nata ta gaya masa bata nan,ta tafi kuma ba zata dawo ba,bata boyewa abdur rahman din komai ba ta gaya mishi.          Ya jima yana jinjina kansa sannan yace "Idan zaki amince ina da buqatar muqullin dakin naki zan duba shi ko da taimakon da zan iya miki,kinsan fannin magungunan musulunci na karanta,yanzun haka ma yaya mukhtar din nazo kawowa katin gayyata zuwa bude asibiti da zamu dinga treating cututtuka da magungunan musulunci" cike da gamsuwa ba tare da haufi ba ta shiga daki ta miqa masa muqullin ya amsa ya mata sallama ya fice,a qofar gidan ha tsaya ya fidda wayarsa ya kira mukhtar ya shaida masa,take ya bashi izinin shiga,sai da yayi sallama sau biyar duka aka masa tare da dora "Dalla a shigo an cikawa mutane kunne da wata sallama" a tunaninta yaya yahanasu ce ta mata aike,kai tsaye ya doshi dakin sumayyan ya bude ya shiga.           Cikin nutsuwa ya dinga nazarin dakin bayan wasu addu'o'i da ya dinga karantawa a bayyane,fa'iza na tsakar gida kame da qugu tana leqen dakin gabanta na faduwa,addu'arta daya kada ya zamto ya karya duk wani kafi da shiri da tasa aka yiwa dakin.          Tsawon mintina talatin ya kwashe cikin dakin yana karanta wasu ayoyi sannan ya kulle dakin ya fice,da kallo ta bishi fa'izar kamar idanunta kamar zai fado,sai da taga fitarsa sannan ta saki ajiyar zuciya tare da zama gefan rijiya.              Saidai bai wuce wasu mintina talatin din ba sai gashi ya dawo,hannunsa dauke da kaskon wuta mai garwashi sai qwarya,dakin ya sake budewa ya shiga bayan ya tari ruwa cikin qwaryan,zama yayi sosai kan daya daga cikin kujerun yayi bismillah ya fara karanta ayatur ruqya gabaki dayanta,sannan yabi kowanne lungu da saqo na dakin ya yayyafeshi tas da ruwan,komawa yayi falon ya ajjiye qwaryar ya bude wata farar leda mai dauke da 'ya'yan habbatus sauda ya watsa cikin dakin ya shiga turare dakin ciki da falo.            Kasa daurewa fa'iza tayi ganin sai da ta dangana da bakin qofar dakin sumayyan ganin hayaqi mai qauri na fitowa daga dakin,gabanta ya fadi tana tunanin wani qullin ake mata,cike da masifa tace "Wai malam waye kai ne?,meye haka da zaka shigo gidan mutane kana wasu qananun surkulle,bana ciki da rainin hankali da iskanci zo ka fice mim daga gida tun ban tara maka mutane ba".           Dago idanunsa yayi ya watsa mata,take wani kwarjininsa ya daureta,jikinta yayi laqwas bakinta ya mutu,duk tijarar da taso yi ta koma ciki,kafeta yayi da idanu har ta saki qofar labulen ta koma dakinta,zama tayi bakin gadonta tana ta'ajjubin wanne irin mutum ne wannan yaron?,tana zaune nan har ya kammala ya kulle dakin ya fice.            Gidan ya koma ya riski sallar magariba tare da malam sannan daga bisani ya nemi kebewa da shi,cikin falonsa dake zauren gidan suka shiga,bayan sun sake gaisawa abdur rahman din ya gabatarwa da malam maganar sannan ya dora " a abinda na fuskanta malam ba qaramin mugun nufi aka nufi sumayya da shi ba,saidai koma mene Allah ya taqaita darajar addu'a ya rage kaifin QADDARAR TATA,naje gidan kuma na aiwatar daga cikin abinda Allah ya horemin na sani kan irin wadan nan mashaakilat din,kuma in sha Allahu komai yazo qarshe babu abinda zai sake samunta da izinin Allah"gyara zamansa malam din yayi sannan yace "Hakane,tunaninmu yazo daya abdur rahman,mun gide qwarai da gaske daka nuna kulawarka kan lamarin,Allah yayi albarka,kuma in sha Allahu zamu ci gaba da addu'ar,Allah ya tsare gaba" "Amin amin malam" ya amsa a ladabce sannan daga bisani sukayi sallama ya bawa malam muqullin dakin shi ya wuce.            Qarfe takwas na dare suna tafe kan babur dinsa bayan ya daukota,wani farinciki ke ratsa zukatansu,jinsa yake tamkar wani sabon aure.             Murtala suya spot ya zarce ya siya musu kaza da damammiyar fura sannan suka qarasa gida.              A tsakar gida suka taddata tana ta faman safa da marwa,tunda ya sheqa wanka ya fice da magariba ta kasa samun sukuni,far gabarta qara daduwa take duk bayan wata daqiqa,qofar gida kuwa ta leqata yafi sau a qirga tana addu'ar ganinsa ya dawo shi kadai,sallama sumayyan tayi hannunta dauke da leda kanta tsaye ta doshi dakinta,sai da ta tsaya bakin qofar dakin tayi addu'a sosai sannan ta shiga,cikin ikon Allah abinda ta zaci zata ji bata jishi ba,dakin gadonta ta wuce ranta qal tamkar babu wani abu da ya taba faruwa da ita,tabbas babu shakka addu'a takobin mumini ce.             Sai da ya kulle gidan sannan ya tako zuwa tsakar gidan,ya ganta amma ya dauke kai tamkar bai ganta ba yana shirim wucewa,sam har yau ya kasa sonta,ya kasa jinta a jikinsa ko zuciyarsa ko da qanqani je,baisan dalili ba kwata kwata ya tsaneta bata burgeshi.            Ganin da gaske wucetan zaiyi ga wani dan banzan kishi na sakadarta ya sanya ta saurin shan gabansa "Wai me kake nufi ne?,wallahi babu inda zaka,daga dawowarta yau shine saboda rashinvadalci zaka debi kwana ka kai maga,ai sai ka bari sai gobe ko" wani banzan kallo ya jefeta da shi,yau din cikin farinciki yake kuma baya buqatar abinda zai tarwatsa masa farincikin da yake sa ran samu a yau,cikin kakkausar murya yace "Ki matsa daga gabana,umarni ne ba shawara ba" ya fada a tsawace,taji tsoro amma taurin kai ya sanya ta shanye,ta bude baki zata sake magana ya sanya hannu ya janyeta gefe daya ya wancakalar yayi wucewarsa.              Wani kukan baqinciki da takaici ta saka,wankin hula na neman kaita dare,duka magungunan da yaya yahanasu ta amshi kudadenta ta kawo mata tana zuzuta mata aikinsu sam ba haka ta gani ba,haka kawai sun hadata da diyar malamai tana ta faman wahala da ita,wahalar ma ya banza,eh ta banza mana tunda ko hankalin mukhtr din ma da akeyi don shi har yau ta kasa janyoshi gareta,kullum kwanan duniya kamarvsake sabunta qaunar sumayyan ake cikin ruhinsa ba qoqarin fidda ta cikin zuciyarsa ba?,abu goma da ashirin kenan,sam wallahi ba zata sabu ba bindiga a ruwa.            A fusace ta shiga dakinta ta lalubi wayarta,lambar yaya yahanasu ta kira da niyyar yi mata wankin babban bargo saidai kash ta daki gurbi wayar tata a kashe take,da sauri ta sauya akalar kiran nata zuwa ga fadima,cikin sa'a ta sameta,tun kafin fadiman tace wani abu fa'iza ta soma sauke mata kwandon rashin mutunci,zagi na tsamar nama ta dinga luluqa mata tare da laqaba musu sunan macuta,sai da ta tabbatar ta rage farashin baqincikin da take ciki sannan ta datse layin tana huci tare da cin alwashin gobe har gida zata yi tattaki taje ga yahanasun ayita ta qare,don ba zata dauki asara ba sai ta biyata kudinta,tunda ai ba ita daya ke da buri ba suma suna da buri don me zasu dinga cutarta suna wankarta ana amfani da kudinta kadai?.              Kwanan baqinciki tayi tare da kusan qarar da daren nata wajen zirga zirga tsakanin dakinta da window din sumayya,su kam suna ca wata duniya basu san ma me takeyi ba,kwanan farinciki qauna bege da faranta ran juna sukayi,yayin da tayi kwanan gadi da safa da marwar da babu lada. *tabbas duk wanda ya saki Allah yana tare da tarin wahala maras qarewa* _wannan kenan muje zuwa masu karatu,har yanzu da sauran qaddarori wa sumayyan taku_ *zuku ji shiru gobe in sha Allah sakamakon uzirin dake gareni,idan kuma ya samu to amma kada ku sanya rai,na gode.* *mrs muhammad ce* 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍✍✍✍ ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 1⃣5⃣ ___________________________ *Bismillahir rahmanir rahim* *wama tadri nafsun maza taksibu gada* _____________________            Kwanaki biyun da yayi a dakin sumayyan shi kansa ji yake ya zama tamkar ango,zuciyoyin su fes,duk wani buduri da fa'izan keyi basu san da shi ba,soyayyarsu kawai ta ishesu rayuwa.             Cikin kwanakin da suka biyo baya damina ta shigo,wanda hakan shi yayi sanadiyyar zubewar ginin maqotan yaya yahanasu ya fadowa gidansu har ya janyo rushewar wani bangare na gidan,hakan ya sanya mukhtar yace su baro gidansh su dawo gidansa don a samu sararin gyaran gidan nasu,ko bayan rasuwar mai gidan anty yahanasu kusan shine jigo dake d'awainiya wa su yaya yahanasun.            Qarfe biyu na azahar suka iso gidan tare da yaranta biyu jamila da sayyada,sumayya na tsakar gida a lokacin tana wankin kayanta,da fara'arta ta taso tana musu sannu da zuwa tare da qoqarin karbar jakar hannun yaya yahansun bayan yara sun gama shigewa da sauran kayayyakin nasu d'akin fa'iza,kaucewa tayi gami da jifanta sa wani kallo tana fadin "Kada ki kuskura ki taba min jaka,matsa da Allah ki bawa mutane guri" ta fada tana wuceta sauran yaran suka mara mata baya,a salube ta koma kan wankinta taci gaba da yi har ta kammala tana jiyo shewarsu cikin dakin fa'izan kai kace yaya yahanasun sa'arta ce,ya tabbatar cewa da ita ke shewa haka da yaya yahanasun sai ace bata da mutunci bata da kunya,amma ga fa'iza na faman shewa da qyaqyatawa gabanta,matar da ko sau daya sumayyan bata iya hada idanu da ita,biyayya take mata tamkar uwar mijinta haka ta dauketa sakamakon ganin irin girman matsayin da take da shi gun mukhtar.           Tana kammala shanya kayan ta shige wanka saboda tana so taje kitso sakamakon ita ke da girki gobe,har ta fito ta gama shiryawa ko alamun dora abinci babu gun fa'iza,itama bata damu ba sai ta hada shayi kawai ta sha tayi ficewarta ta barsu.              Qarfe biyar ta dawo gidan saboda layi da ta taras a gidan kitson,tun daga qofar gida ta soma jin muryar fa'iza cikin balbalin bala'i,ta kutsa kai cikin gidan cikin mamakin ita da wa,dai dai lokacin da fa'izar ke fadin "Yo da kika damen da zancan ciki laifin uban waye mayun 'ya'ya?,qanin naki yayi min cikin mana ya gani idan ban dauka ba,wata uwar yake yimin idan kwana na ne banda kwanciya da zaki uzzura min,to wallahi babu ma mai kwanarmin cikin daki balle ya sanya min ido,dama daki ba daki ba ya zuciyar talaka,sai ku nemi gun kwana" ta fada tana komawa cikin dakin tare da banko labulenta.            Idanu sumayya tabi tsakar gidan nasu da shi,ko ina kaya ne na yaya yahanasun a barbaje a qasa,gaban sumayyan ya fadi,jikinta yayi sanyi,ta qarasa tsakar gidan,hannu ta sanya tana tattare kayan nasu waje daya,tsawa yaya yahanasun ta daka mata "Kada ki sake taba mana kaya shegiya munafuka 'yar gidan malamai,to wallahi bari na gaya miki idan ma shiga tsakaninmu kikayi da fa'iza kinyi kadan,hakan da takeyi bazai tunzura zuciyata tunda nasan ba cikin hayyacinta take ba,ke sayyada maza ku hade mana kayan gefe guda mu jira shi muntarin ya dawo" sororo tayi tana dubanta "Daina kallo na mayya,li'ilafi quraishi,ni baki isa ki cinyeni ba" sai ta kauda kai ta wuce kai tsaye dakinta ta bude ta shige.             Bata sake fitowa yayi zamanta cikin dakin,sai ta qirqiro wasu 'yan qananun ayyaukan ma cikin dakin nata don kawar da duk wani tunani da zai dameta,tana aikin tana ambatar hasbunallahu wa ni'imal wakil,allahumk finihim bima shi'ita,hakan ba qaramin taimaka mata yayi ba,sai ya tafiyar da lokacinta cikin sauqi har aka kira sallar magariba,ta miqe ta fito domin daura alwala,suna zaune gefe daya na tsakar gidan da qullin kayansu,sosai har cikin zuciyarta taji babu dadi,bai kamata mukhyar yazo ya taras da su haka ba,ko babu komai 'yan uwansa ne jininsa ne,kuma tayi imami cewa idan wani nata ne shima mukhtar din ba zaya wofantar da su haka ba,ta danne zuciyarta ta qarasa gurinsu,cikim sanyin murya tace "Don Allah yaya ki shigi dakina,ko da ba zaki zauna din ba ki shigo idan yaso idan ya mukhtar din ya dawo sai asan yadda za'ayi din" wani kallon banza ta bita da shi "Ke wallahi ki fita a idona,wai ke wacce iriyar mayatacciya ce ne,nace bazan shiga ba dole ne,to bari kiji,idan ma wani laqani aka baki na sai na shiga sannan zaki samu galaba a kaina to wallahi ki gayawa malaminki kunyi qarya kun kwana da yunwa" jikinta sai yayi sanyi ta kasa tafiya,zuciyarta na gaya mata basu zama masu kyautawa mukhtar ba indai yazo ya tadda jininsa a wulaqance,duk da tarin izgilu cin fuska da cin mutunci da ita yaya yahanasun ke jifanta da shi,ba ita take dubawa karamcin mukhtar take dubawa.           A haka mukhtar din ya shigo ya riskesu,tayi masa sannu da zuwa ta karbar kayan hannunsa duk da ba ranar girkinta bane,ya amsa yana duban yaya yahanasu."a'ah,yaya yanzu kuka zone na ganku a nan a zaune ku da kayanku"kai ta girgiza "Inaaa,ai tun azahar muna gidan nan" cikin mamaki ya dubeta tare da zaro ido sai ya dubi sumayya yana jifanta da tuhuma,qas tayi da kanta don bata da ta cewa,ganin haka yasa ya dubi yaya yahanasun "Amma kuke zaune a nan?,kada kice min nan kuka wuni?" Waiwayawa tayi ta dubi sumayya "Sai ki bamu guri ko ko ban isa ba?" Bata ce uffan ba ta koma dakinta duk da alwala ta fito da niyyar daurawa.                Sai da taga shigarta dakin sannan ta maido dubanta ga fa'iza "Mutuniyar tamu,wallhi lafiya lau ta karbemu,daga yi mata tambaya kan naji shiru har yanzu mun samu qaruwa ko a'ah ta shiga masifa ta inda take shiga ba ta nan take fita ba,qarshe tayo mana waje da kayanmu" sosai ransa ya baci,ya soma huci cikin fushi yace "Fa'izar?,to da tayi muku haka gidanta ne ko nawa?,bazan lamunci wannan iskanci ba" ya fada yana juyawa zuwa ga dakinta wanda fa'izar na ciki tana jin kowa tayi lakur abinta.          Da sauri yaya yahanasun ta dakatar da shi "Kaga muntari bana son hauka fa,laifi muka yi mata mu mika bata mata rai,nasan kuma zata huce,don haka bance kaje ka sake bata mata rai ba,kadai lallabata har ta yarda mu zauna taren" jagale yayi tare da juyiwa yana duban yayar tasa,take kuma ya tuna sunfi kusa fa ita da fa'izan,ya ma kamata a yau din ya qyaleta taga halin fa'izan taga wace ita ra'ayil ain wato ganin ido,saboda haka sai ya saki murmushi cikin salon canza shawarar da yayi farat daya,gyada kai yayi "Shikenan,muje to a lallabatan" da sauri suka miqe yaya yahanasun tana cewa "To,to ai kaga hakan yafi" tabi bayansa.           Tana miqe daga kan gadonta tana taunar chewing gum dai dai,zama sukayi kan kujerarta dake fuskantar gadon,yayin da mukhtar ya qarasa gefan gadon ya tsaya,duk da cewa ransa a matuqar bace yake,ji yake kamar ya janyo fa'izan ya yi mata dan banzan duka ya watsar amma sai ya dake "Fa'iza,me yasa ba zaki bar yaya ta zauna dakinki ba,ai ina ganin bai kamata ba" hura hanci take tana tunanin ko yanzu mukhtar ya soma tsoronta,inko haka ne kowa tasa ta qare,tabbas sai kowa ma yaci ubansa cikin gidan "Mukhtar banga dama bane,bari kaji" ta fada tana miqewa zaune kan gadon "Na farko bansan sa ido gaskiya kuma na fuskanci su sun fara koyar wannan halayyar,na biyu na fuskanci ni aka rainawa wayo,ga mai daki ciki da falo can ba'a dosheta ba saini mai daki daya kamar zuciyar talaka" ba qaramin dukansa maganar tayi a zuciya ba amma ya hadiye don so yake ya jata aje gun ta dora da "Saboda haka su nemi gurin kwana don ni bazan zauna da wadan nan qattan a daki na ba" wani qullutun abu ne ya tokare masa wuya qanda ya hanashi sake magana,sai yaya yahanasu da tace "Haba ke kuwa fa'iza,kwana nawa ne duka duka mun koma gidanmu,ai ban zaci ko wani na turo gidan nan ki masa sauki a dakinki ba zaki kasa,kada fa ki manta nice silar zuwanki gidan nan" zabura tayi tana dakatar da ita "Kinga kada ki sake kice zaki mun gori,don ke kika kawoni gidan ai bake kike aure na ba,buqatar maje haji sallah kuma da taku buqatar ai ba haka siddan kika kawoni ba,sabida haka kuje ni don Allah kada ku cikan kunne,tunda kun nace sai kun zauna a dakin kuje zanyi tunani,ko kwana daya ne kuyi kafin ku koma inda kuka fito".          Ba qaramin daurewa kan yaya yahanasun yayi ba da kalaman fa'iza,duk yadda fadima ke gaya mata sai yau ta sake tabbatarwa da lamba daya ce ita wajen rashin mutunci tsiya da tsiyataku " fa'iza ni kike gayawa haka"kanga tsaye babu kunya tace "Na fada din,ke kike aurena ne nace wai kawai da zaki takuran,wannan fa kamar kina lissafin sau nawa nake kwanciya da mijina ne"tuni maganar ta sake dora yaya yahanasun kan dokin zuciya " ke qaramar mara kunya,ko bani nake aurenki ba kinsan ina da power din da zan sa ungulu ta koma gidanta na tsamiya ko?" "Bismillah,sai mu gani " ta fada tana murguda baki gami da turo daurinta gaban goshinta ta dage kanta idanunta na kallon ceiling din daki.           tabbas tana jin yau idan bata nunawa fa'iza isar da take da ita a wajen mukhtar ba bata huce takaici ba,idanunta taf da bacin rai ta dubeshi "Mukhtar,ina so a yau yau din nan ka sawwaqewa fa'iza,yanzun nan" ta qarashe cikin daga murya.         Duk da cewa ranshi ya kai qololuwa wajen baci kan abinda fa'izq ta yiwa yaya yahanasun amma sai ya danne komai tamkar bai b'aci ba,ai dama duk wanda ya sai rariya yasan zata zub da ruwa,to ya kamata yaya yahanasun taga yadda tata rariyar ke zubar da nata ruwan,ruwan kuma da baiyi qasa a gwiwar malalowa ya jiqata sharkaf ba,kai ya kada sannan yace "Kan me zan saki fa'iza yaya,ni babu abinda ta yimin,hasalima fa'iza ai zabinki ce,kinga bai kamaci na wofantar da ita ba,zan riqeta hannu bibbiyu kamar yadda kika umarceni" tsawa ta daka masa "Mukhtar,kai makaho ne?,ko kuwa kai kurma ne,baka ganin abinda ta yimin ne,ni na umarceka nace ka saketa kamar yadda na umarceka ka aureta a baya" kai ya sake kadawa tare da yin tattaki don barin dakin yana cewa "Ki gafarceni yaya,amma yanzu na fara zama da fa'iza,don ni bata aikata min komai ba" sai ya fice abinsa ya barsu ana kallon kallo.              Kira ya qwalawa sajida ya sanyata suka dinga jidar kayayyakinsu yana tayasu suna kaiwa dakin sumayya wadda ke zaune kurum tana ji da ganin sarautar Allah,sai da suka kammala tsaf yaya yahansun na dakin fa'iza suna cecekuce,ganin abun na sake qamari ya sanyashi shiga dakin ya janyeta yana fadin "Kiyi haquri yaya yahanasu,kizo ku zauna dakin sumayya tunda itan da kuke so ta qiya" sai ta waiwayo ta bishi da ido galala tana kallonsa,mukhtar din da baison bacin ranta?,mukhtar din da baiso a tabata amma yau an mata cin kashin data jima rabon ta da irinsa amma ya kasa cewa uffan,kardai mallaka fa'iza tayi masa wadda baya iya qetare umarninta?,ranta ya shiga suya ta shiga fatar cewa Allah yasa ba haka bane,bata da wani zabi a yanzun illa ta bishi,idan yaso daga bisani tayi tunanin mafita a tsanake.             Bayan sun shiga dakin ta zauna sannan ya kira sumayya ya fice zuwa dakinsa.            Zaune ta tadda shi dafe da kansa,a hankali cikin kasala ta zauna gefansa,ta sanya tafin hannunta tana shafar bayansa a hankali,tasan fushin mukhtar din,saboda haka ta tabbatar ransa na a bace ne,kusan minti goma baice komai ba kafin daga bisani ya dago ya dubeta "Sumayya" ya kira sunanta,a tausashe ta amsa sannan ya dora "Gasu yaya yahanasu nan zasu zauna dakinki,kinsanta sarai ita da yaranta baki daya,baki buqatar muraja'a kansu,na shaideki da haquri wannan halinki ne,to amma don Allah ki nunka haqurinki,baqunta zasu mana na wani d'an lokaci,insha Allah zanyi qoqari na kammala musu gyaransu cikin qanqanin lokaci,idan da na kammala ma gini na sabon gida na can zan ara musu su zauna gudun fitina,kiyi haquri da su don Allah ki sake ninka kawaicinki" kai ta girgiza "Haba ya mukhtar,ai ba roqona zaka yi ba,umarni kadai zaka bada,da kai da kaya ai duka mallakar wuya ne,nima yaya take agurina,insha Allahu babu wata matsala ko damuwa" "Na gode,Allah yayi miki albarka" "Amin yaya" ta fada tana sakin qayataccen murmushinta wanda har sai da ya sanyashi tsura mata idanu,hannu ta turo sautin idanunsa kamar zata tsone masa yaja baya suka saki dariya baki dayansu.              Cikin dakin ya barta ya fita sallah,kasancewar tana faashin sallah sa'an nan kuma dakin nasa na hargitse don fa'iza ba kasafai take tsayawa ta gyara ba ya sanyata tsayawa tana dan kakkabe dakin haka ya dawo ya cimmata,kafin ya kai ga zama fa'iza ta fado dakin hannunta riqe a qugunta,shi ya fara cewa "Me aka girka" ran nan nashi a hade tsaf wanda ita a nata zaton aikin da take kansa ya fara tasiri,saboda haka kanga tsaye tace "Yau duka ma banyi girki ba wlh a gajiye nake" ta fada tana yatsina,sam ya tsaneta har yau ya kasa jinta dai dai da qwayar zarra cikin zuciyarsa,bata dameshi ba dama bisa lalura kawai yaje rabarta,qoqarin adalci ne kawai irin nasa tunda ta riga da ta rataya a wuyansa bisa alfarmar igiyoyinta uku dake hannunsa.             Hannu ya miqa mata a daqile yace "Bani muqullan locker din kayan abinci na" ba musu ta fice don dauko masa,ya juya ya dubi sumayya "Yau ba'ayi girki ba gida na,me kuka bawa yaya taci ita da iyalanta?" Kanta ta duqar qasa sannan tace "Ka mance na tambayeka zani kitso?,tunda na fita ban samu na dawo ba sai bayan la'asar,dana shigo kuma nima yadda ka taddasu haka na taddasu" kai ya gyada ba tare da yace komai ba,ta dawo da muqullin ta miqa masa,kai tsaye ya danqa su ga sumayya "Jeki ka samar mana da abinda zamuci" hannu biyu tasa ta amsa kana ta danyi jim,da kamar taqi abinda ya sata din,sai kuma taga hakan bai dace ba,idan bai isa da fa'iza ba ita ai ya isa da ita,miqewa tayi zata fice fa'iza ta saki wani mugun murmushi,ga zatonta sumayya ta shiga cakwakiya mukhtar zai soma azabtar da ita kenan,fadawa tayi saman katifar kusa da shi tana fadin "Ammmmm......idan kin gama kizo na gaya miki me mi kuma zaki dafamin" wannan karo kasa hadiye takaicinsa yayi sai da juyo yace "Da yake baiwar gidan ubanki ce ko,wato saboda kinga na miki shiru ne ko......hmmmmm.....ki kiyayi ranar qin dillanci wallahi,wuce kije sumayya",sai ta juya ta fice din,itakam ta ma rasa na cewa gaba daya,gaban fa'iza ya fadi,kaddai jiya i yau ne dai mukhtar din,sai ta kasa hadiye qanin zagin da yayi mata ta miqe tsaye " wacce rana ce ranar qin dillanci,ba ranar da hajar mai gari ta bata ba?,idan ba'a ganta a gun fa'iza sai me?"ta murguda baki tana niyyar ficewa,zuciya ce ta ciyoshi ya miqe cikin zafin nama ya fincikota ya zabga mata wani lafiyayyen mari,a gigice ta dafe kuncinta don bata zaci haka ba,karo na farko da mukhtar din ya soma taba lafiyarta,ashar ta danna sannan tace "Ni ka mara muntari,kayyasa kace yau da bala'i,wallahi baka daki bulus ba sai na rama" .            Daga hannunta tayi da niyyar kaiwa fuskarsa mari ya cafe hannun tare da murdeshi har sai ta qashin hannun ya bada wani qasss da alamu ya targadata,tsananin azaba ya sanyata sakin qara wadda ta sanya sumayya dake kitchen barin abinda take ta taho dakin cikin hanzari,dadin da taji data lura su yaya yahanasun da suka qure kallo cikin t.v dinta basu san me ake ciki ba,tun fara masa rashin kunyar duk cikin kunnenta ne saboda muryar fa'izan na sama ne sosai.              Sanda ta isa dakin ya daga hannu da niyyar sake bata wani marin,cikin hanzari ta shiga tsakiyarsu taba riqe hannunsa,cikin taushi ta langabar da kanta tana duban tsakiyar idonsa wanda hakan shi ya karya lagonsa,ya zare hannunaa daga nata,bakinta bai mutu ba sai data wurga masa kalmar "Wallahi wallahi sai kayi dana sanin dukan fa'iza,sai ka biya farashin duka na da kayi,zaka gani,ke kuma ku zuba mu gani" sannan ta fice.          Tabbas ba don har tanzu bai cimma qudirinsa ba akanta da yau babu abinda zai hanata kwana cikin gidan ubanta,gefensa ta zauna ta sanya hannunta cikin nashi sannnan tace "Sam hakan ba girmanka bane ya mukhtar,tunda nake ban taba gani ka daki wani ba ma bare matarka ta aure,yin hakan ba daidai bane,na roqeka don Allah kada ka sake sai ka fara bani tsoro ai" ta qarasa fada a shagwabe,sai ya dago yana dubanta da murmushi,take kaso saba'in cikin dari na bacin ransa ya zabge ga fadi sai ya dora hannunsa shima saman nata "Banaso ki fara jin tsoro na sumy ta,idan kika fara tsoro na na zauna da wa?,bazan sake ba,kiyi haquri" kai ta girgiza tana murmushi "Kai ya kamata nace kayi haquri yaya ka yafe mana,yau mun sanyaka cikin bacin rai" kasa magana yayi sai ua rungumeta kawai cikin jikinsa yana jin duminya,yana ganin girma da qimar wannan halitta mau tsananin hankali da biyayya a gareshi,shikam mai zai hana shi faranta nata matuqar yana da iko?,me ya isa ya hanashi sonta a duniya?,babu shi,babu shi ko mene,koda QADDARA ce baijin tana da wannan qarfin ikon,baya fata ma QADDARAR tazo masa ta wannan sigar,gwara ta kowacce siga amma banda wannan,wala'alla ya iya jurewa.           Sai da suka fara jiyo qaurin girkinta sannan ya saketa ta miqe da hanzari ta fice tana ce masa tana zuwa. *mrs muhammad ce* 📚📚📚📚✍✍✍✍ ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 1⃣7⃣ ________________________ *Bismillahir rahmanir rahim* *ma asaba min musibatun fil'ardi wala fi anfusikum illa fi kitabim min qabli an nabra'aha* _______________________              Cikin mintuna qalilan ta kammala jallope din taliyar ta rarraba cikin coolers,mukhtar din ta fara kaiwa,tana niyyar juyawa ta fita yace da ita "Wannan cooler din fa na waye?" Ta dubi cooler din sannan ta dubeshi "Na fa'ixa ne a ciki" "Ajjiye a nan" ya fada yana gwada mata inda zata ajjiye din da idonsa,bata kawo komai cikin ranta ba ta ajjiye din ta nufi dakinta.             Can ta taddasu sun baje suna kallo,duk da cewa kallo daya zaka yiwa yahanasun kasan tabbas har yau ranta a bace yake,ta dire cooler din tana cewa "Ga abincinku yaya" wani banzan kallo ta watsa mata "Eh zamu ci ai kuma zamu ambaci sunan Allah,in sha Allahu babu abinda zai samemu,makira,idan ma shiga kika tsakaninmu da fa'iza har take wannan tashan rashin kunyan to ni zanyi maganinku ke da iyan baki daya" kai ta kada ba tare da tace komai ba ta shige uwar dakinta,ta tube kayanta ta sauya na bacci,sai tayi zamanta gefan gado ta janyo RIYADUL JANNAH littafin addu'o'inta da malam ya bata wanda bata rabi da shi ta soma duba wasu shafuka.           Sumayyan na fita ya dauki cooler din baki daya ya fita da ita waje,wasu almajirai da rabonsu ya rantse ya samu qofar gida zazzaune ya basu,take suka karba suka rabe a tsakaninsu suna zabga godiya banza ta faadi garesu.              Yana kammala rufe gidan sukayi karo da fa'iza wadda ta dawo daga dakin sumayya ta bankade labulenta ko kallo su ya yahanasu basu isheta ba ta qwallawa sumayya tambayar ina abincinta,tana daga cikin dakin ta gaya mata yana gun yaya mukhtar.           Dubansa tayi"ina abinci na?"banza ya bawa ajiyarta yayi wucewarsa,sai ta bishi da kallo,bata haqura ba tabi bayansa tana sake tambayarsa,wani wawan birki yaci wanda sai da ya sanyata ja da baya "Baki daku ba kenan ko?,tare muka hada muka siyo abincin?,ko kinzo da bayi ne daga gidanku?,uban wani ne ya hanaki dafawa kici,ki fice min daga nan tun kafin na hasala na sake kikkifa miki mari" tana qunquni ta juya ta fice ranta qunci fal,ga uwar yunwar dake sakadarta,abinka da mutum mai shegen ci ta riga da ta saba.             A tsakar gida taci karo da jamila na wanke hannunta,da gayya ta bangajeta tayi taga taga ta fadi,sai ta miqe kuwa ta lailayawa fa'izar ashar abinka da itama tana ji da tata rashin kunyar,ai kuwa fa'izan tayo kanta zata huce bisa kan nata,dai dai sanda yaya yahanasu ta qaraso tayi hanzarin riqeta ta gabza mata mari dama tana ciki da ita ne,tana waiwayowa kuwa ta cakumi wuyan yaya yahanasun take jamila ta shigarwa uwarta nan fada ya kaure tsakanin su ukun.            Sumayya ce ta fara fitowa,cikin tashin hankali taje dubansu idanunta a waje,dambe da yaya yahanasu?,tab,lallai fa'iza ta kai,dakin mukhtar ta nufa da hanzari tana mamakin me ya hanashi fitowa,ga mamakinta yana tsaye bakin window yana kallonsu,saidai idanun nan sun kada sunyi jazur,a hankali ya juyo ya zuba mata su,itama sai jikinta yayi sanyi,tausayinta ya kamashi,babu shakka wata jarrabawa ce ta fado rayuwarsu,idanunta suka cika taf da qwalla ta tausayin mijin nata,sai kawai ya saki labulen ya taka a hankali ya fita tsakar gidan,wata gigitacciyar tsawa ya sakarwa fa'iza dake tsakiyarsu tana cin na jaki wadda tsawar sai data sanya hanjin sumayya hadewa ya cure guri guda,ta runtse idanunta tana jin ruguginta na ratsa kunnanta.          Nuni kawai ya yiwa fa'iza da hanyar dakinta yana mata wani irin kallo mai cike da tsana,ba musu ta wuce jikinta na rawa,ya juya ya dubi yaya yahanasu sai kawai ya kamata yayi dakin sumayya da ita.           Bakin rijiya ta zauna,sai ta kasa daurewa idanunta ya shiga fidda qwalla,wannan wacce iriyar masifa ce lokaci guda,duk wani farinciki da zaman lafiya na gidansu yayi qaura lokaci daya?,tana share hawayen idanunta tana tausayin mukhtar dinta.            Tana zaune a nan mukhtar din ya fito ya shige dakin fa'iza,a nan ne ta jiyo tashin muryarsa saidai nan din ma bata ji duka abinda yake fadi ba,daga bisani ne ya fito,ta miqe tsaye ta isa gabansa tana kallonsa,tabbas taso ace yau ranar girkinta ne,ta lallashi mukhtar din,saidai sam bata da wannan damar,karyar da kai tayi murya a tausashe tace "Kayi haquri don Allah yaya mukhtat,komai na duniya mai wucewa ne,jarrabawa ce daga Allah" murmushin qarfin hali ya saki ya shafi gefan fuskarta "Babu komai my sumy,kije ki kwanta,kuma ban lamunce ki sanya abun cikin ranki ba,ki kwanta kiyi bacci sosai" ya sanya bakinsa yayi kissing  goshinta,sai ya bata kunya har ta dan murmusa,yana tsaye har ta wuce dakinta sannan ya juya nashi.            Ko da ta isa dakin tuni ta taras da su sun rarrashe kan gadonta,sai yaya yahanasu dake zaune gefan gadon tana huci,abinda take da buqata ta dauka zata fice taji sakin qwafar da yaya yahanasu tayi,ranar kan doguwar kujerar falo ta kwana,saidai tayi qoqari kamar yadda mukhtar ya buqace ta tayi bacci ta qoqarta tayi na 'yan awowi. *******************         Cikin kwanakin gaba daya mukhtar ya fita harkar fa'izan duk da cewa daman can ba shiga yake yi ba,saidai duk wani abu da yake haqqinta ne kansa yana sauke mata bakin gwargwado.            Zaman yaya yahanasu a gidan ya dauki sabon salo,wani irin zama ake a gidan,sosai yaya yahanasun kejin haushin fa'izan gami da ganin baikenta tun farko data daure gindin dan uwanta ya zama miji gareta,sai dai kuma duk da wannan bai hanata jin haushin sumayya ba,gani taje tamkar itace ta shiga tsakaninsu.           Duk kwanan duniya gari na wayewa da zarar mukhtar din ya sanya qafa ya fice itama fa'izan ke ficewa,ba zata dawo ba sai yaba gab da dawowa koda kuwa ranakun girkinta ne,sai a sannan zata tsiri girkin dare shima tsoron hukuncin mukhtar din ya hau kanta take,ba qaramin horata yayi ba lokacin da ya amshi maqullin locker din abincinsa daga hannunta ba,da rana kuwa saidai kowa tashi ta fishsheshi,shiga su jamila suke kitchen kansu tsaye su girka duk abinda suka ga dama,su din ma ba baya bane wajen iya barnar abinci da ta'adi,sam ko sau daya sumayyan bata taba daga kai ta dubesu ba bare ta gwadawa mukhtar abinda sukeyi cikin gidan,dakinta kam tuni ta sallama musu shi,ta dauke kai baki daya da shi saboda yadda suke abinda suka ga dama cikinsa,wani abun da gayya da gadara suke mata,koda bata tankasu ba sukan bude baki suce "kayan dakin da kudin dan uwansu aka sauya su" sau tari dariya abun yake bata,ta kuma godewa Allah da ya sanya iyayenta masu rufin asiri da zuciyar yiwa iyalinsu ne,suma sun san da haka,babu shakka da Allah kadai ne yasan halin da zata tsinci kanta ciki,hatta da kayan sawarta sai suka fara dauka dai dai da dai dai suna sanyawa idan zasu fita wata unguwa ko biki,ranar da mukhtar ya soma gani ransa ya baci matuqa,bai iya jurewa ba sai da ya kirasu ya musu jan kunne.             Ganin haka ya sanya mukhtar yace ta debe duk wani abu nata mai amfani ta dawo da shi dakinsa,ya bude ma'ajiyarsa ya adana mata ciki.             Fa'iza kuwa tsakaninsu da yaya yahanasun da yaran ma baki daya sai harare harare da baqar magana,wanda yawanci ma sunfi yi da jamilan ko sayyada,bata san me mukhtar ya gaya musu ba amma da alama shi ya kawo wannan dan qaramin sauyin da aka samu.           Cikin wata d'aya kacal mukhtar ya kammala musu gyaran suka tattara suka koma nasu gidan,ko a ranar da zasu tafi din ma sai da ka kusa kwata ta ranar da suka zo din,da zagi suka rabu,ba qaramin qona ran yaya yahanasun abun yayi ba ganin mukhtar din ya gaza daukar kowanne irin mataki,abinda bata sani ba shine ya fita jin takaicin abinda ke faruwar,saidai ya riga da ya tsarama ransa sai sun gama d'aukar darasin rayuwa tukunna. *********************            Qarfe takwas na dare ya iso gida tun bayan fitar da yayi da safe sakamakon aiki da suke a shagon sa na kasuwa,sosai yake a gajiye tiqis,saidai yasan cewa abu mafi muhimmanci shine ya adana gajiyarsa,matuqar fa'iza ke da girki babu wani abu da yake iya tsinta ko ya dorar a wunin ranar baki daya,qarin gajiyarsa machine dinsa yau da ya masa tsiya ya baroshi gun bakinike ya tari adaidaita ya iso gida.          Babu wutar nepa a unguwar tasu hakan shi ya sabba ba duhun da gidan yayi,sai hasken fitila daga dakin sumayya dakin fa'iza da kuma kitchen din gidan.            Bashi da sha'awar yin tozali da fa'izar ko kadan,saboda haka ya bude dakinsa ya shige da zummar zuwa ya rage kayan jikinsa ya koma bayi ya tanadi ruwan wanka,hular kansa ya cire ya jefata saman gadonsa,ya balle maballan rigarsa ya zareta ya ajjiye sannan ya nufi window dinsa ya yaye labulen don ya bawa iska damar shigowa.             Kamar wanda aka kira idanunsa suka sauka kan kitchen,fa'iza ya hango,da farko yayi niyyar dauke kansa,saidai wani abu da ya hango shi ya ja hankalinsa,idanu ya zuba sosai don yana son ya tabbatar da abinda idanunsa ke gane masa,baiso yayi hukunci bisa kuskure zato ko tsammani.             Sakin labulen yayi sannan a hankali ya fita izuwa kitchen din cikin takun sanda,bakin window ya isa sannan ya lafe daga jikin bangon yana kallon komai tar kamar yadda idanunsa suka soma nuna masa daga cikin dakinsa,yana tsaye harta sheqe da dariya sannan tace.............. *mrs muhammad ce* 📚📚📚📚✍✍✍✍ ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 1⃣8⃣ ______________________ *Bismillahir rahmanir rahim* *innal laha huwar razzaqu zul quwwatil matin* ______________________ "Mukhtar!,mukhtar!!,hmmmmm" haka ta fadi sannan ta maida murfin food flask din ta rufe tana ci gaba da dariyarta cike da nishadi da jin dadi. A hankali ya zare jikinsa,cikin tafiya ta sand'a kamar yadda yazo haka ya koma,bakin gado ya zauna ya dafe kansa da dukkan hannayensa biyu,zuciyarsa na rawa saidai baiso ya bata dama,oh Allah!,tun yaushe?,tun yaushe ya fara turawa kansa wannan qazantar?,me ya samu yaya yahanasu ne har udanunta suka rufe ta kai ga nannade hannu zata jefashi ramin halaka?,me ta gani ne wai gun fa'iza ya burgeta har ta nemi suyi tarayya wajen hada zuriyya. Sallamarta ta katse masa zaren tunaninsa,ya daga kansa wanda idanunsa suka kada jazur ya dubeta,tayi ado yau cikin shadda koriya sgar,bakin nan ya sha jan jambaki tamkar ya digo,zai iya rantsewa da Allah yau ne karo na farko da zai iya cewa ya ganta tayi wata aba mai suna kwalliya tun bayan qare kwanakinta bakwai na amarci. Wani kwarkwasa na musamman yau din take masa,wanda dai dai da qwayar zarra bata qara farashin qaunarta cikin zuciyarsa ba face rageta ma da tayi,haushi takaici da baqinciki suka cika shi amma yayi namijin qoqarin dannewa "Sannu da zuwa yaya mukhtar,yau kam ka jima baka shigo ba,Allah ya sanya lafiya" ta fada tana zama dab da shi tare da kashe masa ido,tausar zuciyarsa yayi don yana son ya ga gudun ruwanta,don idan baka iya kama b'arawo ba shi sai ya kamaka,tsawon zamansu duk iya inda ya kai darensa indai ba a dakin sumayya bane to shi ta shafa bata da damuwa,koda wasa bata taba tambayarsa ba "Lafiya lau" ya fada yana miqewa tsaye,sai ta dubeshi gabanta na faduwa tana fatan ba asarar aikinta zai mata ba yau ma dai "Ina zuwa yaya mukhtar gashi na shirya maka abinci?" "Wanka zan shiga nayi" ya fada bayan yayi kamar bazai amsa mata ba,ta miqe tana fadin bari ta hada masa ruwan wanka sai ya dakatar da ita kan ta jirashi. Kai tsaye dakin sumayya ya shiga,tana kwance saman doguwar kujera hannunta riqe da wayarta tana kallon wani film 'DAN KUKA,dariyarta take mai sanyi a hankali cikin nutsuwa,ya jima tsaye kanta yana dubanta cike da qauna da burgewa har sai da ya sanya hannunsa ya zare wayar sannan ta miqe a firgice tana ambaton "Bismillahi,hasbunallahu wa ni'imal wakil" sai suka hada idanu,ta shagwabe fuska cikin muryar shagwaba tace "Kai yaya mukhtar wallahi ka tsoratani" girarsa qwaya daya ya dage mata "Eh amma naji dadi da kika ambaci sunan Allah yayin da kika tsorata din,haka akeso" murmushi ta danyi,duban screen din wayar yayi ya tsayar da film din,cikin shagwaba shima yace "Wato yau ko ki nemeni ko my sumy?,hala ma kin daina damuwa da ni,kina nan kina kallonki kina ta dariya abinki bayan bakiji shigowar sahibinki ba ko?"idanu ta zaro tare da dafe baki sannan daga bisani ta hade hannayanta guri guda alamar roqo " ka yimin afuwa don Allah,wallahi kewarka ce ta dameni shi yasa ma kaga ina rage lokaci da kallon,ai kasan yaya kallo ba damuna yayi ba ko?"ta qarasa maganar da sigar yarinta,idanu yasa yana kallonta sosai,babu shakka yana daya daga abinda ke sake rura qaunarta cikin zuciyarsa wannan shagwaba da quruciya tata,murmushi ya sakar mata "Na miki sumayya ta,ai baki laifi a gurina" ya fada yana miqa mata wayar tate da cewa "Zan shiga wanka" "A fito lafiya ranka ya dade" "Allah yasa my sumayyata" ya fada sannan ya juya ya fice yana murmushi. Kai tsaye sif dinsa ya wuce ya fidda jallabiya ya saka tana ta faman zuba masa surutu,ko daya bai kula ta ba sai sabgarsa ma da yake,har ya kammala ya zauna. Cikin hanzari ta jawo abincin gabansa tana fadin bari ta zuba masa,idanu ya zuba mata harta kammala ta dago ta dubeshi suka hada idanu,signa ta masa sannan tace "Gashi ya mukhtar sai ci ko" "Qwarai kuwa" ya fada yana janyo abincin gabansa,fatanta daya kawai taga ya sanya koda loma guda bakinsa ne,hakan ya sanya ta bata dukka lokacinta yau ko girkin rana batayi ba cikin gidan ta tsara masa abincin da tasan yafi so. Kamar ta sume don dadi sanda taga ya kai loma guda bakinsa sai kuma ya dakata ya ajjiye cokalin ba tare da yaci din ba,ya dubeta ya sakar mata wani murmushi "Yau tare da ke nake sha'awar muci abincin,matso bismillah" tamkar an sanya guduma an doki qirjinta haka taji amma tayi hanzarin mazewa ta girgiza kai "Haba ai ba girmanka bane,baka ne kai kadai" idanu ya zaro "Au bakison samun matsayi kenan irin na sumayya bayan naga shi kike ta fafutukar samu maza matso,na saba tare muke cin abinci da ita duk ran girkinta" sai ta wani kamme ido a dole sai ta ja ra'ayinsa "Haba muntari wannan ai ba tarbiyya bace,miji na diba kema na diba,kaci kawai ni a qoshe ma nake" kafada ya daga alamun rashin damwa daman ya san da kwanan hakan "To shikenan,ba damuww,bari na kira sumayyan ta tayani ci" kamar ta tashi ta riqo shi haja taji amma don kada ta bada kanta sai ta dake. Daga bakin qofar dakinsa ya coge ya kirata don kada ma ta samu damar sauya masa abincin,cikin mintuna qalilan sumayyan ta shigo dakin,kallonta yayi cikin salo na burgewa "Yayarki ta qi tayani cin abinci shi yasa na gayyatoki ki tayani" sai ta danyi jim duk da murmushin da ta sanyawa fuskarta,ta sani cewa suna hada kwanon cin abinci ne kadai idan ranar girkinta ce. Matsowa yayi da kwanon da sauri gabanta don kada ma ta musanta masa "Oya,matso mana" da sauri fa'iza tayi tsallen albarka ta dira gabansu,ta sanya hannu ta rufe abincin,cikin daurw fuska tace "Nifa gaskiya bana son haka,wannan ai bai kamata ba,ni ina shiga sha'aninku ranar kwananta ne,to nima ban lamunta ba girki kai daya na yiwa shi kuma kai zakaci" kallonta yake a nutse tsaf riqe da habarsa kamar yadda sumayyan ke kallonta,murmushi ya aje cikin nutsuwa "Ikon Allah,to aikam nima ban yarda ba cikin biyu dole ki zabi daya,ko ki tayani ci ko my sumy ta tayani" ya fada yana sareta da idanunsa. Take gumi ya yanko mata,ta fuskanci idan batayi da gaske ba wankin hula zai iya kaita dare,kafin ta kai ga cewa komai nepa suka kawo wuta,haske ya wadaci dakin,ba bata lokaci fuskar fa'iza ta bayyana,wadda tuni gumi ya yiwa jikinta sharkaf,ganin yadda suke kallon gumin ya sanya ta fara nade tabarmar kunya da hauka,wadda ta sake tonawa kanta asiri tsaf a gun mukhtar din ba tare da ta sani ba "Lallai muntari,to me kake nufi?,kana nufin baka yarda da ni ba kenan?,ko kama nufin wani abu na zuba maka a ciki?" "Ni bance kin zuba wani abu ba,amma tunda kika fada din akwai qamshin gaskiya cikin lamarin" miqewa tsaye tayi zata nade tabarmar kunya da hauka "Lallai ma muntari,sharrin da zakamin kenan,sharrin d'a namijin da ake fada kenan yau yazo kaina,eh lallai ba shakka" tsawa ya daka mata ganin zata masa hauka ya miqe tsaye. Kallon fuskarsa tayi ta tabbatar babu rahama a cikinta,take tsoro ya dirar mata abu ya hadu kuma da rashin gaskiya,sai taja da baya ganin yadda yayi dab da ita har tana jin hucin numfashinsa,tana niyyar guduwa ya damqi hannunta har da taji azaba har tsakiyar kanta "Fa'iza!" Ya kira sunanta a matuqar kausashe,hantar cikinta ta kada tamkar zata saki fitsari a wandonta "Basai na bata lokacina nayi doguwar magana da ke ba,wallahi wallahi duk ranar da kika sake yunqurin zuba min wani abu mai kama da sihiri ko surkulle sai kin raina kanki,ki kuma tabbatar daga ranar sunanki SAKAKKIYA!" ba qaramin dukan qirjinta kalmar tayi ba,sam bata koda sha'awar jin wata kalma makamanciyar haka daga bakin muntarin,don ko kusa bata marmarin komawa gidansu wanda yake mata daidai da gidan kurkuku,gidan da talauci yunea babu masifa da rashin tarbiyya ya yiwa katutu. Sakar mata hannu yayi cikin rawar jiki ta juya zata fice don baya da abun cewa,yanayinsa kadai ya tsoratata,balle ko shakka bata yi tasan cewa ya ganta ne muntarin,tsawa ya kuma daka mata ya bata umarnin ta dawo ta kwashe abincinta tasan yadda zatayi da shi baya da buqatar sa,haka ta kwashe kwanukan jiki na rawa ta fice. *kuyi haquri da wannan* *mrs muhammad ce* 📚📚📚📚✍✍✍✍ ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 1⃣9⃣ _________________________ *Bismillahir rahmamir rahim* *ala bi zikrillahi tad'ma innul quluub* ______________________ Mamaki fal zuciyar sumayya,kanta ya daure tamau,ta kasa furta ma komai sai kallon mukhtar da takeyi,ta tabbata ba qarya ya yiwa fa'iza ba domin ba halinsa bane,amma halayyar fa'iza har ta kai haka?. "Ina naki abincin?" Mukhtar ya tambayeta,ta katse tunaninta ta dago ta dubeshi "Ya d'aki" "Ki dauko,ban amince kema. a yau kici ba,ki zuba a leda ki saka a shara a zubar,shiga kitchen ki samar mana abinda zamu ci koda indomie ce sai ki hada mana da qwai" ya fada yana kashingida gami da lumshe idanunsa,tsam ta miqe ta fice don aiwatar da abinda ya umarceta. ************************ Cikin kwanakin ta dage sosai da addu'ar neman tsari,ta san tabbas shartin mutum girma gareshi,zuwa yanzu ta kuma sallama kaidin fa'iza,ta fahimci irinsu matan da suka dauki kishi ko a mutu ko ayi rai,irinsu wadanda zash iya aikata komai saboda kishi,sosai take takatsantsan kan duk wani motsi da kai kawo nata a gidan,ba ruwanta da sabgar fa'izan bare wani abu ya shiga tsakaninsu,koda fa'izan zata shekara tana takalar tashin hankali bata bi ta kanta,don ta riga ta tabbatar cewa akwai banbancin gida da kowaccensu ta fito,bai kyautu ta biye mata su zamana kamar wadanda suka fito daga gurbi guda ba. ******************** Tun da asubahin ranar suka dinga jiyo kakarin amai a tsakar gidan nasu,sumayya ta dubi mukhtar dake gefanta wanda basu jima da kammala sallar asubahin ba kasancewar sun makara basu tashi da wuri ba "Ya mukhtar,kamar kakarin amai nake ji fa a tsakar gida" shi din ma taji amma sam bai da muradin fita,tamkar bazai tanka ba sai ya daure yace "Eh nima naji" yaci gaba da jan carbinsa,ganin yayi shiru ya sanya ta sake cewa "Ya mukhtar ka duba mana,inajin kamar fa'iza ce fa" shiru ya sake mata ganin hakan ya sanya itama ta tsuke bakinta tayi shiru tana ci gaba da sauraran kakarin wanda yake fita tamkar da kayan cikinta,ya kammala azkar dinsa ya haye gado abinsa ya kashingida. Zuciyar musulunci ya sanyata ta kasa daurewa,sai ta miqe ta fidda hijabin jikinga ta nufi qofa,sanya baki yayi ya kirata tare da tambayarta ina zata "Zanje na duba ne,bai kyautu da mutane cikin gidan ba kuma aqi fita a dubata ba,bamu san meke damunta ba" kai ya girgiza "Dawo tausa nake so kimin" "Kayi haquri naje na dubata din minti biyu kawai zan dawo sai na maka tausar" "Idan ban isa da ke ba shikenan kina iya hakan" ya fada yana maida kansa ya kwantar kan pillow,sai jikinta yayi sanyi bata son saba masa ko kadan,saboda haka ta juyo a sanyaye tahaye gadon. A tausashe take masa tausar tana leqen fuskarsa ganin yaqi kulata,har ta soma tara qwalla bata iya jure fushinsa,sai taji kawai ya birkitota ya danneta da rabin jikinsa yana dariya qasa qasa "Raguwa kawai sarkin kuka" ya fada yana lakuce mata hanci,dariya ta saki ya shiga mata cakulkuli daga haka suja shige duniyar ma'aurata wanda hakan shi ya hanasu fitowa da wuri. Qarfe goma ya gama shirinsa zaya fita,a tsakar gida daga can bakin qofar dakin fa'izan suka ganta zaune dirshan a qasa,ta wani wargaje can qafa can qafa tana numfashi da qyar,da sauri sumayya ta qarasa inda take tana fadin "Hasbunallahu lafiya fa'iza?" "Bani da lafiya" ta fada qasa qasa da qyar,ta daga kai ta kalli mukhtar da bai qaraso gun ba,yana tsaye abunsa bakin qofar dakin sumayyan yana daura agogo "Yaya mukhtar,ko asibiti zamu?" Baice komai ba sai hannunsa da ya sanya cikin aljihun wandonsa ya zaro naira dubu biyu ya miqa mata "Gashi sai kun dawo Allah ya kiyaye hanya" ya sanya kansa soro ya tada machine dinsa ya fice. Tana jin rufe qofar gidan nashi ta miqe tamkar ba itace hajaran majaran ba,duk da yanayin jikinta ya nuna bata da qwari sosai,ta sakarwa sumayya harara sannan ta wafce kudin dake hannunta "Babu inda zaki rakani munafuka" ta fada tana shigewa dakinta,kada kai sumayya tayi cikin zuciyarta tana fadin "Allah ka shirya,wato hali zanan dutse". Tana daki tana shafa mai bayan ta kammala wanka ta jiyo fitar fa'izan. Suna zaune zasu ci abincin dare bayan ya kammala komai,tana gabansa tayi kyau cikin kwalliyar lace ja mai adon baqi tana zuba masa abincin data shirya musamman saboda shi fa'iza tayi sallama ta shigo dakin fuskarta qunshe da murmushi hannubta riqe da farar takarda,daya daga cikin kujerun dakin sumayyan ta samu ta zauna,fuskarsa a hade ya dubeta " daga ina kike takwas na dare?"sai ta rausayar da ido "Haba mana muntari,ka tsaya kaji ji da nazo maka da daddadan labari" "Ba wannan ba ki fara amsa min tambayar da na miki tukunna" "Kash,labarin da zan baka yanzun duka yafi wannan muhimmanci,amma tunda ka nace sai kaji to daga asibiti jikina ya rikice sai na wuce gida na kwanta acan,sai da magariba na danji dama dama" shiru yayi ya soma cin abincinsa,ganin haka ya sanya tace "Ka godewa Allah muntari,Allah ya kusa cika maka burinka da ka dade kana fata,ka kusa zama baba,an auna ni ina da juna biyu har na wata biyu". Qwarewa yayi da lomar abincin da ya kai bakinsa,sai ya soma tari babu qaqqautawa,cikin hanzari sumayya ta miqa masa ruwan tana jujjuya maganar cikin ranta,indai hakan gaskiya ne to ya tabbata ITACE BATA HAIHUWA?. Sai da ya sha ruwan sosai sannan ya ajjiye cup din,hannu kawai ya miqawa fa'iza wadda keta doka murmushi tana tunanin farinciki ya sanya mukhtar qwarewa,tabbas burinta ya kusa cika,zaman sumayya cikin gidan ya kusa zuwa qarshe,ta kusa raba mukhtar da kowa sai ita. Takardar ta miqa masa don ta fahimci ita yaje son gani,ya bude ta sosai ya shiga nazarinta daga farko har qarshe,gashinan rubuce a jiki,cikine dan sati takwas,amma sati takwas fa suka rubuta,har ya bude bakinsa zaiyi magana sai kuma ya fasa,a yanzun ba muhallin yin maganar bane akwai muhallin yinta,saboda haka ya nannade takardar ya cusa cikin aljihunsa ya janyo abincinsa yaci gaba da ci. Dukkaninsu sumayyan da fa'iza sai suka zuba masa ido cikin mamakin ganin bai ce komai ba,fa'izan ce cikin zaquwa da son jin abinda zaya fadi din tace " ya baka ce komai ba muntari,Allah ya yi maka kyautar da ka dade kana jira amma banga ka nuna komai ko kace min komai ba"kansa ya daga ya dubeta "Naji ai kuma na gani,zan kuma magantun amma lokacin yin maganar ne baiyi ba,jeki sai da safe Allah ya inganta ko?" Jiki a sanyaye ta miqe ranta cike fal da mamaki,tayi zaton zai dauketa ne suyi rawa suyi juyin murna,ta yadawa sumayya habaici yadda taga dama,amma duk da hakan ai lokaci na zuwa. A sanyaye sumayya ta dubeshi bayan fitar fa'izan "Amma yaya mukhtar kamar bai dace ba abinda kayin,sai nake ganin murna ya kamata ka nuna irin wadda baka taba nunawa ba,d'a fa da kuje muradi shi Allah zai baka?" Kansa ya daga yana dubanta fuskarsa qunshe da murmushi,sai kuma taga ya qyalqyale da dariya "Yanzu my sumy koda haka ne ya cancanci nayi murnar hada iri da waccar matar?,fa'iza fa? Wadda ni da ke duka munsan halinta,bani da muradin samun zuriyya da kowacce mace a duniya sai ke,kece nakeso ki zamo ta farko da kika samamin zuria,ki bar maganar nan don Allah bana so in sake jin bakinki game da ita indai na isa da ke" "Insha Allahu" ta fada zuciyarta na karyewa,ina ma inama,ina ma tana da qarfin yaqi da QADDARARTA?,ina ma tana da ikon baiwa kanta haihuwa?,ina ma ace zata iya samarwa da mukhtar cikon farincikinsa,duk da bata da wannan ikon amma bata jin dai dai da daqiqa daya bakinta zai rufu ko ya gajiya wajen roqon mai badawar da ya albarkaceta ya azurta ta ya kuma bata haihuwa saboda karamci tausayi da kuma jin qansa,sai tayi qas da kai hawaye na diga,da sauri ya daga kanta suka hada idani,da murmushi yake dubanta gami da kada kai "Bana so sumayya kin sani,ko ya kike sumayya haka nake sonki,sonki so ne na fisabilillahi cikin zuciyata ba don wani abu da kike da shi ko kika rasa ba" bata buqatar itama bata ransa saboda haka ta saki murmushi tasanya hannunta da kanta ta goge hawayen. Sosai fa'iza ta soma tsiro da tsurfa kala kala,gobe tace wannan jibi tace wancan,da fari sumayya na qoqarim yo mata mukhtar na fuskantar haka yace bai yarda ta sake hidimta mata kan komai ba,idan tana so ta tashi ta girka da kanta,nan ma ya fuskanci an shiga babin barna da almubazzaranci shima ya soke yace taci duk abinda ka dafa ko ta haqura,sosai abun ya qona ranta,duk yadda taso samu yaqi samuwa. Sai aka tsiro tsirfar zuwa dubiya kuma,daga bangare mukhtar zuwa na fa'izan,saidai ko da wasa bata ga qafar yaya yahansu ko yaranta ba,saidai fadima da ta zo,ita din ma sama sama fa'izan ta mata sannan ta tattarata ta watsar,sai data gaji da zama ta ja qafafunta ta tafi,gidan sai ya zama kamar wani gidan biki,wuni sumayya take tana karbar habaice habaice daga bakunan maziyartan gidan kala daban daban,bata taba jin tsananin so da buqatuwar haihuwa ba irin na wannan karon,sai ta zama wata mai raguwar zuciya,mikin data jima tana dannewa cikin zuciyarta na rashin magaji ya zame mata sabo fil,duk sanda suka goranta mata sai ta kasa daurewa har sai ta zub da qwalla ta rage radadin da take ji cikin zuciyarta. Cikin hakan mukhtar ya fuskanci ta fara rama,juyin duniya yayi tambaya tace masa lafiya babu abinda ke damunta,tilashinsa ya haqura saidai ya zuba ido sosai bisa yadda lamuran gidan ke gudana. A irin haka katsaham ya dawo gida ranar qarfe uku da minti talatin da takwas ana shirye shiryen kiran sallar la'asar,wasu masallatan ma har sun fara kiran,a lokacin tana qofar kitchen zaune tana hada girkin dare,yayin da dakin fa'iza ke qunshe da baqin da qafarsu bata daukewa zuwa gidan da sunan dubiya,suci na rana wani lokaci idan an kammala na dare ma suci sannan su tafi,musamman ranar girkin fa'izan wanda taso qwarai a dauke mata girki mukhtar yace bata isa ba. Yazo kuwa a gaba dai dai sanda suke jeranto gorin nasu,bai kula kowa ba sai da suka kammala duk abinda suka zo da shi suka karkade qafafunsu,kowacce tazo fita sai tayi turus ganin mai gidan zaune tsakar gida kusa da sumayyan yana tayata aikin kitchen duk da babu wanda yacewa kowa komai cikinsu,sai su kama borin kunya kana su fice sumi sumi. Sai da suka gama ficewa tsaf sannan yayi kirab fa'izan ya kafa mata sharudai,duk randa ya sake ganin qafar wani ya shigo har cikin gidansa ya ciwa matarsa mutunci to sawunta a likkafa ta hada kayanta ta bisu tum gabanin ya dawo gidan,wannan hargagi shi ya sake janyo tsana da jin zafin sumayya mai yawa a zukatan mutane da yawa masu qinta musamman uwar tafiyar fa'izan,ta kuma sake cin alwashi mai yawa akan sumayya,wannan kuma shi ya kawo taqaitar zirga zirgar 'yan bani na iya din *RANA DUBU TA BARAWO* Tunda ta tashi yau kanta ke ciwo,don haka a daki ta kusa yini,koda yaranta suka zo ma gida ta korasu don bata son hayaniya,naana ce kawai ta zauna kasancewar duka ta fisu nutsuwa. Har tayi baccin qailula ta farka yarinyar na gefanta zaune,ta miqe tana salati duk da cewar kan nata ya rage ciwo amma bai sauka ba duka,ta cire hijabin data kwanta da shi sabida zazzabin da ta fara ji ya fita tsakar gida ta dauro alwala,cikin takaici taje duban tsakar gidan yadfa yayi kaca kaca,girkin fa'iza ne amma bata damu ta gyara ba haka al'adarta take,matuqar sumayyan bata gyara ba to saidai gidan yayi ta zama haka,to ita din ma bata da qyashi son jiki ko ganin ido batq damuwa wai don bata gyara ba yin abinta take,hatta da wankin toilet zata iya rantsewa bata taba ganin fa'izan tayi ba tunda ta shigo gidan. Tana shiga d'aki ta sanya naana taje ta share mata tsakar gidan ita kuma ta tayar da sallah. Kafin ta kammala sallar nanan ta gama kasancewarta yarinya mai kazar kazar da son aiki shi yasa sumayyan ke sonta,ta dawo gefanta ta zauna tana kallon sumayyan har ta idar. Tana shafa addu'a ga mamakinta fa'iza ta shigo d'akin dauke da cooler dinta ta dire tayi ficewarta,tana nannade abun sallar sai ta lura naana nata kallonta tana kuma satar kallon kwanon abincin,tasan akwai magana a bakinta ne ta kasa fadi,kuma hakan yana da nasaba da hanasu dauko magana daga wani guri su gaya mata. Har ta koma saman kujera ta kwanta don bata da sha'awar cin komai taga yari yar naci gaba da kallonta idan ta lura da kyau ma kamar qwalla ce a idonta,a hankali ta miqe ta zauna tayi kiranta,yarinyar ta iso gabanta ta zauna "Me ya faru?me ya sameki naga kamar zakiyi kuka,ko yunwa kike ji?" Sai ta girgiza kai "To mene ne gaya min" cikin raunin murya kamar kukan zai qwace mata tace "Anty sumayya don Allah kada kici abincin nan" sai sumayyan ta hade rai tana dubanta "Me yasa?" "Anty,naga amarya ta bude leda sanda kika sakami yin shara tana ta leqe sannan ta koma kitchen ta bude flask din ta debo wani yalon abu ta barbada a ciki ta juya ta rufe ta wanke hannunta" sosai taji gabanta ya fadi,saidai bata son ta bawa yaran damar da zasu dinga labe ko qoqarin dauko gulmar fa'izan suna kawo mata,saboda haka ta sake hade rai "Ke me yasa kika labe kina kallonta?" Da sauri ta girgiza kai "Allah ba labewa nayi ba,tsintsiyar ce ta kunce a bakin kitchen din sai na tsaya daureta shine fa na gani" shiru tayi tana jinjina zancan cikin zuciyarta,sam bata son ta baiwa kanta qofar da zata zargi fa'iza kan abinda idanunta basu gane mata ba,saboda ko ubangiji ya fadi cewa HAQIQA WANI SASHI NA ZATO ZUNUBI NE,kai kawai ta kada bayan ta koma ta kwanta "Shikenan,bazan ci ba,amma kada ki gayawa kowa abinda kika gani kinji nana?" "To anty" ta fada tana kada kai "Zan tafi anty lokacin islamiyya yayi" ta amsa kana ta laluba gefanta ta dauko alawa guda uku 'yan naura biyar biyar da takan ajjiye saboda su ta miqa mata,bata fiya son basu kudi ba don kada su saba da su ta bata ma iyayensu tarbiyyar yaransu,don ba kowa keson ka yiwa yaronsa kyautar kudi ba sabida gudun kada su saba da su,randa kuma basu samu ba su nema kota halin qaqa,Allah ya kiyaye. Sosai ta zurfafa cikin tunanin maganar da naanan ta gaya mata,sai ta kauda tunanin daga ranta ta shiga addu'a cikin zuciyarta,ALLAHUMMAK FINIHIM BIMA SHI'ITA ta dinga maimaitawa cikin zuciyarta,tana fata koma mene Allah ya mata maganinsa ya sanya tsarinsa a gareta har wani baccin ya sake daukarta. Koda ya dawo yau bai samu yin wanka ba sai bayan yayi sallar magariba,yasan cewa ba samun ruwan wankan nasa zaiyi ba saidai ya debawa kansa,hakan ne ya sanya yana shigowa ya tara ya shiga bandakin,har ya shiga ya manta da towel dinsa hakan ya sanyashi fitowa. Da hanzarinsa ya dawo zai shige,saidai wani abu da ya fisgi zuciyarsa ya sanya shi dawowa da baya,abinda ya faru watannin baya yake ji a jikinsa tamkar zai sake maimaita kansa ne a yau,a hankali ya zarw slippers dinsa ya taka zuwa qofar kitchen din,idanunsa suka sauka kan cooler din sumayya dake bude gaban fa'iza wadda ke dauke da dafa dukan shinkafa qarshen qurewar girkin fa'iza kenan. Cike da hanzari fata da buri take barbada garin cikin abincin,don ta fuskanci cewa sam sumayya ko bude kwanon abinci bata yi ba,amma wannan karo taci alwashi kota halin qaqa sai ta sanya ta taci ko loma daya ce kai tama yankewa kanta ko dura ce sai tayi mata. Tana karkade hannunta cikin nishadi taji caraf an riqe hannunta,tun kafin ta fahimci wake da alhakin riqe mata hannu gabanta yayi wata mummunar faduwa,a hankali tamkar wadda ta warke daga cutar laka ta daga kai suka hada idanu da mukhtar,wani matsanancin tsoro ya shigeta wanda kadan ya rage ta saki fitsari cikin wandonta sakamakon yadda taga idanunsa sun sauya kala cikin sakannin da basu wuce biyar ba. Wani lafiyayyen mari ya yarfa mata wanda kafin ta ankare da a wanne hali taje ciki ya sake bin fuskarta da wani,hakan ne ya tilasta mata sakin wata gigitacciyar qara saboda ji taje tamkar fuskarta na shirin tsagewa ne,wannan shi yayi silar zaburar sumayya ta miqe ta fito a razane tana tsammanin ko gobara ce ta kama gidan nasu tunda ta bar fa'iza ne cikin kitchen. Fitowarta yayi dai dai da wurgo fa'iza da mukhtar yayi zuwa filin tsakar gidan "Subhanallahi" sumayya ta fada da qarfi tana nufar inda fa'iza take don ta d'agata "Kika tabata sai mun samu mummunan sabanin da bamu taba samun makamancinsa ba ni da ke,sai nayi matuqar saba miki" taji mukhtar na ambata cikin wata kakkausar murya da bata taba zata yana da ita ba. Yadda ya sake nufo fa'iza gadan gadan ya tsoratasu baki daya,sumayya ta janye gefe jikinta na rawa,bakinta na ambatar duk wata addu'a da tazo bakinta tare da neman agajin Allah ya kawo sauqin kowacce iriyar masifa da zata faru yau a gidan,yayin da tsoron da fa'iza taji ya sanyata sakin ihun neman agaji domin tsantsar bala'in da zata fuskanta ya fito muraran cikin idanun mukhtar tun kafin ya kai ga aiwatar da shi a kanta. *mrs muhammad ce* 📚📚📚📚✍✍✍✍ ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 2⃣0⃣ _____________________ *bismillahir rahmanir rahim* *wa may yatawakkal alal lahi fahuwa hasbuh,innallaha baligu amrih* _____________________              Duban sumayya cikin shaqaqqiyar murya yace "Jeki ki rufemin qofar gidan" tsayawa tayi tana dubansa jikinta na rawa,ta fuskanci me yake nufi,wato don kada ma ihun fa'iza ya sanya ta samu masu kawo mata dauki kenan "Jeki ki rufemin qofar gida nace" ya maimaita cikin tsawa ganin bata da niyyar tafiya,jikinta na rawa ta wuce taje ta rufo,bata kai ga dawowa tsakar gidan ba kuwa taji ana bugun qofar gidan,daga inda yake ya bata umarnin kada ta bude ta dawo ciki.              Ga mamakinta fa'iza ke bawa mukhtar haquri hannu bibbiyu take roqonsa,bai ko dubeta ba sai sumayya da ya kalla "Shiga kitchen ki dauko min cooler dinki wadda take zuba miki abinci" babu musu wannan karon ta shiga ta fito da ita,ya nuna maga gaban fa'iza da ido ta dire anan din ta koma gefe ta tsaya jikinta na rawa.               "Maza bude ki cinye abincin dake ciki yanzu yanzun nan" wani rugugin aradun tashin hankali ya rufto mata,tirqashi,ai data ci abincin ciki gwara mukhtar din ya kwana ya wuni yana jibgarta,domin cin abinci koda shinkafa qwaya tak dake ciki ne dai dai yake da ban kwana da duniyarta,sai ta zube a qasa tana sake roqarsa yayi haquri kuskure tayi kuma ba zata sake ba,wani murmushi mai tauri da d'aci ya saki "Ko baki fada ba ai dama har abada ba zaki sake aikata irn wannan mummunan aikin ba cikin gidan mukhtar,afuwa daya da zan iya yi miki idan kina da buqatarta shine ki dauki abincin nan ki cinye salun alun" "Wallahi muntari bazan iya ci ba,zan iya rasa rayuwata,kayi haquri"sai yayi turus ya zuba mata idanu cike da fargaba da kuma bacin rai " kice ma niyyar kisan kai kika yi?,sumayyar tawa zaki kashemin?"ya fada cikin wani irin zafin rai,da sauri ta girgiza kai tare da sake debo wata rantsuwa don gyara baran baramar da take gab da sake tafkawa,ganin taqaddamar take qarewa har muntarin na nade hannu zaiyiwa fa'iza dure ya sanya sumayya dake gefe kamar mutum mutumi magantuwa,ta tabbata tunda har fa'izan ta toge kan bazata ci ba komai zaya yi mata ya nuna akwai wani mummunan abu da ta qulla cikin abincin,wanda su kansu basu san meye ba,ba kuma su san sakamakon da hakan zaya haifar ba idan taci din "Ya mukhtar,ka qyaleta don Allah,koma meye tunda Allah ya kubutar da ni bayan muna da masaniyar ba wayon mu bane sai mu gide masa ko?" "Ok,haka ne fa" ya fada yana gyada kai tare da duban sumayyan,saidai kallo daya tayi masa ta fuskanci bawai yana nufin ya haqura din bane "Shikenan ki bar cin abincin" ya fada yana juyawa zuwa dakinsa.            Murmushin nasara da farinciki fa'iza ta saki tana duban sumayya duba na wulaqanci "An gaya miki haihuwa kayan banza ce?,ni na sani ko darajar cikinsa dake jikina kawai ta isheni,banza mara amfani ke zaki ci gaba da diban kayan takaici juya kawai wad...........".                Fitowar mukhtar dauke da belt ita ta maqale sauran zazzafar maganar da take da burin ci gaba da yabawa sumayya,tsayawa yayi gabanta yana gyara belt din tare da fadin " babu batun cin abinci amma wallahi baki ci banza ba,sai na fanshe wahala da baqinciki rashin zaman lafiya da rashin kwanciyar hankalin da kika shigo kika haddasawa gidanmu,kinga gobe sai ki koyi darasin zaman duniya"kafin su ankara ya fara jibgarta tako ina,tsoro da firgici ya hana sumayya tabuka komai,abinda iyatsawon rayuwarsu bata taba gani mukhtar yayi ba,duka duka koda ga qaramin yaro bare ga matarsa ta aure,lallai babu shakka fa'iza na shirin koyawa mijinsu mummunar aqida idan bata tashi tayi da gaske ba,don daga haka miji ke farawa idan ba'ayi wasa ba.                Ta nufeshi da hanzari da niyyar dakatar da shi saidai tuni ya hankadata gefe cikim zafin rai ba tare da ya san yayi ba,a rashin sa'a ta fadi kuwa kan hannunta wanda sai da ya bada wani sauti ta saki kalmar wash! Cikin azaba,bata sake yunqurin tashi ba ta zubawa sarautar Allah ido.               Sai da ya tabbatar ta daku sannan ya dakata yana dubanta "Ki tatattara duk wani tarkace naki da kika san kin shigo gidan nan da su ki koma inda kika fito,na sakeki saki biyu" wani ihu ta kurma kamar zautacciya tana shirin miqewa tsaye "Wallahi baki isa ba muntari,zama daram wallahi sai na haife abinda ka qusa min ma rainshi sannan" wata dariya ya saki sannan ya miqa hannunsa ya fincikota tare da fusge zanin jikinta.                Idanu sumayya dake zaune dirshan kan sumunti ta qwalalo ganin abinda ya fado jikin fa'iza wanda da shi ake canza tafiya ake burga ake kira ciki ne,cikin ma kuma wai na mukhtar dinta,tarin zannuwa ne aka hadasu aka qulle cikin zani daya fa'izan ke daurawa "Indai ciki ne gashi nan yau kin haifeshi ko,rainonsa kuma sai ki ajjiyemin kayana  ko ni zan raini abu na" ya fada yana qyalqyalewa da dariya,gaba daya wani muzanci ya kama fa'iza,me kenan?,meke shirin faruwa?,dama mukhtar yasan ba ciki bane shi yasa ya qyaleta,shi yasa bai nuna farinciki ba da result din bogi data bashi,bata kammala karanta wasiqar jakin ba maganar mukhtar din ta kuma katseta "Kin maida mukhtar wawa shashasha jaki irinki ko?,don kinci sa'a na qyaleki tun lokacin ban hukunta ki ba kan raina kin wayo da kikayi ba?,to wallahi kada ki yadda na fito a wanka na taddaki cikin gidan nan,idan ba haka ba kowanne laifi da kika aikata cikin gidan nan iya tsawon zaman da kikayi cikinsa sai na miki hisabinsa tare da hukunci akansa daya bayan daya" ya fada yana yarda belt din ya dauki sabulunsa da ya watse gefe ya shige wankansa.              Cikin tsananin radadin ciwukan da taji ta miqe ta shige dakinta,bata yi ko minti biyar ba ta fito dauke da jaka da hijabi,har ta gota ta dawo da baya ta dubi sumayya "Wallahi wallahi kada ki dauka kinci nasara a kaina,yanzu aka fara wasan" ta fada tana mai ficewa da sauri jin motsin mukhtar na niyyar fitowa saga bandakin.             Bin qofar data fice din yayi da kallo domin yaso ya taddata,sai a lokacin ya maida dubansa ga sumayya "Me take gaya miki?" Bata amsashi ba sai niyyar miqewa da take amma ta kasa,ganin haka ya sanyashi qarasa gurinta da sauri yana nufin riqe mata hannu ta saki qara da sauri sabida gun ciwon ya taba "Subhanallahi,hannu kuma sumayya?" Ya tambayeta yana duban gun,banza tayi da shi cikin son yunqurin tashi yayi niyyar taimaka mata da sauri tace "Barni,bana so" ta tattara qarfinta ta miqe ta nufi dakinta.             Binta yayi a baya da sauri,tana shirin shiga dakin ya cafkota,qara ta saki saboda hannun ya riqe,sosai ya murde hannun har sai da ya bada qara alamun inda ya gulle ya koma dai dai,kafin ya kammala ta gama hada gumi,jikinta yayi laushi ya jata cikin jikinsa yana goge mata hawaye da gumin da ta hada.          Cikin kujera ya ajjiyeta yana maida ajiyar zuciya ya fice zuwa dakinsa. _busy!busy!!! Wlh_ *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍✍✍✍ ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 2⃣1⃣ *innal laha ma'assabirin*             Cikin qanqanin lokaci yayi wankan ya shirya cikin shadda sea grean,sosai tayi masa kyau,itama sabuwa ce cikin sabbin dinkunan da yayi shima,ya kulle gidan suka fito.            Sai daya bude mata gidan gaba ta shiga sannan ya zagaya shima ya shiga daya bangaran yana duban ta,yadda fuskarta ta cika da farinciki tana masa addh'a,sosai yaji dadi cikin zuciyarsa shima,yayi bismillah ya tada motar suka fice daga layin a hankali.                Suna tafe suna hirarsu cikin nishadi da walwala har suka iso qofar gidansu sumayyan,cikin zumudi ta bude ta fice mukhtar ya bita da kallo yana murmushi,tamkar yau ne ta fara zuwa gidan sai murna take.                A tsakar gida ta tadda maman zaune saman tabarma sai fitilar qwai dake kunne a gefanta kasancewar babu wutar nepa,ba kowa tsakar gidan sai ita kadai "A'ah,sumayya da kece haka da daren nan?" Mama ta fada tana sake bude tabarmar da take kai,gefanta ta qaraso ta zauna bakinta yaqi rufuwa "Wallahi mama nice,ke kadai ce?" "Eh duka sun tafi makarantar dare,amma gab suke da dawowa" "Malam fa?" "Sun tafi dubiya asibitin murtala shi da abubkar,maqwafcin mu malam sule ba lafiya" "Ayyah baba sule,Allah ya sawwaqe......bari na yiwa yaya mukhtar din magana to ya shigo ku gaisa" "Au tare ashe kuke......maza shigo da shi" inji mama tana janyo hijabinta dake gefanta ta zura.              Cikin girmama juna suja gaisa sannan ya fada mata motarsa ya kawo su sa mata albarka,tayi kuwa addu'a sosai don babu damar ta leqa malam din baya nan,nan ya fice qofar gida ya barsu.               Bai jima da fitar ba mama ta matsa mata ta shi su tafi tunda zasu gidan yahanasu,ta miqe suka yi sallama da maman ta fito.              Sai ta tadda mukhtar din da su zainab da halima ya bude musu motar suna ciki,malam kuma yana gefe da alama isowarsa shi kenan don gaisawa ma suke,ta qarasa cikin girmamawa itama tabi sahun mukhtar ta duqa ta gaidashi sannan ta gaida ya abbakar,ya shiga tsokanarta ta hanyar cewa tayi qiba ta zama lukuta me mukhtar ke dura mata ita kadai,ta kasa tanka masa sai dariya da takeyi kanta a qasa saboda kunyar malam da takeyi.           "Ai sai ku wuce ko kada dare ya muku" cewar malam yana shigewa gidan bayan sunyi sallama,mukhtar ya fidda dubu biyu ya bawa su halima yace su sayi kayan kwalliya,qin karba sukayi sai da sumayyan ta sanya baki sannan suka amsa auna godiya suka shige gidan.              Shiru ya biyo baya cikin motar,mukhtar ya sauke ajiyar zuciya sannan yace "Tarbiyyan gidanku na birgeni sumayya,naso a ce ina da wani dan uwa namiji da babu shakka sai na aura masa halima ko zainab" murmushi kawai sumayyan tayi sabida tasan koda yana da dan uwan babu ta yadfa su yaya yahanasu su yadda su sake hada zuri'a da 'yan gidansu.          Mintina qalilan suka isa gidan,ya kashe motar ya fice ta bishi a baya bakinta cike da addu'a.            Dukansu suna tsakar gida zaune kan tabarma suma saboda zafin dake dan busawa a 'yan kwanakin,ga matsalar rashin isashshiyar wutar lantarki da muke fama da ita ta kowanne bangare na qasar nan.            Da fara'ar ta ta amsa sallamar amma jin muryar sumayya yasa ta gintse 'yar fara'ar data yo tsaraba,jamila dake gefen tabarmar ta matsa ma mukhtar,yayin da sayyada taqi motsawa ko su samawa sumayya wani abun zaman,hakanne ya sanya mukhtar din dubanta fuska a hade "Ke,tashi ki bata guri" tuni ta miqe saboda tana shakkarsa kuma tasan halinsa sarai,daki suka shige ita da jamilan baki daya.              A girmame yake gaisheta ta amsa sannan sumayya ta gaidata,sama sama ta amsa mata suka shiga hira da mukhtar din.            Jamila ta fito da ruwan pure water mai sanyi guda biyu ta cup ta ajjiye gaban mukhtar din sai ya turasu duja gaban sumayyan yana cewa "Bude kisha,kince min kina jin qishirwa dazu" zuciyar yaya yahansu ta tunzura,ta dinga jifansu da harara tana qwafe da su,ya maida dubansa gun yaya yahanasun "Mota na kawo miki ki gani yaya,ta iso dazun da safe" sai ta harareshi "Au shine sai yanzu kaga damar kawo min na gani kenan sai da ka gama nunawa duniya" "Ba haka bane,data iso din ma a gareji na wuni ana mata service,ina dawowa gida kuma nayi wanka naci abinci muka taho kawo miki" "Sai kace makaho da baka iya tahowa kai kadai,kai Allah ya kyauta,ya warware mana wannan masifar" ta fadi cike da haushi da tsana,don ya kauda zamcan don kada yayi nisa sai ya miqe yana fadin suzo su ga motar,haka suka miqe suka fice suna hayaniyar murna,tana zaune gun burinta kawai yace ta taso su tafi,Allah ya taimaketa sayyada ta leqo tace ta fito su tafi.          Tana zaune gaban motar shima haka amma sai zuba zance yayan taje wanda ya hana musu tafiya "To Allah ya tsare ya rabaka da sharrin masu sharri,Allah ya qara budi ya kawo masu yi maka addu'a ya rabaka da wannan matsiyacin zaman kadaicin" bai amsa ba ya ciro dubu uku ya miqa mata yana fadin " ga wannan ku qara"hannu tasa ta karba zata sake barkewa da wani surutun ya samu yaja motar suka wuce.            Duk yadda taso boye damuwarta amma sai da ya fuskanta,kan dole yake zuwa da ita gidan saboda yaya yahanasun dolensa ce,amma banda haka da tuni ta bar zuwan gidan,da tuni ya yanke alaqar dake tsakaninsu,kan hanya ya tsaya ya siya musu yoghourt manyan roba biyu masu sanyi da tsire mutumin sumayyan don duk ya faranta mata,a hankali ya dinga janta da hira da labarukan ban dariya,sosai ta sake sake masa jiki tana qyaqyata dariya wanda hakan shima ya masa dadi. *~TSUGUNNE BATA QARE BA~*               Shi da ita duka suna zaune cikin falon nata da ya sake gyara mata shi,sanye suke da kayan barci saidai sai banbanta gun zama da ayyukan yi,shi yana zaune kan qaramar kujera ta zaman mutum daya dauke da computer yana aiki,yayin da ita ke kwance saman doguwar kujera tana kallo a tashar mbc inda suke hasko film din ashqui,kusan bata taba zama ta kalli film din complete ba sai yau.            Dakin ya dauki shiru kasancewar kowa ya bada muhimmanci kan abinda yakeyi,wayar mukhtar dake saman jakar laptop dinsa ta dauki tsuwwa,ya dubi wayar sai yaga baquwar lamba ce,kusan ya jima da daina daukar ire iren lambobin,to amma sunyi da wani costumer dinsa zaya kirashi kan wasu kaya da zai siya a shagonsa,sai yayi zaton shine saboda haka ya daga "Assalamu alaikum" mukhtar din ya fada,kana yayi jim kusan daqiqa talatin sannan ya sake cewa "Wacce zainab?,daga ina?" Ya sake yin shiru na sakan biyar sannan ya ja tsaki ya kife wayar yaci gaba da binda yakeyi.             Ba'a cika minti biyar ba wani kiran ya kuma shigowa,ya dubi wayar ba tare da yayi niyyar dagawa ba,lambar dazun ce dai sai ya sake dauke kansa yaci gaba da abinda yakeyi din ransa na quna.             Kiran da aketa maimaitawa a kai akai shi ya dami sumayya har ya ja hankalinta,tana daga kwancen ta dubeshi "Don Allah yaya mukhtar ka daga,wallahi ta dameni" ta fada a shagwabe,bai dubeta ba yace "Bazan daga ba,barta kawai" sai ta maida kallonta din batason ko gu daya ya wuceta.            Bai haqura ba mai kiran yaci gaba da nacin kiran har sai da sumayyan ta sake tankawa ya bata amsa irin ta dazun,sai ta tashi zaune tana gyara wuyan rigar barcinta da ya salube tare da fadin "Shikenan,bari ni na daga maka ko a bar kunnuwanmu su huta" "Kema ba zaki daga ba" ya fada bayan ya dago idonsa wannan karon ya dubeta,dariya ta saka tana tunanin wasa yake mata,dai dai lokacin da kiran ya sake shigowa ta sanya hannunta da sauri ta suri wayar ta daga ta kara a kunnenta tana masa gwalon taci nasara ta daga ba tare da wafce ba kamar yadda yayi niyyar yi da farko.             A hankali ta cire wayar daga kunnenta qirjinta na bugawa jin muryar macace tana gaya mata mukhtar take nema,miqa masa wayar tayi jiki a sanyaye. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 2⃣2⃣ _______________________________ *Bismillahir rahmanir rahim* *ma yaftahillahu lin nasi min rahmatin fala mumsika laha,wama yumsik fala mursilalahu bin ba'a dihi* _Allah ka sanya mu daga cikin wadanda zaka yita saukar da rahamarka garesu,alfarmar sayyadina rasulullahi S A W_ _______________________________          Hannu ya sanya ya amsa,sai ya latse wayar ya kasheta baki daya ya ajjiyeta gefansa yaci gaba da aikinsa,wanda yana duba yanayin ginin gidansa wanda a yanzun ake daf da kammalashi "Sai da na gaya miki kada ki daga" ya fadi idanunsa na kan computer din,cikin wata iriyar mutuwar jiki da kasala ta lallaba ta koma kan kujerar data tashi taci gaba da kallonta,saidai sam ta daina fuskantar komai,wani abu mai kama da zazzafan kishi ne ya shiga taso maga,ta dinga ambaton sunan Allah har zuwa sanda suka qare film din ta koma dakin gadonta.            Sam bacci yaqi zuwa mata face nazari da take tayi ita kadai har mukhtar din ga gama abinda zaya yi ya cimmata akan gadon,jikinsa ya janyota sannan cikin taushin murya yace "Meke faruwa ne sumy uhmmm?" "Babu komai" ta furta can qasan maqoshinta "Ban santa ba nina sumayya,abinda kawai na sani customer dina ce,tazo shago na siyayya ita da 'yan uwanta,ta buqaci number dita saboda koda zasu tashi zuwa wani lokaci,tun daga ranar take matsanta min da kira ba yau ta fara ba,na gargadeta na kuma ja mata kunne amma bata ji ba,wannan shine abinda na sani" shiru sumayyan tayi taba nazarin maganar,sosai wani kishinsa ke taso mata "Allah ya kyauta" ta iya cewa kawai,sai ya juyo da ita ta fuskanceshi "Haka ma kadai zaki fada ko?,wato ma baki kishi na kenan sumayya" ya fada yana matse mata yatsu har sai da taji zafi ta saki 'yar qaramar qaara,sai ya hade bakinsa da nata cikin wani irin salo da ya mantar da su komai          ***     ***       ***             Ta maida kiransa ya zame mata tamkar ibada,idan ma bai daga ba zata yita jelan tura masa saqonni iri iri wadanda dukkaninsu a akwatin share saqonni yake zuba su.            Sau tari wani abun dariya yake bawa sumayya,tana mamakin yadda mata suka sauke farashinsu ya fadi qasa warwas,tana jin inda ita dince sam ba zata iya haka ba,ko babu komai akwai kunya irin ta diya mace,duk da ta sani cewa koda matar ma'aiki ta farko nana khadijatul kubra ta nemi ma'aiki da ya aureta,amma bata irin wannan sigar bace,ta siga ce mai tsafta,mai ban sha'awa mai cike da hankali nutsuwa da kuma KARAMCI,sa'an nan ta nemi a aureta a inda take da yaqinin samun qauna da kulawa,a 'inda ko babu qauna akwai tausayi girmamawa da kuma MUTUNCI.             Sau da dama idan saqonni da kiran ZAINAB ya ishi mukhtar yakan zauna yayita sababi,sai ta sa baki da haqurqurtar da shi,wani lokaci kuma ta zolayeshi shi kuma ya bita da harara,ko ya ranqwashi kanta,a haka lamarin yaci gaba da wanzuwa har tsawon watanni uku cur babu sassauci haka na babu sauyi. *Wace ce zainab?*        Zainab haifaffiyar garin kano wadda ke zaune cikin unguwar sheshe,suna da rufin asiri dai dai gwargwado,gida ne wanda ya kasance ya samu rarrabuwar kai da sabanin mabanbantan ra'ayi ga jama'ar gidan,maman zainab itace amarya a cikin gidan yayin da zainab ta kasance 'yarta ta uku baya ga maza biyu da ta biyo,mama amarya mahaifiyar zainab ta zamewa mata biyu data tarar cikin gidan qarfen qafa,babu wanda ke da fada a ji cikin gidan sai ita,ita ke juya kowa ciki harda mai gidan,taci karenta babu babbaka har zuwa lokacin da Allah ya yiwa mai gidan rasuwa aka raba musu gado kowa ya kama gabanshi,koda zainab tayi auren fari mama amarya ba irin mijin da take so zainab din ta aura ba kenan,miji take so ta samu koda ba mai kudi ba amma yana da abun hannunsa,wanda zasu maqale suyita tatsarsa suna tara abun duniya,talaka ne bashir futuk,qarfin soyayyar da zainab din ke masa ya rufe mata idanu har ta aureshi,tayi aurenta ne bayan data kammala kataratun ta na NCE a federal college of education kano wato FCE,kusan zamu iya cewa bashir abokin karatunta ne tare suke daukan lactures course dinsu daya,bayan kammala karatu kuma aiki bai samu ba,sai shagon wani maqocinsu dake kasuwa yake zuwa yana masa jira ana biyansa.          Duk iya yadda mama amaryan taso ta fahimtar da zainab din taqi fahimta,duk da kusan cewa babu abinda ta baro na daga halayen uwarta,bata cimma nasara ba sai bayan da akayi auren,sukaci soyayyarsu suka cinye,a lokacin da gishiri ya fara fita daga kan kaza ne zainab din ta fahimci bashir bai dace da ita ba,daya bayan daya ta dinga bin sawun duk wata dabi'a da huduba da uwar ke azata kai.         Cikin watanni biyar kacal suka balle auren,a lokacin tana dauke da ciki na watanni uku,duk yadda suja zo zubar da cikin abin ya gagara,a cewar mama amaryan baya da wani amfani tunda ubansa bai mallaki komai ba bare su saka ran samun wani alfanu tattare da shi.           Saidai kuma ina,maqaginsa ya riga ya QADDARA sai ya taka doron qasa,bayan wata bakwai ta haife yaronta namiji,ko yayeshi bata yi ba ta soma balle zawarci mai lasisi,a lokacin ta sake haduwa da qawaye kala kala idanunta suka bude,tasan duniya sosai har fiye da yadda uwarta ta sani ta koma dorata akai,hakan ya so tsorata maman har ta soma shirin hanata wasu abubuwan,amma ina.......maqeri ya riga mabada hali,tuni zainab din tasa aka rufe bakin maman da yayyenta maza biyu,duk wani abu da zata aiwatar bata laifi a idanunsu,musamman idan ta samo ta yaga musu.            Tun randa taga mukhtar zuciyarta ta yaba da shi,bata bata lokaci ba wajen bada sunanshi aka mata bincike a kansa,yadda takeso haka sakamakon yazo mata,mukhtar din yayi dai dai da ra'ayinta,saidai bata qaunar kishiya ko misqala zarratin,amma da ta samu labarin wace sumayya sai hankalinta ya kwanta,ta tabbatar ba matsala bace a gunta,aiki guda daya tak zata mata rana guda ta koreta daga gidan,duk da tana diyar malamai ai bata da maganin kirsa ko?.         ***       ***      ****     Hankalinta bai kwanta ba sai data gana da yaya yahanasu,wadda bata tunkareta ba sai data yi shiri sosai akanta,qwarai yaya yahansun taji wata qauna da aminta wa zainab,musamman data ji cewa ta taba haihuwar d'a namiji ma,nan zainab din ta zube mata alkhairai masu tarin yawa tare da tsara yadda zasu cimma nukhtar din duk da taimakon yaua yahansu wadda ke kiran kanta YAAYA kuma UWA a gunsa.         ***       ***    ***           Suna shirin cin abincin dare kiran yaya yahanasun ya baqunci wayarsa,dama ya tsammaci hakan saboda tun yammacin jiya da ya ziyarci gidan yaga gilmawar wata cikin layin nasu tamkar zainab din,zuciyarsa bata gasgata masa hakan ba tunda ya riga da ya sani bata san muhallinsu ba,amma duk da haka zuciyarsa bata samu nutsuwa ba har zuwa wannan lokaci. "Kiyi haquri yaya,amma yanzu bazan samu damar fitowa ba" ya sanar da ita kai tsaye. "La'ilaha illallahu,mukhtar yaushe kayi wannan riqar,akwai ranar dama da zata zo zan buqaci ganinka kaqi mukhtar" sai ta sa kuka "Lallai ba shakka sumayya ta gama da mu,taci galaba akanmu ta sake cutar min da d'an uwa" sam baya son yaji kukan nata kamar yadda zuciyarsa ke quna idan yaji tana zagi aibata ko zargin sunayyarsa,hakan ya sanya ya amsa mata kan cewa yaba zuwa.           Wayar ya sauke yana duban sumayya "Sumayya bana son fitar nan,ina zargin wani abu"ya fada idanunsa na sauya launi da alamun ransa ya fara motsuwa,kai ta kada "Ka zargi alkhairi ya mukhtar,tunda kasan koma mene yaya jininka ba zata taba cutarka tana sane ba ko?" Shiru ya danyi sannan yace "Na sani,amma matuqar abinda nake zaegi taje shirin aiwatarwa wannan karon wallahil azim sunayya ba zata kwashe mana da dadi ba,bazan yarda a ringa walagigi da rayuwarmu" duk da cewa a dunqule yayi maganar amma sai data haifar mata da matsanancin faduwar gaba wanda ta sanya har ta kasa tankawa, ya miqe ya shiga dakinsa ya dauki hularsa ya zura da muqullin babur dinsa don ya riga da ya ajjiye motarsa a inda take kwana ya fice daga gidan.         Kan kujera ta koma ta kwanta rigingine gabanta na ci gaba da lugude,a hankali ta dinga ambaton "Ya rabbi yassir wala ta'asir" sabida neman gudun mawa da daukin wajen ubangiji.            Cikin falonta ya taddata wanda tun kafin ya kai ga shiga ya dinga jiyo dariya da hirarsu ita da yaran da alama cikin nishadi suke da walwala,sallamarsa ya katse hirar tasu,da daya da daya suka fice a dakin ya zama daga shi sai yaya yahanasun.         Suna kan gaisawa jamila ta shigo da jug guda biyu ruwa da lemo da kofuna ta dire masa,ya dauke kai ya dubi yaya yahansun yace "Gani" sai ta dan murmusa "Haba muntari,sai kace wanda ake gutsura,ko ruwa ai ka sha ko?" Sai yaga rashin dacewar yadda yazo matan,ko babu komai tsakaninsu ta bashi shekaru,saboda haka ya rusuna ya tsiyayi ruwan yayi kurba daya ya ajjiye kofin.           ***    ***    ***          Tana jin qarar babur dinsa ta miqe da hanzarinta,har ya shigo da shi ya kulle gidan ya qaraso falon tana tsaye,sam hankalinta ya gaza kwanciya a haka ya sameta a tsayen.          Saidai yanayin da taga fuskarsa ya zabge kaso mafi yawa na tashin hankalin da ta shiga,har ta saki bayyananniyar ajiyar zuciya ba tare da ta sani ba,'yar qaramar dariya ya saki yana fadin "Me ya tsorataki haka?" Qwayar idanunta ta juya "Kaine mana,hankalina ya qi kwanciya tunda ka fita" "To ya kwanta,don babu komai sai alkhairi" duk da bata ji farinciki ko kadan ba yadda ta tsammata sai tace "To Allah ya lamunce ya shige mana gaba" tayi maganar tana zama.            Ko kadan baiyi mata maganar komai ba,babu abinda yace mata kan hakan har bayan kwana biyu,a tsarinta mutum ce da bata shishshigi cikin lamuran da suka shafi rayuwar wani,hakanan ko da ga mukhtar din ne bata tambayarsa wasu lamura nashi na daban saidai idan shi yaga dama don rad'in kansa ya sanar mata,hakan ya sanya itama bata tambayeshi ba sai tayi zaton wani lamari ne da ya shafesu shi da 'yar uwar tasa. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 2⃣3⃣ ________________________ *Bismillahir rahmanir rahim* *wa'asa an takrahu shai'an wa huwa khairul lakum,wa'asa an tuhibbu shai'an wa huwa sharrul lakum,wallahu ya'alamu wa'antum la ta'alamu* *Allahumma farrij hammal mahmumin,Allahumm farrij karbal makrubin* _______________________________ *Bayan kwanaki biyu* *** *** *** ***              a hankali ta shigo dakin ganin tunda ya kammala wanka ya shiga bai fito ba bayan ta kammala shirya abincin dare sa zasu ci,turus ta tsaya tana dubansa.             Tsaye yake gaban mudubi sanye da sabuwar shaddarsa ruwan qwaiduwar qwai dinkin boda,taje sumar kansa yake,sosai kayan suka masa kyau,sai ta jingina da bango ta harde hannayenta tana dubansa,da alama ma baisan ta shigo ba.         "Da kyau,irin wannan kwalliya haka da akemin?" Juyowa yayi ya dubeta yana murmushi "Girmanki ne ai,amma zan danje unguwa tukunna" sai ta danyi jim gabanta na faduwa,take ranta ya darsa mata wani abu,batasan sanda bakinta ya subuce ba "Zance zaka kenan" juyowa ya sakeyi yana ajjuye cumb din tare da takowa gabanta "Ya akayi kika canka?,naso ace da kaina na gaya miki my sumy" wani irin abu taji yana ratsata tun daga kanta har qafafunta,yanayin fuskarta ya sauya "Wai don Allah da gaske kake ko wasa?" "Da gaske nake mana sumayya,na taba miki irin wannan wasan" ya fada yana qoqarin janyota jikinsa,sai ta zame jikin ta kana ta ja da baya,jikinta ya soma rawa hawaye na shirin zubo mata,hakan ya sanya ta tallafi kanta ta hanyar zama gefan gado,baiyi qasa a gwiwa ba ya bita ya zauna gefanta "Yi a hankali mana sumayya,me na daga hankali kuma,koma wace zata zo ai kema kinsan a bayanki take ko?" Idanunta ta dago wadanda suka cika da qwalla har sun fara gangarowa ta dubeshi "Meye na tada hankali kuma,shin ban cancanci nayi kishinka bane ya mukhtar?" "Kin cancanci fiye da haka ma sumayya,amma kiyi haquri,in sha Allahu ina saka ran wannan karon alkhairi ne auren da zanyi".          Cike da mamaki ta watsa masa wani kallon " wanne alkhairi ya mukhtar?,har ka manta wuyar da mukaci cikin shekara guda kacal?....." "No....ki kyautata zato sumayya ba haka na sanki ba....", qarar wayar sa ce ta katse abinda yake shirin gaya mata,ya sanya hannu ya daga wayar bayan ya hade fuska kamar yana gaban mai kiran " nace miki gani nan ko?"daga haka ya datse kiran ya maida hankalinsa kanta.           Hannu ya sanya ya share mata hawayen sannan ya miqe "Ki bari na dawo zamuyi magana,ki kwantar da hankalinki sumayya kinji" bata iya amsa masa ba har ya sanya hularsa ya fice.           Wani kuka ta saki bayan da taji tashin motarsa,meke shirin faruwa?,mukhtar ne yau ya tafi zance gun wata a gaban idonta bayan ya ganta tana kuka,mukhtar din da baison bacin ranta balle har yaga hawayenta? "Ya rabbi yassir amrih" ta dinga fada bayan ta zame ta kwanta saman gadon tana digar hawaye.           Kimanin awa biyu sai gashi ya dawo,lokacin qarfe goma har ta dan gota ma,a dakin nasa ya sake taddata kwance,da sauri ya isa gareta ya dagata ya zaunar yana duban idanunta da suka kumbura "Subhanallahi.....sumayya meye haka?" Kamar jira take ta kuma fashewa da kuka,tsawon mintina talatin ya ciyo kanta bayan ya tursasa mata sunci abinci,sai da suka kammala sannan ya nemi magana da ita.            "Ta hanyar yaya yahanasu zainab ta biyo sumayya,babu yadda za'ayi na iya bijirewa maganar,ni kaina ina jin yadda da auren cikin zuciyata bansan dalili ba,ba kamar auren fa'iza ba hakan ya sanya nake zaton QADDARATA ce zainab" yayi shiru yana jin quna can qasan zuciyarsa da wata iriyar takura,saidai daga sama yana jin kamar dole ake masa ya auri zainab.          Jin shiru bata ce komai ba ya sanya shi cewa "Yanzu haka cikin satin nan suke da buqatar na kai kudi a kuma saka rana baki daya,idan da alkhairi sai kiga ta haifa mana yaro ta sanadin haka kema ki samu naki" maganar sai tayi mata duka biyu,batasan sanda ta fashe da kuka ba "Ta haifa maka dai yaya mukhtar,ni sumayya kam banda cikin haihuwa ai" tayi maganar tana mai niyyar miqewa ta bar masa gun,yunqurin riqota yayi ta kauce tana fadin "Ka qyaleni kawai ya mukhtar,ka qyaleni kaje kayi aurenka,ka auri wadda zata haifa maka yara,na yarda nikam juya ce" ta qarashe maganar cikin gunjin kuka kamar zata shide,da azama ya riqotan ya rungumeta yana lallashi,sam sai kalmominsa suka gaza yin tasiri cikin zuciyarta,ta kasa bashi hadin kai wajen yin shiru da haquri "Nace ma ka sakeni kaji ko?!" Ta fada cikin gunjin kuka.          "Naqi na sakekin!" Ya fada a tsawace "Yaushe kika koma haka sumayya?,yaushe kika koyi shegen kishi haka?" Ya fada yana kwantar da murya,a hankali ta daga kai tana dubansa,ta karaya sosai wannan karon,banbanci take hangowa qarara cikin idanun mukhtar din,sai ya janye idonsa daga kanta yana tuhumar kansa akan tsawar da ya mata,a tausashe ya janyeta gefan gado ya zaunar da ita sannan ya zauna daura da ita,cikin sanyin murya yace "Kiyi haquri sumayya,baki na bazai gaji da baki haquri ba yau da gobe da kullum har ABADAN ma sumayya,abu daya zan iya gaya miki shine inaji a jikina dole ne nayi auren nan,bazan iya haqura da shi ba,ki yafemin sumayya,ki yafewa mukhtar dinki mai qaunarki kinji sumayyata" ya fada cikin raunin murya tamkaf mai shirin yin kuka,abinda bata taba ji daga gareshi ba kenan,idanunsa kadai zaka kalla ya tabbatar maka da gaskiyarsa,take tausayi so da qauna sukayi tasiri a kanta,ta rungumeshi tana fadin "Babu komai ya mukhtar,Allah ne ya halatta maka,kaji tsoron Allah kawai ka kuma yi adalci" "In sha Allahu sumayyata,ki tayi ni da addu'a" ya fada yana kuma qanqameta.         ***       ***     ***        Cikin abinda bai wuce sati uku ba aka kai kudi bayan sati daya mukhtar din ya hada kayan sa rana akwati biyu,bai shawarceta ba hakanan batasan zaya yi ba sai ganinsa tayi da kayansa,yace ta duba tace basai ta duba ba Allah ya sanya alkhairi,haka ya janyesu ya miqawa yaya yahansu,suna guda suna gwalli suka je suka kai kafin lefe ya qaraso,fadi suke Allah ne ya karya alqadarinta,wannan karo kam ta gamu da mai qarfin kurwa,kuma in sha Allahu zama daram tazo.          Daga can bangaren zainab din ma haka suka gaya mata,sumayya bata barin mace ta zauna da mukhtar ko anyi auren saita tarwatsa abun,dariya zainab din tayi,don tasan komai game da sumayyan,tasan sarai akwai qarin gishiri cikin maganarsu,ta lura mutane ne masu jarabar son kansu da nasu,tilas tayi maganinsu tun da wjri,din ba zata lamunci abinda sumayyan ta lamunta ba,duk da hakan ba zama zatayi ta zubawa sumayyan idanu ba,koba komai diyar malamai ce bata san nasu shirin ba.           Sosai sumayya ke ganin banbanci wannan karon,ashe da sam ba aure mukhtar din yayi ba,wani rawar kai sosai take gani dangane da shi,sabbin dinkuna yake da lissafe lissafe,tuni ya maida kai wajen ganin an kammala abinda bai kammalu ba na ginin sabon gidansa,ita kanta yace ta kwashe duka kayan dakinta ta siyar ko ta bayar zai sauya mata komai da sabo itama zata tare,saidai abinda ke daure mata kai wani lokaci sai ya hau qunci shi kadai yana fadin baison auren nan,sgifa yana jin tamkar ya fasa,bata san meye matsalar ba,data gaza gano haka sai taci gaba da addu'a kan Allah ya sassauta lamarin ya kawoshi da sauqi,don zuwa yanzu ta tsinke da lamarin kishiya,ashe a da tabbas quruciya ke cinta,batasan dadin mijinta ba sai yanzu,bata san meye kishi ba sai yanzu.           Kayan lefe ya mata itama yadda ya yiwa zainab kowa akwati hurhudu,bata yi mamaki ba saboda budin da mukhtar din keta samu dai dai gwargwado.           Biki ya rage saura sati biyu abdur rahman ya kawo mata ziyara,ta tarbeshi yadda ta saba,suka gaisa cikin mutunci,saidai wannan karo babu walwala da zolayar da suka saba,da ya tambayeta batayi qasa a gwiwa ba ta sanar masa,sosai ya mata nasihar da ta sake kwantar mata da hankali,ya jaddada mata ta riqi addu'o'inta,sosai taji dadi ta kuma gode masa,bai jima ba sukayi sallama ya tafi dama mukhtar din yazo nema kuma bai taddashi ba ya tafi zance gun amarya zainab. Saura sati daya bikin ta shirya ta je gidan anty dije,da biyu taje don ta samu mai bata shawara,don sosai taji dadin shawarwarin da ta bata wancan karon,wuni tayi mata sur ta kuma qaru matuqa da gaske,taji dadin maganganunta wadanda suka sake kwantar mata da hankali. Ranar da akema amarya jere ranar itama aka yi mata nata jeran cikin sabom gidansu,sai ya zama na tamkar amare biyu ne zasu tare,sosai zainab tayi rawar ganin hadawa kanta kayan daki,duk da haka babu abinda zata gayawa sumayyan,don itama wannan karon dai komai sabo ne,babu abinda ta shiga da shi tsoho banda sutura su dinma kusan rabinsu sababbi ne. Ana ya gobe za'a kawo amarya ta tare,tare da 'yan rakiyarta suka je,sosai gidan ya burge kowa,duk da ba wani kantameme bane amma da girmansa dai dai gwargwado,da fari compound ne wanda ya dauke motar mukhtar din da wani space din daban,sai qofar da zaka bude wadda me dauke da babban falo guda d'aya,daga hagu da dama corridor ne guda biyu,daya na sumayyan daya na amarya,kowanne cirridor akwai daki falle biyu da toilet,daga falon akwai qofa biyu,daya ta kitchen dinsu ne mai yalwa wanda ka masa tsarin tsohon kitchen dinsu kowa da kantarsa,daya qofar kuma idan ka bude baya ne inda aka yiwa 'yan shuke shuke,anan falon mukhtar yake da bedroom dinsa shima,gida yayi dai dai gwargwado sai son barka. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 2⃣4⃣ _____________________________ *Bismillahir rahmanir rahim* *Man ja'a bil hasanati falahu ashru amsaaluha,wa man ja'a bis sayyi'ati fala yujza illa misluha* _________________________________       Bata gayyaci kowa ba baya ga mutanen da suka mata rakiya suka ga gida suka kama gabansu,hakan ga sanya randa za'a kawo amarya ita daya ce qwal,cikin dakinta tayi zamanta saboda falon nasu cike yake da 'yan kawo amarya,wadanda tun daga motsinsu ta karanci yanayinsu,su din ma dukkan alamau sun nuna babu arziqi,saboda haka tayi musu aji guda ta sanya su.        Bata fito ba sai da taji motsin 'yan uwan mukhtar wadanda da su aka dauko amarya,fuska sake ta fito falon tana musu maraba,saidai kowanne wanu irin kallo yake binta da shu,ganin babu dole ya sanya ta juya ta koma dakinta tun kafin su yarfata cikin jama'a,yanzun kam ba da bace da quruciya ke dibarta balle ta nace sai an kula ta ko ta faranta ran wanda bai damu da nata farincikin ba.             Ganin tara na dare yayi hayaniyar ta sarara da alama sun watse sun bar masu gidan da gidansu,sai ta miqe ta sanya turaran wuta cikin dakinta zuwa corridor dinta a burner din da anty dije ta siya mata guda biyu kyauta,take qamshin ya karade ko ina har zuwa falon nasu,wanka ta shiga ta tsala ado cikin wani marron material wanda aka yiwa ado da golden din zare,sosai ya fidda salsalar farar fatarta wanda jan lallen da tayi ya sake bada gudun mawa,baga wani cika kwalliya ba ta dai yiwa kanta barin turare kama daga humra,body spray body mist zuwa perfume na kaya.ta yane kanta da mayafi golden ba tare data buqaci daura dankwali ba ta kame gefab gadonta tare da janyo wayarta ta soma 'yan danne danne don ta dauke mata abinda take ji cikin zuciyarta.           Qarfe goma taji sallamar mukhtar din cikin falonsu,burus tayi tamkar bata jishi ba,wani kishi da matsananciyat faduwar gaba suka ziyarceta,sai ta dakata da abinda takeyi din tayi shiru tana sauraron motsinsa da kuma bugun zuciyarta.          A hankali ya yaye labulen yayi sallama,ta amsa ba tare da ta dubeshi ba,idanu ya zuba mata,ta masa kyau sosai tamkar yau take amaryarsa,wanu qaunarta ke taso masa ta wani lungu can dake saqon zuciyarsa wanda wani abu da baisan ko meye ba ke qoqarin fatali da abinda yake ji din,ya rasa me yaje ji cikin zuciyarsa a yau din,koda zaka ritsashi da bindiga ha zaya iya gaya maka ainihin me yake ji ba,farinciki koko baqinciki,ya jima cikin wannan yanayin wanda baisan sanda ya shige shi ba,da yayi yunqurin wani tunani kuma sai ya shagala,tunanin ya qwace masa.         Ganin bata da niyyar cewa komai ya sanyashi qarasowa gefanta ya zauna yana zube ledojin hannunshi a qasa "My sumy.....yau kan arziqin sannu da zuwan ma ban samu ba" ya fada cikin marairaicewa,a hankali ta dago kai ta kafeshi da idanunta wanda suka sanya yaji wata fargaba da kamashi,yayi kyau cikin shadda butter colour dinkin babbar riga,yasha askin saisaye da gyarab fuska wanda ya sakw fidda shape sin kyakkyawar fuskarsa.        Tamkar an dorawa zuciyarta dutse haka taji saboda tsabar kishi,yau nukhtar dinta zai sake zama na wata a karo na biyu,me yasa yaya yahanasu taqi barinsu su huta,me yasa ba zata gane irin yadda take son mukhtar dinta ba,laifi ne dan baka haihu ba?,shine lawai dalilin da yasa suke ta rabata da farincikinta  a lokuta mabanbanta,ina ma ace ana siyar da haihuwa yau da ta sayeta koda zata rasa zanin daurawa,koda zata rasa lomar abincin da zata sanyawa bakinta,don dai kawai su barta da mukhtar suyi rayuwar farinciki.           So take ta bude baki da gaya masa magana ko zata ji sauqin tuquqin da zuciyarta ke maga amma sai ta kasa,girman mukhtar cikin idonta yafi gaban haka,miqewa tayi gudu gudu sauri sauri idonta na saukar da qwalla kan kuncinta,miqewa yayi biyita da sauri cike da muradin cimmata,saidai tuni ta afka toilet dinta ta rufe qofa tare da sakin kuka.          Bakin toilet din ya tsaya yana naci da magiyar ta fito,sai da suka kusa kwashe minti ashirin a haka,ba zata iya kallonsa ya tafi dakin wata ba hakan ya sanyata cikin muryar kuka tace "Bana son ganinka yaya mukhtar ka tafi don Allah ka qyaleni" "Yau nine sumayya baki son gani?.....yau......." Bai kamamala maganar ba wayarsa dake aljihun gaban rigarsa ya hau ruri,hannunshi ya zira,ganin mai kiran ya sanyashi dagawa "Dear m,ina ka tsaya ne wai bayan na ji shigowarka",bazai iya tantance mai yaji ba,so yake ya rufeta da masifa amma sai ya kasa,maimakon haka sai ya bige da cewa " ina gun yayarki zance ko qanwarki ina lallashi"gabanta ha fadi haushi ta turniqeta,kada fa ace duk abinda ake bata labari kan sumayyar gaskiya ne,amma babu komai saura qiris tayi maganin abun "Lallashin me kuma dear bayan ba wannan ne karo na farko ba da aka fara mata kishiya,ka taho ko nazo da kaina na tafi da kai" "Ok gani nan" ya fadi da sauri tare da katse kiran,maida idanunsa yayi ga qofar toilet din,ya tabbatar taji duk abinda suka ce,kamar sumayyan ce ke gabansa ya marairaice "Shikenan sumayya zan tafi,ga ledarki can cikin daki Allah ya bamu alkhairi" ya fada yana juyawa.         Zamewa tayi tayi zaman dirshan saman tiles din bandakin sabon kuka na kubce mata wanda ta sanya tafin hannunta ta toshe bakinta don kada su jiyota,duk da cewa ita tace ya tafin bata yi tsammanin tafiyar tasa da gaggawa ba haka.         Ta jima tana kuka a ciki kafin ta lallashi kanta bayan tayi tilawar wasiyyoyin mahaifiyarta tun daga auren da aka qara mata na fari zuwa wannan da ya kasance na biyu.         Bata bar bayin ba sai da cikakkiyar alwala,ta koma daki ta sauya kayan bacci,doguwar riga ce har qasa mai taushi da kauri,hijabi ta dora saman riga ta shimfida abun sallaha ta tayar da sallah hawaye na layi kan kumatunta.          Yana shiga ta miqe ta taroshi cikin karairaya da yauqi,ta amshi ledar hannunsa ta ajjye kana ta rungumeshi,yaqe haqora kawai yake,ko daya bata burgeshi ba,alamu sun nuna babu kunya ko qwaya daya cikin idanunta,ko daya baiji dadin kasancewarta cikin jikinsa ba amma sai ya kasa cewa da ita komai,sai ya dinga dauko daren farkon sumayya da na fa'iza da nata yana hadawa,tuni lissafin ya wargaje don tako ina sun sha banban.            Biye yake da ita kawai sai ido da yake binta da shi,ita ta hada musu ruwa sukayi wanka sannan ta samo plate ta juye kazar a ciki,kusan ita ta dinga ciyar da shi ta kuma ci da kanta har suka kammala ta janyeshi gado don tuni ta dokanta,kusan ita ta gabatar da komai a maimakonshi,mamaki da haushi ke tuqeshi,gefe guda wani irin takaici wanda idan ya yunqura zaiyi magana sai yaji ya kasa cewa komai,data dubeshi kuma sai yaji komai ya wuce ya bar tasiri cikin ransa.          Kwana tayi zaune bayan ta gaji da yin sallolin,abinda bata taba zata zata iya ba,yaushe mukhtar ya sake zame mata wani na daban haka,ita kanta tana mamakin yadda ta koyi kishinsa har haka,sai da ta gabatar da sallar asuba taji idanunta sun soma nauyi da zugi,duk yadda taso ta yakice baccin amma bata samu nasara ba,haka yazo ya saceta cikin gaggawa ya kuma mata nauyi wanda hakan ya sanya ta gaza sanin meke wakana cikin gidan har misalin qarfe goma da rabi ma safe wanda ta farka a firgice.          Bandakin cikin dakinta ta shiga da yake bayan na corridor akwaai cikin daki,wanka tayi bayan ta wanke bakinta ta dawo cikin dakin,jikinta babu qwari ta shirya cikin atamfa doguwar riga wadda ta mata kyau,duk da bata jin qwarin jikinta amma tayi lite make up wadda ta dace da yanayinta,babu dauda ko qura a rea dinta sai dan kakkabe kakkabe kawai da tayi sannan ta fito don samawa kanta abinda zata ci koda ruwan zafi ne,don jinta take iska na yawo da ita tsabar babu komai a cikinta,ledar jiya mukhtar din ya bata ta dauka ta fice da ita.          Bata kula da su ba sai data shigo cikin falon sosai,mukhyat sanye da yadi mai taushi fari tas wanda ka yiwa aiki da zare ash,sai wandda idanunta suka sake sauka kanta wanda bata tantama itace zainab din.         Macace wadda kallo daya ta yi mata ta fuskanci ta girmesu ita da fa'iza baki daya,A qalla tayi shekaru ashirin ta takwas wanda hakan ke nuna ta girmi sumayyan da shekara goma tunda sai yanzu taje cikin shekararta ta goma sha tara,baqa ce zainab din amma ba baqi can ba,tana da cika wadda za'a iya kiranta qiba kai tsaye duk da wata mai yawa bace,bata daga cikin sahun kyawawa ko kadan amma zaiyi wuya kai tsaye ka kirata da mummuna saboda yanayin iya gogayya da iya salo,saidai tako ina sumayyan ta mata fintikau,abu daya zata iya nuna mata qwala qwalan idanu da suke zagayayyu suka fi na sumayya girma,sakamakon natan lumsassu ne ba kowanne lokaci kake iya gane girmansu ba,sanye take da material mai santsi wanda aka yiwa dinkin riga da skert,breakfast sukeyi wanda ya qunshi tea da soyayyen qwai da bread,sai kaji wanda ba tantama na jiya ne aka sake gasa su.          Shi ya soma ganinta lokacin da zainab ke qoqarin bashi naman a baki,sai ya goce wanda hakan ya janyo hankalin zainab din ta ankara da fitowar sumayyan,murmushi ya sakar mata yayin da itama tayi qoqarin maida masa martani "Kin tashi kenan,na leqaki na taras kina bacci" "Eh,ban jima ai da tashi ba" ta fada tana takowa gabansu "Kinyi kyau sumy ta" ya fada yana sake dubanta wanda kalmar ba qaramin dukan qirjin zainab tayi ba,lokaci daya ranta yayi baqi,sumayyan ta yaga mata tako ina,kyau da quruciya,akwai alamun nutsuwa tattare da ita sosai,hakan ta kwana da sanin lamba daya ce ita cikin zuciyar mukhtar din,don ko darensu na jiya ya bata amsa,duk yadda taso rikitashi ban manta sumayyan ba ita yake kira.       "Na gode ango mijin amarya,da fatan kun tashi lafiya" ta fada wajen kaiwa matuqa gurin boye kishi da damuwarta,sai ta dubi zainab "Amarya ina kwana ya kwanan baqunta" "Lafiya ya kike"ta fada tana yatsina tare da qoqarin baiwa mukhtar tea "Qalau" itama sumayyan ta fada cikin yanayin data amsa mata tare da motsa kafada kana ta nufi kitchen don kaucewa ci gaba da kallon abinda ke faruwa.         Alamu sun nuna iyaka na cikinsu ne abincin,batasan waye yayi ba,amaryar ko mijin amaryar,koma waye dama bata da buqata,sai ta dora tea kan gas da a yanzu shi mukhtar ya siya mata take amfani da shi,ta bude kazar ta sake mata sabon hadi na spices,ta duba dan madaidaicin ovean dinta ta soma kici kicin hadawa tare da duba hanyoyin da ake hadawar.        Cikin haka mukhtar din ya shigi kitchen din dauke da kwanukan da suka ci abincin zainab din na biye da shi,bata bi takan sumayyan ba ta nufi side dinta ta dire kayan,mukhtar ya dubu sumayyan "Me za'a girka mana ne naga ana hada ovean" "Ai baka da buqatar abinci na malam" ta fada cikin gatse,murmushi yayi yana kallonta,lallai sumayyan ta fara zama babbar mace,tunda har tafara banbance tsakanin aya da tsakuwa.           Kafin ya furta komai muryar zainab ta ratsa kunnuwansu tana qwala masa kira cikin wani irin salo,tamkar an soketa a qirji amma saita basar,ya juya yana cewa da ita "Ina zuwa" "Banda buqatar dawowarka ma" ta fada kishi na cinta tana qoqarin danneshi.         Har ta kammala babu shi babu alamarsa,ta juye ta koma daki da abincinta zuciyarta na raunana,saboda wannan ne karo na farko data taba ganin sauyi daga gareshi har irin haka.         ****      *****    ****      Cikin kwanakin wani amarci ta dinga gani cikin gidan wanda bata tsammata ba,baki daya kamar daukar mukhtar din akayi aka sauya mata shi,hutu ya dauka na fita kasuwa har na kwanaki bakwai,ko yaushe suna daki idan kaga fitowarsa salla ce zaya yi,saita wuni sur bata sanyashi cikin idanunta ba,abun na taba ranta saidai bata yarda ta fiya zurfafa lamarin cikin ranta,runda anty dije ta gaya mata dole zata iya ganin wasu sauye sauye duk son da yake mata,amarya kota buzuz ce sai an mata rawar qafa,to bare baya ga wannan babu wani sauyi da ta gani cikin ma'amalarsu shi da ita. *KUNDIN QADDARA TA*           Kwanaki uku take zaton zaya yiwa zainab din tunda bazawara ce,sai gashi ya shiga cikin kwana na hudu biyar shida har zuwa bakwai.         Ranar kwana na bakwai din a ranar zaya soma fita kasuwa,tana kwance dakinta bayan sha daya na safe taji sallamarsa,sai ta miqe ta zauna tana amsa masa,fuskarta babu yabo babu fallasa,gefanta ya samu ya zauna yana fadin "Ranki ya dade kinyi wuyar gani" ido ta daga ta dubeshi,lallai ne wai ita za'a yiwa halin maza,magana yake gaya mata a fakaice koko yaya,duk da hakan sai ta dake ta kuma basar ta kaufa zancan ta hanyar fadin "Ina kwana" "Lafiya sumy ta,kinga na qarawa zainab kwana ko,kinga baquwace tace kuma tan tsorom zama ita daya" wani haushi ya taso ya turniqeta,budurwa ce zainab din ko yau ta fara zaman gidan aure,ko ko tsabagen rainin wayo ne,wadan nan kalaman takeson gayawa mukhtar din amma girmansa da take gani yasa ta gaza furtasu ta hadiye kayanta sai ta bige da cewa "Ko,Allah sarki" daga yanayin da tayi maganar kawai ya tabbatar masa cewa ta inda zancansa ya shiga ta nan ya fice.          Kafin su sake cewa wani abu zainab din ta daga labulen dakin ta danno tana fadin "Dear fito mana na rakaka,ina ta jira fa" "Ai gani nan" ya fada yana fiddo kudin cefane daga aljihunsa,wani banzan kallo da sumayyan batasan ta iyashi ba sai yau ta jefawa zainab sannan ta miqe zata fice ta bar musu dakin,mukhtar yace "Ina kuma zaki sumayya bamu gama magana ba" "Baka shirya yin maganar da ni bane" ta fada tana shigewa toilet abinta ta soma daura alwalar sallar walhar da dama ita take shirib tashi tayi.         Tana jiyosu daga nan zainab din na gaya masa ya qyaleta yazo su tafi,yace a'a taje falo ta jirashi zaya fito yanzu,a bandakin ya cimmata ta gama alwalar tana gyara daurin kallabinta,fuska a hade cikin kakkaurar murya yace mata "Wai wane irin hali kika koya sumayya wanda ban sanki da shi ba,wannan wannw irin wulaqanci ne ina miki magana kina tafiya gaban zainab salon ki koya mata yadda zata raina ni", tsayawa tayi tana kallon ikon Allah,lallai a daki mutum a kuma hanashi kuka.         " ai tare muka siyi foam din makarantar koyon sabbin halaye ni da kai muka cike,muka kuma fara daukar darasi a ciki"sarai yaso ya fahimceta amma sai ya waske "Wai duka sumayya don na qarawa zainab kwanaki kike wannan abun,yanzun ban isa da gidana ba kenan?" "Isa kai,tunda gashi ka nuna salon taka isar" ta fada tana kashe famfo tare da qoqarin rabeshi ta wuce,sai ya janyota jikinsa ya matse gam,yasan kan abarsa take ya fara sauke mata fushinta,yayi nasara kam don itama bata bijire masa ba,don babu qarya tayi kewar mijinta sosai.         Ita ta fara zame jikinta sannan tace "Ka gayawa matarka kada ta sake shigo kin daki kanta tsaye,sabida hakan ya sabawa dokar addinin musulunci idan ita din bata sani ba" sai ya lumshe ido ya dafe kai "Oh sumayya harda mita ma sai da kika koya,to ayi haquri" daga nan sukayi sallama ya ajjiye mata kudin cefane duk da suna da komai.         Sosai zainab din ta qulu,ta fara lura sumayyan ta shalle zatonta,amma daga yau zata fara dasa bamabamanta cikin gidan,shanye komai tayi ta masa rakiya kamar ta hadeshu,duk yadda ya nuna jin dadinsa a fili amma zuciyarsa ta gaza karbar hakan,a boye ma Allah Allah yake ta koma ya samu ya fice daga gidan.         Da azahar ta shiga kitchen ta musu girkin rana,tana fitowa ta samu zainab din a falon zaune tana kallo,qafarta daya kan daya tana amsa waya,har sumayyan ta gifata ta taji ance "Ke!" Da fari tayi zatan cikin wayarta ne sai taji ta sake cewa "Ke dake nake magana sumayyata" waiwayowa tayi tana tsaye daga inda take "Wai da ni kike?" "Akwai wata mai sunan ne bayanke a gidan nan,koma ki dauko min abinci na".          Baki ta sake tana kallonta cikin mamaki,ita kuma nata salon kenan,sai ta kada kai kawai tace " idan kin damu ki shiga da kanki ki dauko" "Ni kike gayawa wannan maganar,lallai yau zaki gane niba irin sauran kishiyoyinki bane,wallahi yau sai kin gane matsayina gun mukhtar" bata tsaya bi ta kanta ba tayi komawarta daki don tana da abunyi.         Lambar mukhtar ta soma laluba tana huci,yana tsaka da sallamar custumer yaga kiran nata,sai da yaji wani dumm cikin kansa da yaga sunar,ko kadan baiyi farinciki ba amma sai ya gaza share kiran "Amarya bakya laifi,ya gidan" "Gida ba lafiya ba,mukhtar na fuskanci ka auroni ne don matarka ta rainani" "Ya salam,me ya faru me tayi miki?" "Bazan hanaka sana'a ba kabari idan ka dawo kaji koma mene ne,amma wallahi idan baka dauki mataki ba bazan ci gaba da zama cikin gidan nan ba" sai yaji wata faduwar gaba da sauri yace "Haba zainab ki daina fadar wannan maganar mana,mai rabu mu ai sai Allah,bari na kira ita sumayyan naji" da sauri ta katseshi don bata son ya mata fadan tun yanzu lamarin ya wuce ba tare data iza wutar tafi haka ba "A'ah nidai ban saka ba,nace ka bari kawai ka dawo" "To shikenan sai na dawo din" ya fadi yana sauke wayar,sam jikinsa bai bashi sumayyan zata aikata wani abu na rashin mutunci ga zaina din ba,amma sai ya samu kansa da yarda da duka magan ganun zainab din.            Tun shuda saura ta gama fesa kwalliya tare da bade jikinta da turarenta data tanada na musamman wanda ke hargitsa tunani da lissafin mukhtar ya dinga maida su ba dai dai ba.         Cikin izza da isa ta fito daga dakin nata hannunta dauke da jug na kwalba wanda ta cikashi da lemin zobo da cups dinsa,tana tafe tana murmushin tarkon data d'ana ta ratso ta falo don fita harabar gidan,so take mukhtar din ya fara karo da ita kafin kowa saboda abinda ta tsara ya tafi dai dai ba tare da mishkila ba,idanunta ne suka sauka kan sumayya tada tsume cikin tata kwalliyar,wani irin material ne mai santsi kamar yanayin shufom saidai ya fishi kauri da aka matsawa dinkin wata shegiyar gown wadda ta fidda duk wata qira tata,kalar pink(ruwan hoda) ne mai turuwa,tayi amfani da dankunne da siririyar sarqa fashion baqaqe,hakanan abun hannunta zuwa zobe,take farincikin dake ranta ya ja baya ta raina tata kwalliyar data hasko farar fata ta hadu da pink da baqi,kishi ya sake taso mata,ya zama lallai kota halin qaqa tayi rugu rugu da gwamnatin sumayyan cikin zuciyar mukhtar ya zama tata ke wannan tashen,ta yadda zata yaga yarinyar yadda taga dama,yarinyar na neman fin qarfin zatonta,don ba'a rufe awa ba taga yadda ta tashi hankalin gidan da qamshin girkin abincin dare,ranta na suya ta fuce fuuu wanda sumayya bata ma lura da ita ba sai ficewarta ta gani kamar guguwa. _tofa,yanzu ake yinta,muje zuwa_ *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 2⃣5⃣ ____________________________ *wa tawakkal alal hayyul lazi la yamutu wasabbih bi hamdih* _kayi tawakkali ka dogara da rayyayyen(Allah S W T)da baya mutuwa,kayi tasbihi/ka tsarkakeshi ka kuma gode masa_ ____________________________         Guguwar dawowarta sumayya da taji ya sanyata daga kai ta bita da ido har ta shige dakinta.           Cikin mintinan da basu wuce biyu sumayyan ta fara jiyo qauri wanda yake da alama da wani abu aka sanya cikin garwashin wuta,data lura sosai sai ta fuskanci daga bangaren zainab ke fitowa,mai da kanta tayi taci gaba da kallonta,cikin sakanni qaurin ya buwayeta,hakan ya sanya ta koma dakinta ta dauko burner da turaren wuta ta fito falon wanda hakan yayi dai dai da sake ficewar fa'izan zuwa harabar gidan,jikin socket din dake daura da kayan kallon ta jona ta cikata da turaren wuta,mintina qalilan ya danne qaurin ya koma qamshi.           Tana zaune taji bude get din gidan da qarar motar mukhtar din,wanda hakan ke alamta dawowarsa,sai ta miqe ta koma daki ta sake feshe jikinta da turare sanna ta nufo harabar gidan.            Turus tayi ganin zainab gefan mukhtar tamkar zata shige jikinsa tana dubansa,hannunsa riqe da cup wanda ta cika masa da zobo wanda tuni ya fara kwankwada,yi tayi kamar ta juya saboda takaici sai kuna taga sam hakan baiyi tsari ba,zai kuma faranta ran zainab har taci karenta babu babbaka tunda ta riga da taga tsaiwarta.          Fuskarta ta fadada da fara'a,sannu a hankai ta soma takowa gun wanda takalmin qafarta duj da plate ne ya dinga bada sauti,hakan shi ya janye hankalin mukhtar ya zuba mata ido,ta masa kyau sosai,ji yake kamar ya tafi ya sureta ya daga sama yadfa suka saba,yau ta sauya masa sosai sumayyan,da wannan tunanin ta qaraso inda suke ta tsaya gabansa tana jifansa da murmushi,so yake take sumayyata kinyi kyau,so yake ya yaba mata,amma wani dunqulallen abun ya danne zuciyarsa,ya sake duban qwayar idanunta sai yaji wani bacin rai ya kamashi,murmushin da yakeson maida mata sai ya musanyashi da hade fusjarsa tsaf wanda hakan ya baiwa sumayyan mamaki,saidai duk da haka bata karaya ba ta miqa hannu ta amshi jakarsa tana masa sannu da zuwa.           Bai amsa ba don ji yayi ya gaza amsawar "Wash" zainab ta fada wanda shi ya sanya su duja suka dubeta,baikai ga tambaya ba ta dora da nata jawabin "Ka gani ko mukhtar,kaga abinda nake gaya maka ko?,yanzu fisabilillahi duk fadin gurin nan bai isheta ba sai ta takani saboda tsabar raini?" Mamaki fal zuciyar sumayya take dubanta,ya Allahu,nata salon kenan?matar da tazarar dake tsakaninsu ya isa tiqa tiqan mata biyu su tsaya shibe zata ce har ta taka ta?,tamkar dama neman abun fadan yake ya sake tunzura yana ji ana azqlzalar zuciyarsa,juyawa yayi yana jifan sumayyan da wani irin kallo "Halayyar banzan da kike son koya kenan ko sumayya?,halayyar da ban sanki da ita ba?,to bari kiji ni bazan lamunta ba,bana son tashin hankali kin sani,har sau yaushe zan huta daga dawowata ko iskar gidan ban gama shaqa ba daga shigowarki zaki tada mana fitina?,to ki shiga hankalinki da ni idan ba haka ba zanyi mugun saba miki", bata data cewa,to me zata fada ma tunda ya riga ya yarda ya hau kai kuma ya zauna?,bata baki ne kawai tsayawa kare kai,saboda haka aladabce tace " bansan na taka ta ba in sha Allah hakan bazai sake faruwa ba kayi haquri ya mukhtar"sai da yaja fasali sannan yace "Shikenan ta wuce" "Au ni ba zaka ce ma ta ban haquri ba shikenan na gane matsayina wallahi" ta fada a zafafe tana fashewa da kukan kirsa sannan ta kwasa tayi cikin gidan da sauri,don sosai ta shaqa ba haka taso ya kasance ba,so tayi cikin biyu ayi daya,imma yace sumayyan ta durqusa ta bata haquri,ko kuma tayi qoqarin kare kanta ko ta masa turjiya ya jibgi banza a gabanta taci dariya ta more.          Da idanu sumayyan tabi mukhtar din ganin yadda ya diba shima ya bita cikin wani tashin hankali da yaji ya rikito masa sanda ya fara jiyo sautin kukanta,wanda babu qwalla ko daya sai tsabar ihu da iya manaqisa,kai sumayya ta kada zuciyarta ta karye,lallai babu shakka wani sabon SHAFIN QADDARAR TA NE YA SAKE BUDEWA CIKIN KUNDIN QADDARARTA,sau ta lallashi kanta kawai ta shige ciki da jakar tasa ta ratsa ta cikin falon nasu ta wuce sashen sa.           A qalla ta dauki kusan minti talatin zaune kafin ya shigo bangaren nasa,fuskarsa kadai zaka duba ta bayyana maka yanayin da yake ciki,kallonta yayi tana zaune gu guda,tausayinta nason masa tasiri amma wani abu mai qarfi na maye gurbin tausayin da jin haushi "Na kai maka ruwan wankanka" tace da shi,bai amsa mata ba illa rage kayan jikinsa da yayi ya shiga wankan kawai.          Tana zaunw taga yana shiryawa cikin yadin kaftan ruwan zuma,ya kammala ya zira hularsa tare sa daura agogom hannunsa,muqullin motarsa da taga ya dauka shi ya tabbatar mata da cewa lallai fita zaya yi,da hanzarinta tace. "Ya mukhtar baka ci abincinka ba fa,kuma naga kana shirin fita" "Sai na dawo" ya fada yana ficewa ba tare da ko ya waiwayeta ba,sai ta zube agun ta sanya kuka,da sauri ta sanya tafin hannunta ta qunshe kukan saboda fadan da zuciyarta tayi mata na ba kuka zata yi ba,take ta kama ambaton 'Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahla,wa anta taj'alal hazna iza shi'ita sahla'.          Tana daga nan amma tana iya jiyo muryar zainab wanda hakan ya tabbatar mata fita zasuyi kenan.           Kusan awa guda da rabi ta share zaune tana ambaton sunayen Allah,ya zuwa lokacin quncin dake cin ranta ya ragu qwarai,wayarta ta soma ruri,ganin sunan mukhtar ya bata mamaki amma sai ta daga gabanta na faduwa jikinta na gaya mata ko dai ba lafiya ba,a daqile ya amsa sallamarta sannan ha dora "Ya zuwa yanzu nasan abinda kika girka tun yamma yayi sanyi,ina so ki tashi ki hada min fried rice nan da awa guda ina bisa hanya" bata da hurumin da zata musanta masa tunda iko yake da ita,biyayya a gareshi kuma tilas ne matuqar bai sabawa mahaliccinta ba,tuni ya katse wayar don haka itama ta ajjiye ta nufi kitchen  kai tsaye.          Komai suna da shi alhamdulillah tunda yanzun kam arziqi ya zaunawa mukhtar din gwargwado,da hanzarinta ta shiga hada komai,cikin abinda yai qasa da awa daya da rabi ta gama tunda ba wata mai yawa bace can,bugu da qari kuna ta horu wajen aiki.          Dakinta ta wuce ta debo kayan baccinta ta koma sashen mukhtar din,cikin toilet dinsa tayi wanka ta shirya tsaf,wannan duka cikin karatun anty dije ne,falonsa ta koma ta kwanta saman doguwar kujerarsa,a hankali tunani yayi awin gaba da ita tanayi taba sauke ajiyar zuciya.          Tarayyarsu da mukhtar tun farkon aurensu kawi yanzu,bata taba sanin so ba sai a kansa,da shi ta saba da shi ra qarasa mallakar hankalin kanta,dashi ta qarsa cikasa kammaluwar hankali da rayuwarta,ta yaya zata iya jure wani baqin lamari daga gunsa ta farad daya?,ya zata iya lamuntar juya baya daga gunsa,idan ma har laifi ta masa a yau kam zata kawo qarshen horon da yake mata.          Tana tsaka da tunanin ta jiyo muryarsu suna shirin turo qofa,hakan ya sanya tayi hanzari foge qwallarta,tare suka ahigo manne da juna,sai ta kauda kanta daga saitinsu din ragewa kanta kaifin kibiyar mashin da ta soketa,ba haka zainab taso ba,wacce iriyar mayyace yarinyar mara zuciya,ita miji bai bata mata rai tayi fushi da shi ne,sai ta zame jikinta daga na mukhtar tana masa sallana hannunta dauke da leda mai dauke da tambarin SS store.         Wuceta yayi kamar bai ganta ya ya shiga daki fuskarnan kamar ta mayunwacin zaki,tamkar ba shine ya shigo yanzun yana dariya ba,jikinta sai ya mutu murus ta kasa tashi har aka kusan cin minti talatin sannan ta yunqura ta tashi.         Gefan gado ta sameshi yana waya wanda da alama da zainab din yakeyi,ya ilahi ba yanzu suka rabu ba kuma?,sumayya ta fada a zuciyarta,kafin ta qaraso ciki ya kashe wayar yana qoqarin kwanciya "Yaya kace na maka fried rice kuma naga kana shirin kwanciya baka ci ba" a banzace yace "Bani zanci ba,don ni naci abinci gidansu zainab na cika cikina,ita zaki kaimawa ita ke sha'awar ci" shiru tayi ta tsaya cak kamar an kafata,me kenan?,wannan zallar wulaqanci ne,dama saboda cikin zainab din ya tasheta tara saura na dare ta hau sanon girki? "Ko ba zaki bane ni na taso da kaina na kai mata?" Ya fada yana daga kwancen,tabbas da ta iya rashin kunya yau da zata yiwa mukhtar ko yaya take,saidai kowanne tsuntsu ance kukan gidansu yakeyi, tunda ta taso gidansu dai dai da rana daya bata taba katarin ganin innarta ta yiwa malam musu ba duk girma da wuyar umarnin da ya bata,sai ta kada kai da dauki flask din ta nufi sashen zainab din.         Har ta rufe qofar falonta amma ta qwanqwasa mata saboda cika umarnin mukhtar din,minti biyu tsakani aka bude,tana sanye da kayan bacci,kallonta tayi daga sama zuwa qasa sannan ta yatsina "Ya akayi" "Abincinki" ta bata amsa a qaice "Mtsweeew,bazan iya ci ba gaskiya" bata jira sauran abinda zai biyo bakinta ba ta juya,taku na shida cikin na bakwai taji tace "Kawo dai na taimaka miki na dandana kada kiyi wahalar banza" idan kujerun dake gun sun amaa to itama ta tanka,banza ta baiwa ajiyarta taci gaba da takunta,sai ta tsinto muryarta "A sannu dai yarinya,kishi da zainabu abu babu dadi,hattara wlh da ni,yanzu kika fara gani sai kin fice sa qafafunki" ta fada tana qoqarin maida qofarta "Ni nafi qarfinki,na kuma fi qarfin ire irenki,irinki dubu ma wallahi saidai suga sumayya su qyale" cike da mamaki tace "Au haka kikace?,bari Allah ya kaimu gobe zaki amshi sakamakon wannan diban albarkar da kika yimin hannun mukhtar,sai nasa ya dakaki wlh cikin gidan nan" tsaki sumayyan ta ja sannan tace "Mukhtar ne taqamarki ni kuwa Allah na riqe,da ni dake maga wanda yayi riqo da kakkaurar igiyar da bata tsinkewa" daga haka ta juya ta barta gun sake da baki tare da saqa mugun zare sake tada qaimi a kan sumayyan,babu shakka sai tasa an mata daurin butar malam yadda zata zamo qarqashin ikonta kamar yadda ta soma maida mukhtar.         Ta jima tsugunne gaban gadon tana zubda hawaye tare da roqon ya yafe mata idan ta masa wani laifine da ya canza shi,yana jinta zuciyarsa na masa suya yana tuhumar kansa na dalilinsa na quntatawa sumayyar,saidai wani sashe mai qarfi na zuciyarsa na gaya masa yayi dai dai,da wannan ya shareta har ta gaji da tsugon nan ta miqe.          Bata bari tayi asarar daren ba,alwala ta daura,ta kuma duqufa qwarai wajen roqon ubangiji ya kawo mata haske,ya tsaresu ita da mukhtar din,tana yi ta zubda hawaye masu dumi,lallai sai yanzu tasan meye rayuwar aure,ashe a baya duk wasa takeyi?kallon kitse take yiwa rogo?,ya jima cikin bargon yana kallonta,tausayinta na son tasiri cikin zuciyarsa amma hakan ya gagara,a haka bacci yayi awon gaba da shi.         ****     ****    **** *WATA RAYUWA..........*        Wata bahuguwar rayuwa mai ban mamaki ta soma yi cikin gidan wadda ko cikin nafarkai mafarkinta bai taba biyowa ta irin wannan bigiren ba.         Zainab ta zama tauraruwa mai wutsiya cikin gidan,a zahiri idan kayi naxari da tsinkaye ba zaka kawo ita ke sarrafa lamuran gidan ba,saidai ga duk wanda ya taba katari da fadawa halin da sumayya ke ciki tashin farko zai fuskanci inda zaman gidan ya sanya gaba.           Ta bawa asiri amanna,kusan shi ya zame mata jagorar zamowarta mata ga mukhtar din,baya ga haka,macace mai tsananin kissa wadda ta cakuda ta da asirin take matuqar tasiri kan mukhtar din,cikin salo da sanabe zata bashi umarni kai tsaye zaya aiwatar,wanda idan kai dake gefe ka kalla zakayi zaton tsabar iya biyayya ce da iya zama da miji,saidai ina sam ba haka abun yake ba,asiri ke yawo kan qirji da qwaqwalwarsa,dukkan wani lamari da ikon sarrafawa na hannunta,abu GUDA DAYA TAK da yayi mata karen tsaye cikin tafiyar da aikinta shine SUMAYYA,ta kasa maida ita qarqashin mulkin nallakarta,wanda hatta su yaya yahanasu yanzun na qarqashin ikonta,,suna jin zafin yadda take mulkasun amma koda kudi basu isa suyi qorafi ba,saidai a bayan idonta suyita zagi da qorafi iyakarsu kenan.         Abu guda data fuskanta shine,sumayyan ta lazumci karanta qur'ani,alwala ta zama abokiyarta,qur'ani ya zama abokin hirarta,koda wani abu ya tsorata ta abu na farko dakw fitowa bakinta shine SUBHANALLAH KO BISMILLAH,bata mantawa akwai ranar da aka kawo mata yaronta da ta haifa da bashir wato nafi'u,yaro ne maras ji sosai suka batawa mahaifinsa tarbiyyar yaro tunda yanzun haka yana hannun mama amarya ne mahaifiyat zainab,yana wasa da macijin roba,daidai fitowar sumayya ya wurga mata shi wanda sam bata ma kula da yaron na gurinka ba,sosai ta tsorata amma abinda ya fara fitowa daga bakinta shine BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM,daga haka ta shige zainab din na taya dan nata dariyar yadda ya tsorata sumayyan kallo basu isheta ba.           Kusan babu wanda yasan halin da take ciki banda anty dije itama don tana ganin ita daya hankalinta bai kai mizanin sarrafa matsalolin irin wadan nan ba ita daya,tana amfani da shawararta kuma ta qaruwa tare da ganin nasarori,duk da ayanzun ta tattara lamarin mukhtar tana biyarshi da addu'a,sau tari wani lokacin ko ganinta ta fuskanci baison yi,abinda tafi daga mata hankali kenan,wasu lokutan kuma sai ka ganshi kamar ba shi ba ya koma mata yaya mukhtar dinta.           Duk abinda ta gani tana dorashi ne kan mizanin nan da hausawa kance AURE IBADA NE ta yadda kumma tayi imani da hakanne,don sau tari anty dije na maimaita mata kalmar. _muje zuwa babi na gaba_ *ina jin dadin comment dinku,ku karbi jinjina daga gareni* *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 2⃣6⃣ _______________________ *Bismillahir rahmanir rahim* *wa may yattaqil laha yaj'al lahu min amrihi yusrah* _duk wanda yaji tsoron Allah Allah zai sanya masa sauqi cikin lamuransa_ _______________________         Su biyun ne zaune cikin falon kowa na sabgar gabanta,sumayya na guga saboda socket dinta ya lalace ya tilasta mata fitowa falon don yin gugar,yayin da zainab ke zaune saman kujera qafa daya kan daya kamar yadda ta saba zama kenan cikin izza da nuna ita watace,gama share falon da mopping dinta kenan ga zauna don ta huta,duk wanda ke da girki shike wannan aikin,ba laifi zainab din nada tsafta dai dai gwargwado.           Sallamar da ake zabgawa daga harabar gidan shi yaja hankalinsu,zainab ce ta miqe tare da ajjiye remote din hannunta ta bude qofar ta fita,fadima ce ita da jamila diyar yaya yahanasu,bakinsu a washe suka soma takowa zuwa inda take "Ku tsaya daga nan da Allah ku cire takalmanku kada ku batawa mutane waje yanzu na gama mopping" da fari jamila tayi dum amma ganin fadima ta tsugunna ta cire nata ya sanya itama dole ta cire,juyawa tayi fuska a cusgune su kuma suka bi bayanta.            Zama tayi kan kujerar ta maida qafarta yadda take,suna shirin zama saman kujerar da sauri tace "A'ah,da Allah ku zauna a qasa,ai carfet ne,idan kuma baku iyawa ku tafi can ga nata kujerun can ku zauna a kai" tsabar qin da suka yiwa sumayyan suka gwammaci zama a qasa,suka gaidata ta amsa da qyar,ko kusa baau dubi sumayya dake guga ba,haka suma ko qurar data kwasosu bata kalla ba "Dama yaayaa ce ta aiko mu gun yaya muntari" inji fadima,wani kallo ta watsa musu "Bacci yake,ku fadi saqon sai na gaya masa idan ya tashi" shiru suka dan yi sannan suka dubi juna alamar basu son fada,hakan yasa ta dubesh kai tsaye "Sai ku tashi ku koma da saqonku,ko kuma wadda ta aiko kun tazo da kanta" "Yaaya yahanasun?" Suka fada tare cikin mamaki "Eh,ita din mana,to meye?,kunga ku tashi ku bani guri da Allah,muta ne sai shegen binbinin tsiya haba" ta fada tana jan tsaki tare da mai da kanta gun t.v.          Zuciya ce ta zowa jamila wuya,bayan sun miqe sai ta kasa shiru "Kema halin fa'izan gareki?,lallai akwai butulu a duniya da yawa,to wlh bari kiji,baki isa ki shiga tsakaninmu da dan uwanmu ba wallahi"kallon banza ta yi mata sannan ta saki murmushi tana kada qafa "A'a'ahhhhhh.....yaro man kaza,quruci dangin hauka" "Ke za'a gayawa wannan ai mahauk......." "Idan kika sake bakinki ya qarasa wallahi sai na tashi na tsitstsinka maki mari,na kuma tattaka ki naga wanda ya tsaya miki...." Ganin yadda ta yunquro kamar zata sanya musu dukan ya sanya fadima ta janyeta suka fice jamilan na ciccika baki tana cewa "ai umman zata zo naga uban da ya isa ya hanata ganin dan uwanta,mata duka sai shegeb butulci duk wadda ka yiwa rana sai ta yi maka dare" itakam sumayya na gefe,ci kanku bata ce ba balle ta dago ta dubi abinda ke faruwa,tana jin zainab din na ci gaba da banbaminta mai kama da jirwaye da kamar wanka "Ni wallahi babu wata yar miji da zata shiga rayuwata tunda ba ita ke aurena ba,idan da can an saba muku toni wallahi bazan lamunci a dinga tatsemin miji ba" ita dai ko kallo bata isheta ba,cikin hakan mukhtar ya fito sanye da doguwar riga jallabiya "Ke dawa haka ina daki ina jiyoki?" "Ni da danginka mana,haka akeyi basu da aiki sai zuwa roqo tsakani da Allah?" Zancan sai ya baiwa sumayya mamaki,iko sai Allah,ke kudin nan ba naki bane,kuma wanda suka roqa din ai dan uwansu ne ko?. Tsaki yaja yana zama kan daya daga cikin kujerun "Kudi take so zata biya kudin makarantar yara,na kuma gaya mata tayi haquri ribar hannuna na baki zaki fara saida mayafai,kasuwa kuma yanzun sai a hankali ba kamar da ba amma ta qi yarda,gwara da suka tafi din don ko sun sameni ba ni babu abinda zan iya bayarwa" "Ato nidai na kora musu jawabi" ta fada tana tafa hannuwa "Samamin ruwan zafi du Allah" ya fada yana kashingida. "Gaskiya muntari na fara gajiya,aikin gidan nan fa akwai wuya kawai ka sama min mai aiki" ta fada a shagwabe,murmushi ya danyi sannan yace "Kada ki damu,kafin a kama azumi za'a samar mikin ki bada cigiya"fari tayi da ido cikin salo" kai dear na ko gode....bari na kawo maka"miqewa tayi tana wani rangwada tare da sakin wani dan qaramin fito na jin dadi,a duniya bata da burin wulaqanta sumayya,tunda ita taqi samuwa to ko ta hanyar mukhtar din kawai ya isheta tunda tana cimma burin cusguna mata.           A hankali idanunsa ya sauka kanta,tana gefe daya tana guga abinta,sai ka rantse bata cikin falon ko batasan meke faruwa ba,saidai can qasan zuciyarta ita kadai tasan meke nuqurqusar zucida da gangar jikinta baki daya,baki daya ba mukhtar dinta take ganin ba a yanzun,siffar ce kadai tasa,rabon da ta sanya shi idaunta kwanaki uku kenan,idan yaso yana iya daukar kwananta ma ya kaiwa zainab din,saidai ci kanka bata taba ce masa,ta debo idanu kawai ta sanya musu.         A nutse yake nazarinta wani abu na fisgarsa,sosai yaga ta fada ta sake haske,qirjinta ya sake cika sosai sai hancinta da ya sake fitowa saboda rama,riga mai dogon hannu da skert ne a jikinta na wani yadi mai roba,kanta na kame da ribbom don ta jima rabonta da kitso "Sumayyah" ya furta a hankali ba tare da ya san kalmar ta fito ba,sarai ta jishi amma sai tayi zaton gizo kunnenta yake mata,saboda haka tayi banza da shi "Sumayya ba zaki kula ni ba?" Ya kuma fada a tausashe,sosai muryar ta bugeta,murya ce irin wadda yake mata amfani da ita a zamanin BAYA,hakan ya sanya ta gaza daurewa,sai ta daga idanunta da suka cika taf da qwalla ta azasu kansa,kallon kallo suka farayi kowa zuciyarsa da gangar jikinsa na shirin motsa masa soyayyar dan uwansa da suke tunanin sunyi bankwana da ita.          Muryar zainab dake takowa daga kitchen ta raba tsakaninsu,sai ta gaza ci gaba da gugar ta zare socket din ta tattara kayanta ta wuce dakinta,kan gado ta fada ta saki wani marayan kuka,zuciyarta da jikinta na azabtuwa da qaunar mukhtar da kewarsa.                  ****     ****      ****        Da izzarta da bacin rai ta diro gidan tun qarfe tara na safe,saidai ga mamakinta tana qarasowa cikin falon ta qwala sunan zainab din wadda ta fito cikin kayan bacci sai ta nemi duk wani bala'i da ta tanada ta rasa,hasalima ma sai ta fara gaida zainab din,sheqeqe tace da ita "Lafiya?,me kika zo yiwa mutane a gida tun farar safiyar nan,ko farkawa masu gidan basu yi ba?" "Haba ko hutawa ai nayi ko zainabu abu" "Hutu kika zo yi gidan da ba naki ba?" Ta fada tana rungume da hannunta a qirji "A'ah....to....to daka jiya na aiko yara zasu karbi kudin makarantarsu ne sai kuma basu samu ganin kawun nasu ba,shine ni na biyo sahu,saboda koda yaushe za'a iya korarsu daga makaranta" gyara tsaiwarta tayi "Au basu gaya miki rashin mutunci da rashin tarbiyyar da suka zo suka yimin ba?" Duk da cewa tasan komai amma sai ta samu kanta da gaza nunawa "Su su fadiman?" "Eh su din fa,don haka ina mai sanar miki cewa sun jaza miki,ba zaki samu damar ganin mukhtar ba,bacci yake koma ba haka ba wallahi ba zaki ganshi ba,ki tashi sawunki a likkafa ki tafi,babu mai matsawa mijina da shegen roqe roqe" idanu yaya yahansun ta zuba mata,tana so tayi masifa amma ta kasa,kamar an wanke zuciyarta haka takeji.       Tunda ta idar da sallar walha ta bingire da baccin da batasan sanda ya dauketa,muryar zainab din ta dinga jiyowa sama sama wanda shi ya farkar da ita,bata da niyyar fitowa amma tilas ta fito din sabida yunwar da ta tashi da ita.          Zainab din na tsaye kan yaya yahanasun tana zubda shika shikan rashin mutunci,yaya yahan tayi muqus kamar ba ita ba sai idanu da take bin zainab din cike da mamaki ba tare da ta iya tankawa ba,fes sumayyan ta fuskanci meke faruwa tunda na jiya ma gaban idonta akayi,sosai taji ranta ya baci,a rayuwarta ta tsani wulaqata babba sam,a kwanakin quruciyarta har kuka idan taga babba cikin wata iriyar rayuwa,ko ba komai ko bata girmesu ba yaya yahanasun ai tsatson mukhtar ce duk lalacewarta,ranta taji yana baci hakan ya sanya ta gewaye ta bayan kujerun ta bude qofar da zata sadata da falon mukhtar zuwa dakin baccinsa kai tsaye ta shige,wanda hakan shi ya ja hankalin zainab,da sauri ta fara kiranta da niyyar tsaidata saidai ko qurar data kwaso bata kalleta ba bare ita,hakan ya sanya ta rufa mata baya,tana shiga falon ta bame qofar dai dai lokacin da zainab din ke qoqarin sanya qafarta a falon,tana iya jiyo hayaniyarta akan ta bude qofar kada ta tasar mata miji,banza ma ta fita saboda haka ta nufi dakin gadon.            Kan side bed drower idaninta ya fara sauka sanda take qoqarin isa ga mukhtar din wanda ke daga can saman gadon yana barci,garwashi ne tare da wani qullin tsumma a kai,a hankali ta taka zuwa inda kayan suke,idanu ta zuba musu tana nazarinsu,babu alamun turaren wuta zata sanya don bata ganshi ba,hakanan taji bata aminta da qullin ba musamman da taga launin wani irin tarkace dake ciki,sai ta kunce qullin bakinta dauke da addu'o'i ta tura bandakin mukhtar din ta shiga,cikin masai ta zazzage dukkan maganin tayi plushing dinsa.         A hankali ta soma ambaton sunansa hannayenta harde a qirjinta fuskarta a dinke tsaf,idanunsa ya soma warewa kanta kafin ya gama budesu baki daya cike da mamaki,ya manta rabonsa da ya ganta cikin dakin,zai ambaci sunanta ta dora yatsanta kan lebanta sannan kai tsaye tace "Tashi" ba musu ya yaye bargon ya tashi,sai ga taka zuwa gefansa ta zauna,idanunta sosai cikin nashi ta soma magana muryarta can qasa "Wacece yaya yahanasu a gunka?" Cikin rashin fahimta yake dubanta,sai kuma ya bude bakinsa a hankali "Yayata ce" "Zainab kuma fa" hade rai yayi yana jin qin wani abu da zai taba martabarta cikin ransa "Mata ta ce" "Cikinsu wa zaka iya sauyawa" take yaji zuciyarsa ta harzuqo "Kinga....bansan....." "Riqe maganarka tukun" itama ta katse shi "Ka tashi ka wuce kaje tana son ganinka yanzun nan" ta fada kanga tsaye cikin bashi umarni tare da miqewa abinta tana shirin ficewa,binta yayi da ido cike da mamakin yadda yau ta dumfareshi kai tsaye a yau din tana kuma bashi umarni,hakanan yaji ya kasa musanta mata,sai ya sauko da hanzari ya zura takalminsa yabi bayanta.          Bakin qofa suka tadda zainab,ga mai hankali kallo daya zaya yi mata ya gane hankalinta a matuqar tashe yake,ita kadai tasan wahala da kuma kudin da ta kashe kafin samuwar maganin,a yau akeso ta yiwa mukhtar din ya kuma shaqi hayaqin sosai,kusan sai yau ta samu wannan damar,amma ta fuskanci tana naman bare mata,saboda haka suna fitowa ta fada dakin don duba abinda ke wakana ba tare da ta kuma bi ta kan su yaya yahanasun ba. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 2⃣7⃣ ______________________________________ *Bismillahir rahmanir rahim* *wa may yattaqil laha yaj'al lahu makhraja,wa yarzuquhu min haisu la yahtasib* _duk wanda yaji tsoron Allah to Allah zai sanya masa mafita(cikin lamuransa),ya kuma azurtashi ta inda baya zato_ *ya Allah kai mana baiwa da jin tsoronka,ka azurta mu da dukkan kyakkyawa* ___________________________________          Tana bayansa har suka qarasa inda yaya yahanasu taje zaune tana kallon ikon Allah,a mutunce sumayyan tace "Yaya ina kwana?" "Lafiya" ta amsa babu yabo ba fallasa,tana son ganin kyawun kyautatawar data mata idan da hali ta mata godiya amma sai ta kasa,dama sumayyan ba domin ita tayi ba,tayi ne domin girman Allah da kuma girman da zumunci ke da shi a wajen ubangiji,hakanan ko ita ba zata so ace yau yaya abbakar ya auri wata da zata rabashi da su ba,ko ita ta haifa ya auri wadda zata rabasu din,kitchen ta wuce ta soma hadawa kanta dan abinda zata iya ci,ko kafin ta kammala ta fito ma falon babu kowa da alama ta tafi,sai ta zauna ta fara kurbar ruwan shayinta.          Kamar daga sama zainab din ta fito tana banbamin masifa kamar zata ci baki mukhtar na biye da ita yana son shan gabanta amma ya gaza cimmata,qerere tayi a kan sumayya wadda ko mutuncin kallonta bata samu ba "Uban wa ya saki ki tabamin turaren wuta na?" Sosai abun ya bata mamaki,har tana iya bude baki tayi cigiyar kayan data tabbatar ba na Allah bane?,qare matsota tayi tana huci ta kuma maimaita tambayar tata,ganin zainab din na qoqarin kai hannunta jikinta ya sanya sumayyan dubanta "Kada ki soma,don fankan fankan bata kilishi wallahi kika dakeni bazan dubi girmanki ba tsaf zan rama" idanu ta zaro tana nuna qirjinta "Ni zaki daka don ubanki,to dokeni din" "Wai meye haka ne zainab ba tun cikin daki nake miki magana ba?,ke sumayya tashi ki koma dakinki" wani kallo ta watsa masa sannan ta dakata da shan tea dinta "Kayi haquri amma bata isa ba wlh don yanzu na fito ban kuma kammala uziri na ba,kana iya janye matarka idan na gama na tafi ita ta fito" ta fada tana ci gaba da kurbar shayinta duk da wata iriyar tafasa da zuciyarta ke mata,jinta take dai~dai sa su baki dayansu,banda daraja da girman sa da take gani babu abinda zai hana ta yayyaba masa baqaqen maganganu masu zafi "Muje nace zan biyaki kudin ko?" Sai ta sauke ajiyar zuciya,dama abinda yafi damunta kenan,don sake samun wani maganin wannan da sauqi   "Allah ya ceceki" ta fada tana huci sannan ta juya tabi mukhtar din,cak shayin ya tsaya mata a wuya,ambaton sunan Allah ta dinga yi don ya kawo mata dauki,tabbas sai yau ta tabbatar mukhtar dinta ba cikin hayyacinsa yake ba,kayan karin da bata gama ci ba kenan. **** **** *****          Wani nannauyan bacci ne ya dauketa tun bayan kammala sallar asuba,hakan ya sanya bata tashi ba sai wajen sha daya saura na rana saboda zafin rana da ya fara hudo labule.             Da wata mahaukaciyar yunwa ta farka,saboda haka bandaki kawai ta shiga ta wanko bakinta ta shiga kitchen don samarwa kanta abinda zata ci,don bata sa aka ba tasan ba samun abun kari zata yi ba,haka ne yake faruwa duk ranar girkin zainab din,shi kansa mai gidan wani lokaci sai dai ya fita haka.           Sam bata lura da meke faruwa ba sai data shiga cikin kitchen din sosai,nafi'u ne yaron zainab tsaye dare dare kan stool yana sauke dukkan farantanta na tangaran dake jere cikin glass drower dinta yana sakinsu qasa daya bayab daya suna tarwatsewa.         Da sauri ta qarasa ciki tana kiran sunansa cikin tsawa,ko gezau baiyi ba bare ya fasa aikata abinda yakeyi din,hannunshi ta riqe gam kana ta saukeshi daga kan stool din tana dubansa ransa a bace "Baka da hankali?,ko bakasan me kake yi ba?,ko bakasan abin amfani kake lalatawa ba?",cikin rashin kunya yace mata "na sani mana"abun sai ya bata haushi ta kama kunnansa ba tare da ta murde ba tace " wato tsabar rashin ji ne kenan ko?" "Sakarmin kunnena ai kema bake kika siya ba,kuma Allah ya isa na da tabamin kunne da kikayi" sosai yaron ya bata haushi da mamaki,ta sanya tafin hannunta ta buge masa baki,wata qara ya saki kamar wanda aka sanya wuqa aka yanke masa maqogaro yana fadin "wayyo bakina wayyo mama ta fasamin baki".          A hautsine ta fado kitchen din dama tasan hakan na iya faruwa,don ita ta sanyashi,saboda har yau bata huce takaicin asarara maganinta da sumayyan ta jawo mata ba,duk da mukhtar din sai da ya biya ninkin kudinsa,da sauri ta qarasa inda suke tsaye ta ture sumayya tana fadin "me kika yi masa?,me tayi maka nafs(da yake haka take kiransa)" "Bakina ta dakarmin mama duba ki gani"hannunsa ta sauke tana duba bakin,babu wani abu da yayi tunda duka duka dukan data masa ba wani mai zafi bane,waiwayawa tayi ta dubi sumayya dake tsaye rungume da hannu tana dubansu " dukarmin yaro kikayi saboda bakisan ciwon haihuwa ba ko?,to wallahi sai na rama masa"sai kuwa tayo kan sumayyan gadan gadan.          Ko alama bata motsa ba har ta qaraso inda take,ta daga hannu da niyyar zuba mata mari caraf ta kama hannun nata ta yarfar da shi gefe,sannan cikin bacin rai tace mata "Bansan ke din wace iriyar uwa bace,ban kuma san irin tarbiyyar da kika bama yaronki ba,amma bari na gaya miki,matuqar irin wannan tarbiyyar ita kika bashi to ba shakka kin cuci kanki,abu na gaba duk iya zaluncin da zaki aikata cikin gidan nan kiyi,Allah na sane da ke,amma kada ki soma gigin daukar hannu kice zaki dake ni,don baki haifeni ba,ba kuma kisan ciwo na ba kamar yadda kika ce bansan ciwon haihuwa ba,kuma kema ba Allah kika yiwa fadanci ba ya baki,ganin........".ihun da zainab din ta qwalla gami da dora hannu bisa ka ya dakatar da ita daga maganar da takeyi,sai tayi sororo tana dubanta tare da tunanin ko zainab din nada ciwon hauka ne dake tashi lokaci bayan lokaci?.          Sam bata fahimci tarko bane ta dana mata sai data ga shigowar mukhtar cikin kitchen din a rude,ashe tuni taga giftawar inuwarsa ita zainab din,binsa tayi da kallo sanda ya nufi zainab,ta manta kwana nawa rabon da ta sanyashi cikin idanunta,ranar qarshe kawai zata iya tunawa da bata kuma ganinsa ba sai yau,itace randa ya rufeta da fada tamkar zaya daketa,sabida tayi dan wake abincin dare,ita kuma zainab tace sam bazata ci ba ai dan wake ba abinci bane,ya umarceta ta shiga kitchen ta yiwa zainab din shinkafa da miya qarfe goma na dare,umarnin ya yi mata tsauri saboda haka bata ko tanka ba ta wuce dakinta tayi kwanciyarta bayan ta kulle qofarta,don tana da yaqinin zaya iya biyota,ilai kuwa ya biyo sahun nata,yayi bugun duniya taqi ta bude masa,hakan ya sake harzuqa shi,haka ya koma tare da ci mata alwashin sai ya sabar mata,to tun daga ranar rabon data karbi girki ma cikin gidan,saidai idan sun kammala a barshi a kitchen,idan tana da sha'awarci ta diba,idan bata ga dama ba ma ko kallo bai isheta ba.        "Wato ke kin zama 'yar iska mara mutunci ko?" Ya fada yana nufota cikin huci bayan zainab ta gama tsara masa qarya kan abinda ya faru,hannu tasa ta toshe bakinta saboda yadda taji kanta ya mata dummm,kalmar ta yiwa qwaqwalwarta tsauri haka nan ta yiwa kanta nauyi,ita mukhtar ke kira da 'yar iska?,kalmar da babu wani mahaluqi da ya taba jifarta da ita?,da sauri ta juya ta fita daga kitchen din cikin sassarfa saboda kukan dake shirin qwace mata ba wai don mukhtar din dake nufota ba. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 2⃣8⃣ _________________________ *Bismillahir rahmanir rahim* *lillahi mulkus samawati wal'ard,yakhluqu ma yashaa,yahabu limay yasha'u inasan wayahabu limay yasha'uz zukur,au yuzawwijihum zukranaw wa inasaa,wa yaj'alu may yasha'u aqima* _mulkin sammai da qassai lallai na Allah ne,yana halittar abinda yaso,ya bawa wanda yaso kyautar(d'a) 'ya'ya mata ya bawa wanda yaso kyautar 'ya'ya maza,ko kuma ya cudanya musu maza da mata,ya sanya kuma wanda yaga dama ya zamo bakarara(wanda baya haihuwa)_ *ya Allah ka azurtamu da managartan zuriyya shiryayyu saboda annabinka S A W* __________________________       Yau babu tantama abinda ke mata kaikawo a zuciya ya tabbata,mukhtar ya daina sonta ya daina mararin ganinta,wannan wacce iriyar rayuwa ce?,haka mata keji duk sanda suka samu juya baya daga wajen mazajensu ba tare da haqqinsu ba?,me yakai wannan zunubi shiga tsakanin ma'aurata?,shiga tsakanin masoya?,masoyan da suka gina zuciyoyinsu da qaunar juna,tsaftatacciyar qauna ta fisabilillahi. Wani mugun amai mai zafi taji yana taso mata,da qyar ta samu ta isa bandaki,ta dinga kakarin aman tamkar hanjin cikinta zai fito,saidai banda wahala da yunquri babu abinda abinda ya fita din saboda babu komai cikin cikin nata,don a yanzu ba kowanne lokaci take yarda da abincin zainab ba. Haka ta gama wahalarta sai yawu kawai data fitar ta sakarwa kanta shower tana wanka tana kuka har ta kammala sannan ta dawo cikin dakin iska na dibarta ta zabi doguwar riga ta sanya ta koma saman gadonta tayi dai dai,jinta take wani iri daban,zazzabi taji na son rufeta,haka ta yunqura ta sha paracetamol ta dawo ta kuma kwanciya,tunani ta shiga mai zurfi lokaci lokaci tana dauke hawayen dake bin kuncinta.        Kamar daga sama ta dinga jiyo sallamar zainab qanwarta,daurewa tayi ta miqe ta dawo bakin qofar dakinta don ta sanar mata tana ciki kada zainab tayi qaryar bata nan,sai data tabbata zainab din taji sannan ta koma bakin gadonta ta zauna har ta shigo. Kallo daya ta yiwa sumayyan tace "Lafiya kike kuwa anty" qoqarin qaqalo murmushi tayi sannan ta dan ja tsaki "Qalau nake,yau ne kinga na tashi bana jin dadin jikina da bakina gaba daya" "Yaya kamar fa kuka naga kinyi" sai ta basar ta hanyar fadin "Barni kawai,nida mukhtar ne ya matsan sai da nasha magani,ni kuma kinsan bana son qwayoyi" sai zainab din ta gamsu da maganarta ta zauna tana fadin "Kamar kuwa mamanmu ta sani kinga tace sai na tsaya tayi dambu mutuminki na kawo miki",ba jira kuwa ta sanya hannu ta janyo flask din ta bude ta soma ci. Sosai taji dadinsa cikin bakinta,sai data ci fiye da rabi sannan ta ajjiye.       Bata sake fitowa daga dakin ba ranar,kusan yini sukayi ita da zainab tana mata 'yan gyare gyare cikin dakin,koda ta yunqura don sama mata abinci sai tace azumi ma takeyi,a nan take gaya mata mama tace taje ta yiwa anty dije sallama zasu koma abuja ita da mai gidanta,gwamnatin tarayya ta qara masa matsayi,duk sai jikinta yayi sanyi,bata son rabuwa da anty dijen,idan ta tafi bata da gun wanda zata je su shawarta matsalarta kenan,anty dije zata tafi ta barta a sanda alamu ke nuna matsalolinta qara qarfi suke. Sai taji zuciyarta na neman raurawa amma sai ta aro dakiya da juriya ta yafa wa kanta gudun kada zainab din ta fahimci wani abu.           Sai yamma lis zainab ta tafi ko banza ta debe mata kewa sosai kuwa,a ranar ta sanar da mukhtar tana so taje wajen anty dijen washegari,saboda jibi zasu tafi,Allah ya dorata a kansa ranar tambotsan nasa da sauqi,don a dakinsa ma ta kwana duk da zaman kurame sukeyi.      ****      ****      ****       Tun goma na safe ta kammala shirinta tsaf cikin shadd ja wadda aka yiwa adon stone work baqi,ita kanta sai data tsaya ta kalli kanta,duk damuwar da take ciki amma sai taga ramarta bata fito kamar baya ba,mamakin yadda ta qara haske da cika takeyi,haka ta yafa baqin mayafi a kanta ta saqala baqar jaka ta fito.           A harabar gidan sukayi clashing da su kasancewar harabar ba mai girma bace,tilas idan zata wuce din su ganta,yana zaune cikin mota zainab na tsaye riqe da murfim mota,kudade ta yanka masa zai bata shine ta biyoshi amsa,tana karba ta juya tayi ciki abinta,zuwa lokacin sumayyan ma har takai ga ficewa daga gidan.          A hankali yake bin bayanta,sosai ya rage gudun motar yana tafiya a hankali don baison ya wuceta,tafiya take cikin nutsuwa,idan ka kalleta sai ka rantse da Allah bata taba aure ba,sosai shaddar ta haska jar fatarta,ga komai nata yayi mata cif a jikinta duk da da shigarta babu inda ta bayyana tsiraici,a haka har suka kai bakin titi,yana so yace ta shigo ya kaita amma kamar an masa shamaki da ita haka yakeji,haka ya karya kan motarsa ya wuceta ya hau kwalta sosai. Itakam sai a lokacin ne ma ta lura da shi,da idanu ta rakashi sannan daga bisani ta dauke kanta tana hadiye wani abu mai d'aci.           Sosai ta lula tunani tsaye a bakin titin wanda hakan ya sanya ta kasa ankara da horn din da yake ta zabga mata,murmushi tayi ta qaraso gaban motar bayan ya sauke glass din "Wa nake gani kamar abdur rahman cikin mota?"ta fada tana duban motar samfurin *vibe* fara qal da ita,sosai motar ta mata kyau Murmushi yayi yana fadin "Eh mana,ya son ranki?" Cikin dariya tace "Fes wallahi" "Ina zuwa haka da safe?" "Zani gidan anty dije ne zamuyi sallama suna shirin bar mana kano su gudu abuja" "Shigo ciki ma qarasa maganar ai hanya ta ce indai gidan da take har yanzu shine" ya fada yana bude mata mazaunin gaba "Rufan asiri nan ai na qanwata ne,nan ma ya isa" ta fada tana shiga baya "Yayarki dai,kina nufin nidin ban girme miki da wajen shekara uku ko hudu ba?" "Jimin mutum da shegen son girma,shekara hudu kakar wata shekara arba'in,kai uku ne ma" "Ko second daya ne dai na fiki ko?" Ya fada yana dariya,don sun saba da wannan caftar indai shi da sumayyan ne,itama dariya ta saki sannan suka shiga gaisawa a mutunce,ta tambayeshi mutanan gidan da kawunsa wanda qani ne ga mahaifin mukhtar. "Kinsan tun ranar nan naso kawowa yaya mukhtar mota ta ya gani da kuma takardar zanen filin da zamu fara gina islamic clinic to ban samu dama ba" "Da kyau masha Allah abdhr rahman,Allah ya sanya alkhairi ya kade fitina,kace yanzu sai bude asibiti" "In sha Allah duk da aikin ginin ba qaramin abu bane,har kwantarwa nake sa ran zamu dinga yi,zamuyi amfani da likitancin musulunci da kuma na'urorin bature" "Kace mun kusa fara kiranka alhaji abdur rahman" "Da ba alhajin bane?,mijinki zaki cewa haka,gashi har yau ya kasa zuwa ko ina,ya zama sai a hankali wallahi" sai ta danyi shiru tana sauke boyayyar ajiyar zuciya don ha taba mata inda yake mata qaiqayi "Ina fata kina ci gaba da addh'o'inki ko?" "Babu abinda na fasa abdur rahman,sauqin ne sai a hankali" "Haka ne,kada ki gaji,kinsan ita cuta farad daya take shiga sauqi kuma samuwarsa sai a hankali,Allah ya yaye ma dukkan musulmi baki daya" "Amin abdur rahman,na gode" haka suka ci gaba da hira jifa jifa yana kwasarta da tsokana,har qofar gidan anty dije ya sauketa sanna ya mata kyautar dubu uku,da fari taqi karba sai da ya bata rai sannan ta amsa tayi godiya tare da bashi saaon gaisuwa gun qanwarsa bahijja da mamarsu. Anty dije taji dadin ganinta sosai,nan suka wuni suna hira,ta tayata hada ragowar kayayyakin da bata kammala hada kansu ba,tuni yaranta sunyi gaba don su qarasa kammale gidan kafin isowar maman tasu. Suna hada kayan tana mata nasiha mai ratsa jiki,idanun sumayyan ya hada qwalla har ta kai ga gangarowa,ta share qwallar tana fadin "Yanzu shikenan anty?,gurin wa zan dinga zuwa" sosai ta bata tausayi,yarinyar da dududu bata wuce shekara sha tara ba amma ta hadu da kaidin kishiyoyi kala kala,sai ta saki abinda take ta koma gefanta ta zauna "Kina da Allah sumayya,baya ga haka akwai waya hannunki,duk abinda ya shige miki duhu ki kirani ki tambayeni,koda babu kudi a ciki kimin plashing zan kiraki da yardar Allah,ki ninka haqurinki kawai,domin duk wata mace da kika ga ta zama wata gidan mijinta ki tambayeta wanne irin haquri ta hadiya kafin ta kai ga cimma wannan matakin" "To anty na gode" "Babu godiya,ke diyata ce kamar su yasmin kike a gurina.....amma sumayya yanayin jikinki kamar ya sauya?,ko baki kula ba?" Ta fada tana kallonta "Me kika gani anty?" "Bakya jin wani sauyi a jikinki?" "Babu abinda nake ji" ta fada tana kallon anty,shiru ta danyi sannan tace "Shikenan.....koyaya kika ji wani abu kada ki zauna,kije asibiti"duk da bata fahimci abinda take nufi ba amma ta amsa mata da to. Ana gab da sallar magariba ta koma gida,a gajiye ta koma,bandaki kawai ta fara shiga tayi wanka ya daura alwala,sai da ta kammala sallahr magariban sannan ta fita,cikin kitchen taji motsinta sai ta tura qofar ta shiga,tana tsaye tana hada food flask na abincin mukhtar,qarasawa tayi kusa da ita ta mata sallama,kai kawai ta daga ta dubeta ta maida kai taci gaba da abinda take ba tare data amsa ba,ita din ma bata damu data amsa ba kai tsaye ta jeho mata tambayar da ta fito da ita "ina abincina zainab,banga flask dina ba" Dagowa tayi sosai ta sake kallonta,sai ta saka wata dariya data sanya dole sumayyan ta tsaya tana kallonta cike da alamar tambaya,sai da ta tsagaita don kanta sannan tace "Ince ko baki samu labarin baki da abinci a gidan nan ba" jin maganar tayi banbarakwai,ba kuma ta fahimci inda ta sa gaba ba,saboda haka taci gaba da kallonta,dauke kai tayi daga bisani sai ta nufi dan qaramin store din dake kitchen din da niyyar fiddo da ko indomie ce ta tafasa,sai ta tarad da store din a garqame da kwado,waiwayowa tayi ta sake duban zainab din "Naga alamun baki fahimta ba,amma bari nayi miki bayani dalla dalla,mukhtar ya soke baki abincinsa,walau ni na dafa ko ke kika dafa kin fahimta ai yanzu ko?" Sosai maganar ta daketa,sai ta kasa furta komai baya ga wani abu da ya tokare maqoshinta,bata fahimci me hakan ke nufi,tilas ta jira dawowarsa tunda shi ya ajiyeta ba zainab ba,wannan maganar ba tata bace. Wuce zainab din tayi ta nufi sashenta ta dauki tukunya ta tari ruwa ta dora kan gas tare da jefa lipton,tilas ta sanya wani abu a cikinta ba don haka ba abinda take ji cikin zuciyarta bata jin wani abu mai suna abinci zai iya wucewa ta maqogoronta. Hannayenta ta harde saman qirjinta tana jiran ruwan ya tafasa,tamkar zata fadi haka take ji,ga yunwa ga bacin rai,tana kammalawa ta juye a cup ta nufi daki,bata ko bi ta kan qananun habaicin da zainab keta jefawa cikin waqe,don yanzu bata ita take ba ta kanta take. Tea ta hada da kayan shayinta wanda dama a dakin suke. Ko rabi bata sha ba ta soma yunqurin dawo da shi,sai data amayar da shi tas sannan ta dawo ta zube qasan carfet din dakin cikinta naci gaba da juyawa,rasa abinda ke mata dadi tayi,fashewa tayi da kuka tana kiran sunan Allah. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 2⃣9⃣ _________________________ *Bismillahir rahmanir rahim* *Bismillahir rahmanir rahim* *kullu man alaiha faan,wa yabqa wajhu rabbuka zuljalalu wal ikram* _dukkan wani abu dake kanta(duniya)qararre ne,zatin ubangijinka mai girma da daukaka ne zai dawwama_ _________________________ *Na sadaukar da wannan page da dukkan wani makarancin littafin KUNDIN QAgDDARATA,haqiqa zan so ace ina da lokaci da zan iya binku daya bayan daya na amsa commenta naku,saidai ina fatan wannan shafi ya isar muku,na gode qwarai* _masu qorafe qorafe kuyi haquri,ku karbi littafin a duk yadda yazo muku,da fatan kunyi duba da ayar da tazo a farkon shafin,ita kadai ta isa ku fahimci me nake nufi,godiya nake_           Kwananta biyu kwance cikin dakin babu abinda take iya hasalawa,daga kwanciya sai bacci,ga wani shegen zazzabi da yaqi sauka daga jikinta,duk lokacin da ta yunqura ta yiwa kanta duren shayi tofa qarshensa ya dawo baki daya,abinci kuwa ko kadan bata da sha'awar cin komai,hakan ya sanya ta haqura ta zubawa sarautar Allah ido,banda ruwa babu abinda take kurba,roqon Allah take ya sassauta mata ko ya jefo mata wanda zaya taimaketa,hatta da wayarta bata san inda ta cillata ba,a haka ta shafe kwana hudu cur bata ga kowa ba rana gurzar ciwnta ita daya,duk da cewa taci ranar girkinta har ta fita amma bata ga idon mukhtar ba,to idan da sabo dama ta riga data saba da hakan,data ga irin hakan tasan an karbi kwananta ne an qarawa zainab.       ****     *****     *****      Cikon kwana na biyar din cikin ikon Allah ta ji sauqi sauqin jikinta,tana jin qwari qwari a jikinta,har ta iya shiga da yammaci gab da magariba bandaki tayi wanka,tana fitowa ta soma laluben wayarta,can cikin jakar da ta dawo daga gidan anty dije ta ganta,a nan taci karo da dubu ukun da abdur rahman ya bata,sai taji dadin kudin don bata da ko siai a hannunta,to ina ma taga mai batan tunda ita ba sana'a take ba,caji ta sanya a socket din dake daura da madubinta,ta dawo bakin gadonta ta zauna ta soma shafa mai,daga inda take zaunen tana iya hango kanta sosai cikin madubi,ta rame sosai tayi wani fayau da ita,sai uban fari da ta qara kamar wadda ta hadiyi qwayar qara hasken fata.         Tura qofar dakin nata da akayi shi ya maidota cikin hayyacinta,ta dubi bakin qofar,mukhtar ke shigowa,sanye da yadi tissue na maza orange wanda ya ciza,yayi kyau sosai amma sai taga kamar ya rame,duj da bata sani ba ko idanunta ne,don idan ba makuwa tayi ba rabonta da shi yau kwanaki shida cif. Kanta ta dauke don bata ga dalilin ci gaba da kallonsa ba,ta soma lalubar mayafinta ta lullube jikinta saboda guntun towel ne kawai daure a qirjinta.        Shikam kallonta yake ci gaba da yi yana son lalubar sonta cikim zuciyarsa amma ya rasa duk da dumbin qaunar da yake jin tana zanga zanga cikin zuciyarsa wadda ya azata a bigiren tausayi,uban haushinta da yake ji yau babu shi kamar yadda bai jin soyayyarta cikin zuciyar tasa. Bata sake bi ta kansa ba har ta gama shafa manta,ta bude drower dinta ta fidda kayan da zata sanyasai a lokacin ta kuma dubansa "Ka fita don Allah zan sanya kaya" ta fada idanunta tsakar nashi "Me ya sameki haka sumayya naga kin rame?,ko duk shegen kishin da kika sanyawa ranki ne kamar yadda zainab ta fada?"ya fadi ba tare da yayi duba ga qorafinta na farko ba "Kan bala'i" ta fada cikin zuciyarta,wani baqinciki na takore mata qirji,wannan rainin hankalin da me yayi kama?,ita yake tambaya ma meke damunta? "Ba wannan ne a gabana ba,ka ficen a daki" ta fada ranta na suya,sai ya fara takowa inda take,wani shauqinta na fusgarsa,son kasancewa kawai yake da ita,yayi kewarta kwanakin bakwai din nan da bai ziyarceta ba "Bari na qaraso ki gayamin nawa muka hada muka gina gidan da har dakin ya zama naki". Qarasowarsa ke da wuya qamshin turarensa ya daki hancinta,wani tashin hankali ya ziyarceta,take ta saki kayan hannunta ta buqaci bandaki,nan ta fara kelaya aman da yayi sanadiyyar ficewar ruwan tea din data samu yau ya zauna mata.        " lafiya sumayya?,meke damunki?,me ya sameki?"haka ya dinga fadi yana riqe da ita,dukkan alamun tashin hankali sun bayyana a fuskarsa wanda hakan yayi matuqar daurewa sumayya kai,mukhtar din tamkar wani bugun jinnu haka ya koma,idan yaso ya dinga gasa mata aya a hannu shi da matarsa,amma wani lokaci sai ya dinga yunqurin juyewa ya koma mata yaya mukhtar dinta sak wanda ta sani a can baya.        Ganin qamshin turaren ke sake dugunzuma tunaninta ya sanya ta buqaceshi da ya matsa ya barta bata so,haka ya koma baya ya zuba mata ido har ta kammala ta gyara wajen ta dawo bakin gadon ta zauna tana maida numfashi "Kishirya na kaiki asibiti,ni bansan baki da lafiya ba" duk da yadda take fidda numfashi dai dai amma hakan bai hanata maida masa magana ba "Bani buqata,me magani zaya yimin?,shin wai damuwa kayi ma da wata sumayya?,na tabbata bakaqi na mutu ba,tunda har zaka iya hanawa a bani abincin gidanka ina a matsayin matar ka" ta qarashe maganar tana sakin kuka don sosai batun ke ci mata qoqon zuciya,ba wai don ta damu da abincin ba,a'ah,ta dauka tafi qarfin komai a gidan mukhtar din,ta dauka ita din mai iya dauka ce ta bayar ma kyauta,sai gashi ita ake hanawa abinci "Wallahi ni bansan lokacin da akayi hakan ba,waye ya gaya miki ni na hana?"maganarsa ta ratsa kunnenta,sai ta daga ido tana dubansa tana daga kwancen,gani take kawai raina mata wayau zai yi,aljanu gareshi ko farfadiya ce ta kamashi lokacin da ya bawa zainab din umarni?,baqinciki ne ya hanata magana,ganin tayi shiru ba tare da tace komai ba sai kukan ta data ci gaba da yi yasa yace " duka mubar wannan maganar muje asibitin a dubaki tukun,zanje nayi sallah ma dawo"ya fada yana ficewa.         Da fari taso taqi yarda,amma jin tsaiwa na niyyar gagararta sanda zata bada faralin sallar magariba yasa ra taushi zuciyarta ta amince,ita kanta zata so taji meke damunta bawai tayita zama da ciwo ba,tunda tunda take bata taba jin irin hakan ba.         Ba jimawa da idar da sallar sai gashi ya dawo,zuwa lokacin da qyar ta samu ta gama tata sallar aman ya sake tsinke mata,jikinta yayi laushi tubus sai numfashi da take maidawa,yaso taimaka mata wajen fita amma tace bata buqata,haka ta dinga bin bango har suka isa cikin motar.          Wani private hospital dake cikin unguwar tasu ya kaita,bayan taga likita ya bata takardar gwaji taje lab,minti goma ta karbi sakamakon ta koma dakin ganin likitan ta kai masa "Alhamdulillah,sai ka godewa Allah,madam na dauke da juna biyu"baki dayansu wuta ce ta dauke musu kada ma sumayya taji labari,sai ta fara girgiza kai hawaye na sauko mata,magana take son yi amma bakinta ya gaza furta komai " likita don Allah ka daina mana irin wannan wasan sai ka dauki haqqinmu"ta fusgi kalaman da qyar,sau ya dago kai ya dubeta "Bama yiwa patient wasa cikin abinda ya shafi lalurar da ta kawo su,ki baki yarda bane hajiya,ai muna da na'urar daukan hoto bismillah ga gado can hau in nuna miki" kasa tashi tayi baki daya,ga rashin qwarin jiki ga luguden da maganar tayi mata,mukhtar dake son tabbatar da gaskiyar labarin shi ya taimaka mata har suka isa bakin gadon.        Cikin qwarewa ya shiga nuna masu dan qaramin tayin dake cikinta wanda duka baifi wata biyu da rabi ba,basu iya ganewa amma sun lura da wani dan digo wanda shike alamta yaronsu kenan,wata doguwar ajiyar zuciya ya saki tare da lumshe ido yana jinsa cikin wata sabuwar duniyar,yayin da sumayyan ta fashe da kuka,jikinta baki daya rawa yake,ashe tana daga cikin mata masu haihuwa?,ashe akwai rabon zata ga yaron kanta?,ashe ita ma din watan watarana zata zama uwa?,zata yi raino ta kuma bada tarbiyya?,lallai ubangiji babu wanda ya kaishi iyawa cikin mulki da kyauta,babu ko shakka ubangiji baya bacci,baya mantawa da duk wanda ya ambaceshi ya kuma nemi agajinsa.         Barinsu likitan yayi suka gama murnarsu,don ya fahimci dukkansu ba'a cikin hayyacinsu suke ba sannan ya sanarwa mukhtar din jikin sumayyan ba qwari,zasu riqeta su sanya mata drip(ruwa)har zuwa safiya ko zata ji karsashi,sannan ya rubuta magungunan da zatayi amfani da su wadanda zasu taimaka mata ita da abinda ke cikinta,sannan ya jadda masa alfanun cina abinci mai kyau da gina jiki da qara kuzari a gareta,karba yayi saida ya tabbatar an gama komai an sanya mata drip din sannan ya fita siyo magungunan.        Ya jima zaune cikin mota ya kasa tayar da ita,ina zaikai wannan kayan farincikin?,da wa ya kamata ya raba wannan farincikin kada ya masa yawa ya masa illa?,da sauri ya zaro wayarsa daga aljihu ya soma daddanna wasu lambobi kyakkyawan murmushi kwance a kan fuskarsa,jinsa yake cikin wata duniya mai dauke dimbin farincikin da ya jima bai jishi ba,jinsa yau yake wani na daban.      ****      *****     ****         Ji take idan ga zauna gu d'aya tamkar wani mummunan abu zai faru ne tare da ita,tana jin qwaqwalwarta ko zuciyarta daya daga ciki zai iya tarwatsewa,tunda take bata taba cin karo da mummunan labari da ya firgita duniyarta ba irin wannan labarin,idanunta basu taba mummunan gani ba irin na wadan nan kwanakin,sumayya kishiyarta da ciki?,ita kuwa tana me?,wanne shirme take?,wanne baccin asarar tayi har mukhtar ya yiwa sumayya ciki duk da uban takatsantsan din da take?,duk da raba tsakaninsu da tayi ya daina sha'awarta?,tabbas idan har ta bari sumayyan ta rigata haihuwa cikin gidan ta dibga babbar asara,hakazalika bata ci sunanta,gidan da take da buri a cikinsa,gidan da take so shi da mamallakin gidan duka su zama qarqashin ikonta shine wata zata riga ta fara ajjiye iri?,tun yanzu ta fara ganin manya manyan sauye sauye ina ga ta haihu?,tun yanzun mukhtar ya ruguza dukkan wani plan data yi cikin gidan,wani kukawa yake bawa sumayyan wanda hakan ke nuni da qiris ya rage sun koma su dinke kamar daa koma sufi daa dinkewa,abinda idan har ya faru ba zata taba gafartawa kanta ba,lallai ko zatayi yawo tsirara sai ta tabbatar ta kawar da duk wata barazana dake shirin tunkaro ta.       Kamar mahaukaciya haka ta suri wayarta ta soma laluben lambar wayar aminiyarta qawarta,wadda bata aiwatar da komai sai da shawarat,zama tayi dabas gefan gadonta jin wayar ta shiga,cikin qananun sakanni mamallakiyar lambar ta daga,ko ta kan gaisuwar da take jefo mata bata bi ba ta soma zayyano mata abinda ke gudana cikin gidan.       Tsawon minti talatin ta dauka kan layin wayar suna qulla saqa a mugun zare,sosai taji dadi da shawarar data baga,shi yasa bata da kamarta,shawara ce mai sauqi wadda babu zuwa gun boka ko malami,hakanan babu barnar kudi,amma fa buqata zata biya,don dama babbar matsalarta yanzun duka jarinta ya karye warwas,saboda ribar da uwar kudin duka sun tafi gun 'yan tsubbu,bata kwana arba'in bata je an mata service ba,tun tana tsoron hadisin data taba tsintar wasu yaran 'yan makarantar islamiya na karantawa na cewa duk wanda yaje gun boka ko dan duba,to sallarsa ta kwana arba'in Allah bazai karbeta har tazo ta dake tama manta da hadisin baki daya bare ta tunoshi ya zame mata birki. (daya daga cikin abinda Allah ke jarabtar masu biye biyen malamai kenan,basu taba tara abun hannunsu,kullum suna kan hanyar rabawa matsubbata da 'yan duba,ko kishiya gareki mai irin wannan biye biyen ki lura da kyau,duk abinda miji zai baku sai ki nemi nata ki rasa,kullum cikin babu da bani bani take,ba zaki taba ganin burbushin abun ba ko a dakinta ko a jikinta ko a jikin yaranta,Allah ka kiyashemu ka tsare mana imaninmu).        Tana kammala wayar ta saki murmushi ita daya take magana da kanta "Kissa ai tafi magani,ba shakka quruciyarki ta yimin rana,zan amfana da ita sosai" ta fada tana ficewa a dakin inda kai tsaye ta nufi dakin sumayya.         Tana kwance saman carfet din dakin nata tayi matashin kai da pillow,duk da ba yadda mukhtar baiyi ta dora kan nata saman cinyansa ba amma ta qiya,yana zaune dirshan gabanta da faranti a tsakiyarsu wanda ke dauke da kankana da tuffa da gwanda,ayaba yake bare mata yana miqa mata tana daga kashingide take amsa tana ci,dubansa take kawai cike da mamaki,yana son dawo mata mukhtar dinta,"Allah yasa ba yaudara bace,ya Allah kasa kada ya juyan baya"haka ta dinga fada cikin ranta tana binsa da kallo wanda shi sam bai ma kula ba,hannu ta sanya ta shafi cikinta wansa daga can qasa ta fara jin dan tudu kadan,lumshe idonta tayi tana jin qauna cakude da farinciki na ratsata,duk kwanan duniya takan shafa cikin sau babu adadi,wani lokaci takan tsaya gaban madubi ta dage rigarta tayita kallon fatar cikinta tana mamaki yau ita ke dauke da juna biyu,idanu ya zuba mata shima yana kallonta farinciki na bibiyar duk wara gaba ta jikinsa,a haka ta bude idanunta karaf cikin nashi,sai kunya taso kamata,murmushi yayi sannan yace "Bakiyi laifi ba sumayya ki qaunaceshi yadda ya kamata,wallahi Allah a duniya ban taba jin son wani abu a rayuwata ba kamar yadda nakejin son cikin dake jikinki ba,zan iya rasa komai sabida shi,zan iya rabuwa da komai saboda shi,don Allah ki kularmin da kanki da abinda ke cikinki komai runtsi" ko bai fadi ba tasan zancan daga zuciyarsa kai tsaye yake fitowa,ita kanta bata san irin son da takewa cikin ba,kai ta sunkuyar tana murmushi tare da furta "In sha Allah ya mukhtar".        Dukkan wannan maganganun cikin kunnen zainab suka yisu wadda ta sawo kai don shigowa dakin " ka nunawa kucciya baka"ta fada sannan ta shigo dakin da sallama tana sake sai saita nutsuwarta,gaban sumayya ya fadi har sai data runtse ido cikin zuciyarta tana fadin "Allahummakh finihim bima shi'ita(Allah ka isar min da su da abinda kaso)(addu'a ce mai kyau ga wanda yaji tsoron zaluncin wasu mutane)" murmushi taje jifarsu da shi wanda shi kansa mukhtar din sai da yayi mamaki "Ashe kana gun uwar gidanmu my mukhtar" ta fada tana zama kusa da shi,amsa mata yayi sannan ta dora "Gwara ai ka kular mana da ita sosai musamman da take dauke da cikar muradinmu,Allah mun gode maka daka nuna mana wannan lokaci" ta fada tana maida hankalinta ga sumayya,hannunta tasa ta riqe nata hannun,ji take kamar ta kama garwashin wuta amma sai ta dake "Sannu sumayya ya jikin naki?" Da qyar ta bude labbanta tace "Da sauqi" "Allah ya inganta ya qara miki lafiya kinji,na godewa Allah da zaki samarwa mukhtar sanyin idaniya,naji dadi qwarai dama ke ya cancanta ki fara samun wannan matsayin,don Allah duk abinda kike da buqata ki sanarmin kada kice zaki yiwa kanki wani abu,kada ki duba duka wasu abubuwa da suka faru a baya,sharrin shaidan ne da kuma zuciya wadda bata da qashi,in sha Allah ba zasu sake faruwa ba,sai yanzu na fahimci kyakkyawar zuciya da kuma haqurin da kike da shi,don Allah mu hada kai mu zauna lafiya kinji?" Duk da bata gama gamsuwa ba amma taji dadin maganganun zainab din,ko babu komai wake son tashin hankali?,ai babu abinda yafi zaman lafiya dadi "Ba komai maman nafi'u,Allah ya sake hada kanmu" "Ba amin ba,don wallahi da kai na ya hadu da na kishiya gwara na qare rayuwata kan nawa na ciwo" ta fada a zuciyarta,amma afili sai ta saki murmushi tana fadin amin.         Sake matsowa tayi ta karbi bare ayabar daga hannun mukhtar din,ita ta dinga barewa sumayyan tana miqa mata,tanayi can qasan zuciyarta na mata suya,amma fuskarta kuwa murmushi da kulawa ne kwance a cikinsu. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 3⃣0⃣ ___________________________________ *Bismillahir rahmanir rahim* *iy yansur kumullahu fala gaaliba lakum,wa iy yakzulkum faman zal lazi yansur kum min ba'a dih,wa'alal lahi fal yatawakkalil mu'uminin* *_idan ubangiji ya taimakeku babu wanda ya isa yaci nasara a kanku,idan kuma Allah ya qyaleku(ya fita daga sha'aninku) waye zai taimakeku bayan shi?,ga Allah kawai muminai na qwarai suke dogaro_* *Ya Allah ka taimakemu cikin dukka lamarun mu* _________________________________        Kulawa ta musammanzainab ke bawa sumayya wadda zata kwantar da hankalin dukkan wani mai zargi,ta hanata komai,babu abinda sumayyan keyi cikin gidan banda wanke goma ta tsoma biyar,hatta da ruwan wanka ita ke dafa mata ta ajjiye mata a bandaki,girki kowa saidai kawai taci kuma mukhtar ya kwana dakinta,sau tari zainab din kan yafewa sumayya kwananta a zuwan yaje su kwana tare tafi samun kulawa,ta dauke dukka ayyukan gidan bisa wuyanta,ita kadai tasan me take ji cikin zuciyarta,wani lokaci zuciya kan raya mata ta shaqe sumayyan kawai ta mutu ta huta da ganinta da ganin abinda ke cikinta,saidai mardiyya qawarta kan yawaita ja mata kunne da cewa,matuqar ba zatayi haquri ba to kuwa ba zata cimma nasara ba,hakan shike yawaita taka mata burki tana jira har zuwa lokacin da zata kammala qudirinta.         Qwarai mukhtar na jin dadin yadda take kula da sumayyan,yana yaba mata sosai,hankalinsa ya kwanta,duk da cewa har ya zuwa yanzu akwai tasirin ragowar sihirinta a jikinsa,a duniya yanzu babu abinda yake so irin cikin jikin sumayyan,shi yasa hakan da takeyi yake sake saka farinta a idonsa,shi din ma ba'a barshi a baya,hidima da tattali yake mata kan jiki kan qarfi,duk da sai data masa tutsun abinda ya dinga mata a baya,saidai abun mamaki yaje bashi,ya sanar mata sam baisan sadda hakan ta dinga faruwa ba,kallon ya raina mata hankali ta dinga masa,hakan da ya lura da shi ya sanya ya karbi lefin kawai ya kuma bata haquri.         Ita din ma sumayyan ba'a barta a baya ba wajen tattalin kanta da abinda ke cikinta,duk wani abu da tasan zaya kawo tarnaqi ga lafiyar cikinta tana kauce masa,har yau bata bar mamaki ba wai itace yau da ciki bayan shekaru kusan takwas cikin na tara da aurenta,bayan da ta riga ta debe haso?,lallai rabon kwado baya taba hawa saka ko ya hau din ma rabi zaya sauko da shi,babu ranar da zata fito ta fadi bata godewa ubangiji ba.       Mama mahaufiyarta kuwa kullum cikin kiranta a waya take da turowa a duba mata ita,duk sanda zata aiko da abinda zata kawo mata na kayan qwalama na masu ciki,ita kanta yaya yahanasu da taji labarin laqwas jikinta yayi,sai ta rasa me take ciki farinciki ko baqinciki,amma jikinta yayi sanyi ta kuma taya mukhtar din murna,saidai har yau bata je ta ganta ba,tanq gudun wulaqancin da zata taras a gun zainab,don ta yanka musu gargadi kan zuwa gidan duk sadda suka ga dama. *.........KAYAN KWALABA*           _MAFARI_         Zaune yake gefan gadon dakinsa yana sanya maballan rigarsa a shirin sa na fita kasuwa. Ahankali zainab ra bude qofar dakin ta turo ta a hankali kamar wadda qwai ya fashewa a ciki,kujerar madubu ta janyo ta zauna tana fuskantar mukhtar idanunta a kansa,shi ya soma magana "Lafiya dai ko?,na lura tun jiya jikinki a sanyaye yake,mu da muke cikin farinciki a kwanakin nan" "Kake cikin farinciki dai,kuma na kusa datse igiyar farincikin". A zahiri sai ta soma goge qwalla da ta fara sakkowa a idanunta tana kallon mukhtar din " mukhtar,wannan farincikin da muka samu idan bamuyi wasa ba yana gab da qwacewa daga cikin gidan nan,bansan me yasa take ta qoqarin aikata haka ba,bansan me yake damunta ba"barin sanya takalman da yake qoqarin yi yayi,ya dago ya dubeta idanunsa cike fal da tambaya,har ya gaza boye hakan sai da ya furta "Kamar yaya fa?,me yake faruwa ne?" Kai ta shiga girgizawa cike kirsa "A'ah mukhtar,barin maganar nan shi yafi alkhairi,don bansan ya zaka dauketa ba" "Idan kina tunanin wani abu ne da zai cutar da ni qauna ce ki boyemin kiqi gayan,gaya min zainab" dan shiru tayi a zahiri fuskarta dauke da tashin hankali,yayin da zuciyarta ke cike fal da murna da farinciki tare da fata da addu'ar samu nasara tamkar wata wadda zata aikata abun arziqi,bata kuma magana ba har sai da mukhtar din ya jaddada sake tambayarta,taba goge qwalla tace "Mukhtar,sumayya ce......sumayya ce naji tana magana da wata baquwa da tayi,bansanta ba,ina tunani ko qawarta ce ko qanwarta ko 'yar uwarsu,wai wallahi sam batayi farinciki da samuwar wannan ciki ba,ina ita ina haihuwa bayan ko shekara ashirim baga gama rufawa ba,dama ita can kawai nunawa take tana son haihuwa amma wlh sam bata qaunarta,bare wai ta lura ba wani kulawa take samu yanzu daga gareka ba,tunda kwanakin baya ka juya mata baya yanzu haka data haihu qila ka sake komawa halayyarka,yanzu haka maganar da nake maka har ta bata shawarar ta sha maganin da zai barar da cikin kawai ta huta".          Tamkar guduma zainab ta sanya ta daki qahon zuciyarsa haka yaji,take maganar da yaya yahansu ta ta sha gaya masa shekarun baya suka bijiro mada suka cakudu da wannan sabon batun " kai idan zaka farka gwara ka farka,matarka fa ba son haihuwa take ba,bata ma sha'awarta,tunda kuke ka taba gani ta sha wani magani don ta haihu ko ta taba maka maganar kuje asibiti a dubaku?,ina kyautata zatan ma ita tasha maganin da zata hana kanta haihuwa,banda haka yarinyar dake da quruciya mai zai hanata haihuwa a irin wannan lokacin?". Wani fushi da bacin rai mai tsanani ya sauko masa,sai kawai ya miqe,burinsa kawai yaje ya samu sumayya yanzun nan,da sauri ta riqeshi don ba yanzu take da muradin nakiyar ta fashe ba " a'ah mukhtar ina kuma zaka?" "Sakeni zainab,sakeni naje na sameta" wani mugun marairaicewa tayi sannan tace "Shi yasa fa naqi gaya maka tun jiyan,yanzu me zakaje ka yiwa yarinyar mutane kana cikin fushi haka?,idan baka iya kama barawo ba sai shi barawo ya kamaka,zauna muyi magana akwai mafita" babu musu ya koma ya zauna yana maida numfashi "Mukhtar,kada ka damu,ni mai qaunarka,ina son abinda kake so,idan baka manta ba nike kulawa da sumayya...to kada ka damu,zan sanya ido sosai a kanta,sannan zan hana duk wani abu faruwa har Allah yasa ta haihu lafiya na maka alqawari" hakanan yaji kalamanta sun kwanta masa a rai,sai ya sauke ajiyar zuciya "Na gode zainab,don Allah na roqeki ki kula da ita,a duniya yanzu babu abinda nakeso sama da cikin nan don Allah" wani shegen kishi ya takore mata,cabdi,a haka zata bari sumayya ta fara haihuwa,ai ba zaya yiwu ba,a fili tace masa "Na maka alqawari tare ma zamu dinga wuni insha Allahu kada ka damu" jikinsa a sanyaye ya gama shirin zuciyarsa na bugawa,mamaki da haushin sumayya ne fal cikin zuciyarsa,da kamar ya wuce abinsa ba tare da ya mata sallama ba zainab din ce ta tursasashi kan sai ya shiga din,koda ya shiga sumayyan sai taga yanayinsa ya sauya sosai,ba kamar yadda ya saba mata ba,gabanta ne ya dinga faduwa tana fatan ba halayensa na baya bane zasu dawo,don ko kusa bata da buqatar wannan yanayin.        Har ya juya zai fita sai ya sake waiwayowa ya dubeta "Ki kularmin da cikina,din bazan iya jurewa ko yafiya gareki ba ga duk wani abun qi da zaya samu cikin nan ba" dai ya juya ya fita,kanta ne ya daure sosai,me yake nufi kenan,ta jima tana qoqarin lalubo amsar,daga qarshe abinda qwaqwalwarta ta bata shine tsabar son cikin da mukhtar din keyi ne haka ta barwa ranta taci gaba da sabgoginta.       ****     ****     ****     Bata gushe ba tana ci gaba da cusawa mukhtar tunani kala kala kan zub da ciki sumayya ke qoqarin yi,amma ta nuna masa tana bala'in takatsantsan akan faruwar hakan,sosai ya shiga damuwa da tashin hankali,mamakin sumayyan yake yi,da ya matsanta kan sai ya mata magana yana son daukar mataki,bazai iya jura ba idan wani abun ya samu cikin sai ta masa alqawarin zata nuna masa da idanunsa zai gani saboda hukunci da hujja yafi. *KUNDIN QADDARA* *_BAQAR RANA_* Tun da safe ta hada mata shayi kamar yadda ta sabarwa kanta,duka yana cikin qudurinta da tsarinta. Ranar kusan da wuri mukhtar ya fita,tana kwancan har ya fita din ko abin kari ma bata masa ba saboda mugun qudirinta data qulla aiwatarwa a yau din nan ko farkawa bata nuna tayi ba,hakan ya sanya data shiga da shayin ta zauna tana jan sumayyan da hira,bata bar dakin ba sai data tabbata ta kammala shan shayin,sannu a hankali ta soma hamma,zainab din ta dubeta fuskarta qunshe da murmushi wanda ke dauke da manufofi uku,manufar cimma nasara da manufar mugunta,sai kuma dadi daya kamata saboda tafuskanci magungunanta zasu soma aiki lokaci guda yadda take so "Kwanta ki huta qanwata na fuskanci kamar bacci kike ji" "Wallahi kuwa,duk jikina ya mutu" ta fada tana jan pillow ya yada kai saboda nauyi da taji kanta ya soma yi sakamakon bacci mai nuyi daya lullube idanunta. Leqa fuskarta tayi ta tabbata ta soma baccin sannan ta sake sakin murmushi,a nutse ta nufi drower din gefan gadon sumayyan ta fiddo magungunan da suke soke cikin rigar mamanta,magunguna ne har saches uku dukka na zub da ciki ne,saches daya aka balla guda gudu wanda ita tayi amfani da shi ta zubawa sumayyan cikin ruwan shayin data kammala sha yanzu,sai wata 'yar qalamar kwalba da wani saches din wanda duka maganin dake bugarwa ne da saka bacci wanda yawanci 'yan shaye shaye aka sani suna ta'ammali da shi. Dorasu duka tayi kan drower din sannan ta fice. Kitchen ta shiga ta samo kofi cikin kayan sumayyan ta zuba ruwa ta dawo kusa da magungunan ta ajjuye,ta bude kwabar kayanta ta ciro hijabi ta ajjiye saman kanta sannam ta nufi ma'ajiyar takalmanta ta ciro ta sanya mata daya daga ciki a qafafunta,sai data qare mata kallo ta tabbatar komai ya kammala sannan ta saki dariya ta fice zuwa dakinta. Tazarar mintina goma ta bada kamar yadda aka ce mata magungunan zasu fara aiki amma maganin baccin zai sa ba zasu tashi aikinsu gadan gadan ba sai bayan minti ashirin,dakin ta sake nufa ta leqata sai ta tarar har yanzu baccin take amma tana motsawa akai a kai,jinjina kai tayi ta sake komawa dakinta. Kai tsaye ta dauki wayarta ta laluba lambar mukhtar,bugu uku ya daga tare da yin sallama,bata bi ta kan amsawa ba ta soma magana cikin yanayi na matuqar rudewa qwarai da gaske "Wayyo Allah mukhtar mun shiga uku,mukhtar na kasa riqe amanar da ka bani" cikin wani mugun tashin hankali ya miqe tsaye daga inda yake zaune sannan ya fara tambayarta "Lafiya zainab yi magana mene ne?" "Kasan ka barni a daki ina kwance ina bacci,to ina tashi naga lokaci ya ja,sai na tuna sumayya na barta bata ci komai ba,da sauri na shiga kitchen na hada mata abun kari na nufi dakinta,ina shiga naga babu kowa na duba gidan baki daya ban ganta ba,ina falo ina taraddi ina ma shirin kiran wayarka ko kasam zata fita?,kawai sai gata ta dawo dauke da wata baqar leda ita da wannan 'yar uwar tata,da nayi mata magana ma kallon banza ta yimin tayi tsaki ta wuce daki,sai ma qyaleta sabida nasan masu ciki da fushi,sai daga baya na sake leqata sai na tarar tana shan wani magani,na mata zancan abinci tace ta qoshi bata buqata taci a waje,na qyaleta na dawo ina hidimar gida,bayan wajen minti talatin sai na fara jiyo ihunta tana wayyo cikina wayyo bayana inzo in taimaketa" sai ta fashe da kuka kamar gaske,ya gaji da dogon jawabi kawai jira yake azo gurin "Ki gayan me ya faru?" "Jini ma gani daga jikinta mukhtar yana fita wanda ke nuna kamar bari tayi" "Me!" Ya fada da madaukakin sauti,kafin ta kai ga amsawar ta soma jiyo kumar sumayyan na kiran sunata,dadi ya kamata komai yazo a daidai kenan?,sai ta sake dububurcewa "Tana kirana mukhtar don Allah kayi sauri kazo mu kaita asibiti kada mu rasa cikin nan" sai ta katse kiran kawai cikin gaggawa ta nufi dakin sumayya. Murququsu ta cimmata tana yi da malelekuwa daga saman gadon har qasan carfet din dakin,tun daga kan gadon jini ne har qasan dakin,wata azaba ke ratsata ilahirin jikinta,duk da azabar da takeji bai hana hankalinta tashi ba,tasha jin ana cewa zubar jini hadari ne gun mace mai ciki tun daga shigar ciki zuwa haihuwarsa,tsoro fal da fargaba ke zaga zuciyarta,tsoron rasa cikin jikinta,tsorom rasa gudan jininta "Ki taimaka kin don Allah amarya kada na rasa baby na" ta fada hawaye da gumi na hade mata saboda tsabar azabar radadin da mararta ke mata,ga tarin mamakinta sai taga zainab din ta sheqe da dariya "Kadan kika gani,ci gaba da karbar gashin ciwon rasa d'a kafin ki rasa mijinki ma baki daya,nice sila ba zan iya taimaka miki da komai ba,burina nake so ya cika" sai ta sake takowa zuwa gabanta ta ranqwafo "An fada miki akwai ranar da kishiya zata so kishiyarta ne?,an gaya miki ni sauna ce da zan dinga miki bauta?ko an fada miki wawiya ce ni bansan me nake ba?,lallai dukkan wanda ya riga ka kwana tilas ya rigaka tashi,wannan ya isheki ishara game da kaidin kishiya,ke yarinyace,bakisan komai ba sumayya,daga yau zaki shaidi kaidin kishiya" ta fada tana juyawa ta fice ta barta a dakin tare da komawa falo tayi zamanta. Runtse idanunta tayi wani abu na dawafi kan qwaqwalwarta,babu shakka ayanzun maganganun da zainab ta furta mata sunfi mata ciwo fiye da ciwon dake nuqurqusarta,tana nufin ita ta mata silar abinda ke faruwa yanzun da ita?,me ta aikatama zainab din haka mai muni da zata zama silar rabata da abinda ta jima tana dakon isowarta gareta?,don kawai sun hada miji?,saboda kawai suna qarqashin inuwa daya?WANNAN ITACE KAWAI HUJJAR?dafe mararta tayi tana ci gaba da kallon yadda jini ke kwaranya yanabin qafafunta tare da bin lafiyar carfet dinta. Tana jin qarar tsaiwar motarsa ta miqe da hanzari ta shige dakin sumayyan,kanta tsaye ta nufi kan drower din ta kwaso magungunan dake ajjiye a kai ta riqe a hannunta tana kallon sumayyan taba murmushi sannan tace "Yanzu zaki ga babban kaidina don na tabbatar bakisan da zaman wadan nan magungunan ba,baki ta saki tana kallonta tare da jijjuya kai cike da azaba,ko magana ma ta kasa yi,sai da taji takun shigowarsa yana qwala musu kira ta saki kuka tana jujjuyasu tare da matso hawaye tana fadin "Me yasa kika aikata haka sumayya?,me yasa zaki raba shi da farincikinsa?,abinda ya jima yana nema sumayya shine yau zaki zama silar rabashi da shi,ina ma ni Allah ya bawa sumayya kin cika butulu ta gaske,wayyo Allah yau mun rasa yaronmu"sai ta rushe da kuka,wani duka zantukanta suka yiwa dodon kunneta,sai ta daga kai tana duban baki qofa saboda ganin inuwar mutum,take idanunta suka sauka cikin na mukhtar wanda ke dauke da tsantsar bala'in da bata taba katarin ganinsa cikin idanun nashi ba,tsaf mukhtar yaji duka abinda zainab din ke fada,yi tayi kamar bata ganshi ba taci gaba da cewa " yanzu har da maganin 'yan shaye shaye sumayya da tarbiyyarki da komai...... "Kasa ci gaba da daukar batun kunnuwanta sukayi,dummmm taji sunyi mata,a hankali ta soma jin jiri na kwasarta tana daga zaune,cikin 'yan sakanni wani duhu ya mamaye idanunta ta daina gani ta daina ji. **** ***** ***** Sannu a hankali ta soma yunqurin bude idanunta har taci nasara ta kammala budesu baki daya,idanunta suja sauka kan ruwan dake rataye yana shiga jikinta sannu a hankali,take abinda ya faru da ita ya dawo mata tar,tayi hanzarin fadin " la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minaz zalimin"bakinta ya furta "Hmmmm,kamar gaske" muryarsa ta daki dodon kunnuwanta,da sauri ta waiga ta dubi bangaren da sautin ke fitowa,mukhtar ne tsaye hannayensa nannade a qirjinsa,duba daya zaka yi masa ka fuskanci a yamutse yake,har yanzu idanunsa jajur suke tamkar an badesu da barkono,kafin tace wani abu ya tako zuwa gaban gadon da take. Babu shakka da zata iya da tashi zata yi ta arta ana kare saboda yadda kamanninsa suka sauya baki daya kamar wani mayunwacin zaki "Sumayya,ban taba zaton soyayya zata juye ta koma qiyayya ba sai yau,babu shakka kin cuce ni kin zalunceni,kuma Allah ya isa tsakanina dake,don bazan taba iya yafe miki ba,na zauna da ke tsawon shekaru ina kare martaba da mutuncinki,ina tattalin farincikinki ashe ni nawa kike rusawa,meye aibuna da bakison ki haihu da ni?,me yasa baki gaya min ba tun wuri nayi nesa da rayuwarki?,a yau na tsaneki tsanar da ban taba yiwa wata halitta makamanciyar irinta ba,na gani da idona ba gaya min akayi ba"zuciyarta na mata wata iriyar muguwar suya ta bude baki don kare kanta duk da rashin qwarin gwiwar da take da ita,sai ya watsa mata magungunan da kuma sakamakon gwajin da ka yi mata na dalilin barinta wanda ya nuna maganin zub da ciki ta sha "Allah ya saka min sumayya na dora buri kanki amma kin zalunceni" abun mamaki kawai saiga hawaye na fita a idonsa,abinda bata taba tsammanin ganin ba agreshi "Zan bar rayuwarki kije kiyi duk yadda kika ga dama da ita,KIJE NA SAKEKI SAKI UKU don bazan tab iya ci gaba da rayuwa da ke ba" wani tashin hankali ya rikito mata,sai ta ware baki daya idanunta tana son tabbatar da gaskiyar lamarin,ko dai barin da tayi ya shafi awaqwalwarta da jinta?. "Haba my dear wannan danyan hukunci haka?,ai yayi tsauri" ta fada tana isowa gareshi cike da kisisina *Dakata da Allah!"ya katseta cikin kakkausar murya,gabanta yayi mugun bugawa saboda ta tuno da sharadin da malam ya gindaya mata nacewa kada ta kuskura tace komai har a qare lamarin,saboda ba qaramin so yakewa cikin ba hakanan har yau duk da daurin da aka yiwa zuciyarsa da sanya masa ganin baqin sumayya har yau sonta na da sauran tasiri cikin zuciyarsa,itadai kawai ta sanya layarta cikin bakinta tayita taunawa,jajayen idanunsa da suka firgitata ya zuba mata "Tunda sumayya ta iya yimin haka a rayuwa,to babu macen da zan aura ta kasa aikata min haka,saboda haka kema kije na sakeki saki uku!" "Iyeee!" Ta fada cikin madaukakiyar murya fitsari na kubcr mata take ya fara bin qafarta saboda azabar rudewa,kai ya sanya ya fice daga dakin,wanda kammala fita su mama(babar sumayya) suka sanyo kai da alama dama suna cikin asibitin. _kuyi haquri fa kawai ku ci gaba da bibiyata don cimma darasin dake cikin labarin da kuma rayuwar sumayya_ *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 3⃣1⃣ ________________________ *Bismillahir rahmanir rahim* *wa bashshiris sabirin,Allazi a iza asabathum musibatun qalu innalillahi wa inna ilaihi raji'un* _ka yiwa(ya annabin Allah) masu haquri bushara,sune wadanda idan musiba ta samesu suke fadin daga Allah muke kuma gareshi zamu koma_ *Allah ka sanya mu cikin wadanda zaka yiwa kyakkyawan sakamako sanadiyyar fadan wannan kalma* _________________________________           Zainab qanwarta ce akan gaba,sai mama da yaya abubakar halima na biye da shi,umma sadiya qanwar babansu na biye da su "Yaya sannu yanzu muka ga ya mukhtar din ma ai ya fita" ta fada ba tare da sun ankara baki daya da yanayinda take ciki ba,haka ma basu lura da zainab dake tsaye gefe ba tana tsuma tare da kallon fitsarin da ya gama wanke mata qafafu. Kallo daya mamanta ta yi mata ta fuskanci ba dai dai taje ba duk da cewa akwai ciwo tattare da ita.         Da idanu kawai take binsu tana fata ta farka daga mummunan mafarkin da takeyi,sai da maman ta qarasa gefan gadon ta zauna ta soma yi mata sannu sannan sumayya ta tabbatarwa kanta idanuntq biyu,a zahiri komai ke faruwa,wata cukuikuya ta yiwa maman nata tana sauke wata ajiyar zuciya tare da fadin "Ya sakeni mama,ya rabu da ni bayan bani da wani laifi",cikin rudani suke kallonta duk suna zaton zafin ciwo ne "Sumayya zafin ciwo ne duka hakan?" Sai ta fashe da wani kuka mai azabar cin rai tana maimaita fadin "Walllahi mama ya sakeni,yanzun nan da kuka ganshi ya fita sakina yayi mama" salati suka saka baki daya wanda ya dawo da zainab hayyacinta "Allah ya isa 'yarku ta jawo min masifa,ta jawo min zawarci kashi na biyu garin qoqarin zubar da cikinta" ta fada tana wucewa fuuuu ta bar dakin.        Shiru ya ratsa dakin,babu wani abu dake tashi sai shashsheqar kukan sumayya wanda zainab da halima ke tayata saboda tsantsar tausayin 'yar uwarsy,yayin da zuciyoyin sauran ke quna,zancan zainab kuma ke musu kai kawo "Mama har saki uku yaya mukhtar ya yimin,mama wallahi ban aikata ba,na fishi son naga na haihu mama ki......." Sai ta fara jan numfashi da qyar wanda hakan ya sanya su sake rudewa,da sauri yaya abubakar ya nufi reception don kiran nurse ko likita,cin qanqanin lokaci sai gashi tare da likita wanda yake gab da tashi Allah yasa bai fita ba,waje ya fid dasu baki daya sannan ya rufe dakin,take suka rude da koke koke cike da tashin hankali.        Kusan mintina talatin sannan likitan ya fito bayan ya gama dubata ya mata allurar bacci tare da sanya mata wani ruwan,ya sanar musu bata buqatar hayaniya,sannan don Allah su guji tada mata hankali idan baso suke ta hadu da hawan jini ba,don ko a yanzun jini nata ya fara sama,bugu da qari kuma ta zubda jini mai yawa,godiya suka yi masa sannan suka koma dakin kowa ya samu gu ya zauna zugum,dukkansu da abinda suke saqawa zukatansu,daga bisani yaya abubakar ya fice dan yi musu siyesiyen abubuwan da zasu buqata kafin suga yadda hali zaiyi.        Tun a hanya take sumbatu,ko da wasa bata taba zaton ramin da ta haqa zai rufta da ita ba,bata taba ganin masifa irin wannan ba,taga samu taga rashi,gidan da takewa kanta hasashen samun abun duniya yau dare daya an rabata da shi "Ina!!!,wlh sam bazai yiwu ba,mukhtar ko baka qaunar Allah sai ka ci gaba da zama da ni,babu wanda zan sanarwa ma ka yimin saki uku,wallahi yanzu na fara aurenka" maganar da tayi kenan wadda ta sanya mai adaidaitam juyowa ya dubeta,banda kayan jikinta da basu nuna alamun akwai hauka tattare da ita ba da babu abinda zai hana yace mahaukaciya ce,a qofar gidansu ya sauketa ya juya ya kama gabansa.         Tunda ya bar asibitin gida ya wuce kansa tsaye tamkar wani mahaukacu,kuka yake wiwi da haka ya kashe motarsa qofar gidan ba tare da ya samu qwarin gwiwar tura dan matsakaicin get din ba bare ya iya shiga da ita,dakinsa ya wuce ya fada saman gado yana dafe da kansa,me yasa sumayya zata yi masa haka?,wanne abu ya mata da zata saka masa da wannan?,zata rabashi da gudan jininsa,sata rabashi da burin rayuwarsa,shin ta manta cewa samun d'a shine CUKAR BURINSU shi da ita?,wani kukan ya sake saki kamar qaramin yaro,sai a lokacin ya fara ambaton sunayen Allah daya bayan daya,sannu a hanakali nutsuwa ta fara saukar masa,yabar tumurmusa gadon da yake yayi luf saman gadom cikin yanayin na kwanciyar rub da ciki idanunsa na ci gaba da fidsa qwalla masu zafi.       ****    *****   *****        Kwana daya rak amma sunfi kwanaki dubu ciwo da wahala a rayuwarta,baki daya ta sauya kamar ba sumayya ba,tayi wani mugun dashewa wanda ya sanya nurses suka soma tunanin tana buqatar qarin jini ko babu jini jikinta,da likita ya duba sai yaga magungunan qarin jini ma kadai sun isheta sai maida kai gun cin abin mai lafiya.        Ko kallon abincin bata yi bare ta kai ga ci,ko ruwa bata iya kurba a bakinta,ki da yaushe tana kwance idanunta rufe kamar mutum mutumi,sai da malam yazo shi daya ya shiga dakin sukayi magana ta tsawon mintina kusan ashirin shi da ita sannan aka fara samun salama,takan karbi duk abinda aka bata taci koda zata yi amansa,hakan ba um ba um um sai zubda hawaye tamkar qwayar idonta zai tsiyaye,kusan kowa tausaya mata yake tare da girgiza da al'amarin,duk da cewa har yau malam kawai ta iya yiwa bayanin abinda ya faru shi kuma ya sanar da abubakar da umma sadiya,sosai umma sadiyan ta fusata qwarai tace sam ba zasu yarda ba tilas su maka mukhtar a kotu shi da zainab din baki daya,baisan halin sumayyan bane?,yarinyar da kusan shi ya qarasa yi mata tarbiyya,malam ne ya hana yace sam hakan baida amfani,tunda koda sun aikata hakan ba zasu iya maida hannun agogo baya ba,ba zasu iya gyara lamarin ba tunda abinda zai faru ya riga da ya farun,da wannan zancan suka rufe batun suka maida hankali wajen kula da lafiyar sumayyan.          Da wani yammaci sumayyan na zaune jingine da bango,bata jima da yin wanka ba tana sanye da atamfa,mamanta ne da zaina da halima sai khadija da hajara cousing dinta zauneba dakin suna dan taba hirarsu,sallama akayi suka kalli bakin qofar baki daya suna amsawa,haj salamatu ce wato umma mahaifiyar abdur rahman ita da qanwarsa bahijja,duk da quncin da zuciyarta ke ciki saida sumayyan ta washe haqora ta sake gyara zama tana mata sannu da zuwa.       Cikin mutuntawa suka gaisa su halima suka gaidata tare da miqewa suka fice don zuwa karbo canjin ruwan da suka siya cikin shagon asibitin a dazu "Sannu sumayya ya jiki?,ya kuma mukaji da wannan abu" umma ta fadi fuskarta dauke da alhini da tsantsar tausayi,qasa tayi da kanta hawaye na zirarar mata "Alhamdulillahi umm" ta fada muryarta a karye "Ki yi haquri kan haquri sumayya,duk da na sanki dama ke gwanar haqurin ce,haqiqa Allah ba azzalumin sarki bane,ni sam bansan meke faruwa ba,abdur rahman da bahijja dai sunje zasu miki sallama da yake zai sake koma wa jami'atu ummul quraa zai hado masters dinsa,to da suka dawo sai suka ce sun tadda gidan naku a kulle,babu wanda ya kawo komai don har mukhtar din ya kira ya masa sallama baice da shi komai ba,sai jiya da safe saiga mukhtar din yazo gaida kawun nasa,a nan yake gaya masa duk abinda ya faru,wallahi mama ina jin batun na tabbatar sharrin kishiya ne da asiri ke dawainiya da yaron,cikin kwana uku tal da faruwar lamarin kada kiso kiga yadda ya fige ya lalace,babban abun haushin ma duk yadda muka so tunatar da shi wace sumayyan wallahi yaqi fuskanta yaqi gane wacece ita,har yau da haushi da zargin abun a ransa,amma babu komai mai gaskiya yana tare da Allah,kuma in sha Allahu Allah zai miki KYAKKYAWAN SAKAMAKO".        " babu komai ai umma,kowanne bawa da irin tasa QADDARAR,kuma shi aure rai ne da shi,da zarar zaman ya qare sai kiga ko babu sanadi an rabu".hawaye ne kawai ke ci gaba da tsiyaya idanun sumayya,tamkar ta zura a guje haka take ji,bata qaunar jin duk wani zance da ya danganci mukhtar din,tunda mukhtar ya yi mata haka a duniya yaqi bata dukkan yarda da amincinsa bayan yasan wace ita to babu wanda bazai iya cin zarafinta ya ha'inceta ya wulaqanta ta ba.      Maganganu masu sanyi umma ta dinga fada mata masu kwantar da rai wadanda suka sauke kaso mai yawa na bacin rai baqinciki da firgicin da take ciki,sosai taji sukuni cikin zuciyarta,sai wajejan la'asar sannan umma ta musu sallama ta tafi bayan ta ajjiyewa sumayyan dubu uku tace tasha lemo. **** ***** **** Cikin kwana biyar jikinta yayi sauqi sosai,hakan ya sanya likita ya bata sallama tare da gargadarta ta rage damuwa ta kuma kula da lafiyarta. Sosai take samun kulawa daga dukkan wani da yake cikin gidan nasu,kowa haba haba yake da ita,dakinta daban wannan karon malam yasa aka ware mata don kada su takura mata,amma duk da hakan wani lokaci cikinsu haliman take kwana,ganin yadda kowa ke son farincikinta ya sanyata warewa,tayi qoqari qwarai wajen fidda damuwa daga ranta duk don saboda su,duk da abadini hakan ba mai yiwuwa bane gareta. Watanta guda da komawa yayanta abubakar ya siya kata foam na wata makarantar koyon sana'o'in hannu na mata don rage mata kewa da dauke kaso mafi tsoka a cikin lokacinta wanda hakan zai taka rawa matuqa da gaske wajen hanata tunani ko damuwa,kama daga dinkin labulaye,zannuwan gado,suturu kayan sawa,carfet zuwa saqa,hadin su humra,sabulu,man shafawa man kitso da sauransu dukka suna koyawa,sosai take jin dadin makarantar hakanan ta maifa hankalinta sosai tana dauke duk wani abu da aka koya mata,har ya zuwa lokacin ba'a debo kayanta daga gidan mukhtar ba din baki daya ta tsane su ta tsani ganinsu,hakan ya sanya umna halima tace idan an tashi daukosun a wuce da su gun masu saida furniture a siyar kawai. *ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA* Kusan a yanzu ya zame mata al'adarta,takan kwashi lokaci mai tsawo kwance cikin nazarin da tunani kafin bacci ya samu nasarar daukarta. Yauma kamar kullum tana kwance ruf da ciki,duk da cewa dakin babu hasken fitila amma idanunta a bude suke tar,kwanyarta na aikin sarrafa tunane tunanen dake bijiro mata daya bayan daya. Zumbur ta miqe sakamakon motsin da take ji can qasan mararta,wanda wannan shine karo na barkatai da take jin hakan cikin wannan satin,sau tari takanyi kasaqe tana sauraran motsin har zuwa sanda zai lafa mata,hakan ce ta faru wannan karon,bayan motsin ya lafa sai ta koma ta kwanta rigingine tana mai lumshe idanunta,tana tunanin gobe zata sanarwa mama don tana zaton ba lafiya saboda bata taba jin irin hakan ba. Qarfe takwas na safe tana tsakar gidan tana shara bayan ta kammala duk wani aiki na gidan qannanta sun wuce islamiyya wadda suke shiga tara zuwa biyat da rabi na yamma,tunda tazo ta koma al'adarta ta da,tun kafin tayi aure ita ke hidimar gidan duk da qarancin shekarunta a lokacin,sai abinda yafi qarfinta ne kawai wanda ba zata iya ba take barma maman nata shi,to hakan ce ta kasance wannan karon,duk da maman na hanata kai bama ita ba har su haliman idan suna nan basa yarda tayi komai,amma takan qiya saboda hakan na matuqar debe mata kewa da sata jin qwarin jikinta. Tana daga rumfarta zaune amma tana iya hango duk abinda ke faruwa cikin tsakar gidan kasancewar labulen falon a dage yake don ta samu iska ta shiga inda take,da idanu take bin duk wani motsi na sumayyar da kallo,tausayi da qaunar yarinyar tata na ratsata,sai kima wasu sauye sauye da take ci gaba da gani dangane da ita,har sai da ta kammala komai sannan ta shigo falon "Wash" ta fada wanda hakan ya sanya maman juyawa ta kalleta "Lafiya dai ko?" "Lafiya lau,kawai gajiya nake ji da kasala mama" shiru ta danyi sannan ta sake dubanta,tunani ne fal cikin zuciyarta amma bata aminta da abinda zuciyarta ke kawo mata ba don bata jin hakan zai yiwu "Bakijin komai a jikinki sai kasalar kawai?" Dan shiru tayi sannam tace "Ummmm,wani lokaci inajin motsi mama har nace zan gaya miki ko zanje asibiti,sai kuma naji motsin ne kawai baya ko ciwo cikin nawa" ta fada cike da quruciya dake nuni da rashin sanin abinda ke faruwa da ita "Tun wajen yaushe kike jin hakan?" Ta tambayeta tana dubanta da saka ran jin amsa "Eh wajen kwana goma kenan" "Lallai kuwa ya kamata mu koma asibiti" maman ta fada tana jinjina kai cikin qarafafawa wanda hakan ya bawa sumayyan tsoro,take hantar cikinta ya kada,kodai wani babban ciwo ke shirin samunta?,gaza yin shiru tayi saboda tsabar tsoro "Mama!......bani da lafiya ko?" Ta fada kamar zata saki kuka,murmushi ta saki don kwantar mata da hanakali,bugu da qari itama bata da tabbas din abinda take zato kansa "Lafiya lau kike,dauko min wayata na kira malam in sanar da shi idan yaso sa muje kiga likitan" "To" ta fada jikinta a sanyaye qirjinta na bugawa duk da maman tace mata lafiyarta lau,dakin gadon maman ta shiga ta fiddo wayar ta dawo ta miqa mata sannan ta samu gefe ta koma ta zauna. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 3⃣2⃣ _________________________ *Bismillahir rahmanir rahim* *wa iyyamsaskallu bi durrin fala khashifa lahu illa huw,wa iy yuridka bi khairin fala raadda li fadhlih,yusibu bihi man yasha'u min ibadihi wa hul azizul gafur* _"idan Allah yaso ka da cuta(lalura,abubuwa marasa dadi)babu wanda zai yaye maka face shi,idan kuma ya soka da alkhairi babu wanda ya isa ya maida falalarsa,yana sowa ga wanda yaga dama cikin bayinsa,haqiqa shi madaukaki ne mai gafara"_ _____________________        Cikin abinda duka bai wuce awanni biyu ba isar su asibitin da shiga dakin ganin likitan,umartar ta yayi da tahau wani dan gado wanda kusa da shi na'urar daukar hoton ciki ne.        "Allahu akhbar" shine abinda likitan ke fadi yana jinjina kai tare da girmama iko na ubangiji,yaro ne kwance cikin mahaifarta ga motsi nan yana yi ga bugun zuciyarsa da komai,dukkansu ba wanda idonsa bai gani ba daga sumayya har mama,mamaki fal zukatansu tare da girmama lamarin buwayi gagara misali,sai da ya kammala komai har EDD sai da ya duba mata sannan yace ta sauko ya koma kan tebur dinsa ya soma rubuce rubuce.        Magunguna ya rubuta mata wadanda zasu qara mata lafiya sannan ya bata wasu gwaje gwaje da ya kamata ace a wannam stage din da cikin ke da watanni hudu da sati uku tayi su "Likita lafiyarsa qalau"furucin ya subuce ya fita daga bakinta jikinta a sanyaye,murmushi yayi yana dubanta " lafiya qalau komai yake,babu wata damuwa tattare da shi"sai da ya bata amsar sannan kunya ta kamata ta sadda kai qasa,batasan cewa tana bala'in qaunar abinda ke cikin nata ba sai yanzu,wani qwarin gwiwa karsashi da soyayya take ji cikin ruhinta,banu shakka wannan karon tanajin zata iya yaqi kan cikinta a shirye take.        Basu bar asibitin ba sai da suka kammala duk wani gwaji suka siyi magungunan suka nufi gida.         Har yanzun maman ta kasa cewa komai kamar yada sumayya ta kasa magana,sam basuyi zato ba,basu tsammaci akwai sauran ciki jikin sumayyan ba,ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA ko ana muzuru ana shaho sai yayi kenan. Hakanan sumayyan ke jin zuciyarta fes da ita,bini bini ta saki murmushi tare da shafa cikin nata,maman na ankare da ita,tausayinta ya dinga ratsata,haqiqa babu dan halak din da zai guji haihuwa,babu wata halitta da bazato ganin jininta ba,dole dan adam ya koka idan ya rasa baya wato 'ya'ya,abu ne mai ciwo da cin zukata,Allah kuma maji roqo da addu'ar bayinsa ne,a yau gashi duk yadda akaso rabata da rabon da Allah ta bata amma hakan bai yiwu ba,ya riga ya QADDARA yana cikin QADDARARTA haihuwarsa da dadi ba dadi,saboda hikimarsa sai ya bawa yaron kulawa ta musamman,ya boyeshi daga kallon idanuwa,ta yadda ko mahaifiyarsa bata san da zamansa ba sai yanzu da buwayin sarki yaso ta sanin.        Tun daga sanda suka koma gida daga asibitin maman ta fara bata kulawa ta musamman,ta hanata yin komai komai qanqantaraa,duk da babu wani ciwo ko laulayi da sumayyan keji,lafiya qalau take jin jikinta. Malam na dawowa maman ta sanar masa,sosai shima ya jinjina lamarin yana qara girmama isa da buwaya ta ubangiji,to ita kanta sumayyan ma alokacin ba'a zaci zata kai ba bare d'an dake cikinta "Yanzu ya zama dole a sanarwa uban yaron saboda yasan da zaman cikin" inji mama. "Wannan ya zama dole ai,zan sanya abubakar yayimin kiransa ko zuwa gobe ne" cewar malam.        ****      ****    ****       Kansa na duqe amma gumi tsatstsafo masa yake har ta kafar farcensa,babu shakka baya ga girman tsohon da yake gani da kuma farin sani da yayi masa kan wane shi da tashin farko zai qaryata batun da a yanzun yake gaya masa. "Amma ga wadan nan ka duba hoton cikin ne da aka yi mata a jiya,idan ma duka basu gamsar ba kana iya zuwa gobe sai kuje da ita da su halima wani asibitin a sake gwada maka har da watannin cikin" malam ya fadi yana zube takaddun scanning da komai da komai a gabansa,jikinsa na rawa ya dauka ya soma dubawa,tsaf daya lissafa watannin cikin zuwa yanzu dai dai suke,sau taji wani abu na zaga shi,madaukakin farinciki ya wadatu a zuciyarsa "Na gode maka ya Allah da baka bata damar salwantar min da ciki ba" ya fada cikin zuciyarsa idanunsa a lumshe,duk da zuwa yanzu yana mamakin me yasa ta aikata masa haka?,zuciyarsa kuma na kokwanton ita din ce da kanta?,wani sashi na zuciyarsa kan gaya masa ita dince mana,tunda kaga shaidu na magungunan cikin dakinta,kuma a baya likita ya tabbatar da ta sha din.       Sallamarta ita ta katse dogon nazarin da yake,sanye take da dogon hijabi har qasa mai hannu wanda idan zata shigo wajen malam din haka take sanyashi,din yanzu baki daya irin wannan shigar tafi mata armashi,duk da dama yana daya daga cikin dressing dinta tun a da,sam bata ma san da zuwansa ba,tazo ne karbar rubutun da malam din yace mata zata dinga sha daga tsakanin magariba zuwa isha'i,gefe ta samu kusa da malam din ta zauna har ya zuwa yanzu bata luta da mukhtar din ba dake satan kallonta,abu biyu yake ji dangane da ita,haushin yunqurin zub da masa ciki da kuma qaunar jininsa da take dauke da shi.        "Ka duba su da kyau gasunan" inji malam,wanda maganar da yayi ce ta ja hankalin sumayyan ta lura da mukhtar din,da sauri ta dauke kanta bayan sun hada idanu,qasa qasa tace "Ina yini" kamar wadda aka tilasta ta fada,tasan dole ne ma ta gaidashi saboda malam dake gun "Lafiya qalau,ya jiki naki" "Alhamdulilla" ta fada da qyar tana jan tsaki cikin zuciyarta tare da fadin "Me ya shafeshi da jiki na ji da nake mai laifi" "Malam rubutun nazo karba" ta fada a hanzarce don so take ta bar falon ba zata juri zama cikinsa ba "duba gefan akwatincan ki dauko min farar gorar can" ya fada yana nuna mata,ta miqe ta isa gun yayin da idanun mukhtar din ke kanta,baki daya yanayinta ya nuna mace mai ciki ce,cikin ma da ya soma qwari.       Cikin wata silver mai dauke da rubutun yasin da ayatul kursiyyu ya fara zuba rubutun ya bata ta shanye sannan ya dura mata wani cikin jarka ya miqa mata,a hanzarce ta karba ta fice a dakin.         Kasa tsaiwa tayi a falonsu sai data dire zuwa dakinta ta ajjiye rubutun gefe ta zauna saman gado dafe da kanta,kuka ne ya kubce mata wanda ba zata iya fadar dalilin sa ba,sosai ta koka sai data ji sanyi cikin ranta sannan ta rarrashi kanta.         Cikin kunya da nuyin da ada bai jisu ba sai yanzu suke saukar masa ya dubi malam bayan sun gama tattauna abinda zasu tattauna din "Malam ina son jin abinda ake da buqata wanda zatabyi amfani da shi" kai malam din ya gyada yana nazarinsa,duk ya fara qarewa kamar wani kudin guzuri,addu'a yake masa cikin zuciyarsa Allah ya yae masa abinda ke damunsa "Babu wani abu da muke sa buqata,yadda sumayya take diyata kaima d'a na nae,tunda ko babu komai alaqa ta sake qulluwa darajar abinda take dauke dashi" nauyinsa ya sake kamakashi,ya sadda kai qasa "Na sani malam,amma ka fini sanin haqqina ne yanzu in ci da ita har ta haife abinda take dauke da shi,don Allah a fadamin na sauke haqqin da ya rataye a wuya na" dan shiru malam din yayi sai daga bisani ta numfasa "Shikenan,kaje ka kawo duk abinda kasan zaka iya" Kanshi a qasa ya masa godiya sosai,karamcinsa na sake daureshi,yadda malam din ke mu'amalantarsa kamar ba wanda ya sakar masa diya ba,sakin ma kuma mai kankat.        Cikin mota jikinsa yayi sanyi baki daya,da qyar yake iya tuqi,a yau ji yake ina ma bai saki sumayya ba duk har yanzun akwai haushi da zargin yunqurin zubar masa da ciki da tayi,mai yasa baiyi haquri ba ko ya dauki mataki wanda bai zama na rabuwa ba,a lokacin baisan me ya sanya yaji rabuwa da ita ne kawai maslaha a rayuwarsa ba tunda har bata da buqatar hada zuriya da shi "Ke kika jawo sumayya,me yasa?,me yasa kika aikata abinda ya zama silar datse alaqarmu?" Haka ya dinga fada yana tafe yana tambayar kansa.         Tamkar wanda qwai ya fashewa a ciki haka ya faka motar sannan ya rufeta ya nufi cikin gidan,sosai yayi mamakin ganin qofar falon a bude sabanin dazun da take a kulle,sai yayi zaton ko 'yan uwan zainab sunzo kwasar kaya bayan fitarsa a gidan saboda har yau sunqi kwashe kayanta "Sannu da zuwa my mukhtar" yaji muryar zainab na ambata,da sauri ya maida idomsa inda yake jiyo muryat,zainab din ce ta qure ado sanye sa wata matsiyaciyar doguwar riga wadda ta bayyana suffarta baki daya,fari take masa tana sake takowa kusa da shi,da sauri ya daka mata tsawa "Ke wacce iriyar maca ce,wato da na hanaki bina kasuwa shine kika sauya salon biyoni gida,to ina gargadinki wallahi ki gaggauta ficewa daga gidan nan don gamuwarmu ba zata yi kyau ba,don na tsani kowacce mace tunda sumayya ta ha'ince ni taso cutata ba don Allah ya riga ya rubuta mai taka doron qasa bane" maganar sa ta qarshe ita ta girgizata,idan har tayi dogon nazari da tsinkaye yana son ce mata cikin sumayya yana nan zata haifeshi nan gaba?yana nufin ita ta tashi banu riba?,ita tayi biyu babu ko daya?,bata samu sukunin tambayarsa ba ya daka mata wata tsawa wadda ta dawo da ita hayyacinta ta soma dubansa tana kada kai "Wallahi bazanyi biyu babu ba mukhtar,kana nufin taci riba?" Sam tunaninsa bai kai ga fassara maganarta ba,burinsa guda kawai ta fice masa a gida a yanzun kadaici yake da buqata,ganin zata bata masa lokaci ya sanyashi fincikar hannunta ya watsa ta waje,sannan ya dawo ya yibi mayafinta da jakarta ya wurga mata har kan fuskarta ya kulle gidan. Dawowa yayi ya zube saman kujera yana maida numfashi zuciyarsa na ci gaba da tuhumar sumayya,ta zamo silar yankewar duk wani jin dadi nasa,wayarsa ce ta soma takura masa da ruri ya dagata ya duban sunan mai kiran,yaya yahanasu ce,baya da buqatar qarin matsala akan wadda yake ciki,saboda haka ya kashe wayar baki daya ya ajjiye "Wallahi ban tafi kenan ba zan dawo,na dinga bibiyar rayuwarka kenan saboda ni da kai kadai zan rayu" ya jiyi zainab na aiko masa da maganar daga inda take,tsaki ya ja don ya fara daukarta a matsayin mai matsalar qwaqwalwa     ****    ****    ****    ****       Siyayyar dukkan wani abun buqatuwa ga sumayyan shine abu na farko da ya soma yi a safiyar washegerin ranar,kai hatta da man goge baki bai rage ba cikin siyayyarsa,sannan ya dora kudi dubu goma akai.        Sanda kayan suka iso gidan tashi tayi ta bar wajen ma baki daya ta koma daki,yadda bata da buqatarsu haka bata da buqatar ganinsu,kuka ne sosai ya kubce mata,har yanzu mamakin mukhtar take da har ya iya amincewa da ta aikata mummunan laifi irin wannan,ba wannan take buqata ba,baki daya mukhtar ya gaka rushe duk wani tanadi na raino da suka ciwa yaran da zasu haifa buri,itakam mai yayi saura,ba gwara ya qyaleta ba baki daya tasan cewa ta rasashi har abada?,dukkan wata kulawa a yanzun da zai nuna babu wani zaqi da zata mata ballantana ta burgeta.        Tun daga lokacin ya zamto duka qarshen wata zai mata siyayyar dukkan wani abu,tun daga na ci zuwa na buqata,duk da malam na hana wasu abubuwan amma sam bai yarda ba,yana jin haqqi ne a kansa kuma nauyi ne da ya rataya wuyansa ya kula da ita saboda yaronshi da take dauke da shi.        Kusan duk zuwansa yakan tsaya ne daga sori,su gaisa da mama da sauran yaran ya bada saqon ya juya,baki daya gashi nan dai a tafe ne,amma sam babu wani abu dake faranta masa illa idan ya tuna ya kusa daukan 'yarsa ko dansa.         Ta bangaren yaya yahansu kuwa sanda taji labarin sakin,sosai na zainab ya faranta mata,sai a lokacin ta dinga tuna abinda zainab din ra dinga yi musu,ta tabbatar har su ta hada ta asirce shi ya sanya suka gaza tabuka komai,jikinta kuma yayi sanyi da sakin sumayya,ita kanta ta dunga tunanin anya abinda mukhtar ya gaya mata ya faru ba tuggun zainab din bane?,tilas ta bar batun tunda abinda ake gudu ya riga da ya faru,amma lokacin da ya sake dawo mata da batun cikin na nan wani farinciki taji ya mamayeta,tana da muradin zuwa taga sumayyan amman kunya ta hanata,tana ganin kowa yasan gallazawar sa ta yiwa sumayya,da wanne ido 'yan uwanta zasu dubeta?,sai a yanzun take sake tausayin dan uwan nata ganin yadda ya sauya kamar ba muntarinsu ba.     ****      ******    *****       Hakanan yau ya tashi da muradin ganin cikinsa,amma ya kasa tantance cikin yake son gani ko sumayyar duk da zuciyarsa tafi afuwa ga cikin yake son gani,don rabonsa da ganinta tun randa malam ya gaya masa zancan cikin na nan a falonsa.          Saura kusan kwanaki bakwai lokacin da yake mata siyayyar ya cika,amma duk da haka da yammacin ranar ya shiga store din da ya saba siyayyar,shugaban gurin na ganinsa ya san me dame yake buqata,shi ya sanya aka hada masa komai sannan akayi total ya biya ya karba ya fice.          Qarfe biyar a qofar gidan tayi masa,yana sanye da wani yadi mai qarancin kauri ruwan bula mai haske wanda aka yiwa aiki da ruwan bula mai turuwa,duk da sauyawar yanayinsa da rama amma hakan bai hanashi kyau ba,sam rayuwar gidan bata masa dadi saboda a yanzun shikewa kansa komai,hakan ya sanya ya nemi wani saurayi wanda ke zuwa ya masa share share.          Halima ce ta soma ganinsa,ta yiwa mamansu magana aka bashi izini ya shiga,duk da yaran yanzun basa sakewa da shi kamar da,hakan baya masa dadi sam don baiga abinda su ya shiga tsakaninsu ba.         Cikin girmamawa ya gaida maman ta tambayeshi su yahanasun ya amsa mata duk lafiya qalau shi kuma ya tambayi masu jiki(wato sumayya),ba wata hira dama tun da can ke shiga tsakaninsu ba daya wuce gaisuwar,hakan ne ya sanyashi ya miqe bayan an gama shigo da kayan ya musu sallama ya fice.         Sai ya kasa tafiya ya tsaya a soron,yana da muradin ganin cikinsa gashi ko gilmawarta bai gani ba bare yaji muryarta,hakan babu wanda ya masa zancanta,jingina yayi da bangon soron hannunsa harde a qirjinsa yana tunanin ta yadda zai ganta din,cikin ikon Allah sai ga zainab ta fito tana sanya hijabinta zata shagon kusa da gidansu ta karbo klien zata wanke kwanukan da suka kammala abincin dare da su "Yauwa zainab,don Allah taimaka min ki fito min da yayarki mu gaisa" ya fada yana gyara tsaiwarsa,mamaki ya cikata,kamar tace wani abun kuma sai ta fasa ta juya ta koma ciki.          A dakin sumayyan ta tarad da maman tsaye kanta tana mata fadan rashin fitowa su gaisa da mukhtar,tundanko banza dai ai uban d'anta ne,abinda ya faru kuma babu wanda ya ruga ya gogeshi cikin KUNDIN QADARARTA,hawaye ta soma gogewa abinda maman bata so kenan "Amma mama meye amfanin fitar tawa mu gaisa,tunda dai lafiya qalau nake" "Na san da wannan,ko banza ai ko baya ta taki zai so ya tabbatar da lafiyar abinda ke cikinki ko" maman ta fadi "Shikenan kiyi haquri mama zan dinga gasheshi" tausayinta ya kamata,tana shirin yin magana zainab din ta shigo ta fada mata abinda mukhtar din ya buqata "Kin gani ai,sai kije ku gaisa" ta fada ta juya tana ficewa,hajibinta ta janyi dake rataye jikin sif ta zura sannan tayo waje.        Tunda ta fito ya zuba mata ido yake kallonta,sosai wannan karon cikin ya fito fiye da waccan karon,hatta tafiyarta ta soma sauyawa,kanta ma qasa din bata son hada ido da shi har ta qaraso,daga can gefe guda ta tsaya sannan tace "Ina yini" ba tare data daga kai ta dubeshi ba "Lafiya lau,ya jikin naki" "Alhamdulillah" ta fada cikin sanyi,sai shiru ya biyo baya kowa da abinda ke saqawa cikin zuciyarsa,tsaiwar ta fara mata tsauri har ya lura da haka,sai ya waiwaya ya gangaro mata wani dutse da suke tokare qofa da shi ya furta "Ga guri zauna" bata musa ba ta zauna din don tana da buqatar hakan "Me yasa sumayya?,why?,kinga ayanzun kin zama silar da zamu raini yaronmu a mabanbanta gurare abinda ko a mafarki ban taba hasashen faruwarsa ba"ya furta wani daci na zagaya harshensa,idanuwansa na sauya launi,da sauri ta daga kai ta watsa masa fararen idanuwanta,take wani bacin rai ya soma bijiro mata,wato har yanzun zarginta yake kenan?,dama abinda yake son gaya mata kenan da har ya fiddo ta tana zaman zamanta tana lallaba rayuwarta.        Qin tankawa tayi sai ma yunqurin miqewa da ta soma yi saboda bata ga alfanun ci gaba da tsaiwa a gabansa ba,ganin tana niyyar wucewa ba tare da ya gaya mata abinda zaya fadi ba yace " idan nayi lissafi dai dai cikin ya kusa shiga wata na tara,zuwa yanzu ya kamata ace anyi siyayya,ki rubuta duk abinda kike da buqata jibi zan dawo na karba in sha Allah" "Ka kawo duk abinda kake ganin zaka iya" ta fada tana mai shigewa gidan ba tare da ko ta waiwayoshi ba zuciyarta na suya,idanunta na zafi. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ KUNDIN QADDARATA✍ 📖📖📖📖📖 NA SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA WATTPAD:HUGUMA HASKE WRITERS ASSO (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 3⃣3⃣ Zuwa ga marubuciyya safiyya abdullahi musa huguma mujin shuru kwana muna ta xuba ido mu masoyanki Allah yasa dai lafiya dan Allah ki taimaka ki cigaba da post muna jin dadi littafin sosai. Na gode daga masoyarki. Aysha M Adam ( maman muneepha) Dan Allah duk wanda ya gani ya tura gaba har ya isah garaita plx. 👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 3⃣4⃣ ______________________________ *Bismillahir rahmnair rahim* *tsarki ya tabbata ga Allah wanda mulki ke hannunsa kuma mai iko ne akan komai,wanda shi ya halicci rayuwa da mutuwa,ya halicci cuta da lafiya* *haqiqa kalmomin bakina sunyi qaranci wajen nuna tsantsar godiya ta ga ubangiji bisa alfarmar samun lafiya da yayi min,bani da abun cewa face roqonsa ya bani ikon morarta ta hanyar bauta masa da yi masa biyayya* *godiya ga iyaye na,babu shakka soyayya irin ta mahaifa babu kamarta duk fadin duniya,naga zallar ta a idanuwa da ayyukansu,ban da abin biyansu,saidai bazan gaza ba wajen yi musu addu'ar ubangiji ya musu kyautar Aljanna madaukakiya,ya musu kyakkyawan qarshe,yasa su cika da kalmar shahada,ya jiqan magabatansu,ya cika musu burikansu duniya da lahira,ya cika rayuwarsu da farinciki lafiya wadata da kwanciyar hankali* *fans ina matuqar godiya a gareku,'yan watpadd bani data cewa sai fatan Allah ya muku kyakkyawan qarshe,'yan watsapp bazan manta karamcinku a gareni ba,ubangiji ya hadamu cikin jannatul firdausi,addu'o'in alkhairinku gareni fans ina roqa muku ninkinsa wajen ubangiji* *_wannan shafi sadaukarwa ne a gareku_* *mariya SB* *aysha abubakar(maman khalipha)* *mariya yola(mamam shuraim)* *mommy maimuna musa* *Allah ya saka da alheri ya qara zumunci* ______________________________ Hakanan yau ya tashi da muradin ganin cikinsa,amma ya kasa tantance cikin yake son gani ko sumayyar duk da zuciyarsa tafi afuwa ga cikin yake son gani,don rabonsa da ganinta tun randa malam ya gaya masa zancan cikin na nan a falonsa.          Saura kusan kwanaki bakwai lokacin da yake mata siyayyar ya cika,amma duk da haka da yammacin ranar ya shiga store din da ya saba siyayyar,shugaban gurin na ganinsa ya san me dame yake buqata,shi ya sanya aka hada masa komai sannan akayi total ya biya ya karba ya fice.          Qarfe biyar a qofar gidan tayi masa,yana sanye da wani yadi mai qarancin kauri ruwan bula mai haske wanda aka yiwa aiki da ruwan bula mai turuwa,duk da sauyawar yanayinsa da rama amma hakan bai hanashi kyau ba,sam rayuwar gidan bata masa dadi saboda a yanzun shikewa kansa komai,hakan ya sanya ya nemi wani saurayi wanda ke zuwa ya masa share share.          Halima ce ta soma ganinsa,ta yiwa mamansu magana aka bashi izini ya shiga,duk da yaran yanzun basa sakewa da shi kamar da,hakan baya masa dadi sam don baiga abinda su ya shiga tsakaninsu ba.         Cikin girmamawa ya gaida maman ta tambayeshi su yahanasun ya amsa mata duk lafiya qalau shi kuma ya tambayi masu jiki(wato sumayya),ba wata hira dama tun da can ke shiga tsakaninsu ba daya wuce gaisuwar,hakan ne ya sanyashi ya miqe bayan an gama shigo da kayan ya musu sallama ya fice.         Sai ya kasa tafiya ya tsaya a soron,yana da muradin ganin cikinsa gashi ko gilmawarta bai gani ba bare yaji muryarta,hakan babu wanda ya masa zancanta,jingina yayi da bangon soron hannunsa harde a qirjinsa yana tunanin ta yadda zai ganta din,cikin ikon Allah sai ga zainab ta fito tana sanya hijabinta zata shagon kusa da gidansu ta karbo klien zata wanke kwanukan da suka kammala abincin dare da su "Yauwa zainab,don Allah taimaka min ki fito min da yayarki mu gaisa" ya fada yana gyara tsaiwarsa,mamaki ya cikata,kamar tace wani abun kuma sai ta fasa ta juya ta koma ciki.          A dakin sumayyan ta tarad da maman tsaye kanta tana mata fadan rashin fitowa su gaisa da mukhtar,tundanko banza dai ai uban d'anta ne,abinda ya faru kuma babu wanda ya ruga ya gogeshi cikin KUNDIN QADARARTA,hawaye ta soma gogewa abinda maman bata so kenan "Amma mama meye amfanin fitar tawa mu gaisa,tunda dai lafiya qalau nake" "Na san da wannan,ko banza ai ko baya ta taki zai so ya tabbatar da lafiyar abinda ke cikinki ko" maman ta fadi "Shikenan kiyi haquri mama zan dinga gasheshi" tausayinta ya kamata,tana shirin yin magana zainab din ta shigo ta fada mata abinda mukhtar din ya buqata "Kin gani ai,sai kije ku gaisa" ta fada ta juya tana ficewa,hajibinta ta janyi dake rataye jikin sif ta zura sannan tayo waje.        Tunda ta fito ya zuba mata ido yake kallonta,sosai wannan karon cikin ya fito fiye da waccan karon,hatta tafiyarta ta soma sauyawa,kanta ma qasa din bata son hada ido da shi har ta qaraso,daga can gefe guda ta tsaya sannan tace "Ina yini" ba tare data daga kai ta dubeshi ba "Lafiya lau,ya jikin naki" "Alhamdulillah" ta fada cikin sanyi,sai shiru ya biyo baya kowa da abinda ke saqawa cikin zuciyarsa,tsaiwar ta fara mata tsauri har ya lura da haka,sai ya waiwaya ya gangaro mata wani dutse da suke tokare qofa da shi ya furta "Ga guri zauna" bata musa ba ta zauna din don tana da buqatar hakan "Me yasa sumayya?,why?,kinga ayanzun kin zama silar da zamu raini yaronmu a mabanbanta gurare abinda ko a mafarki ban taba hasashen faruwarsa ba"ya furta wani daci na zagaya harshensa,idanuwansa na sauya launi,da sauri ta daga kai ta watsa masa fararen idanuwanta,take wani bacin rai ya soma bijiro mata,wato har yanzun zarginta yake kenan?,dama abinda yake son gaya mata kenan da har ya fiddo ta tana zaman zamanta tana lallaba rayuwarta.        Qin tankawa tayi sai ma yunqurin miqewa da ta soma yi saboda bata ga alfanun ci gaba da tsaiwa a gabansa ba,ganin tana niyyar wucewa ba tare da ya gaya mata abinda zaya fadi ba yace " idan nayi lissafi dai dai cikin ya kusa shiga wata na tara,zuwa yanzu ya kamata ace anyi siyayya,ki rubuta duk abinda kike da buqata jibi zan dawo na karba in sha Allah" "Ka kawo duk abinda kake ganin zaka iya" ta fada tana mai shigewa gidan ba tare da ko ta waiwayoshi ba zuciyarta na suya,idanunta na zafi.       Babu kowa cikin tsakar gidan nasu kai tsaye ta fada dakin tana jan numfashinta tana jin zuciyarta na mata nauyi,qwalle ke layi kan kuncinta daya na bin daya,a addafe ta nemi gefan katifa ta zauna tana jujjuya kanta cikin zuciyarta tana addu'a wadda bata tantance mai take roqa ba,abu daya zuwa biyu zata iya tantancewa shine haushi da tsanar mukhtar dake mata yawo cikin zuciya,sai kuma zainab wadda take jin ba zata iya yafewa karan tsayen da ta tiwa rayuwarsu ba musamman ita din,wanda gangar jikinta da zuciyarta bata saba da kowa ba sai mukhtar din tun zamanin quruciya zuwa girma.       Ta dauki a qalla mintuna talatin a haka kafin sautin qarar wayarta dake yashe gefe ta katse mata yanayin da take ciki,sunan anty dije ke yawo bisa screen din,tamkar an kwance qullin dake zuciyarta taji zuciyar ta karye hawaye ya sake balle mata tun kafin ta kai ga daga wayar.       Muryarta kawai anty dije taji jikinta ya bata akwai damuwa,fada ta shiga yi tun kafin taji matsalarta akan kan mene ne za'a dinga bata ranta,ta gaya mata me aka mata waye ya bata mata,ganin ta gaza bata amsa yasa ta katse kiran ta nemi layin maman,tana daga daki ta juyo muryar maman da alamu anty dijen ta sameta,jikinta ta komar ta jinginar a bango ta lumshe idanunta tana matse hawaye.      Batasan ya sukayi da mama ba daga bisani ta kirata ta gaya mata idan har taga ba zata iya ba tayi tahowarta abuja gurinta ta zauna ta haihu a nan,godiya ta mata tare da ce mata to ba don tana jin tafiya can din ba,maida kanta tayi ta kwanta sosai saman katifar tana maida ajiyar zuciya   ****     ****    ****   ****     La'asar ce sosai misalin qarfe biyar na yammacin,tana zaune saman kujera 'yar tsuguno tana tsinke danyan zogale,halima na bakin kurfeti wanda take kwashe tuwon dare,mama na saman tabarma daga gefen sumayya tana daka gyada da daddawa,sai zainab wadda ke wankin kayan sumayyan wanda basu wuce kala hudu ba,hira suke irin wadda ta shafesu,sosai hirar kewa sumayya dadi don har qyaqyata dariya take.         Sallamar yaro ce ta katse musu hirar wanda ya sanar musu mukhtar na gaidasu,mama ce ta fadawa yaron yace ya shigo wanda hakan ya sanya sumayya sakin zogalen hannunta ta dafa qasa tare da yunqurawa ta miqe,bat fara'ar dake fuskarta ta bace,a hankali ta juya ta shige dakin yayin da maman ta bita da kallo lokacin da take qoqarin zura hijab a jikinta.         Yara ne suka fara shigo da kaya,akwatu ne har seti uku matsakaita masu kalar ruwan hoda da ruwan toka(ash and pink)masu azabar kyau,sai da suka ajjiyewa suka fice sannan mukhtar din ya shigo.         Sanye yake da shadda ruwan madara(milk)dinkin tazarce wadda tayi masifar masa kyau,sosai ta dace da shi duk da irin ramar da yayi,kamar ko yaushe ya gaisa da maman cikin kunya da nutsuwa kafin shiru ya biyo baya na 'yan daqiqu sannan yace "Kaya ne mama gasu nan,idan akwai abinda babu ciki sai a sanarmin don Allah mama" addu'ar fatan alkhairi tayi sannan daga bisani ya miqe bayan ya ajjiye wasu kudi gaban maman ya fice yana kiran halima.         Kusan duk cikin kunnenta komai ya faru,idanunta na a rufe har ya fice daga gidan,wani gudu gudu zuciyarta ke mata tare da wani zafi,duk sanda ta tunashi kota jishi ko ta ganshi wani miki ke motsawa cikin zuciyarta,har yanzu cikin jin haushinsa da zarginsa babu abinda ya ragu cikin zuciyarta,a ko yaushe zuciyarta na gaya mata tunda mukhtar ya zargeta aduniya waye zai gasgata ta?,waye zai yarda da gaskiyarta,a haka ta zame ta kwanta ko zata samu sauqin zugin da zuciyarta ke mata.       Bayan sallar isha'i mama ta nunawa mallam akwatunan,bai buda ba yayi addu'a dai kawai,cikin sauri halima da zainab da suka qagu suga meye a ciki suka matso gaban akwatim suka soma budewa,sumayya na daga saman kujera wadda tunda ta yiwa malam sannu da zuwa bata sake cewa komai ba,sanye take da hijabi hannunta riqe da qaramin alqur'ani tana karantawa qasa qasa,sam idanunta bai kansu karatunta kawai take kamar batasan meke faruwa ba.         Ba qaramin tafiya da su halima kayan sukayi ba,kallo daya zaka musu ka tabbatar mukhtar yayi rawar gani,kaya ne masu dan uban kyau da tsada unisex,takalma huluna,riguna fidoji,tarkace dai kala kala wami abun ma basu san sunanshi ba,akwati biyun duka na jarirai ne,yayin da ta qarshen atamfofi ne super biyu,lace daya shadda daya,sai materials masu kyau guda biyu jaka takalmi da mayafi sai sarqa da awarwaro,kana kallonsu kasan na uwar yaro ne na fitar suna "Masha Allah,wannan yaro ko yarinya anyi dan gata,don Allah anty sumayya dago ki gani" zainab ta kasa shiru ta fadi haka. A hankali ta daga idanunta ta watsawq zainab din wanda ya sata dawowa hayyacinta,sai tayi shiru ta sadda kai yayin da sumayyan taci gaba da karatunta ba tare data sake tofawa ko dubansu ba.        Qememe taqi yarda a ajjiye kayan a dakinta kusa da ita,tun yaya abubakar na tsokanarta suna dauka wasa ne har suka gane bil haqqi da gaske take,don kuka ta fashe musu da shi,tilas ya abubakar ya karbi kayan ya musu ma'ajiya a dakinsa.   ****   ****   ****   ****     Tunda ta idar da sallar isha'i ta kwanta bayan taci tuwon dare,wani mugun ci tayi masa har halima na mata dariya tana tsokanarta duk da yadda take jinta a takure saboda yadda baya da mararta ke ciwo kadan kadan. Bacci taso ya dauketa saidai yaqi zuwa juyi take lokaci bayan lokaci saboda yadda kwanciyar taqi mata dadi duk da cewa idan da sabo ta saba tunda cikinta ya fara nauyi,a haka har su halima suka gama bidirinsu suka shigo suka kwanta bacci ya kwasheta idanunta biyu.        Sannu a hankali taji ciwon yana ci gaba da qaruwar mata daga mararta zuwa baya,sai ta miqe a hankali jin motsin mama da tayi a tsakar gida tana rufe kitchen da alama bata kwanta ba,tana qoqarin shiga daki sumayyan ta kira sunanta,waiwayowa tayi cikin mamaki ta amsa don a tunaninta ta jima da yin bacci tunda ta riga kowa kwanciya. "Mama marata da baya ne kemin wani irin ciwo,gashi na kasa bacci" idanu ra zuba mata tana nazarinta sannan tace "Tun yaushe ne?" "Tun dazu" ta fada tana cije lebe saboda yadda aka mintsineta,kai ta gyada sannan ta juya ta bude dakinta maimakom dakin malam da take niyyar shiga tace da ita "Shiga ki kwanta anan ina zuwa" ta fadi tana sake juyawa zuwa dakin malam din.         Koda maman ta dawo bakin gado ta sameta zaune saboda kwanciyar ta gagareta,ji take kamar ana tsaga mararta ana karya gadon bayanta,tuni gumi ya fara yi mata sallama,yarfa hannu take tana kiran sunnayan Allah tare da mirgina kai hagu da dama,kofin hannunta maman ta miqa mata cike da tausayi tace ta shanye,kallo daya tayi mata ta tabbatar naquda take,daga kai tayi ta shanye baki daya sannan ta dire kofin a wahalce,cikin mintina qananu ciwon ya sake yin gaba.        Awa daya ta wuce shiru biyu shiru hakan ya sanya mama ta sake komawa gun malam ta kuma karbo mata wani rubutun ta sake shanyewa,tun tana daurewa har hawaye suka qwace mata ba tare data shirya ba,ba shakka zamantowa uwa ba qaramin abu bane haka ta dinga rayawa cikin zuciyarta.          Qarfe biyar saura na asubahin ranar talatar ya zamanto mata ranar tarihi a gurinta,dai dai lokacin da yaron cikinta ya shaqi iskar duniya,kukansa ya karade ilahirin gidan wanda ya sanyawa ilahirin wanda ke gidan yana bacci farkawa,malam kuma dake zaune dungurgur yayi hamdala ga ubangiji yana qarawa.       Ware idanunta tayi sosai sanda iskar sanyin asuba ke busata,tana son tabbatarwa kanta da gaske ne abinda ke cikinta ne ya iso duniya yake cala kuka haka?,da gaske ne a yau itama ta zama uwa?,ta shiga sahun iyaye?,da gaske yau itama zata riqe ta kalla ta kuma raini danta na cikinta?,ta fita daga sahun juya?,wannan kalma ta zama tarihi cikin rayuwarta?,a yau ta haifawa mukhtar da wanda yake buri gareta buri gareshi,sai dai kash,ba zaya samu irin tanadin da suka yiwa rainon da zasu bashi ba,wata qaqqarfar QADDARA ta shigo ta farraqa kasancewarsu tare,a yau zasu raineshi ne a mabanbantan gurare,sai ta saki kuka a fili wanda cikin zuciyarta tana tasbihi ne ga ubangiji,cikin mamaki mama ke dubanta "Lafiya ko wani guri ke miki ciwo kuma?" Ta tambaya sanda take tsaka da qoqarin dauke yaron da gyara gurin,kai ta girgiza tana ci gaba da kuka,tuni maman ta gano kukan me take saboda haka taci gaba da aikinta tana cewa "Godiya ya kamata ki yiwa ubangiji ai".        Kafin gari ya waye tuni komai yayi tsaf daga uwar har dan har gurin da akayi naqudar,maman ce ta shigo da yaron dake nannade cikin shawul ruwan sararin samaniya bayan sunqufe shi da akayi cikin lallausan kayan sanyi suma ruwan bula din,malam ta kaiwa shi bayan ya dawo sallar asubahi ya ganshi,ya sha addu'a kuwa bayan wasu sirrika da ya hada ya dangwala masa a baki,sumayyan na gefan gadon mamam riqe da kofin shayi mai kauri da maman ta hada mata kan ta fita da yaron,har yanzu ta gaza shanyeshi saboda bacci dake dibarta " karbeshi ki ganshi sumayya ki masa addu'a"maman ta fada tana dora mata shi saman cinyarta bayan ta karbo kofin shayin data samu ta shanye.      A hankali kamar mai tsoron tabashi ta sanya hannu ta tallabeshi,take idanunta suka cika taf da qwalla,a sanyaye ta sanya hannu ta yaye rufin fuskarsa idanunta suka sauka kan fuskar tasa wadda idanunsa ke rufe ruf yana ta sheqar bacci cikin lumana da kwanciyar hankali,kallo daya tayi masa ta hango kamanni na kai tsaye da yaje da babansa duk da ba idanunsa biyu ba,a kallon farko taji wata iriyar qauna da soyayyar yaron ta mamayeta,irin qauna ta da da mahaifi,tausayinta kuma ya samu gurbi cikin zuciyarta karon farko data tuna irin siradin da rayuwarsa ta tsallake kafin ya kai ga isowa zuwa ga wannan fili da muke kira da duniya,sai gashi Allah ya nuna ikonsa,yaro qato kyakkyawa mai cike da qoshin lafiya,wanda ko cikin mafarkinta bata taba tunanin zata haifi kamarsa ba "Bawan Allah" ta furta ba tare da tasan a fili ta ambaci hakan ba qwalla na kwaranyo mata,daga shi tayi zuwa fuskarta ta karkata kunnensa na dama ta karanta masa kiran sallah ta karkata na hagu ta karanta masa iqama sannan ta ambata masa sunansa *ABDALLAH* bawan Allah.      Murmushi mama tayi ta dubeta "Amma kya jira babansa yazo ya zaba masa suna ko?" Kai ta girgiza "Kiyi haquri mama,ni yafi kamata mama na sa masa suna,ni kadai nasan wahalar da nasha,daga ni sai ubangiji na ma......." Sai ta kasa qarasawa saboda karyewa da zuciyarta tayi "Kukan ya isa haka,yau ranar murna ce,ajjiyeshi kusa da ke,maza so nake ki kwanta kiyi bacci sosai" bata musa ba din tayi yadda maman tace,tun tunaninnika na bijiro mata har wani nannauyan bacci mai dadi yayi gaba da ita. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 3⃣5⃣ _______________________ *Bismillahir rahmanir rahim* *wallazi yumutuni summa yuhyi,wallazi adma'u ay yagfirali khadi aty yau maddin* ______________________________ A makare ya tashi yau wanda hakan ya sabba ba masa yin sallar asubahi cikin gida,tunda ya idar da sallar yake zaune saman daddumar bai tashi ba kamar yadda bai aiwatar da komai ba,tunanin sumayya ne fal zuciyarsa yau ya wayi gari da shi,hakanan yake jin wunin yau ba zai iya qarewa ba ba tare da yaje ya ganta da lafiyar abinda ke cikinta ba,kusan tunda ta shiga watan haihuwarta da ita yaje kwana yake tashi. Qarar wayarsa ce ta katse masa hanzari,ya juya bangaren da take ya jawota ya duba,baquwar lamba ce,ya latsa sannan ya kara a kunnensa,runtse idanunsa yayi zuciyarsa ta soma quna saboda muryar wadda yaji,bai taba jin ya tsani wani abu tsana mai tsanani ba irin na mamallakiyar muryar,zainab ce take magana cikin maqale murya da wani irin salo nason tafiyar da hankali,tun a daren jiya bokanta wanda take kira da malam ya bata wannan sa'ar ya kuma tabbatar mata bayan sallar asubahi ne zata sameshi,sanda ya daga wayar zuciyarta sai ta cika da farincikin samun nasara,don dama ya sanar mata bayan sallar asubar a gobe bazai koma bacci ba,jin tana ta magana ya mata shiru ya sanya ta fashewa da wani makirin kuka "Habaa my mukhtar,dama laifin wani kan iya shafar wani?,mene laifina ni a ciki?,duk iya yina nayi don inga abinda ke cikin yarinyar nan ya kubuta,duk tarin hidima dana dinga yi da ita rana daya duk ka mance ka watsar da alkhairi na a gareku ka sakeni,kuma ma tunda an samu cikin na nan ba shikenan ba komai ya wuce sai ka maidani daki na ko?". Kamar garwashin wuta haka yaji kalaman nata,cikin harzuqa ya dakatar da ita " ke wacce iriyar jahila ce wai?,shin kin manta zama ni dake a yanzu ya haramta ne sau nawa zan nana ta miki,ke koda kuwa ma zamanmu ya halatta bazan iya zama da kowacce mace ba a yanzu,tunda sumayya da na raina da kaina ta iya min haka babu wata diya mace da ba zata iya aikata min makamancin haka koma fiye da shi ba,saboda haka gargadina dake na qarshe,kada ki sake gigin kiran layi na ko tarar hanyar da kika san zan bi,idan kuma kinqi ji ba zaki qi gani ba"daga haka ya katse kiran ya ajjiye wayar a fusace. Daga daya bangaren nata itama ajjiye wayar tayi tana huci sannan ta dubi qawar tata "Wannan wanne irin mutum ne haka?,duk zama da wuyar da muka sha wajen malam ta tashi kenan a banza,kinji maganganun banzan da yake gaya min?,to wallahi wannan karon babban aikin zan saka a masa koda duniya zata zageni,ko zanyi yawo babu zanin daurawa" kafada ta daga tana fadin "Au ho sai yanzu kika gane kenan?,tuntuni ai malam din ya gaya miki ki saki naira kiga aikin da ko uwarsa dake kabari ba zai ganta a gabansa ba sai ke" miqewa tayi ta fice daga dakin fuuu tana fadin "Ai anzo gurin kuma". A hasale ya kuma waiwayowa ga wayar tasa jin ta sake tsuwwa a karo na biyu yana zaton ita din ce ta sake kiransa,sai jikinsa yayi sanyi gabansa ya fara faduwa ganin sunan abubakar kan screen din,cikin sanyi da sallama ya amsa wayar,lumshe idanuwa yayi wata rahama na sauka cikin zuciyarsa lokacin da abubakar ke furta masa albishir mafi dadi da ya taba sauraro tsawon rayuwarsa,sumayya ta haihu ta haifa masa yaro,baisan adadin lokacin da ya dauka ba cikin duniyar madaukakin farinciki shidai ya farka yaga har kiran na abubakar ya katse. Faduwa yayi saman a bin sallar yayi sujudush shukur yana mai tasbihi ga ubangiji,bai wani jinkiri ba ya miqe ya fada makewayi ya shiga wanka,cikin mintina talatin ya fito,kai tsaye gaban sif dinsa ya isa bayan ya tsane jikinsa,ya bude yana kallon kayan,a sanyaye ya sauke hannayensa yana duban kayan kala bakwai da suke sababbi dukkansu,ba zai manta randa ya bada dinkinsu ba,tun cikin sumayya na da wata uku a lokacin tana gidan,musamman ya tanadesu ya dinkasu saboda ya sanyasu tun daga rana ta farko da aka haifa masa yaronsa har ranar suna,baya iya manta lokacin da take dariya tana tsokanarsa da cewa gandoki,sai ya koma bakin gadon ya zauna yana yarfa hannu,yana jin yadda bacin rai ke taso masa yana son danne farincikin da yake ciki,baisan mai yasa har yau zuciyarsa ta kasa daina jin ciwon abinda tayi masa ba duk da cewa an cimma nasarar tsallakewar cikin gashi har yau Allah ya nufa ya iso duniya. Da qyar ya samu ya hadiye wani dunqulen abu mai daci sannan ya miqe ya shirya cikin wani yadi mai kyau na maza fari sol wanda ya masa kyau sosai,ko abinda zai sawa cikinsa bai nema ba ya fito don dama ba ko yaushe yake samun damar karyawar safe ba,yana shirin tada motarsa ya kira ya yahansu ya shaida mata,hamdala ta dinga yi matiqa da gaske tana jin dadi a zuciyarta,ta kuma shaida masa lalle ya biyo gidan nata kafin ya wuce. Kafin sha daya na safe tuni gidan ya cika da jama'a 'yan uwa da abokan arzuqi,kowa barka yake mata tare da tayata farincikin wannan rana da aka jima ana saka ran zuwanta,sam ita bata san me ake ba ma,bacci take sosai ita daya a dakinsu,yaron shima nashi baccin yake,sai da ya farka ya fara kuka alamar yunwa sannan mama ta baro dakinta wanda suke zaune da mutane ta shigo dakin ta tasheta,sai data sake hada mata shayi mai kauri ta sake sha sannan ta dora mata shi saman cinyarta ta fara koya mata yadda zata shayar da shi,runtse tayi sannan ta fara qorafin zafi maman tace "A haka zaki daure har ki saba". Sallamar da kunnuwanta ya jiyo shi ya sanya jikinta saki,sai ta zubawa bakin qofar dakin ido tare da barin qorafin da takeyi,halima ce ta shigo " mama ga yaya mukhtar" "To ya shigo mana" ta fada tana gyara mayafin jikinta,qasa sumayya tayi da kanta tana duban yaron dake saman cinyarta yana tsotsar nono a hankali,sallama yayi cikin dakin sannan ya qaraso a nutse hannunsa dauke da qatuwar baqar leda,baki daya idonsa na kan sumayya da yaron wadanda kowannensu yake jin mabanbantan yanayi a kansa cikin zuciyarsa,wata qauna ta musamman yaji ta dirar masa tun kafin yayi tozali da gudan jinin nasa,yayin da tausayi da kuma wata daraja ta sumayya ta daban yaji ta ginu a ransa,a mutunce suka gaisa da maman sannan ta miqe ta fice,shiru ya ratsa dakin bayan ficewar tata,shi yana zaune yana aukin kallonsu ya rasa daga inda zaya fara,yayin da itama taqi motsin kirki dukkan idanunta na kan yaron nata tana dubansa,tana jin yadda yake zuqar mama har cikin ranta,ci gaba yayi da dubansu wani yanayi na ratsashi,sai suka burgeshi sosai,karo na farko da yaji zai iya yafewa sumayyan kome tayi masa,yana ji a yanzu ta cancanci yafiyarsa. Cikin qwarin gwiwa da karsashi yayi gyaran murya tare da muskutawa yace "Sannu sumayya"ta dan cije lebe kadan sannan ta amsa can qasa " yauwa" "Sannu da qoqari,Allah ya saka miki da alkhairi,na yafe miki sumayyan duk wani abu da kika yimin" da sauri ta daga kai ta dubeshi sannan ta kau da kai "Bana buqatar yafiyarka tunda ni din ban aikata maka ko wanne laifi ba,hasalima ni nafi cancanta da a nemi yafiya ta" mamaki kalaman nata suka bashi,bai kai ga furta komai ba mama ta sake shigowa hannunta dauke da kofi cike da kunun kanwa yana tururi "A'ah,baki bashi shi ya ganshi ba,ki cire shi haka idan ya gama ganinsa yaci gaba da sha ko" ta fada tana dire kofin tare da ficewa. Bata kammala ficewar ba ya taso da kuzarinsa ya qaraso gabanta sanda ta cire maman daga bakinsa tana gyara masa rufa,ya miqo hannunsa ta dora masa shi saman hannun nasa tana fadin "Ga abdallah nan"sai ya cira kai ya dubeta,tabbas suna ne mai kyau da asali,ko shi din ma sunan yayi masa,baice komai ba ya koma da baya ya zauna inda ya tashin yana kallon yaron,baisan fuskarsa ta wadata da murmushi ba,baisan hawaye na bin fuskarsa ba sai da yaga digarsu kan kuncin yaron wanda hakan ya sanya yaron bude idanunsa yana kallonsa,wata qaunar sumayyan ke son dawowa cikin zuciyarsa,ko babu komai koda ta aikata laifin tayi fama da dakon wannan qaton babyn cikin cikinta tsawon watanni tara ta kuma yi naqudarsa ta haife masa,rana da wani matsayi na daban wanda babu diya macen da ta takashi cikin rayuwarsa,ita din ma dubansu take tana daga zaune,wani wawan rauni keson ziyartar zuciyarta,saidai zargin saurin yanke hukunci na mukhtar da rashin bincike ke naushin zuciyarta,sai ta dauke kai daga dubansu tana jin kuka nason qwace mata tana qoqarin maida shi. Ya jima zaune yana aikin kallon yaron da yi masa addu'a tamkar zai maidashi ciki,sam kamar ma bashi da niyyar tafiya,har sai da aka sake yin baqi sannan ya miqe ya dora mata shi saman cinyarta,ya sunkuya ya sumbace har tana jin hucin numfashinsa wanda hakan ya sanya ta ja da baya,ya dago yana dubanta bayan ya ajjiye ledar da ya shigo da ita a gefanta ya dora kudi a sama " ga wadan nan ko zakuyi amfani da su,ban yarda a dorawa kowa wani nauyi wanda yake nawa ne,Allah ya qara muku lafiya"ya fada yana juyawa ya fice daga dakin a sanyaye tamkar bai son tafiyar **** ***** **** **** Cikin kwanakin hidima aka dinga yi sosai cikin gidan,duk wani dan uwa na jiki ko aboki babu wanda baizo ya tayasu murna ba,mukhtar kuwa kullum qafarsa na gidan babu ranar da bazaizo ganin fuskar Abdallah ba,sau tari saidai sumayyan tasa a miqa masa shi tana daga cikin gida. Yaya yahanasu tazo a kunyace saidai ita daya don sauran duk sun kasa zuwa,atamfa ta kawowa sumayya turmi biyu sai dan qaramin akwati na qarshen wanda ta cikoshi da kayan baby,ba wanda ya nuna mata komai suka karba suka mata godiya. Suna akayi na gani na fadan tamkar tana gidanta,hatta anty dije dake abuja ba'a barta abaya ba sai data halarta ita da yaranta baki daya,duk da cewa suna tsaka da zangon karatu amma sai da suka dauki uzuri suka zo,rago da saa mukhtar ya yanka masa,sosai abdallah yaga gata,yaron yazo da farinjini da goshi mai yawa,qauna da soyayya ko ta ina,kowa gwada masa kalar tasa yake yi. **** ***** ***** Jego take sosai irin na daa shi mama take mata,sosai take gasata ta kuma cikata da cimaka,irinsu romon nama,tuwon dawa kunun kanwa kunun gyada da sauransu,hakanan babu fashin wankan ganye safe da yamma take yinsa har sai data cika kwanaki arba'in harda doriyar kwana biyar,zuwa lokacin ta murje ta dada kyau,idan ka dubeta ba zaka taba cewa ita ta haife abdallah ba,yayin da abdallahn yayi wani irin wayau da qiba dauka da nishi ajjiyewa da nishi,kullum mukhtar na hanyar gajin yaronsa,sau tari yakan bawa mama da malam tausayi yadda baya ko gajiya,duk sanda zaizo hannunsa dauke da wani abu yace na abdallah ne,har da abinda bazai yi masa amfani a yanzu ba saidai ko nan gaba,itakam sumayyan bata ma yarda su hadu bada yaron take ta shige daki,yakan jima yana yiwa yaron wasa tare da jin qaunarsa da kewar mahaifiyarsa cikin zuciyarsa. **** ***** ***** **** Rayuwa ta mata kyau saboda ta samu gata yadda ya kamata,cikin watanni uku abdallah ya soma iya zama,wata na biyar rarrafe ya miqa,sosai yaron yake da shiga zuciya da daukan hankali,saboda tsafta da kukawa da yake samu,ko yaushe zaka ganshi tsaf cikin shiga ta gayu kamar wani saurayi,idan manyan kaya ta sanya masa kai kace babban mutum ne,idan kuma qananun kaya ne sai ka dauka saurayi ne,baya rabo da qamshi shi yasa har maqota aikowa suke daukarsa,zuwa wannan lokaci mukhtar wani lokacin yakan zo ya daukeshi ya jima wajensa wani lokaci har kasuwa yake leqawa da shu,tun tana bata rai mama na mata fadan na zata raba da da uba ba har ta saki ranta ta haqura,wata goma ya qware a tafiya sosai,idan ka ganshi sai ka zaci yayi shekara daya da rabi ne.  A lokacin yaya abubakar ya sama mata foam na wata makaranta dake koyar sana'o'i,ta zabi ta koyi yadda ake saqa da humra turaren wuta da na kaya da na tsugu no,hankali kwance take zuwa makarantarta ta dawo don bayan layinsu take,abdallah kuwa bai cika rigima ba sai idan yaso,saboda haka a gida take barinsa taje abinta ta dawo,koda ya sa rigima ma zainab ko halima kan daukeshi su kai mata shi,a lokacin ta sake wani kyau da cika,saika rantse da Allah bata taba aure ba balle har ta haifi yaro. ***** ****** ****** Qarfe hudu da mintuna ta iso gida a gajiye,tana sallama abdallahn ya kubce daga hannun zainab dake shafa masa hoda a wuya da alama wanka aka sake masa,riga ce mara hannu a jikinsa sai wando three quater,yayi kyau sosai,da gudunsa ya taho ya tareta yana mata gwalantu wanda ke nuna alamar fara koyon magana,daga shi sama tayi tana juya shi suna qyalqyala dariya sannan ta direshi tana amsa maganar zainab wadda ke mata qorafin yau abdallah ya bata kaya sunfi uku "Kunfi kusa ai,bake ke kareshi ba idan za'a masa fada" tayi maganar tana qarasawa bakin fanfo don daura alwala tana sake fadin "Mama fa?,naji gidan shiru" zainab dake tattara kayan kwalliyar abdallah ta amsa mata "Eh sun fita ita da ya halima gidan maman shafa'atu ganin salima" "Kice biki ya kusa kenan" "Wlh saura 'yan satittika basu wuce uku ba" "Allah ya sanya alkhairi" ta fada tana gyara daurin dankwalinta ta shige daki donyin sallah abdallah na biye da ita a baya yana mata surutu. Tana kammala sallar abdallah na saman jikinta yana faman qiriniya da nuqurqusarta taji sallama kamar ta bahijja,kafin ta yunquro taji ana tambayar tana nan zainab ta amsa da eh,bahijjan ce kuwa,hannu bibbiyu ta karbeta sai da suka fara gaisawa ta sanar mata tare da abdur rahman suke yazo ganin abdallah,idanu ta zaro tana dariya "Iyeee,kice da tare da larabawan madina kuke kada kai ace har an gama karatun?" Cikin murmushi bahijja tace "A'h,yadai samu hutu ne yace tunda ya shekara bari yazo yaga gida" "Da kyau.....zainab zoki dauki carfet ki shimfida masa a zaure(soro)"ta fadi tana murmushi tare da qoqarin miqewa. Tare suka fito da bahijjan saboda abdallahn na hannunta,ji take kamar kada ta ajjiyeshi yaron ya shiga zuciyarta sosai. Tun kafin ta qarasa soron wani kalar qamshi na daban ya ziyarci hancinta,zaune yake ya hakimce kan carfet din,yana sanye da shadda ruwan siminti sai qyalli take,kansa saye da baqar hula,baki ta riqe tana murmushi,sosai abdur rahman din ya sauya,ya zama wani babban mutum lokaci daya,kai bakace abdur rahman din dake tayata zama bane sanda tana amarya mai qarancin shekarun da basu gaza goma sha uku ba,ya zama mai cikakkiyar kamala da haiba,fatar nan tayi fresh da ita,duk yadda taso ta zolayeshi da tsokana kamar yadda suka saba sai ta kasa sanda shi yake tsokanarta da iyeeem ba,yarinya ta girma gata da yato ta zama mama,bayan sun gama barkwancinsu kasancewarsa mutum mai yawan son barkwanci sannan ya shiga jajanta mata abinda ya faru tun daga samuwar cikin abdallan zuwa haifeshi,suna tattaunawa yana wasa da abdallahn har bahijja ta gaji ta tashi ta koma ciki wajen zainab ta barsu a nan. Sosai yaron ya masa ya tafi da shi har ya gaza boyewa sai da ya furta,murmushi kawai tayi suka ci gaba da hirarsu a haka mama ta cimmasu,a mutunce suka gaisa tana mamakin ganinsa da sauyawarsa ta tambayeshi mutanan gidan ya amsa duka lafiya ta dubi sumayya "Amma ai abdur rahman ba baqo bane da zaki barshi a soro,maza tashi ka dawo tsakar gida" cikin tsokana yace "Atoh mama na sani ko rowar gidan ake min,ni kuma naga gun hira kuwa har na koma,tunda nayi aboki" hararar wasa sumayyan ta masa tana cewa "Dadinta ai na maka tayi kace a'a tunda mama bata nan nan zaka zauna" ta fada tana shigewa cikin gidan. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 3⃣6⃣ _____________________________ *Bismillahir rahmanir rahim* *huwallazi yuhyi wa yu miit* *sannan shi (Allah) shi yake rayawa yake kuma kashewa* ______________________________        A tsakar gida zainab ta sake shimfida musu wata tabarmar suka koma ciki.        Hira sosai suka dinga yi har da mama,abdur rahman na basu labarin garin ma'aiki madinatul munawwara har aka kirayi sallar magariba,tare suka fita sallar shi da malam da yaya abubakar,koda suka dawo ma bai tafi ba tare suka ci abincin dare sannan ya musu sallama.          Hannunsa dauke da abdallah ya fito daga gudan,bahijja da sumayya na bayansa wadda ta fito don ta dan taka musu,a bakin motarsa sabuwa da ya sauya qirar range rover yaja burki yana duban sumayya "Tsarabar abdallah bata qaraso ba,ko zaki dan rakamu waccan titin dake gabanku naga akwai wami super market na dan masa siyayya kafin su iso?". Kai ta kada tana dubansa " haba sabida dorawa kai wahala,mun yafe duk sanda suka iso ma amsa".kunu ya dan sha yana dubanta "Dorawa kai wahala kuma?,niba babansa bane?,ko kina so kice ba yarona bane?" Baki ta bude tana dariya tare da dubansa tace "Ni na isa in fadi haka,kai matsala ta da kai son girma fa" "Ban kai naso girma ba ko sumayya?" Ya fada cikin wani irin salo da ya sauya yanayin muryarsa idanunsa cikin nata,wanda ya haifarwa da sumayyan rage farashin dariyarta,karon farko da taji duban qwayar idonsa ya mata nauyi,sai ta janye idonta tana cewa "A'ah,ai ko da sakan daya mutum ya girmeka ya girmemaka har abada" dan shiru yayi sannan ya gyara tsaiwarsa yana miqa mata abdallah "Karbeshi yau mun wunar muku,sai kuma gobe idan Allah ya kaimu" ta amsheshi tana cewa "Allah ya nuna mana goben" cikim zuciyarta ta dauka da wasa yake,hannun abdallahn ya bude ya sanya masa 'yan dubu dai dai guda uku yana cewa "Kasha sweet my son" "Habba abdur rahman...." Katseta yayi ta hanyar cewa "Shshshshsh!,ai bake na bawa ba ko?,kuma wai bakijin kunyar fadar suna na haka gatsal?" Galala ta saki idanu ta bishi da kallo "Kunyar kamar yaya?" Ta fada tana dubansa,murmushu kawai yayi ya bude gaban motarsa ya zauna sannan yace "Sai goben ko 'yamma ta?" Murmushi ta saka mamakin abdur rahman din na kuma kasheta "Nice kuma yau 'yammata abdur rahman ga yaro na a hannu?" "Oh,kuma fadar sunan nawa dai kika yi?" Ya tambayeta yana kada kai,shuru ta masa tana zagayawa wajen bahijja ta dubeta "Bahijja ki gaida mama kinji,naga alama wannan yayan naki bayan karatu sa ya tafi qarowa ya qaro yadda ake canjin hali" dariya bahijjan tayi tana amaa mata da zata ji,shima dariyar yayi sannan ya tada motar tasa yayin da sumayya ta shige gida.         Tunda ya shigo da motarsa layin su sumayyan ya hagi tsaiwar wata motar a qofar gidansu,har zuwa yanzu da motar tazo ta wuce ta gefan tashi yana binta da kallo tare da qoqarin tantance waye a ciki,saidai duk qwaqqwafinsa ya kasa gane waye a ciki saboda glasa din motar mai duhu ne,hakanan sai yaji wani abu mai tauri ya riqe masa wuya,rabin 'yar walwalar da ya samu wunin yau ta kau baki daya,a sannu yaci gaba da tuqa motar tasa har ya qaraso qofar gidan ya tsaya ya fito ya samu yaro ya aikashi ciki,ba jimawa yaron ya fito dama sun riga da sun saba duk sanda aka aika akace ana gaida mama to mukhtar din ne kuma sun san me yazo yi,sai halima ko zainab ta kawo masa abdallahnsa,nan cikin mota yake zama da shi su qaraci wasan su sannan yayi horn su fito su karbeshi da abinda ya kawo masa sannan ya wuce,sau tari yakanji sha'awar ganin sumayyan saidai babu wannan damar,rabon da ya ganta ma bazai iya tantance adadin kwanakin ba,tilas yaje danne komai don ya sani a yanzu ta fita a huruminsa.         Yau din ma kamar kullum hakan ce ta kasance,abdallahn nata masa gwalanto saidai bai gane me yake cewa ba biye masa kawai yake,bai wani jima ba ya maida shi ya tafi zuciyarsa na sakutarsa kan motar da ya gani,ya mance cewa a yanzun sumayyan rabon mai rabo ce ba mallakinsa bace   ****    *****   ******  ****           *BAYAN KWANA BIYU*       Tun daga ranar abdur rahman ya maida gidan gurin hirarsa,wani lokaci yazo shi kafai wami lokaci ya taho da bahijja,da yake su biyu Allah ya bawa mamansu,sukan dauki lokaci da sumayya suna hirarsu,yayin da wani lokaci idan ya furta wata maganar sai ta sanya ta a duhu,wani sa'in takan yi murmushi ta alaqanta hakan da girma da abdur rahman din ya sake yi,ya fara zama babban mutum shi yasa yanayin hirarrakinsa suke sauyawa,bata taba kawo komai cikin zuciyarta ba saboda ita din rainon mutum daya ce da mutum daya ta taba gina duniyarta wato mukhtar,ba komai take iya ganewa ba ko fahimta game da wasu baqin al'amura a gun d'a namiji ba.      Sau biyu mukhtar na katarin ganin motar na tasiwa daga qofar gidansu ta fice daga layin,saidai har yau bai samu nasarar gano waye ba,lamarin ya tsaye masa a zuciya,duk da yasan baida hurumin hakan amma zuciyarsa ta gaza daurewa,hakan ne ya sanyashi cin washin zuwa ya tadda ko waye.     Tunda ta fito daga makarantar tasu ta lura yake bin bayanta cikin mota wanda hakan ya matuqar tsorata ta musamman data lura yau unguwar tasu babu yawaitar jama'a,hakan ya sanya ta qarawa qafarta sauri.       Ganin tana neman bace masa ya sanya shi faka motar sannan ya fito ya biyo bayanta,gabanta taga an sha wanda ya hakan ya dan tsorata ta taja baya taba dubansa,matashi ne wanda a qalla zaiyi shekara arba'ain da biyu,dogo ne baqi maras jiki sosai,za'a iya karansa da chaculet colour,babu laifi yana da kyau dai dai gwargwado,kana kallonsa kasan yana cikin rufin asiri da wadata dai dai gwargwado "Assalamu alaikum" ya fada yana murmushi wanda sallamar ta dauke kaso mafi yawa daga cikin tsoron da ya cika zuciyarta,cikin qarfin hali ta amsa masa "Don Allah kiyi haquri,nasan ban tsaidaki a yanayin da ya dace ba,nidai suna na lukman,na gaza daurewa zuciya ta ne shi yasa ni aikata hakan,na lura kamar a darare kike da ni,idan ba zaki damu ba ki bani lambar wayarki sai muyi magana" kamar kuwa ya sani a takuren take,saboda wannan shine karo na farko da ta fara tsaiwa da wani namiji,ga masu shugewa jifa jifa suna faman binta da kallo,hakan ya sanya cikin rudewa ta karanto masa lambar halima don bata da niyyar bashi tata,yayi serving yana murmushi gami da yi mata godiya,bata ko jirayi amsa masa ba tayi gaba da sauri shima ya wuce ya tada motarsa ya fice a layin.         Tun daga nesa take hangowa kamar shine sabe sa abdallah ya zuba mata idanu,sai data qaraso gab da shi ta tabbatar shi din ne kuwa,hannunsa dauke da leda wadda ta tabbatar abdallah ya yiwa siyayya kamar yadda ya saba "Waye wancan?" Ya tari numfashinta ya furta fuskarsa a dan daure ta hanyar riga ta yin magana,dan galala tayi tana dubansa cikin mamaki,sai kuma ta basar ta saki dariya cikin tsokana tace "Bazawari na ne" "Bazawarinki?" Ya tambaya cikin nanatawa har sau uku yayin da ta tsaya tana sake dubanshi "Eh mana" ta fada kanta tsaye,shiru yayi kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya sauya akalar abinda zai fada din da cewa "Ok,muje qofar gida akwai maganar da nakeso muyi" ya fada cikin magana ta gaske yana yin gaba,kamar an qulle bakinta sai ta ja qafafunta ta bishi.       Qofofim gaban motar ya bude ya shiga nashi mazaunin yana dauke da abdallah wanda baiko damu da ganin maman tasa ba,ya wani lafe jikin abdur rahman din yana ta fama da biscuite,dubanta yayi ganin tana tsaye qiqam a waje "Bismillah shigo ki zauna" kafadunta ta daga "Haba,ai kaima kasan bai kamata ba,mu shiga cikin gida kawai ko meye ai ina ga sai yafi dadin tattaunawa ko ba cikin mota ba" "Ai nasan da cikin gidan,amma maganar bata cikin gida bace,idan kuma kina da wani gu da zamu mu tattauna kuma to" kanta ya daure tana mamakin wacce iriyar magana ce haka da yakeso suyi da sai su kadai? "To amma kuma malam fa,idan ya dawo ya ganni cikin motarka" "Indai malam me baki da matsala,na gaya miki hakan da gaske" dan shiru tayi sannan ta sake bude murfin ta shiga ta zauna ba tare da ta maida murfin ta rufe ba,abdallah ne ya soma yunqurin tahowa gunta hakan ya sanya ya miqa mata shi,sai da ta zaunar sa shi sosai ya nutsu a gunta sannan ya soma magana "Sumayya..." Yadda yayi kiranta ya sanya ta daga kai ta dubeshi "Kinsan cewa tun kafin a haifemu Allah ke rubuta mana dukkan wani abubda zai faru da mu har ya zuwa ranar mutuwarmu ko?".kai ta jinjina tana bashi dukkan nutsuwarta " a gaskiya sumayya bazan cuci kaina ko na zalunci kaina ba,sumayya.....haqiqa na ga dukkan wasu halayya na mace ta gari,naga dukkan wasu dabi'u na macen da za'a iya aure ta zama uwar 'ya'ya,na gamsu na nutsu,nagano alkhairai a tattare da ke sumayya,da haka zuciya ta ta fara qaunarki sumayya,zuciyata ta gamsu da ke a matsayin wadda zamu rayu tare,ina sonki ina qaunarki,ina buri ki zama mata ta,ina kuma fatan zaki amince da maganganuna,kin san ko waye abdur rahman sumayya tun ba yau ba,saboda haka mene ne ra'a yinki a kaina?" Dariya dariya ta saki duk da tarin mamakin dake cunkushe cikin zuciyarta "Kai abdur rahman,Allah ka iya wasan kwaikwayo,kyanka dramer" "Sumayya!" Ya kira sunanta da dan qarfi wanda shi ya sake jan hankalinta gareshi "Dubeni da kyau!,kinga wasa a idanu na da fuska ta bare kalamaina?,wallahi billahi babu wasa cikin lamari na,da qarfina nazo gareki sumayya ko yau kika amince a shirye nake da a daura min aure da kai".       Sosai maganar ta daki qirjinta,sai ta shiga kada kai kamar qadangaruwa,da qyar ta qwaci kalmar " haba abdur rahman,ka rufamin asiri mana,ka manta kai waye ne?,kai dan kawun mukhtar ne fa,ko ka manta mukhtar kamar yaya yake a gare ka?,baya ga haka ma so kake duniya ta zage ni?,nifa bazawara ce har da yaro na,kai kuwa matashin saurayi ne da ko auren fari baka yi ba"murmusawa yayi yadda yaga tsantsar tashin hankaki kan fuskarta kamar wadda aka ce za'a yanka,sai maganarta ta biyu data bashi dariya,dududu ita din ma nawa take,'yammata da yawa wasu masu shekaru irin nata ma ba'a fara zancan aurensu ba,wasu kuwa sai a lokacin suka isa auren ma,shekara ashirin kacal da take da su din,idan ba ita ta fada ba babu mai yadda tayi auren fari ma bare haihuwa,kai ya kada da ya tuna ita din farin shiga ce,baki daya ta rude,dole ya bita a hankali har ta sake da shi "Dukka wadan nan basu isa hujjoji a gareni ba sumayya,jeki gida ki nutsu kiyi shawara,na baki nan da sati guda,amma kada ki manta ni din ina sonki kuma in sha Allahu sai na aureki". Har wani tsoro ta dinga ji haka taja qafafunta da sukayi sanyi tamkar an buge mata su ta fita daga motar ta rufe masa ita,sai ta kasa motsi har yaja motar ya soma fita a layin tana jin motar da idanu.        Horn din da aka danne shi ya sanya ta dawowa daga karanta wasiqar jakin data tsaya yi a qofar gida,abdallah na kafadarta duk ya bata mayafinta da nashi bakin da burbushin biscuite amma sam bata ma ankara ba,idanunta ta juya zuwa gabanta,mukhtar ne zaune cikin motarsa yana dubanta,fuskarsa a hautsine kamar wanda aka kikkifawa mari,a hanzarce ya fito daga motar ya zagayo zuwa inda take yana fidda wani huci " waye waccan?"ya tambaya yana mata nuni da motar abdur rahman dake gab da qulewa zuwa kan babban titi,sai tabi inda yake nunin da kallo kamar bata san motar da yake nunawa din ba,mamakin tambayarsa da dalilin fusatarsa ya taru ya sake daskarar sa qwaqwalwarta,cikin qarfin hali tace masa "Gurina yazo,sai me?", mamaki ya kamashi,shi sumayyan ke gayawa haka,zuciya ta taso masa iya wuya,hannu yasa ya fincike abdallah daga hannunta har ya dan tsorata ya tabe baki zai sa kuka,sai ya rungumeshi a aqirjinsa,yayi luf kuwa abinsa don tuni ya jima da gane shi,akwai sabo da shaquwa sosai tsakaninsu,cikin tsantsar bacin rai yace da ita " sai me kuwa?,ba damuwata bace,saidai ki sani bashi da alaqa ya yaro na,kiyita fitowa gunsa amma badai da yaro na ba"sai ya juya ya bude motarsa ya shige ya tada ta ya bar layin.       Kuka ta saki ta shige cikin gida da gudu wanda ya ja hankalin mama dake bakin qofar madafi zaune tana gyara kwanukan abincin daren malam,tsaye ta miqe tana tambayarta lafiya "Mama ya karbe abdallah ya tafi da shi" "Waye?,waye ya tafi da shi" ta tambaya cikin rudewa "Mukhtar mana" ajiyar zuciya ta saki hankakinta na kwanciya,tayi zaton wani ne ma daban,harara ta  balla mata "Sai aka ce miki saceshi yayi?,ko ce miki akayi bazai dawo da shi ba?".kai ya gyada " bazai dawo da shi ba mama"harararta ta sake yi "Maras kunya,idan bai dawo da shi din ba sai me,ba ubanshi bane,ke yanzu akan dan farin kika tsaya kina min kuka?,matsa ki bani guri"janye jikinta tayi ta shige daki tana ci gaba da matsar qwalla,ta yadda lallai har yau akwai sauran quruciya akan sumayyan,ko tsabar tabara ce oho.      Har maman ta gama abinda take bata iya yin shiru ba,ji take kamar ta fita ta karbo yaronta,ganin bilhaqqi da gaske kukan take ya sanya maman binta daki ta kwantar mata da hankali,ita dai jin maman take kawai,gani take bazai dawo mata sa shi ba,da qyar ta fita ta dauro alwalar sallar magariba ta dawo ta tada sallar tana kasa kunnen ta inda abdallanta zai bullo,abun sai ya hadu ya dagule mata,ga zancan abdur rahman ga kewar yaronta. _tofa masu karatu,nasan yanzu zamu fara raba team,ga team ABDUR RAHMAN,ga MUKHTAR ga kuma wata sabuwa LUKMAN_ *MRS MUHAMMAD CE*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 3⃣7⃣ _____________________________ *Bismillahir rahmanir rahim* *wa'iza sa'a laka ibady anny fa inni qarib,ujibu da'a watad da'i iza da'aan* *_idan bayina suka tambayeka game da ni kace ni makusanci ne(ina kusa da bayi na),ina amsa addu'ar mai addu'a idan ya roqeni_* _______________________________       Har ta idar sallahr isha'i babu abdallah ba mukhtar,sai ta rushe sa kika ganin qarfe takwas na neman gotawa,komawa tayi ta jingina da jikin katifa tana maida numfashi tare da sakin ajiyar zuciya.         Kamar daga sama taji muryar mukhtar din kamar daga can soro suna magana da yaya abubakar,sai ta miqe zumbur ta zauna tana saurare har zuwa sanda abubakar din ya daga labulen qofar dakinta ya leqo "Kije ki karbi abdallah,wai yau ni zaiwa rashin m yaga babansa yaqi yarda na karboshi" ya qarashe zancan yana sakin labulen,tana ji yana ma mama qorafi tana musu dariya,zumbur ta miqe kamar mai jira,dama tun hijabin da tayi sallah shine a jikinta bata cireshi ba.        A soron ta tadda su tsaye yana rungume da abdallan,tana zuwa ta miqa hannu alamar ya bata shi,banza yayi kamar bai gane me take nufi ba,ya dubeta fuskar nan a dinke tsaf "Duk randa kika sake gigin fitowa gun bazawarinki da yaro na,idan har na tafi da shi ya tafi kenan har abada" ya qare maganan sannan ya miqa mata shi wanda tuni bacci ya fara dibansa,hannu tasa cikin azaba ta karbeshi,cikin hanzarin ta shige gida kamar wanda zaice mata dawo da shi,binsu yayi da kallo har suka shige,ya jima tsaye cikin soron ba tare da ya iya tafiya na a haka abubakar ya cimmasa sannan sukayi sallama ya tagi,har yanzu bai cimma burinsa na ganin wanda ke zuwa gun sumayyan ba,amma babu shakka ba zai guahe ba har sai ya gano waye.         Dare ya fara miqawa amma tana kwance idanunta biyu,abdallah na jikinta yana ta barcinsa,a haka halima ta daga labulen dakin ta shigo "Yaya sumayya wani ne keta kira tun dazu yana cewa sumayya yake nema,nace masa ba ita bace amma yace ita ta bashi number din " "Wani?" Ta tambaya cikin mamaki,don har ga Allah ta mance shaf da luqman. "Eh,yace dazu da yamma" sai a lakacin ta tuna da shi,don baki daya abdur rahman ya hargitsa tunaninta,maganar sa ta mata girma,ga mukhtar shima da yaso hautsina ta,kafin tace komai wayar ta sake ruri,haliman ta kalleta "Yaya gashi,shi ya sake kira" tsaki ta dan ja tana ganin baiken kanta tun farko da bata bashi lambar bogi ba,kanta ta maida kan filo sannan tace "Kice da shi nayi bacci" "Amma yaya....." Haliman taso yin qorafi saboda ba sabonsu bane yin qarya "Don Allah ki fita ki bani guri ki gaya masa yadda nace din ko kisan me zaki gaya masa" ganin sumayyan ta harzuqa har haka wanda basu saba ganin hakan tattare da ita ba ya sanya ta juya ya fice ba tare data amsa wayar dake ta faman kururuwa ba. *****     ******    *******        Cikin kwanakin da suka biyo baya gaba daya haka take wuni sukuku,ga maganar abdur rahman dake mata amsa kuwwa a kai,gefe guda kuma ga luqman daya matsanta da kiran waya ba dare ba rana,duk da ko daya bata taba amsa wayarsa ba amma hakan bai sanya ta gajiya ba.         Gani take baki daya abdur rahman ta shigo da maganar ne don ya dagula lissafinta,domin shi kansa yasan yana magana ne kan abinda bashi yiwuwa,ta yaya zata aure shi bayan ta auri dan uwansa?,ta yaya zata yadda ta sake maida kanta cikin ahalin da bata da farinjini ko sau daya a gunsu?,ahalin da tasha wahala tasha jinyar zuciyarta duk a kansu,ahalin da basu ganin alkhairi tattare da ita?,duk a ture ta wannan ma yaushe zata aure musu abdur rahman?,matashin saurayin da ko auren fari baiyi ba?,sam bata jin zata iya wannan abu koda a mafarki ne ballanta na kuma a gaske.         Ranar da ta fara amsa wayarsa suna zaune ne baki dayasu a falon maman suna cin tuwon dare wayar haliman ta sake tsuwwa karo na wajen uku kenan,mama ce da ringing din wayar ya soma damu ta dubi halima "Wai halima idan ba zaki daga wayar nan ba ki kashe ta mana haba" "Mama bani ake kira ba yaya ake kira,yau kusan kwana hudu kenan wlh taqi ta daga ko sau daya" sai maman ta juya tana suban aumayya wadda ta cika tayi fam sabida halima ta gayawa maman "Ke sumayya wake kiranki" cikin murya mai kama da shagwaba wanda sau tari idan ranta na bace bata aon magana haka yanayin muryarta ke komawa tace "Wani ne nima mama ban sanshi ba"hade rai maman tayi sannan tace "Ha'aa,baki sanshi ba kamar yaya?,ina cewa ke kika bashi lambar ko?" Dan jim tayi sannan ta gyada kai "To maza bana son shashanci karbi ki amsa kirab,na gane take takenki sarai,kuma kinfi kowa sani malam ya fara maganar baiga kina magana da wani ba,kinsan halinshi sarai tun da can baya ma shi ba mai barin yara su girme a gabanshi bane,su kansu su halima rashin tsayayye ye ne ya sanya har suke gida iwar haka" gabanta ya fadi fargaba ta lullubeta,wani irin aure kuma?,duka duka mutuwar auren nata da bai wuce shekara biyu ba?,tilas ta karbi wayar ta miqe ta shige daki.         Sun dan dauki lokaci kan wayar yana qoqarin shigar da kansa a gunta,ba yabo ba fallasa ta amsa masa duk wata magana da yayi mata,da qyar ya shawo kanta ta bashi lambarta,yayi murna da godiya sosai tare da alqawarin zai kirata gobe,tabe baki tayi tana bin wayar da kallo bayan sun gama wayar,sai ta miqe nan saman katifa tayi kwanciyarta taqi komawa falon don koda ma mama ta sake baro wata maganar.    *****    ******     ******      Kullum ta Allah baya fashin kiranta,koda kuwa bata dauka ba zai mata tex,qoqarin kafa kanshi yake sosai da gaske,duk da gaya masa ita din fa ba budurwa bace har da yaronta,yace babu komai shi hakan ma yake so,a haka har sati dayan da abdur rahman ya diba mata ya cika,satin guda cif bai sake nemanta ko takowa gidan ba har cikar wa'adin kwanakin.        Tun safe take addu'ar kada Allah ya dawo da shi,a haka har lokacin tafiya makaranta yayi ta shirya ta tafi tare da abdallah wanda yau ya tubure sai ya bita.       Yau sai kusan biyar suka taso,tun daga qofar gidan ta hangi motarsa,a hankali ta dinga takawa jikinta a sanyaye har ta isa gab da motar,qofar mazaunin direba a bude take alamun mamallakin motar yana ciki,tuni abdallah ya gane motar waye,ya zame daga jikinta yayi wajen motar yana kiran abba,hankalin abdur rahman yayo wajen ya waiwayo yana murmushi sannan ya fito ya dage shi sama ya cafe suna dariya,sanye yake da yadi irin na maza blue black,hula da takalminsa sau ciki duka baqi,yayi kyau sosai. Ya sauke idanunshi a kanta yana kallonta "Yau kam kin dade,kinsan tun nawa nake nan ina jiranki?" Kai ta girgiza ba tare da tace komai ba,yatsun hannunsa ya daga guda hudu ya nuna mata,sannan ya dora da fadin "Shine yau kika dauke abokin hirar ko?" Kai ta sake kadawa sannan tace "Shine ya nace yau sai ya biji,nima bana son tafiya da shi" "Mukam muna maraba da shi ko yaushe,shiga ki kintsa kafin naje can qasan layinku na dawo na baki minti talatin" "Amma dai da ka shigo ciki ko?" "Amma dai kinsan gunki nazo ko?"ya bata amsa da salon yadda tayi tata maganar,ta lura jan magana yake ji saboda haka ta sanya kanta gida tana fadin "A dawo lafiya".        Salla kawai tayi wadda lokacinta ya kubce mata,ko abincin ta kasa ci tanaa zaune tana nazarin hanyar da zata bi abdur rahman ya janye zancansa salin alin ba tare da an kai ruwa rana ba,don gaskiya bata jin zata iya maida kanta cikin familyn su mukhtar,an gudu ba'a tsira ba kenan,ko kuma tsugune bata qare ba?,cikin haka zainab ta shigo dakin ta gaya mata taje ya abdur rahman na waje ta karbi abdallah.       Kamar wancan karon wannan ma haka ya tilasta mata shiga motar tasa,shuru ya ratsa motar na wasu daqiqu ba wanda ya sake cewa uffan bayan abdur rahman ya gama jaddada bayanansa a gareta "Da farko abinda zan fara cewa shine na gode na gode matuqa,na yaba da qaunata da kace kana yi,har ka nuna sha'awar zamantowa abokiyar rayuwarka duk da ban cancanci wannan darajar ba,amma abdur rahman kayi haquri,bazan iya aurenka ba,saboda wasu dalilai wadanda ni da kai duka mun sansu wasunsu kuma ni da ubangiji na ne kawai muka sansu" kai yake jinjinawa yana dubanta sannan yace "Ban gamsu da baya nanki ba ko kadan,babu wani abu da zai sanya ni janyewa daga batun neman aurenki sumayya,ina sonki babu wanda zai hanani"so take ya fahinceta bilhaqqi don su bar maganar sun wuce gun,sai ta sake fuskantar sosai wani abu na taba zuciyarta na daga abubuwa da suka faru da ita a baya " ta yaya abdur rahman kake so na sake komawa cikin danginku,bayan kaima kana daya daga cikin mutanan da zasu shaidi irin rayuwar da nayi a cikinsu,ya kake so ka sake maidani rayuwar baqincikin da nayi bankwana da ita?,ko kuwa zaka sauya dangi ne saboda zaka aureni ni sumayya 'yar gwal,ko ka manta waje mijina na baya,ka manta alaqar da take tsakanin ku,don Allah abdur rahman muci gaba da mutunci mu ajjiye zancan soyayya a gefe"ta qarashe maganar tsohon mikin dake zuciyarta na taso mata,sai ta sanyo qafafunta waje ta fito daga motar,da sauri shima ya fito ya zagayo inda take tsayen,kafin yace mata komai suka ji tsaiwar mota,waiwayawa sukayi dukkansu don ganin waye.        Mukhtar ne,tun yana cikin motar tasa yake qarewa motar kallo,babu shakka wannan motar yake tawan gani a qofar gidan su sumayyan,kenan yau zai ga waye mamallakinta zaiga wake zuwa gunta,amma idan idanuwansa na nuna masa dai dai kamar abdur rahman yake gani tsaye tare da sumayya,to meye yake haka a gidan?,meyw hadinsu?,shine mai motar da yake gani kullum na ficewa daga layin?,don samun amsaoshin tambayoyinsa sai ya balle murfin ya fito bayan ya kashe motar ya nufosu idanuwansa a kansu zuciyarsa na azalzala tare da ayyana masa wani abu wanda baya fatan kasancewaraa.         Sallamarsa ita ta katse abdur rahman daga kallon sumayya da tuni idanunta suka cika da qwalla,sannan suka katse shi dag fadar abinda yake shirin fada,dukkansu waiwaya suka yi suka dubeshi,fuskar abdur rahman din dauke da murmushi ya miqawa mukhtar hannu yana fadin "Ah,ya mukhtar kai ne?" Baiqi miqa masa nasa hannun ba suka yi musabaha yana fadi tare da tsareshi da wani irin kallo "Eh,ya kawu da sauren mutanen gidan" "Duka lafiya alhamdulillahi" ya fada yana sakin hannun mukhtar din sannan ya juya ga sumayya "Ki nazari a nutse,kada ki ruda kanki,kada ki cuci kanki ki cuceni,gobe in sha Allah zan dawo" ya fada yana juyawa zuwa wajen motarsa,dukkansu ita da mukhtar din suka yi masa rakiyar idanuwa,saidai kowa da abinda ke kai kawo cikin zuciyarsa,ya bude motar ya shiga bayan ya bawa abdallah 'yar madaidaiciyar baqar leda cike da biscuite da choculet ya saukeshi ya tada motar ya wuce. Busy kuyi haquri da wannan *mrs muhammad ce* *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 3⃣8⃣ ____________________________ *Bismillahir rahmanir rahim* *wala taqulanna li shai'in inni faa'ilun zalika gada,illa ay yasha Allah,wazkur rabbaka iza nasit* _kada kace ni zan aikata wani abu gobe,face sai ubangijinka yaso,ka tuna ubangijinka idan ka manta_ ______________________________         Wani abu ne ya tokare masa wuya yana jin wani irin bacin rai na taso masa,sai yayi qoqarin dannewa ta hanyar daukar abdallah da ya nufo gunsa kai tsaye yana fadin daddy daddy,motsawa sumayya tayi don shigewa cikin gidan cikin hanzari ya sha gabanta "Me abdur rahman ke zuwa yi gunki?" Idanunta ta dora a kansa kanta tsaye tace "Alheri" "Alheri wanne iri?,kada kice min gonata yake son shigowa?"wani irin kallo ta masa "Yaushe ka fara noma?,dama kana da gona ne?,alheri kuma duka alheri ne babu wani banbanci" ta fada tana rabeshi zata wuceshi ranta a bace,baisan ya riqo gefen hijabinta ba hakan ya sanyata waiwayowa tana dubansa a mamakance "Me yasa kike cutar da ni haka sumayya me na miki a rayuwa da zafi?" Ya fada zuciyarsa na zafi yayin rauni ya bayyana qarara a fuskarsa "Cutarwa?,ni nake cutar da kai ma mukhtar!" Ta fada tana nuna qirjinta da yatsa cikin mamaki,sai ta juyo baki daya tana dubansa sosai "Bance ka cutar da ni ba mukhtar ni da ka saka saki uku ina kwance?,bance ka cutar da ni ba ni da ka yanke min hukunci kan zato da zargi,ka yanken hukunci ba tare da kayi bincike ba?...." "Wanne bincike sumayya bayan ba labari aka bani ba,na gani da ido na,sannan bincike na likita ya sake tabbatar min da kinsha din wanne bincike kike da buqata nayi bayan wannan" a kaikaice takw dubansa sannan tace "Ok ko?,to shikenan,yayi kyau hakan ai,amma shawara zan baka ka fita daga dukkan harkoki na,ko da maza dari zaka ganni da su wannan ba damuwarka bane,tunda dai a yanzu ba qarqashin ikonka nake ba,gashin kaina nake ci sai ka shafamin lafiya" tana gama maganar ta juya tayi shigewarta cikin gida ta barshi da abdallah.      Binta yayi da kallo,taushe sunayya ta koma haka,yaushe bakinta ya bude da magana haka?,saidai batayi laifi ba yana ganin baiken kansa,tabbas ba shakka gaskiya ta fadi yanzun ita din ba huruminsa bace,baisan me ya sanya ya shishshigewa lamarin rayuwarta har haka ba,jiki ba qwari ya koma mota ya dauko siyayyar abdallah ya riqoshi har bakin qofar da zata sadaka da tsakar gidan ya ajjiyeshi ya wuce,cikin mota yana tuqi yana tunanin yadda zai raba kansa da shiga lamuranta,don bisa gaskiyarta take,wani sarawa kansa yayi wanda hakan ya sanyashi yin parking motaraa gefan titi ba shiri,ya dauki a qalla sama da mintuna talatin kafin yaci gaba da tafiya.    *****    *****    *****     Duk yadda taso abdur rahman ya fahimci abinda take nufi yaqi fahimta,sai ta tattarashi ta janye masa jiki,sau tari takan qi dawowa daga makaranta akan kari,tana kuma dawowar lokacin sallar magariba ne,daga nan kuma suna zama karatu da malam wanda ya sanya musu wasu litattafan addini wanda suke hadda ce wasu abubuwa a ciki,sam ta daina bada wani gaf ko wata dama da zasu kadaice har suyi magana,idan ana tare cikin jama'a zasu yi magana da shi kamar kowa.       Ta bangare daya kuwa luqman shima ya matsa lamba,tilas ta bashi dama yazo gidan sau daya,a ranar malam ya dawo ya ganshi suka gaisa,saidai malam din baice mata komai ba kamar yadda ta zata,hakanne ya sanya ta saki jiki har ta sake bashi wasu damammakin yazo wai koda hakan zai sanya abdur rahman ya janye daga qudirinsa,saidai duk da hakan babu abinda ya girgiza shi,har mamaki abun ke bata,cikin lokaci qarami ya sanyata ta saki jikinta da shi,mutum ne mai barkwanci da yawan bada labarai,ko bata son magana sai ya sanyata dariya.        Abinda bata sani ba malam din na sane da komai,bata san da hakan ba sai ranar da aka kai kudin auren abubakar da saka rana wanda baki daya aka tsaida watanni biyu,washegarin ranar malam din yayi kiranta falonsa,bayan ya kammala duka abubuwan da yake ya dubeta "Am sumayya,nasan cewa kinsan tsarina da al'ada ta gidan nan,sannan alhamdulillah kin san mutuncin mace dakin mijinta,baki da inda yafi nan daraja,dukkan wani abu da ya faru a baya mu ajjiyeshi gefe haka Allah ya tsarama rayuwarki,cikin KUNDIN QADDARARKI yake,babu wanda ya isa ya goge miki ko ya kautar miki da shi" "Haka ne malam" ta fada kanta na duqe zuciyarta ba bugawa kamar zata bullo,addu'a take kada Allah yasa malam ya bullo mata da zancan da bata da buqatar jinsa a yanzu "Sumayya,yaron nan abdur rahman yazo guna ya gabatar min da kansa a matsayin manenin aurenki,to amma kasancewarki bazawara a yanzu addini ya baki damar zabawa kanki mijin aure ya sanya nace sai na tambayeki naji mene ne ra'ayinki,kada ki zalunci kanki a yanzu kina da dama,sannan zaman aure zama ne bana yau ko gobe kawai ba,zama ne na har abada". Wani tashin hankali ne ya rikito mata,abubuwan da suka dinga faruwa da ita zamanin tana auren mukhtar tsaf suka dinga dawo mata,a hankali ta bude bakinta muryarta na rawa "Kayi haquri malam,abdur rahman dan uwa ne ga mukhtar dan wan babansa ne nasan kasan haka malam" murmushi ya saki "Sumayya,sumayya kenan,wannan duka ba abun damuwa bane tunda dai aure ya halasta a tsakaninku ba haramun bane" tashin hankali ta fada cikin zuciyarta,'yan uwan mukhtar fa sune dai 'yan uwan abdur rahman,ba'a canzawa tuwo suna "Malam,ina tsoron sake kasancewa da ahalin su mukhtar...." Sai tayi shiru ta kasa qarasawa,shima shirun yayi yana nazarin maganarta,tabbas sumayya yarinya ce mai matuqar zurfin ciki,a iya zamanta na aure bazai iya fadar ranar data kawo matsalarta ba,saidai idan an fahimta a maganta mata. "Ke kike da zabi a hannunki ai,ba zan miki auren dole ba" "Malam,ina so abdur rahman ya janye daga qudurinsa,bana son sake shiga ahalinsu" ta fada zuciyarta na raurawa muryarta na rawa "Shikenan zancansa ya wuce,sai ki fidda miji ina son hada aurenki da na yayanki abubakar idan ta kama har da su halima baki daya" "Amma malam ba......." "Sumayya,bana son qorafi ko wata magana,kinsan ba zaiyiwu kici gaba da zama a gida ba,shekara nawa,shekara daya ana gab da cika ta biyu" shuru tayi don tafi kowa sanin waye malam,amma ina mafita meye mafitarta?, "Sumayyan luqman fa?" Taji ya jefo mata tambayar wadda ta sanya dago kanta ta dubeshi,murmushi ya kuma yi yana dubanta "Mamaki kike yadda na sanshi?,ya fara zuwa gunki ba da izini ba ya karya doka ta,hakan ya sanya nayi bincike a kansa,na samu gamsassun bayanai a kansa,mutumin kirki ne bakin gwargwado" sai ya dan ja fasali yana dubanta kafin yaci gaba da cewa. _yauma dai amin uziri_ *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 4⃣0⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *innal laha la yugayyiru maa bi qaumin hatta yugayyiru ma bi'an fusihim* _haqiqa Allah baya canzawa mutane(halin ko yanayin da suke ciki)har sai sun canza da kansu_ ______________________________         Ungawa ce mai matuqar kyau da tsari,akwai nauikan mutane daban daban cikinta,saidai akasarin mzauna cikinta din masu hannu da shuni ne da kuma masu rufin asiri ko wadanda suke ma'aikatan gwamnatin tarayya ta basu gida su zauna kamar su anty dije.        Sai da mansur ya fidda kayanta baki daya ya shigar mata cikin gidan ta masa godiya sosai sannan ya ja motarsa ya shige wani katafare kuma hamshaqin gida dake kallon nasu.          Dukka yaran gidan na nan kasancewar ranar qarshen mako ce,laila ita ce babba,sai hafiz mai bi mata,sannan khalifa sai nasir sai auta amina minal,a qalla laila zata yi shekaru goma sha hudu,ita ta fara ganin shigowar sumayya falon,ihu ta sanya wanda ya janyo hankalin 'yan uwanta ta nufi sumayya ta rungumeta,haka sauran suka baibayeta wanda ya janyo musu faduwa a qasa dukansu suna dariya,da qyar ta samu suka dagata suka koma saman kujera sannan ta soma tambayarsu anty dijen don bata ji motsinta ba,dining laila ta nuna wa sumayyan tana cewa "Kinga yaya sumayya can duka abincinki ne,tun dazu mama ke jiranki baku iso ba har ta gaji ta shiga gidan daddy prof,amma bari naje na kirata" ta fada tana yafa dan yalolon mayafinta tayi waje da sauri,khalifa sumayya tasa ya fara nuna mata toilet ta shiga tayi alwala,tana kammala alwalar anty dije na shigowa "Sai yanzu?,gaskiya kunyi nauyi a hanya kamar wadanda suka hau motar haya inji hajiya bilki" murmushi sumayya tayi tana duban anty dije wadda ta sake gogewa bisa dukkan alamu zaman garin ya karbeta matuqa,ta kuma zama 'yar gayu ita da yaranta baki daya "Wallahi anty sai da muka biya kasuwa muka karbo wasu kaya sannan har mun dau hanya wani oga ko yallabai ya maida ku zoo road karbo dinki" "Eh inaga man ne dinkunan su'ad ce,maza yi sallar kizo kici abinci kafin mu zauna hirar yashe gamo" ta fada tana sanya su laila dauke akwatunta zuwa wani daki da aka tanada saboda baqi irinta.       Sai da taci ta qoshi sannan suka baje a falon ana hiran yaushe gamo,kusan haka suka qarar da wunin ranar,ko da malamar lesson din yaran ma tazo guduwa sukayi suka qi zuwa sai tafiya tayi,da dare ma yayi da qyar suka tafi dakinsu don cewa sukayi tare da sumayyan zasu kwana,saida anty dije ta korasu saboda tana son suyi zance,sosai suka sake kuwa don mai gidan ta baya nan sun tafi semina lagos,sosai anty dije ta sake kwantar mata da hankali tare da bata shawarwari ta rufe da fadi cikin sigar tsokana "Duk da nasan sumayyan tawa zuwa yanzu ta fara girma,hankali ya fara zuwa mata" itama dariya tayi,sai wajen sha daya da rabi sannan ta fita ta barta,to nan din ma lukman bai barta ba da hira sai data ce tana jin bacci sannan yace "Ki kula min da kanki to na baki amanar kanki my dear kinji"ajiyar zuciya ta saki sannan ta amsa masa ta katse kiran,taso kiran halina taji ya abdallah yake,amma ganin dare yayi nisa ya sanyata ta haqura ta barwa gobe,duk sai taji tana kewar yaron nata.    ******     ******     ******       Kwanakin da tayi a garin kwanaki ke da suka yi mata dadi sosai,kullum yaran na nanuqe da ita suna hira,sauqin abun sun gama jarabawa hutu kawai suke jira,wani lokaci da yammaci anty dije kan debe su da motar mai gidan da ya barta a gida ta kaisu park su dan sha iska suyi ciye ciye su dawo,hakan na yiwa sumayya dadi,lallai ko yaya ka motsa daga wani gu zuwa wani gu zaka samu sauyi zuciyarka zata yi dadi.         Duk wani abu da ya kamata a yiwa amarya anty dije da kanta ta yiwa sumayya,cikin kwana goma ta hadata tsaf.        Ana ya gobe zasu koma kanon laila na kwance kan cinyar sumayya sumayyan na tsefe mata kitsonta zasu wankin gashi da yamma anty dije ta fito ta dubesu "zan dan shiga gidan daddy prof zamuyi sallama da su,Allah baiyi da ni za'a yi sunan nan ba"sumayya ta daga kai ta dubi anty dije " au haihuwa akayi halan?" "Sai yau zaki tambaya kenan,kwana na nawa ina leqa su amma baki taba karar ki shiga ku gaisa da mutanen ba,direban gidan ya dauko ki daga kano fa,surukar gidan ce ta haihu" murmushi sumayya tayi "To ai ban sansu bane anty" "Ni ai na sansu kuma gashi na gaya miki,mutanen akwai tsabar mutunci da karrama mutum,duk yadda Allah ya musu tsabar arziqi amma basu raina na qasansu,mai gidan bakiga yadda ya dauki abban khalifa ba kamar dan cikinsa,su khalifa kuwa ya maidasu tamkar jikokinsa" jinjina kai sumayya keyi sannan tace "Allah ya saka musu da alkhairi,kice ina musu barka" "Zasuji tunda ba zaki din ba" inji anty dije ta fice tana mita sumayya ta bita da dariya.        Basu jima da kammala tsifar ba anty dijen ta dawo hannunya dauke da baqar leda,ta cillar kan cinyar sumayya "Da baki iya zuwa gaida mutane ba gashinan haj bilkisu tace na kawo miki kiyi fitar biki,ta yaba da zabin leshin ki wai kin iya zabar kala,ashe tare kuka shiga shagon da mansur din". Baki ta saki sanda ta fiddo leshin taga daya daga cikin wadanda suka siya dinne "Anty kinsan kuwa nawa ne farashinsa duk guda daya?". Dariya anty dijen tayi "Hmmmmm,bakisan mutan gidan bane sumayya,kinga ku tashi ku shirya ku wuce wankin kan nan kada dare yayi muku hanya"ta furta tana miqewa ta nufi kitchen.    ******    *******    *******       Sanda suka isa kwanaki biyu sukayi saura a daura aure don babu wani event da sumayyan ta tsara yi,yaya abubakar ne kawai zaiyi walima bayan an gama daura aure.        Kusa awa guda kenan da shigowarta gidan amma bata ga wulgawar abdallah ba,tun tana kawaici bata tambaya ba har sai data magantu "wai nikam ina abdallah ne?" Maimakon maman ta amsa mata sai tace da ita "Kije malam nason magana da ke" hakanan taji jikinta bai bata ba,ta miqe ta zura hijabinta ta fice.       A ladabce ta gaisheshi ya amsa yana tsokanarta abuja ta karbeta,sai ya bata kunya ta sunkui da kai tana murmushi yayin da tausayinta kuma ya darsu a zuciyar malam din "Sumayya maganar da zamuyi da ke nasan ba zata miki dadi ba,domin raba da da uwa sai Allah,saidai babu yadda muka iya,bayan tafiyarki mukhtar yazo ya karbi yaronsa...." A firgice ta dago ta dubeshi muryarta na rawa idanunta na fidda ruwan hawaye "Amma malam me yasa zaimin haka,rabamu ken......."kaaa qarasawa tayi tayi qas da kanta " kiyi haquri sumayya,shi ya fiki a haqqu da shi,sannan ya riga da yace baiso yaron yayi zaman a golanci gidan wani kamar yadda shima yayi,kiyu haquri nasan ba wai ya rabaku bane na har abada saboda yadda yazo mana bada nuna isa ko qarfa qarfa bane,abinda na lura shine bazai iya jurar rashin ganin yaron bane,tunda idan har kika tafi da shi bashi yiwuwa ya dinga binki gidan mijinki da sunan yazk ganin dansa,kiyi haquri babu komai ai kuna tare,na tabbata za'a dinga kai miki shi"malam ya fada cikin tausasawa. Haka malam din ya dinga lallashinta yana bata kalamai har ta samu ta danji sauqin zugin zuciyarta,saidai abinda take ji na game da kewar yaron har yau bai sauya ba.        Data koma daki taga sauran kayayyakinsa kasa ci gaba da daurewar tayi,ba shakka raba da da uwa ba qaramin abu bane,shi yasa aka ce ko mutuwa tana shakkar idon uwa,yaya wadanda suka rabu da 'ya'yayensu suke ji rabuwa ta har abada?,ashe da sauqi ita tunda yana nan cikin duniyarta kusa da ita amma duk da haka ta gaza daurewa,kuka tayi mai yawan gaske wanda shi ya haifar mata da zazzabin da ciwon kai mai tsanani har ranar da aka daura auren,haka nan aka tattarata aka kaita dakinta tana mai ci gaba da kuka mai qunshe da abubuwa iri daban daban      **** *9:30 pm*  *****       Lukman Bashir shine asalin sunansa,haifaffen garin kano cikin qaramar hukumar kano municipal,yayi karatunsa iya N.C.E sai ya fada kasuwanci gadan gadan,mahaifiyarsa hajiya kubra shi kadai tallin tal ta haifa,hakan ya sanya ta dauki so da qauna da kulawa ta dora masa,wannan shine dalilin da ya sanya duk lokacin da yayi aure ta fuskanci yana mutuwar son matar take rabasu don wai ba zata bari a mallake mata yaro ba tana kallo,kasancewar gidansu daya part guda yayi mata da ya tashi ginin gidansa,a haka a haka ta sanya lukman ya rabu da mata kusan hudu kenan duk da cewa yana dacen matan aure masu matuqar haquri da biyayya saidai ita sam bata gani,haquri da biyayyar da sukewa lukman din ita ke jawo musu qauna gunsa,amma ita gani taje tsabar asiri ne matan suke yi,sam matan basu da sukuni,hatta zanin daurawa idan zai musu ita ke karbar kudin ta siyo ta bada adinka musu ita kuwa sai wanda ta zaba zata sanya,hakanan duk cikin matan da yake aurowa mutum daya ce ta haihu da shi don na wani dadewa take bari suyi ba,ita din ma a gidansu ta haife sai da ta yaye hajiyan tasa aka karbota,'ya mace ta haifa wadda ake kira da nuwaira.        Hausawa suka ce alhaki kwikuyo ne,a irin haka ne Allah ya hada lukman da KARIMA gogaggiya mai idanu a tsakiyar kaa wadda ita ta haifa masa yara uku dukka mata zaitun marwa da radiya,da fari kariman lumbu lumbu ta yiwa hajiyan har ta saki jiki da ita,sannan daga bisani ta sanya gaba daya daga lukman din har hajiyan aka sanya su qarqashin ikonta,daga lukman din har hajiyan umarni suke karba daga wajenta,babu wanda ya isa ya tsallake abinda ta shimfida masa,sai a bayan idonta su yita takaici da jimami amma a gaban idonta ko tari ba wanda ya isa yayi,mutane da yawa sunyi murna sunyi shewa da wannan sauyi domin ya zamewa hajiya kubra izina.        Tun bayan da ya auri karima bai kuma gigin qara wani auren ba sai a yanzu da yake KUNDIN QADDARArsa na rubuce da auren sumayya,sanda yake gaya mata zai qara aure a tsorace yake,ita kanta tayi matuqar mamaki,a fusace ta shiga dakinta ta kira wayar malaminta ta sanar masa,wayar tace ya kashe zaiyi bincike nan da awa guda zai nemeta,ya kuwa nemetan ya sanar mata wannan aure ba makawa sai an yishi saboda yarinyar nada addu'a hakazalika 'yar gidan malamai ce,wannan kalma ta sake tunzura karima ta sanya aka sake sabunta aiki mai kyau akan hajiya da lukman don kada sumayyan ta samu kafar rusa mata shirinta wanda ta riga ta qudurceshi cikin ranta,haqura tayi saidai duk wani harkar biki kama daga lefe da sauransu ita tayi su,komai sai data ninka kudinsa sannan kuma ta zuba abinda ranta yaga dama,sauqin daya gidansu sumayyan gida ne na dattako babu wanda ya damu dabtsada ko yawan abinda aka zuba cikin lefen.          Qarfe tara da rabi na daren bayan an kaita gun hajiya an gabatar da ita yayin da ita kuwa hajiyan ke fadin tabi karima wanda ya baiwa kowa mamaki sannan aka dawo da ita dakinta wanda falo ne guda daya makeke sai dakunan bacci na kowacce mace da bandaki a cikinsa,sai dakin yara da mai gida kitchen da bandaki duk cikin babban falon,cikin falon dai ya kira sumayya don dama ita karima na zaune a falon tun kan a kawo sumayyan har kowa ya watse "To sumayya wannan itace uwar gida na uwar 'ya'ya na,idan kika bita kamar kin bini ne,na auroki ne ba don bana sonta ba,bana so kuma ki raina min ita,hatta hajiya farincikinta shine farincikin karima da fatan kin gane" kanta ta cira a hankali tana dubansu baki daya,cikin zuciyarta ta furta "Ikon Allah,yau kuma da wacce kalar Allah ya hadani?". Miqewa kariman tayi cikin izza tana yatsina " idan ka gama ka sameni a daki,kada ka wuce minti biyar" "To....to to" ya amsa cikin inda inda tare da binta da kallo har ta wuce dakinta,da sauri ya dubi sumayya "Amarya ta muje na rakaki daki kinji" ya fada cikin kwantar da murya,ba musu ta miqe tayi gaba mamaki na kasheta,wai dama haka lukman din yake?me yake shirin faruwa ne?.       Bakin gado ya zaunar da ita yana duba agogo don kada yayi laifi "Zauna bari naje,in Allah ya yarda zanyi qoqarin dawowa,ga kaxarki nan idan kina jin yunwa kici kafin na dawo" ya fada yana juyawa ya fice da sauri,binsa tayi dakallo baki daya qimarsa da mutuncinsa da take dan gani a da suna ficewa fit daga ranta,hawaye suka soma fita daga kuncinta data tuna rayuwar gidan mukhtar makamanciyar wannan,saidai sam da alamu bata kai qazancewar wannan ba,ita kuma nata salon QADDARAR kenan?. Juyawa tayi ta kwanta tana faman zubar da hawaye.        Har bacci ya soma fusgarta taji yana ambaton sunanta sama sama,ta bude idanunta tana dubansa,murmushi yake yana kallonta shima tare da duba bakin qofar dakin kamar wani ya biyoshi,ganin ta tashi ta zauna ya sanyashi maida qofar dakin ya murza key,kamar wanda ke sauri jirgi zai tashi ya barshi yake magana "Tashi maza ki dauro alwala,ina fatan dai kinci abincin ko?.....kinyi sallar isha'i?.....dauro alwala sumayya babu lokaci...."ya fadi yana satar kallon qofar dakin Cikin mamaki take dubanshi duk ya wani firgice,lokaci kada ya qure kamar yaya take tambayar kanta " don Allah tashi mana sumayya kada ta....."bai qarasa fada ba aka fara dukan qofar kamar za'a ballata "Innalillahi wa inna aihi raji'un" ya fada yana dafe kansa. "Zaka bude ko sai na sassaba maka,maci amana" inji mai buga qofar,jiki ba qwari ya nufi qofar ya bude mai bugun ta fado dakin tana raba idanuwa,kubra ce sai data qarewa dakin kallo ta fuskanci babu abinda ya faru sannan ta kalleshi "Ni zaka ci amana ka karya alqawarin daka yimun?,to wallahi ko kwana a dakin baka yi butulu kawai,maye,tunda ni ban isar maka ba,wuce muje nace ka tsaya ka kafeni da idanuwa" sai ya waiwaya yana duban sumayyan har sai data ingiza qeyarsa sannan ya fice yana waiwaye.      Kan sumayya ta dawo da kallonta"da sauran quruciyarki amma kin zabi nakasta rayuwarki,idan don kwanciyar aure kika zo gidan nan to kinyi babban kuskure don yadda kika zo haka zaki koma,don babu wasu 'ya'ya da za'a haifa a gidan nan sai nawa yaran,itama wadda aka haifa din don uwarta ta rigani zuwa ne,wlh da ni na rugata zuwa da bata isa ta haifeta ba,keda lukman kuwa saidai kallo" "Ke lukman ya dama,kuma ta Allah ba taki ba,ni an bani ilimin yarda da QADDARA mai kyau ko akasinta,hikinar ubangiji kuma yawa gareta,hakanan sanin gaibu sai Allah,duk kuma nisan jifa wataran qasa zai fado,mai yiwuwa ma idan ya tashi fadowar ya dawo tsakiyar kan wanda yayi jifan" "Ke ki iya bakinki wallahi idan baso kike kiyi kwanan gidanku ba" "Idan kinso kina iya karbe aron numfashin ma da kika bani idan yaso nayi kwanan kabari baki daya" sumayya ta fada hankalinta kwance,don ya zuwa yanzu tana jin ta gama daukar haquri da rainin wayon kishiya,bata cuce su ba don me su zasu dinga cutar da ita,tabbaa dafi da gubar zainab har yau bata bar illata zuciya da gangar jikinta ba,don kusan ita ta zama silar data sake cillota wannan muhalli da take ganin wata rayuwa miji ke biyayya wa mata. Mamaki ya cika kariman don ta jima rabon da a mayar mata da magana haka,sai zuciyarta ta tuna mata daga inda sumayya ta fito,take gumi ya fara tsatstsafo mata,tabbas sai ta sake shiri a kanta,qwafa taja sannan ta juya tana fadin "Da karimatu kike zancan lallai bakisan wace ni ba"bata yi nauyin bakin maida mata amsa ba don kada ma ta fita bata ji ba "hakanan bakisan wace sumayya ba,ki zuba ido kisha kallo". Bayan fitarta muqulli sumayya ta sanyawa qofarta ta shiga toilet ta daura alwala,sam bata ji wata damuwa na barinta da angonta yayi ita daya a dakin ba,kaya ta fiddo ta sauya wadanda zata sake a cikinsu sannan ta sanya hijabi ta tada sallah,kyawawan nafiloli ta raya daren sosai da su kafin bacci ya rinjayi idanuwanta. *asuba ta gari amaryar lukman* *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 4⃣1⃣ *Bimillahir rahmanir rahim* *wattaqu yauman turja'una fihi ilallah,summa tuwaffa kullu nafsin ma kasabat wa hum la yuzlamun* *_KUJI TSORON WATA RANA DA AKE KOMAR DA KU IZUWA GA ALLAH A CIKINTA (RANAR LAHIRA),SANNAN A SAKAWA KOWACCE RAI ABINDA TA AIKATA (SHARRI KO ALHERI)ALHALIN SU BA'A ZALUNCESU BA(BA WANDA ZA'A ZALUNTA DUK ABINDA KA AIKATA SHI ZAKA GANI)_* ______________________________ Qarfe tara na safiya tayi wankanta,ta shirya cikin atamfa dinkin riga da zani,ba wani kwalliya tayi ba amma tayi kyau,dakin ta sake karkadewa ta goge sannan ta koma bakin gadonta ta sake kwanciya,idanunta ta lumshe tana saqa da warwara,kewar abdallah take ji sosai cikin zuciyarta har qwalla na shirin kawo mata,tunani ne fal zuciyarta tana wassafa yaya rayuwa zata kuma kaya mata cikin wannan gidan. Hayaniya ta dinga jiyowa cikin falon da surutai,ta bude idanunta ta kalli agogon dakin,goma tayi har da mintina arba'in da biyu,saita bude sif dinta ta ciro hijabi ta zura kana ta sanya silifas dinta ta murda qofar dakin ta fito. Duk uban hayaniyar da take ji yara hudu ne cikin falon,yarinyar farko wadda ita ta sake hautsina yanayin falon ma hakimce kan kujera kamar wata babbar mace duk da du du du ba zata wuce shakara sha uku ba,kallo take a tashar mbc three ta qure volume kamar ita da mutum dari suke kallon,sai yarinya ta biyu wadda batafi shekara uku ba dake zaune qasanta kan carfet taci uban indomie ta hadeta da ruwan shayi tana wasa da ita,daga can wajen step na dining kuwa wasu yaran ne su biyu,daya shekarunta goma daya takwas suna karyawa,su biyun kadai sun dame gurin kamar qanwar tasu dai,ta sake wurga idanunta,wata yarinya ce data tasamma zama matashiya wadda ta kusa shekara goma sha hudu takure a saqon kujeru,kallo daya zaka mata kasan daban take kamar yadda kamanninsu ya bambanta da sauran yaran dake falon,don dukkansu kamarsu daya ita kadaice kamarta daban kamar yadda ta fisu kyau baki dayansu. Dukkansu sun ga fitowarta saidai babu wanda ya kulata,ta dubi qofar dakin karima wanda ke garqame ta sake dauke kai "Ina kwana anty" Taji an ambata daga bayanta,saita waiwaya,yarinyar dake zaune ce saqon kujera ta gaidata tana murmushi,maida mata murmushin itama tayi tana mamakin zarnin dake tasowa daga jikinta "Lafiya qalau,an tashi lafiya?,me sunanki?" "Nuwaira" "Sunan mai dadi" sai tayi murmushi tana cewa "Na gode anty". "Ko zaki rakani wajen kakarku?" "Wa?,hajiya" "Eh" "Muje in rakaki anty" ta fada tana wucewa gaba sumayya na rufa mata baya. "Wallahi bari umma ta fito sai na gaya mata duk abinda kika yi,bata ja mana kunne ba?" Yarinyar daje saman kujera ita ta ambaci hakan tana jijjiga kai,cak yarinyar ta tsaya kamar an ambata mata mala'ikan mutuwa,idanunta na tara qwalla tace "Kiyi haquri don Allah kada ki gaya mata" "Wallahi sai na fada saidai ta kasheki" ta fada tana buga hannu alamun babu fashi,wani abu ya tsayawa sumayya a wuya,takaici da mamaki suka cikata,sai ta janye nuwaira tana fadin "Muje babu abinda zai faru dake kinji kada ki damu" jikinta babu qwari ta bi sumayyan suka fice. Kafin su qarasa gun hajiyan sumayya ta dubeta "Me yasa kinsan kina fitsarin kwance da kika tashi baki sauya kayanki ba nuwaira?,kinsan fa ba'a son mace da qazanta" sai yarinyar ta fara qwalla ta soma sharewa tana cewa "Wallahi anty tunda bana fitsarin kwance,saddiqa keyi sai a hadamu kwanciya gado daya,idan tayi duk sai ya jiqani,idan ta tashi ita sai nuratu ta sauya mata kaya,ni kuma ba zan canza ba har sai umma ta gama bacci tayi wanka ta fito sannan zata nunan wadanda zan sauya din,koda asuba bana samu nayi sallah sai rana ta fito" ta fada da alamu abun na ci mata tuwo a qwarya,shiru sumayya tayi tausayin yarinyar na kamata,wannan wanne irin zalunci ne,tun kallon farko da ta yiwa yarinyar ya nuna tana jin jiki a gidan,amma tana tunanin kamar ita ce yarinyar nan daya da karima jiya ta gaya mata uwarta daban,don ta tabbatar sai ta tambayeta "Ina mamarki to?" "Mama na tayi aure a wani gidan,tun kafin a yayeni aka karboni aka bawa hajiya ni,to da abbanmu ya sake aure ya auro umma sai umman ta karbeni nake gunta"take tsanar karima ta darsu a zuciyar sumayya,lallai ba shakka bayan shirkar tsafi ma harda azabtar da yarinyar da bata ji ba bata gani ba,wai me mutane suka dauki duniya ne?,kowacce mace son kanta ya mata yawa?,burinta ta mallaki miji ta rabashi da kowa nasa?,ta rabashi da 'yan uwansa da tazo ta samesu tare,'yan uwa da suka zamar masa bango marufar asiri tun yana zanin tsumma har kawo yau,ta rabashi da duk wani alkhairi uwa uba ta rabashi da mahaliccinsa,ta sakashi a musibar da ranar gobe qiyama bazai iya tsallaketa ba,ta rabashi da hankalinsa bare ya kula da addininsa,wanda ya cancanci a bashi haqqinsa ta hana ya basu yanzu duka wannan qauna ce?,sai tace sonshi take shi yasa ta aikata haka,wannan ko babban maqiyinka ba shakka iya cutarwar da zai maka kenan,da irin wannan tunani suka isa bangaren hajiyan. A duqe suka sameta tana share falon nata dake malale da carfet,kallo daya sumayya tayi mata ta fuskanci shekarunta basukai ace tayi tsufar da tayi a yanzu ba,da sallama suka shiga ta dago tana amsa musu riqe da qugunta wanda bisa dukkan alamu ciwo yake mata,nuwaira ce ta gaisheta ta amsa babu yabo ba fallasa yayin da sumayya ta qarasa tana amsar tsintsiyar hannunta tana gaidata,amsawa tayi tana dubanta yayin da sumayya ke qarasa mata sharar har ta kammala sannanbta dawo inda hajiyar ke zaune tana yiwa nuwaira masifar sai zuba zarni take taje bandakinta ta wanke jikinta,mamaki ya cika sumayyar,to ko batasan meke wakana bane cikin gidan?,batasan ba laifin nuwairan bane karima ce ta cancanci fada idan da duka ma ayi mata?,tashi yarinyar tayi ya shige bandakin hajiyar sannan hajiyar ta maido kallonta ga sumayyan "Ban gane fuskar ba wace ce ne?" Murmushi kawai tayi ta dan sad da kai "Oho,ko amaryar lukman ce" kai sumayyan ta gyada. Shiru ne ya biyo baya,hajiyan na dan satar kallon sumayyan,sai taji ta dan sake da yarinyar duk da ba hira suke ba zaman kurame ne,a haka har nuwaira ta fito daga bandakin sanye da jiqaqqun kayanta wadanda ta wanke bayan ta dauraye jikinta ta maida su a haka "Wani nuwaira nikam bakuyu abin kari bane yau,gashi har sha daya na shirin gotawa yau ba'a kawo kin komai ba,ko luba mai aikin bata zo bane?"cike da madaukakin mamaki sumayya ke sauraron zancan "Tazo hajiya,bansan ba'a kawo miki ba,don ko nima yau ban karya ba,naga dai su nuratu na karyawa ni ma ba'a bani nawa ba"ta fadi babu alamun damuwa tattare da ita bisa dukkan alamu ta riga da ta saba da hakan,yamutsa fuska hajiyan tayi "gaskiya na fara jin yunwa wlh,wannan abu Allah kayi mana maganinsa" "Amma hajiya ai naga kina da sauran kayan abincinki da kika ce bazaki iya ci gaba da girki ba ai abba bai debe su ba ko?" "To idan banda abinki ina fama da lalura ina zan iya,sharar ma don bazan iya zama cikin qazanta bane nake daburtawa nake yinta" ta fada ta muskutawa da alamu yunwa na sakadarta,tausayinta duka sai ya kama sumayya ta dubeta "To hajiya idan ba damuwa sai na shiga na girka miki ai ko?"haba ta riqe " a'a,har kya fara shiga madafi ta sanadina?,ki barshi babu komai idan da sabo ai mun saba da irin wannan gashin,ke dai kawai Allah yayi mana magani"murmushi tayi kawai ta miqe tana tambayar nuwaira inda kitchen din yake. Sallamar karima a gadarance ita ta maida hankalinsu bakin qofar,ita ke gaba gogan na binta a baya riqe da wani dan qaramin flask wanda bako shakka abun karin hajiyan ne a ciki,idanunsa na kan sumayya yana faman sakar mata murmushi ,wani takaici da haushinsa suka qumeta saita dauke kai tana jin kamar taje ta shaqeshi,haka nan kawai taji jarumin namiji yana burgeta,sai ta tuna sanda zainab ta fara murza kambunta lokacin tana gidan mukhtar,tabbas ko a lokacin mukhtar din kan tauna tsakuwa wani lokaci. Hajiyan da za'a yiwa sannu a gaisheta ita ke faman yiwa kariman sannu tare da gaisheta,lukman ya koma gefan hajiyan yana gaidata cikin dari dari suke gaisawar kamar suruki da suruka duk don kada su batawa karima rai,baki sumayya ta saki tana kallon abun mamaki bayan hajiya ta bude flask din da aka kawo mata,wani gantalallen soyayyen dankali ne da rabin wainar qwai babu ko tea amma hajiyan sai godiya da sannu take mata "Saidai yau kici haka hajiya don kafin na fito jikokin naki sun shanye shayin" "Ai babu komai,idan baka yiwa jikanka ba wa zaka yiwa" ta fada fara'a kamar gonar auduga. Kallon sumayya karima tayi bayan sumayyan ta gaida lukman wanda ke faman binta da kallo kamar tsohon maye "Ke baki iya gaida mutane ba" ta fada fuska a tsuke kamar wata uwarta,waigawa sumayyan tayi ta watsa mata kallo "Su waye mutanen?" Ta tambayeta bayan ta tsareta da ido,sai kawai taji sumayyan ta mata kwarjini da irin kallon da take mata,janye idonta tayi ta dubi hajiya "Hajiya kina gani dai a gabanki ko?" Ta fada cikin zafin rai,lukman yayi saurin karbewa "Bana son rashin zaman lafiya fa sumayya a gida na kinji ko?" Kallon da wa kazo ta watsa masa sannan ta dauke kai,hajiya cikin rawar jiki tace "Ke yarinya,farincikinmu shine farincikin karima,saboda haka dole ki mata biyayya ki kiyaye" girman hajiyan take gani,saboda haka ta dan rusuna "Insha Allahu hajiya kiyi haquri" ta fadi da sauri tana shigewa kitchen din hajiyan don bata son ma ta sake kallon fuskar lukman bare ta karima. Tana kitchen tana hada girkin duk da wasu kayan buqatun babu,mamaki da tunani fal ranta,a haka taji sallamar hajiyan,ta juya tana amsa mata,qarasowa hajiyan tayi ta kama hannun sumayya kamar zata saki kuka "Kiyi haquri sumayya da abinda nayi miki dazu,yarinyar nan idan ta umarcemu da abu daga ni har lukman bama iya musa mata,amma nasan alhakin yaran jama'a ne yake bibiyata,haka kawai naji kin kwanta min sumayya zan gaya miki wace ni me na aikata ga rayuwata da rayuwar yarona" Kafin sumayyan tace wani abu tuni hajiya ta fara bata labarin dukka aure auren da lukman yayi wanda ita ce sila,da fari haushin hajiyan ta dinga ji,amma daga bisani sai tausayinta ita da lukman ya baibayeta baki daya,tabbas abu na farko data fuskanta ya janyo wannan matsalar sakaci da rashin riqe ubangiji hannu bibbiyu,har qwalla sai data yiwa hajiya da lukman din saboda aikin kariman ya shallake hankali. Cikin sanyin jiki ta riqe hannun hajiyan ganin tana zubda qwalla "Kiyi haquri hajiya ki fawwalawa Allah lamarinki,ba shakka inna idan ma alhakin ne ba mamaki,Allah na sonki shi yasa zai hukunta ki tun a duniya,din hukuncin lahira da shi gwara na duniya sau babu adadi,in sha Allahu ni zanyi iya bakin qoqarina wajen ganin na daidaita lamarin iya abinda Allah ya huwace min,ina so daga yau kisa a ranki ba zaki qara jin tsoron karima ba,ba zaki sake bin umarninta ba sai abinda ya dace shi zakiyi,a duk sanda kika ganta idan kika ji faduwar gaba ko tsoro ki karanta ALLAHUMMAKH FINIHIM BIMA SHI'ITA matakin farko kenan,sannan daga yau kada ki sake cin duk abinda ya fito daga hannunta,ki umarci lukman ya kawo miki kayan abincinki a zuwan zaki ci gaba da girki,ni kuma in sha Allahi zanci gaba da dafa miki" kai take gyadawa cike da gamsuwa tana jin tamkar damuwarta na gab da yayewa "Sannan lukman danki ne hajiya,bakin uwa kaifi gareshi,ki dage da yi masa addu'a,Allah ya yaye masa bala'in da ya fada ta sanadin abinda ke kika aikata shi,bashi kadai ba,har ke dinma saikin dage da addu'a wa kanki na neman tsari" Kai ta sake jinjinawa "Har na manta rabon da na sashi a addu'a ta,na gode da tunatar da ni da kikayi,na gode sosai" "Sannan hajiya,kinsan rayuwar da nuwaira take cikin gida kuwa?" Ta tabo inda yafi mata qaiqayi "Na sani sumayya na sani,saidai bani da ikon magana bani da ikon gyarawa" ta fada cikin jimami,don har ga Allah duk cikin jikokinta tafi qaubarta,din ta fita daban a cikinsu,nutsuwarta da komai da komai,shiru sumayyan tayi sannan tace "Babu komai,zanyi iya bakin qoqarina itama akanta kafin Allah ya kawo qarshen lamarin" "Na gode sumayya na gode,haqiqa kin zamo *HASKE* cikin gidan d'ana cikin kwana daya tal,ina miki fatan alheri sannan kuma ina miki fatan samun nasara,Allah ya albarkaci rayuwarki da alkhairi masu tarin yawa,ya tsareki" amin sumayya ta dinga cewa tana jin dadin addu'ar har cikin ranta,ko da can ita din mai son wani na gaba da ita ne ya albarkaceta,kusan tare suka gama aikin ta kammalewa hajiyan cikin kula yadda tasan zai ishesu ita da nuwaira,tace zata turo mata ita taci na rana dana dare,don ta lura bata samu albarakacin cin na safe ba,sai na hajiyan da suka yayyafita. Nan tayi zamanta gun hajiya,ita kanta hajiyan sai ta dinga jin dadi cikin ranta,nuwaira ma ta dinga sato jiki tana leqowa har sanda sumayyan ta koma bangarensu. ***** ****** ****** Cikin kwanaki hudu rak sumayya ta gama dukkan wani shiri nata na tunkarar wakeken qalubalen data fuskanci yana danqare a gidan,ita kanta mamakin kanta take yadda zuciyarta ta taurare baki daya har take ganin zata qalubalanci karima wadda baki daya ta rusa rayuwar gidan ta dora ta kan turbar da take so,sam sam yaranta irin yaran nan marasa tarbiyya ko qanqani,su zagi babba duk girmansa ba komai bane a gunsu,sam sam sumayya bata shiga shirginsu ko sakar muau fuska tunda ta fuskanci inda tarbiyyarsu tasa gaba,hakan ya sanya suka fara shakkarta,sai kuma mai biwa babbar da ta soma son kula sumayya,sau tari takan qwanqwasa qofarta idan ta bude mata tace ta shigo kuma sai taqi,sai ta fuskanci shakkar mamarta take,hakan ya sanya ita sumayyan ta fara qoqarin janyota a jiki,ga shegen gulma munafunci da iya kawo labari,hatta da mahaifinsu suna iya dauko gulmarsa su kawo mata ita kuma ta tuhumeshi kan haka,sumayyan na sha'awar hatta da tarbiyyar yaran ta saisaita musu ita,don ta kula sam daga makarantar boko babu kuma wata makaranta ta biyu da yaran ke zuwa wadda ake kira da makarantar addini ko islamiyya,baki daya idan ka dauke sumayya banu mai rayuwa kan ra'ayinsa sai abinda ta shinfida,tun abun na bawa sumayya haushi har ya koma bata tausayi,ita sam ma baki daya bata ta angon ko kadan,wanda zuwa yanzu hatta lokacin fita da dawowarsa gida karima ta sauya masa duk don kada su hadu da sumayyan,ta saka an qara narka masa aikin mantau akan sumayya wadda ko gefen silifas dinta lukman din ma baije ba,sau tari takan tambayi kanta me yasa ta auri lukman sai ta rasa dalili,amsa daya ke zuwa kanta "Qila don kizo ki ceci rayuwar 'yar gidan ne" ita kanta tafi gamsuwa da wannan ce sahihiyar amsar ****** ******* ******* Cikin satittika qalilan shaquwa ta fara shiga tsakaninta da hajiya,kusan koda yaushe can take wuni,ta yima haijan aikace aikace sannan suyi girkinsu abinsu,sannu a hankali sauyi ya fara samuwa tattare da hajiyan,sumayya ta zaburar da ita ta kuma koya mata addu'o'i sosai,rana ta farko da suka fara fuskantar zuwan sauyi shine randa kariman ta shigo da abincinta wanda aka saba sanwa hajiyan don bazance bata ba,duk da hajiyan ta jima bata ci amma sumayya tace ta dinga karba kada ta gaya mata idan yaso saita dinga bayarwa,tunda ta shigo ta lura hajiyan sam bata rawar qafa yadda ta saba idan ta shigo gunta,abu na biyu tana jiran taga hajiyan ta gaidata yadda ta saba sai taga tayi fuska,ta maida hankalinta gun sumayya dake shafa mata man zafi a gwiwarta data riqe mata take mata ciwo,wanda abaya bata da wannan gatan saidai taci ciwonta ta warke don dolenta. Kanta yayi masifar daurewa,abu na farko da yazo kanta aikin hajiyan ya fara sako sako don dama kwana biyu tafi maida kai a kan lukman din "Ga abinci nan" kariman ta fada a wulaqance,juyowa hajiyan tayi tana duban flask din ranta cike da takaicin yadda ma ta dinga karbar wannan abincin "Wai ni?,ai da kinyi gaba da abinki don na jima banci abincinku ba,'yata na girkamin kullum" ta fada tana duban sumayya,take tsoro ya shigi karima,ashe tayi sake har haka?,ashe fa diyar malamai wannan karon lukman ya kwaso mata,lallai ba shakka shi yasa taga bata taba tambayar abincinta ba a gidan duk yadda ta sha alwashi akan yi mata kaca kaca duk sanda ta tambayi a bata abinci. Hankalinta tashe ta fito daga bangaren ciken da tsoron lallai idan ta gama da hajiya babu shakka lukman zata dawowa,kacibus sukayi da nuwaira wadda ke dawowa daga gidan kitso da sumayya ta turata tayi saboda ba zata iya mata ba jiya ta yanke da wuqa a hannunta,baki ta saka tana duban nuwairan yadda ta canza cikin sati biyu kacal da kariman tayi bata nan,ta tilasta lukman ya biya musu umra ita da shi don har sai da yaci bashin wajen dubu dari biyar sannan ya cika musu,su kuma yaranta da zata tafi ta tattarasu ta maida su gidan iyayenta ta bar nuwaira ko oho,don dama ta saba yi mata irin hakan,tsoro ya kama nuwairan sai ta rabe gefe sannan ta tattakura ta sheqa da gudu sai bangaren hajiya,don kayan dake jikinta na waccar sallar ne shekara uku da dinka su,bata barinta ta sanya su sai wani abun ya tashi duk da cewa suna da lodin kaya harda wanda bata taba sawa ba ma sababbi,ta riga ta saba kayanta koda yaushe haka suke tamkar tsummokara,a haka ma sai an bata umarnin wadansa zata saka,bayan 'yan uwanta kullum cikin saka mai kyau suke. Bata bi ta kan nuwaira ba don ba ita ce yanzu a gabanta,bangarenta ta wuce hankalinta a matuqar tashe,tabbas lallai babu shakka idan batayi wani abu ba ta lura duniyar rayuwarta gab take da girgiza koma rugujewa baki daya,dole ne gidan ya koma yadda yake,dole kowa ya koma yadda take so ciki kuwa harda sumayyan ****** ******* ****** Tunda ya karbeshi kusan shi ua zame masa uwa da uba baki daya,yana matuqar debe masa kewa,yana sanyashi nishadi,wata qauna ta yaron nasa yake ji cikin jikinsa da jininsa,sau tari ya kanyi mamakin kansa yadda yake zama yayita kallon abdallan kamar babu gobe,babu yadda yaya yahansu batayi ba akan ya bata shi amma ya qiya,ya bata haquri don bazai iya bata shi din ba. Da safe tare suke shiryawa ya bashi abinci su fita kasuwa tare da shi,zuwa azahar zai bar kasuwa ya dan fita da shi su zaga gari su dawo da la'asar,qarfe shida subar kasuwa su dawo gida,har gado ya siya na yara ya sanya masa can cikin shagon,nan ma idan sun dawo sunyi wanka sannan suci takeaway din da ya tsaya hanya yayo musu,daga nan ya zube masa kayan wasansa yana tayashi yana kallon t.v har yaron yayi bacci,wani lokaci yakan bata lokaci saman abun sallah yana wa yaron nasa addu'a tare da yiwa kansa,wanda hakan ya sake samarwa da ruhinsa nutsuwa,shikewa Abdallahn komai,dai dai da rana guda mukhtar bai taba jin ya qosa koya gajiya ba,kai kanka idan ka kalli yaron ba zakayi zaton bai tare da mahaifiyarsa ba,kusan kullum sabon kayan mukhtar zai sanya masa,ado yake masa sosai,hakanan idan shadda zaya sanya ko yadi anko suke abinsu,duk wanda ya gansu a hanya zasu burgeshi,wata qauna ta musamman ce tsakanin d'a da ubansa,wani lokaci idan ya soma rigiman mamansa sai ya kaishi gunsu halima ya wuni don bai iya barinsa ya kwana,da dare yazo ya dauki abinsa su wuce. Sau daya yaya yahansu ta taba tuntubarsa da batun bazayayi aure bane,murmushi kawai yayi mata yace tabar batun don ko sha'awar sa bayayi,tilas ta ja bakinta ta tsuke,domin har yau tana tuhumar kanta da cewa ita ce sila,zuwa yanzu itama ta fara gani,don kuwa yaron da jamila ke ao kamar ta mutu shima yayarsa ta hana auren sam tace bata yarda ba,ga fatima nan ma a gabanta babu wani bayani,fiddausi kuwa uwar miji ta sakota gaba,yau tana gidanta gobe tana gidan yaya yahanasun *_KOMAI NISAN JIFA_* Tunda dukka ayyukanta suka kammalu wajen malaminta data bawa hadin kai wanda har ta kaita da kwanciya da shi,ki a jikinta babu abinda taji tunda har ya mata alqawarin tabbas tamkar ta samu kukhtar ta gama koda kuwa zata sanar masa ita ta shirya duk abinda ya faru a baya da sumayya,babu abinda zai iya aikatawa ba zaiga aibunta ba face sabuwar soyayya da zata sake ballewa a tsakaninsu. Ranar lahadi ta shirya zuwa har gida saboda ta tabbatar a ranar bai fita kasuwa,dinki na musamman tayi sabo,baya ga sabon kitso da gidan kwalliya da taje duka aka sauya halittar Allah,saboda tana rayawa matuqar ciniki ya fada tofa ba lallai bane ma ta dawo gidansu ba saidai a biyota da kayanta,tunda har yau a matsayin saki daya yayi mata haka ta sanarwa mamanta,wanda koda sakin ukun tace an mata ta kuma ce zata koma babu abinda uwar ta isa tayi don ba a bakin komai take a gunta ba. Qarfe sha goma na safe ta kammala komai,a nan cikin shagon masu kwalliya wadda ta sanya fitowa tunda safen tayi mata ta sauya kaya,double ta biya kudin makeup din hakan ya sanya ta yiwa jakarta qarqaf,bata da damuwa tunda tana saka ran kome wanda zata fanshe dukkan abinda ta kashe gun mukhtar,ba shakka sai ta rama wahalar da ya bata ba zata sassauta masa ba. Qarfe goma sha daya saura mintuna goma ta sauka qofar gidan mukhtar din,wani farinciki ya lullubeta ta soma shaqar iskar komawa cikin gidan,cikin sa'a tana tura qofar gidan ta taddata a bude,a hankali take takawa saboda cogen dake qafarta har ta sada kanta da falon gidan,a hankali take qarewa falon kallo yadda ya sake maidashi ya gyarashi bayan barinsu gidan,sai abun ya sake burgeta,ko ina tsaf kamar akwai mace a ciki kasancewar yana da mai share share da goge goge,cikin kallon da takeyi ne idanuwanta ya saukan kan abdallah dake zaune tsakiyar falon,sanye yake da jallabiya fara tas ta yara wadda ta masa kyau kamar dan larabawa,wasansa yake da kayan wasa turmus a gabansa nau'i daban daban. Idanuwa ta zuba masa kamar yadda shima ya zuba mata idanuwa yana kallonta tamkar ya santa,karkata kai take tana gano kamannin mutum biyu tattare da shi,sumayya sumayya mukhtar mukhtar,ci gaba tayi da kallon nasa tana son tantance dan waye?,miqewa yaron yayi yana ci gaba da kallonta sai kuma ya saki kuka tare da juyawa a guje ya shige bangaren baban nasa wanda ke ciki. *mrs muhammad ce* *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 4⃣2⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *wala tahsabannal lazina qutilu fi sabilillahi amwaataa,bal ahya'u inda rabbihim yurzaqun* *_kada ku zaci wadanda aka kashe ta hanyar Allah(shahidai)matattu ne,rayayyu ne a gun ubangijinsu ana azurtasu_* _______________________________ Mukhtar dake falo zaune saman abun sallah yayi saurin sallame raka'arsa ta qarshe wadda dama zaman tahiya yake,qarasowa abdallah yayi yana kebe baki ya fada jikin mukhtar,tambayarsa yake menene kamar wani babba,babu baki sai gwalanto da yake masa wanda bai gane mai yake cewa,miqewa yayi da sauri sabe da shi a kafadarsa sabida tunawar da yayi dazu da ya fita siyo ma abdallan alawa ya manta ya bar qofar gidan a bude. Tana zaune qafa daya kan daya tana kadasu hankalinta kwance,tana jin ba ma sai taje nemansa ba da kanshi zai fito,qamshin turarensa da ta ji shi ya maida hankalinta zuwa qofarsa,shi dinne dauke da abdallah sanye da jallabiya sak irin ta abdallan,har ga Allah bai lura da ita ba sai da yaji an ambaci "Ranka ya dade" cak ya tsaya sannan ya waiwayo ya dubeta,idanunta ya dan juya don tabbatar da cewar ita din ce?,ita ce don kuwa zuwa yanzu gabansa take takowa,dab da shi ta qaraso tamkar zata shige jikinsa,cikin narke murya ta soma magana "Haba my mukhtar,ka riga da kasan irin kamun da soyayyarka tawa zuciyata,ta yaya kake tunanin nisanta kanka da ni bayan kasan cewa ina mutuwar sonka,a yau ina so ka maidani dakina ba sai gobe ba domin shine burina kaji" ta qarashe maganar ta sigar bada umarni. Wani bala'i ke cinsa,ya tabbata cewa idan har baiwa zainab akuyanci ba ba zata taba barin rayuwarsa ba,yarinyar da kullum kwanan duniya ya zauna tunani yake tare da tambayar yaya akayi ya aureta ma wai?,mene ya ja hankalinsa,ko da yaushe yakan godewa Allah da bai QADDARA rabon zuria a tsakaninsu ba. Cikin tsantsar bacin rai ya soma nuna ta da yatsa kamar zai tsone mata idanuwa "Cikin halittun dabbobi ke wacce iriya ce a cikinsu?,bakiji gargadin da na miki ba kenan?,tunda nake ban taba ganin ballagazar mace irinki ba,sha sha sha kawai wawiya,to wallahi zan miki gargadi na qarshe,duk sanda kika sake shiga rayuwata sai na miki abinda ko hanyar da nake bi aka ce kibi ba zaki biba,bace min da gani banza qazama kawai" ya fada kamar zai hankadata. Tsantsar tashin hankali da baqinciki suka taso suka tokareta,amma data tuna yadda bokanta ya jaddada mata kyawun aikin da yayi mata sai taga bari ta sake gwada sa'arta "Wai mukhtar me na maka da zafi haka,nina shiryawa sumayya dukkan wata gadar zare kuma a idanunka sumayya ce ta aikata laifin,to amma na lura tsanar da ka yimin baka yi mata koda rabinta ba" sosai maganar ta daki kunnensa gangar jiki da zuciyarsa duka lokaci daya,wani abu yaji yana zagaya kansa,wani irin sanyi jikinsa yayi ya zubawa zainab ido har baisan sanda yace "Kika shirya mata gadar zare kamar yaya?" Wani fari tayi da idanuwa tana ci gaba da kallonsa,a tunaninta sanyin da jikinsa yayi aikinsu ya fara shiga jikinsa ne,sai ta kama hannunsa babu musu ya bita zungui zungui,don baya gane komai a yanzu,abinda ke yawo kansa kawai shine irin abubuwan da suka dinga faruwa tsakaninsa da sumayya a lokacin,sai da ta kaishi gefan kujera ta zaunar sannan ta zauna gefansa. A hankali ta dinga warware masa zare da abawa tamkar wadda ake umarta,ko da yake umarni ne na rabbil izzati da yaso ya fidda bayinsa daga wani mummunan sharri,ta qare da cewa "Dukkan wannan saboda tsananin qaunarka da kishinka da nakeyi ne ya janyo na aikata hakan,kuma babu abinda bazan iya aikatawa duk don saboda kai saboda na mallakeka ni kadai,a shirye nake na sadaukar da dukkan abinda na mallaka" ta fadi tana karya wuya tare da sakin murmushin alamun samun nasara a tunaninta. Gaba daya daina zagayawa jini yayi a jikinsa,kansa ya masa nauyi,cak qwaqwalwarsa ta tsaya da aiki,wani duba yakewa zainab din mai cike da tsantsar tsana,daki daki musgunawa da zargi da kallon tsana da ya dinga yiwa sumayya ya dinga dawo masa kamar bitar karatu,yanzu duk baki daya ba bisa laifinta bane ashe?,ashe ita din bata aikata komai ba kamar yadda tasha sanar masa?,bai taba jin ya tsani wata halitta a duniya ba kamar yadda yake jin tsanar zainab na yawo cikin jininsa da ruhinsa ba,sai da wuta ta dauke masa na wasu mintuna kafin ya fara tunaninsa ya fara dawowa kan hanya. Yana jin yau idan bai ci uban zainab a duniya ba yayi asarar rayuwarsa,baisan wanne ne hukunci na qarshe da ya cancanci yayi mata ba,miqewa yayi da hanzari ta ruqo hannunsa "Ina zaka?" Wani kallo ya juya ya watsa mata wanda ya sata sanqamewa,fargaba ta lullubeta tana fatan ba abinda take tunani bane ke shirin aukuwa "Gidan uwarki da ubanki zani,zauna ki jirani" ya fada a tsawace yana tsige hannunsa daga nata,wani malolon takaici ya cika zuciyarta,kada dai ace mukhtar din na cikin saitinsa tayi wannan barin zancen?,yana nufin aikinta baiyi tasiri a kansa ba?,waishin wani irin mutum ne mukhtar din?,yana nufin dukka kashe kudi bata lokaci da sadaukar da jikinta da tayi ya tashi a banza?,to wallahi wannan karo kam bai isa ba,bai isa ya sanyata ci gaba da yin asara ba,kota hanyar tsiya kota arziqi,tsaye ta miqe a zafafe tana dubansa "Kai mukhtar,na gaji,na gaji da asarar lokacina da kudina a kanka,me yasa bakasan darajar soyayya ba?" Dauketa yayi da wani zazzafan mari wanda ya haddasa mata ganin wulgawar wasu taurari tare da zubewa warwas a qasa,lokaci guda jini yayi kwance gefan qwayar idanuwanta,kafin ta kai ga dawowa hayyacinta tuni ya garqame qofar falon sannan ya wuce ciki cikin matsanancin sauri,bedroom dinsa ya shiga ya kwantar da abdallah da bacci ya daukeshi kan fadar mukhtar din sannan ya fito ya rufe qofar dakin baccin ya rufe ta falo baki daya don bai fatan yaji ko yaga abinda yake shirin aikatawa,wani irin suya qirjinsa yake a fuskarsa yana jin wani hucin zafi na fita kamar wanda aka cilla cikin rumbun gasa biredi. Nan saman kujerar ya sameta zaune tana shafawa tare da jajjabin kuncin da ya mareta wanda lafiyayyun yatsunsa suka fito rada rada tamkar an zana su,bata lura da fitowarsa ba sai da flower vase din dake kan t.v stand ta fado ta fashe saman tiles sanadiyyar finciko wayoyin dake jikin kayan kallon ta ankarar da ita,nufota ya soma yi wanda hakan yayi matuqar firgitata,gaba daya kamanninsa sun sauya mata,ganinsa take kamar wani mayunwacin zaki yaga abun farauta "Me kake shirin yi mukhtar,kada dai kace dukana zakayi" "Idan akwai abinda yafi duka yau zaki dan dana shi,inaso gangar jikinki ta fara dandana azaba kafin na kai ga ruhinki,yau zakiyi dana sanin raba masoya,daga yau ko a shirin film aka ce ki fito a matsayin jarumar dake raba masoya ba zakiyi marmari ba" "Amma dai kasan......." Sai maganar ta katse sakamakon ihun da ta tsala saboda kyakkyawan masauki da wayar ta samu a gadon bayanta,duka kota ina ya dinga kai mata,baki daya ya fice hayyacinsa kamar yadda itama ta fara dan dana kudarta,duk duka daya da zai kaimata sai ya tuno baqar azabar da sumayyan ta sha a wancan lokaci,tun zuwan zainab din gidan har ya zuwa ranar data kwanta gadon asibiti,ranar data zamto rana ta qarshe a tarihin zamantakewar rayuwar aurensu. Duk inda ta nufa da nufin samun mafaka ko maboya sai ya bita,tuni takalman qafarta sukayi nasu guri daban,haka dankwali da mayafinta,ganin abun nasa na gaske ne babu alamun sassauci yasa ta fara bashi haquri,saidai sam baya fahimtar me take fada,sai bada haqurin ya zamo tamkar tana qunduma masa zagi ne a gurinsa. Tun zainab na iya ihu da neman agaji har muryarta ta dakushe,tuni fuskarta ta cabe baki daya,kwalliya tayi nata guri,baka iya tantance ina kwalliyar tata bare fuskarta,babu inda bai fasa ba ajikinta har wani sashe na kayan jikinta ya yage saboda tsantsar dameta da kayan sukayi,jagaf ta jiqa kayanta da gun da ta dinga malelekuwa da fitsari,wurgar da bulalar yayi gefe kamar yadda zainab ke yashe gefe daya tana fidda qwalla hadi da numfashi,sai yau ta yarda da maganar hausawa na cewa kuka ma rahama ne,gashi a yanzun bata da qwarin ma fidda sautin kukan,azaba take ji na shigarta takowacce kafa ta jikinta,dukan da tunda tazo duniya ba'a taba yi mata kwatankwacinsa ba duk da kasancewarta yarinya gagararriya tun a wancan lokacin,yana haki numfashinsa na fita da qarfi saboda tsananin bacin rai,ji yake kamar ya shaqeta ta mutu ya daina kallonta,duk duba daya da zaiwa fuskarta tsanarta ke ninkuwa cikin ruhinsa,ba shakka wannan duka babu abinda ya rage cikin zuciyarsa na daga bala'in da yake ji,qafarta daya ya kama ya bude qofar falon ya dinga janta tamkar kayan wanki,bai direta ko ina ba sai bakin qofar gidan,ya koma ya kwaso tarkacen takalmi jaka da mayafinta ya watsa mata,yana tsaye a kanta ya nunata da yatsa "Ba qarshen hukuncinki kenan ba,ki jirayi abinda zai biyo baya" ya fada yana juyawa cikin gida. Wani irin jiri ya dinga kwasarsa,da qyar ya kai kansa cikin dakin baccinsa inda abdallah ke baccinsa lakadan baisan meke faruwa ba,gefansa ya zauna ya zuba masa idanu yana kallonsa cike da tausayinsa tausayin kansa da kuma tausayim sumayya baki daya,tambayar kansa yake ta yaya ya yarda sumayya zata iya aikata haka ma wai?,sumayyarsa ce fa?,rainonsa ce,tarbiyyarsa ce,yaya akai har ya gaza bincike tashin farko ya yarda ya dora zarginsa kan halittar da bai taba samunta da cutar da wani qwaro ba ballanta na mutum dan adam mutum din ma shi mukhtar,mukhtar dinta,wannw iri kaidi ne mata suke da shi haka?,wanne irin halakakken kishi ne wannan?,yunqurin kisan kai fa kenan a taqaice,ta yaya zai ga sumayya?,ta ina zai fara neman yafiyarta?,da wanne ido ko fuska zai kalleta?,shi kansa baisan amsar dukkan wadan nan tambayoyi ba,haqiqa ya cutar da ita,ya cutar da zuciyarta,babu shakka shi yasa tun daga ranar da ya saketa bai sake samun sukuni nutsuwa ko farinciki cikin zuciyarsa ba,ya sani haqqinta ne Allah bazai taba barinsa ya huta ba bayan ya cutar da ruhin dake masa qauna ta domin Allah,sai kawai ya dafe kansa da hannu bibbiyu wanda yakejin kamar zai tsage,kuka ya saki mai tsuma zuciya hawaye na bin fuskarsa,fata yake ya samu sauqin azabar da zuciyarsa ke masa,fata yake ya samu salama qirjinsa ya bar suya,baisan wanne hukunci ya dace ya sake yiwa zainab ba,ba shakka wannan hukunci yana ji har cikin zucuyarsa bai gamsar da shi ba yayi kadan. _kuyi haquri da wannan_ *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 4⃣3⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *fazakkir fa innaz zikra tanfa'ul mu'uminin* *_KA TUNATAR DOMIN TUNATARWA TANA AMFANAR DA MUMINI_* _______________________________          Nan gefan abdallah ya kwanta yana ci gaba da kuka tamkar wani qaramin yaro,jin zuciyarsa yake kamar zata fashe,janyo abdallah yayi cikin jikinsa yana magana qasa qasa mai cike da kalmomin nadama yana ci gaba da kuka.           Sai da rana ta soma bugun naman jikinta sannan ta iya miqewa a daddafe ta yafa mayafinta,takalmi kuwa basu sakuwa a hannu ta riqesu hadi da jakarta,da qyar da jan qafa ta kai kanta titi ta tari adaidata sahu ta hau duk da cewa bata da qwadalar da zata bashi,qofar gidansu ya sauketa tace ya jira ta miqo masa kudin,tana sallama ta zube a tsakar gidansu tana maida numfashi,mamarta dake wanki bakin fanfo ta dago tana dubanta,mamaki ya cikata saidai bata da ikon tambayar ta abinda ya sameta,murya can qasa da qyar ta qwalawa qanwarta kira "Idan akwai naira dari jakarki fita waje ki bawa mai adaidaita sahu,mama dora min ruwan zafi" kowannansu da to ya amsa mata,maman ta saki wankin ta shiga kitchen.       Gashi tayiwa kanta sosai tamkar kai jego,tanayi tana runtse ido zuciyarta na zafi da quna,tana tuna yadda mukhtar ya dinga jibgarta kamar wanda ya sayi jaki mai taurin kai,dakinta ta koma ta shafe jikinta da man zafi ta samu ta kwanta sannan ta janyo wayarta tayi kiran abokiyar shawara da shaidancinta zinatu,tana dagawa ta buqaci ganinta,cikin sa'a kuwa tana kusa.       Cikin mintuna qalilan zinatun ta iso,suka gaisa da maman wanda ke zaune tsajar gida tana shirin dora abincin rana,da kallo tabi zinatun har ta shige dakin, "Lafiya?,na zaci zaki cemin gaki gidan mukhtar anyi kome sai nazo na sameki kina tashi da qyar haka?"baqinciki ya sake tokare zainab,cikin bacin rai ta soma fadin " ni malam zai ciwa kudi zinatu,ni zai ha'inta?,kalli jikina ki ga abinda mukhtar ya yimin duba zinatu" "La la lal" shine kawai abinda zinatu ke fada tana gyada kai "Garin yaya haka zainab" tas ta kwashe yadda komai ya faru ranta na quna ta qunduma ashar sannan ta dora "Ba sai na warke ba gobe gobe zamu koma wajen malam,wallahi sai na nuna masa ni 'yar tasha ce,duk abinda ya buqata nayi masa,kwana nayi yana sasukata duk warin dake tashi a jikinsa amma ban damu,shine ni kuma zai rainamin wayo an gaya masa ni gara ce,to wallahi Allah ya nuna mana gobe shege ka fasa" haka ta dinga bambami zinatu na tausarta da haka sukayi sallama da niyyar gobe da sassafe zasu dirarwa malam   *******  *******   ******        Tana zaune bakin gadonta tana ninke kayan sawarta a hanakali,tunanin abdallah na kai komo cikin ranta tun safe,tunda ta haifeashi basu taba rabuwa daidai da kwana guda ba banda sanda ta yayeshi sai wannan lokacin,yanzu haka watanni kusan shida kenan bata sanyashi a idanunta ba,gidan nasu yau shiru yake tun safe har yammaci,hajiya na bangarenta yau bata jin dadi,tunda ta kammala mata girki sai ta barta ta dan kwanta ta huta,karima ta hada kan yaran sun tafi sunan qanwarta data haihu,bata kuma bar nuwaira ba haka ta kada ta suka tafi tare,yaran baki daya sunci ado banda ita,a haka da sauqi tunda sumayya ta tattara dukkan yagaggun kayanta ta boye ta hanata sakasu tafiddo mata da wasu,haka karima ta haqura bayan sa'insar da suka sha da sumayyan,a yanzu bata da goyon bayan hajiya lukman kuma bai gari yayi tafiya bare ta hadata da shi.         Hudu da rabi na yammacin taji sallamarsa bakin qofar dakinta,a hankali ta daga kanta tana dubansa,ta mance yaushe rabon data sanyashi a idanuwanta tun kafin yayi tafiyar nan wadda ita kanta satinsa biyu kenan baya nan,sanye yake da shadda dinkin tazarce da hula saman kansa sai takalmi sau ciki,kafadarsa rataye da jaka ta matafiya,kallonta yake yana mata murmushi "Sannu da zuwa" ta fada tana gyara daurin dan kwalinta "Yauwa sumayya,ya gidan?" Ya fada yana zama gefanta yana mai ci gaba da kallonta "Lafiya qalau" ta fada tana hada kayanta waje guda tare da miqewa ta zura hijabinta tana shirin ficewa "A'ah,ya haka kuma,ya zaki fita ki barni" "Au da dawa nake barinka" ta fada tana gyara zaman hijabinta gami da kallonsa "Amma dai ai yau gidan babu kowa ko?,wa zai kula da ni?" Qugu ta riqe tana duban idanuwansa "Sai babu kowa cikin gidan sannan nake da amfani a gunka?,to gun hajiya zani na dubata na barota bata jin dadin"damuwa qarara ta gani ta bayyana kan fuskarsa karo na farko kan maganar da ta shafi mahaifiyarsa " subhaballahi tun yaushe?,muje na ganta"ya ajjiye jakarsa ya miqe yabi bayanta.        Ganin yadda ya damu qwarai ya sanyata cewa "Ba wani ciwo me mai zafi ba,qafarta ce kawai ta motsa"tayi furucin tana kallon gabanta,ajiyar zuciya yayi bai sake cewa komai ba har suka qarasa dakin hajiyar.       Tana kwance a falo da alama sallah ta idar,sosai tayi mamakin ganin lukman din wai tazo dubata,saidai bata nuna masa ba,suka gaisa fuskarta a sake,shi da itan duka wani dadi suke ji,sai gashi suna hira kadan kadan,hatta da sumayya sai data dinga jin dadi,ta dade da sanin dadin da iyaye ke da shi a gun d'a,hakanan zuwa yanzu tasan yadda uwa ke jin dadi a duk sanda ta daga ido ta kalli danta ko diyarta cikin kyakkyawan yanayi.      " kaje ka huta lukman ka dawo daga baya idan hirarce"hajiyan ta fada qasan zuciyarta a karye,don tasan ita kanta fada kawai tayi,saboda babu lallai ya sake zama da ita irin haka matuqar karima baqar daga ta dawi cikin gidan,ta fada ne don kawai kada ta shiga haqqinsa shi da iyalinsa,saboda zuwa yanzu ta yarda kura kuran da ta tafka a baya zunubinsu ke bibiyarta,amsawa yayi da to don shi kansa yanason kasancewa da matarsa,miqewa yayi yayi gaba wanda tilas sumayyan tabi bayansa don tana kunyar hajiya da ganin girmanta,bata son ta fuskanci komai daga gareta.         Gaba ya sanyata har zuwa dakinsa,karo na farko data fara taka dakin tun zuwanta gidan,kan gado ya zube yana dubanta "Hadamin ruwan wanka na gaji sumayya,sai ki yo alwala idan na fito zamuyi sallah" "To" kawai tace masa tana tunanin lokacin sallar magaribar ai baiyi ba aqalla akwai kusan awa guda nan gaba,sai daya shiga wankan sannan tayi alwalar kamar yadda ya buqaceta,a nan gabanta ya shirya duk da dauke kai da tayi sannan ya umarceta da tatashi suyi sallah,bata fuskanci abinda yake nufi ba sai suka idar da sallar taji yafara addu'a,take jikinta yayi sanyi,tsoro kuma ya cikata,tana jin ta yaya zata sake wata sabuwar rayuwar da wani sabon mutumin na daban ba wanda ta saba da shi ba?,saidai babu yadda ta iya din saboda tana da cikakkiyar masaniyar cewa da mijinta take tare wanda ya biya sadakinta shaidu kuma suka shaida,to shi kansa kamar baqo haka ya bijiro mata,sai daga bisani ya fara warewa a hankali,hawaye ne suka dinga gangaro mata,ambaton Allah ta dinga yi cikin zuciyarta.         Tana gaban madubi tana gyara gashin kanta bayan ta gogeshi tare da maida masa ribbom dinsa,shi kuma na zaune bakin gado yana kallonta,tabbas babu shakka kyauta Allah ya masa,a cikin mata hudu da ya aura har da karima cikon ta biyar din bai taba cin karo da mace kwatankwacin sumayya ba cikin duniyar ma'aurata,babu abinda ke kai kawo cikin qwaqwalwarsa sai yadda ya samu sumayyan cikin sahun mata na musamman wadanda suke 'yan kadan ne cikin daruruwan mata,amma sai ya fuskanci babu wata fara'a ko walwala sam a fuskarta,wanda hakan sai yaji sam bai masa dadi ba,a hankali ya kira sunanta ta amsa gami da waiwayowa tana daura dankwalinta ba tare da ta dubi qwayar idonsa ba "Sumayya,naga kamar bakya farinciki da ni ko?,nasan fushi kike da ni haushina kike ji,nasan dole kiji haushi bake bama koma wacece,don Allah don annabi kiyi haquri sumayya,wallahi ba laifina bane,bansan dalilin da ya sanya idan karima ta bani umarni ba nake kasa bijire mata,bansan me ya sanya ba nake tsananin tsoronta,duk da cewa a yanzu cikin kashi dari inajin babu kashi hamsin yana raguwa sosai,kiyimin haquri sumayya ina saka ran in sha Allahu komai ya kusa dai daita,ina miki godiya kan namijin qoqarin da kike kan gyaruwar gida na,ina sane kuma ina lura da komai,wasu kuma karima ta sanarmin sa niyyar na na taka miki birki,wallahi sumayya ban taba ganin mutumin dake taka karima itama kuma take shakka shakkarsa ba saike,kiyi haquri kici gaba da yin haquei komai mai wucewa ne in sha Allah" yanayin yadda yake maganar kawai ya isa ya sanar mata bilhaqqi da gaske yake,sai taji tausayinsa ya kamata,mutum cikakke kamar lukman amma sharrin mace ya maidashi wani iri "Babu komai,kowanne bawa da irin tasa QADDARAR  a rayuwa,Allah ya mana magani ya shige mana gaba,ka riqe addu'a kaima insha Allahu HASKE na nan zuwa....".       Bai kai ga bata amsa ba suka soma jin bugun qofa mai tsananin qarfi "ka bude lukman bude,ina fatan ba abinda nake zargi bane,wallahi idan har shine ka kuka da kanka"idanuwansa ya runtse gabansa na faduwa,sumayya dake zaune a nutse abinta ta soma nazartarsa da nazartar yadda ya tsorace,babu laifi da sauqi,tunda idan da dane da tuni ya arta da gudu yaje ya bude din " ka ambaci Allah cikin ranka hakan shi zai cire maka tsoron dake cikin ranka" "Allahumkhfinihim bima shi'ita"ya fara ambata daya daga cikin addu'ar da yaji hajiyansa na ambata tun bayan zuwan sumayya gidan aduk lokacin da taga karima.       Sumayya ce ta tashi ta isa bakin qofar dakin ta murza key din ta bude,karima ce tsaye bakin qofar rataye da jaka,shigowarta gidan kenan ta hangi motar lukman fake,ta tambayi mai gadi ya sanar mata kusan awanshi biyu da kenan da dawowa,dama tun tana gidan sunan taji hankalinta yayi gida,abun mamakin shine dukka yaranta na tsaye bayanta harta da qaramarsu,abinda ya sake daurewa sumayya kai kenan,nufinta a gabansu zata tijara babansu?,da yanayin da tazo mata taso itama ta tarbeta,amma ganin yaran ya sanya sumayyan murmushi "A'ah,maman nuratu,kece kuma da yaran baki daya haka?"harara ta balla mata sannan tace " munafukar Allah bake nake nema ba,babban magulmacin nake nema,matsamana mu shige"murmushi ta kuma yi tana gyada kai "Mai zai hana na barki ki shiga,ke da dakin mijinki,amma bai kamata ku dunguma baki daya ba,saboda bakisan a yanayin da zaku ruskeshi ba" ta fadi maganar tata ta qarshe qasa qasa yadda kariman ce kawai zata iya ji "Bismillah" sumayyan tace sa ita bayan ta janye mata jiki,sai data ja tsaki sannan ta wuce kamar zata bangajeta,yaran suka yunquro zasu shiga ta sha gabansu,ta dubi nuwaira wadda ta tabbatar itace mai hankalin cikinsu "Nuwaira,maza ku tafi dakinku ku sauya kaya,mamanku na fitowa,kama hannun basma ku wuce ko?" "To anty" ta fada tana kama amma da nuratu sukayi gaba,tsare sauran tayi da idanuwa tilas duk rashin kunyarsu suka bi bayan nuwaira daidai sanda maganganun karima cikin ihu suka soma tashi "Na shiga uku na lalace,yanzu lukman sai da ka kwanta da matarnan,lallau namiji d'an kunama ne,wayyo Allah yau naga ta kaina" ta fada tana dora hannu a ka tare da qarewa gadon nasa kallo,tsaye sumayya tayi harde da hannayenta tana kallonta,wato badon ta kora yaran ba nufinta gabansu zatayi wannan tambelan?,gaskiya ne dole wasu matan su janyo a dinga kiran mata masu naqasun hankali,takawa tayi ta dafa kafadarta wanda ya sanya karima waiwayowa tana dubanta "Meye na tashi hankali haka?,tun ranar farko kenan?,bakisan somin tabi bane yanzu aka soma?,ki godewa Allah ma da bakizo kin samu ana third round ba" ta fada tana kewayeta tare da komawa bangaran gadon ta soma gyara bedsheet din tana murmushi.        Ashar ta lailayo ta danqarawa sumayyan irin wadda bata taba jin irinta ba "Wallahi kinyi qarya kin kwana da yunwa duk malantar ubanki baki isa ba,duk wanda yaci tuwo da ni miya ya sha,wallahi sai kin gane kurenki,saikin gane shayi ba komai bane face ruwa,sai na cusa miki baqinciki fiye da wanda kika cusa min" sai ta waiwaya inda lukman ke zaune,tayi tsammanin ganin tashin hankalinsa qarara yadda aka saba sai ta ganshi zaune ko gezau "Kai kuma tashi mu wuce dakina" ta fada a tsawace "Ba inda zanje" ya fada yana jin shakka shakka na tasowa can qasan ransa yana qoqarin danneta,idanuwa ta zaro,jikinta ya soma bari,ba shakka alqadarinta gab yake da karyewa,kasa magana ma tayi sai kallonsa da takeyi "A'ah,ki wuce mana kije tunda dai shi din yace bashi zuwa" a fusace ta waiwayo ta tunkuda sumayyan wadda bata zata ba,hakan yayi sanadin da tayi taga taga zata fadi lukman din ya tareta,sai ta miqe daga jikinsa tana murmushi kamar ba ita aka yiwa ba "Babu komai,duk cikin haushi ne" qwallar baqinciki ce ta fara qoqarin zubo mata,da hanzari ta juya ta fice a dakim saboda batason sumayya ta gani har ta gane ta soma samun rauni,qofar sumayyan tabi ta kulle sannan ta dawi ga lukman wanda ta lura hankalinsa ya soma tashi,sosai ta zauna gabansa tana karanta masa abubuwan da suka dace har ya soma daidaita,sannan suka tashi suka sake komawa duba jikin hajiya wadda mamaki ya sake kamata ganin sun sake dawowar duk da taji shigowar karima gidan.      Qarfe goma da rabi suna dawowa daga wajen hajiya suka ratso ta falon,islam suka gani na matse hawaye ta tari gaban uban tana cewa "Abba kaga kasa mamanmu ta hada kayanta ko ta tafi,kuma tace ba zata dawo ba" wani matsanancin faduwar gaba ya ziyarce ya zaro ido yana dubanta "Tun yaushe?" "Dazu,naje dakinka baka nan" duk sai sumayya taji babu dadi,kada dai abinda ya faru dazun ya sata bar musu gidan,sai ya kama hannun yarinyar yana fadin "Ya isa,kada ki damu mamanku gobe zata dawo kinji,sumayya jeki da su suna dakinsu ina zato" amsa masa tayi,saidai qememe yarinyar taqi yarda ta kama hannuwanta haka suka tafi,koda ta shiga dakin suna zaune baki dayansu tsuru tsuru,duk sai taji tausayinsu ta dinga jin babu dadi,da fari duka qin sakin jikinsu sukayi da ita sai nuwaira kawai,amma ganin nuwairan ta saki jiki sai basma qaramar cikinsu itama ta ware,daga baya nuratu ta sake itama,sai islam kawai da tayi kicin kicin taqi shiga sabgarsu,ba ita ta barsu ba sai da taga sunyi bacci sannan ta musu addu'a ta bar dakin. Sumayya na wucewa wayarsa ta dauki ruri,lambar karima ce hakan ya sanyashi dagawa cikin hanzari yana cewa "Haba karima,haba karima,meye haka din da zaki bar yaranki ki kwashi kaya,yaji da girmanki da komai" "Saurara ba wannan na kiraka ka gaya min ba,kiranka nayi na gaya ma ka sanar da wannan matar taka diyar malamai masu kwanan buzu cewa,ta bar murna karanta ya kama kura,babu inda zani ina nan dawowa,kuma dawowata ba zata yi mata dadi ba wallahi wallahi sai ta gwammace kida da karatu,don babu wata 'ya da zan bari ta shigarmin rayuwa ba tare da na nuna mata kuskurenta ba,kuma kada ka soma wahal da kanka kace zaka nemeni don ba samuna zaka yi ba,har sai randa na dawo da karan kaina,ina fata ka gane"qit ta datse kiran sai yabi wayar da kallo yana kada kai aljihu ya maidata yana amsa sallamar da sumayya tayi masa. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 4⃣4⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *innal laha la yazlimu misqala zarrah* *_haqiqa Allah baya zalunci daidai da qwayar zarra(ko qasa ma da abinda yafi qwayar zarra qanqanta)*_ _______________________________      Gefansa ta zauna cikin rashin jin dadi,tana jin kamar ta raba yaran da mamansu ne,ta dubi lukman "Ya kamata zuwa gobe kaje ka dawo da mamarsu islam,kada a ja abun yayi nisa don Allah,yaran na buqatar mamarsu" kai ya kada baison gaya mata wani abu da zai daga mata hankali,a yanzun da karima ta dan tura ta bar gidan sai yake jin kamar an zare masa wata qaya data tsaya masa a maqoshi "To naji" kawai ya fada.      Kwana biyu tana masa mitar yaje ya dawo da karima arana ta uku yace kada ta sake masa maganar baiso,idan lokacin dawowa yayi zata dawo,ai ta saba ba yau farau ba,hakan ya sanya ta tsuke bakinta,hankalinta ya dan kwanta ganin yaran basu tada hankali sosai kan rashin dawowar mamansu ba.        Cikin kwanakin da suka biyo bayan tafiyar karima baki daya gidan yayi dadi,kada ma lukman hajiya da nuwaira suji labari,da fari sumayya ta fara fuskantar matsala daga yaran saboda qarancin tarbiyya da suke da ita,amma sai ta jure tayi amfani da hikima irin tata,a hankali ta fara janye qananan,nuratu basma da syyada,islam ce kawai ta taqi biyuya,ta soma kwaso halin uwarta tsaf,hakan yasa ta tattarata ta watsar gefe,zasu hadu suci abinci tare,suyi karatu,ta basu labarai na annabawa da sahabbai,suna bala'in so ta basu tarihi,har rigima suke idan tace ta gaji,sosai ta shiga jikin yaran suka soma shaquwa da ita,ta koya musu abubuwa da dama wadanda ya kamata ace sun iya amma basu iya ba,kamar alwala,sallah,sallama idan zasu shiga guri,addu'ar sanya kanya,addu'ar bacci da tashi daga bacci,addu'ar shiga bandaki data fitowa,addu'ar fita daga gida da ta shigowa da yin bismillah da hamdala kafin da bayan gama cin abinci,su kansu yaran dadi sukeji,nuwaira tafi kowa murna takance "Anty dama tuntuni kema 'yar gidan nan ce,ai da tuni nayi saukar qur'ani ko?" Dariya takanyi tace "To ai yanzun ba gashi na zo ba?,kuma zakiyi ne in sha Allah",tarbiyya take basu sosai mai wuyar bari ko mantawa,tana musu ne bilhaqqi fisabilillahi,don har ga Allah tana son yaran,ko ba komai babansu da kakarsu na gwada mata qauna.       A hankali sai itama islam din ta fara biyuwa,ta shige cikinsu,idan kaga sumayya da yaran zakayi zaton qannenta ne,dama gata gwanar son yara,abun ya yiwa hajiya dadi,wani lokaci har takan tsinci kanta da addu'ar kada Allah yasa karima dawo,don ita kanta yanzu anan bangaren take wuni sai dare zata kwashi jikokinta suje su kwana tare da ita a can,a yanzu sumayya ta koya musu qaunarta da ganin girmanta,ta bangaren lukman kansa yana mamakin yadda hankalinsa yake a kwance,sau tari ma sai ya mance da wata karima,kwanciyar hankali da nutsuwa ya samu sosai irin wadda bai taba samun irinta ba tunda ya fara aure,ba shakka sumayya ta dabance,zai kuma yi fatan kasancewa da ita har qarshen rayuwarsa,hatta da mai gadi da mai aikin gidan sunga sauyi,sun kuma ga banbanci,suma sun samu 'yanci.        Kwanci tashi har aka kusa shafe wata biyu ba motsin karima,sam sun mance ma basa maganarta,banda yaran da wani lokaci zasu dan tada zancanta shikenan an wuce gun,ta maida qaunar dake tsakaninsu baki daya saboda haka nuwaira ta samu matsayinta na babba a gidan,a yanzu takan iya tsawatarwa dukkaninsu sabanin daa da bata isa ba,basma ma na iya dungurinta ta wuce,da tace musu abu babu kyau zasu daina saboda ta gaya musu wanda keyin abinda babu kyau Allah zai sashi a wuta,ta wassafa musu yadda wuta take dai dai da tunaninsu yadda zasu gane haka ma aljanna,don haka da tace abu da kyau tofa zasu shiga yi saboda sun san aljanna sun san wuta.        Da kanta ta nemi lukman kan ya sanya yaran islamiyya,saboda duk wanu ilimi da zai basu matuqar babu karatun addini aikin banza ne,ya yarje mata kan ta nema musu ya amince,da kanta ta duba islamiyar dake qarshen layinsu,ta gamsu da yanayin karatunsu saboda haka ta yankar musu foam,cikin kwanakin da basu wuce uku ba aka gama musu komai har dinkin unifoarm suka fara zuwa,su kansu yaran murna suke da fara zuwa makarantar,idan suka dawo tare suke bitar dukka karatuttukansu,wani dadi hajiya da lukman din ke ji,sai yanzu suka gane tabbas ashe da rayuwa suke cikin duhu sai da Allah ya kawo musu SUMAYYA HASKE.     *KUNDIN QADDARARTA*       Ya sake bude mata shafi ne daga lokacin da karima ta cika wata biyu da rabi da barin gidan,sauyin data fara gani daga lukman din,kusan tun bayan tafiyar karima sumayya ta dorashi kan ibada saboda gunewa faruwar wani abu,cikin sati gaba daya ta fuskanci ya zama mai son jiki da wata muguwar kasala,da qyar yake iya sallolinsa na farilla balle akai ga na nafila,idan qur'ani suka dauko zasuyi tilawa yadda suka saba sai ya soma gyangyadi daga nan sai bacci,idan sallar asuba ce kullum sai ya makara sai tayi da gaske,duk wani abu na ibada ya zama very lazy akansa,tun abun na bata mamaki har ya soma bata tsoro,hakan ya sanya ta samu hajiya da maganan,sam bata kowa komai ba tace sumayyan taci gaba da haquri da kuma qoqarin ci gaba da dorashi a hanya har ya daina,kuma itama zata yi masa fada      A hankali sai abun ya soma cin tura,hatta idan yana bacci bai da aiki sai kiran sunan karima,idan ya tashi kuwa washegari haka zai yini babu wannan walwalar sam.haka kawai yake jin rayuwarsa da zuciyarsa cikin takura da qunci,ji yake kamar yana cikin wata kurkuru,burinsa kawai yaga karima cikin gidan,saidai duk da haka bai taba furtawa sumayya ba.       *_Bayan sati d'aya_*          Bayan sallar isha'i ne dukkansu suna zaune a falom gidan banda hajiya dake bangarenta saboda yau da wuri ta kwanta,sumayya da nuratu da nuwaira na zaune tana koya musu aikin gida(assigment)da aka basu a makaranta,basma na saman kujera tana bacci tun sanda suka gama cin abincin dare,sai islam dake kwashe kwanukan da suka ci abinci da su tana shigarwa kitchen.        Lukman ne ya fito falon a gaggauce wanda tunda ya dawo daga kasuwa yana cikin daki bai fito ba sai yanzu,hannunsa riqe da dan mukulli,daya hannun nasa kuma riqe da hularsa,kana ganinsa kamar wanda aka jefo ko aka tunkudo,daga kai sumayya tayi tana dubansa sanda ya giftasu zai fice ganin bai cewa kowa komai ba "Abban nuwaira" waiwayowa yayi yana dubanta tare da amsawa "Ina zaka fita haka tara na dare?" Ta fada a marairaice "Sorry airphort zani,yanzu zamu dawo" ya fadi yana ficewa da sauri jin wayarsa na ringing,kanta ta maida suka ci gaba da assigment din da yaran,hakanan taji gabanta na yawaita faduwa,hasbunallahu wa ni'imal wakil ta dinga maimaitawa,suna gamawa ta tattara yaran duka suka tafi dakinsu,sai da kowa ya sanya kayam baccinsa ya karanta addu'ar kwanciya bacci suka kwanta sannan ta rufo musu dakin ta koma nata dakin,alwala tayu tayi shafa'i da wutirinta sannan ta zauna ta karanta suratul mulk,har ta gama abinda take bata ji shigowarsa ba,saboda haka ta sanya hijabinta ta nufi bangaren hajiya.       A kashingide ta sameta riqe da carbi,ganin sumayyan ya sanyata zama tana murmushi "Yanzu kuwa nake zancanki a zuciyata" itama murmushin take tana cewa "Hajiya baki bacci ba?" "Kin ganni nan wlh banyi ba,gabana ne yake ta faduwa sai na tuna dazu banyi waraddallahu ba,sai nake yinta yanzu (waraddallahul lazina kafaru bi gaizihim lam yanaluu khairaa,wa khafallahul mu'umininal qital,wa kanallahu qawiyyan aziza,ana karanta ta ne qafa dari bayan sallar asaba kariya daga dukkan kaidin wani maqiyi dake nufarka da shi in sha Allah)" "Ai gwara hajiya" ta fada tana tunanin faduwar gaban da itama take ji tayi dai dai data hajiya kenan "Ina lukman din kuma?" "Ya dan fita ne hajiya yara kuma sun kwanta saboda makaranta goben" "Sannunki kedai sumayya,Allah yayi albarka" "amin hajiya"ta fada tana murmushi kanta a qasa,shiru ne ya biyo baya kafin su soma taba hira kadan kadan,ganin har sha daya na dare tayi ya sanyata yiwa hajiyan sallama ta koma sashenta.       Tana zaune har sha daya da rabi sannan taji muryar lukman,a hankali ta tashi ta leqa,shine a gaba janye da akwati daya hannun jaka,sai KARIMA dake biye da shi a baya,da sauri ta saki labulen ta koma da baya tana kiran sunayen Allah,sannu a hankali nutsuwa ta saukar mata,sai ta daura alwala ta kwanta,don jikinta na bata lukman ba zaya nemeta a yau ba.       Ilai kuwa bata sake jin motsinsa ko na karima ba har bacci yayi awon gaba da ita.    ******    *******    *****       Washegari yadda suka saba haka tayi bata fasa ba,ita ta tashi yaran baki daya sukayi sallar asuba,sannan ta dafa ruwa mai zafi islam ta fara yi sannan nuwaira ta dinga yiwa qananan tana tura su islam na shiryasu ita kuma tayi daga qarshe,sumayya kuma na kitchen tana hada breakfast da wanda zasu tafi da shi makaranta,abinda dukka a da basu saba yi ba amma a yanzu ya zame musu jiki.        Sun shirya tsaf suna karyawa ya zagaya ta buga dakin karima don taga idan sun tashi ta tura yaran su gaida mamansu kan su wuce,saidai har ta gama bugunta ko tari bata ji anyi ba,abinda bata sani ba lukman na jin bugun,ya kuma san sumayyarsa ce,kamar ya zura a guje ya bude saidai ina sam bai isa ba,saboda bai samu umarni ba,tunda ta dawo a jiyan qasan zuciyarsa ke a cunkushe cike da baqinciki bacin rai da tsananin tsoronta,amma a fili tsantsar farinciki ne da tsananin biyayya bayyane a fuskar tasa,abinda zai baka mamaki tunda ta dawo bai taba kwatanta tambayarta inda ta tafi da aurensa a kanta ba kuma ba tare da izininsa ba har na tsawon wata biyu ba,a lokacin ma yana bandaki yana wanke mata tana son shiga wanka saidai ya hada qura a tsawon wata biyu da bata nan tunda ba wani ke shiga ba gun nata na a rufe ne.        Dawowa tayi inda suke kowa ya kammala mai adaidaitan dake kaisu ma ya iso ta dubesu " mamanku fa ta dawo jiya da daddare"ta tsammaci zata ga tsantsar farinciki a fuskokinsu,sai taga babu yabo ba fallasa,babu wani zumudi ko doki,nuwaira kuwa tsoro da fargaba ne ma ya mamayeta,a haka ta rakasu suka fice sannan ta dawo ta gyara falo zuwa kitchen ta barwa mai aikinsu wanke wanke idan ta iso tayi wanka ta leqa bangaren hajiya,sai ta sameta tana bacci,saboda haka ta mata 'yan gyare gyarenta ta fito ta barta ta dawo falo ta zauna tana jira sha daya da rabi tayi ta karya,sai ta kunna t.v tana kallon arewa 24 don ta debe mata kewa,zuwa yanzu sum shaqu sosai da yaran,idan basa tare duk sai taji babu dadi kasancewarta mai son yara.        Tana jiyo qarar bude qofar karima amma bata maida hankalinta kai ba har sai da taji cikin taqama tana fadin "Ina yara na" cikin ladabi kamar bawa da uban gidansa taji lukman na cewa "Eh sun tafi makaranta ai sumayya ta turasu" cikin harzuqa tace "Eh wato suma an shige musu za'a shanyesu a rabani da su kenan?" Sai ta saki wani shu'umin murmushi tana kada kai "Mu zuba mu gani,muje ka rakani naga hajiya nata salon ita kuma" ta fada tana yin gaba,jiki na rawa yana tafe yana waiwayen sumayya yabi bayanta,kai ta jinjina bayan fitarsu "Innalillahi wa 'inna ilaihi raji'un" ta fada tana kada kai ganin hannun agogo nason komawa baya game da lamarin lukman din. Zuwanta gun hajiyan ta taddata fiye da yadda ma ta barta,don fada hajiyan ma ta mata kan dalilin tafiyarta wani gu bayan tana da aure,sosai hajiyan keji qarfin zuciyarta sam babu wani dar da taji balle taji tsoron karimar,sai lokacin ta yadda lallai idan kayi sakaci da addu'a babu abinda ba zaya iya faruwa da bawa ba duk da cewa akwai QADDARA amma babu abinda ke sauya qaddarar irin ADDU'A. Ko da rana da yaran suka dawo sun gaidata,baki ta saki tana kallon yadda suka sauya baki daya,tana kallon yadda suke girmama nuwaira da islam,lallai sumayya ta sauya mata yara,ya akayi bata sanya an musu farraqu ba ita da au ta barsu suka shaqu haka,tana gani suka sauya kayansu zuwa na islamiya bayan sunci abinci,suna sanya hijabansu sumayya na tsakiyarsu tana hada musu litattafan islamiyar su kariman ta banko qofar dakin tana huci,tsayawa tayi tana dubansu fuska a tsuke,sumayya data kalleta saita maida kai taci gaba da abinda take "Laaa,mama bakiyi sallama ba fa,kuma babu kyau shiga gu ba sallama" nuratu ta fada,mamaki ya kama kariman sai ta waiwaya tana kallonta amma sai ta wayance da cewa "Ku cire kayan nan,babu wata makaranta da zaku sake zuwa daga dawowarku daga boko ko hutawa bakuyi ba" islam ce ta maqe wuya tana cewa "Mama ki barmu muje,idan mun dawo ma huta din,idan kana fashi fa ana wuceka a karatun" ido ta kuma zarowa mamki na sake kasheta,lallai sumayya tayi amfani da irin surkullensu ta rabata da yaranta,tsawa ta daka musu tana cewa "Don ubanki da ni kike jayayya,ku cire kayanku nace babu inda zaku" sumayya ce ta bar abinda take ta tako zuwa inda take tana cewa "Haba maman nuratu,meye na zagi har haka?,ina cewa ke zaki fi kowa farincikin zuwan yaranki makaranta,ba girmanki bane" sai ta waiwaya ga yaran da sukayi carko carko suna kallon karimar "Maza ku wuce ku tafi mamarku ta haqura" da sauri suka fice kuwa daya bayan daya,sai da suka kammala ficewa tas sannan karima ta kalli sumayya "Yaro man kaza,ke da su baki daya baku da bambanci a gurina,lokaci na baki shi nake jira" tana gama fada ta fita "Allah ya fiki,Allah ya isar min da ke akan dukkan wani nufinki,alkhairin ubangiji nake nemawa rayuwata" ta fada tana gyara dakin yaran da suka bata tare da killace kayan makarantarsu gu guda kafin su dawo su wanke Baki daya sai aka koma 'yar gidan jiya kan halayen mukhtar,yayin da bangare guda sauyawar yaranta da hajiya ke ciwa kariman tuwo a qwarya,saidai ta kammala dukkan wani shirinta na maida hannun agogo baya ranar kawai take jira,wanda hakan ya sanya ta sanyawa kowa ido,wannan kuma ya bada damar da shaquwa mai qarfi taci gaba da gudana tsakanin sumayya yaran da hajiyar. ****** ******* ****** Qarfe daya na rana ne wanda saika dauka qarfe takwas ne na safe saboda yanayin sanyin da ake zabgawa a garin,tuni ta kammala abincin rana ita da mai aikin gidan qwaya daya saboda biyu na rana yaran zasu dawo ta baiwa kowa haqqinsa,kasancewar tunda karima ta dawo gidan bata ko dubi kitchen ba. Tayi sallar azahar dinta sai ta qudundune kan gado kafin yaran su dawo,bude qofar dakin nata da akayi shi ya sanyata daga kai ta kalli qofar,karima ce cikin kwalliya da daurin ture kaga tsiya,jambaki kamar zai digo daga bakinta,itace a gaba lukman na biye da ita janye da trolly,sallama kariman tayi wadda ta bawa sumayya mamaki,qarasowa tayi bakin gadon tana duban sumayya "Mijinki ko mijina?....oho koma meye,shi na rako ya miki sallama zaiyi tafiya,wadda itace zata kasance sallama ta qarshe tsakaninku" ta qarashe tana dariya dariya,ta waiwaya ta dubi lukman dake tsaye,fuskarnan tamkar zai sanya kuka ,amma tana dubansa sai ya saki murmushi "Bari na baku guri ko don kuyi sallama sosai" sai ta juya ta fice. Sakin akwatin yayi ya qaraso inda take ya zauna gefanta,sai ta tashi daga kwanciyar ta zauna sosai tana kallon fuskarsa gabanta na faduwa "Kiyi haquri sumayya,kiyi haquri don Allah,ba laifina bane sumayya,haka nan nake jin bazan iya ci gaba da ke ba,haka kawai nake jin idan naci gaba da zama da ke akwai cutarwa,sumayya ki yafemin akwai QADDARAR dake bibiyar rayuwata,ina sonki har cikin zuciyata amma bazan iya zama da ke ba...." "Ya isa lukman,ka fadi abinda kake son fada,ka fadi a wuce gurin" ta fada cikin rawar murya,bai kai ga cewa komai ba karima ta sake shigowa dakin,cikin daga murya tace "Wai me kakeyi ne hakan har yanzu,kasan dai jirgi baya jira saidai a jirashi ko?" Ta fada tana tsareshi da ido,cikin sanyi jiki ya sanya hannunsa a aljuhunsa ya fiddo takarda a ninke ya miqa mata,hannu kawai ta sanya ta karba,koda baiyi mata bayani ba tasan takardar meye,saboda haka bata da buqatar budeta,kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki haka ya miqe yaja akwatinsa yana waiwayenta har ya fice karima ta rufa masa baya. Cikin dogon tunanin da batasan tsawon lokacin data dauka cikinsa ba taji islam na girgiza kafadarta "Momy,tun dazu muke sallama shiru baki amsa mana ba" sai ta daga kai ta kallesu,dukkansu suna tsaye gabanta suna kallonta cirko cirko,alamun damuwa duka sun bayyana kan fuskokinsu,tausayinsu sai ya lullubeta duk da a yanzu tafi jin tausayin kanta,don nasu mai sauqi ne,qwalla ta cika mata idanu amma sai tayi ta maza ta hadiyeta,ta qaqalo murmushi tana cewa "Wa'alaikumus salam warahmatullahi wabarkatuhu,banjin sallamar taku bane,muje maza a shirya yau kun dawo a makare ko?" Ta fadi tana saukowa daga kan gadon,biyo bayanta sukayi kowa na bata labarin yau na makaranta,tana shiryasu tana biye musu,yayin da qarqashin zuciyarta ke a cunkushe,tausayinsu naci gaba da lullubeta musamman nuwaira,duk da tana da yaqinin insha Allah ba zata tozarta kamar baya ba tunda a yanzu an samu kan 'yan uwanta da kakarta,sosai tayi jarumtar danne damuwarta,saidai duk da haka nuwaira sai da taso dagota,don ta saci kallonta sai daya taga tana dauke qwalla,duk sai yarinyar ta tsargu taqi sakin jiki,duk inda sumayyan tayi tana biye da ita da idanu,har suka gama dabdalarsu bataji motsi ko giftawar karima ba,da haka ta shiryasu suka fice,ko sanda zasu fita din sai data juyo ta sake kallonta ita kuma ta rakata da murmushi. Sai data fara hada kayanta sannan taji kuka ya qwace mata,bakin gado ta koma tayi kuka san ranta sannan ta hada duk abinda zata buqata cikin akwati ta zira hijabinta ta janyo akwatin nata bayan ta saka takalmanta. Sallama tayi bangaren hajiyan ta amsa mata tana murmushi tana tsokanarta "Yau sanyi ya boyeki ko sumayya" ganin yanayin fuskar sumayyan ya katse fara'ar hajiyan,gefan hajiyan ta zauna kanta na a qasa "A'ah lafiya kuwa sumayya?" Cikin rawar murya tace "Zuwa nayi muyi sallama hajiya zan tafi" cikin tashin hankali tace "Sallama,tafiya zuwa ina?" Kasa bata amsa tayi saita miqa mata takardar dake nade a hannunta,da sauri hajiyan ta karba tana dubawa,salati ta saki."yaushe hakan ya faru?,me yasa ban gaya min ba dazu yamin sallama zai je ghana,sumayya...."sai ta rasa abinda zata fada "Haka lukman zaimin?,to wallahi nima bani zama a gidansa,yaci gaba da zama da karima ita kadai" Cewar hajiyan,sai kuma ta saki kuka,da sauri sumayya ta goge nata hawayen ta kama hannun hajiyan tana girgiza kai "A'ah hajiya don Allah ki daina masa kuka,zaki sake jefashi cikin wani bala'in bayan bai fita daga wanda yake ciki ba,hajiya,lukman danki ne ke kika haife abinki,ke kika san zafinsa,idan bakiyi yaqi a kansa kin saita rayuwarsa ba duk duniya wazai miki wannan aikin,hajiya ke zaki zauna kici gaba da aikin da na fara"wajen mintuna ashirin ta kashe tana yiwa hajiyam bayani tare da jan hankalinta sannan ta fara samun nutsuwa " naji sumayya,nan zaki zauna gurina,tilas na nemo lukman duk inda ya tafi,dole ya dawo da ke,akwai sauran igiya daya tsakaninku"kai ta kada tace "A'ah hajiya,kada ki tilas ta shi wanda hakan zai iya haifar da wani abun daban,babu abin buqata a yanzu fiye da dawowarsa kan hanya,Allah ne mafi sani kan dalilin faruwar hakan,na yadda cewa wannan ma na cikin QADDARAR rayuwa ta,koda yaushe Allah nake miqawa zabi kan rayuwata ya zaba min abinda yake gani shine dai dai ba abinda ni nake ganin shine dai dai ba,na gode masa ma da ya bani ikon fiddaku ke da su islam daga halin da na riskeku,abun da nake so hajiya kimin alqawari shine,ba zaki sake zubda masa qwalla ba,ba zaki saki addu'o'inki ba,ba zaki bar su islam su koma irin rayuwarsu ta baya ba,sannan ba zaki gaji da nemawa lukman kubuta da tsiraba,wannan yaqin naki ne,duk na dora miki hajiya zan kuma tayaki da addu'a" "Insha Allahu sumayya in sha Allahu,Allah ubangiji ya albarkaci rayuwarki,kuma in sha Allahu ina mai tabbatar miki da yardar Allah zaki sake dawowa gidan nan,duk inda lukman yake zan nemeshi zan nemeshi ya dawo da ke" ta fada zuciyarta a raunane,cikin irin wannan yanayi mai ban tausayi sukayi sallama. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 4⃣5⃣ _____________________________ *wa asa an takrahu shai'an wa huwa khairul lakum,wa'asa an tuhibbu shai'an wa huwa sharrul lakum,wallahu ya'alamu wa antum la ta'alamun* *_SAU DA YAWA ZAKU QI ABU AMMA ALKHAIRI NE A GURINKU,SAU DA YAWA ZAKU SO ABU AMMA SHARRI NE A GURINKU,HAQIQA ALLAH SHINE YA SANI AMMA KU BAKU SANI BA_* ______________________________ *ZAINAB* Kamar yadda suka tsara ita da zinatu hakan ce ta kasance,qarfe goma na safiyar washe gari a gidan malam ta yi musu,duk da dan uban ciwon da jikinta ke mata amma sam bata kula ba,burinta kawai ta ganta gaban malam din,da yake safiya ce bata taras da mutane da yawa ba a gidan mutum daya ne ya fito suka shiga. Kamar ko yaushe mutumin da suke kira da malam ya kuma shiga rigar malamai yayi bake bake yana zaune kan buzu,yaci babbar riga da rawani gefe litattafan addini jere wadanda ko zaka kasheshi layi guda bazai iya karantawa ba balle har ya iya gane me ya karanta din. "Zainabu abu,ina fata buqata ta biya don na ina nan ina ta kewarki,ban manta daren mu ba na......" "Dakata dalla malam,ni zaka yaudara?,kayimin aikin banza lalataccen aiki da tunda na fara yawon bin malamai ba'a taba min matsiyacin aiki irinsa ba,to wallahi da sake bazai yiwu ba"turbune fuska yayi ainun yana dubanta " ke kisan fa agaban wa kike,bana son tsiya"sake harzuqa tayi tana cewa "Eh dole mana ka fadi haka,bayan ka gama amfana da albakatun jikina ko?" "Ke sha shashasha,ai ba kanki farau ba,kuma ke kika kawo kanki,dama tunda kika rabu da Allah babu irin qazantar da ba zaki fada ba,kinga ki fadamin abinda ke tafe dake kada ki batamin lokaci customers na tafe a hanya kada ki bata min aiki" cikin masifa ta sake takowa gabansa tana dubansa "Amma malam bansan kai ba qaramin dan akuya bane sai yau,to wallahi baka isa kaci bulus ba,ni babu wanda ya isa ya takani wallahi na qyaleshi ban dau fansa ba ko uban waye kuwa" dariya ya barke da ita ya dinga qyaqyatawa har suka saki baki suna kallonsa "Saidai cin bulus na gaba,bulus kuma ai na gama cinta tunda na hadaki da CUTA MAI KARYA GARKUWAR JIKI?" wata saukar guduma sukaji bisa kawunansu,ba zainab kadai ba hatta da zinatu "Cuta mai karya garkuwar jiki!" Zainab ta tambayeshi cikin qaraji,dariyarsa ya ci gaba da yi yana kada kai "Qwarai kuwa,wannan tsaraba ce da muke baiwa dukkan macen data bijirewa Allah,ta zabi biyan buqatar duniyarta akan ta lahira" sulalewa kawai tayi a gun,zinatu ta fasa kuka tayi kanta,ganin suna neman tara masa jama'a ya sanyashi samo mai adaidata sahu ya dorasu ya saita musu hanyar asibiti. *MUKHTAR* Tun ranar da sirrin ya yaye masa baki daya ya sauya,tamkar ba mukhtar ba,hatta da abdallah sai da ya samu sauyi da naqasu wajen kulawar da yake samu,ya kusa wata bai zuwa ko ina yana gida,sai abdallah ya matsa da rigima yake fita waje ya dan tattaka da shi a qafa ya dawo,babu abinda ke bijiro masa sai tausayin sumayya da tunanin da wanne ido zai kalleta?,ko wane minti daya tana dawo masa ne da irin abubuwan da ya aikatawa sumayyan,tun daga auren zainab zuwa ranar rabuwarsu,wasu abubuwan gani yake tamkar a mafarki suka faru ba a zahiri ba,kuka kam ya yishi sau babu adadi,baisan iyaka ba,yana so yaje ya warwarewa su malam komai amma yana jin wata 'yar banzan kunya da nauyinsu wadda a da bai jita ba,kusan ya mance kwanansa nawa rabonshi da gidan,saidai ya zame masa dole yaje gidan don sauke nauyin dake kansa. **** ****** ***** Zaune take gefan gado sanye da hijabinta tana ci gaba da sharce hawaye,tsahon kwana biyu da faruwar lamarin amma ta kasa tsaida hawaye a idanuwanta wanda ita kanta ta rasa dalilin haka,kukan nata ya dadu ne tun bayan gama wayarsu da anty dije wadda kejin tamkar a kanta hakan ya faru. Halima ce ta shigo dakin "Yaya sumayya kije inji malam" jikinta ya qara sanyi a zatonta magana a kanta ne bata qare ba,duk da cewa babu abinda ya fada face yi mata addu'a bayan ya gama saurarar rayuwarta a gidan mukhtar,fada daya yayi mata na rashin neman taimako daga wanda tasan ya fita gogewa da sani kan irin wadan nan lamuran,al'amura ne da kake buqatar addu'a koda daga wajen iyayenka ne daga bakunansu,tunda addu'ar tasu karbabbiya ce a wajen ubangiji. Cikin sassanyar murya tayi sallama a falon nasa,da abdallah idanunta suka soma tozali,ko kadan batayi tsammanin ganinsa a lokacin ba shi ko mahaifinsa,ai da gudu ya baro jikin mukhtar din ya iso inda take tsaye ya riqeta yana kiran amma na,jikinta da zuciyarta baki daya a raunane suke,hakan ya sanyata zubewa shima ya fado jikinta,sai ta rungumeshi a jikinta tayi qas da kanta hawaye ya balle mata a boye,cikin dabara take shareshi. "Sumayya" taji malam ya kirata "Na'am" ta amsa murya a sarqe "Ga mukhtar nan yazo neman gafararki kan abunda ya faru tsakaninki da shi a baya,wanda mu nasan ya riga da ya wuce a gunmu saidai tsakaninku dai" ya fada yana miqe ya fice ya turo halima ta zauna da su tunda ya sani a lokacin bai halatta ya barsu su kebe ba,har a sannan tana matsayin matar lukman har zuwa sanda ta kammala idda. Dauke idanunsa yayi da sauri daga kanta saboda tunawa da yayi matar wani ce,rabonsa da ya sanyata a idanunsa ya mance,tun kafin aurenta. "Sumayya,nazo gareki a matsayina na mutum mai tarin laifi,a matsayina na mutumin da yafi kowa laifi duk duniya a gurinki,nasan cewa kalmomina basu isa su haqurqurtar da ke kan abinda na aikata a gareki ba cikin jahilci,gaggawa da yanke hukunci cikin rashin bincike,tun ranar da na san gaskiyar lamarin naso neman gafararki amma hakan bazai yiwu ba saboda kina gidan wani,yanzun ma mama da malam mazo sanarwa ya gayan kina kusa,don girman Allah sumayya na roqeki ki yafemin,koda kuwa wannan ne alfarma na qarshe da zakiyimin,babu shakka zainab ta zalunce ni ta zalunceki ta kuma zalunci danmu,kimin afuwa don Allah" tsam ta miqe ba tare da tace komai ba ta dauki abdallah ta fice daga falon,sai yayi qasa da kansa zuciyarsa na masa zafi,yayin da nauyi ya kama halima,sai ta miqe tabi bayan sumayya itama. Ranar bacci barawo ne kawai ya dauketa,zafi goma da ashirin ke bugun zuciyarta,ta duba ta laluba kaf rayuwar aurenta babu wanda ya ruguza farincikinta sai mata 'yan uwanta,babu abinda ta aikata musu don kawai sun hada miji?,me yasa kishiya ta zame mata qalubale cikin rayuwarta baki daya?.         Sannu kwanaki suka dinga hada satittika,satittika suka hadu suka bada watanni,ta miqawa Allah dukkan lamarinta baki daya,ta yadda babu bawan da ya isa ya gujewa qaddararsa,watanni uku cif cif iddarta ta cika,ta godewa Allah bisa baiwa da ni'inar lafiya da ya bata,ta watsar da dukkan wani abu ta rungumi rayuwarta,riqon Abdallah ya dawo wajenta,hakanan taci gaba da makarantarta na koyon sana'o'i,wanda zuwa lokacin ta qware sosai wajen iya humra kwalakca da turaren daki na kaya da na tsuguno,ya abbakar shi ya bata jari ta soma gwadawa,Allah kuwa ya sanyawa abun albarka don ciniki take sosai,don kana shigowa gidansu zakasan ana saida humra balle kuma jikinta,nutsuwa sosai ta sake zuwa mata,wani girma da hankali na musamman ya soma gameta,mukhtar kuwa har yau bata yarda ta sake ganinsa ba ma bare ya dagula mata lissafi.     ****   *****   ******   *****       Qarfe bakwai na bayan sallar magariba ta gangaro cikin layinsu abdallah na sabe a kafadarta,tun daga makaranta ta wuce gidan anty maryam qanwar mama sai gab da magariba ta fito.        Tana gab da gidan nasu ta kula da motar wadda ko daga bacci ta tashi zata iya ganeta,motar mukhtar ce,sai ta dauke kai tana qoqarin wucewa cikin gidan,saidai abdallah dake kafadarta wanda ya soma zillo ganin babansa yaqi bada hadin kai,tilas taja tunga ta saukeshi da niyyar ta wuce ta barshi a gun,saidai tana dagowa daga durquson da tayi ta tsinci mukhtar din tsaye a gabanta "Zan wuce malam" ta fada ranta a hade "Kiyi haquri malama" ya fada da irin salon muryarta,kicin kicin tayi ganin yadda yake son maida lamarin wasa "Ka bani hanya da Allah kana batamin lokaci bana son shirme" tsit yayi yana kallonta,ita kanta sai taji kalma ta mata nauyi,don haka ta basar ta hanyar gyara hannun hijabinta "Sumayya" ya kirata da wani irin salo wanda ada can yake kiranta da shi,kira ke da idan yayi mata take jinsa har cikin jikinta "Ki yafemim sumayya,a kullum tsahon wata biyar kenan cikin neman yafiyarki nake,idan na kira baki dauka,idan nayi miki saqo baki reply,kiyi haquri ki yafemin,na yadda nayi babban kuskure a rayuwata amma na girbe abinda na shuka ai,na rasaki na tsahon wasu shekaru,ban taba tunani a baya akwai abin zai rabani da ke ba idan ba mutuwa ba,tunda na rabu da ke sumayya ban taba samun nutsuwa ta minti guda ba,Allah ya hukuntani tunda har kin shiga gidan wani sumayya,ki zama mai afuwa da yafiya kamar yadda na sanki nasam halinki a baya,mukhtar dinki ne sumayya bazan daina neman yafiyarki ba matuqar baki yafemim ba har sai ranar da numfashina ya bar gangar jikina...."da sauri ta katseshi don yana neman karya mata zuciya " don Allah ka bani hanya,na gaji da jin kalaman bakinka"murmushi ya saka yana kada kai "Shikenam sumayya,idan kinso ma ba zaki sake gani na ba tunda haka kika buqata,amma bazan daina neman afuwarki ba,na barki lafiya"ya fada yana juyawa ya danqawa Abdallah wani dan madaidaicin kwali ya wuce motarsa,sai ta samu kanta da tsayawa cak a gun ta kasa tafiya har ya bar layin,tausayinsa nason rinjayar zuciyarta,tuna wahalhalun da tasha shi ya bijiro mata ya taurarar da zuciyarta,kama hannun abdallah tayi suka shige ciki.    *****   ******    ******       Tunda ya bar gidan yaso tilastawa kansa cireta daga zuciyarsa saidai ya gaza hakan,wata sabuwar soyayya da qaunarta ke yawo ko ina cikin jinin jikinsa fiye da irin qaunarta da yake ji a da,sai ya soma komawa wani iri,ko da yaushe cikin tunani,ga wani matsanancin ciwon kai dake matsanta masa wanda ke kwantar da shi,yana mamakin yadda ya kasa haqura da ita,ji yake tamkar idan ya haqura da ita din zai rasa numfashinsa,hakan ya sanya ya shirya da kansa wani dare bayan ya yiwa abbakar waya ya sanar masa ya gayawa malam zaizo zasu tattauna,idan da hali abubakar din ma ya zauna.         Qarfe takwas yana sitring room din malam din dake qofar gidansu,hakan ne ya sanya babu wanda yasan da zuwansa a cikin gidan *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 4⃣6⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *wa yuhazzirikumul lahu nafsah* *_Allah yana tsoratar da ku game da kansa_* _______________________________        Duk yadda ta kai ga tunanin duniyar gidanta zata sameta yadda takeso ba haka abun yazo mata ba,komai na neman lalace mata bayan ta tabbatar da cewa tayi nasarar tuge sumayya daga gidan,gaba daya yaranta yadda ta sansu a yanzu ba haka suke ba,baki dayansu kansu a hade yake,qarami na girmama babba,haka babba na tausayin qarami,nuwaira na cikinsu tamkar cikinsu daya da ita,ita ke jagorancin ragamar sauran a matsayinta na babba,duk yadda taso ga sake raba kansu abun yaci tura,duka ne a yanzu basa tsoron dukanta,da tayi abu zasu ce mama babu kyau fa abu kaza,ko daya daga cikin tarbiyyar da sumayya ta dorasu babu wadda suka watsar,a yanzu haka sunfi qaunar zama wajen hajiya akan wurinta,saboda babu abinda ke shiga tsakaninsu sai duka hantara da tsawa saboda basa mata yadda takeso,babu mai bin umarninta cikinsu matuqar ba kan dai dai bane hatta da qaramarsu basma,bata fuskanci sumayya ta gama da rayuwar gidanta ba sai da yaran suka dinga gudunta,idan ranar makaranta ne ba zata sanyasu a idanunta ba sai dare,don idan suka dawo daga boko don kada ta hanasu zuwa uslamiyya gun hajiya suke togewa su shirya su wuce abinsu,ranakun qarshen mako kuwa gun hajiyar suke wuni,idan ka gansu a bangarensu to wani abu suka zo yi suyi su sake komawa.       Lukman kuwa mallakar data yi masa sai ra soma damunta,ba irinta take buqata daga gunsa ba,ya zama kamar irin dolayen nan,komai tace sai yace to,ya zama kamar qaramin yaro,hatta wanka da cin abinci sai tace yayi,sai ya zame mata qarin nauyi cikim rayuwarta,bashi da wani tunani ko kadan,ko wuta tace ya sanya hannunsa ba musu zai tsumbula,abinda ta fuskanta har yau sumayya na maqale cikin zuciyarsa,sau tari zai zauna ya yita kallon qofar dakinta babu qaqqautawa har sai tazo ta koreshi,hakanan ko sunan sumayya yaji an kira koda a hanya ne sai yayi firgigit kamar wanda aka tasa daga bacci,idan kuwa su nuwaira na zaune suna hirarta sai ya zauna daga gefansu yana saurararsu yana tambayarsu kan wasu abubuwa ko sanya musu baki,a kan hirarta da suke zama suyi sai da karima ta tara su ta musu dukan tsiya,ta kulle nuwaira kuma a daki sai da hajiya ta shigo taci mata mutunci ta bude ta tace kada kuma ta sake dukar mata jikoki itace abar a daka ai basu ba,nan ta saki baki ta dinga caccabawa hajiyan magana,bata bu ta kanta ba ta kada kan jikokinta suka fice. Wannan shine halin da karima ke ciki. *******   *******    ********       Kansa na sunkuye a qasa yana mai jin nauyi da kunyar abinda zai fito daga bakinsa,saidau tilas ya furta din saboda yana mai cike da fata da burin inganta rayuwa ne ta mutum uku,shi abdallahnsa da sumayyarsa,kasa magana yayi har sai da malam ya maimaita fadin ina jinka,yayin da ya abubakar ya gyara zamansa,kawu sulaiman wanda yake qani ga malam ma yazo kawowa malam ziyara suyi hira kamar yadda suka saba kasancewar su biyu suka rage raye a duniya ya tadda zuwan mukhtar din "Malam,ina mai jin kunyar neman wannan alfarma daga gunku,nasan cewa na muku laifin da dukkan iyaye zasu ji babu dadi a cikin ransu,saidai malam wannan alfarma da zan nema ina fatan zata shafe dukkan wani abu mara kyau da ya faru a baya,sannan zata inganta rayuwar mu baki daya" dan shiru yayi sannan daga bisani ya dora "Malam,don Allah don annabi ina son ka bani auren sumayya karo na biyu" shiru dakin ya dauka kowa da abinda yake saqawa cikin zuciyarsa,tsawon wani lokaci babu wanda yayi magana,jinjina kai malam yake kafin ya motsa "Mukhtar,babu shakka kai mutum ne na qwarai,wanda shine babban abinda yaja hankalina karon farko na baka auren sumayya,na sani na shaida cewa dukkan wani abu da ya faru tsakaninku sharri ne da makirci wanda babu wanda bazai iya fadawa cikinsa ba,abu na biyu kuma sakaci da addu'a,na ukunsu rashin game hankali guri guda tare da yin dogon nazari da bincike kan lamura,ammm....mukhtar" Sai ya dago yana mai amsawa zuciyarsa na gudu daya bayan daya,duk da cewa yana da cikakken fata na cewa zai cimma nasara "A qa'ida ta addinin musulunci bazawara ita ke da ikon zabawa kanta miji,saidai idan har anga tana neman jefa kanta wajen wanda bai cancanta ba bayan ga wanda ya cancanta a gefe,kada ka manta sumayya bazawara ce ita ke sa ikon zabawa kanta miji duk da nasan cewa ko a yanzu nayi mata zaben miji ba zata musanta min ba,to amma dai zan bata damarta,mukhtar,bazan hanaka neman sumayya ba,amma kadai zan amince ne idan ta yarda da aurenka".        Shiru yayi kafin daga bisani yace " malam,na gode da wannan alfarmar da ka yimin,amma ina mai neman alfarma ta gaba" "Uhmmm,ina jinka" "Malam,don girman Allah ina neman alfarma a gunka da ka karbi sadakin sumayya daga gurina,nayi maka alqawari tsakanina da ubangiji na matuqar sumayya taqi aminta da ni zan karbi sadakina zan haqura,na maka wannan alqawarin" shiru ne ya sake biyowa baya,kowa da abinda yake nazarta qasan ransa,malam na gudun shiga haqqin sumayya,yayin da ya abbakar ke tunanin tabbas dama ce wannan,don shi kadai yake iya fahimtar yaren sumayya,saidai ya hango alamun rashin amincewa qarara a fuskar malam,yayin da mukhtar ke duqe yana mai cike da fatan samun nasara,ya abbakar ne yayi saurin yankan hanzarin malam din "Malam,ina ga ka bawa mukhtar wannan damar,domin ni na shaida cewa sumayya na son mukhtar,hakanan na tabbata ba za'ayi nadamar karbar sadakin nan ba in sha Allahu gyara ne zai tabbata a tsakaninsu" kusan abinda kawu sulaiman ke ayyanawa cikin ransa kenan,don ko shi yana tausayin sumayya da abdallah,saboda haka ya ari bakin malam ya ci masa albasa "Kaje muntari,an baka wannan damar,kaje ka kawo sadakin amma tare da manyanka zaka dawo". Jinsa yayi kamar ba a duniya yake ba,godiya ma rasa wacce iriya zaiyi,ya tabbata yana jin karsashin samun nasara da shawo kan sumayyansa.             **************        Kasancewar juma'a ce ta zamo washegarin ranar,qarfe hudu bayan sallar la'asar mukhtar ya iso gidan shida kawunsa wato mahaifin abdur rahman da kuma baffansa wanda yake wa ne ga innarsu da qanin innar yasu su hudu kenan,kawu sulaiman da babban dansa sai yaya abubakar su suka sake karbar sadakin sumayya karo na biyu,wanda ita wadda ma ake batun sam batasan ana yi ba,don a lokacin ta tafi kitso,ta dawo dai ta tadda mutane cikin sitting room din malam,saidai batasan ko su waye ba tunda bata shiga ciki ba cikin gida ta zarce,bayan malam din ya sallami kowa ya shigo cikin gida ya tadda mama ya buqaci ganinta sannan ya sanar mata tare sa gaya mata baya son ta sanrwa kowa har sai sun hada kansu da kansu,to ita din macace,kuna tasan burin kowacce mace ta zauna da uban 'ya'yanga,hakanan kowa ya san nagarta da kyawun halayen mukhtar tun kafin wannan qaddarar ta afkowa rayuwarsu.               *ZAINAB*        Tunda ta farka daga suman da tayi take qaraji tana kuka,sai data tada hankalim duk marasa lafiyan dake dakin,babu yadda zinatu batayi kan ta lallabata ba amma taqi yin shiru,duk yadda take jin dadin halin da taga zainab din a ciki amma ji take kamar ta zura da gudu,dadi take ji sosai da wannan labarin na samuwar cutar qanjamau jikin zainab din,ganin yadda zainab din ke firgita musu marasa lafiya  ya sanya suka canza mata daki.       Kusan kwana tayi a haka kafin daga baya ta fara sassauta qugin da takeyi saboda ta fara jin sassaucin radadin da take ji a zuciyarta.       Tana jingine a bango har zinatu ta gama bata shayin,saidai har a lokacin bata ce komai ba sai faman jinjina kai da take,kanta ta daga ta kalli zinatu da jajayen idanuwanta kamar na maza murya a kausashe tace " kin gayawa wani a gidan mu abinda ke faruwa ne"kai ta kada tana ajjiye kofin hannunta "A'ah,babu wanda na gayawa" "To bana buqatar kowa ya sani" "To" kawai zinatun ta fada tana dariyar mugunta cikin zuciyarta. "Cutar qanjamau zinatu" tayi furucin tana kallon zinatu tamkar mai neman tabbaci kan wata magana,cikin fuskar tausayin qarya tace "Don Allah ki bar daga hankalinki zainab,mutum nawa ne masu irin cuwin ke rayuwarsu hankali kwance" "Dalla can malama daqiqiya kawai,bani da dama kenan ta komawa mukhtar ko kin manta?" Shiru zinatu tayi zagin da tayi mata yana mata ciwo amma ba zata iya maidawa ba "Zinatu,hakan fa yana nufin mutuwata gab take da ni kenan" Kallonta kawai zinatun tayi ba tare da tace komai ba,kamar zararriya sai ta miqe tsaye tana girgiza kai "Inaaa,wallahi bazai yiwu ba,wallahil azim bazan mutu ni kadai ba,kai ka zama silar kasancewata cikin wannan hali,kaine sila,kai ka jawo min" ta fada tana zarya cikin dakin,mayafinta ta figa ta yafa tana fadin "Ki nemo kudinsu ki biyasu ki sameni a gida zamu warware" tayi maganar tana ficewa daga asibitin. *tofa,muje zuwa masu karatu* *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 4⃣7⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* _____________________________ *wa may ya'amal misqala zarratin khairan yarah,wa may ya'amal misqala zarratin sharran yarah* *_duk wanda ya aikata dai dai qwayar zarra na alkahiri zai gani,duk wanda kuma ya aikata dai dai da qwayar zarra na sharri zai gani_* _______________________________ *Gaisuwa da fatan alkhairi gareku*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽 *sis farida muhammad abbas* *sis rabi'ah haroun* *sis dada* *Bilkisu mai gadon zinare* *mrs alqali* *maman sayyid*      Bayan sallar isha'i ne,idarwarta kenan abdallah ya soma rigima tilas ta kwantar da shi gefanta ta soma lallabashi,don kwanakin abinda ya koya kenan rigima idan zaiyi bacci,ya Abbakar ne dake shirin wucewa gidansa ya leqo "Kinyi baqo sumayya" "Baqo?,baqo kuma ya abbakar?" Ta tambaya cikin mamaki da faduwar gaba,waye yake son jawo mata jarfa tana zamanta lafiyar Allah "Eh baqo,kiyi ki fito kada ki zauna" ya fada cikin halin ko in kula da yanayinta yana sakin labulen ya fice,magabar tayita juyawa cikin ranta,sai ta banzatar da zancan jin yaya abbakar din na yiwa mama sai da safe ya wuce gidansa.      Minti kusan goma da fitar tasa mama ta dago labulen ta shigo "Wai ba yayanki ya fada miki kina da baqo ba" kamar zata saki kuka ta dubeta "Mama ban fa san ko waye ba" "Idan kinje kya ga ko waye din yana sitting room din malam,tashi maza ki wuce kuma  saura kije ki yiwa mutane sakarci",tilas ta miqe bayan ta kwantar da abdallah a kan gado ko hijabin jikinta bata cire ba ta fito zuciyarta fal quna.        Turus tayi bakin qofar ragowar sallamarta ta koma ciki,da hanzari ta juya tana mai neman fita,cikin zafin nama ya sha gabanta wanda saura kadan jikinsu ya hadu,sai ta ja baya tana dubansa,mukhtar ne sanye da dinkim shadda ruwan sararin samaniya babu hula kansa,ta masa kyau sosai saidai ramar da yayi ta bayyana,hancinta ya cika da qamshin turarensa ya dinga tuna mata baya,saboda haka da sauri tace " matsamin na wuce" "Babu inda zakije sumayya yau sai kince wani abu game da ni,kin yafe min ko baki yafemin ba,sumayya ya ina kike so na dora raina?,laifi ne na aikatashi na nemi afuwarki sumayya amma kinqi kice komai,kinsan kullum ya nake kwana ya nake tashi da rashin cewa komanki?,kinsan me nakeji cikin qirji na" sai kuma ya sassauta murya cikin sanyi "Kinfi kowa sanin wane mukhtar sumayya,kinfi kowa sanin wane irin zama mukayi a baya,sumayya ki tausaya min koda ba zaki tausayamin ba ki tausayawa abdallah,abdallah ya zama marayan qarfi da yaji,abdallah na buqatar mu ni da ke a tare,idan baki tausayawa mana ba sumayya waye zaiji tausayinmu duk duniya?,taba qirjina sumayya kiji" ya fada yana fincikar hannunta zuwa qirjinsa,sosai taji zuciyarsa na bugawa,gaza cire hannunta tayi sai da taji ya ambaci wash,da sauri ta dubeshi sai taga yana dafe da kansa yana layi,batasan sanda ta riqeshi ba a rude tana cewa lafiya?,ganin yana neman gun zama ya sanya ta zaunar da shi tana masa sannu,tsahon mintina biyar sannan ya sauke numfashi ya gyara zamansa tana zaune can nesa da shi ya dubeta "Ciwon kai nake fama da shi,amma wannan duka ba damuwata bace burina kawai ki yafemin" ya fada yana duban qwayar idanunta,a hankali ta janye idanuwanta zuciyarta na mata bitar waye mukhtar agurinta, "Na yafe maka" ta furta murya can qasa "Allah ya yafe mana baki daya" wani wawar ajiyar zuciya ya saki,baki daya jikinsa ya saki,wani farinciki yaji yana ratsa kowacce gaba ta jikinsa,yana so yaje ga sumayyan amma sam jikinsa babu qwari ko kadan,sai ya miqa mata hannu "Taso sumayya kizo kusa da ni don Allah" sai ta girgiza kai ba tare data motsa ba,tilas ya tattaro duk wani ragowar qarfinsa ya kiqe ya isa gareta,kusa da ita ya zauna har tana gogar kafadarta,hakan ne ya sanyata ta janye da sauri tana hada rai "Meye haka,don nace na yafe maka ai hakan ba yana nufin kai mijina bane ko zan sakw aurenka ba" da sauri ya sake matsawa kusa da ita babu gun matsawa a gunta don ya kaita qarshen kujerar sai ya kama hannunta ya matse cikin nashi "Sumayya,na sake miki wani laifin don na bada sadakinki,amma bisa sharadin matsawar baki amince ba zan karbi kaya na na haqura" Wani abu taji yana ratsa zuciyarta mai kama da farinciki,zuciyarta ta karye hawaye ya biyo kuncinta,cikin raunanniyar murya ta kwabe fuskarta "Ni nace maka ka kai sadakina ba tare da sani na ba?,ai kuwa sai kaje ka karbi abinka don ni ban amince ba,kuma......" Bata ankara ba ya hade bakinsu waje daya wanda hakan yayi sanadiyyar katsewar maganarta,sun dauki kusan minti goma a haka sannan ya janye yana dubanta,qasa tayi da kanta kan fuskarta qaramin murmushi na fita a fuskarta "Magana ta qare,na sanki tun ba yau ba,dukkan abinda zaki fada a yanzun nasan aji ne kawai za'a jamin ko ba haka ba" sake hade fuska tayi kamar gaske "Nidai na fada kaje ka karbi sadakinka,bana yi" "Ok to bari na kira ya abbakar na sanar masa" ya fada yana fiddo wayarsa daga aljihun gaban rigarsa,ganin da gaske lambar ya abbakar yake nemowa ya sanyata qwace wayar "A'ah,ki bani mana na isar mishi da saqonki" "Ni bance ba" ta fada a shagwabe,sai yayi jagale yana kallonta saboda tuna masa da baya da tayi ta salon yanayin maganar da tayi "Kada ki hanani fa tafiya gida yau na kwana a nan" "Bismillah mana ai ga guri nan" sai yayi kalar tausayi yana dubanta "Yaushe za'a tara shaidu sumayya ki koma dakinki" idanu ta juya ta dan murguda baki "Sai shekara iwar haka" qirjinsa ya dafe yana kallonta "Mutuwa kike so nayi kafin lokacin sannan ko?" Rai ta hade "Ka daina fadin haka mana ya mukhtar,ni kunya nake ji gaskiya ka bari idan ja shirya zan fada maka ka sanarwa ya abbakar" hannunta wanda ke cikin nashi ya sumbata yana fadin "Na gode,na gode,na gode sumayya,na gode da karamcin da kika nuna min a rayuwa,na gode da kika nuna ke mai qaunata ce har yanzu" sai ya dakata yana fidda zoben azurfan dake yatsansa ya zura a nata,ya mata yawa hakan ya basu dariya baki dayansu,sai ya cire ya sanya mata a yatsan tsakiya duk da haka ya mata yawa "Ina son zoben nan sumayy,amma sai naga yafi kyau a hannunki,ki ajiyemin zan karba" "Idan kuma naji dadinsa bazan maida maka ba" Dariya ya danyi sannan yace "Babu komai,ai da kai da kaya duka mallakar wuya ne" sallamar halima ta sanya sumayya miqewa,shigowa tayi dauke da abdallah tana fadin "Wallahi yaron nan ya koyi rigima,tunda ya tashi yaje zunduma ihu nayi tsammani ma kin jiyo shi" "Ina zata jiyoshi ta shiga kogin qauna" mukhtar ya fada cikin salon zolaya yana miqa hannu ya amshi abdallah dake ta dokin zuwa gunsa yana kiran abba na,murmushi halima tayi tana yiwa sumayya kallon tsokana ta fice,ita kanta wani dadi taji don babu wanda yaji dadin rabuwarta da mukhtar,qafarta har qaiqayi take taje ta bawa zainab labari.      'Yar kallo sumayya ta koma sanda mukhtar suka soma wasa da abdallah,bata taba ganin d'a da uba irin haka ba,sai wajen qarfe goma ya fito zai tafi,qin tafiya yayi har sai data masa rakiya bakin mota,har ya shiga ya fito ya sake kallonta "Ban son tafiya sumayya,banqi ace tare da ke zan tafi ba,don Allah ki taimaka ki gama shirye shiryen da duk zaki da wuri,ni na amince ma duk abinda baki qarasa ba ki qarasa shi a gida na zan baki wannan damar,ji nake kamar lokaci na qure mana" murmushi tayi tana jin maganar tasa na sauka sosai cikin zuciyarta "Kada ka damu ya mukhtar,ka qarasa gida dare yanayi" ta fada tana taka masa,sai da yaja motar ya bar layin sannan ta koma cikin gida.    *******     *******   ******      Cikin abinda bai gaza sati biyu ba mukhtar ya sabunta soyayyarsa baki daya,kullum yana tare da ita idan baizo ba kuwa ranar katin waya zaici ubanshi,har tsokanarta su halima sukeyi,wai sai kace wasu masu auren fari,ya dawo mata ya mukhtar dinta sak,sai ta samu kanta da dokanta wajen ganin ta a gidanta cikin sabuwar rayuwa ita da mukhtar dinta da yaronta.         Sati na zagayowa aka maida auren sumayya da mukhtar karo na biyu ranar jum'a bayan an sauko daga masallaci,a ranar mukhtar ya matsanta mata sai ta sanya ranar tariya,sati biyu tace ya tuburr mata kan ya masa yawa,tilas ta haqura ta maida shi sati dayan,don dama tana jiran aiken da anty dije tace zata yi mata nan da kwana goma.   *******    ********   *******       Juma'a asabar lahadi litinin kwana hudu da mai da auren ran litinin mukhtar yace ta shirya da daddare zata masa rakiya zai yi siyayyar kayan da yake son sauyawa cikin gidan,mama ta sanar,Allah ya tsare sai kun dawo abinda maman tace kenan.      Tana idar da sallar magariba ta soma shiryawa,kwalliya tayi wadda rabonta da yin kwalliya irinta har ta manta,tsaf ta shirya cikin material na one million stone peach ne da adon mint green,fitted gown aka mata da shi,ya masifar yi mata kyau,zainab ke dubanta tana cewa "Kai yaya sumayya,sai kace zaki dinner,ai kya bari sai nan da kwana hudu wannan kwalliyar,karfa ki sanya ya mukhtar yaqi maidoki" daquwa sumayya tayi mata tana cewa "Ni sa'arki ce,naga alama kin soma rainani" dariya ta sanya "Yi haquri yayanmu,amma dai ba hijabi zaki sanya ba ko?,naga kina da mayafi kalar kayan" "Kyaji da shi" sumayyan ta fada tana feshe jikinta da turaruka,ita kanta tasan cewa tayi kyau,sai da tazo fitowa sai taji kunyar wuce mama a haka,da qyar ta fice kanta na sunkuye mama bayan ta barwa zainab abdallah wanda yau yayi baccin wuri.       Baki kawai mukhtar ya saki yana kallonta har sai data hure masa idanu,dariya sukayi baki daya "Ki amince kawai yau mu wuce gida my sumy"kicin kicin tayi " amma dai unguwa kawai kace zan raka ko?"murmushi ya saki "Afuwa ranki shi dade,na tuna,muje" suna tafe yana tuqi amma baki daya ya wani narke mata bini bini ya kalleta har suka isa gun ya kashe motar ya zuba mata ido ba tare da ya fita ba "Sumayya,ina jin wata sabuwar qauna taki na dasuwa cikim zuciya ta,da ace a yanzu ne wani ya aureki mutuwa zanyi wallahi,ina sonki sumayya ina fata mu kasance tare har ABADAN" murmushi ta saki tana kada kai "Nima ina fatan haka ya mukhtar" Sai da ya sumbaci goshinta sannan ya bude motar suka fita.      Kayayyakin amfanin gida suka siya sosai,harda kayan kitchen sai da ya siya wasu abubuwa daga ciki,motarsa ta cinye kayan a ciki aka zuba masa sannan suka fito,sake tsayawa yayi a wani gu da saida kayab qwalam da maqulashe ya sayi kaji biyu gasassu da ice cream,sai damammiyar fura ya dawo ya tada motar yana dubanta,hira suke qasa qasa duk ya wani sukurkuce,wani kallo yake jifanta da shi,sai taga ya dauke kan motar ya sauya hanya,shuru tayi ta kasa tambayarsa hakanan sai ta biye masa har suka isa qofar gidansu,gidanta ne a da wanda a yanzu ma ya sake zama mallakinta "Bismillah muje ciki ko?" "Ya mukhtar na bar abdallah a gida fa" "Babu komai,minti talatin kawai ina son ganinki ne sumayya" nan ma bata ce komai ba ta fita suka shiga gidan,tayi mamakim ganin komai a tsaftace a killace,bai tsaya ko ina ba sai dakin gadonsa,ya dubeta sanda yake cirw hularsa tare da tattare hannun rigarsa "Nasan bakiyi sallar isha'i ba ki daura alwala muyi sallah sai mu wuce ko?" Cikin shagwaba tace masa "Wai nikam bansan gaggawar me kake ba ya mukhtar,saura kwana hudu fa na dawo gidan baki daya" murmushi kawai yayi bai amsa mata ba ya shiga bandakin.        Bayan sun idar ya matso inda take,hannunsa ya sanya cikin nashi yana kallon qwayar idonta "Sumayya,Allah ne kadai yasan yadda nake jin sonki a zuciyata" murmushi tayi tana girgiza kai."ya mukhtar,sai kace yau kasan sumayya,sai sake jaddada qaunarta kake bayan ta riga da tasan hakan"murmushin shima yayi "Hakane fa ko sumayya,amma wannan karon wata qauna ta daban nakeji,sumayya,ina so ki kasance tare da ni har qarshen rayuwata" "Na maka wannan alqawarin" "Na gode" Sai kuma shiru ya biyo baya har ya qosa taji me zai sake cewa,sai daga bisani yace "Sumayya,zaki yimin alfarma na kasance tare da ke cikin wannan daren?"idanu ta daj fiddo "Ya mukhtar,kwana hudu fa ya rage" "Na sani sumayya,amma so nake kimim wannan alfarmar indai ban keta iyakar ubangiji ba" "Na maka ya mukhtar" ta fada kanta tsaye "Allah yayi miki albarka" ya fada yana janyota ta fada jikinsa kowannansu cuke da kewar dan uwansa,kada ma mukhtar yaji labari,ji yake kamar an masa bushara da aljanna.        Qarfe goma saura na dare ta fito daga bandaki,mukhtar tuni ya kammala shiryawa yana zaune yana jiran fitowarta,binta ya dinga yi da kallo,ji yake tamkar ya hadiyeta ya maidata ciki,har yanzu baiwar nan da ya santa da ita na tattare da ita,ganin ta kammala ta yafa mayafi tana saba jaka ya sashi saurin cewa "A'ah,amarya guda bai kamata ace bata ci komai ba" sai ta saki murmushi cikin jin kunya "Ya mukhtar yau ka manta da abdallahnmu?,munfa barshi a gida"miqewa yayi da sauri yana fadin "Kai kai hakane fa,jikina ya bani ma fa ya farka" dariya ta saki "Uhmmm,sannu masu 'ya'ya" "Wallahi kuwa,d'a ba wasa bane" ya fada yana kama hannunta suka fice.        Ihu take so ta kwarara ko zataji sanyi a ranta amma zinatu ta hanata don kada ta tara musu mutane,wadda ita ta kawo mata labarin komawar auren sumayya da mukhtar,maimakon haka saita maida dubanta ga zinatu cikin daga murya "Wallahi wallahi sai na aikata abinda na qudurta babu mai hanani aikatashi wallahi,mukhtar nawa ne,nawa ne ni kadai,bazan juri ganinsa da wata ba ba ni ba" ta fada kamar zararriya tana mai ficewa daga layin cikin qunar zuciya kamar zatayi aman zuciyar tata. Ko da ya sauke ta ma sai da ya sake tsareta,kamar bazaya tafi ba har sai dayaga giftawar malam da alama ya shigo gida kenan sai da safe sannan sukayi sallama bayan ya cikata da kalamai masu tsayawa a zuciyar wanda ake so. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 4⃣8⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *kullu nafsin za'iqatul maut,summa ilaina turja'un* *_DUKKAN RAI SAI TA DANDANI MUTUWA,SANNAN IZUWA GAREMU ZAKU KOMO_* _________________________________ Tana shirin kwanciya wayarta ta dauki ruri,mukhtar ne sai ta kumahe idanu tana murmushi "Na kasa bacci my sumy,ganinki nake kusa da ni".'yar qaramar dariya ya tasa tana fadin " baban zumudi ka zama ya mukhtar ne?"shiru ya danyi sannan ya saki ajiyar zuciya "Bakisan me nake ji ba game da ke sumayya". Hira suka kashe lokaci suna yi,a nan yake gaya mata ran rakota tare da yaya yahanasu za'a zo,har mamaki take idan taji yadda yaya yahasun ta sauya take nuna mata qauna,basu suka rabu ba sai daya na dare,ta dubi agogo tana zaro ido ganin lokacin da suka shafe tare,sai ta fita ta daura alwala tayi sallah raka'a biyu sannan ta kwanta. ****** ******** ******* Shirye shiryen tariya sun kankama sosai,tayi gyaran jiki hadi da qunshi da kitso,kayanta baki daya ta kammalesu. Ranar alhamis ana ya gobe zata koma,da azahar suna falo ita da halima da zainab suna hira ita kuma tana gugar ragowar kayan abdallah da bata gama shiryawa ba,sai anty salma qanwar mama wadda anam zata kwana,wayarta dake daki ta soma burari,abdallah ne ya miqe da gudunsa ya dauko ya miqa mata,anty salma ta talle masa qeya tana cewa " kaji dan jakar uba wai yasan kayan uwarsa,sai kace wani yace zai dauki wayar ne"dariya sukayi dukansu halima tace "Indai Abdallah ne kadan kika gani anty" ita kuwa sumayya miqewa tayi ganin lambar mukhtar ce ta fita ta koma dakinta "Lafiya abban abdallah naji muryarka can qasa?"murmushi ya saki sannan yace " lafiya qalau,a yanzu ma ina gida kwance ina hutawa,babu abinda nayi amma wata gajiya nakeji sosai a jikina,kewarki nake sumayya goben nan kamar ba zata zo ba"tamkar yasan abinda take ji jikinta itama kenam,sai ta saki ajiyar zuciya tana masa murmushi "Au dariya ma kike min?,naji na gode,amma da zaki taimaka min da kinzo na ganki kinji my sumy" sai ta kasa musa masa,dama suna da agender fita karbo dinkunan sumayya gidan wata mata bayan sallar la'asar ita da anty salma "Babu damuwa ya mukhtar,amma sai bayan la'asar"cikin zumudi yace "Da gaske sumayya ta?,kada fa ki shirgani"dariya ta qyalqyale masa da ita " da gaske nake mana abban abdallah,ka jirayeni,amma fa gobe ba za'a rakoni da wuri ba tunda yau ka sake gani na" "Babu komai,ai goben ta Allah ce,Allah yayi miki albarka sumayya ta" tana jin dadi ya sanya mata albarka don haka da sauri ta amsa da amin. A gidan mai dinki ta bar anty salma tace zata je ta dawo,ta riga da tasan inda zata din saboda haka tayi tayi abdallah ya zauna qememe yaqi har da kukansa ammi zai bi tace madallah yayi ta binta din sai sun dawo. A qofar gidan mai adaidaita sahu ya sauketa,ji tayi ana malam ga kudinka,tana waiwayowa sai taga mukhtar ne,cikin mamaki take tambayarsa "Ya akayi kasan na qaraso" "Jikina ne ya bani" ya bata amsa yana amsar abdallah daga hannunta yana masa cakulkuli suna qyalqyala dariya tana biye da su har zuwa falon gidan,kallon gidan take ya sauya komai kamar wanda zai kawo budurwa,komai fes gwanin sha'awa,zubewa sukayi kan kujera mukhtar na biyewa abdallah suna ta wasanninsu yayin da sumayyan ke zaune gefe guda "Wai nikam 'yar kallo kuka maidani ne,nazo amma ba'a tani,bayan nemana akayi" ta fada tana murguda baki,dariya mukhtar din ya saki yana duban abdallah."lah,abdallah kaga mamanka na kishi da kai"sai ya kada kai kawai yaron don bai fahimci me yace ba,juyawa yayi gunta "Dama taimaka mana kika yi kika dafa mana wani abun madam" "Kamar me?" Ta tambayeshi "Abinci mai sauqi da dadi" "An gama" ta fada tana miqewa "Ammm,madam,amma da kin taimaka kin cire wannan hijabin tunda gaban mijinki kike ko?" Dariya ma ya bata yadda yayi maganar a dake,bata ce komai ba ta cire din,sai ta miqawa abdallah hannu "Muje kayi fitsari sai ka dawo ko?" Lafewa yayi jikin mukhtar din qememe yaqi yarda da ita "Barmin yaro na ana dole ne,yayi fitsarinsa babu komai cinyar babanshi ce".don haka ta juya zuwa kitchen ta barsu nan. Tana tsaka da girkin mukhtar ya shigo goye da abdallah,saura qiris ta dona hannunta cikin gas garin dariya " ka ganka kuwa da goyon nan,don Allah tsaya na maka hoto"shi din ma dariya yake, "To ya zanyi,yaqi yarda na kwantar da shi kwata kwata"hoto ta musu wajen kala biyar ta nuna masa suka dinga sheqa dariya,tex din da ya shigo wayarta ya katseta,anty salma ce ke gaya mata ta wuce gida uta kam sai ta taho,tana niyyar kiranta tace ta jirata tana tahowa mukhtar ya riqe hannunta " qyaletq ni da kaina zan maidaki".qarshe tare suka gama girkin wajen sallar magariba sannan ta karbi abdallah da qyar zata kwantar,sai ya farka ya riqe mukhtar gam gam yana sakin kuka,tilas yace ta qyaleshi suka dauro alwala sukayi jam'in sallar magariba tare sannan ta gabatar masa da abincin. Tare suke ci baki dayansu,saidai duk daga kan da zatayi idanuwansa na kanta,saidai ya sakar mata murmushi ta maida masa martani,sake hada idanuwa sukayi karo na barkatai,sai ya kauda kallonsa ya maida kan abdallah "Na godewa Allah da ya sake gwadamin wannan lokaci cikin rayuwata,lokacin da zan zauna ni da matata abar sona da kuma diyan cikina,ina fata Allah ya rayamin kai" ya fada yana shafa kan abdallah,sai yaron ya dago kai yana kallonsa kamar yasan ma'anar abinda yake cewa "Ina da buri kanka abdallah" ya sakw fadi,sai ya dubi sumayya "Ki taimaka min wajen tarbiyyar abdallah don Allah" murmushi ta saki zuciyarta na bugawa kadan kadan "Banda abinka ya mukhtar ai saidai mu taimaki juna tunda tare zamuyi tarbiyyarsa" girarsa daya ya dage "Haka ne fa,to Allah ya bamu aron rai" "Amin ya Allah" ta fada tana ci gaba da cin abincin,sai daga bisani ta lura ba wani cin abincin sosai mukhtar din keyi ba sai aukin kallonsu "Ai bama cin abincin kake ba fa yaya,wannan kallon duka na meye?" Murmushi ya kuma saki."kallon so da qauna nake muku"dariya ya bata sosai "Naga alama sai na maka dura" ta fadi tana debo abincin da spoon tana bashi,qarshe ita ta qarasa basu abincin dukansu sannan ta gyara gun,kayan wasa taga yana ta hadawa abdallah sannan ya janye ta bedroom yace zata tayashi wani aiki,bata fahimci wayo yayi mata ba sai da labari ya soma shan banban. Daf da kammaluwar komai sai ta tsinci hawaye na diga idanunsa,tasa hannu ta shafo sai taji itama nata idanun na fidda ruwan qwallar da batasan dalili ba "Ya mukhtar ko na yi ma laifi ne?" Ta tambayeshi cikin sanyin jiki,sai ya sake qanqameta yana sakin ajiyar zuciya tare da murmushi "Babu abinda kika yimin,tsakani na da ke sai fatan alheri,Allah ya haskaka rayuwarki,qwallar farinciki nake musamman idan na tuna gobe zamu sake sabon zama sumayya" dariya tayi tana kwantar da kanta a qirjinsa "Na gode ya mukhtar" "Nine da godiya sumayya,ina so ki sake yafemin ki dauka tamkar babu abinda ya taba faruwa tsakaninmu mara dadi" cikin shagwaba tace "Ni na manta ma fa ya mukhtar,ni babu abinda ya taba faruwa tsakanina da kai,kai fa uban 'ya'ya na ne". Da qyar ya yarda zai maidata gida,da sdrd yayi tayi zamanta meye marabar yau da goben,ko a motar ma sai da ya gama yawo da su guri guri ya loda uban siyayya sannan ya kaisu gida,riqe hannunta yayi sanda take shirin fita ya sumbaci bayan hannun nata,itama sai ta maida masa martani,ta jima tsaye a soronsu tana leqensa ganin ya tsaya bai tafi ba,sai daga bisani taga ya ja motar ya tafi. *JUMA'A* Tun mafarkin da taji daren jiya jikinta a mace yake,tana farkawa ta kira mukhtar din ta tabbatar da lafiyarsa,har yana zolayarta kodai ta qagu ne kawai a kawota,shi bacci ma yakw ta tasheshi,dariya tayi cikin jin kunya sukayi sallama,har zuwa wayewar garin juma'ar jikinta a mace yake,tun safe take kwance ta kasa katabus,tana jiyo koke koken abdallah da yau ya tashi da rigima amma ta kasa cewa komao,har ya shigo dakin ya gama kukansa da kawo mata qarar walida 'yar anty salma ya gaji ya fice ba tare da tace masa komai ba. Qarfe hudu na yammacin ranar tana tsaye tana shiryawa cikin dinkin atamfa riga da zani anty salma na tsaye kusa da ita tana bata turare wayarta ta dauki kuwwa,sunan mukhtar ne ya bayyana gabanta yayi mummunan faduwar har qafafuwanta taji sunyi sanyi,sai ta koma bakin gado ta zauna tana amsa wayar cikin fargaba "Assalamu alaiki amarya ta" muryar mukhtar ta ratsa dodon kunannata,sai ta amsa masa tana lumshe idanuwanta,cikim salon soyayya suka gaisa sannan yace "Ina fatan kin fara shirin tahowa gidanki" dariya ya bata ta murmusa "Yanzun haka ma shirin nake angom doki" "Eh naji na yarda ina abdallah" "Yana waje,yau tun safe yake ji da rigima wallahi" nemo min shi mu gaisa" "Bai kusa fa ya mukhtar" ta fada a shagwabe,tuburewa yayi tilas ta qwalawa zainab kira ta kawo shi ta hadasu da wayar taci gaba da shiryawa,sai da ta gama sannan ta karbi wayar "Nima ina gun masu dinki zan karbi dinkuna na,SAI KIN TAHO?" "To ya mukhtar,ka kularmin da kanka" "To my sumy". Ajjiye wayar tayi tana sakim ajiyar zuciya. Bayan sallar magariba 'yan rakiyar nata sukayi mata sallama kowa ya kama gabansa,ganin har isha'i tayi shiru sai ta daura alwala tayi sallar isha'inta,sam gidan ba,gabanta ke yawaita faduwa tana ambaton hasbunallahu wa ni'imal wakil,ga abdallah na tare da mukhtar tare zasu taho da shi,ganin shirun yayi yawa sai ta miqe ta kunna saudi qur'an Allah ya taimaketa ma akwai wutar nepa ta zauna tana ci gaba da saurara zuciyarta na mata wani iri babu dadi. Firgigit ta dawo hayyacinta tana duba agogo,goma na dare ta dubi wayarta dake ta faman ruri,sunan malam ta gani kam screen dinta,sai taji gabanta yayi mummunan faduwa har sai da ta furta hasbunallahu wa ni'imal wakil a bayyane sannan ta kara wayar a kunnenta "sumayya kina ina?" Abinda taji malam ya fadi kenan,sai tambayar ta bata mamaki "Ina gida na malam" "Yauwa to maza kashe wayarki ki fito qofar gida abubakar na jiranki,yace yana ta bugu bakiji ba"sai ta amsa da to kawai tare da bin umarnin malam din kawai tana jin wani yanayi nabin fata da tsokar jikinta,hijabin data idar da sallah ta zira ta fito kai tsaye qofar gidan ba tare data rufe gidan ba. Ya abbakar ne tsaye jikin adaidaita sahu kansa a kife,qarar bude gidan ya janyo hankalin sa,sai ya kalleta "ya baki kulle gidan ba,malam ke son ganinki" "To" kawai ta kuma cewa ta koma ta jajjanyo qofofin,tana fitowa ta miqawa ya abubakar wayar tata don ji tayi ta fara yi mata nauyi a hannu,kallonta kawai yayi ya sanya hannu ya amshi wayar ya sanya a aljihunsa suka shiga adaidaita sahun ya jasu suka bar qofar gidan ba tare da kowa ya sake cewa komai ba. Cikin harabar asibitin mai adaidata ya faka ya abbakar ya biyashi suka fito,binsa kawai take a baya ba tare da tasan inda take jefa qafarta ba,tarin tambayoyi ke yawo kan kwanyarta amma ta gaza furta koda guda?,shin waye a asibiti?,me ya faru ko meke faruwa?.gab da zasu haura saman asibitin ta iya tambayarsa "Ya abbakar,wai me yake faruwa?,waye ba lafiya?" "Babu komai muje kawai" Tun daga farkon barandar ta fara cin karo da mutane,yaya yahanasu,malam,kawu mahaifin abdur rahman da hajiya mahaifiyarsa,jamila yarinyar yaya yahanasu,sai mamanta da wasu mutane uku da batasan su waye ba,tunda taga yaya yahanasu mukhtar ko abdallah ne suka fado ranta,jikinta ya fara rawa sai ta fara qoqarin faduwa sanda suka had ido da yaya yahanasu taga ta saki kuka,da sauri hajiyan abdur rahman ta qaraso ta tareta ta zaunar da ita kan kujera tana fadin "Yi a hankali sumayya,babu komai in sha Allah Allah zai bashi lafiya,kiyi masa addu'a" "Waye hajiya me ya sameshi" malam ne ya qaraso yayi mata bayani,hatsari mukhtar din ya samu yana hanyar tahowa gida shida abdallah gab da sallar magariba,yanzu haka mukhtar din na tare da likitoci amma sunce yanzu zasu fito da shi saidai ICU zasu kaishi,wani irin tauri taji zuciyarta tayi "La haula wala quwwata illa billah" ta dinga maimaitawa,jin jikinta take kamar ba nata ba. Bata ce komai ba har zuwa sanda aka bude qofar wani daki aka turo gadon,mukhtar ne kwance tamkar gawa,babu abinda ke aiki a jikinsa sai numfashinsa dake fusga duk bayan wasu daqiqu,kansa nannade da bandeji fari wanda jinin da ya ci gaba da ratsowa ke barazanar sauya masa kala,a haka ma sun gyarashi sun dan gogeshi,wani kalar tashin hankali ya ruftowa sumayya,sai ta miqe tsaye har suka wuce da shi intensive care unit din,kukan yaya yahansu na haduwa da nata tashin hankalin yana yamutsa qwaqwalwarta,qunshe bakinta tayi cikin hijabi ta saki wani irin kuka qasa qasa ta soma furtawa "Ya ubangiji na,na roqeka kada ka sanya wannan ya zama cikin KUNDIN QADDARA ta,Allah na tuba,na tuba ubangiji na" abinda ta dinga maimaitawa kenan qasa qasa,hajiyan abdur rahman ita ta dinga lallashinta,saidai babu abinda ke qara mata sai tashin hankali ahaka sha biyu na dare ya cimmasu dai dai lokacin da likitocin suka fito,bayani suka yi masu kan dakin bai buqatar shigar mutane ciki,haka nan mutum daya suke da buqata wanda zai zauna da mara lafiya "Don Allah don annabi malam ku qyaleni na kwana,wallahi bazan iya tafiya gida ba" sumayya ta fada tana fashewa da kuka,babu wanda tausayinta bai kama ba anan,ganin babu yadfa za'ayi a barta ita daya kawu da ya abbakar zasu kwana cikin asibitin,ita kuma ta kwana gun mukhtar din. A hankali ta dinga takawa har gaban gadon da mukhtar din ke kwance,ko ina na'ura ce ke aiki a jikinsa,baki daya fuskarsa ta sauya kamar ba mukhtar ba,kallo daya zaka masa kasan lallai ya bugu sosai a kansa don tuni har ya kumbura kan nasa,kujera ta ajjiye bakin gadon tana qoqarin danne zuciyarta tare da tuna nasihar da malam yayi kata kafin su tafi "Kuka baya maganin komai,addu'a ita ke magani" abinda ya gaya mata na qarshe kenan,kanta ta girgiza tana sake baiwa kanta qwarin gwiwa,sai ta kama tafin hannunsa ta sanya cikin nata,a hankali murya can qasa mai cike da rauni ta soma karanto ayoyin qur'ani wadanda su suka dinga debe mata kewa tsawon daren,saidai abinda ke daga mata hankali dai dai da second daya babu wani abu da taga ya motsa daga jikinsa,wanda likitocin sunce ta kula ko yaya taga ya motsa ta sanar musu,duk da lokaci bayan lokaci suna shigowa suna sake dubashi. Sai da suka saitu sosai kan hanya sannan mama tace "Ina abdallah" tofa,sai lokacin hankalin kowa ya dawo jikinsa,duk cikinsu babu mai amsar tambayar,don hatta jama'ar da suka ceci mukhtar dim babu wanda yace yaga yaro,take wani sabon tashin hankalin ya samesu,mama kam kasa daurewa tayi saboda tsananin tausayin sumayya sai kawai ta sanya kuka,kai tsaye malam ya nemi alfarmar mai abun hawar ya canja akalarsa zuwa policestation wanda tafi kusa da inda al'amarin ya faru don si shigar da report cike da matsanancin tashin hankali. Kiran sallar asubar fari sanyi ya fara busowa,sam bata lura ba tana gyara zamanta,tana daga kai suka hada idanu,ya bude idanuwansa tar yana kallonta,wani farinciki ya dinga zagaya ta,ga mamakinta taji sai taji ya kita sunanta,cikin matsanancin farinciki ta amsa "Qarfe nawa?" "An kusa sallar asuba" "Daura min alwala sumayya banyi sallar magariba da isha ba" girgiza kai tayi "Ya mukhtar jikinka duka kayan aiki ne,ka bari likita yazo sai ayi maka" tubure mata yayi hakan ya sanya ta lallaba ta shashshafa masa ruwan iya inda zai yiwu,yana daga kwancen ya dinga halarto da sallar yana yi har ya kammala baki daya tana zaune tana kallonsa,yana sallamar qarshe kansa saitinta ne sai ya zuba mata idanu,murmushi tayi tace "Sannu ya mukhtar" kai ya kada mata sannan yace "Ina abdallah" abdallah,ta dinga nanatawa,idan kunnuwanta basuyi mata qarya ba ance tare suke da abdallah,to ina yake ina yayi? "Ina fata lafiya yake babu abinda ya sameshi" tabbas lafiya yake idan da ba lafiya ba da sun gaya mata "Lafiya yake ya mukhtar" ta fada cikin salon son kwantar da hankalinsa "Alhamdulillah" taji ya fada sai ya maida kansa,cikin farinciki da tada sallah itama. Shaquwa taji ya soma yi wadda kan ta idar da sallar ta qara yawa,tana sallamewa tayi kansa tana masa sannu,da hanzari ta dauko ruwan roba ta bude ta fara bashi a hankali,sosai ya sha ruwan kuwa sannan ta cire roban daga bakinsa ta qulle tana masa sannu,minti biyar tsakani shaquwar ta dawo,ta sake matsawa gunsa tana riqe da hannunsa tana masa sannu cikin tashin hankali ganin yadda qirjinsa ke dagawa wannan karon "Bari na qara maka ruwan" ta fadi tana shirin juyawa inda gorar ruwan take,sai taji ya damqe hannunta,juyowa tayi tare da tsayawa cak kamar an kafeta,idanuwansa taga sun fara juyewa,jikinta ya hau rawa ta qanqame hannunsa tana fadi a fili "La'ilaha ilallah,muhammadur rasulullah" abinda ta dinga maimaitawa kenan a fili babu qaqqautawa,a hankali taji ya kama yana maimaitawa,kusan minti biyu yana fada shima cikin fusgar numfashi sai taga idanunsa na lumshewa,riqon da ya yiwa hannunta tsaurinsa ya sassauta (Abinda ake so ga kowanne majinyaci kenan,mutuwa na da sa gigita da daga hankali,amma gata ake so ka yiwa mamaci wanda shine qarshen qaunar da zaka nuna masa,a yayin daka fuskanci wasu alamu na fitar ruhi daga gangar jikin majinyaci,bakinka ya dinga ambaton la'ilaha ilallahu muhammadur rasulullah ko za'a dace mamaci ya kama,ba cewa ake fadi abinda na fada ba,ko kuma cene la'ilaha ilallah,a'a ka dinga fadi yadda kunnuwansa zasu iya ji,idan Allah ya qaddara bawansa ne na gari sai ya kama ya kuma cika da ita,Allah kasa mu cika da wannan kalma mu da daukacin musulmi baki daya,amin). Hannunta ta zare qirjinta na fat fat fat,hawaye ne ke bin kuncinta,wasi wasi ya cika zuciyarta,fata take ba abinda take zato bane,wannan tunani ya sanyata fita da gudu tayi ofishin likitan. *mrs muhammad ce* *Fatan alkhairi ga* *oum imaan* *mmn husna* *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 4⃣9⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *assalamu alaikum* *da fari ina neman afuwa ga wadanda na sanya kuka,Allah yayi mana kyakkyawan qarshe,haka rayuwa take zaqi da madaci* _abu na biyu da nake so makaranta su gane shine,haqiqa Allah baya barin wani don wani yaji dadi,ko kuwa don kuna tsaka da farinciki sai Allah ya kasa dauke bawansa alhali ajalinsa yazo?,na tabbata ni ke ko kai an taba dauke mana masoyanmu,uwa,uba, 'ya'ya,qawaye maqwafta ko dangi,wala allah muna tsaka da jin dadin rayuwarmu bamu zatan musu mutuwa ba,ba kuma tare da sunyi sallama da mu ba,amma Allah ya daukesu saboda lokacinsu yayi kamar yadda Allah madaukaki ke fada a alqur'ani_ _(iza ja'a ajluhum la yasta'akiruna sa'atan wala yastaqdimun/idan lokacinsu yazo ba'a jinkirta musu sa'a daya kuma ba'a gaggauto da ita ma'ana su tafi alhalin suna da sauran minti daya cikin duniya)_ _(kullu nafsin za'iqatul maut)_ _(kullu man alaiha faan)_ _duk abinda ke kanta(qasa)qararre ne_ _mutuwa dole ce idan tazo sai an tafi,babu wanda zai dawwama cikin duniya ko shekara miliyan nawa zaiyi sai ya tafi,cikin dadi ko wuyar da kake ciki babu ruwan ubangiji,na tabbata babu wanda ba'a taba yiwa mutuwa ba,babu wanda bai taba rashin wani nasa ba,fatanmu Allah yasa mu cika da kyau da imani_ *sannan ina cewa masu karatu sun manta sunan littafin kenan KUNDIN QADDARATA?,kowa ya san rayuwa tafe take da qaddara,cikar imanin mumini kenan a jarrabceshi,jarrabawa na zamowa kankarar zunubi ga mumini,Allah ya bamu ikon cinye jarabobinmu* *wa bash shiris saabirin,Allazina iza asabathum musibatun qalu innalillahi wa inna ilaihi raji'un* *_KA YIWA MASU HAQURI BUSHARA,SUNE WADANDA IDAN MASIFA TA SAMESU SUKE CEWA MU DAGA ALLAH MUKE KUMA MU GARESHI NE ZAMU KOMA(innalillahi wa inna ilaihi raji'un)_* ________________________________        A rude ta fada ofishin likitan tana kiransa,likita ne mai kirki,ya gane ko wacece saboda haka ya miqe kawai ya biyota,zata fada dakin ya dakatar da ita yace ta jira a waje "Sumayya,jikin muntarin ne?" Kawu wanda idar da sallarsu kenan daga masallaci suka yo cikin asibitin suka tambayeta "Kai kawai ta iya daga musu hawaye na bin kuncinta,don bata jin zata iya cewa komai,jiri ta fara ji yana neman kayar da ita saboda tashin hankali da mintinan da suka kwashe a tsaye,sabida haka sai ta daddafa ta zauna kan kujerar sake barandar dakin.       Likitoci biyu ne suka zo suka sake shigewa dakin suna nan zaune,awa guda ta kusa shudewa dai dai lokacin da mama halima da zainab suka iso,yayin da malam ya fara biyawa ta police station ko an samu labarin abdallah,jikin mama ta jingina kawai ta kwantar da kanta a kafadarta ba um ba um-um,sannu maman ke mata tana tambayar jikin mukhtar din,kawu ne ya amsa mata da cewa da sauqi don baki dayansu hankalinsu bai jikinsu.        Budewar qofar dakin ne ya ja hankalinsu,likita na farko ya wuce baice musu komai ba,na biyu ma haka,na ukun ne ya tako gabansu a hankali sannan ya dubesu " dukkan mai rai mamaci ne wannan alqawarin Allah ne babu mai zama cikin duniya sai ya tafi,ina mai baku haquri,Allah ya yiwa mara lafiyanku cikawa,sai kuyi masa addu'a",kuka ne da salati ya gauraye wajen,wani dogon numfashi sumayya ta ja,cikin daga murya wadda bata san ta yita ba ta furta "INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN,ALLAHUMMA AJIRNI FI MUSIBATI WA AKHLIFNI KHAIRAN MINHA" tun daga haka bafa dada ba bata rage ba,don ba sosai take ganewa ba,bin kowa kawai take da idanuwa.      Isowar yaya yahanasu shi ya sake ruda gurin,zubewa tayi a qasa tana kuka kamar ranta zai fita,daga bisani ta sume a nan,sai da aka bata taimakon gaggawa sannan ta dawo hayyacinta,zuwa lokacin an kammala settling na tafiya da gawar mukhtar,motar asibiti suka basu a kaishi ciki(ambulance)itakam sumayya ido kawai take bin kowa da shi,sai ajiyar zuciya da take ta faman saki har suka isa gidansu na aure,gidan da suka tanada domin sabunta rayuwar aurensu,gidan da suka ciwa burin sake gina kyakkyawar alaqa da danganta har gaban ABADAN,ashe wannan mafarki nasu bazai cika ba,ashe wannan buri nasu yankakke ne,ashe sunyi zaman qarshe da mukhtar kenan a daren jiya?,abinda ya dinga bijiro mata kenan,kallon mutane take suna kuka,sai ta dinga jin dama itace su,dama itama zatayi kuka,domin kuka ya fiye mata sau dubu akan bala'i da sukar da take ji a qirjinta.         Cikin uwar dakanta aka wuce da ita aka zaunar da ita,har lokacin babu um ba um um sai ido kawai,a falo aka kwantar da mukhtar,aka bawa makusantansa dama suka wanke shi aka maaa suttura sannan aka buqaci 'yan uwansa suje suyi masa sallama,take gidan ya sake rudewa da koke koke,hakanne yasa anty salma tace a bar kowa ya gama shiga sannan sumayya ta shiha daga baya,da qyar aka fidda su yaya yahanash,kuka take tana ya yafe mata,itakam ta yafe masa dan bai taba saba mata ba,tsakaninsu biyayya ce irinta d'a da uwarsa tunda ta fara riqonsa har ta aurar da shi.       A hankali take takowa cikin falon da taimakon hajiyan abdur rahman wadda ta riqeta,gaban gawar mukhtar ta durqusa wadda ke lullube cikin likkafani aka sake rufeta da wani mayafin,kanta ta duqar zuciyarta na suya tana jin zafin yana ratsa dukkan sassan ilahirin jikinta,tana daga kai suka hada idanu da malam,da idanu ya mata nuni ta masa addu'a,hakan ya qwarara zuciyarta,a hankali ta soma fadin "Allah ya jiqanka ya mukhtar ya gafarta maka,ya Allah ka tsareshi daga azabar qabari da fitinarsa,ya Allah gashinan yana mai buqatuwa izuwa rahamarka,kai mawadaci ne daga barin azabtar da shi,idan ya kasance mai kyautatawa ya Allah ka qara masa kan kyawawan ayyukansa,idan ya kasance mai sabo ya Allah kayi masa afuwa,ya ubangiji ga mukhtar nan,bawanka ne Allah ka gafarta masa kayi masa rahama,ka yalwata masa makwancinsa,ka wankeshi daga laifuffukansa da ruwa da qanqara kamar yadda ake tsaftace farin tufafi daga dauda,ka sauya masa gida wanda yafi gidansa,da iyali wadanda suka fi nasa,da mata wadda tafi tasa......."sai ta sake yin qasa da kai,karo na farko da hawaye ya samu gurbi cikin idanuwanta,babu wanda bata burgeshi ba a gun da irin jarumtarta,kamar yadda babu wanda tausayinta bai ratsa shi ba,alfaharin haifar diya irin sumayyan ta kama malam,Numfashinta ne ya yanke,duhu ya fara mamaye idanuwanta,kunnenta ya daina jin komai,daga nan ta daina gane komai sai daukarta akayi aka fita da ita,kamar yadda aka dauki gawar mukhtar zuwa gidansa na gaskiya,gidan dake jiran kowanne bawa.        Bata sake sanin inda kanta yake ba sai gab da sallar la'asar,har ana shawarar kaita asibiti idan aka kammala sallar la'asar din bata farfado ba,da kalmar shahada ta farka,daga bisani kuka ta sake qwace maga,qanqame anty salma tayi tana rusa kuka mai tsuma zuciya,wanda hakan ya sake sanya wadanda ke dakin fashewa da kuka,babu wanda bai tausaya mata ba,ba shakka mutuwar miji babban al'amari ne gun diya mace,mijin ma irin mukhtar,shiru kam yaqi ywuwa a gurinta,har sai da malam ya shigo da kansa ciki wanda basu jima sa dawowa daga wajen 'yan sanda ba,hankalinsu a tashe yake don babu labarin abdallah,baiso wannan labari ya kai kunnen sumayya,so yake kafin komai ya lafa a ga abdallahn a duk inda yake,ya jima da ita a daki kafin ya fito,tayi shiru amma har hanzu hawaye basu bar bin kuncinta ba,haka nan bata fasa ambatar innalillahi ba cikin zuciyarta. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 5⃣0⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *fasbir sabran jamilah* *_kayi haquri haquri mai kyau_* _________________________________      Cikin kwana daya tal amma ji take duniyar ta mata daurin huhun goro,babu abinda qwaqwalwarta keyi sai bitar rayuwarta da mukhtar,idanunta sunqi dakatawa da zubda hawaye dai dai da second d'aya,cikin kwana gudan tal ta rame ta fige ta fita hayyacinta,ba ta cewa uffan sai ido kawai,ko gaisuwa aka yi mata saidai ta amsa da ka,daga jiyan zuwa yau babu abinda ta kai bakinta illa ruwa da take kurba lokaci zuwa lokaci idan an matsa mata,sam abincin bai iya wucewa ta maqogaronta balle ya kai ga uwar hanjinta,a washegarin ranar anty dije ta iso hankali tashe,sai sabon kuka ya balle tsakaninsu,ba qaramin tausayawa sumayya take ba,yarinya qarama amma taga jarabtar rayuwa iri iri,da qyar aka sha kansu.       Bayan sallar la'asar tana saman abun sallah tana lazumi cikin dakin gadonta,anty salma ya yahanasu antu dije da mama ne zaune a dakin sai ita ta biyar,sai yaran 'yan uwa dake gefe suna wasa,idanuwanta da hankalinta na kansu "Abdallah" sunan da ya fado kanta kenan,cak ta tsaya da lazumin tana lissafin ina abdallah yake?,bata ga abdallah ba duk cikin kai komon yata,haka bata ganshi gaban gawar mukhtar ba "Ina Abdallah" lokaci na farko da tayi magana tun bayan tsawon awanni kusan talatin,dif dakin sukayi don babu mai amsar bata,tuni hawaye ya cika idanuwan anty dije ta sanya mayafinya ta soma sharewa,mama tafi kowa shiga cikin taraddadi,don ba'ayi minti goma ba malam ya kirata yace suna gun 'yan sanda,sumayyan dai bata yi maganar sa ba ko?tace masa eh "Ina abdallah yake?" Ta kuma tambaya wannan karon tana dubansu hawaye na bin kuncinta "Don Allah kuce min wani abu kunyi shiru,ko shima ya mutu ne?,shima yabi sahun mukhtar?,ku daina boyemin ku gaya min don Allah" "Abdallah na nan a raye bai mutu ba,kiyi haquri kinji sumayya" inji yaya yahanasu ta fada tana share hawaye,murmushi mai dauke da hawaye tayi wanda ya sanyasu yin jagale suna kallonta "Meye na boyemin idan shima ya mutun,ban isa nayi komai ba saidai nayi haquri,ku fadan don Allah na sashi cikin addu'ata idan har ya mutun" mama ce cikin hawaye ta taso ta iso gabanta ta soma share mata qwallar "Haka ne sumayya,kiyi haquri kan wanda kika yi,a iya binciken da jami'an tsaro sukayi abdallah bai mutu ba,saidai ya bata an rasashi ba'a san inda yake ba,amma in sha Allahu ana gab da samunsa 'yan sanda na nan suna bincike kan inda yake" shiru sumayyan tayi tana duban maman,sai ta sake qas da kanta bata sake cewa komai ba sai taci gaba da jan carbinta,ta riga ta sallama abdallah ya riga ya tafi kamar yadda mukhtar ya tafi ya barta,kasa zama anty dije tayi sai ta miqe ta fice tana hawaye,ba'a yi sallar magariba ba wani zazzafan zazzabi ya rufeta.       Zazzabin shi yaci gaba da jigata ta da wahal da ita tsahon kwanaki biyu har ranar sadakar bakwai,qarin ruwa kam ta shashi har ta godewa Allahi,idan ka ganta baka cewa itace sumayya,ita kadai tasan me take ji a gangar jikinta da zuciyarta,ta riga data sallamawa rayuwa baki daya.      *****   *******  *****      Zaune take a falon gidan sanye da hijabi da carbi,idarwarta kenan daga sallar walha,gidan ba kowa sai yaya yahanasu wadda ke zuwa kullum ta wuni ta tafi anty dije halima da matar kawun abdur rahman,tun shekaran jiya da akayi sadakar bakwai kowa ya watse aka barta da su.      Anty salma ce ta fito daga kitchen dauke da cup ta qaraso inda sumayya ke zaune "Ungo ai kin idar da sallar karbi kisha" kai ta gigirza hawaye fal idanuwanta "Bazan iya sha ba anty salma,babu dadi,tsayamin yake a wuya" "Haba sumayya,haba sumayya,ana yabonki sallah kuma ya haka,kowa na yabawa tawakkalin da kikayi,akwai ciwo rashin miji da batan da'a,amma kinsan babu yadda za'ayi rayuwa ta yiwu ba abinci,tunda abun nan ya faru baki sake sanya abu cikinki ba,mu kanmu da muke tare da ke kinsan ba zamu ji dadi ba,daure ki karba kisha don Allah ko kurba uku ce" hawaye na bin kuncinta ta karba ta kafa kai tare da rintse ido kamar wadda zata sha guba,kurba uku tayi masa ta dire kofin tana maida numfashi,dai dai lokacin da aka yi sallama bakin qofar falon amsawa sukayi halima ta duba tace 'yan sanda ne,anty dije tace eh abban laila ne ya turosu su shigo suke bincike kan batan abdallah da musabbabin hadarin mukhtar,gaban sumayya yayi mummunan faduwa idanuwanta kan qofar falon har suka shigo,suka samu gu suka zauna,tambayoyi suka yiwa sumayyan suna saurarenta har ta gama,daya daga cikinsu wanda da alama shine babbansu ya fiddo wata leda wadda kana iya hango abinda ke ciki ya miqo musu "Kince gab da lokacin da abin zai faru kunyi waya,munga komai nashi cikin motar saidai bamu ga wayar tasa ba,ko akwai wanda yayi kiran lambarsa tun bayan rasuwar?" Anty yahanasu dake zaune gefe tace "Gsky a'ah" "Ok,ko zamu iya samun lambar wayar tasa?" "Eh" anty dije tace,ita ta karanta masu lambobin yana rubutawa,ya kammala rubutawa sannan ya latsa kiran,cikin second uku kiran ya shiga,tsit dakin yayi kamar babu wani mai numfashi suna sauraren shigan kiran wayar "Waye me magana" wata murya ta fada daga can bangaren "Am,mukhtar nake nema don Allah" wata dariya aka saki wadda cika falon kasancewar a hands-free ya sakata "Ai mukhtar ya dade da wulawa barzahu,idan ma qarin bayani ake nema bari nayi maka,mun kashe mukhtar,hakanan d'ansa yana hannunmu mun daukeshi,zamuyi masa irin tarbiyyar da muka ga dama mu kuma moreshi sannan mu aikashi inda babansa ya tafi,na tabbata wannan ya ishi babbarsa itama tabi sahunsu" qit aka katse kiran,salati suka dauka baki dayansu,basu ankara ba sai ganin sumayya sukayi ta sulale a gurin,tashin hankali sabo,a rude baki dayansu sukayi kanta.       A hankali ta bude idanuwanta tana fadin "Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahla,wa anta taj'alik hazna iza shi'ita sahla" idanunta ya sauka cikin falon,wannan karon mutane sun dadu sabanin dazu,malam ya abbakar kawu da mijin anty dije wato umar farouq duka suna cikin falon,sai ta sanya kuka tana kiran sunan Allah,tausayinta ya kama kowa,wannan karon babu wanda ya hanata,don sunsan cewa abun ya mata yawa,dole ta zubda hawaye ko zata samu sauqin radadin dake cikin zuciyarta,a qalla kimanin minti goma tana kukan mai fidda sauti kafin ta koma yin na zuci,sai a sannan 'yan sandam suka samu damar yin magana,wanda yayi magana dazun wannan karon ma shi ya maganta "Alhamdulillahi mun gode Allah,ba shakka wannan bincike ya zo mana cikin sauqi,cikin ikon Allah sun sauqaqa mana wahalar bincike" "Haka nace cikin zuciyata ASP,yanzu me kake ganin za'ayi,don ya kamata cikin gaggawa a nemo yaron kada  su samu nasarar cutar da rayuwarsa" cewar mijin anty dije cikin tsananin takaici da zaquwa "Hakane alhj farouq,ina ganin zamuyi amfani da hikimar tracing layin har don mu gano indo suke" "Good,hakan yayi,kamar zuwa yaushe kenan ?"alh farouq ya sake fada " daga yau zuwa gobe in sha Allahu zamu aiwatar da komai" "Na gode ASP,na gode qwarai" alhj farouq ya fada yana bawa ASP hannu,sukayi sallama daga nan suka fice.      Hankalinsa ya maida ga su malam "Malam,sai mu dage da addu'a,Allah ya bada nasara a gano ko su waye,ba shakka idan aka ganosu ba zamu qyalesu ba,sai mun bi haqqin ran mukhtar da yardar Allah....sumayya saiki qara haquri,Allah ya baki juriya ya baki ladan haqurin da kikeyi". Godiya sosai su malam ya yiwa farouq gajin yadda yayi uwa yayi makarbiya kan lamarin,bai gari ma sanda abun ya faru amma ya dawo ya karbi ragamar al'amarin,a nan sukayi sallar azahar sannan suka tafi bayan ban baki da suka sake yiwa sumayya. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 5⃣1⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* _______________________________ *Innal laha ma'al lazinat taqau wallazina hum muhsinun* *haqiqa Allah yana tare da masu jin tsoronsa,kuma yana tare da masu kyautatawa* ____________________________     A hankali jerin gwanon motocin jami'an tsaron suka dinga kutsa kai cikin hanyar don baza'a kirata layi ba,saboda sabuwar unguwa ce wadda ba'a kammala ginin nikan dake cikinta ba balle a samu sukunin gabe layuka,kana iya bi ta ko ina,cikin gonaki ko filayen dake daura da wajen wucewarka,motar dake gaba mutumin dake kusa da mazaunin direba wanda shine shugaban 'yan sanda shi ya dauki wata waya da jami'an tsaro suke magana don bada umarni zuwa sasanni dabaj daban ya kara a bakinsa yana bada sanarwa ga sauran motocin dake biye da su a baya a kan su kashe jiniya,sannan ko wannensu ya shrya don suna gab da qarasawa gidan da na'ura ta musu nuni cewa a wannan gun layin wayar mukhtar ke aiki.       Sosai suka dinga rage gudu har suka qaraso daura da gidan inda suka faka motocinsu,ogan nasu ya sauka ya bawa kowanne umarni kan inda zai tsaya,kafin wani dan lokaci sun zagaye gidan baki dayansa,daya daga cikinsu wanda ke sanye da kayan gida saidai akwai qaramar bindiga boye a aljihunsa ya nufi qofar gidan kai tsaye,yayi bugu kusan sau goma kafin ya jiyo wata kakkausar murya na tambayar wane,nine yace aka sake maimaitawa da cewa kai wane "Gun oga nazo,idan na baza'a bude ba ai harkar ba dole bace sai na koma akwai masu jira na"ya fada cikin zafi zafi " bari na sanar masa"mai maganar yace yana mai juyawa zuwa cikin gidan,a falon gidan ya samesu harda ZAINAB dake zaune tana dakon zuwan mutumin da zata saidawa abdallah da shi,wanda abdallah ke zaune gefe daya a falon cikin kashi da fitsari,kwanukan da yake cin abinci da su suma sun gauraya cikin qazantar,yana sanarmusu baqo yazo oga ya bada umarni a bude masa ga zatonsu mao siyan yaron ne yazo.       Yana kammala bude qofar yayi caraf ya damqeshi,bindiga ya nuna masa saitin kansa yana cewa "Duk wani motsi da zaka yi wanda zai alamtawa abokan aikinka akwai matsala dai dai yake da harba alburushi cikin kwanyarka,muje ka nuna mana inda suke" kai ya kada idanuwa a warwaje kamar an shaqe mujiya,alama ya yiwa sauran jami'an tsaron da zasu shiga ciki suka biyo bayansu.        Kusan su biyar ne a falon,ganin an taso dan uwansu da bindiga ya sanyasu saita tasu "Ku ajjiye makamanku,idan ba haka ba ku baqunci lahira" cewar wani gabjejen dan sanda cikin kakkausar murya,da fari sun so suyi gardama,amma daga bisani da suka ga yawan jami'an tsaron ya sanya su ajjiye makaman nasu aka tattarasu gu daya sannan aka fara aikin daure musu hannayensu don yin gaba da su.       Tuni cikin zainab ya duri ruwa,ta tabbatar cewa matuqar batayi wani abu da zata wanke kanta ba tun anan babu shakka tata ta qare,saboda haka tayi hanzari ta faki idanuwansu ta zagaya inda abdallah ke zaune cikim qazanta yana kallon kowa ta kunceshi ta qanqameshi a jikinta duk wari da zarnin da take shaqa ta hadiyeshi,sai ta saki kuka mai gunji tana fadin "Allah na gode maka da ka kubutar da mu daga hannun wadan nan azzaluman,Allah abin godiya" kukan nata na qarya yaja hankalinsu,wannan kakkauran dan sandan daya gama qullesu ya kalleta yana zare ido,cikin daga tsawa yace "Kefa?,daga ina?"ance mara gaskiya ko cikin ruwa gumi yake,take jikinta ya kama rawa cikin rawar murya tace " nice....nice uwar dannan,sato mu sukayi"baki dayansu 'yan sanda suka zuba mata ido,kowa dai yasan case din rasa abdallah,hakanan sunsan uwa da ubanshi,to ita wannan din wace da zata ce uwarsa ce "Wallahi qarya take yallabai,ita ta bamu kwangilar kashe......." Wanda ya bude musu qofa wanda da alama duk ya fisu tsoro ya fara rattabo bayani cikin rawar jiki "Qarya ne sharri zai min" zainab ta fada cikin daga murya tare da yunqurin hanashi tona mata asiri,take sai musu yaso ya balle tsakaninta da shi,shi yana son bayyanawa ita tana son hanawa,yayin da ogan nasu haushin zainab ya tsaya masa a wuya,ya tabbatar koma meye wannan kama sun yana da alaqa da aikinta da suka aiwatar mata,ji yake ina ma bai ya da bindigarsa ba,da babu shakka sai ya fasa mata kai da harsashi a take,amma babu komai,idan kere na yawo zabo na yawo zasu hade,tsawa shugan 'yan sandan ya buga musu wadda ta sanyasu yin tsit "Lawan,dauke abdallah,idris ka sanya mata ankwa itama,ko meye ma ya kawota nan din muje bincike zai nuna" ya fada yana ficewa tare da yi musu umarnin su tafi,zainab na zare ido na komai aka buga mata ankwa aka hadata da tsagerun aka tura cikin mota,sun fara tafiya kenan ogan ya faki idon dan sandan dake tsare da su ya daga kafceceyar qafarsa ya daki ta zainab cike da jin haushinta da ganin ta jaza musu masifa,ji kake qasssssss zainab din ta saki wata razananniyar qara ta sume,shugaban 'yan sanda shi yace aci gaba da tafiya kada a tsaya idan anje station a mata duk taimakon da za'ayi,yayin da yasa suka qara dora kula a kan oga don gudun kada ya subuce musu. Tun safe da taga fitar malam alhj farouq da kawu hankalinta ya kasa kwanciya,duk da cikin damuwa take sai damuwar tata ta ninka ta da,jan carbi take wanda shi ya zamo mata abokin hirarta tana share hawaye,har aka yi sallar la'asar babu labarinsu,abunda ta kula da shi shine lokaci lokaci anty dije na daga waya tana kiran mai gidanta,saidai babu wanda ta tambaya kamar yadda babu wanda ya yimata bayani. Cikin dakinta tayi sallar magariba tana jiran isha'i,ta zurfafa a cikin tunani anty dije ta shigo "Kizo inji su malam" "To" ta fada ba tare da ta iya motsawa ba,gabanta ne ya tsananta faduwa,zuciyarta ta ta cire tsammani ,wala'alla ba'a samu nasara ba,wala'alla ta rasa abdallanta kamar yadda ta rasa mahaifinsa,shikenan haka Allah ya tsarama rayuwarta,sai ta kife kanta jikin gado ta saki kuka "A'ah,subhanallahi sumayya kuka dai?,ke da nace kije su malam da abban laila(alhj farouq)na jiranki,tashi don Allah ki bar kukan nan haka" anty dije ta fada tana qoqarin dagata,ita ta dafa don ba cin abinci take ba balle ta samu qwarin jikinta a haka har suka isa falon. Bata san ta saki anty dije ba,bata san kan qafafunta take tafiya ba sai data isa gaban abdallah ta zube wanda ke kan cinyar ya abbakar,wani sabon kuka ta saki tana yunqurin daukar yaron ganin yadda ya sauya cikin kwanakin da basu wuce goma ba,yayi baqi ya rame goshinsa har da ciwo,a haka ma sai da aka kaishi wajen mama tayi masa wanka ta bashi abinci yaci aka sauya masa sababbin kaya,qanqameshi tayi tana sake sakin kuka mai cin rai,kowa tausaya mata yake tare dayi mata kyakkyawar addu'ar yankewar qaddarorinta haka nan,a hankali alhj farouq ke bayani "Alhamdulillahi an kama Abdallah tare da wasu wadanda babu shakka su sukayi sanadin mutuwar mukhtar kamar yadda sukayi iqirari da kansu,tunda an kamasu da wadansu abubuwa dake sake bayyanar da hakanne,cikin wadanda aka kama harda wata ZAINAB wadda da fari ta musu iqirarin cewa itace mahaifiyarsa" da sauri sumayya ta dago kai tana maimaita zainab cikin ranta gabanta na ci gaba da faduwa,alhj farouq ya dora "Amma abinda su yaran suka ce shine ita ta dauki ta basu aikin kashe mukhtar,sannan daga bisani da taga ba zata iya biyansu sauran kudin ba ta sauya shawarar daukar abdallah ta tafi neman kudi da shi,taga gwara su saida abdallah ta biya kudin sauran tayi harkar gabanta" ba sumayya ba wannan karon,baki daya jama'ar dake falon ba qaramin girgiza sukayi ba,wannan waccw iriyar masifa ce,tamkar ba diyar musulmi ba,tamkar babu digon musulunci a jikinta,wannan karon cak kukan sumayya ya tsaya,sunayen Allah ta dinga kira,tsoron zainab na kamata kamar tana wajen,kisa zainab,kisa?,kisan mukhtar?,daga bisani wani hawayen ya sake subuce mata,har ta gaji da kuka haka nan,ko da yaushe idanunta zafi suke mata saboda kuka,har wani lokaci take gani hatsa hatsa,sai ta rufe idonta tana godewa Allah daya QADDARA mata sake rayuwa da d'anta,ya kubutar mata da d'anta cikin aminci da salama,bata san da wanne baki zata godewa uncle mukhtar mijin anty dije ba,ta sake jinjina masa da yadda yayi zumunci irin haka sanda taji yana fadin idan aka kammala bincike cikin 'yan watanni qalilan insha Allah za'a soma shari'a,don dole abi kadin haqqin rai a kuma hukunta duk wanda ke da hannu cikin lamarin,tabbas babu shakka indai har da zainab cikin wadanda suka aikata wannan aiki mutum ya zama abun tsoro,to idan babu sa hannunta shin me ya kaita wajen?,har tana iqirarin abdallah danta ne?,ita ce mamarsa? "Ya Allah ka yimin gata,ka shigemin gaba,ka yimin jagora cikin al'amuran rayuwa ta" abinda ta dinga fadi kenan tana maimaitawa rungume da abdallah a jikinta,shi kansa yaron kallonta yake tayi yana kiran ammi lokaci zuwa lokaci,haka yayi luf a jikinta jikinsa a sanyaye yana jin dumin mahaifiyarsa. ****** ******** ****** *wai ina lukman ne?* *kuyi haquri da wannan sabgogi sun sha min kai,ku tara gobe in sha Allahu* *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 5⃣2⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* _________________________________ *Allahu waliyyul lazina amanu yukrijahum minaz zulumati ilannur* *haqiqa Allah shine majibancin lamarin wadanda sukayi imani yana fitar da su daga duhu izuwa haske* _________________________________ *ina muku fatan alkhairi baki dayanku kafatanin groups dake karanta KUNDIN QADDARATA* *GIDAN LUKMAN* Baki daya rayuwar gidan ta yiwa karima baqi,kusan ita kadai ke rayuwarta cikin gidan,yaran baki daya sun kwashe kayansu sunyi qaura zuwa bangaren hajiya,tsakaminta da su kallo daga nesa,suna dai shigowa su gaidata su kuma tambayeta mai zasuyi mata na aiki,hakanan duk abinda tace suyi matuqar bai sabawa addini ko al'ada ba hajiyan na umartarsu suyi mata,lukman kam tunda ya hada kayansa yayi tafiya zuwa legos tsawon watanni rabonsa da gida,saidai yakan kira wayar hajiya wanda ya siya ya ajjiye musu a bangaren hajiya,yana kira suyi hira da yaran ya kuma gaisa da hajiyan,sau tari idan tace ba zai dawo ba haquri yake bata,yace sam yaji gidan ya fice masa ne a rai tunda sumayya ta bar gidan,hakanan yana zama yana bata ran hajiyan,amma tayi haquri lokaci ne idan yayi zai dawo,sam karima bata san ya sauya lamba ba saidai idan ta kira tayi ta jin is switch off,hakanan a yanzu ba zata iya cewa ga inda lukman din yake ba,sai dai lokaci lokaci tana jin alert na transper din kudi daga account dinsa zuwa naga,kudin buqatunta na yau da kullum,sannu a hankali hankalinta ya fara tashi,wannan karon saboda rashin lukman din a kusa bata da isashshen kudi gunta da zata koma wajen malaminta. ******** ***** ******** Sannu a hankali rayuwa ta dinga juyawa,kwanakin takabarta na raguwa,ta fawwalawa Allah lamarinta baki daya,hakanan ta karbi QADDARArta hannu bibbiyu,saidai ba'a raba zuciya da tuna abubuwa masu d'aci da suka gabatar mata,yanayin sumayya ya sauya baki daya,ta sake zama mai yawan shiru shiru,sai kallo da idanuwa,har yau jikinta ya kasa komawa dai dai,ta rame,sai uban fari data sake yi sanadiyyar ramar da tayi,anty dije ta koma sai ita a gidan da zainab da halima,su kawu sukace ta zauna tayi iddarta a dakinta don haka addinin musulunci yafi so,lokaci lokaci ya abbakar da matarsa da suke kira anty sukan leqosu. Ranar wata asabar wanda ya kama wata biyu da rasuwar mukhtar alhj farouq ya iso kano,cikin falon sumayya suke zaune kamar yadda suka saba idan zama irin wannan ya kamasu,bayan gaishe gaishe da qarin wani jajen alhj farouq ya soma gabatar da maganar data tarasu "Bayan dukkan wani bincike da jami'an tsaro suka gabatar ya bayyana cewa zainab ita ta dauki nauyi ta kuma bada umarnin kisan mukhtar" duk sa suna zargin hakan amma sai da maganar ta sake razanasu,kuka yaya yahanasu ta sanya tana salati da kalmar shahada tare da ambatar sunan zainab,alhaj farouq bai kula ba ya dora "Ta bayyana dalilinta na yin hakan da cewa bacin ran wulaqancin da mukhtar ya mata ne na saki uku kuma yaqi maidata bayan kaahe kudaden da tayi wajen bin malamai amma babu nasara,qarshe ma ya bita da dukan kawo wuqa,daga bisani kuma ta tsinci labarin ya maida aurensa da sumayya bayan ita ta kamu da cuta mai karya garkuwar jiki ta sanadinsa,tunda taga haka ta tabbatar bazai mayar da ita ba,sai taga gwara ayi biyu babu kowa ya rasa,baya ga haka dama tana jin haushin sumayya na tsallake rijiya da baya da tayi har ta haifi abdallah"alhj farouq ya saurara yana maida numfashi cike da bacin rai,ji yake kamar ya shaqe zainab a lokacin da take wannan bayanin,tun asali shi mutum ne mai tausayi da jin qai,baya qaunar zalunci sam a rayuwarsa "La ilaha illa anta,yanzu sakayyar da zainab kika yi mana kenan,ashe kece ajalin muntari?" Yaya yahanasu ta fada tana sakin kuka mai qarfi har da sheshsheqa,tana jin cewa itace da alhakin mutuwar mukhtar,durqushewa tayi sannan ta ja jikinta da qyar ta isa gaban sumayya wadda abdallah ke zaune a kan cinyarta tana dubansh,idanuwanta sun gaji da kuka sai na zuci take wanda yafi ciwo "Sumayya,don girman Allah,don darajar ma'aiki da iyayenki ki yafemin,babu shakka ina ji a raina nice sikar ajalin muntari,Allah ya bawa muntari mace ta gari,ta daga hankalina na hanaku zaman lpy don kawai baki samu abinda Allah ne kadai ke da ikon bawa bawa ba,na yi masa aure na farko suka rabu bai isheni ishara ba,na sake dauko masa wata na tsaya kai da fata sai da ya kawota cikin rayuwarku,ashe ita ce ajalinsa,itace silar tarwatsa rayuwarku,nayi gaggawa na shiga hurumin ubangiji,idan da na haqura ashe akwai rabon mukhtar bazai taba barin duniya ba sai ya haifi abdullahi,sumayya ki yafemin,kimin afuwa,wallahi na tabbatar idan baki yafemin ba haqqinki bazai taba barina cikin rayuwa ba....." Sai ta kasa qarasa abinda take da niyyar cewa muryarta ta sarqe kamar idanuwanta zash tsiyaye saboda kuka. Dubanta sumayya keyi kawai,ita yanzu a rayuwa me ya rage mata?,me zai bata mata rai?,mene ribar taqi yafewa yaya yahanasun tunda mai afkuwa ta afku,babu mai goge abinda ya faru,idan ta qullaceta mai hakan zai maganta mata?,koba komai taci darajar mutum biyu MUKHTAR da ABDALLAH "Allah ya yafe mana baki dayanmu" abinda ta fada cikin raunin murya,babu wanda hakan bai burgeshi ba,godiya ta dinga jerawa sumayyan tare da binta da kyawawan addu'o'i sannan ta juya ga malam "Malam kaima ina neman afuwarka,abinda na yiwa diyarku da kuka bamu ita cikin aminci da amana tun tana shekara sha uku amma naci amana,na bada gudun mawa wajen mutuwar mijint...." Nan ma kasa qarasawar tayi saboda yadda lamarin ke mata ciwo cikin zuciyarta "Ya isa yahanasu,babu mai rayawa ko kashewa sai ubangiji,komai akwai sanadiyya amma kuma Allah ya riga ya tsara komai,abinda ake so ga bawa dama shine,a duk sanda ya fahimci yayi wani kuskure to ya nemi afuwa ya kuma guji aikata laifin a gaba,Allah ya bamu dacewa baki daya" "Amin ya Allah,amin" duka suka amsa,sumayya ta miqe don komawa ciki,haka take bata son zama cikin jama'a balle tayi doguwar magana,a nan alhj farouq ya sanar musu cewa ranar litinin za'a miqa zainab da sauran yaran kotu,amma basai sumayyan taje ba insha Allahu tunda sun amsa laifinsu ba wata doguwar shari'a za'ayi ba. ******* ****** ******** Kwana goma ya rage mata ta kammala takabarta aka gama shari'ar wadda ta dauki wata biyu ana yinta,bincike ya nuna zainab na da hannu dumu dumu wajen mutuwar mukhtar,ita ta biyasu suka kunce tayar motar mukhtar a sanda yake shagon dinki zai amso kayan dinkin sa,yayin da yaran data dauka aiki anjima ana nemansu,irin mutanen da ake hayarsu ne suyi kisa,sun kashe mutane da dama hakan ya sanya aka yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya,zainab kuwa aka yanke mata hukuncin daurin rai da rai,aka fara wucewa da ita asibiti,sabida a lokacin cuta mai karya garkuwar jikin dake jikinta ta fara mata tasiri,zaman gidan kurkuku da tayi ba tare data fara shan magani ba ya sata bayyana lokaci guda,alamominta duk sun gama bayyana,sannan qafarta da oga ya daka ta karye aka mata dori dorin baiyi kyau ba,don da aka kwance gun har ya fara ruwa yana neman lalacewa...... ****** ****** ******* Ranar da ta kammala takabarta a washegari malam yace su dawo gida,kawun abdur rahman shi ya nemi alfarma gun malam din yayi haquri a gama tattara dukiyoyin muntari a raba gado,shikam yace babu komai duk abinda suka zartas dai dai ne amma kawun yace a masa alfarmar dai,cikin qanqanin lokaci aka kammala hada komai na mukhtar din,aka raba gadon kamar yadda ubangiji ya tsara,kusan dukiyar baki daya abdallah ya cinyeta kasancewarsa d'a namiji qwaya daya tal wajen mahaifinsa,kawu ya tattaro dukiyar baki daya ya kawo gaban malam,sam malam yace yaje ya riqe ya kula da ita amma qememe kawun yaqi,daga qarshe suka yanke shawara aka danqawa ya abubakar ya juya masa cikin kasuwancinsa da yake na saida atamfofi,addu'a sosai suka yiwa abubakar din kan Allah ha tayashi riqo *SABUWAR RAYUWA* A kullum ta kebe kanta ita daya tunani take yi yaya rayuwa zata kaya mata?,meyw kuma kundin qaddararta na gaba?,wanne shafi kundin zai bude mata kuma?,amma a zahiri ta saki jikinta ko don yadda 'yan uwa da iyayenta suka damu da ita,burin kowannansu ya faranta mata ya sanyata dariya,kowa tausayinta yake,tana ganin bai kyautu ba taci gaba da zama cikin damuwa har ta sanya wasu,mukhtar dai ya riga ya tafi ba kuma zai taba dawowa ba har abada duk kuwa yadda take qaunarsa,qauna daya ce tsakaninsu kada ta manta da yi masa addu'a,hakan yasa ta rungumi rayuwarta ta kuma rungumi danta,a lokacin cikin kudinta na tumunin takaba ya abbakar ya ware mata wani abu yace ta fara sana'a,dama can sumayya ta iya sana'arta,saboda haka babu bata lokaci ta shiga kasuwar kurmi ta saro kayan humta turaren wuta na daki kaya dana tsugunno sai kwalakca ta koma tsohuwar sana'arta,mutum ce ita mai nasibin sana'a,duk abinda ta sanya kanta ta fara saidawa sai Allah ya kama mata,cikin ikon Allah kuwa sai wannan karon abun nata ya sake bunqasa,cikin abokan ya abbakar akwai mutum uku da iyayen gidansh ke da supermarket,suka buqaci ta kawo su gwada cikin shagon,ta samu kwalabe masu kyau da tsari ta zuba,ba'ayi sati ba suka qare suka kawo mata kudinta suja sake nemam wasu,cikin lokaci qanqani abun ya habaka,sai ta sanya halima da zainab ciki sukeyi tare,tunda ta aikama anty dije itama take karba ta amfanin gida,wani lokaci ta saida ko tayi kyauta. Sana'ar da take yi ta dauke hankalinta sosai,ta rage mata zaman tunani da kuka,saidai duk da haka babu wani abu da ya ragu na tunanin mukhtar cikin ranta,hakanan duk dare kafin bacci ya dauketa sai tayi kuka mai isarta. ****** ***** ******** *_Bayan shekara daya_* Koda kwana daya ne ya ratsa cikin rayuwar bawa ta iya yiwuwa kaga sauyi tattare da rayuwar nan tasa,walau a sarari ko a boye,hakan ce ta kasance ga rayuwar gidan su sumayya,wanda a wannan shekara guda din an sauya fasalin gidansu san sake musu gini mai kyau da tsari cikin ribar kudin abdallah sumayya tasa aka yi wannan aiki,sun sake samun rufin asiri sosai,babu abinda ta nema a rayuwarta ta rasa,ci da sha da sutura baki daya,don har taimako takanyi cikin ribar sana'arta wanda bai gaza dubu hudu zuwa qasa ba,an kawo kudin auren zainab wanda ba'a sanya rana ba ana jira zuwa wani lokaci kafin na halima ya gama shiryawa kamar yadda yace a bashi lokaci. ***** ********** ****** Sanye take da dogon hijabi mai hannu wanda har jan qasa yake,qafarta na sanye da safa sai niqabi daure a fuskarta,wannan itace shigar data koma yi tun randa ta taba fita wani ya biyota ta yiwa kanta alqawarin canza shiga,duk da dama can ma'abociyar sanya hijabi ce,daga ranar ta bada kudi aka dinka mata su kaloli masu kyau har kala biyar,ko ina zata su take sanyawa duk tsadar suturar dake jikinta,ko yaushe kar suke a goge cikin tsafta da qamshi,shigar na matuqar yi mata kyau qara mata kwarjini da kuma boye kyawun sufarta baki daya,dawowarsu kenan daga gidan anty salma ita da halima ta kai mata humra da turaren wutar da ta yiwa wata amarya da za'a yiwa aure 'yar maqotanta,daga nan ta tsaya aka musu lalle ita da haliman bayan ta shiga kasuwa ta sayi kayan humra,saboda anty dije tace sati na sama tana nan zuwa kano,har tana tsokanarta da ita zata koma abuja don ta fuskanci bata qaunar zuwa abujan ko kadan,dariya sumayyan ta dinga yi tana tsokanar anty dijen itama da cewa zaman garinku sai wanda ya saba,haka kawai kaje a qunsheka cikin gidan ba motsin yara bana maqota saidai idan kai ka shiga. Sam bata damu da sabuwar motar da ta gani ajjiye qofar gidansu ba suka wuce zuwa cikin gidan ita da halima suna 'yan hurarrakinsu,tun daga soron gidan su qamshin turare ke dukar hancinsu ba kuma irin turaren humrarta ba da ya kama gidan,daga bakin qofar falonsu ta hangi takalma sau ciki na maza bata kawo komai a ranta ba tadage niqaf dinta tayi sallama cikin falon. Abdur rahman ne zaune cikin daya daga cikin kujerun falon sanye da shadda ruwan madara wadda ta haska fatarsa,kansa hula ce zanna,hankalinsa na kan mama suna taba hira da alama labari yake bata,sallamar su ce ta maido hankalinsa bakim qofar,baki ya saki yana kallonta cikin mamaki kamar yadda ta saki baki itama tana kallonsa cike sa mamakin yaushe ya diro nijeria "Kai kam baka da aiki sai zuwan bazata?" "Kawai kice yaushe a gari inji maqi baqo" ya fada yana murmushi,sai data samu gu ta zauna sannan ta dubi mama "Wai don Allah mama yaushe yazo?" "Fitarku ba dadewa" sai tayi murmushi tana gaida shi,amsawa yake shima cikin sakin fusakar suka fara dan tsokanar juna yadda suka saba,halima ce ta shigo wadda sai da ta tsaya ta daura alwala,a ladabce ta gaidashi ya amsa yana dubanta "Wai shekara daya tal naga duk kum qara girma,halima ke kam ashe ke kika debo kamar sumayya"dariya tayi ta shige daki don tada sallah,mama ta miqe jin zainab na kiranta tazo taga ruwan miyar tuwon daren data tsayar ya isa. Maida dubansa yayi ga sumayya "sumayya ya kuma bayan saduwa,bayan tafiyata lamura masu yawa sun wakana,Allah ya jiqan yaya mukhtar,ya gafarta masa ya masa kyakkyawan masauki a aljanna yasa ya huta" "Amin ya Allah" ta fada wani miki na neman motsuwa a zuciyarta,zuciyar na son karyewa hawaye na neman zuba,shuru ya ratsa dakin yana nazarinta,ya fuskanci ya taba mata mikin dake zuciyarta "Tunda nazo nake tambaya ina mutumina ashe yana gidan gwaggwo yahanasu,da yake ban leqa gidan ba,jiya na shigo qasar" sai ta murmusa tana cewa "Ayyah,ai da ya samu hutu sai tazo ta daukeshi da kanta" idanu ya zaro "Kice abdallah an fara makaranta,lallai an girma"murmushi ta kuma tana bashi amsa sanda mama ke dawowa cikin falon "eh,ai yana cika shekara ya abbakar ya sanyashi" "Wacce makaranta ce?" "New egypt international" kai ya kada "Masha Allah" hirar sai ta koma gun mama sai ta miqe itama tayi sallar la'asar,bashi ya bar gidan ba sai da yayi magariba suka gaisa da malam sannan ya ajjiye musu tsaraba dangin alawoyi da jallabiya ta maza data mata tasu sumayya zainab da halima,sai tarin qananan kaya na abdallahnsa. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 5⃣3⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* _________________________________ *Allahu waliyyul lazina amanu yukrijahum minaz zulumati ilannur* *haqiqa Allah shine majibancin lamarin wadanda sukayi imani yana fitar da su daga duhu izuwa haske* GAISUWA MAI TARIN YAWA DA FATAN ALKHAIRI GAREKU 'YAN WATTPAD,BA SHAKKA INA JIM DADIN COMMENT DINKU,HAKA INA GODIYA DA ADDU'O'INKU. _________________________________ *GIDAN LUKMAN* Baki daya rayuwar gidan ta yiwa karima baqi,kusan ita kadai ke rayuwarta cikin gidan,yaran baki daya sun kwashe kayansu sunyi qaura zuwa bangaren hajiya,tsakaminta da su kallo daga nesa,suna dai shigowa su gaidata su kuma tambayeta mai zasuyi mata na aiki,hakanan duk abinda tace suyi matuqar bai sabawa addini ko al'ada ba hajiyan na umartarsu suyi mata,lukman kam tunda ya hada kayansa yayi tafiya zuwa legos tsawon watanni rabonsa da gida,saidai yakan kira wayar hajiya wanda ya siya ya ajjiye musu a bangaren hajiya,yana kira suyi hira da yaran ya kuma gaisa da hajiyan,sau tari idan tace ba zai dawo ba haquri yake bata,yace sam yaji gidan ya fice masa ne a rai tunda sumayya ta bar gidan,hakanan yana zama yana bata ran hajiyan,amma tayi haquri lokaci ne idan yayi zai dawo,sam karima bata san ya sauya lamba ba saidai idan ta kira tayi ta jin is switch off,hakanan a yanzu ba zata iya cewa ga inda lukman din yake ba,sai dai lokaci lokaci tana jin alert na transper din kudi daga account dinsa zuwa naga,kudin buqatunta na yau da kullum,sannu a hankali hankalinta ya fara tashi,wannan karon saboda rashin lukman din a kusa bata da isashshen kudi gunta da zata koma wajen malaminta. ******** ***** ******** Sannu a hankali rayuwa ta dinga juyawa,kwanakin takabarta na raguwa,ta fawwalawa Allah lamarinta baki daya,hakanan ta karbi QADDARArta hannu bibbiyu,saidai ba'a raba zuciya da tuna abubuwa masu d'aci da suka gabatar mata,yanayin sumayya ya sauya baki daya,ta sake zama mai yawan shiru shiru,sai kallo da idanuwa,har yau jikinta ya kasa komawa dai dai,ta rame,sai uban fari data sake yi sanadiyyar ramar da tayi,anty dije ta koma sai ita a gidan da zainab da halima,su kawu sukace ta zauna tayi iddarta a dakinta don haka addinin musulunci yafi so,lokaci lokaci ya abbakar da matarsa da suke kira anty sukan leqosu. Ranar wata asabar wanda ya kama wata biyu da rasuwar mukhtar alhj farouq ya iso kano,cikin falon sumayya suke zaune kamar yadda suka saba idan zama irin wannan ya kamasu,bayan gaishe gaishe da qarin wani jajen alhj farouq ya soma gabatar da maganar data tarasu "Bayan dukkan wani bincike da jami'an tsaro suka gabatar ya bayyana cewa zainab ita ta dauki nauyi ta kuma bada umarnin kisan mukhtar" duk sa suna zargin hakan amma sai da maganar ta sake razanasu,kuka yaya yahanasu ta sanya tana salati da kalmar shahada tare da ambatar sunan zainab,alhaj farouq bai kula ba ya dora "Ta bayyana dalilinta na yin hakan da cewa bacin ran wulaqancin da mukhtar ya mata ne na saki uku kuma yaqi maidata bayan kaahe kudaden da tayi wajen bin malamai amma babu nasara,qarshe ma ya bita da dukan kawo wuqa,daga bisani kuma ta tsinci labarin ya maida aurensa da sumayya bayan ita ta kamu da cuta mai karya garkuwar jiki ta sanadinsa,tunda taga haka ta tabbatar bazai mayar da ita ba,sai taga gwara ayi biyu babu kowa ya rasa,baya ga haka dama tana jin haushin sumayya na tsallake rijiya da baya da tayi har ta haifi abdallah"alhj farouq ya saurara yana maida numfashi cike da bacin rai,ji yake kamar ya shaqe zainab a lokacin da take wannan bayanin,tun asali shi mutum ne mai tausayi da jin qai,baya qaunar zalunci sam a rayuwarsa "La ilaha illa anta,yanzu sakayyar da zainab kika yi mana kenan,ashe kece ajalin muntari?" Yaya yahanasu ta fada tana sakin kuka mai qarfi har da sheshsheqa,tana jin cewa itace da alhakin mutuwar mukhtar,durqushewa tayi sannan ta ja jikinta da qyar ta isa gaban sumayya wadda abdallah ke zaune a kan cinyarta tana dubansh,idanuwanta sun gaji da kuka sai na zuci take wanda yafi ciwo "Sumayya,don girman Allah,don darajar ma'aiki da iyayenki ki yafemin,babu shakka ina ji a raina nice sikar ajalin muntari,Allah ya bawa muntari mace ta gari,ta daga hankalina na hanaku zaman lpy don kawai baki samu abinda Allah ne kadai ke da ikon bawa bawa ba,na yi masa aure na farko suka rabu bai isheni ishara ba,na sake dauko masa wata na tsaya kai da fata sai da ya kawota cikin rayuwarku,ashe ita ce ajalinsa,itace silar tarwatsa rayuwarku,nayi gaggawa na shiga hurumin ubangiji,idan da na haqura ashe akwai rabon mukhtar bazai taba barin duniya ba sai ya haifi abdullahi,sumayya ki yafemin,kimin afuwa,wallahi na tabbatar idan baki yafemin ba haqqinki bazai taba barina cikin rayuwa ba....." Sai ta kasa qarasa abinda take da niyyar cewa muryarta ta sarqe kamar idanuwanta zash tsiyaye saboda kuka.Dubanta sumayya keyi kawai,ita yanzu a rayuwa me ya rage mata?,me zai bata mata rai?,mene ribar taqi yafewa yaya yahanasun tunda mai afkuwa ta afku,babu mai goge abinda ya faru,idan ta qullaceta mai hakan zai maganta mata?,koba komai taci darajar mutum biyu MUKHTAR da ABDALLAH "Allah ya yafe mana baki dayanmu" abinda ta fada cikin raunin murya,babu wanda hakan bai burgeshi ba,godiya ta dinga jerawa sumayyan tare da binta da kyawawan addu'o'i sannan ta juya ga malam "Malam kaima ina neman afuwarka,abinda na yiwa diyarku da kuka bamu ita cikin aminci da amana tun tana shekara sha uku amma naci amana,na bada gudun mawa wajen mutuwar mijint...." Nan ma kasa qarasawar tayi saboda yadda lamarin ke mata ciwo cikin zuciyarta "Ya isa yahanasu,babu mai rayawa ko kashewa sai ubangiji,komai akwai sanadiyya amma kuma Allah ya riga ya tsara komai,abinda ake so ga bawa dama shine,a duk sanda ya fahimci yayi wani kuskure to ya nemi afuwa ya kuma guji aikata laifin a gaba,Allah ya bamu dacewa baki daya" "Amin ya Allah,amin" duka suka amsa,sumayya ta miqe don komawa ciki,haka take bata son zama cikin jama'a balle tayi doguwar magana,a nan alhj farouq ya sanar musu cewa ranar litinin za'a miqa zainab da sauran yaran kotu,amma basai sumayyan taje ba insha Allahu tunda sun amsa laifinsu ba wata doguwar shari'a za'ayi ba. ******* ****** ******** Kwana goma ya rage mata ta kammala takabarta aka gama shari'ar wadda ta dauki wata biyu ana yinta,bincike ya nuna zainab na da hannu dumu dumu wajen mutuwar mukhtar,ita ta biyasu suka kunce tayar motar mukhtar a sanda yake shagon dinki zai amso kayan dinkin sa,yayin da yaran data dauka aiki anjima ana nemansu,irin mutanen da ake hayarsu ne suyi kisa,sun kashe mutane da dama hakan ya sanya aka yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya,zainab kuwa aka yanke mata hukuncin daurin rai da rai,aka fara wucewa da ita asibiti,sabida a lokacin cuta mai karya garkuwar jikin dake jikinta ta fara mata tasiri,zaman gidan kurkuku da tayi ba tare data fara shan magani ba ya sata bayyana lokaci guda,alamominta duk sun gama bayyana,sannan qafarta da oga ya daka ta karye aka mata dori dorin baiyi kyau ba,don da aka kwance gun har ya fara ruwa yana neman lalacewa...... ****** ****** ******* Ranar da ta kammala takabarta a washegari malam yace su dawo gida,kawun abdur rahman shi ya nemi alfarma gun malam din yayi haquri a gama tattara dukiyoyin muntari a raba gado,shikam yace babu komai duk abinda suka zartas dai dai ne amma kawun yace a masa alfarmar dai,cikin qanqanin lokaci aka kammala hada komai na mukhtar din,aka raba gadon kamar yadda ubangiji ya tsara,kusan dukiyar baki daya abdallah ya cinyeta kasancewarsa d'a namiji qwaya daya tal wajen mahaifinsa,kawu ya tattaro dukiyar baki daya ya kawo gaban malam,sam malam yace yaje ya riqe ya kula da ita amma qememe kawun yaqi,daga qarshe suka yanke shawara aka danqawa ya abubakar ya juya masa cikin kasuwancinsa da yake na saida atamfofi,addu'a sosai suka yiwa abubakar din kan Allah ha tayashi riqo *SABUWAR RAYUWA* A kullum ta kebe kanta ita daya tunani take yi yaya rayuwa zata kaya mata?,meyw kuma kundin qaddararta na gaba?,wanne shafi kundin zai bude mata kuma?,amma a zahiri ta saki jikinta ko don yadda 'yan uwa da iyayenta suka damu da ita,burin kowannansu ya faranta mata ya sanyata dariya,kowa tausayinta yake,tana ganin bai kyautu ba taci gaba da zama cikin damuwa har ta sanya wasu,mukhtar dai ya riga ya tafi ba kuma zai taba dawowa ba har abada duk kuwa yadda take qaunarsa,qauna daya ce tsakaninsu kada ta manta da yi masa addu'a,hakan yasa ta rungumi rayuwarta ta kuma rungumi danta,a lokacin cikin kudinta na tumunin takaba ya abbakar ya ware mata wani abu yace ta fara sana'a,dama can sumayya ta iya sana'arta,saboda haka babu bata lokaci ta shiga kasuwar kurmi ta saro kayan humta turaren wuta na daki kaya dana tsugunno sai kwalakca ta koma tsohuwar sana'arta,mutum ce ita mai nasibin sana'a,duk abinda ta sanya kanta ta fara saidawa sai Allah ya kama mata,cikin ikon Allah kuwa sai wannan karon abun nata ya sake bunqasa,cikin abokan ya abbakar akwai mutum uku da iyayen gidansh ke da supermarket,suka buqaci ta kawo su gwada cikin shagon,ta samu kwalabe masu kyau da tsari ta zuba,ba'ayi sati ba suka qare suka kawo mata kudinta suja sake nemam wasu,cikin lokaci qanqani abun ya habaka,sai ta sanya halima da zainab ciki sukeyi tare,tunda ta aikama anty dije itama take karba ta amfanin gida,wani lokaci ta saida ko tayi kyauta. Sana'ar da take yi ta dauke hankalinta sosai,ta rage mata zaman tunani da kuka,saidai duk da haka babu wani abu da ya ragu na tunanin mukhtar cikin ranta,hakanan duk dare kafin bacci ya dauketa sai tayi kuka mai isarta. ****** ***** ******** *_Bayan shekara daya_* Koda kwana daya ne ya ratsa cikin rayuwar bawa ta iya yiwuwa kaga sauyi tattare da rayuwar nan tasa,walau a sarari ko a boye,hakan ce ta kasance ga rayuwar gidan su sumayya,wanda a wannan shekara guda din an sauya fasalin gidansu san sake musu gini mai kyau da tsari cikin ribar kudin abdallah sumayya tasa aka yi wannan aiki,sun sake samun rufin asiri sosai,babu abinda ta nema a rayuwarta ta rasa,ci da sha da sutura baki daya,don har taimako takanyi cikin ribar sana'arta wanda bai gaza dubu hudu zuwa qasa ba,an kawo kudin auren zainab wanda ba'a sanya rana ba ana jira zuwa wani lokaci kafin na halima ya gama shiryawa kamar yadda yace a bashi lokaci. ***** ********** ****** Sanye take da dogon hijabi mai hannu wanda har jan qasa yake,qafarta na sanye da safa sai niqabi daure a fuskarta,wannan itace shigar data koma yi tun randa ta taba fita wani ya biyota ta yiwa kanta alqawarin canza shiga,duk da dama can ma'abociyar sanya hijabi ce,daga ranar ta bada kudi aka dinka mata su kaloli masu kyau har kala biyar,ko ina zata su take sanyawa duk tsadar suturar dake jikinta,ko yaushe kar suke a goge cikin tsafta da qamshi,shigar na matuqar yi mata kyau qara mata kwarjini da kuma boye kyawun sufarta baki daya,dawowarsu kenan daga gidan anty salma ita da halima ta kai mata humra da turaren wutar da ta yiwa wata amarya da za'a yiwa aure 'yar maqotanta,daga nan ta tsaya aka musu lalle ita da haliman bayan ta shiga kasuwa ta sayi kayan humra,saboda anty dije tace sati na sama tana nan zuwa kano,har tana tsokanarta da ita zata koma abuja don ta fuskanci bata qaunar zuwa abujan ko kadan,dariya sumayyan ta dinga yi tana tsokanar anty dijen itama da cewa zaman garinku sai wanda ya saba,haka kawai kaje a qunsheka cikin gidan ba motsin yara bana maqota saidai idan kai ka shiga. Sam bata damu da sabuwar motar da ta gani ajjiye qofar gidansu ba suka wuce zuwa cikin gidan ita da halima suna 'yan hurarrakinsu,tun daga soron gidan su qamshin turare ke dukar hancinsu ba kuma irin turaren humrarta ba da ya kama gidan,daga bakin qofar falonsu ta hangi takalma sau ciki na maza bata kawo komai a ranta ba tadage niqaf dinta tayi sallama cikin falon. Abdur rahman ne zaune cikin daya daga cikin kujerun falon sanye da shadda ruwan madara wadda ta haska fatarsa,kansa hula ce zanna,hankalinsa na kan mama suna taba hira da alama labari yake bata,sallamar su ce ta maido hankalinsa bakim qofar,baki ya saki yana kallonta cikin mamaki kamar yadda ta saki baki itama tana kallonsa cike sa mamakin yaushe ya diro nijeria "Kai kam baka da aiki sai zuwan bazata?" "Kawai kice yaushe a gari inji maqi baqo" ya fada yana murmushi,sai data samu gu ta zauna sannan ta dubi mama "Wai don Allah mama yaushe yazo?" "Fitarku ba dadewa" sai tayi murmushi tana gaida shi,amsawa yake shima cikin sakin fusakar suka fara dan tsokanar juna yadda suka saba,halima ce ta shigo wadda sai da ta tsaya ta daura alwala,a ladabce ta gaidashi ya amsa yana dubanta "Wai shekara daya tal naga duk kum qara girma,halima ke kam ashe ke kika debo kamar sumayya"dariya tayi ta shige daki don tada sallah,mama ta miqe jin zainab na kiranta tazo taga ruwan miyar tuwon daren data tsayar ya isa. Maida dubansa yayi ga sumayya "sumayya ya kuma bayan saduwa,bayan tafiyata lamura masu yawa sun wakana,Allah ya jiqan yaya mukhtar,ya gafarta masa ya masa kyakkyawan masauki a aljanna yasa ya huta" "Amin ya Allah" ta fada wani miki na neman motsuwa a zuciyarta,zuciyar na son karyewa hawaye na neman zuba,shuru ya ratsa dakin yana nazarinta,ya fuskanci ya taba mata mikin dake zuciyarta "Tunda nazo nake tambaya ina mutumina ashe yana gidan gwaggwo yahanasu,da yake ban leqa gidan ba,jiya na shigo qasar" sai ta murmusa tana cewa "Ayyah,ai da ya samu hutu sai tazo ta daukeshi da kanta" idanu ya zaro "Kice abdallah an fara makaranta,lallai an girma"murmushi ta kuma tana bashi amsa sanda mama ke dawowa cikin falon "eh,ai yana cika shekara ya abbakar ya sanyashi" "Wacce makaranta ce?" "New egypt international" kai ya kada "Masha Allah" hirar sai ta koma gun mama sai ta miqe itama tayi sallar la'asar,bashi ya bar gidan ba sai da yayi magariba suka gaisa da malam sannan ya ajjiye musu tsaraba dangin alawoyi da jallabiya ta maza data mata tasu sumayya zainab da halima,sai tarin qananan kaya na abdallahnsa. Mrs muhammad ce✍ ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 5⃣3⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *innash shaidana lakum aduwwun fattakizuhu aduwa* *HAQIQA SHAIDAN ABOKIN GAABARKU NE,KU RIQE SHI ABOKIN GAABA* ___________________________ *Afuwan nayi mistake na number,yau ne zamu tashi page na 53* ___________________________________         Yanayin sanyi ya fara ja baya,yayin da zafi ya fara sako kai,wannan shike nuna alamu na tahowar damuna,mafi yawanci lokutan zafi bata iya bacci mai yawa,hakan shi yake sanya ta tashin wuri,qarfe goma tuni ta kammala ayyukan gidab,bata ma jirayi tashin zainab ko halima ba,wanka tayi ta sanya kaya sa'annan ta debi kayan kari daga kitchen ta shiga falon mama,a zaune ta sameta itama tana gyara mafitai tunda lokacin amfaninda su ya zo,kasancewar ba ko da yaushe ake samun wuta ba,nan ta zauna tana karyawa suna hira da mama,bayan ta kammala ta dauko kayan hadin humrarta tana fadin "Mama bari kiga na fara hadawa anty dije tata,saura kwana biyar tazo kada lokaci ya quren" "Ai kam don idan tazo baki matan ba ke da ita,ya taku kada ku sakani ciki" dariya sumayyan ta danyi tana bude robar ruwan turare "Ai ba'a shiga fadan uwa da d'a mama,Allah mama tun ina mamakin irin qaunar da anty dije kemin har naxo na daina" murmushi mama tayi "Ko sanda muna gida tamu tafi zuwa daya ai,dana haifi abubakar lokacin bata yi aure ba cewa tayi da sai ta karbeshi,sanda na haifeki kuma basa garin nan ita da farouqu da tuni gunta zaki tashi,kinga kuma kina da shekara sha uku aka aurar da ke" kai take jinjinawa tana hadin humrar tare da jin dadin labarin da mama ke bata.       Halima wadda bata jima da tashi a bacci ba ta shigo dauke da wayar dake burari sumayya wadda gunta wayar ta kwana tana miqa mata "Yaya ana kiranki" kanta ta daga ta dubeta "Waye?" "Baquwar lambace" ta daga mata kiran sannan ta miqa mata,karawa tayi a kunnenta tana mai sallama daga daya bangaren aka amsa mata sannan ta buqaci sanin waye,ajiyar zuciya ya saki yana lumshe idanuwansa "Amma kam banji dadi ba da har cikin sauri haka kika manta da ni sumayyah" gabanta ne ya fadi,idan ba gixo kunnenta ke mata ba muryar lukman ce,dakewa tayi cikin qarfin hali tace "Ba abun mamaki bane don na mance muryar wanda ban sani ba" dariya ya dan saki sannan yace "Lukman ne sumayya,lukman tsohon mijinki wanda kuma yake fatan sake zamantowa mijinki a karo na biyu" jikinta ne ya dauki bari,sai kawai ta katse wayar tana duban halima da ta zuba mata ido tana kallonta,mamanta shiga uwar daki maida mafitan "Halima lukman ne wai" ta fadi muryarta na rawa "Mene?,me ya gaya miki?" "Ba komai" "Shine kuma duk kika bi kika rude yaya,har yau kamar mune yayun kece qanwar wlh,kinga,ki tsaya kiji me zai fadi bawai ki katse waya ba" "Cewa yayi tsohon mijina mai kuma fatan sake zama mijina" "Dole aka ce haka ce zata tabbata?" Ta tambayeta tana kallonta,shiru tayi bata amsa mata ba,ganin bata da alamar ansawa ya sanyata juyawa zata fice,sai sumayyan ta niqa mata wayar tace ta tafi da ita.        Gabanta ne ya dinga faduwa,sai aikin nata ya koma sukuku sabanin dazu da take yinsa cikin karsashi,har mama ta ankara saidai bata tambayeta ba,tana zaton ko mukhtar ta tuna,da yake yawancin lokuta haka na faruwa da ita idan ta tuna shi,tana shirin miqewa ta adana kayan haliman ta sake shigowa riqe da wayar,idanuwa ta tsareta da shi "Ya aka yi?" "Ba lukman bane wannan karon ya abdur rahman ne" tsaki ta ja tana ci gaba da ayyukanta,ta gama lura da take takensa "Duk kanwar ja ce,dauki kice bana kusa" "To" haliman ta fada tana daga wayar gami da ficewa daga dakin.       Sai bayan kusa awa daya sannan ta dawo dakin tana dariya ta dubi sumayy "Wlh yaya kin ban kunya,kinga ya abdur rahman ya gane fa,cewa yayi har da ni a yi masa qarya ko,yace zaya zo anjima zamu hadu" shiru tayi ba tare da ta ce komai ba,bata fata ko buri abdur rahman ya dora daga inda ya tsaya wajen yada manufarsa,domin a yanzu bama abdur rahman ba,bata buri kowanne namiji ya sota,don kwata kwata bata ji a rayuwarta zata iya sake yin aure,idan tayi tana jin kamar taci amanar mukhtar ne,gwara taci gaba da rayuwarta a haka har itama tata tazo ta tadda ita ta hadu da mukhtar dinta a jannatul firdausi.       Idanu ta dinga zubawa tana addu'a kada yazo,addu'arta kuwa taci don baizo ba din har suka kwanta,saidai washegari da yammaci ta gama wanka kenan tana shafa mai taji muryarsa a tsakar gida,yau duka a kasalance ta wuni cikin mutuwar jiki,saboda yadda lukman ya matsanta mata da kira da turo saqonnin ban haquri yafiya da kuma yunqurin dawowa gareta,baki daya ya birkita mata kwanya,baisan yadda ta tsani batun aure ba yanzun,sam ya fice mata a kai,ta yaya zatayi marmarin abunda tasha wuya cikinsa,baki daya tarihin rayuwarta wahalar aure ce wadda ta cimmata ta jigata ta cikin qananun shekaru.       Ta kammala sanya kayanta tana shirin tada sallah wadda zata yita ne a makare don lokacin ya fita zainab ta shigo wadda ta gama shiryawa zasu yinin biki ita da mama "Ya sumayya kizo inji yaya abdur rahman" "Ina zuwa" tace tana yunqurin tada sallah "To mu mun tafi inji mama,tace ki kula da yadfa halima zata sa sanwa kada tayi yawa tunda yau banda malam" kai ta gyada mata don ta riga ta tayar din.        Falo zuwa tsakar gida ta duba duka baya nan,hakan ya sanya ta leqa soronsu a bakin sitting room ta hangi takalmansa,sai ta sanya silifas ta fita zuwa can,da sallama ta shiga ya daga kamsa daga wayar da yake daddannawa ya dubeta,gefe can ta samu ta gaidashi ya amsa idanuwansa na kanta,kallon ya fara mata yawa saboda haka ta kau da kai tana shirin magana sai kuma ya rigata "Nima sai an ja min aji sannan za'a fito?" Idanu ta watsa masa wadanda suka sanyashi lumshe nashi idon,sau tayi murmushi ba tare da ta dubeshi ba tace "Wanne irin jan aji kamar saurayin da yazo zance gurin budurwarsa" "Ai hakanne,saurayin ne yazi zance gun budurwarsa ko kin manta?" Sai ta sake dubansa,Maganar ta taba ta duk da ta tsammaci haka,shima ita yake kallo,cikin son maida maganar wasa tace "Ah ko?,to ai kayi kuskure,ka manta ni din ba budurwa bace,saboda haka saidai bazawari yazo guna ba saurayi ba,saurayi sai budurwa ai" "A haka na gani nake kuma matuqar so" shi kuma ya fada ba tare da alamun wasa ba,ganin yanason maida zancen gaske sabanin yadda take son maidawa saita waske da cewa "Yau kuma tsurfa ce ta tashi daga toge a sitting room maimakon ka shiga ciki yadda ka saba?" "Neman aure nazo,kinga bai kamata naci gaba da shiga cikin falom surukai ina zama ba" sai ta danyi dariya duk ason bagarar da zancan "Ah wai...auren halima ko?"ya fuskanci da gangan take watsi da manufofin da yake son yadawa,hakan ya sanya ya kira sunanta wanda ya tilasta mata dubansa "kinsan ko a da idan na fadi magana irin wannan da gaske nake ko?,to har yau din ma hakan take,da gaske sumayya na dawo neman aurenki ke karo na biyu babu wasa,kuma ina fata wannan karon ni zan jefa qwallon"shuru tayi tana jin yadda zuciyarta ke bugawa,mukhtar dinta ta tuna,ta daga kai tana kallon abdur rahman idanuwanta fal qwalla "yanzu kaima sai ka yarda naci amanar ya mukhtar?" Cikin rashin fahimta ya tsuke gira "Cin amana kamar yaya,da aurensa ne a kanki?,ina cewa koda yana raye halas ne na aureki bare ya rasu?" Kalmar ta mata ba dadi sai ta miqe "A gunka mukhtar ya rasu amma ni a cikin zuciyata rayayye ne tamkar yadda kake a raye" sai ta juya ta fice kuka na qwace mata,sam bayi tunanin wannan maganar ta isa bata rai ba,amma da ya tuna cewa har yau tana cikin zafin mutuwar uban danta sai ya mata uziri,hakan ya sanya daga sitting room din ya wuce ba tare da ya dawo ciki ba,har dare ranta na a jagule,tana zaman zamanta yana neman jagula mata lissafi,tana ganin kiransa ta share shima da yaga bata daga ba sai ya tura mata tex ya qyaleta.   *******    *******   ********       Batasan cewa ana shirin jagula mata lissafi ba sai washegari da azahar data tsinkayi sallamar su nuwaira a tsakar gidansu,baki daya yaran ne cikin kyakkyawar kaka data bayyana mata har yau basu sauya kan turbar data dorasu ba,zuciyarta ta dinga bugawa tsoro ya cikata,duk da a bangare guda tayi farinciki da ziyarar tasu.        Sosai taji dadin zuwan yaran,basma ta dubeta "Anty abbanmu ne ya kawo mu,yace wai kema zaki dawo gidanmu ko?" Yarinyar ta tambayeta,murmushi tayi tana shafa kanta "Basma,har yau surutu na nan kenan" ta fada da sigar son bagarar da maganar,tare suka wuni da ita,suna zagaye da ita suna bata labarun gidansu da yadda lamura suka sauya,inda sukayi dai dai ta yaba musu,inda suka kuskure ta gyara musu ta nuna musu yadda akeyi.      Da yamma bayan sun gama sallar la'asar sun sake cin abinci nuwaira ta dubi sumayya "Anty,don Allah ki daure ki dawo gidanmu,abba yace mu roqeki,muna sonki wallahi anty,baki ga yadda hajiya ma ke son ki dawo ba,naji tana cewa ne ba zata sanya baki ba tun yanzun,kada nauyinta ya sanya kiyi abinda bakiyi niyya ba ta shiga haqqinki,don Allah anty ki dawo" ta fada tana karkatar da kai,sai islam ma ta matso "Eh wallahi anty tunda kika tafi baki daya gidan babu dadi,ko abba ma barin garin yayi,baifi wata daya da dawowa na,da ya dawo kuma kullum masifa suke da mama,gidan ba dadi muna gun hajiya ko yaushe,ki dawo anty don Allah kinji" kasa magana tayi baki daya,wato lukman kwaso mata yaransa yayi kenan su masa campaign ko su daure ta da jijiyar jikinta? "Anty baki ce komai ba" cewar nuwaira wadda ta qagu taji sumayyan ta amsa,murmushi ta sanya ta kama hannayensu ta hade waje guda "Kunsan komai nufin Allah ne,kuma ko wanne bawa da irin tasa qaddarar,to ku yita addu'a idan akwai alkhairi zan dawo in sha Allah kunji?" "To anty" suka fada jikinsu a sanyaye,duka sai suka bata tausayi,babu shakka yaran abun tausayi ne,su masu uwa ma kenan bare mara uwa a gidan,ko da yake dace da uwa ta qwarai shine jigon farinciki da jin dadin rayuwar 'ya'ya duniya da lahira.        Qarfe biyar saura yaro yayi sallama gidan yace su nuwaira su fito,tuni basma ta sheqa da gudu ta gano abban nasu sannan ta dawo "Abba ne,yace ku fito",kyautar humra da kwalakca ta yiwa kowannansu,sannan ta zuba wata da yawa ta hada da turaren wuta tace su kaiwa hajiya.        A bakin qofar soro ta ja tunga tana musu sallama,nuwaira ta dubeta tana narai narai da idanuwa "anty iya nan ko qofar gida ma ba zaki rakamu ba?"dariya tayi,ta fuskanci wayo wai yarinyar keson yi mata "shikenan muje"ta fada don faranta musu,yana tsaye bakin mota ya bubbude qofofin,da dai dai yaran suka dinga shiga tana musu sallama sannan ta rufe musu qofar motar,tana dagowa suka hada idanu "Ku gaida gida ku gaidamin hajiya" ta fada tana juyawa da niyyar shigewa ciki,da sauri ya tari gabanta "Haba mana sumayya,ko gaisuwa ai kya tsaya kuyi ko?" Ta tabbata idon yaran yana kanta hakan ya sanyata tsayawa tana dubansa "Don girman Allah sumayya kimin alfarma ki koma gida na,kimin alfarma ko don rayuwar yara na" "Ni kuma tawa rayuwar fa?" Ta masa tambaya kai tsaye "Sumayya gida na ya sauya a yanzu,da qafafuna nake tsaye,hijabin dake lullube da idanuwa Allah ya yamin shi,ki taimaka ki koma gidana ki sa cikasa mana sauran haske da farincikin da muke da buqata,kowa a gida na na buqatarki sumayya,don Allah kada ki gujemu". Kai ta kada " lukman,bani da buqatar nayi aure har na koma ga mahalicci na,domin ina fata naje na hadu da mijina uban 'ya'yana,ina mai baka shawara tun wuri kayi haquri da ni"ta qarashe zancan zuciyarta na raurawa ta kewayeshi ta wuce ciki,jiki babu qwari a sanyaye shima ya koma cikin motar ya tada ita ya bar layin. Tana shiga zainab na miqa mata waya,bata san ko waye ba haka bata tambaya ba,tama yi tsammanin anty dije ce don tace anjima zata kira ta,wayar ta maqala a kunne,muryar abdur rahman ta mamayi dodon kunnen nata "Ba mukhtar kadai ba,ashe har lukman ma na raye a zuciyarki?" Tambayar da ya fara jefo mata kenan wadda ta sanyata saurin janye wayar daga dodon kunnenta,yaushe abdur rahman ya ganta da lukman?,tambayar data yiwa kanta kenan,kawai sai ta tsinci kanta da fashewa da kuka,saman katifarta ta fada tana kife kanta a saman filo,baki daya cikin kwanaki hudu zuwa biyar kacal suna son lalata zaman lafiyar zuciyarta ruhinta da ma gangar jikinta?,wa yace musu tana da buqatar aure a yanzu?,wa yace musu tana buqatar wani daga cikinsu?,akan me zasu yi mata kutse cikin rayuwar data lallabata ta fara samun nutsuwa da dangana?su suke suce ta mance da mukhtar ta fara sabuwar rayuwa da su?,ta mance da mutumin da shi ya fara gina tunani da zuciyarta?. Qarar wayarta karo na biyu ya sake katse mata tunanin da ya karade ilahirin qwaqwalwarra,kamar ba zata daga ba sai taga lambar anty dije ke yawo bisa fuskar wayar,qara fashewa tayi da kuka da taga sunanta,zuciyarta ta sake karyewa,tasan a irin wannan yanayin babu wanda take budewa damuwarta irin anty dijen,taso ace a yanzu tana kusa da ita,sai ta daga kiran da sauri,saidai maimakon sallama da anty dijen ta tsammata sai taji sautin kukan sumayya ya karade kunnuwanta. *mrs muhammad ce*👑 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 5⃣4⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *Rabbukum a'alamu bima fi nufusikum* *(haqiqa)ubangijinku shine mafi sani ga abinda yake cikin zukutanku* _________________________________        A rude anty dije ta soma tambayarta "Lafiya sumayya?,me yake faruwa?,ko wani ne ya mutu?" Ta jero mata tambayoyin baki daya,jin tayi shiru bata tanka ba ya sanyata itama shirun tana sauraren kukanta,ta tabbatar wata matsalarce ta taso mata haka jikinta ya bata,tausayin yarinyar take ji,sai yaushe ne zata fita daga matsala,sai data dauki a qalla minti goma sannan ta soma magana cikin karayar zuciya "Anty,lukman da abdur rahman" "Me ya samesu?" "Anty......dukkaninsu sun dawo,kowanne so yake na aureshi,fisabilillahi anty ni bazan huta ba?,duka duka yaushe na soma samun nutsuwa?,anty bana buqatar sake wani auren yanzu,tsoro nake ji kada su nufi malam da maganar,idan malam ya umarceni anty bazan iya bijire masa ba" sai ta fashe da kuka,tsaki anty dijen tayi sannan tace "Zancan banza,kema kin riga da kinsan cewa malam yasan haqqinki na hannunki yanzu,ke zaki zabawa kanki miji ko?,sannan tsakanin lukman da abdur rahman akwai wanda ya isa ya aureki ne bada amincewarki ba da zaki tadawa kanki hankali ki dinga zubda hawayenki?,duk wanda kika zubar a baya bai isheki bane sumayya?,ko so kike wani ciwon ya sokeki?,to nikam na gaji da ji da gani,kishirya da gaske idan nazi tare zamu koma,idan yaso naga wanda zai qara bata ranki" ta fada tana katse wayar.        Shiru tayi tana juya wayar a hannunta,ba haka taso anty dije tace ba shawarar yadda zata kubuce daga tsakanin da lukman da abdurrahman suka sanyata take so ta bata,amma da tayi tsai sai ta lura lallai babu hanyar da zata zille musun idan ba barin garin kanon zata yi ba kamar yadda anty dije tace,sai ta sauke ajiyat zuciya tana goge hawayenta,tana qiyasta idan ta bar kano koda na tsawon wata daya ne itama ta samu hutu,ta samu ta manta da wasu lamuran ta manta da damuwoyinta.   *******  *******   *******   Washegari ta shirya don zuwa gidan yaya yahanasu ta dauko abdallah tunda duka duka saura kwana biyu anty dije tazo,tana tsaye a falon mama tana sanya hijabinta tare da yiwa mama sallama suka ji sallamar abdur rahman,kamar ta juya ta shige daki amma tasan idan tayi hakan kamar ta nunawa mama akwai wani lamari tsakaninsu irin wanda ya faru a baya,abinda bata da buri ko fatan kowa ya fahimta kenan "Ina yini" sumayyan ta gaisheshi tana shirin ficewa bayan sun gaisa da mama "Lafiya......ina zuwa haka?" Ya tambayeta yana dan dubanta,cikin hanzari ta soma sanya takalmanta tana bashi amsa "Zan dauko abdallah he gidan ya yahanasu" "Yauwa,nafi jin dadin tafiya,dama jiya da naje na yiwa abdallah alqawarin yoghourt" ya fada yana miqewa tsaye,kamar ta zura da gudu haka taji,take yanayin fuskarta ya sauya wanda tashin farko ya fahimci bata ji dadin shishshigin da ya mata ba,saidai sam bashi da damuwa matuqar zai kasance da ita,inda zata iya zata ce masa bata so amma idanuwan mama ya sanya ta kasa cewa komai "Sai mun dawo mama" "Allah ya kiyaye hanya ku gaida min yahanasun"maman ta fada ba don son ranta ba,don ba kasafai take barinsu suna shiga motocin gida ba koda na 'yan uwa ne,tafi ganewa su hau ta haya "Zataji" inji zainab wadda ita ce 'yar rakiyar.       Gaban motar ya bude mata da kansa,sai da yaga ta shiga ta zauna sannan ya zagaya nashi mazaunin ya tashi motar suka tafu,shiru ya ratsa motar,babu mai magana tsakaninsu,sai ya sanya hannunshi ya dannan plate jikin redion motar,cikin sakanni lacture malamin dake cikin fefan ta fara tashi,ya daj qaro volume din sannan ya dauke hannayensa ya maida kan sitiyarin motar "Nikam bansan wanne irin baqin jini ne da ni ba" ya fada qasa qasa yadda ita da shi ne kawai zasu iya jin me yake fadi,ta gefen ido ta kalleshi don ta tabbatar da ita yake ko kuwa,sai ta gane da ita din yake saboda yadda yake kallonta kadan kadan,shiru tayi bata da niyyar tankawa saboda bata fuskanci ma inda zaurancen nasa ya sa gaba ba "Sumayya me nayi da jiya baki sona,yau ma kinqi karbata,ko na aikata miki wani laifi ne?,ko ina da wani aibu da ban cancanci a soni ba?" Ya tambayeta yana mai muradin jin amsarta "Baka aikata komai ba,amma don son annabi mubar maganar nan,kada ka manta har yau jinyar zuciyata nake bata warke ba,ban kuma san ranar warkewarta ba" ta fadi tana duban gabanta ba tare da ta dubeshi ba.      Shuru yayi yana jin yadda ransa ya quntata,karo na farko da ya soma jin kishin nukhtar har cikin ransa,mukhtar jininsa ne wanda har ya mutu babu wani abu mara dadi da ya taba hadasu,hakan ya sanya bai sake tofa komai ba har suka iso gidan yaya yahanasun,tayi zaton zai shigo ne da ya ajjiyesu,sai taga ya juya kan motar yayi gaba.       A tsakar gida suka samu abdallan,yana ta wasa da dan qaramin keke da yaya yahansun ta siya masa,jamila na faman binsa tana sauya masa kayansa da yayi kaca kaca da su da miya amma yaqi yarda,ya maidata abar wasansa sai zagaye suke yana dariya,yana ganinta yayi cilli da keken ya taho a guje ya dafeta yana dariya,itama dariyar take,sai taji sanyi a cikin zuciyarta,yaya yahanasu da taji muryarsu ta fito cikin fara'a tana musu sannu da zuwa.       Ina ka saka ina ka ajjiye take tayi da su,kamar zata goya sumayyan,abdallah ya wani ajiye kumatu,abinda yakeso kawai yake cikin gidan,sai bayan sallar magariba sannan suka shirya tafiya,qeme me abdallah yace ba zai bisu ba,saidai sumayyan itama ta dauko kayanta ta zauna anan,dariya suka dinga yi,ganin haka ya sanya sumayyan tace a barshi,duk sanda ya gaji ya dawo.       Ga mamakinta suna fitowa ta tadda abdur rahman tsaye qofar gidan,qofa bude yana kallonta,ta fuskanci me yake nufi saboda haka babu musu ta shiga,zainab ma ta bude gidan baya ta shiga,sau daya rufe sannan taga ya shiga gidan,baifi mintina biyar ba ya fito suka tafi,har suka je gida baice uffan ba,ya saukesu ta masa godiya ta wuce,tana shirin kwanciya saqonshi ya shigo wayarta,saqo ne dake dauje da kalamai masu nuna tsantsar qauna,da nuna ba za'a rabu da abinda ake so ba,tana gama karantawa ta goge ta kwanta,tana ayyana ta kusa nesa da dukkan wadan nan rudanin.   ******   *********   *****    *BAYAN KWANA BIYAR*    Anty dije suka iso kano ita da yaran da mai gidan baki daya,gidansu na da anan suke masauki duk sanda suka zo din,bata samu zuwa gidansu sumayyan ba sai bayan kwana biyu da zuwan nata.        Sha daya da rabi na rana suka iso baki dayansu,sun sauya baki daya daga anty dijen duka sunyi kyau da wata irin gogewa,kana ganinsu kasan kwanciyar hankali da hutu sun samu wajen zama,duk suna falon mama,maman da anty dije suna hirarsu ta zumunci,yaran duka sun kewaye sumayya suna ta bata labari,mutuniyar tata minar na zaune dare dare kan cinyarta,laila ce ta soma tambayar Abdallah wanda hakan ya janyo hankalin anty dije "Nima fa ban ganshi ba" injita,murmushi mama tayi "Mu zai nunawa 'yan ubanci ai,tunda yahanasu ta daukeshi kinga yaqi dawowa,uwar ma taje da kanta yaqi biyota" haba anty dijen ta riqe tana dariya "Yanzun haka zamu tafi ki barshi a kano?" Tayi maganar ta sigar tambaya tana duban sumayya,dariya sumayya tayi "Wai da gaske anty sai na bikin?,to idan naje ma kwana nawa ne zan dawo ai ba dadewa zanyi ba" dubanta anty dijen tayi cikin mamaki "Wai meke damunki da baki son abuja ne kamar ana gutsurarki" tabe fuska tayi kamar qaramar yarinya "Garin ne ni banjin dadinsa anty haka kurum" kanta ta dauke daga kan sumayyan tana cewa "Sai kiyi kuma,mu me ya cimu?," "Yaya asama'u(sunan mama na asali)Allah yasa dai malam na gari,don tun yau nakeson sanar masa da sumayyan zan tafi,na lura kamar ku din a nan bata samun kwamciyar hankali da nutsuwar data dace,dama can baya kun yimim alqawarin bani ita kuma aure ya fado mata da wuri,kinga yanzu sai a cikamun alqawari na"dariya mama tayi tana cewa "Malam yana nan ya fita ne taron bude wani sabon masallacin juma'a da aka gina,amma nan da biyar ko shida na yammaci zai dawo" "To Allah ya dawo dashi lpy,ina nan har ya dawo" "Amin" inji mama. "Momy,wai anty da ita zamu tafi?" Khalipha ya fada cikin murna da doki yana dora hannunsa hannunshi kan cinyar anty dije "In sha Allahu" ta bashi amsa, "Yeeeeeyyyyyy" yaran suka sanya ihu baki daya har suka sanya sumayyan ta tuntsire da dariya duk da yadda jikinta yayi sanyi da zancan tafiyar tata. Anty dije ko bata tafu din ba har sai da malam ya dawo,sanda ta tuna masa tsohon alqawarin da suka mata dariya ya saka sosai,don shi sam ya manta da maganar ma baki daya,shi kansa cikin yaransa yana son sumayya,tana da baiwa da wasu halaye na daban da ba kowa ke da su ba,amma babu yadda ya iya,tilas ya cika alqawarin da ya dauka duk da cewa tsoho ne,yace ya basu sumayya halak malak indai suna so,da yake gaban alhj farouq akayi shima yaji dadi sosai,har da shi a godiya,don shima yasan halayen sumayyan,ya tabbata ko zama tayi cikin yaransa zasu qaru da ita,hakanan zata taimaka ma matarsa zasu dinga ganin nasu na gida a kusa da su saji dadi. Sanda labari ya iske sumayyan sai jikinta yayi sanyi saidai a fuska bata nuna komai ba ko don darajar yaran dake ta munnar zata koma gidansu,ya zata iya rabuwa da mahaifarta?,inda ta taso tayi wayo ta gabatar da rayuwarta baki daya?,inda anan dukkan wani tarihi na rayuwarta ya samo asali ya kuma kafu?,zata bi anty dije amma bata jin zata iya zama a garin din din din,zainab ce ta zungureta tana fadin "Wai nikam wacce iri ce ke yaya sumayya don Allah,ina ma nice anty dihe tace zan koma gurinta,wallahi da kinga yadda ake abu" harara ta watsa mata "Yanzun ma ki gayawa Abdulmalik kin fasa aurensa sai kizo ayi musaya da ni ke ki bita ni na zauna" dariya ta tuntsire da ita,tana son taga yaya sumayyan tata na masifa,sai tayi mata wani iri saboda bata saba ba ba al'adarta bace "Bazan iya ba wallahi,ni da abdul malik jini da hanta ne" "Madalla" ta fada taba juyawa taci gaba da abinda take cikim zuciyarta tana musu kyakkyawan addu'a da fatan dacewa da rayuwar aure mai inganci ba irin tata ba data kasance farkonta zaqi,qarshenta madaci wanda har yau take fama da taunarsa dacin bai bar bakinta ba,har yau duk farincikin da take ji idan ta tuna mukhtar sai ya gushe,duk sukunin da take ciki idan ta tunashi sai ya tarwatse,ko a yanzun data yi wannan tunani sai da hawaye suka biyo kuncinta. To sati daya anty dijen ke da niyyar yi,siyayya dama zasuyi kasancewar ba zasu sake dawowa kano ba sai bayan qaramar sallah,haka ta dinga zuwa tana daukan sumayyan suna shiga kasiwa siyayya,a kwanakin baki daya sumayya bata zama bata da sukuni,hakan ya sanya abdur rahman ko lukman babu mai sukunin ganinta,saidai kullum ta Allah saqonninsu na tafe ta ma'adanar saqonnin na wayarta,wani lokaci har da tarin misscall na kiran da bata daga ba,taso sumayyan ta dauki kayayyaki amma tace bata buqatar komai,data matsane ta yanki sababbin yadin hijabai da zasu kai mata har qasa ta bayar a dinka mata,anty dijen nata tsokanarta mai hijabai bqta ce komai ba ta dai yi dariya don ita a yanzun babu shigar dake mata dadi irin ta hijaban. Ana ya jibi zasu tafi bayan sun dawo daga kasuwa,suba zaune falon anty dije sumayya na tayata hada kaya wayar anty dije daga hannunsu laila ta dauji ruri,da sauri lailan ta sauko saga kan kujera ta nufi anty dijen tana cewa "Hajiya mama ce take kiranki" "Kamar kuwa tasan suna raina" anty dijen ta fada tana karbat wayar,sumayya nata shirya kayan ita kuma na wayar har ta kammala tana fadin "Komawa kasuwa ya kama mu fa gobe sumayya" tana zuge zif din jakar matafiya ta trolly ta dago kai ta dubeta "Naji kamar dazu kince kin kammala siyayya ko kinyi mantuwa ne?,nikam ma gaji da shiga kasuwan nan wlh kinsan ban taba shiga kasuwa haka ba?"tana zama gefan kujera tace "Nima kaina na gaji sumayya,amma hajiya mama ce tafi qarfin komai gunmu,ko abban laila sai da ya soma qorafi jiya wai kasuwannin kano zamy siye ne baki daya har yau bamu gama siyayya ba?" Ta qarashe tana dariya sumayya na tayata "Amma idan nace masa hajiya mama ce nasan bazai hana ba,ki kwana nan kawai gobe sai muje,atamfofi take so supers zatayi barka"idanuwa sumayya ta zaro "da super zatayi barka?"murmushi anty dije tayi "hajiya mama ce fa?,akwai yin harkar girma" shiru sumayya tayi sai data gama ta ture jakar gabanta sannan tace "Nikam bazan kwana a nan ba,ni da ku ganni sai randa zamu tafi ku biyo daukata,zanje na qarasa jin dumin tsohuwata" hararata anty dije tayi "Kome zaki fada saidai ki fada an riga an bamu ke kuma kin badu,so kike kice zaki ji duminta kafin jibi mu rabaki da ita ko?" Dariya ta qyalqyale da ita "Ni ba haka nake nufi ba anty" "Koma hakanne gobe da yamma kizo muje" "To" ta amsa tana dan miqewa saboda bayanta da ya qage,kiran abdur rahman ya katse mata hutun nata,da kamar ba zata daga ba sai kuma ta kasa "Gimbiya sumayya,ni yanzu lallabawa nake,naga alama ganinki sai an cike foam" "Baka fara cike foam din ba ka dai kusa ka fara cikewa" ta fada a zuciyarta,a fili kuwa sai tayi 'yar qaramar dariya data sanyashi lumshe iso saboda yadda sautin ya ratsashi "Ko kadan,sabgogi ke sukayi yawa,ina tare da anty dije kasan jibi zata koma" "Ayyah,amin gaisuwa gurinta don Allah,naso in shigo mu gaisa na fara kamun qafa saidai yanzun haka ina sokoto,baki ma sani ba saboda baki damu da ni ba" murmushi kawai tayi mishi,a ranar ta sake masa sun taba hira,hakan ya masa dadi sosai,itama sai ta danji dadi a ranta,saboda rabon tayi hira haka da wani har ta mance,sanda ta gama taga misscall din lukman kusan goma,bata bi ta kaiba ta kashe wayar,anty dije ce ta dinga tsokanarta kodai ta barta kanon kawai,murmushi tayi wanda baikai zuci ba,don har ga Allah bata son ayi mata maganar aure,sai magariba sannan ta koma gida. IDAN NA SAMU LOKACI WATAQIL ANJIMA KU SAMU WANI,IDAN KUMA KUNJI SHIRU TO BAN SAMU DAMA BA. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 5⃣5⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *wa lillahi Aaqibatul umur* *qarshen al'amari mallakar Allah ne* __________________________________ *WANNAN SHAFIN SADAUKARWA NE GAREKI* *UMMU RAMLAT(meena slimzy novel group)* Qarfe sha daya na safiya su Anty dije ta qaraso da motar su wadda drivern su ne zai ja motar kamar yadda suka zo,alhj farouq tuni shi ya riga su komawa saboda kira da ya samu daga wajen aikinsu. Tuni aka sanya kayanta a mota saidai ta tsaya sallama da mama,hawaye ne ya balle mata sanda suke sallaman,dariya maman tayi "Saikace wadda aka ce idan ta tafi ba zata dawo ba,jeki don Allah sunata jiranki kada ku bata lokaci a hanya" halima da zainab ne suka rakota har bakin motar,tana shirin shiga halima tace "Yaya sumayya,me za'a cewa yaya abdur rahman idan yazo,baki sanar masa ba fa,sannan baki bar saqo ba" "Ki fada masa duk abinda kika ga ya dace" dariya sukayi don sun fuskanci gatse take musu,tana shiga yaran suka fara raba gardama,kowa na fadin kusa da shi zata zauna,motar akwai yalwa,sit uku ne da ita harda gun mai tuqi na hudu,hakan ya sanya ta tattara ta koma sit din cab qarshe ita da laila da minal,khalifa da hafiz na sit na biyu,anty dije ita kadai na sit na uku wanda ke kusa da driver tana rubuce rubucenta da lissafi na siye siyen da tayi don ta taba kudinta sosai har ta so shiga kudin abban lailah shi yasa tace su barta tayi lissafi,saidai duk da ita daya ce a sit dinta hayaniyarsu bata barta tayi aikin da take so ba,sun cika motar da karadi sumayya na biye musu,duk da zuciyarta babu dadi amma haka ta dinga biye musu har suka hau kwalta sosai,minal ita ta fara bacci sannan hafiz da yake bashi da son hayaniya sosai,khalipha shima yabi sahu sai laila ta dinda dariya tana cewa "Yauwa kwa qyalemu ni da anty sumayya ta muyi hirarmu",su biyu suka dinga hirarsu tafiyar tasu naci gaba da gangawarawa,kafin a kai zaria sai ya zamto motar babu kowa sai sumayya da anty dije wadda sai lokacin ta samu sukunin yin aikinta. Suna shiga kaduna suka farka baki dayansu,nan anty dije ta sanya salihu direban nasu ya wuce da su wani gidan cin abinci (restaurant)da sukan tsaya suci abinci duk sanda zasu taho kano ko zasu koma abuja,cikin mintina qalilan suka isa da yake kamar kan hanya yake,sai da suka fara shiga masallacin dake daura da wajen suka bada farali sannan duk suka fito sumayya na dauke da minal take ta saje da 'yan garin,tun a hanya ta dinga qarewa yanayin garin kallo,akwai yawaitar mata masu dogon hijabi da niqab kamar nata,sai kuma qabilu data lura suna da wani kaso na musamman cikin garin,baka tafiya daya biyu baka gansu ba cikin irin nasu shigan,hakan ya sanya ta yiwa garin hasashen gari mai tarin mabanbantan qabilu da yare. Table biyu suka kama kowanne nada kujeru uku uku,daya sumayya laila da minal,sau dayan kuma anty dije hafiz da khalipha,salihu kuma na can wajen wani tsohon abokinsa ya karbi nashi abincin yana ci suna hira. Kowa cin abincinsa yake cikin kwanciyar hankali,saidai sam ita ta kasa cin nata,hasalima jinta take a takure tamkar ita kowa yake kallo saboda bata taba zama gu irin wannan taci abinci haka cikin guri dake cakude da maza da mata ba,ko da can ita mai kunya ce rashin sabo da rashin saurin sakin jiki,don haka minal kawai take ta bawa abincin idanuwanta na kan minal din duk motsin da take,don a tsarge take. tunda ta shigo gun ya zuba mata na mujiya,sau biyu suna hada idanu yana jifanta da murmushi,hakan ya sanya ta saka hannunta ta maida niqabin fuskarta,duka anty dije na ankare da yadda take a takure,saidai bata san dalilinta na sakin niqab din ba,ta dai dauka rashin sabo ne na shiga irin wadan nan wuraren,laila ce ta dubeta tana dariya "Wai anty sumayya anan din ma sai kin rufe fuskarki,wurin cin abinci ne fa kowa abinci yake ci,duba ki gani" ta fada tana waiwayawa tare da yi mata nuni da ido,sai itama lailan idanuwanta ya kai kansa,matashine wanda zaiyi shekara talatin da biyu,fari ne sosai,yana sanye da shadda ruwan madara dinkin yarbawa,kansa babu hula,kallo daya zaka masa kasan cewa hutu ya ratsa jikinsa,su uku ne saman teburinsu shi da wasu matasan da aqalla zasuyi shekaru daya,biyun cin abincinsu suke suna duba wayar da take hannun na kuaa da shi,sam basu ma lura da yanayin da dan uwansu ke ciki ba "Anty sumayya,kinga wani sai kallonki yake ya sanki ne?" Laila ta fada cikin sigar gulma murya qasa qasa taba ranqwafowa kan teburin "Ku da kuke wucewa ta gun baki sanshi ba sai ni da yau na fara zuwa" sumayya ta fadi tana gogewa minal baki da tissue bayan ta gama bata abincin "Ku taso mu wuce ko?" Anty dije tace tana daukar minal don ta ragewa sumayya tayi gaba suka bita a baya,da kanta taje wajen biya da yake har sun saba da su sosai,tasa aka hado takeaway saboda sumayya don ta lura bata ci komai ba ta amsa sannan suka wuce. Suna shiga motar laila tace "Lah,wallahi anty sumayya kinga har ya biyo mu ya koma,ta fada tana qyalqyala dariya" "Waye ya biyo mu" anty dije ta tambaya tana qoqarin maida atm dinta jaka "Ba kowa" sumayya ta fada da sauri sannan ta juya tana kallon laila,harararta tayi sannan tace "Bana son surutu komai kika gani kiyi magana kai,idan ba haka ba bazamu shirya ba" "Sorry anty sumayya" ta fada tana narke fuska don ta cikawa su hafiz baki ita ce ta gaban goshin anty sumayya bata son su gansu a rana "Shikenan" ta fada tana gyara zamanta,sai da suka sake daukar hanya sosai sannan ta lalubi wayarta da niyyar kiran yaya yahanasu,sai taci karo da misscall din abdur rahman,sai kuma saqon SMS _garin masoyi baya nisa,ina miki fatan alkhairi_ abinda kawai ya rubuta kenan,bata fahimci zaurencen nasa ba saboda haka ta share ta lalubi lambar yaya yahanasun ta danna kira,ringing biyu ta daga,cikin mutunci suka gaisa sannan aka nemo mata abdallah aka hadata da shi,hira ya dinga mata wani shirme wani abun dariya haka ta dunga dariya,daga bisani su laila suka amshe wayar suka yita shirmensu su da shi sai da suka cinye nata credit dinta tatas sannan suka haqura,bayanta ta maida makarin kujerar ta lumshe idanuwa zuciyarta fes tana jin dadi da jin muryar abdallah da tayi,tabbas d'a ba wasa bane,ababe ne masu wanke zukatan mahaifansu koda da shirme da quruciyarsu kadai,tunanin mukhtar shi ya ratso cikin farincikinta ya gusar da shi cikin yab sakanni qalilan,taje fuskarta ta sauya,damuwa ta lullube zuciyarta,taso abdallah ya rayu da mahaifinsa,yaci gaba da cin gajiyar gata da mahaifinsa ya tanadarwa rayuwarsa saidai ina,tsarin ubangiji shine daidai,tana jin hayaniyar su laila amma tayi fakare kamar mai bacci,bata sake bude idanuwanta ba har suka shiga garin abuja. Qarfe biyar da rabi suka isa garin,bata mance yadda unguwar tasu take ba saidai an sake samun sauye sauye,sabbin gine gine da kuma sabunta tsoffin. A falo suka zube baki dayansu wanda basu tashi ba sai da lokacin sallar magariba yayi sannan kowa ya debi kayansa zuwa daki,a dakin laila da minal ta zabi zama,kasancewar gado uku ne a dakin,daki ne madaidaici wanda ke shimfide da tiles da labulaye sai fenti dukkansu kala daya,wardrobe ce irin ta jikin bango wadda ta cinye bango guda,sai madubi a wani bangon daban,daya bangaren kuma gun ajitar takalma ne zuwa su jakankunan makarantarsu,daura da nan kuma qofar bandaki ne,sallah ta sanyasu suka fara yi sannan suka bude kayansu suka koma maidasu muhallinsu,a wanke a goge suke dawo da kayansu kamar yadda suka tafi da su. Anty dije ce ta turo qofar dakin ta shigo,wannan karon ta sauya kayan jikinta da alamu ma wanka tayi don sai qamshi take zubawa ta dubesu tana zama gefan daya cikin gadajen dakin "Sannunku da himma,hala ma ko wanka ba wanda yayi a cikinku ko?" "Ummi sai mun gama gyaran kaya"inji laila "eh kam bakwajin yunwa ne" anty dije ta sake fada,murmushi sumayya tayi din itakam ba yunwa tattare da ita,miqewa anty dije tayi "Idan kun gama ga takeaway can da abban laila ya shigo da shi sai ku dauka kuci,nikam ina ga sai da safe zamu sake haduwa da ku" Minal ce ta miqe da sauri "Ummi zani gun abba" "A'ah,ya shiga daki shima a gajiye ya dawo,abba sai da safe ki kwanta ga anty sumayya nan sumayya sai da safe,ayi kwanan baqunta lafiya" dariya duka sukayi sumayya tace "Allah ya bamu alkhairi anty" "Amin" ta amsa tana ficewa. Kamin wani lokaci sun gama kintsa komai,sai da suka ci abincin sannan suka yi wanka kowacce tayi shirin kwanciya,tana saman gadonta lullube da bargo saboda ac da laila ta kunna wayarta ta soma haske sabida ta maidata silent,abdur rahman ne kamar ba zata daga ba saboda bacci take da buqatar yi,amma sai taga hakan bai dace ba,a mutunce ta gaida shi ya shaida mata ya kirata dazun kiran bai shiga,ta sanar masa,mai yiwuwa lokacin suna kan hanya ne ba service,qorafi ya shiga yi mata kan dalilin tafiyarta bata sanar masa yace "A qalla ko addu'a sumayya na miki ko?,har yau kinqi gayan dalilin da ya sanya baki sona" baki ta bude kamar yana ganinta "Ni bance ma bana sonka ba abdur rahman,kawai dai ina da buqatar hutu ne cikin rayuwata,har yau zuciyata da qwaqwalwata basu zama fresh ba,kuma ko baya ga haka ma banson na zalunceka,don banajin akwau mahaluqin da zanso kwatankwacin mukhtar,zanfi so na qarashe rayuwata a haka naje na tadda shi a inda yake" shiru ya ratsa wayoyin nasu kafin daga bisani ya sauke ajiyar zuciya "Wannan ba hujja bace,amma har zuwa yaushe kike ganin qwaqwalwarki zata zama fresh din na daga miki qafa zuwa wannan lokacin?" "Ban sani ba nima abdur rahman,ban da masaniya" ta fada da alamun ta fara karaya,shuru ya sakeyi,ta tabbata sumayya abar tausayi ce,hakanaj dole ayi mata uziri,amma ya ya iya bazai iya rabuwa da ita ba,tsakanin jiya da yau kawai lissafinsa ya dagule,aikin da ya tafi sokoto domin shi ya gaza aiwatar da komai "Zan bar miki maganar da baki so har zuwa sanda zaki buqaci haka,saidai ina son don Allah mu maida dangantakar mu ta baya ta wa da qanwa,idan na kiraki ki amsamin kamar dan uwanki kin yarda?" "Anya hakan ma zai yiwu?" "Mai zai hana kin manta abdur rahman ne dan zaman dakinki?" Dariya ya sanyata wadda ta taho da hawaye,ya tuna mata wani abu can baya,wani abu da bazai taba goguwa cikin KUNDIN tarihin rayuwarta ba,dadi yaji cikin ransa da ya fuskanci ta sake,bai wani cikata da surutu ba sosai yace ta kwanta tayi bacci zaya kirata gobe yaji yaya kwanan abuja. *WAI INA ZAINAB NE?* Tun sanda aka kaita asibitin ta soma gane Allah da girma yake,ga cutar qanjamau dake cin kowane sashi na jikinta,ga qafa wadda ta tasamma rubewa koma ace ta rube,ga hannu daya kullum daurw da ankwa jikin qarfen gado,gwajin farko aka gano cancer ta shiga ciwon saboda haka tilas a yanke qafar kada dayar ma ta harbu,kuka ta dinga yi wiwi da idanuwanta sanda aka nemi kudin da za'a biya ma a samu a yanke qafar aka rasa,ita ta shawarci mamarta da cewa "Mama,ko kadarorina dake cikin dakina za'a diba a saida a biya tunda ku kun kasa biyamin,bakusan bala'in da nake kwana nake tashi a cikinsa ba" kallon banza maman tayi mata ganin cewa har yanzu bakin zainab din bai gama rusuna ba,duk da halin da take ciki "Wadanne kadarori kuma kike da su,bayan wadanda kika aiko zinatu ta diba ta saida miki ta kaiwa alqali kudin don ki samu nasara kan shari'arki,da yake Allah ba azzalumin bawa bane gashinan abinda kika aikata yana bibiyarki" ihu ta kwarara wanda ya janyo hankalin jami'an tsaron dake gadinta,wadanda basa rabuwa da ita koda tayi bacci,rantse rantse ta shiga yi kan cewa ba ita ta aiko zinatu ba,maman taje ta nemota duk inda take damfararta tayi,kudin da take sa ran za'a dinga juya mata ana aiko mata da su don tayi rayuwa mai kyau da'yanci cikin kurkuku(kujifa,ita da aka yankewa hukuncin daurin rai da rai amma zuciyar da sauran buri har wata rayuwa mai kyau take hangowa kanta),rirriqeta ta jami'an tsaron sukayi sannan suka sanya likita yazo ya danna mata allurar bacci maman na kallo,a hankali jikinta ya saki har bacci ya dauketa,kuka maman ta sanya bayan 'yan sanda sun aikata waje don basa bari ma a ga zainab din,tausayin 'yar tata kuma sai ya kamata,duk da irin tsiyar da zainab din ta shuka tun tana budurwa kawo yanzu,asirin data yiwa maman ma kusan sai da aka daureta gidan yari ya saketa, ta sani cewa maiyiwuwa zaluncin da itama ta tafka tsakanin kishiyoyi zamanin mijinsu na raye shine alhakin ke bibiyarta Allah ya sauko mata da wannan jarabawar,wato shi sharri kare ne maishi yake ba,hakana sharri dan aike ne,duk inda yaje gun wanda ya aikeshin yake dawowa. ******* ******** ******* Washegari da gyaran gidan suka tashi kasancewar 'yar aikin anty dijen itama ta tafi garinsu,babu tabbacin dawowarta ma don suna tsammani aure za'a yi mata,basu samu kansu ba sai la'sar sannan suka kammala komai,daki sumayya ta shiga tayi wanka sannan ta fito ta shirya cikin riga da zani na atamfa,ta zura hijabinta kenan zata tayar da sallah wayarta ta dauki ruri,mama ce sai ta koma bakin gado suka gaisa,sannan daga bisani ta buqaci ta kaiwa dije zasuyi magana ta kira nata layin a kashe,kiran ta katse sannan tayo falo don ta haura sama ta miqawa anty dijen wayar. Kyakkyawar budurwa ce tsaye a bakin qofar falon,farace mai matsakaicin tsaho,sanye take da yadin material plain mai santsi da kauri ruwan makuba(maroon)tayi rolling da mayafi ruwan hoda wanda ya sauka iya kafadunta,takalmin qafarta mara tudu(plate)ne shima ruwan hodar,fuskarta fayau babu kwalliya sai kwalli kawai,kallo daya zaka yi mata kasan cewa akwai hutu kwainane da boko zalla a gun,a qalla zasuyi sa'anni da sumayya,minal na tsaye gabanta tana ta tsalle,yayin da budurwar ke qoqarin budewa minal choculet data shigo mata da ita,daga kai tayi suka hada ido da sumayya,sai ta maida kanta ga minal,hakan ya sanya sumayyan itama dauke kanta don bata santa ba ta nufi matattakalar benen don ta haura sama,sai muryar anty dije dake saukowa ta dakatar da ita "A'ah amira ya kike tsaye,samu gu ki zauna mana" "Ba komai umman khalipha,sauri nake zamu fita ne da anty su'ad,sai malam alqasim yace min yaga dawowarku na shigo inga mutuniya ta" dariya anty dijen tayi tana qarasa saukowa "Mutuniyarki kam ai gata nan,yasu maamaa" "Maamaa lafiya tace in gaidaki" "Ina amsawa,kice su'ad anzo kenan" dan murmushi tayi "Eh wlh,bari na wuce umman khalipha" "Af tsaya mana na baki saqo wajen maamaa" "Umman khalipha sauri nake,amma may be idan mun dawo da wuri zan biyo na karba mata,banso ma akai su'ad na nan" ta fada a shagwabe kamar wata qaramar yarinya,dariya anty dije tayi don tasan dawar garin "To shikenan,sai kun dawo" "Tom" ta fada tana jan kumatun minal tana mata bye bye bayan ta dan sake duban sumayya dake danna wayar ta tana laluben mama don ta kira ma anty dije ita sannan ta miqa mata wayar,karba anty dije tayi tana fadin "Kun gaisa ne da amira" kai kawai ta kada "Kai amma dai baki kyauta ba,da na ganku tare ai na zaci kun gaisa sumayya" "Bansanta ba anty,kuma ko da na fito bata min magana ba,hasalima dauke kanta tayi" "Qaniyarki,ba gidanku tazo ba" dariya tayi cikin tsokana tana rufe baki "Af,na manta gidanmu fa tazo afuwa umman khalipha" itama ta fada,sai ta baiwa anty dijen dariya,saboda kusan da wuya kaga sumayyan na zolaya ba al'adarta bace sai lokaci zuwa lokaci,daki ta juya ta shige tana fadin "Idan kin gama anty ki bawa laila don Allah ta samun chargy" "To" anty dijen ta amsa tana amsa kiran wayar. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 5⃣6⃣ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *Wa wassainal insaana bi walidaini ihsaanaa* *mun yiwa mutum dan adam wasiyya/umarni da kyautatawa iyaye(uwa/uba)kyautayawa(matuqar kyautatawa)* ________________________________       Tana idar da sallar minal ta shigo dakin da gudu "Anty kizo ana kiranki a waya" "Waye yake kirana?" Bata amsa mata ba yarinyar sai jan hannunta da ta soma tana nuna qofa da yatsarta,murmushi tayi don tasan halin minal din,sai kawai ta miqe ta bita,tayi tsammanin wayarta dake gun anty dije ake kira,saidai bata tsaya ko ina ba sai kitchen,ta dangana da ita zuwa bakin wayar su ta landline "A nan ake kiranki" cikin mamaki tace "A nan kuma,ba wayarku bace ta gida,saidai ko anty ake kira ko?" "A'ah sumayya suka ce" inji anty dije dake shigowa kitchen din,cikin shakka da ko kwanto ta daga bayan wayar ta sake sakin qararrawa.       Nemam wajen zama ta soma yi jin muryar namiji,gabanta ya yanke ya fadi tsoro ya kamata,ta tsani abinda zai hadata da namiji,ta amsa gaisuwar da ake mata sannan mamallakin muryar ya soma magana "Nasan baki sanni ba duk da kin taba ganina sau daya,amma nasam zaki iya tunani,shekaran jiya na ganku a wani restaurant dake kaduna ke da qannenki da yayarki,so naso na tare ki na miki magana sai kuma kunyar idon mamanki ya hana,na lura akwai sanayya tsakaninku da masu wajen,gurinsu na amshi lambarku ta gida" "To sai kuma akayi yaya?" Ta fada gabanta na faduwa tana neman wajen zama saboda sanyi da jikinta yayi,tana mai fatan alaqar ta yanke daga nan,murmushi yayi wanda har sai data jiyo "Haba yi a hankali mana beauty,ni da nake so mai qulla dangantaka da alaqa mai kyau?" "Me kake nufi?" Ta tambayeshi gabanta na faduwa "Kin gane,tun ranar da na dora idanuwana a kanki Allah ya dora min qaunarki,duk duniya naji babu wata diya mace da zuciyata ke so da qauna sai ke,hakan ya sanya na kasa haquri da ke,ina kuma fatan zaki karbi maganar da hannu bibbiyu" "Hmmmm,Allah sarki" tayi qarfin halin fada tare da kife kan wayar ta miqe ta fice daga kitchen din,baki daya jin zuciyarta tayi ta quntata,itakam duk yadda take qoqarin killace kanta bata tsira ba?.        Kusan ragowar ranar baki daya a daki tayi ta,dadin abun ma suna tare da su laila,kwanakin qarshen mako ce,sai jibi litin zasu koma.   *******   *******   *******       Washe gari tana zaune falo ita da hafiz da minal suna kallo,hafiz kuma na goge musu uniform dinsu,da yake da kansu suke wankinsu saboda suna da inji wanki(washing machine),sumayya ke girkin dare suna ta murna yau zasu ci tuwo saboda haka hankalinta ta rabashi gida biyu,anty dije ce ta sauko daga sama laila na binta a baya hannunta riqe da turamen atamfofi guda biyar,har suka qaraso falon laila na wa anty dujin rakin kayan sun mata nauyi "To hafiz guga yake muku da ya rakaki,khalipha kuma nasan idan ya bikin ba dawowa zaiyi da wuri ba,kuma aiki ne da shi zaiyi gyaran jakankunan makaranta,idan kinje bakin get baba haruna ya karba miki ku qarasa ciki" "To" lailan ta fada tana nishi ta fice,dariya sumayya ta dinga yi mata tana tsokanarta wai taji kunya.       Minti kusan ashirin shiru laila bata dawo ba har sumayyan ta kammala abincin dare,anty dije dake shirin shiga wanka ta sauko qasa tana duban sumayya "Kinji lailan itama shiru kamar an aiki bawa garinsu?" "Ko a tura khalipha ya ganota tunda har yanzu hafiz bai gama gugar ba?" "A'ah,ai duk kanwar ja ce,sanya mayafinki don Allah ya rakaki ki gano min ita" fuska ta yamutsa "Banson fita anty wlh"hararata tayi "ke kam ko gajiya da zama a gida bakiyi,tun jiya da kika shigo ko waje baki leqa ba,to ba wani gu bane gidan Baabaa prof ne,gashinan yana kallon gidan nan" dan jim ta sake yi,haka kawai bata son shiga gidan,don tun daga qofar get din zaka ga banbamci qarara da sauran gidajen da ke dukka layin da kewayen unguwan,ba yadda ta iya ta shiga daki ta fiddo dogon hijabinta ta dora saman riga da skert na atamfa dake jikinta ta zura silifa ta fito khalipha ya biyo bayanta. Khalipha na gaba tana biye da shi har bakin tamqamemen get din gidan,qwanqwasawa ya shiga yi a hankali,daga ciki taji ance cikin wata dattijuwar murya "Kai,waye a nan" "Khalipha ne" "A'ah,khalipha khalipha 'yan kano" taji ana fadi kafin taji motsin bude qofar,dattijo ne wanda a qalla zaiyi shekaru sittin tsaye a gabansu hannunsa riqe da buta yana murmushi "Ina wuni baba halliru" "Lafiya qalau khalipopi,dazu naga laila ta wuce ai tana tafiya da qyar da kaya a hannu,sai haruna ne ya qarasa mata da su" baban ya fada yana basu hanya su wuce,russunawa rayi cikin girmamawa kamar yadda halayyarta take ta gaidashi amsawa yayi cikin fara'a,khalipha uban 'yan surutu yayi caraf yace "Yayarmu ce baba daga kano muka taho da ita" "Sannu da zuwa" baban yace ta amsa da yauwa sannan ta ja khalipha suka wuce ciki. A darare taki bin bayan khaliphan wanda yayi gaba abinsa da alamun sabo da gidan a tattare da shi,girma da kyawun gida ya ratsata tare da bata mamaki,zata iya cewa kaf rayuwarta bata taba ganin gida kwatankwacinsa ba,ko ina ka kalla qasan gidan a shimfide yake da grass carfet,babban gida ne wanda aka tsara gininsa,sannan aka baje fasaha aka fidda sassa sassa a gidan a zamanance masu kyau da kama da juna,gidan na dauke da sassa biyu manya,kowanne sashe akwai sasanni a cikinsa guda uku masu yalwa da tsari kuma kowanne ma dauke da bene,babban sashin dake hannun dama sashi ne na mai gidan da matansa guda biyu,daya sashen kuma sashe ne da tun usuli yake mallakar yaransa maza su uku tun zamanin samartakarsu har ya zuwa yanzu da dukkansu sukayi aure mallakarsu ne suna amfani da shi lokaci zuwa lokaci,kallo daya zaka yiwa gidan ya burgeka saboda tsarinsa da yanayinsa,komai luf luf a tsaftace a killace,kama daga wajen hutawa dake gefe guda,gun ajiyar motoci wajej wasannin motsa jiki da lambun dake daga bayan gidan. Sashen dake hannun dama khalipha ya dosa,ganin sun tunkari wata qofa ya sanya sumayya riqeshi "Kai,wai ina zamu?" Dariya yayi "Kiran anty laila mana" "A wanne guri?" "Gun ummee ko gun anty maamaa" sakinsa tayi tana kokwanto kafin daga bisani ta bishi. Shi ya tura qofar falon da sallama kafin itama tayi tata,saka kanta kawai ya sanar mata akwai sauyin yanayi sosai tattare da gun,falo ne na alfarma wanda ya ginu ya kuma tsaru abun burgewa da sha'awa ga idanuwa,tsit falon yake babu kowa sai tafkekiyar t.v plasma dake barazanar mamaye bango dake manne tana aikinta a tashar sunna t.v,carfet ne mamaye da falon duk girmansa a maimakon tiles,labulaye da kujeru na alfarma kalar carfet din mai azabar taushi,flower vase ce masu kyau qirar qasar chaina a sakaye a kowacce kusurwa ta falon,sai tarin kayan turaren wuta da humra dake ajjiye cikin tsari gu guda,da qananun centre table dake tsakanin kujeru don ajjiyewa baqo abin sha,ba wani tarkacen qyale qyale bane a falon amma ya tsaru,hakanan duk abinda ke cikinsa mai kyau ne da tsada,qamshi da sanyin da falon ke bayarwa kadai ya ishi zuciya samun nutsuwa. Sallama ta qarayi tana wuwwurga idanuwa cikin falon jin shuru ba motsin mutane duk da tana iya jiyo qamshin girki dake tasowa bisa dukkan alamu kitchen din na cikin falon duk da bata iya gano qofar da kitchen din yake,jin still shiru yasa ta juya ta dubi khalipha "Wai ina ka kawo mu nan ne khalipha,kasan dai nan babu alamun laila,inda tana nan da tuni ka jiyo ka......." Qarar takalmi da ta jiyo alamun ana saukowa daga saman benen ya sanyata yin shuru ba tare da ta qarasa fadar abinda takeson fadin ba "Ha'an,khalipha ne?" Taji ana fada wanda hakan ya sanyata daga kai. Farar mace wadda a qalla za'a kira da mai matsakaitan shekaru wanda hutu da tsabta suka kwakwashe shekarunta suka boye,a zahiri ta tasamma shekara hamsin da uku amma kai baka ce haka ba,fara ce tas kamar yadda nace a baya wanda har wani yellow takeyi,kallon farko zaka san cewa zamanin quruciya an kasa maza da yawa a kanta,akwai kyau da kansa zaune a fuskarta,duk da shekarun da take da su amma basu ci nasarar boye kyawun nata ba wanda hakan ke nuna na asali ne ko kuma ace na gado ne,tana da matsakaicin tsaho yayin da jikinta ke a murje,sam babu rama ko qiba tattare da ita,fuskarta a sake take saukowa daga saman tana sanye da jar atamfa da ta haskata dinkin riga da plain zani "Ummee ina kwana" murmushi ta saki har sai da fararen haqoranta suka bayyana "Ina kwana ko ina wuni khalipha sarkin shirme,ku zauna mana sai mu gaisa ko?,baquwa mukayi" an aosa masa inda ke masa qaiqayi "Eh yayarmu ce muka taho da ita ummee,itama ta dawo nan ta zama 'yar gidanmu" dariya sosai ya bawa ummeen duk da kasancewarta mara son hayaniya,gu ta samu ta zauna,hakan ya sanya sumayya dake qame gu daya ta qaraso a hankali kanta a qasa ta samu gefan kujera ta zauna,hakanan take jin matar ta mata wani kwarjini da girma "A'ah tashi baquwa ki koma saman kujera... Me sunanta khalipha?" "Anty sumayya" "Tashi sumayya ki koma sama" kai ta girgiza don ta qagu ta koma gida "Yanzu zamu koma laila muka zo dubawa anty taji shiru" ta fada sannan ta soma gaidata,amsawa tayi tana cewa "Na tsammaci ai ta koma tun dazun data kawomin aiken ta fita,amma ba mamaki suna wajen maamaa bilkisu,don nayi hayaniyan yaran gunta" "To sai anjima" ta fada tana miqewa "Yauwa rakata khalipha wajen maaamaanku,ki yiwa khadijan godiya naga sautu sunyi kyau" "To zataji" ta fada suna nufar qofar fita daga bangaren nata,saidai kafin sukai ta shigo,budurwar rannan ce sanye take da gown mara nauyi wadda take armless bata da hannu,sai siririn mayafi data yane tulin tsefaffen gashin kanta da shi ,kumatunta duka biyun da hannunta jagale suke da wani abu kamar butter,sallama tayi tana dariya idanunta a kan ummee dake dubanta itama,harara ta watsa mata "Da kyau,sannu shugabar masu shiririta,shine kika dora mishi girki sannan kika tafi kika tara yara kuna wani birthday din shirme,to sai ki wuce ki duba Allah yasa ya qone,wallahi ya shigo kada ma ki dosheni don baxan qwaceki ba a hannunshi" idanuwa ta qwalalo cike da tsoro,sannan ta kwashi sauri ta nufi hanyar kitchen din fuska a kwabe kamar zatayi kuka tana cewa "Wayyo ummee na banu don Allah kada kicemin girkin ya qone" "Ke kika sani" ummin ta fada. Shikam khalipha fuska ya bata bayan sun fito "Ina ga yau bithday din siddiqa shi yasa ma anty laila taqi dawowa gida tunda aka aiketa,tunda naga anty amira ma nasam da qyar idan ba yau bane,dama tun kafin mu tafi kano anty amira tace an kusa,wayyo mami duk ita ta hanamu zuwa" ya qarashe kamar zaiyi kuka,itakam sumayya bata ce komai ba,duban hanya take ganin sun nufi wani sashen na daban. Tun kafin su shiga ta tabbatar akwai banbanci tsakanin waccen sashen da wannan,tun a qofa ta fara jiyo hayaniya da ifce ifcen yara,da banbancin kam,don wannan falon cike yake da yara sun kusa su goma sha biyu,qananu da matsakaita,baki dayansu sanye suke da gown suma mara hannu,dukkan rigunan irin daya ne,hatta safunan qafafunsu(socks)iri daya ne,yaran sunyi kyau gwanin sha'awa,tsakiyar falon qaton cake ne wanda suka dora kan center suna ta wadaqarsu da shi,da alamu shi ya bata jikin budurwar data gani dazu,kusan ba wanda yaji sallamarsu sai wata mata dake tsaye daura da su tana kallonsu idan zasuyi ba dai dai ba ta gyara musu,ita ta juyo murmushi dauke a fuskarta tana amsa musu sallamar idanuwanta kan sumayya,gaidata tayi tana duban laila da ta nufo gun saboda taga shigowarsu "Wuce muje" sumayya ta fada tana mai juyawa tare da cewa sai anjima tasa laila a gaba. Daf da zasu fice taji matar na fadi cikin daga murya "kuyi maza ku kwashe kayayyakinku zansa a gyara gurin kada uncle ya shigo ya tadda wajen haka...." Bata qarasa jin me suke cewa ba don sun fice. Suna gab da fita daga gidan baba halliru cikin gaggawa ya budewa motar wadda aketa faman danna horn kamar za'a tashi unguwar,baqar motace wadda ke dauke da baqaqen glass baqi wanda har baka iya hango wanda ke ciki ta danno cikin gidan a guje wanda badan grass carfet dake harabar gidan ba da anga tashin qura "Hmmm,gata nan ta dawo Allah yasa an tashi ma" laila ta fada tana hararar motar sanda suke qoqarin fita "Anty su'ad ko?" Inji khalipha ya tambaya yana kallon laila tare da tabe bakinsa "Itace mana,nifa shi yasa idan tana garin bana son shiga gidan baabaa wallahi anty sumayya" ta fadi tana duban sumayya tana son bata labari,saidai hararar ta sumayyan tayi "Ke kam laila ke da khalipha bansan wanda yafi wani surutu ba wallahi" "Wallahi ya fini" inji laila tana dariya,take musu ya sarqe tsakaninsu da khaliphan har suka qarasa cikin gidan. Shigarta ta tadda wayar gidan nata faman ruri anty dije na kuma saukowa da alama fitowarta kenan daga wankan "Qarar wayar nan ce ta isheni,tunda kika fita aka dinga kira,hafiz ya daga akace ke nema ya gaya musu baki kusa amma basu daina kira ba,don Allah jeki daga ko kunnuwanmu sa huta" bata fuska tayi ranta na baci,jikinta ya bata mai kiran jiya ne wanda ya kira kansa da alqasim "Ni wa na sani anty da zai kirani da lambar wayar gidanku,na gaya musu bani bace amma anqi daina kira" "To amma ya akayi haka?,shikenan....bari na daga na musu bayani" antyn ta fada tana nufar kitchen,sai sumayyan tayi saurin barin falon ta shige dakinta haushinsa na kamata,haka kawai don musiba yana son ya zame mata jarfa,ta bar kanon amma don ta samu hutu ta nutsu amma bata samu nutsuwar ba,ina dalili,su qarke qalau da anty dijen. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 5⃣7⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *wallahi tallahi billahil azim duk wanda baibi Allah ba ya shiga uku,duk wanda baiji tsoron Allah ba ya kade,duk wanda tsoron Allah bai hanashi bin son zuciyarsa ba yana cikin babbar musiba,dan adam ba kowa bane hakanan ba komai bane shi,kaji tsoron ubangijinka kayi biyayya a gareshi KAJI TSORON AZABARSA KAYI KWADAYIN RAHAMARSA sai ka samu rabauta,ka guji duk wani abu mara kyau,kayi riqo da kyawawan ayyuka, 'YAR UWA,KI KARANTA YADDA UBANGIJI DA MA'AIKI SUKA WASSAFA MANA JAHANNAMA,ALLAH KAYI MANA TSARI DA ITA BADON HALAYENMU BA,KADA KA NUNA MANA ITA KO NA QIFTAWAR IDO NE,KA BAMU IKON YIN BIYAYYA A GAREKA,KA KADE MANA ZUKATANMU DAGA TUNANI KO AIKATA DUK WANI SABO KO ZALUNCI* ______________________________________ Kwanaki nata tafiya,tun tana a takure da zaman garin har tazo ta fara sakin jiki,abu daya ke damunta kewar abdallah,tausayinsa take hakanam tausayinsa ya ninku a zuciyarta tun daga randa ya rasa mahaifinsa,kullum takan kira a bata shi su gaisa susha hirarsu,abinda ya sake kwantar mata da hankali a nan ba inda take zuwa bare ta gamu da wani yace mata yana sonta,hakanan kiran waya ma da ake ana nemanta tun ranar da anty dije tayi magana aka samu sauqim kiran,sai jifa jifa shi din ma ba dagawa take ba,abdur rahman ne kadai ke kiranta su sha hirarsu har ta riga da ta saba,babu wata rana da zata fito ta fadi bai kirata ba,ta sake sosai don bai qara yi mata wata magana daban ba banda ta zumunci,anty dije tayi ta mata tsiyar batasan muguwar kifin rijiya bace ita sai yanzu,bata son zuwa ko ina,ko gidan baabaa prof shigarta biyu kwata kwata shima da dalili na farkon kiran laila da taje,na biyu kuma da sumayyan tayi dambu gidan ba yara ta sata ta kaiwa anty maamaa da yake ita mai son dambu ce,kota shiga din ma bata wuce minti biyar ko goma ta fito,hakan ya sanya anty dije ta bada sautun kayan turare da humra aka kawowa sumayyan ta soma yi a nan,cikin designers kwalabe take zubawa,nan take kuwa ta soma ciniki,duk da wani gu ake kaiwa,'yan unguwar ne kawai ki zuwa siya cikin gida. Yau ma kamar kullum babu yara a gidan suna makaranta,gab suke da fara jarabawa ayi musu hutu saboda gabatowar wata mai alfarma na azumin watan ramadan,suna zaune da anty dije a kitchen tana anty dijen ke girki yau sumayya na ganin yadda take yi din don bata iya irinsa ba,iya zamanta da anty dijen ta qaru da abubuwa da dama ta fannin zamantakewar gida,girki iri iri,gyaran jiki da kuma uwa uba iya gayu,wayarta anty dijen ta daga wadda ta fara ruri ta kara a kunne,ganin haka sumayya ta karbi yankan cabbage din da takeyi taci gaba,sai data gama sannan ta dubi sumayyan "Sumayya,inaga fa ke zaki miqawa anty maamaa humrar nan,kaya take hadawa kuma kinga yaran basu dawo ba" kasaqe tayi,sarai anty dijen ta gane bata son zuwa ne,bata san me yasa bata qaunar shiga gidan ba amma sai ta shareta,ta gane mai anty dijen ke nufi tilas ta miqe tace to,dakinta ta shiga ta sanya dogon hijabinta har qasa sannan ta jawo ledar data jera humrorin wadda anty maamaa ta bata tayi mata,saboda umrar azumi da zasu tafi ita da maigidan da kuma ummee,sai babban yaron gidan shi da matansa biyu sai qaninsa da tashi matar,sai manyan jikokin gidan su biyar duk da basu wuce shekara sha hudu zuwa qasa ba,duk laila aku(sunan da idan taso take kiranta da shi kenan kusamman idan tayi hali ) ke bata wannan labarin tunda ita ba shiga take ba ballantana ta sani. Kamar kullum a hankali ta dinga ratsa gidan bayan sun gaisa da mai gadin dake gadin wannan qofar sa suke shigowa da yake akwai wata qofar ta baya,mutumin ya haifeta shi yasa take ganin girmansa,mutum me mai faran faran da son jama'a,duk da ganinsa da sumayyan baifi uku ba amma yana yabawa hankalinta yadda take rusunawa ta gaidashi,duk da yasan iyalan gidan alhj umar farouq ba baya bane wajen tarbiyya. Kanta a qasa qirjinta na bugawa ta dinga kutsawa cikin gidan,batasan me yasa take yawan faduwar gaba ba idan ta shigo gidan,ko don tana ganin kamar akwai banbancin matsayi tsakaninsu bai kamaci ta dinga shiga musu gida ba. Tazo mararrabar sashin anty maamaa data ummee sai taso ta manta wane waje ne na anty maaman don bata rarrabewa da sunayensu,a hankali ta juya idanuwanta tana canki canki,karaf idanuwanta suka sauka a kansu,zaratan samari ne ke tsaye su biyu suna magana da junansu,dukkaninsu dogaye ne saidai daya yafi daya masu matsakaicin jiki,kowannensu na sanye da t.shirt da trouser masu mabanbantan kaloli kowa da kalar nasa,farare tas da su kamar yadda ta dan fahimci haka kalar fatar masu gidan take,fuskar daya kawai taje gani bata ganin ta dayan kasancewar ya juya baya ne yana magana da dayan,da alamu kuma duk hankalinsa na kanshi,shima ya ganta,idanu ya sanya yana kallonta har waccan ya kammala fadin abinda zaice yayi gaba ya shige daya sashen. Rudewa tayi kamar mara gaskiya,jikinta ya soma rawa ta fara qoqarin juyawa ta koma inda ta fito ganin kamar yana takowa inda take "Wa kike nema?" Ya tambayeta fuskarsa ba yabo ba fallasa,cikin qoqarin daidaita nutsuwarta ta hada kalmar "Sashen anty maamaa nake nema" "Ko gun amira kika zo?" Ya sake tambayarta yana kallon ledar hannunta,bata ma gane wace amirar ba,sai tave masa "A'ah,saqo na kawowa anty maamaa" sai taga ya saki murmushi "Yauwa,muje ma na rakaki,Allah yasa wannan turaren mai dadi aka kawo mata wanda tamin alqawari" ya fada yana yin gaba cikin mishadi,ta bishi a baya tana cike da mamakin sauqin kai irin nasa,batayi tsammanin haka ba. Falon suka shiga yana sallama cikin daga murya,wannan budurwar da take zaton ita ce amirar ta fito da sauri daga kitchen tana dariya,bata lura da sumayya dake bayansa ba,ganinsa ya sanyata tsaya tana dubansa tana qyalqyala dariya,da alama wani abu da ya faru dazun tsakaninsu taje tunawa "Ya akayi yaya mahmoud?" Ta fada tana sake tuntsira dariya "Zaki zo hannu ai kin sani.....yanzu ba wannan ba ga baquwa nan tazo wajen anty maamaa" dan leqowa amiran tayi inda sumayya ke tsaye,sai tayi murmushi "Ba baquwa bace a gidansu umman khlipha take,duk da dai baquwa ce a gidan nan saboda na fuskanci bata son mutane" ta fada tana murmushi "Ke kuma gaki da shegen kwashe kwashe ko,ki bata guri parrot tukunna,ki gayawa anty zan dawo anjima,yanzun yaa man ya aikeni ne" ya fada yana juyawa zai fice,ganin haka yasa amira daga murya "Don Allah ya mahmoud ka siyo min na tuba" ta fada a shagwabe tana kama kunnuwanta guda biyun,harara ya watsa mata yayi ficewarsa,sai ta narke fuska kamar zata yi kuka har ya bace a falon kafin ta maida kanta wajen sumayya. Murmushi tayi mata sannan tace "Ga waje zauna,amma sai kin dan jira antyn don tana wajen dan tsohon mijinta,kinsan ba'a kiranta idan ya shigo sai mutum ya jirata" ta fada cikin salon tsokana tana dariya,itama sumayyan sai ta saki murmushi,kusan haka halayyar anty dije take,take mukhtar ya fado mata,a hankali sai murmushin nata ya soma gushewa damuwa ta fara bijiro mata,take ta fada kogin tunani tana tuna wasu lokuta masu dadi daga cikin rayuwar da sukayi tare da shi. "Ga lemo bismillah" amiran ta fada tana ajjiye tray data dora lemo da kofuna a kai,kai sumayya ta kada cikin murmushin yaqe tace "Alhamdulillah,a qoshe nake" "Al'adar gidan anty maamaa ne,dole kisha wani abu kafin ta fito" ta fada tana tsiyaya mata a cup,kallonta sumayya tayi tana yaba karamcin hakan,sai a sannan taga kamanni da wanda ta kira mahmoud a dazu,da alama kwai dangantaka ta jini mai qarfi tsakaninsu,hannu ta saka ta karba tana fadin "Na gode" "Ba komai,bari na duba girki kada ya kama" "To" sumayyan tace,kurbe daya tayi masa ta ajjiye damuwa ke sakadarta,a haka taji an bude wata qofa dake can wani sashe daban na falon,anty maaman ce ta fito tana cewa "Ayyah tun yaushe kika zo" murmushi tayi "Ban jima ba,ina yini" ta gaidata amsawa tayi tana zama tare da amsar ledar humrorin,budewa tayi tana shanshanawa tare da yaba yadda sukayi bala'in qamshi,godiya tayi mata sosai tamkar ba biyanta tayi ba,miqewa tayi tana shirin tafiya "Umhmmm,za'a gudun ne?" Amira take baro kitchen ta fada tana dan murmushi,waiwayawa tayi tana dubanta itama fuskarta qunshe da murmimushin,sam batayi zaton zata yi sauqin kai haka ba "Na baro aiki ne a gida shi ya sa" "Ayyah to sai yaushe?,ko sai na shigo?" "Allah ya kawoki lafiya" "Amin,ni sunana sumayya na gaskiya,sunan mamar babanmu ce ake kirana amira,kefa?" Murmushi ta saki "Nima suna na kenan?" Idanu amiran ta zaro gami da rufe baki "Kai kai,dama baabaa na kusa ya ganki,yaga mai sunan mamarshi,yana son mai sunan mamarsa wallahi,me ake ce miki to?" "Shi ake gayan" kai ta kada sannan tace "Gaskiya ni bazan fadi haka ba,zan dinga kiranki kema da amira,amiran umman khalipha" dariya sosai sumayya tayi "Shikenan to" ta amsa mata sannan sukayi sallama ta juya da niyyar fita tana dariya amiran,kusan zasuyi shekaru daya da ita,saidai yanayin inda ta taso da gata sai take ganin kanta kamar qaramar yarinya,duk da aqalla zasuyi shekaru ashirin da daya. A bakin qofar shigowa falon taji tayi karo da abu har yana bangazar kafadarta,da sauri ta ja baya tana fadin "Subhanallah" "Mtsweeeeww" taji an tsaki,baya ta sake ja tare da daga kanta tana kallonta wanda ita dinma kallonta take,saidai nata kallon yasha bamban da wanda sumayyan ke mata,kallon farko ta fahimci macace mai izza da jin kanta,haka yake don sumayya bata yi qarya ba,matashiya ce dake jin duniyarta dai dai,wadda a qalla ta doshi shekara ashirin da takwas a duniya,doguwa ce sosai hakanan siririya ce,fara ce itama sosai kamar yadda sauran suke,sanye take da wani baqin hight rise slim leg jeans da v neck t.shirt mai gajeran hannu,hakan shi ya fiddo surar ta da shape dinta baki daya,kanta yane da wani dan kwali mai santsi don ba za'a kirashi mayafi ba,idanunta saye da sun glases da ya kusa cinye rabin fuskarta,wani kallo take wa sumayyan na sama da qasa cikin izgilanci kafin ta zare gilashin nata,tsaki ta ja kafin ta wuce tana taku dai dai tana duban amira "Maamaa fa?" Ta tambayi amira kamar bata son yin magana "Ta haura sama" ta fada tana nufo sumayya dake gab da ficewa daga falon,da sauri ta daga murya "Kiyi haquri sumayya" amiran ta fada cikin damuwa,sai ta waiwayo tana sake mata murmushi tare da fadin "Kada ki damu", sai da sumayyan ta fice sannan ta dawo da kallonta cikin falon ta saukesu kan wadda ta shigo din,sai ta kada kai kawai ta shige kitchen ganin ta zauna saman kujera tana jiran saukowar maamaan,ta sani sarai ba zata iya haurawa saman ba dama idan ba da wani qwaqqwaran dalili ba,shi ya sanya tayi saurin komawa kitchen don kada ma tace zata aikata. Tana hanya tana tuna irin kallon da ta yi mata,a qa'ida ita ta bigeta,ranta yaao baci amma sai ta dorama kanta laifin,ko ba komai ita tazo musu gida,tana isa gidan ta bawa anty dije labarin amiran, "Amira kam akwai son mutane ai haka take ita da mahmoud ai mutane na ne" "Eh kam na ganshi shine ma ya rakani wajen anty maamaa,yana da kirki sosai" "Shine d'a na uku a wajen ummee" "To ita amiran 'yar waye ne anty,yau tana can gobe tana nan" "Itama d'iyar ummee din ce" "Ita ummin bata da yara ne?" Hararta tayi tana cewa "Yau kin zama 'yar jarida,to ban sani ba,ai baki son jama'a ne,banda haka watanki nawa a gidan nan yaci ace kin gama saninsu,tunda alhamdulillah mutane ne masu kirki karamci da son jama'a" dariya sumayyan tayi tana kame bakinta da yatsunta "Ni dama amiran nake son na san 'yar ina ce kuma an gayan" sai suka yi dariya anty dije na qorafin qib sakin jiki na sumayyan. Da daddare dukkansu suna zaune a qasa suna cin abincin dare har da mai gidan,sumayya ce kawai ke zaune can gefe tana cin nata,babu yadda anty dije da uncle farouq baiyi ta dinga cin abinci cikinsu ba amma ta kasa,kunya gareta,bata da sabo sosai idan ba wajen yara qananu ko mutanen gidansu da suka taso tare ba,tun suna qorafi har suka suka haqura suka zuba ido a haka suka saba saboda sun lura halittarta ce ba zata sauya ba. Sai da suka kammala baki dayansu sannan hafiz yace cikin doki "Abba,wanne albishir ne da kace sai mun gama cin abinci zaka yi mana?"idanu ya zaro yana murmushi yana duban hafiz din " ummm,wannan zumudi haka?" "Eh wallahi abba nima na qagu ya rigani fada ne kawai a baki" juyawa yayi yana kallon lailan,wannan karon dariya ce ta subuce masa "Au kema?" "Eh abba" ta fada itama tana dariyar,sai ya dubi anty dije "Kefa madam?" Murmushi tayi tana gyara zama "Ai yara sun gama magana,nima na zaqu inji wanne albishir ne?" Dariya ya sake yi "Uhmmm,shine kenan to tunda bakinku yazo daya" ya fada yana gyara zamanshi,sumayya na gefe tana satar kallonsu,yanayin rayuwarsu tana burgeta,soyayya dake tsakanin uncle farouq da anty dije kullum kamar wasu sabbin aure,waiwayawa yayi ya fito sumayyan da hannu "Taso kema ya shafeki" sai tayi qasa da kanta sannan ta miqe ta qaraso tana murmushi,gefan laila ta samu ta zauna,duk sukayi shiru suna sauraronsa. "Alhamdulillah,Alhamdulillah" ya fara cewa "Wato a yau labari ya iskemu gwamnatin tarayya ta aiko da takarda ma'aikatarmu,ta zabemu mu goma zamu tafi london bayan sallahn nan mai zuwa da sati daya,zamu qaro karatu don samun qwarewa kan aikinmu na tsawon shekara guda" ya fada yana sauke numfashi,duk sai fuskokinsu suka sauya,kowa da abinda ya fara yawo cikin zuciyarsa,suna wassafa yadda zai tafi ya barsu da yadda zasuyi kewarsa,dariyan da ya saki ita ta maido hankalinsu kanshi "Jibi fuskansu,to gwamnati ta bamu daman tafiya da iyalanmu amma kada su wuce mutum hudu,shine babbar matsalar,gashi mu mun kai mu shida,tunani daya wa za'a bari da wa za'a tafi?" Shuru dakin ya dauka,murna ta soma komawa ciki,kowa na zulumin kada ace shi za'a cire,banda sumayya da farinciki ya mamayeta zata koma kano kenan har tsawon shekara daya,don dama ko a mafarki bata zaci ma zata bar state dinta ba balantana akai ga qasarta,ganin ba wanda yace komai sai sumayyan tayi gyaran murya don fidda abinda ke cikinta,dubanta uncle farouq yayi yace "Ummm,me zaki ce?" A ladabce tace "Dama uncle.....cewa nayi.....ni mai zai hana a cireni a lissafi sai na koma kano kafin dawowar taku?" "Shawara bata karbu ba" anty dije ta fada kanta tsaye,sai ya saki dariya yana kallon sumayya "To kinji abinda antynki tace" yana maganar tare da mai da hankalinsa kan anty dije "To ke hajjaju mai zai hana cikin taskarki din nan da ake boyo ki dauki nauyinmu baki daya?" Ya fada cikin zolaya wanda hakan ya sanyasu dariya baki dayansu,sai da suka nutsa sannan yace "Ni a binda nake gani,hafiz,kai zakayi haquri saboda karatunka a yanzu yake buqatar nutsuwa da dagewa,kai zamu bari a nan garin,sumayya kuma kema 'yar mu ce,kinga kuwa mai 'ya mace bazai dinga barinta wani gu ba,ni zan yi mata passport da visa a kudina,shikenan madam?"murmushi ta saki " yayi yallabai,mun gode Allah ya saka da alkhairi ya qara arziqi"hafiz wanda sam baiji dadi ba har cikin ranshi,amma da yake yarone mai hankali da haquri,da wuya ka gane bacin ranshi sai yace "A wanne gida abba Zan zauna?" "Duk inda ka zaba,ko gidan inna(kakarsu da yake nan ya dawo da ita,ba wata tazara bace mai nisa tsakaninsu),ko gidan baabaa prof,kayi haquri kaji hafiz,girman kenan kaji?" "Ba komai abba" ya fada,sai ya baiwa antu dije tausayi "Ni har ka tunan ma abban laila,ina zuci zuci sukai sumayya ta gaidata,innan tace wai ba zata iya gane sumayyan yanzu ba" Yana miqewa yace "Kinsan tsufa sai a hankali,ai babu damuwa ko zuwa gobe ko jibi sai suje" "Allah ya kaimu" injita,miqewa hafiz din yayi yabi bayan abban nasa da ya kirashi yace yazo ya karbi wani abu,take falon ya sarqe da murna,laila anata wassafa kai a jirgi,sumayya na dubanta tana dan murmushi duk da hankalinta ya kasu kashi biyu,ran qwashi anty dije ta zuba mata tace kota nutsu ko ta saka a cire sunanta a saka na hafiz take ta kame bakinta duk da bata fasa mutsu mutsun murna ba. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 5⃣8⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *KO KUNSAN ACIKIN 'YAN WUTA WAYE MAI QANQANUWAR AZABA MAFI SAUQI?,WANDA AKA FI SAUQAQAWA??* *Shine wanda za'a sanya garwashin wuta a tafin qafafunsa guda biyu,kowanne tafi daya garwashi daya,sai qwaqwalwarsa ta dinga tafasa* *ALLAHUMMA AJIRNA MINANNAR* __________________________________       Falon anty dije ta basu tana fita laila ta dora daga inda ta tsaya,har gwada irin shigar da zata dinga yi take idan suka tafi,sumayya na gefe tana kallonta tana dariya,can qasan ranta kuwa tana ta jujjuya maganar,wai itace zata wata qasa wata uwa duniya a jirgi har london?.        Suna haka hafiz ya fito daga wajen uncle farouq,fuskarsa qunshe da murmushi hannunsa dauke da laptop sabuwar qar,idanun laila suka fara kaiwa kai "Laaah,ya hafiz sabuwar laptop abba yayi ne?" "Wannan ba ta abba bace,tawa ce wanda ba za'a london da shi ba" ya fada yana zama tare da budeta ya kunna,tuni laila aka fara raba ido,ta matso kusa da shi "Da gaske kake ya hafiz" hararta yayi "Da da wasa nake miki" shiru tayi sannan daga bisani tace "Allah ko nima na fasa zuwan ne a siya min,kada muje mu dawo dadi ya qare kai kuma ga abarka nan kama mora?" Dariya ta qwacewa sumayya,tana niyyar cewa wani abu anty dije itama ta fito daga dakin hannunta dauke da wata laptop dim,gefansu sumayyan ta zauna tana kallon hafiz "Tofa,an samu nayi ko?" Murmushi yayi kawai yana danne dannensa dadi ya cikashi,sumayya ta miqawa laptop din tana cewa "Ungo wannan" amsa tayi tana duban antyn "Daki zan kai miki?" "A'ah taki ce,abba laila ya siya miki yace zai miki bayani,akwai abinda ya shirya miki kan bunqasar karatunki yana so kiyi karatu ne da ita,idan mun tafi ina tsammanin akwai makaranta da zai sama miki da zaki koyi karatu ma shekara gudan,nasan baki da matsala ta karatu da rubutu duka kin iya,hakanan turancinki ba laifi zaki iya karantawa ki fahimci wasu abubuwan,fahimtar sosai da maidawa yadda ya kamata ne kawai matsalarki" qamewa tai a gun tana mamaki,to ita ya zata iya da wannan aba da uncle din ya mallaka mata,kasa magana tayi har sai da laila ta saki dan ihu tana karbarta daga hannunta "Wayyo!,muma munyi computer,ya hafiz ka daina mana kallon banza" cikin sanyin murya da sake gasgata qaunarta da anty dije tace "Anty na rasa wacce iriyan godiya zan muku,na gode na gode Allah ya saka muku da alkhairi,ya biya muku dukkan buqata ya jiqan magabatanku,ya hada kan zuriyyarku baki daya" "Amin" anty dijen ta amsa tana shigewa ciki.         Da sauri laila ta miqe ta jona mata chargy hadu da kunnata,tana da rawar kai hakan ya sanya ta iya laptop din kamar wadda ako koyawa,don suna game sosai a cikin ta muhsina daya daga cikin qawayenta jikokin gidan baabaa prof,nan ta fara duba games din ta ta tarar a ciki,ta zabi daya ta fara bugawa minal ta matso tana kallo.         Daga bakin qofa akayi sallama,dukkansu hankalinsu na kan laptop din sai sumayua wadda ta amsa yana waiwayowa,amira ce ke shigowa fuskarta qunshe da murmushi,sanye take da black gown brided tube midi mai adon zane orange a jiki mai dogon hannu,kanta yane da mayafi medium orange haka plate shoes dinta,hannunta riqe da wayarta,fuskarta ba makeup saidai akwai alamun hoda da lipstic,bayanta wata matashiya ce,sanye da baqin skert da t.shirt ruwan omo dukkansu na yadi,sai dan madaidaicin hijab dake wuyanta,kallon farko zaka gane 'yar aiki ce,eh tana daya daga cikin ma'aikatan gidan baabaa prof,qarasowa tayi cikin falon wanda hakan ya ankarar da su laila "Anty amira ina wuni" suka gaisheta baki dayansu ta amsa tana zama gefan sumayya "Kin ganni da daddare ko?" Murmushi kawai tayi tana janyo lemo da ruwa nata wanda tun dazun bata sha ba da suka gama cin abinci ta ajjiye gaban amiran tana cewa "Bismillah" "Um_um,a qoshe nake,shopping naje nayo sai nace bari na shigo,ina so dama na baki haquri ne kan abunda ya faru dazu" kusan ta mance ma ma ya farun "Mefa?" Sumayyan ta tambayeta "Bigeki da antynmu tayi dazu,kiyi haquri don Allah,antynmu ce saidai bata da kirki sam,kiyi haquri" murmushi ta kuma yi har fararen haqoranta na bayyana "Babu komai,ai karo mukayi"kai amira ta girgiza " duk da haka,nasan halinta ai,kiyi haquri" "Bafa komai" ta sake maimaitawa,maida dubanta tayi ga wadda suka shigo din tare,tana tsaye har yanzu "Ki zauna mana" sumayya tace mata,murmushi tayi tace "No madam,na gode". Kan ta sake cewa komai wayarsu ta tafi da gidanka dake  kitchen ta fara burari,laila ta subi khalipha " jeka duba khalipha"kanta na ga laptop don bata son a mata game over,da sauri ya miqe ya shige kitchen din minti daya tsakani ya fito "Anty sumayya ke ake nema" yana fada alqasim ya fado mata,fuska ta tsuke "Kace bana nan" "Yace don annabi ki daure ki daga" khaliphan dake tsaye bakin qofar kitchen din ya fada,goshinta ta dafe da tafin hannunta,bata so a hadata da ma'aiki taqi yin abu,amira ta miqe tana dubanta "Kije ki amsa mana namecy,zan tafi sai da safe ki gaida umman khalipha" ta fadi tana murmushi "Sai da safe ki gaida gida" sumayyan ta fadi itama tana miqewa,ita tayi kitchen su suka fice ita da mai aikinta.       Murya a sanyaye ya mata sallama,a dake ta amsa "Bakisan halin da zuciyata ta fada sanadinki ba sumayya,please don Allah ki daure ki dinga daga wayata ko ba zaki ce min komai ba"shiru ta danyi ta rasa me zata ce da shi,zuwa yanzu yaci ace yayi zuciya ya bar nemanta "me kake so nace mai kake buqata?" "Yauwa beauty,a qalla ko gaisuwa ma ta wadatar" kusan wannan ne abinda abdur rahman ya gaya mata,gashi yana neman jefata cikin tarkon sabo da jin muryarsa,wannan wanne irin wayo ne,ba zata yarda ba kam "Sai anjima" tace masa tana kife kan wayar ta fito daga kitchen din tana sauke numfashi,inda ta tashi nan ta koma ya zauna ta janyo wayarta tana laluban lambar mamanta tana son jin muryar abdallah. ******    ********    ********        Ramadan ya rage saura kwanaki uku,nan sumayya taga tsari,yadda anty dije ke tsara gidan nata tare da sauya abubuwa sabida shigar watan,baki ta sake tana mamaki don su duk basu irin wannan,dariya anty dije tayi "Da kike mamakin nawa gyaran kice idan kika ga na gidan baaba prof saikin yada idonki?"ido ta qwalalo "duk kyau da tsaruwar wannan gidan sai an sake masa wani tsarin?" "Duk shekara iwar haka sai dukka gidan sun sake komai nasu,sai su rabar da tsofaffin ga 'yan aikinsu,wasunsu har kayan sawa da yayi shekarar nan ake canza wardrobe baki dayanta" baki sumayya ta sake tana duban anty dije kamar ita ce ke sanya su "Gaskiya mutanen nan mabarnata ne,yanzu wannan gidan ba ya isheka har qarshen rayuwarka ba,wani ma idan yana wani gu baisan da wani ba,har meye ne zai tsufa a shekara a sauya shi?"dariya sosai anty dije tayi " lallai har yau bakisan wannan familyn ba,kowa da irin matsayinsa fa,ita rayuwa kowa da inda Allah ya ajiyeahi,idan kaga rayuwar wasu kai a gunka barna ce da almubazzaranci,ko kaga tsabar warya ce ko bazata yiwu ba,amma kaima da Allah zai kaika irin wannan matsayin babu shakka sai kayi kamar ko fiye da abinda yakeyi,yanzu kamar ni din nan,da wasu zasu ga abinda nake cewa zasuyi nima almubazzaranci bane,amma ba haka bane,idan Allah ya wadataka kana da shi ka sauya to ka bawa na qasa da kai wancan su amfana suma,ba ka qanqame ba ka qanqame jama'a ba,amma.....zauna na gaya miki su waye wadan nan family din kinji"ba musu sumayyan ta zauna tana baza kunne,itama anty dijen zama tayi,kafin tace komai laila ta shigo tana sanar mata tayi baquwa tilas suka katse hirar ta fita wajensu,sumayya ta tashi ta kama mata aikin da ta tafi ta bari.   *********  ******  ********       Baki daya a yanzu rayuwar gidan bata yiwa karima dadi,bata da buri a yanzu da ya wuce taga yaranta da mijinta kusa da ita amma abu ya gagara,kowa tsoro da haushin zama kusa da ita yake,hatta da lukman din ma kwanciyar bacci kadai ke kawoshi bangaren,ya sauya mata irin sauyin da bata taba zata ba,bai shiga shirginta indai ba haqqinta na aure zai sauke mata ba,wanda shima yasan idan ya take mata sai Allah ya tuhumeshi,a nan takan so jan ra'ayinsa amma abu yaci tura,da ya gama yake wanka idan an kusa asuba ya zauna karatun qur'ani da addu'o'i har sai an kirayi asuba ya fita yayi sallah,idan ya dawo ya zarce wajen hajiya su hafu da yara suyi karatu sannan su shirya ya miqa su makaranta,idan ya dawo shine zai shigo mata yayi wanka ya fice ko sauraron abincinta baiyi gun hajiya shima yake ci,hakan shi ya sake taka muhimmiyar rawa wajen rugujewar duk wani aiki da zata masa,walau na abinci ko na jinnu,ya tsayawa addu'a abincinta kuwa baici bare ya dameshi,bata gane bata da wayo ba sai sanda taso ta gwada yi masa tawaye kan yadda yake maganar sumayya da daukar yaranta ya kaiwa mama su,ranar taga tijarar da tunda Allah ya hadata da shi bai taba yi mata ba,tayi kuka na fitar rai,a hankali kuma sai ta soma tunanin me yafi zaman lafiya dadi?,me zaisa ba zata haqura da komai ba ta kawo qarshen wannan zaman fagen yaqin da sukeyi,abinda bata sani ba tanqwara busashen itace abune mai wahala,ta riga da ra yiwa kanta mummunar lamba wajensa.       Duk sanda yaje yakanyi yunqurin karbar adreas din sumayya wajen zainab ko halima,saidai duk sanda yaso yin hakan sai ya taras basa nan suna tahfiz,ita kuwa mama ba wani riqe adress din tayi ba,yaciji yatsa yaji ciwon abun da tun lokacin aurensu da tace zata gidan anty dijen lokacin da shima zaije abujan bai bita ba yaga gidan,da tuni yanzu bakinsa alekum sai ya kama hanya,wayarta kuwa idan ya kira sau biyar idan yaci sa'a zata daga sau daya su gaisa ta tambayi yara,daga haka zata katse kiran sai kuma wani lokacin. ******   ********   ********        Ranar lahadi da daddare watan azumi ya bayyana,hakan ya sanya litinin daukacin al'umar musulmin duniya suka tashi da azumi a bakinsu,duk gidan kowa na azumi banda minal saboda shekarunta basu qarasa ba,ta fara gwadawa zuwa sha biyu anty dije ta bata abinci,kafin azahar su laila anyi laqwas saman kujera,khalipha an fara mutstsuka idanuwa,dariya sosai sumayya ta dinga sheqa musu yayin da anty dije tayi kicin kicin da fuska don kada ma wani yaga fuskar da zaice zai karya,hafiz ne kadai da qwarinsa da yake shine babba.        Biyu da rabi bayan sumayya ta kammala sallar azahar tana tilawar qur'ani anty dije ta taddata da hijabi jikinta itama da alama bata jima da gama sallarta ba,gefe ta zauna hakan ya nunawa sumayya magana tazo yi da ita saboda haka tana kaiwa qarshen shafin ta rufe tayi addu'a ta shafa ta waiwayo ga anty dijen "Ya ibada,ke kam azumi nasaj gwaninki ne,tunda kina na litinin da alhamis dama" murmushi tayi "Wallahi kam anty" "Allah ya kawo min sauqi wannan karon shi yasa nace bari nazo na sameki,kinsan duk watan azumi nike wa baabaa prof abinci har a kammala azumin,abban laila ne yasa a dinga yi saboda karamcin dattijon,yana son abinciccikan gargajiya duk da kasancewarsa dan boko,to su mutan gidan sun fishi boko,da azumi basa wani abincin azo a gani sai abinciccikan zamani,ummee ce ke masa lokaci lokaci don itama tana so,to wannan karon ummee sun tafi umra mazan ne kawai suka rage a gidan,duk da kowa na da mai aikinsa amma shima baabaan baison girkin ma'aikata shi danshi ya gado" ta fada tana dariya data tuno shi "nasa gwanar girkin gargajiya ce ke,ni ki barni da girkin gida ki dinga na baabaa" murmushi tayi "To ai zan iya ma anty duka,haba,sai kace ba mace ba" "Nasan zaki iya,ai ranon mama ce,amma kya dai tayani na gidan" "Tom anty" miqewa anty dijen tayi "Naga yau garin kam masha Allah akwai hadari,ko yau zamu samu ruwan farko a ranar farko?" "Allah yasa anty,dama tun muna kano naga irin garuruwan nan kunfi ko ina samun ruwa,ga damunarku itace qarshe wajen tafiya" "Wallahi masha Allah,muna shan ruwa kam,saidai zafi" "A hakan anty,duk wannan ac da kuke kwankwada" "Saikin fita ai sumayya zakiji a jikinki" "Saidai haka" ta miqe itama tana nannade abun sallahr ta don shiga kitchen saboda su kammala komai kan lokaci.       Ana la'asar kuwa ruwan farko ya soma sauka zuwa qasa,tana kitchen din a lokacin,sai ta zuge glass tana kallon yadda ruwan ke juqa shukoki yana tayar da qamshin qasa,a rayuwarta tana son damina,murmushi ya subuce mata data tuna sanda suna tare da mukhtar,duk sanda baya gida takan fito ita da yaranta dake tayata zama susha wankansu a ruwan sama,kafin ya dawo ta share gidan ya sauya kayanta kamar bata shiga ruwa ba,amma kallon farko idan ya mata yake gane ta shiga ruwa,musamman gashinta dake saurin fallasata saboda cikarsa da tsahonsa bai bushewa da wuri,abinka da quruciya a lokacin yaron da bai saba qarya ba idan yayi ma sai an ganeshi,sai ta fitittike tace masa wankan tsarki tayi "Wanne wankan tsarkin,me ya sameki bayan fitata da zakiyi wankan tsarki?" Narai narai take da ido tace itadai wankan tsarki tayi a tunaninta shi kadai ne mafitar da zai yadda ba wasan ruwa tayi ba tunda wankan tsarki ne kadai ake jiqa kai idan za'ayi,idan yaga ta dage sai kawai ya qyalqyale da dariya ita kuwa ta sake hade rai don kada ya gano,tilas yake sakin murmushi yace ya yadda,tana kawowa nan a tunaninta ta saki itama murmushin qwalla na bin kuncinta "Allah ya gafarta maka ya mukhtar,ya kyauta makwancinka" tayi furucin tana goge hawayen da tafin hannunta,baki daya sai walwalarta ta tafi kamar yadda hakan ke faruwa yawancin lokuta idan ta tunashi,girkin take amma zuciyarta babu dadi,duk da haka hakan bai hanata hanzari ha,kafin kace me wannan ta gama girkin baabaa prof,dashishi ta masa da miyar ganye,wanda kallonta kadai ya isa ya tsinkar maka da yawu,tun ba yau ba tun tana qaramarta haka hannunta yake da iya sanwa,ballantana a shekaru takwas zuwa tara da tayi gidan aure ya sake maida ta gwana fagen iya girki.       Ko da anty dije tazo tayi mamakin saurin girkinta,don tuni suma ta musu miya,miyar qwaice da alayyahu tayi shar tayi kyau sosao,gun any dijen ta koya amma sai take ganin kamar ta fita ma iyawa,kasancewar sumayya bai bala'in qwaqwalwa da saurin dauke abu,cewa tayi ta bar mata sauran ta qarasa tunda tayi kusan rabin aikin gidan bayan na baabaan.       Daki ta shiga tayi wanka,saura kusan awa guda kafin a sha ruwa,ta fito ta shirya kanta cikin atamfa riga da zani,kanta ta daure da dan kwali ta dauki carbinta ta fito falo,dariya ta zo mata ganin yadda laila ta sake bajewa saman kujera,khalipha kuwa tuni bacci yayi awan gaba da shi,bata ce musu komai ba ta sauya tasha zuwa sunna t.v wanda suka sako tafsirij shehun malaminta sheik Ali ibrahim isah fantami,sosai take jin dadin tafsir din har zuwa wani lokaci data koma kitchen din ta tadda anty dije ta kammala komai,ita ta dinga kwaso kayan tana shiryawa saman dining anty dije kuma ta shiga wanka ganin saura mintuna akira sallah.      Lokaci qalilan gidan ya kacame,kowa na kaiwa baki,daga nan uncle farouq ya kada kansu zuwa masallaci sukayi sallar magariba.      Babu kowa gidan duka sun fita sallar asham tarawih,ta sanya hijabinta zata tada tata kenan cikin gidan anty dije ta shigo itama sanye da hijabi "Sumayya,yanzu abban laila ya kirani,yace ki miqa abincin baabaa prof,ga driver nan yana waje zai amshi nashi abinci sai ya riqe miki wasu kwanukan" babu musu yau kam sai faduwar gaba jin an ambacin gidan tace to,dirvan nasu shi ya dauki kwandon ita kuma ta dauki flask daya da ya rage.      Tana gaba yana binta a baya har suka isa bakin qofar,a mutunce suka gaisa da baba harunaya bude mata qaramar qofar suka shiga,harabar gidan tarwai take da haske da fararen qwai,ko ina a haskake tamkar rana,ma'aikatan gidan sanye da unifoarm nata kaikawo kowa na aikinsa,grass carfet da shukokin dake jere a tsare sun samu ruwan sama sunyi kyau gwanin sha'awa,kamar yadda garin yayi dadi,iska mai dadi mai cakude da qamshin qasa na kadawa,sai ta dinga jin wani mishadi na shigarta,tana shaqar iskar tana mata dadi har cikin qirjinta,ta dinga takawa a hankali har zuwa tsakiyar harabar gidan,su biyu ta fara hangowa tsaye da alama magana suke kamar rannan,mahmoud din kawai ta iya ganewa saboda shike fuskantar qofar shigowar,kamar wancan karon dai dayan na fuskantar mahmoud sai bayansa kawai ta iya hangowa,yana sanye da jallabiya ta maza fara sol da silifas farare a qafarsa,hannunshi riqe da dadduma,tana gab da isa garesu ya juya ya shige ta wata qofa da zata iya sadashi da waje,yayin da mahmoud har ya juya sai ya hangeta,tsayawa yayi yana murmushi har ta qaraso,hanmunsa ya miqa zai amshi flask din hannunta yana fadin "Bisa alamu abincin baabaa ne" murmushin itama tayi tana miqa masa "Eh shine" "Masha Allah,a gaida umman khalipha" sai ya dubi drivan yana miqa masa hannunshi alamar ya bashi ,rusunawa yayi cikin girmamawa ya miqa masan sannan ya juya zuwa qofar fitan,dubanta yayi "Muje nayi sauri na rakaki kada liman ya tada salla na rasa wata raka'ar,don na tabbata ya isa masallaci saura minti biyar a tayar" dan baya ta ja kadan "Ai ba sai na shiga ba ma,ina cewa ma duka masu gidan basa nan,ka kaima baaban kawai kace ina gaidashi" murmushi yayi "Kamar ya sanki,na tabbata baki taba zuwa kin gaidashi ba,sannan ko ba kowa a gidan su anty farida da sauran yara na nan" murmushi ta sake yi "Zanzo na gida baabaa in sha Allah,su anty farida kuwa ka gaishesu na tabbata suma basu sanni ba,amma kace ina gaishesu,nima sallah zanje nayi" "Is ok,ki yiwa umman khaliphan sannu" "Zata ji" ta fada tana juyawa a hankali ta fice daga gidan.       Tana shiga ta isarwa anty dije saqon,sannan ta shige dakinta,da hanzari ta tada isha jin an fara kiran sallar tarawih don sun gama isharsu,cak ta tsaya lokacin da limamin ya fara karanta fatiha,daina aiki qwaqwalwarta tayi na wucin gadi,babu abinda kunnuwanta ke ji sai karatun dake fitowa daga lasifiqar yana karade unguwar kasancewar masallacin na daura sa su ne,muryar da bazata iya mancewa da ita ba komai tsawon zamani,komai sauyawar yanayi,komai dadi komai wuya,muryar MUKHTAR dinta take ji tana karade kunnuwanta,wani irin faduwa gabanta ya dinga yi har ya haifarwa da gabban jikinta yin sanyi,tana so ta zauna amma ta kasa,jin kunnuwanta take kamar zasu zaunce,hannunta ta sanya ta toshe kunnen nata ko zata daina jin amsa kuwwar karatun amma hakan ya gagara,kanta ta shiga girgizawa "A'ah,ba mukhtar bane,wanda ya mutu baya dawowa" ta fada tana ci gaba da girgiza kanta hawaye na shirin soma sauko mata,a sukwane ta juya ta fito zuwa falon gidan ba tare da tasan me zata aiwatar ba. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 5⃣9⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *KO KUNSAN RANAR QIYAMA ANA DAURE DAN WUTA DA SARQA MAI TSAHON ZIRA'I SAB'IN KAFIN A JASHI ZUWA JAHANNAMA* *Astagfirullah wa'atubu ilaih* ___________________________________      Birki ta ja a falon zuciyarta na wata iriyar bugawa,idanu ta shiga rarrabawa qwaqwalwarta ta daure tamau,muryar na ci gaba da ratsa kunnuwanta cikin daddadan sautin karatun mai qunshe da muryar mukhtar,me zata aikata?,abinda ta kasa baiwa kanta amsa kenan "Ya mukhtar,ya mukhtar" ta soma fada hawaye na zubo mata,shigowar laila a guje wadda fitsari ya korota daga wajen sallar ya dawo da ita hayyacinta,bata jirayi qarasowar lailan ba ta isa gareta ta riqe kafadarta "Laila,wake karatun sallah a masallaci?,mukhtar ne?"dariya ta saki tana kallonta tare da yin tsalle alamar fitsarin ya matseta "A'ah,yaya ne fa,duk azumi shi yake jan sallah" ta fada tana zillewa ta ruga bandaki,sam bata fuskanci bayanin laila ban ta ji anty dije na cewa "Shike limanci fa,nan da goman qarshe zai tafi a saudiyya yake sallah sai dai malam usman ya qarasa" firgigit tayi tana duban anty dije,sai ta kada kai kawai ta juya jiki a sanyaye zuwa cikin dakin nata ba tare da ta furta komai ba,zama tayi bakin gado tana jingina da jikin gadon,tamkar wadda aka zarewa laka,ta kasa kowanne irin tunani,muryar ce kawai ke ratsa dodon kunnenta tana mata shawagi,runtse idanunta tayi ta koma ta kwanta a gefan hannun damanta,wani abu take ji yana yana zagaya kanta kamar ana yamutsa qwaqwalwarta,haka hawaye yaci gaba da tsiyaya ta gefan idanuwanta.         Sallar da bata iya yiba kenan har aka kammala sallar laila ta shigo kiranta tazo suci abinci,can qasa ta amsa mata data qoshi sai anjima zata ci,haka taci gaba da kwanciya,tana ganin tarin misscalled din abdur rahman amma ta kasa dagawa har ya gaji ya bar kiran ya turo mata texs,baccin dole ne ya dauketa,bata wani jima ba ta farka,har a lokacin tana jin wata iriyar damuwa na ratsata,sallar isha'in da bata yiba tayi,sannan tayi tarawih din raka'a bakwai har da wutiri.   *******   ******   *******        Daga ranar karatun shi ya zame mata abun sauraronta daga sallar isha'i har a kammala,sosai karatun da muryar ke debe mata kewa ya sanyata nutsuwa,wani lokaci tana ji tana hawaye don ba qaramin tuna mata mukhtar yake yi ba,babu wanda yasan halin da take ciki sai ita kadaj,kawai dai anty dije taga ta rage walwala,bata kawo komai ba ta dauka ibadar da ake ciki ne.        A haka aka kammala azumi ashirin cif,ranar ashirin da daya sai taji ba waccan muryar bace,duk sai taji ta damu,ji take kamar ta fita ta gano me ya kawo wannan sauyin,daga bisani ta tuna anty dije ta gaya mata goman farko da na tsakiya kawai yake jan sallah,to wannan wane ne?,babu shakka ba don anty dije ta sanshi ba babu abinda zai hana tace mukhtar dinta ne,baki daya sai ta jita sukuku,ba qaramin dadin jin muryar take ba,a ranar uncle farouq ya shigo musu da kayan sallarsu,kowannensu kala shuda shida a dinke,sumayya laila da anty dije kam harda mayafai takalma da jakankuna,daga mayafin kawai sumayyan tayi ta ajjiye gefe,tun mutuwar mukhtar ta sake qanqame hijabi duk da cewa dama al'adarta ne sanyashi,sai dai a baya tana sanya mayafan lokaci lokaci,anty dije ta lura sai ta bada sautun yadin hijabai masu kyau aka yi mata irin wadanda take so,anty dijen ita ta sanya kudinsu ta saya musu dan kunnaye da awarwaro da sarqa fashion designers masu kyau kala uku uku.          Washe gari akayo aike daga gidan baabaa prof,duk da cewa a jiya ya daga saudiyya shima zasu dawo tare da iyalansa a ranar sallah,a qasarsa yake nashi bikin sallah saboda ziyara da ake kawo masa tako ina,abokai 'ya'ya jikoki 'yan uwa da abokan arziqi,daya daga cikin ma'aikatan gidan ne,sanye da unifoarm dinsu,a mutunce ta gaida anty dijen sannan ta miqa mata wata qatuwar baqar leda dake dauke da tambarin wani company dake dubai,company ne da yaje mallakin daya daga cikin iyalin baabaa prof din,shahara da daukakar company din ya sanya wasu suma saka jarinsu a ciki "Kiyi haquri umman khalipha,tun jiya baabaa ya bada saqon,sai yau na samu sauqin aiki,munata ayyuka ne" "Babu komai shema'u,baabaa dai kam bai gajiya,Allah yasa a gama lafiya" murmushi tayi "Baabaa badai alkhairi ba,ko mu bai mana mu kadai har 'yan uwa na kusa alherinsa bai barsu ba,ina zaton wannan karon har baquwarki da nata kayan,naji kamar ita taiwa baabaan abincin kwana ashirin ko?" Dariya anty dije tayi "Sumayya,eh itace" "Ai baabaa na jin dadin abincin nan kam qwarai,rannan har yasa a kira ta su gaisa sai yayi baqi kuma ya sha'afa" "Allah sarki,ai idan suka dawo da kaina zan tura ta ta gaidashi,Allah ya saka masa da alheri,yaci gaba da shirya masa zuria" "Amin ya Allah" Shema'u ta fada tana ficewa.        Juya ledar anty dije tayi tana murushi,tambarin kamfanin kadai data gani tasan ba kaya bane masu qananun kudi,bude ledar tayi ta fara zarosu,diguwar riga ce irinta mata mai bala'in kyau da tsari wadda aka zauna aka yiwa aikin duwatsu daga sama har qasa,iya dutsen kadai idan ka kalla kasan ba qaramin kudi zaka sanya ba kafin ka mallakesu,yadin kansa abin kallo ne bare dutsen,guda daya baqa ce,sai dayar fara ce qal da aka yiwa aikin baqaqen duwatsu,dayar kuma ruwan jinin kare ja ba dau ba ya dan rusuna amma baikai duhun maroon ba,tana duba size din rigar ta gane sune na sumayya,kowacce akwai vail da ya dace da ita,murmushi tayi don tasan aikin amira ne wannan,wani shegen fashion mai zubin gwal guda daya da banguls dinsa,haka na lailaa suke saidai banbancin tsaho da kala,tasan laila kam za'a sha murna,duk shekara ya saba haka yake musu,duk cikin kayan sallarta tafi ji da kayan gidan baabaa prof,mazan ma baki dayansu jallabiua ce irinta maza mai tsada,sai gezna wadda kana mata kallon farko itama kasan ansha kudi kala bibbiyu duka kalolin iri daya,sanda aka kawo su sumayya basanan sun tafi wankin kai,da suka dawo baki sumayya ta saki,zata iya cewa banda lace din da aka bata taba kaya masu tsada haka ba,ko lace din ta tabbata baikai kudin wadan nan ba,yana ajjiye ma bata dinkashi ba,godiya tayi sosai kamar suna wajen tare da yaba dimbin karamcin ahalin gidan.       Cikin ranakun goman qarashen so kadan bata yi sanya wajen zabga addu'a gareta da d'anta da sauran yaran musulmi ba da al'umma ba,musamman ranakun da suke mara,wato ranakun da ake tsammacin dare lailatul qadr,tayi addu'ar samun kyakkyawar rayuwa da kuma kyakkyawar QADDARA,sai ta dinga jin nutsuwa da kwanciyar hankali,tsoro da damuwarta suka dinga raguwa a hankali.         Ran ashirin da tara ga wata aka tabbatar da ganin watan sallah waahegari idin qaramar sallah kenan,a gajiye ranar suke don wuni sukayi gidan qunshi,da cewa sumayyan tayi ma bata yi,anty dije ce ta matsanta mata tilas ta bisu,ga wainar shinkafa da ta tsara zata yi musu a ranar sallah,Allah ya taimaka kafin ta kwanta tayi miyarta,zumudin zuwan sallar take sosai wannan karon,saboda uncle farouq yace sallah da kwana biyar zasu tafi kano,a qalla zasuyi sati guda sannan su dawo su fara shirin tafiya london. *******   ******    *********         Qarfe goma na safe tuni an sakko daga sallah,zuwa lokacim sumayya ta kammala aikinta,wankanta tayi ta shirya cikin daya daga cikin dinkin da abban laila ya musu,ba wani makeup tayi ba amma kayan sun mata kyau,rabon abincin sallah anty dijen tayi kamar yadda ta saba.        Da yammaci su laila da khalipha nata hada barka da sallah sabbin kudi baki yaqi rufuwa,sai shigowa suke suna bawa sumayya labari su wance sunzo gidan baabaa su wane sunzo,itakam kusan bata sansu ba saidai tace musu to,dariya anty dije tayi "Abokansu ne jikokin baabaa prof, 'ya'yan babban dansa da me bi masa,kinsan duk wani da nashi da jika dake nesa a gida yake sallah". Abban lailan nata baqi,wasu na zuwa wasu na tafiya kusan haka suka wuni.         Wajen biyar tana sama dakin anty dije tana gyara mata,saboda yau baki daya ta kasa zama saboda baqi,hayaniya ta dinga jiyowa da qarar motoci,sau ta miqe a hankali,ta yaye labule tare da bude qofar da zata sadaka da balcony din anty dije dake saman,bata fiya budeshi ba sai lokacin zafi ko kuma idan ta kama saboda idan ka fita kana iya hango jama'an waje suma suna iya ganinka musamman da yake yana center din tafkeken get din shiga gidan su amira,duk da cewa waccar babbar qofar da akafi shiga  wadda jami'an tsaro ke gadinta tana daya daya layin nasu,wannan a nan suka fi harkokinsu.       Motocine na alfarma qirar zamani,wanda ke dauke da lamba mai tambarin sunan baabaa prof,wanda hakan ke alamta mallaki ne na ahalinsa,kimanin mota shida kowacce na qoqarin shiga gidan ba tare da wata ta gogi wata ba,sai da suka kammala shiga baki daya sannan wadanda suka wangame get din suka rufe shi,ajiyar zuciya ta saki sannan ta juya ta koma cikin dakin wanda hakan yayi dai dai da shigowar anty dije "Kai,har kin gama?" Tana duba yadda ta gyara kayan "Na gama anty" inji sumayya tana dan kashingidewa "Kinga yanzun abban laila ke gayan su baabaa sun dawo,amma dai wannan karon zaki ki masa sannu da zuwa ko ku gaisa"dan murmushi ta saki yana yamutsa fuska "Eh anty,amma dai ba yanzu ba ko?" "Nima ai bance yanzu ba,kinji an ambaci maqiyinki shiga gidan baabaa ko?" Dariya ta tuntsire da ita har tana kwanciya ganin irin yadda antyn tayi maganar.   *****  ********    ******     Washe gari da yammaci hudu da ashirin bayan ta gama yima anty dijen komai,sai ta shirya cikin wasu kayan nata,swiss ne mai asalin tsadar wanda aka tsara mata dinki na riga da skert,babu kwalliya a fuskarta kamar ko yaushe tun bayan rashin mukhtar cikin rayuwarta illa hoda jagira da liptsic,sabon hijabinta mai hannu wannan karon iya gwiwarta ta zura wanda yayi marching da lace din jikinta,tayi kyau sosai kayan sun haska ta,tun dazun take laqai laqai na zuwa gaida baaban,hakan ne yasa ma ta tsiri yi masa dambun zallar tsokar kaza.        Anty dijen ita ta sake turo qofar dakin karo na biyu tun bayan shigarta wanka "Baki gama bane har yanzu?" "Na gama anty" ta fada tana fesa turare "To,saidai fa ki shiga ke daya kya tadda lailan acan,don duka suna can gidan,ta kasa jiranki,don naji tana kamar zasu park ne" "To" ta fada badon ranta ya so ba,takalmi ta zura mara tsahon dunduniya sannan ta fito.         Daga qofar gidan baka gane gidan na qunshe da baqi ba sai ka kai ga shiga harabar gidan,yara ne da 'yammata kala kala,wadanda kana duban yanayin shigarsu zaka tabbatar da cewa lallai boko ya ratsasu,wayewa da kuma sanin kam duniya,kamar yadda group group ya rabu haka kowacce da irin tata shigar,ta wannan tana wace wance,nan da can zaka ga mutum biyu uku har hudu ma a tsaitsaye,kowa na sabgar gabansa saboda wadatar guri da kujerun zama a ko ina,wanda suke nuna lokaci irin wannan ake fiddo su ayi amfani da su.        Sai taso ta rude baki daya,ta dinga takawa a hankali tana tunanin inda zata shiga "Muje na rakaki,naga alamar ko yaushe tsoron shigowa gidan nan kike,ko wani ne zaya kamaki?" Taji an ambata daga gefanta,waiwayawa tayi a hankali,mahmoud ne,yayi adonshi cikin shadda ruwan sea blue,ta masa kyau sosai ta fidda ainihin surarsa,murmushi ya subuce mata,sai ta girgiza kai kawai tana gaidashi,ya amsa mata suka fara takawa zuwa ciki "Naga kowa tun daga ranar sallah da muka dawo zuwa yau,amma ke kam ban ganki ba,su laila tun dazu suna gidan nan,zaman gida bai damunki ne?" Murmushi ta sake saki tana kada kai "To ina zanje,ba wanda na sani" "Nan fa,nan ma gidanku ne,ko bakiga yadda su laila suka maidashi gidansu ba?" "Haka ne" ta amsa masa don batasan me zata ce ba,shima shirun yayi suka ci gaba da takawa,suna gab da shiga bangaren anty maamaa yace "Dama dai wani abun dadi kika kawowa baba,yau a gunsa zan maqale,kinsan ni da yaa man bamu cin abinci idan akayi buda baki har sai an kawo na gidan umman khalipha,yace shikam bai gane mana wannan wayon namu ba da muke maqale masa a kwanon,har gwara ni gauro ne shifa yaayaa fa" dariya ya bata har sai data murmusa,ta fuskanci mahmoud irin mutanen nan me masu barkwanci faran faran da saurin sabo da mutane.         A falon anty maamaan suka ci burki,wasu 'yammata ne zaune a falon biyu na saman kujera biyu na qasa,kowacce ta baje kayan kwalliya suna makeup,baki daya sun cika falon da hira da karadi,kayan sawarsu na aje gefe da alamu fita zasuyi wata unguwa,kana dubansu zakasan suna daga cikin baqin da gidan ke karba a irin wannan lokaci,sallamar mahmoud ita ta janyo hankalinsu "Anty maamaa" kawai ya fadi,daya daga cikinsu wadda ke qoqarin daura dankwalinta tace "Tana G-kitchen" juyawa yayi ya dubi sumayya "Idan baki gaji ba muje bata cikin nan" bata ce komai ba tabi bayansa yayin da 'yammatan suka bishi da kallo,wadda ke daura dankwalince ta tabe baki,kishi ne fal bayya ne a fuskarta,ta kusa da ita ce ta zungurota ganin yadda take binsu da kallo "Uhmmm,yadai?" Qaramin tsaki ta ja "Nikam baisan me yasa Allah ya zubawa mazan gidan nan girman kai ba,suna jin kamar su kadai ne halittar maza da Allah ya qirqira a ban qasa,jibi,kamar baisan wace ni ba" dariya wadda ke shafa powder ta qyalqyale da ita sannan ta tsaya da abinda take yi "Kema kinsan su isa sun kai suyi girmankan,karfa ki manta su su waye?,kina zaton samunsu a bagas ne,nikam banga laifi ba don sunyi girman kai sun kai suyi ne,kibi a sannu idan da rabonki zaki shiga familyn prof,nikam tuni na sallama" ta fadi tana ci gaba da murza hodarta,shiru tayi bata sake cewa komai ba sai taci gaba da gyara daurin dankwalin nata cikin sanyin jiki.       Bayan suka zagaya sai gasu cikin wani qaton kitchen wanda idan ba wajajen kayi ba ba lallai kasan da zamansa,kitchen ne babba mai dauke da electrics kala daban daban da manyan tukwane,kayan girki nau'i daban daban,kitchen ne da ma'aikatan gidan ke haduwa suyi amfani da shi duk lokacin bikin sallah irin wannan,biki ko suna na gidan idan ya tashi,gaidasu sumayyan tayi tare da yi musu sannu da aiki,antyn na tsaye sanye da jar shadda wadda keta maiqo da qyalli dinkin bubu da aka yiwa adon baqin zare,duk da ta tasamma shekara arba'in da kusan biyar amma sai ka zaci 'yar talatin ce,anty mama kam badai ado ba,tana sabe da wata kyakkyawar yarinya wadda aqalla zatayi shekara daya,an mata kwalliya cikin riga da wando,gashin kanta kuwa adin ribbom ne kala kala,ma'aikatan take sanarwa mai za'a dafa a mazaunin abincin dare a gidan baki daya "Ah mahmoud yadai?,kun fasa tafiyar ne?" Ta fada bayan sun gama gaisawa da sumayya,shi kuma yana jan yarinyar dake kafadarta din da wasa wadda da alama itama jikar gidan ce,sumayyan na tsaye gefanta antyn riqe da hannunta daya "A'ah,wannan mai tsoron shigowa gidan nan din na rako zata gaida baabaa" murmushi tayi ta juya tana kallon sumayya,haka nan sumayyan take burgeta tun ganin farko,da alamu zatayi nutsuwa,bata da rawar kai da fi'ili irin na 'yammatan zamani,shigarta kadai ta tabbatar mata da cewa daga babban gida ta fito,koda ba gidan da suke da kudi da ababen more rayuwa ba,a'ah,babban gida na nufin gidan mutunci da karamci,gidan da aka san dattako,gidan da usuli ilimi tarbiyya da wadatar zuci,gidan dake cike da tarbiyya da daraja "Ba tsoro bane,baqunta ce" inji antyn tana murmushi,kusa da antyn ya matso bayan ya ajjye mata kwanon "Nidai anty gashi nan,a tuna da ni idan baabaa zaici abinda ke cikin kwanon nan" hararsa tayi "Haka fa,anqi aure anbi an takura mana miji,kunqi barinsa yayi auki,komai zaici sai kun tayashi" dariya ya sanya yana ficewa tare da fadin "Wannan tsohon mijin naki anty ana ji da shi" itama dariyar tayi sabida tasan halin zolayar mahmoud,qarasa lissafa musu abinda ya dace tayi sannan ta dubi sumayya tace "Bismillah" ta soma qoqarin tafiya tare da daukar kwanon,ganin haka ya sanya sumayyan matsawa kusa da antyn ta miqawa yarinyar hannu,zubawa sumayyan ido tayi tana kallonta,dariya anty tayi "Wannan uwar qyuyar,Allah yasa ta yarda,uwarta na can ta tafi yawon saloon din da ba'a yishi ba sai yau ta barni da rigimamma" kamar taji kuwa abinda antyn tace sai ta miqawa sumayyan hannu alamar ta dauketa,ba antyn ba har masu aikin ta basu dariya,saboda kowa yasan qyuyarta ba da kowa take yarda ba "Lallai kin ciri tuta mai sunan umma" ta kira sumayyan da haka saboda tuna sunan wace garesu,murmushi ta danyi tabi bayan antyn tana duban yarinyar,sai ta tuna mata abdallahnta,ko yanzu me yake?,tana kewarsa sosai,ta qagu lahadi tayi ta ganshi,sai kuma ta tuna yaranta wadanda ke tayata zama tun suna tsohon gidansu da mukhtar,su naana kam tasan yanzu sun girma,tana saka ran in sha Allah da zarar ta koma zata ziyarcesu,itakam tasan cewa son yara a jininta yake haka halittarta take,duk inda taga yaro ya dinga burgeta tana kallonsa kenan. A hankali suke ratsa gidan anty maamaan na janta hira kadan kadan,jefi jefi suna gaisawa da mutane a kan hanya wanda da alama basu hadu bane tun safe sai yanzu,ba mamaki saboda girman gidan wanda ya iya hadiye duka baqin dake ciki,tun daga farkon sashen ta tabbatar da cewa akwai banbanci da sauran sasannin gidan,antyn dai na gaba tana bin bayanta,yarinyar na ci gaba da kallon sumayya tare da yi mata shirmen surutu irin na yaran dake son koyon magana ita kuwa na biye mata anty na binsu da murmushi har suka isa qofar da zata sadasu da babban falon dake mallakin mai gidan ne.       *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 6⃣0⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *SHIN KO KUNSAN DUK LOKACIN DA AZABA TA TSANANTA GA DAN WUTA,FATAR JIKINSA TA KWASHE TA QONE,ANA SAUYA MASA WATA FATAR NE SANNAN ACI GABA DA GANA MASA AZABA* *Allahumma la tada a lana zanban illa gafartah* ____________________________________         Dattijo ne mai kimanin shekaru sittin da biyar zaune kan daya daga cikin kujeru na alfarma dake zagaye da falon,haiba kwarjini da kamala sun bayyana qarara kan fuskarsa,Allah yayi masa baiwar furfura tun daga gemu zuwa kansa,farin gilashi ke saye a fuskarsa baya ga shaddar dake jikinsa fala sol,dogon wando da riga mai gajeran hannu iya gwiwa,da alamu akwai babbar rigarsu wadda bai sanya ta ba,gefensa daga hannun dama samari ne guda uku,wanda ke daura da shi yana fuskantarsa sosai,bisa alamu magana suke mai muhimmanci,kyakkyawan matashine mai cike da kyau kwarjini izza da haiba,sanye yake da irin kayan tsohon bisa dukkan alamu anko sukayi,shi dinma fuskarsa sanye take da gilashin,daya hannun nashi ma wasu matasanne su biyu sai mata guda biyu.      Tunda suka shigo falon gabanta ke mugun faduwa,sosai ta dinga qoqarin baiwa kanta qwarin gwiwa saboda haka sai ta sadda kanta qasa har suka qaraso cikin falon suna sallama,dattijon ne ya amsa da wasu daga cikin mazauna falon,idonsa na kan antyn da sumayya har suka qaraso,gefe ta samu ta zauna daga qasan carfet din,da sauri baabaa yace "A'ah,tashi ki koma saman kujera mana" murmushi tayi kanta na qasa,ta soma gaidashi tare da yi masa sannu da zuwa,fuska sake tamkar ya santa ya amsa mata,anty ta dubeshi "Nasan baka santa ba" sake dubanta yayi yana gyada kai "Gaskiya kam,koda na santa to ta kwanta min,kinsan shekarun sun fara turawa sai a hankali" sauran dake zaune sukayi danyi dariya banda mutum daya da tun shigowarsu ya dauke kansa ya maida hankalinsa kacokam kan wayarsa yana tura saqonni,hakanan ransa yake a bace. "Itace wadda ka dinga bamu labari ka kwashi girki na kwana ashirin ka dinga zabga santi" baki daya dariya suka kuma saki wanda hakan ya dan ja hankalinsa,har ya sanyashi daga kai ya mata kallo daya tak ya sake maidawa kan wayarsa yaci gaba da abinda yake "Masha Allah,Allah yayi albarka,naji dadin abinci kam qwarai da gaske,Allah yayi albarka" "Amin baabaa,na gode" ta fada cikin jin dadi bisa dabi'arta ta son na gaba da ita wanda take saka ran addu'arsa zata iya binsa ya sa mata albarka,hannu ya miqawa husna wadda ke hannun sumayya,ta kuwa lafe a jikinta tamkar ta santa,qememe taqi zuwa,sai ya zura hannunshi cikin aljihun rigarsa ya zaro alewa,kasancewarsa mai yawan kyauta,musamman a irin wannan lokaci da jikokinsa ke kasancewa a gidan tare da shi,hakan ya sanya baya rabo da alewa da sabbin kudi,miqa mata yayi take kuwa ta tafi gurin nasa,hannu yasa ya dagata yana dariya jama'ar falon na tayashi,tsaki ya ja qasa qasa yana miqewa,shikam bai san me yasa abun dariya bai yiwa su mu'azzam wuya ba,shi baki daya ma baiga abun dariya ba,yarinyar ma tunda ta shigo baki daya ma yaji ransa ya baci,musamman katse musu hanzarin da tayi kan muhimmin batun da suke tattaunawa,tun dazun dama yake addu'ar kada wani ya shigo saboda baison abinda zai katse masa bayanin da ya daukowa baban,ya san mutum ne shi mai mutunta baqo,kome yakeyi yana iya katsewa ya saurari baqonsa,sarai baaban ya ganshi amma sai ya qyaleshi,yasan halin kayansa sarai,da idanu ya rakashi har ya fice,ganin ya fita ya sanya sauran miqewa "Baabaa kada fa ya tafi ya barmu" "Jeku,don tsaf zai iya aikatawa,musamman da kun zo da tsarin da baiyi masa ba"dariya suka yi sannan sukayi sallama da baban suka fice,tattambayarta baabaa yayi kan wasu abubuwan tana amsa masa,har alokacin kanta na duqe,ta miqe bayan wasu mintuna ta masa sallama,sai anty ta ajjiye masa kwanon tana masa bayani,qwarai da gaske yaji dadi,domin shi mutum ne da baya raina alkhairi komai qanqantarsa,koda yafi qarfin abu ka bashi shi yana ganin girmansa abun agunsa,dakatar da ita yayi yana fadin "bari na baki zamzam da bagaruwa ko" "To" ta fada tana murmushi,antyn yama kwatance cikin dakinsa,cikin sakanni ta shiga ta fito da wata jarka "Ba ita ba,zamzam din da nayi dawafi da shi" mamaki antyn tayi,don irin wannan zam zam din ba kowa yake bawa shi ba,dashi yaje dawafi da addu'o'i,yakam zama magani cikin ikon Allah ga duk wanda ke jin lalura ya bashi yayi amfani da shi,duk da kasancewarsa tantagaryar dan boko amma akwai ilimin addini mai yawa tattare da shi,jarka ce guda tayi tsawon ta faro qarami ya zuba mata,sannan ya cika mata leda da bagaruwa da dabino,godiya tama baban sosai ta kuma ji dadin kyautar tasa,tare suka fito da antyn "Anty zan koma" "Haba daga shigowarki,kodai tsoron kike ji kamar yadda mahmoud ya fada,naga ko mutuniyar taki amira baki gani na,bayan ita tunda muka dawo take maganarki,na tabbata baqi ke suka hanata fitowa da tuni kin ganta,sannan baki shiga kin gaida ummee ba" sam bata so antyn ta debo mata wannan bayanin ba,amma sai ta sadda kai tace "To,bari na shiga" "Yauwa,ki gaida ummam khalipan don Allah idan kin koma,nasan itama baqi ke suka hanata leqowa,dukkanmu irin wannan lokacin sai haquri baqi muke ba dauke qafa" "To zataji" ta furta sanda antyn ke yunqurin amsar husna,nan ma qi tayi,dariya antyn ta dinga "Shikenan kuje da ita kin samu qanwa,idan tayi kuka ko laila kaya bada ta kawota" "To anty" tafada tana dariya tare da yin gaba.         Baki daya falon ya sauya ba kamar waccan karon data shigo shi ba,da alama gyaran azumin ne,komai ya canza a falon,saidai tun kafin ka kai ga qarasowa cikin falon zaka jiyo muryarta,tana tsaye tsakiyar falon hannunta riqe a qugu tana zuba masifa,bisa alamu da 'yanmatan dake zaune a falon take,sun kusa su hudu harda amira dake gefe tana shan ice cream hankalinta kwance kamar ma bata falon "To bani cike da iskanci,ran kowa sai ya baci wallahi,bazan dauki raini ba,kuma wanda ya fasa karbo greeting cards na 'yammata yana kawowa bai cika ba mu zuba ni da ku,aikin banza kawai" tana gamawa ta juya a fusace tana taku kan tsireren takalminta mai igiya,kowa sanye da suturar al'ada banda ita,wando ne a jikinta irin straight leg din nan,sai riga one shoulder a jikinta,gefe sumayyan ta janye tana dubanta,dariya taji 'yammatan suka saki bayan fitar tata banda amira fake ci gaba da abinda take,daya daga cikinsu tace "Duk wayon amarya wallahi sai an sha manta"sai a lokacin sumayyan ta maimaita sallamarta,amira ce ta amsa cikin fara'a ta miqe "amiran umman khalipha kinsan kina raina,sannu ga guri zauna" tana mata nuni da wata kujera dake can gefe babu kowa,qarasawa tayi tana zaman amira ta sake cewa "Ina kika tsinto wannan uwar qyuyar,daina kallona kina wani saukar da kai ban daukanki zanyi ba nima" ta fada tana dan daga murya da zaro ido da alamu tana jin haushin irin qyuyar husnar,murmushi sumayya ta saki tana dafe kan husna wadda ta kwantar da kanta aqirjinta "Dole fa ta miki qyuya,kina mata irin haka" "Allah bata da kirki" gaisawa sukayi ta mata sannu da zuwa sannan ta tambayi ummin "Ummi na sama,bari na miki kiranta" "To" ta amsa,satar kallonta 'yammatan suka ci gaba da yi itakam hankalinta na kan husna tana mata wasa a haka amira ta dawo ta tadda su,ba dadewa ummin ta sauko,abinda sumayya ta dan lura da shi shine,ummen irin mutanen nan ne da basu son hayaniya da yawan surutu.        A mutunce ta gaidata ta amsa mata fuska a sake itama tana son daukar husna,saidai itama husnar ta watsa mata qasa a idanu kamar sauran,tilas ta barta sumayya na mamakin qyuyar yarinyar,bata wani jima ba tayi musu sallama ta fice sabida yadda 'yammatan ke kallonta.        Anty dije ma tayi mamakin ganinta da husnar,goyata tayi bayan ta bata abinci,ba jimawa kuwa tayi bacci a bayan nata,gab da magariba sukaji sallama a falon,sumayyan ce ta fito goye da husnar tana amsawa,magidanciya ce wadda zata doshi shekara talatin da hudu,fuska a sake sumayya tayi mata sannu da zuwa,leqa bayan sumayyab tayi tana riqe baki cikin fara'a "Wai lallai raino yayi dadi,ashe kam da gaske tana nan din,ni ina can hankalina na kanki uwar qyuya ashe ke kin haye bayan mutane kina bacci abinki" dariya sumayya ta danyi sai alokacin ta fuskanci mamarta ce,yunqurin saukota tayi tana fadin bari ta bata ita "A'ah,barta mana idan ba'a matsa miki ba,haba sai kace bare,da nan da gidan baabaa ai duka daya ne,kawai dai idan ta tashine nasam zata taba miki darunta,sai azo a dauketa" "To" ta amsa tana gyara goyon "Ina anty dije" ta ambaceta da sunan da suke kiranta a kano sabanin yadda taji mutan gidan na kiranta da umman khalipha "Yanzun nan ta shiga wanka" "Sarkin kwalliya wa miji,idan ta fito kice ina gaidata" ta fada da sigar zolaya,bisa alamu sun saba sosai.       Bata farka ba sai bayan magariba sumayyan ma na shirin tada isha'i,daukota tayi daga kan gadon ta cire mata pampers tare da zuba abinci ta bata,sai da taga ta qoshi sannan ta sabata a kafada ta zura hijabin sallarta wanda ke kusan sharar qasa tace khalipha yazo ya rakata.         Tarwai gidan da haske kamar kowanne lokaci,saidai yau akwai yawaitar mutane a harabar gidan,sashen anty maamaa ta shiga tacu sa'a ko ta tadda maman husnar,amsarta tayi tana yiwa sumayyan sannu tare da godiya.        Tunda ta tako daga sashen anty maaman ya zuba mata idanu,haske gidan kadai ya wadatar masa ya gane wace ita,mahmoud da ya gaji da yi masa magana ya dafa kafadarsa wanda hakan ya sanyashi daga kai da sauri yana dubansa "Mahmoud,sumayya ta nake gani a gidanku" waiwayawa yayi zuwa inda yaga alqasim din na kalla,tabbas sumayya ce ke tahowa "Wannan sumayyan ce sumayyarka dama?" "Wallahi itace" alqasim ya fada a rude,dariya mahmoud ya saki "Ai tazo gidan sauqi,amma fa ba abune mai sauqi ba shawo kanta haka na fuskanta" "Please mahmoud" alqasim ya fada cikin damuwa yana hade hannayensa ganin sumayyan na gab da su "Don't mind"mahmoud ya furta yana waiwayawa yadda zata iya ganinsa idan ta qaraso,sam bata lura sa su ba duk da hasken da ya wadatar da gidan tamkar raba,hanakalinta na gefe can inda wasu 'yammata ke zaune suna hira,kusan basu suka dauki hankalinta ba ma yaran dake wasansu kusa da su ne,wanda daya daga cikinsu keta kiran abbanaa da alama labarin abban nasu yake basu,tana ganin sa'o'in abdallah a ciki,cikin ranta ta raya suna cikin farinciki da gata,sabanin abdallah da take fatan zai tashi cikin farinciki saidai baisan dadin uba ba,qwalla ta taru idonta sai tayi hanzarin sadda kai da qara sauri a tafiyarta don ficewa daga gidan,tun jiya ranta a jagule yake,hakanan ta wuni da tunaninsa cikin ranta,wanda ya haddasa mata kasala da mutuwar jiki wunin baki daya,shi ya qara mata qyuyar fitowa waje "Yi a hankali kada ki fadi" mahmoud ya fada yana dubanta,cak ta tsaya tana dubanshi tare da qaqaro murmushi "Hala sauri ake a fice daga gidan namu"dariya ma yaso bata saidai bata yin ba sai murmushi saboda damuwar da zuciyarta ta shiga daga tuna mukhtar " kadai camfani" "Ko kadan,to daina saurin,ga baqo kinyi,yanata nemanki wata da watanni sai yau Allah ya qaddara haduwarku" a zabure kamar wadda ta yiwa sarki qarya ta daga kai,suka hada idanuwa da alqasim,farinciki yake ji sosai cikin ransa,takowa yayi gefanta yana dubanta "Zakaran da Allah ya nufa da cara sumayya,mai yiwuwa Allah ya qaddara wani lamari ne mai girma tsakaninmu,shi yasa ya kado hankalina abuja gidansu abokina mahmoud,ashe rabon na ganki ne" ba shakka tana ganin girma da qimar mahmoud,tunda shi ya soma tsaidata,banda haka da tuni ta yankawa alqasim warning cikin daqiqun nan tare da kaucewa.         Saye yake da quater zip sweater mai dogon hannu ta kamfanin armani maroon colour saboda sanyin da ya soma busawa sakamakon hadarin da ya hadu dazu bai zub da ruwa ba sai ya bada sanyi wa garin baki daya,wandon jeans baqi,sai high top sneakers,hannayensa saye cikin aljihun wandonsa ya fito zuwa harabar gidan yana duddubawa,kusan al'adarsa ce wannan a lokaci irin wannan,kafin yaje ya kwanta sai ya dudduba ko ina saboda baqin dake gidan,ya tabbatar babu yarinyar data fita yawo balle akai ga zuwan saurayi zance gidan,yace duk mai buqatar hakan ta bari idan ta koma gidansu tayi abinda taga ya mata amma ba cikin gidansu ba,tsarin ya yiwa baabaa prof saboda haka baice komai ba,a irin hakan wasu daga 'yammatan wadanda suke zaton wayewa ce garesu,iliminsu da gogewarsu ta kai wani mizani,sukan fita ciye ciye ko siyayya da samarinsu,wani lokaci sukan kai goma ko tara na dare basu dawo ba,yayin da wasu sukan maida harabar gidan filin baje kolin gayyatar saurayi suyi zance,hakan ne ya sanyashi sanya wannan doka wadda ta yiwa manyan dai dai saboda tsaron tarbiyyar kowacce yarinya har ta koma gidansu,hakanan duk wanda ke kawo ziyara gidan a irin wannan lokaci ya san da dokar,walau mace ko namiji. Cikin izza da ginshira yake takowa tsakiyar harabar gidan yana qarewa kowacce kusurwa ta gidan kallo da idanunshi,tuni hayaniyar wajen ta soma raguwa kowa ya soma shiga taitayinsa,wasunsu suka shagala da kallonsa,masu gulmarsa qasa qasa nayi. Kamar ta sanya kuka haka sumayyan keji,yayin da alqasim kuma ya dage wajen ganin komai ya daidaita kafin barinta wajen,idanunsa ya sake wurgawa wani sashen,a can saka masa kamu,maca ce tsaye da hijabinta har qasa da wani saurayi tsaye a gabanta,sai wani saga gefanta,ranshi ya matuqar baci,ya tsani ya sanya doka a karya masa,a ganinshi wannan daya ne daga cikin alamun raini,idanu ya zuba sosai sai ya dinga hango kamar mahmoud ne dayan dake gefe,cikin bacin rai ya soma takawa idanuwansa na wajen,sam mahmoud bai ankara da fitowarsa ba shakka da tuni ya sallameta,ya riga da yasan halinsa sarai mutum ne mai doka da qa'ida,bazai karya dokar wani ba so shima kada a karya tasa shine zaman lafiyar mutum. "Mahmoud" ya ambaci sunanshi bayan isowarshi gun,wani abu taji ya caketa tun daga tsakiyar kanta zuwa tafin qafarta da taji muryar mukhtar gab da ita,kuma a bayanta,kamar mai ciwon wuya haka ta dinga waiwayawa a hankali har ta kammala juyawa baki daya,tsaye yake harde da hannayensa yana yiwa mahmoud da alqasim magaba cikin bacin rai,idanuwansa na kansu,wanda sam bata iya jin abinda yake gaya musu illa bakinsa da take gani yana motsawa,muryar ce taci gaba da yi mata amsa kuwwa cikin kunnuwanta,a hankali ya dinga juye mata zuwa mukhtar dinta,sannu sannu jikinta ya soma rawa tamkar wadda aka tsoma cikin ruwan sanyi,bata ankare ba taga yana qoqarin juyawa ya bar gurin,batasan lokacin da ta daga murya cikin qaraji daya sabbaba har wadanda ke daura da su jin sautinta ta ambaci "Mukhtar!" Cak ya tsaya tare da waiwayowa yana dubanta,kallonsa take tana takowa zuwa gurinsa a hankali,tsayawa kawai yayi yana dubanta,tun dazun haushi ya tsaye masa a wuya,tunda ya tsaya gun ya lura da yadda ta zuba masa udanuwa,abinda ya tsana kenan cikin kafatanin halayen 'yammatan wannan qarnin,kallon tsiyawa d'a namiji,babu wata kunya tattare da su "Mukhtar kai ne?,kaine mukhtar!,dama kana nan,dama baka mutu ba?" Cikin bacin rai da yi mata kallon mai tabin hankali ya dubi mahmoud "After All ma ashe da mai lalurar tabin hankali kuke tsaye?,sai kuzo kusan yadda zaku fidda ta tun kafin ta soma yiwa mutane barna" "Mukhtar nice fa,sumayyarka ce mukhtar,nike da tabin hankali?" Har yanzu bai gasgata mai hankali bace,amma sai ya nutsu tsaf ya dubeta,babu alamu na hauka tattare da ita,ayyanawa yayi kawai tsabar rainin wayo ne da son samun guri,wanda ba tun yau ba ya gama haddace kissa ta son samun guri na 'yammata masu cusa kai kala daban daban,wani tsaki ya ja,sannan cikin dakakkiyar muryarsa wadda ta sake taimakawa wajen sawwara mata surarsa zuwa ta mukhtar yace "Ban ciki da hauka da gidadanci kinji ko,ki kama kanki tun bai gudu ya barki ba,kama hanyarki ki koma inda kika fito" ya juya yana yunqurin barin wajen,a zabure ta bishi har ta samu nasarar riqo dantsensa,cikin tsananin bacin rai ya juyo yana dubanta cikin ido,wani kallo ya jefe ta da shi wanda tabbas da cikin hayyacinta take tuni ta sake shi saidai sam ko a jikinta "Sake tafiya zakayi ka barni?" "Sakeni!" Ya daka mata tsawa "Bazan sake ka ba" itama ta fada cikin tsawa da bacin rau,take zuciya tanzuroshi,marinta yaso yi amma yaga rashin dacewar hakan,maiyiwuwa akwai tabin qwaqwalwar da batasan tana da shi ba,yaga kuma alama matuqar yaci gaba da tsaiwa zata iya ma rungumeshi kaban wadan nan yaran ta zubda masa mutunci,saboda haka sai ya fincike hannunshi tare da tunkudata yayi gaba,wani irin zafi yake ji da haushinta,baya tayi cikin rashin qwarin jiki,sun tsammaci zata turje ta tsaya sai kawai suka ga ta sulale ta zube baki daya,cikin firgici da tashin hankali mahmoud ya soma qwalawa amira kira don babu damar taba ta wadda fitowarta kenan shan iska batasan ma meke faruwa ba,ganin sumayyan kwance ya daga hankalinta ta koma ciki a sukwane,nan sukayi kacibus da anty farida mamar husna ta kamo hannunta suka yo wajen. Ba amira da anty farida ba,hatta mahmoud da alqasim hankalinsu tashi yayi,kowa mamaki yake,meke faruwa ne haka,abu kamar dramer cikin sakanni qalilan,tana ta faman kiran mukhtar shi kuma wannan ALMUSTPHA ne abinda suke tunani kenan,cikin hanzari anty farida ta soma yunqurin dagata da taimakon amira,idan ka dubi fuskar wasu dai daikun 'yammatan dake gun jimami da tausayi ne bisa fuskrsu,addu'a suke mata kan Allah yasa ba qoshin wahalar da suka afka bane itama ta afka cikinsa,yayin da wasu dadi ya rufesu kamar su taka rawa,ko banza basu zama su kadai ba cikin wadanda suka rasa wannan damar. A hankali ta ja numfashi tana ambaton sunan Allah,idanunta ta bude,jinta take kamar wadda ta tashi daga bacci,idanuwanta ta sake lumshewa take abun ya sake fado mata,kalamansa da muryarsa suka fara yi mata amsa kuwwa cikin kunne,take idanuwanta suka tara hawaye masu dumin gaske suka soma bin gefen kunnenta,sake rintse idanuwanta tayi,kamanninsa suka fara dawo mata ganin farko data yi masa kafin idanuwanta su rudeta,da sauri ta bude idanuwanab tana girgiza kai,tabbas ba mukhtar bane,babu kamannin mukhtar ma tattare da shi idan ka dauke murya,me ya shiga kanta ta aikata haka sai kace wadda jinnu suka juyawa tunani?. Saitin fuskarta taga an turo screen din waya,idanuwanta ta bude kan screen din,shine,shine wanda ta gani dazun,sanye yake da qananun kaya kyakkyawar fuskarshi qunshe da murmushi,hotonsa ya cika fuskar wayar baki daya,a yanzun ta sake tabbatarwa bata ga kama tsakaninsa da mukhtar dinta ba,sai ta waiwaya don taga wanda ke haska mata hoton,amira ce zaune gefanta,idanuwa suka hada sai ta janye wayar tata ta kasheta tana duban sumayya "Wannan yaya nane,mama da baabaanmu daya,ummee ita ta haifemu,sunanshi MUSTAPHA ko ALMUSTAPHA duk daya ne,anty dije ta bani labarin waye mukhtar a gunki,matuqar suna kama da mukhtar kuma yayi miki na miki alqawarin zaki zama mallakinsa,duk da nasan babban aiki na daukawa kaina saboda sanin waye YAYA MAN,amma abinda yayi miki ya bata min rai,ina jin tamkar ni aka yiwa,ko don saboda wannan indai kina sonshi amiran umman khalipha na miki alqawarin aurensa". *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 6⃣1⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *SHIN ko kunsan RUWAN DAN WUTA,RUWAN MUGUNYA NE(KAMAR RUWAN CIWO QURJI)TAFASASHSHE MAI AZABAR ZAFI DA TURURI,A DUK LOKACIN DA YA BUQACI SHAN WANI ABUN SHA SABODA TSANANIN QISHIRWAR DA YAKE JI SHI ZA'A BASHI YA SHA,YAYIN DA YAKE SHA DIN SABODA TSABAR ZAFI DA TAFASA HAKA ZAI DINGA YAYYANKA DA TSITSTSINKA MASA HANJINSA,YANA ZAGWANYEWA* *Subhanallah,muji tsoron azabar Allah 'yan uwa* ____________________________________ Shuru amiran tayi tana duban sumayya cike da qwarin gwiwa da kuma yaqini cikin zancanta,itama dubanta sumayyan keyi kafin ta saki murmushi sannan ya kada kai "Ni nayi kuskure amira,ni na yi masa kallon mukhtar dina bayan bashi bane kamanceceniyar iya murya ce kawai,koma waye zaiyi zaton ba lafiya tunda baisan farkon lamarin ba,amira,bana jin so ko qaunar ko wanne namiji bare na yi sha'awar zaman aure da shi,banqi a ce nabi mukhtar ba muyi zamanmu cikin rahamar ubangiji,abunda kawai nake tausayawa abdallah na" ta fadi cikin karyewar murya da rauni,duk da qoqarin kaucewa hakan da takeyi,tausayinta ya sake kama amira "Da gaske amiran umman khalipha kin taba aure kuma ma har da boy?" Ta tambaya cikin zumudi,kai ta gyada mata tana murmushi "Zanso naga boy din nan,na tabbata zaiyi kyau kamar mamarsa" wannan karon har dariya taso sara,saboda ta tabo gudan jininta,yaron da shima tun kafin ya shaqi iskar duniya ya fara fuskantar gwagwarmaya da matsalar rayuwa,koda ya shigo cikin duniyar ma ba'a barshi ya huta ba sai da aka so saida rayuwarsa,zainab ta fado mata,ko yanzu tana wacce duniya,baki daya sai taji son aure ya sake fita daga zuciyarta,itakam yanzu me zata ci da aure "Amma zanso amira ki amincewa qudirina,na tabbata cewa rayuwar yaya man zata sauya zuwa yanayin da muke masa fata da hange,zan iya cewa ANTY SU'AD bata da wani amfani a rayuwanshi" cewar amira tana duban sumayya,kai ta shiga girgizawa "Duk mai qaunata amira ba zai sake min sha'awar aure ba a yanzu,nikam me zanci da aure,auren ma na mai mata" "Me kike cewa ne?,amira zanso sanin wace ke,na tabbatar akwai wani abu a rayuwarki ba wai mukhtar bane zalla" miqewa tayi a hankali ta zauna tana duban amiran "Babu lokaci,duba kiga goma na dare" "Ko zan kwana anan nasan babu damuwa,ina son ki ban labarinki don Allah,naji anty dije na fadin wasu abubuwa da ban gane ma kansu ba"murmushi tayi "Me zakici da labarina banda kayan sanya hawaye a ciki,babu komai a labarina face wuya da naci game da kishiyoyi da abokan zama na" idanuwa amiran ta zaro "Kina nufin bama aure daya kika yi ba amiran umman khalipha?,ina cewa zamuyi sa'anni dake fa?" Dariya tayi wannan karon "Hala mass com kika karanta ko,ina ce miki dare yayi amma baki damu ba?" Dariya itama ta saki tare da miqewa ba don taso ba "Zan tafi,amma zan dawo ki bani labarinki" "Sai kinzo,sai da safe na gode" "Nice da godiya kuma kiyi haquri da abinda ya faru" "Babu komai QADDARA CE!" ta ambata wani abu na taba ranta,juyawa amiran tayi ta fice tana murmushi ****** ******* ******* Sukuku haka ta wuni washegari,duk da ba wani abu take ji na ciwo a jikinta ba amma baki daya bata da kuzari kamar wadda aka zarewa laka,da yammaci tana kwance a falon,babu kowa gidan daga ita sai anty dije,su laila sun tafi gidan kakarsu,itama rashin qwarin jiki ne ya hanata zuwa taji muryar amira tana sallama,miqewa tayi daga kwanciyar tana amsawa tare da maida daurin dankwalinta da ya zame,sai taga ashe su biyu ne ita da anty maamaa,miqewa tayi fuskarta qunshe da fara'a tana musu sannu da zuwa,kitchen ta juya ta dauko lemo saman tray ruwa da kofuna ta ajjiye musu sannan ta haura sama don kiran anty dije. Tare suka sauko,fuskarta dauke da fara'a itama take musu lale da zuwa,ta zauna suka gaisa sannan sumayya ta gaida antyn kafin ta waiwaya ga amira suka gaisa "Zuwa nayi dubiya,jiya muna cikin gida ashe haka abu ya faru,sam ban sani ba sai dazu da mahmoud ya shigo yake gayan,sai kuma farida itama ta sanarmin su suka kawota gida" "Wallahi kuwa,abin sai addu'a,damuwar dake ranta ce ta mata tasiri har ta haifar da hakan" "Allah ya kiyaye gaba,baki daya ma banga mustaphan ba yau,yana ta shirye shiryen komawa,inason tambayarsa ya akai hakan ta faru,banji dadi ba sam bai kyauta ba,ai ba'a haka.....sannu sumayya ya jikin?" A kunyace kanta na qasa tana murza yatsun hannunta,tana jin tamkar ta jawowa kanta wani babban abun kunya ne,kada ma wasu su tsammaci saboda shi ta suma tace "Na warke ai anty" "Allah ya sawwaqe ya qara afuwa" "Amin anty dije ta amsa,amiran ce ta dubi sumayya "muje ina son in ganki"tana dariya,sai ta miqe tayi gaba amiran ta biyo bayanta. Bakin gado suke zaube baki dayansu amiran ta kalleta "ina alqawarina?" "Labarina bazai yiwu ba yanzu amira,ki bari na sake samun sauqi ko?"shiru ta danyi tana kada kai "To shikenan,Allah ya qara baki lafiya" "Amin" ta fada tana murmushi,jefi jefi amiran ta dinga sako mata hita,wata ta 'yan uwa wata ta qawayenta wata ta gidansu duk don ta sake sakin jiki,yawanci duka bata sansu ba,amma abun yana burgeta,saidai tayi murmushi kawai,a nan ta fahimci su'ad itace matar mustapha. Suna zaune anty dije ta leqo tace anty zata tafu,miqewa tayi tana cewa "Nima tafiya zanyi,zamu je unguwa ne yau duka 'yammatan,sai na dawo" "Allah ya tsare,na gode ki gaida ummee" "Zataji kuwa,don batasan abinda ya faru ba,da yau ya man ya shiga uku wallahi,inaga ma sai na guntsa mata batun" ta fada tana dariya gami da ficewa,sumayyan nason ce mata kada tayi amma tuni tayi gaba abinta. Kiran wayar bdur rahaman ita ta qarasa tayata hira har sha biyu na dare sunata hira,yana ta bata labarin yadda shirye shirye suka kankama na bude islamic clinic dinshi,yana so ya soko mata maganar yadda yayi missing dinta da kuma yadda yake son ganinta saidai yana tsoron kada damar da ya samu ya rasata,sam bata gaya masa zata zo kano ba har sukayi sallama. ******* ******* ******** A hankali ya dinga takowa cikin tafiyar sa ta qasaita har cikin falon baabaa prof din,sanye da short sleev polo t.shirt jaa da touches na baqi,straight leg trouser sai safa a qafarnshi,hannunsa soke a aljihun wandonsa,wanda ya zame masa al'ada idan ya sanya qananun kaya,idan ba waya hannunshi to zaka samu hannayen cikin aljihu ko harde a qirji. Sallamarsa ce ta sanya baabaan dago kai yana dubansa,mai hali bai sauya halinsa,wasu daga al'adar turawa har yau sunqi barin mustaphan,ko da yake ta yaya zasu barshin bayan har yau shima bai bar cikinsu ba,sam baison manyan kaya,da wuya ka ganshi da su,cikin girmamawa ya qaraso ya duqa gaban baabaan yana gaida shi,amsawa shima yayi saidai fuskanshi sam babu walwala sabanin yadda ya saba ganinsa "Yaushe ne zaka koma" hannayensa soke cikin juna ya amsa kamar wanda baison yin maganar "Cikin wannan satin in sha Allah" "Allah ya lamunce" "Amin ya Allah". Shiru ne ya dan ratsa tsakaninsu,shi mustpha na sauraron me baaban zai gaya mishi tunda shi ya aikata takanas sashensa aka kira shi,yayin da shi kuma baaban yayi banza da shi,yana so yau ya qure miskilancinsa,yaci gaba da bude shafukan jaridar dake hannunsa,sam baka rabashi da duba jaridu,duk da bai cikin sabgogi da al'amuran gwamnati a bayyane amma a badini gangar jiki da zuciyarsa na tare da su. Har ya kammala karatun jaridarsa baiji yace komai ba,hasalima da ya daga kansa sai yaga ya jingina bayansa da jikin kujera gami da miqe qafafunsa idanuwansa a lumshe,ajjiye jaridar yayi yana sauke ajiyar zuciya,glass dinsa ya zare shima ya ajjiye gefe yana dubansa "wato ba zaka iya tambayar dalilin da ya sanya na kiraka ba kenan"miqewa yayi ya zauna sosai yana duban baaban "nayi zaton baka kammala abinda kake bane,banson kuma katse ka"shuru yai ya jinjina kai,duk cikin 'ya'yansa bai haifi kamar mustapha ba har yau ta kowanni fanni ya tsrerema 'yan uwansa maza da mata "me ya kaika ture yarinyar mutane har ta suma" "Yarinyar mutane har ta suma?" Abinda ya dinga maimaitawa ciki kwanyarsa kenan,sam ya mance wace ce,wa baabaa ke fadi ya ambata cikin zuciyarsa "Yarinya baquwa 'yar gidan alhj farouq" har ga Allah bai fuskanci kan wa baba ke magana ba,don shi baki daya ya mance lamarin,baaban ya kalla kamar yanason qarin bayani kan abinda yake cewa,baabaan yasan irin kallo,indai mustaphan yayi ba shakka yana buqatar qarin bayani "Tashi kaje,ka kyauta ka kuma yi abinda ya dace,nima zanyi abinda ya dace din" duk da bai gane da wa yake nufin ba amma ya miqe kasancewar ya riga ya bashi umarni,cikin girmamawa ya rusuna yana cewa "A huta lafiya" baban bai amsa shi ba har ya miqe ya juy,har ya taka daya biyu sai kuma ya juyo ya dawo ya sake rusunawa aladabce "Dambun naman naka ya qare?" Ya fahimci me yake nufi,dambun naman da sumayya tayi masa ne,ya ganshi yana ci ya tsokaneshi da cewa gun saidawa aka siyo masa don yasan baison cimar siyarwa,yace idan ya qare zai masa magana ya sake siyo masa a inda aka siyo "Bai qare ba" baban ya bashi amsa idonsa akanshi har ya miqe,baiyi qarya ba,mustaphan daban yake cikin yaranshi,kamar yadda yake da wasu baqin halaye haka dabi'unsa na kula da iyayensa suke,daban ya daukesu,martaba da darajarsu bai hada ta daya data wani halitta ba,cikin kowanne yanayi ko motsi nashi yakan sanya shi gaba,fatarshi da addu'arshi daya Allah ya azurta shi da zuriyya dayyiba saliha,wadda zata ji qansa yadda yake jin qan nashi iyayen. ***** ****** ****** ***** Daren da zasu tafi kanon kasa bacci tayi baki daya,tsaf ta gama hada komai,hatta da kayan da zata sanya goben ta waresu gefe,cikin irin wannan zaman taji kuwwar wayarta,ta janyota tana dubawa,baquwar lamba cr,maidata tayi ta aje don a yanzun tsoron daga baquwar lamba take,sai data fuskanci wayar na neman hanata sakewa ya sanya ta dagawa,muryar alqasim ce ta bayyana,yasan kadan daga aikinta ta datse wayar wanda baya fatan haka,saboda yaci wahala kafin ya kai ga samun lambarta,hakan ya saka ya cikata da magiyar ta tsaya ta saurareshi,bai kyautu ta watsa masa qasa a ido bo saboda qimar mahmoud,hakan ya sanya ta tsaya tana sauraronsa zuciyarta fal da mamakin inda ya samu ainihin lambarsa,gaisuwa sukayi ta mutunci ya sake mata sannu da jiki ta amsa masa,shiru yayi kamar ba zaice komai ba hakan ya sanya ta buqaci kashe wayarta,wanda shi ya zaburar da shi ya soma magana,tatsuniyar gizo dai bata wuce ta qoqi, "Alqasim,ni bazawara ce na taba aure,ko da ina da ra'ayin aure banda ra'ayim auren saurayi,ballantana ma mi ban hango shekarun da na tsara ba kafin na sake aure,babu lokaci,saboda haka ina mai godiya bisa qaunar daka nunan,kuma ina mai baka haquri tare da addu'ar ubangiji ya baka wadda ta fini" ta kaiwa qarshe ta kashe wayar ta cillar gefe tare da mirginawa ta kwanta ta runtse ido tana son bacci ya dauketa ko zata samu damar tashi gobe da wuri ta shirya. ******** ******* ******* Qarfe sha daya na rana dukkan shirin tafiya ya kammala,wannan karon har da abban laila zasu tafi a mota daya,sun gama komai har motar ma drivern ta faka ta bakin get din gidan,duka suna ciki zaune,abban laila kawai da ya shiga yiwa baaba sallama suke jira,wanda sabonsa ne baiyin kowacce tafiya bai sanarwa baban ba,saboda ya daukeshi a mazaunin mahaifi. Anty dije ce tayi mantuwa cikin gidan,botiki ne data zubawa mama sabulun salo mai yawa a ciki wanda su zainab zasu hada sabulun gyaran jiki,sau biyu tana aiken laila bata ganshi ba,ganin zata bata mata lokaci kada abbansu ya fito ba'a dauko ba ya sanyata tura sumayya. Kunnenta maqale da waya suna waya da abdur rahman,yayin da daya hannun ke riqe da dan botikin,ta sanyo qafarta waje kenan kunnenta ya jiyo mata muryar tasa ginshira yana fadin "Amma why not kubi jirgi,akwai jirgi daga nan zuwa kano 12"dariya uncle farouq yayi "wannan kam ai su ku manya,ba damuwa,awa biyar ne ba dadewa zamuje" hannu ya bashi yana fadin "Allah ya tsare" "Amin amin,wataqil kafin mu dawo kun koma,sai gani na gaba" murmushi kawai yayi ya juya,har a lokacin tana labe bakin qofar,hakanan jikinta ke rawa har wayar hannunta ta subuce ta fadi bata sani ba "Ah ah,ashe kin dauko me kuma kike a tsaye a nan?" Anty dije ta tambayeta wadda ta biyo sahunta jin shirun yayi yawa "Ba komai...fitowa zanyi dama" ta fada muryarta na rawa tana durqusawa tare da soma tattare wayarta data watse a gun,bin wayar anty dije tayi da kallo cikin ranta tana tambayar kanta me ya faru har ta kammala tattarewar ta juya tabi bayanta bayan ta rufe gidan. TOFA! *Mrs muhammad ce👑* 📚📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [23/02, 11:51] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 6⃣2⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *KO KUNSAN SABODA BALA'I DA JAHANNAMA KE DA SHI HAR WANI SASHE NATA YANA NEMAN TSARI DA WANI SASHEN?* *Allahumma ajirna minan nar* _________________________________         Luf tayi cikin motar idanuwanta a lumshe,duk da hayaniya da karadin da suke tayi cikin motar amma babu ita,bata san me ya haddasa mata mutuwar jiki ba,batasan me take tsoro ba,abu daya ta sani muryar na daga mata hankali,muryar na sanyata ta tuna da mukhtarinta,anty dije ma tayi tsammani bacci take saboda ta san jiya batayi wani isashshen bacci ba,yau kuma ta riga kowa sammakon tashi,tun tana jin hayaniyarsu sama sama har bacci barawo yayi awon gaba da ita.       Kamar kullum yau ma sun tsayawa wannan restaurant din don cin abinci saidai banda ita,zaman ta tayi cikin mota sai takeaway sukayi mata sannan suka wuce.       Yamma lis suka isa kano ta dabo tumbin giwa,ko da me kazo an fika,gari ba kani ba dajin Allah,wani farinciki ya dinga shigarta tun kafin su qarasa gida,iskar garin na kano take shaqa sosai,taje farinciki ya lullube zuciyarta,doki ya mamaye zuciyarta,kewar mama malam abdallah dama su zainab suka dawo mata sabuwa fil,kamar kuwa uncle farouq ya sani yace a fara biyawa gida a sauke sumayyan,anty dije zatayi qorafi kan ba haka ba su wuce gida idan sun huta baki daya sazo gobe yace a'a sam tana son taga mamanta,hakan ya mata dadi matuqa duk da ta boye dokinta,suna sauketa kuwa suka wuce kan sai gobe zasu shigo,tana fara'a ta daga musu hannu sannan ta sanya kanta cikin gidan yaran maqota na shiga mata da jakarta.       A tsakar gidan ta ware muryarta tana kwada sallama,abdallah ne ya soma fitowa da gudu halima na biye da shi,da gudu ya qarasa wajenta yana kiran "Mami na" "Abdallah na" itama ta fada cike da kewa ta durqusa tare da ware hannayenta ya fada ciki ta miqe rungume da shi tana dubansa fuskarta fal murmushi,ya qara kyau wayo da girma kamar ba abdallahnta ba,kallo daya zakayi masa ka tabbatarwa kanka yana cikin kwanciyar hankali tare da samun cikakkiyar kulawa,yayi bul bul da shi,fes kamanninsa da babanshi kan fuskarsa.        Dakin mama ta shige tare da su halima da maman,tana sanya kanta falon taga amina zaune matar abubakar ciki a gaba,baki sumayyan ta bude tana kallonta "Antynmu kice kema kina gidan namu yau?" "Gidanku ko gidanmu,aike kam yanzu baquwarmu ce" dariya sumayya tayi "Allah sarki anty amina,kice kinyi nauyi shi yasa kika kasa tasowa ki tarbeni" dariya aminan tayi a dan kunyace saboda mama na gurin,gaban maman sumayya ta qarasa idonta a kanta tana jin wani dadi na gajin mahaifiyar tata,itama maman kallonta take,a gabanta ta durqusa ta gaidata,cikin farinciki maman ta amsa tana tambayarta ina dijen kuma,nan ta sanar mata sai gobe zasu shigo,hira ce ta barke babu qaqautawa tsakaninsu abdallah na kan cinyarta,yaqi yarda ko nan da can yaje,halima ke dungureshi tana cewa "Zata tafi ta barmu da kai ne mai qaton kai da kaqi zuwa wajen kowa" amina ke kareshi "Barshi malama,yaro da uwarsa,ai yayi qoqari ma,yaushe rabon da ya ganta?" Har magariba suna hira,sai da aka gama sallah magariba sannan sumayya ta cewa zainab ta hada mata ruwa zata yi wanka,dariya zainab tayi "Wankan lafiya da daren nan?" "Bazan iya bacci ba sai nayi wallahi" dariya ta kuma yi "Kice ba banza ba yaya sumayya kika dad wannan dan banzan kyan,wallahi abuja ta karbeki,baki ga yadda kika koma 'yar gayu ba" "Hada min ruwan sai kizo kici gaba da sharhin naki" sumayya ta fadi tana dariya,anty amina ce ta karbe "Gaskiya ai ta fadi,wallahi garin ya amsheki sosai" "Kin biye mata kenan antynmu" ta fada tana dariya anty aminan na tayata.        Bayan tayi wanka ta sake shiryawa cikin doguwar riga ta wani cotting din yadi mau gajeran hannu,ta yane kanta da dan qaramin mayafi ta dawo falon mama,a nan suja zuba tuwon dare baki daya idan ka dauke maman,suna ci suna ci gaba da hira,har yanzun idanuwan maman ma kanta,ita kanta tasan diyar tata ta soma sauyawa kamar ba ita ba,ta tabbatar sauyin rayuwa ya fara samuwa a gareta,cikin zuciyarta ta dinga mata addu'ar Allah ya azurta ta da miji na gari,wanda zaici gaba da dawainiya da ita cikin ingantacciyar rayuwa.       Suna gab da kammala cin tuwon malam da yaya abubakar sukayi sallama,amina tayi saurin janyo hijabinta ta sanya,yau malam da kanshi ya shigo falon maman,fuskanshi shina dauke da farincikin ganin diyar tasa,cikin girmamawa ta gaida malam din ya amsa yana tambayarta mutan abuja,tace kowa lpy suna gaida ka,amma gobe su antyn zasu shigo,madallah malam din yace sannan ya fice yana cewa bari ya barta ta huta da gajiyan hanya,murmushin jin dadi kawai tayo ganin yadda kowa cikin 'yan uwanta ke qoqarin nuna mata qauna da kulawa.        "Hala nan gaba kadan zamu kasa ganeki sumayya,irin wannan kumatu haka" sosai ya bata dariya,bama ita kadai ba duk jama'ar falon,don babu wata qiba da tayi tsabar tsokana ce,saidai duk wanda ya kalleta zauga yadda fatarta ta murje tayi kyau,hutu da wayewa suka sake bayyana a jikinta,sai da ya gama tsokanar tasa sannan yace "Dazun dama nake cewa ko baku zo ba cikin satin nam zaki ganni kafin ku wuce london,inaso muyi maganar kudin abdallah dake hannuna,sun fara yawa gaskiya ya kamata kuma ayi tunanin sake fadada wani kasuwancin da su" dubanshi tayi "Haba ya abbakar,kaima fa kamar uba kake gunsa,duk abinda ka yanke dai dai ne,baya ga haka ga malam ga mama ga yaya yahanasu ko su sun isa kayi shawara da su ku zartar da duk hukuncin da ya dace ko?" "Eh duk munyi magana da su kuma su suka ce aji ta bakinki,amma koma me ake ciki kan ki koma zamuyi magana,yaushe zaku koma?" "Ba zamu wuce sati daya ba" "To ba damuwa....ke taso mu tafi" ya fada yana miqewa,amina tasan da ita yake,sai ta shiga yunqurin miqewa "Dakata mata mana,yanzu fa ta gama cin abinci ko fada mata baiyi ba,koma ki zauna ki shirya a nutse" cewar mama tana hade rau,dariya ta kama sumayya,ba shakka idan da duka haka surukai suke da ba'a dinga samun baraka tsakanin surukai ba. "Idan kin gama ki kirani a waya,zan je ayimin aski" ya fada yana ficewa ta amsa da to.       Halima ce ya shiga tsokanarta kan tafiyarsu london "Yaya sumayya dama nice,ki barmim don Allah" haka ta dinga fada,murmushi kawai tayi tana kallonsu,abinda basu sani ba ita din ce ke jin dama ita ce su,basu taba fuskantar wata matsala ba,ko yaushe suna tare da mamarsu da babansu,suna cikin garinsu,basu da wata damuwa da ke hanasu bacci ko ta sanyasu a halin tunani,tana ganin quruciya ce kadai ke sasu sha'awar zamowa ita.         Sai takwas na dare amina suka tafi da ya abubakar,zuwa lokacin itama bashin baci da gajiyar hanya sunyo mata kabbara,tilas ta musu sallama ta dauki abdallah da yayi bacci kan kafadarta suka nufi daki.   *******   *******   *******      Washe gari kusan tare sukayi aikin gidan ita da mama,kasancewar qarfe shida da rabi su halima na fita makaranta sai goma na safen suke dawowa a irin wadan nan ranakun,a yanzu haka ma shirin tafiya musabaqa suke wanda suna daya daga cikin wadanda aka zaba,sunayi suna hira irin ta tsakanin da da uwa,zuciyoyinsu fes,sumayya na jin gata ga mamanta kamar kar ta sake tafiya,yayin da maman ke farincikin sauyawar diyar tata,tara da rabi suka kammala har karin kumallo,wanka sumayyan ta shiga tayi sannan ta shirya cikin atamfarta super wadda tayi mata kyau ainun,ta dan taba kwalliya kadan sannan ta sanya hijabinta ta nufi dakin malam.      Karyawa take sanda ya shiga,ta gaidashi ya amsa mata yana fara'a "Mutanen abuja yau anyi kwanan kano" kanta tai sunkuyar tana dariya "Ai malam,duk wanda ya bar gida gida ya barshi" tace tana wasa da yatsunta "Wannan kuma gaskiya ne" labari take bashi kadan kadan game da abinda ta fahima kan rayuwar garin har mama ta cimmasu a haka "Qarfe sha daya ne daurin auren fa malam" maman ta tuna masa,a gogo ya duba sannan ya miqe "Au,au,ai kuwa na manta,gashi sha daya saura kwata,hira ta dauken hankali,idan na dawo ma qarasa ko?"dariya tayi." To,a dawo lafiya" "Allah yasa".       Falon mama ta koma don ta karya itama,tana tsaka da hada tea abdallah ya tashi,dole ta bar karyawar ta yi masa wanka ta karbi kayansa wajen mama ta sanya masa "masha Allah"ta fada tana dubansa tana murmushi ganin yadda yayi kyau,shima sai ya maimaita abinda tace din,dariya ya bata dai dai sanda mama ta shigo bayan ta sallami malam "gaskiya mama bakin yaron nan ya kuma budewa" "Ba dole ba,yaron dake zuwa makaranta me zai hana bakinsa budewa", su halima ne suka shigo hakan ya sanya ya qyaleta yayi wajensu can yana buga musu rigima,gefe ta koma ta soma karyawa tana jinsu tana dariya cikin ranta.         Sallamar abdur rahman data jiyo ita ta sanya ta kusa qwarewa,da sauri ta dauki ruwa ta sha,tare da janyo mayafi ta yafa kafin a amsa iso,yana sallama cikin falon ta soma tattare kayan breakfast din ba tare data kammala karyawa ba ta maida kitchen,tunda ya shigo idanuwansa na kanta,don bai tsammaci tazo garin ba,bayan sun gama gaisawa da mama ta miqe ta fice,su halima ma suka gaidashi sannan suka fice don sauya unifoarm da kama aikin abincin rana na gidan.        Idanu ya zuba mata har sai da taji nauyinsa ta kau da kai "kin kyauta qwarai,tunda har baki iya gayamin cewa zaki zo kano,matsayin yaya ma da nake tunani an bani ashe ba haka abun yake ba na bar murna" murmushi ta saki tana kada kai "Ba haka bane,afuwa,suprise naso baka" "Da shi dai kike so ki fake,amma inda hakanne ai da a yau da safe zaki kirani ki gayan,ko kuma tun a jiyan ki sanarmin kina zuwa kano ko?" "To nayi laifi babban yaya ayi haquri" ta fadi cikin raha,numfashi ya dan dauke kadan,kwata kwata baison sunan,wannan sunan bai masa ba,so yake yaji ta kirashi da wani suna dake qunshe ko yake nuni da zallar qauna,kai ya gyada kawai yana murmushi,sabida ya lura idan baiyi wasa ba wankin hula na neman kaishi dare "Ina abdallah?" Sai ta dan ware idonta kamar tana nemansa "Yanzun na masa wanka na bashi abinci,ina zaton ya fita"nashi idanun shima ya waro " kan me zaki dinga barmin yaro yana fita waje?"dariya ta danyi "To duka ma yaushe na dawo garin ni?,abdallah ya riga ya saba da fita tunda ya tashi gidan yara" halima ya kira yasa ta dauko masa abdallahn,ba dadewa ko ga dawo da shi,yayi budu budu da qasa da alama ya sha wasan qasansa ya qoshi,kicin kicin da fuska abdur rahman din yayi ya hau fada,tilas ta tashi ta sake gyarashi.        Sai da ya tabbatar ta gyarashin sannan ya miqe yana dubanta "Har zaka tafi?" Ta rigashi fadi "Eh,dama ai zuwan ba naki bane,tunda ba'a gayan zuwan ba,amma zan dawo ko zuwa gobe,idan ba gobe ba jibi,akwai muhimmiyar magana da nake so mu tattauna" shiru ta danyi "Allah ya nuna mana,ka gaida bahijja da hajiya don Allah"hararar wasa yayi mata "bazan gaya mata ba,maruqar ba zaki je ki gaidata ba,ko kara ma sumayya fa baki da ita"dariya tayi a kunyace,ita kanta tasan bata kyauta ba "Kayi haquri in sha Allah bazan koma ba sai naje na gaida hajiya" kafada ya daga yana fadin "Da dai yafi" sallama ya musu ya danqawa abdallah kayan qwalama kamar yadda ya saba sannan ya wuce.        Kwanakin ta a kano jinta take kamar wata sabuwar duniya,wuni suke hira,hakama anty dije idan ba wani gu zata ba tana gun mama,ranar da abdur rahman yace zaizo har yammaci taji shiru,hakan ya sanya ta shirya don zuwa tsohuwar unguwarsu kamar yadda tayi alqawari,halima da zainab ne 'yan rakiya,sai laila wadda a gidan ta kwana,sumayyan tayi kyau cikin wani leshi wanda daya ne daga cikin kayan sallarta da uncle farouq ya siya mata,mayafi ta yafa bisa matsantawar halima,duk da babba ne amma tayi kyau matuqa,talkalmi da jaka komai da tayi amfani da shi ya dace da kalolin jikin lace din,sai oga abdallah shima da tayi masa kwalliya cikin qananun kaya,da rufaffen takalmi irin na maza.       Tana tsakar gida suna sallama da mama suka ji sallamarsa a soro kamar yadda ya saba bai shigowa har sai an masa izini,maganar da suke da mama ta katse tana duban soron,sai da maman ta sanya hijabin sannan aka masa iso,tunda ya shigo idanuwansa na kanta,tayi masa kyau fiye da duk lokutan da ya saba ganinta,yai yayi kamar yayi sallama da mama ya fito saidai ita tasan ba tafiya yayi ba,suna fitowa suka ganshi hakimce jikin mota,shi din ma yayi kyau cikin wani yadi mai taushi ruwan qwaiduwar qwai,gaban motar kawai ya bude mata tare da cewa "Bismillah" kai ta rausaya ganin yadda ya tsareta da idanu kawai ta shige,su laila suka shiga baya sannan ya shiga ya tada motar.         Sai da suka fice daga layin sannan yace "Ina zuwa ranki ya dade?" Kanta ya sake rausayarwa tana murmushin sunan da ya laqaba mata "Tsohuwar unguwar da muka zauna ni da ya mukhtar" wani kishi ne ya soki zuciyarsa,amma sai ya danne ba tare da ya nuna ba,kamar ta fahimci mekw tsinkulinshi sai tace "Zanje mu gaisa da yara da iyayensu da muka zauna tare" "Hakan nada kyau" ya bata amsa,da fari motar tayi shiru,sai daga bisani abdur rahman din ya sako hira,kadan kadan suke tabawa har suka isa unguwar.       Unguwar na nan kamar yadda ta santa,saidai tsohon gidansu da suka zauna wanda mutanen da suka siyeshi suka masa kwaskwarima,gidan maman naana suka fara shiga,taso ta kasa gane sumayya sai da naana ta fito daga daki,da gudu ta nufi sumayyan tana ihun kiran sunanta,rungumeta tayi tana dariya itama tana kiran sunanta,daga nan maman naanan tayi mata iso zuwa falo "Wallahi sam fuskarki taso bacemin sumayya saboda canzawar da kika yi,kin sake zama babbar mace?" Maman naanan ta sake fada cikin mamaki,murmushi kawai sumayya tayi sannan suka fara gaisawa,naana na gefe bakinta yaqi rufuwa,tashi tayi taje ta siyo wa sumayyan pure water mai sanyi da lemo,dubanta sumayyan tayi tana murmushi,ba zata manta ba wannan na daya daga cikin rainon da ta yiwa yaran na girmama baqo,ashe har yau basu manta ba,ita kanta nanan ta girma ta sauya,nan sumayyan ta dinga tsokanarta na ganin girman da tayi.       Kafin ta bar gidan sai ga yaran na shigowa daya bayan daya,da alama nana ke shiga gida gida tana gaya musu zuwanta,dui wadda ta shigo rungume sumayyan take cikin jin dadi,itama mamakin girman yaran take,kusan awa daya da wani abu tayi a gidan sannan ta dinga shiga gida gida yaran na rakata,kowa mamakin sauyawarta yake inda ita kuma sam bata ganin sauyawar da tayi,duk gidan data shiga sai ta ajjiye musu dubu daya,cikin kudin da ya abbakar ya bata jiya a ribarta na kudinta da ake juya mata,sunyi murna kuwa sosai,sai magariba sannan suka bar unguwar duka abdur rahman na cikin mota yana jiransu.         Sai wajen isha'i suka koma gida,don daga qofar gida da ya ajjiye motar masallaci ya tafi sallar isha'i,sai da ya dawo yayi kiranta a waya kan ta fito ya dawo,sanda ya kira din fitowarta kenan daga wanka,don ranar ta gaji da wuri take sonyin bacci.         A sitting room dinsu ta sameshi wanda halima ta bude masa ta masa masauki a can,kamar kuwa tasan sumayyan bata son komawa cikin motar,kallonta yake sake yi,komai ta sanya kyau yake mata,rigar data sanya ba wata ta azo a gani bace amma ta mata kyau duk da hijabi ne a jikinta saidai qarami ne.        "Sumayya,zuwa yanzu na gaji da zaman kare a karofi da nakeyi,lokaci yayi da zamu fukancu gaskiya baki dayanmu,ni na sani cewa bazai yiwu naci gaba da biye miki a yadda kike so ba,kamar yadda kema kika sani cewa indai da rai da lafiya malam bazai taba barinki babu aure ba" abdur rahman yayi shiru yana maida numfashi tare da nazartar yanayin da sumayyan ta shiga sannan ya dora "Ko baki so sumayya dole a ce mukhtar ya koma ga Allah,kin sani na sani haka ma duniya ta shaida,don wani wanda kake so ya rasu ba shine zaisa kace kai kuma ka bar yim taka rayuwar ba,yin hakan dai dai yake da gayawa Allah bai maka dai dai ba kenan,tunda ya dauke wanda yaga dama ne ya kuma bar wanda yaga dama babu wanda ya isa ya tilastashi,gata daya zaki masa shi da yaronshi ki killata kanki a gidan aure,ki bani dama sumayya na cike miki gurbin farincikin da kika rasa" "Sumayya!" Ya kira sunanta cikin kaurara murya "Inason yau ki gayamin matsayina,mu bar wannan zaman qaryar,zaki iya aure na ki zauna da ni?" Shiru tayi maganganun abdur rahman na ratsata,babu shakka gaskiya ya fada mata,wanda shine ya fara gaya mata karo na farko tun bayan rashin mukhtar idan ka dauke malam da mama "Idan har kin yarda ki barni na yiwa malam magana,tunda a yanzu yana tunanin na janye tunda har kin sake wani auren,ya taba gayan hakan cikin wasa,saidai ni sam cikin zuciyata ba haka bane,har yau sumayya sumayya ce bata sauya ba a idanuwa na" Shiru ya sake yi don ya bata damar fadin ra'ayinta da abinda ke zuciyarta. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [23/02, 11:51] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 6⃣3⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *MANZAN ALLAH S A W YANA CEWA,KUJI TSORON WUTA KODA DA TSAGIN DABINO NE* _____________________________________       "Ka yimin afuwa,a yanzu haka tafiya zanyi ta shekara daya,ka barni har na dawo don Allah,na sani cewa ka cika mutum,kuma ka nunan dukkan wata qauna da halacci,amma ina son ka barni har zuwa sanda zan dawo daga wannan tafiyar,wala'alla zuwa sannan zuciyata ta sake sanyaya daga rashin da nayi,ka sani abdur rahman yadda mutuwa ke da ciwo da wuyar barin zuciya,kayi haquri da ni don Allah" ta qarashe maganar muryarta na rawa idanuwanta na tara hawaye,tausayinta ya kamashi,ya sani cewa raba zuciyar sumayya da mukhtar ba qaramin abu bane,a kanshi ta fara sanin so da qauna,a kansa ta fara sabawa da wani namiji baare,ta soma iya magana da d'a namiji,tilas yaci gaba da haquri kafin ya cimma burinsa,zaici gaba da addu'ar samun zabi mafi alkhairi,kafin lokacin dawowarta ya tabbatar shima duk wasu burikansa sun gama cika,ya kammale hankalinsa guri guda,dubanta yayi cikin sigar lallashi "Na sani cewa shekara daya ba kwana daya bace,amma gurin Allah ba komai bace,Allah ya nuna mana,amma kema sai kinyi yaqi da zuciyarki,sannan kada ki bawa wani dama bayan ni,kinyi alqawari?" Murmushi tayi saboda maganar ta bata dariya,to shi dinma tanqwara zuciyarta take qoqarin yi ina ga ace ta bawa wani dama,ko ya mance zuciyarta ba lafiyayya bace? "Baka da wannan damuwar" ta fadi tana kada kai,maganar tayi masa dadi sai yayi murmushi ya soma janta da hira,bai tafi ba sai da ya rage mata damuwa sannan sukayi sallama.        A daren kasa bacci tayi baki daya,juyi ta dinga yi daga farkon gado zuwa qarshensa,tunani fal zuciyarta,zuciyarta sam babu dadi,rayuwa kenan,yau zaqi gobe madaci,abinda ya dinga yi mata kai kawo kenan har bacci barawo ya dauketa.        Kwanakinsu a kano sunyi mata dadi qwarai,ana ta gabatar da hawayan sallah irin na al'ada don ma saura suka tarar,garin cike yake da baqi cikin kowanne sassa na duniya masu zuwa kano daga qasashe daban daban,kama daga qasashen turawa har na larabawa don ganin hawan sallahr garin kano,wanda babu irinshi kaf arewa saidai a kwaikwayeshi,ta yadda tabbas kano nan ake morewa bikin sallah ba kamar sauran garuruwa ba da basusan ana yiba ma,tayi hira da mama malam da qannenta iya son ranta,abin dadin uncle farouq ya qara musu kwanakim yace su cikashe kwana goma,randa suka cika sati suka soma zaga 'yan uwa da qawayen anty dije suna musu sallama,kusan ko ina da sumayyan aka je don itama ta yiwa dangi sallama,kwana biyu suka kammala ya rage musu kwana biyu su koma abuja don fara shirin tafiya uk london.      Washegarin ranar da zasu tafim bayan ta gama hada kayanta baki daya ta shirya tsaf ta shirya abdallah,ta riga data yiwa driver magana zata unguwa,gidan yaya yahaa take son zuwa don yi mata sallama,anty dije tace zaya zo ya kaita,qarfe sha biyu na rana ya iso,ta yiwa mama sallama ta dauki abdallah suka tafi.        Daga falo suke amsa sallamar tata,yaya yahanasun ce kawai ta dauki murya,jamila fatima da fiddausi nr zaune duka a falon,gefe kwanon koko ke da kofuna da alama shi suka gama sha,baki daya fiddausin ta fige ta fita kamanninta tayi baqi kamar ba ita ba,yaranta uku a yanzu (banda yaran data haifa wanda sumayya taje sunansa)har yau tana gida babu wani ci gaba,uwar miji tace ba zasu iya ba ta cika haihuwa,danta ba qarfi gareshi ba,sai su fatima da rashin aure kan lokaci yasa suka soma tsotsewa,jamilan ta qwallafa rai kan wanda takeso shi kuma yayarsa ta hana tace auren gida zaiyi,fatima ma kuwa babu maganar kowa,baki dayansu anty dijen ke riqe da su,abun akwai tausayi,mataimakin madogarar dama qwaya daya ne MUKHTAR,a yanzu da babu shi kuwa babu wani mai dubansu,dukkaninsu washe bakin ganinta suke itama tana amsa musu fuska sake har tayi matsugunni kan daya daga cikin kujerun,tuni abdallah yayi wajen yaya yahanasu,ta rungumeshi tana shafa kansa tare da duban fuskarsa,qwalla ta cika mata idanuwanta har ta soma gangarowa,duk sanda taga yaron mukhtar yake tuna mata,kamanninsu daya,tana jin kanta a mai laifi,a wadda tayi silar maida shi maraya,kullum kwanan duniya sai ta yiwa zainab Allah ya isa.       Baki dayansu jikinsu yayi sanyi ganin yadda yayan ke share hawaye,tuni itama sumayya ta fara goge tata qwallar,tsawon mintuna kafin su bawa zukatansu haquri sannan suka shiga gaisawa,baki dayansu kunyar sumayyan sukeji,ga wani girma da suke bata na daban,ranar anan ta wuni,har la'asar,sai ina kasa ina ka ajjiye suke da ita,sai da tayi sallar la'asar sannan tayi sallama da su bayan ta ajjiye ma yaya yahanasun sabulai klien da su maggi cikin leda mai layi layi,sannan ta baiwa fatima da jamila dari biyar biyar,fiddausi dubu daya duk cikin irin kudadenta.        Hakanan ta tsinci kanta bayan fitowarta da yiwa mai a daidaita sahun data tsaida kwatancan gidanta,ma'ana gidan qarshe da suka zauna da mukhtar,wanda tun wajen raba gado ya shigo cikin kasan su,daidai madaidaicin get din gidan ya ajjiyeta,ta sallameshi ta dauki abdallab,jakarta ta laluba cikin sa'a muqullan na ciki ta sanya ta bude fa shiga.       A hankali ta dinga takawa tana duban gidan,duk taku guda na dawo mata ne da duk wata rayuwa tata da ta shude can baya,sannu a hankali zuciya da gangar jikinta suka raunana,ta dinga takawa a sannu har ta kai ainihin falonsu,duk kayanta na jere ma ciki babu abinda ta fitar,saidai gidan yayi qura sosai saboda rashin kasancewar kowa a ciki,shimfide abdallah tayi saman kujera wanda ya soma bacci tun cikin adaidaita,idanuwanta suka wurga zuwa qofar da zata sadaka da bangaren mukhtar,sai ta miqe tana duban qofar harta sada kanta da ainihin dakin gadonshi,babu komai ciki kamar yadda mamallakin gun bai duniya,sai ta gaza riqe hawayenta suka fara sintiri kan kumatunta,gefe guda ta duqe tana bin bango saboda rawar da jikinta keyi ta rushe da kuka mai tsuma rai da zuciya,ta jima tana kokawa sannu a hankali har nauyin dake cikin zuciyarta ya soma raguwa,ta share qwallar tata ba don ta qare ba ta juyo da niyyar miqewa,abdallah ta gani tsaye bayanta yana kallonta "Wa ya saki kuka ammi?"hannu ta miqa masa alamar ya taho,ya taho din kuwa ya fada jikinta ta rungumeshi tana ci gaba da goge hawaye.        Sai data samu nutsuwa cikin ranta sannan ta qarasa zagaye gudan,duk inda ta taka da abinda zau tuna mata,a haka ta kai har biyar da rabi sannan ta lalubo abdallah dake can wani gu yana wasansa ta sauya masa kaya ta rufe gidan suka fito idanu jajur na kukan da ta sha.        Washegari suka kama hanyar abuja,hankalinta yasi dagawa na barin abdallah da zata sakeyi,bata so yayi maraici irin na mahaifinshi,babu uwa babu uba,saidai ganin yadda sam bai damu ba shi ya kwantar da hankalinta,da fari ya soma maqale maqale amma daga bisani sai ya ware har da shi a masu daga mata hannu,ajiyar zuciya ta saki bayan sun hau hanya sosai ta maida idanuwanta ta rufe,sam bata son komawa abujan nan,tafi qaunar garinta kano,koba komai kowa nata yana can,da zata iya data roqi su anty dijen su barta a can din,saidai yin hakan tamkar butulci ne ga qaunar da anty dijen ke nuna mata fiye da dukkan wata 'ya dage cikin danginsu,duk da 'yan maganganu da ke fara tsowa na hassadar riqon nata da antyn keyi.        Kasancewar basu taso da wuri ba shi yasa basu suka isa gida ba sai takwas na dare,a gajiye kowa yake,saboda haka kowa gun kwanciya ya nema idanuwa cike da bacci,dama tuni sunci abincin darensu kan hanya.        Washe gari da gyaran gidan suka tashi,suka kintsa ko ina,kafin wani lokaci gidan ya dawo hayyacinsa,basuyi dai break da wuri ba saboda aiki.         Zuwa la'asar har abincin dare sun gama,su khalipha na dakinsu suna gayaran kayayyakinsu tare da fara ware wanda zasuyu tafiya da shi,sumayya na zaune falon tana hutawa,hannunta riqe da waya tana neman lambar mama don su gaisa ta kuma ji ya abdallah yake,sallamar amira ita ta katse mata abinda take shirin yi din,ta shigo sanye da yadin sartin baqi sidik wanda aka yiwa doguwar riga,sai dan madaidaicin jan mayafin data yane kanta da shi,cikin fara'a sumayyan ke dubanta har ta qaraso ta samu wajen zama "Mutanen kano ta dabo,sauka ba sanarwa?" "Kada ki qorafi,saukar dare ce,har yanzun kuma bamu gama watstsakewa ba,sai dazun muka gama saita gidan" "Gaskiya kam,ko mu muna nan muna hutu,baqi sun tafi sun barmu da kewa,gidan ba kowa duka ba dadi,kowa ya koma inda ya fito,dadin abun daya nima next week zamu koma school" murmushi kawai tayi,suna hutawa tamkar sunyi hidima da baqin,bayan komai akwai masu aiki dake gudanarwa "Gaskiya kam ansha baqi,saidai Allah ya bada lada" "Amin" amira ta fada tana lalubo wata number cikin wayarta qirar iphone 7 "Ki duba dakina can wajen bedside drower akwai black bag ki kawomin gidan umman khalipha" abinda tace kenan cikin salo na bada umarni ta kashe wayar,sumayya ta ajjiye lemo da ruwa gaban amiran tana tambayar maman husna,murmushi tayi tana daukar gorar ruwa "Husna mutuniyarki,sun koma inda suka fito" idanuwa sumayyan ta dan fiddo "Suma ba nan suke ba?" "Eh,mijin anty farida custume ne,basu zama gu daya,yau suna can gobe suna nan,amma lokaci lokaci suna zuwa hutu da kuma lokacin bikin sallah kamar haka" kai ta jinjina "Allah ya taimaka" "Amin"hira suke tabawa kadan kadan har ta shigo bakinta dauke da sallama.      Sumayyan ta ganeta tare hadimar amiran ce,tare suke shigowa,isa da qasaitar gidan baabaa prof kusan kowa dame masa aikinshi shi daya,gaida sumayya tayi saidai ta kasa amsawa ta maida mata gaisuwar suka gaida juna,kusan zata dan girme musu saidai ita din yare ce,sannan ta rusuna cikin girmamawa ta miqawa amira jakar mai kyau,amsa tayi sannan tace "zaki iya tafiya,idan ummee ta tambaya kice ina gidan umman khalipha" "To madam" ta amsa ta fice,miqawa sumayya jakar tayi tana fadin "Ga tsarabarki ta saudiyya,babu yawa a karba da haquri" murmishi ta saki tasa hannu ta karba tana godiya tare da fadin "Mai yawan kenan" tana fidda kayan ciki,turaruka ne designers masu kyau guda uku,agogo cikin dan akwakunsa,sai hijabai saqar qasar oman suma guda uku masu azabar kyau,sun burge sumayya qwarai har sai data fidda murmushi saman lebanta "Naga kina sonshi ne sosai" "Naji kuwa dadin kyautarsa fiye da komai cikin kayan nan" "Ina fata kin yaba" "Qwarai da gaske" suka sa dariya baki daya,a nan anty dije ta fito,gaisawa sukayi sumayya ta nuna mata kayan ta gani ta tayata godiya. Wayar amiran ce ta dauki qara,dagawa tayi tana dubawa,idanu ta zaro,a fili ba tare da tasan ta fadi ba "Na shiga uku ya man yau kuma?" Da hanzari ta daga kiran ta kara kunnenta "Ok,to yaya" ta fada tana miqewa "Amiran umman khalipha na wuce,ya man ya aikeni na kaiwa umme waya kada ya qara kira ban je ba,ya kira wayarta taqi shiga haka land line din part dinta" "Ok,muje na taka miki" sumayya ta fada tana miqewa "Na gode" ta fada tana murmushi,don haka nan Allah yasa mata qaunar sumayya,burgeta take sosai. Jerawa sukayi suka fito,suna gab da kaiwa qofa amira tace "Uhmmm,ko ki tambayi ma mutuminki ko?" "Ayyah,ya mahmoud,ki gaidashi don Allah nayi laifi kam" "Um um,ni ba ma shi nake nufi ba,ya mustapha mana" shiru ta danyi gabanta na duka tunda ta ambaci sunam nashi,da ido amiran ke karantarta ganin bata ce komai ba har tana shirin fita ya sanya ta bar zancan ta soko wani "Yaushe zaki shigo gaida baabaa,yana ta maganan baiga mamanshi ba" dan qaramin murmushi ta saki,sai taji tayi kewar tsohon duk da ba sabawa sukayi ba,amma saidai ko kadan bata sha'awa ko marmarin sake shiga gidan,tun daga randa abun ya faru. "Ki gaida min baabaa da kyau don Allah,zan shigo idan Allah ya yarda" ta fada da siga biyu don bata da niyyar zuwa din "Allah yasa da gaske ne,saikin shigo din na gode" "Nike da godiya,ki gaidamin su ummee ma" "Zasuji" ta fada tana ficewa tare da jin dadin yadda sumayyan ta nuna kulawa ga ahalinta. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 6⃣4⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *haqiqa Allah yana son masu yawan tuba* ___________________________________        Cikin sati guda suka kammala duk wani shiri nasu na tafiya,ya kama ranar lahadi zasu tashi zuwa uk,hafiz ne kadai abun tausayi,don su kansu su laila sun daina dariya da tsokana sai tausayinsa,ranar asabar da daddare abbanshi da anty dije suka kaishi gidan kakarshi sannan suka dawo.         Da daren ana ya gobe zasu tafi tana zuge jakar matafiyanta wayarta ta dauki qara,bata duba ba ta dauka ta kara kunnenta,sai taji muryar lukman,murya a sanyaye  bayan sun gaisa ya soma fadin "Da gaske sumayya baki damy da ni ba baki damu da yaranki ba,kizo kano kiyi kwanaki har goma ki kasa gayan,bare kice zaki ki gaida hajiya,sumayya me muka yi miki haka?" Sai a lokacin ta tuna ma tace zata gaida hajiyan abdur rahman,baki daya ya mance,ta kuma san shima yana sane shiru kawai ya mata ya zuba mata na mujiya "Kayi haquri,babu abinda kuka yimin,tunda naje ban zauna ba munata shiga kasuwa da sallamawa 'yan uwa da dangi?" "Sallama wacce iri" dan jim tayi tana jin nauyin fada masa,saidai dole ne ya sani din yanzu "Gobe in sha Allah zamu tashi zuwa uk,sai bayan shekara daya zamu dawo" baki daya jikinsa ya saki,jijiyoyinsa suka yi laushi,idanunsa ya lumshe wadanda ke masa zugi,ya budesu da qyar muryarsa kamar wanda zai saki kuka yace "Da qyar ne idan ban rasaki ba sumayya,burinsu nuwajra na ki dawo musu bazai cika ba,na saddaqar sumayya kin subuce min" ya fadi yana kada kai tamkar yana gabanta,shuru tayi ba tare data ce komai ba,don batasan me zata ce din ba,itama sai ya kashe mata jiki baki daya,tausayin yaran ya taso mata,nannauyar ajiyar zuciya y saki "Shikenan sumayya,ina miki fatan alkhairi,Allah ya tsare ya dawo daku lafiya,saidai hakan bai nuna na miqa wuyan rasaki,bazan fidda da rai da rasakin ba sai randa naga an daura miki aure da wanu wanda nake fatan wanin ya zamanto nine" ya qarashe muryarsa na dan rawa,sabida ba zaya taba mance kulawa da kwanciyar hankali da farincikin da ya samu a aurenta ba,duk da cewa baki daya zaqin da dadin na wasu taqaitattun watanni ne,amma hakan ba zai taba barin kwanyarsa ba har ya mutu,sumayya ba irin matan da kake saurin mancewa da rayuwar da kayi da su bane,tana da wata iriyar baiwa ta musamman mai tsayawa a wuya "Na gode,a gaida yaran" "Zasuji,da fatan zan samu number dinki ta can idan kun isa ko don ku dinga gaisawa da yara" "In sha Allah" ta fada tana datse kiran,jikinta a sanyaye ta sauke wayar,tana mamakin yadda ta shiga rayuwar wasu mazaje,har suke iya bata muhimmanci mai yawa haka a rayuwarta,bayan ita din bata ga wani abu da take da shi ba wanda za'a kwadaitu wajen zama da ita,da wannan tunanin taci gaba da aikinta har ta kammala ta kwanta don ta huta.      *RANA BATA QARYA*      Dukkansu sun hallara cikin lafiyayyar zungureriyar motar data dauke kayansu baki daya,wanda baabaa prof shi ya bada ita yace a kaisu a cikinta,anty dije data shiga sallama da su ita da uncle farouq suke jira.         Harara anty dije ta aika mata da ita bayan sun fito wadda batasan ta mece ba har sai data bude baki tayi magana "Kinji dadi a ranki ko?,ai yanzu sai ki shiga ki musu sallamar tunda mai gidan da kansa ya nemeki" sosai taji kunya da har baabaa prof ya cigiyarta,bata son shiga gidan sam,haka ta sauko a hankali ta nufi gidan cikin shigar wata iriyar gown mai dogon hannu A shape,wadda anty dijen ce ta siyo musu tace ita zasu sanya,tayi rolling da dan madaidaicin mayafinta,kayan sun mata kyau matuqa,saidai baki daya jinta take a takure saboda rashin sabo,ta riga ta saba ta adana jikinta cikin hijabi.         Gabanta na faduwa ta sanya kanta zuwa sashen baabaan "Laaah ilah" taji an ambata a bayanta,da sauri ta juya,amira ce ke tsaye tana kallonta,fuskarta dauke da dariya hannunta riqe da mayafi "Ai yanzun nake sauri naje rakiya kada ku tafi ki barni,na lura sam wlh amiran umman khalipha baki damu da ni ba,nike ta taki" "Kiyi haquri don Allah kada kice haka,yimin jagora na yima baabaa sallama"bata amsa ba face gaba data soma yi wai ita taji haushi sumayyan tabi bayanta tana dariya,saidai kafin su qarasa din bakin amiran ya kasa shiru " gaskiya dole amiran umman khalipha ki dinga boye jikinki cikin hijab,dama haka kike?,wannan idan muka jera ai sai ki kashe mana kasuwa,haka kika hade?"ta fada cikin sigar wasa da mamakin irin kyawun sumayyan,wani irin kyau me tsari da ban sha'awa,dariya sosai ta baiwa sumayya har ta kai mata duka ba tare data shirya ba,itakam babu wani kyau sam data gani daga gareta,ita amiran bata kalli kanta ba,kyau hutu wayewa da kwalliya duka,ta ina zata kashe mata kasuwa,ita bama neman kasuwar take ba don haka taci kasuwarta hankali kwance,ta qarashe sauran maganar a fili,dariya sosai ta baiwa amiran "Wai kina nufin ba zaki sake aure ba?" Wani abu ne ya soki sumayya sai ta kasa amsawa,kai kawai ta kada mata ba tare da tace komai ba,ganin hakan ya sanya amiran jan bakinta tayi shiru,don dama ko can ita ba mai yawan bin qwaqwqwafi bace har suka isa sashen baban.        Yana falonshi zaune kan kujerunsa na alfarma,idanunsa saye da gilashi yana kallon tashar VOA,gefansa jarida ce,daya barin kuma damammiyar furarsa ce da umme ta gama dama masa yanzun nan,don ko falon bata kai ga ficewa ba.        Cike da kunya girmamawa da mutun tawa ta isa gabanshi kanta a qaaa,kwarjini dattijon yake mata kamar malam dinta,cikin ban girma ta gaidashi sannan ta gaida ummee dake zaune gefansa,ta amsa itama fuska sake,hakanan take jin nauyin mutanen,duk da baki dayansu baifi gani biyu zuwa uku tayi musu ba "Da tafiya zaki mama na bakimin sallama ba?,haba,shekara daya ba nan kusa bace bafa?,kika sani ko kafin ki dawo ta Allah ta kasance a kanmu" sai taji ba dadi,ita din saurin karayar zuciya,zuciyar tata ta karye,duk sai taji babu dadi har sai data dago ta dubeshi,ya tuna mata da mukhtar dinta yayin da mutuwa ta daukeshi a ranar da yake shirin sake angwancewa da ita,tabbas mutuwa bata da sabo,amma bata fatan hakan ta kasance kan dattijon,tana jin qaunarsa a ranta kamar malam dinta,duk sanda ta kalleshi yana tuna mata da malam din "Bama fatan haka baabaa,Allah qara muku tsawon kwana da lafiya mai amfani" "Amin amin" umme amira da baban suka amsa baki daya,amira ke turo baki tunda baban ya fadi maganar,ta kasa shiru sai data tanka "Wai baabaa fata kake ne ka mutu ka barmu,kullum sai kayi zancan mutuwa,bayan ko aurena ni auta baka gani ba,ga yaya mahmoud da usama" dariya yayi irinta dattawa sannan yace "Mama na kenan,banda abinki ita mutuwa ina ruwanta da wanu tsari naka,duk sanda tazo daukarka zata yi bafa zata fasa ba,ko babu ita akwai rabuwa,zaka rabu da mutum wanda ba lallai ka sake ganinsa,kamar yadda har yau nake burin ganin wani tsohon abokina da mukayu rayuwa a karkara tare,har yau Allah bai nufi zan ganshi ba,har yau kuma yana raina" tuni idanunta ya soma digar hawaye kanta na a qasa,baabaa yayi mata fami sosai,baima lura da ruwan hawayen nata ba,ya ciro wasu kudade irin na qasar engaland din masu kauri ya miqa mata "Ungo wannan mamana,kiyi amfani da su kinji sune tsarabata" bata son ta daga kai yaga hawayenta,sabida haka ta sanya hannu bibbiyu ta amsa tana masa godiya mai cike da fatan alkhairi sannan ta miqe ta juya ta fita,amira ce ta kalli baabaa "Baabaa,zan rakasu airphort don Allah" umme ce ta cafe zancen "Umhummm,wato zaki raka qawarki ko?,ina cewa nan su'ad tayi tayi ki rakata randa zasu tafi kika qi,sai yanzu jikinki na rawa zaki ce zaki,to ba inda zaki din" "Saurara KILISHI,Allah shike hada qauna tsakanin mutum da mutum,haka kawai Allah ya hada jininta da yarinyar,barta taje,mama na sai kun dawo,daga nan kada ki biya ko ina,ki dawo kizo kimin lissafin me kike buqata na komawa makaranta kinji" cikin murna kamar qaramar yarinya tace "Yauwa baabaa na,na gode"ta juya da sauri don ta ruski su sumayya.        Cikin motar amiran ke basu labarin yadda garin yake,duk da yake akwai banbancin gari,garin data zauna su ba nan zasu zauna ba,su laila an kasa kunne ana kwashewa,murna da doki sun cikata burinta kawai su isa.        Cikin qanqanin lokaci suka isa filin sauka da tashin jiragen sama na Nnmdi azikwe dake garin abuja,bai wuce mintuna talatin ba lokacin tafiyarsu yayi,sabida haka uncle farouq ya sallami driver din wanda ya tilasta amira yiwa sumayya sallama saboda tare zasu koma,duj fuskarta ta nuna rashin jin dadin tafiyar tasu,kai kace sunyi mugun sabo da juna " nikam irin wannan qauna haka da amira ke gwada miki,bata da saurin sabi da sakin jiki wa mutane fa,amma ke naga ta sake miki"murmushi sumayya tayi kawai tana miqawa anty dije kudaden da baaban ya bata,kanta qulle tamau da mamakin wanne irin arziqi baabaa ke dashi haka,duk da batasan kan kudaden waje ba amma tana jin labarin darajarsu fiye da namu na naija,kuma yanzu haka wadanda ke hannunta ba daya biyu uku biyar bane,sunfi haka,ido itama ta zaro "Wa ya miki kyautar wadan nan kudin?" "Baabaa ne" "Kai baabaa,baabaa,alkhairinsa yawa gareshi,Allah ya saka masa da alkhairi" "Amin,amma anty su basujin kyauta haka" murmushi ta kuma "Haka suke,hannun kyauta garesu,suna da mutunci da karamci,yaci ace kisan ko su waye su din,amma bari mu shiga jirgi zan gaya miki su waye su" bata kai ga amsawa ba wayarta da zuci zucin ta kashe ta soma ruri,number amira ce,cikin mamaki ta daga "Ya mahmoud ne zai magana da ke" ta fada tana hadata da shi "Babu fada me ya kawo gaba gimbiyarmu,yanzu fi sabilillih zaki bar naija amma ko ki sanar da abokina why?" Murmushi ta danyi "Tunda ka sani ka wakilceshi ya mahmoud,kaa gaya masa" "A'ah,wannan saqon ai na masoya ne,amma tunda kince haka zan gaya masa,ta inda kuma zaki wanke kanku guna indai ni yayanne ki bada num dinki idan kun isa na bashi" dariya ma ya bata,saidai yana da qima idanuwanta,shine mutum na farko da ya fara tararta cikin fara'a da girmamawa sanda ta tsoma qafarta gidan baabaa prof "Babu matsala" "To ina godiya,inawa umman khalipha fatan alkhairi ki sanar mata" ya datse layin,tana shirin maida wayar jaka saqon fatan alkahiri daga abdur rahman ya shigo mata,ta karanta a gurguje ta mayar masa da reply.        Idanu sumayyan ta shiga bazawa bayan tsintar kanta da tayi cikin jirgi ya soma dagawa da ita zuwa sararin subhana,bata samu nutsuwa ba sai bayan shudewar wasu lukatai sannan,anty dije ce a damanta "Bari na cika alqawa ko,na gaya miki tarihin gidan baabaa prof" "To anty ina jinki"   *IYALAN GIDAN BAABAA*      BAABA prof ba shine asalin sunanshi ba,suna ne da ya samu ta dalilin zuzzurfan ilimin boko da yayi har ya kaishi ga zama professor,cikakken sunansa shine MUKHTAR MUHAMMAD ADAM GWAMBE,haiffen wani qauye da ke cikin pantami,mahaifinsa Adamu wanda aka fi sani da mai dabba,wanda ya ci sunan nashi ne sabida yadda Allah dora masa so da iya kiwon dabbobi tun yana qanqaninsa,ga tausayi ga dabbobi,bama dabbobi kadai ba hatta da mutane,ana amfana qwarai da tarin dukiyar da Allah ya huwace masa,wajen taimako ga mabuqata,bafulatani ne gaba da baya,ma'abocin iya kiwo,wanda kuma Allah ya albarkaceshi da tarin dabbobi,kama daga tumakai awakai raguna tinkiyoyi da shanu bila addin,wand kaf qauyensu da kewayenshi babu wanda ya kaishi yawan garke,matarshi daya khadijatu,ita ta haifa masa muhammadu da yayyensa guda biyu,dukkaninsu suna ganiyar samartaka suka rasu sai muhammadun kadai da Allah ya bar masa,yaro ne da yafi shiga ransa duk cikin yaranshi,ya debo kyawawan halayensu tsaf har da ma qari,sannu a hankali muhammadu ya girma aka hadashi aure da wata yarinyar wani malami maqocinsu mai suna naja'atu,cikin watanni tara kacal Allah ya albarkaceta ta haifi MUKHTAR baabaa prof,wanda ba'a jima da haihuwarsa ba Allah ya yiwa mai dabba rasuwa,ya rasu ya bar matarshi,bayan share makoki aka raba gado aka baiwa khadija matarsa da dansa muhammadun,ya karbi dukiyar mahaifinsa kuwa a sa'a don habaka tayi tayi,abu ya dinga dad gaba,saidai daga baya ya fuskanci kamar kiwon wahala ce kawai,ya saida shanun ya rage wasu daga ciki ya barwa mukhtar kyauta halak malak,yace shima ya taba aikin gado,dama can shi mai son kiwo ne,tare suke fita da shaqiqin abokinsa wanda tun yana da shekara daya a duniya baida aboki sama da SULAIMAN sule,babu abinda ke rabashi da sule,hatta bacci ma wani sa'i tare suke,musamman idan matar babanshi taso tsiyar tata,tausayinsa yake,qaunarsa yaje fusabilillah,mahaifiyarsa ta raau tun randa ta haifeshi ko waiwayowa batayi taga abinda ta haifa din bata yi ba,sai suka qulle sosai,muntari baida qani balle ya debe masa kewa,haka sule ma baida dan uwa sai hashimu,shi kuwa bai isa ya rabeshi ba don tuni altine ta shiga tsakaninsu ta raba zumuncin Allah qarfi da yaji,duk da hashimun na qaunar dan uwansa,tare suka dinga fita kiwo shi da sule,yayin da babansa muhammadu kuma ya soma saida zannuwa a cikin garin gwambe,dukkaninsu Allah ya sanya musu albarka baki dayansu,har mamakin yadda dabbobin muntarin keta habaka babansa muhammadu keyi,shida sule kiwo suke haiqan,duk da babu dabbar sulen ko daya a ciki amma sabida qaunar dake tsakaninsu wani lokaci a shike fitar ma muntarin da su,altine tayi dukan,tayi dukan don ta raba tsakninsu saboda yadda taga suke na samun kulawa a gidansu muntarin amma a banza wai man kare,saboda tare malam muhammadu ke musu komai,bai rasa ci ko sha ba balle sutura,ba'a rabasu a gidan sule dai dai yake da muntaru,data gama dukan zata kuma gansu tare,abun ya tsaya mata a rai,sai ta koma ziga gun babansa,to shi din ma baici nasarar rabasu din ba,saboda yadda qauyen aka soma zaginsa shi da matarsa kan yadda suka qwallafawa dan marayan Allahn. Cikin haka turawa suka shigo qauyen nasu,suka kawo musu makarantar boko har cikin garin nasu,kowa ya tsame dansa yace babu shi a wannan batu,muntari na bala'in sha'awar karatun,ya samu babansa ya sanar masa kan ya sanyasu shi da sule,da fari shima yace sam kada muntarin ya sake wannan magana,bayan dogon nazari da malam muhammadun yayi sai ya amince,ya hadasu da sule ya kaisu amma yace saidai suyi jeka ka dawo(day),altine zani a hannu ta shaidawa mahaifin sule abinda malam mahammadu yayi,ai kuwa ya wanke qafa yaje har gida ya ciwa malam mahammadu mutunci,a lokacin sule na gidan tare da muntari,kuka ya dinga yi yana jan baban nasa kan ya daina zaginsa amma ya mangareshi ya qara gaba,tilas malam ya lallashi sule kan yayi haquri tunda babansa baya so,haka ya haqura ba don rai naso ba,ya ci gaba da fitar da shanun muntari kafin ya dawo daga makaranta sai ya taddashi a jeji suci gaba da kiwon tare da yammaci su dawo gida,malam muhammadu yace ya ya daina,ya bari idan muntarin ya dawo sa fita tare su dawo tare,amma sam yace a'a,ai shi da muntarin duka daya ne,duka a lokacin basu wuce shekara goma sha uku uku ba. A haka shanun muntari suka sake yawa,ga cikakkiyar lafiya dake garesu,ganin haka ya sanya muntari ya shawarta da malam muhammadu zai raba dabbobin biyu ya baiwa sule rabi,saboda wahalar da yake da su ko shi sai haka,ba musu dukka suka amince har da mahaifiyarsa,randa ya sanar da sule cewa yayi bazai karba,shi don Allah don qauna da amincin dake tsakaninsu yake masa,tilas daga qarshe malam muhammadu ya tilas ta shi ya karba,godiya ya dinga musu harda hawaye,din suna da yawa baiyi tsammanin mallakar wani abun duniya kwatankwacin haka ba. Randa yaje da maganar gida da yammaci ne,altine kasa bacci tayi sai data dangana da bokanta,kafin wayewar gari ya yiwa sule kurciya,kurciyar data kawo rabuwarsa da muntarinsa,rabuwar da har yau fuskokinsu basu qara ganawa ba,duk da yadda muntarin keta nemansa ko ina loko da saqo na garinsu saidai babu labarinsa,tun da quruciya yake nemansa har girmansa,har yau yana kewar dan uwansa kuma amini shaqiqinsa sule saidai har yanzu Allah baisa an dace ba. Muntari yayi kuka yayi kuka har wasu ma suka tayashi kokawa,da qyar aka samo kansa,amma shima daina kiwon yayi ya haqura ya kama karatunsa gadan gadan,bayan rasuwar khadijatu mahaifiyar malam mamman kaka ga mukhtari baabaa prof,garin ya daina musu dadi baki dayansj,sai ya tattara ya koma cikin ainihin garin gombe inda dama kasuwancinsa ya riga yayi qarfi qwarai a can,ya saida dabbobin muntari saidai muntarin yaqi a saida wanda ya baiwa sule,ya samu fili daya na babansa ya zubasu ya maidashi kamar dan qaramin gidan gona yaci gaba da kiwata masa su,yayi alqawarin duk randa Allah ya sake hada fuskokinsu matuqar yana raye saiya cika wannan alqawari. A kasuwa mahammadu ya zuba kudin muntarin,suka ci gaba da juyawa tare,gefe guda kuma ga karatunsa bai fasa ba,kafin wani lokaci muntarin ya zama dan birni sosai,ya goge,ilimi ya ratsashi,ya zama saurayi wamda har ya kammala secondry dinsa ya soma jami'a. Kyau tsantsa irin na usilin fulani Allah ya baiwa mukhtar shi,tsantsar farin jini kamun kai kamala da kwarjini wanda shi ya janyo masa tarin masoya maza da mata,yana faran faran da son jama'a,'yammata kuwa ba'a cewa komai,duk da 'yamata ne irin na da,masu tsananin kunya da kamun kai,da wuya kaji tace tana sonka,saidai ka gani a ayyukanta,a hakan ma ana ganin kansu ya bude suna jami'a,a jami'ar ma babu yawan matan,sabida har lokacin jama'a basu karbi karatun boko ba sam sai daidaiku. Zuwa lokaci dukiyarsu ta sake ninkuwa,irin dukiyar da a lokacin tsoro ma kake asan kana da ita saboda yawanta da rashin hanyoyin boyeta da sarrafata kamar a wannan zamanin,tuni malam muhammadu ya tashi daga malam ya koma alhaji,ya tamfatsa gida irin na masu kudin da,irin gidan da a da saidai gida na sarauta,mai sarautar ma wanda ya isa,kamar sarki ko waziri,gwamna ko shugaban qasa,tun mota da babur da handset sai wane da wane mukhtar yake hawa yake riqewa,arziqi ya zauna musu na ban mamaki,gefe guda bai fasa kiwata dabbobin sule ba,wadanda sukayi albarka suka zama hamshaqin gidan gona,wanda ke fidda kaji,madarar shanu,qwai,a kuma sarrafa yoghourt wanda yayi sunan ba gombe kawai ba har a arewa a wannan lokacin,duk abinda aka saida yana tara kudin a gu na daban yana ajjiyewa sule,har lokacin bai fasa nemansa ba,bai fidda ran kuma ganinsa ba,yakan ce IDAN DA RAI DA RABO. Kaf qauyensu babu wanda baici arziqinsu ba,mutanen da suka kai maka Allah yayi yawa sa sh,tun a lokacin mai zuwa maka a jirgi sai wane da wane,hatta da mahaifin sule wanda altine ta yashe ta gudu ta barshi cikin tsananin talauci da yunwa,mkhtar ya fidda kudi cikin kudin sule ya biya masa hajji,kafin ya dawo aka buge gidan sa aka sake masa gini da ya dace da irin wancan zamanin,kuka ya dinga yi yana shiwa muntari albarka yana roqon Allah ya bayyana masa dansa,don hashimun ma ta gudu da shi baisan inda yake ba,sosai baban sulen yaci arziqinsa kafin Allah yayi masa rasuwa. Muntari baabaa prof sun hadu da matarshi ta farkoZUWAIRIYYA wadda ake kira KILISHIa makaranta,a lokacin yana karatun degreed dinsa na biyu a jami'ar bayero dake kano,diya ce sarkin rano,yarinya ce mai kamun kai,miskilanci da haquri,akwai dan jin kai tattare da ita dan kadan wanda jinin sarauta dake yawo jikinta ya haddasa hakan,saidai akwai fada da tsiwa idan ka tabota,kusan abinda ya zama silar qulluwar alaqarta da mukhtar kenan,haduwarsu wajen cin abinci dake makaranta,sukayi fada daga qarshe ya nemota ya nemi soyayyarta,ta dan garashi sannan daga bisani ta amince ta yarda da aurensa,ba wani lokaci aka dauka ba kasancewar akwai sanayya tsakanin alhj muhammadu da mahaifin kilishi,saboda shahararsa a kasuwanci,zaka samu wani lokaci akwai alaqa ko abota tsakanin masu sarauta da 'yan kasuwa. Babu bata lokaci akayi komai aka gama,alhj mahammadu ya danqarawa tilon dansa gida cikin kano da kudinsa da kansa a daura da jami'ar bayero,wanda a sannan ba unguwa bace face irin unguwannin nan marasa gidaje sabbin unguwanni,a nan suka tare cikin qauna da aminci da kula da juna,shi yana nashi karatun itama tana nata hankali kwance,da ya gama ya juya masters ita kuma data hada degree ta tsaya hakanan ta maida hankalinta kan kula da gidanta,macace data iya zaman aure,tsantsar kula da miji,iya tarairaya da nuna qauna,shekara uku da aurensu suka samu qaruwar d'a namiji,ba bata lokaci mukhtar baabaa prof ya sanya ma yaron sunan kakansa wato adam,shekara na zagayowa kilishi ta sake sambalo d'a namiji wanda C.S aka yi mata. Abinda basu taba gani ba wato alhj muhammadu yazo gidansu,da kansa wannan karon yazo ganin jariri bayan sallamarsu daga asibiti zuwa gida,tun a daren kilishi da adam ke kira ummee ta dinga dariya tana fadin lallai wannan yaro yayi goshi,sanda aljh ya daukeshi kallonshi ya dinga yi yana murmushi,yayi wata magana data sanyaya jikinsu ta kuma basu dariya "Inama rai zai bani aron lokaci da rayuwa naga girman wannan yaro,ba shakka na tabbatar akwai wani lamari tattare da shi,shi na daban ne cikin yaran da nake gani,tun a daren da aka ciroshi jikina ya bani haka" kilishi da ta maida abun wasa dariya tayi "Alhj ya akai ka sani" da yake shi wasa yake musu tamkar jikokinsa,dariyar shima yayi "Zaku ce na gaya muku,lokaci zai nuna,ba shakka shi MUSDAFA ne,zababbe ne" "Shikenan baaba,ka sanya masa suna,dama sunanka nakeso na saka wannan karon,MUHAMMAD MUSTAPHA" yaji dadi qwarai a zuciyarsa,har ya gaza boyewa,ya daga mustapha yadinga masa addu'o'i,wasu cikin kunne wasu cikin baki wasu cikin ido,addu'o'i ne wadanda ko diyan cikinsa mukhtar bai masa su ba,yana son yaron,yana jinsa har cikin zuciyarsa,sosai ya roqa masa albarkar rayuwa duniya da lahira. Mustapha bai cika wata ukuba duniya ba Allah ya yiwa alhj muhammad rasuwa,dan kasuwa mai gaskiya da amana,tausayi da taimako,kowa nashi ne,kowa cin arziqinsa yake,ba iyalansa kadai sukayi rashi ba hatta da kano da gombe baki daya,mukhtar ya dauko mahaifiyarsa ta dawo gidansa dake kano da zama,ya sake yiwa gombe nisa,abinda ya sake sakashi kenan ya rage zuwa gomve,sai yayi wata shida ko shekara baije ba,hakan ne ya sanya har sule yaje ya tafi basu hadu ba,sanda yaje aka gaya masa kamar zaiyu hauka,sai ya koma zuwa akai kai amma har ya gaji ya watsar sulen bai kuma dawowa ba,da alama har yanzu baqin abun da aka yi masa na cikin jikinsa. Nauyi sai ya sake yiwa mukhtar yawa,ga dukiyarsa ga wanda mahaifinsa ya bari aka raba musu,mahaifiyarsa ta dauki tata ta damqa masa,don bata da wani itama sama da dan nata,haka duka ya hada,ga karatu da ya kasa haquri ya bari saboda yadda yaji dadinsa,ga kasuwanci ya sakoshi gaba,bayan shekara biyar da haihuwar mustapha kilishi ta sake haihuwar 'ya mace wadda taci sunan farida,zuwa lokacin sun fara ganin abinda alhj muhammadu ya fada akan mustaphan,ba shakka shi na daban ne tsakaninsa da dan uwansa,akwai banbance babance sosai,bayan haihuwarta ba dadewa itama innar mukhtar ra rasu tabi mijinta bata cika shekara ba aka haifi mai sunanta naja'atu suna kiranta da huda,haka suka ci gaba da gudanar da rayuwarsu,ko yaushe arziqinsu bunqasa yake albarkacin taimako da suke yiwa bayin Allah da nemanta sa suka ci gaba da yi ta hanyar Allah. Mukhtar bai bar karatunsa ba sai da ya zama farfesa,a lokacinne suka hadu da ABDUS SAMAD wanda ya zame masa aboki,kusan bai qara amini tun bayan rasa sulensa da yayi sai a kan abdus samad,abdus samad na qaunar baabaa prof qwarai da gaske,a lokacin ya fara taba siyasa,ya shigeta da qafar dama,ko ince ya shigeta da gaskiya da amana,da magana daya tak idan ya fadeta,abinda yawancin 'yan siyasarmu suka rasa,ba wani abu yake nema cikinta ba sabida babu abinda ya nema ya rasa a duniya,arziqin duniya da dukiya Allah riga da ya bashi saidai ya nemi na lahira,wanda yana amfani da dukiyarsa yana nema saidai Allah ya karba masa,ba takara ya tsaya ba,amma yana supporting gwanatin dake nema sabida yadda da yayi da ingancinta da,cikin ikon Allah kuwa ta samu nasara,hakanne ya sanya aka bashi matsayin AMBASSDOR jakadan nijeria a merica,sosai abdus samad yayi farinciki,don shima iyalinsa na can,matarshi daya alokacin hajiya khaulat,abinda ya zaunar da ita can acan abdus samad ya ganta ya aureta sabida mahaifinta pharmacist ne acan a wani asibiti yake aiki,,itakam tace ba zata bishi nijeria ba,tilas ya yadda ya aureta a can suka zauna a can,bai wani damu sosai ba,don shima acan yake nashi aikin irin ma surukinsa,damuwarsa kawai yaran da zai haifa kada su tashi da tarbiyyar can. Gidan da abdus samad suke zaune me block biyu ne,hakan ya sanya yace muntari ya zauna a nan,amma yace a'ah,saidai abdus samad yazo su zauna qyatacce kuma yalwataccen gidan da gwamnatin tarayya ta bashi ya zauna iya wa'adin aikinsa,hakan suka tattaro suka dawo,duk da khaulat bata so ba,saboda macace mai tsananin izza girman kai da ji da kai,macace dake son taga kowa a qasanta ita ce a sama,hakan ya sanya jininsu yaqi haduwa da kilishi ummee,saboda sam bata da wulaqanci,barta da miskilancinta fada da rashin son raini,sam ta tsanu halayen khaulat,duk da yadda ita khaulat din ke maqale mata,saboda tasan daga babban gida ummeen take,bugu da qari girma ne da cinyewa a wajenta ace tana hulda da mace irin ummeen,mata a wajen ambassador muhammad mukhtar muhammad adam,kuma diyar gidan sarauta. Komawarsu america ummee bata saki tarbiyyar yaranta ba,basu fi shekara guda ba Allah ya hada baabaa prof da Bilkisu,yarinya mai tarbiyya hankali faran faran da jama'a,sanda ya zowa ummee da zancan tasi tayi bore,amma tilas ta haqura da mahaifinta ya tsawatar mata,yace a nijeria ma bilkisun zata zauna,sosaj khaulat taso zuga ummee,saidai ko kallo bata isheta ba,don jininsu bai gama haduwa ba,ita dinma tana da hankali,bata da shegen kishi da iskanci irin na 'yammatan yanzu da zasu nemi tasarwa uwar gida hankali,tun kafin ta shigo ma sai suka fahimci juna,tana yawan kiran ummee a landline tasu suna gaisawa,tun ummin na basarwa har ta saki jiki,sai Allah yasa mata qaunar bilkisu har akayi auren,shekara guda ta haifi danta na fari mahmoud,baki daya suka je nijeria suna da yaranta baki daya,sukayi sati suka dawo. A lokacinne kaulat ta samu ciki,bata taba haihuwa ba,wannan ita ce haihuwar fari da zatayi,ita ta dakatar da haihuwar a cewarta bata da buqatarta a kusa,bayan wasu watanni ta haihu,ta haifi SU'AD,tun a sabitin tasa aka juyar da mahaifar,wannan wuya wai ba zata iya ba,da yake turawa ne ba ruwansu suka yi mata abinda take so. So da qaunar duniya ita ta dauka ta dorawa su'ad,yarinyar ta taso a sangarce,abinda take so shi take yi,babu kwaba babu hantara,kallon banza kayi mata sai ta saka ihu tun tana qanqanuwarta,hakan ya sanya sam tasu bata zo daya da yaran ummee ba musamman mustapha,miskilin yaro wanda jinin sarauta ke yawa a jikinsa kamar uwarsa tun yana da qananun shekaru,ko kallo yarinyar bata isheshi ba,idan tana gu bai zama,shu kadai ke iya bugunta ta haqura ta shanye bata kai qara ko ta tashi hankalin gidan ba,shi kadai ke hukuntata yadda yaga dama,hatta babanshi da shi yake hadata idan ta addabeshi,bala'in tsoronsa Allah ya dora mata da qulafucinsa,bai damu da ita ba amma idan ta wuni bata ganshi ba ta dinga binbini da tambotsan nemansa tana yiwa uwarta rigima,kota shigo wajen ummee ta liqe mata tana buga rigimarta,da ya shigo kuwa kallo daya zai mata ta shiga taitayinta. Kai kai,yau nayi abun kai,4932 words?,ku biyoni a gaba don jin qarashe wannan family. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [23/02, 11:51] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 6⃣5⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *innalillahi wa inna ailaihu raji'un* *Allah subahanahu wata'ala yana cewa cikin qur'aninsa* *RANAR DA ZAMU CE DA JAHANNAMA SHIN KIN CIKA?,SAI TACE AKWAI QAARI NE?(na mutanen da za'a zuba mata)* *subhanallah,Allahumma ajirna minan nar* ____________________________________        Ba yadda ummee ta iya wani lokaci haka take biyewa tsiyar su'ad,ta lallabata,takan yiwa mustapha fada idan ya mata tsawa ko ya niyyaci dukanta,sam bai son sangartarta,bai shiga gidansu ma sabida halayyarta data uwarta da bata yi masa ba,ummee bata son yadda yake mata,takan ce yarinya ce fa mustapha su'ad har yanzj,cikin zuciyarta kuma bata ganin laifin kowa sai na uwarta,tunda ance ice tun yana danye.....,haka nan barewa bata gudu danta yayi rarrafe.         Tun yana qaraminsa Allah ya zuba masa miskilanci,halinshi ne,halittarsa ce haka gado yayi,yaro ne shi mai zubin gidan sarauta,yana qaunar doki,kayan sarauta da duk wani abu daya danganci hawa doki,kusan yadda halayyarsa take tamkar babban mutum ya sanya abokansa yaran turawa ke tsokanarshi da sunan MAN,mukhtar baabaa prof shima yakan tsokaneshi lokaci lokaci,daga haka sunan ya bishi,son dokinshi ya sanya baabaa prof tun a lokaci yakan siya masa ticket yaje kallon wasan polo tun a american,yawan kallon wasan polo ya sanya su'ad itama wasan ya soma burgeta,bai da abokin tafiya duk sanda zashi kallon,sai ita ke nacewa zata rakashi,tun yana daka mata tsawa yana korarta yana cewa ba zata rakashi ba har ya fara barinta tana binsa,saidai har suje su dawo bai tanka mata,ita kuwa ta cikashi da surutu,abinda baiso kenan,yanzu kansa zai hau ciwo,don ciwon kai bai masa wuya.         Tsabar qwaqwalwa da Allah ya zuba masa ya sanya aka daukeshi daga nursery zuwa primary,a can din ma suka fuskanci basirarsa ta girmewa gurbin da suka bishi,tilas aka sake turashi ajin da zasu kammala secondry a shekarar,        A shekarar ne baabaa yaga dacewar ajjiye aikinsa ya dawo gida ya tattara kan iyalinshi baki daya,anty maamaa dake abuja da ummee dake tare da shi a america,maida hankalinsa sosai yayi ya tasamma gina katafaren gidanshi a abujan,gini ne dashi kansa yasan cewa ya kashe masa maqudan kudade duk da ba komai bane abinda ya cira wajen ginin cikin irin dukiyar da Allah ya hore masa,a yanzu ya tabbatar baida wasu family na jikinsa sosai baya ga sauran dangi tsiraru da suka rage banda yaransa da ya haifa,wanda a yanzu sun zama su bakwai,ummee na da biyar ADAM MUSTAPHA FARIDA(UMMAN HUSNA) HUDA sau auta SUMAYYA(AMIRA) Bilkisu anty maamaa na da yara biyu duka maza MAHMOUD da USAMA        Gini yayi yana mai hasashen gaba,yana son yaransa maza su zauna da shi idan Allah ya hukunta hakan cikin gida daya,hakan ya sanya yayi sassa biyu,ko wane sashi akwai wasu sassan ciki,duk a lokacin ma adam da yake babba a lokacin yake ss two a can american,sanda suka tashu tafiya aka bar adam ya kammala secondry dinsa,yayin da uncle abdus samad mahaifin su'ad ya nemi alfarmar a bar masa mustapha,saboda ya lura da yadda su'ad ke daga hankalinta daga jin labarin tafiyarsu,da fari mustapha yaqi ya murje idanunsa,sabida asalan shi mutum ne da bai boye abinda ke ransa koda ba zai maka dadi ba,gaskiya ce zaya fadeta komai dacinta,saida baabaa prof ya jashi yayi masa fada kaca kaca,ya gaya masa abdus samad babansa ne kamar yadda shima yake babansa,yarone mai biyayya da bin umarnin iyayensa komai tsaurinsa,baison bata musu ko yaya,hakan ya sanya ya sunkuyar da kai,bai sake cewa qala ba har akayi aka gama suka tafi suka barshi hannun abdus samad da matarsa khaulat,murna cikin khaulat kamar tayi me,a take ta dinga hasasowa ranta hada mustapha da su'ad,tabbas ba zata bari 'yarta tayi asarar babban gida irin wannan ba,zata so hada alaqa da gudan professor mukhtar muhammad,tabbas ba qaramin kankaro mutunci bane ku samu relation da attajirai irinsu,shu'umin murmushi ta saki,kusan ita ta qara kitsawa su'ad soyayyar mustapha,tunu yarinya ta hau turba,dama gata cikin turawa,batasan kunya ba ko kadan,a shekarun har tasan wani soyayya da i love you,a haka shekaru suka fara tafiya,adam ya kammala karatunsa yana niyyar komawa naijeria,yana son qasar tayi masa,ba kamar mustapha ba da ya lura tunda aka tafi aka barshi bai kuma zancan qasar ba,fushi ne ko ameriacn tafi yi masa oho?.       Koda ya koma nijeria adam makarantar gaba da secondry aka sama masa ya sake komawa,yayin da mustapha tuni ya shiga secondry,yana aji biyu junior suka daukeshi suka maidashi senior aji biyu saboda gifted ne na tashin hankali,kishinsa classmate dinsa suka musamman turawan nan,suna ganin bai isa ba yana asalin dan nijeria yace zaizo ya dokesu,kunsan mai jan kunne da shegen kishi da ganin kai baqar fata baka isa ba,to indai mustapha ne basu isheshi duba ba,karatunsa yake haiqan,babu wanda ya isa yayi gigin tabashiduk iskancinau,sunsan waye ubansa,ko baya ga haka ma suna sane da halin jarumta irin tashi,sau da yawa abubuwa na tsoro sai su kasa shike gabatar da su,baison raini ko kadan yana da zafi,bai shiga sabgar da bata shafeshi na,wadda ta shafeshin ma ba lallai ya bata muhimmanci ba,karatu ya zaunar da shi kuma shi yakeyi,tilas suma suka sallama masa,cikin qanqanin lokaci yayi fice yayi suna cikin makarantar,tare ake kaisu a daukosu shi da su'ad,saidai ko kadan basa shiri saboda yadda ta cika rawar kai da kule kulen maza,amininshi daya ne tal a duniya har ya zuwa yau din nan,HAMZA ABUBAKAR JAHUN,babansa aiki ne ya kawoshi qasar suke zaune,shi daya yasan ta kan mustapha,ya iya zama da shi hakan ya sanya tasu tazo daya.         Duk da wannan halayya tasa mutum ne shi mai tausayi,yana da tausayi ga mata tun asali yasan su masu rauni ne,sannan qananan yara musamman idan aka ce wannan maraya ne,Allah ya zuba masa tausayin maraya walau uwa ko rasa ko uba,ko kuma dukka baki daya,tun a sannan ya yiwa kansa alqawarin gina gidan marayu idan ya girma,yasan idan ya yiwa babansa maganar shi mai ginawa ne,to amma yafison ya gama karatu ya kama aiki,ya ginda da kudinsa daya nema da guminsa.      A can mustapha ke halartar wata makaranta,duk da yake aji guda ne saidai kowa da inda ake masa qari,alqur'ani ake koya musu da littafan addini wanda ya shafi fiqhu,tauhid/aqida,da kuma hadith,mutumin dan qasar pakistan ne,da fari su'ad na binshi suje,duk da ba wani abun arziqi take koyowa ba,daga bisani bayan shekara daya ta watsar,saboda a ganinta ta girmi zuwa makarantar islamiyya,tayi zamanta da jahilcinta tana yiwa wasu kallon gidadawa kidahumai,mustapha bai gushe ba yana zuwa makarantar har ya sauke bayan haddar izifi talatin cif da ya samu,wanda har zuwa yanzu tana nan a kanshi. A hankali shekaru suka fara ja,girma yazo wa kowannensu,su'ada an zama budurwa,tana ss 2 a lokacin,yayin da mustapha ke universty,a duniya baida sha'awar kowanne karatu irin karatun likita,yana son karantar bangaren cututtukan yara,sai aka samu akasi kasancewarsa ba mai magana ba,uncle abdus samad ya cike masa fannin mata,wato gynocology,sam wannan fannin bai burgeshi ba,amma da sukayi magana da ummensa,ta nuna masa cewa bangare ne mai muhimmanci da irin adadin matan da zai iya taimaka,sai ya gamsu ya karba hannu bibbiyu,ya shiga karatu ka'in da na'in,kowa ya sani cewa karatun likita ba abu bane mai sauqi kamar sauran bangarorin,balle agun mutum mai daukan lamuransa da gaske irin mustapha,bashi da lokaci komai sai na karatunshi,fanni guda suke karanta shi da abokinsa hamza,a hankali suka hadu da abokai daidai su,wadanda karatu kawai suka saka gaba,cikin qanqanin lokaci group dinsu yayi shura,su shida ne cif,dukkansu babu baya cikinsu,ta fannin kyau,nasaba da dukiya,mustapha,hamza,usman,musaddiq,lamin,huzaifa,suna da ra'ayoyi iri guda ta wani fannin,yayin da kuma suka saba ta wani bangaren,abu guda dai wanda sukayi tarayya a kai shine,aqidun turawa da sukayi tasiri cikin gangar jiki da zuciyoyinsu,sakamakon dadewa da kowannansu yayi cikin qasar,lamin me kawai da musaddiq karatu ne ya shigo da su,ba wanda ke harkar banza a cikinsu anutse suke,saidai kama daga abinci,sutura zabi na irin matar aurensu,doka da qa'ida da mu'malaolinsu na yau da gobe dukka aqida da halayen nasara ya shiga cikinsu yayi kane kane. SU'ADAH Yarinyar da tun tana qanqanuwarta aka nuna mata ta ginu ta kafu kan raina talaka,dukkan wanda bai da shi bai da qima baida daraja a idanuwanta,kai hasalima bata masa kallon cikakken mutum mai 'yanci,yarinya ce mai yawan izza da jin kanta,yarinyar da bata mu'amala da dukkan mutumin da bai fisu arziqi ba,matuqar kina so ko kana so kuyi qawance ka tabbatar ka fito daga gidan da yafi nasu arziqi ko kake dai dai da ita,ta dauki kanta da girma,ta ajjiye kanta can nesa sama qololuwa,komai nata high class ne,komi da zata mallaka sai ta tabbatar yasha banban da na kowa,bata taba yadda wani ya fita ko ya shalle mata,bata lamunci kallon banza ba bare ka furta mata maganar banza,taku take iya qarfinta,jin kanta take tamkar diyar DONALTRUMPH ko kuma BILLGATE,kallon da takewa mutane ma dabanne,duban farko ga mai hankali zai fuskanci kallo ne na qasqanci da ganin kowa bai isa ba face ita din nan dai,masu hidimawa gidansu kallonsu take tamkar bayi da suka siyesu,babu wanda baifi qarfin ta takashi ba matuqar arziqinka ya gaza nasu,wayewarta ta wuce iyaka,ta wuce tunaninka,duk wani abu da baturiya zatayi shi a matsayinta na farar fata wadda bata da cikakken addini bare kunya shi su'adah zata yi ba,babu uban wanda take jin kunya,abu guda ne bata taba yiba bada mutuncinta,saboda ta riga ta sanyawa ranta bata da miji daya wuce mustpha,har yau batayi katari da namiji kamar mustaphan ba,duk wanda ta kalla sai taga mustaphan ya masa fintikau,tamkar yadda sama ta yiwa qasa nisa,bugu da qari ta tabbatar ta jewa mustapha a fanko babu abinda zaya hana wulaqanta duniyarta,babu abinda zai hana yayi fatali da dukkan wata qauna da take masa ya hukuntata mafi tsananin hukunci,tana yarfa tare da wulaqanta maza da yawa,kama daga hausawa har zuwa turawan,idan har kaga ta tsaya ta kulaka tofa ka tabbatar babanka an sanshi ya san wani shima,sunansa ya zama tambari a duk qasar da kuke da zama,su'adah bata san sanya atamfa ba balle daurin zani,dankwali kuwa saidai ta gani a kan wasu,yadda americans ke shigarsu itama haka yake,ta sanya rigarta da wando,ta fito da gashi ta fice abinta haka,a da har ra tsiri saka mini skert,mustapha yaci ubanta ya taka mata birki,tana qwafa tana kumburi bayan fitarsa tana ba zata daina ba,kaulat da take kira mom ta mata fada,ta fuskanci sam a cikin kaso dari na rashin nutuncin su'adah itakam ko arba'in bata yi ba,dama wai ance sai mai koyo yafi qwararre qwarewa "Ke da kike son aurensa,ta yaya zaki qi yin abinda yake so,idan dai baso kike ki jawo mana asara ba,jira nake kawai ki gama secondry na qyasawa babanku maganar,don kada ma ya hango wata ya jawo mana asara" kan haka ya sanya ta daina sanyawa,ta kuma nemi dankwali take sanyawa akanta don dole wanda data fice yawonta zata figeshi sai kuma idan zata dawo gida. A irin zaman hostel da sukeyi idan jarabawa ta kusa,suna zaune su shidan bayan kowanne yayi karatu ya gaji,sai kuma suka barke da hira,mustapha dake kashingide gefansu yana duba handout,shi kadai ne bai ajjiye tasa ba,sun riga kusan da sun saba da irin wannan halayya tasa,yadda yake na daban komai nashi dabanne,bai gajiya sam da karatu,iskar gun nayi mishi dadi qwarai,saboda wadatar shuke shuken dake wajen,a hankali suka gangaro kan hamza,shi sukewa tsiya kan yaci baya,ya rasa wadda zaya aura sai 'yar afrika,afrikan ma nijeria,nijeria ma yarinyar da kwalin secondry school kadai gareta,ra'ayinsa ne,don duk cikinsu ya fisu sassauqan ra'ayi,baiga dalilin da zai daukarwa kansa jangwam ba,yana mamakin yadda 'yammatan da idanunsa ke bude tarwai suke burgeshi,shikam ya sheqa yaga babu qwaya gwara ya auri local ya wayar da abunsa,kusan mustapha yafi kowa jin baqincikin batun,shi gaba daya atsarinsa ma baijin zai iya auren matar da bata da kwalin degree zuwa sama,matar da tasan abinda take yi,yana jinsu suna ta kumfar baki,daga bisani da yaji sun fara cikashi ya miqe zai bar gun,don kada ma ranshi ya baci kan lamarin,bai son cewa komai,haka ya kwashe litattafansa ya sauya gu yana ganin baiken hamza,tare da mamakin meye amfanin wayewa da karatunsa da zai dauki irin wadan nan yaran a matsayin matar aure,wadda babu wayewa tattare da su,a ganinsa saidai kawai kasha kayan haushi,babu wata kulawa da zallar soyayya mai maqalewa zuciya da zasu iya yi ma,a yadda yake din nan mayen soyayya ne,mutum ne shi mai burin samun macen da zasu baje kolin soyayya,ta soshi tamkar ranta,ta kula da shi kamar sabon jinjiri,ta shagwabashi kamar dan auta,ta bawa lamuransa muhimmanci ta fifitashi fiye da kowa ina zaya samu wannan ga irin wadancan matan?. Lokacin da mustaphan ya gama karatunsa baki daya har ya samu aiki a wani babban asibiti dake garin,wanda da gudu suka daukeshi,sun jima dama suna bibiyar irin qwazonsa,don a daliban da jami'ar ta yaye a shekarar banu dalibin da ya kai qwazonsa,ranar baabaa prof yayi farinciki da samun d'a kamar shi,ya runa kalaman mahaifinsa muhammadu,ba shakka suna ganin abinda malam ya gaya musu zahiri,mustaphan daban yake tun daga haihuwarsa zuwa yau,haka ma ummee don baki daya suka rankayo harda anty maamaa suka zo bikin yaye su din.   familyn tun a lokacin family ne mai ban sha'awa da burgewa,cike yake da qaunar juna da hadin kai,dukkansu daga ummee har anty maamaa sun tsarkake zukatansu,kowacce ta riqe 'yar uwarta fusabilillab,sai Allah ya shiga lamarinsu ya kade musu dukkanin abun qi. Ana ya gobe su baabaa prof din zasu koma uncle abdus samad ya sanarwa baabaan niyyarsu ta hada auren mustapha da su'adah,ba qaramin farinciki baban yayi ba,yana ganin lokaci ne na qara danqon aminci da zumuncin dake tsakaninsu,ko a lokacin sai da ya tuna da sulenshi,inama ace diyar sulenshi ce zai aurawa mustapha?,kowa yayi na'am da batun sabanin mustapha daya shiga tashin hankali da bacin rai,tunda shi kam babu wata alaqa ta soyayya data taba shiga tsakaninsa da yarinyar sam,hasalima bata cika sharadan da yake so ba,don candy kadai tayi,kawai dai ya dauketa ne matsayin qanwarsa,amma da batun yaje kunnen abokan nasa su suka kwantar masa da hankali,a ganinsu babu komai,a daura auren taci gaba da karatunta,shima yaci gaba da aikinsa,idan yaso sai yayi rainonta har takai matakin da yake so ta kai,ya dorata kan dukkanin tsarinsa,tunda babe din ta hadu,abinda basu sani ba dukkansu shine su'adan ta girmi tunaninsu,shi sam shawarar ma bata yi masa ba,abu guda da ya sanyashi amincewa shine ranar wata lahadi da ya jiyo muryar kaulat na kururuwa,su'adah din ya dirki guba saboda ta lura mustaphan baya sonta,abun ya tsoratashi,ta dauki halayen yahudawa baki daya na rashin yadda da qaddara,ko data farfado cewa tayi zata kashe kanta,roqon sa da uncle din ke masa kan ya aureta shi ya masa nauyi,ba tare da bata lokaci ba ya amincewa aurenta,yana tunanin yayi amfani da shawarar abokansa kawai. Cikin iya duniyanci da gogewa sannu a hankali ta soma jan ra'ayinsa,sai ya sakar mata ya zuba mata ido,cikin kaffa kaffa take lamuranta,don tasan halinshi sarai bai daukar wargi,a hankali ta soma bude wata qofa daga cikin zuciyarsa,wanda hakan ya sanya ya dan sakar mata kadan,a wannan bigiren sukayi aure. Baki daya ta bata tsarinsa na yayi rainonta,abu guda ne ya dore ci gaba da karatu da tayi,don itama tana masifar son karatu,tana son tayi karatun da zata zama wata,watan da duniya zata dinga maganarta da kwatancenta,ta riqi karatunta da masifar muhimmanci,tana ganin shine tsanin mataki na biyu da zai sanya ta zama wata a duniya,bayan zamantowarta daya daga cikin iyalin PROFESSOR MUHAMMAD MUKHTAR MUHAMMAD ADAM GOMBE. Rayuwar gidan aurensu rayuwa ce irin wadda suka ga mazauna qasar nayi,rayuwar 'yanci,kowa yana da right,har wani lokaci mace tafi namiji dama,saidai a wannan bangaren mustaphan ya riqe kambunsa,yayi riqo da bahaushiyar al'ada,ya bata damarta,saidai fa bata isa ta tsallake umarni qa'ida ko dokarsa ba,wannan kadai take gani ya takura ta,shike bata mata rai,to amma ba komai bane a gunta saboda masifaffen son da takewa mustaphan,tanaji a acikin ranta ko ummee da tayi naqudarsa bata kama qafar son da takewa mustaphan ba. Tsakaninta da mustapha ya biya mata buqatarta,ta aure kota kudi,taci sa'a kuwa gwanin kyautatawa iyali ne,bata san cinsa ko shansa ba,batasan tsaftar muhalli data tufafinsa ba,suna da kuku suna da mai share share suna da mai wanki da guga,sam ita a rayuwarta ma baki dayanta bata taba shiga kitchen ba,shege ruwan zafi saidai ta ganshi kawai,rayuwa ce irin ta banasaren mutum zallah suke gudanarwa,shima bai damu ba,amma wani lokaci sai yayi mamaki idan yaje nijeria yaga yadda su umme ke dawainiya da majinsu,basu duba tsufansa ko girmansa ko kuma yawan ma'aikatan dake gidan,wanda duk abinda kake so daka fada ta cikin waya za'a gabatar maka da shi,sai ya watsar tare da dora hakan kan mizanin banbancin al'ada da dabi'a. Yana tsaka da aikinsa wani babban asibitin kudi suka yi masa tayin aiki a asibitinsu,ya duba yanayin asibitin yaga yayi masa,akwai nisa sosai tsakanin jahar da suke da jahar da asibitin yake,hakan ya sanya ya duba gida mai kyau a can ya siya,bedroom biyu falo sai kitchen ya koma can da aiki,yayin da ya bar su'ada a nan tana ci gaba da karatunta,don cewa tayi ba zata bishi ba gaskiya taba tsaka da karatunta,shima bai wani damu ba yayi tafiyarsa,saidai sam baida lokacin zuwa inda suke,ita dince idan ta motsa mata zata kwashi kayanta ta bishi,tayi masa weekend ta dawo taci gaba da sabgoginta. Tafiya ta fara nisa,babu haihuwa wajen su'adah ba dalilinta,bata yi mamaki ba,don tuni ta jima da fara hadiyar qwayoyin tsaida haihuwa tun satin farko na aurensu,kusan tafi uwarta iya shege,don daga bisani ma zuwa tayi ita aka juyar da mahaifar,don tace bata ga me zata ci da haihuwa ba,ita da iyayenta suna da arziqin da basai ta nemi taimakon da ba,tunda dama don ya taimakeka kake haifarsa(a tunaninta),sam mustaphan bai san da wannan badaqalar ba ko kadan,ya dauka kawai Allah ne bai kawo ba,baya ga aikin da yakeyi yana kasuwanci sosai,wanda har yaso yafi baabaa prof qashin arziqi,cikin qanqanin lokaci dukiyarsa tayi haukatar ban mamaki,hakan ya sanyashi diban maqudan kudade ya zo nijeria,kowacce state din nan da muke da ita ciki harda abujan ya danqara asibiti,wanda idan da na private ne sai ka isa ma zaka iya zuwanshi,amma yace kyauta komai za'a dinga yi ciki,shi da kansa idan ya samu lokaci yazo nijerian yana zabar states din da yake ga zai iya zuwa ciki harda gombe wadda bai fashin zuwanta sabida tuna asali da tushe ya ziyarci a asibitocin,ya karbi cases masu girma da asibitin ya samu ya zauna yaga marasa lafiyan yayi musu abinda ya dace,asibitin abuja kuwa sati biyu yake yi yana ganin marasa lafiya kowanne iri matuqar lalurar ta shafi mata,hakan ne ya sanya kaf fadin najeria babu asibitoci mafiya inganci taimako da kula da marasa lafiya irin nasu asibitocin,girmamawa ta musamman gwamnati ta yi masa saboda taimako da gudun mawar da ya baiwa al'ummarsa. Baya ga wannan ya gina gidan marayu,kano daya gombe daya abuja daya,gidan marayu mafi girma da baiwa marayu tallafi da kulawa a nijeria,shike daukar nauyi da dawainiyar komai nasu,yana daga can yana turo duk wani abun buqata nasu,ya sake samun bunqasar arziqinsa ne lokacin da ya zuba hannun jarinsa cikin wani company dake dubai wanda ke saqa nau'in dogayen riguna na maza da mata masu tsada da kuma masu matsakaitan kudi,daga bisani masu hannyen jarin kowa yaso janye nasa,shi ya biya kowa ya mallakin company,ya zauna tare da taimakon hamza,musaddiq lamin da usman suka sake yiwa companyn garambawul ya sake tashi a aiki,suka sauya masa suna wanda yake amfani da tambarin MM mustapha mukhtar,sai gashi ya zama company mai daraja ta daya dake sarrafa dogayen rigunan dai nau'i daban daban,kaloli daban daban,companyn na daya daga cikin zuciyar arziqin da ya mallaka. Rayuwa ta yiwa su'adah dadi,sai yanzu take sake kallon irin gatan da mamanta tayi mata na maqalewa tare da naqalta mata auren mustapha,tana jin dadi tana alfahari ta juya a duniya tace itace matar MUHAMMAD EL-MUSTAPHA,wanda ya kasance cikin jerin sahun farko na matasan shahararrun masu arziqin da nijeria ta mallaka. Rayuwa ta yi masa kyau,burikansa suna dab da cika,wannan karon yana yawan waiwayar nijeria,idan azumi ya kusa kamawa a nan zaizo yayi guda ashirin,goman qarshe su wuce umra shi da duk wanda Allah tsaga da rabonsa ko wanda baabaan shima ya biyawa,duk shekara bai dauke sunan ummensa babanshi da anty maamaa,sai autarsu sumayyatul amirah,shike biya musu,bai yadda suyi amfani da kudinsu wajen biyawa kansu ba saidai wanda suka ga dama cikin 'ya'ya dangi ko surukai,idan ta rayawa su'adah tace zata bismillah,idan kuma 'yan abun basa kusa taqi zuwa,wani lokaci da taje can ta gwammace ta siyawa kanta da qawayenta tikiti na maquden kudade su tafi kallon wani wasan a can wani shahararren gun kallon wasa duk inda yake a duniya saidai idan ba'a ginashi ba,hakanne ya sanya take matuqar qawance da qasar DUBAI,daga bisani Allah ya hukunta mustaphan aikinsa ya dawo dubai din,hakan ya masa dadi saboda yayi masa kusa da company dinsa,duk da dama bai da damuwa yana da abokai masu kama da 'yan uwa dake kula da shi,kasancewar dukkansu basu kai budin mustaphan ba,sai dubai ta sake zamewa su'ad din gida,tana iya baro karatunta ta taho dubai din takanas kallon film ko wani wasan,daga nan ta shargalle agun mustaphan idan taga dama ta wuce,hakan ya sanya karatun nata ke kwan gaba kwan baya,har yau yaqi ya qare. Sukan dawo daga umra ranar sallar,daga nan idan baijin gajiya zai sake hawa jirgi a washegari ya taho rano wajen kakanninsa,da shi ake hawan sallah,abun na qayatar da shi,kusan tawagarsa daban take,duk sanda zai wuce sai ya ja hankalin mutane saboda kwalliyarsu daban take,bayan ya gama hawan sallah sannan ya dawo ya koma kan ayyukanshi,haka rayuwarsa take,kusan baida wani lokaci na banza a rayuwarsa,duk daqiqa daya mai amfani ce a wajensa,yana tafiyar da ita wajen ayyukanshi,hakan bai damu su'adah na wai bata samu cikakkiyar kulawa ba,arziqi dukiya da rayuwa mai aji da tsada take buri kuma ta samu,buqata ce idan ta taso mata duk inda yake zata siyi ticket ta bishi ta fansheta ta dawo. Hakanne yasa a hankali qannensa mata suka fara lura da irin rayuwar da yayansu yake,rayuwa ce mai kama data gauro,bai da wata mace a gefansa da zai dafa ta aduk sanda wani abu ya taso masa na gaggawa,bashi da wata mace dake tare da shi kullu yaumin da zata tsara masa lamuransa,lokutansa da rayuwarsa,ko da yaushe yana cikin aiki,aiki dai,shi yana gabas kasuwanci da aiki matarsa tana yamma karatu,sam baida wani family da zai nuna nashi kamar yadda sauran 'yan uwansa ke da shi. Misali: babban wansu adam a yanzu haka yana da matan aure biyu,ta farko na'imah Allah bai bata haihuwa ba ya sake aure ya auri fahriyya,yanzun haka yana fa yara hudu,biyu maza biyu mata,yana aiki a legos cikin shima nashi company na qashin kansa,yana zuwa gida da su baki daya idan ya faru ko kuma daya tazo a bar daya a can,qanwarsa farida tayi aure,tana da yara uku,mai bi mata huda itama tayi aure yaranta biyu,mahmoud ya kammala karatunsa,yana juya dukiyar baabaa prof shi da dan uwansa usama,baaban baya komai sai kula da gidan gonan sulensa,har yau sule yana ranshi yana saka ran haduwarsu kafin mutuwa da ruski dayansu,gidan gonan da zuwa lokacin yayi rassa jahohi daban daban har nan abujar,duk da cewa usama akwai sauran nauyin karatu a kansa da bai kammala ba,amma daga can inda yake yana kasuwancin,thailand ne,shi da mahmoud din ke shigo da kayan su rarrabawa 'yan kasuwa,kowannensu ya fidda macen aure,lokaci kawai ake jira,sosai baabaa yaga alfanun yiwa yaran nasa sashensu,don ya zame musu tamkar mahada ko masauki duk sanda suka baro wajajensu kowa nada bangarensa da zaya sauka cikin gidan kusa da babansu,akan ga kowa a gida akai akai amma ganin mustapha yakan zama aiki,balle madam din nasa,wadda lokacin bikin sallah ne take biyoshi don ta san cewa gidan nasu kan kasance cikin baqi 'yammata da samari,takan biyoshi ne ta kasa ta tsare,abinda har yau bata sani ba kenan halayyar mijinta,itace shaida ta farko da zata fadi kan mustapha baida idanuwan kallon mata baki daya,amma ita sai take ganin hakan isarta ce tasa har yau ita kadai yake gani,ta sani cewa mustaphan nata irin mazan nan ne dake tsada,mazan da mata ke marmarin samu,ba wai saboda tsurar kyau kawai ba,a'ah,kwarjini haiba kamala da cikar zati da halitta,ita kanta ta tabbata Allah ne kawai ya kashe ya bata,tana sane da yadda ake farautar mustaphan,kama daga yammata kyawawa masu taqama da kyau da arziqi irin nata ko fiye da natan ma,zuwa manyan hajiyoyi masu juya naira,abun yakan bashi mamaki ganin yadda mata ke farautar d'a namiji,yakan jima yana jinjina lamarin,wasu na roqon aure ya hadasu,yayin da wasu ke roqo ko da harkar banza yazo suyi,son so ace yadda haduwar mustaphan take baida komai,da sun yaudareshi koda da dukiya ce,saidai kash,sai suka sameshi da arziqin da zai iya daukar nauyin danginsu ma baki daya. Sirrin samuwar nasararsa ta ta'allaqa ne ga biyayya da tsananin kyautatawa iyaye,bai iya tsallake umarninsu,uwa uba kuma tausayi da taimako. Wannan shine familyn baabaa prof. TOFA ADDU'RKU TACI,YAUMA NA KUMA KO? *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [23/02, 11:51] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 6⃣6⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *Allah s w t yana cewa* *HAQIQA SAI NA CIKA JAHANNAMA DA MUTANE DA ALJANU BAKI DAYA* *Ya Allah ka yi mana tsari,ka suturta mu* __________________________________      "Wannan shine cikakken tarihin familyn baabaa sumayya,na tabbata zuwa yanzu kin fahimci komai" murmushi sumayyan keyi tana gyada kai,sosai labarin asalin zuriyyar ya burgeta ya qayatar da ita,very interesting,ta tsinci darussan masu yawa a ciki,sunyi gadon karamci mutunci da halacci,qasan ranta take raya amma shi kam bata san inda ya tsinto nashi halayyar ba,tana masa duban mutumin da bai girmama mutuntaka ta dan adam,mutum mara saurin fahimta da dogon tsinkaye da bada hanzari "Wa kenan"ta tsinci muryar anty dije na tambayarta "Na'am"sumayya ta waiwayo da hanzari tana tambayarta,don bata tsammaci da ita take ba "Idan na canka dai dai mustapha kike wa wannan yankan hanzarin ko?" Da sauri ta kada kai "Ko kadan,me kika ji nace?" Murmushi antyn tayi ganin tana son musanta mata,cikin sigar tsokana tace "Kiyi dai a hankali,kada kema ki fada tarkonshi,naga ba wuya 'yammata sun zurma cikin komarsa" wata matsananciyar faduwa gabanta yayi,kai ta soma kadawa "Allah ya sawwaqe anty,ya rufamin asiri duniya da lahira,yanzu kyamin wannan fatan haba anty?,na kai su'adah ina,baya ga haka ma wallahi baiyimin ba ko kadan,banga abun burgewar ba anan wajen" dariya antyn tayi sosai har su laila dake sit din gaba suka waiwayo suna dubanta sai data ce su juya "Dukka yadda akayi kallon tsoro kika yi masa,kece mutum ta farko da naji kin ambaci haka,ko minal dake da qarancin shekaru cemin take,mami uncle man yana da kyau kamar na 'yan india,ta yaya ma zaki gane shi bayan kallon mukhtar kika yi masa ba ainihin kamarsa kika gani ba,kuma ma meye na saurin rantsuwar baiyi miki ba?,kika san inda rana zata fadi?" "A inda ta saba faduwa mana anty,komai kyansa bazan gane ba anty daga kan mukhtar an gama namiji" ta qarashe zancan fuskarta na nuna rauni da karaya da zuciyarta tayi,hakan ya sanya antyn yin shiru,yayin da itama tayi shirun tana maida numfashi tare da hadiye yawu da qyar.         Kai ta girgiza bayan ta gama wassafa ta yaya zata zauna zaman aure da wani bayan mukhtar din,sam,ji take ba zata iya ba,babu wannan mafarkin cikin rayuwarta,kamar soyayyar da take nuna masa bata cika ba kenan.         Cikin hukuncin Allah suka isa qasar lafiya,tun daga airphort sumayya ta soma gane banbanci baro baro da tata qasar,haka tayi ta kalle kalle sanda taxi ke dauke da su zuwa masaukinsu,sai ta samu kanta da yiwa qasarta addu'a tare da fatan samun ci gaba kamar wannan qasar.          Da suka isa a gajiye suke,gida ne wanda ke dauke da falo guda daya,sai kitchen,bedroom uku,kowanne da manne da toilet,sallolinsu kawai suka rama kowa ya kama makwancinsa,kusan ita ce qarshen bacci a gidan,ta jima tana juyi kan gadon,hakanan take da tsananin baqunta,duk sanda ta sauya muhallin data saba da shi tana dadewa kafin bacci ya dauketa.        Tunda suka je uncle farouq bai zauna ba,yana ta zirga zirga kan abinda ya kawoshi tare da yi musu siyayyar abubuwan da zasu buqata na gida,sai da suka ci sati guda cur kafin komai ya daidaita,ya miqa laila da khalipha wata makaranta wadda ke nan cikin unguwar,yayin da ya samawa sumayya wata center ta manya dake karantar da su dukkan wasu karatuttuka irin na 'yan secondry tun daga matakin farko cikin shekara guda su baka certificate dinka,itama babu nisa tsakaninsu,ko a qafa zaka iya zuwa,idan kana da buqata kuma kana fita bus zata zo ta daukeka ta qarasa da kai,da fari sumayyan ta tsure,tsoro take ji,tana tunanin ta yadda zata dinga zuwa wajen ita daya,ta zauna cikin baqin fuska,fararen fata,wadanda akwai banbancin addini harshe da al'ada tsakaninsu,kamar tayi qwalla saboda tsoro,anty dije ta dinga tuntsira mata dariya "To ko ni zan dinga rakaki?" Ta zolayeta "Dole fa ki saki jikinki sumayya,nan qasar babu ruwan wani da wani ce,kowa abinda ya kawoshi shi yakeyi,ki zama mai budadden kai,so nake a kasa ganeki duk sanda muka koma gida" da irin wadan nan kalaman ta qarfafi gwiwarta.        Ranar farko gabanta na dukan uku uku  haka taje,tayi tsurutsuru cikin ajin,sam bata fahimtar me suke fadi bata fahimtar turancinsu,a wani hade yake bare ta iya tsintar abinda zata iya tsinta din,tana nan zaune tsuru taji an dafa ta,ta waiwaya tana kallonta "Sannu,ke baquwa ce ko?" Sai ta sake kallonta sosai,baqar fata ce 'yar uwarta wadda a qalla zasuyi shekaru daya,amsa mata tayi,fuskarta sake ta nemi wajen zama kusa da sumayyan tana gabatar mata da kanta,kusan ita tayata zama har aka tashi suka taho tare,ashe basu da nisa saboda haka ta samu abokiyar tafiya tare suka taho,sunanta zulaiha ta sanar mata,itama baquwa ce a qasar bata kai shekara guda da zuwa ba.        Cikin satittika suka soma sabawa da zulaihan,anan take gaya mata dan uwan mahaifiyarta ke ruqonta,mamanta na aure ne a kano qauyen sumaila,itace autarsu,tana da shekara sha takwas mahaifiyar tata ta rasu,babanta na son yi mata auren dole,yayan mamanta shi yaji labari yazo ya dauketa,ya taho nan da ita inda yake sana'ar drivern taxi,da yake qasa ce ta neman arziqi,jama'armu da yawa musamman daga qasashe na afirka kan tafi neman kudi irin wadan nan qasashe,idan zamanta ya karbeka duk sana'ar da kake sai kaga albarka cikin arziqinka,sam ba zaka ce yana tuqa taxi ba anan musamman idan yazo gida nijeria,matarsa daya dansu daya.       Akwai banbanci tsakanin sumayya da zulaiha,zulaihan ta fita wayewa da gogewa qwarai,idan ka ganta ba zakayi tsammanin ga daga inda ta fito ba,mutumce mai son jama'a da faran faran,hakan ya sanya take da qawaye sosai,sai a lokacinne sumayyan tasan alfanun qawa da dadinta,musamman idan ka hadu da mai kyakkyawar halayya irin ta zulaiha mai sonka da zuciya diya,da fari sumayyan ta fara tababa kan yadda zatayi shiga ta fita ba irin wadda ta saba ba,zulaihan ita ta karbi kudi wajen anty dije ta rakata ta siyo irin sutturun qasar,wanda zaki sanya basu fidda tsiraicinki ba,wadanda zaka dace da zamani ba kuma tare da ka fidda tsiraicinka ka sabawa al'adarka ba da addininka baki daya,sau tari idan ta shirya zata makaranta laila kan tsokaneta "Wallahi anty sumy kin canza cikin watanni kadan,bakiga yadda kayan nan ke miki kyau ba,kamar ba sumyn malam ba,maman abdallah" anty dije na tayata "Kin rigani a fili na rigaki a zuciya,ta koma wata qaramar baturiya,haskenki ne kadai ba qarasa nasu ba,inaga ma kafin mu koma fa kim saje da su,kayan sun amsheki" ita kanta ta sani amma sai ta saki dariya "Ina wani kyau a kayan banasaren mutum anty,dadinta daya kawai basa fidda tsiraicin mutum" duk da haka bata bar hijabinta ba,don babu sutura mafi daraja a gunta irin hijabin,saidai duk sanda ta sanya kafin ta kai makarantar suna shan kallo ita fa zulaiha,har zulaihan kan ce "Ke kuwa sumayya ki haqura mana" "Babu abinda zai rabani da hijabi sai mutuwa,sai randa likkafani ya zama sutura ta ta qarshe" dariya zulaihan keyi "Nima wasa nake miki".        Wata baiwar qwaqwalwa Allah ya baiwa sumayyan,cikin wata biyu kacal harshenta ya fara juyewa,su kansu uncle farouq da anty dije mamaki suke,ganin tana ganewan ne ya sanya ya yanke shawarar sanyata wata makarantar dake training wa mata zamantakewar rayuwa,ciki harda nau'in girke girke na kowacce qasa,duk randa zakuyi girkin wata qasa tofa malamar 'yar asalin qasar ce,makarantar akwai tsada don ko ita anty dije ta burgeta,ba don tayi tsada da yawa ba itama taso shiga,amma tunda 'yarta ta samu tace ba komai ta dinga koya mata.         Watansu biyu da daddare uncle farouq ya kwashesu suka fice suga gari karon farko tun bayan zuwa,don sam bai da lokacin zama a gida,awa biyu kacal sukayi suka dawo saboda yana da aikin da zaiyi,suna gab da shiga gidan ya tuna dawowar qanin abokinsa wanda gidansa ke daura da nasu,sunje ganin gida ne shi da matarsa sai shekaran jiya suka dawo,baki dayansu suka nufi gidan don a gaisa,anty dije ta riga data sansu dama,mai gidan na girmama uncle farouq kasancewarsa abokin yayansa.        Gidane qarami kamar nasu,ga mamakin sumayya matar gida matashiya ce wadda kusan zasuyi sa'anni da ita,yaronta daya itama wanda ya kusa shekara hudu,nafisa asalin shuwa ce,tana aure da mijinta Dr auwal wanda qarin karatu ya kawoshi qasar,shekararsu biyu kenan,shekara biyu ya rage musu su koma gida,shekararsu hudu da aure,yaransu daya khalid wanda shima shekararsa hudun dai dai da shekarar aurensu,saidai har yanzu bata qara wata haihuwar ba,ita din ma karatu take,yanzu haka ta kusa hada degree dinta a fannin kasuwanci,abinda tafi sha'awa kenan tun tana yarinya,kusan gado tayi,sabida kasuwanci shine sana'ar mahafinta .         Ba qaramin dadi taji ba da ganin iyalan uncle farouq din,sai ta jita kamar a gida nijeria,nan kusa da su dama babu wani dan nijeria,duk a tsakiyar fararen fata 'yan asalin qasar take,tun kafin su tafi ganin sumayya sa'a take a gunta ta dinga fadin "Na samu 'yar uwa" "Lallai kam,wannan,ai sai kinyi da gaske nafisa,bata da son mutane,ga shegen qulafucin zaman gida,makaranta kadai ki fidda ta" "Zamu saba ai ko sumayya,zaki zama qawata" ta fada tana kallonta,tashin farko taji sumayyan tayi mata,nutsuwarta ta burgeta,murmushi sumayyan tayi "Insha Allah maman khalid" "Kamar gaske" cewar anty dije "Haba umman khalipha kada ki sage mana gwiwa mana" inji nafisan.         Sumayya kam ta gwada mata halinta,mutum ce mai yawan janye jiki ga baqin mutane,musamman wanda ta fuskanci rayuwa bata ajesu bigire guda ba,bata son sanya kanta inda zai zame mata matsala ko dana sani a gaba,ko kuma inda ya fi qarfinta,qwarya tabi qwarya haka nata ra'ayin yake,wanda ta gada ne daga wajen mahaifanta,mutane masu sanin daraja da qimar kansu,masu wadatar zuci da yakana,bata manta nasihan mama da kullum take gaya musu,kaso duniya mutane su qika,ka qi duniya mutane sai su soka,ka guji kwadayi,don shi din mabudin wahala ne,matuqar ka hau motar kwadayi to la shakka babu inda za'a saukeka sai tashar wulaqanci,mutunci yafi kudi,mutunci abu ne da idan ya zube qasa bai yiwuwa ka kwasheshi,mutunci abu ne da kudi ko wata isa basu iya siyanshi,ire iren wadan nan maganganu ke mata tasiri,takan zama mai tsantseni duk inda ta samu kanta,takan koma dora mutuncinta gaban komai nata.         Nafisa 'yar gata ce gaba da baya,itace auta a gidansu baya ga maza yayye da take da su guda hudu,ita daya ce diya mace qwal daya tilo da iyayenta suka haifa,hakan ya sanya take ganin gata,baya ga arziqi da Allah ya yiwa mahaifanta,nafisa irin mutanan nan ne masu son jama'a,sakin fuska da jan mutane a jiki,ko kadan ba zata taba yin wani aiki da zai nuna maka ga daga inda ta fito ba,saidai idan kai idanuwanka suka kai ka gani,tunda taga sumayya taji tayi mata,take jin ta samu 'yar uwar data rasa a baya,duk da cewa tana da tarin qawaye amma sai taji sumayyan ta zame mata daban.         Tun sumayyan na janye jikinta har ta saki jiki,nafisan ita ta soma koya mata cumputer,ta naqalceta sosai,itama halayen nafisan sun burgeta,yadda ta tsammaci halin masu kudi duka guda ne ashe ba haka abun yake ba,taga misali daga kan nafisa da kuma amira,a yanzu haka amiran ko yaushe na kan kiran sumayyan,har tana mamakin bata ganin kudin da take qonewa wajen kiran nata?,kullum nafisan na kan qorafi da mitar yadda sumayya taki sakin jiki da ita bayan ta dauketa 'yar uwa,kan hakan har tasowa sukayi takanas ita da mai gidanta suka zo suka kawowa uncle farouq qarar sumayya wai bata sonsu,wanda tilas hakan ya sanya ta soma sakin jiki da itan,shima mijin nata auwal da yake dan taya bera bari ne ya biye mata,akwai tsantsar qauna shaquwa da fahimtar juna tsakaninsa da matarshi,qauna ce mai yawa da tsafta tsakaninsu,wani lokaci idan sumayyan taje taga yadda ake zuba soyayya kunya kamata take,takan ce bari naje gida,bazan iya wannan badalar taku ba,dariya nafisa ke saki "Wallahi sister(haka take ce mata)sai kin fini tsula tsiya,bari kiyi auren" kyabe baki sumayya keyi "Wane aure,ai mu mun bar muku shi,mu da shi sai a qiyama" kalaman da sun jima suna daurewa nafisa kai,ga tsammaninta sumayyan budurwa ce bata taba aure ba,sau tayi yunqurin tambayarta sai kuna taja bakinta ta tsuke,ba kasafai take son yiwa mutum shishshigi cikin lamuransa ba,randa taga sumayyan na waya da abdallah a ranar ta kasa daure tarin tambayoyinta "Ke wallahi baki isa ba,kullum ki sani a duhu ki gudu,to yau kam sai kin gayan wace ke" nafisan ta fada cikin yin kicin kicin,dariya tayi mata "Wace kuwa ni din bayan sumayyan da kika sani" sakinta nafisan tayi tayi baya ta zauna "Shikenan tunda haka kika ce,na fuskanci baki daukeni yadda ni na daukeki ba,inda kin daukeni yadda na daukeki da ba zaki boyen komai dangane da ke ba,tunda dan uwa bai boyewa dan uwansa sirrinsa,naga har shawara nake dake sumayya kuma ina ganin haske cikin dukkanin shawarar da kika bani" shiru tayi ganin yadda fuskan nafisan ta nuna rashin jin dadi qarara,babu shakka dukkan wata qauna ta fisabilillahi nafisan ta nuna mata,bata shayi ko shakkar yin kowacce shawara da ita,ajiyar zuciya ta saki "Shikenam kiyi haquri mom khalid,yanzu ki bari naje gida na yiwa anty abincin dare kinga bata nan sun fita da uncle,amma na miki alqawarin idan na kammala zan dawo na baki labari na" sake hade rai tayi don ta nuna mata gaskiyan abinda take fada "Na amince saidai da sharadin idan kinzo nan gidan zaki kwana,tunda kin sani yau dadyn khalid bai gida kwanan makaranta zaiyi" dariya sumayyan ta bushe da ita ganin yadda ta hade rai tana mata muzurai kamar wadda ta hadiyi kunama "Idan anty ta barni zan kwana" "Zata ma barki saidai baki so ba" bata qara cewa komai ba ta miqawa khalid hannu dake kallonta,jira dama kawai yake tace su taho,wani shaquwa sukayi sosai da yaron,ganinsa take kamar abdallanta,ta sabi khalid din suka fice nafisa na binsu da kallo,murmushi ta saki tana jin dadi,jin sumayya take kamar ciki daya suka fito,Allah shike hada qauna da soyayya a tsakanin mutane har ma da jinsin dabbobi,haduwar jini wani abu ne na daban daga Allah.       Tana zaune kan sofar dake dakin baccin nafisan sanye da nata kayan bacci cotton masu kauri riga da wando wadatattu,khalid na saman cinyarta yayi bacci,hannunta na saman sumar kanshi tana shafawa don bai jima da yin baccin ba,lokaci lokaci takan daga kai ta dubi nafisa dake tsaye gaban madubi tana ta faman shafe shafe da goge goge bayan fitowarta daga wanka,mamaki duka ya cikata bacci akewa wannan hidima haka,gaskiya mana ko yaushe fatar nafisan kamar ta dan jariri,duk da fara bace choculet ce,har haqurin sumayyan ya qare ta tanka "Wai duka wannan wankan naki meye amfaninshi bayab wanda ake mawa baya nan mrs auwal kamar zaki sauya fata?" Murmushu tayi tare da ajiye body mist da ta fesa ta dubi sumayyan "Au sai noor yana nan sannan zanyi haka,ai ya riga da ya zame min al'ada ta" "To ai saiki bada himma,nikam na fara jin bacci,ina jin labarin nan bai yiwuwa sai gobe" ta fada tana gyarawa khalid kwanciya saman gado,da sauri ta zura 'yar saman rigar baccin nata ta qaraso inda sumayyan take itama ta haye gadon tana cewa "Sorry,na kammala,kema dab kike daki fara wannan sanaben ai" baki ta kama "Niii,rufan asiri,ku din dai sai kuyita yi,haka naga laila ma 'yar qwailarta da ita ta fara daukan course" dariya nafisa tayi "Wallahi da gaske nake,jiya na hau internet,naga D&G sunyo sabbin mai na gyaran fatar fararen mata,set ne harfa perfume,sure,da subulunshi,na riga ma da na siya miki,jiran isowarsa kawai zamuyi,a yadda suka ce gobe zasu kawo min" shiru tayi tana saurarenta,wannan wace irin qauna nafisan ke mata haka?,daga ganin abu babu wanda ta tuna sai ita din? "Am ready fa,ke nake jira" ta katsewa sumayyan tunani tana dubanta.        Gyara zamanta tayi bayan ta jingina jikinta da bango,a hankali ta soma warware mata wace ce ita,babu abinda ta boye mata,sumayya kuka nafisa kuka,babu wanda zai rarrashi wani,bala'in tausayin sumayyan ya kama zuciyar nafisa,yayin da sumayya ta tsokano wani danqararren tabo da dama har yau bai ida warkewa ba,janyo sumayya tayi ta kifa kanta saman cinyar nafisan tana ci gaba da kukan tana bubbuga bayan itama tana tayata ba tare da ta tsaidata ba,cikin zuciyarta taba cike fal da mamakin irin rayuwar da sumayya tayi,bata taba hasashen zata iya yin rayuwa irin wannan ba,shi qunci da matsin rayuwa gami da QADDARA hadi da JARRABAWA kenan babu ruwansu da girma ko qanqantar shekaru?. Sai da zuciyarta ta samu salama sannan nafisa ta soma magana "Ashe akwai irin wannan rayuwar a duniya?,rayuwar da mutum mai kimanin shekaru kwatankwacin nawa zaya fuskanceta da tsanani har kamar haka?,na jinjina miki sumayya,Allah ne kadai yasan me ya tanadarwa rayuwarki,irin wannan yarda da qaddara da karbarta hannu bibbiyu bau tashi a banza,Allah ya jiqan mukhtar ya raya mana abdallah,kici gaba da haquri,amma kada ki sake hasashen ba zaki sake yin aure ko jin dadin rayuwarki ba,kin sani kowanne bawa da yadda Allah ya tsara masa zai rayu,dole kowa ya rayu bisa tsari da doron da mahalicci ya QADDARA,kici gaba da addu'a,zan tayaki da yardar mai duka,yayi miki zabin kyakkyawar rayuwa,ya cire dukkan qunci da damuwa da kika taba tsintar zuciyarki a ciki",ta jima tana fidda hawaye masu dumi wadanda suka dinga wanko zafi da radadin dake cikin zuciyarta maganganu ta dinga bata masu kwantar da hankali har ta samu nutsuwa cikin zuciyarta. Washe gari ta tashi fuskarta ta dan tasa saboda kukan data raba dare jiya tana yi,baki daya nafisa sai ta damu tana ganin kaman laifinta ne,murmushi sumayyan ta dinga tana girgiza kai tana qoqarin nuna mata ba laifinta bane,dole ne ga duk mutumin da yake da miki cikin rayuwarsa ya koka duk sanda wannan ciwon ya motsa. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [23/02, 11:51] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 6⃣7⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* Allah madaukaki yana cewa *duk wanda ya sallamawa Allah dukkan lamuransa alhali yana mai kyautatawa haqiqa yayi ruqo da igiya qaqqarfa wanda bata tsinkewa(yankewa/rabewa)* _____________________________________         Wuni nafisa tayi ta kasa sukuni da tausayin sumayya,a haka auwal ya dawo ya taddata,baki daya wani qaunarta na sake shigarta,haqiqa bata yi zaben tumun dare na aminiyar qwarai ba.          Washegari da kanta taje gidan anty dije dauke da ledar mayuka da turarukan data siya matan,dariya sumayyan ta dinga tana kallon tarkacen kayan,ko ba'a fada mata ba tasan cewa sunfi qarfin mai rangwamen gata irinta,saboda zuwa yanzu kanta ya soma budewa,tana iya gane abu mai tsada,balle ta san nafisan sarai,komai nata designer ne,kuma komai nata a set dinsa take amfani da shi "Wai kina nufin ni kike so na dinga amfani da wannan kayan?" "Qwarai kuwa da wace?" Kai ta kada tana dariya "So nake naga kin sauya sis,so nake naga kin fara sabuwar rayuwa" kai taci gaba da kadawa tana dubanta,kafin tace wani abu anty dije ta shigo dakin,kayan ta dinga dauka tana dubawa tana dariya "Allah yasa a baki hadin kai" "Idan ma taqi ina kallon fatarta zan gane,don sun tabbatar min suna da kyau,suna gyara fararen mata" itama ta fadi tana dariyan,godiya anty dije ta taya sumayya,sun jima suna hira kafin nafisan ta koma gida don dora abincin dare,don auwal baison take away idan ba lalura ba ta kama.         Anty dije ke jinjina tsadar kayan "Bansan ya zata kaya ba idan kayan suka karbeki ba,suna da kyau amma akwai tsada" cewar anty dijen. Kiran wayar daya shigo wayar sumayya ita ta katse hirar da sukeyi din,fuskar ta washe baki bude take fadin "Amiran baabaa ce anty" "Kice ina gaidata" inji anty dije tana miqewa don ficewa daga dakin ta fara jiyo hayaniyar minal da khalipha da alama rigima suke shi da ita "Autan baabaa(haka take kiranta idan taso tsokanarta)" "Mutanen uk,wai nikam yaushe zaku dawo,nifa na gaji wlh daga gida sai makaranta,ni daya kamar mayya,idan bakuyi wasa ba fa zaku ganni wlh na biyo sahu" dariya sumayya ta dinga yi ganij dududu watansu nawa ma da tahowa "Kamar yaune fa zaki ga mun dawo din,yi haquri takwara" dariya sukayi baki daya sannan suka soma taba hira,amiran na bata labarin abubuwan da suka faru bayan tafiyarsu "Amiran umman khalipha,baabaa fa ya karbi kudin aurena har da sa rana watanni shida masu zuwa dai dai sanda zan kammala degree dina" ta fada cikin nuna farinciki,cikn zumudi sumayyan tace "Kai haba dai takwara" "Wallahi amira,amma nikam tsoron yin auren nan nakeji takwara,duk da saifullahi na matuqar sona da qaunata,hakanan na amince da tarbiyya da halayyarsa" gefe daya na zuciyar sumayya itama jimamin da take mata kenan,saidai ba lallai abinda ya samu dan uwanka kaima ya sameka ba,kowa da tashi kalar qaddarar,bare amiran ita ba mai mata zata aura ba,ita daya ce a gunsa "Meye wani abun tsoro?misali su ummee da sukayi auren su wani abu kika ga ya samesu?" Kai ta kada kamar tana kusa da ita "Um um,kawai banson rabuwa ne da gida,ina son family na" "Ba shakka familynki abunda zaka yi marmari da begensu ne idan ka barsu,duk wanda ya kalli yadda kuke son juna ba zaiyi mamakin haka ba" sumayya ta zantawa ranta,amma afili sai ta bagarar da zancan da nuna rashun muhimmancinsa "Duk mace 'yar wani gidan ce,ko su su ummeen ce miki akayi gidanku ne gidansu,suna nasu familyn fa suka baro ko?" Sai amiran ta qyalqyale da dariya "Kinji umme tace ah to,ashe taji me kika fadi,kinsan abinda anty maamaa ta gama gayan kenan dazu" itama dariyan tayi,ta shiga tsokanar amiran "Kawai kice mu fara shirin baki,ina ga ba zamu wuce wata guda da dawowa ba zamu shiga hidima,ummm,bari na gayawa anty dije mu fara taru" "Ahto,don kune amarori,shi yasa na dage saidai asanya wata shidan,daa qasa da haka za'a saka,nasan kafin sannan kun dawo"ci gaba da tsokanarta sumayya tayi a haka suka rabu cikin barkwanci. Bayan ta aje wayar ta samu anty dije na sauyawa minal kaya da alamu bata wadancan tayi don ba'a jima da yi mata wanka ba " nikam saura qiris na sauya qawa,wannan qawa tawa qazamiya ce"sumayya tayu maganar tana duban minal tare da yamutse fuska "Yadai fi wallahi,duk gidan nan babu mai bata kaya kamar nata"inji anty dije,fuska ta kyabe tana shirin sakin kuka " na daina anty,wayyo Allah na"ta fada tana bubbuga qafafunta zata hau bori "To shikenan,ya isa,ai ke qawata ce ta amana,babu mai rabamu,uwata ce fa ta kaina" sai ta soma dariya tana tsallen murna sumayya na dubabta tana murmushi,duk yaron data gani tuna mata yake da abdallahnta,dauke kanta tayi ta maida ga anty dije "Anty an sanya bikin amira fa,wata shida mai zuwa" sakin maballin da take ballewa minal tayi dama ta kusa gamawa ta juyo tana duban sumayya "Tabdijan,kice akwai gangami kenan,bikin auta guda?,bikin amira ni 'yasu?" Antyn ta fada cikin jinjina lamarin,kai sumayya ta gyafa tana nade qafafunta saman gado tana murmushi "Jar uba,kice abuja zata motsa,familyn baabaa prof za'ayi bikin da aka jima ba'ayi kamarsa ba,to ai ina ga da na su mahmoud za'a hada tunda suma wata bakwai ne inaga yayi saura cikin ranar auren da aka sanya musu ko,Allah ya nuna mana,sai mu fara shiri tun yanzu,sumayya kuna da biki" inji anty tana murmushu gami da jinjina kai "Wallahi anty haka tace,ni kam mai zan iya cikin hidimar,ni da ban taba bikin qawa ba?" "Aikuwa dole ki ware ayi komai da ke,yadda amira ta daukeki kada kuce zaki watsa mata qasa a ido,nasan halayyarki sarai" dariya sumayya tayi ganin yadda antyn ta camfata tana kwantar da kanta saman filo "Allah ya bamu iko to anty" kan ta gama rufe bakinta kira ya shigo wayarta,lambar alqasim ne,tana mamaki da har yau bai rabu da ita ba,bayan ta zayyana masa ita din bazawara ce har da yaro,sai ta latse wayar ta kasheta baki daya tana jan qaramin tsaki ta gyara kwanciyarta abunta,ita yanzun babu mai daga mata hankali,ko lukman idan ya kira sai taga damar dagawa,darajar yaranshi dake sonta kawai take dubawa,badur rahman je kadai ke da wannan qinar na daga kiransa a duk yayin da ya kira din.         Cikin qanqanin lokaci da fara amfaninta da mayukan da sabulan taga banbanci,ita a karan kanta taga sauyi,wani laushi da santsi fatarta ke sake yi tamkar wadda ke zuwa gyaran jiki,baki daya qamshin jikinta ya sauya zuwa wani qamshi na musamman ma daban wanda ya kama kayanta sabida turaren da take amfani da shi set na man da sabulun,cikin watannin da basu gaza biyu ba sumayya ta sake komawa wata ta daban,komai nata ya sauya,sau tari laila na tononta tana cewa "Wlh anty sumayya kin koma 'yar gayu" hakan ya yiwa nafisa dadi qwarai a ranta,bisa dukkan alamu zata cimma qudurinta cikin sauqi kan sumayyan,tana son sumayyan ta zama wani sashe na familynsu,dukkanin halayyarta sun mata babu na yarwa. *******     *******    ********          Yau da gobe kayan Allah,sannu a hankali kwanaki ke mirginawa suna wawasar kwanukanmu a duniya,da kuma kwanakin dukkan wani abu da muka sanya masa lokaci,zuwa yanzu su sumayyan na da watanni takwas cikin qasar ta uk,ba qaramin karba qasar ta yiwa sumayyan ba,bugu da qari kuma ga nafisa daga gefe data kafe kai da fata zata sauya sumayyan malam din zuwa wata sumayyan ta daban,sumayyan uk,qudirinta kuwa ya karbu,a yanzu idan kaga sumayyan zaka sha mamaki,komai nata ya sauya,wani irin kyau da da can yake boye a yanzu ya soma bayyana kansa,hutu jin dadi da kwanciyar hankali suma na bada tasu gudun mawar,hatta da anty dije kan kalleta mafi yawancin lokuta,dadi take ji cikin ranta da ta sanadiyyarta sumayyan ta soma samun canjin rayuwa,ashe da can damuwa rashin kwanciyar hanakali da tension ita ta tasamma kassara sumayyan da gurgunta tunaninta,a yanzun kai baka ce sumayya bace wadda ta taba aure,'yar shekara ashirin da biyu har da yaro ba,sai kayi zaton tana cikin shekararta ta sha shida ne,tun da can Allah ya bata sanyin murya nutsuwa da iya magana,sai abun ya sake zame mata ado,zakayi zaton daga wani babban gida ta fito.        Gefe daya karatun ta ya kankama haiqan,turanci ba damuwarta bane a yanzu bare hausa,mai gaba dayan larabci dama ya jima da zama kan harshenta tun tana qanqanuwarta,tana daya daga cikin zaqaquran ajinsu a yanzu,zaka yi mamakin yadda harshenta ya karye,tana karbar karatunta da kyau,tuni wata daya baya ta kammala makarantar koyon girki da mu'amalar yau da kullum,ta fita da cetificate mai kyau,a yanzu kusan anty dije ta zama 'yar kallo ta fannin kitchen,kowacce rana da kalar abincin qasar da sumayyan zata girka,uncle farouq da taya bera bari shike basu kudi suje suyi siyayyan kayan da za'a buqata a ranar tunda shi bai sansu ba,laila ce 'yar rakiya,kai na rawa zata bita suje,zuwa yanzu ta sake tana iya zuwa gurare wadanda ke kusa da su ba nisa can ba,idan kuma suka so yin nisan nafisa ce jagora,zata debesu guri guri da yake ita din tamkar 'yar gari ce a garin,ranar haka zasu wuni a waje,sau tari sumayya na noqewa saboda ganin yadda nafisan ke kisan kudi idan sun fita amma taqi bata dama,duk abinda ta siyawa kanta sai ta saiwa sumayyan duk tsadarshi,dole tayi surrender ta tabbatar Allah ne yayi wannan hadin tsakaninsu. *******     ********    *******      Kamar ko yaushe yau ma tafe suke su shida,nafisa,sumayya,laila,khalipha,sai minal da kuma khalid dake riqe a hannu,ganyayyakin abinci suka sayo daga can suka wuce suka sha coffe a wani gun shan coffee dake daura da gun,zasu hau bus nafisa ta hana,a qasa suka dinga takowa tana nuna musu gurare tana musu bayani,sosai yanayin ya yiwa sumayya dadi qwarai,murmushi kawai ke tashi a fuskarta,sanye take da dubai abaya wadda tayi mata cif a jiki,ja ce mai dan turuwa kadan,bata yi amfani da mayafin rigar ba saboda yayi mata qanqanta,sai ta yafa wani medium vail dark blue wanda ya lullube har kafadarta.       Idan ka kalleta dole ta burgeka,murmushin dake tashi kan fuskarta kawai abun sha'awa ne,kayan sun haskata matuqa,khalipha da minal da laila sunyi gaba abinsu suna ta tsalle tsallensu laila na qoqarin saitasu,ita da nafisan ke ci gaba da takawa a hankali suna hira tana bata labarai.        Maganar da nafisan ta fada ta sanyata juyawa tana kallonta dariya ta kubce mata,sam bata lura da gabanta ba ji tayi ta bangaji abu,taga taga tayi zata fadi murya a sama taji ance "Hey!" Tare da riqo hannunta,tashin farko ta gigice,abubuwa biyu cikin lokaci daya suka hargitsa ta,walainiya idanuwanta suka shiga yi zuciyarta na bugawa,man ne,mustapha,sanye cikin three pieces slim fit suit navy blue wadanda sukayi matuqar yi masa kyau tare da fidda sigar kyawunsa,idanuwansa saye cikin sun glasses,ya kafeta da tsinin idanuwanshi duk da bata iya hangosu fes amma tana ganin alamunsu,jikinta ya soma rawa sanda ya saketa sai ta sake tafiya zata fadi nafisa ta tarota tana fadin sunanta,tsaye yake qyam yana dubanta,duba mai dauke da bacin rai,tuni baturen dake tare da shi ya kammala tsince wayoyinshi da suka zube qasa yana masa sannu cikin harshen nasara,dauke idanuwanshi yayi ya maida kan wata rantsatstsiyar baqar mota data faka a gabanshi,qaramin tsaki ya ja sannan ya juya cikin takunshi ya nufi inda motar take,da alama dama ita yake jira,baturen ya mara masa baya cikin hanzari ya bude masa mazaunin baya kafin shi kuma ya shiga gaba,jan nafisa ta soma yi jiki na rawa tana waiwaye har suka shige motar suka tayar suka bar wajen. Waiwayowa tayi inda nafisa ke tsaye bayan ta cikata,sai ta tsinci nafisan na kallonta "Waye wannan sumayya?" Ta jefo mata tambayar ba tare da ta shirya ba,boyayyar ajiyar zuciya ta saki gabanta na bugawa,hakanan Allah ya dora mata wani tsoronsa "Nima ban sanshi ba" ta fada tana ci gaba da jan nafisan don su bar wajen,batasan me zata ce mata din ba,saidai baki daya gwiwoyinta sun sare kamar an doke mata su,kamar qafarta ba zata iya kaita gida ba "Taya zaki ce baki san ko waye ba bayan na shinshino alamun sanayya tattare da ke?" "Kiwa Allah kada ki qara tambayata,don ban sanshi din ba" "Ala kyauta" nafisan ta fada ba tare data sake tambayar tata ba,haka suka isa gida tamkar kurame. Cikin sanyi jiki ranar baki daya ta wuni,girkin ma data fita ta sayo ingredient din bata iya yinshi ba,ta cewa anty dije bata jin dadi,sai ta koma daki ta kwanta kawai lamo,bata fadawa anty dije ga wanda ta gani,to tace mata me?,tace taga wa?,meye hadinta da su da zata sanar mata haduwarsu?,ta tabbata su laila basu ganshi ba tunda bata ji sunyi maganarsa ba. ******* ****** ******** Sannu sannu kwana nesa,yau da gobe kayan Allah,sai gasu sumayya sun fara hada komatsansu waje guda,wasu suna aikowa da su nijeria wasu kuma suna faka su waje daya,wata daya ne ya rage musu wa'adin zamansu a qasar ya qare,wato sati hudu zuwa biyar masu zuwa zasu bar qasar,tuni nafisa ta soma qaguwa suma su koma gida,ta fuskanci lallai idan su sumayyan suka barsu qasar sam ba zata ji dadin zama ba,zulaiha ce abar tausayi,wadda Allah ne yasan ranar komawarsu,zata yi kewa ba kadan ba,saidai tilas ta haqura. Hutun sati guda uncle farouq suka samu,hakan ya sanya suka zauna sukayi dukkanin lissafinsu na abinda zasu saya wanda zai musu amfani,ranar da daddare suka shirya zuwa wani katafaren mall wanda ke saida dukkan wani abun buqata,kama daga mai qaramin kudi zuwa mai babban kudi,duk wani abu na amfanin dan adam,sutura zuwa abinci da abunsha suna saidawa a wajen,basa bude gurin sai qarfe shidda na magariba har zuwa tsakiyar dare. Uncle farouq ya kira ya buqaci taxi da zata kaisu ya bada adress dinsa,cikin mintuna qalilan ta iso,shine zaune a gaba shi da minal,su kam suna baya,hira suke sosai cikin motar,wanda ita bata ma san me suke cewa ba saboda tana amsa wayar abdur rahman ne,bayan ta kammala ta maida wayar jaka,dubanta anty dije tayi cikin salon tsokana "Nafa lura kwanaki biyun nan ana dasawa da abdur rahman,ko yaushe cikin waya,ko dai da shi za'ayi ne?" Kunya ta bata saboda uncle farouq dake cikin motar,sai ta kasa magana ta saki murmushi kawai,dariya ya danyi yana daga gaban motar yace "Allah dai ya zaba abinda yafi alkhairi kurum" "Amin" cewar anty dije. Ta kai kimanin aqalla minti ashirin tana nemansu cikin katafaren shagon bata gansu ba,ta duba anty dije da uncle farouq babu su ba alamunsu,tuni ta soma tsurewa,ta ajjiye kwandon dake hannunta ta soma laluben hanyar fita nan ma ta kasa ganeta,qwalla ta cika idanuwanta jikinta ya soma rawa,ina yaran sukayi?,ina su anty dijen suke?,idan ta rasasu ta yaya zata iya komawa gida?,wannan tunanin ya sanyata qara sauri,data fita daga wannan bagaren saita fada wancan saidai ko qyallinsu bata gani ba. Wani irin burki ta taka wanda ba don tayi saurin dakatawa ba babu abinda zai hana su yin karo da juna,dubanta yake kamar yadda take dubansa,kamar ko yaushe fuskar nan a murtuke babu walwala,kai kace bai taba dariya ba a duniya,gabanta ya shiga faduwa kamar kullum,ji take kawai tata ta qare,ta rasa da mutumin da zata hadu sai da wannan?,kamar yadda al'adarsa take,saye yake da suit qirar company dolce anda gabbana baqaqe,hannayensa saye cikin aljihunsa kai kace babu abinda yazo siya,daga ita har shi babu wanda ya motsa,ita bata wuce ba tana kallonshu,yayin da shi kuma ke duba turarukan dake jere reras yana karanta sunayensu daya bayan daya,tuni hawayen da take adanawa suka soma samun hanya da zuciyarta ta raya mata su anty dijen sun bace mata fa,wata qila ma sun bar mall din suna nemanta suma,tattaro ragowar qarfin ta tayi da niyyar rabewa ta wuce don yana tsaye ne tsakiyar hanyar,ya raba hanyar gida biyu. Hannunta guda daya taji an riqo,wata zabura tayi ta waiwayo qirjinta kamar zau fado,taushi da laushin tafin hannun nashi na ratsa jiki da jijiyoyin jininta,bai ko dubeta ba ya soma jan hannun nata,bata da wani qwarin gwiwa da qarfin da zata qwace,ko wacce gaba ta jikinta an zare mata laka,abu daya zuciyarta ke raya mata,yau tata ta qare,don wannan mutumin babu alamu na imani ko tausayi tattare da shi,Allah ne kadai yasan me zai aikata,hawayenta suka qaru tana biye da shi tamkar raqumi da akala. Wani farin ciki ya mamayeta saboda hango su anty dije da tayi su da yaran bangaren kayan yara,a hankali ya zare hannunshi cikin nata tare da juyawa ya barta a wajen,sai ta waiwaya tana duban yadda yaje tafiyarsa ba tare ko ya sake waiwayowa ba "Laaaaah,ga anty sumayya can,yaa mustapha ne ya kawota" cewar khalipha wanda shi daya ta hangi isowarsu gun,tuni mustapha ya bace a gun,anty dije ta dago tana dubanta,sai kuna tayi turus ganin hawaye fuskar sumayyan "Lafiya?,ke kuma me aka yi miki?" "Amma anty nayi tsammanin kun tafi fa,idan na bace nan gun wa zai maidani gida?" Dariya ma ta baiwa anty dijen ganin yadda sabbin qwalla ke sake saukar mata "Kina nufin har yau da sauranki sumayya?,ta yaya zamu taho da ke mu koma babu ke?,bakiji sanda nake gaya miki kici gaba da siyayyarki ba zamu zo nan gun ki samemu wajen biyan kudi?,to don Allah ya ma za'ayi ki bace wajen da duka ko ina cctv camera,an fada miki nan irin nijeria ce?,ti waye ya rakoki?" Ta rufe maganar tana dariyar wautar sumayyan ciki ciki,kafin ta amsa khalipha ya bata amsar tambayar "Hala yaganki kenan kina kuka kamar qaramin yaron da ya bata" laila sau ta sanya dariya,harara sumayyan ta maka mata don kusan itace ta sanya bata ji sanda anty dijen tace mata suna zuwa ba,isowar uncle farouq yana dariya ita ta tsaida dramer da akeyi "Tom,musty yace mu kula,ya lura yarinyar nan sakarai ce,kada ta janyo mana abinda za'a kamamu kan mu bar qasar nan,kinsan su mai jan kunnuwa akwai kula da haqqin dan adam" dariya suka sanya shi da anty dijen yayin da wani abu ya tsayama sumayya a wuya,ita za'a kalla a cewa sakarya?,aikin banza ita tace ma ya kawota da zai gaya mata magana,ita kadai ke masifarta cikin zuciya ta qulu ta cika tayi fam,siyayyar da bata qara darawa nan da can ba sai anty dije ce ta qarasa zabar mata abinda taga ya dace,gani take ko ya ta matsa zasu sake yin clashing da shi. Sai da suka shiga mota sannan ta dubi anty dije,shaf ta manta cewa sunyi zata bata kudin da baabaa ya bata randa zasu taho zata siyawa amira wani abun a gift din biki "Anty,banfa daukawa amira komai ba" "To me za'a siya mata,su fa irinsu komai suna da shi,amma ki bari idan mun koma gidan kwayi shawara da nafisa sai ki siya mata abinda ya dace" "To" ta fada tana jingina da kujerar cikin mutuwar jiki hannayenta runguma a qirjinta. Da sukayi shawara da nafisan sai taga kawai tayi mata danginsu humra,turaren wuta na daki kaya dana tsuguno,collucture tana ganin zasu burge,shawara kam tayi mata,tasan amiran kuwa da jarabar son humra,akwai wani company wadanda ke qera crystal kala kala masu azabar kyau,nafisan tayi oder din kwalaben da sumayyan zata zuba kayan idan tayi,batasan da su ba sai kiranta nafisan kawai tayi ta nuna mata bayn an kawo,kwalaben humra kadai saiti uku uku sai data siya saiti bakwai kusan kwalaba ashirin da biyar,haka ta turaren wuta da wasu dogaye da za'a zuba collucture,kwalaben kansu abun kallo ne,wani irin design aka yi masu masu matuqar tafiya da hankali,kasa magana sumayya tayi,karamcin nafisa ya girmi qwaqwalwarta,sai ta zauna akwai tana kallon nafisan ita kuma tana murmushi,baki ta bude da niyyar hada kalmomin godiya sai tayi hanzarin tararta "Kada kice komai,kada ki godemin,nima gudun mawata na baki ki baiwa qawarki,duk da bamu taba haduwa da amira ba amma tana da kirki iya gaisawar da muke,kuma taci darajanki sister", anty dije kanta rasa me zata ce tayi,sai albarka take sanya mata tare da fatan dorewar zumuncinsu da addu'ar kade fitina,cikin kaya suka shirya kwalaben yadda ba zasu fashe ba. ********* ****** ******** Randa zasu koma nijeria nafisa na tare da sh,ita da auwal suka suka rakasu har airphort,jirgin dare zasu bi,batasan me ya sauya lokacin tashinsun ba,don da taji uncke farouq na fadin jirgin safe ne,tuni sukayi sallama da zulaiha,har kuka sai data yi,ji take kamar tabi sumayyan,to itama din nafisan tuni ta narkewa auwal ta soma masa qwalla,khalid kuwa ba'a magana jiki duka ya mutu,ya fuskanci anty sumayyan tafiya zata yi ta barsu,ai kam ashe kuka na gaba,sai da suja zo tafiya auwal ne ya janyeta yana rarrashinta "Is ok dear,muma fa nan da wata daya zamu koma keye ya rage ne?,wata dayan kwanaki nawa ne?,haba momyn khalid,goge qwallar khalid na dubanki" da qyar ta tsaya sukayi sallama auwal yayi dabarar dauke khalid sannan nafisan ta biyo bayansu. Mamaki ne ya kama sumayya ganin su a VIP wannan karon,tasan dai ba'a VIP din suka zo ba,sai tayi zaton ko daga gwamnatin tarayyar ne,abinda ta lura kuma da shi shine iya su kadai ne,baki ta tabe don batasan meke faruwa ba ta fiddo wani littafi da nafisan ta bata ta fara duba shafin da take,don son bata sha'awar yin hira yau,kewar zulaiha da nafisa take,ba shakka sabo turken wawa,karatun ya soma yi mata dadi,yayin da wani qamshi mai taushi ya dinga shiga hancinta,qamshin yayi mata,sai ta lumshe ido tana jin yadda ke ratsa qofofin hancinta,sai tayi tsammanin wani abun ne a cikin jirgin,lol "Barka da dare uncle" taji su laila na fada,cikin mamakin yadda lailan mai shegen rawar kai da surutu ke magana a kintse ya sanyata ajiye littafin ta dago kai da niyyar tsokanarta,so tayi tace "Allah ya nuna mana ma'aiki yau laila ke magana cikin nutsuwa irin haka?"sai maganar ta maqale mata,zaune yake kujerar dake bayanta wadda ke daura da mazaunin uncle farouq,magana suke qasa qasa da uncle farouq din,idanu suka hadu,da hanzari ta juya ta maida idanuwanta mazaunin gabanta,qirjinta na bugawa da sauri,ta rasa wannan wace iriyar masifa ce haka,ba dama ta ganshi yanayinta ya burkice,anya ma ba maye bane wannan mutumin,sanye yake da fararen suit qal wadanda suka dace da takalminsa,yayi kyau cika da wani irin kwarjini,bata san me ya shigo da shi jirgin da zashi nijeria ba,idan bata manta ba anty dije ta gaya mata gun aikinsa na dubai " matsa man sumayya,ina ta magana tun dazun kamar wata kurma"anty dije ta fada tana tsaye kanta,jiki babu qwari ta matsa din anty dijen ta zauna tana bude zip din jakarta tace "Kun gaisa da mustapha ne?,wannan karon zashi nijeria ba lokacin zuwansa ba,nasan baabaa zaiji dadi,dan gaban goshi zaizo,diyar ambassador din nijer anan ya dubawa aikin da yayi mata a dubai,baban nata abikin baaba prof ne sun taba aiki tare" kanta kawai ta kada ba tare data iya amsawa ba,bata ma ga mai ya hadata da wannan sharhin ba,giyar qaunar ahalin baabaa ta kama su anty dijen sosai,ko da yake babu abinda KARAMCI baya iya maida maka mutum ta raya a qasan zuciyarta "Kinga muma yau mun dana,gamu a VIP,mustapha yayi abinda ya saba" ta fada tana dariya tare da qoqarin kashe wayarta,duk maganar da anty dijen keyi bata fahimtarta,zaune take kurum,ta rasa abinda yasa jikinta sam baison hada inuwa daya da shi,ta tabbatar da cewa taqi jininsa ne tun ranar da ya yarfa ta gaban tarin jama'a,har yanzu tana iya jin zafin abunda yayi mata,baka san waye mutum ba,bakasan wanne yana yi yake ciki ba amma kayi masa haka amatsayinshi na dam adam irinka?,itakam jin anty dije kawai da take yaba kyawun halayensa,eh,ta yadda da mutunci da karamcin ahalinsu amma bata jin shi yana ciki. Laila ta sake taimakawa wajen dagula lissafinta data nace da tabata kan sai ta juyo taga abinda take nuna mata cikin laptop dinta "Idan ba zaki iya kalla ke daya ba zan karbi abata kinji ko?" Hakan data gaya mata shi ya sanya ta sarara mata. Mintuna arba'in kowa ya nutsu a kujerarsa yana abinda zai fishsheshi,duk yadda ta kai ga matse fitsarin da take ji amma yaqi sarara mata,ta fuskanci ya zame mata dole tayi,ko kusa bata son tashi daga inda take,saboda matsawar zata shiga bandakin tofa sai ta gifta ta kusa da su,a hankali ta waiwaya sai taga baki daya ya aza hankalinsa ga system,hakan ya bata qwarin gwiwa ta miqe anty dije ta matsa mata ta wuce,cikin sanda kamar wata barauniya haka ta wuce,baima san da wucewar wani a gun ba har ta gama fitsarin ta dawo. Daidai lokacin da yake magana da uncle farouq cikin nutsuwa,muryarsa ta shiga dodon kunnuwanta,ya salam,muryar mukhtar take ji muraran cikin tashi muryaf,ya ilahi wannan kamanceceniyar murya dame tayi kama?,ta tabbata abinda take ji yana da nasaba da muryar mukhtar dinta wanda ko wanne lokaci yayi magana tuna mata da shi yaje,ji take kamar shine a raye a kusa da ita,har marmari take taji ya furta wani abu. Dumi da taji yana ratsa rigarta da qarar fasgewar cup shi ya ankarar da ita karo da tayi da daya daga cikin 'yammatan ma'aikatan dake kara kainam baiwa kowanne passinger abinda yake da buqatar ci ko sha,baya tayi jikinta na rawa yayin da itama budurwar tayi baya tana baiwa sumayyan haquri cikin harshen nasara,a qa'ida sumayyan ke da laifi,saboda tayi qoqarin kauce mata amma sai data bugeta,iya tafi da custumer nasu ya sanya take bata haquri tare da bata hanya ta wuce ko kuma ta koma toilet ta wanke hadaddiyar doguwar rigar shadda dake jikinta wadda sabuwa ce kar ranar ta soma sanyata,lemon green da aka yiwa adon orange,mayafin data nannada saman kanta shima orange ne,ba tare da wani dogon tunani ba ta wuce zuwa mazauninta sabida ta kasa tantance me ya kamata ma tayi. Qarasawa tayi dauke farantin da pieces glasses din cup din tana baiwa mustapha haqurin bari ta sake kawo masa wani,sai a sannan ya daga kansa daga abinda yake yi din,kallon da yayi mata ya rudata,sai ta fara yi masa bayanin ta kawo ne sukayi karo da madam ya zube,da hannu ya tsaidata yace taje kawai bai buqata,haquri ta bashi sannan ta juya,ya fahimci me ya faru,don yana iya jiyi anty dije na tambayar bata qone ko taji ciwo ba ko?,tsaki yaja qasan ranshi yana ayyana anya tana da lafiyan qwaqwalwa kuwa,haduwarsu ta farko ya tuna,sannan ya gangaro haduwarsu ta biyu,haduwarsu a mall da girmanta tana wani hawaye shabe shabe kamar 'yar yaye,sai kuma yau,yaso tambayar alhj farouq sai kuma ya tuna ba abunda ya shafeshi bane yaci gaba da harkansa,amma ya barwa ransa akwai wani abu a qwaqwalwarta don bai taba ganinta a nutse ba. #mrs muhammad ce *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [23/02, 11:51] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 6⃣8⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* Allah yana cewa *(RANAR QIYAMA YAYIN DA AKA BAWA DAN ADAM LITTAFIN DUKKAN AYYUKANSA ABINDA YA AIKATA SANDA YANA RAYE ZA'A CE DA DAN ADAM)KA KARANTA LITTAFINKA!!!,YA ISHEKA AKAN KANKA KA YIWA KANKA HISABI* ya subhanallah,ya rahmanu kada kayi mana hisabi ka yafemu. ____________________________________ TEAM ABDUR RAHMAN YA DA SAURIN KARAYA IRIN HAKA NE,NAGA HAR KUN FARA SAREWA FA,ITA FA MACE ALLURAR CIKIN RUWA CE MAI RABO KA DAUKA,KADA 'YAN ADAWA SUYI MUKU DARIYA FA,TAM. _____________________________________ Bata sake yunqurin tashi ko motsawa daga wajen ba har zuwa sanda suka iso qasa nijeria,anty dijen na lura da ita,ta kuma kusa ankarewa da dalilin gushewar nutsuwarta,daya daga cikin motocin alfarma dake mallakar mustaphan ita tazo ya kwashe baki daya,kallo daya zaka yi musu ka tabbatar sabuwa ce dal,laila sai bude baki take saboda yadda motar tayi mata dadi,qasa qasa take cewa da sumayya "Anty sumayya dama kada aje gida don kada mu sauka daga motar nan,dadi wallahi" dariya ta baiwa sumayyan har sautin murmushinta ya fito,hada idanuwa sukayi sanda ya waiwayo yana tsammanin ko wani abun ne ya sake faruwa,da sauri ta kawar da kanta tana gintse dariyar. Kowa na ficewa daga motan yayin da yake zaune baiko da niyyar motsawa,amma ta danganta hakan da cewa shi za'a shige da shi cikin gida ne tunda su zasu sauka ne su shiga nasu gidan,tsoron ta yadda zata giftashi ya kamata,duka sun fice saura ita daya,a hankali ta durqusa zuciyarta na bugawa har ta isa bakin qofar inda anty dije ke tsaye tana tsumayin fitowarta din cirar maqullin gidan dake jakar sumayyan,daidai sanda ya fara magana cikin izza da nutsuwa yana baiwa driva umarnin su wuce ciki,kadan ya rage ta fadi anty dije ta tallafeta tana dubanta cikin salon tuhuma "Wai mene haka sumayya lafiyanki kuwa" "Bab....babu komai,qafata ce ta harde" bata ce komai ba ta karbi maqullin sannab suka jera zuwa cikin gidan "Ya kamata ki sanyawa ranki nutsuwa,na fuskanci duk sanda mustapha yayi magana saiki rasa sukuni da nutsuwarki,bafa mukhtar babe,bai kuma san mukhtar ba,kada ki sake ki sake aikata irin gangancin da kika aikata" da sauri ta dubi anty dijen,ya akayi ta karancin halin da take ciki,itama bata sani ba,batasan dalilin da yake sanyawa take kasa controlling kanta ba aduk sanda taji muryarshi wadda ke zubi sak data mukhtar dinta,abinda kawai zai banbanta tashi data dan fi ta mukhtar laushi,bata da bakin magana saboda haka bata ce komai ba jikinta a sanyaye suka qarasa cikin gidan. Washe gari haka ta tashi jiki duk a mace,ba dadi haja take ji cikin ranta,bata so anty dije tayi mata wani duba na daban,ba ita ta dorawa kanta ba tasani daga Allah ne,muhimmancin da mukhtar ke da shi a rayuwarta zaiyi wuya tayi saurin mance duk wani abu da yayi kamanceceniya da tashi rayuwar,ba abunda ta iya tsinanawa daga wanka sai kwanciya,ita kanta anty dijen ta lura,sai itama taji ba dadi,tana tsammanin ko fadan data yi mata ne ya sanyata zama haka?. Wajen sha biyu ta sameta dakinta tana fitar da kayan da suka dawo da su tana kuma shirya wasu cikin wata jakar daban "Sumayya,meke damunki?,ko don na miki fada jiya" kamar mai jira sai taji qwalla ta cika mata idanu,kai take girgizawa tana duban anty dijen "Ba don wani abu yasa na miki magana ba,na fuskanci abinda ke faruwa da ke ne,ina so ki sauya kanki ne" da sauri ta tareta "Ki daina fadar haka anty,wlh ba haka bane,ke uwa ce a gareni,kina da ikon zartar da duk hukuncin da ya dace da ni,nima bansan me yasa a duk sanda yayi magana nake zamowa haka ba,mukhtar dina nake tunawa anty har yau yaqi barin zuciyata,muryar mukhtar nake ji cikin tasa,sai na dinga jin kamar shine tare da ni" tausayin sumayya ya kamata,ta kama hannuwanta tana duban idanuwanta tana murmushi "Na fahimceki sumayya,amma shi baisan da haka ba,bana son ya raina min ke ko yayi tunanin wani abu na daban,nafa ji zafin abinda ya miki da fari,ban fadi miki bane saboda yayi ne cikin rashin sani......ki zama jaruma pls,ki dinga tunawa ba shine mukhtar ba....any way,mu ajjiye wannan maganar a gefe,me zakiyi da wadan nan kayan da kike shiryawa a jaka?" Hawayen take gogewa da tafin hannunta itama tana murmushi "Kano nake so gobe na tafi" idanu ta zaro "Kano sumayya gobe daga dawowarmu jiya,ko dai wani abun daban aka yi miki?" Marairaice wa tayi "Don Allah umman khalipha ki daina cewa an min wani abu,kin taba gani uwa ta yiwa 'yarta wani abu ba dai dai ba,kuma diyar ranta ya baci?" "To idan ba haka ba ai kya bari ko zuwa next week ne atleast ko?,zuwa sannan kin warware gajiyar tafiya kin fidda tsarabar su malam" "Anty inata kara amma baki gane me nake nufi ba,na qagu any naga abdallah,i missed him alort anty,shima kuma nasan haka ne" kama baki tayi taja dariya "Iyeeee,lallai yarinya,ga malam ga mama duka su bakiyi missing dinsu ba sai yaronki gaskiya ne" kunya ta kama sumayyan ta kifa kanta saman hannun anty tana dariya qasa qasa,ba zata iya boyewa ba,tabbas tayi missing yaronta "Shikenan,Allah ya kaimu,amma fa saidai ki bari sai jibi,zamu bude jaka afidda kayan su malam" duk da cewa ba hakan taso ba amma anty dije tafi gaban tayi jayayya da ita haka ta amsa mata da to. Misalin uku na rana suna zaune suna cin abincin rana amira ta shigo,bisa dukkan alamu daga makaranta take,don ga handout nan a hannunta da key din motarta,wani daj ihun farinciki ta saki tana qarasowa kusa da sumayya,gaisawa sukayi da anty dije tana tsatstsokanar su laila khalipha da minal,baki daya tace sun sauya,lallai garin ya karbesu,sai ta maida dubanta ga sumayya "Umman khalipha wai wannan amiran umman khalipha ce ko wata kuka samo a can?" Dariya suka saki baki daya kowa ya gane me take nufi,cikin salon zolaya itama sumayyan tace "Sun baro waccar a can,wannan musanyota sukayi" dukan cinyar sumayyan amira tayi tana fadin "Kina kallon mudubi kuwa?,wallahi kin bala'in zama wata queen namesake,ni zan fara yiwa alqasim wannan albishir din" harara ta aika mata tana murmushi "Ban aikeki ba,bismillah sa hannu muci abinci" idanuwanta ta maida kan abincin wanda saura duk da miya suke ci banda ita,fara da man take jin ci don an dade ba'a hadu ba "Wai wai,an kuwa zanci,shinkafa da wake da manja ne da yaji ko?,ga kuma salad,rabona da abincin nan da dewa,ina son fara da mai da yaji,su kam saidai suyi miya,musamman idan waccan baturiyar tazo,bama tasan fara da mai ba,idan taga wani yana ci har kyabe baki take wai muna cin abinci gaya" ta fada itama tana tabe baki,murmushi anty dije tayi "Dan gidanku yayarki ce dai,kuma kinsan baki isa ku fadi ba gaban maigidanta" amsa mata ta soma bayan tayi cokali daya "Me ruwa na da su,shima shi yaga zaya iya,haka kawai mutum bashi da maraba da gauro,kowa yana ci gaba ta fuskan family amma banda shi,haka kawai jiya har na kwanta ya tada ni wai na hada mishi fruit salad baturen kawai ga abinci ba zaya ci ba wai yayi masa nauyi" "Ke amira,zakici gidanku,ba yayanki bane?" Saki tabe fuska tayi kakar zata saki kuka "Ni umman khalipha bama wannan bane ya qonan raj,Allah anty su'adah 'yar rainin sense ce,na shiga kai mishi naji suna waya,ta baro america ta biyoshi dubai wai bata tadda shi,yace bai nan yana naija wai gobe zata biyoshi,wannam ai ba matar aure bace matar yawo ce,kuma kowa yw zuba mishi idanu wai matarshi ce haka suka tsara rayuwansu,to wallahi aure zamu masa" baki daya ta basu dariya saboda salon yadda tayi maganar bilhaqqi,har sumayya na qwarewa sai data kurbi ruwa "To ba sai ki masa ba tunda kece gaba da shi,kijimim tsaurin ido,musty zaki ma aure?,yo ko adam ai bai usa yace zaya yi masa aure ba bare ke" tsaki sumayya ta ja bayan ta samu tarin ya tsaya tana dan dukan cinyar amiran "Kinga malama,ki dinga maganar da zata amfanemu,juyo muci abinci" waiwayowa tayi tana duban sumayya "Uhmmmm,wallahi kuwa,don wannan babu ranar sauyawarsu" sai tayi qasa qasa da murya "Kefa kawai nake jira ki dawo a fara tsara mai yiwuwa,jibi za'a kawo lefe fa,kuma da sati uku zasu zo kwanakin bikin" "Komai kika tsara dai dai ne,amma ni jibin zan wuce kano" idanu ta zaro tana tsaida cin abincin da take "Me kika fada namesake,ina ce miki jibi kawo lefe kina cemin jibi zaki tafi kano,a satin nan fa zamu je dubai siyo kayan kitchen,tare da ya musty zamu koma,shigowar nan da nayi passport naki nazo karba za'a buga mana visa" cabdi,wane musty din,mustaphansu?,ta godewa Allah da ya bata idea din tafiya kano,don ko ana yankan jikinta ba zata bisu ba,wannan dan jin kan?,dan wulaqancin dan rainin wayo? "Kice wani abu mana kinyi shiru,duk kin rusan plan,wallahi idan baki je ba da wannan matar tashi zaya hadanu siyan kayan kitchen,bayan babu abinda tasan amfaninsa a kitchen saidai ta ganshi da ido,sai shegen izza da dagawa,zata siya min kayan shirme ne masu dan banzar tsada tana ganin kudin mijinta ne,kamar an gaya mata shi mai kudi baisan ciwo da zafinsu ba" ajiyar zuciya ta saki "Banji dadi bane amira,amma zuwa kano ya zame min dole jibi,malam na son ganina" ta hada da qarya,sai anty dije tayi saurin tashi ta doshi kitchen don kada amira ta roqeta ta hana sumayyan zuwa,don qaryan sumayyan ta mata dai dai,koda tana abuja ba zata barta taje ba,don ta fuskanci inuwa daya bata zaunuwa tsakanin sumayyan da shi uban gayyar,bare tafiya ma wata uwa duniya babu muharramin sumayyan ba zata yarda tayi ta ba. Shuru amira tayi wanda hakan ke gwada baki daya bata ji dadi ba,jikinta a sanyaye taci gaba da cin abincin,sai da daqiqa kusan biyar ta shude sannan ta iya cewa "Malam yafi gaban komai amira,sai kin dawo Allah ya kiyaye,amma don Allah ki dawo da wuri,sannan kimin alqawari zaki shiga ayi komai da ke,zaki dauki kanki kamar diyar baabaa,wallahu tun wancan satin baabaa ke tsokanata,wai idan baki dawo ba baisan ya zanyi ba,qila saidai ya daga bikin ko?" Murmushi tayi,alqawarin yayi mata girma da yawa,amma tilas ta dauka,anayi da kai yafi ba'a yi da kai,masoyinka kuma yafi maqiyinka "Kada ki damu,nayi alqawari in sha Allah" "Amma kafin ki wuce zaki shigo ki gaida su ummee,daga nan kiga ankon da aka fitar ko,ku hudu amma kalar naku daban,ke da qawaye na su uku" "Me zai hana,in sha Allah" ta fada kawai din a wuce gun,amma mai zai kaita gidan a irin wannan lokacin da wannan mutumin ke qasar,daga haka ta ware suka ci gaba da hirarsu. ******** ******** ******** Tun dare ta kasa bacci,gani take kamar gari bazai waye ba,bata ji kwanciyar hankali ba sai data ganta a mota sun dauki hanya,babu wanda ta gayawa tana zuwa don so take tayi masu ba zata. Qarfe daya da minti ashirin na azahar a qofar gida tayi musu kasancewar sun fito ne da wuri,ita ta fara shiga kafin driver din su anty dijen ya soma shiga mata da akwatunta da qatuwar jakar dake dauke da kayan tsaraba. Halima ce a kitchen,mama na bakin fanfo tana daura alwalar sallar azahar,yayin da zainab ke mopping falon mama wanda ta dage labulensa,hakimin abdallah na kwance abinsa saman kujera yana kallon cartoon,zainab na mopping din tana mitar ya hanasu kallon kowacce tasha sai ta 'yan aljanu,mama na fadin ai yafi,sunfi son suyita kallon waqe waqe da raye rayen banzan nan da wofi. Tana sallamar halima ta saki kwashe miyar da takeyi ta fito,zainab ta saki mopper,yayin da mama tayi tsaye tana dubanta tare da amsa mata sallamar fuskarta dauke da madaukakin murmushi,kusan a tare suja ruqunqumeta suna ambatar sunanta,dadi ya cika kowannansu,sam abdallah bai fahimci me ake ba sai da suka shigo falon,dirowa yayi daga kan kujerar yayi kan sumayya yana kiran "Mamiiiiiiii naaaaaaa" baki daya ya cukuikuyeta kamar zai shige jikinta,itama tsam ta rungumeshi tana dariya farinciki fal zuciyarta kamar an wanketa da ruwan qanqara. Baki daya sun baibayeta,idanuwanta na kam abdallah,photocopy na mukhtar take kalla,cikin shekara guda tal ya sake wani girma da wayo na ban mamaki,ya fara zama dan saurayi,shekara kusan biyar ba wasa bace,girman dan mutum babu wuya,duba daya ya wadatar da kai ka gane yaron na samun gata da kulawa,don suturar jikinsa ma kadai amsa ce,zainab da halima kowa da abinda zai fadi "Yaya sumayya kin ganki kuwa?,kamar irin hajiyoyin nan" "Yaya sumayya kin zama budurwa wallahi,irin 'yammatan abujan nan,gaskiya tafiyan nan ta karbeki,kaman an canjoki baki daya" dariya take ta rasa abin cewa,tunda ta sauko daga mota ta lura da kallon da jama'ar unguwar tasu ke mata wasu ma kamar basu ganeta ba,haka su halina suka cikata da surutu har sai da mama ta korasu halima taje ta zubo abinci ta kaima driver a waje din da yayi salla zai koma,sannan ta zubowa sumayyan ma, zainab kuma ta kai mata kayan daki,sai bayan fitarsu sannan suka ji kunnuwansu,abdallah na maqale jikinta yana ta bare choculets yana gama musu aiki. Haka suka wuni ba wanda ya fita a gidan,sai maqota dake shigowa jifa jifa yi mata sannu da zuwa,wanda wasunsu labarin yadda sumayyar ta koma suka ji suka zo ganewa idanuwansu. Koda ya abbakar yazo shima baki ya saki "Lallai nasan gobe mutuniyar anan zata wuni" "Ni ya kamata naje yaya,ina babymu nasan ta fara wayi bata san mamarta ba(da yake matarsa ta haihu)" "Ke dai kawai sai kin ganta,na tabbata ba zata iya haquri har kizo ba", malam ne kawai bai shigo da wuri ba amma ta gaza bacci sai da taga shigowarshi,kusan raba dare sukayi suna hira da shi,zuciyarsa na masa dadi duk sanda ya kalli diyar tashi,babu shakka rayuwa ta soma yi mata kyau,saidai a yanzun yana ganin ya kamata ta fidda abokin rayuwa ta sake aure,ko bai mata maganar yanzu ba zai fara yi mata jirwaye mai kama da wanka,zai tashi haiqan wajen yi mata addu'ar katari da miji na gari ita da 'yan uwanga baki daya,sai wajen sha biyu da rabi na dare suka rabu taje ta kwanta. ******** ******** ******* Washe gari a dakin malam din ta karya,ko wanka bata yi ba kayan bacci ne jikinta rida da dogon wando masu kauri,ta dora dogon hijabinta mai hannu,bayan sun kammala suka ci gaba da taba hirarsu,gayaran murya malam din yayi "tunda gaki Allah ya dawo dake auren 'yar uwarki ina jin ba zai wuce wata biyu ba,dama su suka matsa da magiyar a bari ki dawo,basa son ayu bikin wai bakyanan,shima kuma abubakar ya goyi bayansu" murmushi tayi ta dan sadda kai a zuciyarta tana lissafin bayan bikin amira da sati hudu kenan? "Alhamdulillahi,Allah ya tabbatar mana da alkhairi" "Amin ya Allahu,gwara ayi,hankalina sai yafi kwanciya,burina naga kowacce dakin mijinta,shine cikakken mutuncin 'ya mace,duk inda kika kai ga isa da dukiya nasaba da ilimi matuqar baki da aure baki kammala zama cikakkiya ba,don shine rabin,sai muyita addu'a,shi dama ibada ne,idan ka dace ka godewa Allah,idan ya jarabceka kayi haquri ka kuma nemi lada a wajensa" "Haka ne malam,Allah ya tabbatar da dukkan alkhairi" kai ta sunkuyar,jikinta yayi sanyi,ba shakka ta fuskanci zaurencan malam,gugar zana yake mata,ita kam ina zata tsomala rayuwarta a yanzu idan malam ya taso mata da batun aure,da sauri ta nemi tsari kada Allah ya karkato da hankalinsa. Cikin siyasa da qwarewa ta cikim hirar da suke yake jan hankalinta dangane da halayen rayuwa,babu shakka dukkan maganarsa izina ce kuma abar dauka,sosai taji dadin hirar da shi saboda yadda yayi mata tuni sosai game da wasu lamura masu matuqar muhimmanci ga rayuwar diya mace,ranar malam bashi ya fita ba sai sha biyu na rana,tun mama na leqosu taga ko ya gama shirin fitar har ta gaji ta barsu. Sanda ta fito zuwa falon mama ashe anty amina matar yaya abubakar har tazo,dariya ta saki tana dubanta "Tab,wlh anty kwata kwata banji shigowarki" "Ina zakiji 'yar gaban goshin malam" zainab tayi caraf ta karbe "Wallahi anty kema kya fada,baki daya faadar malam tata ce" karyar da wuya amina tayi "Dole malam yaji da sumayya don gaskiya ba daya kuke ba,kun manta yadda rayuwa tayi da ita ne,QADDARA ta wajiga ta?" "gaya musu dau matar yaya" ta fada tana amsar babyn fuskarta qunshe da fara'a tana cewa "Ga babbar jika,ga babbar jika a mata" yarinyar kuwa dariya ta dinga bangalawa kamar ta gane wace sumayyan a wajenta,yarinyar kyakkyawa sosai ta biyo jinin gidansu sumayya. Amina ke ta bin sumayya da kallo har sai data tanka "Wai sumayya me anty dije ke baki haka,kinga yadda kika koma kuwa?" Dariya ta saki "Haka kowa ke fada anty" "Wallahi kin sauya baki daya masha Allah,boyayyen kyawun nan duk ya fito,yau dai na yarda kinfi abban yusra kyau" dariya ta tuntsire da ita,sabida sau da dama suna musu kan hakan amma taqi yarda,sai gashi yau ta sallama. ******* ****** ****** Washe gari qarfe sha biyu na rana ta shirya tsaf cikin african abaya,abaya ce me mix da atamfa wadda tasha kwalliyar duwatsu,tayi kyau qwarai,jaka da takalminta duka marching colour,gidan hajiya tayi niyyar zuwa yau,hajiyan abdur rahman,so take ta wanke kanta,don tasan sam bata kyauta ba,shiru kawai wancan karon abdur rahman yayi mata. Ita da halima zasu je,saboda zainab ita yau ke da girki,suka yiwa mama sallama suka fice bayan tace su gaida mata hajiyan da bahijja,don shima abdur rahman din kwana biyu kenan bai leqo ba,abinda idan yana gari bai taba tsallake kwanaki biyun bai leqo ba,ba wani tazara ce mai yawa tsakaninsu ba,hakan ya sanya cikin mintuna arba'in mai adaidaita sahu ya saukesu bakim get din gidan suka sallameshi suka nufi gidan. Tun kafin su shiga abdallah ya soma fadin "Zamu gun daddy A ko?,gun hajiya da bahijja" kallon mamaki sumayya ke masa kafin ta maida dubanta ga halima "Kai,wai yaron nan har gidansu abdur rahman ya sani?" Murmushi halima tayi "Me zai hana,yaron dake wuni a gidan" shuru kawai tayi tana kada kai har suka shiga gidan. Daga can bakim setting room ta hangi takalma,wanda hakan ke alamta masu gidan na da baqi maza,babu kowa falon sai bahijja dake kwance kan doguwar kujera,sallamarsu ita ta sanyata miqewa zaune,fuskarta taf da fara'a takewa sumayya sannu da zuwa gami da miqewa tsaye saboda murna da mamakin ganin sumayyan,ana haka hajiyan ta fito daga dakin da yake mallakin bahijja hannunta dauke da magunguna,lale marhabin ta shiga yiwa su sumayya suna gaisawa da halima,yayin data ja abdallah jikinta tana fadin "Matso mai gida na,kwana biyu ban ganka ba,daddynka ya shiga rububi bude asibiti ya hanashi sukuni,hala ma kun ganshi?,don yana sitting room tare da baqi" murmushi sumayyan tayi a aladabce "Bamu ganshi ba,amma kamar akwai mutane a wajen" "Masha Allah,mutanen uk,tafiya ba sallama" ta fada cikin zolaya,sai kunya ta kamata ta sadda kai "Wallahi hajiya,shirin tafiyar duk shi ya cinye lokacin amma naso zuwa" "Babu komai,ai komai sai Allah ya nufa,kun dawo lafiya yasu dijen,kina wajenta ko?" Kai ta kada tana fadin "Eh,lafiya qalau suna gaisheku" "To madalla muna amsawa,bahijja miqe ki sama musu wani abu a kitchen kafin a gama abinci" "Halan bata da lafiya ne hajiya?" Sumayya ta tambaya tana duban bahijja "Bata jin dadi,kuma saboda wani iya shege bata da lafiya amma taqi shan magani,ta ina lafiya zata samu" "Gaskiya kam" sumayya ta fada,ita da halima suka shiga,haka suka fito da snacks ruwa da lemo,yayin da hajiya ta ajjiye maganin ta basu wuri tana dauke da abdallah ko nauyinshi bata ji,yaron itama yana tuna mata mukhtar,akwai tsantsar kama mai yawa tattare da su. Suna zaune suna hira bayan sun idar da sallar azahar suka ji sallamarsa,sanye yake da jallabiya ruwan madara mai haske,kanshi babu hula sai takaddu masu yawa dauke a hannunshi,idanu suka hada da sumayya wadda ke amsa sallamarsa "Hala batan hanya kika yi?,ko ba sumayya bace?" Ya fada tamkar da gaske yake,dariya suka bushe da shi baki dayansu har ita,ya qaraso ya samu gefan hajiya ya zube cikin gajiya yana ajjiye tarin takardun hannunshi abdallah ya maye gurbin takardun ya haye masa cinyar,surutu ya fara yi masa yana biye masa yayin da yake amsa gaisuwar halima "Hala ke kika tuna mata da mu ko halima?matar da ko ki sanarmin zaki dawo nijeria banyi wannan matsayin ba" Ya fada yana dubanta,hararar wasa tayi masa sabida hajiya ta bar wajen "Tunda ita ta tunamin sai na tafi sai na tuno don kaina sai na dawo" "Ni kike harara?,lallai idanunki sai isa yanka" dariya ya bata suka dara sannan ya soma tambayarta gajiyar tafiya mutanen abuja da sauran abubuwa tana amsa masa,saidai ta kasa sakewa saboda wani kallo da yake binta da shi,hakan ya sanya babu shiri qarfe uku na rana tayi haramar tafiya,ko ya lura a takure take ya sanya ya sauke abdallah bayan ya kammala cin abinci yace "Bari na shiga na watsa ruwa sai na zo na kaiku" kai kawai ta daga ba don taso ba,ta sani dole a yau akwai abinda zai faru,tana tsananin kunya da jin nauyinsa a yanzu,ba yadda ta iya tilas suka jirayi fitowarshi. Cikin wani yadi ruwan omo ya fito,yayi kyau sosai,yace su sameshi mota sanda suka tsaya yiwa hajiya sallama,ta ajjiyewa hajiyan turare da turmin atamfa data siyo mata,sai wata qaramar jaka mai kyau mai garai garai wadda ke dauke da set na kayan makeuo data siyawa bahijja,murna sosai bahijja ta dinga yi,yayin da ta dauki mayafinta tace zata rakasu dama ta gaji da kwanciya ko zata ji qwarin jikinta,godiya sosai hajiyan ta dinga mata tamkar bata fi qarfin abun ba,dama shi alkhairi dadi gareshi koda wanda ka yiwa din yafi qarfin abun indai yasan karamci. Duka baya suka shiga ita da shi ne a gaba,bini bini ya juya ya kalleta,wani lokaci su hada ido wani lokaci ta basar,bai dai ce komai bar zuwa sanda wani go slow ya riqesu,wasa wasa sai gashi suna shirin cin mintuna goma bai motsa ba,ga hadari ya soma haduwa ya sanya garin yin duhu duk da har yanzu bai fara zubda ruwan ba sai zafi da ake fama da shi,bata mantawa lokaci iwar haka suka bar nijeria lokacin damina sai gashu sun sake dawowa sanda take shirim kamawa. Baki daya motar dake gefansu wajen guda uku sun rufesu kasancewar sunfi nasu tudu,sai ta sauke glass din motar qasa,abdallah dake sit din baya ya zuro hannunsa yana qoqarin sanya mata yoghourt a bakinta wanda hajiya ta bashi wai tasha,bata kai ga sha din ba ya zuba mata a jiki,baki daya ya bata saman cinyoyinta "Ya salam,ya salam abdallah ka bata min kwalliyar mata" abdur rahman ya fada yana laluba gefanshi ya dauko ruwa a cikin jarka ya miqa mata "Budr murfin motar ki dan wanke gefan da ya baci kafin mu qarasa gida" karba tayi ta balle murfin motar ta dan zura jikinta waje zata soma wankewa,ganin mayafinta na niyyar shiga ya shafa shima ya sanyashi sanya hannu yana janye mata,dai dai lokacin da motar dake daura da su aka sauke nata glass din wanda zafi ya ishi wanda ke zaune sit din baya,tsaki yaja mai qarfi saboda ko kadan baisan a.c din motar ta lalace ba,driven bai gaya masa saboda sabbabi ne ko wata daya basuyi ba,wannan ne kuma hawanshi na biyu zashu rano,yayi niyyar hawan jirgi kuma babu jirgin da zai tashi kano to abuja a irin lokacin da yake son ya taho din,hakan ya sanyashi hawa mota. Kyakkyawan gani idanunshi suka yi masa,da fari ya dauke kanshi kasancewarsa wanda baison shiga sabgar da ba tashi ba amma sai qwaqwalwarsa ke gaya mishi kamar ya santa,sake maida idanuwansa yayi wajen,ita dince,gaban motar wani yana janye mata mayafi,ci gaba da kallon wajen yayi har ta kammala ta ta maida kanga ciki taja murfin ta rufe "Yammatan yanzu?,duka sammakal suke ne?" Ya tambayi kanshi,sai ya danna madanni glass din ya koma ya rufe yadda yake,wani tsakin ya kuma ja,gwara ya yita shan zafin da idanuwansa su dinga shishshigi kan lamuran da ba huruminsa bane. Sam bata ma san abdur rahman ya janye mata mayafin ba,ta kammala ta kiqa masa gorar tana masa godiya "Ai yiwa kaine" ya fada yana murmushi,itama murmushin tayi don a yanzu ita ba qaramar yarinya bace ta fuskanci me yake fadi. Fita sukayi dukansu har bahijja tace zata shiga ta gaida mama,bai hanata ba don yana da buqatar sararin da zaiyi magana da ita,kallonta yake har ta gaji ta tanka "Kada fa ka cinyeni" "Da hakan zai yiwu da nafi kowa farinciki,kinga idan ma cinyeki kin tabbata mallakina ni kadai har abada,wani ma bazai ganki ba bare ya qyasa" kunya kalamansa suka bata,saita maida kanta daya barin tana sauke murmushi "Naga ma sai wani shamin qamshi ake,ko da yake girmanki ne,shekara kwana inji 'yan magana,ina maganarmu ta kwana sumayya?,nayi haquri sosai fa,dukkan kuma wani abu da nake saka ran kammaluwarshi ya kammala,jibi in sha Allah za'a bude asibiti,ya muke ciki,ko baki yarda ba wannan karon inajin ta qarfin tuwo zan qwace ki" "Amma dai kasan ko budurwa bai halatta ayi mata auren dole va bare bazawara" ta fada tana dariya qasa qasa "Kada ki yimin haka sumayya" ya fada a marairaice,ta jima tana nazarin abdur rahman din,bata da wata mafita yanzu,babu hanyar tsira,koda bata auri abdur rahman ba dole ta auri wani a gaba wanda bata san wayeshi ba,ta tabbata malam bazai barta ta rayu haka ba tunda har ya fara yi mata gugar zana,zata tanqwara zuciyarta,ta kwatanta karbarsa taga ni,bata san me gaba zata haifar ba,amma me mutane zasu ce idan sukaji zata auri dan wan baban mukhtar,wanda shi saurayi ne ita din bazawara ce?,wacce iriyar fassara zasu masu,meye matsayar hajiyarshi?,da wace fuska zata kalli batun "Ka cancanta abdur rahman,bazan hanaka damarka da Allah ya baka ba,amma kamim haquri kada ka sanar da malam har zuwa sanda za'a kammala bikin zainab,na tabbata idan ka gaya masa yanzu zaice zai hada da ni ne,wanda ya kamata kafin sannan ace mun sake fahimtar juna kan zaman da zamu tukara da tsara abinda ya dace" hannunshi ya dunqule kawaj saboda tsabar farinciki "Amincewa da yardarki kawai ta isheni farinciki,na godewa Allah,bazan takura ki ba ki kammala shirinki a nutse,amma don Allah a yimin alfarma nayi azumim bana a dakina"ya fada a marairaice,dariya ya bata har sai data qunshe bakinta,wai a dakinsa sai kace wani mace "Allah ya zaba mana abinda yafi alkhairi" "Amin ya Allah,ki shiga ki sauya kaya ki huta naga kaman yoghourt din dake jikinsu ya hanaki sakewa,bazan iya shiga gun mama ba kunyarta nakeji kinsan ta zaka suruka,sai gobe insha Allah zan kawo musu katin gayyatar bude asibitin shi da yaya abbakaf,ki turon bahijja" ya fada yana sanya mata kudade a jakarta,kudi sam ba matsalarta bane yanzun amma tun kafin tace komai yace baiso tace komai din,tilas ta dauki jakar tana masa godiya ya bita da kallo har ta shige gidan wani madaukakin farinciki na ratsashi. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [23/02, 11:51] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 6⃣9⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *KU SHIGO CIKI KUJI* *ALLAH YANA FADA CIKIN QUR'ANINSA MAI GIRMA* *MISALIN ALJANNAR DA AKA YIWA MASU IMANI ALQAWARI,A CIKINTA AKWAI QORAMU  NA RUWA WANDA BAI JIRKITA BA,DA QORAMU NA NONO WANDA DANDANONSA BAI SAUYA BA,DA QORAMU NA GIYA WADDA TAKE MAI DADIN DANDANO GA MASU SHA(WADDA BATA SAKA MAYE KO TAMBELE),DA QORAMU NA ZUMA TATACCIYA,KUMA A CIKINTA SUNA DA(SU 'YAN ALJANNA)NAU'IN KOWANNE IRIN KAYAN MARMARI(DAN ICE)* *kai jama'a wannan ni'ima da yawa take,idan kaso ka zama TATACCEN QASAITACCEN DAN GIYA AMMA FA NA ALJANNAH,ya Allah ka sanyamu cikinta don rahamarka* ________________________________________        Kafin su kai ga fita daga airphort din ruwan sama ya sauka,hakan ya hadu da duhun magariba ya kawo qarancin jama'a bisa titi,idanuwan sumayya qur bisa kwalta yadda ruwan ke sauka yana wanketa,a duk sanda ruwam sama zai sauka sai ya mata tunin mukhtar kamar ko yaushe.                Rashin daukewar ruwan har suka isa gida shi ya sabbaba driban ya shige da su baki daya cikin gidan baaban ba tare da sumayya ta samu damar sauka ba kamar yadda taso,saboda Abdallah wanda ya jima da yin barci kan cinyar amira,ruwan na iya tabashi,da ita daya ce da da sauqi.        Lema kubra ta shiga ta dauko musu sannan suka fito,suka taka har cikin gidan.      Lallai kam wannan biki ba qarami bane,baki daya harabar gidan ko ina an kafa tempol,duk da gidan bai wani cika rana ba,duk da ruwan da ake tsulawa hakan bai hanaka ganin mutane na kai kawo daga wannan sashi zuwa wancan sashi ba,a haka suka qarasa bangaren ummee,falonta cike yake da baqi,yan uwa qawaye da abokan arziqi,ga 'yan rano nan wanda ko ba'a gaya ma ba kana kallonsu kasan jinin ummee ne,jinin sarauta,ga 'yammata nan ko ina zazzaune kowa na nashi harkan,shigar amiran ya sanya hanaklin sh dawowa kanta,masu tsokana nayi masu mata barka da dawowa nayi,da qyar ta yakice suka hau falon sama na ummee wanda tana can.        Karon farko da sumayyan ta taba shigarshi,falo ne dan gaske,wanda ya mallaki duk wasu kayan alfarma,baki daya kwalliyar falon ta da duk abinda aka zuba mishi na sarauta ne,kama daga royal chairs zuwa fentin falon,yayi matuqar burge sumayyan ba kadan ba,ummen ma zaune kan daya cikin kujerun falon tana irga sabbabin kudi wanda suke daure a rafarsu,ita da wasu mata ne wadanda kusan cousin dinta ne da suka taso tare tun zamanin 'yammatanci,qarasawa amira tayi ta kwantar da abdallah kan daya cikin kujerun,ummee ta dubeshi tana musu sannu da qarasowa ita da sauran 'yan dakin,a ladabce sumayya ta qarasa gabanta ta duqa tana gaidata,ta amsa fuska sake tana cewa "Amira ta hanaki sakat ko sai data daukoki" murmushi tayi kawai amiran tace "Ummee ba'a shiga tsakaninmu" "Au ai dama itaku amira" ta fada tana kiran daya daga cikin ma'aikatanta ta wayar hannu tana tambayarta an gama gyara dakin da tace,sai data gama wayar ta dubi amira "Kije an gama gyara muku dakin,saiki sanya a kawo muku abinci,ki duba abinda kuke da buqata ki kira mama uwani ki sanar mata,su ummu salma ma ina zaton suna dakin tun dazun suke qorafin rashin dawowarki gashi gobe kamu" "To ummee na" amiran ta fada tana miqewa "Muje,ummee idan abdallah ya tashi ki bada shi a kawo mana shi" ta fada tana nuna abdallahn dake kwance yana baccinsa lakadan,kai ummim ta daga don bata son yin magana ta sake bata a lissafin.         Dakina babba sosai wanda ya babu komai cikinsa sai carfet da aka malale shi da shi,katifune saman carfet din ko ina aka kwakwkwantar,yayin da aka lullube kowacce katifa da zanin gado abun rufa da filo qwaya daya alamar kowacce ta kwanciyar mutum guda ce,sai toilet qwaya biyu cikin dakim,da qaton madubi da ya kusa cinye rabin bango,mutum biyar suka taras a dakin,wasunsu na hira wasu na cin abinci,shewa suka sanya da ganin shigowar amaryar,kowacce da abinda zata fadi,nan suka zube aka gaisa suna ci gaba da surutaj,itakam sumayya na gefe tana kallonsu,rayuwar wayewa kawai ake a wannan familyn,kowacce ka gani tana ji da wayewa kyau da arziqin gidansu,akwai alama dake nuna suna da zumunci da kara,sannan akwai sabo da fahimtar juna tsakaninsh,wanda hakan baya rasa nasaba da yadda baabaa prof ya hadasu baki daya ya rungume kowa,duk sallah babba da qarama duk 'ya'yan 'yan uwan na gidansa,baya banbantawa da nashi dangin dana matansa,shi ya sanya kowa yasan kowa,'yammata ne hadaddu wannan na wace wancan ta fada a ranta tana murmushi.        Agogon fata na kamfanin gucci purple dake daure a hannunta ta duba ganin ruwan ya tsagaita sai yayyafi wanda take iya gani ta window din dakin albarkacin hasken lanatarkin da yake tarwai kowane lungu da saqo na gidan "Zan wuce fa amira" inji sumayya ganin yadda amiran ta bararraje tana kwasar hira,duka sai hankalin su ya dawo kanta har taji nauyin yadda kowa ya dora mata idonshi "Wasa fa kike amirah,kin manta alqawarinmu,ai ga gun kwanaki nan har na bar gidan nan" sai ta karyar da wuya tana murmushi "Amma dai ai kya bari naje naga anty ko?" "Eh,wannan kuma,kuma ai ban ma gama ganinki ba,muje part din anty maamaa akwai abinda zaki gani idan kin dawo na nuna miki sauran" ta fada tana miqewa,itama tashin tayi suka fito,har sun kai qofa tace "One minute don Allah sis,bari na dauko kayan waccan jarababbar na kai mata,Allah yasa ya musty bai nan" kafin tace komai har ta juya da sauri ta koma,tsayawa tayi tana jiranta gabanta na faduwa,tana addu'an kada Allah ya sa tace sai ta rakatan,don gaskiya ba abinda zai hanata ce mata ba zata ba.         Tana shiga ummu salma tace da ita "Amira wai ina kika samu wannan babe din haka mai shegen class,wallahi tamun,ta burgeni da ganinta akwai nutsuwa" "Ga kyau,muryarta ce ni kuma ta burgeni" inji hafsat,dariya suka bata,dukkansu 'ya'yan yar ummee ne,tasu ta bala'in zuwa daya da amira saboda halayyarsu kusan daya ce,ba ruwansu suna da matuqar kirki "Nan fa gidan anty dije wadda ta muku fried rice da sunan hanan,a nan take" "Masha Allah wallahi tayi" "Ai baku ma san tayi ba sai mu da muka je gidansu...." Eesha da hassada ta cikata tace "Me tayi,mr suke da shi a gidan nasu" amira wadda har ta sanya qafarta zata fita ta fasa ta dawo jin abinda eesham tace,dama tana lura da take takenta akan sumayya,wadda bata ga ita sumayyan abinda ta yi mata ko ta tsareta mata ba "Basu da komai,amma suna da rufin asiri,suna da wadatar zuci,basu taba kuma roqon wani ba,baya ga haka suna da karamci kyautatawa da girmama baqo,wadan nan abubuwa sun basu komai na rayuwa koda basu da shi din" inji amira ranta a bace sannan ta juya ta fita ranta a bace,humaida ce wadda itama ke jin haushin abinda eeshan keyi ta dora "Arziqi ba kudi bane eesha,wadatar zuci sanin darajar kai,mutunci yakana da karamci sune arziqin,kana da cin yau kana fa na gobe jibi wata ko shekara ma,kana sanya suturarka ta mutunci,baka taba roqa a baka ba,baka tashi ka rasa abin kaiwa baka me kake nema?" "Kinga malama,ni ba wani nace mata ba da zaku isheni da dogon wa'azi,ha'an..." Ta qarashe tana jan tsaki,caaa suka mata sun fita yawa ala tilas tayi shiru. A inda ta barta a nan ta taras da ita,suka ci gaba da takawa ba tare data nuna wa sumayyan akwai wani abu ba,bangaren anty maamaa suka soma shiga,itama bangaren nata masha Allah da mutane,suka gaisa sannan taja hannunta suka tsallake zuwa kitchen dinta,suna shiga tana yunqurin fitowa hannunta dauke da tray wanda aka jera tangaran mai garai garai guda daya wanda ke dauke da hadin salad mai kyau,sai wata qaramar butar shayi irin ta larabawa da cups dinta wanda ke dauke da baqin shayi wanda yasha kayan qamshi iri iri,su'ad ce,fuskar nan a hade tana faman kumburi,ko kunyar idon mutane bata ji,ta zama baturiyar qarfi da yaji,sanye take da dogon wando wanda ya kama jikinta da t.shirt mai gajeran hannu,kanta babu dankwali sai uban qarin gashi wanda aka dasa shi kamar nata na ainihi,ta sanya ribbom ta kameshi,takalmin qafarta kuwa irin mai igiyar nan je,wanda tsininsa ba kawai abun kallo ne,amma akace sabo da yi gawa da gatsine,da yake ta saba tafiya da abunta sam bai dameta ba,hannyenta kuwa farce ne wanda tasha nail polish,gefe suka janye bata ko kallesu ba ta wuce abinta,da kallo amira ta bita tana tabe baki kafin ta maida kallonta ga anty maamaa "Kumburin banza kawai,shi wanda kike ma kumburin ma baisan kina yi ba,ba kuma ki isa kiyi masa a gabanshi ba,abincin ba bake zaki girki ba ki karba ki kai masa yaci kina baqinciki kamar da kudinki aka sarrafa,wallahi ni yanzu baiken ya musty ma nake gani,kana aure amma kamar ba magidanci ba,babu wani ci gaba da ka samu ko sauyi dangane da tsohuwar rayuwarka" daquwa anty maaman ta jefeta da ita tana fadin "Sau nawa zan miki magana kan dauke ido daga rayuwarsu?,ke ke zaune da ita?,ko kinga ta kulaki sansa zata fita" shigin shagwaba amiran ke kumbure kumbure tana fadin "Duk ku kuke sake bata su wallahi,ni da ganin wannan takacin gwara kayi aurenka ma kayi gaba a barku da su" dariya ma ta baiwa anty maaman sai ta dauke kanta tana duban sumayyan "Qaraso amiran umman khalipha mu gaisa ki qyale wannan tuburarriyar qawar taki,rana iwar haka dai naga wanda zata yi mawa" dariya sumayyan ta saka itama tana qarasowa inda anty maman take,a ladabce ta gaidata tana tambayar yadda ta baro mutanan gidan,sai da suka gama gaisawa sannan tace "Anty mama,bedroom dinki na bude,zamuga wadan nam kayan" kai ta kada mata suka juya suka fice. Har bedroom din ta dangana da ita,aljannar duniya sumayya ta kira dakin,cupboard din antyn ta bude ta jawo wata akwati ta ajjiye gaban sumayyan,ta sake janyo wata ta ajjiye sannan ta fara hudewa tana fadin "Ga kayan da zaki saka na biki baki daya,komai da komai,sarqa kawai zaki buqata bansan choice dinki ba" baki kawai sumayyan ta sake tana kallonta,ta soma ware mata wanda zata sanya gobe kamu,wani dandatsetsen lace ne brown mai yarfin milk wanda aka yiwa dinkin fitted gown,rigar ta dinku iyaka,sai takalmi milk na companyn vinci wanda ke da tsini dunduniya,sake dago wata doguwar riga tayi wadda ta tafi da imaninta,ire iren rigunan da baabaa ya basu da salla ita da laila mai dauke da tambarin companyn MM,itama da takalminta ruwan kwalliyar duwatsun dake jikin rigar tace wannan ta jibi ce ranar arabian night,sake janyo wani shegen yadi tayi wanda bata tantance wanne ba,baqi ne baki dayansa an masa ado da milk din zare tsalli tsalli da milk din qulalai a jiki,shima fitted gown ce,har tafi ta farko fitinuwa,sai wani shegen hill shoes mai igiyoyi ruwan adon jikin yadin da jaka purse mahadin kayan ga "ankon dinner dinki" amira ta fada tana murmushi,rasa bakin magana kawai tayi tana duban amira,dariya ta sanya sanda ra motsa zata yi magana "Wallahi idan kika ce wani abu sai mun bata,baabaa ne duka ya bada yace na zabi na dinkawa babbar qawata" kai kawai ta dinga kadawa kafin ta furta kalaman godiya,kunnuwanta ta tasihe da nufin bata son ji. Daya akwatin kuwa baki daya kayan amarya ne da zata yi fitar biki,fadin irin kyawunsu ma bata baki ne,sai data daga mata su daya bayan daya sannan ta rufe ta maida ma'ajiyarsu tana cewa "A nan zamu dinga shiryawa,don haka anan zamu bar kayanmu,sai muje kiga lefe dama baki gani ba" dariya tayi "So kike dai dare yamin banje naga anty ba,ai basai na gani ba amira". " shikenan,muje ki rakani na miqawa waccan kayanta,sai na rakaki qofa kije ki dawi din"fuska ta narke,ta langabe kai duk don amiran ta haqura da wannan rakiya "Habbaaa amira,muje dai ki wuce ki kai mata ni kuma na wuce gida" "Ke kika ce sai na amso mata dinkin ina zaman zamana,saboda haka dole ki rakani" tayi maganar tana gyara nadin mayafinta,miqewa tayi jikinta babu qwari tabi bayan amiran suka fice. Daf da zasu shiga bangaren wanda ta baya suka biyo da yake qofofi biyu garesu,akwai qofar gaba wanda zaka shiga ta falo,akwai qofar baya wanda zaka shiga ta kutchen wannan qofar suka biyo,daga hannun hagu na bakin qofar,a qawace yake da wasu irin nau'in furanni da shukoki masu kaloli daban daban da kuma kyau,baki dayansu kansu daya babu wadda tafi wani tsaho,an qawata gun tamkar wani dan gurin hutawa,kaf gidan nan dinne kadai ke da irin wadan nan shukokin,wanda qilan mamallakin bangaren ne ya siyi abunshi yasa aka tsara masa su a haka,yara ne kusan su hudu,maza biyu mata biyu,a qiyasce zasuyi sa'annin juna baki dayansu,kowanne qananun kaya ne a jikinsa,sun kunna fanfunan suna ta faman wasan ruwa,amira ita ta fara hangosu,sai ta dakata tana daga murya "Hibba!!,yayi muku kyau da wasan ruwa kunji ko" baki daya suka waiwayo suna dubanta,kyawawan yara ne wanda kallo daya zaka yi musu ka tabbatar jinin gidan baabaa prof ne,wadda aka kira da hibba ita ta matso "Anty amira,gasar yin alwala muke,su hibban duk basu iya ba,zo kiga na fisu iyawa" "Matsa ki ban gu,yanzu ban da lokacin shirmenku kinji,tawa ta isheni" sai ta karyar da kai fuskarta kamar mai shirin yin kuka tace "Don Allah anty amira kizo ki gani" idanunta ta zaro tana dubanta "Ina wasa dake ne,bakiga ina cikin hidima ba,matsa a wajen nace" sumayya na tsaye tana murmushi tana dubansu,yarinyar ta burgeta,zuciyar son yaranta ta motsa mata,dauke idonta yarinyar tayi daga duban amira ta maida kan sumayya "Tunda ba zaki ba ai ga wata antyn ko?anty zaki je ki gani?" "Me zai hana" sumayya ta fada tana murmushi,tsalle ta fara wanda hakan ya sanya sauran yaran qarasowa din jin me ya faru "Ba inda zata,Allah hibba kin baci da yawa,itama tana da abunyi" "A'ah,nifa sai naje" inji sumayya wadda dama hanyar kubuta take nema "Kije ki fito kya sameni a nan" ta fada tana yin gaba din tuni yarinyar ta riqe mata hannu "Anty muje waccan fanfon,wannan na uncle man ne,zai zanemu ya ganmu a gurin,amma idan mukayi kuka sai ya bamu chaculet yace mu daina" murmushi tayi kawai tace "Allah" "Allah anty,kuma duk yafi sona" hibba ta fada suna qarasowa wani waje wanda shima akwai fanfo saidai baikai wancan kyau ba. Jin muryar yara ya sanyashi daga idanunshi daga kan laptop din dake gabanshi yana duba wasu sababbin design na dogayen riguna da kamfaninsa ke son fitarwa a sabuwar shekara,gefanshi butar shayi ce da cup qwaya daya,a rayuwarshi yana son ababen nan,yanayi na damuna irin wannan bayan gama saukar ruwan sama,da guri wanda ke da wadatar korayen tsirrai,iskar wajen mai dan sanyi sanyi kadan hade da qamshin qasa da qamshin furanni na masa dadi qwarai,ganin yaran tare da wata ya sanyashi maida kanshi yaci gaba da abinda yake. Daya yaron ne ya tabe fuska yana cewa "Qarya ne anty,yafi sona,ko za'a tambaya ma" yatsanta ta dora kan lebenta tana zaro masu idanu alamun yayi abunda ba mai kyau ba "Bakasan ba'a cewa babba qarya yake ba,lala ba kyau,kace Allah na tuba" kan kunnensa kalaman suka sauka sai ya daga kai ya sake duban inda suke tsaye,har yanzu bai gane wace ba,amma yana iya gane yaran saboda baki daya yasan muryoyinsu,hannunshi ya sanya ya tsiyayi shayin ya kai bakinsa yana ci gaba da sauraronsu,a rayuwa Allah ya zuba masa qaunar yara,zama cikinsu yana debe kewanshi a duk sanda ya samu kansa cikin kewa,hakan ya sanya wani lokaci yakan bata lokaci cikin gidan marayunshi,akwai yaran da suka shiga ransa da dama a gidan,baisan so yaushe ne zai daina rayuwar kadaici ba. Murmushi tayi ganin yaron yayi saurin rufe bakinsa yana cewa "Allah na tuba" "To yanzu muje mu gwada inga alwalar kowa din,duk wanda yafi iyawa shi ya m....." Sai ta kasa qarasa sunan "Wanda duk yafi iyawa shi aka fi so" ta sauya salon maganar tata,tsalle suke har suka isa gaban fanfon,tana tsaye tana kallon kowa daya bayan hannayenta harde a qirjinta,kamar yadda yake zaune saman kujera yan kurbar tea mai zafi yana kallonsu,sai da suka kammala tsaf,tabbas hibba ta fisu iyawa,amma ita dinma akwai gyare gyare,a hankali ta yaye yalwataccen mayafin data suturce jikinta da shu,wanda hakan ya bayyana shape dinta sosai kasancewar riga da skert ne a jikinta,tun bayan zuwanta abuja kayan suka dan kamata kasancewar ta murje ta cicciko,idanuwanshi ya lumshe saboda gujewa kallin haramun dinshi,sai ya kasa sake bude idanuwan mashi ya barsu a lumshe yana sauraron ta tana fadin "Sai kuyu haka,yauwa haka,haka" bai bude ba har sai da yaji tana fadin "Idan kayi haka,kayi alwala mai kyau" a hankali ya bude idanuwan nashi,wannan karon fuskarta tarwai take ta haske qwan lantarkin da ta tsaya saitinsa,ya dan qura mata idanuwa yana son tuna inda yasan fuskar "Mai kuka a uk mall" qwaqwalwarsa ta birkito file dinta,qaramin murmushi ne ya subuce masa,wanda idan baka kula da kyau ba na zaka gane hakan ba,saboda cije leban qasan bakinsa da yayi "Tana acting kamar wata babba" ya raya hakan a ransa. Riqeta yaran suka sake yi,nurain daya daga cikin yaran yace "Anty ki mana tatsuniya,baabaa lami mai aikin momi tana mana" murmushi ta saki,ta lura suma lallai yaran masu son mutane da sabo ne,saidai suna son riqeta gashi tana son tafiya gida ne "Ban iya tatsuniya ba saidai na baki tarihi" "Laaaah,irin wanda uncle man ya taba yi mana rannana?" Zaitun daya yarinyar ta ambata da salon tambaya,duk da bata sani ba amma sai ta daga kai "Ita,amma yanzun inaso naje gida na gaida anty na,sai wani lokacin na muku ko?" "Yaushe?" Inji hibban,kai ta girgiza qaramar dariya na son subuce mata,yaaraan akwai wayo,tana som tana yaro mai wayo da kaifin qwaqwalwa irin haka,ta tabbatar basirar da wayon bai tashi a banza,zai zama abu ne mai amfani a nan gaba "Wataran in sha Allah". A hankali ya janye idanuwanshi daga kansu jin qarar wayarshi,ya cirota daga aljihun black trouser din dake jikinsa yana duba mau kiran,su'ad ce,dan qaramin tsaki yaja,ba matsala yake so ta qara maishi ba,ya riga da ya yanke magana,ya gaji da auren asha ruwan tsuntsaye da sukeyi,ita tana kano shi yana daura,kusan tun jiya bayan isowarshi garin da yaje gidan hamza abun ke dawainiya da shi,kasancewar wanda amiran zata aura cousin suke da hamza,wata rayuwa ya gani ba irin tasu rayuwar ba,ba irin rayuwar gidanshi ba,yana iya tuna sanda hamza ya dagewa auren yarinyar suna ganin baikensa,ashe akwai abinda ya gano?. Rejecting call din nayi sannan ya maida kansa kan laptop dinshi da niyyar ci gaba da aikin da yakeyi,wani tsakin ya kuma ja ganin lokacin da ya bata yana kallon sha'anin da bai shafe shi ba,yayi asaran time dinsa a banza,saidai yadda take kiranshi a jejjere ya hanashi aiwatar da komai,wani wawan tsakin ya sake ja,a rayuwarshi ya tsani abinda zai takurashi,sai ya ciro wayar a fusace ya daga ya kara a kunnenshi,cikin shagwaba da karyar da murya ta soma fadin "haba my man,please....please kada muyi haka da kai,ka duba fa ka gani duka duka shekara daya ya rage min na kasance tare da kai fa?" "Keep quite su'adah please....na riga da na gama magana,idan zaki iya zama gu daya fine,idan ma ba zaki iya zama ba duk daya,amma kada ki zargeni nan gaba" ta tabbatar da cewa shi din kaifi daya ne,baha magana ya sauyata,mutum biyu ne tal a duniya ke sauya masa ra'ayi koda baiyi daidai da mizanin mashi ra'ayin ba,baabaa prof sai ummee,sanin baya qaunar kuka ko misqala zarratin,koda na qaramin yaro ne ya sanyata saka kuka har da sheshsheqa,sai ya lumshe idanuwansa yana sauraren sautin kukan nata,a hankali ya zame wayar daga kunnenshi sannan ya kasheta baki daya ya cillata aljihu,shutting down din system din yayi sannan ya miqe tsaye yana jira ta qarasa mutuwa,ya laluba aljihunsa yaji muqullansa na jiki,ya dauke system din sannan ya dinga takawa a hankali ya nufi inda yayi niyya,baki daya baya marmarin komawa bangaren bare taci gaba da jagula masa lissafi,saboda haka ya isa ga qarama cikin motocinsa ya bude ya ajjiye kayanshi ciki ya tada ta ya fice ba tare da ya nemi kowa ba. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [23/02, 11:51] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 7⃣0⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKIL* ___________________________________ Mamaki ya kama anty dije ganin sumayya,dariya ta dinga yi tana cewa "Maganinki,da kika qi dawowa ga mai gaba daya nan taje ta taho mana da ke ai" itama sumayya dariya take "Hmmm,amira,amira rigima amira tabara,sai ganinta kawai nayi wallahi" "Ina sane ban gaya miki ba ai" guri sumayyan ta samu ta zauna tana ci gaba da dariya. Nan ta shantake suna ta hira da anty dijen,bata tashi farga ba sai taga har sha daya tayi,hakan ya sanya ta bude dakinta tayi kwanciyarta,anty dije je cewa "Abdallah fa?" "Barshi anty,babu lallai yayi rigima" ****** ****** ******* Qarfe goma na safe tayi wanka bayan ta gama hada breakfast ta barwa anty dije sauran aikin gidan,doguwar riga ta saka ta wani irin yadi mai talewa,hijabi ta zura wanda ya saukar mata har saman tafin qafarta,niqabinta ta daura sannan ta fita ta tadda anty dije na goge kayan kallo a falo "Anty zan wuce,nasan amira tana can ta cika fam,fashewa kawai take jira tayi" ta fada tana qyalqyalewa da dariya,dariyar itama tayi "Ato,yau mai rabaku sai Allah" tana dariya ta saki niqab din nata ta fice a gidan. Ya kusan a qalla mintuna talatin zaune cikin corridor din dake saman benanshi,bata san sanda ya shigo ba,tun daren jiyan taje zaman jiran shigowarshi taji shiru,ta kira wayar babu adadi saidai duka amsa daya ce wayar a akashe take,tun tana kumbura har zuciyarta ta fara saukowa,ta sani cewa fushinsa bashi da dadi,tana shan wuya a duk lokacin da yayi fushi,hakan ya soma daga hankalinta,kusan ranar bata yi cikakken bacci ba,saidai duk da haka bata san shigowarshi cikin gidan ba. Cikin qanqanin lokaci zuciyarsa tayi fes,fuskarsa ta soma washewa,yaran dake shawagi kan idanunshi a harabar gidan,yaro daya tak yake hangowa cikinsu wanda bai sanshi ba baquwar fuska ne,saidai a yadda wasan da yaran ke gudana duka ya fisu kuzari da wayo,motsin yaron ya dinga bi da kallo yana sakin murmushin gefan baki. Sai data tsaya suka gaisa da baaba mai gadi kamar yadda suka saba sannan ta sanya kanta cikin gidan,tunda ta shiga gabanta ke wani irin faduwa,kusan yara sunfi yawa a harabar gidan suna wasanninsu,jifa jifa mutane na kai kawo,juyiwar da abdallah zaiyi ya hangota,duk da niqabin dake fuskarta da hijabinta hakan bai sanya ya kasa ganeta ba,da gudu ya tafi yana kiran "Ammiiiii....amminaaaa" cak yaran suka tsaya suna kallonshi ganin suna tsaka da wasa ya bar gun. Da idanuwa yabi yaron ganin yayi wani guri da gudu,hannayenta ta bude baki daya duk da har yanzu niqabin na kan fuskarta amma murmushi ne kan fuskarta,durqusawa tayi ta daga shi tana nishi saboda nauyin da abdallahn ya dan yi mata sannan ta dage niqaf din,fararen jerarrun haqoranta a waje "Wai abdallah,na kusa fara kasa dagaka,me kaci yau ka qara nauyi?" Dariya ya saki irin ta quruciya sannan yace "Ammi,wata ummi ce,na kwana a dakinta,ta yimin wanka ta bani chips da qwai ni kadai na cinye,harda tea da suger sosai" dariya ta kamata,har sai data dora tafin hannunta kan bakinta,kafin tace wani abu hibba tayo gaba da gudu itama sauran yaran suka biyota,bata ankara ba taji an ruqunqumeta ana fadin "Anty,kin dawo zaki mana labarin?" Waiwayowa tayi tana dariya,ta sauke abdallah tana fadin "Kin manta yau ana bikin anty ameeraa?,sai idan an gama zan muku,muje ku rakani inda anty amiran take" gaba tayi yaran na binta a baya wannan ya riqe hannunta wannan ya riqe hijabinta a haka suka tafi. Baisan yana binsu da kallo ba sai da suka bacewa ganinsa,ya lumshe idanunsa sannan ya bude a hankali,abun ya burgeshi ya bashi sha'awa,yana son yara har cikin zuciyarsa,bayansa ya jinginar jikin kujerar yana fidda zazzafan huci daga bakinsa "My man" yaji an ambata a tausashe,yasan ko wace hakan ya sanya yaqi waiwayawa,sannu a hankali ta tako gabanshi,sanye take cikin riga da wando,ire iren shigar da tasan yana muradi suna burgeshi qwarai idan tayi,jikinta na fidda wani irin qamshi mai dadi,duka hannayenta ta zuba a kafadarsa,cikin shagwaba salon da tasan yafiso tace "My man,ka sanyani a damuwa jiya,kasan cewa ina buqatar ka,baki daya kwanakin da zamu kasance tare ba masu yawa bane,amma man ka qauracemin" ko kadan bai da buqatar maganarta,hakan ya sanya ya saka hannunshi ya sauke hannayenta dake kafadarsa sannan ya ture kujerar ya miqe tsaye ta juya yana shirin barin gun,ranta ne ya baci,hankalinta ya tashi,ta tabbatar cewa ya hau bigerin da shawo kansa zaiyi wuya,bata kuma isa ta sha gabanshi don hakan zai iya jawo mata wata matsalar,tilas ta janye jiki tana kallonshi ya wuceta,hannayenta ta saki zuciyarta na zafi,idanuwanta na neman tara qwalla,babu shakka idan banda mustapha mustapha ne da babu namijin da zata zauna a duniya yayi mata haka,saidai mustaphan na dabanne kamar yadda yake daban a zuciyarta,mafita daya gareta ta kaishu gaba inda za'a sashi tilas yayi mata abinda take so din,bama inda ta saba kaishi ba wannan karon na can zata kaishi ba,sai ta juya da dan sassarfa ta ratsa ta dakinsa zuwa falonsa ta sauko qasa ta nemi hanyar ficewa ba tare data damu da sauya kaya ko daukar babban mayani ta suturta jikinta ba ko don girman wanda zata gurinsa. A dakinsu na jiya sumayyan ta tadda su,tana qunshe dariya ta qarasa,dariya amiran ta saka tana harararta "Wallahi kin maida ni wata iri amira,godiya nake" "Afuwa namecy,afwa"ta qarasa ciki suna gaisawa da 'yammatan dake ciki,gira ta daga " to ya zanyi da ke,ni na kai kaina inda ba'a damu da ni ba,muje kimin rakiya wajen baabaa" "Ya kamata,don nima ina son inje in gaidashi" eesha dake shan tea ta ajjuye cup din tana yiwa sumayyan duban ita kuma a wa?,kamar zata furta sai kuma ta fasa,ta miqe itama tana yafa dan yalolon mayafi kan kayan baccinta tana cewa "Muje nima nayi rakiya" "Owk" amira ta fada ta dubi su hibba "Oya,ku wuce ku tafi wasanku" juyawa sukayi hibba ta tsaya ta karbi abdallah suka wuce. Sai da suka shiga wajen anty maamaa da ummee ta gaidasu sannan ta suka wuce zuwa sashen tsohon. Zaune yake gefan umminsa daga shi sai itayana kurbar coffee,idan da kowa a gun ta tabbata bazai sha ba,wanda ta shiga kitchen da kanta ta hada masa,dubanshi take qasa qasa,ita daya take iya gane mustaphan,tayi tsammanin idan yayi aure shikenan komai ya qare,matarsa zata fahimceshi fiye da kowa,saidai kash,sabanin haka ne ya faru,matarsa itace wadda bata fahimceshi ba fiye da kowa,a yanzun kallo daya tayi masa ta fahimci yunwa yake ji,bazai iya gaya mata ba,zai iya ci gaba da zamansa haka har sai an bashi,idan ya gaji ya kuma yana iya fita can wani wajen cin abincin yaci abinshi,time to time yakan sanya matarsa tazo ta karba masa idan yunwar taci tura,hatta da amira tafi matarsa sanin ko shi waye,wani irin mutum ne shi mai wuyar sha'ani,ba kowa ke iya fahimtarsa ba,bai iya sharing damuwarsa ko shawararsa da kowa idan ka dauke ummeen da baabaansa,tayi zaton idan yayi aure wannan zai zama aikin matarsa,saidai ina ma yaga matar bare ta dauki wannan responsibility din,saidai komai tana ganin ya kusa zuwa qarshe tunda gaf su'adan take da kammala karatunta,tana zaton idan ta gama din zata nutsu ta tara hankalinta waje guda ta kula da mijinta kamar kowacce matar aure. Yana tsaka da amsa waya ta shigo falon kai tsaye tare da sallamarta,a hankali ya daga kanshi don ganin waye,kansa ya kawai gefe yana jin kunyar ganinta a haka a matsayin surukarshi,baki daya babu al'adar bahaushe ko digi cikin jini da jijiyarta,komai nata na mai jan kunne ne,ko qanqanin bata jin kunyar keta gidan a haka,duk da tarin baqi dake gidan,yana yiwa yaronshi sha'awar sauyin rayuwa,duk abinda ke faruwa cikin rayuwar yaron shi da yakeso fiye da kowa cikin yaransa idan ka dauke amira yana sane,saidai baison jefa kanahi cikin sha'anin da ba'a nemi agaji ko tallafinsa,dattijon suruki ne wanda yasan ciwon kanshi da mutucinsa,amma tabbas mustapha ma cikin wani wadi daya cancanci a tallafeshi,tun fari laifinshi ne da bai ganin aibun rayuwar mai jan kunne,gani yake rayuwa ce ta burgewa,baisan babu komai cikinta face tsantsar wahala da rashin nutsuwa. Cikin sheshsheqar kuka ta zube a gabansa "Baabaa don Allah kayi masa fada,ka masa magana,yana son takurani,yana son tauyen 'yancina" sosai yake dubanta,a nutse yace "Nutsu su'adah,zauna,zauna sosai,gayamin,me ya faru?,me ya hadaku" zama tayi gabansa tana goge hawayen nata da tissue,don ko dan mayafin da zata kama ta goge hawayen babu a jikinta "Baabaa,mustapha ne,haka kawai muna zamanmu yadda muka saba,shekaran jiya yaje gidan hamza,ya gano wata zamantakewa ta daban yace dole muma irinta zamuyi,bayan zamantakewar tasu sam babu 'yanci ko walwala a cikinta,sai dinbim takura kai da rayuwa cikin duhu da rashin wayewa,lallai wai saidai na dawo nan qasar na zauna daku na qarasa karatuna don bai amince da duk qawaye na da abokaina ba,sannan wai idan na kammala na bishi dubai mu zauna tare na dinga kula da shi,don Allah baaba wannan ba takura bace,ni ban taba ganin inda da quruciyarki kike rayuwa irin haka ba,a gun africans kawai nake gani suma rashin wayewa ce da duhun kai" idanu baban ya runtse kafin ya bude,duka ta hadu ta zagesu su da iyayensy,babu shakka ba qaramin tasiri rayuwar yaro take ba a duk inda aka haifeshi ko ya taso,sai Allah ya taimaka iyaye sunyi tsaiwar daka sannan za'a samu yaro ya tashi da dabi'a halayya da al'adunshi. Cup din ya dire dai dai sanda wayarshi tayi tsuwwa,ya duba yaga kiran daga baabaa ne,tun kafin ya daga ranshi ya raya masa mishkilar su'adah ce,daya daga din kuwa ce masa baabaan yayi "Kana ina?,duk inda kake kazo ka sameni a falo,ina jiranka" daga maganar tasa kawai ya fahimci mawuyaci ne ba qararsa ta kai wajen baabaan ba,duk da cewa hakan ba baqon lamari bane wajensa,amma abun yayi masa ciwo fiye da kullum,ranshi bace ya maida wayar aljihunsa yana duban ummee "Baabaa na kira" ya fadi a taqaice "Ok,ka qoshi kenan coffee kawai ya isheka,bayanshi banga kaci komai ba?" "I'm ok ummee" ya fadi yana takawa ya fice daga dakin. Cikin sanyi da qasaita yayi sallama cikin falon baaban,wani kallo yajefa mata wanda ya sanyata sadda kanta qasa,take jikinta yayi sanyi,nadamar kawo qarar ta baibayeta,kwarjininsa kadai ya ladabtar da ita,cikin girmamawa ya isa gaban baaban ya zauna gami da lanqwashe qafafunsa,ajjiye takaddun hannayensa yayi sannan ya maida hankalinsa gareshi "Mustapha,me ya shiga tsakaninka da matarka" shiru yayi na wasu daqiqu kanshi na qasa,idanunshi bisa carfet din dake dakin,a hankali ya motsa bakinsa "Baabaa,ina da buqatar mata ta ne kawai kusa dani,na buqaci ta ajjiye karatunta ta zauna tare da ni" yasan a rina,mustaphan ba mai boyon abu bane cikin zuciya,komai tsaurin gaskiya ko dacinta sai ya fadeta,tabbas mustaphan bashi da laifi cikin maganarlaifinshi daya tun fari a haka ya tarbiyyanci matarsa,amma kowanne magidanci zaiso kasancewa da iyalinshi,bawai kowannansu da inda ya sanya kanshi ba sannan ace wai a haka za'a rayu,tausayinshi ya kama shi,yana jin wannan karon ya kamata yayi wani hobbasa cikin rayuwar yaron nashi "Baka kyauta ba mustapha" maganar data sanyashi daga ido cikin mamaki ya tsare babaa da kallo,yayi zaton shine na farko da zai goya masa baya?,ya zaci shima yasan ba haka rayuwar ma'aurata take ba "Tun farko haka ka dora bigiren rayuwarku kai da ita,ka manta ice tun yana danye ake tanqwarashi,basai ya bushe ba sannan kace zaka tanqwarashi" kai su'adah ke kadawa cike da jin dadi tare da alamun samun nasara cikin zancan baban ba tare data fuskanci dungun dake cikin maganar ba "Mustapha,komai ya kusa qarewa,ka qyale matarka ta kammala karatunta a inda ta fara,shekara guda ya rage mata ta kammala,idan yaso koma meyw zai biyi baya sai ka zauna ku yanke" shiru ne ya ratsa falon,kowa da abinda yake saqawa cikin zuciyarshi,zuciyar su'adah ciki fal da fatan samun nasara. Bayajin a duniya akwai wani umarni da baban zai bashi ya tsallakeshi,ya numfasa a hankali sannan ya furta "Na barta baabaa" "Yes dad,thank you" sa'adah ta fada cikin daga murya,murmushi ya subucewa baabaan,addu'a yaje da fatan saisaituwar halayen su'adah ko kyakkyawar rayuwa zata samu ga diyansa,miqewa tayi cikin farinciki ta fice,fes taje jin ranta,don ta mustapha tana tunanin tasan yadda zata shawo kansa,don ko kadan bata jin zata iya tabbata cikin nijeria tayi rayuwa a cikinta. Fitarta sukayi kacibus da su amira na niyyar shigowa,babu wanda ta kalla cikinsu tayi gaba abinta,yayin da eesha ta bita da harara kamar idanuwanta zai fado,babu wanda ta tsana a duniyarta sama da su'adah din,tana ganin baki daya ta kanainaye rayuwar mustapha,ta hanashi duban kowacce mace da qima,bayan ita din ba wata uwa take tsinanawa gareshi ba,abinda bata sani ba,abun a jininsa yake,tsaki ta ja wanda ya sanya amira waiwaya ta dubeta,tasan meke kai kawo a zuciyarta,saidai koma mene bata fatan Allah ya ida nufi,don qwaryar sama ke dukan ta qasa,banbancin ita da itan kadan ne. Bayan sallama da tayi ganinsa shine abu na biyu daya biyo baya bayan shigowarta falon,nutsuwarta yaji na nemam gushewa "Bafa mukhtar bane,ba kuma zai taba zama mukhtar ba" wannan shine kalaman sa suka dawo mata cikin kwanyarta,sai ta lumshe ido taja dogon numfashi kafin ta ajiye nunfashi ta kuma daidaita nutsuwarta. Fuskarsa dauke da fara'a yake dubansu "Mommies dina ne da kuma mai sunan uwar mumunai" ya furta cikin fara'a,su dinma fuskarsu washe take suka samu waje gefe da shi suka zauna,yayin da eesha tafi daura da mustapha,satar kallonshi take,baki daya man din ya sake tafiya da tunaninta, "Allah ka mallakamin shi" ta fada cikin zuciyarta tana lumshe idanuwa tana ci gaba da satar kallonshi,wanda sam shi baisan ma tana yi ba,abinda ke gabansa kawai shi ya dameshi,gaisuwansun ma bai dago kai ba bare ya gane su waye ya amsa musu baki daya kudin goro,ba haka eesha taso ba,gaida baabaa sukayi baki daya ya amsa cikin fara'a "Mutan kano,gaki ga mutuniyar dai,bata qyaleki ba,nan ta addabeni sai da na siya musu ticket ta taho" dariya suka dan saka baki dayansu. A hankali ya miqe yana shafa sumar kanshi,jin maganansu yake kamar a tsakiyan kanshi kasancewar bai son hayaniya,baabaan ya fuskanci me yake son fadi,saboda haka yace "Shikenan,kana iya tafiya" juyawa yai a hankali ya fice a falon fuska a daure kamar ko yaushe,eesha ji take kamar ta bishi ta rungumeshi,saboda yadda kullum kwanan duniya yake sake tafiya da ita,yayin da sumayya kanta ke qasa tana wasa da yatsunta zuciyarta na bugawa,amira ta bishi da kallo kamar yadda baaba shima ya bishi da kallo,shiru yaci gaba da ratsa falon har ya fice din sannan baabaa ya dauke idanuwansa daga kanshi ya maida kansu,ya dubi amira "Aishatu ta rakaki amira kuje ku amso min saqo wajen ummenku" "To abba" ta fada tana miqewa,tasan babanta sosai,hakan ya sanya bata ce sumayya ta taso na,tunda taga haka tasan akwai manufarsa na aikensu su biyu,baki daya taji wani nauyi ya sake kamata bayan fitar tasu,falon yayi shiru ta kasa motsawa sai kanta dake qasa har yanzu "Mamana,ki saki jiki mana,nima fa babanki ne ko ba haka bane" murmushi tayi "Haka ne abba" shiru ya sake ratsa falon na wasu sakanni kafin ta sake jin muryarsa "Mama na,wata alfarma nakeson na roqeki,saidai ina jin nauyin haka" mamaki ya kamata,ita din wace?,wacce alfarma babban mutum kamar baabaa prof din zai nema daga gareta,bayan ita din ba kowa bace,bata kuma mallaki komai ba "Baabaa,yanzu kace kai abbana ne,kuma na yarda haka ne,me yasa uba zaiji nauyin bawa diyarsa umarni" sosai wani irin qima da darajarta ya qaru a idanuwanshi,ya jima baiga nutsuwa da hankali tattare da yarinya mai makamancin shekaru irin nata ba,nutsuwarta da kaifin hankalinta shine abu na farko daya fara bashi mamaki tattare da ita,tana da wani irin dattako kunya nutsuwa da ganin darajar manya,wanda zaiyi wuya a wannan zamani ka samu mace kamarta da wannan qualities din "Allah yayi miki albarka maman,haqiqa iyayenki sunyi nasara wajen tarbiyyarki,sun rabauta da diya ta qwarai,mamana.....kinga yayankun nan da ya fice yanzu?" Gabanta ya buga,sai ta kasa daga kai ta kalli baabaan,Allah yasa ba wani sharrin yayi mata wajen baban ba,kai kawai ta kada "Mamana,zaki taimaka min ki taimaka masa wajen inganta rayuwarsa?" Duburburcewa tunanunta yayi,sam bata gano me baban ke nufi ba,inganta rayuwarsa kamar yaya,ya manta bata da komai ne qarqashin wasu take itama,duk yadda taso ta fassara maganar tsakaninta da qwaqwalwarta ta gaza gano ainihin ma'anar maganar,har rudun hakan ya bayyana saman fuskarta. Murmushi baaban ya saki,ya yadda har yau ita dinma akwai sauran quruciya tattare da ita,baison rudata,saboda haka yace "Baki fahimci baaba ko,shikenan,tashi kije kuci gaba da sabgoginku,idan kika fahimci ma'anar maganar ina son ganinki a lokacin,amma fa kada ki zurfafa tunani,kune qawayen amarya,kusha bikinku kinji mamana,Allah yayi miki albarka" "Amin baabaa,na gode" ta fada tana miqewa,hakanan taji jikinta yayi wani mugun sanyi,rashin jin dadin kasa fahintar maganar baban ce har ya dago haka ko kuwa mene?. Naso yafi haka but am busy fans. #mrs muhammad ce *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [23/02, 11:51] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 7⃣1⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* Allah S W T yana cewa *"DUK INDA KUKE SAI MUTUWA TA RUSKEKU"* Allah kasa mu cika da imani ____________________________________      Qarfe biyar na yammacin ranar baki daya gidan ya sake dinkewa da jama'a saboda shirin fara gabatar da kamun amarya,sumayya na tare da amiran duk inda ta sanya qafarta sai ta janyota,kamar yanzu da suke can uwar dakan anty maamaa suna shiryawa,daga sumayyan sai amira sai humaida da humaira,amiran akewa kwalliya an kusa kammala mata,tayi kyau qwarai da gaske cikin wani irin yadin saqi na fulani mai azqbar kyau da daukan hankali,saqin fulani je wanda aka zamanantar da shi da kayan ado dana qawa,maroon ne sosai da yarfin kwalliyar golden a jiki,walwali kawai take zubawa,ta lura da yadda sumayyan ke yawaita shiru,saka bakinta cikim hirarta yayu qaranci sosai,hannu ta sanya ta tabota,ta daga kai ta dubeta tana murmushi,da hannu ta yi mata alamar lafiya,sai kawai ta girgiza kai ba tare data ce komai ba,duk yadda taso barin zancan da baabaa yayi mata abun yaqi barin kwanyarta,zuciyarta ta nace da son gano ainihin me maganar tashi ke nufi "An gama min,saura ke" inji amira tana isa bakin mudubi tana duba kwalliyar tata,kai ta kada "Powder kawai za'a shafa min a jamin jagira sun isa" idanu amira ga watso mata "Bazaiyiwu ba wallahi,kina babbar qawar amarya?" "Ki barni ayimin hakan don Allah,naga dai yau aka fara abin nan ko?,gaba a yimin" ta fada tana zama gaban mai kwalliyat,dariya humaida ta saka,yanayi da halayen sumayyan ke qara bata sha'awa,sam bata da rawar kai ko iyayi irin na 'yammata.        Duk da cewa ba wani kwalliyar azo a gani aka mata ba amma tashi daya ta sauya,tayi wani sihirtaccen kyau mai sanyi wanda babu hayaniya a cikinshi,su kansu sai da suka yaba,biyar da kwata kiran ango saifudden ya shigo wayarta,yake sanar mata sun iso,da yake tare za'a kama su shi da ita,falon anty maamaan suka sauko sannan suka hadu sa sauran qawaye da 'yan uwa suka fito.        Qyashi da hassada fal ran eesha,duk yadda taso taga ta wuce sumayyan a kwalliya abun yacu tura,ira kadai ta tsone mata duk taton 'yammatan nan,saboda kaf cikinsu bata ga wadda tayi ya kyawunta ba,duk da yake akwai wadanda suka saka suturar da suka fi nata kayan qaawa da tsada,amma ba'a nan take ba wai aj dannewa bodari kai,abinda bata sani ba baki daya sumayyan jinta take a wani mugun takure,karo na farko a rayuwarta data taba shiga makamanciyar wannan,qememe amira ta hanata sanya mayafi sai ratayashi kawai tayi gefan kafadarta guda daya,kayan sunyi masifar amsarta kamar wanda ya saqa su ya saqasu ne musamman saboda ita,takalmin ne kawai ya gagareta tafiya,subaleshi tayi ta nemi plat cikin na amiran ta saka,a ranar tayi adon gashinta wanda yasha gyara aka fito mata da shi cikin daurinta sai sheqi sa walwali yake,ta saje cikin 'yammatan amaryar har ta zama kamar wata fitila ta daban cikinsu.         Bata gane wautar data tafka ba sai bayan da suka iso gurin taron,wanda a cikin gidan aka shirya kujeru rumfuna da decoration na alfarma da kece raini,saika rantse da Allah wani event center ne mai tsada aka kama,ita ke riqe da amiran amma sai ta kusa faduwa saboda yadda idanuwa suka mata caaa,idanunta ta lumshe tana kiran sunayen Allah,ko ina abokan ango ne gogaggu kuma wayayyu tsaitsaye suna jira a qaraso musu da amaryar,hannun anty huda ta danqa ta sannan ta juya har tana hardewa saboda ido ta juya,su'adah na tsaye gefan huda din,india ta tafi baki daya,sari ne a jikinta wanda ya amsa sunansa,sak irin dinki 'yan qasar hindun ne jikinya skert da 'yar fingilar riga,sai mayafin kayan a jikin skert din ta nannade jikinta,yayin da kanta ke a bude kamar nasu,sai gashin dokin da aka dinkeshi da ainihin nata ya tashi tamkar nata,ta rabashi kafadar hagu da dama kakar yadda 'yan qasar hindun keyi.      Tana juyawa suka ci karo da anty farida umman husna,bakinta a washe take duban sumayya "Wai wai,kunyi wuyar gani,ko diyarki baku hadu ba" murmushi sosai kan fuskarta cikin girmamawa ta gaida anty farida sanan ta wuce ummee dake cikin gida bata fito ba ta aikota wajen amiran.        Wayarta dake hannunta ta dauki vibration sanda amarya ta samu zama a gurbinta ita da angonta,sunan nafisa ta gani,mamaki ya cikata ganin number dinta ce ta nijeria,qarar lasifiqan wajen bazai barta taji ba,hakan ya sanya ta soma takawa don barin wajen tana duban kiran,can baya inda zata iya jin ta ta tsaya ta soma lalubarta saboda kiran ya riga da ya katse "Am at home sisi" idanu ta fiddo waje "Da gaske?" "Suprise wlh naso baki,shigo gidan anty ki shigo dani yau traditional setting na amira ina lissafe dama" "Wayyo sis,gani nan" ta fada cikin zumudi da murna ta kashe wayar,daidai sanda kida ya soma tashi daga inda ake gabatar da bikin,tsalle ta dan saki kadan farinciki fak ranta "Yi a hankali gimbiya kada ki fadi ki batan kwalliyar" abinda taji an ambata kenan,da sauri ta waiwayo,alqasim ne tsaye sanye da shadda ya kawo hula gaban goshinsa yana qare mata kallo yana murmushi,daidaita natsuwarta tayi sannan ta juya da niyyar ci gaba da tafiya,saurin shan gabanta yayi,ya wani karyar da kai "Haba sumayya,ko gaisawa i kya tsaya muyi ko?" shiru tayi tana dubansa ba tare data ce komai ba,ji take kawai zai bata mata lokaci ne,bata da buqatar wani abu a yanzu,tana cewa ta gama da babinsa,tunda tuni ta gaya masa ita din ba budurwa bace bare ya saka ran zata biye masa,idanunta tarufe tare da yin banza da shi,tana jinshi yana magana ci kanka bata ce masa ba.        Tunda suka fara tashin kidan ya tashi ya shiga bathroom ya sake wanka,jin kidan yake kamar a tsakiyar kanshi,duk wani abu da zai zama tamkar hayaniya bai qaunarsa,ko qwaqwaran motsi ne ya fiya yawa yanzun zai dameshi,sau tari babban wansi adam kance "Kai ko mustapha kamar mai aljanu,koyaya motsi yake sai ya dameka" amma hakan bai rasa nasaba da ciwon kan da yake fama da shi tsawon shekaru,wanda idan ya tayar masa baya masa ta dadi.          Ta baya yabi don bai muradin haduwa da kowa bare a tsaidashi a cikashi da suruti,baki daya yau zucuyarsa a quntace take,saidai ko kai daka sanshi baka isa ka fadi hakan ba,sakamakon yadda ko yaushe haka fuskarsa take a daure koda cikin farinciki yake indai ba girmama farincinkin yayi ba shine zaka ga fuskar ta sake washewa fiye da yadda take da,yatsanshi saqale yake da maqullin motar da yake sha'awar fita cikinta,tun kafin ya shiga wankan ya turawa P.A dinsa ya shirya haduwarsa da mutanen da yace jiya bazai samu damar ganinsu ba qasa da awa daya yana hanya kada su wuce haka,sannan ya turawa driver dinsa shima ya shirya motar da zai fita,kanshi a qasa yake takowa cikin shigarsa ta qa'ida trouser da t.shirt v neck wanda ta fidda structure ta jikinsa sosai,kwata kwata saka manyan kaya bai cikin tsarinshi,duk wanda yasan mustapha cikin duniyarsa yasan ba ma'abocin sanya manyan kaya bane,kana iya gama mu'amalarka kaf da shi baka ganshi da manyan kaya ba,daidai gun da jiya suka zauna wasa ya tuna,yaron ya fado masa,ya tuna shegen wayonsa,wani qaramin murmishi da bai shirya masa ba ya kubce masa,a hankali ya daga kanshi sai ya hangosu,tsaye yake a gabanta yayi kane kane kamar zai hade gaf din dake tsakaninsu,yayin da take tsaye hannayenta harde a qirji tana dubanshi,rashi ya baci,dan salaman da ya samu ta gushe,yana daya daga cikin abinda yasa kenan baison baqin 'yammatan cikin gidansu,yana zaton daga daga cikin 'yan matan family din nasu ne,sauya akalar tafiyar tasa yayi zuwa wajen,sai da yaje dab ya lura alqasim ne "Itakam haka take,gobe wancan mutumin jibi wannan?" Ya qarasa bayansu,daidai sanda take fadin "Na riga na gama magana da kai ko?,ba zaka taba samun abinda kake so ba,so don Allah ka qyale rayuwata" ta kammala fadi sannan ta juya a hankali ta soma barin wajen,burinta kawai ta isa ga nafisan gashi ya bata mata rai da lokaci baki daya,binta yayi da kallo har sai data bacewa ganinsa sannan ya juyo yana sakin ajiyar zuciya,sai suka hada idanuwa da mustaphan yana kallonshi,kunya ta kamashi,yana bala'in ganin girman almustapha da mutuncinsa,girmama shi yake qwarai da gaske,ya dan diririce yana fadin "Barka da fitowa yaya" bai amsa ba ya qara taku zuwa inda yake yana dubanshi,haushi yakeji,hashi ya kamashi,ji yake kamar shi akawa haka "Kan me ka tsaya mace na gaya maka irin wannan maganar ibrahim?,kai namiji ne ka manta?,so kayi maintaining dignity dinka,akwai mata da yawa a gari ka zabi wata mana,kar ka cusa kanka inda ba'a sonka,ba'a so dole,i hope ka fahimta?,ba ita daya bace mace akwaisu da yawan gaske" kai ya rusuna yana gyadashi alamun gamsuwa,cikin zuciyarshi yana cewa "Ya mustapha kai baka hango abinda na hango ba,baka hango personalityn dana gani tattare da ita ba,hmmmm ke ka ganin so wani abu mai sauqi ne tunda kullum cikin neman son ake a wajenka"amma a fili sai yace "na gode,Allah ya qara girma" kai ya jinjina ba tare da yace komai ba ya juya ya bar wajen.       Kamar ta goya nafisa haka taji lokacin data ganta,tayi ado sosai tana rungume da khalid,ta amshi khalid din kai tsaye suka koma wajen da ake kamu,sanda suka je tuni al'amura sun fara nisa,bayan gabatar da abubuwan da suka dace sannan aka kama amira kafin daga bisani a bada damar yiwa amarya da ango liqi,basu suka tashi daga kamun ba sai qarfe takwas na dare,kamu ya qayatar matuqa da gaske,tafiya nafisa tayi bayan sun gaisa da amira sama sama,taso riqeta tace a'ah tayi haquri abban khalid din ya iso,saidai zata zo dinner insha Allah wanda za'ayi ranar alhamis.        Washegari akayi arabian night wanda aka gabatar da ita itama cikin gidan baabaa prof,gidane gari guda hakan ya sanya basu da damuwar sai sun kama waje,ba qaramin qawata wajen akayi da kayan ado ba,ranar duk wani ahali da ya shafi baabaa prof sanye yake da abaya ta mata,maza kuma doguwar riga ce da hirami,kai ka rantse a ranar baqin larabawa aka yi a unguwar.  ******* ****** ********      Washegari tana kwance tana baccin gajiya,kasancewar alhamis ce ranar babu event din da za'a yi sai gobe idan Allah ya kaimu,ji tayi an daka mata duka,tilas ta farka tana mutstsike idanu,amira ce zaune gefanta "Sannu,ai wallahi bacci bai ganki ba bai kuma kamaki ba,qarfe hudu zamu lunching na maman saifullahi,kuma ba kowa ne zashi ba,bamu da yawa" zama tayi sosai tana hamma hannunta kan bakinta "Shine zaki dakamin wannan dukan,badon inajin kunyar idanun saifullahi ba sai na rama" dariya ta qyalqyale da ita "Ato bismillah,ni kinga ina da mai ramamin,ke kuwa nasan ko na dakeki na daki banza,waccan mutumin da na gani a kano babu abinda zaya iya" ta sani sarai da abdur rahman take,bata san meye hadinta dashi ba data saka masa tsama haka da yawa,harara ta jefa mata sannan ya shiga bandaki ta wanke bakinta ta dawo ta amshi katin tana dubawa,komai a tsare yake harda dress code na maza da mata,mata shigan baqi zasuyi maza shigan fari.         Kusan baki daya kayanta sai data baje su saman gado,ta rasa wanda zata zaba,a haka anty dije ta cimmata,dariya ta dinga yi mata "Ato wallahi gwara ki qure adaka,don suma dangin saifullahin ba baya bane"sai data gama ruwan idonta sannan ta zabi wani shegen lace a cikin kayan wanda yake baqi ne an masa adon ja mai daukar idanuwa,zuba kayan tayi a jaka don ta nufi gidan baabaa don amira na can na jira,sanda ta isa an gama mata kwalliya,tayi masifar kyau cikin baqar wedding gown,sumayyan zama tayi itama aka soma yi mata tata.          Wani irin sihirtaccen kyau ke fita daga kwalliyarta hadi da tsumammen qamshi,kunya ta kamata da mamakin kanta,riga da skert ne wanda suka fitar da baki daya qirarta gaba da baya " wow"abinda amira ta dinga fada kenan tana qarewa sumayya kalo "Haka baqin kaya ke miki kyau amiran umman khalipha?,ya Allah" kai ta kada "Ai kam cire kayan nan ya zamemin wajibi,ina zan iya fita cikin jama'a haka amira" ta fada tana yunqurin cire daurin dankwalin da aka bata lokaci ana mata shi,da sauri amiran ta riqe hannunta tayi kicin kicin da fuska "Allah idan kika cire sai mun bata,ke komai ma bakison ya miki kyau,kina da kyau kina da aji kina da isar da za'a dama dake,kibar yin haka don Allah" yanayin yadda tayi maganar ta bata dariya,sai ta zame hannunta tana hada mata kayayyakinta data yi amfani da su kasancewar yau cikin dakinta ta shirya "Bari na maida su sashin anty maamaan ko" "Godiya namescy na" murmushi tayi ta fice a dakin.        A shirye ta tadda anty mamman,kasancewar ita zata yiwa amiran rakiya,wani irin biki suke a tsarin familynsu,suna gayyatar amarya ne da manyan yayyenta da iyayenta,inda zasu kawo musu ita suyi mata nasu bikin ma musamman haka sukeyi,ta ajjiye kayan tana saukowa suka sake kacibus da anty maamaa wadda ke kai kawon hadawa baabaa kunun alkama,haka matan suke,duk rintsi basa wasa da cikin mijinsu "Amiran umman khalipha zo don Allah ki kulamin da kunun nan in qarasa hadawa babanku hadin salad din nan"aladabce ta asawa ta bita kitchen din,cikin sauri sauri take hada komai saboda lokacin tafiya yayi,sau uku amira na aikowa sumayyan tazo su tafi,antyn bata sani ba,sai ana hudu taji aiken da ake mata ta dubeta "Jeki amira,na qarasa na biyoku daga baya" murmushi tayi tana noqe kafada "A'ah anty suje kawai,ma taho".      Cikin mintuna talatin suka gama,babu abinda jikinta yayi,saboda haka goge hannunta kawai tayi,sannan ta fidda kwalakcarta ta goga a hannayenta,ta sake shafe jikinta da turaren humrarta mai fidda wani sihirtaccen qamshi,wayarta dake ruri anty maman ta daga ta kara a kunnenta sannan tace "Eh na gama,gani nan" ta dubi sumayya tana maqala kyakkyawar jakarta "Muje ko amira" ta amsa.        Tuni maman ta rigata yin gaba saboda hill shoes din dake qafarta wanda ya sake sauya yanayin tafiyarta,sannu a hankali take takawa,sai ka dauka wani salon tafiya ce ta daban,koko tsabar yanga ce da iyayi ga wanda baisan takalmin ne ya takurata ba,baqar rantsatstsiyar mota ce wadda har sheqi take da daukan ido saboda tsabar sabunta da kyau,ita daya ta rage tsaye a wajen,da alamu dukka an tafi,baya anty mamaan ta bude ta shiga,yayi kyau cikin farin qal din trouser da lallausar short sleeve t.shirt baqa mai adon fari a jiki,wadda ta fidda sirrin hannunshi na tarin gargasa wadda ta kwanta har saman tafin hannunshi,da wani sashi na murdadden dantsensa wanda kana gani kasan ya saba daga qarfe,daya daga cikin abinda ya sanya kenan bai fiya saka kaya masu gajeran hannu ba,black hight top snickers ne a qafarsa,tsintsiyar hannunshi daure da agogon fata na kamfanin gucci mai matuqar tsada da kyau,yadda jikinsa ke fidda wani sihirtaccen qamshin wani turare da mawuyacine ka gane wani iri ne haka motar ki fidda sanyayyan qamshin freshner,komai nasa mai kyau tsafta da aji ne,jin yana niyyar tayarwa ya sanya tace "Tsaya,akwai mutum daya" a kasalance ya kashe motar,ka kadan baison tuqi da kanshi idan ba kamawa tayi ba kamar irin hakan,qarasowa tayi tana niyyar bude bayan anty maamaa tace "Koma gaba amira" don tasan halinshi sarai,ya tsani ya dauko mutane su shiga baya baki dayansu,yana alaqanta hakan da sai driver,jin an ambaci sunan amira ya sanyashi juyowa,daidai sanda take daidaita zamanta gaban motar suka hada idanu,idanuwanta suka fada cikin nashi,tashin farko kowanne ya janye idanunshi,qirjinta na bugawa,qamshin turarenshi na ratsa qofofin hancinta,idanunta ta ragewa girma tana duban gaban motar,tana ji kamar ta zura da gudu ta bar motar,wani dabaibayi taji na daureta,kwarjininsa ya mata yawa,tana jin zamanta a bigiren bai dace ba,a kasalance ta sanya hannu zata rufe murfin motar taji kamar muryar laila na kiran sunanta,itace tafe riqe da hannun abdallah da yayi kyau cikin baqaqen suit na yara,sai baqin sau ciki na yara da baqar safa baki daya,suka qaraso bakin motar inda take zaune "Anty,mami tace na kawo miki shi,kuka ya soma yaqi zama" dubanshi tayi cikin sigar lallashi "Abdallah,ina cewa na gaya maka tun dazun bazanje da kai ba,ka koma gida ka zauna da su laila,yanzu zan dawo bazan jima ba" qafafunshi ya sa bubbugawa yana sakin kuka sosai kamar wanda ake yanka yana fadin "Allah ni sai naje" ranta ya baci ganin yadda yake tsala kuka kamar tayi mishi wata uwa,sake lallaminshi tayi baiji na,maimakon haka ma sai ya buge hannun laila ya taho inda take ya shigo sit din da take,abinda bai taba yi ba kenan,yana qarasowa kuwa ta daga hannu ta kai masa mari,ta kuwa sameshi gefan fuskarshi,kafin anty maama ta furta maganar daga bude baki zata yi wata tsawa ta karade motar,tuni laila ta ja baya a tsorace,hannunshi ya miqo inda suke ya janyo abdallah wanda ke sakin kuka cikim jim zafin marin ya dorashi kan cinyarshi yana shafa inda ta mareshin "U r very stupid,how dare you zaki mari qaramin yaro har haka?,saboda bakisan ciwonshi ba?,bakisan ciwon haihuwa ba?,idan baki iya riqeshi mai ya sanya ba zaki sa a maidashi wajen mamarshi ba,fice min a mota!" ya fada cikin bacin rai da zafin rai,bata ankara ba taji hawaye sun soma layi bisa kuncinta,ji take kamar mukhtar ke mata fadan,me ya fusata ta ta mari abdallah itama bata sani ba,hannunta ta sanya kan mabudin motar ta tura da niyyar fita anty maamaa ta dakatar da ita "A'ah zauna,kuyi haquri mutapha,baki kyauta ba amiran umman khalipha,saurin hannu wa yaro bai kamata ba,ki kiyaye gaba" "To maamaa" ta fada ba don taso ba ta koma ta zauna,so tayi ta qyaleta ta fita,wani nauyi taji zuciyarta tayi,tana jin hucin numfashinsu su biyun.       Luf abdallah yayi kan cinyar mustapha wanda ya zaunar da shi suna facing juna ya rungumeshi cikin jikinshi yana ci gaba da shafa inda tayi marin,ci gaba da kallonshi abdallahn yayi,a hankali ya furta "Abba!" Sannan ya sake narkewa cikin jikinshi,wani nauyi zuciyarta ta sake yi,sai ta kasa daurewa ta sanya kanta a tsakiyar qafafunta,tausayin abdallahn yasake qara yawan hawayen dake fita a idanunta.         Bubbuga bayan abdallahn yaci gaba dayi kadan kadan har sai da yaji alamun ya huce,hannun ya sanya gefanshi ya ciro gorar ruwan da ya dauko da niyyar sha ya bude mishi ya saka mai a baki,sai da yasha sosai sannan ya rufe ya maidata gurbinta,ya sake zaro wayarsa ya latso wasu lambobi ya kara a kunnenshi yayi magana a taqaice "Eh,ka sameni gidan,ka tambaya adress din" ya katse kiran ya ajjiye,tada motar yayi sannan ya ya jata a sukwane abdallah na kwance jikinsa.         Shiru ne ya ratsa motar ba wanda ya sake magana,sumayya na kife har yanzu kan cinyarta tana qoqarin control din hawayenta,ambaton sunayen Allah ta dinga yi daya bayan daya har ta samu hawayen suka tsaya saidai bata iya dagowa ba har suka isa wajem,anty maamaa ce ta soma fita,tuni tayi gaba saboda suna isowa taji ana nemanta ta lasifiqar dake cikin wajen taron.        A hankali ta daga kanta ta gyara yafen mayafin dake kanta sannan ta bude murfin motar ta fice,ta gefan ido yake dubanta har ta bace a wajen,gajeran tsaki ya ja,yana jin bazai iya ci gaba da zama a wajen ba,daga yarin yayi ya dubeshi har ya soma bacci,sai yaji tausayinshi ya kamashu,haushinta ya sake qumeshi,cikin zuciyarshi ya dinga masifa shi kadai,bude motar yayi ya saba abdallah a kafadarsa suka koma sit din baya,kwantar da shi yayi sannan ya zauna gefansa.        Tana tsaye bakin get din gidan jingine jikin motarta hannunta harde a qirjinta,sam wajen bai dace sa tsarinta ba kasancewar a gargajiyance suka tsara komai,bugu da qari ranta a jagule yake,yadda almustapha ke ninka nuna hakin ko in kula da lamuranta,shigowar motar yaso ya dan ja hankalinta kadan,saboda irin motar mustaphan da take mutuwar so,wadda a yau ita taso hawa amma yaqi bata hadin kai,dauke kai tayi daga kallon motar don kada ta zubda ajinta,a dauka 'yar matsiyata ce kamar yadda take rayawa a ranta,ganin fitowar anty maamaa daga ciki shi ya sake maida hankalinta kan motar "Kada dai ace almustaphan ne?,yazo ya dauko maamaan a ciki amma ni ina matsayin matarsa ya watsan qasa a ido?" Take raya haka a ranta tana qarewa motar kallo,bata jin mustaphan ne,don tunda itama yaqi daukota ya kawota tabbas babu wanda zai kawo koda kuwa iyayenshi ne(a tunaninta),ita kanta motar bai taba hawanta ba sai yau,hakan yasa ta yin kwadayin ace ita ya fara dauka a ciki,mutum ce ita mai son taga tafi kowa,komai a gunta aka fara ganinsa,bata gama wannan tunanin ba sumayyan ta bude murfin motar itama ta fito cikin salon wata tafiya da zaka tsammaci ta yanga ce,saidai tsabar kasala quncin zuciya da tsinin takalminta ya haifarwa da mai kallonta ganin cewa yanga take kai tsaye,wani bala'i ne ya dirarwa zuciyarta,take ta tattara kallonta baki daya a wajen,ci gaba tayi da kallon sumayyan wadda sam hankalinta bai wajen taci gaba da yi har ta wuce,zuciyarta na tsaka da bata shawarar zuwa ta duba matuqin motar don tabbatar da cewa mustapha dinta ne cikin motar ko wani ne daban mai farcen susa ya yaci nasarar mallakar irin motar mijin mata,hutassheta akayi saboda fitowar da yayi ya koma gidan baya yana sabe da abdallah,ta gane yaron,yaron data cuccusawa zagi jiya da daddare saboda ya gyara mata gyaran alwalarta,huci ta soma fitarwa saboda wani zafi da taji qirjinta yana yi,me kenan?,me hakan ke nufi?,ba bata lokaci ta soma takawa zuwa bakin motar.       Bude murfin motar tayi sannan ta cusa kai cikin motar kai tsaye,hannunshi na saman kan abdallah yaji shigowarta,juyowa yayi ya dubeta sannan ya dauke kai yaci gaba da abinda yake kamar bai santa ba,ta sani sarai bazai tanka mata ba idan in zata shekara matuqar ba ita tayi magana ba,ko ita din tayi bata da tabbacin amsarsa "Tsakani da Allah ka kyauta kenan man,naci burin hawa motar nan ka watsan qasa a ido amma sai naga ka kawo wasu,har wata banza can ka baiwa damar zama gefanka wanda ni kadai ke da wannan matsayin?" Ta fada cikin son dai daita fushinta don kada ta fita daga hanya ta jawa kanta wani sabon lamarin,ta san duk sabida zancan qarasa karatunta ya sake zame mata wani badadde,ilai kuwa shiru ne ya biyo baya,kishin sumayya data gani yaci gaba da mintsinin zuciyarta "Wai shin ma meye alqarka da ita waccan yarinyar da har ta samu matsayin daukota cikin motar da koni ban taba shigarta ba,sannan ko kai kanka yau ka fara shigarta?" Bai da ko niyyan waiwayowa ya dubeta bare ta saka ran samun amsa,wayarsa ce tayi tsuwwa ya saka hannu inda ya ajjuyeta ya dauko yana dubawa tare da amsa kiran da ya shigo din "Bude ka shigo a bude take" ya gayawa drivern nasa a taqaice,dama shi yake jira,sauke wayar yayi still bai dubeta ba yace "Idan kin gama kina iya sauka ko?"wani abu ya tokare mata wuya,sai ta zuba ido tana kallonshi,sonshi kamar ta lasheshi,haushi kamar ta hafiyi zuciyarta,idanunta ya cika taf da qwalla,cikin rawar murya da son karya lagonsa da kuka ta soma cewa " ni kake ma haka mustapha?"hannu yayi saurin daga mata wanda dole ta shanye sauran maganarta,sai ta bude murfin ya fice da hanzari,budewa drivan yayi ya shiga cikin girmamawa ya russuna bayan ya zauna ya gaidashi,a taqaice ya amsa mishi,sai da ya tayar da motar suka bar layin suka hau kwalta sosai sannan cikin girmamawa yace da shi "Ranka ya dade ina zamuje?" "Maitama" ya bashi amsa a taqaice,baice komai ba ya qara gudun motar suka lula titi.          Sosai lunching din ya qayatar,ba qaramin qauna iyalin saifullahi suka nunawa amira ba,basu tashi ba sai qarfe bakwai na dare,wannan karon tare da su amiran suka koma,saidai ko kadan bata da walwala,a takure take jim zuciyarta baki daya,hatta da amiran ta lura,amma bata ce mata komai ba saboda ta tambayi anty mama abdallah taje gaya mata abinda ya faru,ana saukesu ta dubi amira "Kimin afuwa zan wuce gida sai gobe,kaina ke mij ciwo sosai" ba qarya take ba da gaske kan nata ciwo yake mata,sai ta daga kai "Na miki,Allah ya bada lafiya,ya tashemu lafiya" ta bude murfin motar ta fice.         Wanka ta fara yi sannan tayi sallolinta,anty dije tace mata ga abinci tace sai anjima,duka abinda take hankalinta bai wajen yana wajen abdallah,ina yake?,ina ya kai mata shi,tun tana kasa kunne da ido har ta kwanta saidai shiru kake ji,kasa haquri tayi ta miqe da hijabin sallarta ta qwanqwasa dakin anty dije ta mata izinin shiga,kwalliya ta tadda ta tanayi "Uhm,ya akai amara qirjin biki" murmushi ta danyi wanda yafi kama da yaqe "Anty wannan yayansu amiran ya amshi abdallah tun dazun,har yanzu ban ganshi ba bashi ba abdallahn" cikin ko in kula tace "Wa?,wai musty,kada ki damu kisa a ranki kamar kina tare da abdallah ne,ai mayen yara ne,indai mustapha ne a rina" hankalinta ya dan kwanta da jin hakan,sai ta koma daki tayi shirin kwanciya,don ita kadai take da buqata a yanzh,tun tana sauraren ta ina abdallahn zai shigo har bacci ya sureta.          Washe gari sam bata shiga gidan ba ma sai da yammaci tayi aka soma shirin tafiya dinner,nan ka bata ga abdallan ba,ba kuma wanda ya mata maganarsa,haka taci gaba da daurewa har sanda anty maamaa ta dan tsokaneta "Abdallah kam anyi wuyar gani anyi sabon daddy" murmushi kawai ta danyi ta basar.        Wani qayataccen event center suka kama,hmmm masu abu da abinsu,kada kaso kaga yadda gun ya qawatu yayi matuqar tsaru,ranar sumayya anyi abun gani,ita ta zauna mazaunin babbar qawar amarya,tayi komai yadda zata faranta ran amiran duk da a takure take matuqa,idanuwan maza bisa kanta sunyi yawa,kai har ma wasu daga cikin matan,sai da guri ya gama tumbatsa sannan su'adah ta iso,a nan tayi burgar data saba,tsakiyan abokan ango cikin dinkim riga da skert na wani shegen leshi mai azabar tsada wanda aka ci mutuncin tsadar tasa aka yi masa dinki na ganin dama,tsagar skert din har kusan gwiwarta,dinkin ya kamata dam,banda dankwalin da aka tsarawa dauri babu komai a kanta,don ko tuna sunan mayafi bata yi ba,liqi ta shiga yi da 'yan dubu dubu sabni kar wanda ita kanta bata san nawa ta barar ba,abin nema ya samu ta dauki idanuwan jama'a,ta kuma qona zukatan 'yan baqinciki wadanda bas son tarayyarta da mustapha,to su gani ya tsaya mata,sai data yi mai isarta sannan ta sauka daga step din ta koma mazauninta. Sai sha daya na dare aka tashi kowa ya koma inda ya fito. *******    *******    ******         Tun qarfe goma na safe layin nasu ya tumbatsa ya dinke da jama'a kasancewar goma da rabi ne daurin auren,bacci ranar tayi sosai dakin anty dije,bata tashi farkawa ba sai qarfe tara da rabi na safe,tarin missed call ta taras duka na amira,da hanzari ta miqe ta fada toilet tayi wanka,a gurguje ta fito ta shirya cikim shaddar da sukayi anko wadda tayi masifar haduwa,kamar yadda dinkin doguwar rigar ya dace da jikinta,komai da tayi amfani da shi kalar zaren da akayi aikin shaddar da shi ne,ta fito fes mashaAllah,daidai sanda laila ta shigo,baki ta sake tana kallon sumayyan,ta qaraso dakin ta samu bakin gado ta zauna "Wai dama don Allah anty sumayya haka kike da kyau" dariya yarinyar ta bata saboda bihaqqi ta fada "Sai an tambayo" ta fadi hankalinta ka can gidan baba,saboda hayaniyar data dinga jiyowa na tashi ta tabbatar layin yayi tumbatsar da babu damar ta fita,valcony din saman benan anty dije ta bude ta fita ciki,layin ya shaqara da mutane ya cika masha Allah,kai ta dinga kadawa don tasan dole ta haqura har sai an ragu. Kujeta ta ja ta zauna daga gefe yadda zata iya hango komai,ta bude wayarta ta soma lalubar lambar amira don ya bata uzurinta,hakanan taji yana yinta ya soma sauyawa kamar ba ita daya bace a gun,kamar fisgar mayen qarfe haka idanuwanta suka jata zuwa inda yake tsaye tsakiyan wasu zaratan samari kamarshi. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [23/02, 11:51] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 7⃣2⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *ALLAH YANA GAFARTAWA WANDA YASO YA KUMA AZABTAR DA WANDA YASO* YA ALLAH KA GAFARTA MANA ___________________________________ *TAB,BIGI SAI BIGI,BABBAN GORO SAI MAGOGIN QARFE,IDAN KAJI WANE BA BANZA BA,INA MA'ABOTA KARATUN LITATTAFAN HAUSA,KAMA DAGA NA QUNGIYAR HASKE HARMA WANDA BA NA HASKE BA,SHIN KUNA DA BUQATAR JIN WANI SABON KUNDI WANDA YA TATTARE LABARAI NAU'IN DABAN DABAN WADANDA SUKA SHAFI AL'AMURA NA ZAHIRI DAKE FARUWA CIKIN RAYUWARMU TA YAU DA KULLUM?.......TO MAZA KU GARZAYA KU NEMI LITTAFIN KUNDIN HASKE,WANDA KE QUNSHE DA LABARAI DAKE DAUKE DA NAU'IN RAYUWA IRI DABAN DABAN,LABARAI NE WANDA KE DAUKE DA DIMBIN DARUSSA MASU RATSA ZUKATA,DUMBIN ILIMI MAI JAWO HANKALIN DAN ADAM ZUWA SAKE LURA DA GYARAN RAYUWARSHI,MAZA KA/KI GARZAYA KADA A BAKI LABARI,BA SHAKKA ZA'A CI DA RABONKI MATAUQAR KIKA BARI YA WUCEKI,AKWAI SHI A WATSAPP DA APP DIN WATTPAD BAKI DAYA* *SADAUKARWAR WANNAN SHAFIN GA:* *SADIYA ZABURA* *UMMU RAMLAT* *MAMAN SAYYID* *DA MARUBUCIYA* *AYSHA DAN SABO* *RABBI YA BAR QAUNA*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽😍😍😍        Kyawawan idanuwanshi wanda suka wadatu da gashin idanu kamar yadda girarsa take masu kama da na wanda ke jin bacci suke kan ta,shi daya ne tak sanye cikin qananun kaya sabanin dukka sauran wadanda suke tsaye tare,baki dayansu shadda ce jikinsu dinkin tazarce kaloli daban daban,kusan tare suka janye idanuwansa,gabanta ya shiga faduwa,kasa zaman wajen tayi,batasan ana iya gajin mutum ba,gashi ko mayafi babu a jikinta,sai ta miqe jikinta na rawa gabanta na faduwa ta bar wajen,ta tura qofar ta kulle ta dawo cikin bedroom din anty dijen.       Gefan gado ta kwanta rub da ciki tana sauke numfashi,maganganun baabaa suka soma dawo mata,har yau ta kasa gane me yake nufi,tana da buqatar qarin bayani,tana buqatar taimako wajen wanu ko zata fahimci me yake nufi,amma ta taimaka masa wajen gyara rayuwarsa kamar yaya kenan,wanu mummunan abu yake mara kyau yakeso ta saka baki?,amma ita a wa?,bata da wannaj power din,ganin qwaqwalwarta na neman daurewa yasa ta kada kai tare da yin watsi da maganar,maimakon ci gaba da tunani sai ta sake daukan wayarta ta lalubi zainab ta kirata,din jiya suna wajen dinner taga misscall dinta baya kuma samu ta bita ba.         Bayan sun gama gaisawa da mama ta musu Allah ya sanya alkhairi zainab ta karba,nan take gaya mata jiya aka kawo lefe sati uku kuma aka sanya,murmushu sumayya ta saki tana tsokanarta "Kice mu fara shirin tahowa kano ko?" "Wallahi yaya,kizo ayi tsare tsare masu kyau" "Insha Allah,ina huce gajiyar wannan bikin zaki ganni,Allah ya nuna mana da rai da lafiya" "Amin yaya,ina abdallah na" "Uhmm,ni kaina bansan ina yake ba,yana gidan biki" "Ki gaisheshi tunda ya manta da mu" dariya ta danyi "Zaiji,ki gaidan halimaty,wayarta bata shiga" "Zata ji" suka katse wayar.        Tana sauke wayar ta jiyo muryar abdallah yana karadi daga qasa shi da sh hafiz,sauka tayi daga gadon ta sauko qasa,yayi masifar kyau cikin wata arniyar shadda ash wadda batasan inda ya samota ba,hulace kanshi zanna wanda sau faman zuba qyalli take,qafafunshi saye da takalmi sau ciki,abinka da uwa da da,yana ganinta ya tako da gudu ya daneta,murmushu tayi ta zube saman kujera yana faman zuba mata surutu da bata labari.         Ganin sha daya tayi ga gidan babu kowa sai ita ya sanyata yin shahada ta yafa mayafinta ta fito,kamar zata nutse haka ta dinga ratsa mutane a darare tana wucewa har ta kai ga cikin gidan bayan ta kira humaida ta gaya mata inda suke,ko ina harabar gidan 'yan uwa da abokan arziqi ke kai kawo,kowa ka ganshi cikin kwalliya da walwala,daga gefe guda ta hango mahmoud da tarin abokansu ciki har da alqasim,suma sun ganta saboda haka ta qara sauri don kada su rusketa.        Batayi aune ba sukayi karo kanta ya daki qirjinsa,tayi taga taga ta komo ta fada qirjinsa,zuciyarta kamar zata fito saboda tsoro,tayi yunqurin janyewa,ta samu nasara saidai hannunta na cikin nashi hannun yana duban qwayar idanuwanta,sai yanzu ya samu amsar inda ya samu qamshin da ya buwayeshi tun shekaran jiya,wanda har kuka su'adah tayi sabida jin qamshin,don ta tabbatar hadin humra ce ta mata ta musamman ba turaren namiji bane,gaba ta tusashu tana tambayarsa ina ya samu turaren,baki daya zuciyarta ta gama zayyana mata yana neman wata ne,idan banda haka ina zai samo turaren mace a hannunshi?baya ga haka ta lura wannan karon sam baya marmarinta,baya nemanta idan ba ita ta buqata ba,bayan a baya ta sani cewa duk sanda suka hadu har sai ta gaji ta hada kayanta ta gudu yake qyaleta,amma wannan karon sam ba haka bane,yana jinta yayi mata banza ya gama shirin baccinsa ya kwanta tare sa juya mata baya,don bashi da amsar bata,shi kansa yana jin qamshin cikin hancinsa amma baisan inda ya sameshi ba,baijin zai iya bata lokacinsa ya mata wannan bayanin tunda har tana zarginsa,to ta dauki duj hukuncin da take gani zata iya dauka,hakan ya sake hassala zuciyarta,itama ta shiga fushi da shi gadan gadan miqe ta fice ta sauya dakin kwana,bata san cewa ba shi ta yiwa ba kanta ta yiwa,tunda ba yau farau ba da yake kwana shi daya tamkar gauro,idan da sabo ai ya saba.        So take ya sakar mata hannu ko don idanuwan mutane da ke kai kawo a wajen,uwa uba ga haramci na riqe mata hannu da yayi,tayi yunqurin zame hannun nata amma abu yaci tura yana tsaye qyam yana dubanta,babban goro sai magogin qarfe,ya kusa lullube tsahonta baki daya,dududun nata tsawon bata fi iya qirjinsa ba,ga wani kwarjini daya cika wajen,ganin masu wucewa sun soma ankara ya sanyata cewa "Ka sakar min hannu" cikin izza da motsa labbansa "Saikin gayan abinda ke baki tsoro,me ya koroki bayan kowa na kai kawo a nutse amma banda ke?" Daga fararen idanunta tayi ta watsa mishi su,duk da yadda qirjinta ke bugawa,lumshe idonsa yayi ya bude ya janye nashi idanun daga kallonta,bai taba ganin mace mai farin qwayar idanu ba kamar haka ya raya a ransa,tsaki yaja a fili sannan ya saki hannun nata "Ki kula next time,ban son irin wannan shirmen" ya fada yana duban gefanta,ita ke shirmen ma?,abun ya bata haushi,sai ta banka masa harara ta gefan ido duk da yadda gabanta ke faduwa qasa qasa tace "Kaima sai ka kula tunda kana da idanu ai ba ni kadai ke da idanuwa ba" batasan tayi kuskure ba saboda kaifin ji da Allah ya hore mishi,ko yaya magana take yana iya jiyota,yana daya daga cikin wadanda Allah ya yiwa baiwar ji,har wani lokaci ba'a iya gulmarsa matuqar yana cikin gidan,har yayi gaba ya juyo a mamakance yana dubanta,karo na farko kenan da wata 'ya ta taba maida masa magana,bakinta ta murguda duk don ta sake bashi haushi tayi gaba abinta,wani abu ya tsaya mishi a rai,ranshi ya baci,yau shi akewa rashin kunya?,abinda yafi tsana kenan a rayuwarsa tun lokacin quruciya,abinda ya fara hadashi kenan da su'adah tun tana qaramarsa,lallai zaiyi maganinta,wace ita da har take jin karanta ya kai tsaiko,babu shakka sai ya hukuntata.       A bangaren anty maamaa ta tadda su,tana zaune tsakiyar yayunta anty farida da anty huda da matan yayyen ta ni'imah da fahariyya,sai qawayenta da cousins dinta irinsu eesha humaida ummu salma da sauransu,a hankali ta qaraso saboda lasalar da take ji cikin jikinta tana karbar saqon harara daga amira,duk da haka murmushi ne kan fuskarta,ta riga da ta sani itace mai laifi,sauran da suka san mekw faruwa dariya suka dunga yi sunsan za'a kwashi daramer,amma sai sumayya ta kashe mata gwiwa da fadin "Ta zama ta saifullahi,ayya yarinya zata bar gida" ai kuwa sai ta soma qwalla,tana dariya ciki ciki ta qaraso ta zauna gefanta ra mata rada a kunne ma tsawon minti biyu,sau gani sukayi ta saki dariya tana share hawayen,huda ce taja tsaki "Au qaryar banza,dama fa son aurenta take 'yar banza bansani bane,saifullahin da ake ji da shi kamar a lashe mishi mazaunai" dariya ta kamasu baki daya,dqi dai da dai dai sumayya ta bi ta gaida kowa,batasan matan yaya adam ba sai lokacin ni'imah da fahariyya,fahariyya ita ta fara tahowa ni'imah ta jira maigidan sai jiya suka taho tare da daddare,bata ga fahariyyan ba saboda 'yar jin kaice itama kamar yadda amira ke gaya mata,ni'imah din ce babu ruwanga,hakanan take haquri da halayyar fahariyya na goranta mata da take lokaci lokaci akan rashin haihuwa,saidai zaman nasu babu yabi ba fallasa,rashin mutuncin fahariyyar da sauqi sakamakon cewa adam din tsayayyen namiji ne,bai yarda a wulaqanta masa uwar gida ba,sam basa shiri da su'adah da fahariyya saboda kowacce na jin kanta da jin cewa ta isa saidai daya tabi daya,duk da a zahiri duk cikin yaran gidan babu wanda ke da dukiyat almustapha,wannan ya qara kishin su'ad cikin zuciyar fahariyya,itakam ni'imah 'yar babu ruwa na ce,ta kama mutuncin kanta,don iyayenta ba wasu bane rufin asirin Allah ke garesu,sai a yanzu da tayi dace da miji na qwarai suke samun sauyin rayuwa sanadiyyarsa,duk da haka dama tana da managartan halaye wadanda su suka fusgi adam zuwa gareta,duk da tarin yaran masu kudi dake sonshi a lokacin,ta kasance ta daban a gunsa har a yanzun duk da bata taba haihuwa da shu ba,sakamakon haquri biyayya da tsantsar iya zamantakewa da miji mai tafiyar da hankali.         Da daidai suka miqe suka fice ya rage saga sumayyan sai anty ni'imah sai humaida,suma sun maqale ne saboda suna kwasar wasu sirrika da lacture da anty ni'iman ke bawa amira,wanda baga fara ba sai bayan da wadancan suka fita,ba amira ba hatta su sumayya sun qaru da ita sosai,a nan suka zauna suka ci gaba da hirarsu,ni'imah ba dai sauqin kai ba,kamar qannenta haka ta daukesu,aqalla zata girme musu da kusan shekaru goma,amma sam hakan bai wani nuna ba sosai sabida tsabar gayu.       Qarfe bakwai na magariba aka tafi kai amarya,babu wani takura ko neman mota kasancewar kusan kowa ya mallaki motar hawanshi,wanda ya taho daga wani garin ne bai taho da abun hawanshi ba sukayi amfani da motocin gidan baabaa,ga kuma ta familyn saifullahi.        Ba shakka wannan shi ake kira qwarya tabi qwarya,ba shakka amiran ta shiga gidan da yayi dai dai da ita,gidane na alfarma wanda ke tafiya da tunanin mai tunani,sanda aka fara tafiya amiran ta riqe sumayya gam kan sai ta jira anzo an sayi baki,sun riga da sun gama tsarawa babu batun siyan baki,ko akwai din ma ita batajin zata tsaya,saboda mutum biyu daga cikin abokan saifullahi da suka uzzurawa rayuwarta tun ranar kamu,ta musu qaryar a niger take,saboda haka bata son su hadu bare su takura ta,dabara tayi mata cewar bari taje tayi fitsari daga haka ta arto gida.       Biki ya tashi lafiya,ummee da kanta ta yi ma sumayyan godiya tare da godiyar kayan humra data yi mata wanda su aka jerawa amiran ma,kunya ce ta kama sumayyan,duka duka me tayi,su basu duba tarin karamcinsu wanda ya kai ga cancantarsu kan yi musu komai.        Tun a daren ta kashe wayarta kwata kwata,don ta tabbatar cewa gobe kamar da qasa sai amira ta nemeta,jikinta ya gaji tubus irin gajiyar da bata taba yin irinta ba,lallai biki ba wasa bane,tunda ta kwanta bata tashi ba sai da gari ya waye,ta makara sallar asuba,don sai shida da rabi ta yita,tana gamawa ta koma ta sake kwanciya,ba ita ta farka ba sai sha biyu saura na rana,yunwa ta sadakarta,a guje tayi kicin ta tadda anty dije na soya miya qamshinta ya cika gidan baki daya,ba magana ta mata nuni da kayan break dinta dake ajjiye gefe,tana kaiwa baki daya yiwa antyn sannu da aiki "Ai ke zanwa sannu,yaran nan sunso tadaki badon ma hanasu ba,shi yasa da abbansu zai fita na hadasu da shi ya kaisu wajen inna(kakarshi)" "Kai kina ji da ni anty na" ta fada tana jan kujera don ta ji dadin cin abincin sosai "Ba dole ba,kece fa babbar diya" suka sanya dariya baki daya sannan suka ci gaba da hira suna tattauna wasu daga lamuran da suka faru yayin bikin,antyn na juye miyar cikin warmer tace "Ai ke kam bakiga hutu ba,saura sati uku a shiga wani bikin" "Wallahi anty shi yasa nakeso nayi kamar kwana uku haka ina bacci,don so nake next week na wuce kano" hararata antyn tayi "Dama na sani ai,ke kam garin nan kamar yana mintsininki,gidan fa baki daya baya dadi wallahi idan kika tafi,hatta da abbansu ya dinga mitar kin dade,amma wani lokaci sai na rayawa a raina dole fa mu saba tunda wataran zaki aure,idan kika tafi kuma ya zamuyi" shiru sumayyan tayi taci gaba da kurbar tea,saboda anty dijen ta kawo zancan da bata qauna cikin hirar tasu,sai data gama sha ta sure cup din tana goge hannunta sannan tace "Anty,wata tambaya ce da ni" "Uhmmm,Allah yasa na sani" shiru ya danyi tana tsara yadda zata jefa mata tambayar kafin tace "Wai idan wata ko wani yazo ya cewa budurwa ki taimaka ki gyara rayuwar wane,wai me hakan yake nufi?" Waiwayowa tayi ta kalleta har sai da gaban sumayya ya fadi,Allah yasa ba wani mummunan abu bane,kamar antyn ta tambayeta wa ya fadawa wani hakan sai kuma ta fasa,taci gaba da aikinta tana bata amsa "Maganar na da ma'ana bangare biyu,nq farko idan har aka fadi haka ga wani ko wata makusanciya ta mutum ana nufin ta dinga bashi shawara da hanashi aikata wasu abubuwa,ko kuma wani abu na son faruwa da shi ana son ka taimaka kada ya fada cikin wannan abun,sannan ma'anar na iya daukan AURE ko SOYAYYA,abun nufi.......shi wanda ya gaya miki maganar yana ganin kamar kina da wasu qualities da wani namiji ke buqata,wanda wannan qualities din zau taimaka masa wajen gyaruwa ko ingantuwar rayuwarsa,babu kuma hanyar da zaki gyara ko ki inganta rayuwar tasa sai ta hanyar AURENSA ko yin SOYAYYA da shi,to sai a baka maganar a dunqule" tunda ta dauko maganar gaban sumayyan ke faduwa "Da gaske baba na nufin kenan ta auri almustapha?,abinda baabaa ke son fadi mata kenan" kai ta shiga girgizawa cikin zuciyarta ta soma furta "La haula wala quwwata illa billah,Allah ka sani ina ganin qima da darajar wannan bawa naka,ya Allah ka fidda masa wannan tunanin daga zuciyarsa a kaina,ka jefa masa tunanin wata,Allah kada ka bashi iko ya tambayi abinda bazan iya masa ba" "Ke sumayya meye haka?" Inji anty dije ganin yadda take kada kai tana mus mus da baki,murmushin yaqe na musamman ta qaqalo sannan tace "Ba komai,kawai ina mamakin yadda muka kasa fassarar maganar,wani ne ya gayawa wata" ta fada tana miqewa tsaye sannan ta fice daga kitchen din,da kallo anty dije ta bita,cikin zuciyarta tana addu'a,Allah ubangiji ya sanya sumayyan tayi gamo da miji ne dan gaske,wanda zata huce takaicinta,babu shakka zata so za kuma tayi burin sumayyan tayi auren da zata huta ta sanadiyyarta,juyawa tayi taci gaba da aikinta tana addu'a cikin ranta.         A sanyaye ta zauna bakin gado maganar na sake y mata yawo,indai haka ne ba shakka dole ta qauracewa haduwar ta da baabaa,kai ya zame mata jazaman tafiya kano,kuma bata jin zata dawo nan kusa idan ta tafi din,zata yita qirqiro dalilai ne wadanda zasu zaunar da ita a can.        A daddafe ta haqura ta kai ranar alhamis kamar yadda ta gayawa anty dije,sannan ta shirya tafiya,wanda ya rage sauran kwanaki goma sha hudu bikin,anty dije ta bata saqonni gun mama sannan tace suma nan da kwana bakwai suna tafe,wannan karon saboda tsabar zaquwa ta tafi bata iya jira abban laila ya dawo daga kaduna da yaje ba ya hadata da driver,motar haya ta hawo ta tafi,ba yadda anty dije bata yi ba amma ta kasa daurewa ta jira.         Tana hanya taji kira,lambar amira ce,tun kafin ta daga ta saki murmushi "Amaryar saifullahi bada kanki a sare" kamar wadda ke shirin sakin kuka ta soma mata qorafin kota nemeta ko?,sun hada baki da saifullahi sun sace mata wayarta,shi din ma ya rufe gidan ba shiga ba fita wai sai sun huta,ya kuma hanata wayarshi sai yau ya bata wayan,dariya ta dinga mata din yasan da wannan plan din,sai da ta gama qorafinta sannan suka gaisa tace yaushe zata zo don Allah "Kin ganni hanyar kano,wani bikin ya sake kira na,bikin zainab dita" "Wayyo,dama a kusa da namu ne,naci burin zuwa fa namecy" dariya tayi "saidai ki tara ana halima idan Allah ya kawo"haka nan suka gama hirarsu ta baiwa saifullahin suka gaisa sannan sukayi sallama.    Kamar ko yaushe sunyi murna da zuwanta,mama nata tsokanar abdallah wai ya qara qiba "Amma dai zaka koma ko?" Wuya ya maqale a kafadarsa "Nan yafi dadi,can kullum kuna rufe a gida" dariya suka saki don abdallahn badai son yawo da wasa ba,hararshi sumayya tayi "Nima babu inda zaka bini,rigimammen kawai" ko a jikinsa dariyarsa ma ya sanya abinsa,washe gari yaya yahansu tazo ta daukeshi ma sukayi tafiyarsu,sai ranar kamun zainab tace zata dawo da shi.        Tunda tazo babu zama suna ta shirye shirye ba kama hannun yaro,ita da anty salma qanwar mama da anty amina matan yaya abubakar,sunyi waya abdur rahman bai nan amma zai dawo da shi za'a yi daurin auren shi yasa take hidimarta hankali kwance ba wani damuwa ko takura,cikin ikon Allah da baiwarsa komai yana tafiya daidai,sumayya taga yadda ake komai cikin tsari saboda haka ta dage ta tsarawa 'yar uwarta komai yadda zai qawatar ya kuma burge,kudi sosai tasa yaya abubakar ya bata bayan wanda anty dije da uncle farouq suka bata,dinkuna sosai ta yiwa mama,atamfofi masu tsada da kyau,harda mayafai da takalma duk da yaya abubakar yayi musu amma tace wannan nata ne,sannan ta siyawa malam gezna ta asalin wadda zai sanya ranar daurin aure,takalmi mai kyau harda agogo da turare da sabon rawani fari qal,kasancewar malam din ba baya bane wajen tsafta shi yasa kusan kayansa galibi farare ne,aka yi masa dinkin babbar riga 'yar ciki da wando,ita kam dama bata da matsalar sutura sai anko kawai data yi,sai abdallah data masa shaddar daurin aure duk da dumbin kayan da yake da su,saura kwana tara biki kuwa saiga anty dije da iyalinta,nan aka shiga hidima sosai.       Kan hanyarsa yake ta dawowa daga airphort bayan ya kai anty dije da yaranta sun tashi zuwa kano,tun daga nesa yaga kamar motar baabaa prof a tsaye,hakan ya sanya ya rage gudun motar ya qaraso a hankali ya faka tashi motar bayan tasu sannan ya bude ya fito.       Baabaan ne tsaye gaban motar,kana dubanta kasan matsala ta basu,qarfen nasara da bashi da tabbas,motar kwata kwata shekararta guda,ba yadda mustapha baiyi kan a canzata ba kamar yadda ya saba sauya masa motocin hawanshi amma yace a sauya sauran amma ita banda ita,yana jin dadin motar,da ita yake zuwa gidan gonan sulensa duk qarshen sati,duk randa zai tafin baya tafiya da wasu motocin face wadda ita kadai zai hau,kuma daga shi sai druvansa,yana jin dadin zama gidan gonar,ya zazzaga yaga gidan gonar sosai,yanajin nishadi da farincikin yadda dukiyar sulensa ke habaka,fatanshi Allah nuna masa ranar da zaiga sulenshi,a irin haka ne yau motar ta tsaya musu a hanya.        A aladabce uncle farouq ya qaraso "Subhanallah,baba kada dai ace qarfen nasara ya muku tsiya?" Cikin murmushi mai dauke da dattako yace "Wallahi kuwa,to ya za'ayi,yau da gobe ai sai Allah,babu wani abu dake matabbaci" "Gaskiya ne" inji uncle farouq yana fidda waya daga aljihunshi yana fadin "Bari a kira gida to a turo wata ko baabaa,tamu motar ba lallai ka iya shiga irinta ba" murmushi ya kuma subucewa baban,har ya sanyashi ya juya ya sake kallon motar duk da ya santa,motace mai lafiya wadda bata da wani aibu ko makusa,ko kai waye zaka iya hawanta,amma ya sani cewa irin motocin da mustapha ke ajjiye masa yana hawa shi ya sanya farouq din tunanin yafi qarfin wannan "Haba faruqu,saidai kawai idan rawar hawa motar take kake min,amma ni din waye da bazan hau wannan motar ba" ya fada yana dariya,bakinsa ya rufe shima yana dariya "Afuwa baabaa" ya fada yana bude masa gaban motar,kafin ya shiga ya waiwaya ya dubi drivan nashi "Kada ka tsawaita tsaiwa a nan,ka kira bakaniken nan,idan bakaniken ya iso ka bashi muqullan ka taho gida" a ladabce yace "Yallabai man yace kada a sake barinka ka hau motar da baniken hanya ya tabata ranka ya dade" murmushi ya saki "Qyale wannan,idan na biye masa ma a jirgin sama zan dinga yawo,ni waye da bakaniken hanya bazai taban mota ba,shi yasa na hana a kira gida agaya musu motarmu ta tsaya nasan zai iya jin zancan ya damu mutane da batub sauyan motoci,bayan ni din duka kwana nawa ya rage mana a duniya,kayi yadda nace kawai" "To ranka ya dade" inji drivan,baban ya juya ya shiga motar faruqun ya rufe ya zagaya shima ya shiga ya tadata suka fara tafiya.        "Asalina daga qauye na fito faruqu,kiwon dabbobi  na dinga yi ni da aminina,da can ko jaki bani da shi na hawa bare a kai ga mota,din me zan dinga manta asalina,ita duniya gaba dayanta yadda ka dauketa haka take zuwa maka,mafi daraja cikin mutane shine wanda a zahiri ya isan amma yake daukan kanshi ba'a bakin komai ba,girman kai rawanin tsiya ne,wanda ke zaton ya isa kuma sai Allah ya qasqantar da shi a duk inda baiyi zato ba" kai uncke farouq ke gayadawa cike da gamsuwa,tsohon dattijon qwarai ne,yana bala'in son zama da shi saboda dole ka dauki darasin rayuwa,idan ya shiga cikin wasu baka isa kace shine wannan professor din ba,kuma tsohon jakadan nijeria a qasar amurka.       Danja ta tsaidasu uncle farouq yaci burki da sauri saboda yana dan gudu,wanda hakan ya sanya katinan dake zube gaban motarshi suka zubo,jiya ya karbosu shi yasa aka yiwa malam su na daurin auren zainab ya baiwa anty dije ta tafar mai da su ragowar ya ajjiye wajansa zai bawa kawunshi "Bismillahi" malam ya fada yana cewa "Kaima ashe kana dan taba irin tuqin almustapha kenan ko?" Ya fada yana murmushu tare da duqawa yana kwaso katinan sa sukw zube din.        Caraf idanunshi suka kai kan sunan dake jikin katin wanda ke qunahe sa sanarwar daurin auren SULAIMAN AMINU DAHIRU GOMBE,sake maimata sunan yayi,sunann da ya kasance sak irin na tsohon amininshi sule,tsohon aminin da kullum zuciya ke begen ganawarsu,maimaita sunan ya dinga yi tare da kallon rubutun da aka tsarashi kalar golden,tamkar zai gano masa da zargin da zuciyarshu ta fara yi,uncle farouq ya lura da hakan sai yace "Bikin qanwar mai sunan mama ne,wato 'yar yayar khadija" wawiyar ajiyar zuciya ya sauke ya maida dubanshi ga farouq "A ina suke faruqu" "A kano suke" "Kano?,meys asalin mai gidan" kai ya girgiza cikin kokwanto "Bamu taba zancan gaskiya da ita ba,amma dai a kano na sansu,wani abu ne baabaa?" Kai ya kada yana maida katinan mazaunansu "Sunan ne kawai ya yimin kama da na wani tsohon aminina wanda har yau nake neman bayan ya bata tsahon shekaru" "Ayyah,Allah ya bayyana shi" "Amin amin faruqu". Bai bar babaan ba sai daya dangana da shi har cikin gidan sannan baabaan ya sauka yaba masa godiya,kunya duk ta kama faruqun,a rayuwa babu wani abu da zaiwa baban da har zai masa godiya,bayan babu wani nau'in karamci da kyautatawa da baban bai masa ba tun daga sanda ya sanshi har zuwa yau.       Tunda ya koma gidan baki daya ya kasa sukuni,katinan da sunan sun tsaye masa a rai,daren ranar kasa cikakken bacci yayi,yayi salloli sosai kafin ya samu bacci yayi awon gaba da shi,da asuba da ya tashi da abun ya tashi cikin ransa,har gari yayi haske,sai kawai ya tsinci kanshi da jawo kiran wayar uncke farouq ya buqaci adress din gidan mamallakin sunan da ya gani jikin katin,babu haufi ya tura masa don baya shakka cikin nagartan baabaan,yasan cewa koma mene alkhairi ne IN SHA ALLAH.         Waya kawai ya sake dagawa,ya lalubi lambar mahmoud ya buqaci ganinsa,ba bata lokaci ya iso kasancewar yana cikin gidan,sanar masa yayi ya laluba idan akwai jirgin da zai tashi daga abuja zuwa kano ya yankar masa ticket guda hudu,shi daya mahmoud din daya mus'ab wanda yazo biki bai koma thailand ba,da kuma drivansu,bai wani mamaki ba saboda yasan lokaci zuwa lokaci baaban nasu nayin tafiya kota ziyara ko duba gidajen gonar wannan babban aminin nashi da tunda suka taso suke jin sunanshi suka kuma haddaceshi,tare da riqe girma da matsayinsa wajen babansu,lokaci lokaci sukan yi bita da tilawarsa,saidai har kawo yanzu idanuwa basu taba ganinshi ba,cikin sa'a aka samu jirgin azaman wanda zai tashi ne da la'asar qarfe hudu na yamma,ba haka baban yaso ba amma haka ya karba.         Qarfe hudun jirgin ya lula da su sararin subhana zuwa kanon dabo,wanda cikin mintuna suka isa cikin yarjewa da ikon ubangiji tare da sahalewar ci gaban zamani irin na yanzu,kano tamkar gida take wajen baaban,saboda haka suna sauka suka tarar da motoci guda biyu suna jiran isowarshi,ba bata lokaci suka shiga suka fice daga airphort din.        Wayarsa baban ya ciro,ya lalubo adress din ya soma karantowa drivan,kasancewarsa dan kano ne tuni ya fahimci wajen,sannu a hankali suka dinga keta unguwanni har suka qaraso unguwar da ya buqata,a bakin qofar gidan sukayi parking,drivan ya sake tambaya aka tabbatar masa nan ne gidan malam sulaiman,yaron ya aika ciki ya tambayo yana nan kamar yadda baabaa ya buqata,saidai yaron ya sanar musu baya nan amma bayan sallar isha'i yana gida,ya sake aika yaron yace idan ya dawo a gaya masa yayi baqo,amma zai dawo bayan sallar isha'in ya tsumayeshi don Allah,sai da ya isar da aiken sannan suka tada motocin suka bar layin yaron na bin motocin da kallo saboda yadda suka yi masa kyau. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [23/02, 11:51] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 7⃣3⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *HASBUNALLAHU WANI'IMAL WAKIL* __________________________________        Baabaa prof ji yake kamar isha'in ba zata yi ba,fata yake cikin ransa Allah ubangiji ya sanya sulensa ne,Allah ya qaddara saduwarsu,haka kawai yake jin zumudin zuwan sallar isha'in yayi yaje yayi tozali da mai wannan suna.        Kai tsaye gidansa daya fara zama cikin garin kano tun zamanin quruciya can aka wuce da shi,gidan har yanzu yana nan da kyansa da daukar hankali,kasancewar bai bar gidan ya lalace ba,ko yaushe sake sabunta shi ake saboda ba'a rasa cikin iyalansa mash zuwa kanon,gida take kano a gun kowa,ko baka shigo ka zauna cikinta ba baqunta ko kasuwanci ya kawoka,ko ba haka ba ma hanya ta wuce da kai ta cikinta,wanka yayi ya sauya shiga sannan suka wuce masallaci shi da mus'ab da mahmoud baki daya kasancewar dab ake sa fara sallar magariba.        Basu suka baro masallacin ba sai da akayi sallar isha'i,kai tsaye hassan driver ya koma gida ya fiddo motar ya kawota bakin masallaci suka shiga,tafiya ce da bata wuce minti talatin ba ta maidasu unguwar,guri suka samu sukayi parking sannan suka aika yaro yaje ya sanar da malam ana sallama,cikin sakanni ya dawo ya gaya masa yana fitowa.       Tsaiwar mintuna biyar kacal ya hangoshi,idanuwa ya zuba masa baki daya ko qwaqwaqwaran motsi baya yi,tun kafin ya kai ga qarasowa inda suke ya shaidashi,girma ko tsufa baiyi isar da zaya sanya ya kasa gane sulenshi ba,dadi ko wuya babu abinda zai mantar da shi sule,shima takowa yake saidai sam bai kula da wanda ke gabansa,kasancewar yafi ganin mahmoud da musa'ab dake tsaye gaban baabaa prof din,a hankali ya qaraso ya dubi su mahmoud a nutse "Yan samari kuke sallama da ni?" "Basu bane,muntarinka ne,muntarinka ne sule,suken mai gado" da hanzari ya daga kai shima din gani waye?waye wannan dake ambatarsa da sunan nan qwaya daya jal da yasan duk gadin karkararsu shi kadai ke kiransa da shi,ya sanya masa sunan me tun daga lokacin da malam muhammadu(mahaifin baabaa prof) ya basu tarihin annabi sulaimanu da nana bilkisu,kutsawa yayi tsakiyar su mahmoud yana fatan kayalinsa ya zama gaskiya,ya tabbata kuwa,muntarinsa ne,muntarin da kullum matuqar rana zata fito ta fadi walau yana da cikakkiyar lafiya koko babu ita sai ya tunashi,sai yayi begen ganinsa,da sauri suka qarasa zuwa ga juna suka rungume juna kowa na ambatar sunan dan uwanshi,kowannansu jikinshi na rawa,lamarin ya yiwa su mahmoud nauyi ganin yadda dattawa ke fidda ruwan hawaye,yara masu wucewa suka soma tsayawa suna tunanin wani abu ne ya faru ga malam din,mus'ab ne yayi qarfin halin cewa "Amm,baabaa yara fa sun fara tsayawa" abinda ya fargar da malam kenan ya saki muntari yana kallonshi,ji yake kamar zai sake bace masa bazai kuma ganinsa ba,ko kuma mafarkin da ya saba ne yake yi "Ina zuwa" malam ya fada cikin sauri har yaja tuntube ya shiga gida a gaggauce ya karbi muqullin sitting room wajen mama yana shaida masa yau ga muntarinsa a gidansa,muqullin kawai ta bashi tana tantama,muntarin da tunda suka hadu take jin sunanshi daga bakinsa amma bata taba ji sun hadu ba shine tau aka ganshi?.        Jikinsa har rawa yakeyi ya bude sitting room din suka shiga,har yanzu kowannansu gani yake kamar almara "Sule kaine?,ko almara ce?" "Nima haka nake ji muntari,saidai lamarin ubangiji yafi gaban haka,shi sami'ud du'a ne" "Qwarai kuwa ba shakka"doguwar gaisuwa sukayi bayan sun gama sumbatun ganin juna,sam sun mance ma da wani mus'ab da mahmoud a wajen,har sai da mahomud da mus'ab din suka matso suna gaida malam ya amsa fuskarshi na fitar da annuri,dukkan wani nauyi dake cikin zuciyarsa ya yaye,a yau ya tabbata farinciki bazai barshi yayi bacci ba " wadan nan 'ya'ya na ne sule,gasunan,akwai biyar a gida,baya ga jikoki da suka kusan tasamma guda goma matan aure biyu,kaifa sule?,ya rayuwa ta kasance?"ya fada yana dubansa,wani sashi na zuciyarsa na masa susa ganin alamun sulen bai kama koda kaso daya cikin goma na arziqin da shi yake da shi ba,bayan kusan tare suka sha wuyar tattala da tara dukiyar,saidai alhamdulillahi kana ganinsa kasan baya cikin wahala,yana cikin matuqar rufin asiri,miqewa mahmoud sukayi shida mus'ab suka koma qofar gida don bash waje suji dadin ganawa sosai,gyaran murya malam yayi sannan yace "Bayan barina garinmu muntari na jima bansan inda hankalina yake ba,da na tashi kawai na tsinci kaina cikin makarantar allo ta almajirai,wani malami dake yawon rarraba almajirai ya tsintoni ya hada da yaran da zai kawo kano,sai na karbi rayuwar a yadda na ganni,na riqe karatuna da hannu bibbiyu,na zama daya daga cikin hamshaqan dalibai haziqai da malam ke ji da su,gefe daya kuma kasan tun asali bani da matacciyar zuciya,a duk lokutan da ba na karatu bane nakan fita neman na kaina,duk aikin da na samu zanyi kowanne iri indai na halal ne,batun gida kam baki daya na manta ma ni din dan wanne gari ne,tun malam na damuwa yana qoqarin tambayata har ya haqura ya watsar a haka rayuwa taci gaba da turawa,na samu cikakkiyar haddar alqur'ani mai girma,na zama daya daga cikin amintattun malam,'yan gaban goshinsa,muntari ban tashi tunawa da garinmu ba sai sanda Allah ya yiwa mahaifina rasuwa,naje na tadda rasuwarshi,na kuma samu labarin dukan abun arziqin da kake yi,na tambaya saidai kash ko daya ba wanda yasan inda kuka koma acikin gari,suce zuwa musu kake ka koma,da haka na isa ga dangin mahaifiyata wadamda suma mutuwa ta daddaukesu sai 'yan ragiwa,muka gaisa na dawo cikin gari na hau cigiyarka,wasu suce min sun sanka amma basu san matsugunninku ba,wasu suce ma basu sanka ba,da haka na haqura da dawo kano bani qwarin gwiwa,bayan wasu shekaru ban haqura ba na sake komawa,sai naje na tadda ma baki daya kunyi qaura daga gombe kun dawo kano,naji dadin hakan saboda ina zaton zan sameka ta sauqi tunda muna gari daya,saidai na manta cewa kano nada girma da fadi yawan al'umma da yawan qabilu,akwai tarin qananan hukumomi qarqashinta,haka na qaraci nemana tsawon shekaru,tun inayi tuquru da qarfina har na haqura.        Uwar 'ya'yana a yanzu diyar malam ce,wanda saboda yadda da gamsuwa da yayi da kyakkyawar halayena da dabi'una ya bani aurenta,na samu tarin ilimi daga wajen malam har bayan rasywarshi sunan malam ya dawo kaina,duk da ban iya ci gaba da kula da almajiran ba kowa ya koma garinsu,amma ban fasa bada karatu ba wa dalibai masu zuwa su tafi,a yanzu haka muna da yara hudu da jikoki biyu,sannan cikin qarshen wannam satin zan sake aurar da yarinyata ta uku,kazo a daidai muntari,ko yaushe ina bege idan wani abu da ya shafi iyalina ya taso,inama ace muntarina na nan"cikin farinciki baabaa ke dubanshi "Allah ya amsa addu'armu sule,Allah shine abun godiya" a hankali baabaan shima ya soma zayyane masa yadda yayi tashi rayuwar,gyada kai kawai malam yake yana kallon muntarinsa yana jin dadi,baabaa prof din ya qare da cewa "A yanzu haka sule na kaima kana da taka dukiyar ta kanka,kyautar da nayi maka ban fasa ba sule,itace naci gaba da kula maka da ita har kawo yau,a yanzu haka duk wani gidan gona ko yoghourt ko fresh milk dake dauke da tambarin S.A.D mallakinka ne" mamaki ya kama malam,girma matsayi na muntarinshi ya sake ninkuwa cikin idanunshi,samun mutum mai amana irin haka a wannan zamani abu ne mai wuya,samun aboki irin muntarinsa a zamanin nan tashim hankali ne,bai manta wani waqe da wani balaraben mawaqi ya tabayi yana cewa'a yanzu zaka samu cewa,zukatan abokan gaba sune a jikkunan abokai'ma'ana a fili a bokai suke a idanun kowa,amma a badini kowannensu gagarumin abokin gaba ne ga dan uwansa,bai qaunarsa,bai son ganin ci gabanshi,burinsa kawai yaga faduwa hasara sa damuwa tattare da shi,kai malam ya kada "Duka wannan ba shine abun damuwa ba,haduwata da kai kafin Allah ya zare numfashi daga jikina shine babban abu,kuma Allah ya cika mana wannan burin" shima kai baabaan ke kadawa "Dukkan abunda muntari ya mallaka na sule ne,yana da iko da shi,bare wata qaramar kyauta da ya masa tun zamanin quruciya?,haqqinka ne sule dole ka karba,munyi haka tun a gaban idanuwan malam,A yanzu bayan qaaa ta rufe idanunshi sai mu sauya?,sam haka bazai faru ba" inji baabaa.         A daidai qofar gidan kai napep ta saukesh,ita ne da zainab da halima,a gajiye suke matuqa,don sunyi yawo sosai gidan 'yan uwan mamanta rabon chewing gum,burin sumayya kawai ta samu inda zata jefa haqarqarinta ta kwanta,don ko ta abinci bata yi,Allah ya sota tayi sallolinta baki daya.        Kamar ance dubi can ta hangi mahmoud zaune saman motarsu yana jajjefa qafa yana murmushi,bisa dukkan alamu yana jin dadin yanayin,haka sauyin waje zuwa unguwar da bai santa ba bai taba zuwanta ba hakan yayi masa dai dai,idanu ta zuba sosai wai ko idanuwanta ke mata gizo,ta sake matsawa wajen,tabbas shine,daidai sanda ya waiwayo shima,baki ya bude yana mamaki "Wa nake gani haka?,me ya kawoki unguwarnan?" Ya fada yana murmushi tare da saukowa daga saman motar "Da gaske kai ne?,to me kake yi a kano kuma a unguwarmu a qofar gidanmu?" "Kina nufin nam shine gidanku?" Ya fada yana nuna gidansu da yatsa "Qwarai kuwa,nan aka haifeni" "Malam shine aminin baabaa dama,sulen muntari?" Wannan magana ce kawai ta kasa gane me yake nufi,sai ta dubeshi tana neman qarin bayani,baisan ta yadda zai fasaara maga zancan ba sai ya dora da cewa "Tare da baabaa prof muke fa sumayya,babanku shine tsohom aminin nan masa da yake yawan ambata,wanda ba yadda zakuyi magana da shi ta awa daya bai sako zancansa ba" ya fada yana murmushi har cikin zuciyarsa yana jim dadin yadda a yau burin mahaifinsu na tsahon shekaru ya cika,mamaki ya kamata qwarai,tabbas babu shakka zata iya tunawa ko ita yana sako mata zancansa lokaci lokaci idan hira ta dan hadasu "Malam dinmu?,baaba yanzu yana ciki?" Duka tayi tambayar a tare lokaci guda cike da dimbin mamaki,wai babanta shine tsohon aminin baabaa prof,bugu da qari kuma wai baban ne yau a gidansu "Qwarai kuwa,mun fito mun nasu guri ne din kinsan tsaffin abokai idan aka hadu ba dama,kada a tuno wata quruciyar aji kunya a gabanmu" ya fada cikin irin salonshi na tsokana,dariya ya basu baki daya "Allah mai iko" sumayyan ta fada har yanzu abun nata na bata mamaki "Bari naje na gaida babanmu" ta fada tana yunqurin wucewa "Wannan qani na ne,shike bi mini,mus'ab dake thailand,gashi nan ku gaisa" ya fada yana dukan kafadarsa,a mutunce suka gaisa sannan ta sanya kai zuwa cikin gidan cike da zumudi da mamaki.        Sai da tayi sallama biyu aka bata izini sannan suka sanya kai cikin dakin,suna zaune irin zaman da kama dubansu kasan muhimmiyar ganawa suke,ganawa kuma mai dauke da qauna da fahimtar juna,duk da ruwa dake lemukan gaban baabaa prof babu wanda ya taba,ganin sulenshi da sauraron labaranshi ya fiye masa komai,daga kai baaban yayi cikin mamaki yana dubanta "A'ah,mama na,daga ina haka" kanta a qasa cikin murmushi ta qarasa gabanshi ta duqa "Baabaa,yau kaine a gidanmu?" Sai ya maida dubanshi ga sule yana fadin "Kada dai kace min sumayya diyarka ce?" Cikin murmushi ya daga kai "Tabbas,ita ce diya ta tabiyu,ita ce kuma ta haifamin babban jika na" kai baabaan ke dagawa,wani madaukakin farinciki na mamayarsa,tabbas Allah na sonshi,Allah na duba ga zukatan bayinsa ya musu taimako cikin ayyukan alkhairin da suka sanya gaba,a ladabce sumayya ke gaidashi da su zainab ya amsa cikin farinciki yana sanya musu albarka.        Sosai wani irin farin ciki ke shigar shi,ji yake tamkar babu wanda ya kaishi farinciki yau a duniya,mamanshi cikin zuriyyar sulenshi?,babu ko tantama Allah yana nufinsa da alkhairi,sosai yake jansu da hira abinshi,tun su zainab na dari dari na rashin sabo har suka saki jiki "Ba don bikin da za'a yi ba shakka sai na daukeku baki daya,dama ita mama na 'yar gida ce" baabaa ya fada yana murmushi,dariya suka sa baki daya suna sake jinjina girman qaunar dake tsakanin iyayensu,sumayya ce ta janyesu tace bari su shiga ciki suma don su sake basu waje sosai,murmushi ne dauke a fuskar baabaa prof har suka fice sannan ya maida idanunsa kan malam.     "Sule,dama sumayya diyarka ce?,wannan abu ya faranta min fiye da yadda kake zato,tun sanda naga yarinyar naji ta kwanta min,na yaba da halayyarta,haka naji ina qaunarta kwatankwacin yadda nake qaunar amira,ashe jininmu ce,jinin sulenmu ce" murmushi malam keyi sannan yace "Mai sunan inna daban take muntari cikin 'ya'yana,Allah ya yi mata baiwar ilimi hankali haquri da nutsuwa,zakayi mamaki odan na baka labarin irin rayuwar data fuskanta,da irin qaddarorin da suka fuskanceta,cikin ikon Allah ta cinye jarrabawarta,dubeta,yanzh waye zai ce ta taba fuskantar matsi da qunci makamancin haka,waye zai ce harda maraya gareta?" Dubanshi kawai baabaa keyi,don shi bai san sumayyan ta taba aure ba "Kana nufin kace mama na ta taba aure?" Kai malam ke kadawa don tabbatar masa "Qwarai kuwa,har da yaro" gaban baabaa na faduwa cike da faata yace "Ina fata amma a yanzu bata da aure ko maganar wani kanta?" Cikin mamakin gambayar da muntarinsa ya masa ya amsa masa da eh,sauke ajiyar zuciya baabaa yayi yana furta "Alhamdulillahi,sule,ko zaka iya taimakamin ka bani auren mama na?" Dubanshi yake alamun bai fahimta ba "Ina nufin ka bani auren mama na na karbawa d'aana mustapha?" Murmushi ya subucewa malam din,amma sai ya gaza cewa komai,baaba ya dora da bayani "Mustapha na cikin yara mafi soyuwa a wajena kamar yadda mamana take,tabbas da dan adam keda ikon tsarawa dan uwanshu rayuwa bazan zabawa almustapha rayuwan da yake yi ba a yanzu,taimako nake da buqata ka yiwa yaronka mustapha,don Allah kada a hanashi,bari na gaya maka wanne irin rayuwa mustapha keyi da iyalinshi" hankali kwance baabaan ya zayyanewa malam komai,kai kawai malam ke kadawa,shi kam bai ma tabajin rayuwar aure ta tsantsar nasaranci ba irin wannan,baiyi yawon duniya ba bare ya santa,wadda tazo cikin qur'ani da sunna da wadda akeyi cikin kowanne gida a society dinmu kawai ya sani,shi da ko karatun boko bai bari anyi a gidansa ba banda zamani daya tilastashi ya bar halima da zainab sukayi candy, "tabbas wannan wani taimako da jihadi zakayi sule,saboda yau da gobe tafi qarfin wasa,almustapha lafiyayye ne,yana da tarin dukiya wadda tafi tawa,kai duka cikin zuriyata babu mai dukiyarshi,'yammata na qasashe daban daban na sonshi koda ba soyayyar aure ba,yana da iko da 'yancin yin komai,WA YASAN GOBE?,wa yasan gobe mai zata haifar,gwara tunda ina da ikon kawo gyara na kawowa rayuwarsa gyara ta hanya halastacciya" mamaki ke ci gaba da ratsa malam wamda ya haddasa masa kasa magana,wannan wace iriyar mace?,ita zata iya daga hannu tayi tutiyar ita din matar aure ce?,murmushi ya saki ganin yadda muntarin ya zuba mishi idanu yana jiran amsarsa,irin kallon wanda ke tsoron jin fitowar amsa mara dadi daga bakin wani "Ba qaramar kunya ka sanya naji ha muhtari,yanzu don Allah ka cancanci ka roqeni kan neman auren mai sunan inna?,ashe ma ba daya muke ba,ashe ma yadda ka daukeni ban kai nan ba,sannan baka amince da yadda matsayinka yake a guna ba,har kwanan gobe muntarim ban sake aboki ko amini wanda nake jinsa kamar ni da shi tagwaye muke ba tunda muka rabu da kai,muhtari,ba almustapha ba,ko kai keson sumayya na baka ita halak malak bare tsatsonka,kai,ko moqocin maqocinka kesom sumayya wlh yaci albarkacinka,kana iya aurar da ita ma ba tare da na sani ba,NA BAWA ALMUSTAPHA SUMAYYA HALAK MALAK,amma wani hanzari ba gudu ba,sumayyan tayi aure ba guda daya ba har biyu harda yaro,kana ganin hakan ba matsala bace?" Kai yake kadawa "Naji dadi sule,na gode da wannan karamcin naka,sumayya ko aure dubu tayi matuqar nace wa mustapha ina so ya aureta babu musu sai ya aureta,baaga auren budurqar ba anyi meye ne a ciki?,bazawara nada tata baiwar ta musamman kuma ta daban matuqar ta tsare mutuncin kanta tasan ciwon kanta,hankalinta da na budurwa ma kadai akwai banbanci,nasan mustapha cikin 'ya'yana,ni inda nake kokwanto mamana,kada muyi abinda zai sabawa ra'ayinta" dariya malam yayi "Muhtari kenan,wacce maman namu?,yadda kake da tabbas kan danmu almustapha haka nake baka tabbas kan maman taka" cikin farinciki suka saki dariya dukansu,hannayensu damqe cikin juna farinciki na shawagi da su cikin duniyarshi,tamkar baabaa ya tashi ya taka rawa haka yake ji,yau Allah yayi mishi baiwa manya manya guda biyu,ko yau Allah ya dauki ranshi tabbas ya cika masa burikansa,a hankali malam ya warwarewa baabaa labarin sumayyan da irin gwagwarmayar da tasha,tausayi da qaunarta ta sake yawa a ranshi,qimarta ta dadu,tabbas wannan itace macen aure,ba shakka irin wannan matar ita ta dace da a nema,ya godewa Allah data kusa zama halak malak din familynsa,wannan shi ya sake motsa baabaa ya dubi malam "Sule,idan zai yiwu ina son a hada auren nan da na 'yar uwarta,idan yaso bayan an daura a nutse sai ta tare ko bayan kwanaki nawa ne,ji nake kamar wannan damar zata subucewa mustapha" dariya ta subucewa malam "Haba muhtari,tunda na bada sumayya wa almustapha duk duniya banga wanda ya isa ya maida wannan alqawarin ba,kawai ina ganin shi kansa yaron bai sani ba tunda naji kace yana can dubai wajen aikinshi,amma tunda sai kafi nutsuwa da hakan hakan za'ayi,za'a hada da zainab din in sha Allah,ubangiji ya tabbatar mana da dukkan alkhairi yasa wannan hadin ya zamo abun alfahari da farinciki wa zuri'ar ta da taka" "Amin ya rahmanud dunya wal'aakhira" cikin madaukakin farinciki baabaa ke amsawa,shigowar mus'ab sitting room din shi ya katse sauran maganar da sukeyi,ya dan rusuna yana fadin "Afuwa,baabaa sha daya na dare,nace ko nan zaka kwana mu mu wuce?"ya fada cikin salon tsokana,daquwa baabaan ya watsa masa " baka gama fahimtar waye sule a gurina bane,da da hali kwanan zanyi,amma na tabbatar idan na kwana din kwanan zaune zamuyi ni da shi,don hira tsakaminmu ba mai qarewa bace,ni sai naga ma kamar daren yana gudu"dariya ya basu don babu wani gudu da dare keyi,idanuwanshi ne kawai,har bakin motarsu malam ya takowa aminin nashi masoyinshi,gab da baabaa zai shiga motar ya dubeshi "Gobe ya kama saura sati guda kenan daurin auren ko?" "In sha Allahu" "To madalla,ina zaton gobe zan koma gida na sanarwa da mutanen gida muma mu fara shiri,don wancan auren da yayi ba'a qasar nan aka daura ba,hakan yasanya daidaiku ne suka je masu ikon zuwa,amma wannan karon d'aana zai auri diyata sai inda kati ya qare" dariya sukayi a tare,malam ya rufe mishi murfin motar yana mausu fatan alkhairi da fatan wayewar gari lafiya.        Sai da suka fara tafiya a titi sannan mahmoud ya dan zunkuda kadan,tun dazun daya tsinci maganar ake mintsininshi,so yake yaji shin abunda yake zato ne? "Am....baba daurin auren waye kuma nan da sati guda?" Waiwayawa baabaan yayi ya dubeshi sannan yace "Yayanku almustapha in sha Allahu" idanu suka waro mahmoud yace "Shi da wa?" "Diyar sule aminina sumayya mai sunan mama na" ya basu amsa kai tsaye,duk sai kasa furta komai,babu abinda ke yawo kansu irin halaye da tsare tsaren yayan nasu almustapha wanda babu wanda baisan halayyarshi ba,shin baabaa na shirin daura masa aure kenan baida masaniya da yarinya 'yar afrika?, "Yarinyar tayi,tayi wlh bata da makusa,ga nutsuwa ga hankali,koni a lokacin da na soma ganinta don dai kawai akwai alqawari tsakanina da rahma da tuni na saka kai" ya fada yana dan kauda ido waishi kunyar baabaa,murmushi baban ya saki,idan da sabo ya saba da irin wannan barkwancin tsakanin mus'ab da mahmoud,yaso ace haka halayyar mustaphanshi take kan barkwanci,saidai kowa da yadda Allah ya tsara masa halittarsa,suna hira da raha sosai da shi,sun maida shi tamkar kakansu,yabon da ya sake yi kan sumayya ta sake faranta masa rai,kafin ya sake cewa komai mus'ab ya muskuta yace "Hmmm,dan gaban goshi,auren gata wannan karon za'a masa,yana can yana harkokinshi an nema masa aure,mu kuwa gamu nan tamu maganar ma ko ya ake ciki ne mahmoud?" Ya maida tambayar kan mahmoud,dole dariya ta qwacewa baabaa saboda salon yadda mus'ab din yayi furucin,daquwa ya watsa masa sannan ya dafa kafadarshi "Kai ka jawo tsaiko da karatunka bai gama kammala ba,amma ku din ma ba zaku wuce nan da wata biyar ba" sai suka saki dariya kuma suna jin kunya,su kamsu sunsan yayan nasu yana buqatar dauki,sunsha rayawa a ranau idan sune ba zasu iya wannan auratayyar ba,saidai da yake maza ne babu wanda ya gayawa dan uwanshi ko suka zauna suka tattauna batun,saidai kowa yayi shida zuciyarshi,da haka suka qarasa gida ko zuciyarshi fes.    ******   ********    ******        Washe gari tun tara na safe suka gama shirin fita ci gaba da shirye shiryensu,sabida a yau sumayya keson su gama rabon i.v saboda ta gaji,gashi uwa uba kuma so take da anfarawa zainab din gyaran jiki kada ta sake fita,tuni anty dije wadda yau tare zasu fita ta iso,tana wajen malam suna hirarsu ita da shi da yaya abubakar wanda yau bazai fita kasuwa ba ya taho gidan hira,amina ma na nan zuwa anjima don kusan gidan take wuni tunda satin bikin ya kama,sai da suka kammala sumayyan ta leqa falon malam din tana fadin anty dijen ta taso su tafi sun gama shiryawa don ma nafisa ta tsaidata ta tsaya amsa kiranta wadda ta tabbatar mata zata halacci bikin zainab,don zata zo kano dama gaida iyayen mijinta mahaifan auwal "Jeki ki kira min babarku ku taho tare ke da ita" inji malam,haka kawai taji qirjinga ya buga,tashin farko jikinta yayi sanyi,ta juya zuwa bakin fanfo inda maman ke daura alwalar sallar walha ta gaya mata,qafafunta kawai ta kammala wankewa ta bita suka nufi dakin.        Sai da suka samu gu suja zauna suka nutsu sannan malam din yace "Haqiqa na tabbatar da cewa duk wanda ya kwana ya tashi cikin gidan nan yasan abun farincikin da muka kwana da shi na bayyanar aminina,to bayan mun gama farinciki na ganin juna muna hira bayan ke sumayya kun shigo kun fita ya bijiromin da wata buqata,na sani kun san cewa duk da baku taba ganin muhatari ba amma kunsan muhimmancinsa gareni da irin shaquwa da halaccin da yake tsakanina da shi,ya bijiromin da wata buqata wadda na tabbatar yagi qarfinta a wajen iyalina,duk da nasan cewa haqqin sumayya ne amma na amshi buqatar hannu bibbiyu saboda nasan cewa na isa da ita sannan ba zata taba watsan qasa a ido ba" tun kafin yaci gaba qirjinta ya fara wata iriyar sukuwa,kanta yayi nauyi ta kasa dagashi,maganar da sukayi da shi kafin tahowarta kano da fassarar da anty dije tayi mata suka fara dawo mata daki daki "Ya nemi na bawa yaronshi auren sumayya bisa wasu hujjaoji daya zayyanamin wadanda sun isa sun kai baya ga matsayin muhtarin a gurina a bashi auren ita sumayya,saboda haka na bada auren sumayya ga yaron nashi wanda za'a daura auren ranar juma'a tare da na zainaba insha Allah" wani kuka ne ya qwace mata wanda sautinsa yaso fitowa tayi hanzarin sanya hannu ta rufe bakinta, "Alhamdulillah" kawai anty dije ke jerowq,kamar ta tashi ta taka rawa haka ta dinga ji,ta kasa zama waje daya sabida farinciki,ba shakka tana mai tabbatarwa kanta sumayyan tayi kyakkyawan gamo mai dauke da dumbin alkhairai "Kiyi jaquri sumayya,na miki shishshigi,saidai ina mai baki haquri tare da neman alfarma kan ki yimin wannan alfarmar kada ki watsan qasa a ido" maganar malam din ta hadu ta sake yi mata nauyi a ka,duk da halin ha'ula'in da take ciki amma haka ta tattara kalaman "Don annabi ka daina fadan haka malam,ka daina bani haquri,ni bani da wani da na cancanci a nemi alfarmata a kansa,kaine silata kai ka haifeni,duk yadda kayi da ni malam daidai ne,na tabbatar ba zaka taba cutar da ni ba,na amince na miqa wuya a gareka,roqon da nake maka kadai shine malam ka bini da addu'a,ka sakani cikin kowacce addu'a taka,Allah ya qarfafeni,ya hanani gazawa bare na watsa maka qasa a ido,na samu juriya mai yawa da zata kaini ga cika burinka" tana kaiwa nan ta gaza dairewa,sai ta fashe baki daya da kuka zucuyarta na tuna mata abubuwa masu yawa,wadanda suka faru da wadanda kan iya samunta a gaba,fata take Allah yasa SHAFUKAN KUNDIN QADDARARTA sun qare ashe akwai wasu sabbin shafukan kar a gaba,sai yaushe ne zata kammala bitar wannan kundi mai dan karen wuya da sanya zuciya da gangar jiki yin rauni,rauni kuwa bana wasa ba,ya barwa zuciya da rayuwa tabbai masu wuyar warkewa,masu wahalar sha'ani da sarrafawa tare da tanqwara zuciya a kansu,duk wanda ke dakin jikinsa yayi sanyi,sunsan mai take tunawa "Insha Allahu sumayya daga wannan karon ba zaki sake kuka ba,da yardar ma duka lokacin dariyarki ne yayi,na tabbatar da cewa ban kaiki imda zaki wulaqanta ba,na kaiki ne cikim ahalin da suka gaji karamci da mutunci tun daga tushe,ko bana raye ina da yaqinin muhtari ya isheki uwa da uba ma baki daya,addu'a kuwa kullum kina cikin addu'o'ina,zaki rabauta sumayya da yardar Allah,tashi kije,Allah ya albarkaceki da dukkan wani abu da ya shafeki" "Amin" baki daya mazauna dakin suka amsa,sai ta kasa tashi saida anty dije ta kamata,kai tsaye dakinta ta kaita ya zaunar da ita sannan ta zauna gefanta tana kallon yadda take kuka kamar hawayenta zai qare,bata cemata ta tafas ba har sai data soma tsagaitawa don kanta,bawai don ta gaji bane ko ta samu sassaucin da take son samu,ta tsagaita ne saboda yadda idanunta suka soma radadi da kuma yadda ta fuskanci antyn nason tayi magana da ita "Sumayya kuka kike saboda auren almustapha?" Ta jefa mata tambayar kamar wadda batasan batun ba "Na tabbata bakisan waye almustapha ba,banda haka da sai nace kukan da kike kin yiwa Allah butulci" jajayen idanunta ta daga ta kalleta alamar tamabaya,ciki yaqini anty dijen ke kada kai "Tabbas abinda na fada hakan yake,kinsan irinsu mustapha suke tsada a wannan lokaci?,kinsan yadda mustapha ya tara managartan halaye kuwa?,kin taba tambayar kanki me yasa su'ad ke tsananin kishinsa duk da kishin banza take tunda batasan yadda zata riqeshi ba?,kin manta waye baabaa da karamcinsu?,kina zaton idan kika qi aurensa zaki ci gaba da zama haka ba tare da kinyi aure ba?,kinwa kanki wadan nan tambayoyin?" Kai take girgizawa bayan ta gama sauraronta,cikin rawar murya ta soma furta "Anty a fuskata almustapha bashi da kirki,bai taba kyautata min ba ko sau daya,anty...kin manta yadda auren soyayya ke kayawa a wannan zamanin ina ga irin wannan?,baki daya almustapha anty ba ajina bane kamar yadda nake nima ba ajinsa bace,babu dacewa tsakanina da shi anty,komai nawa da nashi ya sha banban,ra'ayi yanayi al'ada wayewa da dabi'u,ta yaya zamanmu zaiyi daidai,baya ga haka ma baki daya anty KISHIYA!,kishiyar ma irin su'adah,kin manta anty ina kika baro wannan?,kin manta kishiya duk inda na shiga itace babbar qalubalena,bayan bansan me na musu ba,ko don ni yarinyace?,ko din bani da qarfin qwatarwa kaina 'yanci,ko don ban iya mugunta da baqin hali ba,wadan nan sune dalilan?" Ta fada wasu hawayen masu dumi na bin kuncinta,hannunta anty dije ta riqe tsam cikin nata,madadin taga tashin hankali bisa fuskarta sai taga murmushi ne ma kwance kan fuskarta "Almustapha?,ko ba haka bane sunanshi?,kin manta shi namiji ne?,namiji kuwa ko wayeshi ta bangaren zamantakewar auratayya dole ya sakarwa mata,ki manta da wannan ki cire rashin soyayya a tsakaninku a matsayin matsala,kishiya ita kike tsoro?,ina zaton zuwa wannan lokacin kin horu sumayya,meye yayi saura meye bakiji baki gani ba,sai d'ai d'ai,wannan karo ki sama ranki cewa kishiya ga gama yin nasara a kanki da yardar Allah,waccan karon ma dan dai kawai yana cikin KUNDIN QADDARARKI ne,ke mai bawa wata labari ne,dame kishiya zata tsorataki sumayya,bayan kina da Allah,kina da tsarkakakkiyar zuciya,ke matuqar su'ad ma ta baki tsoro sumayya ke kika so,ki kwantar da hankalinki damuwa ba taki bace,bakisan sirrin da Allah ya boye ba har ya turo baabaa dai dai wannan lokaci,bana son qara ganinki hawayenki daga yau" Kai kawai ta gyada mata ba don tana tsammanin samun salama cikin ruhinta ba,komawa tayi kawai ta lafe kan gado kanta na sarawa,ita kadai tasan me take ji,kai kawai take mirginawa tana jin nauyi da girmam zancan a qirjinta,su halima da zainab ne suka shigo a sanyaye saboda ganin yanayin sumayyan,antyn tace suje kawai ba zata samu zuwa ba ita da sumayyan,bata son ta tafi ta barta a yanayin da take ciki,wayarta dake gefanta tayi ruri,kiran abdur rahman ne,idanuwanta ta runtse tana kiran sunayen Allah,sai a sannan ya fado mata,me zata da shi?,me zata gaya masa ya yarda da ita,tabbas bata da abinda zata ce masa,hakanne ya sanya ta qyale wayar taci gaba da rurinta har ta katse don karan kanta,qarar wayar kawai qara mata ciwon kai yake,wanda zuwa lokaci wani zazzafan zazzabi ya rufeta ta kwanta sosai,saidai bata bari kowa ya gane ba. ****** ******* ******** Tunda ya isa gida kafatanin al'umar dake cikin gidan suka fuskanci akwai wani gagarumin al'amari na farinciki da ya faru da mai gidan,tun daga manyan ma'aikata na gidan har qananu,take ya yiwa kowa qarin albashi sabida tsananin farinciki da nuna tsantsar godiyarsa ga Allah. Bai samu ganawa da matan gidan ba sai bayan sallar magariba,ya warware musu komai,babu abinda ummee tace,ita kanta tasan yaron nata yana da buqatar sauyin rayuwa,kawaici kawai irin nata yasa basa tsomala baki cikin lamuransa,saidai sauyi wanne iri?,sauyin zai yiwu kuwa ta wannan bangaren,bayan kowa yasan ra'ayim almustapha wajen zabar matar aure?,kai hasalima kaf tarihin rayuwarshi bashi da muradi ra'ayi ko sha'awar yin mata biyu sam sam,bata manta yadda ya dinga qananun maganganu sanda yayansu adam zai sake aure na biyu,saidai a tarbiyyarsu sam babu musu ko jayayya kan duk hukuncin da jagoran gidan ya yanke,saidai su tayashi bin dokarsa ko hukuncinsa,bangaren anty maamaa ma tayi farinciki,don a dan zamanta da sumayya ta karanci halayenta,ta kuma san ta sha banban da halayyar su'ad,saidai itama tata fargabar ta yaua almustaphan baqin bature dan ra'ayin riqau mai doka da qa'idoji zai amshi wannan lamarin,gashi uwa uba baban yaja kunnen kowa da kada wanda ya sanarma almustapha maganar shi da kansa zai sanar masa,kome meye tasan na dan lokaci ne zai wuce,to baki dayansun masu biyayya ne gareshi,sannan babu wanda baida burin ganin farinciki cikin rayuwar mustaphan. Anty farida da huda kam da suka ji lamarin har wani ihun farinciki suka saki,kasa zama sukayi sai da suka dangana da baabaan suka yi masa godiya tamkar su ya yiwa,murmushi kawai yayi yasan lamarin na damun kowa,koma dai meye shi ya fisu farinciki da shigowar jinin sule cikin tashi zuriyar. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [23/02, 11:51] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 7⃣4⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *Allah S W T yana cewa* *KACE HAQIQA MUTUWAR DA KUKE GUJE MATA MAI RUSKARKU CE,SANNAN KUMA KU KOMA IZUWA GA MASANIN ABINDA KE FILI DA NA BOYE YA BAKU LABARIN ABINDA KUKE AIKATAWA* Ya Allah kasa ta ruskemu kana masu farinciki da mu,muna masu farincikin haduwa da kai ______________________________________        Gaba daya ta koma ta zama wata irin cikin kwana biyu kacal,duk wani kuzari da buri data ci na bikim zainab yayi nashi wuri,tsantsar tashin hankali take shiga a duk sanda ta tuna lamarin dake tunkarota,ko ya zata qare?,ko meye zai faru da ita wannan karo?,shine tambayar da take yawaita yiwa kanga,uwa uba Abdallah da ya tsaye mata a rai,ana ya gobe kamu nafisa ta iso gidansu,wani kallo take binta da shi tana tabe baki "Ke yanzu sai kace wadda zatayi auren fari kamar wadda yau zata fara zama da kishiya shine kika bi kika susuce haka?,a haka zaki qwaci kanki duk kin fafa zabgewa kina ramewa?,amma wallahi kin bani kunya" cewar nafisa,daga kai tayi tana kallonta tare da mamakin wanda ya gaya mata zancan "Me kike kallo na,munyi waya da amira ta gayan komai,ta kuma ce tana kiran wayarki amma kullum switchoff,na gaya mata zan shigo kanon tace na duba mata ke don Allah" ta sake fadi tana duban sumayya,fada ta zarce da yi maga,kuka ya qwacewa sumayyam,wau su don Allah ita kadai take gano abinda take ganowa,su basu hangen komai,ta gama fadanta sannan ta koma lallashinta,inda daga qarashe ita ta tilastata ta miqe tayi wanka tace zata rakata siyayya,jiki babu qwari haka ta shirya,ga zazzabin dake sakadarta a hankali,bugu da qari ga wani ciwon mara da ya saukar mata,wanda bata sani ba ko tashin hankalin da take ciki ne ya jawo shi oho.        Wani katafaren shago wanda ke saida kayan jiki na zamani nafisa ta kaisu,da idanu sumayya ke kallonta sanda take loda kayan tana zaba,harda wanda sumayyan yanzu ke amfani da shi tun wanda ta taba siya mata a uk har yau da shibtake amfani da yake ya karbeta,suna cikin mota take shaida mata yadda zata yi amfani da sauran,haushi ya kama sumayyam,yamzun suna nufim wami namiji zata yiwa hidimawa jikinta saboda za'a daura mata aure da shi "Wallahi da kin gayan ni kika  siyawa bazan barki ba,sabida asarar kudinki kawai kika yi babu abinda zanyi amfani da shi cikinsu" a fusace nafisan tace "Wallahi baki isa ba kinyi kadan,amfani da su wallahi ya wajabta a kanki" ganin yadda nafisan ta hasala ya sanyata yin shiru,saboda ko qwaqwaqwarar magana bata sonyi yanzu kanta zau fara sara mata.        A bangaren baabaa kuwa shirin daurin auren yake babu kama hannun yaro,kai kace wannan shine karon farko da za'a yi daurim aure cikin familyn baabaa prof din,ana ya gobe daurin aure suka baro abuja suka sauka gidanshi dake kano,saboda ya kasance kusa da abokinsa,duk wanda ya dace ya san da daurin auren babu wanda baabaa bai aikawa ba.        Duk abinda ake idanu ne nata sai ta koma 'yar kallo sabanin daa da itace amara,katunan daurin aure masu dan karen kyau tsari da tsada baabaa ya sanya aka buga ya baiwa malam wani shima ya raba wani,duk wanda yaji daurin auren ya zama na mutum biyu harda sumayya sai yayi mamaki,saboda kowa yasan babu ita a batun,da kansa baba ya sanya cikin kwanaki hudu aka yima sumayyan akwatu uku na suttura wadanda zata sanya kawai bawai lefe bane,lefanta yace sai almustaphan yayi kamar yadda ya yiwa su'ad,kaya ne masu kyau da tsada dinkakku,kama daga shadda laces atamfa material sa sauransu.         Da ido kawai take binsu lokacin da aka zo yima amarya zainab lalle,almara kawai take ganin komai,wai ita za'a daurawa aure nan da kwana uku?,abinda ko cikin mafarki bata taba hasashensa ba,qememe taqi bada hannunta ayi mata komai,anty dije tace a barta kada a matsa mata,tasan cewa akwai lokacin da ita anty dijen da kanta zata sanya ayi mata kuma dole ta bada hannunta.         Ana ya jibi daurin aure kwana tayi tana kuka saboda nasihar da mama tayi mata,ta gaya mata duk wanii motsi da zata yi wanda bai dace ba tamkar ta watsawa mahaifinta qasa a ido ne,ga gidan ya fara amsar baqi,haka ta tashi washegari da zazzabi da ciwon kai amma haka ta dinga cijewa tana shiga jama'a,wanda hakan bai amfana mata komai ba face sake qaruwar ciwon kanta.           Bayan sallar isha'i tana kwance cam uwar dakan maman kan abun sallah,hasbunallahu wa ni'imal wakil kawai take ambata babu qaqqautawa saboda yadda taji nugun zuciyarta na daduwa,sallama taji anayi tsakiyar gidansu wadda ta sanyata miqewa dungur gur ta zauna tanq raba idanu kamar wadda aka ritsa da wuqa a maqogaro,muryar abdur rahman ce,sai gabanta yaci gaba da faduwa ta fashe da kuka qasa qasa tana cusa kanta tsakanin cinyarta.          Daga airphort direct gidan ya zarto ko gida bai nufa ba sakamakon mummunan labarin da ya sameshi ta bakin bahijja,kai tsaye aka yi masa iso falon malam wanda shigowarsa gidan kenan,a mutunce suka gaisa saidai kallo daya malam yayi masa yaga sauyi tattare da yanayinsa "Ina fata lafiya malam abdur rahman" cewar malam din,kai ya girgiza cikin sanyin murya "Malam,na jima ina neman yarda da amincewar sumayya tun kafin rasuwar yaya mukhtar har kawo yau din nan,na fara samun hadin kanta a kwanakin nan,saidai ta nemi alfarmar na bar maganar har ka kammala aurar da zainab,kwatsam sai jiya na samu labarin wai za'a aurar da sumayya malam haka ne?" Kai ya jinjina kafin yace "Wannan haka yake abdur rahman,zan aurarwa dan aminina sumayya,sam banyi tunanin kana ci gaba da neman sumayya ba abdur rahman,ban kawo haka a raina ba" sosai ya girgiza da jin amsar malam din,idanunsa suka kada ya dubi malam din "Malam ni nafi cancanta da sumayya,ka yimin alfarma ka aurar min da ita" cikin tausayawa malam din ke dubanshi "Kayi haquri abdur rahman,wannan wanda zan baiwa sumayya wa familynsu sunfi qarfin na musu haka,idan da wani ne can daban babu abinda zai hana na maida auren kanka,amma zan gaya maka kadan daga labarin muntari,zan gaya maka kadan daga cikin waye muhtari a gurina" warware masa yayi DANGANTAKAR dake tsakaninsa da baabaa prof,dangantakar kuma da suke fata da burin ba zata sake katsewa ba har ABADAN,wanda hakan suna burin ya zama hanyar ci gaba da yado da qarfafa zumunci da dangantakarsu.         Cikin gamsuwa abdur rahman yakw gyada kai,babu shakka irin wannan dangantaka dake tsakanin malam da muhtari ko shine idan yana da diya abinda zai iya faruwa kenan,ba zaiso ya zama silar datse wannan kakkaurar tsohuwar igiya ba da ka qullata tun duniya na kwance,tun basu gama sanin su waye su ba kawo yau,saidai rabuwa da sumayyan ba abu bane mai sauqi tattare da shi,wani mugun ciwo ne da zai ci gaba da illata shi "Shikenan malam,ina muku fatan alheri,saidai mu a tayamu da addu'a,Allah ya bamu haqurin jurewa" ya fada cikin karyewar murya "Allah ya yi maka albarka,ya sanya juriya a zuciyarka,ya musanya maka da wadda ga fita alkhairi a gareka" "Amin malam,na barka lafiya" ya fada yana mai miqewa,cikin tausayawa malam din ya bishi da kallo,har ya kai qofa ya kirashi ya dawo ya tsugunna kansa a qasa "Abdur rahman" "Na'am malam" "Idan har babu takura kuma ba zaka damu ba,mai zai hana ka nemi halimatu 'yar uwar sumayyan,a tunani kamar zata iya maye maka gurbinta" "Indai malam kana ganin hakan yayi daidai bazqi haifar da wata matsala ba na karba,ina kwadayim zuriyarka ne malam,na tabbatar akwai alkhairi ga dukkan wani d'aa da ya fito daga gidan nan" murmushi malam din ya saki cikin jin dadi "Kayi tunani a nutse,kada kayi abinda kasan zaka takura,idan halima tayi maka ka dawo zan baka ita,idan bata yi maka ba babu komai zan biku da kyakkyawar addu'a" "Ta yaya malam zanqi jininka,halima jininka ce jinin sumayya,na karba malam,kuma in sha Allahu a gobe zan bada sadakina nima kada itama na rasata"murmushi ya subucewa malam,sosai ya sanya musu albarka tare da jan doguwar addu'a ta fatan alkhairi a garesu baki daya,yace yaje sitting room a bude yake zai turo masa haliman,miqewa yayi kansa a qasa yana yiwa malam din godiya,abun mamaki cikin qanqanin lokaci tashin hankalin daya tsinci kamsa kaso dari sai yaji babu hamsin ciki,ya taka ya fice sitting room din gidan yana jiranta.       Malam yana daga falon ya qwalawa haliman kira,gama cire lallenta kenan taji kiran malam din,ta goge hannum nata ta sanya hijabinta ta shiga dakin "kije sittin ro abdur rahman na jiranki" jin maganar tayi banbarakwai sai ta daga kai ta dubi malam "Ni ko yaya sumayya dai?" Daquwa ya mata "Dan gidanku na kasa gane sumayyan sai ke zan kira?,ke nace ba sumayya ba" bata sake cewa komai ba ta miqe ta fito ta nufi sitting room din gabanta na faduwa.       Tsaye yake tsakiyar sitting room din hannayensa goye a bayansa ya zubawa qofar shigowar idanu,tana sallama suka hada ido,karom farko taji wata faduwar gaban da bata taba jin irinta ba don ta kalleshi,idanu ya zuba mata yana amsa sallamar,sai yake hango yanayinta da sumayya muraran,ya taba kula da hakan shekarun baya amma ba kamar yanzu ba,ga mamakinsa murmushi sai ya subucewa lebansa,ya zuba mata ido yana ci gana da kallonta har ta qaraso gabanshi,cikim diriricewa tace "Ya abdur rahman gani.....malam yace wai.....kana jira na" "Bismillah zauna" babu musu ta taka ta zauna kan daya daga cikin kujerun,gabanta ya iso a hankali ya zube a gabanta wanda hakan ya sake haddasa mata faduwar gaba da,sai ta jita ta takura sabida basu taba zama gab da gab irin haka na,duk a qasa yake zaune a gabanta amma yana kusa da ita "Halimatus sa'adiya,malam baice miki komai ba?" Kai ta gyada da sauri sabida ta gaji da yadda gabanta ke faduwa,murmushi ya dan saki,wato shi zai yiwa kansa yaqi kenan ko?,daga idonsa yayi ya zubesu a kanga,sai ta janye nata idanuwan "Halimah kina sona zaki iya aure na?" Taji tambayar babu zato na tsammani,ido ta zaro tana dubanshi,kasa cewa komai tayi har sai da ya maimaita,bakinta na rawa tace "Yaya abdur rahman.....yaya sumayya.....ita yaya sumayya fa?" Murmushi ya saki "Bakya gidan ne?,bakisan malam ya bata wani ba?,ni kuma a yanzu malam ya bani ke zaki iya aure na?" Shiru tayi gabanta na faduwa,yayin da kunya ta kamata ta sadda kai qasa qwalla na taruwa a idonta,hakan taji tsoro ya kamata,malam zai aurar da ita kenan itama,jin shiru ya sanyashi sanya yatsunsa ya daga fuskarta,kallo daya tak yayi mata ya fuskanci ta karbi lamarin duk da bata bayyana ba muraran sabida kunya da tsoro "Kice wani abu mana halimah,koda baki sona ki amince min zan saki ki soni kinji,kada nayi asarar zuriyar malam baki daya ace na rasa ko daya,da wallahi barin garin zanyi" dariya taso qwace mata saboda yadda ua shagwabe mata,kunya ta lullubeta saita qudundune kanta cikin hijabi,dariya ya saki "Iyeeee,ko baki ban amsa ba ma na gano a bata,ashe dai har kunyar abdur rahman din akeji,lallai na samu karbuwa,koba haka bane?" Shiru tayi taqi amsa masa "Shikenan tunda ba zaki ce komai ba bari na haqura na tafi,kuma ba zaki sake ganina ba,zan kuma gayawa malam baki amince ba sai na haqura" ya fada kamar mai tafiyar,da sauri ta daga kanta tana shirin cewa wani abu,sai ta ganshi tsaye a gabanta,kunya ta sake kamata tayi qasa da kai suna dariya baki daya.        Komai na Allah ne haka komai nufin Allah ne,sai gashi ya shantake har qarfe tara da rabi yana gidan,halima akwai kunya saidai alamu baki daya sun nuna ta karbeshi,sai goma saura sannan yayi mata sallama,ya zuba hannayensa a aljihu yana dubanta "Ina wayarki" cirota tayi daga hijabinta,karba yayi yana qoqarim cire layin ciki ya zura a aljihunaa sannan ya ciro daya daga cikin layukansa ya saka mata yana cewa "Gashinan,ni kadai zan dinga kiranki kafin na siya miki wani layin,ina da kishi bana son wani ya sake jimin muryar mata ta,sai da safe muje na rakaki" har bakin qofar shiga tsakar gida ya rakata sannan ya juya ya fice,zuciyarsa fes yana mamakin lamarin Allah,ya riga ya qaddara sumayya ba matarsa bace shine masanin GAIBU mai rubuta QADDARAR BAYINSA,Allah kenan mudabbirul amri mai jujjuya al'amura a lokaci da baka zata ba,ya shigo gidan cikin tashin hankali da jimami ya fita cikin farinciki da annushuwa,babu abinda zai cewa dattijon arziqi mai karamci sai godiya tare da yi masa fatan kyakkyawan qarshe.         Tana shiga tsakar gidan taga shigar zainab dakin mama wadda ta fito daga kitchen ta dafawa sumayya tea,da sauri tabi bayanta don fatinciki ke cinta,bata da 'yar uwar da take sharing sirrikanta da ita kamar zainab din,tsaye ta taddata tama fifitawa sumayya tea din,sam halima bata kula da sumayya dake dakin ba ta dane bayan zainab wanda hakan ua sanya tea din hannunta tangal tangal zai zube "Wayyo zainab,yau Allah nima ya bani yaa abdur rahman,zainab mallam ya bawa abdur rahman ni,a gobe nima zanbi sahunku zan zama matarshi" sak sumayya tayi tana dubanta,tun dazun take jira taji wani abu daga wajen abdur rahman din ko malam amma taji shiru,gani tayi zainab tayi shiru kawai saita sake kallonta "Baki ce komai ba ya kikayi shiru" da idanu tayi mata alama da wani na gun,ta wurga idonta saita hangi sumayya,da sauri cikin jin nauyinta ta juya zata fice,cikin kasalalliyar murya tace "Zo yaki halima" cikin jin nauyinta ta iso inda take ta zauna,ta karbi tea din da zainab ke miqo mata ta aje gefanta "Meye na jin kunyata halima kamar wadda ta aikata haramci,wallahi har ga Allah naji dadi da wannan hadin da malam yayi,sannan abdur rahman ya cika mai sonmu tsakani da Allah da son iyalan gidan nan,ki saki jikinki ni yayarku ce har abdur rahman din ba tun yau ba dama,ki manta da cewa abdur rahman ya raba sona,Allah shine dama yasan abinda ya boye shi yasa bai taba darsamin soyayyarsa ba ko qanqani,illa ganin girma da mutuncinsa da nake,babu wani abu da ya isa shiga tsakaninmu,dan uwa ba wasa bane,idan banda Allah babu wanda ya isa yayi maka kyautar dan uwa,Allah ya baku zaman lafiya ya tabbatar da alkhairi" "Amin" suka amsa baki daya,taji dadin addu'ar sumayyan sosai,to tsakanin daren zuwa wayewar gari sun sake wata qwaryar qwaryat shaquwa,kusan kwana sukayi suna waya sumayya na jinsu,wadda tuni ta goge duk wani abu da ya shafi abdur rahman daga wayarta,tayi lamo bisa gado,kewa ta kamata,ta dinga matse hawaye tana tuna mukhtar,mutuwa mai tonon silili,idan banda mutuwa ta dauke mata shi da tuni sun jima da shimfida sabuwar rayuwa,wataqila ma da tuni ta sake haifa masa 'ya'ya,saidai tsarin Allah shine tsari,(Allah kasa mu dace ka cika mana burikanmu kasa mu cika da imani don alfarmar sayyadina rasulullahi S A W)amin. Washe gari kawu da wansa da qaninsa mahaifin abdur rahman sai gashi da safe yazo nemawa abdur rahman din auren halima,wanda ya bawa malam dariya,yace ai da abdur rahman da halima duka nashi ne,ko basu zo ba sai ranar daurin auren ya riga ya bashi ita,a nan kawun yayi godiya qwarai suka tafi,a nan suka bar abdur rahman ya sake baje kolin soyayyarshi,sai da aka soma nemansa a asibiti sannan ya tafi,binsu sumayya take da kallo,wato bawa bai gujewa Qaddararsa. *KUNDIN QADDARA* Rana bata qarya saidai uwar diya taji kunya inji malam bahaushe,wannan haka yake,domin yau take juma'a wadda ta kasance rana ce mai girma da muhimmanci da kuma dumbin tarihi wajen malam sulaiman gombe,wanda zai aurar da duka diyoyinshi mata da Allah bashi cikin mutunci da rufin asirj,wanda abun farinciki ne da godewa mahalicci a irin wannan zamanin namu mai cike da rudi da abubuwan firgici ga 'ya'ya mata Allah ya yi maka baiwar aurar da diyoyinka mata baki daya hannun nagartattun maza da kake saka musu ran zasu musu riqo na mutunci,ta hannu daya baabaa prof shima cike yake da farinciki,domin kuwa tun qarfe tara ya iso wajen a maimakon qarfe goma da za'a daura auren. Daga cikin gida kuwa tuni zainab ta yi wanka kwalliya irin ta amare,tana sanye da wani lace mai azabar kyau wanda sumayya ce ta siya musu,haka amarya halima na sanye cikin shadda wadda ready made ce abdur rahman ya aiko mata da ita,tayi mata kyau ainun,dukkaninsu idan ka dubi fuskokinsu qunshe take da fara'a sabanin sumayya dake kwance ko wankan ma bata kai ga yi ba,binsu take da idanu tana rayawa cikin ranta,kowa yana rayuwar farinciki banda ita,ita kadai ke fadawa halin jarrabawa cikin yaran gidan nasu?,nafisa ce ta sanyata a gaba wanda tilas ya sanyata tashi tayi wanka ganin tana son qara mata ciwon kai,ta fitar mata da wani dan banzan lace cikin kayan da aka kawo mata dinkin skert da riga mai dogon hannu,kamar yadda ya qawatu lace din haka ya qawatata ta,babu abinda ta shafa banda turare mai da hoda amma sai ta fito cas gwanin sha'awa,fuskar ta tayi fayau ta dashe tare da ramar da tayi,naji ance amarya daban take ko batayi kwalliya ba,to kusan hakanne ya tabbata ga sumayya,komawa tayi ta kwanta abinta,don hayaniyar data cika gidan kadai ma damunta take bare ta waje,wanda tuni layin ya soma dinkewa,tana iya jiyo kwaroroto da muryar maroqa iri daban daban,sun baje hajarsu kowanne yana kwasar rabonsa,basa wasa da bikin daya shafi gidan professor mukhtar muhammad adam,don idan kazo a sa'a wani daga ranar ya daina roqo sai ya samu jarin da zai isheshi sana'a,ballantana yau da sunan almustapha ya bayyana baro baro na cewa shi zai sake aure. Cikin qanqanin lokaci layin ya cika ya tumbatsa da jama'ar baabaa prof,jiniya iri iri ke tashi wadda ta qusoshin gwamnati ne da jami'an tsaro,kowa yana iya jiyo yadda daurin auren ke kayawa sakamakon maroqan dake bayyana dukkan abinda ke faruwa a wajen,auren zainab sulaiman gombe aka fara daurawa da angonta abulkhairi muhammad bala kan sadaki dubu talatin,sannan aka daura na halimatus sa'adiya sulaiman gombe da angonta abdur rahman Ahmad yusuf kan sadaki naira dubu hamsin,daurin auren qarshe shine na doctor muhammad almustapha professor mukhtar adam gombe wanda aka daura kan sadaki naira dubu ashirin,sai kuma kyautar mota duka cikin sadakinta take,daidai kunnenta nafisa tazo ta rangada guda,jin gudar take kamar ana zaqular qwaqwalwarta,saita dunqule ta cure waje daya,ta saki wani marayan kuka wamda bai fidda sauti,ita kadai yasan me take ji cikim zuciyarta,shikenan yau din ta sake zama mallakim wani bayan mukhtar?,wanin ma da baisan daraja ko qimarta ba,ya zata kaya musu?,ya zata kasance?,bata da amsar wannan. Kusan ranar haka ta wuni,da daddare ta dauki kayan sawarta kala uku ta gudu gidan anty dije,a can ta barje kukan ta son ranta,saboda a can babu dama saboda idon mutane,itama antyn batasan tana nan ba,sai wayar mai gadinsu ta ara ta gayamata don kada su nemeta,washe gari aka sha yini sosai,duk abin nan da ake sumayyan na gidan anty dijen,haka ta wuni kwanciya don mai gidan baya nan,ita kuma antyn a can gidansu ta kwana,sai gobe zata dawo idan an kai amarya,halima itama sai next week za'a kaita,kafin nan an kammala yi mata tata siyayyar. ******* ****** ******** Zaune take a uwar dakan anty dije wadda jiya bayan kai amarya ta dawo gida,tana ta faman shirya kayansu cikin trolly abinta,sumayya na zaune daga bayanta,sanye take da doguwar riga 'yar kanti mai qaramin hannu,kanta ba dankwali sai gashinta mai baqi da santsi data hade cikin ribbom,jingine take da kujerar dake dakin qafafunta amiqe,hannunta riqe da cup din tea wanda tun dazun aka hado mata shi har yana gab da hucewa bata yi masa kyakkyawan shaa ba,idanuwan nan a kode tamkar danyen nama kamar yadda fuskarta take a kode alamun ko yaushe cikin kuka take,sam anty dije taqi bata fuskan kawo wani qorafi ko wata magana kan auren,tunda dai an riga an daura ta riga data zama matar almustapha,abu guda ne kawai yanzu a gaban anty dijen yadda zata shirya diyar tata fes ta iya shiga kowanne bigire na rayuwa,abinda ke sake karya zuciyar sumayya yadda taga ita antyn ma murnarta take,hannunta tasa ta shafa gashinta hadi da lumshe ido tana kiran sunan Allah qasa qasa,ita kadai tasan meke yawo cikin kwanyarta,kamar ta cire qwaqwalwar ta huta haka take ji,waiwayowa antyn tayi tana cewa "To zaki bimu abujan ne ko kuwa sai munzo daukar amarya?" Mai neman kuka ne aka jefeshi da kashin awaki,aisai kawai ta saki kukan ta sosai ta dire cup din tea din,baki anty dije ta kama dariya na subuce mata "La'ilah,ku jimin yarinya,wai ita bilhaqqi da gaskiya bata son almustapha,mutumin da ake so ko kallon arziqi ya yiwa wasu,to wallahi saidai kiyita kukanki kada ki fasa bazan lallasheki ba,tunda kinqi jin lallashi ballantana shawara,da kinsam tun usilu ba zaki iya biyayya wa su malam ba ai da kin gaya musu tun sanda suka tasamma hada auren,sai yanzu saboda yankan baya zaki tasani gaba da kuka me zan miki,haka zakije ki yi gaban su'ad din,tabdi wallahi da kuwa kin jawa kanki,idan kin gama kukan kya tashi kiyi abinda ya dace,don tun jiya malam ke tambayarki bai gqnki ba zai damqa miki sadakinki" anty dijen ta juya tana ci gaba da aikace aikacenta har sanda laila ta shigo da wayar sumayyan hannunta tana fadin "Anty amira ce a layi" ta miqawa sumayyan,harara ta danqara mata hakan ne ya sanya anty dije karbar wayar ta kara a kunnenta bayan ta sanyata a handsfree tana fadin "Ai amira kema ta shafeki ba zata amsa wayarki ba,ke da jin muryarta sai bayan wani lokaci"dariya ta qyalqyale da ita " don Allah anty matsa kusa da ita nayi kata waqar ta zama ta zama,nima haka ta yimin,ranki ya dade amaryar yayanmu ayi mana haquri,amma dai ya musty ne ya riga ya zama mijin sai haquri,anty barta ko bata yi magana ba yanzun zata yi idan muka zo sayan baki"dariya suka sanya baki daya,hakan ya sake qular da zuciyar sumayya,sai ta miqe ta fice tana kuka muraran kamar wata qaramar yarinyar,binta anty dije tayi da kallo tana dariya,har yau da sauran quruciya sosai tattare da sumayyan,gata nan a zahiri ta bayyana. Tunda aka daura auren ranar juma'a baabaan bai bar kano ba har zuwa yau litinin,misalin qarfe takwas na dare bayan ya gama cin abincin dare ya dauki wayarsa ya soma lalubar musty man. Dawowarshi kenan daga asibiti,yau a gajiye yake saboda mutum uku ya yiwa c.s,kayan jikinsa kawai ya cire ya rataye suit dinshi a inda yake rataye kayan da za'a wanke masa,ya zaluqo daya daga cikin towel daga ma'ajiyar towel ya daura sannan ya shiga wanka,kwanciyarsa yayi luf cikin ruwan wankan mai azabar dumi da qamshi,duminsa na ratsa kowacce gaba ta jikinsa,idanunsa na alumshe sai ka rantse da Allah bacci yake saidai idanunshi biyu,tunani ne kala kala kan kwanyarsa yake yawo,ya soma gajiya da zaman wannan hotel din wanda kusan a ciki yake rayuwa,duk da yana da gida mallakinsa cikin qasar,saidai hakanan yafi sha'awar zamam hotel din yana ganin kamar ya fi masa sauqi,idan gidan ne dole sai ya nemi ma'aikata da zasu zauna cikin gidan su kula masa da tsaftarsa da komai da komai wanda shi ba kasafai yake son ma'aikata haka barkatai ba,musamman a qasar da ba taka ba,tun yana cikin bayin ya dinga jin rurin wayarshi,data katse wani kiran ke shigowa,sai ya saki tsaki ya sake gyara kwanciyarsa ba tare da koya bude idanunshi ba bare yayi haramar fitowa,ga tsammaninshi su'ad ce don kimanin sati guda rabon da ya nemeta,ta kirashi dazu zai shiga thiather ya dakatar da ita,saboda abu na farko data fara da shi shine mitan ya watsar da ita sabida ta koma zata qarasa karatunta,shikam a yanzun yana ganin matsalarta ce,shi ya gama da wannan issue din,sabgogin dake gabansa ma kawai sun shasa masa kai,sai da ya kammala wankansa a nutse sannan ya fito ya daura towel dinsa a qugu wanda hakan ya fito da dukkan suffa da zatinsa na cikakken namijin da ya amsa sunanshi,ya qarasa wani sashi daban ya daura alwala ya fito. Zai gifta wayar kenan ta sake ruri,ya waiwaya kadan ya dubeta sai yaga sunan abbu na yawo saman screen din,sunan da ya sanyawa baabaa prof kenan,da hanzari ya fasa abinda yake ya isa ga inda wayar take ya daga cikin girmamawa tamkar yana gabanshi cikinnn nutsuwa da sanyin murya "Barka da warhaka" ya fadi "Barka kadai,ina ka shiga ne haka tun dazun ina kira ko kana asibiti ko company?" "A'a wanka nake" ya fada a taqaice,don a tsarinsa bai fiya doguwar magana ba,kadan ce mai ma'ana "To madalla" "Lafiya kuke baabaa ya kowa da kowa?" "Kowa lafiya qalau yake almustapha" "Masha Allah" "Ammm,almustapha kawai tsarin zuwanka gida ne nan kusa?" Dan jim yayi kafin ya amsa "A'ah,saidai ko idan kana son ganina ne?" Yana mamakin yadda yake da kaifin qwaqwalwa da cimma abun tun kafin ka kammala bayaninka,sau tari suna fara magana da baabaan yake gane mai yake da buqata tun bai qarasa ba "Tabbas,ina buqatar ganinka,wani muhimmin batu ne ya taso ma rayuwarka nake so mu gana a kai,yaushe kake da chance din zuwa?" Duk da maganan ta dan sanyashi a duhu amma bai da niyyar tambaya "Yaushe kake son gani na?" "Eh to,ko kamar nan da sati biyu haka" "Sati biyu masu zuwa ina zuwa da yardar Allah" "To masha Allah,Allah yayi maka albarka,sai kazo" "Amin,na gode" a hankali ya ajjiye wayar yana binta da kallo,zuciyarsa na son sawwara masa muhimmin batun da baabaa yace ya taso wa rayuwarshi,duk iya hasashensa bai canka ba,hakan ya sanya ya dage kafadunsa biyu na rashin damuwa ya nufi inda ya ajjye kayan shafarshi a tsare kamar wata mace,komai nashi mai aji da tsada irin wanda maza ke amfani da shi,yana shiryawa yana tunanin yadda tafiyan zata kasance,dama yana son zuwa daya daga cikin asibitocinsa dake kano kwana biyu bai leqa yaga maike faruwa ba shu da gidan marayunsa,duk da yana da wakili dake gano duk abinda ke tafiya kuma a kai duk abinda ake da buqata wuraren,amma bai saki komai ba balle kowa yayi mishi yadda yaga dama,mutum ne shi mai doka da qa'ida baison kuma a saba masa ko a taka mishi kamar yadda bai taka dokar kowa. Yana shiryawa yana kiran lambobin da ya saba kiran idan yana buqatar abinci,duk da sun san kusan cimarsa ta dare,ba wani abu mai nauyi yake ciki ba,a ladabce suka amsa buqatarsa ya kashe wayar,wanda kamar jira ake ya kashe wancan kiran wani kiran ya shigo,su'ad ce da layinta na america,yana kallon kiran yayi banza da shi har sai daya gaji ya katse,haka ta dinga kira har ta hada masa wajen miscal biyar,wanda tuni ya maida wayar silent don baison hayaniya,daga qarshe saqon tex ya shigo yasan kuma daga ita ne,baibi ta kai ba ya share ya tada shafa'i da wuturi,da wuri yake son kwanciya yau ya huta sosai saboda gobe yana da meeting da ma'aikatan companynsa na saqar abaya. To masu karatu yanzu fa kusan aka soma ko?,saidai gobe kumin uziri idan ina da sabga idan kun samu to ba lallai ya kai na yau ba,idan kuma kunji shuru sai uziri,kasancewar duk sanda kuka ji shiru daga wajen marubuci uziri ne ke kama shi irin uzirin dake kama kowanne dan adam,babban nauyi marubuci keji cikin kansa da qirjinsa idan ya soma rubutawa jama'a labari,baya jinsa fayau sakayau har sai randa ya kammala,Allah ya bar zumunci. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [23/02, 11:51] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 7⃣5⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *ALLAH S W T YANA CEWA* *ALLAH BAYA JINKIRTAWA WATA RAI IDAN AJALINTA YAZO* ______________________________________         Wannan karo anty dije daga ita sai yaranta suka koma abuja cike da kewa,kowa cikinsu sai yaji babu dadi,kasancewar sumayyan ta riga ta shiga jikinsu.          Sati guda malam ya yiwa baabaa maganar ya za'a yi da jeran sumayya,ce masa yayi babu ruwanshi wannan ba huruminsa bane,murmushi kawai malan din yayi "Ku qarata kai da 'yar taka" ya fada yana dariyaanty dije ce ta matsa kan ko daki daya abasu su saka mata kaya,tilas baabaan ya sanya aka bude daki daya dake saman aka basu shi suka saka kayan gadon da malam ya siya mata,idan baku manta ba gidan baabaan na da sashe biyu ne,ko wanne sashi akwai sassa a ciki,sashin daya barwa yaran nashi daya na wansu ne adam da matan shi,daya nasu mahomud ne da mus'ab,daya na almustapha ne,kowanne sashi yana dauke da balcony sama da qasa,sannan babban falo da dakunanan bacci manya manya wanda zasu iya cinye kayan gado set biyu,bedrooma din cikin corridor suke wanda ke hagu da daman falon,sai ka fito daga ciki zaka samu falon,sai qofar kitchen daga can gefe wanda qofa daya ce amma idan ka shiga zata tadda qofofin kitchen biyu biyu,akwai wata qofar daban da zaka fita vantilation,kusa da kitchen dining area ne,saman babban falo ne shima da dakunan bacci guda uku,daya ne makeke wanda a ciki mustaphan yake,kowanne sashe nada girma da yalwa,duk yadda ka kai ga son jin dadinka.         Dakunan baccin duka guda biyun again dake qasa baabaa yasa aka shirya mata su ba tare da sanin kowa ba,illa ya yiwa kamfani waya ya basu adress,royal beds ne set dinsu masu azabar kyau da tsada,hakanan kitchen din aka zuba qawata shi da dukkan wani kayan qawa da kayan amfanin buqata na kitchen,falon ma ba'a barshi haka ba,sai da ya sanya aka sauya duk wani abun amfani,a taqaice dai tashin farko sashen ya sake sauyawa sosai,duk da dama sashe ne wanda ya tsaru ya qawatu tun da can,yafi kowanne sashe kyau da qyale qyale,kasancewar mai sashin mai son tsafta da gyara,yayin da matar sashen ta zama mai dagawa da son nuna iyawa da kuma qaunat ganin tafi kowa.        Ba wai don almustapha bai da wani gida ba,yana gidan daya kusa a qalla shekara hudu ana gininshi yana narka masa kudi,har rade radi aka dinga yi a rean cewa da qyar idan ba gidan wani shugaban wata qasar vane,babu abinda bai zuba ba a cikin gidan,dai dai da cokali gidan baya buqata,hatta da kayan sangawa baki daya cupboard din gidan a cike take,wani irin tsari aka yi masa mai bala'in kyau da daukar hankali,hatta da qasashen da suka ci gaba samun irin wannan gidan sai an tona,to saidai babu wanda yasan da gidan do ba wanda ya gayawa,shi wani irin mutum ne da bai fiya son fadin abubuwan da yake yi ba,da fari yaso maida su'ad ciki,saidai irin rayuwar da yake so ya shimfida cikin gidan ba ita ta shiryawa yi ba,rayuwar soyayya da kulawa zalla tsagwaronta yakeson shimfidawa cikin gidan wanda dama ya ginashi ne don ya morewa rayuwarshi da arziqin da Allah ya mallaka masa,duk sanda ya kalli gidan yana sanyashi nishadi da walwala,ya zuba ido yana jiran yaga ranar da su'ad zatayi daidai da tsari da ra'ayinsa,ta shiryar karbar irin rayuwar da yake so,to a lokacin yake saka ran maidata gidan wanda har yanzu hakan bata samu ba,a qalla kusan watanni shida kenan da kammala komai na gidan,saidai lokaci lokaci idan yana buqatar kebewa ko hutawa yaje ya wuni ko ya kwana daya ya dawo,cikin dribobinsa ma mutum daya kacal yasan da gudan kasancewar shi ke kaishi.   *******  *******    *******       Duk yadda taso kauda da damuwa cikin ruhinta ko don saboda malam abun yaci tura,a yadda take yaqe da qoqarin zama cikin mutane duk da gidan nasu yanzu sun sake raguwa,daga ita sai mama,abdallah ma yaqi zama kasancewar gidan yayi shiru da yawa,ya gudu wajen yaya yahanasu don acan yake baje kolin tabararsa yayaan da su jamila na biye masa,ga yara 'yan wasa kamarshi,kana duban sumayyan kasan akwai kwantacciyar damuwa a zuciyarta,a hankali ciwon marar ke sake matsanta mata wanda ta kai ga cewa har sai ta sha paracitamol wani lokaci yake barinta tayi bacci.          Sati guda cif da daura aurensu malam baice mata komai ba,itama bata tambaya ba bata ma damu taji komai ba,addu'a ma take Allah yasa tayi zamanta a haka,kan me zata damu?,ta damu da mijin da batasan haqiqaninshi ko wani abu nashi ba?,da zaiyita zama bai nemeta ba ma ita haka take so,ko banza sunanta matar aure ba za'a matsanta mata kan aure ba tunda akwai igiyar wani a kanta.       Ranar da suka cika kwana takwas ranar litinin abdur rahman zaizo daukar tashi amaryar,tun rana halima ke faman shiri duk da cewa jikinta a sanyaye yake,kusan sumayya ce qarfin shirin duk da ciwon marar dake tsunkulinta haka ta dinga shirya ta tana mata hira da gaya mata abubuwa masu amfani duk don ta saki jikinta,zuwa sanda aka idar da sallaf magariba ta kammala shiryata tsaf sai tashi qamshi take mai sanyi wamda duka cikin taskar hadaddiyar humrar sumayyan ce,sumayyan ce ta raka haliman har zuwa falon malam,gabanshi suja zauna kan haliman a duqe,a hankali malam din ya dinga yi maya nasiha mai narjar da zuciya wadda kusan dasu yake baki daya,hatta da sumayyan sai data yi qwalla,ta sake taqinin duniya ba'a bakin komai take ba,hakanan mace bata da wata riba a rayuwa indai bata yi biyayya wa mijinta ba,ta ina zaki ci rina bayan aljannarsa na qasan qafarki idan kika saaba masa ya take fa?,da qyar halima ta iya roqon gafarar baabaa sabida kukan da yaci qarfinta,tashi sumayya tayi ta basu waje jin baabaa na yiwa abdur rahman izinin shigowa wanda ta tabbatar shina nasihan baabaa zaiyi masa,fuskarsa sai qyalli da annuri take,yana sanye da wata danyar shadda fara qal dinkin 'yar ciki da babbar ruga,kana kallonshi kaga ango sak,dakinta ta shigi ta samu gefan gado ta zauna tana fidda hawaye bayan taji tafiyarsu,shikenan,kowa ya fashe ya barta,kowa ya tafi wajen nashi masoyin,saura ita,ko ya zata qare?(nidai huguma nace Allah A'alamu).       Babban dakin taron wanda ke cikin qasaitaccen kamfanin na MM dauke yake da ma'aikata wanda a qalla sun doshi su arba'in,manyan ma'aikata daga qasashe daban daban wanda ya qunshi naijeria,pakistan,china,gahana da india,kowanne zaune cikin tsari kan tashi kujeran wanda suke a jere hagu da dama,tsakiya kuma dogon tabureni wanda kana kallonshi kasan cewa kamfanin da suka qerashi ba qaramjn fasaha garesu ba,shine teburin wadan nan kujerun da ma'aikatan ke kak,gaban kowanne dauke da ruwa da lemo,saidai baki dayansu ba wannan ne gabansu ba,sun tattara hankalinsu ne kan ogansu wanda ke hakimce a kujefa qwaya daya tal dake tsakiyar teburin,sanye kowa cikinsu yake da suit baqi da fari sabanin shi dake sanye da tashi tsumammiyar suit din ruwan sea blue mai dan turuwa,ta sake fidda sigar kyawunsa da zatinsa,wadda kana kallon suit din kasan tasha banban data duk wani mahaluqi dake dakin taron,jikinsa na jingine ne da  makarin kujerar yaja juyawa kadan kadan hagu da dama tamkar mai hutawa abinsa,saidai ina,bayani yake cikin gamsarwa da hikima da fasaha ta iyawa da qwarewa a kasuwanci,kusan sun gama tattauna komai conclusion yake musu,tafi kowannensu ya sanya bayan ya gama yana rufewa da idan akwai mai tambaya yayi,minti uku ya bada babu wanda yace komai kasancewar ya gama hadiye komai cikin jawabansa,ya duba agogon fata na kamfanin gucci dake daure tsintsiyar hannunshi,awa biyu ya rage jirgin fly emirate da zaibi zuwa nijeria,hakan ya sanyashi miqewa,wanda ke tsaye kusa da shi cikin baqin kaya da baqin glass ya soma tattare dukkan wasu files da takardu ya dauka masa yayin da ya bishi a baya zuwa office dinsa.       Yana gab da shiga elavator ya jiyi muryar hamza na qarasowa,hakan bai sanya shi ya tsaya ba ya shige ciki abinsa,da dan gudu hamzan ya qaraso ya shige ta rufe da su bayan ya amshi files dinsa dake  hannun wannan mutumin,harara ya juya ya gallawa almustapha "Maan,nifa banson wulaqanci da iskanci,nidin macace da zaka wani jaamin aji,idan ban narka maka dundu ba kace ba nine hamza ba" hararar shima ya watsa masa "Haka kawai don ka zubda mana mutunci sai ka dinga ma mutane wannan kiran mafarautan kaman zan bar garin,sai kace bakasan inda office dina yake ba,baka ganin yadda ka taramin jama'a suna kallona wadancan yaran sun wami qwalolowa mutane idanu kamar zasu cinyeshi danye" dariya hamza ya bushe da ita ya dunqule hannu ya daki kafadarsa yana fadin "Shege man,ashe kana kula,banda abinka kai da keson yaran wata qasar mai zai hana cikin indiyawan nan ka qara da daya" ya fada cikin salom tsokana sanda akwakun qarawa tafiya hanzari (elavator) ta iso da su block din da ofishinsa yake,bai kula shi ba shi kuwa hamza yabi bayanshi yana sheqa dariya abinsa,kusan duk duniya su kadai ke iya taba musty su dinma ba kowanne lokaci ba,bai tanka masa ba har ya sanya kati qofar lafiyayyen office dinshi ta bude wanda ya wadatu da tsafta qamshi da sanyi ya shige hamzan ya biyoshi,freezer ya bude ya fidda lemonsa da yake matuqar so ya daga ya soma sha yana takowa inda hamza ke zaune yana masa shaqiyanci,ya kammala sha ya jefa kwalin dustbin yayi kamar zai wuce sai ya shammaci hamzan ya damqo shi sosai ya riqe wuyan rigarsa yana dubanshi "Ni kake ma shaqiyanci yau zaka gane kuranka" dariyarsa yaci gaba da yi don time to time sun saba haka da mustaphan wanda a wannan fage shi daga suke hakan koda su lamin bai sake musu haka,hannunshi hamza ya ware yana ci gaba da diyarsa yace "Ah to,laifi nayi,wallahi aure ya kamaceka ka qara musty kowa yasan hakan" tsaki ya ja ya saki kwalarsa yana komawa da baya "Allah ya sawwaqe,ni na gaya maka ina da buqatar aure don ubanka"cikin sin ya tunzurashi yace "Basai ka gaya min ba,last night naje wajenka a hotel na taddaka kana mafarki,har wawurata kayi da qyar na sha" ya qarasa cikin matsananciyar dariya,naushi ya kawo masa ya kauce,sumarshi mustaphan ya shafa,ya fuskanci caakar da shi hamza ke son yi,qarancin suruti da yake da shine ya sanya bai iya maida raddi ko wasu amsoshi masu zafi ba matuqar ba cikin bacin rai yake ba,yanzun ma lalubar mai zai maida masa yake "Kai zaka qara aure bani ba mayen mata" "For what?,Nikam alhamdulillah,abida ta tsaren gaba ta tsaren baya,tun jiya wayarta ke damuna ma tayi missing dina tana buqatar na dawo gida,cikin satin nan kuwa zan gudu tunda mun gama daidaita komai samfuran kawai zamu fara saqawa,kai ke buqatar aure har yau aurenka babu riba,nan da few months za'a soma kirana da daddy" maganar ta daki mustapha,sai yayi shiru bai iya nada amsa ba,komawa yayi saman doguwar kujera ya kwanta gami da miqe qafafunshi bayan ya cire sau cikinshi da safar sa,duk da hamza baiyi da niyyar cin fuska ba tsokana ce kawai irin tasa sai ya dinga ji kamar bai kyauta ba,kamar ta bata ran abokin nashi,shima sai ya koma ya zauna yana fadin "Am sorry musty,i dont mean to hurt you" "Is ok" ya fada can qasa idanunshi a lumshe yana shafa fuskarshi da tafin hannunshi.        Tsawon minti talatin suja zaune a haka hamza na shan lemo bayan ya gama amsa wayar abida mustaphan na sauraran duk abinda suke cewa,duk da shi ba mutum bane mai sanya idanu kan lamuran wasu ba ba ruwanshi amma wannan karon kunnenshi sun kasa haqura,soyayyar ta burgeshi qwarai,shi mutum ne mai son yaga ana nuna damuwa da kulawa a kansa,zumbur ya miqe daga kwanciyar kamar wanda aka tsikara ya janyo wata sabuwar safar yana sanyawa cikin wani dan abu dake gefanshi don ya gama da waccar da ya cire yana fadin "Muje ka saukeni airphort,sauran awa daya da rabi jirginmu ya tashi" "Zuwa ina?" Hamza ya tambaya "Nijeria" ya bashi amsa a taqaice kamar yadda ya saba,baki hamzan ya sake yana kallonshi,wani irin mutum ne mustaphan,yanzun suna tare zai tafi nijerian amma ya kasa bude baki ya gaya musu?,yasan halinshi sarai yafi gaban haka ma indai mustapha ne. "Me zaka yo bayan ba time din zuwanka bane" "Baabaa ke nema na" cikin son ya tsokaneshi yace "Allah ya sanya wata 'yar naijan ya nema maka aure kai Allah yasa ma har an daura muga ya zakayi da 'yar africa tunda wadan da ba african ba ma kaqi" wata muguwaf harara ya watsa masa,haka kawai ya dinga ki kamar hamza ya masa baki ne "Da kuwa sai na nada maka duka mummunan fatan da ka yimin,kafin na sanyata da qafafunta ta koma inda ta fito,na maka kama da wanda zai tara mata?,mace daya ta isheni rayuwa,dayan ma da ana bada rabi karba zanyi" sosai maganar mustaphan ta bashi dariya,yasan yaddq zai tsinkuleshi sosai.       miqewa yayi ya dire cup din yayin da mustapha ya gama gyara wuyan suit dinshi ya kwashi wayarsa da sauran abinda yake da buqata ya kashe duk wani electric dake office din suka fito, "Kwana nawa zaka yi?" "Ban sani ba nima" ya fada yana maida wayar aljihun suit dinshi "Wacce iriyar masa ce haka kai har abada bayani wa mutane wuya yake maka?" "Oh god,ka fiya tambaya,ka sanyani magana da yawa,bayan kana gani yanzu muka gama meeting nayi maganar da ba adadi,zaka sanya qirjina ciwo fa?" "Bari na rufa maka asiri nayi shiru,don idan ya soma cuwon baka da mai jinyarka ko kwantar ma da hankali,amma ka sani this week nima zanyo gida" "Sai ka iso" ya fada a taqaice,don yasan idan ba haka yayi masa ba bazai barshi ba,murmushi hamza yayi yana yiwa abokin nashi addu'ar Allah ya hadashi da mace ta gari wadda zatasan zafinsa da darajarsa,yasan dama bazai hana shi tafiya ba mutum ne mai kula da haqqin iyali ko na nashi ba. *******    ********    *******         Kano ta yiwa baabaa dadi,tunda ya baro abuja lokacin daurin aure bai koma ba,har yau rana irin ta yau da mustapha ke isowa nijeria wajenshi wanda a yau yammacin yau ne yake saka ran zai koma abuja shida matan nashi guda biyu,kullum yana kusa da abokinshi har yau labarin bayan saduwar bai qare ba.       Bayan gama shirin nashi cikin qaton dakin nashi falle daya dake dauke da faffadan gado da malalen carfet,wanda shine dakinshi na farko daya tabayi kuma shi dinma har yau ba rabu da shi ba,anty maamaa ta aiko mishi da abinci yaci sannan ya fito don ya gaisa da su.      Bangaren ummensa ya fara shiga,ya taddata zaune a falo tana gyaran farcenta,gefe da ita kadan ya samu ya zauna sosai ya tanqwashe qafafu,fuskarta fadade da fara'a take dubanshi,gashi mutum zam sak amma rashin iyalin qwarai na wasa da nutsuwarshi "Barka da rana ummee,na sameku lafiya?" "Lafiya qalau almustapha,ya hudimomi da sabgogi?" "Alhamdulillahi ummee" ya fadi yana shafa suman kanshi "Ya kowa da kowa?" "Duk suna lafiya" ta bashi amsa,tasan da su amira huda da farida wanda ke dakin aure yake,yakan yawaita tambayarta yanayin zamansu,shiru ya dan ratsa tsakaninsj,shi bai da abin cewa kasancewarsa ba mai yawan magana ba,yayin da ummee ke kai kawon yadda almustaphan zai amshi maganar aurenshi,don ta tabbatar da cewa a yau baabaa zai gaya masa maganar "Kunyi waya ne da yayanku?" Kai ya girgiza alamar a'ah idanunshi cikin na ummeen,ya gama karantar akwai wani lamari tattare da ita,bai wasa da dukkan lamuranta hakan ya sanya bashi wuya wajensa karantar yanayinta "Okey,zaka wajen mahaifinka zakuyi magana da shi,abinda nake son gaya maka mahaifinka mahaifinka ne kafi kowa sani,bani da buqatar kayi jayayya ko mujadala da shi,tashi kaje nasan yana can yana jiranka" miqewa yayi yana amsa mata da to,yayin da zuciyarsa ke wassafa masa meye wannan wai da ya faru haka da shi wamda shi bai sani ba?,bai wuce ba sai da ya shiga ya gaida anty maamaan,cikin kulawa itama ta amsa masa,saidai ya lura itama tana masa irin kallon da yaga ummee na masa,yayim da tace masa sanda zai fita "Almustapha,ka daure ka dore kan halinka na biyayya kaji?" Itama to dince amsar,sai ya samu kansa da hanzarin isa wajen baabaan don yaji koma mene,don shi mutum ne da baison boye boye,sak yake,fadin gaskiya komai dacinta.        Da murmushi baabaa ya masa nuni ya iso har gabanshi,ya sanya masa ludagi cikim furar da yake sha,kasancewarsa yasan almustaphan da son fura,kadan ya sha saboda qagara da yayi da jin dalilin zuwanshi nijeria cikin qanqanin lokaci,sai da baban ya kammala ya kira anty maamaa ta kawo masa wayarta ta fita sannan ya soma magana da shi "Almustapha,kowa na da labarin bayyanar tsohon abokina sule ciki kuwa har da kai nasan labari ya isa gareka" qaramin murmushi ya saki don har ga Allah ya taya mahaifin nashi murnar ganin wannan amini da tun haihuwarsu suke ji labarinsa sai a yanzu ya bayyana,kai yake jinjinawa yana murmushi,yana zaton malam zaice ne yaje ya gaidashi "Almustapha ungo nan" ya fada yana miqa masa wayar anty mama,babu musu ya sanya hannu ya karba yana duba wayar,hotonta ne,daya daga cikin hotunanta na bikin amira,ta fito tayi tar ta cika screen din wayar fuskarta qunshe da murmushu da ya sake fidda sigarta mai sanyi da kyau,janye wayar yayi daga fuskarshi yana duban baabaa,gabanshi na faduwa yana addu'ar kada Allah yasa baabaan yace ya auri wannan 'yar mitsitsiyar yarinyar ne,amsar wayar baabaa yayi sannan ya dora "Nasan maiyiwuwa zaka iya ganeta,yarinyar dake gidan farouq maqotanmu na abuja,diya ce ga aminina sule?,almustapha" ya sake kiran sunanshi cikin yanayi na gaske,fararen idanunshi kawai ya daga ya dubi baaba "Na nema maka aurenta saboda mutuncinta,na nema maka aurenta saboda nutsuwarta,na nema maka aurenta saboda addininta,na nema maka aurenta saboda daga gidan data fito daga tsatson data fito,uwa uba na nema maka aurenta saboda TA DACE DA KAI!" baki daya kalmar baabaan ta qarshe taso tafiya da majiyar kunnensa,bai gama lalubo duniyar da yake ciki ba yaji wani sautin na cewa "Ta taba aure tana da yaro daya,tana da hankalin da zata iya zama da kai ta baka dukkan abinda ya kamata" ai wannan karon bansan sanda ya daga kai ya dubi baabaa ba,take wasu irin jijiyoyi suja fito a goshinsa,qoqarin danne zuciyar tasa yake da irin bala'in da yake ji cikinta amma bakinsa yaqi bashi hadin kai "Baabaa,ban santa ba,bata sanni ba,bata sona bana sonta,baabaa aure yanzu?,auren ma na bazawara da d'aa baabaa,please baabaa i beg you idan na maka wani laifin ne ka yimin duk wani hukunci da ya kamata amma banda wannan"murmushi baban ya saki " ba hukunci bane mustapha gaata ne na maka" "Gaata baabaa" ya fada cikin nuna shakku da taraddadi "Baabaa ba wannan gatan nake so ba baabaa ka sauyan wani umarnin zanbi amma banda wannan" nan ya shiga roqo iri iri yayin da baabaan ya zuba masa idanuwa yana kallonsa,yasan dole za'a samu rudani amma bai tsammaci abun zaya kai haka ba,ganin yanata zuba ya sanya baabaan daka masa tsawa "Muhammad almustapha!" Sunan da ya kira shi da shi yasanya hankalinsa dawowa jikinsa "Ni muhammad mukhtar!,indai ni na haifeka na baka umarni ka karbi auren sumayya umarni ba shawara ba,tashi ka bani waje!" Da qyar ya iya miqewa kamar wanda ya sha abun maye ya lalubi hanya ya fice.      Ya jima zaune gefan gadonshi aqalla awa guda yana yamutsa hannayensa cikin kwantacciyar sumarshi mai santsi da laushi,gumi ko ina yana keto masa,miqewa yayi ya soma zare kayanshi yana jefarwa cikin dakin,sai da ya rage saga shi sai boxer sannan ya fada bandaki,ruwan sanyi ya sakarwa kansa tsakiyar shower,ya jima tsaye sanyinbruwan na ratsashi tare da qoqarim control din kansa,ya sake barnatar da awa guda cur a haka har sai da tunaninsa ya dawo yadda ya kamata,qwaqwalwarsa ta fara yi masa bita,ya tabbatarwa kansa bai yi kalaman da suka dace ba ga mahaifinsa,baabaa ne,masoyinsa,wanda qaunar da yake masa ta daara ta dukkan wani daa ko jika dake cikin zuriyarshi,dakin gadon ya dawo ya sake lalubar wasu kayan ya sanya,wannan karon jallabiyya ce,ya gabatar da sallar la'asar,zama yayi kawai yana karanta yadda wannan QADDARAR ta fadowa rayuwarshi a lokacin da bai zata ba,yana nan a haka bai ankara ba yaji kiran sallar magariba,a nan gun itama ya yita a haka isha'i ta ruske shi,sai a sannan ya samu qwarin gwiwar miqewa ya sake daura alwala ya sanya hular tashi ka fiya naci ya nufi masallaci.        Sahunsu daya da baabaa,har aka idar bai motsa ba sai da ya ga baabaan ya gama addu'o'inshi ya miqe zai fita sannan ya mara masa baya,yana gaba yana binshi a baya,baban ya san da haka amma yayi banza da shi bai ko nuna ya ganshi ba,sai da zai bude qofar gidan yayi sauri ya bude mishi yaci gaba da binshi har sanda ya isa falonshi sannan ya waiwayo yana sake tamke fuska duk da yasan dama hakan zata faru,yasan halin mustaphan zai sake waiwayowa a duk sanda nutsuwarshi ta dawo jikinsa "Lafiya kake bina,zan shiga na kwanta ne idan akwai bashin da kake bina ban kammala biyanka ba sai ka gayan ko?" Kai ya sadda yana jin nauyi da kunyar maganar da baabaan ya fada,qarasawa yayi gabanshi sannan ya zube kan gwiwarsa "Kayi min afuwa baabaa kayi haquri kan baata makan da nayi,nayi kuskure wanda bana fatan sake yinsa,na amshi dukkan hukuncin daka yanke me kake buqata yanzu daga gareni" dawowa yayi ya samu waje ya zauna sannan yayi masa nuni da ya dawo kusa da shi ya zauna,sosai baabaan ya dinga kwatanta masa manufofi da hujjojin da yake jin sun isa su sanyashi qara aure,daga bisani ya rufe "Ka gwada zama da ita mustapha na cika maka baki tare da kurin samunta fiye da yadda kake zato ko tsammani,nasan jinin sule ba zai taba kasa gadon halinshi ha,mustapha,ka riqemin sumayya da mutunci da amana,idan ka wulqantata ka dauka ni ka yiwa,haka idan ka bata daraja,bazan iya maka afuwa ba aduk sanda na sameka da lafin wulqantata ba bisa haqqi ba" "Na yi maka alqawari insha Allahu" "Allah ubangiji ya albarkaceka,yq cika makq burikanka,ya kyautata rayuwarku kai da ita baki daya,kiran da nayi maka kenan zuwa nijeria,yaushe zaka dauki matarka?,sannan a ina kake son ajjyeta?" "Duk yadda kace baba haka za'ayi" murmushi ya saki yana dukan kafadarsa "Kaine fa mijin kuma kai ke aurenta bani ba da zaka turon zabin" "Ka isa damu ne baki daya baba" "Idan ta nine ko yau kaje ka dauko matarka,sannan ka wuce da ita dubai,don nima ina son naga daana ya fara dandanar zaqin aure" duk da rudin da yake ciki maganar baban ta qarshe sai data sanyashi jin nauyi "Zanyi yadda kace,amma amin afuwa zuwa gobe" "Ba lallai bane ai,kana iya barinta abuja idan kaso,amma sai bayan kun gama fahimtar juna da ita kun fara sabawa,fatana ka riqeta da mutunci" "Insha Allah baaba" addu'a yayi masa mai kyau da tsaho,wanda tilas mustapha ya dinga lallaba kansa da zuciyarsa ya zauna sukayi hira da malam din na wasu mintuna sannan ya tashi ya wuce.        Kamar zai zauce cikin dakin shi daya haka ya dinga ji,kiran hamza ya shigo wayarshi,wata bahaguwar harara ya ballawa wayar,ganu yake hamzan ne da shegen bakinsa ya masa wannan fatan,to amma ai ba fatan hamza bane tunda baifi awanni da yi masa shi ba,anya kuwa hamza baisan da wannan maganar ba ya munafunceshi?,yana kallon kiran har ta ya gaji da kiran nasa ya haqura,yana tsagaitawa lambar su'ad ta danno kai,wanda shi sam yama mance da ita,ya kuma mance rabon da suyi waya,hannu ya sanya cikin mutuwar jiki ya daga kiran ya kara akunnensa,tun kafin yace wani abu sheshsheqar kukanta ta cika kunnuwansa wanda hakan ya hadu da tashin hankalin da yake ciki take suka saukar masa da ciwon kai,sai ya runtse idanu yana saurarenta "Almustapha,ni zaka ci amana?,ni zaka yaudara almustapha,dama zakq iya kqllon wata mace macen ma 'yar afrika bayan ni?,almustapha kana jina kayimin banza da kai nake musty!" Ta fada cikin qaara da qaraji,tasan sarai yana jinta tafi kowa sanin halinshi na rashin son hayaniya da kuka,shirunsa ya sake tunzurata,mamanta dake gefe ta rada mata abinda zata yi,itama a ganinta hakanne ya dace tunda da irin wannan taci nasarar aurenshi "Wallahi almustapha sai na kashe kaina,sai nasha poison don bazan iya hada ka da wata can ba,wallahi sai na kashe kaina....." Ga mamakinta tun kafin ta kashe wayar shi ya kashe,bama kashewa kadai ba sai da yaja mata wani mugun tsaki sannan ya kasge wayar baki daya ya cillar,miqewa yayi cikin tangadi ya sauya kayan bacci ya koma gado ya duqunqune cikin bargo,yayin da qwaqwalwarsa ta kasa aikin komai a tsaye take cak.    ******   ******   *******       A shirye ya fito cikin baqaqe sidik three pieces slim fit suit,ba qaramin kyau suka yi masa sun haskashi matuqa,saidai shi kadai yasan izayar da yasha daren jiya,tilas ya dauki sun glases wada ya dace da shigarsa ya sanya,tamkar don ado ya sanyashi ba don kare idanunshi da suka sauya launi ba saboda rashin wadataccen bacci yayi masa kyau sosai shima,ya yanke shawarar gwara yaje asibitinsa ko wasu daga cikin marasa lafiyan da zai iya dubawa ya duba ko hakan zai rage masa zafi da radadin da yake ji.      bai samu baabaa ba saboda ya fice wajan aminin nashi malam kan maganar yadda zai gabatarwa da malam dukkan gidajen gonanshi wanda yakeao a yanzu su dawo hannunshi ya karbi dukiyarsa,yaga kamar malam din yana bagarar da zancan yaqi tsayawa su tattaun,yau yake so ayita ta qare,saboda haka anty maamaa maan kawai ya gaisar ya wuce wajen ummee,tana kwance ta fito ya gaidata ta amsa tana dubanshi,basai an gaya mata ba tasan da walakin goro a miya,ta gabatar masa da break fast,bai iya cin komai ba sai coffe da yayi qoqarin sha don kada ya daga hankalinta,yana sha tana gefansa a hankali tace da shi "Dukkanin mai biyayya zaici ribarta a gaba,bijirewa iyaye koda kan gaskiyarka ne bashi da wani alfanu,zaiyi wuya idan baka ci karo da tashin hankali ba a gaba sanadiyyar wannan bijirewar,almustapha,na roqeka ka riqe musu yarinya da mutunci,ka fiddani kunya kada ka watsan qasa a ido,yanzu ne lokacin da zaka nuna irin tarbiyyar daka samu daga gareni" jikinsa duk sai yayi sanyi,shi wai iyayensa da suka isa da shi ke roqo?,akan me?,duka akanta?,akan yarinya qwara daya tal,cup din ya dire yana fadin "In sha Allah" cikin sassanyar murya sannan ya fice yana dauke da brief case,tuni drivanshi ya gama shirya komai,maimakon baya da yake shiga wannan karon gaban motar ya shiga,baice komai ba don shima ya lura akwai abinda ke faruwa da ubangidan nashi ya shiga ya tada motar masu tsaron qofa suka bude masu wakekem get din suka fice.        Daga kadan kadan ciwon marar ke sake yawaita mata,wanda hakan ya sanya maama ta takurata kan lallai yau sai taje taga likita,itakam baki daya bajin dadin rayuwar ma take ba,amma tilas ta shirya zuwa don cika umarninsu da samun kwanciyar hankalinsu,qarfe tara ta gama shiryawa bayan sun gama waya da anty dije ta bata adresa din wani asibi,ta gaya mata komai kyauta ake saidai akwai tsantsar kulawa tamkar asibitin da ka fidda kudinka ka biya,ba kyautar ce zata kaita ba,kulawar data fada shi yasa zata,don bata da matsalar kudi,don baabaa ya ajjiye mata su tamkar baisan zafin su ba,hatta da abinda zata ji bai yarje taci na gidan ba,sabida yace yanzun ba dolensu bace.         Sai data shiga ta gaida baabaan a kunyace sannan sukayi sallama da malam kan zata asibitin da yake baaban yace izinin fitarta ya damqawa malam din kafin qarasowa mijinta,dakatar da ita baaba yayi ya fidda wayaraa ya kira daya daga cikin direbobin dake dakon fitowarsa ya bashi umarnin kaita ganin likita,cikin girmamawa ya amsa,shiru tayi cikin lafiyayyar motar wadda idan ba gargada ta kai gargada ba ba lallai ka fahimci ana tafiya ba,ire iren motocin da suke mallakin familyn professor mukhtar,motar da ada ko a mafarki bata darsa shiga irinta ba,ajiyar zuciya ta saki sannan ta fidda wayarta ta duba kiran dake shigowa amira ce,murmushi ta saki duk ciwon marar dake neman sake tsananta mata,amsa wayar tayi ta kara akunnenta. Masu karatu muje zuwa,wanne asibiti sumayya zata????. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [23/02, 11:51] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 6⃣7⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* Allah madaukaki yana cewa *duk wanda ya sallamawa Allah dukkan lamuransa alhali yana mai kyautatawa haqiqa yayi ruqo da igiya qaqqarfa wanda bata tsinkewa(yankewa/rabewa)* _____________________________________         Wuni nafisa tayi ta kasa sukuni da tausayin sumayya,a haka auwal ya dawo ya taddata,baki daya wani qaunarta na sake shigarta,haqiqa bata yi zaben tumun dare na aminiyar qwarai ba.          Washegari da kanta taje gidan anty dije dauke da ledar mayuka da turarukan data siya matan,dariya sumayyan ta dinga tana kallon tarkacen kayan,ko ba'a fada mata ba tasan cewa sunfi qarfin mai rangwamen gata irinta,saboda zuwa yanzu kanta ya soma budewa,tana iya gane abu mai tsada,balle ta san nafisan sarai,komai nata designer ne,kuma komai nata a set dinsa take amfani da shi "Wai kina nufin ni kike so na dinga amfani da wannan kayan?" "Qwarai kuwa da wace?" Kai ta kada tana dariya "So nake naga kin sauya sis,so nake naga kin fara sabuwar rayuwa" kai taci gaba da kadawa tana dubanta,kafin tace wani abu anty dije ta shigo dakin,kayan ta dinga dauka tana dubawa tana dariya "Allah yasa a baki hadin kai" "Idan ma taqi ina kallon fatarta zan gane,don sun tabbatar min suna da kyau,suna gyara fararen mata" itama ta fadi tana dariyan,godiya anty dije ta taya sumayya,sun jima suna hira kafin nafisan ta koma gida don dora abincin dare,don auwal baison take away idan ba lalura ba ta kama.         Anty dije ke jinjina tsadar kayan "Bansan ya zata kaya ba idan kayan suka karbeki ba,suna da kyau amma akwai tsada" cewar anty dijen. Kiran wayar daya shigo wayar sumayya ita ta katse hirar da sukeyi din,fuskar ta washe baki bude take fadin "Amiran baabaa ce anty" "Kice ina gaidata" inji anty dije tana miqewa don ficewa daga dakin ta fara jiyo hayaniyar minal da khalipha da alama rigima suke shi da ita "Autan baabaa(haka take kiranta idan taso tsokanarta)" "Mutanen uk,wai nikam yaushe zaku dawo,nifa na gaji wlh daga gida sai makaranta,ni daya kamar mayya,idan bakuyi wasa ba fa zaku ganni wlh na biyo sahu" dariya sumayya ta dinga yi ganij dududu watansu nawa ma da tahowa "Kamar yaune fa zaki ga mun dawo din,yi haquri takwara" dariya sukayi baki daya sannan suka soma taba hira,amiran na bata labarin abubuwan da suka faru bayan tafiyarsu "Amiran umman khalipha,baabaa fa ya karbi kudin aurena har da sa rana watanni shida masu zuwa dai dai sanda zan kammala degree dina" ta fada cikin nuna farinciki,cikn zumudi sumayyan tace "Kai haba dai takwara" "Wallahi amira,amma nikam tsoron yin auren nan nakeji takwara,duk da saifullahi na matuqar sona da qaunata,hakanan na amince da tarbiyya da halayyarsa" gefe daya na zuciyar sumayya itama jimamin da take mata kenan,saidai ba lallai abinda ya samu dan uwanka kaima ya sameka ba,kowa da tashi kalar qaddarar,bare amiran ita ba mai mata zata aura ba,ita daya ce a gunsa "Meye wani abun tsoro?misali su ummee da sukayi auren su wani abu kika ga ya samesu?" Kai ta kada kamar tana kusa da ita "Um um,kawai banson rabuwa ne da gida,ina son family na" "Ba shakka familynki abunda zaka yi marmari da begensu ne idan ka barsu,duk wanda ya kalli yadda kuke son juna ba zaiyi mamakin haka ba" sumayya ta zantawa ranta,amma afili sai ta bagarar da zancan da nuna rashun muhimmancinsa "Duk mace 'yar wani gidan ce,ko su su ummeen ce miki akayi gidanku ne gidansu,suna nasu familyn fa suka baro ko?" Sai amiran ta qyalqyale da dariya "Kinji umme tace ah to,ashe taji me kika fadi,kinsan abinda anty maamaa ta gama gayan kenan dazu" itama dariyan tayi,ta shiga tsokanar amiran "Kawai kice mu fara shirin baki,ina ga ba zamu wuce wata guda da dawowa ba zamu shiga hidima,ummm,bari na gayawa anty dije mu fara taru" "Ahto,don kune amarori,shi yasa na dage saidai asanya wata shidan,daa qasa da haka za'a saka,nasan kafin sannan kun dawo"ci gaba da tsokanarta sumayya tayi a haka suka rabu cikin barkwanci. Bayan ta aje wayar ta samu anty dije na sauyawa minal kaya da alamu bata wadancan tayi don ba'a jima da yi mata wanka ba " nikam saura qiris na sauya qawa,wannan qawa tawa qazamiya ce"sumayya tayu maganar tana duban minal tare da yamutse fuska "Yadai fi wallahi,duk gidan nan babu mai bata kaya kamar nata"inji anty dije,fuska ta kyabe tana shirin sakin kuka " na daina anty,wayyo Allah na"ta fada tana bubbuga qafafunta zata hau bori "To shikenan,ya isa,ai ke qawata ce ta amana,babu mai rabamu,uwata ce fa ta kaina" sai ta soma dariya tana tsallen murna sumayya na dubabta tana murmushi,duk yaron data gani tuna mata yake da abdallahnta,dauke kanta tayi ta maida ga anty dije "Anty an sanya bikin amira fa,wata shida mai zuwa" sakin maballin da take ballewa minal tayi dama ta kusa gamawa ta juyo tana duban sumayya "Tabdijan,kice akwai gangami kenan,bikin auta guda?,bikin amira ni 'yasu?" Antyn ta fada cikin jinjina lamarin,kai sumayya ta gyafa tana nade qafafunta saman gado tana murmushi "Jar uba,kice abuja zata motsa,familyn baabaa prof za'ayi bikin da aka jima ba'ayi kamarsa ba,to ai ina ga da na su mahmoud za'a hada tunda suma wata bakwai ne inaga yayi saura cikin ranar auren da aka sanya musu ko,Allah ya nuna mana,sai mu fara shiri tun yanzu,sumayya kuna da biki" inji anty tana murmushu gami da jinjina kai "Wallahi anty haka tace,ni kam mai zan iya cikin hidimar,ni da ban taba bikin qawa ba?" "Aikuwa dole ki ware ayi komai da ke,yadda amira ta daukeki kada kuce zaki watsa mata qasa a ido,nasan halayyarki sarai" dariya sumayya tayi ganin yadda antyn ta camfata tana kwantar da kanta saman filo "Allah ya bamu iko to anty" kan ta gama rufe bakinta kira ya shigo wayarta,lambar alqasim ne,tana mamaki da har yau bai rabu da ita ba,bayan ta zayyana masa ita din bazawara ce har da yaro,sai ta latse wayar ta kasheta baki daya tana jan qaramin tsaki ta gyara kwanciyarta abunta,ita yanzun babu mai daga mata hankali,ko lukman idan ya kira sai taga damar dagawa,darajar yaranshi dake sonta kawai take dubawa,badur rahman je kadai ke da wannan qinar na daga kiransa a duk yayin da ya kira din.         Cikin qanqanin lokaci da fara amfaninta da mayukan da sabulan taga banbanci,ita a karan kanta taga sauyi,wani laushi da santsi fatarta ke sake yi tamkar wadda ke zuwa gyaran jiki,baki daya qamshin jikinta ya sauya zuwa wani qamshi na musamman ma daban wanda ya kama kayanta sabida turaren da take amfani da shi set na man da sabulun,cikin watannin da basu gaza biyu ba sumayya ta sake komawa wata ta daban,komai nata ya sauya,sau tari laila na tononta tana cewa "Wlh anty sumayya kin koma 'yar gayu" hakan ya yiwa nafisa dadi qwarai a ranta,bisa dukkan alamu zata cimma qudurinta cikin sauqi kan sumayyan,tana son sumayyan ta zama wani sashe na familynsu,dukkanin halayyarta sun mata babu na yarwa. *******     *******    ********          Yau da gobe kayan Allah,sannu a hankali kwanaki ke mirginawa suna wawasar kwanukanmu a duniya,da kuma kwanakin dukkan wani abu da muka sanya masa lokaci,zuwa yanzu su sumayyan na da watanni takwas cikin qasar ta uk,ba qaramin karba qasar ta yiwa sumayyan ba,bugu da qari kuma ga nafisa daga gefe data kafe kai da fata zata sauya sumayyan malam din zuwa wata sumayyan ta daban,sumayyan uk,qudirinta kuwa ya karbu,a yanzu idan kaga sumayyan zaka sha mamaki,komai nata ya sauya,wani irin kyau da da can yake boye a yanzu ya soma bayyana kansa,hutu jin dadi da kwanciyar hankali suma na bada tasu gudun mawar,hatta da anty dije kan kalleta mafi yawancin lokuta,dadi take ji cikin ranta da ta sanadiyyarta sumayyan ta soma samun canjin rayuwa,ashe da can damuwa rashin kwanciyar hanakali da tension ita ta tasamma kassara sumayyan da gurgunta tunaninta,a yanzun kai baka ce sumayya bace wadda ta taba aure,'yar shekara ashirin da biyu har da yaro ba,sai kayi zaton tana cikin shekararta ta sha shida ne,tun da can Allah ya bata sanyin murya nutsuwa da iya magana,sai abun ya sake zame mata ado,zakayi zaton daga wani babban gida ta fito.        Gefe daya karatun ta ya kankama haiqan,turanci ba damuwarta bane a yanzu bare hausa,mai gaba dayan larabci dama ya jima da zama kan harshenta tun tana qanqanuwarta,tana daya daga cikin zaqaquran ajinsu a yanzu,zaka yi mamakin yadda harshenta ya karye,tana karbar karatunta da kyau,tuni wata daya baya ta kammala makarantar koyon girki da mu'amalar yau da kullum,ta fita da cetificate mai kyau,a yanzu kusan anty dije ta zama 'yar kallo ta fannin kitchen,kowacce rana da kalar abincin qasar da sumayyan zata girka,uncle farouq da taya bera bari shike basu kudi suje suyi siyayyan kayan da za'a buqata a ranar tunda shi bai sansu ba,laila ce 'yar rakiya,kai na rawa zata bita suje,zuwa yanzu ta sake tana iya zuwa gurare wadanda ke kusa da su ba nisa can ba,idan kuma suka so yin nisan nafisa ce jagora,zata debesu guri guri da yake ita din tamkar 'yar gari ce a garin,ranar haka zasu wuni a waje,sau tari sumayya na noqewa saboda ganin yadda nafisan ke kisan kudi idan sun fita amma taqi bata dama,duk abinda ta siyawa kanta sai ta saiwa sumayyan duk tsadarshi,dole tayi surrender ta tabbatar Allah ne yayi wannan hadin tsakaninsu. *******     ********    *******      Kamar ko yaushe yau ma tafe suke su shida,nafisa,sumayya,laila,khalipha,sai minal da kuma khalid dake riqe a hannu,ganyayyakin abinci suka sayo daga can suka wuce suka sha coffe a wani gun shan coffee dake daura da gun,zasu hau bus nafisa ta hana,a qasa suka dinga takowa tana nuna musu gurare tana musu bayani,sosai yanayin ya yiwa sumayya dadi qwarai,murmushi kawai ke tashi a fuskarta,sanye take da dubai abaya wadda tayi mata cif a jiki,ja ce mai dan turuwa kadan,bata yi amfani da mayafin rigar ba saboda yayi mata qanqanta,sai ta yafa wani medium vail dark blue wanda ya lullube har kafadarta.       Idan ka kalleta dole ta burgeka,murmushin dake tashi kan fuskarta kawai abun sha'awa ne,kayan sun haskata matuqa,khalipha da minal da laila sunyi gaba abinsu suna ta tsalle tsallensu laila na qoqarin saitasu,ita da nafisan ke ci gaba da takawa a hankali suna hira tana bata labarai.        Maganar da nafisan ta fada ta sanyata juyawa tana kallonta dariya ta kubce mata,sam bata lura da gabanta ba ji tayi ta bangaji abu,taga taga tayi zata fadi murya a sama taji ance "Hey!" Tare da riqo hannunta,tashin farko ta gigice,abubuwa biyu cikin lokaci daya suka hargitsa ta,walainiya idanuwanta suka shiga yi zuciyarta na bugawa,man ne,mustapha,sanye cikin three pieces slim fit suit navy blue wadanda sukayi matuqar yi masa kyau tare da fidda sigar kyawunsa,idanuwansa saye cikin sun glasses,ya kafeta da tsinin idanuwanshi duk da bata iya hangosu fes amma tana ganin alamunsu,jikinta ya soma rawa sanda ya saketa sai ta sake tafiya zata fadi nafisa ta tarota tana fadin sunanta,tsaye yake qyam yana dubanta,duba mai dauke da bacin rai,tuni baturen dake tare da shi ya kammala tsince wayoyinshi da suka zube qasa yana masa sannu cikin harshen nasara,dauke idanuwanshi yayi ya maida kan wata rantsatstsiyar baqar mota data faka a gabanshi,qaramin tsaki ya ja sannan ya juya cikin takunshi ya nufi inda motar take,da alama dama ita yake jira,baturen ya mara masa baya cikin hanzari ya bude masa mazaunin baya kafin shi kuma ya shiga gaba,jan nafisa ta soma yi jiki na rawa tana waiwaye har suka shige motar suka tayar suka bar wajen. Waiwayowa tayi inda nafisa ke tsaye bayan ta cikata,sai ta tsinci nafisan na kallonta "Waye wannan sumayya?" Ta jefo mata tambayar ba tare da ta shirya ba,boyayyar ajiyar zuciya ta saki gabanta na bugawa,hakanan Allah ya dora mata wani tsoronsa "Nima ban sanshi ba" ta fada tana ci gaba da jan nafisan don su bar wajen,batasan me zata ce mata din ba,saidai baki daya gwiwoyinta sun sare kamar an doke mata su,kamar qafarta ba zata iya kaita gida ba "Taya zaki ce baki san ko waye ba bayan na shinshino alamun sanayya tattare da ke?" "Kiwa Allah kada ki qara tambayata,don ban sanshi din ba" "Ala kyauta" nafisan ta fada ba tare data sake tambayar tata ba,haka suka isa gida tamkar kurame. Cikin sanyi jiki ranar baki daya ta wuni,girkin ma data fita ta sayo ingredient din bata iya yinshi ba,ta cewa anty dije bata jin dadi,sai ta koma daki ta kwanta kawai lamo,bata fadawa anty dije ga wanda ta gani,to tace mata me?,tace taga wa?,meye hadinta da su da zata sanar mata haduwarsu?,ta tabbata su laila basu ganshi ba tunda bata ji sunyi maganarsa ba. ******* ****** ******** Sannu sannu kwana nesa,yau da gobe kayan Allah,sai gasu sumayya sun fara hada komatsansu waje guda,wasu suna aikowa da su nijeria wasu kuma suna faka su waje daya,wata daya ne ya rage musu wa'adin zamansu a qasar ya qare,wato sati hudu zuwa biyar masu zuwa zasu bar qasar,tuni nafisa ta soma qaguwa suma su koma gida,ta fuskanci lallai idan su sumayyan suka barsu qasar sam ba zata ji dadin zama ba,zulaiha ce abar tausayi,wadda Allah ne yasan ranar komawarsu,zata yi kewa ba kadan ba,saidai tilas ta haqura. Hutun sati guda uncle farouq suka samu,hakan ya sanya suka zauna sukayi dukkanin lissafinsu na abinda zasu saya wanda zai musu amfani,ranar da daddare suka shirya zuwa wani katafaren mall wanda ke saida dukkan wani abun buqata,kama daga mai qaramin kudi zuwa mai babban kudi,duk wani abu na amfanin dan adam,sutura zuwa abinci da abunsha suna saidawa a wajen,basa bude gurin sai qarfe shidda na magariba har zuwa tsakiyar dare. Uncle farouq ya kira ya buqaci taxi da zata kaisu ya bada adress dinsa,cikin mintuna qalilan ta iso,shine zaune a gaba shi da minal,su kam suna baya,hira suke sosai cikin motar,wanda ita bata ma san me suke cewa ba saboda tana amsa wayar abdur rahman ne,bayan ta kammala ta maida wayar jaka,dubanta anty dije tayi cikin salon tsokana "Nafa lura kwanaki biyun nan ana dasawa da abdur rahman,ko yaushe cikin waya,ko dai da shi za'ayi ne?" Kunya ta bata saboda uncle farouq dake cikin motar,sai ta kasa magana ta saki murmushi kawai,dariya ya danyi yana daga gaban motar yace "Allah dai ya zaba abinda yafi alkhairi kurum" "Amin" cewar anty dije. Ta kai kimanin aqalla minti ashirin tana nemansu cikin katafaren shagon bata gansu ba,ta duba anty dije da uncle farouq babu su ba alamunsu,tuni ta soma tsurewa,ta ajjiye kwandon dake hannunta ta soma laluben hanyar fita nan ma ta kasa ganeta,qwalla ta cika idanuwanta jikinta ya soma rawa,ina yaran sukayi?,ina su anty dijen suke?,idan ta rasasu ta yaya zata iya komawa gida?,wannan tunanin ya sanyata qara sauri,data fita daga wannan bagaren saita fada wancan saidai ko qyallinsu bata gani ba. Wani irin burki ta taka wanda ba don tayi saurin dakatawa ba babu abinda zai hana su yin karo da juna,dubanta yake kamar yadda take dubansa,kamar ko yaushe fuskar nan a murtuke babu walwala,kai kace bai taba dariya ba a duniya,gabanta ya shiga faduwa kamar kullum,ji take kawai tata ta qare,ta rasa da mutumin da zata hadu sai da wannan?,kamar yadda al'adarsa take,saye yake da suit qirar company dolce anda gabbana baqaqe,hannayensa saye cikin aljihunsa kai kace babu abinda yazo siya,daga ita har shi babu wanda ya motsa,ita bata wuce ba tana kallonshu,yayin da shi kuma ke duba turarukan dake jere reras yana karanta sunayensu daya bayan daya,tuni hawayen da take adanawa suka soma samun hanya da zuciyarta ta raya mata su anty dijen sun bace mata fa,wata qila ma sun bar mall din suna nemanta suma,tattaro ragowar qarfin ta tayi da niyyar rabewa ta wuce don yana tsaye ne tsakiyar hanyar,ya raba hanyar gida biyu. Hannunta guda daya taji an riqo,wata zabura tayi ta waiwayo qirjinta kamar zau fado,taushi da laushin tafin hannun nashi na ratsa jiki da jijiyoyin jininta,bai ko dubeta ba ya soma jan hannun nata,bata da wani qwarin gwiwa da qarfin da zata qwace,ko wacce gaba ta jikinta an zare mata laka,abu daya zuciyarta ke raya mata,yau tata ta qare,don wannan mutumin babu alamu na imani ko tausayi tattare da shi,Allah ne kadai yasan me zai aikata,hawayenta suka qaru tana biye da shi tamkar raqumi da akala. Wani farin ciki ya mamayeta saboda hango su anty dije da tayi su da yaran bangaren kayan yara,a hankali ya zare hannunshi cikin nata tare da juyawa ya barta a wajen,sai ta waiwaya tana duban yadda yaje tafiyarsa ba tare ko ya sake waiwayowa ba "Laaaaah,ga anty sumayya can,yaa mustapha ne ya kawota" cewar khalipha wanda shi daya ta hangi isowarsu gun,tuni mustapha ya bace a gun,anty dije ta dago tana dubanta,sai kuna tayi turus ganin hawaye fuskar sumayyan "Lafiya?,ke kuma me aka yi miki?" "Amma anty nayi tsammanin kun tafi fa,idan na bace nan gun wa zai maidani gida?" Dariya ma ta baiwa anty dijen ganin yadda sabbin qwalla ke sake saukar mata "Kina nufin har yau da sauranki sumayya?,ta yaya zamu taho da ke mu koma babu ke?,bakiji sanda nake gaya miki kici gaba da siyayyarki ba zamu zo nan gun ki samemu wajen biyan kudi?,to don Allah ya ma za'ayi ki bace wajen da duka ko ina cctv camera,an fada miki nan irin nijeria ce?,ti waye ya rakoki?" Ta rufe maganar tana dariyar wautar sumayyan ciki ciki,kafin ta amsa khalipha ya bata amsar tambayar "Hala yaganki kenan kina kuka kamar qaramin yaron da ya bata" laila sau ta sanya dariya,harara sumayyan ta maka mata don kusan itace ta sanya bata ji sanda anty dijen tace mata suna zuwa ba,isowar uncle farouq yana dariya ita ta tsaida dramer da akeyi "Tom,musty yace mu kula,ya lura yarinyar nan sakarai ce,kada ta janyo mana abinda za'a kamamu kan mu bar qasar nan,kinsan su mai jan kunnuwa akwai kula da haqqin dan adam" dariya suka sanya shi da anty dijen yayin da wani abu ya tsayama sumayya a wuya,ita za'a kalla a cewa sakarya?,aikin banza ita tace ma ya kawota da zai gaya mata magana,ita kadai ke masifarta cikin zuciya ta qulu ta cika tayi fam,siyayyar da bata qara darawa nan da can ba sai anty dije ce ta qarasa zabar mata abinda taga ya dace,gani take ko ya ta matsa zasu sake yin clashing da shi. Sai da suka shiga mota sannan ta dubi anty dije,shaf ta manta cewa sunyi zata bata kudin da baabaa ya bata randa zasu taho zata siyawa amira wani abun a gift din biki "Anty,banfa daukawa amira komai ba" "To me za'a siya mata,su fa irinsu komai suna da shi,amma ki bari idan mun koma gidan kwayi shawara da nafisa sai ki siya mata abinda ya dace" "To" ta fada tana jingina da kujerar cikin mutuwar jiki hannayenta runguma a qirjinta. Da sukayi shawara da nafisan sai taga kawai tayi mata danginsu humra,turaren wuta na daki kaya dana tsuguno,collucture tana ganin zasu burge,shawara kam tayi mata,tasan amiran kuwa da jarabar son humra,akwai wani company wadanda ke qera crystal kala kala masu azabar kyau,nafisan tayi oder din kwalaben da sumayyan zata zuba kayan idan tayi,batasan da su ba sai kiranta nafisan kawai tayi ta nuna mata bayn an kawo,kwalaben humra kadai saiti uku uku sai data siya saiti bakwai kusan kwalaba ashirin da biyar,haka ta turaren wuta da wasu dogaye da za'a zuba collucture,kwalaben kansu abun kallo ne,wani irin design aka yi masu masu matuqar tafiya da hankali,kasa magana sumayya tayi,karamcin nafisa ya girmi qwaqwalwarta,sai ta zauna akwai tana kallon nafisan ita kuma tana murmushi,baki ta bude da niyyar hada kalmomin godiya sai tayi hanzarin tararta "Kada kice komai,kada ki godemin,nima gudun mawata na baki ki baiwa qawarki,duk da bamu taba haduwa da amira ba amma tana da kirki iya gaisawar da muke,kuma taci darajanki sister", anty dije kanta rasa me zata ce tayi,sai albarka take sanya mata tare da fatan dorewar zumuncinsu da addu'ar kade fitina,cikin kaya suka shirya kwalaben yadda ba zasu fashe ba. ********* ****** ******** Randa zasu koma nijeria nafisa na tare da sh,ita da auwal suka suka rakasu har airphort,jirgin dare zasu bi,batasan me ya sauya lokacin tashinsun ba,don da taji uncke farouq na fadin jirgin safe ne,tuni sukayi sallama da zulaiha,har kuka sai data yi,ji take kamar tabi sumayyan,to itama din nafisan tuni ta narkewa auwal ta soma masa qwalla,khalid kuwa ba'a magana jiki duka ya mutu,ya fuskanci anty sumayyan tafiya zata yi ta barsu,ai kam ashe kuka na gaba,sai da suja zo tafiya auwal ne ya janyeta yana rarrashinta "Is ok dear,muma fa nan da wata daya zamu koma keye ya rage ne?,wata dayan kwanaki nawa ne?,haba momyn khalid,goge qwallar khalid na dubanki" da qyar ta tsaya sukayi sallama auwal yayi dabarar dauke khalid sannan nafisan ta biyo bayansu. Mamaki ne ya kama sumayya ganin su a VIP wannan karon,tasan dai ba'a VIP din suka zo ba,sai tayi zaton ko daga gwamnatin tarayyar ne,abinda ta lura kuma da shi shine iya su kadai ne,baki ta tabe don batasan meke faruwa ba ta fiddo wani littafi da nafisan ta bata ta fara duba shafin da take,don son bata sha'awar yin hira yau,kewar zulaiha da nafisa take,ba shakka sabo turken wawa,karatun ya soma yi mata dadi,yayin da wani qamshi mai taushi ya dinga shiga hancinta,qamshin yayi mata,sai ta lumshe ido tana jin yadda ke ratsa qofofin hancinta,sai tayi tsammanin wani abun ne a cikin jirgin,lol "Barka da dare uncle" taji su laila na fada,cikin mamakin yadda lailan mai shegen rawar kai da surutu ke magana a kintse ya sanyata ajiye littafin ta dago kai da niyyar tsokanarta,so tayi tace "Allah ya nuna mana ma'aiki yau laila ke magana cikin nutsuwa irin haka?"sai maganar ta maqale mata,zaune yake kujerar dake bayanta wadda ke daura da mazaunin uncle farouq,magana suke qasa qasa da uncle farouq din,idanu suka hadu,da hanzari ta juya ta maida idanuwanta mazaunin gabanta,qirjinta na bugawa da sauri,ta rasa wannan wace iriyar masifa ce haka,ba dama ta ganshi yanayinta ya burkice,anya ma ba maye bane wannan mutumin,sanye yake da fararen suit qal wadanda suka dace da takalminsa,yayi kyau cika da wani irin kwarjini,bata san me ya shigo da shi jirgin da zashi nijeria ba,idan bata manta ba anty dije ta gaya mata gun aikinsa na dubai " matsa man sumayya,ina ta magana tun dazun kamar wata kurma"anty dije ta fada tana tsaye kanta,jiki babu qwari ta matsa din anty dijen ta zauna tana bude zip din jakarta tace "Kun gaisa da mustapha ne?,wannan karon zashi nijeria ba lokacin zuwansa ba,nasan baabaa zaiji dadi,dan gaban goshi zaizo,diyar ambassador din nijer anan ya dubawa aikin da yayi mata a dubai,baban nata abikin baaba prof ne sun taba aiki tare" kanta kawai ta kada ba tare data iya amsawa ba,bata ma ga mai ya hadata da wannan sharhin ba,giyar qaunar ahalin baabaa ta kama su anty dijen sosai,ko da yake babu abinda KARAMCI baya iya maida maka mutum ta raya a qasan zuciyarta "Kinga muma yau mun dana,gamu a VIP,mustapha yayi abinda ya saba" ta fada tana dariya tare da qoqarin kashe wayarta,duk maganar da anty dijen keyi bata fahimtarta,zaune take kurum,ta rasa abinda yasa jikinta sam baison hada inuwa daya da shi,ta tabbatar da cewa taqi jininsa ne tun ranar da ya yarfa ta gaban tarin jama'a,har yanzu tana iya jin zafin abunda yayi mata,baka san waye mutum ba,bakasan wanne yana yi yake ciki ba amma kayi masa haka amatsayinshi na dam adam irinka?,itakam jin anty dije kawai da take yaba kyawun halayensa,eh,ta yadda da mutunci da karamcin ahalinsu amma bata jin shi yana ciki. Laila ta sake taimakawa wajen dagula lissafinta data nace da tabata kan sai ta juyo taga abinda take nuna mata cikin laptop dinta "Idan ba zaki iya kalla ke daya ba zan karbi abata kinji ko?" Hakan data gaya mata shi ya sanya ta sarara mata. Mintuna arba'in kowa ya nutsu a kujerarsa yana abinda zai fishsheshi,duk yadda ta kai ga matse fitsarin da take ji amma yaqi sarara mata,ta fuskanci ya zame mata dole tayi,ko kusa bata son tashi daga inda take,saboda matsawar zata shiga bandakin tofa sai ta gifta ta kusa da su,a hankali ta waiwaya sai taga baki daya ya aza hankalinsa ga system,hakan ya bata qwarin gwiwa ta miqe anty dije ta matsa mata ta wuce,cikin sanda kamar wata barauniya haka ta wuce,baima san da wucewar wani a gun ba har ta gama fitsarin ta dawo. Daidai lokacin da yake magana da uncle farouq cikin nutsuwa,muryarsa ta shiga dodon kunnuwanta,ya salam,muryar mukhtar take ji muraran cikin tashi muryaf,ya ilahi wannan kamanceceniyar murya dame tayi kama?,ta tabbata abinda take ji yana da nasaba da muryar mukhtar dinta wanda ko wanne lokaci yayi magana tuna mata da shi yaje,ji take kamar shine a raye a kusa da ita,har marmari take taji ya furta wani abu. Dumi da taji yana ratsa rigarta da qarar fasgewar cup shi ya ankarar da ita karo da tayi da daya daga cikin 'yammatan ma'aikatan dake kara kainam baiwa kowanne passinger abinda yake da buqatar ci ko sha,baya tayi jikinta na rawa yayin da itama budurwar tayi baya tana baiwa sumayyan haquri cikin harshen nasara,a qa'ida sumayyan ke da laifi,saboda tayi qoqarin kauce mata amma sai data bugeta,iya tafi da custumer nasu ya sanya take bata haquri tare da bata hanya ta wuce ko kuma ta koma toilet ta wanke hadaddiyar doguwar rigar shadda dake jikinta wadda sabuwa ce kar ranar ta soma sanyata,lemon green da aka yiwa adon orange,mayafin data nannada saman kanta shima orange ne,ba tare da wani dogon tunani ba ta wuce zuwa mazauninta sabida ta kasa tantance me ya kamata ma tayi. Qarasawa tayi dauke farantin da pieces glasses din cup din tana baiwa mustapha haqurin bari ta sake kawo masa wani,sai a sannan ya daga kansa daga abinda yake yi din,kallon da yayi mata ya rudata,sai ta fara yi masa bayanin ta kawo ne sukayi karo da madam ya zube,da hannu ya tsaidata yace taje kawai bai buqata,haquri ta bashi sannan ta juya,ya fahimci me ya faru,don yana iya jiyi anty dije na tambayar bata qone ko taji ciwo ba ko?,tsaki yaja qasan ranshi yana ayyana anya tana da lafiyan qwaqwalwa kuwa,haduwarsu ta farko ya tuna,sannan ya gangaro haduwarsu ta biyu,haduwarsu a mall da girmanta tana wani hawaye shabe shabe kamar 'yar yaye,sai kuma yau,yaso tambayar alhj farouq sai kuma ya tuna ba abunda ya shafeshi bane yaci gaba da harkansa,amma ya barwa ransa akwai wani abu a qwaqwalwarta don bai taba ganinta a nutse ba. #mrs muhammad ce *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [23/02, 11:51] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 6⃣8⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* Allah yana cewa *(RANAR QIYAMA YAYIN DA AKA BAWA DAN ADAM LITTAFIN DUKKAN AYYUKANSA ABINDA YA AIKATA SANDA YANA RAYE ZA'A CE DA DAN ADAM)KA KARANTA LITTAFINKA!!!,YA ISHEKA AKAN KANKA KA YIWA KANKA HISABI* ya subhanallah,ya rahmanu kada kayi mana hisabi ka yafemu. ____________________________________ TEAM ABDUR RAHMAN YA DA SAURIN KARAYA IRIN HAKA NE,NAGA HAR KUN FARA SAREWA FA,ITA FA MACE ALLURAR CIKIN RUWA CE MAI RABO KA DAUKA,KADA 'YAN ADAWA SUYI MUKU DARIYA FA,TAM. _____________________________________ Bata sake yunqurin tashi ko motsawa daga wajen ba har zuwa sanda suka iso qasa nijeria,anty dijen na lura da ita,ta kuma kusa ankarewa da dalilin gushewar nutsuwarta,daya daga cikin motocin alfarma dake mallakar mustaphan ita tazo ya kwashe baki daya,kallo daya zaka yi musu ka tabbatar sabuwa ce dal,laila sai bude baki take saboda yadda motar tayi mata dadi,qasa qasa take cewa da sumayya "Anty sumayya dama kada aje gida don kada mu sauka daga motar nan,dadi wallahi" dariya ta baiwa sumayyan har sautin murmushinta ya fito,hada idanuwa sukayi sanda ya waiwayo yana tsammanin ko wani abun ne ya sake faruwa,da sauri ta kawar da kanta tana gintse dariyar. Kowa na ficewa daga motan yayin da yake zaune baiko da niyyar motsawa,amma ta danganta hakan da cewa shi za'a shige da shi cikin gida ne tunda su zasu sauka ne su shiga nasu gidan,tsoron ta yadda zata giftashi ya kamata,duka sun fice saura ita daya,a hankali ta durqusa zuciyarta na bugawa har ta isa bakin qofar inda anty dije ke tsaye tana tsumayin fitowarta din cirar maqullin gidan dake jakar sumayyan,daidai sanda ya fara magana cikin izza da nutsuwa yana baiwa driva umarnin su wuce ciki,kadan ya rage ta fadi anty dije ta tallafeta tana dubanta cikin salon tuhuma "Wai mene haka sumayya lafiyanki kuwa" "Bab....babu komai,qafata ce ta harde" bata ce komai ba ta karbi maqullin sannab suka jera zuwa cikin gidan "Ya kamata ki sanyawa ranki nutsuwa,na fuskanci duk sanda mustapha yayi magana saiki rasa sukuni da nutsuwarki,bafa mukhtar babe,bai kuma san mukhtar ba,kada ki sake ki sake aikata irin gangancin da kika aikata" da sauri ta dubi anty dijen,ya akayi ta karancin halin da take ciki,itama bata sani ba,batasan dalilin da yake sanyawa take kasa controlling kanta ba aduk sanda taji muryarshi wadda ke zubi sak data mukhtar dinta,abinda kawai zai banbanta tashi data dan fi ta mukhtar laushi,bata da bakin magana saboda haka bata ce komai ba jikinta a sanyaye suka qarasa cikin gidan. Washe gari haka ta tashi jiki duk a mace,ba dadi haja take ji cikin ranta,bata so anty dije tayi mata wani duba na daban,ba ita ta dorawa kanta ba tasani daga Allah ne,muhimmancin da mukhtar ke da shi a rayuwarta zaiyi wuya tayi saurin mance duk wani abu da yayi kamanceceniya da tashi rayuwar,ba abunda ta iya tsinanawa daga wanka sai kwanciya,ita kanta anty dijen ta lura,sai itama taji ba dadi,tana tsammanin ko fadan data yi mata ne ya sanyata zama haka?. Wajen sha biyu ta sameta dakinta tana fitar da kayan da suka dawo da su tana kuma shirya wasu cikin wata jakar daban "Sumayya,meke damunki?,ko don na miki fada jiya" kamar mai jira sai taji qwalla ta cika mata idanu,kai take girgizawa tana duban anty dijen "Ba don wani abu yasa na miki magana ba,na fuskanci abinda ke faruwa da ke ne,ina so ki sauya kanki ne" da sauri ta tareta "Ki daina fadar haka anty,wlh ba haka bane,ke uwa ce a gareni,kina da ikon zartar da duk hukuncin da ya dace da ni,nima bansan me yasa a duk sanda yayi magana nake zamowa haka ba,mukhtar dina nake tunawa anty har yau yaqi barin zuciyata,muryar mukhtar nake ji cikin tasa,sai na dinga jin kamar shine tare da ni" tausayin sumayya ya kamata,ta kama hannuwanta tana duban idanuwanta tana murmushi "Na fahimceki sumayya,amma shi baisan da haka ba,bana son ya raina min ke ko yayi tunanin wani abu na daban,nafa ji zafin abinda ya miki da fari,ban fadi miki bane saboda yayi ne cikin rashin sani......ki zama jaruma pls,ki dinga tunawa ba shine mukhtar ba....any way,mu ajjiye wannan maganar a gefe,me zakiyi da wadan nan kayan da kike shiryawa a jaka?" Hawayen take gogewa da tafin hannunta itama tana murmushi "Kano nake so gobe na tafi" idanu ta zaro "Kano sumayya gobe daga dawowarmu jiya,ko dai wani abun daban aka yi miki?" Marairaice wa tayi "Don Allah umman khalipha ki daina cewa an min wani abu,kin taba gani uwa ta yiwa 'yarta wani abu ba dai dai ba,kuma diyar ranta ya baci?" "To idan ba haka ba ai kya bari ko zuwa next week ne atleast ko?,zuwa sannan kin warware gajiyar tafiya kin fidda tsarabar su malam" "Anty inata kara amma baki gane me nake nufi ba,na qagu any naga abdallah,i missed him alort anty,shima kuma nasan haka ne" kama baki tayi taja dariya "Iyeeee,lallai yarinya,ga malam ga mama duka su bakiyi missing dinsu ba sai yaronki gaskiya ne" kunya ta kama sumayyan ta kifa kanta saman hannun anty tana dariya qasa qasa,ba zata iya boyewa ba,tabbas tayi missing yaronta "Shikenan,Allah ya kaimu,amma fa saidai ki bari sai jibi,zamu bude jaka afidda kayan su malam" duk da cewa ba hakan taso ba amma anty dije tafi gaban tayi jayayya da ita haka ta amsa mata da to. Misalin uku na rana suna zaune suna cin abincin rana amira ta shigo,bisa dukkan alamu daga makaranta take,don ga handout nan a hannunta da key din motarta,wani daj ihun farinciki ta saki tana qarasowa kusa da sumayya,gaisawa sukayi da anty dije tana tsatstsokanar su laila khalipha da minal,baki daya tace sun sauya,lallai garin ya karbesu,sai ta maida dubanta ga sumayya "Umman khalipha wai wannan amiran umman khalipha ce ko wata kuka samo a can?" Dariya suka saki baki daya kowa ya gane me take nufi,cikin salon zolaya itama sumayyan tace "Sun baro waccar a can,wannan musanyota sukayi" dukan cinyar sumayyan amira tayi tana fadin "Kina kallon mudubi kuwa?,wallahi kin bala'in zama wata queen namesake,ni zan fara yiwa alqasim wannan albishir din" harara ta aika mata tana murmushi "Ban aikeki ba,bismillah sa hannu muci abinci" idanuwanta ta maida kan abincin wanda saura duk da miya suke ci banda ita,fara da man take jin ci don an dade ba'a hadu ba "Wai wai,an kuwa zanci,shinkafa da wake da manja ne da yaji ko?,ga kuma salad,rabona da abincin nan da dewa,ina son fara da mai da yaji,su kam saidai suyi miya,musamman idan waccan baturiyar tazo,bama tasan fara da mai ba,idan taga wani yana ci har kyabe baki take wai muna cin abinci gaya" ta fada itama tana tabe baki,murmushi anty dije tayi "Dan gidanku yayarki ce dai,kuma kinsan baki isa ku fadi ba gaban maigidanta" amsa mata ta soma bayan tayi cokali daya "Me ruwa na da su,shima shi yaga zaya iya,haka kawai mutum bashi da maraba da gauro,kowa yana ci gaba ta fuskan family amma banda shi,haka kawai jiya har na kwanta ya tada ni wai na hada mishi fruit salad baturen kawai ga abinci ba zaya ci ba wai yayi masa nauyi" "Ke amira,zakici gidanku,ba yayanki bane?" Saki tabe fuska tayi kakar zata saki kuka "Ni umman khalipha bama wannan bane ya qonan raj,Allah anty su'adah 'yar rainin sense ce,na shiga kai mishi naji suna waya,ta baro america ta biyoshi dubai wai bata tadda shi,yace bai nan yana naija wai gobe zata biyoshi,wannam ai ba matar aure bace matar yawo ce,kuma kowa yw zuba mishi idanu wai matarshi ce haka suka tsara rayuwansu,to wallahi aure zamu masa" baki daya ta basu dariya saboda salon yadda tayi maganar bilhaqqi,har sumayya na qwarewa sai data kurbi ruwa "To ba sai ki masa ba tunda kece gaba da shi,kijimim tsaurin ido,musty zaki ma aure?,yo ko adam ai bai usa yace zaya yi masa aure ba bare ke" tsaki sumayya ta ja bayan ta samu tarin ya tsaya tana dan dukan cinyar amiran "Kinga malama,ki dinga maganar da zata amfanemu,juyo muci abinci" waiwayowa tayi tana duban sumayya "Uhmmmm,wallahi kuwa,don wannan babu ranar sauyawarsu" sai tayi qasa qasa da murya "Kefa kawai nake jira ki dawo a fara tsara mai yiwuwa,jibi za'a kawo lefe fa,kuma da sati uku zasu zo kwanakin bikin" "Komai kika tsara dai dai ne,amma ni jibin zan wuce kano" idanu ta zaro tana tsaida cin abincin da take "Me kika fada namesake,ina ce miki jibi kawo lefe kina cemin jibi zaki tafi kano,a satin nan fa zamu je dubai siyo kayan kitchen,tare da ya musty zamu koma,shigowar nan da nayi passport naki nazo karba za'a buga mana visa" cabdi,wane musty din,mustaphansu?,ta godewa Allah da ya bata idea din tafiya kano,don ko ana yankan jikinta ba zata bisu ba,wannan dan jin kan?,dan wulaqancin dan rainin wayo? "Kice wani abu mana kinyi shiru,duk kin rusan plan,wallahi idan baki je ba da wannan matar tashi zaya hadanu siyan kayan kitchen,bayan babu abinda tasan amfaninsa a kitchen saidai ta ganshi da ido,sai shegen izza da dagawa,zata siya min kayan shirme ne masu dan banzar tsada tana ganin kudin mijinta ne,kamar an gaya mata shi mai kudi baisan ciwo da zafinsu ba" ajiyar zuciya ta saki "Banji dadi bane amira,amma zuwa kano ya zame min dole jibi,malam na son ganina" ta hada da qarya,sai anty dije tayi saurin tashi ta doshi kitchen don kada amira ta roqeta ta hana sumayyan zuwa,don qaryan sumayyan ta mata dai dai,koda tana abuja ba zata barta taje ba,don ta fuskanci inuwa daya bata zaunuwa tsakanin sumayyan da shi uban gayyar,bare tafiya ma wata uwa duniya babu muharramin sumayyan ba zata yarda tayi ta ba. Shuru amira tayi wanda hakan ke gwada baki daya bata ji dadi ba,jikinta a sanyaye taci gaba da cin abincin,sai da daqiqa kusan biyar ta shude sannan ta iya cewa "Malam yafi gaban komai amira,sai kin dawo Allah ya kiyaye,amma don Allah ki dawo da wuri,sannan kimin alqawari zaki shiga ayi komai da ke,zaki dauki kanki kamar diyar baabaa,wallahu tun wancan satin baabaa ke tsokanata,wai idan baki dawo ba baisan ya zanyi ba,qila saidai ya daga bikin ko?" Murmushi tayi,alqawarin yayi mata girma da yawa,amma tilas ta dauka,anayi da kai yafi ba'a yi da kai,masoyinka kuma yafi maqiyinka "Kada ki damu,nayi alqawari in sha Allah" "Amma kafin ki wuce zaki shigo ki gaida su ummee,daga nan kiga ankon da aka fitar ko,ku hudu amma kalar naku daban,ke da qawaye na su uku" "Me zai hana,in sha Allah" ta fada kawai din a wuce gun,amma mai zai kaita gidan a irin wannan lokacin da wannan mutumin ke qasar,daga haka ta ware suka ci gaba da hirarsu. ******** ******** ******** Tun dare ta kasa bacci,gani take kamar gari bazai waye ba,bata ji kwanciyar hankali ba sai data ganta a mota sun dauki hanya,babu wanda ta gayawa tana zuwa don so take tayi masu ba zata. Qarfe daya da minti ashirin na azahar a qofar gida tayi musu kasancewar sun fito ne da wuri,ita ta fara shiga kafin driver din su anty dijen ya soma shiga mata da akwatunta da qatuwar jakar dake dauke da kayan tsaraba. Halima ce a kitchen,mama na bakin fanfo tana daura alwalar sallar azahar,yayin da zainab ke mopping falon mama wanda ta dage labulensa,hakimin abdallah na kwance abinsa saman kujera yana kallon cartoon,zainab na mopping din tana mitar ya hanasu kallon kowacce tasha sai ta 'yan aljanu,mama na fadin ai yafi,sunfi son suyita kallon waqe waqe da raye rayen banzan nan da wofi. Tana sallamar halima ta saki kwashe miyar da takeyi ta fito,zainab ta saki mopper,yayin da mama tayi tsaye tana dubanta tare da amsa mata sallamar fuskarta dauke da madaukakin murmushi,kusan a tare suja ruqunqumeta suna ambatar sunanta,dadi ya cika kowannansu,sam abdallah bai fahimci me ake ba sai da suka shigo falon,dirowa yayi daga kan kujerar yayi kan sumayya yana kiran "Mamiiiiiiii naaaaaaa" baki daya ya cukuikuyeta kamar zai shige jikinta,itama tsam ta rungumeshi tana dariya farinciki fal zuciyarta kamar an wanketa da ruwan qanqara. Baki daya sun baibayeta,idanuwanta na kam abdallah,photocopy na mukhtar take kalla,cikin shekara guda tal ya sake wani girma da wayo na ban mamaki,ya fara zama dan saurayi,shekara kusan biyar ba wasa bace,girman dan mutum babu wuya,duba daya ya wadatar da kai ka gane yaron na samun gata da kulawa,don suturar jikinsa ma kadai amsa ce,zainab da halima kowa da abinda zai fadi "Yaya sumayya kin ganki kuwa?,kamar irin hajiyoyin nan" "Yaya sumayya kin zama budurwa wallahi,irin 'yammatan abujan nan,gaskiya tafiyan nan ta karbeki,kaman an canjoki baki daya" dariya take ta rasa abin cewa,tunda ta sauko daga mota ta lura da kallon da jama'ar unguwar tasu ke mata wasu ma kamar basu ganeta ba,haka su halina suka cikata da surutu har sai da mama ta korasu halima taje ta zubo abinci ta kaima driver a waje din da yayi salla zai koma,sannan ta zubowa sumayyan ma, zainab kuma ta kai mata kayan daki,sai bayan fitarsu sannan suka ji kunnuwansu,abdallah na maqale jikinta yana ta bare choculets yana gama musu aiki. Haka suka wuni ba wanda ya fita a gidan,sai maqota dake shigowa jifa jifa yi mata sannu da zuwa,wanda wasunsu labarin yadda sumayyar ta koma suka ji suka zo ganewa idanuwansu. Koda ya abbakar yazo shima baki ya saki "Lallai nasan gobe mutuniyar anan zata wuni" "Ni ya kamata naje yaya,ina babymu nasan ta fara wayi bata san mamarta ba(da yake matarsa ta haihu)" "Ke dai kawai sai kin ganta,na tabbata ba zata iya haquri har kizo ba", malam ne kawai bai shigo da wuri ba amma ta gaza bacci sai da taga shigowarshi,kusan raba dare sukayi suna hira da shi,zuciyarsa na masa dadi duk sanda ya kalli diyar tashi,babu shakka rayuwa ta soma yi mata kyau,saidai a yanzun yana ganin ya kamata ta fidda abokin rayuwa ta sake aure,ko bai mata maganar yanzu ba zai fara yi mata jirwaye mai kama da wanka,zai tashi haiqan wajen yi mata addu'ar katari da miji na gari ita da 'yan uwanga baki daya,sai wajen sha biyu da rabi na dare suka rabu taje ta kwanta. ******** ******** ******* Washe gari a dakin malam din ta karya,ko wanka bata yi ba kayan bacci ne jikinta rida da dogon wando masu kauri,ta dora dogon hijabinta mai hannu,bayan sun kammala suka ci gaba da taba hirarsu,gayaran murya malam din yayi "tunda gaki Allah ya dawo dake auren 'yar uwarki ina jin ba zai wuce wata biyu ba,dama su suka matsa da magiyar a bari ki dawo,basa son ayu bikin wai bakyanan,shima kuma abubakar ya goyi bayansu" murmushi tayi ta dan sadda kai a zuciyarta tana lissafin bayan bikin amira da sati hudu kenan? "Alhamdulillahi,Allah ya tabbatar mana da alkhairi" "Amin ya Allahu,gwara ayi,hankalina sai yafi kwanciya,burina naga kowacce dakin mijinta,shine cikakken mutuncin 'ya mace,duk inda kika kai ga isa da dukiya nasaba da ilimi matuqar baki da aure baki kammala zama cikakkiya ba,don shine rabin,sai muyita addu'a,shi dama ibada ne,idan ka dace ka godewa Allah,idan ya jarabceka kayi haquri ka kuma nemi lada a wajensa" "Haka ne malam,Allah ya tabbatar da dukkan alkhairi" kai ta sunkuyar,jikinta yayi sanyi,ba shakka ta fuskanci zaurencan malam,gugar zana yake mata,ita kam ina zata tsomala rayuwarta a yanzu idan malam ya taso mata da batun aure,da sauri ta nemi tsari kada Allah ya karkato da hankalinsa. Cikin siyasa da qwarewa ta cikim hirar da suke yake jan hankalinta dangane da halayen rayuwa,babu shakka dukkan maganarsa izina ce kuma abar dauka,sosai taji dadin hirar da shi saboda yadda yayi mata tuni sosai game da wasu lamura masu matuqar muhimmanci ga rayuwar diya mace,ranar malam bashi ya fita ba sai sha biyu na rana,tun mama na leqosu taga ko ya gama shirin fitar har ta gaji ta barsu. Sanda ta fito zuwa falon mama ashe anty amina matar yaya abubakar har tazo,dariya ta saki tana dubanta "Tab,wlh anty kwata kwata banji shigowarki" "Ina zakiji 'yar gaban goshin malam" zainab tayi caraf ta karbe "Wallahi anty kema kya fada,baki daya faadar malam tata ce" karyar da wuya amina tayi "Dole malam yaji da sumayya don gaskiya ba daya kuke ba,kun manta yadda rayuwa tayi da ita ne,QADDARA ta wajiga ta?" "gaya musu dau matar yaya" ta fada tana amsar babyn fuskarta qunshe da fara'a tana cewa "Ga babbar jika,ga babbar jika a mata" yarinyar kuwa dariya ta dinga bangalawa kamar ta gane wace sumayyan a wajenta,yarinyar kyakkyawa sosai ta biyo jinin gidansu sumayya. Amina ke ta bin sumayya da kallo har sai data tanka "Wai sumayya me anty dije ke baki haka,kinga yadda kika koma kuwa?" Dariya ta saki "Haka kowa ke fada anty" "Wallahi kin sauya baki daya masha Allah,boyayyen kyawun nan duk ya fito,yau dai na yarda kinfi abban yusra kyau" dariya ta tuntsire da ita,sabida sau da dama suna musu kan hakan amma taqi yarda,sai gashi yau ta sallama. ******* ****** ****** Washe gari qarfe sha biyu na rana ta shirya tsaf cikin african abaya,abaya ce me mix da atamfa wadda tasha kwalliyar duwatsu,tayi kyau qwarai,jaka da takalminta duka marching colour,gidan hajiya tayi niyyar zuwa yau,hajiyan abdur rahman,so take ta wanke kanta,don tasan sam bata kyauta ba,shiru kawai wancan karon abdur rahman yayi mata. Ita da halima zasu je,saboda zainab ita yau ke da girki,suka yiwa mama sallama suka fice bayan tace su gaida mata hajiyan da bahijja,don shima abdur rahman din kwana biyu kenan bai leqo ba,abinda idan yana gari bai taba tsallake kwanaki biyun bai leqo ba,ba wani tazara ce mai yawa tsakaninsu ba,hakan ya sanya cikin mintuna arba'in mai adaidaita sahu ya saukesu bakim get din gidan suka sallameshi suka nufi gidan. Tun kafin su shiga abdallah ya soma fadin "Zamu gun daddy A ko?,gun hajiya da bahijja" kallon mamaki sumayya ke masa kafin ta maida dubanta ga halima "Kai,wai yaron nan har gidansu abdur rahman ya sani?" Murmushi halima tayi "Me zai hana,yaron dake wuni a gidan" shuru kawai tayi tana kada kai har suka shiga gidan. Daga can bakim setting room ta hangi takalma,wanda hakan ke alamta masu gidan na da baqi maza,babu kowa falon sai bahijja dake kwance kan doguwar kujera,sallamarsu ita ta sanyata miqewa zaune,fuskarta taf da fara'a takewa sumayya sannu da zuwa gami da miqewa tsaye saboda murna da mamakin ganin sumayyan,ana haka hajiyan ta fito daga dakin da yake mallakin bahijja hannunta dauke da magunguna,lale marhabin ta shiga yiwa su sumayya suna gaisawa da halima,yayin data ja abdallah jikinta tana fadin "Matso mai gida na,kwana biyu ban ganka ba,daddynka ya shiga rububi bude asibiti ya hanashi sukuni,hala ma kun ganshi?,don yana sitting room tare da baqi" murmushi sumayyan tayi a aladabce "Bamu ganshi ba,amma kamar akwai mutane a wajen" "Masha Allah,mutanen uk,tafiya ba sallama" ta fada cikin zolaya,sai kunya ta kamata ta sadda kai "Wallahi hajiya,shirin tafiyar duk shi ya cinye lokacin amma naso zuwa" "Babu komai,ai komai sai Allah ya nufa,kun dawo lafiya yasu dijen,kina wajenta ko?" Kai ta kada tana fadin "Eh,lafiya qalau suna gaisheku" "To madalla muna amsawa,bahijja miqe ki sama musu wani abu a kitchen kafin a gama abinci" "Halan bata da lafiya ne hajiya?" Sumayya ta tambaya tana duban bahijja "Bata jin dadi,kuma saboda wani iya shege bata da lafiya amma taqi shan magani,ta ina lafiya zata samu" "Gaskiya kam" sumayya ta fada,ita da halima suka shiga,haka suka fito da snacks ruwa da lemo,yayin da hajiya ta ajjiye maganin ta basu wuri tana dauke da abdallah ko nauyinshi bata ji,yaron itama yana tuna mata mukhtar,akwai tsantsar kama mai yawa tattare da su. Suna zaune suna hira bayan sun idar da sallar azahar suka ji sallamarsa,sanye yake da jallabiya ruwan madara mai haske,kanshi babu hula sai takaddu masu yawa dauke a hannunshi,idanu suka hada da sumayya wadda ke amsa sallamarsa "Hala batan hanya kika yi?,ko ba sumayya bace?" Ya fada tamkar da gaske yake,dariya suka bushe da shi baki dayansu har ita,ya qaraso ya samu gefan hajiya ya zube cikin gajiya yana ajjiye tarin takardun hannunshi abdallah ya maye gurbin takardun ya haye masa cinyar,surutu ya fara yi masa yana biye masa yayin da yake amsa gaisuwar halima "Hala ke kika tuna mata da mu ko halima?matar da ko ki sanarmin zaki dawo nijeria banyi wannan matsayin ba" Ya fada yana dubanta,hararar wasa tayi masa sabida hajiya ta bar wajen "Tunda ita ta tunamin sai na tafi sai na tuno don kaina sai na dawo" "Ni kike harara?,lallai idanunki sai isa yanka" dariya ya bata suka dara sannan ya soma tambayarta gajiyar tafiya mutanen abuja da sauran abubuwa tana amsa masa,saidai ta kasa sakewa saboda wani kallo da yake binta da shi,hakan ya sanya babu shiri qarfe uku na rana tayi haramar tafiya,ko ya lura a takure take ya sanya ya sauke abdallah bayan ya kammala cin abinci yace "Bari na shiga na watsa ruwa sai na zo na kaiku" kai kawai ta daga ba don taso ba,ta sani dole a yau akwai abinda zai faru,tana tsananin kunya da jin nauyinsa a yanzu,ba yadda ta iya tilas suka jirayi fitowarshi. Cikin wani yadi ruwan omo ya fito,yayi kyau sosai,yace su sameshi mota sanda suka tsaya yiwa hajiya sallama,ta ajjiyewa hajiyan turare da turmin atamfa data siyo mata,sai wata qaramar jaka mai kyau mai garai garai wadda ke dauke da set na kayan makeuo data siyawa bahijja,murna sosai bahijja ta dinga yi,yayin da ta dauki mayafinta tace zata rakasu dama ta gaji da kwanciya ko zata ji qwarin jikinta,godiya sosai hajiyan ta dinga mata tamkar bata fi qarfin abun ba,dama shi alkhairi dadi gareshi koda wanda ka yiwa din yafi qarfin abun indai yasan karamci. Duka baya suka shiga ita da shi ne a gaba,bini bini ya juya ya kalleta,wani lokaci su hada ido wani lokaci ta basar,bai dai ce komai bar zuwa sanda wani go slow ya riqesu,wasa wasa sai gashi suna shirin cin mintuna goma bai motsa ba,ga hadari ya soma haduwa ya sanya garin yin duhu duk da har yanzu bai fara zubda ruwan ba sai zafi da ake fama da shi,bata mantawa lokaci iwar haka suka bar nijeria lokacin damina sai gashu sun sake dawowa sanda take shirim kamawa. Baki daya motar dake gefansu wajen guda uku sun rufesu kasancewar sunfi nasu tudu,sai ta sauke glass din motar qasa,abdallah dake sit din baya ya zuro hannunsa yana qoqarin sanya mata yoghourt a bakinta wanda hajiya ta bashi wai tasha,bata kai ga sha din ba ya zuba mata a jiki,baki daya ya bata saman cinyoyinta "Ya salam,ya salam abdallah ka bata min kwalliyar mata" abdur rahman ya fada yana laluba gefanshi ya dauko ruwa a cikin jarka ya miqa mata "Budr murfin motar ki dan wanke gefan da ya baci kafin mu qarasa gida" karba tayi ta balle murfin motar ta dan zura jikinta waje zata soma wankewa,ganin mayafinta na niyyar shiga ya shafa shima ya sanyashi sanya hannu yana janye mata,dai dai lokacin da motar dake daura da su aka sauke nata glass din wanda zafi ya ishi wanda ke zaune sit din baya,tsaki yaja mai qarfi saboda ko kadan baisan a.c din motar ta lalace ba,driven bai gaya masa saboda sabbabi ne ko wata daya basuyi ba,wannan ne kuma hawanshi na biyu zashu rano,yayi niyyar hawan jirgi kuma babu jirgin da zai tashi kano to abuja a irin lokacin da yake son ya taho din,hakan ya sanyashi hawa mota. Kyakkyawan gani idanunshi suka yi masa,da fari ya dauke kanshi kasancewarsa wanda baison shiga sabgar da ba tashi ba amma sai qwaqwalwarsa ke gaya mishi kamar ya santa,sake maida idanuwansa yayi wajen,ita dince,gaban motar wani yana janye mata mayafi,ci gaba da kallon wajen yayi har ta kammala ta ta maida kanga ciki taja murfin ta rufe "Yammatan yanzu?,duka sammakal suke ne?" Ya tambayi kanshi,sai ya danna madanni glass din ya koma ya rufe yadda yake,wani tsakin ya kuma ja,gwara ya yita shan zafin da idanuwansa su dinga shishshigi kan lamuran da ba huruminsa bane. Sam bata ma san abdur rahman ya janye mata mayafin ba,ta kammala ta kiqa masa gorar tana masa godiya "Ai yiwa kaine" ya fada yana murmushi,itama murmushin tayi don a yanzu ita ba qaramar yarinya bace ta fuskanci me yake fadi. Fita sukayi dukansu har bahijja tace zata shiga ta gaida mama,bai hanata ba don yana da buqatar sararin da zaiyi magana da ita,kallonta yake har ta gaji ta tanka "Kada fa ka cinyeni" "Da hakan zai yiwu da nafi kowa farinciki,kinga idan ma cinyeki kin tabbata mallakina ni kadai har abada,wani ma bazai ganki ba bare ya qyasa" kunya kalamansa suka bata,saita maida kanta daya barin tana sauke murmushi "Naga ma sai wani shamin qamshi ake,ko da yake girmanki ne,shekara kwana inji 'yan magana,ina maganarmu ta kwana sumayya?,nayi haquri sosai fa,dukkan kuma wani abu da nake saka ran kammaluwarshi ya kammala,jibi in sha Allah za'a bude asibiti,ya muke ciki,ko baki yarda ba wannan karon inajin ta qarfin tuwo zan qwace ki" "Amma dai kasan ko budurwa bai halatta ayi mata auren dole va bare bazawara" ta fada tana dariya qasa qasa "Kada ki yimin haka sumayya" ya fada a marairaice,ta jima tana nazarin abdur rahman din,bata da wata mafita yanzu,babu hanyar tsira,koda bata auri abdur rahman ba dole ta auri wani a gaba wanda bata san wayeshi ba,ta tabbata malam bazai barta ta rayu haka ba tunda har ya fara yi mata gugar zana,zata tanqwara zuciyarta,ta kwatanta karbarsa taga ni,bata san me gaba zata haifar ba,amma me mutane zasu ce idan sukaji zata auri dan wan baban mukhtar,wanda shi saurayi ne ita din bazawara ce?,wacce iriyar fassara zasu masu,meye matsayar hajiyarshi?,da wace fuska zata kalli batun "Ka cancanta abdur rahman,bazan hanaka damarka da Allah ya baka ba,amma kamim haquri kada ka sanar da malam har zuwa sanda za'a kammala bikin zainab,na tabbata idan ka gaya masa yanzu zaice zai hada da ni ne,wanda ya kamata kafin sannan ace mun sake fahimtar juna kan zaman da zamu tukara da tsara abinda ya dace" hannunshi ya dunqule kawaj saboda tsabar farinciki "Amincewa da yardarki kawai ta isheni farinciki,na godewa Allah,bazan takura ki ba ki kammala shirinki a nutse,amma don Allah a yimin alfarma nayi azumim bana a dakina"ya fada a marairaice,dariya ya bata har sai data qunshe bakinta,wai a dakinsa sai kace wani mace "Allah ya zaba mana abinda yafi alkhairi" "Amin ya Allah,ki shiga ki sauya kaya ki huta naga kaman yoghourt din dake jikinsu ya hanaki sakewa,bazan iya shiga gun mama ba kunyarta nakeji kinsan ta zaka suruka,sai gobe insha Allah zan kawo musu katin gayyatar bude asibitin shi da yaya abbakaf,ki turon bahijja" ya fada yana sanya mata kudade a jakarta,kudi sam ba matsalarta bane yanzun amma tun kafin tace komai yace baiso tace komai din,tilas ta dauki jakar tana masa godiya ya bita da kallo har ta shige gidan wani madaukakin farinciki na ratsashi. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [23/02, 11:51] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 6⃣9⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *KU SHIGO CIKI KUJI* *ALLAH YANA FADA CIKIN QUR'ANINSA MAI GIRMA* *MISALIN ALJANNAR DA AKA YIWA MASU IMANI ALQAWARI,A CIKINTA AKWAI QORAMU  NA RUWA WANDA BAI JIRKITA BA,DA QORAMU NA NONO WANDA DANDANONSA BAI SAUYA BA,DA QORAMU NA GIYA WADDA TAKE MAI DADIN DANDANO GA MASU SHA(WADDA BATA SAKA MAYE KO TAMBELE),DA QORAMU NA ZUMA TATACCIYA,KUMA A CIKINTA SUNA DA(SU 'YAN ALJANNA)NAU'IN KOWANNE IRIN KAYAN MARMARI(DAN ICE)* *kai jama'a wannan ni'ima da yawa take,idan kaso ka zama TATACCEN QASAITACCEN DAN GIYA AMMA FA NA ALJANNAH,ya Allah ka sanyamu cikinta don rahamarka* ________________________________________        Kafin su kai ga fita daga airphort din ruwan sama ya sauka,hakan ya hadu da duhun magariba ya kawo qarancin jama'a bisa titi,idanuwan sumayya qur bisa kwalta yadda ruwan ke sauka yana wanketa,a duk sanda ruwam sama zai sauka sai ya mata tunin mukhtar kamar ko yaushe.                Rashin daukewar ruwan har suka isa gida shi ya sabbaba driban ya shige da su baki daya cikin gidan baaban ba tare da sumayya ta samu damar sauka ba kamar yadda taso,saboda Abdallah wanda ya jima da yin barci kan cinyar amira,ruwan na iya tabashi,da ita daya ce da da sauqi.        Lema kubra ta shiga ta dauko musu sannan suka fito,suka taka har cikin gidan.      Lallai kam wannan biki ba qarami bane,baki daya harabar gidan ko ina an kafa tempol,duk da gidan bai wani cika rana ba,duk da ruwan da ake tsulawa hakan bai hanaka ganin mutane na kai kawo daga wannan sashi zuwa wancan sashi ba,a haka suka qarasa bangaren ummee,falonta cike yake da baqi,yan uwa qawaye da abokan arziqi,ga 'yan rano nan wanda ko ba'a gaya ma ba kana kallonsu kasan jinin ummee ne,jinin sarauta,ga 'yammata nan ko ina zazzaune kowa na nashi harkan,shigar amiran ya sanya hanaklin sh dawowa kanta,masu tsokana nayi masu mata barka da dawowa nayi,da qyar ta yakice suka hau falon sama na ummee wanda tana can.        Karon farko da sumayyan ta taba shigarshi,falo ne dan gaske,wanda ya mallaki duk wasu kayan alfarma,baki daya kwalliyar falon ta da duk abinda aka zuba mishi na sarauta ne,kama daga royal chairs zuwa fentin falon,yayi matuqar burge sumayyan ba kadan ba,ummen ma zaune kan daya cikin kujerun falon tana irga sabbabin kudi wanda suke daure a rafarsu,ita da wasu mata ne wadanda kusan cousin dinta ne da suka taso tare tun zamanin 'yammatanci,qarasawa amira tayi ta kwantar da abdallah kan daya cikin kujerun,ummee ta dubeshi tana musu sannu da qarasowa ita da sauran 'yan dakin,a ladabce sumayya ta qarasa gabanta ta duqa tana gaidata,ta amsa fuska sake tana cewa "Amira ta hanaki sakat ko sai data daukoki" murmushi tayi kawai amiran tace "Ummee ba'a shiga tsakaninmu" "Au ai dama itaku amira" ta fada tana kiran daya daga cikin ma'aikatanta ta wayar hannu tana tambayarta an gama gyara dakin da tace,sai data gama wayar ta dubi amira "Kije an gama gyara muku dakin,saiki sanya a kawo muku abinci,ki duba abinda kuke da buqata ki kira mama uwani ki sanar mata,su ummu salma ma ina zaton suna dakin tun dazun suke qorafin rashin dawowarki gashi gobe kamu" "To ummee na" amiran ta fada tana miqewa "Muje,ummee idan abdallah ya tashi ki bada shi a kawo mana shi" ta fada tana nuna abdallahn dake kwance yana baccinsa lakadan,kai ummim ta daga don bata son yin magana ta sake bata a lissafin.         Dakina babba sosai wanda ya babu komai cikinsa sai carfet da aka malale shi da shi,katifune saman carfet din ko ina aka kwakwkwantar,yayin da aka lullube kowacce katifa da zanin gado abun rufa da filo qwaya daya alamar kowacce ta kwanciyar mutum guda ce,sai toilet qwaya biyu cikin dakim,da qaton madubi da ya kusa cinye rabin bango,mutum biyar suka taras a dakin,wasunsu na hira wasu na cin abinci,shewa suka sanya da ganin shigowar amaryar,kowacce da abinda zata fadi,nan suka zube aka gaisa suna ci gaba da surutaj,itakam sumayya na gefe tana kallonsu,rayuwar wayewa kawai ake a wannan familyn,kowacce ka gani tana ji da wayewa kyau da arziqin gidansu,akwai alama dake nuna suna da zumunci da kara,sannan akwai sabo da fahimtar juna tsakaninsh,wanda hakan baya rasa nasaba da yadda baabaa prof ya hadasu baki daya ya rungume kowa,duk sallah babba da qarama duk 'ya'yan 'yan uwan na gidansa,baya banbantawa da nashi dangin dana matansa,shi ya sanya kowa yasan kowa,'yammata ne hadaddu wannan na wace wancan ta fada a ranta tana murmushi.        Agogon fata na kamfanin gucci purple dake daure a hannunta ta duba ganin ruwan ya tsagaita sai yayyafi wanda take iya gani ta window din dakin albarkacin hasken lanatarkin da yake tarwai kowane lungu da saqo na gidan "Zan wuce fa amira" inji sumayya ganin yadda amiran ta bararraje tana kwasar hira,duka sai hankalin su ya dawo kanta har taji nauyin yadda kowa ya dora mata idonshi "Wasa fa kike amirah,kin manta alqawarinmu,ai ga gun kwanaki nan har na bar gidan nan" sai ta karyar da wuya tana murmushi "Amma dai ai kya bari naje naga anty ko?" "Eh,wannan kuma,kuma ai ban ma gama ganinki ba,muje part din anty maamaa akwai abinda zaki gani idan kin dawo na nuna miki sauran" ta fada tana miqewa,itama tashin tayi suka fito,har sun kai qofa tace "One minute don Allah sis,bari na dauko kayan waccan jarababbar na kai mata,Allah yasa ya musty bai nan" kafin tace komai har ta juya da sauri ta koma,tsayawa tayi tana jiranta gabanta na faduwa,tana addu'an kada Allah ya sa tace sai ta rakatan,don gaskiya ba abinda zai hanata ce mata ba zata ba.         Tana shiga ummu salma tace da ita "Amira wai ina kika samu wannan babe din haka mai shegen class,wallahi tamun,ta burgeni da ganinta akwai nutsuwa" "Ga kyau,muryarta ce ni kuma ta burgeni" inji hafsat,dariya suka bata,dukkansu 'ya'yan yar ummee ne,tasu ta bala'in zuwa daya da amira saboda halayyarsu kusan daya ce,ba ruwansu suna da matuqar kirki "Nan fa gidan anty dije wadda ta muku fried rice da sunan hanan,a nan take" "Masha Allah wallahi tayi" "Ai baku ma san tayi ba sai mu da muka je gidansu...." Eesha da hassada ta cikata tace "Me tayi,mr suke da shi a gidan nasu" amira wadda har ta sanya qafarta zata fita ta fasa ta dawo jin abinda eesham tace,dama tana lura da take takenta akan sumayya,wadda bata ga ita sumayyan abinda ta yi mata ko ta tsareta mata ba "Basu da komai,amma suna da rufin asiri,suna da wadatar zuci,basu taba kuma roqon wani ba,baya ga haka suna da karamci kyautatawa da girmama baqo,wadan nan abubuwa sun basu komai na rayuwa koda basu da shi din" inji amira ranta a bace sannan ta juya ta fita ranta a bace,humaida ce wadda itama ke jin haushin abinda eeshan keyi ta dora "Arziqi ba kudi bane eesha,wadatar zuci sanin darajar kai,mutunci yakana da karamci sune arziqin,kana da cin yau kana fa na gobe jibi wata ko shekara ma,kana sanya suturarka ta mutunci,baka taba roqa a baka ba,baka tashi ka rasa abin kaiwa baka me kake nema?" "Kinga malama,ni ba wani nace mata ba da zaku isheni da dogon wa'azi,ha'an..." Ta qarashe tana jan tsaki,caaa suka mata sun fita yawa ala tilas tayi shiru. A inda ta barta a nan ta taras da ita,suka ci gaba da takawa ba tare data nuna wa sumayyan akwai wani abu ba,bangaren anty maamaa suka soma shiga,itama bangaren nata masha Allah da mutane,suka gaisa sannan taja hannunta suka tsallake zuwa kitchen dinta,suna shiga tana yunqurin fitowa hannunta dauke da tray wanda aka jera tangaran mai garai garai guda daya wanda ke dauke da hadin salad mai kyau,sai wata qaramar butar shayi irin ta larabawa da cups dinta wanda ke dauke da baqin shayi wanda yasha kayan qamshi iri iri,su'ad ce,fuskar nan a hade tana faman kumburi,ko kunyar idon mutane bata ji,ta zama baturiyar qarfi da yaji,sanye take da dogon wando wanda ya kama jikinta da t.shirt mai gajeran hannu,kanta babu dankwali sai uban qarin gashi wanda aka dasa shi kamar nata na ainihi,ta sanya ribbom ta kameshi,takalmin qafarta kuwa irin mai igiyar nan je,wanda tsininsa ba kawai abun kallo ne,amma akace sabo da yi gawa da gatsine,da yake ta saba tafiya da abunta sam bai dameta ba,hannyenta kuwa farce ne wanda tasha nail polish,gefe suka janye bata ko kallesu ba ta wuce abinta,da kallo amira ta bita tana tabe baki kafin ta maida kallonta ga anty maamaa "Kumburin banza kawai,shi wanda kike ma kumburin ma baisan kina yi ba,ba kuma ki isa kiyi masa a gabanshi ba,abincin ba bake zaki girki ba ki karba ki kai masa yaci kina baqinciki kamar da kudinki aka sarrafa,wallahi ni yanzu baiken ya musty ma nake gani,kana aure amma kamar ba magidanci ba,babu wani ci gaba da ka samu ko sauyi dangane da tsohuwar rayuwarka" daquwa anty maaman ta jefeta da ita tana fadin "Sau nawa zan miki magana kan dauke ido daga rayuwarsu?,ke ke zaune da ita?,ko kinga ta kulaki sansa zata fita" shigin shagwaba amiran ke kumbure kumbure tana fadin "Duk ku kuke sake bata su wallahi,ni da ganin wannan takacin gwara kayi aurenka ma kayi gaba a barku da su" dariya ma ta baiwa anty maaman sai ta dauke kanta tana duban sumayyan "Qaraso amiran umman khalipha mu gaisa ki qyale wannan tuburarriyar qawar taki,rana iwar haka dai naga wanda zata yi mawa" dariya sumayyan ta saka itama tana qarasowa inda anty maman take,a ladabce ta gaidata tana tambayar yadda ta baro mutanan gidan,sai da suka gama gaisawa sannan tace "Anty mama,bedroom dinki na bude,zamuga wadan nam kayan" kai ta kada mata suka juya suka fice. Har bedroom din ta dangana da ita,aljannar duniya sumayya ta kira dakin,cupboard din antyn ta bude ta jawo wata akwati ta ajjiye gaban sumayyan,ta sake janyo wata ta ajjiye sannan ta fara hudewa tana fadin "Ga kayan da zaki saka na biki baki daya,komai da komai,sarqa kawai zaki buqata bansan choice dinki ba" baki kawai sumayyan ta sake tana kallonta,ta soma ware mata wanda zata sanya gobe kamu,wani dandatsetsen lace ne brown mai yarfin milk wanda aka yiwa dinkin fitted gown,rigar ta dinku iyaka,sai takalmi milk na companyn vinci wanda ke da tsini dunduniya,sake dago wata doguwar riga tayi wadda ta tafi da imaninta,ire iren rigunan da baabaa ya basu da salla ita da laila mai dauke da tambarin companyn MM,itama da takalminta ruwan kwalliyar duwatsun dake jikin rigar tace wannan ta jibi ce ranar arabian night,sake janyo wani shegen yadi tayi wanda bata tantance wanne ba,baqi ne baki dayansa an masa ado da milk din zare tsalli tsalli da milk din qulalai a jiki,shima fitted gown ce,har tafi ta farko fitinuwa,sai wani shegen hill shoes mai igiyoyi ruwan adon jikin yadin da jaka purse mahadin kayan ga "ankon dinner dinki" amira ta fada tana murmushi,rasa bakin magana kawai tayi tana duban amira,dariya ta sanya sanda ra motsa zata yi magana "Wallahi idan kika ce wani abu sai mun bata,baabaa ne duka ya bada yace na zabi na dinkawa babbar qawata" kai kawai ta dinga kadawa kafin ta furta kalaman godiya,kunnuwanta ta tasihe da nufin bata son ji. Daya akwatin kuwa baki daya kayan amarya ne da zata yi fitar biki,fadin irin kyawunsu ma bata baki ne,sai data daga mata su daya bayan daya sannan ta rufe ta maida ma'ajiyarsu tana cewa "A nan zamu dinga shiryawa,don haka anan zamu bar kayanmu,sai muje kiga lefe dama baki gani ba" dariya tayi "So kike dai dare yamin banje naga anty ba,ai basai na gani ba amira". " shikenan,muje ki rakani na miqawa waccan kayanta,sai na rakaki qofa kije ki dawi din"fuska ta narke,ta langabe kai duk don amiran ta haqura da wannan rakiya "Habbaaa amira,muje dai ki wuce ki kai mata ni kuma na wuce gida" "Ke kika ce sai na amso mata dinkin ina zaman zamana,saboda haka dole ki rakani" tayi maganar tana gyara nadin mayafinta,miqewa tayi jikinta babu qwari tabi bayan amiran suka fice. Daf da zasu shiga bangaren wanda ta baya suka biyo da yake qofofi biyu garesu,akwai qofar gaba wanda zaka shiga ta falo,akwai qofar baya wanda zaka shiga ta kutchen wannan qofar suka biyo,daga hannun hagu na bakin qofar,a qawace yake da wasu irin nau'in furanni da shukoki masu kaloli daban daban da kuma kyau,baki dayansu kansu daya babu wadda tafi wani tsaho,an qawata gun tamkar wani dan gurin hutawa,kaf gidan nan dinne kadai ke da irin wadan nan shukokin,wanda qilan mamallakin bangaren ne ya siyi abunshi yasa aka tsara masa su a haka,yara ne kusan su hudu,maza biyu mata biyu,a qiyasce zasuyi sa'annin juna baki dayansu,kowanne qananun kaya ne a jikinsa,sun kunna fanfunan suna ta faman wasan ruwa,amira ita ta fara hangosu,sai ta dakata tana daga murya "Hibba!!,yayi muku kyau da wasan ruwa kunji ko" baki daya suka waiwayo suna dubanta,kyawawan yara ne wanda kallo daya zaka yi musu ka tabbatar jinin gidan baabaa prof ne,wadda aka kira da hibba ita ta matso "Anty amira,gasar yin alwala muke,su hibban duk basu iya ba,zo kiga na fisu iyawa" "Matsa ki ban gu,yanzu ban da lokacin shirmenku kinji,tawa ta isheni" sai ta karyar da kai fuskarta kamar mai shirin yin kuka tace "Don Allah anty amira kizo ki gani" idanunta ta zaro tana dubanta "Ina wasa dake ne,bakiga ina cikin hidima ba,matsa a wajen nace" sumayya na tsaye tana murmushi tana dubansu,yarinyar ta burgeta,zuciyar son yaranta ta motsa mata,dauke idonta yarinyar tayi daga duban amira ta maida kan sumayya "Tunda ba zaki ba ai ga wata antyn ko?anty zaki je ki gani?" "Me zai hana" sumayya ta fada tana murmushi,tsalle ta fara wanda hakan ya sanya sauran yaran qarasowa din jin me ya faru "Ba inda zata,Allah hibba kin baci da yawa,itama tana da abunyi" "A'ah,nifa sai naje" inji sumayya wadda dama hanyar kubuta take nema "Kije ki fito kya sameni a nan" ta fada tana yin gaba din tuni yarinyar ta riqe mata hannu "Anty muje waccan fanfon,wannan na uncle man ne,zai zanemu ya ganmu a gurin,amma idan mukayi kuka sai ya bamu chaculet yace mu daina" murmushi tayi kawai tace "Allah" "Allah anty,kuma duk yafi sona" hibba ta fada suna qarasowa wani waje wanda shima akwai fanfo saidai baikai wancan kyau ba. Jin muryar yara ya sanyashi daga idanunshi daga kan laptop din dake gabanshi yana duba wasu sababbin design na dogayen riguna da kamfaninsa ke son fitarwa a sabuwar shekara,gefanshi butar shayi ce da cup qwaya daya,a rayuwarshi yana son ababen nan,yanayi na damuna irin wannan bayan gama saukar ruwan sama,da guri wanda ke da wadatar korayen tsirrai,iskar wajen mai dan sanyi sanyi kadan hade da qamshin qasa da qamshin furanni na masa dadi qwarai,ganin yaran tare da wata ya sanyashi maida kanshi yaci gaba da abinda yake. Daya yaron ne ya tabe fuska yana cewa "Qarya ne anty,yafi sona,ko za'a tambaya ma" yatsanta ta dora kan lebenta tana zaro masu idanu alamun yayi abunda ba mai kyau ba "Bakasan ba'a cewa babba qarya yake ba,lala ba kyau,kace Allah na tuba" kan kunnensa kalaman suka sauka sai ya daga kai ya sake duban inda suke tsaye,har yanzu bai gane wace ba,amma yana iya gane yaran saboda baki daya yasan muryoyinsu,hannunshi ya sanya ya tsiyayi shayin ya kai bakinsa yana ci gaba da sauraronsu,a rayuwa Allah ya zuba masa qaunar yara,zama cikinsu yana debe kewanshi a duk sanda ya samu kansa cikin kewa,hakan ya sanya wani lokaci yakan bata lokaci cikin gidan marayunshi,akwai yaran da suka shiga ransa da dama a gidan,baisan so yaushe ne zai daina rayuwar kadaici ba. Murmushi tayi ganin yaron yayi saurin rufe bakinsa yana cewa "Allah na tuba" "To yanzu muje mu gwada inga alwalar kowa din,duk wanda yafi iyawa shi ya m....." Sai ta kasa qarasa sunan "Wanda duk yafi iyawa shi aka fi so" ta sauya salon maganar tata,tsalle suke har suka isa gaban fanfon,tana tsaye tana kallon kowa daya bayan hannayenta harde a qirjinta,kamar yadda yake zaune saman kujera yan kurbar tea mai zafi yana kallonsu,sai da suka kammala tsaf,tabbas hibba ta fisu iyawa,amma ita dinma akwai gyare gyare,a hankali ta yaye yalwataccen mayafin data suturce jikinta da shu,wanda hakan ya bayyana shape dinta sosai kasancewar riga da skert ne a jikinta,tun bayan zuwanta abuja kayan suka dan kamata kasancewar ta murje ta cicciko,idanuwanshi ya lumshe saboda gujewa kallin haramun dinshi,sai ya kasa sake bude idanuwan mashi ya barsu a lumshe yana sauraron ta tana fadin "Sai kuyu haka,yauwa haka,haka" bai bude ba har sai da yaji tana fadin "Idan kayi haka,kayi alwala mai kyau" a hankali ya bude idanuwan nashi,wannan karon fuskarta tarwai take ta haske qwan lantarkin da ta tsaya saitinsa,ya dan qura mata idanuwa yana son tuna inda yasan fuskar "Mai kuka a uk mall" qwaqwalwarsa ta birkito file dinta,qaramin murmushi ne ya subuce masa,wanda idan baka kula da kyau ba na zaka gane hakan ba,saboda cije leban qasan bakinsa da yayi "Tana acting kamar wata babba" ya raya hakan a ransa. Riqeta yaran suka sake yi,nurain daya daga cikin yaran yace "Anty ki mana tatsuniya,baabaa lami mai aikin momi tana mana" murmushi ta saki,ta lura suma lallai yaran masu son mutane da sabo ne,saidai suna son riqeta gashi tana son tafiya gida ne "Ban iya tatsuniya ba saidai na baki tarihi" "Laaaah,irin wanda uncle man ya taba yi mana rannana?" Zaitun daya yarinyar ta ambata da salon tambaya,duk da bata sani ba amma sai ta daga kai "Ita,amma yanzun inaso naje gida na gaida anty na,sai wani lokacin na muku ko?" "Yaushe?" Inji hibban,kai ta girgiza qaramar dariya na son subuce mata,yaaraan akwai wayo,tana som tana yaro mai wayo da kaifin qwaqwalwa irin haka,ta tabbatar basirar da wayon bai tashi a banza,zai zama abu ne mai amfani a nan gaba "Wataran in sha Allah". A hankali ya janye idanuwanshi daga kansu jin qarar wayarshi,ya cirota daga aljihun black trouser din dake jikinsa yana duba mau kiran,su'ad ce,dan qaramin tsaki yaja,ba matsala yake so ta qara maishi ba,ya riga da ya yanke magana,ya gaji da auren asha ruwan tsuntsaye da sukeyi,ita tana kano shi yana daura,kusan tun jiya bayan isowarshi garin da yaje gidan hamza abun ke dawainiya da shi,kasancewar wanda amiran zata aura cousin suke da hamza,wata rayuwa ya gani ba irin tasu rayuwar ba,ba irin rayuwar gidanshi ba,yana iya tuna sanda hamza ya dagewa auren yarinyar suna ganin baikensa,ashe akwai abinda ya gano?. Rejecting call din nayi sannan ya maida kansa kan laptop dinshi da niyyar ci gaba da aikin da yakeyi,wani tsakin ya kuma ja ganin lokacin da ya bata yana kallon sha'anin da bai shafe shi ba,yayi asaran time dinsa a banza,saidai yadda take kiranshi a jejjere ya hanashi aiwatar da komai,wani wawan tsakin ya sake ja,a rayuwarshi ya tsani abinda zai takurashi,sai ya ciro wayar a fusace ya daga ya kara a kunnenshi,cikin shagwaba da karyar da murya ta soma fadin "haba my man,please....please kada muyi haka da kai,ka duba fa ka gani duka duka shekara daya ya rage min na kasance tare da kai fa?" "Keep quite su'adah please....na riga da na gama magana,idan zaki iya zama gu daya fine,idan ma ba zaki iya zama ba duk daya,amma kada ki zargeni nan gaba" ta tabbatar da cewa shi din kaifi daya ne,baha magana ya sauyata,mutum biyu ne tal a duniya ke sauya masa ra'ayi koda baiyi daidai da mizanin mashi ra'ayin ba,baabaa prof sai ummee,sanin baya qaunar kuka ko misqala zarratin,koda na qaramin yaro ne ya sanyata saka kuka har da sheshsheqa,sai ya lumshe idanuwansa yana sauraren sautin kukan nata,a hankali ya zame wayar daga kunnenshi sannan ya kasheta baki daya ya cillata aljihu,shutting down din system din yayi sannan ya miqe tsaye yana jira ta qarasa mutuwa,ya laluba aljihunsa yaji muqullansa na jiki,ya dauke system din sannan ya dinga takawa a hankali ya nufi inda yayi niyya,baki daya baya marmarin komawa bangaren bare taci gaba da jagula masa lissafi,saboda haka ya isa ga qarama cikin motocinsa ya bude ya ajjiye kayanshi ciki ya tada ta ya fice ba tare da ya nemi kowa ba. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [23/02, 11:51] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 7⃣0⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKIL* ___________________________________ Mamaki ya kama anty dije ganin sumayya,dariya ta dinga yi tana cewa "Maganinki,da kika qi dawowa ga mai gaba daya nan taje ta taho mana da ke ai" itama sumayya dariya take "Hmmm,amira,amira rigima amira tabara,sai ganinta kawai nayi wallahi" "Ina sane ban gaya miki ba ai" guri sumayyan ta samu ta zauna tana ci gaba da dariya. Nan ta shantake suna ta hira da anty dijen,bata tashi farga ba sai taga har sha daya tayi,hakan ya sanya ta bude dakinta tayi kwanciyarta,anty dije je cewa "Abdallah fa?" "Barshi anty,babu lallai yayi rigima" ****** ****** ******* Qarfe goma na safe tayi wanka bayan ta gama hada breakfast ta barwa anty dije sauran aikin gidan,doguwar riga ta saka ta wani irin yadi mai talewa,hijabi ta zura wanda ya saukar mata har saman tafin qafarta,niqabinta ta daura sannan ta fita ta tadda anty dije na goge kayan kallo a falo "Anty zan wuce,nasan amira tana can ta cika fam,fashewa kawai take jira tayi" ta fada tana qyalqyalewa da dariya,dariyar itama tayi "Ato,yau mai rabaku sai Allah" tana dariya ta saki niqab din nata ta fice a gidan. Ya kusan a qalla mintuna talatin zaune cikin corridor din dake saman benanshi,bata san sanda ya shigo ba,tun daren jiyan taje zaman jiran shigowarshi taji shiru,ta kira wayar babu adadi saidai duka amsa daya ce wayar a akashe take,tun tana kumbura har zuciyarta ta fara saukowa,ta sani cewa fushinsa bashi da dadi,tana shan wuya a duk lokacin da yayi fushi,hakan ya soma daga hankalinta,kusan ranar bata yi cikakken bacci ba,saidai duk da haka bata san shigowarshi cikin gidan ba. Cikin qanqanin lokaci zuciyarsa tayi fes,fuskarsa ta soma washewa,yaran dake shawagi kan idanunshi a harabar gidan,yaro daya tak yake hangowa cikinsu wanda bai sanshi ba baquwar fuska ne,saidai a yadda wasan da yaran ke gudana duka ya fisu kuzari da wayo,motsin yaron ya dinga bi da kallo yana sakin murmushin gefan baki. Sai data tsaya suka gaisa da baaba mai gadi kamar yadda suka saba sannan ta sanya kanta cikin gidan,tunda ta shiga gabanta ke wani irin faduwa,kusan yara sunfi yawa a harabar gidan suna wasanninsu,jifa jifa mutane na kai kawo,juyiwar da abdallah zaiyi ya hangota,duk da niqabin dake fuskarta da hijabinta hakan bai sanya ya kasa ganeta ba,da gudu ya tafi yana kiran "Ammiiiii....amminaaaa" cak yaran suka tsaya suna kallonshi ganin suna tsaka da wasa ya bar gun. Da idanuwa yabi yaron ganin yayi wani guri da gudu,hannayenta ta bude baki daya duk da har yanzu niqabin na kan fuskarta amma murmushi ne kan fuskarta,durqusawa tayi ta daga shi tana nishi saboda nauyin da abdallahn ya dan yi mata sannan ta dage niqaf din,fararen jerarrun haqoranta a waje "Wai abdallah,na kusa fara kasa dagaka,me kaci yau ka qara nauyi?" Dariya ya saki irin ta quruciya sannan yace "Ammi,wata ummi ce,na kwana a dakinta,ta yimin wanka ta bani chips da qwai ni kadai na cinye,harda tea da suger sosai" dariya ta kamata,har sai data dora tafin hannunta kan bakinta,kafin tace wani abu hibba tayo gaba da gudu itama sauran yaran suka biyota,bata ankara ba taji an ruqunqumeta ana fadin "Anty,kin dawo zaki mana labarin?" Waiwayowa tayi tana dariya,ta sauke abdallah tana fadin "Kin manta yau ana bikin anty ameeraa?,sai idan an gama zan muku,muje ku rakani inda anty amiran take" gaba tayi yaran na binta a baya wannan ya riqe hannunta wannan ya riqe hijabinta a haka suka tafi. Baisan yana binsu da kallo ba sai da suka bacewa ganinsa,ya lumshe idanunsa sannan ya bude a hankali,abun ya burgeshi ya bashi sha'awa,yana son yara har cikin zuciyarsa,bayansa ya jinginar jikin kujerar yana fidda zazzafan huci daga bakinsa "My man" yaji an ambata a tausashe,yasan ko wace hakan ya sanya yaqi waiwayawa,sannu a hankali ta tako gabanshi,sanye take cikin riga da wando,ire iren shigar da tasan yana muradi suna burgeshi qwarai idan tayi,jikinta na fidda wani irin qamshi mai dadi,duka hannayenta ta zuba a kafadarsa,cikin shagwaba salon da tasan yafiso tace "My man,ka sanyani a damuwa jiya,kasan cewa ina buqatar ka,baki daya kwanakin da zamu kasance tare ba masu yawa bane,amma man ka qauracemin" ko kadan bai da buqatar maganarta,hakan ya sanya ya saka hannunshi ya sauke hannayenta dake kafadarsa sannan ya ture kujerar ya miqe tsaye ta juya yana shirin barin gun,ranta ne ya baci,hankalinta ya tashi,ta tabbatar cewa ya hau bigerin da shawo kansa zaiyi wuya,bata kuma isa ta sha gabanshi don hakan zai iya jawo mata wata matsalar,tilas ta janye jiki tana kallonshi ya wuceta,hannayenta ta saki zuciyarta na zafi,idanuwanta na neman tara qwalla,babu shakka idan banda mustapha mustapha ne da babu namijin da zata zauna a duniya yayi mata haka,saidai mustaphan na dabanne kamar yadda yake daban a zuciyarta,mafita daya gareta ta kaishu gaba inda za'a sashi tilas yayi mata abinda take so din,bama inda ta saba kaishi ba wannan karon na can zata kaishi ba,sai ta juya da dan sassarfa ta ratsa ta dakinsa zuwa falonsa ta sauko qasa ta nemi hanyar ficewa ba tare data damu da sauya kaya ko daukar babban mayani ta suturta jikinta ba ko don girman wanda zata gurinsa. A dakinsu na jiya sumayyan ta tadda su,tana qunshe dariya ta qarasa,dariya amiran ta saka tana harararta "Wallahi kin maida ni wata iri amira,godiya nake" "Afuwa namecy,afwa"ta qarasa ciki suna gaisawa da 'yammatan dake ciki,gira ta daga " to ya zanyi da ke,ni na kai kaina inda ba'a damu da ni ba,muje kimin rakiya wajen baabaa" "Ya kamata,don nima ina son inje in gaidashi" eesha dake shan tea ta ajjuye cup din tana yiwa sumayyan duban ita kuma a wa?,kamar zata furta sai kuma ta fasa,ta miqe itama tana yafa dan yalolon mayafi kan kayan baccinta tana cewa "Muje nima nayi rakiya" "Owk" amira ta fada ta dubi su hibba "Oya,ku wuce ku tafi wasanku" juyawa sukayi hibba ta tsaya ta karbi abdallah suka wuce. Sai da suka shiga wajen anty maamaa da ummee ta gaidasu sannan ta suka wuce zuwa sashen tsohon. Zaune yake gefan umminsa daga shi sai itayana kurbar coffee,idan da kowa a gun ta tabbata bazai sha ba,wanda ta shiga kitchen da kanta ta hada masa,dubanshi take qasa qasa,ita daya take iya gane mustaphan,tayi tsammanin idan yayi aure shikenan komai ya qare,matarsa zata fahimceshi fiye da kowa,saidai kash,sabanin haka ne ya faru,matarsa itace wadda bata fahimceshi ba fiye da kowa,a yanzun kallo daya tayi masa ta fahimci yunwa yake ji,bazai iya gaya mata ba,zai iya ci gaba da zamansa haka har sai an bashi,idan ya gaji ya kuma yana iya fita can wani wajen cin abincin yaci abinshi,time to time yakan sanya matarsa tazo ta karba masa idan yunwar taci tura,hatta da amira tafi matarsa sanin ko shi waye,wani irin mutum ne shi mai wuyar sha'ani,ba kowa ke iya fahimtarsa ba,bai iya sharing damuwarsa ko shawararsa da kowa idan ka dauke ummeen da baabaansa,tayi zaton idan yayi aure wannan zai zama aikin matarsa,saidai ina ma yaga matar bare ta dauki wannan responsibility din,saidai komai tana ganin ya kusa zuwa qarshe tunda gaf su'adan take da kammala karatunta,tana zaton idan ta gama din zata nutsu ta tara hankalinta waje guda ta kula da mijinta kamar kowacce matar aure. Yana tsaka da amsa waya ta shigo falon kai tsaye tare da sallamarta,a hankali ya daga kanshi don ganin waye,kansa ya kawai gefe yana jin kunyar ganinta a haka a matsayin surukarshi,baki daya babu al'adar bahaushe ko digi cikin jini da jijiyarta,komai nata na mai jan kunne ne,ko qanqanin bata jin kunyar keta gidan a haka,duk da tarin baqi dake gidan,yana yiwa yaronshi sha'awar sauyin rayuwa,duk abinda ke faruwa cikin rayuwar yaron shi da yakeso fiye da kowa cikin yaransa idan ka dauke amira yana sane,saidai baison jefa kanahi cikin sha'anin da ba'a nemi agaji ko tallafinsa,dattijon suruki ne wanda yasan ciwon kanshi da mutucinsa,amma tabbas mustapha ma cikin wani wadi daya cancanci a tallafeshi,tun fari laifinshi ne da bai ganin aibun rayuwar mai jan kunne,gani yake rayuwa ce ta burgewa,baisan babu komai cikinta face tsantsar wahala da rashin nutsuwa. Cikin sheshsheqar kuka ta zube a gabansa "Baabaa don Allah kayi masa fada,ka masa magana,yana son takurani,yana son tauyen 'yancina" sosai yake dubanta,a nutse yace "Nutsu su'adah,zauna,zauna sosai,gayamin,me ya faru?,me ya hadaku" zama tayi gabansa tana goge hawayen nata da tissue,don ko dan mayafin da zata kama ta goge hawayen babu a jikinta "Baabaa,mustapha ne,haka kawai muna zamanmu yadda muka saba,shekaran jiya yaje gidan hamza,ya gano wata zamantakewa ta daban yace dole muma irinta zamuyi,bayan zamantakewar tasu sam babu 'yanci ko walwala a cikinta,sai dinbim takura kai da rayuwa cikin duhu da rashin wayewa,lallai wai saidai na dawo nan qasar na zauna daku na qarasa karatuna don bai amince da duk qawaye na da abokaina ba,sannan wai idan na kammala na bishi dubai mu zauna tare na dinga kula da shi,don Allah baaba wannan ba takura bace,ni ban taba ganin inda da quruciyarki kike rayuwa irin haka ba,a gun africans kawai nake gani suma rashin wayewa ce da duhun kai" idanu baban ya runtse kafin ya bude,duka ta hadu ta zagesu su da iyayensy,babu shakka ba qaramin tasiri rayuwar yaro take ba a duk inda aka haifeshi ko ya taso,sai Allah ya taimaka iyaye sunyi tsaiwar daka sannan za'a samu yaro ya tashi da dabi'a halayya da al'adunshi. Cup din ya dire dai dai sanda wayarshi tayi tsuwwa,ya duba yaga kiran daga baabaa ne,tun kafin ya daga ranshi ya raya masa mishkilar su'adah ce,daya daga din kuwa ce masa baabaan yayi "Kana ina?,duk inda kake kazo ka sameni a falo,ina jiranka" daga maganar tasa kawai ya fahimci mawuyaci ne ba qararsa ta kai wajen baabaan ba,duk da cewa hakan ba baqon lamari bane wajensa,amma abun yayi masa ciwo fiye da kullum,ranshi bace ya maida wayar aljihunsa yana duban ummee "Baabaa na kira" ya fadi a taqaice "Ok,ka qoshi kenan coffee kawai ya isheka,bayanshi banga kaci komai ba?" "I'm ok ummee" ya fadi yana takawa ya fice daga dakin. Cikin sanyi da qasaita yayi sallama cikin falon baaban,wani kallo yajefa mata wanda ya sanyata sadda kanta qasa,take jikinta yayi sanyi,nadamar kawo qarar ta baibayeta,kwarjininsa kadai ya ladabtar da ita,cikin girmamawa ya isa gaban baaban ya zauna gami da lanqwashe qafafunsa,ajjiye takaddun hannayensa yayi sannan ya maida hankalinsa gareshi "Mustapha,me ya shiga tsakaninka da matarka" shiru yayi na wasu daqiqu kanshi na qasa,idanunshi bisa carfet din dake dakin,a hankali ya motsa bakinsa "Baabaa,ina da buqatar mata ta ne kawai kusa dani,na buqaci ta ajjiye karatunta ta zauna tare da ni" yasan a rina,mustaphan ba mai boyon abu bane cikin zuciya,komai tsaurin gaskiya ko dacinta sai ya fadeta,tabbas mustaphan bashi da laifi cikin maganarlaifinshi daya tun fari a haka ya tarbiyyanci matarsa,amma kowanne magidanci zaiso kasancewa da iyalinshi,bawai kowannansu da inda ya sanya kanshi ba sannan ace wai a haka za'a rayu,tausayinshi ya kama shi,yana jin wannan karon ya kamata yayi wani hobbasa cikin rayuwar yaron nashi "Baka kyauta ba mustapha" maganar data sanyashi daga ido cikin mamaki ya tsare babaa da kallo,yayi zaton shine na farko da zai goya masa baya?,ya zaci shima yasan ba haka rayuwar ma'aurata take ba "Tun farko haka ka dora bigiren rayuwarku kai da ita,ka manta ice tun yana danye ake tanqwarashi,basai ya bushe ba sannan kace zaka tanqwarashi" kai su'adah ke kadawa cike da jin dadi tare da alamun samun nasara cikin zancan baban ba tare data fuskanci dungun dake cikin maganar ba "Mustapha,komai ya kusa qarewa,ka qyale matarka ta kammala karatunta a inda ta fara,shekara guda ya rage mata ta kammala,idan yaso koma meyw zai biyi baya sai ka zauna ku yanke" shiru ne ya ratsa falon,kowa da abinda yake saqawa cikin zuciyarshi,zuciyar su'adah ciki fal da fatan samun nasara. Bayajin a duniya akwai wani umarni da baban zai bashi ya tsallakeshi,ya numfasa a hankali sannan ya furta "Na barta baabaa" "Yes dad,thank you" sa'adah ta fada cikin daga murya,murmushi ya subucewa baabaan,addu'a yaje da fatan saisaituwar halayen su'adah ko kyakkyawar rayuwa zata samu ga diyansa,miqewa tayi cikin farinciki ta fice,fes taje jin ranta,don ta mustapha tana tunanin tasan yadda zata shawo kansa,don ko kadan bata jin zata iya tabbata cikin nijeria tayi rayuwa a cikinta. Fitarta sukayi kacibus da su amira na niyyar shigowa,babu wanda ta kalla cikinsu tayi gaba abinta,yayin da eesha ta bita da harara kamar idanuwanta zai fado,babu wanda ta tsana a duniyarta sama da su'adah din,tana ganin baki daya ta kanainaye rayuwar mustapha,ta hanashi duban kowacce mace da qima,bayan ita din ba wata uwa take tsinanawa gareshi ba,abinda bata sani ba,abun a jininsa yake,tsaki ta ja wanda ya sanya amira waiwaya ta dubeta,tasan meke kai kawo a zuciyarta,saidai koma mene bata fatan Allah ya ida nufi,don qwaryar sama ke dukan ta qasa,banbancin ita da itan kadan ne. Bayan sallama da tayi ganinsa shine abu na biyu daya biyo baya bayan shigowarta falon,nutsuwarta yaji na nemam gushewa "Bafa mukhtar bane,ba kuma zai taba zama mukhtar ba" wannan shine kalaman sa suka dawo mata cikin kwanyarta,sai ta lumshe ido taja dogon numfashi kafin ta ajiye nunfashi ta kuma daidaita nutsuwarta. Fuskarsa dauke da fara'a yake dubansu "Mommies dina ne da kuma mai sunan uwar mumunai" ya furta cikin fara'a,su dinma fuskarsu washe take suka samu waje gefe da shi suka zauna,yayin da eesha tafi daura da mustapha,satar kallonshi take,baki daya man din ya sake tafiya da tunaninta, "Allah ka mallakamin shi" ta fada cikin zuciyarta tana lumshe idanuwa tana ci gaba da satar kallonshi,wanda sam shi baisan ma tana yi ba,abinda ke gabansa kawai shi ya dameshi,gaisuwansun ma bai dago kai ba bare ya gane su waye ya amsa musu baki daya kudin goro,ba haka eesha taso ba,gaida baabaa sukayi baki daya ya amsa cikin fara'a "Mutan kano,gaki ga mutuniyar dai,bata qyaleki ba,nan ta addabeni sai da na siya musu ticket ta taho" dariya suka dan saka baki dayansu. A hankali ya miqe yana shafa sumar kanshi,jin maganansu yake kamar a tsakiyan kanshi kasancewar bai son hayaniya,baabaan ya fuskanci me yake son fadi,saboda haka yace "Shikenan,kana iya tafiya" juyawa yai a hankali ya fice a falon fuska a daure kamar ko yaushe,eesha ji take kamar ta bishi ta rungumeshi,saboda yadda kullum kwanan duniya yake sake tafiya da ita,yayin da sumayya kanta ke qasa tana wasa da yatsunta zuciyarta na bugawa,amira ta bishi da kallo kamar yadda baaba shima ya bishi da kallo,shiru yaci gaba da ratsa falon har ya fice din sannan baabaa ya dauke idanuwansa daga kanshi ya maida kansu,ya dubi amira "Aishatu ta rakaki amira kuje ku amso min saqo wajen ummenku" "To abba" ta fada tana miqewa,tasan babanta sosai,hakan ya sanya bata ce sumayya ta taso na,tunda taga haka tasan akwai manufarsa na aikensu su biyu,baki daya taji wani nauyi ya sake kamata bayan fitar tasu,falon yayi shiru ta kasa motsawa sai kanta dake qasa har yanzu "Mamana,ki saki jiki mana,nima fa babanki ne ko ba haka bane" murmushi tayi "Haka ne abba" shiru ya sake ratsa falon na wasu sakanni kafin ta sake jin muryarsa "Mama na,wata alfarma nakeson na roqeki,saidai ina jin nauyin haka" mamaki ya kamata,ita din wace?,wacce alfarma babban mutum kamar baabaa prof din zai nema daga gareta,bayan ita din ba kowa bace,bata kuma mallaki komai ba "Baabaa,yanzu kace kai abbana ne,kuma na yarda haka ne,me yasa uba zaiji nauyin bawa diyarsa umarni" sosai wani irin qima da darajarta ya qaru a idanuwanshi,ya jima baiga nutsuwa da hankali tattare da yarinya mai makamancin shekaru irin nata ba,nutsuwarta da kaifin hankalinta shine abu na farko daya fara bashi mamaki tattare da ita,tana da wani irin dattako kunya nutsuwa da ganin darajar manya,wanda zaiyi wuya a wannan zamani ka samu mace kamarta da wannan qualities din "Allah yayi miki albarka maman,haqiqa iyayenki sunyi nasara wajen tarbiyyarki,sun rabauta da diya ta qwarai,mamana.....kinga yayankun nan da ya fice yanzu?" Gabanta ya buga,sai ta kasa daga kai ta kalli baabaan,Allah yasa ba wani sharrin yayi mata wajen baban ba,kai kawai ta kada "Mamana,zaki taimaka min ki taimaka masa wajen inganta rayuwarsa?" Duburburcewa tunanunta yayi,sam bata gano me baban ke nufi ba,inganta rayuwarsa kamar yaya,ya manta bata da komai ne qarqashin wasu take itama,duk yadda taso ta fassara maganar tsakaninta da qwaqwalwarta ta gaza gano ainihin ma'anar maganar,har rudun hakan ya bayyana saman fuskarta. Murmushi baaban ya saki,ya yadda har yau ita dinma akwai sauran quruciya tattare da ita,baison rudata,saboda haka yace "Baki fahimci baaba ko,shikenan,tashi kije kuci gaba da sabgoginku,idan kika fahimci ma'anar maganar ina son ganinki a lokacin,amma fa kada ki zurfafa tunani,kune qawayen amarya,kusha bikinku kinji mamana,Allah yayi miki albarka" "Amin baabaa,na gode" ta fada tana miqewa,hakanan taji jikinta yayi wani mugun sanyi,rashin jin dadin kasa fahintar maganar baban ce har ya dago haka ko kuwa mene?. Naso yafi haka but am busy fans. #mrs muhammad ce *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [23/02, 11:51] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 7⃣1⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* Allah S W T yana cewa *"DUK INDA KUKE SAI MUTUWA TA RUSKEKU"* Allah kasa mu cika da imani ____________________________________      Qarfe biyar na yammacin ranar baki daya gidan ya sake dinkewa da jama'a saboda shirin fara gabatar da kamun amarya,sumayya na tare da amiran duk inda ta sanya qafarta sai ta janyota,kamar yanzu da suke can uwar dakan anty maamaa suna shiryawa,daga sumayyan sai amira sai humaida da humaira,amiran akewa kwalliya an kusa kammala mata,tayi kyau qwarai da gaske cikin wani irin yadin saqi na fulani mai azqbar kyau da daukan hankali,saqin fulani je wanda aka zamanantar da shi da kayan ado dana qawa,maroon ne sosai da yarfin kwalliyar golden a jiki,walwali kawai take zubawa,ta lura da yadda sumayyan ke yawaita shiru,saka bakinta cikim hirarta yayu qaranci sosai,hannu ta sanya ta tabota,ta daga kai ta dubeta tana murmushi,da hannu ta yi mata alamar lafiya,sai kawai ta girgiza kai ba tare data ce komai ba,duk yadda taso barin zancan da baabaa yayi mata abun yaqi barin kwanyarta,zuciyarta ta nace da son gano ainihin me maganar tashi ke nufi "An gama min,saura ke" inji amira tana isa bakin mudubi tana duba kwalliyar tata,kai ta kada "Powder kawai za'a shafa min a jamin jagira sun isa" idanu amira ga watso mata "Bazaiyiwu ba wallahi,kina babbar qawar amarya?" "Ki barni ayimin hakan don Allah,naga dai yau aka fara abin nan ko?,gaba a yimin" ta fada tana zama gaban mai kwalliyat,dariya humaida ta saka,yanayi da halayen sumayyan ke qara bata sha'awa,sam bata da rawar kai ko iyayi irin na 'yammata.        Duk da cewa ba wani kwalliyar azo a gani aka mata ba amma tashi daya ta sauya,tayi wani sihirtaccen kyau mai sanyi wanda babu hayaniya a cikinshi,su kansu sai da suka yaba,biyar da kwata kiran ango saifudden ya shigo wayarta,yake sanar mata sun iso,da yake tare za'a kama su shi da ita,falon anty maamaan suka sauko sannan suka hadu sa sauran qawaye da 'yan uwa suka fito.        Qyashi da hassada fal ran eesha,duk yadda taso taga ta wuce sumayyan a kwalliya abun yacu tura,ira kadai ta tsone mata duk taton 'yammatan nan,saboda kaf cikinsu bata ga wadda tayi ya kyawunta ba,duk da yake akwai wadanda suka saka suturar da suka fi nata kayan qaawa da tsada,amma ba'a nan take ba wai aj dannewa bodari kai,abinda bata sani ba baki daya sumayyan jinta take a wani mugun takure,karo na farko a rayuwarta data taba shiga makamanciyar wannan,qememe amira ta hanata sanya mayafi sai ratayashi kawai tayi gefan kafadarta guda daya,kayan sunyi masifar amsarta kamar wanda ya saqa su ya saqasu ne musamman saboda ita,takalmin ne kawai ya gagareta tafiya,subaleshi tayi ta nemi plat cikin na amiran ta saka,a ranar tayi adon gashinta wanda yasha gyara aka fito mata da shi cikin daurinta sai sheqi sa walwali yake,ta saje cikin 'yammatan amaryar har ta zama kamar wata fitila ta daban cikinsu.         Bata gane wautar data tafka ba sai bayan da suka iso gurin taron,wanda a cikin gidan aka shirya kujeru rumfuna da decoration na alfarma da kece raini,saika rantse da Allah wani event center ne mai tsada aka kama,ita ke riqe da amiran amma sai ta kusa faduwa saboda yadda idanuwa suka mata caaa,idanunta ta lumshe tana kiran sunayen Allah,ko ina abokan ango ne gogaggu kuma wayayyu tsaitsaye suna jira a qaraso musu da amaryar,hannun anty huda ta danqa ta sannan ta juya har tana hardewa saboda ido ta juya,su'adah na tsaye gefan huda din,india ta tafi baki daya,sari ne a jikinta wanda ya amsa sunansa,sak irin dinki 'yan qasar hindun ne jikinya skert da 'yar fingilar riga,sai mayafin kayan a jikin skert din ta nannade jikinta,yayin da kanta ke a bude kamar nasu,sai gashin dokin da aka dinkeshi da ainihin nata ya tashi tamkar nata,ta rabashi kafadar hagu da dama kakar yadda 'yan qasar hindun keyi.      Tana juyawa suka ci karo da anty farida umman husna,bakinta a washe take duban sumayya "Wai wai,kunyi wuyar gani,ko diyarki baku hadu ba" murmushi sosai kan fuskarta cikin girmamawa ta gaida anty farida sanan ta wuce ummee dake cikin gida bata fito ba ta aikota wajen amiran.        Wayarta dake hannunta ta dauki vibration sanda amarya ta samu zama a gurbinta ita da angonta,sunan nafisa ta gani,mamaki ya cikata ganin number dinta ce ta nijeria,qarar lasifiqan wajen bazai barta taji ba,hakan ya sanya ta soma takawa don barin wajen tana duban kiran,can baya inda zata iya jin ta ta tsaya ta soma lalubarta saboda kiran ya riga da ya katse "Am at home sisi" idanu ta fiddo waje "Da gaske?" "Suprise wlh naso baki,shigo gidan anty ki shigo dani yau traditional setting na amira ina lissafe dama" "Wayyo sis,gani nan" ta fada cikin zumudi da murna ta kashe wayar,daidai sanda kida ya soma tashi daga inda ake gabatar da bikin,tsalle ta dan saki kadan farinciki fak ranta "Yi a hankali gimbiya kada ki fadi ki batan kwalliyar" abinda taji an ambata kenan,da sauri ta waiwayo,alqasim ne tsaye sanye da shadda ya kawo hula gaban goshinsa yana qare mata kallo yana murmushi,daidaita natsuwarta tayi sannan ta juya da niyyar ci gaba da tafiya,saurin shan gabanta yayi,ya wani karyar da kai "Haba sumayya,ko gaisawa i kya tsaya muyi ko?" shiru tayi tana dubansa ba tare data ce komai ba,ji take kawai zai bata mata lokaci ne,bata da buqatar wani abu a yanzu,tana cewa ta gama da babinsa,tunda tuni ta gaya masa ita din ba budurwa bace bare ya saka ran zata biye masa,idanunta tarufe tare da yin banza da shi,tana jinshi yana magana ci kanka bata ce masa ba.        Tunda suka fara tashin kidan ya tashi ya shiga bathroom ya sake wanka,jin kidan yake kamar a tsakiyar kanshi,duk wani abu da zai zama tamkar hayaniya bai qaunarsa,ko qwaqwaran motsi ne ya fiya yawa yanzun zai dameshi,sau tari babban wansi adam kance "Kai ko mustapha kamar mai aljanu,koyaya motsi yake sai ya dameka" amma hakan bai rasa nasaba da ciwon kan da yake fama da shi tsawon shekaru,wanda idan ya tayar masa baya masa ta dadi.          Ta baya yabi don bai muradin haduwa da kowa bare a tsaidashi a cikashi da suruti,baki daya yau zucuyarsa a quntace take,saidai ko kai daka sanshi baka isa ka fadi hakan ba,sakamakon yadda ko yaushe haka fuskarsa take a daure koda cikin farinciki yake indai ba girmama farincinkin yayi ba shine zaka ga fuskar ta sake washewa fiye da yadda take da,yatsanshi saqale yake da maqullin motar da yake sha'awar fita cikinta,tun kafin ya shiga wankan ya turawa P.A dinsa ya shirya haduwarsa da mutanen da yace jiya bazai samu damar ganinsu ba qasa da awa daya yana hanya kada su wuce haka,sannan ya turawa driver dinsa shima ya shirya motar da zai fita,kanshi a qasa yake takowa cikin shigarsa ta qa'ida trouser da t.shirt v neck wanda ta fidda structure ta jikinsa sosai,kwata kwata saka manyan kaya bai cikin tsarinshi,duk wanda yasan mustapha cikin duniyarsa yasan ba ma'abocin sanya manyan kaya bane,kana iya gama mu'amalarka kaf da shi baka ganshi da manyan kaya ba,daidai gun da jiya suka zauna wasa ya tuna,yaron ya fado masa,ya tuna shegen wayonsa,wani qaramin murmishi da bai shirya masa ba ya kubce masa,a hankali ya daga kanshi sai ya hangosu,tsaye yake a gabanta yayi kane kane kamar zai hade gaf din dake tsakaninsu,yayin da take tsaye hannayenta harde a qirji tana dubanshi,rashi ya baci,dan salaman da ya samu ta gushe,yana daya daga cikin abinda yasa kenan baison baqin 'yammatan cikin gidansu,yana zaton daga daga cikin 'yan matan family din nasu ne,sauya akalar tafiyar tasa yayi zuwa wajen,sai da yaje dab ya lura alqasim ne "Itakam haka take,gobe wancan mutumin jibi wannan?" Ya qarasa bayansu,daidai sanda take fadin "Na riga na gama magana da kai ko?,ba zaka taba samun abinda kake so ba,so don Allah ka qyale rayuwata" ta kammala fadi sannan ta juya a hankali ta soma barin wajen,burinta kawai ta isa ga nafisan gashi ya bata mata rai da lokaci baki daya,binta yayi da kallo har sai data bacewa ganinsa sannan ya juyo yana sakin ajiyar zuciya,sai suka hada idanuwa da mustaphan yana kallonshi,kunya ta kamashi,yana bala'in ganin girman almustapha da mutuncinsa,girmama shi yake qwarai da gaske,ya dan diririce yana fadin "Barka da fitowa yaya" bai amsa ba ya qara taku zuwa inda yake yana dubanshi,haushi yakeji,hashi ya kamashi,ji yake kamar shi akawa haka "Kan me ka tsaya mace na gaya maka irin wannan maganar ibrahim?,kai namiji ne ka manta?,so kayi maintaining dignity dinka,akwai mata da yawa a gari ka zabi wata mana,kar ka cusa kanka inda ba'a sonka,ba'a so dole,i hope ka fahimta?,ba ita daya bace mace akwaisu da yawan gaske" kai ya rusuna yana gyadashi alamun gamsuwa,cikin zuciyarshi yana cewa "Ya mustapha kai baka hango abinda na hango ba,baka hango personalityn dana gani tattare da ita ba,hmmmm ke ka ganin so wani abu mai sauqi ne tunda kullum cikin neman son ake a wajenka"amma a fili sai yace "na gode,Allah ya qara girma" kai ya jinjina ba tare da yace komai ba ya juya ya bar wajen.       Kamar ta goya nafisa haka taji lokacin data ganta,tayi ado sosai tana rungume da khalid,ta amshi khalid din kai tsaye suka koma wajen da ake kamu,sanda suka je tuni al'amura sun fara nisa,bayan gabatar da abubuwan da suka dace sannan aka kama amira kafin daga bisani a bada damar yiwa amarya da ango liqi,basu suka tashi daga kamun ba sai qarfe takwas na dare,kamu ya qayatar matuqa da gaske,tafiya nafisa tayi bayan sun gaisa da amira sama sama,taso riqeta tace a'ah tayi haquri abban khalid din ya iso,saidai zata zo dinner insha Allah wanda za'ayi ranar alhamis.        Washegari akayi arabian night wanda aka gabatar da ita itama cikin gidan baabaa prof,gidane gari guda hakan ya sanya basu da damuwar sai sun kama waje,ba qaramin qawata wajen akayi da kayan ado ba,ranar duk wani ahali da ya shafi baabaa prof sanye yake da abaya ta mata,maza kuma doguwar riga ce da hirami,kai ka rantse a ranar baqin larabawa aka yi a unguwar.  ******* ****** ********      Washegari tana kwance tana baccin gajiya,kasancewar alhamis ce ranar babu event din da za'a yi sai gobe idan Allah ya kaimu,ji tayi an daka mata duka,tilas ta farka tana mutstsike idanu,amira ce zaune gefanta "Sannu,ai wallahi bacci bai ganki ba bai kuma kamaki ba,qarfe hudu zamu lunching na maman saifullahi,kuma ba kowa ne zashi ba,bamu da yawa" zama tayi sosai tana hamma hannunta kan bakinta "Shine zaki dakamin wannan dukan,badon inajin kunyar idanun saifullahi ba sai na rama" dariya ta qyalqyale da ita "Ato bismillah,ni kinga ina da mai ramamin,ke kuwa nasan ko na dakeki na daki banza,waccan mutumin da na gani a kano babu abinda zaya iya" ta sani sarai da abdur rahman take,bata san meye hadinta dashi ba data saka masa tsama haka da yawa,harara ta jefa mata sannan ya shiga bandaki ta wanke bakinta ta dawo ta amshi katin tana dubawa,komai a tsare yake harda dress code na maza da mata,mata shigan baqi zasuyi maza shigan fari.         Kusan baki daya kayanta sai data baje su saman gado,ta rasa wanda zata zaba,a haka anty dije ta cimmata,dariya ta dinga yi mata "Ato wallahi gwara ki qure adaka,don suma dangin saifullahin ba baya bane"sai data gama ruwan idonta sannan ta zabi wani shegen lace a cikin kayan wanda yake baqi ne an masa adon ja mai daukar idanuwa,zuba kayan tayi a jaka don ta nufi gidan baabaa don amira na can na jira,sanda ta isa an gama mata kwalliya,tayi masifar kyau cikin baqar wedding gown,sumayyan zama tayi itama aka soma yi mata tata.          Wani irin sihirtaccen kyau ke fita daga kwalliyarta hadi da tsumammen qamshi,kunya ta kamata da mamakin kanta,riga da skert ne wanda suka fitar da baki daya qirarta gaba da baya " wow"abinda amira ta dinga fada kenan tana qarewa sumayya kalo "Haka baqin kaya ke miki kyau amiran umman khalipha?,ya Allah" kai ta kada "Ai kam cire kayan nan ya zamemin wajibi,ina zan iya fita cikin jama'a haka amira" ta fada tana yunqurin cire daurin dankwalin da aka bata lokaci ana mata shi,da sauri amiran ta riqe hannunta tayi kicin kicin da fuska "Allah idan kika cire sai mun bata,ke komai ma bakison ya miki kyau,kina da kyau kina da aji kina da isar da za'a dama dake,kibar yin haka don Allah" yanayin yadda tayi maganar ta bata dariya,sai ta zame hannunta tana hada mata kayayyakinta data yi amfani da su kasancewar yau cikin dakinta ta shirya "Bari na maida su sashin anty maamaan ko" "Godiya namescy na" murmushi tayi ta fice a dakin.        A shirye ta tadda anty mamman,kasancewar ita zata yiwa amiran rakiya,wani irin biki suke a tsarin familynsu,suna gayyatar amarya ne da manyan yayyenta da iyayenta,inda zasu kawo musu ita suyi mata nasu bikin ma musamman haka sukeyi,ta ajjiye kayan tana saukowa suka sake kacibus da anty maamaa wadda ke kai kawon hadawa baabaa kunun alkama,haka matan suke,duk rintsi basa wasa da cikin mijinsu "Amiran umman khalipha zo don Allah ki kulamin da kunun nan in qarasa hadawa babanku hadin salad din nan"aladabce ta asawa ta bita kitchen din,cikin sauri sauri take hada komai saboda lokacin tafiya yayi,sau uku amira na aikowa sumayyan tazo su tafi,antyn bata sani ba,sai ana hudu taji aiken da ake mata ta dubeta "Jeki amira,na qarasa na biyoku daga baya" murmushi tayi tana noqe kafada "A'ah anty suje kawai,ma taho".      Cikin mintuna talatin suka gama,babu abinda jikinta yayi,saboda haka goge hannunta kawai tayi,sannan ta fidda kwalakcarta ta goga a hannayenta,ta sake shafe jikinta da turaren humrarta mai fidda wani sihirtaccen qamshi,wayarta dake ruri anty maman ta daga ta kara a kunnenta sannan tace "Eh na gama,gani nan" ta dubi sumayya tana maqala kyakkyawar jakarta "Muje ko amira" ta amsa.        Tuni maman ta rigata yin gaba saboda hill shoes din dake qafarta wanda ya sake sauya yanayin tafiyarta,sannu a hankali take takawa,sai ka dauka wani salon tafiya ce ta daban,koko tsabar yanga ce da iyayi ga wanda baisan takalmin ne ya takurata ba,baqar rantsatstsiyar mota ce wadda har sheqi take da daukan ido saboda tsabar sabunta da kyau,ita daya ta rage tsaye a wajen,da alamu dukka an tafi,baya anty mamaan ta bude ta shiga,yayi kyau cikin farin qal din trouser da lallausar short sleeve t.shirt baqa mai adon fari a jiki,wadda ta fidda sirrin hannunshi na tarin gargasa wadda ta kwanta har saman tafin hannunshi,da wani sashi na murdadden dantsensa wanda kana gani kasan ya saba daga qarfe,daya daga cikin abinda ya sanya kenan bai fiya saka kaya masu gajeran hannu ba,black hight top snickers ne a qafarsa,tsintsiyar hannunshi daure da agogon fata na kamfanin gucci mai matuqar tsada da kyau,yadda jikinsa ke fidda wani sihirtaccen qamshin wani turare da mawuyacine ka gane wani iri ne haka motar ki fidda sanyayyan qamshin freshner,komai nasa mai kyau tsafta da aji ne,jin yana niyyar tayarwa ya sanya tace "Tsaya,akwai mutum daya" a kasalance ya kashe motar,ka kadan baison tuqi da kanshi idan ba kamawa tayi ba kamar irin hakan,qarasowa tayi tana niyyar bude bayan anty maamaa tace "Koma gaba amira" don tasan halinshi sarai,ya tsani ya dauko mutane su shiga baya baki dayansu,yana alaqanta hakan da sai driver,jin an ambaci sunan amira ya sanyashi juyowa,daidai sanda take daidaita zamanta gaban motar suka hada idanu,idanuwanta suka fada cikin nashi,tashin farko kowanne ya janye idanunshi,qirjinta na bugawa,qamshin turarenshi na ratsa qofofin hancinta,idanunta ta ragewa girma tana duban gaban motar,tana ji kamar ta zura da gudu ta bar motar,wani dabaibayi taji na daureta,kwarjininsa ya mata yawa,tana jin zamanta a bigiren bai dace ba,a kasalance ta sanya hannu zata rufe murfin motar taji kamar muryar laila na kiran sunanta,itace tafe riqe da hannun abdallah da yayi kyau cikin baqaqen suit na yara,sai baqin sau ciki na yara da baqar safa baki daya,suka qaraso bakin motar inda take zaune "Anty,mami tace na kawo miki shi,kuka ya soma yaqi zama" dubanshi tayi cikin sigar lallashi "Abdallah,ina cewa na gaya maka tun dazun bazanje da kai ba,ka koma gida ka zauna da su laila,yanzu zan dawo bazan jima ba" qafafunshi ya sa bubbugawa yana sakin kuka sosai kamar wanda ake yanka yana fadin "Allah ni sai naje" ranta ya baci ganin yadda yake tsala kuka kamar tayi mishi wata uwa,sake lallaminshi tayi baiji na,maimakon haka ma sai ya buge hannun laila ya taho inda take ya shigo sit din da take,abinda bai taba yi ba kenan,yana qarasowa kuwa ta daga hannu ta kai masa mari,ta kuwa sameshi gefan fuskarshi,kafin anty maama ta furta maganar daga bude baki zata yi wata tsawa ta karade motar,tuni laila ta ja baya a tsorace,hannunshi ya miqo inda suke ya janyo abdallah wanda ke sakin kuka cikim jim zafin marin ya dorashi kan cinyarshi yana shafa inda ta mareshin "U r very stupid,how dare you zaki mari qaramin yaro har haka?,saboda bakisan ciwonshi ba?,bakisan ciwon haihuwa ba?,idan baki iya riqeshi mai ya sanya ba zaki sa a maidashi wajen mamarshi ba,fice min a mota!" ya fada cikin bacin rai da zafin rai,bata ankara ba taji hawaye sun soma layi bisa kuncinta,ji take kamar mukhtar ke mata fadan,me ya fusata ta ta mari abdallah itama bata sani ba,hannunta ta sanya kan mabudin motar ta tura da niyyar fita anty maamaa ta dakatar da ita "A'ah zauna,kuyi haquri mutapha,baki kyauta ba amiran umman khalipha,saurin hannu wa yaro bai kamata ba,ki kiyaye gaba" "To maamaa" ta fada ba don taso ba ta koma ta zauna,so tayi ta qyaleta ta fita,wani nauyi taji zuciyarta tayi,tana jin hucin numfashinsu su biyun.       Luf abdallah yayi kan cinyar mustapha wanda ya zaunar da shi suna facing juna ya rungumeshi cikin jikinshi yana ci gaba da shafa inda tayi marin,ci gaba da kallonshi abdallahn yayi,a hankali ya furta "Abba!" Sannan ya sake narkewa cikin jikinshi,wani nauyi zuciyarta ta sake yi,sai ta kasa daurewa ta sanya kanta a tsakiyar qafafunta,tausayin abdallahn yasake qara yawan hawayen dake fita a idanunta.         Bubbuga bayan abdallahn yaci gaba dayi kadan kadan har sai da yaji alamun ya huce,hannun ya sanya gefanshi ya ciro gorar ruwan da ya dauko da niyyar sha ya bude mishi ya saka mai a baki,sai da yasha sosai sannan ya rufe ya maidata gurbinta,ya sake zaro wayarsa ya latso wasu lambobi ya kara a kunnenshi yayi magana a taqaice "Eh,ka sameni gidan,ka tambaya adress din" ya katse kiran ya ajjiye,tada motar yayi sannan ya ya jata a sukwane abdallah na kwance jikinsa.         Shiru ne ya ratsa motar ba wanda ya sake magana,sumayya na kife har yanzu kan cinyarta tana qoqarin control din hawayenta,ambaton sunayen Allah ta dinga yi daya bayan daya har ta samu hawayen suka tsaya saidai bata iya dagowa ba har suka isa wajem,anty maamaa ce ta soma fita,tuni tayi gaba saboda suna isowa taji ana nemanta ta lasifiqar dake cikin wajen taron.        A hankali ta daga kanta ta gyara yafen mayafin dake kanta sannan ta bude murfin motar ta fice,ta gefan ido yake dubanta har ta bace a wajen,gajeran tsaki ya ja,yana jin bazai iya ci gaba da zama a wajen ba,daga yarin yayi ya dubeshi har ya soma bacci,sai yaji tausayinshi ya kamashu,haushinta ya sake qumeshi,cikin zuciyarshi ya dinga masifa shi kadai,bude motar yayi ya saba abdallah a kafadarsa suka koma sit din baya,kwantar da shi yayi sannan ya zauna gefansa.        Tana tsaye bakin get din gidan jingine jikin motarta hannunta harde a qirjinta,sam wajen bai dace sa tsarinta ba kasancewar a gargajiyance suka tsara komai,bugu da qari ranta a jagule yake,yadda almustapha ke ninka nuna hakin ko in kula da lamuranta,shigowar motar yaso ya dan ja hankalinta kadan,saboda irin motar mustaphan da take mutuwar so,wadda a yau ita taso hawa amma yaqi bata hadin kai,dauke kai tayi daga kallon motar don kada ta zubda ajinta,a dauka 'yar matsiyata ce kamar yadda take rayawa a ranta,ganin fitowar anty maamaa daga ciki shi ya sake maida hankalinta kan motar "Kada dai ace almustaphan ne?,yazo ya dauko maamaan a ciki amma ni ina matsayin matarsa ya watsan qasa a ido?" Take raya haka a ranta tana qarewa motar kallo,bata jin mustaphan ne,don tunda itama yaqi daukota ya kawota tabbas babu wanda zai kawo koda kuwa iyayenshi ne(a tunaninta),ita kanta motar bai taba hawanta ba sai yau,hakan yasa ta yin kwadayin ace ita ya fara dauka a ciki,mutum ce ita mai son taga tafi kowa,komai a gunta aka fara ganinsa,bata gama wannan tunanin ba sumayyan ta bude murfin motar itama ta fito cikin salon wata tafiya da zaka tsammaci ta yanga ce,saidai tsabar kasala quncin zuciya da tsinin takalminta ya haifarwa da mai kallonta ganin cewa yanga take kai tsaye,wani bala'i ne ya dirarwa zuciyarta,take ta tattara kallonta baki daya a wajen,ci gaba tayi da kallon sumayyan wadda sam hankalinta bai wajen taci gaba da yi har ta wuce,zuciyarta na tsaka da bata shawarar zuwa ta duba matuqin motar don tabbatar da cewa mustapha dinta ne cikin motar ko wani ne daban mai farcen susa ya yaci nasarar mallakar irin motar mijin mata,hutassheta akayi saboda fitowar da yayi ya koma gidan baya yana sabe da abdallah,ta gane yaron,yaron data cuccusawa zagi jiya da daddare saboda ya gyara mata gyaran alwalarta,huci ta soma fitarwa saboda wani zafi da taji qirjinta yana yi,me kenan?,me hakan ke nufi?,ba bata lokaci ta soma takawa zuwa bakin motar.       Bude murfin motar tayi sannan ta cusa kai cikin motar kai tsaye,hannunshi na saman kan abdallah yaji shigowarta,juyowa yayi ya dubeta sannan ya dauke kai yaci gaba da abinda yake kamar bai santa ba,ta sani sarai bazai tanka mata ba idan in zata shekara matuqar ba ita tayi magana ba,ko ita din tayi bata da tabbacin amsarsa "Tsakani da Allah ka kyauta kenan man,naci burin hawa motar nan ka watsan qasa a ido amma sai naga ka kawo wasu,har wata banza can ka baiwa damar zama gefanka wanda ni kadai ke da wannan matsayin?" Ta fada cikin son dai daita fushinta don kada ta fita daga hanya ta jawa kanta wani sabon lamarin,ta san duk sabida zancan qarasa karatunta ya sake zame mata wani badadde,ilai kuwa shiru ne ya biyo baya,kishin sumayya data gani yaci gaba da mintsinin zuciyarta "Wai shin ma meye alqarka da ita waccan yarinyar da har ta samu matsayin daukota cikin motar da koni ban taba shigarta ba,sannan ko kai kanka yau ka fara shigarta?" Bai da ko niyyan waiwayowa ya dubeta bare ta saka ran samun amsa,wayarsa ce tayi tsuwwa ya saka hannu inda ya ajjuyeta ya dauko yana dubawa tare da amsa kiran da ya shigo din "Bude ka shigo a bude take" ya gayawa drivern nasa a taqaice,dama shi yake jira,sauke wayar yayi still bai dubeta ba yace "Idan kin gama kina iya sauka ko?"wani abu ya tokare mata wuya,sai ta zuba ido tana kallonshi,sonshi kamar ta lasheshi,haushi kamar ta hafiyi zuciyarta,idanunta ya cika taf da qwalla,cikin rawar murya da son karya lagonsa da kuka ta soma cewa " ni kake ma haka mustapha?"hannu yayi saurin daga mata wanda dole ta shanye sauran maganarta,sai ta bude murfin ya fice da hanzari,budewa drivan yayi ya shiga cikin girmamawa ya russuna bayan ya zauna ya gaidashi,a taqaice ya amsa mishi,sai da ya tayar da motar suka bar layin suka hau kwalta sosai sannan cikin girmamawa yace da shi "Ranka ya dade ina zamuje?" "Maitama" ya bashi amsa a taqaice,baice komai ba ya qara gudun motar suka lula titi.          Sosai lunching din ya qayatar,ba qaramin qauna iyalin saifullahi suka nunawa amira ba,basu tashi ba sai qarfe bakwai na dare,wannan karon tare da su amiran suka koma,saidai ko kadan bata da walwala,a takure take jim zuciyarta baki daya,hatta da amiran ta lura,amma bata ce mata komai ba saboda ta tambayi anty mama abdallah taje gaya mata abinda ya faru,ana saukesu ta dubi amira "Kimin afuwa zan wuce gida sai gobe,kaina ke mij ciwo sosai" ba qarya take ba da gaske kan nata ciwo yake mata,sai ta daga kai "Na miki,Allah ya bada lafiya,ya tashemu lafiya" ta bude murfin motar ta fice.         Wanka ta fara yi sannan tayi sallolinta,anty dije tace mata ga abinci tace sai anjima,duka abinda take hankalinta bai wajen yana wajen abdallah,ina yake?,ina ya kai mata shi,tun tana kasa kunne da ido har ta kwanta saidai shiru kake ji,kasa haquri tayi ta miqe da hijabin sallarta ta qwanqwasa dakin anty dije ta mata izinin shiga,kwalliya ta tadda ta tanayi "Uhm,ya akai amara qirjin biki" murmushi ta danyi wanda yafi kama da yaqe "Anty wannan yayansu amiran ya amshi abdallah tun dazun,har yanzu ban ganshi ba bashi ba abdallahn" cikin ko in kula tace "Wa?,wai musty,kada ki damu kisa a ranki kamar kina tare da abdallah ne,ai mayen yara ne,indai mustapha ne a rina" hankalinta ya dan kwanta da jin hakan,sai ta koma daki tayi shirin kwanciya,don ita kadai take da buqata a yanzh,tun tana sauraren ta ina abdallahn zai shigo har bacci ya sureta.          Washe gari sam bata shiga gidan ba ma sai da yammaci tayi aka soma shirin tafiya dinner,nan ka bata ga abdallan ba,ba kuma wanda ya mata maganarsa,haka taci gaba da daurewa har sanda anty maamaa ta dan tsokaneta "Abdallah kam anyi wuyar gani anyi sabon daddy" murmushi kawai ta danyi ta basar.        Wani qayataccen event center suka kama,hmmm masu abu da abinsu,kada kaso kaga yadda gun ya qawatu yayi matuqar tsaru,ranar sumayya anyi abun gani,ita ta zauna mazaunin babbar qawar amarya,tayi komai yadda zata faranta ran amiran duk da a takure take matuqa,idanuwan maza bisa kanta sunyi yawa,kai har ma wasu daga cikin matan,sai da guri ya gama tumbatsa sannan su'adah ta iso,a nan tayi burgar data saba,tsakiyan abokan ango cikin dinkim riga da skert na wani shegen leshi mai azabar tsada wanda aka ci mutuncin tsadar tasa aka yi masa dinki na ganin dama,tsagar skert din har kusan gwiwarta,dinkin ya kamata dam,banda dankwalin da aka tsarawa dauri babu komai a kanta,don ko tuna sunan mayafi bata yi ba,liqi ta shiga yi da 'yan dubu dubu sabni kar wanda ita kanta bata san nawa ta barar ba,abin nema ya samu ta dauki idanuwan jama'a,ta kuma qona zukatan 'yan baqinciki wadanda bas son tarayyarta da mustapha,to su gani ya tsaya mata,sai data yi mai isarta sannan ta sauka daga step din ta koma mazauninta. Sai sha daya na dare aka tashi kowa ya koma inda ya fito. *******    *******    ******         Tun qarfe goma na safe layin nasu ya tumbatsa ya dinke da jama'a kasancewar goma da rabi ne daurin auren,bacci ranar tayi sosai dakin anty dije,bata tashi farkawa ba sai qarfe tara da rabi na safe,tarin missed call ta taras duka na amira,da hanzari ta miqe ta fada toilet tayi wanka,a gurguje ta fito ta shirya cikim shaddar da sukayi anko wadda tayi masifar haduwa,kamar yadda dinkin doguwar rigar ya dace da jikinta,komai da tayi amfani da shi kalar zaren da akayi aikin shaddar da shi ne,ta fito fes mashaAllah,daidai sanda laila ta shigo,baki ta sake tana kallon sumayyan,ta qaraso dakin ta samu bakin gado ta zauna "Wai dama don Allah anty sumayya haka kike da kyau" dariya yarinyar ta bata saboda bihaqqi ta fada "Sai an tambayo" ta fadi hankalinta ka can gidan baba,saboda hayaniyar data dinga jiyowa na tashi ta tabbatar layin yayi tumbatsar da babu damar ta fita,valcony din saman benan anty dije ta bude ta fita ciki,layin ya shaqara da mutane ya cika masha Allah,kai ta dinga kadawa don tasan dole ta haqura har sai an ragu. Kujeta ta ja ta zauna daga gefe yadda zata iya hango komai,ta bude wayarta ta soma lalubar lambar amira don ya bata uzurinta,hakanan taji yana yinta ya soma sauyawa kamar ba ita daya bace a gun,kamar fisgar mayen qarfe haka idanuwanta suka jata zuwa inda yake tsaye tsakiyan wasu zaratan samari kamarshi. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [23/02, 11:51] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 7⃣2⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *ALLAH YANA GAFARTAWA WANDA YASO YA KUMA AZABTAR DA WANDA YASO* YA ALLAH KA GAFARTA MANA ___________________________________ *TAB,BIGI SAI BIGI,BABBAN GORO SAI MAGOGIN QARFE,IDAN KAJI WANE BA BANZA BA,INA MA'ABOTA KARATUN LITATTAFAN HAUSA,KAMA DAGA NA QUNGIYAR HASKE HARMA WANDA BA NA HASKE BA,SHIN KUNA DA BUQATAR JIN WANI SABON KUNDI WANDA YA TATTARE LABARAI NAU'IN DABAN DABAN WADANDA SUKA SHAFI AL'AMURA NA ZAHIRI DAKE FARUWA CIKIN RAYUWARMU TA YAU DA KULLUM?.......TO MAZA KU GARZAYA KU NEMI LITTAFIN KUNDIN HASKE,WANDA KE QUNSHE DA LABARAI DAKE DAUKE DA NAU'IN RAYUWA IRI DABAN DABAN,LABARAI NE WANDA KE DAUKE DA DIMBIN DARUSSA MASU RATSA ZUKATA,DUMBIN ILIMI MAI JAWO HANKALIN DAN ADAM ZUWA SAKE LURA DA GYARAN RAYUWARSHI,MAZA KA/KI GARZAYA KADA A BAKI LABARI,BA SHAKKA ZA'A CI DA RABONKI MATAUQAR KIKA BARI YA WUCEKI,AKWAI SHI A WATSAPP DA APP DIN WATTPAD BAKI DAYA* *SADAUKARWAR WANNAN SHAFIN GA:* *SADIYA ZABURA* *UMMU RAMLAT* *MAMAN SAYYID* *DA MARUBUCIYA* *AYSHA DAN SABO* *RABBI YA BAR QAUNA*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽😍😍😍        Kyawawan idanuwanshi wanda suka wadatu da gashin idanu kamar yadda girarsa take masu kama da na wanda ke jin bacci suke kan ta,shi daya ne tak sanye cikin qananun kaya sabanin dukka sauran wadanda suke tsaye tare,baki dayansu shadda ce jikinsu dinkin tazarce kaloli daban daban,kusan tare suka janye idanuwansa,gabanta ya shiga faduwa,kasa zaman wajen tayi,batasan ana iya gajin mutum ba,gashi ko mayafi babu a jikinta,sai ta miqe jikinta na rawa gabanta na faduwa ta bar wajen,ta tura qofar ta kulle ta dawo cikin bedroom din anty dijen.       Gefan gado ta kwanta rub da ciki tana sauke numfashi,maganganun baabaa suka soma dawo mata,har yau ta kasa gane me yake nufi,tana da buqatar qarin bayani,tana buqatar taimako wajen wanu ko zata fahimci me yake nufi,amma ta taimaka masa wajen gyara rayuwarsa kamar yaya kenan,wanu mummunan abu yake mara kyau yakeso ta saka baki?,amma ita a wa?,bata da wannaj power din,ganin qwaqwalwarta na neman daurewa yasa ta kada kai tare da yin watsi da maganar,maimakon ci gaba da tunani sai ta sake daukan wayarta ta lalubi zainab ta kirata,din jiya suna wajen dinner taga misscall dinta baya kuma samu ta bita ba.         Bayan sun gama gaisawa da mama ta musu Allah ya sanya alkhairi zainab ta karba,nan take gaya mata jiya aka kawo lefe sati uku kuma aka sanya,murmushu sumayya ta saki tana tsokanarta "Kice mu fara shirin tahowa kano ko?" "Wallahi yaya,kizo ayi tsare tsare masu kyau" "Insha Allah,ina huce gajiyar wannan bikin zaki ganni,Allah ya nuna mana da rai da lafiya" "Amin yaya,ina abdallah na" "Uhmm,ni kaina bansan ina yake ba,yana gidan biki" "Ki gaisheshi tunda ya manta da mu" dariya ta danyi "Zaiji,ki gaidan halimaty,wayarta bata shiga" "Zata ji" suka katse wayar.        Tana sauke wayar ta jiyo muryar abdallah yana karadi daga qasa shi da sh hafiz,sauka tayi daga gadon ta sauko qasa,yayi masifar kyau cikin wata arniyar shadda ash wadda batasan inda ya samota ba,hulace kanshi zanna wanda sau faman zuba qyalli take,qafafunshi saye da takalmi sau ciki,abinka da uwa da da,yana ganinta ya tako da gudu ya daneta,murmushu tayi ta zube saman kujera yana faman zuba mata surutu da bata labari.         Ganin sha daya tayi ga gidan babu kowa sai ita ya sanyata yin shahada ta yafa mayafinta ta fito,kamar zata nutse haka ta dinga ratsa mutane a darare tana wucewa har ta kai ga cikin gidan bayan ta kira humaida ta gaya mata inda suke,ko ina harabar gidan 'yan uwa da abokan arziqi ke kai kawo,kowa ka ganshi cikin kwalliya da walwala,daga gefe guda ta hango mahmoud da tarin abokansu ciki har da alqasim,suma sun ganta saboda haka ta qara sauri don kada su rusketa.        Batayi aune ba sukayi karo kanta ya daki qirjinsa,tayi taga taga ta komo ta fada qirjinsa,zuciyarta kamar zata fito saboda tsoro,tayi yunqurin janyewa,ta samu nasara saidai hannunta na cikin nashi hannun yana duban qwayar idanuwanta,sai yanzu ya samu amsar inda ya samu qamshin da ya buwayeshi tun shekaran jiya,wanda har kuka su'adah tayi sabida jin qamshin,don ta tabbatar hadin humra ce ta mata ta musamman ba turaren namiji bane,gaba ta tusashu tana tambayarsa ina ya samu turaren,baki daya zuciyarta ta gama zayyana mata yana neman wata ne,idan banda haka ina zai samo turaren mace a hannunshi?baya ga haka ta lura wannan karon sam baya marmarinta,baya nemanta idan ba ita ta buqata ba,bayan a baya ta sani cewa duk sanda suka hadu har sai ta gaji ta hada kayanta ta gudu yake qyaleta,amma wannan karon sam ba haka bane,yana jinta yayi mata banza ya gama shirin baccinsa ya kwanta tare sa juya mata baya,don bashi da amsar bata,shi kansa yana jin qamshin cikin hancinsa amma baisan inda ya sameshi ba,baijin zai iya bata lokacinsa ya mata wannan bayanin tunda har tana zarginsa,to ta dauki duj hukuncin da take gani zata iya dauka,hakan ya sake hassala zuciyarta,itama ta shiga fushi da shi gadan gadan miqe ta fice ta sauya dakin kwana,bata san cewa ba shi ta yiwa ba kanta ta yiwa,tunda ba yau farau ba da yake kwana shi daya tamkar gauro,idan da sabo ai ya saba.        So take ya sakar mata hannu ko don idanuwan mutane da ke kai kawo a wajen,uwa uba ga haramci na riqe mata hannu da yayi,tayi yunqurin zame hannun nata amma abu yaci tura yana tsaye qyam yana dubanta,babban goro sai magogin qarfe,ya kusa lullube tsahonta baki daya,dududun nata tsawon bata fi iya qirjinsa ba,ga wani kwarjini daya cika wajen,ganin masu wucewa sun soma ankara ya sanyata cewa "Ka sakar min hannu" cikin izza da motsa labbansa "Saikin gayan abinda ke baki tsoro,me ya koroki bayan kowa na kai kawo a nutse amma banda ke?" Daga fararen idanunta tayi ta watsa mishi su,duk da yadda qirjinta ke bugawa,lumshe idonsa yayi ya bude ya janye nashi idanun daga kallonta,bai taba ganin mace mai farin qwayar idanu ba kamar haka ya raya a ransa,tsaki yaja a fili sannan ya saki hannun nata "Ki kula next time,ban son irin wannan shirmen" ya fada yana duban gefanta,ita ke shirmen ma?,abun ya bata haushi,sai ta banka masa harara ta gefan ido duk da yadda gabanta ke faduwa qasa qasa tace "Kaima sai ka kula tunda kana da idanu ai ba ni kadai ke da idanuwa ba" batasan tayi kuskure ba saboda kaifin ji da Allah ya hore mishi,ko yaya magana take yana iya jiyota,yana daya daga cikin wadanda Allah ya yiwa baiwar ji,har wani lokaci ba'a iya gulmarsa matuqar yana cikin gidan,har yayi gaba ya juyo a mamakance yana dubanta,karo na farko kenan da wata 'ya ta taba maida masa magana,bakinta ta murguda duk don ta sake bashi haushi tayi gaba abinta,wani abu ya tsaya mishi a rai,ranshi ya baci,yau shi akewa rashin kunya?,abinda yafi tsana kenan a rayuwarsa tun lokacin quruciya,abinda ya fara hadashi kenan da su'adah tun tana qaramarsa,lallai zaiyi maganinta,wace ita da har take jin karanta ya kai tsaiko,babu shakka sai ya hukuntata.       A bangaren anty maamaa ta tadda su,tana zaune tsakiyar yayunta anty farida da anty huda da matan yayyen ta ni'imah da fahariyya,sai qawayenta da cousins dinta irinsu eesha humaida ummu salma da sauransu,a hankali ta qaraso saboda lasalar da take ji cikin jikinta tana karbar saqon harara daga amira,duk da haka murmushi ne kan fuskarta,ta riga da ta sani itace mai laifi,sauran da suka san mekw faruwa dariya suka dunga yi sunsan za'a kwashi daramer,amma sai sumayya ta kashe mata gwiwa da fadin "Ta zama ta saifullahi,ayya yarinya zata bar gida" ai kuwa sai ta soma qwalla,tana dariya ciki ciki ta qaraso ta zauna gefanta ra mata rada a kunne ma tsawon minti biyu,sau gani sukayi ta saki dariya tana share hawayen,huda ce taja tsaki "Au qaryar banza,dama fa son aurenta take 'yar banza bansani bane,saifullahin da ake ji da shi kamar a lashe mishi mazaunai" dariya ta kamasu baki daya,dqi dai da dai dai sumayya ta bi ta gaida kowa,batasan matan yaya adam ba sai lokacin ni'imah da fahariyya,fahariyya ita ta fara tahowa ni'imah ta jira maigidan sai jiya suka taho tare da daddare,bata ga fahariyyan ba saboda 'yar jin kaice itama kamar yadda amira ke gaya mata,ni'imah din ce babu ruwanga,hakanan take haquri da halayyar fahariyya na goranta mata da take lokaci lokaci akan rashin haihuwa,saidai zaman nasu babu yabi ba fallasa,rashin mutuncin fahariyyar da sauqi sakamakon cewa adam din tsayayyen namiji ne,bai yarda a wulaqanta masa uwar gida ba,sam basa shiri da su'adah da fahariyya saboda kowacce na jin kanta da jin cewa ta isa saidai daya tabi daya,duk da a zahiri duk cikin yaran gidan babu wanda ke da dukiyat almustapha,wannan ya qara kishin su'ad cikin zuciyar fahariyya,itakam ni'imah 'yar babu ruwa na ce,ta kama mutuncin kanta,don iyayenta ba wasu bane rufin asirin Allah ke garesu,sai a yanzu da tayi dace da miji na qwarai suke samun sauyin rayuwa sanadiyyarsa,duk da haka dama tana da managartan halaye wadanda su suka fusgi adam zuwa gareta,duk da tarin yaran masu kudi dake sonshi a lokacin,ta kasance ta daban a gunsa har a yanzun duk da bata taba haihuwa da shu ba,sakamakon haquri biyayya da tsantsar iya zamantakewa da miji mai tafiyar da hankali.         Da daidai suka miqe suka fice ya rage saga sumayyan sai anty ni'imah sai humaida,suma sun maqale ne saboda suna kwasar wasu sirrika da lacture da anty ni'iman ke bawa amira,wanda baga fara ba sai bayan da wadancan suka fita,ba amira ba hatta su sumayya sun qaru da ita sosai,a nan suka zauna suka ci gaba da hirarsu,ni'imah ba dai sauqin kai ba,kamar qannenta haka ta daukesu,aqalla zata girme musu da kusan shekaru goma,amma sam hakan bai wani nuna ba sosai sabida tsabar gayu.       Qarfe bakwai na magariba aka tafi kai amarya,babu wani takura ko neman mota kasancewar kusan kowa ya mallaki motar hawanshi,wanda ya taho daga wani garin ne bai taho da abun hawanshi ba sukayi amfani da motocin gidan baabaa,ga kuma ta familyn saifullahi.        Ba shakka wannan shi ake kira qwarya tabi qwarya,ba shakka amiran ta shiga gidan da yayi dai dai da ita,gidane na alfarma wanda ke tafiya da tunanin mai tunani,sanda aka fara tafiya amiran ta riqe sumayya gam kan sai ta jira anzo an sayi baki,sun riga da sun gama tsarawa babu batun siyan baki,ko akwai din ma ita batajin zata tsaya,saboda mutum biyu daga cikin abokan saifullahi da suka uzzurawa rayuwarta tun ranar kamu,ta musu qaryar a niger take,saboda haka bata son su hadu bare su takura ta,dabara tayi mata cewar bari taje tayi fitsari daga haka ta arto gida.       Biki ya tashi lafiya,ummee da kanta ta yi ma sumayyan godiya tare da godiyar kayan humra data yi mata wanda su aka jerawa amiran ma,kunya ce ta kama sumayyan,duka duka me tayi,su basu duba tarin karamcinsu wanda ya kai ga cancantarsu kan yi musu komai.        Tun a daren ta kashe wayarta kwata kwata,don ta tabbatar cewa gobe kamar da qasa sai amira ta nemeta,jikinta ya gaji tubus irin gajiyar da bata taba yin irinta ba,lallai biki ba wasa bane,tunda ta kwanta bata tashi ba sai da gari ya waye,ta makara sallar asuba,don sai shida da rabi ta yita,tana gamawa ta koma ta sake kwanciya,ba ita ta farka ba sai sha biyu saura na rana,yunwa ta sadakarta,a guje tayi kicin ta tadda anty dije na soya miya qamshinta ya cika gidan baki daya,ba magana ta mata nuni da kayan break dinta dake ajjiye gefe,tana kaiwa baki daya yiwa antyn sannu da aiki "Ai ke zanwa sannu,yaran nan sunso tadaki badon ma hanasu ba,shi yasa da abbansu zai fita na hadasu da shi ya kaisu wajen inna(kakarshi)" "Kai kina ji da ni anty na" ta fada tana jan kujera don ta ji dadin cin abincin sosai "Ba dole ba,kece fa babbar diya" suka sanya dariya baki daya sannan suka ci gaba da hira suna tattauna wasu daga lamuran da suka faru yayin bikin,antyn na juye miyar cikin warmer tace "Ai ke kam bakiga hutu ba,saura sati uku a shiga wani bikin" "Wallahi anty shi yasa nakeso nayi kamar kwana uku haka ina bacci,don so nake next week na wuce kano" hararata antyn tayi "Dama na sani ai,ke kam garin nan kamar yana mintsininki,gidan fa baki daya baya dadi wallahi idan kika tafi,hatta da abbansu ya dinga mitar kin dade,amma wani lokaci sai na rayawa a raina dole fa mu saba tunda wataran zaki aure,idan kika tafi kuma ya zamuyi" shiru sumayyan tayi taci gaba da kurbar tea,saboda anty dijen ta kawo zancan da bata qauna cikin hirar tasu,sai data gama sha ta sure cup din tana goge hannunta sannan tace "Anty,wata tambaya ce da ni" "Uhmmm,Allah yasa na sani" shiru ya danyi tana tsara yadda zata jefa mata tambayar kafin tace "Wai idan wata ko wani yazo ya cewa budurwa ki taimaka ki gyara rayuwar wane,wai me hakan yake nufi?" Waiwayowa tayi ta kalleta har sai da gaban sumayya ya fadi,Allah yasa ba wani mummunan abu bane,kamar antyn ta tambayeta wa ya fadawa wani hakan sai kuma ta fasa,taci gaba da aikinta tana bata amsa "Maganar na da ma'ana bangare biyu,nq farko idan har aka fadi haka ga wani ko wata makusanciya ta mutum ana nufin ta dinga bashi shawara da hanashi aikata wasu abubuwa,ko kuma wani abu na son faruwa da shi ana son ka taimaka kada ya fada cikin wannan abun,sannan ma'anar na iya daukan AURE ko SOYAYYA,abun nufi.......shi wanda ya gaya miki maganar yana ganin kamar kina da wasu qualities da wani namiji ke buqata,wanda wannan qualities din zau taimaka masa wajen gyaruwa ko ingantuwar rayuwarsa,babu kuma hanyar da zaki gyara ko ki inganta rayuwar tasa sai ta hanyar AURENSA ko yin SOYAYYA da shi,to sai a baka maganar a dunqule" tunda ta dauko maganar gaban sumayyan ke faduwa "Da gaske baba na nufin kenan ta auri almustapha?,abinda baabaa ke son fadi mata kenan" kai ta shiga girgizawa cikin zuciyarta ta soma furta "La haula wala quwwata illa billah,Allah ka sani ina ganin qima da darajar wannan bawa naka,ya Allah ka fidda masa wannan tunanin daga zuciyarsa a kaina,ka jefa masa tunanin wata,Allah kada ka bashi iko ya tambayi abinda bazan iya masa ba" "Ke sumayya meye haka?" Inji anty dije ganin yadda take kada kai tana mus mus da baki,murmushin yaqe na musamman ta qaqalo sannan tace "Ba komai,kawai ina mamakin yadda muka kasa fassarar maganar,wani ne ya gayawa wata" ta fada tana miqewa tsaye sannan ta fice daga kitchen din,da kallo anty dije ta bita,cikin zuciyarta tana addu'a,Allah ubangiji ya sanya sumayyan tayi gamo da miji ne dan gaske,wanda zata huce takaicinta,babu shakka zata so za kuma tayi burin sumayyan tayi auren da zata huta ta sanadiyyarta,juyawa tayi taci gaba da aikinta tana addu'a cikin ranta.         A sanyaye ta zauna bakin gado maganar na sake y mata yawo,indai haka ne ba shakka dole ta qauracewa haduwar ta da baabaa,kai ya zame mata jazaman tafiya kano,kuma bata jin zata dawo nan kusa idan ta tafi din,zata yita qirqiro dalilai ne wadanda zasu zaunar da ita a can.        A daddafe ta haqura ta kai ranar alhamis kamar yadda ta gayawa anty dije,sannan ta shirya tafiya,wanda ya rage sauran kwanaki goma sha hudu bikin,anty dije ta bata saqonni gun mama sannan tace suma nan da kwana bakwai suna tafe,wannan karon saboda tsabar zaquwa ta tafi bata iya jira abban laila ya dawo daga kaduna da yaje ba ya hadata da driver,motar haya ta hawo ta tafi,ba yadda anty dije bata yi ba amma ta kasa daurewa ta jira.         Tana hanya taji kira,lambar amira ce,tun kafin ta daga ta saki murmushi "Amaryar saifullahi bada kanki a sare" kamar wadda ke shirin sakin kuka ta soma mata qorafin kota nemeta ko?,sun hada baki da saifullahi sun sace mata wayarta,shi din ma ya rufe gidan ba shiga ba fita wai sai sun huta,ya kuma hanata wayarshi sai yau ya bata wayan,dariya ta dinga mata din yasan da wannan plan din,sai da ta gama qorafinta sannan suka gaisa tace yaushe zata zo don Allah "Kin ganni hanyar kano,wani bikin ya sake kira na,bikin zainab dita" "Wayyo,dama a kusa da namu ne,naci burin zuwa fa namecy" dariya tayi "saidai ki tara ana halima idan Allah ya kawo"haka nan suka gama hirarsu ta baiwa saifullahin suka gaisa sannan sukayi sallama.    Kamar ko yaushe sunyi murna da zuwanta,mama nata tsokanar abdallah wai ya qara qiba "Amma dai zaka koma ko?" Wuya ya maqale a kafadarsa "Nan yafi dadi,can kullum kuna rufe a gida" dariya suka saki don abdallahn badai son yawo da wasa ba,hararshi sumayya tayi "Nima babu inda zaka bini,rigimammen kawai" ko a jikinsa dariyarsa ma ya sanya abinsa,washe gari yaya yahansu tazo ta daukeshi ma sukayi tafiyarsu,sai ranar kamun zainab tace zata dawo da shi.        Tunda tazo babu zama suna ta shirye shirye ba kama hannun yaro,ita da anty salma qanwar mama da anty amina matan yaya abubakar,sunyi waya abdur rahman bai nan amma zai dawo da shi za'a yi daurin auren shi yasa take hidimarta hankali kwance ba wani damuwa ko takura,cikin ikon Allah da baiwarsa komai yana tafiya daidai,sumayya taga yadda ake komai cikin tsari saboda haka ta dage ta tsarawa 'yar uwarta komai yadda zai qawatar ya kuma burge,kudi sosai tasa yaya abubakar ya bata bayan wanda anty dije da uncle farouq suka bata,dinkuna sosai ta yiwa mama,atamfofi masu tsada da kyau,harda mayafai da takalma duk da yaya abubakar yayi musu amma tace wannan nata ne,sannan ta siyawa malam gezna ta asalin wadda zai sanya ranar daurin aure,takalmi mai kyau harda agogo da turare da sabon rawani fari qal,kasancewar malam din ba baya bane wajen tsafta shi yasa kusan kayansa galibi farare ne,aka yi masa dinkin babbar riga 'yar ciki da wando,ita kam dama bata da matsalar sutura sai anko kawai data yi,sai abdallah data masa shaddar daurin aure duk da dumbin kayan da yake da su,saura kwana tara biki kuwa saiga anty dije da iyalinta,nan aka shiga hidima sosai.       Kan hanyarsa yake ta dawowa daga airphort bayan ya kai anty dije da yaranta sun tashi zuwa kano,tun daga nesa yaga kamar motar baabaa prof a tsaye,hakan ya sanya ya rage gudun motar ya qaraso a hankali ya faka tashi motar bayan tasu sannan ya bude ya fito.       Baabaan ne tsaye gaban motar,kana dubanta kasan matsala ta basu,qarfen nasara da bashi da tabbas,motar kwata kwata shekararta guda,ba yadda mustapha baiyi kan a canzata ba kamar yadda ya saba sauya masa motocin hawanshi amma yace a sauya sauran amma ita banda ita,yana jin dadin motar,da ita yake zuwa gidan gonan sulensa duk qarshen sati,duk randa zai tafin baya tafiya da wasu motocin face wadda ita kadai zai hau,kuma daga shi sai druvansa,yana jin dadin zama gidan gonar,ya zazzaga yaga gidan gonar sosai,yanajin nishadi da farincikin yadda dukiyar sulensa ke habaka,fatanshi Allah nuna masa ranar da zaiga sulenshi,a irin haka ne yau motar ta tsaya musu a hanya.        A aladabce uncle farouq ya qaraso "Subhanallah,baba kada dai ace qarfen nasara ya muku tsiya?" Cikin murmushi mai dauke da dattako yace "Wallahi kuwa,to ya za'ayi,yau da gobe ai sai Allah,babu wani abu dake matabbaci" "Gaskiya ne" inji uncle farouq yana fidda waya daga aljihunshi yana fadin "Bari a kira gida to a turo wata ko baabaa,tamu motar ba lallai ka iya shiga irinta ba" murmushi ya kuma subucewa baban,har ya sanyashi ya juya ya sake kallon motar duk da ya santa,motace mai lafiya wadda bata da wani aibu ko makusa,ko kai waye zaka iya hawanta,amma ya sani cewa irin motocin da mustapha ke ajjiye masa yana hawa shi ya sanya farouq din tunanin yafi qarfin wannan "Haba faruqu,saidai kawai idan rawar hawa motar take kake min,amma ni din waye da bazan hau wannan motar ba" ya fada yana dariya,bakinsa ya rufe shima yana dariya "Afuwa baabaa" ya fada yana bude masa gaban motar,kafin ya shiga ya waiwaya ya dubi drivan nashi "Kada ka tsawaita tsaiwa a nan,ka kira bakaniken nan,idan bakaniken ya iso ka bashi muqullan ka taho gida" a ladabce yace "Yallabai man yace kada a sake barinka ka hau motar da baniken hanya ya tabata ranka ya dade" murmushi ya saki "Qyale wannan,idan na biye masa ma a jirgin sama zan dinga yawo,ni waye da bakaniken hanya bazai taban mota ba,shi yasa na hana a kira gida agaya musu motarmu ta tsaya nasan zai iya jin zancan ya damu mutane da batub sauyan motoci,bayan ni din duka kwana nawa ya rage mana a duniya,kayi yadda nace kawai" "To ranka ya dade" inji drivan,baban ya juya ya shiga motar faruqun ya rufe ya zagaya shima ya shiga ya tadata suka fara tafiya.        "Asalina daga qauye na fito faruqu,kiwon dabbobi  na dinga yi ni da aminina,da can ko jaki bani da shi na hawa bare a kai ga mota,din me zan dinga manta asalina,ita duniya gaba dayanta yadda ka dauketa haka take zuwa maka,mafi daraja cikin mutane shine wanda a zahiri ya isan amma yake daukan kanshi ba'a bakin komai ba,girman kai rawanin tsiya ne,wanda ke zaton ya isa kuma sai Allah ya qasqantar da shi a duk inda baiyi zato ba" kai uncke farouq ke gayadawa cike da gamsuwa,tsohon dattijon qwarai ne,yana bala'in son zama da shi saboda dole ka dauki darasin rayuwa,idan ya shiga cikin wasu baka isa kace shine wannan professor din ba,kuma tsohon jakadan nijeria a qasar amurka.       Danja ta tsaidasu uncle farouq yaci burki da sauri saboda yana dan gudu,wanda hakan ya sanya katinan dake zube gaban motarshi suka zubo,jiya ya karbosu shi yasa aka yiwa malam su na daurin auren zainab ya baiwa anty dije ta tafar mai da su ragowar ya ajjiye wajansa zai bawa kawunshi "Bismillahi" malam ya fada yana cewa "Kaima ashe kana dan taba irin tuqin almustapha kenan ko?" Ya fada yana murmushu tare da duqawa yana kwaso katinan sa sukw zube din.        Caraf idanunshi suka kai kan sunan dake jikin katin wanda ke qunahe sa sanarwar daurin auren SULAIMAN AMINU DAHIRU GOMBE,sake maimata sunan yayi,sunann da ya kasance sak irin na tsohon amininshi sule,tsohon aminin da kullum zuciya ke begen ganawarsu,maimaita sunan ya dinga yi tare da kallon rubutun da aka tsarashi kalar golden,tamkar zai gano masa da zargin da zuciyarshu ta fara yi,uncle farouq ya lura da hakan sai yace "Bikin qanwar mai sunan mama ne,wato 'yar yayar khadija" wawiyar ajiyar zuciya ya sauke ya maida dubanshi ga farouq "A ina suke faruqu" "A kano suke" "Kano?,meys asalin mai gidan" kai ya girgiza cikin kokwanto "Bamu taba zancan gaskiya da ita ba,amma dai a kano na sansu,wani abu ne baabaa?" Kai ya kada yana maida katinan mazaunansu "Sunan ne kawai ya yimin kama da na wani tsohon aminina wanda har yau nake neman bayan ya bata tsahon shekaru" "Ayyah,Allah ya bayyana shi" "Amin amin faruqu". Bai bar babaan ba sai daya dangana da shi har cikin gidan sannan baabaan ya sauka yaba masa godiya,kunya duk ta kama faruqun,a rayuwa babu wani abu da zaiwa baban da har zai masa godiya,bayan babu wani nau'in karamci da kyautatawa da baban bai masa ba tun daga sanda ya sanshi har zuwa yau.       Tunda ya koma gidan baki daya ya kasa sukuni,katinan da sunan sun tsaye masa a rai,daren ranar kasa cikakken bacci yayi,yayi salloli sosai kafin ya samu bacci yayi awon gaba da shi,da asuba da ya tashi da abun ya tashi cikin ransa,har gari yayi haske,sai kawai ya tsinci kanshi da jawo kiran wayar uncke farouq ya buqaci adress din gidan mamallakin sunan da ya gani jikin katin,babu haufi ya tura masa don baya shakka cikin nagartan baabaan,yasan cewa koma mene alkhairi ne IN SHA ALLAH.         Waya kawai ya sake dagawa,ya lalubi lambar mahmoud ya buqaci ganinsa,ba bata lokaci ya iso kasancewar yana cikin gidan,sanar masa yayi ya laluba idan akwai jirgin da zai tashi daga abuja zuwa kano ya yankar masa ticket guda hudu,shi daya mahmoud din daya mus'ab wanda yazo biki bai koma thailand ba,da kuma drivansu,bai wani mamaki ba saboda yasan lokaci zuwa lokaci baaban nasu nayin tafiya kota ziyara ko duba gidajen gonar wannan babban aminin nashi da tunda suka taso suke jin sunanshi suka kuma haddaceshi,tare da riqe girma da matsayinsa wajen babansu,lokaci lokaci sukan yi bita da tilawarsa,saidai har kawo yanzu idanuwa basu taba ganinshi ba,cikin sa'a aka samu jirgin azaman wanda zai tashi ne da la'asar qarfe hudu na yamma,ba haka baban yaso ba amma haka ya karba.         Qarfe hudun jirgin ya lula da su sararin subhana zuwa kanon dabo,wanda cikin mintuna suka isa cikin yarjewa da ikon ubangiji tare da sahalewar ci gaban zamani irin na yanzu,kano tamkar gida take wajen baaban,saboda haka suna sauka suka tarar da motoci guda biyu suna jiran isowarshi,ba bata lokaci suka shiga suka fice daga airphort din.        Wayarsa baban ya ciro,ya lalubo adress din ya soma karantowa drivan,kasancewarsa dan kano ne tuni ya fahimci wajen,sannu a hankali suka dinga keta unguwanni har suka qaraso unguwar da ya buqata,a bakin qofar gidan sukayi parking,drivan ya sake tambaya aka tabbatar masa nan ne gidan malam sulaiman,yaron ya aika ciki ya tambayo yana nan kamar yadda baabaa ya buqata,saidai yaron ya sanar musu baya nan amma bayan sallar isha'i yana gida,ya sake aika yaron yace idan ya dawo a gaya masa yayi baqo,amma zai dawo bayan sallar isha'in ya tsumayeshi don Allah,sai da ya isar da aiken sannan suka tada motocin suka bar layin yaron na bin motocin da kallo saboda yadda suka yi masa kyau. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [23/02, 11:51] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 7⃣3⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *HASBUNALLAHU WANI'IMAL WAKIL* __________________________________        Baabaa prof ji yake kamar isha'in ba zata yi ba,fata yake cikin ransa Allah ubangiji ya sanya sulensa ne,Allah ya qaddara saduwarsu,haka kawai yake jin zumudin zuwan sallar isha'in yayi yaje yayi tozali da mai wannan suna.        Kai tsaye gidansa daya fara zama cikin garin kano tun zamanin quruciya can aka wuce da shi,gidan har yanzu yana nan da kyansa da daukar hankali,kasancewar bai bar gidan ya lalace ba,ko yaushe sake sabunta shi ake saboda ba'a rasa cikin iyalansa mash zuwa kanon,gida take kano a gun kowa,ko baka shigo ka zauna cikinta ba baqunta ko kasuwanci ya kawoka,ko ba haka ba ma hanya ta wuce da kai ta cikinta,wanka yayi ya sauya shiga sannan suka wuce masallaci shi da mus'ab da mahmoud baki daya kasancewar dab ake sa fara sallar magariba.        Basu suka baro masallacin ba sai da akayi sallar isha'i,kai tsaye hassan driver ya koma gida ya fiddo motar ya kawota bakin masallaci suka shiga,tafiya ce da bata wuce minti talatin ba ta maidasu unguwar,guri suka samu sukayi parking sannan suka aika yaro yaje ya sanar da malam ana sallama,cikin sakanni ya dawo ya gaya masa yana fitowa.       Tsaiwar mintuna biyar kacal ya hangoshi,idanuwa ya zuba masa baki daya ko qwaqwaqwaran motsi baya yi,tun kafin ya kai ga qarasowa inda suke ya shaidashi,girma ko tsufa baiyi isar da zaya sanya ya kasa gane sulenshi ba,dadi ko wuya babu abinda zai mantar da shi sule,shima takowa yake saidai sam bai kula da wanda ke gabansa,kasancewar yafi ganin mahmoud da musa'ab dake tsaye gaban baabaa prof din,a hankali ya qaraso ya dubi su mahmoud a nutse "Yan samari kuke sallama da ni?" "Basu bane,muntarinka ne,muntarinka ne sule,suken mai gado" da hanzari ya daga kai shima din gani waye?waye wannan dake ambatarsa da sunan nan qwaya daya jal da yasan duk gadin karkararsu shi kadai ke kiransa da shi,ya sanya masa sunan me tun daga lokacin da malam muhammadu(mahaifin baabaa prof) ya basu tarihin annabi sulaimanu da nana bilkisu,kutsawa yayi tsakiyar su mahmoud yana fatan kayalinsa ya zama gaskiya,ya tabbata kuwa,muntarinsa ne,muntarin da kullum matuqar rana zata fito ta fadi walau yana da cikakkiyar lafiya koko babu ita sai ya tunashi,sai yayi begen ganinsa,da sauri suka qarasa zuwa ga juna suka rungume juna kowa na ambatar sunan dan uwanshi,kowannansu jikinshi na rawa,lamarin ya yiwa su mahmoud nauyi ganin yadda dattawa ke fidda ruwan hawaye,yara masu wucewa suka soma tsayawa suna tunanin wani abu ne ya faru ga malam din,mus'ab ne yayi qarfin halin cewa "Amm,baabaa yara fa sun fara tsayawa" abinda ya fargar da malam kenan ya saki muntari yana kallonshi,ji yake kamar zai sake bace masa bazai kuma ganinsa ba,ko kuma mafarkin da ya saba ne yake yi "Ina zuwa" malam ya fada cikin sauri har yaja tuntube ya shiga gida a gaggauce ya karbi muqullin sitting room wajen mama yana shaida masa yau ga muntarinsa a gidansa,muqullin kawai ta bashi tana tantama,muntarin da tunda suka hadu take jin sunanshi daga bakinsa amma bata taba ji sun hadu ba shine tau aka ganshi?.        Jikinsa har rawa yakeyi ya bude sitting room din suka shiga,har yanzu kowannansu gani yake kamar almara "Sule kaine?,ko almara ce?" "Nima haka nake ji muntari,saidai lamarin ubangiji yafi gaban haka,shi sami'ud du'a ne" "Qwarai kuwa ba shakka"doguwar gaisuwa sukayi bayan sun gama sumbatun ganin juna,sam sun mance ma da wani mus'ab da mahmoud a wajen,har sai da mahomud da mus'ab din suka matso suna gaida malam ya amsa fuskarshi na fitar da annuri,dukkan wani nauyi dake cikin zuciyarsa ya yaye,a yau ya tabbata farinciki bazai barshi yayi bacci ba " wadan nan 'ya'ya na ne sule,gasunan,akwai biyar a gida,baya ga jikoki da suka kusan tasamma guda goma matan aure biyu,kaifa sule?,ya rayuwa ta kasance?"ya fada yana dubansa,wani sashi na zuciyarsa na masa susa ganin alamun sulen bai kama koda kaso daya cikin goma na arziqin da shi yake da shi ba,bayan kusan tare suka sha wuyar tattala da tara dukiyar,saidai alhamdulillahi kana ganinsa kasan baya cikin wahala,yana cikin matuqar rufin asiri,miqewa mahmoud sukayi shida mus'ab suka koma qofar gida don bash waje suji dadin ganawa sosai,gyaran murya malam yayi sannan yace "Bayan barina garinmu muntari na jima bansan inda hankalina yake ba,da na tashi kawai na tsinci kaina cikin makarantar allo ta almajirai,wani malami dake yawon rarraba almajirai ya tsintoni ya hada da yaran da zai kawo kano,sai na karbi rayuwar a yadda na ganni,na riqe karatuna da hannu bibbiyu,na zama daya daga cikin hamshaqan dalibai haziqai da malam ke ji da su,gefe daya kuma kasan tun asali bani da matacciyar zuciya,a duk lokutan da ba na karatu bane nakan fita neman na kaina,duk aikin da na samu zanyi kowanne iri indai na halal ne,batun gida kam baki daya na manta ma ni din dan wanne gari ne,tun malam na damuwa yana qoqarin tambayata har ya haqura ya watsar a haka rayuwa taci gaba da turawa,na samu cikakkiyar haddar alqur'ani mai girma,na zama daya daga cikin amintattun malam,'yan gaban goshinsa,muntari ban tashi tunawa da garinmu ba sai sanda Allah ya yiwa mahaifina rasuwa,naje na tadda rasuwarshi,na kuma samu labarin dukan abun arziqin da kake yi,na tambaya saidai kash ko daya ba wanda yasan inda kuka koma acikin gari,suce zuwa musu kake ka koma,da haka na isa ga dangin mahaifiyata wadamda suma mutuwa ta daddaukesu sai 'yan ragiwa,muka gaisa na dawo cikin gari na hau cigiyarka,wasu suce min sun sanka amma basu san matsugunninku ba,wasu suce ma basu sanka ba,da haka na haqura da dawo kano bani qwarin gwiwa,bayan wasu shekaru ban haqura ba na sake komawa,sai naje na tadda ma baki daya kunyi qaura daga gombe kun dawo kano,naji dadin hakan saboda ina zaton zan sameka ta sauqi tunda muna gari daya,saidai na manta cewa kano nada girma da fadi yawan al'umma da yawan qabilu,akwai tarin qananan hukumomi qarqashinta,haka na qaraci nemana tsawon shekaru,tun inayi tuquru da qarfina har na haqura.        Uwar 'ya'yana a yanzu diyar malam ce,wanda saboda yadda da gamsuwa da yayi da kyakkyawar halayena da dabi'una ya bani aurenta,na samu tarin ilimi daga wajen malam har bayan rasywarshi sunan malam ya dawo kaina,duk da ban iya ci gaba da kula da almajiran ba kowa ya koma garinsu,amma ban fasa bada karatu ba wa dalibai masu zuwa su tafi,a yanzu haka muna da yara hudu da jikoki biyu,sannan cikin qarshen wannam satin zan sake aurar da yarinyata ta uku,kazo a daidai muntari,ko yaushe ina bege idan wani abu da ya shafi iyalina ya taso,inama ace muntarina na nan"cikin farinciki baabaa ke dubanshi "Allah ya amsa addu'armu sule,Allah shine abun godiya" a hankali baabaan shima ya soma zayyane masa yadda yayi tashi rayuwar,gyada kai kawai malam yake yana kallon muntarinsa yana jin dadi,baabaa prof din ya qare da cewa "A yanzu haka sule na kaima kana da taka dukiyar ta kanka,kyautar da nayi maka ban fasa ba sule,itace naci gaba da kula maka da ita har kawo yau,a yanzu haka duk wani gidan gona ko yoghourt ko fresh milk dake dauke da tambarin S.A.D mallakinka ne" mamaki ya kama malam,girma matsayi na muntarinshi ya sake ninkuwa cikin idanunshi,samun mutum mai amana irin haka a wannan zamani abu ne mai wuya,samun aboki irin muntarinsa a zamanin nan tashim hankali ne,bai manta wani waqe da wani balaraben mawaqi ya tabayi yana cewa'a yanzu zaka samu cewa,zukatan abokan gaba sune a jikkunan abokai'ma'ana a fili a bokai suke a idanun kowa,amma a badini kowannensu gagarumin abokin gaba ne ga dan uwansa,bai qaunarsa,bai son ganin ci gabanshi,burinsa kawai yaga faduwa hasara sa damuwa tattare da shi,kai malam ya kada "Duka wannan ba shine abun damuwa ba,haduwata da kai kafin Allah ya zare numfashi daga jikina shine babban abu,kuma Allah ya cika mana wannan burin" shima kai baabaan ke kadawa "Dukkan abunda muntari ya mallaka na sule ne,yana da iko da shi,bare wata qaramar kyauta da ya masa tun zamanin quruciya?,haqqinka ne sule dole ka karba,munyi haka tun a gaban idanuwan malam,A yanzu bayan qaaa ta rufe idanunshi sai mu sauya?,sam haka bazai faru ba" inji baabaa.         A daidai qofar gidan kai napep ta saukesh,ita ne da zainab da halima,a gajiye suke matuqa,don sunyi yawo sosai gidan 'yan uwan mamanta rabon chewing gum,burin sumayya kawai ta samu inda zata jefa haqarqarinta ta kwanta,don ko ta abinci bata yi,Allah ya sota tayi sallolinta baki daya.        Kamar ance dubi can ta hangi mahmoud zaune saman motarsu yana jajjefa qafa yana murmushi,bisa dukkan alamu yana jin dadin yanayin,haka sauyin waje zuwa unguwar da bai santa ba bai taba zuwanta ba hakan yayi masa dai dai,idanu ta zuba sosai wai ko idanuwanta ke mata gizo,ta sake matsawa wajen,tabbas shine,daidai sanda ya waiwayo shima,baki ya bude yana mamaki "Wa nake gani haka?,me ya kawoki unguwarnan?" Ya fada yana murmushi tare da saukowa daga saman motar "Da gaske kai ne?,to me kake yi a kano kuma a unguwarmu a qofar gidanmu?" "Kina nufin nam shine gidanku?" Ya fada yana nuna gidansu da yatsa "Qwarai kuwa,nan aka haifeni" "Malam shine aminin baabaa dama,sulen muntari?" Wannan magana ce kawai ta kasa gane me yake nufi,sai ta dubeshi tana neman qarin bayani,baisan ta yadda zai fasaara maga zancan ba sai ya dora da cewa "Tare da baabaa prof muke fa sumayya,babanku shine tsohom aminin nan masa da yake yawan ambata,wanda ba yadda zakuyi magana da shi ta awa daya bai sako zancansa ba" ya fada yana murmushi har cikin zuciyarsa yana jim dadin yadda a yau burin mahaifinsu na tsahon shekaru ya cika,mamaki ya kamata qwarai,tabbas babu shakka zata iya tunawa ko ita yana sako mata zancansa lokaci lokaci idan hira ta dan hadasu "Malam dinmu?,baaba yanzu yana ciki?" Duka tayi tambayar a tare lokaci guda cike da dimbin mamaki,wai babanta shine tsohon aminin baabaa prof,bugu da qari kuma wai baban ne yau a gidansu "Qwarai kuwa,mun fito mun nasu guri ne din kinsan tsaffin abokai idan aka hadu ba dama,kada a tuno wata quruciyar aji kunya a gabanmu" ya fada cikin irin salonshi na tsokana,dariya ya basu baki daya "Allah mai iko" sumayyan ta fada har yanzu abun nata na bata mamaki "Bari naje na gaida babanmu" ta fada tana yunqurin wucewa "Wannan qani na ne,shike bi mini,mus'ab dake thailand,gashi nan ku gaisa" ya fada yana dukan kafadarsa,a mutunce suka gaisa sannan ta sanya kai zuwa cikin gidan cike da zumudi da mamaki.        Sai da tayi sallama biyu aka bata izini sannan suka sanya kai cikin dakin,suna zaune irin zaman da kama dubansu kasan muhimmiyar ganawa suke,ganawa kuma mai dauke da qauna da fahimtar juna,duk da ruwa dake lemukan gaban baabaa prof babu wanda ya taba,ganin sulenshi da sauraron labaranshi ya fiye masa komai,daga kai baaban yayi cikin mamaki yana dubanta "A'ah,mama na,daga ina haka" kanta a qasa cikin murmushi ta qarasa gabanshi ta duqa "Baabaa,yau kaine a gidanmu?" Sai ya maida dubanshi ga sule yana fadin "Kada dai kace min sumayya diyarka ce?" Cikin murmushi ya daga kai "Tabbas,ita ce diya ta tabiyu,ita ce kuma ta haifamin babban jika na" kai baabaan ke dagawa,wani madaukakin farinciki na mamayarsa,tabbas Allah na sonshi,Allah na duba ga zukatan bayinsa ya musu taimako cikin ayyukan alkhairin da suka sanya gaba,a ladabce sumayya ke gaidashi da su zainab ya amsa cikin farinciki yana sanya musu albarka.        Sosai wani irin farin ciki ke shigar shi,ji yake tamkar babu wanda ya kaishi farinciki yau a duniya,mamanshi cikin zuriyyar sulenshi?,babu ko tantama Allah yana nufinsa da alkhairi,sosai yake jansu da hira abinshi,tun su zainab na dari dari na rashin sabo har suka saki jiki "Ba don bikin da za'a yi ba shakka sai na daukeku baki daya,dama ita mama na 'yar gida ce" baabaa ya fada yana murmushi,dariya suka sa baki daya suna sake jinjina girman qaunar dake tsakanin iyayensu,sumayya ce ta janyesu tace bari su shiga ciki suma don su sake basu waje sosai,murmushi ne dauke a fuskar baabaa prof har suka fice sannan ya maida idanunsa kan malam.     "Sule,dama sumayya diyarka ce?,wannan abu ya faranta min fiye da yadda kake zato,tun sanda naga yarinyar naji ta kwanta min,na yaba da halayyarta,haka naji ina qaunarta kwatankwacin yadda nake qaunar amira,ashe jininmu ce,jinin sulenmu ce" murmushi malam keyi sannan yace "Mai sunan inna daban take muntari cikin 'ya'yana,Allah ya yi mata baiwar ilimi hankali haquri da nutsuwa,zakayi mamaki odan na baka labarin irin rayuwar data fuskanta,da irin qaddarorin da suka fuskanceta,cikin ikon Allah ta cinye jarrabawarta,dubeta,yanzh waye zai ce ta taba fuskantar matsi da qunci makamancin haka,waye zai ce harda maraya gareta?" Dubanshi kawai baabaa keyi,don shi bai san sumayyan ta taba aure ba "Kana nufin kace mama na ta taba aure?" Kai malam ke kadawa don tabbatar masa "Qwarai kuwa,har da yaro" gaban baabaa na faduwa cike da faata yace "Ina fata amma a yanzu bata da aure ko maganar wani kanta?" Cikin mamakin gambayar da muntarinsa ya masa ya amsa masa da eh,sauke ajiyar zuciya baabaa yayi yana furta "Alhamdulillahi,sule,ko zaka iya taimakamin ka bani auren mama na?" Dubanshi yake alamun bai fahimta ba "Ina nufin ka bani auren mama na na karbawa d'aana mustapha?" Murmushi ya subucewa malam din,amma sai ya gaza cewa komai,baaba ya dora da bayani "Mustapha na cikin yara mafi soyuwa a wajena kamar yadda mamana take,tabbas da dan adam keda ikon tsarawa dan uwanshu rayuwa bazan zabawa almustapha rayuwan da yake yi ba a yanzu,taimako nake da buqata ka yiwa yaronka mustapha,don Allah kada a hanashi,bari na gaya maka wanne irin rayuwa mustapha keyi da iyalinshi" hankali kwance baabaan ya zayyanewa malam komai,kai kawai malam ke kadawa,shi kam bai ma tabajin rayuwar aure ta tsantsar nasaranci ba irin wannan,baiyi yawon duniya ba bare ya santa,wadda tazo cikin qur'ani da sunna da wadda akeyi cikin kowanne gida a society dinmu kawai ya sani,shi da ko karatun boko bai bari anyi a gidansa ba banda zamani daya tilastashi ya bar halima da zainab sukayi candy, "tabbas wannan wani taimako da jihadi zakayi sule,saboda yau da gobe tafi qarfin wasa,almustapha lafiyayye ne,yana da tarin dukiya wadda tafi tawa,kai duka cikin zuriyata babu mai dukiyarshi,'yammata na qasashe daban daban na sonshi koda ba soyayyar aure ba,yana da iko da 'yancin yin komai,WA YASAN GOBE?,wa yasan gobe mai zata haifar,gwara tunda ina da ikon kawo gyara na kawowa rayuwarsa gyara ta hanya halastacciya" mamaki ke ci gaba da ratsa malam wamda ya haddasa masa kasa magana,wannan wace iriyar mace?,ita zata iya daga hannu tayi tutiyar ita din matar aure ce?,murmushi ya saki ganin yadda muntarin ya zuba mishi idanu yana jiran amsarsa,irin kallon wanda ke tsoron jin fitowar amsa mara dadi daga bakin wani "Ba qaramar kunya ka sanya naji ha muhtari,yanzu don Allah ka cancanci ka roqeni kan neman auren mai sunan inna?,ashe ma ba daya muke ba,ashe ma yadda ka daukeni ban kai nan ba,sannan baka amince da yadda matsayinka yake a guna ba,har kwanan gobe muntarim ban sake aboki ko amini wanda nake jinsa kamar ni da shi tagwaye muke ba tunda muka rabu da kai,muhtari,ba almustapha ba,ko kai keson sumayya na baka ita halak malak bare tsatsonka,kai,ko moqocin maqocinka kesom sumayya wlh yaci albarkacinka,kana iya aurar da ita ma ba tare da na sani ba,NA BAWA ALMUSTAPHA SUMAYYA HALAK MALAK,amma wani hanzari ba gudu ba,sumayyan tayi aure ba guda daya ba har biyu harda yaro,kana ganin hakan ba matsala bace?" Kai yake kadawa "Naji dadi sule,na gode da wannan karamcin naka,sumayya ko aure dubu tayi matuqar nace wa mustapha ina so ya aureta babu musu sai ya aureta,baaga auren budurqar ba anyi meye ne a ciki?,bazawara nada tata baiwar ta musamman kuma ta daban matuqar ta tsare mutuncin kanta tasan ciwon kanta,hankalinta da na budurwa ma kadai akwai banbanci,nasan mustapha cikin 'ya'yana,ni inda nake kokwanto mamana,kada muyi abinda zai sabawa ra'ayinta" dariya malam yayi "Muhtari kenan,wacce maman namu?,yadda kake da tabbas kan danmu almustapha haka nake baka tabbas kan maman taka" cikin farinciki suka saki dariya dukansu,hannayensu damqe cikin juna farinciki na shawagi da su cikin duniyarshi,tamkar baabaa ya tashi ya taka rawa haka yake ji,yau Allah yayi mishi baiwa manya manya guda biyu,ko yau Allah ya dauki ranshi tabbas ya cika masa burikansa,a hankali malam ya warwarewa baabaa labarin sumayyan da irin gwagwarmayar da tasha,tausayi da qaunarta ta sake yawa a ranshi,qimarta ta dadu,tabbas wannan itace macen aure,ba shakka irin wannan matar ita ta dace da a nema,ya godewa Allah data kusa zama halak malak din familynsa,wannan shi ya sake motsa baabaa ya dubi malam "Sule,idan zai yiwu ina son a hada auren nan da na 'yar uwarta,idan yaso bayan an daura a nutse sai ta tare ko bayan kwanaki nawa ne,ji nake kamar wannan damar zata subucewa mustapha" dariya ta subucewa malam "Haba muhtari,tunda na bada sumayya wa almustapha duk duniya banga wanda ya isa ya maida wannan alqawarin ba,kawai ina ganin shi kansa yaron bai sani ba tunda naji kace yana can dubai wajen aikinshi,amma tunda sai kafi nutsuwa da hakan hakan za'ayi,za'a hada da zainab din in sha Allah,ubangiji ya tabbatar mana da dukkan alkhairi yasa wannan hadin ya zamo abun alfahari da farinciki wa zuri'ar ta da taka" "Amin ya rahmanud dunya wal'aakhira" cikin madaukakin farinciki baabaa ke amsawa,shigowar mus'ab sitting room din shi ya katse sauran maganar da sukeyi,ya dan rusuna yana fadin "Afuwa,baabaa sha daya na dare,nace ko nan zaka kwana mu mu wuce?"ya fada cikin salon tsokana,daquwa baabaan ya watsa masa " baka gama fahimtar waye sule a gurina bane,da da hali kwanan zanyi,amma na tabbatar idan na kwana din kwanan zaune zamuyi ni da shi,don hira tsakaminmu ba mai qarewa bace,ni sai naga ma kamar daren yana gudu"dariya ya basu don babu wani gudu da dare keyi,idanuwanshi ne kawai,har bakin motarsu malam ya takowa aminin nashi masoyinshi,gab da baabaa zai shiga motar ya dubeshi "Gobe ya kama saura sati guda kenan daurin auren ko?" "In sha Allahu" "To madalla,ina zaton gobe zan koma gida na sanarwa da mutanen gida muma mu fara shiri,don wancan auren da yayi ba'a qasar nan aka daura ba,hakan yasanya daidaiku ne suka je masu ikon zuwa,amma wannan karon d'aana zai auri diyata sai inda kati ya qare" dariya sukayi a tare,malam ya rufe mishi murfin motar yana mausu fatan alkhairi da fatan wayewar gari lafiya.        Sai da suka fara tafiya a titi sannan mahmoud ya dan zunkuda kadan,tun dazun daya tsinci maganar ake mintsininshi,so yake yaji shin abunda yake zato ne? "Am....baba daurin auren waye kuma nan da sati guda?" Waiwayawa baabaan yayi ya dubeshi sannan yace "Yayanku almustapha in sha Allahu" idanu suka waro mahmoud yace "Shi da wa?" "Diyar sule aminina sumayya mai sunan mama na" ya basu amsa kai tsaye,duk sai kasa furta komai,babu abinda ke yawo kansu irin halaye da tsare tsaren yayan nasu almustapha wanda babu wanda baisan halayyarshi ba,shin baabaa na shirin daura masa aure kenan baida masaniya da yarinya 'yar afrika?, "Yarinyar tayi,tayi wlh bata da makusa,ga nutsuwa ga hankali,koni a lokacin da na soma ganinta don dai kawai akwai alqawari tsakanina da rahma da tuni na saka kai" ya fada yana dan kauda ido waishi kunyar baabaa,murmushi baban ya saki,idan da sabo ya saba da irin wannan barkwancin tsakanin mus'ab da mahmoud,yaso ace haka halayyar mustaphanshi take kan barkwanci,saidai kowa da yadda Allah ya tsara masa halittarsa,suna hira da raha sosai da shi,sun maida shi tamkar kakansu,yabon da ya sake yi kan sumayya ta sake faranta masa rai,kafin ya sake cewa komai mus'ab ya muskuta yace "Hmmm,dan gaban goshi,auren gata wannan karon za'a masa,yana can yana harkokinshi an nema masa aure,mu kuwa gamu nan tamu maganar ma ko ya ake ciki ne mahmoud?" Ya maida tambayar kan mahmoud,dole dariya ta qwacewa baabaa saboda salon yadda mus'ab din yayi furucin,daquwa ya watsa masa sannan ya dafa kafadarshi "Kai ka jawo tsaiko da karatunka bai gama kammala ba,amma ku din ma ba zaku wuce nan da wata biyar ba" sai suka saki dariya kuma suna jin kunya,su kamsu sunsan yayan nasu yana buqatar dauki,sunsha rayawa a ranau idan sune ba zasu iya wannan auratayyar ba,saidai da yake maza ne babu wanda ya gayawa dan uwanshi ko suka zauna suka tattauna batun,saidai kowa yayi shida zuciyarshi,da haka suka qarasa gida ko zuciyarshi fes.    ******   ********    ******        Washe gari tun tara na safe suka gama shirin fita ci gaba da shirye shiryensu,sabida a yau sumayya keson su gama rabon i.v saboda ta gaji,gashi uwa uba kuma so take da anfarawa zainab din gyaran jiki kada ta sake fita,tuni anty dije wadda yau tare zasu fita ta iso,tana wajen malam suna hirarsu ita da shi da yaya abubakar wanda yau bazai fita kasuwa ba ya taho gidan hira,amina ma na nan zuwa anjima don kusan gidan take wuni tunda satin bikin ya kama,sai da suka kammala sumayyan ta leqa falon malam din tana fadin anty dijen ta taso su tafi sun gama shiryawa don ma nafisa ta tsaidata ta tsaya amsa kiranta wadda ta tabbatar mata zata halacci bikin zainab,don zata zo kano dama gaida iyayen mijinta mahaifan auwal "Jeki ki kira min babarku ku taho tare ke da ita" inji malam,haka kawai taji qirjinga ya buga,tashin farko jikinta yayi sanyi,ta juya zuwa bakin fanfo inda maman ke daura alwalar sallar walha ta gaya mata,qafafunta kawai ta kammala wankewa ta bita suka nufi dakin.        Sai da suka samu gu suja zauna suka nutsu sannan malam din yace "Haqiqa na tabbatar da cewa duk wanda ya kwana ya tashi cikin gidan nan yasan abun farincikin da muka kwana da shi na bayyanar aminina,to bayan mun gama farinciki na ganin juna muna hira bayan ke sumayya kun shigo kun fita ya bijiromin da wata buqata,na sani kun san cewa duk da baku taba ganin muhatari ba amma kunsan muhimmancinsa gareni da irin shaquwa da halaccin da yake tsakanina da shi,ya bijiromin da wata buqata wadda na tabbatar yagi qarfinta a wajen iyalina,duk da nasan cewa haqqin sumayya ne amma na amshi buqatar hannu bibbiyu saboda nasan cewa na isa da ita sannan ba zata taba watsan qasa a ido ba" tun kafin yaci gaba qirjinta ya fara wata iriyar sukuwa,kanta yayi nauyi ta kasa dagashi,maganar da sukayi da shi kafin tahowarta kano da fassarar da anty dije tayi mata suka fara dawo mata daki daki "Ya nemi na bawa yaronshi auren sumayya bisa wasu hujjaoji daya zayyanamin wadanda sun isa sun kai baya ga matsayin muhtarin a gurina a bashi auren ita sumayya,saboda haka na bada auren sumayya ga yaron nashi wanda za'a daura auren ranar juma'a tare da na zainaba insha Allah" wani kuka ne ya qwace mata wanda sautinsa yaso fitowa tayi hanzarin sanya hannu ta rufe bakinta, "Alhamdulillah" kawai anty dije ke jerowq,kamar ta tashi ta taka rawa haka ta dinga ji,ta kasa zama waje daya sabida farinciki,ba shakka tana mai tabbatarwa kanta sumayyan tayi kyakkyawan gamo mai dauke da dumbin alkhairai "Kiyi jaquri sumayya,na miki shishshigi,saidai ina mai baki haquri tare da neman alfarma kan ki yimin wannan alfarmar kada ki watsan qasa a ido" maganar malam din ta hadu ta sake yi mata nauyi a ka,duk da halin ha'ula'in da take ciki amma haka ta tattara kalaman "Don annabi ka daina fadan haka malam,ka daina bani haquri,ni bani da wani da na cancanci a nemi alfarmata a kansa,kaine silata kai ka haifeni,duk yadda kayi da ni malam daidai ne,na tabbatar ba zaka taba cutar da ni ba,na amince na miqa wuya a gareka,roqon da nake maka kadai shine malam ka bini da addu'a,ka sakani cikin kowacce addu'a taka,Allah ya qarfafeni,ya hanani gazawa bare na watsa maka qasa a ido,na samu juriya mai yawa da zata kaini ga cika burinka" tana kaiwa nan ta gaza dairewa,sai ta fashe baki daya da kuka zucuyarta na tuna mata abubuwa masu yawa,wadanda suka faru da wadanda kan iya samunta a gaba,fata take Allah yasa SHAFUKAN KUNDIN QADDARARTA sun qare ashe akwai wasu sabbin shafukan kar a gaba,sai yaushe ne zata kammala bitar wannan kundi mai dan karen wuya da sanya zuciya da gangar jiki yin rauni,rauni kuwa bana wasa ba,ya barwa zuciya da rayuwa tabbai masu wuyar warkewa,masu wahalar sha'ani da sarrafawa tare da tanqwara zuciya a kansu,duk wanda ke dakin jikinsa yayi sanyi,sunsan mai take tunawa "Insha Allahu sumayya daga wannan karon ba zaki sake kuka ba,da yardar ma duka lokacin dariyarki ne yayi,na tabbatar da cewa ban kaiki imda zaki wulaqanta ba,na kaiki ne cikim ahalin da suka gaji karamci da mutunci tun daga tushe,ko bana raye ina da yaqinin muhtari ya isheki uwa da uba ma baki daya,addu'a kuwa kullum kina cikin addu'o'ina,zaki rabauta sumayya da yardar Allah,tashi kije,Allah ya albarkaceki da dukkan wani abu da ya shafeki" "Amin" baki daya mazauna dakin suka amsa,sai ta kasa tashi saida anty dije ta kamata,kai tsaye dakinta ta kaita ya zaunar da ita sannan ta zauna gefanta tana kallon yadda take kuka kamar hawayenta zai qare,bata cemata ta tafas ba har sai data soma tsagaitawa don kanta,bawai don ta gaji bane ko ta samu sassaucin da take son samu,ta tsagaita ne saboda yadda idanunta suka soma radadi da kuma yadda ta fuskanci antyn nason tayi magana da ita "Sumayya kuka kike saboda auren almustapha?" Ta jefa mata tambayar kamar wadda batasan batun ba "Na tabbata bakisan waye almustapha ba,banda haka da sai nace kukan da kike kin yiwa Allah butulci" jajayen idanunta ta daga ta kalleta alamar tamabaya,ciki yaqini anty dijen ke kada kai "Tabbas abinda na fada hakan yake,kinsan irinsu mustapha suke tsada a wannan lokaci?,kinsan yadda mustapha ya tara managartan halaye kuwa?,kin taba tambayar kanki me yasa su'ad ke tsananin kishinsa duk da kishin banza take tunda batasan yadda zata riqeshi ba?,kin manta waye baabaa da karamcinsu?,kina zaton idan kika qi aurensa zaki ci gaba da zama haka ba tare da kinyi aure ba?,kinwa kanki wadan nan tambayoyin?" Kai take girgizawa bayan ta gama sauraronta,cikin rawar murya ta soma furta "Anty a fuskata almustapha bashi da kirki,bai taba kyautata min ba ko sau daya,anty...kin manta yadda auren soyayya ke kayawa a wannan zamanin ina ga irin wannan?,baki daya almustapha anty ba ajina bane kamar yadda nake nima ba ajinsa bace,babu dacewa tsakanina da shi anty,komai nawa da nashi ya sha banban,ra'ayi yanayi al'ada wayewa da dabi'u,ta yaya zamanmu zaiyi daidai,baya ga haka ma baki daya anty KISHIYA!,kishiyar ma irin su'adah,kin manta anty ina kika baro wannan?,kin manta kishiya duk inda na shiga itace babbar qalubalena,bayan bansan me na musu ba,ko don ni yarinyace?,ko din bani da qarfin qwatarwa kaina 'yanci,ko don ban iya mugunta da baqin hali ba,wadan nan sune dalilan?" Ta fada wasu hawayen masu dumi na bin kuncinta,hannunta anty dije ta riqe tsam cikin nata,madadin taga tashin hankali bisa fuskarta sai taga murmushi ne ma kwance kan fuskarta "Almustapha?,ko ba haka bane sunanshi?,kin manta shi namiji ne?,namiji kuwa ko wayeshi ta bangaren zamantakewar auratayya dole ya sakarwa mata,ki manta da wannan ki cire rashin soyayya a tsakaninku a matsayin matsala,kishiya ita kike tsoro?,ina zaton zuwa wannan lokacin kin horu sumayya,meye yayi saura meye bakiji baki gani ba,sai d'ai d'ai,wannan karo ki sama ranki cewa kishiya ga gama yin nasara a kanki da yardar Allah,waccan karon ma dan dai kawai yana cikin KUNDIN QADDARARKI ne,ke mai bawa wata labari ne,dame kishiya zata tsorataki sumayya,bayan kina da Allah,kina da tsarkakakkiyar zuciya,ke matuqar su'ad ma ta baki tsoro sumayya ke kika so,ki kwantar da hankalinki damuwa ba taki bace,bakisan sirrin da Allah ya boye ba har ya turo baabaa dai dai wannan lokaci,bana son qara ganinki hawayenki daga yau" Kai kawai ta gyada mata ba don tana tsammanin samun salama cikin ruhinta ba,komawa tayi kawai ta lafe kan gado kanta na sarawa,ita kadai tasan me take ji,kai kawai take mirginawa tana jin nauyi da girmam zancan a qirjinta,su halima da zainab ne suka shigo a sanyaye saboda ganin yanayin sumayyan,antyn tace suje kawai ba zata samu zuwa ba ita da sumayyan,bata son ta tafi ta barta a yanayin da take ciki,wayarta dake gefanta tayi ruri,kiran abdur rahman ne,idanuwanta ta runtse tana kiran sunayen Allah,sai a sannan ya fado mata,me zata da shi?,me zata gaya masa ya yarda da ita,tabbas bata da abinda zata ce masa,hakanne ya sanya ta qyale wayar taci gaba da rurinta har ta katse don karan kanta,qarar wayar kawai qara mata ciwon kai yake,wanda zuwa lokaci wani zazzafan zazzabi ya rufeta ta kwanta sosai,saidai bata bari kowa ya gane ba. ****** ******* ******** Tunda ya isa gida kafatanin al'umar dake cikin gidan suka fuskanci akwai wani gagarumin al'amari na farinciki da ya faru da mai gidan,tun daga manyan ma'aikata na gidan har qananu,take ya yiwa kowa qarin albashi sabida tsananin farinciki da nuna tsantsar godiyarsa ga Allah. Bai samu ganawa da matan gidan ba sai bayan sallar magariba,ya warware musu komai,babu abinda ummee tace,ita kanta tasan yaron nata yana da buqatar sauyin rayuwa,kawaici kawai irin nata yasa basa tsomala baki cikin lamuransa,saidai sauyi wanne iri?,sauyin zai yiwu kuwa ta wannan bangaren,bayan kowa yasan ra'ayim almustapha wajen zabar matar aure?,kai hasalima kaf tarihin rayuwarshi bashi da muradi ra'ayi ko sha'awar yin mata biyu sam sam,bata manta yadda ya dinga qananun maganganu sanda yayansu adam zai sake aure na biyu,saidai a tarbiyyarsu sam babu musu ko jayayya kan duk hukuncin da jagoran gidan ya yanke,saidai su tayashi bin dokarsa ko hukuncinsa,bangaren anty maamaa ma tayi farinciki,don a dan zamanta da sumayya ta karanci halayenta,ta kuma san ta sha banban da halayyar su'ad,saidai itama tata fargabar ta yaua almustaphan baqin bature dan ra'ayin riqau mai doka da qa'idoji zai amshi wannan lamarin,gashi uwa uba baban yaja kunnen kowa da kada wanda ya sanarma almustapha maganar shi da kansa zai sanar masa,kome meye tasan na dan lokaci ne zai wuce,to baki dayansun masu biyayya ne gareshi,sannan babu wanda baida burin ganin farinciki cikin rayuwar mustaphan. Anty farida da huda kam da suka ji lamarin har wani ihun farinciki suka saki,kasa zama sukayi sai da suka dangana da baabaan suka yi masa godiya tamkar su ya yiwa,murmushi kawai yayi yasan lamarin na damun kowa,koma dai meye shi ya fisu farinciki da shigowar jinin sule cikin tashi zuriyar. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [23/02, 11:51] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 7⃣4⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *Allah S W T yana cewa* *KACE HAQIQA MUTUWAR DA KUKE GUJE MATA MAI RUSKARKU CE,SANNAN KUMA KU KOMA IZUWA GA MASANIN ABINDA KE FILI DA NA BOYE YA BAKU LABARIN ABINDA KUKE AIKATAWA* Ya Allah kasa ta ruskemu kana masu farinciki da mu,muna masu farincikin haduwa da kai ______________________________________        Gaba daya ta koma ta zama wata irin cikin kwana biyu kacal,duk wani kuzari da buri data ci na bikim zainab yayi nashi wuri,tsantsar tashin hankali take shiga a duk sanda ta tuna lamarin dake tunkarota,ko ya zata qare?,ko meye zai faru da ita wannan karo?,shine tambayar da take yawaita yiwa kanga,uwa uba Abdallah da ya tsaye mata a rai,ana ya gobe kamu nafisa ta iso gidansu,wani kallo take binta da shi tana tabe baki "Ke yanzu sai kace wadda zatayi auren fari kamar wadda yau zata fara zama da kishiya shine kika bi kika susuce haka?,a haka zaki qwaci kanki duk kin fafa zabgewa kina ramewa?,amma wallahi kin bani kunya" cewar nafisa,daga kai tayi tana kallonta tare da mamakin wanda ya gaya mata zancan "Me kike kallo na,munyi waya da amira ta gayan komai,ta kuma ce tana kiran wayarki amma kullum switchoff,na gaya mata zan shigo kanon tace na duba mata ke don Allah" ta sake fadi tana duban sumayya,fada ta zarce da yi maga,kuka ya qwacewa sumayyam,wau su don Allah ita kadai take gano abinda take ganowa,su basu hangen komai,ta gama fadanta sannan ta koma lallashinta,inda daga qarashe ita ta tilastata ta miqe tayi wanka tace zata rakata siyayya,jiki babu qwari haka ta shirya,ga zazzabin dake sakadarta a hankali,bugu da qari ga wani ciwon mara da ya saukar mata,wanda bata sani ba ko tashin hankalin da take ciki ne ya jawo shi oho.        Wani katafaren shago wanda ke saida kayan jiki na zamani nafisa ta kaisu,da idanu sumayya ke kallonta sanda take loda kayan tana zaba,harda wanda sumayyan yanzu ke amfani da shi tun wanda ta taba siya mata a uk har yau da shibtake amfani da yake ya karbeta,suna cikin mota take shaida mata yadda zata yi amfani da sauran,haushi ya kama sumayyam,yamzun suna nufim wami namiji zata yiwa hidimawa jikinta saboda za'a daura mata aure da shi "Wallahi da kin gayan ni kika  siyawa bazan barki ba,sabida asarar kudinki kawai kika yi babu abinda zanyi amfani da shi cikinsu" a fusace nafisan tace "Wallahi baki isa ba kinyi kadan,amfani da su wallahi ya wajabta a kanki" ganin yadda nafisan ta hasala ya sanyata yin shiru,saboda ko qwaqwaqwarar magana bata sonyi yanzu kanta zau fara sara mata.        A bangaren baabaa kuwa shirin daurin auren yake babu kama hannun yaro,kai kace wannan shine karon farko da za'a yi daurim aure cikin familyn baabaa prof din,ana ya gobe daurin aure suka baro abuja suka sauka gidanshi dake kano,saboda ya kasance kusa da abokinsa,duk wanda ya dace ya san da daurin auren babu wanda baabaa bai aikawa ba.        Duk abinda ake idanu ne nata sai ta koma 'yar kallo sabanin daa da itace amara,katunan daurin aure masu dan karen kyau tsari da tsada baabaa ya sanya aka buga ya baiwa malam wani shima ya raba wani,duk wanda yaji daurin auren ya zama na mutum biyu harda sumayya sai yayi mamaki,saboda kowa yasan babu ita a batun,da kansa baba ya sanya cikin kwanaki hudu aka yima sumayyan akwatu uku na suttura wadanda zata sanya kawai bawai lefe bane,lefanta yace sai almustaphan yayi kamar yadda ya yiwa su'ad,kaya ne masu kyau da tsada dinkakku,kama daga shadda laces atamfa material sa sauransu.         Da ido kawai take binsu lokacin da aka zo yima amarya zainab lalle,almara kawai take ganin komai,wai ita za'a daurawa aure nan da kwana uku?,abinda ko cikin mafarki bata taba hasashensa ba,qememe taqi bada hannunta ayi mata komai,anty dije tace a barta kada a matsa mata,tasan cewa akwai lokacin da ita anty dijen da kanta zata sanya ayi mata kuma dole ta bada hannunta.         Ana ya jibi daurin aure kwana tayi tana kuka saboda nasihar da mama tayi mata,ta gaya mata duk wanii motsi da zata yi wanda bai dace ba tamkar ta watsawa mahaifinta qasa a ido ne,ga gidan ya fara amsar baqi,haka ta tashi washegari da zazzabi da ciwon kai amma haka ta dinga cijewa tana shiga jama'a,wanda hakan bai amfana mata komai ba face sake qaruwar ciwon kanta.           Bayan sallar isha'i tana kwance cam uwar dakan maman kan abun sallah,hasbunallahu wa ni'imal wakil kawai take ambata babu qaqqautawa saboda yadda taji nugun zuciyarta na daduwa,sallama taji anayi tsakiyar gidansu wadda ta sanyata miqewa dungur gur ta zauna tanq raba idanu kamar wadda aka ritsa da wuqa a maqogaro,muryar abdur rahman ce,sai gabanta yaci gaba da faduwa ta fashe da kuka qasa qasa tana cusa kanta tsakanin cinyarta.          Daga airphort direct gidan ya zarto ko gida bai nufa ba sakamakon mummunan labarin da ya sameshi ta bakin bahijja,kai tsaye aka yi masa iso falon malam wanda shigowarsa gidan kenan,a mutunce suka gaisa saidai kallo daya malam yayi masa yaga sauyi tattare da yanayinsa "Ina fata lafiya malam abdur rahman" cewar malam din,kai ya girgiza cikin sanyin murya "Malam,na jima ina neman yarda da amincewar sumayya tun kafin rasuwar yaya mukhtar har kawo yau din nan,na fara samun hadin kanta a kwanakin nan,saidai ta nemi alfarmar na bar maganar har ka kammala aurar da zainab,kwatsam sai jiya na samu labarin wai za'a aurar da sumayya malam haka ne?" Kai ya jinjina kafin yace "Wannan haka yake abdur rahman,zan aurarwa dan aminina sumayya,sam banyi tunanin kana ci gaba da neman sumayya ba abdur rahman,ban kawo haka a raina ba" sosai ya girgiza da jin amsar malam din,idanunsa suka kada ya dubi malam din "Malam ni nafi cancanta da sumayya,ka yimin alfarma ka aurar min da ita" cikin tausayawa malam din ke dubanshi "Kayi haquri abdur rahman,wannan wanda zan baiwa sumayya wa familynsu sunfi qarfin na musu haka,idan da wani ne can daban babu abinda zai hana na maida auren kanka,amma zan gaya maka kadan daga labarin muntari,zan gaya maka kadan daga cikin waye muhtari a gurina" warware masa yayi DANGANTAKAR dake tsakaninsa da baabaa prof,dangantakar kuma da suke fata da burin ba zata sake katsewa ba har ABADAN,wanda hakan suna burin ya zama hanyar ci gaba da yado da qarfafa zumunci da dangantakarsu.         Cikin gamsuwa abdur rahman yakw gyada kai,babu shakka irin wannan dangantaka dake tsakanin malam da muhtari ko shine idan yana da diya abinda zai iya faruwa kenan,ba zaiso ya zama silar datse wannan kakkaurar tsohuwar igiya ba da ka qullata tun duniya na kwance,tun basu gama sanin su waye su ba kawo yau,saidai rabuwa da sumayyan ba abu bane mai sauqi tattare da shi,wani mugun ciwo ne da zai ci gaba da illata shi "Shikenan malam,ina muku fatan alheri,saidai mu a tayamu da addu'a,Allah ya bamu haqurin jurewa" ya fada cikin karyewar murya "Allah ya yi maka albarka,ya sanya juriya a zuciyarka,ya musanya maka da wadda ga fita alkhairi a gareka" "Amin malam,na barka lafiya" ya fada yana mai miqewa,cikin tausayawa malam din ya bishi da kallo,har ya kai qofa ya kirashi ya dawo ya tsugunna kansa a qasa "Abdur rahman" "Na'am malam" "Idan har babu takura kuma ba zaka damu ba,mai zai hana ka nemi halimatu 'yar uwar sumayyan,a tunani kamar zata iya maye maka gurbinta" "Indai malam kana ganin hakan yayi daidai bazqi haifar da wata matsala ba na karba,ina kwadayim zuriyarka ne malam,na tabbatar akwai alkhairi ga dukkan wani d'aa da ya fito daga gidan nan" murmushi malam din ya saki cikin jin dadi "Kayi tunani a nutse,kada kayi abinda kasan zaka takura,idan halima tayi maka ka dawo zan baka ita,idan bata yi maka ba babu komai zan biku da kyakkyawar addu'a" "Ta yaya malam zanqi jininka,halima jininka ce jinin sumayya,na karba malam,kuma in sha Allahu a gobe zan bada sadakina nima kada itama na rasata"murmushi ya subucewa malam,sosai ya sanya musu albarka tare da jan doguwar addu'a ta fatan alkhairi a garesu baki daya,yace yaje sitting room a bude yake zai turo masa haliman,miqewa yayi kansa a qasa yana yiwa malam din godiya,abun mamaki cikin qanqanin lokaci tashin hankalin daya tsinci kamsa kaso dari sai yaji babu hamsin ciki,ya taka ya fice sitting room din gidan yana jiranta.       Malam yana daga falon ya qwalawa haliman kira,gama cire lallenta kenan taji kiran malam din,ta goge hannum nata ta sanya hijabinta ta shiga dakin "kije sittin ro abdur rahman na jiranki" jin maganar tayi banbarakwai sai ta daga kai ta dubi malam "Ni ko yaya sumayya dai?" Daquwa ya mata "Dan gidanku na kasa gane sumayyan sai ke zan kira?,ke nace ba sumayya ba" bata sake cewa komai ba ta miqe ta fito ta nufi sitting room din gabanta na faduwa.       Tsaye yake tsakiyar sitting room din hannayensa goye a bayansa ya zubawa qofar shigowar idanu,tana sallama suka hada ido,karom farko taji wata faduwar gaban da bata taba jin irinta ba don ta kalleshi,idanu ya zuba mata yana amsa sallamar,sai yake hango yanayinta da sumayya muraran,ya taba kula da hakan shekarun baya amma ba kamar yanzu ba,ga mamakinsa murmushi sai ya subucewa lebansa,ya zuba mata ido yana ci gana da kallonta har ta qaraso gabanshi,cikim diriricewa tace "Ya abdur rahman gani.....malam yace wai.....kana jira na" "Bismillah zauna" babu musu ta taka ta zauna kan daya daga cikin kujerun,gabanta ya iso a hankali ya zube a gabanta wanda hakan ya sake haddasa mata faduwar gaba da,sai ta jita ta takura sabida basu taba zama gab da gab irin haka na,duk a qasa yake zaune a gabanta amma yana kusa da ita "Halimatus sa'adiya,malam baice miki komai ba?" Kai ta gyada da sauri sabida ta gaji da yadda gabanta ke faduwa,murmushi ya dan saki,wato shi zai yiwa kansa yaqi kenan ko?,daga idonsa yayi ya zubesu a kanga,sai ta janye nata idanuwan "Halimah kina sona zaki iya aure na?" Taji tambayar babu zato na tsammani,ido ta zaro tana dubanshi,kasa cewa komai tayi har sai da ya maimaita,bakinta na rawa tace "Yaya abdur rahman.....yaya sumayya.....ita yaya sumayya fa?" Murmushi ya saki "Bakya gidan ne?,bakisan malam ya bata wani ba?,ni kuma a yanzu malam ya bani ke zaki iya aure na?" Shiru tayi gabanta na faduwa,yayin da kunya ta kamata ta sadda kai qasa qwalla na taruwa a idonta,hakan taji tsoro ya kamata,malam zai aurar da ita kenan itama,jin shiru ya sanyashi sanya yatsunsa ya daga fuskarta,kallo daya tak yayi mata ya fuskanci ta karbi lamarin duk da bata bayyana ba muraran sabida kunya da tsoro "Kice wani abu mana halimah,koda baki sona ki amince min zan saki ki soni kinji,kada nayi asarar zuriyar malam baki daya ace na rasa ko daya,da wallahi barin garin zanyi" dariya taso qwace mata saboda yadda ua shagwabe mata,kunya ta lullubeta saita qudundune kanta cikin hijabi,dariya ya saki "Iyeeee,ko baki ban amsa ba ma na gano a bata,ashe dai har kunyar abdur rahman din akeji,lallai na samu karbuwa,koba haka bane?" Shiru tayi taqi amsa masa "Shikenan tunda ba zaki ce komai ba bari na haqura na tafi,kuma ba zaki sake ganina ba,zan kuma gayawa malam baki amince ba sai na haqura" ya fada kamar mai tafiyar,da sauri ta daga kanta tana shirin cewa wani abu,sai ta ganshi tsaye a gabanta,kunya ta sake kamata tayi qasa da kai suna dariya baki daya.        Komai na Allah ne haka komai nufin Allah ne,sai gashi ya shantake har qarfe tara da rabi yana gidan,halima akwai kunya saidai alamu baki daya sun nuna ta karbeshi,sai goma saura sannan yayi mata sallama,ya zuba hannayensa a aljihu yana dubanta "Ina wayarki" cirota tayi daga hijabinta,karba yayi yana qoqarim cire layin ciki ya zura a aljihunaa sannan ya ciro daya daga cikin layukansa ya saka mata yana cewa "Gashinan,ni kadai zan dinga kiranki kafin na siya miki wani layin,ina da kishi bana son wani ya sake jimin muryar mata ta,sai da safe muje na rakaki" har bakin qofar shiga tsakar gida ya rakata sannan ya juya ya fice,zuciyarsa fes yana mamakin lamarin Allah,ya riga ya qaddara sumayya ba matarsa bace shine masanin GAIBU mai rubuta QADDARAR BAYINSA,Allah kenan mudabbirul amri mai jujjuya al'amura a lokaci da baka zata ba,ya shigo gidan cikin tashin hankali da jimami ya fita cikin farinciki da annushuwa,babu abinda zai cewa dattijon arziqi mai karamci sai godiya tare da yi masa fatan kyakkyawan qarshe.         Tana shiga tsakar gidan taga shigar zainab dakin mama wadda ta fito daga kitchen ta dafawa sumayya tea,da sauri tabi bayanta don fatinciki ke cinta,bata da 'yar uwar da take sharing sirrikanta da ita kamar zainab din,tsaye ta taddata tama fifitawa sumayya tea din,sam halima bata kula da sumayya dake dakin ba ta dane bayan zainab wanda hakan ua sanya tea din hannunta tangal tangal zai zube "Wayyo zainab,yau Allah nima ya bani yaa abdur rahman,zainab mallam ya bawa abdur rahman ni,a gobe nima zanbi sahunku zan zama matarshi" sak sumayya tayi tana dubanta,tun dazun take jira taji wani abu daga wajen abdur rahman din ko malam amma taji shiru,gani tayi zainab tayi shiru kawai saita sake kallonta "Baki ce komai ba ya kikayi shiru" da idanu tayi mata alama da wani na gun,ta wurga idonta saita hangi sumayya,da sauri cikin jin nauyinta ta juya zata fice,cikin kasalalliyar murya tace "Zo yaki halima" cikin jin nauyinta ta iso inda take ta zauna,ta karbi tea din da zainab ke miqo mata ta aje gefanta "Meye na jin kunyata halima kamar wadda ta aikata haramci,wallahi har ga Allah naji dadi da wannan hadin da malam yayi,sannan abdur rahman ya cika mai sonmu tsakani da Allah da son iyalan gidan nan,ki saki jikinki ni yayarku ce har abdur rahman din ba tun yau ba dama,ki manta da cewa abdur rahman ya raba sona,Allah shine dama yasan abinda ya boye shi yasa bai taba darsamin soyayyarsa ba ko qanqani,illa ganin girma da mutuncinsa da nake,babu wani abu da ya isa shiga tsakaninmu,dan uwa ba wasa bane,idan banda Allah babu wanda ya isa yayi maka kyautar dan uwa,Allah ya baku zaman lafiya ya tabbatar da alkhairi" "Amin" suka amsa baki daya,taji dadin addu'ar sumayyan sosai,to tsakanin daren zuwa wayewar gari sun sake wata qwaryar qwaryat shaquwa,kusan kwana sukayi suna waya sumayya na jinsu,wadda tuni ta goge duk wani abu da ya shafi abdur rahman daga wayarta,tayi lamo bisa gado,kewa ta kamata,ta dinga matse hawaye tana tuna mukhtar,mutuwa mai tonon silili,idan banda mutuwa ta dauke mata shi da tuni sun jima da shimfida sabuwar rayuwa,wataqila ma da tuni ta sake haifa masa 'ya'ya,saidai tsarin Allah shine tsari,(Allah kasa mu dace ka cika mana burikanmu kasa mu cika da imani don alfarmar sayyadina rasulullahi S A W)amin. Washe gari kawu da wansa da qaninsa mahaifin abdur rahman sai gashi da safe yazo nemawa abdur rahman din auren halima,wanda ya bawa malam dariya,yace ai da abdur rahman da halima duka nashi ne,ko basu zo ba sai ranar daurin auren ya riga ya bashi ita,a nan kawun yayi godiya qwarai suka tafi,a nan suka bar abdur rahman ya sake baje kolin soyayyarshi,sai da aka soma nemansa a asibiti sannan ya tafi,binsu sumayya take da kallo,wato bawa bai gujewa Qaddararsa. *KUNDIN QADDARA* Rana bata qarya saidai uwar diya taji kunya inji malam bahaushe,wannan haka yake,domin yau take juma'a wadda ta kasance rana ce mai girma da muhimmanci da kuma dumbin tarihi wajen malam sulaiman gombe,wanda zai aurar da duka diyoyinshi mata da Allah bashi cikin mutunci da rufin asirj,wanda abun farinciki ne da godewa mahalicci a irin wannan zamanin namu mai cike da rudi da abubuwan firgici ga 'ya'ya mata Allah ya yi maka baiwar aurar da diyoyinka mata baki daya hannun nagartattun maza da kake saka musu ran zasu musu riqo na mutunci,ta hannu daya baabaa prof shima cike yake da farinciki,domin kuwa tun qarfe tara ya iso wajen a maimakon qarfe goma da za'a daura auren. Daga cikin gida kuwa tuni zainab ta yi wanka kwalliya irin ta amare,tana sanye da wani lace mai azabar kyau wanda sumayya ce ta siya musu,haka amarya halima na sanye cikin shadda wadda ready made ce abdur rahman ya aiko mata da ita,tayi mata kyau ainun,dukkaninsu idan ka dubi fuskokinsu qunshe take da fara'a sabanin sumayya dake kwance ko wankan ma bata kai ga yi ba,binsu take da idanu tana rayawa cikin ranta,kowa yana rayuwar farinciki banda ita,ita kadai ke fadawa halin jarrabawa cikin yaran gidan nasu?,nafisa ce ta sanyata a gaba wanda tilas ya sanyata tashi tayi wanka ganin tana son qara mata ciwon kai,ta fitar mata da wani dan banzan lace cikin kayan da aka kawo mata dinkin skert da riga mai dogon hannu,kamar yadda ya qawatu lace din haka ya qawatata ta,babu abinda ta shafa banda turare mai da hoda amma sai ta fito cas gwanin sha'awa,fuskar ta tayi fayau ta dashe tare da ramar da tayi,naji ance amarya daban take ko batayi kwalliya ba,to kusan hakanne ya tabbata ga sumayya,komawa tayi ta kwanta abinta,don hayaniyar data cika gidan kadai ma damunta take bare ta waje,wanda tuni layin ya soma dinkewa,tana iya jiyo kwaroroto da muryar maroqa iri daban daban,sun baje hajarsu kowanne yana kwasar rabonsa,basa wasa da bikin daya shafi gidan professor mukhtar muhammad adam,don idan kazo a sa'a wani daga ranar ya daina roqo sai ya samu jarin da zai isheshi sana'a,ballantana yau da sunan almustapha ya bayyana baro baro na cewa shi zai sake aure. Cikin qanqanin lokaci layin ya cika ya tumbatsa da jama'ar baabaa prof,jiniya iri iri ke tashi wadda ta qusoshin gwamnati ne da jami'an tsaro,kowa yana iya jiyo yadda daurin auren ke kayawa sakamakon maroqan dake bayyana dukkan abinda ke faruwa a wajen,auren zainab sulaiman gombe aka fara daurawa da angonta abulkhairi muhammad bala kan sadaki dubu talatin,sannan aka daura na halimatus sa'adiya sulaiman gombe da angonta abdur rahman Ahmad yusuf kan sadaki naira dubu hamsin,daurin auren qarshe shine na doctor muhammad almustapha professor mukhtar adam gombe wanda aka daura kan sadaki naira dubu ashirin,sai kuma kyautar mota duka cikin sadakinta take,daidai kunnenta nafisa tazo ta rangada guda,jin gudar take kamar ana zaqular qwaqwalwarta,saita dunqule ta cure waje daya,ta saki wani marayan kuka wamda bai fidda sauti,ita kadai yasan me take ji cikim zuciyarta,shikenan yau din ta sake zama mallakim wani bayan mukhtar?,wanin ma da baisan daraja ko qimarta ba,ya zata kaya musu?,ya zata kasance?,bata da amsar wannan. Kusan ranar haka ta wuni,da daddare ta dauki kayan sawarta kala uku ta gudu gidan anty dije,a can ta barje kukan ta son ranta,saboda a can babu dama saboda idon mutane,itama antyn batasan tana nan ba,sai wayar mai gadinsu ta ara ta gayamata don kada su nemeta,washe gari aka sha yini sosai,duk abin nan da ake sumayyan na gidan anty dijen,haka ta wuni kwanciya don mai gidan baya nan,ita kuma antyn a can gidansu ta kwana,sai gobe zata dawo idan an kai amarya,halima itama sai next week za'a kaita,kafin nan an kammala yi mata tata siyayyar. ******* ****** ******** Zaune take a uwar dakan anty dije wadda jiya bayan kai amarya ta dawo gida,tana ta faman shirya kayansu cikin trolly abinta,sumayya na zaune daga bayanta,sanye take da doguwar riga 'yar kanti mai qaramin hannu,kanta ba dankwali sai gashinta mai baqi da santsi data hade cikin ribbom,jingine take da kujerar dake dakin qafafunta amiqe,hannunta riqe da cup din tea wanda tun dazun aka hado mata shi har yana gab da hucewa bata yi masa kyakkyawan shaa ba,idanuwan nan a kode tamkar danyen nama kamar yadda fuskarta take a kode alamun ko yaushe cikin kuka take,sam anty dije taqi bata fuskan kawo wani qorafi ko wata magana kan auren,tunda dai an riga an daura ta riga data zama matar almustapha,abu guda ne kawai yanzu a gaban anty dijen yadda zata shirya diyar tata fes ta iya shiga kowanne bigire na rayuwa,abinda ke sake karya zuciyar sumayya yadda taga ita antyn ma murnarta take,hannunta tasa ta shafa gashinta hadi da lumshe ido tana kiran sunan Allah qasa qasa,ita kadai tasan meke yawo cikin kwanyarta,kamar ta cire qwaqwalwar ta huta haka take ji,waiwayowa antyn tayi tana cewa "To zaki bimu abujan ne ko kuwa sai munzo daukar amarya?" Mai neman kuka ne aka jefeshi da kashin awaki,aisai kawai ta saki kukan ta sosai ta dire cup din tea din,baki anty dije ta kama dariya na subuce mata "La'ilah,ku jimin yarinya,wai ita bilhaqqi da gaskiya bata son almustapha,mutumin da ake so ko kallon arziqi ya yiwa wasu,to wallahi saidai kiyita kukanki kada ki fasa bazan lallasheki ba,tunda kinqi jin lallashi ballantana shawara,da kinsam tun usilu ba zaki iya biyayya wa su malam ba ai da kin gaya musu tun sanda suka tasamma hada auren,sai yanzu saboda yankan baya zaki tasani gaba da kuka me zan miki,haka zakije ki yi gaban su'ad din,tabdi wallahi da kuwa kin jawa kanki,idan kin gama kukan kya tashi kiyi abinda ya dace,don tun jiya malam ke tambayarki bai gqnki ba zai damqa miki sadakinki" anty dijen ta juya tana ci gaba da aikace aikacenta har sanda laila ta shigo da wayar sumayyan hannunta tana fadin "Anty amira ce a layi" ta miqawa sumayyan,harara ta danqara mata hakan ne ya sanya anty dije karbar wayar ta kara a kunnenta bayan ta sanyata a handsfree tana fadin "Ai amira kema ta shafeki ba zata amsa wayarki ba,ke da jin muryarta sai bayan wani lokaci"dariya ta qyalqyale da ita " don Allah anty matsa kusa da ita nayi kata waqar ta zama ta zama,nima haka ta yimin,ranki ya dade amaryar yayanmu ayi mana haquri,amma dai ya musty ne ya riga ya zama mijin sai haquri,anty barta ko bata yi magana ba yanzun zata yi idan muka zo sayan baki"dariya suka sanya baki daya,hakan ya sake qular da zuciyar sumayya,sai ta miqe ta fice tana kuka muraran kamar wata qaramar yarinyar,binta anty dije tayi da kallo tana dariya,har yau da sauran quruciya sosai tattare da sumayyan,gata nan a zahiri ta bayyana. Tunda aka daura auren ranar juma'a baabaan bai bar kano ba har zuwa yau litinin,misalin qarfe takwas na dare bayan ya gama cin abincin dare ya dauki wayarsa ya soma lalubar musty man. Dawowarshi kenan daga asibiti,yau a gajiye yake saboda mutum uku ya yiwa c.s,kayan jikinsa kawai ya cire ya rataye suit dinshi a inda yake rataye kayan da za'a wanke masa,ya zaluqo daya daga cikin towel daga ma'ajiyar towel ya daura sannan ya shiga wanka,kwanciyarsa yayi luf cikin ruwan wankan mai azabar dumi da qamshi,duminsa na ratsa kowacce gaba ta jikinsa,idanunsa na alumshe sai ka rantse da Allah bacci yake saidai idanunshi biyu,tunani ne kala kala kan kwanyarsa yake yawo,ya soma gajiya da zaman wannan hotel din wanda kusan a ciki yake rayuwa,duk da yana da gida mallakinsa cikin qasar,saidai hakanan yafi sha'awar zamam hotel din yana ganin kamar ya fi masa sauqi,idan gidan ne dole sai ya nemi ma'aikata da zasu zauna cikin gidan su kula masa da tsaftarsa da komai da komai wanda shi ba kasafai yake son ma'aikata haka barkatai ba,musamman a qasar da ba taka ba,tun yana cikin bayin ya dinga jin rurin wayarshi,data katse wani kiran ke shigowa,sai ya saki tsaki ya sake gyara kwanciyarsa ba tare da koya bude idanunshi ba bare yayi haramar fitowa,ga tsammaninshi su'ad ce don kimanin sati guda rabon da ya nemeta,ta kirashi dazu zai shiga thiather ya dakatar da ita,saboda abu na farko data fara da shi shine mitan ya watsar da ita sabida ta koma zata qarasa karatunta,shikam a yanzun yana ganin matsalarta ce,shi ya gama da wannan issue din,sabgogin dake gabansa ma kawai sun shasa masa kai,sai da ya kammala wankansa a nutse sannan ya fito ya daura towel dinsa a qugu wanda hakan ya fito da dukkan suffa da zatinsa na cikakken namijin da ya amsa sunanshi,ya qarasa wani sashi daban ya daura alwala ya fito. Zai gifta wayar kenan ta sake ruri,ya waiwaya kadan ya dubeta sai yaga sunan abbu na yawo saman screen din,sunan da ya sanyawa baabaa prof kenan,da hanzari ya fasa abinda yake ya isa ga inda wayar take ya daga cikin girmamawa tamkar yana gabanshi cikinnn nutsuwa da sanyin murya "Barka da warhaka" ya fadi "Barka kadai,ina ka shiga ne haka tun dazun ina kira ko kana asibiti ko company?" "A'a wanka nake" ya fada a taqaice,don a tsarinsa bai fiya doguwar magana ba,kadan ce mai ma'ana "To madalla" "Lafiya kuke baabaa ya kowa da kowa?" "Kowa lafiya qalau yake almustapha" "Masha Allah" "Ammm,almustapha kawai tsarin zuwanka gida ne nan kusa?" Dan jim yayi kafin ya amsa "A'ah,saidai ko idan kana son ganina ne?" Yana mamakin yadda yake da kaifin qwaqwalwa da cimma abun tun kafin ka kammala bayaninka,sau tari suna fara magana da baabaan yake gane mai yake da buqata tun bai qarasa ba "Tabbas,ina buqatar ganinka,wani muhimmin batu ne ya taso ma rayuwarka nake so mu gana a kai,yaushe kake da chance din zuwa?" Duk da maganan ta dan sanyashi a duhu amma bai da niyyar tambaya "Yaushe kake son gani na?" "Eh to,ko kamar nan da sati biyu haka" "Sati biyu masu zuwa ina zuwa da yardar Allah" "To masha Allah,Allah yayi maka albarka,sai kazo" "Amin,na gode" a hankali ya ajjiye wayar yana binta da kallo,zuciyarsa na son sawwara masa muhimmin batun da baabaa yace ya taso wa rayuwarshi,duk iya hasashensa bai canka ba,hakan ya sanya ya dage kafadunsa biyu na rashin damuwa ya nufi inda ya ajjye kayan shafarshi a tsare kamar wata mace,komai nashi mai aji da tsada irin wanda maza ke amfani da shi,yana shiryawa yana tunanin yadda tafiyan zata kasance,dama yana son zuwa daya daga cikin asibitocinsa dake kano kwana biyu bai leqa yaga maike faruwa ba shu da gidan marayunsa,duk da yana da wakili dake gano duk abinda ke tafiya kuma a kai duk abinda ake da buqata wuraren,amma bai saki komai ba balle kowa yayi mishi yadda yaga dama,mutum ne shi mai doka da qa'ida baison kuma a saba masa ko a taka mishi kamar yadda bai taka dokar kowa. Yana shiryawa yana kiran lambobin da ya saba kiran idan yana buqatar abinci,duk da sun san kusan cimarsa ta dare,ba wani abu mai nauyi yake ciki ba,a ladabce suka amsa buqatarsa ya kashe wayar,wanda kamar jira ake ya kashe wancan kiran wani kiran ya shigo,su'ad ce da layinta na america,yana kallon kiran yayi banza da shi har sai daya gaji ya katse,haka ta dinga kira har ta hada masa wajen miscal biyar,wanda tuni ya maida wayar silent don baison hayaniya,daga qarshe saqon tex ya shigo yasan kuma daga ita ne,baibi ta kai ba ya share ya tada shafa'i da wuturi,da wuri yake son kwanciya yau ya huta sosai saboda gobe yana da meeting da ma'aikatan companynsa na saqar abaya. To masu karatu yanzu fa kusan aka soma ko?,saidai gobe kumin uziri idan ina da sabga idan kun samu to ba lallai ya kai na yau ba,idan kuma kunji shuru sai uziri,kasancewar duk sanda kuka ji shiru daga wajen marubuci uziri ne ke kama shi irin uzirin dake kama kowanne dan adam,babban nauyi marubuci keji cikin kansa da qirjinsa idan ya soma rubutawa jama'a labari,baya jinsa fayau sakayau har sai randa ya kammala,Allah ya bar zumunci. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [23/02, 11:51] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 7⃣5⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *ALLAH S W T YANA CEWA* *ALLAH BAYA JINKIRTAWA WATA RAI IDAN AJALINTA YAZO* ______________________________________         Wannan karo anty dije daga ita sai yaranta suka koma abuja cike da kewa,kowa cikinsu sai yaji babu dadi,kasancewar sumayyan ta riga ta shiga jikinsu.          Sati guda malam ya yiwa baabaa maganar ya za'a yi da jeran sumayya,ce masa yayi babu ruwanshi wannan ba huruminsa bane,murmushi kawai malan din yayi "Ku qarata kai da 'yar taka" ya fada yana dariyaanty dije ce ta matsa kan ko daki daya abasu su saka mata kaya,tilas baabaan ya sanya aka bude daki daya dake saman aka basu shi suka saka kayan gadon da malam ya siya mata,idan baku manta ba gidan baabaan na da sashe biyu ne,ko wanne sashi akwai sassa a ciki,sashin daya barwa yaran nashi daya na wansu ne adam da matan shi,daya nasu mahomud ne da mus'ab,daya na almustapha ne,kowanne sashi yana dauke da balcony sama da qasa,sannan babban falo da dakunanan bacci manya manya wanda zasu iya cinye kayan gado set biyu,bedrooma din cikin corridor suke wanda ke hagu da daman falon,sai ka fito daga ciki zaka samu falon,sai qofar kitchen daga can gefe wanda qofa daya ce amma idan ka shiga zata tadda qofofin kitchen biyu biyu,akwai wata qofar daban da zaka fita vantilation,kusa da kitchen dining area ne,saman babban falo ne shima da dakunan bacci guda uku,daya ne makeke wanda a ciki mustaphan yake,kowanne sashe nada girma da yalwa,duk yadda ka kai ga son jin dadinka.         Dakunan baccin duka guda biyun again dake qasa baabaa yasa aka shirya mata su ba tare da sanin kowa ba,illa ya yiwa kamfani waya ya basu adress,royal beds ne set dinsu masu azabar kyau da tsada,hakanan kitchen din aka zuba qawata shi da dukkan wani kayan qawa da kayan amfanin buqata na kitchen,falon ma ba'a barshi haka ba,sai da ya sanya aka sauya duk wani abun amfani,a taqaice dai tashin farko sashen ya sake sauyawa sosai,duk da dama sashe ne wanda ya tsaru ya qawatu tun da can,yafi kowanne sashe kyau da qyale qyale,kasancewar mai sashin mai son tsafta da gyara,yayin da matar sashen ta zama mai dagawa da son nuna iyawa da kuma qaunat ganin tafi kowa.        Ba wai don almustapha bai da wani gida ba,yana gidan daya kusa a qalla shekara hudu ana gininshi yana narka masa kudi,har rade radi aka dinga yi a rean cewa da qyar idan ba gidan wani shugaban wata qasar vane,babu abinda bai zuba ba a cikin gidan,dai dai da cokali gidan baya buqata,hatta da kayan sangawa baki daya cupboard din gidan a cike take,wani irin tsari aka yi masa mai bala'in kyau da daukar hankali,hatta da qasashen da suka ci gaba samun irin wannan gidan sai an tona,to saidai babu wanda yasan da gidan do ba wanda ya gayawa,shi wani irin mutum ne da bai fiya son fadin abubuwan da yake yi ba,da fari yaso maida su'ad ciki,saidai irin rayuwar da yake so ya shimfida cikin gidan ba ita ta shiryawa yi ba,rayuwar soyayya da kulawa zalla tsagwaronta yakeson shimfidawa cikin gidan wanda dama ya ginashi ne don ya morewa rayuwarshi da arziqin da Allah ya mallaka masa,duk sanda ya kalli gidan yana sanyashi nishadi da walwala,ya zuba ido yana jiran yaga ranar da su'ad zatayi daidai da tsari da ra'ayinsa,ta shiryar karbar irin rayuwar da yake so,to a lokacin yake saka ran maidata gidan wanda har yanzu hakan bata samu ba,a qalla kusan watanni shida kenan da kammala komai na gidan,saidai lokaci lokaci idan yana buqatar kebewa ko hutawa yaje ya wuni ko ya kwana daya ya dawo,cikin dribobinsa ma mutum daya kacal yasan da gudan kasancewar shi ke kaishi.   *******  *******    *******       Duk yadda taso kauda da damuwa cikin ruhinta ko don saboda malam abun yaci tura,a yadda take yaqe da qoqarin zama cikin mutane duk da gidan nasu yanzu sun sake raguwa,daga ita sai mama,abdallah ma yaqi zama kasancewar gidan yayi shiru da yawa,ya gudu wajen yaya yahanasu don acan yake baje kolin tabararsa yayaan da su jamila na biye masa,ga yara 'yan wasa kamarshi,kana duban sumayyan kasan akwai kwantacciyar damuwa a zuciyarta,a hankali ciwon marar ke sake matsanta mata wanda ta kai ga cewa har sai ta sha paracitamol wani lokaci yake barinta tayi bacci.          Sati guda cif da daura aurensu malam baice mata komai ba,itama bata tambaya ba bata ma damu taji komai ba,addu'a ma take Allah yasa tayi zamanta a haka,kan me zata damu?,ta damu da mijin da batasan haqiqaninshi ko wani abu nashi ba?,da zaiyita zama bai nemeta ba ma ita haka take so,ko banza sunanta matar aure ba za'a matsanta mata kan aure ba tunda akwai igiyar wani a kanta.       Ranar da suka cika kwana takwas ranar litinin abdur rahman zaizo daukar tashi amaryar,tun rana halima ke faman shiri duk da cewa jikinta a sanyaye yake,kusan sumayya ce qarfin shirin duk da ciwon marar dake tsunkulinta haka ta dinga shirya ta tana mata hira da gaya mata abubuwa masu amfani duk don ta saki jikinta,zuwa sanda aka idar da sallaf magariba ta kammala shiryata tsaf sai tashi qamshi take mai sanyi wamda duka cikin taskar hadaddiyar humrar sumayyan ce,sumayyan ce ta raka haliman har zuwa falon malam,gabanshi suja zauna kan haliman a duqe,a hankali malam din ya dinga yi maya nasiha mai narjar da zuciya wadda kusan dasu yake baki daya,hatta da sumayyan sai data yi qwalla,ta sake taqinin duniya ba'a bakin komai take ba,hakanan mace bata da wata riba a rayuwa indai bata yi biyayya wa mijinta ba,ta ina zaki ci rina bayan aljannarsa na qasan qafarki idan kika saaba masa ya take fa?,da qyar halima ta iya roqon gafarar baabaa sabida kukan da yaci qarfinta,tashi sumayya tayi ta basu waje jin baabaa na yiwa abdur rahman izinin shigowa wanda ta tabbatar shina nasihan baabaa zaiyi masa,fuskarsa sai qyalli da annuri take,yana sanye da wata danyar shadda fara qal dinkin 'yar ciki da babbar ruga,kana kallonshi kaga ango sak,dakinta ta shigi ta samu gefan gado ta zauna tana fidda hawaye bayan taji tafiyarsu,shikenan,kowa ya fashe ya barta,kowa ya tafi wajen nashi masoyin,saura ita,ko ya zata qare?(nidai huguma nace Allah A'alamu).       Babban dakin taron wanda ke cikin qasaitaccen kamfanin na MM dauke yake da ma'aikata wanda a qalla sun doshi su arba'in,manyan ma'aikata daga qasashe daban daban wanda ya qunshi naijeria,pakistan,china,gahana da india,kowanne zaune cikin tsari kan tashi kujeran wanda suke a jere hagu da dama,tsakiya kuma dogon tabureni wanda kana kallonshi kasan cewa kamfanin da suka qerashi ba qaramjn fasaha garesu ba,shine teburin wadan nan kujerun da ma'aikatan ke kak,gaban kowanne dauke da ruwa da lemo,saidai baki dayansu ba wannan ne gabansu ba,sun tattara hankalinsu ne kan ogansu wanda ke hakimce a kujefa qwaya daya tal dake tsakiyar teburin,sanye kowa cikinsu yake da suit baqi da fari sabanin shi dake sanye da tashi tsumammiyar suit din ruwan sea blue mai dan turuwa,ta sake fidda sigar kyawunsa da zatinsa,wadda kana kallon suit din kasan tasha banban data duk wani mahaluqi dake dakin taron,jikinsa na jingine ne da  makarin kujerar yaja juyawa kadan kadan hagu da dama tamkar mai hutawa abinsa,saidai ina,bayani yake cikin gamsarwa da hikima da fasaha ta iyawa da qwarewa a kasuwanci,kusan sun gama tattauna komai conclusion yake musu,tafi kowannensu ya sanya bayan ya gama yana rufewa da idan akwai mai tambaya yayi,minti uku ya bada babu wanda yace komai kasancewar ya gama hadiye komai cikin jawabansa,ya duba agogon fata na kamfanin gucci dake daure tsintsiyar hannunshi,awa biyu ya rage jirgin fly emirate da zaibi zuwa nijeria,hakan ya sanyashi miqewa,wanda ke tsaye kusa da shi cikin baqin kaya da baqin glass ya soma tattare dukkan wasu files da takardu ya dauka masa yayin da ya bishi a baya zuwa office dinsa.       Yana gab da shiga elavator ya jiyi muryar hamza na qarasowa,hakan bai sanya shi ya tsaya ba ya shige ciki abinsa,da dan gudu hamzan ya qaraso ya shige ta rufe da su bayan ya amshi files dinsa dake  hannun wannan mutumin,harara ya juya ya gallawa almustapha "Maan,nifa banson wulaqanci da iskanci,nidin macace da zaka wani jaamin aji,idan ban narka maka dundu ba kace ba nine hamza ba" hararar shima ya watsa masa "Haka kawai don ka zubda mana mutunci sai ka dinga ma mutane wannan kiran mafarautan kaman zan bar garin,sai kace bakasan inda office dina yake ba,baka ganin yadda ka taramin jama'a suna kallona wadancan yaran sun wami qwalolowa mutane idanu kamar zasu cinyeshi danye" dariya hamza ya bushe da ita ya dunqule hannu ya daki kafadarsa yana fadin "Shege man,ashe kana kula,banda abinka kai da keson yaran wata qasar mai zai hana cikin indiyawan nan ka qara da daya" ya fada cikin salom tsokana sanda akwakun qarawa tafiya hanzari (elavator) ta iso da su block din da ofishinsa yake,bai kula shi ba shi kuwa hamza yabi bayanshi yana sheqa dariya abinsa,kusan duk duniya su kadai ke iya taba musty su dinma ba kowanne lokaci ba,bai tanka masa ba har ya sanya kati qofar lafiyayyen office dinshi ta bude wanda ya wadatu da tsafta qamshi da sanyi ya shige hamzan ya biyoshi,freezer ya bude ya fidda lemonsa da yake matuqar so ya daga ya soma sha yana takowa inda hamza ke zaune yana masa shaqiyanci,ya kammala sha ya jefa kwalin dustbin yayi kamar zai wuce sai ya shammaci hamzan ya damqo shi sosai ya riqe wuyan rigarsa yana dubanshi "Ni kake ma shaqiyanci yau zaka gane kuranka" dariyarsa yaci gaba da yi don time to time sun saba haka da mustaphan wanda a wannan fage shi daga suke hakan koda su lamin bai sake musu haka,hannunshi hamza ya ware yana ci gaba da diyarsa yace "Ah to,laifi nayi,wallahi aure ya kamaceka ka qara musty kowa yasan hakan" tsaki ya ja ya saki kwalarsa yana komawa da baya "Allah ya sawwaqe,ni na gaya maka ina da buqatar aure don ubanka"cikin sin ya tunzurashi yace "Basai ka gaya min ba,last night naje wajenka a hotel na taddaka kana mafarki,har wawurata kayi da qyar na sha" ya qarasa cikin matsananciyar dariya,naushi ya kawo masa ya kauce,sumarshi mustaphan ya shafa,ya fuskanci caakar da shi hamza ke son yi,qarancin suruti da yake da shine ya sanya bai iya maida raddi ko wasu amsoshi masu zafi ba matuqar ba cikin bacin rai yake ba,yanzun ma lalubar mai zai maida masa yake "Kai zaka qara aure bani ba mayen mata" "For what?,Nikam alhamdulillah,abida ta tsaren gaba ta tsaren baya,tun jiya wayarta ke damuna ma tayi missing dina tana buqatar na dawo gida,cikin satin nan kuwa zan gudu tunda mun gama daidaita komai samfuran kawai zamu fara saqawa,kai ke buqatar aure har yau aurenka babu riba,nan da few months za'a soma kirana da daddy" maganar ta daki mustapha,sai yayi shiru bai iya nada amsa ba,komawa yayi saman doguwar kujera ya kwanta gami da miqe qafafunshi bayan ya cire sau cikinshi da safar sa,duk da hamza baiyi da niyyar cin fuska ba tsokana ce kawai irin tasa sai ya dinga ji kamar bai kyauta ba,kamar ta bata ran abokin nashi,shima sai ya koma ya zauna yana fadin "Am sorry musty,i dont mean to hurt you" "Is ok" ya fada can qasa idanunshi a lumshe yana shafa fuskarshi da tafin hannunshi.        Tsawon minti talatin suja zaune a haka hamza na shan lemo bayan ya gama amsa wayar abida mustaphan na sauraran duk abinda suke cewa,duk da shi ba mutum bane mai sanya idanu kan lamuran wasu ba ba ruwanshi amma wannan karon kunnenshi sun kasa haqura,soyayyar ta burgeshi qwarai,shi mutum ne mai son yaga ana nuna damuwa da kulawa a kansa,zumbur ya miqe daga kwanciyar kamar wanda aka tsikara ya janyo wata sabuwar safar yana sanyawa cikin wani dan abu dake gefanshi don ya gama da waccar da ya cire yana fadin "Muje ka saukeni airphort,sauran awa daya da rabi jirginmu ya tashi" "Zuwa ina?" Hamza ya tambaya "Nijeria" ya bashi amsa a taqaice kamar yadda ya saba,baki hamzan ya sake yana kallonshi,wani irin mutum ne mustaphan,yanzun suna tare zai tafi nijerian amma ya kasa bude baki ya gaya musu?,yasan halinshi sarai yafi gaban haka ma indai mustapha ne. "Me zaka yo bayan ba time din zuwanka bane" "Baabaa ke nema na" cikin son ya tsokaneshi yace "Allah ya sanya wata 'yar naijan ya nema maka aure kai Allah yasa ma har an daura muga ya zakayi da 'yar africa tunda wadan da ba african ba ma kaqi" wata muguwaf harara ya watsa masa,haka kawai ya dinga ki kamar hamza ya masa baki ne "Da kuwa sai na nada maka duka mummunan fatan da ka yimin,kafin na sanyata da qafafunta ta koma inda ta fito,na maka kama da wanda zai tara mata?,mace daya ta isheni rayuwa,dayan ma da ana bada rabi karba zanyi" sosai maganar mustaphan ta bashi dariya,yasan yaddq zai tsinkuleshi sosai.       miqewa yayi ya dire cup din yayin da mustapha ya gama gyara wuyan suit dinshi ya kwashi wayarsa da sauran abinda yake da buqata ya kashe duk wani electric dake office din suka fito, "Kwana nawa zaka yi?" "Ban sani ba nima" ya fada yana maida wayar aljihun suit dinshi "Wacce iriyar masa ce haka kai har abada bayani wa mutane wuya yake maka?" "Oh god,ka fiya tambaya,ka sanyani magana da yawa,bayan kana gani yanzu muka gama meeting nayi maganar da ba adadi,zaka sanya qirjina ciwo fa?" "Bari na rufa maka asiri nayi shiru,don idan ya soma cuwon baka da mai jinyarka ko kwantar ma da hankali,amma ka sani this week nima zanyo gida" "Sai ka iso" ya fada a taqaice,don yasan idan ba haka yayi masa ba bazai barshi ba,murmushi hamza yayi yana yiwa abokin nashi addu'ar Allah ya hadashi da mace ta gari wadda zatasan zafinsa da darajarsa,yasan dama bazai hana shi tafiya ba mutum ne mai kula da haqqin iyali ko na nashi ba. *******    ********    *******         Kano ta yiwa baabaa dadi,tunda ya baro abuja lokacin daurin aure bai koma ba,har yau rana irin ta yau da mustapha ke isowa nijeria wajenshi wanda a yau yammacin yau ne yake saka ran zai koma abuja shida matan nashi guda biyu,kullum yana kusa da abokinshi har yau labarin bayan saduwar bai qare ba.       Bayan gama shirin nashi cikin qaton dakin nashi falle daya dake dauke da faffadan gado da malalen carfet,wanda shine dakinshi na farko daya tabayi kuma shi dinma har yau ba rabu da shi ba,anty maamaa ta aiko mishi da abinci yaci sannan ya fito don ya gaisa da su.      Bangaren ummensa ya fara shiga,ya taddata zaune a falo tana gyaran farcenta,gefe da ita kadan ya samu ya zauna sosai ya tanqwashe qafafu,fuskarta fadade da fara'a take dubanshi,gashi mutum zam sak amma rashin iyalin qwarai na wasa da nutsuwarshi "Barka da rana ummee,na sameku lafiya?" "Lafiya qalau almustapha,ya hudimomi da sabgogi?" "Alhamdulillahi ummee" ya fadi yana shafa suman kanshi "Ya kowa da kowa?" "Duk suna lafiya" ta bashi amsa,tasan da su amira huda da farida wanda ke dakin aure yake,yakan yawaita tambayarta yanayin zamansu,shiru ya dan ratsa tsakaninsj,shi bai da abin cewa kasancewarsa ba mai yawan magana ba,yayin da ummee ke kai kawon yadda almustaphan zai amshi maganar aurenshi,don ta tabbatar da cewa a yau baabaa zai gaya masa maganar "Kunyi waya ne da yayanku?" Kai ya girgiza alamar a'ah idanunshi cikin na ummeen,ya gama karantar akwai wani lamari tattare da ita,bai wasa da dukkan lamuranta hakan ya sanya bashi wuya wajensa karantar yanayinta "Okey,zaka wajen mahaifinka zakuyi magana da shi,abinda nake son gaya maka mahaifinka mahaifinka ne kafi kowa sani,bani da buqatar kayi jayayya ko mujadala da shi,tashi kaje nasan yana can yana jiranka" miqewa yayi yana amsa mata da to,yayin da zuciyarsa ke wassafa masa meye wannan wai da ya faru haka da shi wamda shi bai sani ba?,bai wuce ba sai da ya shiga ya gaida anty maamaan,cikin kulawa itama ta amsa masa,saidai ya lura itama tana masa irin kallon da yaga ummee na masa,yayim da tace masa sanda zai fita "Almustapha,ka daure ka dore kan halinka na biyayya kaji?" Itama to dince amsar,sai ya samu kansa da hanzarin isa wajen baabaan don yaji koma mene,don shi mutum ne da baison boye boye,sak yake,fadin gaskiya komai dacinta.        Da murmushi baabaa ya masa nuni ya iso har gabanshi,ya sanya masa ludagi cikim furar da yake sha,kasancewarsa yasan almustaphan da son fura,kadan ya sha saboda qagara da yayi da jin dalilin zuwanshi nijeria cikin qanqanin lokaci,sai da baban ya kammala ya kira anty maamaa ta kawo masa wayarta ta fita sannan ya soma magana da shi "Almustapha,kowa na da labarin bayyanar tsohon abokina sule ciki kuwa har da kai nasan labari ya isa gareka" qaramin murmushi ya saki don har ga Allah ya taya mahaifin nashi murnar ganin wannan amini da tun haihuwarsu suke ji labarinsa sai a yanzu ya bayyana,kai yake jinjinawa yana murmushi,yana zaton malam zaice ne yaje ya gaidashi "Almustapha ungo nan" ya fada yana miqa masa wayar anty mama,babu musu ya sanya hannu ya karba yana duba wayar,hotonta ne,daya daga cikin hotunanta na bikin amira,ta fito tayi tar ta cika screen din wayar fuskarta qunshe da murmushu da ya sake fidda sigarta mai sanyi da kyau,janye wayar yayi daga fuskarshi yana duban baabaa,gabanshi na faduwa yana addu'ar kada Allah yasa baabaan yace ya auri wannan 'yar mitsitsiyar yarinyar ne,amsar wayar baabaa yayi sannan ya dora "Nasan maiyiwuwa zaka iya ganeta,yarinyar dake gidan farouq maqotanmu na abuja,diya ce ga aminina sule?,almustapha" ya sake kiran sunanshi cikin yanayi na gaske,fararen idanunshi kawai ya daga ya dubi baaba "Na nema maka aurenta saboda mutuncinta,na nema maka aurenta saboda nutsuwarta,na nema maka aurenta saboda addininta,na nema maka aurenta saboda daga gidan data fito daga tsatson data fito,uwa uba na nema maka aurenta saboda TA DACE DA KAI!" baki daya kalmar baabaan ta qarshe taso tafiya da majiyar kunnensa,bai gama lalubo duniyar da yake ciki ba yaji wani sautin na cewa "Ta taba aure tana da yaro daya,tana da hankalin da zata iya zama da kai ta baka dukkan abinda ya kamata" ai wannan karon bansan sanda ya daga kai ya dubi baabaa ba,take wasu irin jijiyoyi suja fito a goshinsa,qoqarin danne zuciyar tasa yake da irin bala'in da yake ji cikinta amma bakinsa yaqi bashi hadin kai "Baabaa,ban santa ba,bata sanni ba,bata sona bana sonta,baabaa aure yanzu?,auren ma na bazawara da d'aa baabaa,please baabaa i beg you idan na maka wani laifin ne ka yimin duk wani hukunci da ya kamata amma banda wannan"murmushi baban ya saki " ba hukunci bane mustapha gaata ne na maka" "Gaata baabaa" ya fada cikin nuna shakku da taraddadi "Baabaa ba wannan gatan nake so ba baabaa ka sauyan wani umarnin zanbi amma banda wannan" nan ya shiga roqo iri iri yayin da baabaan ya zuba masa idanuwa yana kallonsa,yasan dole za'a samu rudani amma bai tsammaci abun zaya kai haka ba,ganin yanata zuba ya sanya baabaan daka masa tsawa "Muhammad almustapha!" Sunan da ya kira shi da shi yasanya hankalinsa dawowa jikinsa "Ni muhammad mukhtar!,indai ni na haifeka na baka umarni ka karbi auren sumayya umarni ba shawara ba,tashi ka bani waje!" Da qyar ya iya miqewa kamar wanda ya sha abun maye ya lalubi hanya ya fice.      Ya jima zaune gefan gadonshi aqalla awa guda yana yamutsa hannayensa cikin kwantacciyar sumarshi mai santsi da laushi,gumi ko ina yana keto masa,miqewa yayi ya soma zare kayanshi yana jefarwa cikin dakin,sai da ya rage saga shi sai boxer sannan ya fada bandaki,ruwan sanyi ya sakarwa kansa tsakiyar shower,ya jima tsaye sanyinbruwan na ratsashi tare da qoqarim control din kansa,ya sake barnatar da awa guda cur a haka har sai da tunaninsa ya dawo yadda ya kamata,qwaqwalwarsa ta fara yi masa bita,ya tabbatarwa kansa bai yi kalaman da suka dace ba ga mahaifinsa,baabaa ne,masoyinsa,wanda qaunar da yake masa ta daara ta dukkan wani daa ko jika dake cikin zuriyarshi,dakin gadon ya dawo ya sake lalubar wasu kayan ya sanya,wannan karon jallabiyya ce,ya gabatar da sallar la'asar,zama yayi kawai yana karanta yadda wannan QADDARAR ta fadowa rayuwarshi a lokacin da bai zata ba,yana nan a haka bai ankara ba yaji kiran sallar magariba,a nan gun itama ya yita a haka isha'i ta ruske shi,sai a sannan ya samu qwarin gwiwar miqewa ya sake daura alwala ya sanya hular tashi ka fiya naci ya nufi masallaci.        Sahunsu daya da baabaa,har aka idar bai motsa ba sai da ya ga baabaan ya gama addu'o'inshi ya miqe zai fita sannan ya mara masa baya,yana gaba yana binshi a baya,baban ya san da haka amma yayi banza da shi bai ko nuna ya ganshi ba,sai da zai bude qofar gidan yayi sauri ya bude mishi yaci gaba da binshi har sanda ya isa falonshi sannan ya waiwayo yana sake tamke fuska duk da yasan dama hakan zata faru,yasan halin mustaphan zai sake waiwayowa a duk sanda nutsuwarshi ta dawo jikinsa "Lafiya kake bina,zan shiga na kwanta ne idan akwai bashin da kake bina ban kammala biyanka ba sai ka gayan ko?" Kai ya sadda yana jin nauyi da kunyar maganar da baabaan ya fada,qarasawa yayi gabanshi sannan ya zube kan gwiwarsa "Kayi min afuwa baabaa kayi haquri kan baata makan da nayi,nayi kuskure wanda bana fatan sake yinsa,na amshi dukkan hukuncin daka yanke me kake buqata yanzu daga gareni" dawowa yayi ya samu waje ya zauna sannan yayi masa nuni da ya dawo kusa da shi ya zauna,sosai baabaan ya dinga kwatanta masa manufofi da hujjojin da yake jin sun isa su sanyashi qara aure,daga bisani ya rufe "Ka gwada zama da ita mustapha na cika maka baki tare da kurin samunta fiye da yadda kake zato ko tsammani,nasan jinin sule ba zai taba kasa gadon halinshi ha,mustapha,ka riqemin sumayya da mutunci da amana,idan ka wulqantata ka dauka ni ka yiwa,haka idan ka bata daraja,bazan iya maka afuwa ba aduk sanda na sameka da lafin wulqantata ba bisa haqqi ba" "Na yi maka alqawari insha Allahu" "Allah ubangiji ya albarkaceka,yq cika makq burikanka,ya kyautata rayuwarku kai da ita baki daya,kiran da nayi maka kenan zuwa nijeria,yaushe zaka dauki matarka?,sannan a ina kake son ajjyeta?" "Duk yadda kace baba haka za'ayi" murmushi ya saki yana dukan kafadarsa "Kaine fa mijin kuma kai ke aurenta bani ba da zaka turon zabin" "Ka isa damu ne baki daya baba" "Idan ta nine ko yau kaje ka dauko matarka,sannan ka wuce da ita dubai,don nima ina son naga daana ya fara dandanar zaqin aure" duk da rudin da yake ciki maganar baban ta qarshe sai data sanyashi jin nauyi "Zanyi yadda kace,amma amin afuwa zuwa gobe" "Ba lallai bane ai,kana iya barinta abuja idan kaso,amma sai bayan kun gama fahimtar juna da ita kun fara sabawa,fatana ka riqeta da mutunci" "Insha Allah baaba" addu'a yayi masa mai kyau da tsaho,wanda tilas mustapha ya dinga lallaba kansa da zuciyarsa ya zauna sukayi hira da malam din na wasu mintuna sannan ya tashi ya wuce.        Kamar zai zauce cikin dakin shi daya haka ya dinga ji,kiran hamza ya shigo wayarshi,wata bahaguwar harara ya ballawa wayar,ganu yake hamzan ne da shegen bakinsa ya masa wannan fatan,to amma ai ba fatan hamza bane tunda baifi awanni da yi masa shi ba,anya kuwa hamza baisan da wannan maganar ba ya munafunceshi?,yana kallon kiran har ta ya gaji da kiran nasa ya haqura,yana tsagaitawa lambar su'ad ta danno kai,wanda shi sam yama mance da ita,ya kuma mance rabon da suyi waya,hannu ya sanya cikin mutuwar jiki ya daga kiran ya kara akunnensa,tun kafin yace wani abu sheshsheqar kukanta ta cika kunnuwansa wanda hakan ya hadu da tashin hankalin da yake ciki take suka saukar masa da ciwon kai,sai ya runtse idanu yana saurarenta "Almustapha,ni zaka ci amana?,ni zaka yaudara almustapha,dama zakq iya kqllon wata mace macen ma 'yar afrika bayan ni?,almustapha kana jina kayimin banza da kai nake musty!" Ta fada cikin qaara da qaraji,tasan sarai yana jinta tafi kowa sanin halinshi na rashin son hayaniya da kuka,shirunsa ya sake tunzurata,mamanta dake gefe ta rada mata abinda zata yi,itama a ganinta hakanne ya dace tunda da irin wannan taci nasarar aurenshi "Wallahi almustapha sai na kashe kaina,sai nasha poison don bazan iya hada ka da wata can ba,wallahi sai na kashe kaina....." Ga mamakinta tun kafin ta kashe wayar shi ya kashe,bama kashewa kadai ba sai da yaja mata wani mugun tsaki sannan ya kasge wayar baki daya ya cillar,miqewa yayi cikin tangadi ya sauya kayan bacci ya koma gado ya duqunqune cikin bargo,yayin da qwaqwalwarsa ta kasa aikin komai a tsaye take cak.    ******   ******   *******       A shirye ya fito cikin baqaqe sidik three pieces slim fit suit,ba qaramin kyau suka yi masa sun haskashi matuqa,saidai shi kadai yasan izayar da yasha daren jiya,tilas ya dauki sun glases wada ya dace da shigarsa ya sanya,tamkar don ado ya sanyashi ba don kare idanunshi da suka sauya launi ba saboda rashin wadataccen bacci yayi masa kyau sosai shima,ya yanke shawarar gwara yaje asibitinsa ko wasu daga cikin marasa lafiyan da zai iya dubawa ya duba ko hakan zai rage masa zafi da radadin da yake ji.      bai samu baabaa ba saboda ya fice wajan aminin nashi malam kan maganar yadda zai gabatarwa da malam dukkan gidajen gonanshi wanda yakeao a yanzu su dawo hannunshi ya karbi dukiyarsa,yaga kamar malam din yana bagarar da zancan yaqi tsayawa su tattaun,yau yake so ayita ta qare,saboda haka anty maamaa maan kawai ya gaisar ya wuce wajen ummee,tana kwance ta fito ya gaidata ta amsa tana dubanshi,basai an gaya mata ba tasan da walakin goro a miya,ta gabatar masa da break fast,bai iya cin komai ba sai coffe da yayi qoqarin sha don kada ya daga hankalinta,yana sha tana gefansa a hankali tace da shi "Dukkanin mai biyayya zaici ribarta a gaba,bijirewa iyaye koda kan gaskiyarka ne bashi da wani alfanu,zaiyi wuya idan baka ci karo da tashin hankali ba a gaba sanadiyyar wannan bijirewar,almustapha,na roqeka ka riqe musu yarinya da mutunci,ka fiddani kunya kada ka watsan qasa a ido,yanzu ne lokacin da zaka nuna irin tarbiyyar daka samu daga gareni" jikinsa duk sai yayi sanyi,shi wai iyayensa da suka isa da shi ke roqo?,akan me?,duka akanta?,akan yarinya qwara daya tal,cup din ya dire yana fadin "In sha Allah" cikin sassanyar murya sannan ya fice yana dauke da brief case,tuni drivanshi ya gama shirya komai,maimakon baya da yake shiga wannan karon gaban motar ya shiga,baice komai ba don shima ya lura akwai abinda ke faruwa da ubangidan nashi ya shiga ya tada motar masu tsaron qofa suka bude masu wakekem get din suka fice.        Daga kadan kadan ciwon marar ke sake yawaita mata,wanda hakan ya sanya maama ta takurata kan lallai yau sai taje taga likita,itakam baki daya bajin dadin rayuwar ma take ba,amma tilas ta shirya zuwa don cika umarninsu da samun kwanciyar hankalinsu,qarfe tara ta gama shiryawa bayan sun gama waya da anty dije ta bata adresa din wani asibi,ta gaya mata komai kyauta ake saidai akwai tsantsar kulawa tamkar asibitin da ka fidda kudinka ka biya,ba kyautar ce zata kaita ba,kulawar data fada shi yasa zata,don bata da matsalar kudi,don baabaa ya ajjiye mata su tamkar baisan zafin su ba,hatta da abinda zata ji bai yarje taci na gidan ba,sabida yace yanzun ba dolensu bace.         Sai data shiga ta gaida baabaan a kunyace sannan sukayi sallama da malam kan zata asibitin da yake baaban yace izinin fitarta ya damqawa malam din kafin qarasowa mijinta,dakatar da ita baaba yayi ya fidda wayaraa ya kira daya daga cikin direbobin dake dakon fitowarsa ya bashi umarnin kaita ganin likita,cikin girmamawa ya amsa,shiru tayi cikin lafiyayyar motar wadda idan ba gargada ta kai gargada ba ba lallai ka fahimci ana tafiya ba,ire iren motocin da suke mallakin familyn professor mukhtar,motar da ada ko a mafarki bata darsa shiga irinta ba,ajiyar zuciya ta saki sannan ta fidda wayarta ta duba kiran dake shigowa amira ce,murmushi ta saki duk ciwon marar dake neman sake tsananta mata,amsa wayar tayi ta kara akunnenta. Masu karatu muje zuwa,wanne asibiti sumayya zata????. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 7⃣6⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *la haula wala quwwata illa billahil aliyyul azim* _____________________________________         Cikin babbar haraban asibitin motar ta ajjiyeta a muhallin da aka tanada saboda ajiyar motoci,cikin rashin qwarin jiki ta bude murfin motar ta fita sanda drivan ke kashe motar yana sake daidaita tsayuwarta,kai tsaye reception ta isa,aka bude mata file kasancewar komai kyauta ne,tayi mamakin kyau da tsaruwar asibitin,wanda ta tabbatar da cewa inda mamallakin asibitin yayi shine saboda kudi ba shakka ba qananun kudi zaya samu da asibitin ba,tsarin ya burgeta,ba qaramar dabara yayi ba,saboda tasan ladan da zaya samu ba kadan bane,d'aya daga cikin abubuwan da masu kudinmu basa ganewa kenan,sun gwammace suyi saboda kasuwanci,ba don ya zame musu sadaka mai gudana ba wadda zata yita bibiyarsu har bayan rayuwarsu ba,abune wanda koda sunyi ba komai bane cikin dukiyar da Allah ya basu ba,Allah madaukakin sarki yana cewa "Yaku wadanda kuka bada gaskiya da Allah ku ciyar daga abinda muka azurtaku tun kafin ranar da babu fansa a cikinta(da zata yi maka amfani),ba abokantaka (a cikinta da zata yi maka amfani),ba ceto(sai da izinin ubangiji)tazo muku(wato ranar qiyama",bayan mai bada katin ya gama cike mata ya miqa mata yana nuna mata inda zata kai a saka ta a layi yana fadin " kinyi sa'a kuwa malama,yau oga ne da kansa ya zauna,ba kowa ke samun sa'a irin haka ba ranar garkonshi"ya fada yana washe baki,don tunda ta shigo tayi masa,duk da kasancewarta cikin zabgegen hijabi har qasa amma hakan bai gaza bayyana kyawunta ba "Na gode" kawai ta fadi ta amshi folder din ta kai inda yace mata,akwai mutane kusan goma sha biyar a gabanta,saboda haka dole ne tayi zaman jira,bata jima da zaman ba kiran nafisa ya shigo wayarta,wanda shine ya sake dauke mata hankali da radadin da take ji,don a qalla sun bata kusan minti talatin suna waya kafin su rabu.        Sannu sannu suka soma raguwa,duk wanda ya fito fuskanshi qunshe take da fara'a saboda an duba shi yadda ya kamata,uwa uba zai samu magunguna masu kyau fiye da kullum,wanda kusan yawancinsu masu ciki ne,duk na gabanta suka qare layi yazo kanta,wanda bayan fitowar matar qarashe ta miqe ta isa qogar office din ta tura ta shiga.       Lafiyayyen office ne wanda yake a tsaftace sannan a tsare kamar yadda ilahirin asibitin yake,office ne mai girma wanda daga hannun hagu ke dauke da rukunin wasu irin kujeru kusan guda hudu da table dinsu a tsakiya,kana shigowa kuma table din likitan ne wanda ke dauke da tashi kujerar da kuma kujeru guda biyu a gaban table din suna fuskantar juna wanda anan patient ke zama yayi bayani,daga bayan tashi kujerar wami dan katako ne a tsaye wanda yake rataye 'yar saman suit dinshiba jiki,sannan gaban table din kadan dan gado ne wanda ke hade da na'urar sacanning ta musamman da sauran tarkacen likitoci,daga hannun dama kuwa qofofi biyu ne kulle,daura da su freezer ce girke a kanta akwai set na warmers da cups na tea da na ruwa,sai coffe maker daga gefe.       Tsaye yake gaban gadon scanning din inda ya baiwa qofa baya,hannunshi dauke da takardar da ya gama yiwa wata mata scanning yana dubawa,ranshi a bace yake sosai har hakan ya nuna saman fuskarshi,yana mamakin yanda a yanzu maza ke wasa sa haqqunanau kan matayensu,kana da mata tana dauke da cikinka,wanda rayuwarta na cikin qila wa qaala ne,ko ta mutu ko dan ya mutu ko a rasa su baki daya idan kuma ta kasance daga cikin masu sa'a su rayu baki daya,amma ka kasa tsayawa ka bata kyakkyawar kulawa?,abincin da zata ci mai kyau ya gagareta?,kullum tana cikin tashin hankali da masifa,tayi wahalarka tayi ta yaranka?,akan me?,saboda me?,duka cikik zuciyarsa yake wannan maganan.        Turo qofan tayi sallama a bakinta,ya amsa ba tare da qwaqwalwarsa ta bashi wace ba,dan tsayawa tayi saboda batasan inda zata zauna ba,ga faduwar gaban sata rusketa lokaci daya sai daga bisani ganin ba'a ce mata komai ba sannan ta taka ta isa gun kujerun ta zauna.         Takardar ya nade ya ajjiyeta gefe yana sakin tsaki sannan ya juyo a hankali ta tako zuwa nashi muhallim ya ja kujerar ya zauna ba tare da ya dubi wadda ke zaune din ba,duk da yana shaqar wani qamshi da kamar yaso ya sanshi,ya jawo file dinta ya bude,ganin sabo ne alamun zuwanta na farko ne ya sanya shi fadin "Uhm,meke damunki?",ita din ma bata dubeshi ba har sai da sautin muryarshi ya daki kunnenta,da sauri ta daga kanta idanunta suka sauka kanshi,tsabar ciwon dake murda mata ya hadu da firgitar da tayi ya so riqe numfashinta,qoqarin miqewa take amma ta kasa,har ya kammala rubuta date din da zaiyi baiji an amsa ba,hakan ya sanyashi daga kansa yana tsammanin ko kurma ce,idanunshi ya dan ware a kanta,kafin yq maidasu yadda suke,wanda hakan ya taimaka wajen sanyata miqewa da hanzari dom barin ofishin,ta gwammace ta haqura da ganin likitan baki daya,cak ta tsaya jin sautin muryarsa kuma muryar mukhtar yana bata umarnin dawowa inda ta tashi din,har cikin zuciyarta tana jin ba zata iya tsayawa ba,a inda daga shi sai ita?", sai ta sake daga qafarta don cikin yunqurin cimma ficewa daga office din ba.        Batasan ya akai ba,yaushe ya iso inda take?,sai kawai ji tayi an tado qafafunta,wanda hakan yayi sanadiyyar wancakalar da jakarta sannan ta tafi zata fadi dama jikin babu qwaru,tuni ya tarota da hannayenshi,bai cikata ba har sai da ya kaita kan rukunin kujerun nan guda hudu ya zaunar da ita,tsaye yayi a kanta hannayenshi harde cikin qirjinsa yana dubanta,qare mata kallo yake yana sake shaidawa kansa cewa matarka ce,duk abinda zakayi kayi controlling kanka,duk da bai iya kallonta yadda ya kamata sakamakon hijabin da ya lullube dukkan jikinta,tafin hannayenta kawai yake iya gani sai fuskarta wadda itama bata fita ba saboda kanta na sunkuye ne a qasa,so yake ya gani ta inda ta dace da shi,so yake ya gani yadda zaiyi ya zauna da ita,ya kuma gano ta inda zata iya taimakonsa ko amfanarsa,bai gani digon wayewa ko dis tattare da ita ba,hasalima shi tunda ya santa cikin hijabi yake ganinta,sau daya ya taba ganinta ba cikin hijab ba ranar bikin amirarsa,wannan itace zata iya zama da shi ta samaasa farinciki wanda ita kanta bata samawa kanta ba?,ya tabbatar gwara su'ad sau dubu da ita,wanda ko ita su'ad dinma data san ta kan duniya ta kasa iya tafiyar da shi,ta kasa shayar da shi soyayya mai zafi irin wadda yake muradi balle wannan da kullum take a qunshe?.        Idanuwansa ya lumshe sannan ya hadiye wani abu mai tauri daya tsaya masa a wuya sanda ya fuskanci kuka take,qaramin tsaki ya ja cikin zuciyarsa yana cewa "Ko uban me nayi mata oho?" Motsa bakinsa yayi da niyyar daka mata tsawa sai kuma ya tuna ita din wacece wajen baabaa?,me baabaa ya gaya masa game da ita,hannunsa ya dunqule ya daki daya tafim hannun nasa wanda hakan ya darsa tsoro a ranta,sai ta runtse idonta tana jira taji mai zai faru.       A hankali ya tako zuwa gabanta bai gushe ba sai sa ya zo gab da gwiwoyinta sannan ya durqusa,dora hannunshi guda daya yayi  saman kujerar gab da inda cinyarta take saidai basu hadu ba,ya sake motsa bakinsa zaiyi magana aka soma knocking qofar,dauke fuskanshi yayi ya maida qofar yana cewa "Yes" wanda hakan ya baiwa mai son shigowar daman budewa ya shigo,daya daga cikin ma'aikatan asibitin ne,cikin mamakin ganin ogan nasu a haka yayi saurin cewa "Am sorry sir" ya juya da niyyar ficewa,cikin sanyin murya yace "Baka da damuwa,ya ake ciki?" Jin haka ya sashi dawowa yana satar kallon sumayya wadda kanta ke qasa,tuntube yayu da rug din dake shimfide wajen bai kula ba saboda kallon da yake matan,da sauri yace subahanalla sannan yayi hanzarin maida idonshi ga mustapha,wata muguwar harara ua watsa masa wadda ta sanya hanjinsa kadawa,ba tun yau ba yasan murtala mayen mata ne,ya sha bashi warning akan yadda yaje zuwa ya taddashi da mata suna hira suna qyaqyata dariya,cikin rawar jiki ya miqa masa wasu takaddu "Gasu yallabai,mun gama komai mun bata gado,an gayara dakin thierther din" "Good,kun tabbatar tun jiya bayan isha'in bata sake cin komai ba?" "Eh yallabai" "Ok,nan da one hour zamu shiga in sha Allah" "To yallabai" ya fada yana juyawa,har ya kai qofa mustaphan ya sake tsaidashi "Ban amince ku bad mijinta ya shiga dakin ba koda yazo,sannan ku san yadda zakuyi da sauran patient din dake jira,kwashe wadan can files din ka fita da su" "To" ya amsa cikin rawar jiki ya tattare ya fita da su saboda yadda yake ta faman jifansa da wani irin kallo.        Da idanu ya rakashi har sai da yaga fitarsa sannan ya dauke idonshi ya sake maidawa kanta ya kafeta da su "Da ba sai kinzo ba ma,ko baki zo ba dole baaba yace yau nazo" da sauri ta watsa masa idanunta wadanda ke jiqe da hawaye,me yake so yace?,biyoshi tayi?ciwon da take ji ita shi ya dameta,amma dole ta fahimtar da shi don bazata lamunce tana ji tana gani ya mata wata fassara ba "Allah ya sawwaqe...i bab...ba kai na biyo ba,bansan ka ba bare....." Takaici ya turnuqeta ta kasa qarasawa "Idan ba haka bane mai ya kawoki?,na tambayeki baki amsa ba,tabbacin maganata tana kan gaba kenan" banza tayi da shi tana digar hawaye,yayin da shi kuma yaci gaba da kallonta yana nazarinta,sai a sannan ya lura da hannunta wanda ke zaune saman mararta,hannun yabi da kallo sannan ya maida dubanshi fuskarta "Tashi ki cire hijabin na duba miki" ya fadi yana matsawa da baya sannan ya miqe tsaye,shiru tayi masa kamar bata jiba,don bata ga dalilin da zai sanyata cire hijabinta ba,ransa ya soma baci da shariyarta,abinda bai qauna tsawon rayuwarsa,uhmmm wanzami dama hausawa suka ce baya son jarfa,sake matsawa baya yayi hannayensa zube cikin aljihunsa yana dubanta "Ko kaxa baaba ya bani da hannunshi yace na kula da ita daga ranar tafi qarfin wulaqanci ko tozarci a wajena,kina neman ki hasalani nayi miki abinda banyi niyya ba ko?,kada ki yarda raina ya baci,idan kuwa ba haka ba bazakiji da dadiba,kina iya tashi ki tafi idan har ba zaki bari baaban yasan asibitina kuma gurina kika zo ba,kiyita zama da cutarki wannan ba damuwata bace" ya qarashe maganar yana daga kadunshi,hakan ya bata qwarin gwiwa ta muqe da hanzari duk da ciwon da takeji na tsikarinta,ta isa ga jakarta ta tattare kayanta ta maida ciki cikin hanzari,wanda hakan ya sabba ba mata manta hotunan mukhtar guda biyu qananu wanda suka zube ta doshi qofa abinta.        Wata zuciya ta taso masa,tana jin bata da kunya kenan?,ita din wace?,bai manta rashin kunyar data yi masa ba randa ta bigeshi duk don yace ta dinga kula,me take da shi da take wani qunshe qunshe,taku daya biyu ya isa inda take,hannunshi ya sanya ya finciko hijabin baki daya ya fiddashi daga jikinta wanda hakan ya sanya gashin kanta warwarewa baki daya,dama daureshi kawai tayi ba tare data sanya komai ba,hakan ya tilas ta mata tsayawa cak,waiwayowa tayi da niyyar sauke masa magana kwarjininsa ya cika idanuwanta "Mijinki ne",kalaman malam suka dawo mata,ita din ba mai tsiwa ko rashin kunya bace tun da can baya,tun daga aurenta daga mukhtar zuwa lukman,bata iya kallon tsabar idon wanda ya girme mata tayi masa rashin kunya ba,sai yanzu zata fara?,a kan dan mutumin dake qaunarta,uba a gareta babban masoyi amini ga mahaifinta,sai ta runtse idanuwa,yayin da juyawar tata ya tilastawa mustapha kau da idamuwansa daga kanta,skert ne a jikinta da riga 'yan kanti,irin masu robar nan wadanda suke bin jikin mutum,gajeran hannu gareta,wuyanta kuma v.hape ne wanda ya fidda kyawun wuyanta zuwa qirjinta "Idan ka wulqanta sumayya ka tabbatar wa kanka ni ka wulaqanta" maganar baabaa ta dawo mishi shima kwanyarsa,dukkaninsu lokaci guda umarnin iyayensu ya yi musu linzami,lokaci guda ya sauke dukkan wani abu da kowannansu keji game da dan uwansa a zuciyarsa,hijabinta ya wurga mata ba tare da ya dubeta ba,da yatsa yayi mata nuni da gadon dake bakin na'urar scanning,bata ce komai ba ta maida hijabinta jikinta,ta taka a hankali zuwa bakin gadon ta hau,sai da ya bada wasu mintuna sannan ya soma takawa zuwa kan gadon "Kwanta" yace mata,idanu ta fiddo har sai da ya sake dubanta,da baya ta koma ta kwanta saman gadon "Janye hijabin da rigarki" ya sake fada yana duban wani gurin,hijabin ta janye amma sai ta kasa janye rigar,sake waiwayowa yayi yaga abinda tayi,bai ce mata komai ba ya sanya hannunshi ya dage rigar,idanunta ta runtse zuciyarta na bugawa,da sauri ya sake rigar ya koma da baya,bai iya tuna mata nawa yayi wa scanning tun daga farawarsa aikin likita kama yau,mata daga nau'in yare jinsi da qasashe daban daban,amma haka kawai yake jin wannan bazai iyaba.         Bakin teburinsa ya isa ya soma qoqarin kiran reception ta wayar landline yana tambayarta "Duk wata kina period dinki?" "Eh" ta bashi masa murya can qasa cikin jin haushi da kunya "When last kika ga period din" shiru tayi tana tunani,a qalla kusan watanni biyu kenan baizo mata ba "Wata biyu"tabe baki yayi yana mamakin rashin damuwa da kai da har zakayi wannan watannin baka ga al'adarka ba kana zaune.        Wata nurse ce ta shigo wadda a qalla ta kusa shekara arba'in,cikin harshen nasara da tataccen engishinsa yake gaya mata abinda zata yi duka sumayyan na jinsu sai,a ladabce ta amsa ta qarasa inda sumayyan ke kwance,yayin da shi kuma yayi lamo cikin kujerarsa idanunshi a lumshe,yanajin yadda wata gajiya da kasala ke saukar masa,bai sake motsawa ba har nurse din ta kammala ta masa bayani idanunshi na arufe yana gyada kai,idanuwa sumayyan ta fiddo jin tana zancan scanning din da ake ta qasa za'a yi mata wanda nurse din bata iya ba,qirjinta ya dinga bugawa,ta soma ayyanawa a ranta yadda hakan zata kasance,sai data bayyana bayaninta tsaf sannan ya bude idanunshi wanda suka sauya launi kadan,ya jawo wata paper yayi rubutu da baifi layi hudu ba ya miqa mata yace ta karbo masa yanzu yana jira,karba tayi a ladabce ta fice.        Shiru ya ratsa office din sai qarar a.c dake buso sanyi tare da wani ni'imtaccen qamshi dake gauraye da office din,tana kwance wajen zuciyarta na bugawa "sauko"ya fadi yana miqewa tsaye ya shige toilet,da hanzari ta sauko ta sanya takalmanta sannan ta dauki hijabinta ta nufi qofar,sau uku tana murzawa taqi buduwa,dole ta dawo ta zauna,wanda tana zama nurse din ta sake turo qofar ta shigo,saman teburin kawai ta dora maganin ta fice.        Fitowa yayi daga toilet din fuskarsa da hannayenaa wanda ya nannade hannun 'yar cikin suit dinsa jiqe da lema,da alamu alwala ya daura duk da ba lokacin yin sallah bane,bai dubeta ba ya isa gaban teburin ya fidda magungunan ya dudduba sannan ya koma gaban freezer din ya ciro ruwan roba,ya balli magungunan ya zube gabanta tare da ruwan sannan ya juya ya bude daya qofar wanda ke kusa data toilet ya shige bayan ya sanyawa qofar office din baki daya key,ba musu ta kwashi magungunan ta zuba a bakinta baki daya ta kora da ruwa ta hadiye,duk yadda taje qin magani haka ta hadasu baki daya ta hadiye,wannan karon ma ta sake jarraba bude qofar don bata ga mai zai zaunar kuma da ita na saidai taqi buduwa,a gaban idanunta ya rufe ba kuma tasan yanda zata bude din ba.        Fitowa yayi sanye da kayan da likitoci ke sanyawa duk sanda zasu shiga yin c.s,saidai nashi sun dan banbanta,saboda ash ne nasa,wanda suke a wanke fes da karin guga muraran a jikinsu,riga ce iya cinya mai qaramin hannu,sai dogon wando da hula,kamar ba kayan aiki ba sun masa kyau,qafanshi sanye takalmi plate sabanin dazu da yake sanye da ciki,qwanqwasa qofar aka soma yi baki dayansu suka dubi qofar,yana qoqarin sanya abun hanci yace "Waye" "Ranka ya dade Dr maqarfi ne" aka fada daga waje,takawa yake zuwa bakin qofar yana fadin "Ki koma wancan dakin,ki dauki jakarki" "Gida zan wuce,me zanyi a ciki?" Ta fada cikin zafi zafi,bai gasa nufar qofar ba bai kuma juyo ba yace "Ba shi na tambayeki ba,kada ki yarda ya shigo ua ganki a nan"cikin qunan rai ta miqe ta dauki jakar tata,tana gunguni cikin zuciyarta ta tura qofar ta shige.      Baya yi zaton ganin dakin ba haka,daki ne sosai mai dauke da madaidaicin gado wanda ya wadatu da shimfidar bedsheet fara qal bayan lallausar katifar dake kai,shimfide dakin yake da carfet maroon sai fararen labulaye,daga daya bangon kwaba ce ta glass wadda aka tsarata cike da littattafai da suka shafi aikin likitanci,saj wata iriyar hanger kai kyau ta silver ta rataye kaya,qamshi dakin yake kamar ba cikin asibiti yake ba,gefan gadon ta qarasa a hankali ta yiwa kanta mazauni gefan gadon tana kalle kalle tana jiyo maganan mutumin da ya kira kanshi da dr maqarfi a cikin office din,magana suke kan tiyatar da zasu shiga yanzu.        Sauka idanuwanta sukayi kan wani dan qaramin frem dake zaune kan wata 'yar bedside,idanu ta saka sosai sai ta gane su'ad ce,sanye take cikin qananun kaya masu fidda sura,tayi makeup sosai tana dariya cikin hoton,kanta ta dauke tana wassafa yaya zama zai kasance tsakaninsu,tun tana karanta wasiqar jaki har bacci ya fara rinjayar idanuwanta,batasan sanda ta jingina da fuskan gadon ba yayi awon gaba da ita.        A qalla kusan awanni biyu suka share dakin c.s din saboda mutum biyu suka yiwa,kowanne anyishi successfull,a gajiye yake saukowa daga sama inda sukeyi aikin zuwa qasa,ya sanya maqulli ya bude,ya sanya qafafunshi masinjanshi na biye da shi,da sauri ya dakata sabida tunowa da yayi tana ciki,ya karbi kayansa dake hannunshi ya sallameshi sannan ya shiga ya rufe office din,sai da ya sanya wani sabulu ya wanke hannunshi cikin wani dan sink kana ya doshi qofar dakin,yana tura qofar ta farka,idanunta ta bude baki daya wadanda suka qara girma sakamakon baccin da tayi ta zubesu fes cikin nashi,sai ya janye nashi idanun yana fadi cikin zuciyarsa "Kaman mayya" bai taba ganin idanun da yake jin nauyin sanya nashi ciki ba ko na waye irin wadan nan idanun,hakan ya sanya yake jin haushinsu,da hanzari ta gayara zamanta daga kashingidar da tayi saboda ganinsa da ya tuna mata inda take,wuceta yayi ya nufi inda kayanshi suke da alama zai canza ne hakan ya sanyata miqewa ganin lokacin azahar yayi,da sauri ta koma ta zauna inda ta miqe din zuciyarta ba bugawa,jini ne digo digo a inda ta tashin "Yaya akai haka?,yaushe al'adan har tazo mata bata sani ba,bayan dazun nan ta lissafa wata biyu bata ganta ba" kamar wadda aka daure haka take jinta,bayansa tabi da kallo sanda ya kwashi kayansa yana yunqurin ficewa,tamkar ta tsaidashi haka take ji,ya zatayi  da jikinta?,ya zata yi da wajen?,abinda ta dinga fada kenan har ya fice,tana jiyo sanda aka ja waccan qofar ta office dim,wanda hakan ke nuna mata ya sake ficewa ne baki daya,hakan ya bata damar miqewa da hanzari,yaye zanin gadon tayi cikin sanda ta shige toilet din dake cikin dakin da shi,bandaki ne madaidaici wanda aka qawatashi,akwai komai a ciki na amfani harda soson wanka da nau'in sabulai ma ruwa da daskararre,wata roba dake manne da tambarin klien ta bude ta zazzaga ta soma wanke wajen,sai data tabbatar ya fita sannan itama ta gyara jikinta,fitowa tayi da zanin gadon ta baje shi saman katifar don ya matsu sosai,tana qoqarin maida hijabinta ta juyo sallama cikin office din,a hankali cikin sanda ta fito,nurse din dazu ce,cikin fara'a ta miqa mata wata leda wadda ke dauke da tambarin sunan gidan abincin seven thirty tana cewa "Gashi inji yallabai" murmushi itama tayi mata da alama matar na da kirki ta amsa tana fadin "Na gode" har ta juya zata fita ta dawo "Ammm,ranki ya dade ba don kada nayi shishshigi ba da na tambayeki,don Allah matarshi ce ke?" Girma tambayar tayi mata,amma saita waske tana murmushi "Qanwarshi ce" cikin murmushi ta sake miqa nata hannu "Naji dadin haduwa da ke,suna na nurse barira" miqa mata yi itama tana murmushin "Ameera" sakin hannun nata tayi sannan ta fice tana murnar ganin jinin gidansu doctor almustapha.       Ledar ta bude qamshin da ya daki hancinta shi ya tabbatar mata abinci ne,sau wata ledar wadda tana budewa taga always ce a ciki,idanu ta zaro tana mamakin yadda akayi yasan tana buqatarta,bata wani tsawaita tunani ba ta dire abincin ta ciri pad din ta shiga bandaki ta saka ta jefa saurar a jakarta,gyara zaman hijabinta tayi sannan ta rataya jakarta ta fice a office din.        Rufe laptop din yayi cikin dakin hutawarshi dake asibitin bayan ya gama kallon duk abinda tayi din,yana iya ganin kowane sashi na asibitin a dakin hutawar tashi ta na'urar cctv camera dake asibitin,ya dire cup din coffen da ya gama sha sannan ya tattare kayanshi ya sauko zuwa qasan.        Idanu ta shiga rabawa ganin babu motar data kawota babu alamarta,da alama ya gaji da jiranta kenan ya tafi,babu mamaki,tun qarfe tara na safe suke gashi yanzun har uku tan gab da yi,bata ga laifin drivan ba ba,haka kawai ya wani tsareta bayan bata ga alfanun tsaretan da yayi ba,hakan ya sanya ta soma takawa a hankali don taje titi ta samu abun hawa gangar jikinya da zuciyarta duka a gajiye. Tana yunqurin fita mai tsaron qofar wanda yake dattijo ne ya qaraso cikin girmamawa fuskarsa qunshe da fara'a "Ranki ya dade,ai ya tafine wanda ya kawoki,yallabai yace ya tafi zaku tafi tare,yace ki tsimayeshi idan kin fito" murmushi tayi cikin gajiyawa "Babu komai zan samu abun hawa,ina sauri ne kuma bai kammala abinda yake ba" ta sake sanya kanta zata fice sai ta kuma jiyoshi yana cewa "Ranki ya dade gashinan ya fito ma ai" ya tunkaro get din yana qoqarin bude masa,tilas ta ja birki ta koma da baya ta soma takawa zuwa wajen get din saboda yadda idanuwa suka yi mata yawa,batasan me mutanen ke kallo tattare da ita ba haka. Gidan baya ta sanya hannu ta bude ta shige ba tare da tayi tsammanin a bayan yake zaune ba,sai data rufe qofar sannan ta ankara da shi,yana zaune hakimce abinsa,maimakon suit dake jikinsa dazun yanzun shadda ce jikinsa mai gajeran hannu,iyakarta gwiwa da dogon wando "Zaki ci wuyar zama da ni matuqar zaki kasance mai taurin kai da rashin jin magana" ya fada cikin muryarsa qasa qasa,ta gefan idanu ta kalleshi wayarshi yaje dannawa kafin ta maida idanunta kan titi,wayar ya ajjiye gefansa ba tare da ya sake cewa komai ba. A tunaninta zasu maidata gida ne sai taga sun canza hanya,dubanshi tayi tana sake kallon titin "Ba nan bace hanyar" ta yi magana tana kallon titin,sai da ya shaqi isaka sannan ya amsata "Wacce hanya kenan?" "Gidanmu mana" "Baki da abinda zaki koma gidanku kuyi,so kin taho kenan" idanuwa ta zaro tana kallonshi cikin mamaki,wannan wacce iriyar magana ce haka?,me hakan ke nufi?,kallon mamaki taci gaba da yi masa kafin tace "Ban gane ba,kawai daga zuwa asibiti sai ka zarce wani gun da ni haka akeyi?" "Haka baba yace nayi,idan kuma ni din kwartonki ne sai ki gayan" ya fadi yana balle kwalin lemo ya kai bakinsa,ci gaba tayi da kallonsa baqinciki fal zuciyarta,so yake ayi abunda ba'a taba yinshi ba cikin tarihi kenan,idan wani ya fahimta wani bazai fahimta ai,wani zai iya dauka ita ta kai kanta "Amma ba haka al'ada ta tanadar ba ai" "Addini fa?,me ya tanadar?" Ya maida mata amsa cikin yanayin ko in kula,bata haqura ba dai duk a qoqarinta na fahimtar da shi,duk da yadda ranta ke baci "Ko 'yar tsana ce ai tayi sallama da mu......" "Shut up,idan kika sake magana zaki fitarmin a mota!" Ya fada cikin hargagi wanda ya tsoratata ya sanyata yin shiru,kanta ta kwantar jikin kujerar motar,bata ankara ba hawaye suka fara bin kuncinta tana daukesu,wai me yasa ba tun fari bata zabi abdur rahman ba?,ta tabbatar da cewa koba komai da tuni tana can cikin farinciki,itakam gaskiya bata jin zata iya da wannan mutumin mai shegen girman kai izza da taqama. Bata fahimci airphort suka zo ba sai da motar ta tsaya ya fice yana bata umarnin fitowa,binsa kawai take jiki a sanyaye baki bude,qarar wayarta ta dawi da ita hayyacinta,number malam ta gani cikin hanzari da daga "Jirgin naku bai tashi bane sumayya?" Cewar malam din,mamaki ya cikata,me kenan?,malam ya sani ne dama,kamar yasan me yake kai kawo a ranta yace "Drivan muntari da ya dawo ya sanar mana shi mustaphan yace abuja zaku wuce,Allah ya tsare hanya,ki riqe aurenki da kyau mamana,kiyi biyayya kiyi kuma haquri,ki kauda kai ki zama mai kara,ki ninka haqurinki,in sha Allah ba zaki tozarta ba,ni nasan ba zaki taba wulaqanta ba gidan muhtari,Allah ya tsare hanya ga mamanki" "Daga zuwa ganin likita sai ki gudu abinki kuma?" Cewar mama cikin salon tsokana,a zaton sumayya da gaske maman take sai ta sanya kuka "Wallahi mama ban san shine ba,bansan tafiya zaiyi da ni ba" "Keee,a kul na sake jin kukanki,wanne irin shirme ne wannan daga tsokana?,to dama me zaki dawo kiyi?,dukka qannanki fa kowa ta tafi nata gidan" "Amma mama ni kadaice ba'a rakani ba,banyi muku sallama ba babu" "Sallamar me zaki mana,sannan abujan baquwarki ce da sai an rakaki,mu kuma ba gashi muna sallama ba,kibi mijinki sumayya kiyi biyayya,yi nayi bari na bari,ki girmamashi ki tuna waye shi a wajen mahaifinki,kada ki sake yayi kuka da ke" nasiha tayi mata qwarai mai ratsa jiki,duk sai ta tafiyar da wani zafi da take ji cikin zuciyarta,kafin suyi sallam ta wanke mata zuciyarta fes da kyawawan kalamai sukayi sallama,bata ajjiye wayar ba sai data kira nafisa ta gaya mata tahowarra,jin ta fara cikata da tsokanar amarya ya da biyo miji haka babu ko 'yan rakiya,sai tazo tsuma amarya wai,sai ta kashe tana kada kai,tsokana cikin nafisa ita da amira tana da yawa,anty dije ta sake laluba ta kirata ta gaya mata,bata damu ba itama da jin tahiwarta ita da shi,saima farinciki daya cikata ta musu addu'ar isowa lafiya tare da shirin tarbar sumayyan,tayi niyyar kiran amira amma ta fasa,sai kawai ta tura mata tex ta kashe wayar. Bayan ya gama sallamar drivan ya tako a hankali zuwa inda take tsaye don batasan abunyi ba,wayarshi dake aljihu ta dauki tsuwwa,ya laluba ya cirota yana duba mai kiran,su'ad ce,shafa wajen ansawar yayi ya daga ya kara kunnenshi "Mustapha ina tafe zuwa abuja a daren yau ba sai gobe ba,ina son kafin na qaraso ka tabbatar ka saki wannan kidahuma bagidajiyar yarinyar mai yawo a hijabi,idan ba haka ba wallahi sai na tashi abuja" tsawa ya daka mata cikin matsanancin bacin rai tamkar tana gabanshi "Kin manta da waye kike magana?,kin manta waye almustapha?,ok.....naga alamun kin manta,amma ina jiranki idan kika iso zan tunasar dake waye muhammad almustapha" ya datse kiran cikij bacin rai,ya zuqi iska mai zafi yana fesarwa,ya kashe wayar baki daya ya jefa aljihu yayi gaba,yana jin lallai wannan karon idan su'ad batayi wasa ba zai juna mata qaramin hauka ta iya ga inda ake babban,zai koya mata darasi mai girma,binshi tayi cike da tsoro da taraddi,haka yake da fada?,haka yake da saurin hawa?,wace tayi kiransa ya dugunxuma haka?,baki ta tabe tana biye da shi koma meye ba sabgarta bace. Wayar ta sauke daga kunnenta tana duban mahaifiyarta dakezaune gefanta,wadda itace ta karanta mata dukkan abinda zatayi din "Nifa mom gaskiya ina jin tsoro,ina son mijina kada naje nayi abinda zai zame mana dana sani,nasan halin almustapha sarai baya daukar raini" harara ta galla mata tana huci tamkar ita aka yiwa kishiyar "Ai sai ki zauna dan ubanki,ke yanzu ba abun kunya bane gareki ace wai an miki kishiya?,uwarki ma har ta qaraci quruciyarta har zuwa tsufanta bata zauna da kishiya ba?,ki tashi ki masa hauka ki qwaci 'yancinki,rashin qwatar 'yancin naki shi zai haifar da abinda kike tsoron na rasa mijin naki,kishiya bala'ice masifa ce annoba ce,ke kishiya ta wuce duk inda kike zatonta,ki tabbatar ya zaba ko ke ko ita,ke yarinya ce baki sani bane,inda ina da ita 'yancin da kika samu a rayuwarki da baki same shi ba,ban taba sanin hajiya kilishi da gaske har yau bata qaunata ba sai yanzu,daboda ita ta zauna da kishiya shine suka hada baki suka yi miki,dama can ba jituwa muke ba,aurenki da danta ne ma ya sake sawa muke hulda ta dole,to wallahi zata ga tsantsar rashin arziquki,ki tashi tsaye kada ki raga mata har sai kin raba tsakaninsu,sannan duk wanda ke gidan kada ki raga masa ciki harda hajiya kilishin,ku juye rashin mutuncinki son ranki,har sai kowa yayi laushi ya nemi daidaito da ke,indai nonon khaulat kika sha rainon america ce ke" kalamai masu nauyi ta dinga amfani da su tare da nuna mata cewa ba zata taba mallakar almustapha ba matuqar yana da wata matar,kalaman sunyi tasiri matuqa a kunne zuciya da gangar jikin su'ad,hakan ya sanya ta soma hada kayanta haiqan don isowa nageria ta bashi zabin zama da ita ko zama da amaryarsa,wanda baki daya haushin jama'ar gidan takeji musamman data samu labarin diyar aminin baabaa prof ce,tana jin dama can suna adawa da ita,suna adawa da zamanta da mijinta,saboda ya dauke mata komai tana juyawa da takunta yadda taga dama,ba shakka ba zata raga ma kowa ba indai akan almustaphanta ne. To masu karatu,ku biyoni muje. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [23/02, 11:52] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 7⃣7⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* ___________________________________       Bayan sun shiga cikin jirgi bata sake ganinshi ba,batasan inda ya zauna ba sai da suka sauka,cikin motocin gidan aka zo daukarsu,tana tsaye har ya shiga sannan itama ta bude ta shiga,yana zaune daga daya bangaren itama haka,motar tsit,shi yana danne dannen wayarshi yayin da ita kuma ta bige da kallon titi tamkar yau ta soma ganin garin a haka har suka qarasa.        A hankali motar ke kutsawa cikin unguwar tasu,tana kallo suka wuce qofar gidan anty dije,kamar tayi tsalle ta fita haka take ji,saidai ba yadda zata yi,yanzun a qarqashin wani take dole,ajiyar zuciya ta saki tana sauke jumfashi,a yau a kuma wannan lokacin gata ta sake dawowa cikin gafin,saidai cikin wanu matsayi na daban,ta dawo cikin garin a matsayin matar wani kuma surukar gidan baabaa professor,ma'ajiyar motoci motar ta tsaya bayan mai gadin ya bude masu wakekiyar qofar gidan,a hankali ta sanya hannunta ta bude murfin motar bayan tsayawar motar,qafarta ta zura guda daya waje ihun amira ya karade kunnuwanta,kafin tace wanu abu tuni ta ruqunqumeta "Wayyo amaryarmu oyoyo oyoyo" murmushi ya subucewa sumayya,da ido takewa amiran nuni da bayanta,sam bata ankara ba karadinta kawai take "Ke matar nan kiji tsoron Allah,har an fara sanin dadin miji ko?,anty ta bani labari daga zuwa ganin doctor sai kawai ayi mai gaba daya,kodai......" Bata kai ga qarasawa ba ya fito daga cikin motar,wanda hakan ya tilasta mata sanyawa bakinta fulasta sabida kallon da ya jefeta da shi,magana ce fal cikinta amma tilas ta saita kanta,a ladabce tace "Barka da isowa yaya" "Sake mata hannu ko?" Ya fadi ba tare da ya damu da amsa gaisuwar tata ba,hannun ta saki tana baata fuska ta janye gefe,kafeta yayi da idanu yana mata alama data wuce yana yin gaba,binsa tayi a baya amira ta rufa musu baya,duk da haka bata haqura ba sai data tsaya saitin sumayyan murya qasa qasa "Wannan hadi yayi kyau,Allah ka nunamin idanuwan su'ad naga ya zata yi" ta gefan idanu ta jefa mata harara amma hakan bai sanya ta fasa ba,waiwayowar musty din ne ya sanyata ja da baya tana raba idanu.       Kai tsaye bangaren ummee suka soma shiga,a hankali suke takawa jere da junansu tamkar wasu shaqiqan masoya,su biyun ke zaune a falon ummee da maamaa,da alama suna tattauna wani abu ne,amsa sallamar sukayi kowacce fuskarta a sake,idanun umme bisa fuskarshi,shi ya soma yiwa kansa matsuguni kan daya daga cikin kujerun falon kafin ta qarasa takowa a ladabce zuwa cikin falon,kanta a qasa a kunyace ta qarasa amira na gefanta,wata kunya da nauyinsu take ji a yanzu wadda ta ninka ta da,musamman ummee wadda dama can ba wani sakewa ko sabo sosai tsakaninsu,gefe ta zauna qasan carfet kan ta a qasa "Tashi ki koma saman kujera mana,wacce irin tafiya ce haka almustapha?" Ta tambayeshi tana dubansa,kanshi ya shafa yana yana yiwa ummeen magana da idanu zuwa sashen da su sumayya suke,ta fuskanci mai yake son fadi amma duk da haka bata fasa sake magana ba "Babu sanarwa ba komai,halan ma baka barta ta kintsa ba ka tattago ta ko?" Inji ummeen tana bata rai,don tuni amira ta fesa mata yadda ya dauko sumayyan,cikin salon bada uziri yace "Ummee,umarnin baba ne"dauke idanunta tayi ta maida kan sumayyan wadda suke gaisawa da anty maamaa,cikinnurmushi ta soma gaidata "Ummee ina yini" "Lafiya qalau ya gajiyan hanya" "Alhmdlh" ta fadi cikin ranta tana fadin wacce gajiya gurin mutumin da yayi tafiya a jirgi "Anty kun yini lpy?" Cewar almustapha yana miqewa tsaye "Lafiya qalau almustapha,ashe kuna hanya babu sanarwa bare ayi abun tarbar baqi" qaramin murmushi kawai ya saki na gefan baki,bai amsa ba sai ya jefo tambaya "Baabaa fa?" "Ya fita,yana can suna lissafin gidajen gonar nan" "Ok" ya fada a taqaice yana takawa zuwa hanyar barin falon,ko motsawa sumayyan batayi ba,wanda hakan ya burge ummee da anty maamaan baki daya,ta tabbatar da cewa da su'ad ce da tuni miqe ta rufa mishi baya "Kada ka rufe sashen idan ka shiga,anjima zamu kawo amarya" inji anty mama "Ok" kawai yace yana ficewa a sashen,kamar jira amira takeyi ta buga tsalle ta iso gaban sumayyan "Tashi muje namecy" harara ummee ta buga mata "Saura ki hanata sakewa kuma bare ta huta gajiyan data kwaso ko?" Dariya amira tayi yayin da sumayya ta miqe ta bita tana murmushi kanta a qasa. Hira ce sosai ta barke tsakaninsu,sumayya kallon amiran take,da alama auren ya karbeta qwarai,ta sake haske ta murje,tsokanan da amiran keyi mata ya soma isanta hakan ya sanya itama ta soma tsokananta kodai ta samo musu baby,wannan ya taqaita tsokanan da take mata ta barta ta sarara mata,sai da akayi sallar magariba amira ta shiga alwala sannan ta kira antyn ta shaida mata isowarsu,ta soma roqonta ta turo mata laila "Madalla amarsu,su laila zasu zo amma ban fadi yaushe ba,ke ke da ki gansu ma sai na gamsu da yadda kike zamantakewarki" kai ta langabe kamar tana gabanta "Kai anty,haka zamuyi dake?" "Har ma fiye da haka idan baki zama jarumar mace ba,baki kuma yi fiye da yadda nake son gani ba" ta fada tana datse layin,dariya ma maganar anty ta bata,bayi ta shiga itama don sauya pad din jikinta bayan fitowar amiran. Gefan gado ta kuma zama ta lalubi lambar yaya yahansu don taji abdallah,bugu uku aka daga,shi din ne ma ya daga,murmushi ta saki kan yadda yayan ke shagwaba abdallah "Amminaaa" ya fada cikin muryar quruciya "Abdallah na,kai baka damu kaga amminka ba ko?" Dariya ya qyalqyale da ita yana cewa "A nan ma ai ina da wasu ammin,ga mama ma,ga anty jamila,ga anty yaya(yaya yahanasu)"taji dadi qwarai cikin ranta jin bai tare da wata damuwa,amma sai ta dan tsokaleshi "Shikenan na sake komawa abuja na barka ai" "Nima bana son zuwa,su kullmun ana gida,nan kuwa zamuyi wasa da su walid,amma kicewa daddy na wannan wanda ya daukeni a motarsa ina gaisheshi" sarai ta gane almustapha yake nufi,sai tayi murmushi kawai ta kauda zancan "Me kake so a kawo maka yanzu" "Ba komai ammi,dazu ma da inason indomie anty jamila ta dafa min naci na qoshi,ta kuma bani bobo" "To an gaida anty jamila,ayi karatu da kyau abdallah,banda rigima" "Ai bazanyi ba,tunda ga malam dina dazu ma naje wajensa" dariya ta saki sannan tace "Ok ilove you my abdallah" "I love you too ammina"tayi hanzarin datse layin jin yaya yahanasu na qoqarin karba,nauyinta take ji sosai bata jin a irin wannan yanayin zata iya magana da ita " ki gama cin amarcinki zuwa zamuyi mu dauko abdallahn mu"cewar amira,murmushi kawai tayi din bata jin mutanan kano zasu iya basu abdallah,musamman yaya yahanasu da take jinsa kamar mukhtar,bata son ya motsa ko nan da can,shima kuma yaron kamar yasan yadda aka rabu da mahaifinsa cikin kewa baya yadda ya yiwa gida nisa,bai wuce gidansu ko gidan yaya yahanasun ko na wuni daya kuwa. Bayan sallar magariba suna hira sama sama anty maamaa ta shigo dakin "Amarya taso baabaanki na fada yace na miqa ki dakinki" a kunyace ta motsa ta miqe,gabanta na wani irin faduwa,fargaba ta cikata,haka ta fito antyn na riqe da hannunta amira na biye da su,a falo suka samu ummee,antyn ta dubeta "Ummeen yara zaki rakamu ne?" Ta fada cikin salon tsokana,wanda tasan ba zata din na,baki ta tabe tana murmushi gami da girgiza kai "Um um,sai kun dawo,ki dai jawa d'anki kunne idan yana nan" ta fada tana miqawa sumayya wani babban kwali,amira ce ta qaraso ta amsa tana taya sumayyan godiya sannan suka fice. Karon farko data fara shiga sashen tunda take zuwa gidan,kamar sauran sassan gidan haka yake saidai duka ya fisu qaawa da burgewa,biye take da anty maamaa jikinta asanyaye,kai tsaye anty maamaan ta miqawa amiran muqullan hannunta ta bata umarnin bude dakunan,sannan ta jiya da ita kafin amiran ta bude dakin suka nufi qofofin kitchen,nata ta bude mata ta nuna mata,komai na a tsare masha Allah,babu abinda ba'a tanadarwa kitchen din ba na kayan amfani,dakin farko ta fara nuna mata sannan na biyu,a nan ta zaunar da ita gefan gado sannan itama ta zauna kan kujerar dake fuskantar gadon "To mamanmu,ga gidanki nan ga dakunanki nan,daya dakin naki yana sama saidai naga kamar mai gidan kamar baya nan shi yasa bai kanki can ba,nasan zaya nuna miki idan ya dawo,duk abinda zan gaya miki nasan tuni an fada miki tun daga gida,almustapha dai mijinki je biyayya gareshi wajibi ne a gareki,kamar yadda tilas ne ya kyautata miki,bari na fada miki wani sirri na mallakar miji cikin sauqi,yi nayi bari na bari,ma'ana biyayya da kyautatawa,haquri da kai zuciya nesa,wannan shine kadai abinda zan qara miki a kai,Allah ya baku zaman lafiya ya hada kanku baki daya,ga kayan lefanki can kusan fiye da rabi a dinke suke,nasan baki taho da abubuwan buqatarki ba saidai kina iya amfani da su,amira ki tayata ku sanya kayan cikin wardrobe amma kada ki wuce awa daya,kema wucewa zakuyi keda saifullahi kada yazo yayita jiranki" "To anty" ta fada tana miqewa,kusan sumayya bata da kuzarin da zata yi aikin,amiran ce ta shirya mata duo kayan dake a dinke,sai data gama ta dubeta cike da tsokana tana mata nuni da cikin sif din "Wadannan kayan gida ne,nan bangaren qananun kaya ne na zaman falo,don bance ki raga ba wajen sanyasu,can sashin kuma kayan daukan magana ne na zuwa turaka kin gane ai?" Ta fada tana daga gira,duk yadda take ji a zuciyarta sai data bata dariya "Kin fara rainani amira,kada ki manta nifa yayarki ce yanzu" "Eh wallahi afuwa,amma sai mun fadi gaskiya,sai ma nan da kwana hudu zamu dawo ni da nafisa,sai mun baje miki aiki" ta fada tana ficewa daga sashen da gudu tana dariya,da idanu sumayya ta fita kafin daga bisani ta dauke idanunta tana girgiza kai,tana ji dama itace amiran,ba shakka babu abinda yake rayuwa cikin farinciki ba tare da matsala ba dadi. Kowanne huduba da ta samu daga kowanne sashi tayi tasiri cikin ruhi da zuciyarta,ta fuskanci kowanne sashe dake da muhimmanci a rayuwarta na supporting wannan aure,wanda ita har yau zurfin tunaninta baikai ga hango abinda su suka hango din ba,a hankali ta bude qofar toilet din dake maqale cikin bedroom din,bandaki ne wadatacce wanda aka qawatashi da dukkan wasu kayayyakin amfani na bandakin zamani,ruwan zafi dana sanyi ta hada yadda take buqata ta shower don bata fiya son shiga bathtube ba. Ta jima gaban kayan tana kallon yadda amiran ta shirya mata su,kai kawai take kadawa,batasan wacce iriyar qauna amiran ke mata ba,bata da abinda zata saka mata da shi qauna ce daga Allah,da hannu ta dinga taba kayan baccin har ta ciro wasu cotton masu kauri,riga da wando ne dogon wando,iyakar rigar cinya saidai hannun nata dogo ne,bayan ta sanya ta isa gaban mudubi,ga mamakinta irin mayukan da take amfani da su ne da turarukanta,ta tabbatar da cewa wannan aikin amiran ne shima,murmushi ta sake saki tana fadin "Amira?,amira?,hmm"sai data hade gashinta waje daya sannan ta soma mutststsuka mai bayan ta feshe jikinta da turarukanta. A fujajan haka ta shigo gidan tamkar wadda aka koro,akwatinta qwaya daya aharabar gidan ta barshi tana baiwa hadiman gidan umarni da su biyota da shi,babu kowa a falon,sauyin da falon ya sake samu kawai ya tabbatar mata ba shakka a yanzun ba ita daya bace mamallakiyar sashen,hakan ya sake tabbatar mata da cewa almustapha zai zama nasu ne su biyu ita da wata,kamar zautacciya haka ta shiha karkada kai ita daya tana fadin "Ina!,sam wallahi zuciyata ba zata jure wannan ba" ta fada tana haurawa sama cikin hanzari,zuciyarta nata mata saqe saqen irin yanayin da wai zata iya zuwa ta tadda almustapha shi da amaryarshi,kishinta na hauhawa zuciyarta na sake haukata idanunta na kuma rufewa. Tsaye yake bayan ya fito daga wanka yana sanya kayan baccinsa,a gajiye yake matuqa,so yake ya kwanta ya huta hakanan ko qwaqwalwarsa zata samu irin hutun da yake fata,sashe daya na zuciyar nashi na masa tunanin me zaya bata taci kafin ta kwanta?,tilas dunsa ne cinta da shanta na a wuyanta,duk da ya tabbata baza a rasa abinci cikin gidan ba amma shi kam bazai tambaya a kawo din ba,mutum ne da tun asali ba mai roqo ba,hakanan baison roqo,dalili da yasa har yau yawan roqo irin na sy'ad ke bashi mamaki,a hankali ta tura qofar zuciyarta na bugawa tamkar zata fito waje,wata wawiyar ajiyar zuciya ta saki ganinshi tsaye shi kadai sanye da kayan bacci,da gudu ta banko dakin wanda kafin ya kai ga waiwayowa ta ruqunqumeshi ta baya tana sakin kuka,bai ce mata uffan ba bai kuma juyowa ba,saidai yana sauraren sautin kukan da take fitarwa,tuni kukan ya soma hawa masa ka,ta sani ya tsani kuka amma hakan bai hanata rerashi ba aduk sanda tayi niyya,da faru baiyi niyyar lallashinta ba ko kadan saboda maganganun data gaya mishin dazu,amma tunawa da yayi yasha jin mata na fadin irin qunci da bacin ran da suke fuskanta takura da kuma kishi shi ya sanya shi zagaya hannunshi ya dawo da ita gabanshi suna fuskantar juna sannan ya zaunar da ita gefan gado kafin shima ya zauna,hakan yayi mata kyau da dadi qwarai,zuciyarta ta shiga gaya mata cewa ba shakka tana da nasara "Ya kamata ki nutsu kiyi controlling kanki,aurena bai nufin konai zai sauya tsakanina da ke"cikin sheshsheqar kuka tace "Almustapha,wallahi bazan iya zama da kowacce diya mace ba amatsayin wai itama matarka ce bazan iya ba wallahi,ya zama tilas ka saketa wannan dole ne" fubanta yake yana qoqarin controlling kansa jin yadda take bashi umarni kai tsaye tamkar uta din ita tayi naqudarsa kafin daga bisani yace "Look su'ad,bana so ki sake tada wannan magana,kada ki sake ambaton saki cikin maganarki don babu shi duka ciki qwaqwalwata,ki iya bakinki ki san me zaki furta" ba qaramin hasalata kalaman sukayi ba,tuni zuciyarta ta dinga gaya mata tsananin sonta yake,qaunarta yake shi ya sanya har yake gaya miki hakan a kanta,take kalaman mom dinta suka fado mata na kada ta ragawa kowa,tayi hauka sosai don ta qwatarwa kanta 'yanci,miqewa tayi tsaye tana qanqan da idanunta,hannayenta riqe a qugunta,karo na farko data shirya kallon tsabar qwayar idanunshi ta masa rashin kunya "Ai dama namiji ba dan goyo bane,gaskiya mana naji kidahuman matan africa na fadin haka,mu dama mun jima da sanin haka,to wallahi almustapha bari na gaya maka wani abu,duk eani qulla qulla da munafuncin da aka hada kan auren nan tilas ya rabu,don ni bazan taba zama da kishiya ba wallahi bata isa na hada miji da ita ba,wallahi dole ka saketa idan ba haka ba zan dauki mafi munin mataki wanda bazaiw kowa dadi ba,zan iya kashe...." Wata gigitacciyar tsawa ya daka mata wadda ta sanya ta yin shiru,cikim zafi da fushi wanda suka bayyana muraran a fuskarshi ya soma nuna ta da yatsa "Kada bakinki yayi ganganci ko kuskuren zagar min iyaye,idan kuwa kika aikata hakan ki lissafashi cikin ganganci na farko da kika taba yi cikin rayuwarki" cikin tsiwa da bushewar zuciya tace "A daki mutum a hanashi kuka,na fuskanci almustapha baka qaunata har yanzu?"cikin fushi da son cusa haushi shima yace " ke sai yau kika sani?"baki ta saki galala tana dubanshi hawaye na malala bisa kuncinta,q maimakon ya qasqantar da kai ya lallasheta shine yake gaya mata wannan baqar kalmar da ya raba fada mata can wasu shekaru baya da shka wuce,tuni ya miqe yaci gaba da daura zaren kayan baccin dake jikinsa,kai ta shiga girgizawa zuciya na tunzurata,juyawa tayi ta sauka qasa da gudu,yabi bayanta da kallo yana jan wani mugun tsaki,kai tsaye kitchen ta nufa ta zari daya daga cikin setin wuqaqenta wadda sabuwa ce dal,bata taba amfani da ita ba kasancewar babu abinda ta taba shiga kitchen din tayi tunda aka tanadar mata sji,saidai ta karbo musu koma meye wajensu umme in har ma tazo qasar,saman ta koma ta banka qofar dakin sanda yake qoqarin zama gefan gadon ta qaraso gabansa ta tsaya "Almustapha,wallahi gwara na kashe kaina da naci gaba da sauraron kalaman qi daga gareka,gwara na kashe kaina dana zauna da wata" ta fada tana daga wuqar da niyyar dabawa cikinta,cikin wani irin zafin nama ya sanya hannunshi ya riqe wuqar,wanda hakan yayi sanadiyyar yankewarsa jini ya soma diga,bai kula da wannan ko ya damu ba,don ya lura su'ad mahaukaciya ce wadda aqidar yahudawa ta gama ratsata,wannan shine karo na biyu da tayi yunqurin hallaka kanta saboda shi "Ke wacce iriyar dabba ce mara hankali,shashashar banza mahaukaciya kawai"zuge wuqar tayi daga hannunshi wanda zafin sai da ya ratsashi har cikin kwanyarsa "Kome zaka fada saidai ka fada,amma almustapha amma yau ko ban kashe kaina ba zanje na kasheta idan yaso nima a kasheni" ta fada tana juyawa da sauri ba tare data damu da ciwon data ji masa ba,da hanzari ya fincota tana waiwayowa zata sauke masa rashin kunya ya zabgeta da wani irin lafiyayyen mari daya tarwatsa tsarin qwaqwalwarta sannan ya hankadata ta fada saman gado,yasanya qafarshi ya take hannunta wanda hakan ya tilasta mata sakin wuqar ya zareta "Ban taba dana sanin saninki ba su'ad sai yau,ashe ke din ba mutum bace har kike ikirarin kashe kanki ki kashe wani?,banza wawiya kawai mara hankali" ya fada yana nufar qofa zai fice,wannan ya watstsakar da ita daga marin da yayi mata ta yunqura tana fadin maganganu cikin ihu da zummar binsa,tuni ya fice dauke da wuqar,ya sanya key ya rufe qofar sannan ya qarasa kan kujerun falon ha zaune yana dunqule da tafin hannunsa,yana iya jiyo surutanta wani cikin hausa wani cikin harshen nasara tana bugun qofar,daga bisani ya dinga ji qara ta gilasai wanda da alama barna ta soma masa cikin dakin,hakane kuwa,don duk wani glass na dakin ka daga t.v palsma,mirrow,bedside lamp babu wanda bata hada ta kwankwatse ba,cikinbqanqanin lokaci itama ta jiwa kanta ciwo,zuciya ke tunzurashi ya bude qofar ya shiga yayi mata dukan kawo wuqa yana qoqarin danne fushinsa,ya tabbatar idan yaci gaba da zama komai zai iya faruwa,zai iya gaza ci gaba da yin haquri ya bude dakin wanda ya tabbata gamuwarsu a wannan lokacin bazai haifar da d'aa mai ido ba,hakan ya sanyashi ya miqe ya gwammace ya sauko qasa,don baiga abinda zai kashi nata dakin ba. Kwance take lamo bisa gadon nata tana iya jiyo hargowa saman gidan,tuni ta dauke muryar su'ad ta kuma tabbatar itace,fargaba da tsoron irin hayaniyar data dinga ji ita ta kamata,sannu a hankali ta dinga kiran sunayen Allah,sannu sannu fargabarta da tsoronta suka gushe,kalaman anty dije suka dawo mata sanda zata taho abuja "Idan har su'ad ta tsorataki kinyi asara,wacce kalar kishiya ce baki gani ba,kada ki yadda ki kasa kyautatawa mijinki saboda wata,zaku taru ne dukanku ku zama daya,don qwace goruba hannun kuturu ba abu bane mai wuya,samun almstapha a tafin hannunki saidai idan baki so ba" tabbas haka maganar anty take,ya kamata zuwa yanzu ace ta tsike,ya kamaceta ace ta fara qwatar 'yancinta hannun kishiya,su dinma fa mata ne kamarta,don me zata zauna suna garata daga wannan waje zuwa wannan?,akanme zata zuba musu ido su dinga yin yadda suka ga dama da rayuwarta,'yanci shi take buqata wannan karon,ta kuma bawa kanta tabbaci da qwarin gwiwar tabar bari ana cutarta yadda itama ba zata cuci kowa ba to a zauna lafiya,tana buri da fatan wannan ya zame mata gidanta na qarshe koda banu soyayya da shaquwa tsakaninta da mai gidan,amma akwai da dama masu zamansun a haka girmamawa da kyautatawa ita ke musu jagora. Sallamar data ji cikin falon nasu anata yi ita ta sanyata miqewa ba tare da shayi ko fargaba ba ta zira hijabinta ta bude qofan ta fito,biyu daga cikin ma'aikatan gidan ne dauke da kwanduna guda biyu,cikin girmamawa suka dan rusuna wanda hakan ya bata kunya suna gabatar da kansu sannan suka ce "Abincin dare ne maamaa tace a kawo muku,wannan kwandon abincin yallabai ne,saidai ummee tace don Allah a sashi yaci kada yasha coffee yace zaya zauna haka" murmushi ya subuce mata wanda hakan ya bayyana fararen haqoranta,kunyar ummeen ta kamata duk da bata wajen,masar kwandunan tayi tana cewa ayi musu godiya da sannu,shka juya suka fice zucuyarsu fal mamaki da murna,ganin sauyi muraran yau a sashen yallabai,abinda ba'a taba yi musu ba,sau tari idan suka kawo abincin ma tana yatsina zata sanyasu su shiryashi saman tebur,idan kuma bai mata ba tana masifa zata basu umarnin abinda zasu dafa din komai dare. Tunda ma'aikatan suka shigo yana kwance saman kujerar yana dubansu,saidai su ba zasu iya ganinshi na sakamakon nutsewa da yayi tsakiyar kujeru runtse da hannunshi,wuqar na ajjiye saman center table dake daura da shi,to ita din ma bata lura da shi na,a nutse ta wuce taje ta shirya abincin kai dining,sannan ta sauko a hankali tana tunanin yadda zata cika roqon da umme tayi mata,ta yaya zata tasoshi kenan?,wani adon dan qullutu dake jikin kujerar da yake kwance shi ya riqe gefan hijabinta,ta waiwayo da niyyar cirewa sai ta gashi kwance,cikin dakewa da boye rudunta ta cire hijabin nata sannan ta qaraso inda yake kwancen "Ga abinci an kawo umme tace kaa......" Sai ta gaza qarasawa sakamakon ganin irin yankar dake hannunshi,gefe kadan sharbebiyar wuqar da jini ke kwance jiki,take ta tsorata,ta sanya tafin hannunta baki daya ta rufe bakinta "Ya salam,subhanallah,me yake faruwa?"ta ambata cikin rawar murya da tsorata,baiko motsa ba yana kwance ya zuba idanunshi a kanta,yanayim yadda ta firgita ya sanyashi ya miqe ya zauna wanda hakan ya sanyata zabura data hangin jinin da ya zubar wanda ya kwanta saman tiles "C'mon,kada ki taramin jama'a" ya fada cikin dakiya "Amma haka ka zauna bai da kyau fa ga lafiya zubar jini irin haka" ta fada tana kama hannun cikim rudewa ba tare da yasan ta riqe din ba,hannunshi yayi hanzarin janyewa,itama da sauri ta janye nata hannun tana zaton zafi yake ji,wannan wanme irin yanka ne daya shiga hannunshi sosai haka "Sannu zafi ko?dame za'a tsaida jinin?"tilas ya soma gaya mata inda first aid boxs dinsu yake,sai kuma ya tuna yana dakinsa ne su'ad kuma na qulle ciki "jeki kawai bai kusa" ya fada yana lumshe idanunshi tare da tunanin mai zai saka ya tsaida jinin,tunawa tayi dazun kamar taji qamshin na'a na'a da suka shiga kitchen dinta,da sauri ta shiga ta bude kitchen din,cikin sa'a ta sameta kuwa,ta debo a tafin hannunta ta sake dawowa inda yake din,har yanzu idonsa rufe yake,baisan me ake sawa atsaida jini ba bayan kayan aikin su na likita,a tausashe yaji an riqe tsaintsiyar hannunshi,ya bude idanuwansa ya zubesu a kanta,tana duqe bayan ta cire hannayen hijabinta ta sanya tissue da kwalinta ke saman table din ta goge jinin sannan ta shiga jera barbadata a saitin wajen ciwon,sai data kammala sannan ta tsaya na wajen minti hudu taga jinin ya tsaya sannan ta saki ajiyar zuciya ta saki hannun,miqewa tayi ta koma kitchen don dauko mopper bayan ta dauke wuqar,wadda har tashi tsigar jikinta keyi idan ta kalleta,da idanu ya bita kafin ya dauke idonsa ya dawo dashi kan hannun nashi yana duban abinda tayin kafin daga bisani ya maida idanuwan nashi ya sake lumshewa,ya akayi tasan wannan hanyar ta tsaida jini?,mopper da dettol ta dauko gyara wajen tas,baki daya zuciyarta a jagule take,ta tabbatar wannan ciwon na da nasaba da hayaniyar data ji na tashi dazun,wannan wane irin ta'addanci mata keyi?,mace mai laushi da taushin zuciya mai cike da tausayi ce ke iya aikata haka?,tabbas idan har ita ta aikata hakan ba zata saurara mata ba ballantana ta samu damar gwada hakan a kanta ba. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [23/02, 11:52] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 7⃣8⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* ___________________________________          Kayan ta koma maidawa kitchen,sai ya bita da kallo yana duban hannun nashi har ta shige kitchen din,a hankali ya miqe ya haura saman,a yanzun falon tsit yake da alamu ta gama haukan nata ko gajiya ce ta sata sadudar dole ganin babu wani alamu na zaya bude qofan.        Falon ta dawo da niyyar gabatar mai da abincin kamar yadda ummee ta roqi alfarma saidai bata taddashi ba,ta danyi jim don batasan inda zata sameshi ba,tilas ra juya ta koma dakinta ta sakaya qofar sannan ta haye kan gadon bayan ta sauya hasken dakin zuwa na bacci,baki daya bata da sha'awar cin komai,tunani ne fal zuciyarta,tana so tasan ta yaya haka ta faru a gidan nasu,dama su'ad din tana cikin gidan me koko yaya?.         A hankali aka turo qofar dakin sanda take tsaka da tunanin,sai ta sake lamo tana son taga waye,almustapha ne,cikin takunshi na nutsuwa ya qaraso ciki a hankali,da idanu ta dinga binsa har ya isa kan doguwar kujerar dake dakin ya zauna akai tare da miqe qafafunsa,bayansa na jingine da hannun kujerar yayin da qafarsa ke tokare da daya hannun,duk tsawon kujerar ya cinyeta tsaf da nashi tsahon,hannun nashi na ajjiye saman cinyarshi,idanunsa ya maida ya lumshe yana jin yadda zugin ciwon ke ratsa ko ina ajikinsa,bai san wanne irin hukunci ne ya dace ya yankewa su'ad ba,wacce iriyar yarinya ce haka?,wadda batasan darajat rai ba,bata san darajar al'ada da mutunci ba?,wanne irin raino ta samu wacce iriyar tarbiyya ce?,iliminta me ya amfana mata da shi?,wadan nan tunanukan su suka jagoranci qwaqwalwarsa,suka hana idanunshi runtsawa,lokaci lokaci yana tashi ya sauya yanayin zaman nashi,dukka abinda ke faruwa a idanun sumayya ne,duk wani motsinsa tana lura da shi,karon farko taji tausayinsa ya kashi,wacce iriyar mace yake aure?,rashin kan gadon nata har ya kai ta sanya makami ta yanki mijinta,mijin da take ji duk duniya tafi kowa sanshi?,ita dinma kusan duka juye juye ta dinga yi saman gadon,wanda hakan yaso ankarar da shi idanuwanta biyu,a hankali ya miqe yana tsurawa inda take kwancen ido cikin duhu duhun dakin,qarasawa yayi inda makunnin dakin yake ya sanya hannunsa ya kunna qwan,take haske ya gauraye dakin wanda hakan ya sanya ta cikin hanzari ta runtse idanunta,ido ya zuba mata yana kallonta,jikinsa ya bashi idanunta biyu,cikin dakewa murya can qasa yace "Saiki tashi ki zauna,don ba dolen yin baccin aka yi miki ba" shiru tayi ta sake yin likimo kamar mai baccin gaske,sai kawai ya qyaleta ya kashe qwan ya sake komawa inda ya taso din,kusan bacci barawo ne kawai ya fauci idanuwan kowannansu.        Tana motsawa ya farka,sai ta tsaya sak sai data ga bai sake motsawa ba,yana kallonta ta shige bandaki,pad din jikinta ta cire ta sauya wata bayan tayi tsarki da ruwan dumi,sannan ta wanke bakinta ta daura alwala ta dawo cikin dakin,gadon ta sake komawa,saidai wannan karom maimakon ta kwanta sai ta zauna sosai ta jingina da fuskar gadon idanunta alumshe tana karanta azkar,ta riga data saba koda tana al'ada ne sai tayi wannan alwalar sannan ta karanta addu'o'inta,wannan na daya daga cikin sirrin nasararta na kubcewa kamuwar sihiri a jikinta.        A hankali ya miqe ganin ana gab da sallame sallar asubahin ya nufi qofa ya fice a dakin,kai tsaye ya sake nufar saman,ya sanya muqulli ya bude dakin,kallo daya zaka yiwa dakin ka rabbatarwa kanka an masa barna ba kadan ba,don kusan duk wani abu da zai iya fasuwa an sauya mishi kamanni,a hankali yake takawa saboda kwalaben dake dakin dai dai ko ina,wanda idan baka kula ba kana iya takata,zaune take dirshan a can lungun gadon ta hade kanta da gwiwa da alama a haka ta kwana,baki daya gashin dokin dake kanta ya wargatse kai kace anyi barin shinkafa bisa kwalta,bakin gadon ya qarasa ya zura takalman da yake amfani da su idan yana cikin bedroom ya nufi toilet,a bakin toilet din ya cire wannan ya saka na shiga bandaki ya murda qofar ya shige,wanda warar bude qofar shi ya farkar da ita daga baccin da ya saceta,da hanzari ta duro daga gadon wanda hakan yayi sanadiyyar yankewarta da kwalbar dake tsakar dakin,bata damu ba ta isa bakin toilet din ta tsaya yana kiran fitowarsa,wanda badon shakkar kada ya aikata mata wani mummunan abu ba afkawa kawai zatayi.        Ruwa ya hada mai dumi yayi wanka sannan ya daura alwala,ya zira rigar towel ta wanka ya fito,bai kula da ita ba har sai data ce "Almustapha!" Wani kallo ya juyo ya watsa mata wanda ya sanya ta nemi iskancin data tsara yi masa ta rasa,bai sake waiwayarta ba sai ya wuce ma'ajiyar kayansa ya bude,bin bayansa tayi ta tsaya tana qoqarin bawa kanta qwarin gwiwar yi masa wata tijarar,fidda jallabiya ruwan madara yayi ya sanya da hular tashi ka fiya naci bayan ya feshe jikinsa da turare,sannan ya dauki darduma yana niyyar wucewa,gabansa ta sha cikin gunjin kuka "Almustapha ni zaka wulaqanta?,wallahi wallahi nafi qarfin wulaqancin namiji,kuma wallahi yau sai na tashin hankalin kowa a gidan nan"hannu ya sanya janyeta gefe guda ya wuve,don ya tabbata matuqar yaci gaba da saurarenta hannunshi zai kai ga tumurmusata cikin fasassun kwalaben dake dakin.       A guje ta fito daga bangaren nasu ba tare data damu da suturar dake jikinta ba ko ciwukan data ji ba,kai tsaye bangaren baabaa ta nufa wanda gab da zata shiga suka kusa karo,da sauri ya ja da baya a tsorace yana ambatar "Subhanallahi waye haka?" Kuka ta saki iya qarfinta wanda duk mutumin dake daura da su zai iya jiyota "Baabaa kun jawo min masifa da bala'i ina zaman zamana,me nayi muku haka kuka bibiyeni da irin wannan sharrin?" Sam bai ma fuskanci me take fadi ba,don sai da ya gyara gilashin idanunsa sosai ya iya gane wace,duk da hasken ya fara gauraye garin,kasancewar babu wanda yasan da dawowar tata "Wuce ciki muje kada ki tara jama'a da sassafen nan" cewar baaban yana mai juyawa zuwa ciki lura da irin shigar dake jikinta,ba zaya so ma'aikatan gidan maza su fito su ganta haka ba,dole ta bi bayansa tana jin kamar ta danna masa ashar,dole tabi a sannu don ta sha kansa ya sanya mustapha ya saki wannan auren.       Ummee na tsaye falon tana kintsa shi kasancewar su ke masa gyaran da kansu,sanye take da doguwar riga da hijabinta wanda sallah ta idar ta fito falon "Bata hijabi kilishi ta sanya" cewar baabaa yana wuce bedroom dinsa,waiwayowa tayi cikin mamaki tana duban su'ad,mamakin irin ciwukan dake jikin su'ad din wanda duka kusan yanka ne,itama idanun su'ad din qyar cikin nata,wata tsanar ummen take ji,tana jin laifinta ma yafi na baabaan yawa,tunda uwarta ta gaya mata tun usuli ummeen dama bata qaunarta,bata furta komai ba kamar yadda su'ad din bata ce ba ta juya daki ta fiddo hijabin ta kawo mata,kamar wadda aka bawa kashi haka ta sanya hannu ta amsa,bata tunanin kaf rayuwarta ta taba sanya hijabi,amma ya zata yi da wannam tsohon dole ta saka don cikar burinta,yanayinta kawai da ummee ta gani ya sanya ta sake tsare gida taci gaba da aikace aikacenta,ta tabbatar akwai wata a qasa,don dama can macace da bata daukar raini a hakan baabaan ya fito.        Cikin sheshsheqar kuka bayan ya sake tambayarta ta soma magana "Yanzu an kyauta min kenan baabaa an yimin adalci,haka akeyi bada sani na ko yarda ta ba kawai a yimin kishiya(nace hmmmm ko ta dauka a america take)?" Murmushi ya dan sake kafin yace "Banda abinki su'ad ai ita kishiya lokaci ce,idan lokacinta yayi sai tazo ko ka yarda ko baka yarda ba,zancan sani kuma mai gidanki shine a haqqu da ya sanar da ke" "Amma ai bakinku daya shi yasa shima bai gaya min ba,gaskiya baabaa ni dai idan ana son zaman lafiya tofa a raba auren nan,ka duba jikina baki daya daga jiya zuwa yau,nan gaba abun sai yafi haka" a nutse baabaa ya soma yi mata bayani da kwantar mata da hankali tare da bata kyawawan misalai na kishiyoyin dake zaune lafiya,ciki kuwa harda su ummee,ga zatonshi tana saurarenshi ne amma kafin ya kai qarshe sai kawai ta saki ihun kuka,miqewa ummee tayi tana tabe baki sabida baabaa ya hanata magana,ficewa tayi don ba zata iya ganin wannan iskancin ba,itama miqewar tayi "Wallahi ni bazan zauna da shi ba" ta fada tana yage hijabin jikinta ta wurgar ta fice,miqewa baabaan yayi cikin nutsuwa ya taka a hankali yabi bayanta zuwa sashen nasu,karo na farko da  ya soma zuwa sashen.          Yanayin tafiyar tasu ba daya ba,hakan ya sanya ya cimmata a falo sanda take yunqurin haurawa sama,kiran sunanta yayi tare da bata umarnin tazo ta samu waje ta zauna,kwarjini yayi mata amma da niyyarta ko 'yar harara ta banka masa,sai ta kasa haka ta dawo ta zauna din tana rusa kuka.        A hankali cikin nutsuwa ta bude qofar dakin nata ta fito,gama tilawarta kenan tana rufe alqur'anin da niyyar sake kashingida kasancewar lokacin bakwai na safe tayi sai taji kamar muryan baabaan,fuskarta qunshe da murmushi kunya da girmamawa ta qaraso inda yake tsaye,ta rusuna har qasa tana gaidashi,shi din ma fuskarsa sake take,farinciki na ratsashi ya amsa gaisuwan nata "Yaya kwanan baqunta?" Ya tambayeta,kunya ta kamata ta sadda kanta qasa "Maza kiramin almustapha" cewar baabaa,miqewa tayi cikin ranta tana taraddadin inda zata nufa,shahada kawai tayi ta nufi saman yayin da su'ad ta bita da kallo mai dauke da harara zuciyarta na zugi "Banza kawai 'yar qauye" take ambatan hakan cikin zuciyarta,fata take barazanarta ta kafu cikin zukatansu,addu'a take Allah yasa almustaphan na saukowa baabaa ya sanyashi ya sallameta ta huta.        Idanu ta shiga rarrabawa tsakanin qofofin,ta tsaida idonta kan qofar da tafi kowacce fadi cikin qofofin dakunan dake saman,nan ta nufa ta sanya hannunta cikin fargaba da runtse ido ta tura qofar,tashin farko ta taka daya daga cikin kwalaben dake dakin,zafin ya ratsata har qwaqwalwarta "Wash" ta furta wanda hakan yayi sanadiyyar dago da kanshi daga kallon dan qaramin qur'anin dake hannunshi,wanda tun bayan daya kammala sallar asubah yake tilawa duk don nemawa kanshi sauqin zugi da radadin da zuciyarsa keyi,babu shakka sai ya hukunta su'ad din hukunci mafi tsanani don gayara mata zamanta,ba'a taba nuna masa raini irin wannan ba,ya fuskanci ya sakar mata mara ne da yawa,bai fuskanci illar sakar mata din ua yayi ba kamar yadda su hamza ke nusasheshi ba sai yanzu,to ba zaya lamunci wannan iskancin ba,idan taga zata iya zama bisa doka da tsarinsa ta zauna,idan kuma ba zata iya ba tana iya yanke duk hukuncin da take so,amma tilas idan tana son zama da shi tabi dokarsa,idanunshi ya maida kan qafarta data dage sannan ya sake maidawa kan fuskarta,yaso ya share sabida yana ganin duk sune silar damuwarsa cikin satin musamman tsakanin daren jiya zuwa yau,sai kuma ya gaza daurewa kasancewarsa mutum mai tausayi,uwa uba kuma kulawar data bashi daren jiya har yau tana yawo tsakanin idanunshi "Tsaya a nan" ya fada yana ajjiye alqur'anin hannun nashi,a hankali ya tako zuwa inda take tsaye ya duqa,yana son kama qafar saidai ya rasa ta inda zaya fara,yayin da ta runtse ido sabida zafin da take ji,a hankali ya sanya hannun shi dai fai idon sahun ta,ya sanya yatsunsa uku ya zaro ragowar kwalbar ya cillar gefe,mitsa qafar tayi da alama taji zafin haka,a hankali ya saki qafar sannan ya miqe tsaye,wanda hakan ya zamanto suna tsaye dab da juna,idamunsu suka hadu da sauri ta janye idanunta tana ja da baya saboda yadda taga yayi dab da ita,caraf taji ya kama hannunta cikin daga sauti yace "Kula!" Ta dan tsorata,ta waiwaya baya sai taga madubi ne fasashshe dab da qafar tata saura kadan ta taka,hannun ya saki tayi qoqari tsayawa daidai "Baabaa yana kiranka,yana jiranka a qasa" idanuwanta na qasa bashi take duba ba,sai ya gewayeta zai fice,har ya murda qofar cikin sanyin murya tace "Ya hannun naka?" Waiwayowa yayi cikin sa suka sake hada idamu,wannan karon shi ya fara kauda kanshi,a gajarce yace "Alhamdulillah",ya ambata yana qarasa ficewa daga dakin,maida idanunta tayi cikin dakin,mamaki ya kamata na ganin yadda dakin ya zama kamar wata bola ta gilasai,komawa tayi ta lalubi tsintsiya da paka ta soma tattare kwalaban cikin taka tsantsan da tsantseni. Cikin lokaci qanqanin ta kwashe duka kwalaban tsakar dakin wanda ta gani,ta zuba cikin wani dan kyakkyawan kondon shara dake bayan qofa,ta dago kenan aka banko qofar wanda hakan ya sanya goshinta bugewa duk da bata wani buge sosai ba amma taji zafi,dafe wajen tayi tana dubanshi,ko baka sanshi ba kana duban fuskarshi kasan ya kai qarshe wajen fushi da bacin rai,su'ad ce biye da shi wadda dukkan hudubar da baabaan yayi musu ta bayan kunne tabi,wanda badon tsoro da tsinin idon almustapha ba saita gaggaya masa magana,biye take da shi tana ambatar sunanshi wanda ya wuce kai tsaye zuwa ma'ajiyar kayanshi ya fidda suit ash and pink ya ajjiye yana lalubar tie din da zai daura,bayanshi ta tsaya cikin kuka da masifa tace " wallahi almustapha sai na tafi ko baka so,ba kuma zaka sake gani na ba"a wani fusace ya waiwayo yana mata kallon banza,cikin masifa tamkar wanda zai fidda garwashin wuta daga bakinsa yace "Wa ya riqe qafafunki?,kina mafarkin ni mustapha zan tsaidaki na hanaki tafiya?,idan kinso kifi iska ko guguwa gudu,amma ina son kisan abu daya,ni muhammad almustapha kada ki damo zaton cewa zan biyo sahunki,kada ki soma mafarkin zan taka qafata muhallinku da sunan biko,zaki gane cewa ni din cikakken dan halak ne,jinin......." Da hanzari ta ajjiye fakar da tsintsiyar ta fice zuwa falon,don bata da hurumin sauraran wannan case din,yana kammala fadin haka ya ci gaba da abinda yakeyi,cikin zafi zafi ya soma shiryawa,juyawa tayi da wani irin sauri ta fice tana sakin kuka,bata taba zaton cewa ita din ba kowa bace bata kai matsayin kowa ba wajen almustaphan sai yau,ta tabbatarwa kanta sai tayi nisan da zai mance wace su'ad,ta hakanne kadai take ganin zata iya hukuntashi,yadda idanunta suka rufe ya sanya bata kula sam da sumayya ba har ta sauka qasan a gurguje tana kuka. A gaggauce ya fito daga cikin dakim zuwa falon,jeat da shi ba qaramin kyau shigar tayi masa ba,saidai zuciyarsa a hargitse take sabanin yadda shigarshi take a tsare,inda take din ya qaraso a gaggauce,hannunshi ya sanya ya daga nata hannun wanda take dafe da goshinta saboda dan zugi zugin da yake maga,kalla yayi sannan ya saki hannun nata,hannunshi ya zura aljihunsa ya fiddo takarda da kudi ya ajjiye mata yayi gaba yana cewa "Kada ki damu da cewa sai kin gyara dakin,ga number nan da zaki kira wanda zai kawo miki dukan abinda kike buqata,if kinason kiyi breakfast a wani waje ki kira duka za'a kaiki" ya qarashe maganar yana ficewa yayin data bishi da kallo,cikin qanqanim lokaci ta fuskanci tabbas akwai wata hargitsatstsiyar rayuwa da dangantaka cikin duniyarshi,har ga Allah taji tausayinshi ya tsarga mata,ta jima kafin ta miqa hannunta ta dauki takardar,rubutu ne a tsare wanda kana kallo kasan gwanin iya rubutu ne ya tsarashi sabanin rubutun likitoci da mafi yawa bai da kyau,ajjiye takardar tayi saman kudin ba tare data damu taga ko nawa bane,dakin ta sake komawa cikin nutsuwa ta kintsa komai ta goge ko ina,cikin qanqanin lokaci ya dawo hayyacinsa,sai rashin kayan qawa kawai da yayi. Qarfe goma saura ra sauko,falon babu kowa,saidai tana iya jiyo motsi mai qarfi wanda yake tabbatar mata daga sashen su'ad ne,dakinta ta koma tayi wanka ta shirya cikin dinkin atamfa riga da zani plain,mai powder lipstic su kadai ta buqata,sannan ta feshe jikinta da turare,mayafi ta samu wadatacce ta yafa saman kanta wanda ya dace da shigarta ta fito matar bahaushe zam,plat din takalmi tayi amfani da shi sannan ta rufe dakin ta fice baki daga sashen. Bangaren ummee ta nufa kai tsaye,tana gab da zata shiga ta jiyoshi "Matar yayanmu" waiwayowa tayi fuskarta qunshe da murmushi,mahmoud ne shima dariya yake ya qaraso inda take "Allah ya taimaki matar yaya,an tashi lpy,ni qi bansan da isowarku da gurinku zanci abincin dare" dariya yaso bata,wanne gu zaici abinci,gidan da tunda suka shigoshi zuwa yau babu cikakken nutsuwa da kwanciyar hankali,koshi mai gidan bata tsammani yasanya wani abu cikinsa daga jiya zuwa yau din,tare suka jera suka taka zuwa ciki tana amsa masa yana zolayarta. Ummeen na zaune a falon tana karyawa,a hankali ta qarasa gabanta ta zube tana kwasar gaisuwa,ajjiye cup din ummen tayi tana dubanta,lokaci guda yarinyar ta soma burgeta,tana hango tsantsar nutsuwa hankali da tarbiyya irin na diyan bahaushen asali tattare da ita,zata iya cewa kaf DANGANTAKAR da suka taba da su'ad bata taba gani ta ko russuna ba wajen gaida daya daga cikinsu,gaisuwa take musu irin ta turawa,a tausashe cikin qauna ummeen ta masa kafin tace "Na aika a kai muku abun kari,su kuma gyara sashen halan kunyi sabani ne" "Eh ummi,amma na kammala gyaran sashen ma" "Masha Allah" ummin ta fada cikin farinciki gane da sauyin da ya fara samuwa shiru ya biyo baya saboda ficewar mahmoud bayan ya gama tsokane tsokanenshi "Kije ku gaisa da maamaa ko,idan kun gama ki hawo sama ina so muyi magana" a ladabce ta amsa mata kana ta miqe a nutse ta fice. Bata jima wajen anty maman ba ta dawo,a darare ta haura saman,ta tura qofar dakin ta shiga bayan ta nemi izini wajen ummeen tayi mata,nuni tayi mata da gefanta inda take zaune gefan gado,a kunyace sannan a darare ta zauna,hannayenta baki daya ummee ta kamo cikin nata "Ki saki jikinki amiran umman khalipha,ki daukeni kamar mamanki kamar yadda na daukeki tamkar tawa amiran" kai ta gyada alamun to "Ina fata jiyan kin min alfarmar dana roqa wajenki ko?" Ta jefo mata tambayar,nauyi ya saukar mata,ta yayq zata gaya mata baici abincin ba sabida abinda ya faru a sashen nasu?sai data gama karantarta sannan tace "Kada ki damu,na tabbata jiya akwai abinda ya faru mara dadi a bangarenku,tunda yau naga ya fice ba tare da yazi gurina ba,yakan yi hakanne matuqar akwai matsala,baya son yazo naga damuwa kan fuskarshi bare hakan ya shafi tawa walwalar......sumayya" "Na'am ummee" ta amsa kanta a qasa "Ta iya yiwuwa baki son almustapha,ta iya yiwuwa bai miki ba,ni da baabaanshi duka shaidane biyayya ce ta hadaku kuke zaune,ban sani ba ko zan iya neman wata alfarma wajenki" "Ummee ki fadi ko meye,in sha Allah ni mai biyayya ce a gareki" ajiyar zuciya ta saki "Sumayya,ina son don Allah don annabi ki dauka min alqwarin bawa almustapha dukkan wata kulawa da macen qwarai ke baiwa mijinta,ki taimaka ki zama sikar dawowar walwala da jim dadinsa,rashin kyakkyawar zamantakewar auren mustapha ta jima tana cimin rai,ba tonon asiri ba sam almustapha baisan dadin aure ba,bashi da abun fada game da aure tsawon shekarun daya kwashe,yana da buqatar samun wata mace a gefansa,macen data kasance ba uwa bace,macen da zata karbi sunan abokiyar rayuwa mai tallafar damuwa farinciki nasara dama asara,macen da zqi jingina da ita ya sauke damuwarsa,macan da zata iya daukar role na mahaifiya a bigiren da mahaifiyar tayi nisa ko babu ita,macen da zata kasance ko yaushe daura da shi,zaki iya zama dukkan wadan nan abubuwa a rayuwar mustapha?,zaki iya min wannan alfarmar wadda ni ban isa na yiwa rayuwar tasa ba?,zaki taimaka wajen gyaran rayuwarshi kamar yadda baabaa ya taba roqa daga gareki?" Nauyi kunya da tausayin ummeen suka dabaibayeta,babu shakka kowacce uwa tana qaunar danta,tana buri da fatan ingantuwar rayuwarsa,don me ba zata yiwa wadan nan mutane masu karamcin wannan karamcin ba? "Nayi miki ummee nayi in sha Allah,saidai ki yimin afuwa aduk sanda aka samu gazawa kan hakan" madaukakin farinciki ya kama zuciyar ummeen,lallausan murmushi shinfide kan fuskarta tace "Ina roqon ubangiji ya albarakaci gabaki da bayanki,damaki da hagunki,samanki da qasanki,ya faranta miki yadda kika saka farinciki a zuciyata,kike kuma da burin sakawa a nan gaba cikin ruhin daana,ba shakka bana zaton za'a samu kasawa,zan tsaya miki sumayya da dukkan tsayawa wadda ta dace suruka tayi cikin rayuwar surukuwarta,na gaya miki waye mijinki almistapha?,me ye tsarin rayuwarsa?,me yafi so me kuma yafi qi?" Kunya ta dabaibaye sumayya,tayi qas da kanta tana murmushi,haqiqa bata taba cin karo da uwar miji ba a tarihin rayuwar aurenta irin ummen "Daina kunyata,ni uwace amira,ni da nake tsammatar zuwanki gareni neman shawara idan abu ya shige miki duhu"murmushi ta sake saki kawai ba tare da tace komai ba,a hankalu ta dinga gaya mata ra'a yoyin almustaphan,wasu su bata mamaki,wasu taji sunyi mata tsauri,sannan ta rufe da cewa "ina fata zaki rufe tarihin kaiwa mijinku abinci a duk sanda yake qasar nan,kamar yadda duk lokacin da adam ke gari babu wanda ke aikawa da abinci sashinsa" "In sha Allah ummee" "Da kyau,saiki fara daga yau,duk da nasan cewa mawuyacine yadda ranshi ke bacan nan idan bai tsiri komawa dubai ba a gobe,a duk sanda hakan ta hadashi da ita yakan dauki wannan mataki me don ragewa kansa bacin rai,saboda bashi da wani abu da zai iya kawar masa da wannan bacin rai a ganinsa sai nisantar inda ran mashi ya baci,tun yana qarami haka yake,rashin tsayyar mace kusa da shi ya zame masa al'ada,ina kuma fatan nan da lokaci kadan zaki maida wannan al'adar tasa ta zama tarihi,kada ki damu,sannan kada ki hanashi,hakan ma wata dama ce da zaki sake bitar halayensa da shirya yadda zaki bullo" "To ummee" "Allah yayi miki albarka" ranta qal take amsawa,tana jin cikim zuciya da gangar jikinta wani muhimmin taimako da sadaukarwa zata yi,karo na biyu a rayuwarta tun bayan barinta gidan lukman (Gareku iyayenmu mata,wallahi na qaramin lamari banr roqawa yaronki mace ta gari cikin addu'arki tun yana qaraminsa,MACEN JARABA ba qaramin hatsari bace cikin rayuwar d'aa namiji,babu babban dacewa da jin dadin rayuwa ga namiji irin samun MACE TA GARI,manzan Allah S A W yana cewa mafi jin dadin duniya shine mace ta gari,rayuwarshi zata iya tarwatsewa ya rasa walwala har ya koma ga Allah a dalilin rashin mace ta gari,Allah kasa mu dace,ka hada 'ya'yanmu,'yan uwanmu,iyayenmu qannenmu yayyenmu mazajenmu da mata na gari). Kusan yadda ta dawo qasar bada sanin kowa ba a gidan haka ta hada kayanta ta nufi airphort da zummar komawa america,tana jin wannan karo duk son da takewa muhammad almustapha zata yakiceshi gefe ta hukuntashi,ta azabtar da zuciyarsa ta hanyar yin nesa da shi da hana shi ganinta,sai ta rama ninkin wulaqancin da yayi mata. Wannan kenan. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [23/02, 11:52] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 7⃣7⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *Allah S W T yana cewa* *RANAR DA WASU FUSKOKI ZASUYI HASKE,WASU FUSKOKI KUMA SUYI BAQI(RANAR QIYAMA)* ___________________________________          sai la'asar sannan sumayyan ta koma bangarenta,sosai taji dadin zama wajen,sunyi hira mai muhimmanci da ummee,wanda tun tana jin kunya da d'ari d'ari har ta soma sakin jiki,ta sake qwarai cikin ma'aikatan gidan,wucewa tayi bangarenta tana tunanin me zata tanadar masa,kasancewar baison cin abun mai nauyi da daddare,yayin da itama ummee ta shiga tata sabgar tana tunanin yadda zata bullowa mustaphan matuqar ya tada maganar tafiya dubai,wanda tasan mawuyacine bai ambaceta ba.        Qarfe takwas na dare da mintuna ashirin ya tako cikin falon wanda babu motsin kowa sai na na'urori da kuma hasken qwayaye,samanshi ya nufa kai tsaye yana furzar da hucin iska daga bakinsa,shi daya yake tuno gamonsa da su'ad lamarin na sake bata ranshi,ya tabbatar da cewa ta tafin kamar yadda ta fadi,hakanan shima yana kan nashi qudurin na baiga abinda zai sanya shi nemanta ba koda zasu shekara dubu a haka,turus ya danyi yana mamakin yadda dakin ya dawo hayyacinshi bayan yasan me gayaran dakinshi baya nan,don bai gaya mishi zuwanshi abuja ba,da yake idan ba kowa a sashin sallamarsu yake har sai randa suka zo,a hankali tamkar mai ciwon qafa yake takawa yana duban yadda komai ya zama neat kamar ba'a yi waccar barnar ba ciki,a haka har yaqarasa bakin gado ya soma fidda kayan jikinsa yana mamakin wanda ya aikata hakan,bandaki ya shige yana niyyar hada ruwan wanka,tsayawa yayi cike da shakku yana tunani ta ina aka samu ruwan wanka haka?,mai dumi da qamshi,cikin kokwanto ya sanya hannunshi cikin ruwan,anya ba jinnu ke neman yi masa wasa da hankali ba,take sha'awar yin wankan ta sake kamashi,saboda ruwan yayi masa dai dai irin yadda yake so,bai bata lokaci ba kuwa ya shige kwamin wankan abunshi,ya kwanta luf a ciki gajiya na warwarewa daga jikinsa yana zaton anya ba ummee bace tayi masa duka wannan hidiman,yasani cewa ita kadai duk duniya tafi kowa sanin abunda yake so,saidai a iya sanshi ummen bata taba takowa sashen nasu ba,a hankali zuciyarsa ta shiga masa tariyar awannin da suka shude dazu,sanda ya cimmata tana tattare kwalaben dakin,anya ba ita tayi wannan aikin ba "Ba ita bace,me zata iya wannan,bai tunanin tana da fikirar da zata iya duka wannan aikin,ita dinma bata ma yi masa kwata kwata kalar masu kuzari a jikinsu da zasu iya wannan aikin ba daga safe zuwa yanzu(nace lol saboda baka saba gani cikin gidanka ba)" hannunshi ya daga ya kalla inda yankan yake yana kallo,har yanzu wajen jazur yake abinka da farar fata,yayi mamakin yadda wajen ya kame haka da wuri,sannan zugin ya ragu sosai,ya tuna yadda tayi masa treating hannun,bai taba dauka ana irin hakan ba a gaske,yasan dai a fina finai hakan na faruwa,ko kuma ga matan turawa wa mazajensu ko samarinsu,tunanin ya dauka ya ajiye gefe,yana da buqatar barin qasar nan a  gobe ko zai samu nutsuwar zuciya,yana jin bai da wani abunyi a cikinta,wannan tunanin ya sanyashi miqewa daga cikin ruwan wankan ba don ya gama awannin da ya sabayi ciki ba,ya saba kunfa ya qarasa wanke jikinsa ya daura towel ya fito.        Bakin madubinsa ya tsaya da niyyar yin shafa,sai a sannan ya lura madubin nashi ya koma babu komai a kai saboda haukar daya fuskanta a daren jiya,wani mugun tsaki ya ja,yana sake jin zafinta da haushinta,tana kuma sake fice masa a ka,wani dan abu ya danna gefan gadonsa ya janyo wata qaramar locker,take dukkan wasu kayan shafe shafensa suka bayyana,ya kwasosu ya watsa saman madubin yana dauka daya da daya yana amfani da kowanne a muhallinshi,bayan ya kammala ya fitar da qananun kaya ya saka sanann ya sanya takalmi wanda ya dace da kayan.        A nutse yake saukowa qasa,har yanzu falon shiru yake "Me taci tun safe zuwa yanzu bayan lawal yace ba wanda yayi kiransa" yake rayawa cikin ranshi,mutum ne mai qoqarin sauke haqqin da ya rataya wuyanshi,hakan ya sanya ya taka a hankali ya isa cikin corridor da dakunanta suke,ya murde qofar ya tura,tsaye take cikin nutsuwa saman abun sallah,sanye da yalwataccen farin hijabi wanda ya saukar mata har saman qafafunta,hannayenta na hade saman qirjinta kanta a sunkuye tana karatun sallah murya qasa qasa,sakin qofar yayi ya koma da baya idanunsa a kanta kafin ya juya baki daya ya fice,idanunsa ya lumshe kana ya budesu yana ficewa daga sashen ba tare da ya iya tuna komai ba.      Ummeen na zaune gefan baabaan yana cin abincinsa,yayin da bangare guda kuma ya bata dukkanin kunnuwanta yana saurarenta cikin gamsuwa,sai data kammala tsaf sannan yace "Wannam shawarar taki tayi dai dai,don nima abinda na yanke kenan cikin raina....." Sallamarsa ita ta katse hirar tasu,baki dayansu idanuwansu na kanshi wanda hakan ya tabbayar masa maganarshi suke,cike da girmamawa ya qaraso gurin,ya zauna a gabansu kamar yadda suma suke zaune saman rugs din dake wajen ya lanqwashe qafafu "Barkanku da warhaka" kusan lokaci guda suka amsa mishi,sama sama suka fara hira da baabaa ummee na gefe tana kallonsu tare da karantar yanayinsa,tana hango irin yadda mustaphan zai koma matuqar tsarinsu ya cimma gaci,mustphan irin mutanen nan ne da basu iya so kadan ko qi kadan ba,hakanan idan abu ya fita a kanshi zaiyi wuya ya kuma waiwayarsa "Baka son abu mai nauyi at night,gashi naga kaman kana son tuwo...." "Barshi baabaa.....matarshi tayi masa kalar abinda yafi wayo a gun" ummee ta tari numfashin baabaa,waiwayowa yati fuskarsa qunshe da murmushi yana duban almustapha,farinciki yaji,wato hakan na alamta fara samun sauyi kenan cikin rayuwar mustaphan "To kaji abinda ummenka tace,sai ka barmin abincin tsaffin mata na" kansa ya dan sadda qasa yana sakin murmushi "Baabaa,ina tunanin gobe in sha Allah nakeso na wuce dubai,na baro company kan aiki,mun fara fidda sababbin design da wasu companies keso na sabuwar shekara,wannan karon harda vails mukeso mu fidda" kai baba ke kadawa cike da farinciki da kuma alfahari kan irin qwazon da Allah ya bawa almustaphan "Masha Allah,Allah yayi albarka ya kuma taimaka,saidai ita mai dakin naka ai bata da visan shiga dubai ko?" Addu'a ya soma cikin ranshi kada baban ya ballo masa ruwa "Baba ai nan da nakeso ta zauna......" "Ban yarda ba,ka daga tafiyarka sai jibi ko gata zuwa lokacin na sa an buga mata visa,and then bana son zaman hotel,ina son zaman hotel ya qare maka,ka koma naka gidan" kanshi a qasa yana dawurwura,da zai iya da ya nemi alfarma wajen baaban,saidai bazai iya musu da shi ba "Shikenan,za'ayi yadda kakeso din in sha Allah,amma baba gidan zai dauki a qalla wata uku kafin ya zaunu,saboda akwai wearing na abubuwa da za'a yimishi,kasan komai na qasarsu a tsare yake saida amincewar gwamnati zaka yi" "Ba komai,sannan gobe ka zauna gida ka huta hakanan,ko don ciwon hannunka" baisan me zai zauna yayi a gida ba,amma ko bazaiyi komai din ba babu musu tsakaninsa da baba "In sha Allah" "Kira maman tawa ta kawo passport dinta idan yana kusa" rasa yadfa zaiyi yayi din bashi da numberta,baiso kuma ya fada hakan ya bata ransu,iyaye ba wasa ba tuni dukkaninsu suka fahimci hakan "Ka amshi number wajen mamanka tunda sai an gaya maka abinda ya dace,tashi kaje ka kirata" ba musu ya miqe yayi hanyar waje,da idanu suka rakashi,kowannansu zuciyarsa cike da farinciki tare da cikakken alfahari da shi,mustapha na dabanne cikin zuriyar gidan,tsananin biyayya da qaunar iyayensa na dabanne cikin zuciyarsa.        Riga da skert ne a jikinta na atamfa wadanda suka zauna cas a jikinta,ta rasa wanme mayen tela ne har ya iya fidda qirarta haka,ta tabbatar sharrin amira ne,gashinta ta ware bayan ta gama feshe jikinta da turaren jiki da na gashi,dariya ta subuce mata sanda take taje kan,tana kwatanta zata iya tunkarar mustapha kenan zuciyarta ke nufi.      Turo qofar da akayi shi ya sanyata juyowa da hanzari,tsaye yake a bakin qofar hannunshi riqe da handle din qofar,janye idanunshi yayi daga cikin nata idon ya maida kan gashinta wanda ya sauka har qasan kafadunta,baki ya tabe a zuciyarsa,wato itama tana jona gashi irin wanda su'ad keyi kenan,wanda sunsha kai ruwa rana da shi akan gashin dokin,duk sonshi da gashi bai son attachmen "Ki fito ki sameni a falo tare da passport dinki,wannan abun kuma da kika qarawa kanki ki tabbatar kinje an cire miki shi" ya nuna kanta da bakinshi,a hankali ta daga hannunta ta dora saman kanta don taji me yake nufi,itakam idan banda gashinta bata ji komai ba,bata fahimceshi ba bata kuma zurfafa tunani ba ta daure gashin nata ta zari hijabi ta zura,sannan ta janyo jakar hannunta ta fiddk passport din nata wanda dama tunda suka dawo daga uk yana ajjiye a ciki ta fito falon cike fal da mamakin me zaiyi da passport dinta kuma?.        A tsaye ta taddashi hannayensa cikin aljuhunshi,da idanuwa yayi mata nuni ta wuce gaba,kanta a qasa tayi gaba ya bi bayanta,tamkar wanda aka sarqafe idanuwanshi haka ya dinga bin duk wani takunta da kallo,tamkar wadda ke rangaji haka take ajjiye takunta anutse,duk jin kan su'ad da jin ita din wata ce wajen iya gayu maqale magana da tafiya bai taba ganin tayi irin wannan salon ba,ko don bai kallon mata banda su'ad ne oho,shi a nashi tunanin ko wacce mace tana sane take nau'in waccan tafiyar saboda tashi madam din kawai ya sani,baisan komai da ya shafi shirgin mata ba,tsakaninshi da su ya duba su idan lalaura ta taso.       "Wait" ya ambata sanda take gab da shiga sashen,ya qaraso a hankali ya daidaita da ita sannan suka shiga,kamar ko wanne lokaci haka ta gaida baabaan,ya miqa hannu ya karbi passport din nata "Ki shirya in sha Allah zaku wuce dubai gun aikin mijinki,ina ga kamar hakan zaifi ko?" Kanta sunkuye cikin fargana da gaduwar gaba tace "Duk yadda kace baba yayi" murmushi ya saki don dama yasan ba matsala tattare da ita,yana fatan hakan zai haifar da alaqa mai tsafta kyau da danqo a tsakaninsu,kai yake gyadawa cikin farinciki ya sanya musu albarka kana ya sallamesu yace su wuce sai da safe,tare suka sake jerowa,saidai suna zuwa gab da sashen ya ja da baya ya koma ya yiwa kansa mazauni kan daya daga cikin kujerun hutawar daya qawata wajen da su,daura da inda fanfunan nan suke,hannunsa ya sanya ya fidda wayarshi dake burari,hamza ke kira,dora wayar saman tebur yana kallonta har ta qaraci kukanta ta katse,sai da ya hada misscall wajen biyar sannan ya dakata,bai bi takansa ba,yana ciki da shi,ji yake kamar shi ya masa bakin da ya bishi sanda zai taho daga dubai,sai da ya mula don kansa sannan ya daga wayar ya kirashi,bai iya fushi da hamzan amini ne na qwarai "Maan,ina ka shiga ne inata kira,ko ana angonci mode" ya fada dariya na son subuce masa "Allah ya isa tsakanina da kai wallahi hamza shege mai mugun baki" dariyar da yake son dannewa bata barshi ba sai data subuce,wanda har sai da mustaphan ya dage wayar kadan daga kunnensa sabida dariyar da yake zabga mishi,tuni hamzan ya samu labarin komai "Me kuma nayi,sunnar ma'aiki na maka fatan sake rayawa fa kuma ta tabbata" "Na rantse idonka idona sai na karkatar maka da baki,idan yaso tayi jinyarka da kyau waccar 'yar kazar taka" "Qarya kake wallahi abida ta wuce kaza a wajena giwa ce,kuma zaka bada bayani dalla dalla duk sanda ka shiga hannu wallahi,gwara ka fara saita kanka tun yanzu,ni nasan me nake aure shi yasa na sallamawa matan africa espicially na nijeria,nijerian ma AREWA,they are special over wlh" "Close your mouth malam...yaushe zaka koma,kayan dake warehouse sunyi qasa fa sosai" "Kai barni,haka kawai ina tsaka da shan amrcina,mun shigo abuja ni da madam dazu da zahar,gobe ma in sha Allah da yammaci zamu kawo muku ziyara daga nan muga amarya" "Ganin amarya ko gulma?" Ya fada yana datse kiran,dariya hamza ya dinga yi abunshi,yq riga ya saba da dukka halayen mustphan,tex ya tura masa na musaddiq(daya daga cikin abokanshi)na neman wayarshi bai samu ba,pls ya kira shi,tsaki ya ja,yasan tsiya ce zasuyi mishi,don sarai yana da yaqinin hamza ya baza labarin wai an masa auren dole,kamar yadda yake tsokanarshi kenan,kiran daya daga cikin MD na kamfanonin da suke karbar riguna a wajensu ne ya shigo,nan ya jima wajen zaune suna waya,wanda sai da suka bata tsahon awa biyu kafin suyi sallama.   *******    ******    *******              Qarfe hudu saura ya sauko daga saman cikin sassarfa wanda tunda gari ya waye bai sauko ba din sai yanzu,sau uku tana hawa cikin fargaba tana dubashi sai ta tadda yana bacci,hakan ya sanya ko breakfast data shirya masa su daukewa tayi bai ci ba,tunda ta ganshi kwance tasan baida niyyar fita,hakan ya sanya ta quduri aniyar shirya abincin rana,sam bata ma san da zuwan baqi gidan ba.       Yana sanye da long sleeve t.shirt baqa mai dauke da logo din armani,slim fit  jeans din jikinsa baqi ne shima,kamar yadda hight top sneakers din qafarshi yake baqi,baki daya shigar saita haska farar fatarshi sosai kamar wani jinsin ba hausa fulani ba,da sassarfa yake saukowa don bada oder na abinda za'a kawo ma su hamza idan sunxo,ya saba,ta zame masa al'ada matuqar zaiyi baqi saidai ya siya musu abin fitar kunya,masu aiki su shirya shi a gun cin abinci,yana step din qarshe wayarsa ta dauki ruri,lambar hamzan ce "Munfa iso,a zo a qaraso da mu" inji hamzan,wayar ya mayar aljihu yana furzar da iska tare da shaqar daddadan qamshin abincin da yafi zaton kodai daya daga matan adam tazo abuja ne?,ya taka a nutse ya fice zuwa parking space.          Suna tsaye shida abida,wadda itace matarshi,matashiya mai matsakaicin kyau,nutsuwa cikakkiyar tarbiyya da iya mu'amala,cikin shigarta ta bahaushiya zam suna tsaye da hamzan ta dan jingina da mota saboda cikinta daya soma nauyi,kana dubansu kasan akwai kyakkyawar DANGANATAKAR ZUCI data fili a tsakaninsu,a haka ya iso ya taddasu,tana matuqar jin nauyin mustapha yana mata kwarjini,hakanan tana girmamashi,saboda haka abayansu ta tsaya tana biye da su fuskarta washe da murmushi tana duban yadda take wakana tsakanin hamza da almusphan.        Baki dayansu suna shiga suka san akwai wani gagarumin sauyi dake shirin faruwa a rayuwar mustaphan,duk da basu fiya zuwa gidanshin ba kasancewar ko kadan su'adah bata mu'amala da matan abokanshi,a cewarta duka basu waye ba,ta raina ajinsu,bata qawance da diyoyin africa masu duhun kai,idan kika ga tana harka dake to matar wani hamshaqin ne wanda yake babban abokin kasuwancin kamfanin MM abaya,mazauni kowanne ya yiwa kansa a inda ya dace hamza naci gaba da takalar almustapha wanda ya daure gira acewarsa ya fita daga shirginsa,a mutunce abida ta gaidashi sannan tace "Amaryar fa?" "Barshi my wife,rowa zai mana halan" bugu ya kai masa da qafa sannan ya miqe yana tunanin inda zai samota,jin qarar kwanuka a kitchen ya sanyashi nufar can kai tsaye,tsaye take tana goge sink bayan ta kammala girkin ta zuba komai cikin kyakykyawan mazubi,hatta da kwanukan baki daya ta wankensu goge wajen kawai take.        Atamfa ce a jikinta kasancewar tafi son sanyata,saidai baki daya dinkin na falle biyu ne,tana mutuwar son atamfar sanda ta ganta,falle biyu ta rage agun saidawar aka dinka mata,bata taba sanya kayan ba sai yau,hakan ya sanya dinkin ya mata dam,eight pieces ne skert din ya fidda shape din qugunta qwarai,rigar kuwa baki dayanta iya karta qasan cibiya,gashinta na fake tsakiyar kanta jelar na reto gadon bayanta,bata daura dankwali ba kasancewar tasan cewa ita daya ce a gidan,tana da yaqinin koda ya tashi baccin babu abinda zai kawoshi kitchen din,Allah Allah take ta kammala girkin taje ta cire kayan saboda sun takura mata,saidai ta barwa zainab ita zasu fi yiwa,tun jiya data ji labarin tafiyar take cikin fargaba,yaya zaman zai kasance musu?,wannan shi take yawaita tambayar kanta.        Safa(socks)din dake qafarsa ita ta hanata jin takunshi,idanuwansa na bisa bayanta tana ta goge goge abinta ba tare da kawo komai cikin ranta ba,zaj iya cewa bai taba ganin hips zaunannu jikin mace irin haka ba,da gaske matan africa sunfi matan kowacce shiyya structure ta jiki?,ya taba jin haka daga bakin hamza sanda yana kan ganiyar neman auren abida,wata kasala ta saukar masa sanda ta sake motsawa kadan ta gyara tsaiwarta,wanda hakan ya sake fitar da shape dinta,idanunshi ya dauke,sai ya tsaya cak yana tunanin yadda zai mata magana,kawai sai yaja ya tsaya gami da jingina da bango hannunsa cikin aljihunsa yayi crossing qafafunshi tare da maida idanunshi wani sashe daban,haka nan yaji yana son ya duba yaga ta gama,ta gama goge wajen,kwanukan take gogewa da tsaftataccen towel na kitchen tana jerasu a ma'ajiyarsu,dakin girkin na da tsaho da fadi hakan ya sanya zaiyi wuya kayi saurin ganin wulqawar mutum,sai yaci gaba da kallonta jikinsa na mutuwa,karon farko da ya taba ganinta a haka cikin rufin daki guda da 'yar qaramar tazarar dake tsakaninsu cikin muhalli guda,idanunsa ya lumshe yana son sake yiwa kansa shamaki da kallon nata,da hanzari ya tashi daga jikin ginin ganin bazai iya jira har ta ganshi ta kanta ba,freezer ya nufa ya bude wanda qarar taba tan ya sanyata juyowa a razane don tayi matuqar tsorata,hakan ya sanya plates din biyota suka fado suka tarwatse saman tiles din kitchen din,inda Allah ya taqaita na plastic ne da robobi,yadda ta tsoratan qwarai ya qawatar da shi,kamar wata qaramar yarinya,yana son mace mai tsoro wanda har ya manta akwai wannan halayyar wajen diya mace,su'ad nada dakiya da taurin zuciya irin ta wasu matan turawan,ba komai ke sanyata firgici ba tunda sun saba ganin bindiga da sauran makamai a banza,ruwan ya maida ya tako a hankali zuwa gabanta wanda taqin dake tsakaninsu bai da yawa,duqawa yayi ya soma tattare kwanukan tana tsaye jinkine da kantar hannayenta dafe ita tana maida numfashi cikin tsoro,ko bata fada ya tabbatar taji zafin yadda kwanukan suka zube mata saman qafa,sqi da ya gama tattarawar sannan ya tuna da kwalbar data taka itama jiya,ba zato taji ya daga qafar tata,ya sanya yatsanta guda daya yana shafa wajen data yanka din,idonta ta runtse tsam,yayin da ya kai ya kawo a gurin wajen sau biyar,da sauri ya saki qafar saboda tuna qafan wace a hannunshi da kuma wadanda ya bari a falo,tsaki yaja yana jin haushin kansa me ya zaunar da shi,bai bata umarnin ta fito ba kawai ya wuce,me ya kaishi tattare mata kwanuka bayan ita ta barar,me ye damuwarsa da ciwonta "Saboda itama ta nuna kulawa da naka ciwon" ya amince da amsar,mutum ne mai nuna kulawa ga wanda ya kula da shi,miqewa yayi yaja da baya "Me jiya na gaya miki game da wannan gashin dake kanki,bance ki cire ba?"ya tambaya cikin dakakkiyar murya da tsare gida,kai ta girgiza ba tare data iya duban idonshi ba saboda yadda yau yayi mata wani kwarjini "ba saka nayi ba,nawa ne"hannu ya zura har qirjinsa yana gogar nata ya kama jelar da niyyar fincika,saidai lushi santsi da taushinsa kadai ya bashi amsar mallakinta ne tun kafin ya fincika din,da sauri ya saki saboda wani shock da yaji a jikinsa,haushin kanshi ya kamashi,me zaisanya jikinsu ya dinga haduwa haka?,da hanzari ya juya yana fadin "kada ki bata musu lokaci" "Amm,don Allah ka taimakamin da hijabi a daki?" Waiwayowar da yayi ya sanyata sunkui da kai,kallo ya qare mata tun daga qafarya har kanta,yayin da ya dawo ya tsaida idanunsa saman qirjinta wanda matsewar rigar ya takurasu suma,haka kawai yaji ya gamsu dari bisa dari da dauko hijabin,baice komai ba ya fice.        Yanayin qamshin dakin daban yake da saura,komai na kintse a muhallinsa,kan gado ya hangi hijabin,saidai akwai littafi kan hijabin,hannu yasa ya dauki littafin yana jujjuyashi,littafine dake qunashe da qananun hadisai guda d'ari saboda hadda,maidashi yayi saman bedside drower din ya fito,daga bakin qofar ya cilla shi ya fito.       "Haba malam,tsakani da Allah ka kyauta,ka barmu ni da madam daga kiran amarya saika tsaya yada manufa,ai ka bari mu baku waje ko?" Inji hamza dake fadi qasa qasa yadda abida ba zata ji ba,yatsunshi ya kama wanda saida hamzan yaji a jikinsa sannan ya sakar masa,bai damu ba tunda yasan shi ya tsokano.        A nutse take takowa hannunta dauke da farantin wanda kansa ke dauke da lemukan kwali da kofuna sai kuma ruwa,sallama tayi musu hamza da abidan suka amsa,abida ta miqe ta rage mata wasu sumayyan na murmushi tace "Kai,dama kin barshi" "Babu komai,ai sunyi miki yawa" "Ai kuwa da kin qyaleta,aikin wannan mutumin ne" inji hamza da bai daddara ba,da idanu mustapha yayi masa gargadi sannan ya sake tsare wuri.        Bata zauna ba sai data jera dukkan wani abun ci da nasha wajen,lamo yayi cikin kujera ya wani lafe yana binta da kallo,abun yayi matuqar burgeshi,irin abinda yake gani gidan wasunsa kamar su hamza yau gashi gidansa,sai yake ji wani izza da girma na shigarshi "Kai nifa abincin zan fara ci gaskiya hirar nan bata yiwuwa,my abida bismillah,sumayya sai kiji kema da angonki" kunya ta kama sumayyan sai ta saki murmushi tana sadda kanta,ya dan saci kallonta wanda zakayi tsammanin idanunshi a lumshe suke,tuni abida ta qarasa kusa da shi,wanda hakan ya tilastata miqewa,daura kadan da shi ta qarasa,wanda tana iya jin qamshin turarenshi kamar yadda yake iya shaqar humrarta,ta kiyaye tsarin cin abincinsa tsaf,qasa qasa gake dubanta yana mamakin yadda har ta iya gane ra'ayinshi da qa'idarsa,duk da sam baijin zai iya sanya komai a bakinsa,idanuwan hamza da abidan kawai ya sanyashi yayi shiru "Barakallahu fiki" cewar hamza bayan ta gama zuba masa,kusan tare suka miqe sukayi dakin sumayyan don su basu waje.       Tuni hamza ya soma kaiwa cikinsa,ko ba'a fadi ba ya tabbatar ba'a qasa ta tsinci qwarewarta wajen girki ba,gyara zamansa yayi duk da yadda qamshin ya buwayi hancinsa,taba shi yayi "Ya dai?,ko soyayya ta cika maka ciki?" Ya zolayeshi,miqewa yayi sosai ya zauna,wanda yanayin zamanshi kadai ya alamtawa hamza magana zasuyi mai muhimmanci,yana jin zuwa yanzu yana buqatar abikin shawara,wanda babu mutumin da yasan cikinsa irin hamzan,kasancewarsa mutum mai yawan zurfin ciki "Hamzah"ya kira sunanshi da gaske "Na'am" "Hamza,bana jin yarinyar nan ta dace da ni,bana jin zamanmu zai yiwu,hamza komai namu ba iri daya bane,ban hangi abinda zai kawo dacewar zamanmu ba,amma na fuskanci tana qarqashin goyon bayan baba,kasan yanzu haka ya matsa sai mun wuce dubai tare?" "Ka manta hausawa sunce duk abinda babba ya hango yaro ko ya hau dala da gauron dutse bazai hangoshi ba?,akwai wani abun qyamata guda daya tak daka gani tattare da ita iya awannin da kuke tare?" "Ta yaya zan gane?,bayan duka awananin da mukayin baifi ka qirgesu da yatsun hannunka ba,kawai ban son raini hamza kai ka sani" "Duka macen data samu cikakken tarbiyya daga gidansu ba zata taba raina duk wani namiji da ya amsa sunan mijin aurenta ba,amma tunda haka ne kasan me yafi?" Kai kawai ya kada "nisantarta duka bazai daidaita komai ba,ka zauna da ita,ka mu'amalanceta kamar mu'amalar yaya da qanwarsa,ta nan ne zaka karanceta,zaka gane halayyarta,,zaka dasa mata girman da kake so ta gani naka(yayi dariya cikin zuciyarsa shi yasan kan tsiyar shi yasa ya gaya masa haka)"shiru yayi ya koma ya lafe idanunsa a qulle yana nazarin maganganun hamza.         Cikin 'yan awanni suka saba sosai da abida,tana da kirki da son jama'a,sunyi hira mai amfaji qwarai,wanda hakan ya sake sanyawa sumayya wasu mafarke mafarke da hange mai tsaho kan zamantakewar gidanta.sai da sukayi sallar magariba sannan suka wuce.           Da daren ya shaida mata ta shirya da wuri gobe akwai inda zasu,bata san ina zasun ba har sai data gansu garin kano,murna da farinciki kamar zara yi me?kamar wadda ta shekara bata ga kowa ba,saidai bata samu ganin kowa ba,amma taga abdallahnta,don wunu sukayi tare,ta tabbatar abdallah ya samu iyaye fiye da nashi na asali,sauketa kawai yaayi suka wuce ahida driver,batasan ina yayi ba,bai shigo gidan ba sai da yammaci da zasu tafi,a lokacinne ya shigo suka gaisa da malam da mama,satar kallonshi take kawai,wato mutum me shi da yasan darajar iyaye koda ba nashi bane,sallama ya yiwa malam kan zasu wuce dubai,addu'a sosai malam din yayi musu.       Cikin mota ta tsinci kanta tana kuka,a hankali ta dinga share hawayenta da gefan hijabinta,ji take kamar idan ta tafi ba zata dawo ba,waiwayowa yayi ya dubeta sai ya dauke kai yaci gaba da abinda yake,fata yake kada tayi mai sauti yadda zai dameshi,to kukan ma baiyi tsaho can ba sabida yadda ta tilastawa kanta yin haquri,tayi lamo tana tilawar nasihan mama.         Duk da yadda ta gaji bata kwanta ba sai data gama shirya dukkanin kayanta,haka kawai ta tsinci kanta da sauya yanayin kayanta baki daya,hijabi biyu kawai ta dauka madaidaita saboda sallah,ita kanta batasan manufar yin hakan ba batasan me yasa tayi haka ba,wanka tayi bata huta ba ta shiga kitchen,tana son gabatar da duk abinda ummen ta sanar mata,tukunya ta dora bayan ta zuba ruwa,ta duba inda suke ajiyar kayan hade haden shayin su tayi wani hadi na musamman wanda ya bada qamshin shayin wata qasa,cikin qanqanin lokaci ta juye cikin cup mai plate ta sake dorawa kan wani plate din tayi shahada ta haura sama,motsin ruwa data ji a toilet ya sanyata ajjiyewa ta sauka qasa bayan taja qofar tana fatan ya sha kada ya barshi kamar yadda yake barin sauran kayan abincin,tunda ya fito a bandakin ya dinga neman inda yake jin wannan qamshin shayin,qamshin da ya san a dubai kadai yake samunshi,sai da ya gama komai na kwanciya sannan ya qarasa gadon,a lokacin ya lura da shi sanda yake qoqarin kashe fitilar gefan gado,a hankali ya sanya hannunshi ya dauka,kamar wanda ke tsoron kurba haka yakai bakinsa ya kurba,idonsanya lumshe na tsawon mintuna dadin shayin na ratsashi,sai ya jishi ya koma qasar dubai,kadan kadan sai gashi ya tashi da cup din,saidai bai gamsar da shi ba,hakan ya sanya ya soma qoqarin sauka daga gadon don ya samo qari.        Da dan sassarfa ya sauko qasan ya nufi kitchen kai tsaye,babu komai cikin tukunyar da alama kai da kai aka dafa,sai ya bude locker bayan ya kunna gas ya maida tukunyar cike da karambani don bai taba yi ba,canke canken ganyayyakin ya dinga yi,haka ya hadasu ya zuba suka tafasa ya juye,kurba daya yayi fatali da cup din ya furzar da na bakinsa yana yamutsa fuska,tilas ya wanke bakinshi ya fice daga kitchen din ya koma saman,zuciyarsa na son yasha amma baijin zai iya sanyata ta sake mishi. To masu karatu,ga Almustapha ga sumayya zuwa wata qasa,koya zaman zai kasance. *SADAUKARWAR WANNAN SHAFIN GA ZAMA NA AMANA GROUP DAKE FACEBOOK,ina godiya da fatan alkhairi ga dukkan wani member dake group din,haqiqa comment dinku na qayatar da ni,Allah ya qara zumunci,LOVE YOU ALL* *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [23/02, 11:52] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 8⃣0⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* Wannan page sadaukarwa ne ga HUGUMA CONVERSATION GROUP HUGUMA NOVELS GROUP ZAUREN BIEBIE ISAH ZBI MAMAN HANEEF NOVELS MAMAN AYSHA NOVELS INSPIRING STORIES HASKE WRITERS FANS GROUP KUNDIN HASKE GROUP KUNDIN QADDARA NOVEL GROUP DA KUMA IYAYEN GAYYAR HASKE WRITERS ASSO DA KUMA FOLLOWERS DINA NA WATTPAD MUSAMMAN MASU KANKARO MUTUNCI(LOL) DA COMMENTS DINSU ALLAH YA QARA ZUMUNCI,INA GANIN COMMENTS INA GODIYA,SOMETIMES ZAKUGA NA AMSA WASU WASU BAN AMSA BA SABODA YAWAN MUTANEN,SAIDAI GASKIYA ALQALAMINA BAI IYA TSALLAKE KYAWAWAN ADDU'O'INKU NA FATAN GAMAWA DA DUNIYA LAFIYA DA KUMA SAMUN ZURI'A DAYYIBA,INA GODIYA. ___________________________________ Sha daya ne na safe,tana zaune cikin girmamawa a gaban baabaa,sanye da daya daga cikin baqar abaya wadda aka yiwa adon fari,tun daga zare kama duwatsu,tayi rolling da mayafinta wanda ya fidda shape din fuskarta da sirrin kyawunta,hill shoes ta sanya fari qal da 'yar madaidaiciyar jaka wadda mariqinta bai wuce ka saqala shi a gwiwar hannu ba,tsintsiyar hannunta daure take da farin agogo na fata mai baqar fuska,qamshi jikinta ke fiddawa mai sanya nutsuwa da kwantar da hankali,gama shirinta na tafiya kenan tayi burki a bangaren baban,nasiha baban yake mata mai ratsa jiki,wadda tabi kowacce gaba ta jikinta,yana sake tunasar da ita haqqin daya rataya a wuyanta,cike da gamsuwa cikin sanyin jiki ta soma yi masa godiya,a daidai sanda uban tafiyar ya shigo,cikin shigarsa tako yaushe ta suite,baiyi tsammanin zai tadda ta a nan ba,sallama yayi dai dai lokacin da baban yake cewa "Goge hawayen,duka abun bana kuka bane ai" ta gefan idanu ya kalleta,karon farko da irin wannan shigar ta soma burgeshi,kwata kwata ba shigar su'ad bace wannan,bai taba ganinta sanye da abaya ire iren wadan nan ba,a hankali ya kau da kanshi yana maidawa kan baban,ya isa gabanshi nesa da ita ya duqa yana masa sallama,sanda ta yunqura zata tashi don basu wuri baban ya dakatar da ita "Almustapha ga amanar sumayya nan na danqa maka,kada ka cutar da ita don kana ganin kunyi nesa da gida,kasan muhimmanci amana,ko ban gaya maka ba aure amana ce ta mace da ake danqawa namiji,wanda duk kuma yaci amana Allah bazai qyaleshi ba,na tabbata diyata bata da matsala,idan naga wata matsala to daga kaine,ka kuma kuka da kanka don bazan taba daga maka qafa ko baka uziri ba,ki kiyaye" kowa amana dai amana duk saboda ita?,abinda ummee ta gama gaya masa kenan yanzun daya fito,tana jaddada masa cewa ko rama taga tayi to shi zata tuhuma "Insha Allahu zan kiyaye,Allah ya qara girma,ya qara lafiya da nisan kwana" "Ameen summa ameen,Allah yayi muku albarka"inji baban,sannan yaja musu addu'a suka shafa. Su biyu ne zaune bayan motan sai driver a maxauninshi,hawaye ya ziraro mata sanda suke gifta gidan anty dije,ta tuno sallamarsu ta jiya,ita kanta antyn wannan karan ta kasa daurewa sai da tayi qwalla,gefe tayi da kanta tana damqe littafin da antyn ta bata wanda har yanzu bata kai ga budewa ba "kowa amana yake bani,ni me yasa ba'a bada tawa amanar ba?"kunnuwanta suka jiyo mata shi yana fada cikin mafi soyuwar sauti a wajenta,kamar zata juya kuma sai ta fasa,taci gaba da barin kanta a inda yake,ya motsa bakinshi kamar zaice wani abu sai kuma ya fasa ya ciro wayarsa dake ruri,yanayin yadda taji yayi sallamar kawai tasan hamza ne,bisa dukkan alamu shima bai wuce wannan satin zaya koma,wayar bata qare ba har suka isa airphort din wanda hakan ya sanya bai samu damar qarashe maganar da zaiyi ba. A baya take biye da shi cikin nutsuwa,yau airphort din ba laifi akwai yawaitar jama'a,hakan bai rasa nasaba qila da yawan matafiya masu sauka da masu tashi a safiyar yau din,sai taga ya fara rage saurinsa har ta cimmasa,da idanu yayi mata nuni kan tayi gaba,wucewar tayi kamar yadda ya umarcetan suka ci gaba da tafiya a hakan,idanunshi ne biye da ita duk inda ta taka qafarta tamkar mai qididdige adadin takun nata,a jikinta takejin akwai idanuwa a kanta baya ga idanun jama'ar dake kai kawo wajen,hakan shi ya sanyata ta fara jin rudewa,tun baya can mutum ce da aka raineta cikin tsaftataccen yanayin da bata iya cudanya da ajnabiyyanta ba,bata sakewa da kowa a lokacin idan ba malam ko yaya abubakar ba,koda wani taro ne na dangin mama matuqar ya hada da maza kamar daurin aure da sauransu bata sakewa,hakan na daya daga cikin dalilan da suka ja ko bikin amira da qyar ra iya sakewa(gareku iyaye mata,wannan dabi'a ce mai kyau,ana son a dasawa diya mace dabi'a ta rashin yarda da sakewa,dari dari da takatsantsan da duk wani jinsin d'aa namiji,wannan dabi'ar na taimakawa qwarai da gaske wajen dakusar da sharrin mai sharri cikin jinsin maza,misali masu baata yara da sauransu,ko da yayye gareta ko qanne maza ki nuna mata yadda zata dinga kamewa a cikinsu,to balle wani d'aa namijin a wajen,idan yayanta ne namiji ki nuna mata girmama shi zata dinga yi,bawai su dinga wasu wasa don tana qanwarshi ba,ko zama a jikinsa kada ki yarda ta yawaita yi don yana wanta,wannan dalili ne yasa ma'aiki yace mu rabawa yaranmu maza da mata wajen kwanciya da zarar sun fara wayo,idan qannenta ne kuma ki koya mata kama girmanta,bata shiga suyita wasu wasanni ba,koya mata sanya hijabi kallabi,saka sutura mai rufe jiki,kada kiyi tunanin ai yarinya ce babu komai,a'ah,ita rai dabi'antar da ita ake akan abu,ta yadda komai tsahon zamani zata dawwama a kan wannan dabi'ar). Ba tare data ankara ba taji ta harde tana yunqurin kaiwa qasa,cikin matsanancin zafi ya tarota ta fada a qirjinsa idanunsu suka harde cikin na juna "Sannu,da fata dai bakiji ciwo ba ko?" Cewar wata dattijuwa cikin mutanen dake kai kawo a wajen ita samarin yaranta su uku "Eh banji ba mama" "To Allah ya taqaita" "Amin na gode" ta fada cikin siririyar muryarta data ratsa kunnenshi,idanunshi ya daga yaga yadda idanuwa sukayi caaa a kansu,hakan yasan baya rasa nasaba da kasancewarshi sananne cikin fadin nijeria,wani abu yaji ya taba ranshi na yadda dukka idanuwa ke kanta,haushin ta jawo musu kallo ne kokuwa meye ne oho,sai ya fasa sakinta,ya jata sosai cikin qirjinsa ya rungumeta baki daya tamkar mai duba qafartata "Ki nutsu kada ki sake jawo mana idanuwan jama'a" ya fada cikin kunnenta yana sabule jakar dake hannunta,jikinta taso janyewa,ya fuskanci hakan sai ya daga lumsassun idanuwansa ya watsa mata su cikin salo na harara a fakaice,baki daya ta qarasa gigicewa kamar yadda yakejin sauyin yanayi tattare da shi yana qoqarin kokawa da feelings din,da da hali sakinta zaiyi saidai idan yayi hakan kan idanun jama'a kamar ya tona sirrinsu ne,jikinta ya saki qirjinta na wata iriyar bugawa sanda ya kewaye hannunshi a bayanta zuwa daya kafadar tata yaci gaba da tafiya da ita jakarta na hannunshi,tsoro da firgici duka suka kamata,zuciyarta ta dinga bugawa,yayin da gefe guda qamshinta ke neman buwayar hancinsa,nan da nan suka sake zama abun kallo ba tare da sun ankara ba,abinka da irin yanayin tamu qasar kenan,kanta na jingine a kafadarsa cikin kasala idanubta a qasa saboda kunya da nauyin jama'a data dinga ji,dai dai sanda zasu wuce eesha ta fito,baki ta saki tana dubansu,ya man ne wata?,tamkar taso kuma tasan fuskar,sam ba su'ad bace,kodai gaske ne labarin da humaida ta gaya mata ta zaci tsabar hassada ce?,abinda ya barota daga gida kano kenan ta taho abuja da safiyar nan tazo ta tabbatar,ko gida bata je ba daga hostel direct sai airphort,don bata son taje gida ma a bata labari gwara ta tabbatarwa idanuwanta,tunda ta samu labarin yana abujan,tuni ta zare sun glasses din idanuwanta ta maidashi saman goshinta,sun riga sun wuce shingin bincike tilas ta juya ta fice a sukwane jikinta na rawa,tana fatar samun mota da wuri don isa gidan baba prof,bata jin zata iya yiwa ummee waya har ta jira driver yazo daukanta,wace ce haka take tunanin ta mata shigar sauri?,wace take son sake sanya nisa mai tsaho tsakaninta da muradin ranta?,ta tabbatar da cewa koma wace ba qaramin kamu tarkonta yayi ba,tunda har cikin dumbin jama'a ya man da ko matarsa yake dake mawa amma ya iya rungumarta cikin jikinsa hannunshi dauke da jakarta. Wani zama ne sukayi cikin jirgi,tunda suka shiga wani babban yaron abokin kasuwancinsa yayi masa magana taga ya sake tsare gida,mutum ne shi da baison shishshigi,mu kuma kusan tamu al'adar kenan,sau tari wasu basa tashi yiwa mutum magana ko kulashi sai sun ganshi tare da iyalinsa,to bare wannan yasan cewa su'ad kadai ya sani,mai yiwuwa wannan yana masa kallon ko ya soma hutawa da 'yammata kamar yadda su sukeyi,kujerunsu na jere da juna,hakanan ya sanya tafin hannunshi cikin nata yana sake matsowa kusa da ita yana magana qasa qasa,idan daga nesa ne zaka rantse shauqin soyayya ke yawo da su duka su biyun sararin samaniya,amma idan a tsakanin kujerun nasu kake idan ka qware wajen iya gulma zaka ji yana fadin "Banson kiyi komai sai nace kiyi,idan nace kiyi din kuma kiyi babu musu ko tambaya,kibi a hankali" kai ta gyada zuciyarta na bugawa,laushi da taushin tafin hannunshi kadai ke ratsata,yayin da shima ya sauke boyayyar ajiyar zuciya yana jin wani dumi cikin tafin hannunta yana bin kowacce jijiya ta jikinsa. Gulma ta hana mutumin da yaji ya ambata da bashir zama,ya taso daga tashi kujerar ya nufosu,ya ganshi hakan ya sanya da sauri yace mata "Kwantar da kanki a kafadata,bance ki dago ba har sai na gaya miki" idanunta ta daga ta dubeshi,saidai ba itama yake kallo ba,yanq danne dannen waya ne da yake qoqarin kashewa yaga tasowar bashir,a hankali ta dora kan nata saman kafadarsa,dumin jikinsu ya soma gauraya,taja wani numfashi wanda ya zuqo dukkan tattausan qamshin jikinsa,kana ta sauke numfashin a hankali tana lumshe ido qamshin nayi mata dadi,gab da zai qaraso ya lura da yanayin almustaphan,ya sanshi sarai,hakan ya sanya ya koma da baya,haushi ya cikashi,baison me ya hanashi zaman VIP ba wannan karon,irin wannan shishshigin ne da takura baiso,shi yasa yake zama can. Jin baice mata komai ba ya sanya bata bude ido ko daga kanta ba,tayi lamo tana sheqar daddadan qamshinsa,a hakan batasan sanda bacci yayi awon gaba da ita ba,shi dinma ya sha'a fa,sai da jirgin ya lula zuwa sama yana niyyar gyara zamanshi sannan ya tuna,juyawa yayi ya dubeta,yana iya jin yadda zuciyarta ke bugawa a nutse,wanda hakan ya tabbatar masa bacci take,zai janye kafadarsa me ya tuna sai kuma ya fasa,ya jingina da kujerarsa shima yana lumshe idanuwansa. Cikin tsari da nutsuwa fasinjojin ke sauka daya bayan daya daga jirgin,waiwayawa yayi yana kallonta,bata motsa ba bai kuma san ta yaya zai tayar da ita ba,a hankali kamar wadda aka bawa umarni ta bude idonta,fes suja sarqe cikin nashi,cikin hanzari ta daga kanta daga jikinshi tana jan mayafinta daya zame,baice komai ba ya miqe ya soma takawa,itama miqewa tayi tana biye da shi,gab da matattakalar ta lura babu jakarta "Jakata" ta ambata qasa qasa,sai ya waiwayo yana dubanta da idanunshi,ya kafeta da su kafin ya furta "Ohhh,u mean naci gaba da yi miki dako?" Bata ce komai ba ta koma ta baya ta dauko,zuwa lokacin har ya gama sauka yana farfajiyar a tsaye. Motar dake mallakinsa ce tazo daga company daukarsu,lafiyayyar mota ce dake da sit daban daban kusan hudu,sarai yaga bashir din,haka ya sanya shi saka hannu ya bude mata motar,yana tsaye ta shiga dai dai sanda ya qaraso yana murmushin gulma "Yallabai,ko zaku saukeni hanya?" "Babu waje" ya fada cikin dakiya ya shige shima tare da rufe motan ya bawa drivan umarni yaja suka tafi. Tun daga hanya take kallo har suka isa qawataccen hotel din,wanda hotel ne na isassu sai kaci ka tada kai kake iya zama cikinsa,hotel ne mai kyau da tsari,duk wani mazaunin cikinsa da ya kama daki yana jinsa ne kamar a gidansa,saboda babu ruwan wani da wani,hakanan babu abinda zaka buqata ka rasa,saidai tun a nan ta fahimci bisa dukkan alamu akwai na matan da mazan dake kai kawo ciki masu wata mu'amala ta daban,hakan baya rasa nasaba da yadda taga almustaphan na riqe da hannunta har suka cimma dakinsu. Komai a gyare yake neat a dakin,kasancewar ya bada sanarwar dawowarshin,hannunta ya sake da sauri don dama Allah Allah yake su isa ya saki hannun,tsaye take a gefe,baquwa zam tana dan kalle kalle,yayin da yake tsaye gaban gado yana qoqarin sassauta tie dinsa,da alama daya daga cikin rigunan jikinsa yake son ragewa,wayarshi dake saman gadon ta dauki ruri,sai data katse bayan ya gama sassauta tie din sannan ya dauka yana dubawa,hannunshi daya riqe a qugunshi yana takawa zuwa bakin window din hotel din,ya bude yana kallon harabar shi,magana yayi wadda bata wuce ta minti daya ba taga ya dawo da hanzari ya maida safarshi da takalminsa,ya maida tie dinsa ya matse,wayarshi kawai ya dauka da maqullin dakin nasu ya fice da hanzari ya rufe qofar. Ajiyar zuciya ta saki bayan ficewar tasa,wanne irin mutum ke shi da bai hutawa rayuwarshi?,baki daya ko minti goma cikakke basuyi da shigowa dakin ba amma har ya sake ficewa,ta yaya matarshi zata samu kulawar da take so?,Allah ma yaso ba soyayyarshi cikin ranta bare hakan ya baqanta mata,ta fada cikin zuciyarta tana daga kafadarta tare da yarfe hannaye. Gefan tattausan gadon ta zauna tana duban dakin,falle daye ne dauke da makeken gado,sai kujera doguwa guda daya da qananu guda biyu ajiye daga can wani sashen daban,babbar ma'ajiyar zuba kayan sawa,madubi bedside da kuma qofar toilet,daki ne mai matuqar fadi da yalwa,ta dauki lokaci zaune har sai data duba taga lokacin sallar azahar yayi sannan ta miqe ta shiga toilet din kasancewar dazu da asuba ta samu tsarki,bandaki ne mai tsari,komai neat yake,ko ina qamshi ya kama,qamshin duka abinda yake mu'amala da shi,kama daga turare sabulu turaren gashi da sauransu,sai data kammala sallar sannan ta janyo kayanta ta fiddosu daya bayan daya ta fara jerawa ganin cewa babu abinda zata yi,akwai makekiyar t.v plasma dakin saidai batayi sha'awar kunnawa ba bare ta debe mata kewa,bayan ta gama jera nata ta janyo nashi,ta zuge a hankali,a jere kayan suke gwanin sha'awa suna fidda qamshi mai sanyi,haka ta dinga fitar da su tana jerawa daga daya side din a tsare,komai ta sanyashi a muhallinsa sannan ta sanya jakankunan nasu a wani bangare daban na sif din,zuwa lokacin sallar la'asar yayi,ta soma jin yunwa,saidai babu komai a dakin na ci,hatta freezer dake dakin babu komai ciki,idan zaiyi tafiya yakansa ma'aikatan su kwashe duk wani abu dake cikin freezer din,alwala ta sake daurawa ta dawo ta gabatar da sallar la'asar din,sai ta kwanta lamo saman abun sallah yunwa na nuqurqusarta,dama bata karya ba suka fito,haka cikin jirgi babu abinda taci saboda bacci da ya dauketa. Wasa wasa a wanni suka shiga shudewa,duhu ya fara sako kai,lokacin magariba yayi,a daddafe ta tashi tayi sallar magariba ta dawo ta kwanta,a haka akayi isha'i,zuwa sannan ta fara raina kanta,tuni ta fara fidda ruwan hawaye,tunanin da gayya al mustapha yayi mata haka ya cika zuciyarta,tana daga kwancan amma jiri take ji saboda tsabagen yunwa,ta dinga share hawaye tana juyi saman abun sallah,tuni idanunta suka sauya launi saboda kuka da yunwa. Tunda ya fita wunin baki daya bai zauna ba,gagarumar matsala ce ta taso cikin companyn tsakanin qananun ma'aikata ta qabilanci,wanda hakan har ya kai kunnen hukumar qasar,tun jiya abun ya faru amma ba'a sanar masa ba sai yau yana sauka qasar,kasancewar akwai jinsin daban daban kuma 'yan qasa kala kala dake aiki qarqashin company,tunda ya fita banda coffee cup biyu babu abinda ya sanyawa cikinsa,shaf har ga Allah ya manta da ita baki daya,har sai da aka idar da sallar magariba cikin masallacin dake cikin kamfanin,yana tsaka da azkar ya tuna,katsewa yayi cikin hanzari ya soma lalubar wayarshi,sai ya tadda ya barota a office,cikin hanzari da sassarfa ya miqe ya nufi office din,inda yake rataye keys yaga key din dakin,sai a sannan ya tuna da rufeta ma yayi,hakan ya sanya babu shiri ya kira P.A dinshi yace ya sallami kowa sai gobe zasu qarasa zaman,yayi kiran drivansa yace su hadu a parking space. A gaggauce suka tsaya wani gun saida abinci da bashi da tazara da kamfaninsa inda anan yake order din abincinsa yayi musu takeaway,sunyi mamakin ganinsa saboda kiransu yake kawai su kai masa yau sai gashi da kanshi,bazai iya jira bane kawai shi yasa yayi hakan,abinda ya saba ci da dare tayi order,ita din baisan me take so ba sabida haka kawai ya saimata abinda yaga amira tafici idan tafiya irin wannan ta kama,tafiyar minti arba'in cif tsakanin companyn da hotel din suka isa,ficewa yayi daga motar dauke da kayan yana bashi umarni cikin harshen nasara kasancewar dan india ne ya gyara parking din motar ya bada key din a reception. Tana daga kwancen taji ana yunqurin bude qofar,sai ta sake tsurewa ta zaro ido tana duban bakin qofar,a nutse ya turo qofar ya shigo kana ya maidata ya rufe,a kanta idanunshi suka fara sauka,sai ya tako a hankali zuwa inda take kwance wanda tuni ta runtse idonta da hawaye ya jiqe zara zaran gashin idonta,durqusawa yayi ya gabanta yana sauke ledojin tare da cewa "Na manta da ke ne,tashi ga abinci kici" haushi ya qumeta,ya manta da itama kenan tsahon awanni sabida rainin wayo,sai ya miqe bayan ya gama bude mata ledojin yana cire suit din sama "Wannan amanar da kace zaka riqe ce?" Ta furta cikin subutar baki muryarta na rawa,batasan zai fito ba maganar,abinda ke zuciyarta ne kawai,cak ya tsaya da abinda yake,ya sake takowa a hankali bayan ya janyo wata kujera mai siffar zero wadda jikinta baki daya cushion ce katifa ce baga da nauyi ya ajjiye gabanta "Am so sorry" ya furta yana janyo ledojin gabanshi,da mamaki ta daga idanunta ta dubeshi,batayi zaton jin kalmar daga bakinsa ba,bai dubeta ba ya fito da soyayyar shinkafa da gasashshiyar kaza,bayan ya ajiye robar fresh milk data tataccen ruwan inibi,kusan wadan nan sune abun shansa,cikin park din akwai wani dan plate na qarau mara qwari,a kai ya juye mata ya sanya cokali sannan ya daga kai ya dubeta "Tashi kici" tazarar sakan uku kafin ta miqe cikin rashin cikakken kuzari tana goge qwalla,idonsa ya dauke daga kanta,ya tsani kuka,musamman wannan kukan da yake jin shi ya zalunceta,baison zalunci shi yasa yake jin kukan har ranshi,kaman fushin baba zai sauka a kansa haka yake ji,can qasa bayan ya kauda kansa wani sashe yace "Stop crying" bata amsa ba illa jan plate din data yi ta soma tsakuran abincin,baifi loma biyar ta kai cikinta ba taji cikinta ya dunqule waje guda,take ta soma yunqurin amai,almustapha dake gaban t.v ya waiwayo yana dubanta,kafin yace wani abu tuni ta fara kelaya aman,a gaggauce ya qaraso ya tsaya kanta,baisan ya akeyi ba,baisan me ake cewa ba,sai data gama tsaf sannan ya miqa mata ruwa ta kuskure bakinta,ta rasa inda zata zuba yace "Zuba anan" yana danna waya,jikinta ta janye gefe tana maida numfashin wahala,magana yayi a recption,cikin qanqanin lokaci saiga leburori,ya matsa musu yana tsaye harde da hannaunshi a qirji har suka kammala gayarawa,jifa jifa yana dora idanunshi a kanta,suna yunqurin ficewa wani ma'aikacin ya sake shigowa da butar shayi da qananun cups,sai da suka fice ya maida qofar ya rufe sannan ya nufi inda butar shayin take,ya tsiyaya cikin daya daga cikin kofunan ya qarasa inda take ya miqa mata "Karbi" ya fada a taqaice,hannunta na rawa ta amsa sai ya bita da kallo,sai da yaga ta shanye baki daya sannan ya miqe ya shige toilet. Tsahon awa guda sannan ya fito daure da rigar towel wanda da kadan ta zarta gwiwarsa,hakan ya sanya kwantacciyar gargasarsa data sha ruwa kwanciya luf,idanu suka hada sanda yake fitowa,ta dauke idanunta da sauri ta maida idonta ta rufe,tana jin yadda ruwan dumin ke warware hanjinta,gun jakar kayansa ya nufa sai yaji babu komai ciki,hakan ya sanya y nufi drower din ya bude,cikin mamakin yadda kayan ke jere a tsare yake kallonsu,kadan ya waiwaya yana son satar kallonta sanda ransa ya raya masa ita ta gyara,tunda dakin na rufe bare yace wani ne yayi,kayansa ya diba ya koma toilet ya saka sannan ya fito,pyjamas ne na maza me v.neck wanda igiya ce ke daure da su,wani sashi na gashin dake cike a qirjinsa kwance luf ya bayyana,dogon wando ne da ita sai takalmi slippers a qafarsa,gun ya sake dawowa ya janyo abincin ya miqa mata,da idanu ya mata nuni data ci,fuska ta soma yamutsewa tana tsoron kada ya sake dawowa,kafeta yayi da idanu wanda hakan ya tilastata yin yadda yake so din,baki daya cin abincin kawai take saboda yadda ya rutsata da idanunshi yana bibiyar motsinta,qarar wayarshi ce kawai ta ceceta,miqewa yayi daga gun ya koma gefan gado bayan ya dauki tashi ledar ya janyo center table ya dora,baki daya abincin daren nasa chips ne da hadin salad kamar ko yaushe da ruwan inibi,sai fresh milk wadda ya jima bai shata ba saboda wasu dalilai,baya kuma sha din sai ya tabbatar bai da matsala,sai da ya zauna sosai sannan ya fara amsa wayar. Ya jima yana wayar wanda har batasan sanda ya kammala ba sakamakon gyangyadi data soma a wajen data gama cin abincin saboda wata mutuwar jiki da kasala data rufeta,wutar dakin na akashe sai hasken wasu qwayayen bacci guda biyu masu duhu,jikinta ya bata yayi bacci saboda haka ta miqe ta kunna haske wayarta ta fidda doguwar rigar baccinta wadda keda santsi,silk ce sosai mai bin jiki ta wuce bandaki,cikin sanda take takawa don kada ya motsa har ta shiga,saidai abinda bata sani ba idanunshi biyu,hakanan yana iya ganintar tar sakamakon ya jima cikin duhun dakin shi yasa bai ganin duhun sosai,so yaje yayi bacci amma abun ya gagareshi,dalilin da yasa baya shan irin wadan nan abubuwa kenan,duk sonshi da fresh milk da yoghourt ya haqura da su don ya zauna lafiya,yana son kunun aya matuqa haka shima ya ajjiye shi gefe,koda yaje gida ya tadda ummee tayi saidai yace baisha,acan ta wanke hannunta,sannan tayi brush ta sauya kaya sannan ta fito. A hankali ta ja qofar toilet din ta rufe,idanunshi suka sauka a kanta,haske pink din rigan baccin na yawo cikin dakin,binta yaci gaba da yi da idanu har ta qarasa bakin mudubi ta dauki turarenta ta mutsetsike jikinta duk idanunshi na biye da ita,take qamshin humrar ya karade dakin ya isa har inda yaje kwance,bai san mai yaje sake jansa ga kallonta ba har ta kai saman doguwar kujerar ta haye tana karanta addu'o'i tana shafe jikinta da su,bayan ta yane jikinta da mayafi ta kwanta tana rufe idonta,baki daya abincin data ci ya sanya mata mutuwar jiki,bacci kawai take da buqatar yi. Sai a sannan ya dauke idanunshi yana sauke numfashi hadi da ambatar sunan Allah,wani irin juyi yayi ya sauya yanayin kwanciyarsa idanunsa a rufe yana son tilastawa kansa yayi bacci,saidai yasan yaci qarya,ba kasafai a irin wannan yanayin yake iya bacci ba,yayi juyi yafi sau arba'in,take ya soma ganin baiken kansa,mai ya kaishi shan abunda yasan zai zame masa damuwa,sannan ya bige da kallon abinda baiji cikin ranshi har yanzun nashi ne,a qalla ya kwashe kusan awanni biyu a haka kafin ya fara samun sassauci,gumin da yaji yana yi shi ya tabbatar masa da komai yazo qarshe,kimanin minti talatin sannan ya miqe ya kunna qwan dakin ya shige bandaki. Fitsari ne ya farkar da ita,ganin saman gadon wayam ba kowa ya sannan ga motsin ruwa a bandaki ya sanyata zaman jiran fitowarsa,minti biyar tsakani ya turo qofar ya fito daure da towel jikinsa jiqe da ruwa,baiyi tsammanin farkawarta ba,dauke kai yayi cikin dakewa da daure fuska tamkar ita ta kar zomon ya bude ma'ajiyar kaya,yayin da ta miqe wuf ta fada bandaki saboda wani nauyi da kunya da suka lullubeta,ganinshi a haka yayi matuqar yi mata tsauri,bata fito ba sai data bada tazarar minti goma sannan,saman abun sallah ta ganshi yana salla,da sauri ta koma saman kujerar ta qudundune bayan ta duba agogo ta tabbatar tsakiyar dare ne,ya bata aqalla awa daya kafin ya koma saman gadon ya kwanta bakinsa dauke da tasbihi a haka bacci ya daukeshi. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [23/02, 11:52] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 8⃣1⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *ya hayyu ya qayyumu bi rahmatika astagis,aslih li sha'any kullahu,wala takilni ila nafsy darfata aynin* ___________________________________ Qarfe takwas na safe ta farka bayan baccin data koma bayan ta kammala sallar asuba,babu kowa a dakin sai ita daya,alamu sun nuna ma ya fita,gefe daya ta tarar da kayan break fast,komai da komai irin wanda zata iya ci,toilet ta shiga tayi wanka ta dawo ta gyara dakin sannan ta sanya kayan taja kayan ta karya,kwanciya ta sake yi bayan ta gama,ba dadewa wani baccin yayi awon gaba da ita,bata farka ba sai data ji ana knocking qofar,ta miqe ta isa ga qofar,ga mamakinta a bude take muqullin ma na jiki yau bai rufe ba kenan. Matashiya ce sanye da kayan ma'aikatan hotel din,cikin murmushi ta dubi sumayya ta gaidata da harshen larabci cikin kokwanto,don bata da tabbacin zata ji,murmushi ta saki tana mamakin jin larabci mai kyau a bakin matar,tasan yawanci larabcinsu ba irin wanda ake mana amakarantu bane ta maida mata,sai ta sake fadada murmushinta ganin cewa tana jin yaren,ta miqa mata wani abu a nade da wata leda mai qyalli tana shaida mata abincin ranarta ne,sannan ta nuna mata tarin lemuka da ruwa tace idan ba damuwa zata sanya mata a fridge,matsa mata tayi tana fadin "La ba'as,tafaddal" ta koma ciki ta biyota,tana tsaye ta gama shirya komai sannan ta maida qofar ta rufe bayan tayi mata godiya,sai data fara sallar azahar sannan ta bude,gasashshiyar kaza ce da soyayyar taliya sai hadin coleslow,ba wani da gawa taci ba ta rufe kasancewar bata jin yunwa. Kusan haka ta wuni ba cas ba as,har kwanciyar ma ta isheta,ita ba sanin kan hotel din tayi ba ballantana ta fita,sai daga bisani ne ma ta koma bakin window din dakin tayi zamanta kasancewar tana ganin mutanen dake kai komo ta nan. Kusan haka zaman nasu ya kasance har kusan kwanaki goma,da safe zata tadda ya fita amma ga breakfast dinta,da rana wannan matar zata kawo mata lunch,da yammaci ta dawo ta tambayeta koda wani abun,sai kuma na dare zata sake kawo mata shima,sau tari kafin ya dawi tayi bacci,sai haduwa tayi wuya a tsakaninsu idan ba da asubahi ba,sai data ta farka taga an fidda abincin da bata cinye ba a ajjiye mata wani,abinda ta fuskanta shine shi din mutum ne wanda bai san dadin jikinsa ba,mutum ne da ya baiwa sana'a da business muhimmanci mai tsoka cikin rayuwarsa,bashi da wani lokaci sai na kasuwancinsa,bugu da qari kuma ta lura da yadda matsalan kamfanin ta sanyashi a gaba,sam ba haka rayuwarsa ya kamata ta kasance ba,ya qare qarfinsa wajen kasuwanci ba kawai,tana ganin hakan bai dace ba,ita kanta ta soma qosawa da zaman garin,don baki daya bata ga wani amfani da zamanta ke da shi ba,tunda bata ganin wanda take zaunen saboda shi,saidai kullum taci ta sha ta kwanta,hakanne ya sanya yau ta qudurce ba zata yi bacci ba har sai ya dawo,tanas son tayi waya da 'yan gida,mama,malam abdallanta,zainab da halima baki daya,ga anty dije,layinta tunda suka shigo qasar ya daina amfani,kuma batasan inda zata samu wani layin ba bare fa nemesu. Tana idar da sallar magariba ta shiga tayi wanka,zama tayi bakin mudubi bayan ta fito ta mutstsike jikinta da turaren humra bayan ta shafa mai,ta goge fuskarta da powder sannan ta wadata lebbanta da man lebe mai taushi da qyalli,kwalli ta zizarawa fararen idanuwanta wanda hakan ya sake fito da kyawunsu sannan ta gyara jagirarta,kai tsaye ta wuce gun kayanta ta fito da atamfarta,holland ce dark brown ne jikinta,yayin da aka yi maya ado na mint green da yarfi yarfin fari,riga ce da zani simple,saidai rigar tayi maya cas a jikinta,daurin ture kaga tsiya tayi saidai baiyo gaba sosai ba,wanda yake fitar da kyan fuskarta da tulin gashinta dake daure,takalmi ta sanya plate fari qal,sabone shima kamar yadda kayan jikinta suke sabbi,wani masifar kyau tayi,kallo daya zaka yi mata ya tabbatar maka cikakkiyar BAHAUSHIYA CE,a qalla tasan zata iya kashe awa biyu kafin ya shigo,hakan ya sanya ta yanke shawarar fita waje ko hakan zai ribaci idanunta har ya dawo. Karo na farko data fara fitowa tunda suka shiga dakin,doguwar corridor ce a qawatacciya mai kama da falo wadda ke dauke da dakuna ajere reras cikin tsafta qamshi da tsari,kamar zaka zuba abinci a qasa kaci,a hankali ta dinga takawa,har ta fice daga corridor din bata ga kowa ba,ta karya kwana ta fita wata varender wadda aka tanadeta saboda hutawa,an tsarata da kujeru da 'yan shukoki cikin qananun tukwane masu kyau,daga nan kaya iya ganin harabar hotel din sarai da dukkan abinda ke kai da kawowa,ta nan zaka iya sauka zuwa qasa ko kuma ka wuce zuwa ciki,hakan yayi maga,sai ta jita sakayau,ta tsaye dafe da makarin varender wanda yake na silver ne tana kallon komai daidai fuskarta a washe tana more iskar gun da kalle kallen da takeyi. A qalla sai data share awa biyu sannan taji ta soma qosawa,hakan ya sanya ta juya a hankali ta koma ciki,har yanzu bata jin bacci,saboda haka ta koma bakin window din dakin ta sake tsayawa hannunta harde a qirjinta bayan ta cire mayafin dake lullube a kanta ta ajjiye. A gajiye ya turo qofar dakin,sam baiyi tsammanin samunta ido biyu ba kamar ko yaushe,amma duk da haka bai fasa sallama,jin an amsa masa ya sanyashi daga idanunshi cikin mamaki yana dubanta,itama nata idanun cikin nashi suke,sai ta saki hannayen nata ta ta ko a hankali tana janye idanunta daga nashi "Sannu da zuwa" ta furta cikin sanyin murya lokacin da take yunqurin karbar jakar hannunsa,sai ya sakar mata cike da mamaki karo na farko da wata ta soma yi masa hakan ba masinjansa ba,juyawa tayi cikin nutsuwa ta nufi inda taga yafi ajiye jakar don yi mata mazauni,sai ya tsinci kansa da binta da kallo da idanunshi,ta zama cikakkiyar bahaushiya zam,karo na farko daya taba tsayawa ya dubi wata matashiyar bahaushiya cikin shiga ta atamfa,ashe atamfa sutura ce har haka dake fidda ainhin mutuncin BAHAUSHIYA HAUSA DA HAUSAWA?,ganin tana niyyar juyowa ya sanyashi saurin janye idanuwanshi ua soma ragewa kanshi rigar samanshi yana ratayeta a mazauninta "An dawo lafiya?" Ta kuma ambata cikin yin qas da murya wanda hakan ya sanyashi jin wani yam a jikinsa,bata tsaya sauraren amsar sa ba,don tuni ta wuce toilet,ruwan wanka ta hada masa mai dumi bayan ta wadatashi da irin turarukanshi na wanka da yake amfani da su,ta jawo lallausan towel mai yalwa ta rataye masa sannan ta fito. Yana zaune ne bakin gado yana cire agogon hannunshi bayan ya rage riguna biyu dake jikinsa,saura wandon coat din da t.shirt mai dogon hannu dake can ciki,jira yake ta kammala nata uzirin ta fito ya shiga yayi wanka,yana ganin fitowarta ya moqe yana balle botiran rigarsa tare da shigewa. Kan kujera ta koma fa zauna tana janyo littafin da anty dije ta bata wanda sam ta manta da shi sai yanzu,shafin farko ta soma budeww,rubutu ne kamar haka "A sanda kake son ganin rashin isar namiji duk kuwa isarshi,d'ana masa tarkon mace" "Matuqar kin amsa sunanki na mace zaki iya sauya mijinki a duk sanda kika so ko kika ga dama,domin kuwa su din tamkar qananun yara suke" murmushi ya subuce mata,kunya ta kamata kamar antyn na gabanta,sai ta janye littafin wani tunani ya fado mata "Da gaske haka yake?,indai kuwa hakanne zata yi gwaji koda kuwa a gobe ne,sai ta miqe ta lalubo takarda da biro inda ta fuskanci yana ajiyar abubuwan rubutu,ta koma saman kujerar ta soma tsara rubutu,tana yi tana murmushi saboda tunanin ta yadda zata isar da takardar da kuma saqon. Dai dai fitowarshi kenan idanunsa ya fada kanta,dan zuba ido yayi yana dubanta,fararen haqoranta a waje,me take rubutawa da ya sanyata nishadi?,bayan ban bata wani abu da ya cancanci tayi farinciki haka ba?,wannan ne karon farko da yaga murmushinta muraran haka,sai ya janye idanunshi yana qarasowa cikin falon,baisan me yasa duk sanda ta hada masa ruwan wanka yakeji dadinsa fiye da wanda zai hada kanshi ba,dumin yana masa daidai,qamshin yana burgeshi,gajiya na saurin sauka daga jikinsa,tayi nisa a rubutunta bata ji fitowarshi ba sai qarar bude sif,da sauri ta maida kanta ganinshi sanye da rigar wanka. Har ya kammala shiryawa bata gama ba har sai daya zauna cin abinci sannan ta gama,ta ninke takardar tana murmushi ta daga pillow dinta dake saman kujera ta saka a qasa,yana cin abincin amma a zahirance hankalinsa duka na kanta,baisan me yasa ya damu da abinda takeyi din ba,bayan shi mutum ne da bai damuwa da lamuran da ba nashi ba,sai ta nade qafafunta saman kujeran ra rungume pillow a qirjinta tana satar kallonshi,sau uku suna hada idanu kowa yana basarwa,a na hudun suka kama juna,sai ya gyara zamanshi,cikin yanga kamar wata mace ya soma magana a hankali "Ina fatan ba damuwa bace ta hanaki bacci kamar yadda kika saba ba?" Kai kawai ta kada masa idanuwanta na duban bezar da aka yiwa filon ado bayan ta dauke idaon nata daga kan abincin da yake ci,tana mamakin ta yadda mutun zai dinga cin wadan nan abunuwan da dare kadai wai sune abincin darensa,banda hutu da kudi da yasa jikinsa da fatarsa murjewa da babu abinda zai hana ya shiga sahun ramammu,saidai babu qashi a jikinsa wanda zai nuna maka ramarsa,amma idan ya samu kulawar data fi haka ba shakka jikinsa sai yafi haka cika,ajjiye spoon din hannunsa yayi "To me ya hanaki bacci as usual?"motsa bakinta tayi itama a yangance tamkar bata son yin maganar ta maida masa "nothing"yanayin yadda labbanta da suka sha lips balm suka motsa ya sanyashi tsaida idanuwanshi kansu,sai kuma ya janye yana ci gaba da cin abincin a nutse "sai haquri,haka nake haka aikina yake"ya sake fada "ba matsala"ta amsa a taqaice itama,duk da yayi mamakin yadda ta amsa din amma bai nuna ba,zai iya tuna duk sanda su'ad ta kawo masa ziyara ta sameshi cikin aiki haka har ta koma tana mita da qorafi,shi a kan kansa yasan yana hora kanshi da aiki over,saidai yana ganin hakanne ya dace da shi,baiso ya baiwa kansa wata kafa da zaiji wani feeling a jikinsa da zai hanashi sakewa,dubai qasa ce ta cin gashin kai,zaka iya duk harkokin da kaga dama,mata sai kalar wanda ka zaba babu qabilar da babu,mai ko wanne irin kyau kuma,musamman idan kana da abun hannunka har inda kake sana'arka za'a kawo maka tallarsu,kai ko ba'a kawo maka ba su da kansu idan suka samu wargi zasu kawo kansu,musamman idan kayi musu koda ba zaka biya ha zasu iya kasancewa tare da kai,bazai iya tuna adadin mutanen da ya daina hulda da su ta sanadiyyar haka ba,idan kuma yana ganin qimarka ya yanka maka babban warning,(da wannan nakeson jan hankalin matan da mazansu ke tafiye tafiye,ku tsaya tsayin daka ku kula da mazanku,na tabbatar babu kalad matan da basa gani,wadanda sun fimu komai,matuqar akwai fahimtar juna tsakaninki da mai gida kuka zauna yana bakin labarin qasashen da yake zuwa zaki ji irin wadannan labaran,wanda da dama marasa tsoron Allah sun fada harkar neman mata saboda suna ganin suna wata duniyar babu mai ganinsu,ko kuma ke kinyin sakacin da har yaga wata mara kintsin ta burgeshi,wanda tsoron Allah da irin kyautatawar da kike masa shi kadai zai tsallakar da shi,Allah ka tsare ka kiyaye mana musulminmu a duk inda suke). Kana dubanshi zai yi wuya ka dauka ba bacci yake ba,sakamakon lamo da yayi saman gadon cikin tattausan bargo yana sauraren wani recording na tattaunawar sirri da hamza yayi da qananun ma'aikata yayi recording bada saninsu ba ya turo masa don gano bakin zaren matsalar dake shirin kunno kai a companyn,a tunaninta yayi bacci saboda haka ta miqe ta ajjiye littafin hannunta ta dauki kayan baccinta ta shiga toilet ta sauya "La haula wala quwwata illa billah...." Ya fada qasa qasa yana jan numfashinsa tare da kulle idanuwansa,ba wani tsiraici bane da rigar baccin saidai yadda ta lafe a fatarta ya fitar da sigarta ya kuma haskata,daga sanda ta fito bai sake fahimtar audion din da yake saurare ba,sai yaci gaba da binta da idanu har ta kai ga yafa mayafin ta kwanta abunta bayan ta gama addu'o'inta,saidai a banza,tamkar bata yafa ba haka yake gani,ya tabbatar bazai sake samun nutsuwa ba matuqar tana a haka,zumbur ya miqe zaune saman gadon,ya miqa hannunshi ya kunna qwan dakin bayan ya rufe jikinsa da bargo,hasken da ya mamaye dakin shi ya farkar da ita "Nemi hijabin sallarki ki saka,wannan kayan sam basu dace da ke ba" ya fada cikin dakiya yana kau da kai sannan ya gayar filonsa ya maida kansa ya ya kwanta bayan ya kashe wutar dakin,ba musu ta ja hijabin ta zura tana mamakin me maganarshi ke nufi?,ita dai tasan ba aibu a kayanta,asali ma suna da kaurin da yawonta a dakin zata iya,baya ga haka ga mayafi data lullube jikinta da shi,ture tunanin tayi gefe absa dole saboda bacci da yaci qarfinta. ******** ****** ********* Yau kan idanunta aka kawo break din,tana zaune saman kujera lokaci lokaci tana satar kallonshi bayan ta tabbatar ta sanyabtakardarva muhallin da zai fara karo da ita a duk sanda ya buqaci aiki da jakar,hannunta riqe da cuo din tea data hada bata kai ga sha ba,ya fiya ado kamar mace,haka take gulmarsa cikin ranta,tsaf ya kammala shirinsa ya dauki wayoyinshi da jakarsa,da sauri ta isa gabanshi,sai kuna ta rage saurin bayan ta isa dab da shi,cup din ta miqa masa tana kallonshi,shima ita yake kallo,ummee,ummee ce ta fado masa a rai,ita kadai duk duniya har yau ke masa haka,tunawa yayi da wace ita wajen ummee da baba,sai yasa hannun damanshi ya karba sannan ya koma gefan madubi yadan jingina kadan daukar yin hani da shan abu a tsaye daga ma'aiki S A W,a nutse yake kurba yana dubanta kadan kadan inda take zaune tana wasa da yatsun hannunta,baifi rabi ya sha ba ya tako a hankali inda take,wanda bata ji takunshi ba sai qamshinsa gab da ita,ya dire cup din a teburin dake kusa da ita,murya qasa qasa ya furta "Thanks" ya juya yana niyyar fita "Ina zan samu layi ina son yin magana da 'yan gida" tsayawa yayi cak,kafin ya daj dawo da baya kadan,ya fidda wayoyinsa dake aljihunsa ya zari daya ya sake dawowa kusa da ita ya ajjiye "Aro" ya fadi a taqaice kafin ya fice. Bin wayar tayi da kallo,fara ce qal kamar hannu baya tabata,wayar kanta sai tayi mata kwarjini,saka hannu tayi ta dauka,qamshinsa daya ratsa dukkan wani abu da yake mu'amulanta shi ya kama wayar ita kanta,bata taba ganin waya mai kyau data burgeta haka ba,tasa hannu ta shafa screen din ya bude,kasancewar babu password a kai. Murmushi tayi ta ajjiye wayar gefe,sai data yi wanka ta karya sannan ta zauna sosai saman kujera ta soma kiran duk wanda zata kira din daya bayan daya ciki kuwa har da ummee wadda ba qaramin murna tayi da jinta ba,ta sake jaddada qorafinta na kullum ta kira almustapha kan ya bata sai yace yana company shin bai hutawa ne shi?. Tafe yake yana duba wani file da daya daga cikin manyan ma'aikatansu wanda shine mataimakin hamza a sashen da suke kula da irin auduga da zararrukan da suke siya daga wasu kamfanoni,takardun jimillar audugar da suka shigo da su ne yake dubawa,dab da zai shiga elevator sukayi kacibus da hamzan,sai ya miqawa wancan da ake kira ramadan yace anjima ya kawo mishi ya qarasa dubawa,don su kammala lissafin dukkan kudin da suka fita ta wannan fannin. "Ya dai yau naga kamar kadan so makara baka shigo da wuri ba" "Jiki da jini ke kawai" "Gaskiya ne,me kake tunani kan audion daka saurara jiya?" "Mu qarasa na yi maka bayani", a haka suka qarasa office din. Kan kujerarsa ya nufa kai tsaye ya zauna yana dora jakarsa saman teburin,yayin da hamza ya fara bude fridge ya dauko ruwa yana sha,qoqarin bude jakar ya fara yi amma mazugin ya cije,ya daga jakar don ganin mai ya hanashi wucewa sai yaga takarda lanqwashe a jiki,cikin mamaki ua ciro takardar ya soma warwareta,rubutu ne a tsare tamkar da injin buga rubutu aka tsara shi,sannu a hankali ya soma bin rubutun yana karantawa,yana karantawa kanshi na shiga duhu,shawarwarine a tsare game da yadda zai warware matsalar kamfanin cikin sauqi,daya bayan daya kowacce kalma dake qunshe cikin takardar mai muhimmanci ce,kanshi bai fita daga duhu ba sai da yazo layin qarshe "ina fatan alkhairi tare da fatan warwarewar matsalar cikin sauri,saboda ka dawo nutsuwarka,iyalinka na da buqatar zamanka waje daya da kuma samun cikakkiyar nutsuwarka,kulawar ubangiji ta tabbata tattare da kai" sosai kalaman suka dinga ratsashi,sai ya samu kanshi da maimaita kalaman,karon farko a rayuwarshi da ya taba samun wadan nan kalamai masu kyau da tsari daga wajen wata mace dake qarqashin ikonshi,a hankali murmushi ya subuce masa sanda ya kammala karanta sadarar karo na biyar "Lafiyanka qalau kuwa zaka zauna kana dariya kai kadai,mutumin da murmushin naka ma wataran sai anyi kamar za'a biya kafin a ganshi?" "Hauka nake" ya bashi amsa kai tsaye cikin gatsali yana gintse fuskarsa tare da miqewa tsaye,takardar ya dunqule zaiyi jifa da ita yana jan tsaki sai kuma ya fasa,ya daga takaddun dake gabanahi ya saka ta a tsakiyarsu,hakanan sai yaji wani sashe na zuciyarsa na bashi qwarin gwiwar gwada amfani da shawarwarin dake qunshe cikin wasiqar,jawo wayar land line yayi dake gabanshi ya fara latsawa,cikin qanqanin lokaci ya bada umarnin tara dukkan ma'aikatan dake cikin kamfanin a babban dakin taro dake kamfanin,freezer ya isa ya ciro ruwan shima yana kurba a hankali,binsa hamza yake kallo kafin yace "Wai meke faruwa haka musty?" "Zaka gani" bakinsa yaja yayi shiri,yasan tunda ya fara magana haka a taqaice ba mai sanya shi fadadawa,tilas yayi shiru har sanda aka isar masa da saqon gama haduwar ma'aikatan baki daya sannan ya dubi hamza "Taso muje,meeting ne na qarshe". Cike dakin taron yake da baki daya ma'aikatan kamfanin,kowanne zaune kan mazauninshi cikin tsari,shigowarsa ya sanya kafataninsu miqewa cike da girmamawa,ba wanda ya zauna sai da ya zauna kan tashi kujerar ta musamman wandda ke a center,hamza ya zauna kan wadda ke daura da tashi sannan suka zauna,kowa ya shiga taitayinsa don sun san kan matsalar da har yau ake tattaunawa,musamman da kowannensu yasan halayyar ogan nasu,sosai ya kashingida tare da lafewa cikin kujerarsa yana duban kowa daya bayan daya,wanda hakan ya sake ladabtar da su,a hankali ya soma jefa bayani daya bayan daya yana karantar yanayin kowa cikin tataccen turancinsa,cikin qanqanin lokaci dakin ya soma rudewa,wata uwar tsawa ya daka tare da dukan table din dake gabanshi,shiru dakin taron ya sake yi,kowa ya sake shiga taitayinsa,dorawa yayi da bayanin wanda cikin qanqanin lokaci gaskiya ta fara fitowa,tsawon sa'a biyu sai gashi komai ya bayyana,ya bawa kowa hukuncin daya dace da shi,wadanda suka cancanci ya dakatar ya dakatar da su saboda ya zama jan kunne a guresu,tare da kafa sabbin dokoki masu tsauri sannan ya sallami kowa. A hankali yake jin nutsuwa da kwanciyar hankali sanda yake takawa don komawa zuwa office dinshi,bai taba tsammanin shawarwarin dake rubuce zasu warware damuwar cikin sauqi haka ba "Wai maan,ya akayi komai yazo da sauqi haka" "Daga Allah ne......inaso mu zauna mu tattauna kan yadda ya kamata mu fara noman audugar da muke amfani da ita da kanmu.....but amma yanzu zan wuce,zamu hadu gobe in sha Allah" binshu yaje da kallo,yau almustapha ne zai bar office tun la'asar?. Shirt ce a jikinta irinta mata wadda ta fidda shape din jikinta mai gajeran hannu,sai wrapped skirt mai roba wanda ya zauna mata daidai jikinta,kanta ba dankwali tunda ta idar da sallah ta cire hijabin sallar tata ta ajjiye gefe,kwance take rigingine saman kujera riqe da wayar tana duba hotunan ciki,zaman kadaicin ne ya isheta,hakan ya sanya bayan ta kammala sallar la'asar ta sake daukar wayar tana duba hotunan don debe mata kewa,don tunda ta gama kiran da zatayi ta ajjiye wayar bata kuma tabata ba sai yanzu. Kusan duka hotunan shi ke ciki,wanda da alama ba'a cikin wayar aka yiba,turasu akai kawai,babu hoton da baiyi kyau ba ciki,da yawa daga ciki da alamu baisan am daukeshi ba,baki daya sanye yake da suit,bata taba ganinshi da shigar manyan kaya ba tunda take,tamkar bature haka yake wajen sanya sutura,ta shagala sosai wajen kallon hotunan,daya bayan daya,sannu a hankali ta soma sakin murmushi,ko cikin hotunan halayyarsa tana fitowa,kusan duka adake yake cikin hotunan wani kuma zaka sameshi cikin aiki yake ko yana bada umarni. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [23/02, 11:52] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 8⃣2⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *Allah S W A yana cewa* *BAMU KASANCE MASU AZABA BA HAR SAI MUN AIKO MANZO(MAI GARGADI DA BUSHARA)* ______________________________________ *nasan zan wanke muku zukatanku with dis longest page*❣☺ *i wish za'a wanken tawa with ur beautiful prayers duk da dama sabonku ne,ina godiya,shukran lil jamiii'i* Gyara kwanciyarta tayi haka fuskarta dauke da murmushi,hakanan take jin dadin kallon hotunan,tunda ya shigo hotel din har ya kai ga qarasowa dakin ya jima kanta tsaye bata sani ba "Wannan mutum" ta fada a fili qasa qasa "Fuska kaman an maka mutuwa,smile sunnah ne fa" ta kuma fada tana wucewa zuwa hoton gaba,kowanne hotu da irin yanayin da aka yishi,ta yadda ta kuma sake tabbatarwa yanayinsa daga Allah ne kurum "Ya salam" ta furta a hankali sanda tazo kan wani hoto nashi da yayi cikin kayan sarauta baki daya harda alkyabba,wani dan banzan kyau yayi ba na kadan ba,wannan ne karo na farko data ganshi bata suit ba,tashi tayi zaune tana gyara zamanta,sai ta hangi kamar inuwar mutum,wani tsoro ya shigeta zuciyarta ta fara gudu,wani yunquri tayi ta miqe zatayi bayan gado da gudu taji an cafketa,sai ta bude baki zata saka ihu,cikin hanzari ya dora bakinsa kan nata ya rufe nata bakin,idanu ta qwalalo tana son fahimtar meke faruwa da ita tare da daga idanunta sama don son ganin waye,da sajen gefan fuskarshi ta gane,sai yanayinta ya sauya daga firgici zuwa tsoro,bugun zuciyarta ya sake qaruwa ta dinga yunqurin janye bakinta amma batasan me ya hana hakan tasiri ba. A hankali ya zare bakinsa yana janye jikinsa baya,yana jin yadda feelings dinsa ke sauyawa,fuska a hade yana tuhumar kanshi,juyawa kawai yayi ya soma cire takalmin qafarshi da safarsa sannan ya shige toilet kai tsaye,ragwab ta fadi saman kujera tana dafe da kanta,ta rasa me zata iya tunawa cikin abu biyu,ruqon da yayi mata da tsoron da ya bata,ga wani mutuwar jiki sakamakon tsoratar da tayi tun da fari,tana naj zaune dafe da kanta har taji bude qofar toilet din,idanunshi ya sake sauka kanta,hargitsatsen gashinta da rigarta data cukuikuye ya kalla,hakan ya tuna mata kayan dake jikinta,sai tayi hanzarin saka hannu ta janyo hijabinta ta zura,idanunta a qasa ra furta "Sannu da zuwa"yana takawa zuwa gaban madubi ya amsa "yauwa..." Shuru ya sake dan ratsawa kadan,ba wanda ya sake furta komai har sai daya kammala shafa mai sannan yace da ita "Ki shirya zamu fita" ya fada a taqaice,bata tsaya fahimtar komai ba ta fada toilet,don dama neman mafaka take,ta jima ciki tana sauke numfashi kamin ta soma wanka,batasan me yasa abun ya tsaye mata a rai ba. Yana tsaye gaban mudubi yana gyara sumarshi tare da duban kanshi,ya kalli labbansa a hankali ya sanya harashensa ya kasheshi,qwaqwalwarsa ke qoqarin bijiro masa taushin da yaji saman lips dinta yana qoqarin fada da hakan,tsaki ya saki bayan ya gama gyara sumar tashi yayi jifa da cumb din sannan ya nufi wajen kayan sawarshi ya fidda shirt da trouser baqi da ja ya shirya,ya sanya takalma high top tare da maqala sun glasses don sakaye idanuwanshi ya bude qofar ya fice. Sanda ta fito baya nan,tunani take ina zasu haka?,duk da batasan inda zasun ba amma hakan ya mata dadi,koba komai zata fita waje tasha iska,tsaf ta shirya cikin abaya maroon data fito da hasken fatarta wadda samanta ke a tsuke qasan a bude qwarai akwai yalwa,ta gyara sumarta ta daureta da band sannan yi rolling da mayafinta,ta daura agogo kana ta sanya zoben dake mahadin agogon ne tsakiyar yatsanta,takalmin data sanya mai tsini ne duk da bata saba sanya irinsu ba amma ta yiwa kanta alqawarin koyar saka su,wani fitinannen kyau tayi tamkar wadda ta fito daga jinsin larabawa,bakinta yasha jan janbaki radau ya sake fitar da sigar dan qaramin bakinta,dududu bata fi sati uku ba cikin qasar amma fatarta ta sake haske da gogewa kamar wadda ta shekara,tana tsaye gaba mudubi tana shafe jikinta da humra ya turo qofar,tsayawa yayi kadan yana dubanta,ko yaqi ko yaso tayi masa kyau,dalili kenan da ya sanya yake jibgowa amira abaya tun a gidan,shigar tana burgeshi,mutum ne mai son kwalliya matuwa da gaske,hakan ne ya sanya tasu ke zuwa daya da amira kota wajen siyayya,saboda tafi farida da huda ado,ganin tana yunqurin waiwayowa ya sanyashi dauke kai,ya qaraso cikin dakin yana daukan wayarsa "Bani wayata idan kin gama min kallon qurillar da kuma gulmar" mamaki ya kamata,wato dazun dama tsayawa yayi yana ganinta taba kallon hotunanshi?,kunya ta kamata sai ta zunbura baki cikin harshen larabci da take tsammatar ba zqiji abinda take fada ba qasa qasa tace "Gulma?wai kallon qurilla,to me zan kalla?" Dagowa yayi yana murmushi qasan ransa ba tare da bayyana saman fuskarshi ba,yasan tayi maganar ne ga tunaninta baiji ko bazaiji me zata ce ba,hannunshi ya harde a qirji yana dubanta har ta dauko wayar ta sake nufowa wajensa ta miqa masa,ya kafeta da mayun idanunshi yana mata kallon qurilla,baiko bi ta kan wayar da take miqo masa ba,ya motsa bakinsa kamar wanda baison yin magana "Qarya nayi kenan?,na gaya miki me kike kallon ko zaki iya tunawa da kanki?" Cikin mamaki ta daga kai ta dubeshi,saidai nauyin da idanunsa suka yi mata ya sanyata sadda kai ba shiri,ashe yana ji?,ta shiga uku ita kam,me ya kita kallonsa koda a waya ne bare tayi masa qunquni?,sake matsowa yayi gab da ita yana son hade tazarar datayi saura tsakaninsu yana duban lips dinta,haka kawai yaji ya bashi sha'awa yadda jambakin ya kwanta saman farar fatarta "Uhummm,ki bani amsa ko ni na amsa miki,na lura kamar baki da kunya fa sosai" gabanta ya fadi,jikinta yayi sanyi,ba'a taba mata shaidar rashin kunya ba sai yau,yanzu idan da malam ko ma zasuji ya fadi hakan Allah ne kadai yasan fadan da zata sha,sai idanuwanta suka tara qwalla,bata so yayi mata wannan shaidar ba,muryarta na rawa alamun fara kuka ko da yaushe tace "Kayi haquri,bada niyya bane?" "Kika yi me?," ya fada yana sake takowa saura kadan ya hade jikkunansu,tsoro ya hajata daga qafafunta bare taja baya,gani take yau Allah ne yasan me zaya yi mata "Komai ma" ta fada tana dauke qwallar data ziraro mata ta ido daya ta daya idon tana shirin fitowa itama,hakan yaji tausayinta ya kamashi,a yau din nan fa ita ta fiddashi daga matsalar daya kusa sati biyu ciki,bata cancanci tayi bacin rai a yau din ta sanadinsa ba,bata da kowa a qasar saishi,kwananta kusan ashirin da wani abu tana wuni cikin kewa ita daya qulle a dakin,zaya so a yiwa amiransa haka?,bai manta ba hamza yace ya dauketa tamkar qanwarshi sai a yanzun yaji zai iya hakan. Ga mamakinta sau taji ya kama fuskarta da hannayenshi biyu ma'ana fuskarta da tsakiyar tafin hannunsa "Shshshshsh....ya isa,ba laifi kika yi ba,amma indai kika bar daya hawayen ya zuba to zan miki hukunci,maza hadiyeshi" maimakon ya koma din sai ya qarasa silalowa,idonsa ya runtse yana jin ba dadi,baya son kuka ko kadan,sai ya sanya hannunshi a aljihun trouser dinsa ya ciro handkherchief ya goge mata hawayen ta yadda kwalliyarta ba zata baci ba,sannan ya dora shi saman lebanta ya soma rage mata janbakin "Yayi yawa,kadan ya isa" ya fada yana kallon lips din nata tare da maida handkherchief din aljihunsa,itakam bata ga wani yawa ba da yayi "Is ok,kada ki sake kuka,ki riqe wayan saboda gida before ki samu wani layin,muje" ya fadi yana dubanta,gaba tayi cikin mamakinshi,wane sabon halayya ne haka?,shi kuma ya take mata baya har suka fice daga dakin ya rufe. A reception ya tsaya ya karbi muqullin motar sannan suka fice tana gaba yana bayanta.   A hankali suke takawa suna wucewa zuwa gurin ajiyar motoci,abun mamaki duk inda suka gifta tun daga cikin hotel din sai sun dauki hankali,tsammata ake wasu shaqiqan masoya ne,yanayin shigar kowannensu ya dace da shi,a haka har suka qarasa wajen motar,da kanshi yau zaiyi driving din saboda haka kai tsaye ya wuce mazaunin driver.          Wani nutststsen tuqi yake yi wanda ke qarawa zuciya da ruhi nutsuwa,bazaiyi qarya ba kam yau wani annushuwa yake ji,hakan kuma yaba tunanin bai rasa nasaba da warwarewar matsalarsa cikin sauqi,shiru kake jin motar,idanunta na bisa titi a fakaice tana qarewa garin kallo,haqiqa yayi matuqar tafiya da ita fiye da uk da ta je,gari ne mai cike da qyale qyale da kayan qawa masu matuqar jan hankali,dan satar kallonta yayin kafin ya maida kanshi bisa titi "Thanks" taji ya ambata,a hankali ta maida idanunta kanshi wanda titi yake kalla kafin ya dauke kanta,murya qasa tace "Dame fa?" Shiru ya biyo baya kamar bazai amsa ba,har tayi zaton ma ya bar zancan sai taji ya kuma cewa "Shukhran alat taujih" sake daga kanta tayi tana dubanshi murmushi na son subuce mata,ta rasa ya akayi yaji larabci haka,wati dazun tayi shuka ne idon makwarwa,ta gode Allah da ba wata magana ta fadi ba,sai ta kauda kanta "Babu komai,abinda ya kamata ne nayi shi" sosai maganar ta burgeshi,kusan shi daya yake warware matsalolinshi idan sun taso mashi ya riga ya saba,shi yasa wannan karon yake jin tayi mishi wani gagarumin aiki data cancanci a gode mata,ba shakka samun abokin shawara da yin shawara a kuma baka shawarar yana da matuqar muhimmanci kamar yadda ummee ta saba gaya masa "Ko zaiyiwu na riqeki personal adviser?" "Aikin kowacce macen gida ce matuqar an lamunce mata hakan" itama ta fada ba tare data dubeshi ba,tana jin qarin mamakinsa cikin ranta,kamar yasha wani abu ne?,wannan ne karon farko tsawon sanayyarta da shi da suka taba zance mai tsahi makamancin hakan,ta nashi bangaren mamakin irin tata baiwa da fasahar yake,yana ganin matan arewa basu da wannan fikirar amma a yanzu yaga guda daya?,haka suke ko kuwa wannan ce kawai?(hmmm,mun wuce haka ma malam almustapha,muje dai zuwa).         Bai tsaya ko ina ba sai zabeel park,tunda suka shiga wajen yayi matuqar qayatar da ita,karon farko a rayuwarra data taba shiga wani park,guri ne da family kan iya zuwa,miji da mata da yaransu,koma miji da mata kawai,a hankali suke takawa jere da juna,saidai idanuwanta na wulqawa ko ina tana kalle kalle abinta cikin hikima ba tare daka fuskanci ta matowa gurin ba,wani sashe daban suka nufa wanda ke dauke da wasu rubuce rubuce na SEASON four dubai garden glow,hakan ke nuna lokaci lokaci wajen ke a bude,gurin biyan kudin shiga ya biya aka nasu ticket sannan suka shige.         Bata taba ganin abubuwan data gani cikin garden din ba,wani irin garden ne da aka baje fasaha wajen yinsa,kowa na harkarshi cikin wajen,kama da yara qananu da matsakaita,maza da mata,masoya gasunan birjik kowa na baje kolin tashi soyayyar,wani guri na musamman suka yi mazauni sanda wayarshi ta fara ruri ya cirota yana qoqarin amsawa yayin da ita kuma taci gaba da bawa idanunta abinci,a hankali idanuwanta suka sauka kan wani family,miji da mata ke sai yaransu uku,mace babba sai mai bi mata namiji sai qaramin shima namiji,a yadda suke raha kana kallonsu kasan banu abinda ya shafi rayuwarsu,sisai yaron suka burgeta kasancewarta mutum mai son yara qwarai,suna ta wasanninsu suna kaiwa suna kawowa wajen iyayensu,ta sake dauke idanunta ta maida kan wasu matasa biyu mace da namiji,namijin ke bawa macen ice cream yana ta faman lallabata ya kasa ya tsare,tayasu dariya tayi ta hanyar sakin murmushi sanda ya dangwala kata shi kan hancinta sanyinsa ya ratsata ta fidda idanuwa,abinda bata sani ba duk abinda take almustaphan na ankare da ita,har ya kammala wayar bata sani ba,maidata aljihu yayi ya hade hannayensa waje guda yana nazarin yadda annuri ke fita daga fuskarta,take ya sake karantar yanayinta na tsantsar son yara,ta sake maida idanunta wajen wasu yara dake daura da su wajen su biyar da wata 'yar matashiya tsakiyarsu da alama ita ta kawosu,wasa sukeyi abinsu na buya,yarinyar dake cikinsu wadda bata wuce shekara uku ba ta taho a guje ba tare data lura da sumayyan ba ta boye bayan kujerar da take zaune tana fadi cikin harshen larabci "Ki boyeni",murmushi ya qwacewa sumayyan sai ta sake bude doguwar rigarta ta boye yarinyar ga sake lafewa tana sakin dariya irinta quruciya,nemanta suka shiga yi wanda dariyar da take qyalqyalawa ya sanya suka gano inda taje,sai ta cukuikuye sumayya tana dariya tare da kifa kanta acinyarta,daukanta tayi itama tana murmushi sannan ta miqe sanda yaran suka qaraso ta ajjiye musu ita,sake diba sukayi da gudu ta koma ta zauna tana binsu da kallo tana murmushi.              A nutse suka ci gaba da takawa suna qarewa kyawun wajen da tsarinsa kallo,har yanzu murmushu bai bar fuskarta ba,zuciyarta fes,Allah ya sani tana son yara "Allah ka bani yara da yawa"ta furta can qasa sosai lebanta na motsawa "Da wa?" Zuciyarta ta tambayeta,,matuqar yaran takeso saidai tare da mustapha fa kenan,a hankali ta daga kai ta dubi mustapha,sai suka hada idanuwa,tare kowa ya dauke kanshi,kaifin ji gareshi kamar me,yaji sanda tayi addu'ar,shirun minti wajen biyar tsakani taji ya jeho mata tambayar da bata san amsarta ba "Haihuwa kike so kenan?" Sosai tambayar ta doketa,ya akayi tayi maganar yadda zaya ji,sai ya tsaya cak da tafiyar ya kafeta da idanu ta cikin gilashinsa,bata ce komai ba sai dauke kanta da tayi "Uhummm,ki amsa mana,kina so ki samu ciki ne ki haihu?" Gani take kamar ma wani nishadi yake yana son qureta,hakan ya sanya ta cire kunya ba tare data dubeshi ba tace "Kuskure ne?,kai din baka so?,shekarunka nawa a duniya?,ina tsammanin zuwa yanzu zaka yi kwadayin samun diyan kanka" shi din ma ba qaramin dukanshi furucin yayi ba,amma ya sai ya tsinci kansa qaramin murmushi na subuce masa,ya lura qarfin hali tayi ta furta maganar,yana son mutum mai confidence qwarai,zaya so kacici kacicin nasu ya dore saboda haka yace "Why zan qi hakan,ina so,but bani da matar da zata haifa min.....ko ke zaki iya?" Waiwayowa tayi da hanzari ta dubeshi,sai ta sake kasa ci gaba da jurewa kallon nasa,ta kuma juya baya tana harde da hannayenta a qirji,yayin da,nashi hannayen ke zube a aljihu yana dubanta,yana son qure confidence din da take ji tana da shi,kai ta girgiza bayan ta samo amsar bashi "A'ah ni a su wa,ban shirya ba,after all ma bazan iya ba" ta fada tana watsa hannuwanta,dariyarshi ya danne don ya hango karaya muraran a kalamanta "Me zaya hana ne wai?,ai sai an gwada aka san na qwarau,if u can try u can do it" ya fada yana kama qugunta da hannayenshi tare da mannata a jikinsa,har ga Allah yayi da wasa don kuma ya qureta,saidai yaji a jikinsa fiye da yadda ita taji,don ita tsoro ne ya lullubeta,dakiya da taurin zuciya ya hanashi sakinta,sai da yace "Tunda kika fada dole ki gwada,sai an banbance aya da tsakuwa tukunna" sannan ya saketa,da hanzari tayi baya tana jingina da jikin wasu qarafuna dake tsaye wanda aka yiwa ado saboda yadda qafafunta sukayi sanyi,tsahon mintina qirjinta na bugawa ta rasa ta cewa,batasan sanda ya sayi ice cream din ba ta dai ga yana miqo mata,a sanyaye ta saka hannu ta amsa.         Basu bar wajen ba sai wajen takwas na dare,duj wata kewa da takura na tsahon satittikan sun baje sunyi nasu guri a park din,don ma baki daya ta kasa ci gaba da sakewa tun maganar da sukayi da shi,kunya nauyi da tsoro sun cikata duk da bai sake dubanta ba bare yace mata wani abu,har suka koma gida yayi wanka yayi shirin bacci tana takure guri daya,tuni yayi luf saman gado,ta qididdige lokutan data saba bashi ja zatonta cewa yayi bacci sannan ta miqe ta shiga toilet tayi wanka ta sauya kayan baccinta,kusan tuni ya haddace sanda take sauya kayan,hakan ya sanya ma yau bacci bai daukeshi ba,tamkar mai jira yaga fitowarta din kuwa sai gata ta fito,a gajiye take don haka a sannu take takawa cikin kayan baccin riga da wando ne,rigar iya cinya wando kuma ya wuce gwiwarta iya qauri,idanunsa ya lumshe yana ajiyar numfashi kadan kadan,kansa ya wani sara mishi,sunan Allah ya ambata tare da addu'ar kada ya zamana ciwon kansa ke shirin tashi,yau yayi surutu ta waya da yawa,ga inda suka je din akwai hayaniya ba laifi,bugu da qari jiya bai samu isashshen bacci ba saboda wannan matsalar,a haka ciwon kan ya dinga sakadarshi har kuaa da asuba kafin ya samu bacci.   ******      ******    *******          Qarfe tara na safiyar washegari ta fito daga toilet bayan ta wanke bakinta,yana zaune gefan gado yana amsa wayar hamza,kallo daya ta yi masa taga sauyi a idanunshi,sun sauya sun fada kadan ba kamar yadda suka kwanta daren jiya ba,ta daya bangaren hamza ke ce masa "Muna da baqi fa maan,ka shirya kasan yadda za'ayi"yadan motsa fuskarshi "Su wafa kenan?" "Usman,huzaifa,musaddiq,lamin,on their why to dubai tomorrow in sha Allah(abokan asali su shida tun suna universty a america idan kun tuna)" miqewa yayi a hankali ya fice a dakin sannan yace "Kaifa dan iska ne wallahi hamza,ka girma amma bakasan ka girma ba,sai kasan yadda zakayi don nasan gulma ce zata kawo su ka sanar musu komai ko?" Dariya hamza ya dinga harda qwalla "Wallahi baka isa ba,ai baqinka ne,congratulating dinka zasu zo suyi sai kace min kuma nasan ya zanyi da su,can ta matse maka" ya fada yana katse kiran,lalubar hamzan ya soma yi,yasan kadan daga iskancinsa yasanyasu suzo mishi daki haka kawai,bugu daya ya daga tunda yana kusa da ita yasan sarai zai kirashin "Ya akayi?" Inji hamza "Ya kake ganin za'ayi?" "Kafi kowa sanin halin guys din nan zuwa daram wllahi" "Jokes apart don Allah,ka saukesu gidanka,idan yaso sai muzo nan" "Ka nemi maslaha,tunda kai kafi ganewa zaman hotel,Allah ya sawwaqa" "Ka rufen baki malam,ka cuci mutane kawai..."ya katse wayar yaja jan tsaki tare da furzar da iska daga bakinshi,hamza bai da mutunci amma sai ya rama zaiji dadi,ya tabbata shi ya gaya musu don bai manta abinda suka dinga masa sanda zai auri abida 'yar africa,juyawa yayi ya koma dakin yana tunanin da me zasu karya,kadan kadan yake jin shima ya soma qosawa da zaman wajen,shekarunshi nawa yana siyan abinci gun saidawa,da a gidane ya tabbata ko coffee zaya samu yasha tunda yaji ta iya dafa shi. *******    ******    ********         Washegari bayan fitarsa office ta wayarshi dake hannunta ya tura mata texs ta shirya ga driva nan zai kaita gidan hamza,cikin murna ta hau shiryawa,ko banza yauma zata miqe qafarta,minti talatin kacal ta gama shiryawa cikin african abaya wanda tayi masifar karbarta,ba wani makeup ta yiwa fuskarta ba amma saida duk abinda tayi amfani da shi ya dace da shigarta,hakan shi ya qawata kwalliyarta,dakin ta rufe cikin zumudi sannan suka wuce.        Gidajene wadanda ke dauke da qawatattun madaidaitan apartment daidai rayuwarku ku babu matsi balle takura,wanda ke nuna na haya ne,falo ne madaidaicin mai kyawun tsari wanda ke dauke dining mai kujeru shida baya ga kujeru set daya,sai dakunan bacci guda biyu kowanne da toilet,sai kitchen daga can daban wanda ke da vantilation,cikin murna da farinciki abida ta tarbeta,wanda ta sauketa da drinks da kayan snacks,abun yayi mata sosai,duk sai taji rayuwar hotel din baki daya bata yi mata ba,bayan sun dan taba hira abida tace "Ina fata kinzo da shirinki,ogogi na da baqi,kitchen zamu nufa yanzun" baki ta tabe cikin mamaki "Nikam yace min kawai ja shirya a kawoni wajenku" murmushi abidan tayi "Almustapha,har yau bai sauya ba miskilancinsa na nan" miqewa sumayya tayi tana dariya "Muje kawai ki tayani hira,don ke da wannan cikin ai idan ba'a hutashsheki ba ba'a saki wahala ba" miqewa tayi tana gaba sumayya na bin bayanta tace "Ke!,waya gaya miki?,irin wadan nan mazan namu da suke ganin mata kala kala aisai da miqe tsaye,babu abinda na fasa in gaya miki,daka saki baki saidai ayi babu ke" dariya ta kama sumayya,yayin da maganar ta dan maqale mata a rai.        Kusan abida 'yar kallo ta zama duk qwarewarta a girki tana daukan style wajen sumayya,kafin wani lokaci komai ya kammala abinka da na'ura,sumayya na zaune gefan gadon abida sanda abidan ta shiga wanka,wayar almustapha dake jakarta ta dauki kidan wani sassanyan ringing,ta ajjiye littafin da take dubawar ta ciro wayar MY SU'AD shine sunan da ya bayyana saman screen din hadi da hotonta,ta jima tana kallon wayar har kiran ya katse,wani kiran ne ya sake shigowa ta sake daga kai ta zubawa wayar ido,batasan me take ji ba a qirjinga saidai tana jin wani abu na neman cushe mata wuya,a haka abida ta fito ta taras da ita "Ah ah,waya nata ringing fa" "Bani ake kira ba" ta fada tana dauke kanta daga saitin wayar "To wayar wane?" "Wayarshi ce" "Ki daga to ki gayawa mai kiran bashi kusa ko wani abu mai muhimmanci ne ya....." Sai maganar tata ta katse sanda taje kusa da wayar don daukar bargon da zata tsane jikinta da shi ganin sunan su'ad "Bar shegiya wallahi kada ki daga" cewar abida cikin tsantsar kishi,dubanta sumayya tayi ganin yadda abidan ya sauya maganarta lokaci daya,bata dubi sumayyan ba ta nufi bakin mudubi abinda ta soma shafa mai,har kiran ya katse babu wanda yace uffan sai daga bisani abidan tace "Sumayya,Allah ne ya hada jinina dake,wlh kinga baifi sau biyu muka taba haduwa da su'ad ba amma baki daya bansan me yasa jininmu sam baizo daya ba,bana son mutum mai dagawa da jin kai,don Allah kada ki sake komi bari taga wallenki bare ta rainaki,ki zame mata dodo,ki daukaka darajar almustapha a idanuwanga tasan cewa ba kowane ke iya jefar da daimond ya dawo ya tsinceshi ba awajen,ba taba ganin sakaryar mace ko a labari ba irin su'ad wallahi" ajiyar zuciya sumayyan ta saki ta furta "Na gode,Allah ya bar qauna" daga haka suka rufe chapter din suka shiga wata hirar daban,yayin da wayar tacu gaba da burari aqalla sai data hada miscal goma sha biyar sannan ta haqura ta bi bayansu ta tex wanda bata sake taba wayar ba ma balle taga me ta rubuta din.         Bayan idar da sallar la'asar baki dayansu suka iso cikin lafiyayyar motar almustapha wadda ta cinyesu baki dayansu,hira da musu ta cika motar baki daya,baka jin komai sai muryoyinsu,yayin da almustapha ke daga zaune yana dariya,ya jima baiyi dariya irin wannan ba,ba shakka aboki wani abu mai muhimmanci ne a rayuwar mutum,musamman idan kayi dace da samun aboki na gari,hamza shine kan gaba suna bayansa,da irin wannan hirar suka shigo falon wanda ya wadata da qamshin turaren wuta wanda sumayya ce ta mata kyautarsa irin wanda tayi da hannunta,sosai yanayin falin ya yiwa almustapha,haka qamshin dake tashi,take ya soma wassafa komaea nashi gidan yana tsara yadda hakan zaya kasance.        Dukan cinyarsa musaddiq yayi bayan hamza ya wuce dakin abida "Maann,Allah na qagu naga wacce 'yar afrika ko ince arewar ce tayi nasarar sace ka haka?" Dariya suka sanya baki daya,usman yace "Ai wallahi tunda maan ya sallama kowa ma ya sallama,nikam dama tuni na miqawa sahar kaina,wallahi na sallama" "Bare ni da naga zuhra" cewar huzaifa yana latsa waya yana dariya,harara dukka ya watsa musu,yasan baki dayansu hamza ya kwaza musu yadda akai auren "Ina fata har yau baku manta waye maan ba ko?,kubar ganin kun fara neman aure har yau baku girmi na daddaki bakinku ba wallahi qattin banza" ihu suka sake sanyawa "Allah ya shiryeka,mata biyu amma har yau basu sanyaka ka girma ba" haka suka dinga fadi,ganin fitowar hamza ya sanya su nutsuwa yana sanar musu gasu nan fitowa,yadda suka nutsu suna jiran ganin fitowar tasu hakanan mustapha ya dinga jin kamar yace kada su fito suyi zamansu.        Wani abu ya dinga motsa masa sanda suka fito,abida na kan gaba dauke da try sumayya na bayanta dauke da wani try din me snacks a ciki,sai yake ganin duk cikin shigarta ta yau kamar ta musamman tayi,ganin abida ta nufi gaban hamza ta dire itama ya sanyata isa gabanshi ta dire "Amma wannan tsabagen son kaine,mazanku kurum kuka sani?" Cewar musaddiq idanunshi na kan sumayya wadda ta saki murmushi idonta a qasa,baki daya wanu nauyi take ji bata saba shiga cikin maza haka ba,idanun almustaphan shima na kanta,can qasan murmushin nata yake hango damuwa kadan kadan,almustaphan ne ya sanya qafarshi ya tura plate din gabansa "Gashinan malam sai ka saurara haka ko?" Ya fada cikin dakewa,dariya ya tuntsire da ita,kusan halinsu daya da hamza,yaci alwashin yau sai ya wana almustapha ya manna masa hauka,dama an dade ba'a hadu ba "Amma dai da ka barta ta kawo da kanta a matsayinmu na baqinsu" ya fada sanda suka gama gaisawa suka koma kitchen don shirya musu abincin saman tebur,wani banzan kallo ya watsa masa "Tunda tare muka hada muka biya sadakin ko?" Ya fada cikin subul da baka,dariya suka sake kwashewa da ita,lamin ke nuna shi da yatsa,hamza na danne dariyarshi ya sauka qasa ya soma zuba musu kunun aya da sumayya ta hada mai sanyi da yasha madara da flavour cikin cups yana miqawa kowa,ya zuba na qarshe ya miqawa almustapha,sai yaqi masa ya zuba ma hamzan ido yana aika masa da gargadi "Karbi mana malam ka sanya min ido haka?" Wannan maganan ita ta ja hankalin sauran,musaddiw yace "Wai man har yau kana kan bakanka baka shan irin wadan nan abubuwan,ina cewa komai ya sauya tunda now u r married baka da case" "Keepquite malam,ni na gaya ma haka?" Ya fada yana amsar cup din daga hannun hamzan don baison suyi masa dogon sharhin nan nasu,ya kai bakinsa ya kurba,sosai abun yayi masa dadi,ya lumshe ido yana jerowa hamza Allah ya isa cikin zuciyarsa,ya tabbatar yau ya jefashi a masifa ne kawai,usman ne da yake shi ya dan biyo almustapha kadan "Kai maaaan,wallahi ko cikin larabawa ka samu yarinyar nan ka more,idan zaka saki jiki ka kwashi gara tun lokaci bai qure maka ba ato" "Gaya masa dai mutumina,komai fa yaji wallahi,gaba da baya duka babu makusa" wanu abu yaji ya soki zuciyarshi,ranshi ya baci wanda ko a wasa bai taba zaton zai baci ba,dukkaninsu suka lura da hakan saidai basu fasa dariyarsu ba "Koma ciki!" Almustaphan ya fada cikin dakakken sauti da daga murya sanda take fitowa daga kitchen dan kawo kayan abincin saman dining,sosai maganar ta ratsata,sai ta koma da abincin ta samu wajen cikin kitchen din tayi zamanta,sai a sannan suka lura da sauyawar yanayinsa,hakan ya sanya suka rage tsokanar suna yiwa juna magana da ido tare da danne dariyarsu, don duk basu dauki abun zaiyi tasiri haka ba.        Hamza shi ya qarasa shirya komai,yayin da suka shiga wata hirar,shi dinma dannewa ya dinga yi yana sin tabbatarwa kansa ba wani abu bane ya faru,har sanda suka zauna kan dining hamza yayi serving kowa sannan suka fara kaiwa baka,take kuma sai aka koma santi,suka soma tambayar inda suka siyo abincin,shikam yasan ba taste din abincin abida bane,duk ita gwanar girki ce,sai ya ciro waya yasanya handsfree ya kirata yana tambayarta inda suka siyo abinci,dariya ta qyalqyale da ita "Dear ba wani gidan abinci,girkin sumayya ne,taga nayi nauyi ne ta amsar min aikin" "To masha Allah" ya fada yana katse kiran ya dubesu yana kai wata lomar bakinsa "To kunji girkin amaryar musty ne" take kowa ya soma yaba girkin,lomar da yayi ta tsaye masa a wuya,sau kawai ya dauki ruwa ya kora ya miqe tana duban hamza fuska a dinke "Tashi ka kiramin ita mu wuce" dubansa yayi yana qoqarin hadiye abinci "A'ah man,bamu tattauna komai bafa,dududu ko awa bamuyi ba agidan nan" "Zaka kira min ita ko sai na shiga dakin da kaina" dariya suke qasa qasa,lamin ne ya dake ya soma masa bayani ba wani abu suke nufi da matarshi ba tsokanarshi kawai suke,hannu ya saka ya daki teburin "Ce muku nayi wannan ne ya bani haushi,shut up da Allah"yau sunga bala'i sai suka sanya masa ido,miqewa hamza yayi ya isa kafadarshi ya dafa shi ya soma masa magana wanda basa jin me yake ceww,ajiyar numfashi yayi ya juya ya dubesu,sau ya saki qaramin murmushi "kunci bashi wlh zakusan kunyi da musty,amma kiramin ita mu wuce din kawai na riga da na tashi,after eight zamu hadu a masauki ba case"dariya suka saki baki daya,cikin minti biyi sumayyan ta fito "amarya ki gaida gida"suka ce mata ta amsa da to tabi bayanshi.       Tuqinsa yake a hankali saidai har yau abinda ke tokare a zuciyarshi bai baje ba,sau biyu yana satar kallonta,har yanzu mode din damuwa yake iya gani kan fuskarta,ya lura da wayarshu dake ta haske a jakarta amma baice komai ba kamar yadda bata ce masa ba,a zaman kuramen suka isa gida.        A waje yayi magariba da isha'i,sanda ya dawo da zummar yin wanka sai ya sameta nannade saman doguwar kujera,ko t.vn ma da ya kunna kafin ya fita a kashe take,hakanan yaji ya fasa fita,wayoyinsa biyun da suke gunsa ya kashe ya shiga yayi wanka ya dawo ya sanya pyjamas masu taushi farare qal bayan ya wadata jikinsa da turarensa kamar ko yaushe,tana kwancen bata motsa ba,jikinta duka na arufe sai kanta dake a waje,qwayayen dakin ya kashe ya kunna na bacci duk da a sannan dududu qarfe tara na dare,gadonsa ya haye yaja lallausan bargonsa ya rufa iya qirjinsa bayan ya zauna sosai saman gadon yana karanto addu'o'i,sai yaje yayi bacci da wuri tun kafin abinda ya sha ya soma taso masa.        Wayar dake saman kanta ta soma haske,hannu ta sanya ta duba,miscal ne da qarin saqonni,tsaki ta ja kamar ta maidata ba tare data gaya masa ba sai taga hakan bai dace ba,mai kiran zatayi tsammanin ya ganu ne bai kula ba,kuma ko banza matarshi ce,motsa bakinta tayi murya can qasa a tausashe kamar maijin bacci tace "ana kiranka akwai kima sms" "Tun yaushe?" "Rana" "Waye?" Dan jim tayi sannan tace "Su'ad na gani" shiru yayi yana ci gaba da addu'arsa har sai daya kammala sannan yace "Me saqon yace?" Kai ta girgiza tana daga kwancen "Ban duba ba" "Me yasa?" "Ba saqona bane,ba kuma hurumina bane" amsar tayi masa,wannan itace cikakkiyar amana "Ok,karantomin naji" shiru tayi don bata da muradin karantawar har ranta,sai da ya sake maimaitawa,janyo wayar tayi ta bude,a hankali ta isa ma'ajiyar saqonni wanda tunda wayar ke gurinta ko gefan bata je ba,ta dannan saqon daya fara shigowa da fari ta soma karanta masa,idanu ya lumshe muryarta da tayi low tayi sanyi na ratsashi,har ta qare kusan bai fahimci me ta karanta din ba,sai da yaji shiru alamun ta gama karanta saqonnin sannan ya farga,gyara zamanshi yayi tare da bude idanuwanshi "Banjin me kike karantawar,dawo nan kusa" ya fada yana mata nuni da gefansa,duk da babu wadatar haske amma tana iya ganinsa,ba tare da tunanin komai ba ta miqe tsaye,ta nufoshi tana maida mayafinta daya zame daga kan tulin gashinta dake daure cikin ribbom,a hankali ta zauna daga gefan gadon da tazara mai yawa tsakaninsu qafafunta na zube a qasa ta jingina da fuskar gadon sannan ta sake bude saqon da nufin maimaita masa. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [23/02, 11:52] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 8⃣3⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* ___________________________________       Idanunsa lumshe murya can qasa ya mata nuni da filon dake daura da shi "Nan zaki dawo" daga kai tayi ta dubeshi,ganin idanunsa a rufe yake ya sanyata matsowa ta sake rage muryarta ganin tana kusa sosai da shi babu buqatar daga murya,don har tana iya sheqan daddadan qamshin turarensa "A daga wayata,nasan cewa kana kusa,kana shirin wulaqantani ne kawai,kafi kowa sanin zuwa yanzu zan iya rasa kudi hannuna,naji kuma ka share baka da alamun sauke nauyin dake kanka" cikin harshen turanci ta turo wannan saqon,salon yadda take karanta saqon da tataccen engilishinta ya matuqar burgeshi,ta karya harshe sosai tamkar yarenta,sautin muryarta ya dinga ratsashi ya hanashi sukuni,jin tayi shiru yasa yace "Uhmmm,ci gaba" ba tare da ya bude idanunshi ba,sake bude dayan tayi wanda shi kuma da hausa ne "Kana wacce qasa?,ina son nazo na sameka mu warware sabanin dake a tsakaninmu,kafi kowa sanin bazan iya jurewa rashinka ba......" "Is ok" ya fada yana amshe wayar daga hannunta,don bashi da lokacin saurarar shirmen su'ad din,ya lura ta maidashi wani qaramin yaro,ya tabbata buqatarta ce ta taso,mai hali baya fasa halinsa,ba zata taba canzawa ba,a hankali ta soma motsawa da niyyar sauka daga gadon,caraf taji an ruqo hannunta,da sauri ta waiwayo,still har yanzu idanunsa na rufe "Ina zaki?" "Kwanciya zanje nayi bacci nake ji" "Ni kuma bana jin bacci so ya za'a yi dani?" Ya qarashe fada bayan ya ware manyan idanuwansa fes a kanta wadanda suka sauya launi,sunkui da kai tayi saboda wani abu da taji yana fisgarta,hannunta ya saki yace "Dawo ki zauna" bata musa ba cikin mutuwar jiki ta sake dawowa gurbin data matsa,saidai wannan karon baki daya a takure take,saboda waiwayowa da yayi yana fuskantarta gami da zubo mata ido,baisan me zaya ce mata ba,baisan ta ya zai fuskanceta ba,bai taba tsammani akwai wata rana da d'iya mace zata yi masa kwarjini ba,shi kadai yasan me yake ji cikin jikinsa,meke zagawa jini da jijiyarsa,tabbas yana buqatar dauki,ya godewa Allah daya kasance akwai halalinsa a kusa,da ya tabbatar yau babu abinda zai hana ya yanki ticket zuwa america,zuwa yanzu nauyin da yake ji ya fara guduwa,ya soma daina fahimtar kunya nauyi izza da isa dake tattare da shi,zuciyarsa ta fara kaiwa maqura,ajiyar zuciya ya sauke "Bani labari.." Ya fada yana dubanta,a wannan karon yadda mamaki ya kasheta shi ya hanata motsi bare ta dago kai "Bani da labari" ta yanke masa hanzari tun kafin taji me yake shirin fada,shiru ya ratsa tsakaninsu,yayin yaci gaba da qare mata kallo ta cikin lullubinta wanda mayafin ba wani kauri gareshi ba,numfashi ya fitar da qarfi sannan yace "Shekaran jiya kin yimin tayin samun 'ya'ya ko?" Ya fada yana duban sumarta wanda mayafin ya zame ba tare data sani ba,sai a sannan ta dago ta dubeshi tana mamakin me ya maido wannan maganar,kanta ta maida qasa tana murza tafin hannunta "Ta wuce ai,tunda baka da matar da zata haifa maka din" "Idan kuma ya kasance kece matar fa?" Gabanta ya fadi tsoro ya kamata "Idan kuma bazan iya ba fa?"wani salon murmushi mai fidda qaramin sauti ya fitar yana matsowa dab da ita "qarya ne,wanda kika taba haifa fa a baya?"wannan karon ma sai data dubeshi,ya akayi yasan ita ta haifi abdallahn?duk da ya gansu a tare amma ta tabbata baisan itace mamarshi ba,duba da tsawan daya taba yi mata sanda ta mareshi,tsareta yayi da idanuwanshi yana karantarta,tuni tsoro ya mamayeta,idanuwanshin kadai sun karantar da ita me yake nufi,to amma da wacce siga yake son kasancewa da ita,mutumin da bai gama aminta da cewa matarsa bace ma?,mutumin da bai taba cewa yana sonta ko yana qinta ba,ita kam wai a haka rayuwarta zata kasance,ta zama rabon mutum uku kenan nan duniya?,zuciyarta ta karye tana jin wannan karon ba zata iya ba har sai ta tabbatar da matsayi ta,da azama ta sake motsawa da niyyar sauka,saidai ina halittar ba daya bane,cikin zafin nama ya danne rigar baccin tata ta gefe daya ya aza duk nauyinsa,tilas ta durqushe,jikinta ya fara rawa idanunta suka tara qwalla "ka yima Allah ka barni matuqar kasan ba zaka iya ci gaba da zama da ni ba har qarshen rayuwarmu,kada ka shiga rayuwata daga baya ka fice ka barta" ta fada kuka na qwace mata,baki daya jikinsa sai ya mutu amma hakan bai kashe kaifin abinda yake ji cikin zuciya da gangar jikinsa ba,tabbas ya sani ta taba aure amma baisan me ya rabata da gidajenta ba,abu daya kawai ya sani ya kuma yarda da shi,baban bazai taba zaba masa macen da bata kamaci rayuwarsa ba,tafin hannunshi ya sanya tsakiyar nata yana murzawa a hankali idanuwanshi a kanta,ya tabbatar koma mene wani miki ne dake zuciyarta me yiwuwa take amayar da shi ta hanyar hawaye,a hankali yaci gaba da mutstsuka tafin hannunsu dake hade waje guda,wani abu na yawo cikin jikinsa,sannu a hankali kukan nata ya soma tsagaitawa,har cikin jininta take jin mutstsutsukawar da yakewa tafin hannunta,cikin sanyi ta daga kanta sai ta tsinci idanuwanshi na kanta,kai ya girgiza mata alamun a'ah,sai ta maida sabuwar qwallar dake shirin zubowa,hannayensa ya bude mata baki daya alamun ta taho,haka nan wani shauqi ke jansa zuwa gareta,kai ta kawar gefe alamar ba zata iya ba,birkitota yayi baki daya tayi masauki saman faffadan qirjinsa,jikinsa ya hadu da nata,lallausan fatarta ta sake bashi gudun mawa wajen samun himmar aiwatar da abinda da kaikawo cikin jiki da zuciyarsa,tamkar wanda ake kadawa gangi haka ya dinga tsuma,cikin zafi zafi yaje aika mata da saqonni masu nauyi,wanda har suka nauyaya cikin qirji da zuciyarta,tsoro ya kamata,tunda take bata taba tsintar kanta cikin duniyar daya jefa ta ba,saqonni ne masu rikita qwaqwalwa da kashe gangar jiki,data rasa abunyi sai kawai ta sake masa kuka,sam baya son abinda zai kawo cikas ga abinda ya nufata,yayi nisan da bai tsammanin kira zai dawo da shi,bai buqatar kukanta a wannan lokaci,sai ya hade bakunansu waje guda tare da sake jefata a wata duniya mai nisan gaske wadda bata taba tsammatar akwaita ba.       Tana kwance saman faffadan qirjinsa duk da kusan shudewar awanni biyu suna a haka amma hakan bai dameshi ba,shauqi ke shawagi dashi cikin sabuwar duniya kamar tsuntsun daya samu sararin sama,abunda bai taba faruwa ba tsakaninsa da su'ad ba,hasalima Allah Allah yake ya tashi ya tsaftace jikinsa,saidai wannan karon jinsa yake wani daban,ya kasa rabata da jikinsa,ya kasa tashi,hakanan ya kasa lallashinta kukan da take fitarwa,saboda yana da yaqinin idan ya lallasheta din akwai wani lallashin a gaba,saboda baijin zai iya barinta aziyara daya,anya daidai kunnensa ya jiyo masa sanda baban ke fadin bazawara ce da yaro guda daya tsaga jikinta ya fito?,har yau ya kasa tantance ainihin duniyar da yake,duk yadda yaso sake koyi da sunna wajen yin alwala amma ya gaza samun wannan qwarin gwiwar,burinsa kawai shine ya koma duniyar da ya fito,kuka ta sake saki sanda ya sake maidata jikinsa,tana tunanin rayuwarta kawai yau yake nema,maganin kukan ya sakeyi karo na biyu sanda ya rufe bakinta gaba daya da nashi.   ******    *******    ********       Ya jima zaune saman abun sallar da suka idar da sallar asuba yana dubanta,yayin da take takure waje daya itama kan abun sallar tana zub da qwalla,tasbihi kawai takewa ubangijinta tare da godiya a gareshi,tasan shi kadai ke yadda yaso da rayuwar bawa,sosai kukan nata ke sukarshi,ya rasa ta yadda zai lallasheta,yana jin tamkar bai kyauta mata bane,don me ya gaza haquri ya shiga gonarta ba tare da amincewarta ba,sai ya jingina da gadon yana qarasa azkar dinshi,ya kammala ya shafa,har yanzu bata sauya zani ba,wani mugun firgita tayi sanda taji ya sureta gaba daya,karon farko data yarda suka hada idanuwa tun daren jiya bayan faruwar abun,baki daya idanuwanta suyi luhu luhu sunyi ja,hawaye ne cike da idanun,ya fuskanci me take nufi,tana tsoron ko wani abun zai sake,shi kansa yayi makin yadda taji jiki haka,yadda ya saba tafiyar da su'ad haka yayi mata,dauke kanshi yayi yana ci gaba da takawa har kan gadon,gyara filo yayi ya kwantar da ita "Ba abinda zan sake miki,bacci kawai nakeso kiyi" ya fada yana ja mata bargo zuwa kafadunta,luf tayi tana sharar qwalla gami da fitar da ajiyar zuciya "I hate crying" taji ya fada "Idan baki daina ba kuma zan miki abinda bakyaso" har ga Allah tsoronsa take ji,bata marmarin sake gamuwarsu,sai ta rage jan hancin da take,kashe qwan dakin yayi tana jinsa ya bude qofar ya fice ba tare da tasan inda zashi ba,a hankali idanuwanta suka fara nauyi,bacci mai dadi ya sureta wanda batayi tsammanin zuwanshi nan kusa ba.          Minti talatin ya dawo a sanda yake zaton tayi bacci,sai ya janyo kujerar soso ya dawo da ita gabanta bayan ya kunna qwan dakin,qaramin qur'ani ya dauka cikin ma'ajiyarsa ya bude ya dora da tilawarsa daga inda ya tsaya cikin zuciyarsa yake yi,saidai lokaci lokaci yakan daga kai ya dubeta,fuskarta ta sake wani haske,kamar yadda kan hancinta da saman idanuwanta suka yi ja sabida kukan data sha,hakanan tausayinta ya dinga ratsashi,baisan tausayin na meye ba,ya dinga tuna wasu abubuwa da ya gani game da ita tun daga sanda igiyar aurensa ta hau kanta zuwa yau,yasan dai koma me yayi halalinshi ya karba,amma baisan me yasa yake jin wani bawai ba,ganin bai fahimatar karatun sai kawai ya rufe qur'anin yaci gaba da kallonta,har yanzu akwai lema kan zara zaran gashin idanuwanta,dan qaramin bakinta wanda kalarshi take pink ya kalla,sai ya lumshe ido yana jin wani sabon shauqi na taso masa,ba shakka tilas su bar hotel din nan su koma gidansa kowa ya kama dakinsa,idan ba haka bai baijin zai iya jure ci gaba da zamansu a muhalli daya ba tare da faruwar wani abu ba,bazai iya kallon giftawarta ta gabanshi ba tare da yaji komai ba,murmushi ya kufce masa sanda ya tuhumi kansa yaushe ka koma haka almustapha?,bai mancewa yakan jima baiji wani abu akan su'ad ba,wani lokaci har sai ta nemeshi sannan zaiyi ashe akwai feeling tattare da shi,har qorafi take masa bai zuwa wajenta saidai idan ita ta matsu ta biyoshi,hannunsa ya sanya qasan gadon ya ciro wayarshi wadda tun jiya ta fada,yama manta da su hakanan baibi ta kansu ba sai yanzu,kunnasu yayi baki daya har ta hannunta wanda ta soma karanta mishi saqo,murmushi ya sake saki sanda ya tuno yadda take karanta saqon a tsare cikin muryarta mai dadin amo,yadda kowanne harafi take furtashi cikin qwarewa,baisan yaushe yakai gareta ba,murmushi ne kwance saman fuskarshi yana zancan zucinsa shi kadai,saqonnin su hamza lamin musaddiq ne suka dinga shishshigowa a jajjere,dan qaramin tsaki ya ja,baki daya ya mance da cewa ya musu alqawarin zasu hadu a masaukinsu jiya da daddaren,baibi ta kan saqonnin nasu ba ya soma lalaubar lambar kamfanin da suka yi mishi aikin ginin gidansa,ba bata lokaci suka daga ya basu umarnin qarasa dukkan sauran abinda ya rage cikin gidan tare da basu kalolin furniture din yake so a zuba dakinsa da daya dakin "Sir sauran dakin fa?" Waiwayawa yayi ya dubeta,baison wanne kala tafi so ba,dauke kanshi ya sakeyi "A sanua orange da fari" ya amsa musu,bai ajjiye wayar ba sai da ya musu transfer na dukka kudin da ya rage.       Yana shirin ajjiye wayar kiran baba ya shigo,a ladabce ya daga kiran yana gaida baban,yayin da yake amsawa shima tare da tambayarsa harkokinsa,ya tabbatar masa komai lpy "Masha Allah,ina fatan komai yana tafiya dai dai ko?" "Komai lafiya baba" "To madalla,kadai kula da amana,Allah yayi maka albarka ya sake hada kanku" "Amin ya Allah,Allah ya qara girma,ya jiqan mahaifa ya saka da alkhairi" ya samu kanshi da kwararowa baban addu'o'in "Amin ya Allah,ga umminka ita keson magana da kai" ya fada yana miqawa ummeee wayar,cikin girmamawa ya gaidata ta amsa tana fadin "Ina amirata?" Sake dubanta yayi,tana baccinta cikin nutsuwa,karon farko daya taba ganin wani mutum wanda bacci ya yiwa kyau irin haka "Nace ina amira?" Ummen ta sake maimaitawa jin shiru bai amsa ba,sam ya mance tan kan layi "Tana bacci ne ummee" "Ba rana ta soma fitowa ba nan?,Ina fatan dai lafiyarta qalau ko?" Kunya ta kamashi,yana ganin kamar ummeen zata fahimci wani abu,cikin qoqarinsa nason boye komai yace "Lafiyarta qalau,kawai batai isashshen bacci bane jiyan....." Da hanzari ya katse maganar da yake sanda ya soma fahimto zaiyi baran barama "To madalla,ka gaisheta idan ta tashin,anty maamaa tana gaidaku" "Zataji insha Allah" ya fada yana datse layim cikin hanzaei,idanuwa ya fitar waje yana furzar da iska daga bakinsa.        Daya wayarce ta soma ringing,da sauri ya amsa kiran yana duban sumayya dake kwance,haka kawai baya son ta tashi,hamza ne tashi yayi ya koma saman doguwar kujera ya miqe a can sannan yace "Lafiya malam da zaka damu mutane da kira da sassafe haka?" Dariya hamza ya bushe da ita "Wai ko ba musty na kira bane?" "Ban sani ba dan iska,da bakasan waka kira ba?" "Dole na fadi haka,amazingly na kiraka kana na tasheka da sassafe,naga kai din baka da lokacin kira,any time ur available" yasan tabbas magana ya gaya mishi don hakan yake,su din ne har basu so a fiddasu daga gida da daddare ko a sasu tashin wuri,hakanan yau yake jin kansa shima as magidanci ,yake jin kansa wani na daban,ashe haka suke ji idan aka kirasu da sassafe haka,shi daya ne baya damuwa saboda baisan ana jin haka ba idan aka kira mai iyali da wurwuri ko idan dare ya fara turawa ba "Naga alama ka fara rainani wallahi hamza,ni kake gayawa am available always?" "To qarya nayi,idan banda rainin wayo jiya saika shanyamu muna ta jiranka har sha daya na dare na baro abida ita daya a gida?" "Sannu tattabara sarkin aure,to nima fitarce bazan iya ba na bar....." Idanunshi ya dauke ya dora a kanta yana ware mata kallo,sai ya rasa sunan da zaya kirata da shi,dariyan da hamza ya qyace da ita ta sanyashu runtse ido,hayaniyar har tsakiyar kansa "Hey,ar u mad,a kunnena kake wannan gadar?" "Aci amarci lpy my maan,sai ka fito" ya fada yana datse kiran,maimakon yaji haushi yadda suka saba yi da hamzan sai murmushi ya subuce masa,ya sauke wayar daga kunnensa yana kwanciya rigingine yana kallon saman dakin,hannunshi kan sumarshi yana shafata a hankali,jinsa yake fresh tamkar wani sabon mutum,wani farinciki ke ratsashi "Iyalina,matata,mata ta na bar ta ita kadai,matata bata son wannan,mata ta tana son abu kaza,mata ta tana buqata ta,mata ta ce ta kirani,mata ta ce ta yimin,ina son naji muryar mata ta,nayi kewar mata ta,iyalina sunyi kewata,mata ta zan siyawa,mata ta tace na siyo mata,mata ta tana neman izini na" dukka wadan nan lafuzan a bakin hamza da sauran abokai yake ji,dai dai da kalma daya cikin jerin gwanin wadan nan kalmomi baisan da zamansu ba aduniyar ma'aurata,duniyar zamantakewar aure,sai gashi cikin watanni hudu ya soma sanin wasu daga cikin kalmomin,kamar jiya da ya kasa fita saboda karantar wani yanayi na takura da rashin sakewa tattare da ita,ajiyar zuciya ya saki yana sake maida idonshi kanta,maganganun da baba ya gaya mishi ke masa bita daya bayan daya cikin qwaqwalwarsa.           Cikin jin kunya da nauyi take komai,duk inda ta motsa tana jin idanuwanshi a kanta,har ta kammala azkar dinta ta miqe ta nade sallayar bata dubeshi ba,rabonta da kallonshi kwanaki hudu kenan,duk abinda zaice mata saidai ya fada tana duban wani gun,sauqin abun ma kwana biyu suna wani taro na mutanen da suka mallaki kamfani a qasar,bai shigowa sai bayan magariba,takanyi qoqarin yin bacci ko na qarya ne kafin ya shigo din,bata san me ya sanya take jin kunya da nauyinshi ba,irin nauyin da bata taba jinsa ba tattare da sauran mazan data aura,shima qoqarin tura mata saqo sau biyu a rana najin lafiyarta,duk don kiyaye amanar da aka bashi,bata bata dubawa ba sakamakon tana tunanin duka saqonnin nashi ne,saidai abu daya daya tsaye masa a tunaninsa wanda ya rasa dalilin haka,dare qwaya daya tak wanda yayi karen tsaye a tunaninsa,har yau yaqi goguwa daga idanuwanshi,sau tari tunanin wannan dare yakan wafci duk aikin da yake ya fado ciki,saidai ya tsinci kansa ya saki murmushi yana girgiza kai,yayin da hamza aka sa masa ayar tambayar wai me ya maidashi haka?,harara yake watsa masa yace zai daddaki hancinsa idan bai fita sabgar rayuwarshi ba,dariya yake masa tuburan ya bashi waje,yasan dai tabbas ruwa baya tsami banza,haka nan ya samu kansa da yin addu'ar Allah ya sanya canjin da suke fata ne ya soma samuwa.       Qoqari yake su hada idanu amma abun ya faskara taqi yadda,duk inda ya kalla sai ta kauda kai,tun daga ranar taqi yadda ta dubeshi,har abun ya zame musu tamkar game,shi ya dage sai yaga qwayar idonta ita kuma qememe taqi,kamar yanzun data gwammace ta zubawa t.v idanu,wanda yasan hakan ba al'adarta bane,tunda suka zo bata taba kunna tv don radin kanta ba,dan qaramin murmushi ya saki na gefen baki,sai ya miqe ya isa ga makunnin tv ya kashe,janye idanuwanta tayi,ta rasa inda zata tsoma ranta,yayin da shi kuma bai fasa kallonta ba,shigarta qarewa kallo yana ambatar bahaushiya cikin ranshi,atamfa ta sanya dinkin zani simple,sannan ta saka riga halp buba wadda iyakarta gwiwa,kayan sun mata kyau duk da cewa baki dayan dinkin simple ne "Miqo min ruwa" ya fada wai ko zata kalleshi,miqewa tayi tsam ta isa ga freezer tana mamaki,don bai taba sata yin wani abu ba saidai idan tayi niyya don radin kanta.        A hankali take takowa zuwa inda yake yana satan kallonta har ta qaraso ta tsugunna ta zuba cikin cup ta miqa masa,sai ya hade cup din da hannunta baki daya,sai a sannan ta daga kai da sauri ta dubeshi jin yadda ya matse hannun jikin cup din sanyin na ratsata,da hanzari ta maida idanun wani wajen,baisan sanda murmushi ya subuce masa ba,ashe haka kunya ke yiwa mace kyau?,abar data sanya auren 'yan arewa ya fice masa a kai kenan da fari,jin cewa kunya ta sanya sun zama wasu iri,basu iya nunawa miji zallar qauna,sai gashi yau yaga kunya a muhallin data burgeshi "Tashi ki tafi,tunda tsoron kallona kike" kunya ta sake kamata,sai ta miqe zata bar wajen,qafa ya sanya mata ta dawo da baya baki daya ta fadi jikinsa,sai ya lullubeta da hannayensa gaba daya ya soma yamutsata yana sane,so yake yaga ya zata yi,ai kuwa tuni ta bare baki zata saki kuka,har yanzu cinyoyinta basu bar ciwo ba hakan yasanya ya sake ta babu shiri,idanunta sun cika da qwalla,sai ya sake sakin murmushi,yanayin kawai ya burgeshi,ya motsa bakinsa da niyyar tambayarta shekarunta saboda yadda quruciya ke bayyana aduk wani motsinta sai kuma ya fasa,hannunsa ya sanya ya dauki wayar da ya batan wadda ke daura da shi,a nan yaci karo da dukka saqonninsa da yake turowa ba guda daya data taba "Wannan fa?" Ya fada yana haska mata wayar,duban wayar tayi na wasu 'yan sakanni kafin ta dauke kai "Ban zaci nawa bane" dauke idonshi yayi daga kanta ya maida kan wayar,deleting din saqonnin yayi baki daya sannan ya kashe wayar ya sanyata cikin aljihunsa. ****** ****** ******* Zaune yake cikin ofice dinsa,aika saqo yake cikin zafin nama qwarewa da kuma gaggawa saboda yana son ya gama ya saurari hamza dake zaune yana jiransa "Kuskure ne?,kai din baka so?,shekarunka nawa a duniya?,ina tsammanin zuwa yanzu zakayi sha'awar samun diyan kanka" magan ganunta suka fado masa ya tuna yadda qaramin bakinta ke motsawa sanda takw furucin,murmushi ya subuce masa yana girgiza kai,tana da confidence,saidai akwai tsoro da kunya tattare da ita "Man anya lafiyanka daya kwana biyu kuwa?" Maganar hamza ta katseshi daga duniyar tunanin da ya tafi,idanunsa ya zubawa hamza baki daya gami da dauke hannayensa daga kan madan nan cumputer din ya dafe kanshi da su "Tambayarka nayi lafiya kake?" "Na haukace" yayi furucin kansa tsaye yana ci gaba da kallonsa,dariya hamzan ya saki "Kana gab dai da haukacewar,don iya sanina da kai ban taba ganinka kana murmushi kai daya ba tsawon rayuwarmu sai wannan qarnin,anya baka fada tarkon soyayya ba?" "Ba tarko na fada ba rami na rufta qaramin mara mutunci,sau nawa zance ka fita harkata hamza?" "Anqi a fita din,idan kaji haushi ka bayyanawa duniya ka soma son wata diya mace sai ka huta da binbini na" apple din dake gabansa ya dauka ya jefa masa ta sameshi a qirji ya cafe yana dariya "Na gaya maka zuciyata ba'a halicceta don tayi soyayya ba,kudai da kuka afka sai mu tayaku da addu'a Allah ya......" Zancansa ya katse sanda wayarsa ta soma ruri,umme ce ke kira,saboda haka ya saki duk abinda yake ya amsa kiran,cikin girmamawa ya gaidata ta amsa mishi sannan ta dora da cewa "Na kira ne na shaida miki bikin qannenka nan da three weeks,so nasan ba lallai kai ka samu zuwa ba qila sai ana ya gobe daurin aure,so ina so ko nan da sati daya ka turo sumayyan ta fara yo gaba,taje gida ta musu sati idan yaso satin bikin idan ya kama sai ta taho nan" "Hakan ya miki ummee?" "Eh idan ban takura muku ba" "Yadda kika ce haka za'ayi,Allah ya sanya alkhairi"ta amsa tana sanya masa albarka sukayi sallama,idanunshi ya maida kan cumputer din yana ci gaba da danne danne "yaran nan sun dage sai sunyi auren nan daga kammala karatunsu hamza" "Sai aka ce halinku sai ya zama daya dole,me yafi ransu,dai dai kenan,to me zasu jira?" "Allah ya taimaka" ya fada yana ci gaba da aikinsa. Sai da ya gama ya saurareshi,rigunan da aka gama hadawa ya kawo masa yaga irinsu "Na bawa wadancan guys din zasu zuba lefansu" "Ba laifi" ya fada yana ajjiye rigar "Ya sunyi?" "Kasan ba ganewa nake ba, abawa stores din samfuran su gani idan design din yayi" daya hamza ya fidda yana ajjyewa gabanshi "Wannan karon zaka gane idan ka ganta a gidanka tunda ba'a saba sawa ba,ka kaima sumayya ta gwada maka sample ka gani yadfa abida kemin" baki almustapha ya tabe yaba dubanshi "To sarkin abida madalla" "Zakayi bayani ne" inji hamza yana dariya tare da ficewa. ***** ***** **** ***** Cikin kwana hudu ya gama shirya mata tafiyar ba tare data sani ba,randa komai ya kammala ya tashi office qarfe shida na yammaci saboda baqi da sukayi,yana tattare files dinshi yaci karo da rigar da hamzan ya bashi tun rannan,jefata yayi cikin jakarshi ya dauka ya fice. Sai daya tura qofar yayi sallama,tana zaune saman abun sallah tana karatu,yana mamakin yadda bata gajiya,bayan kowacce sallah sai ta zauna tayi tilawa,karatun ta katse kanta na gefe tayi masa sannu da zuwa,ga mamakinta yau bai amsa ba,safa takalmi 'yar saman suit dinshi duka ya cire ya shige bandaki,wanda dama yana dawowa wanka yake fara yi kafin ya saurari abinci,wanda sunsan lokacin da suke kawo masa dama daga wani wajen saida abinci dake daura da hotel din,duk sai taji ta wani iri saboda rashin amsa matan da baiyi ba,qur'anin ta rufe kamar yadda ta saba ta dauke socks da takalmin ta musu waje,haka suit din ta ratayeta sannan ta samu waje ta zauna tana jiran fitowarshi. Kanta ta sake daukewa sanda yake fitowa daga bandakin daure da towel a qugunshi,wanda hakan ya bayyana uban albarkar gargasar dake ilahirin jikinsa,abinda bai taba yi ba fitowa haka,saidai ya fito da rigar wanka,nauyinsa taji ya kamata,sai ta miqe a hankali tana maimaita yi masa sannu da zuwan tana nufar qofa "Dawo ki zauna" ya bata umarni ba tare daya amsa sannun tata ba,cikin jin nauyi ta koma da baya ta zauna,ya isa gaban mudubi ya soma tsane jikinsa yana qare mata kallo ta cikin mudubin,baki daya a takure take kamar zata zura da gudu,dariya ta taso masa amma ya danneta,ta maidashi kamar wani dodo tun daga ranar da suka hada shimfida,baki daya bata iya masa wani cikakken kallo "Yau zanga qarshen kunya" ya fada a ransa "Zo nan" yace da ita "Ni?" Ta tambaya tana raba idanu,kicin kicin yayi "Da wa?" Miqewa tayi tana takawa a hankali har ta iso bayanshi ta tsaya,towel ya miqa mata cikin halin ko in kula "Jikina zaki tsanemin" sakato tayi kamar zatayi kuka,baice uffan ba ya kafeta da ido,a sanyaye ta karbi towel din,cikin sanyin jiki,sai ta gaza motsawa tayi tsaye riqe da towel din "Uhm,bismillah ina so na shafa mai ne fa"qwal qwal tayi da idanu sannan ta matso tana dauke idonta daga kallon jikinsa saboda yadda yayi mata kwarjini,bugu da qari sai tq zama wata 'yar cukul a gabanshi,sai da ya wanata,dariya a cikinsa kuwa kamar zata fito amma yana maidata,wanda a zahiri fuskarsa ba haka take ba sannan ya amshi towel din yana fadin "ba abinda kika iya ma"baki ta tura cikin ranta tana qunquni "Haka kawai dama mugunta ce tasa kace sai nayi,kai ko kunyar abinda ka aikata ma baka ji" bude jakarshi yayi ya fito da abayar ya miqa mata sannan ya zuba mata shanyayyun idanunshi. Kuyi manage da wannan,ina da uziri,koda gobe baku jini ba kuyi haquri,idan kuma ya samu falillahil hamdi,na gode. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [23/02, 11:52] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 8⃣4⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *Allah madaukaki yana cewa* *HAQIQA ABINDA AKE YI MUKU ALQAWARI/ALWASHI(NA ALQIYAMA)MAI ZUWA NE,KU BA MASU TSEREWA ALLAH NE BA* Allah ka sanya farinciki a zukatanmu a wannan rana,ka sanyamu qarqashin inuwarka. _____________________________________ *WANNAN SHAFI SADAUKARWA NE GAREKU,HAQIQA ALKHAIRINKU GARENI BAZAN MANTA BA* *SISTER AINA'U(HUGUMA CONVERSATION)* *TASH (INSPIRING STORIES GROUP)*        Hannu biyu ta sanya ta karbi rigar tana kauda kai daga kallon da yake mata wanda sam bata sonshi,yana sanyata jin wani irin abu da nauyi cikin jikinta "Inji hamza" ya fadi yana juyawa gaban madubi yana ci gaba da taje sumarshi hankali ta furta "Na gode,Allah ya saka da alkhairi" bai amsa ba saici gaba da kallonta da yake ta cikin mudubi,bai tsammaci jin wata addu'a ko godiya daga bakinta ba,don hamzan yasha yiwa su'ad kyauta wanda ta ninninka haka saidai ta karba ayatsine,wani lokaci idan ta duba ma takance "Shikam baisan me yasa bai iya kyauta ba,yana qarqashun mijina yana aiki yana cin arziqinsa ya rasa mai zai bani sai wannan?" Harara yake jifarta da ita almustaphan sannan yace "Ki shiga hankalinki su'ad,hamza ba aiki yaje qarqashina ba kafada da kafada muke aiki,ba tilas sai ya miki kyauta ba don ba qasanki yake ba,ki gyara bakinki" hakan na mata ciwl,don ita a duniya ba abijda ta tsana irin a daidaita matsayinta dana wani,wanin ma dake gain kamar bai isa komai ba.       Wayarshi ce ta fara tsuwwa,ga zatonshi ma umme ce zata ce ya hadata da sumayya,saboda haka bai ko dubaba ya daga yana karawa akunnensa,ya maqaleta a kafadarshi yana ci gaba da shafarshi,muryar su'ad ce cikin bacin rai da kwantar da murya cikin harashen nasara "Ashe da gaske ne abinda akefadi idan namiji yayi aure wulaqantaki yake?,yanzu a haka kakeso na yarda na karbi kishiyar da ka yimin mu zauna tare?"shiru yayi tamkar bai kam layin har sai data kira sunanshi,kawai sai ta saki kuka harda sheshsheqa,cikin harshen hausa da son dawo da qauna cikin zuciyar wanda kuke magana tace "almustapha kasan duk duniya babu wani abu da nake qauna sama da kai don me zaka yimin haka?" "Look su'ad,wannan baki daya matsalarki ce ni ban da case da duka zantukanki,i think na gaya miki dukkan wani rules nawa ko?,so pls idan zaki iya bi bismillah,if not ki qyaleni na huta hakanan" "Ni kake wulaqantawa haka maan?"cikin fushi yace "if u dont like how things are,take control,decide how u ar going to change it,kada ki sake nema na daga yau,take me as iam,or leave me as iam"katse layin yayi ya jefa wayar gefanshi,cikin bacin rai yaci gaba da shiryawa sauri sauri,sumayya kam tunda taji ya ambaci su'ad ta miqe ta shige toilet,dama wanka take sonyi wanda yau bata samu tayi da wuri ba tun na safe da tayin.          Cire wayar su'ad tayi daga kunnenta sanda ta fahimci ya katse kiran nata,duk da ba yau ne farau ba idan tazo masa da shirme amma wannan yayi matuqar baqanta mata,gani take kawai saboda ya sake aure ne ya sake qaro wulaqanci fiye da wanda ta sanshi da shi,hawaye na bin idanuwanta ta dubi mamanta,sannan ta dubi qanwar maman nata anty kubra dake zaune tana kallonta wadda ke zaune ita mijinta a south africa,ta zo ne american wajen yayarta ta tadda wannan cakwakiyar "Ba sai kince komai ba naji komai,ai wallahi laifinki ne khaulat,ta yaya har zaki bari su'ad tayi wasa da damarta,kunfi kowa sanin samun damar auren irin su mustaphan sai wanda Allah ya zaba nan gidan duniya,tun tuni kallonku kawai nake,yarinya tana gantalinya da sunan karatu,karatun uwar me?,me zata ci da karatun?,me take nema da shi?,dame mijinta ya rageta?,bata taba tambayarsa abu komai yawansa yace mata babu ko bazai bayar ba saidai ma ya ninka mata,kuna zaton miji irin mustapha wanda Allah ya yuwa baiwar kyau da kudi zai zauna bai sake aureba bayan yana da mace irin su'ad?,to ta godewa Allah ma daba neman mata yake ba ya kwaso wata cutar ya laqaba mata,kinga idan zaki zubar da wannan gantalallen karatun naki kije ki kwashu makaman qwatar mijinki kije ku buga ke da ita mai rabo ka dauka to,ta taki qatuwar sa'ar samun auren elmustapha bayan gwagwarmayar da aka sha,duk da tasan cewa ba sonta yake ba amma tausayi da qaunar da take masa ya sanya ya amincewa aurenta" ta fada tana maida numfashin takaici "To kuma kubra me ya kawo tonon silili haka?,abinda ya wuce ai ya riga ya wuce ko?,kawai shawara muke da buqata" "Ki tattarata ta koma gidanta,ko a kango yace ta zauna ba nijeria ba ta zauba,bare ma meye marabar gidan nata da nan din?don kawai tana cikin family house,kowa ya sani qaryarka kace gidan mutum kamar almustapha an rasa jin dadi da walwala da dukka wata qawar duniya,idan zata koma taje kowa ta qwaci mijinta to,idan kuma zama zatayi bismillah saikici gaba da dorata akeken bera ki kuma share mata wajen zama,kinsan dai ko auren ta kaso wallahi duk yadda takejin kan nan nata a sama ba zata samu wanda ya koda kama qafar doctor mustapha ba" "Ya isa kubra don Allah,ke dole sai kin zagi mutum zakiji dadi" waiwayawa haj khaulat tayi ta dubi su'ad dake zaune hawaye shabe shabe,har cikin qirjinta taje jin kishin mustapha,tamkar ta dauki ran wadda ta aure mata shi haka take ji,kullum kwanan duniya ji taje kamar ta yanki ticket ta koma masa,don tun kafin a kai ko ina ta soma raina kanta,ta tabbatar rabuwa da mustapha kamar yadda tayi iqirari ba mi yiwuwa bane a rayuwarta,ko sakinta yayi tana jin ba zata iya qara aure ba har ta mutu,don gani take nan duniya babu kamar yashi "Zaki shirya ki koma wajen mijinki,daga yau so nake kada ki saurara kada ki daga qafa,duk inda ya sanya qafa ki bishi,sai kin tabbatar kin mamaye rayuwarshi,sannan cijin gidan bance ki saurarawa uban kowa ba,fin baki dayansu munafukai ne,suna da masaniyar qara auren nasa su suka hada,ki taka uban kowa koda kuwa hajiya zuwairiyya ce uwarsa kinji na gaya miki,ki fara shiri,naji labarin biki ya tasi a gidan,zaki isa ranar daurin aure don kiga idon uban kowa,uban kowa yaga naki idon ihee"kai su'ad ta gyada cike da gamsuwa da samun qwarin gwiwa,itadai kubra na gefe tana kallonsu tana tabe baki,ta tabbatar zamansu bazai taba daidaita da mustaoha ba matuqar tace zata taba iyayensa,kai ta dauke tana qissima yadda dramer zata kwashe.         Minti talatin cif ta fiti daga bandakin,ba kowa cikin dakin alamar ya fita,hakan ya sanya cikin nutsuwa ta fara shiryawa bayan ta kulle qofar,sai data gama komai tsaf sannan ta bude ledar daya bata ta zari rigar ta wareta,sosai rigar tayi mata bata taba ganin irin desing dinta ba,bisa dukkan alamu sabuwar design ne dako kasuwa bata kai ga fita ba,sai taji tana sha'awar sanyawa,saboda haka kai tsaye ta zirata ta daidaita ta ajikinta,cif cif tayi mata har fadin tamkar an gwadata,ta fidsa shape din qirjinta sosai zuwa faffadan qugunta,qila hakan baya rasa nasaba da tsahonsu da ya kusa zuwa daya da abida,saidai abidan ta fita jiki,don sake qawata rigar a jikinta sai ta bude inda take ajiyar dankunnayenta,ta sanya dankunne da 'yar sarqar hannu wadda ta dace da kalar dutsen da aka qawata rigar da shi,yafa mayafin kawai tayi bayan ta daure gashinta,sai ta fito tamkar wata balariyar qasar,murmushi ta saki sanda ta kalli kanta a madubi,ba shakka tayi amsheta rigar,wayar dake gefanta ta jawo ta dauki hoto guda biyu,zata qara sai ta tuna ta almustapha ce,ajjiyeta tayi inda ta dauka ta wuce zuwa saman kujera kuma gadonta ta koma ta zauna ta janyo littafin wajen anty dije taci gaba da karantawa karo na biyu tunda ta bata shi.        A quntace yake takowa zuwa qofar dakin nasu cikin tafiyarshi ta qasaita,ranshi har yanzu a matuqar bace yake,hannunshi ya sanya ya murda handle din da niyyar turawa ya shiga sai yaji qofar a rufe tanke,ranshi ya dan baci,ya soma knocking a zafafe,littafin ta ajjiye cikin fargabar yadda ake qwamqwasa qofar,ta isa bakin qofar cikin siririyar muryarta tana fadin "Ana zuwa" ta janyo qofar baya,idanunshi suka fada kanta ba tare da ya shirya ba,kallo ya shiga qare mata tun daga yatsun qafarta zuwa kanta,ya dawo ya dire a qirjinta,boyayyar ajiyar zuciya ya saki,bai taba tsammanin rigar da suke fitarwa ta kai kyawun haka ba duk da yasan yadda suke zuba fasaha wajen saqata ba sai yau,dalili kuwa bai taba tsayawa ya qare mata kallo jikin wata ba sai yau din,koda ya kawowa su'ad bai taba gani ta saka ba,hasalima saidai ta bayar ko tayi kyautar neman suna,ita dole ace mijinta ke da MM VAIL AND ABAYA INTERNATIONAL COMPANY,amma bata taba rabata a jikinta ba,a cewarta tayi mata nauyi ko zata bata mata tsarin shigarta duk kuwa da yadda abayar ta kai ga kyau da tsada,sosai shigar abaya ta sake burgeshi duk da dama can yana sonta,da sauri ya hade fuska sanda suka hada idanu ta kama shi yana kallonta,baya taja a hankali cikin tsoron irin kallon da yake kata,takowa ya soma yi zuwa ciki murya a dake yana fadin "Idan da wani ne kuma kr bugawarfa,kawai saiki bude ba tare da kin tambayi waye ba?" "Ai nasan kai kadaine zai shigo" "Ba tabbas,hotel ne dont do this again" "In sha Allah" ta fada kai tsaye kuma cikin sanyi,sai amsar tata tayi masa dadi,a hankali sai ya dinga lalubar bacin ran nashi yana rasawa har zuwa sanda ya dubeta sanda take nannade saman kujera tana ci gaba da duba littafin "Ki shirya kayanki,nan da gata zaki je naijeria" a ba zata maganar tazo mata,sai ta dago kai tana ware fararen  idanuwanta a kansa tana bude baki cikin tsananin farinciki har batasan sanda tace "Da gaske?,da gaske kake don Allah" "Ni abokin wasanki ne" ya fada yana mai fatan ta janye fararen idanuwanta daka kanshi,wani feelings akanta ke son kamashi,idanuwa ya lumshe sanda ta girgiza kai alamun a'a ta janye idanuwan nata daga kanshi,saidai murmushin dake saman fuskarta yaqu boyuwa,sake bude idanuwan nashi yayi a hankali ya azasu kanta,wanda ita bata ma sani ba ta tattara hankalinta ga littafin duk da ba karantawa take ba,zai iya cewa bai taba ganinta cikin farinciki haka ba,sai ya sake maida su ya rufe again,baya son abinda yake ji a kanta yaci gaba da tasiri a kanshi,don matuqar yaci gaba da tasirin to zai jagoranceshi ya aikata koma mene,tun wancan daren zuwa yanzu bai taba samun sukuni ba duk sanda tunanin moment na daren ya fado masa,sai yaji kamar ana mintsini ko tsikarinshi,baiso ya karya alqawarin da ya daukarwa kanshi a kanta,hakan ya sanya tilas ya kwanta duk da baijin bacci,da qyar ya samu bacci ya daukeshi. *******   ********    ********       Baki daya ta kasa sukuni tunda ya shaida mata tafiyar,ji take kamar tayi tsuntsuwa ta ganta a gida,har ya fura lura da irin dokin da takeyi,ana ya jibi zata tafi kuwa ta kwashe kusan duk wani abu nata mai muhimmanci tayi parkinga nasa waje guda.        Ana ya gobe kuwa zata tafi har ya kwanta tana ta zirga zirgan hada komai nata,ya jima kwance cikin bargo yana kallonta cikin kayan bacci,wanda ita har ga Allah ta tsammatar masa bacci,mamakin irin zumudin da take kawai yakeyi,sai tayita sakin murmushi ita kadai.         Shi da kanshi yake tuqa motar zuwa filin sauka da tashin jirage na qasar,yayin da m'aikatansa biyu ke binsu a wata motar ta daban dake bayansu,har suka isa airphort din wani farinciki na ratsata,musamman data duba ticket dinta taga jirgin zai sauka kano ne,hakan na nuna cewa gida zata fara isa,waiwayowa tayi sanda aka fara kira matafiyan da zasu tashi zuwa nijeria ta dubeshi,sai ta sadda kai ta rasa me zata ce "Allah ya tsare,ki gaida su"ya fada hannayensa zube cikin aljihunsa,wani yanayi ke ratsashi wanda baisan na meye ba,kamar wani abu na neman gushewa daga gareshi wanda ya jibanceshi,ranshi a bace yake haka kawai baijin duk wani karsashi da farinciki,dagowa tayi ta dubeshi suka hada idanu "zasu ji,na gode" "Ba case" ya fada yana ci gaba da dubanta ba tare da ya janye idanuwanshi ba,a hankali ta daga qafafunta tana takawa,tana jin idanuwanshi a kanta,ita dinma sai taji karsashinta da murnarta na dan raguwa,sabo ne take zato wanda hausawa ke cewa turken wawa,ko dabba ce kana tare da ita randa kuka rabu sai kaji wani iri,yana nan tsaye hakanan ya kasa tafiya har ta bacewa ganinshi sannan ya juya a hankali ya bar wajen,kwance yayi cikin salo na kashingida abayan motar drivan ka janshi wanda ya kama tashar gidan redion dake qasar,umarni mustapha ya bashi kan ya kashe,baison hayaniya, "Sorry sir" ya fada yana kasheta.      Cikin awannin da basu da yawa suka iso qasata nijeria,tuni mota daga gidan baba prof dake kano ta iso tana jiran ta,tamkar jira wayarta take ta soma ruri network ya dawo,ta laluba aljihun jakar na baya ta zaro wayar tana dubawa,amira ce,murmushi ya subuce mata tana mirgina kai "Wohoho amira,i missed you wallahi so much" ta fada a fili sanda take shigewa bayan motar sannan ta daga wayar,wani ihu da amiran ta sakiwa kunnuwanta sai data rufe ido "Kunne na amira kunne na" "Wallahi kaman a mafarki namecy ashe kin iso,last week muka je umra na takurawa my saif sai munje wajenki wallahi yaqi wai nauyin ya musty yake ji,wayyo namecy kina ina?" "Saukata kenan ko gida ban qarasa ba,ina mota a kani na sauka,next week insha Allah zan qaraso" "Qarasa gida namecy ki huta akwai labarai wallahi" ta fada tana dariya,murmushi sumayya ta saki "To ba damuwa" "Ki gaidan mama,amma fa idan naga ba dama zan biyoki na zaqu wallahi naga matar yaya na" dariya suka sa baki daya sumayya ta kashe wayar,har yau amira halin dai bai sauya ba.         Saboda murna bata iya tsayawa an shiga mata da kayanta ba,wanda itama batsan da kayan bama sai da suka sauka ta gansu,da sallama ta kutsa kai tsakar gidan,wata dake shirin shiga kitchen ta dakata ta juyo,halima ce,ta zama wata babbar mace,haliman da ake zaton ba zatayi qiba ba saiga kumatu a fuskarta,da gudu ta nufo sumayya suia rungume juna kowa na ambatar sunan dan uwansa,hayaniyar ita ta sanya mama dake falon ta daga labule ta leqo "Kada dai kicemin gudu kike halima me yasa kike da kunnen qashine wai?" Sak maman tayi sanda sumayya ke dagowa,bakinta har kunne,da hanzari sumayya ta saki halima ta nufi mama tana kiran sunanta,hannayen mama ta kama ta riqe gam qwalla na taruwa a idonta "Me kuma na kukan ne sumayya?" Maman ta fada cikin farinciki sanda sumayyan ta fada jikinta,dakin suka shige baki daya farinciki zuciyar kowannansu ba magana.         Nan da can kowa ya kasa motsawa cikinsu,anata hirar yaushe rabo,mama nata kallon sumayyan,farinciki na zagayata,bata taba ganin diyar tata cikin kyakkyawan yanayi makamancin wannan ba tunda take aure,wani kyau haiba da cikar kamala,ta sake zama babbar mace qwarai,da alama hankali ya fara gameta,ita kuma sumayyan na duban halima sannan ta dubi mama "Wai dama mama halima zatayi qiba?" Murmushi ya subucewa maman "Gata nan kuwa sumayya" "Masha Allah,lallai abdur rahman ya iya kiwo" "Har ya kai yayanmu,wai baki kallon madubi ne yaya,wallahi sanda kika shigo na zaci baquwar balarabiya mukayi Allah kuwa kada ki dauka sharri ne ko mama baki gani ba?" Murmushin jin dadi maman ta saki "Masha Allah kam" sai kunya ta kama sumayya tadan rausayar da kai,idanunta ya sauka kan abdallah dake kwance yana bacci,baki ta bude "Kai dama mama yaron nan na gunki?" Dubanshi sukayi baki daya "Sunzo dai tare da mamarshi halima,abdur rahman yayi uwa yayi makarbiya ya karbe abdallah daga gunmu baki daya,baki ga dambun tsiyar da aka dinga yi tsakaninsa da yahanasu ba amma yace saidai tayi haquri shida mu saidai ziyara" kai take gyadawa taba duban halima,dariya ta saki "To ai koni bazan bada abdallah ba Allah yanzu ko kece saidai ki haqura" dariya ta saki "Ni meye mawa,dama abdallah ai danku ne,kuyi duk yadda kuka ga dama da shi,Allah ya qara zumunci" miqewa mama tayi ta basu waje don sauke tukunyar abinci,wanda halima ba zata iya ba sabida an hanata duk wani motsi mai qarfi sabida juna biyun da take da shi wanda bai wuce wata daya da rabi ba,a nan haliman ke gayawa sumayya da kuma barin da zainab tayi wanda ita taje dubawa ma ta biyo ta gida,baki sumayya ta saki tana dariya tare da duban halima "Kai halima ko kunyata bakiji,Allah ya inganta mana ya raba lafiya" cikin jin 'yar kunya ta amsa.         Sosai sumayyan ta zage ta daki abincin,ba qaramin missing abincin gida tayi ba,wanda kullum suna fama dana hotel,wanda idan ba fried rice ba bata iya cin wani abu sosai saidai kawai ta taba sama sama,da qyar ta yakice ta kira nafisa ta shaida mata zuwan ta,kamar ta ballo itama tazo haka take ji,amma sumayyan ta gaya mata satin sama tana tafe,tace tana nan tana jiranta,daga nan anty dije ta kira,bakin antyn har kunne,itama ta zaqu taga sumayyan,sun dan jima kan layi kafin suyi sallama,sun sha hira qwarai,a nan mama ke bata labarin irin gidajen gonar da baba prof ya damqawa malam yace nashine,tun tsohuwar dukiyarsa da bai tsaya da juya masa ba,irin hayayyafar da tayi,kai kawai sumayyan ke kadawa,babu shakka samun abota irin wannan tana da wuya a wannan zamanin,wani qima da mutuncin baba ke sake hauhawa cikim zuciyar sumayya,qaunarsa na sake kamata,qauna ta fisabilillahi wanda tun kafin tasan matsayinsa wajen mahaifinsu take masa ita "Allah ya saka da alkhairi ya cika masa burikansa duniya da lahira" amsawa itama maman tayi,tana sake gaya mata ci gaban da aka samu,kwanaki kadan ya rage subar wannan gidan zuwa wani sabin gidan da malam din ya saya,wanda da baba ne zai biya malam din yaqi,dawainiyar da karamcin tayi yawa inji malam.        Farincikin da malam yaji sanda yaga diyar tashi ba mai misaltuwa bane,ido ba mudu ba yasan kima,yasan cewa bisa dukkan alamu addu'ar da yake binsu da ita dare da rana zatayi tasiri a kansu,sun jima sosai suna hira da malam har kusan sha daya na dare,shi da kansa ya sake warware mata abinda ya faru na danqa masa gidajen gonakinsa da baba yayi,wanda har yau basu ma je na wasu garuruwan ba,addu'a sosai ta yiwa baban malam na amsawa.         Washegari tare suka karya ita da malam din da abdallah,wanda abdur rahman yace a barshi yaga mamanshi har sanda zata tafi,shi kansa abdur rahman din tsokanarta ya dinga yi yana cewa manyanmuyaya sumayya,raha suka yi sosai kamar babu wani abu da ya taba faruwa tsakaninsu,dariya ta dinga kawai,shi kansa ya sauya ya sake zama magidanci,alamun hutu da kwanciyar hankali baki daya sun bayyana tattare da shi,cikin zuciyarta tana gode ma Allah,tasan ko ba komai 'yar uwarta na cikin rayuwar jin dadi da walwala kamar yadda take fata.        Kwalayen jiya ta bude ta duba,uwar tsaraba ce a ciki,akwai wasu dake nannade da sunayen malam da baba,bata taba ba ta miqa musu cikin mamaki,sai take jin wata qimarsa cikin ranta (Gareku maza,abune mai kyau ka dinga kyautatawa iyaye da 'yan uwan matarka,don haka na qara qimarka a idanunsu da idanun matar taka gaba daya,ko yaya alkhairi yake dadi gareshi,Allah ya hore ya kuma bada iko amin),sai data gama sannan ta shirya zuwa gidan zainab,ranan can ta wuni baki daya,ta sameta cikin kyakkyawan yanayi itama kamar 'yar uwarya,jikin nata ma ya warware gaba daya,washegari kuma gidan yaya yahanasu ta wuni,kallonta yayan ta dinga tana qarawa,har sai data kasa shiru "Allah qadiran ala may yasha'u,ashe sumayya ke din rabon wani ce da muntarinmu ba,kowanne bawa da kalar tashi qaddarar" ta fada tana matse hawaye,hakan ya sosa tabon dake zuciyar sumayyan,duk da haka sai ita ta lallashi yaya yahanasun,sai la'asar taje ta gaida hajiyan bahijja da abdur rahman,sosai taji dadin ganin sumayyan,ita ta tsaidata ma bata wuce gida ba sai magariba.          Again washegari kuma gidan yaya abubkar ta wuni,amina ta rasa inda zata sanyata saboda murna,itama dubanta take kamar yadda kowa kallonta,sosai sumayyan ta sauya mata cikin 'yan watanni "Masha Allah sumayya masha Allah,dama haka almustaphan naki ya iya kiwo?" "Kai anty kai" ta fada tana qyalqyala dariyar irin yadda meena tayi maganar.    ******   *******   *******         Qarfe sha daya na dare ya dawo daga office din,baki daya ranar ya maida kanshi busy,sosai ya tsaya da kanshi cikin kamfanin yana zagayawa waje waje yana ganin yadda ma'aikatan ke gudanar da aikinsu,abinda tunda suka taho tare da sumayyan baiyi ba,baisan me ya hanashi ba,daga qarshe ya tuqe a warehouse nasu,hamza ne ya dubeshi a gajiye "Gaskiya maan na gaji gida zan wuce,magariba fa ta gota,na tabbata abida na can na zuba ido" cikin ko in kula yana duban bangaren da suke ajjiye kayan aikinsu yace "Wani ya hanaka tafiya?" "Ok,dama kai na tsaya,na lura kuma kai yau aikin naka ba mai qarewa bane,ko don yau gauro kake?" A nutse ya waiwayo ya maka masa harara "Ba yau na fara ba bare ka gaya min ba dadi" dariya hamza ya saka "Gaskiya ne wannan,ko zaka zo mu wuce tare kaci abinci wajena?" "Bana buqata" ya fada yana ci gaba da takawa hannunsa zube a aljihu,haka kawai yake jin sam baida sha'awa ko karsashin komawa hotel din,a haka hamza ya juya ya fice ya barshi a wajen,yasan tunda yace bashi zuwa to bazashi din ba.          A hankali ya tura qofar dakin,babu haske a dakin kasancewar babu kowa,ko ina dumdum yake da duhu,kunna qwai yayi yabi ko ina na dakin da kallo,sai yaga dakin tamkar bashi ba,komai ya canza,wani fili yaga dakin ya sakeyi kamar an dauke wani abu,wata gajiya ta musamman ta saukar masa,ya taka zuwa cikin dakin ya zauna gefan gadon idanuwanshi na kan doguwar kujerar data saba zama,yana fidda takalmin qafarshi da safa yana jefarwa,gadon ya fada baki daya yana fidda iska daga bakinsa,a qalla ya kai kusan minti goma a haka kafin ya miqe ya zauna dai dai,wayarsa ya fidda ya kira ya bada umarnin a kawo mishi dinner sannan ya miqe ya cire kayan jikinsa ya fada toilet,turus yayi yana duban bathtube wanda yake wayam babu komai a cikinsa,sabanin watannin baya da idan ya dawo yake tadda shi cike da ruwa mai qamshi da dumi,cikin kasala ya soma tara ruwan kafin ya shige cike,qaramin tsaki ya ja,baki daya ruwan bai masa ba,sabanin nata da yake jin baison fita a ciki,a gurguje yayi wankan ya fito yana tsane jikinsa da towel aka yi knocking,sai daya sanya doguwan riga sannan ya bude ya karba,shafa'i da wutiri yayi kafin ya dauko computer dinsa ya kunna bayan ya jonata chargy,sosai ya zauna a qasa ya bayan ya janyo abimcin ya bude ya soma kaiwa bakinsa,lokaci lokaci yakan daga kai ya kalli inda ta saba nadewa duk lokaci irin wannan da yake zama cin abinci ko yin wani aiki,lokaci lokaci yakan kamata tana satan kallonshi da fararen idanuwanta,ko ita wani lokacin ta kamashi ko su kama juna,kowa yakan dauke kai da sunan ba kallon dan uwanshi yake ba,qaramin murmushi ne ya subuce masa,ya ture abincin dake gabanshi,yana tuna sanda tayi yajin aikin daina kallonshi tun faruwar lamarin a wannan daren,kai yake girgizawa yana sake tuna duk wani minti daya daya gifta musu a daren,cikin hanzari ya soma kokawar kauda tunanin,ya jawo computer din ya soma kunnata cikin bawa zuciya da gangar jikinsa karsashi da qwarin gwiwa,saidai duk yadda yaso da nuna jarumta lamarin yaci tura,gajiya da kasala sun mamayeshi,haka ya sanya dole ya kashe wutan dakin ya fada gado,idanuwanshi still kan kujerar tata,sannu sannu idanuwan suka dinga lunshewa bacci ya rinjayesu.        Ko da ya tashi da safe abu na farko daya fara takawa shine takalminsa,tsaki ya ja sanda ya tuna jiya bai kwashesu ba ya kaisu muhallinsu,ya saba da zarar ya cire bai zuwa ya taddasu wajen,haka ya duqa cikin kasala ya janyesu gefe sannan ya wuce,yana shiryawa yana sake duban duk wani muhalli da takanyi kai kawo a wurin da safe irin wannan,musamman inda ta saba zama tayi karatun qur'ani ko taja carbi,kai ya girgiza yana tsaki tare da tuhumar kansa me ya sameshi ne haka?,a gurguje ya shirya ya fice zuwa office.       Ko da ya dawo yau dinma kamar jiya,bai shigo da wuri ba,haka ya dinga wasiwasi cikin dukka ayyukanshi,kanshi ya shafa idanuwansa a lumshe,yana tunanin tsananin sabo ne ke dawainiya da shi,don me zata zauna cikin tunaninshi haka?,don me zai kwana ya tashi ya wuni cikin tunaninta ita daya?,bai taba fuskantar irin wannan yanayin ba tsawon rayuwarshi,to yau ko cikin baccinsa ma bai samu hutu ba,sai da ta kawo masa ziyara,wanda hakan ha sabbaba masa yin wankan tsakiyar dare,hakan kusan sai ya zame masa kamar al'ada ko wani jarrabi cikin kwanakin,idan yau baiyi ba gobe zaiyi,duka ya tattara hakan ya dora bisa mizanin sabo da kuma cikakkiyar lafiya da Allah ya bashi.        Cikin kwana na biyar da tafiyar tata cikin dare bayan yayi wanka ya dawo sai baccin yayi nashi waje,haka ya dinga juyi shi kadai,baisan me yasa garin baki daya ya daina masa dadi ba ya fita masa a kai,miqewa yayi ya janyo wayarshi ya hau binciken da baisan dalili ba,cikin haka hannunshi ya kai kan bigiren hotuna,tunani yake bari ya gwada abinda yaga rannan tana yi,yana tsammanin zasu debe masa kewa kamar yadda yazo ya tarad da ita tana kallon hotunan cikin wayarshi,hoton farko dake bangaren camera nata ne,cikin shigar doguwar riga,da sauri ya wuce zuwa hoton gaba nan ma ita ce,sai ya sake wucewa,nashi hoton ya gani,ya jima tsaye kan hotonsa sai ya samu kansa da dawo da hoton baya,kamar wanda ake umarta ya sanya hannunshi yayi zooming,komai ya fito tar cikin hoton,tana tsaye gaban mudubi tana murmushi,fararen idanuwanta zuwa dan qaramin bakinta mai dauke tattausan labba yake kalla,bai manta laushin da yaji a wajen,bai manta hasken wadan nan idanuwan ba,da sauri ya fita daga hoton ya ajjiye wayar,ba shakka sha'awa ce kawai ke fusgarsa,ita ke damunsa,amma me yasa baijin haka wajen su'ad tun asali?,shima bai sani ba,yaye bargon yayi ya koma toilet ya daura alwala ya dawo ya shimfida abun sallah ya tada nafila. *******     ******     *******         Washegari a makare ya isa office duk da sunyi da hamza huzaifa da lamin zasu hadu,dubansa lamin yake sanda almustapha ke yiwa jakarsa mazauni shima yana neman zama,yayi kyau cikin suit mint green wanda suka haska farar fatarshi data jiqu da hutu,agogon hannunsa lamin ya kalla "Maan ban sanka da karya alqawari ba,saidai yau gashi ka saba,but idanunka suna nuna ma kamar baka samu isashshen bacci ba" "Shi kuwa ya samu isashshen bacci,uban wa zai hanashi bacci yana shi daya a daki,d same thing fa yanzu muke" inji huzaifa yana duba wani file kamar bashi yayi maganar ba "Gaskiya ka fada my guy" inji hamza wanda tun dazu yakeso ya takeshi dama,idanuwanshi yacu gaba da zuba musu bayan ya sarqe yatsunshi cikin juna,duka sai da suka gama iskancinsu sannan lamin yace "Ga allocation din da gwamnati ta bamu ka duba" ya fada yana tura masa file gabanshi,banza ya masa,yaja wayar landline ya bada umarnin yanka masa ticket da zai tashi daga dubai zuwa nijeria wanda zai sauka a aminu kano international airphort kano,ji yake tamkar wani abu na janshi zuwa nijeria,baibtaba tsammatar tafiya cikin tsukin wadan nan kwanakin ba,ya kife wayar ya musu transfer kudinsu sannan ya ja file din yana dubawa ba tare da yace musu uffan,kana dubansa kasan halinne ya motsa,kusan duk sun sani,shikam hamza yaci alwashin sai ya sanyashi magana "But maan me zaka je yi kano" sai da ya daga kai ya dubeshi "Ka mance zan aurar da qanne?" "Amma ai ina cewa jiya muka gama maganar next week kaman friday haka zamu wuce baki dayanmu har da su huzzy" "I change my mind" ya fada kai tsaye "Ko kuma she changed your mind ba" sake dagowa yayi yana dubanshi "Me kake nufi?" "As i said" ido ya zuba masa yana duban hamzan kamar mai nazarin wani abu,sai murmushi ya qwace masa,girgiza kai yayi ya maida kansa kan file yana ci gaba da kada kai,su huzaifa na dariya qasa qasa "Iam telling you,he became crazy wallahi cikin watan nin nan,shi kadai sai ka ganshi yana murmushi,kun tuna yadda murmushi ke masa wuya a baya?,kana wasa da mata maan,mata ba abun wasa bane,duk yadda kake ganin u r powerfull nasu power din yafi naka,so ka bisu a hankali man tun ba'a saka ka fara kneeling ba kana begging" "Saurara malam,naga ka fara wuce gona da iri,ni...ni zanyi kneeling ina begging,begging for what?"yayi saurin tarar numfashin hamzan "For love ko?" Inji huzaifa yana rufe bakinsa da wata takarda saboda shegiyar dariyar dake sakadarshi "God forbid wlh,an gaya muku kowa irinku ne?,mtsweew,kunga idan wannan ta kawoku na tashi na barmuku office din,idan kun gama kwa kirani,i have alort to do" dole duka suka zama seriouse suka hau tattaunawa kan abinda ya tarasun,kowanne yana so ne yaga yadda maan zai fara buga nashi love din da wadda yakeso,duk cikinsu ba wanda bai kwana da sanin cewa shi din mutum ne dake bala'in qaunar soyayya cikin rayuwarshisau tari idan suna hira ko siyan gift wa 'yammatansu tabe baki yake yace basu iya komai ba duk yadda suka kai ga qure adaka,wani irin mutum ne mayen love,shi yasa suka jimanta masa a sanda baiyi dace da dai dai ra'ayinsa ba,a nutse suka soma tattaunawa kowa na maida hankalinsa kan lamarin,bude sabbin reshe da suke so suyi a qasashe biyar kowanne branch zai baiwa daya daga cikinsu ya riqe ragama,bawai don kowannansu bai mallaki abun kansa ba a'ah,tsabar qauna yarda da aminci dake tsakaninsu ne,da kuma koyi da yin abota mai kyau da doctor almustapha ke da buri da kwadayin yi irin na mahaifinsa professor mukhtar. Ga almustapha da su'ad zuwa nijeria,muje zuwa readers.............. *Ummu muhammadiyya.* *mrs muhammad ce*👑 *Ummu muhammadiyya.* 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [23/02, 11:52] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 8⃣5⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *wannan page din kuma naku ne* *sparkling son sorians by batool mamman* *Allah ya bar zumunci* _____________________________________          A qalla ya kusa minti talatin zaune cikin motar a qofar gidansu,ya dubi agogo karo na kusan biyar yaja dan qaramin tsaki,baisan me ya jawoshi qofar gidan ba,to idan ya shiga yace me?,me ya kawoshi?,la'asar ne bare yace malam yazo gani,bai da tabbacin yana cikin gida a wannan lokacin,tun suna hanya ya dinga kai kawo cikin wayarsa bangaren adana lambobi baiga komai ba da zai iya amfani da shi,ya motsa labbansa da niyyar bawa drivan umarnin yaja motar su wuce sai yaga fitowar malam din,sanye da shadda milk babbar riga,fuska akwai ruwa da alama alwala ya kammala masallaci ya nufa zaiyi sallar la'asar,cikin hanzari ya balle murfin motar ya fito,dakatawa malam yayi ya zubawa wajen ido sanda yake qarasowa "A'ah,mustapha ne?,saukar yaushe?yanzu dama tasan da zuwanka amma ta fita unguwa?" A ladabce ya fara shirin rusunawa malam ya dakatar da shi da hanzari "A'ah,miqe kada ka bata jikinka" duk da haka sai da ya dan rage tsawonshi suka gaisa "Bari na baka ruwa ka daura alwala idan mun dawo sai mu shiga ciki ko?" Malam ya fada yana niyyar juyawa ciki,jin haka ya sanya drivansa saurin komawa mota don dauko masa ruwan riba,da hannu ya dakatar da shi,suna tsaye malam ya iso da butar ya miqa masa,ya koma saman dandamalin qofar gidan ya fara daura alwalar,a hankali yara suna fara giftawa suna kallonshi,kafin ya kammala sai ga yara sun soma taruwa suna kallonshi,a tsakaninsu suke qus qus din balarabe ne wlh,murmushi malam ya saki don ya jisu,karbar butar malam yayi ya aiki daya daga cikin yaran ya maida gida sannan suka wuce masallacin tare.      Tare suka jero da malam din suna hira jefi jefi har suka qaraso gidan,da kansa malam din ya bude masa sitting room yace ya shiga ya zauna,bai musa ba ya shiga ya zauna din yana qarewa falon kallo,ciki malam ya koma ya sake kiran sumayya ya shaida mata duk abinda take ta baro ta taho tayi baqi,cikin mamakin wanne irin baqi tayi haka tace masa tana dab da shigowa unguwar ta iso tuntuni.        Cikin sanda ta shigi soron,idanuwanta kan takalmin sau ciki dake qofar sitting room din,cikin gidan ta wuce kai tsaye,mama ta taras a falo tana wanke wani rubutu,tun da tazo taga tana yinsa kullum da yamma batasan dai ko na meye ba,baki sake maman ta kalleta "Me kika shigo kuma yi?,baqon ai yana sitting room"gabanta ke faduwa hakanan da wani irin tsoro " waye mama?" "Idan kin shuga kya gani,tsaya ki karbi wannan ki shanye tunda kin riga da kin shigo" inji maman tana juye wani rubutun daga wata jarka wanda ke gauraye da zuma ta miqa mata,bata musa ba ta karba ra kwankwade,sannan ya zare niqab dinta daga saman zabgegen hijabin dake jikinta,don tunda tazo ta koma wannan shigar,sakamakon yadda aketa tanka canzawar da tayi,bugu da qari da yawan kallon da take fuskanta wajen maza idan ta fita,jakarta ta sabule ta ajjiye saman kujera ta dubi mama "Kayana an kawo gugar?" "Akwatin ma a hade yake,ba jibi ko gata zaki wuce ba?" "Eh amma mama nikam banson tafiya wlh,da sai ranar daurin aure kawai" harararta maman tayi "Ban koya miki sabawa umarnin miji ba,randa yace ki tafi koda yau ne tafiya zakiyi" murmushi ta saki kawai ta juya ta fice,tunda tazo maman bata da aiki sai ja mata kunnen tabi miji.        Tun kafin ta kai ga shiga dakin take ji qamshin wani turare kamar ta sanshi,hannu ta sanya ta yaye labulen bakinta dauke da sallama,idanu ya zuba mata yana dubanta,baki daya ko ina na jikinta a lullube yake tun daga saman qafarta har zuwa kanta da hijabi,wani sanyi yaji ya ratsashi,karon farko yaji shigar tayi masa,ba abinda ke nunawa a jikinta,idanu suka hada ta saki labulen tana takawa a hanakali kamar mai taka qaya,wani shegen kwarjini yayi mata,ya cika mata idanu baki daya,bai fasa kallonta ba har ta qaraso kan daya daga cikin kujerun dake zagaye da falon ta yiwa kanta matsugunni,gababshi kewaye da ruwa da lemuka saidai babu wanda ya taba "Sannu da zuwa" ta fada tana dubanshi qasa qasa "Ina kika je?" Ya tambayeta maimakon amsa "Gidan aunty na,aunty salma" "Wa kika tambaya?" Wannan karon dagowa tayi ta zuba masa idanu cikin mamaki,taga dai dole idan tazo ya sani zata gidan 'yan uwa dai,janye nashibidanun yayi wannan karon,kallon da take masa yana sake kasheshi da narkar da duk wani sashe mai muhimmanci dake jikinsa "Tashi ki dauko kayanki mu wuce?" Ranta ya baci,take idanunta suka hada qwalla "Amma sai jibi ai zan wuce abujan ko?,yau fa kwana na shida fa anan din?" "Haka nake da buqata idan kuma ban isa ba to" idanunta ta kawar qwallar na zirarowa a idanunta,ta miqe tamkar zata rushe da kuka ta fice.       Kuka ta sanyawa maman da qyar ta ciyo kanta ra gaya mata abinda ya faru,idanu maman ta zuba mata "Shikenan don yace zaku wuce zaki zo kina rusan wannan kukan?,da can kinsan zaki zo din ne ka din ya barki?,so kike ku taru duk ku zama taron tsintsiya babu shara,ai da nasan abinda kike wa kukan ma da tuni naci mutuncinki,tashi ki dauko kayanki" maman ta fada tana miqewa zuwa uwar dakinta,waya ta dauko ta kira malam ta shaida masa,yace Allah ya tsare baya kusa ya fita daga unguwar amma ta tabbata sun tafi,idan ta zauna me zata musu.          A tsaye ta sameta a falo tana goge hawaye riqe da jakar matafiya mai taya,hannun maman dauke da wani babban kwali "Ga tsaraba nan ki kaiwa surukar taki" "To mama,abdallah fa?" "Zasu zo da malam daurin aure ran asabar din in sha Allah idan babanshi ya barshi,shi bai ta taki ma,ko maganarki ake bai damuwa,Allah ya riga ya sanya masa son jama'a,Allah ya tsare hanya sai munyi waya,kibi mijinki shine aljannarki" "Na gode mama" ta fada tana karbar wani rubutu cikin jarka a hannun mama sai qamshin kanunfari da zuma yake ta saka jakarta duk da batasan na meye ba.         Maimakon taga sunyi hanyar airphort sai kawai taga sunyi gidan baba dake kano,bata tanka masa ba har suka isa gidan,shima waya yake tayi da ma'aikatan asibitinsa har suka je din,fes suka tadda dakin nashi kamar da mutum a ciki,hakan baya rasa nasaba da ma'aikatan dake gidan kulli yaumin koda masu gidan basa nan,gefan gado ta zauna har yanzu idanuwanta na fidda hawaye,kayan jikinsa ya soma cirewa saboda yana da buqatar wanka,baiko dubi sashen da take ba,hakanan kukanta ke taba zuciyarsa fiye da ko yaushe,meye abun kukan?,toilet ya shige ya rufo qofar.        Har ya fito a nan ya taddata,ya gama shiryawa tana nade a wajen,silifas ya zira ya bude qofar dakin ya fice,miqewa tayi a hankali ta fidda hijabin jikinta ta shige toilet,wanka tayi ta hado da alwala ta dawo ta fidda kayan shafawarta,sallar ta soma yi,sannan ta shirya tsaf cikin sababbin kayan data siya a wani gurin saida kayayyaki,gown gown ne fitted masu roba wanda suke saukowa har qauri,matsatstsen dogon hannu gareta,rigar tabi lafiyar jikinta sosai ta fitar mata da qira,gashinta ta shafawa mai ta taje sannan ta daureshi da qaramin ribbom,hakan ya bawa jelar damar fitowa sosai da nuna irin yawan da gashin yake da shi,gefan kujera ta samu tayi zamanta abunta,ko dankwali bata nema ta daura ba,sai ta jawo wayarta tana danne danne tana duba watsapp dinta,wanda tunda aka bude mata bata bi ta kanshi ba sai yanzu,har yanzu ranta a dan bace yake,saboda tana ganin yana mata mulkin kama karya ne kawai,a duk sanda yaso tafiya da ita saidai ta ganshi kwatsam,kuma yace lallai ta taho su tafi haka ake?. Qofar aka turo,almustapha ne hannunshi dauke da takeaway,amsa sallamar tayi ba tare data daga kanta ba,hakan ya bashi damar qare mata kallo son ranshi,karon farko da ya ganta cikin irin shigar turawa "Hasbunallahu wa ni'imal wakil" ya fadi cikin ranshi saboda wani abu da yaji na yawo cikin jikinshi "Komai ma yi mata kyau yake ne?" Ya sake tambayar kanshi har zuwa sanda ya qarasa qasan carfet ya zauna yana fidda abinda ya siyo,harar kayan tayi a fakaice tana rayawa cikin ranta itakam ta gaji da wannan ciye ciyen,wato za'a koma 'yar gidan jiya,da iliminta na iya girki gaskiya ba zata zauna ta qare a takeaway ba,ta lura baki daya aqidun turawa sun ratsashi. Abincinsa ya fara ci hankali kwance yana qarewa shigar tata kallo a fakaice,ta zama tamkar wata 'yar baby ko yarinya 'yar sha hudu "Zo nan" ya fada yana wani cin mur,daga kanta tayi ta kalleshi,babu faraga saman fuskarsa hakan ya sanya ta miqe tsam ta soma takawa zuwa inda yake,kasa dauke idanunshi yayi daga kanta,komai yana juyawa da kuma motsawa tamkar wadda ake bawa umarni,zakayi tsammanin da gangan take aikata hakan,saidai ko kadan haka nata salon tafiyar yake,haushin da take ji ya sanya bata ma yi tunanin saka hijabin ba,salon tafiyar tata ya sake kashe almustapha,abu na farko da yake marmafi da muradin wajen macen da zaya auda tun da can bayan,sanin wannan dalili ya sanya su'ad koyon irin tafiyar da yake so din,saidai duk yadda ka kai ga aro abu ka yafa ba kamar yadda yake a halittar ka ba,nuni yayi mata da kusa da shi,cikin shan mur ta zauna har ma fiye da inda ya nuna matan,qamshin turarukanta suka soma kai saqo qwaqwalwarsa,nuni yayi mata da plate din da yake cin abinci,kamar zata saki kuka haka ta sanya hannu,saidai baki daya ta kasa sakewa bare taci,ga idanunshi da suka mata nauyi wanda ya azasu kacokam a kanta,so yake lallai sai ya gano wani abu na daban dake tattare da ita,wanda yake haddasa masa jin wani irin mai nauyi cikin zuciyarsa da qirjinsa,ya rasa meye wannan mai qarfi dake yawan fusgarsa zuwa gareta. Shi ya soma tsame hannunshi,ya shiga toilet yayi brush,kai tsaye saman gado ya nufa ya zauna,ya kawo laptop dinsa ya soma aiki,jifa jifa yana dubanta tana zaune gaban abincin wanda har yanzu kusan wasa kawai takeyi da shi,kasala da wani irin feelings da yake ji ya hanashi ci gaba da aikin,sai ya kashe cumputer baki dayanta ya ajjuyeta saman bedside,hannayenshu ya hade guri daya cikin zuciyarshi yana wani dan tunani,ya dan bita da kallo sanda ta miqe tana tattara kwanukan,ta gyara wajen tsaf,sannan ta shiga bandaki don sauya kayan baccinta ganin har ya sauya hasken dakin,idanunshi bisa kanta sanda ta fito din,abinda yake ji ya dinga bunqasa,ya hanashi sukuni,tilas ya miqe yana fidda numfashi ya miqa hannunshi ya kunna fitilar gefan gado,waiwayowa tayi suka hada idanuwa "Dauko min ruwa" ya fadi yana lumshe idanunshi numfashinsa na fita da sauri,ganin sauyawar yanayi tattare da shi ya sanya tayi tsammanin bai jin dadi,sai ta miqe a hankali,ta isa ga freezer ta ciro ruwa ta hada da kofi,gadon ta haye baki daya ta tsiyaya ruwan ta miqa masa,hannunshi ya sanya ya karba ya kafa kai ya shanye,miqa mata ya sakeyi ya mata nuni da idanu kan ta dado masa,sake tsiyayawar tayi ta miqa masa,amsa yayi sai yayi jifa da kofin tare da fincikota cikin jikinsa wanda tuni ya soma rawa numfashinsa na fita da sauri,lullubeta yayi cikin qirjinsa yana lalubar bakinta,tsoro ne ya kamata wanda hakan ya bayyana har cikin idanunta,ganin hakanne ya sa ya sauya salo,cikin kunnuwanta ya shiga gaya mata wasu kalamai wanda suka mata nauyi a qwaqwalwa da kunnenta,sannu a hankali suka zare duk wani tsoro da ya mamayeta,suka cire duk wani qarfi da yayi saura a gabbanta,zata iya cewa bata san ya akayi ba,saidai ta sake tsintar kanta cikin duniyar mustaphan,duniya mai cike da al'amura masu nauyi da tsayawa a zuciya ruhi da gangar jiki,wannan karon yaci galaba wajen sanyata sake masa,ta bar mata ragamarsa ya jata inda yaga dama,ba laifu wannan karon ma taji a jikinta,cinyoyinta suka dinga mata ciwo. Sai da komai ya kammala sannan ta farga,nauyi da kunya suka sanyata kuka,itakam me yasa sam bata da wayo ne bata ganema wayonshi sai ya gama budirinsa,yana jin kukanta a sanda yake hutawa yana sauke numfasji tare da shaqarsa d'ai d'ai,yana jin wani wasai a qirjinsa da gangar jikinsa tamkar waccan karon,wata iska ta musamman yake ji yana shaqa a qofofin hancinsa,yatsunsa ya tura cikin sumarta yana yamutsa gashin ta anutse,santsi da sulbinsa na aika saqo har cikin qwaqwalwarsa,hakanan yana sake burgeshi,salon yadda yake matan ya sanya kukanta raguwa,sannu a hankali wani irin bacci data jima bata ji irinsa ya ziyarceta. A nutse ya zareta daga jikinsa ya kwantar da ita saman filo,hannunshi ya sanya ya yaye gashinta da ya rufe fuskarta,fuskartata ta bayyana na mai dauke da lemar hawaye "Lazy girl" ya fada murmushi na kubce masa,a hankali ya sauka daga gadon yana maida tufafinshi,ya taka ya qarasa gaban mudubin dake dakin,hannunshi ya dora kan fuskarshi yana shafata a hankali,murmushi ya kuma subuce masa sanda ya tuna kalaman da suka dunga subucewa daga bakinsa suna fitowa cikin awannin da suka shude,shi kadai ya soma magana da kanshi "Wai meke damunka almustapha?,kaine kuwa?,yaushe ka koyi maqalema mace?" "There is something special tattare da ita" ya fada a fili,girarsa ya dage yana tambayar kansa tare da son tabbatarwa "Really?" Ya kuma tambayar kansa,murmushi ya kuma saki yana dan dukan kanshi "U r crazy man,gaskiya hamza ya fadi kenan" kafadanshi ya daga ya juya zuwa toilet don tsaftace kanshi. Wannan karon ma haka ta dinga qunbiya qunbiya,ita kanta batasan ya akayi ta sake masa haka ba,kunyar kanta ta dinga ji,shikam yana zaune abinshi yana karyawa,yayin data kasa sakewa riqe da cup din tea tana juyashi da cokali,ta lura tun dazun yakeso ya takaleta da magana saidai taqi bashi fuska "Hey" ya fada murya can qasa,fararen idanunta dake burgeshi ta daga ta dubeshi "Come here" ya bata umarni yana dubanta da wani kallo qasa qasa,bata son musu tsakaninsu,sai ta dire cup din ta miqe zuwa inda yake,inda ya nuna matan gabansa ta dawo ta zauna,batasan me yasa yake yawaita son kiran sunanta ba,ci gaba yayi da dubanta kamar dalilin da ya sanya ya kirata kenan,a qalla minti goma sannan ya ture plates din dake gabansu "Let me tell you something,baki iya making love yadda nakeso ba,sai kuka,sai kunya,wadanne irin lusaran maza kika taba aura?" Maganar ta mata zafi sai ta daga kai tana dubanshi,tuni qwalla ta cika mata ido,wannan cin fuska ne,yana nufin har da mukhtar cikin lusaran? "Can i teach you how i want you to be?" Kai ta girgiza,sai ta saki kuka,dariyarsa yake boyewa,hawayen dama kawai yakesin gani cikin idanunta,a jiya ya kura da wani kyau da idanuwanta sukayi sadda qwalla ta cikasu,kamata yayi suka miqe tsaye baki dayansu,bai saketa ba har sai da suka isa gaban mudubi,yana tsaye a bayanta "Look at your self,i think crying is ur hobby ko?"duban fuskar tata yayi kamar yadda yace,shabe shabe da hawaye kamar ta abdallah,sai ta dubi tashi fuskar,wata kunya ta kamata tayi qas da kanta,mannata yayi a jikinta ya dora kansa saman kafadarsa,hucin numfashinsa ya shiga kunnenta,tsigar jikinta ta tashi "na baro wata qasa na iskeki,wannan tarbar na cancanta?,you must learn yadda zaki dinga tarbata..." "Ai na iya" ta fada da sauri cikin subutar baki saboda yadda ya sake mannewa da jikinta,murmushi ya subuce masa ganin yadda ta amsa da gaggawa tun bai gama fadin abinda zai fada din ba,kallonshi take tana duban yadda yake murmushin,wani kyau taga yayi mata "Daina kallona" ya fada yana dan hade rai kaman bashi ba,itama sai ta sake hade rai,juyo da ita yayi suna fuskantar juna hannayenshi aka qugunta,a hankali tamkar mai rada ya soma zayyano mata dukkan yadda yakeso ta dinga masa idan suna tare,idan ba gab da su kake ba ba lallai kaji me yake gaya mata,wayyo Allah kamar qasa ta tsage ta shige haka ta ji,idanunshi a kanta yake maganarshi kanshi tsaye,ko kunyan duban idanunta baiji,wanne irin mutum ke shi da bai da kunya,zille zille ta soma yi saboda yadda maganar ta soma fin qarfin kwanyarta,muryarshi ratsata take,salon maganarshi daban ne,murya ce mai matuqar tsada da daraja a tarihin rayuwarta,sai yayi shiru ya tsaya cak yana dubanta tana mutsu mutsu "Haddacewa nake so kiyi,shi yasa nake gaya miki a yanayin da ba zaki manta ba" shiru tayi ta rasa abin cewa,karata yayi da jikinsa cikin qirjinsa "Tsaya anan idan kin gaji da tsaiwa ne naga qafafunki na rawa kici gaba da haddace abinda nake gaya miki" sake sauya salon muryarshi yayi yana ci gaba da gaya mata,wannan karon hatta da bugun zuciyarta sai da ya sauya,ta rintse idanuwanta tsigar jikinta na tashi,ya kwashe a qalla minti talatin kafin ya dan janyeta "Ina so na gani practically,zamu fara gwada wannan,shirya min ruwan wanka,zanje na dawo qarfe hudu zamu wuce abuja ki zama ready" dama neman gun kubuta take,da hanzari ta juya har qafafunta yana sarqewa har sai da yace "Kula" bata bi ta kanshi ba ta shige toilet din,gefan bathtube ta zauna tana sauke numfashi kamar tayi gudun famfalaqi saboda yadda bugun zuciyarta ya qara gudu,maganganunshi ke mata yawo ko ina cikin sassan jikinta,muryarsa mai mai dauke da wani amo na ratsata tamkar yanzun yake maganar,curewa tayi waje daya murmushi na subucewa a tattausan lebanta. *kuyi manage sabgogi sun sako kai,sai ranar lahadi idan Allah ya yarda* *gareku 'yan uwana al'ummar qasata,ka sani cewa quri'arka itace 'yancinka,kana da damar zaben duka mutumin daka ga dama,quri'arka zata iya zama sanadin jin dadi da walwalar al'ummar qasarka,hakanan zata iya zama silar shigarsu qunci,saidai kar ka manta da wannan,RANAR QIYAMA ZAKA TSAYA GABAN MAHALICCINKA KA BADA HUJJARKA NA DALILIN ZABAR MUTUMIN DAKA ZABA DIN,kada ka manta tsayawa gaban wanda ya halicceka babban lamari ne,mu tsaya mu zabi shugaba na gari,wanda zaton alkhairin da al'umma suke masa ya rinjayi na sharrin,MU ZABI CANCANTA BA JAM'IYYA BA,hakanne kadai zai sanya mu saka qwarya a gurbinta,kada mu yarda wasu su shiga rigar jam'iyya su cucemu,mu duba cancanta da dacewa,mu yiwa kamu alqalanci,kada mu jefa kanmu a fitina da musibar da bamusan ranar qarewarta ba,Allah kasa mu dace ka yi mana jagoranci kada ka barmu da iyawarmu* *muyi zabe lafiya cikin aminci da kiyayewar mahaliccinmu* *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [23/02, 11:52] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 8⃣6⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *Allah madaukakin sarki yana cewa* *haqiqa muminai 'yan uwan juna ne kuyi sulhu tsakanin 'yan uwanku* _____________________________________            Qarfe uku saura na rana suna zaune bayan motar driva na jansu,tattausan tafin hannunshi na cikin nata,yana zaune gab da ita sabanin daa da kowa ke zama tashi shiyyar,kunya ta sanya ta maida kanta bangareb window tana duban hanya cikin baqin glass din da motar take da shi,yatsunsa ya sanya ya juyo da fuskarta gareshi,ya dage gira daya "Ina son miki qari kan abinda na fadi miki dazu,zayyano min naji kin haddace?" Wata iriyar kunya ta kamata,ta yaya zata iya maimaita kalaman dazu masu nauyi da girma,kanta ta qwace daga hannunshi ta sake maida kanta ga window murmushi na son kubce mata,ganin haka ya sanyashi janyota jikinsa ya sanya hannu ya matseta "Maganinki zanyi,naga alama baki fara daukan lacture ko daya ba,yadda nake daban haka nakeson matata ta zama ta daban,you must be ready,qarin karatu guda daya,dole ki koyi zama a jikina,bazan lamunci zama a mabanbantan wurare ba ba,idan baki son haka ki daina zama waje daya da ni" ya fada yana shan mur,baki ta murguda wanda yayi nasaran hangota,cikin zuciyarta tana mita,wuta ce ta dauke mata sanda taji hannayenshi cikin rigarta,ta daga kai ta dubeshi tana narke fuska,idanunshi lumsassu ya zaro mata waje yana mata nuni data daina kallonshi,tilas ta sauke qwayar idanunta,tana ji tana gani haka ta haqura ya dinga yadda yaga dama da ita,sai da yaji tsaiwar motar sannan ya zare hannunshi da jikinshi,hannun nasa ya sanya ya gyara mata rigarta da yafen mayafinta,wanda atamfa ce a jikinta ta dora mayafinta saman ka,kanta na a qasa cike da jin nauyi har ya kammala,bata dago ba sai da taji yace "Oya,lets go".         Tayi zaton ganinta a airphort sai ta gansu cikin wani makeken guri wanda yaso yi mata zubi da gida,mutane ke kai kawo,kama daga qananun yara saffa saffa da kuma manya,yana fitowa wasu tarin ma'aikata suka qaraso wajem,cike da girmamawa suka tarbeshi,a mutunce yake gaisawa da su,sannan ya saka hannunshi cikin na sumayyan sanda suke masa rakiya zuwa cikin wani babban gini dake gabansu,ta daga kanta a hankali a naj taci karo da wani rubutu cikin manyan haruffa daga saman gidan wanda aka rubuta MUHAMMAD ALMUSTAPHA ORPHANS HOUSE,cikin ranta take rayawa gidan marayu dama gareshi.        Babban office aka bude wanda shine mallakinsa,office din nada girma qwarai,akwai kyau tsari da wadatar tsafta ko da yaushe,sun sani haka yake,ya saba kawo musu ziyarar ba zata,sai a gama waya da shi yau anjima ku ganshi cikin gidan,duka yana haka ne saboda ya tabbatar kowa ya riqe amanar aikin da aka bashi,saman doguwar kujerar cusion suka zauna shi da ita kafin su shiga gaisawa da wadanda ya dorawa nauyi da alhakin kula da gidan,cikin nutsuwa da sanin aiki kowa ke masa bayani kan nashi bangaren da yake riqewa,kusan mintina talatin kafin ya buqaci kewaya fadin gidan.        Hannunshi tsam cikin nata tafin hannunsu a hade,kunya duka ta kamata,baijin kunyar jama'ar da suke tare?,eanda ta lura wasu sai satar kallonsu suke,a hankali suja fara kewayawa bangaren makarantar yaran inda suke karatu,makaranta ce mai zaman kanta,nursery primary zuwa secondry duka cikin gidan suke,bangaren wajem wasannin yara daga cikinsu,gurin koyon sana'ar manya,da dan madaidaicin asiniti don duba lafiyarsu,duk inda suka zo wucewa suka ci karo da wasu idan manya ne sukan qaraso fuskarsu dauke da madaukakiyar fara'a,abinda zai baka mamaki yadda suke bashi hannu kai tsaye suyi musabaha cikin yanayi na sabo da jan mutum a jiki,idan mata ne sukan duqa cikin girmamawa su gaidashi su wuce suna murna,yara qananu maza da mata da gudu suke qarasowa wajensa,yakan daga su ya sumbacesu,ko ya shafa kansu idan sunyi girman da zaya dagasu,idan yaga wani cikin yanayin da bai masa zai tambayi ba'asi ko dalilin barinsa haka?,bare ma da wuya kaga wani cikinsu cikin mummunan kama,kowa neat yake cikin tsafta da tufafi mai kyau,tun tana satar kallonshi ta gefan idanu har ta koma ta gaban idanuwa,karon farko da taji ya burgeta a rayuwa,wanne irin mutum ne shi mai tausayi haka,sauqin kai jin qai da son yara?,yadda yake mu'amalantarsu abun yayi masifar burgeta,ko banza tana da maraya,tasan ciwon rashin uba,bare wadaj nan da ba'a rasa yaran da ake kira shegu a cikinsu,wanda basu da kowaba duniya,an yardasu tun suna da qananun shekafunsu,basuji ba basu gani ba,ba'a barsu da tabin da aka haifar musu ba na rashin fitowa ta hanyar data dace ba,sai da aka sake cika rayuwarsu da tabo da quncin rashin sakin waye uwa uba kuna dangi a garesu,ba shakka yayi wani abu mai girma arayuwarsa wanda koda shi daya yayi a duniya ya cimma nasara,ma'aiki S A W yana cewa 'nida mai kula da maraya kamar haka muke a aljanna(sai ya kwantanta da yatsansa dan manuni dana tsakiya)' me yafi wannan alkhairi na zama maqoci a aljanna wajen fiyayyen halitta?,ba sai kayi da yawa ba,ko guda daya ka kula da shi kana da wannan garabasar bare kuma kayi serving rayuwar daruruwa,koda baka jin rahama da tausayi cikin zuciyarka kana jinta kamar a qesashe ka dimanci shafa kan maraya kamar yadda ma'aiki ya umarci wani sahabi,Allah ka bamu iko ka bawa masu ikon da qargin cikinmu ikon taimakawa marayan.          Sannu a hankali suka ci gaba da takowa,dubanta yayi kana ua dauke kai yana jawota zuwa jikinsa sosai,kunya kamar qasa ta tsage ta shige,kasa daurewa tayi "Ammm,akwai mutane fa da suke tare da mu" "Shshshs,na fiki sani ai ko?,ko wani abu na daban na aikata bayan haka,it seems kin soma gajiya da tafiyar" ya qarasa fada yana tarota sosai,shiru tayi don ta fuskanci ci gaba da bayanin bashi da wani amfani,har zuwa sanda suka qarasa dakin kwanan yaran,don baya shiga sashen 'yammatan,yana baiwa masu kula da su mata ne su dama tambayi matsalarsu,a nan auka ci karo da wata yarinya wadda ta nufoshi da gudu,durqusawa yayi ya dauketa yana sakin murmushi,yana tausayin yaran,yana jinsu a jikinsa,ba shakka rayuwarsu akwai ban tausayi,ka tashi bakasan hatta wadanda sukayi silar kawoka duniya ba,me yafi wannan ciwo?,yana dauke da ita suka ci gaba da takawa wanda ya sanya sakin sumayya daga jikinsa,sam taqi yarda ya sauketa,yarinyar akwai surutu da wayo,tambaya take masa kan me yasa ya dade bai dawo ba?,ko da ya amsa mata sai kuma ta waiwayo ga sumayya tana tambayar wacece wannan,waiwayowa yayi ya kalli sumayya "Sai ki bata amsa" ya fada yana tsareta da ido,murmushi ta saki wanda ya bayyana fararen haqoranta tana duban yarinyar,maqe kafada tayi "A'ah uncle kai zaka fada min" gira ya dage murmushi na subuce masa yana duban yarinyar wadda shi ya sanya mata suna randa aka tsintota ya sanya mata amatullah "Matata ce abokiyar rayuwata,qawata kuma qanwata" ya qarashe fada idanunsa na kan sumayyan,wani abu ne ya tsirga mata daga kai har tafin qafa,janye idanunta tayi tana maimaita kalamanshi "Mata ta masoyiya?,yaushe na zama masoyiyarsa?" Waiwayawa yayi ya miqawa daya daga cikin masu kula da yaran amatullah sanda suka isa bakin office dinsa yana fadin su jirashi yanzu zai fito madam ta gaji zata huta.        Shike gaba tana bayanshi,suna qarasa shiga ya waiwayo da hanzari cikin shammata ya hadeta da qofan office din da faffadan qirjinsa,yayin da ya sanya hannunsa ta bayanta yana murzawa qofar muqulli,qugunta ya kama ya riqe da hannu daya,yayin da ya dafe qofar da daya hannun,hucin numfashinsa na sauka saman fuskarta,ya cika mata idanu ya mata wani mugun kwarjini "Uhumm.....baki yarda bane da nace kedin matata ce kuma masoyiyata?" Ya tambayeta kanshu tsaye,jin tayi shiru yasa ya dora "If kina doubting kiyi magana" ya sake fada yana dage mata girarshi,qarar wayarshi ya ceceta daga kallon da yake mata,ya dan ka baya yana amsa kiran wanda daga driva ne yake tuna mishi kada su makara har jirgi ya tashi "Ok" kawai ya fada ya ja da baya,saman teburin ya nufa ya dudduba wasu takardu sannan ya nufi qofa wanda tana tsaye nan tana qoqarin didaita numfashinta,hannunta ya sanya cikin nata kaman yadda suka shigo suka fice bayan ya bar key din jikin qofar yasan akwai mai kullewa,a nan ya samu ma'aikatan,ya yabawa kowa yadda zasuji qwarin gwiwar ci gaba da kula da ayyukansu,sannan ya umarci dalhatu wanda shine shugaba baki daya daya turo mishi bayanan dukkan wata matsala damuwa ko buqatar da suke da shi ta emil dinsa,idan da hali a dauki masa vidiom duk wani mai matsala ko wata buqata koda a rubuce idan zasu iya a masa sending,zai samu lokaci ya duba a nutse in sha Allah,ya bude 'yar jakar dake hannunshi ya musu rabon kudi bawai don ya gaza albashinsu bane,wannan sabonshi ne haka yake duk sanda yazo,wanda wannan na daya daga cikin abinda yasa suke son yazo din da kansa,ya sake jadadda musu muhimmanci amana sannan suka fara tako masa don yi masa rakiya.        Gab da zai shiga motar tashi ya hangosu su uku,matasan yammata ne wanda zasu doshi shekara sha shida shida riqe da wata a tsakiyarsu tana dingisawa,sai da suka matso sosai ya kula da jini dake diga a qafarta,cikin tashin hankali ya kirasu suka yo wajensa,benci ya sanya aka dauko suka dorata akai,duk sun rude suna tambayar meta taka suka ce kwalba ce,hankalinshi tashe ya tsugunna da kanshi sanda suke yunqurin aje masa kujera ya dakatar da su,cikin rudewa yake yunqurin kama qafar ya duba inda ta shiga din caraf yaji an riqe qafan,sumayya ce,kusa da shi ta tsugunna ba tare data dubeshi ba,yayin da shi kuma ya biya da kallo yana janye nashi hannun,hakanan kawai taji wani abu ya soketa sanda ya tsugunna gabanta yana qoqarin kama qafar,batasan ta kai wajen ba,daga qafar tayi ta hasko mishi wajen tana duban 'yar budurwar "Kina budurwa me ya kaiki yawo ba takalmi har ki taka kwalba haka?" Ta tambayeta "Takalmin nake duba inda na ajjiyeshi ban kula ba she kwalbar na gaba na sai na taka" kai ya daga ya basu umarnin shiga clinic ya gaya musu abinda zasu dauko masa,cikin sakanni suka dawo,ya dauki wani daj qarfe da zai zaqulo kwalbar ya tunkari qafar,da sauri ta sanya hannu zata karba,sai ya sakar mata yana dubanta cikin mamaki,shi ya dinga nuna mata yadda zatayi har ta gama tayi mata dressing,tana cire safar hannun nata bayan ta gama qasa qasa yake dubanta,yana mamakin yadda tayi aikin perfectly,tayi kicin kicin da fuska,baisan me yasa ta hanashi yin aikin ba. Suna zaune cikin mota murmushi ya subuce masa sanda wani tunani ya fado masa,kai ya kada yana cije lebansa na qasa,ya miqa hannunshi ya damqo nata hannun dake ajjiye saman cinyarta,waiwayowa tayi tana dubanshi,ido daya ya kashe mata,murya can qasa wanda sai ka mugun kasa kunne zaka iya jiyo me yake cewa "Kada ki yarda ki soma kishina tun yanzu" fuska a hade ya fada,cikin mamaki take dubanshi,sai ta samu kanta da tabe baki "Na meye zanyi kishinka?" "Saboda na lura kin fada tarkon sona,ko kina jayayya"mamaki ya sake kamata,yaushe hakan ta faru da zai fadi haka,cikin dakiya tace " qwarai kuwa"da qarfi ya janyota ta sake matsowa kusa da shi,idanuwansu cikin na juna yana dubanta kamar zai cinyeta danya,daga idanuwanta zuwa jajayen labbanta da suka sha jambaki,ji yake kamar ya cinyesu "Me yasa kika hanani ta qafarta?" "Wa kenan?" Ta ambata cikin dakiya,duk da yadda takeson janye idanunta saboda yadda kallon ke aika saqo har cikin qwaqwalwarta,murmushin gefan baki ya saki,he love her style har cikin zuciyarshi hakan ke burgeshi "Kin qware wajen pretending,uumm?" Ya sake fada yana jifanta da wani salon kallo,so take ta janye idanunta amma ta kasa,har sai da ya samu nasarar jefa kasala da mutuwar jiki tattare da ita "Idan haka ne,kada ki sake hanani aikina ko ma akan waye" ya fadi yana sakinta "Dama ba hanaka nayi ba,taimakonka kawai nayi" ta amsa tana gyara zamanta "Really?,dis is d begining of love,taimako and tausayi,alright?"ya fadi yana daga kafadunsa cikin i dont care manner,shiru tayi maganarsa na mata kaikawo,bata son ya sake kasheta da wannan mayun idanun nashi hakan ya sanya batayi musu shi ba. Karo na biyu ta sake shigowa garin abuja a matsayinta na matar almustapha suruka ga baba prof,sai ta tsinci kanta cikin tsantsar kunya da nauyin ahalin gidan,sanda suka isa alamu na nuna gidan ya soma karbar baki kamar yadda hakan ya zama al'adar gidan duk yayin da wani sha'ani ya tashi,kai tsaye bangaren ummee ta nufacu zuwa,saidai ya sanya hannunshi ya riqe nata hannun ya sauya akalarta zuwa nasu bangaren "me kika yimin sa zaki nufi wani gun,idan na kammala duka abinda zanyi kina iya zuwa but not now" shiru ta masa tana jin yadda idanuwa sukayi yawa akansu,akwai 'yammata zaune harabar gidan suna sheqar iskar almuru wanda ke busowa kasancewar an kusa sallar magariba,hakanan garin yana dan hade da hadari mai bada iska,sai yanayin ya dinga haifar da wani yanayi cikin zuciyarta,sai ta samu kanta da lafewa a jikinsa har suka shige bangarensu,sai da suka bacewa idanuwansu sannan suka dauke kansh daga wajen,daya daga cikin 'yammatan ta doka hannunta saman tebur "Kan bala'i,wai ya akayi haka ne ta faru?,wacce iriyar rashin sa'a garemu da aka gaza samun ko daya daga cikinmu ta shiga rayuwar man din can?" "Rashin sa'a babba ma kuwa,sai nake ganin fuskar yarinyar ma kamar na santa fa"dariya dayar ta saki "haba sakina,bakiga yanayinta ba,ba lallai bafa ma a qasar nan ta tashi ba itama,kinsan man din nan yake da bala'in aji da daukar kai,dukanmu munsan ra'ayinshi da aqidarsa irin macen da yake buri,da alama kuma ya samu,don wallahi wannan sai taci uban su'ad a komai da komai"da sauri wadda da alama duka abun yafi tsumata tace "Yes,gaskiyanki shuhuda,u know what?,ina ganin ma fa soyayyar da yake mata akwai banbanci,i never ever seeing him rungume da su'ad,but ku dubu wannan fa,tana jikinsa,dan gararin idanunshi a wanke,na tabbata ya ganmu but ko a jikinsa,kai i love this man wallahi naso ace ni na samu wannan sa'ar,dole eesha ta shiga wani hali" ta fada abun na tsumata,ci gaba sukayi da tattaunawa kowa na fadin albarkacin bakinsa,'yammata ne dabkowacce ke jin ta burunqasa,kowacce tana burin zamantowa suruka cikin gidan,wadda dukkansu sun kwana da sanin cewa a gurinsu babbar sa'a ce ka zama wani ahali na jini cikin gidan,ko yaya sha'ani yake na gidan basa wasa da shi,mutane ne masu son budawa da kuma babbar harka,idan kuwa suka iso gidan suna samun dukkanin yadda suke so,duk da kowaccensu mahaifinta ba baya bane shima,saidai hausawa sunce baba ma da babansa,kafi wani wani ya fika,haka Allah ya qaddari rayuwarmu,yadda da hakan kadai shi zai sama maka rayuwa mai cike da wadatar zucci,da kuma cikakkiyar godiya ga Allah bisa dukkan wani bigire da ya azaka,Allah kasa mu dace,ka bamu wadatar zuci wadda itace babbar wadata itace babban arziqin duniya. Sannu a hankali suke takowa zuwa bangaren ummi,jifa jifa suna wuce mutane da suka yo sammakon zuwa bikin tun farkon satin,sanye take da abaya baqa mai zubin dinkin buba,ta yane kanta da mayafin rigar,yayin da yake sanye da qananun kaya shirt da trouser baki daya shima baqaqe,zo kaga wani kyau da sukayi,musamman da yake riqe da hannunta saboda yadda ya lura akwai yawaitar 'yan sanya idanu,takanji wani nauyi duk sanda ta tuna yadda ya ritsata awa daya da suka shude a toilet daure da towel tana shirin yin wanka,yana jaddada mata wajibcin yin wankansu tare fuska daure,saidai baki daya yanayin da ya ganta ya sakar masa da jiki,ya zuba masa kasala da wani irin feeling a jikinsa,yayin data yayibi wani towel din ta rufe kanta hakan ya tunzurashi ya dinga takowa inda take har ya qureta a bango "Yau zaki san kinyi kuskure,me kike boyemin" ya ambata yana dauke towel din dake kanta,gashinta ya bazu zuwa kafadarta,abinda ke sake burgeshi da tafiya da shi kenan,baya ta sake ja taha qoqarin boyewa cikin jacuzzi,cikin sa'a ya samu nasarar danqo ta,idanunta suka fito ganin yana niyyar sanyata cikin bathtube,tsoron dama yake son gani cikin idanunta,wani abu daban take koma masa mai kyau,bai bari ba kuwa sai daya sanyata sannan ya soma rage kayan jikinsa "Saiki jira na gama nawa wakan sannan kiyi naki tunda baki son muyi tare sannan kuma cikin toilet dina kike ba naki ba" "Amma ka bari na fita idan ka gama na dawo" "Is too late" ya fada ko a jikinsa yana tubewa abinsa,idanuwanta ta runtse sanda yake qoqarin cire bixer din da shi kadai ya rage,sai qyarma take,bata taba ganin jiki mai lullube da siffar qarfi haka muraran a gabanta ba,gargasar jikinsa kawai abar kallo ce,karon farko data soma ganinsa a hakan,ko a jikinsa ya kammala wankansa tas sannan ya nade jikinsa da towel ya fice. Dawowa tayi daga duniyar data tafi sanda taji yana matsa hannunta,tuni sun iso qofar falon ummeen ita yake jira ta cire takalmanta,a nutse ta zaresu sannan suka sanya kai ciki,shi yayi sallama yayin da suka jiyo muryar ummee tana amsawa,kunya da nauyi suka cika sumayyan,kamar ta koma bayanshi ta boye haka ta dinga ji,tana qoqarin zame hannunta dake cikin nashi amma yaqi bata dama,saima rada daya soma yi mata "I want to show them i care with amanar da suka bani,nasan haka ne so ya kamata suma su gani,sai suyi alqalancin waye ya kasa kula da tashi amanar ko?" Sunne kai tayi ganin idanun ummee na kansu,fuskarta dauke da murmushi da kuma mamaki,don ta taji yara na fadin zuwan nashi bata yarda ba,don an riga da an saba,yawanci sai ana ya gobe daurin aure yake zuwa,wani lokaci ma sai ran daurin auren,awa daya kafin a daura ko minti talatin,musamman idan na yaran 'yan uwa ne,suma sai na kusa saboda tsabar busy,amma yau sai gashi kwanaki shida saura a daura auren,wannan wane irin gagarumin canji ne haka ke tunkarar rayuwar yaron nata,bata gushe ba tana musu barka da isowa fuskarta tamkar gonar auduga,yayin da eesha dake gefe bata daga kai ba tana danne dannen waya har sai da taji muryarshi,karaf idanunta suka fada kansu,zumbur ta miqe tsaye tana rarraba idanu,kada dai ace ta fara samun matsalar idanuwa,wannan yarinyar ya aura?,ko daga bacci ta tashi duk sauyawar da taji da samun cikakkem hutu dake kwance a jikinta ba zata manta ta ba,haka kawai yarinyar ta tsaye mata a rai "Mutanen UAE" haka ummin ke fada wanda wannan kawai ya isheta amsa,sai ta hau girgiza kai ta shige dakin da ta sauka da gudu,sai sannan hankalin ummen ya kai kai,takun gudunta yaja hankalin almustapha da ya kai sumayya har gaban ummee,kunyarta ta sake burgeshi karo na biyu musamman sanda ta zame daga samn kujera zuwa qasa gaban ummeen,abinda bai taba gani kenan ba wajen su'ad,yana zama kujerar dake daura da ummin yace "Waccar fa?,sunzi zasu fara haukar nasu kenan ko?" "Kai kuma kazo zaka fara kenan ba" "A'a ummi ni ban da case da kowa,just su kiyaye rules din da na sawa zuwansu gidan nan" "Allah fa ya kawo mu,amiran umman khalipha ya fama da wannan" ta fada tana duban sumayya,alamun qarfi taba ga mai qiba,daga yanayin fuskar almustapha kawai ya isa ya sanar mata akwai gagarumin sauyi daya fara nasar rayuwarsa,yanayinsa baki daya akwai sauyi koda shi din bai san ko ya lura da hakan ba,kunya ta sake kamata tayi qas da kai tana gaidata,ta amsa cike da kulawa da farinciki,shima tashi gaisuwar ya dora ta amsa cikin jin dadi tana tambayarsu ya suka baro dubai "Sai kuma gaku tun yau?" Ta tambaya cikin mamaki,satar kallonta yayi wanda ummin ta kula da haka "Eh ummi,akwai wani aiki da nakeson yi,shi ya taso ni dole,tunda naga yayi daidai da date din daurin auren" ta fahimci salon magana ce kawai ta qwatar kai,tunda da aiki ne da tuni ya shaidawa baba,amma ko baban baisan da zuwanshi ba.           *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [23/02, 11:52] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 8⃣7⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *SANARWA DA BABBAR MURYA* *BA NUFIN MU CIN ZARAFIN WANI KO BATAWA WANI BA,SABODA GUDUN RUBUTA MUNANAN AYYUKA CIKIN LITTAFIN AYYUKANMU,WANDA SAI MUN TSAYA GABAN UBANGIJI MUNYI BAYANI RANAR GOBE QIYAMA,AMMA TURA TA KAI BANGO,AN FARA SHIGA SHINGENMU ANA MANA BARNA,BAYAN MUN KAME KANMU DAGA DUKKAN WANI ABU DA ZAI ZAMA SHIGA HURUMUN WANI BATANCI KO CIN ZARAFI A GAREMU* *GAREKU MASU SATAR FASAHA ZANCE KO BARAYIN ZAUNE* *Ina mai shaidawa duk wani mahaluki da yasan cewa yaci da gumi na,ya dauki wani littafi nawa da na zauna na bata lokacina na rubutashi da hannu na don al'ummar ma'aiki su amfana,MALLAKINA ya kaishi wane waje ya saida yana zuba kudin a aljihunsa cewa NI SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA BAN YAFE BA,BAN YAFE BA,BAN YAFE BA,KUMA INA ROQON ALLAH YAYI MIN SAKAYYA KAYANA DA AKA DAUKA ANA SAIDAWA* *GAREKA KO GAREKI BARAUNIYA A OKADA,DUK WANDA YA SANSHI KO YA SANTA YA ISAR MASA/TA* *ABADAN DAYA SATA KOTA SATA,AKA KAISHI OKADA ANA SAIDAWA AKAN KUDI NAIRA DARI BIYU,NACE ALLAH YA ISA BAN YAFE BA,INA ROQON ALLAH KUMA YA FITAR MIN HAQQI NA MATUQAR BANI NA ZALUNCESU BA SU SUKA ZALUNCENI,TUNDA BAN TABA DAUKAR HAQQIN WANI MALLAKIN WANI NA MAIDA SHI MALLAKINA BA,ALLAH YA BIMIN HAQQINA,INA FATAR ZAKU SADAR DA WANNAN SAQO ZUWA GARESU* *SANNAN WANNAN LITTAFI DA NAKE RUBUTAWA DAMA SAURAN LITTATTAFAINA,MALLAKINA NE,NA YISHI NE KYAUTA BA NA SAIDAWA BA,A DUK SANDA NAKE DA BUQATAR SAIDAWA ZAN SIYAR DIN,AMMA BAN BAIWA KOWA IZINI YA SIYAR MIN BA,WANDA KUMA YAYI HAKAN NA BARSHI DA FITOWAR RANA DA FADUWARTA,NA BARSHI DA MAI SAMA,MUGA ALFANUN DA ZAI SAMU CIKIN KUDIN DA KA SAMU TA HANYAR SAIDA ABUN SATA* *WALLAHI WALLAHI ALLAH MU GUJI CIN HAQQIN WANI,BILLAHILLAZAI LA ILAHA ILLA HUWA DUK WANDA KA GANSHI RAN QIYAMA YA QETARE TO BABU HAQQIN WANI A KANSHI,WANNAN ALQAWARI NE NA UBANGIJI,SAI YA FITARWA DA DUK WANI BAWA HAQQINSA KAN DAN UWANSA,KODA DABBA CE TA ZALUNCI 'YAR UWARTA DABBA* *ALLAH KASA MU DACE* _____________________________________         ta fahimci salon magana ce kawai ta qwatar kai,tunda da aiki ne da tuni ya shaidawa baba,amma ko baban baisan da zuwanshi ba,koma meye tana maraba kuma tana fatan alkhairi da samun wannan kyakkyawan canjin,sai ta saki murmushi "Masha Allah" ta fada tana maida dubanta ga sumayya "Me zaku ci,ko zaki shiga kitchen ki sama muku ko snacks ne,yau duka ma'aikatan na can baya suna aikace aikace suma" "Am ok ummee" almustapha ya fadi,farinciki ya mamayetq,ta tabbata tunda ya fadi hakan hakanne,sai ta waiwaya ta dubi sumayya "To kefa amira?" "Nima ummee na......" "Qarya take,ba abinda naga taci tunda muka taho" almustapha ya katseta yana tsareta da ido,murmushi ya subucewa ummee,salon da bata taba gani wajen almustaphan ba yau sai gashi da shi "Maza shiga ki samu wani abu kici,halan shi kin sama masa wani abun yaci ke baki ci komai ha ko?" Cikin kunya tana murmushi ta miqe kanta a qasa tayi kitchen din,yayin da ya bita da kallo yana yabawa salon kunyarta,yanayin yadda take ganin girma da darajar mahaifansa,tunanin yadda cikin qan qanin lokaci kan ya gama shiryawa ta hada misi wani hadadden patatoe salad ya fado masa,ya jima baici hadin salad da ya masa dadi irin wannan na,murmushi ua dan qwace masa,yanayim takun ta na burgeshi,ya dauke kai sanda ta kai ga shigewa kitchen din,sai suka hada ido da ummee,shi yai qasa da kai kunya na lullubeshi,ita kuma ta dauke kai tana sakin murmushin tsantsar farinciki,waskewa yayi da cewa "Ummee ya adam bai qaraso bane?" "Ka fadi haka mana tunda wannan karon ka rigashi zuwa,ina zaton sai wajen laraba zai qaraso,amma dai ni'ima ya hadato da yaran sunyo gaba,dazun da safe suka sauka,shi da fahariyya sai ran laraban"kai ya gyada cikin gamsuwa "Kunje kun gaida maamaan ne?" "A'ah" "To bari ta fito sai kuje ku gaisa,da alama itama batasan da zuwan naka ba,babanku kam baya gari,ya tafi jigawa ta'aziyyar wani abokinsu da ya rasu,amma gobe ma zaya dawo" ta fadi tana daga wayarta dake ringing wanda amira ce ke kiranta,bayan sun gaisa take shaida mata zuwansu sumayyan,ihu ta saki har almustapha dake zaune yana jiyota,hararar wayar yake kaman amiran ma wajen,magiya ta dinga kan ummee ta bata sumayyan ta kira wayanta a kashe,dai dai sanda sumayyan ke fitowa daga kitchen din,ummi ta miqa mata wayar,a ladabce ta amsa ta koma gefe tana fidda murmushi,addu'a kawai take kada amiran ta baro zance ta bata kunya,ai kuwa zuba ta hau yi "Amma namecy kinci amanar qauna da baki gayan har kin iso abuja ba,halan soyayya ta fara zaqi har kin soma mancewa da kowa sai wannan miskilin mijin naki,ina fatan kina bada wuta wajen sukurkuta masa shi muga ta tsiya,tab ai wallahi jibi nima zan taho Allah,ina fata kin samo mana tsaraban baby,wallahi har so nake naga babynku,kyau tako ina,wazai dauko uwa ko uba?,wa yaga ya man ya baby" gaba daya kunya ta cika sumayyan,yadda almustapha kadai ya kafeta da ido tasan yanajin komai amiran ke fada,ta sanshi sarai da kaifin ji,yunqurin datse kiran take sai ya miqa mata hannu,a hankali ta tako ta miqa masa wayar,ya kara akunnensa sanda amiran ke cewa "Wayyo soyayyya zamu sha kallo......" "Gidanku mara kunya fitsararra,idan naga qafarki gidan nan jibi sai na karyata na zubar,idan kin musa kuma bismillah" ya datse kiran,daga bangaren amira sai ta kwabe fuska zata sanya kuka,saifullah dake zqune gefanta ya dunga tiqa dariya har da qwarewa da lemon da yake sh,haushi ya sanyata daukan filo ta dinga maka mishi shi kuwa yana fadin "Maganin aku kuturu mai shegen zance kenan,tun dazun nake kwabarki kiyi a hankali may be suna tare amma kika qi ji,tunda kuwa ya man ya fadi haka ke da zuwa gida sai ana gobe daurin aure"kuka kuwa ta sanya taba buga qafa "wallahi wallahi ban yarda ba,don kawai kaji ya almustapha ya fada ko?"sai ta saki filon ta wuce bedroom alamaun taji haushi ya miqe da sauri ya bita domin yayi lallashi.         Boye dariya ummin ta shiga yi tana basarwa,don itama taji wani abun,sauka yayi daga bangaren kira ya shiga wajen adana lambobi,da dai dai ya dinga bi har ya iso wajen lambar da ya tabbata tata ce saboda ga hotonta nan saman lambar,ya dauki wayar shi ya kwashe lambobin ya adana a tashi wayar,ganin yadda kunya ta rufe sumayyan yasa tace "kuje ku gaida maamaa,daga nan ku wuce sashenku sai da safe ma hadu" "To" ya fada yana sauke qafarshi wanda ya dora daya kan daya ya miqe ya isa gefan ummin ya ajjiye mata wayarta "Sai da safe ummee" suka hada baki wajen fada sai da ya waiwayo ya dubeta,dauke kanta tayi ummen ta amsa "Sai da safe,Allah ya bamu alkhairi".        Kusan bangaren anty maamaa wannan karon yafi jama'a,hakan baya rasa nasaba da kasancewar ita keda bikin wannan karon,auren yara biyu tak duka maza da Allah ya bata,baki ta kama itama "almustapha?,tun yanzu?"murmushi kawai ya saki yana fatan kada ta sake cewa wani abu saboda 'yammatan dake falon,bai ko zauna ba hannunshi zube a aljihun wandonshi ya soma gaidata,ta amsa cikin farinciki itama,don ta tabbata lallai hasashen baban ya soma zama gaskiya,tunda ga mustpha ya waiwayi gida ana daurin auren qannenshi saura kwana shida,sumayya kam tuni tana wajen humaida,wadda sukayi farinciki ganin juna,ya waiwaya bayan sun gaisa,ganinta wajensu ya sanya ya basar ya juya ya fice,cikin sakewa suka gaisa da anty maman tana dan tsokanar sumayyan kafin ta miqe ta fice ta basu wuri,ta sake sosai cikinsu humaidan aka dinga hira,abinka da mata gwanayen gulma,kusan kowa kallon sumayyan yake,kowa da irin gulmar dake cinsa arai,yayin da dama daga cikinsu ke jin dama sune sumayyar,a qalla sai gashi sun kwashe wajen awa daya suna shan hirarsu,don humaida har kiran amira tayi ta saka handsfree aka dan taba da ita,hakan ya sake tsokalota taji kamar tayi tsuntsuwa ta taho.        Tun da ya shigo yaje duba agogo yana kasa kunne amma yaji shiru,har ya kammala shirin kwanciya cikin wasu hadaddun pyjamas masu shegen kyau da suka haska shi,yana son ya daure ya basar amma sai zuciyarsa ta gaza,a hankali ya sauko ya soma takawa ya sauka qasan benen,ya bude dakunan baccinta bai ga alamun ta shigo ba,ya koma sama ya bude dakin baccinta dake sama nan ma babu alamun an shiga,dakinshi ya koma ya zauna gefan gado yana son samin meke sanyashi damuwa haka da lamuranta?,laluba lambarta fake cikin wayrsa wadda yayi servinn dazu yayi sannan ya shiga bangaren aikawa da saqonni ya tura mata gajeran tex "Come back", suna tsaka da hiransu saqon ya shigo,sai abun ya daure mata kai kasancewar bata da lambarsa,daga bisani ta ajjiye wayar tana zaton batan kai saqon yayi ba wayarta zai shigo ba,mintina goma suka shude shiru,ya sake lalubo lambar ya kira,bugu kusan uku sannan ta daga ta kara kunnenta,yana iya jiyo hayaniyar su ta cikin wayar,haka kawai tasha jinin jikinta duk da batasaj number din ba "Assalamu alaikum" ta furta a nutse,har cikin zuciyarsa sallamar ta ratsashi,cikin zuciyarshi ya amsa a fili kuma yace "Bance ki dawo gida ba?" Ta fahimci muryar sarai amma sai tace "Waye ke magana?" "Ok,baki gane ba kenan?" "Eh" ta fada tana sani "Well" ya ambata shima yana katse wayar,sai ta ajjiye wayar yana qoqarin saukowa daga saman gadon.        Anty maamaa ce ta sauko daga sama tana duban sumayya "Lalala amiran umman khalipha?,me kike har yanzu baki wuce gida ba?,ya zaki baroshi shi kadai waya gaya miki ana wannan sakacin,tashi ki wuce tun bai biyo sawunki ba wallahi" ta fadi don tasan halin mustaphan sarai,murmushi ta saki yayim da su humaida suka sanya dariya,humaida tace "Allah sarki mu da yake warin takalmi muke mu kwana muna hira ma ko anty" "Yo wa ya damu da ku?", ta fada tana juyawa sama tare da yiwa sumayya sallama,dif dariyansu ta katse baki daya,kowa ya kama kanshi,hakan ya sanyata dagowa,sai ta ganshi tsaye cikin kayan bacci,takowa ya dinga yi a nutse har inda take sandare a atsaye,yasa hannu ya zare wayarta dake hannunta ya dauke cak,baki daya 'yammatan sukayi mutuwar zaune na wucin gadi har ita sumayyan,ko a jikinsa ya juya dauke da ita ya fice daga falon.        Kallon kallo aka soma yi tsakaninsu,humaida ce ta soma tuntsirewa da dariya,abun ya matuqar burgeta,kamar a fina finan india " to wallahi tunda guy din nan ya soma haka mu rufawa kanmu a siri mu dinga kora masa matarsa da wuri,idan ba haka ba wataran sai munga abinda idanuwanmu ba zasu iya dauka ba" "Wai shi dan air ba" inji wata daga cikinsu,wadda a zahirin gaskiya hassada take ji cikin zuciyarta,don itama taso ace ta zama daya daga cikin matanshi "Ba wani dan air wallahi,har ga Allah abinda ya sanya nakesom auran irin mazan nan,nuna so babu limit ko a gaban waye wallahi,wani miskilin namijin bai iya nuna miki qauna ba,idanunshi basa gani balle suji kunyar kowa" dariya suka sanya suka ci gaba da tattaunawa kowa na fadar albarkacin bakinshi.          Bai direta ba sai da ya saita mata hanyar matattakala,ya harde hannunshi yana mata nuni da idanu kan ta hau,babu musu ta haura saman kunyar abinda ya mata cikin jama'a na kama ta har cikin dakinshi,qofa ya maida ya kulle ya waiwayo cikin shammata ya turata saman gadon,baki daya ya danneta,ya dora mata nauyinshi,fuskarsa kawai ya dago yana dubanta,idanunshi cikin nata suna musayar numfashi,sosai ta gane kuranta,numfashinta ya soma mata nauyi "Qirjina ka daga ni" "Eh ai so nake na nuna miki banbancin,don na lura kin soma rainani saboda kinga makwancina.....me kike gayawa amira take rawan qafan zuwa ta sameki?,sannan me kike gayawa wadan can shashashan suke babbaka dariya kaman hauka sabon kamu?" Narai narai tayi da idanuwa,yatsansa ya dora saman lebansa yana fadin "Shshshshsh,banson wani kuka,idan kuwa kika sake kikayi yau tilldown zanyi sai an miki ruwan zafi"cikin taushin murya a shagwabe da son qwatar kanta tace "Allah babu komai ka yarda dani"sosai ta masa kyau,shagabarta ta taba zuciyarsa qwarai,murmushi na son qwace masa amma ya dake,bai son ta gwada abinda su'ad taso dauka dabi'ar yi,wato kwarzantashi da yabonshi da fadan qwarewarshi a kan shimfidarsu gurin qawayenta,randa kunnensa ya ji masa Allah ya sanya ranar ta soma,mutum biyu ta gayawa,ranar taga tashin hankalin da bata taba gani ba,don cewa yayi tunda ta gaya musu to ta sa a ranta sai ya auresu babu fashi,har ciwo sai da yaso kamata,babu shiri ta fatattakesu sukayi baran baran bata sake ganinsu ba,da qyar ta sha kanshi "ta yaya zan yarda da ke?" "Saboda da gaske nake,ba aninda zan gaya musu,nasan fa haramunne mace ta dinga fadin sirrin mijinta,Allah ya la'anci mai aikata hakan"murmushin da baiso dole ya kubce masa,sai ya samu kansa da sanya hannunshi kan hancinta yana jan hancin "au Allah,ashe ni din mijinki ne" kunya ta kamata,ta rasa inda zata tsomala ranta,sai kawai ya rintse idanuwanta "Kada fa ki tsammaci na haqura,dole ki bani wani abu da zai sanyani na haquran,idan ba haka ba,Allah yau sai jikinki ya gaya miki" ya fada yana shan qamshi,da sauri ta bude idanunta,kamar zata saka kuka "To ni mai zan baka?,banda abinda zan baka" "Akwai" ya fada yana jifanta da wani kallo wanda shi kansa baisan yana mata shi ba,sosai take amsar saqon da yake aikata mata,sai ta kasa janyewa daga kallonshi tamkar masu kallon quda,nuni yayi mata da bakinshi yana cewa "Kiss me,shine kadai zai sanya na haqura" da sauri ta dago kanta da niyyar yi masa din don ya barta,nauyinsa da kunyarsa take ji amma shi baya gani ne wai,tana dora bakin nata ya hade su waje guda ya shiga sarrafa shi yadda yake so,bashi ya barta ba sai da ya tsotsi lips dinta son ranshi,da gudu ta fada toilet,tana iya jiyoshi cikin rarraunan murya mai taushi yana cewa "Be carefull,ke da su yanzu akwai banbanci"mamakinsa take,wai almustapha ne haka?,dama haka yake?,tayi maganar a zuciyarta tana tsaye gaban mudubi tana duban kanta murmushi ya qwace mata,wanka ta sake yi saboda kwanciya sannan ta daura alwala ta fito.        Gaban drawer ta ganshi tsaye ya zuge jakarshi,jikinta ta shafe da turaruka bayan ta shafa mai wanda ya qarawa fatarta laushi,ta taka a hankali ta isa inda abun sallah yake ta shinfida zata yi shafa'i da wutiri,har ta idar yana tsaye kaman mai nazari,qaramin tsaki ya saki ya koma gefan gadon ya zauna ta daga kai tana son dubanshi,wai meke sauyashi haka ne?,dazu da zata shiga toilet murmushi ne kwance saman fuskarshi amma yanzu ba haka bane,can qasa taji yace "Gobe adam zaizo zamu wuce jigawa wajen baba,i think sai wajen alhamis zamu dawo tare da shi" "Allah ya nuna mana" ta fada tana miqewa ta fahimci kayan sawarshi yake son hadawa ya kasa,hakan ya sanya ta qarasa bakin cupboard din ta soka zaqulo kayan daya bayan daya,sai ya bita da kallo,yana son yaga damuwar tafiyar da zaiyi ya barta ko qanqani ke saman fuskarta,mutum ne shi mai son a kula da shi,rashin hango hakan da baiyi ba sai ya sake dagula masa lissafi,sam baison zuwa jigawar nan,saidai umarnin baban babu abinda zai hanashi binsa matuqar hakan bai sabawa mahalicci ba.          Wani tsakin ya sake ja,yanajin duka lissafinshi ya dagule,bai taba jin wata tafiya ta dameshi ba sai wannan 'yar qanqanuwar tafiya da bata kai matsayin komai ba a irin tafuye tafuyen da ya saba yi,ya bar gida tsawon wata da watanni ba'a ganshi ba shima baiga kowa nashi ba "Bar kayan,zan samu wasu a can,zo nan" ya fada yana dubanta,ta waiwayo sannan ta tako a hankali zuwa inda yake,da idanu ya nuna mata hijabin jikinta,gabanta ya fadi,bata tsammaci zai ce ta fidda shi ba shi ya sanya ta gwada wata riga da amira ta bata,ta mance da ita baki daya sai yau cikin kaya ta ganota,idanunshi a kanta yana tabbatar mata da cika umarninsa,haka ta sanya hannu tana ji tana gani ta cire din "Sunbahanallah" ya fada da wani irin amo,hannunshi ya bude mata yana jingine da gadon,sai taci gaba da takowa har inda yake ta shige jikinsa ya rufe hannayensa yana shinshinar qamshinta,ta jima ajikinsa yana abinda ranshi keso,zuwa sannan ya soma sakin layi,a kunnenta ya rada mata "Naso na barki to have some rest,but i will miss you gobe,zan iya kasancewa dake?,kin amince?" Kanta ta daga masa cikin kasala "Thank you,thank you soo much" ya fada cikin murya mai cike da shauqi,yanayin yadda ya tafi da ita ya tilasta mata bashi cikakken hadin kai wanda hakan ya yi masa dari bisa dari.       Tana jikinsa amma tunaninta yake,wannan daren ya sake zamar masa na musamman,wani abu ya tsaye masa game da ita,ji yake kamar ya nemi alfarma wajen baba ya barshi a nan,ko kuma ya dauketa su tafi tare,saidai babu damar hakan,ya tabbata tunda baban ya nemi ganinsu wani muhimmin abu zasu yi a can.         Yana tsaye yana shiryawa itama tana tsaye kusa da shi tana miqa masa duk abinda zaiyi amfani da shi,yau din ma dai surukuta suke taqi kallonshi,duk da yadda taso ta morewa kallon nashi,sakamakon shigar shadda da yau yayi,duk da cewa ba dinkin tazarce bace amma tayi masifar yi masa kyau,kwalliyar taso ta tafi da ita don dai kawai ta maze,ga kuma kunyar da jiya ya bata,har ya kammala shiryawa tsaf ta miqa masa kofin hadden coffe wanda ta daidaita masa zafinshi,kofin na riqe a hannunshi,tururinsa da qamshinsa na shiga masa hamci,yayin da dukkan idanunsa da tunaninsa suke kacokam a kanta,ya lura sarai shigar tayi mata,amma bai furta mata ko nuna mata ba "Wai dama haka aure yake?,haka ake ji?" Yake qiyasatawa a ransa,a hakan yasan bata gama sakewa da shi ba,baisan wanne matsayi ta bashi cikin zuciyarta ba baya ga matsayin miji,sarari yake nema wanda zai zauna ya dasa mata zazzafar soyayyarsa cikin zuciyarta,don har yau baisan a wanne rank ta bashi ba,sai data gaji da shirun ta waiwayo ta dubeshi "Yana sake hucewa,yaya kuma na jiranka" "Eh jira dama nake ki gama yajin aikin kallona din sai na sha" ya fada yana kai kofin bakinsa,kai ta kautar tana murmushi a boye,a haka sai ka rantse bai iya magana ba sam,amma idan ya yankota a nutse sai ta tsaya maka.         Ta baya taji ya ruqota,ya mannata da jikinsa kansa saitin kunnenta "Me zan samu?" Ya fadi yana duban wani kwantaccen gashi dake wuyanta mai santsi,shiru tayi tana tunanin me yake nufi,ganin bata ce komai ba sai ya dora "Zan wuce,kada ki fiya fita wajen gidan nan,coz nasan akwai baqi da yawa da za'a iya yi a kwanakin nan,ok?"kai ta gyada tana jin wani iri babu dadi,sakinta yayi sanda wayarshi ta soma ruri ya duba yaga yaya adam ne,wanda ya gama shirinsa shi kadai yake jira,ya tsammaci ma shi zai rigashi gama shiryawa kamar yadda aka saba,sai gashi wannan karon almustaphan yana son ya makarar da su,juyawa yayi a hankali zaya fice,sai ta biyo bayanshi cikin sanyin jiki tace "adawo lafiya,Allah ya tsare hanya,a gaishemin da baba"saqon yayi masa dadi,sai yayi kamar zai juyo sai kuma ya fasa,ya amsa da "ok" yana ficewa,bayanshi tabi da kallo,bata taba ganin mutumin da kayan hausawa suka masa kyau har haka irinsa ba.        Haka kawai take jin ba dadi,wani yanayi na shigarta,qarfafa jikinta tayi ta gyare ko ina tsaf,sannan tayi wanka tare da yin madaidaiciyar kwalliya ta yafa wadataccen mayafi ta fice wajen su ummee,sai data shiga ta gaida,gidan babu laifi ya sake cika,ga jikoki nam sun soma halartar gidan,yaran huda anty farida da 'ya'yan adam yaran kishiyar ni'ima data taho da su,a wajen maamaa ta hadu da ni'iman,fuska sake suka gaisa,hira ta dan gudana tsakaninsj,haka nan ni'ima ta kwantawa sumayya kamar yadda sumayyan ta kwantawa ni'ima,daga bisani tace bari taje wajen ummee,a can ta tuqe wajen ummeen,cikin siyasa ummen ke janta da hira tana son taji ya zaman nasu yake,sosai tayi qoqarin nuna mata komai lafiya yake,hakan ya sake faranta ran ummeen matuqa,sai ga amira da azahar a gidan,ranar sunga tabara,tunda taji labarin yaa man din sun tafi jigawa tace sai ra taho,ya saif ya iya da tabara,haka ya barta amma da sharafin wuni kawai zata dinga ta dawo,wunin baki daya ya zowa sumayya cikin sakewa,hankalinta kwance,babu gilmawar eesha sam,bata san ina tayi ba,bata san meke faruwa ba don haka babu abinda yazo ranta gamenda eeshan,bata koma sashenta ba sai bayan isha'i,kasa zama tayi,baki daya sashen nata yayi mata babu dadi,hakan ya sanya ta koma neman 'yan kwana,da fari kowa qi yayi,sabida sashen ba wajen zuwan kowa bane,daga mai sashen har uwar gidansa ba masu jan jama'a bane,humaida da humaira suka ce sai sunje,hakan ya sanya nadiya da yusra binsu suma,a dakin gadonta na qasa ta saukesu,hakan ya debe mata kewa matuqa,don suna tsaka da hira bacci ya kwashesu.          Washegari ummee ta danqa mata kayan fitar biki kamar yadda ta yiwa ni'ima fahariyya da su'ad,haka ummeen take,duk wani sha'ani idan ya taso sai ta yiwa jikokinta da 'ya'yanta kayan fitar biki,macace mai hannun kyauta,hakan ya sanya mutane da dama kejin dadin zama da ita,kowa takan masa dinkin ne daidai da ra'ayinsa ko abinda taga zaya dace da shi,godiya sosai ta yiwa ummeen har taso tafi wadda ni'imah ke mata,bangarenta ta koma ta dora girki,karo na farko,girki tayi musu mai shegen dadi wanda ya janyo wasu ma bangaren nata,ta diba wani da kanta ta kaiwa ummeen,ba qaramin burgeta abincin ya yiwa ummee ba,ba shakka almustapha ya dace,ya samu macen da suka jima suna masa addu'ar ya samu,godiya ta dinga mata har hakan ya bata kunya,har gidan wanda ke musu dinki yazo ya karbi dukkan dinkunansu wanda zai gama musu ne a kwana biyu kacal,abinka da kudi qare magana,shi dama haka dinkinshi yake,manya mutane yakewa dinki saidai fa babu saba alqawari,kaman qaramin kamfani ne,yana da ma'aikata,kowa da abinda yake hadawa,wani hannu,wani gaban riga,wani bayan riga,wani kalmasa haka dai da sauransu Laila,khalipha,hafiz da minal duka sun shigo,ta rasa yaya zatayi da laila,ta addabeta,duk bayan mintina sai ta tanka ta "Wai,wallahi ansha da mami da batazo taga yadda 'yarta ta koma ba,don Allah khalipha zaka ce anty summynmi ce wannan" da yake shima uban magana me sai ya biye mata sukayi tayi,dariya ta shata ta gode Allah,batasan sanda lailan zata daina shegen surutu ba haka,antyn dijen ce taqi shigowa,ta dinga kiran layinta tana qorafi amma saidai tayi dariya tace zata shigo,gashi ita babu damar fita tunda bata sanar masa zata fita ba,haka kuma kunya take ba zata iya kiranshi ba, Ranar laraba mai qunshin dakewa su ummee tazo har gida,daki ne babba aka ware a can bayan gidan anan take zama idan tazo musu qunshin,ummeen da kanta tasa aka kira mata sumayya tace ta shirya za'a yi mata qunshi,qarfe hudu na yamma aka gama mata baki daya ja da baqi,kowa yasan yadda lalle ke yiwa farin mutum kyau walau ja ko baqi,kamar ka cire hannun saboda yadda ya zanu ya zauna sosai kamar dorashi aka yi,ita kanta ummen sai da tace masha Allah,ta dubi sumayyan tana cewa "Kije kinyi baquwa,umman khalipha sai yau taga damar zuwa" farinciki ya cikata, bata iya tsayawa ta qarasa cire lallen na hannunta sai ta miqe ta nufi sashen nata,da gudu ya qarasa ta rungume anty dijem,sarkin kuka har ta soma tara qwallar "Au ashe har yanzu baki girma ba sumayya?,inaga tare zaka daina kukan quruciya ke da abdallah da alama" sai ta saki antyn tana dariya,daki suka shige da anty dijen,farinciki fal zuciyarta,kallo daya zaka yiwa sumayyan kasan cewa kwanciyar hankali ya fara samuwa,kasa gayawa antyn komai tayi,sai take jin kunyarta,to ita din ma bata damu sai taji ba,ta dai sake jan hankalinta kawai,sun jima tare kafin antyn fa fidda wasu kayayyakin gyaran jiki ta bata "Hajiya lami ta kawo min su,suna da tsada amma akwai kyau,wannan wata hadaddiyar dilka ce,kwana biyu kadai zakiyi amfani da ita zaki ga yadda zaki sauya,da kanki zaki nemesu nan gaba" sai wata gumbar aya ta kankana data dabino da madara,sabo dadinta da gardi tuni sumayyan ta kusan cin rabi a haka suna zaune suna hira,riqe antyn tayi sai da akayi sallar magariba sannan ta tafi,kasancewar bangaren nata babu kowa duka suna gidan amare sunje musu kamu. Sai data yi sallar sannan ta janyo kayan dilkar ta soma hadawa tana fadin bari ta gwada,ta gama rsaf ta shafe jikinta bayan awa daya ta murje ya shiga wanka,ba shakka mai kyau ce haka ta dinga fadi a ranta yadda fatarta ta sake wani santsi bayan na da,su humaida basu shigo ba sai wajen tara da rabi,har ta shirya zata kwanta ma,yau bata jin qwarin jikinta sosai,tun safe tunaninsa ya dinga kawo mata caffa,tunda ya tafi bata ji muryarsa "Akuyar daure ta samu sake yau mun wataya wallahi wannan miskilin mijin naki bai nan" humaida ta fada tana dariya tare da tsokanar sumayya,murmushi kawai ta saki cikin kara da yakana tace "Ai kunfi kusa" baki humaira ta rufe "Rufamu ki saya mu,wacce kusar?,ai shi bashi da kusa,matanshi kadai za'a cewa sunfi kusa,shekara nawa amma har yau kamar bai san mu su waye dinsa ba,ku dai ku dauki mijinku kuje ku qarata" "A'ah fa,kada kuma a wuce gona da iri" inji sumayya cikin zolaya,dariya suka sanya baki daya,kusan wannan hirar ce ta sake dauke mata hankali. Cikin dare baccin nata ya katse,ita kadai ta dinga juyi saman gadon,tana kallon yadda su humaida ke baccinsu hankali kwance,wayarta ta janyo tana dubawa,babu wani abu sabo tattare da ita,sai ta samu kanta da lissafin awannin da suka rage gare ya waye musu zuwa ranar alhamis. Washegari tana wajen ummee amma baki daya hankalinta bai wajen,tana yi tana duba agogo,tun la'asar ta koma sashenta,awanni suka dinga shudewa amma babu labarin dawowarsu,a haka dare ya cimmata,cikin daren ta kasa bacci,ta miqe a hankali daga dakinta ta haura sama zuwa nashi dakin,ta tura qofar ta kunna fitilar wayarta ta haska makunni ta kunna qawayayen dakin,a hankali ta qarasa bakin gadon ta zauna,da kdanu take bin ko ina na dakin da kallo,wanda dazun ta gyarashi fes,komai a killace,wani irin yanayi take ji mai kama da kewa,sai ta qudundune cikin bargo tana sakin ajiyar zuciya,qamshinsa take shaqa har cikin qwaqwalwarta,juyi ta shiga yi daga farkon gadon zuwa qarshensa,haka kawai taji zuciyarta ta karye kuka take so tayi,hawaye ne masu dumi suka fara zirya saman fuskarta,cikin haka taji wayarta na fidda sauti mai dadi,da fari ta tsorata,amma daga bisani ta tattara hankalinta ta janyo wayar,babu suna akan lambar,amma sai taji zuciyarta ta tafi kan ta daga,karata tayi a kunnenta ba tare da tace komai ba "Baki bacci ba ko?,dama jikina ya bani hakan"tsumammiyar muryarsa ta ratsa dodon kunnenta,bai damu data amsa ba ya dora da tambayoyinsa " me ya hanaki bacci qarfe daya saura na dare?"zuciyarta ta kuma karyewa da jin muryarshi,hawayenta ya qaru,sam batasan kukan nata ya fara fidda sauti ba sai da taji amon muryarsa ya dan qaru sabanin dazu da take kama da ta maijin bacci yana fadin "Subhanallah?,me ya sameki?," rasa me zata ce masa tayi,sai 'yar qaramar sheshsheqa da take fitarwa,to me zata ce masa?,tace masa ta kasa bacci?,ko tace masa gidan ba dadi?,duka saboda me?,sabida shi ko saboda wani dalili na daban,idanunsa na lumshe daga can bangaren yana sauraren sheshsheqarta,cikin sanyin murya yace "Is ok,ya isa,ya isa.....tunda ba zaki gaya min ba ni bari na gaya miki,saboda ke na kasa bacci,saboda baki a kusa da ni,tunaninki da kewarki tunda nazo banji dadin garin nan ba,ta yaya kika yiwa zuciyata ta'addanci har haka ba tare da na farga ba?"shuru tayi kukan ya dauke duf tana saurarensa,ya qware wajen watso kalaman dake taba zuciya,wai da gaske ma ita yake gayawa haka?,kodai yaudararta yake son yi? "kema haka ne a zuciyarki uhmmm?" Ya ambata cikin salon rada wanda ya sake hautsinata,baki ta turo kaman yana gabanta "Umm ummm.nifa ba haka bane" "To meye?" Ya fada dariya na qwace masa wadda baisan ta fito ba,jin shiru bata ce komai ba sai ya dora "tunda ba haka bane sai na bari sai wani satin na dawo,dama aiki ne ya tsare mu yau din bamu dawo ba na gama komai kenan a hankali na taho daga baya ko?koda zuwa satin sama ne"shiru tayi qirjinta na bugawa "shikenan.....sai da safe tunda ba wani abu sabo" "Nifa bance ba....." Tayi hanzarin fada tana tsoron kada ya kashe wayar,abun ya bashi dariya ya kuma burgeshi tare da tabashi,hakan dama yakeson ya ji ko ya gani,reaction dinta kawai ya wadatar da shi "To me kika ce?" "Ba komai" ta fada a shagwabe "Uhm,to shikenan,muna hanya tomorrow in sha Allah" sai ya datse wayar daga haka,wani sanyi taji yana ratsata wanda batasan dalili ba,murmushi ya kubce mata,sai ta soma goge ragowar hawayen fuskarta tana jin kunyar kanta kuma daga baya,ya ta bari har ya ganota?,oho itama bata sani ba ta baiwa kanta amsa,sosai ta kwanta saman gadon tana 'yan tunane tunane,zuciyarta fes,quncin da take ji ya ragu,da haka bacci yayi awon gaba da ita nan cikin dakinshi saman gadonsa. *ko wanne namiji ya banbanta da wani,wani abunda ke burgeshi shike bawa wani haushi,so ya kamata mata mu kula mu lura musa nutsuwa,mu banbance meke burgesu duk qanqatarshi,da kuma meke basu haushi duk girmansa,ba lallai abinda waccan tayi ya burge mijinta ba ke in kinyi ya burge naki,qasaitacciyar mace na zuba ido tasa nutsuwa ta karanci yanayin mijinta ,Allah yasa mu dace.* *ina masoyan SU'AD,to fa ku shirya ku hada qarfinku waje guda,a next page jarumar taku zata iso gidan baba prof,to ko ya zata kaya Allah masani,sai kawo mata gudun mawa,lol*😜😜🤪😂 *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [23/02, 11:52] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 8⃣8⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *wa qadimna ila ma amilu min amalin faja'alnahu haba'an mansura* *YAN UWA MU YAWAITA KARANTA WANNAN AYA,ALLAH YAYI MANA MAGANIN MACUTA AZZALUMAN SHUGABANNI,WADANDA SUKA TASAMMA KASSARAMU SU KUMA KASSARA QASARMU,ALLAH YA FIMU SANIN NUFIN KOWA DA ABINDA KE QULLACE A ZUCIYAR BAYINSA,ALLAH KAYI MANA MAGANINSU KO SU WAYE,KODA CIKIN GIDAJANMU SUKE,MATUQAR ZASU ZAMA BALA'I GA AL'UMMAR MUSULMI BAMU DA QARFI BAMU DA MADOGARA SAI KAI YA ALLAH,KAJI QANMU KO DON QANANUN YARA DAKE RAYUWA A TSAKANINMU* ______________________________________         Sallar asuba ce ta farkar da iya,sai data kammala sallar sannan ta sauko qasa ta dawo wajensu humaida,tsokanarta suka dinga yi kan ina ta gudu?,bayan sunsan oga baya nan,murmushi kawai tayi tana tuna abinda ya faru daren jiyan,mamakin kanta ta dinga yi,batasan me ya sameta haka ba.         Bata damu tayi wanka tunda wuri ba,zani ta daura saman kayan baccinta ta zura hijabi suka fice tare da su humaida ta gaida mutanen gidan,hada hada tayi yawa a gidan kasancewar gobe daurin aure,babu abinda zasuyi cikin gidan kasancewar komai na gidan da za'a gabatar akwai ma'aikata wadanda zasuyi,qarfe goma ta koma bangaren nata,ta kintsa ko ina,saiga sallamar mai kitso da anty dije ta gaya mata zata turo mata ita,babu bata lokaci ta fara mata,'yar maiduguri ce,ba qaramin iya kitso Allah ya hore mata ba,ga sauri a wajenta,cikin awa biyu ta gaka yarfa mata shi wanda ya zauna a kanta kamar an saqa shi,baki daya jelar ta kwanta gadon bayanta,rabon da tayi kitso irin haka har ta manta,sannan kai tsaye ta wuce kitchen dinta,samun kanta tayi da tunanin me zata tana dar masa wanda zaya burgeshi,murmushi ta saki sanda ta gama wassafa mai zata dafa sannan ta hau aiki.        A wanni biyu kacal ta kammala,abinci iri biyu tayi,daya na baba ne daya na almustapha,tuwon alkama ta yiwa baban miyar karkashi wanda ya tuqo sosai yana santsi,dakinta ta koma ta sheqa wanka sannan ta fito tayi sallar azahar,tana shirin fara shiryawa ta jiyo shigowarsu amira,saukowa tayi jin amiran ma qwala mata kira "Wallahi tunda na shigi nake jin qanshi iri daban daban,me kika girka ne haka?" "Zaki ci?" "Na waye?" "Yayanki mana" ta fada tana juya ido,baki amiran ta rufe "Wallahi duk maitata na haqura,wannan sanwa tafi qarfina" dariya sumayyan ta saka ta haura sama tana fadin ina zuwa,komawa tayi ta shirya cikin kwalliyar atamfa peach ce da adon yellow,fitted riga da skert wanda aka yi masa wata iriyar wrapper,ta zauna ta tsara daurin dankwali tamkar head din amare ya zauna dam a kanta,cas cas kayan suka mata kamar a jikinta aka dinka,ta bi jikinta da turate ta feshe shi sannan ta sauko,babu wanda bai tanka adon nata ba,har suka sanyata dariya. Har misalin hudu da rabi na rana hira sosai suke wadda ta dauki dadi matuqa,ta sake a cikinsu ana kwasar cafta,turo qofar falon da akayi shi ya maida hankalinsu wajen,almustapha ne,sanye da straight leg da longsleeve shirt,qafanshi snickers ne baqi,idanunshi saye da glass mai haske wanda kana hango qwayan idanunshi,hannunshi soke a aljihunsa kafadarsa rataye da jaka,tuni shiru ya ratsa falon kowa ya kama bakinsa,wadanda suka cire mayafi suka fara lalubarsa suna yafawa,tunda ya shigo idanunshi na bisa kanta,cikin izza yake takowa har zuwa tsakiyan falon,baki daya suka hau gaidashi,amsawa daya kacal yayi musu baki daya ya haye saman,tsam ta miqe tana fadin "Ina zuwa" "A'ah madam saidai mun ganki" inji humaida tana qyaqyata dariya,harararta sumayya tayi saboda shirin bata kunya da takeyi ta juya ta haye saman. Bakin qofar ta tsaya gabanta na duka,wani farinciki taji na mamayarta,cikin zumudi da son basarwa ta tura qofar dakin ta shiga,yana tsaye ya baiwa qofa baya,ko takalminsa bai cire ba bare a kai ga zama,waiwayowa yayi baki dayansa ya motsa bakinsa yana amsa sallamarta,idanunsa duka suna kanta,wani abu yaji na ratsashi,kyawun da yaga tayi masa ba mai misaltuwa bane tun daga qafafunta da yasha lalle ja da baqi ya qawata qafar ya bita da kallo ya dire a kafadarta wanda jelar kitsonta ta sauka,takowa yayi a hankali kamar mai sanda ya tsaya gan da ita,wanda tsaiwar baida maraba da runguma,tana niyyar bude baki ya rigata "Kinsan zan dawo kika tara min wadancan?,sauka ki sallame su idan baso kike ayi abun kunya a gabansu,ke zaki ji ba dadi don na fuskanci kunyarki tayi yawa ni ko a jikina" daga kai tayi ta dubeshi,sai ya kashe mata ido daya,da sauri ta dauke kan ta ta juya da hanzarinta,a iya zamansu kadai ta soma fuskantar sa,ta soma gane sauyawar yanayiyyika tattare da shi,fargabarta daya me zata gaya musu?,zata ce su fita su bata waje?,riqota taji yayi,ta sake juyowa suka hada idanu "Kada ki jima,kizo ki shiryani kayan jikina sun dameni" ya fada a wami shagwabe,wata bahaguwar kunya ta mamayeta,saita qara wuta zata fice kamar zata hantsila,haka ta dinga sauka har ta kai qasan. Wayam taga falon babu kowa,wani dadi ya kamata don batasan me zata ce da su ba,abinda bata sani ba shine tana hawa saman amira ta dubesu "To 'yammata nifa warewa zanyi wlh tunda mai gu yazo,gwara mu bashi waje tun bai koremu ba da kanshi" "Ai naga take takenshi zai aikata kadan daga aikinsa" inji shukra "Nikam dama wai haka yake ya man?" Inji humaira,dariya amira ta saka "Ai yafi haka ma,sarari ne bai samu ba sai yanzu,yana auren waccen iccen ina zamu sani" dariya suka sheqe da ita sanda suke ficewa daga sashen don baki dayansu haushin su'ad suke ji,girman kanta da dagawarta sun girmeta,data tashi baya dauki dai dai ita ba,ganin babu kowa ya sanyata juyawa ta koma. Har yau still bai yi komai ba,saidai wannan karon yana zaune ne bakin gado,qarasowa tayi tana taku cikin wani salo har ta iso gabanshi,ta duqa baki daya da zummar cire masa takalmin qafanshi tana gaidashi wanda hakan ya baiwa qirjinta damar fitowa,dif yaji tunaninsa ya dauke,yaci gaba da morewa kallonta har ta gama fidda masa takalmin da safa,ta miqe da niyyat hada masa ruwan wanka,sai ya fisgota ta dawo saman cinyarsa ta zauna,ya soma shinshinar wuyanta yana cewa "Qarya kike wallahi,kin damen da kuka sannan na dawo ki gaza duban qwayar idanuna naga yadda kikayi missing dina,ko lacture din tamu baya zo nan ba" ya qarasa fada yana zira hannunshi cikin rigarta,muhallin da tun dazu data tsugunna ya tsone masa ido "Uuummm" ya fada yana shinshinar jikinta,qamshinta na tafiya da tunaninsa,tsam ya hadeta da jikinsa yana magana can qasa "Uhhmmm,tell me yaya kikayi missing dina?" "Nima ban sani ba,bansan ha zance ba" ta furta a tausashe idanunta na lumshewa "Kin kasa cin abinci saboda ni?ko kin dinga jinki wani iri duk saboda ni.....oya....tell me.....gaya min gaskiya kada kiyi qarya" "Yes,duka na kasa....na kasa" "Why,meye dalili?" Ya sake tambayarta idanunshi a lumshe cike da shauqi "I dont know....ban sani ba" "So ne?" "Nooooooo" ta fada tana jan kalmar cikim jin kunya tare da tura kanta a wuyanshi "Nace kada kimin qarya fa,tashi ki gayan" ya fadi yana qoqarin hade fuskarsu waje daya,goshinsu ya hade kamar yadda tsinin hancinsu ya hade,suka fara musayar numfashi,muryarta a sanyaye tace "Kace kaima baka iya komai,kaima so ne?" "Yeah,feeling ne dake yawo cikin zuciyata da ban taba jin mamakamancinsa ba,so that na yarda so ne,sone unexpected....."nannauyar ajiyar zuciya ta sauke,abu guda suke ji a cikin zukatansu lokaci guda,indai ko haka ne ita din ma son ne?,amma ta yaya zuciya daya ke iya son mutum biyu,taso mukhtar yanzu kuma almustapha?saidai idan tayi rantsuwa ko kaffara ba zata yi ba,abinda take ji a yanzu bata taba jinsa kan wata halitta ba,ba mamaki dalili kenan da ya sanya ta gaza gane meke damunta "Why you keep silence?" Kai ta girgiza duk da fuskarsu na hade waje daya tana kuma sauke numfashi "Babu komai" "Akwai....na sani bazanji irin wannan abun ni kadai ba at the first time in my life,idan baki sani ba lissafo min me da me kike ji,ko yaya...konyaya inason naji wani abu mai dadi,lafazi mai dadi kamar yadda sauran maza keji" a hankali ta soma lissafa masa kamar mai koyon magana "Tsoro....kunya.....nauyi....tausayi...kewa son ganinka....damuwa....faduwar gaba......" Sai tayi shiru tana jan numfashi wanda ke cakude da nashi mumfashin da qamshin lallausan turarensa,yana mata kwarjinin da bazata iya kammala fada masa ba,murmushi ke fita daga fuskanshi,dukka wadan nan sun tabbatar masa akwai wani abu mai girma dake son wanzuwa cikin zuciyarta dangane da shi,don kada ya matsanta mata da yawa sai janye fuskarshi daga tata "Is ok,hakan ma ya gamsar da ni,hadamin ruwan wanka kafin a kawo min abincin da nayi order" sai ta kwabe baki tana dubanshi "Abinci na jiranka,no need sai ka yi order" ta fada taba niyyat shigewa toilet din,murmushi ya sake kube masa,binta yayi da kallo har ta shige,ba shakka akwai banbanci,akwai banbanci wanda kullum sai yaga wani sabon abu,tunda suke da su'ad bata taba jera abinci yana jiransa ba,duk da orser yake amma ganda take kafin ya fito ta fidda komai daga park dinshi ta ajjiye masa inda ya dace. Yana shiga wanka tayi hanzarin ficewa ta dauki abincin baba ta kaiwa anty maamaa kan ta bashi sannan ta juyo ta dawo,saidai tayi nawaa,saboda tana tura dakin ta ganshi har ya fiti,qugunshi daure da towel yana shirin soma shafa mai,sai ta dauke idonta "Ina kika je?" "Naje gaida baba ne" "Amma dai kin gani gidan a cike yake har da maza ko?" Sai ya danja tsaki "Banjin gidan nan zaya zaunu,ki shirya zamu basu waje" idanu ta fidda tana son tambayarsa inda zasu,saidai taja bakinta tayi shiru,ta qarasa inda yake zaune gefan gadon ta lakato man ta soma shafa masa,daya daga cikin lacture din da yayi mata,duk inda ta motsa binta kawai yake da kallo,baki daya ta kashe masa jiki,sai ya miqa hannu ya karbi man yana cewa "Barshi kawai,kasala kike saka min,jeki shirya,bana so magariba tayi mana a nan",bata jima da yin wanka ba amma ta fuskanci mai muradin haka ne,shi ya sanya ta juya ta koma bayi,ta cika turaren wanka a ruwan ta sake wani wankan,sanda ta fito bai saman,tuni ya sauka qasan,bai iya jira ba yayi sarving kansa ya fara cika tumbinsa,dadin abincin ya dinha zagayawa wata duniyar da shi. Cikin minti qalilan ta shirya cikin riga da skert na lace,ta yafa mayafi hill shoes ne a qafarta,yana zaune saman kujera qarar takalminta ya sanyashi daga ido,ba qarya tayi kyau,kome ta sanya kyau yake mata,saidai wani kishinta ya rufeshi,gani yake idan ta fita haka kowa ma kalleta zaiyi,bazai iya barinta ta fita hakan na,da idanu yayi mata nuni shigarta bata masa ba,tq kalli jikinta sai ta juya ta koma samam,ta fidda kayan jikin nata tana tunani,bangaren atamfofinta ta nufa,ta ciro wata super,kalarta tayi kyau qwarai,itama riga da skert ne masu fidda shape qwarai,sai ta fitar da lafaya wadda ta dace qwarai da atamfar ta nannade jikinta tamkar 'yar maiduguri,takalmi da jakarta mahadin juna ce,takalmin na da tudu maimakon na dazu mai tsini,sak ta fito a bahaushiyar kanuri tun kafin ta gama nada lafayar,wajen nannadota ta baya hannunta ya gaza kaiwa,tana yunqurin janyo inda ya nade din ta hangoshi cikin mudubin,qarasowa yayi ya sanya hannunsa ya juyo da ita suna fuskantar juna,da kanshi ya qarasa nada matan sannan yaja baya rungume da hannunshi yana kallonta,yana matuqar son tayi shigar arewa,shugar na burgeshi wani lokaci har tafi ya abaya kyau,kwalliya na burgeshi,wani bangare ne na abinda yake so a wajen matarsa,kasa daurewa yayi,ya hada yatsanshi manuni da babban dan yatsansa a hankali ya furta "Kinyi kyau" murmushi ta sakar masa tana saqala jakarta suka jero suka fito lokaci lokaci yana satar kallonta. Ko ina mutane ke kai kawo kowa na sabgarshi,saidai duk inda suka gifta sai sun wafci ganin wasu,su burge wasu,masu hassada kuma su tanka,kacibus sukayi da fahariyya wadda tabi sumayya da kallo,tuni almustapha yayi gaba abinshi,dama idan baiso ba ba shiga shirginta yake ba,har gwara ni'imah yana ganin yanayin hakayyarta da hankalinta ya banbanta dana wannan sukan gaisa a mutunce cikin ganin mutuncin juna,fahariyya kam sai yaga dama,don bai daukar raini ko wargi,yanayin nasu ya burgeta saidai haka kawai kishin sumayyan ya soketa,fuskar sumayyan da fara'a ta qarasa wajenta tana fadin "Ina yini maman hibba?" A yatsine kamar wadda ka yiwa dole ta amsa da "Lafiya ya kike?" "Lafiya qalau wallahi,tunda kika iso bamu samu mun hadu ba sai su hibban na gani" "Oh Allah?,k'nnn,ina ciki ina hutawa" "To yayi,ki gaida yaran" ta fadi tana juyawa sabida ganin yanayin fahariyyan,yayin da ta bisu da kallo,ba shakka ba haka aka so ba qanin miji yafi miji kyau,a da tana kishi da su'ad wadda mijinta ne kawai yafi nata mijin komai da komai,a yanzu kuma saiga wadda mijin nata yafi nata,hakanan ita dinma ta fita,shi ya bude mata sai da ya tabbatar ta shiga ya rufe sannan ya zagaya ya shiga wajenshi,hakan ya tsayawa fahariyya a wuya,su'ad suna dan dasawa wani lokaci rashin jituwarsu yafi yawa,amma sai gashi yau taba taya su'ad din kishi,ya akayibtayi sake haka ta faru?,lallai bari ta iso,ta fada aranta tana yin gaba ta bar wajen,yana yunqurin tada motar tace "Su ummee fa,basu san bama nan ba" sai da ya tada motar sannan ya amsa "Ba ruwansu da mu,we r free". Baki daya gidan ya tafi da ita,kaf rayuwarta bata taba katarin shiga gini irin wannan ba,gida ne wanda idan baku manta ba yake mallakin almustaphan,wanda babu wanda yasan da zaman gidan banda shi din,a hankali suka dinga ratsawa,basu tuqe ko ina ba sai lafiyayyen bedroom dinshi,wanda kusan dukkan abinda ke jere a ciki ba daga nijeria ya fito ba,bedroom ne wanda kallo daya zaka yi masa kasan cewa mamallakinsa yasan abinda ake kira da TSARI,dole tsarin dakin ya burgeka,komai na ciki fari ne qal,tun daga qwayaye,bed lamp fenti,kayan gadon,labulaye,bedsheet,sofa guda biyu,table na galss,tiles da rug dake ajjuiye can gefe guda,hatta da qofar bayi zuwa ga ac ta girke dake tsaye kusurwa daban ta dakin,tattausan qamshi da sanyi mai dadi ke gauraye a dakin,ya matuqar burgeta,tana tsaye idanunta na kan tafkeken frame mai ruwan gold da aka rubuce ayatul kursiyyu da wani daura da shi da aka rubuta addu'o'in bacci kala kala ya qaraso gareta ba tare data sani ba,a hankali ta maido kanta gareshi,babu wani space a tsakaninsu baki daya ya hadeshi,batasan me yasa yake son ritsata haka ba,baisan nauyin da yake haifarwa zuciyarta ba,jakar hannunta ya sabule ya ajjiue gefe guda,yasa hannunshi duka biyun ya riqe kafadarta,cikin sanyi yace "welcome to my world" murmushi na fita saman fuskarsa "I wish zan samu wani gagarumin abun da bazan taba mantawa da shi ba" murmushin itama ta saki,hannunta ya kama yana duban lallenta "Ya miki kyau,but daga yau jan kawai nakeso,yafi lafiya ya kuma fi yimiki kyau,at d first time da naga wannan abun hannun wata kusa da ni sosai kamar haka,yana muku kyau" "In sha Allah" ta fadi,sai ya saki hannun ya zamw dankwalin kanta,hannunshi ya dora saman kitson yana shafawa "Wow,masha Allah" ya fada har cikin zuciyarsa saboda yadda kitson ya burgeshi,ya jima baiga kitso haka ba kan mace,har ya manta cewa mata na kitson,inda ya qarasa girmanshi dai ba kitso suke ba,haka matarshi a nata ganin kitson wai qauyanci ne,tafi ganewa taje a sanya mata gashin da zatayi parking tamkar nata,a haka ya zarce da warware mata lafayar dake jikinta tana tsaye idanuwanta alumshe,sannan ya janyeta zuwa ni'imtaccen gadonshi wai tazo ta nuna masa yadda akayi kitson,daga nan labari yasha banban. ******* ****** ******** Yana zaune abinsa hankali kwance kan kujerun dake falon kamar wanda sam bai da niyyar zuwa daurin auren ma,zirga zirga take tsakanin kitchen da dining area cikin wani hadadden lace da aka yiwa dinkin buba,duk inda ta gifta idonshi na kanga,shigar tayi masa,shi baiqi suyita zama a hakan ba,sam baya son su je gidan,don ya tabbatar zuwa yanzu hayaniyar dake cikin gidan sai Allah,baki daya hankalinta ya soma yin gida,awa daya da rabi ya rage lokacin daurin auren yayi,amma taga shi kamar ma ko a jikinsa,sai data kammala ta tako gabanshi ta russuna "Breakfast din ya zama ready,nd saura awa daya da rabi fa lokaci yayi" kanshi ya mirgina yana sake kashingida "Koda babu ni ai ba za'a fasa daura auren ba,ban amshi waliccin kowa ba" kai ta rausayar ta miqe,sai ya janyota cikin jikinsa ya soma shinshinarta,yasa hannu ya ture dankwalinta yana shafa jelar kitson "Kinyi kyau,wannan kitson ya yimin" sai ya soma yamutsata,wayarshi ita ta katse masa qudurinsa,ummee ke kira sai ya gyara zamanshi,ta tambayi lafiya ne saboda ta aika sashen anata bugu ba'a bude ba,yace komai lafiya,bata tsaya jin komai ba tace to alhamdulillahi ta katse kiran dama lafiyar take son ji,a akasalance ba don yaso ba ya karya sannan ya koma dakin don ya shirya. Tayi ready,hatta da mayafinta na yafe a jikinta,tukunshi taji,a hankali ta daga kanta "Fatabarakallahu ahsanul khaliqin" ta ambata har bakinta na motsawa,sanye yake da shadda fara qal dinkin tazarce sai walainiya take,hular kansa baqace kamar yadda takalminsa na kamfanin batozzi halfcover yake baqi,agogon fata dake daure a tsintsiyar hannunshi ma haka,karon farko data soma ganinsa cikin shigar manyan kaya haka,kasa daina satar kallonshi tayi har ya qaraso gabanta "Mu wuce ko?" Ya tambayeta,ba musu ta miqe din,tana niyyar gaba ya riqota "Wallahi baki isa ba,u have to say something,na lura shigar na burgeki,nayi saboda ke kice zaki wani fuske" yadfa yayi kicin kicin yaso bata dariya "Masha Allah tayi kyau" "Ita tayi kyau ko ni nayi" "Kaine" "Allah ya ceceki yau da babu inda zaki fita har sai jibi zamu bar gidan nan" ya fafa yana yin gaba ta biyo bayanshi tana sakin murmushi,tabbas ba qarya yayi kyau,sai ta tuna yadda su'ad ke kishinsa duk sanda ake sha'ani cikin gidan bata so taga ya gifta don kada a kalleshi?,haka zasu ratsa gidan kenan?. Qarfe tara da rabi taxi dake zirga zirgar kai jama'a daga airphort zuwa gidajensu ta sauke su'ad din qofar gidan baba prof,ta kira layin almustapha tana son shaida masa azo a dauketa don abun kunya ne tana matar fitaccen mutum kamar doctor elmustaphan ta shiga motar haya har ta gode Allah bai daga ba,dole daga qarshe dai ta dauki drop din motar ta kawota gida,wanda ta mance when last data shiga motar haya a rayuwarta cikin nijeria ko da a america ne sai ta kama take shiga din,tun daga harabar gidan take ganin al'umma saidai babu wanda ya isheta kallo,a haka ta dinga ratsawa dauke da jakar ratayenta qatuwa,ko baba mai gadi da ya matso yana mata sannu da zuwa da niyyar kuma amsar jakar hannunta ya kai mata bangaren nata bawai don mutuncinta ba,saboda daraja da girman baba da almustapha ne,wani matsiyacin kallo ta watsa mata tana tsartar da yawu "Kada ka soma matsowa inda nake,bastard" ta fadi tana wucewa ciki,kusan duka wadandanta taras 'yan zafin kaine saboda haka ba wanda ya kulata har ta shige bangarenta,hakan ya mata ciwo,dama ga zargi fal cikin ranta sai take ganin da gayya aka mata hakan. Sauyin yanayin qamshi da ya samu falon ya tabbatar mata da zarginta na ba shakka almustapha na abuja,kuma tare da yarinyar,tunda ta kira layikansa na nan qasar duka sun shiga,wanda abaya idan bai naija layinsa baya shiga saidai ta gwada na wata qasar,kai tsaye ta nufi samanshi,ta tura dakin ta shiga,neat dakin yake,saidai shima akwai cakuduwar wani qamshin bayan qamshinsa data sanshi da shi,wanda bata raba dayan biyu qamshin yarinyar ne,kishi ya lullubeta,wai ya akayi haka ne?,me yasa ta tafi har ta basu sararin cakufuwa danjuna haka cikin kwanciyar hankali,me yasa bata zauna ba ta daga musu hankali,kowa ya qeaci almustaphan idan zai iya,wanda tana da tabbas ita ke da nasara,sabida tana da gogewa da wayewar da zata iya aiwatar da haka,yanzun ma ai bata makara ba(a cewarta)sai ta ja qofar dakin ta rufe ta nufi nata dakin,komai yayi qura,bata jin zata iya amfani da dakin,dole ta samu ma'aikatan gidan su gyara mata,sabida haka ta koma dakin almustapha ta sake wanka ta shirya cikin wando wanda daga same yake a dame,daga qasa kuma wajen qafafun ya bude sosai,riga ta sanya spaghetti hand wadda ta dameta dai dai jikinta,gashinta ta taje ta daureshi,sannan ta janyo takalmanta masu tsini hade da igiy kamar zata tsokale idanun duniya ta daura,'yar hula ta samu ta sanya akanta wai din idon jama'a sannan ta feshe jikinta da turare ta sauko qasan tana fatan shigowar almustapha bada dadewa ba don daidaita tsakaninsu. Gab da zata fice sukayi kacibus da fahariyya tana shigowa,baya suka ja suna wa juna kallon kallo,tsaf fahariyya ta qarewa kayan jikin su'ad kallo,tasan ko na wanne kamfani ne,bazau wuce armani ko D&C ba,don bata siyan kaya a kamfani mai arha,lallai almustapha ya tsaya mata fahariyyan ke rayawa a ranta,waskewa tayi "Ai naga shigowarki nace bari na leqo mu gaisa,ban tsammaci zuwanki ma bikin ba" "Bashi ne ya kawoni ba" "Da alama kam,tunda na lura kaman ma bakisan mai gidan bai sashen ba" idanu tabi fahariyyan da shi "Tun yaushe?" Ta tambayeta "Jiya da dare sun fita shi da amaryarsa" wani qunci ya ziyarceta,ina ya dauketa suka tafi?,wato ma basu kwana gidan ba?,bai taba mata haka ba duk yadda bata qaunar zaman gidan "Da kyau almustapha,ni almustapha zaiwa haka?" "Ai kadan ma kika gani,matuqar baki sanya himma kin fiddata daga gidan ba,ni ga tawa nan ta zamarmin ciwon ido,bata haihuwa amma ta fini power da fada wajen mai gidan,sai kiyi kamar kinayi" ta fada tana juyawa ta fice,burin ta ya cika,dama so take ta tura mata takaici,ta kuma samu nasarar haka. Da qyar su'ad ta iya jan qafarta ta fice saboda neman masu mata gyara,kishi da baqinciki ya cika mata zuciya,yaushe har tayi wannan saken da har wata ke watayawa da almustaphanta yadda taga dama?. Duk da cinkoson masu wucewa gidajen amaren daurin auren hakan bai sanyashi tsaida motar waje ba,dai da ya dangana da oarking space wanda tuni ya yiwa drivansa waya yazo ya sameshi a nan ya kaishi inda za'a daura auren,kashe motar yayi ya jingina da kujerar yana dubanta qasa qasa,sai daya gaji don kanshi sannan ya bude bakinsa "Kijr but,banson ki cika yawo cikin gidan,nan da awa daya nasan gidan zaya sake cika da mutane,ki zauna gu daya" kai ta kada tana mamakinshi,wannan tsananin da takatsantsan duka na meye?,hannunta ta dora zata bude qofar motar ya hangin gungun angwayen tafe cikin shigar babbar riga,hayaniyarsu nata tashi,bisa dukkan alamu yanzu zasu wuce wajen daurin auren ne "Wait....." Ya gada yana miqewa daga jinginar da yayi,haka kawai ranshi ya baci daya hango alqasim a cikinsu,ita dinma ta ganshu ta gane kuma me yasa ya tsaidata,sai da suka wuce sannan yace "Muje" ya furta yana cire belt dake daure a jikinsa,ya bude murfin motar itama ta bude ya zagayo suka daidaita kafada kana suka jera. A hankali ta daga kai ta dubeshi sanda ta hangi sa'ad na takowa,cak su'adan ta tsaya sannan ta canza direction zuwa inda suke,kanta ta daga ta dubi almustapha,sarai shima ya ganta,amma sai ta lura da cewa ko a jikinshi,ba wani yanayi nashi da ya sauya,hasalima hannunta da ya kama bai saki ba,suka ci gaba da takawa su'ad itama na takowa zuwa nahiyar da suke idanunta qur bisa kansu duka su biyun. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [23/02, 11:52] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 8⃣9⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *la haula wala quwwata illa billahil aliyyul azim* *la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin* _____________________________________         Ci gaba tayi da tunkararsu ba tare data dauke idonta daga garesu ba,tamkar zuciyarta zata fito waje saboda tsananin kishi,kamar ta kurma ihu ko zata ji sauqin abinda ke sukar zuciyarta,bata taba jin bala'i irin wannan ba arayuwarta,ashe a baya duka qaryar kishi take kan almustapha?,almustaphan nata ne riqe da hannun wata haka?,sun kuma jero suna tafiya kan bigire guda?,ko a jikinsa wai an mintsini kakkausa,shi sam baiyi zaton ganinta ba ma a wannan lokaci,sai da suka qaraso dab da juna sannan ya zame hannunshi daga na sumayyan ya dubeta "Idan kika shiga bana so ki fito,bana son yawo ki zauna waje guda,nasan duka nan za'a dawo akwai walima da zasuyi" sai ta samu kanta da narke masa cikin wani irin salo "Ina so naje wajen umman khalipha fa,tunda nazo ban shiga ba" girarsa ya dage salon ya matuqar qayatar da shi "Ko zakin ba yanzu ba,idan na dawo zan sanar miki" kai ta gyada tana jifanshi da wani irin qayataccen murmushi daya sake narkar da shi "Ok,to a dawo lafiya,Allah ya tsare hanya" idanu ya lumshe addh'a ta masa dadi,qarakin murmushi ya subuce masa "Amin,thanks" kai ta gyada tana juyawa cikin takunta na nutsuwa,baki daya idanuwa su'ad ta bita da shi,ji take kamar ta fincikota ta yarfa mata mari,ba'a tabacin fuskarta irin haka ba,a gabanta wata ke soyewa da mijinta?,ita dun da dukkan 'yammatan danginsa sunsan halinta sarai ko cikakken kallo bata so taga ka fiya masa yanzun zata ci miki mutunci?,saiga wata a gaban idanunta tana narkewa mijinta,ga sumayya kuwa sanda ta juya sai ta dinga jin wani abu na mintsininta cikin zuciya,sai taji kamar ta koma,me yasa ta barsu su biyun?,zuciyarta ta cunkushe,kallon data lura su'ad na mata bai dameta ba,qarfin gwiwar da bata taba jinsa kan kishiya ba wannan karon shi take ji,ba abinda zai sanyata taci gaba da barwa wasu matan mazanta,ta tabbata ko ba'a gaya mata ba babu zancan zaman arziqi tsakaninta da su'ad,ta santa tun ba yau ba,ta santa tun kafin miji ya hadasu,bata da kirki bata da mutunci,bata ganin girman kowa,a haka taci gaba da takawa zuciyarta dake cike da kishi na bata shawarar ta waiwaya amma ta daure zuciyarta ta hana kanta aiwatar da hakan.       Yatsan tsakiyarsa da babban yatsanta ya hada ya murza a fuskar su'ad din wadda tabi sumayya da kallo,kishi ke sukarta,sam bata gane ma sumayyan ba,saboda ba duka wanda yayi mata qaramin sani irin wanda su'ad din tayi mata bane zai iya tantanceta ba tashi guda,idanunta da suka kada ta dauke ta maida kan almustapha,shigar jikinsa kadai ta bata mamaki,bata taba ganinsa da manyan kaya ba tunda suke sai yau din,wani qyama da takaici ya kamata,ya auri 'yar nijeria arewa ta fara zuba masa duhun kai kenan,to wallahi bazata lamunta ba,wata babbar riga harda hula sai kace wani limami,bakinta na rawa cike da tsantsar kishi tace "Almustapha?,ashe da gaske baka sona?" Shanyayyun idanunshin nan kawai ya zuba mata yana dubanta "Almustapha ka dubi yadda kake nuna qauna da kulawa ga wata bayan ni,dama zaka iya aikata hakan?" Ci gaba yayi kawai da dubanta,karon farko da ya soma ganin aibun irin shigar da takeyi,cikin qasarsa gidansu kuma gidan iyayensa surukai a garesu,ba shakka ta nan shine babban mai laifi,amma sam bai gane illar hakan bane sai yanzu,tunu hawaye ya soma wanke mata fuska,sai ya saki hannayenshi ya sake matsowa inda take ya kama hannayenta,ya sani qwarai kishi abu ne mai zafi cikin zuciya,abu daya ne wanda zai janyo mata ta rasa dukkan wata dama daga gareshi shine taci gaba da hauka da tashin hankali "Enought.....daga gani na sai kuka,ya isa" wani ratsawa wadan nan taqaitattun kalaman sukayi har cikin zuciyarta,sai kawai ta fada jikinsa rungumeshi tana sake sakin kukan,hakan bai dace ba saboda suna tsakar filin gidan,kowa ma na iya ganinsu a haka,dagata yayi daga jikinsa yana fadin "Zan wuce ne wajen daurin aure kada na makara,ki koma ciki,but ki sauya kayan jikinki kafin na dawo zuwa atamfa lace ko shadda,coz akwai maza da zasu shigo da yawa bayan dawowar tamu bana son kowa ya sake zuwa ya ganki da wannan shigar,ya kamata ta zama tsakamin ke da ni ne kawai cikin gida,understand?"mamaki ya kusa kasheta,bai taba furta mata makamanciyar wannan maganar ba sai yau,me yake son maida ta ne,irin kidahumar matarsa?,taga sarai shigar jikinta,ta nannade kanta da wani material kamar gawa ba wajen shan iska,itakam ba zata iya ba "sai na dawo ko?" Bata saba yi masa a dawo lafiya ba ko wata addu'a tun da can ma da ake zaman dadi bare yanzu,saboda haka har ya juya ya koma wajen motarsa driver ya bude masa ya shiga suka fice tana tsaye wajen,ashariya ta lailayo ta qunduma cikin harshen nasara,tana jin nemawa kanta 'yanci ya zama dole,ba zata taba lamunta ta zauna cikin irin wannan rayuwar ba,da wannan tunanin ta tattaka cikin sassarfa ta wuce nasu bangaren.         Wajen anty maamaa ta soma shiga ta gaidata,suja gaisa da dukka 'yan uwanta a mutunce ta musu Allah ya sanya alkhairi,cikin farinciki tare da yabawa suke amsawa,lokaci daya ta burgesu ta shiga ransh,don babu wanda su'ad ta taba duba da irin wannan sigar tsawon saninsu da ita,ta dan kashe wasu mintina masu dama kamin ta wuce wajen ummee.          Dukka 'yammatan yau na falonta,amira uwar daba na cikinsu anata sabga,tsokanarta suka shiga yi har ta rasa na karewa,amiran tace "Ku dubarmin wannan mata,daga dawowar miji saiki tattara ki bishi,wai ku don Allah baku gajiya da zaman hotel?" Duka kan cinyarta sumayyan ta kai mata "Baki da kunya fa,nu yayarki ce ko kin manta?" "Tuba nake,Allah ya ja da ran babbar yaya" dariya duka suka saka,barkwancinsu abin sha'awa ne da burgewa,ta gaisa da kowa cikin fara'a da mutuntawa,eesha dake zaune tun shigiwar sumayyan gaba daya sauran fara'ar da tayi rara a fuskarta ta bace bat,kusan a wannan bigiren tafi kishin sumayya fiye da su'ad,saboda su'ad din kusan bata da wani amfani ko tasiri mai yawa cikin zuciya da rayuwar almustapha,babban abin tashinbhankali kuwa data gano wasu sabbin sauyi da halaye da duka almustaphan ua qaro matuqar yana tare da sumayya,itama eeshan bata dameta,ita a yadda taje ji yanzu ko kishiya bazata bari ta dameta ba,balle wata wadda batasan me ya hadata da uta ba,abinda ta sani dai kawai eeshan nada izza izgilanci da jin kai,tun daga sanda tazo gidansu a kano tun bikin amira,ita kuwa a rayuwarta zata iya mu'a mala da kowa tayi haquri da shi banda mutum mai wadan nan halayen,don bata ga abinda zara nuna mata ba,mutunci da rufin asiri dai dai bakin gwargwado Allah ya basu,to kuma name zata zubda mutunctakarta ta dan adam kota yarda a zubda mata?,amiran ita ta miqe don raka sumayyan sama wajen ummee,suna haurawa saman ta dubeta "Kinsan wajen ummee mijinki ya gaji halinshi,miskilancin tsiya rashin son hayaniya,daga wajen anty mamaa fa ta dawo wai kanta ke ciwo tana daki kwance" harara ta watsawa amira "Eh kam su ai sun huta,ba irinku ba akun kuturu" baki amira ta riqe "Iyeee,wai yau ya man kike tarewa?" "To ya ranki?" Ta fada tana juya idanu,suka sanya dariya baki daya,ran amira ya mata fes,burinsu ya cika,dangantakar da suke fatan ta qullu tsakanin sumayya da almustapha bisa dukkan alamu Allah ga qulla ta cikin ruwan sanyi.        Knocking suka yi mata ta basu umarnin shigowa,amira ke gabasai sumayya,tana zaune a dakin ita da qannenta biyu da yayarta,idanunta kan sumayya fuskarta qunshe da fara'a,yayin da kunya ta yiwa sumayya katutu,don ta tabbata tasan ba gidan suka kwana ita da almustapha ba,a ladabce ta qarasa ta duqa tana gaidasu suka amsa a sake,nabila qanwar ummee wadda itama babba ce don tana da yara samari ke tsokanar sumayya "Har yau baku kai mana ziyara kano ba,duk da dama wannan sarkin hade gabas da yamman sai sallah sallah yake zuwa mana,saidai ki jisu suna waya da mai martaba,da alama ma baisan jikinsa ya motsa ba bai gaya masa da tuni kin ganshi ya tashi hankalin kowa" dariya suka sanya ummee tace "So nake kafin ya koma i yayi qoqari ya kaisu baki daya ita da su'ad din,don ita dinma dudud zuwanta nawa?" "A'ah kibar ta wannan,itakam tunda baquwa ce sai ya kaitan,idan tana da sha'awa da kanta zata ko tasa ya kaita" inji hajiya saudat yayar ummee,hira suke kadan kadan kafin su fice don komawa bangaren anty mamaa,tsabar hadin kai da fahimtar juna ya sanya duk sanda wani abu ya taso cikin gidan walau na hajiya mamaa ne kona hajiya kilishi wato ummee 'yan uwan kowaccensj basa qasa a gwiwa wajen zuwa,run daga kan matasa yammata zuwa manya,akwai hadin kai da fahintar juna mai yawa tsakaminsu,kowanne family sunsan kowanne,haka 'yamnatan kowanne vangare na mu'amala dana kowa,kasanceqar duk sha'ani za'a hadu,sai duka suka zama kamar family daya.        "Ina almustaphan ya shiga ne?" Akunyace ta amsa mata "Ya wuce wajen daurin aure ne" "To masha Allah" inji ummeen dadi yaja ratsata, "Allah ya saka da alkhairi fa amiran umman khalipha,naji dadin yadda na fara ganin sauyi wajen almustapha,bama ni ba hatta da babansu,Allah ya qara miki juriya da qwarin gwiwa,naji labarin abokiyar zaman taki tazo,ina son inja hankalinki da don Allah kada ki biye mata da duk wautar da zata zo da shi,ki dauke kanki kiyi haquri da ita,idan kika fuskabci akwai abindabtake miki na cutarwa da ba zaki iya dauka ba,ki samu mijinku cikin salama ki sanar masa ya warware muku matsalar,kada ki soma yarda ki biye mata ku dinga abinda ba dai dai ba,kada ki yarda saboda ita ku dinga bata ran mijinku kinji" "insha Allah ummee" "Allah yayi miki albarja,ya akbarkaceku da zuriya dayyiba" addu'ar tayi mata nauyi,amira ce ta cafe "Amin ummee,kai Allah dai ya nuna mana ranar,ummi da ido daya zaki bacci ina jin" ta fada cikin tsokana tana qyaqyata dariya,murmushi ya subucewa ummee "Kinci gidanku,kin maidani kakarki ko?" Ta fada tana harararta,murmushi itama sumayya tayi,gwara da zancan ya tsaya nan kada ta hanata sukuni gaban ummeen.        Bata jima ba ta wuce bangarenta,sanda ta shiga babu kowa falon,sai ta shige dakinta ta ware lafayar dake jikinta,kitchen ta wuce kai tsaye ta soma tunanin me zata dafa mishi?,don tuni ta sani wajen ummee baicin abincin taro idan ana yi,yankewa tayi tayi masa jallop din couse,sai ta tanada masa wani abun shan,shine zata gama cikin sauri kafin su shigo,cikin qanqanin lokaci ta hada komai ta dora. Cikin mintina ta kammala jallop din wadda ta wadata ta kayan lambu da kuma hanta wadatacciya a ciki,kammala komai tayi waje guda ta soma hada lemo,shima bai dauketa lokaci mai tsaho ba ta gama ta kammale komai waje daya ta soma gyara wajen. Cikin takun isa da izza ta shigo kitchen din,ta sauya kaya kamar yadda ya umarceta,a yanzun tana sanye da fitted gown na wanu lace mai azabar kyau da tsada,saidai bata daura dankwalin ba,sam sumayyan bata ji shigowarta ba,sai takun takalmanta masu tsini wanda ke haduwa da tiles din wajen suna bada wani sauti,a hankali ta waiwayo ta dubeta,sai ta dauke kai taci gaba da aikinta ganin ta shigo mata ne ba tare da sallama ba,bata tsaya ko ina ba sai data ci birki a gaban sumayyan wadda ke wanke sink data kammala amfani da shi,wani kallon sama da qasa ta yiwa sumayyan cike da tsantsar raini wanda sumayyan bata ma san tana yi ba bare ya dameta,aikin gabanta kawai take ci gaba da yi,itakam bata hango komai tattare da ita ba banda kyau da take da shi,sai tsantsar duhun kai,idan banda haka meye hadinta da daura zani?,meye na shiga kitchen tamkar matan daa? "Ke" ta ambata cikin gatsali,sam bata nuna ta san da ita take ba,hakan ya quleta "You african women dake nake" nan ma tayi banza da ita taci gaba da dauraye wajen tana gogewa da qaramin towel dake hannunta,hannu ta dora kan kafadar sumayyan ta juyo da ita suna fuskantar juna,murmushi sumayyan ta saki sannan ta dora hannunta saman na su'ad din ta saukeshi daga kafadarta tana fadin "Sallama ya kamata ki soma kafin shigarki waje a matsayinki na diyar musulmi" ta juya taci gaba da aikinta,wani abu ya tsaya mata,itama za'a koyawa abinda ya dace "Banga dama ba kuma bazanyi na,domin bani da shamaki cikin shiga duka inda naso a cikin gidan nan,gida dai na mijina ne so mallakata ne,ba wanda ya isa hanani shiga duk inda naso a sanda naso" waiwayowa tayi ta sake saki mata murmushi,mata na baki mamaki a yawancin lokuta,wato su duka son kansu ya musu yawa ne?,babu zaman lafiya idan su suka sameka cikin gidanka kamar yadda babu zaman lafiya idan kai ka tadda su,saidai zuwa yanzu ta tsike ya kamata itama ta shiga a dama da ita "Oh sorry fa,may be labarin shafa fatihar dake tsakanin sumayya da almustapha bai isa kunnenki ba,idan kuwa har ya isa kunnenki to ya kamata kisam cewa nima matarsa ce kamar yadda kike matarsa,so kinga kenan matsayinmu daga,babu wanda nima zaimin shamakin shiga inda nakeso,saidai ni nawa addinin ya gayamin duk inda zan shiga na nemi izinin mai mallakin wajen kafim shigar tawa,wannan kadai shi zai sanyani neman izini bawai don nima ba matar doctor mustapha bace" kalamanta sunyi matuqar qona mata rai,ita take kallon idanuwanta take gaya mata cewa itama matar almustapha ce,sai ta gyara tsaiwa fuskarta na sauya launi saboda kishi "Anzo point din,dama abinda nazo na baki shawara kenan a kai,ina mai baki shawarar sawunki a likkafa ki fita rayuwar mustapha,ki tattara ya naki ya naki ki koma gidan ubanki tun baki gamu da tuggun kishiya ba" abun ma sai yaso baiwa sumayya dariya,ta matse towel din data gama wankewa bayan ta gama goge gogenta ta dubu su'ad "Ina zaton ke din farin shiga ce kan tuggun kishiya ko?,to mu ba yau muka fara gani ba,zagi kuwa ban tashi naga ana yi ba,don nasan makomar wanda ya zagi iyayen wani,shawara kuwa da kike ambata ai ciwo ce,baya ga haka ma kina iya riqe abarki wataqila nan gaba zata miki amfani" daga haka ta juya kan qafafunta ta soma takawa da niyyar barin kitchen din,zage zage su'ad din ta soma yi,tana son yayuaba baqa kamar yadda aka gaya mata saidai babu cikakkar hausa,hakan ya sanya ta dinga hadin gambiza da turanci "Idan baki wasa ba nice ajalinki" shine kalmar qarshe data shiga kunnen sumayya yayin da take niyyar fita,hakan ya sanya ta waiwayo tana sake jifanta da murmushi "Idan numfashina a hannunki yake yau kada na kwana a duniya" ta juya ta fice abinta,sam ko a jikinta,tasan sarai zata fuskanci sama da haka ma daga wajenta,saidai ba yau farau ba balle zuciyarta ta quntaya,meye ba'a yi mata ba?,har farautar rayuwar tata anyi. Toilet ta fada ta sake wanka,sannan ta shirya cikin atamfa plain zani da fitted riga,ta fuskancu shigar na yawan qawatar da almustapha,yakan yawaita binta da kallo duk sanda ta yita,tana tsaka da shafa mai bayan ta sanya kayan ta jiyo sallama,hakan ne ya sanyata fitowa daga dakinta ta ratsa ta corridor dinta ta fito falon,abida ce matar hamza,cikin farinciki ta tarbeta ta jata sukayi dakinta "Wai wannan wawuyar ta dawo ne na sameta tana zirga zirga tsakanin falo da dakinta ta kasa zama" abidan ta fada sanda take shirin zama saman doguwar kujerar dake dakin,sumayyan na saman dressing chair tana kwalliya,baki sumayyan ta tabe kana ta saki murmushi "Gata kuwa kin ganta" "To Allah ya kyauta,sai ki sake zage damtse ki rungumi mijinki" dariya ma ta baiwa sumayyan har sai data dara,daga nan suka shiga hirarsu,tana gaya mata ai ta dan jima ma wajensu ummee,hamzan ne ya sauketa ya wuce wajen daurin aure su da lamin,ta nan zasu dawo idan an kammala daura auren. Bata fi minti talatin ba ta jiyo sallamarshi cikin muryarshi mai cike da izza da kwarjini,kamar wadda aka yiwa allura ta miqe,dariya abida ta saki sumayyan ta kalleta cikin dan jin nauyi don ta tabbatar qila yadda taga tayi saurin miqewan take wa dariya "Mene ne" kai ta kada "A'ah babu komai jeki abinki ina nan ina jira" ta fada tana miqewa saman kujerar,feshe jikinta ta sake yi da turare sannan ta fice. A hankali ta tura qofan dakin baccinsa dake sama cikin nutsuwa,idanunshi cikin nata bayan muryar su'ad da ta soma dukan dodon kunnenta,shike fuskantar qofa su'ad ta juya baya,magana take cikin bacin rai harda qwallarta a idanu,yayin da ya zuba hannunshi cikin aljihun wandon shaddarsa yana dubanta,tuni ya cire babbar rigar sai 'yar sama da dogon wando,baya ta koma a hankali da niyyar komawa tunda ta fuskanci wata magana suke wadda wala'alla abune da su'ad din bazata so taji ba,a hankali ya motsa baki har yau bai daina kallonta ba,ta masa kyau matuqa,komai nata mai nutsuwa ne da shiga cikin zuciya cikin wani irin sanyi "Zo nan" ya kirata yana ci gaba da kafeta da idanu,maganan da yayi ya sanya su'ad yin shiru daga rattabo maganar da take yi,ta waiwaya a hankali idanunta kan sumayyan,bawinciki ya sake ninka mata fiye da na dazu,har wani canjin kwalliya take,ita har a nuna mata ado,gabanshi ta qaraso,kafin tace wani abu ya bata umarni "Rage kayan jikina ki hadakin ruwa,ina sin yin wanka" idanu ta dan fiddo,ta yaya hakan zai kasance ga su'ad wajen na tsaye,yadda ya kafeta da idanu tasan zata jama kanta wani abunne hakan ya sanya ta nufeshi ta soma balle masa botiran gaban rigarshi cikin taushi da sanyi,idanunsa ya dauke daga kan sumayyan ya mayar kan su'ad "Uhmmmm,ci gaba ina jinki,na taho da jama'a na jira na" kai ta kada tana yunqurin danne hawayenta don kada sumayya ta ganta bare ta rainata,ta sani sarai tunda har ranshi ya baci sai ya horata,koda zata ciyo kansa to sai ya hukuntata,wanda bai iya hukunci ta dadin rai ba,idan ya maka sai kaji babu dadi "Ka barshi kawai,idan ka dawo mayi maganar" "Ke kika tada maganan yanzu kk?,bayan na gaya miki cewa ki barta sai na nutsu,ki qarasa kawai idan ba gaka ba daga wannan muhallin banson na sake jin komai daga gareki,idan na dawo zan ganku ne kawai baki daya ina fata kin fahimta" ita kanta tasan indai har zaman lafiya take so da mustaphan to ta bar maganan,ta yarda ya gabatar da su wa juna,idan yaso ta ruwan sanyi zata dafa yarinyar,zata ga barikanvi,zata ganar da ita rainin america ba irin na nijeria bane,zata nuna mata akwai banbanci,za kuma ta nuna mata almustapha nata ne iya daya da ita kadai ya dace. Busy busy,need ur prayers,we shall meet tomorrow in sha Allah. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [23/02, 11:52] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 9⃣0⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *YA UBANGIJI KADA KA JARRABEMU DA AZZALUMAN SHUGABANNI SABIDA ZUNUBANMU KAJI QANMU,YA ALLAH DUK MAI NEMAMMU KO NUFINMU DA SHARRI ALLAH KA MAIDA MASA DUK ABINDA YA YI TANADI A KAN KANSA YA KOMA MASA* ____________________________________        Kai kawai ta kada ta juya ta fice daga dakin,bata so tayi wani abu da zai sanya almustapha yayi misbehaving dinta gaban sumayyar,don ta riga data sani ta bata masa rai qwarai,ta kaishi bango,hakanan fushinsa bai da kyau ko kadan,idanunsa ya dauke daga kanta bayan ta fice ya dubi sumayyan sanda ta gama,daga boxer sai singlet,da idanu ya nuna mata singlet din,a kunyace ta cire mishi,ya sake nuna mata boxer din,sai ta kauda kai tana turo baki,itakam ba zata iya ba,shi ko nauyin su'ad baiji ba zai wani ce ra cire masa kaya,zata juya kenan ya janyota jikinta,ya matseta cikin jikinshi yana goga fatar jikinsa jikin tata,tsigar jikinta ta zuba saboda yawan gargasar dake jikinsa "Ina zaki baki gama ba?" "Na gama mana,na bar baquwa ne a qasa" "Idan ina nan kisa a ranki babu wani a gidan nan sai ni da ke,abidan ce baquwa?,ki tambayeta haka takewa hamza?" Shuru tayi murmushu na qwace mata,sakinta yayi ya nufi bandaki yana cewa "Kayan nan akwai zafi,but akwai dadi da kyau kayan al'ada" kanta ta maida inda ya yasar da babbar rigar,kana kallonta kasan bata jima jikinsa ba,hakan yake ko a can din ma cireta yayi ya riqe a hannunshi,gefan gadon ta koma ta zauna,wayarshi ta soma ruri,musaddiq ke kira,ganin haka ya sanya ta daga ta shaida musu wanka yake "Au shine ya zube mu a wannan da yake shine agwagwa sarkin wanka?,tell him muna jiranshi" murmushi kawai tayi ta datse kiran,abotarsu na burgeta,kawai sun dauki kansu daya ne baku daya su shidan,qaraso yayi ya miqa mata hannu sai ta dora wayan saman tafin hannunsa,ya fara shafawa yana tambayarta waye ta sanar masa,sai ya dan tsuke fuska "Why you permit him yaji muryanki?" "Afuwan" ta fada a sanyaye,sai ya dan saki fuska yana ajjiye wayar tare da takowa inda take zaune,gab da ita ya zauna har suna gugan juna "Ina da kishi,matsanancin kishim da bansan ina da shi ba sai da muka kasance tare,please ki kiyaye" "In sha Allah", mai ta dauko ta soma shafa masa bayan ta gama tsane masa jiki,duk inda ta zagaya ko ta gifta qamshinta na bibiye da ita tare da cika masa hanci,cikin wani cotton yadi fari qal mai adon ash ya shirya,ba qaramin kyau kayan suka masa ba,sai ta dinga satar kallonshi ba tare data sani ba,shigar na qawatar da ita,jikin bango ya rutsata tsaye,tana shirin yin qasa da kanta ya riqe fuskan "gulma.....kema kin iya,me yasa ba zaki bude baki ki magana ba?" Murmushi ta saki,sai ta saka idanunta sosai cikin nashi ta juyasu tamkar mai yin faari,hakan ya rudashi,ya sanya tattausan lebbansa ya sumbaci idanun nata,qarar wayarshi ta katse masa abinda yake shirin yi,ummee ke kira,ta sanar masa baba na son ganin sumayya a falonshi,ya sauke wayar yana dubanta "Baba ne ke kiranki,but bana so ki fita,a cike wajen yake,muje na rakaki" "To" ta amsa ta juya da niyyar ficewa,har ta sanya qafarta waje yace "Hey" juyowa tayi tana dubanshi,da hannu yake kwatanta mata "Ina hijabinkin nan babba wanda ya sauko qasa?"kai ta gyada " yauwa,shi zaki sanya" "To" ta amsa tana ficewa,wayarshi ya ciro ya kira su lamin ya shaida musu yana zuwa zaije wajen baba ne ya dawo,a dakin ta tadda abida har ta soma gyangyadi abinta,tace tana zuwa "Babu komai,gama uzurinki,ni wannan kwanciyar ta fimin komai dadi" murmushi tayi ta fice tana tausayin abidan,tayi nauyi qwarai,duka duka watanni kadan suka rage mata ta haihu,ba lallai ma tabi hamza a gida taje tunanin zama har sai ta haihu din.        Tana gaba yana biye da ita kamar wani body guard,hakan ma yayi masa,tunda ko banza yana morewa kallonta,kasa control din kanta tayi sa'ar da taga malam da abdallah,da gudu yaron ya nufota ta duqa ta tarbeshi ya fada jikinta ta rungumeshi "Ammi......ashe nan kika dawo kin bar gidan umman khalipha.....laaaaaa,daddy?" Ya katse maganar tasa ya dora da wannan sanda suka hada idanu da almustapha wanda ke tsaye hannayenshi harde a qirji,sosai abun ya masa,sai ya tuna sanda ya ganta da hijab cikin ranakun bikin amira,ta bude hannunta kamar haka yaran suka shige,kwadayin samun yaranshi ya taso masa ya kuma sake nunkuwa fiye da da,don a wannan lokacin haka kawai yaji yafison yara fiye da baya,yana jin dama ace abdallan nasa ne,yaron ya shiga zuciyarshi,amma tana nufin itace mamarshi?,Allah ne ya kiyaye bai kai mata bugu ba randa ta bugeshi kenan,sam bai sani ba,barin jikin sumayya yayi ya nufo almustapha,cak ya dagashi sama murmushi na subucewa daga fuskanshi,sama ya dinga juyashi abdallahn na dariya,yana son ayi masa hakan dalilin da yasa ya kasa manta almustapha kenan,dauke kanta tayi wani farinciki na ratsata ta isa gabansu baba ta duqa,cikin qauna ladabi da girmamawa take gaidasu,cikin kukawa baki daya suke amsawa kafin baba ya dora "Haduwa tayi wuya mamana,tunda kuka dawo ban ganku ba" kai ta sadda qasa tan murmushi "Ummee tace kaje jigawa ai sanda muka iso" "Gaskiya ne kam,ina fatan komai lafiya?,ko da yake alamu sun nuna hakan,saidai muci gaba da binku da addu'a" murmushi taci gaba da yi ba tare data tanka ba,dai dai sanda almustapha ya qaraso ya durqusa gabansun kamar yadda sumayya tayi ya soma gaidasu suna amsawa,ta dan saci kallonshi sanda yake tambayar mama da yaya abubakar,baba ne yace a basu waje da sauri malam yace "Haba muhtari,waye baqo cikinku,me zan gaya mata me zata gayan,ka daina min haka" dariya baba ya saki ya koma ya zauna,hira suka taba sama sama duk da sumayya ta kasa sakewa,daga bisani ta dauke abdallah ta basu waje,malam din ba sai ta kawo masa komai ba,idan ta aikata hakan ma kamar tayi rashin kunya kenan,don ita kanta ba zata iya qayyade yawan abincin dake gabanshi ba.         Suna tafe abdallah na kafadarta duk nauyinsa,tana tambayarsa yana rattabo mata labarai kala kala "Ummu abdallah" taji an ambata daga bayanta,almustapha ne,cikin kunya ta sauke abdallah,ya qaraso ya karbi hannunshi "Don me zaki fito ki barni ni kadai,wuce sashenki" ya fada yana gyarawa abdallah hannun rigarshi,ba musu ta wuce ta barsu a nan.         Wajen ummee ya wuce,kasancewar duka yau bai shiga ya gaidata ba,tana cikin baqi ta miqe ta bishi saman,ta samu daya daga cikin kujerun ya zauna,abinda ya burgesu yadda abdallan ya duqa har qasa ya gaida ummen,ji take da ana qwacen d'aa da ta qwace abdallah ta baiwa almustapha,saidai babu komai duka tushiya daya ce,tana fatan wadda ta samar da wannan ta samawa nata dan itama,cikin kulawa da juna suka gaisa sannan yace "Su'ad fa ta shigo kun gaisa?" "A'ah,amma wataqila ka ganta,ai ba tafiya zata yi ba yau din,ko zuwa gobe ma duka daya ne zamu gaisa" take ranshi ya baci har fuskarshi ta nuna hakan,dama ya zargi haka saboda baiji baba ya masa maganarta ba,duk yadda akayi shima baisan da zuwanta ba,ko zai lamunci komai amma banda bangaren iyayenshi,sun fiye masa kowa da komai a rayuwarshi,yana da azamar miqewa ta dakatar da shi "Bance kaje kuyi bacin rai ba har hakan ya kai kunnen babanka gida cike da jama'a" ajiyar zuciya ya sauje,tafi kowa saurin karantarsa abinda yayi niyya kenan yaje ya sameta,ya dan jima wajen ummeen suna tattauna lamuranda suka jima basuyi hira akai ba kafin ya fita daga bangaren.         Wajensu hamza ya koma,ya taddasu har sun gama ciye ciyensu,wanda duka sumayyan ce ta sa aka kai musu,ba qaramin faranta masa hakan yayi ba,a da aikin ummee ne,ga hidimar baqinta ga na abokanshi,wannan karon kam kafin ummeen ma ta farga har tasa an gama musu komai,musaddqi ke cewa "Munci mun qoshi,saura a turo mana amarya mu gaisa" wani shegen kallo ya watsa masa,suka tuntsire da dariya baki daua,hamza kam murmushi kawai ya saki yana qarewa almustapha kallo,kusan yafi kowa cikinsu farinciki da samu sauyawar rayuwar abokin nasu,ko makaho ne kai kana kallonshi kasan cewa akwai sauye sauye masu girma tattare da shi.          Sai yamma sannan malam yayi shirin komawa kasancewar a jirgi yazo a nan kuma zai koma,ba yadda baba baiyi da shi ya bari sai gobe ba amma yawi,yace zasu zo zuwa na musamman,lokacin sumayya na raka abida da nafisa wadanda suma zasu koma "Amma malam da zaku bar mana shi ya kwana biyu wajenmu?" Murmushi malam ya saki yace "Gaku nan gashi" ai kuwa yana jin abinda aka fada ya noqe kafada yana narke fuska,dariya malam ya saki shida baba "Shifa kamar wanda aka haifa tare da gidansu,baison matsawa nan da can,ki baya ga haka ma abdur rahman na tabbata sai ya biyo sahu idan ba'a koma da shi ba,don yana dari dari ya bafa shi gani yake kaman bazai dawo ba" sumayyan tana ji tana gani cike da kewa abdallah ya tafi,taso qwarai ya zauna wajeta yayi wasu kwanaki,tana tsaye tana duban motar data daukesu zata kaisu airphort harda baba,sai da suka fice sannan ta saki ajiyar zuciya,ta baya taji an rungumota,ta dan firgita kadan,sam ta mance hana tsaye gefanta,tun daga sanda yarom ya tafi yaga sauyin yanayin fuskarta,habarshi a saman kafadarta ya rada mata "Ba ke ba,nima ina buqatan yara,zakiyi himma ki bamu namu da wuri my wife?"tilas murmushi ya kubce mata,kunya ta kuma kamata,ta soma yunqurin raba jikinsu saboda idanun mutane,duk da wajen ba gun wucewar jama'a bane sosai,amma tana iya hango eesha na tahowa da alama hanya ce ta biyo da ita ta wajen,shima sarai ya ganta,ya kuma gane abinda yasa sumayya keson qwacewa,sai ya ma sake hade fuska ya kuma janyota cikin jikin nasa sosai "baki amsa min ba my life" "Am ready" da sauri ya juyo da ita suna fuskantar juna "Really?"kai ta gyada a kunyace,sai ya soma juyi da ita wajen,cikin kunnenta ya rada mata "ki zama cikin shiri yau"sai ta sinne kanta,ya soma manna mata kisses wanda hakan yaso tsaida bugun zuciyar eesha,qara sauri tayi ta bar wajen zuciyarta na bugawa,tsaki ya ja sanda ta gama wucewan "stupid....ki kula da yarinyar can,banson wata hulda tsakaninku" inda ta wuce din sumayya tabi da kallo sai ta maida kallonta wajensa,gira ya daga mata kafin ya raba jikinsu,cikinsa ya soma shafawa da hannunshi yana yamutse fuska "Yunwa" ya furta a hankali,sanoda tun safe rabinshi da abinci,idanu ta zari waje,shaf ta manta "Am really sorry don Allah,Allah na yi maka abinci tun dazun na zaci kaci na bikin ne" ta fada cikin kwabe fuska,yana son salon maganar nan tata,sai ya sake mata murmushi ba tare da ya shirya ba "Ban haqura ba" ya fada yan akwaikwayon salon maganar tata,dariya ya bata har sai da farareb haqoranta suka fito,idanu ya zuba nata yana kallon yanayin dariyar tata cikin ban sha'awa da burgewa,sai data gama tsaf sannan yace "Zan turo a dauka min abincin" ya furta yana takawa kan qafafunshi ya matso dab da ita "Wuce ciki tukunna" juyawa tayi sai da yaga ta wuce ciki sannan shima ya wuce        Qarfe biyar da rabi na yammaci aka soma shirin zuwa dauko amare,dai dai lokacin ya shigo cikin gidan,kwance ya sameta saman gadonshi,idanunta baki daya sun tasa sunyi jajur da su,kanshi ya dauke daga bangarenta,su'ad ta cancanci dukkan wani hukunci daga wajenshi,abubuwan bacin ran data yi masa ba zasu qirgu ba,bai mata yadda baba ya bata lokaci yana musu nasiha ba,da kuma yadda shima yayanka mata warning amma hakan duka bai hanata tsallakewa tayi tafiyarta ba,bugu da qari kuma saboda ta raina mishi iyaye ta dawo cikin gidansu amma babu wanda ya isa ta nemeshi?.ta lura idan batayi da gaske ba wankin hula zai kaiya dare,don wasu takaddu ya diba ya juya yana da nufin sake ficewa,da gudun tsiya ta cimmasa,ta rungumoshi ta baya tana sakin kuka,cikin turanci tace "Kayi haquri ka yafemin,nasan na bata maka na maka abubuwa marasa dadi,amma duka kai ka janyo da aka hada baki da kai aka dauko mana wata cikin rayuwarmu" dan janyeta yayi daga jikinsa ya waiwayo yana dubanta cikin bacin rai "Har yau baki hankali ba,duk sanda kika fahimci kinyi kuskure mayi maganar da zamuyi" ya sake juyawa da nufin ficewa,maqalqaleshi tayi bakj daya wanda hakan ya tilasta masa tsayawa,cikin kisaa ta dinga fidda kuka tana bashi haquri,bata da wata mafita data zarve hakan,tasan bazai taba iya shallakewa kukanta ba,kasancewarsa mai yawan tausayi da rashin son kuka,a hankali ya janyeta zuwa gadon suka zube baki daya,hannunshi ya sanya ya goge mata hawayen,har yanzu tana maqalqale a jikinsa,sai da gama goge matan kafin ya dora "Tun ba yau ba na baki damarki tafi a qirga kan ki gyara,idan baki gyara ba duk abinda ya biyo baya kada kiyi kuka da ni,duk da hakan kika sanya qafa kika shure maganata,mutum nawa kika tadda a nan gidan?,su me ya cisu da suka zauna tare?,me ya gutsiresu gayamin?" Ya fadabyana zuba mata idanu,wani abu ya takoreta,haushin su ummee ya sake kamata,ta tabbatar yana mata kwatance ne da su,tilas ta bude baki a cunkushe tace "Ba komai" "So ki iya bakinki ki kyautata kalamanki,kada ki manta wandanda suka sanya baki kan auren su su waye a wajena,iyaye na ne wadanda ba wani abu da matsayinsa yayi dai dai da su ko mene ne shi a duniya" shiru tayi haushi na cikata,tsanar mutanen na sake cikata,itakam wlh bata ga abinda zai sanya ta fasa yi musu abinda tayi niyya ba,amma sai ta kawai ta gyada kai a sanyaye "Amma almustapha baka daina sona ba har yanzu?,sannan kayi missing dina" murmushi ya subuce masa na gefan baki,kai ya gyada "Duk yadda kika fada haka ne" qanqameshi tayi tana jin quncin dake ranta na raguwa "I love u,i love u so much my dear",nan ta narke ta dinga dauka masa alqawuran sauya duk wani abu da baiso,daga qarshe ta masa alqawarin ta bar karatun zata zauna da shi,zata yi dukkan abinda yake so,daya daga cikin abinda ya sake sauko da shi kenan       Ta jima tana kwatanta yadda zata kirashi ta sanar masa tafiyan nasu,bata son sake shiga dakin balle ta gansu irin na dazu,ba mafita dole ta soma kiran lambar da take kyautata zaton tashi ce,wayar na kusa da shi sai ya miqa hannu ya dauka,capital S ya sanyawa sunan tun wancan lokacin,sai ya daga ya kara kunnenshi ba tare da yace komai ba,sallama tayi ya amsa mata kafin shiru ya biyo baya " amm,dama.....dama ni da amira ne zamu je gidan amaren ana tafiya"shiru ya danyi kafin ya amsa "Kice ta wuce ta tafi,ke kuma kizo ina nemanki" ya kashe wayar daga haka,cikin mintuna sumayya ta turo qofan hade da sallama,tayi kyau cikin wani yadin material mint blue mai haske wanda aka yiwa adon baqi,dinkin doguwar riga ne wadda ke da shape na umbrella,ba qaramin kyau shigar tayi mata,ta baro mayafinta a daki bata yafa ba,hakan ya bayyana asirin jelar kitsonta da kuma baqaqen fashion data saka wadanda suka qara haska farar fatarta,duk yadda yaso ya kaucewa kallonta ya kasa har su'ad ta lura da hakan,a nutse ta qaraso tana dauke idanunta daga kansu,wani abu data tabbatar zuwa yanzu kishi ne ya riqe mata wuya,saboda su'ad na jikinsa kamar zata shige cikinsa,kanta na kafadarshi,abinda ya hanata zama kenan tana daga tsayen tace "Gani" "Na ganki,u look so beautiful,da da wannan shigan zaki tafi wani gidan amare?,ba inda zaki" duk da hakan bai mata dadi ba amma kishin dake cinta yafi mata zafi kan furucinsa,sai kawai ta juya tana cewa "Ba damuwa" mamaki ya kama su'ad,taso ace ta masa musu sun fara sa'insa ya bata mata rai kamar yadda nata ran yake a bace,amma sai taga akasin hakan,kishi ya sake maqureta sanda taji su'ad na ambatar wash na gaji yake cewa ta kwanta ra huta,bai son ta qara kuka.         Daki ta shiga ta fada kan gado idanunta na mata zafi kamar yadda zuciyarta ke mata,bata tabajin makamancin wannan kishin ba akan duka mazajen data aura har da mukhtar kuwa,sunan Allah ta dinga ambata kadan kadan har ta soma ji zuciyarta na mata sanyi,miqewa tayi ta isa gaban mudubi tana duban kanta,sai ta soma zargin kanta da zafafa kishi?,meye ne a ciki?,su'ad matarsa ce,meye ke bai miki ba kema?ta tambayi kanta,sai ta saki murmushi tana baiwa kanta qwarin gwiwa,ganin lokacin sallar magariba yayi sai ta shiga bayi ta daura akwala,ta dawo ta sake sabunta kwalliyarta ta zura haijabi ta tada sallah,bata bar kan abun sallar ba sai wajen takwas na dare bayan tayi sallar isha'i tare da karatun qur'ani saboda ta sake samun nutsuwar zuciya,ta kuwa sameta,don sakayau take jinta,bata san ya tsarin gidan nasu zai kasance ba,hakan ya sanya batayi gigin dora komai a matsayin abincin dare ba,sai data gama sallar ne ma ta shiga kitchen,cikin qanqanin lokaci ta shirya haddaden salad,ta fere abarba ta markada ta tayi lemon abarba wanda yaji flavour mai dadin qamshi.        Tana fitowa a kitchen suka kusa karo,yana sanye da shirt da trouser dukkansu baqaqe,sun matuqar yi masa kyau,kallo daya zaka yi masa kasan cewa ya sake wanka ne,kishi na nemon taso mata ta danneshi,ya tsareta da idanu,sai kuma ya sake matsowa dab da ita,ta dan matsa baya ya sake biyota,sai da suka dangana da jikin bango,sunkuyo da kanshu yayi daidai kunnenta ya rada mata wata magana data sanyata saurin kallonshi,sai kuma ta sake yin sauri ta kauda kanta,murmushi ya saki ya kamo fuskarta saitinsa "Me kike kitchen da daren nan" cikin cool voice tace "Abincin darenka,amma ban sani ba ko ka qoshi" ba qarakin burgeshi tayi ba,wanu banbarakwai yake jin kansa,abinci direct ba tare da yayi oder kashe kudi ya jira an kawo masa ba "Thanks" ya furta a sanyaye,idanunta ta watsa masa kafin tace "Dutyn kowacce mace ne" sai ya dage giranshi yana murmushi "Oh haka ne?" Da idanu ta amsa masa,sai ya lumshe idanunshi kafin ya bude,wannan idanu nashi na tafiya da shi,sau tari sukan so karya dukkan wata mzantaka tashi lokaci guda,su kuma tafi da nutsuwarshi.        Yana tsaye yana duban nata suka ji takun sawun takalma,su'ad ce cikin qananun kaya riga da wando wadanda suka dameta sosai,zamewa sumayya ta danyi ta goce,sai ya bita da kallo yana fadin "Sorry madam,zan ganku ne ke da ita" "Yes sir" ta fadi cikin wani irin salo da ya sanyashi murmushin dole.      Tuni hakimar ta hakimce saman kujera qafa daya kan daya,kusa da su'ad din ya zauna sannan ya kama hannun sumayya dake qoqarin zama waje daban ya janyota wanda hakan har yayi sikar fadawarta jikinshi,da sauri ta tashi tana daure fuska ta zauna kusa da shi kamar yadda ya buqata,hannun kowacce ya sanya cikin nashi,wanda hakan yayi tasiri a jikinsu da zuciyarsu baki daya "Dukkaninku kowacce cikinku tasan cewa ita matata ce,sadaki na biya na kawo kowacce cikin gida na qarqashin kulawata da sunan matata ko?,.....to ba dogon zance zanyi ba,ku zaina lpy bana son fitina ko tashin hankali ko hayaniya duk kun sani,ba wanda zan saurarawa matuqar ya nemi tada fitina ko hargitsa zaman lafiya,saboda haka ku kiyaye" cikin dabara sumayya ta janye nata hannun kana qasa qasa tace "In sha Allah" don ita bata ga meye abun tashin hankali ba imdai da su'ad ne,tashin hankalin da ba yau ta soma fuskantarshi ba,abu daya ta snai wannan karon babu mau fiddata daga gidan,koda QADDARARTA kuwa zata yaqeta da addu'a wadda take fatan ta sauya mata ita da iko da kuma izinin ubangiji "Ina da magana" su'ad ta fada qunci na cika mata zuciyarta,din gani take ajinta ya fado raga raga matuqar ma qawayenta suka samu labarin ita aka yiwa kishiya "Ya za'ayi da rabon kwana?,sannan girki kowa mai aikinshi ta masa,kuma ban lamunce mutum ya ganka ba cikin ranata" kafada ya dage gami da girarshi "Wannan tsakaninku ne,kawai abinda na sani shine,da rana ina da ikon yin mu'amala da kowa,sannan zanyi magana da duk wanda naso,da darene zaki kwana da ni,zancan kwana kuma bibbiyu kaman naga ana yi,idan ma ba haka akeyi ba abarshi hakan" sai ya dubi sumayya "Can i have my dinner?" Bata ce komai ba ta miqe tsam ta wuce kitchen,su'ad ta rakata da harara kafin ta maida idonta ga almustapha "Kada kace min aninci gida zaka ci,kuma abincim waccan?"fuska ya bata yana dubanta " bana son kowaccenku ta dinga min zanca 'yar uwarta,mind your own business" ya dauke kanahi daga gareta,rabe baki tayi har tau halin yana nan sannan ta narke fuska tana dubanshi "Me zan ci as dinner ne dear,yunwa nake ji" yana sauya tashar dake kan t.vn zuwa wata yace "Akwai komai a kitchen ko?,ki samawa kanki wani abu mana" idanu ta zaro kamar wadda aka sheqawa mari "Habba dear,so kake nayi baqi,kamar wata baqauya,kawai zanyi order nan da few minute nasan za'a kawo min" ta furta tana latsa wayarta tana neman lambar gidan abincin da suka saba order idan suka zo garin.       A nutse ta fito da komai,ta iso gabanshi ta soma shiryawa,kishi ya cika su'ad,ta rasa me zata yi ta bata ranta,ta lura kamar ma bata gabanta,bazai yiwu wata 'yar nujeria 'yar arewa wadda bata san kanta ba ta dinga bata ranta a  banza ba ba tare data rama ba "Dear..." Ta fada a shagwabe,waiwayowa yayi ya dubeta ba tare da ya amsa ba "Amma yau kwana na ne ko?" "Like how?" "Eh,haka za'ayi,ban qoshi ba dear...." Ta fada tana sakin murmushi "But its better a fara rabawan daga gobe ko?,tunda bansan da zuwankin ba bare mu tsara haka" fuska ta bata wanda sumayyan ta lura da haka,sai ta saki murmushi tana duban almustapha,ido daya ta kashe masa cikin tausasa murya tace "Baqonka fa annabinka,babu komai na bar matan,nima na huta ko?,jibi sai mu hadu" haka kawai yaji ranshi ya baci kamar yadda ran sj'ad din ya baci,duk da taji dadin bar matan data yi amma sai ta tsuke fuska ta hau daddanna waya,harara ya jefeta da ita ya janyo plate din salad din wanda ada yake zumudin ci amma manarta ta sanya kaso hamsin cikin dari na shauqin salad din nashi ya tafi,ganin tana niyyar miqewa ya sanyashi cewa su'ad "Daukomin cumputer na a daki" a kasalance ta miqe,daya daga cikin abinda ta tsana ya aiketa tana zaune tana hutawa,qafa ya sanyawa sumayya dake niyyan barin wajen,ai kuwa ta fado samansa baki daya,ruqon tsauri yayi mata wanda ya sanyata jin zafi,ta saki qaramar qara "Wa ya baki iznin yin kyauta da kwananki ba tare da yardata ba?sabida kin tsaneni" idanu ta qwalalo sannan a shagwabe tace "Gani nayi ta fini buqatar ka" "Ok,ke kin gaji dani kenan?" "A..a'ah...ba haka bane bafa" "Kin gudu ne baki tsira ba,zaki biya bashin da sai kin gwammace bakimin kyauta da kwanana ba,oya miqe kiyi feeding dina" ya fada yana sakinta,boyayyen murmushi ta saki,itakam bai dameta ba hakan,saboda tana son ta shiryawa wannan zamanne sosai,sai ta sanya su'ad ta banvance tsakanin aya da tsakuwa,zata gane matan areea ba kanwar lasa bane kamar yadda take hasashe.      Gabansa ta tanqwashe qafa cikin wani irin salo da ita kanta bata san tana yi ba ta soma zuba masa cikin plate,baki daya ya raja'a a kallonta har baisan da isowar su'ad ba wadda ganinsu haka take jin kamar ta sanya bakin bindiga ta harbe sumayya,baisan me yasa take daukan hankalinshi haka ba,komai tayi daban yake ganinshi da na saura,hannu ya sanya ya amshi cumputer din ya budeta,kan ta gaka zuba kasa salad zuwa lemo ya soma danne dannenshu,tura plate din tayi gabanshi "Bismillah"bai dubeta ba yace "u seen what am doing,so feed me" ya fadi yana bude bakinshi" "Amma rana ta ce nike da right da zanyi feeding dinka ba ita ba" tayi hanzari katse sumayya,sai kawai sumayyan ta tura spoon din bakinshi ba tare data dubeta ba,tamkar ma wani qwarin gwiwa taji ta qara mata,sai da ya hadiye na bkinshi sannan yace "Ki bari idan kin girka naki sai kiyi feeding dina,ba adalci ta hada ke kuma ki bani,gwara ra qarasa ladan" kusan da biyu ya fadi hakan,tun ba yau ba yasha fama da ita kan ko ruwan coffe ta hada mishi amma bata taba gwadawa ba,kanta ta dauke don ita din ma tasan bazata taba yarda ta shiga kitchen da sunan yi masa abinci ba,sam ba zata iya ba,ai ranan tana jin qila sai ta kwanta asibiti an qara mata ruwa,ina zata iya shaqan qaurin abinci warin gas da zafinshi. *YA UBANGIJIN ANNABI MUHAMMADU KA ZABA MANA SHUWAGABANNI NA GARI,YA ALLAH KANA GANINSU,KA SANSU,KASAN FILI DA BOYENSU,ZAHIRI DA BADININSU,ALLAH IDAN AKWAI MUMMUNAN NUFI DA QUDURI BOYE CIKIN ZUCIYARSU KAN BAYINKA,ALLAH KA KARYASU KARYUWAR DA BAZASU TABA DORUWA BA HAR ABADA KO WANE SHI YA ALLAH,ALLAH KAI KACE MU ROQEKA ZAKA AMSA MANA,ALLAH KAYI MANA WANNAN GATAN,KADA LAIFUKANMU SU SANYA KA SALLADA MANA SHUGABA AZZULUMI MARA IMANI,ALLAH KAYI MANA GATA ALFARMAR SHUGABA MASOYINKA DAN GATANKA ANNABI MUHAMMAD S A W* *BANDA NI CIKIN RIKICIN ZABE,MU JEFA QURI'ARMU CIKIN NUTSUWA DA BIN DOKA,ALLAH YASA MU DACE,SAI ALLAH YA KAIMU RAN LAHADI KUMA IDAN MUN SAMU DAMA* SUBHANAKALLAHUMMA WABI HAMDIKA,ASH HADU AN LA'ILAHA ILLA ANTA,ASTAGFIRUKA WA'ATUBU ILAIKA *mrs muhammad ce*👑✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 9⃣1⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *Allah S W T yana cewa* *HAQIQA DAN ADAM MAI YAWAN ZALUNCI NE MAI KUMA BIJIREWA* ______________________________________ Sai da ta kammala bashi sannan ta tattare dukkan kwanukan dake wajen tayi kitchen da su,ta tsaya ta daurayesu ta maidasu muhallinsu,daga kitchen din ta lallaba ta shige dakinta,fin bata son komawa cikinsu,bata ga ma amfanin komawar ba baki daya,sai data shiga toilet ta sake wanka,ta sauya kayan bacci sanda ta nufi gadonta. Shiru tayi saman gadon ita daya,juyi ta dinga yi daga wannan bangare zuwa wanacan,baki daya dakin yayi mata girma da fadi,ta manta yaushe rabon ta xa kwana ciki daya ita daya kamar haka?,qwan wutar lantarkin dakin da aka kunna shi ya sanyata yin firgigit ta daga kai,almustapha ne tsaye bakin qofa harde da hannahenshi,sanye yake da kayan bacci ruwan hoda kalar da su'ad tafi so kenan,sun masa kyau sun haska kalar fatarshi,idanunshi a kanta ya dinga takowa a hankali har ya qaraso inda take,shigowanshin bai sanyata tashi zaune ba,tana daga kwancen take kallonshi irin kallon qasan idanun nan,wani abu ke sukan zuciyarta. Kai tsaye gadon ya hauro bai bata lokaci ba ya danneta ya aza mata nauyinshi,murya qasa qasa yace "Baki damu da ni ba ballantana ki tsaya muyi sallama ba ko?" Qoqarin tureshi take ta miqe saidai ta kasa,cikin nishi tace "Ba haka bane,bacci nake ji shi yasa" dagowa yayi yana duban fuskarta yayin da taqi yarda ita din ta kalleshi "Uhummm,yaushe kika fara qarya?,ko dama can maqarayaciyar ce,idan bacci kike ji me ya hanaki yi yanzun?" "Akwai abinda na tsaya yi ne" dagata yayi yana 'yar qaramar dariya "Gaskiya ne,coffee nazo ki hadamin in sha kafin na kwanta" ya ambata yaba gyara wuyan rigar baccibsa wadda ke da V shape,dagowa tayi ta dubeshi "Amman ita yafi cancanta ta dafa makan,tunda gunta kake" ta fada tana qoqarin hadiye kishin dake taso mata,eh tabbas ya sani ita zata dafa din,amma shi kansa yasan wasa ne ma,ta yaya su'ad din zata iya wani dafa mishi coffe koda ta iya bayan yasha wanka ta harde saman gado tana jiranshi?,hasalima ita ta bashi daman ya kira masu aikin gidan su dafa mishi "Bazan samu ba kenan?" Kai ta kada tana yunqurin sauka daga kan gadon,binta yayi da kallo,kayan duk da na bacci ne amma sun amsheta sosai,ta sake kyau a idanunshi,saukowan shima yayi ya biyo bayanta,ta dora hannun saman hijabinta da niyyar sanyawa ta fice ya riqe hannun nata,dagowa tayi suka hada idanu "Muje na rakaki kitchen din,a haka nake son ganinki" ba musu ta saki ya sanyata a gaba suka fice. Cikin kitchen din yana tsaye jingine da freezer hannunsa harde a qirjinsa,duka motsinta da kaikawonta idanunshi na kanta,komanta a nutse a tsaftace abun burgewa,ta gama komai ta zuba cikin dogon cup wanda yake da riqe zafi ta miqa masa,hannu biyu ya sanya ya amsa yana murmushi,tun kafin yasha din kwadayi ya kamashi,qamshin ya cika masa ciki,baisan yau wanne kalar coffe tayi masa,ganyayyakin da yaga tana hadawa dabanne "Thank you" ya furta a tausashe,har cikin zuciyarta lafazin ya sauka,sai ta samu kanta da maida masa martanin murmushinsa "Albarka nake son ka sanyamin" ta fada a kunyace,murmushinsa ya fadada "Qwarai albarka tafi lafazina na thank you,Allah yayi miki albarka" ya maimaita har sau uku tana amsawa da amin,gaba ya sake sanyata suka fice,sai dayaga ta shige corridor dinta sannan ya juya ya haura sama da tea din hannunshin,don a bedroom dinta na qasa tayi kwanciyarta bata ma yi sha'awar hawa na saman ba. ***** ****** ***** **** Misalin sha daya da rabi ne na safiyar washegari,yana tsaye kanta sanye da wani lallausan yadi ruwan qwaiduwar qwai,hannunsa zube cikin aljihun wandonshi yana dubanta sanda take shiryawa,baki daya ji take jikinta kamar ba'a jikinta yake ba,kwana sukayi jiya suna abu daya ba cikakken barci,gashi yau tunda asussuba ya tasheta wai tayi wanka tayi sallah,hakanan ta tashi ba don taso ba,ta tsani yadda yake tilasta mata tashin asubar nan,agogon hannunshi ya duba,tunda gari ya waye ba wanda ya fita a dakin shi da ita "Ki sauri zamu je mu gaida su ummee ne kada baba ya fita" tamkar ya soka mata wuqa a qahon zuciyarta haka taji,me zata je tayi musu,magulmatan mutanen? "Gaskiya bazan samu zuwa yanzu ba kaje kawai na shiga daga baya" take yanayin fuskarshi ya sauya,me take nufi?,a hakanne take cewa ta sauya zata dinga duk abinda yake so?,ashe ma wasu halayen ta dado?,tunda ada ko sau daya a rana takan shiga ta gaidasu sai gashi yanzun tana neman sake bijirewa "Kada ki yadda su'ad,kada ki yarda tun ba'a je ko ina ba tafiyar nan ta sake watsewa,kada ki yarda raina ya baci kan hakan?,sai na maimaita miki abinda na fada miki jiya kenan ko?,to iyayena sunfi min kowanne mutum muhimmanci da daraja cikin duniya koda kuwa wane shi,ba'a haifi macen da zata rainamin iyaye ba wallahi ko ita din wace" ranta ya sake baci,biyayya tamkar wanda suka shanye?,tana son zaman lafiyarta hakan ya sanya ta miqe ta soma lalubar kayan da zata sanya,riga da wando ta dauko cikin kayanta ta soma qoqarin sanyawa,wani kallo ya watsa mata "Ki nemi wasu kayan ki sauya,kin daina wannan shigar matuqar ba ni da ke bane kawai" kasa daurewa tayi tayi kicin kicin da rai "Wai duka meye haka ne almustapha?,me ya shiga kanka ne ya canzaka haka?" "Tunani da gayara.....dole ki sauya kamar yadda kike ganin kamar na sauya,sabida wannan shine dai dai" "Amma meye hadin sauyina da tufafin da zan sanya" soma takawa yayi zaya fice daga dakin,ya fuskanci idan ya tsaya biye mata sai ta sanyashi ciwon kai "Ki sauya kaya na mutunci ki sameni qasa,fine..." Ya fadi yana bude qofa ya fice daga dakin,kayan data debo din ta watsar gefe daya cikin huci,hakanan tana ji tana gani ta shiga dakinta ra dauki atamfa riga da skert ta sanya,sai yalolon mayafi data yane kanta da shi ba tare data damu da daura dankwakin ba,duk da dai sun matseta amma sunfi wadancan. Tana cikinsu anty farida huda da amira dake falon ummee suna hirarsu tamkar sun shekara da sabawa da sumayyan,karyawa suke a qasan tiles din falon husna na saman cinyarta tana bata tea kadan kadan da cokali yayin da suke karyawa suka sauran banda ita,tun takwas ta kasa komawa bacci bayan ta farka daga dan baccin da ya kwasheta bayan sallar asuba,hakan ya sanya ta miqe ta shiga kitchen,cikin awanni biyu tayi kunun gyada da alala lafiyayye,ta diba nata ta ajjiye sannan ta samu wasu warmers masu kyau ta zubawa ummee da baba,wanka tayi ta shirya cikin shadda maroon mai adon milk doguwar riga ta yane kanta da madaidaicin milk din mayafi ta fita,taci sa'a kuwa ta tadda ummee zata wajen baban ta bata nashi bayan ta bata nata itama,tayi zamanta cikinsu farida suna hirarsu gwanin sha'awa wanda a baya basu samu wannan damar ba. Sallamarshi ta sanya dukansu waiwayowa suna amsawa har da sumayyan,saidai ita ta dauke kanta ne taci gaba da baiwa husna tea din da takeyi,har ya qaraso idanunshi na kanta,ta iya shigar hausawa ainun,duk yayin da tayi shiga takan tuna masa da ummensa zamanin quruciyarta,bazai manta salon adonta ba,husna tayi kyau a hannunta tamkar diyarta,kujera daya suka zauna da su'ad din wadda tunda ta shigo sumayya ta tsone mata idanu,a ladabce suka gaisheshi baki daya ya amsa yana tambayar farida ina yaran tunda yaga yaran huda a hanya,tace jiya abbansu yazo ya daukesu,sunyi kaduna gidan kakanninsu za'a soma bikin qanwarshi next week,ba yabo ba fallasa suka gasheta kasancewarta matar yaya a wajensu duk da sun girme mata,ta amsa hanci a sama,don babu wanda bata jin haushinsa,tana ganin duka bakinsu daya da shawararsu aka kwaso mata abokiyar zama,sumayya ta dan waiwaya kadan ta gaidashi,sai ya amsa mata kamar sauran,cikin basarwa da dakiya,wanda hakan ya dan sosa ranta,zuciyarta tasi karyewa,ta tuno rayuwarta gidan mukhtar tsakanin fa'iza da zainab,rayuwar gidan lukman da karima,kada fa ace dare daya tak zai soma sauya mata,ya rusa dukkan wata alaqa data soma ginuwa tsakaninsu,zuciyarta ta daure ta gaida su'ad wadda bata kulata ba tunda suka shigo gun,amma itama ganin ta girmemeta yasa ta gaidata din,banza tayi da ita tamkar ba da ita take ba,falon ya dauki shiru,itakam ko a gefan takalminta,don ta saba ganin hakan wajen kishiya,tunda ta sauke nata nauyin falillahil hamdi,har sai da almustapha ya maida wayarshi aljihu ya dubeta ta gefe daya "Ba dake ake ba?" "Lafiya lau" ta fada a dake,zuciya ta zowa amira wuya,haushi ya tuqeta,don me ma sumayyan zata gaidata,me yasa batayi watsin tsiya da ita ba itama,shine zata zo tana ma mutane dagawa da daga kai?. Shigowar ummee falon ya sanya su miqewa,ummee ce ta tsaida sumayyan saura suka shige ciki,a ladabce cikin qauna da kulawa ya gaidata,ta amsa fuskarta fadade da fara'a,su'ad itama ra gaidata kadaran kadaham,duk da tana jin ba don almustapha dake wajen ba wallahi ba zata gaidata haka ba "Ya kika baro su khaulat din" sai data raya,munafuka kamar gaske cikin zuciyarta sannan ta amsa da "Lafiya lau" "To masha Allahu" "Inaga sai kayi hanzarin zuwa ka tadda baban naka,don ina tunanin zai fita,na barshi yana karyawa" "To ummee" "Me za'a kawo maka me zaka ci?"ta tambayeshi tana dubanshi,kunya ta kama sumayya ta sadda kanta qasa,tana ganin kamar ummee zata ga ita din ma ta gaza tunda gashi yana shirin komawa 'yar gidan jiya cin abinci wajenta,saidai ita ummeen tuni ta fahimci cewa yau ba kwananta bane,indai kuwa hakanne kamar yadda take zato ba shakka bazaya samu abin kari ba saidai yaci a waje "me kuka dafa?" "Akwai tea,akwai chips,sai farfesun kayan ciki da amira tayi,sai kuma amiran umman khalipha data kawo alala da kunun gyada" satar kallonta yayi sanda ita kuma taje duban wani waje,duk da sarai taji alamun yana kallonta din,yaushe rabon shi da yaga kunun gyada ko alala ya mance tsahon lokacin,yaushe har ta tashi ta gama dukkan wadan nan ayyukan har ta shirya ta fito "A kawomin abinda ya samu" duban su'd dake hakimce ummee tayi "Su'ada shiga kitchen zaki ga kayan jere,ki deba masa abinda zai iya cinyewa" dauke kan da ummeen tayi ya sanya bata lura da sauyawar fuskar tata ba,gani take da gayya ummeen tayi mata haka,ita waccar baqauyar me ya hana ta aiketa sai ita,wanzuwar almustapha a wajen shi ya takawa abinda ta taka burki,miqewa tayi cikin bacin rai ta nufi kitchen din. A qalla sai data bata wasu mintuna masu dama kafin ta fito dauke da farantai kamar wadda ta dauko duniya,ba zata iya tuna ranan data shiga kitchen tayi wani aiki kamar haka ba,tana isowa ta saki tray din har da suka tsorata saboda yadda ta soma yarfe hannu tana kiran Allah,hanzarin kama hannun yayi yana dubawa,tsammani yake ko qonewa tayi,saidai ba haka bane,daukan kwanukan da tayi takewa haka,tsam ummee ta miqe saboda takaici "Idan ka gama ina saman" ta fada tana niyyar haurawa,sai sumayyan itama ta miqe ta rufa ma ummeen baya,binta yayi da kallo kamar ya dakatar da ita,domin ko gaisuwar da sukayi bata yi masa ba,ji yake kamar ya shekara ne bai ganta ba,amma sai ya dake ya maida kallonsa ga su'ad,hararar wasa ya jefa mata "Raguwa,sai kace wadda ta qone,oya....yi serving dina" tamkar wadda tayi aikin shekara haka ta dinga zuba abincin,wani bakin kwanukan duka ya baci. Da kansa ya haura saman don kiran sumayyan suje su gaida baban,umme ta gaya mishi tana daya dakin tare da su farida,sanda ya shiga anty farida na toilet,huda ta shiga kitchen damawa yaronta madara,sai amira dake zaune kusa da sumayyan wadda ke rabawa husna gashinta tana daure mata shi suna hirarsu qasa qasa da amira da alama gulma suke,turo qofanshi ya dakatar da su,idanunsa har yau a kanta,da idanu ya yima amira alamun ta fita,tsam ta miqe "Koma ki dauketa" ya nuna mata husna da ido,komawa tayi ya dauketa daga cinyar sumayya ta fice,bata motsa daga inda take ba sai ta wayance ta karkade jikinta duk da ba wami qura ko gashinda ya zuba,ta soma hada qananun ribbom din dake zube qasa tana maidawa cikin ledarshi,gabanta ya qaraso ya tsugunna,ya riqe hannunta tsam dake tattare ribbom din,sai ra dagi ta dubeshi da fararen idanunta "Shariya?.....ni zaki dinga sharewa haka?,hmmm lallai yarinya bakisan waye almustapha ba" zuciyarta ta karye,wani irin qaunarshi lokaci guda taji tana kutsawa cikin zuciyarta,kallon da yake mata kadai na dabanne,zuciyarta ta raurawa wanda batasan dalili ba,ta shagwabe masa ba tare data shirya ba "Ni kuma?.....me kuma nayi?"sai tsugunan ya gagareshi ya zauna sosai a gabanta "ki tashi da safe baki neme ni ba ki fice binki?,kiyi breakfast abunki duka babu ni?,kin daina damuwa da ni ko?" "Ni vance haka ba sai kai zaka fadi?" Ta furta a zuciyarta,ta bude baki zatayi magana qofar bandakin ta bude,anty farida ce ta fito,ganinsu a hakan ya sanyata qara mai ta fice a dakin "Ya man abun ya motsa kenan,yanzun ne ake baje kolin da da ba'a baje ba" take gulmarshi cikin ranta a haka ta qarasa dakin umme tana tuntsirewa da dariya "Me haka lafiyarki?'ummee ta tambayi farida "ba komai ummee,eata soyayya na gano ana bajeta yanzun nan" shiru ummeen tayi tana ci gaba da sabgarta,don ta gane inda zancan ya nufa. "So kake naje na buga muku qofa?,ko so kake na yi ma abinci ba ranar kwana na ba?" "Ko?" Ya fada yana dage mata gira tare da kallon lips dinta da suka burgeshi,shiru tayi ba amsa,tana qoqarin sadda kanta ya riqe fuskarta,sai da ya tsotsi lebunan son ranshi sannan ya kamata ya miqar tsaye "Muje mu gaida baba",yana tsakiyarsu haka suka jera,kowacce da abinda take ji cikin ranta. Ranar kusan wuninta tayi wajensu huda,sai da yammaci laila tazo da su khalipha harda hafiz,nan ta dinga kwasarshi " kai kam hafiz rashin son jama'arka ya baci wlh,yanzun sai yau zaka zo gurina"dariya yayi "Kiyi haquri anty sumayyanmu" basu bar gidan ba sai wajen gab da magariba,bayan laila ta bawa sumayyan saqon da anty dijen ta kawo mata. Washegari gidan anty dijen ta yiwa tsinke,da qyar ya barta,sai da hamza ya kirashi zasu fita sannan ya mata tattaki har qofar gidan ta shige,sosai taji dadin wunin wajen antyn,ta rabauta da sirrika masu yawa,da kanta ta baiwa antyn kudi a sake kawo mata dilkar nan saboda yadda ta karbi fatar jikinta,saidai a sanyaye ta dawo gida saboda albishir da antyn tayi mata na cewa uncle farouq ya sanyi gida zasu tashi daga nan,hakan ya daga hankalinta,amma abun alkhairi ne ci gaba ne ya samesu dole ta tayasu murna. Sanda ta dawo gidan gimbiya su'ad na zaune a falon qafa daya kan daya,an tsuke ana danna waya,yayin da ma'aikatan ta da aka dawo mata da su suke kitchen suna girka abincin dare,ko sallamarta bata amsa ba,itama bai dameta ba tunda ba zamanta take ba,ta wuce dakinta kai tsaye abinta,sai data gama duk abinda take sannan tayi wanka,sallar magariba ta soma yi,ta shirya cikin riga da skert na atamfa,tana son atamfa har cikin zuciyarta,lite make up tayi ta murza daurin dankwai sannan ta fesa turare,ta dubi kanta a mudubi yadda fatarta ta sake kyau,juyawa tayi ta fice a dakin don shiga kitchen ta samarwa kanta abinda zata ci kafin akira isha'i,tunda kowa zai dinga girkinsa ne shi da mai gidan ranar girkinsa. Har yanzu tana falon zaune,saidai wannan karon ta sauya kayan jikinta,riga da wandon ne amma fari da yellow,fukarta radam da makeup,tsaki ta jiyota ta ja sannan ta furta "Villager,always atamfa atamfa,thats d problem of arewa women" maganarbummee na kada ta soma yarda suyi cecekuce ta fado mata,don haka ko ta waiwayo ta dubeta batayi ba bare ta nuna taji abinda take fada,bata da lokacin cecekuce sam tana tunanin ta wuce wannan babin,a da can zamanin da take da qananun shekaru ma bata yiba ballantana yanzu?,daqiqi shike maimaita aji amma ba mai qwaqwalwa ba,kai tsayi ta nufi kitchen,gab da zata shiga qofar tata kitchen din ma'aikatan suka fito sanye da unifoarm da warmers da suke shiryawa wajen dining,a ladabce suka gaisheta,ta amsa musu fuska sake tayi gaba,tana jiyo ashariyan da su'ad ke dura musu saboda gaidatan da sukayi "Uban wa ya dauko ku wa kuke wa aiki?,zaku koma inda kuka fito wlh duk randa naga wata na mata wani abu,talaka talaka ciwon kai ne wallahi" kai ta gyada tana mata fatan shiriya,ita sam mai aiki ma bata burgeta bata cikin tsarinta,idan bata tashi ta yi hidamawa gidanta ba daga wayewar gari zuwa faduwar rana to meye amfaninta?,taci ta kwanta tayi bayan gida?,idan ya cika akwashe?,abinci mai sauqi ta dora cikin tukunya mafi qanqanta a cikin tukwanenta,cikin kitchen din ta zauna hannunta harde a qirji tana tunani kadan kadan har ta kusa kammala ta juye ta fito. Tana fitowa a kitchen din yana shigowa falon,da ita ya soma tozali tunda tana tafiya ne zuwa dakinta,boyayyen murmushi ta saka tana son basarwa,saboda duba daya tayi masa ta karanci tsantsar gajiya tattare da shi,batasan ina hamza ya jashi ba dai yau kam,ido daya ya kashe mata alamun na ganki ne zamu gamu,ta kauda kai tana masa sannu da zuwa,yana amsawa ta kutsa kai corridor dinta abinta ta barshi da su'ad wadda ta taso da dan hanzari tana tsammanin wajenshi sumayyan ta nufa,murmushi ya sake mata kamar yadda ta sakar masa,saidai baki daya rabun hankalinshi na gun sumayyar,wayoyinsa ya miqa mata ta karba yana kama qugunta "Kinyi kyau" ya furta yana kallonta,idanunta ya juya kanta na kumbura,a duniya tana son taga ta fifita fiye da kowa,tana son taga tafi kowa,sama suka haura tana zuba masa yauqi. Turus yayi sanda ya dubi bathtube din yaga wayan babu ruwan wankan da ya sanya ran samu ciki,yana daga bandakin ya qwala mata kira,ta ajjiye wayarta da take dannawa ta amsa cikin qosawa ta miqe,tunda ta dawo ta tsiri chart da qawaye da abokai tunda yanzu ba'a kusa ba kuma ranar komawa,da idanu ya mata inkiya da bahon wankan sai ta tambayeshi me yake nufi "Ruwan wanka" hannunta ta yarfar sannan ta taka a hankali ta soma tara masa ruwan "Ka fara zama sangartaccen,naga da kai ke hada ruwan dear da kanka ko?,gaskiya an bata min kai" ta fada sanda ta duqa yadda bazai iya gano fuskarta ba taba hade rai "U can go if you can'nt do it" "Sorry" ta fada cikin wani salo,yana tsaye har ta gama hadawar ya zare towel dinshi ya shige,ruwan ya masa zafi amma bai tanka mata ba ya miqa hannunshi ya kunna famfon ruwan sanyi ya saisaita zafinsa. Hannunshi riqe da cokali yana dubanta har ta gama zuba mishi ta zauna a gajiye "Kai,wai dama haka hidimar aure take?,dole mata su dinga cewa aure akwai wuya" ta fada tana langabe kanta tana dubanshu,haushi bai barshi ya tanka mata ba,sai yaja plate din kawai gabanshi ya sanya cokali ya fara ci,duka duka me tayi yau din?,zai iya lissafa dukkan abinda tayi da yatsun hannunshi "Dearrrr" ta fada a shagwabe "Ni zanyi feeding dinka nima yau"ware hannyenshi yayi sannan ya ajjiye cokalin,ta matso cikin zumudi ta soma bashin,ci kawai yake,sai yake jin akwai banbancin dandano mai girma tsakanin girkinta da wannan girkin,hakan ya ma su'ad daidai yadda take bashi abincin ya mata dadi,saidai zata so ace sumayyan na wajen,don itama ta cusa mata haushi "dear ka kira ta mana ko akwai abinda yayi mata a nan ta diba?" Hakan ya burgeshi,sai yayi zaton hankali ta soma,ba musu ya janyo wayarshi ya kirata. Wayar na hannunta tana neman number malam tunda ta kira ta mama bata shiga ba,gaidashi take sonyi,tunda ta zubo abincin taji ta kasa ci,baki daya cikinta ya cushe bayan yau ba wani abun kirki taci ba,a nutse ta daga kiran ta amsa,to tace sannan ta miqe,sai data sake tsayawa gaban mirrow ta sake shafa hoda ta mutstsika turare sannan ta fito,idanunta ya sauka kansu sanda take kai cokalin abincin bakinsa,da hanzari ta dauke kanta zuciyarta na bugawa,sai ta dinga karanto la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalilm,tana gayawa kanta matarshi ce,kema kinyi gabanta,so meye itama don tayi,dubanta yake sanda take takowa,fuskarta sake da murmushi har ta iso,dadi ya kama su'ad,sai ta sake tura plate din gabanshi tana ci tana bashi "Sannunku,wai *our man*, wannan abinci sai da ruwa ko anty na,let me help you" wani kallo ya jefeta da shi mai cike da ma'anoni masu tarin yawa sautin muryarta dab da kunnenshi na ratsashi,,salon maganar kadai abar burgewa ce,sumayyan ta balle murfin gorar ruwa ta tsiyaya cikin cups guda biyu ta tura gabansu "Thanks" inji almustapha "No thanks,albarka" murmushi ya sake yana hadiye lomar bakinsa "Allah yayi albarka,ga abinci wai ko zaki ci?"ya fadi cikin ginshira da ajjiye kowanne lafazi d'ai d'ai,Sai ta soma bude warmers din,ba abinda ya bata sha'awa,ta qarshe ce taga farfesun zallar tsoka da kayan lambu,sai ya bata sha'awa har da hadiyar yawu,sam bata so ci ba amma sai ta tsinci kanta da zama sosai ta sanya plate ta dibi gwargwadon wanda take tunanin zata iya cinyewa "Wannan ya isa" ta fada tana duban su'ad wadda take jin wani abu ya tokare wuyanta,sam wannan dabarar batayi ba,me zata yi mata ne ta huce? "Na gode anty" ta fada tana sakar mata murmushi,don ta tabbatar ba'a banza tasa aka kirata ba,akwai wata a qasa,koma meye ta tura mata aniyarta,juyawa tayi a nutse ta wuce abunta zuwa dakinta,ba haka su'ad sam taso ba,taso taga zallar bacin rai baqinciki da kishi idanunta,idan da hali ma ta tanka ayi bacin rai,kuma daga bisani ta janye almustapha su wuce sama,hakan ya dagula ranta,fara'arta da walwalarta ya ragu sosai har suka kammala suka bar wajen. Tana shiga ta tadda wayarta na ruri,amira ke kira da yake tun jiya almustaphan ya kora kowacce dakinta,ta ajjiye plate din ta daga kiran nata tana zama gefan gado fuskarta qunshe da murmushi,suka soma gaisawa cikin barkwanci,ta tambayeta ummee ta bata saqon wani dabino tace "eh,na meye ne?" Dariya ta sanya "Sai kinci kawai basai na gaya miki ba"nan ta gaya mata yadda zata dinga ci kafin su shiga wata hirar kuma,tsahon mintuna talatin kafinnsuyi sallama,ta sauke wayar ta maidata silent saboda dare,idanunta ya sauka kan farfesun data shigi da shi,murmushi ya subuce mata,itakam tasan akwai dalilin yi mata tayin da su'ad tayi,bata manta lafuzan data jefeta da su ba dazu,sannan ta lura da kallon data bita da shi,haqiqa jiya ba yau ba,ita din yanzun ba yarinya bace,zata iya banbance salon kowanne kallo da kishiya tayi mata dai dai gwargwado,sai ta sake sakin murmushi tana kada kai tare da neman tsari kan duk wani sharri,sake nadewa tayi abunta ba tare data bi takan dukkan abinciccikan ba,nata da nasun ta soma danne dannen wayarta,duk yadda taso taqi cin farfesun amma sai qamshinsa ya dinga cika mata hanci,yawunta ya dinga tsinkewa,janyo shi tayi ta sanya spoon ta fara ci,idanu kawai ta dinga lumshewa dadin na ratsa harshenta,bata ankara ba ta tashi da kwanon baki daya,mamakin kanta ya cikata,itadai tasan ba wani hadi na musamman aka yi masa da zai sanyata santi haka ba har ta iya tashi da shi,hannunta ta wanke a toilet gami da yin brush,ta kuskure bakinta da hadin kayan qamshin baki sannan ta sauya kayan bacci ta dawo ta nade saman gado,wani irin bacci ya dinga fusgarta bata ankara ba tuni yayi awon gaba da ita. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 no✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 9⃣2⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *Assalamu alaikum warahmatullah MY DEARS FANS* *ina son nayi amfani da wannan damar damun wajen sanar muku da cewa,lallai ne ni da sauran marubuta 'yan uwana muna buqatar ku dinga yi mana uziri* *nasan cewa akwai da dama da suke turon saqonni na gaisuwa da tambayoyi ta numberta,saidai wani lokaci saqon yakan iya yin kwana biyu uku sati daya zuwa biyu ma wani bai samu reply ba,hakan baya rasa naba da yawan saqonnin da nake fama da shi,nakan samu saqo wallahi sama da dubu takwas cikin wayata daga na groups zuwa private charts,banda na Wattpad,face book kuwa wannan sai na samu lokaci ma,kunga idan kuka duba abun da yawa,ka zauna kayi typing mai tsaho,kayi editing,ka tura cikin duka groups din da kake ciki,akwai masu comment ka zauna ka amsa musu,kunga baki daya wannan lamarin bazai yiwu ka iya aiwatar sa shi lokaci daya ba,sau tari wasu basa fahintar haka har wani ma kan gaya maka baqar magana saidai kawai ka shanye kayi masa kawaici* *masu numberta kuma ta kira da sukemin plashing don son annabi su daina min plashing,wlh bana qaunarsa,sannan kiran dare,'yan uwa dare fa mahutar bawa,wasu kuma kira da asuba,su fadar maka da gaba ka dauka wani mummunan abu ne ya faru,wanda yake kira kuma bana dagawa shima yayi uziri,wayata a silent take ban fiya barinta a ringing ba,wasu lokuta kuma ina rejecting to sometimes ina typing ne idan layin yana cikin wayar da nake typing da ita.* *ina fata fans kun fahimceni,duk wanda yaga yayi min magana baiga reply ba yayi haquri,wani saqon na danne wani idan sukayi yawa,sau tari ma idan ina online ka turo shi yana sama sama ina qoqarim amsawa,mu dinga yiwa juna uzuri,nasan duka qauna ce kuma na gode,Allah yasa mu dace ya bamu ikon ci gaba da haquri da juna* ______________________________________       Kusan a makare ta tashi,idanunta cike taf da bacci tayi sallah,saman abun sallar ta sake bingirewa bacci na fusgarta,sama sama ta jiyo muryanshi,tsaye yake a kanta cikin farar jallabiya yana kallonta,bata tantance shi sosai ba ta gaidashi tana daga kwancen idanunta na lumshewa,cikin mamaki ya amsa yana kallonta,sai yaga ta juya taci gaba da barcinta,ya jima tsaye yana kallonta qudundune cikin hijabi,yana mamamin wanne irin bacci take haka?,tsawon wasu daqiqu yana tsaye kafin ya juya ya fice.         Qarfe tara na safiya ta sake farkawa,barcin tamkar bai isheta ba,ga mutuwar gabbai,sai ta shige bandaki tayi wanka saboda taji qwarin jikinta,duka dai sammakal,amma dai kasalar ta ragu,gaban madubi ta shirya cikin gown mai A shape ta wani material mai kyau,ta yane kanta da qaramin mayafi wanda ya dace da material din ta wuce kitchen,falon fes yake da alama masu aiki sunzo sun gyara duk da dama ba datti yake yi ba,rasa abinda zata dafa tayi,ta jima tsaye tana tunani,sai kawai ta dauko dankalin turawa ta fere,ta dora a wuta ta dafashi,ta sauke ta murmusheshi,kifin gwangwani ta bude ta murmusheshi saman dankalin,ta zuba mai a kasko tu juye dankalin da kufin,a hankali take juyawa tsawin mintuna sannan ta kada qwai ta yanka albasa a kai da maggi ta juye kan dankalin da qwan taci gaba da juyawa har sai da qwan shima ya soyu sannan ta juye a plate,ta tsiyayi ruwan shayin da yaji kayan qamshi ta fito falo.        Kacibus sukayi da anty ni'ima matar yaya adam,cikin fara'a ta sauya akalar tafiyar tata "A'ah,anty ni'ima,shigo mana" itama fuskarta dauke da fara'ar ta qaraso,duka sukayi masauki saman kujerun falon,sumayyan ta janyo center table ta dora plate da cup dim hannunta suka soma gaisawa da ni'iman sannan tayi mata tayi,abun ya burgeta duk da bata san meye ba ko ya akeyi,ba musu ta sanya hannu suka soma ci,sumayyan ta tambayeta ko a zuba mata ruwan zafin tace alhamdulillah,wannan ma ya isa,suna ci suna hira tamkar sun shekara tare.         Tas suka tashi da shi,ni'ima ta kalli sumayya "Kai amiran umman khalipha,wannan abun yayi dadi,amma fa akwaisa kwadayi,ya ake yinshi?" Dariya ta saki "Kai anty ni'imah,simple abu ne fa" a tsanake ta kwatanta mata yadda tayi din sannan ta dauke farantan tayi kitchen da su ta dawo suka ci gaba da hirarsu.          Tare suka sauko tana biye da shi a baya,ji take tamkar ta dawo da kwanakin baya,bata so ta tuna cewa yau zata sallamawa waccar 'yar qauyen mijinta da tafi so fiye da komai a duniya,sam fuskarta babu walwala haka suka ci gaba da takowa,muryar ni'ima ya jiyo,ya waiwayo ya dubesu,cikin girmama juna suka gaisa,sannan sumayya ta gaidashi tana dan dauke kai,kishinsa itama take ji har cikin zuciyarta,saidai bata son ta nuna,dining din da masu aiki suka shirya da kayan kari suka nufa,yayin da ni'imah ta miqe "Bari na wuce,ko wajensu ummee ban shiga ba" sam bata son ni'iman ta tafi,taji dadin zuwanta,sai ta miqe tana fadin "Bari na dauko mayafi mu shiga tare,nima ban je ba" tana nan tsaye sumayyan ta shiga daki ta dauko mayafinta,hankalinshi na kansu duk da yadda su'ad ta tare gaba da baya,da biyu take yin komai,a nutse ta qaraso bakin dining din a ladabce tace "Zanje mu gaisa da su umme ni da anty ni'imah" ba tare da ya dago ba yace "Ni din ma banje ba,ta wuce ma taho" sam bataji dadi ba,sai ta dawo a sanyaye "Anty ni'imah tare zamu fito" murmushi ta sakar mata "ba damuwa sai kun fito"daya daga cikin kujerun dake falon ta samu ta zauna tana jiranshi ya kammala,tana iya jiyo duka abinda su'ad ke fadi,hirar darensu na jiya take ta sako mishi yana basarwa,jin bacin rai na neman mamayarta ya sanyata miqewa tsam tayi shigewarta dakinta.         Tana gaban mudubi tana gyara zaman kayan makeup dinta ya shigo cikin nutsuwa,har yanzu ranta a bace yake,sai taqi dagowa ta dubeshi duk da yadda take jin tsaretan da yayi da idanunshi "muje na kammala"ya fada a a taqaice "Kuje na taho" itana ta maida masa da yanayin da yayi mata maganar,sarai ya fuskanci ranta a bace yake "Muje nace" "Nace na taho" shiru ya ratsa na wasu muntuna "Ummu abdallah" da hanzari ta daga kai ta dubeshi,ita yake kalla da shanyayyun idanunshi masu dauke da wani irin magadisu mai qarfi da tasiri,yana kallon yadda cikin kwana biyu fatarta ta skma sauyawa tana wani qyalli,ko idanunshi ke mashi gizo?,ya tambayi kansa,shidai yaga sauyi qwarai tattare da ita,kawar da kanta tayi,saidai sunan yayi mata dadi har cikin ranta,cikin qaramin lokaci ya soma saukar da sanyi a ranta,shima sai ya dauke nashi kan,ya taka zuwa inda mayafinta yake ya dauko,ya iso gabanta,sai ji tayi ya soma yafa mata yana fadin "Idan baki shirya takawa da qafafunki ba,am ready to carry you,komai ta fanjama fanjam" dan qanqani daga cikin aikinsa kenan,hakan ya sanya yana gamawa ta motsa tayi gaba yabi bayanta.         Kamar jiya haka suka rankaya su ukun baki daga,saidai ita bata dawo bangaren nata ba sai wajen qarfe biyu,bayan ta bada saqon abubuwa da take ganin tana da buqatar amfani da su,bayan ta kammala sallar azahar din dakinshi ta haura,dai dai sanda su'ad ta fito cikin heavy makeup,idanunta manne da sun glasses da cogen takalminta tana karkada muqullin mota tare da taunar chewing gum ta fice bayan ta watsawa sumayyan wani banzan kallo,kau da kanta tayi itama tana jan tsaki,ya ilahi batasan ma me yasa take kishin almustapha haka ba.         A yamutse ta tadda dakin,ita ta gyara kowacce kusurwa ta dakin,ta dauko sabon zanin gado ta sauya,ta gyara toilet,ta hada dukkan under wears dinshi ta tsaftace da hannunta ba tare da taimakon washing machine ba ta shanya cikin toilet din,tana saukowa aka kawo mata saqon,ta amsa ta nufi kitchen kai tsaye.        Lafiyayyar sakwara ta shirya tare da water leaf soup,wadda taji ganyen water leap,ogun,ganda,tsokar na da stock fish,blander ta jawo ta niqa aya da kwakwa da dabino ta hada lemo ta sanya a fridge,nono mai kyau da aka siyo mata ta hada da fura ta dama bayan ta wats kwakwa a ciki ta saka shima cikin fridge,sai data tabbatar da kammaluwar komai sannan ta rufe kitchen dinta da key,don bata mance rayuwar da sukayi da fa'iza ba,wuyat data sha kasancewar kitchen dinsj daya,kalanzir gishiri,suger duka a girkinta,murmushi ta saki tana rayawa a ranta,duniya labari,ko ina fa'iza ta shiga yanzu ohi,Allahu A'alamu.      Lokaci ta bata sosai a toilet tana murje jikinta,ita kanta mamakin yadda fatarta ke sheqi da laushi tayi,saidai tana ganin kayan gyaran jikin data yi amfani da su ne suka amsheta,kwalliya tayi maras yawa saidai ta dace da kyakkyawar madaidaiciyar fuskarta,ta sake kuma fito da armashin kyanta,ta jima tana saqe saqen wanne kaya zata saka,wando ta ciro belted high top wide leg trouser ash colour ta hadashi da long sleeve t.shirt fara qal wadda aka yiwa adon ash daga wuyan rigan zuwa qasanta,kisonta ta raba jelar gida biyu ta kama kowanne da qaramin ribbom ash,ba qaramin kyau tayi ba,duk wani tudu da kwari na jikinta ya fito turarukanta na musamman tayi amfani da shu,wadanda qamshinsu ke tashi a hankali har su gama cika hancin mutum,kwalabar turarenta babba ta dauka bayan ta kammala komai,ta zira wani irin plate din farin takalmi mai taushi ta soma bin duk inda burner take a gidan tana zuba turaren,a haka har ta qaraso falon.         Tana durqushe kusa da burner din dake bakin matattakala tana zuba turare a ciki taji an bude qofar sashen,batayi tsammanin ganin kowa ba hakan ya sanya ta fito haka,a nutse ta juya,almustapha ne a gaba su'ad na biye da shi "Hasbunallahu wa ni'imal wakil" ya ambata yana lunahe idain nasa sanda idanunshi sukayi tozali da nata,karon farko da ya soma ganinta cikin suturar da ta bayyana duk wani structure ta jikinta,su'ad dinma idanuwanta na kanta,mamaki da kishi suka cikata,take wani bacin rai ya lullubeta,dama yarinyar tasan sanya ire iren kayansu?,ba sai an gaya mata tahowarta din nan taga shigen kayan a shagon da take siyayya acan,taso siyosu saboda tasan zasu burge almustapha kuma sun burheta itama,bugu da qari kayan sabbin design ne da suka fito sati sati uku kacal da suka wuce,amma saboda kudin hannunta yayi qasa ta haqura,kishin yanayin halittar da Allah yayi mata ya cika mata zuciya,ba zata manta ba har mai ta saya na qara mazaunai da qirji amma almustapha ya hanata shafawa,ya zaunar da ita yana gaya mata irin illolin dake tattare da irin wadan nan mayukan da kuma na bleeching,duk da bata taba bleeching ba ita,natural farinta ne,to amma ko banza yau gashi ya dauko mai abun,ita tana zaune,kewayeshi tayi ta wuce corridor dinta da zaya kaita ga dakinta kai tsaye,zuciyarta na tafasa,kamar ta shaqe kanta,ta wurga jakarta saman gado tare da tuje mayafin kanta ta wurgar shima tana yamutsa gashin kanta "No....no,it can't" ta dinga maimaitawa tana girgiza kai,sai ta sake takowa a hankali ta dawo corridor din nata,ta tsaya tsakanin labulayen da suka rabata da hango falon kai tsaye,ta sanya hannu ta yaye labulen ta yadda zata iya hangosu.       Tattausan murmushi ya soma sakin mata idanunshi cike taf da mayen qaunarta,ita dinma duban shi take fuskarta dauke da murmushi,duban cikin idanunshi kadai sun gamsaf da ita,wani irin qauna take ji na daban na ratsata,qwafin gwiwa game da shi take ji,ya bude dukka hannayenshi yana mata alama ta taho,sai ta noqe kai kamar qaramin yaro yaso quya cikin wani salo na daban,ya motsa bakinsa cikin muryarsa da har gobe take sake daukaka darajarshi cikin idanunta "Don't kill me babe,taho please" a yangance ta soma takowa,sai ya kasa jiranta har ta qaraso inda yake,ya soma shima takawa a hankali suka hade tsakiyan falon,kyakkyawan masauki yayi mata a qirjinsa yana sakin wawuyar ajiyar zuciya,baisan ta taka wannan matsayin cikin zuciyarsa ba karo na biyu sai a yau ya sake tabbatarwa,qamshin dake tashi kawai jikinta ya isar masa samun nutsuwa da kwanciyar hankali,sumbarta ya soma yi a ajejjere tako ina cikin nuna zallar soyayya da shauqi.        Cikin matsanancin tashin hankali ta saki labulen ta shiga dakinta a sukwane ta soma ball da jakarta data yar a bakin qofa "No almustapha,no,why u r doing this" ta ambata tana dukan bango da hannunta,kana ta tafi saman madubinta ta soma watsar da dukkan abinda ta gani samanshi suna sauka qasa gami da tarwatsewa saman tiles,wannan bai isheta ba sai data dauki kwalbar turarenta ta doka jikin madubi,tunu ya tarwatse dai dai ya kuma yi silar yankarta.         Qarar wannan fashewar kayayyaki ita ta dawo da almustapha hayyacinsa,idan dai dai kunnuwansa ke jiye masa daga dakin su'ad ne,cikin hanzari ya raba sumayya daga jikinsa ya juya zuwa dakin,hawaye shabe shabe ya sameta tanayi bayan tarwatsa gashin ta dake daure da tayi,bata damu ba tana ci gaba da jifa da dauk abinda hannunta ya kai kai ciki har da t.v plasma dake manne a bangon dakin ta kwada mata make up kit din data wawuro,riqota yayi yana ambatar "Meye haka su'ad,hankalinki daya kuwa" yunqurin qwacewa take "Leave me almustapha,leave me" ganin haukar tata da gasje take ya sanyashi daka mata tsawa wadda ta sanya sumayya dake tsaye falo hankalinta yayi matuqar tashi "U r mad?!,baki ganin wai me kike yi ne?" "I know almustapha,am going to kill my self ma gaba daya" tsatstsauran riqo yayi mata sanda yaga tana laluben kwalabar dake farfashe a wajen,ya damqeta baki daya ya hankadata saman yamutsatstsen gadonta,ranshi ya kai qololuwar baci,sai kace tabin jinnu?,yanzun nan fa suka shiga gidan tare lafiya lau,binta gadon yayi ya mata riqon tsauri tana gunjin kuka tare da yunqurin qwacewa.          A qalla sun tasamma kashe mintuna goma a haka kafin ta soma sassauta haukan da take yi,sai kuma kuka da taci gaba da yi,cikin fargaba da nutsuwa sumayya tayi sallama bakin qofar dakin,a karon farko kenan,sanye da dogon hijabinta har qasa,waiwayowa yayi da jajayen idanunshi ya zubeta kanta,wadda ita kuma idanunta ke qarewa yadda dakin ya hargitse kallo,ko bai bata amsa ba ta soma hasashen abinda ke faruwa,ba zata manta ba,ba zata manya daren data yankeshi a hannu ba sanadin kishi "Jeki am comming,everything will be okey" kai ta jinjina ta juya ta fice,idan da tasan ma abinda ke faruwa kenan ba zata bata lokaci ta shigo duba abinda ke faruwa ba,ranta ya dinga baci,me mata suka mayarda kishi ne?,tabbas babu halittar da bata da kishi,kishi halitta ce,kuma dole kayi kishin abinda kake so,hatta dabba tana da kishi,to amma meye amfanin hankali kenan?,meye amfanin ilimi?,meye amfanin girma da shekaru?,sai ta tsinci kanta ta mai jan tsaki data tuna zainab fa'iza karima ga kuma su'ad.         Miqewa yayi cikin takatsantsan don ma qafanshi da sau ciki ya laluba inda suka ajiyan kayan akwatin taimakon gaggawa,ya qaraso inda take,har yau qwalla na bin idanunta,tsugunnawa yayi ya soma mata dressing inda ta yanke ba tare da yace komai ba,idonta na kanshi ta soma maganganu cikin dashewar murya,tsaf ya fahimci abinda ya jawo mata aikata hakan,baya ga kishi har labe kenan ta soma?,abinda ya tunzura shi kenan,yana jin kamar ya dauketa da mari zuciyarsa na tausarshi,har ya kammala wanke mata tsaf,yayi kama hannunta ba tare da ya dubeta ba yayi mata allurar rage radadin ciwo ya maida akwatin muhallinsa ya juya da niyyar ficewa,qam ta riqe hannunshi ciki marairaicewa "Kada ka tafi ka barni na roqeka almustapha,kada kaje wajen yarinyar nan,duk abinda kake so zan maka" idanunsa da suka sauyi launi kadai da ya watsa mata ya sata laushi kaso hamsin cikin dari "Sake ni!" Ya fada a tsawace,sakin nasa tayi yaja baya baki bude tana kallonshi har ya fice a dakin,a falo ya tsaya ya fiddo wayarsa ya kira ummee yace ta turo ma'aikatan nan dakin su'ad zasuyi dan wani aiki,ya gama ya maida wayar aljihunsa ya wuce bedroom dinshi.        Har suka zauna cin abinci alamun bacin ran basu sakeshi ba,hakan ya matuqar taba ranra itama,yana zaune saman dining ya hade hannayenshi waje guda yana dubanta,qoqari yake ya saita kanshi don kada ya shiga haqqinta ko ya sanyata damuwa kamar yadda yaga kuzarinta ya soma raguwa,baki daya warmers din ta bude wanda take qamshi ya cika wajen,sai ta koma kujerar dake daura da shi ta zauna,idonta cikin nashi tana sakar masa murmushi,a hankali ta sanya hannunta saman hancinsa ta ja madaidaicin hancinsa da ya zauna das bisa fuskarshi ya qawata kyawunsa "Me zaka iya ci ciki mu gani?,kai din cikakken bahaushe ne?ni duka ma fa nakeso ka cinye" ta qarashe maganar taba dage masa girarta,murmushi ya subuce masa lokaci guda,ya raba hannyenshi yana rarraba ido tsakanin kwanukan,abincin da ya jima baici ba kenan,kusan ya manta ma da ita a jerin abinciccika,ya maida kallonshi kanta "Kina son miji lukuti me qiba kenan" qayataccen murmushi ta saki masa "Idan na cinye wannan abincin duka yau anan gun zan kwana,bazan iya kai kaina daki ba" dariyar data riqe ce ta subuce mata,ganin yadda ya soma kwatanta yana shafa sumar kanshi "Dariya kike?,ke zakiji a jikinki,don ba lallai ki iya daukan lukuti ba idan na qara qiba" kunyar maganar ta bata,sai ta soma gunqurin zuba masa abincin yana binta da kallo,komai nata burgeshi yake sake yi duk kwanan duniya,dabi'u da al'adun masu burgewa da kuma mabanbanta kullum yake sake gani wajenta,wasu ya manta da su tana tuna masa su daya bayan daya,wasu yana sane da su saidai baisan inda zaya gansu ba yau gasu cikin gidanshi a gabanshi,spoon ya amsa da niyyar fara ci,sau ta langabe kai tana dubanshu,yau wani irin abu take ji yana fusgarta zuwa gareshi "I promise to feed you when we r together" "Thanks" ya fada murmushin na fita a fuskarshi "No" ta fada tana girgiza kai,ya gane mai take nufi,zuwa yanzu ya fara fahimtarta,tafi qaunar ya sanya mata albarka fiye da godiya,hakan baya rasa nasaba da muhimmancin albarkar wajenta fiye da godiyar,shima hancinta ya ja "U r smart,barakallu fiki" "Wa laka" itama ta maida masa,ta debi abinci ta kai bakinshi da cokali,sai yasa hannunshi ya amshe cokalin ya ajjiye "Da hannunki nakeso ki bani" ba musu ta sanya hannun,ta miqa bakinsa yayi bismillah sannan ya soma amsa,kasa cewa komai yayi sai jinjina kai da yake a fakaice,wasa wasa sai gashi yaci leda hudu,ya dubeta suka hada idanu sai suka qyalqyale da dariya baki dayansu "U r the best cooker apart from my mom da na sani" yabon yayi mata dadi qwarai,sai ta jangi jug na tana tsiyaya masa lemon da tunda ta fara zubashi ya zuba masa idanu,ta cika glasa cup ta kai bakinsa,ya kurba,sai ya cire yana duban cup din tare da hadiya na bkinshi "Kunun aya?" Kai ta gyada masa,dariya ta subuce masa,yayi qas da murya "Kinsan barnar da yake min ko?,halan kin shirya gyarota" ido ta zaro don har ga Allah batasan komai a kai ba,matsowa ya sake yi dab da ita,cikin kunnuwanta ya gaya mata komai,kunya ta sanyata sunne kai,sai yayi relax jikin kujera yana dubanta murmushi na fita a fuskarshi "Can you remember our first night?,the day i start......." Sai ya kasa qarasawa yana dariya "Hamza......shi ya hadani da shi,ashe gata yayimin,ya zama silar shigata wata sabuwar duniya mai qunshe da ababan mamaki da jin dadi masu tarin yawa,sai ta dire cup din tana dariya idanunta a qasa,riqe hannun nata yayi caraf yana fadin "Saikin qarasa bani ai,kin dandana min zuma a baki kuma ki janye,u r at my side ai,nasan ba matsala ko?" Haka ta dinga zuba masa yana shanyewa,ya masa dadi qwarai da gaske,cup biyu yasha qwarara sannan ya haqura jin yadda ya qoshi,ya jima baiji qoshi a jikinsa irin hakan ba.         Darene data kaishi wata duniya da bata taba kaishi ba,duk wani hanya data sani da wadda ya koya mata wadda ke tafi da mutum sai data masa,abinda ya sake sukurkutashi kenan,ya kuma sanyashi tafiya mai nisan gaske cikin kogin sonta.         Suna idar da sallahr asuba ta dauke wayoyinshi baki daya ta kashe,taci alwashin maida shi mutum mai cikakken lokacin kansa,tayi alqawarin rage masa jibgin sabgogi da hidindimu da yake wuni yi,walau yana kano abuja america ko dubai,babu hutu cikin lokutansa baki daya,tamkar kuwa ta sani yau qarfe goma na safiyar zaiyi taro da dukka ma'aikatan asibitinsa dake abuja,sannan sunyi da hamza zasu je yaga gonakin da suka siya domin fara noman auduga,wanda hakan zai sake habaka kamfaninsu,tare da rage musu kudaden da suke kashewa wajen sayen zare da auduga wajen wasu kamfanoni na waje,hakan kuma zai kuma samar da ayyuka ga matasan qasarmu.        Tana gaban mudubi tana qarasa daurin dankwalinta goma na safe sanda almustapha ke kwance saman gado yana bacci nannade cikin bargo,cikin cikakkiyar nutsuwa da kwanciyar hankali,knocking aka fara da qarfi tamkar an samu bangon dakin,barin abinda take yi tayi tana tunanin waye?,sai ta dauki turarukanta ta fesa sannan ta nufi qofar ta bude a hankali,su'ad ce a wani birkice,babu wannan kwalliyar kwata kwata tattare da ita,neman hanya take kawai zata sanya kanta cikin dakin,lura da haka ya sanya sumayya rage fadin qofar ta hanyar karo qofar ta riqeta a hannu,sauran wajen da yayi ragowa kuma ta tsaya tana dubanta "Anty su'ad lafiya kuwa?"kallo ta watsa mata mai siffar harara "bake nake nema ba matsa kiban waje" murmushi ta saki cikin kwanciyar hankali da nutsuwa "Kin manta kin shardanta cewa kowa dan girkinsa ba ruwan miji da 'yar uwata?,ke kika fadi hakan,amma kasancewar nasan akwai haqqinki rataye bisa wuyanshi bazan hanashi ganinki ba,amma banda yanzun don Allah,don bacci yake,yana buqatar isashshen hutu,amma idan ya tashi na gaya masa" "Ke baki isa ki hanani ganinsa ba wallahi" ta fada a zafafe,sai kawai sumayya taja baya ta kuma maida murfin qofar ta rufe.         Baqinciki ya hanata aikata komai,sai kawai ta juya ta sauka tana laluben wayarta ta nemi almustaphan kawai,saidai kash ta buga rashin sa'a tunda sumayya ta jima da kashesu,batayi tsammanin ya farka fa,saidai tana waiwayowa suka hada ido da shi,yana zaune daram yana kallonta,hannunsa ya bude mata fuskarshi a dan tsuke cike da miskilanci,a nutse ta iso gareshi ta fada jikinsa a tausashe ya maida hannu ya rufe "Hausa girl" ya rada mata a kunneta,shigar atamfa tana mata kyau tana kuma burgeshi,dalili da ya sanya take yawanyi itama kenan "Meyw dalilin kashemin wayoyi,sannan aka qi tashina?,kina son na soma halin da ba nawa ba karya alqawari?" Ya fada har yanzu tana jikinsa,kai ta girgiza "You need some rest" "I know,kuma nima bansan fitan,ya kamata ace idan nazo qasata ina hutawa sa iyalaina kadai basai wani sabgar ya shigo cikin wadan nan lokutan ba,sai yanzu na gane muhimmancin hakan.....amma duk da haka zanje meeting da ma'aikata a asibiti,so ki shirya,zaki min rakiya?"kai ta gyada masa,sosai taji dadi,ko banza zata miqe qafa,tunda tazo banda gidan anty dije bata je ko ina ba "Ok,shirya min ruwan wanka" "Jiranka ma yake" ta furta itama cikin salon rada,sai ya matseta cikin jikinsa "Kina son hanamu fitan ma kenan baki daya ko?" Da sauri ta girgiza kai tana dariya,don tasan me tayi masa "Dagani to" ya fada yana dubanta,ta janye jikinta a hankali sannan ya miqe ya shige toilet din.         Tare suke saukowa baki dayansu,cikin shigar cikakkiyar bahaushiya take,plain zani da riga fitted,tayi daurinta das biasa kanta,lullubinta har saman ka,yayin da ya kasance shi kuma cikin yadin kufta da aka yiwa aiki irin na gidan sarauta,cikin kayan da ya bayar ayi masa tun daga randa ya fahimcu ire iren shigar na burgeshi, "Wait" ya fadi yana nufar wajen su'ad,gefan kujera ta samu ta zauna tana tsumayinsa.        Fitowarta daga wanka kenan daure da towel,tana ta qamshin shower gel dinta mai matuqar tsada da take amfani da shi duk din saboda tattalin fatarta,ranta a quntace yayi sallama,ciki ciki ta amsa shima don tasan yadda suke qarewa da shi idan bata amsa ba,abu na farko data fara shine qorafin taje wajensa sumayyan ta mata rashin kunya,ta kira wayoyinshi kuma a kashe,bai ko tanka mata ba ya duba ciwukan nata "Suna zafi har yanzu?"kai ta girgiza tana tabe baki,ya qarasa bakin mudubinta ya ajjiye mata kudi "baka ce komai ba na maka magana but ka share" ita batasan bacin ran mutum bane?,a nutse hannayensa cikin aljihunsa ya dawo inda take tsaye "Bakisan abinda kika aikata jiya ba dai dai bane?"kafada ta daga "to sai me,kishinka nake kuma dole na nuna"idanunshi ya zuba mata wanda ya sanyata rusunar dole ta janye nata idanun,cikin bacin rai yace "Wannan ba kishi bane hauka ne,kin dauki aqidar da ba taki ba kin yafawa kanki?,daga ranki ya baci saiki hau yanka kanki koki yanka wasu?,zubar jini wannan baki daukeshi a bakin komai ba?,zan miki warning na qarshe,kinyi na farko kinyi na biyu,kada ki yarda ki sake na uku,if not zan dauki mataki a kanki,take note" ya fadi yana juyawa ya fice a dakin,tabbas ba qaramin illa baqin al'adu ke mana ba da yaranmu,sai yaji baki daya zaman wata qasar bashi da fa'ida karon farko a rayuwarshi,ya tabbatar sanda suna zuwa islamiyya a america da su'ad bata yaye kanta ta daina zuwa ba wasu halayen nata ba zasu ta'azzara har haka ba. Wajen ummee suka fara biya,cikin farinciki ta tarbesu suka gaidata,farinciki fal ranta,yau almustapha ne ya kusa dosar sati biyu a abuja bai nemi komawa inda ya fito ba,wanda ta tabbatar da da ne da tuni ya koma din,a qalla ma yayi kwanaki uku kacal,sallama suka yi mata ta rakasu da addu'a suka fice,suka gaida anty mama sannan suka wuce,don baba ranar baya nan,sun fita shi da su mahmoud angwaye.          Kana ganin asibitin kasan nashi ne,baida maraba da na kano har tsarin ginin,tun a hanya yake karbar gaisuwar ma'aikata manya da qanana,yana riqe da hannunta har suka shiga babban office dinsa,ya mata mazauni kan daya daga cikin kyawawan kujeru masu siffar duniya dake office din,baki daya ma'aikatan asibitin ba wanda baisan da zuwanshi ba,hakan ya sanya kowa ke cikin taitayinsa,landline dake office din yayi amfani da ita,aka tabbatar masa da cewa duk wanda ya dace yana babban dakin taron dake asibitin suna jiranshi,ya ajjiye wayar yana dubanya,itama shi take kallo,yanayin jagorancinsa na burgeta,yasan abinda yakeyi,komai nashi kan doka da tsari yake "Zanyi missing dinki na kusan two hours,ko zaki rakani muje muyi meeting din mu dawo?" Hakanan taji tana sha'awar binsa,murmushi ta saki tana gyada masa kai,hakan ya masa dadi,ba musu ya kama hannunta bayan ya dauki laptop dinshi da yake ajjiye record na komai suka wuce.        Cikin girmamawa ma'aikatan suka miqe baki dayansu,bai tsaya ko ina ba sai kan babbar kujerar da take tashi ce shi daya,janyo mata ita baya yayi,ta dubeshi sannan a hankali cikin nutsuwa ta zauna,daga kai yayi ya baiwa kowanne damar zama kowa ya koma mazauninsa,laptop dinsa ya bude a gabanta ya kunnata,yana tsaye kan sumayyan har komai ya daidata,wani cikin ma'aikatan ya miqe yana daukan kujerarsa ya kai masa,hannu ya daga masa yayi qaramin murmushi yace ya barshi ya gode,tsaiwan ma is ok,a hankali suka soma tattauna abinda ya tarasu,tsahon wasu mintuna,ya waiwaya da niyyat soma shigar da abubuwan da yake buqata,a fakaice yake dubanta cikin mamaki,tuni tayi misa wajen shigar masa da muhimman batutuwan,cikin qwareea da nutsuwa,baisan ta iya sarrafa computer haka,saboda bai taba ganin ta taba masa tashi ko ya ganta da ita ba,kawai sai ya dora hannunshi saman nata hannun dake kan madannan computer din ya dan matsa a hankali alamun dariya,murmushi ta saki ba tare data dago ba taci gaba da abinda take. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 9⃣3⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *ya Allah ka sanya farinciki a zukatan musulmai,ya Allah ka wadatar da talakawan cikinsu,ya Allah ka qosar da duk wanda ke cikin halin yunwa,ya Allah ka dawo da matafiyanmu lafiya,ya Allah wanda bashi ya masa yawa ka biya masa,ya Allah ka tufatar da wanda ke cikin tsiraici,ya Allah duk wanda ke da mummunan hali cikin musulmi ka gyara mana halayyarsa,ya ubangiji dukka wanda yake cikin tsananin baqinciki ka yaye masa* *ya Allah* *ka fada cikin qur'aninka mai girma* *idan bayina suka tambayeka game da ni kace musu lallai ni makusanci ne* *ya Allah* *kai kayi umarni da mu roqeka(zaka amsa mana),ka kallafawa kanka amsawa(addu'ar bayinka),ya ubangiji ka amsa mana,ka biya mana dukkanin buqatunmu,ka cika mana burikanmu ya ARHAMAR RAHIMIN* _____________________________________          Ya jima zaune saman table din office din yana duba yadda ta shigar da komai a tsare,wani abun ma da shi bai taba yunqurin dubashi ko shigar da shi ba,murmushi ne keta fita a fuskarshi,ya dauke idanunshi sanda ta fito daga bandaki bayan ta daura alwala zata tada sallah,da kallo yake binta,yana jin cewa ya samu wata babbar kyauta ne daga Allah,cikin watanni Allah ya sauya rayuwarshi sauyin da bai taba zaton akwaishi ba.         Har ta sallame sallar yana zaune yana dubanta,sai ya miqe ganin ta gama yana daukan hularshi wadda tun dazun yake cireta yana riqeta a hannu saboda rashin sabo "Lets go,muje muyi lunch" ya fada yana dubanta,ta shafa addu'an ta waiwayo,cikin shagwaba tace "Kashe kudi ko?,muna da komai a gida muje na dafa maka wani abun" kai ya girgiza "Gida?,ba yanzu ba,ba yanzu zamu koma ba",bata sake tankawa ba juya ta janyo jakarta ta bude,ta fidda qaramar hoda ta gyara fuskanta,ta ciro turarenta ta matsa a hannunta ta goge jikinta da shi,yana daga tsaye qamshin ke dukanshi,sai ya tako ya tsaya a bayanta,ya riqe hannunta dake riqe da turaren yakai hancinsa,lumshe idanu yayi "I love iy,ina son wannan qamshin" murmushi ta saka,ta maida turaren jaka suka jera suka fito.         Tafiya ta wasu mintuna suka qaraso qofar katafaren wajen cin abincin,wajen cin abinci ne da kusan duk wanda ke garin yasan da zamansa,domin yana dacewa da duk yanayin da kake so,kaman almustapha da baisom cin abincin cikin jama'a,yakan kama waje na musamman wanda yake kaman VIP,saidai yana da tsada fiye da sauran guraren,qofar shigar wajen ma na musamman ne kamar yadda kujeru da teburan wajen suma suke na daban.          Daya daga cikin ma'aikatan wajen ne ya qaraso cikin rawar jiki,don ya tabbata yau sunyi babban kami,cikin girmamawa ya rusuna ya gaidashi,ya amsa sanda ya miqa hannu yana amsar na'urar dake hannunshi ya soma duba abubuwan da yau suke da shi,bayan ya zaba yawa can kitchen din sending na abinda yake buqata da number sit dinsu kamar yadda tsarin wajen yake sai ya tura na'urar gabanta,dubanshi tayi ya mata alama da idanu ta zabi abinda take so,maida idanuwanta tayi kai ba tare data taba ba tana qarewa list din kallo,haka kawai taji babu abinda ya bata sha'awa a ciki,hannunta yakai kan irin abinda yayi order itama ta dannan kawai ta daga wayan da niyyar miqawa ma'aikacin,almustaphan yahi saurin karba daga hannunshi ya miqa masa ya karba ya juya ya bar wajen,ya motsa bakinshi da niyyat cewa wani abu wayarshi ta soma ringing,sai ya fasa fadin abinda zaya ce din ya soma laluban wayarsa dake aljihun wandonshi duk da bai dauke idanunshi daga kanta ba,ta rasa wane irin kallo ke wannan duk sa'ad da suke tare,duk yadda taso ga yawaiya dubanshi idan suna tare ita kasawa take saboda nauyi da kunya,yana soma amsa wayar kamar hadin baki tata wayar ta dauki ringing,ta cirota a jakarta tana dubawa,halima amarya ce,murmushi ta saka cikin nutsuwa ta daga suka soma gaisawa,daga bisani ta miqawa abdallah dake kusa da ita,aifa nan ya dinga zuba yana bata labarai kala kala,harda labarin ya gama nursery one zai shiga nursery two,idanunta ta lumshe tana tasbihi ga Allah,ba shakka shekara kwana,a yanzu a qalla abdallah ya tasamma shekara biyar kenan,tun tana daurewa har ta biye masa ta dinga sakin qaramar dariya,abdallah badai wayo ba,hatta cikin halima sai da yace cikin mummy ta zama qato yace baby zata siyo mana sabuwa,sai data gaji sannan tace "Baiwa mummyn to wayar,duka ka cinye mata credit" haliman ya miqawa sukayi sallama,ta kashe ta soma qoqarin maida wayar jaka "Ummu abdallah" taji ya ambata a tausashe,daga kanta tayi tana dubanshi,sai yanzu ta lura,tunda ta fara wayan idanunshi na kanta,kunya ta dan kamata ta janye idanunta,qasa qasa yayi da murya tare da matsowa dab da ita "Ya kamata nima a bani nawa abdallah haka.....i need him tunda an hanani wannan ko?" Kai ta sunne tana murmushi,ya bata kunya ba kadan ba salon yadda yayi maganar,dai dai da isowar ma'aikata biyu dauke da abincin nasu,suka ajjiye gabansu suka jiya suka wuce,ba bata lokaci ya warware spoon dake nannade ya sanya cikin abincin ya soma ci a nutse kuma a yangance,itama cokalin ta sanya saidai ta kasa kai koda loma daya bakinta,gaba daya abincin taji bai mata ba kuma,duk da yadda yayi kyau tun a ido balle a kai baki,yana ankare da ita,naman dake gefan abincin ta jawo ta cinyeshi tas,suna hada ido ta kau da kai,take kunya ta kamata,batasab me yasa ta yin haka ba,hannu ya daga ya kira wani ma'aikacin wajen da yazo kawowa wasu mata da miji da suka shigo yanzu wajen nasu order din "Kuna da meat haka,gasashshe?" Cikin rusunawa yace "Eh amma ranka ya dade ya qare saidai ko zata jira,amma akwai farfesun kayan ciki" "Jeka kawo" ya fada yana yagar tissue ya gige bakinsa,komawa yayi ya jingina da kujera yana dubanta,duk sai kunya ta dabaibayeta "Nifa bana ci" ta fada a dake "Bake dama nace a kawowa ba" ya bata amsa yana ci gaba da nazarinta,mintina qalilan ya dawo dauke da bowl na tangaran mau kyau ya ajjiye sannan ya juya ya tafi "Bude wannan bowl din ki dauka kici,bance kuma kice wani abu ba" ya qarashe maganarsa yana jan wayarshi yana dannawa cokalin ta ajjiye ta jawo bowl din ta bude,habawa wani yawu ta hadiya kaman mayya,farfesun kayan ciki ne hanta tumbi qoda sai zuciya,ajjiye murfin tayi ta saka cokali ta soma kaiwa baka,wani dadi ya ratsata,kaman ta dauka ta juye a cikinta ta huta da tauna haka ta dinga ji,ci kawai take ba kama hannun yaro,bata ankara ba sai ganim kwanon tayi babu komai saura romo,sai a sannan ta tuna da wanda ke gabanta,ta daga kai kamar munafuka ta saci kallonsa qasa qasa,ita kuwa yake kallo,mamakin yadda take cin abinci haka yau a gabanshi a sake yake yi,yayin da ita kuma take zaton naman da yaga tana ci ne,sai ta bata fuska ta janyo tissue din itama tana goge bakinta,kanshi ya dauke yana murmushi qasan ranshi "Wai itama lallai bata son raini" ya fada a zuciyarshi yana miqewa,ma'aikacin ne ya sake dawowa,almustapha ya miqa masa atm card dinshi yace su cira kudinsu su kawo masa card din mota.         Sallaman drivan yayi ya amshi muqullin motar,da kanshi yake tuqasu,motar shiru sai sanyin a.c dake ratsa jikkinansu,hakan yayi tasiri wajen haifar mata da kasala,kafin kace wani abu bacci yayi awon gaba da ita,cikin mamaki ya taba qirjinta,ya akayi bacci ya dauketa haka da wuri?yake tambayar kansa,ya dan tabata kadan ta bude idanunta wadanda suka dan qara girma saboda baccin da ya dauketa "In daukeki ne?" Ya fada yana daga mata gira,kafada ta noqe kamar yarinya,sannan cikin kasala ta zuro qafafunta waje ta fito bayan ya zagaya da kanshi ya bude mata qofar,kallon gidan ta dinga yi kamar waccan karon,gidan da suka taba zuwa ne,murmushu ta saka qasan zuciyarta,gidan yana burgeta sosai,a haka suka dinga takawa har suka qarasa ciki,wayoyinshu ya zube ya kutsa bedroom din ya bude ya shiga da niyyar rage kayan jikinsa,zamewa tayi saman kujerar wani bacci mai dadi na sake kwasarta.         Tsayawa yayi cikin mamaki yana dubanta,daga shiganshi zuwa fitowarsa har ta sake wani baccin?,sai ya koma shima daya daga cikin kujerun ya dauki system dinsa ya fara aikin dake gabanshi.          Tsahon awa guda yana tsaka da aikinsa yaga miqewarta zumbur kamar wadda aka tsirawa allura,a gigice take neman hanyan toilet saidai ta rasa,kafin ta sake wani yunquri aman da take dannewa ya kubce mata,cikin wani irin zafin nama ya tareta sanda ta soma yunquri mai qarfi wanda yaso zubar da ita a wajen,yana riqe da ita har ta kammala aman baki daya,duk wani anu data ci daga safiyar yau zuwa dazun yafita baki daya daga cikinta "Kai na" ta fada tana dafe da goshinta saboda yadda yake sara mata kamar zai rabe biyu,sai da ya bata ruwa ta kuskure bakinta sannan ya riqeta har zuwa bedroom din ya zaunar da ita gefan gado,bata iya zaunawa ba sai ta sulale ta kwanta,wayarshi ya ciro ya sanarwa ma'aikatan su shigo su gyara wajen ya ajjiyeta cike da damuwa ya tako inda take,gabanta ya durqusa ya riqe hannunta cikin nashi "Me ya sameki haka?,daman baki da lafiya amma baki gayan ba?" Kai ta girgiza "Meke miki ciwo?" "Kaina.....da......" Sau ta kasa qarasawa duk da yadda mararta ke mutstsukarta "Uhmmm,dame?" Ya fada yana miqewa ya dawo kusa da ita "Marata.....Cikina" a hankali ya sakera ya miqe,kai tsaye dakin da ya ware cikin gidan tamkar qaramin asibiti na gidan ya nufa,ya duba magungunan ciwon ciki da na ciwon kai ya kawo mata,sai da ya tabbatar ta sha sannan ya umarceta ta kwanta,yana zaune gefanta hannunshi saman goshinta,addu'a yake tofa mata lokaci bayan lokaci haf wani bacci yazo ya fauceta.          Tun yana duba agogo har ya haqura ya daina,yana ganin tilas su kwana cikin gidan don bazai iya tashin ta ba,da qyar ta tashi tayi la'asar da magariba ta koma ta sake kwanciya,wayarsa ya ciro ya lalubi lambobin su'ad,ringig biyu ta daga "Ina ka tafi almustapha,wai me yasa baka ganin qimata ne?,bani da lafiya amma ka dauki matarka ku bar gidan tun safe har dare baka damu da halin da nake ciki ba?" Ta fada tana niyyar sakin kuka "Yanzun ma ba yau zan dawo ba,ina tunanin sai gobe,kada ki damu din baki ga shigowata ba ki rufe sashen kiyi kwanciyarki" bau tsaya jin me zata fada ba ya katse,don ya tabbata bacin rai kawai kunnuwansa zasu jiye masa,kiran hamza ne ya shigo ta daya wayar tashi ya daga yana karawa a kunnensa "Ya zamuyi haka dakai fisabilillahi ka ajjiyemu muna jiranka?" Banza yayi dashi kamar ba da shi yake magana ba,sai da ya mula don kansa yace "Kada ka saka min ciwon kai malam,matar gidan tace bata buqatar naje wani guri so kowa ma dole ya haqura da ganina" "Wace?,wai su'ad?" Ya tambaha cikin tantama,don dai itakam yasan haka bata taba faruwa ba,kuma bata isa hana almustapha ficewa ba duk sanda yaso "Shafa kaji" ya amsa masa cikin gatse,tuni hamza ya hasaso wace ce,dadi ya lullubeshi ya dinga tuntsira dariya,amma don tsiya sai yace "Wooo mutumina,yaushe mata suka fara juya akalarka?" "Kasan dai halina ko hamza,zan iya biyoka har gida wallahi naci maka dama ba yau muka soma ba" bai damu ba yaci gaba da kwasarsa har sai da ya katse wayar,texs ya dinga jero masa kan ya daga suyi maganar ya daina tsokanar,da qyar yaciyo kansa ya daga suka shiga maganar da zasuyin,tuni su hamzan sunje sunga guraren sunyi,zasuyi kyau da noman audug,an gama shurya komai ma kawai ma'aikata za'a samu shikenan a shiga aiki.         A hankali ta motsa tana bude idanunta,baki daya a yanzu wasai take ji bata jin komai,idanunsa a kanta yayi mata sannu,shi ya taimaka mata ta miqe duk sa bata jin komai "Kiyi wanka sannan kici abinci,me zaki ci?"dan shiru tayi sannan a hankali kamar mai tsoron fada tace "nama" "Irin na dazu?"kai ta gyada masa,miqewa yayi ya fice falo din bada oder ita kuma ta shige bandaki,a gaba ya sanyata bayan ta fito wanka ta shirya cikin kayan bacci,tana cin naman yana kallonta suna zaune a dandagaryar,dukkan alamu sun nuna tana jin dadinshi sosai,sai data kammala tace " ba gida zamu wuce ba?"kai ta kada "Noo,a nan zamu kwana,baki jin dadi sosai har yanzu ko baki fada ba na sani" kai ta mirgina,don bata son su kwana din hakan ya dasa wani abu a zuciyar su'ad "Am feeling better,zamu iya tafiya" "Am not feeling better ni kuma...." Ya fada yana jifanta da wani kallo hannunsa nade a qirji,hannunshi ya miqa ya jawota,ya ware qafafunshi ya sanyata a tsakiya habarshi saman kafadarta saitin kunnenta,cikin yin qasa da murya yace "Tunda muka zo gidan nan babu abinda kika bani ko qwaqwqwaran kiss ban samu ba,sai amai sai bacci.....you know gidan nan na love ne,shi yasa na kawoki.....me zan samu ne?" Kunyarshi ta kamata,ta sake kafewa a qirjinsa kanta na qasa "Wai ma na tambayeki......meke damunki?" "Dazu ciwon kai ne,amma yanzun ba komai" "Haka akeso......zan samu wani abun to?" Ya fada yana juyo da ita suna fuskantar juna,idanunta ta saka a nashi,sai ya kashe mata ido yana sake tausa murya "Pleeeeaaaase......ko kadan ne" a kunyace ta daga masa kai,ya miqe da hanzari yana dariya tare da dagata suka wuce babbar headquater. *****   ******   *****    ******              A safiyar ranar yana tsaye yana shiryawa gaban mirrow,yayin da itama taje tsaye gabanshi suna fuskantar juna,sanye take da da wata gown mai dogon hannu,wadda tsahonta bai qarasa idon sahu ba,mai roba ce rigar saboda haka tayi cif a jikinta tare da fitar da duk wani tudu na jikinta,baqa ce sai touches na fari,ta yane kanta da wani farin dan kwali mai tsaho don bai kai mizanin mayafi ba,sabuwa ce batasan da itaba cikin gidan da safen ya dauko ya bareta ya bata yace ta sanya tunda basu zo da shirin kwana ba,hannunta dauke da suit dinshi mai three pieces,neck tie,vest da safarshi,tana miqa masa da dai dai yana amsa yana sanya kowanne a muhallinsa a jikinsa,kusan hakan ta sabar masa,ita ke kiqa masa komai shi kuma yana shiryawa,babu magana tsakaninsu saidai salon kallon da kowanne kewa dan uwansa yana sadar da saqo kai tsaye zuwa gareshi ba tare da ya magantu ba,wani yare suka dinga amfani da shi a tsakaninsu dake wanzuwa tsakanin zuciya da zuciya,lokaci lokaci zaga daya daga cikinsu ya saki murmushi,a haka har ya kammala komai tsaf,yayi kyau cikin black nd white suit,ya kammala sanya safanshi ya dago,sai ya janyota jikinsa cikin ba zata,ta baya ya rungumeta ya dora hannayenshi a qugunta,sam taga ma kaman bai da niyyan maidata gida a yau din,a hankali ya ware tafin hannunshi ya soma shafo har saman damammen cikinta,sau da yawa yana mamakin yadda wai a haka har ta haihu amma har yau cikinta a dame yake,darensu na jiya kawai yake tunowa,irin jarumtar data nuna,shi kansa sai da yaji cewa kada ya cutar da ita fa "Yau zamu wuce gida ko?" Kai ya girgiza "Ba yau ba,saikin warke" narkewa tayi tare da rage fara'ar fuskarta duk da bai iya gajin fuskar baki daya sai gefanta "Amman anty su'ad fa yau girkinta ne" "I know babe,think dai sai magariba sannan aka shiga time dinta ko?,so sai na dawo tukunna,zan fita just one hour zan dawo,ya kamata na dinga hutawa hakanan" shiru ta danyi na wani lokaci "kin gaji da ni kenan ko?gwara mu koma gida?"baki ta bude tare da waiwayowa tana dubanshi,kai ta girgiza alaman a'ah,sai ya saki qaramin murmushi wanda ya sanyata sake juya masa baya itama tana dariya qasa qasa,mamaki wani lokaci yake bata,wai wannan almustaphan ne ya koma haka? "Me ya saki ciwon mara ne jiya?ina fatan ba irin na wancan karon bane"ya sauya akalar maganar "Nima ban sani ba" ta fada a shagwabe,sai ya sanya hannunshi saman mararta ya danna "Wash" ta fada saboda dan zafin da ta ji,cikin hanzari ya juyo da ita suna fuskantar juna,idanunsa cikin nata a rikice yace "Yaushe rabonki da al'ada?" Idanunta ta juya alamun tunani,idan zata iya tunawa tun sanda ya daukota ya taho da ita daga kano ba tare data shirya ba,idanu ya zuba mata yana ci gaba da kallonta,sai kuma ya kama tafin hannunta yana kalla kamar mai neman wani abu,wani irin riqo yayi mata "Please when last kika ga period dinki....tell me" sai ta tsorata ta fara zaro idanu ganin yadda ya rude lokaci daya,cikin rawar murya tace "Tun.....tun sanda muka taho daga kano....sanda nayi ciwon mara" riqeta yayi ya ajjiyeta bakin gado,binsa tayi da kallo sanda ya juya ya fice,dakin nan mai kama da qaramin clinic ya shiga,ya dauko syringe ya dawo ya sameta zaune,yana daga tsaye ya farke,idanu ta fiddo,idan akwai abinda ta tsana a duniya allura ce,rabinta da ita kuwa tun haihuwar abdallah,qarasowa gabanta yayi ua duqa,ya riqe hannunta ya janye hannun rigan yana duban cikin idanunta,tayi wani kicin kicin,qwalla kwance can qasan idanunta,ya gama fuskanta sarai tsoron allura take,sai ya basar ya daura farar robar da zata bashi daman ganin jijiya,ta runtse ido sanda allurar ta ratsata,ya zuqi iya jinin da yake so sannan ya warware mata robar ya zare syringe din ya miqe "Ina zuwa" ya fada yana nannade syringe din da tushu ya fice da sassarfa,binsa tayi da kallo sai da ya fice sannan ta janye idanunta,da baya ta koma ta kwanta cikin ranta tana tunanin me zaiyi da jininta kuma?,sai tsoro ya dinga shigarta,kada dai ace wata cutar ya gano a jikinta,gabanta ya fadi,sai ta gaza kwanciyar ta zauna daram samam gadon tana ambatar sunan Allah "Ya ilahi,kada dai a ce har yau ban gama bitar SHAFUKAN KUNDIN QADDARA TA BA" ta ambata a ranta hawaye na qwace mata tsoro na dabaibayeta,yanzu ina zata saka ranta ina ta nufa idan wani abu ya hango tattare da ita?,ta ina zata soma rayuwa bayan tuni ya riga data haqiqance wani qaqqarfan abu wanda idan har akwai abinda yafi so qarfi to ba shakka ya kama zuciyarta dangane da shi,ya riga da ya dasa shaquwa qauna shauqi da bege mai zurfi fadi da girma cikim qirjinta,tsoka da jininta "Ya rabbi ka kula da ni" ta fada wata qwallar na bin wata. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 9⃣4⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *Allah madaukakin sarkin yana cewa* *CENE DA SU HARAM DA HALAL BAZAI DAIDAI BA,KODA KUWA YAWAN HARAM DIN NAN YA QAYATAR DA KAI(KO YA BAKA MAMAKI),KUJI TSORON ALLAH YA MA'ABOTA HANKULA DON KU RABAUTA* _______________________________________         Tamkar wanda aka jefo haka ya shigo dakin,hantar cikin sumayya ta kada,sai ta sake qudundunewa a zaune ta cusa kanta tsakanin cinyarta,muryarsa taji saman kanta cikin wani irin amo "A ina kika samo wannan cutar,ba dake nake ba" tsananin rudewa ya sanyata daga kai ba tare data shirya ba,abun mamaki fuskarsa wani annuri take fitarwa,kafin ta kai ga yunqurin komai ua sureta baki daya ko nauyinta baiji ya soma juyi da ita,qanqameshi tayi sosai hawaye na zirya saman kumatunta,batasan me take ji ba cikim zuciyarta zuwa yanzu,ciki?,ciki kums ita din?,tayi zatombdaga abdallah ta gama,shin da yaya ma aka samu abdallah?,ciki jin abun take tamkar almara,a hankali ya direta saman kujera ya duqa bisa gwiwoyinshi baki daya,hannunsa ya sanya cikin nata tafin hannun yana matsawa,sai motsa bakinsa yake amma ya rasa kalmar da zai furta,ita din ma shi take kallo,tunda suke zata iya rantsewa bata taba ganin annuri saman fuskanshi kaman haka ba "I dont know me zan fada,ummu abdallah......pls idan mafarki nake taimakeni ki tada ni,i cant blieve it" sai ya kasa zama ya miqe daga durquson da yayi,ya kama hannunta tsam ya miqar da ita,bai tsaya ko ina da ita ba sai clinic din cikin gidan,ya hau nuna mata gwajin da yayi,itakam ba abinda ta gane tunda ba bangarenta bane,jin tayi shiru sai ya daga ta baki daya ya aza saman gadon scanning,ya kunna na'ura ya daidaitata sannan ya janye rigar dake jikinta ya dora na'uarar bayan ya zuba cream saman cikinta "Ya salam.....ya salamm....oh my god..." Abinda ya dinga maimaitawa kenan yana ci gaba da yawo da na'urar saman mararta yana kallon allon scanning din,cikin wani irin sanyi ya gyaara mata rigar bayan ta dagata ta zauna sosai,ga mamakinta hawaye ne fal idanunshi,ya Allah wanne irin so yakewa haihuwa haka?,tamkar yaji abinda take rayawa a ranta ya soma girgiza kai "Bansan ina son haihuwa har haka ba sai a yanzu,da gaske ne nima ashe zan iya zama uba?,zan iya ganin jinina?" Tamkar ita yakewa tambayar da ita kanta bata da amsarta,hannunshi ya dora saman mararta "Alhamdulillahil lazi bi ni'imatihi tatimmus salihat" ya furta hadi da fitar da nannauyan ajiyar zuciya,har a lokacin juya lamarin take cikin mamaki "Ki tambayi duk abinda kike so a duniya zan mallaka miki shi matuqar mallakata ne please,ki roqeni ina son ko yaya ne na faranta miki nima..."ya fada yaba matsa yatsun hannunta "Baki ce komai ba ummu abdallah....ko baki murna....ko ba zaki iya ba kaman yadda kika taba gayan a dubai?" Da hanzqri ta girgiza kai "Bana son komai,kawai ki riqe amanata,kada ka wukaqanta ni,sannan nima bani ke badawa ba ai Allah ne ya baka" "Ya bani ko ya bamu?....kada dai kice min har yau babu wani matsayi da na taka cikin zuciyarki?" Murmushi ta saki,sai ya sake matsowa tare da yin dan tsalle ya haye shima gadon,duka hannuwanshi ya sanya ya kamo fuskarta "Tell me wanne matsayi ke gareni?.....bana son baby na yazo duniya ya fuskanci babanshi is nothing" so take ta qwace fuskarta saboda yadda yake azawa qirjinta nauyi da yawa amma ya qiya,sai ya koma magana da gaske "Am seriouse madam,am not even hear you kina fadin i love you,baki taba fada ba,why?" "Ba komai" ta fada a sanyaye "Bakya sona?" Ya sake tambayarta,shuru ta masa zuciyanta na bugawa,wannan tambayar titsiye ce kawai,ta yaya zaiyi wannan maganar "Sumayya!" Ya kira sunanta karon farko a rayuwarsu cikin wani irin taushi wanda ya tilastata daga kai ta dubeshi "Bana soyayya da wasa kowa ya sanni,idan nace ina son abu zan tabbatar da hakan har daukewar numfashina bana canzawa,sonki na tabbatar bai shiga rayuwata don ya tafi ba,na fara sonki a lokacin da ni kaina ban sanshi ba......kin shigo rayuwata da tarin alkhairan da banga kamarsu ba..." Shiru yayi yana maida numfashi sannan ya dora "Gaya min kina sona indai kina son naci gaba da rayuwa" kunya ta kamata,tana yunqurin kau da kanta ya sake tallafe fuskar "Nooo,a yau a wannan muhallin bana buqatar kunyarki.....ki gayan abinda nakeso naji" "I....love...you" ta fada ararrabe cikin muryar rada,idonshi ya lumshe kalmomin na ratsashi tamkar ranar aka soma gaya mishi su "Basu gamsar da ni ba.....please.....i need more"kafeshi tayi da idanu sanda nashi idon ke lumshe,tana jin yadda wani feeling da so mai zafi ke ratsa jininta,qaunarsa na fusgarta da wani irin qarfi "ina sonka da dukkan zuciya ruhi da gangar jikina.....ban taba jin so irin wannan ba a duniyata sai wannan karon,na tabbata kai na dabanne shi yasa Allah ya jarrabeni da qaunarka.....ina sonka baki dayanka bawai wani abu da ka mallaka ba....kai din dai zallarka kai nake......." Idanunshi da ya bude tar tsakiyar nata shi yasa ta gaza qarasa furta abinda take son fada,zallar soyayyar da take gani a qwayar idanunsa kadai ta isa sake narkar da masoyi "Wani irin zazzafan so nake miki ummu abdallah....taba qirjina kiji yadda ya sauya bugu daga jin kalamanki" ya kama hannunta yana mannawa a qirjinsa saitin zuciyarsa,ba shakka bugunta ya sauya,da mamaki take dubanshi,da gaskene mutane masu tsananin miskilanci da rashin lura da sabgar wasu,yawan shiru basu iya fadawa tafkin soyayya ba?,ta tabbatar da cewa irin son da take gani cikin qwayar idonsa da wanda yake furta mata ba irin nata bane,jikinsa ya janyota yana sakin qatuwar ajiyar zuciya "Na gamsu da kalamanki matata,uwar 'ya'yana da yardar Allah" kusan awa guda suka bata cikin dakin suna jaddada kalaman soyayya tsakaninsu,wanda wani abun almustaphan bai taba tunanin shi kanshi zai iya faruwa ba tsakaninsu,kusan ya samu yadda yake so,irin soyayya da kulawar da yake muradi.       Maganar fitarshi tasha ruwa,ya lalace wajen sumayyan,abun har dariya ya dinga bata,ya kasa ya tsare,data motsa ya hau tambayarta,nama ya sanya an kawo mata shi kala kala ya kusa kala biyar,soyayye,gasashshe,farfesu,mai romo duka ita daya,taci kuwa ta more son ranta,gaba ya sanyata yana kallo abinsa yadda naman ke mata dadi kamar mai shan zuma,itakam sam ko a jikinta har mamakin hakan ta dinga yi,yadda take abinta gaba gadi. Sai bayan sallar la'asar sannan suka shirya,tayi kyau abinta cikin lafaya,duk inda ta gifta binta yake da kallo,wani kyau na musamman ta qara,suna hanya kafin su qarasa ya sake tambayarta me take so?,kai ta kada alamun babu komai,qarfe biyar da rabi suka isa gidan,tun a mota naman taji yana mata suya a qirji tare da taso mata,hakan ya sanya bata jirashi ba tayi gaba zuwa bangarensu. Jiri ne ya dinga dibanta,ta dinga takawa a hankali har ta kai cikin falon,zubewa tayi kan daya daga cikin kujerun ba tare da ta iya qarasawa ciki ba,aman dake taso mata ya soma galabaitar da ita,hakan ya sanya sam bata lura da su'ad dake hakimce kan daya daga cikin kujerun ba,ta tsuke cikin riga da wando,plate ne a hannunta mai dauke da yankakkiyar apple tana jefawa bakinta,sumayyan ta yunqura da niyyar tashi ta qarasa ciki take aman ya balle mata,cikin hanzari su'ad ta miqe taba jefa mata kallon banza cike da qyanqyami,durqushewa tayi a nan tana ci gaba da kwarashi "Wannan wanne irin iskancin banza ne da wofi,banda tsabagen wulaqanci ki rasa wajen amai sai da kika zo gabana ina zaune ina hutawa?"ta fadi tana nazarin sumayyan sosai,tunanu ya darsu a ranta,taci gaba da dubanta tana yatsine fuska,sam bata damu da itaba bare ta fahimci me take cewa ko take yi,ta kanta take,dai dai lokacin da almustapha ya qaraso,wani kallo ya watsawa su'ad,tunda ya shigo ya cimmata tsaye ko kusa da wajen bata dosa ba,ya san halinta sarai sai ya dauke kanshi,cikin hanzari ya iso gabanta ya durqushe yana riqe da ita saboda yadda take yunquri mai wahalarwa,sai data amayar da dukkan naman data ci,sannu kawai yake jera mata,ya miqe da kanshi ya ciro ruwa ya bata ta kuskure bakinta tana maida numfashi,kamata yayi ya zaunar da ita saman kujera ya amshi maqullan dakinta da niyyar bude mata tukunna kafin ta tashi ta isa ga dakin. Duk da yadda take a galabaice amma sai data daga kai ta dubi su'ad sanda ta sheqe da wata shaqiyyar dariya "Su ciki manya,oh Allah ya rufamin asiri,wallahi yarinya kin tashi a aiki,sai yanzu zaki san baki da wayau" dariya ta sake saki "Allah ta inganta" ta fada farinciki fal ranta,hango yadda komai zaizo qarshe tsakanin sumayyan da almustapha cikin sauqi,mutum ne shi mai bala'in tsantsami,ta tabbatar bazai iya daurewa qazantar laulayi ba sam,itakam wanne tsautsayi ne zai aiketa daukan ciki?,ai gwara da tayi mai dungurun gum haihuwa da damuna,ta raba kanta da haihuwar rabuwa ta har abada,yanzun irin wadan nan wahalhalun ina zata iya da su tana tsaka da morewa duniyarta,rangaji taci gaba da yi murmushi na fita a fuskarta "Hahaha.....zamu ga ya zata kaya kuma,sannunki da kayan nauyi" lumshe idanunta tayi tana sauke numfashi a hankali,bata da lokacin sauraren shirmenta sam,don ra fuskanci akwai wani abu da take son gaya mata wanda ta tabbatar ba zayayi amfani gareta ba,koma ace baki day bai shafeta ba,dawowa ya sake yi cikin falon,gabanta ya qaraso,ya sunkuyo inda take jingine da kujerar yana duban qwayar idanunta,cikin taushi yace "Sannu babe......" Kai ta gyada tana lumshe idanu sannan ta bude "Zaki iya tashi?" Langabe kai tayi "Saidai ka dagani"kusan da biyu ta fadi hakan saboda su'ad dake tsaye ta zuba musu idanu,zuciyarta kamar ta tsinke "Daukarki ma zanyi cancankat" ya fada yana gyara hannun suit dinshi murmushi na fita a fuskarshi "Meye hakan almustapha?"waiwayowa yayi yana barin gyara hanunshi da yake ya zuba mata ido "amman dai kasan cewa ranar girki na ce ko?,bai kamata ace kana tabata ba"hannunshi duka biyu ya riqe qugunshi "Zoki taimaka mata ta tashi" ya fada a dake,ranshi a bace yake yana qoqarin dannewa ke kawai,tunda ya tafi tsakamin jiua da yau babu wanda ta shiga ta gaisar a cikin mutanen gidan,sannan yana jin sautin dariyarta bayan shigarsa daki,saidai bai ji me take fadi ba,fuska ta bata "Gaskiya bazan iya ba,ta gama aman yanzun sannan na tabata?....a'ah gaskiya" ta fada tana kada kai,juyawa yayi ba tare da ya sake dubarta ba ya daga sumayyan cak ya wuce da ita,binsa tayi a zabure ranta a bace,cikin tsantsar mamakin yadda ya taba jikinta babu wannan qyamar bare qyanqyamin,me yake nufi kenan?ya shirya ci mata fuska ne?,sai kuma ta dakata a bakin qofar dakin saboda tuna wani abu da tayi. Gyara mata kwanciya yayi ya rage mata kayan jikinta sannan ya sumbaceta a goshi "Ki kwanta ki huta,banson ko qwaqwqwarar magana ki sake yi,zan kawo miki maganin tsaida amai.....zanje nayi wanka yanzun" "Na gode" ta furta a tausashe,murmushi ya saki yana shafa saman kanta,ji yake tamkar ya maidata jikinsa su koma abu daya "Shshshshsh......nine da godiya,kin manta cewa babban gift kika bani wanda ba wanda ya taba bani kwatankwacinshi?"murmushi ta sake masa,ya sake sumbatar labbanta masu taushi dake burgeshi sannan ya soma takawa da baya da baya ya fice,ido ta rufe bayan fitarshin,tabbas so shike iya juya mutum ya sauya masa halayya komai girma isa da qasaitarsa. Saura kadan yaci karo da ita sanda yake fita don bai tsammaceta a wajen ba,dauke idonshi yayi yayi gaba tabiyoshi a baya tana sauri don ta cimmasa,daidai sanda daya daga cikin ma'aikatan dake shirya abincin dare a kitchen ta fiti,da hanzari ta koma da baya zata koma kitchen din ganin tahowar almustaphan "ki qarasa bakin qofan can ki gyara wajen ya baci da amai" "To yallabai" ta furta kanta. aqasa cikin ladabi "Amma girki take mana,ya za'ayi ta je ta taba qazan......"harara ya watsa mata wadda ta hanata qarasa fadin abinda take da niyyar fada,yayi gaba ta sake bin bayansa. Yana tsaye yana ragw kayan jikinsa yayin da take tsaye bayanshi tana lissafo qorafe qorafanta daya bayan daya,tie dinshi ya cire ya wurgar saman gadon,cikin zafin nama ya fincikota sandan take tsaye bayanshi ya zaunar da ita bakin gadon da yake tsaye,ba waramin tsorata tayi ba da ganin yanayinshi,cikin kakkausar murya ya soma magana "Wace irin macace ke da bakisan komai ba sai qorafi da tashin hankali?,wace iriyar macace ke da komai na mijinki bai dameki ba,lalurarki da buqatar ki itace gaba akan ta kowa,a haka kike so na kyautata miki?, ahaka kike so naji dadin zama da ke,bakisan komai nawa ba,bakisan duk wani abu da ya shafeni ba,na dauka laifi nane da fari na zaunar dake na karanta miki komai da yadda nakeson komai ya zama amma a banza,shin wai sai yaushe zaki sauya ne?,sai yaushe?,dame na rageki da shi na dukka haqqinki da Allah ya dora min?me kike so nayi miki?"ya qarashe maganar yana jin zafi har cikin zuciyarshi,idanu ta zuba masa tana dubanshi,idanunsa ya lumshe yana komawa da baya ya zauna,qoqarin cooling temper dinsa yake,baiso wani abu ya bata zallar farincikin da yake ciki a yau. Kuyi manage da wannan,ba lallai gobe wani ya samu banyi alqawari ba,naso yau na barshi sai gobe na hada na turo muku mai yawa amma nasan zaku fison a baku ko kadan ne. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 9⃣5⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *LA HAULA WALA QUWWATA ILLA BILLAHIL ALIYYUL AZIM* ___________________________________       Zuba masa ido kawai tayi tana jin wani zallar bacin rai na ratsata,hawaye na bin kuncinta,ji take a duniya ya gama tozar tata,ya gama wulaqantata,a dacan ba haka ai ta sanshi ba,ta ina zata fara debo irin rayuwar da yake da muradi,sam ko daya ita ba zata iya ba "Yanzu na sake tabbatarwa cewa baka qaunata almustapha,kanka tsaye kake gayan wadan nan maganganun?" Ta furta tana nuna qirjinta da yatsa,a nutse ya daga idanunshi ya zuba mata su,wato wanda yayi nisa baijin kira,barin hali sai mutuwa?,duk yadda ya kai ga dorata a hanya kenan qaryarshi ta sha qarya,bazata taba fahimta ba,ya fuskanci duk abinda yake gaya mata ashe bata bakinsa yake,kwanaki biyun da yayi dakinta ya bata lokuta sosai yana nusasheshe da ita abubuwa da dama,ta kuma kwantar da kai ta nuna tana dauka,ashe duka busa yake mata cikin kunnuwanta ba magana ba.         Tsam kawai ya miqe ya ci gaba da rage kayan jikinshin,ya daura towel ya shiga toilet,yana tsaye riqe da qugunshi yana tarawa kanshi ruwan wanka ta turo qofat,hankalinshi kaf bai wajen,ya kasu gida biyu,wani na wajen sumayya yana tunanin tayi bacci kuwa?,yayin da daya ke kai kawo kan halaye da dabi'un su'ad "Kana nufin kai maisheni banza da baka da lokacinta kenan?,amma ita waccar ai kana da nata lokacin ko?,har kana iya kamata bayan qazantar data futar,wanda iyakar sanina da kai kana da qyanqyamin da bansan lokacin daka zama haka ba" shiru yayi mata baice mata kanzil ba,iya tsahin rayuwarshi mutum ne da baya son hayaniya,tubewa yayi ya shige bathtube abinshi ya barta tsaye,sai ta fashe da kukan baqinciki ta juya ta fice zuwa uwar dakin.           A nutse yayi wankanshi,ranshi na sake fari da haske a duk sanda ya tuna cewa nan da wasu watanni shima zai zama baba,nan da wasu watanni zai dinga gajin gilmawar yaro ko yarinua cikin gidanshi,yaron da za'a kirashi da d'anshi,mallakinshi,jininshi,murmushin farinciki ne ya subuce masa sannan ya miqe ya fito.         Kwance rub da ciki ya tadda ta tana rusgar kuka,ya bude ma'ajiyar kayanshi ya fitar da shirt da trouser ya sanya,ya shirya tsaf abinshi ya fice ya sauka qasa,dining ya wuce yayi serving kanshi yaci abinci ya qoshi sannan ya wuce zuwa sashen ummee.          A kwance ya taddata tana kallon news a al-akhbar,sallamarshi ta sanyata miqewa ta zauna tana amsawa,suna ranta shi da sunayyan tun jiya da bataji motsim daya daga cikinsu ba,ya qaraso wajenta fuskarshi dauke da murmushi ya zauna gefanta suka soma gaisawa "Ya sumayyan take?"ummin ta tambayeshi ba tare data tambayi su'ad ba,rabonta data shigo ta gaidasu tun shekaran jiya da suka shigo tare da shi,amma ita hakan ba damuwarta bace tunda dama ba zamansu take ba zaman mijinta take,indai kuma suna zaune lafiya lau to da sauqi "Lafiya.....na barota tana bacci" "To masha Allah" hira suka shiga yi irin ta da da uwa,cikin daqiqu kadan ta fuskanci yaron nata na cikin farinciki da annashuwa qwarai,sai ta danganta hakan da cewa tsantsar farinciki kulawa da walwalar da yake samu ne daga wajen abokiyar zamanshi,ya jima gurin ummeen sosai sunyi hirar da suka jima basuyi irinta ba,bai bar wajen har bayan sallar magariba,sai da aka kirashi a waya ya qarasa baqin get wajen masu gadi da kanshi ya amshi saqon da ya bayar ayi masa order.           Sanda ta farka taji dadin jikinta sosai,hakan ya sanya ta shiga toileta ta hada ruwan wanka mai dumi ta wanke jikinta,ta dawo gaban madubi daure da towel ta janyo kujera ta zauna kai,don kasala take ji ba zata tsaiyawa ba,haka kawai take jin wani farinciki da annashuwa tana ratsata,ta dinga kallon kanta a madubi tana sakin murmushi,lokaci lokaci tana shafa cikin nata wanda yake a dame da hannunta,itakam ciki na zuwa mata a bazata,tun yanzun Allah ya dasa mata so da qaunar abinda take so tamkar yadda taso abdallah tun kafin ta haifeshi,gababta ya yanke ya fadi sanda ta tuna irin gwagwarmayar da tasha hannun zainab,tsantsar makirci zalla da kuma wuyar da tasha kafin abdallah ua kai labari,ambaton sunan Allah ta dinga yi tana nemawa kanta da abinda ke cikinta tsari tun daga lokacin,bata fatan makamancin abinda ya faru da ita wancan karon ya sake maimaituwa da ita, akasalance ta dinga shafa man gabanta na faduwa ta wani bangaren.         A nutse ya turo qofan dakin wanda sam bata ji ba saboda yadda hankalinta yayi gaba,takowa yake amma idanunshi na kanta yaja qarewa halittar Allah kallo,saboda banda qirjinta zuwa mazaunanta ba inda yake a rufe,dogon wuyanta da santala santalan cinyoyinta a bayyane suke,fatarta data sake kyau sai sheqi take yi,wani qaunarta da shauqinta na fusgarshi,a haka ya qarasa ya sanya hannayenta ya rufe idanunta,taushi da sanyin hannunshi kadai sun isa gaya mata waye?,ballantana da zuwa yanzun koda bata ganshi ba matuqar yana muhallin da take sai jikinta ya bata,matuqar tasiri yayi cikin rayuwarta,ya mallaki duk wani tunaninta,shiga da fitar numfashinta na tattare da nashi,bata son ta fiya zaqewa ne da yawa kawai,tunda ta sani cewa ba ita daya bace ta mallakeshi.        Sautin murmushin dat fitar kadai ya sanar da shi ta gane waye,shima yana murmushin ya cire tafukan hannunshi daga fuskarta yayi kissing wuyanta a tausashe,sannan ya zagaya gabanta ya dane saman mudubin yayi zamanshi hannayenshi harde a qirjinsa bayan ya ajjiye ledan takeaway din daya shigo mata da shi na abinci yana ci gaba da qare mata kallo,baki daya ta takura,kunya ta lullubeta "Me yasa baki taba zama nayita kallon ki a haka ba bayan kinsan hakan ashe ba qaramin qayatarwa gareshi ba?" Murmushi ta saki cikin kunya,bai tsaya jin amsarta ba ya dora "Tunanin me kike haka ummu abdallah?,kinsan hakan yana da illa ga lafiyarki?"kai ta gyada sannan ta maida masa amsa "Babu komai abu abdallah" sosai sunan ya masa dadi har qoqon ranshi,sai da ya lumshe idanunshi sannan ya bude bisa kanta "Kada ki cemin bakiyi bacci ba" "Nayi,na farka ne naje nayi wanka da sallah" ta fada tana murmushi "Ummee na gaisheshi" idanu ta dan zaro "Shine kayi tafiyanka baka tsayani munje na gaisheta ba ita da baba,kwana nawa ban gansu ba" ta qarashe maganar a shagwabe,binta kawai yake da kallo,ko iya nan ta samu wata madaukakiyar daraja da baiga macen data sameshi ba,ta maida iyayenshi tamkar naga,tana sonsu so na bilhaqqi,ya samu kabarin tun kafin suyi aure take sonsu da ganin girmansu,abinda har yau su'ad ra kasa fahimta daga gareshi,mutum ne shi wanda da iyayensa kadai zaki iya cinsa da yaqi,saboda daraja da matsayi ya basu bana wasa ba,yace bazai taba yin wasa da aljannarsa ba,duk duniya idan suka take masa ita babu mai bashi,ki ubangijinsa bai isa ya tunkara ba bayan babu kyakkyawar alaqa tsakaninshi da su,saboda yardar Allah tana tattare da yardar iyaye,hakan fushinsa yana tare da nasu fushin,sirrin nasararsa da daukakarsa ba'a komai take ba face ga albarkar iyaye,koda bata mallaki komai wanda za'a sota ba yana da yaqinin ya samawa yaranshi uwa ta gari,ya tabbata yaransji zasu tsira da sanin girman na gaba "Yanzun ma banje wajen baba ba,shirya idan na idar da isha'i zan shigo muje" ya fada yana duba agogonshi tare da sauka daga saman madubin "Ina fata amma baka gayawa ummee komai ba ko?" Ta fada saboda tana jin nauyinta,bata son ummeen ta fuskanci akwai wani abu,murmushi yayi,ya gano sarai mai take nufi "Don me zanqi gaya mata?" Tuni idanunta sukayi qwalqwal da hawaye,sai ya dawo da baya,ha dagata suna fuskantar juna,nauyi ya cikata,yadda yake sake qare mata kallo a kaikaice "Banason naga wani abu mai kama da hawaye a fuskarki......kinsan me?" Kai ta girgiza tana dubanshi "Nima kunya nakeji,bansan me zance musu ba,espicially baba,na masa ba dai dai ba sanda ya bani aurenki ya damqa min amanarki....yanzu idan nace kina da ciki kinsan me zaice?" Kai ta sake girgizawa,sai ya jawota ya rungumeta tsam,jikinsu na gogar na juna,ya dora bakinshi a kunnenta "Zai iya rayawa a zuciyanshi....dan banza,yace baya so ashe har yayi aiki irin haka?" Dariya ta qwace mata cike da kunya,sai ta tura kanta a qirjinsa tana dariya qasa qasa,shi dinma dariyar yake ya dan janyeta yana dubanta "Ki shirya muje,idan kin shirya jin wannan kunyar sai a sanar mai,amma nikam ban shirya ba gaskiya,ga abinci nan kici kafin na dawi,ba nama kawai zalla ba za kiyita ci" ya fada yana juyawa,dan rage dariyar tayi tana bin bayanshi da kallo "Me kayi masa naba dai dai dinba sanda yace ya aura maka ni?....." A ba zata tambyar tazo masa,sai ya tsaya cak ba tare da yaci gaba da tafiyar ba,jin yayi dif ya sanyata tace "Kace masa baka sona ko?" Ta baiwa kanta amsa tana ci gaba da duban bayanshi,a nutse ya waiwayo sannan ya sake takowa zuwa gabanta,hannunshi daya ya dora kan kafadarta ya riqe yana dubanta "Sumayya......daga kanki ki dubeni" ya bata amsa cikin kakkaurar murya,a hankali ta daga kan ta dubeshi "Ci gaba da kallon qwayar idanuna,ina son ki bawa kanki amsa ne,kada na fadi ki dauka wasa nakeyi" a hankali ta saka idanunta cikim nashi,tsahon mintuna aqalla hudu,kamar masu kallon quda,saiga tsaiwa na neman gagararta,tuni ta janye daga kallon nashi,ba zata iya jurewa ba,ya tareta suka fada gefan gado "Uhmmmm,zaki iya explaining?"kai ta girgiza tana niyyar tureshi,murmushi ma subuce mata,sai yanzu ta karanci wayau yayi mata,yau ta sake yarda da maganar anty dije da tace vatasan sanda sumayya zata girma ba "Ko ni kike so nayi miki?" Da sauri ta dora hannunta saman bakinshi yana girgiza kaj,sai yayi murmushi yana sauke hannunta daga kan bakinsa "Okey......daga yau duk ranar da kika sake min tambaya makamanciyar wannan zan hukuntaki fiye da haka,mace nada dataja wajena.......macen ma matar aurena na......matar aurena wanda ta soma kawon cikakken farinciki cikin rayuwata......kinsan wani abu?.....uwar d'ana.....dole ta zama ta daban,dole na bata wani matsayi na musamman,koda kuwa kuturwa ce gurguwa ce makauniya ce....balle ke...ke din da kika zama wata ta musamman a dukka tarihin rayuwata,kika kafamin tarihin da ban taba cin karo da shi cikin rayuwata ba" tabbas ta gamsu,ta gamsu koda bai fada ba,miqewa yayi "Ki shirya zan kiraki muje mu gaidashi"kai kawai ta iya gyadawa,har ya fice kowannensu na murmushi.          Saman kujerar falon sama ya tadda ta wannan karon zaune,sai ua dauke kai kamar bai ganta ba yayi niyyar wucewa ciki,ganin haka ya sanyata cikin hanzari ta isa gareshi ta rungumeshi ta bayansa,cikin salon kwantar da murya ta soma fadin "am sorry my dear,am sorry,ba nufina na bata ranka ba,u know i love you thats why,but am sorry"baisan ya zaiyi ta zama yadda yake so ba,har ga Allah bai nufin tozarci ko wulaqanci gareta,saboda bazai manta hadisin da annabi ke wasiyya ga maza su kyautatawa mata da alkhairi ba,but hakan baya nufin idan ta kauce kayi qoqafin nusashsheta taqi kabi dukka hanyoyin da zaka ladabtar da ita wadanda suka dace ba tare daka cutar da ita ba,hannunshi ya sanya ya zagayo da ita gabansa ya sanyata a jikinshi "shikenan,ya wuce,amma kiyi qoqarin sauyawa,kiyi koyi....." Sai kuma ya katse bai qarasa din na,saboda bai kamata yayi mata misali da itan ba zata ga kaman cin fuska ne "Ki gyara ki zaka yadda nake so,koda ba duka ba kiyi qoqarin kamantawa" "Thank you,thank you verry much" ta fada cikin farinciki,don ba zata iya missing wannan daren ba,ta tabbatar ya juya mata baya ba komai bane wajenshi,ko a jikinsa tun sanda suke su biyu bare yanzu da yake da wata,alwala ya daura ya fice masallaci,sanda ya dawo zai sake fita ta tareshi kan ina zaya je yace zashi gaida baba "Sau nawa kika je gaidasu bayan bana nan?" Ya tambayeta yana tsareta da ido,sai ta rausayar da kaibtana son basarwa,ranshi ya quntata,amma gyara yake son kawowa,dole yabi abuna hankali cikin hikima "U know what?" Da sauri ta juya tana dubanshi gami da girgiza kai "Duk yadda zaki soni....ko hadiyeni zaki kina fiddo ni,zan qaryata son da kike min matuqar baki bawa iyayena darajar data fi wadda kika bani ba" ya gaya mata da yaren da zata fi ganewa,sosai zancan ya shigeta,cikin zuciyarta ya soma mitan wanne irin sone wannan da zaya takurata da taso iyayenshi,itakam bata ga ana irin haka ba a al'ummar data taso,kuna iya kai iyayenku gidan gajiyayyu ma idan suka soma zama nauyi kanku,ko ka kai qararsu ga hukuma matuqar suna takura ka,kana iya komai gaban idanunsu ma ba kwaba ba hantara,suna yin nasu zasuyi,amma shi ko hugging dinta bai taba ba a gabansu,randa ma tayi gigin yin hakan sai da ya sabar mata,daga haka bata sake gwadawa ba,to kuma haka kawai ba zamansu take ba zai tilastata hulda da su,wannan qaddara da yawa take,ba yadda ta iya ta shiga daki ta sauya kayan jikinta zuwa gown,sakakkiya ce ba'a matse take ba,har ya soma sauka tabi bayansa,yaji dadi sosai har y fuskanshi ya nuna hakan,wanda itama hakan ya sanyata jin dadi cikin ranta.        A bakin qofa ya tsaya yayi mata knocking,koda taji tasan cewa shine,sai ta zura dogon hijabinta kan riga da skert dake jikinta ta fito,sun sanyashi tsakiya saidai ba wadda ke cewa da 'yar uwarta kanzil,suna tsaka da tafiya hibba ta hangosu ita da hibban yaran fahariyya da adam yayan almustapha,gudu ta debo ta iso inda suke kai tsaye ta ruqunqune sumayya iya qarfinta tana kiran anty "Sake antyn taku hakanan kada ta fadi hibbah,bata jin dadi" cewaf almustapha,tana dariya ta gaidashi hibban ma haka,suka gaida su'ad sannan suka gaida sumayya "Anty...tun ran nan rananan din cannnn.....da kika je zaki bamu labari baki bamu ba har yanzu" murmushi ta saki tana shafa kanta,tana mamakin kaifin qwaqwalwa irin ma yarinyar da har yau ta kasa mancewa sa maganar "Zan baku in sha Allah" "Yaushe anty" "Ba yanzu ba sai ta warke" almustapha ya fada "Abbanku na gida?" Ya kuma tamyarsu,hibban ne ya amsa,yace suje suce yana sin ganinshi amma ya shiga wajen baba tukunna "Yana wajen baba prof din ai muma daga can muka fito" "Is ok,ku shiga gida to ba kyau yawo da dare" da gudu suka juya suja wuce shi,su kuma suka ci gaba da takawa "Anya son yaranki baifi nawa ba" murmushi ta saki "Yara ai rahama ne,ko wajen ubangiji sau tari albarkacinsu muke ci,ba don su ba da wataqila ko ruwan sama mun daina samu" ta fada tana murmushi tare da dan dubanshi,kusan da biyu ta fadi haka,raddi ne kan maganar da su'ad ta gaya mata dazu na ta gama aiki tunda ta dauki ciki "Gaskiya ne" ya furta a fili,cikin zuciyarsa yana sake jinjinawa baiwa da fasahar zancanta,tsaki takeso tayi amma dole ta bame bakinta,don bata son abinda zai bata daren nasu.          Da sallama suka shiga wajen baba,yana tare da adam yayan almustapha suna hirarsu,kusan ranar sumayya zata ce ta soma ganinshi,akwai 'yar kama tsakaninsu,kana ganinshi zaka san jininsa ne,saidai almustaphan ya fishi kyau da quruciya,ran baban yayi qal ganinsu dukkansu su ukun a tare,murmushi yaqi yankewa daga fuskarshi ya tarbesu suka zauna suna gaidashi "Sa'adatu(da yake wani lokaci hakan yake kiranta,abinda ta tsana kenan,ita aginta bata suna ne)yanzu muka gama waya da babanki" "Allah sarki" kawai ta fadu,har ga Allah haushin tsohon take ji,gani take shine ummul Aba'isin komai ma da ya faru da ita,kanwa uwar gami,sai ya waiwaya ga sumayya wadda ta gama gaida yaya adam a mutunce "Maman tun daga randa naci tuwo kuma sai kiyi batan dabo,inata nemanki na bada tukuici" qas tayi da kai tana wasa da yatsun hannunta kawai,ya tambayi lafiyarsu baki dayansu suka amsa mai,ganim almustapha sun soma hira da adam yasa almustapha yace suje wajen ummeen shi zaizo,su'ad ita ta fara yin gaba,sumayya na bayanta,ganin tayi wucewarta bata ko saurari bangaren anty maamaa ba ya sanyata ita shiga ta gaidata,taji dadi kuwa sosai,bangaren itama sai ita daya,dama can yaran mazan ba zama suka fiya yi ba,bare yanzu da kowa ya kama nashi gidan,don su a waje suke zaune,saidai kowanne yace idan yana sha'awa zasu zo suyi kwana biyu cikin gidan tunda suna fa wajensu,sosai taji dadi suka dan taba hira atsaitsaye ta wuce zuwa sashen ummee,tana gab da shiga su'ad ta fito tana hura hanci,ganin tana yunqurin bangazarta ya sanyata ja gefe,wani kallo su'ad din ta watsa mata sannan cikin harshen turanci tace "Banza" murmushi ta jefeta da shi,cikin salon nuna qwarewa itama ta karya nata harshen da salon data koya a uk "Banzayen ai suna da yawa ba daya bace,suna da yawa,bansan wacce daga ciki kike nufi ba"cewar sumayya sannan ta juya hankali kwance tayi shigewarta.         Cikin kulawa suka gaisa ta samu gefan ummin ta zauna,bakin kowanme yayi nauyi,sumayya ya kunyar ummin ita kuma yau ummin surukuta ce ta motsa,saidai duk motsin sumayya tana lura da ita,sai take ganin ta soma sauyawa baki dayanta,jefi jefi suka dinga hira da ita har almustaphan ta shigo ya taddasu,baiyi zaton zai sameta har tsawon lokacin a nan ba,a sannan ummi ta shiga kitchen tana hanyar fitowa ta jiyoshi yace "Baki gaji da zama ba?,akwai magungunan da zaki sha fa?" "Me ya sameta?" Ta fada tana fitowa akitchen din tana fatan jin abinda zuciyarta keta faman raya mata,kanshi ya shafa yana jin nauyin ummin "Ciwom ciki ne,kuma tana shan magani yanzu haka yana samun sauqi" ta san zurfin cikinshi qwarai,sai ta zauna tana cewa "Allah ya sawwaqe,lallai kam ki kula da shan magani"ta miqawa sumayya wani dan bowl na plastic mai garai garai wanda akayi wrapping dinshi,maganar tata sai ya jita kamar a baibai,gaba yayi cikin jin nauyi yana cewa ta taso su tafi,ummi ta bita da kallo sanda ta miqe tayi mata sallama,sai taji tamkar ra tsaidata taji ainihin meke damunta,saidai kuma koma meye tasan indai da gasken ne abinda take zato to nan da wani dan lokaci qanqani zata fasu,suna ficewa ta samu kanta da yin sujuddushshukur,duk da bata tabbatar da cewa hakan bane,wani farinciki data jima bata ji irinsa ba yana ratsata,tamkar bata taba riqe jika ba. *******     ******    *********       Bai taba riskar kansa cikin farinciki ba irin na wadan nan kwanakin,bai taba tunanin haka samun d'a yake dadi ba sai wannan karon,ashe daa baki daya hasashene kawai yake yi,sumayya kam na fama da laulayi sosai,saidai Allah ya bata wata juriya da qwarin gwiwa,tana matuqar qoqari wajen boye ma almustapha,saboda kullum kwanan duniya tunaninshi na kanta ita da abinda ke jikinta,bai da sukuni yana gida koko baya gida,dawainiya yake da ita bilhaqqi,idan da yana da iko numfashi ma shi zaya yi mata,bata taba cin karo da soyayya kwatankwacin wannan ba,bata taba zaton ita din sumayya abar soce har haka ba,bangaren su'ad kuwa gani take Allah ya sita da bata taba gwada daukan ciki ba,musamman duk randa amai ciwon kai ko zazzabi ya make sumayyan,da yake sautari yanzun tana yawaita zaman falo,haka kawai sai taji bata sin zaman dakinta,a falo kawai take jin dadi,idan zata kwana tana amai ba abinda ya shalli su'ad,saidai ta watsa mata baqar magana "waya kaiki da zaki cikawa mutane kunne da kakari?"ba yau ta soma gani ba balle ya dameta,saidai idan taga dama ta rama wani lokaci kuwa tayi banza da ita,abu daya ke damun su'ad shine yadda wani lokacin take vcin karo da zallar kulawa da sumayya ke samu daga wajen almustapha,tarairaya da damuwa,kalar wanda taci burin yayi mata koma fiye da haka,abu daya kawai ta sani shine indai sai ta dauki wannan kayan wahalar to kuwa ba zata samu wannan abun na,jira kawai take sumayya tayi nauyi kota haife,ta tabbatar a sannan duk wata gayya zata watse.        Ko daya sumayya bata bari laulayinta ya hanata yin duk abinda ya dace ba,saidai abinda ba'a rasa ba wanda dole ka gaza saboda sauyawar yanayi,a hakan ma takan faki idanun almustapha ne ko,idan baya nan,idan kuwa ya dawo kaman yayi kuka,takan sanya dariya tace "amman dai kai likita ne,ku kuke bawa matan mutane shawara su dinga motsa jiki sanda suke da juna biyu ko?"cafkota yake ya hukuntata son ranshi,ba hukunci na duka ko zagi ba hukunci ne zallar qauna.        Ummi taso daurewa amma ganin dukkansu ba wanda ke da niyyar sanar mata komai bayan raga dukka wasu canje canje da suka wajaba ga mai ciki,randa ta gaji ta tsare sumayyan tazo gaidata da safe,kunya ta kamata,ta sumkuyar da kai,kamar zata nutse haka take ji,murmushin farinciki ummu ta saki tana furta alhamdulillah a fili kafin tace "shine kika biye masa amiran umman khalipha zaku boye mana?,kyaci gidanku"itakam kunya take ji,don ko anty dije ta kasa gaya mata,da yake kwana biyu basanan sunyi tafiya ita da yara da mai gidan baki daya bikin 'yar qanin babanshi dake bauchi,kuma sun dan jima a can shi yasa ko rashin lpyr bata sani ba,zaunar da ita ummi tayi ta dinga zayyano mata dukkan wasu dabaru na kula da kai da ciki,ta kuwa qaru sosai,ummi tamkar ta jawo dare yayi haka takeji don wannan kyakkyawan labari ya isa ga kunnen baba prof.         Yana zaune baban yana shan fura,jifa jifa yakan daga kai ya dubi ummi dake zaune gabanshi,ba don ya qoshi ba ya ajjiye mazubin yana dubanta "Fadi kawai abinda ke bakinki....ummin su adam yau tunda na shigo naga bakinki nata motsi,tunda naga hakan nasan akwai magana sarauniyar miskilanci yau zan sha labari" murmushi ta saki,har yau baba bai daina tsokanarta ba,bai daina tuno mata gamonsu ba akaron farko wanda shi ya zama silar wanzuwar alaqar mai albarka dake tsakaninsu a yanzu "Babban albishir ne wannan,bai kamata na baka shi haka ta sauqi ba me zan samu" murmushi yayi ya maida bayansa jikin kujera "A'a a'ah,bazan fada ba sai naji girman albishir din tukunna" "Kasan girmansa kuwa?" "Har yakai na ganin sule na?" "Yana da alaqa ai da sulen naka" jin ta ambaci sulensa ya sanya shi gyara zamanshi "Wanne irin albishir ne haka zuwairiyya gaya min" "Mun samu qaruwa fa agidan nan?" Dubanta yayi "Ke ko maamaa?" Dariya ta saki yana toshe bakinta "Kai.....haba prof..rufamana asiri don Allah,muna haihuwa surukai nayi....mamanka ke da juna biyu?" "Maman tawa biyu ce ai wacce?" "Mai dakin almustapha" daukewa wutar baba tayi kafin yace "Allahu akhbar!,Allahu akhbar!!,kilishi.....da gaske kike ko da wasa,kada fa ki sani nayi abun kunya" dariya sosai ta dinga yi masa ganin yadda ya diriri ce "Ta bakinsu nima naji,dama na jima ina zaton haka"kabbara hamdala da hailala baban ya dinga saki,tammat burikansa sun cika a rayuwa,Allah yayi masa baiwa ba shakka,a take ya daura alwala yayi sallah raka'a biyu ta godiya wa ubangiji,kallonshi kawai ummi take,gani take kamar yama fita jin dadi qwarai nesa ba kusa ba. Daga daya bangaren sumayya ke fitowa daga bandaki bayan tayi wanka saboda kwanciya,wankan da bata samu yi ba sai a lokacin,ta hada har da kanta ta wanke,saboda sam ta tsani zuwa salloon,tunda almustapha ya taba gyara mata a gida taji tafi son nashi,yana zaune saman gado yana aiki kan system,fitowarta ya ja hankalinshi,ya daga kai yana dubanta,tayi kyau cikin rigar bacci,tana gaban mudubi tana daukan mayuka da hand drayer dinta ta zo dab da gadon ta jona ta sannan ta miqe,ta daga kai suka hada ido da shi,kusan ta saba da irin wannan kallon daga wajen almustapha,abun mamakin kuma idan suka fita sai ki wuceshi baima san dake ba,hakanan bai fiya gane mata ba,amma batasan ya akai ya koyi irin wannan kallon haka a kanta ita daya ba,iska ta hura masa a fuska suka saki murmushi tare "baka sanni bane?" "Kullum sabuwa kike koma min,daga zuciyata har idanuna,i dont know why?,ko kin iya sihiri ne?" Murmushi ta saki tana juya ido "Yessss....tunda har na iya sihirce zuciyarka" kai yake gyadawa yana qaramar dariya "Na yarda kam,tunda gashi kin hana mu koma wajen aiki....amma in sha Allah next week zamu wuce dubai baki daya,kinga...sai munfi sakewa ko?,saboda ina buqatar kulawa sama da haka gaskiya" fara'ar fuskarta ce ta ragu,baki daya taji baga qaunar sake komawa garin,duk da taji yana maganan gidanshi zasu wuce,amma tana ganin gwara kawai ita ya barta nan ya wuce da su'ad ita taji da kanta,system din ya ture ya amshi drayer din daga hannunta ya zaunar da ita a gabanshi ya soma busar mata da kan "Nikam ko?,ina ganin kawai da zaka wuce da su'ad ni ka barni nafi son nan" wani abu ya taba zuciyanshi,tana zaton zasu iya raba gari shi da ita?,kwana biyun ma da yake ba tare da ita ba shi daya yasan me yake ji "Ba haka na tsara ba" ya fada a taqaice,don bai son ta sake cewa komai "Amma ko don yanayin jikina wai ko?" "Na fiki sanin hakan ai" "ina son cikina ya sake......." "Shut up sumayya,kada ki gayan abinda kike ganin ya dace mana...."ya fada a kausashe. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 9⃣6⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *wata rana annabi S A W yazo wucewa ta wasu* *qaburbura guda biyu,sai yace da sahabbansa* *"haqiqa(mutanen dake cikin kabarin) ana musu azaba,ba kuma wani* *babban abu bane yasa ake musu azaba* *saidai(ma'abocin kabari daya)ya kasance baya suturtuwa daga fitsari,amma dayan* *SHI KUMA YA KASANCE YANA YADA ANNAMIMANCI"* *sadaqa rasulul karim* *qalubale ga munafukai,qalubale ga masu daukan zantukan wancan bangare su kaiwa wancan,su dauki naka su kai wa wani bangare,qalubale ga masu haddasa husuma,masu qiren qarya don su haddasa husuma da rigima tsakanin mutane,qalubale a garesu baki daya,GA MAKOMARKU NAN,RUWANKU KU GYARA RUWANKU KUCI GABA* *FITINA AKWANCE TAKE ALLAH YA LA'ANCI MAI TADA TA* *FADA CE TA MA'AIKI* *ABINDA KUKA SHIRYA BAI YIWU BA,SAIKU SAKE SABON SHIRI,NI DA MAMUHGHEE DUKA BA JAHILAI BANE,MAIMAKON SHARRI DA KUKA SO QULLAWA SAI ALLAH YA JUYA ABIN YA ZAME MANA ALKHAIRI,GODIYA TA TABBATA GA ALLAH* *ubangiji na cewa* *YAKU WADANDA KUKA BADA GASKIYA DA ALLAH,IDAN FASIQI YAZO MUKU DA LABARI,TO KUYI BINCIKE KADA KU AFKAWA WASU MUTANE CIKIN JAHILCI/RASHIN SANI,SAI KU WAYI GARI KUNA MASU NADAMA AKAN ABINDA KUKA AIKATA* *HAQIQA DUK WANDA YAYI AIKI DA UMARNIN UBANGIJI BA ZAIYI DANA SANI BA,MUN GODEWA ALLAH DAYA SA MUKA KASANCE CIKIN MASU IMANI* *ALLAH KA SHIGA TSAKANINMU DA SU,KA FI KOWA SANIN BAMA NUFIN KOWA DA SHARRI,TSARKAKE ZUCIYARKA SAI ALLAH YA KUBUTAR DA KAI* *muna muku fata Allah ya shiryeku,don wannan mummunan ciwo ne kuke dauke da shi,ciwon dake iya dawwamar da bawa cikin azabar kabari* *ALHAMDULILLAH* _______________________________________            Shiru ne ya ratsa dakin,bata sake cewa komai ba,kamar yadda shima bai sake cewa komai ba har ya gama mata gyaran ya hade mata shi waje guda,tana kwance lamo tunani kala kala cikin zuciyarta,har ga Allah bata marmarin binsa,ba don komai ba saboda ta horu cikin abdallah,tana tsoron sake faruwar wani abun,su da zasu tafi can wata qasa wata uwa duniya,wazai tallafeta idan wani abu ya sameta wanda bata fatanshi?,shi da ba zama yake ba,ko yaushe aiki aiki?.          Washegari ya sake birkice mata,sanda suka je gaida su baba da ummee,ya sanar musu komawarsu ranar lahadi kwanaki uku masu zuwa,ita dinma ummen so take ya barta nan cikin ya sake qwari tukunna,baya ga haka tana tunanin haukar su'adah kada ta yiwa sumayya saukarsa,tun sanda ta yanki almustaphan take jinjina batun,dannan daga bisani itama tazo raiwa kanta illa,to wayr ba zata iya yiwa ba kuma?,hakan ya sanya kamar tasan zaizo da zancan tafiya ta gayawa baba shawararta,yayi na'am da hakan,don shi kansa tsarin yayi masa,ya wuce da su'ad din ya bar sumayyan bayan wata biyu yazo ua dauketa.        Sanda ummee ke rattabo masa bayanin kanshi na wasa,kusan tare suka daga kansu gaban sumayya na faduwa,kada fa yayi zaton qararshi ta kawo kan ba zata bishi ba?,da hanzari ya daga kanshi yana duban ummee,a hankali ya motsa bakinshi "Amma ummee nan da can din duka daya ne ai,zata samu dukkan kulawar data dace" "Ba daya bane almustapha,ka barta nan ta sake koyon yadda zata kula da kanta,a can fa kada ka manta bata da kowa..." "Amma ummee tana da ni" ya amsa ummin bako kunyar nan fuskarshi,hankalinshi a tashe yake,kawai yadda zai tafi ya barta yake kwatantawa,ji yake sam ba mai yiwuwa bane "Munsan da kai din ai,awa nawa kake zama a can din....kaga...magana ta wuce tashi ka tafi,kada ayi visa da ita" a hankali ya miqe bai ko dubi sashen da take ba,duba daya zaka yiwa fuskanshi kasan yana cin fushi,ya juya a nutse ya ficea binshi,binshi tayi da idanuwa kamar zata sanya kuka,bacin ran data gani kawai saman fuskarshi ya daga hankalinta "Amirah" taji ummi na kiran sunanta,da sauri ta maida hankalita wajen tana amsawa "Kada ki damu kinji,rabu da shi,ciwon 'ya mace na 'ya maca ne,kina wannan halin na yau lafiya gobe babu ta yaya zaki tafi inda baki da mataimaki sai Allah,qyaleshi ko yayi fushi zaya sauko,ni nasan bazai iya fushi dake ba" maganan ummin ta qarshe ta bawa sumayya kunya,sai tayi qas da kanta tana amsawa da to,duk da haka zuciyarta bata nutsu ba.        Sallamar amira kamar wadda aka jefo ita ta katse maganan da ummi ke gaya mata,da gudunta ta kwaso bata zube gaban kowa ba sai sumayya,ruqunqumeta tayi tana cewa "Wayyo matar yaya na,kin biyamu wallahi,Allah jiya kasa bacci nayi,labarin yazo mun katsam,anty farida ce ta gayamin,sai naga gari kaman da gangan yaqi wayewa don kada nazo na ganki" kunya ta kama sumayya,zungurinta take kan tayi shiru amma ina amira ma ba fuskantarta take ba,ganin yadda kunya ta kama sumayya ya sanya ummi miqewa tsam ta basu waje,ummi na fita ta dalawa amiran duka a cinya,wajen take sosawa tana dariya "Ba komai,wallahi koda zafi ni banji zafin ba,bakya laifi ai ko kin kashe dan su'ad" dariya suka bushe da ita baki dayansu sannan sumayya tace "Kefa iskancin naki ma naga sabon lasisi kukaje ke da saifu aka yi masa,antyn take ma kin daina anty saidai su'ad gatsal,ke kin isa ki kashe mata daa ba sai tayi gunduwarki ba" dariya ta sake saki harda tafa hannu "Wa ya gaya miki son 'ya'yan take,ai ni tuni na san da wannan.....ke mubar zancan waccar.....amiran umman khalipha da gaske anty farida take?" "Shafa kiji" ta bata amsa tana hararta,dariya ta saki "Ai wlh duk wanda ya kalleki yasan da magana.....amma fa kin rame da alama kina shan jiki....Allah ya raba lafiya,kai Allah ya nuna mana wannan rana,zamu karya qugu da kwankwaso" "Ki komawa saifu a gurguwa ko?" "Ba komai sai ayi maleji......can na gano mai dakin naki" "Amira baki da mutunci,waye mai dakina" "Waye banda yaya maan,waishi kuwa har yau bai daina wannan shegen dacin ran nashi ba,na gaidashi ko amsani baiyi ba ya figi mota ya fice kaman wanda aka yiwa dan banzan duka?" Shiru sumayya ta danyi,wato a fusace yake kuma cikin fushi ya fita kenan "Ranshi ne a bace amira" "Haka kullum yake" "Malama ki kiyayi zagarmin miji a gabana......" Ta fada tana hararta,dariya ta saki sosai harda kwantawa qasa "Ikon Allah....yau da bani da aure da nasha haushi,gayamin me akayi masa" "Anqi din" ta fada tana tureta "Habba....nice fa ta hannun daman" ta fada tana lallashinta,sai data ga dama don kanta sannan tace "Dubai yakeso mu koma ni shi da su'ad,daren jiya nace mishi su tafi ni sai cikina ya dada qwari zan taho,ya nuna bai amince ba,yau ummi tace masa ya barni a nan,kaman yadda jiya nace masa.....amira zaiyi tunanin na kawo qararsa ne" "Dai dai kenan....kina zaton a barki cikinki bai qwari ba kibi waccan mai qirar amurkawan ta murqushe mana baby?,sai jikinki yayi qwari yadda baki buqatar mataimaki....ya almustapha kuma qyaleshi,tunda ummee ta fada haka dole zai haqura" shiru tayi tana nazari,kusan maganarsu na kan hanya,ba yau tasan mugun halin kishiya ba,ita sam bata ma yadda da yadda su'ad ke nuna cikin ko a jikinta ba bai dameta ba.         Fitowar ummi ta sanya amira miqewa ta daneta tana cewa "Ummina,i missed you" "Nikam bansan me yasa saif ke biyewa shirmenki ba,duka duka yaushe kuka zo gidan nan wai?" Rai ta bata tana janyewa "Wai ummi nufinki tun yanzu kin fara gajiya da ni,kinsan bazan iya zama ba banzo naga matar yaya ba,qaruwa fa muka samu" ta fadi tana maida kallonta gun sumayya data kauda kai tana mata dariya "Gaskiya ne,kun kyauta ai" ta fadi tana zama amiran ta zauna tsakaninsu suna gaisawa.         Kusan nan ta wuni saboda ba ranar kwananta bane bare ta koma gida aiki,zuwan amiran ya debe mata kewa sosai,sunsha hira kaman ba gobe,abinda bata sani ba shine,dawowan almustapha gida uku yana dubata ya tadda bata nan,abinda ya sake qona masa rai kenan,gani yake ita ta kai maganan wajensu ummi,abinda bai duba ba shine daga daren har wayewar gari suna tare baiga ta fita ba,ta ina zata iya kai qararshi.          Sai bayan magarib ta baro bangaren,a sannan yana saman dining zaune da niyyar cin abincin dare,ya tasa abincin ne kawai a gabanshi,abu goma da ashiri ,ko kusa baya son abincin kuku,sannan ga damuwar sumayya a gefe guda,da sallama ta shiga falon,yana daga can saman dining,binta yayi da kallo cikin bacin rai ba tare da ya amsa sallaman ba,tun kayan safiya ne a jikinta abinda bai taba gani ba,hali take so ta sauya?mema taci wunin yau bayan yasan banda nama saiko shinkafa 'yar kadan take iya sawa cikinta,magungunan ta na yau ya duba baki daya ba wanda tasha,tana dab da shiga balcony da zai sadata da dakunan baccinta ta jiyo dakakkiyan muryarshi a atsawace yana kiran sunanta,hanjin cikinta ya kada ta runtse idanunta kafin ta waiwayo "Daga ina kike?"daga kai tayi ta dubeshi don maganar ta mata banbarakwai,yana zaune ya hade hannayensa cikin na juna yana dubanta "wajen.....waj....ummi"ta fada cikin dan daburcewa,sai ya miqe tsaye yana zuba hannayenshi a aljihun wandonshi ya dan tako kadan zuwa bakin step din dining din "Ba sai kinyi haka ba zaki nuna baki qaunar kasancewa tare da ni,duka ba wannan ce damuwata ba...me kika baiwa babyna yau?,....tsaftar jikinki wanda tun kayan safe ne jikinki" "Ai naci abincin da amira......" "Amira?.....amira ita ta tsaidaki kenan ko?,ita tazo?" Ya fada cikin sigar tambaya da jin zafi,shiru tayi bata amsa ba,hakan ya sanyashi cikin hanzari ya fara saukowa daga kan step din zuwa qasa yana fadin "Na baki mintina goma ki tabbatar kin sake wanka...ki canza kayanki....ki dauki abincinki kici kisha magani..." Ya qarashe maganar cikin huci yana kewayeta ya fice.          Dariya su'ad ta saki wadda ta riski zancanshi na qarshe "Sai haihuwa manya.....kinga kadan daga illolinta ko?,har kin fara qazanta kenan.....baki sani ba,bama zama da qazami,hakan yana nufin kin fara saitawa kanki hanya"ta fadi tana saukowa daga sama tsuke cikin riga da dogon trouser qoqarin daidaita kanta tayi kafin ta qiriqiro murmushi " wani ko zai shekara baici ba wa ya damu da shi?,ke dai kiyi ta kanki,wadda ba'a damu da wuninta cikin gida ko waje ba,koda watar qasar ce kuwa ta shekara can,duka daya wajen wanda ya ajjeta"ta juya ta shige ta bar su'ad abin na mata zafi a rai,da ita take,tana yaba mata magana ne kan zamanta america almustapha na dubai,ranta ya baci qwarai,ta tsaya nan saman matakalar bene tana ciza yatsa.         Duk data rama hakan bai hana zuciyarta suya ba,komai zai mata ya kasance su biyu,bata son ace har gaban su'ad yana yi,haka dabi'arta take ko a gidajenta na baya,sai ta fashe da kuka maimakon ta shiga bandaki yin wanka sai ta fada saman gado tana ci gaba da rusa kuka.        Bangaren ummi ya wuce direct zai saukewa amira,taimakon da Allah yayi mata ko layin motarsu bata gama ficewa ba ya shigo neman nata "Sun tafi yanzun nan,lafiya?" Ummi ta tambaya tana karantarshi,fushi ne taf cike a zuciyarshi da fuskarshi,batasan me ya taboshi haka ba,tunda ita bata dauki maganan hanasu tafiyan ta kai haka ba "Ba komai...." Ya fada yana juyawa wannan karon a sanyaye ya fice,sai ta bishi da kallo kawai ta girgiza kai tana ci gaba da yin abinda take.         Yana shiga su'ad ta taroshi,har saman dining ya zauna tana karairaya fari da karkade karkade,babban abin takaicin sai da yace "Bani abinci" yana lumshe ido saboda yunwa da fushi,yau duka saboda bacin rai baici komai ba,zuba masa tayi ta tura gabanshi tana debo masa labaran da sam basu shafeshi ba tana masa,idan yayi loma daya sai ya jima baiyi ta biyu ba,ga surutunta da ya soma hawa masa ka,sam labarin da take bashin sake caja mishi kai yake,labarin abokanta karatunta maza da mata,duka bata lura da hakan ba bare ta sarara,rabin hankalinsa baki daya ya karkata bangaren sumayya,yana so yaji daga gareta,haka kawai ya kasa nutsuwa,baya so kuma ya shiga haqqin su'ad ya bar ta wajen hakan bai dace ba.         Wayarta dake daki ta soma kira tana sanar mata da sunan wanda ya kirata,qawarta ce zulee,wadda idan suka soma waya tana bata labarin bayan dawowarta nijeria har sai a qalla sun kashe kusan awa,da hanzari ta miqe tace mishi tana zuwa,kai kawai ya kada yana ci gaba da tura abincin,qoqari yake ya ture tunaninta daga zuciyarshi amma ya kasa,daga qarahe dai ya tabbatar bazai iya din ba,ture plate din gabanshi yayi wanda ya sanya abincin zubewa ya miqe,kai tsaye ya durfafi dakin.         A kwance ya cimmata kamar dazun tana fidda hawaye,taji motsin shigowarsa amma bata motsa ba,qare mata kallo yayi sannan ya sauya akalarsa zuwa bandaki,ruwan wanka ya hada mata sannan ya dawo dakin gadon ya tsaye a kanta cikin dakiya "Tashi ki wuce kije kiyi wanka,wannan ya zama last da zan kanki kina kuka,idan ba haka ba ranki zaiyi mummunan baci" a kasalance ta miqe tana rangaji tare da qwalla ta shige bandakin,locker dinta ya jawo ya fidda magungunanta ya ajjiye,ya shiga kitchen dinta ya fiddo plate ya juye gasashshen naman daya siyo mata da shinkafa 'yar kadan a gefe guda.        Tana yafe da qaton towel ta fito,a sanyaye ta qaraso bakin gadon ta zauna,tura mata dan table din daya saka abincin da magani yayi a kai ya juya a hankali ya fice,yayin data bishi da kallo qwalla na taruwa a idanunta.        Cikin dare ya kasa bacci,ji yake kamar yaje ya roqeta ta bishi amma wani sashe na zuciyarshi na hanashi,a hankali ya sauka daga saman gadon,ya zura slippers dinsa ya fice bayan ya dauki wayarshi,qofar ya tura a hankali,dakin lullube yake da duhu,ya ci gaba da takawa har ciki bayan ya kunna fitilar wayarshi,har lokacin itama bacci bai dauketa ba,wani iri take ji cikin jiki da zuciyarta,tana jin shigowarshi tayi hanzari rufr idanunta tare da qara yin luf tamkar mai yin bacci,ragowar hawayen dake maqale a fuskarta ya tona asirin baccin qarya take,ya dauki wajen minti biyar yana duban kyakkyaar fuskarshi,fuskar dake sanyaya mishi rai,fuskar da duk duniya ayanzun bayan ta umminsa yana jin yafi qaunarta,don me zata guje mishi a sanda yake tsaka da tsananin buqatarta ita da abinda yake cikinta,kada dai ace har yau bata sonshi?,har yau bai cimma nasarar zama wani sashe na rayuwarta ba?,sai ya juya a hankali zuwa inda ya ajjiye mata abincin,yasa hannunshi ya bude,ba abinda ta taba aciki,ya duba magungunan ta balla ta sha duka,hankalinshi yaji ya tashi ranshi ya dugunzuma,sai ya kunna wutar dakin baki daya "Wakeup" ya fada a taqaice,shiru tayi ita adole bacci take "Ki tashi nace miki!", ya fada a dan tsawace,cikin hanzari ta miqe,daukan abincin yayi ya isa gabanta ya zauna suna fuskantar juna,cokali ya sanya mata ya mata alama da ido kan ta dauka taci,hannunta har rawa yake saboda yunwa,hakan ya sanya ya amshe cokalin ya soma bata a tausashe duk da fukarshi a dinke take,a hankali ta soma karba,tana ci tana satan kallonshi,saidai ko kadan yaqi ya kalleta, "Abu abdallah"ta kirashi tana kallonshi,yana son sunan qwarai amma wannan karon sai yaqi dubanta,hakan ya karya mata zuciya ta kuma sakin kuka harda 'yar shashsheqa,sai ya ajjiye cokalin yana hade yatsunshi waje daya tare da zuba mata ido,kukanta na ratsa zuciyarshi tamkar ana yankar tsokar zuciyarshi,tsahon minti biyar sannan ya motsa bakinsa "yanzu fisabilillahi ni me nayi miki?me ke damunki?" Ya fada murya can qasa a tausashe,wanda hakan ke nuna raunin dake cikin zuciyarshi "Kain....ne" ta fada cikin sheshsheqa,ci gaba yayi da dubanta kafin yace "Saboda Allah a dakeni a hanani kuka?,saboda ni ban da bakin kukan?,kinsan zafin da nakeji a qirjina?,ina tunanin har yau baki gama yarda da wacece ke cikin rayuwata ba shi yasa kike son aikata min haka,amma babu komai....Allah ne ya jarabceni kuma ina fatan ya yayemin,tunda baida amfani sanya mutum cikin zuciya,da can da ban sanya ba kinga rayuwata lafiya lau..." Bata ji dadin furucinsa ba,sai ta sake sakin kuka "Kayi haquri don Allah" "Zan haqura ne kadai idan kika shaidawa ummi zaki bini,ke kadai zaki fada mata ta yarda" kai ta girgiza,ba zata iya watsawa ummin qasa a ido ba,tace mata meye?,kafadanshi ya daga sannan ya miqa mata ruwa,tare da tsareta da ido,tilas ta sha ya kauda kayan ya ja mata bargo zuwa saman cinyanta ya gyara mata filo,bai sake sauraran komai ba ya kashe qwan ya ja mata qofar ya fice. Washegari yaje kaima baba qara,saidai duka bakinsu daya da ummi,hakan ya sake jagula lissafinshi,haka ya fice jikinsa ba qwari,baki daya sai yaqi zaman gidan,ya wuni waje,yayin data wuni begen ganinshi,amma bata ga gilmawarsa ba,wuni tayi bata leqa ko ina ba tana daki akwance abinta. Randa ta amshi girki ya rage saura kwana biyu su tafi abida ta haihu,su'ad anata rawar kai tare da shirin tafiya,jifa jifa idan sun hadu a falo tana yadawa sumayya habaicin zasu tafi banda ita,ita tana tsammamin uban tafiyar ne yace ba zata je ba,sabida tana laulayi,ko kallonta batayi bare tasan tana yi,ita ayanzun fushin almustaphan yafi komai daga mata hankali,kaf ta laluba walwalarta ta rasa,ji take kamar taje ta cewa ummin zata bishi,saidai hakan ba mai yiwuwa bane,kawai kunya mai tsanani tattare da hakan. Ana ya gobe zasu tafi suka je yima abida barka,ta samu santalelen danta namiji tubarkallah da shi,babyn ya burge su su duka,sai taji kwadayin son ta haihu ya sake kamata,ta shafi cikinta ta cikin mayafi tana ddu'a cikin ranta,tana son taga ta tara yara da yawa,wanda ta fuskanci ra'ayin almustaphan ma kenan,su'ad kam dama bai mata tayin zuwa ba,don ko yayi mata dama bata zuwa,don ba shirin arziqi tsakaninta da abida,ta raina ajawalin abida yayin da ita kuma abidan bata daukan raini sam,bata roqa komai daga gareka ba don haka kada ka raina mutincinta,kowa ya tsaya matsayinshi,ya dauki sumayyan bayan sun biya wani katafaren shago sun mata siyayyan kayan barka masu yawa kyau tsada da kuma quality,har ita abidan sai da ya saya mata kayan fitan suna masu kyau bawai don hamza ya gaza ko bai da shi ba,kawai ya wuce komai a wajensa,ya dora musu kudin dinki dubu dari a saman kayan,tun jiya take dubanshi,duk abinda yake kawai gashinan ne babu karsashi sam tattare da shi,tana jin hamza na kwasarsa kan me ya sanyashi laushi amma yayi masa shiru bai ce masa uffan ba,shi ya tuqasu hakan ya sanya su biyu kenan suka fita,a parking space ya tsaida motar ya kasheta,sai ta kasa fita tana dubanshi kawai,bai dubeta ba ya dage gilasan motar,ya kwantar da kujerar ya miqar da bayanshi a kai,hakan ya nuna bai da niyyar fita kenan,ta jima tana dubanshi kafin tace "Kayi haquri don Allah" ya jima shiru kafin ya bude idanunsa da suka kada "Da kikayi me?" "Na rashin tafiyarmu tare" ta fada tana murza yatsunta "Ba abun damuwa bane ai tunda bake kadai bace" maganar ta soketa,ranta ya baci,kishi ya soma cinta "Haka ne" ta fada tana dora hannunta kan mabudin motar ta bude ta fice,ta gefan ido ya bita da kallo,ya rasa yadda zaiyi controlling kanshi,bai taba damuwa da wani abu haka ba,sonta ba qaramin mamaya ya yiwa zuciyarsa ba,yana son ya daure kan rashin tafiyar tasu tare ko don abinda ke jikinta amma ya kasa,tun yanzun kewarta ke damunshi,nan yaci gaba da kwanciya,baison ya shiga ya taddata cikin rashin walwala ko kuka,hakan na tabashi,bashi ya shiga ciki ba sai sha daya na dare. A falon qasa ya tadda su'ad sanye da kayan bacci,tsaye bakin t.v tana shan ruwa cikin gora,dubanshi tayi tana sakin murmushi,wani dadi ke ratsata a kwanakin nan,ta fuskanci kamar akwai wata a qasa tsakanin sumayyan da almustapha,bugu da qari kuma ga tafiyar da zasuyi daga ita sai shi "Welcome" ta fada tana murmushi "Yauwa....baki bacci ba?" Fari tayi da idanu tana cewa "Wlh ban kammala shirina bane"dubanta yayi cikin mamaki,don bai taba ganinta cikin zumudi haka ba irin wannan lokacin,don ko tafiya ta kamasu tare wano lokaci idan tana wata sabgar saidai su raba flight ita ta biyoshi "Ya kamata kam ki gama da wuri,don tafiyar safe ce" "Ba damuwa ai" ta sake fadi tana faari "Sai da safe" ya fada yana ci gaba da takawa,binsa tayi da kallo kafin tace "Ok goodnight" ba haka taso ba,so tayi ta bata masa lokaci a nan,har sumayya ta gaji da jira taga bai shigo da wuri ba,koma tazo ta samesu tare. Sanda ya shiga tana gaban mudubi sanye itama da kayan bacci tana gyara gashinta,kaya ne da bata taba sanyasu ba cikin kayanta,sun bala'in karbar fatarta,abinka da mai yaron ciki,ga wani kyau na musamman data ajiye,kanshi ya dauke ranshi na suya idan ya tuno gobe warhaka basa tare?,har ta kammala shirinta ta kwanta bai gama nashi ba,bacci ya soma rinjayar idanunta,cikin baccin taji ya janyota cikin jikinsa ya rungumeta tsam,shiru tayi ba tare data yi qwaqwqwaran motsi ba,saqonni ya fara aika mata kafin daga bisani su shiga babbar headquater. Sosai ya moreta tamkar wani mai biyan bashi,sam bata isarshi ko yaji ya gaji da ita,kamar ana sabunta masa ita ne,tana kwance jikinsa baki daya gabbanta sun mutu,amai ya dinga taso mata,ga yunwa da take ji,bata ankara ba ta soma sheqashi,ya miqe da hanzari ya riqeta gam,sai data amayar da duk abinda taci,tana jikinshi bai damu da yadda ta bata shi ba,sai daya gyara mata jikinta sannan ya gyara gadon ya sauya zanin gado ta koma can,yace ta zauna ta huta kafin ta sake kwanciya "Abinci" ta furta a hankali,da kanshi ya shiga kitchen karon farko ya dumama mata a na'ura sannan ya kawo mata,yana zaune opposite dinta yana kallon yadda take cin abincin hannunshi rungume a qirji,zallar tausayinta ke ratsashi,bai taba zaton haka mata ke dawainiya da shan wahala da ciki ba sai yanzu,a haka har wasu ke iya yadda ayi musu cikin shege?,su haifan yaro su iya yarwa?,ko su bayar?,ko su kashe shi da kansu?,sai ya tuna gidajen marayunshi da irin yawan yaran da ya qunsa, "A irin wannan halin kikeso na tafi na barki ke daya?" Ya samu kanshi da furtawa a sanyaye ba tare da yasan furucin ya fita ba,dubanshi tayi itama cikin sanyi tace don kewarshi ta fara bugunta tun jiya "Haka ummi suka tsara,nasan saboda qaruwarmu sukayi hakan,kuma na tabbata ummi zata kula da ni fiye da yadda zaka yimin,dukkanmu ta fimu sanim zafin haihuwa" ko yaushe kalaman girmama iyaye daga bakinta sune gaba dan komai,idanunsa ya lumshe yana jin kamar yace ya fasa tafiyar,ji yake kamar zasu rabu ne ba zasu kuma ganin juna ba,da sauri ya kori wannan mummunan tunanin daga ranshi tare da yin ta'awizi. *saura naji an zage mustapha tsaf,lol😂😂kada kuyi qorafi,duk dadin zamanku wataran dole a samu sabawa juna* *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 9⃣7⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *Allah madaukakin sarki yana cewa* *haqiqa Allah ma'abocin falala ne abisa mutane,saidai,yawancin mutane basa gode masa* ______________________________________         Wani dare suka gabatar wanda kusan rabinshi basu samu bacci ba,sai da suka idar da sallar asuba wanda shi yayi limanci sannan wani bacci mai nauyi ya dauketa,dubanta ya dinga yi saman abun sallahn,tausayinta yake ji,daren jiya kawai amma sai yaga ta fada baki daya,kanshi ya dauke a hankali yana ci gaba da karanta azkar dinshi.          Bugun qofan aka soma yi a kai a kai,wanda hakan yayi sanadin farkawar sumayya,a hankali ya miqe yana mamakin waye wannan,bude qofan yayi,su'ad ce tsaye cikin kayan bacci tana jifarshi da murmushi "Lafiya?" Ya tambayeta cikin mamaki,fuskarta dauke da murmushi tace "Cewa nayi ko zaka zo muje ka shirya" waiwayawa yayi ya dubi agogon dake manne bangon dakin,baki daya qarfe bakwai da minti hamsin da hudu na safe,sai ya maida kanshi wajenta "Halan baki ji qarfe nawa nace miki zamu tafi ba ko?,sha biyun rana shine har zan fito ma shirya yanzun?" Kasaqe tayi,tayi nufin janyeshi ne,yadda sumayyan ba zata sake ganinshi ba,wataqila ma sai bayan sun dawo "Shikenan" ta fada gwiwa a sage tana juyawa,ya maida qofar ya rufe sannan ya tako zuwa cikin dakin,tana zaune tana murza yatsunta a inda ta tashin,da alama ba isarta baccin yayi ba bugun shi ya tasheta "Ina kwana" ta gaidashi kanta a qasa "Lafiya lau,ya jiki" ya tambayeta yana komawa inda ya tashi ya sake zama "Alhamdulillah" ta maida masa tana miqewa,toilet ta nufa ya bita da kallo har ta shige. *Bayan awa hudu* Kwance take lamo cikin dakin dake bangaren ummi wanda ta ware mata,tun bayan awanni hudu da tafiyarsu babu abinda ta iya tsinanawa sai juyi da take daga farkon gadon zuwa qarshenshi,ba wani loko ko saqo dake jikinta wanda kewarsa sonshi da qaunarshi basu bi sun illata mata ba,hango sallamarsu take da kuma sallamarsu tsakanin shi da ita,hawaye ya gangaro mata ta sanya hannu ta sharce,har ya tafi tana iya hango damuwa qarara kan fuskarshi,furucinsa na qarshe sanda ya sanyata cikin jikinshi suna sauraron bugun zuciyar junansu "Ki taimakeni ki bini.....ki cewa ummi zaki" a sanyaye ta girgiza kai duk da tana kwance qirjinshi "Bazan iya ba.......kunya nakeji....kayi haquri" bai sake cewa uffan ba face zareta da yayi daga jikinshi,ya fiddo kudi da kuma daya daga cikin ATM dinshi ya ajjiye gefanta,ya tsugunna gabanta a hankali ya yaye rigar jikinta zuwa saman cikinta,ya dora tattausan lebbansa ya sumbaceta sannan ya miqe,duka wannan abun da yakr yaqi yarda ya dubeta kamar yadda take nacin duban qwayar idanunshi,a hankali cikin takinshi ya juya har ya fice daga dakin idanunta na kanshi. Ba irin sallamar da takeso suyi ba kenam,saboda haka tunda ya fita take faman kiran layinshi saidai ba'a daga ba,bata daina kira ba har sai da aka tabbatar mata wayar a kashe take,abinda ya sake karyar mata da zuciya kenan har yanzu yake fidda hawaye,zuciya da gangar jikinta baki daya a quntace suke,wunin ranar baki daya a quntace tayi shi,duk da yadda ummi ke nan da nan da ita,duk abunda take buqata dama wanda bata buqata ta tanadar mata shi. Bata sake tabbatar da cewa lallai almustapha ya zama wani sashe na rayuwarta ba sai da dare yayi,baki daya bacci ya gudu a idanunta,fafur yaqi zuwa,dole ta shiga bandaki ta daura alwala ta yi sallolinta yadda zata iya,duk juyin da zata yi sai ta dibga hangoshi gefanta sanda yake bata kulawa,cikin jikinta take jin tamkar ta rasa wanu babban sashi daga jikinta. Washegari kallo daya ummi tayi mata ta fuskanci batayi bacci ba,wannan dalili ya sanya ta sanyata gaba sai data tabbatar ta samu isashshen bacci,ta sani fushin mijinta ke damunta,saidai baki dayansu kuwa suyi haquri,don ba zata taba bari wani abu mara dadi ya faru ga sumayya ba,idan da ace su'ad din mai aiki da tunaninta ne babu abinda zai sanyata rabasu,zata barau suyi tafiyarsu tare,amma a irin wannan qadamin da ake ba zata lamunci tafiyarsu wata uwa duniya ba a sanda sumayyan ke da buqatar taimako,a yammacin ranar iyalan adam suma suka shirya komawa lagos wajen mijinsu,sumayya na zaune falon ummi tana kallon wani comedy,babu abinda ya dauke mata na daga kewarshi da take,saidai ya dan dauke hankalinta,anty ni'imah ce ta shigo cikin shirinta,sanye take da doguwar riga ta atamfa da yalwataccen mayafi,bayanta hibba ce da hibban,sai nasrin da take riqe da hannunta,yaran baki dayansu sanye suke da qananun kaya,sam gori da rashin mutuncin fahariyya bai hana anty ni'imah riqon 'ya'yan tamkar ita ta haifesu ba,bugu da qari ya adam din tsayayye ne a tsaye yake hakan shi ya sauqaqa tsiya da wariyar launin fata da fahariyya taso koyawa yaran,fuskokinsu ita da sumayya dauke da murmushi suke gaisawa,su hibba suka gaidata suka shige kitchen kiran ummi,murmushi ni'imah ta sakeyi tana duban sumayya "Sannu anty amarya(yadda yaran sukan kirata wani lokaci kenan),ashe qaruwa muka samu" a kunyace sumayya tayi murmushi ba tare data amsa ba "Allah ya inganta ya raba lafiya ya kawo na 'yan baya" nan ma bata masa ba saboda kunya,dubanta tayi "Ina miki addu'a kice amin wallahi,haihuwa ai babbar ni'imah ce" ta fada wani abu na taba ranta,yanayin fuskarsa ya dan sauya,dubanta sumayyan tayi tana karantar yanayinta,wani yanayu data taba tsintar kanta can baya shekaru biyar zuwa shida a baya ya soma dawo mata,tasan me take ji,ba shakka ba kowanne mutum ke iya fuskantar yanayin da mata irin su ni'imahn ke ciki ba sai wanda ya taba tsintar kanshi ciki,al'amari ne mai taba zuciya da tsayawa a ran dukkan wata diya mace sata tsinci kanta cikin irin wannan jarabawar,sai ta tsinci kanta da kamo hannun ta,ta daga kai suka hada idanu,tuni qwalla ta cika idanun ni'imah,qaqalo murmushi tayi sumayya ta maida mata "Kada ki damu anty ni'imah,lokaci wataran sai kinga gamkar ba'ayi ba,kinsan na taba tsintar kaina cikin yanayin da yafi naki muni?" Cikin mamaki take duban sumayya,kai ta jinjina mata alamar tabbatarwa "Kan na samu abdallah na sha wuya anty,ba wanda ya taba tsammatar abdallah zaizo duniya....amma yanzu fa.....kinga kamar ba'a yi ba ko?,to kema kusan hakane in sha Allah" "Allah ya amsa amiran yaya musty...don yanzu bata umman khalipha bace" ta fada tana qoqarin maida qwallarta tare da jin sanyi cikin zuciyarta da addu'ar da sumayyan tayi mata,daidai sanda ummi ta fito tana cewa "Wai tafiyar ce ne?" "Eh wlh ummi" anty ni'imah ta fada cikin girmamawa tana murmushi,qarasowa ummin tayi ta zauna sukayi sallama,sannan ta miqe suja fice sumayya na dagawa su hibban hannu. Da dare sai ga babbar 'yar anty farida sajida,ummu tasa aka daukota duk don sumayya taji dadin zaman gidan,tunda gidan ya dade babu kowa,sajida akwai hankali nutsuwa da wayo,hakan ya sanya sumayya ta fara jin dadin zama da ita sosai,akwai surutu,a qalla zatayi shekara goma sha biyu,ta nan gidan take tafiyarta makaranta,idan ta dawo sumayya tayi mata qarin karatun addini,tunda a sannan an musu hutun islamiyya. *Bayan sati daya* Sha biyu saura na sare tana saman gadonta,sajida na gefanta kwance,tuni ta jima da yin bacci,kamar kullum tunaninsa ke faman yi mata kaikawo cikin zuciyarta,idan har cikin sati gudan tace ta samu walwala ta minti biyu tayi qarya,duk da tsantsar kulawa da take samu daga bangaren mutane ukun nan,ummi anty maamaa da shi kanshi baba prof,tun daga randa ya kira ummi ta sanya dukkan kulawarta kan wayarta ko zata ga kiranshi amma babu shi ba alama,ko saqon tafi da gidanka bata ci nasarar ganin gilmawarsa ba daga gareshi balle kira,kusan sau uku tana jinsa suna waya da ummi amma bai taba nemanta ba,wayar tata ta janyo ta bude tana duban lambobin wayarshi data dauka daga wayar ummi,amma gefe daya na zuciyarta ya hanata kiranshi,akan me ma zata nemeshi bayan shine a haqqu daya nemeta,ya sani ai tana son binsa amma dole subi umarnin na gaba da su,haka taci gaba da juya wayar a hannunta wanda ba jimawa wani zazzafan a mai ya taso mata,tuni ta miqe cikin hanzari,saidai bata kai ga kaiwa toilet ba ta durqushe a nan ta soma kelayashi ba qaqqautawa. A daidai wannan lokacin almustapha ne zaune bakin system yana aiki,tun yanayi da qarfinshi tuquru har ya soma gazawa,baki daya ta tafi da dukkan wani walwala da karsashinsa,hatta da manya da qananun ma'aikata sunsan walwalar yallabai ta ragu,duk da dama can shi ba mai yawan fara'a bane,amma karsashinsa da son aikinsa cikin kaso dari babu hamsin,hannunshi ya dora saman kanshi yana shafa bayan ya jinginar da bayanshi jikin makarin kujerar,a hankali zuciyarshi ke masa quna,wani bala'in qishirwarta na ratsashi,ji yake a lokacin da yana da ikon komawa tsuntsu ba abinda zai hanashi yin fiffike ya isa gareta,duk wani qwarin qwiwa da burin yin aiki da ya taho da shi babu su duka sun yi nasu guri,duk wani alwashi da yaci na nesantarta tunda bata buqatar zama tare da shi ya ruguje,kwanaki bawaki kacal da baiji ta jinsa yake tamkar wani dabaj cikin jinsin mutane,yanzu haka cikin jikinshi zuciyarsa ke gaya masa idanunta biyu batayi bacci ba,idanunsa ya bude ya janyo wayarsa kamar ko yaushe,ya bude hotonya tun wanda tayi cikin wayar sanda suna dubai da doguwat riga,hotunan da yayi mata a dubai garden glow wanda batasan da su ba,wadanda sukayi bala'in yin kyau,tamkar ta kirata ta amsa,hannunshi ya sanya yana shafar fuskar tata,kewayaen labbanta wadanda idan ya tuna taushinsu tsingar jikinsa ke zubawa,kyakwawan idanunta da kwantacciyar sumarta,tamkar wanda aka bawa aikin zana taswirar fuskarta haka ya dinga zooming yana qare mata kallo,wata wawuyar ajiyar zuciya ya saki tana jin zuciyarshi kamar zata fito waje,ba tare da ya shirya ba ya samu kanshi da yin dialing number dinta,ya zubawa wayar ido yana sauraren jin koda saukar numfashinta ne,saidai wayar harta qaraci rurinta ta tsinke ba'a daga ba. Sumayyan na zaune dirshan a inda tayi aman tana maida numfashi,ta hangi wayar na haske,saidai ko data miqe ta dauko taga number dinshi ce sai ta maidata ta ajjiye,ranta na wani irin baci,sai yau zaya nemeta,sai yau yaga daman magana da ita?,wato kota mutu ko tayi rai ko?tunda yana da wata matar,zuciyar kishi ta soma saqa mata wannan maganan,hawaye ne ya balle mata wani mahaukacin kishin su'ad na ratsata,ta shiga toilet ta dauko mopper ta gyara wajem fes sannan ta dawo saman kujera ta zauna tana maida numfashi,tana kallon wayar nata fidda haske alamun kira ne,amma saita lumshe idanunta ma ta daina ganin wulgawar haskenta baki daya,hangoshi kawai take shi da su'ad cikin walwala wanda hakan shi ya sanya kenan ita ya bagarar da ita. Baki daya hankalinsa ya dugunzuma,tunda yake ita ce mutum ta farko a duniya daya taba kira sama da sau biyu,duka shi ba wannan bace damuwarshi,me ya hanata daga kiranshi bayan jikinsa na bashi idanunta biyu?,tun yana zaune har sai da ya miqe tsaye,baisan sanda ya samu kansa yana kiran layin ummi ba ha tare daya tuna cewa dare ya fara nisa ba ko kuma tana wajen baba,cikin tsakiyar baccinta taji qarar wayar tata,dama ba wani nisa can baccin nata yayi ba,gama sallolin nafikarta kenan ta kwanta din ko hijabin jikinta bata cire ba,macace mai yawan tashi dare,bata fiya kashe darenta baki daya wajen yin bacci ba,sunan almustapha data gani ya dan sata faduwar gaba "Lafiya dai almustapha sha biyu da minti biyar na dare?" Sai a sannan hankalinshi ya koma jikinshi,ya dan gyara muryarshi "Aaaa.....dama....ba komai...inata kiran sumayyah bata daga bane" ajiyar zuciya ta saki "Ka sani fa lokacin bacci je yanzu,kuma kasan muhimmancinsa wajen mace mai ciki,ka bari da safe ka kirata ko ita ta kiraka don na tabbata yanzun ta dade da yin bacci,don yau ana gama sallar isha'i taje ta kwanta" gabanshi ya soma faduwa,addu'a yake kada Allah yasa ummi ta tursasashi kan ya bari sai goben,shi kadai yasan me yake ji a qirjinsa game da ita,muryarta kawai yake da muradin ji,Allah yasa ta fahimceshi "Batayi bacci ba ummi.....don Allah ko zaki hada....." Sai kuma ya kasa qarsawa,nayin ummin yake ji,itama a nata bangaren kasaqe tayi,tausayi irin na d'a da uwa ya kamata,ta tabbata ba zaya samu rabin kulawar da yake samu wajen sumayya ba,tsanin miji da mata sai Allah,kada kuma ta shiga haqqinsa da yawa "Barin kai mata" cewar ummi "Yauwa ummi thanks" ya fada cikin wani irin zumudi tare da sauke ajiyar zuciya wadda har sai da ummin ta jiyo,murmushi ta saki tana saukowa daga saman gadon,tasan halin yaronta sarai,tun yana qarami bai iya son abu ba,bai iya sanya abu a zuciya ba,duk abinda yake so bai riqonsa da wasa,hakan ya sanya tun da can baya ta duqufa masa addu'ar samun mace ta gari wadda zata masa yadda yake so ba tare data wahalar da shi ba. Qofar dakin data ji an turo shi ya sanyata bude idanunta,suka hada ido da ummin sanda ta kunna wutar dakin "Me kike zaune kikeyi amira?,da gasken ashe baki bacci ba"murmushi ta dan qaqalo "gajiya nayi da kwanciyar sai na zauna na dan huta" "Ko dai wani abu ke damunki?,ki gayan gaskiya" kai ta kada kanta a qasa "A'ah ummi babu komai,kawai na gaji da kwanciya ne" "To ko dakina zaki koma?" Ta fadi tana qarasowa gabanta "Nan din ma yayi fa ummi" "Indai akwai wani abu da bai miki dai dai da yadda kikeso kada kiyi nauyin baki ki sanar min......mijinki ne dama ya tasoni....maimakon ya kira taki wayar" ta fada tana dan murmushi tare da miqa mata wayar sannan ta juya zata fice "Idan kin gama ki barta nan wajenki ko zuwa safiya na karba" ta fada tana ficewa tare da rufe mata qofar,wayar sumayya tabi da kallo sanda ta sake ruru,sunanshi ya fito baro baro,sai ta kauda kai kibiyar kishi na sukarta,wani kiran ne ya sake shigowa,a hankali ta shafa wajen amsawa ta daga ta kara a kunnenta "Sumayyah!" Ya fada a tausashe cikin salon muryarshi dake ratsa zuciyarta,muryar nan da take mutuwar so, "Sai yau kaga daman nemana?,ba ruwanka da hakin da nake ciki ko?,dama ba sona kake ba baka damu da ni ba...." "Sumayyah" ya sake kiran sunanta karo na biyu ya katse ta a tausashe,kiran sunanta kadai ya karya mata zuciya kawai sai ta saki kukamai hade da sheshsheqa,idanunsa ya lumshe bugun zuciyarsa na qaruwa "Ya salam!" Ya dinga furtawa can qasa tana shiga cikin kunnenta,ita kanta batasan me ya saka ta kukan ba,daga inda yake tsayen sai tsaiwar ta gagareshi,komawa yayi saman kujerar shima yayi kwance rigingine,wani dafi take zubawa zuciyarshi ba tare da ta sani ba,nadama ta kamashi,me yasa ya watsar da ita don kawai taqi binshi,shi kansa yasan cewa kansa da kansa ya hora,yama fita jigata,sabida shi din ya rasa komai,duk wani abu data sabar masa da shi a yanzu babu,sannu a hankali ta soma tsagaita kukan don kanta,bayan taji zuciyarta ya soma yin sanyi "Kiyi haquri" ya fada kamar yana mata rada "Ki yafemin.....na kasa sabawa ne.....na kasa daurewa rashinki....kamar maraya haka nake jina....am really sorry banyi da niyya ba" ajiyar zuciyar itama ta sauke,tana jin yadda kewarshi ke illatata,kalamanshi kamar sake tunzura qaunarsa suke cikin zuciyarta,saidai sarautar ta motsa,sai tayi mishi shuru kaman bada ita yake ba "Summy....kice wani abu mana" yadda ya kira sunan nata sai taji kaman mukhtar,sake narkewa tayi cikin kujera ta kuma qi cewa komai din "Samayyahh...." Ya kuma kiran sunanta,ya gane cewa kawai azabtar da shi take sonyi,kamar ya saki mata kuka haka yake ji "Ki kulani ko don babynmu mana,i missed him alort shima fa" nan ba amsa,amma can qasan ranta wani sanyi na ratsata,wanda yayi tasiri har saman fuskarta,ta soma fidda wani boyayyen murmushi "Wallahi tallahi na rantse idan baki ce min komai ba a gobe zaki ganni abuja" dariyar da take boyeea ta qwace mata,zata fi kowa son hakan,saidai bata masa adalci ba idan har tasa daga komawarsa cikin sati guda ya kashe kudin ticket dinshi ya sake dawowa,me zata cewa su ummi ya kawoshi "My happiness...." Ta amsa mishi cikin wani irin salo wanda ya saukar da gungun farinciki wa zuciyarshi,ya sauke qatuwar ajiyar zuciya "Ki tabbatar min da cewa kina lafiya keda baby na"a shagwabe tace "ba wani.....bayan baka damu dani ni da babyn ba...." "Ya ilahi....daina fada don Allah kada ki sani cikin wani hali.....ki fadi abunda zai miki yanzu wanda zan wanke kaina,wanda zai nuna miki tsantsar damuwar da nayi da ku" "Just kiss me...." Ya subuce daga bakinta ba tare da tasan ta fadi hakan ba,wani wawan kiss ya bata ta cikin wayar wanda babu inda bai aika saqo ba cikin gangar jikinta da ruhinta sannan ya dora "Ku raba ke da baby na" "Baby yana godiya.....ka kwanta da safe mayi waya,sabida su'ad" ta hada kalaman da qyar,idanunshi ya daga ya dubi qofar bedroom din da take ciki,tunda suka zo ungulu ta koma gidanta na tsamiya,wani abun ma don yana taka mata birki ne "Ban yarda ba" ya maidawa sumayya amsa "Da gaske my happiness.....kaga idan ni kama haka ko bazanji dadi ba" shiru yayi yana murmushi kamar tana gabanshi,sunan data kirashi da shi ya tsaya masa "Da gaske ni happiness dinki ne?" "Sosai.....ban kuma sake tabbatar da hakan ba sai yanzu,na rasa farinciki da walwala na tsahon sati guda sabida batan dabo daka yiwa rayuwata,sai gashi cikin mintina qalilan da jin muryarka komai ya dawo min,farinciki na yadawo,sai tsananin kewarka da nake ji kamar zata rabani da ruhina..." Ta bashi amsa kai tsaye tare da katse kiran saboda tana ji tayi amfani da kalamai masu nauyi,mutuwar zaune kawai yayi daga wancan bangaren,kalan soyayyar da yake da buqata,kalan soyayyar da yake nema ido rufe yau gashi Allah ya bashi,baki daya ta gama kasheshi,dan qaramin ihu ya saki shi kadai kaman wanda ya soma zaucewa,gaskiya wannan karon baya jin zai iya bin umarnin su baba,ko sato matarshi sai yayi,bazai iya jurewa zama ba tare da ita ba,haka ya dinga jera kiranta amma tawi dagawa,daga bisani ta tura masa saqo tana shaida masa bacci zatayi sai da safe,wanda ita kanta bata gaji da jin muryarshi ba,tayi hakanne kawai don kada ta shiga hurumin su'ad. Bacci tayi wanda ta jima bata yi irinsa ba,cikin nutsuwa da kwanciyar hankali da walwala,wanda har kusan makara tayi sallar asuba,ita kanta ummi washegari taga canji sosai,komai nata cikin walwala da kuzari take,kaman yadda kowa yaga sauyi tattare da almustapha har cikin kamfani,ciki har da su'ad,wadda ita bata lura da bai cikin walwala ba,koda ra kura ma watsar da shi tayi ta tsammaci miskilancin nashi ne ya motsa,koma shi dinne ita ba damuwarta bane tunda dole ya zauna da ita,hakanan kuma kudi taba samunsu fiye da yadda ma takesl,abu daya ke damunta yadda ya tikastata saka digayen kaya,haka duk inda zata sai ta tambayeshi,ko zuwa cinema ma ya hanata baki daya,yadda taci burin sakewa da qawayenta bata isa ba,saidai suzo gida su sameta,shima dole su kama gabansu gab da lokacin dawowarshi. ******* ****** ******* Baki daya ya zame mata wani chewing gum din waya,indai ka ganta da waya tofa almustapha ne,har sajida ta soma ganewa,da taga ta soma waya zata basu sarari,duk wani motsinta ha san da shi,wani sa'ilin har kukan shagwaba yake mata kan ta gudo zaya shirya mata komai,saidai kawai taci dariyarta tace bata iyawa,da wanne idanun zata kalli ummi da baba?,. Cikin sati uku kacal ta soma sauyawa,jikinta yayi bul kamar ka taba jini ya fito,laulayi ya fara sauqi sai dan abinda ba'a rasa ba,yanzun kuma sai shegen kwadayi data koya,ci wannan ci wancan,duk da bata rabu da na hannun daman nata ba wato nama,ita kanta mamakin sauqin wannan cikin take. Kwananta shirin anty dije ta dawo,ta gaya mishi zata wajenta,bai hanata ba yace ta gaidata ta kuma kula masa da kanta,sajida ta dauka suja tafi bayan ta yiwa ummi sallama,ummi ta bada wasu tararuka masu kyau ta kaiwa anty dijen. Da minal mutuniyarta taci karo suna wasa da khalioha,dukansu suja durfafota da gudu,ta daga minal tana mata waqarta ta tsokana tana ta dariya abinta tana cewa "Anty sumayya na girma fa yanzu" "Ai naga alama,irin wannan kumatu haka?" Sumayya ta fadi sanda anty dije ke fitowa zuwa falon "Kai kai kai,sauketa....sauketa nace" anty dije tace da sumayya,murmushu tayi tana sauke minal din,kaddai antyn har ta gano ta,numfashi anty dije ta sauke "Ki rufan asiri sumayya don Allah kizo gida na lafiya ki koma lafiya" wannan karon dariya ta baiwa sumayya sai data qyace "Kai anty....kai anty.....wai meye don ma dauki minal,naga ko da can ina daukanta" daquwa antyn ta watsa mata "Da kika ce amma banda yanzu,na haramra,idan baso kike almustapha ya saka mu a black list ba ko ya dauremu baki daya" yatsina fuska sumayyan tayi "Habawa,shi ya fara" ta bi bayan antyn zuwa dakin hara bayan abida ta gaidata nan ta barsu da minal da khalipha. Laila da hafiz ne a dakin suna gyaran kaya,rungume sumayya laika tayi niyya anty dije ta harareta tana mata gargadi,ita dai bata gabe ko meye ba ta gaida sumayyan daga bisani ta hau zuba mata surutu,hafiz dama ya gama abinda yake cikin dakin,shi dama ba gwanin surutu ba,suja gaisa da sumayyan suka dan taba hira ya fice,laila kuwa sai da anty dije ta koreta ta hadata da qarasa girki a kitchen sannan ta fice,fuskar anty fes,farinciki kaman ta hadiye sumayya,kallo daya zaka mata maga sauyi baro bari tattare da sumayyan,ta zama wata matar hutu "Waini zaki boyewa ciki sumayya?,to amira ta gaya min tun muna can" dariya ta saka tana kama baki. "Oh su amira an iya gulmaaaaa" "Abin farinciki ai ba'a biyeshi,ko abbansu khalipha bakiha dadin da yaji ba,yace ko shi yasa rannan da suka hadu da man fuskar nan kaman gonar auduga,abinda bai taba gani ba" dariya suka sanya baki dayansu,ranar hira suka yi sosai da anty dijen,basu koma gida ba sai bayan sallar magariba. A falon ummi tayi sallama tana riqe da hannun abida suna hirar masu tsaron gidan da suka ga an sauya,ummin ce zaune tana kallon labaran duniya,ta amsa musu dai dai lokacin da eesha ke fitowa daga daya daga cikin dakunan dake falon,sanye da gown mara hannu,kanta ba dankwali sai waya riqe hannunta tana dannawa,bisa dukkan alamu bayan fitarsu gidan anty dije ne ta iso gidan,idanu suka hada eeshan ta jefeta da wani kallo,yayin da sumayya ta dauke kanta ta waraso ciki ta yiwa ummi murmushi,ta zauna kan kujera kaman yadda eesha ta samu kujera daya ita ta zauna "Wato gida dadi ko?,sai yanzu?" Murmushi tayi tana cewa "Bansan lokaci yayi haka bama ummi,umman khalipha na gaidaki" "Ina amsawa....kin tafi kin bar wayarki gida wancan sarkin kiran ya kira ya kusa sau hamsin" cewar ummi,sai tayi murmushi tana miqewa,don itama wuni daya kawai amma tayi kewarshi,sajida ce ta gaida eesha ta amsa tana tambayarta mamanta "Au eesha bakiga sumayya bane?sumayya ga eesha zata mana hutu kan ta wuce school"sai data daga kai ta dubeta sanda take shirin wucewa,wani kishinta na sukarta fiye da yadda take kishin su'ad,kyau da hutun daya ratsata ya tsaya mata awuya,komai nata yaji yadda akeso,itama sumayyan juyowa tayi,ta dan saki fuska saboda maganan da ummin tayi "na ganta...mun wuni lpy?" Ta fada adake "Lafiya ya mutan gidan..." Tafada tana yin gaba,qasa qasa ta amsa mata bata sake juyowa ba tayi wucewarta,ta rasa me ya tsarewa eesha a rayuwa,taqamaimai batasan me tayi mata ba,ta san dai kawai rashin jituwarsu tun fara ganin eeshan data yi,sanda amira ta biyota kani satin bikinta,abinda kawai ta sanyawa ranta eeshan nada raina talaka,wanda idan har haka ne ita kuwa ba zata bari ta taka ta ba,tunda itama ta mutuntata ta karramata. Bata sake saukowa ba tana can suna soyewarsu da almustapha kaman su hadiye juna,wanka kawai tayi ta kirashi ya katse ya biyota,ya jima kwance dama ya kasa tsinana komai,muryar tata kawai yake sonji,sun jima suna hirar sannan yace da ita "Af....naso na manta....kaman dazun naji ummi na cewa aisha tazo ko?" Dan jim sumayya tayi sannan ta amsa "Eh haka ne" "Well....,ban so ki shiga shirginta,ki tuna ko yaushe akwai banbanci tsakanin ki da ita" kai ta kada tana mamakin me yasa sam ba jituwa tsakaninsu,ya washi ganinya,bata manta randa ya sake nanuqeta ba a bayan gida bayan ya hango tahowar eeshan,ba shakka ruwa baya tsami banza imma dai ta taba masa wani laifi irin wanda baya so ayi masa ko kuma wani abu makamancin haka "An gama yallabai" "Ba yallabai ba....wancan sunan nake so" dariya ta qyalqyale da ita "To my.....happinesssssss...." Ta fada a rarrabe tare da jan S din wanda sautinta ya ratsa dodon kunnenshi "Ohhhh....babe....ki shiga hankali fa...so kike ki tsokaneni ko?" Dariya ta kuma saki "Ni na isa...kaga ma Allah ya bamu alkhairi sai da safe" "Kina kashen waya gobe zan sa a satoki a kawo min ke,bar wayar a haka ki gama shirin baccinki kizo na saki bacci" idanu ta zaro,tasan me zaiyi mata "Kudin wayanka fa na tafiya" "And so what?" Ya tambayeta a tausashe "Ok...am sorry,amma fa zan iya minti arba'in kamin na gama shirina" "Ba damu bane" ya furta yana kwance rub da ciki saman sofa "Okeyyyy,sai na dawo" "Take care..." Yace mata kaman ya hanata tafiyan. *to ga eesha tazo?ko me zai faru?,ku biyoni muje* Assalamu alaikum fans,ya haquri da ni,sabgogi ne ba yadda bawa ya iya,kana naka Allah na nashi,wani lokaci suyita zuwa maka ajajjere kuma dole ka aiwatar da su,haka zamuyita haquri har mu kammala labarin,ina gaisuwa gareku baki daya,Allah yasa mu dace. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 9⃣8⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *Allah S W T yana cewa annabin rahama sanda ya shiga damuwa kan rashin musuluntar kafirai* *haqiqa kai(annabi muhammad S A W)baka shiryar da wanda kake so,saidai Allah yana shiryar da wanda yaga dama* Saboda haka 'yan uwa kayi qoqarin nusasheshe da bawan dake kan bata,shiriya ka barwa Allah tashi ce. ______________________________________          Washe gari qarfe tara na safiya ta farka da wata iriyar yunwa,kasancewar jiya suna tsaka da waya da almustapha bacci ya dauketa ba tare data ci abinci ba,sajida na gefe tana ta baccinta ta shiga toilet ta wanke bakinta sannan ta dawo ta daura zani kan rigar baccinta ta zura hijabi ta fice.       Kitchen ta shiga tana yin sallama,mai aikin ummi uwani na tsaye gaba gas tana fere dankalin turawa ita juyo cikin sakin fuska ta amsa,hakanan take son sumayyan,ta yaba hankalinta sosai,sam basu taba jin dadin zama da abokiyar zamanta ba shi yasa suke mamakin halayyarta,hasalima umarni ne kawai tsakaninsu,ka saba kuma taci mutuncinka ko gaban waye,kaman bayi take daukansu,gefe daya eesha ce sanye da kayan bacci tana jingine da freezer,hannunta daya riqe da cup,daya hannun kuma waya ce tana amsawa,uwani duka ta girme musu don ta kusa sa'ar ummi,mai aikinta ce da suka jima tare,amanarta da hankali yasa tasu tazo daya da ummi,tunda sumayya ta dawo wajen ummin ita kewa sumayya komi duk abinda take da buqata,fuskar sumayya qunshe da murmushi ta qarasa kusa da uwanin sanda take yunqurin gaida sumayyan tayi maza cikin girmamawa ta soma gaidata,ta amsa tana fadin "Halan wani abun kike da buqata uwar dakinmu?" Murmushi sumayyan tayi "Ai naga ma kaman aiki kike ko?" "Ba matsala fadi abinda kike so sai ayi miki ai......" "Ba aikin wanda zakiyi har sai kin gama min nawa" eesha ta fada tana sauke waya daga kunnenta idanunta a akansu "Ai duka zan iya hajiya aisha....nata aiki yafi mu....." "Bakiji me nace bane?,ko sai na sake maimaita wa?" Ta kuma fadi a gadarance,murmushi sumayya ta yiwa uwani "Kada ki damu baba uwani...ci gaba da aikinki" ta fada tana matsawa gaba,ta samu tukunya ta dauraye ta zuba ruwa da duka kayan qamshin da take buqata ta dora saman daya gas din,sannan ta bude freezer ta fitar da nama ta zuba masa ruwa don ya narke ta janyo kujera ta dawo gefan baban ta zauna suna hira jefi jefi,wannan dabi'a ta sumayyan na daya daga cikin abubuwan da ya sanya baki daya ma'aikatan ke qaunarta,bata dauki rayuwa da zafi ba,komai nata a sauqaqe yake,idanuwan eesha na kanta,baqinciki ya cikata,so tayi taja zancan da tsaho ta yayyaba mata magana ta qona mata rai,saidai anyi katari sumayyan bata bi ta kanta ba,wani wawan tsaki ta ja sannan tace da baba "Saura bayan fitata ki kama aikin wasu,zan shiga wanka kafin ma fito a shirya min saman dining" "To" kawai baban tace da ita,sai ta juya ta fice tana wani taku tana jin kanta dai dai da kowa,da kallon takaici sumayya ta bita sai data fita ta dauke kai,batasan me ta dauki rayuwa ba,yanzu kaman baba data yi sa'a da uwarka idan ba dole ba ma yaushe zaka sanyasu wani aiki "Kiyi haquri baba don Allah" sumayyan ta fada cikin rashin jim dadi,dariya baban tayi "Banda abinki uwar daki ai babu komai,tana cin albarkacin hajiya ne da alhaji,dukkansu su da yaransu an shaida mutanen arziqi ne,don wannan tayi ai ba komai na lokaci ne zata koma inda ta fito" kai ta jinjina kawai suka ci gaba da hirarsu,kusan tare suka gama,wanda hakan yayi dai dai da shigowar sauran ma'aikatan,suka gaisa baki daya sannan ta fice ta basu waje,bayan an kai kayan karin dining saboda harda ummi tayi,gasashshen nama ne da kayan lambu,sai breadin inibi da ruwan shayi,na eesha kuwa chips ne da qwai sai nata ruwan shayin.           Ta tadda sajida ta farka harta gama gyara dakin tayi wanka abinta,sam yarinyar anty farida bata yi mata rainon yaran masu kudi ba,ta iya qananun aikace aikace dai dai da ita,ta iya shata tsaf da gyaran gado,ta gaida sumayyan sannan ta shige toilet tayi nata wankan,ta shirya sannan suka sauko,sun tadda ummi itama ma saukowa a dining suka hade baki daya harda eesha,a ladabce sumayya ta gaida ummi ta amsa fuska sake tana tambayarta ya jiki tace alhmdlh "Amma dai ai zuwa yanzu amai ya tsaya ko?" Kai eesha ta dago tana duban sumayyan,tunda tazi take zargin hakan dangane da sumayyan saidai bata da tabbas sai yanzu,kanta a qasa cikin jin nauyi ta amsa mata da eh "Alhmdlh haka ake so Allah ya qara afuwa" "Amin" tace da ita,kafin ta sake cewa wani abu yaron gidan da ummi ta aika ya soma danna qararrawa daga bakin qofar falon,sumayya zata miqr ummin ta dakatar da ita,ta miqe da kanta ta tafi amsowa,jawo kwanukan data yi abincin tayi ta soma budewa tana zubawa cikin plates uku,nata ummi da sajida,yayin da eesha ke gefe daya tana jefa chips bakinta,gaba daya abincin yayi mata,hakan ya sanya sumayya na gama zubawa ta kai hannu ta bude ta janyi wani plates din "Ci zakiyi ne?" Sumayya ta tambaya,don tana so ya kai mata ne har wajem sha biyu zuwa daya kafin nan an gama girkin rana,din bata fiya son wahalar da masu aikin ba tayi ta sasu dafa mata abinci kamar kanta aka soma ciki,banza tayi da ita kaman ba da ita take magana ba,sai ma fara yunqurin diba da tayi,hakan ya qona ran sumayya,hakan ya sanya ta sake maimaitawa "Magana nake dake" sai a sannan ta daga kai ta dubeta "Tunda ba abincinki bane saiki sauraramin ko?" "Gaskiya kika fada,amma kiba nawa bane ni na dafa saboda haka sai wanda naga dama sannan zaici" ta fada tana janye flask din ta maida murfin ta rufe shi ruf,sajida ta miqawa tace ta kai mata daki,ta amsa kuwa tana murna ta haye saka da shi,din jiya itama eeshan sai data zalunceta don kawai ta takata bata sani ba,hakan ya bata ran eeshan matuqa,tana ganin kamar ita zata sumayyan zata yiwa haka?,idan ma da tasan cewa ita tayi da ba zata nuna kwadayinta a kai ba,amma tunda har hakan ta faru dole ta taka mata birki ko don gaba "Kece matsiyaciya,ba sabanba,duk inda dan talaka yake sai ya nuna hali?" Idanunta ta watsa mata,a fuska zaka rantse bata damu da maganar data watsa mata ba,a nutse tace da ita "Ko 'yar qaruna?" Isowad ummi wajen yasa sumayya ta ja abincinta ta soma ci,cikin murmushi ummi ta dubi nata plate din ba tare data lura da sauyin yanayin fuskar sumayya ba "Wannnnan dai ba girkin uwani bane....sumayya ya aka haihu a ragaya?" Ta fahimci sarai me take nufi,tuni ta hanata yin komai,itakam bata iyawa ta wuni sur ba tare data tsinana komai ba,murmushi tayi kanta a qasa "Ummi na gaji da kwanciya ne,sai naje ja tayata muka yi" "Ki dai dinga kula,don wannan mijin naki wallahi yazo yaga ba dai dai ba sai ya daga hankalin kowa" ta warashe tana dariya,ta ja plate dim gabanta ta soma ci cikin zuciyarta taba yaba qwarewar girkin sumayya,gefe daya na zuciyarta kuma yana tausayawa almustapha,tasan ko ba'a fada ba yayi kewar abinci mai kyau dadi da tsafta.         Eesha na gefe ta cika tayi bam,gani take maganar ummin na qarshe ma kamar da ita take,wato ciki ne da ita shine take wannan iskancin?,jan kujerarta tayi baya sannan ta miqe,binta da kallo ummi tayi sannan tace "A'ah,ya haka" "Na qoshi ne ummi,zan koma bacci" ta fada tan zare jikinya daga wajen "Aikin kenan fa,sam baku gajiya da bacci,kudai rago ko don saboda aure" "Uhmmm....." Kawai ta fada tana nufar daki.         Ko data shiga kasa zaune tayi bare tsaye,ta kai ta kawo ta rasa sakat,zuciyarta kaman ta fashe,batasan kishin sh'ad da takeyi salama bane akan na sumayya sai yanzu,wayarta ta cilla saman gado sannan tabi lafiyar gadon tana tunanin ina mafita?,tilas ta samawa kanta qofar shiga gidab mustapha koda tsiya koda tsiyatsiya.        Itakam bayan sun gama wucewarta tayi wajen anty maamaa,dawowarta kenan daga sashen mai gidan wanda yanzun ya fita "Uwar biyun mu" anty maama ke tsokanarta,dariya ta saka,tana jin kunyar antyn ita kanta "Baki gajiya kullum sai kinzo gaidani?,da kinyi zamanki ma" ta fada suna gaisawa da sajida data rakota,hira sukayi sosai abinsu,anty maama babu ruwanta,tana da sauqin kai da dadin zama tun asali,abinda yasa zamansu yayi qarko kenan da ummi.       Suna tsaka da hira mahmoud ya shigo,ya sake wata qiba da haske,ta jima rabon data ganshi,fuskarshi qunshe da murmushi yake fadin "Antynmu matar yayanmu" "Ka fadi haka mana tunda kayi wuyar gani kai da mus'ab,amaren ma rowarsu ake mana har yau ba'a kawo mana su ba" ta fada cikin sigar tsokana,anty maama na gefe tana dariya "Habba anty,sashen naku ne kaman wani tsaro naga yaa man ya qara masa,tunda ya fahimci alqasim abokina ne shikenan naga ya soma nima ciccije min,kinsan halin mutumin sai a hankali,dama yaya lafiyar kura" ya fada bayan ya zauna daura da anty maama yana dariya "Kaci gidanku,yayanka ne,sannan banda tsaurin ido a gaban mace ka dinga sille mata miji ha'an?" Dariya suka sa baki dayansu sannan suka fara gaisawa ya dora da cewa "Amare gobe zasu zo dukansu,sun so zuwa dubaki ance bakiji dadi ba,to sai naji ya man ya koma dubai na tsammaci tare kuka koma" "Kace gobe muna da manyan baqi,to Allah ya nuna mana" "Ke tsohuwa,yaiushe sirutunki ya ragu ne?" Ya tsokani sakida dake zaune gefe,dariya ta saki "Yana nan bai ragu ba" "Au to,na fasa tayaki murnar da nayi niyya" dariya sunayya tayi,akwai wasa tsakaninsu,shikam mahmoud ba ruwanshi,wani lokaci akwai ban dariya sumayya ta fada tana dariya,hira sukayi abinsu sosai kafin daga bisani ta musu sallama ta koma wajen ummi.        Data koma eesha ce kawai a falon,itama bata zauna ba daki ta koma ta nade kan gado,saboda lokacin yin wayarsu da almustapha ya kusa. ********   *****   *********         Washegari akayi rasuea maqotan gidan baba prof,hakan ya sanya duka ummi da anty maama basa nan suna gidan rasuwar,gidan daga ma'aikata sai ita sai eesha,sajida ma ta bisu,ga baqi da zasu zo matan mus'ab da mahmoud,hakan ya sanya bayan sun gana wayarsu da mama,zainab,halima,abdallah da yaya yahansu,kowa sai data kirashi suka sha waya sosai,credit mai yawa ta qarar,sannan ta tashi ta shiga wanka kasancewar bata yi wanka da wuri ba tana fitowa a wankan ta shirya cikin wani yadi mai azabar kyau cikin lefanta,ta dubi kanta a madubi,ta zama wata classy sumayya,ita kanta tasan ta sake kyau da sauyawa sosai,hannunta ta dora saman cikinta data fara jin alamun dagawarsa,murmushi ta saki har cikin ranta tana jin farinciki,tana qissima yaya almustapha zaiyi duk randa yazo yaga cikin nan ya fito?,turare ta fesa ta yane kanta da siririn mayafi medium size ta fito daga dakin.        A falo ta samu eesha saman kujera qafa daya kan daya anata sana'ar danna waya,daga kai tayi ta dubi sumayya,duk da batayi makeup ba amma ba qaramin kyau tayi ba,ta dan zubawa material din jikinta ido,tana da irinshi,daga dubai mamarta ta kawo mata shi,yana daga daga cikin kayan ta da take ji da su,wani kishi ya cika kata ido,dinkin doguwar riga ne wanda ya fitar da sigarta,ta zuba saitin cikinta ido,baiyi fitowar da kowa zai iya ganewa ba,amma matuqar ka qware wajen gulma sa ido da iya munafunci kallo daya zaka yi masa ka gane tana dauke da yaron ciki,wani abu ya tsaya mata a wuya,cikin da bai isa zama mutum ba ya tsone mata ido,saboda ta fuskanci kowa maraba yake da shi,faranta ran kowa yake banda ita,land line dake falon ta dauka tayi kira sashen ma'aikata,tayi sa'a kuwa baba uwanin ce ta dauka ta buqaci ganinta "Gani nan uwar daki" ta ambata,bata tsaya falon ba tayi shigewarta kitchen taba jiranta,qwararan mintuna biyar saiga baban "Baba....yaufa zamuyi baqi me za'a tana darmusu ne?,amarensu mahmoud?" "Eh gaskiya ya kamata,me kike buqatar ayi musu?,ai saiki fada ki samu waje ki zauna" dariya tayi "Baba,wai haka zanta kwanciya kamar ruwa?,kema kin sani motsa jikin ai yana da muhimmanci ko?,yanzu bari kiga" nan ta tsara ma baban abinda za'ayi,baba na tsaye ita tana daga zaune suka soma aikinsu,suna yi baba na bata labaruka suna hirarsu abinsu,kafin su kammala kusan shigowar eesha hudu,tazo ta bude freezer ta fice,ko waiwayowa sumayya bata yiba bare ta nuna taga shigowarta,ita dai abun na daure mata kai,ta rasa meke tsakaninsu?,bayan da suka kammala sumayya ta dora tuwan semo wanda duja baifu malmala shida ba,tayi miyar kuka wadda taji nama da tantaqwashi,ita take sha'awa,tana dab da barin kitchen din amira ta fado,daga gidan mutuwar take,saboda suna da alaqa da familyn saifullahi "Uwar biyu" ta soma fadi sannan ta bude freezer ta dauki ruwan sanyi ta sha sosai saboda ranar da ake yi,sumayyan na tsaye tana dubanta "Ya na ganki haka afujajan" kai ta kada "Ke dai bari kawai,wallahi bacci kazo nayi kafin yamma na wuce gida,drivan ma na sallameshi na karbi key din na koma da kaina" dariya ta danyi "Wannan bacci wannan bacci amira anya qalau kike,jiya fa ina jiyo ummi na miki fada kin dora girki kinje ki kwanta kin barshi ya soma qonewa,vanda Allah ya sanya mai aikinki bata tafi gida ba gobara zaki hada" "Shaye shaye na fara" ta fada cikin sigar tsokana "Ko kuma da kin riga kin sha din ba" itama ta maida mata cikin tsokanar suka soma takawa don ficewa daga kitchen din suna dariya "Allah amiran yaya musty(da yake taa sauya mata suna)bansan meke damuna ba,yanzun fa ko saif bana iya jira ya dawo kan ya dawo na jima duniyar bacci" "Tabdi....kije kiga likita kam,Allah yasa kema kin biyo sahu?" "Allah ko?,kaddau bakin saif ya kamani?" Ta fada tana fiddo ido "Ke dalla,meye ne kika wani waremin idanunkin nan irin na yayanki kamar ni nayi abun" ta fada sanda sukaqaraso cikin falon eesha na zaune,dariya amira ta saki har da d'an ihunta "Kice kawai yayana rikitaki yake da idanunshin nan,kinsan Allah sunfi nawa kyau,ni kaina lokacin ina qarama cewa nake muyi musanye,Allah yasa ki haifo mana mai kama da shi"murmushi kawai tayi tana tuna yanayin kallonshi,yadda ya iya hukunci da ido,yana rikita ta ba qarya ba a duk sanda ya ritsata da kallonshi,murmushi ya subuce mata a sarari ba tare data sani ba "yar is,kinzo ko ki nemi hanyar gidan ko?,wallahi kada kiyi aure ki tsammaci zan dinga jelan zuwa gidanki" sumayya ta tsinci amira na gayawa eesha,dariya eeshan tayi "Ke kuwa zuwa ya kama,idan akayi 'yar gida ai kinga ko bako qaunar Allah dole kizo,ko banza na zama yayarki"ta fada da biyu,tabbas maganan ta samu shiga zuciyar sumayya,ta kuma fahimci sarai inda zancan eesha ya dosa,saidai batasan ka wa take maganan ba,mahmoud da mus'ab har yau basu cika wata biyu da aure ba,ya adam bai garin ma baki daya matanshi biyu ga yara kusan hudu,ya girme mata ma sosai,almustapha fa?,wani sashe na zuciyarta ya gaya mata,sai ta soma juya zancan a hankali cikin ranta "Ah lallai fa,ga mai yawan rai kenan.....kinga bacci zanje nayi na wasu awannai,bari naje na dawo sai mu qarasa zancan....wai nikam me ya samu number salama bata shiga?" Ta tambayi eeshan tana yin gaba "Salama?,bakisan muhsin ya sauya mata layi ba,bikinta bai wuce one month ba yace bai sonta da tsohon layinta,but dazun ma tace na tura mata num dinki ba mamaki kiji ta kiraki" "Kice akwai shagali....saura ku sai ku bada himma" ta fada tana dariya "Me kike ci na baka na zuba" eeshan ta fada tana yatsina fuska "Eesha shegiyar gari....wai ina bash ne?" "Standby zaki ce,jeki dawo kizo na gaya miki" "Alright"Amiran ta kuma fada tana bin bayan sumayya da tunitayi gaba.        Suna shiga amira ta kama kafadar sumayya dake qoqarin daure gashinta don shiga wanka "ke wai baki karanci komai tattare da eesha ba?,ba kya ganin irin kallo da take binki da shi" murmushi sumayya tayi duk da itama abun ya tsaye mata a rai,har yau kuma bai daina bata mamaki ba "Kinsan wai yaya man take so?"amira ta fada tana kecewa da dariya ta fada saman gado,maganar ta daki sumayya,sai yanzu ta gano abinda ya sanya eesha bata qaunarta,amma sai ta dake "to Allah ya tabbatar da alkhairi" harara amira ta watsa mata sannan tace "Haka zaki fada?,ke yanzu fatar kishiya kikewa kanki banda waccar da take gabanki?" Cikin dakiya tace "To meye?,bakiji abinda kema kika fada ba,nima wata nazo na taras" "Amma wallahi baki son ya almustapha amira,da eesha da su'af meye banbancinsu?,qasar haihuwa ce kawai ta raba su,ai ko mata sun qare bazan masa fatan auren eesha ba wkh duk da tana 'yar uwata,amma duk dan uwa na gari zaya so yaga nashi na auren magartacciyar mace kaman ke" "Lallai kam,idan rabonshi ce ai ba wanda ya isa ya hana ko?" Ta fada a fili tamkar ba komai,cikin zuciyarta kuwa kaman zata fashe "Allah ya tsari gatari da saran shuka,kinsan ma duk cikin yaran family ba wanda sam basa hada inuwa da yaya almustapha irin eesha?,itafa ta sanya ya saka dokar hana samarinsu zuwa gidan nan matuqar suka zo hutu da sallah,tun randa ya ganta da wani cikin mota suna har harkoki" "To Allah ya kyauta,kedai kwanta kawai kiyi baccinki"ta fadi tana daukar towel saboda ta sake watsa ruwa "naqi din,kuma kamar a kunnen ya almustapha kin masa mugun fatan auren eesha"dariya ta baiwa sumayyan saboda yadda tayi kicin kicin kaman ance mata saif zai qara aure,toilet ta shige don ta tabbata ta biyewa amira sai su bata lokaci a wajen.          Tana fitowa wayarta ta soma ringing,tana dubawa sunan almustapha ne a sama,murmushi ya subuce mata,halan yau 'yan rigimar ne a kusa,dududu awa uku fa da gama wayarsu,sai ta zauna bakin madubu ta daga kiran ta kara kunnenta tare da yin sallama "kewarki nake" ya soma fada,murmushi ta sake masa mai dan fidda sauti har cikin kunnenshi "Awa uku da rabuwarmu fa?" "Jinta nake makan shekara uku,ummu abdallah kaman ma baki tausayi na,ashe haka so yake wahal da zuciyar mutum?,kinsan yanzhn haka wani asibiti ke buqatar taimakona za'a yiwa matan wani aiki amma na gagara zuwa,ko naje din ma nasan ba abinda zan iya aiwatarwa....please my summy kiji tausayina mana" ya qarasge zanacan a shagwabe,dariya ta saki salon magananshin ya tsumata "Wallahi abu abdalla ka zama wami shagwababbe,anty su'ad ta lalata ka" "Zaki gane hakan idan na kamaki a hannu,kinsan Allah....ranan ko babynmu bazan tausayawa ba bare ke,zaki zo hannu" ya fada yana katse kiran,murmushi ta dinga fiddawa,bata ajjiye wayar ba sai data tura masa sms da tasan zata haukatoshi sannan tayi switchoff din wayar yadda koya kira bazai sameta ba,ido ta lumshe tana sakin murmushi,ba qarta ita kanta tasan ba qaramin rashin mijinta tayi ba "Laila majnoon,idan kun gama baqin sunzo" amira dake kwamce ta fada,ita kanta abun ma burgeta,wato haka yaya almustapha yake baje soyayyarshi,amma idan ka ganshi a waje sai kace wani zaki,musamman idan ya soma muzuran nan nashi ko bada umarni,baka ce ya taba dariya ba,amma yanzu ya wani narke kaman dan yaye,sam ita sumayya ma ta manta da ita sai da tayi magana "To 'yar sa ido" dariya suka sanya baki daya,amira ta miqe daga saman gadon ta zauna sosai "Seriouse amiran yaya musty....wai meye sirrin don Allah,salon soyayyarkun nan a bani nasha don Allah" "Min indillah" ta bata amsa tana ciro kayan da zata saka "Da gaske?" "Biya sai na gaya miki" "Ko nawa ne ko zan nada indai za'a gayan" dariya ta baiwa sumayya sosai,ita kanta wani lokaci ta zauna ta kanyi mamakin kansu,ita da kanta batasan akwai duniyar data qunshi zallar farinciki har haka ba sai yanzu,duba da irin bigire na nau'in rayuwa daban daban data afka,taso mukhtar a sanda bata mallaki hankalinta ba,a sanda bata banbance so qauna da shaquwa,wasu mata sun shiga rayuwarsu sun kawo naqasu wa farinciki da shaquwar dake tsakaninsu,sannan bayan duka wannan tazo ta rashi a sanda bata da kowa sai shi kadai ta mallaka,bata saba da kowanne namiji ba sai shi,tazo ta auri lukman bisa tsautsayi da qaddarar data hauta na dole sai ta shiga rayuwar wasu,daga qarshe ta samu almustapha,wanda ta sameshi ne a lokacin da hankali ya gama gameta,ta gama sanin zaqi da madaci,so qauna da shaquwa da kuma,tasan dama da hagunta.          Aina da asma'u sune matan mus'ab da mahamoud,dukkaninsu basu fi sa'annin sumayya ba,koda zata girme musu bazata basu shekara ba,bare kana ganinsu zaka musu kudin goron sa'anni ne,dukkaninsu wayayyu ne masu matuqar kirki,karatunsi da wayewarsu bai hanasu kasancewa 'yammata nutsatstsu masu cikakkiyar tarbiyya ba,kowacce ta samu tarbiyya daga gidansu,kamar asm'u wadda makaranta daya sukayi karatu da mahmoud wata private university dake nan garin abuja,saidai tana matakin farko ne mahmoud yana matakin qarshe,kamun kanta da nutsuwarra shi ya fara jan hankalinsa,abinda bai fiya gani ba wajen 'yammatan dake manyan makarantu na jami'o'i,bare irin nasu makarantun na yaran masu da shi,kowacce ta dauki tabara da rashin tarbiyya rashin cikakken kamun kai a amtsayin wayewa,wannan ya zama ruwan dare cikin makarantunmu na walau na gwamanti ko kuma na kudi.       Dukkaninsu suna da kyau  abinsu,faran faran da mutane,nan suka hadu suna hira abinsu,irin hiran farkon haduwa ba sakin jiki can da yawa,eesha na gefe tana hura hanci,ta dora qafa daya kan daya,ta san asm'u,duk da wuce asm'un da aji daya,hakan ya sanya ko ayanzun ka take jin ta fita,gidan 'yan uwansu take,bugu da qari ita dangin miji ce,su dinma da yake kowacce ta iya takunta daga gaisuwa basu damu da me take ba,a haka ummi tazo ta taddasu,hakan ya mata dadi qwarai,ta kuma yaba da tanadin da sumayya tasa aka musu,hatta da anty maamaa sai data ji dadi,duk da alkunya data yi tace baqin ummi ne dama,sunje dai sun gaisa da ita sannan suka dawo suka ci gaba da sabgoginsu.          Basu tafi ba sai yamma liqis bayan sunyi musayar lambobin waya,cikin motar mus'ab duka zasu koma,sun tafi suna yabawa da sumayya,cikin qanqanin lokaci suka saba da hirarta suka a baki suka isa gida.         Tunda suka tafin eesha ta dawo falon qasa ta zauna bayan data tabbatar ta gama shirya duk wani abu data tanada,rana saka ran cewa wani dalili ya sauko da ita daga dakinta zuwa kitchen din,hakan ya sanya ta kasa ta tsare ta zauna a falon,tana danne danne waya tare da kallon wani film a MBC action amma rabin hankalinta ja matattakala zuwa qofar kitchen din,duk wani ma'aiki da zai buqaci shiga kitchen din ta sallameshi tun yamma,ummi dama ita ke da girki taga fitarta zuwa sassan baba prof.          Sajida ce ta sauko da sauri sauri,sannan da hazarinta irin mai tattare da quruciya ta nufi kitchen din,cikin hanzari ta dakawa sajidan wata iriyar tsawa data sanyata tsayawa cak "Uban me zaki shiga ciki kiyi kanki na rawa?" Kaman zata saki kuka tace "Anty amira ce tace na dauko ovaltine zata hadamin wani abu" sosai abin yayi mata dadi,da alama haqanta zai cimma ruwa,sai ta sake kaurara murya tana zare mata ido "To koma kije kice mata nace ba zaki shiga ba,idan ta matsu ta sauko da kanta ta diba" tsayawa sajida tayi tana dubanta,don a ganinta ita kanta eeshan ta yiwa sumayya rashin kunya,bugu da qari ma gidan ba wanda akewa get na amfani da wani abu tunda basu gaji rowa ba,kowa na gaban kanshi je ciki kuwa harda ita eeshan "Ba zaki wuce ba kika tsareni da ido ko sai na qaraso nan na babballaki na zubar" ganin hargagin da take mata ya sanya ta dole komawa saman da sauri.         Sumayyan na zaune riqe da qaramin qur'ani tana karanta falaq da nasi da ikhlas tana qarashe addu'anta sajida ta dawo,maganan da eeshan ta gaya mata ta daure mata kai,bata ce komai ba ta gama addu'ar ta shafa,sannan ta miqe da hijabin jikinta tace da sajida "Zauna,bari na debo miki" "To" sajidan ta fada sumayya ta fice,dadi ne ya dinga ratsa eesha sanda taga sumayya ta shige kitchen din,tuni ta ajjiye wayar gefe ta miqe tsaye tana shirin ko ta kwana murmushi na fita a fuskarta.         Sam sumayya bata lura ba har sai data dauko gwangwanin ovaltine din ta dauki hanyar fitowa,ji tayi ta tafi baki daya sululu zata kifa ta baki "Hasbunallahu wa ni'imal wakil" ta furta,cikin wani irn hanzari ta saki gwangwanin ta dafe freezer dake daf da ita,duk da haka sai da qafarta ta amsa ta rintse ido tana sake kiran sunan Allah,da gudu taga shigowar eesha wanda hakan har yaso ya sake firgitata ta soma dudduba jikin sumayya tana cewa "Innalillahi wa inna iliahi raji'un,me ya sameki?,kinji wani abu ne?,me ya samu jikinki?" Shigowar ummi cikin rudani wadda shigowarta falon kenan taga eesha ta runtumo kitchen din da gudu ta biyo bayanta,sumayya ta soma yu qurin tashi ummi ta nufeta,eesha ta dakatar da ita tana qarasawa wajen sunayya tana taka wajen cikin taka tsantsan ta kama sumayya tana dudduba qasan data fadj "Ai babu ma abinda ya sameki" eeshan ta fada haushi na cikata,so tayi tazo ta ganta male male cikin jini,ta fadi kan cikinta tayi barin dan tayin dake cikinta,wani irin kallo sumayya ke bin eesha da shi wanda ita eeshan bata kula ba,baqincikin rashin cimma nasarar da bata yiba kadai ya cika mata qoqon zuciya,ta dora dukkan alamomin tambaya kan eeshan,zainab ce ta fara fado mata a cikin abdallah,take jikinta yayi sanyi,gabanta ya yanke ya fadi taci gaba da nazartar eeshan a fakaice,duk wasu abubuwa da take son gani ta samesu,tuni ta janye baya ta bar sumayya hannun ummi ummi na duban wajen "Me ya kawo miyan kuka nan wajen har ya janyo miki faduwa,subhanallah" ummi ta fada tana janye sumayya daga wajen "Ita tayi ta mai shegen warin daddawa" ta fada tana yatsine fuska,kai sumayya ta gyada "Ni nayi,sai gata kuma ta taho har nan" ta ambata tana duban eesha,dauke kanta tayi ta juya ta fice daga kitchen din tana kumbura "Bakijin dai komai a jinki ko?" "Eh ummi,ba komai" ta bata amsa tana miqewa "Bi a hankali,idan kina jin wani anu ki fada,don Allah nidai daga yau na yafe shigowa kitchen din nan" ummin ta fada cikin damuwa "To ummi" ta fada tana nufar qofar kitchen din,zuciyarta cike fal da mamaki,me ta yiwa eesha,don tana son almustapha sai ta nemi rayuwar dan cikinta,d'an kuma wanda take iqirarin tana so,lallai dole ta sanya ido da takatsantsan da eeshan,don ba zata taba lamunta yaran da tun kafin ta haifesu su dinga shan wuya ba haka kawai ba tare da laifinsu ba,biyo bayanta ummin tayi,sai data sake tabbatarwa komai lafiya sannan hankalinta ya kwanta,saukowa qasa tayi,ta tara ma'aikatan dake kula da kitchen baki daya ta tsawatar musu,sannan taja kunnensu da kada ta kuma gani sun bar sumayyan ta shiga kitchen sannan ta sallamesu kowa ya koma muhallinsa bayan sun gyara gurin. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 9⃣9⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *Allah S W T yana cewa* *duk wanda ya aikata daidai da qwayar zarra na alkhairi(komai qanqantarsa) zai gani(cikin littafin ayyukansa,zai ganshi a rubuce kuma za'a masa hisabi da hukunci a kansa),hakanan duk wanda ya aikata dai dai da qwayar zarra na sharri zai ganshi. __________________________________________           Tun daga lokacin sumayyan ta zubawa eesha ido cikin nutsuwa,tana kula da takatsantsan da duj wanu taku nata,a bangaren eesha kuwa ko daya bata sauya qudurinta ba,ko da yaushe tunaninta daya na yadda zata illatar da sumayyan ne.    ******    ******    *******       Qarfe goma da rabi ranan ta sauko bayan farkawarta daga bacci wanda kusan almustapha ne ya tasheta,sai data gama biye masa sannan ta shiga tayi wanka ta shirya ta sauko don ta karya,bata da damuwa tasan cewa komai na shirye,tun daga randa wancan abun ya faru bash sake barinta shiga kitchen ba.         Tare suka sauko da sajida,ummi na sashen anty maamaa,sajida ta wuce dining don ta karya,ita kuma kiran halima da ya shigo wayarta ya sanya ta wuce saman kujerun falon ta zauna tana amsawa,qarar sajida data jiyo shi ya sanyata sakin wayar ta miqe,bata jin nauyin jikinta haka ta nufi sajida da tayi zaman 'yan bori saman step na dining area,wajen ta isa tana dagata gami da tambayarta "Faduwa nayi anty" ta bata amsa tana shirin sakin kuka saboda qafarta ta bugu sosai,idanunta sumayya ta kai wajen sai taga ruwa ne ya zube wajen "Ya akayi kika zubda ruwa haka sajida?" "Bani bace nima haka naga wajen,kuma ban kula ba har sai da na fadi" wani tunani ne ya darsu ran sumayya,ta sanya hannun ta cikin ruwa sai taji yana santsi da qanshin klien,to waye ya zubda ruwa haka?,tasan cewa babu yadda za'ayi ma'aikatan su zubda ruwan su tafi ba tare da sun gyara ba,ummi bata nan sajida ba ita ta zubar ba "Eesha" zuciyar sumayya ta raya mata,kai ta girgiza,batason ta zargeta bayan bata gani da idanunta ba,riqe sajidan tayi don dawo da ita saman kujera,tana juyowa suka hada idanu da eeeshan,sai ta juya ta shige dakinta,mamaki ya kama sumayyan,wai me eeshan ke nufi,take ranta ya baci,ta zaunar da sajida saman kujerar ta kama qafarta tana mammatsawa,gefe guda ke mata ciwo,sai ta isa bakin dispenser ta tari ruwan zafi ta dawo kusa da sajidan ta gasa mata qafar sosai,cikin ikon Allah wajen ya saki,ta shafa mata man zafi a wajen sannan taje da kanta ta goge wajen sannan ta hada mata abin break din taci ta kwanta.        Tana saman kujera zaune kanta a qasa,ranta a tsananin bace yake,don me zata dinga neman cutar da ita?,tana tunanin dai dai gaggawar unguwar zoma ta bari a haihu ko?,ta bari su hada miji tukunna,meye na hanzarin son cutar da ita tun yanzun,saqar data dinga yi kenan cikin zuciyarta,qara qofar dakin eesha tayi,itace ta bude ta fito,tana tafe dai dai ta hura hanci,idanunta da suka kada saboda bacin rai ta zuba mata "Aisha..." Ta kira sunanta cikin kakkausar murya wadda ta sanyawa eeshan tsayawa ta kuma juyo tana dubanta "Jan kunne nakeso nayi miki na qarshe....duk abinda zakiyi kiyi qoqari ya tsaya iya ni,kada ki bari sarkarcinki da haukanki ya sake taba wani cikin gidan nan,yanzun da kin karya musu yarinya kuma kice me?,haka rannan kika watso ruwan zafi saura kadan a fuskar sajida,kina gidan kakanninta kina cin arziqinsu kina neman salwantar musu da jikoki?"maganar sumayyan ta qarshe ta sosa mata rai,ita zata yima gori bayan ita ya cancanci ta yiwa gori "idan kuma banji jan kunnen naki ba me zaki iya diyar malamai masu ci da buzu da tawada?"murmushi ta sake mata sannan ta bata amsa cikin nutsuwa "alhamdulillah da na kasance diyar malamai magada annabawa,zancan rashin jin gargadina kuwa....koni zan iya miki hukunci.....amma da yake ni din mai uwace a gindin murhu,kunnen mutum daya maganar zata je kiga yadda dunuyarki zata gigita" ta fahimci sarai tana son hadata da almustapha ne ko shi ko baba,to har gwara ma baban akan shi din,kuma ta sani sarai qarshen lamarin bazai mata da dadi ba "Duk abinda zakiyi baki isa ki hanani shiga gidan almustapha ba wallahi,baare ma ya sameshi bare kuma na gida" murmushi ta kuma yi "Kan me zan hanaki dama?,nima fa wata ta taras,sannan kuma ba kanku na soma zama da abokan zama ba,abu guda kawai nakeso daga gareki.....koda zaki auri almustapha to ki kiyayi taba lafiyar jama'ar da basu ji basu gani ba.....ki taqaita haukanki....ki adana shashashanki har zuwa sanda zaki shiga gidan nashi"tana yunqurin maidawa ummi tayi sallama,hakan ya sanyata dole yin shiru,bata ji ke suke fada ba taga dai sajida kwance "a'ah lafiya kuwa?" Ta tambayi sajidan tana dubanta "Ruwa ne ya zube sai na fadi" ta bata amsa,gefe ummin ta samu ta zawa "garin yaya ruwa ya zube a wajen?" Ta tambaya cikin mamaki,wannan karon sumayya ce ta karbi zancan "Wallahi ummi,sashen dai ba kowa,ni da ita kuma tare muka sauko sai ihunta kawai naji" waiwayawa ummin tayi tana duban eesha "Aysha ya akayi ruwa ya zube wajen?" "Nima ummi ban sani ba" "Bake na bari wajen ba kina karyawa?" Sai ta langabar da kai "Tea ne ummi,ina so ma goge kuma na mance naje na kwanta" "Amma ya kamata ki dinga kulawa tunda kinsan yadda wajen nan ke da santsi,ko su lami kika saka zash goge,yanzu da amira ce ta taka wajen Allah ne kadai yasan me zai faru,ki kula sabida gaba" "To" ta fada tana zumbura baki ta koma daki,ranta cike fal da baqincimi,ita wacce iriyar mara sa'a ce,kuma wai ummin har take goyon bayan wata bare a kanta,lallai kam ba zata qyake wannan abu ba zatayi mai gaba daya ne kawai komai ta fanjama fanjam,ruwa ummi ta buqata ta gasawa sajida wajen,sajidan tace ai anty ta gasa mata,hakan yayiwa ummin dadi,daya daga cikin abinda yasa har kullum take sumayyan ke sake shiga ranta kenan sanin ya kamata,ba qaramin jin dadin zama take da ita ba,ba shakka da zaiyiwu riqe sumayyan zatayi wajenta har ta haihu,amma tasan hakan ba maiyiwu wa bane,ita kanta tasan alkunya almustapha kawai yake mata,wanda dukkan alamu sun nuna ya fara gajiyawa,don ya soma yi mata qananun qorafi,ko haka kawai ba gaira ba dalili sai ya dinga tashinta cikin dare yana sata kaiwa sumayya waya. ***** ******** ****** Kimanin takwas ne na dare yau ta kwanta da wuri,so take tayi bacci sosai,jin kanta take kamar wadda ta shekara batayi bacci ba saboda yau tayi tashin wuri,don haka yau tun magariba ta kashe wayarta don ta huta sosai,har ta kwanta qishirwa ta tasheta,ta miqe ta zura hijabinta ta sauko qasa,cikin sandata bude fridge ta dauki ruwa saboda duk saman babu ruwa mai sanyi,ummi ta hana ta sha shi yasa ake ajjiye mata mara sanyi,ita kuma qaunarshi take,idan bata sha ba har wani abu take ji ya tokare mata qirji. Tana tsaka da bude robar taga fitowar eesha ta haura sama,da alama wajen ummi zata,kamar tace mata ummin na sashen baba sai kuma ta fasa tunda ba shirginta take shiga ba,ta kammala shan ruwan ta ta maida robar ta rufe ta kama matattakalar benen ta soma haurawa saman,tana tsakiya eeshan ta fara saukowa,bata dubeta taci gaba da hawa abinta,tana step din qarshe eeshan ta iso inda take,wata wawuyar bangaza da bata zata ba bare tsammata eeshan tayi mata,wanda hakan ya sanya sumayyan yin taga taga baki daya tayi baya,ta gama saddaqarwa ta gama yawo,saboda step.ne ya kusa ashirin wanda ba shakka idan har ta samu nasarar komawa da baya sai ta gangara ta kan kowanne,cikim azama tare da kiran sunan Allah taji kamar an turata gaba,singalin qafarta ya daki qasa ya bafa wata qara,ta sanya hannayenta ta dafe qasa sanda take faduwa,wanda banda hakan da saman cikinta zata fada,suma hannayen qarar suka bayar ta zube ta gefen hannunta na dama daidai sanda taji muryar ummi cikin qaraji tana fadin "Hasbunallahu wani'imal wakil,innalillahi wa inna ilaihi raji'un aisha!!" Ta qarashe fadi tana haurowa saman cikin wata iriyar sassarfa da gaggawa,idanu eesha ta soma fiddawa gabanta na wata matsananciyar faduwa,tasan tata ta qare,ya akayi har ummi ta iso wajen bata lura ba?. Tuni ummi ta isa inda sumayya ke yashe,azaba da radadin da hannunta da qafarta daga buge kadai sun isheta,ambaton sunan Allah akwai take tana jin yadda qashin qafarta ke zugi da tsuko,a rude ummin ke tambayarta da qyar ta bata amsar qafafunta,ta matsa qafar sai ta sanya qara sabida azaba,cikin matsanancin bacin rai ummi ta waiwaya ta dubi eesha "Ashe baki da hankali eesha?" "Wallahi ummi....." Ta soma fada cikin rawar jikibda rawar murya,tsawa ta daka mata wadda ta sanya hantar cikinta kadawa tana gaya mata ta bace da wajen,sai da taga saukarta sannan ta maida hankalinta ga sumayya taba mata sannu,tausayinta na kamata,taimaka mata tayi sai data jinginata da kujera sannan ta dauki waya ta kira baba da anty maamaa. Kusan lokaci daya suka shigo,salati anty maamaa ta dinga yi,shi kanshi baban shiru yayi ranshi na sosuwa,ba bata lokaci ya kira driver yasa ya fito da mota suka sanya sumayyan ciki "Inaga ba asibiti ya kamata aje ba,wajen masu gyara za'aje a duba mata qafan da hannun,tunda Allah yasa bata fadi kan cikin ba" inji ummi,hakan ya sanya baba ya kira mutumin dake musu irin wannan aikin,basu da nisa sosai shi yasa bai bata wani lokaci ba ya iso. Sai daya duddubata sannan ya tabbatar musu qafarta gocewar qashi ce,hannun kuma targade ne,zaiyi mata gyara,dui wanda ke wajen sai daya tausaya mata,tasha wuya sosai wajen gyaran,haka ta dinga hada gumi taba kiran sunan Allah kaman zata suma,murqususu take ga ciki a gaba daya fara tasawa,kafin a gama ta hada gumi sharkaf,ya gama ya baiwa ummi maganin da za'a ringa shafa mata da kuma yadda za'a kula da wajen,yace duk bayan kwana bibbiyu zaizo ya dinga dubawa,godiya baba yayi mishi sannan ya sallameshi. Kusan kasa runtsawa sukayi baki daya,sai daga bisani baba ya fara tafiya,anty maamaa kam bata iya tafiya ba ita kanta sai wajen biyu na dare,ummi kuwa kwanan zaune tayi tare da sumayyan,sajida ma da qyar tayi bacci,duk tausayin sumayyan ya cikata,eesha kuwa tunda ta shige ba'a sake jin motsinta ba,ita so tayi cikin ya zube idan yaso ayi mata hukunci baki daya,ran ummin ya kai maqura wajen baci,tausayin sumayya kawai ya isheta,ta riga ta gama yanke hukunci a gobe aysha zata bar gidan,kome mamanta zata fada saidai ta fada,don ba zata yarda tana jibtana gani a bata amana ba kuma ta kasa riqewa,me zata cewa almustapha idan wani abu ya samu cikinsa? A dakin ummin ta kwana,nan ummi ta kawo mata ruwa da roba ta daura alwala saboda yadda qafar tayi mata tsami,a hankali ta waiwayo tana gaida ummin bayan ta idar da sallar,amsawa tayi tana tambayarta jiki ta amsa mata alhmdlh,sannu ta sake mata tare da bata baki kan abinda eeshan tayi,ita kunya ce ma ta kamata,sai kace ummin ce ta aikata?. Qarfe biyun rana ummi ta isa dakin eeshan ta taddata kwance,zumbur ta miqe tana gaidata,a tsautsaye ta amsa tana ajjiye mata kudi "Ki tashi maza ki shirya ki wuce gida,koda wasa kada kice zaki sake dawowa gidan nan a yanzu,tunda ba yau ashe kika soma qoqarin aikata mata hakan ba,idan banda tsabaar rashin mutunci eesha bata ci darajata ba a wajenki?,ko duka bata ci darajar wannan ba ai taci darajar dan tayin dake cikinta ko?,to ki tashi ki shirya ki wuce gida" kuja eesha ta saki,abinda take bege wato so yake yayi mata nisa,garin neman gira zata rasa idanu "Yanzu ummi sabida ita zaki raba zumuncin dake tsakaninmu?" Cikin mamaki ummin ta waiwayo tana dubanta "Van raba ba,amma a yanzu dai na raba har sanda zata bar gidan nan,na riga na gama magana da mamanki" ta juya tana ficewa,abun takaicin ma sam bata ga nadama tattare da ita ba,don ko qafar benen bata taka da niyyar zuwa dubata kan abinda tayi mata ba. Wunin ranar yini tayi tana tofa fatiha a wajen,haka ya kawo mata sauqi sosai kan radadin dake damunta. ****** ***** ******* Ranar da abin ya faru baki daya bai samu zama sosai ba,ayyuka sunyi musu yawa can company,sau uku yana kira yaji a kashe. A gajiye ya dawo,a falo ya sami su'ad din,tana kwance dai dai saman kujera,sanye da gajeran wando da qaramar vest iya ciki,ko ina baja baja da kwalayen data gama ciye ciye,yayin da bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita,tsallaketa yayi ya nufi bedroom dinshi kai tsaye ya rage kayan jikinsa,duk abinda yake tunanunta na mqale a ranshi,yau daya tak da baiji muryarta ba jinsa yake kaman maraya,yayi tsammanin zai iya share mata kaman yadda ta shareshi amma sai yake ji abun ba mai yiwuwa bane a wajenshi,towel ya dauka ya wuce bathroom yayi wanka. Ko mai bai iya shafawa ba bare ya ya sanya kaya ya janyo wayarshi ya soma lalubar wayarta,a kashe aka sake ce masa take,sai yaji hankalinsa bai kwanta,lambar ummi ya soma laluba cikin sa'a ta shiga,fitowar ummin daga dakin kenan taga shigowar kiran "Ummi an yini lpy?" "Lpy lau almustapha ya aiki?" "Alhamdulillah" sai kuma yayi shiru,halin nashi ya motsa,itakam da zaiyu shirun da yafi mata,tasan wal'alla sumayyan yake nema,ita kuma batasan zancan yaje kunnenshi,tafiso matarshi ta warke saidai yazo ya tadda labari kaman ma ba'a yi ba "Ummi.....sumayya" ya fada kaman mai tsoron fadin "Uhmmmm,wani abu ne?" "Tun jiya bamuyi magana ba,ko zan samu jinta?" Kaman ta hanashi saidai ba yadda zata hanashi magana da matarshi "Kashe zan kai mata" "Ummi batta a haka zan jira" dariya ma yaso bata har sai data ce "Almustapha?,kaman wanda network din zai gudu?" Kunya ta kamashi amma sai ya dake yayi shiru yana sauraron tafiyar ummin. Tana zaune ta gama shirin baccinta tana karanta wani qaramin littafin labarai na larbci,qafarta na saman matashi mai laushi,hannunta daya na ajjiye saman cinyarta,wayar ummi ta miqa mata tana cewa "Almustapha" littafin ta ajjiye ta karba gabanta na faduwa ta kara kunnenta sanda ummin ke juyawa ta fice,shiru yayi kawai yana saurarenta tamkar baya kan layin yana hadiye wani abu,fitar numfashinta kawai ya soma samar masa da nutsuwa,sallama tayi masa sai da ya bada tazarar wasu sakannni sannan ya amsa "Why sumayya why?,wato idan ban nemeki ba ba zaki neme ni ba?" "Ba haka bane.....wayarce bansan inda ta fada ba" "Kaman yaya?" Ya tambayeta,da sauri ta gyara zancanta "Amm...ina nufin ta dauna daukan chargy ne" tsaki ya ja sannan yace "Kamanni ace wayar matata ta har takai matsayin da don kanta zata daina daukan chargy?,ki cire layukanki ki bar amfani da ita,gobe da safe za'a kawo miki wasu,daya ni kadai zan dinga kiranki da ita always ta zama akunne kusa da ke,dayan kuma ki kira duk wanda kika ga dama" "Na gode Allah ya saka da alkhairi ya qara arziqi" "Amin.....nifa gaskiya na fara gajiya,haquri na ya kusa qarewa fa....a qa'ida ai cikinki ya shiga wata uku...am a doctor nasan yadda zan kula da mata ta" gabanta ya fadi,yau bisa dukkan alamu rigima yake ji tunda taji muryanshi ta fuskanci haka,tayi qas da murya "Habba mana.....duka saura sati nawa lokacin da suka ce ya cika,ka qara haquri mana please kaji?" Shiru kawai yayi yana sauraren muryarta yana nazari "Me ya sameki?" Taji ya furta kai tsaye,sai ta hau fiddo da idanu tana kalle kalle,ta daga wayar ta duba voice call ne ba vedio call ba bare tace yana ganinta "Ni?...ba bau komai me ka gani" "Akwai wani sauyi tattare da muryarki,kuma jikina ya bani haka"murmushi tayi duk don ta dauke hankalinsa "wrong doctor,baka canka dai dai ba,am fine,ina shirin yin bacci ma ummi ta shigo" "Ban yarda ba,but....tunda kince haka ne is ok,ki kunna wayarki kafin a kawo wata" "An gama yallabai" murmushi yayi,yanajin kaman tana lallabashi ne kawai ya sauka daga kan layin,sai kawai ua datse kiran yana jin wayar kawai bata yi masa ba,jikinsa bai bashi ba,sam ma ba irin wannan hirar yakeso suyi ba,hankalinsa baki daya yayo nijeria. Ajiyar zuciya ta saki da taga ya datae layin,da alama halin ne yau ya motsa,dole ta tashi sajida ta sanyata ta dauko wayar ta jona a chargy sannan ta kunnata kafin ta kwanta. ****** ****** ******* Washegari misalin sha daya na safiyar ranan yana tsaye gaban mudubi yana shiryawa,kominshi a nutse a tsare,ya gama komai tsaf yana taje sumarshi ya janyi wayoyinshi dake gefe,tun jiya da ita ya kwana cikin ranshi,yana jin mawuyacine idan baiyi rashin ta ido ba yaje kawai ya daukota,yana jin kaman sun shekara goma ne basu ga juna ba,number baba ya soma don ya gaidashi kaman kowacce safiya,idanunshi suka sauka kan takardar dake gefanshi,ya saka hannu ya dauko ya bude ta,ranshi ya baci sosai ba wai don kudin da ya kashe kawai kan takardar ba,sai na yanda su'ad tayi burus da maganarshi. Yana tsaka da duban takardar ta fito daga wanka tana tsane jikinta da towel "Yanzu wai har ka shirya zaka fita,nifa gaskiya na gaki da wuni a gida ni kadai kaman mayya,bayan nasan wuraren shan iska birjik amma ka hanani zuwa ko guri daya" "Mene wannan?" Ya tambayeta yana nuna mata takardar,daga kai tayi ta kalleta sai kuma ta basar tana hade rai "Nifa gaskiya banda interest shi yasa na ajjiyeta" ranshi ya kuma baci,ya gyara tsaiwarshi yana kafeta da idanunshi masu sanya mutum yin laushi "Kinsan nawa na biya miki?,kudin mutum nawa na biya ake kadai don kije ki koya ke kadai din?" "Sai na biyaka kudinka kamin total,amma bazan iya zuwa ba gsky,ai ba ajina bane ba aganni wani ina koyon girki,haka kawai Allah ya maka arziqin da zamu iya daukan kowanne irin cook kawai sai na bata wa kaina lokacin koyon dafe dafe?" Ta amsa mishi ba tare data dubeshi ba ta soma shafa mai,kai ya gyada yana qoqarin hadiye bacin ranshi,ya maida takardar saman madubin ya ajjiye,shi kadai yasan hukuncin da zaya yanke mata,sai ya janyo jakarshi ya riqe a hannunshi,daya hannun kuma yana riqe da wayoyinshi ya soma takawa zai fice "Ka mance yau zani siyayya?" Ta furta cikin harshen nasara,banza yayi da ita yaci gaba da takawa har ya fice. A falo ya tadda mai musu girki ta kammala shirya abinci,cikin girmamawa ta rusuna da harshen larabci ta gaidashi ya amsa yana tsaidara,jakarsa ya bude ya fidda rafar kudi irin na qasar dubai masu azabar kauri da yawa ya miqa mata,shaida mata yayi ya sallameta a aiki ga wannan taje na nemi sana'a tayi,cikin rawar jiki ta sanya hannu biyu ta amsa,ita kanta tasan kudin ba qananun kudi bane,zasu isheta yin duk sana'ar da takeso,tabbas ba qaramin taimakonta yayi ba,ta duqa tayi masa godiya mai yawa sannan ta fice. Yana kurbar tea yake lalubar lambarta,muryarta kawai yake so ya soma ji a wannan safiyar kafin ya fice,daidai lokacin da a wancan bangaren sumayya take takawa a hankali har ta fice daga dakin saboda mai gyaran ya gaya mata ta dinga takawa ko yaya ne. Sajida na tsaka da mopping tsakar dakin ta jiyo ringing din wayar sumayyan,ajjiye mop stick din tayi ta nufi inda wayar take,sai taga sunan man,tasan halinshi sarai,idan ya kira mamarsu kiran ya zama miscal yayita fada kenan,hakan ya sanya ta daga ta sanar masa yanzu zata kaima sumayyan kada ta zama misscall,gaidashi ta soma yi sannan tace "Antyn ta fita tattaka qafarta,amman bari na kai mata" jikinshi ya sake bashi irin yanayin jiya,sai ya ajjiye cup din hannunshi yana tattara hankalinshi gareta "Tattaka qafarta?,me ya samu qafan?" Ya tambayeta yana addu'an kada dai ace cikin ne ya soma sanya mata kunburin qafa har yanzu "Faduwa tayi" gabanshi yayi wani mummunan faduwa,a rude yace "Subhanallah?,garin yaya?" "Anty aysha ce ta turota daga upstair" bai san sanda ya miqe tsaye zumbur ba,cikin matsanancin tashin hankali da qaraji yace "Upstairs?,mahaukaciya ce ita?,me ya sami qwaqwalwarta?"tsoro ya kama sajida kaman ita tayi laifin,cikin rawar murya "ban sani ba uncle"ganin yarinyar ta tsorace ya sanyashi qoqarin sanyaya ranshi saidai bakan ya gagara,sai ua rage sautin muryarshi yana tambayarta yadda akai abun ya faru,bata boye masa komai ba ta kwashe duka ta gaya masa,harda nata wanda ta zuba ruwan klien ta fadi,ranshi ya kai qololuwar baci " kada ki gayawa kowa munyi waya kin gayan me ya faru,ok?" "Yes uncle" ta fada tana addu'a cikin ranta Allah yasa unclr man yaci uban anty aysha,dama taji haushi sosai abinda ta yiwa anty amira,har kuka tayi,kullum kuma sai ta tausaya mata idan taga tana dingisa qafarta. Ya jima jingine jikin kujera yana huci shi daya kamar wani mayunwacin zaki,ya rasa wanne hukunci ne ya dace da yarinyar,ba shakka mutum biyu ne rak a duniya zasuyi masa haka ya qyalesu daga ummi sai baba,ya kamata ya nuna mata wa ta tabo,ya kamata ta gane kuskurenta,baiga dalilin ma da zai sanya ya qyale ta ba,data aikata mishi wannan abun data aikata din gwara tayi masa gagarumar sata,gefe guda haushin sumayyan ya kamashi,don me zata boye mishi?,me yasa ba zata gaya mishi ba,yanzun da wani mummunan abu ne ya sameta haka zata yi shiru,batasan muhimmancin lafiyarta a gareshi ba?,kai bama lafiyarta ba,batasan muhimmancin kanta baki daya tattare da tashi rayuwar ba,bazai iya jira har sai ya koma gida sannan ya dauki mataki ba,hakan ya sanya ya soma lalubar lambar CP,bugu uku kacal ya daga,bayan gaisuwa sama sama da kuma ya bayan saduwa ya soma shaida masa abinda yake da buqata,eesha yake so su kamo mishi ita su sanya masa ita bayan kanta,kuma ko waye yazo nemanta kada su sake su bada ita,kai baya so ma su bari asan a station din da suka ajjiyeta,duk da baban eeshan wani ne amma sahun gwiwa ya take na raqumi,hakan ya sanya ba musu suka amsa mishi bayan ya musu bayanin laifin data aikata,ya tambayi mahmoud adress na school dinsu ya aika musu,a yau yaje da buqatar ta kwana bayan cell,wayar ya kashe yana furzar da iska,tabbas sai ta gane shayi ruwa ne. Yana tsaka da duba number ma'aikacin kamfanin jirgin fly emirate dake yankar masa ticket su'ad ta sauko,cikin taku dai dai kai tsaye ta haye dining,ta soma jawo kayan break din tana duba abinda ma'aikaciyar ta dafa ba tare data lura da sauyawar yanayin almustapha ba,tsaki taja don ita duka abincin bai mata ba,choice din almustapha ne,kenan bata mata nata ba,baki ta bude ta shiga qwala mata kira,saidai har tayi ya gama shiru maqatau ba dalilinta,sai ta miqe da niyyar shiga kitchen nemanta tana zazzaga masifa,banza yayi da ita har taje ta gama bulayinta ta dawi,zuwa sannan ya gama waya da su,saidai dole yayi haquri yabi jirgin gobe da safe shine zai sauka dubai to abuja direct,hakan bai masa ba amma tilas ya karba haka,miqewa yayi ba tare da ya damu da qarasa karyawar ba,sai daya sauka daga step din sannan yace mata "Na riga dana sallameta,tunda ba tare na auroku ba" "Wata zaka sauya mana?" Ta tambayeshi ba tare data fuskanci me yake nufi ba "Ki shirya fara girki da kanki karon farko tunda kika zama matar aure" ya bata amsa yana ficewa,zumbur ta miqe ta sauko da hanzari tabiyo bayanshi tana cewa "Haba man,ya zamuyi haka da kai?,kaima kasan abinda bazai taba yiwuwa bane" "Saiki maidashi mai yiwuwar" ya bude motar da kanshi duk da qoqarinbda drivern keyi wajen bude masa motar ya shige abinshi tare da bawa drivern umarnin ya shiga su tafi,binsa tayi da kallo baki daya tunaninta ya koma ga kitchen,gata can gaban tukwane tana fama da gas,kai ta girgiza wlh abinda bata taba yi ba ba zara fara ba yanzu,cikin fushi ta koma ciki kai tsaye ta shiga daki ta dauko wayarta,lambar hajiya khaulat ta soma nema wanda cikin sakanni ta daga,sai ta fashe mata da kuka,daga daya bangaren ta soma fadin "Yaya?,lafiya?,waye ya taban ke?" "Mommy man ne,wai kinji ya kori kuka na wai na fara girki da kaina daga yau,don kawai ya siya min foam na catering school nace bana iyawa,kuma na gaya masa ya gayan nawa ya kashe na buyashi,yanzu don Allah mommy nayi kama da wadda zata shiga kitchen zafi da tururi na qonata?" Wani shegen tsaki haj khaulat ta ja "Shegen yaro tsagera,sai shegen zafin kai da taurin zuciya,to bai isa ba wlh,bamu aura masa ke don ki dafa masa abinci yaci ba,idan ma iya daukan nauyin mai girkin ne bai iyawa ko kuma girkin ne bata iya ba,nan kusa da mu akwai qwararrun masu girki professional zan aiko muku da daya,a aljihuna zan dinga biyanta,cikakkiyar baturiya ce ba abinda bata iya dafawa ba" murmushi su'ad ta saki tare da ihu "Shi yasa nake sonki mamana wallahi" "Uhmmm" tace "Ni wlh wannan yaro ba don abinda ya mallaka ba da tunu na rabaku,qabli da ba'adi iri daban daban,yau wannan tsurfar gobe wancan?,duk ya maidaki wata mara 'yanci" "Kai mummy kada ki kwafsa mana haba da Allah,ke matsalarki kuma kenan auren mutu ka raba mukayi,kawai ki turotan ni zan biya kudin visa da ticket cikin satin nan keso tazo" "To shikenan babu damuwa"da haka sukayi sallama su'ad na aje wayar k babu damuwa a ranta ko kadan,saima ta hura saman dining din ta soma karyawa tana tunanin inda zata musu order abincim dare kafin ya dawo. To fans alhamdulillahi rabbil Aalamin,yau zamu tsaya anam sai kuma bayan zabe idan Allah ya kaimu,amma wannan karon zamu iya kaiwa lahadi bamu dawo ba,idan kuma ya samu lahadin to amma banyi alqawari ba kada na kasa cika muku. Ina kira ga dukkan wani dan qasa da ya tsaya ya fidda son zuciya ya zabi shugaba na qwarai,wanda ko gaban Allah ya riqi kyawawan hujjojin da zai bawa ubangijinsa kan zaben mutumin da yayi,dukkanmu muna da hankali muna ga da tunani munsan abinda ya dace. Ya Allah muna roqonka da kyawawan sunayenka da siffofinka wadanda muka sani da wadanda bamu sani ba,ka zaba mana shuwagabanni na gari,wadanda suke qaunarka suke qaunar fiyayyen halitta suke tausayin bayinka har cikin zukatansu,suje tsoronka da tsoron gamuwarsu da kai,wadanda suka tsaya bada wata manufa ba sai ta taimakon Al'umma,ya Allah duk wanda ya tsaya da wata manufa Allah ka karya mana shi koshi waye,Allah ka nuna isarka ka tallafi raunanan bayinka. Ya Allah duk wanda zai kasance alkhairi a rayuwarmu data addininmu Allah ka damqa masa ragamarmu ko muna so ko bama so,Allah ka zama jinmu ganinmu dama furucinmu,Allah kayi maja jagoranci alfarmar shugaba annabi muhammad S A W 'Yan uwa da garuruwansu ake fama da rikici Allah ka tsayar da wannan tashin hankali,ka zaba musu shugaban da zai zama farincikin zukatansu,sanyin idaniyarsu alfarmar shugaba S A W. Mu guji saida quri'armu domin kuwa QURI'ARKA ITA CE 'YANCINKA,duk dan adam din da bai da manufa akwai babban gyara cikin rayuwarshi. Daga qarshe ina son jan hankalinmu da cewa AKWAI RAYUWA FA BAYAN ZABE kada muci mutuncin juna aibata juna ko bata ran juna sabida wanda mukeso yaci wanda baya so shi ya fadi,basu suka hadamu ba bai kamata su raba mu ba,alkhairi muke nema da kyakkyawan shugabanci,Allah kayi mana zabi mafi alkhairi ka kyautata qarshenmu. WANNAN KIRA NE BAGA AL'UMMAR GARI NA KAWAI BA,KIRA NE GA DUKKAN WANI DAN QASATA NIGERIA,ALLAH YA TALLAFI QASARMU. Subhanakallahumma wabi hamdika,ashhadu an la'ilaha illa anta,astagfiruka wa atubu ilaika. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 1⃣0⃣0⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *subhanallahi wa bi hamdih,subhanallahil azim* ______________________________________         Har yaje ya dawo abun na damunsa cikin rai,ko cikin company ranan kowa yasan lallai an tabo oga,duk wanda ya kuskure sai ya sha fada idan ma baice ya bawa mutum hutun satittika ba,har ya dawo din bai sake kiran sumayya ba ko wani cikin gidan.        Bayan sallar isha'i bayan yayi wanka,sanye yake da vest da boxer yana zaune saman dining,fitowa tayi daga kitchen dauke da ledoji niqi niqi a hannunta ta zauna saman dining ta soma fiddo da dinner din data musu order,idanu ya zuba mata yana kallonta,yasan za'a rina,lallai raina shi su'ad tayi,bata ji me ya gaya mata kafin ya fita ba kenan "Wannan fa?" Ya fada yana nuna abincin da idanunshi "Abinci ne na mana order" "Shi nace miki zanci?,da na order nake so kinsan dai na fiki iyata ko?,wanda kika dafa cikin gidan nan nakeso" kai ya lanqwasar tana dubanshi "Amma dai kai zaka bawa wani labarin ban taba dafa wani abu ba ko?"kafada ya daga in idont care manner "Wannan ke ta shafa,tunda na baki dama ki koya,so wataqil dama can kin iya ko shi yasa kika wulaqanta foam din kanshi da na saka kudade masu yawa na siya miki" "Iyawa ne gsky bazan yi ba,tunda nasan kana da arziqin da zaka iya dauka min kuku ko nawa nake da buqata" "Ba kuku bane matsalata,abincin mata ta nake so naci,ke ba zakiyi min abinda nake so ba saidai ke nabi ra'ayinki.....to ba zaiyiwu ba,ni ba sakaran namiji bane,dole ki sauya,dole ki koma kan tsarin da nakeso tunda na fahimci ke bakisan lallashi ba" a fusace yake maganar,yana kaiwa nan ya miqe a zafafe ya shige dakinshi,binsa tayi da kallo har ya wuce,ta dauke idonta tana tabe bakinta,kome zayayi ba zata lamunci yin wami girki ba kamar 'yar aiki,jawo tata ledar tayi ta bude ta soma cin abincinta hankalinta kwance,        A daren da kanshi ya soma hada kayanshi cikin wata qaramar jaka mai kyau ta matafiya,ba wani kaya zai diba can ba saboda ko ina yana da kayan amfaninsa komai da komai,su'ad na nade saman gado tana kallon wani horror film,jakar da ya fita da ita ya janyo ya bude ya ciro ticket ya ajjiye gefan su'ad "Ki shirya gobe da azahar zamu wuce nigeria" da hanzari ta dago ta dubeshi,sam bata taba zaton haka ba,itafa bataqi su dauna zuwa ba ma baki daya tunda ta daukoshi wa ta ajjiye can da zata damu sai taje "Me zamu je yi a can din?,naga duka bamu yi cikakken wata biyu kai daya da rabi ma da dawowa ba....nikam gaskiya da ka sani na america ka siya min,tunda ina da sauran visa ta bata qare ba naje na qarasheta" "Sai kin dawo" ya bata amsa cikin halin ko in kula,farinciki ne ya kamata "To zaka siya min din?" Waiwayowa yayi yana dubanta "Kudin da na miki transfer accnt dinki jiya....duka ina kika kaisu?" Fuska ta bata,ya iya saninta tunda suke da shi babu lissafi tsakaninsu,bai taba mata irin haka ba,ko yau ta nemi kudi gobe ta nema zai maya transfer ba tare da ya damu da me zata yi da su ba "Na kashesu" shuru ya mata bai sake bi ta kanta ba yaci gaba da abinda yake,yayin da ya barta cikin qila wa qalan zai biya ne koko a'ah?.          Qarfe sha biyu na rana ta fito daga luctures,takowa take cikin yauqi da isa inda zata jira drivan ya dawo daukarta,har yau bata da walwala,ranta a bace yake,ta qullaci sumayya qwarai,ba ita kadai ba hatta da ummin ta sanya bigiren da zata sanyata,gani take ma duka ummin ce ta hana ruwa gudu,banda haka tana da tabbacin matuqar ta yiwa almustapha izinin aureta ko musawa bazaiyi ba tilas ya amince,sanda tazo mata da kukanta haquri ta bata,tana nuna mata almustaphan bai jima da yin aure ba bazaiyiwu ace ya sake wani nan kusa ba,kawai taci gaba da addu'a idan rabonshi ce ita dole zasuyi aure,sai yanzu take shinshinar cewa sonta ne kawai bata yi ta fake da haka.         Tun daga nesa ta hango tahowar motar 'yan sandan amma sai ta dauke kai saboda tasan bata da wata alaqa da su,ga mamakinta gabanta suka tsaya,a wulaqance ta daga kai tana dubansu zata soma zazzage musu ruwan masifan sunzo gabanta sun tsaya sun tada mata qura,fitowar daya daga cikin 'yan sandan ya tsaya qiqam gabanta shi ya katse mata masifar data so yi "Malam lafiya?" Hannunshi ya saka a aljihun gaban rugarshi ya fito da ID card dinsa ya nuna mata yana cewa "Suna na inspector uba labaran,ina fata kece Aisha jamil?" Kai take gyadawa "Eh yes nice,ya akayi kazo gabana kamin wani qiqam?" "Akwai qorafi a kanka wajen yunqurin aikata laifi,sabida haka muna gayyatarki zuwa ofishinsu ki riqe bayananki duka kya yisu a can" miqewa tayi cikin masifa "Me kake nufi malam,wannan wanne irin iskanci ne,rashin mutuncin naku na 'yan sanda haf ya kai haka,kawai kazo ka sameni kace wai ana tuhumata,waye yake tuhumar tawa?,wai tsaya ma malam kasan wace ni kuwa?" "Eh mun sani,wanda kuma ke tuhumar taki ya fiki shi yasa muka zo tafiya da ke" wata gajeriyar baqar mace dake sanye da unifoarm ta fada tana qarasowa gefan eeshan,kallo daya zaka mata kasan fuskarta babu rahama "Lallai kunyi kuskure,baru na kira mahaifina qila watan rasa aikinkune ya kama" ta fada tana yunqurin fiddo da wayarta daga jaka,damqe jakar matar tayi ta karbeta daga hannunta tana fito da ankwa daga aljihunta tana duban eeshan "Ko ki wuce salin alin mu tafi,ko kuma ta qarfin tsiya mu saka miki wannan sannan mu tafi da ke" wanu gagarumin baqinciki ya rufe eesha,ta tabbatar matuqar tayi gardamar matar haka zata aikata mata din,bugu da qari kuma ga mutane sun soma cika a wajen,yawancinsu sun santa,sun san dagawa da daga kai irin nata da taka duk uban wanda taga dama,bata ragawa kowa,kada ma dai a ce babanka ba wani bane "Kawai ki wuce ku tafi sister eesha kada su qaqaba miki wannan qarfen ki kafa tarihi" cewar titi kenan hatsabibiyar yarinyar da suke takun saqa da eesha kaman suna ganin hanjin juna,saboda kowa na taqama da kudin ubanshi,sauran 'yan jam'iyyarta suka sheqe da dariya,ba yadda zata yi,da wani tozarcin ya sameta a nan gwara ta bisu koma mene sa qareta a can,haka ta taka matar ta bude mata motar ta shige suka rufe suka ja suka bar wajen.        Cikin motar ta kallesu tace "Ni bansan me nayi ba,amma ko mene ku bude jakata akwai kudi nasan su kuke nema zasu isheku ku raba" wani kallo matar ta watsa mata,tuntuni ta fuskanci yarinyar tana da dagawa da izgilanci "Ko nawa ne jakarki wanda ya turo mu idan su muke buqata zai iya linka mana su" haushi ya tuqeta,cikin tsiwa da masifa tace "Ni dinma zan iya,akwai atm cikin jakar,ku dauka ku ciri ko nawa kuke so a ciki,nasan dai kudin ciki duka sun muku yawa" "Munce miki bama so ki rufe mana baki,laifi kikayi kuma dole mu kamaki" "Mtsweew,ai matsiyaci ko a tandun mai ka sanyashi ka tsamoshi qamas zai fito,kada Allah yasa kuso,labari ya kai kunnen babana zakuyi biyu babu ne,ba kudin ga kuma asarar aikinku da zakuyi"dariya matar tayi,tabbas ba dan yace kada su taba lafiyarta ba da sai ta bawa wannan fuskar da rake taqama da ita lafiyayyun marin da har ta mutu ba zata taba mantawa da su ba "ina jin baban naki ne ma idan baiyi wasa ba zai rasa hanyar cin abincinsa,dom wannan mutumin lallai an taboshi,ban taba ji yasa an kama wani saboda kan kanshi ba,kuma wallahi kika sake mana magana ko rashin kunya sai na magutsa bakinki a nan na sauya miki kamannin fuskarki" ba shakka eesha naji da fuskarta,ganin yadda matar ta soma huci tana fito da jajayen qananun idanunta ya sanya eeshan yin laqwas,ranta da zuciyarta na tafasa,so take kawai tasan waye yayi mata wannan tozarcin da tunda tazo duniya ba'a taba yi mata irinsa ba,lallai bata da maqiyi kamarshi ko waye.          Suna isa station din suka karbi duka kayanta,sannan aka bude wani daki wanda ba kowa suka saka ta ciki suka maida qofa suka rufe,kukan baqinciki ne ya qwace mata ta soma maganganu tana zage zage,ba wanda ya kulata sai data gaji don kanta tayi shiru,dakin ta fara bi da kallo kusurwa kusurwa,banda duhu da wari ba abinda ke tashi ciki,ga kukan sauro tun yanzu da ranar Allah,ina ga dare yayi,tsaiwa tayi taqi zama sabida qyanqyamin wajen da takeyi,sai daga bisani da taga ba sarki sai Allah qafafunta na neman sandarewa tilas ta tsugunna tana hawaye,addu'a kawai take Allah ya kawo babanta,ba shakka dukka 'yan sandan sai ta sanya an koresu daga bakin aiki.          Qarfe biyu da rabi na rana ya sauka a filin sauka da tashi na jiragen sama dake abuja,a masallacin dake cikin filin ya sallaci azahar,zuwa sannan drivanshi na nan abujan ya iso da daya daga cikin motocinsa na hawa ba bata lokaci suka dauki hanyar gida.           Suna zaune ita da ummi da sajida ne kawai,ummi da sajida na saman kujera,yayin da sumayya ke zaune qasan carfet sajida na ware mata kalabar da amira tayi mata guda takwas sanda tazo dubata,wadanda jelarsu ta sauka a bayanta,hira suke kadan kadan suna tuna haujar amira sanda taji abinda eesha tayi,cewa tayi wallah har gida zata Allah ne kadai take tunanin zai rabasu da eesha,zagi kuwa ranan babu wanda eesha bata shashi ba,sanda ummi taji ta hanata zuwa amira harda qwallar takaici,ita sam bata damu da ko yaron cikin dake jikinta ba,so take kawai taje su casheta,ta rasa ita da amira wa yafi wani quruciya ne.         Shirt ce ajikinta mai shirt sleeve irin ta mata fara qal wadda aka yiwa adon pink,sai A line skert shima pink ne kaman adon pink dake jikin rigar,mayafin da ta dan yane kafadunta da shi fari saboda nauyin ummi da take ji duk da ita ba ruwanta ita tace ta dinga saka su tana shan iska,kalbar an tsafe biyar bata taje ba saura uku.        A nutse ya sanya hannunshi ya turo qofar falon tare da sallama kan labbansa duk da bai bude muryarshi sosai ba,fararen idanunta ta daga suka sauka cikin nashi sanda yake takowa cikin falon ummi na masa duban mamakin zuwan ba zata,sosai ta dauki hankalinshi tayi wani fresh ta qara kyau kaman zane,amma sai miskilancin ya motsa,haushin abinda tayi masa ya taso masa,sai ya janye idanunshi daga kanta ya maida kan ummi fyskarshi kadaran kadaham "Lafiya dai ko almustapha wannan zuwan ba zata?" "Lafiya qalau..." Ya fadi sanda yake zaman saman daya daga cikin kujerun falon idanunshi kan qafar sumayya dake miqe saman filo,wani abu ya tokareshi,wato abun har ya kai a nade mata qafa haka?,cikin ladabi yake gaida ummin tana amsawa,ta lura da yanda qafar sumayyan ke jan hankalinsa sai tace "Kaga tsautsayin da ya faru ko?" "Na gani" ya fadi kawai yana duban qafar,yanayin yadda ya amsa din kaman yasan komai sai ya bata mamaki,ita dai tasan bata gaya masa ba haka ma sumayya,sai tayi shiru ba tare data idasa bayanin ba,miqewa ummin tayi don son basu waje tana cewa "Me za'a kawo maka?" "Ruwa....ruwa ma ya isa" "To....taso sajida ki kawo masa" badon babu ma'aikatan da zasu kawo masa din ba don ta basu waje nw ta fada tana yin gaba.        Har suka bace a falon idanunshi na zube qur a kanta,baki daya wani nauyinshi take ji ya koma mata wani baqo,tunda suka soma jituwa basu taba nesa da juna haka ba,ribbom ta janyo tana qoqarin tattara gashinta waje guda "Barka da zuwa,an iso lafiya?"ta ambata tana kunyar kallonshi,bai amsa ba kaman yadda bai bai dauke ido daga kallonta ba,a nutse ya miqe tsam daga inda yake ya tako a hankali zuwa gabanta,durqusawa yayi saman qafafunshi,ya sanya hannunshi ya daga qafar tata dake miqe saman filo ya soma warware nadin da aka yiwa qafar,idanu ta zaro sannan cikin sauri tace "yau zaya zo ya cire da kanshi tunda....."wani kallo ya watsa mata da idanunshi da ke cike taf da bacin rai,da sauri ta janye idanunshi shi kuma ya maida kai yaci gaba da warwarewar,bai dakata ba sai da ya gama tas sannan ya yar da tsumman gefe cikin tsantsami,duk da cewa ba wani abu yayi ba fes yake,miqewa yayi tsaye ya miqa mata hannunshi alaman ta taso,fargabar tashin take da kuma fargabar taka qafar,gashi lokaci guda ya sauya mata,babu annuri ko kadan kan fuskarshi,ba yadda ta iya haka ta zira hannunta cikin nashi ya dagata ta miqe tana rintse ido.     Baki daya tayi luu zuwa cikin jikinshi saboda ragowar radadin da qafarta take mata,qirjinsa ta fada tana riqe da shi,kusan lokaci guda suka saki ajiyar zuciya,duk yadda yaso boye tasa sai data bayyana sabanin tata da tayita a boye,abinda ke cunkushe cikin zuciyarshi yaji ya soma sauqi,nauyin da qirjinsa yayi ya soma raguwa,wani wawan shauqi kewa da qauna ke ratsashi,take wani abu ya soma kai kawo cikin jikkunansu.          Sajida ce ta fito dauke da cups da gorar ruwa,zata koma da baya almustapha ya dakatar da ita "jeki dauko mata hijabi cikin kayanta" "To" ta amsa tana dire cup din sannan ta juya ta haye sama da gudu,dan janyewa tayi daga jikinsa tana dubanshi,so take ta tambayeshi ina zasu bayan mai gyaran zaizo duba qafarta amma ta kasa,yayi mata kwarjini da yawa,daure fuskarshi ya hanata katabus,har sajida ta sauko ta miqa mata hijabin ta sanya ya dubi sajidan "Ina ummi?" "Wanka ta shiga" "Idan ta fito kice mata mun tafi" "To,a dawo lafiya" cewar sajida tana juyawa ciki,da idanu ya mata alaman su tafi,saidai ta kasa yin gaba,ji tayi kawai yayi sama da ita ko a jikinshi ya soma takawa da ita ya fice daga falonsatar kallon idanunshi take,wadanda tayi kewarsu matuqa da gaske,bata sake yarda da abinda take ji tattare da shi ba sai yanzu da suke tare da juna,hada ido sukayi sai ya dauke kai yana ci gaba da takawa zuwa ma'ajiyar motoci,kunya ta cikata,ganin jifa jifa ma'aikatan gidan na giftawa,saidai duk wanda ya sako kai ya gansu sai ya koma baya ya lafe yana jiran wucewarsu,ko a jikinsa shi kam,sabida tun asali duk abinda zaiyi yanayinsa ne kai tsaye matuqar ya dace da ra'ayinsa ya kuma yi masa dai dai,bai direta ko ina ba sai cikin mota sit din baya,shima ya shiga ya baiwa driva umarnin yaja suje.           Shiru ne ya biyo baya cikin motar,kanta na qasa baki daya tana takure,bai ce mata uffan ba shima,duk da yadda yake jin cikin zuciyarshi game da ita kaman ya jawota ya hadiyeta,farinciki ya sake mamaye zuciyarshi musamman sanda yaga matashin cikinta ya soma kutso kai waje,saidai dole ya nuna mata fushinsa ko don gaba,kada ta sake maimaita irin wannan kuskuren,shine mutum na farko da yafi cancanta ace yasan dukkanin wani abu da ya sameta na dadi ko akasin haka,yana son su zama verry close,aminan juna,qawaye,dangantakarsu ta zama daga gangar jiki har zuciya,qofar wannan gidan nashi wanda ta yiwa laqabi da lovehouse suka kutsa,a katafaren wajen parking din ababaen hawa ya tsaida motar,almustapha ya bude motar sannan ya sanya hannu ya dauketa baki daya ya taka anutse zuwa ciki,bai sake ajiyeta ba sai daya dangana da madaidaicin clinic dake gidan bisa gadon kwantas da marasa lafiya,duk wani abu na amfani da zaya buqata ya janyo kusa da gadon bayan ya girke kujera gaban gadon ya zauna ya soma aikin da yake da buqatar yi.         Da ido take bin duk wani motsinsa,sam yaqi kallonta ma ballantana taga fara'a kan fuskarshi,yaqu furta komai gareta,lokaci sukan hada ido sai ya hade girar sama data qasa kawai ya sake dauke kai,sosai ta shiga damuwa,idanunta sukq dinga tara qwalla,to me tayi masa haka?,itakam har yau bata san abinda tayi masa ba,sai da ya gama scan ya duba komai,ciki harfa edd dinta,ya tabbatar da cewa komai lafiya sannan ya koma kan qafar,a nan ne ma ta dinga jin dan ciwo sama sama sanda yake tabawa,ya gama ya ciro wani mai mai zkama da vaseline ya shafa mawa dai dai wajen sannan ya dagata ta zauna.                   Gab da sallan magariba ya fito falon inda take zaune,shirye tsaf cikin wani tattausan yadi na maza fari mai adon ash,dinki ya bala'in yi masa kyau,takalmin qafarshi sau ciki ya dace da shigar da yayi,babu hula kanshi sai agogon fata da yake daurawa a hannunshi,inda ya ajjiye mata abinci ya kalla,babu wani abu data ci a ciki,sai ya dauke kanshi baice da ita komai ba har sai da ya gama daura agogon sannan ya qarasa gabanta,wrapping din da aka yiwa plate din ya yage,ya sanya cokali a ciki ya miqa mata tana tsareta da ido,jiki a sanyaye ta karba zuciyarta na karyewa,wai ke ta masa haka ne?,ko fushin tafiyar ne har yau,amma ita ai tasan sun sasanta wannan matsalar,hasalima ko shekaran jiya sun raba dare sosai suna waya yana tsumata da kalamanshi,amma tsakanin jiya da yau baki daya ya sauya?,haka ta dinga cusa abincin ya tsiyaya mata ruwa ya miqa mata,sai da yaga ta shanye sannan ya juya yana ficewa tare da fadin "Ki samu waje ki kwanta" ya fice daga gidan,can qasan zuciyanshi tausayinta ne kwance,ya sani cewa inda su'ad ce eeshan ta yiwa haka da tuni labari ya sha banban,wanne irin haquri gareta haka?,har kuma ta kasa sanar masa abinda ta masa,tabbas itama sai taji a jikinta kaman yadda ta gwada mata rashin tausayi.           Da kanshi ya isa station din ta hanyar drivansa,sun gama magana da cp tun a hanya bai kusa amma tana nan a station din,cikin girmamawa DPO ya fito ya taryeshi,farinciki ya cikashi yau ga mutum kaman doctor muhammad almustapha cikin station dinsu,office dinsa ua saukeshi suka zauna daga shi sai shi suka gaisa sannan ya suka soma tattaunawa kan eeshan "Ranka ya dade me zai hana kawai a kaiku kotu?" Murmushi almustapha yayi yana girgiza kai "A'ah,iya nan ma ya isa,banson maganar taje kunnen kowa ma bare kotu,ba wulaqantar da ita nake so nayi ba,so nake kawai ta gane girman laifin data aikata.....zan iya ganinta?" "Me zai hana.....kai....bala!" Ya qwalawa dan sandan dake kan kanta kira,cikin girmamawa ya shigo ya sara masa sannan ya qame "Jeka fito da yarinyar nan wadda ta zagi asabe jiya ta kakkwada mata mari" "Yes sir" ya fada yana juyawa cikin hanzari,dubanshi almustapha yayi "Amma officer na gaya muku kada wanda ya daketa ko?" Cikin girmamawa yace "Sorry yallabai,wallahi yarinyar ce sam bata da kunya,ga bakinta baya mutuwa,an kawo mata shinkafa da mai da yaji ta kwafar tana durawa asabe zagi,to dama tun jiya da suka je daukota take zaginsu,asabe kuma ba haquri shine data fusata ta zabga mata mari" "Kada ta qara to" "In sha Allahu yallabai" ya fadi dai dai sanda aka shigi da eesha,wadda tsahon kwana daya da wuni baki daya ta soma sauyawa,tun daga fuskarta da yatsun asabe suka fito rada rada,ga sauro ya yagi rabonshi a fatar da ake so da tattali da kashe mata kudi wajen siyan mayuka masu tsada,dauda ta soma zama ajikinta,ita kanta jinta take baki daya ta soma muzanta tun daga yau,matar da a rana sai tayi wanka sau uku biyu a rana,sai gashi rabonta da wanka tun na jiya da safe da tayi kafin ta fito makaranta,tana ganin almustapha wani dadi ya saukar mata,tuni ta fara qissima yadda zata ci uban baki daya 'yan sandan "Ya man" ta fada cikin farinciki,saidai yanayin fuskarshi ya sage mata gwiwa,bata wani kawo cewa shi ya qulla mata wannan abun ba,tafi bada cewa miskilancin nashi ne ya motsa,amma koma meye tunda zai ceceta ayi shi daga baya,kujera dan sanda ya tura mata saitin almustapha,kallon banza ta watsa masa tana tunanin ya soma ladab tunda yaga babban mutumin da yazo belinta,zai nuna shi na Allah ne sabida ta sassauta masa idan ta tashi hukuntasu "Zaka ci ubanka wallahi duk sai kun rasa aikinku" ta fada cikin tsiwa da gadara,idonta kaman zai fado saboda harara,wani abu mai tauru ya hadiye dan sandan,ba shakka ba din sanin waye a gabanshi ba da sai ya gabza mata mari kaman yadda sabe tayi mata dazu,ya lura babu digon kunya ko mutunci tattare da yarinyar sam,ba wanda ya furta mata sai DPO da ya daka mata tsawa cikin kakkausar murya yana bata umarni ta zauna,sai data ja tsaki sannan ta zauna DPO ya fice tare da daya dan sandan suka barsu su biyu.         Idanunshi ya tsareta da su yana kallonta,yayin da ta soma sheshsheqar kuka sannan ta fara magana "Kaga abinda suka yimin ko ya almustapha,cin mutunci har cikin makaranta tsakiyar dalibai" bashi labarin yadda komai ya faru ta soma yi,yana kallonta baice uffan ba har sai data gama,cikin izza ya motsa bakinsa "Ni na sanyasu ba wani bane" cikin mamaki da tsoro take dubanshi,ya tsareta fes da ido yana mata kallon banza ranshi a bace,zamanshi ya daidaita sosai ya zauna saman kujeran yana ci gaba da kallonta "Kin soma zama 'yar ta'adda,wadda keson kashe uwa da abinda ke cikinta ko?" Idanuwa ta zaro gabanta na faduwa,ta shiga uku indai yaji wannan zancan,qirji ta dafe tana nuna kanta "Ni din?,yaushe?a ina?"kai yake gyadawa yana jin baki daya ya raina masa wayau ma,shi kam babu abinda yafi tsana sama da qarya,shi yasa sam bai iya ta ba,ko zai maka me yafiso ka gaya masa gaskiya,qila gaskiyarka ta cece ka a wajensa "Ni kike tambaya?,da kyau" sai ya miqe tsaye "Duk randa kika tuna lokaci da wajen da kika aikata abun kya fito" kuka ta saka,kunya nauyi da baqinciki duka suka cikata, "Wallahi sharri akemin" wani kallo ya mata sannan ya juya ba tare da ya sake bi ta kanta ba ya fice,a kan kanta ya samesu,suka sake tattaunawa da DPO ya sake jaddada masa baiso kowa yasan inda take tsare,sannan koda an sani bai lamunce a bada belinta ba,ya fiddo kudi ya danqa masa kudin abincinta ya kuma yi musu ihsani sannan ya tafi.         A hankali ya ke takawa har ya isa cikin dakin baccin nashi,sam baiyi tsammani ba ya sameta zaune saman abun sallah,tana sanye da kayan bacci riga da wando sai hijabi dake jikinta,kana duban idonta kasa kuka ta sha ba kuma kadan ba,da qyar ta daga kumburarrun idanunta ta dubeshi sannan tayi qasa da su tana masa sannu da zuwa,yarrrrrr yaji tsigar jikinsa ta zuba,ranshi ya baci,duka eesha ce ta jawo faruwar hakan?,kayan jikinsa ya cire ya daura towel,sannan ya isa gaban ac ya kunnata saboda zafin da yake ji,hannunshi yaji ta riqe sanda yake yunqurin wuceta "Don Allah kayi haquri.....idan wani abu nayi maka ka yafemin...ko ka gayan na nemi yafiya wajenka" ta fada cikin rawar murya,tamkar wani abu aka zuba masa haka yaji cikin jikinsa,sai ya dawo a hankali gabanta ya zauna sosai,idanunsa dake bayyana tsantsat bacin ranshi yake dubanta da su "Sai ta kasheki sannan za'a gaya min sumayyah!" Ya fada abun ma taba ranshi,sunanta fes cikin bakinshi cikin wani salo "Wanne irin ganganci kika si yimin da rayuwar mutum biyu masu matuqar muhimmanci a waje na?" Ya qarashe maganar cikin salon tambaya,shiru tayi kawai kanta a qasa,hawayen da take maqalewa suka balle mata,sai ya sake matsowa dab da ita suna jin dumin numafashin juna "Sumayya!.....da wani abu ya sameki fa?,ya kike tunani?,kina tsammanin zan ci gaba da rayuwa kaman yadda kowanne dan adam keyi?....kinsan kuwa muhimmancinki a wajena?,me yasa bazan zama mutum na farko da zamu raba lafiyarki da akasinta ba?,mutum na farko da zamu raba jin dadinki da akasinsa ba,kinsan me nake so matata ta daukeni?,amininta abokinta mafi kusanci da ita,bana so matata ta raba matsalarta da kowa,bana so ta raba damuwarta da kowa,so nake na zama jigonta majinginarta,don me zaki boyen abu mai hatsari irn haka?saidai wata ta gaya min?,ba don Allah ya kiyaye ba kinsan me zaya faru a gaba?" Tuni kuka ya qwace mata,cikin muryar kukan tace "Har yau bakasan wace sumayya ba,sumayya ta saba ganin hakan cikin rayuwarta,taga sama da haka ma,shi yasa bata dauki hakan baqon lamarin da zai girgizata sosai ba,abinda ta saba gani yau da gobe ne,fa'iza,karima,uwa uba zainab" ta furta tana son danne kukanta,sai jikinsa yayi sanyi,ya kasa jure kukanta,sai ya janyota cikin jikinsa ya matseta tsam,suka soma raba radadin dake cikin zuciyarta,cikin wani irin salo yake rarrashinta,wanda hakan ya bashi nasarar tsaida kukan nata cikin taqaitaccen lokaci "Su waye su zainab?me suka yi miki haka?" Ya tambayeta tana kwance a jikinsa,nannauyar ajiyar zuciya ta sauke,sannu a hankali ta soma warware masa ita din wace ba tare data boye masa komai ba. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 1⃣0⃣0⃣1⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *Allah S W T yana cewa cikin qur'aninsa mai girma* *IDAN ZAKUYI UQUBA KUYI UQUBA DA GWARGWADON MISALIN ABINDA AKA YI MUKU UQUBA DA SHI(ma'ana idan zaku rama wani abu da aka yi muku ku rama gwargwadon abinda mutum yayi muku babu qaari)IDAN KUKAYI HAQURI SHINE MAFI ALKHAIRI GA MASU HAQURI* Sadaqallahul azim __________________________________          Da fari labarin dariya ya dinga bashi,quruciyarta ta dinga burgeshi tana masa dadi,ya dinga leqa fuskarta yana tsokanarta,a hankali sai yanayin ya sauya ya koma na kishi,zallahn kishin mukhtar,yayi shuru yana saurarenta,daga bisani kuma sai mamaki ya bijiro masa,tausayi shi ya zama abu na qarshe,kafin ta gama bada labarin saiga hawaye shabe shabe kan fuskarta,yayin da zuciyar almustapha ta dinga motsawa,ji yake kaman ya dawo da hannun agogo baya,kamar ya dawo da baya ya ciro fa'iza zainab har ma da karima ya hukuntasu,lallai dole ta dauki eesha ba a bakin komai ba,tausayin abdallah da qaunarshi suka kamashi,ashe maraya ne,marayan da tun kafin ya iso duniya ya fara fuskantar qalubale na rayuwa,lallai dole yayi maganin eesha,bazai yarda ta sake fuskantar irin wannan rayuwar ba.        Dubanta kawai yake bayan ya gama rarrasarta,mamakin irin rayuwar da take kawai yake,saidai zuciyarsa cike take fal kishin dukka mazajenta,ina ma ace shi ya fara samunta tun a wancan shekarun,da lallai ba shakka bazai bari tayi irin wannan rayuwar ba,saidai kuma qaddara data rigayi fata,ko a hannunshin ne tunda yazo cikin KUNDIN QADDARARTA dole hakan ya faru da ita.         Kwanansa biyu cikin gidan baya fita ko nan da can,wata sabuwar rayuwa mai cike da soyayya da qauna suke shimfidawa cikin gidan,wata kulawa sumayyan kr bashi wadda ada can bai taba hakaito ta iya bawa miji kulawa kwatankwacin haka ba,duk sai ya narke ya koma wani shagwababben qarfi da yaji,jinsa yake tamkar qarakin yaro,irin soyayyar da yake hasashen samu ga matar aurensa ita yaje gani zallarta ba algus,shima baiyi qasa a gwiwa wajen bata kulawa ba,ji yake kaman ya lasheta ita da abinda ke cikinta,sau tari yakan sata ta saka qananun kaya kawai don yaga zaman cikinsa a jikinta,wata qimarta ke dada hauhawa cikin zuciyarshi,ta zama wata ta musamman cikin rayuwarshi,labarinta ya tsaye masa a wuya,yana jinjina mata yadda ta fuskanci duk wani qalubale na rayuwarta,yaci alwashin sai ya shafe duk wani tabo da yayi saura qasan ranta da qarfin qwanji da na zuciyarsa.         Randa suka cika kwana uku a gidan,bayan sallar magariba ne,yana zaune a falo sanye da gajeran wando da vest duka farare qal,qafafunshi harde yana kallon wrestling,fuskarshi qunshe da murmushi duk da ba abin dariya ake ba a allon t.v,yayi shiru yana sauraren fitowar sumayya daga kitchen,wanda yasan me ya qulla maya shi yasa yake dariya,kukan shagwabarta ya jiyo tana fitowa a kitchen din,sanye take da vest itama da wando iya gwiwa baki dayansu blue da pink,kayan sun fito da cikinta muraran ya zauna das a jikinta,gashinta na daure a ribnom qwaya daya ya sauja bayanta sai qyalli yake,wanda aikin almustaphan ne shi ya gyara maya shi dazu da yamma,waiwayowa yayi yana kallonta hadi da qunshe dariya ya dage gira ya ware mata hannayeshi alamun ta taho "Babe....me ya faru?" Harararshi take tun kafin ta iso "Nama na.....ina nama na?" Sake qoqarin boye dariyarshi yake ya soma zagaya idanunshi sannan yace "I think akwai bera ko mage fa gidan nan,dazun naji motso a kitchen may be su shuka janye" sai ta sake sakin kuka ta fado jikinsa a hankali,da sauri ya tarbeta yana sakin dariya,ya cusa hannunshi bayanshi ya ciro kwanan ya dire mata "Hala baki kallon mudubi....gaba daya kina cin nama yana komawa kumatunki yana zama" ya qarashe yana dariya,dariya itama ya bata,sai ta harde hannayenta tana kallonshi "Okey.....yanzu ya kake so ayi,na daina ci kenan?" Hannunsa ya daga sama "Ni bance ba,ci abinki tunda baby na so...." Magananshi ta katse sanda wayarshi ta dauki ruri,ummi ke kira,sai ga miqa hannu ya dauki wayar yayin da ya maqaleta a kunne,ya soma bude plate din yana motsawa sumayya naman don ya huce yadda zai mata dadin ci.        Gaisawa sukayi don yau duka basu je sun gaida su ba "Almustapha ka kira gwagwgwanka hasiya ka mata jaje fa,yau kwanaki hudu ba'a ga aisha ba ba'asan kuma inda take ba,anyi nema har an gaji" "Wace aisha ummi?"ya tambaya tamkar bai santa ba din "Aisha 'yar gidan asiyan uncle balarabe?" "Ohhh....Allah ya bayyana"ya fada yana miqawa sumayya naman cikin bakinta "Nace ya kamata kasaka hannu ko Allah zai saka a ganta,barinta gidan nan da kwana uku abin ya faru,tunda Allah yasa kana da idon sani ka saka hannu ko Allah zaisa a ganta" "Ummi....ku barta kawai,alhakine fa.....kisa taso yi cikin gidan Allah ya tsare,may be alhakin ne yake wahal da ita" ya fada kaman da gaske baisan komai ciki ba "Almustapha......qaniyarka,qanwarka ce fa,tunda har Allah ya tsare din mai ya taso da wannan maganar?,c'mn ka sanya hannu a nemota hankali asiya a tashe yake" "Zanyi qoqari ummi in sha Allah" "To Allah yasa a dace,ina 'yata" murmushi yayi ya dubi sumayya dake kallonshi "Gata nan....nama take ci"murmushi ummi ta saki cikin jin dadi "qyaleta kar ka tseta,ka gaidamin ita,jikin nata kuma fa?,daka dauketa ka hana mai magani qarasa aikinsa" murmushi ya saki "Zan kawo miki ita gobe,zaki mamaki ummi,ya za'a yi ina likita a kira mai maganin gargajiya ya taba min mata?"baki ummin ta riqe tana murmushi,wannan qauna ba qarama bace ta tabbata almustaphan kewa sumayya "sannu masu mata,mu ai da yakeazanmu basa sanmu da idan irin haka ta samemu suke kiran masu maganin gargajiyar su dubamu" sai kuma kunya ta kamashi,ya saki dariya yana katse wayar da sauri.       "Uh,me kike kallona?" Ya fadiwa sumayya yana lakace mata hanci,kai ta girgiza "Don Allah baby ka barta ta koma gida haka" ta fada a shagwabe,fuska ya dinke "Wa fa?" "Aisha mana,kaga hankali yanzu ya tashi,ya kamata ta koma gida"shuru yaui kaman bazai tanka ba,yaci gaba da miqa mata naman,sai da yaga taqi karba sannan yace "sati guda na diba mata kuma sai ta yishi,kiyi addu'a a sanda ta cika satin ta yarda ta aikata abinda ta aikata din,matuqar ta sake maimaita min abinda tayi tace sharri ne aka mata wallahi sai ta sake wani satin har sai ta yarda ta amince ta kuma nemi yafiya,zuciyata ba zata lamunci cutarwa tattare da ke ba,ki fitar da kanki daga maganar nan banson kice komai bare ki nunawa ummi na aikata hakan....kin gane?" Shiru tayi kawai ta gyada kai,don ta fuskanci ya dauki lamarin da zafi qwarai.    *******   *****   ********         Da yammaci suka shirya kaman yadda ya alqawarta kaita wajen ummi,tayi kyau cikin atamfa vlisco,ta cika sosai fatarta ta sake fresh,ta zama wata 'yar duma duma,duk inda ta gifata sai ta bat ragowar qamshinta,duk yadda yasi dauke idanunshi daga kanta hakan ya gagara,daga bisani janyo abarsa yayi ta sauka jikinsa tana dariya "Baby.....so nake na gama fa mu tafi,na qagu naje naga ummi" "Anya fitar nan kuwa yau zata yiwu?" Idanu ta zaro tana dubanshi "Saboda me?" Murmushi ya saki,ba qaramin kyau ta sake masa ba data zaro idon,ya saka hannunshi ya ja hancinta "Kinmin kyau,ya kamata muje mukai wa babynmu ziyara ko ba haka ba madam?" Ya qarashe yana kashe mata ido,ta fuskanci sarai me yake nufi indai yace zai kaiwa baby ziyara ne da shi yake fakewa,ta rasa ya akai ya sake ninka jarabarsa kan tada,sai ta soma tureshi tana bubbuga qafarta "Ba wani ziyara.....yau wajen ummi kawai zamu" dariya ya soma yana cusa hancinsa lungu da saqo na jikinta yana shaqar daddadan qamshinta tare da yamutsata,tsuwwar da wayarsa ta fara shi ya sanya shi sakinta yana dubawa,ya ajjiye wayar yana dubanta da idanunshi da suka rage girma tare da sauya kala "Hamza ya iso shi da matarshi,yace zasu wajenmu ne can gida nace masa bama nan,dazun na tura masa adress sun iso" gyara daurinta da tuni ya wareshi ta soma tana cewa "Ok,to muje mana" kai ya girgiza yana kallonta "A hakan zan fita?,bayan kin yamutsani,so kike hamza ya shekara yana addabata da tsokana kenan,jirani minti biyar na watsa ruwa" ya fada yana miqewa harda dan tsallenshi ta bishi da kallo har ya shige bandakin,murmuahi ta saki tana gyafa kai,wani irin mutum mai bala'in dadi zama tayi katari da shi cikin rayuwarta,sau tari idan yayi wani abun sai taga kaman ba almustapha ba,mayen soyayya ne na qarshe,yasan darajar auratayya da qimar matarshi.         Yana maqale da hannunta suka iso harabar  gidan inda hamza ke tsumayinshi,gurim abida sumayya ta isa fuskarta qunshe da murmushi tana yunqurin amsar baby,yayin da almustapha ya qarasa wajen hamza "Maan.....yaushe ka soma shiga cikin wannan duniyar taka?" Ya fada cikin sigar tsokana murya qasa qasa "Lokacin shigarta ne yayi" ya fada yana fidda qaramin murmushi,dariya hamza ya saki irin ta mugunta yana dan dukan saman hannun almustapha "Musty.....kace kawai kaima kayi dumu dumu cikin soyayya kaman yadda mukayi" "Na sabawa Allah?....ka fita a idona fa hamza" bai fasa dariyarshi ba,yana jin dadi yaga ya kwashi almustapha "Ina mutane na suzo suga yadda ake bugata" "Dallah malami idan zaka shigo muje,idan ba zaka shiga ba ka sauka lafiya" ya fada yana yin gaba,wanda su abida tuni sun shige,binsa yayi yana ci gaba da dibarsa,shikam murmushi yake a boye,babu wanda ke kwasarsa son rai koda cikin abokanshi irin hamza,ya zaiyi da shi?,abotarsu haduwar jini ce daga Allah ne.        "Kai matar maan...gaskiya gidan nan naku ya tafi da ni,anya ba nan zamu zo ku bamu daki ba?" Abida ke tsokanar sumayya sanda take jere mata abun motsa baki,dariya sumayya ta saki "Kunfi qarfin daki,saidai a baku sashe" dariya itama abidan tayi "Na tabbata waccar batasan da gidan nan ba....inda ta san da shi wallahi nan zata dawo da zama,ki godewa Allah sumayya,kin shiga rayuwar maan fiye da zatonki,kallo daya mutum zai masa yasan yana cikin zazzafar soyayyarki,baki ga yadda yake ta kaffa kaffa dake ba da ido kawai bare aikinshi,ba shakka soyayyarku ta dabance,saiki yi qoqari kici gaba da riqe kambunki wajensa" murmushi ta kuma saki bayan ta zauna gefan abida ta sake amsar baby suhail "Gaskiya ne,ni kaina wani lokaci ina mamaki,ni a tunani na banda komai da za'a min irin wannan soyayyar" murmushi abida tayi tana zuba lemo a cup "Ke kike ganin haka malamarsu,duk wanda ya san kanshi kallo daya zai miki yasan kin cancanci haka,wanda ba lallai ke kisan da hakan ba" hirarsu suke irin ta mata wadda ba'a rabasu da ita idan sun hadu har tsahon wani lokaci kafin mustapha ya turo qofar "Jeki kiji da mijinkin can kafin na fito,kija masa kunne ya rage shiga hurumin da ba nashi ba" murmushi kawai abida tayi ta  miqe ta fice tare da bar musu suhail dake hannun sumayya,qarasawa yayi inda take zaune,ya hadasu baki daya ya rungume yana lumshe ido "Ya Allah ka nuna min nima,kina kyau da yaro babe" murmushi ta saki,ya janye jikinshi baya kadan ya karbi suhail ha kwantar "Tashi ki gyara,tare zamu fita baki daya zasu gaida ummi suma" kusan shi ya shiryata cikin lafaya saman atamfar dake jikinta,sannan yace "Muje ko?" Ya fada yana saba yaron a kafadarshi "To ka bani shi" cikin shagwaba,ido ya zaro sannan ya kada kai "A'ah.....muje,dazun ma bakisan kaman a zuciyata ba sanda kika daukeshi" tare suka taka yana mata magana wanda ta sata ta dinga sakin murmushi.        A motar hamzan suka isa gida,baki daya suka rankaya sashen ummi,sun taddata cikin falonta sanye da hijabi,qaramin qur'ani ne a hannunta,yayin da gefe daya t.v ke kunne saudi qur'an ke aiki cikin volume can qasa,daga qasa kuma sajida ce zaune take gyara sarqar duwatsu da baba uwani ta bata,ajjiye qur'anin tayi cikin farinciki take amsa musu,yayin da sajida ta miqe itama cikin farinciki ta nufi sumayya "Anty...nayi missing dinki,Allah yasa kin dawo kenan" almustapha ne ya dan harareta "Dama 'yar gidanku ce?" Ya tambayi sajidan,sai ta girgoza kai tana dariya tare da rufe bakinta "To oya samu waje ki zauna tun baki bigeta ba" ya qarashe maganarshi ko ajikinsa,bai damu da hamza dake ta masa signa na ummi na dubanshi ba "Zoki zauna tun bai bigeki shi din ba" ta fada cikin yanayin abun dariya,dariya suka saka baki daya yayin da kunya ta kama sumayya tayi qas da kai,shi dinma yaji kunyar sai ya hau shafa kanshi yana basarwa.      Tarba ummi ta musu sosai,ta sake abinta cikinsu sunata hirarsu,basu suka fita ba sai da aka kira magariba,suka wuce masallaci suka barsu nan ita da abida,bayan sun dawo suka dunguma baki daya suka nufi sashen baba,sanda ya gansu shima farinciki ya cikashi,sannu kawai yakewa sumayya,shi kadai yasan farincikin da yake ciki,nan ma hirarsu suka dinga yi da baban "Almustapha....wai bakaji me ya samu 'yar uwarka aisha ba?" Baba ya tambayeshi "Naji ummi ta gayan" "Ta gaya maka ka sanya hannu wajen nemanta ko Allah zaisa a dace?" Kai ya kada "Ta gayan,zan qoqarta" kallo daya hamza ya masa yasan cewa akwai qulalliya,yana iya gane yanayin almustaphan ta farat daya,suka hada ido da hamza sai mustaphan yasha mur,da ido hamzan ya tambayeshi ya akai,sai ya share kawai,a nan suka ci abincin dare tare da baban,su kuma suka koma wajen ummi anty maamaa bata nan tayi tafiya bare suje wajenta,ganin har sun gama basu fito ba yasa sumayya jan abida suka shiga wajen anty dije,nan gidan ya rude,duk yaran na nan,duka minti ashirin suka mata sumayya tace zata dawo idan sun dawo gida suka fito,ran anty dije fes,ba shakka tafi kowa murna da wannan aure.       Suna fitowa daga bangaren baban hamza ya dubeshi "Maan....nasan halinka baka da kirki idan baka ga dama ba,me yarinyar mutane tayi maka ka batar musu da ita?" "Dakeni ubana sai in gaya maka" kai ya girgiza "Seriouse almustapha...ka kama musu yarinya kuma kana wani cewa Allah ya bayyanata don iya shege?" Kanshi ya shafa,har yay yana jin haushin abun,haushin yarinyar yaje ji ainun,yanajin dama yana wajen tayi yunqurin turo sumayyan ba shakka ita zai wurgo "Abinda tamin mutum biyu ne a duniya zasuyi shi na qyalesu,babe taso hankadowa daga bene bata ko lura da abinda ke jikinta ba" kai hamza ke kadawa,eh lallai almustapha zaiyi fiye da haka ma akan wannan "Bata kyauta ba sam.....amma kayi haquri ka fito da ita ko don iyayenta" kai shima ya kada "Na riga da na rantse sai tayi sati,saboda haka kada ma ka bata yawun bakinka,sai jibi zata fito" ya sani kaifi daya ne shi,tunda ya fada din bazai canza ba,tilas ya haqura ya qyaleshi.   ******    *******  ********      Da yammacin ranar ya isa policestation din,kaman waccan karon a office din DPO suka zauna,ta rame zuwa lokacin tayi baqi kaman ba ita ba,ba abinda jikinta yake sai buga tsami,baki daya taji ta muzanta gaban almustaphan,kallon da yake mata kadai ya sata jin nadama,ga kunyar yanayin da take ciki,bata san cewa haka zai faru ba da ko kallon banza bata yi mata ba "Ya akai 'yammata?,kin tuna kece kika yi aikin ko har yau sharrin ne dai aka miki?" Kai ta kada hawaye na zubo mata,don bata fata ace ta sake komawa dakin nan koda na sakan daya ne "Nice wallahi...." Fuska ya sake dinkewa "To me tayi miki?" "Wallahi sharrin zuciya ne da sharrin shaidan" "Qarya kike.....saboda kina sona shine zaki kashemin mata?,na miki kama da sa'an aurenki?" Sai tayi shiru magana ta mata nauyi "Nace na miki kama da wanda zai kwasheki?" Ya sake tambayarta a tsawace har yana buga teburin wajen,tsoro ya kamata da sauri ta hau girgiza kai "A'ah....kayi haquri" "Kinsan me?" Kai ta kuma girgizawa "Yadda qasa ta haramta wajen jemage ya takata saidai qarar kwana,to haka aurenki ya haramta awajena....sumayya da kike gani...tabata dai dai yake da tashin hankalin rayuwarki" "Kayi haquri don Allah ya almustapha" yatsanshi ya dora saman lebansa sannan yace "Ai baki horu ba,zaki koma ne baban naki da kike taqama da shi har kike zagin na sama dake kike tutiyar zaki hanasu cin abincinsu ki ciresu daga bakin aikinsu ya nemoki yayi kuma belinki" ya fada yana miqewa alamun tafiya zaiyi,tuni ta saki kuka ta sauko qasa tana roqarshi tana bashi haquri,sai da ya gama shan qamshinsa sannan ya waiwayo,ya nuna mata kujerarta yace ta koma kai,tuni ta miqe ta koma "Zaki tafu gida yau bisa wasu sharadai,sharadi na farko....sumayya....kada ki yarda ko kallon banza ya hadaku bare kiyi yunqurin taba jikinta,saboda indai ina raye ta gama shan wuyar mata irinku.....sharadi na biyu wallahi kiki dora da halinki na wulaqanta jama'a zaki dawo cell,ba kuma wannan cell din ba,inda sai kinyi sati bakiga hasken rana ba,and last...ruwanki ne kice ni na kamaki na kulle...ruwanki ne kiyi shiru duk daya" yana kaiwa nan ya miqe,cikin zumudi tace "Na gode...baxan sake ba in sha Allahu" "Damuwarki" ya fada yana ciro kudi a aljihunsa ya jefa mata ya fice,a can ya basu umarnin su bata jakarta da sauran kayanta,ya riga ya bata kudin mota,ya sallamesu suna masa godiya ya wuce.         Kwanansu goma yace ta shirya wannan karon ba inda zashi sai da ita,da kanshi ya murje idanunshi ya tunkari baabaa kai tsaye da maganar,murmushi kawai baban yake yana kallon yadda mustapha ya zama mara kunya yanzu,duk da hakan ya masa dadi,alamune dake nuna zama na dadi tsakaninsu,sai yayi niyyar tsokanarsa,saboda haka ya hade fuska "Sannu mara ta ido,umminnaka kenan kana nufin batayi dai dai ko bata iya riqo ba ko?,to ka tafi akwai sauran wasu watannin nan gaba ta biyoka tunda ba riqe ta zamuyi ba ai" anty maamaa dake boye dariya tace "Haba prof,ka barshi mana ya dauki matarsa,ina cewa nan ganin gida naje kwana uku amma ka matsanta sai na dawo" "Ba ruwanki bilkisu" baban ya dakatar da ita,cikin damuwa ya daga kai ya dubi baban,ji yake kaman ya rusa ihu,murya a shaqe yace "Idan na tafi ba lallai na dawi nan kusa ba" "Kada ma ka dawo sai ta haihu" wayyo kadan ya rage ya rusa ihu,sai kawai ya ware baki daya ya fito masa amutum "Don Allah baba kayi haquri idan laifi nayi ka bani matata,wallahi zan......" "Allah ya tsare hanya sai kun dawo" ya fada dariyar daya qunshe tana fitowa,kunya ta kama almustapha,lallai yaro yarone komai shekarunshi kuwa wajen babba,sai ya fara shafa kai ya miqe zumbur yana musu sallama,suka amsa suna rakashi da dariya.         Shima da yaje sai daya wana sumayyan yadda akayi masa,yace nan zata ci gaba da zama shi zai koma,ta amsa amma baki daya kamar wadda aka zarewa laka,sai da suka gama shirin kwanciya sannan ya cafkota yana mata dariya "Iyeeee,ashe yarinyar ta sab ciwon miji ko?" Dariya ta kubce mata tana kai masa dukan wasa tare da fadin sai ta rama.   ******    ******    ********        Sama sama cikin barcinta ta dinga jiyo tamkar muryarsu shi da su'ad,tunda suka iso qasar ta lura akwai abinda ke faruwa tsakaninsu,saidai ta dauke kanta tunda bai shafeta ba kuma basu sanyata ciki ba.         Randa su'ad ta iso da baturiyar kukunta ranar daga sumayyan har su'ad ding sunga tashin hankali da ainihin almustaphan,su'ad na daga kai suka iso gidan tare da ita,ta kuma bata umarnin shiga kitchen ta dafa musu ita da almustapha nau'in abinci kala kala tunda girkinta ne,da yake sun riga su'ad din isowa da kwana biyu,hakan ya sanya sumayyan bata bi ta kanta ba ta miqa mata kwananta.        Tunda aka jere abincin ya dinga binsu da kallo daya bayan daya,kallo daya ya musu yaji baki daya basuyi mishi ba,zuciyarshi ma sam ta kasa aminta cewa order tayi musu "Wadan nan abincin fa daga ina?" Ya tambayeta yaba dubanta,murmushi tayi tana zaton ta burgeshi ne "Kuku na taho mana da ita ta musamman,kuma mommy ce zata dinga biyanta" wani abu ne ya tsaya masa a wuya,baturiyar mai dafa abinci cikin gidanshi wadda baisan da zamanta ba?,babban abinda ya fara baqanta masa rai wai mommy ce zata biyata albashi,me suke nufi kenan?,ya gaza shi din,wani abu mai daci ya tsaya masa awuya,mutum ne shi da baisan raini,irin mazan nan ne da basa buqatar tsinke ki taimaka masa da shi cikin gidansa,Allah ya hore masa yafi qarfin duka buqatunshi,bai marmarin ko daga waje ayi ma iyalansa kyautar abin amfanin gida,yafiso komai suyi amfani da abinda ya fito daga aljihunsa,kallo yaci gaba da binta da shi wanda take jikinta yayi sanyi,ta rasa wanne irin kallo ne "Ce miki akayi na gaza daukar nauyin kuku?,ke zaki bada labarin cewa babu irin kukun da bazan iya ajjiyewa cikin gidana ba ko daga ina yake daga fadin duniya,sai dai me?,banda ra'ayi,ke din ke nakeso ki shiga kitchen da kanki a matsayinki na matar aure ki dafa min" sai a sannan ta gane har yanzu yana kan bakansa,tun a can mummyn ta riga ta zigota kan kada ga yarda ya tauyeta tunda ba shi zai biyata ba,hakan ya sanya ta fara fadin maganganu,ransa ya baci ainun,ya sanya mata ido kawai,da yaga bata da niyyar saurarawa ya daka mata tsawa,wadda ta kada hantar sumayya dake cikin nata falon tana kallon film tare da shan fruit,tsoro ya kamata ra ture plate din gefe tana kiran sunayen Allah "Na baki nan da minti goma ki tattarata ta bar gidan nan" "Ba inda zata almustapha wallahi" ta bashi amsa daidai sanda kodaddiyar baturiyar ta fito,sanye da mini skert  wanda idan tayi kyakkyawan tsuguno ba abinda zai hanaka ganin mazaunanta da t shirt mai gajeran hannu,wani baqinciki ya sake shaqeshi ya dakawa baturiyar tsawa cikin yaren da zatafu fahinta yake sanar mata ta wuce ta tattara duk abinda tazo da shi ta fice masa daga gida,tuni ta soma rarraba ido don bata taba zatar haka ba,idan ta fita din ma ina zata?,sai su'ad din ta rushe da kuka iya qarfinta ko hakan zaisa almustapha ya sauya qudurinsa,ihun kukan su'ad din shi ya daga hankalin sumayya,ta tsammaci ba lafiya,sabida haka ta yafa mayafi saman doguwar rigar dake jikinta ta fito zuwa babban falo,dai dai sanda mujadala ta harqe tsakaninsu,tuni yace ta hada kayanta itama ta bita,wanda hakan ya sage nata gwiwa,maimakon hana mai girki tafiya sai ta koma qoqarin yadda ita din zata zauna,kallo daya zaka yi masa kaga zallar bacin rai shimfide a fuskarsa,ita kanta sumayyan sai da tsoro ya kamata ganin yadda ya birkice,da addu'a a bakinta ta nufi inda yake zaune saman dining yana fuskantarsu,gefanshi ta tsaya cikin kwantar da murya "Haba yallabai,haba.....bai kamata ba,ba fa cikin qasarmu muke ba,yanzu ta yaya don kawai ta maka laifi zaka ce tabi baquwar fuska subar gidanka?,kasan kuma yanzun qarfe nawa,a karamcinka ko mai aikin bai kamata kace ta fita ba,koba komai macace mai rauni,balle kuma matarka ta sunna....kayi haquri don Allah ka sawa zuciyarka ruwan sanyi,yanzu kaga baki daya fushinka ya hautsina gidan ummm,ina kake so musaka ranmu?" Shiru yayi yana sauke numfashi sannan ta juya ga su'ad "Anty....tunda baiso kiyi qoqari gobe ki saya mata ticket ta koma a zauna lafiya don Allah" harara ta wurgawa sumayyan amma bata ce komai ba,saboda ko banza taji dadin ganin almustaphan yayi shiru,miqewa yayi ya dauki muqullin motarshu dake ajjiye kan freezer ya fice,dukkansu suka bishi da kallo,sai da ya gama fita kowacce ta dauke idonta,suka hada ido sumayya da su'ad,sumayyan tace "Don Allah anty kiyi qoqari ki karanceshi ku daina musayar yawu haka da shi,gaban baquwa fa ba don Allah yasa bata jin yaren ba,haramunne mace ta dinga daga murya sama data mijinta,miji sama yake da kai dole ka saukar da kanka qasa ka bishi,tana janyowa kanta tsinuwar mala'ikun Allah" ta fada a tausashe "Ke da Allah sauraramin,a naku tsarin ba,ba wanda yafi wani tsakanin mata da miji kowa mai 'yancin yin yadda yaga dama ne,wai wa ya saka da ke ma?" Kada kai tayi babu alamun jin haushu a fuskarta "Allah ya baki haquri idan kinji haushi"ta juya a nutse ta shige falonta ta zauna taci gaba da binda take,saidai lokaci lokaci hankalinta na kan agogo,har ta soma gajiya da zaman ta buqaci kwanciya bata ji motsin shigowar almustaphan ba,har dare ya soma shiga sha daya da kusan rabi,duk da su a can daren ba komai bane wajensu,hakan ya daga hankalinta,ta dauki wayarta ta dinga qoqarin nemansa saidai sam bata samunshi,sai data gwada a qalla wajen sau biyar ana shida ta dace ya shiga,a jiyar zuciya ta sauke "haba yallabai,ka tashi hankalinmu fa" shima ajiuar zuciya ya sauke,muryarta ta soma rage masa bacin ranshi "Me ya faru?" "Ka fita cikin iyalanka cikin fushi,sannan kuma har war haka ace baka dawo ba ai dole hankalinmu ya tashi ko?" "Lafiya nake,kawai yau bazan kwama gidan bane,sai gobe idan Allah ya kaimu,ki kwanta kiyi bacci sosai,good night" ya katse wayar yana jin dadin yadda ra kula da shi har ta nemeshi,ya tabbatar idan su'ad ce kota nemeshi qorafi ne abu na farko da zata fara ba tare da kwantar da murya ba,ranan haka ya kwana sai da safe sannan ya dawo cikin gidan,to sai gashi yanzu tana tsaka da bacci ta soma jiyo muryansu,wanda hakan ya sanyata farkawa ba shiri,uwa uba da kuma yunwa data fara tambayarta,har ta shiga toilet rayi brush ta fito tana jiyosu,ga yunwa tana sadakarta,bata so ta fita ta taddasu haka,amma dole ta sanya hijabinta ta fice sanoda yadda cikinta ya soma motsawa saboda yunwa. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 1⃣0⃣2⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *ya zul jabarutu wal malakutu wal kibriya'i wal'azmati* _____________________________________        Tunda ta fito ta fuskanci maganar dai kusan kan shiga kitchen ne,ita kanta ta gaji da wannan jeka ka dawo magana daya tak mai sauqi amma ta rasa dalilin su'ad na qin yarda da maganar tashi,har zata rabe ta wuce sai kuma ta fasa sakamakon tuna fadar Allah da tayi "Haqiqa muminai 'yan uwa ne kuyi sulhu tsakanin 'yan uwanku", a nutse ta qarasa wajen da suke tsaye,ta sanya hannunta ta riqe hannun almustapha ta gefe ta yadda su'ad din na zata gani ba ta soma matsawa a hankali idanunta cikin nashi,cikin 'yan kwanakin nan su'ad tasa ta ga halinshi da bata taba gani ba,ta fuskanci yana da fushi saidai yakan jima ba'a ga fushinsa ba,barshi dai da miskilanci wannan tambarinshi ne,sai data fuskanci hankalinshi ya soma dawowa gareta yayin da su'ad rayi carko atsaye tana jiran kota kwana "maan" karon farko ta kirashi da sunan da mutane ke yawan kiranshi,saidai yaji sunan ya zama wani sabi na musamman daga bakinta,a tausashe hadi da karyar da wuya tace "Bai kamata ba....." Dakatar da ita yayi da hanzari ra hanyar daga mata hannu sannan ya waiwaya ya dubi su'ad "Option ne na baki,na kuna rantse yau ko zaki kwanta asibiti sai kin dafa tea din nan,naga wanda zaya sake min order din abinci cikin gida na" yana fadin haka ya zame hannunshi daga nata ya wuce zuwa sashensa,da kallo suka bishi,yayin da gaban su'ad ke faduwa,ta tabbatar da cewa yau din matuqar bata yi abinda yace ba babu abinda bazqi iya faruwa ba,saidai ta yaya zata ta ina zata soma tunkarar kitchen?,sai kawai ta wuce fuuu kaman guguwa ta shige kitchen dinta,sam abun baiwa sumayya dadi ba,hakan ya sanya batayi qasa a gwiwa ba ta bishi zuwa dakinsa.       Yana tsaye gaban window,hannayenshi zube cikin aljihun wandonshi,qoqari yake yayi controlling kansa tare da hana zuciyarsa aikata abinda take raya masa,so yake yaga ta ina ya gazawa su'ad,ci?,sha?,sutura?,kudin kashewa?,walwala ko adalci,duka babu,babu ko daya daga ciki,hasalima ta wani bangaren tafi sumayyan samun wasu abubuwa,tunda suka fara tarayya da sumayya bazai iya tuna rana qwaya daya tak da ta tambayeshi wani abu ba,saidai shi don gashin kansa ya bata,ko idan su'ad din ta tambaya yayi adalci itama ya bata duk da bata tambaya ba,abinda ya lura ma shine tara su take,ba abinda take da su,shi kansa yasan babu wani anu qwaya daya da na kusa da shi bama iyalinshi ba da zasuyi kukan basu da shi ko yafi qarfinsu,shi a ganinsa babban abun kunya ne ma ace kai din wani je,ko Allah ya maka rufin asiri,ana maka kallon mai rufim asiri,a ganka cikin kama kai kyau amma iyalinka a wahale ko cikin mummunar kama,wannan shine babban abin kunyar da magidanci zai aikata wanda zai jawo masa tur da ala wadai a bakunan al'umma.        "Abu abdallah" ta furta a nutse,tunda yaji sunan yasan itace,amma hakan bai sanyashi ya waiwayo ba,sai ya nutsu yana jin yadda take takowa zuwa inda yake tsaye,bata dakata ba sai data sha gabanshi,ta tsaya tana dubanshi idanunta cikin nashi kaman yadda nashi yake,duk da cewa a cikin hijabi take,duk da cewa daga bacci ta tashi batai wanka ba,duk da cewa ba ko digon kwalli cikin idanunta amma bata fasa yin kyau ba cikin idanunshi,kyanta cikarta da kamalarta sun fito muraran,ta jima tana kallonshi wanda sannu a hankali dumin da zuciyarsa tayi ya soma sauka,da wannan damar tayi amfani ta soma cewa "Ina ganin bata haka ya kamata ka bullowa anty ba....bazaiyiwu dare daya kace sai ta maka girki ba bayan can bata saba ba,a mata haquri a bata dama ta koya tukunna...." "Wacce damar?,wacce dama za'a bata ne sumayya?" Ya furta cikin sanyi,saidai daga yanayin yadda yake maganar kawai kasan ranshi akwai sauran damuwa a ciki "Akwai damar data wuce na sai mata rana guda cikin ranakun makaranta catering school?,ta koya ita kadai?,cikin gida ko a can duk wanda take so?......daga yau bana son ki sake sanya baki cikin wannan matsalar...ki barmu" ya fada cikin salon dakatarwa,yawu ta hadiye kafin ta sake lanqwasa murya "Kayi haquri idan hakan ya bata maka,banyi ba da niyyar shishshige...rayuwarka rayuwata ce,haka nan rayuwarka rayuwar su'ad ce,hakan na nuni da cewa dukkaninmu abu guda ne...kwanciyar hankali nutsuwa da zaman lafiyar dayanmu yana da amfani a garemu baki daya,bazanso ace kullum kai da ita ba kwanciyar hankali ba....hakan zai iya shafata zai iya shafar iyalin da muke son samarwa nan gaba,tunda dai muna tare da ku"idanu ya zuba mata yana karantar tsantsar gaskiyar dake cikin zuciyarta da takeson fadi,hankali nutsuwa da karamci ne zallah cikin kalamanta,don me yasa ta samu dama irin wannan maimakon tayi qoqarin tarwatsa zamansu da su'ad ta mallakeshi ita daya saima take qoqarin gyarawa?,kyakkyawar zuciya ce itace amsa,wadda ba kowanne bawa Allah yake wa baiwarta ba,sai 'yan baiwa daga cikin bayin nasa,maimakon ya bata amsa kawai sai ji tayi ya janyota cikin jikinsa ya juyata da hanzari ya rungumeta ta baya yana shinshinarta,duk da cewa batayi wanka ba amma hakan bai hana wannan qamshin nata mai sanyi fita daga jikinta ba,dumin fatarta ya dinga ratsawa cikin tashi,hannunshi ya dora saman cikinta yana yawo da shi,wani farinciki na maye gurbin bacin ranshi,duk sanda ya farka da shi yaje farkawa cikin ranshi,kullum yana lissafe da ranar da zaya iso cikin duniya "Wannan ne abu mafi muhimmanci da ya kamata ace kinyi zaki tsaya kina wani tsarani" dariya ce ta kubce mata ta soma qoqarin boyeta "Au tsara ka ma nake yaya?" "Waye yayan naki,yau kuma yaya na zama?" Girarta ta dage sanda yake leqo fuskarta "Eh....ko nayi laifi?" "A'ah....bakiyi ba" ya fada yana cikata tare da durqusawa gabanta,tasan me zayayi tunda ya fara kware mata hijabi,ba dama su tsaya inuwa daya sai ya fara lalubar cikinta,baya ta ja tana ware ido tare da kada masa yatsa alamar a'ah,sosai idanun nata suka fito sun sake wani fari tas da su,hakan yaso shagaltar da shi "Sulhu nazo nema ba gaidaka muka zo yi ba" sai ya miqe daga durquson da yayi yana ci gaba da kallonta tare da nuna kanshi da yatsa "Ni kuka yiwa haka?,zamu hadu,awa ashirin cif suka rage" dariya ta saki ganin yadda yake kwatantawa da hannunshi,ta juya taba niyyar ficewa,duk da yadda tayi kewar lafiyayyar fatarsa amma hakan bazaisa ta bashi dama suyi wani anu sq zai sosa ran su'a din ba,abinda ko ita aka yiwa ba zata taba jin dadi ba "Amma kaman zazzabi naji jikinki ko?" Waiwayowa tayi tana dubanshi "Ina jin hakan idan na tashi da safe,amma da nayi wanka shikenan bana sake ji" "Ko nazo na dubaki?" Ta gane sarai wayo yake son yi mata sai ta saki qaramar dariya sannan ta juya ta fice tana cewa "Mun yafe".        Kacaniya sosai ke tashi a kitchen din kamar wadda zata dafa abincin baqi dari,ta rasa inda zata tsomala kanta,gefanta sumayyan ta nufa da niyyar dafa ko couse couse ne sharp sharp tunda tana da miyar hanta a fridge,har ta dauko tukunya taji su'ad ta fasa ihu,da sauri ta waiwayo kana ta nufeta,tukunya ta soma dorawa bayan ta kunna gas din,sai da tukunyar ta dauki zafi sannan ta taro ruwa ta soma zubawa,tururin da taga ya taso ya nufo hannunta shi ya sata sakin qara ta yarda cup din ruwan nan ua tarwatse a wajen har ya kashe wutar gas din gas ya soma fita,da hanzari sumayya ta qarasa tana ambatar subhanallah ta kashe gas din,sannan ta dubi su'ad data janye gefe "Amma dai bakiji ciwo ba?" Harara ta watsa mata,dukkan komai itace ummul aba'isin data tsiri yi masa girki da ya sashi cewa itama sai tayi,da can ai basu san dora tukunya gidan ba idan ba kuku ne yake nan ba,ganin bata amsa mata ba ya sanyata nufar wajen ta sauke tukunyar daga saman gas din ta zubda ruwan ta zuba sabo sannan ta sake kunnawa ta dora,inda suke ajiyan kayan tea ta nufa ta hada ganyayyaki masu dandanon da tasan almustapha naso ta dinga gwadawa tana zubawa ta gama ta sanya ganyan shayin ahmad tea ciki sannan ta maida murfi ta rufe,su'ad na gefe haka kawai taji kishi ya rufeta yadda taga sumayyan nayi,itakam bata lura ba tace da ita ne kawai "Idan ya dahu zakiji yana qamshi sai ki juye a flask" tsaki ta bita da shi "Nima na iya ai basai an nunan iyawa ba" bata bi ta kanta ba tayi ne dama kawai saboda mijinsu,tunda ta sani tunda ya kafe tofa sai tayi kuma sai ya dandana ko baici ba,idan bai masa ba dandanon baci zaiyi ba haka zaya fita da yunwar cikinsa.        Tana tsaka da bare plaitain ta soma jiyo qamshin dahuwar shayin,cikin flask din tea na alfarma dake kitchen din su'ad ta zabi daya ta fiddoshi ta bude ta ajjiye cikin sink,tukunyar ta tsurawa ido,yadda take tururi kawai ya sanya ta tsorata,ta yaya ake juyewa kawai take tunani,haka tayi qundunbala ta janyo towel hand socks dake maqale a hanger da suke ajiye towels na kitchen ta zura a hannunta,murfin ta fara budewa tayi wancakali da shi nan ma tayi gefe tana haki,ta dauki a qalla minti biyar ta rasa ya zata sauke,murmushin mamaki ya qwacewa sumayya,ashe da gaske akwai irinsu su'ad a duniya?,wannan mece a cikin mata,sai kawai ta miqe ta isa bakin tukunyar ta ciri safa daya ta sauke tea din tana juyeshi a flsk din,tana tsaka da juyewa ta matso kuda da ita "Waike wa ya sakaki,ce miki akayi bazab iya ba?" Sai data gama juyewa ta daga kai ta kalleta "Na san zaki iya ai,kawai taimako ne kuma ba laifi hakan ko a musulunci" shiru tayi tana daure fuska tare dq zare idanu har ta gama ta kulle flask din bayan ta daurayeshi ta wuce gurin nata sabgar.       Kusan dai har ta gama bata san me su'ad ke ciki ba,tana gamawa ta juye plaitain dinta ta dumama liver souce dinta ta fice ta bata kitchen din.        Tun daga lokacin matuqar tana kitchen din zata mata iya gyaran da ya dace,bata damu da duk abinda zata fada ba,tana yine kawai saboda almustaphan,tun tana masifa har ta dawo saidai harara,sau tari dariya take baiwa sumayyan,saboda ta lura da cewa tsabar girman kai ne kawai ke dawainiya da su'ad din,wani lokaci qunshe dariyarta take kawai idan tana girki,abin sai wanda ya gani,taka hau yanar gizo ne ta dubo yadda ake yi,wani abun bai ciyuwa hatta gurin wanda ya takura din sai ta dinga yi,idan har ya ciyu to ranan sumayya na kusa ta sanya hannu,cikin qanqanin lokaci su'ad din ta fara gane shayi ruwa ne,tayi roqon tayi magiyar ya samo mata mai aiki yayi funfurus da ita,har kukan takaici da wuya duka sai da tayi ,ya share tamakar baisan tana yi ba,don wannan ce kadai hanyar da zai hora ta kan iskancin da take ji saman kanta,har sumayya a wani dare take roqarshi ua samo matan wadda zata kama mata,saboda tana ganin yadda ake gwagwagwa wajen dafa shayi ma kawai,har yau ta kasa dauke yadda ake,ita dinma shiru ya nata kaman baiji me tace ba,ganin hakan ya sanya taja bakinta ta tsuke,tasan tunda yayi hakan baison zancen ne,sai da ya tabbatar ta dahu sannan ya samo wadda zata dinga taimaka mata,da sharadin tare zasu dinga yi tana ganin yadda akeyi.       Abu na gaba daya soma jan hankalinta shine yadda ta fuskanci maan din na nuna tsantsar kulawa da riritawa ga cikin dake jikin sumayyan,da fari ta dauki abun duka wasa,sannu sannu ta soma fahimtar soyayyar da bata taba gani yana yiwa wani abu ba ita yake gwadawa abinda ke cikin dako duniya bai iso ba,bata tabbatar da haka ba sai a wani yammaci wanda ranar sumayya zata karbi girki.        Tun da yamma tana zaune babban falonsu,bata faye zama cikinsa ba sai jifa jifa amma yau ta kasa ta tsare,sam sumayyan bata damu da zamanta ba,sabgoginta take hankali kwance,zuwa qarfe biyar ta gama shirya masa dining tsaf da kalar abincin da yace yana so,bayan itama ta hada wanda ranta ke so,shinkafa ta dafa ta zuba wake a kai ta bare kifin gwangwani a kai,sannan ta soya manja ta yanka salad tumatir albasa da cocumber,tana da yajinta tun daga gida wanda kusan shi ya tada mata kwadayin cin fara da man ma,salad dinne kawai bata gyara ba don haka ta barshi ta shiga wanka,ta shirya tsaf cikin wani wando ya lafe a jikinta kamar a jikin nata aka dinka shi,da kadan ya zarta gwiwa,wandon baqi ne hakan ya sanya ta saka shirt fara,ta gyara gashinta ta daureshi da baqin ribbom ya sauka har saman kafadunta,fashion tayi amfani da su baqaqe masu adon farin stone ajiki,lite make up ce a fuskarta wadda tasan tafi burge almustaphan,feshe jikinta tayi da turare sannan ta laluba cikin kayanta ta zaro abaya,har ta zura sai kuma ta cire,sam yau sai taji bata sha'awar saka ta,bata bari su'ad ra ganta cikin irin wannan shigar,yawanci tafi zama haka sanda suke falonshi ko nata falon su biyu,wasu slippers masu kyau baqaqe da suka bayyana kyan farar qafarta ta zura sannan ta tako a hankali ta fito.       Qarar bude qofar falon nata da rufewa ita ta soma jan hankalin su'ad din,idanu ta zuba mata baki daya,sannu a hankali wani kishi ya soma sokarta na ganin yadda sumayyan tayi kyau kamar 'yar tsana,kai kace drowing ne na girly,cikin da take tsammani zai batata sai gashi ya zame wani ado a jikinta,ya shiga wata na biyar ya zauna daras a jikinta abin sha'awa,ko daya bai tafi  da hips da boobs da take da su ba saima qara fito da su da yayi,karon farko data soma ganinta cikin yanayin shigar,a hankali ta janye idanunta daga kanta kishi na nuqurqusarta,da ciki ma kenan ina ga tana ita kadai?,ta yiwa kanta wannan tambayar,da qyar ta iya hadiye yawu ta maida idanunta kan t.v taci gaba da kallo ba don tana fahimta ba,itakam dukkan abin nan da take batasan tana yi ba,kanta tsaye ta shige kitchen tana daga tsaye ta soma gyaran salad dinta.         Tunda ya shigo baki daya tayi gaba da dukkanin imaninsa,ruwa ya shigo sha amma baki daya ya nemi qishirwar ya rasa,sai kawai ya harde hannunshi a qirji ya jingina da qofa yana kallonta,baiso ma tasan ya shigo bare ya ta daina kaikawonta,ilahirin jikinta yake bi da kallo,wani sanyi da farinciki na saukar masa,godiya yakewa Allah cikin zuciyarsa,ba shakka duk yadda yaso ga son dai daita matsayinta cikin zuciyarshi da sauran mata yasan yayiwa kanshi qarya,abune ba mai yiwuwa ba,koda ciwon makanta da ciwon bacewar tunani zai kamashi yana da tabbacin zai iya gane randa yake ranar girkinta,tun daga harabar gidan da yake iya ajje motarsa kama da duk wani lungu da saqo na gidan sauyawa yake,ba'a magana qamshi tsafta da sauransu,sai yake jin kamar harda iskar gidan ma sauyata ake,babu mamaki ko don tsananin soyayyarta da kullum kwanan duniya ake linka masa ne?.         Sai data gama yankawa ta isa gaban famfo ta tara shi cikin ruwa,da hanzari taji an jawota,ko da daga bacci ta tashi tasan waye,mannata yayi da jikinsa ya zagaye hannayensa saman cikinta,sannan ya dora kanshi kan kafadarta "Barka da dawowa....barka da dawowa sanyin idaniya hasken cikin gidansa....tun dazu naji yanayin gidan ya sauya ashe yariman maza ne ya iso" baisan sanda ta juyi da ita suna fuskantar juna ba,idanunta cikin nashi tana masa wani irin kallo,shi dinma kallon yake jifarta da shi,ya gaza cewa komai,ko yaushe furucinta na musamman ne a gurinsa,duk abinda zata furta ya isa kunnenshi mai dadi ne,mai laushi ne,mai taushi ne mau faranta zuciya tare da zare mata gajiya da baqinciki,kasa cewa komai yayi sai kallon kallo tsakaninsu tare da jifan juna da murmushi,bakinsu kawai ya hade waje daya yana aijata mata da wasu kisses masu zafin gaske,ganin yana neman wuce gona da iri a muhallin da bai dace ba ya sanyata tureshi suna maida numfashi,ya matsa din amma bai bar jikinta ba,dubanta yake da rikitattun idanunshi da suka sauya lokaci daya,cike da shauqi yake dubantan nata "A kitchen muke fa" ta fada a shagwabe,hancinta ya kama ya dan jaa "To waye ya jawo?,irin wannan shigar ko gaban wa na ganki hakan na iya faruwa" ya fada da qyar cikin muryarshi dara fara jirkicewa "Bamu gaisa da baby ba" murmushi ta saki "Wannan baby......wanne irin qauna ne haka my maan" kada kai kawai yayi yana murmushi,qugunta ya riqo baki daya da hannayenshi "Qauna?,indai wannan ce qauna to kam bakiga komai ba,babu abinda kika gani babe....banajin zan iya bayyana qaunar da nake mishi ko mata,daga cikin dalilan da ya sanya kenan ban damu da duba me zaki haifa min ba,ko me kika haifamin ina so ina maraba da shi,gudan jin muhammad almustapha ne da summyn malam" murmushi ta saki sosai saboda sunan da ya kirata da shi har fararen haqoranta na bayyana,dubanta yake shima yana murmushi wani farinciki na shigarshi,da kanta ta yaye masa t.shirt din dake jikinta zuwa saman cikinta,ya durqusa a hankali hannunshi saman cikin.      wani wawan tsaki mai shiga kunnuwa suka ji anja,su'ad ce wadda tun shigowarshi cikin kitchen din ta kasa samun nutsuwa,baki dayan hankalinta ya karkata kitchen ne,ta kasa zama har sai data biyo bayansu,kusan duk rabin maganar tasu cikin kunne da idanunta suja yisu,wanda sam basu san da shigowar tata ba banda yanzun,ko kusa ko alama bata taba sanin cewa haka almustaphan ke qaunar haihuwa ba,tayi tsammanin cewa ra'ayinsu daya a qidarsu daya,saboda ganin ko alama bai taba mata magana kan rashin samun juna biyunta ba,abinda bata sani ba shine yana sawa rashi lokaci ne,idan yayi zata haifa masa,bugu da qari yana tausayim macen da bata haihu ba,hakan ya sanya yake ganin girma da qimar ni'imah har gobe "Amma dai wannan abun bai dace ba ko?" Ta fada zuciyarta kamar zata fadi qasa,waiwayowa yayi yana dubanta "Shigowa kai tsaye ba tare da yin sallama bane bai dace ba ko ko meye?" Kasa cewa komai tayi don tasan ita ta kawo kanta,ta sani cewa duk ranan girkinta hatta da zurga zurga sumayyan bata fiya ba,data gama uzurorinta ta masa sallama shikenan sai da safe,mazewa ta sake yi kishi na cinta "Kitchen wajen kowa ne,na shigo daukar abu sai na fasa saboda ku?" "Yaushe kika fara labe?,kina tsammamin banga shigowarki ba?,kina tsaye tsohon minti goma?" Mamaki ya cikata,bata yi zaton ya ganta ba,da shigowa daukan abu tayi niyyar fakewa tayi boren qarya,da idanu ya tsatstsareta yana hukuntata da kallonshi,wanda ta san fassarar hakan sarai,duk sai ta daburce,numfasawa yayi ya dauke kanshi daga gareta fuskanshi daure ya maida ga sumayya data soma wanke salad dinta "Muje ki shiryan ruwa nayi wanka"amsa masa tayi da to,ta rufe salad dinta ta ajjiye gefe sannan ta ratsa ta fice,sai data fice daga kitchen din sannan ya maida kallonsa ga su'ad dake tsaye tana cije baki cikin takaici,a hankali ya tako zuwa gabanta,daf da ita ya tsaya tazarar dake tsakaninsu bata da yawa "Me yasa ko yaushe baki daukan gyara?,baki gyaran kuskurenki cikin sauqi?,Kada kiyi abinda zai siya miki raini,ki guji yin abinda bai dace ba,abinda duk kikasan ba'a yi miki ki nisanci yiwa wani,umarni na baki ba shawara ba" baya ya danja sannan ya juya shima ya fice,yafi kowa sanin halinta,tafi gane tsauri,daukar sauqi take tamkar wata isa ce tata tasa ake mata hakan.        Dukkanin maganganunsa ba damunta sukayi ba a yanzu,abu daya tak ke mata yawo cikin kwanya da qwaqwalwa,so qauna kulawa da tsantsar soyayya da ta gani zalla a qwayar idanunshi yana nunawa ga ciki dama wadda ke dauke da cikin,me yake shirin faruwa ne?,shine tambayar da take wa kanta,a hankali qwaqwalwarta ta soma mata tariyar wasu shekaru can baya da suka shude,shekarun da a cikinsu ta fidda mahaifarta,a sanda anty kubra ke zabga mata fada,a lokacin da take gaya mata tayi kuskure,take gaya mata zata iya dana sani a gaba,take shaida mata matakin kama almustapha a hannu da kyau shine ta ajjiye masa iri,ta hada jini da irin gidan baban,shine zata samu dukkan abinda take so,zata zama tasu ta har abada,jinta take kawai a sannan,gani take labarin qanzon kurege ne kawai,tunda bata ga wani damuwa ko alamu tattare da da almustaphan ba,saidai a yanzu jikinta ya soma sanyi,wutar kishi ta soma nuna mata akwai wani abu dake shirin faruwa,tattalin da take gani wajenshi a kanta ya zarce soyayyar da yake mata ita daya face harda ta abinda ke cikinta,indai ko haka ne itace mafi cancanta data samu wannan launin soyayya da qauna mai ratsa gangar jiki da zuciya,saidai zata sanya ido taga shin abinda take hasashen haka ne?. *gobe ina da uziri,idan kuka jini shiru saidai kuyi haquri,duk da zanso ace na muku,so nake mu kammala littafin nan kusa in sha Allah,na gode* *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 1⃣0⃣3⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *Allah S W T yana cewa* *kuyi guzuri,amma mafi alkhairin guziri shine TSORON ALLAH* ___________________________________         Cikin nutsuwa da kwanciyar hankali take renin cikinta,wanda bata taba sanin hakan kwanciyar hankali ke da dadi ba yayin rainon ciki sai yanzu,bata da wata matsala yanzu gaba daya a kafatanin rayuwarta,kullum kwanan duniya farinciki ke sake riskar rayuwarta,tako wanne bangare rayuwa na mata kyau fiye da yadda take so,gefe guda ga mai gidanta mai share kukanta yana tare da ita ako da yaushe,ba abinda ta nema cikin rayuwarta ta rasa,ko da yaushe suna waya da dukkan 'yan gida,halima tuni cikinta ya tsufa dab take da haihuwa,abdallah har yau na wajensu ya dawo wajenta baki daya,ya zama tamkar danta,kai idan ba gaya maka akayi ba bazaka taba cewa basu suka haifeshi ba su da abdur rahman,zainab ma ta samu wani cikin bayan barin da tayi,amira ana can ana fama da laulayi wanda ya sanyata tayi laqwas,ashe da wasa farin garki,nafisa qawarta matar auwal itama ana can ana fama,ko yaushe suna waya tare da yiwa juna fatan sauka lafiya.        Sulaiman wato malam mahaifin sumayya tuni lamura sunyi nisa,ci gaba ake ci gaba da samu cikin gidajen gonakinsa,ya dauki ma'aikata sosai da zasu kula masa da gidajen gonar nashi dake gwambe kano da abuja,shike kula da na kano,na gwambe sun sake diban samarin dake cikin ainihin karkararsu,na abuja kuwa ya bar komai wajen baban tunda yafishin sanin ya yanayun garin yake,tuni malam din ya soma zama wani na musamman shima,gida ya gina musu yalwatacce wanda aka qawati shi da kayan alatu da more rayuwa,sashe biyu ne madaidaita hakan ya sanya yaya abubakar dauko meenat matarshi suka dawo daya sashen da yaransu guda uku,hakan ya yiwa mama dadi qwarai,don dama gidan ya zama sai ita kadai,gashi ya mata girman da bazata iya zama ita kadai din ha,amma dawowarsu amina da jikokin maman hakan sai yayi mata dai dai,zumuncin baba da malam din kuwa sai abinda yayi gaba,don basu cikakken wata basu ga juna ba,ko malam din yazo ko kuma baba yaje,da haka wani lokaci suke zuwa da matansu,wanda hakan ya haifar da sabo sosai tsakanin anty maamaa mama da kuma ummi.        Ta gefan hajiya su'ad kuwa baki daya ta gama karance takun almustapha tsaf ta gane komai,son haihuwr yake kaman ya jawo randa yaron zai fito duniya,cikin qanqanin lokaci jikinta yayi sanyi ya mutu baki daya,a hankali ta soma tunanin me yasa bata fahimvi yana son yara ba?,me yasa bata gane ba?,tun daga sanda yace zaya bude gidan marayu da yanda yake nacin zuwa yaci ace ta karanci cewa shi din mutum me mai son yara da son mu'amala da su,kullum kwanan duniya ta kwanta tunaninta shine yadda zata gyara kurenta,ta yaya zata ganta da ciki?,ta yaya zata haihu?,har yau abinda ke sakadar zuciyarta kenan,batasan da wa zata yi shawara ba,anty kubra ce,saidai ta tabbatar cewa fada zata sha kafin daga bisani tace ita din ba ruwanta,da mamarta kawai zata shawarta,saidai maman sunyi tafiya da babanta basa samun zama,lokaci kawai take jira na dawowarta ta zauna susan yadda zasu gyara lamarin.   ******  *******    ********        A hankali take tako lallausan carfet dake dakin zuwa inda yake zaune shirye cikin jallabiya ta maza dark brown,ya dora hirami akanshi wanda ya dace da jallabiyar,hannunshi daure da baqin agogo,system ce gabanshi yana rage wasu ayyuka yayin da yake tsumayin fitowarta,zasu je siyayyan kayan baby ne,duk da cewa yana daga gida zai iya fadin duk abinda yake so a hado masa daga dukkan kamfanin da yakeso cikin fadin duniya,saidai yana so su fita su shiga kanti da kanta don sumayyan ta tattaka da qafafunta tayi zagaye saboda lafiyarta.        Sanye take da abaya peach mai adon duwatsu masu qyalli,peach mai turuwa da mai haske,tayi rolling da wani wadataccen mayafi  dark peach,plate shoes ne a qafarta shima kalar rigar,sosai cikinta ya fito kai kace yau ko gobe ne haihuwar,wanda alokacin baki daya bai wuce wata bakwai da sati biyu ba,a jikinsa yaji fitowarta ya daga kai a hankali yana kallonta,baisan sanda murmushi ya subu ce masa ba,aduk sanda kake da buqatar ganin fara'a qarara kan fuskarshi to yayi tozali da sumayya tana takowa zuwa gareshi dauke da cikinsa,duk duniya shine abu na farko dake faranta masa rai a duk yanayi ko matakin da ya tsinci kanshi,sau tari yakan ayyana me zata haifa cikin ranshi,jikinsa na bashi cewa twince ne musamman idan yana mata awo,saidai bai taba sha'awar duba meye acikinta ba,yace koma meye yana marhaban da zuwanshi,miqeww yayi tsaye ha cimmata a inda take kafin ta qaraso,ya bude tafin hannunshi ya sanya nata yana murmushi "Wai wannan cikin naki anya babe?" "Mene?" Ta tambayeshi tana daga gira,tattausan murmushi ya sake mata yana kada kai "Shikenan.....muga qafar taki,ina fata ba kumburi ko?" Silifa din ta zame tana tayashi duba qafar tare da cewa "Eh yanzu kam babu,tun jiya bai sake yi ba" gabanta ya durqusa yana mammatsa qafar kafin ya miqe yana cewa "Masha Allah,Allah ya raba lafiya" dariya ta qwace mata ta dubeshi yanayin yadda ya furta maganar kaman mace "Amin abu abdallah" "Ummu abdallah...da zarar kin haihu fa za'a sauyan suna,saboda na zama daddyn yara da yawa,zan koma ABUL AULAD ke kuma UMMUL AULAD" idanu ta lumshe tana jifanshi da wani kallo,sosai sunan yayi mata,tana mamaki idan taju yana larabci,duk da hakan bai rasa nasana da zamanshi cikinsu,kai take gyadawa cike da gamsuwa "Hakan yayi,amma har yara nawa zamu haifa da suka zama AULAD?" idanunshi yadan zaro yana kallonta "Ko dozen haka ai sunyi ko?" Dariya ta tuntsire da ita shina yana tayata "Eh lallai kayi dariya mana,bakusan yadda ake ji ba,a haifa muku kawai" qugunta ya kama suka fara takawa yana bata amsa "Da gaske wallahi Allah nake miki,ina son naga wannan ya dane min wuya,wannan ya zauna acinya,wancan ya kaman kunne,wannan yana jamim hanci,wannan yamin fitsari wancan yamin bayan gida" dariya sosai ta kamata yadda ya taqarqare yana zuba bayani,har sai sata dafe cikinta tare da dakatawa da tafiya tana dubanshi "Kace nanny zaka koma kenan cikin gidan?" Giranshi ya dage mata "Laifi ne?,bakisan ma'aiki yana taya matanshi ayyukan gida ba?,sunnah ne fa" murmushi taci gaba da yi,sai yayi bala'in burgeta ba kadan ba,haqiqa kyawawan halayensa basa rasa nasaba da iliminsa "Haka ne,Allah yasa mu dace" "Amin beauty" ya fada yana jan hancinta wanda ya bude ya sake girma,sai ta kwabe fuska tana dubanshi shi kuma yama boye dariyarsa "Kawai kace mummuna mana ha'an?" Dariyar ta qwace masa baki daya,yasa hannu yana toshe bakinsa,sai ta soma kukan qarya tana buga qafa daya don babu damar yin rigima sosai,riqe hannayenta yayi sosai yana bata haquri kafin yace "Ba wani yanayi da zaizo wanda zai sanya na kasa ganin kyanki,ko yaushe ke mai kyau ce a wajena,ko da kuwa duka duniya basa gani,bare ma ha wannan ba,matuqar dabi'unki na tattare da ke ko kece sarauniyar munana na duniya haka nakeson abata,kinsan me?" Sai ta kada kai tana sauraronshi "Dabi'a furuci lafazi da mu'amala sune abu na farko dake tallata dan adam,sune abubuwa dake jefa soyayyar mutum cikin zukatan kowanne bil'adam,koda mutane basu shirya sonka ba,sai kyawawan dabi'unka su rinjayesu su soka,haka kika mamayeni babe,sonki ya cika qirjina" murmushi tayi ta sadda kai,shima fuskarsa dauke da murmushin ya saka hannunshi ya daga kanta "Ita kunya daure take da imani,idan aka dauke daya dole daya ya tashi haka annabi S A W yace,kenan,duk wajen da kaga babu kunya to tabbas babu imani a wajen,haka wajen da babu imani to kunya tayi qaura,duka kin hada my summy,don haka kin cancanci duk wanu nau'in so da kulawa" yatsunshu uku ta riqe tana dubanshi "Ummm ummmm,daina fasamin kai" "Kin taba ji ko ganin na miki qarya" kai ta kada alamar a'a,don bai taba yi matan ba,koda gaskiyar da zai fada zata qona mata rai bai fasa fada din "Na gode,ubangiji yaci gaba da shiga cikin lamarinmu" sai da yayi kissing goshinta sannan ya amsa da amin "Muje ki kira su'ad mu wuce ko?" "To....." Sautin bai gama fita ba suka ji anja tsaki,suka waiwaya suna dubanta sanda take daga labule tana ficewa,ranshi ya baci sosai,me ya kawota har cikin falon sumayyan?,bayan can ba shigowa take ba?,bama wannan ba,tunda suke tsaye tana wajen tana kallonsu,da wani abu suke kuma na daban fa?,ba sallama ba neman izini?,sumayya bata ce komai ba haka shima,sai yayi gaba ta tako a hankali ta biyo bayanshi, "Shiga kice mata ta fito" ya fadi yana gyara agigon hannunsa "To" ta fada tana takawa da irin tafiyar masu ciki,ya bita da kallo da idanunshi har ta shiga.       A falom ta sameta tana tsaye,idanunta sun kada sunyi ja,tabbas kalaman da ta jiyo suna fita daga bakin almustaphan su suka sata shiga taji me yake gaya mata,kalamai ne masu nauyi dake fita daga ainihin qwaryar zuciya,tana zaton mawuyacine fa idan batayi kuskuren da zai hanata sukuni a rayuwarta ba "Amm....anty yace ki fito zamu tafi" "Kije kice masa ba zani ba,fitar min daga daki tun ban zagi uban ubanki ba"ta fada cikin tsawa da hargagi idanu ta daga ta dubeta kawai ta jiya a nutse ta fice,tabbas ba don tana tsoron abinda zai biyo baya ba da babu abinda zai hanata shaqo wuyan sumayyan tayita jibgarta kamar Allah ya aikota har sai taga ita da dan cikin nata sun daina motsi,amma ta tabbatar yin hakan dai dai yake da rasa komai cikin rayuwarta,ciki kuwa harda igiyar aurenta da almustaphan.        A tsayen ta sake taddashi ya tsurawa qofar falon ido,ta iso inda yake ta bude bakinta zata roqeshi yaje yaji damuwar su'ad din sai ya daga mata hannu "wuce mu tafi"kawai yace da ita yana dubanta,ba musu tayi gaba,duk sanda yake cikin fushi yakan koma mata almustaphan nan data sani a farkon rayuwarta,rufa mata baya yayi suka fice.        Cikin katafaren shagon da sukayi fice wajen samar da kayan jarirai suke zagayawa,tana daukan duk abinda taga yayi mata shima yana tayata,fuskarshi a sakw kaman ba dazun ranshi ya baci ba,kayane masu kyau da tsada wanda jinsin mace ko namiji zai iya sanyawa(unisex).          Daga gefansu kadan idanunta suka dinga mata gizo,kaman nuwaira take hangowa ita da wata mata suna zaban kayan yara maza,sai ta ajjiye rigar dake hannunta ta taka a hankali ta qarasa wajen "Nuwaira" ta fada a hankali,da sauri ta juyo suka hada ido,take fuskarta ta washe da wani madaukakin murmushi,ba don tsinin cikin data gani jikin sumayya ba ba shakka rungumeta zatayi "Anty sumayya?.....mama kinga anty sumayya,anty sumayyarmu,wayyo yau su basma zasu ji labari naga anty sumayya,yau ya hajiya zata ji saboda dadi" nuwaira keta jero wannan magana ba tsayawa,matar dake gefanta tana murmushi kawai,wanda duba daya zaka mata kaga tsantsar kaman dake tsakaninsu da nuwaira,kyakkyawar macace blcak beauty,wadda kallo daya zaka mata kasan nutsuwa ta ratsata,tana daukw da tsohon ciki wanda ke nuna alamar haihuwa yau ko gobe "Oh nuwaira,nutsu mana ku gaisa ko tukunna" murmushi itama sumayyan take bakinta yaqi rufuwa suka soma gaisawa da matar sannan ta gabatar mata da kanta "Ni sunana rumaisa,nice mamar nuwaira,ke kuwa nasan kece sumayya,matar da lukman ya taba aura haka ne?" Kai sumayya ta kada taba murmushi cikin mamaki "Hakane,amma yaya akayi kika ganeni?" Murmushi itama tayi "Dole na ganeki ai,mai gida mamarshi da duka yara kullum sai sunyi maganarki...ashe da rabon zamu hadu" "wallahi kam" sumayya ta fada tana duban nuwaira "Nuwaira,kinga yadda kika zama budurwa sosai,lallai aure nan kusa kenan" dariya ta saki cikin jin kunya tace "Anty maman ce fa ta dawo gidan abba na" kai take gyadawa ko bata fada ba ta tsammaci haka "Naga alama nuwaira masha Allah,Allah ya bada zama lafiya" hango almustapha tayi yana lalubenta da idanunshi don bai san tayi nan ba "Ni zan wuce nuwaira ina kukayi masauki?"rumaisa ce tace "nazo ganin likita ne amma nan da kwana hudu zamu koma,amman ki bani adresa dinki in sha Allah zamu zo har gida,nima naji dadin ganinki don naji dukkan wani qoqari da kikayi kan rayuwar diyata da kuma gidan baki daya,kin cancanci muzo mu gode miki" murmushi kawai tayi sukayi musayar lambar waya,ga rubuta adress din jikin qaramar takarda ta bata sannan sukayi sallama suka rabu.          Cikin mota shiru sumayyan tayi,tana tunanin yadda rayuwa take sauyawa bawa a duk sanda Allah yaso,haqiqa rayuwa abar tsoro ce ga dukkan mai tunani,wannan kadai ya isa bawa ishara yasan cewa babu wani abu dake dawwama nan duniya banda ikon Allah,walau dadi ko wuya,komai na wuceea ne tamkar a mafarki,gefw daya tunanin su'ad ya fado mata "Babyyyyy...." Almustapha ya kira sunanta wanda hakan shi ya sanyata dago kanta ta dubeshi,sai ta dora hannunta saman nashi hannun dake kan giyar motar "Tunanin me kike yi?" Kai ta kada "My...meke damun su'ad?" Kai ya kada yana duban titi "Nima ban sani ba" "Amma ya kamata ka binciki damuwarta kaji ko?", kusan shekaran jiya abinda yayi kenan,ya tsirata da tambaya,bata da amsa daga bisani ma kuka ta sanya mata tana gaya masa so taje ta gansu daga shi sai ita,duj da akwai wannan cikin zuciyarta amma babban abinda yafi damunta shine ta yaya zata dauki ciki itama kaman sumayyan?,ta samu soyayya tattali da kulawa irin tata?,duk da babu abinda ya rageta da shi "bansan me take so na mata ba cikin duniya,ban rageta da komai ba,ba abinda ban bata ba babu kuma abinda bana mata,ko yaushe qoqarin tanqwara zuciyata nake don ma saba da halayyarta amma ko da yashe sabon hali take qirqiromin,bana son na aikata mata wani abu da ba dai dai ha ko don mutuncin mahaifinta,ina girmamashi,ina ganin qimarshi....amma ko yaushe kamar ina tunzura ta haka na......" Shiru yayi ba tare daya qarasa ba,ko da can shi bai tattauna matsalar wata cikinsu da wata,ya sani cewa inda hakan me yiwuwa ne sumayya abokiyar shawararshi ce,halayenta sunyi dari bisa darin da ya tabbatar zata iya bashi shawara da mafita kan koma mene ne,shiru itama tayi,ta tabbatat da cewa ya kai maqura shi yasa har yau yake furta wadan nan kalaman,hannunshi take matsawa a tausashe har sai da taji ya saki ajiyar zuciya sannan a hankali ta furta "Am sorry....Allah ya shiga lamuranmu" "Amin" ya furta yana jin dadin lafazinta.        Maganar noman audugar da ya sanya ake masa a qasar kano jigawa da zaria ta taso,hakan ya sanya ya shirya zuwa nigeria cikin satin,cikin ikon Allah sai kuma ga haihuwar halima,wadda ta sauka lafiya ta samu namiji,daman can yana da niyyar tafiyar da su don haka ra'ayinshi yake,saboda haka yace su shirya,zasu sauka kano da sumayya,zai barta nan su wuve jigawa da zaria da su'ad tunda ita sumayyan tafiyar zata iya yi mata wahala,hakan itama yayi mata,ko banza tasan zatayi hidimar sunanta hankali kwance,kishin dake damun su'ad cikin zuciyarta tace sam ita ba zata je ba,me zata je yi wani zaria da jigawa?,ta rasa wajen zuwa sai nan?,ranshi ya baci,shima kuma ya motsa qwanjinsa ya nuna mata mazantaka yace sai taje,hakanan ba yadda ta iya ta haqura zata bishin,itakam sumayya ko a jikinta,shiri ta soma yi sosai tana siyan tsaraba,duk da ya hanata fitan tana daga gida take siyayyar ake kawo mata.        Ana gobe su nuwaira zasu tafi suka kawo mata ziyara,tana daki kwance aka shaida mata tana da baqi,ta miqe cikin farinciki ta tar besu har zuwa falonta,duk da nauyin data yi bata zauna ba sai data tana dar musu komai,zata dora abinci rumaisa tace a'a sam,itama tana fama da kanta ne,suma kuma a qoshe suke snack din kawai ya isa,bata rabo da kayan snacks zuwa su dambun nama saboda almustapha,wani lokaci su kadai yake ci a matsayin abinci,hakan ya sanya take yinsu ta saka su a freezer sanda zaici sai ta dauko idan na soyawa ne ta soya masa,idan na gasawa ne ta gasa masa.       Hira suke wadda kusan rabinsu da nuwaira suke yinta,jifa jifa rumaisa ke saka musu baki "Ina maman naku karima ne?" Murmushi nuwaira tayi "Daddy ya saketa ta koma garinsu,yanzu kullum bakiga yadda take masa naci ya maidata ba wai ta tuba hajiya tace sam bata dawowa wa,yanzu ma wai ta kusa aure a can" kai sumayya ke jinjinawa,abinda ya faru shine,baki daya rayuwan yaran da mai gidan komawa tayi wajen hajiya,sai kariman ta koma tamkar wata saniyar ware a cikinsu,suna sashen hajiya suna walwalarsu tana vangarenta ita kadai kamar mayya,duk wani qoqari na dawo da yaran rayuwarta da mai gidan amma abu yaci tura,a hankali karima ta soma fita daga kansa,a lokacinne ita kuma ta soma gane kurenta,tayi laqwas ta soma biyayyar qarfi sa yaji saboda ta fuskanci ba wata mafita gareta,saidai ina tunu ta gama fita akan lukman din baki daya,bare hajiya wadda tayi shiru ne kawai saboda darajar yaran da kariman ke da su,uwa uba kuma tayi alqawarin ba zata sake saka dan nata ya saki wata cikin matanshi ba har abada,don taga ishara,Allah ya kawo qarshen zaman nasu,hajiya ta wayi gari lukman ya saki karima har saki biyu,qememe yace bazai maidata ba,don ya kamata da kanshi tana zuba wani abu cikin abincin hajiyan,wanda magani ne qarshe aka bata matuqar baiyi aiki ya dawo mata da rayuwar gidanta yadda take ba daa to malamin nata ya gaya mata tayi haquri kawai,sai gashi bata zuba a sa'a ba ya zama silar tsinkewar igiyar aurenta.        Bayan mutuwar auren da wasu watanni hajiya ta soma sha'awar dawowar rumaisa mahaifiyar nuwaira gidan,wadda ita daya ce ta haihu da lukman,macen kuma data fi duka saurab matan da ya taba aura tsantsar haquri da biyayya,faduwa tazo daidai da zama,don shi dinma rumaisan ke kai kawo cikin ranshi,tunda ya tabbatar da ceea ya rasa sumayya,wadda kabatin aurenta a abuja ya gigitashi fiye da zato,ya soma binciken wanda ta aura,sanda yaci karo da labarin cewa doctor muhammad almustapha mukhtar gombe ne tilas ya aro haquri ya yafawa kanshi,saboda ya kwana da sanin babban goro ne sai magogin qarfe,hakanan bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane,bayan sun rabu da karima sun hadu da rumaisan kusan sau uku a gurare daban daban,saidai ko dubanshi bata yiba bare ya samu fuskar tunkararta,soyayyar da sukayi bata zaci zai rabu da ita haka da wuri ba ba laifin tsaye ba na zaune,ya karbi umarni kawai daga mahaifiyarsa,da qyar aka shawo kanya harda hajiyan wajen lallashi sannan ta yarda aka maida aurensu,wanda dawowarta ya sake dawo da walwalar gidan kaman zamanin da sumayya kenan,duk da hakan basu manta da ita ba kullum kwanan duniya su da hajiya sai sunyi zancanta,wanda har rumaisa ta saba da ji,takan zauba ta tayasu wani lokaci,ko daya rumaisa bata bari abinda karima ta yiwa diyarta yayi tasiri a ranta ba har ta rama kan yaranta guda hudu data bari,ta hadasu ta rungume kamar ita ta haifesu,sannan taci gana da dorawa kan tarbiyyar da sumayya ta azasu wanda hakan yayi mata dadi sosai.        Wannan shi ake kira da QADDARA saiga rumaisa ta zama ita din dai itace matar lukman,dawowarra ba dadewa harkokin lukman suka bude sosai,wanda hakan bai rasa nasaba da yadda ya maida kai wajen kyautatawa hajiyarshi ita kuma taci gaba da binsa da addu'a,cikin qanqanin lokaci ya sake habaka,ya sauya gida da abubuwa masi dama cikin rayuwarshi data yaranshi,basu dade da komawa sabom gida ba rumaisa ta samu juna biyu,wanda yanzu haka siyayyar haihuwa tazo yi sanda yayarta dake kasuwanci zata zo dubai lukman ya masu visa ita da nuwaira suka taho,wanda yace girma yake bi,zuwa na gaba kuma mai biwa nuwaira da ita za'a babbar yarinyar kariman.         Basu wuce awa biyu ba suka yi sallama zasu wuce,suka rabu kowannensu na tsokanar dan uwansa kan sai sunzo suna,ta musu alaqawarin indai tazo kano matuqar mai gidan ya barta zata shigo ta gaida hajiya,amma su isar mata da gaisuwar tata wajen hajiyan kafin ta iso da su basma baki dayansu,a haka suka rabu.        Kwana hudu tsakani suma suka tashi zuwa kano,saukar yamma sukayi saboda haka kai tsaye suka wuce gidan baba wanda nan suke sauka dama,ba haka sumayya taso ba,so tayi ya barta ya sauka gida amma ya hade gabas da yamma ya qiya,saboda yau ne zata amshi kwananta,farincikinsa shine sama da nata saboda haka itama ta danne tata buqatar ta haqura. Yana bakin gado yana shafa mai ta fito itama daga wanka,daure da towel amma ya dage mata saboda tsinin cikinta,kallonta yake cikin shauqi yana lumshe idanu,saboda yadda ta masa wani kyau,fatarta kana kallanta kasan ta samu hutu,ruwan wanka yayi dai dai kan fatarta,miqews tsaye yayi ya isa bayanta inda take tsaye gaban madubi tana tsane jikinta,ya kama qugunta ya manna a jikinsa,sai ta lafe tana dubanshi ta jikin mudubi fuskarta wasai "Wannan cikin naki kaman ya wuce watanninsa fa.....na qagu ya fito zuwa yanzu ya soma hanani aiwatar da wasu abubuwa yadda ya kamata,baki daya kin zama wata lazy,perfomance dinki ya ragu babe" kanta ta langabar saman kafadarshi a shagwabe "Duk rawar gaban hantsin da kake sha abinka noor?" Habarta ya kama ya riqe "Yanzun idan nace ina son mu shiga babbar headquater nayi rawar gaban hantsin za'a barni?" A gajiye take tabbas,amma ta sani so yake ya qureta don ya samu abun tsokana,hakan ya sanya ta dan janye jikinta ta waiwayo tana dubanshi "An gaya ma raguwa ce ni?" Gira ya dage dariya na cinsa ya daga kafadarsa "Wa yasani?" "Bari in nuna maka" ta fada tana nufar saman gado,sosai dariya ke cinsa,shikenan ya gama mata wayo,baisan yaushe sumayyar zatayi wayo ba,duk da yana maraba da irin wannan rashin wayon nata,gunta ya isa yana qunshe dariyarsa,yayin da ya lullubeta cikin qirjinsa,yana aika mata da zafafan saqonminsa cikin zafi zafi masu dumama duniyar ma'aurata wadda ke qunshe da tsantsar soyayya qauna da kuma shauqi. Ranar baki daya ba inda ya fita,da qyar ta lallabashi ya rakata kitchen ta musu abinci mai sauqi suka dawo daki. Washegari suka shirya shi da ita tsaf don su'ad na nade bata ga wajen fita ba,wani qauye a 'yar gaya dake kano nan ya dauketa suka tafi shi da ita da driver,sai wata motar guda daya a bayansu akwai PA dinshi da kuma wanda ya barwa aikin da zasu je gani a hannunshi,gonaki ne masu fadi da tsaho wanda iya ganinka auduga ce,sosai taji dadin zuwa wajen don ko ba komai zata tattaka,uwa uba kuma ranar garin babu rana,sai da ya gama zagayenshi sannan ta fito suka fara takawa tare,wajen da matan dake musu aikin cire audugar zaije yaga yadda suke,hannunta cikin nashi yana dan tsokanarta yana mata dariya,murmushi take tanajin dadi qasan ranta,tana godewa Allah kullum kwanan duniya da irin mijin da ya bata,bakin wata bishiya suka nufa,Allah sarki matan karkara,rayuwarsu abar dubawa ce,cincirondon mata ne,wasu na aikin wasu na qasan bishiyar suna baiwa yaransu nono,yayin da wasu ke gefe suna hutawa,sosai ta tsurawa daya daga cikin matan dake bawa danta nono tana hira data kusa da ita,yanayi take mata da fa'iza sosai,duk da wannan ta soma komawa tamkar tsohuwa,saidai ga mai dogon nazari da tsinkaye yana mata kyakkyawan duba zai san wahala ce ta maidata hakan da tsantsar rashin kulawa ci sha sutura da muhalli mai kyau. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 1⃣0⃣4⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *la ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin* _____________________________________        Har ta qarasa wajen basu lura ba,sai data tsaya dab da su sannan hankalinsu gaba daya ya dawo kanta,idanu kowa ya zuba mata yana mata kallon qurilla "Fa'iza?" Sumayyan ta fadi tana dubanta,jin tayi shiru bata amsa ba ya sanyata sake cewa "Ko ba fa'iza bace?" "Nice,nice mana" ta fada tana yanqare haqora tare da cire yaronta daga bakin nonon,farinciki fal ranta yau cikinsu su wajen goma 'yar gayu ta mata magana ita kadai har tana nuna ta santa,har ga Allah sam bata gane sumayya ba "Fa'iza kece haka?" Sumayya ta fada cikin mamaki da al'ajabi "Eh wallahi...amma na kasa heda fuskar taki" "Sumayya ce fa....sumayya kishiyarki wadda kuka taba auren mukhtar tare" miqewa fa'izan tayi dafe da qirji tana cewa "Keeee.....sumayya?,da gaske?" Ta fada tana matsowa kusa da ita ta soma shafa kayan jikinta tana qare mata kallo,sai kuma ta fashe da kuka tana cewa "Kina nan dama sumayya?,naji labari ashe mukhtar ya rasu?" Cikin raunin zuciya ta gyada "Mukhtar ya rasu fa'izw,shekara kusan shida kenan" "Wayyo Allah,dama mukhtar na raye na roqeshi gafarar cusguna muku da nayi" gefe fa'izan ta janye sumayya,kan wasu duwatsu guda biyu dake wajen suka zauna,nan take sanar mata labarinta,bayan fitowarta gidan mukhtar kamar wadda aka yiwa baki ba wanda ya taba zuwa taya aurenta,ko dama can bata da farinjinin samari ko kadan,hakanne ma ya sanya aka hada ta da mukhtar din,sai daga bisani baban yaron dake cinyarta ya fito neman aurenta,wanda yanzu yaransu uku,wannan ne qarami,bayan auren ba komai ta tsinta ciki ba sai wahala,matanshi hudu kowacce ita ke dauke da dawainiyar kanta data yaranta,zai zube musu hatsi ne kawai a rumbu saura kuma ya rage nasu,sosai taji ta tausayawa fa'izan,wato rayuwa kowa da irin jarrabarsa,hakan duk abinda ka shuka dole wataran saika girba,ko ka jawa yaranka gadon wahala su su girbe abinda kaine ka shuka shi,gashi dai taqi uarda ta zauna gidan mukhtar dake cikin birni,yana da matarshi daya da rufin asirinsa qwarai,babu abinda bai dauke musu ba na dawainiyar gida,sai gashi ta fada gidan mai mata uku,banda hatsi bai kula da komai naku ba,ga haihuwa tanayi "Ya taki rayuwar sumayya?,da alama komai ya miki kyau" ta fada tana qare mata kallp,tun daga takalmin qafarta zuwa lafiyayyen material dake jikinta,dankunne agogo sarqa da jaka,murmushi kawai ta saki sannan tace "Kowanne bawa da kalar tashi qaddarar,kuma ba shakka duk inda kayi sai ta bika,saidai Allah yakan yiwa bawa sakayya gwargwadon abinda ya shuka,idan alkhairi ne bayan Allah ya gama jarrabaka sai ya maka sakamako mai kyau,haka idan sharri ne ma" a taqaice ta bata labarin komai,ta dinga jinjina kai tana sake nutsuwa tare da dana sani kan abinda ta aikata a baya,nan ta nemi gafarar sumayya,bata da riqo sam ballantana ma ita bata ga abin da za'a riqe fa'iza da shi ba,don baki dayarta abar tausayi ce,yafe mata tai sannan ta bita da alkhairi,ta tambayeta nawa take buqata na jari,wanda zata bar wannan aikin taje ta riqe iyalanta "Dubu uku ma ni ta isarmin" ta fafa cikin zumudi,baki dayanta kalar tausayi ce,jakarta ta bude,ta zaro dubu goma 'yan dari biyar biyar sababbi ta miqawa fa'izan,ai batasan sadda ta dire danta dake kan cinya ba hannu na rawa "Don Allah kada kice min da wasa kike" ta fada bayan ta gama qirga kudin,murmushi sumayya tayi tausayinta na kamata "Ba wasa nake miki ba fa'iza,ki riqe kija jari,don Allah ki baiwa yaranki tarbiyya da kuma ilimi,shine kadai gatan da zaki musu" "Da izinin Allah sumayya na gode na gode na gode" sai ta fashe da kuka tana sake jaddada godiyarta.        Daya daga cikin matan ne ta iso wajen tana sanar da fa'iza ta taso za'a biya su kudin aikinsu na yau,sannan mai gonar zai basu wani abu,daa tace ba sai taje ba,sumayya tace haqqinta ne taje ta karba ta hada,baki dayansu suna tattare waje daya,tare suka isa wajen,almustapha na tsaye jikin motarshi,tun dazu yake raba ido yaga ta ina zata bullo,gefan matan itama ta tsaya cikin tausayi take dubansu,tana godeww Allah matuqa kan ni'imar da yayi mata,ba tare da wayo ko qarfinta ba,da idanu ya dinga binta,tausayin da ya gani zallah cikin idanunta ya sake burgeshi,ko da yaushe dabi'arta tasha banban data saura daya saba gani masu shekaru irin nata,take yayi wani quduri cikin ranshi,ba shakka zata dace da a bude mata wata qungiya ta tallafawa mata marasa galihu da koyon sana'o'i,da alheri almustaphan yabi kowaccensu,dukkansu ko sai da suka dara saboda kudin da ya basu,shi kanshi tausayi suke bashi,ina mazansu da haqqin ciyarwa da shayarwa ke kansu suka barsu suna wahala da fadin tashin ci da kansu,sai da suka gama kaf sannan sukayi sallama fa'iza na sake jadda da mata godiya,ta karbi lambar sumayyan tace ko cikin gari zata dinga shiga tana kiranta suna gaisawa lokaci zuwa lokaci.          Yana nade saman gado yana duba saqonnin hotuna da lamin ke turo masa na gonakin da suke nema yadda noman yayi kyau,lokaci lokaci yakan daga kai ya kalleta sanda take shirin bacci gaban madubi,ya lura tunda suka dawo jikinta a sanyaye yake,haka yake,tana tuna wato rayuwa garanbawul ce,haka sharri tamkar jifa ne,duk sanda ka yishi komai daren dadewa sai ya dawo ya sauka tsakar kanka,a hankali ta hauro gadon,sai ya bar abinda yake ya zuba mata idanu kafin daga bisani ya bude mata hannayensa,dama abinda take jira kenan,ba bata lokaci ta isa jikinsa ta lafe tana shaqar tattausan qamshin da yake fitarwa,bugu da qari tafin hannunta na kan singalalin hannunsa dake cike da gargasa tana shafawa,hakan ya sakashi lumshe ido saboda yadda tsigar jikinsa ke zubawa "Babe....mai ya sakaki mutuwar jiki haka?,ko baby ne?" Kai ta girgiza sannan ta soma kwatanta masa fa'izan da ya gansu tare,yace ya ganeta,nan ta bashi labarin yanayin da take ciki,shiru yayi yana jinjina mata,ba shakka ba kowacce mace bace haka,ya tabbata da wata ce dariya zatayi tayi shewa kafin ta shelantawa duniya,zata ce Allah ne yasaka mata abinda fa'izan tayi mata,sau gashi ita neman hanyar da zata fiddata daga cikin qunci take "Kin taimaka mata ai ko?,ba sai an sake wani abun ba"shiru tayi kaman ba zata yi magana ba sannan tace "A'ah....ranka ya dade da zaiyiwu a qara mata jari,a baiwa mai gidan wani qwaqwqwaran sana'a da zau kula da iyalinshi baki daya" "Babe.....ta cutar min da rayuwarki fa?" Kai ta kada "Na sani...amma na yafe mata,tunda gasji daga qarshe ni naci riba,Allah ya yimin kyakkyawan sakamako da gwarzon miji kuma masoyi irinka,daya tamkar da million" ta qarashe maganar cikin wani salo mai kwantar da rai,dariya ya dinga saki sannan ya ruqunqumeta cikin jikinsa yana jinta har cikin bargonshi "Duk abinda kika ce shi za'a yi" ya rada mata akunne cikin salo na rada kaman wanda zai shide.   ********   *****   ********        Washegari shi da su'ad suka wuce jigawa,yayin da ita kuma ta tattara ya nata ta nata sai gida.        A falo ta tadda mama ita da anty meena suna hiransu tamkar uwa da da,cikin farinciki suka tarbeta,mama kam kallon sumayyan take taba sambarka tare da godiya wa Allah,yaran meena biyu suna makaranta sai qaramin yasir sulaiman mai sunan malam ne,wanda baifi wata uku ba,gida kam yayi kyau masha Allah ya burge sumayya qwarai,ta dinga shiga tana fita tana godewa Allah,har da tsokanar mama cewa bata ga dakinsu ba,dariya anty meena tayi "Kukam ai an gama yayinku tunda an yaye ku" suka sa dariya baki daya,a nan ta yiwa mama barka,da anty meenan ma baki daya.       Kusan itama anty meena nan ta zauna da su,ranan bata je gidansu masu jego ba duk da kusan kullum sai taje,sai da zata dora abinci ta fita ta barsu,kafin sannan yaran sun dawo daga makaranta,abin mamaki duka sun santa,don yaya abbakar na nuna musu ita akai akai yana gaya musu sunanta,abinka da yaro da riqe abu,saidai basu sake da ita sosai ba kaman yadda suke sakewa da su halima.        Tare malam suka shigo da yaya abubakar,kowannensu murna fal cikinsa da ganin sumayyan,sun sha hira sosai har ya abbakar ya gaji ya wuce bagarensa ya bar sumayyan da malam,labari yake ta bata kan irin ci gaban da rayuwa ta samu,yana sake jaddada mata irin soyayyar dake tsakanin baba prof da shi,da kuma yadda ko da yaushe zumuncinsu ke sake gaba yaba habaka,sosai take sake ganin qimar baban cikin ranta,ba shakka shi aboki ne kuma masoyi ne daya tamkar da dubu.        Washegari suka dunguma gidan halima,baki daya harda yaran yaya abbakar nabila da yusuf da anty meena mamansu,almustapha ya bar mata mota da driver,wanda zai dinga kaita duk inda taje da buqatar zuwa,sanda suka je gidan 'yan barka nata shiga da fita,'yan uwan abdur rahamn,wasu ta sansu musamman na bangaren babanshi tunda sun hadu da mukhtar ta nan wajen,wasu kuma bata sansu ba,duk wanda ya santa a sanda take gidan mukhtar a yanzu da ya ganta sai ya kalleta ya sake juyawa ya dubeta,munagukan da a da suka cusguna mata baki daya jikinsu a sanyaye yake,baki daya sun kasa zama kusa da ita,kunya da kuma ganin yadda sumayyan ta sauya ta zama wata babbar mace duk ta cikasu,itakam bata dauki komai ba,tamkar basuyi mata komai ba haka ta sake musu fuska,abu daya ta sani shine an rige an wuce wajen,yanzu kam rayuwa ta baiwa kowanne certificate din abinda ya aikata,a gidan ta tadda zainab wadda shigowarta kenan,itama tana ta fama cikinta ya shiga wata na tara,sumayya ce nata keda wata bakwai da satittika,dukkansu suna zagaye da 'yar uwarsu,fuskarsu qunshe da farinciki,yaron yana saman cinyar sumayyan tana kallon tsantsar kama tsakanin yaron da babanshi abdurrahman,wato duk bawan da bai yarda da QADDARAR ubangiji ba lallai zai ci wuya cikin lamuranshi,matar mutun kabarinsa,yau ga yaron abdur rahman da halima saman cinyarta,sannan gata dauke da cikin almustapha,mutumin da ko a mafarki bata taba saninsa ba,sanda qaddara ta gindaya kuma ta sanshi din bata taba koda hasashen zama irin na auratayya zai hadasu ba,hira suke sosai gwanin sha'awa,wadda ke nuna zallar hadin kai da fahintar juna dake tsakaninsu,abdallah baya nan yana tahfiz sai azahar zai dawo.         Sanda taga abdallah masha Allah,wani baragen girma gareshi,ya fara zama wani babba,ga wani hankali da nutsuwa tattare da shi,kana gani kasan ya samu isashshiyar tarbiyya,girma yake abdallan sosai,sanda ya ganta fuskarshi washe da fara'a ya iso gefan cinyarta bayan ya gaida duk wanda ya taras cikin falon yana fadin "Ammi....ashe kinzo baki gaya min ba?"murmushu ta saki ranta fes,tana sake ganin girma da qimar abdur rahman har da ma haliman "to ai gashi yanzu ka ganni ko?" "Ammi kinga munyi sabon baby ko?,wai abba yace da ni yake kama?" Ya fada yana wasa da 'yan hannun jaririn dake cikin safar hannu,murmushi sumayya ta saki "Sosai ma,kama kai" murmushi ya saki cikin jin dadi,nan ya soma bata labarin makaranta,kai kawai take kadawa tana murmushi,ganin abun take kaman mafarki,kaman ba ita ta haifi abdallah,qaunar yaron nata da tausayinshi suka dinga ratsata,ta kasa daurewa har sai data dora hannunta saman kanshi sanda ya kawo mata ruwa mai sanyi ya ajjiye mata yace tasha ta shafa a hankali ta furta "Allah ya yi maka albarka kai da sabon qaninka mai kama da kai" "Amin ammi na", basu suka bar gidan ba sai dare,don sai data jiraci dawowar abdur rahman tayi masa barka,yaji dadin zuwan nata sosai,yayi zaune abinsa a cikisu,sun dan taba hira,wanda yawanci kam abdallah ne,yanayin baiwar da Allah yayi masq,akwai basira da hazaqar karatu qwarai da gaske,wanda hakan ya sanya ake masa tsallaken aji,a hasashensu bazai wuce shekara goma ba zai shiga j.s,kayan barka ta yiwa babyn masu yawa kyau da tsada,akwati guda,sannan ta yiwa halima atamfofi biyu lave biyu,mayafi takalmi da jaka,ta mata godiya itama,saidai bataso godiyan ba,don bata ga abinda zata samu nak duniya 'yan uwanta basu mora ba,sai wajen takwas suka koma gida bayan sun sauke zainab har qofar gidanta suka taho da abdallah,tace bata yafe zuwan ha itama sai anzo mata har gida,tayi murmushi ta amsa mata,ranta fes ta koma gida,baki daya 'yan uwan nata suna cikin rayuwarsu cikin wadata da walwala,ba wata maiatsala a cikinsu,ci sha sutura da muhalli mai kyau kowacce bakin gwargwado ta mallaka.        Washegari ya abbakar ya sake tareta suka sake lissafi kan dukiyar abdallah,abin ba'a cewa komai sai albarka Allah ke sawa dukiyar,ta nunku fiye da zatonsu,bayan sun gama ta fidda tsaraba cikin kwalaye wanda batasan da ita ba,almustapha ya tanada kawai taga ana sauke mata su,haka yake,mutum ne da idan zaiyi alkhairi bai fiya son a sani ba,zaiyi abunsa ne a boye,shi yasa ko zaman tsarabar bata san da shi ba,na mama daban na malam daban,har da yaya abbakar,saura yace ta baiwa wanda taga ya dace cikin 'yan uwa,sai yammaci ta sake shiryawa suka fice ita,abdallah,yusuf da nabila sai gidan anty yahanasu,ba qaramin murna tayi da ganinsu ba,duk da abdallah dama bai sati biyu abdur rahman bai kai mata shi ba,sun zauna hira nan taji duk abinda ke gudana,auren jamila da fatima Allah yayi za'a yi din,saidai kayan gado nason kawo tsaiko,don ma abdur rahman ya dauke nauyi duk abinda za'a ci ko a sha a bikin har a gama,kowa cikin dangi ya nade hannu,dama can danginsu ba masu riqe zumunci bane,hakan ya sanya ko sanda iyayensu suka mutu ita taci gaba da riqon mukhtar,sosai taji ba dadi,ta dauki nauyin kayan gadonsu jamilan da fatima,kunya da nauyinta suka ishesu,godiya suka dinga mata,itakam bata kula ba,iyalan mukhtar sunfi qarfin komai a wajenta,ko banza abdallah ya hada haduwar da babu rabuwa cikinta,data koma gida sukayi shawara da ya abbakar da malam,ta barwa yaya yahansu gidansu wanda suka zauna a qarshe ita da mukhtar kyauta,tunda yanzu dukiyar abdallah ba komai bane don su barwa yayan gidan,kuka kam haka ta dinga yinshi,har sai data saka sumayya qwalla,tace mata babu komai haka rayuwa dama take,nan yayan ta fara shiryen shiryen komawa,tunda fes yake akan shiha lokaci lokaci ayi gyara yaya abbakar bai barshi haka ha don kafa ya lalace,gidan da suke ciki kuma zasu saka 'yan haya,sumayya tace ta dinga amsar kudin tana buqatunta na yau da kullum da su.       Suna suka sha hankali kwance,tayi kyau sumayyan sosai,duk wanda ya santa idan ya kalleta sai ya sake dubanta,kana kallon nata zaka san cewa nutsuwa da kwanciyar hankali sun samu muhalli cikin rayuwarta,a nan ta barsu drivanta ya dauketa ya maidata gida wajen mama,tafison ta ganta kusa da ita. ********    ******   ********       Da safe suna zaune falon mama ita da abdallah,yusra da yusufa da maman suna karyawa,yaran na gabanta baki daya kowa na karyawa tana fama da su,gyarawa wancan kofi gyarawa wancan zama,kayan bacci je jikinta ko wanka bata yi ba,yunwar data ke ji ta sanyata zama karyawa,ya abbakar dake shirin fita shi ya shigo yana fadin "Mama...ga surukinki zai shigo ki gaisa...da alama sauri yake halan ka wucewa zasuyi" sam bata gane wa ya abbakar din yake nufi ba,kafin ta farga har mama ta masa izini,sai muryarshi taji a bakin falon yana niyyar shigowa.        Almustapha ne sanye cikin shadda dinkin tazarce,riga da wando,kanshi babu hula sai sumarshi dake kwance tana zuba qyalli,yayi kyau maqura har taji gabanta na faduwa sanda suka hada ido,ko yaya suka danyi kesa da juna na kwanaki sai taji ya sake zame mata sabo,ta soma tattare kofunan yayin da ya shigo ya tsugunna gaban maman yana gaidata,cikin jin kunya irin na surukuta suka gaisa,yana yi yana satar kallonta,ta kasa daga kai ta dubeshi kaman ta nutse,su yusra suka gaidashi yayin da abdallah ya isa gabanshi ya durqusa yana murmushi ya gaidashi,hannu ya miqa masa sukayi musabaha shina fuskanshi dauke da murmushi,yana son yaron sosai cikin zuciyarshi,saidai tarihin sumayyan da yaji yasan bazasu bashi shi ba,saidai yana kan bakanshi ko nan gaba sai ya dauke yaron,yadda yaron ua sake nutsuwa da girma sai yaji dama danshi ne,dama jininshi ne,saidai ko a yanzun yana jinsa cikin jikinsa tunda akwai jinin sumayya tattare da shi "Tashi kije mana sumayya" mama ta bata umarni sanda almustaphan ya gama gaisheta ua fita zuwa dakin saukar baqi,a kunyace ta amsa,ta koma daki ta zura hijabi ya sake feffesa turare,dui da cewa qamshi ya kama jikinta,ko daga bacci ta tashi baka rasa jin qamshi a jikinta,don sai ta shafe loko da saqo na jikinta da turare ko ba kwananta bane kuwa,ko da basu tare.        Yana tare da abdallah hannunshi cikin nashi,da alama tambayoyi yake masa kan karatunshi,yana bashi amsa,kuma yana bashi amsa yadda ya kamata don akwai alamun gamsuwa tattare da shi,shigowarta ya sanya abdallan zame hannunshi ya fita ya basu waje,tsaye tayi suna duban juna,ya miqe ya isa gareta ya hadata da jikinsa "Meye haka?,salon horo ne ko kuwa?,ni zakiyiwa qwalele?,kinsam bazan juri kallonki haka ba ko?" Murmushi ta saka tana ajiye boyayyar ajiyar zuciya,dududud satinsu guda basu ha juna ba amma tana jin kaman sun yi wasu watanni masu dama "Tsoro nake ji ne?" Ta furta a hankali "Tsoron me?" "Ina tsoron ko kazo tafiya da nine ba tare da na shirya ba,in sake tafiya in bar mama" murmushi mai sauti ya subuce masa,sannan ya soma rada mata "Hakan naso matata,saboda mi kadai nasan yadda nayi kewarki,saidai idan hakan bai miki ba...zan iya zama na jiraki har tsahon sanda zaki gama abinda kike yi,ba abinda bazan miki ba,kinsan saboda me?" Kai ta girgiza alamar a'ah,sai ya juyo da ita suna fuskantar juna idanunshi cikin nata "Ke din macace ta musamman,mai fifita farincikin mijinta akan nata,mai fifita buqatarta akan tasa,ina sane da cewa,sau tari kikan dauki zabina ki bar naki,kikan gabatar da komai nawa gaban naki,kin maida kanki tamkar baiwa a gareni" sai ya saketa ya durqusa gabanta kan gwiwarsa "Don me nima bazan zama bawa a wajenki ba?,wannan shine qarshen adalcin da zan miki,Allah ya halicci zuciya da son mai kyautata mata da qi da kuma gudun duk abinda zai munana mata" bata ankara ba qwallar zallar farinciki ta subuce mata cakude da murmushi,jin kanta take tana shawagi a sama,cikin wata duniya wadda take mata kwatankwanci da duniyar SARAUTAR MATA,sai ya miqe da hanzari ya rungumeta ta baya saboda cikinta ya masa shamaki ta gaba,sun jima a haka sannan ya janye yana dauke mata hawayen da yatsansa "Ko a yanzun ma ka buqaci mu tafi ni mai biyayya ce a gareka" kai yake girgizawa cikin farinciki "A'ah....kije ki gama shirinki a nutse" kai itama ta girgiza "Um...um,bazan barka kana jira ba haka noor,kaje ka dawo" "Na yadda,amma zaki rakani asibiti?,zanje na duba bayin Allah" "Sam'an wa d'a atan noor" murmushi ya saki kalman ta masa dadi,kissing dinta yayi sosai,sannan yace mata zaya dawo da yammar su je.         A nutse ta fara shirinta,tana yi lokaci lokaci murmushi na qwace mata,lallai kam gaskiyar masu magana da suke cewa namiji tamkar yaro yake,sannan idan kika maida kanki baiwa shima zai zamto bawa a wajenki musamman idan yasan suka haqqoqinki da Allah ya dora masa.        Da la'asar sakaliya ya iso kuwa,ya dauketa suka tafi,a nan yake tambayarta abdallah,tace babanshi yazo ua dauke abinsa,tana dariya tace shikam ko yauahe gani yake kaman zan daukeshi ne "Akwai kam lokaci,lokacin da zamu daukeshin kuma babu yadda zaiyi" murmushi tayi don bata data cewa,kaman kowanne lokaci sunji dadin zuwanshi,suka dinga gaidasu cikin girmamawa,kan ya wuce office sai da ya bincika,komai yana tafiya kan tsari da kulawa tamkar yana nan,daga bisani suka wuce office din yana maqale da ita.       Murmushi yaga taba saki sanda suka shiga office din,ya tambayeta mai ya fari?,sai ta kada kai tace mishi ba komai,kamota yayi ya matseta,ta saki qara a shagwabe,ya sake tambayarta,cikin muryarta mai sanyi tace "Kawai ina tuna last zuwanmu office din nan,abinda ya faru" shima ya tuna sai ya saki murmushi ya lumshe idanunsa ya bude sannan ya kashe mata ido "Na tuna babe....amma kada ki soma cewa zaki tsokaneni....kinsan me?,wani kwarjini kikamin wanda ban taba jin wata diya mace duk fadin duniya tun tasowata tamin ba a sannan na kasa miki scan,sannan ga wani shock da naji sanda naga skin dinki....kai babe,you are unique wlh" dariya ta saki ta dora kanta kan qirjinsa,daga gefe idanunta suka sauka kan hotunan mukhtar dake saman table dinsa,ta qurawa hotunan idanu,a hankali ya maida kansa inda yaga ta maida hankalinta,sai ya jata zuwa wajen,ya sanya hannu ya daga hoton yana kalla kafin ya dubeta "Mukhtar?" Ya fada cikin sigar tambaya,idanu kawai ta zubawa almustaphan "Am sorry" ya fada sannan ya hadesu waje guda ya yagasu qananu ya ajjiye saman teburin sannan ya waiwayo ya dubeta "Ina da kishi a kanki babe.....am sorry if i hurt you" ya fadi yana duban idanunta da son karantar yanayinta,saidai taqi bashi dama,hannunta ya kama yana ci gaba da kallonta bayan ya matso da ita dab da shi har suna musayar numfashi "Na yarje miki ki masa addu'a,ki sashi a addu'o'inki,amma banda nan" ya dora hannunshi saitin zuciyarta "Nan din mallakata ce ni daya har ABADAN"knocking din da aka yi shi ya qwaceta,don ya soma dora mata wani nauyi,tamkar yana jiran amsar da zata bashi,daya daga cikin nurses din ne ta shigo dauke da file na mutanen da zai gani,cikin harshen turanci ya tambayeta na mutum nawa ne?,tace masa talatin,yace mata ta rage guda goman qarshe ta maida musu ashirin zai iya gani "Sir....suna son ganinka da gaske ne goman da kace a cire din...."da hannu ya dakatar da ita kana ya mata nuni da idanu kan ta rage kaman yadda yace mata,qarasawa tayi ta irga ta debe din,sumayya ta matso kusa da shi murya can qasa "sorry sir,ayi haquri a gansu" hararar wasa ya jefa mata "Ke zaki tayani?,da wuya fa?" "Na maka alqawarin ba zaka gaji ba,ina gefanka fa?" "Really?" Ya fada yana dage mata girarsa guda daya,idanunta ta juya kafin tace "Yes sir" tana sakin murmushi,kiranta yayi ta dawo da su din sannan ya sa mata kujera daura da shi ta zauna,da dai dai da dai dai patient ke shigowa yana dubasu,wani abun wanda yasan zata iya ya sanyata ta tayashi,wanda ba zata iya ba kuma yayi abinshi tana kallo,suna tsaka da haka wata budurwa ta shigo,kana kallonta kasan tana ji da kanta,cikin yauqi ta zauna kan kujerar da marasa lafiyan ke zama suyi bayani,sai fama take tana wani basarwa,sam bai daga kai ba bare yasan wanda ya shigo,hankalinshi na kan sumayya dake cike takardar wadda ta fita take shigar da wasu abubuwa da yace ta shigar,akwai fikira tattare da ita da basira mai dimbin yawa,komai tayi sai kaga hikima a ciki,tamkar likita haka ta tsara komai yana kallonta murmushi irin na gefen baki na fita kadan kadan,hakan ya sake sanyawa ya tafi da patient din data shigo "Me kika karanta ne?" Ya tambayi sumayya fa kanta ke duqe tana rubuta kwanan wata,dubanshi tazo yi sai suka hada idanu da ita tana dubansu,hakan ya sanya maimakon ta bashi amsa sai ta masa alama da idanu na ana jiranshi,sai a sannan ya dauke kai ya dubi patient din,murmushi ta sakar masa,ya dauke kai yana bude file din nata "Me sunanki?" Ya tambaya saboda yaga kaman ba suna kan file din da alama sabo ne "Meela" ta bashi amsa tana yauqi "Meye ne meela?" Ya tambaya a akausashe don ya soma jin haushin yadda take wani gwalangwaso "Eh da shi ake kira ne amma real name din ja...." "go straight to the point,akwai masu jira,meke damunki?" Ya tambaya yana rubuce rubucensa,sumayya na gefe dariya na son qwace mata,ya koma sak doctor almustaphan dan gidan baba prof data sani a baya,nuqu nuqu ta soma yi saboda ganin sumayya a wajen,tsaf ya karanceta,sai kawai ya rufe file din nata ya tura mata gabanta "Zaki iya tafiya" ya fada yana kafeta da mayun idanunshi "Ai..ai sirri ne" ta fada cikin in ina,juyawa yayi ya dubi sumayya da dariya ke ci,amma sai ka zata batasan meke faruwa ba "I said the door is opened ko?" Ganin cewa da gaske yake ya sanya ta samawa kanta nutsuwa ta soma masa bayani,magunguna ya rubuta mata yace taje ta karba ya sallameta ta miqe ta fice. Dariya sosai sumayya ta saki kafin nxt patient ta shigo "Me?" Ya tambayeta yana kallonta,da kanshi kuma ya saki fuskar yana dariya,ya gane me takema dariyan,sai ya cafko yatsunta ya soma lanqwasa mata,ga dariya ga zafin lanqwasa matan da yake,da qyar ta qwaci kanta "Ku kam mata wlh i dont know.....kai...kai" ya fadi ba tare da ya gama fadan me zaice din ba "Duka ke kika jawomin,da tuni na gama mun tafi ina gida ina hutawa,ko baby bamu gaisa da shi ba" ya fada yana shafa cikinta,turo qofan da akayi ya sanyashi janye hannun nashi,a nutse yaci gaba da dubasun har ya gama sannan suka tattara suka nufi gida. Cikin falon nashi dake dauke da dakin bacci biyu suka sameta kwance tana kallo,sanye da riga shimi doguwa zuwa gwiwa,gajeran hannu ne da ita hannun vest,ciki ciki ta amsa sallamar tasu sannan ta daga ido ta bisu da kallo. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 1⃣0⃣5⃣ *Bismillahir rahmanir rahim* *Allah S W T yana bayyana kansa cikin qur'ani mai girma da* *FA'AALIL LIMA YURID(mai aikata abinda yakeso* *ya Allah muna gareka kayi mana jagoranci* _____________________________________ *Wannan shafi sadaukarwa ne ga* *HAUWA'U AG tare da diyanta AHMAD*         Ba wanda ta amsa sallamarsa a cikinsu,hakan ya sanya sumayya tayi wucewarta ba tare data sake cewa komai ba.         Satinsu biyu dai dai a kano suka koma dubai,bayan sun ziyarci gidan maimmartaba sarkin rano,mahaifin ummi,tsoho mai ran qarfe,karon farko kenan da sumayya ta kai ziyara,tsantsar soyayyar da tsohon kewa almustaphan ta shafi sumayya,kowa haba haba yake da su yana neman wajen ajjiuesu,taga kara taga karamci,ba qaramin dadi zuwan yayi mata ba,duk da bata samu zuwa gidajen sauran 'yan uwa ba,amma tayi alqawarin duk sanda tazo kano toba shakka zata sake zuwa musu,kyautar girma tsohon yayi musu shida matanshi,duk da mahaifiyar ummi ta rasu,amma matan baban nata sun daukeata tamkar diyarsu,suna farinciki da juna suka rabu,tun a sannan ummi taso riqe sumayya har sai ta haihu amma almustapha ya shafawa idonshi kwalli yace ba yanzu ba zai kawota idan lokacin yayi,yayin da cikin zuciyarshi ma sam ba haka bane,don baida niyyar kawota din,yana ganin meye amfaninsa a matsayinsa na likita kenan.       A hankali kwanaki suka ci gaba da wucewa,ba abinda ta daga qafa ko ta sauya game da kyautatawar da takewa almustaphan,dukkan wani abu data sani cewa yana so takan sanyashi gaba da komai nata,lamarin su'ad kam sam baya damunta,duk wani iskancinta da tambotsanta basa gabanta,sai taga dama ma zata ganta bare wani sabga ya hadasu,abu daya take qoqari a kai shine tausar almustapha a duk sanda ta kunnoshi,sam bazata so ace su'ad din tabar gidan na,kullum fatanta shine Allah ya shiryata ta gane illar abinda take yi,ta tabbatar da cewa duk duniya bata da wata mafita matsawar almustapha ya sawwaqewa su'ad tofa za'a ce itace sila,bayan duk wanda zaiyi alqalancin baisan meke wakana game da zamantakewar auren su'ad din cikin gidan ba,saidai hasashe dai kawai.        A haka cikinta ya shiga watanni tara har ya soma yunqirin shiga na goma,kallo daya zaka mata ba zaka so sake dubanta ba sabida tausayi,sosai cikin yayi wani girma har wani lokaci sai ta tallafeshi idan tana tafiya saboda girmansa da yadda ya sauko qasa,ta sauya kamanni sosai kamar ba sumayyan ba,munin da tayi a da nafila ne,har bata son kallon kanta a mudubi,sau tari idan taga almustapha na kallonta sai ta kau da kai tana tunanin munin da tayi yake kallp,saidai shi sam ba haka bane cikin zuciyarshi,tsananin tausayinta ke damunshi,ba don kada yayi riga malam masallaci ba da tuni ya yankata ya cire mata cikin ta huta,yakan tallafo fuskarta ya saki murmushi "Ki daina boyen fuskarki,a hakan kinmin kyan da ban taba ganin kin yimin irinsa ba,kinsan me?" Sai ta kada kai cikin murmushi "Da zaki sake zama haka nan da wata takwas ma bayan kin haife wannan cikin ina so,da nafi kowa murna" "Kayimin addu'a Allah ya rabani da wannan ma lafiya" "Yadda zuqar numfashina ya zamemin dole haka wannan addu'ar ta zamemin dole" ya fada yana karata da jikinsa tare da shafa bayanta a hankali yana ci gaba da yi mata addu'a cikin ranshi.        Semina ce ta kamashi ta sati guda wadda za'a yi a china ta 'yan kasuwa,sam yace ba zashi ba,ita ta tausashi da qyar tace ba'a jiran haihuwa sai sanda Allah ya kawota,ko kadan baison tafiya don ko fita ya rage,tausayi take bashi matuqa,hatta tashi sai tayi da gaske take iya yinsa ko shi ya dagata,ita ta tayashi hada kayanshi tana yi tana tsokanarshi wai ya zama rago,jawota yayi jikinsa yana dan mintsinarta yadda ba zata ji zafi ba yana murmushi "Laifin wa?uhmmm babe,bake kika maidani haka ba?" Dariya ta saki,ta jawo hannunsa ta dora saman cikinta "Laifin wannan ne ba nawa ba"sake matseta yayi a jikinsa yana sakin murmushi,tasan duka hanyar da zata sashi nishadi.        Sai da ya hadata da babban asibitin dake qasar wanda anan yake musu aiki lokaci lokaci,ya basu lambarta lambar gidan da adress,sannan itama ya bata number dinsu,sannan ya karba mata nurse guda daya wanda suka tanada saboda jinyar marasa lafiya wadda zata dinga zuwa tana kwana da ita,sam bai fadawa ummi ba don ya tabbatar cewa zatayi ya turota nigeria,shikuwa baison ko daya abinda zai rabashi da ita dai dai da minti daya        Tattaki ta masa har zuwa cikin falonta,kasancewar ranar girkinta ne,ya jawota kusa da shi ya riqe dukkanin hannayenta cikin nashi yana duban qwayar idanunta "Kimin alqawari zaki kulamin da kanki har na dawo,ba tunani ba damuwa,kinyi alqawari?" Murmushi ta sakar masa mai kwantar da zuciya ta gyada kai "Nayi maka noor,Allah ya tsaremin kai ya dawo min da kai lafiya" "Amiiin baby na" ya furta yana lumshe idanunsa sannan ya matso da ita gab da shi yayi kissing goshinta zuwa wuyanta.        Tare da su'ad suka rakoshi har bakin mota,sai da driver ya ja suka fice sannan kowacce ta juya zuwa ciki,wani kallon banza take jifar sumayyan da shi gami da jan dogon tsaki,bata kulata ba don idan da sabo ta saba,tayi wucewarta ciki abinta.    *******    ****   ********      Bayan kwanaki biyar da tafiyarshi ne inda suke saka ran dawowarshi jibi,tun safe take jin ciwon mara kadan kadan,saidai bata gayawa ko nurse dinta ba saboda tunda cikinta ya shiga wata na goma take fama da irin hakan kadan kadan lokaci zuwa lokaci,yanzun ma fitsari ne ya tasheta,sai data dauki a qalla minti biyar ta iya yunqurawa ta miqe,mararta ta amsa sai data ce wash sannan ta iya miqewa a daddafe ta qarasa bandakin mararta na ciwo sosai,koda taje fitsarin kadan tayi sai ciwon da ya dadu,dawowa tayi cikin dakin ta soma kai kawo a tsakar dakin,a jikinta take ji tabbas naquda take,bata da maraba da abinda take ji lokacin haihuwar abdallah.       Tsahon awa daya tana gumurzu babu sassauci,hakan ya sanya ta fito falo a daddafe,ta dauki waya ta kira lambar nurse din,cikin sakanni kadan ta iso ta dubata ta tabbatar haihuwa ce,saidai akwai saura,asibitin ta sanarwa,babu jimawa saiga mota sun aiko da ita suka daukesu suka wuce,su'ad taji motsinsu,ta dauka wasu ne ta leqo da taga sune ta koma tayi kwanciyarta abinta.       Daki ne na musamman suka bata,dauke da na'urori kala daban daban bayan ta sauya riga zuwa ta asibiti,tun tana daure ciwon har abun ya soma wuce tunaninta,naquda take haiqan saidai haihuwa tawi zuwa,tun biyu na dare har gari ya waye haihuwa bata zo ba,daga gefan almustaphan ya kira wayarta yafi a qirga saidai ba amsa,saboda sun baro wayar a gida,ya kira su'ad tace bata sani ba,bata gama bashi cikakkiyar amsa ba ma ta kashe wayarta,yayita kira switchoff,take hankalinsa ya tashi,sai sannan yayi dana sanin me yasa ko baba uwani baisa an kawo ba?,kai tsaye ya kira asibitin nan suka shaida masa tana nan tun daren jiya,ranshi ya baci hankalinsa ya tashi,fada ya hauyi kan me yasa basu shaida masa ba?,sannan ya za'ayi su barta tun jiya har yanzu wayewar gari tana naquda har ta kusa cinye awanni da aqa'idar likitoci ba'a so ta gama su bata haihu ba,haquri suka shiga bashi,bai sauraresu ba ya katse layin ya soma tattara ya nasa ya nasa ba tare da ya kammala abinda ya kaishi ba,hankalinsa gaba daya yayo dubai,jinsa yake kaman yayi tsuntsuwa ya ganshi a can.         Qarfe hudu na yamma ya iso dubai,kai tsaye ya yiwa drivan umarni ya wuce da shi asibitin,kai tsaye ya wuce dakin da take,kwance take saman gadon,kallo daya zaka mata kasan cewa ta jigata qwarai,duk sanyin dake dakin bai hanata gumi ba,muryarshi kawai taji ta daga kanta taba dubanshi,tuni ya ajjiye jakar dake hannunsa ya qarasa inda take,nurses din dake dakin suka fice daya bayan daya,tafin hannunta ya laluba ya sanya nashi hannun ciki,hannunsa saman kanta yana shafawa a hankali,baki daya zuciyarsa ta karye "Baby......sannu baby" ya fada idanunsa cikin nata,ga mamakinsa murmushi ta sakar masa a wahalce "Ka dawo?" "Eh...." Maganar tasa ta katse sanda ta furta "Hasbunallahu wa ni'imal wakil!" Cikin madaukakin sauti ta soma murqususu cikin matsanancin ciwon da ya taso gadan gadan,tamkar dama jiran zuwan almustaphan yake,yanayin yadda yaga tanayi ya sanyashi sake dubata da kanshi,nan ya tabbatar haihuwar ce,nurses din da suka fita ya kirawo don su taimaka masa,din bashi da qwarin gwiwar da zai iya karbar haihuwar shi kadai,yana riqe da ita yana gaya mata addu'o'i tana maimaitawa cikin wahala,a qalla mintuna goma kafin jaririyar ta samu isowa duniya,kukanta ya karade ilahirin dakin baki daya har zuwa waje,basu gama tantance komai ba ta sake wani yunqurin,wani sabon kukan ya sake karade dakin suka hadu suka cika ilahirin dakin zuwa harabar dakunan da kukansu,nurses din ne suka dauke yaran yayin da baki daya hankalinsa ya raja'a a kanta,gumin da ya mata sharkaf ya soma goge mata yana jero mata sannu babu qaqqautawa,dubanshi take yadda ya rude baki daya,kukan yaran na yawo cikin kwanyarta,tasbihi take wa ubangijin talikai,yau gata a karo na biyu ta sake samun diyoyi,diyoyin da suka fito daga tsatsonta,kasa dauke idanunata tayi daga shiyyar da yaran suke sankda nurses suka gama rabasu,kukansu suke sosai suna wutsil wutsil da qafafu da hannyensu,sakayau a yanzu take jinta kamar sun fita da duk wani ciwo dake damunta.        Cikin mintuna qalilan nurses din suka soma gyara yaran,shi kuma ya gyara ta da kanshi a wani daki daban,komai ya kammala,aka maidata zuwa wani dakin ita da yaran baki daya.         Zaune take saman gadon sosai tana jingine da bango,murmushi ne sosai kan fuskarta wanda har sai da ya sanya haqoranta bayyana,idanunta taf da qwalla sanda almustapha yake nufota dauke da daya daga cikin jariran wadda ke nannade cikin wasu irin kayan sanyi masu azabar kyau set da abun daukansu,gabanta ya qaraso shima idanunsa cike da qwalla yana dubanta tare da duban babyn,miqa mata ita yayi sai ta dauke idanunta qwallar data cika mata idanu tana gangaro mata saidai har yau murmushin dake kan fuskarta bai bace ba,da hanzari ua sake matsarta ya kama hannunta yana matsawa cikin rauni da rawar muryar da bata taba ji daga gareshi ba yace "Kada kice zaki ji kunya babe....karbi diyarki ki gani in dauko miki dayar....duniyarmu ce baby duniyarmu....daga ni sai ke sai su karbi ki gani", ya qarashe maganar yana dora mata yarinyar saman cinyarta,tuni ta sanya hannu ta karbeta,cikin sakanni qalilan qaunar data ke musu taji ta soma ninkuwa cikin zuciyarta,sak jinin gidan baba prof,kana dubanta ko makaho ya shafa yasan jikar mutanen gwambe ce,photocopy na almustapha,sake komawa yayi ya dauko dayar ya dawo saman gadon ya zauna sosai kusa da ita yana bude mata fuskarta " kalli usaina baby.....ba wadda ta miki kara?"ya fafa yana sakin dariya wadda ke qunshe da zallar farinciki,jinsa yake yau kaf duniya babu dan adam din da ya kaishi farinciki,ba wanda kuma ya kaishi sa'ar zuwa duniya,itakam murmushi kawai take bakinta ya gaza furta komai,Allah kenan,buwayi gagara misali,cikin rayuwarta kaf bata taba kawowa kanta haihuwa bama bare kuma aje ga haihuwar 'yan biyu,dai gashi a yau,Allah yayi mata kyautar da bata taba hasashenta ba,haqiqa Allah mai tsananin karamci ne,sosai almustaphan ya dinga sumbatu wanda tasan na tsantsar farinciki ne tana dubanshi tana dariya,ita din ma jinta take saman wata duniya ta farinciki tana yawo,ta kasa dauke idanunta daga yaram,ba don yaranta bane,amma zata iya cewa bata taba ganin jarirai masu ban sha'awa irinsu ba,sam ya mance da ya wanu kira gida ya fada sai data tuna mishi,a sannan ne ya dauko wayarshi,ummi ce mutum ta farko da ya soma kira,danda yake gaya mata tsaye ta miqe tana kabbara,bata qarasa jin zancan ba ta rankaya falon baba,saidai kash kafin ta isa tuni anty maamaa ta rigata kai labarin,wanda ta jishi je sanda take shigowa wajen ummi,a take baban ya mata kyautar kudi masu tsoka,ta dinga ma ummi dariya tana cewa saidai a tara a gaba,itama dariyan ta dinga tace rabonki ne,duk yadda baban yaso sakaya farincikinsa abun yaci tura,haka shima ya dauki waya ya dinga kiran abokai da 'yan uwa yana sanar musu,cikin lokaci qanqani labarin haihuwar ya karade kowanne sakaye,tsakanin baba da malam sai aka rasa wanda za'a yiwa murna,amira kuwa da anty dije kukan farinciki suka sanya,ta dinga kiran almustaphan tana roqonshi zata taho yace sam,sai ta saka kuka,tana so ace cikin dangi itace mutum ta farko data fara daukan yaran,abu daya ne ya saka mata haquri hoton yaran da ya dauka ya tura mata ta email adress dinta,don shi baya watsapp.       Da kanshi ua sallami matarshi bayan ya tabbatar da cewa komai lafiya suka kama hanya zuwa gida,yana bayan motar shi da ita,baki daya yaran na hannunshi ya hana mata ko daya,ji yake idan ya rufe idanu zaiga kamar mafarki kamar almara,ashe duk arziqinka duk dukiyarka,duk farincikin da kake taqama kana ciki bai gama kammaluwa ba matuqar baka samu diyoyin da zaka alaqanta da jininka ba,ashe zallar farincikin da zata fadeshi sai randa ka ganka dauke da zuriya taka ta kanka.         Daidai sanda suka nufi gidan su'ad na tsaye tsakar dakinta tana amsawa wayar da suke da mahaifiyarta "Nifa gaskiya su'ad na soma sarewa,kinga tsantsar farinciki da doki da professor yake ciki sanda ya kira mahaifinki kamar ranar aka soma haifa masa jikoki,anya kuwa su'ad ba muyi kuskure ba?,ina da yaqinin Allah kadai yasan dukiyar da zasu samu su kuma mallaka tun suna qananunsu,wanda dukkan abinda suka samu zai koma fa hannun mahaifiyarsu ne" qatuwar ajiyar zuciya ta saki "Bama wannan ba momy,wallahi na tabbatar na shiha uku,duk wani soyayya da tattali da adalci da almustapha ke qoqarin gwadamin ina da yaqinin sai ta ragu,tun cikin bai fito duniya ba kinga abinda yake?,ina ga ya fito sannan kuma twince mommy?,shi yasa nake tunani anya ba zamu sake plan ba?,na nemi dalilin haihuwa nima ko don na sake janyo hankalinshi zuwa gareni baki daya?" "Dqlla can rufewa mutane baki,ke ta soyayyarsa ma kadai kike,soyayyar vanza,ana miki maganar kudi abokan tafiya qare magana,so nake fa ki zama cikin jerin attajiran da duniya ke lissafinsu kaman yadda a yanzu mijin naki yake,ke kadai ce fa 'yata ke daya na mallaka,saboda haka ina so naga kinyi shaharar da ko d'a namijin da yayi shekara arba'in yana gwagwarmaya baiyita ba" "To yanzu ya za'a yi momy?" "Cikin satin nan kisan yadda zakiyi kizo nan mu warwareta" "An gama" ta fada tana katse wayar saboda motsi da taji kaman ana shigowa,a hankali ta tako ta fito zuwa falon,almustapha ne riqe da baby daya,wata mace mawociyarsu 'yar asalin qasar saudiyya dauke da dayan,fuskarta a washe tana tana yaba kyawu da girman yaran cikin harshen larabci,duk da bata fahimtar me take fada amma daga yanayin matar tasan tana yabawa ne da yadda yaran suke,idanu ta zuba musu tana karantar fuskar almustapha wanda bata san da dawowarshi ba saibyanzu,tunda sukayi magana ya tambayeta sumayya tace bata sani ba bai kuma kira ba hakanan bata bi ta kanshi ha itama,iya tsahon zamanta da shi bata taba ganinshi cikin wannan hali na matsanancin farinciki ba, saidai ba wanda ya kula da ita a cikinsu saboda tana daga bayan labule ne har suka shige.       Yana fitowa daga dakin ya lura da ita,fuskarshi sake yake dubanta,bacin rai da take dannewa ya taso yafi qarfinta,sai kawai kuka ya qwace mata,sai ta juya da gudu gudu ta koma ciki,tausayinta ne ya sauko masa lokaci guda,yana tunanin rashin samun tata haihuwar shi ya motsa mata,wanda hakan zai iya faruwa ga kowacce mace,kowanne lokaci kuma yanayin kan iya motsuwa cikin zuciyarki har ki kasa controlling din kanki,sai ya rufa mata baya,samunta yayi kuwa zaune saman kujera tana buge buge da hannunta,dama ace dama ace ce fal cikin zuciyarta,zata so a ce itace ta samu wannan yaran ba sumayya ba,wai shin me ya hanata tsayawa ko guda daya ta samu ne?,ba shakka tana ji a jikinta lokaci yayi da zata tashi ta dawowa da kanta dama ta samun haihuwa a gareta,a tausashe ya zauna gefanta yana riqeta,baison idan wani abu ya sameta ta dinga irin wannan acting din dake nuna zallar rashin yarda da qaddara,cikin taushi ya soma ce mata "Am sorry dear....ba kuka zakiyi ba,addu'a zakiyi Allah ya kawo mana,komai a duniya yana da lokaci sannan komai yai farko yana da qarshe banda ikon Allah,matuqar kina da rabo ta babu makawa sai kin haifa kema" "Ko bani da rabo wallahi sai na yishi,sai na haihu nima" tsauri maganar tayi masa,haqiqa ba qaramin illa da tasiri dabi'un yahudawa marasa tauhidi suka yiwa su'ad din ha,saidai yana da burin sosai wajen ganin ta daidaitu,duk da hakan ma alhamdulillah,ya rabata da shigar banza ya sata tsaida sallah,koda kuwa zata yita ne bayan wucewar lokacinta "Subhanallah,kiyi istigfari,babu bawan da yafi qarfin QADDARA,saidai addu'a na maida MUMMUNAR QADDARA ta koma zuwa KYAKKYAWA,ki roqi Allah sai ya kawo komai a sauqaqe,ba wayonki ko dabararki ba,ita kanta ada can an taba kiranta juya,an fidda mata rai zata haihu,amma a yanzu gashi ke ya faru?" Cikin hikima yake gaya kata kalaman kwantar da hankali,saidai jinsu take kaman busat sarewq,abu daya ne ya dan kwantar mata da hankali,kasancewa da yayi tare da ita duk da ba ranarta bace,da kuma yadda yake lallashinta,saidai ba shakka cikin satin nan zata san yadda zata wuce america don bazata juri rasa cika burin data qudurtawa ranta ba.       Maqota biyu da suke da su wadanda ba yarenta ba saidai 'yan uwantaka ta muslunci da tsananin kirki da suke da shi,wanda batasan suna da shi ba sai yanzun da haihuwar 'yan biyu dake da farinjini suka sa tasan hakan,suna kula da ita sosai,akai akai suke leqota da kalar abinci da kulawa da sukewa maijego,akwai mai tayata zama guda daya daya samu wanda ta kasance mutuwar qasar ghana ce,zaman sana'a yasa take zaune a qasar,sai ta kasancewa sumayya tamkar yar uwa,sosai matar ke kula da ita,tana da qoqari da zafin nama qwarai,babu abinda sumayyan ta nema ta rasa,hatta da shi mai gayya mai aikin idan ya fita sha daya,biyat na yammaci ya dawo gida,koda yashe burinsa ya ganshi tare da su,a haka ma idanun su'ad yasa ya dan rage wasu abubuwa tare da danne daukinsa,don har ga Allah tausayinta yake ji,yasan cewa rashin haihuwa babbar damuwa ce dakan iya zamewa wasu matan ciwo cikin zukatansu,abinda bai sani ba shine ta soma girbar abinda ta shuka ne ba tare da shi karan kanshi ya sani ba,wani tsananin son hauhuwa ne ya mata mugun kamu cikin kwanakin da basu haza hudu ba,sosai walwala da kuzarinta ya ragu,kishin yaran da uwarsu baki daya ya gallabeta,ko sau daya tak bata taba kusantar dakin sumayya ba bare tace zata ga yaran,wani abu ke tokare mata wuya duk sanda taji sautin kukansu,ji take kaman ta kaudasu ko ta samu hutu.        Daga daya bangaren kuma tuni ummi ta gama duk wani shirinta na zuwan yaran da mamarsu,kwana biyu taji shiru hakan ne yasa ta tuntubeshi,sai yace 'yar matsala ce aka samu wajen siyan ticket,tuni ta baroshi,wanne matsala ce za'a samu wajen siyan ticket kawai?,shi kansa yasan qaryar bata hadu ba saboda ba sabonshi bace,ko kadan ne kawai baya son su tafi su barshi,baya jin zaman garin zai yiwu gareshi idan suka tafi din,shi a son ranshi duk maison zuwa cikin gidan nasu zai siya masa ticket,wanda bai da visa zai masa suzo suga yaran,sam bazaiyiwu ba ummi ta gaya masa,su a wajensu tamkar haihuwar fari ne,saboda haka dole ya kawo 'yar mutane a kula da ita sosai,sannan itama tana da yan uwa tana son zama cikinsu ai,shikam baiga wacce kulawa akeson bata ba bayan wanda take samu nan daga wajensa,yana kallonta take saka towel cikin tafasasheshen ruwa ta gasa kanta sosai,ta fito taci abinciccika masu gina jiki,ga magungunan da yasa zasuyi mata matuqar amfani a jiki da take sha,hakan ya sanya hatta da ruwan nono ta samu wadatacce,kana kallonsu zaka san kulawa kam sun sameta,daga ita har yaran kai kace sunfi kwanaki hudu da haihuwar,warshe dai haquri ya baiwa ummi yace suna tahowa.        Sai ana ya gobe zasu cika kwanaki bakwai sannan ya siya musu ticket har da shi da su'ad zasu tafi,dakin su'ad ya fara zuwa,ya taddata zaune tana latse latsen waya,sam sumayya bata gaya mishi bata taba zuwa taga yaran ba,shima kuma bai taba kawo ba zata shiga din ba,gefanta ya samu ya zauna yana fuskantar fuskarshi a sake sosai,kai ta daga ta dubeshi,as usal bata iya sannu da zuwa ba ko gaisuwa "Baki gajiya da danna waya?" Ya tambaya yana daukar remote ya rage saitin kidan dake tashi a tv "Idan ban danna ba me kake so nayi?" Ta tambayeshi cikin yanayin bacin rai,idanu ya zuba mata yana karantar yanayinta,sai kuma ya hadiye ya dauke kanshi daga fuskarta yaba bata amsa "Karatun qur'ani,istigfari da sauransu" "K'nnnnn" ta ce a taqaice,tun daga ranar zuciyarta da shaidan suke gaya mata ta gama burge almustapha fa,yanzu ba sonta yake ba ba kuma qaunarta yake ba,yaranshi da uwarsu su kadai yake so da qauna,bayan babu wani abu da yayi mata wanda ke nuna haman,illa ma lallashinta da yake saboda yana tunanin rashin samun nata yaran na kanta ke damunta "Gobe zamu shiga nigeria,su ummi sun matsa sai mun dawo a yi suna a can kowa yaga yara"qafafunta ta miqe ranta na baci "wannan ku ta shafa sai kun dawo" idanunsa ya qanqance yana dubanta,wati mai hali bai fasa halinsa,duk yadda yake tattali da rarrashinta wato shi din banza ne baisan ciwon kanshi ba? "Kamar yaya fa?" Ta tambayeta yana son qarin bayani "Ai suma su ummin tsabar gulma ce,babu gidan uban da zani,wato nake inje aji dadin nuna ni gani ban haihu ba wata tazo bayan bayana ta haihu ko?,to bazanje ba,dama an dade ana ruwa qasa na tsotsewa,muna fukin auren ma duk ha sune sila ba sabida kai an tsaneka ba'a sonka" cikin tsananin bacin rai ya daka mata tsawa,nunata yake da yatsa cikin bacin rai "Hey idiot.....Kar ki soma kuskuren fadin maganar banza kan mahaifana,ki kintsa bakinki kada furucinka ya jawo miki nadama......iyayena sun fiye komai da komai da na mallaka nake da shi,su din wasu abubuwane masu daraja da babu kamarsu,kudi ko qarfin iko basu isa su baka su ba.....ban gaya miki zamu nijeria ba wai don ina neman shawararki ba,umarni nake baki kaman yadda wadanda suka isa da ni suka bani umarni nabi,kema dole kibi umarni na don na isa da ke" ya miqe yana niyyar ficewa ranshi a bace "To wallahi ba inda zani daga nan nima gidanmu zan wuce ai ina da gidan uba...." Waiwayowa yayi yana mata wani kallo daya sanyata rusuna ba tare data shirya ba "Really?,....ok,indai haka ne idan kinje kada ki sake ki dawomin gida kinji ko?,ruwanki kije nigeria ruwanki kije ameria amma ki zauna acan,kada qafarki ta dawo gidan muhammad almustapha" yana kaiwa nan ya wuce yana mai buga qofar cikin fushi,kanta ta dafe,tabbas bata da wata mafita,zai iya aikata dukkan abinda yace din,saidai ta gama rayawa ranta abinda zatayi,zuwa gida babu fashi.           Da sallama bakinsa ya shiga dakin sanda take gaban sif tana fidda kayansu tana shiryawa cikin akwati,yaran na kwance cikin gadonsu suna bacci hankalinsu kwance,cukin tsafta da qamshi,a qunshe suke cikin kayan baby masu taushi pink,yanayin muryarshi kawai taji ta saki abinda take ta waiwayo tana dubanshi,duk sanda taji muryarshi haka tasan ranshi a bace yake koda yayi yu qurin boye mata,bai dubeta ba har ya isa gaban gadon yaran ya bude dan net din dake matsayin qofa ya zura kanshi,kissing kowannesu yayi yana lumshe idanunshi,qamshinsu da kyan da suka yi suna ratsashi,kaso hamsin cikin dari na bacin ranshi take ya kwaranye,sai da ya gama duddubasu sannan ya sake rufesu,ya waiwayo suka hada idanu da sumayya,kusan tare suka sakarwa juna murmushi,qare mata kallo yake yana takowa inda take tsaye,rigar jikinta ta kamata ta fidda surarta qarara,ga na shanunta fa suka cika sun zauna das jikinta har wani qyalli suke,hankalinshu bai kwanta ba sai da yasanyata cikin jikinsa ya dora hannayenshi saman qirjinta yana yawo da shi yana lumshe ido "Me kike a tsaye...ke da na gaya miki bacci nakeso kiyi?" A tausashe tace "Na gaji noor,kuma gobe zamu wuce kaga dole na hada mana kayan da zamuyi amfani da su ko?" Kai ya kada "noo,kada mi wahalar da kanki,babu wani abu da zaku dauka a nan,akwai komai can an tanada" mamaki ya kasheta,kada dai ya gaya mata ya sake wata siyayyar ne bayan wadda yayi a nan,bakinta ta bude da niyyar magana,saidai ba bata dama ba ya hade bakin nasu waje daya ya soma aika mata da saqo.       Da qyar ta qwaci kanta gajin yana yunqurin wuce makadi da rawa tana maida numfashi,da baya ta soma ja ya dinga binta idanunsa kafe a nata yana dariya "Me na tsorata haka babe?"Kai ta langabe "jego fa nake noor...ni wallahi na yafewa anty su'ad kai ka manta yadda mukayi da kai jiya?" "Don kin yafe kata kuma sai ki haramtamin romancing dinki?,baki isa ba wallahi,wannan tamkar rai da numfashi ne kinga babu mai rabawa ko?" "Haba noor ka tausaya min mana" ta fada kaman zatayi kuka sanda ya cimmata,kamata yayi sosai yana duban qwayar idanunta "Toni cewa nayi zanyi wani abu?,kawai dai a barni na dinga hutawa,kuma Allah idan kika yarda kika wani zauna zaman me ake cewa zaki gani shayi ruwa ne,ko an miki tayi kice kawai ni zaki biyo,sati daya kawai zamuyi mu dawo,if not kuwa wallahi takanas zan baro dubai na taho nigeria suburbudarki in koma abina" sosai kalmar ta bata dariya har tana toshe bakinta,yayin da shima ya saki qaramar dariyar yana rage zafi,motsin farkawar usaina ya sanyashi sakinta "Kina da zabi kan sunayen yaran nan?" Kai ta kada tana kallonshi "Bani da zani,duk abinda ka yanke dai dai ne" murmushi ya saki,ko yaushe tana maida shi yana jin kansa tamkar wani sarki,komai yayi da rayuwarta bata da zabi dai dai ne,hakan ke qara mata qima a idanunshi "Amatullah da amatur rahman" idanunta ta juya tana murmushi,sunayen sun mata,sunaye ne masu kyau da ma'ana,bai bi iyayi ko dadin suna a baki ba "Allah ya musu albakarka,ya sanya ma'anar sunayen ta bisu" "Amin ya rahman ya rahim"shi yaje ya daukota ya kawo mata ita,har yau bai taba ganin tana shayar da su ba quru quru,hakan ya sanya yau ya titsiyeta,ganin ta tsaya nuqu nuqu ya sanyashi zura hannunshi da kanshi ya dauko mata ya sa mata a baki sannan ya sake daidaita mata riqonta yadda isaka ba zata shiga bakin yarinyar ba sanda take shan nono,dubansu yake cikin shauqi qauna soyayya da burgewa,har sai da tayi kaman zata tsole masa ido tace "Kada ka cinye mu mana ha'an?" Qawataccen murmushi ya saki,ya jawota jikina yana cewa "Da zai yiwu hadiyekun zanyi na huta wallahi baki daya,saboda bansan ya zan fassara miki yadda nake jinku cikin zuciyata ba" lumshe idanu tayi,kalamansa na ratsata,tana godewa Allah tare da qarawa kanta qwarin gwiwar yadda zata ci gaba da yi masa biyayya don ta mallaki zuciyarsa fiye da yadda ta mallaka a yanzu,saboda sau da yawa kyautatawa itace ke mai da d'a ya zama bawa,to itakam kyautatawar da take masa ta sanyashi ya zama tamkar bawa a gareta.    ******     ******    *******        Cikin cikakkiyar kama da kamala take sanye cikin atamfa riga da zani da wadataccen mayafi,haka almustapha ke sanye da wani yadi irin na sarakai da aka yiwa aikin gidan sarauta,takalmi zuwa hular kanshi duka irin na gidan sarauta ne,sunyi kyau sosai,zallar farinciki qauna da girmamawa juna ta bayyana a tsakaninsu,su'ad ma na sanye da doguwar riga ta gown,saidai a sake take bata kama wani sashe na jikinta ba,almustapha ke dauke da hassana ita kuma na dauke da usaina,karon farko data fara daukar yaran,wanda ganin idanun almustapha yasa ta daukesu,tana son tayi wani abu da zai barta zuwa gida,saidai tana ji kaman tayi jifa da yarinyar,kamar wadda ke dauke da garwashin wuta haka take jinta,tun daga harabar gidan ya isa ya sanar maka akwai baqi a gidan,hakan kuwa yake,anty farida da yaranta,huda da yaranta,oga amira,anty ni'imah wadda ta taho da hibba da hibban sun bar biyu a gida legos tare da mamarsu sai ana ya gobe suna zasu iso.       Ashe baki daya suna daga gefe suna jiran qarasowarsu ciki,take kowa yayi tsaye bakin motar fuskarshi qunshe da murmushi,ba don shakkar ya man din ma da suke ba da babu shakka tuni sun ruge bakin motar suna rigengeniyar daukarsu,amma duk da tsare gidanshi hakan bai hana amira saurin amshe usaina dake hannun su'ad ba,tunu ta sakar mata dama neman mai dauka take,a rayuwarta kusan zata iya irga sau nawa ta dauki jariri,ko da can ita ba mai son yara bace,balle ma ina ta gansu,anty maamaa ita ta karbi hassana,take waje ya kacame da murna,hayaniyarau ta soma tashi,suna mata sannu tare da nuna tsantsar farinciki da kyautar da Allah ya yiwa ahalin nasu na 'yan biyu,wanda wannan ne karon farkonda suka samesu,hakan ya sanya shi janye sumayya zuwa sashen ummi wadda alkunya ta sanyata bata fito ba tun basu saka shi ciwon kai ba.       Nauyi da kunya suka hanata hada ido da ummi,itakam wannan karon ummin yakice ku yar tayi,don sai data rungume sumayya cikin jikinta tana mata sannu sannan ta zaunar da ita saman kujera bayan tasa an kashe ac da fankar dake falon,a nan kowa ya shigo hira sabuwa murna da hada hada ta tashi,gefanta ya zagaya ya rada mata "Kada ki bari su wahalarmin da daughters,kema ban yarda kiyi hayaniya can ba" a kunyace ta gyada kai,suka hada ido da wasu daga cikin wadanda ke wajen,sai ya tsare gida ya fice abinsa zuwa bangarensu wanda can su'ad ta nufa dama.        A ranar nafeesa dake garin tazo qaraso gidan,suna tare har anty dije,sai ga abida ma wadda dama su tun jiya ita da hamza suka yo gaba,tana son duba mamarta da aka kwantara asibiti duk da ta warware ma,bata samu kanta ba sai da suka tafi,sanda ta sake wanka ta kuma ci abincin,yaran ma tuni anty maamaa ta wankesu ta shiryasu tsaf zasu wajen baba su gaisa,ta dan kama kumatunsu taba cewa "Saura kuje ku qwace mana miki kuma,kubar ganinku haka farare nunar rana" dariya amira dake zaune wajen tayi "Haba maamaa kema kinsan saidai kuyi haquri keda ummi,gwamnatinku ta rushe rumumus" ta fada itama cikin raha wanda ya sanyasu darawa.        Ita amira da anty maamaa suka fito suka nufi sashen baban,hanya suka ci karo da almustaphan tare da su'ad,wanda da alama can zasun,hakan ya sanya maamaa miqawa su'ad ummulkhair tace "Sai ku qarasa kawai ko na shigo daga baya daman zai kawo mishi kununshi" kamar ba zata karba ba har suka so fahimtar haka,saidai tasa hannu ta karba sheqeqe,kau da kanta sumayya tayi kaman bata gani ba,yayin da amira bakinta ya fara rawa tana son yin magana sumayya ta danneta,ashe hakan ya taba ran almustapha "Kula mana" ya fada a kausashe,dolenta ta gyara riqon suka ci gaba da takawa,saidai amira bata yadda ba tana biye da su'ad a baya har suka isa.       Bayyana irin farincikin da baban ya shiga ma bata baki ne,har qaramar qwalla sai da dauke yana tasbihi ga Allah,basu jima da shigowa ba anty maama ta daeo,saiga mahmoud wanda shima bakinsa ya kasa rufuwa,ko kunyar baban da anty maamaa baiji ba yake cewa ya Allah shima ya bashi kaman hakan,addu'a yayi musu baban sosai mai tsaho wadda har tasa su'ad ta soma qosawa,ta dinga sakin tsaki a boye,guda daya ya shiga kunnen almustapha ya waiwayo yana dubanta,sai ta dake ta saki murmushin yaqe cikin duniyanci sannan ta sake maida kai wajen baban,sai da ya gama ya miqa musu yaran,ya yiwa sumayyan addu'a itama sosai,tun tana amsawa har kuka ya qwace mata,alkhairai yake roqa mata na duniya dana lahira,amsawa take tana kuka addu'ar na sauka cikin zicuyarta tana fatan Allah ya amsa,sai da ya gama da ita sannan ya sanya almustaphan da su'ad a ciki,suka shafa ya jawo wani file wanda da alama musamman ya ajjiyeshi saboda wannan zaman,takaddu ya fito da su ya ajjiye gaban sumayya "Ba abinda bazan iya yiwa yaran almustapha ba,kaman yadda babu irin biyayyar da baiyi min ba,hatta da mahaifina ya soshi tun yana tsumman goyonshi,ba don mahaifin yaran baida shi ba ko ya gaza,a'a,nayi ne saboda murnar zuwansu duniya kaman yadda nake bawa kowanne jika na,saidai su din tasu kyautar ta musamman ce kaman yadda su da iyayensu suke na musamman a wajena" a nutse yake musu bayanin abubuwan da ya mallakawa yaran,wanda duk wanda ke wajen yasan cewa eh lallai ba qaramin matsayi da alkhairi yaran suka zo da shi ba,kyautar ta girgiza su'ad har ta ringa jin kaman kunnenta ba dai dai yake jimata ba,hakan yasa ta saki duk aninda take ta tattara hankalinta tana sauraren sha tara ta arziqin da baban kewa yaran,daga bisani ya rufe da baiwa sumayyan kyautar kujerar umra da kuma sabuwar mota fil wadda take qirar wannan shekarar,koda cikin masu kudi ba kowa ya samu zarafin yin orderta ba,kyautar data sanya su'ad sakin kukan da taso dannewa,motar da take qulafucin samu?,motar da take tattalin kudinta dinta siyeta saiga haihuwa ta siyawas sumayyana bagas,miqewa tayi tana rushin kuka ta fice yayin da kowa ya bita da ido,kusan kowa yasan abinda ya taba ranta amma dattako irin na dattijon sai yace almustapha ya tashi yaje ya rarrasheta "bata da lafiya ne zata je tasha magani ne" "To Allah ya sawwaqe" bai iya amsawa baban da amin ba tsabar takaici,tabbas baiyi qarya ba,hassada mugun ciwo ne,hassada tana cinue kyawawan ayyukan mutum kamar yadda wuta kecinye yayi,ka tashi ran qiyama baka da komai cikin kyawawan ayyukanka duka hassada ta cinye.         Cikin kwanaki hudu da zuwamsu duk wani dan uwa dake kusa yazo yaga 'yan biyu,yaran sunzo da wani irin alkhairi da farinjini,kowa cikin farinciki yake kaman a sannan familyn suka samu jika na farko,kullum gidan baya rabo da jama'a tako ina,ko yauahe qofar gidan a bude take,suna kuwa tun kafin ranan yinsa kullum yinsa ake,saboda ci da sha da ake yi a gidan kullum kwanan duniya,duk wanda zaizo da kyautar da zai ajjiyewa yaran,saboda kowa ya fuskancu yaran 'yan gaban goshi ne ta kowanne bangare,ita kanta ummi da kyautar data musu haka anty mama,bare manyan iyaye anty farida hida da anty ni'imah,hakan ya sake daga hankalin su'ad matuqa,har takai bata da katabus sai tagumi qunci da bacin rai,bata da magana sai da tuni ita ke amsar wannan abubuwan,da tuni itace a wannan bigiren.daga sunan akayi aka maidashi dai dai da randa yaran zasu cika sati biyu a duniya,suna saura kwana hudu saiga malam da mama,tayi matuqar mamaki da farinciki,kwana biyu sukayi,mama ta siyawa yaran barimar gwal da zobe,sai awarwaron azurfa wanda ya musu yawa saidai nan gaba sa saka,randa suka tafi washe gari saiga halima zainab data haihu wata uku kenan ta samu namiji,sai anty meena,har da abdallah,yaya abbakar ne kawai bai samu zuwa bawayyo ranar kasa cin abincin kirki sumayya tayi saboda murna,abin kam ba'a cewa komai,haka ta zauna cikinsu tana jin dadi sosai,dan uwa akwai dadi,duk wanda ya rasa dan uwa yayi kuka kam         Ranar suna ta kasance baabbar rana ga duka ahalin,hidima akai qwarai da gaske kaman ta bikin aure,ranar har kukan farinciki sumayya tayi,babu shakka duk bawan da yayi haquri da qaddara mara kyau gaba Allah zai musanya masa,kuma Allah baya dauke maka wani jin dadi koya jarrabeka khaka kawai sai don ya musanya maka da abinda shi yafi alkhairi a gareka wanda kai bakasan da hakan ba,alkhairi kam sumayya ta sameshi wanda bata taba tsammanin samunshi ba,washegarin suna aminan qwarai musaddiq lamin hamza usman da huzaifa suka hada qawatacciyar walima,wanda iyakan abokansu ne da makusantan mai jego,ranan almustapha yaga tsiya,hamza ya kwasheshi son ranshi,cewa yake "Iyeeeen ba,ashe dai ba jarumin qarya bane,duk tsare gidan nan ba'a banza ba,twince ne ke tafe,amma fa rashin son raini da hayaniya ya zama na banza,ashe tsula tsiyarka kake a daki kaman ba....." Duka ya kai masa wanda da qyar hamza ya kauce,su lamin suka dinga kwasar dariya,can anjima sai ya matso gefan kunnenshi "Yallabai....a bamu sirrin mana,ga wadan nan manyan gaurayen an sanya ranar aurensu shekara daya masu zuwa(lamin musaddiq da huzaifa)" "Zaka gane kuranke ne wallahi hamza kafi kowa sanina ban da kyau" sai da ya masa haka sannan ya shafa masa lafiya,anci am sha an rashi cikin raha da walwala,bayan kowa ya yiwa aminin masa kara da kyauta ta bajinta,don almustaphan ba baya ba,ya riqe aboka qwarai da gaske,bashi da qyashi ko hassada,komai ya taso naci gaba burinsa ya sanyasu a ciki su samu kowa ya samu ci gaba,kusan duka gaban idanun su'ad aka gabatar da komai,hakan ya sanya tun dare ta tashi hankalinta zata gida,kuka ba irin nau'in wanda batai masa ba,amma yayi biris da ita,don bata dauko hanyar da zai barta ba,lafazinta kawai ya isa ya sanya a hana mata duk wani abinda take so,qarahe ma falo ya dawo yayi kwanciyarsa,yana jin kewar sumaya,don a qa'ida kwananta ne,amma jego ya raba tsakaninsu,dako banza zaya samu kulawa da tattali,tsaki ya dinga ja yana juyi,wai dama haka jegon yake?,yanajin wannan jegon bazai iya da shi ba,idan suka hanashi tafiya da ita nan da next week ba shakka zai saceta ne su gudu,su basusan halin da yake ciki ba sai suce dai tayi wani jego. Washegari tun qarfe tara baba ya kirayi wayarshi yace yazo yana son ganinsa,sanda ya isa shi daya ne "Ka siyawa su'adatu ticket taje taga gida" shine unarnin da baban ya bashi,ba musu ko jayayya tsakaninsu har abada,hakan ya sanya bai tambaueshi bai kuma yi masa bayani ya amsa da to ciki girmamawa,ya kuma siya din,saidai da ya siya baban ya kaiwa ba ita ba,daga hakan baban ya gano lallai ba son ranshi bane,saidai tunda ya riga da ya siya haka ya danqa mata,har ta tafi bata ga qeyarsa ba,hakan ba damuwarta bane,tasan cewa lokaci qalilan ya rage ta samu dukkan kulawar data keso,zata shuka tsiyarta za kuma ta zuba iskancinta yadda taga dama,haka take rayawa a ranta. Jakarta kawai ta ajjiye suka fito ita da mommyn nata,ta riga data siya musu tikitin jirgin qasa har ya zuwa unguwar da sibitin yake da zama,tafiya ce ta kusan awanni daya,wanda cikin awa daya da rabi suka isa ga ofishin ainihin likitan da suke nema,doctor james,haifaffan qasar america,mutum da ya tashi da tsantsar aqidar yahudawa ta aihini,sannan ya ginu kan qiyayyar musulunci da musulmai,ko kadan baya qaunar musulmi a zuciyarsa,qwararren likitane na gyni wanda ya qware ya kuma shahara wajen saida sperm yin dashe d'a dana qwayayen haihuwa,shahararsa ta sanya mummu kashe kudade masu yawa domin su ganshi don samun biyan buqatarsu,da idanu yake kallonsu bayan ya gama jin abinda ya kawosu,uasan tabbas ba mai yiwuwa bane,haihuwa ga macen da babu mahaifa tattare da ita kwata kwata,saidai kuma tunda aka masa transfer na sunayensi cikin system dinshi ya tabbatar da musulmai ne,baya jin kuwa zai barsu su fita a office dinsa salin alin ba tare da ya zaluncesu ba,wanda wannan shine babban burinsa,agender dake gabanshi tsakaninsa da wani shahararren mai kudi dake garin nasu ya fado masa,hakan ya sanyashi sakin murmushi,ba shakka zuwansu yayi daidai,haka faduwa tazo dai dai da zama,murmushinsa ya jefa musu zaton cewa nasara ce qarara ya hango,sai ya karkace ya zuba musu bayanin cewa zata haihu kamar kowacce mace,zasuyi mata aikin da bazata farka ba sai da juna biyu,nan da kwanaki uku ta taho asibitin zasu soma aikin nasu,kudi kadan ya yanka musu ahakan ma ya karba ne kawai don kada ya darsa zargi cikin zuciyarsu saboda yasan cewa kudaden da zaya samu zasu mai dashi cikin jerin sahun masu kudin garin,zuciyarsu fes suka bar asibitin,tun a sannan su'ad din ta fara hasashen irin abubuwan da zata shuka bayan bayyanar ciki a jikinta,bata jin zata dagawa wani cikinsu qafa,kowa sai ta takashi dai dai da abinda yayi mata. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 1⃣0⃣6⃣ *KADA KI WUCE BAKI KARANTA BA* *SHIMFIDA MAI MUHIMMANCI* *bismillahir rahmanir rahim* *Allah S W T yana fada cikin qur'aninsa mai girma* *ku koma izuwa ubangijinku ku tsarkake aiki dominsa,tun kafin azaba tazo muku,sannan ba za'a taimakeku ba(da hana saukar azabar idan baku tuba ba* *kubi kyakkyawan abinda aka saukar izuwa gareku daga ubangiji tun gabanin azaba bata zo muku bagatatan bakuyi hasashen zuwanta ba* *tun kafin rai bata ce ba "ya asarata/tabewa ta bisa sakacim da nayi a janibin Allah,haqiqa na kasance cikin masu wasa* *ko tace "da Allah ya shiryeni da na kasance daga cikin masu tsoron Allah* *ko tace lokacin da taga azaba  " da ace ina da damar komawa izuwa duniya izuwa duniya dana kasance daga cikikin mash kyakkyawan aiki* ______________________________________ *WANNAN SHAFIN SADAUKARWA NE GA MEELA ADEEL DA SAURAN DUKA MASOYAN SU'AD*            Kallo daya zaka yi masa ka tabbatar da cewa ba cikin nutsuwa walwala da kwanciyar hankali yake ba,tunda ya diro qasar bayan kira da ya samu na gaggawa daga hajiya khaulat kwana ashirin da tafiyar su'ad din bai sake samun isashen bacci ba cikin nutsuwa,me ya sameta haka har ta fice hayyacinta bata gane kowa?,me ya kawota asibiti cikin wani gari wanda ba nasu ba bayan gidansu suka yi da shi zata je?,me ya sameta haka meye dalili?,babban abinda ya daga masa hankali shine doctor james,wanda a cewar hajiya khaulat shike duba su'ad,tare sukayi karatu da shi,dalibi me cikin jami'ar da yayi karatu,ajinsu daya course dinsu daya,hasalima yana daya daga cikin mutaben da basa shiri sam,saboda aqidarsa ta qin jinin musulunci da musulmai,uwa uwa yana matuqar adawa da qoqarin da almustapha ke da shi,yana daga cikin gungun dalibai 'yan adawarshi,kusan ma shine shugaba,jamea baida kirki ko kadan,bai da tausayi kuma bashi da imani,dalilin wai laifi da suka aikata shi ya sanya aka koreshi yana shekarar warshe a makarantar,saidai sunji labarin ya sauya qasa ya qarashe karatunshi har ma ya bude asibiti,tunda yaje basu hadu da james ba,duk sanda zaije asibitin suna sabani ne,randa suka hadu ya jima yana kallon almustapha,irin kallon da ya sake sanya shakku cikin zuciyar almustapha,bugu da qari daya buqaci bayani kan meye damuwar su'ad bayanin da yayi masa sam bai gamsheshi ba hakan ya sanya ya quduri shiga aikin da kanshi a matsayinsa na likita.        A ranar yayi waya da wani farar fata abokinsa,wanda yake da asibiti shima hafin gwiwa da gwamnati,almustaphan ya sanya aka hada masa daki guda da dukkan abinda yake buqata,wanda a yau ya shirya yin bincike a kanta.       Kaman ko yaushe tana kwance iskar oxcygen na taimakawa numfashinta,yayin da hajiya khaulat ke gefe cikin fita hayyaci,tunda take bata taba fuskantar tashin hankali tsahon rayuwarta ba irin wannan karon,idanuna sun yi luhu luhu,tayi kuka har ta gaji,batasan wanne irin aiki ne haka doctor james ya yiwa diyar tata qwaya daya tilo ba wanda ya sanyata shiga wannan matsanancin halin,sanda taga almustapha ya shigo dakin jikinta har rawa yake,kwarjini yake mata sosai irin wanda ada can baya baiyi mata ba,a mutunce ya gaidata yana maida kallonshi ga su'ad tare da tambayarta jikin nata,ba amsa sai kuka data sanya,ranshi a jagule yake qwarai,ya qagu ya duba abinda ke faruwa,shigowar ma'aikatan jinyar ya katse duk abinda haj khaulat din keson gaya masa,sai data ga suna daukar su'ad daga gadon da take zuwa wanda suka shigo da shi mai taya da alama zasu fita da ita ne sannan ra magantu cikin rawar baki "Mustapha...ina..ina zaku da ita" "Zanje nayi nawa binciken ne,saboda bayanin da james yayimin bai gamsheni ba,nasanshi ya sanni tun ba yau ba" ya fada yana ciro wayoyinshi ya ajjiye gefe guda,ita dinma tana shanshano wani abu,din bata yarda da cewa aikin da suka buqata din kadai yayi mata ba "Amma yau professor da alhaji zasu iso,inaga a bari su iso din ko?" "Ina so kafin suzo din in san amsar da zan basu kan me ya sameta,tunda ku da kuke tare sanda abun ya sameta baku san meye sababi ba" ya fadi haka sanda yake takawa ya fice yana bin bayan masu turatan.       Sanda ya haska fitilar nan mai tsananin haske abu na farko da idanunahi suka fara masa karo da shi hudar dake qasan cibiyarta da kuma wadda ke gefan hannun hagunta,saidai daya ta warke daya kuma danya ce,gabanshi yayi mummunan faduwa,addu'a yake Allah kada ya tabbatar da abinda yake tsammani,a hankali cikim qwarewa da hikima ya jona duk wata cumputer da yake da buqata wadda zata taimakawa bincikensa cikin sauqi ya soma aikinsa cikin lura da taka tsantsan.        Cikin awa guda qwaqwalwarsa ta soma yamutsewa,ba abinda yake ambata sai innalillahi wa inna ilaihi raji'un,gumi ya hada sharkaf,sai ya saki duk abinda yake ya koma saman kujera ya zauna,nanya manyan lamura biyu kowanne yana sukuwa cikin qwaqwalwarsa,kowanne buqata yake ya soma sarrafashi,su'ad babu mahaifa tattare da ita?,babu qodarta ta hannu hagu an illata mata ta dama?,duka aikin waye wannan?,aikin waye?,ta shiga nanatawa kanshi tambayar,cikin wasu qalilan sakanni idanunshi suka kada suka koma jazur,ya dinga fidda huci kaman kumurcin maciji,wani bala'in tausayin su'ad din ya mamayeshi,me ta yiwa wani har ya mata haka?,waye ya aikata mata haka?" "Zai wuce doctor james" wami bangare na zuciyarshi ya bashi amsa,a fusace ya miqe cikin tsananin fushi "To amma me ya hadasu da shi?,me ya kawosu wajenshi?" Cak ya tsaya sanda wani sashe na zuciyarshi ya jefo masa wannan tambayar,a hankali ya koma ya zauna yana kiran sunayen Allah dafe da kanshi.       Ya jima kafin ya samu ya yiwa kansa control,tabbas sai ya saka nutsuwa indai yana son komai ya dai daita,a hankali kaman wanda aka yiwa dukan tsiya ya miqe ya hada mata qarin ruwa ya zuba magungunan da yasan zasu taimaka mata sannan ya sanya ma'aikatan suka maidata dakinta,kai tsaye ya fice daga asibitin shida drivansa.         Bai koma gida ba sai daya samu dukkan bayanan da yake so cikin kwana daya tal,abinda yaji kan doctor james yayi matuqar girgizashi,saidai ya hada dukkan wasu hujjoji da bayanai waje daya,banu nutsuwa ko ta qwayar zarra tattare da shi haka yayi wanka ya sauya kaya,yana ganin tarin misscal na sumayya da saqonni saidai ya kasa karantawa ko yabi kiran haka ya sake ficewa.        "Kiyi haquri ki kwantar da hankalinki kada ki jawo mana ya gane abinda ake ciki,in sha Allahu Allah zai baki lafiya" kai ta girgiza "Ki qyaleni mummy,ki barni,kinsan me likitan ya aikata a gareni?,almustapha akwai nakeson gani,na tabbbatar da cewa rayuwata tazo qarshe kuma wuta zanje bayan na mutu" ta fada kuka na qwace mata,dai dai sanda almustapha ya turo qofar,ajiyar zuciya ya saki sanda ya ganta idanunta biyu,har ma sun cire mata oxcygyn din dake hancinta,idanunta a kanshi har ya shigo,ya qarasa gaban gadon mummyn ta janye baya gabanta na dukan uku uku,hannunshi su'ad din ta kama ta riqe qam tare da sakin kuka "Shshshs....ya isa,ki daina kuka a irin wannan yanayin" ya fada yana shafa kanta cikin tausasawa "Qyaleni almustapha nayi kuka,kasan me na aikata maka?,kasan me nayi maka?"kai yake kadawa bacin ranshi na sake tasowa yana qoqarin dannewa "bance ki gaya min ba,ni kuka kawai nace ki bari" zata sake magana kenan aka turo qofar dakin aka shigo,baba professor ne sai alhj abdus samad mahaifinta da kuma ummee,daga baya sumayya ke biye da su da 'yan biyu wanda sam bai tunanin zuwanta ba,duba daya ta masa taga rama sosai tattare da shi,yayin data dubi su'ad kuma sai hankali ta ya tashi matuqa,cikin mutuwar jiki ta qaraso ciki,haj khaulat ce ta miqe tana musu sannu da zuwa suka amsa suna samun wajen zama,banda alhj abdus samad da ya qarasa gadon da su'ad ke kwance,sannu yayi mata saidai shiru tayi taqi amsa masa,sunyi tunanin ko zafin ciwo ne,baba prof ne ya sake mata sannu ba tare da tunanin zata amsa ba,ga mamakinsu sai ta waiwayo,ta daga hannunta ta yafici baban,cikin mamaki ya miqe,ya isa gefan alhj abdus samad ya tsaya "Baaba,idan mutum ya haihu haka rayuwa take ka qyale yaronaka yayita abinda ransa yake so?,kaman ba haka bane,saboda naga yadda wasu masu yaran suke hana yaransu abinda ransu yake so,amma kaman zalunci ne hakan nake tunani a da,sai yanzu da lokaci ya quremin nake shanshano akwai dalili" kowa yayi mamakin maganar tata,amma sai baba ya gyara zama "Ba d'a ba ko babba daya girma yana buqatar wanda zai dinga masa burki yana saitashi kan hanya,ya hanashi ba dai dai ba ya sashi dai dai" kai take gyadawa cikin gamsuwa "Kaman yadda ka so ka nunamin a baya nace maka bana so kada ka sakemin haka?" Idanu suka hada da alhj abdus samad,bashi da zabi illa yace mata eh "To wannan meye?" "Gata ne kakewa rayuwar yaro" dubanta ta maida kan alhj abdus samad "Wannan ne mahaifina amma baimin haka ba,bai taba tsayawa ya damu da halin da rayuwata ke ciki ba,bai taba zama ya tsawatar min ba,bai tana tsayawa ba bare yaga nayi dai dai ko na kuskure ba,ko yaushe kasuwancinsa ne gaba da komai,kanje gida na qaraci zamana ba tare daya sani ba...." "Su'ad,wai me kike fada haka?" Haj khaukat ta tasi tana fada,saboda kada ta kwance musu zani a akasuwa,sosai idanuta suka firfito tana duban hajiyan "Kada kice komai,inaga qwara shima a kanki,tunda tare yake barinmu ni da ke,duk abinda nace ina so komai girmanshi baki taba cemin a'ah ba,kince talaka ba mutum bane,talaka abun qyama ne na yarda hakanne,naga dabi'u masu yawa a wajenki na doru akai,wanda hakan ya sanya nake ganin namu dabi'un ne kawai daidai,dau tari zanga wasu dabi'um da suka burgeni,amma da zarar nayi niyyar aiwatarwa sai tarbiyyarki ta rinjayi tunani na na watsar,duk abinda nayi dai dai ne,sam baki taka rawarki ta uwa ba,ne zance dake momy?,cikin rashin sani kika dorani kan wannan hanyar ko kinsan ba dai dai bace kika nakasta rayuwata kika dorani?" Shiru ya ratsa dakin,kusan kowa jikinsa yayi sanyi qalau,sumayya tuni ta soma qwalla cikin mayafinta,wani abu take ji yana ratsata,tausayi ne,ita din shaida ce kan su'ad wata iriyar hargitsatsiyar rayuwa take "Baba...." Ta kira sunanshi tana kallonshi,sai ya amsa yana sake nuna kulawarshi a gareta "Ina jin ciwo cikin jikina,ina ji sama sama sanda doctor james ke cinikin qodata,ina jinsa,amma bansan me zan karanta ba wanda zai qwaceni daga sharrinsa,tun yana dariya yana gayamin bansan cewa babu amana tsakanin bayahude da musulmi ba?,bansan cewa basa sonmu nasa qaunarmu ba?,bansan cewa ba zasu taba taimakawa musulmi a banza ba ba tare da wata boyayyiyar manufarsu qasan ransu ba,yace har abada....baba.....magana ta qarshe ta kunne na yaji yace min,wani abokin karatunsa musulmi yaji yana gayawa 'yan uwansa cikin littafinmu Allahn mu yace "yahudu da nasara ba zasu taba yarda da kai ba har sai kabi addininsu"(wannan haka yake aya ce da tazo cikin alqur'ani mai girma,babu yadda babu amana tsakanin musulmi da bayahude matuqar ba addininsu kabi ba,saidai su nuna maka a baka kawai amma sam zuciyarsu ba haka take ba,kuma har yau muna kan wannan qadamin saidai mun kasa fahinta,bama kuna ganewa din har sai sun amana illa sannan zamu zo muna kaico,Allah kasa mu dace),wannan ne lafazin qarshe da yayi min" sai ta saki kuka cikin wahala yayin da sautin kukan sumayya ya fito,qirjinta ya dinga wani bugawa,tsoro ya kamata,lamarin har yayi girman haka?,rabata da qodarta?,sannan ta juya tana duban almustapha da ya kasa motsawa,ya dunqule hannayenshi cikin aljihunsa ya zubasu,idanunsa sun kada jajur "Zo don Allah....zo" tace da shi,da qyar ya iya takawa zuwa inda take,hannunshi ta kama "Da fari dukanmu munyi kuskuren zamantakewa ni da kai,saidai nawa kuskuren yafi naka,tunda har ka rigani gane kuskuren,ka kuma yi qoqarin maidoni hanya amma na bijire,tun kafin nan,naqi mu'amala da matan abokanka,naqi mu'amala da yarena addinina 'yan asalin qasar iyayena bare na gane kuskurena ta silar zamana da su na gyara,gani nake tunda arziqinsu bai kai na mijina ba basu isa ba,ba komai bane su,ban ganin su da gashi,kamin rarrashi a boye wanda daga ni saikai sai Allah muka sani naqi,kazo kamin na fili amma naqi,ban manta lafazin da ka yimin tafiyata ta qarshe wanda daga ita sai sabon aurenka KADA KI ZARGENI NAN GABA....kaci gaba da yimin qoqari naci gaba da sanya qafa ina shurewa,bayan babu abinda ka daukemin na game da haqqina harda wanda bai zama dole a kanka ba,baka fasa adalci tsakaninmu ba,hakanan duk wanda zaiyi ba daidai ba tsakaninmu zaka tsawatar masa,zata daumi nata laifin ta bada haquri ina kallo,amma nikam....sam sam...gani nake nafi qarfin juyawar namiji,nafi qarfin a zaunar da ni ana min fada,na dauka cewa namiji da mace duka dai dai suke......" "Silence please su'ad" ya fada yana qoqarin tsaidata,dukka wannan ba shine gabanshi ba,plan dinsa ta yadda zai samo doctor james,murmushi ta saki "Ka barni na fada na roqi yafiya mana,nasanka farin sani,nasan tunaninka a yanzu kawai na yadda zaka dauki fansa kan james don tunda mommy ta gayan kamin gwaje gwaje ina da tabbacin kaga abubuwan da na rasa a halitta ta,na rasa qodojina na kuma rasa mahaifata" "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" dukkan wanda ke dakin ya furta cikin tsakanin kaduwa,banda momy wadda ta zube a qasa ba tare data shirya ba,duk da cewa furuci daya ne yake sabo a wajenta "Eh....doctor james shi ya saida min qoda ga wani mutumi,amma mahaifa ni da kaina na kai kaina aka cire min ita" rintse idanunsa almustapha yayi "Hasbunallahu wani'imal wakil" ya dinga furtawa can qasan ranshi,bakinshi ne kadai ke motsawa "Nayi tunanin cewa haihuwa bata da wata rana matuqar kana da kudi,na dauka abu mai kyau nayi tunda mommy ta juya tata mahaifar,almustapha,idan kaso ka yafemin idan kuma ba zaka iya ba duk daya nasan idan na mutu wuta zan tafi,amma dai ina roqonka ka yafemin" ta fada tana zubda qwalla,rasa me zaice yayi?,a wacce duniya yake ciki?,hannunta ne kawai riqe cikin nashi,hango sumayya tayi dake sharar qwalla "Zo...zo kema" sautin kukanta ne ya dadu,firgici da tsoro na cikata,wacce iriyar duniya ce wannan muke ciki?,da qyar ta iya tashi a daddafe ta isa gaban gadon itama saitin kanta "Duk naga abubuwan da kike a zamanki da almustapha,wanda a sannan wani abu ya kange zuciyata na kasa ganin kyawun hakan bare nayi koyi,wanda ina da tabbacin ko nice shi a wannan bigiren dole na soki,a baya laifinsa nake gani,amma a yanzu na tabbatar da cewa baida laifi ko kadan,banfa san kwanansa da tashinsa ba,bansan cinsa da shansa ba,bansan me yakeso da wanda ke qona ranshi ba,duka ba ruwana,kawai ya jiqani da kudi ya bani freedom shikenan,girki kadai nasan na taba yi masa wanda zai iya dan shiga sahun nuna kyautatawa bayan shi din tunda muke da shi ban taba nema na rasa ba wajensa,koda zan jera wata ina tambaya,don me ya samu mai masa dukka irin wannan kulawa hakan zai kasa sonta?,ki yafemi kema duk da ba lallai yafiyar taki ta amfane ni ba" kuka ta saka sosai,tana jin su'ad kamar 'yar uwarta,a iya zamanta da ita banda furuci ko kallo bata taba wani abu na cutarwa a gareta koma bayan wannan ba,akan me zata riqeta?,meye zainab karima da a'iza basuyi mata ba?,tamkar zata shide ta furta "Ki daina fadin haka,ki daina yanke qauna daga rahamar Allah,kowanne bawa da kalar qaddarashi,bakisan rayuwar da nayi ba abaya wanda ban taba tunanin a yanzu zanyi rayuwa irin wannan ba,ki godewa Allah daya sanya kika gane kuskuren naki,duk wanda kuma ya yafe maka ta karbu har a wajen Allah,nikam bakiyimin komai ba,ba abinda kika yimin,na yafemiki ina roqon Allah ya baki lafiya,ki yafemin nima idan na taba bata miki koda da mugun kallo ne" murmushi ta saka "Kina da zuciya mai kyau wanda na tabbatar da kece na ganki cikin ciwo irin haka ba lallai na tausaya miki har nayi miki kuka haka ba,baki taba yimin komai ba saboda ko yaushe kina takatsantsan da hakan,koda kin yimin ma ya wuce har bada.....ki riqe almustapha da kyau wallahi kun dace....ya hada duk wani hali mai kyau amma rashin samun tarbiyya ta gari daga iyaye na gari ya janyo min na kasa riqeshi har na mori rayuwa mai inganci....ki kawo min 'yan biyu na sake ganinsu,na tabbatar da ace na zauna nayi rayuwa mai kyau da tuni ni haifesu....ummi" ta kira ummi dake gefe,itana qarasowa tayi "Duk cikin yaranki kinfison almustapha,amma kika yi haquri kika zuba min ido ina yiwa rayuwarshi yadda naga dama,kinso nunan hanya kaman yadda baba yayi amma na taka miki birki,a ranan na miki rashin kunya gatse gatse wanda ina da yaqinim baki gayawa kowa ba sai yanzu dani na fada,kiyi haquri ki yafemin ummi,ki nema min gafara wajen duk wanda na taba batawa" itama ummin share qwalla take,tana ajjiye mata ummulkhir da ummu kulsun gefanta tana dubansu su'ad din "Ba wanda baya kuskure cikin rayuwarshi su'ad,ma'aiki yana cewa tabbas ba don kuna ainata zunubi ba da tuni Allah ya tafiyar daku ya halicci wadansu,kuskure siffa ce ta dan adam saidai mafi alkhairinsu sune masu tuba,na yafe miki har abada,Allah ya tashi kafadarki don ya ara miki daman a nan gaba" "Na gode ummi" ta fada tana shafa kansu ummulkhair a hankali ta furta "I love you my kids"ta fada tana jin qaunar kyawawan yaran har cikin zuciyarta.        Alhj abdus samad dake dafe da kanshi wanda tuni hawaye suka wanke fuskarshi sharkaf ya matso ya kama hannunta bayan ummi ta debe yaran ya soma neman gafararta,ya tabbatarwa da kanshi cewa ba shakka yayi babban kuskure na sakaci da sanya ido a rayuwar da iyalinahi keyi a matsayinsa na uba,wanda yake mai kiwo ne za'a tambayeshi a kan abinda aka bashi kiwo "na yafe maka daddy...amma ko nan gaba Allah ya azurtaka da wasu yaran ka kula da su,na tabbatara addininmu yana da tsari wajen bawa yaro tarbiyya kabi wannan tsarin,ina da yaqinim shi kadai ne ingantaccen tsari" hawayenshi ya dinga sharewa yana jera mata addu'a suna amsawa,wanda yana gamawa ya miqe ya fice,wata nadama na shigarsa,shi kansa sai a yanzu ya farga,meye amfanin dukiyar da yake yunqurin tarawa wadda ta hanashi tsayawa ya duba gidanshi da rayuwar da suke kai?,qememe su'ad din taqi yarda ta kalli mummyn ko tayi magana da ita,so take kawai ta ganta bata dakin,kaman wasa abun amma sai gashi ta birkice da gaske,tilas mummyn ta fita hannunta saman ka tana kuka.       Ranar baki daya sumayya ta dinga kula da su'ad din,sosai su'ad din taji dadj,don addu'o'i ta dinga tofa mata wajen da tace yana mata ciwo,duk inda ta mata addu'ar kuwa sai taji ya lafa sai kuma idan ya sake tasowa,qarfe shida na yamma almustapha yace su wauce masauki ya kaisu,qi sumayyan tayi tace a barta a nan,ummi tace bazai yiwu ba ga yara,duka duka kwansu talatin ko arba'in bata cika ba,duk da nauyin ummin da take ji amma hakan bai hanata sake roqarta ba,baba ne ya sanya baki su barta din,tunda dakin baida maraba da gida ba wata matsala bace,fuskar su'ad kawai zaka kalla kasan taji dadin hakan,sai ta saki murmushi,ranan kusan kwanan zaune sukai da su'ad din,tuni 'yan biyu sukayi barci,itakam tana zaune,tayi sallah ta zauna ta huta,duk motsin su'ad din tana ankare da shi,itama su'ad din idanunta na kan sumayya,sai yanayin nata ya dinga burgeta,sam batasan da wannan rayuwar ta yawan yin sallah ba,banda ma almustapha ya tsaya kanta a tsaye sallar ma ta farilla ojoro take mata,sai daga bisani ya sanyata ta gyara da qyar "Zanso nima inyi sallahr nan haka,akwai lada ko?" Murmushi sumayya ta saki,tana jin tausayinta har cikin zuciyarta,kana kallonta kasan gagarumin ciwo ke cin jikinta,a haka ma akwai kulawa kenan "Akwai lada mai tarin yawa,sallah tana kusantar da bawa zuwa ga ubangijinsa" kai ta kada "To ya za'ayi ina son nayi nima,king tun isha'i ban sake ba"miqewa tayi ta iso gareta saboda ganin tana yunqurin gyara hannunta,a tausashe ta gyara mata tana cewa "ba lallai sai sallah ba kadai zata kawo miki lada,ko jinya ma idan kanayi ai kankarar zunubi ce,idan kina so kina iyayin istigfari salatin annabi da sauransu kina daga kwance" "Ok,kaman yaya?" Koya mata tayi,ta kama ta dinga yi,a hankali ta dinga jin sanyi da sauqi cikin jikinta da zuciyarta,ta dinga satar kallon sumayya sanda take shayar da ummulkhair tana sha'awar rayuwarta,ashe rayuwa mai dadi nutstsiyar rayuwa itace rayuwar da addinin musulunci ya tanada ya kuma koya mana?,lallai iyayenta sun yiwa rayuwarta babban gibi.        Sanda almustapha ya kawosu da safe sannan ummi tace ya dauketa ya kaita gida ta huta anjima sai ta dawo,ba musu ta amsa,kowa yaji dadin yadda yaga salama tattare da su'ad din,suna tafe cikin mota shiru,yana dauke da amatullah wadda ke barci yana wasa ya hannunta,yayi kewar yaran sosai,sai yaga kaman an qara musu girma da wani wayo,sosai kamanninsu ke fitowa da shi,zuciyarshi a cunkushe take matuqa,babban abinda ke gabanshi yanzu yadda zai cimma doctor james,duk da alhj abdus samad yace ya qyaleshi kaman yadda su'ad din tace ita ta jawa kanta,duk abinda mutum yayi kanshi,saidai sam zuciyarshi bata nutsu da haka ba,har suka isa dakin daya kama musu a hotel din wamda babban falo ne da dakuna uku a ciki baice komai ba,ya kwantar mata da yaran sannan ya miqe suka hada idanu,duk itama sai take jinta ba dadi "Ki wanka ga abinci can,ina zuwa" ya fada yana juyawa,binsa tayi da kallo kawai tana kada kai,baki dayansu sun zama abun tausayi cikin qaramin lokaci har ita din.        Cikin kwana goma sha hudu sumayya ke kwana da su'ad din,zama suke cikin asibitin tamkar ya da qanwa,a nan ta koyawa su'ad din wasu abubuwan da take ganin ya kamata ace ta sani,sukan zauna suyi hira sosai da ita cikim sakewa kaman sun jima da soma mu'amala,jikin su'ad din da sauqi sosai,har takan iya zama sumayyan ta jinginata,ita ke gyara mata jikinta,ta bata abinci,ta daura mata alwala idan lokacin sallah yayi,tana yawan sanya sumayya ta jera mata amatullah da amatur rahman tayi ta magana da su kaman wasu manya "Ki musu tarbiyya irin taki don Allah" hakan su'ad ke yawaita fada,murmushi sumayya keyi tace "Tare zamuyi musu har ke,kema mamarsu ce" "Zanso hakan" abinda takan fadi kenan wanda sumayyan ta kasa gane me hakan yake nufi. Hatta almustapha yaga sauyi qwarai wajenta,da ya shigo takan gaidashi ko tayi masa sannu da zuwa,abinda bai taba gani ba,hakan ya masa dadi qwarai ua faranta masa,yakan zauna cikinsu ya bada wasu mintuna suyi hira su duka,duk da bai zama waje daya,ba wanda yasan inda yake zuwa daga shi sai Allahnshi,idan dare yayi yazo ya musu sallama shikenan sai gobe da safe.        Wani dare bayan kowa ya tafi ya barsu,yan biyu na saman gado cikin neat suna bacci su'ad ta kalli sumayya "Wai baki kewar maan,naga ko sau daya baki taba binshi ba" murmushi ta saki "Kin manta jinyarki nake,ladan kuma da ake samu wajen yin jinyar mara lafiya ba kadan bane" kai take gayadawa cikin gamsuwa,duk wani furuci da sumayyan zatayi akwai qaruwa a cikinsa "Wai nikam rannan kaman naji kina min magana kan rayuwarki,bani labari mana?" Dariya ta saki tana kallonta "Kina son ji ne?" Kai ta kada "Eh idan babu takura,don na tabbatar zan samu wani darasi a ciki" "To qara kunne biyu" dariya ta saka "Na qara" a nutse sumayya ta warwarewa su'ad labarinta,gyada kai kawai take,jikinta yayi matuqar yin sanyi qwarai,wato akwai mutane shigenta ko irinta da yawa a duniya "Gaskiya rayuwarki baki daya darasi ce,ke din ta daban ce" ta fada tana jinjinawa yadda sumayyan ta fuskanci rayuwa haka,gyaran murya sumayya tayi wanda ya janyo hankalin su'ad daga duniyar tunanin data tafi "Nikam in roqi wata alfarma mana wajenki"murmushi tahi,ki roqa ko mene idan baifi qarfina ba " so nake ki yafewa mommy,kada ki manta uwa uwa ce komai lalacewarta,na tabbatar soyayyar da take miki ce ta kaita ga kasa tasawatarwa da tsayawa kai da fata wajen ganin ta hanaki aikata abinda kike so matuqar ba dai dai bane,ta kuma doraki kan dai dai din,ba zaka taba iya biyansu abinda suka yi maka ba har abada"murmushi ta saki ta kamo hannun sumayya "Mummy,ina son mummy sumayya,saidai yadda ta tarwatsa rayuwata ta kasa gyarata tana qona min rai a duk sanda na tuna hakan,na jima da yafe mata sumayya,na mata haka ne ko don gaba,duk da cewa ko a yau na tafi na barta ba zata sake samun wasu yaran ba,amma wannan ya isheta izinar da zata bawa 'yan baya labari"kai ta kada "naji,amma gobe ki furta mata cewa kin yafe mata,ki daina gudun ganinta don Allah" murmushi ta saka sumayya na sake shiga zuciyarta "Naji in sha Allah zanyi,nasan tunda kika dage kan maganar kika gyaramin babu kyau abinda nake,zanso ace zan haihu da na sakawa 'yata sunanki" ta fada wani abu na taba zuciyarta,hawaye ya sauko saman fuskarta,goge mata sumayyan tayi tana cewa "Ki daina kuka,ki godewa Allah da lafiyar da kike samu" "Na gode" ta ce da sumayya "Ba abun gode min,haqqina ne dama na kula dake din koba komai miji daya fa muke" murmushi suka sakarwa juna,ranar sunyi hira sosai da su'ad din har take gaya mata "Naga amira na sonki,da fari haka nima ta soni,halina yasa ta gujeni,ki tayani bata haquri don na mata ba dai dai ba da yawa wanda yasa ta daina hulda da ni" "Amira bata da riqo,kuma ke matar yayanta ce,na tabbatar komai ya wuce a wajenta,don kullum sai ta kirani ta tambayeni jikinki,abinda ya hanata tace na baki duk sanda ta kira kina bacci,ni kuma banson tada ke" murmushi ta saki don maganar ta mata dadi,sai da suka raba dare sosai sannan sumayya ta daura alwala ta tada sallah,ta baiwa su'ad carbi ita kuma taci gaba da azkar,sanda ta idar ta waiwaya sai taga carbin ya fadi hannun su'ad din,idanunta alumshe alamun bacci yayi awon gaba da ita. *Bayan awanni uku* Zaune take kawai a gabanta ta zuba mata ido tamkar mutum mutumi,sam kukan da yaran ke tsalawa bai shiga kunnuwanta bare tayi yunqurin daukarsu,dubanta kawai take lokavi bayan lokaci tana kiran sunanta,saidai babu wani alami dake nuna motsa bare ta amsa,tun kan ya qaraso dakin yake jiyo kukan yaran,hakan ya sanya ya qara sauri cikin hanzari ya isa qofar dakin ya bude ya tura,a kansu su biyun idanunsa suka sauka,sai ya sauya akalar tafiyar tasa daga wajen 'yan biyun zuwa inda su sumayyan ke zaune,kallo daya ya yiwa su'ad dake kwance gabanshi yayi mummunar faduwa,tamkar wanda aka bigewa gwiwoyinshi ya qarasa bakin gadon ya duba hannyenta zuwa saitin zuciyarta inda take aiki,abinda yaji ya tabbatar masa da cewa babu rai jikin su'ad din,duk da haka zuciyarshi ta kasa gasgata masa,take ya hautsina kayan aikin dake dakin,ya dinga gwaje gwaje,wanda yana tsaka da aikin abokinsa mai asibitin ya shigo dakin da niyyar duba mara lafiyan,kallo daya ya mata ya tabbatar ta mutu,hakan ya sanyashi janye almustaphan cikin harshensa na turanci yace "Kayi haquri,ta rigamu gidan gaskiya man,Allah ya jiqanta" tuni sumayya ta qarasa rushewa da kukan dake cinta,suka hadu ita amatullah da amatur rahman suka gauraye dakin,baya almustapha yayi ya jingina da bangi yana furta innalillahi wa inna ilaihi raji'un. *bayan awa daya* Dukkansu suna zaune a babban falon dake asibitin wanda na likitan ne ya basu su zauna,kowanne ka dubi fuskarsa cikin baqinciki take,hatta da mazan dauriya kawai suke,saidai almustapha bai iya daurewar ba,karon farko da suka soma ganin hawaye kan fuskarshi,abinda basu taba gani ba tsahon rayuwarshi da su,ummi ma hawaye take sharewa lokaci zuwa lokaci,yayin da sumayya ke kuka tuburan,idanunta da fuskarta gaba daya sun kumbura,yayin da fuskar ta hadu tayi jazur,ummi dake gefanta ita ke lallabata ta bawa yaran nono,tana shayar da su cikin hijabin tana kuka,ba shakka mutuwa kota wanda baka sami bane tana da ratsa jiki da sanya wani sabon imani a zuciyar dan adam,ballantana wadda ta sani sun zauna tare tsahon shekara nesa da juna,gab da zata tafin kuma sukayi zama irin na yaya da qanwa,yaushe zata manta haka?,haka mutuwa take,takan dauke mutum a sanda bai shirya ba hakanan masoyansa basuyi sallama da shi ba,sai mutuwar mukhtar ta fado mata,kukanta ya sake daduwa,wanda hakan ya sake karya zuciyar duka sauran,ba shakka sunga irin zaman da sukayi a tsakaninsu cikin sati uku kacal kafin ta mutu,haka suka dinga bata baki kafin su fara tattauna abinda ya zaunar da su din bayan an kai gawar su'ad mutuware. Alhj abdus samad ne ya fara magana "Zamu wuce nigeria da gawarta,bama gawarta ba har maman tata ma" "Amma alhj kaji fa sunce ita khaulat ta samu stroke,haka zamu tafi da ita" cikin tsantsar baqinciki yana goge qwallarsa yace "Daga rana irin ta yau professor na bar zaman qasar nan har abada,zamu koma qasarmu ta gado da zama,babu abinda na tsinta a zaman qasar nan banda baqinciki da tarwatsewar iyalina tunda har na kasa control dinsu,kowa yana vin gashin kanshi,Allah ya jiqanki su'adah ya gafarta miki" ya qarasa fada yana shafe sabbin hawayen da suka zubo masa da tafin hannunshi "Hakan yayi,a mata suttura cikin dakin mijinta" inji ummi,da wannan shawarar suka soma neman izinin tafiya da gawar su'ad,cikin kwana biyu rak suka samu kasancewar abun na masu da shi ne. Cikin dakinta dake abuja aka mata wanka aka shiryata,almustapha na tsugunne gaban gawarta yana mata addu'a,sosai yayi mata addu'a tare da jaddada yafiyarshi a gareta,sannan ya bawa sumayya guri,alhj abdus samad da duk wani makusancinta,inda aka turo mommy a keke,kuka ta saka ta soma magana,saidai maganar bata fita ba'a jin abinda take fada,sakamakon bakinta daya karkace tun faduwar data yi sanda tayi ido hudu da gawar sy'ad tana ihu tana ita daya ta mallaka ya zata yi mata haka,daga nan ta sume,bayan ta farfado kuma ta gamu da wannan cutar,sosai sumayya ta qunshe kanta a tsakanin qafafunta tana sakin kuka sanda aka dauki gawarta aka fice da ita zuwa gidanta na gaskiya,tabbas duk wanda yayi damara don duniya ya kwanceta,Allah ya bamu sa'ar tafiya,kasa mu riskeka sanda kake farinciki da mu ya Allah. A nan gidan dake abuja suka zauna karbar makoki,kaf 'yan uwan sumayyan ba wanda baizo mata ba,haka yan uwa da abokan ariziqi suka dinga zirya,har eesha ba'a barta a baya ba,tazo jikinta cikin matuqat sanyi,tana tuna yadda suke takun saqa da su'ad din,tana tuna yadda su'ad ta dauki rayuwarta kusan dai dai da yadda itama take jin kanta,hakan ya qara mata mutuwar jiki,sai data dangana da sumayya tayi mata gaisuwa,sannan ta roqi gafararta kan abinda ta nata a baya,murmushi kawai tayi,mutuwa kadai ta ishi mai hankali aya,me ya mata zafi da zata tsaya saka wani mutum a ranta,itakam mantawa ma take da faruwar abin sai idan wani abu ya taso da zai tuna mata da hakan,tace ya wuce har abada,'yan biyu sun jima hannunta,sosai yaran suka shiga ranta,bul bul da su cikin tsafta gwanin sha'awa,duk da mamarsu na cikin alhini amma fes suke,don ummi ke sawa baba uwani ke kula da su akai akai,ba'a maidasu wajen sumayyan sai sun buqaci nono. Kwanaki bakwai akayi kaman yadda al'ada tace kowa ya watse,aka fidda duk wani abu na su'ad din aka miqawa iyayenta,don almustapha cewa yayi ya yafe,bazai iya amsar komai nata ba,ranan mummy khaukat tayi kukan da bata taba makamancinsa ba,tayi nadamat da bata taba tsammanin akwai kamarta ba,ta dinga kallon sumayya tana son gode mata amma babu baki,iya jinyar su'ad kawai zuwa mutuwar nan ta karanci irin kyakkyawar zuciyar da take da ita,da hannu ta dinga mata godiya haka aka turata kan keken guragu suka fice a gidan. Washegari kwana takwas kenan almustapha ya taddata tana gyara dakinta,ita daya ce su amatullah suna wajen ummi,duban junansu suke kowa na kallon irin sauyawar da dan'uwanshi yayi,shaida mata yayi zai koma america,amma baya so ta gayawa kowa can ya tafi,din su dubai yace zai koma,fatan alkhairi ta masa don ta fahimci me zai komar da shi din,itama tana goyon bayanshi,bai kamata mutane irin doctor james ace sun kubuta ba haka nan akwai. Qasa ce da bangarorinta suke da wariyar launin fata da qyama ga musulmai,amma hakan ko kadan bai karya masa gwiwa ba,bai wani tuna cewa shi din baqo bane,ya dan sha wuya amma bai haqura ba sai da ya tabbatar an kamo doctor james an yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya,sannan an qwace duk wani license nashi tare da rushe asibitin da ya gina,wanda hakan ya dauki almustaphan tsahon watanni biyar,bai waiwayi gida ba sai bayan wadan nan watanni,satin guda da kammaluwar lamarin,da wani yammaci wanda a wannan lokacin sumayyan na kwance,bata taba jinta cikin matsi da takura irin na wannan lokacin ba,rashin ganin almustapha har tsahon watanni biyar bata zaci ma zata iya jureshi ba,a kusan kullum sai taci karo da saqonshi ta email dinta na ban haquri da alqawarin dawowarshi nan kusa,bata da amsa face Allah ya bada sa'a,ta tsawaita haqurinta qwarai da gaske,saidai har zuwa yau shiru kake ji,duk sanda ummi ko professor sukayi qorafi,takan nuna ita ta bashi dama babu komai yana gab da dawowa. Qarar wayarta ita ta dawo da ita daga tunanin da take,ta miqa hannu ta daga ta kara a kunnenta ba tare data damu da duba mai kiran ba "Assalamu alaikum warahmatullah" muryar nan mai daraja da qima a wajenta,muryar nan da take bawa girma,muryar nan da babu tamkarta ita ta ratsa dodon kunnenta,tamkar an cire duk wata laka dake jikinta haka taji wata muvuwar kasala,zuciyarta ta karye,take qwalla ta cika idanunta "Wa'a laikumussalam warahmatullah" ta amsa masa bayan ta sauke ajiyar zuciya,idanunsa ya lumshe daga can bangaren yana duban kansa a madubi,ya sauya kaman bashi ba,ya rame saidai ya fara cikowa cikin sati guda,zaya so ace sai daya murmure sosai kafin ya koma mata saidai dauki da son ganin ahalinsa bazai barshi ba,sautin yaji kaman na sheshsheqar kukanta "Ya salam" ya furta yana zama gefan gado "Ummu abdallah ki yimin rai don Allah ki daina kukan nan" ya fada a tausashe,a hankali ya dinga tsarata cikin kalamai masu taushi da di,har sai daya sauke mata duk wani abu dake cikin zuciyarta sannan ya jefeta da albishir mai dadi "Rana ita yau,ki jirayi mijinki masoyinki,ki masa kyakkyawan tanadi da tarba ta musamman,ki gayawa daughters(amatullah da amatur rahman)duk wanda nazo na tadda ya fara gwada tafiya shine best friend dina" murmushi mai dauke da sauti ya qwace mata,ba qaramin dadi albishir din yayi mata ba,uwa uba takan yi dariya duk sanda yake magana da yaran kaman sa'anninshi,saboda tsabagen wayo hat sun soma shaida muryarshi da fuskarshi ta hanyar hoto da kuma waya da sukeyi "In sha Allah" ta furta cikin tsantsar farinciki,a qalla sai da suka kashe awa daya cikakkiya yana sake wa soyayyarshi service kafin suyi sallama,ya jiqata ya tsumata da kalamanshi qwarai da gaske,wanda ta dinga sakin murmushi ita daya kaman tababbiya,kasa zama sashen tayi,ta zura hijabinta ta miqe zuwa sashen ummi,inda su amatallah suke can tun sassafe. Sanda ta sanarwa da ummi zancan dawowar cewa tayi cikin zolaya "To sai a fara shiri da kyau ko?" Kunya ta kamata ta sadda kai tana gyarawa amatallah kalbarta data soma zamewa. In sha Allah last page na zuwa muku nan da anjima,ku zama ready........ *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍ 📖📖📖📖📖 *~NA~* *~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~* *WATTPAD:HUGUMA* *_HASKE WRITERS ASSO_* (HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS) 1⃣0⃣7⃣ *bamu kasance masu azaba ba har sai da muka aiko da dan aike(manzo)* *haqiqa mun aiko ka manzo(annabi muhammad)kan al'ummah,Allah ya isa shaida* *wanda ya yiwa manzan Allah biyayya haqiqa yabi Allah* *haqiqa mun shiryar da shi hanyoyi biyu(dan adam)kodai ya zamanto  mai godiya ko ya zamto mai kafircewa* *haqiqa mun halicci mutum  daga digon maniyyi dake cakude da ruwan mace da namiji muna jarrabashi da takhlifi(nauye nauye na shari'a Allah na nufin jarrabarsa a sanda ya dace)saboda haka muka sanyashi mai ji mai gani* *haqiqa wannan gargadi ce ga talikai to wanda yaga dama sai ya riqi hanya izuwa ubangijinsa* _____________________________________ Sosai ta shiga gyara cikin satin bata zauna ba,ummu kam ta daure mata qarqashi ta kwashe mata su amatallah,duk wani abu daya kamata ta aiwatar da shi,har kwaskwarimar bangarenta sai data yi,kafin ranar dawowarshi komai ya zama neat. Ranar da zai dawo din mahmoud ne zaya je dauko shi,kafin isowarshi ta shirya tsaf cikin shigar cikakkiyar bahaushiya atamfa,ga mata cas a jiki dinkin ya zauna mata,yaran duka ta shiryasu cikin kaya iri daya komai da komai,sun fito sak a twince dinsu,sunyi wani kyau da girma,sanda taji isowar tasu sai ta kasa zaune ta kasa tsaye,kai tsaye wajen baba ya wuce,ya taddashi tare da matan nashi,ba wanda baiyi farinciki da ganinshi ba,sai a sannan ya yiwa baban bayanin me ya zaunar da shi,shiru baban yayi yana jinjinawa namijin qoqarin da yayi cikin qasar daba tashi ba,aqalla ya kusa mintuna talatin kafin ya wuce sashensu. Awa uku da shigowarshi amma ta kasa zama,sai qirqirarwa kanta aiki data yi,zirga zirga take tsakanin kitchen da falo,duk wani motsinta yana kan idanushi,ya ganeta sarai,tana nufin sai ya sake sabon yaqin neman soyayyarta?,kunyarta keson musu shamaki,yana zaune ne da boxer da singlet fara qal bayan yayi wanka,ba abinda ke fita jikinsa sai qamshi mai taushi na turaren safirul hubb da wasu nau'in turarukan,tuni amatallah da amatur rahman sukayi bacci kan qafarshi dake miqe,sai ya yunqura ya miqe da su saman kafadarsa sanda ta sake zuwa ta kwashe duk abinda yayi amfani da shi zuwa kitchenbda alama wanke wanke zata yi,sai da yaje ya kwantar da su din sannan ya nufi kitchen din. Tana tsaye gaban sink kuwa tana wanke wanken,taji shigowarshi amma sai ta kasa waiwayowa,a hankali ya qarasa bayanta,ya sanya hannayenshi ya kamo qugunta ya manna da nashi,sannan ya hade bayanta da qirjinsa ya dora habarshi saman kafadarta,nannauyar ajiyar zuciya ta saki saboda wani saqo na musamman da jikinsa ya aikata mata "Wani abu kake so" ta furta qasa qasa "Ke nake so maman 'yan biyu?,wai baki da labarin nayi kewarki ne?" Sai ta ajjye kwanukan alamar tabar wanke wanken,abinda ahi bai sani ba kunyar shi take ji sosai ta rasa dalili "Um um ci gaba da wanke wankenki,zamuyi hirar a haka....bani labarin bayan rabuwa baby....nikam nayi rayuwa ne kawai,gani nan tamkar mutum mutumin,ina rayuwa ne tsahon wata biyar ba tare da nasan nau'in dandanonta ba,amma alhamdulillah,tunda alwashin da naci na cikashi" ajiyar zuciya ta saki tana dauraye wani kwano "Bansan ya zan misalta maka ba noor,rayuwa babu kai ashe tamkar gangar jikin da babu ruhi ce,kullum sai nayi kukan rashinka,raba dare nake ina kokawa da tunaninka,sai inji kaman ka tafi kenan,kaman ba zaka dawo ba kaman yadda anty su'ad ta tafi...." Sai ta saki kwanukan ta juyo tana kallonshi,sannan ta lafe a qirjinsa kaman mai tsoron wani abu "Don Allah noor.....kada ka sake tafiya ka barmu haka,ni da yara duka muna buqatarka" dagota yayi suna duban juna kafin ya sakar mata qayataccen murmushi mai kwantar da rai "Ba zata sake faruwa ba my summyyy,ni dinma ina tsananin buqatarku cikin rayuwata....,bari in nuna miki kadan wani dan yanki daga cikin yadda nayi kewarku" bai saurari komai ba ha dagata baki daya tana dariya da roqon ya sauketa zata taka amma ya qiya,yace baiso tayi komai wannan karon shi zai sarrafata yadda yaga dama,zai kuma dauke duk wani aiki daya zama nata ya hada da nashi duka yayi. Tun da suka haura saman sai kukan amatur rahman ne ya sauko da shi,bako kunya ya daukesu duka ya kaima ummi,baga ce komai ba ta karbesu ya sanya qafa ya fito abinsa ya koma sashen nasu,ranan kuwa can suka kwana,bai karbosu ba itama ummin bata aiko musu da su ba,da yake yaran sun riga da sun saba,ba kuma su fiye shan nono ba,hakan duka bai masa ba,ji yake gidan yayi kadan ya dauki soyayyarsu,da safe ko karuawa basuyi ba ya sata ta shirya suka fice zuwa gidanshin nan,wanda anan kadai yake gani zasu baje kolinsu,ya kuwa baje kolin sin ranshi,ya yiwa soyayyarsa cikin zuciyarta service ta sake dawowa sabuwa fil,ya kuma sake dasa mata yadda zata soshin,irin soyayyar mai zafi mai tsayawa a rai,wanda bata barin zuciya ta huta bare gangar jiki,yayi qara'i iya son ranshi ita kuna ta durqusa ta tallafi dukkan nau'in abinda yazo mata da shi,na hadda ta haddace,na karba ta karbeshi yadda ya kamata. Kwana daya da wunu taji bai zancan su koma gida,dukan kararta da alkunyarta taci tura,yaranta na cikin ranta abinka da uwa,tana zaune tana miqa masa kayanshi da dai dai yana shiryawa tace "Allah yasa su amatu zaka dauko min"kai ya girgiza "Wa?a'ah,ai kisaka rai kin yayesu kawai,tunda ummi ta gayamin babu abinda basu ci....ke infact ma zaki soma rainon ciki ne" gira ta dan ya mutsa a shagwabe "Wake da cikin,ni?,ni ban gaya maka ba" bai kulata ba har sai da ya gama fesa turarenshi sannan ya fincikota jikinsa ba tare data tsammaci hakan ba,haka ne ya sanyata fadawa jikin nashi gaba daya "Ke kike da ciki,tsakamin kwanakin dawowata ni na tabbatar da cewa nayi ajiya,kuma ni na gaya miki,kema kuma zaki ga alama nan da four to five weeks....am telling you" dariya tayi kawai tana maida abun wasa,dariyar shima yayi sannan yace "Zamu ga wanda dariyarsa zata kasance ta nasara" "Allah ya nuna mana" ta fada cikin basar da zancan,wasa wasa sai ga 'yan biyu shiru har sati guda,suma kuma suna gidan basu komai ba,randa suka cika sati biyu saiga ummi da yaran,cikin girmamawa da kunya ta tarbeta,ummun tace ga 'yan yaye ta dawo da su sunzo kuma ganin gida da Allah ya sanya alkhairi,mamaki ya cikata,wato almustapha yace musu sun dawo nan ne sannan ta yaye yaran,kusan awar ummin biyu sannan ta musu sallama ta tafi ta sanar musu anty maamaa da baba suna nan zuwa. Abun kaman wasa saiga zancan almustapha ya tabbata,da kanta tayi gwaji da PT strip,kuka ta saki cike da tsoro da fargaba,tayi firgai firgai da ita tana jiran dawowar almustapha,ina zata iya da twince wata bakwai ga wani sabon cikin,sanda ya dawo takw gaya masa dariya ya dinga kwasa abinshi hankalinsa kwance "Sanda nake gaya miki kin dauka da wasa nake?" Takaici ya cikata,wato shi ko a jikinsa ma,sai abinci da ya jawo yanaci yana baiwa su amatullah sunata darunau abinsu,sai ta fashe da kuka ta miqe ta shige daki,cikin mamaki ya bita da kallo din bai zaci haka ba,sai yaji wani abu na susar ranshi,mamaki bai cikashi ba har ya gama bawa yaran abincin,kafin ya kammala abinda zaiyi sun bingire da bacci,hakan ya sanya ya kwashesu suka shiga dakin,tana takure waje daya tana jan hanci da alama taci kukanta sosai,sanyasu yayi cikin gadonsu dake gefe daya,ya tofesu da addu'o'i sannan ya nufeta,ya jima yana kalllnta kafin yayi qas da murya "Me ya saki kuka sumayya?!" Tun kafin ta bashi amsa wasu sabbin qwallar suka biyo kuncinta "Yanzu don Allah ya dace ace na sake samun wani cikin?" Kai ya kada "Eh ya dace mana,tunda har Allah ya baki yasan cewa ya dace ne" sai ta barke da kuka tana fadin ni wallahi bana so,tun yana lallashinta sai ya fahimci da gaske take,ya tunzura sosai,maganganun data dinga yi suka qona ranshi matuqa,kanshi ya dinga lallasa bai tsitstsinka mata mari ba,sai kawai ya miqe ya dauki kayanshi ya fice a dakin,ranar farko da suka taba raba makwanci kenan tun randa ta zama ita kadai. Wasa wasa sai qaramin abu ya soma zama babba,dan abu qalilan saita sanya kuka,ta daina kulashi sam,iyakarta da shi gaisuwa sai ko girko,shima sai ya daina ci kota dafa din,yadda ta dafa haka zata zo ta dauke,hakan na bala'in qona mata rai,sam bata jin dadin zaman gidan,amma gani taje itace da gaskiya ita ya kamata a bawa haquri ai,bini bini kuka,ko su amatu ke fada ko rigima yanzu zata sanya kuka,wani lokaci yazo ya kwashe abinsa ta qaracu hamcininta ita kadaj,wani lokaci su kwana ma wajensa,tana can ta kasa bacci saboda rashinsh amma ba zata nuna ko ta sauko ba,abinda ya bata masa fiye sa zato,a hankali ta soma rama,ga laulayi tana fama da shi,cikin haka Allah ya kawo halima abujan sunzo wani seminar ita da abdur rahman ta leqo ta wunan musu,baki kawai halima ga sake tana duban sumayya,yo aiko ita ba zata tafka wannan shirmen ba,shi yasa data shigo tana yabon gida sai uhmm kawai take cewa,abin ma haushi ua bata ta kasa ce mata komai ba harta tafi,dadin abun ma su 'yan biyu babu abinda sukayi,sai girma da suka dada da qiba kaman ana jansu,ashe mama ra zayyanewa komai,ranan raga tashinnhankalin da bata taba gani ba,jin muryar maman ta sauya ya daga hankalinya,ta mata fada kaman ta cinyeta,ta kuma tabbatar mata matuqar bata sauya ba to kaman a kunnen malam,ta kuma sani gamonau bazai mata kyau ba,a rannan ta zauna ta yuwa kanta bita daya bayan daya,istigfari ta dinga yi sanda ta dawo hayyacinta,ta tuna girman zunubin data dauka a wannan tsakanin abinda ta yiwa almustaphan,a ranan ta duk abinda ta danja baya da yi duka ta miqe tayi,tayiwa 'yan biyu kwalliyarsu duk da dama bata fasa ba,amma ta yau din ta musamman ce,ta barau falo cikin kekunansu ta shiga nata wankan,tunda ya shigo ya fahimci sauyi a falon,bai ce komai ba ya kwashe yaransa daketa bangala masa dariya da daga masa hannu kowa na son ya soma daukarta,dariya ta saki ya kwashesu baki daya ta haura sama da su,sannan ya kwashi kekunansun ya kai dakinsa,koda ta fito taga bata gansu ba tasan ya shigo kenan,duk sai taji ba dadi,tabbas bata kyauta ba,ada bai shiga ko fita sai da saninta,amma yanzu duka ta bata wadan nan lamuran,sai data gama shiryawa tsaf cikin wasu sabbanin qananun kaya data taba siya a dubai,bata taba amfani da su ba sai ranar,tayi masifar kyau kai kace sumayyar nan ce 'yar sha takwas,kaman bata haifi yara har uku ba,ta koma saman dining ta kwashe abincin ta jera kan wani kwando mai kyau ta haura saman da su. Sanda ta tura qofar dakin yana zaune saman gado da su abinsa,ko ina birjik da kayan wasansu kala kala,daya na saman qirjinsa daya na saman cinyarsa yana dan kada qafar a hankali,yana dan bubbuga bayan amatur rahman dake saman qirjinsa,da alama bacci suke ji kuma daf yake daukarsu,don ya saba musu idan zasuyi bacci hakan yake musu,da zarar kuwa ya musun baccin zai daukesu ba wuya,abin sai ya burgeta duk da cewa ba karon farko taka hakan ba "Yanzu mahaifi uba irin wannan shi zaki hanawa samun yara?" Zuciyarta ta tuhumeta,sai ta sake jin rashin kyautawar tata sosai "Sannu da zuwa" ta fada a sanyaue,daga kai yayi ya dubeta sai kuma ya kauda idanun nashi,ta masa kyau ba kadan ba,ji yake kaman yaje ya rungumota,saidai miskilancin ya motsa,ga bacin ranta dake sakadar zuciyarsa "Yauws" ya amsa can qasa wanda da qyar ta jiyo amsar,sai data kammala shirya komai baice mata qala ba,ta matso kusa da shi ta sunkuya tana fadin "Sannu da zuwa.....barin dauke maka su kazo kaci abinci" "Dakata,barmin su ai kaya na ne ko?" Ya dakatar da ita ba alamun zafi tattare da shi,amma sigar da yayi maganar kawai kasan akwai fushi cikin maganar tasa "Wai naga ga abinci..." "Bazam ci ba,a qoshe nake...." Sai kuka ya qwace mata,idanunsa ya lumshe yana saurarenta,baiso baison yaji kuka ko kadan,sai yaja qaramin tsaki wanda ya sake karya zuciyar sumayyan,miqewa yayi ya janyo gadajen 'yan biyu ya sakasu a ciki,ya tofa musu addu'a,sannan ya dawo saman gadon ya tattare dukkan kayan wasan nasu da kofunansu da ya hafa musu abinci da feeders ya kammale su waje daya,ya sake dawowa ya miqe bayansa jikin fuskar gadon tare da miqe qafafunaa,har yanzun kukan take bata tsagaita ba,yana jin kamar ana jan ranshi ne,qarasowa tayi gabanshi kanta a qasa ta durqusa "Kayi haquri don Allah ka yafemin,nasan cewa ni mai laifi ce a gareka" "Laifi?,na mefa?,bayan kina jin kinyi daidai sai kuma daidanki ta koma laifi" hawayenta suka sake qaruwa ta sake qas da kai "Na sani,na cancanci duk wani hukunci,amma kayi haquri ka yafemin don girman Allah" har cikin zuciyarsa kalaman suka kai ziyara,sai sun sake taso masa da bacin ranshi,maganganun data dinga gaya masa a sannan "Ke zan bawa haquri ai,tunda ba'a miki dai dai ba ko?" Kai ta kada "Ba haka bane" "To yaya ne?,sumayya ki gayamin,me na rage ki da shi da kike tantamar haihuwa da ni?,mene da ake buqata wanda bakya samu?,meye aibuna?dame na gaza miki?,ci sha sutura ko muhalli?,ki gayan daya daga ciki?,me kike so nayi ina kike so na saka raina,meye laifina?,akan me zanqi na haihu?,meye Allah baiyimin ba,ina da arziqin da ko 'ya'ya million za'a haifa min zan iya daukar nauyinsu,zan iya kula da su,to me yayi saura?,me ya rage min?,so kike ki tunzari ni?,ki tunzurani nayi abinda banyi niyya ba?,kinsan mata nawa ke kawomin kansu na auresu?,duba nan" ya fada yana bude wayoyinshi a zafafe kamar yadda yake maganar cikin zafi ya shiga fannin saqonni ya bude kana ya tura mata dukkan wayoyin gabanta "Su'af bata yi arba'in ba baban yarinyar da na yiwa aiki ambassadorn nijer yake min tallan 'yarshi,duba qasa bayan shi ga saura nan,mutane iri daban daban,ba wadda idan nace ina so za'a hanani,so kike na dauko wata cikinsu dolen dole na kawo rayuwarmu?" Kuka ta fashe da shi qwarai fiye dana dazu,tausayinsa da tausayin kanta ya kamata,tabbas gashinan har da hotunan wasunsu "Kayi haquri don Allah man kayi haquri,wallahi na daina,ina son cikina ina son abuna,kuskure ne" sai tausayinta ya kamashi ganin yadda yake take kuka haiqan,hade hannayensa yayi waje guda yana dubanta "Yanzu ya kike so ayi,a cire miki cikin?" Wata harara da batasan da ita ba ta watsa masa "Wallahi banaso ina son abuna ba wanda zai cire min" a zahiri da ranshi ba'a bace yake ba tabbas dariya ce zata zo mishi,amma da yake yana cikin bacin rai sai harar tata ta saukar masa da sanyi cikin zuciyarsa,ya lumshe idanu sannan ya ware mata hannayenshi,tamkar jira take sai kuwa ta taso da hanzari ta fada ya rufeta ruf ta sake narkewa da wani salon kukam "Relax baby...relax" ya fada yana shafan sumar kanta dake fake waje guda,a hankali kukan ya ragu ta soma sauke ajiyar zuciya "Kace musu kana so?" Ra furta a hankali "Suwa?" Ya tambayeta yana dan tunani "Au" ya fadi bayan ya tuna,sai ya sanya dariya har sautinta na fitowa,wato wani kishi da da can bata da shi a yanzu zata koya "Bance musu ba,amma indai kika sake cewa bakison baby na dake jikinki to ki tabbatar zan auro saliha tayi ta haifo min yara iya yadda nakeso..." Bai qarasa ba ta cika masa kunne da kukan shagwaba "Sorry sorry....bazan sake fadi ba indai kema baki sake ba" ya fada yana dariya tare da sake gayyatota zuwa cikin jikinsa tayi lamo tana dariya ciki ciki,kusan tare suka sauke ajiyar zuciya kowa najin wani nauyi na sauka daga qirjinsa,saboda ba qaramin kewar juna sukayi ba,ba wanda bai jigata ba cikinsu dauriya kawai sukayi,a ranan an biya bashin soyayya qwarai,dama ance fushin masoya hutu ne. Rayuwa mai cike da tsafta da ingantacciyar soyayya ke gudana cikin gidan,gida ne da suka ginashi cikin so qauna da aminci,kowanne farincikin dan uwansa shine nasa,dukkansu kowa ya qoqarin ganin ya kyautatawa dan uwanshi,sai da cikinta yayi wata biyu cif sannan suka daga dubai da kyawawan 'yan biyunsu,sun tafi sun bar mutane da kewarsu,a can dinma gida ya saiya musu mai dauke da falo daya kitchen mai girma da corridor biyu,daya dakunan baccinsu shi da sumayyan,daya kuma na yaran da spare din wani guda,a nan dinma ingantacciyar rayuwa suka shimfida,duk abinda yakeso shi take masa,kaman yadda duk abinda takeso shi yake mata matuqar bai saba dokar shari'a ba. ***** ***** ****** ***** ******* ****** *******        Qatuwar harabar gidan dattijon tsohon professor muhammad mukhtar wanda aka sake sauyawa ginin gidan fasali qawace yake da nau'o'in ado kama daga yadiddika balan balan da launin qwayaye iri iri,kujerun zama da tebura ma alfarma,carfet carfet da ka qawata wajen,iya ganinka yara ne ke sha'aninsu wadanda ba zasu gaza shekara biyar zuwa qasa ba,sai kuma manya jifa jifa wadanda 'yan uwa ne na jimi,daga qofar iya wajen da aka tanada saboda sha'anin makeken hotone na amataullah da amatur rahman,yan biyu kyautar Allah,'ya'ya ga doctor muhammad mukhtar,hamshaqin attajirin nan wanda ya mallaki kamfanoni na sarrafa abaya da mayafai a qasashen duniya daban daban,babban mai noma auduga afadin nijeria,mutum da ya mallaki manya manyan gidan marayu da gajiyayyu wanda babu irinsa a fadin africa dake taimkao ga wadan nan mutane,mijin macen data zama haske wa al'ummar nigeria bama yankinta arewa kawai ba,matar data mallami centers na koyawa mata sana'o'i,centers na horar da yara 'yammata matasa,macen data shahara wajem gina makarantu da masallatai,matar data yi fice wajen samar da maqabartu,tallafawa tsofaffi da masu rangwamen gata wato hajiya sumayya sulaiman abdu,sannan jikoki wajen dattijo mai cike da dattako da karamci,tsohon ambassador muhammad mukhtar gwambe,yau rana ce ta musamman wanda ilajirin jikoki da 'ya'ya wanda suka fito daga barin familyn mukhtar na uwa da uba,da kuma na abokai,da duk wanda ya hada alaqa da sumayya dukkansu suna gidan,rana ce ta murnar zagayowar ranar haihuwar amatullah da amatur rahman,wanda suke cika shekara uku da haihuwa,duk yara matan dake wajen suna sanye cikin dogayen riguna fara qal da aka yiwa don baqi wanda kyauta doctor almustapha ya bada a rabawa suk wanda ya halacci wajen,mazan ma jallabiya ce ta maza fara qal da baqin hirami a kansu,wajen yayi kyau matuqa da irin adon da aka masa na fari da baqi,shewa yaran suka sanya sanda aka iso da qaton cake din 'yan biyun cikin kwali aka sanyashi a muhallinsa aka budeshi jiran fitowarasu kawai ake.         Daga daya bangaren yaran suka fito,sanye da gown golden mai adon baqi,ta cikin tsahonta ya kai gwiwa mai gajeran hannu,sai ta saman mai dogon hannu,kallo daya zaka muau idan bakasan au wayw iyayensu ba kace daga jinsin karabawa aka dauko su,sun kwashi kyau ta kowanne bangare,sunyi kyau matuqa da gaske,takalmin qafarau kawai abun kallo ne,kana dubansu kasan sunji gata iya gata,daga bayansu kuma hajiya sumayyace dauke sa wani yaro wanda saika rantse usainin sumayya ne saboda kama,sanye yake cikin wando na yara three quater da baqin takalmi hightop na yara,sai farar shirt a jikinsa mai gajeran hannu,kan yaron na kwance saman kafadarta,kar kaso kaga sumayyan a lokacin tayi kyau na qin qarawa,sanye take da wani lafiyayyen lace wanda kyawunsa da tsarywarsa kadai ya isa ya gaya maka shi din mai tsada ne,peach ne mai dan turuwa,wanda aka yiwa ado d'ai d'ai da mint green,komai nata ya dace da shigarta,ita dinma kana dubanta kasan cewa Allah yayi halittar mace a wajen,wadda kyau da nutsuwa suka hadu suka nuna hutu da tsantsar nin dadin da take ciki,murmushi kawai take sakewa sanda taga yawan yaran da wajen ya tara,ciki kuwa harda yaran yaya abbakar,yaran halima da kuma yaran zainab,yaran farida huda da uwar gayya amira wadda ke cikinsu tana ta qoqarin saita wajen,sai yaran mahmoud da mus'ab mace da namiji,ga kuma yaran lamin da usman,musaddiq da huzaifa ne basa qasar banda nasu yaran saidai ayi hotuna a tura musu,baki daya wajen ya rude da hargowar yara badon komai ba sai hango boss dinsu amatur rahman,yarinyace mai tsokana rawar kai da surutu,itace usaina saidai tafi 'yar uwarta iya komai,saika rantse itace babba,kusan duk yaran dake wajen dan team dinta ne,dai dai ne suke sabga da amatullah,itakam zamu iya cewa tayo gado ne,gadon miskilanci rashin son magana da shiru shiru,hakan ya sanya amatur rahman ta rainata qwarai,don ma maibi musu ,a hakan ma sumayya tayi tsaiwar daka a kansu,wani lokaci MUKHTAR wanda shike bi musu wanda yaci sunayen mutane biyu shike shigarwa amatullah din,suna kiranshi da qarami yayin da almustapha ke kiransa da aboki,amatullah da amatur rahman kuma daughters,idan daya zai kira zaya ce daughter,qaramin dake hannun sumayya kuma shine MUHAMMAD mai sunan baban professor suna kiranshi amir.       Cikin lokaci qanqani aka soma gabatar da bikin birthday din,wanda yayi masifar qayatarwa,yara sun wala sunyi farinciki qwarai da gaske,a qalla sai magariba sannan suka soma haramar tashi,masu tafiya aka fara zuwa daukansu,masu kwana cikin gidan kuma kowa ya shiga ciki.        Bayan amira wadda kwana zatayi ra saka duka yaran mata sunyi wanka sai ta fice zata wajen ummi ta bawa qaramin yaronta nono,wanda yaranta biyu,babbar itace farha sai qaramin hadim,sumayya ta bari da su tana tsakiyarsu tana fama da su kan kowanne ya nutsu,mai cin abinci yaci mai kwanciya ya kwanta,wahalar da ita suke sosai don amatur rahman ta hada gang sunata tayi,miqewa tsaye tayi kawai tana kallonsu "Wannan yarinya halan fitinar amira ta dauko ne?" Ta raya haka cikin zuciyarta,qaramar dariya taji an saki a bayanta,hakan ya sanyata waiwayowa a hankali,almustapha ne tsaye ya jingina da qofa,hannayenshi harde a qirjinsa yana murmushi da alama ita yakewa dariya,sauke hannyen nashi yayi ya fitota da hannu,don tabbas idan ya sake ya shigo cikin dakin yaran ba zasu barshi ya fita da wuri ba,ta gane sarai me yake nufi,sau ta dubi jikinta,don tunda aka tashi daga wajen batayi wanka ba,abinda take ta sauri tayi kenan kada yazo ya sameta a hakan,sai gashi bata cimma nasara ba,kafadarshi ya dage hadi da girarahi ya watsa hannayenshi yana murmushi alamun babu ruwanshi,ta nuna kanta da yatsa alamar niko?,ya kada mata kai yana nufin eh din,sai kawai ta juya ta dubi su amatallah tace "Amatu.....ga abul_aulad" take kowa hankalinsa yayo kan qofar,kafin kace meye sun moqe aun dunguma kanshi,wayyo sumayyan ta gama masa tsiya,yau yasan ciwon kai babu fashi,idan ba'ayi da gaske ba ma duk yadda ya ciwa yau din buri bazai iya aikata komai ba,tana masa dariyan mugunta ta zame ta barshi da su,hakan ya bata damar yin wanka ta shirya tsaf,sannan a gurguje ta shirya masa abinda zaici sannan ta dawo wajensu.        Daga bayansu ta tsaya tana kallonsu tana sakin murmushi a jejjere,babu shakka haihuwa rahama ce,yara ni'imah ce,koda shashancinsu kawai wani lokaci abun debewa zukata kewa ne,almustaphan da baison hayaniya ko kwaramniya ko qanqani yau sai gashi tsakiyar yara,ya bude musu kwalin chaculets wasu na cin gugguru(popcorn),wasu na fama da ice cream,baki daya sun bata mishi jiki,amma ba yadda ya iya haka yake biye musu,sai data gaji da kallonsu don kanta taga sun fara cakar da shi ya soma riqe kai sannan ta qarasa wajen tana masa dariya,ya daga kai suka hada ido,maimakon harar nuna ta masa laifi fa yayi niyya sai gashi ya buge da zuba mata idanu yana kallonta kaman zai cinyeta,sai data kada hannunta saitin fuskarshi,ta zauna gefan madina 'yar gidan abida ta biyu ta janyi guggurun ta soma ci,gardin madara dana zumar dake ciki na ratsata harda lumshe ido "Madam,u r pregnant fa?kinsan yaushe nayi shi?,randa zamu baro dubai,unforgotable night din nan da kika bani"ya rada mata saitin kunnenta sanda yadda ba wanda zaiji sai su Cak ta tsaya da taunar ta waiwayo tana dubanshi,tasan tunda ya fada din mawuyacine idan ba hakan bane,saboda ba yau ya fara ba kamar wani mai gani har hanji,duk sanda yaui cikinsa shike gaya mata kuma daga qarshe ya tabbata hakanne,haka sukayi cikin qarami da cikin amir,tana son nuna alhinin dake cikin zuciyarta amma tasan sharadin yin hakan bata manta ba,yace duk sanda ta sake nuna bata son cikinsa ta tabbatar da cewa ta bashi license na qara aure ne,har yau diyar ambassador na nijer na nan,duk da an kusa bikinta idan yace yana so babu abinda zai hanasu bashi "amma likita don Allah?" "Na auro saliha?" Kada kai tayi da sauri "Amir fa,shekararsa daya da rabi yanzu fa" "Sanda kika haifi aboki shekarar su amatu daya da wata hudu,me ya sameki?" Kai ta kada "Ba komai" "Kada fa ki yiwa Allah butulci,kin manta sunan da ake kiranki a baya" "Asragfurullah" ta ambata da sauri,har yau bata mance rigimar cikin qarami ba,anty ni'imah cewa tayi tana so a bata ita,tun a sannan jikinta ya sake sanyi,sai yanzu zata sake gwadawa abinka da dam adam kayan Allah "Taimakeni ki sallami yarankin nan don Allah nima aji da ni" ya fada yana langabe kai gwanin tausayi kaman gaske,bushewa tayi da dariya don ya bata dariya,cikin wayo da dabara ta dinga kaisu daki suna kwanciya har da amir kuwa duk da dafarsa,amatur rahman kawai ta rage,ta kafe kai da fata sai an fara bude gifts da suka samu a daren,tun tana daurewa har ta bata haushi ta kai mata duka,tako sameta cinya da daku sosai,kuka ta saki ta soma sosa wajen yayin da sumayyan ta rufeta da hargowa kaman zata sake kai mata wani dukan,kallonta kawai almustaphan yayi sai ya dauke kai,ya janyo amatur rahman din ya yaye rigar jikinta,abinka da farar fata wajen kuwa yayi jazur sosai,shafa mata wajen ya aoma yi yana hura mata cikin salon nusarwa yace "Ba'a yiwa mama musu da taurin kai,haba amatu...ke da kike babba....baku ganu su ikram da su affan duka kin girme musu kuma sun tagi sun kwanta,baki son mama ta huta ne itama?" Kai ta gyada alamar tana so a sanyaye "tun jiya mama bata zauna ba uhm,ki bata haquri kuce ba zaki daina ba" a sanyaye ta dubi sumayya da tayi kicin kicin da rai,ranta na wanu irin baci,wanda abinda tayi mata baikai bacin ran da take ji ba,don idan da sabo da tasa ba da halin amatur rahman "Ammi....kiyi haquri" da yake suna kiranta da sunan da abdallah ke kiranta ne,saboda duk hutu anan yake zuwa yayi,akwai sabo da shaquwa sosai tsakaninsu tamkar uwa daya uba daya,su kansun a yanzun sun dauka babansu shi ya haifeshi,an ce musu shine babbansu yana kano ne yana karatu sai ya gama zai dawo,qin amsa mata tayi sai data maimaita sannan tace "Naji....tashi kije ki kwanta" miqewa tayi har ta soma takawa tace "Ammi....amma yaya abdallah da yace zai kiramu bai kira ba fa" "Ban gaya miki jarabawa yake ba baya waya sai ya gama?!" Ta fada mata a tsawace,sai ta juya sum sum ra fice zuwa dakin,yayin da almustapha ya zuba mata ido,sai da yarinyar ta fice sannan ta ja tsaki suka hada ido da shi,dauke kai yayi ya miqe ya wuce nashi bedroom din,sannan ta miqe ta bishi a baya.        Sanda ta shiga har ya shiga wankanshi,qwafa tayi ganin ya hada ruwan wankan da kanshi kenan,abinda ya kasance aikinta ne ita keyi,hakan ya sanya ta zauna tana hade rau ta janyo wayarta ta soma neman mamanta,ba jimawa ta daga,sunyi hira sosai ta tambayeta 'yan jikokin nata tace duka sunyi bacci,suna gamawa ta katse ta kira halima suka gaisa ta hadata da abdallah wanda keta karatun common intrance za'a shiga secondry,suka gama hirarsu ta masa addu'a sannan ta kira zainab itama suka gaisa,tace gata kwance shiru gidan ba dadi duk sabida ba hayaniyar yara,gashi sabon gida suka koma sabuwar unguwa,dariya tayi tace idan zaki kwanta ma kiyi baccinku gwara kiyi,donsu yanzu haka ma sun jima da yin bacci,dariya tayi suka dan taba hira sannan ta katse ta kira nafisa,itama yaran nafisan na wajenta su biyu,sunyi hira abinsu sosai irinta qawaye kafin suyi sallama,daga qarshe ta kira yaya yahansu wadda a yanzun ta bata jari take business ba saida atamfofi,ba qaramin ciniki take ba,sosai rayuwarta data yaranta dake gidan aure ta inganta sai son barka,dai dai sanda ta ajjiye wayar ya fito yana tsabe jikinsa da towel,suka sakw hada ido ta kauda kai,dariya yake qoqarin boyewa amma ya kasa,ya sani cewa ta koyi fushi cikin kwanakin tun kafin tasan cewa tana da cikin,wanda yasan baya rasa nasaba da cikin da take da shi,kowanne ciki akwai irin yanayin da yake zuwa ma mace da shi,yadda ta hade rai ya sanya dariyar fitowa a dole,sai ta juyo ta dubeshi take ta saka kuka kaman qaramar yarinya,dariya yake sosai ya ajjiye towel din ya tako zuwa inda take "U r craying like a baby,ko qarami bazayayi irin wannan kukan ba,wai mema aka miki,you beat my daughter bance dake komai ba,shi ya bata miki rai ko kuwa?" "Wallahi hancina kakewa dariya" ta fada taba shafa hancin wanda sai yanzu taji alamun ya bude kaman cikin 'yan biyu,wata dariyar ce ta sake hardeshi,yayin data qara volume na kukanta,ganin tana kukan bilhaqqi ya sanya ya fara damunsa,sai ya sassauta dariyan ya tako gabanta,kan gwiwoyinshi ya durqusa,yasa duka hannyenshi ya kama kunnuwansa yana cewa "Is ok...am sorry...am really sorry babe,idan baki huce ba kimin duk hukuncin da kike so" sai ta fara sassauta kukan tana kallonshi,tsahon minti biyar kafin tace "Labari zaka ta bani har na awa daya" dariya ta sake kamashi wannan karon ya maidata,yasani sarai mugunta ta shirya masa,ra ina zai iya surutu na awa daya ai da sai yasha magani,sai ya narke mata kalan tausayi ya sanya tafin hannunshi duka biyu a kumatunsa alaman tagumi "Wayyo ummina....kina ina ana punishing dina"salon yadda yayi maganan dole ya baka dariya,sai data daara sannan ta maze "ba ruwan ummi a nan,ita ta aikeka kayi tsokana?....so tunda karanta labarai ya maka tsauri sai kayi kamun kunne ko tsallen kwado wanne yafi maka?" Hannayenshi ya hade waje daya yana jujjuya kai "Almustapha yau kaga ta kanka wallahi,ka tabo uwar biyun nan" idanu ta zaro "Wa ya gaya maka 'yan biyu zan haifa?" "In sha Allahu,kisa ido ki gani,zuwana umara na qarshe kafin ki samu cikin su na roqa,kuma nasan in sha Allah Allah ya amsa" harararshi tayi,sai ya saki dariya ya miqe yana dagata "Kinga....naga labarin babba ne,muje kiyi wanka kizo kiji" shi ya rakata ya kuna tsayata ta gama wankan suka dawo dakin tare.      Tana jikinsa yana daddanna cumputer yana,bangaron hotunan dake cikin cumputer din hannunshi ya kai,hotunansu amatallah ne amatur rahman aboki da amir,hutuna ne kala kala,wasu cikin gidansu,wasu a makaranta,wasu bakin ruwa wasu sanda suke fita shan coffe,wasu kuma a wasu park park da ya saba kaisu duk qarshen sati idan bai samu dama ba kuma bayan sati biyu ko sumayya ta debesu su fice,da yake dubai gari ne da suke da yawan wajen shaqatawa sai wanda ka zaba,yana son yaranshi qwarai,yana son moment din,sanda zai kaisu wajen wasan yara,ya zauna daga gefe guda yana lura da duk motsin kowannensu,yana musu hoto ko vedios,yana kalla yana murmushi,bashi kadai ke ganin kyawun yaran nashi ba,kowa cikin dangi yana fadan haka,sun fita daban,haka tarbiyyarau abar kwatance ce da misali,duk da zamansu a baquwar qasa hakan baisa sunyi sakaci da tarbiyyarsu ba,hankalin su na tashi qwarai ko yaya suka ga wani canjin dabi'a a wajensu har sai sun tabbatar sun gusar da haka,sai da ya gama kallon tana tayashi suna tattaunawa ko halayen kowanne cikin yaran nasu sannan ya fita ya soma nuna mata wasu sabbin estate da ya gina cikin abuja,sai da ya kammala tsaf sannan yace "Daya naki ne,akwai kudi da na saka miki cikin accnt ki duba" idanu ta zaro zatayi magana,sai ya dora hannunshi kan lebansa "Kada kice komai,a duk sanda kika haihu nayi yunqurin yi miki kyauta sai kice a'ah,wannan karon kam kada ki hanani kuma kada kice komai" qwalla ce ta cika a idanunta,sai ya soma share mata yana murmushi tare da cewa "Kin cancanta,kinfi qarfin komai a wajena" godiya tayi masa sosai da addu'a mai bala'in shiga zuciya da ratsa jiki,bayan ya gama amsawa ya sake cewa "Akwai abinda nakeso a yuwa su'ad da mukhtar,abban abdallah" "Sadaqatul jariya?" Ta tambaya da sauri,murmushi yayi yana dubanta "Eh....dama nasan abun yana ranki,na sanya wani yaro sharu ya binciko min qananun hukumomi dake kano gwambe katsina da jigawa wadanda ke buqatar ruwan sha,masallatai da makarantu,zamu gina Allah ya sanya ladan a mizaninsu,muma zanyi mana,saboda halin rayuwa,duk da gidajen marayu dana gina,da qungiyoyin da tallafi da nake badawa hakan bai gamsheni ba,zamu qara sabida mu tadda kyakyawan guzuri a lahaira,ke ni ummi baba malam har da anty maamaa" kuka ya qwace mata,ta rasa da bakin da zata masa godiya,wanne irin taushin zuciya gareshi haka "Allah yayi maka kyakkyawan qarshe,ya rabaka da iyayenka lafiya" addu'arta ta qarshe da shi kenan,idanu ya lumshe yana amsawa don ba qaramin dadi addu'ar tayi masa ba "Na gama shirya komai,in sha Allah za'a bamu abdallah da zarar ya gama junior secondry a dubai zaiyi senior da jami'a baki daya har sanda zaice karatu ya isheshi" murmushi ta saki tana goge hawayen farinciki "Danka ne noor,duk yadda kayi dai dai ne" "Ina son abdallah baby...Allah ne baiyi zai fito daga tsatsona ba,ina jinsa kaman dana na ciki na" murmushi kawai take,ko yanzu babu abinda abdallah ya rasa banda mahaifi wanda ya haifeshi,amma a rayuwarshi saidai ya yiwa wani ma,kafin tace komai wayarta dake gefe ta dauki ruri,sunan zainab kano ke yawo,ta miqa hannu zata dauka ya rigata daukar ya kashe wayar tana kallo "Time dina ne,na tsani abinda zai dinga shiga tsakanina da ke,banson abinda zai dinga hanani kallonki" murmushi kawai tayi,tasan da biyu yake fadin haka,ta rasa me yasa duk mutanen da suka munana mata yafi riqar zainab akan kowa,bai hanata tayi mata duk abinda tayi niyya na alkhairi ba amma baison tarayyarsu ko kadan,zainab ce ke kiranta wadda sun hadu da ita ne randa ta qaddamar da bude qungiyar ta ta taimakon nakasassu da masu buqata ta musamman dake cikin gidan yari wanda zainab na cikinsu,ranar tayi kuka tayi kuka wanda hakan ya sake bata ran almustapha kaman yadda zainab din itama tayi kuka kaman ta cire idanunta,zainab ce babu qafafu biyu,tana rayuwar tantal bataiti,bata da cikakken wajen zama,mamarta baqincikinta ya kasheta,babansu ya koma qauyensj bayan ya aurar da qannanta,danta nafi'u kuwa an saceshi an nemeshi sama da qasa an rasa,daga bisani bincike ya tabbatar masu yankan kan data so saida abdallah ne da basu sameshi ba suka ce ba zasu haqura ba tunda ta saka musu rai suka daukeshi suka salwantar "Ba za'a sake ba yallabai in sha Allah" ta furta tana murmushi,sai ya saki murmushin shima,ya janyota jikinsa sosai yana shaqar qamshinta wanda ko tafiya yayi yana daya daga cikin abinda ke tsaya masa game da ita acikin ranshi.        "Ranar lahadi zamu wuce kano da duka yaran nan a maidasu gida,sabida birthday kin dauko musu yara haka kawai...tab..wallahi nikam bani iya barin yarana su motsa nan da can" duban idanunshi take tana dariya,Allah ya zuba masa qaunar yaranahi,inda Allah yayi taimako hakan bai sanya sun sangarce ba yana tsawata musu da nasiha idan sukayi ba dai dai ba,cikin salon tsokana tace "Wai da zan barsu nan gidan wajen ummi ma idan zamu koma ko na kai wasu kano wajensu zainab" "Allah ya baki sa'a" kawai ya fada yana kashe system din ba tare daya dubeta ba,hakan ya bata dariya sosai "Ni na isa?,tuba nake yallabai,Allah ya taimakeka,da kai da kaya ai duka mallakar wuya ne,ko ni kaina banda iko da kaina sai abinda ka zaratar" wani juyi yayi cikin zafin nama ya juyeta qasa ya danneta yana duban qwayar idanunta,itama shi take kallo kowannensu na fidda murmushi,suka soma musayar numfashin juna "Sai yaushe zaki daina kambamani ne haka,farinciki da umarni na ne ko yaushe gaba da komai naki koda baki so"cikin siga ta rada da muryarta mai tsananin laushi tace tana girgiza kai "Babu wannan ranar,banganta ba noor....mijine kai na musamman daya tamkar da miliyan.....inaso naci gaba da kasancewa Mace ta gari a gareka,na shiga qabarina kana mai yarda da ni" "Kin dade da amsa wannan sunan baby.....a mace ta garin ma keta musamman ce...,da mutum na bawa dan uwanahi mutum aljanna tun a duniya da tuni na baki sunayyah!,na godewa Allah da ya sanya kika zamo cikin KUNDIN QADDARATA"fari tayi da idamunta cikin tsantsar farinciki da jin dadin lambar yabo da cikakkiyar yardar data samu daga mijinta tace " nice da wannan godiyar MY MAAN,NA GODEWA ALLAH DA YA CIKA KUNDIN QADDARATA DA ZALLAR FARINCIKI DA SAMUN MIJI NA GARI KAMAR KAI,YA SAUYA KUKA NA YA KOMA DARIYATA,FARGABATA DA RASHIN TABBAS YA ZUWA YAQINI DA CIKAKKEN TABBACI"dariyar zallar farinciki ya saki yana sake qanqameta "indai haka ne saidai muci gaba da damqawa junanmu zallar qauna soyayya da yarda,mu kuma yi addu'ar haduwarmu a aljanna ki zame min jagorar mata na ta gidan aljanna" kai ta jinjina tana sake shigewa jikinsa tana jin wani aminci gewaye da da dukkan rayuwarta "INDAI HAKA NE INA MANA FATAN HADUWA GIDAN ALJANNA" "allahumma amin ummu aulady"ya furta cikin zafin nama yana hade bakinshi da nata ya shiga aika mata saqonni,nikam nace Allah ya bar qauna na fice na bar musu dakin,a bankali na fice daga gidan ina musu bankwana dasu,tare da musu kyakkyawan fata har zuwa qarshen rayuwarsu,da ci gaba samun dawwamammen farinciki. *SABO TUREKEN WAWA,KOMAI YAYI FARKO YANA DA QARSHE BANDA IKON ALLAH* Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah madaukakin sarki wanda ya banbamta tsakanin bata da shiriya,ya bambanta tsakanin haske da duhu,tsira da amincin Allah su tabbata ga shugaban talikai annabi muhammad S A W. Ina godiya ga daukacin ilahirin fans dina,na kusa dana nesa,wadanda na sani da wanda ban sani ba,ina miqa matuqar godiyata,grouos din da nake ciki da wadanda bana ciki,jinjinata a gareku HUGUMA CONVERSATION ROOM DA HUGUMA NOVELA ROOM,haqiqa qaunar da kuke nunamin ba kadan bace,ina fatan Allah ya faranta muku fiye da tunaninku,sauran groups bazan manta da ku ba ZAMA NA AMANA GROUP HAUSA NOVELS NA UMAR DALHA HAUSA NOVEL ZAUREN BIEBIE ISAH DA NOVELS SHELF INSPIRING STORIES MAMAN HANEEF NOVELS MAMAM AYSHA NOVELS KUNDIN HASKE HASKE FANS GROUP DA KUMA QUNGIYATA TA HASKE WRITERS ASSO BAZAN WUCE BA BAN GAIDAKU BA MAMAN KHADIJA HAJJA RANO KDEEY DA KUMA ME SUNAN SURUKATA AYSHA DAN SABO ALLAH YACI GABA DA HADA KAN MU INA SAKE GODE MUKU SIS SAHURA SIS RUQAYYA SIS TASH MARIYA SB JAZAKUMULLAH BI KHAIR MASU SON A QARA TSHON KUNDIN QADDARATA ina mai baku haquri,komai yayi farko dole yayi qarshe,hakanan duk abinda duk dadinsa wataran zai fita daga kai ne watan watarana,muyi haquri tunda saqon ya isa,muyi fatan samun lafiya da tsahon rai watarana sai mu sake haduwa a gaba. ZANSO BAYAN TAYA MURNAR KAMMALAWA NAJI WANI DAN TSOKACI DAGA BAKUNANKU GAME DA LITTAFIN HAKAN ZAI BADA MA'ANA. ina sake miqa godiyata ga Allah da ya aran rai da lafiya,ya kuma bani ikon kammala wannan littafi nawa,a daren laraba 20/3/2019,ina roqon ubangiji ya yafemin dukkan kura kuraina dake ciki,dai dai din ciki Allah ya datar da mu ya sanya min a mizani. Ina miqa qoqon barata da kuyimin addu'a ko sau daya ne,ku roqamin Allah ya cikamin burina alfarmar sayyadina rasulillah S A W. Na gode. Ga maiso ya duba status dina don ganin 'yan biyu😄😄 Subhanakallahumma wabi hamdika,ashhadu an la'ilaha illa anta,astagfiruka wa atubu ilaika. #mrs muhammad ce. #ummu muhammadiyya. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽