.*AUREN HUCE HAUSHI* AISHAT ISAH MUSAH Maman Fateemah. 08055362975 Or 09061432330 Page 80. .....….….. Subhanallahi mutanen dake parlourn suka dauka, da sauri Ammah da Aunty Hasana suka matso gurin da Mamar ta Fadi Ammah tana fadin.. "Ikon Allah har yanzu jikin ne kenan da Baki fito ba, Hasana maza Nemo Abdul Hakeem ko Hamza aje asibiti"O. "Gaskiya dai Kam tunda abun Yana neman ya Zama wani Abu daban". Hajiya kaltume ta fada yayinda wata daga cikin bakin tace. "Anya Bata da hypertension kuwa?". "Nima abinda nake tunani kenan gaskiya". Ammah ta fad'a. Cikin kankanin lokaci Hamza da imam suka shigo yayin da a waje Abdul Hakeem ta fito da mota, zilai da sahura ne suka dauketa suka nufi waje da ita, Aunty Hasana ta rufa musu baya suka fice. Saida komai ya lafa sannan su Hajiya kaltume suka samu Damar fuskantar bakinsu,nan da nan aka Fara sauke musu ashirin ta arziki Alawiyya da magaji Wanda Bai bi Yan asibitin ba domin yasan tsabar tashin hankali ne ya haddasawa mama wannan abun ba komai ba, duk Wanda yace ruwan wani baze tafasa ba nasa ko zafi bazeyi ba. Abinci bakin waje suka ringa fita dashi, sai da bakin sukaci abinci sukayi sallah sannan Aunty Surayya ta gabatar da Kayan lefen gasu Hajiya kaltume dasu Inna maimuna wadda tun faduwar Mama taja jikinta gefe tasan mugun nufinta ne ya Fara tambayarta tunda taga duk yanda ta dunga dakile Lamarin Zahra Ubangiji ya nuna Mata shine Arrazzaqu shike daukaka bawa duk kuwa yanda makiya suka so su dankwafe mutum sai ya nuna karfin ikonsa a Kan abun, gashi an waya gari Zahra tayi musu wata irin tazara tamkar tsakanin sama da kasa haka tazarar take,abinda ko a mafarki ko a hasashe babu Wanda ya taba kawo hakan. Sun godiya sosai, sannan Aunty Surayyar ta dauko key ta mikawa Hajiya kaltume tana fadin gashi inji Ammi tace a kawowa Ammah tana gaisheta kafin komai ya lafa tazo su gaisa ace ayi Mata godiya sosai da sosai. Duk gurin ba Wanda baiyi mamaki ba na wannan kyautar girman da aka yiwa uwar Amarya. Matan makotan da suka shigo suka Fara bude kayan ana gani ana Sanya Alkhairi a ciki. Aunty Mahafuza Matar Ya Ibrahim ce tace . "Wai ina amaryar tamu ne a rakamu mu gaisa da ita kafin a kaimana ita". Inna maimuna ce tace "tashi muje ai ba nisa tayi ba tana Cikin dakin nan". Tashi tayi tana fadin gara muyi sabo tun daga Nan na Zama ta farko da zata sani a cikin matan yayun mijinta". Inna maimuna na gaba Mahafuza na binta a baya har kofar bedroom din dasu Zahra suke ita da mujiba da Yan uwanta da sukazo dasu Inna maimunar Salima da Ibtihal, salima ce ta bude kofar su Inna maimunar suka shigo idon Mahafuzar Yana Kan Zahra wadda take zaune a Kan sofa Tasha ubansu lace Wanda ya amsa sunansa tayi wani irin fitinan nan kyau a cikinsa tana daddanna iPhone sixteen plus dinta tana daga sexy eyes dinta sukayi four eyes da Mahafuzar, ba shiri ta hadiye wani Abu Daya sille ya wuce Mata Bata shirya ba. "Tabarakallahu Ahasanul kaliqin, Masha Allah" ta fada a zuciyarta, ai ita a yanda Habibinta ya fada Mata yarinyar Daya gani a part din Ammi da yake tunanin ko budurwar mahmud din ce sai taga Bai iya bada bayanin mutum ba Sam. Da fara'arta ta shigo tana musu sallama da fara'a Suma su salima suka amsa Mata suka gaisheta, Cikin nutsuwa da Jan ajiya da nuna sanin ciwon Kai Zahra ta gaishe da Mahafuza din. Gurin Zama su mujiba suka bawa Mahafuzar suna fadin. "Ki zauna Mana ga guri Aunty". Gefen gadon ta zauna tana duban zahra a kaikaice, haka Nan yarinyar tayi Mata kwarjini sosai sai taji duk ta Raina kanta duk da itama 'yar gayu ce kuma ba laifi da nata daidai kyawun Amma ganin zahra sai taji tayi lakwas tunda da biyu ta nace akan saita biyo masu kawo lefen duk da mutum hudu kawai ake bukata Mata Saida tayi yanda tayi Dan taga kul uwar daka, tunda daga waje taji gwiwarta ta sace tasan wannan da alama tafi gaban raini, to Kuma sai gashi taga itama Zahrar zahra ce ga Jan aji da alama bazata dauki raini ba.. Ganin shirun ya yi yawa yasa Mahafuza tace Amarya zamu tafi "Ni sunana Mahafuza matar Ibrahim Dange yayan mahmud". Dan murmushi zahra tayi. "Na gode Aunty Mahafuza". Tashi tayi tana fadin. "Nima na gode Amaryar mu sai kin Karaso naso ace Ina Cikin masu kwana mu tafi tare". 'yar dariya zahra tayi wadda ta Kara fito da sirrin kyawunta. Bayan ta fita Ibtihal tayi wani tsalle tana fadin. "Yessss! Adda zahra haka nake son Kama Kai da nemawa Kai mutumci". Wayar hannunta ta aje tana fadin. "Ibtihal Baki Jin magana wallahi me Kuma nayi?". "Meye ma bakiyi ba irin wannan jam class haka kamar wata saraunya fa haka kikeyi acting". Dan murmushi zahra tayi tana tuna hudubar Hajiyar makwarari lokacin da take Mata karatun dangin mijinta da yanda zata zauna dasu da yanda zata kama kanta kada ta bada fuskar da za'a Raina ta, wato ta yarda da maganar da Hausawa ke fada na cewar duk abinda Babba ya hango yaro baze hango ba ko ya hau itace rimi sai yau ta yarda da hakan, da gani wannan da salon nata rainin hankalin ta shigo Sai kuma taga an fita iyawa. Suna Nan suna maida yanda akayi Su Aunty Surayya suka shigo Zahra ta gaishe su, Nan Aunty Mahafuza ta gabatarwa Zahra Aunty Surayya da kanwar Abbie maman ya Abbas surukar Aishat sai 'yar kanwar Hajja kakar su Mahmud ta wajen uwa, sun yaba matuka da zabin mahmud sosai, sunyi musu Addu'ar Albarkar Aure sannan suka fita. Aunty Surayya ce ta dawo ganin ta dawo yasa su salima suka fice daga dakin. Kusa da Zahra ta zauna wadda ta sadda Kai saboda wani nauyinta taji ya kamata niyyar zamewa tayi kasa Aunty Surayyar ta hanata. "Zauna magana zamuyi dake, kina jina Zaki shiga sabon guri da wasu mutane Wanda zakiyi rayuwa ta har abada dasu in Sha Allah,to ki nutsu ki fashinci kowa kada kiyi garaje a cikin tafiyar ki saka hankali sosai gurin wadanda Zaki mu'amalanta babu ruwanki da kowa babu ruwanki da 'yan matan family din Nan duk yawancinsu burinsu Kan mijinki yake kada wata ta dauko Abu ta kawo Miki da sunan kyauta naci Kona Sha kiyi amfani dashi idan Kika cire Amminsa to sai Hajiya Inna, koni idan ban Kwanta Miki ba kada kiyi amfani da abunda Zan Baki kinji ko". Kai Zahra ta gyada mata. "Naji Aunty nagode in Sha Allah Zan kula da abinda Kika fada mini". "Yauwa Kinga pass na dinner ko? Aishat tace zakuyi waya ki bawa kawayenki na kusa wadanda Kika San zasuje tunda abune da anan ya Riga ya Dade da wucewa mu a canne yake sabo, Kuma gobe insha Allah zaku taho mu yau zamubi jirgi daga Bauchi zuwa sokoto tunda mu duka har mazan mu bakwai ne, Kuma anan zamu bar Hajiayarsu Abbas da Hajja Asiya tare dasu zaku wuce goben, ki kula ki daraja Ammi tana sonki matuka kinji". Kai ta gyada Mata sai taji matar ta burgeta sosai domin a zamanin Nan babu Mai fada maka irin wannan sai mai kaunarka. Alawiyya ce tayi knocking ta leko tace "ana jiran Aunty Surayya". Sallama ta yiwa Zahra ta fice da sauri. *** Tun kafin aje asibitin Mama ta dawo hayyacinta abun nata kamar iska haka Nan suka karasa a A/E suka dubata, tambayoyi suka shiga Jero Mata akan wane abune ya daga Mata hankali har BP dinta ya Mai dari da tamanin kasan ya Kai dari da goma, dagewa tayi ita babu abinda ya tada Mata hankali, su dai su Aunty Hasana Ido ne nasu, Mama taso su barta su dawo gida Amma suka riketa saboda sunga karfin Hali ne kawai takeyi Amma Bata da lafiya sosai zuciyarta ma tana neman kamuwa da ciwo matukar ba'ayi controlling din jinin ba, dole ta hakura aka saka Mata magani a kasan harshe aka Kuma saka Mata Karin ruwa aka saka Allurar barci dole tanaji tana gani barci yayi awon gaba da ita, Ammah ta kirawo Aunty Hasana ya Kai sau uku tana tambayar ya jikin nata. Daga karshe Aunty Hasanar gida Abdul Hakeem ya dawo da ita ta baro su zilan a can, lokacin data dawo bakin da zasu tafi sun tafi sai mutum biyun da zasu kwana suma Sana can bangaren baki. Kayan ta tarar Makota sun shigo an bude iya Wanda za'a Iya budewa sauran kuma an tattarasu gefe guda Dan bazasu ganu a Kan kanin lokaci ba. Yawan akwatunan Aunty Hasana ta tsaya kallo, Saida ta shiga dakin Ammah ta tsinkayo zancen motar da Ammi ta aikowa da Ammah. Washe gari tun sassafe motocin Kaya biyu suka dauki hanyar sokoto. Tun dare Mama ta dawo daga asibitin, matsa musu tayi akan a sallameta dole suka sallameta duk da Abba yace ta hakura ta barsu suyi aikinsu ta matsa ita dai babu abinda yake damunta. Zahra har dakin bakinsu salima da Ibtihal suka rakata ta gaishe dasu Cikin ladabi da biyyaya, shi Albarka dai zahre ta shata. Lokacin da meyin makeup ne tazo Zahra Ido ya Raina fata da duk gani takeyi kamar wasa ne babu inda zata tafi shi dai ya dawo ya same ta kamar yanda ya Saba. Nan da Nan taji wata irin karaya da tashin hankali ya saukar Mata ai ji tayi wancen wasan yara ne yanzu ne dai za'ayi maganar gaskiya,Cikin abinda be wuce minti talatin ba aka gama komai tayi kyau kamar me, sai Zuba wani kamshi take na musamman, ita kanta Ammah dauriya kawai takeyi Dan ganin abun tayi kamar yanzu ne take bikin wancen Wasa tayi duba da yanzu yanda ake komai da dangin mijinta ba kamar wancen Karon ba da su kadai su kayi budurinsu, ga tashin Hankali Sam babu nutsuwa haka tana gidan Kullum tana zulumi akan yaron kada ya gudu da yarinya ko Kuma ya gudu ya barta da ciki ba Kuma asan asalin inda za'a nema shi ba, Amma yanzu Allah s.w.a ya gama Mata gata ya juya Lamarin 'yar marainiyar Allah ya share Mata hawayen data Dade tana zubarwa akan tozarcin da ake Mata akan aure, sai gashi Ashe wani hanin ga Allah baiwa ne, wa ya taba zaton yaron Nan wani ne ko Dan wani? Ba Karamin toshe kunnuwa Abban Yara yayi ba lokacin da ake Kan ganiyar maganar ana ta ruruta wutar ya aura Mata Almajiri Wanda ba'a San asalinsa ba Dan ba 'yarsa bace Amma ace duk yanda take da kyau da cikar halitta ta Kare a kolo fakiri marar madafa, to gashi hakuri Mai tarar da arziki yau ga Zahra ta Zama farin wata Sha kallo, ga lefen da ba'a taba kwatanta kawo Mata Koda kwata dinsa ba, yanzu haka wancen lefen suna Nan a daki to ga Kuma wannan Sha kumdum din. Wurin Abbanta Aunty Hasana ta rakata yayi Mata Nasiha sosai ya Kara jaddada Mata mashimmancin biyayyar Aure. Kafin karfe Sha Daya gidan ya dinke da jama'a abin har yaso ya bawa Ammah mamaki to ita dai Hajiya kaltume ta dankawa I. V din da Ammi ta aiko dasu na mutanen Ammah ita dai kawai tasan ta Debi shida ta bawa maman mujiba tace ta aikwa makota Koda Wanda zasuje kada abun ya Zama na tsegumi. Zahra ma nata mujiba ta debarwa tace ta bawa kawayensu Amma kadan zata bawa ita kunya ma takeji Ace Wai za'ayi wani Abu kuma na bikinta, daga baya kenan Wai sadaka da bazawara. Ta bawa magaji ya kaiwa Amatu da Aunty safiya sai wasu Kuma ta bawa sauran malaman duk da tasan abune Mai wahala suje tunda ko a Nan basuje ba tunda sukaji labarin ance mijin Almajiri ne. Zahra na dakin Ammah su Inna suna karayi Mata nasihar zanmantakewar aure tana ta sharbar kuka, ficewa Ammah tayi Dan itama daf take da sakin nata kukan. Tun dare Ammi ta Kira Ammah ta fada Mata akwai tickets na mutum goma a Nan hannun wani a Bauchi Wanda zasu rako Zahra dakinta, Sameer Yana Nan shine ze musu komai ze shigo su wuce sauran mutanen Kuma motoci sun taho. Har Cikin jirgi Abbanta ya kaita ya zaunar da ita kusa da Inna mainuna da Hajiya kaltume, Yana fadin. "Hajiya gata Nan a mikata hannun Alhaji Muhammadu ace masa ga Amanar 'yata Nan kafin nazo da kaina,Allah ya saukeku lafiya uwata ayi ta hakuri kinji". Kai kawai ta iya gyada Masa ya juya ya wuce tabe baki mama tayi wadda ta kafa sai taje sokoton ita ta warke abinda yaso ya kawo sabani kenan da Abba sai da Ammah ta shiga tsakani tace ya barta tunda tace zata iya. Karfe Daya da kwata jirginsu Zahra ya sauka a sokoto,wani irin Abu Zahra taji ya tsirga Mata gata a sokoto karo na biyu a cikin girma da mutumci kamar ko wace Mace da ake aurowa daga gaban iyayenta sai yanzu ta Kara fahimtar manufar Ammi na rabata da gidan tun ba'a Farga da ita ba,wato wannan martabar take nemar Mata kenan. A Hankali take sakkowa daga steps din jirgin sanye da rigar material Mai azabar kyau da sari fari tasan Mai ratsin flowers coffee kalar material din Aunty Hasana na biye da ita a baya. Yana tsaye daga gefe shida Tajuddeen ta ringa saukowa wata ni'ima yaji tana saukar Masa, ya yarda ya amince ta zamar Masa wani bangaren jikinsa ganinta kadai ya saka masa nutsuwa Yana binta da Ido har suka karasa gurin motocin da aka tanada Dan daukarta. Tambayar duniya Tajuddeen yayi Masa akan me Suke jira a airport Amma yayi Masa Shiru. Sai da suka wuce sannan Sameer ya Karaso Yana fadin. "Ina Ina zamu nufa ne Wai?". Wani smile yayi Wanda Kama gani kasan Yana Cikin nishadi. "Gidan uwar gida za'a kaita mana ta kwashi albarka, sannan ku kaita gurin Ammin na fadawa Shatu komai kuje Dan Allah Naga idanu sunyi yawa a kanta". "Shegen sama kace wannan model din itace kayo kamu, Wai Dan Allah yaushe ka Sami lokacin mace yanda nasanka baka da lokacin kowa saina sabgarka, Amma India ce ko?". "Bafulatanar Adamawa ce?". Ya fada a takaice yayi gaba inda Naseer yake zaman jiransu, da sauri Tajuddeen yabi bayansa. Su Zahra na dosar inda masu tarbarsu suke Aishat ta taho da sauri tana rike da Afnan Wanda suka dauki wanka gayu dai yaci gidansu a gurin, rungumo Zahra tayi tana fadin. "Amincin Allah da Rahamarsa su sauka a gareki sister Fateemah Zahra. Allah ya albarkaci Aurenku da zuri'a masu Albarka, barka da shigowa DANGE FAMILY you're welcome". Afnan ce ta Fara zillo tana rinjayowa gurin Zahra, wato ta ganeta. Hannu Zahra tasa ta karbi Afnan din daga hannun Aunty Aishat din, Hajiya kaltume da Inna maimuna suka nufi ubansun motar da za'a dauki Zahrar wadda sabuwa ce Zahrar ce farkon shigarta bayan direban Daya tukota. Tun a airport Mama ta Fara Raina kanta yanda taga Mata 'yan gayu na gani kasheni Wai duk masu tarbar Zahra ne, ga wata yarinya Kuma da suka rungume juna itama wanke hannu ka taba ga Kuma yanda taga wata farar mace nata kaffa kaffa da Zahrar. Mama Bata Kara Raina kanta ba sai da suka shigo gidan Hajiya Inna inda taji wasu Mata na fadin. "Wallahi soyayyar Hajiya Inna da mahmud tana burgeni sosai kiga fa Saida ya Fara cewa a kawota gurin kakarsa kafin a kaita gurin mahaifiyarsa". Wata ashariya Mama ta lafta a Cikin zuciyarta tana karewa gidan kallo me kalaman wadannan matan ke nufi? Gidan kakarsa wannan din? Ai jikinta har tsuma yake ta nufi kofar shiga da sauri so take taga zahiri Nan gidan tsohuwa ne, to Ina ga gidan iyayensa da Kuma nasa? Wato maganar malam na Bande ta tabbata da yace wannan yaron yafi ko wane namiji daya taba kwatanta Yana sonta karfin arziki saita dauki maganarsa shifcin gizo yaso ya nuna Mata hanyar da za'a dakile abun duk da yace shi baiga saki a tattare da ita ba. Wato abinda ya gano Mata kenan tayi kunnen uwar shegu da maganarsa, ga abinda Asabe tayi Mata ta tabbata da an aiwatar da abin nan da yanzu wata kila Daya daga Cikin yaranta ne Dan aikin anyi shi da niyyar Zahrar ta bijiere ne taki mahmud fir har Abbansu yaji haushi ya Kara bashi madadinta da Daya daga Cikin yaran nata, sai kuma Asabe tayi batan dabo Wanda har yau ko labarin Wanda ya ganta Mama Bataji ba. Parlour ne na Alfarma tamkar wata fada Dan a tsakanin shekaran jiya da jiya Saida aka canza komai na parlourn tun Inna na mita harta hakura dan tasan ba fasawa za"ayi ba Cikin barkwanci Hajiya Inna da jama'arta suka tarbi amarya da danginta, an Sha dariya Dan Hajiya Inna cewa tayi. "Haba da walakin goro a miya shi yasa ya tubure mini Yana faman rantsuwar baze dawo ba saiya Nemo ki duk inda kike a duniyar Nan ya kawo mini ke har gida a ranar da ze bar gidan Nan, Ashe da abinda ya gano, tofa ko yaya ne dai nice ta karfen Kinga ai niya Fara kawowa ke ko?". Inna maimuna ce tayi 'yar dariyar barkwanci Yana fadin. "Ai Hajiya duk abinda lauje ya yayo ciyawa ce, Kai da Kaya Kuma duk mallakar wuya ne, ga Zahra Nan taki ce tunda mahmud nake ne" Dariya Hajiya innar tayi tana fadin. "Ato gara na fada Mata kada taga Yana kawo min abu Mai maiko tace ya fifitani akanta." Akayi dariya dai, duk Mama na zaune kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki ba wani karsashi ko daya ga rashin dadin jiki karfin Hali kawai takeyi Amma lafiyar dai sai a hankali. Nan cikin part din Aunty Aishat tayiwa Zahrar da Aunty Hasana masauki kusa da bedroom dinsa na part din jiya aka hada dakin komai sabo ne, laffayar Zahra ta cire ta kwanta kusa da diyarta da take ta Wasa da kafafuwa tana dagasu sama da gani tana Cikin farin ciki. Saida Aishat ta fice sannan Aunty Hasana ta dubi Zahra. "Wacece wannan? Naga Suma matukar Kama da mahmud sai dai ita farace sosai". "Twins sister dinsa ce kamar keda Ya Hassan". "Kai! Kice Suma irin mu ne? Ke twins sun sakaki a tsakiya kema Allah ya Baki irin mu". Ta fada tana murmushi. Kwal-kwal Zahra tayi tana kallon Auntyn tata. "Ke! Wai lafiyarki kuwa? kamar wata sabuwar Amarya sai wani rarraba idanu kikeyi tunda muka shigo garin Nan Naga kin kasa samun nutsuwa". Hannaun Auntyn ta riko ta janyo ta kusa da ita kamar tana tsoron wani yaji abinda zata fada. "Wallahi Aunty tsoronsa nakeji nasan no way out a nan". "Ban fahimta ba tsoron sa kamar Yaya? wani Abu yakeyi da kike gudun ya cutar da ke ko menene?". Runtse idanu tayi sai hawaye, sharrrr.. "Aunty wallahi I am afraid about sex.." Wani shock Auntyn ta shiga tana ayyana. Babbar magana! Jarimi wato duk tsawon wannan lokacin kallonta yakeyi kenan Saida ya kawowa iyayensa ita sannan ze nemi hakkinsa duk yanda akayi da dalilinta na wannan shiga rudun. Amma a zahiri sai ta dake taja hannunta suka zauna a gefen gadon. "Haba Zahra me kike son Zama ne?wa kikaga aure ya kashe da zaki tashi hankalinki a banza, ai wallahi samun yaro irinsa a zamanin Nan sai an tona, ke idan kina da lassafi ko tari kin Bari ya kubce miki akan duk abinda yake bukata a gurinki ai wallahi yayi rawar gani, kada naji kada na gani ke ba godewa Allah Zaki ba, ki duba kiga inda ya fito da yanda Allah yayi masa nasibi a rayuwrsa tunda kananun shekaru da fitinannene da Allah kadai yasan adadin yaran daya Bata Amma yasan ke tasa ce malak malak ya iya kauda Miki Kai irin haka ai cewa nake zaki ba marad'a kunya yayi yanda yakeso dake, Naga alamar sai anyi Miki shiri na musamman idan haka zakiyi wallahi kwana kadan ze lafto miki kishiya kina gani ta shiga gabanki ta kwace miki fada duk kuwa irin son da yake Miki idan baya samun gamsuwa a gurinki zeji kin fice Masa daga rai ki nutsu tun dare Bai Miki ba Ashe ganin kitse nake yiwa rogo Ashe ba jaruma bace ke ai sai ki Bari kiji Yaya Abun yake kafin ki yanke masa hukunci, Ina ganinki kin Kai matsayin da Zaki yiwa wata wannan karatun Ashe biri boko ce ai Wallahi shima da nasa laifin har yaushe ze wani saka miki idanu kiyi yanda kike so'. Knocking din kofar da akeyi ya saka Aunty Hasana dakatawa da fadan da take yiwa Zahra ta Dan matsa tana fadin. "Bismillah shigo". Aunty Aishat ce a gaba wasu 'yan matan buzaye farare tas suna biye da ita dauke da manyan basket dauke da kayan abinci. Suka gaishe da Aunty Hasana sannan suka gaishe da Zahra. Aunty Aishar ce ta gabatar da Zahra a gurin yaran sannan Suma ta gabatar dasu ga Zahra Radeeya da mardiyya 'ya'yan Mummy badai'a ne wadda sukaje Azare tare matan uncle Ishaq . Zahra ta nuna farin cikinta Sosai taso su zauna sukace Ammi tace su koma yanzu. Abinci Aunty Aishat ta zuba musu tare da sauran abubwan da aka kawo sai da Aunty Hasana ta ce ta Bari ina zasu Kai wannan abincin sannan ta bari. Sai yamma Zahra ta sake wanka Aishat tazo da Mai yin makeup tayi Mata light ta kawo Mata wata irin Riga da Alkyabba Fara sol ta saka sai tayi wani irin kyau, Mai makeup din sai zuzuta Zahra take tana fadin. "Masha Allah. Wallahi ban taba yiwa amaryar da kwalliyar ta ta tafi da imanina ba sai a kanki". Murshinta Mai ban sha'awa Zahra tayi sai akayi dace Aishat ta dauketa hoto sai tayi wani irin kyau Wanda dole ka kalleta ka Kara, sai Kuma ta Fara daukarta video, tana gamawa tayi review dinsa taga komai yayi ta hada da hotunan ta turawa mahmud. Mota ta dauki Hajiya Inna da Zahra kadai ta nufi gidan Su mahmud dake Kan titin Garba duba. Masha Allah gidan ya dauki haramin Dan mutum motocin a tare suka shigo su mummy Badi'a dasu Aunty Surayya su suka tarbi amarya har cikin master parlourn Ammi wadda Tasha gayu kamar ba gobe an tarbi Zahra da iyayenta tamkar Dade duniya Ammi Bata taba ganin Zahra ba sai yau har gurin da Hajja take zaune su mummy Badi'a suka kai Zahra Aunty Surayya na fadin . "Hajja ga kishiyarki Nan tazo ta gaisheki" Hannu tasa ta bude fuskar Zahra. "Masha Allah sannu yarinya kinji. Allah yayi Albarka ya kade fitina ya hada Arzikinku". "Allahumma Amin" Aka amsa, sannan taci gaba da fadin. "saifa kinyi hakuri da halin mijin namu dan miskili ne ga dukan Mata idan Zaki iya to idan Kuma kin barmana nida Kawata Hajiya Inna to yanda dai Kika yanke muna saurarenki". Anyi dariyar kalaman Hajja sosai Aishat ce tace. "Haba Hajja duk kishin ne haka? kinsan ko ana dara fidda uwa akayi Mai dukan wannan sai ruwan sama shima sai idan ta tsaya Kice dai kina kishi tafi ku komai". Gaishe da Hajjar Zahra tayi sannan suka karasa gurin Ammi itama saka Mata albaka tayi, sanna ta cewa mummy Badi'a su kaita dakinta. Muzanta iya muzanta Mama tayi Dan sai taji Daman batazo ba Dan ko suturar azo a gani Bata zo dasu ba tunda Bata taba kawo hakan zata riski dangin mijinna Zahra ba, sai taga zahiri Ashe ita karyar banza takeyi mijinta Mai kudi Saida tazo taga zahirin inda kude ke magana da kansu Dan yanda aka tsara gidajen da abinda aka zuba kadai ya Isa ka yankewa kanka hikunci,dan Nan guri ne tamkar baza'a mutu ba. Sai kusan magariba 'yan Azare suka samu isowa, part din sameera matar Abbie da suka rabu aka gyarawa Baki, aka saukesu ba Karamin mamaki Mama tayi ba ganin harfa Hameeda a cikinsu. Aunty Hasana ma dakin baki na kusa da Aishat aka bude musu suda su Inna maimuna. Da wuri suka kwanta duk da ba wata tafiya sukayi Mai tsawo ba tunda a jirji sukazo. Wurin Sha Daya mahmud ya kirawo Aishat Yana tambayar ta Ina Zahra? "Tana dakin Ammi fa ni Kuma Ina kasa". "Dan Allah ki fito min da ita wani Abu Zan fada Mata na Kira wayarta a rufe". "Kaima kasan wasa ne naje nace ta fito sai dai ka Kira mummy Badi'a ka fada Mata sai naje na taho maka da ita tunda bazaka iya hakurin goben ba, ni na rasa wane kinibibin ne yasa ka haramtawa kanka abunda Allah ya halasta maka Saida aski yazo gaban goshi Kuma zaka tuburewa mutane kawai ai saura kiris dai kowa ya huta, sai kuje can ku karata a hanyar karaye". "Afuwan Aunty na Kece fa kika rudani wallahi, da kinsan bazaki kawo min ita kamar yanda kikayi min alkawari da Baki turo min hotunan Nan ba gashi kin Sak." Kit ta yanke Kiran taga alama nema yake ya saki layi Kuma gara a tattara a Mika masa ita a wuce gurin, taji suna maganar wani taron yini fa da momin kano tace ta dauki mauyin yinsa. Tashi Aishat din tayi ta nufi sama tana hawa ta Fara jiyo muryar su batool daga dakin da Zahrar take, Dan knocking tayi kafin ta turata ta shiga. "Wai ku menene haka kikeyi? Ku barta ta huta kunsan nisan tafiyar da tayi kuwa da kuka tasa ta gaba da surutu Kuna ma duba time kuwa?". Tashi sukayi sun Kai su shida suka fice. Shigowa tayi ciki tana sakin murmushi tana fadin. "Nazo a bani sirrin Nima Sweet heart ya ringa rikice min kamar yanda Hussein yake rikicewa ko a gaban waye idanunsa rufewa sukeyi, sai ki ringa kula dashi yanda baze ringa sakin layi ba kada ku raba Hali a gaban Ammi yasa kiji kunya". Hannu Zahra tasa ta rufe idanunta tana fadin. "Kai Aunty Dan Allah ki daina fadar haka Ni wallahi ba ruwana fa". "Na sani shine baya iya jure kiyi nesa dashi yanzu ma fa shine yake nemanki a can part dinsa na Cikin gjdan Nan Wai na Kai Masa ke Yana jiranki". Wani kwalalo sexy eyes dinta tayi tana rufe bakinta da tafin hannunta. "Dan Allah Aunty Aishat ki rufa min asiri wallahi bazan iya fita ba, me zanyi masa Kice Masa nayi barci Dan Allah". Idonta ya cicciko da hawaye. "Shikenan kada kiyi kuka Hajiya shagwaba ki Adana abinki tunda Mai lallashin baya Nan". Dan murmushi a tayi a kunya ce tana kauda kai. Ficewa Aishat tayi tana saka wayarta a Airplane mode. * Da safe sosai gidan ya kacame da Baki kowa sai sabgar gabansa yakeyi, Zahra na daki tun bayan da tayi sallah ta shiga ta gaishe da Ammy da Hajja wadda a Nan ta kwana tunda Allah yayi Mata lafiyar kafa daraf take hawa sama. Daki ta koma duk da Hajja taso ta zauna suyi Hira, tana kwance tana chart da dasu Aneesa wadda suka nufo sokoton ita dasu Fatima da Khadija. Sajeeda Kuma sai karfe flight din is karfe biyu zata biyo zuwa sokoto, Jin alamun bude kofa yasa Zahra dago Kai Aunty Rukayya ce da Fateeha suka shigo, da wani uban tsalle Zahra ta tashi ta fada jikin Aunty Rukayya tana fadin. "Daman Kuna Nan Aunty Rukayya? Sannunku da zuwa".. Ta Mika hannu ta karbi Akram. "Wallahi muna Nan Amarya ai harda mutuniyar dasu mommy".." "Kai haba dai harda Hajiyata kuka dauko ga nisa". "To ya za'ayi tace biki na farar kaza Wai balbela ba gayya ce ba, haka fa ta fada min". Anan suka baje tare sukayi break fast da ita, kafin Azzahar gida ya gama cika an yiwa Zahra makeup na garari, ana haramar tafiya gurin walima su Ummee da Aunty Nauwarah da mommy Haneefa suka sauka Mahmud da Kansa ya dauko baikinsa dan ya cewa Ummee zuwansa ne bana Zahra ba, Su Ammy na zaune a parlour sukaga ana shigo da manyan jikunkuna daga karshe su Ummeen suka shigo Mahmud Yana bayansu shida Aunty Nauwarah, 'yan uwa abokan Wasa sai dan biki suke yiwa mahmud akan yanda yayi kyau Yana baza kamshi, sai walainiyar yake a Cikin Gezner milk colour ga wani daukar ido take kana ganinsa ango sak. Har gurin Su Hajja ya raka Ummee Yana fadin. "Hajiya Inna ga Ummen Zahra wadda kwana biyu kuke waya da ita". "Muke waya ko kake Mana tafinta Ni ba iya nata yaren nayi ba itama Bata iya nawa ba,kace Ina musu sannu da zuwa". Ta fada tana daga musu hannu Hajiya ba Ajami. Cikin yaren larabci ya fada musu sakon barka da zuwa da Hajiya da saura mutanen gurin sukeyi musu. Gurin Ammi suka Karaso da yake Ammi makarantar English tayi sai abun yazo da sauki sun gaisa sosai dasu kafin a kaisu masaukin su inda sukaci abinci sukayi salllolinsu. Ammi da su mummy Badi'a da Aunty Surayya suka Kara shigowa suka gaisa dasu Ummeen. Aunty Surayya ce ta fice ta nufi sama lokacin an gama shirya Amarya tsab,ta shiga dakin komai yayi Masha Allah Sai dai mak'iyi. Hannunta Aunty surayya suka fito a hankali suke gangarowa har kasa suna daf da shiga gurin Ummee ta jiyo scent dinsa Dan juyowa tayi shi ta gani Yana tsaye ya harde hannu a kirjinsa ya Zuba Mata Idanu. Ganin kamar Aunty surayyar zata juyo yasa tayi saurin dauke Kai tayi gaba. Suna shiga dakin Zahra tayi arba dasu Ummee ai Batasan lokacin data daka wani uban tsalleba ta shige jikin Ummee tana wata irin murmushi Mai dauke da tsantsar farin ciki. Daya bayan Daya tana shiga jikinsu suna gaisawa. Anan ta zauna dasu tana ta mamakin Wai meu amor ne ya fadawa Ummee Amma ita Kullum ta nemesu Bata samu. Daga Nan Zahra Bata koma sama ba suka wuce gurin walima anci ansha walima ta amsa sunanta anyi wa'azi Mai ratsa zuciya da zaburar da ma'aurata akan hakkokinsu, jiki yayi sanyi sosai Dan an kwankwashi ko wane bangare, duk iya zarin mutum sai dai yaci ya Bari anyi komai na girma da wadatar arziki, ansha hotuna da Amarya da ango Dan burin kowa yayi hoto da ita 'yan matan dake feleke akan mahmud sun raina kansu Dan sun San mahmud yayi musu fintinkau da wata irin tazara Mai girma Mai kamar wannan mezeci dasu. Karfe takwas aka fara Shirin tafiya dinner wadda za'ayi a MABERA EVENT HALL. Su sajeeda dasu Aneesa su Amatu da Aunty safiya duk sunzo sai suka ringa tuna lokacin da wancen biki ya lalace komai ya rikice, Amma yanzu gashi ana kara'i. Sajeeda ce ta kalii Amatullah tana fadin . "Kunga mahmud sai a kyale shi, wato sai an rama masa bikinsa da ba'ayi ba kenan". Aneesa ce tace . "Aini yayi min dai dai wallahi saboda mahassada da 'yan bakin ciki masu yiwa Zahra dariya da shewa da yi Mata tozarci a ranar da aka kaita gidansa suga yanda Ubangiji ke yin nasa ikon susan hassada ga Mai rabo taki ce Kuma dare ga Mai rabo hantsine, yau ga Zahra ganinta ma sai kayi da gaske Dan baka Isa ka haura inda take ba sai anyi maka iso Kinga kuwa ai ko yanzu Allah ya nunawa masu yi Mata hassada iyakarsu. Shiru Hameeda tayi tasan wannan maganar da wannan ke saki an Bata labarin abinda ya faru ne lokacin da Mama da Salma suka sakata tayi rashin kirkin Nan Wanda ya janyo musu sabanin daya shiga tsakaninsu har inda yau din Nan take. Aunty Nauwarah ce ta shirya Amarya da shigarsu ta Amaren larabawa, tunda Ammah ta fada musu halin da ake ciki suka dauro niyyar tahowa duk da daman suna niyyar zuwa ganin Zahrar,sai kuma ga Kiran mahmud ya fadawa Ummee sannan ya tura Musa iv din dinner, shine fa Aunty Nauwarah to shiri na musamman akan dinner din gata Daman gwana a gurin makeup lokacin dasu Aishat suka shigo Basu ganu Zahra ba Dan juyewa tayi tamkar ba ita ba. Dai dai kunnen Zahrar Aunty Aishat din tazo tana Mata magana. "Dan Allah a rangwanta Masa kada ya kasa rike Kansa a gurin fa, irin wannan Abu haka'. Sunne kai Zahra tayi Dan ji tayi kamar kowa yaji abinda ta fad'a. Sai da kowa ya tafi ya rage daga Zahra sai sajeeda wadda Aunty Hasana tace su zauna tare kafin a zo daukarta. Suna zaune suna hira wayar sajeeda ta dauki wani slow music lokacin tana duba wasu kayan da Mama Haneefa ta kawowa Zahra, Jin special ringtone din nan yasa ta baro gurin da sauri tana fadin. "Sunzo garin kenan". "Waye kuma aka samu". "Kinji ki waye kuwa Banda yayanki daya hanani sakat da soyayyarsa". Picking tayi tana nufar kofar fita, saura kadan suyi karo da mahmud Wanda shi kuma ze shigo, da sauri tayi baya tana fadin. "Sorry ban kula yallabai". "No ba laifinki bane nine banyi knocking ba". Ya shigo ita Kuma ta fita da sauri. Tunda Zahra taji muryarsa taji wani abu da batasan ko meye ba ya tsirga mata. A hankali ya tako har inda take ta sadda Kai kasa,shigar babbar Riga yayi irin dai yanda mafi akasarin angunan Hausawa keyi, dagota yayi ya Mikar da ita wani lunshe sexy eyes dinta tayi ba tayi zato ba taji iskar bakinsa mai dauke da kamshin Lister mint ta sauka a Kan fatar idanunta kafin ya zagayo da hannuwansa ta bayanta ya rungumeta tsan-tsan a jikinsa Yana jera ajiyar zuciya a dai dai kunnenta ya rada Mata "preciousss kin gujeni why? kinsan yanda na azabtu da bakya kusa Dani kuwa? Rabon dana jiki a jikina haka fa tun muna India kinsa na Zama marayan karfi da yaji jiya nayi nayi kizo ko ganinki nayi kika k'i zuwa ko? Can gurin lalube lalubensa ya jiyo zif daga gefen wedding gown din ya zuge ya shiga Kai kawo da hannunsa dayan Kuma ya zame Dan veil din da aka makala shi a jikin kamar hula wadda aka saka mata ya Kuma hade bakinsu Nan da Nan ya rikata Mata lissafi, da kyar ya saurara Mata suna maida numfashi . Cikin murya wadda ta dashe ya fara Mata magiyar tazo su wuce basai sunje gurin dinner din Nan ba, bazei iya Kuma tana nufin a haka zata fita duk Nan a waye ana kallo. Yasa hannu Yana shafa saman rigar wadda net ne a gurin. *AUREN HUCE HASHI* AISHAT ISAH MUSAH Maman Fateemah. 09061432330 Or 08055362975 Assalamu Alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu barkamu da sallah muna tayi Al'ummar musulmi Baki idin qaramar sallah,muna rokon ubangiji ya karbi ibadun mu ya Samu a cikin bayinsa Wanda yake 'yantawa Dan Alfarmar Annabi Muhammad s a w w. Page 81 ............Suna tsaye yana kallonta daga sama har kasa Yana Kai kawo akan zuwa dinner din nan yayi dana sanin jan lokacin nan,daya bude aiki da Sai dai ya kawota da ciki ai da ya rufe babin duk wannan bidi'ar da aka bude, Dan zayyan ya turo Masa yanda gurin ya cika da Dan mutum tamkar anyi shelar bikin , ga mutanensa da Sameer ya ringa tura musu da iv ta email dinsu abun har mamaki ya bashi. Dan sunzo ba kadan ba ga alert sai shigowa yake daga different people shi abun mamaki yake bashi to da bikin da aka shirya Masa ne Yaya kenan?. Knocking yaji daga waje agogon hannunsa Rolex ya duba sai yaga lokacin yayi sauri hannunta ya kamo tamkar yanda India suke ya nufo kofar,key din ya murza ya bude. Aunty Aishat ce ita da Aunty Nauwarah,wata irin kunya ta rufe Zahra. Dan Bata taba tunanin da sauran wani a part din ba Dan yau har masu aikin Ammi sun dauki wanka sun fice. Wani irin kyau sukayi yanda suka fito din Nan sai suka bada wata irin colour mai daukar hankali. "Dan Allah menene haka ka wani kanainaye ta kaki Bari ku fita guri ya hadu ku kawai ake jira gara dana rako Auntyn Zahra da baka niyyar fitowa kenan?". Dan matse hannun Zahra yayi yana kallonta kafin ya kalli twins sister dinsa. "Kina da damuwa zuwa fa nayi mu tafi, nifa da wucewa zamuyi bana son wannan bidi'ar naga gurin ya cika da maza Kuma dubi rigar dake jikinta duk Nan fa a waje yake". Ya Kai hannu yana nuna mata, Zahra ji tayi kamar ta nitse a gurin, taga ta kanta shi Wai baya Jin kunyar Aishat din ne. "Allah ya shirya gaskiya gara ku tattara ku Kara gaba Naga alamar idan tana kusa da Kai baka da saiti duk nutsuwarka barin jikinka take, sai kaje ka jiramu abinda Auntyn ta tazoyi kenan tace wannan fitar batayi Mata ba ta dauka akwai wasu events din bayan wannan nace Mata Babu sai budar Kai gobe kawai". Jinjina Kai yayi ya wuce Yana fadin. "Ki fadawa Auntyn Banda Mai net a kirji Dan Allah". Rike Baki Aishat tayi tana binsa da kallo. "Kai Kuma naka salon kenan? Auntyn Afnan kuje Auntyn ki na jiran mu gara ayi abunda za'ayi ku shiga ku kadai ake jira". Kwalkiyar da akayi yanzu tafi ta farko daukar hankali nesa ba kusa sai Zahrar ta zama tamkar fure tayi kyau iya kyau Dan ta farko Wasa ce. Aishat tayi Mata hotuna tamkar ba gobe, wani murmushi ne ya kubce Mata zataga yanda Dan gidanta zeyi da yake complain din wancen gown din to ga wata wadda tafi waccen sai dai ita babu ne daga sama ba'a ganin breast din kamar waccen. Sajeeda ce ta dawo tana fadin. "Bestie kina Ina ne ki fito ana jiranki fa". Ganin su Auntyn yasa ta Dan tsaya tana kallon Zahrar ganin Cikin abinda Bai wuce minti Sha biyar ba an sake Mata wani Shirin na musamman. " Wow! Masha Allah bestie Allah ya kade bakin mutane kinganki kuwa?". Dan murmushi tayi kawai. "Ato gata Nan bansan ya angon naku zeyi ba Naga alamar dan banzan kishi gare shi, wa yace ya kawo ta gidan a haka? Ai dole ya kauda Kai Dan dinner dai sai anjeta babu fashi in Sha Allah". Ita dai Aunty Nauwarah kallonsu take tunda ba Hausar takeji ba. Wasu tsaraddun turarika ta shiga fesa Mata masu sanyin kanshi. Tare suka fito suka raka Zahrar a cikin motar da zasu tafi a ciki, shi Dan gogan kasa magana yayi Dan yana kukan targade saiga karaya ta samu, Yana korafin waccen wedding gown din to Kuma saiga wannan ita ba transference bace Amma ta fiddo da structure din jikinta sosai. Bai daiyi complain ba suka wuce Sameer na jansu, Suna fita motocin guards dinsa dake waje suna dakon fitowarsu suka saka motar a tsakiya suka wuce. Su Aunty Aishat ma suka wuce da sajeeda. Suna shiga harabar gurin sajeeda taga yanda motocin Alfarma suka cika wurin tasan ba karya anzo gurin, Dan tunda suka shigo sukaga yanda Families din mahmud suke suketa mamakin abun bare ita sajeedar da tasan komai a game da shi, tayi mamakin mema ya fitar dashi daga irin wannan daular ya gwammace rayuwar da yayi a Azare da wannan. Ango da Kansa ya budewa Amarya ta fito Yana rike da hannunta suna tafiya Yana gaisawa da jama'arsa suna bin carpet din da a saka musu a hanya photographers sai aikisu suke masu dauka da wayoyin hannunsu Suma suna ta faman daukarsu Dan wani irin perfect match couple ne Wanda kafin a samu irin wannan hadin ana dadewa kyau ne ke dukan kyau. Suna shiga da tawagar abokansa na kusa Dana nesa sai kawayen Zahra,r music din Larabawa na tashi a hankali sai kus-kus mutane kowa na zaune gentle ba wani hayaniya Dan ba karya an hada manya masu ji da kansu a gurin kowa Yana cewa wane kauce bani guri. M.C ne ya Fara bazawa Amarya da ango kirari har suka zauna a inda aka tanadar musu, Nan da Nan guri ya dauki surutun mutane wasu suka taso suna daukar video wasu suna daukar photo, 'yan Mata da yawa masu son mahmud sunyi giving up, sun San idan ba wani kwakwkwaran rabon ba babu yanda za'ayi DANGE ya dubesu da sunan soyayya, wakar Auren su wadda Akayi mc ya saka. A gurguje Sameer ya bada tarihin mahmud har ranar da suka Fara ganin Zahra ita da Abbanta a jirgi ya fada, sai lokacin Abban Zahrar ya tantance inda ya Fara ganin fuskokinsu tabbas anyi haka Dan Mai maganar har Jordan sukaje tare, wato tun lokacin suke bibiyar ta kenan sauran bayanin ne kuma baisan yanda akayi ba. A bagaren Zahra sajeeda ce ta fito ta fadi tarhinta a nan da yawa suka San ruwa biyu ce Dan duk Wanda ya ganta zeyi zaton gaba daya Arab din ce tunda su ta dauko sak, an tanadi abinci Kala-kala da nama ya Kai Kala goma gashin nan serve your self ne ga drinks Nan tamkar banza, Zahra tayi mamakin ganin su Abbanta Koda Wasa Bata taba kawo hakan ba tunda bece Mata zezo ba yace dai sai daga baya ze shigo ya ganta, taga su Ya Abdul Hakeem dasu ya Hamza bare magaji da taga ya Zama Dan gida ya kasa tsugun. An saka kidan larabawa wasu Mata Wanda da alama dasu Ummee sukazo suka shigo sukaga ringa rawar larabawa Mai ban sha'awa. Daga Nan aka bukaci Ango da Amarya suzo su yanka cake Zahra ji tayi duk ta daburce ganin Ido yayi Mata caaaa. Ganin taki motsawa yasa mahmud ya murzawa idanunsa toka Kuma ma dai da biyu yayi hakan Dan yaga wata fuska sanye da musk Kuma ya hakikance Safna ce Dan ko me zatayi bazata taba bace Masa ba. Tsam ya saka hannu ya Mikar da ita abunda yasa matasa dauka tafi Sai Kuma hasken plasher tako ina. Shiya Fara Bata cake din sannan ta bashi duk a kunyace, mc Bai Bari suk koma ba announcement ya Fara Yana neman dangin Amarya da turanci tunda yagansu farare tas, ya saka wakar Amr Diab 'yar kasar Egypt. Ummee ce ta taso wasu Mata biyu suna bayanta dauke da wata jaka tana zuwa ta Fara zazzaga musu ruwan stalling pounds na England sai Kuma su Mama Haneefa dasu Aunty Nauwarah suka shigo suna ruwan American dollars Nan da Nan guri ya dauki tafi, Ummee Bata koma ba saida ta yiwa ango kyautar estate a cikin garin madina sannan aka bashi jajayen rakuma goma da kyauta tickets na kashe biyar na Honey moon. Aunty Hasana ma dasu Inna mainuna sunzo sunyi rawar gani Dan shanu goma ris ta bawa ango sannan wasu goman biyar uwa biyar uba da kuma zunzurutun kudi har miliyan ashirin na dangin uwa da uba sai karsanoni hudu na abokan zaman Ammi sai guda hudu da million daya nasu Hajiya Inna da Hajja dari biyar biyar. Abinda ya girgiza da yawa daga Cikin masu ganin Zahra ba 'yar kowa bace irin fakarahun yayan larabawa Nan ne masu azabar kyau din Nan da yawancin mazanmu masu kudi ke aurowa Dan neman irin Mai kyau Cikin zuri'arsu. Bayan gama tafi da sowar tuwon girman da Ummee tayi aka nemi dangin miji,sun shigo kamar Gori maza da Mata sunyi barin kudi kamar ba gobe Ammi ta fito da tawagarta ta yiwa Zahra liken CFA kudinsu na Niger Hajja ta bawa Zahra kyautar shanu da zunzurutun CFA million goma. Da sarkar zinari wadda kudinta sun tasarwa million tamanin take aka Miko cheque na eco Bank tunda shine bankin ecowas. Amarya da angon sun Sha kyautukan girma suna niyyar komawa wurinsu wata Mata cikin sauri take ta yiwa mc magana, Nan da Nan ya dakatar da tafiyarsu Yana fadin. Ga Mai gayya Mai aiki tazo Fulanin Mai Damagaram aminiya ta hannun damar uwar ango Hajiya zainab. Wata farar Mace Yar gayu tare da amintattun bayinta sai wata yarinya budurwa dake tare dasu Saida suka matso sosai Zahra ta gane yarinyar Wadda ta kafa musu Ido ce a train station lokacin da zasu Jim Corbett national Park a Uttarakhand state. Take Zahra taji wani Abu ya tsaya Mata a kirji, yanda taga yarinyar na Mata wani kallon kasa kasa irin Mai nuna baka Isa din Nan ba. Saboda a wancan lokacin taga irin kallon kurillar data kafesu dashi. Fulanin na zuwa ta rungume Zahra tana fadin. "Tabarakallah Masha Allah, Zahra diyata sannu da kwaramniya". "Yauwa Mama, nagode". Wani kallon banza yarinyar ta gara jifan Zahra dashi tana wani kawar da Kai gefe tana hade rai. Liken kudi Fulanin ta Fara Yi musu haka 'yan tawagarta ma haka da alama an shiryawa wannan ranar, amma ita yarinyar mahmud kadai take yiwa Saida mummy Badi'a tazo ta janye Fulanin daga gurin ganin lokaci ya Fara ja tasan abokansa da kawayen zahrar suna son Suma su nuna tasu bajintar, a gurin dollars dai da pounds sunyi kuka. Mama ta Raina kanta iya rainawa taga inda ake maganar arzikin da babu fariyar a cikinsa sai dai idanunka su fada maka, taga yanda matan uba ke kyautar mamaki Dan kowacce ta bawa Zahra tata kyautar. Ba'a tashi ba sai kusan Sha biyu da rabi. Sai da aka tashi sannan Ammi suka gaisa da Fulani wadda ta sauka a Daren Dan Bata kasar lokacin da Ammi ta kirata ta fada mata danta ya dawi har da tsarabar Daya dawo musu da ita. A gajiye aka dawo gida danma an kamawa mutane da yawa dakunan hotels Dan duk matar da tazo daga Azare a mota ta biyu duka hotel aka kaisu shi yasa sai a gurin dinner Zahra taga wasu mutanen harda su Aunty zilai dinta Dan har liken Yan dari biyar sabbi tayi Mata. Duk yanda mahmud yaso ya wuce da Zahra Aishat da Aunty Nauwarah sun kasa sun tsare,dan Aishat ce tayi Mata tsegumin abinda take zaton ze aikata Dan taga dazu ya birkice da yawa idan aka barshi ko budar Kan baza'ayi ba ga momin Kano kuma ta shirya masa Dan lokacin da akaje da maganar ko a hakura dayin wunin tsalle tayi ta dire akan babu fashi sai anyi me zata yiwa mahmud ta biya shi kaunar da yake yiwa Faruq ya dauke shi tamkar uwa Daya ta haifesu ya bude Masa yanda ya kamata hatta karatun da yayi mahmud ya zabar Masa saboda ya ringa yi Masa ayyukansa. Mahmud yana ji yana gani Sameer ya wuce dasu zahrar ita dasu sajeeda da Amatu. Zahra a gurin su Ummee ta zauna sun Kai kusan biyu Aunty Nauwarah na saka Zahra a wasu irin ruwan magunguna masu azabar kamshi ga turaren jiki Wanda sai da kamshimsa ya game part din gaba daya, abin isar Zahra yayi Dan idan ba so suke yayi Mata lahani ba ya kamata a kyaleta haka ita kadai ranta sai abubuwa ake Mata Babu sasaauci,ko Dan Basu San abinda idanunta suka gani bane. Kawai a Riga suke ganin mutum Basu San sirrin dake lullube bane. Gado Daya suka kwana da Ummee Zahra nata mitar Ummee ta manta da ita, data isheta da magana Ummeen ta fada Mata Abbu ne bashi da Lafiya ai mijinta ya sani Dan yaje har London ya duba shi, shine yayi blocking din layinta a wayoyinsu yace idan aka Bari Kika sani Zaki tada hankalinki gashi kema lokacin yace Baki da lafiya. Gyara kwanciya Zahra tayi tana mitar abun, kamar ta hakura sai kuma tacewa Ummee. "Wai Dan Allah Ummee a Ina Mika san...." Sai Kuma tayi shiru. "A'a Fadi Mana a Ina nasan mijinki". Dariya tayi tana rufe Ido. "Makocinmu ne a can Jordan gidansa Yana kallon namu". Tashi zaune Zahra tayi tana duban Ummee. "Badai wannan gidan da nake cewa yayi min kyau ba gashi Naga an saka Masa suna a samansa GIDAN ZAHRA". Dariya Ummee tayi to ai daman gidan na zahrar ne haka Shima ya fada min tun kafin nasan ke zahrar tawa yake nufi, ko aikin gyaran gidan Abbie ne ya samo Masa masu yin duk sadda ya shigo Jordan Yana gidan mu, Bai Kuma taba fada Mana ya sanki ba Koda wata manufar da take kawosa gidan, sai bayan an bashi ke ya kirani yake fada min an bashi Mata idan ya shigo ze kawo min hotonta na gani. Ranar Daya zo da yammaci ya shigo yaci abinci sannan ya bude ya ringa nuna min hotunanki tun kina 'yar matashiyar ki har na girmanki, ba Karamin mamaki hakan ya bani ba Daman yasan kina da alaka da Dani ko Kuma arashi ne kawai. Dana tambayeshi ba wani rufa-rufa ya fada min yasan matsayinmu a gurinki. Zahra tayi matukar mamaki Amma Dan tahalikin Nan Bai taba nuna Mata yasan su Ummee ba Koda Wasa, Sai dai Daman tayi matukar mamakin yanda taga suke mu'amala abun kwarai ya bata mamaki babu wani bakunta a tattare dasu. Sun Jima Ummee na Bata labarin yanda suka shaku da mahmud din sai taga ita ai ya fita shiga jikinsu ma sosai. Washe gari da wuri Aunty Hasana dasu Aunty Nauwarah da sauran mutanen Ammah Hajiya kaltume ta turasu tare da Aishat wadda zatayi musu jagora suje a duba abinda ya kamata a gyara a gidan da za'a Kai Amaryar tunda company ne sukayi jeren kayan da akazo dasu na zahrar duk da mahmud yace ba gurin saka komai, dole ya bada part dinsa na gidan Hajiya Inna aka zuba kayan tunda baiyi niyyar saka masa komai ba a lokacin domin guda biyu aka Gina Daya na zahrar to an Riga an saka masa furnitures sai dayan da dole tasa aka yi Masa paint da abinda ya kamata aka saka kayan a can. Basu wani Dade ba suka baro can din tunda babu bukatar yi masa komai sai dai turarukan daki da aka saka, Basu dawo gida sai da aka kaisu gidan da za'a Kai Zahra, permanent gidanta gidan Hajiya Inna temporary ne na week end da yada zango Idan an dawo daga tafiya Dan Alkawari ne duk inda yaje ya dawo gidanta ne farkon sauka. Sunyi santin gidan tamkar ba'a Nigeria mutum yake ba Dan Maman mujiba kasa shiru tayi da bakinta lokacin da Aishat ke shiga dasu guri guri a kasa taga parlours sun Kai hudu ga sama sun hau taga common karfen dake Jikin stairs shi Kansa tamkar na zinari sai daukar Ido yakeyi ga gidan ko Ina daukar Ido yakeyi ga haukatan bedrooms ga toilet ga gani na fada Dan wani abun ko a hoto Bata taba ganinsu ba. Ja tayi ta tsaya tana kallon Aunty Hasana. "Dan Allah Hasana Wai Yaya Aljanna take ne?" Ba Wanda baiyi dariya ba a gurin kuma ita har zuciyar ta tayi tambayar. Ganin suna dariya yasa ta Kara fadin. "Wallahi da gaske nake tambayar Nan, ki dubi gidan Nan Wai a sokoto yake? Ni tunda Allah ya halicceni ban taba shiga makamancinsa ba, Nan gidan zahra ne wadda ake tsegumin an aurawa Almajiri kolo marar galihu marar komai, ana ta zunden Alhaji idan ya wuce a unguwar, a cikin gidan Kuma ana sakin habaici an ce kyau ya Kare a Wanda ba'asan asalinsa ba, to yau kowa yazo yaga inda Allah yasa Alhaji Jafar ya kawo marainiyar Allah gidan da hasashe be taba hasasowa ba, tunani Bai taba tunanowa ba, Hasana saka wayarki ki daukar min gidan Nan ciki da waje sai masu tsegumi sun gani da idanunsu, 'yan bakin ciki kuma su mutu tunda Alkawarin Allah baya tashi idan yace Kaine sai kakai, lallai Dan tsiron da Allah keso ko babu ruwa saiya rayu, yau Zahra ta Zama farin wata Sha kallo. Masha Allah Arzikin mutum a jikinsa yake Kuma dare ga Mai rabo hantsine". Guda ta rangada har sau uku tana Kara fadin . "Idan Rana ta fito tafin hannu baya kareta, walkiya inta haska wanene ze iya kareta? Hadari In yayya tsawa rufe kunne baya Hana jinsa ga Zahra ikon Allah sai kallo". Kudi Aunty Nauwarah ta Ciro dollars ne saura Wanda ta zubawa Zahra ta Zubawa maman mujiba Dan ko Bata Jin abinda take fada tasan kurare 'yarta takeyi, ko ita da suke a kasashen da sukaci gaba gidan Zahra ya tafi da ita Dan babu karya anyi gidan tamkar baza'a mutu ba Dan dukiya dai an kasheta tamkar ba'asan ciwonta ba. ****** Saida zahrar tayi barci Mai isarta sannan ta tashi, lokacin wurin Sha Daya. Wanka ta shiga tayi data fito tayi break fast sannan ta shirya, Aunty Nauwarah tayi Mata makeup mai daukar hankali. Doguwar rigar atamfa green Mai milk din fulawoyi ta saka tayi amfani da gyale milk da takalma plat milk, wayarta ta dauko wadda ta sakata a silent tun daren jiya saboda message din data gani na mahmud da yake son dole ta fito Yana ta bayan part din Ammin, idan ta fita akayi Dace wani ya ganta ai noway out, cewa za'ayi har satar jiki take tana zuwa gurinsa, dubawa ta shiga yi na meu amor ta Fara bi kasancewar Aunty Nauwarah Bata Jin hausa yasa hankalinta kwance ta kirasa. Harta yanke be daga ba sai taji wani irin ba Dadi a zuciyarta. Ya Abdul Hakeem ya Nemo wayar taji a Ina suka kwana. Dauka yayi suka gaisa kafin ta Dora da fadin. "Ya Abdul Hakeem a Ina kuka kwana ne? Kuma Ina Abbana wallahi kunyi surprised dina banyi zaton zakuzo ba wallahi". "To Ni dai gani Nan a wata unguwa Wai kome? Na manta Abba kuma sunbi jirgin bakwai da rabi yanzu haka ya sauka a Bauchi sun dauki hanyar Azare". Wayyo Ya Abdul Hakeem yanzu Abbana yazo garin Nan na kasa gaisawa dashi". "Kinsan halin Abba ai yace ze dawo special yaga masaukin ki, kinsan ya w Sun jima suna waya daga baya sukayi sallama. Aunty Hasana ce tazo ta raka Zahra Dakin Ammi ta gaishesu sannan ta mayar da ita masaukin da Ammi tayi mata. Sai wurin karfe biyu mai yin makeup wadda momin Kano ta dauko takanas tazo Shirya Amarya, tayi Mata makeup light, ta Zuba Mata wani material Mai ubansun kyau ta daura Mata head sai zahrar ta fito a tauraruwarta dan komai hassadar mutum ya kalleta ya Kara kallo Dan da gaske zaharar ce. A Hidima event center Wanda ke bodinga road, behind Nipost sokoto south za'ayi yinin, lokacin da aka shiryata photographer yazo anyi hotuna kamar me sunje part din momin Kano ma anyi hotuna a Nan Zahra taga kanwar maman Musbahu Aunty batayi mamaki ba tunda taga musbahun da Faruq tare a Kano da alamar sun jada relation dasu. Daga bangaren Momin akazo tafiya da Zahra gurin da za'ayi event din Mai gayya Mai aikin ya Kira momin da Kansa yace suje za'a kawo ta. Abinda yaso ya Zama na magana a Cikin family kenan sai da momin ta tsawatar saboda momi ba Wasa tasan kanta yanda ya kamata Bata daukar wargi domin itama daga babban gidan sarautar Kano aka daukota, shi yasa tasu tazo Daya da Ammi ma Dan itama Ammi tasan ciwon kanta Kuma da fadarta gurin miji, Sam Bata shiga shirgin tsugune tashi na family din. Sameer yazo ya tafi da Zahra su Amatu sunso subi Zahrar Amma Sameer yace ba can suka nufa ba yanzu da inda ze kaita, dolensu suka hakura da bin motar Amaryar. Direct kalambaina road suka nufa ita dai Zahra ikon Allah take kallo. Gaban wani plat house mai wani irin gini na daukar hankali taga sameer ya tsaya Yana yin Horn har suka Karads shiga ciki wayar Sameer ta dauki kida da sauri ya dauka Yana fadin. "Har munfa karaso". Da yake a handsfree take sai Zahra taji yace . Ku wuce kawai akwai mutane a gidan". Wani sanyin dadi ne ya rufe Zahra Daman tunda suka taho addu'a take haka Nan Bata San kebewarsu a tsakanin Nan dan salon da yake fito Mata dasu yafi karfin dan Karamin tunaninta.gaskiya, hamdala dai tayi tafi ciki carbi. Guri yinin ya hadu ya kuma Tara matan da suka amsa sunan su mata, Dan momin kano ba Karamar gayya tayi ba tunda ita Ammi ta bawa wannan bangaren, mutanen Ammi na Niger sunzo kamar Gori, gurin ya dinke da matan gayu sai sabgogin arziki akeyi an sakata Zahra a wata kujera a tsakiya hall din ga kidan wakokin bikin na tashi Dan a kalla su Kai kala biyar Dan ma abun ne yazo a Qure. Kafin yamma an sakewa Zahra dress ya Kai sau biyar da mahaukatan laces na makudan kudi duk karkashin momin kano tunda itama 'yar kasuwa ce ta gaske Dan wasu abubuwan ma tare da Ammi suke juyawa irin kayan da ake shigo musu dasu daga kasashen dasu mahmud suke da kamfanoni a can. Da yamma Zahra na Dakin da ake Mata canjin dress Hajiyar makwarari ta shigo iita da Aunty Rukayya, Hajiyar Tasha wani ubansun lace tayi gwagqgwaron tsofaffi ga jaka da takalmi da gyale duk iri Daya. "Ina zahara'un take? Zuwa nayi na tofeki da lahaula saboda naji bakin mutane yayi yawa a kanki to kada aje ba'a sani ba Koda Mai kambun baka, gara ki shiga gidanki salin alin salamun qaulin, yo Ina dalili! A sakawa yarinya Idanu kowa wuwww,haba surutu ake cacacccc fadi akeyi ai Daman mahmud sai irin wannan, to idan kasan bakin wani ai baka San na wani ba". "Kai! Hajiya wallahi kin Zama trouble haba Dan Allah tun dazu kike fada da wannan matar ta Baki hakuri Ashe Baki hakura ba sai kin tofeta da Addu'ar'. Ita dai Zahra kallon su take ita da abinda ya Sha Mata kai, mahmud ya sakota gaba da fitinar ta biyewa su Ammi sai wanesa sukeyi su bashi matarsa sun Kiya sai tsaraba suke fito Masa da ita Kala-kala shifa ya gaji hakurinsa ya Kare. Dan murmushi Zahra tayi tana kallon Hajiyar makwararin. "Babu abinda ze sameni Hajiya in Sha Allah, ki rabu dasu kada ace ana fada da kakata ai babu Dadi,kiyi min addu'ar'". "Yauwa yanzu naji magana Amma ke Rakiya ba lafazi Mai Dadi yarinya ta fiki iya kwantarwa". Waje Rukayya tayi tana fadin "Ayi mutum sai rikici gara mu tattara mubar garin inga da Wanda zakiyi Kuma". "Jeki dai bazan Zuba idanu ayi ta yiwa yarinya baki ba a banza, mu tafi din ai dai nazo nayi abinda zanyi dazu har gidanki naje aka yi addu'a kinsan malam na sanka ya taso yaro ya biyoni Nan akayiwa gidan addu'ar tsari, yaushe Zan fadawa wannan fesado din daga sameeru sai mijinki suka sani". Har yamma likis anata sabgar arziki an raba jaka Mai hutunan amarya da ango mabanbanta da turamen atqmfofi wasu shadda wasu lace fa tarkacen kayan biki a ciki duk Wanda Allah yasa rabon mutum ne shi za'a bashi, da gani kudi sun Sha kashi a gurin. Lokacin da suka dawo gida anata Kiran sallar magariba. Ammah ta turo kudi bana Wasa ba tace su Hasana da Hajiya kaltume su bincika yanda Al'adar sokoto take ayi komai a nan, to Masha Allah su maman mujiba da Wanda sukazo tare da Inna mainuna sun shiga kasuwa tare da taimakon masu aikin Ammi sun sawo har da abinda ba'a fada bama, anyi bada komai Cikin girma da wadata. Directly sama su Aunty Hasana suka wuce da Zahra ta gaji iya gajiya, suna kokarin shiga dakin da Ammi ta sauki Zahra aka bude kofar dakin Ammin doctor Haseena ce tare da wasu matan suka fito wata daga cikinsu na fadin "Haba Haseenah kamar ba mace ba ki kasa shanyo Kan mahmud har Karamar yarinya ta shige Miki gaba ta kwace Miki shi kina kallo kin Sha dakon soyayyarsa shekara da shekaru a banza kuma ai..." Sai tayi saurin Kama bakinta ganin su Zahrar a kofar bedroom din dake kallon na Ammin. Wata daga Cikin matan ta nufi su Aunty Hasana tana fadin. "Sannunku Ashe Amaryar tamu harta karaso?". Cikin nuna wayewa da iya zama da mutane Aunty Hasanar tace musu. "Wallahi kuwa gata Nan ta dawo kafin mu wuce mubar muku abinku ai Kuma ta Zama taku mutu ka raba". "Gaskiya Kam Allah ya tabbatar da Alkhairi ya bada zaman lafiya" Matar ta fada lokacin har saura sun wuce saida da suka shiga Zahra ke fadawa su Aunty Hasana harda likitar da mahmud ya turata ta dubata a Kano wadda tace zatayi Mata aiki, ai itace ake cewa tayi dakon soyyaya a banza yarinya ta kwace Mata shi. Nisawa Aunty Hasanar tayi tana tuna maganar da taji wannan yarinyar 'yar da sukazo da Fulanin Mai Damagaram Bata San dangantakar dake tsakanin Zahra da Aunty Hasanar ba ranar dinner ta ringa waya da kawarta a waje lokacin Aunty Hasanar ma taje amsa wayar Daddyn su Faruq taji tana fadin. Wallahi bazata hakura da mahmud ba tunda ta ganshi Kuma yayi Mata yanda take fatan mijinta ya kasance,aurensa Bai dameta ba ko matansa uku zata iya Zama dashi a haka tunda taga type dinta ne, to kuma ga wata, ga kuma labarin da suka Dan samu na dalilin Barinsa gida ga Kuma 'yan matan Cikin family dake Kara kaina a kansa, sai taji tausayin kanwar tata ta shigo Cikin wani rikicin Kuma bayan Wanda Tasha a baya. A hankali ta nisa tana duban Zahrar. "Kina jina ki dage da addu'a bake Kika kawo Muhmud ba Allah ne ya kawo shi Cikin rayuwarki kuma shine ze iya miki da kowa a kansa kada wadda ta Baki tsoro kina da duk abinda ake nema a gurin mace Abu Daya Zaki cire a Zuciyar ki matukar kina son ki Zama 'yar lelensa ciki da waje, to ki jurewa bukarsa a gado kada ki kuskura ya gane ke raguwa ce a wannan fannin, ki zamar Masa briefcase duk inda ya saka kafarsa a duniyar Nan ki mayar da taki, ki rirrata shi kamar jariri ki Hana shi kallon kowace Mace ki, zamar masa 'yar duniya ta gaske a daki ki birkita Masa lissafi, mijimki yaro ne Mai Jini a jika ga dukiya Allah ya bashi idan ba tsarewa ta Allah ba da yanzu dai sai abinda aka gani kawai. Amma Allah ya duba maraicinki yayi Miki kyautar da babu Wanda ya zata, to ki kula matuka ki Kama iyayensa da danginsa Banda rowa duk da nasan ba halinki bane, ki bar ganin masu wadata ne ko kogi Yana son Kari ki yi abinda ze Kara Miki daraja da kima a idunusu kinji. Ina Kuma Kara fada Miki ki cire tsoron Nan nasa ki masa biyayyar aure kinji shi ze Kara Miki matsayi a zuciyarsa ki bashi hadin kai, Kinga baya iya boye soyayyarki a gaban kowa to ki kosar dashi ya kashe duk wata kishirwarki dake tattare dashi". Kai kawai Zahra ta iya gyadawa Auntyn tata saboda wasu hawaye da taji sun cika Mata Idanu, tasan shikenan Nan da 'yan awoyi labarin ze canza, tunda wannan hannu ka Mai sanda ne Aunty Hasanar keyi Mata. Bayan insha'i ne Aunty Nauwarah ta shigo da wasu irin turarika da burnner Dana ruwa na wanka, toilet ta shige ta hada mata komai, ita kanta zahra tasan kamshi dai ya gama Kama Mata jiki dan ko jibi tayi kamshi ke fita daga cikinsa, ita kanshin harya isheta Saida ta Gama tsugune-tsugunen magunguna sannna tayi wanka ta fito Mai makeup na Zaune tana jiranta kwalliya kadan tayi Mata Amma Mai daukar hankali, Atamfa ta saka tayi kyau sosai sai aka Dora Mata Alkyabba Fara tas, su Inna maimuna dasu Ummee su Hajiya kaltume harda Mama Hajiya kaltumen ta hado Dan cewa tayi ta taso itace madadin Ammah ita zata Kai Zahra dakinta. Sun kaita dakin Ammi daga Nan Ammin ta saka Aunty Surayya da Mummy badai'a suka rakasu part din Hajiya Babba dana momin Kano. Gurin Abbie ne karshe Hajiyarsu ya Abbas ce da Aunty Surayya suka raka Zahra yayi Mata nasiha sosai akan biyyyar Aure, mahmud yasa waya ya Kira yace yazo Yana son ganinsa, da take yana Nan kusa a Anka road ba Bata lokaci ya shigo duk da sam baya son hayaniyar jama'a dole ya taho. A master parlournsa ya samesu yayi mamakin ganin Zahra a gaban Abbie dinsa, da sallama ya shigo ya gaishe da Abbie din sannna ya gaishe dasu mummy, ya nemi guri ya zauna kusa da Zahra Yana shakar wani fitinann k'amshin da jikinta ke fitarwa. Dan gyaran murya Abbie yayi Yana duban su mahmud da Zahra wadda kanta ke duk'e. "Mahmud". Abbie ya karawo sunansa. "Na'am". ya amsa a ladabce. "Ga yarinyar mutane Nan kaji tsoron Allah Cikin zamantakewar da zakuyi da ita iyayenta masu karamci ne, sunyi abinda ba kowa ne zeyi a wannan zamanin ba, ka Kare Mata mutuncinta da kimarta kada a bada fuskar da wani zeci mutuncinta ko waye kuwa, idan hakan ta faru za'a ga bacin Raina matuka. lallai naso na riga shi Abban nata zuwa Amma yanayi yasa yazo, mun Dade muna magana dashi ya warware min har abinda baka fad'a Mana ba, yace a Kara Yi maka godiya, yaso mikata dakinta a Karo na biyu, to saboda Yana yin aiki dole ya bar min amanar 'yarsa. Kaje gidan ka jirani Zan kawota da kaina ida yaso masu zuwa ba'a hanasu ba suna iya binta daga baya suga guri.Allah yayi muku Albarka ya Baku zaman lafiya da zuri'a Mai Albarka". " Allahumma Amin". Su mummy suka amsa suna mikewa zasu fice tunda Daman an Shirya ta kawai tafiya za'ayi. "Tashi ka rakata mota na Nan Haruna Yana jiran fitowar mu. *AUREN HUCE HAUSHI* AISHAT ISAH MUSAH. Maman Fateemah 09061432330 08055362975 Wannan littafin ba MALLAKIN kowa bane gurin juya shi ko sarrafi shi Audio ko wata sigar Saida izinin marubuciyar. Page 82. ....... Mahmud na tsaye a compound din gidan motar Alhaji Muhammad ta shigo a hankali har ta tsaya a dai dai steps da ze sadaka da babbar kofar shiga ciki, da sauri mahmud yaje ya budewa Abbie kofar dake tsakiya ya fito yayin da Malam Haruna ya budewa Zahrar kofar karshe ta fito, mahmud ne yaje ya bude kofar Abbie na gaba Zahra na biye dashi. Suna shiga Cikin Zahra taji wata irin karaya tasan karshen tika tik, duk wani zagaye zagaye yau dai ne final, gata a sokoto a gidan mahmud inda ya ta'allaka duk wani burinsa da yake kanta. "Ya Ilahiy!" Ta furta da siririn sauti. Har bedroom dinta Abbie ya kaita yayi Mata umarni data zauna a Kan gadon ta, ba musu ta dosana tare da Bismillah ta zauna a darare, Abbie din da Kansa ya dunga kwararo musu Addu'oi Cikin harshen larabci mahmud na fadin Amin. Abinda ya karyawa Zahra zuciya kenan shaukin mahaifanta ya taso Mata yanzu da itama nata suna Nan da watakila shine a tsaye yake kwararo masu wadannan Addu'oin, duk da su Ammah da Abbanta Basu taba Bari tayi kukan maraici ba,amma masu iya magana na fadin gurbin idon ba Ido bane, ita kaunar d'a da mahaifi daban take Allah s.w.a. ke sanyata a tsakaninsu, ba zato sukaji saukar siririn sautin kukanta. "Haba Fateemah ya zakiyi kuka Kuma? keda nake ganinki jaruma, ai masu babban suna basa kuka, ko su Abban naki da Malam dole sukayi Miki suka hadaki da Hussein? fada min yanzu na koma dake kije ki zabi Wanda kikeso na aura Miki kinji 'yata". Zuru mahmud yayi yana kallon Abbie din yasan da a wancen lokacin ne irin wannan ranar da Abbanta da Abdul Hakeem suka Kai Masa ita ta samu irin wannan damar babu abinda ze hanata fadar Bata sonsa, sai dai yanzu yasan ko tana Shan giyar wake bazata Fara ba Dan shi Kansa yasan ya Bata darussan da barinsa ze Mata wahala duk talauci kuwa Dan yasan duk shegantaka ce ke sakata wannan koke koken Bata ji dai dai ba da tuni labarin ze canza.Amma a juri zuwa Rafi da sannu za'a fasa tulu. Shiru Zahrar tayi tana ajiyar zuciya, dan murmushinsu na manya yayi ya nufi kofa Yana fadin. "Kiyi hakuri haka shine girma kinji Diya ta,idan yayi Miki ba dai dai ba ki fada min nine Zan hukuntashi Allah yayi muku albarka ya Albarkaci aurenku da 'ya'ya masu Albarka ya kade muku fitina ya Baku Zama lafiya ayi ta hakuri kinji 'ya ta Zan tafi, ki yiwa mijinki biyayya ki bashi girmansa da Allah s.w.a ya bashi kinji'. Kai kawai ta iya gyada Masa saboda kukan da takeyi. ficewa yayi daga dakin Yana Jin wata nutsuwa ko ba komai Dan nasa yayi dacen da kowane uba ke fatan dansa yayi, yasan in Sha Allah za'a samu nagartacciyar uwa a gurin Nan. Da sauri mahmud ya biyo shi a baya sai ganinsa yayi. "Yaya ka fito ka barta kaje ka lallasheta Mana kasan mata 'yan lallashi ne". Sunkuyar da Kansa yayi sai yaji Yana Jin nauyin hada Ido da Abbie din nasa, Dan shafa gefen fuskarsa yayi, Shima Abbie din murmusawa yayi ya nufi mota Yana kissima yanda Dan nasa yake Cikin farin ciki Dan masu iya magana suna cewa labarin zuciya a tambayi fuska, Sai dai yana nuna kawaici ne a gabansa. Abbie na barin gidan Shima ya shiga motar da yazo da ita ya fice Yana fita motocin Ammi suka doso gidan Daya Aishat ke ja sauran Kuma be tantance ko su waye ba, fitila Aishat tayi masa tayi gaba itama ta gane shi. A Cikin motar Aishat su Ummee ne sai Mama sauran Kuma su Hajiya kaltume ne 'yan tawagar Ammah sai tawagar Ammi dai saura motocin gidan Kuma jama'ar su Mahmud ne da matan gidan. Tun a kofar gate din gidan Mama ta Raina kanta balle da aka shigo ciki, take taji kirjinta ya Fara ciwo har wani jiri yake daukarta a daddafe ta shiga ciki a Nan Kuma taga abin al'ajabin Daya so ya zautata Dan abinda Bata taba tunanin ze faru bane take gani. Wai wannan gidan na zahra ne itace mamallakiyarsa ita zata rayu a cikinsa. Lungu da sako ba inda Aishat Bata shiga dasu ba,master bedroom dinsu ne kadai Bata bude ba,da yawa sun Zama 'yan kauye a gidan, dan sunga abinda Basu taba gani ba, dakin Zahra da kawayenta Wanda suka shigo Babu dadewa suka shiga suna ta rarinarsu da dauke dauken hotuna. su Hajiyar suka shigo ai ganin da gaske Zahrar ce a zaune a Cikin dakin Kuma da sunan mamallakiyarsa. Wani Abu Mama taji ya soketa a kahon zuci da kyar ta iya sulalewa ta zauna a bayan wata Mata tana dafe kirjinta. Babu Wanda ya lura da halin da Mamar ta shiga tafi minti uku a haka kafin ta samu rangwamen ciwon ta Mike ta fice tana Jan kafa Dan ji tayi sunyi Mata wani irin nauyi. Har goma da rabi gidan da jama'a Amma da yawa bakin sun wuce sai danginsu na Cikin garin sune suka nemi gurin suna baza hajarsu ta yin hotuna, sai Aunty safiya wadda gidansu babu nisa da unguwar da aka Kai zahrar. Yawancin kawayen duk kasa suka sauko ya rage daga Zahra sai sajeeda da Amatullah. Aunty safiya Batasan lokacin yaja haka ba Saida ta duba wayar hannunta taga quarter to eleven sannan ta ankare ta cewa Amatu ta taso su wuce. Sallama suka yiwa Zahra Amatu na fadar. "Kiyi Masa biyayya dai yauwa kada naji kada na gani, ko Aunty safiya?".. Ta fada tana kallon zahrar wadda ta sadda Kai kasa tana Wasa da siririn zoben gold da yake hannunta. "Dan Allah Amatu ki rabu da ita tun safe kika damunta, ba gara ita ba Dan an kusa shatanta ta warke ba, ke kuwa kece a kwana Dan Naga wannan Tajuddeen din da yake dama-dama dake guda ne da alama kema garin namu Zaki shigo". "Ki rabu da ita Aunty safiya Zan rama ne, wallahi yanzun ma Ina Jin kunyar Aunty na ne baiwa bani da bakin magana ba ki Bari dagani sai ke kiji magana, Naga alamar ko irin Jan aji Nan bazakiyi ba Daya kiraki kike Fara tsuma kamar wata tsohuwar kilaki". Ta saka gefen Alkyabbar ta rufe fuskarta dashi tana Mata dariya. "Wallahi kinci bashi saina biya Shi kuwa Dan tsabar iya sharri Zaki wani ce Daya Kira nike kama tsuma". Hannun Amatu Aunty safiya ta janyo tana fadin. "Zomu tafi ramawa tayi tun farar safiya kike Mata Dan biki ai kadan ma tayi miki". Suka fito parlourn farko na sama ba kowa a ciki sai wani irin kanshi da sanyi Mai kwantar da hankalinki a tsakiya Amatu ta tsaya ta rike Qugu tana karewa gurin zuwa dayan parlourn kallo ta Dan busar da iska daga bakinta tana kallon Aunty safiya dake tsaye tana kallon Amatu data ja ta tsaya. "Wai lafiyarki Kika ja tunga Kika tsaya?". "Bari kawai Aunty aini lokacin da kike bani labarin Families din su mahmud jinki kawai nake gani nake kamar kina kurarasa ne kawai. Amma yanda Naga gidan kakarsa kadai sai Naga ai Bakima iya bada labarin ba ban Kara sarewa ba Saida na shiga gidan mahaifiyarsa to ga Kuma Mai kankat, Dan Allah Aunty safiya waye mahmud din Nan nifa na sare da Lamarinsu gaba Daya dole kiyi kokontonsa a wancen gidan Daya sakani Santi Ashe akurkin kaji na gani". Tafin hannuwanta ta bude ta Fara kwararo Addu'a. "Ubangijin sammai da kassai ka zauna da Zahra lafiya a gidan Nan Dan isar Annabin Rahama ka tsareta daga dukkan qalubale na rayuwar Aure ka dubi gwagwarmayar data Sha a baya ka Zama gatanta, ubangiji ka jibinci lamuranta Dan soyayyar ka da Manzon Allah ka dorata a Kan duk wani mahassadi da 'yan bani na iya ka dauwamar da soyayyarta a zuciyar mijinta, ubangiji ka dubi maraicin baiwarka ba Dan ta rasa gata ba". "Allahumma Amin". Sukaji an fada daga bayansu. Da sauri Aunty safiyar da Amatu suka juya, Mahmud suka gani ya shigo ciki ta wani corridor Basu San ta Ina ya biyo ba. Kunya Aunty safiya taji abinda take ta gudu kenan kada ya shigo da abokansa su sameta a gidan duk da ba wani girmansa tayi da yawa ba Amma ita ai Yaya ce". Cikin daburcewa Aunty safiya ta gaishesa tayi Masa Allah ya Sanya Alkhairi, Amatu ma gashesa tayi. Zasuyi gaba mahmud din yacewa Aunty safiyar. "Auntyn mu ko ta Nan Zakibi sai zayyan ya mikaki gida mun gode kwarai". Tana Jin haka tasan abokansa suna kasa da sauri ta juyo tana fadin. "Nagode jazakumullahu khairan". Saida ta gangara kasa sannan ya Ciro waya ya Kira zayyan. "Ga Auntyn mu nan ka mikata gida a fadawa Sameer ya Bata itama". Kit ya kashe wayar Yana kallon Amatu yana murmushi. "Ashe dai sai wani yayi min iso gurin previous din kenan,ai nayi zaton dukkan ku kuka yoye kun bar min ita kadai". "A'a wane mu da barin sarauniyar Mata a daki ita kadai yanzu haka suna tare da sajeeda". Gaba Amatu tayi ta nufi kofar ba wani knocking ta tura ta rike kofar tana kallonsu, sajeeda ce tace. "To uwar iya wace gulmar Kuma ta dawo dake dakin Nan yanzu dai ba kyaleki zamuyi ba tunda babu idanun kunya". Shigowa tayi tana fadin. "Alheri ya dawo Dani Mai gayya Mai aikin ne na rako dungurungun Dan haka kema tattarko ya naki ya naki Mai gurin yazo". Wani irin Ras zahra taji, Ita fa abun Nan ya Fara Bata tsoro Wai me yasa a baya Bata jin haka ne Sai yanzu? turo kofar da yayi ita ta datse Mata tunanin data fada. Shine Cikin shigar shadda sky blue sai walkiya take tamkar a matse Mai a jikinta ga wani ubansu kamshinsa na dindindin Daya kashe na kowa a dakin.idanunsa yana kanta wani irin azababben kyau tayi Masa Ganin ya shagala da kallonta kada a saki layi a gabansu sajeeda yasa tayi magana. " Yallabai barka da dare, ya hidima? Allah ya Sanya Alkhairi ya bada zaman lafiya da zuri'a d'ayyuba. To zamu tafi gata Nan Zan baka Amabarta a karo na biyu, kamar wancen karon, kaji tsoron Allah a Cikin zamantakewar ku ka tsare Mata mutuncinta a da Basu San waye Kai ba, Amma a yau ko baka fada Mana ba mun gani da idanunmu, nasan bestie zata iya fuskantar hari daga masu burin samun matsayi irin nata a gurinka, ko ba'a fada ba tunda a Dan kwaramniyar bikin Nan naji views din Mata da yawa a kanka. Gata Nan Bata da kowa a garin Nan daga Allah Daya halicceta sai Kai daka kawota,ka zamar Mata bangon da zata jingina dashi ka zamar Mata suturar da zata Kare Mata martabarta, kada ka cutar da ita Dan girman Allah Zahra marainiyar Allah ce duk da Bata rasa komai na gatan gidan duniyar Nan ba Amma tana bukatar samun nutsuwa tunda a can akwai 'yar kasan da ake soya Mata Aya a tafin hannuwanta ba tare da an ankare ba Saida tafiya tayi tafiya, Allah ya amintar dake bestie a Cikin gidan Aurenki ya Baki kariya irin wadda yake Kare bayinsa salihai da ita, ya amintar dake kamar yanda ya amintar da Annabinsa Ibrahim A.S daga wutar Namaruzu. Dan Allah kiyi Masa biyayya ki rufe masa sirrinsa kinji, Allah ya Baku zaman lafiya Mai dorewa ya kauda muku fitina".. Sai Kuma muryarta ta Fara rawa, sai hawaye, da sauri ta nufi kofa ta fice. Zahrar ma share hawaye take haka Amatu itama idanunta sun cicciko da hawayen,Shima Dan gogan tunda yarinyar ta Fara magana yaji kamar ta Dora Masa bulo inci Tara a kansa, ya yarda kaunar precious da yarinyar Nan ta gaske ce babu algus a cikinta saboda yayi wani Abu Wanda ya gaskata hakan, Dan ranar Daya bijiro Mata da maganar soyyyarsa dan Karamin hauka sajeedar tayi Masa da kyar ya fahimtar da ita cewar gwaji ne yayi Mata ba Wai da gaske yake ba, duk da haka Saida ta nuna Masa kada ya karayi Mata irin haka za'a iya samun matsala. A can main parlour kuwa abokan angone tare da kawayen Zahra sai wasu 'yan Mata na family din, tun a can ya fada musu Bai Hana zuwa sayen Baki ba Amma babu Mai shigar Masa dakin barci babu Kuma Mai Kara gane Masa Mata Ganin gurin dinner ma Ala amfana. Yasha caccaka gurin friends dinsa yayi kunnen uwar shegu dasu shine dalilin Daya saka yayi amfani da kofar baya ya hauro stairs din shi kadai. A Nan su sajeeda suka Sami su Khadija dasu Aneesah da sauran mutanen, Tajuddeen ne ya taso ya nufi Amatullah yana fadin. "Daman kina sama duk Kiran da nake Miki bakya amsawa?". Dan bude hannunta tayi alamar babu waya a gurinta. Jinjina Kai yayi suka nufi waje. Addu'a sukayi aka shafa sannan kowa ya fito da wata Leda Mai shegen kyau a hannunta da alama kyautar girma ce daga bangaren anguna. Saida suka fito sannan salis ya Kira mahmud Yana fadin . "To yallabai ango mu zamu wuce asuba ta gari". Wani Abu mahmud din ya fada Masa ya fashe da dariya wadda ta janyo Hankalin da yawa daga mutanen gurin Yana fadin. "A'a kayi zamanka wasu har sun Fara ficewa daga cikin gidan ka duba time lokacin yaja da yawa". Tun bayan fitar su Amatu zahra tayi tsilli-tsilli, sai taga yau ya Kara Mata wani kwarjin da girma gani tayi kamar ya cika dakin, numfashi ma neman tsaya Mata yayi wallahi wani irin Abu take gani a cikin idanunsa. Yana sauke wayar daga kunnensa ya nufo zahrar Yana sakin tsadadden murmushi, ya Dan tsuguna a gabanta ya saka hannu ya dago fuskarta wadda hawaye ya bata. "Ya salam!" Ya fada Yana Zama kusa da ita, tafin hannunta Daya Sha lalle ya rike Yana Dan matsawa kada dayan hannunsa ya saka ya zare Alkyabbar daga kanta Yana karewa fuskarta kallo, be tab'a Jin ya gaji da kallonta ba shi dai ya yarda Allah ya jarabcesahi da wata irin soyyaya a kanta shifa ji yakeyi ko baze kusanceta ba ze iya rayuwa da ita har iya rayuwarsa. Wani irin kanshi ne ke fita daga jikinta na musamman ba Wanda ya Zama constant ba a'a an samu Karin wani na musamman a Jikin. "Welcome to Dange's house Mrs Mahmud Muhammad Dange, Alhamdulillahi bini'imatihi titummus salihat, Fateemah Allah yayi Miki Albarka yau gaki a gidan Mahmud Kuma gidanki da Zaki rayu a cikinsa ki dasa Mana bishiyar Zuri'armu a cikinsa ta girma ta yadu har asha inuwarta, Fateemah duk burina na duniyar Nan game da mace a kanki na ta'allaqa shi ki zamar min bargon daze lillib'eni ki hanani Jin sanyi sai dumin jikinki, ki daukemin duk wata kishirwar data addabeni akan diya mace kinji my princess, duk duniyar Nan da ke kadai na aminnta na bayyana Mata sirrina ciki da waje ke kadaice macen data tab'a gani ainishin waye ni tunda nayi Hankalin kaina, ki tallafeni kada ki Bari na shiga rubibi a hannun Mata kinji my previous, na baki amanar kaina da kaina tunda ni babu Wanda ya Baki Amana ta amma ke kowa fada min yake gaki Nan Amana na kula dake to nima ki kula Dani Dan tamkar marayan da bashi da uwa bashi da uba haka nake a gurinki ki bani dukkan kulawa kinji, kuma Dan Allah ki daina tsorona nifa babu abinda Zan Miki na cutarwa idan na cutar dake Nina cutar da kaina, duk wani burina nandora shi a kanki". Ya fada Yana shigar da ita jikinsa Yana sauke ajiyar zuciya a jajjjere, lif tayi a jikinsa Amma fa yaji yanda heart dinta ke beating very fast. Lumshe ido yayi ya rasa meya canza Masa ita take irin wannan Jin tsoron nasa yasan ba dabi'arta bace hakan ko ranar Daya Fara fito Mata a mutum sak ba tayi irin wannan tsumar ba kawai dai ta Dan rikice Masa na dan lokaci Amma Daya saka Mata pressure dole ta nutsu tayi Masa abinda yake so a lokacin harya saida ya samu relief, Amma yanzu duk ta rikice Masa a Hankali yayi Mata magana a kunnenta. "My previous me kike tsoro a tare dani, fada min kinji?". Ya fada Yana Kara shigar da ita jikinsa yana kuma Dan shafa gashin kanta Daya Sha gyara na musamman, sanyi da salama da wata irin nutsuwa suna sauka a cikin zuciya da gangar jikin a lokaci daya. Lif ta qarayi a jikinsa dan da gaske tana Jin wani irin Abu da ada Bata jinsa a tattare dashi, sai yanzu take jin da gaske fa auren ne a kanta sabanin da da take jinta dai gata nan. *AUREN HUCE HAUSHI* _AISHAT ISAH MUSAH _*Maman Fateemah_* 08055362975 My WhatsApps number. *Page 83. ______Kara shigar da zahrar yayi jikinsa, nan da nan yaji labarin Yana neman canza salo shi Kuma harga Allah Yana bukatar privacy saboda matukar ya tab'a wannan shugwababbar 'yar raki sai abinda Hali yayi. Don yasan za'a Sha danger da ita ga mutanen biki suna Nan yasan da safe baza'a rasa masu zuwa suyi Mata sallama ba, yafi son sirri gaskiya. Amma dai zasuyi nafilar da Manzon Rahama yayi umarni da ma'aurata su yita. "Cikin nasa salon da yasan Yana yin rinjaye a kanta ya Dan fara shafa cikinta a Hankali. "Da yunwa a cikin Nan gaskiya, Bari na kawo Miki abinda zakiçi kada Nan gaba ayi min gorin ranar da akazo gidana ko abincin tarba babu Ina ta kurin sokoto aga nayi failing ko ba haka ba?". Ita dai zahra shiru tayi masa shi ya kasa ganewa yau jinta take tamkar Bata taba wata kebewa tare dashi ba,taga sai wani rawar jiki yakeyi abinda ba halinsa ba, duk wannan kanewar ta nemi nata gurin wani sabon mahmud take gani ba Wanda ta sani ba. Ya tambaya Yana kokarin zare Mata Alkyabbar gaba Daya daga jikinta wani fitinan kamshin ya mamaye shi, ga wani mahaukacin feeling da yaji Yana fusgarsa zuwa gareta, kankameta ya karayi a jikinsa da gaske ya shiga wani yanayi,ba Karamin yak'i yayi da zuciyarsa kafin ya sassauta Mata rikon da yayi mata Yana maida numfashi. Alkyabbar ya aje gefen gadon ya Zama daga ita sai wata rigar atamfa wadda akayiwa wani fitinannan dinki Wanda ya fito Mata da ikahirin halittarta ta kirji zahiri, yabi shafaffen cikinta abinda ya Kara fallasa asirin kirjin nata kenan da suke a cike tsan-tsan, ai baisan lokacin Daya Kara mannata a jikinsa ba Yana fadin "Ashe wannan abar ba Karamin sitirtamin kayana tayi ba" Yana Kai hannunsa gurin. Dan zabura tayi ta rike hannunsa ta shagwab'e Masa fuska tare da juya Masa sexy eyes dinta "Please meu amorrr.....ba kyaufa ka Bari Dan Allah". Saitin kunnenta yayi magana a hankali.. "Meye ba kyau din fada min abinda nayi Daya sabawa shari'a? Ina son Jin tempareture din jikinki ne naji kamar tayi high". "A'a...ni lafiya ta qalau". "Ok, to bari nazo". Ya fada Yana gyara Mata zip din rigar, fuskarta ya dan shafa kadan tare da Bata wani light kiss a gefen wuyanta Wanda yasa tadan fitar da wani Karamin sound da yaso ya Hana shi fitar. Babbar rigar ya cire ya aje a kusa da ita Yana nufar kofa ya fice, Dan kwanciya tayi a gefen gadon tana Jin wani Abu Yana circulating a cikin jinin jikinta. Bai Jima ba ya dawo dauka da Leda Mai tambarin na Maru suya spots, da plates da sauran tarkacen su knife da cups da su forks, a kan Karamin Conner table ya Dara idanunsa na Kan Zahra wadda ta lumshe Ido tana sauke numfashi a hankali,wani special smile ya saki yana godewa sarki buwayi gagara misali da yayi Masa irin wannan kyautar, Saida ya aje komai sannan ya nufeta ya tsuguna dai dai saitin fuskarta Yana dan shafawa a hankali narkakkun idanunta ta bude tana kallonsa. "Oya tashi kici abinci". Ta lumshe idanun tayi. "I am ok fa, bana Jin yunwa barci nakeji". Bai saurareta ba ya saka hannu ya dagota daga kwancen Yana fadin "Ni nagano yunwar a tare dake". Nama ne Wanda ita dai bazata ce ga yanda aka sarrafa shi ba, ya gyara hannun rigarsa ya Fara Bata tana mitar ita ta koshi Amma Bai barta ba Saida ya tabbatar da ta koshi sannan ya dauko Mata mutuniyar farm fresh ta strawberry ya cika cup ya kafa Mata a Baki ta Sha rabi ta kawar da Kai kamar yanda yaran goye sukeyi idan suka koshi da Abu. "Pls precious ki shanye mana farm fresh ce fa, ko kin daina yayinta ne? Naga tunda mukazo kabi nema ba alhalin an cika Miki store da ita". A shagwab'e ta dago sexy eyes din ta tana Masa wani kallon Daya nemi jefa shi a wata nahiyar. "Nifa na koshi kamar na cikin mafa ze dawo nakeji". "Ok. Shike Nan Bari na dauke kayan sai ki shiga kiyo Alwala kafin na dawo". Har ya kai kofa ya tsinkayo maganarta tana fadar "pls naga zaka mayar Kai bakaci komai ba". Kafeta yayi da Ido Yana nazarinta "Da kina son naci ai da kin bani, amma Baki bani ba tunda na dauke kuma sai wani jikon Wanda kikaci shikenan is enough for us, koba haka ba?". Ya dage Mata gira ya fice. Tsam tayi da ranta tana hasaso mezeje yazo, ita fa duk lamuransa sun tsaya Mata a Rai yanda ya downgrade din kansa a Azare da yanda ya ringa mu'amalantar Almajiran malam, a yayin zamansa a can, ita fa gani take wallahi yanzu yafi karfin ajinta nesa ba kusa ba duk da tasan itama yes ba karya Ubangiji ya Gama Mata gata ya dauke Mata iyaye Amma cikin Rahamaniyya tasa saiya saukake Mata duk wani tsananin rayiwa, duk da Tasha badaqala a baya sai gashi ya zama tariihi. Allah be Bata ikon tashi ba har ya dawo, ruwan dake hannunsa na laimar alwala ya Dan yarfa Mata sai tayi figigit tana sauke ajiyar zuciya. Gaba yayi ya nufi kofar da take tunanin toilet ne, ta Mike a hankali tabi bayansa hanya ya matsa ya Bata tare da fadin "shiga kiyo Alwala Ina jiranki". Ya juya ya fice daga dakin, brush ta bude sabo ya wanke bakinta sannan tayi alwalar gurin mirror ta nufa ta karewa kanta kallo, wallahi tausayin kanta da kanta takeyi tasan sai yanda hali yayi Dan ita kadai tasan me take hangowa a cikin idanunsa. Tana tsaya taji alamun za'a bude kofar tayi saurin barin gurin, Yana budewa tana zuwa bakin kofar jallabiya ce sabuwa fara Kar a jikinsa sai Zuba kamshinsa nan nasa na musamman yakeyi, hannu ya Miko Mata yana sakin murmushi Yana fadin "inye 'yan matan gidan mahmud Dange, yarinyar Nan kina yanda kike so da Dan malam din Nan wallahi sai cika kike kina batsewa irin kada a kawo Miki wargi din nan ko?". Kauda Kai tayi tana sakin murmushin ta Mai shagaltar dashi "Ni wallahi ka Bari idan wani yaji saiya dauka haka ne fa". Hannu ya rike ta fito daga toilet din. "To da karya na fada ba cikar kike kina batsewa ba kawai Dan ki Sara min allo ki hanani rawar gaban hantsi ni da halaliyata za'a hanani dama daddawata da moda". Ya fada Yana kafeta da tsumammun idanunsa, sadda kanta tayi kasa Dan abinda take gani a can baya ta gani yau muraran a idanun nasa ta rasa wane irin abu ne da yake sakata a rudu haka. "Muje muyi sallar". Hijab taga ya dauko Mata fari sol dashi Mai laushi irin na mutanen Indonesia din nan ya zura Mata,Yana janye da hannunta suka nufi wani guri kamar space din da ake saka dining table suna zuwa taga an yi gurin ne domin ibada kawai ba Bata lokaci ya shige gaba yaja musu sallah, raka'a biyu yayi musu yayi sallama ya Jima Yana musu Addu'oi da harshen larabci Wanda har Saida zahra ta dago da kanta ta Zuba Masa idanu tamkar shine Dan mun gada din, a hankali ya matso inda take saune ya dafa kanta ya ringa kwararo Addu'a, Nan da Nan jikinta ya hau tsuma sai kuka Dan Allah ji tayi tamkar tafi kowace mace sa'ar samun miji Mai addini Dan Bata taba tunanin iliminsa ya Kai haka ba tun a wancen lokacin bare kuma yanzu da taga ra'ayal ainiy. Sai da ya Gama Mata Addu'oin sannan ya daukota cak ya rungume abarsa Yana fadin " pls precious kinsan bana son kukan naki ko? Ki daina kuka babu abinda Zan Miki ki saki jikinki Dani kinji, Nima na gaji sosai babu abinda nakeso sai nayi barci na huta ai kin gane". Kai ta gyada masa tana Kara lafewa a jikinsa tamkar mage, ya yarda yayi amanna itace weakness din da gaske Dan ji yake baze iya matsamata ba gurin sex Dan ya fuskanci tana zulumin abin ba kadan ze da raka da ita ta Kara sakewa yasan duk runtsi ba za'a dauki lokacin da sukayi a baya ba. *****Kuka take tamkar wadda akayi mata babban rashi irin na iyaye,duk iya ban baki Salbiyya babbar hadimar Fulani tayi Mata Amma kamar tana Kara tunzira ta, dan tayi masifar kwallafa ranta a Kan mahmud, guyn yayi Mata karshe taci burirrika masu yawa a Kansa,tun bayan dasu Ammi suka dan tattauna a kan yuwuwar hadasu aure bayan samun matsalar data kusan rusa farin cikin da yawa daga family din nasu mahmud. Tashi Salbiyyar tayi tana fadin "Bari na Kira Giwar Mai martaba tazo taga halin da kike ciki kada ciwonki ya tashi mu shiga uku" Ta dauko wayar ta tana kokarin Kiran Fulani, da sauri Insiyya ta rik'e hannunta tana girgiza Mata kai saboda kukan da yaci karfinta. Fasa Kiran tayi itama barazana ce saboda lokacin kusan Daya da minti goma, daren ya Fara nisa bazaso ta daga Hankalin uwar gijiyar tata ba. "To ya kike son naji Miki ranki shi dade? sai Abu Daya kikeyi tun dawowar mu daga gidan Amaryar Nan Kika birkice min kink'i ki fada min damuwarki ko ina da abinda Zan taimaka Miki dashi". Wasu zafafan hawaye ne suka zubowa Haura'ul insiyya bata damu data gogesu ba. "Ina sonsa,son da bansan ta Yaya na Fara shi ba,batun yanzu nake jinsa a Raina ba sai dai Ganin babu fuska yasa na hakura , sai kuma Mama ta fada min sunyi magana da Ammi zasu had'amu aure tun bayan da aka samu matsalar da tasa yabar gida aka rasa Ina ya shiga a cikin duniya, na gansu a India Shida wannan matar tasa, tun a lokacin naji Ina masifar kishinta, saboda Ina Ganin indai tana gabansa babu wata mace da ze daga Ido ya kalla Wallahi". Ta fada tana share wasu sabbin hawayen da suka ciko Mata idanu. "Haba ranki shi dade har kina tunanin akwai namijin da zece baya sonki? Ai sai dai Idan ba'a bashi ba, ki gafarceni abunda Zan fada, ni bana Miki fatan ki shiga gidan Aurenki a mace ta biyu, fatana ki shimfida rayuwar ki keda mijinki da 'ya'yanki ki juya abinki yanda kikeso, Ina shi yaron da kuke karatu dashi a can Rasha din Dan nan Nigeria Wanda iyayensa sukazo suka gana da takawa ba naji ance Shima jinin sarauta bane? Kinsan dai da wuya Mai martaba yayi magana biyu ki yiwa kanki Qiyamul laili ki Zubar da wannan batun Kinga dai yanda baiji kunyar kowa ba a gurin dinner game da matarsa, haka naji wasu na fada har suna cewa ai a can gurin wayonsa ya samota, to kinga ko kin shiga ba wata daraja zakiyi ba tunda ba shine yace Yana sonki ba, mazan yanzu sun ganki sunce suna so ma Yaya aka k'are ballentana kin Zama matar shige? Babu abunda Zaki tsinta a gidan sai zaman hakuri, ki cire ranki daga Kansa kiyi ta addu'a idan shi Alkhairi ne a cikin rayuwarki Allah ze kawo sanadin haduwarku ya Kuma saka soyayyarki a zuciyarsa kinji, ki share hawayen ki wane gata ne Allah baiyi Miki ba? Da har Zaki Bata hawayenki a banza idan so cuta ne ai hakuri magani ne". Duk Jikin Insiyya Sai yayi sanyi tasan duk abinda salbiyyar ta fada Mata gaskiya ne gara tayi addu'ar idan da Alkhairi Ubangiji ya fita sanin ta inda connection din ze hadu. Salbiyya ta Jima tana kwantarwa da Insiyya hankali, tare da kawo Mata misalai na yanayin rayuwa da zamantakewar aure da irin qalubalen da ake fuskanta a irin auren da take kokarin saka kanta a cikinsa, kafin su kwanta da yake ita ke hidimtawa Insiyyar a Nan. Karfe hudu na asuba alarm din da mahmud ya saka ya fara Kara, a hankali ya Mika hannu ya dauko wayar ya kashe, bedside lamp ya kunna harkenta madaidaici ya haske su. Zahra na kwance a jikinsa tayi lif da ita tana sauke numfashi cikin salama, dabin su na jiya ya tuna da kyar ta yarda dashi akan babu abinda zeyi mata, Dan Saida ya riga ta barci ma sannna ta saki jiki tayi nata barcin. Sai kusan biyu da rabi ya farka ya ganta ta shige jikinsa kamar yanda suke barcinsu normal,sleeping dress din ya Kama ya janye 'yar igiyar da ake daurewa ta sunce ya zare a Hankali suka Sami body contact ya saka blanket ya rufesu, Yana kunna wutar itama ta farka a mamakance take Masa wani kallo ganin ta ba yanda ta kwanta ba, da sauri ta rarumo blanket din tana kokarin rufe saman jikinta da yake bude muraran, wuf ya saka hannu ya rike Yana Mata kallon k'asa-k'asa. "wallahi kina tufewa labarin ze canza salo Bakisan "I will eager to show you...ba ki barni na samu relief mana." Ya fada tana Kai hannunsa inda yasa ta wuntsila gefe ba shiri tana kankame jikinta, Dan ya shammace ta Bata taba zaton haka ba. Dariya yayi ya mike Yana fadin "matsoraciya kawai duk saina cire wannan kunyar dai Naga alama bazata Bari a kularwa da Malam dansa yanda ya kamata ba, gara na rabaki da ita kowa ya huta,kema ki Fara aikin Lada". Binsa tayi da Ido tana mamakinsa Dan da gaske ta yarda maza kunyarsu ragaggiyace wallahi. Toilet ya shige yabar Zahra tana rarraba idanu kamar na shege a rabon gado. Harya fito Bata motsa daga inda take a kudundune ba. Da alama wanka yayi, kusa da kanta yazo ya tsaya Yana mamakinta sosai. wani smile ya saki Yana ayyana shifa yana ganin gara ayita ta Kare kawai duk yanda yaso a samu sirrin yayi hating din abinda akeyi a duniyar Hausawa Wai dole a washe gari sai Baki sunzo gidan Amarya sunga kwakwaf, to amma shi hakurinsa da ya Kare duk yanda yaso ya Dan daga Mata kafa saboda jama'a abun nema yaje yaci tura. Dan jiyama Saida yasha magani, to gara yasan abunyi da wannan shagwababbar yarinyar, ya kamata tasan Allah Daya ne, duk da yasan itama tana bukatarsa a yanda yake gani a cikin idanunta, yasan kawai tana zulumin yanda abun ze kasance Wala Allah tana karanta irin novels din Nan tana Jin yanda take kayawa a irin wannan dareren shine dalilin da yake d'aga Mata hankali. Jallabiya ya zura ya Zuba turarensa, sannan ya dawo ya Dan cire rufar daga fuskata. "Tashi kiyi sallah kada guri ya kure Zan wuce masallaci". Dan mirginawa tayi tana kokarin tashi Bata zata ba yayi Mata daukar jarirai ya nufi katafaren toilet din dakin da ita tana ta magiyar ya sauketa amma yayi Mata fumfurus Saida ya dangana da ita cikin bathtub wanda ya cika Mata da ruwa Mai maraifaicin zafi sannan ya dire ta, Ganin Yana kokarin cire jallabiyarsa yasa ta waro idanunta tana Masa duban rashin fashimta. Gira Daya ya dage Mata Yana murmushin data kasa tantance Kona menene "Ba.. ba.. masallaci zaka tafi ba Naga kana kokarin shigowa". Girgiza Mata Kai yayi "na fasa fita yanzu wankan Zan sake kinsan bana gajiya da Wasan ruwa". Bata San lokacin da dariya ta kubce Mata ba Jin yana fadin Wasan ruwa kamar wani small kid. Ita dai batayi aune ba taji mutum a jikinta, duk iya magiyarta bai rabu da ita ba saida ya gamsu yanda yake so sannan sukayi wankan tare karshe shine yayi musu limanci a gida. Sun jima suna Addu'oinsu sannan suka koma suka Kwanta Dan Shima barcin yakeji ba kadan ba.Amma Saida ya yamutsata iya yanda yake so Dan kirjinta Banda zogi babu abinda yakeyi da ba inda bakinsa Bai Kai ziyara ba Saida ya tabbatar ya Fara goge Mata hadda sannna ya saurara Mata ya sakata a jikansa kamar wata 'yar baby. Wurin goma da rabi karar Kiran wayarsa ya tashi zahra, Mika hannunta tayi ta dauko wayar sai taga MY FIRST LOVE na yawo akan screen din wayar, wata faduwar gaba ce ta ziyarceta har wayar ta yanke bata dawo hayyacinta ba, wani Kiran ne ya sake shigowa cikin barci yaji special ringtone din Yana kadawa da sauri ya tashi sai yaga wayar a hannunta tana masa wani kallon tuhuma wayar ya saka hannu ya karba tana daf da sake katsewa ba tare Daya tanka Mata ba. Yana daga Kiran ya tashi ya nufi kofa ya fice daga dakin. Baki a sake zahra tabi bayansa da kallo tana ayyana "wata sabuwa inji 'yan caca,wacece haka wadda har baza'a daga kiranta a gabanta ba? Harta koma ta kwanta sai kums ta tashi kamar wadda aka tsikara ta nufi kofar ta fice itama daga ita sai rigar barcin Wadda ta fito Mata da ilahirin surar jikinta muraran irin silk din nan ce kijinta ya fito muraran a ciki yayi irin cikar nan, wani yawu ya hadiye babu shiri.. *_AUREN HUCE HAUSHI_* *AISHAT ISAH MUSAH* (Maman Fateemah) 09061432330 Or 08055362975 Page. 84 .......".Good Morning Ammina". Abinda kunnenta ya Fara cin karo dashi kenan Yana fad'a lokacin data fito da azama idonta ya rufe da kishi ganin sunan da yake yawo a Kan screen din nasa, sai Kuma tayi turus taji wani irin sanyin Rahama Yana saukar Mata a cikin zuciyarta, dan ita kanta Bata San tana da irin wannan kishin ba sai yanzu da taga wasu kalmomi dake nuna mace aka alaqanta dasu, da sauri ta juya zata koma tunda babu wata tazara Mai yawa a tsakanin su, ita dai ba zato taji ya saka hannunsa Kan cikinta ta baya harga Allah batayi zaton ya ganta ba kuma Bataji tafiyarsa ko dan Valentino silifas din dake kafarsa masu irin laushin Nan ne, mannata yayi a jikinsa ta baya Yana cigaba da wayarsa ji tayi yana fadin. "Gata nan lafiayrta kalau Bari na Bata ku gaisa da 'yar taki Naga alamar Nan gaba duk tawaye zakuyi min tunda Naga kin damu da ita da yawa kamar an ce Miki Zan gutsiri Naman jikinta". Wayar ya saka Mata a kunne Yana Kara kanainaye ta Yana shafa ruwan cikinta a Hankali. "Assalamu Alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu, Ammy barka da Asuba". Zahra ta fad'a cikin nutsuwa duk da jikinta yana karbar sakon da ake aika masa. "Wa'alaiki Salam warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu, barkamu kadai diyata ya bakunta Ina fatan babu damuwa dai ko?". A kunyace zahra tace Mata "babu komai Ammy na gode". "To Masha Allah haka ake so, Allah yayi Albarka". A zuciyarta ta Amsa da "Ameen". Wayar ya mayar kunnensa yaci gaba da magana da Ammin nasa inda taji tana fada masa ga masu kawo musu break nan. Taso ta zare hannunsa daga kan ruwan cikin nata Amma yaki Bata wannan damar falon saman ya shigo dasu ya zauna kan two seater ya dorata a cinyarta yayi Mata irin rungumar Yara har ya Gama wayarsa da Ammi dinsa. Kallonsa tayi tana dan marairaicewa "pls ka barni nayi wanka kaga Ammy tace Baki sun taho kar ace min kazama fa" Bakinta ya saka yatsarsa ya Dan zageye lips din Yana fadin "waye zece Miki kazama ai ke ko Zaki shekara bakiyi wanka ba babu Wanda zega kazantarki kinsa kuwa baiwar da Allah yayi Miki?". Dan far tayi Masa da fararen sexy eyes dinta tana Masa wani kallon da yake susuta shi tana kokari barin Jikin nasa, tashi yayi tsam da ita Bai koma bedroom din da suka kwana ba, wani taga ya nufa da ita, ita fa sai yanzu taga yanda tsarin sama ma yake tamkar wata fada. Bedroom din da suka shiga tsaruwarsa ta Kai matuka tamkar a gidan duniyar za'a dauwama, bakin katafaren gadon ya zaunar da ita yana fad'in "Ga master bedroom dinki Nan Idan munyi break zamu zagaya kiga gidan naki ki duba kiga ko da abinda beyi Miki ba Sai a canza ko". Security dinsa na gidan ya Kira kafin su shiga wankan ya fada musu idan yaran da zasu kawo abinci sunzo a fada musu su aje a dining room. Sun Bata lokaci gurin wankan Dan da gaske mahmud so yake ya budewa 'yar gidan nasa Ido kafin a shiga daga other room. Dan Saida ya yamutsata yanda yake so sannna ya saurara mata dan harta saddaqar ita Kuma a toilet abun ze risketa sai taga ya basar ya rufe idonsa, yana sauke numfashi da sauri da sauri, ya rigata fitowa Dan da gaske ji tayi wani irin nauyinsa ya mamayeta yanda ya sawa idanunsa toka tasan ranar da Mai abkuwar zata afku sai gyarawa Allah Dan Bata hango abin da sauki ba. Daure da Dan madaidaicin towel pink ta fito Bata gansa ba a dakin sai kamshinsa da dakin yake zubawa, lotion din Aveeno ta dauko ta Fara shafawa tana mamakin wasu abubuwan da yake ajewa da suka danganci cosmetics kusan saita samu abinda take amfani dashi ba kamar perfumes dinta wannan ko kuskure babu. Wani ubansun lace ta saka marar nauyi kalar peach Mai shegen kyau tsada riga ce T bubu da straight siket, ta hade gashin tasa Masa band sannna ta kafa daurin da 'yan Mata ke yayinsa, Sam Bata Saba da yinsa ba shi yasa da tayi yayi Mata wani irin kyau ba kadan ba, bedroom din ya shigo tana cikin saka Karamar sarka a wuyanta, karasowa yayi ya karba Yana saka mata Yana sanye da T-shirt Fara tas da sai Dan karamin tambarin bakin zare da gefen hago saitin zuciyarsa da bakin trouser na kamfanin Herme's yana Zuba mayataccen kamshinsa na ibada, Kansa ya kwantar a gefen wuyanta Yana shakar Wani fitinanan kamshi dake fita a bayan kunnenta da wuyanta. "Previousss..." Ya fada Yana saka hannunsa cikin rigarta Yana shafa shafaffen cikinta, dif wuta ya dauke Mata wuta maimaita Kiran sunanta yayi a saitin kunnenta Yana Dan busa Mata iska a ciki. "Umhumm". Ta amsa Masa a takaice. "Zo muje kina da Baki 'yan uwan Ammi ne Wai yanzu zasu koma akwai masu komawa makaranta". Kai ta gyada Masa tana Dan zame jikinta daga jikinsa ta dauko madaidaicin gyale ta Dan rufa, sai tayi masa wani irin kyau na musamman, Kara matsota Yayi ya saka hannunsa ya zagayeta a jikinsa Yana hade bakinsu. Saida yaji tsayuwar na neman gagarsu sannna ya saurara mata ji yake tamkar ya hadiyeta Dan soyayyarta da take zalzala a zuciyarsa, a Kan sofa ta zube tana mayar da numfashi, Dan ita lamarinsa na yau Yana neman yafi karfin Dan karamin tunaninta, Shima da kyar ya saisaita kansa dan da gaske in dai zasu wuni tare tofa da ranar Allah ze iya bude aiki. Saida suka dawo cikin hayyacinsu sannan suka nufo kasan Dan Lamarin nasa sai kallo ya badawa idanunsa kwallin rashin kunya duk ya hanata rawar gaban hantsi Ina wallahi ada idan akace zeyi haka zata iya rantsewa da Allah bazeyi ba saboda yanda take ganinsa ba ruwansa Dan bawan Allah Ashe dai a wannan fannin ba mumini,kowane kurtu ma duma ne, ga wani tsare gida da taga Yana yinsa a cikin gidansu taga har manya suna shakkarsa. A hankali suka ringa saukowa Yana rike da hannunta Yana Dan murzawa kadan kadan duk yanda taso ta zame hannunsa yaki sakin nata Kamar wadda zata guje Masa, ita ta rasa wace irin fitina ce ke dawainiya dashi yau yi yake kamar ze hadiye ta *_ AUREN HUCE HAUSHI_* AISHAT ISAH MUSAH (Maman Fateemah) 09061432330 08055362975 Page 85. ............. A haka suka jero suna tafiya sunyi wata irin dacewa ta ban mamaki Dan kyaune ke dukan kyau kwarjini ke dukan kwarjini, suna nufo down stairs din ta ringa jiyo maganar jama'a da alama suna da Dan yawa, a haka suka ratsa parlours biyu suka nufi na farko, sai Dan satar kallon gidan zahra takeyi Dan da gaske gidan ya razanata a yanzu sabida Bata taba kawo da ire irensu a cikin kasar ma Baki Daya, suna dosar parlourn ta hangi harda manyan mata, taso ta kwace hannunta Amma dan tahalikin nan yayi mirsisi ya doje har suka shiga, a qalla sun Kai mutum bakwai harda wadda sukaje Azare da ita. Direct gurinta ya nufa Yana amsa gaisuwar da Yan matan ke Masa, kusa da Hajiya zuwaira yaso zaunar da zahrar Amma ta noke ta zauna daga kasa Kan carpet tana gaishe da manyan yayin da sauran kamar sa'anninta da wadanda ta girma suka gaisheta. Radeeya ce ta dan matso tana fadin. "Aunty zahra Ammi tace a fada Miki idan an jina za'a turo Miki da house maid dinki". Kaita kyada Mata kafin tace "na gode madallah kiyi min godiya'. Sun yi musu nasiha sosai kafin su tashi Daya daga cikin matan na fadin "Mahmoud yaushe za'a kawowa su Alhaji ita su ganta". Dan shafa Kai yayi Yana Dan murmushi kasa kasa. "Zamu zo in Sha Allah idan mun dawo daga tafiya". Dago Kai zahra tayi Jin ya ambaci tafiya, wai shi baya gajiya da yawo ne saboda Allah. Har gurin mota suka rakasu suna musu fatan sauka lafiya, sai da suka fice daga gidan sannna suka juya Yana mak'ale da ita, directly dining room suka nufa wasu mahaukatan food warmers ne kusan guda biyar sai tea flasks biyu da saura cas musu kyau. Tashi mahmud din yayi yana fadin "taso muje ki nuna abinda zamu dauko a kitchen". A yangace ta tashi hannunta ya sarkafo cikin nasa Yana Dan sinsinar wuyanta suka nufi kitchen din, duk abinda ake bukata ta dauko shi da kansa ya wanke su a sink Yana Mata hirar tare zasu ringa abinci saboda baya son abinci masu aiki. Abinci ne kusan kala biyar funkaso yace ta zuba musu tare da kunun gyada Wanda yaji kwakwa da Madara, sunci sun koshi sannan suka tashi ya Taya ta suka kwashe kayan da sukayi amfani dasu. Da suka koma parlourn Basu zauna ba lungu da sako na gidan ya shiga nuna Mata ba karamin mamaki zahra tayi ba Dan ko a mafarki Bata taba tunanin rayuwa zata kaita irin wannan gurin ba, kallon mamaki take binsa dashi Amma ya fuske ya nuna kamar baisan abinda take nufi ba, dakin da suka shiga ne yayi muguwar tafiya da imaninta, dakin Yara ne akayi Masa wani decorations masu kyau da daukar hankali ga wasu irin Turkish furnitures child size masu azabar kyau hatta shelves din dake cikin wani kamar Dan dakin glass a bangaren da katayi Dan karatu child size ne, ga colours din purple da pink ne sai ya bada wani yanayi Mai kyau a dakin, Kara shigar da ita Yayi jikinsa yana da shafar abinda yake tsone Masa ido a Hankali. "Yaya me za'a Kara ko a rage banji kinyi comment ba fa tunda muka Fara zagaya gidan naki ko Bai Miki ba a canza Miki wani? Ga Kuma dakin babies dinmu fa yayi ko a canza musu tsarin?". Kasa magana tayi Dan hannunsa ba karamin dagula Mata lissafi yakeyi ba ga Wani numfashi da yake sauke Mata a gefen wuyanta. "Pls talk to meeeee..zMana kinyi shiru,Bai Miki ba ko?". A kasalance ta furta "komai yayi fa Allah ya Kara budi ni amma fa gidan Nan tsoro yake bani yayi min yawa". Wata shafa ya yiwa saman cinyarta Yana fadin "Ai kuwa Saida kiyi hakuri duk gidajenki haka suke wasu ma sun fishi girma so nake ku wataya keda yaran mu a Hankali Zaki Saba Kuma me kike tsoro gani gaki ai ta maganar tsoro ta wuce Kuma". A Nan ma Saida ya tsotseta tas sannan suka fito yana rike da hannunta, suna dawowa kasa Baki suka Kara zuwa 'yan uwan momin Kano ne da su Aneesa dole tasa yabar gidan bayan sun gaisa da bakin. Direct gidan Ammi ya wuce a gurin Abbie ya yada zango sun Jima suna Hira kafin ya nufi bangaren Momin Kano suka gaisa sannna ya shiga gurin Hajiya Babba itama ya gaisheta taso ta tsare shi da surutu sai Allah ya taimake shi aka Kira wayarsa ya fice da sauri. Bangaren Amminsa ya nufa Yana shiga parlourn farko yaci karo da su Batool sun Shirya Wai zasu gidansa suka gaishesa Suka wuce, shi Kuma ya shige Yana gaisawa da jama'ar da suke cikin sauran parlours din. Bedroom din Ammi na kasa ya shiga Bata nan sai Hajja da jama'arta wasu nata Shirin tafiya bare yaran cikinsu saboda makaranta da sallama ya shigo,da wani malalacin kallo Hajjar tabi shi Yana gaisawa da Hajja karima 'yar uwar kakansa uwa Daya uba Daya tana Dan tsokanarsa irin na jika da kaka. "Kai kuma me Zan gani haka daka fito gari da wadannan kayan Wai bakasan yanzu ka manyanta bane ba?". Wata dariya ce ta kwace Masa Yana Zama kusa da Hajjar tare da riko hannunta. "kikace menene? To meye laifi Dan na fito a haka su wadannan ba kaya bane?". Harara ta watsa Masa "Dan Allah rufe min Baki Ina wasu Kayan mutunci a Nan gida cike da jama'a Dan ma surukan naka suna can sabon gininka da kayiwa tawaye kaki zama, Dan Allah kaje ka sake wasu kayan kada ka shigar musu a haka da wannan Kayan kamar ka roko". Wata yarinya ce kamar sa'ar su zahrar jikar Hajja karima tace "Haba Hajji ai hakan shine gayu kinsan kudin kayan da suke jikinsa kuwa wallahi saisu saye duk kayan cikin trolley dinki" . "Karbi Nan sa'ada ai Naga kema jirgi Daya ya dauko ku dashi, Kullum Kuna cikin wadannan kayan da aka daukewa Albarka yo ina dalili 'ya'ya kun dauki daba'ar Nasara kun yafa kunce shine gayu". "Kinga tashina Daman zuwa nayi Naga yanda kuka waye". Ya fada yana kokarin tashi daga kusa da ita "Dawo ka zauna ko lafiyar matar taka ai ban tambaya ba ka sakani surutu, to Yaya ita Fatimar ta tashi". "Lfy kalau Alhamdulillahi, tace na gaisheki da kyau idan nazo".. "To Masha Allah haka akeso Allah yayi Albarka a gaisheta ai zamu shiga muga daki kafin mu tafi da yau naso komawa Baban ku ya Hana yace saina kwana biyu na Dade banzo musu Nigeria ba". "Au da tafiya zakiyi ban sallameki ba ai gidana Zan mayar dake sai kin zauna min kamar yanda na zauna Miki harna fadawa Uncle Ishaq ma tun ranar da kukazo ya Kuma amince Dan cewa yayi aike tawa ce duk yanda nayi yayi dai dai, Dan haka keda Hajiya Inna Zan hada ku mu zauna duk kowa ya ramawa kura aniyarta". "Allah ya tsari gatari da Saran shuka ni naje gidanka na Mike kafa na Kama Zama tare da matarka ku ringa min dibar Albarkar da zata sakani na rasa Dan sauran Idona ko?". Baki bude yake kallonta yayin da saura Yan uwa da suka rage a dakin tunda yawanci yaran sun fice. "Meye kuke min wani kallo karya nayi? ko bakuga yanda yake cukumarta a gaban dubban mutane ba to Ina ga daga mu sai shi ai sai yanda ta yuwu Dan daudu a lahira". Dafe Kai mahmud yayi Yana Kara kallon Hajjar ba tare daya iya furta Mata komai ba,wato Hali zanen Dutse halinta Yana Nan ita hands free ce babu abunda ya dameta Saida idan ta fad'a kayi yanda zakayi kawai. "Allah ya bamu Alkhairi ki gaida gida Amma matata bazatazo Miki Niger ba tunda harda bita da kullin Wai zamu kashe Miki Ido". Yayi waje yana Jin tana kiransa yayi gaba, Bai haura sama gurin Ammin ba komawa yayi asalin part dinsa Daya zauna tunda Yana da Kaya a cikin tunda yawanci kayansa na biki a Nan Sameer ya ajesu. Wani yadin filtex brown Mai kyau da tsada ya saka ya dauko agogonsa Omega ya daura ya zuba turarensa ya kafa hula shi kansa sai yaji yes hakan yayi masa daidai, Dan murmushinsa yayi Yana tuno maganar Hajja Wai kayansa kamar na roko. Ficewa yayi daga part din ya koma na Ammi Amma ta baya ya shiga inda ze sadashi da stairs din basai ya koma ta main entrance din ba. Saman ba hayaniya kamar kasan, knocking yayi a kofar bedroom din Ammin Aishat ce ta bude Masa su uku ne a ciki mummy Badi'a ya Fara gaishewa tana tambayarsa Ina 'yarta, sai Amminsa ita kuma Aishat wani signing din da suke sukayiwa guna da👍 alamar jinjina wannan dabi'ar normal sun saba tun suna yara. Wani Dadi ne ya rufe Ammi fuskarta sai annuri yake fita saboda yanda taga Hussein dinta ya Zama babban mutum ko ba'a fada ba kana ganinsa kasan ya samu kwanciyar Hankali. Kan sofa ya zauna kusa da twins sister dinsa yana kallon yanda suka cika dakin da wasu jakunkuna masu hotonsu Shida zahra,. Yayin da Ammi ke hada wasu Kaya a cikin jaka daga gefe da alamar kowa sabgar gabansa yakeyi, rausayar da Kai yayi Yana kallon Ammi wadda itama rabin hankalinta Yana kansa. "Ammi..na". ya Kira sunanta abinda takeyi ta Bari ta bashi full attention dinta tana sauraren meze fada Mata. Dan sosa Kai yayi kafin yace "munga sako jazakumullahu khairan Ammina, kuma naji kince Zaki turo Mata housemaid ko?". "Eh haka nace duk da nasan akwai naka Wanda suke kula da gidan sai Naga ya kamata a Kara Mata wasu daga nan Kuma wannan kukun naka a canza Masa wani aikin ko Kuma ya koma kamfani yaci gaba da aikinsa a can Dan baze yuwu su zauna da ita ba, a yanda matarka take sai kana kula da irin abokanen ma da zaka ringa shigar dasu gidanka gaskiya". "In Sha za'a kiyaye Daman kukun na mayar dashi kamfanin shinkafa dake can kebbi, Kuma inaga basai an Kai Mata Yara ba ki Bata binta kawai saiki taimaka ki kirawo Amminta ta bar Mana Aunty zilai wadda suka zauna a kano Naga Bata da matsala". "Ok babu laifi saina kirata na gane matar itace wadda ta bawa sako ta kawo min Naga alamar kamar ma'aminciyar su ce". Ya Jima a gurin Ammin kafin Aishat ta rakashi suka je suka gaisa da dangin zahrar Wanda suketa Shirin tafiya Dan kayansu ne su Aishat din suke hadawa su za'a bawa Basu Dade ba suka fito a hanyar da zata kaisu parking lot ne Aishat ke fadar "Wai ya zahrar ne da fatan babu wata damuwa a tare da ita?". "Lafiya kalau take kinsan gidan yau zuwa gobe sai a Hankali gidan yanzu na jama'a ne". "Haka ne Kam ai daga Nan har wani lokaci mutane bazasu yanke a gidan Nan ba sai kayi hakuri bare Kai Mai jama'a ai sai abinda ka gani, ni addu'ata Daya kada 'yan matan dake haukar sonka su ringa je Mata gida da sunan kannenka kasan dai baza'a hanasu shiga ba". Wani malalacin murmushi yayi yana kissima wani Abu a zuciyarsa. "Naga kana murmushi ko ba gaskiya na fada ba?". "Gaskiya ce mana amma inaga ba Sai muna garin ba za'a samu matsalar, nifa na takura mutum da gidansa da matarsa Amma ace ya fito yana teto a titi ai kamata yayi yanzu mutum na gida Yana hutawa". "Ai maganinka kenan Dan sweet heart ma ba karamin bekenka ya gani ba, me ka zauna jira kaida matarka saboda wani dalili naka ka Zuba Mata ido kana kallo har tsawon wannan lokacin". Girarsa ta dama ya dan dage Mata kadan "bazaki gane ba komai Yana da dalilin yinsa, we will talk later in Sha Allah, ai kece best friend dina tunda kin kular min da my previous, yanzu zanje muyi sallama da bakin da Sameer ya gayyato min Dan tsabar daukowa Kai jidali ya saka mutane barin harkokinsu suka taho har nan". "Aini Wallahi yayi min dai dai wani ma Be taba zuwa 9ja din ba sai wannan sanadin". Har gurin mota sukaje suna tattaunawa da 'yar uwarsa Saida ya shiga harya tashe ta Aishat tace Masa. "Wai Ina mutanenka na ganka Kai kadai". "Na Basu hutu amma fa kinsan duk da haka su zayyan suna waje Dan Ina fitowa suka dafa min baya nasan bazasu hakura ba". Motar ya harba yayi gaba saida ya fice daga second gate sannna Aishar ta juya ta koma ciki zuciyarta fal farin ciki Dan uwanta ya dawo tare da wata irin haiba da kwarjini ga uwa uba cikar mutuntaka ta aure. ************* Tun bayan fitar mahmud zahra ke karbar Baki Dan ma Allah ya taimaka su Amatu da kannen Aunty safiya sun shigo,su suka ringa ba mutane kayan garar da aka kawo da sauran tarka na plates dasu jugs sai karamar blender ta hannu Mai aiki da batir Wanda ake Masa charge, sai kusan Sha biyu su sajeeda sukazo Ashe suna asibiti da Mama Hameeda ta kirawota tana kuka ta fad'a Mata ita tunda kuma ta Kira oga Sameer ta fad'a Masa shine ya Kira hotel din aka kaita asibiti da yake jiya Mamar saboda tsabar tashin Hankali wadanda aka saukesu a hotel tabi inda Allah ya taimaketa duk yawancinsu mutanensu ne 'yan Azare cikin dare ciwon kirji ya addabeta tamkar zata mutum. Saida safe su Aunty Hasana suka sani abinda ya kawo musu tsaiko kenan a gurin tafiyarsu saboda jirgin karfe Sha Daya zasubi suda tawagar Ummee duk Sameer ne shida su Bashir suketa Kai kawo akan komai, dole sai su Ummeen ne dasu Hajiya kaltume suka nufi Bauchin da Alkawarin su Ummee zasu dawo sokoton kafin su wuce. A gurguje sukayi sallama da zahrar saboda ya Abba da yazo tafiya dasu ita ummansu,zahra ta bawa su sajeeda Kaya da cosmetics kamar me tunda gasu Nan tamkar kamfanin ne a gidan ga wasu can a Azare har Kashi biyu duk na lefenta ne, suna kuka share share suka rabu sai yamma so sai su Aunty Rukayya da Aunty Fateeha suka tafi yayin da Hajiyar makwarari tace suje jikanta ya maidota Bata Gama abinda zatayi ba. Zuwa magariba gidan ya Zama ba kowa daga Binta yarinyar da Ammi ta kawowa Zahra sai wasu yara da Hajiyar kadai. Zahra Ammi ta Kira tace ta fadawa su Aunty zilai kada suyi komai zata aiko da abinci. Bayan magariba kadan Aunty Aishat suka shigo da abincin lokacin Zahra na sama tayi wanka tana shiryawa, wata Riga ash colour ta saka irin ta mutanen Kuwait tayi rolling da veil din sai tayi wani irin kyau Dan yanzu ne kwarjiinin Amarcin yake bayyana a jikinta. Saman Aishat ta haura tabar su Radeeya a kasa,sau Daya tayi knocking zahra ta bada Umarnin shigowa. Suna arba da Aishat zahra ta rugo kamar yarinya ta shige jikinta tana fadin " Aunty Aishat nayi fushi idan ke bazaki zo ba ai saiki bada a kawo min Afnan Mana duk kewarta da dameni tana Ina ne dan Allah?". Kan sofar dake dakin suka zauna Aishat din na fadin "Afnan sunje Usman Dan fodio teaching Hospital dubiya, Inna Maimuna ce ta goyata kinsanta da son yawo". "Su Inna kuma,to waye bashi da lafiya?" "Naji dai suna cewa Mama kinsan ba sanin mutanen nayi ba". " Ayya! haba shi yasa babu Wanda yazo gurina,Saida na gaji na Kira Aunty Hasana Amma kin fada min tayi sai cewa tayi zasuzo suna da wasu uzururruka ne Ashe Mamace jikin yaki Dadi Allah ya Bata lafiya". "Allahumma Amin". Aishat ta fad'a tana kallon zahra, kokonto ne ya darsu a zuciyar Aishat yanda taga zahra na Yan guje guje nan tasan ba'a gamu ba Amma saboda ta tabbatar saita cewa Zahrar. "Dan Allah dauko min turarenki na gani Yana yi min Dadi sosai". Tsam ta miqe Ras ta tafi ta dauko Mata su ta kawo Mata Aishat din ta dauka tana Kara shinshinawa tana kwarzanta kanshin su. Handbag dinta ta dauki ta bude wasu kwalabe ta dauko tana murmushi sai wani kuma Karamin daurin magani a cikin irin ledar da ake zuba tablet a asibiti ta Mika Mata tana fadin "gasu Nan inji mummy Badi'a ta dauko wani turare Mai colour purple tace "Kinga wannna ki shiga toilet ki dan shafa a kirjinki da kasan mararki sai kuma wadannan guda biyun duka jikinki Zaki shafe dasu, wannann kuma ki zuba Madara ki Sha yau da gobe da jibi ya wadatar, Bari na dauko cups na hada Miki". Zahra duk a kunyace take da Aunty Aishat din, ita mamaki take Bata tamkar ba dangin miji ba ita gani takeyi wallahi Kamar Aunty Hasanarta. Aunty Aishat ce ta tashi ta nufi kofa ta fice. Bata Jima ba ta kawo cups da ruwa da farm fresh da Hollandis free mik, Aunty Aishat din da kanta ta hadawa zahra maganinta da Holladia ta Bata ta Shanye, Bata kayan tayi tace ta Adana kada ta Bari ko mahmud ya gani turaren na Mata ne kawai. Kai ta gyada Mata tana Mata godiya, kasa suka sauko tare da Auntyn sai wurin 8:30 mahmud da Sameer suka shigo gidan, Sameer na ganin Hajiyar makwarari yayi turus Yana kallonta cikin madaukakin mamaki. "Yanzu saboda Allah Baki bi su Rukayya ba Kika koma gida? to ko zaman daki zakiyi musu ne? Oh yau Naga ikon Allah gaskiya ko haihuwa tayi Allah bazan kowaki garin nan ba tunda baki iya cin Dan wake Mai yaji ba sai kin fantsama a ido, gaskiya gara da Allah yasa 'ya'yanki maza basa kusa dake da rawar gaban hantsi zaki Hana su wallahi, kawai kizo ki nemi guri ki zaunawa yarinya kina ganin shige da ficenta dan ki hanata watayawa kawai". Tafi da sallallami Hajiyar ta dauka tana fad'in. "Yau Naga abinda ya isheni kaida ba gidanka naje ba ballentana kace nayi maka ba dai dai ba, su an fada maka irin kane zalamamme Wanda baya kauda Ido akan matarsa ai ban mance abinda kukayi min ba Ina zaune kuka kwakume juna kuna tsotse-tsotse ba kunya ba tsoron Allah saini na bar muku gurin, Amma kaga su da yake Allah yasa suna da ta Ido ko hannunta kaga ya rike a gaban mu eyeh?" . mahmud ne ya matso kusa da Hajiyar Yana fadin. "Hajiya barka da dare, Dan Allah rabu da Sameer baya son zaman lafiya ai Nan dai gidana ne idan ma kin amince Zaki zauna har iya rayuwa kiyi zamanki daki ma sai Wanda Kika zaba zaki zauna". "Allah yayi Albarka ko yanzu ka nuna min Kai cikakken d'ane na halak, Daman Kai nake jira ka mayar Dani yau can gidan ku Zan kwana ba gurin Hajiya Inna ba". "Ok Bari na shirya sai muje na kaiki Nima ban shiga ba Nan nayo ya fada Yana nufar stairs da sauri yayin da Aishat tabi bayansa da sauri, Saida suka bacewa ganinsu Hajiyar ta kalli Zahra tana tabe Baki "ke Kuma miji ya dawo Kika nemi gurin Zama kamar wata kud'd'a marar wayo, baki ga ita 'yar uwar tasa ta bishi ba? Maza tashi ki bishi kinji ba'a sake da Lamarin miji". Su Radeeya dai sai dariya suke musu suna daga d'ayan parlourn Dan da alama wannan har tace Hajja Bata iya ba. "Yo ta Ina zata iya binsa kin kasa kin tsare kin hanata sakewa da mijinta". Sameer ya fada a kule. Shiru tayi masa Bata Kara tanka Masa ba. Aishat Bata Jima ba ta sauko tana fadin "Sameer Bari mu wuce mukam Saida safe". Tsam Hajiyar ta Mike muje ki tafi dani kada wannan Mai dacin ran ya kifar Dani a hanya yanda yake cika Yana batsewa baza'a haifi da Mai Ido ba". Har gurin mota Zahrar ta rakasu tana rike da babbar jakar data hadawa Hajiya nata kayan harda na makotanta ta Bata Wanda take ta Kira ana yiwa zahra Allah Sanya Alkhairi, Saida suka wuce ta dawo. Tana dosar kofar Sameer da shi suka fito,Sameer din rike da wasu files a hannunsa shi Kuma Dan gogan yana waya da wani yare Wanda Bata San ko wane yare bane. Rab'awa tayi zata wuce yayi ram da hannunta Yana binta da wani mayen kallo, marairaice Masa tayi tana Masa nuni da oga Sameer Amma ya fuske saima k'ok'arin mannata a jikinsa da yakeyi. Wani killer smile Sameer yayi ya Kara gaba Dan yaga alamar ogan nasa sai a Hankali yau wuni yayi sakarwa kansa ruwa, Saida ya Kare wayar sannan Sameer ya dawo da laptop a hannunsa Mika Masa hannunsa dayan yayi ya saka Masa ita ya juya Yana fadin. "Good night". Motarsa ya fada Yana sakin murmushi, a fili yace "wallahi ka shiga cikin tsarin dai sai yarinyar Nan ta goge maka hadda tas kazo kana sakin layi a gaban mu, Mata! Mata! Hummm ayi dai mu gani". Ya figi motar ya fice daga gidan ai Kamar jiran ya fice mahmud yake yi ya wani juyo da ita Yana faman shinshina jikinta wani irin kamshi yakeji Yana fita daga jikinta Wanda yake bijoro Masa da wani irin feeling na tashin Hankali, hannunsa ko Ina yawo yakeyi a jikinta da kyar ya saurara mata suka shige ciki a daddafe sukaci cus-cus da vegetable soup sai wani nama Mai ruwa-ruwa da yaji spices da seasoning sai tashin kamshi yakeyi, kwanukan da suka Bata ta dauke ta shigar dasu kitchen sannna suka haura sama Yana rungume da abarsa suna shiga ya wuce toilet yayi wanka duk da kafin ya tafi sallar magariba Saida yayi wankan, tana zaune ya fito daure da towel fari sol a kugunsa Yana goge jikinsa da karamin Shima fari ne. Lotion kawai ya shafa ya nufi clothset dinsu ya sako t-shirt Navy blue da trouser milk Mai haske na kamfanin Armani ya nufota Yana zuba kamshinsa na gado, hannu kawai ya Mika Mata ta Kama ta Mike Bai wani Bata lokaci ba ya kashe wutar dakin suka fito ya daddanna wasu numbers suka mufo down stairs. Wani Dan Abu ya Danna Kamar switch din kunna wuta sai gurin ya bude keys ne a gurin masu yawa Daya taga ya dauko har ze kashe wutar kitchen ya juyo motsin mutum sai lokacin suka tuna da yarinyar da Ammi tasa aka kawowa Zahra ita Kuma Aunty zilai su Aishat tabi tace sai an kwana biyu zata dawo duk da haka ta fadawa Ammi bazata ke kwana a can ba. Ita dai ikon Allah take kallo ta kofar Baya suka fice parking lot ya nufa Yana rike da ita har suka karasa gurin motocin tamkar company sayar da motocin ne a gurin wata BMW ya bude saida ya sakata a front seat sannan ya koma ya zagayo ya zauna a seat din driver yayi Bismillah ya tuka suka nufi gate, tun kafin su karaso securityn dake Zaune bude musu gate din horn kawai yayi musu ya fice daga gidan, Saida yayi balance a Kan titi sannan ya Dan juyo Yana kallonta duk kanshinta da Kuma wani fitinanan kamshi duk sun cika motar. A Hankali ya Dora hannunsa a Kan cinyarta Yana shafawa a Hankali Yana kallon fuskarta sama yayo da hannunsa ta Dan zabura tana rike Masa hannu. "Wai bazaki tambayi Ina zamu bane kikayi min shiru kina kallona?". Juya Masa idanunta tayi masu saka shi cikin wani yanayi. "Nasan duk inda zamu gida ne tunda baka da gefe a Nan garin". "Good lallai yarinyar Nan kin Fara sanin DANGEN naki kenan". A Hankali yake tafiyar har suka shigo mabera, Dan kallonsa tayi. "Kaman gidan Hajiya Iya ko?". "Inye lallai kin zama 'yar gari irin wannan saurin fashimta haka? Wato kin gane daga zuwa Daya kawai, Naga alama kwana kadan Zaki Fara nuna min gari nan". Dan murmusawa tayi kawai Horn Daya yayi aka bude Masa ya shige Yana musu fitila sabanin da da yake tsayawa yanzu saboda zahra yasa ya shige kawai. Har kusan Yan madaidaitan steps din kofar shiga part din ya Kai motar, gidan shiru Kamar ba jama'a duk bakin sun wuce Daman yawancin su danginta ne 'yan kwantagora suka sauka a gidan Dan ma ya saka Faruq ya samarwa da wasu dakuna a hotel, to yau kuma ya bada motar DANGE transport ta kwashesu tare da Sha Tara ta arziki ta mayar dasu. Kwantar da kujerarsa yayi yana bin wakar Daya saka ta wata tsohuwar mawakiya 'yar America Brandy a cikin wakarta ta awanna be down, baya gajiya da jinta duk da tsohuwar Waqa ce. Sun jima a ciki yana manne da ita tamkar masu bankwana da juna yayin rakiyar tafiya, Saida ya mula ya mule Dan kansa sannan ya gyara Mata rigarta ya mayar da rolling din ya bude ya fito Yana Jin duk kasala ta rufe shi. wani daga cikin securities din ne ya nufo shi da sauri Yana gaishe shi, key din motar ya Mika Masa sannan ya zagayo ya bude Mata side din da take zaune ya karbi handbag dinta Yana riko hannunta ya fito da ita Bai tsaya ta amsa gaisuwar da wannan security din ke yi Mata ba suka nufi kofar da zata sada ka da main parlour na part din. Numbers ya daddanna as usual irin na kofifin gidansa suka shige, an gyara parlourn tsab tamkar ba'ayi wata hidima a cikinsa ba,ko Ina sai kamshin turarikan wuta da freshnes na daki ke tashi. Steps din da yake sada mutum da bedrooms din gidan ya nufa turus Zahrar tayi tana Masa kallon neman Karin bayani a gurinsa, ganin ya tasarma shiga bedroom din Hajiya Inna yasa taja ta tsaya. "Lafiya?". Ya tambaya. "Ba komai Bari na zauna ka shiga ka fada Mata munzo idan tayi izini saimu shiga Ina ganin Kamar hakan zefi ko?". Kamar zece wani Abu sai Kuma ya fasa ya nufi kofar yayi knocking a hankali. "Waye kuma da tsohon Daren Nan yake taba min kofa salon a Hana mutum barci cikin salama". Jin tana mita Bata Kuma bada izinin shiga ba yasa ya tura kofar ya shiga, a zaune ya ganta tsakiyar gado da casbaha a hannunta, aje casbahar tayi tana Masa kallon mamaki. "Kai Kuma lafiya? Meya futo dakai yanzu da wannan tsohon Daren ka baro yarinyar mutane a wannan gidan naka Mai Kama Dana narasa gaskiya ai wallahi Ina tausayin ta a cikin wannan gidan naka da bakwa lissafi kuke yin abu". Zama yayi yana Dan kishingidawa kusa da ita. "Maida wukar tare muke da ita cewa tayi nazo na Fara fada Miki kafin ta shigo ta gaisheki". Rike Baki tayi tana kakabin abun. "Wai Kai Dan Allah sai yaushe zaka girma ne? Duka yaushe akayi Daren da shashshawa zata Bata, yanzu Dan rashin mafadi shine ka Fara gwada Mata halinka na rashin Zama guri Daya ka jajibota da tsohon dare kuka rufo, idan Dan a gausheni ne Baga salula ba a kirani Mana sai an biyo dare da 'yar mutane, Naga alama ma haka Nan kake reto da ita baka da katabus". "Meye kuma wani katabus ?". "Ban sani ba Ni jeka ka shigo da ita ka barta ita kadai tunda ka fasa min dangi ka koresu Basu shirya tafiya ba ni na rasa wannan k'ark'abu mutum yana nasa gidan Amma ya hana na wasu su saka su sude sauran ma ka turasu hotel Kamar wasu 'yan bariki". "Gida dai namu ne nida ke Dole a barmu mu wataya Ina son samun hutu ne a gidan ba Dole na sallami kowa ba a barmu mu sake". "Ungu nan". Ta watsa masa yatsunta biyar. Bai bi ta kanta ba shiga daurewa kawai ya keyi abinda ke bijiro masa nema yake yafi karfin tunaninsa. Tare suka shigo dakin da sallma Zahra ta shigo ta Dan tsuguna jikin gadon tana fadin "Hajiya Inna Ina yini?". " Lafiya kalau zahara'u Kuna lafya dai ko? Ya Kuma bakunta? Taso ki zauna kusa Dani kinji ki daina wannan tsugun Nan bashi da ma'ana gurin 'ya mace". Kafin ta yunkura ta tashi yayi wuf ya dagota ya zaunar kusa da Hajiyar Yana fadin. "To Hajiya gata Nan na kawo ta Daman nayi Miki alkwarin bazan dawo ba saida ita to gata Nan itace ba wata ba yanzu Abu Daya ya rage Ina fatan kin tuna yanda mukayi dake a ranar da nabar gida". Wani kallo take masa na neman Karin bayani. "Wai me kake fada ne wace maganar mukayi da Kaine ni ba wani tunawa zanyi ba nasan dai maganar ita zahara'un dai tunda Kullum saika tisa min Kamar karatu". "Ok good tunda shi Bai sille ba saura ma Zaki tuna sun a sannu". Bed side locker dinta ya janyo ya dauki wani Abu ya zura a cikin aljihun trouser dinsa Yana Jin tana fadin "Meye ka daukar min a Nan?'. "Abinda na ajene na dauki kayana". Taso mu tafi ya mikawa Zahra hannuwansa duka biyun saita noke tana kauda kai. "Allah ya shirya wato wannan barin gidan babu abinda ka koyo sai rashin ta Ido, a gabana kake neman kwakume yarinya ba kunya Kota sisin kwabo". "Haba wlh kina da matsala hannunta fa Zan Kama ta tashi shine zakice Wai Ina kwakumarta haba Dan Allah to Wai ba matata bace ne?". Tsam Zahra tayi ta ta zuro kafarta taga idan ta tsaya sai su Bata kunya ba banza tunda taga da alama tasa tayi kaura ko Kuma da dalilinsa nayin hakan. "Hajiya Saida safe". Zahrar ta fad'a tana fucewa daga dakin ba tare data tsaya sauraren abinda Hajiyar zata fada ba. "Allah ya kaimu kinji yarinyar kirki Mai Alkunya, Dan Allah kada ka lalata musu 'ya da rashin ta Ido kaga dai da alamar ita Bata da dabi'ar yaran zamanin Nan, kuje ka mayar da ita gida Dan Allah kada ka Kara fito da ita a Nan kusa sai abun ya Zama na magana tunda Amarya ce".. ""A'a mun Dade da abata kune dai take bakuwa a gurinku". "Eh duk da hakan dai Amma ko me zaka fada Amarya ce dai". Ze Kara magana ta daga Masa hannu "idan ka bawa Allah da manzo daraja ka wuce ku tafi dare nayi Ni Naga abinda ya isheni ka dauko yarinya daga gida ba gaira da Dan dalili kayi ta zuba Kamar tsohon famfon Daya lalace". Har Zahra ta sauko cikin parlour tana mamakin yanda mahmud yake zuba zance, duk Ina miskilancin nasa yake? Ashe haka yake zuba zance idan yaso.Yana fitowa ya karaso inda take yana rike da handbag dinta, dagota yayi gaba dayanta ya shigar da ita jikinsa Yana sauke numfashi ta bude Baki zatayi magana ya hade bakinsu guri Daya ya zura hannunsa cikin rigarta Yana kaiwa da kawowa, ita fa yau ganinsa take Kamar wani mayunwacin zakin Daya samu nama dasun kebe ze Fara yamutsata. Saida tsayuwar ta nemi ta gagare su sannan ya saurara Mata suna sauke numfashi a jajjere, tana jikinsa tayi lif ya nufi wata kofa ya dauko key ya bude Sai gasu a wata baranda Mai kama data gidan da suka zauna a sultan road sai dai wannan tafi waccen yawan filawoyi da karancin haske, wani part suka nufa data gani a rufe ya nufa yana ta layi Kamar Wanda ya bugu da kayan maye. Suna shiga ciki zahra ta raina sauran gidajen data shiga wani irin parlour ne na Alfarma Wanda ya lashi millions of naira da gani anyi shi ne na musamman Basu zauna ba suka ratsa biyu irinsa sai dai banbancin kayan cikin ya tattaka steps ya Haye suka shige wani corridor Wanda aka kwatashi da wasu irin filawoyi masu azabar kyau sai wani irin sanyi da kamshi yake tashi a ciki ga wasu filawoyi an Zuba a kasan siririn carpet da akayi yi Masa hoto qananun heart a jiki,bedroom na farko ya saka hannu ya saka wasu numbers a jikin kofar take ta bada wani sound tare da wani slow music na larabawa da yayi welcoming dinsu, suna suka Kai cikin dakin Zahra ta wani zabura tana kwalalo idanu waje Kamar zasu fado kasa Dan tsabar mamakin abinda ta gani, da wani irin mamaki take kallonsa wani irin k'ayataccen smile yake sakar Mata Wanda ya karawa fuskarsa wani irin kyau da annuri na musamman, a hankali ya Fara matsowa kusa da ita Yana Mata irin kallon dake rikita Mata lissafi Wanda yake hanata sakat tun a wancen lokacin da yake hanata zuwa gaida Baba malam."are you surprised?". Kai kawai ta iya gyada Masa, Dan da gaske ya kashe ta mamakinsa ba kadan ba. "Dai dai kunnenta yayi magana Yana Dan rage tsawonsa "kada kiyi mamakin komai tunda Allah ya hadani dake nake bibiyarki tamkar rai da ajali, Kinga gadon Nan tun ranar da Kika ambata yayi Miki Ina ace naki ne, a ranar duk abinda ke cikin show room din ma Bai kwana a kasar ba Sameer ya aunosu Nigeria amma fa a under probability Dan harna fadawa Sameer ya bawa Abba matsayin gudunmawa ta kunyarsu kawai.Ashe duk juyin da akeyi wannan garar tawa ce". Ya fada Yana Dan Jan cheeks dinta a hankali, kamota yayi ya nufi gadon da ita sai walainiya yakeyi ga wasu haske masu bada kaloli sai haskesu sujeyi a tsakiyar gadon an zuba wasu flowers masu kyau anyi zanen heart sai sunnan ta daga tsakiyar heart din, zaunar da ita yayi Yana kallonta. "Alhamdulillahi bini'imatihi titummus salihat, precious na godewa Allah Daya bani ke a matsayin matar Aure badan tsimina ko dabarata ba sai Dan Rahamarsa wadda Bata karewa ga bayinsa gani a gabanki ki daure ki bani dukkan farin ciki nima na samu nutsuwa kamar saura mazaje ki tallafi rayuwata da dubun Alkhairinki kinji precious". Ya fada Yana zame veil din da tayi rolling, dago kanta tayi tana kallonsa da narkakkun idanunta Wanda suka canza launi itama maganama ta kasa furta masa ko da harafi Daya ne da gaske ya kasheta da mamakinsa. Zip din rigar ya zuge a hankali ya Fara kasa da ita farar bra din data saka ta bayyana sai Kuma wannan mayen kamshin ya cika Masa hanci Wanda tunda ya shaqa a jikinta ya Fara bijiro masa da wani irin feeling Wanda Bai taba jinsa ba to gashi yanzu bashi da shamaki dashi jikansa har rawa yake ya Fara Bata hot kisses tare da bin jikinta Yana mata wata irin shafa wadda ta gigita duniyar ta Saida ya cire Mata duk wani d'ar dake zuciyarta a Kan sex Dan ba karya yasan takan bida mutuniyar tun a baya dole take sallama Masa to bare yau da aka saka ta baza turaren birkito fitina Dan takanas ta Kano mummy Badi'a ta taho dashi daga katsinan maradi da sukaje wani wani biki taji ana zancensu shine ta siya saboda bikin autarsu da za'ayi, to Kuma saiga maganar mahmud din ta taso shine ta watsosu a jaka da nufin idan taga yarinyar tana da sanin ya kamata saita Bata tunda Ammin ta dan fada Mata marainiya ce gaba da baya to tasan wasu irinsu sai a hankali,to sai Kuma ta tarar da fiye da abinda masu iyayen a raye zasu Samu a tare da yarinyar dadin dad'awa ga nutsuwa ga kyau da kunya,sai taji gara ta Bata ta Kama mijinta a hannu taga yanda 'yan Mata ke farautarsa to gara a gyara can din yanda za'a cire Masa duk wani shaukin mace gaba Daya. Da zafi zafi yake sattafata Dan da gaske ya kasa controlling din kansa duk ya gigice sai abubuwa yake Mata Wanda sun girmi karamar kwakwalwarta, Daya bayan Daya ya ringa cire kayan jikinta Yana jefarwa a Nan, Shima nasa ya shiga jefarwa a wahalce, ya taba wani guri jikin gadon hasken ya ragu sannna wani Abu kamar net yayi musu runfa tare da feso musu turare mai tsadedden kamshi blanket ya janyo ya tufesu Yana cigaba da ruda Mata jiki sai Nishi take fitarwa a jajjere ta rasa inda zata Kama, Bata San lokacin Daya kamo kansa ba tana shafawa a hankali, ita kanta mamakin kanta da kanta take yanzu babu wannan mahaukacin tsoron da yake cika Mata zuciya. Saida ya tabbatar babu sauran kwari da shakkarsa da tsoro a jikinta ta ladaftu iya ladaftuwa, sannna ba zato taji Yana jero addu'ar da Annabi Alaihis Salam yayi koyi da akayi idan za'a kusanci iyali, sai lokacin ta Dan dawo hayyacinta Amma bature yana ce, It is too late to cry. Gadan gadan ya doshi hanyar wani iri tsuma jikinta ya Kama tana Kiran sunansa tana masa magiyar ya Bari, amma yayi nisa a duniyar da Bai taba shiga ba ko tunanin da akwai irinta ba shi kansa abin neman fin qarfinsa yake baya gane yaren da take Masa ko kadan Jin kukan nata da magiya sai kiran Ammah take ba k'ak'k'autawa ji yake kamar tana Kara Masa azama ne da shaukin abinda yakeyi, Jin zata raunana Masa zuciya yasa ya hade bakinsu guri Daya sai ruwan hawayene ke ambakiya Yana gudu a kumatunta. Sam bayaji baya gani shi kansa a rikice yake ga wani irin tsumar sanyi da jikinsa ya Fara lokacin daya samu kansa, a hankali ya mirgina gefenta Yana sauke numfashi da sauri da sauri ga wani Zazzabi Daya taso masa lokaci daya. Da kyar ya iya janyo jikinsa ya rungumo ta jikinsa sai yaji jikin ya saki tamkar Bata da rai, ai Nan da Nan ya kunna hasken daya gauraye dakin jikinsa na Kara daukar rawar sanyin, abunda ya Fara gani shiya daga Masa hankali, Bai San lokacin daya dauketa ba cak ya nufi toilet da ita ya sakata cikin bathtub ya sakar musu rawa a kansu Yana jijjigata tare da Kiran sunanta a kidime Yana fadin. "Sorry! Precious I am very sorry ki tashi bazan karaba pls". Saida ruwan ya ratsata ta saki wata ajiyar zuciya tare da sakin siririn kuka tana Kiran "Ammah! Wayyo Ammah Kice Masa ya Bari Dan Allah". Dagota yayi ze sakata a jikinsa ta saka wani uban Kara tana rike shi tare da fadin. "Wayyo Allah na ciwoooo.... Zafi nakeji". "Ya Salam!!!". Ya fada cikin tashin hankali, kirjinta ya kalla yaga yayi wani irin ja. Saida ya sakata a ruwan zafi sau kusan uku sannan yayi wankan ibada har lokacin Zazzabi ne a jikinsa sosai Amma ganin yanda nata jikin yake sai yaji nasa shafar Mai ne da kyar ta iya wankan ya daukota, akan sofa ya kwantar da ita daga ita sai towel a jikinta hawaye kuwa ba'a magana sai sauke ajiyar zuciya take. Bedsheet din gadon ya yaye yaje ya jefa a washing machine ya dawo, duk ya rude ya rasa Yaya zeyi da ita ba zato ya tsinkayo Kiran sallar farko. Shima ga Zazzabi ya rufe shi sosai. *_ AUREN HUCE HAUSHI_* AISHAT ISAH MUSAH (Maman Fateemah) 09061432330 08055362975 Page 86. ........... Da kyar ya lallabata sukayi sallah sai kananun koke-koke take masa, cak ya daukota ya Dora a gadon Yana cire mata hijab din daya saka mata, cikin jikinsa ya sakata yana Dan shafa bayanta a hankali tana ta sauke ajiyar zuciya, duk ta dagula masa lissafi Dan shi kansa dauriya ce kawai kada ayi haihuwar guzuma 'ya kwance uwa kwance, dan zazzabin jikinsa Shima k'aruwa yakeyi, sunanta ya Kira very softly,Bata amsa ba sai Kara shiga jikinsa da tayi tana Dan rawar sanyi tare da rik'e hannunsa tana cije lips dinta na kasa "Pls... precious forgive me,you make me lose my control, iam so lucky to have you... Precious you're special, i love every part of you, every time with you is specia I love you.. Ilove you with all my heart.. Kiran Daya shigo wayarsa shiya dakatar dashi daga abinda yayi niyyar fada. "Kizo Dan Allah Ina mabera sabon parta din Nan, da fatan Kinga text message dina?". "Eh na gani gamu munzo da doctor zainab din Saida na biya na daukota motarta ce taqi tashi". "Ok, ku shigo kawai kofar a bude take". Rigar jikinta ya gyara Mata, sannan ya tattare gashin ya saka masa band ya hade shi a tsakiya ya sakeshi baya. Kalamansa sun tsaya Mata a zuciyarta, mamakinsa ya girmama a gurinta idan ta kalleshi sai taga Kamar bashi bane totally ya canza mata, wani sabon Mahmud take gani ba ainishin wanda ta sani ba. Suna daf da karasawa kofar da zata sada ka da babban parlourn suka tsinkayo muryar Hajiya Inna tana fadin. "Kai su wanene haka da asubar fari suka shigo min gida babu sanarwa? me zakuyi a Nan? to babu kowa a cikinsa da kuka nufa kuna ta sauri Kamar masu amsa Kiran fada, ai Ina Jin karan shigowar mota na leko Naga kun nufo Nan yasa na fito bansan mahalukin Daya bude min kofar bama" .ta karasa fada tana kusanto su Aishat din. Dr zainab ce ta gaisheta, sai lokacin ta gane doctor din tunda itace family doctor dinsu. "A'a likita lafiya Kika zo Mana da sanyin asuba nan Ina ga kinyi makuwa kuwa ai Nan babu kowa kinibibin ne yasa aka gina shi kawai Dan fariya, yo inba fariya ba yaushe za'a kashe irin wanan dukiya a banza". Aishat ce ta matso tana fadin. "Dan Allah Inna ki koma ki kwanta mune ba wasu baqin Ido ba, zamu shigo gurinki yanzu wani uziri ne ya kawo mu, doctor Bismillah". Tsaye Hajiya innar tayi tana kallon Aishar tana ayyana wani Abu a cikin ranta. "Shatu, waye babu lafiya a gidan nawa Wanda ni ban sani ba saike da kike wata unguwar Kika sani?". "Dan Allah ki barta muje daga baya nayi Miki bayani". Ta nufi kofar doctor zainab na biye da ita da sauri, ai itama hajiya Bata tsaya neman wata maganar ba ta rufa musu baya tana fadin. "Muje Naga ikon Allah, tunda abun ya Zama na Qumbiya-Qumbiya Kuma". Suna shiga dukkansu Saida suka girgiza da ganin yanda aka qawata part din ba qananun kudi aka narkar ba a cikinsa, cikin corridor din ta nufa Kamar yanda ya fada Mata a hankali tayi knocking daga ciki ya Basu Umarnin shigowa. "Masha Allah!!" Abinda bakinsu furta kenan lokacin da suka shiga da sallama, saboda babu Qarya ko Mai hassadar mutum saiya yaba bedroom din Nan, suna Kan gadon tana jikinsa, da sauri Hajiya Inna ta natso tana fadin "me Zan gani Mahmudu? Daman Baku tafi ba a nan kuka kwana? Ikon Allah meya sameta Naga lfy-lfy mukayi sallama daku". Dan dafe kansa yayi Wanda ke Sara Masa, ya dago idanunsa Yana kallon Aishat da alamar tuhuma a cikinsu. Basarwa tayi tasan dai maganar Daya ce meyasa ta tado Hajiya Inna, ita Kuma tasan karambaninta ne yasa ta fito Kuma tasan ba komawa zatayi ba shi yasa ta rabu da ita kawai. Doctor ce ta matsa suna gaisawa da Mahmud Wanda har lokacin kanzil Bai cewa Hajiya Inna ba. "Lfy kalau doctor". Ya amsa gaisuwar,Zahra kuwa lif tayi ta rufe idanunta Kamar me barci Dan ji tayi bazata iya hada Ido da Hajiyar ba. 'Yallabai ku dan bamu guri na dubata ko". Kanta ya zame daga kan cinyarsa ya mike Yana fadin "ok doctor Dan Allah a dubata sosai jikinta yayi zafi da yawa, muje ki fada min meya fito dake yanzu da sanyin asubar nan?". Ya riko hannaun Hajiya ji tayi Shima nasa jikin yayi mugun zafi. "Yo ai kaima ba lafiyar gareka ba, yau Naga abinda ya isheni,Ina cikin gida Amma ka kasa fada mini meye amfanina kenan? Maza lalubo min Babanka ya turo likita ya duba min Kai yaushe za'a zauna da ciwo a jiki". Suna ficewa Aishat ta karaso kusa da Zahra ta zauna wadda har lokacin idanunta a rufe suke. "Sannu zahra, ki tashi nasan idonki biyu ga doctor tazo ta dubaki kinji". Rinannun idanunta ta bude ta kalli Auntyn Nan da Nan taji idanunta sun kicciko. "Aunty Aishat Dan Allah kirawo min Aunty Hasana". Sai hawaye sharrrr... Suka biyo kumatunta. Hannunta farare sol Aunty Aishat ta rike tana girgiza Mata Kai. "Pls ki daina kuka gashi Nan za'a dubaki". Kanta kawai ta iya gyada Mata. Tashi Aishat din tayi tana fadin "doctor Bari Naga bros". Tayi waje tare da ja musu kofar tana Jin tausayin zahra da gani Bai saurara Mata ta ko kadan. "Sannu Daughter kinji Bari na duba na gani sai asan abinda za'ayi Miki, hands glove ta saka ta umarci zahrar ta gyara ta dubata. Jikinta tsima ya Kama da kyar ta Bari doctor zainab din ta dubata cikin ikon Allah Bata karu ba sai dai gurin Kam sai a hankali, dan Allah ya taimaketa jikinta irin roba din Nan ne Wanda ko haihuwa masu irin jikin sukayi Basu fiye budewa ba, jikin ba gautsi, a cikin Mata dari da wuya ka fitar da goma masu irin wannan halittar. Ruwan zafi ta shiga ta hada Mata da kanta ta sakata tana hawaye tana komai, Saida ya canza Mata sau uku cikin ikon Allah sai taji jikin Yayi Mata Dadi fitowa doctor din tayi zahrar tayi wanka ta fito simple Riga ta Bata ta saka sannan ta leka ya fad'awa Aishat ta hado Mata tea Kofi daya ta koma a kitchen din bangaren ta hado saboda babu abinda babu a ciki. Tea me kauri sosai ta hado Mata a gefen gado ta Samu zahrar tana Zaune yayin da doctor ke hada wasu allurai. Hajiya Inna ce keta fada akan Mahmud yaki Kira Mata Abbie dinsa ya Kuma Hana Aishat ta kirawo Mata shi. "Dan Allah ki tashi ki koma Zan Sha magani kawai, nifa lafiya ta kalau kawai dai bana Jin Dadi ne". Cikin hukuncin Allah saiga kira ya shigo wayarta alamar mota data gani tasan Mustapha ne da sauri ta dauka Kota Kan sallamar da yake Mata Bata bi ba ballentana ta Sami zarafin amsawa. "Kanaji na Mustapha maza ka taho da likita gidana tunda Aliyu baya gari ya duba min Dan biyu gashi Nan Zazzabi Yayi Masa rigijib ko daga Kai baya iyawa" . Ta kashe wayar, Baki bude Mahmud yabi Hajiya Inna da kallon mamaki Wai ko Kai baya iya dagawa "ikon Allah". Can Kuma uncle Mustapha suna tare da Abbie tun bayan da aka fito masallaci suke Zaune a harabar masallacin suna hirar zumunci shine uncle Mustapha ya Kira Hajiya ta tambayeta ko akwai abinda ze taho Mata dashi Dan daga Nan can gidanta ya nufa. Yayansa ya kalla Wanda shima shi yake kallon domin wayar a speaker take. "Ikon Allah meya Kai Mahmud kuma gidanta shida ga gidansa can, ko Kuma da yaji ciwon ne ya tafi can kasan shida ita tasu Bata baci". Uncle Mustapha ya fada. "To waya sani ka Kira doctor Anka sai ku hadu a can ya duba shi". Sallama sukayi Abbie ya nufi cikin gidan Yana kokarin Kiran Ammi, yayin da uncle shima ya nufi motarsa ya shiga Yana kokarin lalubo number doctor Anka din. Allurai kusan Kashi uku ta yiwa zahra wadda Saida Aunty Aishat ta riketa akayi Mata sannan ta Bata Analgesic table ta Sha ta bawa Zahra wani tube na cream tace ta shafa a can da Kuma Kan breast dinta inda shima ya dade, ta Kuma jaddada Mata shiga ruwan zafi Kamar sau biyu kafin dare Dan yanda gurin yayi sai a hankali kawai Dan ma dai Tana cikin Wanda ubangiji Yayi musu special gift da labarin ba wannan akeyi ba. Tare da Aishat suka fito suna Nan second parlour shida Hajiya innar sallama tayi musu tana fadin "yallabai in ganka mana". "A'a babu inda zaya shima ba lafiyar ce dashi ba,ko meye Fadi Masa a gabana ai ba kunyata yakeji ba tunda ya tsallake gidansa yazo gidana ya taki matarsa ai shikenan Daman ya fada min". 'kai! Hajiya you have a lot problem wallahi, doctor muje gaskiya kina da damuwa wallahi". Yayi gaba ya nufi parlourn farko. "Yo saika Hana na fada ba haka ka fada min ba?". Ita dai Aishat Bata tanka musu ba, tasan sunfi kusa koka shiga kaji kunya bare ita da ba inuwa daya suke Sha ba. Godiya sosai Mahmud ya yiwa doctor zainab din a Nan take fada Masa ya Dan d'agawa zahrar kafa zuwa two to three days haka Dan ma Allah yasa babu ciwo masu yawa. Key din mota ya mikawa Aishat ta Bata tana parking lot sannan yace ta bawa Aishat account number. Godiya take Masa Kamar zata zube masa a Qasa yi take tana karawa Kamar zata Ari baki, itama Aishat din ta tayata yi Masa godiyar, komawa Yayi ciki kawai shi baiga wani abun yiwa irin wannan godiyar ba. A sabuwar motarta doctor zainab ta koma murna kamar me Dan tasan wata Rahama ce ubangiji Yayi Mata, motarta tafi kwanan wata biyu tana fama da ita yanzu haka tana Kan cinikin wata motar jira kawai take a Bata adashenta ta Saida tata ta hada kudin ta tura musu a kawo Mata motar Sai gashi cikin hukuncin Allah da sanyin safiya tayi Gam da katar da motar da Nan kusa Bata tab'a tunanin mallakar mota irinta ba ta millions of naira. Direct bedroom din ya wuce ji yake kamar ya cire mata ciwon daga jikinta, lokaci bayan lokaci Yana sakin smile shi kadai, mamaki yake yi Wai Daman haka lamarin yake ya tsaya Yana cutar da kansa a banza ai da yasan haka ne da gara yayi tun tuni yayi kaffarar rantsuwar a wuce gurin, Bai samu Hajiya a parlourn ba. A ciki ya sameta tana waya a yanda ya fuskanta da Ammi take wayar Dan lafazinta na karshe Daya tsinkaya ji Yayi tana fadin "yauwa turo min da ita Badi'a din tazo da Kayan biqin amaren". "Ilahiy wa Rabbi" ya furta hankali yau ya jawowa kansa barbade Ina maganar privacy a wannan lamari kuma. Gurin zahrar ya karasa Yana Mata wani duban kasa-kasa dan ji Yayi wani Abu na sama yawo duk da Zazzabin dake nukurkusarsa, zama Yayi Yana Kai hannunsa wuyanta. "Are you okay?". Kai ta gyada Mata sexy eyes din ta Nan da Nan sukayi narai-narai da hawaye.baiya wata wata ba ya rungumo kayansa Yana fadin "pls kiyi hakuri Zaki warke na daina kinji my previous". Baiyi aune ba ya jiyo salatin Hajiya Inna a kansa fadi take tana karawa. "Muhammadu Rasulullahi me Zan gani ni Hadiza, Shatu duba min Nan Dan Allah Anya abokin tagwitakar taki ne kuwa?". Ta jefawa Aishat tambaya wadda ta shigo daga raka doctor zainab. "Wannan Kuma ai tsakanin ku ni me zance kiyi hakuri Bata da lafiya ne shi yasa Amma ai badan rashin kunya yayi ba". Kokarin kwace kanta zahrar take itama wallahi Batasan ya akayi ba ta yarda suka manne juna, Amma Yayi musursisi yaki sakinta. "To Inna ya kike son nayi kukan fa zatayi". "To wayace ka jankwalo tsiyar aida saika cigaba da saka Mata Ido tunda abinda ka zaba kenan". Runtse idanunsa Yayi dole ma Yayi hijira daga gidan Nan Ashe martch ya tarowa kansa Bai sani ba. Kiran uncle Mustapha ne ya shigo wayarta Hajiya Innar. "Yauwa ku shigo sabon gurin Nan da aka Gina Dan fariya". Ta yanke Kiran ya juyo tana fadin saika taso idan ka Gama shafe ta kana neman ka lalata yarinya ai Daman tun jiya kake Mata kyarkyara". A parlourn farko suka zauna, Mahmud na gaba Hajiyar na baya tana kananun maganganu. Hannu ya bawa su uncle suka gaisa sannan ya zauna, gaishe da Hajiyar sukayi lokacin tana Zama kusa da Mahmud din. "Likita Dan Allah duba min shi Zazzabi yakeyi duk karfin hali ne kawai yakeyi Amma jikin kamar wuta yake". "To Hajiya za'ayi abinda ya kamata in sha Allah". Zafin jikinsa ya auna tare da 'yan tambayoyi doctor Ankan yayi Masa, Allura ya bashi tare da 'yan magunguna, doctorn ya jima Yana mamkin Mahmud a yanda Allah ya hore Masa dukiya da kananun shekaru ba qaramin mamakinsa Yayi ba, ace yau shine Karon farkon saninsa da mace to Ina isalin labarin Daya dunga yaduwa game dashi?. Lokacin da uncle Mustaphan yazo rako doctor ne uncle saminu shima ya shigo gidan da tasa motar kusan wannan dabi'ar su ce duk safiya suna zuwa suga yanda tsihuwarsu ta kwana. Kusa dasu yayin parking ya fito Yana fadin . "Lafiya doctor na ganka a gidan Nan da sanyin safiya?". Dariya doctor Anka yayi Yana Mika Masa hannu sukayi musabiha sannan sukayi da Uncle Mustapha. "Jarimin kamilin danku nazo na duba" "Wa kenan?". "Mahmud Mana kasan yawanci ko namiji matukar ba mazinaci bane to duk ranar Daya Fara sanin mace sai kaga ya Samu irin su Zazzabi haka da abinda baza'a rasa ba na bakon yanayin da aka samu Kai kai a cikinsa to shima hakance ta kasance wannan shine first time Daya Fara sanin mace a rayuwarsa, gaskiya na sarawa kamewarsa Allah ya taimaki 'yan baya muma ya tsare Mana namu iyalin". "Allahumma Amin ya Rabbi". Tunda doctor ya Fara Kora bayani uncle Mustapha ke yiwa Dan uwansa wani kallo na yau dai an Kama kyafa a tarko Dan shine agent na yad'a Mahmud mazinacine shiya Kama shi da kansa harda shedar hotuna a waya. Uncle Mustapha baiyi kasa a gwiwa ba ya jefawa doctor Anka tqmbaya. "Shin doctor Dan Allah irin wannan Condition din da akan shiga ga sabon shigar Tarawa da iyali shin sau nawa ake iya samun Kai a wannan yanayin?". "Sau daya ne saboda abinda jiki Bai taba jinsa bane daga haka gaskiya ba'a qara shiga irinsa". "Ok thank you very much doctor sai munyi waya". Ya karasa gurin motarsa ya wuce da dunbun mamakin young rich Guy din Nan abinda Bai taba kawowa ko a mafarki bane ace Yana da irin wannan kamewar. Wani duban kaji kunya uncle Mustapha ya yiwa uncle saminu ya wuce ya koma bangaren Muhmud tunda acan ya baro Hajiyar. Tunda Ammi suka Gama waya da Hajiya inna taji wani irin farin ciki ya rufeta fadi take. "Alhamdulillahi! Alhamdulillahi!! Alhamdulillahi!! Allah na gode maka ko yanzu ka wanke min yarona daga zargin Zina ga matarsa ta sunna ma ya dauke Mata Kai tsawon lokaci bare har a jefe shi da kazafin Zina harda cikin shege. Wato wannan 'ya'yan sai a kyalesu wato 'yar uwarsa ya Kira tazo ta kula Masa da matarsa. Wani murmushi tayi tana fitowa zuwa dakin dasu mummy Badi'ar suke, ta labarta mata yanda sukayi da Hajiya Inna, babu b'ata lokaci Mummy bada'ar ta shirya ta dauki duk abunda zatayi Mata amfani dashi suka nufi gidan Hajiya innar tare da Aunty Hasana duk da yau suketa shirin barin garin tunda likitoci sun tabbatar da Bazasu sallami Mama ba sai sun Gama duk abinda ya kamata Dan da gaske ciwon zuciya Yana barazanar kamata shine Mahmud ya Hana a sallameta har Abba ya Kira ya nemi izinin barinta ta warware a nan. Duk hankalin Aunty Hasanar a tashe Dan lokacin da Aishat din ta kirata kafin doctor tace Mata zahrar nata sharbar kuka. Ranar Nan dai kusan yini sukayi da ita Tasha gashin ruwan magunguna gurin mummy Badi'a Dan tsaye tayi a Kan zahra Saida taga yes ta aminta da gurin sannan ta koma,dahuwar Naman rabo Mai kayan maganin bikin amare Ammi tayo Mata da kanta. Zahra ta kirawo Ammah tana Mata kuka shagwaba Wai tace Mahmud ya dawo da ita Azare ita bazata iya Zama a Nan tare dashi ba. Dan murmushi kawai Ammar tayi tasan wasa kenan dama da baisanta ba ya dauko abinsa ya taho da ita to bare yanzu da Mai rabota da wannan garin sai Allah,itama da Dade tana mamakin halin dattako da kawaici irin na yaron. Amma saita lallabata da dadin bakin tayi hakuri zuwa gaba sai Abbanta yayi magana. *AUREN HUCE HAUSHI* AISHAT ISAH MUSAH Maman Fateemah. 09062432330 _Page 87. _________ Sai kusan magariba sannan Aunty Hasana tayi haramar tafiya lokacin suna parlour a zauna su biyu kadai,dan zahrar taji sauki sosai sai dai tafiyar ce sai a hankali take yinta, Kara matsowa Aunty Hasanar tayi kusa da zahra ta gyara Zama tana Mata kallon Kai tsaye. "Kina jina abinda nakeso dake ki kwantar da hankalinki ki nutsu ki aje duk wata shiririta ki fuskanci rayuwa,yanzu kin hau wani stage na girma ki kula da mijinki ba Kada ki bada fuskar da wata zata shiga gabanki a gurinsa ki Zama Mai yuriya a gurin biyan bukatarsa kada ki yarda ya gane Baki da juriya tanan zaku iya samun baraka Mai girma, ki tsaya ki nutsu ki fashimci a wane rukuni mijin naki yake sai kisan yanda Zaki bida kayanki, Kinga yaro ne karami yanzu ne yake Kan ganiyarsa sai kin dage da bashi kilawa sosai gaskiya". Ta Jima tana koya Mata dabarun Kama miji a hannu da yanda zata kame iyayensa, idan Auntyn ta Fadi wani abun kunya take kama zahrar sai taga Kamar ba Aunty Hasanar bace. Saida sukayi sallah sannan zahra ta raka Aunty Hasanar bangaren Hajiya Inna ta kofar baya inda suka hade da part dinta. "A'a wa nake gani kamar zahara'u?". Hajiya Inna ta fada bakinta yaki rufuwa da gani tana cikin farin cikin ganinta ta taka da kafafunta ba kamar dazu ba. Murmushi zahra tayi itama tana kawar da Kai, Dan da gaske kunyarta take ji ba kadan ba, tunda ya Gama Mata tonon silili Kuma ita meta Samu na k'ararwa. Zahra taso ta tsuguna ta gaishe da Hajiya Inna Amma ba hali dole tayi Mata me spring kawai. Sun gaisa da Aunty Hasana sannan ta fada Mata zata tafi driven Daya kawota yana hanya. "Sannu 'yan biyu kinji, Allah yabar zumunci ai naji shi mijin nata na fadin jirgin safe zakubi ko?".. "Eh haka ne in Sha Allah Dan ma jikin Mama ai da tun a washe gari zamu juya to sai lalura ta gitta dole anan zamu barta tunda yayarta tazo dazu ga Kuma Hameeda itama zata zauna tunda sunyi hutu last week". "Allah ya bada lafiya ya tsare hanya, akwai sakonki naba magajiya ta Kai can sai ki Kara tsaraba". Godiya sosai sukayi Mata suka nufi kofar fita ta gaba. Sun daf da fita hajiya Inna ta Kira sunan zahar tsayawa tayi tare da juyowa ta Fara kokarin dawowa. "A'a kuje ki rakata sai ki dawo ta Nan din". "To". Ta fada suka ida ficewa Saida suka gangare steps din a hankali sannan Zahra ta dubi Aunty Hasana. "Yanzu Ashe gobe zaku tafi Amma Baki fada min ba da saidai na wayi gari naji kun wuce". Ta fad'a tana Shirin zubar da hawaye. "A'a ai kinsan bazan bar garin Nan banzo na ganki ba,to saboda waye nazo garin Banda shirirta irin taki ai kema kinsan hakan baze yuwu ba, shi yasa na wuni a gurinki yau, kuma ai zamu dawo da Ammah taga irin daular da Allah ya kawo diyarta ciki, wlh Zahra Lamarin mijinki yafi karfin tunanina na rasa abinda ya kaishi Azare Mai irin wannan mahaukaciyar dukiyar ace ya jure Zama a shagon kofar gida, dubi wannan part din tunda uwata ta haifeni ban taba ganin gado irinsa ba wallahi, ga can gidan Aljannar duniya,Zahra ki Kara godewa Allah Dan wannan Rahamarsa ce ba tsumin mu ba ba Kuma dabararta mu ba, mu dai mun Kaiwa ubangiji kukan mu akan matsakolinki mun nemi sauki da sauyin Alkhairi a gurinsa, to babu abinda zame sai muce Alhamdulillahi Allah ya Qarawa Annabi daraja lallai dogaro ga Allah jari ne, duk Wanda ya dogara ga Allah ya isar Masa". "Haka ne Aunty Nima fa abinsa Yana bani tsoro kinsan abinda ya bawa sajeeda kuwa ranar da aka kaini iPhone ce da cheque na two millions, ko wacce kuma aka Bata waya da five hundred thousand, Dan Allah Aunty waye shi?". "Ikon Allah Wai mace ke tambayar waye mijinta a gurin wani, mu yanzu ai kece Mai bamu wannan amsar Kuma". Kafin Zahra ta Fadi wani Abu sukaga an bude gate wata hamshaqiyar mota ta shigo, suna Nan tsaye harta karaso kusa dasu Sameer ne ya fito daga seat din driver,sai kuma shi uban tafiyar ya fito daga Daya side din kananun Kaya ne a jikina sai yayi Mata wani fresh dashi, sai dai Kamar ya Dan fada kadan. Gaishe da Aunty Hassanar sukayi kafin mahmud yace wa Zahra. "Ga Sameer Nan shine ze mayar da Aunty gida bana son tukin malam salmanu da dare gaskiya ya fiye gudu sosai, Sam baya duba a cikin gari yake, Aunty Allah ya tsare sai mun shigo in Sha Allah". Oga Sameer din yace "madam an wuni lafiya? Ya bakunta kuma?". "Alhamdulillahi oga Sameer yasu d'ana sukaje gida?". "Lafiya kalau d'azu ta kirani take fada min ta Kira wayarki a rufe". "Eh wlh Zan kirata anjima" Ta fada a takaice Hannuwan Aunty Hasana Zahrar ta kama ta rike tana narke fuska. "Yanzu Aunty tafiya zakiyi ki barni a Nan ni kadai ba kowa kusa dani?". "Ikon Allah to baga zilai ba Ina cewa Ammi ta Kira Ammah ta nemi abar Miki ita, ko Kuna nawa auren Zan baro nazo na tare a gidanki? Banda lalurar Mama ma data gitta ai da mun tsufa a gida, kiyi hakuri na fada Miki kwanan Nan zamu dawo da Ammah fa". Rungume Auntyn tayi ta saki kuka cikin kukan take fadar "Dan Allah ki Kara min ko sati Daya ne bani fa da lafiya". Mahmud ne ya Dan matso ya rabata da jikin Aunty Hasaanar Yana fadin "kuje kawai Aunty halin zatayi miki'. Dan zumboro Baki da hawaye sharaf a idanunta tayi tana Masa wani duba Wanda saura kadan yayi abun kunya a gaban suruka. Tana ganin Sun yin ribas ta fada jikinsa tana sakin Dan sirirn kukan shagwaba,cak ya dauketa ganin gurin ba kowa yayi gaba da ita, Bai sauketa a ko Ina ba sai a bedroom dinta Kan sofa Yayi musu masauki yana fadin " Guduna kikeyi ko precious?". Girgiza Kai tayi alamar a'a. "To fada min me nayi Miki kike son ki gudu daga garin Nan kibi Auntyn?". "Ba kamoi fa, Ina son Naga Ammah ne". "Kice na tattara na biki, ni Kuma yanzu ai sai yanda kikayi Dani yanda Kika bude min sabon babin rayuwar nan,Wai Daman Dan Allah haka abun Nan yake Kika kyaleni Ina ta bulayi da faman Shan magani? k'afata k'afarki duk inda Zan shiga a duniyar Nan Wallahi bazan iya twenty four hours ban jiki a jikina ba sai a samu matsala, fada min Dan Allah Wai menene sirrin yau though out ni sai a hankali fa gashi doctor tayi Mana tsakani Wai sai anyi two days bamu had'u ba". Ya Kai hannunsa Yana shafa abinda yafi tsone Masa idonu a Hankali. Hannunsa ta rike tana kara narkewa a jikinsa tare da Dan kukan kissa sabanin na rabuwa da Aunty Hasaanar. " Plsss.... meu Amor ka.....Bari da ciwo fa har yanzu zafi suke". "Ya salam! Bari na duba har can din na gani, sorry SHADI I am very sorry nayi laifi ko? Ni kaina lokacin bana gane komai Allah yayi Miki Albarka ya bamu zuri'a masu Albarka, kin Gama min komai a rayuwa kin bani abinda ban tab'a samunsa ba, kin bani farin cikin da mafarkina da hasashena Basu taba hasaso min akwai irinsa a cikin duniyar nan ba, Dan Allah fada min duk abunda kike bukata a cikin duniyar nan matukar akwai sa zan Nemo Miki In Sha Allah". Ya Gama fada Yana kokarin zuge zip din gaban rigar data saka Mai Dan balance wadda bazata ringa takuta Mata ba saboda ba karya taking jiki a kaijin Nan nata. Tana a'a Saida ya duba ya gani Nan da Nan hankalinsa ya tashi. "Previoussss! Haka gurin Nan ya kumbura gara muje muga consultant na bangaren". "Ni fa yanzu babu ciwon sosai Kuma ai kumburin ma babu a Kan dazu, Kuna ai an bani magunguna ma Kuma Ammah ma ta turowa Aunty Hassana wasu Kuma an sawo su d'azu suma na Sha kawai ka Bari basai munje ko'ina ba". Rigar ya gyara Mata duk jikinsa a sanyaye, Yana zargin kansa da nuna Mata karfin da yayi, Amma Kuma Shima abin ne ya wuce tunaninsa ya kasa controlling din kansa. Kiran insha'i da Kiran wayar Hajiya Inna lokaci Daya ya shigo kunnensu zip din rigar ya gyara Mata sannan ya daga Kiran Hajiyar. "Wai Ina zahara'un ne daga Rakiya Kuma sai naji shiru? To tazo maza yanzu nasa anyi mata irin abincin daya kamata taci Kuma taje dakina ta kwana kafin ta samu lafiya Dan Naga ba iya kawar da Kai kukeyi ba 'ya'yan zamani". Wata munafukar dariya ce ta kubce Masa Yana jinjina karfin halin Hajiyar, tab dole ya tattara su Kama gabansu so take tasa' yayi kwanan tsaye kenan ai shifa yaga guri Yana jin ko tafiya zatayi baze iya barinta tayi kwanaki ba Dan saiya zauce gaskiya. "Wai bakaji abinda na fada bane kayi kunnen uwar shegu dani". "Naji Mana ai bama gidan ne, mun wuce tun dazu mun koma sai dai idan daukoki zansa ayi ku kwana tare a Nan din". Ya fada Yana Dan Jan cheeks dinta yana kashe Mata ido daya tare da dage Mata gira Daya. "A'a Allah ya tsari gatari da Saran shuka ai shikenan Daman gata ne Zanyi muku tunda kun gano ba haka ba ki cinye junan ku ai jiki magayi ba'a kwacewa yaro garma ga gurin Nan Bari ba shegiya bace da ubanta, gashi Nan za'a kawo Mata abinda nasa akayi Mata idan kaga dama ka Bari tayi amfani dashi taci kuma abincin idan kuma ka Hana duk Daya Wai makafi sunyi dare,duk Wanda Rai ze yiwa dad'i ai ba Kamar me Shiba".kit ta kashe Kiran. "Subhanallahi! Allah ya kawo mu kiji min tsohuwa da Hana ruwa gudu, Bari naje masallaci na dawo mu wuce bazan iya da rigimarta ba gara mu Kara gaba kafin ta Kira Abbie yace nayi wani abun". ******* Cikin galabaita Salma ta dubi wadda ke tare da ita a asibiti. "Dan Allah kirowo min nurse din Nan tazo ta dubuta min maganin ciwon baya da mara wallahi ciwo suoe Kamar zasu fita". Tsaki tayi matar Mai suna Saude, tana gadin "ba dole kiji jiki ba Ina cewa da hankalinki da komai Kika biyewa wannan gantaellen yaron Nan kuka dunga badala shi namiji ai ba abin kunya gare shi ba tunda bashi da tabo mace kuwa? Ina Jin baya garin ma ya wuce warri inda yake aikin kamfani ya barki da wahal ga kin rasa martabarta ta har abada,'. Tunda matar tafara mata magana Salma ke kuka tayi Dana sani yafi cikin kwando. Ga mahaifinta da wane Ido zata kalleshi Ranar da yaji wannan.abun data aikata, ga Mama ciwo Yana can Yana ta nukurkusarta a garin mutane,sai kawai ta fashe da kuka Mai Jinyar tata Dan haushi kasa bata hakuri tayi ta wuce Abinta ta nufi Kiran nurse din tana fadin "ba dai bin maza Kika zaba ba bakiga komai ba wallahi yarinya babu abunda Kika nema Kika rasa Amma kin biyewa wani sakarai Wanda Bai San inda yake Masa ciwo ba. *_ AUREN HUCE HAUSHI_* AISHAT ISAH MUSAH Maman Fateemah. 09061432330 08055362975 DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINQAI SALATI DA DAUKAKA DA AMINCI SU QARA TABBATA GA SHUGABAN MU FIYAYYAN HALITTA ANNABIN RAHAMA MUHAMMAD S.W.W.W DA ALAYANSA DASAHABBANSA WANDA SUKA BISHI DA SALIHAN BAYI HAR ZUWA RANAR TASHIN ALQIYAMA AMIN. Muna rokon ubangiji s.w.a ya Dora mu Kan dai dai abinda mukayi na kuskure ubangiji ka yafe Mana Dan isar Manzon Allah s.a.w.w Domi shine Mai gafara Mai jinqai. Page. 88 ________Cikin shigar Atamfa super Riga half bubu da straight siket sai gyale blue black Dan madaidaici kalar touching din ganyen jikin Atamfar ta zuba turarenta Mai sanyin kamshi, a hankali cikin nutsuwa ta ratsa parlours din ta nufi kofar ficewa daga bangaren, haka Nan taji bazata iya biye Masa ba su yiwa Hajiya Inna irin wannan rashin kirkin ba, gara taje Kamar yanda ta umarceta idan ta biyewa drama dinsu sai taji kunya a banza ba abin mamaki bane su tarar ta rigasu zuwa can din to gara ta yiwa tubkar hanci kawai. Katin data gani a jikin wani da dan abu a jikin bangon kofar ta dauka ta zura a kofar ta bude ta fice, har lokacin gidan shiru duk da ba wani dare ne yayi ba,yanzu ba dadewa aka idar da sallar insha'i. Ta cikin barandar Nan da tayi linking da part din Innar tayi amfani da kofar wadda har lokacin ba'a rufe da key ba ta shiga, kafin ta karasa taji Hajiyar na fadin "magajiya hada Mata da wand'ancan kafafun shanun na cikin freezer saita ringa dafa Masa a can nasan tunda yace ya tafi tafiyar zeyi baya magana biyu, Daman ai kinibibi ne yasa ya kinkimo yarinya ya kawo min ita tunda shi baya jaffarar rantsuwa, Kuma ki ... Sallamar Zahra cikin siririyar murya ita ta katse Mata hanzarin abinda zata fad'a. "Wa'alaiki Salam warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu, yau Naga shegantaka ni Hadiza Ashe Kuna Nan ya tadani tsaye da tsohon dare yace min kun wuce gida?". Dan murmusawa Zahra tayi kafin tace "muna Nan fa kawai ya fada ne Dan ya zolayeki, ya fita sallah ne lokacin da Kika Kira Yana cikin gidan Nan". "To qaraso ki zauna muyi magana Daman bana son Yana kusa kinsan ba hakuri gare shi ba akan abinda yasan Yana da gaskiya". Har kusa da ita ta qarasa ta zauna a Kan carpet tana gaishe da Innar. "Tashi ki zauna Nan kusa Dani dan mi Zaki zauna a Qasa akul na gara ganin haka, Nan gidan jama'a ne kada ki Kara yin haka mijinki yaro ne Amma ba karamin mutum bane,Dan Tani babu komai kishiya ce ki dai ringa yiwa iyayensa haka Amma Banda ni kada kiji nauyina ki sake Dani Kamar yanda yake sakewa dani baya boye min komai sai rigimar suce kawai nasan yaqi fada min asalin abin Shima Kuma gajen hakuri nayi na yanke Masa hanzari badan nayi haka ba da Ina tunani babu Inda ze tafi harna tsawon lokaci Nan to mutum Bai isa ya goge qaddararsa ba, haka rubutaccen al'amarin yake Sai hakuri gashi kuma ya wuce har abada in Sha Allah, kina jina ki yiwa mijinki biyayya zakiga Nan gaba yaja Miki layi da wasu mutanen a cikin danginsa to ki bishi da yanda yake so saboda nasan kome za'ayi baze Kara Hulda da wasu ba sai da gaisuwar musulunci da zumunci Amma babu mu'amala irin ta da Kuma bazan Hana ba Dan an Bata Masa kwarai da gaske, kuma Banda yarda da kowa a cikin dangi ki Zama Mai kamewa a gurin ci da Sha kinji ki nutsu ki gane Ina kowa ya dosa kafin ki yarda da kowa, akwai Yara irin ki da wadanda suka d'ara ki babu adadi a cikin dangin kowa kuma zeyo chaaa a kanki to kiyi taka tsan-tsan da kowa, duk Wanda yazo ki karbe shi da girma Amma kada ki yarda da raini a gurin ko way kuwa,ai kinji abinda na fada Miki ko?". "Eh naji Hajiya na gode in Sha Allah Zan kula". "Yauwa haka nake so Bari kici abincin da ze gyaraki da wuri tunda su mazan naku ba masu kauda Kai bane duk nasara sun Bata su". Mukus Zahra tayi Dan da alama Inna irin hands free din Nan ne ba ruwanta komai ma saita fada ita. Magajiya ta saka ta ciro Kayan abincin daga cikin basket din tasa ta shimfida table mat a Nan kusa dasu aka kawo abincin. Sauka ki zuba Mana zahara'u Nima tayaki cin zanyi, ba musu ta tashi ta sauka ba bude babbar warmer tuwon dawa ne kaura Mai kyau sosai irin 'yar katsina din Nan sai miyar kuka wadda taji kayan kamshi da Naman rago sai yajin daddawa da pure man shanu, Zahra na ganin abincin ya tuna Mata da mubi kusan haka abincin Inna mainuna yake. "Matso da wancen kwanon ki Zubar ki Fara cinsa so nake yabi Miki jiki ko kin warware da wuri,Ni Miko min ruwan can da silver na wanke hannu na". Saida Hajiya Inna ta matsawa Zahra ta ci dahuwar kusan rabinsa sannan ta kyaleta tace taci tuwon Shima,Dan kad'an ta zuba Hajiyar Ba tayi Mata korafi ba tasan cikinta ze iya cika Amma ta matsa ta zuba yajin da man shanun sosai a cikin miyar tana cikin cin tuwon ya shigo da sallama da alama ita yake nema dan har wani ajiyar zuciya yayi. A hankali yake takowa har inda suke zauna idonsa Yana Kan Zahra, ita Kuma Hajiya Inna nata idon na kansa tana kallon ikon Allah Dan tamkar ya cinyeta danya yake kallonta. "Kai Kuma lafiya irin wannan kallon qurillah ai har ka gano muninta haba". "Me Kika Bata Naga tana jibi a goshinta duk A/Cn dake aiki?" Wani kallon baka da wayo tayi Masa "abinda nanu iyayen suka bamu a rin wannan lokacin na Bata ba dai ka kawo min ita ba ai kayi Mai wahalar". Zama yayi musa da Zahra Yana Kai hannunsa a goshinta ya Dan shafo gumin. "Kinga fa Hajiya". Ya nuna Mata tafin hannunsa, na gani hakan ai shi nake son gani Daman,gashi Nan Idan zakaci ta zuba maka Idan bashi kake so ba kaje ga naka can a Kan tebirin nasara kaci". "A'a ai kowa yabi tunda taci ai nima dole naci". Hannunsa ya wanke ya saka cikin abinci Zahrar, Loma Daya yayi da kyar ya hadiyeta saboda yaji. "Haba Hajiya kinji kuwa abincin nan? Previous maza cire hannunki ai sai ciwo ya kamata kisani a uku". "Ungo nan, ita ai wannan babu abinda ze Mata sai gyara". "A'a abar shi gaskiya da matsala" ya fada Yana wanke hannunsa. Kallonsa Zahra take duk ya gigice ita fa bataji wani yaji ba tana tunanin abinda taci ne yasa gumin ke tsatsatowa Dan ta Fara Jin can kasanta daga cikin Kamar ana hada wani Abu sai wani Abu takeji. "Ikon Allah na kwance ya fad'i to Kai Daman Ina ruwan biri da gada kaje kaci nake ita ta fada maka bazata iya ci ba Ina ganin idan Allah ya kawo haihuwa Dole ka kawo min ita Nan in dai Allah ya ara Mana numfashin". Gaba yayi baice komai ba ya nufi dining ya zauna,lokacin Zahrar ta ida cinye Dan sauran Daya rage tana wanke hannunsa. "Tashi kije ki bashi abinci, ni Zan shiga daga ciki da safe magajiya zata kawo Miki kayayyakin dana aka hada Miki ki kula da kanki sosai su maza da Kika gansu ba hakuri ke garesu ba bare wannan miskilin Daya shafawa idonds kwallin rashin ta Ido baya Jin komai Dan Ina guri cewa fa yayi ko daukoni za'ayi naje gidan ku mu kwana, to kuwa ba karamin aikinsa bane yayi abinda zesa na fita da gudu, nasan tunda ya ambata tafiyar zakuyi". "Kai Hajiya Dan Allah na kwana a Nan din Mana". "Keni rabi da kinibibi ku Kama gabanku, nagode hakan ma duk da raddi ne ya mayar min". "Dan tagwaye mu kwana lfy na shiga ciki a rufe min kofata ta baya tunda Kaine me abin budewanda rufewar". Tayi gaba abinda. "Allah ya tashemu lafiya". Ya fada tana daddanna wayar hannunsa da alama Abu Mai mashimmanci yake turawa. Kujerar daura dashi ta janyo zata zauna ya janyota ya zaunar a cinyarsa Yana fadin. "Me yasa kikayi min haka keda a gabanki nace Mata bama gidan shine Kika since min zani a kasuwa ko?". Yana kwanto da kansa saitin wuyanta wannan kamshi Mai sakashi a cikin wani yanayi yaji Yana shigar masa hanci. "Ina tambayarki kinyi shiru". Wayar ya aje Kan table din da Alama ya Gama tura sakon, duka hannunsa ya saka ya zayayo ta saman cikinta ya Kara kwantar da kansa sosai a gefen wayan nata Yana Dan hura Mata iska kadan a gefen fuskarta. "Ba komai kawai dai gani nayi nace Mata Zan dawo ne kaga bazataji dad'i ba idan ban dawo ba". Dan lakuce cheeks dinta yayi "Mai wayo kawai,bani abinci naci mu tafi barci nakeji'. Shima tuwon semovita ne da miyar agushi. "Barshi bazanci ba". Dago da kanta tayi ta kalleshi, Kai ya gyada Mata yana mik'ewa da ita tsaye. "Muje ki bani coffee kawai, ji nayi Shima Kamar yajin zanji". Ya riko hannunta suka gangaro parlour. Ta bayan suka fice ya rufe kofar suka wuce. Mai makon taga sun nufi part din da sukayi masauki Wanda ya zamar Mata wani gurin tarihi a cikin babin rayuwarta, sai taga ya nufi wata motar da akayi parking dai dai karshen barandar. "Ina kuma zamu?". "Inda mukafi wayo ai Nan Kuma aikinsa ya Kare sai dai Idan munyi tafiya mun dawo to Nan ne farkon sauka haka tsarin yake Nan ne kashen sallama Kuma farkon sauka". "To muje na dauko kayana Naga Kai baka barin a dauki komai Idan ka tashi kawai gaba kakeyi baka daukar komai Ni kuma da magunguna a ciki". "Cool down shadi, harda turarikan dake hanani sakat na dauko ai ba'a Wasa da garin gona, Fad'a min wai waye ya baki wadannan turarikan ne?". "Ance kada na fad'a maka fa". "Kai! harda sirrin da Zaki boye min yanzu precious? Ni fa na Gama ganin karshen sirrin?. Ya Dan shafi wani guri. "Wash!!! ka Bari Dan Allah, wallahi da ciwooo har yanzu. Kuma turarikan Aunty Aishat ce ta kawo min su fa tace mummy Badi'a ce ta taho min dasu". Baki ya bude ya kasa magana, babbar magana wato su Mata basa girma wallahi, Bai Kara ce Mata komai ba suka nufi motar. Shiya bude Mata ta zauna sannan ya zagayo gurin driver ya zauna. Suna fita taga ya dauki wata hanyar Dan kallonsa yayi. "Ina zamu kuma Naga ka biyo ta wata hanyar?". "Very good, gaskiya kina da sharp brain in some days kin Fara gane Kan garin nan, to Nan bypass ce zamu bi". Sunyi nisa Zahrar ke nuna Masa wata mota a bayansu wadda take binsu sauda kafa Kuma taki wucewa. Hannunta dake cikin nasa ya Dan qara matsewa. "Kina tsoron kada ayi kidnapping dinki sunga kalar da za'a karbi dollars ko?" a tsora ce da dube shi "Da gaske kenan ana yin abin Nan ga garin nan?". "Of course ana yinsa sai dai in Sha Allah kina da kariyar da babu Wanda ze iya cimmiki ta zahiri data badini, wannan motar su zayyan ne a cikinta da Shirin Kota kwana shine Babban guard dina Yana tare da yaransa ne na zahiri kenan, kinsan wasu sun wuce mu suna gabanmu kosu zayyan din Basu San da zamansu ba, wasu Kuma suna bayan su zayyan din ai kin gane, ko ke kadai ce Kika fito to ki qaddara team kusan uku suna biye dake duk inda Zaki shiga kuwa ba mazan ba ba matan ba". "Mata Kuma?'. Kai ya gyada Mata alamar haka ne "kina mamakin hakan ne?". "Eh gani nayi aikin maza ne wannan'. Saida ya shiga wata kwana sannan yace Mata. "Ai kuwa Mata suna bada gudunmawa sossi a cikin aikin DSS sunyi abinda mazan basuyi ba gurin Kama criminals sai da aikin akwai risky a cikinsa sosai gaskiya" .har suka shiga unguwar tasu ta mawadata Yana yi Mata bayanin irin gudunmawar da Mata ke badawa. Lokacin da suka shiga ciki shiru gidan ba motsin kowa Amma ko Ina neat sai kamshi ke tashi da sanyi mai nutsuwa. Hade jikinsu yayi Yana Kara shinshinarta. "Previous da sauki ko? Tunda Naga tafiyar ta Dan gyaru muje kiji dani wallahi a matse nake dake?". Bai jira amsar ta ba yayi sama da ita ya nufi stairs. Kuka take Masa ba k'ak'k'autawa shi kansa ya rasa dalilinsa na koma Mata duk da itama ta bada goyon baya kafin yayo famin Daya ruda Mata lissafi, Tasha sambatu kamar ze zauce yau dai da Bata Suma ma taji abinda ya girmi kunnuwanta Albarka kuwa har Amminta yau Tasha ta saboda jiya baze iya karar da komai ba Amma na yau yayi abin cikin hankali da nutsuwa yaji wani bakon lamari tunda itama ta taka rawar gani kafin labarin yasha banban Amma dai taji jiki saida yayi ta faman ban Baki da lallashi saboda Kuka wiwi ta rirrik'e shi tana yinsa ga Daman ya lafiyar kura. ******** Karfe goma Mai kyau Abba ya sauka a sokota shida Hamza da Abdul Hakeem,. Sameer ne yaje airport ya dauko su direct asibitin suka nufa, lokacin da sukaje dakin likitan bayan Nan yaje round duba patient dinsa basufi minti biyar ba doctorn ya dawo office hannu sukayi dasu Alhaji Jafar tunda ya gansu da Sameer yasan mijin matar can ne patient din DANGE. Tare suka shiga ciki Saida suka zauna sannan doctor din ya cire glass din dake idonsa ya dubi Sameer Yana fadin . "Alhaji ne mijin patient din tamu?'. "Eh shine doctor kuma sirikinku shine mahaifin ita wife dinsa". "Ah haba dai?". "In Sha Allah haka yake". Wata gaisuwar ya Kara yiwa Alhajin Yana fadin . "Ai Dange abokina ne tare mukayi karatu a UK dashi sannu da hanya, to Alhaji Yaya akayi ciwon zuciya yaso yayi karfi a jikina Hajiya Dan yanzu haka zuciyar a kubure take Dan ma anyi Mata allurai Kuma Sameer yaje Abuja jiya ya kawo magunguna tunda mu a nan sun yanke mana, Kuma muna bukatarsu emergency, gaskiya ka zauna da ita a tambayeta me yake damunta da yayi cussing din irin wannan ciwon lokaci Daya Dan da alama da abinda ya tada Mata da hankali ba zato din, yanzu Shawara Daya ce akwai wani asibiti a Egypt suna da consultant cardiologist a can ya kamata a tarbi abun gaskiya". Wani gumi ne ya tsaststafowa Hamza yasan duk abinda ya samu Mama Yana damfare da matsalar Salma sai Kuma abinda yake Mata fada a kansa ta daurawa Kai wahala akan Zahra bare Kuma da tazo taga irin daular da Allah yabawa yarinyar yasan harda wannan damuwar. ' Mun gode kwarai da gaske doctor,yanzu ka bamu address din asibitin kawai idan Allah ya yarda a cikin week din Nan sai muyi komai mu tafi" Alhaji Jafar din ya fada cikin damuwa ya rasa me Rabi'a keso a wannan' rayuwar dai dai kwarkwado tana cikin rufin asirin Allah yasan ko banza bazata rasa kadara da zuzzurutun kudi sama da millions of naira ba tunda duk alherin daya samu matansa suna da kaso Mai tsoka a ciki. "A'a Abba ai an Gama komai tun jiya yanzu visa muke jira naso na shiga Azaren yau sai Kuma Abdul Hakeem yace min Kuna Nan zuwa yau koma Mahmud ban fadawa ba zuwan nake saboda jiyan dare yayi". "A'a doctor bani address maza yaushe za'ayi haka na Zama uban banza kenan,ni fatana a rike min uwata da mutumci bawai na Zama Mai idon cin naira bane, nagarta na duba naba shi bansan shi ba a lokacin duk da da wuya a fadi sunansa a fadin k'asar Nan ace ba'a San shi ba, hotunansa dake yawo da Kuma a social media da banbanci kwarar da gaske da yanayin da muka same a ciki shi babu Hadi ko Daya shi yasa bamu fashimta ba, kuyi hakuri mun gode da wannan hidimar da akayi ma ta wadatar Allah ya saka da Alkhairi". Duk yanda Sameer yaso Abban ya fahimce shi ya nuna Sam baza"ayi hakan ba, doctor din ya Basu full address na asibitin da tsare-tsarensu duka sukayi godiya sosai suka fito Sameer yayi musu jagora zuwa dakin da aka kwantar da Mamar lokacin da suka shiga tana barki sai su Aunty Hassana da suka shigo su ganta ita da Inna mainuna su duba jikin nata kafin su tafi, sunyi mamakin ganin Abba dasu Hamza tunda ba Wanda suka fadawa sai Sameer duba da duka yaushe suka bar garin. Gaban gadon Abban ya tsaya Yana warewa mamar kallo fuskarta da kafafunta sun kumbura harda hannuwanta, gurin sun Aunty Hassana Abban ya juyo Yana gaishe da Inna mainuna ita Kuma ta jajanta Masa lalurar Mamar. "Ina Hameeda da Salman suke ya jefawa Aunty Hassana tambayar dai dai lokacin da Aunty ladi ke shigowa yayar Mama. Duk Saida daburce batayi zaton ganinsa a garin ba a irin wannan lokacin. Cikin alamun rashin gaskiya ta Fara fadin "Alhaji kune a hanyar haka sannu da zuwa, Ina kwana?". "Lafiy kalau ya Mai jikin?". Jikinta da sauki gashi har tana iya barci". Hameeda ce ta shigo da sallama da tea flasks da basket na abincin da aka kawo da dare jiya tasan ana daf da kawo na safe shi yasa ta tafi ta wanko kayan. "Lah Abba sannu da zuwa Ina kwana? "Lafiya kalau Hameeda ya Mai jikin kuma? Ina Salma take ku hada kayanku gida zamu tafi flight din karfe biyu zamu bi". ,Ya Abudul, ya Hamza Ina kwanan ku?". "Lfy kalau ya Mai jikin". "Da sauki, Abba naji kana maganar Ina Aunty Salma ai batazo Nan ba". Hamza Abban nasu ya kalla kallon tuhuma. Cikin kaushin murye yace. "Shin abinda magaji ya fada min da gaske ne Rabi'a tasa ka fita da Salma da Asuba ta kofar baya tana kuka?" *_ AUREN HUCE HAUSHI _* AISHAT ISAH MUSAH. Maman Fateemah. 09051432330 Or 08055362975 *Page 89. _________Cikin kid'ima Hamza ya fara rantse-rantsen babu ruwansa ganin da sameer a dakin yasa inna maimuna yin magana. "Dan Allah Alhaji a bar maganar nan sai an koma gida nan garin mutane ne ga mai lalura tayar da maganar a gabanta baze haifar da d'a mai ido ba, ayi hakuri abi komai a sannu sai Allah yayi magani ko menene". Cikin wani irin bacin rai Alhajin yace " shi kenan inna Allah ya kaimu gidan lafiya". "Yauwa Amin ai hakan yafi". Zuru-zuru Aunty laran tayi tasan idan ta tashi ba karamin ruwa aka ballo mata ba. Da sasarfa Abban ya wuce yabar dakin su sameer suka rufa masa baya, gefe sameer ya koma ya kira Mahmud Wanda lokacin suka tashi daga barci tun bayan idar da sallarsu ta asuba suka koma yana kara lallashinta da kasheta da kalaman soyayyarsa. Zahra na jikinsa kiran sameer din ya shigo ita ta miko masa wayar. Kiran ya daga yana fadin " ya akayi?". "Abban madam ne ya shigo tun wurin ten shida su Abdul Hakeem da Hamza, Amma fa yace maganar fita da Hajiyar mubar zancen biya shi ze dauki nauyin komai abunda akayi a nan ma Ala amfana". Tashi zahra tayi tunda taji duk taji abunda suke fada . " meu amor wai Abban ne yazo garin nan bai nemeni ba? wallahi yanzu Abba ya yayeni baya yi dani". Sai hawaye wasu na bin wasu, wayarta ta dauko ta shiga Neman Ya Abdul Hakeem cikin ikon Allah ta same shi yana dagawa ta fara masa kuka tana fadin "yanzu ya Abdul Hakeem har Abbna yazo garin nan Amma akaqi a fada min nazo na Ganshi tunda shi bazezo yaga inda nake ba kodan ni basu Hameeda bane..."? saita karasa sakin kukan sosai ta jefar da wayar a kan gado. Janyota Mahmud yayi jikinsa yana fadin " Haba precious meye haka Mike fada akan Abbanki kada na qara jin magana mai kama da ita daga bakinki ai Abba bai cancanci haka ba gurin marar lafiya yazo keda ba cewa akayi yabar garin ba, idan ma baizo nan ba ina cewa shiya kaiki dakinki na Azare wancen ai shine farilla na nan kuwa ai tsabar bidi'a ce kawai tashi muje na gasaki da kyau kada muje gurin Abban kina ware kafa ya gane yarinyar tasa ta girma gara idan tukuicin ya fita kowa ya gani ko ba haka bane?" Ya fada yana dauke tears din dake gangarowa da harshensa, jin ze saki layi yasa tayi saurin barin jikinsa tana cije lips dinta saboda zogin da takeji. "Haba Ya Mahmud kaifa malami ne ina ruwanka da irin wannan sabgar karfa dan malam yaqi halin malam naga abun nake fa Yaya ba sauki wai ka manta nifa yarinya ce" Dariya ta bashi wallahi yarinyar nan 'yar duniya ce tun Daren jiya ta Dame shi da wani Yayan shegantaka. Tashi yayi shima suka shiga wanka saida ya qara hada mata ruwan zafi ta shiga sannan sukayi wankan suka fito yana maqale da ita, shiya shafeta da lotion yanayi yana mata dan abinda baza'a rasa ba, ya saka hand dryer ya busar mata da gashin kanta ya gyara shi tsab, ita mamaki yake bata idan taga ya zage yana irin wannan abun kamar ba shi ba. Clotset suka shiga ta saka Riga abaya 'yar dubai shi yayi mata rolling shi kuma ya saka wani wagambari fari tas, lokacin da suka fito har breakfast yazo daga gidan Ammi tunda ta Hana ayi musu a nan duk da jiya binta ta Dawo da gamma tunda bayan sun wuce da dare yayi waya da laminu daya daga cikin masu gadin gidan ya fadawa Tanimu ya kai yarinyar gida tunda 'yar gari ce washe gari da gamma sai ya koma ya daukota. Suna saukowa Abincin ya zama ready yarinyar da alama ta horu da iya aiki, abinci ne kusan kala hudu sai ruwan tea mai hadin su na'a na'a dasu lemon grass da kayan kamshi. A plate daya ta zuba musu cheeps din sai kuma pepper soup din zabbi da fattira ta zuba musu black tea din. ****** Tunda Abdul Hakeem ya fara waya hankalin Abban ke Kansa saida ya sauke wayar Abban yaga yana bata rai ne ya tambaye shi. "Me Uwar ta fada maka daya bata maka rai nan da nan haka?" "Rabu da ita kawai Abba, shirme zata yiwa mutane wai fa kuka ta kama dan an fada mata ka shigo garin, duka da yaushe mukazo da zata fara yiwa mutane halin nata ita batasan ta gima ba, abu kad'an kuka kamar wata baby, ai yanzu kuma sai dai yaranta suyi wannan abun". Dan murmushi Abban yayi. " yi hakuri Abdul maza kirawo min ita ". Tana ganin kiran Ya Abdul Hakeem din tayi saurin dauka tana fadin. " Ya Abdul Hakeem zakuzo dan Allah ". " Ba Abdul bane uwata nine ki kwantar da hankalinki gamu nan, bawa mijinki wayar na fada masa". "To Abbana na gode". Ta mikawa Mahmud wayar,da kallo ya bita sam bata jira taji me zasu fada ba ta nufi kitchen taga me zata yiwa Abban nata mai sauki kuma favourite dinsa. Suna gama waya da Abban Mahmud ya kira zayyan yace yaje ya dauko masa Hajiya Inna Kitchen din yabi zahra ya samu tana ta kokarin hada abinci dan ma da alama wasu abubuwan an dafa su irin su nama haka nan da nan gidan ya dauki kamshi, taya ta wasu kanaun abubuwan yayi nan da nan suka gama suka hada table sannan suka koma sama sake watsa ruwa sukayi zahra na fesa turare taji wayar Mahmud ta dauki slow music Sameer ne. Dauka yayi taji yana fadar " OK ganu nan". "Sun karaso?". Kai ya gyada mata ya nufo In da take tsaye. " oya! Muje mana sun shigo ciki fa". Hannuwansa ta rike duka biyun "nifa kunyar Abban kuma nakeji wallahi sai naga idan ya kalleni kawai ze gane". Ai Mahmud bai San lokacin daya fashe da dariya ba saboda da iya gaskiyar ta tayi maganar. "Wai daga jiya zuwa Yau meya hau kanji wannan yarinyar? Yanzu fa kika gama matse yan hawaye akan baizo ba kuma yazo zaki dauki kinibibin kina jin kunyarsa, yaushe ze wani gane ai ba Wanda ze dauka ba karbi sadakina ba har mukazo nan ki share kawai". Ba zato ya janyo ta gaba daya saida tayi dan kara " oh sorry ke dince sai a hankali". Gaba tayi ta fice daga dakin a hankali take tafiyar cikin nutsuwa dan bata fatan kowa daga cikinsu ya gane ta. Suna parlourn farko, tunda suka dosa gidan Abba ke Hamdala ga Allah s.w.a ko yanzu ubangiji ya fitar dashi daga zargin mutane akan auren da yayiwa yarinyar nan. Kafin ta karasa shigowa Mahmud ya sameta a hanya. Tare suka shiga, tana ganin Abban wani farin ciki ya rufeta da dan sauri ta karasa inda yake zauna shima fara'a fal a fuskarsa fadi yake "Masha Allah uwata" A gabansa ta tsuguna tana gaishe shi, shima Mahmud din kusa da ita ya zauna yana gaishe da Abba hannu ya miki masa sukayi musabaha dashi sannan su Abdul Hakeem ma suka taso suka gaisa, duk yanda Abban yaso Mahmud din ya tashi bai tashin ba itama zahrar da gaske nauyin Abban nata tajeji Yau Kamar wani sirikinta. Tashi tayi ta nufi kitchen lokacin suna hira da Mahmud dasu ya Abdul Hakeem. Binta ta tarar tana wanke kayan da sukayi aiki dasu gaishe da zahra tayi tana fadin "wlh Aunty barci ne ya daukeni bayan ma gama gyaran falukan na shigo da abincin da Baba Haruna ya kawo". " OK babu damuwa ke kinci abincin?" "Eh nayi mana tunda da safe nida security din kofa haka Ammi tace na ringa yi tunda na iya sosai race Amman ke Aunty zilai ce zatana yi miki". Ok. Ga saura can na Wanda aka kawo din ki diba sauran ki fitar musu dashi, yanzu zoki tayani dauka muje can babban parlour Abbana ne yazo ganina". " to Aunty muje" zahra ta dauka itama ta dauka suka nufi can parlourn. "Haba uwata danmi kika wahalar da kanki haka?".. Binta ce ta tsuguna tana gaishe Abban sannan ta gaishe da sauran ta koma dauko sauran. " Abba abinda kakeso fa nayi maka tunda na duba naga da fresh milk ta shanu". Ya Abdul Hakeem ne yace "to kaji Abba Biryqni rice tayi maka kaga kuwa tayi abinda bazakaqi ci ba, kinyi masa mutumin?". Kaita gyada Masa. Table mat Binta ta shimfida guda biyu daya Abba dayan su ya Abdul Hakeem. Saida ta zubawa Abbanta komai sannan ta zuba musu ba karya ta tabbata rainon Ammah abinci tayi dadi iya dadi ga gas meat din Abba shima yayi dan kin cin pepper soup din sukayi sai nasan sukaci Mahmud bai wani ci abin kirki ba tunda basu Dade da yin breakfast ba kawai da dan kada taki ci ne ba dadi. Suna gamawa zayyan ya Karaso da Hajiya inna afujajan dan cewa ba lafiya ba tunda jiya suka bar gidan kuma Yau a tura daukota. Saida ta shiga ne kuma ta samu Salama tunda taga zahra lfy sai hira sukeyi da jama'a. Zahra ce ta tashi tana fadin "sannu da zuwa Hajiya daga ina haka?". " O'o daga gida mana mijinki ya tura a daukoni babu shiri wallahi nayi zaton wani danyan aikin yayi yake nemana" Rufe ido sameer yayi tana ayyana "wlh duk jirgi daya ya kwasosu ba saiti kina sisin kwabo". Sameer din ne ya tashi ya nufi Inda suke dan kada ta kira musu ruwa da bakinsu da babu saiti. " Sannu da zuwa Hajiya ki karaso baki garemu saiku gaisa ko". "To muje din ai hakan zumunci ne". Saida ta shigo sosai taga Alhaji Jafar sai kuma ta fara fadin "ikon Allah yo ai nasan wannan Alhajin ba kai bane ka sauko dani daga kan dutsen Arfa dana hau bara waccen lokacin dasu Mustapha suka bace min?". Dariya Abba yayi saboda ya tuno drama da suka sha a lokacin. " nine mana Hajiya Ashe bazaki manta in ba".." "Kai Haba shege ke mance Alheri ai nayi takaicin rashin tambayarka kai na Ina ne lokacin yo a gigice nake daka rakani gurin ma'aikatan sokoto kuma nayi gaba naga na gida a she da sauran haduwa kaima sana'ar ce ta hadaku da wannan miskilin?". " Dan Allah ki zauna Ku gaisa sai ayi miki bayaninsa". Sameer ya fada. "Kai tafi can lokacin daya taimaka min kuna can kuma taku sabgar ba sai daga baya kika sani ba, shiya yasa bara nace bana zuwa ina jimamin rashin dan tagwaye tunda shine me biya min nida 'yan uwana muje,gara muje umara tunda Allah ya fito min dashi". " Dan Allah ki zauna ku gaisa tukunna sai ayi labarin" su dai dariya kawai sukeyi tsohuwar warka ce bazake ce itace mahaifiayar milliners ba kuma kakar billionaire it's very simple and funny. Alhaji Jafar ne yace "rabu dasu Hajiya sannu da zuwa ya akaji da jama'a?". "Alhamdulillahi Yaya bayan rqbuwa kuma Ashe addu'ata ta karbu ai a gurin d'awafin bankwana saida nace Allah ya had'a fuskokin mu ko a daras salam ne Ashe a nan ma zamu hadu". Zarha ce ta matso suka gaisa da Hajiyar wannan sauran suka gaishe ta. " kai kuma haka ake sai kayi min aike haka wuta wuta duk a tada hankalina". "Kiyi hakuri to daman kiranki nayi ki tayani rokon Abban zahra akan marar lafiyar da kukaje dubawa da Hajiyar maru itace za'a fitar zuwa Egypt to har an gama komai kawai visa ake jira sai yace a'a a bari shine nake son a bashi hakuri ya bari mu ida ladarmu, ayi hakuri Abba ba qararka na kawo ba". " wai kana nufin shine baban zahara'u taka?". Kai ya gyada mata "Ikon Allah kace ta gida ce ka auro yo ai ni tun ranar daya taimaka min ya zama Dana,kuje kuci gaba da aikin ladarku ni nayi izini ai Dana ne ake yiwa wasu ma bare shi ai kujerun makka na wajena duka a kaisu Azare badan babu ba a'a kyauta ce a bawa hadimai da dangi da makota kafin nazo naga guri duk da daman nayi niyyar zuwa naga masu karancin nan da suka bawa dan tagwaye mata irin wannan ga jijyarsa da kukayi bamu da abinda zamu Baku sai dai Allah ya biyaku da mafificin alkhairinsa". " Allahumma Amin Hajiya nagode kwarai da gaske yanda kikace haka za'ayi". Sameer ne yadan risina tana da sadda kai "to min gode Abba kenan basai kun tafi da ita ba ayi hakuri jibi ne zamu wuce sai kuma idan wani ze bimu daga baya Amma nida yayar Hajiyar zamu wuce in sha Allah".. " kai kuje kuyi shirin Ku a banza ma dawa ake yiwa ruwa bare kuma a karkara".. "To mun gode Allah yaja kwana". Hira ce ta balle tsaanin Abba da Hajiyar duk yanda yaso ya yakice hirar yabar gidan taki saida suka fita sallah ne yace a fada mata zeyi mata zuwa na musamman ya bada dubu Dari uku a bata,ko zahra basuyi sallama ba sai ta waya ya kirata ya fada mata dalilinsa. Sai dare aka mayar da Hajiya inna wuni tayi tana fadin " haba shi yasa naji kin kwanta min zahra'u Ashe da walakin goro a miya,kin taso gidan masu nagarta da saninin ya kamata". **** Tunda Mahmud ya fita maida Hajiya bai shigo ba sai gurin Tara tunda har lokacin ya rike su sails bai bari sun koma Azare ba. Tana shafa' da wuturi ya shigo da alama a gajiye yake sosai,wanka ya fada bai jima ba ya fito lokacin tana ninke hijabin ta fito daga gurin sallar. Hannunsa ya bude mata ta taho a hankali ta fada kirjinsa yayi mata murfi da hannuwansa,ajiyar zuciya ta sauke jin sanyin ruwan yana ratsata. Shirya ki rakani unguwa duk da a gajiye nake Amma gara muje kawai gobe in sha Allah babu inda zan fita so nake na zauna dake na fada miki waye ni,da dalilin daya fitar dani daga gida da duk komai nawa tunda naga alamar ko zamu shekara Dari ba tambayata zakiyi ba". Lif tayi tana jin dadin sanyin jikinsa. "Preciousss".. Ya kira sunanta yana dan yawo da hannunsa a jikinta. " Na'am meu amorrr..." "Fada min ina kike son muyi honeymoon din mu kinga ummee tabamu ticket na qasashe uku". Dan Jim tayi kafin tace "nafi son Qasashen middle East gaskiya bana son European countries idan so samu ne mu fara da Saudi Arabia muje Ku ziyarki Qabarin Annabin Rahama muje muyi umara kuma kaga saimu tafi da Hajiya inna ko tunda naji tana fadin zataje". " Tab Allah ya kiyaye na tafi da ita yanzu Ashe ba angwancewar zanyi ba ai ruwa zata hana guru ko tace dakinku daya tasani a bakin duniya idan na hana kada ma kice mata ga India samu kiyi shiru da bakinki idan ba so kike na Dawo nayi dan wuya ba maimakon aga nayi free lamura sun karbeni". Sunne kai tayi a kirjinsa "kai meu Amor kaida Hajiya fa bata baci ka manta lokacin da kace idan mun hadu zaka kai mata qarata akan abincin?". Lakuce mata dan bakjnta yayi " ke bakya mantuwa ne Wai?" "Eh da sauki ai unguwarma na fasa gaskiya ka manta duk ranar dana rakaka unguwa bama dawowa lafiya, haka kawai kaje ka hadani da abinda tafi su bar-bar tunda naga baka da ragi idan ta had'oka da mutane kaje ka Dawo kawai bana zuwa bansan ina zamu ba yauma ace ga mace an kawo maka naje na mutu a banza gara kaje kai kadai". " kai!kai!kai! Ashe ni tsihon mai laifi ne ni wlh ni nama manta anyi wannan abun kice dole su little su taho gida tunda har kina kewarsu". "A'a wallahi bana son ko ganinsu mutuwa ce kawai banyi ba a ranar, shi yasa nake ganin mutuncin zayyan shi yayi min alfarma aka dauke min su fa". " kinsan Allah a ranar hankalina fa yana kanki dan abinda nayi niyyar yi din ma ji nayi bazan iya ba idan na tuna kina cikin wani yanayi kinsan daga ranar zayyan ya Kara samun wata daraja ta musamman a gurina? Kulawa fa da tausayi duka ya muna miki " "Wai dan Allah me kayo a cikin gidan nan nifa har yanzu ban samu nutsuwa ba". Tsinin hancinsa ya fara gogawa a kan nata hancinsa yana dan hura mata iskar hancinsa cikin nata. " kizo muje ki rakani mana a can zakiji wannan amsar taki" Dan rausayar da kanta tayi "gaskiya Ina shakkar binka tunda idan idonka ya rufe ba sauki kaje ka kaini inda Zan kwana Ina kuka ba Mai lallashina tunda idan kana fushi ba ruwanka Dani". "Kai ai da Kennan Banda yanzu yaushe zanyi fushi ai nine a kwana da din ba bansa yanda abun yake bane kinsan ni kifin rjiya ne a wanna fannin. *_AUREN HUCE HAUSH_* AISHAT ISAH NUSAH Maman Fateemah Bismillahir Rahamanir Rahim. Allah ka jikan iyayen mu kayi gafara da jinkai a garesu tare da sauran Alhummar musulmi da suka rigamu gidan gaskiya. Ina gaishe da dukkan masoyana na kiss Dana nesa Allah yabar kauna da zumunci, nagode kwarai. Gaisuwa ta musamman ga 1.Ramatu sunusu Ummi ( Mrs.Sani shehu kazaure ) 2. Fauziyya lawal Ammanj sokoto. 3.Hajiya Zainab Bashir Aliyu ( Mrs Muhammad manga Taraba state. Ina godiya Allah yabar zumunci da kauna. __Page 90. ____cikin abinda bai wuce minti goma ba Mahmud ya gama nasa shirin cikin suit Navy blue Goirgio Armani sai eyeglass daya saka mai azabar kyau yana daura agogo pateks a wrist dinsa, wani iri fitinannen kyau yayi mata ta kasa dauke idonta daga Kansa harya karaso inda take tsaye yana sakar mata da tsadadden murmushinsa mai shagaltar da ita, rumgumota yayi yana fadin "Yaya dai 'yan mata? ko kin kyasa dan malam ne irin wannan kallon haka? Ko dai mu fasa fitar ne dan kina Neman hanani nutsuwa fa, wannan eyes din suna dauke da wani sirrin dake hanani nutsuwa matukar suna kallona,kina tuna abinda ya faru a soron gidan baba malam ranar da Mai mamana Mai sunan Ammi Bata da lafuya?Wlh bansan fa yanda akayi na jiki cikin jikina ba, kinsan abinda kuwa hakan ya jawo min a ranar?nayi Dana sani yafi sau shurin masaki precious, kinsan abinda ya daure min kai dake?". Kai kawai ta iya girgiza masa. " Da kika kasa ko daga ido ki kalleni ko naji mari kamar yards nayi tsammani, amma sai naji shiru kinyi lif kina dibar ni'ima ko?". Sinne kanta tayi ji tayi kamar yanzu abin yake faruwa. "Dan Allah abar zance nan bakaji abinda bature yace ba? Fast is fast present is continue". "OK to shikenan ya wuce princess,zo muje". Shi yake driving din motar su zayyan na biye dasu a hankali suke tafiya yana nuna Mata mahimman wurare a cikin garin bata San ina zasu ba saida taga signed board na Usman dan fodio teaching hospital. Kenan gurin mama sukazo, to meya had'a tambayarta da zuwa gurinta ko kuma daga nan zasu wuce wani gurin ne. A parking space suka tarar da Sameer, batayi mamakin ganinsa ba dan suna tafiya taji suna magana badai tasan koda waye ba. Daga dan nesa da inda sukayi parking su zayyan suka Parker. Shida sameer suna gaba zahra na bayansu bar suka shiga Aminity word na Bangaren retainer ship. Dan knocking sameer yayi a kofar room four Aunty ladi ce ta bude kofar ganin sameer yasa ta matsaya tunda daga hanya tunda tun zuwanta shi yaketa fadi tashi da kai komo abisa 'yar uwarta, shiya turo mace ta zauna da Mama dazu lokacin da yasa a kaita immigration office. Hanya ta bashi tana fadin "yallabai sannu da zuwa". Kamar zatayi Kai kasa, Sam hankalinta Bai Kai Kan su Zahra ba, zaman glass dinsa Mahmud gyara sannan ya riko hannun Zahra suka shiga dakin. Mamar na Zaune an jingina Mata pillow tana Shan wani Abu a cikin cup,tana kurba kafin ta Kai ga hadiyewa su Zahra suka shigo sunyi wata irin dacewa ta ban mamaki kana ganinsu kasan wasu irin couple ne da a cikin dubu da wuya a samu Kashi goma irinsu, basuyi aune ba suka tsinkayo tarin kwarewar ruwa ya sarke Mama babu k'ak'k'autawa Nan da Nan idanunta suka firfito abinka da Mai idanu a warwaje da sauri Aunty laran ta natsa kusa da ita ta karbe kofin tana fadin "sannu Rabi'a kibi a hankali tunda an samu tarin ya lafa". Da kyar ya lafa Mata tana ta faman haki. Daki ne madaidaici Wanda ya hada ababen more rayuwa sosai tamkar gida. Duk yanda Zahra taso Mahmud ya saki hanunta yayi biris da ita. "Sannu Mama ya jikin naki?" Cikin raunin murya ta amsa da gani tana Jin jiki, "yauwa Zahra na gode kwarai da gaske kuyi min godiya gurin mijinki na gode Allah ya saka da Alkhari". "Amin" Zahra dasu Sameer suka amsa shi Dan gogan ko tari Bai kubce masa ba tunda ya shigo sai wani kallo yake bin mamar dashi, ji yayi ya Fadi nauyi yayi faduwar sanho a rairaiyi, shi ashe ganin tsoro yake Mata a Dan ganin da yayi mata, sai yaji duk abinda yayi niyyar ya sauke mata yaji baze iya ba ya barta da wannan kaddarar ciwon data sameta kawai ta isheta musiba. Tun ganin da Mama tayi musu Bata Kara dogo da kanta ta kallesu ba Dan wani irin kunya da nauyi ne suka rufeta yau ga Zahra a gabanta tare da Wanda suka dauka kaskantacce marar galihu a baya Wanda aka dunga fad'a musu da wani haske a tare dashi da yafi na sauran manemanta na baya amma tayi biris da maganar, gata gasu cikin wani irin yanayin da yafi duk wani tunaninta da hangenta. Sai da ya bushi iska sannan yasa hannunsa na hagu ya zare glass din dake idonsa ya yiwa Mama kallon Kai tsaya cikin muryar data saka zuciyarta kadawa ya furta. "Hajiya Rabi'aaaa..!!!". Ba ita daya ambaci sunanta ba su Zahra ma Saida sukaji tasu zuciyar ta kada, Dan Zahra zata iya rantsewa da girman Allah Bata tab'a Jin muryarsa da gautsi irin haka ba. "Ga Zahra nan ki dubeta ki K'ara kinso ki daqile Mata rayuwa ki Hana ta Kai inda ubangiji ya nufa taje kinyi ta kulle-kulle ki dan kada ta cimma rabonta na rayuwa da Allah ya hukunta a kanta, kin manta tun mutum na cikin mahaifiyarsa yake rubuta duk al'amuransa na duniya daga arzikinsa ajalinsa Dan wuta ko Dan Aljanna, an riga an rubuta alkalamin ya karya tawadar ta bushe, alkawarin Allah gaskiya ne baya tashi,gata Nan KAINUWA ce dashen Allah. Kuma duk kullin da kikeyi Allah ya nuna Miki iyakarki naso da lafiyarki da sai kinyi Dana sanin zuwa garin Nan to Amma sai gashi Abu kadan ya Hana zuciyarsa ta zauna lafiya tana neman bugawa a banza, abinda Kika so ya Sami Zahra sai gashi tun ba'aje ko Ina ba ya Sami yarinyarki, kinso Zahra ta lalace sai Kuma ta Zama Dan tsiron da Allah keso ko babu ruwa Saiya rayu,an Bata Almajiri marar galihu Maimakon tausayawa maraicinta a'a sai Kika gano tunda da Dan rufin asiri ba yanda Kika zata ba kina.cewa sai dai kyau ya qare a banza inda sai dai a kare a yawon kakksbar raba, duk da haka sai Kika dauri aniyar wargaza Mata rayuwar Aure saboda naki yaran Basu samu kamar nata almajirin ba, kin manta ayar da Allah subahanahu wata'ala yace cewa wamakaru "wamakarallah wallahi khairul makirin" Bari na maido Miki da abubuwan da kikayi ta fafutukar su zamar Miki tsanin daze ruguza duniyar gidan aurenta naji garin yayi min zafi na manta da ita har abada sai dai Wanda suka hada su gaji su kwance auren ko?" Ya jefa Mata tambayar duk jikinta rawa dake ga gumi ya tsatstsafo Mata a goshi har diga yake, duk tsiyar da kuke k'ullawa Asabe yarinyarki ta fada min komai har garuwan da Kike aikenta neman tsubbace tsubbacen ku, kinci daraja Daya wadda tasa na kyaleki na Kuma kyale 'yan koren naki, shi yasa na raba yarinyar taki da garin Dan matukar tana kusa zanyi Mata abinda asirin ki ze tonu abinda bazan so ace iyalin Abba itace ja Baga a cikin tafiyar, ko Mai gadin gidansa bazan iya keta masa rigar mutunci ba bare matar da yake aure ance ko a lahira wani Yana cin arzikin wani, Wallahil Azim da sai kunyi Dana sanin Baku santa ba a rayuwarku,Kinga zaman lafiya a kiyaye shigia eighteen dinta Amma duk Wanda ya kuskura ya k'ara gigin saka kansa a cikin lamarinta tofa maganar ba irin wannan za'ayi ba, zakuje asibiti na dauki nauyinki da duk Wanda yake tare dake a tafiyar saboda kinzo rako min princess ne ciwon ya tashi tunda dama da akwai shi,to gara ki Fara sheda wutsiyar ragumi tayi nesa da kasa, idan kin raba kanki da ciwon hassada idan Allah ya taimakeki ki samu waraka idan Kuma Yana Nan tofa Saida ya zamar Miki sanadin komawa ga Allah tunda ita dai wannan dai da aka dunga kokarin daqileta kada ta Kai inda ubangiji ya nufa tifa tayi Miki tazarar da za'a iya cewa tamkar tsakanin sama ne da kasa". Wayarsa ya mikawa Sameer. 'Kira zayyan ka fada Masa ya shigo da sakon Nan". Glass dinsa ya mayar a idonsa. Tunda ya Fara zazzaga maganganunsa wuta da daukewa duk wani mahaluki dake cikin dakin Dan wannan dabi'ar ba kowa ne yasan Yana da ita ba, Idan ka tabo shi saiya rama tun Yana yaro haka yake. Ba'afi minti uku da gama wayar ba zayyan ya shigo da ledoji guda biyu a hannunsa ya dan risina Yana fadin "gasu sir". "Ba kowace ta ta". Nan da Nan ya cika Umarnin uban gidan nasa, ya aje Kayan da asabe ta kawo na turarikan wuta a gaban Mama sai Wanda aka karba a gurin asaben dai Wanda ya Zama sanadin da tabar garin da Kuma tatsar bayanai daga gurinta. Gasu Nan idan Kuna da bukarsu a gaba saiyi muku amfani, ke Kuma Idan mun fita saiki nuna Mata wadanda bata kaiga ganinsu ba, Kuma yanzu haka Salma ta sauka a Azare zata amsa tambayoyin Abba tunda kinqi fad'a masa irin tarbiyyar da kike bawa yaransa". Bai Kara tofa komai ba ya janyo Zahra suka nufi kofa su zayyan suna take musu baya, suna Daf da barin dakin suka jiyo kukan Aunty larai tana Fadi "na shiga uku Rabi'a ki tashi" Shi dai Bai juya ba ya dai nunawa su Sameer akan su koma. A hanyar su ta komawa ne suka hadu da doctor zainab ta fito daga Gyne emergency. "A'a wa nake gani kamar 'yata? Yallabai lafiya na ganku da daren nan haka a asibiti daba sai a kirani ba". Gaishe da ita sukayi Zahra sadda Kai qasa Dan ji tayi duk kunya ta rufeta, Mahmud ne yace. "Ba komai doctor munzo gaishe da marar lafiya ne". "A to Allah ya qara sauki, 'yata ya jikin naki?" A kunyace tace "jiki da sauki mummy". ",To Masha Allah, Dan Allah ki kiyaye shanye shqnyen magungunan Nan badan jikinki Mai kyau bane da an samu matsala sosai" .godiya sukayi Mata sannan Sukayi sallama,ta wuce Suma suka wuce, har sukaje gurin mota babu Wanda ya tofa ko kalma Daya a tsakaninsu Dan ita Zahra ji tayi tana wata shakkarsa Bata taba zaton ze iya shafawa idanunsa toka yayi irin wannan rashin kirkin haka ba. *_ AUREN HUCE HAUSHI_* AISHAT ISAH MUSAH (Maman Fateemah) 09061432330 08055362975 Page 91 _________ Tunda suka dauki hanya yake sharara gudu sabanin dazu da suke tafiya a slow, taso tayi Masa magana to ganin Yana yinsa yasa tayi shiru ta zubawa hanya idanu, zuciyar ta fal da mamakin rashin kirkinsa Daman haka yake?. Har suka shigo rukunin gine-ginen unguwarsu Bai tanka Mata ba Saida sukazo dai dai wani gida Mai farin fenti da ash colour sannan ya Dan juyo ya dubeta, "Kinga gidansu dodanniyarki Nan". "Wacece Kuma dodanniyar tawa a garinku nida ko one week ban cika ba a garin da har zanji tsoron wata". "Dr Haseenah ba dodanniyar ki bace?". "Allah ya sauwak'e wallahi meye abin tsoro a tare da wannan Mai siffara mazan, mace ba gaba ba baya, Kace 'yar garinku?". Ba zato taji ya fashe da wata dariya Yana duka sitiyarin motar da hannunsa. "Amma wallahi kin cuceta, tana ganinta Mai zafi Amma ke kina siffantata da maza". Hannu ya Kai ya Dan shafi gefen cinyarta "ba wannan ko?". Dan zumburo Baki tayi tana matsawa "to karya naji Kai idonka baya gani, wallahi har naji bana son unguwar". "Kai! Kuji mu da yarinya haka kike da kishi? Kince kin tsani Kano Kuma my home city din ma sai Kice Bai Miki ba saboda kishi,to Yaya zamuyi dake idan Zan kawo miki 'yar buzuwata diyar Mama filani, Dan ta kirani mun zauna tace idan kin kwana biyu kin Zama 'yar gari ta bani Insiyya in Kara da ita Wai Daya tayi min kadan". Wani irin kallo ya zuba Masa da sexy eyes dinta. "Ki rufa Mana asiri mu karasa gida lafiya,kada kisa a tashi damu a social media ace Amare sabbin Aure sun rigamu gidan gaskiya a sanadin hadarin mota suna tsaka da cin amarci". "To Ni menayi,?". Ta qara kada Masa idanun tayi, wani smile yayi. "Naga alama wannan kin wuce tunanina Bari muje gida kiyi min bayani da yaren da zanfi ganewa tunda kin Fara Zama 'yar hannu". "Meye kuma 'yar hannu?". Dariya ya qara yi "kije ki tambayi hausawa". Ya fad'a Yana saka signal na shiga wata kwanar. "Ina Kuma zamu? Naga ka shigo wani gurin nifa barci nakeji". ",Fadi gaskiya dai yarinya, ko dai...?. Rufe fuska tayi da tafukan fararen Sol din hannuwanta Wanda suka Sha lalle. Wani irin kyau tayi Masa ba kadan ba. "Kunyar wa kikeji a Nan?". Dai dai lokacin da taji ya Danna horn Sau biyu abinda ya tilasta ta bude idon ta kenan. Budewar idanunta da bude gate din sai suka Zama kusan lokaci daya. Hannu kawai ya dagawa securities din yayi gaba, wasu gine-gine ta gani masu azabar kyau ga titi Nan dodar sai haske kamar Rana ga flowers Nan masu kyau an qawata gidan dasu, Bata ankare da Ina bane Saida taga sun karaso main ginin da aka kawota ciki, Bata tab'a zaton girman gidan da Hajiya Inna take fad'a ya Kai irin haka ba,to ai wannan sai a dafa mutum a cinye na wancan gate din ma basujin ko labarin ba, parking lot na motocin gidan Wanda suke tamkar kamfanin siyar da motoci ya nufa da alama ba 'yan milkin bane a kansa Dan tana ganin yawanci sai dai a shigar da Masa da ita ciki. Kallonsa take galala Kamar wata 'yar kauye. "Lafiya irin wannan kallon haka? Duk gidanki ne gate uku gareki dayan sai kin kwana biyu kin warke tas mu zagaya kiga inda yake, gasu Nan compartment compartment sai inda kikeso Zaki zauna". "Ko dai zamu zauna ai Ni Kuma na Gama shiga taitayina nasan wannan gidan mace hudu ne wata kila harda kwarkwara ma tunda da abun". Bai tanka Mata ba ya bude ya fito, itama ta fito tana Kara waiwayen hanyar da suka biyo sai yanzu ta Kara karewa gidan kallo, ita abin yafi karfin sannin ta gaskiya da data ambaci tsoro Ashe ba tsoron takeji ba sai yanzu. "Oya let's go". Ya fad'a Yana janyota jikinsa "Wai tunanin me kike ne haka Kona Dr.din ne?. "Dan Allah ka daina fada min sunanta". "Tona daina muje kiyi min wanka kiyi min tausa yanda zanji Dadi Baki labarin nawa wata Kila mu gama zuwa asuba". *********Tunda su Abba suka sauka a Bauchi yake Kiran wayar magaji Amma amsar Daya ce not available, malam Bala ne yaje dauko su tare suka taho dasu Aunty Hassana da Inna mainuna da Hameeda. Dan daga gidan zahrar airport suka wuce inda suka samu su Aunty Hassanar, tunda su Abba suka baro gidan Zahra Bai Kara kallon Hamza ba Dan idan ya dube shi ji yake zuciyarsa tana wata irin tafasa, Bai tab'a zaton haka daga gare shi ba, yayi zaton hankalinsa da tunani sun wuce haka kenan da hadin bakinsa aka munafurce shi anyi masa lullubin biri. Karfe biyar saura suka shiga cikin garin Azaren katagum. Gidan shuru kamar babu mutane a cikinsa su Aunty Hassanar suka shigo, parlourn Ammah ba kowa sai kamshin turaren daki Dana girki Daya cika shi. Saida Aunty Hassanar tayi sallama sau biyu sannan Alawiyya ta fito daga kitchen tana amsa sallamar tare da fadin "Lah Aunty, Inna sannaunku da zuwa mutanen sokoto ya hanya?". "Hanya Alhamdulillahi mun dawo lafiya, ya muka sameku?". Inna maimuna ta fad'a tana zama a Kan two seater. "Lfy kalau Inna ya aka baro Amarya? mu ai mun tsufa a gida, Ashe Mama bataji Dadi ba a can?". "Wallahi kuwa jiki kam babu Dadi tunda har za'a fita da ita can misira". "Allah ya Bata lafiya, sannu Hameeda ya Mai jikin?". "Jiki da sauki Alawiyya nagode". Ammah ce ta fito daga cikin corridor din bedroom dinta. "A'a Masha Allah! Inna sannunku da hanya, ai tun dazu nake zaman jiranku da naji shiru Baku karaso ba na shiga daki gurin wayata da ake Kira". Abinci Alawiyya ta kawo musu da drinks. "Waini Hajiya Ina su Hanifa ne naji gidan shiru alhalin an bar Miki 'ya 'yan Amana". 'yar dariya tayi "suna gurin Babansu tun safe dayazo gurin Abba suka tattara suka bishi". Aunty Hassana Yi mamaki ba Daman tasan za'a rina Banda ta taushesa da kalamai masu dadi cewa yayi sokoton ze biyota ya gaji ta barshi ba matallafiya. Gaishe da Ammar tayi ta tashi ta shige ciki ta barsu da Inna suna Zaune suna Kara jajanta jikin Mama yayin da Hameeda ta nufi nasu part din ta aje luggage dinta da sauran tarkacenta na biki da aka basu. Kiran sallar magariba ya tashe su daga hirar da Inna ke yiwa Ammah na irin daular arzikin da Allah ya Kai yarinyar su wadda ko a mafarki Basu tab'a zaton hakan ba. Suna sallah sukaji kamar hayaniya daga parlour da sauri Aunty Hassana ta fito tana fadin. "Menene haka nakejin hayaniya?". Ai batasan lokacin daka kwalla Kiran" Daddyyyy....ka Bari wayyoooo Allah Ammah ku fito za'ayi kisan Kai a gidan Nan". Da gudu ta karasa gurin dasu Ya imam da ya Abdul Hakeem keta kokarin banbare hannun Abban daga wuyan Salma wadda take wani irin kakari kamar na fitar Rai. Magaji ne ya shigo da gudu baiyi wata wata ba ya girgije Abban ya raba hannunsa da jikin wuyanta ya dauketa cak kamar yarinya yayi Kan three seater da ita Yana fadin "ku bani ruwaaa..". Da gudu Aunty Hassana ta shige kitchen dauko ruwan sukayi kicibus da Alawiyya ta nufo parlourn da gudu da ruwan hawaye na bin Kumatunta. Da kyar su Abdul Hakeem suka zaunar da Abban sai huci yake Yana fadin. "Wallahi banga amfanin haihuwar ki ba Salma kinci mutuncina kin tozartani kunci amanata keda uwarki da Dan uwanki, damena rage ki? A gidan Nan abinda kukayi min na barku da Allah sai munyi shari'a da Rabi'a a gaban zatin Allah, Kuma a gobe ba jibi ba a gidan miji Zaki kwana ko wanene, Kuma karatu kin Gama a gidana har abada, itama Hameeda su kawo sadaki ko Bai Gama gidan ba ya zaba cikin nawa su tare". "Haba Alhaji idan Rai ya baci ai hankali baya gushewa kada a hau dokin zuciya sai ayi aikin Dana sani, ka Bari abi komai a sannu Allah zeyi maganin komai,kowa da irin jarabawar da ubangiji keyi Masa, wasu ta 'ya'ya wasu ta dukiya wasu ta lafiayrta jiki ayi hakuri dan Allah ka taushi zuciyarka kada kayi aikin Dana sani". Ba zato sukaga hawaye ya zubo Masa abinda Ammah Bata tab'a gani ba kenan duk iya zamansu, sai itama nata Hankalin ya ninka na dazu tashi ta matso kusa dashi tana fadin. "Dan Allah Dan darajar Manzon Allah kada ka Zubar Mata da hawaye kayi hakuri kamar yanda Inna ta fada abi komai a sannu sai kaga an samu masalaha a Kai". "Haba Asma'u wane irin tashin hankali ne wannan ace Dan daka Haifa kake lokarin Kare duk wani haqqi nasa da ubangiji ya Dora maka, amma a ce an wayi gari ya kangare ya Zama fasiqi duba medical report din Nan ki gani".. Ya Mika Mata takardar dake cukuikuye a hannunsa. Jikinta na Bari ta shiga warware takardar,bayani ne tiryan tiryan na adadin cikin da aka Zubar a baya da nasu bincikrn da sukayi da tambayoyin da likitan yayi mata da Kuma irin matsalar da aka Samu garin Zubar da wannan cikin. Zuface keta ketowa Ammah ba qaqqautawa, wannan wace iriyar masifa ce a gidan Nan?. A hankali ta furta "innailaihi wa inna ilaihi raji'un". Ta manta dasu Inna da Yara ma a gurin ta zauna kusa dashi daf tana shafe hawaye.. "Kayi hakuri Abban Yara kowa da tasa' jarabawar Kai taka a haka tazo ka karba kayi hamdala a kowane yanayi sai ubangiji ya saukar maka da Rahamarsa" Su Abdul Hakeem ne suka Fara fita kafin inna ma ta koma daki,Alawiyya ma ficewa tayi daga part din gaba daya, ya rage daga Salma dake mayar da nunfarfashi ruwan hawaye na Mata anbaliya ba sassauci,sai Kuma su Aunty Hassana da magaji sai Kuma su Ammar. Ban Baki Ammah ketayi akan ya janye furucinsa Amma ya kafe ba canji. "Haba Asma'u karuwa a gidana,a cikin 'ya'yana, wace irin masifa ce wannan, Kuma Dan yayarta uwa daya uba Daya ace yayi min irin wannan abun su kansu Dame na ragesu Banda tambadaddune sunki karatu sai sakarci, da sun msayar da hankali da yanzu Basu Samu tudun dafawa ba? Ina cewa tare suka Fara karatu da imam ba ya kasa akayi withdraw dinsa daga makarantar, to Aure babu fashi Kuma kowaye na samu saina aura Mata shi in Sha Allah. Su Aunty Hassana suka shiga da Salma dayan bedroom din Ammah tana ta rusa kukan da baya fitowa.sabida wahala ga zafin ciwon da Bata Gama warwarewa ba. Abban ma bangarensa a part din Ammah suka nufa da kyar Ammah ta lallashe shi yayi wanka ya Sha tea kawai ta bashi pcm ya sha, saida ta saukar da fushinsa Mai zafin sannan ta fito ta nufi parlour lokacin wurin Tara da Arba'in da biyar na dare A Nan ta iske magaji da Aunty Hassana wadda har lokacin Bata tafi ba, dan Ammar cewa tayi magaji kada ya tafi ya jirata a nan. Fuska babu annuri Ammah ta karaso inda suke Zaune. "Me kayi kenan sulaimanu? Ka kyauta kenan ka hada tashin hankalin mutane banda Allah ya tsare me kake tunanin ze faru? kasa ayi Mana kisan Kai a gida, to kaji Dadi hankalinka ya kwanta wato Kai koje sarkin labari ko Kuma suda Mai bakin magana, to kaji dadi ka hada husuma saika zuba ruwa a qasa kashe burinka ya cika Abbanku ya sani sai me kuma?". "Kiyi hakuri Ammah wallahi gani nayi idan nayi shiru naci Amanarsa yanda yake tsaye a kanmu, Kuma ni bada gulma na fada Masa ba kawai dai nace Naga sun fita ta baya da asuba tare da Ya Hamza Mama ta rako Salman tana kuka, daga Nan ban qara ce masa komai ba, bansan Wanda ya fada Masa sauran zancen ba, sai dazu da safe yace min sunyi waya da Ya Mahmud yace Zan raka Bilyaminun gidan Baba Malam Jos, shine fa muka tafi a hanya Ya Mahmud din yayi min text message na inda Zan raka Bilyinun da address din asibitin da zamuje da number likitan da zamu nema, wallahi Ammah ki yarda Dani bansan gurin waye zamuje a Jos din ba Saida likitan da muka samu yayi Mana jagora zuwa dakin da take sannan Naga itace, Ni kaina mamakin abin yaki bani to meya hada Salma da Ya Mahmud Taya akayi yasan halin da ake ciki, nayi tunanin ko Zahra ce ta fada masa sai Kuma nayi tunanin ai Nima fada tayi lokacin Dana fada Mata". Nisawa Ammah tayi tana jinjina maganganun magajin, haka Aunty Hassana ma. "Allah ya kyauta ya rufa asiri, Amma abin da mamaki dai gaskiya". Dan murmushi Aunty Hassana tayi. "Babu mamaki wallahi Ammah, wannan mijin na 'yarki ba karamin mutum bane ni lamarinsa ya daina bani tsoro idan akace miki yasan abinda mu Bamu sani ba a cikin gidan Nan kada kiyi mamaki Dan Naga Bai dauki Lamarin 'yar Nan taki da sauki ba ze iya yin komai saboda ita kina jifa tun zuwan su Zahra Jordan ita da Abba suke bibiyar yarinyar nan". Tashi magaji yayi Yana fadin "Allah ya huci zuciyar sirikar masu abun, nifa yace can Zan koma kusa da Zahra tunda Aminiya ta ce, Ina ga fa hijira lahu ta tabbata a gareni, Idan kin shirya Aunty ki fito na kaiki gida". ",Kai dai Allah ya shiryeka wallahi gidan kanwarka zaka tafi ka tare saboda abun kunya gaba ka bashi ba baya ba". Aunty Hassana ta fada. Dariya yayi kawai ya fice. ******* Zahra na kwance tayi pillow da cinyar Mahmud bayan sunyi wanka Yana tunke Mata gashin kanta Daya zare Banda din yana fadin "precious kinsan Allah na yarda da abinda Hausawa ke fadin ta ciki na ciki ta baka na baka, Naga fuska biyu muraran, Bari na dauko Miki abun daga tushe yanda Zaki fi gane abinda za fada Miki".. Gyara kwanciya tayi tana facing dinsa shi Kuma Yana Wasa da wani zare da ake daure gaban rigar barcin dake jikinta Wanda shi kadai ne ya rufe gaban rigar. "Sunana Mahmud Muhammad Dange mahaifina general Muhammad Dange Dan asalin garin Dangen shuni ne, local government ce Mai zaman kanta a Nan sokoto, mahifinsu Abbie sunansa Alhaji sa'idu jibrin Dange Mai kudine na gasken gaske su goma Sha hudu ne a gurin mahaifinsu goma uwarsu Daya ubansu Daya sai Sa'id shi kadai uwarsa ta Haifa ta rasu sai Kuma Halisa itama uwarka ita kadai ta Haifa Amma ita uwarta tana gidan, sai Allah ya sakawa Alhaji jibrin tsananin soyayyar sa'id tunda yaro ne mai hakuri da wuya ya Fadi anyi masa Abu Saidai idan Alhajin ya gani ya tsawatar, ko a harkar kasuwa Alhajin yafi son ya tafi da Sa'id ko gidajen man petrol dinsa ze je to da said yake tafiya abinda ya kawo rashin jituwa kenan a tsakanin Sa'id da 'yan uwansa, sannu a hankali Sa'id na bin Alhajin guraren cinikinsu har Allah ya hada sa'id da wani Alhaji sani gada,Wanda shine sila ta samun asalin dukiyar data yad'u har jikoki, Dan tankar Mai ya Ringa sauke masa yana bashi a kan farashin kamfani, kafin wata shida jari ya kankama, kafin shekara sa'id ya hada jari na ban mamaki. Ganin haka sai 'yan uwansa suka huro wuta akan kasuwarsa. Sa'id Bashi da tsoro ko alama haka akayi ta juyawa da :yan uwansa. Zuwa lokacin da zasuyi Aure shi sa'id Allah ya hada shi da Hadiza 'yar Asalin kwantagora ta jihar Niger. Cikin ikon Allah 'yan watanni kalilan ciki ya bullo jikin Hadiza sunyi rainon cikin tare, Dan Allah yayi shi mutum ne Mai son 'y'y ga tausayin mace gashi daidai k Lokacin arzikinsa sai Kara habaka yake, abinda ya tsone idanun 'yan uba kenan duk da kowa da nasa rufin asirin sosai tunda Allah ya saka Albarka a cikin neman nasu Amma saboda sa'id ya Zama zakaran gwajin dafi sai yafi tsaya musu a wuya sosai gashi matarsa Hadiza Bata daukar raini duk da itace karama a cikin matan da aka Auro. Lokacin da cikin yakai wata Tara iyayenta sunso ta koma gida kontagora ta haihu Amma sa'id ya shafawa idnunsa toka ya Hana yace sai dai a turo wadda zata zauna da ita Sai hakan akayi, cikin Rahama ta Ubangiji kafin a kaiga turo kowa cikin Daren wata litinin nakuda ta kamata kafin ya kaiga fad'awa kowa Allah ya sauketa lafiya ta haifi yaronta namiji murna ba magana murna gurin sa'id Kamar me haka mahaifinsa da sauran dangi wadanda suke kaunarsa,'yan uwan Hadiza sunzo ranar suna yaron yaci suna Muhammad Auwal sai ake ce Masa mahummad kawai. Tun daga Nan haihuwa ta budewa Hadiza ta haifi Maimunatu sai Mustapha, Saminu, tana goyon saminu ne Allah ya yiwa mahaifinsu sa'id Alhaji Jibrin rasuwa sa'id.yayi kuka Kamar ba gobe Amma dole aka dangana, bayan anyi arba"in akayi rabon gado kowa aka bashi nasa rabon sa'id yaso su hada kasuwanci da 'yan uwansa Amma sai mahaifiyarsu tayi tsalle ta dire tace cutarsu zeyi tunda yafisu sanin Kan kasuwa kowa yaje ya juya nasa tunda kowa Yana da nasa nasibin, dole ya hakura sai Kuma zaman lafiya yayi kaura daga cikin family din Koda yaushe cikin tashin hankali ake ga an tsangwani yaran Hadiza saboda duk cikinsu babu masu nagartar 'ya'yan ta kyawawane sosai, ganin zumunci Yana neman ya lalace yasa kanin mahaifiyar sa'id dake sokoto ma'ikacin gidan ruwa ne har yakai matsayin baturen ruwa na jaha gaba Daya yace ya taso daga dangen ya dawo sokoto hakan akayi sa'id ya bada kudi aka saya Masa gida Mai kyau da tsari tunda lokacin harkar petrol ta bude sosai harya mallaki gidajen Mai kusan uku a cikin kwaryar sokoto. Bai fadawa kowa halin da ake ciki ba sai ranar da zasu bar garin, ba wani damuwa 'yan uwan suka nuna ba ya tattaro Kan iyalinsa suka dawo sokoto, anan yaransu sukaci gaba da zuwa makaranta, bayan an yaye saminu aka haifi Aliyu sai Kuma haihuwar ta tsaya, kafin shekara biyar arzikin sa'id ya habaka sosai Dan Nan da Nan sunansa yayi fice a sokoto ga taimako har 'yan uwansa Bai ragesu ba duk da kowa da nasa rufin asirin, makarantar sojoji aka Kai Muhammad tunda Daman shine ra'ayinsa da taimakon kawun mahaifinsa Allah yasa aka samu a kaduna, Maimunatu Nan kwatarkwashi aka kaita boarding itama sannu a hankali rayuwa na juyawa har Muhammad ya Gama makarantar sojoji lokaci tuni Maimunatu ta Gama secondary dinta ta shiga poly har da maganar Aurenta a gida, shi Kuma Muhammad ya tafi wata makarantar ta sojojin a Jos. Su Mustapha da saminu da Auta Aliyu kowa Yana nasa karatun. Lokacin da akayi bikin Maimunatu Muhammad baya Nan ya tafi wani course America, a can Allah ya hada shi da Mr Johnson baturen ingila kuma masanin sirrin kasuwanci sun hadu dashi ne ta dalilin kanwarsa wadda suke course din tare Anita sunyi sabo sosai da ita tana da kirki yawanci tana tambayar Muhammad abinda ya shige Mata duhu, ta dalilin Mr Johnson Muhammad ya Fara business da kudin da suke samu tunda basu zauna a banza ba idan suka Gama bunda zasuyi suna fita suyi aiki Wanda ake biyan mutum par hours. Da taimakon Mr Johnson din Muhammad ya Fara turowa Dan uwansa Mustapha Kaya idan yayi order sai ya turo Nigeria Kuma cikin Rahama ta Ubangiji Kayan masu da an kawo sai masu sari su sayen ga mahaifinsu ma Yana Kara koyawa Mustapha dabarun kasuwa kafin wani lokacin jarin yayi karfi na ban mamaki abinda yaso ya kawo sabani Kennan tsakanin saminu da Mustapha Dan karara saminu ke nuna Jin zafinsa akan zabar Mustapha da Muhammad yayi ya Dora akan kasuwarsa, Saida Hajiya inna sunan da wani yaron makotansu ya saka mata tayi Jan Ido da fada na tashin hankali sannan abun ya lafa, Dan yanda saminu ke nunawa 'yan uwansa tamkar 'yan uba. Haka akayi ta juyawa har lokacin dasu Muhammad suka dawo lokacin tuni Maimunatu ta haihu yaronta Tahir har Yana yawonsa ko ina, Basu Dade da dawowa ba akayi masa posting Calabar cross river State da matsayi Mai girma, abinda ya tilasta ya tashi neman Aure kenan tunda Daman akwai wata yarinya 'yar makotansu da suke soyaya da ita Ammaratu yaso ta sosai sai dai lokacin da yake kokarin tafiya course dinsa mahaifinta yayi maganar Aure sai aka fada Masa ga inda zaya shi Kuma yace yarinyarsa ta Isa munzalin Aure, abinda ya Hana Auren kenan a wancen lokacin, akayi Mata auren da wani, abun bai kai ko Ina ba ya lalace Wai mijin yace Bata da lafiya dole aka raba Auren, to dawowar Muhammad suka Kara hadewa duk da Da farko Hajiya Inna taso ta Hana Amma Alhaji sa'id ya nuna Mata tayi hakuri ba'asan abinda Allah ya hukunta a tsakaninsu ba, idan da Rai a gaba Saiya auri budurwar, ba'a dauki lokaci ba aka Sha bikin Muhammad da Ammaratu suka tattara suka wuce calabar, yayi mamaki yanda ya tarar da ita budurwa tunda yasan tayi Aure sai lokaci ta bashi labarin ai Bata tab'a yarda da mijin ba shine yace baze iya ba Bata da lafiya. Cikin ikon Allah wata buyi da aurensu ciki ya bullo a jikin Ammaratu zokiga murna gurin Muhammad, namiji ta Haifa yaci sunnan Abdullahi, sai Ramlatu sai Habiba, Ibrahim tana goyonsa suka dawo kaduna lokacin Yana da mukamin canal, daga gefe Kuma kasuwanci yayi wani irin karfi. A kaduna Allah ya hada Abbie da momin Kano 'yar sarautar Kano ce, hutu taje gurin yayanta Allah ya hada su babu Bata lokaci iyaye suka shiga Hajiya Ammaratu tayi tashin hankali Kamar ba gobe dalilin da yasa ta koma sokoto da Zama kenan. Amarya ta Fara tarewa a sokoto kafin su wuce kaduna, itama da Albarkar haihuwa tazo ta haifi ummu Salma da Jamila, tana goyon Jamila wani aiki ya taso na kasa da kasa lokacin yaki ya barke da 'yan tawayen MALI Abbie ne ya jagoranci tawagar sojojin Nigeria zuwa malin. Sun dauki wata da watanni suna fafata yaki da 'yan tawayen kafin a karya lagonsu duk da tallafin da suke samu na makamai daga wasu kasashen duniya, ana murna anci galaba sai Kuma suka bulla wani bangare ba na yankin Agadas ta jamhuriyar Niger Daman Suma ana fama da 'yan tawayen Abzinawa. Dole aka nemi Karin sojoji daga kasashen ecowas aka kara turawa arewacin Niger din, a lokacin ne Abbie ya koma Niger aka Kai wani can MALI din. Cikin ikon Allah suka dakile 'yan tawayen, wata rana suka fita zasuje wani kauyen buzaye sayen Kayan dafa shayi, suna cikin tafiya Hilux dinsu ta samu matsala gashi babu gari a kusa sun fito sunyi cirko-cirko sun rasa abun yi gashi babu order order a tare dasu, sunan a tsaye suka ringa jiyo qugin injin mota ba'a Dade ba motar ta nufosu su Abbie suka Zama cikin Shirin Kota kwana tunda guri ne da babu tsaro ganin sojoji yasa masu motar suka rage gudun motarsu maza ne guda biyu a gaba da alamar uba da d'a ne sai Mata biyu a baya babbar mace sai yarinya budurwa Mai wani irin kyau Mai fisgar hankali a kusa da ita, suna tsaywa Abbie ya karasa ya gaishe da Babban mutumin, sannan suka gaisa da Dan nasa anan yake tambayar meya faru da motar? Bayani yayi masa na Suma Basu San abinda yake faruwa ba kawai sun fito ne zasu shiga kauyen dake gabansu sayen Kayan shayi shine motar ta samu matsala. Dansa Daya Kira ishai ya umarta daya fita su daura igiyar jan mota su fitar dasu daga wannan gurin Mai hadari. Gurin window din da Hajiyar ke Zaune Abbie ya Dan leka ya gaishe da Hajiyar ya dago idonsa ze juya caraf suka sarke Dana yarinyar dake kusa da ita, da sauri ta juyar da fuskarta Dan ji tayi zuciyar ta kamar zata fito Dan dokawar da takeyi. Ba zato taji mahaifiayarta na fadin "wani irin sakarcine haka zainab kina ganin yaro yazo ya gaishe mu ke ki kasa gaishe shi?" Shi dai gaba yayi Bai tsaya yaji me zata fada ba Dan kusan Abu iri Daya sukaji lokacin da suka hada a idon. Basu tsaya a kauyen ba dole suke wuce cikin birni inda a Nan ne za'ayi musu gyaran,Abu kamar Wasa aiki ya Zama Babba dole sukayi waye can camp dinsu kada hankali ya tashi. A gidansa na wannan garin inda ya kasance mahaifarsa Alhaji Haroon ya sauke su da abinci da gurin kwana Mai Rai da lafiya, lokacin Yana ambassadorn Niger a k'asar Rasha sunzo hutun karshen shekara ne suka baro Yamai suka shigo gaishe da dangi Allah ya hadasu, sunga karamci da kyautatawa mutane ne masu karki kamar me, Ishaq a gurinsa ya zauna suna ta Hira a Nan yasa su 'yan Nigeria ne, zainab da wata yarinya suka shigo musu da kayyayakin abinci, tunda ta shigo Abbie keta binta da kallo ita Kuma taqi yarda ta dago saboda taji yanda idanunsa suka yawo a jikinta, serving dinsu zata Fara Abbie yace ta Bari suje kawai saboda yaga yanda abokanen tafiyarsa biyun suke kallonta duk sai yaji ya damu,washe gari ma su suka kawo musu break fast sai kusan goma na Rana sannan masu gyaran suka kawo motar har gida,sunyiwa Alhaji Haroon godiya sosai Dan hanawa yayi su biya ko sisi na gyara sannan yasa akayi musu fulltank na petrol a motar. Har ciki suka shiga suka gaishe da Hajiyar sun taso zasu tafi Hajjar ta Kira zainab tace tazo suyi sallama Kamar zata fasa kuka ta fito tana sadda Kai kasa da gaske mutumin Nan dodonta ne, daga gefe ta Dan tsuguna tana gaishe su. Ya ishai ne ya dubeta Yana fadin kunyarwa takeji da take sadda Kai kasa kamar tana gaban sirikinta. A haka su Abbie suka fice a waje sukayi musanyar number da Ishaq sannan ya karbi ta Alhaji Haroon Wanda suke Kira Abu. Har suka koma sansaninsu Abbie na makale da tunanin zainab haka yayi ta fama da ita a cikin zuciyarsa har tsawon kwana uku Amma Kullum sai sunyi waya da Ishaq da Alhaji Haroon Ambassador a ranar cikon na hudu ne ya kasa daurewa ya dauko mota da ordily dinsa Daya suka biyo Sahara zuwa cikin gari. Sam Alhajin Haroon baiyi mamakin ganin Muhammad ba Dan yasa da walakin goro Miya yanda yake kiransa da yanda yake tambayar su zainab yasa da wata a kasa, Yana zuwa baiya kwauron Baki ba ya fito da bukatarsa ta son Auren zainab inda Kuma ya fad'awa Abu shi Mai iyali ne har buyi a fada Mata idan ta amince zata iya aurensa a haka, Basu bar garinba Saida magana Mai karfi Dan ana tambayar zainab din ta rufe fuska, dariya Hajja tayi tasan za'a rina ita tun ranar da suka hadu a Sahara tasan akwai abinda Allah ya hada Dan taga yanda kowannensu ya nuna da suka had a Ido to abinne na zamani baka zakewa. Cikin Kankanin lokaci sukayi wata irin shakuwa ta ban mamaki tamkar sun shekara suna soyayya sai yaji tamkar Bai tab'a son wata 'ya mace ba a rayuwarsa Dan yanda yake Jin zainab daban ne da yanda yaji a matansa na baya, kafin wani lokaci zainab sunyi sabo da Hajiya Inna ta waya Kuma kusan kowa a cikin family yasan Muhammad Dange zeyi Aure a Niger Dan tuni manya sun shiga maganar babu Bata lokaci akayi biki Daman ta hada karatunta tun shekarar data wuce, Shima suka dawo gida tunda an samu kwanciyar hankali a yankin da ake fama da tarzomar. A lokacin ne Abbie ya Gama katafaren gidansa da Kuma wadan da ya ginawa 'yan uwansa duk da kowa ya Kama kasa a lokacin Amma samun ba Daya bane, da yawa Yan uwan Babansu Wanda suke uba Daya sun dawo sokoto kowa Kuma Allah ya saka Masa Albarka a cikin nemansa sai dai sa'id da yaransa sun Zama zakarun gwajin dafi a cikin Families din Dan babu Hadi ko alama tazarar da nisa tamkar Dangote a cikin zuri'ar Alasawan koki ta Kano haka misalin yake a zuri'ar DANGE da iyalan Alhaji sa'id din. A lokacin Abbie ya dawo gida sokoto da aiki shine musabbabin da momin Kano ta dawo sokoton itama duk abin Jin dadin rayuwa an tanada a gidansa Nan Dan ko daga waje kalli gidan ka Kara kallon komai na furnitures ya zuba Amma dole yasa aka cire wasu Dan iyayen zainab sunce sai sun Mata nasu jeren an kawo Kaya na garari Wanda suka tada hankalin kishiyoyinta da farko ce musu akayi irin 'ya'yan buzayen Nan ne masu yawo suna neman sadaka ya gani a sansaninsu 'yan gudun hijira,Amma ganinta da 'yan uwan ta da irin dukiyar da aka Zubar sai Kuma jiki yayi sanyi Baki ya mutu tanadin wulakancin da akayi tanadi za'ayi ya kau. Zamane aka Zubar na kishin mimmuge ba fada a zahiri Amma akwai 'yar kasa daga gurin babbar gidan wanda da wuya mutum ya gane lokaci daya, gashi Hajiya Inna da Alhaji sun dauki son duniya sun dorawa zainab, Shima Mai gidan wanda take Kira da general yake Mata wani mahaukacin so Wanda baya iya boyewa a gaban kowa gashi tayiwa sauran zarra a gurin komai na auratayya sai abun ya Zama biyu. Ba laifi sunyi amarci sosai Dan Saida ta dauki kusan wata shida suna cin amarci sannan ciki ya bullo Mai wata irin fitinar son kasancewa da miji dole tasa ya dauketa ya tafi da ita wani course da zaya a South Africa abinda yaso ya tada hankali a gidan sai da yayi Jan Ido da kurarin duk wadda bazata zauna ba kofa a bude take sannan aka Samu zaman lafiya. Ya fada Yana Dan Jan tsinin hancin Zahra "kinji yanda Muke muna ciki dan haka dole ki shirya tunda ba rago Kika aura ba tin a ciki ya Sami energy kinsan duk Inna tawa ta bani labarin nan?". Rike Baki Zahra tayi "har wannan Kuma?." "A'a ba direct ta fada min ba fa cewa tayi Wai cikin rashin hakuri ya sakata, Saida na tambayi Hajiyar makwarari ta fada min kinsanta ita handsfree ce".. Kina ji Saida sukayi wata uku suka dawo lokacin cikin watansa shida kuma tun a can a asibitin da take zuwa ante-natal clinic suka fada Mata twins ne mace da namiji Amma Tayi shiru ko Mai abun Bata fad'awa ba saboda abune cikin duhu kada ta fada yazo Kuma a samu akasin hakan, lokacin da suka dawo suka samu momin Kano ma tana fama da nata laulayin ciki wata ukau a watan da suka wuce ta Sami nata itama. A Nan sokoton ma sun fada mata, da watan haihuwa ya Kama Hajiya Inna da kanta tazo ta saka zainab gaba lokacin baya Nan yaje wani aiki Lagos ai kuwa kwana biya da daukarta cikin dare nakuda ta tashi suka garzaya asibiti a cikin ikon Allah kafin asuba ta haifi yaranta biyu murna gurin Hajiya Inna Kamar ba'a tab'a haihuwa a gidanta ba, kafin gari yayi haske suka koma gida kafin wani lokaci gida ya cika da jama'a bare da abun shima uban gayyar yasha mamaki da Inna tace masa Yara biyu ne Sam cikin beyi wani girman azo a gani ba. Ranar suna anyi hidima 'yan Niger sunzo tamkar a Niger mai jegon take yaran sunci sunan Aishat da Mahmud, sun Sami Alheri Kamar me Hajiya Inna ta Hana su Hajja zuwaira su tafi da zainab gida dole suka hakura suka tafi ita Kuma taci gaba da wanka a gidan innar har tsawon wata biyu,Saida Alhajin ya gaji yace Mata Wai bazaki mayar Masa da matarsa ba sai hakurinsa ya Kare kice yayi rashin kunya, ke ba bahaushiya bace ko wannan cika daren da yakeyi a gidan nan Bai isheki ki gane matarsa yake So ki bashi ba,dubi fa tamkar baya da wasu matan. Inna Bata jaba tayi Mata abinda ya kamata ta mayar da ita. Ranar data koma suka Bata girkinta Amma Saida Inna ta karo Mata da yarinya bayan masu aikinta. Kafin wani lokaci yaran sunyi bulbul sunyi kyau Kamar ba twins ba, suna wata hudu momin Kano ta haifi Faruq . Haka haihuwa ta budewa Ammi tayi gambon 'yan biyu Khadija Mai suna Inna ana ce Mata Nur wadda ke Aure a Germany wadda kukayi waya jiya tana kukan ba'a fada Mata ba Dan tana da tsohon ciki. Sai Baool da suhailat kin sansu sai su Jamal da Auwam suna london secondary. Mu dawo baya lokaci da za'a yaye mu Hajja ta dauke mu duka badan Inna taso ba ta hakura, da kyar Aishat tayi sati hudu aka dawo da ita saboda kuka takin cin abinci Kuma, Ni kuma naci gaba da Zama a can har na Kai minzalin sakawa a makaranta Abbie yaso na dawo Amma Alhaji Haroon ya Hana yace in dai makaranta ce za'a sakani wadda suke yin turancin ingila hakan Kuma akayi ban baro Niger ba Saida Zan tafi junior secondary school inda aka kaimu Nigerian Turkish a Abuja nida Aisha da Faruq. A can na hadu da Sameer ajinmu Daya da farko fada mukayi dashi sai Kuma rashin lafiya ta kamani shi da Faruq sukayi jiyyata a sickbay, tun daga lokacin Kuma muka dinke dashi,sai lokacin muka Kara shakuwa da Faruq mutane suyi ta mamaki idan Yana ce min yaya Mahmud sabida suna ganin ya fini garin jiki ma. Har muka Gama secondary muna tare da Sameer, lokacin da muka dawo gida gaba daya mun Gama makaranta lokacin muka Sami Abbie ya Kara Aure ya cike ta hudu, mace ce wayayya Aunty Sameera 'yar Minna ce Niger state bazawara ce da yaranta biyu na mijin baya Wanda ya rasu, sai kanwarta Sakina wadda ake Kira da Safna, lokacin bazata fi shekara Sha uku ba haka yarinya ce Mai saurin sabo Dan bamu fi sati biyu da dawowa ba muka shaku da ita sosai tamkar mun shekara Bata jin nauyin fada min komai saima Ina kwabarta gata da son kashe kudi Nan da Nan zata rokeni kudi, banajin komai saboda kirki Aunty Sameera Amma Ina ganin bekenta gurin tarbiyya gaskiya saboda ita'yar social life ce. Lokacin Dana tashi zuwa Niger taso ta bini na hanata har gurin Abbie ta Kai karata nace masa bazanje fa da ita ba dole ta hakura. A haka Muka share kusan wata hudu a gida ana ta processing na admission din mu inda Abbie ya hada harda Sameer ya Samar Mana a Oxford university ta London inda Aishat suka Bata physiology Ni Kuma business administration inda Sameer yayi Accounting, anan muka hadu da Mutuniyarki Dr Haseenah inda ita Kuma take medicine 'yar abokin Abbie ce tun haduwarmu ta farko ta ringa nuna min sign na soyayya Ni Kuma saina basar saboda Sam Bata cikin tsarin irin macen da nakeso, faruq sun bashi pharmacy haka mukayi ta karatu babu Kama hannun yaro ga Kuma Mr Johnson a gefe Yana kula damu, ba kowace semester ba Mike zuwa gida Muna level two hundred ne Akayi bikin Aishat Dan Kanwar Abbie na biyu Kinsan shi ya Abbas lokacin shima Yana PhD a Nan Auren Aishat ya taimaka Mana kwarai da gaske Dan abubuwa da yawa sunyi min sauki tunda Ina da gurin da inda zan aje abubuwana safe. Idan anyi hutu ban fiye zuwa Nigeria ba sai idan Hajiya Inna ta matsa,a kwai zuwan da mukayi nida Sameer nayi mamakin girman Safna ta Zama budurwa sosai, lokacin hatta abincina ita take dafa min Bata gajiya da Yi min hidima Saidai idan ban bukata ba haka mukayi ta rayuwa idan na dawo mu dinke idan Ina can muna waya Idan na samu sarari, muna shekarar karshe ne munzo hutu lokacin na Dan Fara gwada business zamuje Istanbul ganin wasu Kaya da nayi magana da kamfanin ta website dinsu a ranar na Fara ganinki keda Abba kina Masa tabara da girmanki Wai Baki son seat din da kike kinfi son saitin window, kin tuna wani yazo yace Miki kije gurinsa ki zauna shiya zauna a naki gurin Yana sanye da facemask?". Gyada Kai tayi alamar ta tuna "to nine". Gyara Zama tayi tana kallonsa "shifa wancen yaro ne ba kamarka yake ba". "Kin jini da yarinya to ke lokacin Yaya kike?" Zan nuna Miki hoton ki gani, Kinsan a ranar Saida Sameer ya biku tunda yaji Abban na fadin Jordan zai kaiki hutu shi Kuma ya wuce saudia. Sameer na biye daku har Saida ya tabbatar da inda kujene sannan ya dawo mukayi abinda zamuyi muka wuce London, haka muka ringa juyawa karatun da Dan kasuwanci. Wani hutun da mukazo harda Aishat mukazo lokacin tana da cikin farko na yarinyar data Haifa ba rai. A hutun ne Ubangiji ya bude min kofar nawa arzikin Dan Ina sokoto uncle Ishaq ya kirani a waya yace min ga condensed milk Nan wani abokinsa yayi order dinta Kuma kafin ya Kai kasuwa wasu Kayan nasa da sukafita mahimmanci suka shigo shine yake son ya sayar dasu a tsaye shine ya bani rancen kudin idan an sayar na maida masa da kudin. Kamar wasa aka kawo Madarar da Sameer muka shiga kasuwa muna yiwa mutane talla kafin sati Daya gaba Daya ta kare sai Kuma costumes ta ko Ina ana booking dink Kayan nan da nan uncle Ishaq din yayi magana da kamfanin suka saya lokacin harda powder milk yayi order shi yazo har Nan sokoton ya Kama min store sai daga baya Alhaji kakana yayi ta fadan Dan me za'a Kama hayar store Alhalin gasu Nan kamar banza hakuri uncle Ishaq din ya bashi yace saboda kada abun ya Zama fitina shi yasa Amma idan kudin sun kare ba za'a sake ba. Kafin wani lokacin abubuwa sun bungasa Kota Ina kudi shigowa suke Nan da Nan jari yayi karfi na ban mamaki, da kyar muka koma london saboda kasuwa ta kankama. Cikin ikon Allah muka Gama jarabawar lafiya muka tattaro muka dawo aka Dora daga inda aka tsaya, lokacin su Aishat suka koma India da zama.zuwa lokacin munyi wata irin shakuwa da Safna komai ta nema take zanyi Mata tunda kudi dai Allah ya hore,da taimakon uncle Ishaq muka dunga fita kasashen duniya sawo Kaya da bada aiki a kamfanoni. Kafin shekara biyu Ni kaina bazace ga abinda na mallaka ba lokaci Daya saida muka bude kamfanoni a cikin gida da manya manyan stores na Kayan abinci yawanci a states din mu na arewa muka Fara muke diban yaran mu na gida muke Kaiwa suna aiki sayar da Kayan mukayi musu tsarin kamar makaranta Dan harda Mai gadi idan suka dawo daga sallar insha'i Kuma ba Mai fita Saida lalura saboda yanda zamani ya Zama abinda ya Zama. A cikin shekara ta hudu ne komai ya fito Dan lokacin ne aka bude kamfanin riguna abaya a Dubai da materials da laces na garari aka bude na jewelry a India sai wasu Kuma a China wallahi precious Ni kaina bansan ta ina na samu wannan dukiyar ba nasan dai condensed ce sanadin. Kinsan har lokacin Sameer Yana bibiyar min ke duk inda kikayi makaranta Ina da masaniya ke har korar masu son Aurenki gaskiya mune Abu daya ne bamu da Hannu na yaron Nan Dan uwan momin Kano shi ne dai bansan inda aka haihu a tagayar ba. Wata zabura Zahra tayi, janyo yayi jikinsa. Wata ranar lahadi Ina Zaune a gurin da aka tanada Dan hutawa Ina ta faman aiki saiga Safna ta nufo inda nake da system a hannunta, tayi kwalliya sosai tunda Ni kaina nasan Ina Mata hidima Dan duk abinda na bawa kannena to tare nake Basu da ita Dan irinsu kudi ma saina Bata sau biyar ban Basu sau Daya ba. Sannu Tayi min tana zama daf Dani har breast dinta Yana Dan tabani, ta tashi daga gurin nace Mata saita shagwab'e fuska tana fadin Dan Allah na barta ta zauna kusa Dani wani Abu Zan nuna Mata, kamar rufin Baki saina kasa musa Mata cikin Jin Dadi ta furta Thank you dear. Wani website ta shiga ta Fara nuna min wasu tsala-tsalan sarkoki na gold masu Azabar kyau tana fadin na tayata zabe Wai Aunty Sameera ce zata saya Mata Wanda zata saka tanar bikin kawarta 'yar ministern Albarkatun kasa, ba zato mukaji salati daga bayanmu da sauri na juya sai Naga kawu saminu Yana tafa hannu Yana fadin wane irin rashin mutumci ne haka da yammacin Allah wata'ala na shigewa yarinyar daba muharramata ba irin haka Ashe Nima lalataccen ne. Saboda bakin ciki ko kallonsa banyi ba na dauki wayoyina nayi gaba, ko akan wani bana son a jefe shi da kalmar Nan bare Ni a kaina. Ina gurin Ammi sai gashi ya biyoni Nan muna Zaune ya shigo Yana huci Yana fadin har yaushe nayi arzikin da Zan wulakantashi Yana min magana kada na lalata yarinya tunda giyar nera na dibata shine nayi tahowata na barshi ga banza. Hakuri Ammi ta bashi ya juya ya fice Yana kananun maganganu. Fada sosai Ammi tayi min lokacin tace kada ta Kara Jin makamanciyar irin wannan magqnar a gidan Nan idan son yarinyar nake ayi magana ita Bata son kananun maganganu, na fada Mata babu wata soyayya a tsakaninmu da safna. Abu kamar ya wuce da dare saiga Kira daga Abbie a waya naje Yana nemana. AUREN HUCE HAUSHI AISHAT ISAH MUSAH Maman Fateenah BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM Page 92. _______Ba bata lokaci na shigo mota ni da Abubakar muka nufo gidan ban shiga dakin kai tsaye ba tunda naga kusan takalman mutum biyar, ina nan tsaye saiga uncle mustapha ya fito yana waya saida ya gama ya karaso inda nake tsaye yake tambayata meya farau tsakanina da safna ban rufe masa komai ba na fada masa duk abinda ya faru, girgiza kai yayi kawai cikin bacin rai yace na koma kawai ba saina shiga ba, haka na juya ba musu na nufi mota muka fice daga gidan, ni dai bansan yanda suka kaya ba tun daga lokacin wata magana bata kara tashi ba amma na janyewa safna sosai sai abinda baza'a rasa ba, amma dai ban fasa yi mata hidima ba duk abinda zanyiwa su yaran gidan babu bambanci da ita wani abun ma sai nayi mata ban yiwa su Batool ba tunda Aunty sameera samunta bai kaina su Ammi ba tunda suna business sosai ita da momin kano. Wani sabon salon da safna ta dauko kuma na zuwa part dinmu wai zatayi min gyara ko kuma ta dafa abinda tasan shine favourite dina ta dauko ta kawo min, nayi nayi ta bari amma saita ringa min magiya akan ita bada wata manufa ba takeyi, wannan yawan shige min din da tajeyi saiya kara mana shakuwa da kusanci sosai har ya kasance wata rana Dana dawo da dare na sameta tana barci a dakina sai abin ya daure min kai na juya na futa daga dakin na shiga part din Abbie na sameshi shida uncle mustapha saboda tare muka shigo gidan, kiransa nayi muka fito tare kafin na kaiga yi masa bayanin komai uncle saminu ya nufomu afujajan yana fadain su dai an haifo musu masifa a cikin zuri'a daman duk namiji mai aure aure hakance ke faruwa to azo aga ga yarinya can a dakina na gama lalata da ita. Wani wawan Mari uncle mustapha ya sauke masa yana fadin ban taba sanin kai mahassadi bane kuma masharranci sai Yau wallahi ka guji Fushun ubangiji a kanka yaushe ka zama haka haba ka rasa Wanda zaka ringa jifa da qazafin Zina sai dan zumunka kabar jaki kana dukan taiki, me yaron nan ne ya tsare maka? kullum idanunka da bakinka basa nufin alkhairi a kansa, to ka sake wata dabarar wannan batayi ba tun nagariba muke tare dashi a mabera sai yanzu muka rabu ya nufi nasu gurin Nina na shigo kiran da Alhajin yake mini,ko maganar bamu fara ba ya shigo ya kirani kafin ya kaiga fada min dalilin kiran kazo kana yiwa mutane shirme da girmanka da komai to kaddara ma abinda kake fadar gaskiya ne bazaka iya daukar matakin da saidai a wayi gari a ga ka dauka ba,amma ka zama jakadan yada munafurci da son hada husuma ka yiwa kanka fada wannan ba rayuwa bace,ka bawa shedan dama yana walagigi da kai haba meka nema ka rasa da har samun dan cikinka ze tsone maka idanu ne ayeh?. Tunda uncle ya shara masa Mari ya dafe kunci bai kara dago da Kansa ba, bai kuma kara tofa wata ba yayi min wani kallon qasqanci yayi gaba, tsaki uncle mustaphan yayi yana fadin wahalallan banza Wanda hassada ke dawainiya dashi, gurina ya juyo yana fadin kayi hakuri Mahmud kaji babu wani Abu na batanci daze sameka in sha Allah, lokacin na fada masa safna Dana gani tana barci a bedroom dina, yayi mamaki kawai da gaske tare mukaje amma abun mamaki bata dakin ko alamar mutum ya kwanta a gadon babu, dan murmushi yayi kawai ya juya yana fadin take care. Wallahi a Daren banyi barcin kirki ba saboda damuwa na rasa mena tsarewa uncle saminu ne yake bibiyata da irin wannan Abu na bacin suna? Sai kuma zargin da hadin bakin wani ake min wannan bita kullin. Naso na fadawa Ammi amma saina share, amma naje har part din Aunty sameer, tana ganina ta tarbeni da murnarta asual muka gaisa kafin nayi korafin abinda ya kawoni Auntyn ta rigani da fadin kasan kuwa jiya mutuniyar a dakinka barci ya dauketa tana jiranka wai tayi maka coconut drink ta zauna zaman jiranka saida naga shirun tayi yawa na tura safara'u yarinyar da take min aiki ita ta taso ta, ai kuwa nayi mata fada sosai irin haka ai sai zargin wani Abu ya shiga dan haka nace ta saina shiga part din tunda duk maza ne, wallahi precious duk saita daureni da jijiyoyin jikina na rasa abin fada haka nan na fito daga part din nata. A cikin satin tafiya ta samemu nida sameer muka tafi, a lokacin shares na saya a manyan kamfanin motocin duniya na zuba large share sosai a lokacin ne na canzawa kannena mata sabbin mitoci abinda ya ruda da yawa daga yara mata na family din mu 'ya'yan da iyayen sukayo min caaaa da kowa burinta ace muna tare da ita sai kuma safna ta fara fuskantar yan hamayya daga cikin dangin saboda ta saje da yaran gidan babu bambanci. Lokacin da muka dawo ne aka fara magabar bikin Gambon mu Khadija wadda ke Germany. Aishat ce ta bani bill na duk abinda suke bukata ni kuma na bawa sameer nace yaji dasu, sun kace raini a bikin nan dan komai unique Aishat ta sawo musu a Dubai da sukaje tunda dai kin ganta 'yar gayu ce ta bugawa a jarida kuma duk abinda ta sawo babu bambanci tare da safna tayo shi hatta da gold na mahakatan kudi saida aka sawo da ita. A wannan bikin ne idanun safna suka bude fiye da dah, ta zama babbar yarinya tayi sabbin kawaye tunda ta shigo gari ga motor ta alfarma tana shiga ga suturu na kece raina ga 'ya'yan banki basa mata wahala. A cikin wata hudu tayi wani irin fice a sokoto sai kuma lamarin ya zama marar tsabta ta shiga sabgar samari 'ya'yan Hutu, koda yaushe bata zaman gida ga yawan kawo samari gida barkatai, sabanin yaran gidan,dana samu Ammi da maganar ta takamin burki tace babu ruwana ai mai gidan da sauran yayuna suna gani, haka na zuba ido ina kallo amma bana jin dadin abun ko banza ina kaunar safn tunda zuciya tana son mai kyautata mata,amma dole na dauke idanuna nayi kamar bana gani mataki daya na dauka kawai na saina daina shiga sabgarta na daina tura mata kudin da nake tura mata special na daina mata komai hatta da tsaraba idan nayi tafiya na Dawo wadda sameer ke assasa ayowa yaran na fada masa a daina yi da ita, abun saiya dameta ya tada mata hankali duk yanda tasan zatayi mu hadu ma nayi blocking dinta. Previous Ashe wannan matakin shine ze zaman mafarin faruwar Marsalar shine zaren da aka kulla kaddarar tawa dashi. Ashe shine sanadin da za'a samu sabani mai girma Wanda yasa mahaifiyata barin gidan aurenta na tsawon watanni ya dagula rayuka da yawa ya kawo sanadin da aure ya mutu murus. *_ AUREN HUCE HAUSHI_* _AISHAT ISAH MUSAH_ Maman Fateemah Da sunan Allah mai Rahama Mai jinqai salati da Daukaka da Aminci su tabbata ga shugaban mu Annabin Rahama Muhammad s.a.w.w. Page 93. _____ Precious wato Ranar wata talata 1/6 ranar da ta Zama baqar Rana a gareni da duk wani Mai kaunata, ranar da aka sak'a zaren mummunar kaddarata ranar data rikita Mana zaman lafiya ta Zama ranar da wani ko wasu suka dagula lissafin mahaifina ya Zama sai yanda akayi da shi dama duk wani Mai fada aji ya Zama soko marar katabus. Tunda na tashi da misalin hudu da rabi na asuba yanda na Saba Sam najini a wani yanayi Sam banajin Dadin jikina ga faduwar gaba wadda da ita na tashi har nayi nafilolina na wuce masallaci gani Nan dai, sai da nayi karatun Qur'an sannan na samu relief na faduwar gaban, a ranar ko breakfast kasa fita nayi sai Sajjad autan momin Kano ya kawo min tunda Ammi Bata barin yaranta Mata shigowa part din mu ko Mai aiki Bata Bari su shigo gyaran part din ma maza ne keyi Kuma ko su zayyan basa shigowa gidan suna waje Bata hana suyi min aiki ba Amma Banda shigowa gida. Haka na zauna Ina ta juye-juye a gado na rasa me yake min Dadi ga Sameer lokacin ana ta shirye-shiyen bikinsa a yanda mukayi ma a ranar Zan shiga Kano Dan na tura su naseer a sakawa gidan Dana Gina Masa furnitures tunda komai yazo, ban fito ba sai lokacin sallar Azzahar daga masallacin bangaren Ammi na wuce Ina Nan har la'asar tayi tambayar duniya akan meya sameni amsar Daya ce nake Bata ba komai, haka ta hakura ta kyaleni Amma itama sai Naga ta rage walwala. Daga sallar la'asar ban dawo gidan ba Saina wuce mabera gidan Hajiya Inna a can na zauna nayi ta aikina har kusan Tara da rabi, nida zayyan ne kawai muka taho shiya tuk'o motar Sai goma muka shigo gidan saboda mun tsaya an sawo fruits saboda Dana shiga kitchen Naga sauran kadan Dan Apple da pear ma babu, ban shiga part din Ammi ba Amma na Kira su Batool nace suzo su shiga da kaya ciki. Zayyan ya wuce Nima na shige ciki Dan har lokacin ji nake kamar Wanda aka yiwa duka, na gaji matuk'a. Ina shigowa naji atmosphere din dakin ya canza daga daddad'an kamshin turarikan daki sai wani irin kauri marar dadin shaqa a dakin, ban zauna ba gudun A/C din parlour din na Kara na kunnu electric din da ake zuba masa turaren daki, tun a parlour na cire Kayan jikina wannan kuma normal d'abi'a tace ban fiye shiga bedroom da Kayan jikina ba idan na fita dasu Saida na cire na saka a washing machine ya Zama daga ni sai boxer short na wuce bedroom dina da niyyar nayi wanka na hada coffee na Sha tunda Ina da coffee maker a daki. Ina shiga ba zato ba tsammani naji an rukungumeni gaba daya, sautin muryar Safna naji na fadin Dan Allah kayi hakuri,wallahi ka sakani a cikin mawuyacin Hali ka tausaya min idan ka fita a rayuwata mutuwa zanyi wallahi, Kai kadai nakeso nake muradi a rayuwata, kaji tausayi na, wallahi duk abinda kakeso Zan baka ko kaina Zan baka kaji dadi Dan nasan kana dasu da yawa Nima kazo wallahi kayi abinda kakeso Dani. Rudewa nayi gaba Daya na rasa in da Zan saka kaina, wani abune da bantab'a zaton faruwarsa ba ya sameni bagatatan, kokarin raba jikina da nata nake kokarin Yi Amma kamar Wanda akayiwa dabaibayi a hannunsa sai Kara shigewa jikina take ga ta hade kirjinmu sai goga min jikinta take cikin kukan dana kasa tantance wane iri ne, da kyar na iya kokartawa ba juyar da ita ta tafi zata fada Kan gadona banyi aune ba naji ta fizgoni gaba daya na fada saman kanta kafin nayi wani yunguri Dan tunda na shigo na shaki warin Nan na kara rasa kuzarina, naji an kwalla ihun kuka a saman kaina, abinda yayi saving din kenan daga rikon da Safna tayi min, da sauri na mirgina na tashi, sai lokacin na Farga da suturar dake jikinta, wata rigar barci ce marar Albarka duk breast dinta a waje. Ga hawaye bibiyu na bin fuskarta gashin kanta Mai Kama da hatsin bara ta barbaza shi. Aunty Sameera na gani ta Dora hannu a ka sai kuruwa take yi, da gudu Safna ta tashi tana wani gunjin kuka tana fadin , wayyo Allah Aunty ki taimaka mini wallahi ba laifina bane barazana yake mini Koda yaushe ya lalata min rayuwata batun yau ba Aunty na shiga uku waye ze aureni a haka. Cikin kuka itama aunty ta Fara fadin wallahi Mahmud kaci Amanarmu Dan kana da dukiyar da bazamu iya ja da Kai ko mahaifinka ba shine zaka ringa ketawa yarinya haddi, haba Ashe shi yasa taketa rama a tsaye,wallahi banyi zatonka a haka ba, aiko kana bin Mata Ina ga ka d'agawa yarinyar Nan kafa marainiyar Allah, Kuma inda mutumci ai zaman kanwarka take Dan haka wallahi dole ka aureta tunda Kai ka Fara saninta 'ya mace bazan yarda ba da wannan cin mutuncin da tozarci. Tunda na samu kaina jikina keta faman tsuma ga wani uban jibi Daya rufeni duk kuwa da sanyin A/Cn da yake ratsa dakin, ni dai banga shigowa ko motsin uncle saminu ba sai ganinsa nayi a gabana jikinsa na tsuma baiyi wata -wata ba ya shareni da mari Yana fadin munafuki maci Amana,to yanzu ina masu cewa karya ake maka? Sai suzo suga ta'asar da kake aikatawa da idanunsu tunda suna ganin qazafi akeyi maka, Daman nasan idan zabuwa na yawo kere na yawo wata Rana zasu hadu, nasan za'a rina munafiki wallahi kaji kunya, Zina a cikin gidan ubanka wannan masifa har Ina Allah ya Kara Basu ne da Aure -Aure ba,kadan ma suka Fara gani. Hannun Safna Aunty Sameera ta Kama tana sharbar kuka suka fice daga dakin, saida suka wuce uncle saminu yayi wata dariya Yana fadin. Yaro baisan huta ba in Bai taka ba, ba dai kace bazaka auri Asma'u ba kadan ma kenan sokoto Nan sai tafi karfin zamanka mu zuba kasa Ido wallahi saika Zama mujiya cikin tsintsaye duk kuwa da arzikin da kake yiwa mutane d'agawa dashi dariyar ya qarayi ya Sara ya fice daga dakin. Aunty Sameera na fita part din Ammi ta nufa ta shiga Danna bell ba k'ak'k'autawa Batool ce ta bude tunda itace ke kasa tana zuba Kayan dana kowa a fridge. Da sauri ta bude Jin kukan dake tashi daga wajen, dai dai da shigowar Ammi cikin parlourn tunda itama taji Karan door bell din da akeyi ba sassuci. Da sauri Ammi ta karasa shigowa tana tambayar Aunty Sameera me yake fatuwa? Cikin kuka riris Aunty Sameera ta bude bakinta da kyar ta Fara fadin . Ammin Batool Mahmud ya lalatawa Safna rayuwa wallahi a gado na samesu shida ita tana ta rusa kuka da magiyar ya barta Amma abun yaci turn Ashe Daman haka yake Mata ta kasa fada sai Rama take a tsaye na shiga uku Yaya zanyi da wannan abun kunyar? Kasa ko motsi Ammi tayi haka batool ita abun Daya fi daure Mata Kai duka yaushe hakan ta faru kamar a cikin Shirin film to da yaushe ya shigo gidan da har wannan dogon labarin ze wakana har haka, Amma saboda tarbiyyar da akayi Mata yasa Bata tofa ba ta zubawa sarautar Allah Ido Amma ta yiwa abun question mark. Innailaihi wa innailaihi raji'un, abinda Ammi ta dinga maimaitawa kenan ta kasa furta ko kalma Daya tamkar an saka padlock an rufa bakin da zatayi wani sharshi. Uncle Saminu ne suka shigo shi da Abbie sai Momin Kano wadda ranar girkinta ne Dan a can part dinsa na bangarenta ya iske shi shine ta biyo su ganin hankalinsu a tashe. Da ganin yanda Abbie ya shigo hankalinsa ba a karamin tashe yake ba Fadi yake Ina safnar take maza a Kira doctor innailaihi wa innailaihi ilaihi raji'un , wannan wace irin musibace ta shigo gidana?.Dan cikina ya aikata irin wannan rashin Albarka a cikin gidana, Ina Mahmud din take? Ita Ammi rasa abin cewa tayi ji tayi kamar an Dora Mata bulo inci Tara a kanta ga kirjinta yayi Mata nauyi, sahal ne ya nufi kofar fita da sauri saboda gaba daya suka fito Jin kuka a part dinsu Suma abin ya Basu mamaki Dan a gaban Sajjad na wuce Yana waya, Amma a cikin abinda Bai wuce mintina goma ba wannan kurar ta tashi, tun daga parlour har bedroom suna bude Amma bana ciki dole Sajjad ya koma ya fadawa Abbie bana nan, abunda ya Kara tada kura kenan uncle saminu ne yayi tsagal ya Fara fadin to Daman ta Ina ze tsaya yanda yayi wannan abun kunyar Zina har cikin gida duk wadda ake a waje Bata wadatar ba sai an yiwa yaran cikin gida fyade. Nan da Nan Abbie ya Kara tunzira ya shiga fada sunce yayi fadan da Basu tab'a gani yayi ba Fadi yake wallahi babu shi babu ni ya cireni daga cikin y 'ya'yansa tunda na fita zakka naje ya sallamani gani ga duniyar Nan idan giyar kudi ke rudata Ina Dan k'aruna yake. Jin furucin Abbie yasa uncle saminu tarar numfashinsa Yana fadin idan ya tafi ai yaci bulus a Nemo shi yazo ya aureta dole, idan aka barta a haka ai an zalunceta gaskiya saboda an fita gata, ai tun faruwar wancan abun nace maka ga Asma'u Nan na bashi Amma lokacin saika nuna ba haka ba in da anyi Masa Auren Aida hakan Bata faru ba, da ba'ayi maka halin Dan akuya a gida ba, idan kayi sake sai an Fara shigo da shegu ma cikin gidan Nan. A cikin hasala momin Kano tacewa uncle saminu haba wace irin magana kake fada haka Bai Dace ba Dan zumunka meze Hana abi abun a hankali ita safnar yarinya ce karama da za'ayi ta babatu tayiwa mutane bayanin abinda ya faru Mana. Dan me za'ayi ta dorawa mutum Daya laifi ita meya kaita part dinsu a irin wannan lokacin ayeh?. Cikin tashin hankali uncle saminun ya taso Mata kamar ze daketa Yana fadin. To kice da hadin bakinki yake ketawa yaran mutane haddi kenan, Dan munafurci bazaki Bari ayi Masa hukunci ba tunda Yana kawo Miki abin duniya idan ya lalace Baki da asara Dan kishiya ne ko?. Momi Bata barin ta kwana ta zaburo zata gaggaya Masa magana Abbie yayi Mata Karan tsaye, kofar fita ya nuna Mata alamar ta fice, zata bude baki tayi magana Ammi ta girgiza alamar tayi shiru kawai. Ammin ma juyawa tayi zata bar gurin cikin kaushin murya wadda tunda suke Bai tabayi Mata magana da makamanciyarta ba. Ki fad'awa danki duk inda ya shiga ya fito yazo Ina nemansa idan Kuma ba haka ba wallahi da kaina Zan Mika case din Nan human right kinji na rantse. Yanda Bata tofa ba lokacin da suke babatun yanzun ma wucewa kawai tayi tana jiyo yanda Abbie din ke kwantarwa da Aunty Sameera murya Yana Bata hakuri ita Kuma tana daga murya, Batool ma barin gurin tayi. Hummm previous Ashe kuka Rahama ne bansan haka ba sai a ranar, Dan naso ace Zan iya yinsa konaji sassuci Amma Ina Idanuna sun soye babu alamar hawaye sai zafin zuciya kawai nakeyi. Tunda suka fice daga dakin Nima na zura jallabiya na dauki key nayi waje tunda na fita na rasa Ina Zan nufa nayi ta yawo a cikin gari har sha biyu da kusan minti arba'in da biyar, Dana gaji da yawo na shiga wata primary na yiwa Mai gadin gurin bayani Ina son na yada zango ni matafiyi ne, wallahi haka na kwana ko gyangyadi Bai kamani ba, ban taba tunanin haka akeji idan an yiwa mutum k'azafi ba sai da yazo kaina, ban taba tunanin Alkhairi Yana Zama mugunta ba sai a kaina da Safna ban taba hasasota a haka ba ko cikin mafarki, shi yasa hausawa ke fadin idan kaga mutum a Rana barshi a ranarsa da hikimar da tasa aka aje shi a ranar. Bayan nayi sallar Asuba gida na nufo ban shiga gurin Ammi ba part din mu na nufa Ina zuwa dakin naji wani irin tashin hankali kamar lokacin abin yake faruwa, a parlour na zauna Ina sakawa da kwancewa na rasa tudun dafawa, wurin bakwai da rabi naji ana tab'a kofa ban motsa ba ban Kuma bada izinin shigowa ba, Faruq ne shida saif kanin Ya Abbas ne suka shigo Ina Zaune Ina dafe da goshina kaina na matukar Sara min, daga kallon farko da nayi musu ban sake daga idona na kallesu ba. Cikin nuna damuwa Faruq ya tambayeni Wai meya faru ne jiya shi Yana barci baisan wainar da aka Toya ba, Saida Asuba sahal ke fada Masa abinda ya faru, ta tafasa ban iya tofawa ba Dan bakin cikin dake ci min zuciya haka ya hakura ya tashi amsa Daya na bashi nace masa babu mutumin da ze iya yi Mana shari'a da duk Mai hannu a cikin Lamarin sai Allah. Wurin goma Kiran Abbie ya riskeni banyi kasa a gwiwa ba na nufi part dinsa, Ina zuwa na samu Abbie ne da 'yan uwansa sai Safna da Aunty Sameera. Ina shigowa Safna ta fara share hawaye, Abbie na fara gaishewa Wanda Ni dai da kunnena banji ya amsa ba, sai su Uncle Mustapha nayi musu gaisuwar Jimla. Kamar jira ake Ina Zama aka Fara surfa min fada babu ji babu gani, Auncle Mustapha ne kawai ke supporting dina Yana fadin kowa ya lafa a tambayi ba'asin meya faru ne Amma babu Wanda ya saurare shi, duk yanda yaso ayi adalci a cikin Lamarin abin ya gagara, Dan har gaban Abbie mukaje zanyi Masa bayani Amma ya tashi ya bar gurin abinda ke daure min Kai yanda uncle saminu ya Zama shike bada Umarnin abinda za'ayi Dan yace aure nida Safna babu fashi haka aka tashi baran baran da uncle Mustapha inda ringa fada Yana fadin an fada musu mutane jahilai ne a tsaya ayi abinda ya kamata Mana sai a dauki son Rai a Dora ga gaskiya Amma ana neman taketa da gangan Dan wata manufa ta daban, a gaba uncle Mustapha ya sakani mukaji wurin Ammi Abu mafi bani tsoro Kinsan kallona Ammi batayi ba duk yanda uncle yayi Mata bayanin irin nasa hasashena wallahi Sam ta nuna Bata bukatar jin komai daga bakina haka muka fito Ina rangaji ga Abu goma da ashirin ya tare min inda nake tunanina Zan samu tallafi da tausaywa sai Kuma na Sami aka sin haka, Bari nayi Miki taku ta Mata a lokacin fa kakana Alhaji sa'id ya rasu, nasan da Yana Nan abun baze Kai haka ba. Kiran sallar da aka kwalla shi ya tsayar da Mahmud da dogon labarin da yake bawa zahra, kallon fuskarta yayi sai ganin hawaye yayi suna bin kuncinta Bai hanata ba ya dai gyara Mata kwanciya a cikin jikinsa duk da lokacin sallah yayi. AUREN HUCE HAUSHI. Maman Fateemah. 09061432339 Or 08055362975 Page 94. _______ "Pls previous ki daina kukan Mana, abun Nan fa wani past event ne ya Riga ya wuce kawai dai Ina fada Miki irin Qalubalen Dana fuskanta ne a rayuwa da Kuma irin yanda na koyi iya mu'amala da jama'a Kinsan masu iya magana na cewa na daka baiyi kallon waje ba, to Nima hakan ce ta kasance dani da ba'a Sami wannan matsalar ba da wata kila harna koma ga Allah bazan San wasu abubuwan ba na yanda wasu suke rayuwa, previous na koyi darasin rayuwa yanda bakina baze iya misalta Miki ba, tashi muyi haramar sallah idan Allah ya kaimu wani Daren saina karasa Miki sauran labarin dan nasan daga safe har zuwa dare babu lokacin Zama kinsan Hausawa sai a slow su da gidan Amarya". Ya fada Yana dariya itama duk da zuciyarta babu Dadi Saida taurmusa. Tare sukayi wanka ya wuce sallah itama ta Fara nafila kafin a tayar. Har gari yayi haske Bai shigo ba itama azkar tayi da karatun Qur'an, tana kokarin cire abayar da tayi sallah ya shigo, a hankali ya tako har inda take tsaye Yana zuwa ya Ida cire Mata Yana Fadin. "Meya hanaki barci? dubi idanunki barci ne fal a cikinsu da gani". Dan narke fuska tayi tana Masa wani kallo, dan smile yayi Wanda yake karawa kyakykyawar fuskarsa kyau. "Yaya ko da labari? Nasan jirana akeyi ko kuma gaisawa zamuyi ne?". Kafada ta make irin yanda Yara masu kiwa sukeyi idan suna hannun iyayensu. "Nifa Karatu nayi fa shi yasa ban kwanta ba gara na rabauta da Alkhairin dake cikin safiyar". "Gaskiya ne sayyada". Ya fada Yana dariya, itama murmushi tayi, sunyi barci har kusan Sha biyu sannan suka tashi wanka suka shiga tare sun Jima sannan suka fito suka shirya ita cikin rigar material data Sha beads work shi Kuma cikin shada geezner boda style sai baza kanshinsu suke yi. Lokacin da suka sauko su Aunty zilai suna kitchen ita da binta suna girkin rana, fitowa sukayi suka gaisa sannan suka koma bakin aikinsu, bayan sun Gama break din ne suka dawo second parlour inda Mahmud ya dauki remote control ya canza Tasha daga Tauraruwa zuwa sport news inda ake highlight na kwallayen da akayi. Kasa hakuri Zahra tayi ta jefa Masa tambayar da take ci Mata tuwo a kwarya. "Meu Amor Wai Dan Allah me kikeji idan kana kallon Ball din Nan?". Dan kwantar da kansa yayi a gefen kafadarta Yana shaqar kamshinta Wanda yake sakar Masa da kasala. "Yanda kukeji idan Kuma kallon series ko Kuna karanta novels Dan nasan daidaikun mata ne basa wannan sana'ar, Dan Batool har kwace wayarta na Sha yi lokacin tana secondary, to muma haka muke Jin Ball a cikin ran mu". Jin jina Kai Zahra tayi tana farin "Na gane yanzu kam, ai karatun novel duniya ne Dan Idan book ya dauko Dadi wallahi bana kaunar abinda ze tasheni daga karatun". Wata sinsina ya yiwa wuyanta tare da hura Mata iska ba kunne, hade jikinta tayi tana nuna Masa bangaren kitchen da Hannu. Ido Daya ya kashe Mata. To Nima hakan nake Jin kwatankwacinsa akan Ball din". Sun jima a gurin suna Hira har aka Gama labaran Ball din. Baki ne suka Fara zuwa danginsu na Dangen shuni Mama Bilkisu ce tazo Bata k'asar akayi bikin nasa, da gani sunyi saboda dashi sosai har yaranta, mace 'yar gayu ta ajin karshe ga sakin fuska Dan kamar ta goya Zahra sai fadin Masha Allah takeyi Nan da Nan aka cika gabansu da Kayan tarbar Baki Dan Aunty zilai expert ce a wanna fannin. A cikin hirar da sukeyi ne Zahra ta gane suna k'asar Canada Latin America ita da yaranta inda mijinta yake ambassadorn Nigeria, Mahmud Bai samu fita ba sai lokacin sallar Azzuhar sannan ya samu ya shiga gari can family house nasu, Nan suka yini da Mama Bilkisu mace ce wadda tasan kanta Dan Mahmud na fita bayan sunyi sallah sunyi lunch taja zahra bedroom dinsu na kasa ta zaunar da ita ta ringa koya Mata dabarun yanda zata rike mijinta ita wani abun idan ta fada sai kunya ta rufe zahrar ita kuwa babu ruwanta sai dai tace ki dai Kade kunne ki kwashe a gaba ze amfane ki, sai kusan magariba suka tafi Zahra ta saka Aunty zilai ta hada musu Kayan biki masu yawa sannan ta bawa 'yan matanta designers din turarika da Dubai abaya tunda kamar gorinsu akayi a gurin kayansu, da kyar Mama Bilkisu ta yarda suka karbi Kayan Dan fur cewa tayi sunyi yawa sai an rage Saida Aunty zilai ta saka Baki ta barsu suka karba. A nan falon sukaci gaba da Zama suna hira sai lokacin magariba su Aunty zilai suka wuce part din su ita Kuma Zahra ta koma sama, har akayi insha'i Mahmud Bai shigo ba, Zahra na Zaune ta tsula gayunta cikin English wears maroon Mai duhu tayi rolling da farin veil touching din dake jikin coat din sama ta saka maroon din lipstick a Dan bakinta Sai tayi wanu irin kyau kamar ka dauke ba b'oye tana fesa turare wayarta ta dauki kida Mai dadi da sauri ta nufi wayar Kiran na magaji ne, tunda ringtone dinsa shima daban. Sallama tayi Masa Bai Sami damar Amsa sallamar ba ya Fara fadin. "Allah ya sauwak'e wallahi idan mutum neman taimakon emergency yake a gurinki Allah Saiya mutu, bakiga missed calls dina ba sun kai dari ina ga, tunda zafin abun nake nemanki Amma ba amsa na Kira oga yace min tun Rana baya gida haba ki daina nesa da waya ai abokiyar Hira ce ko Dan kina tare da Aunty zilai ai kin Gama samun abokiyar hira". Katse Masa zubar da yake tayi. "Haba Dan Allah ayi mutum idan ya Fara magana ba comma ba Full stop. Ka fito a mutum sak ka fada min abinda zaka fada ba kayi ta Jan dogon labari ba". "To yau dai ana idar da sallar la'sar Abba ya rangada daurin Auren Salma da Hameeda Dan yanzu haka Salma har sun dira a Miya, can Aka kaita wani tsohon saurayinta ne Ma'aikacin Nefa da yake yawan zuwa gaida Abba kusan duk sati duk da basa tare da ita shine yazo jiya suna bin gidaje raba bill din wuta, Abban yayi Masa tayin Auren salmar Amma fa Saida ya fada Masa gaskiya idan ze iya yace babu komai Yana so a haka. Yaje ya fad'awa magabatansa, daman an fadawa gidansu mai son Hameeda suzo da sadaki shine ya daura musu Auren yau yace a tafi da Salma gobe kayanta zasu biyota, taimakon da Allah yayi Mata Abba ya Basu gida a can Miya din tunda yana da gidajen haya a garin kuma kwanaki akayi modernizing dinsu. Ita Hameeda ce aka bashi hakuri zuwa wani satin ta tare tunda mijin baya Nan Yana kaduna gurin aiki, to kinji fa abinda Zan fesa Miki kike min surutu, yanzu haka Ammah dasu Aunty Hassana da Hajiya Turan gidan maji dadi suna can, ki Bari kawai saina shigo da labari wallahi buhu-buhu Zan shigo in zazzage Miki su ai anyi dai abun kunya wallahi Ashe duk lullubin biri aje yiwa mutane ai Ni Ya Mahmud ya Gama min komai kindsan bibiyar Salma yasa akeyi Masa Ina gida jiya ya kirani yace min sunyi magana da Abba Zan raka bilyan gidan malam Jos, Ashe asibitin da aka kwantar da Salma ya tura ya daukota Ni Kuma da nasan gari nayi masa jagora wallahi sanda ya kirani ya bani address din asibitin Nasha mamakin me zamuyo wannan asibitin ke........" Wayar taji an zare daga kunnenta da sauri ta juya Dan kamshinsa ya fada Mata shine Amma koda Wasa bataji sanda ya shigo ba. Wayar ya duba yaga magaji ne kunnensa ya Kai wayar Yana fadin "ka Adana sauran bayaninka zuwa safe". Ai kafin ya Gama fada Magani ya kashe Kiran Yana rike bakin Al'ajabin Zahra Daman Yana Nan ya zage yana ta an tayo magana. Wayar ya aje yadan matsa baya Yana Kare Mata kallon ta burge shi matuk'a Dan ji yayi kamar ya sakata gaba yayi ta kallo, hannuwa ya bude Mata alamar ta shigo ya rungumeta, sun Jima a tsaye Saida yaji kamar kafafuwansa Bazasu iya daukarsa ba sannan ya Dan zameta suka zauna a gefen gadon, da kyar ya tashi ya shiga wanka Bai wani Dade ba ya fito ya saka Riga armless da wandonta three quater na Adidas dai tunda sune best kamfaninsa gurin sport wears, tana makake a jikinsa suka fito parlourn farko na sama In da aka aje musu dinner dinsu, sakwara ce da miyar Agushi sai black tea Mai Kayan hadin star anise a ciki, Saida sukaci abincin sannan suka dawo cikin parlour na biyu suka zauna duk ya kanainaye ta ya hanata sakat, nema yake ya ruda Mata lissafi ita Kuma Alla Alla take dare yayi ya karasa Mata labarinsa. Saida ya mila ya mile Dan kansa ya Dan ragewa kansa zafi sannan ya fara fadin "Bari muci gaba ko" Kai ta gyada Masa Dan ita kam ba baka sai kunne. "Wato precious Naga gararin rayuwa kowa fa juya min baya yayi babu Mai saurarena sai uncle Mustapha da Batool kawai, abin baqin cikin Wai a tsaya nayi bayani ma abun ya faskara ta ko Ina babu sauki a haka Muka kwana uku idan Kika ganni lokacin Zaki tausaya min a lokacin dukiya ta dai batayi min amfanin ba tunda Bata Hana an wulakqanta ba, a ranar na hudun na tsunci maganar Wai a ranar za'a daura mini Aure da Safna abunda ya yamutsa min lissafi kenan cikin tashin hankali na shiga wurin Ammi wallahi precious Ina shiga Ammi ta Mike tabar parlourn da sauri nabi bayanta Ina hadata da Allah akan ta tsaya taji gaskiyar abinda ya faru Amma kinsan me tace min? Wai fa cewa tayi inje inyi abinda nake so tunda karana yakai tsaiko gani ga rayuwar Nan tunda fasadi na zaba duniya tafi Dan bagaruwa jima, wallahi a lokacin ji nayi kamar na mutu na huta nakeji,ga wani irin Abu da nake jinsa a jikina, precious wallahi Addu'oin da nake na azkar lokacin da kyar nake yinsu,Dana fito mabera na nufa naje yau dai na fada mata halin Dana tsinci kaina a ciki tunda nasan Bata San wainar da ake toyawa ba, Amma kinsan abun mamakin da tashin hankali itama sammankal duk abun iri Daya ya Zama Bata saurareni ba karshe ma maganganu ta yarfa min masu zafi ga shi Daman wani Abu na min sukuwar sallah a cikin kaina, Nan da Nan naji wani bacin Raina ya qaru ban baro gidan ba Saida naci alwashin saina Bata mamaki kuma kozan mutu saina nemoki duk inda kike a duniya Kuma a dakinta a gadonta Zan Fara saninki 'ya mace, kadafa kice Wai bani da masaniyar inda kike hummmm a'a ana bibiyar min ke ciki da waje, kinga lokacin Dana fito daga parlourn Hajiya Inna ko takalmi kafata babu banbi takan motar Dana shigo ba na Fara tafiya a kasa wani Abu Daya bani mamaki a lokacin precious wallahi Ina ganin kamar mutane basa ganina tunda konaje kusa da mutane bana ganin alamar sun San da mutum a kusa dasu gani ba boyayyan mutum ba, haka na dosa wata irin tafiya tamkar kad'ani akeyi kuma tafiyar wata iri ce Mai cin dogon zango a cikin lokaci k'alilan a cikin abinda Bai wuce minti arba'in ba ni dai sai ganina nayi a talatar mafara na fuskanci mutane suna ganina a lokacin Tunda Ina wuce Ina Jin ana fadar bawan Allah ko daga Ina? haka na dinga tafiya wlh ko gajiya banayi Dana baro cikin gari naji kamar Ina Jin barci na kwanta a wurin wata bishiya, to Ni dai daga lokacin bansan kuma Yaya akayi ba ni dai nasan na farka na ganni a asibiti ta tare da Abubakar wlh nayi zaton ko sokoto na dawo sai Kuma Naga bakin fuska su Malam Abu mafi daure Kai ganin Abbanku da nayi sai Lamarin yafi karfin Dan karamin tunanina na wancen lokacin Dan nasan wannan abun wani connection ne daga Allah Daya hadani dasu yasan abinda nake rokonsa dare da Rana, precious nayi dawafi a dakin Allah na Kai mutane suyi min Addu'a akan wani Abu da nake nema duk a kanki Dan Ubangijina kadai yasan yanda ya jarabci wannan zuciyar da soyayarki tun Baki San meye soyayyar bs, Kinsan Kuma shi maji rokon bayinsa ne Kuma mafi tausayin masu tausayi mafi jinqan masu jinkai Naga Ijaba, bana inkari da lamarinsa Amma na Kara samun yakin Dan Rahamarsa ce ta lullubeni ya kawo Habib ya ganni a wancen lokacin, ga wata sabuwa Ina Jin maganar mutane Amma Ni Kuma bana iya magana, lokacin na shiga tashin hankali ba kadan ba Dan ji nayi na koma mutummutumi, asibiti sunyi iya abinda zasu iya suka sallameni Baba malam da Abban ki su suka dunga Fadi tashi akan lafiyata Dan abun babu dadin ji na shiga wata irin rayuwa lokacin na Kara gane mahimmancin lafiya da tasirin Addu'a, su Habib su sukayi jiyyata a dakin soro na gidan malam har Allah ya bani lafiya, lokacin ne Abubakar ya fada min ai aikin da yake komai na tafiya dai dai, dan dai lokacin kina syprus to Nima ganin nesa tazo kusa saina nemi gurin Zama naje Bauchi nayi duk abinda ya kamata akan layikan waya da dasu system da credit card na bank da duk abinda ya kamata banyi kasa a gwiwa ba na Kira Sameer da Bilyaminu muka zauna dasu a dakin Dana Kama a hotel, Abu na farko Dana Fara shine kad'a musu warning akan inda nake kada naji kada na gani duk da Sameer ya fada min hankali fa ya tashi na barina gida gashi uncle saminu ya assasa daura min Aure da Safna, banji komai ba nasan suda ganina ba Nan kusa ba ko zan waiwayesu ba lokacin ba, aiki na bawa Sameer na Nemo ma'aikatan wata ngo's suzo mu zauna Ina son muyi aiki dasu a zahiri Amma ba sune zasu ringa harkar kudi ba, kinsan k'asar mu indai Zaki bada budi to kome kike nema kin samu Nan da Nan suka shigo muka Fara aiki Ni Ina gefe Sameer ne oga, ba Saina Baki labari ba Kinga yanda makarantar Baba malam ta Zama, ke kuma a can syprus din bamu barki sakaka ba sai Dana tura Omer ya shiga jikinki a can ya Zama idanuna ya Kuma yi Miki tayin soyayya sai akayi Dace kince Masa a'a sai dai kuna mutuncin da ta Kai ko siyyaya kikayi shi yake biya koba haka bane? Kuma 'yan Nigeria sai ake Baku wasu kudin scholarship daga wata kungiya MMD anyi haka? Ke naki yana ninka na sauran kunyi bincike kun rasa gano meyasa hakan yake faruwa haka ne? Kai kawai Zahra ta gyada Masa Dan ya kasheta da mamakinsa, cheeks dinta ya shafa a hankali Yana Mata smile har dimful dinsa ya Dan lotsa kadan Kinsan Allah da ban Aureki ba ina ga hummm.... Allah dai ya kyauta da dai Kam.. za'a Sami matsala Dan inaga maza biyu Zaki aura Dan Ni dai bazan hakura ba to sai Ubangijin Daya dasa soyayarki a zuciyar ya ta kaita al'amuran, Kinsan Muneeb Dan yayar mummy Badi"a ne?". Wani kallon warrr tayi Masa na nuna mamaki, ban gane ba kasan shi kenan?. Bar wannan maganar ta wuce sirrina ne bazakiji yanda aka haihu a ragaya ba, Sameer ne ya Zama Dan leken asirina duk yanda kaso aji wani Abu Sameer yaki fadin komai shima nunawa yake Yana zuwa ne Koda hasken da ake samu a Kan tafiyar tawa, Kuma duk abinda nake yiwa Hajiya Inna nace ya Dora Dan a Dan tsakanin jininta Saida yayi mahaukacin Hawa har Egypt sukaje da Uncle Mustapha da Mama mainuna surukar Aishat Ina da masaniyar komai Dan hatta bill dinsu na Asibitin Ina daga can nayi komai abinda ya darsa zargin Sameer yasan inda nake a zuciyar uncle Mustapha. Sameer ne ya kawo min labarin Ashe lokacin Dana bar gida Batool rikicewa tayi a gidan ta Hana kowa zaman lafiya ta Fadi duk abinda ya faru a Ranar da lokacin Dana kawo musu Kaya da lokacin da aka Fara fitinar sai lokacin Sajjad ma yayi bayanin shima abinda ya sani, Kuma aka shiga bincike har gurin securities Suma maganar iri Daya ce data batool sai lokacin mutane suka Fara dawowa cikin hayyacinsu aka shiga tuhumar Safna da tambayoyi na hankali Wanda ya kamata ace tun Ina Nan akayi su, inda ta kafe kaida fata ita maganarta babu canji, Kamar batool ta hakura Ashe gidan uncle Mustapha yaje ta nemi ya shige Mata gaba tana son aiwatar da wani aiki, baiki ba yace ta fada masa menene? A nutse tayi Masa bayanin kamfanin waya na MTN da AIRTEL ze rakata zata bada aiki duk da zata iya amfani da sunan family din ko ID card dinta na dalibar koyon aikin shari'a Amma tafi son suje da Babba yanda za'ayi Mata aikin a Kan Kari. Ba qaramin mamaki uncle Mustaphan yayi ba lokacin da sukaje kamfanin Dan lambobin wayar Sameera da Safna da uncle saminu da wata wadda baisan Kota waye ba ta bada tace wadannan takeso a bibiyar Mata tun daga Kira chart , messages dinsu duka daga Nan zuwa wata Daya haka sukaje Airtel ma ta bada suka caji nasu suma, shi dai uncle Mustapha Dan kallo ya Zama sai lokacin yayi nadamar Hana ma'asuma yin karatun law gasu Nan ridi-ridi babu Wanda yayi irin wannan tunanin sai 'yar cikinsu wadda take dibace ma a fagen karatun Amma harta iya irin wannan nazarin da aiki da hankali Wanda suka kasa su. Cikin ikon Allah komai ya kammala suka Kira uncle Mustapha suka fada masa shi Kuma ya Kira Ammi yace ta turo Masa batool, tare sukaje kamfaninin kusan babu banbanci a aikin nasu sai ma na Daya kamfanin Daya Dara Daya fito da hujjojin zahiri Alfarma suka nema a Basu ma'ikacin da zeyi aikin Ranar da suke son abun ya kasance to kinsan dai yanayin Qasar indai zaka bude bakin aljihu yanzu ne zakaga biyan bukata, suna fitowa uncle Mustapha ya cewa Batool to ita nata aikin ya kare tabar sauran a gurinsa yashi Mata Albarka kamar me,ita fa batool ko Ammi Bata fadawa komai ba duk Fadi tashin da takeyi saboda haushin kowa tajeji gidan. Kwana biyu da zuwansu kamfanin taji ana maganar Abbie na Kiran meeting na duka family a Babban hall din Nan da kukayi walima. Mutane sun amsa Kiran kamar ba gobe Dan sun San da walakin goro a Miya, Uncle Mustapha ne yayi Addu'a da jawabin maraba ga jama'a sannan yace wani Abu yakeso kowa ya maida hankali ya saurara yaji sai mu yiwa kanmu adalci a ciki game da maganar Mahmud da yarinyar Nan safna, Jin haka yasa su Aunty Sameera da uncle saminu zasu tada Zaune tsaye, Abbie ne ya taka musu birki yace ko shi baisan menene ba tosu meye zesa su tada hayaniya Kan abinda bakasan menene asasinsa ba, dole suka hakura Amma zuciyar Safna kamar ta fito Dan mugun bugawar da tajeyi. *_AUREN HUCE HAUSHI_* AISHAT ISAH MUSAH. (Maman Fateemah). 09061432330 Or 08055362975 Page 95. ______Ba'a dauki dogon lokaci ba ma'akacin kamfanin wayar ya hada komai ya saka microphone yanda na nesa zasuji magana, cikin abinda Bai wuce minti biyu ba maganar Aunty Sameera ta karade gurin ita ta Kira uncle saminu ta nemi ganinsa a lokacin take tamyarsa yaje gurin data fada masa a Nan ya fada Mata yaje har ya bada turare Wanda safnar zata shafa taje gurina idan na shaqa ban Isa nayi Mata musun duk abinda ta buqata Koda kuwa kwanciya da ita ne, shine suka hada tazo da system tayi min wannan shishshigewar Dana kasa hanata a Ranar da uncle saminu ya samemu Ni da ita da yamma Wanda yaso tun a Ranar ya hada min gwarama sai Kuma Allah ya Kare abun ya shashance, sai kuma sauran maganganu Wanda Basu shafeni ba, haka aka dunga sauraren yanda suka ringa kulla makirci kala-kala ita da uncle din har turo min Safna daki, Ashe duk setup ne. Sai Kuma wayata da Safna a mabanbantan lokuta babu komai sai gaisawa da zumunci da Kuma requesting na kudi da dai sauransu sai Kuma wayar Safna da number din da Batool ta bada,a Nan kowa ya shiga shock Dan abin ba tsabta Dan duk abinda sukayi tun daga chart dinsu har Kira da voice note har video call ba'a rage komai ba Abu mafi tada hankali a cikin wayoyinsu sunyi maganar zubar da ciki ya Kai sau biyu, da irin yanda suke shirya haduwa a lokutan da take zuwa makaranta, a lokacin ne aka gane Ashe duk lokacin da tace ta tafi Niger state saurayin nata take bi har outside country suke fita, ta Nan aka gane tana amfani da layukan waya hudu da wayar ta yanda idan ta fita makaranta take rufe wayar tace saboda suna lectures ne. Daga karshe aka dawo kansu uncle inda aka dunga sauraren makirci abun dai babu Dadin ji, har na karshen nan Wanda suka hada karfi sukaje har okene gurin wani matsafi suka karbo abinda aka turara min a daki da wasu tsubbace_tsubbacen da akayi Dan kowa yayi min naqi, duk ta waya suke shirya komai Dan a zahiri bazaka tab'a cewa da wata alaqa irin haka a tsakaninsu ba, a Ranar da abun ya faru sun jima suna waya da hada yanda abun ze kasance Dan turaren maganin da aka saka Aunty Sameera ce ta shiga da kanta tayi lokacin yaran sun fice sallah sannan Safna da uncle saminu suka shigo dakin lokacin da uncle din yayi waya da security din gidan Hajiya Inna yace Masa mun fito da zayyan, shine fa suka shirya min wannan makircin Wanda kowa ya kasa gane meye gaskiyar Al'amarin sai batool da Allah ya tsareta ita da uncle Mustapha, tunda aka Fara wannan fallasar su Safna da Sameerar ke zufa Shima uncle sadda Kai kasa yayi, mutane kuwa Nan da Nan guri ya kaure da hayaniya masu Ala tsine nayi masu sharben hawaye nayi masu Ala wadarai nayi, cikin borin kunya Aunty Sameera ta tashi tana zazzaga masifa da hawayenta bibiyu tana fadin wallahi shirya wannan abun akayi ita ba ita bace wadda take magana inpersonate ne akayi Mata bazata yarda ba sai tayi shari'a da masu kamfanin wayar, uncle Mustapha ne yayi Mata zabu -zabu akan idan Bata yiwa mutane shiru ba ze saka a tafi da ita a sakaya masa ita ta jira ai da saura. Computer aka hada wadda akayi connecting da CCTV tiryan-tiryan aka Fara nuna duk abinda ya faru a part din su Mahmud a Ranar tun daga safe har dare,duk shige da ficen kowa gashi Nan kowa ya gani har abinda ba'a fada ba a wayar Saida aka gani in da uncle saminun ya fasa interlock din kofar shiga part din mu ya binne wani Abu da turaren da akayi da shiga cikin dakin da wayar da yayi lokacin da Mahmud ya taho da shigarsu dakin har da Wasan banza da sukayi kafin suji shigowar su Mahmud, sai lokacin akaga Ashe uncle bayan curtains ya shige ita Kuma ta tsaya gefen da kofa zata karareta idan ya bude kofar, duk abinda ya faru kowa yaga zahiri Nan da Nan hankalinsu ya Kara tashi Dan An yanka ta tashi abinda hankali da tunaninsu Bai tab'a kawo musu ba kenan, Abbie ne ya taso idanunsa sunyi jajur sai huci yake Yana fadin Sameera tazo su fice Masa daga gida ya saketa saki uku minti biyar ya Bata idan suka wuce haka sai sunga kaskancin da Basu tab'a tunanin ana yinsa ba, Nan Sameerar ta Fadi tana birgima tana tuma da fadin ta shiga uku wallahi saminu ne ya sakata yace Dan mu mallake dukiyarsa idan mukayi haka Dole sai yanda mukayi dashi da kowa ma Tunda babu Wanda ze iya bude Baki yace Mana ba haka za'ayi ba. Kan uncle saminu Abbie ya juya ya nuna Masa hanya Yana fadin ya fita kada ya Kara ganinsa a gidansa yaje yaji da kunyar tonon sililin da akayi masa, Safna kuwa a Nan da sume Saida aka yayyafa Mata ruwa ta farfado tana sambatun ita babu Mai rabata Dani Tunda an daura Aure take Abbie ya rattaba saki ga safna a madadina Tunda Daman bansan da masaniyar Auren ba. Hajiya Turai ce matar Autan su Alhaji sa'id tasa aka fita da Safna da Aunty Sameera. Saida aka wuce dasu sannan Ammi ta tashi wadda tun lokacin da aka Fara bayanin take hamdala ga Ubangiji Daya wanke Mata yaro daga zargin Zina Daya karade a cikin family. A hankali ta ratso mutane ta fito tsakiya ta Fara fadin ta godewa Allah ko yanzu ta koma ga Allah Bata da sauran bakin ciki saboda Allah maji rokon bayinsa ya amsa Mata addu'arta wadda take yinda babu dare babu Rana, saukar Al'quran ma anyi Mata babu adadi Tunda abin ya faru tana addu'ar Allah ya tona asirin duk Mai Hannu a cikin Lamarin, sannan ta juya ta dubi Abbie tana fadin daga yau kwanan gidan Nan ya qare min abinda nake jira kenan Daman gaskiyar tayi halinta, to Kuma yau Alhamdulillahi gaskiya tayi halinta Dan Haka Nima hanya kasan fita ta. Ta juya ta fice itama, abinda ya tada hankalin Abbaie din kenan ya bita da sauri ya fice shima, Dan Tunda yake a zamanzu magana makanciyarta haka Bata tab'a hadasu ba. "To fa kinji dalilin Daya mayar Ammina niger. Hakan ne ya Kara harzikani saboda anyi min rashin adalci, lokacin fa Sameer yazo min da bayanin na jinjinawa Batool matuk'a yarinyar tayi min bazata Sosai, Abu kamar Wasa Duk Wanda sukabi Ammi babu Wanda ta yarda ta biyo da suka Fara rinjar Hajja ne bayan zuwan Hajiya Inna Ammi ta dawo Damagaram gurin Yayanta kafin ya Yanke Mata hukunci dawowa sokoto dole, hummm Amma fa Ina biyiye da duk motsin Ammina Dan Yanke huldar da nayi ta zahiri ce Amma a badini Ina cikin duka lamuranta Dan Ina zuwa Yamai duk lokacin danaso ganinta sai dai su nemeni su rasa a can garin, ganin nesa ta tazo kusa yasa nayi zamana a garin ku dankwali yaja hula, sauran bayanai da yawa Kuma sirrina ne. Kinji kadan daga abinda ya sameni Dan ma na takaita Miki wasu abubuwan da uncle saminu ya ringa nuna min ke dai abar kaza cikin gashinta kawai, idan ana cin B'aure ba'a tona cikinsa Kuma idan ana sallah ba'a magana, wani sanin sirrin cikin ciki sai dai hanji kawai, Dan haka ban Hana ki gaisa da zuri'ar uncle saminu ba Amma na yanke Hulda dasu har abada kamar yanda mahaifina ya cire Shi a cikin duk sabgoginsa sai dai abinda ba'a rasa ba Dan masu iya magana na cewa hannunka baya ribewa ka yanke kayar,to kinji summary na abinda ya faru Dani ya Zama sanadin da yasa na fito a wancan lokacin sai dai ni Alhamdulillahi hakan wata Rahama ce daga Allah. Jinjina abin Zahra take a cikin zuciyarta ace duk wannan masifa ta dumfari mutum Daya ai sai Wanda Allah ya bawa karfin zuciya da imani ace duk girman family Kamar wannan duk sun maka nak'i Sai mutum biyu kawai lallai anga taskun rayuwa. A hankali ta sauke numfashi tana kallonsa Banda tasan baya son kuka ba da wallahi saita matse yanda zuciyarta ke Mata zafi, Dan ji tayi ta tsani safnar da yayarta tsana Mai zafi wadda ita dai ko Mama da Salma da suka nuna Mata qin jini bataji su kamar wadannan ba. "Me amorrrr....". Ta fada a hankali. Gyara Mata kwanciya yayi a cinyarsa Yana kallonta cikin Ido. "Umhummm.... Fadi ya akayi?". "Allah ya Kara maka juriya da hakuri kaga jarabawa ta rayuwa, lallai Ubangiyi yayi gaskiya da yace shin bazan jarabceku ba?. Amma taka dai Kam sai Mai karfin Imani Dan Mai karamar kwakwalwa sai kansa ya buga koya fada wata harkar Tunda babu ni'imar da Ubangiji Bai maka ba, Allah ya hore maka amma ya baka kariya daga fadawa mugunyar rayuwa, ya tsare min kayana Alhamdulillahi Allah abin godiya". Dagota yayi daga kwancen ya kafa Mata idanunsa da suke razanata a wancen lokacin Wanda Kuma suke tsumata a yanzu. "Kice Kayan naki ne ke kadai, to ya za'ayi da sauran dake kokowar shigowa Kuma?". Wani warrrr tayi masa da sexy din ta Wanda wani irin Abu yake walainiya a cikinsu. "Ai dagani babu wata a yanzu dai saina cinye na sude kayana tas sai dai su samu sudin kwano". Rike Baki Yayi Yana wata dariya kasa-kasa. "Kai yarinyar nan yaushe kikayi Baki haka? "Wato kin Fara gane garin ko?". Dariyarta Mai shagaltar dashi ta Fara tana nuna shi da hannu. "Ni Kuma wane garin na Fara ganewa?". Ba zato yayi Mata daukar jarirai yana fad'in Bari na nuna Miki garin". *****Tunda su Ammah suka shiga garin Miya kukan Salma ya tsananta tamkar zata shide, Banda aikin lallashi babu Abinda su Ammah keyi daga karshe ne Aunty Hassana ta rufeta da fada ta inda ta shiga ba tanan take fita ba. Shi dai malam Bala ko tari Bai kubce Masa ba Dan yasan sakayyar Allah ce kawai ta sauka akan Mama da 'ya'yan ta Dan dashi wani Maci Amana ne da Allah kadai yasan abinda suka shuka shida ita to tun tayin farko ta taka Mata birki da barazanar sanar da Alhajin shine abinda ya kawo basa ga maciji a tsakaninsu. Ba laifi gidansu Anas din da nasu rufin asirin sai dai da alama rayuwa ake ta babu kwaba a gidan Dan yanda kannensa Mata suka ringa yatsina fuska ga babu tarbiyya Kota sisin kwabo a gidan saboda da kyar kanwarsa Haulatu ta bayar da key din dakinta a sauki Baki cewa tayi ita da kayanta kada a Bata mata, sai wani kanin Anas din yayi Mata Jan Ido sannan ta bada, aka bude suka shiga inda aka kawo musu Abinci ba laifi ta Nan sun yaba, amma dai uwar tasa basuga fuska a gurinta ba, sun dai gaisa shima ganinsu Ammah da tayi ba karya sun jiku da naira gayu ya zauna dole ta mayar da makaman yakinta ta Bari idan sun wuce ta baje kolin abinda ta tanadarwa daga salmar har Anas din tunda 'yar kanwarta yake aure Bai Kuma fada Mata ze auro Salma ba saida iyayensa maza zasu tafi daurin auren suka shigo suka fada Mata Tunda Babansu ya rasu. A dofane suka wayi gari inda tun karfe bakwai motar Kayan ta sauka a Miya Dan tun dare Abba yasa akayi lodin Kayan abinda babu yasa su sahura da makotansu suka shiga stores suka sawo, Kayan toye-toye ma gidan masu yin na sayarwa akaje aka sawo saboda Basu da matsalarsu a unguwar da Kuma can bakin kasuwa. Kafin azzuhur gida ya kankama na amarya, Ammah ta saka Salma tayi wanka wadda har lokacin kuka takeyi ga azababban Zazzabi Daya rufeta, a irin kayan da aka dinka na Zahra Wanda magaji ze tafi dasu Ammah ta debo Mata kala kusan goma ta taho Mata dasu Tunda babu Abinda aka tanada bagatatan abun yazo. Su Ammah sun Kara Kai Salma gurin surikarta sun bada Amanarta sannan suka mikata dakinta tare da yayar Baban Ana's din, tana gunjin kuka suka barota Dan abinda Bata tab'a kawowa bane ko cikin mafarki akayi Mata taci burin auren miji na kece raini ta shiryawa kanta rayuwar Jin Dadi da walwala Amma sai gashi ta Kare a auren yaron kamfanin nefa Zama a inda ko cikin hasashe Bata tab'a kawowa ba, haka su Aunty Hassana suka wuce. Saukinta Daya gidan da abunda aka zuba Mata ze kankaro Mata mutunci ko banza ta Nan fannin dai babu raini. *** A cikin sati daya Zahra da Mahmud sunyi wata irin shak'uwa ta ban mamaki,Dan Daya ji yake baze iya rayuwa ba Saida dayan Zahra ta Zama 'yar gari sai tsula shagwaba take Masa shi Kuma duk ya susuce a kanta, ga wani irin fresh da sukayi dan dole idan ka kallesu ka kara, Saida hankalinsa ya nutsu sannan ya zauna dasu Salis da Bashir ya nemi shawararsu akan idan suna ra'ayin aiki dashi to suyi Shawara da gida akan Nan gida suke son Zama suyi aikin ko a waje sannan ya bawa kowa gida a acan Azaren Saida ya fada musu inda gidajen suke Salis yayi murmushi Shima Mahmud din yayi wani Abu suka tuna, lokacin da Mahmud yaja Salis din sukaje ana yiwa gidajen pop Salis ke tambayar ko gidan waye haka sai Mahmud din ke fadin na wani abokin Sameer ne yasa shi ya dube Masa har yake cewa Salis din ko gidan ya burgeka ne Naga kamar kana sonsa? Dariya lokacin Salis din yayi Yana fadin wa zeba Dan rogo rumfa? ai irin wannan gidajen sai wadanda sukaci suka tada Kai. Dariya kawai lokacin Mahmud yayi baice komai ba kawai dai yace Masa ya Taya shi a duba abinda baiyi ba Mai gidan ne yace ayi hakan Nan Salis din ya zage Yana ta fadin Nan kaza ya kamata ayi nan ayi kaza haka suka zagaye gidan har suka Gama bada gyaran, haka suka shiga dayan ma aka rubuta komai, to sai yanzu da yake fadar inda gidajen suka Salis ta tuna da abun, sunyi godiya kamar su Ari Baki Dan Dadi Bashir baisan lokacin da hawaye ya zubo masa sai gani sukayi Yana share hawaye, saboda Tunda ya Gama Karatu Bai Sami aiki ba gashi Dan Mai karamin karfi kullum Yana yawo neman aiki sauda yawa Mahmud Kan fada Masa yayi hakuri da lokaci, in dai aiki ne Saiya zab'a, a lokacin jinsa kawai yake Ashe da gaske yakeyi saiya zaba din tunda gashi ya Basu options na zabar Ina suke da muradin yin aikin. Dariya sosai Mahmud ya ringa yiwa Bashir ganin yanda yake shafe Ido kamar Mace. "Haba bash meye haka be strong mana Dan Allah, kuka kuma? To in banyi muku ba suwaye Zan yiwa kun riqeni Amana lokacin da bakusan daga wace duniyar nake ba, kun ciyar Dani kun dinka mun suturar sakawa, kun bani kudin da kuka nema da karfin jikinku, kun tsaya a gurin jinyata lokacin dasu Habib ke yinta ga abin Hawa an sakar min babu shamaki duk inda zani, an bani Mata kunyi uwa kunyi makarbiya gurin hidima da jikinku da aljihunku to ni kuwa ai bani da abinda Zan biyaku dashi sai dai nace Ubangiji ya biyaku da madaukaliyar Aljanna wallahi tuni na cireku daga abokai kun zamar min 'yan uwa yanzu ga wannan" ya mikawa Bashir Daya fi kusanci dashi E.passport ne yace su saurari visa Sameer ze kawo musu ta umarar Azumin nan Mai kusantowa, yace Kuma kowa ya duba akwai sako a wayarsa, sunyi tsaraba ya Kuma fada musu tickets dinsu na zuwa Bauchi Yana hannun Sameer, bakin godiyar ma rasawa sukayi Dan wata kyautar tafi gaban godiya, Dan ya gigita musu lissafi ba Dan kadan ba. Sameer ne ya shigo da sallama lokacin kwanansa biyu da dawowa daga Egypt gurinsu Mama Dan Saida akayi Mata aiki sannan ya juyo ya barosu a can, Mama tayi kuka tayi kuka akan wautar datayi a baya na nuna hassada da ganin kyashin yarinya marainiyar Allah wadda aka mutu aka Bari ko kanta Bata sani ba Amma shedan yayi Mata katutu a zuciya ta dunga kulle-kullen mugun Abu Tunda masu dubanta suka barbasa Mata yarinyar tana tare da wata irin sa'ar rayuwa duk sai ta rude tana ganin ta Yaya hakan ze faru gata Mai kyau na ban mamaki sannan ace sa'arma tatace tun daga lokacin zuciyarta Bata huta ba, to gashi Alkawarin Allah ya tabbata gata a gadon asibiti a wata k'asar tare da ciwon zuciya Wanda bakin ciki da hassada sukayi sanadinsa, ga Kuma wadda take abun a kanta taje inda Ubangiji ya nufa taje din,tunda Alkawarin Allah baya tashi ga shi Kuma mijin da taketa kangewa kada yazo gurinta shine ya Zama silar samun waraka ga ciwonta, ga mijinta Tunda sukazo bai Kira ba ya bawa banza ajiyarta Bata Kara Jin ko duriyarsa ba tun lokacin da yaje sokoto tana barcin Allura batasan yaje ba,yau ga dan 'yar uwarta Mai ingizata tayi komai Dan Hana Allah ikonsa itace Dan cikinta ya yiwa yarinyar ta cikin shege. Da kukanta share-share ta ringa fadawa Sameer ya nemar Mata yafiyar Zahra akan abubuwan data yi Mata. Kusa da Salis sameer ya zauna ya gaishe da Mahmud sannan suka gaisa dasu Salis din, sannan ya dauko musu tickets dinsu na jirgin Sha biyu da rabi na Rana, godiyar dai suka Kara yi musu har Mahmud na fadin "wallahi idan ya Kara Jin godiyar na zasu bata. ** Ranar da suka cika kwana goma sha biyu Mahmud tun dare ya fadawa Zahra ta shirya da safe ze kaita gidan Ammi shi kuma zeje Lagos wani aiki, Bai barta tayi barcin kirki ba a Daren,dan daga baya ma cewa yayi ta shirya ta raka shi suje su wuni su dawo, da kyar ta samu ta lallabashi da kalamai sannan ya hakura Amma Saida ya Kara rage tafi. Tun asuba zahra ta Kira Aunty zilai suka Fara aikin dabun kaji dasu cake sai da sauran tarkacen snacks Tunda su duka gwanayene kafin takwas da rabi sun Gama hada har breakfast, sama Zahra ta koma lokacin Mahmud ma ya farka Dan nine thirty flight dinsu ze tashi daga sokoto zuwa Lagos. Tare suka fito sukayi break sannan yace ta dauko gyalenta su tafi ya ajeta ya wuce, fada Masa tayi tare zasu tafi dasu Aunty zilai, waya ya yiwa zayyan ya saka wani ya kaisu Aunty zilai can family house nasu, lokacin da akace su fito sai gani yayi ana ta fitowa da manyan warmers ana sakawa a boot din mota, Bai nemi Jin abasin menene ba itama Bata fada masa ba. Su suka Fara yin gaba sannan suma suka fice daga gidan, sunzo wucewa ta kofar gidansu Dr Haseenah ya Dan shafo cinyarta, tsuke fuska tayi tasan abinda yake nufi. "Komu shiga ku gaisa tana garin har yanzu Tunda Nima Ina garin kinsan lokacin da Ina Nan ai a Nan take aiki Saida nabar garin ta koma Kano da aiki Tunda daman a kanon aka riketa kuma masu fada aji ne, jiya da har zatazo ku gaisa sai tace sauri takeyi gurina kawai tazo wani lokacin ida ta dawo ta shigo ku gaisa". Hade Rai tayi ta hade gabas da yamma tayi kicin-kicin duk yanda yaso ta kulashi tayi banza dashi har sukaje gidan. Abbie baya k'asar yaje Benin republic akan wasu Kaya nasa da aka rike a can. Direct part din Ammi suka nufa duk yanda yaso ta saki ranta abun ya faskara Dan da gaske ya Bata Mata rai ita fa ta tsani matar Nan ba kadan ba shi Kuma ya kasa ganewa. Yana tsayawa tayi wuf ta fice Bata tsaya ya fito ba ta wuce Abinta tana ayyana itama ai Amminta ce bazata tsaya shi ba,Amma kafin takai ga kofar parlourn ya cimmata. "Ke meya faru Wai kike ta hade min Rai haka?".kauda Kai tayi tana jin zuciyar na Mata zafi. Janyota yayi ya rungumeta a Nan da sauri ta dago tana rarraba idanu. "Dan Allah ka sakeni kada wani yazo ya ganmu a haka wallahi ba komai,Dan Allah ka Bari kada ace bamu da kunya plssss...." "Baki San anyi min tambarinta ba a gidan Nan wannan ai ba wani Abu bane,nida kace nayi abun a gidan Nan ko kin manta?". "Ai sharri ne wancen, wannan Kuma gamu in reality ne". "To shine me? Ai ba haram bane ko.....," Bai karasa ba yaji alamun za'a bude kofar da sauri ya saketa Dan bazeso kannensa ko Ammi su gansu a haka ba,ko maid din Ammin sai girma ya Fadi. Sahalatu ce 'yar Babban yayansu Abdallah da Afnan da hannunta suka fito, ai yarinyar na ganin Zahra ta Fara zillo tana dariya, itama zahrar dariya tayi Mata ta nufesu da sauri ta karbeta daga hannun sahalatun tayi wuf ta shige tana amsa gaisawar yarinyar. Ammi ce dasu Aunty Aishat a parlourn farkon sai Aunty zilai daga gefe a zaune bintar dai Bata gurin Zahra batayi mamaki ba Tunda ita 'yar gida ce, gaba Daya suka amsa sallamarta cikin nutsuwa Zahra ta karasa kusa da Ammin ta tsuguna har kasa tace "Ammy Ina kwana?". Ammi wadda bakinta yaki rufuwa saboda farin ciki ta amsa Mata "Lafiya kalau Zahra ya gidan naku?". A kunyace ta amsa "lafiya kalau Ammy". Ammin sai hamdala take yiwa Allah Daya azurta danta da irin wannan matar, a Nan Kan carpet ta zauna duk yanda Ammi tayi akan ta tashi ta zauna kiyawa tayi sai hakuri Ammin tayi. Zahra tayi mamakin Ina Kuma ya tsaya Bai shigo ba? Saida ta Jima da Zama sannan ya shigo ta baya Yana amsa waya taji Yana fadin "ka sayi ticket din online yanzu" Tunda ya shigo Ammin taga ya wani Kara girma da haske ga cikar Kamala da taga yayi da gani ya samu kwanciyar hankali. Kusa da Ammin ya zauna Yana gaisheta suka gaisa da Aishat wannan su batool suka gaishe shi, tashi su batool sukayi suka koma wani falon Aunty zilai ma kitchen ta nufa Tunda ta Saba tana Taya masu aikin aiki a Dan zaman da tayi kafin ta koma gidan Zahra. Parlourn ya rage daga Ammi da Yan biyunta sai Zahra da Afnan hira suka Fara a junan su Zahra na Zaune tana yiwa Afnan wasa, hira Mahmud yakeyi Amma 100% hankalinsa na Kan Zahra har dai Aishat ta gaji ta jefa masa tambayar data bashi mamaki. "Waini bros ko dai laifi kayiwa madam ne Naga ka kasa nutsuwa sai kafeta da Ido kakeyi irin na neman sulhu din Nan". Dan murmushi yayi Yana Dan shafa gefen sajen fuskarsa. "Ko Daya kawai burguni sukayi ita da Afnan yanda suke kaunar juna tamkar sun shekara da sanin juna, ki karbeta ma tafiya zamuyi". A tare Zahra da Aunty Aishat suka kalleshi Bai kalli zahrar ba Aishat ya bawa attention dinsa .. "Zuwa Ina kuma mobile?". "Lagos zamu". Ai Zahra Bata San lokacin da bakinta ya subuce ba tace. "Kaiiii..meu amor bafa haka mukayi da kaiba, kace fa wuni zamuyi a Nan Kuma yanzu zaka ce wai tare zamu Dan Allah ka barni na zauna a Nan din plssss...." Saida ta Kai Aya ta Farga da inda suke sauri tayi ya rufe fuska da gyalen dake jikinta. Yau taga ta kanta ita wace iriya ce. Dan murmushi Ammi tayi kawai tasan da wata a kasa saita basar Aishat ce ta shiga maganar "a'a kuyi tafiyarku kawai ba wani wunin da zakiyi Tunda kukazo kafa ya kafa ai nasan tafiyarku Daya idan yayi niyyar ki wunin ai ke kadai zakizo amma fa su binta suka Fara zuwa". Sai lokacin Ammi ta tuna an kawo musu abubuwa ganinsu ya shagaltar da ita. "Zahra munga sako fa. Allah ya saka da Alkhairi mun gode kwarai da gaske". "Meta kawo ne haka Ammi?". "Ina ruwanka ku tashi ku tafi kada kuyi missing flight". Narai narai Zahra tayi da fuska kamar zatayi kuka. "Tashi kuje kinji Tunda haka yakeso Allah ya tsare gobe ma Rana ce sai kizo ki wunar min din kinji". A kunya ce ta tashi tana fadin " To Ammy nagode mun tafi sai mun dawo". Har gurin mota Aishat ta takasu tana mitar Bai Bari zahrar ta shiga sauran parts din gidan ba. "Bari kawai da anan zata wuni sai Kuma ta nemi ta hanani sakat idan na tafi ma babu nutsuwa Dan yanzu ta birkice min a hanya ai gara muje tayi min bayanin abunda nayi Mata, idan tana Nan ai wallahi aiki baze yuwu ba zuwan banza zanyi, nifa Naga alama sai yanda Hali yayi Dan yarinyar Nan..., Ki bari kawai sai mun zauna". Hannu Zahra tasa ta dafe kirjinta, tana mamakin furucinsa. "Wallahi Aunty fada kawai yake ni babu Abinda nayi masa kawai dai bana son Yana min maganar wannan doctor din shi Kuma Koda yaushe sai ya yi ta yi min maganarta ni Kuma banaso". "A'a gaskiya tayi ma hakuri idan nice saina maka yaji wallahi kawai ka tasani gaba kana min zancen wata ai baka taki gaskiya ba" ."Hummm kinsan abinda yarinyar nan tace Mata Ranar dana nuna Mata sabon gidansu?".. Girgiza Kai tayi alamar a'a. "Cewa fa tayi Wai mace ba gaba ba baya" Aishat Bata San lokacin data fashe da dariya ba. "Well done, wallahi ba karya tayi ba to Kai karya ta fada?".Kiran wayar da akayi masa ya katse maganar da sukeyi. Abinda aka fada masa yasa yayi saurin duba agogon dake daure a hannunsa. "Bari mu wuce lokaci yaja kada muyi late". Karfe Sha daya har sun karasa gidansa na Lagos Tunda tsakanin gidan da airport din babu nisa sosai nan ma Aljannar duniya ce dan Sai taga kamar yafi kowane gida kyau ma, dan daya wuce wurin meeting kasa Zama tayi a kowane parlour, bedroom ta koma ta rufe kanta dan abin yafi karfin tunaninta, to Dan Allah shi wace irin dukiya ya mallaka haka da kananun shekaru irin nasa? ita fa tana Jin tsoron irin wannan dukiyar a gurin matashi kamarsa gaskiya. AUREN HUCE HAUSHI. Maman Fateemah 09062432330 08055362975 Page 96 ________Karfe shida da kwata su Mahmud suka shigo gidan shida Sameer da zayyan dake driving dinsu, Basu tab'a tunanin zasu Kai wannan lokacin ba a gurin meeting din, suna cikin meeting ne kiran gaggawa ya shigowa sameer injinan sabon kamfanin hada Madarar gari da 'yar Amana condensed milk suka karaso Wanda za'a bude a Azare,tunda tuni an Gama ginin gurin, to dole suka nufi deport can tincan island, Saida sukayi clearing din komai suka baro gurin, sai Kuma goslow ya rikesu. Mahmud na sauka Shima Sameer ya sauko zayyan ya wuce da motar ma'adanar aje motoci, ciki suka shiga shi Kuma zayyan ya wuce nasa masaukin dake wani bangare na gidan. Shiru parlours din duka babu alamar dake nuna da mace a gidan Dan da alama ko abincin dake saman table ba'a tab'a ba, jakar laptop dinsa Sameer ya aje Yana fadin."Bari naje ba watsa ruwa naji Kiran da madam ke jera min lokacin muna meeting kasanta Bata da hakuri yanzu haka danta ne yake Zazzabi Dan dazu da safe take fada min wai taji jikinsa da dumi ga Kuma mura". Kallo daya Mahmud yayi Masa Mai nuna alamar baka da hankali. "Meya faru kuma?". Coat dinsa ya cire ya nufi ciki ba tare Daya tanka Masa ba, Dan murmushi Sameer yayi yasan halinsa na son Yara da tattalin mace wato yayi laifa kenan. Shima juyawa yayi ya fice Yana ayyana idan oga yayi nasa yaran ko Yaya, yasan dole ya Basu kulawa fiye da tunaninsu dan Sam baya Wasa da Lamarin Yara Allah ya jarabce shi da son Yara matuk'a. A kalla Saida ya shige parlours biyar sannan ya haura steps ya shiga corridor Wanda aka kawata shi da wani irin mirror Mai shegen kyau irin Wanda ake ajewa din Nan a corridor,bedrooms hudu ne biyu na facing din biyu, Wanda ya barta a ciki ya nufa, ya gaji iya gajiya, Kati ya saka ya bude kofar, can karshen gado ya ganta a takure kamar Mai barci, da sauri ya karasa Yana fadin. "Menene precious?". Shiru tayi Masa Dan yau dai tayi dana sanin biyo shi Lagos yafi sau shurin masaki, Dan wuni tayi da yunwa ga fridge din dakin ruwa roba biyu ne kawai a ciki sai tarin lemukan gwangwani irinsu Pepsi da Coke ita Kuma ba kukanta Nan ba. Zama yayi kusa da ita Yana dago da fuskarta, ba zato yaga ruwan hawaye suna bin Kumatunta. "Subhanallahi! Previous meya faru?pls fada mini, baki da lafiya? Me yasa Ina ta kiranki Baki daga ba?". Babu amsa Daya data iya bashi sai kwantar da kanta tayi a jikin gwiwuyinta. "Ya subhanallah! Wai fushin ne har yanzu ba'a huce ba? Kiyi min magana Dan Allah kada ki sakani a damuwa mana, to Bari na Kira Miki Ammi ko Ammah wata qila su ki fada musu Abinda yake damunki". Ya fada Yana kokarin Kiran wayar. Da sauri ta karbe wayar tana fad'in. "Ni wallahi tsoron gidan nakeyi tunda ka tafi ko kofar dakin Nan kasa fita nayi Ni dai ka mayar Dani sokoton gara can da nan, kace wuni Daya zamuyi gashi har dare ya kawo jiki muna garin babu alamar tafiya, Kuma nifa gaskiya hankalina ya kasa kwanciya da abubuwan da nake gani a tare da Kai,Wai kana nufin wannan mahaukacin gidan ma naka ne, idan haka ne to sai dai idan kana da wata sana'ar a boye wadda ba kowa ne ya sani ba" . Mahmud tsayawa kawai yayi Yana kallonta, bil haqqi da iya gaskiyarta take maganar, tsura Mata idunusa yayi Yana Kara nazarinta, yama rasa Abinda ze ce mata. Saida ya hadiye wani busashshen yawu Daya kalato daga bakinsa ya hadiye sannan ya Sami zarafin yi Mata magana. "Kice ko abinci Baki fita kinci ba kenan? To me kike tsoro a gidan Nan Dan Allah? Gida da jama'a a kalla sun Mutum talatin Amma Kika takure kanki? Na fada Miki yanzu ma Zan Kara fada wallahi babu Abinda ze sameki sai ikon Allah Amma Dan mutumci dai Kam kafin ya cimmiki ya Kai kasa da karfin Allah,wayarawa an zo a duba min ke ance bakya Nan a duk parlours din gidan, sera tace Sam throughout Bataga ko gilmawarki ba,na shigo Mai makon special we'll come sai bacin Rai harda hawaye ga zirgina da kika Bari shedan ya sauwala Miki a zuciya, kina zargin ko Ina kauce hanyar Allah a gurin nema na ko? To Bari nayi sallah na dawo nayi Miki Abinda Ina ganin kamar ze gamsar dake". Ya tashi tsam ya wuce toilet ya barta tana shefe hawaye. A gurguje yayi wanka ya fito baibi ta kanta ba ya Dan shafa lotion ya zura jallabiya ya baza turarensa ya wuce masallaci. Itama shiga tayi tayo Alwalarta Bata bukatar wanka Dan wurin biyar da rabi tayi nata da taji wani Abu Yana fita daga jikinta, ita abun harya Fara damunta ita kadai sai tayi ta mutsu mutsu. Bai shigo ba sai kusan takwas da kwata Dan harta kwanta suna chart da sajida da Amatu a group da suka hada mujiba ce Bata online sai Dan biki suke mata data fada musu suna Lagos, Dan caaa sukayi Mata suna fad'in lallai a samu musu Dan Legos ladar meeting. Kusa da ita ya zauna Yana Dan leken wayar boyewa tayi. "Inyeh kice na zage dantse kenan, da Ina Shirin mubi flight din seven thirty,kice na fasa booking din mu kwankwaje a nan tunda bestie ta zabar Mana nan'. Shiru tayi masa kamar kurma. "Ke! Wai Dan Allah me nayi da zafi haka ne? Ki rufa min asiri kada na kasa gane komai, wallahi kinji na rantse Miki duk abinda Kika gani da Wanda Baki gani ba duk halaliyata ne idan Ina wata sana'ar da take haramtacciya ko Ina wani Abu daya sabawa shari'a Ubangiji ya....... Da wani irin hanzari ta toshe bakinsa da tattaussan tafin hannunta tana girgiza Masa Kai, idanunta sun cicciko da hawaye. "Wallahi ba Ina zargin kana sabawa Ubangiji bane kawai abun ne Yana bani tsoro, naganka yaro da Kai Amma ka mallaki Abinda yafi karfin tunanin mai karamar brain irin tawa, amma kayi hakuri bazan sake maka tambaya irin wannan ba Naga kana niyyar debo rantsuwa kawai Dan kaga Ina fushi,na fa maganar Dr din Nan ce banaso, Allah da gaske bana sonta har zuciyatw wallahi". "Sorry my previous na daina har abada kada ayi min tawaye a gudu Jordan kamar yanda akayi niyya a can baya saboda ita, da yake Allah ya tarfawa garina nono yasa a ranar naji kamar ana ingizoni na taho da yake Allah Alhakimu ne Saida aka nemo min ke da tsohon dare danma a lokacin ba wani caring kawai dai gani Nan ana kallona Ina ragaita ba'a nunawa kurciya baka ba, tashi muje ki Samar min Abinda Zan saka a bakin salatina kafin nayi aikin bada hakuri kada ayi min nak'i". Ya fada yana dariyar Nan tasa Mai sakata shagala da kallonsa. Itama dariyar tayi tana kokarin tashi tana fad'in "yau dai anyi abun kirki babu 'yan.." Bata karasa tunanin ba taji saukar hannunsa a jikinta, Batasan lokacin Daya furta "Ashe ba'a yabon dan kuturu Saiya shekara da yatsu". "Gaskiya Kam ai kena gani kamar kina bukata ta a kusa dake ko ba haka bane?". Shiru tayi Masa idan ta biye Masa zeta Bata kunys ne kawai, ta rasa ta Ina ma ya ganota. Basar da maganarsa tayi. "Tashi muje kaci abincin kaji meu Amor,.nasan kana Jin yunwa ko?. "A'a muci dai kema ai bakici ba, tun break din safe". Tare suka fito Yana manne da ita. "Wai me kike tsoro a gidan nifa tsoron Nan naki Yana damuna kinga duk gidajen ki haka suke sai dai idan abokiyar Zama kikeso to wannan fa sai ta ringa debe Miki kewa yanda zakuna Jin motsin juna ai hakan yayi Miki ko?". Da sauri ya raba jikinta da bass kamar wadda huta ta yiwa shocking. "Kishiya Kuma? Har ka gaji Dani Nan da Nan haka? Daman abunda kake fada min ba gaske bane harka Gama Dani Kuma sai wata? Na shiga Tara, Dan Allah Dame na kasa maka ko ba irin type din da kakeso nake ba".. Sai hawaye sharrrr..... "Ya salam.! Previous meya hau kanki ne Wai tsakanin jiya da yau? Wace iriyar magana ce wannan marar dadin saurare, kece na gaji dake? koko ba irin type din da nakeso ba? Wallahil Azim ban tab'a son wata mace ba kamarki tunda Allah ya halicceni idan Kika cire uwata to ba'ayi ba Kuma Ina ganin har abada babu wata mace da zata samu matsayi irin naki a wannan zuciyar, kin Dade da mamayeta tun ban gama Zama mutum cikakke ba, maganar type Kuma ai ni har kin wuce sanina wato so kike na nuna Miki true colour dina a wannan fannin ko? Naga alama kema jirgi Daya ya dauko mu, Bari ki bani abinci mu gani daga Nan zuwa asuba ko mun Kai ga inda muka dosa inaga da tsarabar Lagos zamu koma SKT, da alamar ma Nan gaba kadan saina Fara service gaskiya". Sunne Kai tayi a kirjinsa tana fad'in a'a wallahi bada fa wani Abu na fada ba cewa fa kayi Wai zaka kawo abokiyar Zama ai kowa yaji yasan banyi maka dai dai bane shi yasa zaka karo Aure". "Ya salam! Previous yaushe Mika zama haka Dan Allah? To Bari na fada Miki kinyi min fiye da tunaninki wato Naga kin Zama sai a hankali ko? Kada fa na Fara guduwa da kafata kisa ace min ragon miji". ******Tunda su Ammah suka tafi Salma ke aikin kuka, bakin ciki goma da ashirin gana wannan wulakantaccen Auren gana Makarram ga Kuma uwarta Mai daure mata kugun itama tana wata uwa duniya da tata lalurar,ga mijin da aka Bata Wanda ta rainawa ajawalin shima ko kyeyarsa ma bataci arzikin gani ba har karfe Daya na dare ga unguwar irin sabuwar Nan ce wadda Bata da cikowar mutane, barci dai sai barawo Dan sai ana Kiran sallar asuba ta farka, haka ta wayi gari kamar mayya ita kadai a gida, sai wurin takwas taji ana buga gate din gidan da farko banza tayi Saida taji bugun Yana damunta sannan ta fito sai lokacin taga yanda gidan yake Dan Sam Bata fito ba, Data bude daga cikin kannensa ce mata, ba laifi ita da sauki Bata da halin sauran, murmushi ta yiwa Salma itama murmushin ta mayar Mata duk da zuciyar ta babu Dadi. "Sannu da zuwa". Salma ta fada tana Bata hanyar shiga. "Yauwa sannu Aunty salma". Kofar Salma ta rufe suka juyo cikin gidan ba laifi ya tsaru dai dai misali self content ne sai wani Dan karamin part Kamar boys quater. Basket din hannunta ta aje ta zauna tana fad'in ga abincin break Nan inji Umma tace a gaisheki Kuma kada kiga Ya Anas baizo ba Aunty Bara'atu ce bata da lafiya tunda aka fada Mata Ya Anas din yayi Aure ta Kama Aljanu a kanta aka kwana yanzu ma zasu tafi gumau can Toro local government gurin mai Magani ance dai ko kwana akeyi a can din yace dai sai sun dawo ze shigo Nan gurinki yace na zauna na tayaki Zama zuwa dare". Tunda Hafsa ta Fara rattabo Mata bayani taking wani tashin hankali ya rufeta sai gumin goshi takeyi, wulakanci dai ta tabbata a Nan ya Gama nunawa duniya ita ba komai bace ita da banza duk daya, Bata tab'a Jin tayi nadama ba sai yau, duniya tayi Mata juyin waina, ba haka ta shiryawa rayuwa ba taci buri kala-kala amma karshe ga yanda ta kare, Nan da Nan taji idanunta sun cicciko da hawaye Bata damu ba da Hafsa da take Zaune kuka ta fashe dashi tamkar wadda aka aikowa da sakon mutuwa, bare data tuna hotunan da magaji da mujiba suka Dora na bikin Zahra da irin gidajen da taga ana sabgar a ciki da Kuma gidan da majiba ta Dora hutunansu tana gani tasan shine gidan Zahra Dan taga magaji ma yayi hotuna a cikinsa. Hakuri Hafsa da dinga bawa salma Dan ko ita abun yayi touching din ta Dan ance ciwon 'ya mace na 'ya mace ne. Abincin dai kasa cinsa tayi Dan dankalin Hausa ne sai kunun tsamiya da jallof din taliya, abunci dai gashi nan tasan da gangan akayi Mata shi Dan kada ace ba'a kawo Mata ba. Har dare ya kawo jiki ba Ango ba labarinsa ko Kiran wayarsa babu, Amma dai zuwan Hafsa sai yasa Salma ta Dan ware suna Hira da Hafsa din tare suka dafa abincin Rana tunda babu Abinda Abba baisa anyi Mata ba haka Ammah ma tayi nmijin kokarin hada Mata duk Abinda uwa takeyi, ganin dare ta Fara yasa Hafsa tafiya a tabar salma ita kadai. Zahra a ranar ta karbi kidan general Dan ta gane shayi ruwa ne Lipton kadai ke canza Masa kala, Dan babu daga kafa Saida yaga da gaske ta gaji sannan ya kyaleta, Amma dai ya yaba mata Dan ta shayar dashi ruwan mamaki ta haddace karatun tas har Kari aka samu, Saida sukayi sallar asuba suka kwanta, Dan migonowa yayi jikinta ya rungumota jikinsa ya furta. "Previous.. wallahi kin gama min komai, Allah ya sakawa Ammah da Alkhairi data Baki tarbiyyar da tasa aka dunga Adana mun kayana, kin fa bani mamaki, ilove the way you..,kiss, licked my ears,look at me as you blew me.... Pls tell me who can teached you how to do this special making love?". Wata kunya taji ta rufeta sunne kanta tayi wallahi ya Sanya jin kunyarsa ba kad'an ba. Ganin ta qudundu ne kanta a kirjinsa ganin hakan yasa ya Kai bakinsa kusa da kunnenta Yana hura Mata iska a hankali. "Please precious tell me what should i do to prepare you for second round?". "Ya ilahiy! Shike nan ta tarowa kanta match wallahi". "Ok let's talk about what we can do differently next timeeee..." Ya karasa fada Yana Kara hadeta da jikinsa. "Dan Allah ka Bari wallahi nifa kunyarka nakeji". Wata dariya yayi a hankali. "Amma yarinyar nan, kin sakani a daki kinata sarrafani kamar zan zauce na haukace shine Zaki wani rufe Ido kice kina Jin kunya ta tab da kunya ta Kare a duniya". Saida ya huta yanda ransa keso sannan sukayi wanka, sukayi breakfast sannan ya jata suka fita Sai lokacin ta karewa gidan kallo ba karya ya hadu iya haduwa Kai da gani kasan gidan ya lashe mak'udan kudi Dan karshen gayu dai an tanada a cikinsa sun zagaya ya nuna Mata yanda komai yake sai lokacin taga she ba wani irin Babban Nan bane Dan gidan sokoto ma ya fishi girma sai dai wannan din ma yaji ababen more rayuwa, da yamma suka fita beach anan taga yanda Mata ke yawo cikin tubarriji ba kunya ko tsoron mahalicci dole ta matsa Masa suka nufi irin gurin da ake hutawa, suna Zaune suna Hira duk Wanda ya kallesu Saiya qara kallo, daga gefensu Zahra kaji ance "Jadida". Da sauri ta juya tasan ko wacece tare sukayi F.G.G.C KAZAURE da ita Dan yawanci 'yan class dinsu ke fada Mata sunan wani teacher dinsu Muhammad Naseer mutumin Sudan ya saka Mata suna a washe garin da aka kaita makarantar yake tambayar ta Ana jadida? Saboda ya ganta Balarabiya, ai kuwa sai 'yan class suka dauka wasu ma cewa suke Zahra jadida kawai. Ai kuwa tana juyawa sukayi arba da zainab murtala Aliyu 'yar Jos ce amma mazauna Lagos babanta Dan canji ne. Da sauri ta karaso ganin da gasken itace ta fada ne Dan tabbatarwa ne kawai rungume juna sukayi cikin farin cikin ganin juna babu zato,Saida suka Gama murnar su sannan Zahra ta gabatar da zainab gurin Mahmud suka gaisa tace Mata maigidanta ne, ta gabatarwa da Mahmud zainab kawarta tun suna secondary Nan suka koma gefe Hirar yaushe gabo ta balle anan zainab ke fada Mata itama tayi aure shekara Daya da rabi kenan harta haihu Dan ba rai sai yanzu take da wani cikin sun shagala da Hira sukaji magana daga bayansu ana fad'in. "My beauty wato Hira Kika samu Kika manta Dani ko?". "Wayyo my love wallahi na gamu da friend dina ce, rabon damu hadu tun secondary kaga kuwa ai mun gaisa mu tuna baya ko?". Haka Nan Zahra taji kamar tasan muryar dake magana a bayanta. "Zahra ga my love Mubeen ku gaisa". Dan juyowa tayi tana fadin. "Barka da yamma". Ido cikin Ido sukayi dashi Amma saita dake tayi kamar Nan duniya Bata tab'a ganin Mai Kama dashi bama, Amma shi saida ya Dan so ya rude Dan da kyar ya iya fad'in "lafiya kalau". Zainab Zahra ta kallo tana fad'in "sai munyi way kenan? Bari na wuce sai anjima ku gaida gida". Ta juya ta koma gurin da Mahmud din yake Zaune Yana faman daddanna wayar hannunsa, da kallo Muneeb din ya bita sai kuma idonsa ya sauka akan Mahmud. Da sauri ya nufi inda yake zaune yana karasowa ya Fara fad'in . "Wa nake gani kamar Mahmud Dange a gurin Nan?". "Nine Mana muneeb sale,daman talaka na ganinku?". "Tuba nake yallabai wane ni ai ku ganinku sai Mai sa'ar gaske Nima tsintuwa nayi Allah ya tsaga da rabona a yau, Daman kana kasar nan watannin baya akace min kana uk can ka koma da zama". "A'a gani kuma a Nigeria,kawai dai nayi tafiya ne wadda na jima shine ake cewa nabar k'asar'. Zahra dai Batasan inda suka San juna ba Amma da gani sun yiwa juna farin sani. Zahra Bata San Abinda Mahmud ya bawa Muneeb ba taji dai Yana godiya kamar ba gobe Saida suka tafi Mahmud ya kalli Zahra. "Gafa ex-boy friend dinki Wanda ze min shigar sauri". "Daman kasan shi ne? Naga the way yanda kuke magana da sanayya sosai a tsakani". "Zomu tafi wannan Kuma sirrine". Sai dare suka karaso gida saboda go slown garin, sati daya sukayi a Lagos suka dawo sokoto, sun dasa wata irin soyyaya Mai tarihi a Lagos Dan ba karya sun gane juna yanda ya kamata, da gani kasan suna cikin ganiyar kuruciyarsu ga wadatar arziki sai abun yayi musu wani irin kyawu na ban mamaki, satinsu Daya da dawowa Ammah tazo sokoto, ai tun daga gate din gidan Alhaji Muhammad Dange Ammah ta Fara tasbihi ga Allah s. w. a Dan ko makaho ya shafa yasan da abun Wai an Rana nik'a da Akuya. Ammi ta yiwa Ammah tarba ta girmamawa kamar ta goya Ammah sun Dade suna Hira tamkar Aminai Ammi tayi godiyar karamcin kyautar 'ya sumutum da akayiwa Mahmud ba tare da la'akari ko shi waye ba, an Kai Ammah gidan Hajiya Inna sun gaisa sun aje Mata tata tsarabar da sakon Abba Daya bada a kawo Mata, ai Ammah Bata k'ara tsinkewa da Lamarin ba Saida ta shiga gidan Zahra tasbihi kawai take ga Allah Dan wani garin yafi gaban kunu, Ashe Bataga komai ba Saida idanunta suka nuna mata. Tana kasa suna Hira da Mahmud suka shigo tun kafin su taso magaji ya Kira shi ya fada Masa gasu nan tare da Ammah Amma tace kada a fadawa zahra bazata kwantar da hankalinta ba idan tasan zasu shigo gari, ya dai ce Mata ayi special girki zasuyi Baki,suna zune aka Danna door bell baiyi amfani da remote control ba yace ta tashi ta bude, ba musu ta tashi tana tafiyarta kamar tana tsoron taka kasa ta bude kofar, ai ita dai Zahra Batasan lokacin da tayi wani uban tsalle ba ta fada jikin Ammah sai kuka tana fadin. "Yanzu a kasa fada min gakunan a hanyar zuwa, wallahi magaji mun Bata da kai na fasa rik'on wallahi tunda kaci amanata". "A'a ki tuhumi Ammarki da mijinki sune Basu fada Miki ba,Ni Dan Rakiya da sai yanda akayi Dani". Har suka shigo zahra na jikin Ammah tare suka zauna kamar zata shige cikinta sai dariya magaji yake musu Dan itama Ammar idanunta kamar ruwan hawayen ne, sun gaisa da Mahmud sosai sannan Zahra ta Kira Aunty zilai a waya tace tazo ga Ammah, sai gata da gani harda gudu ta hado, dan Sai daga bayanta sannan Binta ta shigo, murna kamar me sai dariya take yi Mahmud fita yayi magaji ya bishi tunda ya cika cikinsa a gidan Ammi. Bayan fitar Mahmud Zahra ta tashi ita Aunty zalai suka shiga fito da kayan abinci dasu drinks tamkar mutum goma ne zasuci sai da Ammar ta tsawatar musu tana fadin. "Ke Zahra duk waye kuke kawowa wannan abincin haka? Nifa na koshi naci na surukarki mace Mai kirki ga nagarta". Zilai ce ta karbe zancen "wallahi kuwa Ammah kirkinta ya Isa gashi kamar ta goya uwar dakina Dan so da kauna wallahi Ammah ranar Nan Ina mofin a wancen parlourn naji Yana fadin "wallahi Ammi Ina son Zahra ki tayini sonta". Bansan dai Abinda ta fada masa ba naji dai Yana jera Mata godiya". Babu laifi Ammar taci abincin,Saida ta Gama suka haura sama tayi sallah, ta shishshiga ko Ina ta gani tana godewa Allah Daya bawa marainiyar ta gidan da ko cikin mafarki Basu tab'a zato ba. A Nan zahra ta zazzagewa Ammah yanda Mahmud yaje asibiti yayiwa Mama tatas, abun ya bawa Ammah mamaki kenan shi harya gano abunda ta kasa ganewa shekara da shekaru, sannan Ammah ta fada Mata Mahmud ne yasa aka dawo da Salma daga Jos da duk abinda ya faru har tarewar Hameeda wancen satin, duk sai tausayinsu ya Kama Zahra ganin ita 'yar riko ma Abba ya zage dantse yayi abun azo a gani na shidimar daurin Aure to bare Kuma na 'yayan cikinsa wadanda daga su ba saura 'ya mace a gidan Kuma Amma ace abun yazo haka a hagunce babu Dadi duk da ance yayi musu komai Amma dai ba haka akaso ba. Sai karfe hudu da minti goma su Mahmud da magaji suka shigo gidan, a gurguje saboda lokaci jirgin hudu da rabi zasu bi zuwa Bauchi. Mahmud da kansa ya Kai Ammah airport tare da zahra sukaje lokacin da zasu shiga jirgi rike Ammah Zahra tayi tana kuka da kyar Ammah ta lallabata ta wuce lokacin da zata shige ta juyo sai taga Mahmud ya rungumeta da gani lallashinta yake yi. Bayan sati Daya visa dinsu ta fito inda zasu Fara shiga India gurin Baba malam tunda an sallamesu suna gidan Mahmud din, tare suka juya da Aunty Aishat saboda hutun su Abulkhairi ya kusa karewa. Tun daga airport kowa yayi nasa gurin ita Aishat Ya Abbas yazo suka wuce, su Kuma Mr salahuddeen yazo ya daukesu. Sun samu jikin Baba malam yayi sauki sosai Dan Yana tafiya da kafafunsa sai Dan abunda baza'a rasa ba Kuma sunce sai a hankali komai ze zama normal, murna da farin ciki ba magana kamar malam ya hadiyesu Dan farin ciki Dan yanda ya gansu yasan suna cikin nutsuwa da kwanciyar hankali. Da dare ne Mahmud suka zauna da Malam ya warware masa zare da abawar Abinda ya faru dashi Wanda ya sabbaba fitowarsa daga gida, sannan ya juya ya kalli Habib da yake Zaune Yana saurarensu. "Habib". Mahmud ya kirawo sunansa. "Na'am" ya amsa. "Wadannan shugunan na kayan motoci Daman da sunanka nayi komai ai ka sani lokacin har kana korafin ya za'ayi haka nace ka barshi duk Daya ne, anyi hakan?". Kaiya gyada kafin yace "Tabbas anyi haka". "To Alhamdulillahi, Daman nayi ne da sunanka lokacin bani da bakin fadar hakan shine dalilin, sai Kuma shagunan da aka zuba Atamfofi da su laces da materials Dana kayan Yara, ina ga shida ne ko?". "Eh haka suke". "Ok.to na Ammah ne Kai na wakilta kaje ka kaimata takardun shugunan da duka lissafin daka turo min ka mayar dasu cikin Account dinta, Sai Kuma sauran kantin Nan guda hudu na shaddoji da sauran kayqn maza da sabuwar plazar Nan Mai sunnan malam wadda aka bude a katagum road duka na malam ne, gidan kusa da Malam sani Mai wankin hula duk da dai bakasan anyi gininba to na Ashiru mai shayi ne, Shima yayi abin a yaba Masa ya bani shayi ba adadi nayi nayi ya karbi kudin yace a'a Kuma na fadawa Sameer a bashi jarin sana'a bayan shayi badan ya manyanta ba da Kano Zan kawa shi kamfani to nauyin iyali sunndanne shi, ka karbi takardun gidan suna hannun Bilyaminu sai kaba Baba malam ya bashi ayi min godiya kafin na shigo garin". Tunda Mahmud ya fara bayani malam ke jinjina Kai yasan za'ayi haka Dan yayi istihara yafi sau shurin masaki Amma babu canji wata irin daukaka yake gani tare da yaron. "Allah yayi maka Albarka ya shiga cikin dukkan lamuranka yanda ka kyautatawa bayin Allah Ubangiji ya kyautata lamuranka na duniya da lahira yayi maka tukuici da gidan Aljanna ya baka zuri'a dayyiba ya Kare gabanka da bayanka ya Kara arziki Mai Albarka, lallai Ubangiyi maji rokon bawayinsa ne nayi Addu'a tun Ina da kuruciyata Ashe sai girma ya kamani Allah ze tabbatar Mana da abun, sannu mahmudu kaji mun gode! Mun gode!! Ubangiji yayi jagora". Saiya sadda kansa kasa sai Jin shashshekar kukansa sukaji. Nan da Nan Mahmud ya rude Yana tambayarsa menene? Sai da yayi Mai isarsa sannan ya shafe hawayen. "Mahmudu wani Alherin sai kayi hawaye, wallahi yafi gaban dariya me Zan cewa Ubangiji banda nayi ta tahamidi ga sarki rabbil Izzati. Alhamdulillah!. Alhamdulillahi!! Alhamdulillahi,!!! Alakulli halin. Fitowa su Mahmud sukayi Nan compound din gidan shida Habib, suna Ida fitowa Shima Habib ya Fara nasa matse hawayen Yana fadin "wallahi bani da bakin yi maka godiya kayin min gata na gidan duniyar Nan kayi min Abinda bani da halin yinsa akan yayan mahaifita Allah yayi maka sakayya da Aljanna madaukakiya". Kafadarsa Mahmud ya Dan doka kadan. "My man kana bada maza fa gurin yawan kuka nan ai namijin duniya baya kuka duk wuya duk dadi, haba! Be strong Mana Dole ka baro gida ka shiga duniya kaga yanda maza ke yin kwakawrmaya, Zan fadawa Baba malam dole a cikin uku ka zabi Daya ko Nan India ko Dubai ko Kuma China,amma saina hadoka da Ubaidat yanda aikin ze tafi yanda nake son ganinka, zamanta kusa da Kai ze Kara maka support ba kadan ba, tunda Nima ban samu nutsuwa ba Saida kuka bani Kanwar ku, Zan fadawa malam ayi maganar biki a kusan Nan ku tattraro ku taho". Ya fada Yana Masa murmushi, Shima Habib murmushin yayi kafin yace. "Ai Ubaidat an kasani ta samu Mai kudi a Itas gadau Amma mazaunin Abuja har anyi biki wata Daya Daya wuce tayo min text Wai nayi hakuri a gidansu ne aka takura Mata, to nima lokacin lna cikin tawa damuwar ta lalurar Baba malam wallahil Azim ban ji komai ba fatan Alkhairi nayi Mata kawai Kuma Daman a yanda take bijiro min da bukatu na kudi banga alamar zamu dai daita ba da farko ba haka take ba sai daga baya na fuskanci ta fiye rokon kudi Kuma duk mace Mai wannan d'abi'ar sai wadda Allah ya tsare Dan an Bata da yawan 'ya'ya Mata masu irin d'abi'ar". Jinjina Kai Mahmud yake kafi ya nisa yace. "Allah ya kyauta, wato tsakanin hakuri da rashinsa tak'in kadan ne da tayi hakuri babu Abinda zata nema ta rasa da izinin Allah, ka tuna wata magana daka tab'a fada a dakinta mu na Azare? Lokacin da kace min muma ai ba haka Allah ze barmu ba". Dariya Habib yayi ya tuna lokacin da aka bawa Mahmud Auren Zahra ne ya Fadi haka. "Kada ka damu kaje ka nemi suhailat kanwata ce na kori Mai zuwa gurinta sauran masu neman izini ma na fadawa uncle Mustapha ya fada musu anyi Mata miji Daya nemi sanin waye mijin na nuna masa hotonka da irin karamcin da kayi min, take ya nuna goyon baya Shima na saka ya kirata ya fada Mata ya nuna Mata hotonka yace taje tayi tunani idan kayi Mata tana sonka ze kirata bayan kwana biyu, to Alhamdulillahi tayi shiru ta sadda Kai lokacin daya Kara tambayar ta, hakan ya nuna ta amince, to Daman da da maganar Ubaidat din biyu zan maka Rana Daya kaima ga hoton suhailat Nan idan tayi maka idan Kuma batayi ba Dan Allah kada kayi min Kara ka fada min gaskiya idan ka rufe min saimun tsaya gaban Allah da kai". Ya fada Yana mikewa tsaye Yana Danna wayarsa yayi gaba Saida ya danyi nisa ya juyo ya kalli Habib Daya rasa bakin magana. "Ka duba WhatsApp Dinka na turo maka pictures dinta". Ya wuce ciki.. Habib jikinsa har tsuma yake ya bude Whatsapp din ai Bai San lokacin daya Mike tsaye ba Yana tsarkake sunan Ubangiyi buwayi gagara misali, yarinya ya gani danya sharab Mai wani irin kwantaccen kyau da gani gayu yaci gidansu a gurin tayi wani smile Daya kusa ya saka shi zaucewa, shi kadai Fadi yake. "Yessss... Yessss... Tayi".. Take a Nan yayi sujudush shukur Dan yasa Rahamar Allah ta bashi wannan yarinya ba Wai iyawasa ba, ya Kara jinjina girman Qudurar Allah wato idan aka hada wani connection din sai dai bawa ya zuba Ido yayi kallo, a watannin baya da za'a ce Masa za'a baka aure a Family din DANGE dake sokoto ze rantse harda girman Allah hakan bazata tab'a faruwa ba Dan ba'a hada kankana da guna. Komawa yayi ya zauna Yana Kara duba hotunan sai yaga ai Wanda ya Fara dubawa ma Bai Kai sauran kyau ba sai lokacin yaga number wayar ta daga kasa da Dan bayani a kasan number. "Ga number ta Nan ka kirata sauran aikin Kuma naka ne tunda Nima Ni nayi nawa aikin. Ina Maka fatan dacewa kamar yanda Nima AUREN HUCE HAUSHI da akayi Mana ya huce Mana namu haushin Dana iyayen mu. Dariya Habib yayi ya Dan kwantar da kansa jikin kujerar da yake a Kai ya zubawa fuskarta Idanu Yana tasbihi ga sarkin da yake amsa Addu'oin bayinsa, yayi Addu'a iya Addu'a akan neman zabin Allah akan mace ta gari. ****Washe gari su Baba malam dasu Abubakar suka wuce Nigeria, su Mahmud Kuma suka nufi Dubai, a hotel dinsa na gudun hijira suka sauka tunda Shima permanent room ya kama, a MJ.moritte Marquis hotel din, Zahra ta Kara tabbatar da Mahmud bana Wasa bane ganin irin wannan hotel din Daya Kama permanent daki a cikinsa zamansa yake Kuma ana biyan kudin daki duk wata tunda booking din monthly akayi shi. Sun huta iya hutawa sunyi honey moon yanda ya kamata zahra taga gata iya gata taga soyyaya kamar ya hadiyeta sunyi wani irin mahaukacin kyau bare Zahra tamkar ka taba ta jini ya fito tayi Shar da ita ko uhum tace Saiya ce menene a Nan watan Ramadan Mai Albarka ya samesu, dole ya rage Zama har hakan ya tayarwa da zahra hankali Dan baya dawowa sai gaf da Kiran sallar magariba har dai ta gaji tayi masa magana yace Mata aiki ne yayi yawa yanzu, ranar da suka Kai Azumi na bakwai Yana Zaune a office Yana karatun Alqur'ani Kiran Sister twins dinsa ya shigo, bayan sun gaisa ne take tambayarsa " Waime yasa baka son Zama a gurin Zahra ne? kullum idan na kirata sai tace min baka Nan". Dan murmushi yayi yasan juya abin Aishat tayi Amma ba haka abun yake ba kararsa kawai ta Kai gurinta, ita Kuma sai tayi Masa Education. Ba wani rufa-rufa ya bude Mata aiki tunda ba kunyarta yakeji ba. "Kina jina idan na zauna a gurinta wallahi matsala za'a samu dan azumi dai karya shi za'ayi bako tantama saboda wata irin fitina takeji da ita kwanan Nan wallahi wani lokacin sai munyi wanka muke sallar insha'i da asham to gane min idan Ina zama gurinta sai mun shekara muna kaffara wallahi". Tunda ya Fara Kora Mata bayani Aishat ke kunshe dariyarta. "Ok na gane Zan Mata bayani, Amma Anya Bata da ciki kuwa? Kuje a bincika ana samun irin haka ga wasu matan idan suna da shigar sabon ciki". "Kai Anya bana tunanin hakan ba kune kuka dunga zabga Mata hade hadenku ba gashi Nan ya mayar da ita fitinanniya, ga azumi Kuma". Dariyar ce ta kwace Mata Saida tayi Mai isarta sannan tace "nidai ba ruwana gyaran jiki kawai nasa akayi Mata" "Kuka sani dai babu Mai sakani kaffara Ina zaman zamana" dif ya katse kiran, Yana Jin dariyar Aishat din. A ranar Bai shiga ba Saida yayi har asham sannan ya shiga ya sameta a kwance a parlour a kasan Kan carpet sai juyi take da sauri ya karasa Yana tambayar ta menene? Mararta ta nuna masa. "Bari muje Asibiti". Kai ta girgiza masa alamar a'a yanda yaga eyes dinta yasan da magana cak ya dauketa yayi bedroom da ita. Karfe Tara na dare suna gaban doctor Mahmud ne ya fada Masa bukatarsu ta binciken madam saboda tayi fama da matsalar fibroid, Bai fito yace Yana zargin ko ciki ne. Tashin farko ana Dora abun scanning saiga ciki kwance a mahaifarta, kusan wata biyu kuma lafiyayyan cikin da babu tantama, tun a gadon scanning din ya rungumeta Yana godiya ga Allah da yayi musu wannan kyautar da kudi ko mulki basa badawa. Aishat ya Kira yayi Mata Albishir din cikin, yana fadar Ashe da gaske ne Abinda ta fada, kenan ba kowa ke kwanciya ciwo ba yayin laukayin ciki? Dariya kawai tayi masa, duk murna ta cikata tana son ta fesawa Ammi labari. A ranar zahra taga kulawa ta musamman Dan biye Mata yayi ganin da gaske baby dinsa ne ya canzata. Zahra taga soyyaya gurin Ammi Dan cewa tayi ya dawo Mata da ita Nigeria tunda Daman tayi fama da lalura a mahaifa kada cikin ta samu wata matsala tunda lokacin da zahra ta fadawa Mahmud baya zamqn gida mummy Bada'a Aishat ta Kira ta fadawa itace tace ta tambaye Shi dalilin hakan tasa bazeqi fada Mata ba, to bayan ta Kira ta fada Mata yanda sukayi da Kuma Abinda result din scanning ya bayar shine mummy din tace ko gida ze dawo da ita tunda ga yanda abin yake kada su birke cikin, da kyar ya shawo Kan Ammin ta hakura suje umarar daga can suje Jordan din. Sunyi umara sun karasa azuminsu a saudia ranar idi suka koma Madina duk da can suka sauka sukayi ziyarar qabarin Manzon Allah s a.w.w A bin mamaki a can suka samu Ummee da Abie Suma sun zo sunyi umarar sunso Zahra ta kwana a gurinsu Amma kememe ta k'iya tace unguwa zasuje jidda gobe sun dawo,haka tabi Mahmud suka wuce ai Bata son Abinda ze raba su dashi Nan kusa saboda yanzu ne komai ze tafiyar Mata daidai an Gama Azumi Sun Riga su Ummee zuwa Jordan a gidan daya saya kusa opposite dasu Ummee suka zauna gidan da yake tafiya da imaninta ga shi ansa masa gidan Zahra Ashe nata ne. Ranar dasu Ummee suka dawo a can take wuni har dare da yake ba 'yan fitinar bane a kanta,tun a saudia Ummee ke ganin zahra da wata Kama Amma fata furta Mata ba ta dai San da magana. Watansu Daya a Jordan suka wuce Oman 'yar karamar k'asar larabawa ce Mai dadin Zama ga wadatar arzikin man fetur. Nan ma sunyi kwanan wata Daya a cikinta lokacin cikin watansa hudu dai dai lokacin ne Ammi ta hurawa Abbie wutar nacin ya yiwa Hussein magana ya dawo da yarinyar nan gida tunda cikin ya Fara mik'awa dole tasa yayi maganar, badan Mahmud yaso ba suka tarkato suka nufo Nigeria, suna dawowa da sati daya suka nufi Azaren katagum, murna gurin Zahra kamar ta zuba ruwa kasa Tasha zayyan ne ya daukosu daga Bauchi inda suka sauka, Saida suka Fara shiga Azaren sai Kuma wata irin kunya ta rufe zahra a hankali ta Kara shigewa jikinsa saboda da Abinda yayi musu shamaki da zayyan din da Daya daga cikin yaransa dake gaba. "Nifa kunyar Ammah nakeji wallahi tunda magaji ya kirani yace min wai yagi su Ammah suna magana da Ammy Wai Ina da ciki bakaga ko Ammyn na kasa hada Ido da ita ba? Kowa fa yasan Abinda akayi kenan fa". Baisan lokacin daya Fara dariya ba, dan bilhaqqi da gaske kunyar takeji, ya gani a kwayar idonta. "Gyara Mata Zama yayi sannan ya lakuce Mata cheeks dinta. "Ki share kawai kowa yayi aure Abinda ake fatan ganin an samu kenan shine Albarkar Auren ai bakiga idan babu haihuwa ana shiga damuwa ba har ya Zama matsala wani karshen Auren Kennan?". Kai ta gyada Masa badan zata iya murje idanun ba. Sai kusan shida na yamma suka shiga unguwar Famfon shanu direct gidan Malam suka nufa Wanda aka rushe akayi ginin zamani,Sam zahra batayi mamaki ba indai shine to zeyi Abinda yafi haka. Suna tsayawa mutane sukayo chaccc saboda zuwa lokacin an San waye Mahmud din malam, suna Dubai ya turowa da Habib kudi aka sayi shinkafa dasu filawa da suga,mai, gero da masara aka raba a unguwar a wadace harda kakocin unguwar unguwar. Ciki Zahra ta wuce bayan sun gaisa da Baba malam ta samu iya Abu da wasu Mata biyu da alamar bak'i tayi, da farko bata gane zahra ba Saida ta karaso sannan ta waye da ita. Sun gaisa tana ta kakabin yanda zahrar ta koma. Bata Jima ba ta fito har lokaci Mahmud Yana tare da jama'a Amma tun fitiwarta hankalinsa ke kanta harta shige gida, da Auta ta Fara cin karo da gudu ya juya yana fadin "Ammah! Ammah!! Ki fito ga Adda zahra". Magaji ne ya dakatar dashi. "Dallah ka cikawa mutane kunne a gidanwa kaga zahrar bayan dazu mukayi waya nasan kuwa da zasuzo zata fada min". Sallamar Zahra ta kashe Masa fadan da yake yiwa Auta, Ammah ce ta fito tana bin ba'asin fadan da ake yiwa danta sai ganin Zahra tayi tana shigowa cikin parlourn. Ai tuni Zahra ta manta da wata kunya ta fada jikin Ammah. "Kibi a hankali Mana keda bake kadai bace". Sinne kanta tayi jikin kafadar Ammahn. "Kai gaskiya gara dai ki haihu mu huta da halin yaran Nan da kike Mana a gidan Nan". Magaji ya fada Yana nufo inda suke. Bayan magariba Ammah da zahra suna Zaune suna hirar yaushe gamo irin ta da da mahaifi Ammahr ke fada Mata bikinsu Abdul Hakeem fa an saka shekaran jiya duk gaba Daya za'ayi harda kanwar mijinki da aka bawa Habibun malam. Sai lokacin ta tuna sakon sajeeda ta gani tana fada Mata an saka Rana ta basar ta dauka tana zolayarta ne. Baywn insha'i Mahmud ya shigo suka gaisa da Ammah tayi Masa godiya abin Alkhairin da yayi Mata duk da tayi Masa ta waya, gurin Mama yace Zahra ta raka shi ya Kara dubata, sai lokacin zahra ta tuna da ita a gidan Dan tunda ta shigo ko duriyarta bataji ba. Tare suka fita suka nufi dakin a hanya zahra ke tambayarsa. "Amma dai ba rashin kirkin zaka Kara Yi Mata ba dai ko?". "Kai! Nine marar kirkin?". "To ai Lamarin naka ne ba'a ganewa a fuska sai ka aiwatar ake gani". 'yar dariya yayi. "Kinci bashi". Sau biyu zahra tayi knocking sannan aka bude, Saratu ce Autar su Mama ta bude ita gaskiya tana da kirki ba kamar su Mamar ba, da fara'a ta Fara fadin "Masha Allah Ashe Amarya ce, sannunku da zuwa". Ya fada tana Basu hanya, Saida suka shigo ta rufe kofar ta biyo bayansu tana Kare musu kallo ta tashihi ga ubangjiin dake tsara halittar bayinsa. Mamar tana Zaune da casbaha a hannunta tana lazimi, saura kadan dariya ta kubcewa Zahra ita dai iya saninta da Mama Bata tab'a ganinta a Zaune Wai tana zikitillahi ba, tayi collapse tayi wata irin Rama ga bakinta ya karu sai idanu a waje, tana ganin Mahmud ta sadda kanta kasa tana jiran taji yau Kuma Dame yazo. Har kusa da it's suka karasa zuka zauna a kujerar kusa da ita, saratu ta gaishe da Mahmud duk da ta girmesa nesa ba kusa ba,ya jajanta Mata Mai jiki, sannan Zahra ta gaisheta suka gaishe da Mamar da jiki, Zahra dai tayi shiru taji yau Kuma meze baro Amma sai taji yayi shiru daga karshe ya Bata cheque na kudi Wanda suka girgiza zahrar yace a Bata gudunmawar bikin Yara da akayi ta tashi tsam ya nufi kofa Saida ya kusa Kaiwa kofa ya jiyo muryar Mamar tana fadin Dan Allah ka karbi kudinka wallahi Abinda kayi min ma nagode. Baibi ta kanta ba ya fice Zahra ma ta tashi tana fadin "Allah ya Kara sauki". "Amin ya Hayyu ya Qyyum". Saratu ta fada tana faman godiya, Mama na shafe hawaye ta Fara fadin "Zahra Dan Allah ki yafe min Kona samu salama wallahi sharrin.shedan ne da Shawarar Aunty ladi Amma in Sha Allah bazan Kara yiwa kowa mugun Abu ba, Dan Allah ki bawa Abbqn ku hakuri yasa Baki 'yar uwarki ta koma ta karasa karatunta tinda ita shafi ce ta shafeta, to mijin yace sai yaji daga bakin Abban naku ze barta ta koma shi Kuma nayi Masa magana har Ammah ma tayi yace duk Wanda ya Kara masa magana zega bacin ransa". Sai hawaye, itama zahra zuciyar imani sai taji nata idon ya ciko da hawayen da sauri ta nufi kofa ta fice itama, Dan da gaske tausayin Mamar ya kamata babu nuna isa ba izza ba nuna kin jini saima nadama karara a idanunta. Data fito bayanan ya fice sai wurin goma ya kirata yace ta fito su wuce. Satinsu Daya a Azare suka koma sokoto, cikinta nada wata biyar da 'yan satittika aka Fara bikinsu Habib da suhailat, Ya Abdul Hakeem da sajida, sai Aunty Rukayya da zakariyya Ya Abban sajida, ita Zahra abun ya hade Mata amma Kano ta nufa tunda an sassab'a kwanakin programs din da za'ayi.sun hade daurin Auren a Kano tunda na Ya Abdul Hakeem a kanon na suhailat a kanon Dan Alhaji sa'ad mahaifin su Sameer ne ze daura gana Rukayya Shima dai a kanon A masallacin Jama'a na round din Dangi aka daura Auren. Sai dinner ce suka hade ta a Nan Azaren tunda Nan za'a kawo Amaren sajida da suhailat, Aunty Rukayya Kuma sukayi tasu a ShopRite, ranar Azare taga bak'in 'yan gayu na gani kashe ni, anci an Sha a walimar Dan ko yaran makarantar malam Saida aka sabunta musu abinci Dan sun Sha gara a ranar lemon roba da ruwa kuwa tamkar a kamfaninsu, lokacin da ake bikin Ubaidat tazo wani bikin itama a garin Nan take Jin labarin Habib yayi Aure a sokoto a family dinner su wani Mahmud Daya zauna a gidan malam Ashe shine young Rich guy din Nan MM DANGE Wanda yayi fice a kasar Nan harma da kasashen duniya, to shine fa ya bashi kanwarsa Kuma ya bashi aiki a Dubai. Hankalin Ubaidat ba Karamin tashi yayi ba Dan kuwa hangen hadarin nesa tayi Ashe mugun matsolone ta aura bajintar a waje take sai dai da gida Mai kyau Amma wani lokacin taliya da manja ake dafawa tayi data sani tafi sau dari. Zahra Bata raka kowace amarya ba Mahmud ya dauketa suka wuce gidan Dan ta gaji iya gajiya. Da asuba ma da kyar ta tshi tayi sallah, har Mahmud ya fice Zahra na barci Karan wayarta be ya tasheta wurin Sha daya, sunan sajida ta gani yana yawo akan screen din. Dauka tayi tare da sallama, Mai makon taji yanda ta Saba jinta sai ta jiya lukui kamar garin masarar daya sha nikan laushi. ",Ke Wai meye haka Zaki kirani kiyi shiru, ai ba zato taji shashshekar kukanta. Wani murmushi Zahra tayi ta ayyana "anzo gurin". "Bestie menene Wai kike kuka keda ba halinki ba". Daga can taji dif an kashe wayar ta yukura ta tashi tana fadin "ku karata a ke soyayya ba ai gata Nan sai anji jiki kafin a Fara fuskarta komai 'yan Mata anzo hannu". Kwanansu hudu suka juya fir ya hanata zuwa gidan Amaren yace sai sun zama 'yan gari taje shifa yayi hating din wannan d'abi'ar ta malam bahaushe. Sajida tayi mita harta bawa uku Lada ita dai Zahra bada hakurine nata tunda tasan ba'a kyauta Mata ba to yaya zatayi da shi tunda yace a'a. *****Bayan wata uku.**** Zahra na kwance a jikin Mahmud Yana Mata tausa tun bayan da sukayi break taji mararta tana Dan karta Mata kadan bada damuba tasan tana Jin hakan a wasu lokutan to Amma na yau taking gaba yakeyi, tun tana daurewa har abin tafi karfinta Dan babu zato Mahmud yaji ta rirrike hannuwansa jikinta ya dauki wata karkarwa. Cikin zafin ciwo tace. "Wayyo.... Meu Amor.... Mutuwa zanyiiii...bayana marata ciwoooo...". Gaba Daya ya rud'e ya gigice gashi tayi ram dashi, gasu a parlourn sama suna Zaune a kasa Kan carpet tayi pillow da cinyarsa duk yanda yaso ya tashi ta Hana, ga wata irin karkarewa da jikin ya dauka Nan da Nan sai jibi ya rufeta duk da sanyin A/Can daya cika parlourn, wayar ta dake gefe ya dauko duk ya rud'e da kyar ra gano number Ammi ya Kira Batool ce ta dauka tana kokarin gashe shi Yana fadin "maza ki fadawa Ammi ga precious Nan Bata da Lafiya". Ai da gudu gudu ta ringa hada steps tana sauka a kitchen ta samu Ammin ta rattaba Mata yanda sukayi da yayan nata, da sauri ta karbi wayar ta Nemo number zilai tace Mata maza take gurin Zahra Bata da lafiya ta gani ko haihuwar ce su wuce Asibiti. A haka Aunty zilan ta samesu sai muk'ususu take sai jibi ne yake binta, da sauri ta karaso tana fadin.."sannu ikon Allah yanzu fa kuka dauro sumul da ita, tana matsowa tace "ai haihuwa ce ga Zaki Nan Yana fits yallabai kama min ita muje ciki gata Nan inaga faya ce ta fashe'. Dago tan da zeyi tace Aunty zilai cire min wani Abu ze fito. Cikin ikon Allah a Nan ta haifi danta Masha Allah, kalarta sak kana ganinsa kaga Dan larabawa. Nan da Nan Mahmud ya rude gani yake abin kamar a shirin film, da sauri ya nufi kasa Yana Kiran Amminsa. Zahra na rungume da babyn da Aunty zilai ta dora mata a Kan cinyarta tana mayar da numfashin wahala su momin Kano suka hauro saman Dan Ammi na Gama wata da zilai ta Kira momin ta fada Mata. "Ikon Allah! Masha Allah sannu Zahra Allah ya bada lafiya, shi Kuma Bakon sai yanyara kuka yake Yana neman tsotsar hannu. Nan da Nan aka gyara zahra da babyn, aka gyara gurin momi ta Kira doctor zainab tazo ta duba zahra duk da tasan da wahala ta karu tunda tasan yana yin ta. Kafin la'asar labarin haihuwar ya karade Dangi, Ammah sai Kira take tana tambayar babu dai wata matsala ko? Duk Wanda ya kamata ya sani ya sani zahra sai amsa waya take ta masu yi Mata barka, Dan Hajiya Inna daki ta Kama a kasa tace ita zata dunga kula da Mai jegon. Sai kusan karfe Sha Daya Mahmud ya shigo gidan shiru an gyara ko Ina tas gar ze wuce sama yaga Daya daga cikin bedroom din kasa da wuta a kunne Yana karasawa yaga Hajiya Inna a ciki, tura kofar yayi sosai ya shiga Yana fadin. "Nice gaske kikeyi da kikace Nan Zaki dawo?". "Eh ka dauka karya nekeyi ai Ina Nan Ina kula da shige da ficenka kada ku jawa yaro qazamin goyo". Tabe baki yayi meye Kuma qazamin goyo?". "Ban sani ba tafi ka tqmbayi iyayenka inaga su sun sani". Ta fada tana gyara kwanciya . "Ka kashe wutar idan ka tashi fita. Zahra na rike da babyn Wanda yake kuka da alamar makoki ne, Mahmud din ya shigo da sallama,sai sukayi masa wani irin kyau kamar ya lashe su. A hankali ya nufosu ya saka hamnu ya daukeshi very fine baby tamkar Zahra tayi kaki ita ya biyo sak, Zama yayi kusa da ita Yana fadin. " Sannu precious Daman haka mata ke Shan wahala idan zasu haihu gaskiya sannu da kokari,Dan ma dai kin min wayo yaron Nan babu inda ya baroki har idanun anya kunyi min adalci? Nine fa asassin Amma sai na Zama Dan kallo". Dan kwantar da kanta tayi a jikinsa tana fadin . "Raba dai dai mukayi Ni ya dauko kalata da kamanni Kai Kuma ya dauko jinsinka da jarumta irin taka in Sha Allah".. Nan suka saka yaron ga bada har wurin Daya suna kallonsa. A tsakanin kwanakin zahra taga Baki fiye da tunaninta ga kayan baby da zannuwa na kece raini kamar hauka, Su Aunty Hassana dasu momi kaltume duk sunzo, ganin baby ana gobe suna ma suka dawo sunan yayi armshi fiye da tunanin Mai tunani yaro yaci sunan mahaifin Zahra Abbie ne yace ayi Mata Kara. Taro ya tashi lafiya inda Zahra ta samu Kaya da zunzurutun kudi. Yaron suna kiransa da suna Ayyan. Bayan suna babu yanda Hajiya Inna batayi ba akan ta tafi da Zahra gidanta Amma ya k'ek'ashe kasa yace babu wannan maganar dole ta hakura ta zauna a gidan Dan tace bazata zuba Ido ba a cuci yaro. BAYAN SHEKARA BIYU. Yaro ne fine boy Yana sanye da jc na club din real Madrid a jikinsa, suka fito daga cikin stadium ta old Trafford dake ingila ina akayi Wasa tsakanin Manchester United da Madrid din in da Madrid ta lallasa Manchester United da ci uku da nema. Motarsu Mai shigen sport car suka shiga Mahmud ya harba Kan titi, Saida suka dauki hanya sosai sannan ya shafa sumar yaro mai laushi da santsi. "My Ayyan..". Fararen idanunsa ya dago masu Kama Dana uwarsa ya kalli uban. "Yessss my papa" Ya fada da salon iriin Hausar Yara. "Me mameen ka tace ka sawo mata?". Shiru yayi Yana tunani sannan yayi tsalle akan seat din da yake tsaye a gaba kusa Mahmud ya Fara fadin. "A. P.P.L.E". "That is right my Ayyan". Sun biya sun sawo Mata Apple din da sauran fruits suka nufa gida tana kitchen tana girki suka shigo da sauri ta fito tana ga fadin. "Babana Ina sakon Dana baka". Ledar Apple din Mahmud ya mika Mata Yana fadin. Da alama an Dace Dan wannan karon masoyin Apple ne ko masoyiyar Apple ko masoyan Apple". Ayyan ne ya wuce dakinsa da gudu da ledar chocolates dinsa Dan kada Zahra ta rage tace zata hada nasa makaranta. Saida ya shige sannan Mahmud ya bude Mata hannuwa ta shige tana dariya, cikinta ya Dan shafo Yana fadin maman twins muje aji dani Naga alama wannan karon ta juya tunda mune a ciki. Tammat bi hamdillah. Subahanakallahumma wabi hamdik Ashshahadu an la'ilaha illa anta Astagafiruka wa'atubu ilaik.