Advertisements
Chapter 24 Reading Bintu Diyar Bayice Jinin Gado By Khadija Sidi BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Bintu Diyar Bayice Jinin Gado By Khadija Sidi

Author :  Khadija Sidi Category :  Complete Novels

Chapter   24 / 24

69K to 70.2K   out of 70.2K words

ce da Ladiyo

‘’wuce mu tai d’akin horo’’

Da sauri Ladiyo ta yi gaba Bintu na biye da ita, ita kuwa Maman Cangwai bin Bintu ta yi da ido, cikin ran ta kuwa fad’i ta ke lalle dole ta aika da sak’on neman taimako Sa’ayrasa domin kuwa alamu ya nuna Bintu mai yin gaban kan ta ce.

Cikin sak’ar zuci Sadauki wanda ke zaune bisa daddumar da ke shimfid'e a lambu ya ke duban baiwar da ta zo masa da amsar Bintu gare shi. D’aya da ka cikin bayin sa ne ya furta

‘’gide Gimbiya d’iyar Sa’ayrasa ba ta da masaniya akan girman Yarima Sadauki, ko shakka babu za ta tuba Allah shi taimaki Yarima’’

Baiwa na mai gyad’a kai cikin amincewa da maganar na bawan ta ce

‘’kwaran gaske, tuba ta ke ran Yarima ya dad’e’’

Murmushin mugunta Yarima Sadauki ya saki, cikin ran sa ya na mai jaddada dana sanin da Bintu za ta yi bisa ga kuskuran da ta yi a gare shi, tabbas ta tari aradu da ka dama dai ta bar abin ya tsaya ga mijin ta da ya fi mata sauk’i, zai kuwa nuna mata bakin rijiya ba wajan wasan makaho ba ne. Mik’ewa yayi tsaye yayinda bawan sa yayi saurin matso da takalman sa gaban sa. Cike da tak'ama ya sanya bayi na masu ram masa baya su ka d'au hanyar fita.

‘Dakin Horo kuwa Lantana ce ta idda sak’on Maman Cangwai, nan da nan kuwa Dogarin horo ya shiga gyara tsumagiyar sa domin aiwatar da umarnin Gimbiya Fatima. Sauran bayi fada kuwa tuni labari ya zaga, sun yi tattaki zuwa d’akin haro domin ganin yanda baiwa za ta fuskanci hukunci. Kujerar horo aka sanya baiwa ta zauna yayinda aka zuba mata ruwa bisa cinyar ta har zuwa k'asan k'afafun ta yanda ko da zafin tsumagiya zai sa fitsari ku6uce mata ba zai nuna ba. Waje yayi tsit kuka baiwa kad’ai ke tashi yayinda Dogarin horo ya d’aga tsumagiyar sa ya na shirin sauke ta bisa cinyar baiwa muryar Ladiyo ya dakatar da shi ta hanyar fad’in

‘’dakata Dogarin horo, Gimbiya Fatima ce tafe!’’

Tsayawa yayi cak yayinda Bintu ta taho, bayi na bud’a mata hanya haka kuma ba su fasa kai gaisuwa gare ta ba har ta iso gaban dogarin horo. Cikin bayin kuwa har da Bakar number wato babban bawan Barde wanda jin an ambato sunan Bintu ya shiga baza ido domin ganin matar uban gidan sa.

Ganin Bintu gaban sa Dogarin horo ya saki tsumagiya k’asa ya na mai kai gaisuwar sa ga Bintu ta hanyar nuna ladabi da mik’a kai a gare ta cikin aminci. Bintu na duban baiwar da ta had’a hawaye da majina, a hankali ta k’asara gare ta, hannu ta sanya ta tada ita tsaye kana ta ce

‘’gide bar kukan ga haka, wagga hukunci baya bisa kan ki, maza tai abun ki, idan uwar gijiya ba ta zama mai tausayawa ga bayin ta ba shin ana tunanin za mu sami tausaya daga mai duka wanda mu an bayi gare shi?’’

Jin haka bayi su ka hau sowa, shewa da tafi, daga masu fad’in

‘’Allah shi ta ya mi ki, Allahu y ja da ran gimbiya, Allah ya sa ki dad’e ki na yi’’
Sai masu fad’in

‘’madallah da Gimbiyar Sa’ayrasa, mun biki, mu na madallah da ke’’

Ita kuwa baiwa ba ta san sa’in da ta zube k’asa hannayen ta rungume da k’afafun Bintu tsabagen farin ciki ma kasa magana ta yi. Bintu na mai murmushi a gare ta tare da duk kanin sauran bayi da ke wajan ta zame k'afafunta, bayi na mai darewa domin su bata hanya cike da nuna k’aunar su gare ta haka ta d’auki hanyar komawa turakar ta.

Babban bawan Barde da tun kan Bintu ta bar wajan ya ruga domin komawa ga Barde, tuni ya labarta masa yanda ta kasance tsakanin Bintu da bayi, ya k’are da

‘’lillahi warasulihi Gimbiya Fatima ta isa d’iya adala wacce ta san darajar bayi ko shakka babu halayyar ta ya yi kamanceceniya da na ka ran ka shi dad’e, aradu ma kuwa. Bayin Fabarusa za su zama su na alfahari da ita tun daga rana ita yau’’

Barde na mai duban Bakar number, duk maganar nan da ya ke hankalin sa ba gun sa ya ke ba, tunanin K'amariyya ne ya addabi ran sa ya na mai takaicin ina ma dai ita aka d’aura masa ba k’anwar ta ba, shin da wani ido ake so ya dube ta a matsayin mata har ya kai ga kusantar ta?


****

Sadauki da tashi tawagar kuma a nasu 6angaran fitowar shi daga lambu bayan ya gama d’an shawagin sa ya na mai tunanin matakin da zai d’auka bisa matar Barde ya hangi Bintu da Ladiyo a kan hanyar su na komawa turaka. Tsayawa yayi cak idanun sa bisa Bintu ba komai ya ja hankalin sa ba sai yanayin zubi da tafiyar Bintu da ya gani iri d’aya sak da na baiwar nan ta Sa’ayrasa da ya gani a daren jiya har ya kai ga aikawa Gimbiya Fatima muradin sa na ganin bayin Sa’ayrasa. Idanun sa kan Bintu ya furta

‘’gide wagga d’iya ba ita an baiwar Sa’ayrasa da na gani a daren jiya ba?’’

Bawan sa na mai duban Bintu da Ladiyo ya furta

‘’kwaran gaske, waccar mai tafe bayan Gimbiya Fatima na d’aya daga cikin bayin Allah shi taimaki Sadauki’’

Sadauki na mai girgiza kai cikin nuna rashin yarda da maganar bawa ya ce

‘’bayan Gimbiya Fatima? Wacce Gimbiya Fatima? Matar Barde gide? Yoto ai ni bayi biyu na ka gani, waccar mai tahiya irin na d’awisu, ma’ana mai sanye da lifayar can, ko shakka babu ita na gani sanye cikin kayan bayi a daren jiya, ba na mance abu mai kyau, ba zan manta da wagga tahiya irin ta ta ba, duk duniya ita d'ai ta na gani da wagga baiwa na iya taka k'asa kamar d'iyar Saraki'’

Bawa na tsoran kada ya yiwa Yarima Sadauki musu ya fuskanci hukunci, dan haka wannan baiwar da ta kawo sak’on Bintu ya yiwa nuni da hannu ya na mai tambayar

‘’ya ki nan, gide shin ko waccar mai tahiya tare da baiwar Sa’ayrasa baiwa ce?’’

Ko da baiwa ta ware ido ta hangi Bintu tuni ta shiga girgiza kai kana ta ce

‘’ina mai tuba, wagga Gimbiya Fatima d’iyar Sarki Inuwa na Sa'ayrasa ce ran Yarima ya dad’e’’

Jin haka Sadauki ya shiga shafa gashin bakin sa, har ila yau be d’auke idanu daga kan Bintu ba, dan ya tabbata ita d’in ya gani cikin shigar bayi, abun da ya kasa ganewa shi ne

‘’me zai sa Gimbiya, d’iyar Sarki kuma matar Barde shigar bayi? Shin menen dangantaka ko alak’a da ta ke da Shi mai k’arfi haka tsakanin ta da bayi da har za ta aiko masa da bak’ar magana dan kawai ya nemi ya gana da bayin Sa’ayrasa? Ko dan ta san ya gan ta daren jiya ne? Shin akwai wani lamarin 6oye dangane da ita?’’

Tambayoyin da ya ke ainawa cikin ran sa kenan yayinda tunani kala kala ke ratsa zuciyar sa. Ya na mai duban bawan sa ya ce

‘’ban yarda da wanga lamari ba, ina so a yi min bincike akan lamarin wagga Gimbiya, a gaggauta yi ba tare da sanin kowa ba, in kuwa na ji magana ta fita rariya sai da uwar mutum ta haifi wani!’’




🐫🐪🐫🐪🐫🐪

24 / 24