Author : Mamuh geee Category : Complete Novels
taka qafar da qarfi nanma saidata kuma sumewa ya kuma zuba mata ruwan qanqara.
Tana farfadowa ko motsi bata iyayi sbd azaba...
'Daga qafa yayi zai kuma takawa cikin kakkausar murya yace,
Tell me su waye partners 'dinki?
Girgixa kai tayi cikin wasu irin azababbin hawaye sbd ko bakin bazata iya bu'dewa ba sbd galabaituwa.
Wani mahaukacin naushi yakai mata a baki saiga haqoranta biyu sun fa'do tareda jini cikin 'daga murya sosai yace,
Bazaki fa'daba kenan?
A wahalce tace,
Ni ka'dai ce.
Takaici da baqin ciki yasashi rufeta da duka da yana tattaka qafarta.
Saidaya tabbatarda bata motsi ya fice kayansa duk jini ya 'dan ta6asu.
Koda ya isa gida part 'dinsa yaje yayi wanka ya shiryo kafin ya nufo 6angaren.
Ummi da inna Rabi ne kawai a palon suna fira mama kuma na kan dining tana cin abinci.
Gaida ummi yayi kafin inna Rabi dan baima lurada mama ba.
Bedroom 'dinta ya nufa kai tsaye yashiga tareda rufowa.
Bai gantaba amma yaji motsin ruwa a toilet..
Bakin window yaje ya tsaye tareda zuba hannuwansa a aljihu ya lumshe idanuwansa.
'Daureda 'dan qaramin towel ta fito sai wani qaramin a hannunta sbd hadda wankan tsarki tayo na period data gama.
A jiqe dogon gashinta yake haryana 'digar ruwa
Fatarta sai qyalli take sbd lafiyayyen gyara da hutu datake samu.
Sam bata lura dashiba saidatazo gaban mirror ta gansa a tsorace ta juyo cikin rashin sa'a bedroom slippers 'dinta suka janyeta.
Ahhhhhhhh"""ta fa'da da qarfi lokacinda takai qasa kan qafarta ta dama taji azaba.
A 'dan rikice ya juyo yaganta qasa ya matso da sauri tareda riqota cikin lafiyayyar muryarsa mai kashe jiki yace,
Oh god fad'uwa kikayi,,let me help u up.
Banxa tayi dashi tareda fara qoqarin miqewa Cikin azaba,,
Wata qarar tasaki tareda kiran sunan ummi..
Kallonta yayi cikin mamakin yanda hartasan takira ummi afterall ma takaicinsa da haushinsa yake gani a fuskarta bayan yasan ba lafiya ne da ita.....
Unbelievable'''""yafa'da a ransa sbd gano alamar kenan tasamu sauqi...
Hmmnnn well since bata son asani let's do it the way she wants it afterall zanfi jin da'din hakan.
Qura mata oily eyes 'dinsa yayi yana kallon tsakiyar idanuwanta da itama shitake kallo fuska a tamke.,,
Hannu ya 'daga ahankali yakai fuskarta tareda tattara jiqaqqen gashinta ya maida mata baya tareda kashe mata ido 'daya.
Zaro ido tayi cikin takaici takuma zabura zata miqe yayi saurin riqeta tareda matsoda fuskarsa daf da tata tayi saurin rintse idanuwa da qarfi
A kunnenta yakai bakinsa saida ya hura mata iska ahankali yace,
Bazaki iya tashiba so gwara ki nutsu yau nine mai hidimarki.
Turesa tayi da qarfi tareda 'daure fuska tana qara riqe towel "dinta dake qoqarin kwancewa.
Qirjinta da hannuwanta ke kai ya kalla tareda duqawa ba zato taji ya 'daga cak ya zaunar a bakin gado tareda 'daga qafafun ya 'dora mata a gadon.
Wardrobe 'dinta ya bu'de ya 'dauko mata bra da pant cikin undies 'dinta ya miqo mata kasa 'dagowa ta kar6a tayi sbd takaici wai ace jamaal ke ta6a bra da pant 'dinta bama ganiba
Sake budewa yayi ya 'dauko mata doguwar rigar atampa 'dinkin mara hannu.
Matsowa yayi ya zauna kusa da ita tareda 'daga bra 'din ya nufi qirjinta zai Zare towel 'din akai knocking qofa.
Fixge bra 'din tayi da sauri tareda turawa under pillow tana kallon qofar.
Miqewa yayi jiki amace sbd yayi niyar yamutsa tunanin neesar amma Allah ya qwaceta.
Da ido ta nuna masa qofar tana murmushin mugunta batareda data saniba.
Murmushi shima ya saki tareda ranqwafowa ba zato taji ya fixge towel 'dinta daga sama harsaida no**** 'daya ya bayyana tayi saurin riqewa tareda jifansa da pant 'dinta batareda ta ankaraba daidai nan ayeesha data gaji da bugawa ta bu'de qofar pant 'din ya sauka kan fuskarta..
A razane ta 'dago takalli Jamaal 'din ya fuske tareda ra6ata ya fice.
Gurin neesah ta maida kallonta jikinta har wani mazari yake sbd tsabar baqin ciki da kishi.
Juyawa tayi a fusace tabar gurin dan dama dawowarta kenan tazo duba ubanda yake a 'dakin dataji ummi tace yana ciki ta fake da dubo jikin neesar zata.
Ta6e baki neesah tayi tareda jawo bra 'dinta tafara qoqarin sakawa.
Ko Palo bata tsayaba ta fice takoma sashensu.
Zama yayi kusada ummi ya tattaro nutsuwarsa idanuwansa na canxawa yafara fa'dawasu ummi abinda ke faruwa.
Duk inda hankalin ummi yake tashi yayi sbd tsoro da mamaki,,
Mama kuwa hawayen baqin cikin halinda suka saka mata 'yarta ne ya gangaro mata ta share tareda miqewa tabar gurin tareda alqawarin gobe komai zaizo qarshe sbd tashiryawa ayeesha trap 'din dazata tonawa kanta asiri da kanta.
Yusuf ne yashigo ummi ta jinjina masa tareda 'dorawa da fa'din,
Yusuf kuje ayi qoqarin miqata gurin hukuma sbd barinta a hannun Jamaal zai iya aikata komai cikin 6acin rai.
Murmushi Yusuf yayi yace,
Karki Damu ummi so muke mu kama sauran saimu miqasu gaba 'daya.
Miqewa sukai suka fice Jamaal na qara kallon qofar bedroom 'dinta qasaqasa.
Da yamma suna zaune a palo suna 'dan ta6a fira ahankali kiran mamy yashigo wayar ummi ta miqe ahankali tabar palon sbd amsawa.
Mama da neesah dake kwance kawai suka rage a palon
Gyara zama mama tayi zatai magana saiga ayeesha tashigo fuskarta a sake sbd so take ta bugi cikinsu taji ina akakai zeey dan ta tabbatarda zuwa lokacin kowa yagamaji.
Zama tayi cikin sakin fuska ta gaida mama kafin ta kalli neesah tace,
Mama naga neesah ba laifi kamar tana samun sauqi ko.
Cikin sakewar fuska mamar tace,
Kedai bari ayeesha Ai wlh neesah taji sauqi khadija ce tarage itama kwanakin nan sauqi yafara zuwa sbd alluran da kullum Dr sulaiman ke zuwa yanayi mata,,,,
Murmushi ta qaqalo tareda cewa,
Mama nikuwa wannan tsinanniyar qawar neesah dazan ganta dasai na kusa hallakata sbd wannan ai bala'i ce.
Bari kedai ayeesha nima haka nakejin kamar na shaqeta sbd abinda taiwa khadija amma Jamaal ya hana sbd wai da'aka tambayeta dalilinta nayin hakan sai cewa tayi soyayyarsace takaita ga aikata hakan hardafa ikirarin saitaga bayan duk wata matar Jamaal,
Ha'de fuska ayeesha tayi tareda qara kallon mama tace,
Wai itada kanta ta fa'di hakan?
Qwarai kuwa muma shiya 'daga mana hankali kada takuma samun nasarar cutatar da wani.,
Yanxu dai tasaka Jamaal yayi alqawarin zai yafe mata yabarta matuqar ta fa'da masa sauran
Sannan kuma abin haushi wai harya fara tausaya mata mudai tsoranmu karyace zai aureta bayan ta shiryu wlh duk wannan shiyafi 'daga hankalinmu.
Tafarfasa zuciyar ayeesha tafara sbd jin wai dama zeey son Jamaal take Ashe shiyasa tafita zaqalqalewa akan komai,
Sotake yanxu tafa'da masa sunana dan yasa arufeni ita kuma ya aureta kenan...
Tabbas zata nunawa zeey tafita zama kunama dan bazata bari takuma ganin wata safiyarba bayan ta yau.
Ta gefen ido mama takalli ayeesha tareda girgiza kai alamar tarkonta ya kama ayeeshar..
Muskutawa tayi taci gaba da cewa,
Wannan zeey mu bala'i ce shigowarta rayuwarmu dan da ace Jamaal baiyiwa ummi alqawarin harbe koma wanene ta fa'daba da wlh ni zan harbeshi da kaina.
Kasa controlling kanta tayi cikin tashin hankali da masifa tace,
Mama shi jamaal 'din ya nuna zai iya aurenta idan tafa'da masa abinda yakeson ji?
Haka ya nuna saidai mu bamuyi na'am da hakanba hasalima dazamu samu ta mutu dasai ummi tafi kowa farin ciki sbd dagake batason Jamaal ya qaro kowa.
Tsaye ta miqe cikin zurfi a tunani tanajin zuciyarta zata iya bugawa matuqar bata 'dora bindiga akan zeey ta watse kantaba.
Kamar daga sama taji mama na cewa,
A gidansa block 27 presidental Jolly street yakaita wat do you think will happen idan tafa'da masa komai?
Batareda ta tsaya sauraron sauran bayaninba tabar palon a bala'e.
Wani mugun murmushi mama tasaki tareda kallon neesah suka saki murmushi atare.
Direct gidan yakoma bayan sun rabu da Yusuf.
A kwance take kamar gawa ko numfashi da qyar yake fitar mata sbd azababben halinda take ciki sbd qafarta tuni tafara wani kore koren alamar ru6ewa.
Tsayawa yayi akanta tareda zuba hannayensa a aljihun wandonsa ya kalli shu'aibu mai gadi yamai alama da hannu.
Bokitin ruwan qanqara ya 'daga tareda juye mata kafin ya lafta mata wata mahaukaciyar bulalar dukan jakai.
Ko ihu kasawa tayi sai wani 'dan marayan nishi tasaki.
A 'dage yace,
Are you ready to talk bitch***?
Numfashinta taja daqyar idanuwanta na rufewa
Murya na fita da qyar tace,
*_INNA RABI CE_*
Mamuh💋
🌲 *R H F W F*🐄
_Don't forget to vote, follow and comments_