Author : FARKON LABARI Category : Complete Novels
da mahaifiyata wai ita babu mai kiran *yarta da sunan Musulmai Fatima. Shi kuma ya ce ba zai kira *yarsa da suna Rufkatu ba. Mahaifina yana kirana da Fatima. Mutanen gari suna kirana da Prety ma'ana mai kyau. Kowanne suna ina amsawa, amma da aka sakani a makaranta Rufkatu Lamin Mahaifiyata tasa ake rubutawa.
Ina da shekaru hudu aka haifi kanina kamarmu daya aka saka masa suna Bobby, mahaifina ya rada masa suna Abubakar. Bayan ya shekara biyu aka haifi *yar autarmu, mahaifiyata na kiranta da Rebecce Mahaifina yasa mata sunan kanwarsa mai binsa Hajara. Bacin rai sosai ya dasu a zuciyar mahaifiyata danme mahaifina yake yanka mana rago yake rada mana sunayen Musulmai baya kiranmu da sunayen data radamana. Bayan dashi aka yi yarjajjeniya *ya*yansu zasu bi addininta, ya ce ya yarda. Me yake nufi kuma yanzu? Fadan safe daban na rana daban. Ya shaida mata shi ba wai yana nufin *ya*yansa dole sai sunyi sallah ba, amma shi abun kunya ne wataran su shiga danginsa aji sunayensu bana Musulmai ba. Mahaifina yana ta aike a nemar masa gafara wajen Mahaifiyarsa, ace ta yafe masa yasan yayi mata laifi. Dakyar ya samu ta aiko masa da magana mai dadi ta ce ta yafe masa kuma tana masa fatan Allah Ya shirye shi ya kare shi daga barin addininsa kamar yadda ya yarda ya haifi arna a cikinsa. Da ya dauki hutu a wajen aiki, Mahaifiyata ma tana aiki a banki itama ta dauki hutu mu ma aka yi mana hutu a makaranta saiya cika mu a mota muka nufi Gombe muje muga danginsa, dangi kuma su ganmu.
Munsha wulakanci, munga takaici iri-iri domin baro-baro ake nuna mana tsana da zafuta da hantara. Ko randar Kakarmu muka je muka bude muka sha ruwa sai an fasa randar an sayo wata wai marasa tsarki sun saka mata najasa. Bamu isa mu zauna akan tabarmarsu ba balle abun sallarsu sai ayi ta yayyafa ruwa koma a wanke gaba daya. Mahaifiyata taji haushin wannan wulakanci da ake yi mata da *ya*yanta sosai, tasha alwashin har abada ba zata sake zuwa Gombe ba. Mahaifina ma baiji dadin yadda aka yi mana ba, amma ya kasa tarar danginsa balle yajawa kansa. Muka har-hado muka dawo gidanmu Jalingo.
Yaren Fulatanci shine yaren da yawancin *yan garin suke yi don haka fulatanci Mahaifina yake yi mana. Mahaifiyarmu ma haka amma tafi yi mana magana da turanci wasu lokutan da yarenta Igbo. Me rainonmu da mijinta maigadinmu suna zaune a boy's qoutern gidanmu su kuma yarensu Tangala ne mutanen Billiri karamar hukumar Gombe. Tun muna yara suke yi mana yarensu na tashi ina jin tangalanci. Rayuwata tana cike da rudani nakan kasa tantance wazan bi uwata ko ubana. Na tashi naga Mahaifina na yin sallah sau biyar a rana. Haka kuma na tashi naga Mahaifiyata tana zuwa wani waje suna bauta kullum. Gata ma'aikaciyar Banki ce tana fita aiki da sassafe sai da yamma likis take dawowa gida amma da zarar ta dawo ko hutawa bata yi saita shirya ta nufi wajen bauta har dare suna addu'a. Ranar Asabar da Lahadi kuma saita shiryamu ayi mana ado ni da kannene mu tafi wajen bautarsu. Mu bar Mahaifinmu a gida yana karatun Jarida wani lokaci yana karatun kur'ani mai tsarki.
Nafi son Mahaifina fiye da Mahaifiyata saboda nafi zama dashi don haka munfi sabawa. Idan ya fita wajen aiki karfe tara na safe shima baya dawowa sai da yamma likis. Yafi Mahaifiyata sakin fuska da wasa da janmu a jiki musamman ni yafi jana a jiki fiye da kannena, su kuma sunfi son Mamarmu. Ina wasa da Mahaifina kamar wani abokina, ya goyani, muyi wasan *yar tsanata dashi, yasa mana kida da waka ya tashi ni dashi muyi ta rawa. Amma baya garajen ya koya mun karatun kur'ani saboda gudun bacin ran Mahaifiyata.
Watarana ne Mahaifina yana sallar la'asar baisan ina bayansa ina binsa sallah ba. Mu dai munji muryar Mahaifiyata kamar zata tsaga gidan don kara muka juyo a firgice mu dukkanmu ni da shi. Sai ta ci gaba da fadace-fadacenta da zage-zage wai ashe daman idan bata nan sallah yake koyamin? Yayi mata rantsuwa da Allah shi bai san ina bayansa ba ina binsa Sallah. Ranar naga tashin hankali a wajen Mahaifiyata tayi min dukan da tunda nake babu wanda ya tabamun irinsa har jikina ya fashe, masu aikin gidanmu da mahaifina suka dinga riketa suna rokarta tayi hakuri tace sai tabar gidan ita da *ya*yanta baza suyi addinin Musulunci ba kuma zamanta da musulmi ya kare. Dakyar ta hakura, bayan Mahaifina yayi mata alkawarin irin haka ba zata sake faruwa ba.
Shekaruna basu wuce tara ba a lokacin amma kwakwalwata tana da kaifin hankali da tunani. A kullum kuma a koda yaushe bani da abun yi sai tunani ina so in tantance me yasa kowa da abunda yake bautawa? Haka kuma nake bi ina tambayar manyan da shekarunsu sukafi nawa wai shin su me suke bautawa, bayan sun fadamun musulmai ne ko ba Muslmai ba ne. Sai ince me yasa suka zabi wannan addinin basa yin dayan? Sukan rasa amsar da zasu bani sai suyi dariya kawai. Huzaifa wani saurayine makwabcinmu shine baya taba gajiya da bani cikakkiyar amsar duk tambayar da nayi masa akan addininsa da ma wanda ba nasa ba.
Idan na tashi da safe, Tabita me aikinmu sai ta shiryamu mu tafi makaranta. Mahaifiyarmu na da mota ita zata sauke mu a makaranta sannan ta wuce wajan aikinta. Mahaifinmu kuma sai ya dauko mu daga Makaranta shima dai-dai lokacin yake dawowa daga aiki sai mu dawo gida tare. Tabita ta bamu abinci muci, sau da yawa bayan Mahaifinmu ya ci abinci saiya fita wajen abokansa can wata unguwa mai nisa. Kannena kuma sai su kwanta suyi ta barci ko su fita kofar gida wajen abokansu. Da Tabita nake zama muyi ta hira a hankali sai take nuna mun abunda take bautawa. Abunda take bautawa kuma yasha bambam da abunda Mahaifiyata da Mahaifina suke bautawa. Wani sassakekken itace ne anyi mutum-mutumi da shi an rataya masa kahunhunan rago da wasu gashi-gashi. Sai suzo ita da mijinta su durkusa a gabansa suna rokarsa duk abunda suke so wani lokaci har suce nima in zo in durkusa in rokeshi zai ba ni. Wa'iyazubillah. Haka kullum muke yi da su. Idan kuma na gaji da zaman gida sai in sa takalmina in fito in tafi wajen kawayena da muke yin wasa tare, wadanan kawaye nawa ba wasu bane illa arnan daji. Zaka iya hango bukkokinsu daga can nesa da gidajenmu, sunan yaren mumuye.
Ehem,, gaskiya na gaji da zama, za kuji komai daga bakin IMAN..RUFKATU..PRETTY..FATIMA zuwa gobe da yardar Allah.
Reedwan Suraj Isma'il
>>>>>>>>>>>>>> YARENA ADDININA
____CI GABAN LABARIN
Kauyen Mumuyawa ne wajen wasana, mun saba da *ya*yan mumuyawa sosai tun bani da wayo muke tare. Har takai ta kawo ina jin yarensu sosai suma kuma suna jin yaren Fulatanci. A lokacin mutanen kauyen mumuyawa basa saka sutura matansu da mazansu yara maza da mata fata suke daurawa a tsantsarsu su rufe al'aurarsu kawai. Budurwar da batayi aureba ita ke daura fata a kirjinta. Matan aure kuwa kirjinsu a bude haka suke yawo. Ranar Juma'a ne ranar kasuwar Jalingo ranar ne kawai idan zasu shiga kasuwa su sayar da giya, burkutu suke daura zani su cire fata. Karku dauka zani da riga sosai irin na mutane suke daurawa a'a wani dan fatarin siket ne suke dinkawa iya guiwarsu kirjinsu a bude su dau tukunyar giya burkutu a kansu su biyo layi-layi suna tafiya, suna karyar kubewa a gonakin da suke giftawa suna ci gayau-gayau. Masu goyo suna yin goyo da fata.
A kasuwar Yalwa suke cin kasuwar giyarsu a karkashin wata katuwar bishiyar mangwaro suke zama da fulatanci ana kiran wajen (La mangwaro). Babu abunda suka sani sai tsafi kuma wani dodo suke bautawa. Ma'ana wani mutum suke zaba a cikinsu su nada shi abin bautarsu. Yana saka wata riga duk jikinta gashi ne zaro-zaro ko fuskarsa baza ka iya gani ba shi suke bautawa. Matansu da mazansu kansu a aske yake. Haka hudar kunnuwansu da hanci barka-barka. Duk lokacin da amfanin gonarsu ya nuna wato lokacin cin doya akwai biki da suke na musamman na godewa dodansu daya sa doyarsu ta nuna, tayi yawa. Wa'iyazubillahi basu san Allah ba kwata-kwata wanda shi Ya haliccesu, Yasa amfanin gonarsu ya nuna yayi albarka. Kafin ayi wannan bikin cin doyar sai an nemo kai, ma'ana sai sun yankawa dodo mutum sun bashi jini yasha sannan a fara kade-kade asha biki.
Idan dan uwansu ya mutu suna jera itatuwa sai su shimfida tabarma akan itatuwan su lillibe jikin su fito da kai da kafafuwa a waje su dora aka suna gudu a titina suna wake-wake. Haka ranar da za'a binne gawar sai suyi tsafin da gawar zata tashi da kafarta tana layi suna biye da ita ana tafi ana wake-wake taje ta fada a kabarinta sannan su rufe kabarin.
Iyayena duk suna wajen harkokinsu babu mai nemana balle susan ina nake zuwa su hanani. Akwai lokacin da idan na tafi tunda rana sai magaruba in dawo muna ta wasa da *ya*yan mumuyawa, wani lokaci har kayana nake cirewa in daura fata kamar yadda suke muyi ta gadarmu sai zan tafi gida in canja. Idan na kwana biyu banje wasa garin ba kawayena su Mungai su Maho sai su biyoni har gida amma ba shigowa suke ba suna labewa a jikin wunduna suna mun busa da hannunsu da bakinsu sai in gane sunzo sai in saci jiki idan iyayena na gida in fita da gudu wajensu mu dunguma mu tafi gidansu.
Ina da shekaru goma dai-dai na gama makarantar Primary muka dauki jarabawar (common interance examination) kafin jarabawar mu ta fito har zaman gida ya ishe ni. Kannena sun tafi makaranta, iyayena sun tafi wajen aiki saini kadai a gida da mai aikinmu Tabita. Ina bata labari cewa "Ina so muci makaranta daya ni da kawayena. Sai Tabita tace mun inzo in roki abunda take bautawa zaisa muci makaranta daya da kawayena. Inje muyi ta rokar sassakekken itacen nan. Idan naje wajen kawayena mumuyawa suma sai na fada musu bukatata ina son muci makaranta daya da kawayena. Suma sai su ce muje wajen abunda suke bautawa a rokeshi, nan ma muje mu durkusa mu fadawa dodon bukatar sai ya ce mun an gama. Na dawo a hanyata ta tahowa gida dai-dai kofar gidan makwabtanmu wato gidan su Huzaifa na hadu da Bilki, da Amina kannen Huzaifa ne kawayena ne zasu tafi makarantar Islamiyya. Sanye suke da hijabansu har kasa da kur'anansu a hannunsu sun bani sha'awa matuka. Bayan mun gaisa sai nace musu "Inzo muje makarantarku? Wani kallo suka min na wulakanci Amina ta ce "A haka zaki bimu? Kalli riga shimi ce a jikinki da dan karamin siket iya cinya, kanki ba dankwali gashinki a waje. Ance miki makarantar arna ce? Bilki ta ce da Amina "Ke kike mata bayani ma ko tasa hijabi ai ba zata iya binmu ba tunda ba Musulma bace sai anyi mata wankan shiga Musulunci. Suka wuce abinsu suka barni anan a tsaye. Ashe yayansu Huzaifa na gefenmu a zaune akan abun sallarsa ya idar da sallar la'asar yana karatun kur'ani. Nazo zan wuce jikina yayi sanyi babu abinda nake nanatawa a raina sai magnar Bilkisu da Amina. Kaina ya daure ina tunanin su kuma wadannan me suke bautawa da har zasu ce bazan iya zuwa a haka ba sai nayi wankan shiga Musulunci.
Muryar Huzaifa ce ta katsemun tunanin dana ke, daman daga shi sai Mahaifina suke kirana da Fatima. Na juyo da sauri sai naga Hamma Huzaifa ma'ana Yaya Huzaifa da fulatanci. Na karasa wajensa na cire takalmina na zauna akan takalmin a gabansa, fara'ar da na saba yi yaga sai kadan yasan lallai maganar da kannensa suka fadamun tayi min ciwo. Ya ce "Fatima yau bakya fara'a lafiya?
Na gyara zama na ce "Hamma Huzaifa wai shin a addininku wa ku ke bautawa? Huzaifa yaji dadin tambayar dana yi masa yayi murmushi ya ce "Fatima ni Musulmi ne kuma duk wani Musulmi Ubangiji yake bautawa Shine Allah Shine Ya halicci Duniya da Lahira, Ya halicci dukkan mutanen duniya da aljanu, shine Ya ke mana ruwan sama amfanin gona ya fito mutane su girba suci, Shine Yake rayawa kuma Yake kashewa, Shine Ya ke sa rashin lafiya kuma ya bada lafiya, Shi Ya ke azurtawa kuma yake talautawa. Bai haifa ba ba'a haifeShi ba. Ma'ana baShi da uwa baShi da uba bashi da da ko jika. Baya bacci kuma baya gyangyadi. Duk abunda mutane suke a duniya yana kallonmu mune baza mu iya ganinsa ba. Ya aiko mana da Annabi wato Annabi Muhammad (S.A.W) da sallah, azumi, zakka da Hajji idan kana da hali. Duk wanda bai yadda cewa Allah guda daya bane kuma Annabi Muhammad (S.A.W) Manzonsa ne to idan ya mutu zai dauwama ne a wuta. Allah Zaiyi masa azaba har abada.
Kamar hayaki haka naji zuciyata ta turnike nayi minti uku bance uffanba, can na shaki numfashi na ce "Hamma Huzaifa wa Mahaifina yake bautawa? Huzaifa yayi murmushi ya ce "Mahaifinki Musulmi ne, addininmu daya Allah guda daya yake bautawa kuma ya yadda Annabi Muhammad (S.A.W) Manzonsa ne. Na ce "Wa Mahaifiyata take bautawa? Huzaifa ya ce "Mahaifiyarki ba Musulma ba ce, bata yadda da Annabi Muhammad (S.A.W) ba. Nayi shiru can na ce "Wa Tabita me aikinmu take bautawa? Ya tambayeni "Yaya take addinin nata? Na fada masa yadda take sai ya girgiza kai ya ce "Tabita ta bata, tayi shirka tana bautawa itace ne kawai ba Allah ba. Itacen da da kanta ta sassako ta gina ta ce Ubangijinta ne kuma ko yanzu aka dauko shi aka ce ya biya bukatarta bazai iya ba, baya gani, baya magana, da za'a jefashi a wuta konewa zaiyi daman kuma itacen dafa abinci ne kawai.
Nayi shiru ina tunani a raina na ce "Tabbas zancen Huzaifa gaskiya ne, itace ne kawai Tabita take bautawa ko motsi bayayi. Na sake gyara zama na tambayeshu "To me su Mungai suke bautawa kawayena mumuyawa? Yayi min tambaya tsaf yaya suke bautarsu? Na fada masa saiya kyalkyale da dariya ya ce "Wannan mutum ne kamarki, suke nada shi suke saka masa rigar gashi. Babu abinda zai iya basu shima Allah ne Ya halicce shi kuma Allah Zai kasheshi. Bai isa komai ba kuma Allah Zai kona su. Daga nan ban sake cewa komai ba sai nasa takalmina na yiwa Huzaifa sallama na nufi gida zuciyata cike da wasu-wasi ina tafe ina kallon shukoki da bishiyoyi cike da *ya*yan itatuwa ina nanatawa a rai na duk wadannan Allah su Huzaifa ne yayi su. Ban tsaya a ko ina ba sai a boys' quarters mu don nasan Tabita ta gama abincin dare da share-share, ta rufo gidan ta koma dakinta. Ita kadai na samu a tsakar gidan tana cin tuwo. Ina isowa na zauna a gabanta zansa hannu inci abincin sai ta rike hannuna tace inje in wanke hannuna nayi wasan kasa na taba fatar mumuyawa. Naje na sami ruwa na wanke hannuna na dawo zan zauna, ta ce kar in zauna in shiga in roki abunda take bautawa cewar zanci abinci ya samun albarka a abinci. Duk a cikin yarenta muke maganar wato tangalanci. Ban ki ta tata ba amma ko dana shiga dakin bautar sai na tsaya kawai ina kallon sassakakken itacen nan cikin nutsuwa sai naga ashe kawai gunki ne, yayi min kama da *yar tsana. Nasa hannu na taba shi sai naji itace ne. Nayi masa tambaya na ce "Kana ganina ko bana cikin gidan nan? To fadamun da ina da ina naje yau? Shiru bai amsa mun ba. Tabita ta leko ta kwallamin kira ta ce me nake yi har yanzu, in fito ai ya ji saina fito nazo na zauna muke cin tuwo.
Munyi nisa da cin tuwo saina gyara zama na ce "Mama Tabita kinga wancan abunda kike bautawa itace ne kawai baya magana, baya ji baya gani. Idan na jefashi a wuta konewa kawai zaiyi daman kuma itacen tuwo ne. Kema ki dinga bautawa Allah daya wanda ya halicci duk mutanen duniya, Ya halicci duniya da lahira da shuka da bishiyoyi. Yana jinmu, Yana ganinmu mu bama ganinsa, kuma baya bacci ko gyangyadi. Kamar yadda Huzaifa ya fada mata ta haddace tas. Tabita ta kwalla kara ta zabura ta mike tsaye a tsorace ta ce "Pretty kece kuwa? A ina kika san duk wannan? Nayi murmushi na mike tsaye naje na wanke hannuna na dauki mukullin gidanmu a gefenta, murmushi kawai nake yi mata na daga mata hannu na fice na tafi na barta tamkar sassakakken gunki irin wanda take bautawa.
Iman ta surnano da hawaye tayi ajiyar zuciya. Mutanen dake wajen gaba daya sun sami wajen sun zauna daga dukkan alamu labarin Iman yana da shiga jiki. Cike yake da ikon Allah, Suhaif babu abinda yake sai girgiza kai. Reedwan kuma ya kasa kunne sai copy din labarin ya ke. Malamai sai fadi suke "Allahu Akbar" Iman ta ci gaba da cewa.
Misalin karfe bakwai na dare Mahaifina ya dawo ya iske ni a zaune a falo ina kallo. Ya tambayeni "Mummy bata dawo ba? Na ce "Bata dawo ba ta tafi da su Rabecca wurin bauta da yamma. Ya hau kan dinning table yana cin abinci, sai nazo na jawo kujera daya na zauna na dube shi nayi murmushi yayi murmushi shima ya ce "Fatima kina da magana ne? Na ce "Eh Daddy, wai shin Daddy wa kake bautawa ne? Ya dubeni cike da mamaki sai ya tambaye ni me yasa nayi masa wannan tambayar? Na fara bashi labarin addinai daban-daban. Na ce "Wasu na bautawa sassakeken itace. Wasu na bautawa dodo mai gashi duk jikinsa, wasu na taruwa a wani waje suna bauta, wasu kuma suna sallah. Sun yarda Allah daya ne, wanda Ya halicci sama da kasa da mutane da aljanu, da bishiyoyi da komai na duniya. Ya aiko Annabi Muhammad (S.A.W). Sai ya ajiye cokalin da yake cin abinci ya dube ni cike da mamaki ya ce, "To wanne ne addinin gaskiya Fatima? Na ce "Shi ne nake son in sani, sai yayi shiru yana kallona. Na mike tsaye na fara tafiya zuwa falon da kujeru suke,