Advertisements
Chapter 2 Reading JARUMA YAZILA by Abdul'aziz Sani BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

JARUMA YAZILA by Abdul'aziz Sani

Author :  Abdul'aziz Sani Category :  Complete Novels

Chapter   2 / 3

3K to 6K   out of 6.5K words

cikin yaransa ya hau gaban keken
dokin ya fara sarrafa dawakan aka cigaba da tafiya
aka nufi hanyar da ta nufi birnin sin.
Tunda aka fara wannan tafiya zuciyar nuzaira ta fara
bugawa da karfi domin ta tabbatar da cewa da zarar
sun isa gaban sarki Daksar asirinta ya tonu bisa
karyar data shirgawa mijinta cewa yaran sarki
raihanne suka saceta domin shi sarki Daksur ka sur
gumin ma tsafine wanda ka iya ganin duk abinda
yafaru tun gabannin su isa fadar tasa har aka iso
cikin kisra hankalin Nuzaira atashe yake bata da
sukuni al'amarin dayasa barzuk ya dubeta kenan yace
yake matata lafiya naga kamar kina cikin damuwa?
Tunda muka fara wannan tafiya bakice uffanba kuma
babu walwala da annu shuwa afuskarki koda jin haka
sai nuzaira tayi murmushi tace yakai mijina kasani
cewa ban taba shiga fadar sarki Daksur ba da
girmanaba saboda tun ina yarinya wata rana sa'adda
mahaifina ya je dani naga an sare kan wani mutun a
gabana saina firgita ainun na tsandara ihu tun daga
wannan rana kullun sai nayi mafarkin wannan abu
ina firgita acikin barcina saida ma haifina yanaimi
taimako awajen bokansa sannan na daina wannan
mugun mafarki yanzu dakace zamu fadar sarki
daksur sai mafarkin ya fadomin arai saboda haka
nidai bana son shiga fadar sarki Daksur ka samomin
masauki agari kafin mu isa fadar. Sa'adda Nuzaira
tazo nan azancenta sai barzuk ya bushe dadariya yace
kadaki damu yake matata lallai bazanje fadar sarki
batare dake.
Kamar yadda barzuk yayi alkawari haka abin ya
kasance wato da shigarsu birnin kisra sai ya kai
nuzaira cikin wani ka sai taccen gida irin na sarakai
wan da ke dauke da komai na jin dadin duniya harda
baruri da kuyangu masu hidima. Al'amarin daya
matukar bata mamaki kenan domin bata ga lokacin
da
aka biya kudin hayar gidanba kuma da zuwansu kofar
gidan ta ga masu gadin gidan sun tsube kasa sun
kwashi gaisuwa har nuzaira ta bude baki zata
tambaye
shi batun wannan gida sai yace saboda me zakiyi
mamakin mallakar wannan gida agareni ? Shin kin
manta ina daya daga cikin makusan tan sarki?
Nuzaira
tayi murmushi ta ce bana mamakin mallakar wannan
gida agareka amma ina mamakin dalilin da ya hana
ka
sanar dani labarinsa Barzuk yayi murmushi yace
sonake na shamma cekine nabaki mamaki kinga
kenana zamu tare a sabon gida nuzaira tace yanzu
idan katare anan birnin ya zakayi da wakilcin sarki a
kauyen Himsarul Aswad? Barzuk yayi dariya yace aiba
tarewa zanyi ananba kece dai zaki tare a cikin birnin
nan domin na fison 'yarmu tataso da wayewa ta zama
cikakkiyar 'yar birni mai waye war kai in yaso duk kar
shen mako nazo nata fi daku tare kubi yun.
Bayan barzuk ya nunawa Nuzaira bangarenta a cikin
wannan gida harta shiga ciki ta kwanta tana hutawa
kuyangi suka fara mata shidima sai barzuk yayi shiri
yata fi izuwa fadar sarki daksur.
Fadace kasaitacciya wadda aka kawatata da kayan
alatu
iri iri tamkar aljannar duniya sarki daksur na zaune
bisa wata kerarriyar kara gar mulki ta ka saita fadawa
sun kewaye shi a tsakiyar fadar ga wasu tsala tsalan
'yammata sai tikar rawa suke cikin mummunar shiga
mai baiyana tsaraicinsu.
A kaida duk sa'adda sarki ke kallon wadannan
'yammata yayin da suke tikar rawa yana dariya da
murmushi amma a yau sai sarki ya tur bune fuska
babu annuri atare da shi koka dan kuma tun da ya
fito
fadar haka ya ka sance cikin rahin walwala da sukuni
kallo daya mutum zai masa yasan yana cikin tsananin
bacin rai.
Al amarin daya matukar dugun zuma hankalin
fadawa
kenan domin sun sancewa fushin sarki ba karamin ta
shin hankali bane agaresu gaba daya. A na cikin
wannan haline akaga hakimi barzuk ya shigo fadar
cikin farinciki kamar wanda aka yiwa albishir din
mulkin duniya cikin sauri har da hardewa barzuk ya
isa gaban sarki Daksur ya zube kasa ya kwashi
gaisuwa
ya dago kai domin yayiwa sarki baya nin abin farin
cikin da ya sameshi sai sarki yayi farat ya tashi tsaye
kawai sai ya dubi barzuk yace kabiyoni izuwa cikin
dakin gani ina son magana dakai a sirrance. Koda
gama fadin haka sai sarki Daksur yanu fi dakin gani
nanfa Barzuk ya bishi da sauri aka bar fa dawa da
jama'ar gari a zazzaune sun yi tsurutsuru da
idanuwansu suna mamakin abin da ke faruwa. Yayin
da sarki Daksur da Barzuk suka shiga dakin gani sai
sarki ya tsaya a tsaye maimakon ya zauna ya juyo
suka fuskanci juna shida Barzuk yace kazone kayi
mini
aibishir bisa cewa matarka ta haifi "ya" mace koba
hakaba? Cikin muryar rawar murya burzak yace
hakane ya shugabana Daksur yace tokasani kasani
wannan "ya" data haifa ba "yar ka bace "yar" dan
uwanka ce Hukairu amma ita matarka "da" na miji ta
haifa kuma a mace yazo duniya hakika matarka ta yau
dareka kuma karya ta shiryama domin ka jaddada
magana ta yanzu zan nuna maka duk abubuwan da
suka faru azahiri. Kagani da ida nuwanka. Gama fadin
hakan ke da wuya sai sarki yayi nuni da hannunsa
izuwa ga jikin bango take hoton al'amarin suka rinka
gudana tun lokacin da Nuzaira tayiwa 'yar uwarta
Humaira alkawarin cewa lallai awajenta zata haihu
har
lokacin da aka bata jariri yarnan koda ganin wannan
al'amari sai barzuk ya kwarara uban i hu cikin
tsananin bakin ciki jikinsa gaba daya ya kama tsuma
ka wai sai ya zare ta kofi ya juya da nufin yaje ya sare
kan Nuzaira amma sai sarki daksur ya daka masa
tsawa ya tsaya cak ya juya ya durkusa bisa gui
wowinsa a gaban sarki daksur ya mayar ka takofinsa
bisa kubenta ya sunku yar da kansa kasa alokacin da
hawayen ta kaici yake zubo masa yace ya shugabana
yanzu me ya kamata nayi? Sarki dak sur yayi ajiyar
numfa shi sannan yace ya kai Barzuk kayi sani bisa
bin
ciken da nayi idan muka ka bar matarka da wannan
"ya da aka bata wannan fari da annoba da muke fama
dasu a gari zasu kare nan da sati biyu kacal gari zaiyi
lafiya amma inda masifar take shine wannan jaririyar
da matrka ta zo da ita idan har ta girma zama gawur
tacciyar jaruma kuma maya kiya fiye da sarkin
yakinmu sadauki Hauzar bin Mausus duk yakin da
muka taro sai ta sami nasara amma fa duk sanda ta
san sirrin tsafina mun banu mun lalace sai
mulkimmu
ya rushe. Kuma sai talakawanmu sun zama
shugabanninmu sun dauki fansar zaluncin da muka
dade muna yi musu tsawan shekara da shekaru ta
han
ya daya ce ka dai zamubi kada azo da ita fadata kada
abari tayi arba da fuskata kuma kada ka nunawa
matarka bacin ranka koka gaya mata abin da muka
tattauna anan yanzu
A can daji kuwa inda manomi hukairu yayi gidansa
suna wayi garine a cikin farin ciki da bakin ciki dalili
farinkinsu shine na haihuwa da humaira tayi nayaya
tagwaye mata duk da cewa tayi kyautar byar goda ga
rayuwarka nuzaira shi kuwa mummuna mafarkin
wanda himaira tayi a jiya da daddare da safe sa adda
humaira ta farka daga bacci ta fara bawa mijinta
hukairu labarin mafarkinda tayi a jiya al amari daya
matukar dugunzuma humaira duk hankalinsa kenan
dalili kuwa shine a iya saninsa da matarsa humaira
duk abin datayi mafarkinsa saiya tabbata a gaske.
Bawani abu humaira ta ganiba acikin mafarki ba face
saukar wadansu dakaru kamar daga sama wadanda
suka bukawa gidan wuta ya kone kurmus babu abin
da ya tsira. Lokacin da hukairu yaji labarin mafarkin
da humaira tayi sai hankalinsa ya dugunzuma ainun
rasa abin dake masa dadiya shiga tunani mai zurfi
daga can saiya dubi ita humaira yace yake matata
kinsani cewa wajibine a garemu muyi hijra mubar
gabadaya yankin wannan kasa tamu idan har muna
son mu da abin damuka haifa mutsirada rayuwarmu
naji ajikina cewa sarki daksar kasurgumin matsafine
don haka na tabbatar da cewa abinda ya faru tsaka
nimmu da 'yar uwarki nuzaira ya gani kuma ya
nunawa barzuk bisa wannan da lilinne za su turo a
hallakamu lokaci yayi da zan gaya miki wani sirri
wanda bantaba gaya mikiba. Tun muna yara nida dan
uwana barzuk bokan ma haifina wanda muka sami
sirrikan tsafi a wajensa yace mana cewa agaba daya
kasar nan babu wani mahaluki mai karfin sihirinmu
face sarki daksar amma duk 'yar da muka haifa idan
tayi arba da idan sarki daksar to zata samu duk irin
sihirin da sarki daksar yake da shi a cikin kwana uku
harta samu nasarar Hallaka shi ta hau kan kara garsa
face ya kasheta kafin cikar kwana uku shi kansa sarki
daksar ya san da wannan sirri don haka bazai taba
barin abun da muka haifa arayeba dun haka ba zai
barmuba yazama wajibi muyi shirin gaggawa yanzu
muyi hijira mukara gaba. Sa adda hukairu yazo nan
azancensa sai humaira ta ce yanzu ina kake
tsammanin zamu shiga mu buya ba tare da sarki
daksar yaturo an kashemuba Hukairu yace waje daya
ne zamu iya zuwa muyi rayu wa acan kuma mu tsira
daga sharrin sarki daksar da dan uwana Barzuk.
Bawani waje bane face birnin misra inda sarki Raiyan
ke mulki. " Koda jin haka sai idanun Humaira suka
zazzaro tace "ya ya za ayi muje birnin misra kuma
muyi rayu wa alhalin mutanen can sun kasance
musulmai mukuma ma abota tsafine da gunki?
Humaira tace "shin ka manta ne sarki daksur bashi
da wani makiyi wan da yafi sarki Raiyan na birnin
misra? Ai idan sarki raiyan ya fa shinci cewa mu
mutanen birnin kisra ne sai yasa anyi mana kisan
gilla domin ya dauki fansar ran 'yar uwarsa gimbiya
Numaira wacce sarki daksur ya ka she yayin da aka
fafata kazamin yaki da su a shekaru uku baya. "
Hukairu yayi ajiyar numfashi sannan yace "duk nasan
da wannan al'amari amma abinda nake so ki fahimta
shi ne abinda ya koro bera yafada cikin wuta ya fi
wutar zafi. " Koda gama fadin haka sai hukairu ya
mike tsaye yakama hada kayyayyakinsu domin suyi
hijira. Bayan ya gama hada hada komai a waje guda
ya dora a kan rakumansa wasu kuma akan shanunsa
sai yaje tsakiyar filin gidan ya haka rami sai ga shi ya
tuno wata laya. Nan take ya rataya layar a wuyansa,
sannan yakira Humaira ta fito da ga cikin daki goye
da jaririyarta. Ba tare da bata lokaciba suka hau kan
ra kumansu biyu sukayi gaba suna janye dabbobinsu.
Koda hukairu ya juya ya dubi gonarsa da wannan
gida nasa sai idanunsa suka cikoda kwalla saboda
takaicin ya tafiya bAr kasa mai albarkar noma wadda
abu ne mawuyaci ya sake samun irinta.
Bayan kamar sa a hudu da tafiyar hukairu da matarsa
humaira sai ga sarkin yaki haizar bin mausus bisa
doki tare da dakaru dari biyar suna take masa baya
dukkaninsa dauke da muggan makaman yaki tun
daga nesa haizar ya dauko wani gilashi na sihiri
wanda sArki daksur ya bashi ya ce da shi da wannan
gidashi ne kadai zai iya hango gidan hukairu. Haizur
yasa gilashin a kan idanunsa amma bai hango
komaiba dan haka sai suka kara kaimin gudu bisa da
wakansu. Jim kadan da faruwar haka sai suka hango
gidan daga can nesa. Daya daga cikin daka runnasane
ma ya fara hangowa ya nuna masa al'amarin daya
matukar ba shi.mamaki kuma yaba shi tsoro ya fara
tunanin duk yadda a kayi su Hukairu basa gidan kuma
lallai ya tone wannan laya wacce sarki daksur ya
bashi labarin cewa hukairu ya binneta a tsakiyar
gidansa. Tun da ga inda suka hango gidan Haizar
yabada umarnin a fara harba kibiyar wuta izuwa
gidan. Ai kuwa cikin kan kanin lokaci gidan gaba daya
ya kama ya kama da wuta yana ci balbal. Su sarkin
yaki haizar suka karqso gaban gidan aguje bisa
dawakansu suka yiwa gidan kawanya kuma suka dana
kwari bisa baka suna jira suga wani abu mairai yayi
fitar burgu don ceton ransa su harbeshi amma
hargidan yagama konewa kurmus yazama toka ko
kyanwa basu ganiba. A sannanne sarkin yaki haizar
ya sakko daga dokinsa ya duba tsakiyar gidan nan
take kuwa yayi arba da wannan rami wanda hukairu
tone ya cire layarsa ta sihiri. Cikin tsananin ta kaici da
fushi haizar ya kwarara ihu sannan ya dakko
mudubin tsafinsa ya shafeshi sau uku yana mai
karanta wadansu dalasiman tsafi guda uku. Faruwar
hakan keda wuya sai ga fuskar sarki daksur ta
bayyana akan madubin suka dubi juna. Kafin haizar
ya budi baki yace wani abu sai sarki daksur ya tari
numfa shinsa yace "maza ku ruga gaba domin tuni
Hukairu da matarsa sunyi nisa, taza rarku da su ta kai
nisan sa'a hudu. Idan kuka yi sakaci suka shiga yankin
kasar misra shi ke nan baza ku taba riskar suba. Tun
da hukairu na tare da wannan laya baza ku taba ganin
koda sawunsuba amma i dan kayi amfani da wannan
gilashin sihiri da na baka zaka i yaganin sawayensu.
Idan har kana son kariskesu sai kunyi ta fiyar kwana
uku bayada zango babu barci. Idan har kasami
nasarar cika wannan aiki kana dawo wa birnin kisra
zanbaka wazircina kuma zanbaka dukiya ninkin
goman abin da ka mallaka a yanzu. Koda gama
wannan jawabi sai fuskar sarki daksur ta bace bat,
daga cikin madubin sarkin yaki haizar nan take yaji
farin ciki ya lullubeshi dan haka sai yaruga kan
dokinsa yayi tsalle ya haye kan dokin ya zabure shi
cikin matsanancin gudu koda ganin haka sai suma
ragowar dakarun suka sakarwa dawakansu linzami
suka rufa masa baya.
Lokacin da ake wannan mugun artabu
tsakanin Hukairu da Zaihar tuni humaira
ta isa bakin kofar birnin misra amma sai
ta ja linzamin ra kumin ta ta tsaya cak ta
kasa shiga birnin ta juyo cikin ta shin hankali tana
kallon gumurzun da akeyi
tsakanin mijinta da sadauki zaihar.
Lokacin da sadauki zaihar yaga wankin
hula zai kai shi dare sai ya fusata ya fara
amfani da karfin sihiri domin ya hallaka
hukairu amma sai ya ga ashe shima hukairu ba kyalle
bane abangaren tsafi
domin karfi ya zo daya. Haizar yaja da
baya yaduru daga kan dokinsa ya tsaya
cak a waje daya yana tunanin dabarar da
ya kamata yayi. Koda ganin haka sai
shima hukairu ya duro daga kan ra kuminsa ya gyara
tsayuwa yana mai
fuskan tarsa sannan ya kyalkyale da
dariya yanuna haizar da dan ya tsa ya ce
"ya kai wannan tsohon azzalumi ba wan
azzalumai ka sani burin mai gidanka
bazai cikaba a kan iyalina domin sun tsira daga
sharrinkku a yanzu tunda sun haye
iyakar kasarku. Ko a yanzu ka kashe ni
bani da na damar komai. Yayin da haizar
yaji wannan batu sai shima ya kyalkyale
da dariya sannan yace "ai kuwa yanzu
zan kasheka sannan nabi iyalinka har bakin kofar
birnin misra suma na
hallakasu tun dadai sun kasa shiga cikin
birnin sun tsaya suna kallo domin suga
irin mutuwar dazakayi. "
Koda jin wannan batu sai hukairu yajuya
da sauri domin ya dubi bakin kofar birnin misra kafin
ya juyo da kansa tuni Haizar
ya zaro wata wuka siririya mai kaifi da
tsini ya wur gamasa take wukar ta cake
atsakiyar kirjinsa ya dur kushe bisa
guiwowinsa koda humaira ta hango
abinda ya faru da sai ta tsandara uban ihu al'amarin
da ya janyo hankalin masu
gadin kofar birnin misra kenan suka rugo
waje da gudu rike da makaman yaki suda
yawa. Yayin da sarkin yaki ya hango fito
war wadannan mayaka sai ya juyo da
sauri ya ruga izuwa kan dokinsa na sihiri ya zabure
shi da gudu yanufi baya. Ita
kuwa Humaira sai ta diro kasa daga kan
ra kuminta ta falfala da gudun tsiya tana
kuka izuwa inda mijinta yake durkushe.
Koda zuwanta gabansa sai ta tabashi sai
taji ya bingire kasa ko motsi baiyiba alamar cewa
yamutu ba shi da rai nan fa
ta rungume gawarsa tasake fashewa da
matsanancin kuka. Tana cikin wannan
haline dakarun misra suka zo gareta suka
banbareta daga jikin gawar da karfin
tsiya suka tafi da ita izuwa cikin birnin misra tana ta
iface iface da koke koke
tamkar sabuwar mahaukaciya. Wannan
shine abin da ya faru ga Humaira matar
Hukairu bayan srkin yaki ya riskesu ya
kashe hukairu, ita da jaririyar sun tsira
A can birnin kisra kuwa lokacin da hakimi barzuk ya
koma wannan gida nasa inda ya ajiye matarsa
nuzaira
sai ya shaida mata duk wadannan dokoki wadanda
sarki daksur ya shimfida masa a kan jaririyar data
haifa ko da jin wadannan dokoki sai ta cika da
tsananin mamaki ta dubeshi tace to wai shin laifin me
mukayi harda sarki zai kafawa yarmu irin wadannan
dokoki masu tsauri dayawa haka?” Koda jin wannan
tambaya sai barzuk ya tumbune fuska yace ” ni kaina
bansan daliliba amma babu mamaki akwai babbar
hujja data janyo mana hakan saboda haka indai kIna
son mu tsira rayuwarmu da mutuncinmu lallai
kikiyaye wadannan dokoki ” daga wannan rana kowa
nuzaira tacigaba da renon jaririyarta da ranar suna
tazo sai aka radawa jaririya suna yazila tunda nuzaira
ta acikin wannan gida na mijinta acikin birnin kisra
batata bin hanyar gidan sarauta ba bare ma taga
sarki
da idanunta bare kuma jairiyar datake raino. Tafiya
sannu sannu kwana nesa darare na wucewa kwanaki
na shudewa sai aka wayi gari yarinya yazila ta cika
shekara bakwai a duniya nan da yazila tazama
sananniya a birnin kisra saboda kasancewarta tataso
da tsananin kyau dakuma jarumantaka domin tun a
sannan tana iya daga kato komai girmansa ta
rankwalashi da kasa har sai datakai cewa ana shirya
mata gasar kokawa da mazaje majiya karfi tana zama
zakarar gasar daga nan kuma sai lamari nata kara
samun cigaba domin ta fara koyon sarrafa
takofi`mashi`kwarida baka. Duk mutumin daya fara
koya mata amfanida kayan yaki sai yaga tafi kwarewa
acikin kwanaki uku kacal. Tun da yazila ta taso taga
wata farar laya a wuyanta bata son abin da zai rabata
da layarba dare da rana har kwanciyar barci kuwa. A
takaice dai batata cire layarba kuma tana iya tuno
lokacin da mahaifiyarta hakimi barzuk ya samata
layar
sa adda batafi shekara biyarba aduniya. Koda wasa
yazila batata bin hanyar gidan sarki ba kuma kojitayi
sarki zai shigo cikin gari tobazatataba fita daga cikin
gidan domin a rayuwarta babu data tsana tagani ko
taji zancensa face sarki. Abinda batasaniba shine.
Wannan laya da aka rataya mata awuya itace sanadin
dataji batason taga sarki.
Ana nan cikin wannan hali har yazila ta cika shekara
goma sha takwas. Alokacin ne kyawunta yaruda gaba
dayan jama ar birnin kisra ya zaman cewa duk inda
mutun yaje saidai yaji ana labarinta. Afagen jaruman
taka kuwa al amarin maya wuce tunanin mai tunani
domin duk sa adda aka fita yaki da mutanen birnin
misra tana ya musu mummunar barna wata jaruma
guda daya takeci mata tuwo akwarya wadda itace
sarkin yakin mutanen birnin misra a wani lokaci ita
dai larziya taji ana yiwa jarumar kirari da
basadaukiya
dabira babban abin takaita awjen yazila shine
batataba ganin fuskar wannan abokiyar gaba tata ba
domin duk sa adda zata fito yaki tana rufe fuskarta ne
da hular karfe. Akalla yazila da dabira sun fafata
kazamin yaki kamar sau hudu amma duk sa adda
suka
hadu.kare jini biri jini sukeyi. Koda rauni suka yiwa
juna sai kaga raunin yazo adadi daya baya gotawa
sukansu suna matukar mamakin wannan al amari
babu irin kokarin da yazila batayi ba don ganin ta cire
hular karfen datake dabira taga fuskarta amma abu
ya
gagara.
Akwai.wata rana da dabira ta tambayi bokanta wanda
ake kira mushrid bin affan tace dashi yakai abin
dogarona yaza ayina sami nasara akan abokiyar
gabata
absadaukiyar dabira na kai kasa kuma har na cire
hular karfen dake kanta naga fuskarta ?”
Koda jin wannan tambaya sai boka mushrid ya
kyalkyale da dariya sannan yace ” idan har kina son ki
sami wannan nasara sai dai ki cire wannan laya dake
wuyanki kije har cikin fadar sarki daksur ku yi arba da
juna in dai kikayi haka sai kin nasara akan jaruma
yazila har kiyi.mata rauni sama da adadin wanda
zatayi miki. Kuma ki kaita kasa ki cire hular karfen
dake kanta kiga fuskarta amma ki sani cewa ranar da
wannan tashin hankali irin wanda baki tabaga
shigarsab”
Koda jin wannan babu sai jaruma yazila tasa
hannunta
ta kama wannan farar laya dake wuyanta da nufin ta
cireta amma sai ta ji kamar an soka mata allura guda
dubu a sassan jikinta. Ba shiri ta saki layar ta kama
ihu kuma ta fadi kasa

2 / 3