Advertisements
Chapter 23 Reading YAR MAHAUKACIYA Batan Mahaifiya By Sajida BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

YAR MAHAUKACIYA Batan Mahaifiya By Sajida

Author :  Sajida Category :  Complete Novels

Chapter   23 / 26

66K to 69K   out of 77.9K words

yi jigum jigum inda suna waigowa itama Sahla ta suma ( to fa wanzam baka SO à jikinka)


To fans tambayana à nan shin Sahla zata ci gaba da zama à matsayin matar AA ? Haukan hajiya Marhaba ya dace da ita duba da irin abinda ta aikata ? Bawan ALLAH Idriss ya tasa makomar ba masoyiya mahaifiya ta haukace, kanwa ta kauce hanya ? Shin labarin Yar mahaukaciya na kayatar da ku ? Cos ance wai banida masoya 😩😩😩😩😩😩😩😩😩😩😩😩😩😩😩😩😩😩😩😩😩

🇳🇪Belles écrivaines du Niger



*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*



*Na*
*Sajida*






79


*Wayo dadi, daukaka abar gudu abar nema, ni kam na rasa bakin magana sai jazakumlah,*




da gudu ya nufe shi yana jijigashi, inda Yar mahaukaciya ta nufi Sahla saï kuka take dan kuwa ita abi kankani ke rikita mata lisafi, tana kuka ta dago kanta ta kale su zata yi magana kenan sai ga abanta ya shigo da gudu yace " ku kama su mu je asibiti


Mahaifin Idriss wato Ilyas ya dago da kansa ya ce" baza'a kaita asibiti ba, sannan ba zan bisu asibiti à yanzu ba, kawai zan rufeta à daki ne naje wajen tawa mahaifiyar,


Elhaj Muhammad ya zuba masa ido ya SO ya takura sa sai dai yayi wani tunanin kawai ya kamawa Mubasshir suka dauki Idriss suka shiga motar da shi,

Elhaj Muhammad ya kali Mubasshir ya ce" kaje ka dauko matar ka domin kaine muharaminta


Mubasshir ya dago Idannuwansa cike da hawaye ya ce" ka yafe min aba, na saki Sahla saki daya


Elhaj Muhammad ya zaro ido ya ce" why Mubasshir zaka yanke danyan hukunci haka saki cikin fushi ?


Mubasshir ya kawar da kansa ya ce" banyi saki cikin fushi ba, na gama nazarina kafin Nayi sakin nan domin da à lokacin da nake walafawa Sahla soyayata gareta ta canza tunani Bata bani yaourt din nan ba da lale lale bazan saketa ba, aman à cikin zuciyar Sahla kiyayata tafi soyayata yawa dan haka ka yafe min,


Elhaj Muhammad ya rasa ma mai zai ce masa kawai sai ya kada kai ya koma dakin inda ya tarda Elhaj Inyass ya fitar da du abinda ya san zata iya raunata kanta ya rufeta à dakin sai falasa irin aika aikar da tayi take tana busasa dariya,
Elhaj Muhammad yayi gagawar kawar da kansa dan kuwa sai yaji ba dadi,

Su hajiya Rafi'at da hajiya hafsat suka kama suka dauko Sahla wace kitsonta na atch sai yawo yake tsananin tsayinsa a kanta,

Suna sakata irin motar nan ce jeka da iyalinka, lxus suma suka shiga Mubasshir ya tayar ya kama hanyar asibitin idriss

Suna zuwa da gudu aka karbesu BQ tare da tambayoyin abinda ya faru ba suka dukufa domin ceto ransu,


Zaune suke Yar mahaukaciya ta dora kanta saman cinyar auntynta tana ta sauke ajiyar zuciya, itama Rafi'at din du tayi wani iri da ita sai tunani take na rayuwa,

Hajiya hafsat ta kasa zama sai kai kawo take tana dan leka hanyar dakin da aka shiga da su, kuma sai ta kali AA da yayi wani irin ja na Wahala, kansa à kasa yana kalon yatsun kafarsa,

Elhaj Muhammad ya zuba mata ido yana kalonta, wani irin tausayinta da kaunarta suka kara darsun masa à zuciyarsa, ya kuma kali y'arsa dake konce q cinyar Rafi'at, ya juya ga Mubasshir dake kalon kasa, ya girgiza kai à hankali ya Mike ya kamo hannun hajiya hafsat, har yanzu abin nan bai barta ba na idan hankalinta ya tashi ta kasa zama, yayi murmushi ya jawota jikinsa ya Bata kyakyawar runguma, hakan ya saba yi mata idan har yana son ta shiga cikin nutsuwarta, hakan kuwa aka yi sai ta dora kanta à kirjinsa tana sauke ajiyar zuciya, tana karawa,

Ta kusan minti biyu à haka ta tuna su Mubasshir fa na wajen da sauri ta kufce daga rikon da yayi mata tana kara jan zumbulelen hijabinta tana kokarin rufe fuskarta,

Mubasshir ya kawar da kansa yana girmama soyayar sirikansa


Docter Halima ce ta fito ta nufo su

da sauri suka Mike har suna hada baki wajen tambayar ya jikin su,
Mubasshir ya kali Yar mahaukaciya da ta ce" ya jikinsa ? Gabansa ya fadi, Muryar docter ta dawo da su inda ta ce" alhamdulilah jikinsu da sauki cikin ikon ALLAH,

An daidaita lunfashinsu, shi an saka masa ruwa aman munyi masa alurar baci wace tana iya daukan awa uku zuwa Hudu yana baci dan ya samu hutu, sai ita an dora hannun, aman tana bukatar kulawa KO ku dauki nurses masu kula da wannan harkar KO ku dauko Wanda zata tsaya tsayin daka dan lafiyarta ta samu cikin sauki da yardar ALLAH


Mubasshir ya ce" docter muna iya shiga mu ganshi KO ?


docter ta ce" eh sosai ma, kuna iya zama ma ai docter ne, ba wata damuwa,

Elhaj Muhammad ya girgiza kai Jin bai damu da rashin Lafiyar sahlan ba, ya ce" docter Ina bukatar à daukarwa kanwar Idriss nurses uku da mai kula da tsaftarta, da mai kula da abincinta, da mai kula da addininta à kan lokaci, du wata kulawa Ina son à Bata kafin ta dan warware

Docter ta ce" Elhaj akoy tsada fa

Elhaj Muhammad ya kaleta ya ce" ba wannan ba, aikinsu shine biyan bukatarmu


Mubasshir suka yi gaba su hudun suka nufi dakin Yar mahaukaciya kafin ya gama ya tarda su,

suna shiga suka tarar yana konce hanunsa jone da karin ruwa, yana baci aman da ka kale shi sai ka ga ya fada,

hajiya hafsat ta nufi gadon Sahla tayi mata ada'ar samun sauki,

Elhaj Muhammad suka shigo da nurse aka ja gadon Sahla dan à canza mata daki domin jinyar namiji da mace bazai yiwu à daki daya ba


Elhaj Muhammad ya kare yi masa kalo ya ce" da ace inada wata y'ar da na Isa da ita da na aurawa Idriss bisa sharadin idan ta Bata masa ban yafe mata ba

hajiya hafsat itama ta zura masa idon ta ce" ya ALLAH yanda ka yaye mana damuwarmu bisa Imani da muka yi da kai ka yayewa wannan Bawa naka cikin ruwan sanyi sannan ka bashi ikon cinye jarabawar

gaba daya suka amsa da amin, Mubasshir dai na kalonsa kuma sai ya saci kalon Yar mahaukaciya da ta zuba masa idon itama ba tare da wani tunani ba sai tsantsar tausayawa gare shi balatana idan ta tuna Tata rayuwar da ta shude ba'a dade ba


Elhaj Muhammad suka yiwa su hajiya Rafi'at da Mubasshir da Yar mahaukaciya Salama suka nufi gidan su Idriss dan su tarda hajiya Fadimatu dake wajen hajiya hawau suna ta jajantawa da kuma murnar dawowar tunanin Elhaj ilyassssss


bayan tafiyarsu Mubasshir sai ya daina kalon Idriss din gaba daya sai ya dawo da tunaninsa wajen islam da tayi zuru ita da aunty Rafi'at suna ta kalon lumfashin Idriss, wani haushi da mugun kishi ya rufe shi, à ransa ya ce, Tunda ta zura masa ido Bata dauke ba, mai hakan ke nufi ? Tana tsoron ta kawar da kanta ne wani abin ya sami masoyinta ( toh fa eh din Inji ni )

Gani yayi bazai iya jure wannan abin ba, ya Mike yana dan sosa keya ya ce" auntyn mu plz mana bara mu samo muku dan abin matsa baki kafin ya farka


hajiya Rafi'at ta kale shi ta ce" haba freind (domin shekarunsu daya abinka da yan gayu shima idan yana bukatar wata alfarmar ce yake kiranta da aunty) ya zaku barni à nan ni kadai kuma ? Idan ya farka fa ya Zanyi da shi ?


Mubasshir ya ce " ai ba zamu jima ba

hajiya Rafi'at ta ce " toh ka je kai kadai mana


Mubasshir ya zaro ido ya ce" Ina bazai yiwu ba fa hajiya kinga tafiyar mu dan Ina dan yi miki Yar murya aa bye,
Ya ja hannun Yar mahaukaciya wace tayi murmushi diramar auntynta da mijinta na birgeta matuka


Bayan fitar su aikin nata da ta saba ta ci gaba wato kalon sa, Kiran salar da aka yi ne ya saka ta Mike ta cire hijabinta dan taga yana baci kuma zata shiga bayi, ta ajiye à saman kujerar da ta tashi ta nufi bayin

alwallah ta dauro ta fito, tana fitowa ya mayar da Idannuwansa ya rufe ta dauki hijabinta ta dora saman Riga da siket dinta ta jawo dardumar da docter ta Miko ta kabarta sallar la'asar,

Bayan ta gama sallah tayi ta adu'o'inta da ta saba sannan ta daga hannunta sama cikin bayananiyar murya ta fara yiwa ALLAH kirari da shi da fiyayen halinta, ta nemawa iyayenta gafara da Wa'inda suka rigaye mu gidan gaskiya, ta kara nemawa y'ar uwarta kariyar ubangiji da ahalinta baki daya, ta roki gamawa da duniya Lafiya, sannan ta gangaro kan Idriss ta ce" Ya ALLAH alhamdulilah, Allah mun gode maka da wannan rana ALLAH muna rokon ka ka sanya ta zamto alhairi à gare mu, ya ALLAH ga bawon ka nan, kafi kowa sanin dalilinka na ciro kamili daga tsatson Wanda ba kamili ba, ya ALLAH kafi kowa sanin abinda ya dace da wannan Bawa naka domin kai kadai ka san gaibu, ya ALLAH ka sanyaya masa damuwarsa, ka yaye masa kuncin sa, ka bashi ikon kula da mahaifiyarsa da kuma kanwarsa, ka bashi juriyar cinye wannan jarabawar, ka shiryar da kanwarsa, ka baiwa mahaifiyarsa Lafiya, kai kayi komai kai kake da komai ya ALLAH,

*sai da ta gama yiwa kowa adu'a sannan ta fashe da kuka mai tsanani, ta kara daga hannunta sama ta ce" ya ALLAH ka kawo min abokin rayuwana koda da an daura min aure zan koma gareka, ya ALLAH idan wani abin na aikata KO nake aikatawa ka nusar da ni ka yafe min ka bani miji na gari komai talaucinsa, ya ALLAH idan kuwa lokacin Nayi auren ne baiyi ba ALLAH ka kara min hakurin jiran lokacin domin na san da mutuwa da arziki da Aure lokaci ne, ya ALLAH idan..... Ta kuma fashewa da wani kukan ta ci gaba idan kuwa banida raban yin auren ne har na koma gareka ka saka min dangana ka kuma kare ni da sharin Zina ka kara nutsa ni à kogin tsoronka ya ALLAH ka cika min burina amin*


bayan ta gama adu'ar ma sai da ta ci kukanta sannan ta Mike a nutse ta nade salayar ta juyo dan ta ajiyeta

Gabanta ne yayi mumunar faduwa sanadiyar ido Hudu da suka yi , wato Tunda ta fashe da kuka ya zabura ya zauna yana kalon ta kuma yana sauraronta,

wayancewa tayi tana dan murza ido kamar wani abin ya fada mata à ciki ta nufi dan kusa da gadon tana dan inda inda ta ce" """""""""""""






garigajin ganin ji ganjin kara Kaka kara 🙄🙄🙄🙄🙄🙄

🇳🇪Belles écrivaines du Niger

*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*

*Na*
*Sajida*

80

Tana murza ido ta ce" au ka farka ? Yaushe ka farka ? Ya jikin ?

Shiru Taji yayi bai ce komai ba hakan yasa ta dago da kanta suka yi ido Hudu, gabanta ne taji ya yanke ya fadi ta shiga kikifta ido

Idriss dake kalonta yana kokontan anya kuwa shekarun da aka ce ta kai kuwa ? Kamar wata Yar budurwa mai shekara 25 haka, ya lumshe Idannuwansa ya ce" shekarunki nawa ?

Hajiya Rafi'at ta dago kanta ta zuba masa ido tana mamakin tambayar sa, yaro karami da shi yana tambayar shekarunta ita tayi imanin ta bashi wata shekara biyu KO uku, ta kawar da kanta ta ce" ban gane shekaruna ba ?

Zaiyi magana kenan Mubasshir ya turo kofar ya shigo da ledodi manya bakake à hannunsa, Yar mahaukaciya na rike da wayoyinsa,

Suna shigowa ya saki murmushi Ya ce" marar lafiyana ya farka ?

Idriss yayi murmushin shima ya ce" ALLAH ya tashe ni broth

Mubasshir ya Mika masa hanu suka gaisa ya zauna yana kokarin bude dan abin motsa bakin,

Idriss kuwa banda kalon hajiya Rafi'at ba abinda yake, gaba daya ta tsargu, tana tsoron karfa aje yaron nan ya saurari adu'arta, ta girgiza kai à ranta ta ce " da kuWa ya cuce ni sosai,
Muryarsa ta katse mata tunani inda ya ce" tashi ki dauko min kofi na sha magani

À tare suka dago, Yar mahaukaciya ta Mike domin dai ta san bazai aiki auntynta ba duda bashi da Lafiya, ga mamakinsu sai ji suka yi ya ce " No ba ke ba, da *Yarinyar* nan nake

À tare suka zaro ido harda Mubasshir, Hajiya Rafi'at ta waiga ta kali Mubasshir ta ce" Freind KO kwakwaluwar yaron nan ta tabu ne ? Cos yana Farkawa ya shiga tambayana shekaruna, ni kuwa anya ba za'a Kira docter ta duba lafiyarsa ba ?

Mubasshir ya ajiye abarbar da ya wanke ya matsa kusan gadon ya ce" broth are u OK ???????

Idriss yayi murmushi ya ce" tabass lafiyana lau broth, i'm Idriss Ilyass, i'm 31 old, ni Docter ne, sannan à wannan lokacin Ina cikin tashin hankalin mamana mai suna Hajiya Marhaba da ta samu tabin hankali da kuma sisterna mai suna Sahla da ta karye sannadiyar son zuciya da kuma son abin duniya, kuma alhamdulilah na yarda da kadara

Mubasshir ya ce " hajiya Rafi'at ce fa kake Kira da yarinya, to mai zaka yi da shekarunta ? Mai ke damunka ?

Idriss ya lumshe Idannuwansa ya bude ya leko fuskar Rafi'at dake kalonsa tana jiran Jin amsar bakinsa, ya dawo da Idannuwansa wajen Mubasshir ya ce" nima Ina son sanin abinda yake damuna broth, Ina son sanin rigimar dake kokarin dosoni à wannan lokacin, ina rokon ALLAH ya kama mini domin wannan tashin hankalin zai fi rikitani, zai kara kawar min da nutsuwata

daidai wannan lokacin gaba dayansu sun sare du sun kara matsowa kusan sa, harda islam sun zuba masa ido, Mubasshir ya riko hannunsa ya ce" what happen, mai ke damunka broth ka fada min da yardar ALLAH zamu samo mafita

Idriss ya tsare shi da ido ya ce" kayi min alkawarin zaka samo min mafita ?

Mubasshir ya ce " bi'izinillah Zanyi iya yina idan har hakan bai kaucewa hanya ba,

Idriss ya sauke ajiyar zuciya ya zuyo ya kali Rafi'at da tayi tsuru tana kalon sa, ba zato ba tsamani ta ji ya ce" Ina son auren Rafi'at, Ina son Rafi'at, Rafi'at tayi min ita nake son rayuwar Aure da ita, sai dai Ina fargabar KO zata ki *Dan Mahaukaciya ?*

Yar mahaukaciya ta zaro ido ta rike baki, Mubasshir ya saki murmushi ya juyo yana kalon Rafi'at da ta zama tamkar mutun mutuni tana kalon sa, Mubasshir ya ce " shikenan sai ayi tuwona maina

Hajiya Rafi'at ta kuma zaro ido ta ce " Da Wa za'ayi tuwanka manka ? Au KO kunya baka ji ka kali idona ka ce Ni Rafi'at kake SO ? Ni KO auren ne ai sai Wanda ya girme ni nesa ba kusa ba, idan kaji adu'ana ne ka tausaya min to ka tayani da ada'ar ALLAH ya bani Daidai ni ba wai yaro karami ba, ka shiga Ina da ni ka fada min mai ? Ai Nafi karfin Auren kanina

Idriss ya rintse Idannuwansa ya ce " stop, ya Isa haka, Ki dena kalon tsabar idona kina fada min zancen nan, Ki Sani *Namiji baya kadan* kuma da kike maganar wai kin girme ni fada min shekarar biyu da kika bani ne zaki fadi haka ? To ya kike kalon tarihin auren fiyayan halita Wanda akayi duniyar dominsa ? Aure suna ne, ba tausayinki da naji kawai sonki nake, sai dai idan kalmar nan daya zata hannaki aurena wato *Dan Mahaukaciya*

hajiya Rafi'at jikinta yayi sanyi tsoronsa ya darsun mata à zuciyarta ta zuba masa ido tana sauraron duk wata kalma tasa, wai shekara biyu ta bashi, no shekara uku ne, to aman taya zata yarda da wannan abin kunyar ai har Sahla ta goranta mata, itafa har yanzu gani take Idriss baya cikin nutsuwarsa, domin wannan abin da ya dage yana fadi, ta juya ta kali Mubasshir ta ce" ka saka à caje kwakwaluwar kanina kuma abokinka, idan kuwa à cikin hankalinsa yake ka fada masa lale ya cika dan dirama, aman Ina rokonsa ya tsayar da diramarsa haka domin ni kam na cika rauni, tana gama fadar hakan ta juya zata bar dakin da gudu sai ga kofar ta bude an shigo *Elhaj ilyass ne da Elhaj Muhammad* suka dawo da kwondon abinci, gaba daya abinda suka fada à kunayensu,

hajiya Rafi'at tayi saurin sada kanta kasa dan kar su gane hawayenta

Elhaj Muhammad ya ce" where are u going ?

Rafi'at ta ce" zan Kira docter ne ya ya farka

Elhaj Muhammad ya gyada kansa ta juya tana tuna fita ta tari Adaidaita tayi gidan su Mubasshir,

bayan yan gaishe gaishe da karin jawabi kan Idriss yayi hakuri da kadararsa ya ce " ba komai ALLAH ya bani ikon cinyewa
suka amsa da amin, shiru ya biyo baya na dan dakiku

A
Elhaj ilyass ya dago kansa ya ce" son abinda na saurara à kofa kana fada da gaske kake KO kuwa maganar ta Rafi'at ce baka cikin nutsuwarka ?

Idriss ya sada kansa ya ce" dad, Ina cikin nutsuwata, tun ranar da na je gidan su Mubasshir ta bude min kofa na tsinci kaina à wannan yanayin, Rafi'at ita ake Kira da matar rufin asiri domin du irin abinda ya faru tana yi min adu'a da kuma iyayena, nan ya kwashe adu'ar da ya saurara daga bakinta, ya ci gaba" idan har zata juri zama da ni à halin da na tsinci kaina à ciki à yanzu tabas da sai Nafi kowa

23 / 26