Author : 𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 Category : Complete Novels
sannan ta juya ta fice idonta na cika da hawaye a karo na biyu. A jiya ta kwadaita ma Momy cewar gurinta aka zo, saboda zatonta ne, yanzu kuma Momy ta sake zaton hakan a karon kanta. Har ta fito falon rike da wayarta a hannu bata daina fadawa kanta ajinta ya wuce ta tsaya irin wannan tunanin da damuwar akan namijin da ba shi ne autan maza ba, kuma ba ita ce a gabansa ba. A kokarinsa na karramata ya fito daga motarsa ya zagaya ya bude mata front seat, tana kusantar gurin da motar take buri na kusantota. Bude mata motar kawai da yayi kamin ta karaso wani abu ne da ba a taba yi mata ba, and to her wani abu ne dake bayyana halinsa na kula da mace yadda ya kamata.
“Barka da dare”
Kamar wanda ta fado daga wata duniyar haka ta farko daga duniyar tunaninta ta dan kalleshi and a lokacin ne ta fahimci ta karaso kusa da shi.
“Barka dai”
Ta amsa a takaice fuska ba yabo ba fallasa sannan ta shiga motar ta zauna, shi kuma ya rufe murfin motar gently, sannan ya zagaya ga shiga bangarensa, ya kalleta bayan ya rufe bangarensa yana tunanin ko zata masa wani karin bayani ko shawar before su tafi.
“Za mu oya tafiya?”
‘Da gaske umarni na yake jira? Wai duk wannan na miye ne? Meye haka? Why why?’
Ta tambayi kanta, a zahiri kuma sai ta amsa masa ba tare da ta yarda ta kalleshi ba.
“Yea...”
Yayi baya da motar tare da juya kanta sannan suka fice daga gidan.
HURRIYA POV.
Hurriya na kwance jikin Hajiya Binta tana game da keypad dinta, Hajiya ta ce.
“Wato da wani gurin kika fada shi ke nan babu wanda zai biyo bayanki ya binciki lafiyarki, shi sun rufe masa ido su kuma babu wanda Allah yake ranta kowace daga ita sai Yayanta take hange”
“Haka kwanan baya suka laka min sata, Momy ta ce na sace mata sarka da kudi, kuma ban dauka ba, amman Hajiya ma cewa ta yi wai zan iya yi saboda na canja hali, Appa ne kawai ya wanke ni, da Allah kadai ya san dukan da zan sha a gurin Yayana tun da shi ne mai hukunta mutane, kuma da kowa sai ya rika kallo a matsayin barauniya”
Hajiya Binta ta daki kirjinta.
“Sata Hurriya? Sata dai sata? Ke Nafisa ta zarga da sata?”
Hurriya ta tashi zaune tare da amsa mata da kai.
“Har da cewa ta yi ba zata bari da Allah ba, amman ni dai har yanzu ban ji ance an gane barawo ba”
“lallai rashin uwa a gida kukumi ne, saboda suna ganin baki da kowa shi ne suke kwaso sharar sai ya sauke kanki, ai baki gadi sata ba Hurriya uwa da uba, yanzu da uwarki bata da rai haka mutanen nan zasu rika ki? Ke ta ce kin satar mata?”
“Sakar zinari da kudi mai yawa, har da sarkar Yaya Namra kuma ban shiga dakin kowa ba... ”
Ta fadawa Hajiya yadda komai ya faru, idon Hajiya Binta ya cika da kwalla.
“Ashe haka kike ta rayuwa cikin matsuwa a gidan nan? Duk fadin gidan nan da ma'aikatan cikinsa a rasa waye za a zarga sai ke?”
“Ai Appa ya wanke ni yace ni ba barauniya ba ce”
“Me yasa baki fada min ba? Amman ko yanzu bata bace ba”
Hurriya ta kalleta da sauri.
“Hajiya ai ya wuce”
“Be wuce ba, uwarki bata min komai ba sai alheri, Allah ya mata albarka ya bata lafiya, ta kula da ni kamar ni na haifeta, ba zan taba bari yayanta su wulakanta ba, ba zancen sata kadai ba ko wannan korar da aka yi miki ba zan kyale ba, domin idan aka kyalesu nan gaba za su aikata wanda ya fi wannan ma, gobe zan yafa mayafina na tafi duk sai na ci musu mutunci”
Hurriya ta fasa kuka da yafi kama da shagwaba.
“Hajiya Wallahi zaki ja min ne kawai ace na zo na yi minahicci”
“Uwarki bata min komai ba sai alheri, matukar ina raye ita ko yayanta ba za su wulakanta ba”
“Aa Hajiya ni dai dan Allah kar ki yi”
“Ba gidan zaki koma ba balle su ganki su wulakantaki, nan zaki zauna kuma yadda wannan abun ya tsaya min a rai idan ba amayar da shi ba ba ni da kwanciyar hankali”
Duk yadda Hurriya ta so lallaba Hajiya Binta ta hakura da maganar, bata saureta ba.
“Ni da na sani ba zan fada miki ba Hajiya”
“Ai shi yake cutarki, ta nan kika sha banban da dan'uwanki, Hamad komai aka yi masa sai ya rama kuma sai ya fada min, bawan Allah Allah ya masa rahma”
“Ameen”
Hurriya ta amsa cikin rashin ji dadi tare da daga kai ta kalli kofar falon da Namra ta turo ta shigo da Sallama.
Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.
Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... 💃🏻
𝐊𝐇𝐀𝐃𝐄𝐄𝐉𝐀 𝐂𝐀𝐍𝐃𝐘
Littafin nan na kudi ne, ba free ba, idan kika karanta ba tare da biya ba kin daukarwa kanki nauyi domin hakkina ne kika rataya a wuyanki. Biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence of payment to 08036126660
𝐀𝐫𝐞𝐰𝐚𝐛𝐨𝐨𝐤𝐬 @𝐤𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚𝐜𝐚𝐧𝐝𝐲
𝐏𝐚𝐠𝐞 1️⃣9⃣
“Yau Namra ce a gidan na mu”
Hajiya ta fada tana kallonta, cikin karfin hali Namra ta yi murmushi ta nemi guri ta zauna. This is the first time da ta ji bata sha'awar hada ido da Hurriya.
“Hajiya barka da dare”
“Barka, yau na ci arzikin Hurriya kin zo gidan nan kenan”
“Haba Hajiya daman can na kan zo na duba ki fa, karki ce saboda Hurriya na zo”
“To ssboda wa kika zo tsakaninki da Allah?”
“Sabosa Hurriya”
Cewar Namra tana dariya, Hurriya kuma dadi ya cika ranta jin cewar yar'uwarta ta biyo sawunta, sai dai abun da bata sani ba shi ne ba tafiyace ta zuwa gurinta kai tsaye ba tafiya ce ta Salim ba dan ita ba.
“Yaya Namra ina wuni”
“Lafiya Kalau Hurriya”
Ta amsa tana murmushin da ya fi kama da an mata dole.
“Ato ke dai kin kyauta da kika biyo sawu, daman ke kin fita dabam ba da yan'uwanki, amman Nafisa kam da Kaltume rayuwarsu tana ba ni mamaki, yanzu Hurriya ta gama karanta min abun da ya faru, ashe abun har ya kai a laka mata sata Namra?”
Namra ta kalli Hurriya ba tare da tace komai ba ta dauke ido.
“Ban yi zaton zamu yi ma yarinyar nan haka ba, saboda kawai bata da uwa cikin gida sai ta zama abar wulakantawa, ban jidadi ba, yanzu ko korar nan da aka yi mata da ke ce ko Khairy ai babu wanda uwarta zata yarda ta bar gidan, da bata da ni ya rayuwa zata zame mata? Ke kuma ya kamata ace kuna nunawa iyayenku wasu abubuwa be kamata su yi ba, wani abun ba za su lura ba sai an lurar da su”
Hurriya dai kanta na kasa tana jin kamar ta rufe bakin Hajiya Binta. A kokarin Namra na kawar da maganar ta kalli Hurriya tana jin wani abu a zuciyarta game da Hurriya ta ce.
“Da bako nake fa, kuma ke yake jira magana ya zo yi da ke?”
Hurriya ta dago ta kalleta. Hajiya kuma ta tambaya.
“Wane bako kuma?”
“Ita tasan wa nake nufi, ya zo ne yayi magana da ita sai mu tafi”
“Waye ne ban san waye ba?”
“Salim Sarauta... Yana waje”
Namra ta amsawa Hurriya kai tsaye kamar yadda ta bukata. Hajiya Binta kuma ta kalli Hurriya ta ce.
“Saurayinki ne?”
“Aa Saurayin Yaya Namra ne, yana yawan tambaya ne, maybe ko yana son mu gaisa ne”
“To tashi ki tafi, idan kun gaisa sai ki dawo”
“Toh”
Ta amsa umarni, Hajiya ta tashi ta shiga dakin ta dauko hijabinta ta saka sannan ta fito ta fice daga falon. Tana fita Hajiya Binta ta fara karantawa Namra sakon da zata bawa Momy da Hajiya Kaltume. Cikin natsuwa Hurriya ta fita harabar gidan, sai da ta gama kallon ko'ina sannan ta nufo gate domin bata ga bakuwar mota a gidan ba bayan motocin da Appa ya ajewa Hajiyarsa guda biyu. Sai da ta fita gate din gaba daya sannan ta yi arba da motar dake fake gefen gate din gidan, tun kamin ta fito zuciyarta ta raya mata a waje ya aje motar ganin babu bakuwar mota a harabar gidan Hajiya Binta. Kamin ta karaso ya bude motar ya fito yana taba wayar hannunsa, da alama wani abun yake typing amman idonsa yana kanta har ta iso, cikin far'a da sakin fuska ta yi masa sallama da muryarsa mai dadin sauraro.
“Wa'alaikissalam Young Lady”
“Sannu da zuwa barka da dare”
“Barka dai, fatar na same ki lafiya”
“Lafiya Kalau”
“Maa Shaa Allah”
Ya fada yana raba ido, ko za su samu gurin da za su zauna.
“Ko zamu iya rabawa daga can kar na aje ki yi ta tsayuwa, saboda ina da tarin maganganu buhu buhu”
“Allah yasa ba laifi na yi ba, Yaya Namra tace min zamu gaisa ne”
“Laifi kika babba kuwa, kusa kisan kai ma”
Ta zaro ido hankalinta ya fara tashi.
“Ni...”
“Ke fa, amman yanzu mu fara zama tukuna”
“Nan ma ya isa ka fada min laifina ni hankalina har ya tashi”
Yadda take da kin sakin jiki zuciyarsa ta raya masa idan ya bukaci su shiga motar su zauna ba zata yarda ba, ba kuma zai iya forcing dinta suje cikin gidan su zauna ba. Dan haka ya bude mata mota ta gefen da yake ya matsa baya.
“Zauna nan, ni sai na tsaya zan yi magana da ke ne”
Bata son ta musa masa a karo na uku, haka kuma sanin cewar shi din masoyin Namra ne yasa bata son ta aikata abun da zai fusata yar'uwarta. Juyawa ta yi ta kalli gate din gidan. Kamar ya san abun da take sakawa a ranta kamin ta juyo ta tsinkaye shi yana fadar.
“Karki damu, babu wanda zai fito har sai mun gama maganar da zamu yi”
“Ni fa zan iya tsayuwa ko na awa nawa ne”
“Shiyasa Namra ta kasa shawo min kanki, da alama dai kina da kafiya Hurriya kamar zan sha wahala, please ki zauna zaki fi fahimtar magana ta idan kina zauna”
Ta taka ta zauna cikin motar kafafuwanta da fuskarta duka suna waje suna fuskar gurin da Salim yake tsaye. Wayar dake hannunsa ya duba sai ya amsa kira da sauri.
“Ka iso?”
Ya juya bayansa.
“Oh na ganka”
Ya fada tana daga hannu ya tare fuskarsa daga haske motar dake haske fuskarsa. Sauke wayar yayi ya saka aljihunsa.
“Ina zuwa Young Lady bari na mikawa wani, sako”
Ya zagaya da sauri dayan side din, hakan ya bawa motar mai tsananin haske haske fuskar Hurriya har sai da ta saka hannu ta tare idonta da ba lafiyayyen ba. Gammm ta ji an rufe mota sai dai ba zata iya fadar motar da aka rufe ba, ta Salim ce dake neman sako kamar yadda ya fada mata ko kuma ta wanda za a bawa sakon ne? Ganin Hasken dake hasketa ya dauke yasa ta janye hannunta daga idonta sai ta yi arba da mutum tsaye a gabanta nesa kadan da gurin da Salim ya tsaya a dazun, kasansa ta fara kallo har ta daga kanta sama ta kalli fuskarsa, akwai hasken wutar gidan dake haska ko'ina ta bawa kowa damar ganin abun da yake wakana a harabar, sai dai hasken be kai ya tantance mata fuskar waye tsaye a gabanta ba, saboda lafiyar idonta, sai dai tabbas zata iya shaidar wani abu da ba zata kira da shi tsoro ba, kuma ba fargaba ba ce, wani abu ne da ya cika idonta ya aikawa zuciyarta da sako ta fara bugawa da karfi, a rashin zato da tsammani ta samu kanta a tsaye gabansa numfashinta na kokarin sarkewa.
“Me kike yi a nan?”
Muryarta ta daki dodon kunnensa, a nan ta gane duk wani abu da ta ji gabanin fitar sautin muryarsa shimfida ce.
“Ka santa ne?”
Salim ya tambaya yana rufe motar ta dayan bagaren sannan ya zagoyo.
“Ba nan ne gidansu ba, me take yi a nan?”
Ta daga kai da zimmar tantance waye tsaye a gabanta jin furta cewar ba nan ne gidansu ba, wannan abun dai irin na dazun ya sake tare idonta daga kallon fuskarsa idanuwanta suka shammaceta ta sauke su a fadaddan kirjinsa mai matukar fadi da yalwatacce damtse, cikin wani yanayi da yafi kama da sihiri jikinta ya fara kyarma kadan ta kasa tsayar da idanuwanta guri daya.
“Ba magana nake miki ba?”
Muryarsa bata yi kama da muryar da ta taba ji ba, idan ma ta taba to ta manta, balle kuma fuskarsa da kwarjinsa be bari ta kalleta da kyau ba balle ta tantance waye shi.
“Ni na sallamota magana zan yi da ita”
Salim ya fada yana kallon Saurayin dake gabansa da ba zai wuce sa'ansa ba.
“I said ba nan ne gidansu ba”
“Eh amman ta dawo nan a yadda na ji Namra ta fada?”
Mutumen ya kalleshi da kamar mamaki.
“Namra?”
“Ita ma ka santa kenan?”
“Cousin dita ce”
“Wow baka taba fada min ba”
“Dole ne sai na fada maka alakata da kowa? Ina tarkadun?”
“Shikenan kuma ka dawo ba zama lafiya, sai bakar magana kamar dan kishiya, ga su”
Ya mika masa takardun dake hannunsa.
“Tun da ka dawo ba mu samu zama ba, gashi ni kuma an min transfer”
Be ce da shi komai ba har ya gama duba takardun sannan ya juya. Salim ya bishi da kallo yana fadin.
“Ajiyarka ta nan Captain, he's living healthy amman...”
Ya juyo da karfi ya kalleshi fuska babu annuri.
“Ban tambaye ka wani abu game da haka ba, idan ina bukatar sani wani abu game da haka ni zan tuntuba watch your mouth Ethiopian...”
“Akwai maganar da nake son mu yi ne, akwai abun da ya kamata ka sani”
“Ba a nan ba”
Ya nuna gurin da ya tsansa, sai da ya kalli Hurriya sannan ya dauke idonsa ya juya ya cigaba da tafiyarsa. Hurriya ta daga hannunta da sauri saboda haske motar da ya dawo yana haska idonta, sai da ya ja motarsa ya bar gurin sannan Hurriya ta sauke hannunta.
“Sorry na bata miki lokaci, wasu takardun ne na bashi na aikin mu”
Ita dai bata ce uffan ba sai mamakin inda ya santa take.
“Ashe ya sanki, he's very good friend of mine, yana da kirki sosai sai dai akwai zuciya abu kadan ya bata masa rai, yana gaba da ni a aiki amman dai abokina ne sosai”
Ta dauke idonta daga dayan gefen ta kalli kasa.
“Zauna please”
Ta girgiza masa kai alamar ba zata zauna ba, ga bakin nata yayi gum kamar an daure mata shi. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali sannan ya ce.
“Okay, back to our business, Hurriya ina son ki saurare ni da kyau ne, na zo nan ne saboda ina son mu fahimci juna da ke”
Ta kalleshi kai tsaye jin kamar yana kokarin kauce hanya.
“Fahimtar da nake nufi shi ne, ki fahimce manufata da abun da yake tafe da ni, na san Namra ta yi magana da ke jiya, and ta fada min cewar baki karbi sakon da na aiko miki ba, sai dai ban dauke shi a komai ba, maybe saboda baki gama sanina ba ne ko kuma saboda ba wasu dokokin gidanku ne”
Ya gyara tsayuwarsa yana aika mata da kalamai cikin natsuwa.
“Hurriya ba na zo nan ne saboda na bata miki lokaci ko tarbiya ba, Allah ya san abun da yake zuciyata son gaskiya nake miki babu wasa a ciki... ”
“So kuma...”
Ta amsa da karfi with confused.
“Eh na fara sonki ne tun a ranar da na fara ganinki, a Sarauta Mall, shiyasa na biyo motar yayarki, kuma na gwada wasa da ku and...”
Ta daga masa hannu tana jin kamar kalaman sun mata girma.
“Wait... Yaya Namra fa?”
“Ban gane ba?”
A cikin rashin fahimta yayi tambayar ba tare da ya amsa mata nata tambayar ba.
“Yayata fa kake so take sonka, why are you here kana fada min magana haka?”
“Ni... Aa Wallahi ba Namra nake so ba, ke nake so ke na biyo ba ita ba, kawai na lura da ke baki son magana ne ya saka na raba ta hannunta saboda na samu isowa gareki, ita kanta ta san da wannan ai”
Hurriya ta girgiza kai.
“Bata sani ba, ni da ita mun gina fahimtar mu ne akan ita kake so ba ni ba, dan Allah karka saka yar'uwata ta tsane ni, ita ce ta dace da kai ba ni ba, ita ce aka shirya yi ma aure a yanzu ba ni ba, ni ce auta yanzu a gidanmu idan ka cire kane na da baya nan, ina yayyu hudu mata, ban da maza uku ba za a tsallake su ayi min aure ba”
Ya matsa kusa da ita da sauri.
“Zan jira Hurriya zan jira har zuwa lokacin da za'ayi miki aure...”
“Aa ni wani be ma taba cewa yana so na ba, ni ba aure ko soyayya ne a gabana ba, akwai kalubalen da yawa da yake fuskatata su ya kamata na fara samun mafitarsu ba soyayya ba I'm just