Advertisements
Chapter 6 Reading Kanwar Maza 1&2 Complete Hausa Novel Hausa Novels
Advertisements

Kanwar Maza 1&2 Complete Hausa Novel

Author :  Aysha Cool Category :  Complete Novels

Chapter   6 / 61

15K to 18K   out of 182.7K words

yi mata interview, amma ba abin da ta iya, izifi biyun da aka yi mata tambayoyi da ?yar ta kai.

Umar ya shiga tunanin tsawon lokacin da Ruma ta shafe tana zuwa makarantar allon nan, me take yi da ta kasa izifi biyu.

Ransa ba ?aramin Saci ya yi ba, ya hau ta da faWa a gaban mutane.

Cikin kuka ta ce "Wallahi yaya na iya karatu"

"To uwar me ki ka iya, kin kasa izifi biyu"

Ta Wan yi shiru sannan ta ce "Eh na iya, amma ba a allona na rubuta na iya ba, na allon wani almajirin malam babba ne, idan aka ?ara masa nake iyawa, ni kuma sai na kasa nawa"
Murmushi malamin yayi ya ce to biya mu ji "Tiryan-tiryan da ?ira'ar warsh, take karanta suratul Yusuf, ko tuntuSe babu"

Shugaban makarantar yayi mata kabbara ya ce "Ahh gaskiya 'yar baiwa ce, zamu san a in da yakamata mu sanyata, daga islamiyyar har tahfiz Win, zaku ga sauyi in sha Allah zata yi karatu"

Yaya Umar ya ce "To masha Allah, haka muke so" aka saka wani malami ya kai Rumaisa aji.
Tare suka fito da Yaya Umar, ya dubi Ruma ya ce "Ga makaranta nan na kawo ki, idan kin ga dama kiyi karatu, idan baki ga dama ba nan ma ki yi musu halin naki, kiga abin da zai biyo baya" ta sunkuyar da kai kamar ta Allah, yayi faWansa ya gama ya tafi.

Gaba Waya ba tayi murna da zuwa makarantar nan ba, haka aka kai ta aji ta nemi wuri ta zauna.
Gaba Waya Waliban sun mayar da hankali, suna ta zuba karatu, Ruma kuwa sanyin fanka ne ke nema ya sanyata bacci.

"Ke ya ba kya karatun?" Cewar malamin da yake kula da karatun nasu.

Kallonsa ruma tayi, shima uniform ne a jikinsa na Walibai, amma ya tsaya zai yi mata iyayi.

"Sabuwar zuwa ce ni, ban iya wurin ba" ta bashi amsa kanta tsaye.
Bai kuma saurararta ba, ya cigaba da tilawar tare da sauran Waliban.

Ta dubi wata Waliba ta ce "Ke, dan Allah nan aji nawa ne?"
?alibar ta kalli Ruma sannan ta ce "Aji Waya ne"

"Kutmar, ban gane aji Waya ba, kina nufin aji Waya aka kawo ni?"

"Eh mana" yarinyar ta bata amsa.

Ruma ta jinjina kai ta ce "Lallai ma an raina mini hankali, wallahi ba zan zauna a aji Waya ba".

?aliban suna ta tilawarsu, yayin da malamin yake jin haddar wasu, amma Ruma hankalinta na kan yadda zata fita daga ajin, dan zaman ajin ya isheta.
Daga bisani ta koma gefe ta hau gyangyaWi.
Lokacin da aka fita break, yunwa ta saka Ruma a gaba, dan ba ta karya ba Yaya Umar ya taso ta a gaba.
?alibai ne masu yawa sosai a makarantar, dan makarantar sananniya ce sosai a unguwar, dan kusan babu ta biyunta. Daga yanayin mayar da hankalin su Huzaifa da yadda suke bayar da labarin tsananin makarantar ya sanya ta ji ba ta son makarantar sam.
Tun da aka fita break da salla, wuri Waya ta samu tayi zamanta tana bin ko ina da kallo, sai da ta gaji ta tashi ta fara dubawa ko zata ga Yasir ko Huzaifa amma babu wanda ta gani a cikinsu. Haka aka koma aji ba tare da ta samu komai ta saka a cikinta ba.

Aka dawo aji aka Wora da karatu babu ?a??autawa, gaba Waya Ruma ta gaji da zaman makarantar. Malamin ajinsu ya fara yi musu ?ari, ta buWe Alqur'anin ta ajiye, ta cigaba da gyangyaWinta.

Tun da Ruma ta shigo ajin Wazu yake kallonta, sam ya lura babu alamar son karatun a tare da Ruma, daga hamma sai bacci take yi.
?arshe ta haWa jakarta ta cewa malamin fitsari take ji, ya ce taje tayi, ta Wau jakarta ta bar ajin.
Zagayawa take tana lelle?a azuzuwa ko Allah zai sa taga mutum Waya a tsakanin yayyenta, dan har wani irin jiri take ji, dan a duniya ba ta wuce ?arfe Waya ba ta ci abincin rana ba, yau sai ga ta har azahar babu ko karin kumallo.

Ajinsu yayi tsit, sun tattara hankalinsu a kan ?arin karatun da ake yi musu, kamar daga sama ya jiyo muryarta "Huzaifa, dama nan ne ajinki tun Wazu nake neman ku" gaba Waya ajin aka waiwaya don ganin waye yake wannan wautar.

Kallon da ake yi mata bai sanya ta nutsu ta daina maganar ba "ka ganni a makarantar ku ko? Hmm Wan zo ka ji wata magana mana".

"Ke wacece haka, baki ga karatu muke yi ba?" Malamin yayi maganar yana kallon tagar da Ruma ke tsaye.

"Yunwa nake ji, shiyasa nake nemansa" ta faWa tana sake le?o cikin ajin.

Shi Huzaifa mamaki ne ya cika shi, yaushe aka saka Ruma a makarantar nan bai sani ba?.
Ganin babu komai a kan Ruma sai wauta ya sanya malamin ya kalli Huzaifa ya ce "Je ka ka sallameta"

Cike da jin kunya ya tashi ya fita, yana fitowa ta tare shi da murmushi, shi kuma ya haWe rai ya ce "Uban waye ya kawo ki makarantar mu?"

Kallonsa tayi ta kalli harabar da suke ta ce "Sai ka ce wata makarantar arziki, nima ban ce a kawoni ba, wayewar garin Allah kawai mai sunan Baba ya bani uniform ya kawoni, ni wallahi gara na koma na bawa malam babba ha?uri, in koma makarantar allon mu ba zan iya wannan jidalin ba".

"Ke dalla rufewa mutane baki, daga zuwanki kin fara nuna hali, kawai ki zo ta window kina kirana saboda hauka, maimakon ki yi sallama ki tambayi malamin, ke Allah sai kin bar makarantar nan, dan ba zaki zubar mana da mutunci ba".

"Saboda gani annoba ko?" Tayi maganar tana hararasa.

"To ba gara annoba ba, idan aka samo maganin ta shikenan ba, ke kuma maganinki sai Allah, yanzu uban me zan miki?"

Ta yatsuna fuska ta ce "Ni yunwa nake ji, kuma wallahi sonake na tafi gida"
Huzaifa ya ce "Lallai baki da hankali, to ke da gida sai ?arfe biyar, wuce muje ajin su Yasir gara mu raba abin, da ki dinga yi mini ni kaWai"tura baki tayi, ta rungume jakarta, Huzaifa ya sanyata a gaba yana mita suka nufi ajinsu Yasir.
Ita kuma sai mita take, a kan daga yau ba zata sake zuwa wannan makarantar ba da ake uzzurawa mutane.

Yasir kansa salati ya dinga yi da salallami "Dan girman Allah meyasa mai sunan Baba zai yi mana haka, ya saka yarinyar nan a makarantar nan ba a shawarce mu ba, wallahi mun kaWe"

"Oho muku, ku kwantar da hankalin ku, ni ba kuma zuwa zan yi ba, kawai ku bani Abinci"
Yasir ya dungure mata kai ya ce "Shegen ci kamar kazar hausa" suka sakata a tsakiya suna tafe suna zaginta, suka saya mata awara da ruwa ta cinye tsaf, sannan suka korata aji.

Ko da ta isa aji, tuni an gama karatun Alqur'ani, ana jiran wani malamin ya shigo.

"Ya aka yi daga zuwa fitsari ki ka daWe, gashi an gama ?arin Alqur'ani, sati mai zuwa idan Allah ya kaimu zamu bayar da hadda" cewar yarinyar dake kusa da Ruma.
Ruma ta kalleta ta ce "Ina aka biya Win?".
Yarinyar ta buWe Alqur'anin tana nunawa Ruma ta ce "Rabin shafi aka ?ara, gobe in Allah ya kaimu ma za a ?ara rabi, feji Waya kenan sati mai zuwa idan Allah ya kaimu sai ki kawo haddar".

Cikin ko in kula Ruma ta kawar da kanta gefe, alamar zancen yarinyar ma bai shigeta ba.

"Ya na ji kin yi shiru ne? Ki buWe sai na koya miki, idan fa baki iya ba babu ruwan ya sayyadi da sabuwar zuwa ce ke, zaneki zai yi".

Rumaisa da shishshigin yarinyar ya fara ?ular da ita ta ce "To a kasheni mana kar a barni da rai, ba cewa aka yi nan aji Waya bane ba, kuma sai a ?ara mini rabin shafi, kuma wai na haddace yo ta ina zan iya ni, nifa a makarantar da na baro sai nayi wata ina nanata aya biyu nake iyawa, wannan karatun ma na san ba zan iya ba sai dai ayi kwaWona da mai da yaji a cinye" galala yarinyar ta bi Ruma da kallo ta jinjina kai ba ta sake cewa komai ba.

Bayan an kaWa ?ararrawar tashi, malamin da ya yi mata interview ya kirata ya gaya mata cewar za'a fara karSar haddarta daga tushe, sannan za ta dinga yi tana haWawa da wanda ake yi musu a aji.
Da yake ma bata fahimci bayanin da yayi mata ba, hankalinta na kan ta tafi gida, dan ta san ba iyawa za ta yi ba, kuma ta gama yanke shawarar daga ranar ba zata sake zuwa ba sai dai Yaya Umar yayi mata abin da ya ga dama.

Ko su Huzaifa ba ta nema ba, ta nufi gida.
?a da uwa sai Allah, wuni gudan da mama tayi babu Ruma a kusa da ita duk sai ta damu, ta ji gidan babu daWi, gashi tana ta tunanin ko abinci Ruma bata tafi da shi ba, balle ta samu ta ci haka mama ta wuni sukuku.
Tana tsaka da tunanin Ruman ne, ta Waga kai taga Ruman a tsakar gida.

"Meye haka, babu sallama ki shigo ki tsaya?"

Ruma bata amsawa mama ba, sai kumbura baki da take yi, ta cire hijjabinta da jakar makarantar ta dungurar a wurin ta tafi kitchen tana dube-dube.

Ba ta saurari mama ba sai da ta ci ta ?oshi, Sannan ta dubi mama ta ce "Ni fa mama gaskiya ba zan sake zuwa makarantar nan ba".

"To ai ba ni zaki gayawa ba, wanda ya saka ki a makarantar zaki gayawa".

"Mama kin ga uban dukan da ake yi a makarantar nan kamar an samu bayi, kuma dan rainin hankali wai aka kai ni aji Waya ni za a kai aji Waya saboda raini, to wallahi makarantar malam babba zan koma ba zan iya ba"

Mama ta girgiza kai kawai, ta cigaba da aikin da take yi, Ruma ta saki baki ta dinga zuba tana cin alwashin ba zata sake zuwa ba.
Huzaifa ne suka yi sallama shi da Yasir, mama ta amsa musu. Basu kai ga zama ba suka hau mita.

"Mama dan Allah meyasa aka saka yarinyar nan a makarantar nan ba tare da shawarar mu ba? Kin san halin yarinyar nan tun a yau ta fara nuna halinta".

Ruma ta ce "Sha kuruminka ni ba komawa zan ba, daga yau ko za ayi ?uli-?ulina ba zan koma ba, wai saboda tsabar abu wai ?ari shafi guda, kuma wani satin ka kawo hadda, ni aya biyu nake iyawa waye zai yi wannan karatun taS ga uban duka wallahi ba zan sake zuwa ba

Yasir ya ce "Ai makarantar mu ba ta da?i?ai ba ce ba, ki koma inda ki ka fito ba zaki zubar mana da mutunci a makarantar nan ba".

Ba tare da sun san Umar yana gidan ba, yana Waki a kwance suke ta wannan zubar.

Tsuru-tsuru suka yi, musamman ruma da ta fi za?ewa, sai ganinsa suka yi ya fito tsakar gida.

"To dan ubanki ki daina zuwan kin ji ko, daga yau kar ki sake zuwa ki ga yadda zan yi da ke, kuma na gaya musu ba kya jin magana, idan har ba ki yi karatu ba su kama ki su zane ki"

Ruma a ranta ta ce "Ai wallahi sai na yi abin da za a koreni waye zai zauna ana jibgarsa kamar jaki"

Ya kalli su Yasir ya ce "Ku kuma, kune zaku dinga tsayawa a kan karatunta, ku zaku dinga koya mata dan da?i?iya ce, duk daWewar da ta yi tana zuwa makarantar allo ta kasa kawo izu biyu, sai karatun wani ta je tana iyawa, da?i?iya ki yi musu shirme na bayar da damar a zaneki"

Kawar da kai Ruma tayi gefe, Umar ya gama bala'insa ya bar gidan.

Yana ficewa daga gidan, Ruma ta dasa wa mama kuka, a kan lallai sai ta saka Yaya Umar ya cireta daga makarantar, mama ta ce babu ruwanta.

Ko da wasa Ruma ba ta sanya a ranta za ta yi wannan karatu ba, dan idan za a kasheta ba ta ma san in da aka ?ara musu Win ba, ta cigaba da sabgoginta.

Da sati ya zagayo zata koma makaranta, sai da a ka kai ruwa rana, tana kuka su Huzaifa suka sanyata a gaba zuwa makaranta, suna tafe suna zaginta suna mita an haWasu da ala?a?ai.

Yau mama ta bata kuWin makaranta, dan haka ta tsaya ta sayi goriba a ?ofar shiga makarantar.
Duk da babu malami a ajinsu, amma kowane Walibi ya nutsu sun haWa baki suna ta tilawa.

TaSe baki tayi, ta samu lungu ta zauna, ta kashingiWa tana cin goribar ta a nutse.
Shigowar malamin bai hanata cigaba da hangale baki tana gwaigwayar goribarta ba.
Ba ?aramin ?ulewa malamin yayi ba, tun a wancan satin ya lura ba ?aramar gaSuwa ce ba yarinyar.

Yayi mata alama da hannunsa ta je, ta tashi ta fito da jakarta da goribarta a hannu ta ce "gani"

Ya ce "Yauwwa, ta kan ki zan fara jin karatu yau, Wauko Alqur'anin ki ki karanta ?arin da na yi muku, sannan ki bani hadda" Wan waro masa idanuwanta tayi sannan ta ce "Gaskiya ban iya ba wallahi, karatun yayi yawa ina laifin aya Waya ko biyu"

"Koma gefe ki tsaya" babu ban ha?uri babu komai ta koma gefe ta ja ta tsaya.

Ya cigaba da sauraron tilawar 'yan aji, Ruma kuma ta mayar da hankali a kan cin goribarta, ya Waga kai ya kalli Ruma, wani irin takaici ya ?ule shi ko a jikinta abin da ya dameta kawai take yi, ya ce "Ke zo nan"

Ta ?araso ta tsaya, mi?ewa yayi ya Waga bulala zai daketa.
Ta ?walalo ido ta ce "Kar ka dakeni ba a dukana" bai saurari ruma ba, ya zuba mata a ?afarta har sau biyu.

Wani uban ihu ta ?wala, ta zube a kan ?afarta tana jujjuya kai.
Gaba Waya 'yan ajin suka yi shiru suna kallonta, sai a lokacin da ya daketa ya huce sai kuma ya sha jinin jikinsa ganin uban kukan da take yi.

"Wallahi ni sikila ce ba a dukana, shikenan ba zan iya tafiya ba" gaban malamin ne ya faWi, amma ya maze ya cewa 'yan ajin su cigaba da karatu.
A ?alla ruma ta shafe awa guda tana kuka babu ?a??autawa kuma ta?i tashi daga wurin, wai sikilarta ta tashi.

Abu kamar wasa magana har kunnen malamai, kasancewar malamin nasu, Wan ajin da suka yi sauka ne yake koyar da su, ba cikakken malami bane a makarantar.
Malamai suka taru a kan ruma, amma ta?i tashi wai sikila ce da ita, ba zata iya tashi tsaye ba.
Malamin nasu jikinsa sai rawa yake yana cewa "Wallahi bai san ba ta da lafiya ba"

Malamin da yayi mata interview ya ce "Kuma ni a form Winta yayanta bai rubuta tana da wani ciwo ba, ina ne gidanku?"

"Ni ba zan gane hanyar gidan ba, akwai yayyena a makarantar nan ku kira mini su su kai ni gida in ga mama zan mutu"

"Su waye yayyen naki?" Nan gaya musu ajinsu Huzaifa.
Huzaifa yana can yana karatu aka kirashi, yana zuwa ajinsu ruma ya ganta zaman dirshan malamai sun kewayeta.
Nan suka yi masa bayani, turus yayi yana kallon ruma yana son gano ko makircinta ne, dan shi a iya saninsa ruma ba ga da wata sikila, ban da zazzaSi ba ta ciwon uban komai, amma a ina ta samo wata sikila?.
Ya mi?a mata hannu ya ce "Taso in mayar da ke gida"

"Ni na kasa motss ?afata ciwo take mini" tayi maganar cikin kuka.

Huzaifa ya dur?usa ya ce "To hau bayana na mayar da ke" aikuwa ta ja jiki, ta hau bayansa ya Wau jakarta ya ce bari ya kai ta gida.


Sai da suka yi nisa sosai da makarantar sannan ya sauketa, aikuwa ta tsaya cak a kan ?afafuwanta.

Ya kalleta ya ce "A gidan uban wa ki ke da sikila?"

"To gani nayi za a kasheni da duka, naga a makarantar bokonmu ba a dukan wata me sikila, da na ji zafin dukan sai na ji kamar nima ina da sikilar".

Galala ya bi ruma da kallo, 'yar mitsila da ita amma ta iya makirci haka.

"To mu je ki yiwa Yaya umar abin da ki ka aikata"

Marairaicewa tayi ta ce "Dan Allah kayi ha?uri"

"Wallahi ba zan goyo ki a banza ba, ko ni sai na miki shegen duka yau" yana gama maganar ya dan?eta ya saSata a kafaWarsa dan zata iya ?wacewa ta gudu.






Ayshercool
08081012243
[22/06, 9:49 pm] JAKADIYAR AREWA: ?ANWAR MAZA
? ? ? ? ? ? ? ??

Na Aisha Adam (Ayshercool)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES


https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ku yi subscribing? YouTube channel Win
@Cool Hausa Novels, domin samun daWaWan litattafan hausa na sauraro.
Ku yi following Wina a arewabooks a kan account Wina na ayshercool7724
Ko watpad Ayshercool7724 kowanne a cikin manhajojin za ku iya samun litattaiafaina da na yi a baya, da wanda nake yi a yanzu na gode.



*AFUWAN BAN EDITING BA*


P6

Iya ?arfinta take ihu, tana kiciniyar sai ya sauketa, amma yayi burus da ita, sai da ya je soron gida, sannan ya sauketa ya ja hannunta zuwa cikin gidan.

Aliyu ne a tsakar gida yana yiwa mama wanki, ya Wago ya kallesu ya ce "Ya dai, ya kake jan ta tana ihu, makarantar fa?"

Hauzaifa bai amsa masa ya tambaye shi"Mama tana nan?"

"Eh tana nan" Aliyu ya bashi amsa.

Jin ihun ruma ne ya sanya mama katse sallar walahar da take yi, ta fito tana tambayar lafiya.
Hakan yayi dai-dai da fitowar Yaya Umar, shi ma ya yi shirin fita. Duk suka zubo musu ido suna jiran jin ba'asi.

"Mama wallahi yarinyar nan ba ta da mutunci, daga sakata a makarantar nan ta fara tayar mana da hankali, yaushe yarinyar take da sikila ban sani ba?".

Mama ta Wan yi sororo ta ce "Wace irin sikila kuma?"

"To haka ta je ta ce wai sikila ce da ita, ta tashi tsaye ma ta ?i sai a bayana na goyota"

Yaya Umar ya kalleta ya ce "Ke meya sameki?"

Cikin in da in da ta ce "Dukana aka yi, kuma wallahi na ji zafi sosai shi ne na ce musu sikila ce da ni, na ga wata 'yar makarantar bokonmu ba a dukanta saboda sikila ce ita".

"Shi ne ki ke yiwa kan ki fatan ciwo saboda baki da hankali, ke dama za a zauna da ke baki yi abin da za a dake ki bane ba, me ki ka yi aka dake ki?" Yayi maganar cikin tsare gida.

Cikin kuka ta Wage ?afar wandonta, shatin bulala ya kwanta a kan fatarta, ta kalli mama ta ce "Mama kin ga fa, dan Allah a cireni wallahi

6 / 61