Advertisements
Chapter 35 Reading Inaaya Book 1 Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Inaaya Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Billyn Abdul Category :  Adventure Stories

Chapter   35 / 43

102K to 105K   out of 128.5K words

Jin Ayshatouh a zuciyarta.

Dr iklimat mace ce Mai sakewa da faran faran tareda kulawa Musamman tana gane gatan dayayiwa Inayah yawa ta ringa wani lallabata tana janta ajiki
Inayah Kuma dayake dama gata tasaba dashi da tattali take ta saki jikinta ta sake da Dr iklimat din ganin sai wani gata da lallabata takeyi.

Hadiza tayi waya da antyn tata Dr iklimat taqara Mata bayanin komai akan abinda ake ciki na dalilin tafiyar Inayahn Abuja ta biyo Abbinta.

Fada Dr ta ringa Yi sosai tana ganin lefin Hadiza da bazata sake ta cusa 'yarta da gyarataba su qwaci yancinsu agun uwar MAJEED din,

Ita kanta Inayah Saida Dr din Tai Mata fadan uban me take jira da Bata dauki cikiba kowa ya huta masu mutuwa su mutu masu bin duniya subi can su suka jiyo.

Dayake dama Hadiza nada niyar zuwa Abujan yau tun jiya ta yanki ticket Koda suke waya tana airport daman Dan haka ba zato Inayah taganta driver yaje ya daukota da mamaki take kallonta tace"

Umman Dr dazu Koda muke waya kina hanya kenan?

Da farin ciki kan fuskarta tace"

Eh ba Dole nazoba sbd inason na kwana Ina zantawa da 'yata tunda haryanzu Abbinki yaqi yafemun yaban cikakkiyar dama.

Dan murmushi kawai Inayah tayi tana cewa"

To ai ko yanzu ba anan Zan kwanaba anjima zai dawo tafiya zamuyi.

Dariya Dr iklimat tayi tana cewa"

To ai yau de Dole ku hakura anan Zaki kwana.

Kallonta tayi zatai magana Hadiza ta hanata ta hanyar dafa hannunta cikin kulawa tace"

Inayah,
Ba kowace magana ake bada amsartaba,
Ni mahaifiyarki ce
wannan Kuma da kike gani yayatace dukanmu bazamu cutar dakeba
Bakyason kema ki ringa bugun gaban kinada Yan uwan nunawa
koyaushe daga Abbinki sai Abbinki kawai,
Shima yanzu Yan uwansa sun dawo rayuwarsa muma ki bamu Dama mu dawo rayuwarki.

Shiru tayi tana sauraronsu sunata Mata maganganun hikima da lurarwa,

Dr iklimat Bata bartaba Saida tasa Mata ra'ayin son kwana gidan tagani yau abbin zai iya bacci kaman jiya batareda itaba.

Murmushi tasake zancen na Mata Dadi da Dr tace"

Daqyar yau zaiga safiyar gobe.

Ba kunya ta nuna farin cikinta tana tunanin yanda zaiyi.

Hadiza wanka tayi tai sallah kafin taci abinci ta zauna tana shiga firar Dr da Inayah.

A cikin wunin suka fahimci yanda rayuwar Inayah take sosai ba kwabar magana gata yayi Mata yawa sosai hakama soyayyar abbinta tariga ta ginu cikin ranta sosai ta yanda Babu abinda zai girgiza hakan sai ubangijin Daya dasa Mata wannan so da kaunar,

Ta bangare Daya sosai suka jinjinawa MAJEED da ganin girmasa Mai tsanani ya qaru a idonsu sbd yanda Inayah take fada musu yanda take rayuwarta dasuke qiyasta gata da girman son dayake Mata.

Sanyi jikin Hadiza yakuma Yi sbd tasan Koda a hannunta Inayah ta taso bazata Bata irin girman gata da tarbiyar da MAJEED ya bataba.

Dr iklimat kuwa cewa tayi to ai bamuga zamaba tunda 'yar Tamu tagama mutuwa a sonsa koina fada takeyi gaban kowa Dan haka Dole wannan kurman abbin naki ya magantu Dan Naga alaman bazaiga girmanmuba sai 'yarmu tagama da bude Masa Ido.

Ba Bata lokaci suka fara dirka Mata wasu Hadi na natural Kaya na Musamman.

Da farko bataso Amma haka Dr ta bude Mata Ido tasakata Shan abubuwan kala kala.

Hadiza Kam farin ciki take ciki yau ta wuni Zata Kuma kwana da 'yarta ga MAJEED datasukeson saukewa duk wata kamewa ya samu farin ciki da Jin Dadi kaman kowa.

Sai bayan sallar ishai har sunci abinci abbin yazo daukanta.

Da farko marairaice fuska tayi tanajin son binsa Amma su Dr ta bude Mata Ido ta hanata Dan haka ta fasa tareda Dan Kama kanta.

Shigowa dashi akai har Lafiyayyan palon gidan yana shigowa akanta idonsa ya sauka tana fitowa daga hanyar bedroom din Dr iklimat sanyeda wasu kayan dabam.

Da kulawa yake kallonta da kayan data sauya na wata doguwar Riga Mara albarka Dan kuwa rigar robace doguwa har qasa ta lafe jikinta tun daga sama har qasa ta fidda duk wata albarkar shape din jikinta Musamman shafaffen cikinta dayasa kirjinta dake cikin padded push-up bra.

Dan gyara muryarsa kadan yayi tateda dauke Ido daga kanta Yana sake gaisawa da Dr iklimat Dake rokonsa ya tsaya yaci abinci yace aa yariga yayi dinner tareda baqinsa.

Hadiza ce itama ta fito fuskarta a Dan sake jiki ba kwari ta gaishesa.

Yayi mamakin ganinta Amma Bai nunaba ya kalli Inayah dashi take kallo ya amsa gaisuwar Yana Dan kallonta da cewa"

Ashe kina garin?
Allah ya taimaka.

Amin suka amsa ta juya ta shige tabarsu.

Miqewa yayi Yana kallon Inayah yace"

Kije ki shiryo mu tafi time na tafiya.

Kallonsa tayi cikin marairaicewa tace"

Abbi Zan kwana anan tunda gobe zamu koma please..

Kallonta ya juyo yayi da kyau Yana mamakinta sanin Bata iya kwana baqon gurinda batasan kowaba.

Cikin kulawa Yana kallonta yace"

Zaki iya kwana anan?

Gyada Kai tayi tana kallonsa.

Kin tabbata?

Sake gyada Kai tayi tana kallon yanayinsa dayake sake nanata tambayar.

Hannu ya miqa yace"

Zo Nan.

tahowa tayi ahankali tana kallonsa a shagwabe maimakon ta Kama hannunsa saita shige jikinsa ta Dan kwanta tana cewa"

Abbi Zan iya kwana anan Ina sone.

Dago kanta yayi ya kalli fuskarta cikeda kulawa yakuma cewa"

Are you sure?

Yes Abbi" tace ahankali tana kallon fuskarsa cikeda kauna da shagwaba.

Numfashi ya sauke ahankali kafin yace"

Ok shikenan Zan barki anan din Amma idan kin kwanta kinji bazaki iyaba ki kirani Zan dawo na daukeni ok??

Okay, I will miss you my Abbi.

Lumshe fararen idanuwansa yayi tareda sakinta Yana cewa"

Shikenan kije ki saka Kaya masu nauyi ki kwanta akwai sanyi.

Gyada Masa Kai tayi tana sakin hannunsa.

Sallama yayi da Dr iklimat Dake tsaye tana kallonsu cikeda shaawa da burgewa batareda ta damuwaba sbd tanada wayewarta sosai ba komai bane agurinta.

Yana ficewa Inayah ta sauke ajiyan zuciya tana juyawa ciki itama.

Shima Yana fita bayan ya shiga mota numfashi ya sauke me zafi tareda Dan rufe Ido ya bude Yana sake danne zuciyarsa kafin ahankali ya bude Baki yacewa driver sutafi kawai.
##MAMUH#


_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya👇
07040727902

MTN card👇
09134848107
[11/12, 2:41 PM] Ummulkhairi: *_61_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Bedroom din Dr iklimat takoma ta qarasa gefen Hadiza dake zaune kan kujera ta zauna tana kokarin boye sanyin jikinta na rabuwa da Abbin sbd bude Mata idon da zasu iyayi da fada tunda since karta nuna ala Dole Jan aji zasu koya Mata basusan Batasan wannan ba idan akan Abbinta ne.


Dr iklimat ce ta shigo daga baya itama daukeda ruwan kankana da Madara ta miqa Mata tana Zama bakin gado fuska asake tace"

Hadiza lallai wannan sirikin namu yafimu idon yawon duniya.

Murmushi Hadizan tayi tana kallon Inayah dake kurba drink din ahankali tanajin tsikar jikinta na tashi da abubuwan dasuketa Bata tun Rana tana Sha.

Hanata tunani sukai da zantukansu na sabbin abubuwan dasuke koya Mata Wanda suka shafi hanata maganganu da yawan sangartarta.

Sosai suka dage cikin dubara da lallabawa suka koyar da ita wasu abubuwan data rasa daga rashin Zama da mahaifiya.

Sai dare sosai suka kwanta bayan tayita ganin sakon Abbi na tambayarta
ta kwanta?
Tayi bacci?
Is she ok?
Zata iya kwana a Nan ko yadawo ya dauketa?

Wainnan sakonnin nasane sukaita shigowa tana gani ta kasa replying nasa ko so daya sbd jikinta dayake amatuqar mace da abubuwan datasha dakuma farin cikin kwana gado Daya da mahaifiyarta.

Dan kusan ma akan cinyarta tafara bacci sai daga baya ta kwana kan gado tana Jin ranta fes duk da Kuma kewar Abbinta na cinta Amma Kuma shima yawan text din nasa yasata Jin sanyi aranta Dan tasan yakasa baccine Yana tunanin ko Yaya Zata iya bacci anan.

Washe gari tana tashi Kiran abbinta ne yafara shigowa wayarta a kasalance ta dauka tana shagwaba murya tace"

Aslm alkm, Good morning my Abbi.

Ajiyar zuciya da numfashi yafara saukewa a boye kafin cikin nutsuwa da kulawa yace"

Kintashi lfy?

Lfy kalau Abbi kewanka kawai nakeyi....

Ahankali yace"

Kinyi bacci kuwa?

Tashi zaune tayi tana cewa"

Yes Abbi,
Abbi kayi missing nawa?
Kayi bacci?

Wani boyayyan numfashi ya sauke Mara sauti ahankali sbd gabaki daya zuciyarsa Bata samu nutsuwar dazai iya ko kwantawaba bare baccin
Zaune yaga asuba kan kujera Yana jiran reply dinta Amma shiru shiyasa Kai tsaye yakira da safen.

Yes" kawai yace Mata a taqaice Yana cewa"

Ki shirya in time zamu wuce zuwa 2:30 Amma kafin can zamu tafi gidan juwairiyyah da safiyyah.

Ok Abbi.

Sallama sukai ya ajiye wayar tareda rufe idanuwansa dasukai nauyi Yana Dan dafe kansa.

Tashi yayi tareda kashe wayarsa gabaki daya ya nufi gado ya hau a natse ya kwanta sbd yanzu zai iya samu ya Dan Yi baccin kafin anjima.


Acan gidan Dr iklimat kuwa su umma Hadiza wasu mayun turaruka masu shegiyar tsada da mayen qamshi suka siya gurin wata qawar Hadizan Dake Nan Abuja tun daren jiyan sukai Mata waya sai gashi da safen driver yakawo.

Harhada Mata su sukai tareda wasu sabbin fitinannun kayan baccin da Dr iklimat ta fita da kanta ta siyo Mata shima a gurin neighbor dinta me Saro designers daga waje.

Sam Inayah Bata saka mini skirts sbd batadasu a kayanta Amma hardasu suka siyo Mata.

Qarfe daya tagama shiryawa suka zauna jiran zuwan Abbi.

Lafewa tayi jikin mahaifiyarta tanajin kaunarta sbd kwana dayan Nan dasukai duk sun sake saka Mata kaunarsu da Jin dadin dawowarsu rayuwarta gashi suma sunata lallabata kaman yanda Abbinta ya sabar Mata duk da suna Mata fadan wani abin Amma akwai kaunarta sosai ataredasu.

Qarfe daya da rabi ya iso gidan Bai shigoba saidai suka fito.

Fitowa yayi motar suka gaisa dasu a mutunce Yana kallon gefen datake a fisge sbd ganin kaman tasauya Masa sbd harda skin scrubbing sukai mata.

Itama shi take kallo zuciyarta na cika da son kayanta suna hada Ido ta shagwabar da fuska tana sakin murmushin farin cikin ganinsa.

Ahankali Yana Mata wani mayen kallo yace"

Muje ko?

Jikin umma Hadiza ta qarasa ta rungumeta tana cewa"

Kidawo da wuri kema.

Murmushi kawai tayi Tana cewa"

Allah yakaiku lfy Ina gaida su umma yaganah da Haj.

Dr iklimat ta runguma itama tana cewa"

Mommy kince zakizo
Ki cika alqawari kinji?

Gyada Mata Kai tayi tana cewa"

Zanzo Inshallah ki gaida mutan gidan
Allah ya tsare,
Kuma kindai ji abinda na fada Miki.

Gyada Kai tayi tana cewa"

Yes Mommy.

Mota ta juya ta nufa Dan already Yana ciki Yana kallonta da idanuwansa dasuka kasa daukuwa daga kanta.

Tana shiga motar driver yaja suka wuce.

Bai juyoba sbd yawan kallonta matsala ne agurinsa Dan haka ya Dan maida hankalinsa kan waya Yana son Kiran safiyyah dasu juwairiyyah suna gidanta gabaki dayansu da Yara.

Bayan ta dauki wayar da qyar ya riqe kansa tareda kamewa ya sanar da ita suna hanya ya kashe sbd wani mayen Qamshin dayakeji Yana tashi daga jikinta ahankali Yana Shiga hancinsa Yana neman buga kansa.

Gashi taqi zuwa ta maqalesa kaman yanda ta saba tana zaune itama tana duba sakon Neesah data turo Mata ta WhatsApp.

Hankalinta na kan Abbin nata tannuwanta da zuciyarta dasuka Saba zuwa garesa sai kokarin hanasu zuwan takeyi sbd fadan su umma Hadiza dake yawo cikin kanta na hanata zuwa koyaushe tabari yazo da kansa.

Daqyar kowannensu ya iya riqe kansa harsuka Isa gidan anty safiyyah suna fitowa motar su Anty juwairiyyah da 'yayansu suka sake zuba idanuwansu kanta sbd Babu abinda yake jikinta Mara kyau da tsada tun daga kan kyakkyawar halittar da Allah yayi Mata har tsadaddiyar suturar jikinta da wasu matsiyatan designer handbag da takarmin Stuart W.

Babbar 'yar anty juwairiyyah rumanah itace ta saki fuska sosai tareda rungume Inayah din tana cewa"

Uncle sannu da zuwa,
Welcome matan uncle.

Murmushi Inayah tayi tana amsawa ahankali.

Gaidasu anyu juwairiyyah tayi cikin girmamawa da sanyi.

Amsawa sukai anty safiyyah na qarewa Inayah kallo tana yaba kyanta da komaima dan itakam take Inayah Tai Mata Dan shekaran jiya Basu ganta dakyauta sbd dare ne yanzu Kam taganta Kuma wlh tafi Dr farhat komai ta fada a fili tana cewa"

Gskia Inayah is the perfect match wa MAJEED.

Haj umma Dan Allah ta Dena maganar wata macen Kuma.

Dadin maganar Inayah taji Amma Bata kalli Abbinba sukai ciki gabaki dayansu.

Abinci sukaci a babban dining din palon gidan sunata fira da 'dan uwansu yaran Kuma sunatayi da Inayah wadda kusan hankalinta yafi kwanciya da yaran dasuka nuna Mata kauna sai Anty safiyyah Amma Kam anty juwairiyyah Dr farhat sukeyi wuta itada Haj umma.

Sosai anty safiyyah ta sauke kanta tabawa 'dan uwanta hakurin abinda ya faru baya
Bayason tada komai Dan haka ya dakatar da maganar yace abarta ya wuce kawai.

Karfe biyu Saura suka baro gidan bayan yayiwa yaran dasu kansu uwayen yaran kyautar girma Data sake sasu jinjinawa MAJEED din sukaita godiya da Jin Dadi suka rakosu suka wuce.

Kusan late suka Isa airport Dan hakan suna Isa ba Bata lokaci suka tashi.

Ko a jirgi dai Babu wata doguwar Hira data shiga tsakaninsu sai mayen kallo dayake binta dashi Yana Jin sabon yanayi akanta.

Itama yau jinsa take cikin ran nata sosai sbd tunda suka hadu ko hannunsu be haduba Dan haka takejin kaman zuciyarta Zata fashe da sonsa.

Charles ne yazo daukansu airport da Daya daga cikin lafiyayyun motocin gidan.

Saida suka kamo hanyar gida ya kasa hakuri ya juyo ahankali ya kalleta tareda kamo hannunta dake kan cinyarta ajiye tana kallonsa.

Kama hannun nata da yayi kusan atare kowannensu ya saki ajiyar zuciya a boye.

Cikin idonta ya kalli tareda bude Baki ahankali yace"

Are you okay????

Gyada Kai tayi ahankali tana narkar da fuska.

Jin yayi wani a feeling na fizgarsa akanta sbd galabaituwa kusan dayake tun jiya a zuciya,

Tunda take baitaba barinta taje wani gurinba ta kwana sai jiyan,
Duk tafiye tafiyensa hankalinsa yafi kwanciya dayaje duk Inda zashi yabarta gida tareda umma yaganah shiyasa jiyan hankalinsa yakasa nutsuwa.

Bude motar tayi kafin yasake wata maganar ta fice tana satar kallonsa
Tana ganin umma yaganah ta qarasa da gudu tayi kanta ta rungumeta sbd Basu taba rabuwaba duk tafiyansu tare sukeyi sai yanzu.

Ajiyar zuciya yayi tareda sauke numfashi ya dedeta kansa ya fito motar shima yayo ciki su umma dake palon duka suka fara Masa sannu da dawowa cikin farin ciki.

Ana Gama gaisawa ya wuce hanyar palonsa dake gyare tsaf Salimat ta gyara koina Yana fidda sanyin AC da qamshi me Dadi.

Itama Bayan angama murnar ganinsu umma dakinta ta wuce zubbi na biye da ita da kayanta ta ajiye tareda bude akwatin ta fidda komai dake ciki ta kaisa Inda zai zauna ta maida akwatin ta fice daga dakin lokacin Inayah na toilet tini.

Alwalar sallar la'asar da basuyiba tayo ta fito tazo ta sauya kayan jikinta zuwa jallabiya tayi sallar.

Tana gamawa ta saka wayarta caji tareda fitowa ta nufi dakin umma yaganah ta kwanta jikinta tana Bata labarin tareda umma Hadiza ta kwana.

Palo suka dawo gurin Haj umma suka qarasa firarsu itadai Haj umman Bata wani saka Baki sbd bacin ran datake ciki tun ranarda MAJEED yatafi da Inayah abujan batareda sun saniba sai data fito da akwati suka San da ita zaiyi tafiyar Kuma kiri kiri ya dauke 'yar cikinsa zuwa hotel din daya sauka suka kwana acan.

Abin ya Bata mamaki tareda Bata ranta sbd duka tsarinsu na iyayen farhat dazai gani a abujan ya wargaje da damuwa Dr farhat tabar Nigeria duk tashiga damuwa sosai.

Dole lallabata tayi da Bata tabbacin taje kafin tadawo komai ya kankama aure ba fashi.

Sallar magriba tasa kowannensu tashi ya nufi dakinsa yayi sallar.

Tana gamawa Bata fitoba Saida lokacin cin abinci yayi zubbi tazo kiranta tace ta koshi zubbin ta hado Mata cornflakes kawai shi zatasha.

Koda zubbi tazo ta sanar da cewan Inayah tace ta koshi shiru kawai yayi Yana cigaba dacin abincinsa Amma hankalinsa baya gurin Kuma.

Bai wani ci abincinba yaji ya ishesa yasha juice da ruwa kadan ya tashi ya fice zuwa sallar ishai da lokaci yayi.

Yana tashi Haj umma tabisa da kallo sbd Sarai tasan sbd Inayah Bata fitoba yaji abincin ya ishesa.

Numfashi ta sauke tana tunanin tabbas Hadiza da yarta qaddara ce rayuwar 'danta duk sunbi sun firgitar Mata da Natsatsen yaronta.

Inayah tana sane taqi fitowar saidai duk batajin dadin hakan itadai ba lallai Zata iya wannan salon nasu umma Hadiza da Dr iklimat ba

Sallar ishai tayi ta miqe ya nufi dakin umma yaganah tareda qarasa chats dinta a kwance tanajin Nishadi Amma idan Abbinta ya fado ranta saitaji kaman taje ta samesa.

Sai guraren 11 ta tashi ta nufi bedroom dinta ta tube tafada toilet tayo wanka da ruwan zafi ta fito ta shafa Mai tareda shafa normal turarenta na black opium tana kokarin saka kayan bacci Kiran Abbi yashigo wayarta.

Kallon wayar tayi tareda Jin wani sanyi cikin ranta ta saki murmushi tareda daukan wayar ta zauna bakin gado cikin shagwaba tace"

Abbi...

Ajiyar zuciya ya sake a boye sbd tunanin kwananta gidansu Hadiza ya sauya Masa ita shiyasa baya barinta zuwa koina bare kwana sbd sauya Masa tarbiyarta gashi daga kwana daya ta sauya.

Ahankali takuma Kiran sunansa
Ya bude Baki a natse yace"

Meyasa kike Wasa da abinci?
Kici wani abin ne?

Murmushi tasake ahankali kafin tace"

Nasha cornflakes Kuma ya isheni Abbi.

Kaci abincin Kai Abbi?

Alhmdllh" kawai yace Mata a taqaice zaiyi magana saikuma ya fasa kawai ya aje wayar.

Murmushi tasake zuciyarta na cika da farin ciki sbd tasan Abbin saiya sake Kiran wayarta.

Kayan data fidda na bacci zata saka ta maida tareda dauko wata fitinanniyar rigar bacci Mara albarka ko kadan ta kalla taga banbancinta da Babu kawai kala ne,

Hot red ce rigar Dan haka ta saka batareda ta saka bra ba sai wani qaramin red pant data saka ta nufi gaban mirror ta dauki Turaren dasu umma Hadiza suka siya Mata ta bude tareda Ciro abin shafawar taringa shafawa wuyanta zuwa tsakiyar kirjinta.

Jin itama yafara tada tsikar jikinta da Qamshin yasata ajiyewa da sauri tana Dan rage Wanda ta shafa...

Juyawa tayi Zata nufi toilet ta debo tissue ta sake ragewa saiga kofar bedroom din nata an bude Kai tsaye cikin nutsuwa tareda shigowa.

Da sauri ta juyo cikin tsoro sukai Ido biyu da Abbinta Dake kallon rigar jikinta cikin wani gigitaccen yanayi.
##MAMUH#
#HOTLOVE/HOT ROMANCE
#MAJEED/ INAYAH.





_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya👇
07040727902

MTN card👇
09134848107
[11/12, 2:41 PM] Ummulkhairi: *_62_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Kasa motsawa tayi daga Inda take sbd take kunyar rigar jikinta ta kamata a Karo na farko dataji kunyar,

Dauke idonta tayi daga kansa tana Dan fasa qarasawa kofar toilet datai niyar zuwa debo tissue,

Idanuwansa takeji ajikinta suna yawo Dan haka ta Dan motsa kadan tana dagowa ta kallesa...

Wani mayen kallo ya qare Mata cikin sakanni kafin ya dauke kansa ya qaraso Kai tsaye ya nufi 2 seater sofa dake gefen gadonta ya zauna ahankali tareda ajiye wayarsa Dake hannunsa gefensa ya Dan sake dedeta kansa ya dago cikin nutsuwa ya kalleta tana

35 / 43