Advertisements
Chapter 32 Reading Noor Albii Book 1 Complete Hausa Novel Hausa Novels
Advertisements

Noor Albii Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Complete Novels

Chapter   32 / 36

93K to 96K   out of 107.4K words

dauka auren Mai dorewa ne tun farko
Saidai Kuma kaddara da rabo na ubangiji ba'a tsere musu,

Laifi dai anyi Mata na rashin fadar Dan Haka nakeson rarrashinta nabata hakuri duk wannan tashin hankalin zata sakawa kanta damuwane tunda bawa baya wuce qaddararsa....

Laylah Allah yayi dai Matar Turaki ce Kuma uwar yayansa........ Dan Allah kifara tausarta kafin nadawo
Ki Bata hakuri sosai sbd mum Mata laifi mun yarda Amma Inshallah za'a gyara komai....

Mutuwar tsaye Zinat tayi zuciyarta na neman Faso kirjinta tafado tsabar shiga tashin hankali da rudu
Amma dayake gwanace gurin riqe kanta sai Bata bayyanarba ta jinjina kai kawai sbd bazata iya magana ba bakinta rawa yake.

Anne na fita tayi wurgi da Jakarta da keys din motarta tareda dankwalin kanta tanajin kaman zata Ara hauka akaron farko.....

Wane mugun labari ne wannan takeji abakin Anne?

Kallon siddika tayi cikin tsananin tashin hankali tace"

Daidai naji Anne tace Laylah ce Matar Turaki???

Da sauri siddika ta gyada Kai cikin nata zallan mamakin da firgici Dan sai yanzu take sake tabbarda akwai masifa a kwance kenan idan Ms Na'ima ta tashi ta samu wannan sabon zancen.

Zama Zinat tayi tana fifita fuskarta da hannunta Dan wani zafi taji tanaji
Cikin shiga rudin tunani tace"

Tabbas Basu fada Mana cewan Sa'adah Matar Turaki shiyasa shegu tsinannu suka bar Na'iman ta tafi da Laylah wato takai Masa matarsa har gidansa......

Tun farko wane Dan burauban shegen ne Yafada Mana Sa'adahn ce Matar Turaki????" Tafada tana dago da jajayen Idanuwanta ta Dora Kan Siddika da jikinta yafara rawa tana neman zancen fidda Kai tana kokarin magana Zinat ta sauke Mata wasu kyawawan Marika guda biyu tana fizgota tace"

Dama bakida sani akai Kika kawo Mana wannan zancen kokuwa da gayya kikace Mana Sa'adahn ce?

Cikin azabar Marin datasha tafara rarraba Ido tana hawayen tsoro sbd komai zasu iya Mata tunda tafi kowa saninsu ba Imani ne dasuba musamman Haj Zinat din tunda har Ms Na'iman itake fada Mata yanda za'ayi komai.

Dukan fita hayyaci Zinat ta ringa yiwa siddikan tana cewa"

Kece Kika lalatamun komai da shirina na shekaru Dana Jima Ina fafutaka akansa,
Matsiyaci wlh zanyi lokacinki idan nagama da Laylan da Na'iman tukuna..

Tattarawa tayi tabar gidan sbd zata iya kashe siddikan idan Bata bar inda take ganintaba,

Sabon tashin hankali tashiga na musamman sbd na farkon duk Mai saukine a daukansu cikin shege ne jikin Laylan ba Turaki Dan Haka komai zaizo da sauki,
Amma Jin Laylah Matar Turaki ce yasata Shiga matsananciyar tashin hankali sbd Dan halak ne wato zata Haifa masa,

Magajinsa fa kenan??

Magajin dukiyar dasuka Dade suna shirka akanta Dan su mallaketa koba dukaba su mallaka Rabin,

Magajin dukiyar da akanta taketa durawa qawarta dasuka taso tare tun yarinta maganin data juyar Mata da qwaqwalwa ita ke controlling dinta....

Amma ace Rana tsaka wata qanqanuwar yarinya ta samesu daga sama Bayan tagama lalata mata komai na wargaza gashi sanadin hakan Turaki zai iya gano halinda Na'iman take ciki Wanda Yana ganowa tasan labarinta yaqare daga Nan Kuma...

Wlh bazata yardaba,
Komai zata iyayi dan ta tsira,

Yanzu babban burinta ta fito da Na'ima daga gidan,
Sbd sai Na'iman Bata gidan zata samu damar kawar da Laylah da cikinta daga duniya Kai tsaye sai laifin ya rataya Kan Na'iman wadda ita Kuma takardun shedar haukanta zaisa hukunci bazai hau kantaba
Dan Haka duk tsanani saita fidda Na'ima daga gidan
Kuma zata fiddatane daga gidan ta hanyar da Laylah zata daga hankalinta itama ta fito daga gidan.


Washe gari da gangan tana sane taqi zuwa gidan sai dare tazo
Lokacin Na'ima ta farka Amma Bata iya komai sai Ido datake Binsu dashi Haka ta sake sakarwa Na'iman wata allurar data sake maidata halinda ta fito idanuwanta suka rufe Takoma baccin wahala.

Fitowa dakin tayi siddika na biye da ita Saida suka zo palon ta kalli siddikan cikin bayyanarda Mahimmancin aikin da zata sakata ta kalleta tace"

Aiki Mai mahimmanci Zan sakaki
Idan Kika Bata mun aiki wannan karon Wlh yanda na maida Na'ima fin hakan Zan maida rayuwarki,kina Jina????

Gyada Kai tayi tana cewa"

Zan kiyaye Wannan karon.

Ciro qaramar kwalba daga jakar hannunta tayi tareda qaramar lighter ta miqa mata..

Karba siddikan tayi tana bude idonta akan kwalban da warin fetir ke tashi acikinta
Ta hadiye wani mugun yawu tana kallon kwalban da lighter din cikin rawar murya tace"

Wannan fetur.....

Katseta tayi da cewa"

Nafiki sani tunda nice nabaki,

Anjima da daddare ki zuba a akan gadon Na'ima Kuma ki zuba Mata kadan a jiki saiki janyota ki fito da ita daga bakin kofar dakin ki kunnawa dakin wuta,

Karki Kira jama'a sai wutar taci sosai Kuma ki tabbatarda ta shaqa hayaqin wutar saiki fita ki Nemo jama'a,

Kafin akirani idan antambayeki garin Yaya kice itace ta kunnawa dakin wuta da kanta tana cewa kunnawa gidan wuta zatai kowa ya mutu har Laylah.

Tsananin tsoro da mamakin girman rashin Imanin Zinat din da zata cutatarda Ms Na'ima sbd son abun duniya..

Cikin sake bayyanarda zata iya Mata abinda tace zatai Mata idan ta Bata Mata aiki tace"

Idan Kika aikata kuskure daya komai ya lalace wlh ke Zan cinnawa wuta kifara Isa lahiran kafin muzo.

Wucewa tayi tabar siddikan tsaye tana binta da kallon mummunan tsoro da tashin hankali...

Kasa zuwa kitchen tayi da fetir din ta nufi dakin Ms Na'iman dashi ta boye bayan Kan gadonta tana kallon fuskarta...

Akaro na farko da Tausayin Ms Na'iman ya ratsata sbd batada Mai qaunarta bare yabata shawara,

Tayi watsi da qanwar mahaifiyarta data riqeta sbd samun duniya a hannu gashi yanzu tazo tana neman Rasa komai...

Duk da Ms Na'ima Bata kyautata Mata saima izza da bossing dinta datake koyaushe Amma Bai kamata a cutatar da ita hakaba abun yayi yawa bayan arzikin dasuke ci suna Tarawa daga Haj Zinat din har ita duk qarsqashin Ms Na'iman suke samunsa...

Itadai gaskia bazata yarda tayi biyu babuba wlh ta koma rayuwar wahalar data fito,
Dan gwara Mata wulaqanci da masifa harma da bala'in Ms Na'ima akan barin gidan AB TURAKI Dan Haka Dole zatasan yanda zatai bada saninsuba ta bayyanarwa da Anne ko Turakin lalurar da Ms Na'ima take dauke da ita ko za'a rabata da Zinat a cetota tasamu taci gaba da cin arzikinta lfy kafin Zinat din ta wargaza musu Suma komai.


Ba yanda ta iya da daddare Haka ta cinnawa dakin wuta
Aikuwa wuta Mai qarfi ta tashi wadda batama tsammata ba
Tsoro ya kamata ta fito da gudu tunda wuri ta nema jama'a sbd wutar kamar jiratake a kunna koina yafara dauka.



Hankali tashe securities da kowa gidan ya fito,
Anne na dakin Laylah a Daren sbd wani zazzabin datake fama dashi na damuwar Dole data sakawa kanta,
Gashi taqi yadda ko ganin juna suyi da Abban nata sai zaman boyo take a daki duk ta Hana kanta sukunin zuciya shima ta hanasa sbd rashin ganinta yafi komai daga hankalinsa ita kanta rashin ganin nasa ne yaketa nukurkusanta.

Jin hayaniya na tashi a gidan yasa Anne miqewa daga zaunen datake tana bawa Laylah tea abaki tana Sha jiki amace.

Fitowa Palo Anne tayi tana cewa"

Halima lafiya gidan Nan kuwa nakejin hayaniya?

Wutace ta tashi Anne a bangaren Ms Na'ima sosai Kuma wlh..

Subhanallh innalillahi, yanzu?
Ina Na'iman?
Bata ciki dai ko???

Fita tayi da sauri tana faman nanata tambayar Allah yasa Na'iman Bata ciki.

Siddika ce kawai a waje takasa komawa jiki jikinta sai rawa yake hankalinta ya tashi Bata dauka wutar zata juye ta zama hakanba..


Koda Turaki ya fito gurin cikin sauri ya qaraso Yana tambayar Ina Na'ima?

Cikin tsananin kuka da firgici siddika tace tana ciki... Aikuwa Bai tsaya Gama ji ba ya nufa kofar ya shige...

Anne da sauran maaikatan gidan da securities suka fara ihun Kiran sunansa....

Anne da sauri ta bisa zata kamo halima ta riqeta ta hanata shiga....

Ihun Kiran sunan Turakin da ake yasa Laylah fitowa Bata ko ganin gabanta sosai jikinta har rawa yake ta kallesu cikin yanayinda muryarta Bata ko fita sosai ta bude Baki zatai magana sai gashi yafito daukeda Na'iman data Gama shaqar hayaqin harta fita hayyacinta da sauri ya nufa mota da ita Yana cewa A Abdoul daya iso ya bude mota da Sauri.

Shigewa motar yayi Suka nufa asibiti
Suna fita motar kashe wuta na isowa aka fara kashe wutar.

Anne jininta ya Riga ya hau Dan Haka Dole Saida aka kamata aka maidata ciki
Laylah ma daqyar ta maida kanta ciki suka kwantar da Anne bayan anbata maganin Hawan jininta ta kwanta itama ta nufi daki ta zauna sbd bacci kam ya Riga ya qauracewa idanuwanta,
Zazzabin datake ji ma take taji yasake,
Gabaki daya hankalinta ya tashi Kuma sbd koma menene tasan wanna wutar tanada alaqa da abinda yake faruwa..
Gida takeson zuwa kowa yasamu damar samun nutsuwa.
##MAMUH#
[7/10, 9:37 PM] +234 704 076 8969: *_Mamuhgee 51_*
Tsayawa tayi cak daga bakin kofar shigowar ganin lafiyayyar santaleliyar mace kwance kan gadon Turakinta tana bacci hankali kwance..

Rigar jikinta ma ta Turakin ce ita datake matarsa tsayin shekaru masu yawa Bata taba Sanya rigarsa a jikinta ba sai gashi yau tana gani ajikin wata...

Wata irin jijjiga jikinta keyi na tiririn dayake tasowa ajikinta tako Ina
Ta tunkari gadon tana fatan ganin fuskar macen dataiwa rayuwarta da Jin dadinta kutse a gurin Turakin..

Bakin gadon ta Isa ta tsaya tsaf
Tafara sauke idonta akan dogayen fararen cinyoyin Laylan dasuke a bayyane zuwa Kan qaton cikinta daya fito sosai....
Tana Dora idonta Kan fuskar dauke idon da sauri tareda saka hannu ta murza idanuwanta tana fatar Kar makanta tasameta daidai wannan lokacin da Komai yake Shirin Shiga tafun hannunta Dan kuwa idonta Bata yarda da abunda suka nuna Mata.

Sake murza idon tayi da kyau ta Kuma kalla taga tabbas Laylah ce a gabanta,

Wani mummanan faduwan gaba ta daki kirjinta hannuwanta da qafafunta na daukan wata irin rawa take kanta yafara juyawa
Ta girgiza Kan da karfi sbd Bata fatan ciwonta ayau itama ya tashi wannan din lokacine Mai tarin mahimmanci gareta
Duk da hakan Bata yarda da lafiyar idanuwantaba sbd zuciyarta da hankalinta sun kasa dauka Dan Haka takai hannu ahankali ta shafa cikin jikin Laylan taji tabbas cikin gaske ne,

Dan sake latsa cikin tayi taji na gaskene ba mafarki ko tunaninta bane Dan Haka ta Dan bubbuga hannun Laylan cikin wani slow da batasan yaushe ya sametaba ita kanta
tasake Dan bubbuga hannun Laylan tana tada ita Daga baccin datake hankali kwance.

Ahankali Laylan ta bude idonta Dake cikeda baccin gajiya zata mayar ta rufe taga fuskar mum daf da tata tana Mata kallon daf da daf,

Murya a cakude Ms Na'ima tace"

Laylah kece dai kokuwa idon ne yakeda matsala????

Wani mummunan tashin hankali da firgici ne ya dirarwa Laylah har Saida mararta ta kulle
A zabure ta tashi zaune daga kan gadon tana kokarin sauka dukkunin jikinta na rawa.

Laylah"

Ms Na'ima takuma ambatar sunan sbd so take tabbas kunnenta yaji muryan idan ta Laylah ce
Aikuwa cikin tsananin rudewa da tsoron daya Gama fiddata hayyacinta da rawar murya a firgice ta amsa tana cewa"

Mum ki......Wani mahaukacin Marin daya sata fadowa qasa Ms Na'ima ta sakar Mata guda biyu a jere take gefen bakinta ya fashe da jini takasa dagowa ta kalli mum din ko motsawa sai hawaye dasuka balle Mata idanuwanta na sauyawa..


Tunda take kalolin masifarta da bala'in data Saba da duk wata haukarta Bata taba Jin abun daya daki zuciyartaba Kamar abin datake gani ayau din,
Idanuwanta ne sukai jajir take agurin suna kokarin cikowa da hawaye ta maidasu da qarfin bala'i sbd ko Turaki Bata taba zubdawa hawaye Dan Haka bazata zubdawa Laylah ba,

Wani haqayi da tiririn masifa da bala'i taji suna kamawa jikinta tako Ina suna saka jikinta rawa hannunta har wani rawa yakeyi takai ta cakumo Laylan tareda shaqure wuyanta da qarfi tana cewa"

Wallahi yau saikin bar duniya shine kadai abinda zai kawo zaman lafiya
Uwarki Zaki bi kafin sauran su biyoki Dan duk Wanda ya hada alaqa dakema saina sakashi tasa masifar shima....

Fizge fizge Laylah tafara cikin tsananin masifa tana neman ceton kanta idonta na tsiyayar hawayen azaba da nauyin damuwa Amma takasa Koda iya motsa hannun Ms Na'ima bare ta ceta kanta..

A haukace takai hannu ta fizgo qaramin agogon dake zagaye da glass ta daga da qarfin gaske ta buga akan Laylan tana cigaba ihun cewa"

Wlh yau saikin bar duniya
Ko gawarki saina Kona da hannuwana,
Wannan cikin saidai kiyi naqudarsa a lahira........

Rufewa idonta yayi ta ringa dukan Laylan tako Ina tana ihun maganganunda ita kanta bazata tantance metake fadaba sbd yanda har kufan masifa ke fita bakinta jikinta na jijjikar masifa.....

Cikin sauri ya qarasa fitowa daga toilet din Jin kunnuwansa tabbas muryan Na'ima yake jiyo Masa
Daga shi sai farar bathrobe ajiki
A matuqar fusace da qarfin gaske ya fizgo Na'iman daga jikin Laylah data fara galabaita tana hawayen azaba Dan ko kukan bazata iyaba ta jikinta yagama mutuwa da komai...

Fizge fizge Ms Na'ima keyi tana ihun daya qarasa Bata ransa qarshe cikin mummunan bacin Rai ya fizgota ya nufo kofar fita da ita Batareda ya bude Baki yace Mata qala ba Dan iya zafi ransa ya dauka zafi
Bayason aikata abin daba halinsaba na taba lafiyan mace Dan Haka janye Na'iman daga gabansa shine zai basa damar riqe kansa Dan ba qaramin dukan wulaqanci tayiwa Laylahnba...

Fizge fizge take tana qwacewa tana ihun Kiran sunan Laylah
Ta raruma wani qaton flower vase da hannunta daya ta jefawa Laylan tana cewa"

Wlh kin tabo wadda ba'a cin Amanarta tabarwa Allah sai nayi ajalinki harma da gurgun ubanki da uwarki da kowama,
Har Wanda ya daure Miki kikamun hakan bazan ragawa wlh...

Jehota Palo yayi da qarfin gaske ya juya yakoma dakin tareda rufe kofar dakin da key...

Yanaji tanata buga kofa da fashe fashen kayan palon komai tasamu dauka takeyi ta buga a kofar shigowa dakin...

Laylan ya nufa ya daukota gabaki dayanta Yana kallon fuskarta ransa na tsananta baci,
Wani zafi zuciyarsa keyi na fuskarta dayaga gefen bakinta na jini,
Cikin tsananin kulawa yake goge Mata da tafin hannunsa yace"

Are you ok?
Yaya babyn?
Tashi muje asibiti adubaki
Dole zamuga likita yanzun Nan...

Jajir idanuwanta sukai takasa Koda dago Kai ta kallesa bare ta bude Baki tayi mgn sbd radadin da zuciyarta keyi na abubuwan da shikenan sun fito fili Allah ne kawai yasan abunda zai faru Kuma yanzu.

Riga da wandon pyjamas da Abayar datazo da ita tayi sallah da asuba ya saka Mata kafin ya shirya cikin black Rugby's ya kamo hannunta
Fuskarsa babu alamar rahama ko kadan ya kamo Laylan ya shigar da ita jikinsa har lokacin takasa qwaqwaran motsi bare magana ya bude kofar dakin...

Kallo daya yayiwa yanda tayiwa palon mummunan tashin hankali ya dauke idonsa
Tana ganinsu tayo kansu gadan gadan da qatuwar qwalban glass a hannu ta tunkari ckin Laylah......

Ba zato taji saukar lafiyayyan gigitaccen Mari akan kumatunta daya sata faduwa kwance qasa ya sakar mata...

Sakin hannun Laylan yayi Tareda kallonta fuskarsa a matuqar hade yace"

Wuce kintafi Ina zuwa.

Kamar mai naquda tafara daga qafarta ta wuce gaba...

Ms Na'ima ta Kuma zaburowa tana sake damqar kwalban ta jefawa Laylan ya tare da hannunsa take qwalban ta yankesa sosai jini yafara fita a hannun Amma Bai tsaya duba hakan ba ya kalli Laylah data tsaya cikin tashin hankali tana kallon jinin dake zuba a hannunsa yace"

Kije I will handle this.....

Rike Na'ima data taso tana ihun Kiran sunan Laylan yayi yafara Jan hannunta ya sauko da ita qasa ya fito da ita daga bangarensa ya nufi nata bangaren da ita tanata faman daga murya da fizge fizge Bai tsaya da ita koinaba sai cikin palonta ya saki hannunta tareda kallonta da idanuwansa dasukai jajir da wani razanannan sauti da bai taba fada acikinsa ba yace"

Idan Kika fito daga bangaren nan Zakiga hukuncin dazan iya dauka....

Cikin rufewar ido da masifar dake cin koina acikin jininta ta nufi kofar ko gani batayi tana cewa"

Zandawo kanka idan nagama da qara????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? mar karuwar Dana kawo maka cikin gidana.......

Cikin bacin ransa Dake sake bayyana da kalman datake fada da fushi cikin muryarsa Mai amsa amo yace"

I dare you.....ki fita kofar Nan idan kin Isa...

Kafar ta nufa batareda ta tsaya saurarensa ba Dan kuwa Bata Gane komai bayan ganin Laylah a hannunta...

Haj Zinat data iso gidan a gigice da wani irin sauri tayi saurin riqeta ta dawo da ita tsakiyar palon cikin tsananin firgici da ganin irin tashin hankalin Dake gudana....

Jini a jikin Turakin na hannunsa dayake fita duk ya Bata jikinsa Dana Na'iman
Hankali tashe take kokarin riqe Na'iman tana cewa"

Na'ima Dan Allah ki nutsu ayi Abi komai a hankali.....

Gabaki daya ciwon Na'iman yagama tashi Babu yanda zata iya tarota Saida Allura Dan gashi ita kanta Na'iman tajiwa kanta ciwuka da glasses Dan Haka ta riqeta da qarfi tana Kiran sunanta.

Juyawa yayi ya fice batareda yabar bangaren gabaki daya.

Kai tsaye bangarensa yakoma ya sauya Kaya yafito yana Kiran Laylah a waya ta fito zuje asibiti.

Sai alokacin ta iya fasa kuka Mara sauti sosai tana Jin rashin dadin zuciya,.

Kashe wayarsa yayi tareda nufo Sashen Annen Yana kiran dr Meenah a waya yace tazo gidan yanzu.

Kuka take sosai ko daya shigo dakin
Tana hada Ido dashi tasake Jin radadinta na qaruwa sbd ganin yanayinsa tasan baya cikin dadin zuciya da kwanciyar hankali shima
Ga rauni a hannunsa.

Zaunawa yayi gefenta tareda Kama hannunta ya riqe kawai batareda ya iya cewa komaiba sbd Sam ba Dadi cikin ransa,
Baisan Na'ima d iya duka wannan tashin hankalin ba,
Baiyi tunanin zafin zuciyarta yakai hakan ba,
A qataice baiyi tunanin iliminta da wayewanta zasu Bari ta iya wannan abin ba.

Isowar Dr Meenah yasashi fita yabasu guri.

Kallonta Dr Meenah tayi tana son tambayarta lafiya Amma sbd Turakin Dake jiran aduba aga lafiyanta Dana cikin yasa tayi abunda yakawota Kai tsaye ba Bata lokaci.

Fitowa tayi Tai Masa bayanin Babu wata matsalar kawai raunin bakintane daya fashe sai fuskarta data dan kumbura tayi ja sbd kyawawan Marin da Ms Na'ima tayi Mata
Haka Yan ciwukan kawai tayi Mata treating ta tafi.

Bazai iya barin sashen Annen ba sbd Bata Nan Na'ima zata iya zuwa Dan Haka Yana fitowa ya tabbatarwa dasu halima karsu Bari kowa ya shigo Sashen idan ba Anne ce tadawoba ya juya ya fice.

Koina na palonsa a hargitse yake sbd Babu abinda Na'iman ta ragawa duk tabi ta fasa komai Dan Haka a palon qasa ya tsaya Dr faruk yazo gida yaduba nasa raunin akai dressing tareda abubuwan dasuka kamata ya tafi.


*****Allura Haj Zinat ta fidda Jakarta da sauri tayiwa Na'iman da sauri sbd yanda jikin Na'iman ke rawa sosai da tashin hankalin datake ciki..

Tana yimata allurar dukkanin jikinta yayi Sanyi ya saki
Ta jata zuwa bedroom dinta ta kwantar Kan gado
Sai alokacin Ms Na'ima

32 / 36