Advertisements
BANI DA HUJJAH BOOK COMPELET BY Maimoon BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

BANI DA HUJJAH BOOK COMPELET BY Maimoon

BANI DA HUJJAH BOOK COMPELET BY Maimoon
  • Author: Maimoon
  • Category: Complete Novels
  • Compiler: None
  • Association: None
  • Book Series: None
  • Upload Date: 08 Mon 06, 2026
  • File Size: 311.63 KB
  • Total Views: 46
  • File Downloads: 10
  • Last Download: 3 hours ago

Discover

  • ENGLISH DESCRIPTION

    I HAVE NO DEFENSE

    A dark secret has created a deep divide between Aryaan Umar Turaki and his family. Despite his wealth, status, and powerful presence, his heart carries wounds no one truly understands.

    Then there is Salwa. A fragile young woman haunted by fear and tears, trapped in a life she never chose, living under the control of a man she cannot understand.

    When Aryaan's family gives him only sixty days to find a wife, hidden secrets begin to surface. Betrayal, family conflicts, forbidden emotions, and painful truths threaten to destroy everything.

    Why is Aryaan hiding Salwa?

    What is the real connection between them?

    Why does he treat her with coldness when his actions reveal something entirely different?

    Will Aneela become the woman he marries, or is fate leading him toward someone else?

    As the truth unfolds, many people will find themselves with no defense and no excuse.

    I HAVE NO DEFENSE is an emotional family saga filled with romance, suspense, heartbreak, hidden secrets, jealousy, intense drama, powerful emotions, and shocking twists that will keep you turning pages late into the night.

    If you love billionaire romance, forced marriage stories, secret love, emotional drama, family conflict, possessive heroes, and unexpected plot twists, this is a novel you cannot afford to miss.

    This time, not everyone will have a defense when the truth finally comes out.

    HAUSA DESCRIPTION

    Godiya ga Allah buwayi gagara misali da ya sake bani damar dawo muku da sabuwar littafina mai
    suna BANI DA HUJJA!!
    "Kamar  yadda  tafiyar  TANGLED  HEARTS  (RUƊAƊƊUN  ZUƘATA)  ta  kasance  smooth  and  full  of wonderful memories, ina fatan BANI DA HUJJA ma zai samu matsuguni a cikin zukatanmu gabaki"
    ɗaya daga ni har ku.
    "To ga dai BANI DA HUJJA nan. Allah Ubangiji ya sa yadda muka fara lafiya, mu  ƙarƙare lafiya."
    #ARYAAN UMAR TURAKI
    #SALWA AMEENU TURAKI #FAMILY SAGA
    1.
    "A hankali, cikin nutsuwa ya ke sauƙowa daga benen, but at the same time cikin kuzari da"
    "taku irin na cikakkun mazaje, that confident masculine stride of a man da ya san worth  ɗinsa."
    "ƙarasowa falon yayi, ba tare da ya ko kalli sashen da suke tsaye cirko cirko ba yayi wucewar sa ya buɗe  ƙofar palourn ya fice kamar bai gansu ba ko bai san da su a palourn ba, da idanu duk suka bisa kowa da irin abinda ya ke saƙawa a zuciyarsa gabaki  ɗayansu    ɓacin rai ya bayyana  ƙarara akan fuskokinsu, har ya fito babban farfajiyar gidan da akayi parking motoci na alfarma guda 2 banda nasa da ke usual spot din da yake parking a gidan, direct motar tasa ya nufa mai matuƙar kyau da tsada ya buɗe motar    ya shiga sannan ya maida murfin ya rufe tare da sauƙe gajeren ajiyar zuciya, whatever emotions he was carrying, he wasnt ready to share it with the world ya dannesa a cikin  ƙirjinsa, har lokacin ba'a iya ganin furkarsa, bare asalin yanayin da fuskar ke ciki, saboda p-cap din da ke kansa, da kuma shade  ɗin idanunsa, sannan ga nose mask  ɗin da ya sa ya"
    toshe hancinsa da bakinsa.
    "A hankali ya soma driving har ya fice a gidan bayan mai gadi ya wangale masa gate  ɗin, ya cilla motar  titi,  tafiyar  da  baifi  ta  minti  ashirin  ba,  ta  kawo  sa  ƙofar  wani  restaurant,  wanda  daga samansa aka rubuta Amaira Restaurant and co, sauka yayi tare da nufar ciki kai tsaye yana tafiya a nutse,  ƙananun kaya ne a jikinsa as usual dan kafin ka gansa da manyan kaya zaka daɗe he’s"
    "always simple on  ƙananun kaya, mostly ma white ko kuma black shirt,"
    "cikin sauri wani ma'aikaci da ke sanye cikin uniform na ma'aikatan wajen ya  ƙaraso wajensa, ya gaishesa tare da miƙa masa wata leda at the same time yana mamakin shigowarsa ciki da kansa yau kuma, dan on normal days yana isowa yake kira a kai masa har mota."
    "karɓa yayi bayan ya amsa gaisuwar ciki ciki,    ba lallai wanda yayi gaisuwar ma yaji amsar ba ya"
    "juya ya fice a wajen ba tareda ya sake ce masa komai ba, shi dai ya bisa da kallo kawai."
    "Motar ya koma ya shiga ya tada ya bar wajen, sai da yayi tafiya aƙalla ta mintuna ashirin zuwa ashirin  da  biyar  kafin yayi  parking  a  ƙofar  wani  ƙaramin  gida  ɗan  madaidaici  mai kyau,  sauka yayi ya tura gate  ɗin kasancewar babu mai gadi, sannan ya dawo ya shigar da motarsa, ya maida gate  ɗin ya rufe, ledan ya  ɗauka sannan ya rufe motar ya nufi hanyar shiga cikin gidan kai tsaye, a bakin  ƙofar falon    ya tsaya ya ciro makulli    a aljihunsa ya buɗe kofar ya nufi cikin falon da ke da duhu    kasancewar labulayen  ɗakin masu kauri    duka a sake suke, karasawa yayi ba tare da ya kunna fitila  ba, har ya kai  tsakiyar falon, kafin ya  ciro wayarsa tare  da kunna  haske,  ɗakuna biyu ne a cikin falon dake kallon juna,  ƙarasawa yayi kai tsaye jikin  ɗaya daga cikin  ɗakunan, ya buɗe  ƙofar  ɗakin ya zura kafafunsa ciki, yana haskawa da fitilar wayarsa kasancewar nan  ɗin ma"
    ba hasken kirki
    Sai da kalli labulayen  ɗakin da suke sake suma kafin ya Hasketa da fitila yana kallonta ba tare da ya  ƙarasa cikin  ɗakin sosai ba yana tsaye daga bakin  ƙofa ya harɗe hannunsa a  ƙirji girarsa a ha
    ɗe.
    "A zaune take a gefen gado, ta sanya kanta a tsakanin kafafunta, kanta babu  ɗankwali, kasancewar ta haɗa kai da gwuiwa ne ya Sanya gashinta ya sauƙo ya rufe fuskarta har yana taɓa gwuiwarta,"
    "baka iya ganin furkarta sam, saboda irin zaman da tayi a cikin    duhun  ɗakin."
    "second 5 yayi yana kallonta then as if forced ya  Ƙarasa cikin  ɗakin ya tsaya akanta yana cigaba da kallonta, idanunsa suka sauƙa akan hularta da hijab  ɗinta da ta ajiye a gefenta, juyawa kawai yayi ba tare da yace komai ba ya fice a  ɗakin, kusan mintuna 3 da fitarsa sai ga hasken wutan lantarki    ya gauraye ko ina na gidan ya dawo cikin  ɗakin still with his nose mask and shades on"
    yace
    """ke"""
    "bata  ɗago  ba,  kuma  bata  da  niyyar  ɗagowar  bare  ta  kulashi,  sai  kuka  da  take  ƙasa  ƙasa,  bai sake tanka mata ba ya ajiye ledan hannunsa dake  ɗauke da take away  ɗin abinci a bedside daga haka  ya  nufi  ƙofa,  a  hankali  ta  buɗe  idanunta  ta  ɗagosu  daga  gwuiwarta  da  ta  kifa  ta  bisa  da kallo idanunta duk sun kumbure saboda kuka, she couldnt believe he is leaving again, sake tafiya zaiyi  yanzu ya  barta  a wajennan?,    ta tura  baki tana  binsa  da kallo da manyan idanunta  da ke tsiyayar da hawaye, ita babban damuwarta ma yanzu ta san sai ya kashe power  ɗin gidan kafin ya tafi, ta shiga uku, gashi yamma ya soma yi sosai dan its past 4, har ya fice a  ɗakin kafin ta kalli hularta da hijab  ɗinta da tayi sallar la’asar da shi, miƙewa tayi ta sauƙa daga kan gadon ta wuce toilet idanunta na sake cikowa da hawayen takaici da baƙin ciki, gabaki  ɗaya duk wani baki da tsiwa nata ya mutu murus kamar ba ita ba, wanke fuskarta tayi ta wanko hannunta tana kallon"
    "fingers  ɗinta that are so fyn and fragile yadda ruwa ke zuba a tsakaninsu a  ƙarƙashin tap  ɗin,"
    "kafin ta cire su under tap  ɗin ta fito cikin  ɗakin tana tafiya a hankali kamar mara bone sanin har yanzu yana gidan bai tafi ba tunda ga wuta nan bai kashe ba, dan punishment  ɗin da yake mata shine  kashe  wutan  gidan gabaki  ɗaya  idan  zai fita    duk  da yadda take  da mugun tsoro  kamar farar kura haka take zama ita kaɗai kamar mayya gashi ya  ƙi bata wayarta, wannan punishment"
    ɗinnasa scares her more than anything.
    "ƙaramin  ƙugi da cikinta yayi yasa ta dafe shi a hankali, ba  ƙaramin yunwa take ji ba don abincin safe  da  ya  kawo  mata  da  tayi  taurin  kai  ta  ƙi  ci  ɗaukewa  yayi  ya  tafi  da  shi  bayan  uban  aikin gyaran gida da ya saka ta, bata da zaɓi than ta ci wannan  ɗin yanzu, ta  ƙarasa gefen bed ta zauna ta  ja  abincin  ta  soma  ci  hawaye  na  sake  cikowa  idanunta,    sam  ba  abinda  take  so  bane  a takeaway  ɗin,  kaɗan  ta  ci  ta  sha  ruwa  da  ke  ciki  ta  sake  jingina  da  gado  tana  matsar  hawaye, kamar kuma wadda    aka tsikara ta saka kuka tana shure shure akan gadon, gabaki  ɗaya ji take kamar  ba  ita  ba,  kwata  kwata  bata  jin  daɗin  rayuwarta,  duk  duniya  bata  jin  akwai  wanda  ya"
    "tsaneta irinsa, kuka ta dinga rairawa kamar an aiko ta ne dama ta yi shi tana yi tana kiran Daddy."
    Yana  jinta  daga  kwance  da yake  a  dogon  kujera  a  palour  yana  danna  wayarsa  amma  ko  kallon
    "hanyar  ƙofar  ɗakin baiyi ba, jin kukan ya ishe shi ya sa ya miƙe ya fice a falon tare da rufe gidan gabaɗaya    this time around bai kashe wutan gidan ba    ya shige motarsa ya bar unguwar gabaki ɗaya ya nufi gidansa."
    "Parking yayi a space ya buɗe motar ya sauƙo bayan ya kashe ta    ya nufi cikin gidan yana sake tamke fuska ganin har sannan motocinsu na nan a farfajiyar gidan alamar basu tafi ba suna nan suna jiran dawowarsa, gabaɗaya shi sam ya ma manta da ya barsu a gidan ba don motocinsu da"
    ya gani a farfajiyar ba har sannan alamun suna gidan shi wallahi ya mance da su.
    "a falo ya same su, ga baki  ɗayan su fuskarsu babu yabo babu fallasa, infact zunzurutun  ɓacin rai"
    ne ma a kwance akan duka fuskokinsu.
    "Ciki ciki yayi sallama, ta yadda bayi da tabbacin wani acikin su ya ji shi, bai bi ta kansu ba ya nufi"
    sama.
    """Aryan!”"
    "Ya ji an faɗa a bayansa wanda yana da yaƙinin cousin brother  ɗinsa    hamza ne, ba tareda ya bi"
    "takan hamzan ba ya sake cigaba da tafiya, uncle Ameenu ya sha gabansa yana faɗin"
    """Ba ka ji kiran da yayanka ya maka bane? Ko bai kai ya dakatar da kai ba?, iyakar mu kake so ka"
    "nuna mana kamar yadda ka saba? Ina tambayar ka?"" ya faɗa tare da saka hannu ya hankaɗa kafaɗ ar sa, ko gezau bai yi ba, sai idanunsa da suka soma kaɗawa daga farare tass suna surkawa da ja dan yanzu babu shades a idanunsa tun kan ya shigo ya cire shi, ya sauƙe idanunnasa    ƙasa ya  ƙi ya kalleshi, Uncle muhammad da ke tsaye gefe shima ransa a  ɓace ya karɓe da faɗin"
    """Me ka mayar da mu ? mutanen banza? Kiran duniya an maka kaƙi  ɗaukar waya, mu tako Muzo"
    "wajenka  takanas  amma  dan raini  da  wulaƙanci ka  sauko  ka  ganmu,  sai ka  fita  ba  tare  da kace"
    "uffan ba, sannan ka dawo zaka sake hayewa sama, wato ga  ƴan iska koh? Kai waye, me kake jin"
    kanka? Me kake taƙama da shi? Yaushe ma aka haifeka Aryan?”
    Uncle Muhammad ya  ƙarasa faɗa ransa a mugun  ɓace dan ba  ƙaramin zafi abin ya masa ba.
    "Har  lokacin  bai  da  alaman  zai  furta  wata  kalma,  sai  ma  lumshe  idanunsa  da  yayi  yanajin  wani"
    mugun raɗaɗi a zuciyarsa
    Hamza ne yayi  ƙwafa yana kallon mahaifinsa uncle muhammad    ya ce
    """Dad ka gani koh? na faɗa maka wallahi ba zai ce muku  ƙala ba, uwarsa ce ta koya masa duk wannan halin gaba  ɗaya, yaro an koya masa raini da rashin girmama na gaba da shi, ba iya mu"
    "yayunsa ba har ku iyayensa, mara tarbiyya kawai"""
    "ya  faɗa  yana  huci  tare  da  kallon  sa  har  lokacin  yana  tsaye  ƙiƙam,  sai  dai  wannan  karan  yayi"
    "folding hannayensa a  ƙirji yana sauraron duk abinda suke cewa, jin Hamza ya ambaci umminsa yasa ya  ɗago idanunsa ya dube sa,"
    """ƙarya yayi ne? Kake kallonsa da waɗannan    idanunnaka maye? Ko  ƙarya ya mata ne?”"
    "Uncle  Ameenu  ya  faɗa  yana  kallonshi  ,  a  yanda  idanunshi  suka  kaɗa  sukayi  ja  a  lokacin  zai tabbatar maka da ranshi ne yake  ɓaci da tafasa a  ƙarƙashin  ƙirjinsa amma duk da haka bashi da"
    niyyar cewa komai.
    cikin jin daɗin zai tanka ganin reaction  ɗinsa    Hamza ya sake faɗin
    """Oh sorry, the mistress ya kamata ince, dan na tabbata tana can tana abinda ta saba, ta gagara"
    "zaman aure!, matar da ke zaman kanta, waya sani ko kaima abinda kake yi kenan, ka biyo footstep"
    "ɗinta shiyasa ka keɓe kanka, ka rabu da family house ka dawo gidanka kai kaɗai      """
    "Kasa  ƙarasawa  yayi  jin  numfashin  shi  na  shirin  rabuwa  da  gangar  jikinsa,  sakamakon  wani  irin fizgosa da yayi ya buga da bango ya bishi ya shaƙe da iya  ƙarfinsa, zuciyarsa har wani racing take yi,  nose  mask  ɗin  da  ya  sa  ya  toshe  fuskarsa  da  shi  ya  zame  ya  dawo  ƙasan  wuyansa,  cikin idanun  Hamza  yake  kalla  kamar  yadda  shima  yake  kallon  nasa  da  idanunsa  da  ya  zaro  waje"
    sakamakon shaƙar da ya masa.
    In a very shaky voice ya buɗe baki yana cigaba da kallon Hamza cike da warning yana  ƙara shaƙ
    esa da iya  ƙarfinsa yace
    "“Don't  you  dare,  stay  within  ur  limit......""  Sai  kuma  ya  kasa  ƙarasawa  ya  cije  lips  ɗinsa  kawai yana haɗiye wani irin takaici da ya taso masa yana kallon idanun hamza da suka soma kaɗawa, Hamza da yaji  ƙamshin lahira, idanunsa duk sun firfito waje gabaki  ɗaya ga wani yawu da yake ji na  taruwa  a  maƙogoronsa  da  ya  kasa  haɗiyewa,  ya  saka  hannayensa  biyu  ya  rirriƙe  hannunsa"
    dake wuyansa yana  ƙoƙarin cirewa amma ya kasa.
    """Aryaan!!"" uncle Ameenu da uncle muhammad da ya ga ana  ƙoƙarin hallaka masa  ɗa suka shiga"
    kiran sunan sa ganin kamar baya cikin hayyacinsa sai sake tightening shaƙar yake yi
    """kashe shi zaka yi? Baka da hankali ne Aryaan?, ka sake shi na ce!”"
    "sam babu alamar ma yana jin su dan yanda yake sake shaƙe Hamza da gini, da  ƙyar suka iya raba shi  da  wuyan  Hamza  da  shima  ke  iya  ƙoƙarinsa  ganin  ya  ƙwaci  kansa  a  hannunsa  amma  ya hanasa  ƙwaƙƙwaron motsi saboda yadda yayi cornering  ɗinsa a jikin bango, zuwa lokacin  ƙoƙ arin shurawa kawai yake idanunsa duk sunyi jajir, sai  ƙoƙarin dambe yake da shi amma yaƙi bashi space da damar yin hakan."
    "wani wawan mari uncle Ameenu ya sauƙe ma Aryan a fuska, yana faɗin"
    "“lallai wuyanka ya isa yanka Aryaan, la shakka Asiya ce uwarka, to bari kaji ni da kyau ka faro"
    "abinda bazaka iya karasashi ba Aryaan, ka jira hukuncin wannan abin da ka aikata, abin kuma da ya kawo mu dama bai wuce sanar maka da cewa mun baka nan da watanni da basu haura 2 ba ka nemo  mata  muyi  maka  aure  ko  kuma  kaga  mata  a  gidannan  a  cikin  dangin  da  kake  gudu,  dan wallahi baka isa kana yawo kana abinda ka ga dama da yaran mutane a garinnan ba yana dawowa kunnenmu kana  ɓata mana suna ba, da darajarmu da mutuncinmu a garinnan, baka isa ba, idan mu  baka  jin  tsoronmu  sannan  baka  ɗauke  mu  a  bakin  komai  ba  ka  raina  mu  baka  ganin mutuncinmu,  to tabbass zaka  ji kira  daga  mai kankat wato mahaifinka  UMAR kuma  na tabbata kasan haduwarku da shi, dan gwara mu da ka raina a kansa, haduwarka da shi ba zai maka daɗi"
    "ba mara mutuncin yaro,  ɗan iska”"
    "Daga  haka  ya kama  hannun Hamza  da uncle  Muhammad ke  bama  ruwa  ko ta  kansu  bai bi ba,"
    idanunsa sunyi jajir suka fice a gidan gabaki  ɗayansu suka barshi nan tsaye yana huci da sauƙe ajiyar numfashi.
    #banidahujja
    #Maimoon 09041426598
     BANI DA HUJJA!! 
    2.
    Iskar da ya cika bakinsa ya furzar cikin matuƙar  ƙunar rai yana cigaba da bin  ƙofar da suka fita
    da kallo.
    Two months? Is this a joke? Mata a wata biyu? wannan ma ai ba mai yiwuwa bane kamar wani
    "shirin film, a ta ina zai nemo matar a wata biyu kacal, infact shi bai ma shirya zama tied to ko wace mace yanzu ba at all, baya buƙatar aure kwata kwata a rayuwarsa a yanzu, juyawa yayi ya wuce sama jikinsa har tsuma yake."
    """Yaya UMAR baka ga abinda  ɗanka ya mana ba, wallahi ko kare bazai ci ba, tabbass yaron nan shaiɗani ne fiye da yanda muka yi zato, bashi da mutunci bashi da tarbiyya sannan bashi da hankali""    Uncle Aminu ya faɗa yana huci, uncle muhammad da shima ranshi har sannan ke  ɓace"
    ya karɓe da faɗin
    """Kai ba ma wannan ba, ka ga dukan da ya ma Hamza?ya shaƙeshi yana neman kashe shi kawai dan ya faɗa masa gaskiya, gashi nan duk wuyansa yayi jajir sai da aka shafa masa man zafi, kuma a gabanmu saboda bai  ɗauke mu a bakin komai ba ya gama raina mu, wallahi tallahi bazan taɓa"
    "barin wannan abin ya wuce a banza ba, kawai dan ya faɗa masa gaskiya, wallahi bai isa ba"""
    uncle Muhammad ya  ƙarasa faɗa yana nuna masa wuyan Hamza da yayi mugun ja abinku da
    fari sai  ƙyallin man zafi yake.
    "Dad dake zaune  ƙafarsa  ɗaya akan  ɗaya, da cup na coffee a hannunsa wanda shansa ya kasance al'adarsa ya ajiye cup  ɗin hannunsa a kan center table tare da gyara zaman newspaper dake kan table  ɗin kafin ya miƙe tsaye, sam bazaka iya karantar a wani yanayi fuskarsa take ba,    baya ya juya musu tare da folding hannunsa duka biyu ta baya kafin a hankali cikin kamilalliyar muryarsa"
    yace
    """kun isar masa da saƙo na?”"
    "Cikin zafin yanda baice komai akan abinda Aryaan yayi ma hamza ba, uncle Muhammad yace"
    """Ameenu ya isar masa """
    "bai sake cewa komai ba yayi wucewar sa ya barsu a tsaye a wajen, zuciyoyinsu cike da takaici, da"
    baƙin cikinsa.
    "Tun daga bakin  ƙofa take kare masa kallo tana wani irin shu'umin murmushi, a hankali ta soma takowa zuwa cikin  ɗakin       tana tafiya a hankali saboda yanda kayan jikinta ya kamata duk da atampa ce a jikinta amma an mata wani irin  ɗinki na rakani gantali, ga wani uban hill da ke  ƙ afarta,ta zubo da kitson da aka mata da gashin kantin da yayi matuƙar mata kyau har gadon bayanta, sai wani  ɗan siririn gyale sharara da ta  ɗaura bisa kai wanda da shi da babu duk uwar"
    "ubansu  ɗaya, black beauty ce kyakkyawar gaske, komai yaji masha Allah da ita."
    "a hankali take tafiya tana murmushi ganin yanda yake kwance akan gadon ko takalman  ƙafafunsa bai cire ba, daga gani baccin ya  ɗaukesa ne ba tare da ya shirya ba dan half  ƙafafunsa na  ƙasa gefen gadon other half na jikinsa    kuma yana kan gadon, gashin kansa ya rufe masa kusan rabin"
    goshinsa saboda yanda ya kwanta a rigingine.
    "A hankali ta zauna a gefen gadon tare da shafa fuskarsa tana murmushi, gashin nasa da take"
    mugun so ta sa hannu ta shafa a hankali kafin    ta cigaba da shafa gashin da ke da matuƙar santsi
    "ba sai an faɗa ba ya ci kuɗi, tana yi tana kallon fuskarsa cike da nishaɗi, a hankali ya soma buɗe"
    "idanunsa da suka yi ja, saboda bacci da  ɓacin ran da bai gama sakinsa ba,    akanta ya sauƙe idanunnasa kafin a hankali ya yunƙura ya miƙe zaune"
    """Hi My love""."
    "Ta faɗa tana kallon sa, da faffaɗan murmushi  ɗauke a fuskarta, lumshe idanunsa yayi ba tare da ya amsa ta ba, yana jin yanda kansa ya masa nauyi, sai kuma a hankali ya miƙa hannu da"
    "niyyar    ɗaukan wayarsa dake gefenta, da sauri ta rigashi  ɗauka ta    miƙa masa tana faɗin"
    """Love gani a kusa, komai kake so ka faɗamin in baka mana miye anfanina? Ga matarka a kusa ai"
    baka bukatar yin komai da kanka” ta faɗa tana kashe masa ido still smiling
    "Wayar ya karɓa ba tare da yace mata komai ba, da wani irin sauri ya dirga daga kan gadon ganin yadda time ya wuce sosai yana bacci gashi ko sallah bai yi ba, itama da sauri ta miƙe tana kallon"
    "sa, ganin wanka zai shiga ya sa ta faɗin"
    """Can i join u?"""
    Har kamar bazai tanka ta ba amma sanin irin baƙin nacinta kamar tsohuwar mayya ya sa    yace
    """Aneela! i am not in the mood, so i will appreciate if you leave me alone""."
    daga haka ya shige bayi tare da rufo  ƙofar
    "Binshi tayi da ido murmushin fuskarta na raguwa,  ƙarar sauƙar ruwa da taji ya sa ta miƙe a hankali dan ta tabbata tunda yace mata ta tafi politely to idan har ya fito ya sameta he won’t welcome that, sai da ta tattare masa duk abinda ya zuzzubar a  ɗakin which are very few, sannan ta gyara masa gadon kafin ta bar  ɗakin tare da ja masa  ƙofa, falon  ƙasa ta koma ta zauna tana"
    danna wayarta.
    "takun sakkowarsa da taji yasa ta dago kanta a hankali tana kallonsa, kamar yadda tayi tsammani"
    "farar shirt ce tass a jikinsa da jeans harda pcap, tayi shiru tana kallonsa lost in thought, Aryaan mai kyau ne, tasan ana cewa tana da kyau sannan tana ji da kyawunta, but Aryaan  ƙarshe ne ga kyau ga iya  ɗaukan wanka, bata San ya zata kwatanta shi ba but he’s just sooo different da"
    sauran.
    "har ya gama sakkowa bata lura ba, bai bi ta kanta ba    ya nufi  ƙofar fita a palourn,  ƙamshinsa da taji    na yin nesa ya sata saurin buɗe idanunta sa ta lumshe tana faman murmushi, rufe  ƙ ofarsa kawai ta gani, da sauri ta miƙe ta bi bayanshi, har ya buɗe mota tayi saurin zuwa gabansa"
    "ta tsaya, ta marairece cike da    shagwaɓa tace"
    """Love"" ya  ɗage girarsa alamun  “what?” Ganin sai kallonsa take zata  ɓata masa lokaci yasa"
    "hannu ya mayar da ita gefe, zata yi magana ya rigata"
    """Aneela!!"""
    "Yanda yayi maganan ya sa ta fasa tata maganar, ta dinga kallonsa ta tabbata wani ne ya taɓosa a can wani wajen daban cause thats not how he behaves with her, tana kallonsa har ya shiga mota ya tayar tare da barin gidan, ta bubbuga  ƙafanta a  ƙasa kafin ta juya a hankali ta shiga tata"
    motar itama ta fice a gidan.
    "A bakin restaurant  ɗin ya tsaya, ba tare da ya shiga ba ya  ɗau wayansa, bugu  ɗaya ya  ɗaga, a ta"
    ƙaice yace
    """Jameel kawo min ina waje"""
    "cikin mintuna 3 Jameel ya fito da uniform a jikinsa, da leda a hannunsa, window ya sauƙe sannan"
    ya amshi ledan ya ja motarsa ya bar wajen.
    "A  ƙofar gidan ya tsaya, ba tare da ya shigar da motar ba, ya  ƙarasa ya shiga gidan, buɗe  ɗakin yayi bayan ya saka black shades a idanunsa, a zaune ya sameta tana wasa da roban takeaway  ɗin"
    "da yayi mata da safe, ta  ɓaɓɓarka ledan gabaɗaya."
    "Ba tare da yayi magana ba ya tura mata ledan hannunshi gabanta,"
    "bata ko kalli ledan ba ta ci gaba da wasa da yatsunta, har ya kai  ƙofa zai fice sai kuma ya juyo yana kallonta,"
    """SALWA!!"""
    Ya kira sunanta strictly yana folding hannayensa a  ƙirji
    "Idanunta da zuwa yanzu sun koɗe da kuka ta  ɗago tana kallonsa da su, wani irin very Innocent face take dashi, wanda zaka yi tunanin ko yatsa aka saka mata bazata taɓa cizawa ba, wanda ke  ɗ auke da round face da big eye balls  ɗinta masu masifar  ɗaukar hankali, tana da hasken fata tare da very cute  ƙaramin baki    ga dimples guda biyu wanda ko da magana take ko kuka ko dariya lotsawa suke a hankali."
    "kallon second 10 tayi masa ta mayarda kanta  ƙasa tana wasa da  ƴan siraran yatsunta masu kyau, wasu hawayen da take ta riƙewa tuntuni kar su zubo suna biyowa shar agefen fuskarta."
    "daurewa yayi kamar baya so, ya furta"
    "“Eat ur food"""
    "daga haka ya juya, har ya  ɗaura hannu akan handle  ɗin sai kuma ya tsaya cak sakamakon tsinkayo sassanyar    muryarta da    yayi, Cikin rawar murya na kukan baƙinciki    da ke cinta ta"
    soma magana
    """Yaya Please ka mayar da ni wajen Ammina, ka min rai, zan mutu anan, ni bana son wajennan,"
    "tsoro nake ji wallahi yaya kullum idan baka nan, ni kam ka kaini wajen daddyna    "" tana kaiwa"
    nan ta fashe da shagwabaɓɓen kuka that irritates him.
    "Sai da ya jira ta kai aya kafin ya buɗe  ƙofar ya fice abinsa, Wani irin kuka ta sake fashewa da shi tana kallon  ƙofa, wannan wace irin rayuwa ce, idan kasheta zai yi gwara mata ya kashe ta ta huta, idan har lissafinta dai-dai ne to aƙalla zata yi sati  ɗaya da kwana  ɗaya kenan    a wannan gidan"
    "da ko falo bata  ƙaunar fita, eight days fa kenan innalillahi wa inna ilahi raji’un."
    Ganin idanunta har wani zafi suke mata da wani irin hazo hazo ya sata lumshe su a hankali tana
    jinginar da kanta a jikin bangon  ɗakin. A hankali take furta “daddy…” cike da shagwaɓa wanda nature  ɗinta ne magana a haka.
    "Sai da ya tsaya yayi isha’i kafin ya wuce gidan, a ranshi yana jin kamar ya fasa zuwa ya wuce"
    gidansa.
    "Sauƙe glass  ɗin motarsa yayi yana kallon soldier  ɗin da ke riƙe da bindiga fuskarsa a matuƙar ha ɗe,  ɗaya daga cikin abinda ya sa ya tsani gidannan kenan, ba tare da ya kula maganar da yake masa ba ko na sauran soldiers  ɗin da ke gadin wajen ya zuge glass  ɗin ganin sun basa hanya ya"
    wuce ciki
    "A tangamemen gate  ɗin estate  ɗin    yayi horn,  ɗaya daga cikin sojojin da ke gadin    gate  ɗin ya leƙo da kansa,  ƙaramin tsaki ya ja  ƙasa  ƙasa yana kallonsa daga cikin motar, ganin motar  Aryaan  ɗin ya sa sojan buɗe masa  ƙofa da sauri, babban family house ne ko ince estate na gasken gaske wanda yaji komai na rayuwa, ajikin makeken plate name  ɗin da ke gefensa an rubuta    ‘THE TURAKI'S’.    kai tsaye cikin gidan da yake nan tarrr da haske kamar ba dare ba ya nufa da motarsa, sai da yayi tafiya ta atleast 15 minutes akan shinfiɗaɗɗiyar titi dake ko ta ina a cikin gidan yana wuce gine gine wanda dukansu iri  ɗaya ne, sai dai banbancin girma da decorations da wasu suka fi wasu,    sannan ko wani gidan yana da    gate  ɗin da zai sada ka da shi, da security mai gadin wannan gate  ɗin, a ko wani gate da sunan mai shi a jikinsa wanda duka"
    ƙarshensa ke  ƙarewa da TURAKI.
    "Tun da ya tunkaro gate  ɗin gidan mahaifinsa yake jan tsaki  ƙasa  ƙasa saboda sojoji da ke nan burjik suna gadin gate  ɗin kamar zasu hana waɗanda ke ciki mutuwa, tun kafin ya  ƙaraso ya fara horn har ya iso gaban gate  ɗin wanda da alama ginin wannan gidan yafi na kowa a cikin Family"
    "house  ɗin gabaki  ɗaya, duk kuwa da yawan gidajen dake cikin estate  ɗin."
    "Buɗe masa gate  ɗin sukayi ba tare da sun kula shi ba kamar yadda shima bai kula kowa a cikinsu ba, gate  ɗin mai kyau sai dai    bai kai na Main entrance na gidan girma ba, a gaban wannan part an rubuta    CDS. UMAR WAZEER TURAKI, a babban parking space  ɗin da zai iya haɗiye a  ƙalla motoci 10 ko ma fiye    yayi parking, sannan ya fito daga motar yana sake haɗe fuskarsa, a hankali yake tafiya kamar baya son yayi ya nufi main entrance na wani babban part wanda yafi ko wani part girma a gidan, murɗa  ƙofan falon yayi a hankali ya shiga bayan ya zare glasses  ɗin idanunsa,"
    "ya  ƙare ma babban falon da ya gaji da tsaruwa kallo,  ƙamshi ne kawai ke tashi a falon mai sa"
    "nutsuwa ga sanyin ac da ya  ƙarama wajen wani pleasant daɗi, ba tare da ya zauna ba kawai ya wuce ya fara hawa stairs don ya tabbata kowa na gidan na  ɗakinsa, sanin yanayin mai gidan na rashin son hayaniya sam yasa komai a nutse a keyi a gidan. har yakai sama    sannan ya dakata yana kallon  ɗakunan da ke jere a saman guda uku ta gefen daman sa bai bi ta kansu ba ya murɗa wata  ƙofa dake gefen hagunsa, wata haɗaddiyar falo ne ta bayyane mai matukar kyau wanda ke ɗauke da  ɗakuna biyu kacal a cikinta,    sai wani  ƙofa da zai sada ka da falo na biyu, sosai    ya lumshe idanunsa jin kamshin da ke tashi a falon kafin ya  ƙarasa ciki, nan ma babu kowa,  ɗan jim"
    yayi kafin    ya nufi  ɗayan falon yana addu'ar samun Dad anan.
    "Tura  ƙofan yayi a hankali da sallama  ɗauke a bakinsa,    a zaune ya samesa a kan  ɗaya daga cikin manyan kujeru na alfarma, a falon da ya ma gaji da tsaruwa, dan ya ma fi falon farko kyau sai dai bai kaisa girma ba,  ƙafansa  ɗaya akan  ɗaya ga cup akan center table  ɗin gabansa, da wata  ƴar"
    karamar littafi da yake rubutu a ciki that looks like jotter or a diary book.
    "ɗago idanunsa dake cikin fararen medicated glasses yayi ya zuba ma  ɗan nasa idanu, kafin ya kawar da kai daga kallonsa ya cigaba da abinda yake yi ba tare da ya amsa sallaman ba, a hankali Aryaan ya  ƙaraso gabansa, ya zauna a  ƙasa ya sunkuyar da kansa yana kallon haɗaɗɗen carpet  ɗ"
    "in dake malale a  ƙasa, cikin sanyin murya yace"
    """Ina wuni DAD"""
    "bai amsa ba sannan bashi da niyyar amsawa sai ma miƙewa da yayi, yayi folding hannuwansa a"
    baya ya soma tafiya towards  ɗakin dake cikin falon.
    Cikin sauri muryarsa har rawa take Aryaan yace
    """Dad please!"""
    ɗan dakatawa yayi kafin cikin dakakkiyar voice  ɗinsa da ke cike da command yace
    """ARYAAN UMAR TURAKI! Leave immediately, sannan saƙon da baffaninka suka isar maka, make sure ka cika umarni, kwanaki 59 suka rage cikin sittin  ɗin da na  ɗibar maka, bring a wife before then if not    you will leave me with no choice bayan na  ɗaura maka aure da koma wacece, in"
    "tura maka gidanka, since ka fi  ƙarfin zama a cikin  ƴan uwanka""."
    daga haka yayi shigewarsa  ɗaki tare da rufo  ƙofan.
    "Wani irin zuciya ke cinsa yana dannewa, why! Me yasa shi da mahaifinsa are not in good terms at"
    "all, ya zo ne ya gana da shi akan aurennan but sam yaƙi sauraransa, ya ake so yayi? Ta ina zai nemo mata a wata 2 kamar wani magnet? Aneela ce ta faɗo ransa cikin sauri ya shiga girgiza kai"
    """Nooo banda Aneela""    sai kuma ya miƙe dan yasan bayi da choice bayan Aneela  ɗin."
    #banidahujja
    #Maimoon
    09041426598
    https://whatsapp.com/channel/0029VbB1qGBFMqrVuPRZ5f2Q
      BANI DA HUJJAH!!  
    By Maimoon
    3.
    "Zuciyarsa a dagule, fuskarsa a haɗe ya fito daga sashen mahaifinnasa, yana kokarin ficewa daga  ɓ"
    "angaren gabaɗaya suka kusa cin karo da mummy ya matsa baya a hankali ya bata hanya ganin shiga zata yi wajen Daddy, a taƙaice ya gaishe ta shima ciki ciki"
    "“ina wuni” ko kallonsa bata yi ba ta shige ciki abinta ya bita da side eye kafin ya buɗe  ƙofar shima ya fice a gidan, ba tare da kallen kallen komai ba ya buɗe motarsa ya shiga ciki ya tayar aka buɗe masa gate  ɗin Cds. Umar wazeer turaki ya fice yana driving gently, a gaban gate  ɗin barr Ameena wazeer turaki yayi horn ba tareda ya ko kalli opposite house  ɗin da shi kuma aka rubutu DR Ameenu Wazeer turaki ba, aka buɗe masa gate  ɗin ya shiga yayi parking yana kallon motar AMEEN dake parking space  ɗin which means yana gida as expected. Bai samu kowa a palourn ba sai sanyin ac da  ƙamshin turaren wuta mai daɗi nan ma, stairs ya nufa kanshi tsaye yana jujjuya"
    key  ɗin hannunsa.
    "“Aryaan?” Dakatawa yayi tare da juyowa yana kallon Mami da fitowarta kenan daga kitchen, ta"
    ɗan buɗa ido tana kallonsa tace
    “ashe dai kai  ɗinne hamshaƙi” ɗan murmushi yayi kaɗan ya fasa haurawa ya dawo palourn ya
    zauna a kujera yana sake  ƙirƙiro murmushi
    “ina wuni Mami”
    “Da ban wuni ba zaga ganni ne aryaan?” Shiru yayi kawai dan ya san dama dole sai tayi ranting
    "in dai ta gansa, rabonsa da gidan ya kwana biyu tayi mita har ta gaji."
    "“Yau kuma Allah yayi ka tuna mu kenan Aryaan, yanzu abinda kake yi ya kyautu kenan? Yaro  ɗ"
    "an gata amma ka mayar da kanka kamar maraya?” Ta faɗa tana zagayowa ta zauna a kujerar da ke facing  ɗinshi tana ta kallonsa keenly, Nan ma bai ce mata komai ba sai murmushi kawai da yayi,"
    ta sauƙe ajiyar zuciya    a hankali tace
    "“To Allah ya kyauta, ya kake toh? How have u been?” Sai a sannan ya amsa da"
    “Alhamdulillah Mami”
    "“Are u sure?” Gyaɗa mata kai yayi, tace"
    "“Toh Allah yayi albarka, ya tsare gabanku da bayanku, ya baku abinda kuke nema duniya wa"
    "lahira, a cigaba da hakuri a kuma cigaba da yayyafawa zuciya ruwan sanyi, zama lafiya da kowa ya"
    "fi zama  ɗan sarki, komai lokaci ne da shi haka zaka ga watarana kamar ba’a yi ba”"
    "“Amin Mami” ya amsa yana jinginar da kansa da kujera, miƙewa tayi tana kallonsa tace"
    “AMEEN  ɗin ai yana sama kaje bari nima in duba girki ya kusa gamuwa ma    su lailerh zasu
    "kawo muku” gyaɗa mata kai kawai yayi bashi da niyyar tashi, ta miƙe ta wuce kitchen, 10 minutes later ta kuma fitowa, da mamaki take kallonsa ganin har sannan yana zaune a wajen  yana danna wayarsa, hakan yasa bata kulashi ba ta wuce sama dan kiran Ameen  ɗin da kanta, tare suka sauƙo da wani matashin saurayi kyakkyawa wanda zasu yi sa’o’i da Aryaan sai dai ya fi Aryaan hasken fata da glasses a idanunsa dressed casual, ya kalli Ammi bayan ya sauƙo cikin"
    palourn yace
    “Ammi where is he?” Ammi ta  ƙaraso cikin palourn tana kallonsa tace
    “Ji iskanci! Anan fa na barsa shine ya kama hanya ya wuce bai ce min zai wuce ba? Kuma fa har
    abinci nace ya jira amma shine ya wuce ya tafi abinsa koh? Kirawo min shi kace nace ya dawo
    yanzu ya zo yaci abinci”. Ameen ya  ɗan sauƙe ajiyar zuciya yana zama a kujera yace
    “Ki  ƙyaleshi kawai tunda ya tafi ba juyowa zaiyi ba kin sani” zama tayi itama a kusa da shi tace
    “Al’ameen me ke damun  ɗan uwanka ne?” Ya buɗa mata hannu alamun bai sani ba shima
    "yana murmushi,"
    "“Ya zaka ce min baka sani ba, bayan ure closer to him than anyone”"
    "“Allah Ammi ban sani ba, but bari na watsa ruwa inje gida in same sa inji if there’s anything i"
    should know” gyaɗa masa kai tayi tace
    “Idan ya faɗa maka pls ka zo ka faɗa min”
    “Okay Mami” ya faɗa yana miƙewa ya wuce sama murmushi kwance a fuskarsa
    “Lailerh ta kawo maka abinci yanzu?”
    “Ah ah idan na dawo zanci”
    “Toh” ta faɗa tana kallonsa har ya haura kafin ta wuce kitchen dan duba abinda su lailerh da
    siyama ke yi.
    Yana driving yayi dialing lambarsa yana ajiye wayar a gefensa bayan yayi connecting da speaker  ɗ
    "in motar, sai da kiran ya kusa yankewa kafin ya  ɗaga, Al’ameen yayi gyaran murya yace"
    “Malam kana ina ne?”
    “Why?”
    “Ban sani ba! Kana gida ko baka gida?”
    “Bana gida!”
    “Kana ina?”
    “Doesnt concern u!”  Murmushi Ameen yayi kawai ya katse kiran yana nufan gidan nashi
    bayan ya kalli agogo  ƙarfe 10 saura.
    "Buɗe masa gate mai gadi yayi bayan yayi horn once, ya shiga yayi parking a kusa da motar Aryaan dake space kafin ya fito ya nufi cikin gidan,    ba tare da knocking ba ya tura  ƙofar palourn ya shiga ciki yana kallon ko ina, ganin baya ciki ya gyara glasses  ɗin idanunsa ya nufi hanyar sama da takalmansa, motsi da yaji a kitchen ya sa ya dawo da baya ya nufi kitchen  ɗin, a bakin  ƙofa ya tsaya ya harɗe hannu a  ƙirji yana kallonsa, yana tsaye a jikin counter da singlet baƙa a jikinsa against fair skin  ɗinsa, yayi pairing  ɗinshi da three quarter iya guiwarsa dat looks loose, Al’ ameen ya kalli plate  ɗin scrambled egg dake plate da toasted bread guda biyu a gefe, black tea"
    da yake haɗa ma kanshi a lokacin ya kalla kafin yace
    "“Yaushe ka koyi girki bawan Allah” ko kallonsa baiyi ba, barin jikin  ƙofan yayi ya nufe shi yana"
    faɗin
    "“Wulaƙanci ne bana so, sai in juya in koma in da na fito, da ina da zuciya ma wallahi ba zaka ganni a nan ba, ko da yake Mami ce tace na zo ka je kana acting weird a gida kuma before in sauƙ"
    "o ka wani wuce ka tafi, idan ka san baka so in zo waya ce ka zo gidanmu nemana?”"
    “Says who kai naje nema?” Ameen ya hararesa yace
    “To me kaje yi?” Sai da ya ajiye cup  ɗin a gefen tray  ɗin kafin yace
    “Mami naje gaisarwa” Al’ameen yayi wani dariya da ya sa Aryaan kallonsa yace
    "“Ko ba gaishe da Mami ba, u that i know  ɗin koh? Kai dai faɗi me ya kaika kawai, amma"
    "kafinnan haɗa black tea  ɗin da ni banci abinci ba na fito” ko kulasa baiyi ba ya  ɗauki tray  ɗin ya fita a kitchen  ɗin, Ameen ya  ƙarasa ya  ɗauki well cleaned cup da spoon ya biyo bayansa yana fa"
    ɗin
    "“Wannan  ɗin zai ishemu ne?” Bai kulasa ba ya ajiye tray  ɗin akan dinning, tun kafin ya zauna"
    "Ameen ya ja kujera ya zauna tare da  ɗaukar toasted bread guda  ɗaya ya bar masa  ɗaya, ya saka spoon ya  ɗibi scrambled egg  ɗin ya kai baki, zama kawai shima yayi ya  ɗauki  ɗayan bread  ɗin ya soma ci, Al’ameen ya  ɗauki cup  ɗin black tea  ɗin ya zuba a cup  ɗinsa ya raba musu daidai da daidai, kafin ya tura masa nasa gabansa, komai bai ce masa ba ya ja ya fara sha yana  ɗan danna wayarsa fuskarsa a haɗe, sai da suka conye duka kafin ya miƙe ya koma cikin palour ya zauna yana danna wayarsa, kwashe kayan Al’ameen yayi ya kai kitchen ya ajiye a sink ya buɗe fridge ya  ɗauko bottled water guda biyu ya fito da su a hannunsa, jefa masa  ɗaya yayi ya cafe shi kuma ya  ƙaraso yana shan  ɗaya, ya zauna a wani kujeran daban ba wanda Aryaan ke kai ba yana cigaba da shan ruwan, sai da ya gama sha ya ajiye sauran a center table kafin ya kalli Aryaan dake"
    "buɗe ruwan hannunsa a lokacin zai sha, yace"
    “What happened bro? Tell me mana why are u acting all up haka?” Aryaan ya rufe ruwan ya
    "ajiye tare da  ɗan dafe kansa, hakan yasa Ameen putting serious face ya miƙe ya dawo kujeran da"
    yake zaune yace
    “Me ya faru  ɗan uwa?”Ajiyar zuciya ya sauƙe a hankali ya  ɗago ya kalli Ameen da idanunsa da
    suka  ɗan yi ja yace
    “I’m tired Ameen! Please tell me miye nayi ma Daddy?”
    “What happened?” Ameen ya tambaya sounding concerned! Duk abinda ya faru ya kwashe ya
    "faɗa masa from zuwan su uncle Ameenu zuwa zuwanshi gidan, Al’ameen ya sauƙe ajiyar zuciya yana kallonsa har ya kai aya kafin ya dafa kafaɗarsa yace"
    “Calm down bro! Yanzu iya wannan abinne ya saka ka  ɗaga hankalinka haka? Har ya nuna a face
    ɗinka cewa ure tensed? Haba aryaan” wani mugun kallo Aryaan ya masa yana  ƙwace kafaɗarsa yace
    "“Bangane iya wannan abin ba, shey u no comprehend abinda nace maka? Cewa fa nayi Dad and"
    "his brothers so suke in kawo mata nan da two months, how is this possible Ameen? Meyasa sai ni kaɗai suka gani? What happen to u and hamza and the others? Kai da hamza da kuka girmeni ba’ a ce ku kawo mata in so so so time ba sai ni?”  Al’ameen ya gumtse dariyarsa yana kallonsa"
    yace
    "“Wato yanzu ka yarda mun girmeka da yake zancen is not in ur favour, what happened to"
    "watanni ba girma bane? Kuma da kake zancen mu ba’a ce mu kawo mata ba, kai ai ka san dalilin da ya sa suka ce ka kawo mata, baka jin magana Aryaan, i’ll be so happy wallahi idan ma kayi auren ko wasu abubuwanka zasu saitu” Ganin yadda ya haɗe rai ya sa Ameen ya  ɗan bubbuga"
    kafaɗarsa yace
    "“Sorry bro, ka kwantar da hankalinka za fa ka samu mata nan da wata 2” jingina kansa yayi a"
    jikin kujera yana kallonsa yace
    “I was thinking about Aneela…” tun kafin ya kai  ƙarshe Al’ameen ya haɗe rai tare da
    hararansa yace
    "“Over my dead body ne zaka auri yarinyar nan, kai tsakaninka da Allah idan aka barka sai ka auri"
    "yarinyarnan? Sai kace ma yaranka wace irin uwa ka zaɓa musu kenan?” Kallonsa kawai Aryaan yake baice komai ba, Al’ameen ya  ɗauko wayarsa dake ringing ganin Mami yace"
    "“Mami ce, let me come and get going home”"
    "“Spend the night here mana” ya faɗa yana kallonsa,  ɗan shiru yayi sai kuma ya  ɗaga wayan"
    "yana sauraren Mami tare da kallon Aryaan da ya lumshe idanunsa, can yace"
    "“Eh Mami, ill spend the night here gobe zamu shigo tare da shi” shiru yayi sai kuma ya amsa da"
    “Amin” daga haka ya katse wayar yana kallonsa yace
    “Duk ta damu ta  ɗauka wani babban abu ke damunka”
    “Okay yanzu  ƙarami ne ke damuna kenan”
    "“Eh mana daɗi ne yayi maka yawa, ni ace in fito da matar a gani mana da tuni na kai an wuce"
    wajen”
    “To yanzu ma idan ka kai ai ba zasu  ƙi yi maka ba” ya faɗa yana miƙewa
    "“Ah ah barsu dai su tambayeni first ni ai ina da wacce nake so, jira kawai nake a tambayeni in"
    "gabatar da ita gaban kowa da kowa, ba irinka bane ni da kake tunanin auren mace irin zaleena"
    sunanta ko aleena….”
    "“Aneeela..” suka tsinkawo muryarta daga bakin  ƙofa, duk suka  ɗaga kai suna kallonta, idanunta cike taf da hawaye take kallonsu hannunta rike da jakarta sai wayarta a  ɗaya hannun tana sanye da    tshirt mai maɓallai fara da blue jeans, attachment  ɗinta ya xubo har gadon"
    "bayanta, sai siririn  ɗankwali da ta  ɗaura a kai as usual."
    "Kallo  ɗaya Al’ameen ya mata ya haɗe rai tare da miƙewa da nufin haurawa sama yana mamakin irin rashin kamun kanta, yo rashin kamun kai mana idan ba haka mai zai kawo mace da ta san darajar kanta gidan mijin da ba nata ba da wannan daren? Halinta disgust him, Ko da yake its not entirely her fault har da na mai gayya mai aikin dan shi ya bata daman haka shi yayi welcoming  ɗ inta a gidansa anytime idan ba haka ba ai bazata zo ba, wani takaici ya takure shi a wuya ya ja tsaki tare da  ɗaukan wayarsa zai wuce sama, ajiye jakar tayi ta  ƙaraso palourn tare da shan"
    gaban Ameen tana kallon cikin idanunsa tace
    “Al’ameen miye na taɓa yi maka a rayuwarnan da ka tsane ni? Baka  ƙaunata baka  ƙaunar gani
    "na tare da farincikin rayuwata, mai nayi maka da zafi har haka da kake ikirarin over your dead"
    body ya aureni”  wani kallo yake mata irin na malama na miki kama da wanda kika zo wajensa
    "ne, kamar bazai kulata ba sai kuma yace"
    "“I’m glad uve been eavesdropping tun  ɗazu kuma kinji duk abinda nace, aryaan bazai taɓa"
    "auren mace irinki ba God forbid”  juyawa tayi ta kalli Aryaan dake kallonsu kansa a kishingiɗe da kujera, kafin ta juyo ta bawa Ameen amsa ya raɓata ya wuce sama abinsa, ta bishi da kallon tsana"
    kafin ta juyo ta dawo kujerar da Aryaan ke zaune tace
    "“Love ka ji abinda yake faɗa koh? Pls dont listen to him, ure my life ka sani”  miƙewa yayi shima zai wuce sama tayi saurin kamo hannunsa ya juyo yana kallonta, ganin yanda take kallonsa idonta cike da hawaye ya sa ya janyo ta jikinsa yana kallon face  ɗinta ya sa finger  ɗinshi yana"
    "share mata hawayen dake kumatunta,  ƙasa  ƙasa yace"
    "“Go home zamuyi magana later okay?” Ta gyaɗa masa kai tana kallonsa, ya sake ta ya ja da"
    "baya yana kallonta da guntun murmushi akan fuskarsa,  ƙarasawa tayi ta  ɗauki jakarta har ta buɗ e  ƙofa ta sake juyowa ta kalleshi, kashe mata ido  ɗaya yayi, tayi murmushi tana share hawayenta ta fice tare da jan  ƙofar, yana juyawa ya ga Al’ameen a tsaye a jikin stairs ya harɗe hannu yana kallonsa, suna haɗa ido ya haɗe rai, kallonsa kawai Ameen keyi har ya zo zai wuce kafin ya ja tsaki"
    da ya tabbatar yaji ransa a  ɓace ya furta
    "“kayi asara” ko kulashi bai yi murmushi kwance a fuskarsa ya wuce sama, juyawa yayi ya bi"
    bayansa saman ransa a mugun  ɓace.
    Not edited
    #Banidahujjah
    #Maimoon 09041426598
    https://whatsapp.com/channel/0029VbB1qGBFMqrVuPRZ5f2Q
      BANI DA HUJJAH!!  
    4.
    Al’ameen na fitowa daga bayi da pyjamas  ɗin Aryaan a jikinsa ya zauna a gefen bed yana kallon
    "Aryaan dake zaune a kan bed yayi resting bayanshi da headboard, macbook a buɗe akan cinyansa,"
    hankalinsa duka yana kan abinda yake yi a ciki
    “Wai haryanzu baka gama project  ɗinnan ba?”
    "“Uhm” ya amsa a taƙaice, jin Al’ameen yayi shiru ya  ɗago ya kalleshi yace  “ko zaka  ƙarasa"
    min?”
    “Hmm” kawai Ameen yace yana miƙewa ya dawo bedside ya leƙa screen  ɗin yana kallo yace
    “Still on commercial complex?” Aryaan ya bashi side eye ba tare da ya amsa ba yana zooming
    "da adjusting kyakkyawan zane dake screen  ɗin, Ameen yayi murmushi yana kallon abinda Aryaan ɗin ke nuna masa a screen  ɗin, 3D model ne na building  ɗin da yake aikinsa yanzu ya dinga rotating yana nuna ma Ameen  ɗin ba tare da yace komai ba, sai da ya gama nuna masa kafin ba"
    tare da ya kalleshi ba yace
    “Kasan mutuminnan canja facade  ɗin ya sake yi?” Ameen yayi guntun murmushi yana
    kallonshi yace
    "“Sau uku fa kenan yana canzawa, wannan client  ɗin naka sai kai”"
    "“Fourth…” ya faɗa calmly yana jan wani layi across screen  ɗin, kafin ya canza zuwa wani tab  ɗ"
    "in daban wanda ke  ɗauke da finishing materials, shi dai Ameen jingina bayansa kawai yayi yana"
    kallon aikin cike da burgewa.
    "“Previous design  ɗin kwata kwata baiyi balancing da structural load  ɗin ba, idan na biye masa"
    "na bi irin abinda yake so blindly, kwata kwata ginin bazai yi making sense ba”  Ameen ya gyaɗa kai yana miƙewa feeling impressed but not suprised dan ba tun yau ba yasan Aryaan is perfect at"
    what he does.
    "“Kaga barmu a bar da cases,    mun bar muku buildings  ɗin”"
    “Gobe zaka rakani somewhere” Aryaan ya faɗa yana  ɗago kanshi
    “Where?”
    “Zaka gani goben”
    “Hope its after mun je gida?” Ganin ya maida kanshi zai cigaba da abinda yake Ameen yace
    “serious Mami cewa tayi mu zo tare gobe”
    “Allah ya kaimu” ya faɗa a taƙaice
    "Haurawa gadon Ameen yayi ya kwanta dan bacci sosai yake ji, amma yana kwanciya maganar"
    "Aneela ya faɗo masa a rai dan  ɗazu suna haurowa toilet Aryaan ya shige da ya fito kuma still shima ya shiga so bai ma yi masa maganan ba, juyawa yayi ya fuskance shi yace"
    “Aryaan!” Ya juyo ya kalleshi
    “Are u really going to do it?” Fuskarsa da yaga ya nuna alamun bai gane inda maganar ta dosa
    ba yasa yace
    “Da gaske kana so ka auri yarinyar can?” Ɗauke kansa yayi ya cigaba da abinda yake yi
    muryarsa  ƙasa  ƙasa yace
    “As if i have a choice!”
    "“Kar ka raina ma kanka hankali mana, baka da choice as how? Who force u yace dole sai ka"
    "aureta, ka kawo wata daban    mana, ko yaushe ka fara sonta bani da labari”"
    Aryaan ya kalleshi yayi shiru kamar zai yi magana sai kuma ya fasa ya miƙe ya  ɗauki macbook  ɗ
    "insa    ya nufi  ƙofa, Ameen ya gyaɗa kai yana kallonsa yace"
    "“Allah ya baka sa’a, and dont even bother explaining later” kashe masa wutan  ɗakin Aryaan"
    yayi ya koma palour ya ajiye laptop  ɗin ya sauƙa ya haɗa ma kansa black tea ya dawo ya baje ya cigaba da aikinsa peacefully cike da natsuwa dan kwata kwata ko zancen aurennan ba so yake yi a
    masa ba at all.
    Washegari suna dawowa daga fajr Ameen ya kunna tv din palourn tare da kwanciya akan kujera
    "yana rage volumn, shima aryaan da kamar zai wuce bedroom sai kuma ya fasa ya kwabe jallabiya da ya daura kan wandon pj dake jikinsa dan shi dama bai iya bacci da riga ba, pillow ya janyo ya sauke kan lallausan carpet ya kwanta yana kallon wrestling da Ameen ya kunna a haka bacci ya sake yin awun gaba da su, sai wajen tara kafin Al’ameen Yayi miƙa daga saman kujeran    da yake kwance    ya tashi zaune yana sake yin miƙa tare da kokarin miƙewa tsaye sanye da jallabiya da yaje sallah da ita da asuba, komawa yayi ya zauna yana kallon Aryaan da ke kwance akan carpet da dogon wandon pj a jikinsa ba riga yayi matashin kai da pillow  ɗin kujera da ya sauƙe  ƙasa, ya sa  ƙafa ya  ɗan shure  ƙafarsa da ke kusa da tasa,    hakan ya sa ya buɗe idanunsa a hankali ya"
    kalli Ameen da su.    wayarsa ya juya masa yana nuna masa agogo yace
    "“Tashi ka shirya muje gida” ya miƙe zaune tare da saka fuskarsa cikin palm  ɗinsa na kamar 2 minutes kafin ya miƙe tsaye ya  ɗaga pillow  ɗin ya mayar mazauninta ya juya ya wuce  ɗaki,"
    Ameen ya bishi da ido kafin shima ya mike ya    bi bayansa.
    "Aryaan ne ke tuƙi Ameen na zaune a gefe yana danna wayarsa, ganin ba hanyar gida suka nufa ba"
    ya  ɗaga kai ya kalleshi yace
    “Malam ya naga ba hanyar gida muka nufa ba”
    “Yes zamu fara zuwa inda zaka rakani ne ba zamu daɗe ba sai mu wuce gidan” shiru yayi yana
    "kallonsa bai ce masa komai ba dan ba haka suka yi da shi ba amma dai ya share bai ce komai ba,"
    "har suka iso kofar gidan, kallon gidan yayi ya juya ya kalleshi yace"
    “Ba kace ka sayar da gidannan ba?”
    “Eh na sayar”
    "“So..?” Bai kulashi ba ya sauka a motar bayan yayi parking da kyau a waje, Ameen ya bishi da"
    "kallo across motar har yaga ya buɗe gate  ɗin ya shige ciki kafin ya sauƙo ya bishi a baya.    A tsaye ya ganshi a compound  ɗin yana jiransa, yana hangosa ya shigo ya cigaba da tafiya towards  ƙofar palourn, Ameen yabi bayansa still wondering dama ashe bai sayar da gidan ba, ya sa makulli yana"
    buɗe  ƙofar palourn Ameen da ya iso wajen yana kallonsa yace
    “What are we doing here” yana tura  ƙofar palourn yace
    “Sayar da kai na zo yi” Ameen yayi murmushi yana binshi ciki
    “Wane kai”
    "“To sa wasa”  ya  ƙarasa yana kallon labulayen palourn that are hanged ya  ƙarasa kujera ya zauna yana kallon Ameen da ke  ƙare ma madaidaicin palourn kallo, buɗe  ƙofar kitchen  ɗin da ke cikin palourn akayi, kwata kwata bata lura da Ameen ba, dan straight kujerar da yake yawan zama idan ya zo ta kalla jin motsi a palourn, suka kuwa haɗa ido da shi, da gudu ta wuce  ɗakinta hannunta riƙe da ruwan gora kanta ba  ɗankwali, Ameen da ya daskare a inda yake tsaye ya kalli hanyar da ta bi da kallo kafin ya mayarda kallonsa kan Aryaan dan he seriously couldnt believe his eyes, Aryaan yayi kamar bai san shi yake kallo ba sai ma wayarsa da ya fara dannawa, nufar  ɗakin da ta rufe Ameen yayi dan bai gama yarda da abinda ya gani ba ko dai idonsa ke masa gizo? To ko Aneela ce a gidannan  ɗin idanunsa ke nuna masa wata daban da ya tabbata babu dai abinda zai kawota nan  ɗin, Aryaan ya bishi da kallo ta  ƙasan glasses  ɗinsa har ya tura  ƙofar  ɗakin da ta shiga, a tsaye ya ganta a tsakiyar  ɗakin riƙe da ruwan tana kallon  ƙofa kamar mai expecting shigowar wani, suna haɗa ido da Ameen ta wani zaro ido tayi cilli da goran ruwan ta nufosa a guje ta shige jikinsa ta rungumesa ta fashe da sabon kuka, gyaɗa kai kawai Ameen yake still in shock"
    yace
    "“SALWA!?” Ajiyar zuciyar kuka kawai take sauƙewa taƙi ta amsa, ya  ɗagota daga jikinsa yana"
    kallonta yace
    “Me kike yi anan? What happened to morocco? Birthday  ɗin kenan?” Shagwaɓe fuska ta kuma
    yi tana kallonsa a shagwaɓe tace
    "“I never went” tana faɗa wasu hawaye na rige rige a kumatunta, ya gyaɗa kai kawai yana lissafa"
    "irin tsantsar rashin gudun zuciya da gudun magana irin na Aryaan, shi yanzu idan ba tsantsan nema wa kai fitina ba ko da kudi aka ce ya shiga harkar yar uncle Ameenu sai ya shiga? ba  ƙ aramin mamaki abin ya bashi ba har hakan ya nuna  ƙarara a fuskarsa, sake zuwa tayi zata shige jikinsa ya riƙe hannunta yana kallon face  ɗinta da duk ya kumbura tsabar kuka, to dama mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki, salwa on normal days ma ya take da kuka bare kuma an taɓa ta, ya 

Novels You may like