Advertisements
Chapter 19 Reading MACIJINE SHI Asirai Masu Tarwatsa Zuciya by Aunty Mameey BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

MACIJINE SHI Asirai Masu Tarwatsa Zuciya by Aunty Mameey

Author :  Aunty Mameey Category :  Complete Novels

Chapter   19 / 30

54K to 57K   out of 88K words

na rawa ,ba abinda yake son ji sai wanda ya shirya wanann haɗarin.

Mikewa nanny tayi tare da zuwa jikin window ta tsaya ,kallon Adeeb take tare da karantar yanayinsa, kamar yadda shima yake kallonta cike da ƙosawa.

Ahankali ta buɗe baki tace"ba kowa bane ya shirya wannan hadarin face ..........


Wayyo masu karatu cajina ya kare ,amma karku damu mu tara anjima,
Nice dai anty mammynku.


Mrs babi💘💘

Share and comment fisabilillah.

More comment
More typing.
29/08/2022, 11:06 am - Khadijah Salisu Fari: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄


MACIJI NE 🪱🪱🪱


Na mammy kabeer
(Anty mammy)


Elegant online writers📚📚


Free book

Page 59/60




________________Ahankali nanny ta ke kallon Adeeb,kafin ta sauke ajiyar zuciya,tunani take ta yadda Adeeb zai karbi wannan magana,ta yaya zata sanar dashi cewar,amminsa itace silar faruwar komai?shin zai amince da abinda zata faɗa masa ko yaya? Wane irin kallo zai musu idan yasan cewa amminsa ce ta kashe sarauniya Nazli da yaranta tare da baban tareeƙ,kuma abakinsu?anya kuwa basu barowa kansu aiki ba?
"Nanny kiyi magana mana kinyi shiru, ki sanar dani wake da hannu akan hadarin nan?"

Da sauri nanny ta dawo daga dogon tunanin data tafi,kallon tareeƙ tayi cike da karayar zuciya ,amma cikin ƙarfafa gwuiwa tareeƙ ya kalli nanny yana mai jinjina kai da nuna alamun ,kwantar da hankali.
Ajiyar zuciya nanny ta sauƙe Tana mai kallon fuskar Adeeb,kafin ta fara magana.
"Magajin fada kamar yadda na faɗa maka,wasu abubuwan muna kallonsu ne ba a yadda suke ba,ka sani abinda zan faɗa maka ba ƙarya ,ba kuma cutarwa.shiru ta ɗanyi tana jinjina maganar kafin taci gaba"ba kowa ya shirya wannan hadarin ba, face Amminka"nanny ta faɗa tana mai kure Adeeb da ido.

Da wani irin slow Adeeb ya mike tsaye bakinsa bude,zuciyarsa na wani irin bugawa kamar guduma, ji yayi kunnensa ya ɗauki wani ƙara ƙuuuuuuuu!!!
Sai yake jin maganar ta nanny Tana rarrabewa,kamar baiji me take faɗi daidai ba,jikinsa rawa ya kama,ta yadda yana mikewa tsayen yaji kamar zai fadi dan haka da sauri ya koma ya zauna,idanunsa ƙuri,akan fuskar nanny,
Cikin in-ina ya ke cewa"na...nan.,...y mek....Ike ..son....f..a...ɗ..I n..ee." ya faɗa numfashinsa na rarrabewa,ji yake kamar zuciyarsa zata fito tsabar yadda take bugawa.

Da sauri nanny ta ƙaraso kusa da Adeeb ta zauna ,cikin nutsuwa take shafa bayansa tare da kallon fuskarsa cikin tausayawa,dole yaji maganar tazo masa kamar saukar aradu."ka nutsu Adeeb domin Abinda nake faɗa maka yana buƙatar nutsuwa,tabbas Amminka itace ta shirya wannan hadari,tare da taimakon wani ma aikaci dake cikin gidan nan,mai kula da harkokin motocin gidan"nanny ta faɗa cikin sanyin murya tana jin zafin rashin mijinta da uwar dakinta kamar yau abin ya faru.

Kallonta Adeeb yake cikin wani irin yanayi na mamaki ,al'ajabi,tsoro,ruɗu dakuma firgici,ji yake kamar zuciyarsa zata iya fashewa ako wane lokaci,wannan wane irin magana nanny keyi?anya kuwa tana cikin hayyacinta?yaushe nanny ta koma maƙiyarsa ta hanyar hade kai da amma?dan su shiga tsakaninsa da amminsa? Dan kuwa yana tabbatar da cewa wannan shirin amma ne,lallai duniya ba tabbas .cikin zuciyarsa yake wannan maganar,kafin a fili ya kalli nanny ,sannan ya kalli tareeƙ,sai kuma yayi murmushi wanda yafi kuka ciwo ,sannan ya miƙe tsaye yana mai sanya hannunsa cikin aljihu,sannan ya fara magana bayan ya juya bayansa yana kallon bango" ban taba tsammanin cewa matar data raineni tun ƙuruciya zata iya hade kai da makiyana,ɗan ganin sun shiga tsakanina da ammina ba ,yau na kara tabbatar da cewa lallai wanda kake kallonsa matsayin masoyi ,to shine makiyinka aboye, amma bantaba tsammanin haka daga gareki ba nanny;Adeeb ya faɗa cikin zazzafar murya yana mai juyowa ,idanunsa sun kada sunyi mugun jaa, kallo ɗaya zaka masa kasan cewa zuciyarsa akaraye take.ci gaba yayi da cewa"nanny why ?why nanny me yasa zaki canja daga yadda na sanki?me yasa zaki so ganina cikin damuwa?na dauke ki tamkar mahaifiyata,duk wani abinda ya dameni ina zuwa gareki dan samun mafita,ammina tana kula dake da duk wani bukatun ki,amma meyasa kika hada kai da maƙiyanta?me yasa kika saida kanki dan bata alaka tsakanin da da mahaifiya?nanny why?tareeƙ me yasa nanny zatayi min haka?Adeeb ya faɗa yana mai riƙe kafadun tareeƙ idanunsa na zubda kwalla ,gaba ɗaya jinsa yake kamar ba shiba, wani sashen na zuciyarsa yana son karbar maganar nanny,saidai sashe mafi rinjaye na zuciyarsa na tunatar dashi wacece ammi agareshi,dan me zai yarda da batun nanny?.

Cikin damuwa da alhini tareeƙ ya kama hannun Adeeb ,cikin murya mai nuna tabbatarwa ,tareeƙ ke fadin, "yallaɓai ka kwantar da hankalinka,kuma kayiwa maganar nanny kyakykyawar fahimta,da sannu zaka gano gaskiyar dake cikin batunta, yallaɓai munsan abubuwa da dama wanda kai baka sansuba,amma da sannu zaka gane da kanka"tareeƙ ya faɗa cikin marairaita yana kallon Adeeb.

Fizge hannunsa Adeeb yayi tare da dafe kansa da yake jinsa kamar zai tarwatse,kafin ya kalli tareeƙ yana mai jinjina kai"well na gane ,na gane tareeƙ kaima kana bin bayan mahaifiyarka ko?da kai aka hada baki,am disappointed tareeƙ" Adeeb ya faɗa yana girgiza kai cikin karayar zuciya,idanunsa na fitar da hawaye mai tsananin zafi da ƙuna.ahankali ya juya ya nufi ƙofa yana dafe kansa .

Cikin damuwa da zubda kwalla nanny ta miƙe da sauri tana kiran Adeeb" magajin fada karkayi saurin yanke hukunci akan maganata kana bukatar nutsuwa da bincike dan Allah ka yarda dani ɗana, bazan taɓa cutar da kaiba."nanny ta fada cikin zubda hawaye .
Ko waiwayowa Adeeb baiyi ba ya fice daga ɗakin ,cikin sauri, dan ko ganin fuskar nanny baya sonyi ahalin yanzu.zuciyarsa na tafarfasa ,ji yake kansa kamar zai kama da wuta.kai tsaye part ɗin ammi ya nufa ko zai sami salama cikin zuciyarsa.

"Tareeƙ ka gani ko?kaga Abinda nake faɗa maka,Adeeb ya riga ya makance,baya ganin laifin ammi ko kaɗan,yanzu bansan wane kallo zai rinƙa yi mana ba"nanny ta fada cikin kuka.
Kamata tareeƙ yayi ya zaunar da ita akan kujera ,hannunsa ya sanya yana share mata hawayen dake zuba daga idonta,kafin yace " ummee na,ki kwantar da hankalinki,dama shi aikin alheri haka yake,dole saika fuskanci ƙalubale,nasan yallaɓai zaiyi fushinsa na wani lokacin kafin ya sauko,kuma nasan daga yau zai fara bincike akan abinda kika sanar dashi,In Sha Allah muke da nasara ,tunda akan gaskiya muke"tareek ya faɗa cikin yanayin ƙarfafawa mahaifiyar sa gwuiwa.
"In sha Allah tareeƙ ,Allah ya datar damu"nanny ta fada tana share hawayenta.
Ameen yace ,kafin suka ci gaba da tattaunawa akan matsalar.

Kai tsaye ya shiga part din na ammi,ko kula gaisauwar da hadimanta keyi baiyi ba,dan zuciyarsa ba abinda take sai tafarfasa,bai taɓa tsammanin haka daga su nanny ba,lallai mutum bashi da tabbas.
Afalo ya ci karo da sarauniya suhaimat,tana zaune da yaranta,suna cin apple da ya'yan itaceya ,gefe guda kuma suna kallo.
Da gudu su zayyad suka taso suka rungume Adeeb suna murnar ganinsa,kansu kawai ya shafa tare da rungumarsu,shima.
Kallonsa sarauniya suhaimat keyi,dan kuwa taga tarin damuwa cikin idanunsa.
"Sannu yarima ,ya jikin naka?dana yarinyar ?"sarauniya suhaimat ta fada cikin yanayi na nuna damuwa .

Lumshe ido Adeeb yayi cikin damuwa da yanayinsa na rashin son magana yace "da sauƙi" atakaice .
"Allah ya bata lafiya " ta fada da yanayi na damuwa.
"Ameen" Adeeb ya faɗa ahankali.
"Ammin naka tana ciki"sarauniya suhaimat ta fada cikin kulawa.

Kai kawai Adeeb ya jinjina mata kafin ya wuce zuwa cikin dakin.

" Bangane ba ?kamar ya nayi sakacin da kwalbar ta fashe,bayan irin kulawa da ita da nake?kasan irin kuɗin dana kashe akan akwatin da aka ƙera na sanya kwalbar ciki?
Shiru tayi ,da alama tana sauraron abinda ake faɗane daga can bangaren.
"Shikenan ,yanzu muna cikin alhini ne na wannan abun daya faru,dan haka kajira nan da kwana biyu,zan nemeka,dan awannan karon aiki nakeso ayimin na ban mamaki,bana kuma son asami matsala " ammi ta faɗa cikin wani yanayi mai nuna ta shirya mugunta mai zafi cikin ranta.

Gaban Adeeb ne yayi wata irin faɗuwa da har saida ya dafe ƙirjinsa,wane akwati ammi ke magana akai?wace kwalbar ce ta fashe?da wa ammi ke waya?waɗan nan sune tambayoyin da Adeeb ke yiwa kansa,saidai bashi da amsar ko daya daga ciki.
Ganin ammin ta gama wayar kuma tana ƙoƙarin juyowa ne ,dan ta ba ƙofa baya,yasa Adeeb saurin saita kansa yayi sallama tare da shiga.

Da sauri aɗan razane ammi ta juyo tana kallon Adeeb ɗin,dan batayi tsammanin ganinsa yanzu ba, saidai da alama baiji me take faɗi ba,itafa wllh tsoronsa ma ta fara ji yanzu,amma saita maze ta saki murmushi,tare da miƙa masa hannu,alamun ya ƙaraso gareta.
Ahankali Adeeb ke takawa har yaje bakin gadon ya zauna,dan jikinsa sam ba kwari,murmushin ƙarfin hali yayiwa ammi yana kallon fuskarta,

"Habeebee ya jikinka? na tsorata sosai da yanayin dana ganka ɗazu"ammi ta faɗa tana mai janyo Adeeb zuwa jikinta.

Sam yau Adeeb ji yayi baya wani jin dadin kwanciya akan cinyarta,Dan saiyajisa kamar akan ƙaya, dan haka da sauri ya tashi daga kwanciyar da yayi,kafin ya dan saki murmushi,yana mai cewa"ƙalau nake ammi,kada ki damu,ya naki jikin?"ya faɗa sam fuskarsa ba walwala.

"Shafa kansa tayi kafin tace naji sauki dana karka damu"ta faɗa tana kallon fuskarsa ,dan kuwa sam ba haka yake mataba,yau kam ba wannan shaukin da yake nuna mata idan suna tare.

Mikewa yayi yana mai faɗin ammi zanje in duba yarinyar can zan dawo anjima" yana faɗin haka yayi waje abinsa.

"Yawwa yarima ,ina son in duba yarinyar nan "sarauniya suhaimat ta fada tana mikewa lokacin da Adeeb ya zo zai wuce.

Shiru yayi yana ɗan nazari,akwai bukatar ta duba ta ,tunda likita ce itama ,kuma fannin mata ta karanta.
Dan haka yace "ok muje ,tana part ɗina"

Ficewa sukayi tare suka nufi part din Adeeb.


Toh masu karatu ,mubi su Adeeb dan duba Hulwa.

Sai mun hade next page.

Mrs babi ce 💘💘

Share and comment fisabilillah.

More comment
More typing.m
29/08/2022, 11:06 am - Khadijah Salisu Fari: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄


MACIJI NE🪱🪱🪱


Na mammy kabeer
(Anty mammy)



Elegant online writers📚📚



Free book

page 61/62




________________Ficewa sukayi daga part ɗin ammi zuwa na Adeeb, haka kawai gaban sarauniya Nazli ke faduwa,sam ta kasa gane kan wannan faɗuwar gaban nata,saidai kawai ta alaƙa ta hakan da tunanin halin da zata ga yarinyar data sanya tausayi ta cikin zuciyarta.

Su zayyad ma biyo ta sukayi,dan sunce suma son gannin marar lafiyar ,kuma zasuyi wasa agurin uncle Adeeb ɗin.

Suna zuwa Adeeb ya dannan lambobin securityn daya sanya lokacin da zai fice,nan take ƙofar ta bude suka shiga.
"Tana cikin daki" Adeeb ya faɗa yana kallon sarauniya suhaimat wacce ke tsaye cikin faduwar gaba.
Kallonsa tayi cikin tausayawa, tare da jinjina kai .

sam zuciyarsa Adeeb da jikinsa basa masa daɗi, yana cikin matsananciyar damuwa ,abubuwa sunyi masa yawan da har yana rasa me Yakamata yayi.

" Ku zauna anan maza kafin na fito kunji" ta faɗa tana shafa kan yaran nata,kafin tabi bayan Adeeb zuwa cikin dakin.
Tana kwance kamar yadda ya barta,ruwan daya ɗaura mata ya kusan karewa.
Jiki asanyaye sarauniya suhaimat ta karasa bakin gadon da fattu ke kwance .sosai bugun zuciyar sarauniya suhaimat ya tsananta.
Zama tayi tare da ƙurawa fattu idanu,lokaci guda taji wata masifaffiyar kaunar yarinyar tana ratsa dukkan sannan jikinta,ji take kamar bata taɓa son abu makamancin yadda take jin son yarinyar na shiga lungu da sako na jikinta ba.

Hannun fattu ta kamo tare da riƙewa gam-gam cikin nata,wani sanyi taji yana ratsata lokacin data kama hannun fattun,batare da saninta ba kawai ta rungume hannun fattu aƙirjinta ,tare da runtse idonta.wani irin shauƙi takeji yana shiga jikinta irin na ƙaunar dake tsakanin ɗa da uwa.haƙika takamu da matsananciyar kaunar yarinyar lokaci guda.

Kallon fuskar fattu take bata ko ƙifta idanunta,Adeeb na tsaye agefe guda yana kallonta ,mamakin yadda yaga fuskarta ta nuna so da kaunar fattu yake,koda yake haka Allah ke al'amarinsa.ganin ta kasa cewa komai kawai tana rungume da hannun fattu ta kura mata ido yasa shi sauke ajiyar zuciya yana mai faɗin"anty lafiya kuwa naga kinyi shiru "ya faɗa yana mai kallon fuskar sarauniya suhaimat.

Sai lokacin tadanyi firgigit ta ɗago kai tana kallon Adeeb,ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi kafin tace "wllh Prince haka kawai naji ina kaunar yarinyar har cikin raina ,sosai nake jin tausayinta, yanzu ka dan bamu guri inason na dubawa"ta fada ta na mai shafa kan fattu.

Kallon fattu Adeeb yayi cike da tausayawa,zuciyarsa na masa wani irin ɗaci ,kafin ya sauke ajiyar zuciya kana yayi falo gurin su zayyad da yazeed.

Sosai sarauniya suhaimat taji mugun daɗi lokacin data gane fattu period ma take,kuma babu alamun Rashad yayi mata wani abu,hamdala tayi ga Allah tana jin zuciyarta wasai, murmushi kwance kan fuskarta take kallon fattu,wacce ta fara dan motsi tana yamutsa fuska.

Hannunta sarauniya suhaimat ta kara riƙewa da kyau tana mai faɗin"princess buɗe idonki ki ,kalleni kinji" tana faɗin haka tana ɗan buga kumatun fattu.

Ahankali fattu ke buɗe idanunta da suka yi wani irin jaaaa kamar jini ya taru a cikinsu,har ta bude idon fess,tare da kafe silin da ido,bata ko ƙiftawa.da alama tana son tuno wani abune, shiru sarauniya suhaimat tayi tana bin idanun fattu da kallo.
Kusan minti ɗaya fattu tana kallon silin ,kafin ta zabura tare da kwalla kara tana kokarin tashi,da sauri sarauniya suhaimat ta cire mata karin ruwan dan dama ya kare .

"Wayyo Allah na ,wayyo hammana kazo ka ceceni,zai lalamin rayuwa,wayyo baffana,wayyo innata kizo ,dan Allah ka bari wllh niba yar iska bace karkamin bana so banaso wayyoooooo!!!" Abinda fattu ke faɗa kenan tana fizge -fizge ,dan gani take kamar lokacin Rashad ke ƙoƙarin yi mata fyade,janyota sarauniya suhaimat tayi da sauri ta rungumeta tsam-tsam ajikinta ,cikin mugun tausayinta,tana faɗin"ki nutsu princess ba kowa buɗe idonki ki gani,nice ba Rashad bane ya tafi kiyi shiru ya isa"abinda take faɗi kenan tana shafa kan fattu ,wacce ilahirin jikinta ke rawa ,ta rufe idanunta ƙam -ƙam taƙi budewa.

Da hanzari Adeeb ya ƙaraso cikin dakinz su zayyad ma bishi sukayi da gudu ,jin ihu da fattu ta kwalla,har neman faduwa Adeeb yake tsabar sauri,yana zuwa ya zauna abakin gadon tare da kamo hannun fattu ,da sauri ta fizge hannunta tana mai sakin ƙara ,"ahhhhhh,wayyo ni kasakeni banaso ,wayyo hammana kana ina? wayyo Hamma kazo ka taimakeni" fattu ta faɗa tana kokarin zamewa daga jikin sarauniya suhaimat.

Cike da damuwa Adeeb ya ƙara kamo hannunta ya rike cikin nashi ,duk yadda take ta ƙoƙarin kwace hannun nata,amma yaƙi saki,
"Hulwa ki nutsu kinji ,nine hammanki,buɗe ido ki kalleni ,ba Rashad bane nine Hamma" Adeeb ya faɗa cikin sanyin murya yana mai shafa kan fattu.

Jin muryarsa da fattu tayi yasata saurin buɗe kunburarrrun idantuna ,ta sauke akan fuskar Adeeb,ɗan kafeshi tayi da ido,gabanta na faɗuwa kamar zai fado kasa.

"Nine ,hammanki ne Hulwa kalleni ki gani ,nine Hamma Adeeb " ya faɗa yana ɗan matso da fuskarsa saitin Tata.
Ahankali tace "hammana"
"Na'am Hulwa is me "Adeeb ya faɗa yana mika mata hannu.

Da sauri ta fada ƙirjinsa tare da fashewa da wani irin kuka,mai matukar ban tausayi,kukane irin na wanda ke cikin tashin hankali kuma ya sami mai taimakonsa.

"Hamma ina kaje ka barni?wannan mai kama da kai ɗinne yazo zaiyi min fyade,Hamma dan baki yarda shine yayi ta dukana,ya fasamin baki,ya bugamin kaina ajikin katanga,Hamma bana sonshi,bana son ganinsa ,dan Allah Hamma ka fitar dani daga gidan nan bana so"fattu ta faɗa cikin matsanancin kuka muryarta har wani yankewa take kamar numfashinta zai dauke.

Ƙamm ƙamm,Adeeb ya rungumeta ajikinsa,yana jin wani irin zafi akirjinsa, mugun tausayinta ne yake zaga dukkan wata kofa dake jikinsa,haushin kansa ma yake ji,wai me yasa ma ya tafi gurin taron ya barta anan?me yasa bai tafi tare da itaba?
Ahankali yake shafa kanta,yana mai faɗin"am sorry Hulwa,kiyi haƙuri laifinane,dana tafi na barki,na miki alkawarin ba wanda zai sake ƙoda miki kallon banza ne bare hakan ta kara kasancewa,ki yafemin hulwata ,an sorry "ya faɗa yana kara ruƙunkumeta ajikinsa,wasu hawaye Masu zafi suna zirarowa daga idanunsa.
Zuru su zayyad sukayi suna kallon fattu,dan yazeed ma tuni ya fara kuka ,dan shi yana da mugun tausayi.
Sarauniya suhaimat na zaune ta kura musu ido,cikin tausayi take zubda kwalla itama,ji take kamar yarta akayiwa wannan zalumcin ,Allah Sarki Adeeb ya cika dan halak dan ga dukkan alamu yana kula da yarinyar nan,duk da kasancewarta ma aikaciya agidansu,kuma tabbas taga zallar kaunar yarinyar cikin idanun Adeeb.

Sun jima cikin wannan yanayin,har saida Adeeb ya tabbatar Hulwa ta sami nutsuwa ta hanyar daidaiton da yaji bugun zuciyarta yayi,sannan ya rabata da jikinsa.
"Sannu princess hulwar Adeeb"sarauniya suhaimat ta fada ,fuskarta ɗauke da murmushi.

Sai lokacin fattu ta juya tana kallonta .rassa!rassa!!rassa!!! gaban fattu ya yanke ya fadi,ƙurrr ,ta kure sarauniya suhaimat da ido,lokaci guda taji ƙaunar matar na ratsata fiye da yadda tayi tunani,duk kunya irin ta fattu,da bata yarda kuyi ta haɗa ido da ita,amma yau kam ta kafe sarauniya suhaimat da ido bata ko ƙiftawa.

Murmushi sarauniya suhaimat take sakarwa fattu,kafin tace" baki sanni ba ko?
Ta fada cikin yanayi na murmushi.
Kamar wata doluwa haka fattu ta daga kai idonta akan fuskar sarauniya suhaimat.
"Daga yau nice innarki ,danaji kina faɗi kinji "ta faɗa tana mai shafa kan fattu.
Ahankali fattu ta matsa kusa da ita tare da ɗora kanta akan cinyar sarauniya suhaimat tana mai faɗin "innata"ahankali tare da lumshe idonta.

Kallonsu kawai Adeeb keyi,zuciyarsa na darsa masa abubuwa da dama,wannan wane irin shakuwace ta lokaci ɗaya?gaba ɗayansu sun kamu da kaunar juna daga haduwar farko,anya ba wani al'amarine mai ƙarfi atsakinsu ba ?.
Hammmmm mudaije zuwa.

"Sannu anty "zayyad ya faɗa cikin tausayawa.

Ahankali fattu ta ɗago kai tana kallon yaran masu tsananin kama,
Lokaci guda yaran suka shiga ranta.

Masha Allah kyawawa dasu.
Jinjina kai tayi tana kallonsu cike da kauna.

"Maza kuje falo ko anty zatayi wanka" cewar suhaimat.
Kama hannunsu Adeeb yayi suka fice zuwa falon.

Saida Sarauniya suhaimat ta taimakawa fattu tayi wanka ta gyara mata jikinta sosai,ta bata abinci taci ta sha magunguna sannan ta kwanta barci .kafin ta bar ɗakin akan zata kara dawowa ta duba ta.har ta kai bakin ƙofa fattu ta ce"innata" da sauri sarauniya suhaimat ta juyo ,dan har cikin ranta taji sunan ya shigeta.
"Zaki dawo "fattu ta faɗa tana kallonta .
Jinjina kai tayi tana mai yiwa fattu murmushi tace "tabbas zan dawo ƴata"murmushi fattu tayi cikin karfin hali tare da rufe idanunta.ba ɓata lokaci barci yayi gaba da ita.dan kuwa harda maganin barci acikin wanda ta sha.

Koda sarauniya suhaimat ta koma bangaren ammi,zaune ta tarar da ammin ta buga uban tagumi,duk sallamar da take sam ammin bata jiba,dan tayi nisa cikin duniyar tunani,saida ta tabata kafin ta san da zuwanta gurin.

"Suhaimat ina kikaje ?na duba baki afalon?
Ammi ta faɗa da kokarin kawar da samuwar dake kan fuskarta.

Zama suhaimat tayi susa da ammi tace ,wllh yarinyar nan da abin nan ya faru da ita naje

19 / 30