Advertisements
Chapter 11 Reading Ranar Wanka Complete Hausa Novel Hausa Novels
Advertisements

Ranar Wanka Complete Hausa Novel

Author :  Jamsy Category :  Complete Novels

Chapter   11 / 23

30K to 33K   out of 66.9K words

kula da ni."

Rau ta yi da idanunta."Kai ma ka san babu wanda na damu da rayuwarsa kamar kai. Bayan ƴan'uwanta ka ta jini har da shaƙuwa da soyayyar jini, wanda ta kai da har muryar mahaukacin masoyi tana rikiɗa tana zama irin taka."

Gwauron ajiyar zuciya ya saki jin abin fa ta ce. Zuciyarsa ta yi fari ƙal tare da hamdala ganin ba ta gane ba.

Da mamaki ya kalle ta ya ce,"So kike ki yi mini wayo na ɗauka kin damu da ni, amma na tabbata da ace babu son mahaukacin masoyi a rayuwarki, sai ki tausaya mini halin da na ke ciki."

"I do care you! Wallahi kana raina ko da yaushe, amma ka sani Ummu, gata take yi maka, domin duk wanda ya auri mace kamar Anty Wajnah ya yi dace."

Ƙara ɓata rai ya yi tare da buɗe murfin motar ya fito."Please, akwai buƙatar mu tautauna sis, ina tsananin buƙatar shawarki."

"Haɗuwarmu xai yi wuya Yaya, Ummu sam ba ta son ganinmu a tare."

"In mun gaishe da Hajiya ki same ni
a waje ki raka ni gidan Najib."

Kallon sa ta yi da nufin ta musa, amma kallon da ya yi mata ya sanya ta kasa tare da sauke kanta ƙasa.

Ganin ya fita ya sanya ita ma ta fito tare da rufe ƙofar suka jera suna hira.

Hajiya na zaune a falon, su Umnah sun sanyata a tsakiya sai hira suke mata. Sallamar su ya katse dariyar da suke yi mata.

Ganin su ya sanya ta washe bakinta da ke cike da goro tana tafa hannunta.

"Lale marhaba da zuwan jikokina!" Ta furta cikin tsananin farinciki domin tana matuƙar son jikokinnata.

Huwais da fara'a ya isa gareta, tare da zaunawa a gefenta ya ciro wayarsa da ke gana aljihun rigarsa zai ɗauke su hoto.

"Bari na yi hoto da gimbiya autar mata." Ya ce cikin tsigar tsokana.

Hannnunta ta sanya ta ka masa duka da carbin da take ja, ta ture shi tare da kai hannu kamar za ta buge shi, wanda hakan ya sanya ya miƙe yana dariya.

"Bari na gudu domin hannunki kamar icce yake."

"Eh, ai gara ka gudu in ba haka ba, sai na karyaka saboda kishi. Don za ka yi aure sam ka daina zuwa inda na ke. To daɗin abin ba a canzawa tuwo suna, kuma tsohuwar zuma da ita ake magani"

Fara'arsa ta ragu jin abin da ta ce, amma sai ya share ba tare da ya ce komai ba.

Hilah kuwa rungume ta yi cikin tsananin ƙauna ta ce,"I miss you ƴar tsohuwa mai ran ƙarfe."

Murmushi ta ƙara saki tana cewa,"Sannu malama tun da kika ci gaza kika yi kuɗi kin guje mu."

"Kai tsohuwar nan kin iya rigima. Kana jin abin da take cewa Ya Huwais, bayan ko da na dawo sai da na kawo mata nata kason."

Murmushi kawai ya yi,ba tare da ya ce komai ba, ya zauna gefen da Hilah ta zauna hankalinsa na wayarsa da Najib ya turo masa da tsaƙo.

"Ai kya faɗi haka saboda ba ki da gaskiya. Bari mutuminki na nan zuwa, tun da ya ji muna maganar zuwarki ni da Fatima ya ce ba zai koma Kaduna gurin aiki ba sainya ganki, yanzu haka yana hanya. Ni duk na ƙosa ayi auren nan duk mu huta."

Da sauri ya ɗago kansa jin abin da ya ce. Zuciyarsa ta yi baƙinƙirin tare da jin wani irin ɓacin rai. Wani irin ɓacin rai ya ziyarce shi har baya gani sosai.

"Ai ko ya zo wahala zai yi domin zamu bar su Umnah fita za mu yi."

"Ku je ina? Lailai ba wuni ta ce mini za ku yi ba?" Ta yi masa tambayar da sauri.

Miƙewa ya yi tare da ɗaukar makullin motarsa ya kalli Hilah da shi take kallo ganin yadda ya yi fuskar shanu.

"Eh, wuni za mu yi, amma sai ta raka ni anguwa. In zai iya sai ya yi ta jira ɗan wahala kawai. Ni wallahi haushi yake bani, saboda yadda yake wani nuna son mace da nace mata kamar maye." Cikin tsananin xafi ya furta cikin ɓacin rai tare da yi mata nuni da su tafi.


"An gaya maka kowa irin ka ne? Mata ai dole a kula da su, domin sune tushen kowa. Don kai ba ka damu da matar da za ka aura ba, sai aka ce maka kowa haka yake? Ka ji tsoron Allah Huwais, yarinyar nan tana sonka, kuma masoyiyarka ce ta haƙiƙa. Ka tuna iya tsawon lokacin da ta rinƙa jiranka, amma tun da aka sanya ranar ka kasa zuwa ko sau ɗaya ne."

"Saboda bana sonta kun na ce sai na aureta. Ana soyayya dole ne? Na ga ko ke kin sha bani labarin ke da Alhaji auren soyayya kuka yi da mijinki. Sai ni a ayi mini cushenta? Don tana sona sai a tilasta mini, bayan na gaya muku ina da wacce na ke so."Ya ce cikin zafi.

"Sau nawa ake baka damar ka kawo ta amma ka kasa Huwaisu? In dai ba aljana kake so ba, ko kuma aurenta kake son ka yi cikin haramci, ai ya kamata ka nuna mana ita iya tsawon lokacin da aka ba ka."

Haɗiye miyau ya yi da ƙyar, tare da kallon Hilah da ta yi zuru tana kallonsa, a ranta tana son ya aminta da zai nuna musu ita, domin ita kanta tana son sanin wace ce ta sace zuciyarsa har yake fargabar tunkararta?

Hannunta ya kamo yana faɗin,"Zo mu je Hilah, ƴar tsohuwar nan lokacina kawai za ta ɓata."

"Ba dai ka son gaskiya kawai, amma ka sani ko ba ka so Wajnah don kai ba, ka sota saboda ita ɗin ƴar'uwarka ne, saboda karka manta da mahaifiyarka da mahaifiyarta ciki ɗaya suka fito."

"Wannan dalilin zai sanya na aminta a kashe ni kenan?"

Kafin ta ba shi amsa muryar Hamad ta daki kunnuwansu ya shigo da sallama.

Gabakiɗaya suka ɗaga idanu suna kallonsa.

Namiji ingarma da shi kuma mai cikar haiba da kyawu. Yana sanye cikin kaftani mai kalar maroon. Kayan sun yi masa kyau kuma sun dace da jikinsa.

"Yauwa ga shi nan ma ya iso da kake shirin ɗauke masa mata." Hajiya ta furta tare da ƙara fafaɗa fara'arta bayan ta amsa sallamarsa.

Cikin kamala ya ƙaraso cikin falo, tare da zama gefen Hajiya idanunsa, na kan Hilah da ta yi mutuwar tsaye tana kallon Huwais.

A ranta ta sanya cewar matuƙar da ta san zai zo sam ba za ta yarda ta biyo su ba, domin ta san in har suka haɗu ba su kwashewa ta daidai, wanda hakan mamaki yake bata, saboda ta duba tare da mahangarta ta rasa dalilin da ya sanya ya tsane shi, saboda kaf Family nasu an shede shi yana da natsuwa da hankali, amma ba shi da maƙiyi da kamarsa.

Huwais ya watsa masa mugun kallo ta ƙasan ido. A ransa haushinsa matuƙa yake ji, saboda da za a iya ba shi takubba tsaf zai sare kanshi, don ya tsane shi baya jin ɗigon ƙaunarsa, duk da ya kasance ɗan'uwansa, kuma dangantaka na jini mai ƙarfi.

Ƙaramin tsuka ya ja tare da ji kamar ya kifa masa mari. Tuna karanbantar da suka sha ana gobe zai bar Ƙasar ya dawo masa. Haushi da takaici suka ƙara kama shi ya ji kamar ya shaƙeshi.

Bayan Hamad ya gama gaisawa da Hajiya da ta cika da farincikin ganinsa, sai ya miƙa wa Huwais hannu da ya sha kunu kamar ba zai bayar ba. Hannunsa ya noƙe ko mai ya tuna oho ya miƙa masa kamar yana gudun kar ya shafa masa ciwo.

"Ranki ya daɗe gimbiyar mata." Hamad ya furta hakan cikin tautausar murya, wanda ya ji kamar ya soke shi ne.

Ɗan gyaran murya ta yi can ƙasan maƙoshinta tare da tattaro natsuwarta ta ce,"Ina wuni?" Ta furta ba tare da ta iya ɗago idanunta ta kalle su da suke kallonta kamar za su cinyeta.

A maimakon ya amsa sai ya ɗan sakin mata murmushi tare da ƙara masawa kusa da ita."


"Gimbiya da fatan kina lafiya?"

"Hajiya, mu zamu wuce ba xamu jima ba, zamu dawo." Ya ce tare da kama hannunta za su fita.

"Kai Huwaisu, ba na son rashin mutunci. Ɗan'uwan na ka za ka barshi ne a nan, bayan saboda ita ya zo."

"Bai sanar da zuwansa ba, kuma ni na riga na tsara fitarmu."

"Karya damu zan jira shi." Cewar Hamad tare da zama a kujera hankalinsa kwance, saboda tun ranar da suka yi faɗa mahaifiyarsa ta gargaɗesa da karya ƙara kula sa, Hilah dole za ta kasance na sa, domin ko da ace sonta yake yi, ya san cewa babu aure a tsakaninsu ko da sun kasance su kaɗai. Don haka, duk son da yake mata dole ya haƙura ya ɗauke idanunsa a kan zinariyar ƙanwarsa ya bar masa ita, saboda shi Allah ya yi wa wannan tagomashin da samun mace kamarta.

"Huwaisu, ina gaya muku ku sasanta kanku ku rage tsanar da kukewa junanku, musamman kune manya in har ƙanninku suka taso suka ga abin da kuke yi ba za su yi zumunci."

"Hajiya, sai mun dawo." Ya ce tare da kama hannunta suka fara tafiya.

Suna fita ya saki hannunta ya buɗe motar ya shiga.

Hilah kuwa kallonsa take yi cikin mamaki. Ta san yana sonta fiye da kowa duk a cikin ƙanninsa, amma dalilin sa na ƙin yarda da auren Hamad yake ba ta mamaki. Yana da hankali da addini uwa uba ga ƴaƴan banki. A tunanin ƙarfafata zai yi ta amince musamman da yake ɗan'uwa, kuma wanda suka tashi tare suka shaƙu fiye da kowa a cikin family ɗin su.

Har suka fita gidan babu wanda ya tanka ko da tari ne.

Sun yi nisa sosai har sun hau kan titi, kasancewar unguwar da ɗan tazara, ya waiwayo ya kalleta da hankalinta yake kan titi.

"Yaya, ba ya son ko wane namiji ya raɓe ni, amma mai ya sa sam baya nuna hakan ga mahaukacin masoyi?" Kafin ta masa tambayar ta ji muryarsa yana cewa,"

Na tsani wannan gayen, wallahi sam ba ki dace da shi ba!" Ya ƙarashe maganar tare da buga sitiyarin mitar yana huci.


A tunaninka mahaukacin masoyi ya fi dacewa da ni?" Ta yi masa tambayar da ya sanya ya ja burki babu shiri yana kallonta.

Tsoro ne ya bayyana a fuskarta, wanda ya sanya ya tuna a kan titi suke. Cigaba da tuƙin ya yi yana mamakin abin da ta ce.

"A kan me zan faɗi haka? Karki manta mahaukacin masoyinki ke kaɗai ce kika yarda da duniyarsa, domin har yanzu ba mu san mutum bane ko aljani."

"Mutum ne kuma na gari in sha Allahu. Wani lokacin ina mamakin yadda ba ka nuna haushinsa da mu'alamarmu."

"Wataƙila don ban ganshi a zahiri bane, amma sauran karki manya yadda suke nuna tsantsan soyayyarsu yake sawa na ji haushi da tunanin watarana za su raba ni da ke."

"Har abada muna tare kai fa ɗan'uwana ne na jini tamkar jini da hanta muke."


Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).

FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 008144072423


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K

*RANAR WANKA...*



NA



JAMILA LAWAL ZANGO
"JAMCY"



☀️ *First Class Writers Asso* ☀️

Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation


*GARGAGAƊI*

Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️

JAN HANKALI

Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.


SADAUKARWA

Kacokam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a.



PAGE 12

BISMILLLAHI RAHMANINR RAHIM

"Har abada muna tare kai fa ɗan'uwana ne na jini tamkar jini da hanta muke."


Kaɗa kansa kawai ya yi jin abin da ta ce.

"Ya Huwais, ba ka tunanin lokaci ya yi da mahaukacin masoyi zai bayyana kansa ya daina ɓoye kansa?" Ta yi masa tambayar idanunta a kansa.

Ganin bai tanka mata ba, sai gabansa da ya faɗi ya sa ta ɗora da cewa,"Zan gayyace shi bikinka, in har ya ƙi zuwa zuciyata na bani shawarar na haƙura da shi, ko da kuwa son shi xai kashe ni, domin babu soyayyar da na taɓa ganin an yi aure ba tare da haɗuwa."


Wani rin faɗuwar gaba ya ƙara ji dum! Sai ya jikinsa na rawa. Ƙoƙarin daidaita na tsuwarsa ya fara yi, don kar ta fahimci halin da ya ke ciki.

Kaɗa kansa yake kamar ƙadangaren kutu!"Ya kamata gaskiya ki gayyace shi, amma kar ki ce za ki rabu da shi, don ya ƙi zuwa bikina in har kina sonshi, domin jikina yana bani mahaukacin masoyi shi ya fi dacewa ya aure ki. Wani ne can wanda ba ki taɓa tunanin yana sonki ba, ya ke fama da dakon soyayyarki tsawon lokaci. Da ya ke ƙanwata mai zafi ne kuma kyakykyawa dalilin da ya sanya ya kasa bayyana kansa gareki."

"Ni ma haka nake ji musamman a duk lokacin da na yi istikhara."


"Da kyau malamar ƙanwata. Daɗina dake komai sai kin nemi zaɓin Allah. Ki ba shi lokaci matuƙar bai bayyyana kansa ba, ni da kaina zan gaya miki ki haƙura da shi."


"Amma kai ma Yaya kana da kyau, domin ban taɓa ganin namijin da yake da kyau kuma ya iya tsara rayuwarsa da kula da addini kamar kai ba.


Jin abin da ta faɗa kansa ya fasu har ya ji kamar zai cika duniya.

"Duk kyawuna, bai kai ƙanwata sarauniyar kyawu da kula da addini ba."


"Wannan dalilin ya sa na ke jin matuƙar haushin mahaukacin masoyi da kike sonsa."

Ta buɗe baki xa ta yi magana, ya rigata daidai lokacin da suka isa ƙofar gidan, ya tsaya a get ɗin ba tare da ya yi hon ba.


Kashe motar ya yi ya kalle."Please, na gaji da maganarsa as usual. Ke kullum damuwarsa kike kawo mini, da kuma na yi ƙorafi kice ba haka ba."


Dariya ta yi tare da ce wa,"Kai Yaya,"


"Ki bani shawarar yadda zan zauna da Wajnah a matsayin mata."


Kallonsa ta yi kamar ba ta gane mai yake cewa.

"Yes, ina nufin wane irin zama za mu yi, domin kin san ba ta a cikin zuciyata. Tsoro na karna cutar da ita Allah ya kamani."


"Ta ci albarkacin Mommy mahafiyarta. Ka yi adalci a zamanku."

Kwantar da kansa ya yi kawai a saman kujerar motar domin ba haka ya so ta ce mishi ba.


Gani suka yi an wangame get ɗin gidan. Najib ne da matarsa tsaye cikin mamaki suna kallonsu.


"Kai! Wallahi kana da abin mamaki Huwais, na ɗauka amarya ka kawo mini kuka tsaya kana soyewa tun ɗazu a waje ashe ƙanwarmu ce." Ta faɗa daidai lokacin da ya shigo da motar cikin yana ƙoƙarin buɗewa.


Hilah da ke dariya ya watsawa kallo ba tare da ya ce komai ba. Ya ɗauko pos ɗinta da ta barshi a motar ya miƙa mata.

Najib da ya san dawar garin bai yi ƙorafi ba. Ya yi musu jagora suka shiga ciki.

Hilah ta zauna a gefen kujerar da ya zauna bayan ta gaida matar Najib mai suna Samahatu.

Cikin sakin fuska ta amsa mata, daidai lokacin da ta ije musu gorar ruwa da drinks a gabansu.


Huwais ya sanya hannunsa ya ɗauki ruwan ya buɗe, tare da ɗaukar kofi ya zuba mata. Miƙa mata ya yi yana murmushi. Ita ma murmushin ta mayar masa tare da karɓa ta ce masa,"Thanks, Ya Huwais."



Da idanu ya amsa mata tare da ije gorar yana mata wani irin kallo.

Samahatu ne ta tsaya cikin tsananin mamaki tana kallonsa. Ta juya ta kalli Hilah da take kurɓan ruwan cikin yanga kamar ba ta son sha, yayin da hankalinta yake kan wayarta.

Idanunta ta mayar kan Huwais da har yanzu ita yake kallo, duk da maganar da Najib ya ke mishi, amma hankalinsa ba shi a kansa.

Ƙara kallonsu ta yi tana son ƙara ganin kamar su. Ta san cewa Najib ya taɓa nuna mata hotonta har ya sanar da ita ciki ɗaya suka fito. To amma wane irin kallo yake mata kamar na soyayya? Ƙwaƙwalwarta ta rikice sai kuma ta fara tunanin ko dai ba ita ba ce.

Gyaran muryar da ta yi ya sanya dukanninsu hankalinsu ya dawo kanta.

"Baby, bari na haɗo abinci." Ta ce tana sakar masa murmushi.

"Ok, honey, please ki kawo wa Huwais juice ɗin goribar da na haɗa ya ji na iya abinci."


Dariya ya yi jin abin da ya ce ba tare da ya ce komai ba.

Zubbur Hilah ta miƙe tare da kallonsa."Yayana, let me help her." Ta furta cikin taushin murya.

"Haba, ƙanwarmu karki wahalar da kanki ai na kusa gamawa."

"No, kar ki damu in ba ki gama ba, ki ba ta ta yi girkin domin she is the best cooker in the world" Ya furta hakan cikin tabbatar wa.

Murmushi ta yi." No, kar ki damu yanzu xan gama." Ta ce za ta juya.

Hannunta Hilah ta kama tare da cewa,"Mu je Anty Samah, kar ki damu. Amarya ce ke bai kamata ki yi aiki ba."

"Good girl, na gaya miki ƙanaata akwai hankali da son taimako, domin zan iya cewa tafi ko wace mace hankali da natsuwa da iya komi."

Sororo ta yi sai kuma ta yi yaƙe kawai ta kalleta da take murmushin jin kunya ganin yadda yake kurantata.

Harararsa ta yi cikin wasa shi kuma ya aika mata da kallo suka shiga kicin.

"Huwais, kana cika zaƙewa fa! Ba ka tunanin abin da kake yi kowa zai iya gane sonta kake yi? Kuma yabon ta da kake yi ba ƙaramin matsala zai

11 / 23