Advertisements
Chapter 19 Reading Ranar Wanka Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Ranar Wanka Complete Hausa Novel

Author :  Jamsy Category :  Complete Novels

Chapter   19 / 23

54K to 57K   out of 66.9K words

in da ma ace wannan ne ya sanya ni wahala sai na ji daɗi, saboda na tabbata kwana zan yi mala'iku suna rubuta mini lada. Wahida ban san wane irin kalar miji na aura ba, domin wallahi jiya kallon kirki ban samu ba, daga ƙarshe ya tura ni waje ya rufe ƙofarsa." Ta ƙarashe maganar tana share hawaye sai kuma ta ɗora da cewa jin ta yi shiru.

"Na rantse sai Hajiya Zamzam ta biya ni kuɗina, saboda da na shafa turaren kin san Allah, toshe hancinsa ya yi, baya ta gaya mini haka zai rinƙa bina sai yadda na yi dashi."

Matuƙar mamaki ya kama ta matuƙa jin abin da ta ce.

"Anya mijin ki ba aljana ta aure shi ba? Domin na ga ko ni da na ke har na haihu, wallahi ina shafa turaren haka oga yake bina ina shan ƙamshi."

"Babu wata aljana tsabar ƙiyayya ce da taurin kai. Ba ki ji yadda ya rinƙa kushe ni yana yabon wacce yake so ba. Ni da ya kamata jiya ya zamar mini rama memorable sai ga shi na yi kwanar wahala." Ta ƙarashe maganar tana cije baki.

"Ikon Allah, ni kam ban san wane irin miji kika aura ba, amma duk ƙawayenmu da suka yi amfani da shi sun ce ya yi musu."

"Wash! Ki taimaka ki gaya mini abin da zan sha na samu na rintse. Jiya sam ban rintsa ba."

"Kai amma wannan gayen ya ɓata mana show. Ni da na kasa bacci sai zumuɗi na ke yi Allah ya kaimu gobe musha labari. Kuma wallahi ya ja miki abin kunya, saboda duk ƙawayenmu kowa sai ya ba da labarin first night ɗinsa a group sai ke? Kin san yau daren farkon ki shine topic of discussion ɗinmu."

Tsuka taja tare da jin wasu zafafen hawaye sun wanke mata fuska, saboda yau ta yi ninyar babu abin da za ta rage wanda ya faru a tsakaninsu."

Wa'iyazubillahi

"Ya zan yi? Haka nan zan shirga musu ƙaryar period ɗina ya zo kafin na gama na san yadda zan yi seducing ɗinsa."

"Gaskiya ya kamata domin hakan kamar wani abin kunya yake son ya ja miki."

"Ya ma isa ina babban yarinya kamata ya ce zai toxarta ni gurin ƙawayena."

"Allah ya kyau abu dai yi daɗi ba." Cewar Wahida cikin takaici.

"Ko gaya mini abin da zan sha."

"Ki sha kanwa za ki samu sauƙi." Ta ce tare da yi mata sallama ta kashe wayar.

Sororo ta yi cikin takaici da damuwa. Sai yanzu ta fara dana-sanin gaya mata da ta yi. Ta so ace ƙarya ta shirga musu sai dai kuma hakan ba zai yiwu ba, kasancewarsu ta san su da shegen bin ƙididdifi har sai sun gano gaskiya.

Miƙewa ta yi tana tunanin inda za ta samu kanwa amma ba ta gani a kicin ɗinta ba.

Wayarta ta ciro tare da sanar mata ta aiko direba da kanwar.

Huwais kiran sallar farko ya tashi farka daga baccin da ya ɗauke shi. Miƙewa ya yi bakinsa ɗauke da addu'ar tashi daga bacci, sai kuma ya yi salati yana miƙa.

Bayi ya shige ya yi wanka sannan ya fito masallacin gidansa. Shi ya ja musu sallah suka yi sannan ya ɗan zauna a masallacin har gari ya yi sha.

A lokacin da gari ya waye ya fito daga masallacin ya shiga gida, daidai lokacin da Wajnah ta fito direba ya kawo mata kanwar.

Cikin rashin sa'a ya kalle ta wanda ya sanya shi ɗauke kansa da sauri. Dariya ƙeta yake mata a zuciya ganin yadda ta yi wujuju da ita, alamun sam ba ta rintsa ba.

Wucewa ɗakinsa ya yi, yayin da ta bishi da kallo tana ji kamar ta jawo shi ta rufe shi da duka. Da idanu ta raka shi har ya shige ɗaki ya rufe ƙofar. Ajiyar zuciya ta saki sannan ta wuce kicin ta kaɗa kanwar a kofi tasha.

Sai a wannan lokacin ta ɗan fara sanun natsuwa ta shiga bayi ta yi wanka da alwala ta fito.

Bayan ta yi sallar tana idarwa ta ɗauki waya ta kira Mommy. Tana ɗauka ta fashe da kuka.

"Mommy, ban san cewar ƙiyayyar da Ya Huwais, ya ke mini ba ta kai haka! In kika ga yadda ya wulaƙanta ni sai kin tausaya mini. Momy kulle ɗakinsa ya ya bar ni a falo."

Tausayin ƴar tata ya kamata da ma ta san xa a rina, wai an saci xanin mahaukaciya. Sam ba ya ƙaunarta su ne suka nace auren.

"Kina jina ko Wajnah? Dole sai kin yi haƙuri kin zama jaruma, domin kin san babu so a tsakaninku. A hankali cikin kissa da kisisina irin ta ƴa mace za ki karkato da hankalinsa."

"Hmmmm! Ba ki san shi bane, jiya na tsorata da lamarinsa."

"Sam karki tsorota ki ci gaba da yi masa duk abin da kika san zai faranta ransa, kuma karki nuna masa kin ji haushi. In muka ga yaƙi canxawa sai mu sanar da mahaifiyarsa ayi wa abin tufka hanci, amma bai kamata daga aurenku afara kai mata ƙorafi ba."

"To Mommy, yaushe za ki zo? Har na fara kewarki."

Dariya ta yi jin abin da ta ce. "Ina nan zuwa ni da Anty ki Hibba, za ta kawo sauran kayan turaren wutan da ba gaba ma."

"Sai kun zo na gode Mommy." Tana gama wayar bacci mai ƙarfi ya kwasheta.

Huwais kuwa alla-alla yake gari ya waye ya bar gidan. Tun da ya farka idanunsa suke masa gizagonta, musamman da ya kwana mafarkinta.

Yana dawowa daga masallaci, ya shirya cikin shiga mai kyau ya shiga motarsa ya fice daga gidan.

Ƙarar buɗe get ɗin, ya tashe ta wanda ya sa ta miƙe a zabure tare da jaye labulen ɗakin tana hangen harabar wajen

"Kan uba! Ina wannan ɗan rainin wayon xai je da safiyar nan?" Ta yi wa kanta tambayar cikin mamaki a zuciyarta tana ji kamar ta danna masa ashar.

Sakin labulen ta yi, daidai lokacin da ya fice maigadi ya rufe get ɗin yana ɗaga masa hannu.

Zama ta yi tana huci kamar mesa, sai kuma ta shige ɗaki fuuu! Ta jawo waya. Har ta fara neman numbar Wahida za ta gaya mata, sai ta fasa tuna yadda take ta cika musu baki, wanda sanin zaman doya da manjar da suke yi, zai iya sanya wa su yi mata dariya, da gulmanta ko da a bayan idanunta ne. Fasa kiran ta yi ta fara neman numbar Ummu sai kuma ita ma wata zuciya ta hana ta musamman da ta tuna maganar da Mommy ta gaya mata.

Wayarta ta yi jifa da ita, tare da kwanciya a kan gadon tana birgima!

Huwais kuwa, a hanya yana tafe yana tunanin yadda za su kwashe da Ummu, in ta ga ya yi sammakon zuwa gidan, amma duk abin da xai faru sai dai ya faru, domin idanuwansa babu wanda suke son gani sai ita. Saboda tsoron kar ya tashi mutanen gidan a waje ya yi parking ɗin motarsa ya shiga ciki. Kai tsaye falo ya shiga, amma babu wanda ya gani sai ɓuruntu da ya ji a kicin. Ba tare da ɓata lokaci ba, ya nufi kicin ɗin domin ya san ita ce a ciki.

Hilah bayan ta tashi ta shiga bayi sai ta ga ta fara fashin sallah. Gyara kanta ta yi, ta fito daga bayin ta shiga ɗakin su Umnah ta tashe su, sannan ta wuce kicin don shirya abin karyawa.

Ita da autar su Ummu, Sauwama suka fara haɗa abincin karyawar suna yi suna hira.

Bayan sun gama kammala abincin, suka sanya a cikin fulas sannan suka sanya wanda za su kai gidan Huwais a basket.

Hilah na gyara zaman abincin yayin da bakinta ɗauke da tasbihi tana faɗin Subuhanallahi wa bihamdihi wa subuhanallahil azeem. Hadisi ne inagacce wanda ya yi maganar cewa,

Kalomi masu sauƙin faɗi a harshe, kuma mafi soyuwa a gurin Allah masu kuma nauyaya mixani.

Da wannan hadisi take amfani yawanci bakinta ɗauke da shi.

Tana ƙoƙarin ɗaukar basket ɗin ta kai mota ta ɗago idanunta.

Turus! Ta tsaya cikin tsananin mamaki tana kallon agogon da ke manne a saman bangon kicin ɗin. Mamaki ya sanya ta kasa magana sai kallonsa take yi.

"Yauwa ma za ki je ki kai mota. Ni ma bari na gama dama wa Fitha custard sai na ɗauko mayafina muje, saboda yau nake son na koma Gobbe.

Jin ta yi shiru ba ta amsa mata ba, ya sanya ta ɗago idanunta, tana kallon inda take kallo.

"A'a ango da sassafe haka, lafiya ko dai Wajnah ce babu lafiya?"

Shafa kansa ya yi cikin jin kunya yana kallonta da har yanzu ta kasa magana.

"Lafiyarta lau, kewar gida ne kawai ya dame ni.

Dariya ta kubce mata jin abinnda ya ce." Daɗi ne ya yi maka yawa kawai Huwais. Kuma in ban da abin ka namiji ne da kewar gida? Ai kamata ya yi a ce Wajnah ta faɗi haka."

"Please Anty Sauwama yunwa na ke ji, ni fa tun jiya rabona da abinci." Ya faɗa yana shafa cikinsa.

Daga ita har Hilah suka zaro idanu."Ace jiya bikinka amma ka zaina da yunwa? Ita Wajnah aikin mai take yi da ba ta tabbatar ka ci abinci ba kafin ka kwanta?"

Taɓe bakinsa ya yi yana ƙoƙarin ɗaukar filet.

Hilah kuwa karɓar filet ɗin ta yi cikin damuwa tana faɗin,"Yayana, don Allah karka ƙara horar da kanka da yunwa."

Watsa mata kallo ya yi bai ce komai ba.

"Kamata ya yi ya tafi da abincin sai su je can su ci, wataƙila Wajnah ba lafiya ba za ta iya musu abin kari ba"

"No bari na ci nawa anan."Ya ce yana kallon Hilah wacce ta daina ƙoƙarin zuba masa, jin abin da ya ce ta fara zuba masa.

Miƙa masa ta yi sai kuma ta fasa ba shi."Bari na kai maka dinning."

Ba tare da ya ce komai ba ya bi bayanta.

"Thanks," Ya furta yana kallonta da ta miƙa masa ta tsaya a gabansa tana kallonsa.

Bayan Sauwama fa gama haɗa wa ƴarta custard ɗin, sai ta ɗauki kofin ta yi cikin ɗakin Ummu wanda anan suka kwana.

Ummu na zaune da carbi a hannunta, tana wa Allah godiya da ya nuna mata auren ta samu guri ta zauna.

Lamarin Huwais sai a hankali." Ta ce tana dariya wanda ya sanya ta juyo da sauri yayin da gabanta ya faɗi.

"Wai shi da yake da amarya, amma har ya baro ta yazo gidan nan yana ihun yunwa."

Gabanta ne ya ƙara faɗi, wanda ya sa ta miƙe cikin ɓacin rai, tana jin kamar ta kifa masa mari.

"Huwais ɗin ya baro gidan matarsa yana nan?"

"Ki je yana falo yana cin abinci kika sheda, don har mun haɗa abin lari za mu je a kai mas..."

Ba tare da ta ƙarasa jin abin da take faɗi ba ta wuce falo da sauri.

Turus ta tsaya cikin tsananin ɓacin rai, tana kallonsa da ya kashe Hilah da ke xaune gabansa tana murmushi.

Tsananin ɓacin rai ya ƙara kamata. Ji ta yi kamar ta rufe su da duka.

"Huwais," Ta kira sunasa da ƙarfi tana huci.

Gabansa ne ya faɗi, amma sai bai ce komai ba ya amsa yana kallonta.

"Mai ya kawo ka cikin gidan nan da sassafe bayan matarka na gida?"

"Ummu, kewarku na yi kuma yunwa na ke ji."

"Huwais, zan yi maka rashin mutunci matuƙar ka ce za ka wulaƙanta ƴar yayata." Ta furta cikin tsananin ɓacin rai wanda ya sanya Hilah ta yi maza ta shige kicin.

"Ummu, laifi ne don na zo gidan nan?"

"Lai fi ne babba, domin yanzu kai magidancinne kuma matarka na buƙatar lokacinka."

Shiru kawai ya yi, cikin takaici domin ya san dalilin da ya sa take faɗa.

Ummu ta buɗe baki za ta yi magana, sai kuma ta fasa ta koma ta ɗauki wayarta da take kan gado.

Numbar Wajnah ta fara kira. Ringing ɗaya biyu ta ɗauka dama tana kwance a saman gado tana hawaye.

"Sakacin na ki har ya kai, ki bari mijinki ya yi sammakon barin gida a washegarin aurenku? Ka da wayewa ta sanya ki kasa kula da mijinki, saboda ga shi ya zo gida yana cin abinci wai yunwa yake ji."

Takaici ya sanya ta rushe da kuka."Ummu, Ya Huwais ya toxarta ni jiya, saboda in kika ga yadda na ke buga ƙofarsa ina kuka ya buɗe mini, amma ya ƙi bayan ya yi mini zagin ƙare dangi ya sanar mini da wacce yake so a zuciyarsa."

Maganarta suka ƙara ninka tashin hankalinta har ta fara ganin jiri-jiri. "Anya yaron nan na da hankali?" Ta yi wa kanta tambayar sai kuma ta kashe wayar fuuu!Ta yi sama tana huci.

"Abu, yaron nan na lura ba zai taɓa nari na na samu sukuni a zuciyata ba. Ina murna na auren da shi hankalina xai kwanta, amma ga shi can a falo yana karyawa Hilah na gefensa."

Wani gumi ya tsatso masa kallonta ya yi da sauri tamkar yana son sanin ko ƙarya ta yi masa.

Gabansa ne ya faɗi da ƙarfi, saɓanin da tun da Ummu take zafafa lamarin sai yake ganin duk da sauƙi matuƙar aka yi masa aure, don shi a ganinsa sha'awace kawai take damunsa ya ɗora kan ƙanwarsa, amma yanzu da yake da matar da zai sauke buƙatunsa sai hankalinsa ya tashi kwatankwacin kayan masarufi.

"Nufinki yanxu yana gidan nan?"

"Ka je ka ganin ma idannunka, wallahi in har ba mu yi wa Hilah aure ba, sai ya janyo mana abin da xai wargaza farincikinmu."

Miƙewa ya yi, ba tare da ya ce mata komai ba, ya zura jallabiyarsa fara ƙal, ya fita wanda ganin haka ta bishi.

Huwais ganin ta yi hanyar ɗakinta gabansa ya faɗi. Shi kansa mamakin ƙarfin halinsa yake yi, domin duk abin da yake aikawatawa yana jin tsoron iyayen na sa.

Gyaran muryar da Abu ya yi, ya sanya shi tashi da sauri gabansa na faɗi ya ce,"Ina kwana Abu?"

"Kana da hankali Huwais? Kan me za ka baro ƴar mutane da sassafen nan ka zo gida?"

"Umm..."

"Bana son sakarci." Ya katse shi yana faɗin haka sannan ya ɗora da ce wa,"Ma za ka tashi ka tafi gida."

Miƙewa ya yi ba don ransa ya so ba zai fice.

"Da kun barshi ya karya, sai in ya so idan ya gama ya kaimu ni da Hilah da ma za ku kai abinci."

"Sai dai ke da su Umnah, amma Hilah za ta yi mini aiki."

"Ai ba daɗewa za mu yi ba ki barta ta je, saboda tun da muka tashi take murna za ta je ganin gidan Yayanta."

Ummu ta buɗe baki xa ta yi magana Abu ya ce,"Ki barta ta je amma kar ku daɗe."

"Ba zan daɗe ba saboda yau na ke son na koma Gobbe."

"Ok, Allah ya kaiki lafiya." Abu ya furta wanda ta amsa da amin sannan ya juya zuwa ciki.

Harararsa Ummu ta yi sai ta juya ta bi Abu.

Sauwama Hilah ta ƙwala wa kira, tare da sanar da ita ta ɗauko mayafinta. Cikin murna ta juya ta shige ciki.

Yana jin da Hilah za su je abincin ya fita a ransa. Ture abincin ya yi tare da faɗin,"Anty Sauwama mu je."

"A,a ka gama cin abincin mana."

"Karki damu na ƙoshi."

Bin sa da kallon mamaki ta yi ganin bai ci abincin da yawa ba.

Azerh da ta ke saukowa daga sama, tana hamnar sauran baccin da bai saketa ba, ta ƙara so da sauri.

"Ni ma Anty Sauwama zan biku, amma sai yamma zan dawo." Ta furta daidai lokacin da ta ƙara so.

"Ok, yi sauri ki ɗauko mayafinki sai ki same mu a mota."

"To," Ta amsa tare da komawa sama da sauri.

Hannu ya sanya ya karbi yarta, sai da suka je gurin mota ya miƙa mata bayan ta buɗe motar ta shiga.

Lakuce mata hanci ya yi, yana dariya ganin yadda take wangale masa bakin da babu haƙora.

Kafin ya tada motar, Hilah ta karɓe ta tana ta yi mata wasa tana dariya.

A mota Anty Sauwama ce a gaba, sai ita da su Umnah suna baya. Tana riƙe da ƴar Sauwama tana mata wasa. Sai satan kallonta yake yi ganin yadda take ɗaga yarinyar sama tana dariya. Zuciyarsa ta raya masa ina ma ace ƴarsa ce.

Yana ta satan kallonta ta madubi, in aka yi rashin sa'a suka haɗa idanu sai ta sakin masa murmushi, shi kuma ya ɗaure fuska yana harararta cikin wasa.

Suna isa cikin gidan, ya yi parking tare da buɗe wa Sauwama murfin mota.

"Yauwa ɗana ashe kana son albarka." Ta faɗa tana fariya.

Harararta ya yi domin kusan sa'oin juna ne, kuma a hannun Ummu ta tashi.

"Kuma fa haka ne bai kamata na rinƙa girmama ki ba, saboda na san lokacin da kike yawo ba wando."

Wani irin dundu ta sakin masa a baya har sai da ya duƙa.


Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).

FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 008144072423





*RANAR WANKA...*



NA



JAMILA LAWAL ZANGO
"JAMCY"



☀️ *First Class Writers Asso* ☀️

Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation


*GARGAGAƊI*

Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️

JAN HANKALI

Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.


SADAUKARWA

Kacokam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a.



PAGE 21

BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM

"Kuma fa haka ne, bai kamata na rinƙa girmama ki, ba saboda na san lokacin da kike yawo ba wando."

Wani irin dundu ta sakin masa a baya, har sai da ya duƙa.

"Kai Anty Sauwama, wallahi tsaf zan iya rama dundun nan, saboda ba ki ji yadda na ji zafi ba."

"Ashe kuwa zan

19 / 23