Advertisements
Chapter 22 Reading Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel Hausa Novels
Advertisements

Kanwar Maza 3&4 Complete Hausa Novel

Author :  Aysha Cool Category :  Complete Novels

Chapter   22 / 67

63K to 66K   out of 199.9K words

Waga kai suka yi ido huWu, da sauri ta koma cikin wurin dinner.

KwaSe fuska rumaisa take yi, tana nema ta yi kuka, Adam ya Wan sunkuyar da kansa ya ce "Meye kuma?".

"Ni na gaji, sai kallona ake yi, kamar wata mara gaskiya, ni bana son kallo, kuma ma yunwa nake ji, ina jin bacci ma kaina ciwo yake yi, na gaji da hayaniyar nan" ta ?arasa maganar bilha??i za ta yi kuka.

"Yanzu a gaban mutanen zaki yi kuka ranar aurenki, salon ace auren dole za ayi miki, ko ki janyo mini zagi ko?"

Tura baki ta yi ta ce "Ba auren dolen bane, ni na ce na fasa, amma aka ?i fasawa, wayyo mama ni na gaji"

A ransa ya ce na shiga uku, wannan Yarinyar tana neman ta jaza mini abun faWa.

Mc kuwa koWasu kawai yake yi, saboda shagwaSa rumaisa take yi, da ya sake fito da yarintarta, ba shiri adam ya din ga ya?e, dan kar a fahimci wani abu.

Abdallah ya hango, yayi masa alama da ya je, adam ya ce masa ya samo abinci ya zo ya bawa rumaisa, kar ta yi masa kuka.

Sai da Abdallah ya dungure mata kai, ya ce "Wace amaryar ki ka ga tana cin abinci a wurin bikinta?"

"Ni yunwa nake ji, ga su hauwwaliya can suna cin abinci, bari na je mu ci tare"

"Dalla zauna na je na samo miki, wai yunwa ranar aurenki dan abun kunya" ya sauka yana mita, ta bi bayansa da harara.

Da ya samo abincin, sai da su Aliyu suka raka shi, suka yi mata rumfa, ba a iya ganinta, Aliyu ya Webi abinci a cokali ya kai bakinta, wai ita ba abinci za ta ci ba, naman za ta ci, gani ta yi an bawa kowa abinci ita ba a bata ba.

Suka din ga zaginta suna bata naman, shi dai adam jinjina kai kawai yayi, ya yi wa Allah godiya da babu wanda ya san wainar da ake toyawa.

An sha hotuna kamar babu gobe, rumaisa ta Waga kai ta kalli Iman da ta zauna a kusa da ita, mai sunan baba yana gefenta aka yi musu hoto.

Hatta ammi ta je wurin, an yi mata li?i sosai da sosai, an ci an sha, manyan mata sun yi rawa sun yi li?i.

Yayyen rumaisa ma da abokansu, haka suka din ga yi mata li?i, wannan ya ja ta nan ayi mata hoto, sai ka rasa waye angon ma a cikinsu.

Adam ma basarwa yayi, ya din ga yi mata li?i, kuWi ba kaWan ba, ta din ga kallonsa ta ga ko yana sane, amma ya?i kallonta kar ta yi wani shirmen. Babban abun da ya fi burgeta, shi ne fareti, da kuma crossing sword Win da abokan aikin su Adam suka yi musu.

Gajiya kam rumaisa ta yi ta, dan har gyangyaWi ta fara, da ?yar take iya buWe idonta, ga takalmi mai tsinin gaske a ?afarta.

Sai sha Waya da rabi na dare aka tashi, rumaisa tana ta sauri ta bi su yaya Abubakar, amma takawa ya sakata a gaba zuwa motar da suka zo.

Tana shiga ta zauna ce "Wayyo Allahana, na gaji"

Ya kalleta yayi shiru, basu je ko ina ba ta hau bacci, gaba Waya ta kife masa a jiki, kai da jin yadda take sauke numfashi ka san ta gaji da yawa.

Sidi ya ce "Sir amarya ta gaji da yawa"

Adam ya ce "Gashi har ta yi bacci"

Sidi ya ce "Allah mai iko, ba zan manta scene Win da ku ka yi making, ranar da ku ka fara haWuwa ba, and she's now your wife"

Adam ya ce "Shhhhh, a daina tayar da wannan maganar"

"Sorry sir"

Adam ya gyara mata kwanciyarta, ya Waukar pose Win ta, ya buWe, ga sababbin kuWi nan a ciki, fal. Ya girgiza kai ya ri?eta a hannun sa.
Rumaisa kuwa jin ta take kamar a kan katifarta, har da gyara kwanciya.

A ?ofar gida ya tarar da yayyenta, suna jiran su ga ta ina za su ?araso, ya sauke glass Win motar, gaba Waya suka ?araso.

"Ta yi bacci fa" ya faWa yana kallon Usman.

Usman ya ce "Ai haka take, da yin magariba take bin bango, a bata ta ci ta yi bacci, kamar ?ar kaza".

Adam ya Wagata zaune da niyyar ya tasheta, amma ina baccinta kawai take yi.

Mai sunan baba daga in da yake tsaye, yana hango cikin motar, rumaisa ba ta san ma me ake yi ba. Haka nan ya ji wani irin kishi ya taso masa, ?anwarsa a kwance a jikin wani ?ato. Takawa ya Waga kai suka haWa ido da shi, ya wani cukule fuska.

Aliyu ya zura hannunsa, ya Wauko rumaisa gaba Waya, ya nufi gida da ita,, da gayya Adam ya fito daga motar, ya ce "Kai Ali ka yi a hankali, kar ka yi mata rauni fa, a kawo mini nakasashshiyar amarya gobe, ba zan karSa ba, da na san bacci za ta yi daga nan ai gida zamu wuce kawai"
Aliyu ya ce "Tuba nake, zan kula sosai"

Juyawa mai sunan baba ya yi, ya shiga gida, ?asan zuciyarsa istigfari, da tunanin meye nasa na jin haushi kuma, bayan komai daWewa dole wataran ta zama matar wani.

Aliyu ya shimfiWe rumaisa a katifar mama, Gwaggo cewa take "Wannan an yi shashasha amarya, haka take da wannan nauyin bacci haka, ta bar mutane da dakonta".

Mama ta ce a tasheta ta yi sallar isha'i, lawisa ta ce sun yi salla a gidan kwalliya, kafin su tafi.

Tana magagin, mama ta dafa ruwa, ta kaita banWaki ta wanke mata fuska, ta yi mata wanka tas, ta lulluSota ta kawota Waki, ?an biki na ta yi mata dariya, sai dai har a cikin ranta ji take ruman ba ta wuce wankan ba, ?addarar aure zata rabata da ?ar da take matu?ar ?auna.

?akin samarin nan kuwa, kusan kwana suka yi babu bacci, suna ta Wan tattaunawa, a kan biki, da kuma jajanta rabuwa da tilon ?anwarsu, kuma kallabi a cikin rawunansu.

Mai sunan baba kuwa ya naWe, ya lumshe idanunsa ya yi shiru, ba abun da yake ganowa sai kai wa da komowar iman a wurin nan, da yadda suke yawan haWa ido. Tsaki ya ja ya nemi wuri ya kwanta, sai dai tunanin gobe dai-dai lokacin, rumaisa na gidan wani, ya hana shi bacci, ya din ga yi mata addu'ar shiga gidan miji a sa'a.


Bayan idar da sallar juma'a, aka Waura auren rumaisa da adam, ?an unguwar da basu san waye mijin ba a ranar suka ji.
Unguwar ta cika da dawakai, da manyan motoci na alfarma, duk in da ka kalla, jami'an tsaro da kuma masu rawuna ne.

Sai dai tun da aka Waura auren nan, rumaisa jikinta yayi sanyi, take ta uban kuka, duk yadda aka so rarrashinta abun ya gagara.


Tuni hotunan biki suka zaga duniya, kowa da abun da yake tofawa, na alkhairi da akasin haka.


Samha kuwa kaiwa take ta yi tana komowa a Wakinta, tana fatan aikin da ta bayar ayi mata, ya yiwu ba tare da samun wata matsala ko akasi ba, dan ta riga ta ?udirce wa kan ta Waukar fansa, ko da tsiya ko da arziki.

Ammi a wani event center, ta shirya taron wunin bikin, sai dai abu ya so ya zama rigima, in da facalolinta da masu goya wa mummy baya, suka din ga ci mata mutunci, wai saboda Aisha ba ?ar ta ba ce, ta shirya irin wannan biki haka, kuma aka samo yarinya mara galihu ta aurawa mahaukacin Wan ta.
Duk yadda ammi ta so jurewa sai da ta kusa zubar da hawaye, Nusaiba ba ta da hayaniya, balle iman, Laila ce masifaffiya dama, kuma ba ta ?asar da ita kaWai ta ishi duk wani mai bakin magana.

Da la'asar mama ta kira ammi, ta ce mata za a kawo rumaisa nan wurinta, ta gaisheta ta yi mata faWa, sannan a wuce da ita gidanta, ammi ta ce ba sai an kawota ba, saboda wasu dalilai, zuwa magariba zata turo da waWanda zasu Wauki rumaisa.

A yammacin aka yi kilisar dawakai, takawa ya haWe cikin kayan sarauta, rumaisa ma aka yi mata ado da alkyabba, aka yi ta musu hotuna.



Da magariba rumaisa ta yi wanka, ido duk ya kumbura saboda kuka, Yasir da ya shiga ya fita ya ga tana kuka, shi ma sai ya fashe da kuka, ta tashi ta saka kaya ma abu ya gagara mama sai daurewa take yi, amma hawaye ya cika mata ido.

Jiki a sanyaye mai sunan baba ya shiga Wakin, ya tarar da ita a zaune, tana kuka mai taSa zuciya.

"Rumaisa" ya kira sunanta, ta Waga kai ta kalleshi.

"Tashi ki saka kayanki, kar dare yayi sosai".

"Dan Allah mai sunan baba ku yi ha?uri, wallahi na fasa ni ba zan tafi na barku ba, mama dan Allah ku yafe mini ku barni na zauna a gida, ni ba zan iya rayuwa babu ku ba" tayi maganar cikin kuka.

"Tom, mun ji, amma fara saka kayan" da ?yar ya saka kaya, ya ciro turare a aljihunsa ya fesheta da shi, mata sai rangaWa guWa ake yi.

Ta ri?e mama tana wani irin kuka.

Ya saka hannu ya cire nata daga jikin mama, ya ja hannunta yayi waje da ita.

Suna fita mama ta shiga Waki, ta fashe da kuka, dan an kai in da ba zata iya jurewa ba.

Suna tafe a mota tana kwamce a jikin mai sunan baba, tana ta kuka, kamar ta shiWe.

"Am sorry, kiyi ha?uri haka lamarin aure yake, da haka kowace mace take tara nata iyalin, Ubangiji Allah ya baku zaman lafiya, ya sanya alkhairi. Ban da rashin kunya da raina miji, mijinki ne ibada zaki je ki yi, ki nemi aljanna na san duk an gaya miki, ki girmama mahaifiyarsa, matar nan ina ganin mutuncinta saboda son da take yi miki. Sannan kuma Sabir ko Allah ya baki naki Wan, kar ki canza soyayyar da ki ke yi masa, ki yi ha?uri ki saka a ranki, ?ofar sabon ?alubale zaki buWe ki shiga. Duk da ?an?antarki nauyin aure ya hau kanki sai ha?uri, kiyi ha?uri, ki yi ha?uri, ki jure ki daure duk ?alubalen da zaki fuskanta wataran sai labari, ina yi miki addu'a Allah ya sassauta miki jarrabawar gidan aure, don babu auren da babu jarrabawa"
Haka ya din ga yi mata nasiha, har suka je gidan, gida ya tsaru kamar ba na rumaisa ba, ko ina ya ji kaya.

Ana kai rumaisa wata ?anwar ammi, ta sake saka mata alkyabba a kan kayanta, suka din ga yi mata guWa a ka, amarya ?anwar maza, dan su suka kawota Wakin ma.

Sun daWe tare da rumaisa, kowa da irin faWan da yake yi mata. Sai da kowa ya watse, Tawagar angwaye suka ?araso, gida ba kowa sai tsirarin mutane da zabga-zabgan ?arti.

Suna zuwa mai sunan baba ya tashi ya ce su tafi.
Rumaisa ta ri?e rigarsa ta tashi tana kuka "Dan Allah yaya umar, kar ku tafi ku barni, ku tafi da ni, ko ku zauna da ni a nan Win, dan Allah yaya. Yaya usy, yaya Abubakar, dan Allah duk ku zauna, Abdallah kar ku tafi, Yasir dan Allah" mai sunan baba duk ya kaWa musu kai alamar su tafi.

Iman tana cikin waWanda suka rage, gaba Waya tausayin rumaisa ya cika mata zuciya.

A hankali ya fincike rigarsa daga hannunta, ya juya, ta sake ri?o rigarsa.

Ya juya a kausashe ya ce "Wuce ki je ki zauna" a razane ta saki rigar ta sa tana kuka.
Yana juyawa sai hawaye, karo na farko da abu ya daki zuciyarsa ya saka shi kuka. Ya saka hanky ya goge, ya kalli Adam ya ce "Ga ta nan amana ce, marainiya ce, ko ka ci, ko kula da ita" yayi maganar wasu hawayen na cika masa ido.

Adam har mamaki yake, wace irin soyayya suke nuna wa rumaisa haka.

Bashir ya ce "Za a ri?e amana in sha Allah. YallaSai aje a rarrasheta dan Allah, tana cikin damuwa".

Adam ya ce "Sai ma ka faWa? Ba daga ni sai ita zaku tafi ku bari, wannan kuma ya rage nawa" dariya abokansa suka yi, suka yi musu addu'a sannan suka watse.

Ya koma ya shiga Wakin na ta, tana tsaye tana ta kuka, ya ?are mata kallo sannan ya ce
"Yau sarki mai koriyar alkyabba, ya baki alkyabba saura Wana ki a kan doki. Sannan ke kuma ki cika al?awarin sanya shi dur?usa miki a kan gwiwoyinsa".


What's app only please =?O?
Ayshercool.
0808101214
*Paid book ne, ? 500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu bu?atar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book Win. Kar ku manta da subscribing YouTube channel Winmu na Cool hausa novels, domin samun daWaWan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ?anwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel Win*


Wani mugun kallo rumaisa ta yi masa, ta ture hannunsa da yake gyara mata zaman alkyabbar jikinta, ta ce "Ba ruwanka da ni, kuma ka zo ka mayar da ni gidanmu".

"Ni na kawo ki? Sai ki fita ki koma ai, tun da bani na Wauko ki ba".

"Kuma wallahi sai na tafi, ko ka sani ko ba ka sani ba".

Hannunsa ya saka, ya matse mata kumatu, ta saka hannunta ta ri?e hannunsa, saboda azabar zafin da ta ji.
Ya sake kallonta ya ce "You better behave yourself, a gidana ki ke, fita ki bar mini Waki, wancan Wakunan zaki Wauki Waya, da safe zan saka a kwashe miki tarkacenki, a mayar miki can" ya ?arasa maganar yana sakar mata baki.

"Ba in da zani, tun da dai na ga kayan da aka sai mini ne a ciki"

"Kayanki ne, amma gidana ne, sai na kwashi kayan naki na mayar haraba, ki je can ki ?arata" ya yi maganar yana wucewa cikin bedroom Win.

Ya rage kayan jikinsa, ya shiga banWaki.
Har yayi abun da zai yi ya fito, rumaisa tana tsaye, tana kuka.

Ya je yayi salla, ya wuce ta ya je kitchen, ya dawo amma tana tsaye. Nan ya sake sarawa taurin kan rumaisa.

Har ya gama cin abun da zai ci, tana tsaye ?yam, ta juya masa baya, ya kashe fitila, ya kunna A.C, ya kwanta, gajiyar biki da zirga-zirga ya sanya yana kwanciya bacci mai nauyi ya Wauke shi.

Rumaisa gajiya ta yi da tsayuwa, ga tsoro da ta fara ji saboda duhu, ga sanyin A.C yayi mata yawa, dan ba ta saba ba, ta nemi wuri ta kwanta a ?asa, ta du?un?une a cikin alkyabbar ta hau bacci.


Mama kuwa yadda ta ga rana, haka ta ga dare, dan babu wani abu mai kama da barci da yayi shirin Waukar ta.
Haka ma ?an mazan nan, Aliyu cewa yake "Allah ka rufa mana asiri, Allah ya sa kar yayi mata wani, abu yarinya ce ?arama wallahi".

Usman ya ce "To yanzu mu kake gaya wa ko yaya?"

"A'a addu'a kawai nake yi"

Mai sunan baba duk da yana cikin damuwa, amma jin abun da suka faWa da ya haWa ido da Abubakar, kawai Abubakar ya tuntsire da dariya, mai sunan baba kuwa murmusawa yayi, tare da basarwa kamar bai ji me suke faWa ba, haka suka kai har wurin ?arfe biyu, suna hira yadda biki ya gudana, da kuma jimamin ya rumaisa za ta kasance a gidan aure.


Samha ma haka daren nan yayi, ta kasa rintsawa, duk da sun yi chatting da Fauziyya, tana ta rarrashinta, ta tura mata hoton bikinsu Adam.
Amma kasa tsayawa ta yi ta kalla, saboda yadda zuciyarta ke matu?ar tafasa da wani irin masifaffen kishi.
Ko lokacin da ya auri Aisha, ba ta shiga wannan yanayin da take ciki a yanzu ba.



Sai da aka kusa idar da sallar asuba, sannan Adam ya farka, a gaggauce ya shiga banWaki, yayi alwala, sai da ya ga ba zai samu salla ba ko ya fita, dan haka ya ce bari kawai yayi sallarsa a Waki.
Ba tare da ya kunna fitilar ba, ya tayar da salla, bayan ya idar ya din ga jin kamar numfashin mutum, har gabansa ya faWi, dan ya Wauka irin razana shin da aka saba yi ne, ya tashi ya kunna swtich Win Wakin, mai zai gani, madiga ce a kwance take ta uban baccinta, abun ka da a gajiye take dama, duk ta cukuikuye alkyabbarta.


"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ke wai a nan ki ka kwana?" Yayi maganar yana taSa ta.

Oho bata san yana yi ba, bacci kawai take yi.

"Tashi, ki je ki yi salla" nan ma bata tashi ba.

Toilet ya shiga ya Webo ruwa, ya dawo ya zuba mata a fuska.

A rikice ta tashi tana faWin "Huzaifa meye haka wai?".

"Na hauzaifa bane Adam ne, ban ce miki ki bar mini Waki ki tafi ga naki can ba"

Maimakon ta yi magana, sai ta haWe rai tana kallonsa, kamar mafarki take yi ma ba a zahiri ba.

Ganin ta tsareshi da ido, ya sanya ya tashi, ya ri?e hannunta ya yi waje da ita, Waya bedroom Win ya kai ta, ya juya ya tafi ya barta.

Kallon Wakin ta yi, wasu furnitures Win ne a ciki ba nata ba, amma sun yi kyau sosai da sosai.

Ta cire Alkyabbar, ta shiga ta yi alwala, ta fito babu hijjabi. Ta koma Wakin da aka fara kai ta, wato Wakin da Adam ya ce nasa ne, ta buWe drower ya Wau hijjabi, yana zaune yana kallonta, sai murguWa baki take ita kaWai tana harare-harare.

Ta koma Wakinta, ta yi salla, ta idar ko addu'a ba ta yi ba, ta je ta haye kan gadon, ta ji katifar gadon, mai tauri, ta kalli Wakin sai ?amshi yake yi, ta tashi ta yi tsalle a kan katifar, amma taga ba ta lotse ba.

"Allah sarki, zan cewa mama ta dawo gidan nan mu din ga kwana tare a kan katifar nan, su yaya Abubakar kuma sai su Wauki Wakin ?asa, ko shi baban sabir ya koma ?asa, su dawo saman bene, mu yi zamanmu" ta yi maganar tana kwanciya, saboda baccin da yake kanta.


Sai da ta yi mai isarta, sannan ta tashi daga baccin, ta sauko daga kan gadon, tana son ta wanke bakinta, amma babu komai a toilet Win.
Ta fito ta shiga zazzaga saman benen tana kallon yadda gidan yayi kyau, aka tsara shi.

Shiru ta Wan yi tana tunanin mama, da su Huzaifa, ba ta yi aune ba sai hawaye, wani na bin wani, ta din ga gogewa ta ce "In sha Allah sai na fita na koma gida".

"Sai zuwa yaushe zaki yi wanka ki sauya wannan kayan,

22 / 67