Advertisements
Chapter 5 Reading EL-HABEEB by OUM HANAN BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

EL-HABEEB by OUM HANAN

Author :  OUM HANAN Category :  Complete Novels

Chapter   5 / 21

12K to 15K   out of 61.8K words

shiga wata hirar daban.



Yauma kamar kullum kuma kamar yadda ta saba zuwa masa cikin barcinshi yauma haka yau kuma sai
mafarkin nashi ya canza salo dan a yau d'in da kanshi yakai hannu da nufin cire mata mayafin data
lullub'e fuskar tata dashi amma baici nasara ba duk yayin daya kai hannu da nufin tab'ata saiyaji wani
mugun shocking ya kamashi dole yake janye hannunshi da sauri haka dole ya k'yaleta yanaji yana gani ta
juya ta tafi harta b'acewa ganinshi daga nan ya farka daga barcin.

Cikin tsananin b'acin rai ya farka a yanzu wani haushin yarinyar yakeji yadda ta hanashi sukuni a
rayuwar shi yarasa uban da zaiyi mata da kullum saitazo gareshi kuma tak'i yarda yaga fuskarta wannan
wace irin masifa ce?.

A gaggauce ya shiga bathroom yayi wanka yana k'ara jin haushinta ko makarar nan dayayi ita ta jaza
masa.

K'ananun tsaki ya dinga saki lokacin dayake shiryawa cikin k'ananun kaya blue black d'in jeans da black
shirt body hook sai bak'in takalmi sawu ciki simple kwalliya ce amma ba k'aramin kyau yayi ba kayan sun
amsheshi matuk'a musamman daya toshe idanunshi da black space wanda bawai yasashi dan gayu bane
sai dan b'oye idanuwanshi da kallo d'aya za'ayi musu a gane yana cikin damuwa bayason kuma a
dameshi da tambaya saikuma hakan yabada citta 🤩.

Designer's kala kala ya faffesa masu bala'in k'amshi da sanyi sannan ya fita zuwa gaishe da Ummi bayan
ya rufe kofar side d'in nashi.

Kasancewar tasan alhamis ne yana yin azumi shiyasa ma batayi masa tayin breakfast ba bayan sun gaisa
sun d'an tab'a hira ya tashi yayi mata sallama ya fita.

Tunda su Aleeyu sukaga yanayin ogan nasu suka san yau a sama yake yafi mu'amala da farin glass duk
ranar dayasa bak'i kuwa to kuwa kayi hankali dashi dan zai iya sauke maka dan haka suka dinga kaffa
kaffa kowa yana kiyayewa.

Koda suka shiga kamfanin ma da ma'aikata na gaisheshi ko hannun dayake d'aga musu ma basu samu
ba a ranar kai tsaye ya wuce ta elevator ma yabi ranar sab'anin da da kullum yake hawa lifter ba wanda
dai yayi masa magana tunda dai sun rabu dashi lafiya saikuma idan ya sauko.

Su kansu y'an kamfanin duk wanda yake da appointment dashi a ranar saida yayi hak'uri dan abinda
bai taka kara ya karya ba saiya hau mutum da bala'i hatta Mujaheed ranar saida yayi taka tsantsan dashi
baisan uwar da akayi masa ba yake ta musu wannan botsare botsaren.
Yaso ya masa iya shege amma ba dama saboda mutanen dake wajen da kuma yadda ya wani had'e rai
bazakace yasan wani abu dariya ba duk da dai dama bawai yinta yake ba yafi yin murmushi shima saiya
dad'e baiyiba.

Lokacin da suka fito zasu tafi bayan ya tashi aiki a dak'ile yacewa Aleeyu ya fad'awa sauran bodyguard
d'in su wuce zasuje wata unguwa shida Aleeyun baya buk'atar rakiyar kowa, cikin rawar jiki Aleeyu yaje
ya sanar dasu ga abinda yallab'ai yace daga nan ya shiga back seat Aleeyu ya shiga driver seat ya tada
motar yaja suka tafi batare dayasan inda zasuba gashi yanajin tsoron tambaya.

Sai dayaga dai sunata tafiya har lokacin baice masa ga inda zasuba sannan yayi ta maza yace

"Yallab'ai ina muka nufa?".

Saidaya d'auki y'an mintuna sannan kamar mai ciwon baki yace

"ShopRite".

"Kaji wata rigimar kuma, me zaije yayi kuma a ShopRite? shidai iya saninshi duk wasu abubuwan
amfaninshi musamman ake yimasa order d'insu bai cika using dana nan k'asar ba amma dan fitina yace a
kaishi kome zai siya?. Dole ya canza hanya ya d'auki titin dazai sadashi da shopping mall d'in.

Koda suka k'arasa ma sukayi parking bai fitaba gashi dai yana gani anzo amma ko alamun fita bashi
dashi, sam Aleeyu bai tanka masa ba suka cigaba da zama a haka. Kamar ance d'ago kanka ya hango
wasu saurayi da budurwa sun fito daga cikin Mall d'in sai dariya suke yarinyar cikin matsattsun kaya
k'ananu da siririn gyale data d'an yafashi akan tulin gashinta ta manna bak'in google wanda ya kusa
mamaye rabin fuskar tata, wani irin bugawa gabanshi yayi ganin kamar yarinyar nan datayi masa rashin
kunya ya kuma ganta a gidan Hajiya cikin azama ya cire glasses d'in fuskarshi yana k'ara k'ura mata ido
da tunanin kodai kamanni suke da waccan d'in to amma abin mamakin komai na k'irar jikinsu iri d'aya so
yake ta cire glass d'in idonta yadda zai gane itace koba itaba.

Kamar tasani kuwa takai hannu ta cire glass d'in ta mak'alashi a gaban matsattsiyar rigar dake jikinta sai
faman taunar chewing gum take tana murmushi alamun yanayin datake ciki yana mata dad'i, sosai
Habeeb Gashua ya zaro ido ganin yarinyar ce dama ashe tantiriya ce? to uban meya kaita gidan Hajiya?
lips d'inshi ya cije tareda lumshe idanunshi yana d'an sauke numfashi, yana bud'e idanunshi yaga har sun
shiga mota sun hau kan titi.

Cikin zafin nama ya b'alle murfin motar ya fito ya bud'e front seat yana yiwa Aleeyu alamu ya fito daga
motar, zai tsaya tambayar shi ya daka masa tsawa da sauri Aleeyu ya fito shikuma ya shiga yabata wuta
kafin ya figeta da uban gudu yabi bayan motar wannan saurayi da budurwar batare daya tsaya saurarar
Aleeyu daya rud'e yake tambayar shi lafiya ina zaije?

Tsaye Aleeyu yayi yabi bayan motar da kallo yadda ogan nasu yake bata wuta tamkar yana filin tsere ne
ya rasa abinda yake damunshi yau d'in nan da sauri shima Aleeyun ya tare mai napep ya shiga ya nuna
masa motar Habeeb dake can nesa dasu yace ita zai dinga bi dole yabi yabi bayanshi mana tunda hakk'in
kula da lafiyar shi yana hannunshi.
Haka nan yaji zuciyarshi na masa bala'in zafi ganinta dayayi dawani saurayin ga yanayin shigarta sam
babu nutsuwa da kamun kai a cikinta cije baki kawai yake yana sakin k'ananun tsaki da tunanin wai me
ma yasa yake binsu ne? meye damuwarshi da ita haka? ina ruwanshi da ita? duk wad'annan tarin
tambayoyin bai samu nutsuwar dazai bawa kanshi amsar suba burinshi kawai ya samesu to idan ma ya
samesu d'in me zaice musu? me zaice musu a matsayin amsar tambayar da zasuyi masa na dalilin dayasa
yake binsu? wata mota dake gabanshi yaso karawa saboda gudun dayake yayi gaggawar kauce mata
wanda anan ne motar dayake bi ta b'ace masa b'at rage gudun yayi yana k'ara hahhangawa kozai ganta
saidai ba ita ba alamar ta.

"OH my God". yace da k'arfi yana lumshe ido gamida dukan sitiyarin motar da k'arfin gaske cikin
tsananin b'acin rai da takaicin rasasu d'in dayayi.

Gefen titi ya gangara yayi parking ya fito daga motar, hannu d'aya yasa ya rik'e k'ugunshi d'ayan kuma
ya cusashi cikin tulin lallausar sumar kanshi mai azabar santsi da laushi yana yamutsa ta kafin ya kaiwa
motar duka da k'afarshi wanda yayi daidai da saukar Aleeyu daga napep ko canji bai tsaya karb'a daga
wajen mai napep d'in ba ya nufi inda Habeeb Gashua yake tsaye cikin takaici.

"Boss are you okay?". yace a rud'e yana kallon jikinshi da fatan dai wani abu bai tab'a lafiyar shiba.

"Let's go". yace yana cilla masa car key d'in batare daya bashi amsar tambayar dayayi masa ba, cafewa
Aleeyu yayi, da kanshi ya bud'e motar ya shiga shima Aleeyun ya shiga ya tada motar suka tafi.

Kishingid'a yayi a bayan motar ya rufe idanunshi gam yana hasko abinda ya faru yanzu ko zuwa zaiyi ya
tambayi Hajiya WACECE wannan yarinyar? to kuma kar tayi tunanin wani abu ne a ranshi har yakeson
sanin ita wace to wai duk meye ma nasa tunanin yarinyar a ranshi da har zai hana kanshi sukuni gefe
d'aya kuma ga ta cikin mafarkin nan.

"Yaa ALLAH". ya furta hakan can k'asan zuciyarshi yana shafo k'eyarshi zuwa dokin wuyanshi dake
cikeda kwantaccen k'ananun gashi.



Gareku reader's, Heedayah ce kokuma wata ce daban??? A kafta.



Maryam Ibraheem Aleeyu

(Ummee).

Mrs Salees Mu'az 💝




*EL--HABEEB* 💥
©️Oum Hanan.



*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡

(Home of expert & perfect writer's)



No 9.



Har suka k'arasa gidan bai bud'e ido ba, koda sukayi parking Aleeyu yaga bashida haramar fita daga
motar yadda yake a hakan nan kuma tsoron yimasa magana yake sai dayaga zaman nashi yak'i k'arewa
sannan a hankali yace

"Oga mun k'araso fa".

Batare daya bud'e ido ba yayi masa alama da hannunshi ya tafi kawai fita yayi ya rufe motar yabar wajen
yana fatan koma dai meye ALLAH ya sauk'ak'awa maigidan nasu damuwarshi.

Sai bayan wani lokaci sannan ya fita ya shiga cikin gidan duk da baiso shigar ba saboda yadda yanayin
shi yake amma kuma ya riga ya saba yana dawowa saiya dangana da inda Ummi take. A hargitse ya
shigarwa Ummi ko sannu da zuwan da Neehlah take masa baiji ba baima ganta ba sam, tsareshi Ummi
tayi da tambayar lafiya kuwa me yake damunshi? lafiya k'alau yace mata kawai yanayin aikine ya gaji ne
sosai ba yadda batayi dashi ba akan ya fad'a mata idan wani abun ne yace ba komai dan haka tace ya
tashi yaje yayi wanka ya huta tashin yayi ya fita ta bishi da kallo can k'asan ranta bata yarda da abinda
yace mata ba.



Ranar ko abinci kasa ci yayi dama kuma ba ma'abocin cin nashi bane sai coffee daya dinga d'urawa
cikinshi da zafinshi da komai, wanka yayi ya d'aura alwalah yayi sallah raka'a biyu kamar yadda ya saba
kullum kafin ya kwanta sai yayi. jallabiyyahr dayayi sallahr da ita ya cire yasa pyjamas milk color masu
kauri cikin nutsuwa ya karanto addu'ar kwanciya barci ya kwanta, yana kwanciya kuwa tunanin yarinyar
ya addabeshi daya rufe ido da niyyar yin barci saiya hangosu itada wannan saurayin lokacin da suke
dariya.

Da k'yar yasamu barci ya d'auke shi da tunanin ta lokacin da barcinshi yayi nisa kuma yarinyar data saba
zuwa masa cikin barcinshi tazo abu biyu ya had'e masa, wani irin barci yayi a ranar marar dad'i shiyasa
akan kunnenshi akayi kiran sallahr asubah na farko tashi yayi yana jin jikinshi duk ba k'wari wanka yayi
yasa jallabiyyah ya fesa turaruka sannan ya wuce masjeed.
Bayan dawowar shi bai koma barci ba sai Alqur'ani mai tsarki daya d'auka yafara rairo karatunshi cikin
daddad'ar murya dakuma k'ira'ar shi irin ta Mohammad Alkhusary mai dad'in gaske.

Barcin dabai komaba kenan dan lokacin daya gama karatun gari yayi haske sosai dan haka yayi wani
wankan yafara shirin office.





Tun daga ganin yarinyar dayake tsammanin Heedayah ce yake hange hangen inda zai ganta a kullum
idan ya fita ya tsiri zuwa gidan Hajiya akai akai sab'anin da dayake d'iban kwanaki kafin yaje ko ALLAH
zaisa ya ganta amma bai k'ara ganinta ba kuma bawai zuwan ne batayi ba saidai sab'ani da suke samu
wani lokacin data fita zai shigo kokuma idan shi yagaji da zaman ya fita itakuma tazo duk yabi yahana
kansa sukuni shi kanshi a karan kanshi idan aka ritsashi akace saboda me yake nemanta bai saniba
baisan me zaice ba kuma ya kasa tambayar Hajiya labarin yarinyar.



****

Ummi ce zaune akan royal chair d'in da sukayiwa had'add'en falon k'awanya sai k'amshin turarukan
wuta ke tashi na asalin larabawa, gefenta Mujaheed ne zaune a k'asan tattausan carpet d'in dake malale
a k'asan falon sai d'aya gefen nata Habeeb ne shima a zaune a k'asa kowanne kanshi a k'asa. Kallonsu
Ummi tayi d'aya bayan d'aya kafin ta tsaida kallonta kan Habeeb tace

"Abbuna Mujaheed ya kawomin k'ararka me yake faruwa ne?".

Kamar bazaiyi magana ba saikuma yace

"K'ara ta kuma Ummi?".

"Yes" ta amsa masa, kai ya d'an d'aga ya jefawa Mujaheed wata uwar harara yace

"Me yace nayi Ummi?".

"Yayi min complain akan yanzu ka daina maida hankalinka gaba d'aya aka aikinka sun rasa gane kanka".

B'ata rai yayi sosai yace

"Ki daina yarda da maganar yaron nan Ummi munafuki ne so yake kawai ya had'ani dake". Ido
Mujaheed ya zaro tareda dafe bakinshi yana kallon Habeeb wanda yayi mirsisi kamar bashi ya fad'i
maganar ba ya juyar ma da kanshi gefe yana faman kumbura baki.

"Babu wani zancen had'i ko munafunci ni kaina shaida ce kuma nasha tambayar ka abinda ke damunka
saboda nakasa gane kanka a y'an kwanakin nan meye damuwarka ne Abbana". tace cikin rarrashi tana
shafa kanshi, ido ya d'an lumshe yace
"Ummiiii babu komai fa kawai dai......."Wllhy k'arya yake Ummi ko last week saidaya janyo mana
babbar asara a kamfani ko k'arya nayi?". Mujaheed ya katse Habeeb yana hararar shi.

"Asara kuma? wace iri?". Ummi ta tambaya.

Zama Mujaheed ya gyara yace

"Ummi wasu bak'i ne mukayi daga Abuja mun dad'e muna tsumayin zuwansu anata shirye shiryen
zuwansu dayake wannan ne first time da zamuyi hark'alla dasu kuma akwai tarin alkhairai da mukesa
ranshi ta dalilinsu, a ranar da zamuyi zaman dasu kowa ya hallara a d'akin taro damu dasu anata jiranshi
ya fara magana kinsan me yayi Ummi?". Kai ta girgiza kawai, saida Mujaheed ya harari Habeeb da shima
yake hararar shi, cikeda takaicin abinda yayi musu ranar yace

"Wllhy Ummi d'an bawan ALLAHn nan kawai saiya tallafe hab'a ya d'ora d'aya kan d'aya yana kallon
kowa d'ai d'ai dayake d'akin taron ko A baice ba, danaga haka nayi masa magana yak'i kulani sannan
wani daga cikin ma'aikatanmu shima yayi masa magana yak'i kulashi shine sai d'aya daga cikin bak'in
namu wani yayi magana dan sunfara gajiya da zama ga shugaban taro kuma baice komaiba, kamar jira
yake wllhy Ummi ya hau kan mutumin nan da bala'i wai zai koya masa aikinshi ne daya dad'e yana yi ya
dinga masifa duk ya hargitsa d'akin su kuma sukayi fushi sukayi tafiyarsu muka rasa wannan damar, sai
gashi har ana rirrik'eshi wai zaiyi fad'a da mutumin, Ummi bansan meya canza Gashua haka ba mutumin
dayake da salihi ko hayaniya baiso amma yanzu Ummi idan ya zage yana bala'i baza kice shi bane ya koyi
wani zafin rai da masifa dan mutumin dayayi magana daga ma'aikatar tamu ranar da abin yafaru saidaya
bashi suspension wai ya rainashi har yanzu bai dawo dashi ba". Mujaheed ya k'arasa maganar yana
kallon Habeeb da tunda ya fara maganar yake cije baki yana hararar shi baki ya tab'e yana d'an d'age
kafad'a alamun ko a jikinshi.

"Haka akayi babana?". cewar Ummi tana kallonshi, rasa abin cewa yayi sai k'asa dayayi da kanshi yana
shafa k'eya.

Cikin b'acin rai Ummi tace

"Kanaso raina ya b'aci ne a kanka?". Da sauri ya girgiza kai batare daya yi magana ba.

Kai ta kad'a tace

"To ka maida hankalinka kamar yadda kake a baya banaso in k'ara jin labarin ka k'ara yin wani abu dazai
dinga ja muku asara a kamfanin ku saboda amana ce a hannunka, abinda duk yake damunka kuma
ubangiji ALLAH yayi maka maganin shi tunda bazaka fito ka fad'amin ba a matsayina na mahaifiyarka". A
marairaice ya d'ago kai zaiyi magana ta dakatar dashi ta hanyar d'aga masa hannu tareda fad'in

"Ya isa haka tashi kuje ALLAH yayi muku albarka".

Ba musu duk suka tashi suka fice, Habeeb ne a gaba Mujaheed na biye dashi a baya suna fita Habeeb ya
nufi side d'inshi da sauri Mujaheed ya mara masa baya ko waigowa baiyi ba bare ya kalleshi yana shiga
ya zube kan kujera ya d'age kanshi sama yana kallon roofing falon da adon fitilun da aka k'awatashi dasu.
"Meya shigo dakai nan?". yace lokacin da Mujaheed ya shigo falon batare daya d'ago kaiba.

"Abinda ka shigo yi kaima?". Mujaheed ya fad'a hankali kwance yana zama kusa da Habeeb d'in,
d'agowa yayi yana fad'in

"Malam get out tun kafin in sauke fushina a kanka". dariya Mujaheed ya k'yalk'yale da ita yace

"Ka dad'e baka sauke fushin naka ba a kaina Gashua yau bazan bar gidan nan ba saika fad'amin dalilin
canzawar ka kodai har yanzu baby dream d'inka ke caza maka brain ne?". Shirun da Habeeb yayi yasa
yagane eh hakan ne da gaske canzawar shi tanada alak'a da yarinyar dake zuwa masa cikin mafarki
k'aramin tsaki Mujaheed yaja yace

"Kuma dan ubanka saika dinga zuwa kana sauke mana, wadda zata caza maka k'wak'walwa daban mu
kuma daba ruwanmu saikazo kana sauke mana kwandon masifa".

Kai ya d'ago tareda lumshe idanunshi yana sauke numfashi gamida shafa sumar kanshi abubuwan duk
sun had'u sun cakud'e masa ya yini yana tunanin yarinyar gidan Hajiya idan dare yayi kuma ta cikin barci
tazo masa sun sashi a tsakiya ba dole aga canji a wajenshi ba?.

Mujaheed duk saiyaji tausayin d'an uwan nashi kuma abokinshi ya kamashi a hakan ma kuma baisan da
labarin yarinyar zahiri ba, kafad'arshi ya dafa cikin taushin murya yace

"I'm so sorry Gashua ka cigaba da addu'a bata bar komai ba, ni kaina daba ni nake mafarkin nan ba abin
ya fara damuna wlhy I'm sorry My brother". Kai kawai Habeeb ya jijjiga masa yana had'iyar wani yawu
mai d'aci.

"Tashi kaje ka shirya mu fita kasan yauma munada wani zaman da zamuyi saura kuma kaje kayi crossing
legs kana kallon mutane d'ai d'ai ubanka zanci wllhy". ya k'are maganar yana dariya.

"Nida kai zanga mai cin uban wani d'an iska kawai". Habeeb ya fad'a yana mik'ewa tsaye ya wuce
makeken bedroom d'inshi dan yin wanka. Bai dad'e ba ya fito cikin shigar manyan kaya sabuwar shadda
ce fara k'al sai yarari take da d'aukar ido ko gwiwar shi rigar bata k'arasa ba tasha wani uban aiki da ash
color d'in zare hakan yasa ya murza hula zanna wadda ta hau da zaren da akayi aikin sai takalmi mai
mad'auri irin na maza shima ash color sai farin glass daya manna wanda ya k'ara fito da kyawun dayayi
agogon dake mak'ale a hannunshi ma na fata ash ne sai wani azababben k'amshi yake fitarwa wanda ya
karad'e dukkan falon tun kafin fitowarshi duk da girmanshi kuwa, fitowarshi yasa Mujaheed dake rik'e
da waya a hannunshi ya d'ago kai ya kalleshi y'ar dariya yayi yace

"Wow Masha ALLAH so beautiful yanzu wazai ganka yace akwai wadda ke firgita ka cikin barcinka
gaskiya koma wacece na jinjina mata". ya k'arasa maganar yana mik'ewa tsaye tareda salute kamar wani
d'an sanda.

"Useless man". Habeeb yace yana binshi da harara yayi gaba yana d'auko wayarshi a aljihun gaban rigar
wadda tafara wani sautin kid'a mai mai dad'in gaske alamun kira ne ya shigo ya fice yana amsa kiran
Mujaheed ya bishi yana dariya.
Afwan babu yawa 🙏.

Kwana biyu za'a jini shiru sakamakon biki dazamu fara gobe in ALLAH ya kaimu saikuma bayan biki
insha ALLAH.

Nagode.




*EL--HABEEB*💥



©️Oum Hanan.



*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡

(Home of expert & perfect writer's)



Alhmdulillah munyi biki lafiya antashi lpy nagode sosai da addu'oen ku dafatan ALLAH yaba ango da
amarya zaman lafiya dauwamamme ya kad'e dukkan fitina a cikin aurensu dama sauran wad'anda suka
angwance muna musu fatan alkhairi.



No 10.



Kwanaki sun cigaba da tafiya yayin da har yanzu dai bata canza zani ba game da irin mafarkin da
Habeeb Gashua yake, kuma har yanzu dai bai k'ara had'uwa da wannan yarinyar ba wadda kullum
tunanin

5 / 21