Author : OUM HANAN Category : Complete Novels
ta yake caza masa k'wak'walwar kanshi yasha komawa ShopRite d'in ko ALLAH zaisa ya ganta
amma ko mai kama da ita bai tab'a gani ba. Aleeyu yana mamakin abinda yake dawo dasu Mall d'in
tunda tare suke zuwa kuma basa shiga saidai yasashi yayi parking a waje yana kallon masu shige da fice
duk da dai bai fad'a masa ba yasan wani abun yake nema kuma da alamu abinda ya tab'a gani kwanaki
har ya bishi a mota shiyake dawo dashi gurin koma dai meye ALLAH ya kawowa maigidan nashi mafita
gaba d'aya ya wani sukurkuce ya hana kanshi sukuni.
Yau kam shi kad'ai ma yadawo Mall d'in bayan sun koma gida daga office ya k'ara yin wanka ya fito duk
suka taso danyi masa rakiya kamar yadda suka saba ya dakatar dasu har Aleeyun ma dasuke fita tare yau
dakatar dashi yayi yace baya buk'atar rakiyar kowa dan haka aka bud'e masa mota ya shiga yabar gidan.
Ya dad'e zaune cikin mota yana raba idanu kan mutane masu shiga da fita amma dai har yanzu zancen
d'aya ne babu ita babu alamar ta, idanunshi ya lumshe tareda luma hannunshi cikin sumar kanshi ya
shiga yamutsa ta lokaci d'aya yana fesar da wata zazzafar iska daga bakinshi wanda hakan yabawa
daddad'an k'amshin mouth freshner d'in dayayi amfani dashi fitowa mai k'amshin banana, da sauri ya
bud'e idonshi kamar wanda akace yayi hakan ya k'urawa wata Range Rover fara datayi parking ido haka
nan ya tsinci kanshi da son ganin mai fitowa daga cikin motar, koda motar tayi parking ma saida aka
dad'e ba'a fito ba hakan kuma baisa ya d'auke idanunshi daga kai ba gabanshi na wata irin fad'uwa daya
rasa dalilin yinshi.
Luckily idanunshi suka hasko masa hoton wannan yarinyar ta fito daga motar, yau shigar atamfa ce tayi
saidai an ciwa atamfar mutunci wajen d'inki saboda yadda duk ta fito da tsarin halittar jikinta gashi
bawani mayafin kirki d'an siriri ne ta rataya shi a kafad'arta, lips d'inshi ya cije cikeda b'acin rai ganin irin
banzar shigar datayi, kai tsaye ta wuce cikin Mall d'in cikin wani irin taku na yanga da jan hankali tana
k'ara gyara side bag d'inta dake rataye, bayanta yabi da kallo cikin jin haushin yadda take bayyana surar
jikinta kowa na kallo jiyake tamkar ya janyota ya koya mata hankali.
Fita yayi shima daga motar yabi bayanta yana d'ora P. Cap d'in daya fito da ita a hannunshi a kanshi,
koda ya shiga ciki baiga alamunta ba sam, tsaye yayi ya tura hannayenshi duka a aljihun wandon jeans
d'in dake jikinshi yana wuwwurga idanunshi ko zai hangota. Can gurin turaruka ya hangota a tsaye tana
dubawa, cikeda karsashi ya nufi wajen yana zuwa kusa da ita yaja birki ya tsaya dan baisan abinda zaice
mata ba, jin alamun mutum a kusa da ita yasa ta d'an juyo sam batayi tsammanin ita yake bi ba dan haka
tayi gaba tana k'ara duddubawa shima yabi bayanta, ganin dai da gasken ita yake bi yasa ta tsaya ta juyo
idanunsu suka had'u waje d'aya yayin da bugun zuciyarshi ya k'aru itakuma nata yafara daga lokacin.
"Malam lafiya kuwa? me kake nema ne a wajena da kake ta bina tun d'azu?". Cikin tsiwa da rashin
kunya tayi maganar tana masa wani irin kallo duk da yadda gabanta yake fad'uwa wanda kallon cikin
idanun Habeeb ya haddasa mata.
Sosai ya had'e rai ya k'ara matsawa daf da ita murya ba alamun wasa yace
"Meya fito dake da irin wannan shigar? meye yasa bakya kishin kanki ne?".
Sakato tayi tana kallonshi cikeda mamakin abinda yace ikon ALLAH sai kallo bata tab'a ganin mutum ba
yazo kuma ya tsareta yana tuhumarta to me yake nufi?
"Bakya jine?". yace a zafafe yana bud'e mata idanu, wata uwar harara ta sakar masa tace
"Kai dallah malam ya isheka haka ya zakazo kana tuhuma ta batare dana san kai d'in wanene ba daga
jin maganar ka ma hausa bata isheka ba alamu sun nuna kai ba d'an k'asar nan bane dan haka ka
gaggauta komawa k'asar ku ka nemo yarinyar dakake nema". ta k'are maganar da jan wani mugun tsaki
tareda sakar masa harara tayi wucewarta tana cigaba da taunar chewing gum d'in dake bakinta.
Tsaye yayi ya kasa katab'us shi bai juya ya fita ba haka kuma bai bita ba ya shiga duniyar tunani. Gaskiya
shima kanshi yafara tunanin wadda yagani a gidan Hajiya daban sannan wannan ma daban idan ya canka
daidai su d'in twins tunda gashi nan ba abinda ya rabasu da waccan d'in to amma meyasa yaga waccan
cikin shigar kamala da mutunci wannan kuma gani biyun dayayi mata duk ba shigar arzik'i ce a jikinta ba.
"Bambancin ra'ayi". wani sashen na zuciyarshi ya amsa masa, kai anya kuwa? kodai ita d'in ce take so
tayi masa wasa da hankali tayi masa BASAJA shiyasa ta nuna ba ita bace.
"Oh my God". ya fad'a cikin tsananin damuwa yana lumshe shanyayyun idanunshi da suka canza kala,
baisan iya adadin mintunan daya d'auka tsaye a wajen ba yayi zurfi cikin tunani daga bisani ya fito daga
cikin Mall d'in koda yakai dubanshi inda motar data ajiyeta take ba komai alamun har sun tafi kenan.
Cikin mutuwar jiki ya k'arasa inda motarshi take ya shiga yabar wajen da gudu ranshi a b'ace.
★★★___★★★
A yau datake ranar alhamis bayan la'asar Habeeb Gashua yakaiwa wani wani orphanage house
ziyara wato gidan marayu dake cikin garin Kano, daga shi sai Mujaheed saikuma Aleeyu dake driving
d'insu.
Sanye yake cikin shadda light blue d'inkin zamani baisa hula ba sai tarin sumar kanshi datasha gyara
take ta zuba k'yalli k'amshi kuwa ba'a maganar shi lafiyayyen k'amshi ne mai sanyi da sanya nutsuwa ke
tashi a duk ilahirin jikinshi, ya manna siririn farin glass wanda ya k'ara fito da kyawun shi.
Kasancewar an san da zuwanshi yasa duk wasu masu ruwa da tsaki na gidan marayun sun hallara
dayake wannan shine karo na farko dazai fara zuwa da kanshi basu tab'a ganinshi ba sai tarin alkhairan
shi dake riskar su ako da yaushe suna matuk'ar jin dad'in yadda yake taimakawa marayu da tallafa musu
dan haka sukayi shiri na musamman dan tarbar wannan bawan ALLAHn.
Suna isa aka zagaye motar su, kowa kagani cikin farin ciki da annashuwa fitowar Habeeb daga mota
yasa suka k'ara fad'ad'a fara'ar fuskar su suna masa sannu da zuwa shi kanshi bai san lokacin daya d'an
saki fuskar tashi ba sab'anin da datake cunkus da ita ya shiga gaggaisawa da mutane.
Gidan marayun suka shiga zazzagayawa kamar yadda ya nema dan ganin abubuwan da suke da buk'ata
sun shiga hospital d'insu da school da sauran gurare duk inda yaga sunada buk'atar gyara ya kanyi
magana tun a wajen tareda yimusu alk'awarin gyarawa insha ALLAHU sunyi murna k'warai da gaske suka
shiga godiya da fatan gamawa da duniya lafiya.
Check ya rubuta musu a lokacin yabasu bayan kuma gyaran da yayi alk'awarin yi musu, lokacin kam
kasa magana sukayi suka rasa bakin godiya hak'ik'a wannan bawan ALLAHn ba mai saka masa sai ALLAH,
ubangiji yana son a farantawa maraya.
Har bakin motarshi suka rakoshi suna k'ara jaddada godiyarsu da yiwa iyayenshi addu'a wanda yake
tsananin jin dad'in hakan yana matuk'ar son yaji ana yiwa iyayenshi addu'a yakan tsinci kanshi cikin farin
ciki mara misali, d'aya daga cikin masu kula da marayun ne yace bari a kirawo wasu daga cikin yaran suyi
masa godiya sam baiso tsayawa ba suka rok'eshi ya tsaya suma suna son ganinshi. Saida Mujaheed yasa
baki sannan ya hak'ura ta tsaya.
Kanshi a k'asa yana danna wayarshi yaji hayaniya da maganganu, duk da haka bai d'ago kaiba har suka
k'araso suka fara gaisheshi bai amsa ba sai daya kashe wayar ya maida cikin aljihun gaban rigar shi
sannan ya d'ago kai da niyyar amsawa idanunshi suka fad'a cikin na yarinyar nan tana sanye da k'aton
hijab har k'asa mai hannu ruwan zuma fuskarta d'auke da mayalwacin murmushi wanda ya k'awata
fuskar tata sosai saboda jin dad'in ganin wanda yake tallafa musu a yau d'in shiyasa murmushi ya kasa
barin kyakkyawar fuskarta.
Wani irin fad'uwar gaba ne ya ziyarci Habeeb cikeda tsabar kad'uwa yasa hannu ya fige glass d'in
idonshi ko shine bai gwada masa daidai ba still dai itace tsaye cikin sauran yaran tana magana da wata a
kusa da ita, da wani irin sauri ya shiga ratsawa ta cikin yaran dayake daga can k'arshe take daga yaran
har manyan sai aka bishi da kallo cikeda mamaki.
Tsaye yayi a gabanta yana k'ara k'are mata kallo, a kwanakin baya yayi tunanin ko twins ne amma
yanzu yafara zargin yarinya d'aya ce take raina masa hankali, tuni idanunshi suka kad'a sukayi jawur,
yarinyar kuwa jikinta ne ya d'auki rawa ganin irin mugun kallon dayake jifanta dashi wanda batasan
dalilin yi mata shiba baya ta d'an ja kad'an saboda yadda suke daf da juna dashi ya k'ara binta yana fad'in
meya kawota gidan marayu kuma? kota fad'a masa kokuma yasa a d'aureta tunda ita munafuka ce,
girgiza masa kai kawai take yayin da idanunta suka cika taf da ruwan hawaye so take tayi magana amma
ta kasa saboda tsabar tsoron mutumin daya mamayeta lokaci d'aya.
Kowa na wajen idanunshi na kansu an rasa kuma wanda zaije yayi masa magana sai Mujaheed ne ya
kutsa kai ya isa inda suke yasa yarinyar mutane a gaba sai wasu zantuka yake mata wanda ta kasa
fahimtar su hakama mutanen dake wajen ba wanda yasan ko akan me yake maganar, kafad'arshi ya dafa
yace
"Wai Gashua menene haka? me yarinyar nan tayi maka ne koka santa ne?". Mujaheed yace bayan
k'arasawar shi wajen.
Hannu yasa ya cire hannun Mujaheed dake kafad'arshi ya k'ara binta inda ta d'an matsa yace
"K'yaleni da ita kawai MJ,. yarinyar nan munafuka ce tantiriya ce nan da kake ganinta kuma wllhy saita
bar gidan nan a yau". ya k'are maganar yana jifanta da wata muguwar harara, ido Mujaheed ya zaro
yace
"Are you mad Mr Gashua?".
"Eh d'in mahaukaci ne ni Mujaheed". yace cikin d'aga murya.
M&S💝
*EL--HABEEB*💥
©️Oum Hanan.
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)
Jama'a kubi Habeeb Gashua da addu'a yana neman zaucewa😅🤣 Humayrah taki ta sameki fa sweetyn ki
ya sukurkuce ya kamata yaga likitan k'wak'walwa 😂.
No 11.
K'ara rik'oshi Mujaheed yayi yana fad'in
"Please Gashua ka tsaya muyi magana ta fahimta mana me kakeyi haka ne?". fisge jikinshi yayi daga
rik'on da Mujaheed yayi masa idanunshi sun kad'a sunyi jawur jijiyoyin kanshi duk sun tashi, ganin abin
dai babba ne yasa sauran manyan gurin suka nufo inda suke suna tambayar shi lafiya meyake faruwa rai
had'e yake kallonsu yace
"Dole ku kori yarinyar nan idan ba hakaba duk sai nasa an d'aureku". kowa na wajen mamaki ne ya
rufeshi akan me zaice sai an kori yarinya daga ganinta.
Mujaheed daya fara fusata cikin d'aga murya yace
"Wai yaushe ka zama mara imani ne Gashua? idan baka tausaya mata a matsayinta na marainiya ba ai
bai kamata ace ka cusguna mata ba".
"Malam ya isheka haka, kayi shiru da bakinka tunda bakasan abinda yake faruwa ba". Sosai yarinyar
take kuka duk gaban hijabinta ya jik'e da ruwan hawaye tunanin ta d'aya ta yaya ya santa har yake fad'ar
wasu maganganu akanta wanda bata tab'a sanin su ba tafi tsammanin dai wata ce suke kamanni da ita
ya d'auka waccan d'in ce.
Duk yadda suka so su nunawa Habeeb yadda al'amarin yake sam ya kasa fahimta ya zage sai bala'i yake
wanda wasu dayawa daga cikin mutanen wajen ba fahimtar abinda yake fad'a suke ba sun tsinci kalmar
dai dole a koreta ita sukafi ganewa cikin maganganun dayake.
Sarai sun san waye HABEEB IBRAHEEM GASHUA sun kuma san waye mahaifinshi duk da baya raye lallai
idan har basuyi abinda ya umarce su suyi ba zasu iya jazawa kansu dan haka suka amsa masa da to
zasuyi abinda yace d'in.
Kuka yarinyar take sosai wasu y'anmata kamar ta suna tayata kukan tunani take idan har tabar gidan
marayun nan ina zata dosa? wata sani gaba d'aya a duniyar nan banda y'an gidan marayun wad'anda ta
bud'i ido ta ganta tare dasu ashe mugu ne mutumin nan basu saniba in har yayi sanadiyyar barinta gidan
nan bazata yafe masa ba dan ya d'auki alhakinta bataji ba bata ganiba.
Batayi zato ba taji ya kama hannunta k'iiii da uban sauri ya shiga janta har zuwa bakin gate d'in gidan
ya tura ta ya maida gate d'in ya rufe, gaba d'aya ido y'an wajen suka zuba masa an rasa mai yin magana
ko ya dakatar dashi dama kuma Mujaheed ne mai k'arfin halin yin hakan shikuma ya tsunduma duniyar
tunanin anya kan Habeeb d'in bai kwance ba kuwa? to idan ba kwancewar kai ba ya daga ganin yarinya a
gidan marayu sai kora ina tausayi da imanin shi suka tafi da har ya aikata wannan aikin?.
Wata kujera ya samu ya zauna yayi k'asa da kanshi tareda rufe idanunshi gam kanshi na wani irin
juyawa tsabar tension dayayi masa yawa ya rasa ta inama zai b'ullowa lamarin da gaske ne yarinyar nan
FUSKA UKU gareta sai taje ta gama tantirancin ta a waje sannan ta dawo gidan marayu to meye amfanin
zamanta a gidan marayun yana so yasan wacece ita me kuma ya kaita gidan Hajiya?
Wani daga cikin manyan gidan marayun Mujaheed yasamu yayi magana dashi ta fahimta da nuna masa
kar su damu insha ALLAHU zata dawo dama a kwanakin nan sun rasa gane kanshi su kwantar da hankalin
su, daga nan ya sallamesu suka watse cikeda alhini musamman k'awayen nan nata su biyu da har lokacin
kuka suke.
Bayan kowa ya watse Mujaheed da Aleeyu suka k'araso inda Habeeb ke zaune har yanzun bai d'ago
kanshi ba, kusa dashi Mujaheed ya zauna yana fad'in
"Lamarin ka yafara bani tsoro Gashua ya daga taimako kuma zaka b'ige da wannan aiki? dan ALLAH ka
fad'amin damuwarka ko akwai shawarar da zan iya baka ko zata iya zama mafita a gareka".
Ci kanka Habeeb baice wa Mujaheed ba bai kuma d'ago ya kalleshi ba, yasan bazai kulashi d'in ba dan
haka yace ya tashi to su tafi magreebah takawo kai, nan ma banza yayi masa sai dayaga dama dan kanshi
bayan dogon lokacin da suka d'auka a wajen sannan ya d'ago kanshi fuskar nan a cunkushe, a razane
Mujaheed yayi baya yana zaro ido saboda yadda yaga idanun Habeeb ya canza yayi wani irin ja na ban
mamaki Aleeyu ma dake tsaye saida yaji tsoro, bai kula kowa ba ya tashi ya nufi inda motar tasu take
duk saurin da Aleeyu ya dinga yi dan ya bud'e masa motar bai samu dama ba yana zuwa ya bud'e ya
shiga Mujaheed da Aleeyu suka shiga Aleeyu ya tada motar suka bar farfajiyar gidan.
Tunda suka tafi babu mai magana Mujaheed yasan ko yayi masa magana ba tankashi zaiyi ba a wannan
lokacin dan haka yaja bakinshi ya tsuke cikin ranshi tunanin ta yadda zai dawo da yarinyar yake batare
da Habeeb ya sani ba.
Sun d'anyi nisa da gidan marayun can gabansu ya hango yarinyar tsugune a gefen titi ta mak'ure waje
d'aya da alamu kuka take, sosai tausayin ta ya kamashi gaskiya Habeeb bai kyauta ba wllhy in haka ne
meye amfanin taimakon daya yiwa gidan?
"Yi parking Aleeyu". Mujaheed yace yana kallonshi, parking d'in yayi kuwa kamar yadda ya umarce shi,
juyowa yayi ya kalli Habeeb daya kishingid'a idanunshi a rufe yace
"Dubi yarinyar can Gashua abin tausayi shin baka tausayawa maraicinta ne? kokuma baka gudun
ubangiji ya kamaka da hakk'inta? ina rok'on ka Gashua dan ALLAH dan alfarma da martabar annabin mu
kayi hak'uri inje in maida yarinyar nan gidan can baka tunanin duk halin data fad'a a yanzu kaine sanadi?
please and please Gashua".
Ido ya k'ara runtsewa sosai tsigar jikinshi na tashi saboda girman abinda Mujaheed ya had'ashi dashi,
shi wanene da za'a had'ashi da girman ALLAH da ANNABI ya juya baya? ai saidai idan bashi da damar yin
abun, kuma akwai tunanin daya d'arsu a ranshi yanzu bayan barowar su gidan marayun wanda idan
yarinyar tana can aikin zaifi zuwa masa da sauk'i fiye da ace bata gidan ( A tunanin ku me zai aikata
reader's??? ).
Kai ya kad'awa Mujaheed alamun amincewa batare da kuma ya bud'e idanunshi ba.
"WOW thank you very much abokina ALLAH ya saka maka, bari inje". Mujaheed ya fad'a cikin tsananin
farin ciki ya fice daga motar cikeda zumud'i dan sam baiyi tunanin Habeeb d'in zai amince da sauri haka
ba sanin halinshi da yayi na muguwar kafiya da shegen taurin kan tsiya.
Can d'aya side d'in ya tsallaka inda take, ya k'arasa wajenta bakinshi d'auke da sallama, da sauri ta
d'ago kai tana kallonshi kukan datake yasa ko sallamar tashi bata amsa ba ta maida kanta k'asa ta cigaba
da kukanta mai tab'a zuciya ga duk mai imani, y'an sakanni ya d'auka yana kallonta kafin ya durk'usa a
gabanta cikin taushin murya yace
"Kukan ya isa haka, munyi magana dashi zan maidake". Cikeda farin ciki ta d'ago kai tana kallonshi tasa
hannu tana share hawayen idanunta tana murmushin jin dad'i cikin rawar murya tace
"Nagode".
"Never mind". ya amsa mata shima fuskarshi d'auke da murmushi da wani irin tausayin yarinyar.
"What's ur name?". ya tambaye ta.
*"SEEYAMAH*"
"WOw nice name, Seeyamah". yace yana k'ara maimaita sunan, tashi sukayi suka jera yana janta da hira
har cikin gidan marayun dayake ba nisa sosai sai daya damk'ata a hannunsu sannan ya fito ya dawo
wajen motar ya shiga suka tafi.
I'm so sorry ba yawa afwan hidima ce dayawa 🙏.
Rashin comments dinku yasa gaba d'aya labarin yafara fita a kaina wllhy daga wannan page din bazan
k'ara wani ba gaskiya sai naga yanayin comments dinku bawai rashin aikin yine yasa muke rubutun nan
ba naga kamar labarin bai muku ba.
Mrs Salees Mu'az 💝
*EL--HABEEB*💥
©️Oum Hanan.
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)
No 12.
Saida suka fara biyawa ta gidansu Mujaheed suka saukeshi sannan suka wuce.
******
Zaune yake kan kujera bayan yagama shan coffee'n nashi na k'aidah, daga shi sai farin boxer ya hard'e
k'afafunshi dare ne sosai dan k'arfe biyu ma ta kusa ya gaza samun barci sam sau biyu yana kwanciya
barcin yana gagarar shi dan haka ya tashi ya shiga bathroom ya d'auro alwalah yazo ya gabatar da
nafilah raka'a hud'u yayi addu'oen shi ya had'o coffee ya zauna kan kujera ya shiga sha duk da irin turirin
dayake fitarwa haka yasha yana k'ona masa baki sai kace dole, bayan ya gama sha kuma yayi zaune yana
sak'a da warwara kan abinda ya dace yayi duk da dai tun cikin mota ya gama yanke hukunci kan abinda
zai aikata saidai yana ganin kamar ba daidai bane abinda shirin yin amma a halin yanzu dai bashida wata
dabara data wuce yayi hakan idan ma mutum d'aya ce zai sani koma dai meye zai