Advertisements
Chapter 20 Reading Fansar Ƙauna Juyin Soyayya by HADIZA D. AUTA BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Fansar Ƙauna Juyin Soyayya by HADIZA D. AUTA

Author :  HADIZA D. AUTA Category :  Complete Novels

Chapter   20 / 29

57K to 60K   out of 85.8K words

bakinsa ya ji caraf an
riƙe masa hannu. Kafin ƙamshinta ya daki hancinsa ya yi hanzarin ɗaga kai ya kai kallonsa saman
kyakkyawar fuskarta.

"Nurrrrrr!"

Ya ambaci sunan cikin ƙaraji saboda ganin ta a lokacin da bai yi zato ko tsammani ba.
An zo wurin🥲


GARE KU MASU TAMBAYA!
Littafin FANSAR ƘAUNA na kuɗi ne. Ku biya ₦500 kacal ga wannan account. 9032685442 Opay. Waɗanda
tura kuɗi ta opay yake bai wa wahala ku tura ta Bank Account; 1230094555 Access Bank Hadiza D. Auta
Ibrahim.

JERIN LITTAFAINA GA MAI BUƘATA!

1. ABOKIN AIKINA 1K
2. BAƘON YANAYI 1K
3. DAKAN ƊAKA 1K
4. AMFANIN FITILA 1K
5. JIKI DA JINI 1K
6. GIDAN AURE ₦700
7. TARTSATSI 1K
8. MAKANTAR SO 1K
9. ZUBAR HAWAYENA ₦700
10. RUWA DA ƘANƘARA ₦700
11. BAKAN GIZO ₦700
12. MUSAYAR ZUCIYA ₦500
13. DIJE ƘARANGIYA ₦500
14. DACE DA JUNA ₦500




D.
✍🏼 AUTA CE
[2/20, 22:17] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*

*HADIZA D. AUTA*

*AREWABOOKS: Princessdija.*

https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa


*ASHIRIN DA HUƊU.*

Da ido ta yi masa magana kamar yadda ta saba a kan cewa tabbss ita ce ba gizo ba. Hanzarin miƙewa
tsaye ya yi bakinsa yana rawa tare da nuna ta da hannu ya sake cewa,

"Da gaske ke ce nake gani ko a cikin mafarkan da kika saba zo mini ne ko yau ma?"

Wani tsadadden murmushi ta yi wanda ya saka kansa sarawa, babu shiri ya runtse ido tare da dafe saitin
zuciyarsa saboda ƙaƙƙafan bugun da take yi. Cikin hanzari ta riƙe shi ta baya, tare da yi masa katanga da
jikinta. Yayin da ta yi maganar da ke tabbatar masa da tabbas ita ce, kuma wadda ta nan take ya fatattaki
kokwanton da zuciya ke yi masa.

"Babu wani mafarki Jaan! Ni ni ce dai Nur."
Saukar zazzaƙar muryarta kenan a lokacin da ta daki dodon kunnensa, bayan tsadadden murmushin da
take jifar sa da shi, wanda hakan ya jawo masa jirin da ya so jefar da shi ƙasa ba tare da ya shirya ba.

"Ba na son sanabe! Me ye haɗin ki da shi?"

Zulaiha ta yi maganar a fusace tare da buge mata hannun da ta riƙe shi gudun ya faɗi. Saboda haushi da
takaicin da suka haɗe mata wuri ɗaya a kuma lokaci ɗaya. Tsabar ganin samu fili amma rashi ya nemi kulle
mata ƙofar nasara. Hakan ya sa kallon mamakin da Nur take yi mata ya ƙara ɓata mata rai ta shiga auna
mata harara tare da nuna ta tana faɗin,

"Tun da kika hana shi cin abincin, kuma kika yi sanadin da wani ya zube ƙasa; wallahi sai kin biya mu
kuɗinmu don ba za mu yi asara b..."

Wata kalar dariya mai cike da tura haushi Nur ta yi, kafin ta fito daga bayan Jamal bayan ta zaunar da shi
a kan kujerar da ya tashi. Taku ta yi a hankali cikin ƙasaita har ta isa gabanta tana faɗin,
"Ki saka wa ranki cewa daga yau kin ƙulla ƙawance da asarar da kike gudu. Duk da ban so na fito miki a
irin wannan sifar ba, amma sanin halinki da kalar hatsabibancinki; na zaɓi yin ƙwaƙƙwaran shiri tun kafin
zuwan wannan ran.."

"Me kike nufi? Kina magana cikin isa da gadara tamkar kin jima da sani na, ko kuma na yi miki babban
laifin da kika kama ni dumu-dumu."

Nur ta sake yin wani guntun murmushi tare da dafa kafaɗarta ta ce, "Kwantar da hankalinki ƙawata,
mene ne abin firgita tun yanzu kafin mu shiga fagen buga wasar? Ni fa na ɗauka a yadda kike gwanar
jarumta kin shirya taron aradu da ka a kowane lokaci...hummm!"

Ta ƙare maganar tana zagayen ta kafin ta koma kan plate ɗin abincin da ta ajiye wa Jamal ta yamutsa shi
da cokali tana faɗin,

"Abin da kika zuba a cikin abincin nan nake so ki yi bayani da bakink..."

"Kin yi kaɗan ki zo har wurin aikina ki nemi cin zarafina! Me na zuba da za ki yi mini ƙazafi bayan ban san
ki ba kuma ban taɓa ganin ki sai a yau, yau ɗin ma a yanzu da kike ƙoƙarin manna mini sharr..."

"Sharri? Sharri fa kika ce?" Sai da ta yi wata 'yar dariya sannan ta girgiza kai tana faɗin,

"Ni A'isha ba na sharri alheri nake sadawa. Hakan ya sa na baro ƙasata takanas na zo Nigeria saboda kare
Jaan daga sharrink...."

"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un! Wai ke mutum ce ko aljan? Ni fa gabaɗaya kin tayar mini da hankali na
kasa yarda da mace iri na nake magana ko macen aljana?"

Zulaiha ta yi maganar tana nuna Nur da hannu tare da ja baya tana zaro ido, tsabar tsoro da fargaban da
ya yi mata mugun lulluɓi, haɗi da gumin tashin hankalin da ya gama fesowa a jikinta tamkar an watsa mata
ruwa.

"Saurin me kike yi, ke da za ki ga komai a idonk ..?"

"Me zan gani? Ni fa wallahi ban san ki ba kuma ban san na yi komai b.."

"Yanzu za ki sani?"
Nur ta waiga gefenta, tare da nuni ga wani ma'aikacin wurin ya ƙaraso cikin rawar jiki. Umarni ta ba shi da
ido ya shiga danna wayar da ke hannunsa, fuskarta a cure ta karɓa ta kai kallonta a kan wayar kafin ta cira
kai ta kai kallon ta ga Zulaiha da ke tsaye tana waige-waige. Tsabar ruɗewar da ta yi tare da sabon tashin
hankalin da ya yi mata ƙawanya. Gabanta ta isa duk da ja bayan da take yi har ta jingina bango ta tsaya.

"Duba da kanki, sai kin tabbatar ke ce ko za a ɗauki matakin da ya dace da ke."

Nur ta yi maganar cikin wata kalar murya tana dariya tare da miƙa wa Zulaiha wayar ta ƙi karɓa. Saboda ta
gama sarewa da lamarin Nur, kuma ta karɓi laifinta ba tare da wahalar da shari'a ba. Don ƙin karɓar wayar
bai hana ta furta kalaman da ke nuna ta aikata abin da Nur ke tuhumar ta ba. Saboda kai-tsaye ta haɗe
fuska tana haɗiyar yawu tare da goge gumin da ke feso mata a kan fuska ta ce,

"Idan ma ni ce ai ba ki san dalilin da ya sa na aikata ba. Sannan kuma duk ƙoƙarin da kike yi a kan so.
tozarta ni ba ki isa ki ce guba ce na zuba ba. Don haka ko ina aka je zan faɗa ba guba na zuba masa a cikin
abincin ba, idan kuma kina tantama yanzu zan ci abincin don ki tabbatar ba na kisa, kuma babu niyyar a
cikin rain..."

"Yi mana shiru!"

Shugabar Restaurant ɗin ta buga mata tsawa cikin tsananin ɓacin rai, hakan ya ta shanye sauran maganar
da ba ta gama amayowa ba. Ta shiga sosa kai tana muzurai duba da yadda wurin ya cika da mutane kowa
yana kallon ta.

"Kin ba ni kunya Zulaiha. Yanzu duk halaccin da na yi miki da irin wannan sakayyar za ki yi mini? Ki tuna
lokacin da kika zo wurin gwanin ban tausayi kina neman aiki na ɗauke da zummar taimakon ki. Ashe
tsintacciyar mage ce ke wadda ba ta mage! To daga yau kin daina aiki a wurin nan, kuma zan koya miki
hankali a kan ɓacin sunan da kika jawo wa masana'antata. Wadda na rayu da ita sama da shekara goma
cikin gaskiya da rufin asirin Allah. Amma a yau kina neman lalata mana tsari...to ba ki isa ba..ranka ya daɗe
a tafi da ita kawai har zuwa lokacin da zan neme ku."

Hajiya Inno mai abinci, ta ƙare maganar fuskarta a cure saboda ɓacin ran da Zulaiha ta ƙumsa mata.

"Don Allah Hajiya ki yi haƙur..."

"Babu wani haƙurin da zan yi da ke, saboda lokacin da kika shirya munaƙisarki ban sani ba. Kuma idan na
bar ki ban san iya wanda za ki cutar a sanadin aikin ba. Gara kawai ki tafi hannun jami'ai su sanar da ke
bambancin riƙon amana da riƙe gaskiya tsakani da Allah."

Ihu Zulaiha ta fasa a daidai lokacin da ta ga 'yansanda sun zagaye ta.

"Babu wani shaiɗan! Ai ba yau kika fara ba. Kin jima kina yin abin da kike so kawai asirinki ne yau ya ton.."

"Ko aljana ce ke sai na ga bayanki wallah.."

Zulaiha tana maganar ta yi kan Nur cikin zafin nama da nufin kai mata bahagon mari, sai dai kafin ta isa ta
fara jin ɓarin makauniyar kalolin mari a kan fuskarta. Hakan bai yi masa ba sai da ya yi cikin ta da harbin
ƙafa yana ta ƙwallo da ita, yayin da aka samu majiya ƙarfin da ke wurin suka rirriƙe shi, inda ya fara aman
magana cikin matsanancin fushi yana nuna ta da hannu yana faɗin,

"Duk ranar da hannunki ya sauka a jikinta da sunan duka sai na jijjige shi a mazauninsa na wurgar. Kuma
ko da wasa na sake ganin ki a inda duk nake sai na ɗauki mummunan mataki a kank..."

"Wallahi ina son k.."
Zulaiha ta yi maganar cikin kuka tare da ɗaga murya a lokacin da 'yansanda suka kai mata wawuya tana
ƙoƙarin tashi ta yi kansa.

"Allah Ya tsine wa irin wannan son naki da babu komai a cikin sa face haɗari. Don abincin da kika zuba
masa da ya ci Allah ne kaɗai ya san me zai faru, saboda kin saba cutar mazan mutane don ba yau kika fara
haɗa musu tarko ba. A tunaninki kin isa da kanki saboda bokayen da kike biya suna yi miki ƙulunboto kina
wasa da rayuwarsu, hakan ya aa kika zaton shi ma za ki yi nasara a kansa? Kin kuskure, don kin yi shuka a
idon makwarwa. Saboda duk abin da kika tura wa 'Yan Ajin Tubarakallah Group duka na gani kuma na ji
duk zagi da cin zarafin da kika yi kuma kika sa aka yi wa Minal. Sannan na bi diddiginki na gano shirin da
kike ƙoƙarin yi a kansa, wannan dalilin ya sa na hana kaina zama har sai da na tabbatar na kama ki da laifin
hannu dumu-dumu. Saboda ki gano ba kowane lokaci Allah yake dafa wa mutum a kan zalunci ba. Kuma
ina so na karya alkadarinki ko don ki gano ba a fi kare iya kwanciya ba sai dai a nuna masa lulluɓi da bargo.
Sannan faɗuwa tana farawa ne daga ba zan iya ba, amma ke taki faɗuwar ta fara ne tun daga lokacin da
kika yi iƙirarin tabbatar wa duniya cewa, kin kai kuma kin isa wanzar da duk abin da kike so kuma a lokacin
da kika ga dama. Ina miki fatan hakan ya zamo babban darasin da za ki tuba ki dinga bar wa Allah komai
tun kafin mutuwa ta ɗauke ki kina zaluntar mutane."

Daga haka 'yansanda suka wuce da Zulaiha tana muzurai bayan sun saka mata ankwa, ta yi wa Nur wani
kalar kallo mai ɗauke da ma'anoni da yawa tare da ƙwafa tana cije leɓe.

Nur ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi sannan ta kai kallonta ga Hajiya Inno, minti biyu bayan wucewar
'yansandan da Zulaiha, ta sake cewa,

"Na gode sosai Mama, da kika ba ni damar gano gaskiya a kan wannan baiwar Allah. Ubangiji Ya ƙara
girma kuma ya ƙara yi wa kasuwa albarka da ma'aikatanki gabaɗaya. Ni zan wuce saboda jirgin ƙarfe biyar
zan bi na koma gida."

"Babu komai 'yata Allah Ya yi miki albarka, kuma Ubangiji ya kai ki gida lafiya, tun da na karɓi lambarki ai
za mu dinga zumunci."

Taku ɗaya biyu ta yi da nufin ficewa daga Restaurant ɗin Jamal ya yi hanzarin riƙo hannunta. Kallon kallo
suka shiga yi wa juna tsawon sakonni kafin ya yi jarumtar faɗin,

"Ina za ki je?"

Cike da mamaki ta bi shi da kallo bakinta a sake tana cewa, "Zan koma gida ne, saboda na gama aiwatar da
abin da ya kawo n..."

"Ba zai yiwu ba! Ke ma kin sani ba zan bar ki ki sake yin nisa da ni ba."

Shiru ta yi na ɗan lokaci kafin ta ce, "Kada ka dawo da hannun agogo baya, saboda yanzu da inda aka fito
akwai bambanc.."

"Na fahimci bambancin da kike nufi tun a ranar da kika gudu kika bar ni. Kuma a yau zan tabbatar miki
babu inda za ki je ballantana ki koma gudu na. Na yarda na amince ba kya so na, amma hakan ba zai sa na
yi sakacin da za ki sake kufce mini ki ɓace wa idona b..."

"Har da idan na sanar da kai ni matar wani ce?"



Wayyo😆
GARE KU MASU TAMBAYA!
Littafin FANSAR ƘAUNA na kuɗi ne. Ku biya ₦500 kacal ga wannan account. 9032685442 Opay. Waɗanda
tura kuɗi ta opay yake bai wa wahala ku tura ta Bank Account; 1230094555 Access Bank Hadiza D. Auta
Ibrahim.


D.
✍🏼 AUTA CE
[2/20, 22:17] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*

*HADIZA D. AUTA*

*AREWABOOKS: Princessdija.*

https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa


*ASHIRIN DA BIYAR.*

"Wani? Wani fa kika ce!"

Shiru ta yi masa maimakon amsar da yake jira. Nan take ransa ya yi ƙoluluwar ɓaci ƙirjinsa ya shiga
harbawa cikin sauri. Kafin ya haɗiye wani dunƙulallen yawun da ya tsaya masa maƙwagwaro ya sake cewa,

"Yanzu ni kike faɗa wa ke matar wani ce? Yanzu ba ki ji kunya da nauyin idona ki kalle ni ki furta mini irin
wannan maganar ba?"

Ya yi maganar cikin wani kalar sauti mai cike da laushi bayan ƙwalla ta cika masa idanuwa taf.

"Gaskiyar kake so na ɓoye maka?"

Hannu ya saka ya bugar da ƙwallar da ke ƙoƙarin gangarowa a saman fuskarsa sannan ya jinjina kai yana
cewa,

"Tabbas sai yau na ƙara tabbatar da ba kya so na. Don haka ki je ki zauna da wanda kika zaɓa a
madadina. Alhamdulillah na samu Minal a yadda ban yi tsammani ba, ko iya haka na sani Allah Ya mini
kyakkyawar sakayya a kan abin da kika aika min...ki je..ki je..kawai...matar wani ko? Humm...ya yi kyau."

Ya yi maganar tare raɓawa ta gefenta yana tafiya da baya da baya idonsa a kanta yana sara mata. Saboda
matuƙar mamakin da ta ba shi, tare da zafin kishin ta da ke caccakar zuciyarsa.
Maganganunsa da tafiyarsa sun saka kukan da take jarumtar ɓoyewa ya fallasa ƙuncin da ke cin ranta.
Don hawaye ya dinga bin fuskarta shaa tana ƙoƙarin haɗiye amma ya ƙi tsayawa. A haka ta bi bayansa da
sassarfa daidai lokacin da ya isa inda ya ajiye motarsa yana ƙoƙarin buɗewa ya shiga.

"Jaaan!"

Ta kira shi da sunan da ta saba kiran sa. Kiran da ya sa tsikar jikinsa ta tashi yarr kafin ya ɗaga kai ya kai
kallonsa a kanta. Tafiya ta ci gaba da yi zuwa inda yake jiri yana ɗibar ta tare da dishi-dishin da take gani.
Amma hakan bai hana ta isa gabansa ta durƙusa gwiwa biyu ba, kafin ta haɗa hannuwanta wuri ɗaya
alamun roƙo tana cizon leɓenta. Tsawon minti biyu tana haka kanta a sunkuye ba tare da ta ɗago kai ko ta
furta abin da take son furtawa ba. Shi ma idonsa a kanta ko ƙiftawa babu zuciyarsa cike da jin haushin ta
bayan mahaukacin kishin ta da ke kartar ransa.
"Sauri nake yi. Na baro matata a gida babu lafiy..."

Ya yi maganar cikin ƙunar rai, tare da nuna mata shi ma ya ɗau zafi a kan furucinta. Sai da ta zuƙe
majinar kukan da ke yunƙuro mata, sannan ta yi jarumtar goge hawayen idonta, tare da haɗiye ɓacin ran
da ya cusa mata. Zumbur ta miƙe tsaye daidai lokacin da kira ya shigo wayarta. Da hanzari ta fiddo ta a jaka
ta ɗaga kiran, saƙon da aka isar mata a cikin wayar ya sa ta magana cikin sauri.

"Ka jira ni, in sha Allah yanzu zan ƙaraso kafin lokaci ya cika."

Ta katse kiran tare da kai kallon ta a kan agogon hannunta tare da cira kai zuwa kan fuskar Jamal, ido cikin
ido suka dinga kallon juna, sai da ta sauke ajiyar zuciya sau biyu kanta a sunkuye kuma rungume da
hannuwanta a ƙirji, sannan ta sauya akalar zancen da ta so furtawa a farko, cikin murmushin yaƙe ta ce
masa,

"Ni zan wuce jirgin da zan bi ya kusa tashi, idan ka je gida ka gaishe da matarka."

Tana ƙare faɗar hakan ta juya cikin takunta na taƙama kamar koyaushe ta nufi bakin titi iska yana kaɗa
ta. Kallo ya bi bayanta da shi hawaye yana bin fuskarsa saboda wani kalar tashin hankalin da ya dira kansa
cikin zaucewa ya ce,

"Har abada, ba zan fasa kallon ki a matsayin wadda ta cutar da rayuwata ba, matuƙar ba ki sanar da ni
laifin da na yi kika yi kyauta ta ga Minal ba. Sannan ki sani duk taku ɗaya idan kin yi, tamkar tafiya da
numfashina ne kike yi. Don muddin kika tsallake ƙasar nan kika sake bari na kamar yadda kika yi a farko, to
ina tabbatar miki kafin ki isa inda za ki je za ki ji saƙon mutuwat..."

"Jaaann!" Ta kira sunansa tare da juyowa babu shiri, a cikin wani matsanancin firgicin da ya bayyana kan
fuskarta. Ta dawo jikinta yana rawa cikin matsanancin fushi ta isa gabansa tamkar kububuwa. Idonta a rufe
ta ɗaga hannu ta wanke shi da mari, hawaye yana bin fuskarta ta fara nuna shi tana magana cikin kuka
tamkar ta shiɗe.

"Da za ka zamo ajalina a yanzu nan zan iya yafe maka Jaan kuma har a gaban Allah. Amma wallahi!
Wallahi ba zan taɓa yafe maka ba matuƙar ka kashe kanka a kain...ina son ka Jaaan kai ma ka sani wallahi
ina son k..."

Ta ƙare maganar tare da fashewa da wani mahaukacin kuka, tare da faɗawa jikinsa ta rungume shi
tsantsan tamkar za a ƙwace mata shi. Tsawon minti huɗu tana jikinsa tana ta rera kalolin kukan da ya ƙara
raunata ɗan kuzarin da ya rage masa a jiki da zuciya. Saboda ya sandare wuri ɗaya ko motsi ya kasa yi,
amma idanuwansa ba su daina ɓarin hawayen da ke malala a kan fuskarsa ba.
Duk da tarin jama'ar da suka tara wa kansu ba tare da sun sani ba. Kamar yadda surutan da mutanen
suke yi a kansu bai sa sun hankalta sun dawo nutsuwarsu ba.

"Woww! An burge ni... Billahillazi an tashi kaina!"

Ire-iren waɗannan maganganun aka shiga yi, tare da bidiyo da hotunan da ake ta ɗaukar su. Saboda
yanayinsu ya fallasa su a matsayin masoyan da suka samu saɓani, sannan kuma waɗanda ba son

20 / 29