Advertisements
Chapter 21 Reading Fansar Ƙauna Juyin Soyayya by HADIZA D. AUTA BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Fansar Ƙauna Juyin Soyayya by HADIZA D. AUTA

Author :  HADIZA D. AUTA Category :  Complete Novels

Chapter   21 / 29

60K to 63K   out of 85.8K words

rabuwa
da juna.

"Lafiya 'yata? Me ya faru?"

Zancen Hajiya Inno mai abinci kenan, a lokacin da aka sanar da ita cincirindon da aka yi mata a bakin
Restaurant. Cikin rawar jiki ta fito gudun a ƙara jaza mata wata fitinar bayan zafin abin da Zulaiha ta yi
mata ko hucewa bai yi ba, wanda ya jawo ce-ce-kuce a tsakanin ma'aikatanta da customers har ya so ya
koma musu wata sabuwar hatsaniya.

Hajiya Inno ta jawo Nur a jikinta fuskarta a yamutse tana ƙara tambayar dalilin kukanta. Musamman da
ta hango hawaye a idon Jamal sai abin ya ƙara ɗaga mata hankali. Cikin rawar murya ta sake jefa wa Nur
tambaya a ruɗe tana faɗin,

"Kin..ga..kin..ga..don Allah ki sanar da ni abin da yake faruwa. Kalli mutane ki gani gabaɗaya ku suke
kallo! Me ya haɗa ki da shi ne? Ko duk a kan rikicin da aka gama a kan Zulaiha ne?"

Nur ta shiga girgiza mata kai a kan duk tambayoyin da take jera mata. Ranta a ɓace cikin ɗaga murya ta
sake cewa,

"To mene ne? Ki sanar da ni bakiɗaya an ɗaga mini hankali."

Nur ta ja hannunta da nufin su koma cikin Restaurant ɗin, babu musu ta bi ta tare da bai wa Jamal
umarnin shi ma ya biyo su. Rufe motarsa ya yi cikin sanyin jiki ya bi su jiri yana ɗibar shi tamkar ya faɗi.
Tsabar damuwar da yake ciki, a gefe ɗaya kuma tunanin halin da ya bar Minal a ciki.

Wuri na musamman Hajiya Inna ta kai su inda babu zirga-zirga, bayan sun zazzauna ta kalli Jamal cike da
zaƙuwar jin abin da yake faruwa ta ce,
"Kai ne namiji, da kai zan fara. Duk da na san ka tun ba yau ba, amma ban san tsakaninku ba, sai dai ga
dukkan alamu akwai wata keɓantacciyar alaƙa a tsakaninku ba iya yadda ita 'yata ta sanar da ni ba. Don ta
faɗa mini kai mijin 'yar'uwarta ne, amma kuma yanayinku ya nuna ba iya wannan alaƙar ce ta haɗa ku ba.
Duba da yadda ta ce mini tun daga Niger ta zo nan saboda kawai ta kare ka daga sharrin Zulaiha. Don haka
idan kun ɗauke ni uwa kamar yadda nake yi muku kallon 'ya'yan da na haifa, ku sanar da ni gaskiyar abin
da ke tsakaninku idan har na cancanci hakan."



Ku yi manage, jiki da jini yau an taɓo nawa file ɗin ni ma Minal ta sakar mini ciwon.😪



GARE KU MASU TAMBAYA!
Littafin FANSAR ƘAUNA na kuɗi ne. Ku biya ₦500 kacal ga wannan account. 9032685442 Opay. Waɗanda
tura kuɗi ta opay yake bai wa wahala ku tura ta Bank Account; 1230094555 Access Bank Hadiza D. Auta
Ibrahim.


D.
✍🏼 AUTA CE
[2/20, 22:17] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*

*HADIZA D. AUTA*

*AREWABOOKS: Princessdija.*

https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa


*ASHIRIN DA SHIDA.*
Ajiyar zuciya Jamal ya sauke mai ƙarfi kafin ya ɗora kallonsa a kan Nur ya ce, "Ban taɓa tunanin za ki guje
ni ba, saboda yarda da amincin da ke tsakanina da ke. Mun gina so da ƙauna a cikin gaskiya da rashin
ɓoyewa juna matsaloli. Amma sai dai ashe ni yadda na ɗauke ki ke a wurin ki ba haka nan ba n..."

"Kallar ni da kyau ranka ya daɗe, ni za ka yi wa bayanin da na nema, ka ajiye wannan zancen naku kamar
zai fi dacewa a tsakaninku."

Zancen Hajiya Inno kenan a lokacin da ta ji maganar Jamal ta sauka daga layin abin da take son ji.
Murmushin takaici ya yi idonsa a kan Nur ya sake cewa, "Har abada ba zan manta abin da ta yi mini ba
Hajiya, saboda haka ba zan iya bayanin komai ba idan ba cin amanar da ta yi wa rayuwata kike son ji ba."

"Assha! Ranka ya daɗe komai na duniya fa ɗan haƙuri ne. Kuma idan ka nutsu da kyau za ka fahimci ita
ma ba ƙaramin so take yi maka ba, duba da yadda ta baro ƙasarta takanas don tseratar da kai daga
matsal...'

Nur ta yi hanzarin katse ta cikin fushi tana cewa, "Ki bar shi..ki bar shi kawai Mama, ni duk abin da na yi
don Allah na yi da ceton rayuwar 'yar'uwata Minal. Kuma Allah shi ne shaidar ban guje ka don ba na son ka
ba. Kuma na yi abin da na yi ne da kyakkyawar niyya ko da kai ba za ka fahimce ni ba. Sannan ban ce dole
sai ka yarda da duk abin da na faɗa ba, amma ni dai na sani har abada ba zan bari a cutar da kai ba, haka
ma ni da kaina ba zan yi abin da na san zai cutar da kai ba. Saboda haka ka kalle ni a yadda duk kake kallo
na, kuma ka ci gaba da kallo na da irin fassarar da kake yi mini babu komai."

Tana ƙare maganar ta miƙe tana goge ƙwalla ta bar wurin gudu-gudu sauri-sauri saboda kukan da ke
barazanar fallasa ƙuncin zuciyarta. Hakan ya sa duk kiran da Hajiya Innon ke yi mata bai sa ta juyo ko ta
tsaya daga ƙudurinta na son tafiyar ba. Daidai lokacin da kira ya sake shigowa wayarta, inda tana ɗauka
mai maganar ya sanar da ita jirgin da za ta bi har ya tashi, don ya yi ta kiran ta ba ta ɗauka ba, kuma ya
turo mata saƙo ba ta yi masa reply ba. Saboda ya yi ta kiran ta tana danne kiran tun farkon zaman sulhun
da Hajiya Innon ta so yi musu, har zuwa lokacin da ta miƙe da nufin barin wurin a gaggauce ana ta kiran ta,
don ta san dalilin kiran da abin da ke gabanta idan ta koma Niger.

Hannu ta ɗora a ka cikin tashin hankali ta yi magana da wanda ya kira tana cewa, "Ina cikin tashin
hankali Adamu, saboda wallahi babu wanda ya san na zo ƙasar nan, kuma kai ka san uzurin da kenan,
wanda ko ba na so dole na yi tafiyar nan a yau, gudun na shiga wani sabon bala'i."

Shiru Adamun ya yi na ɗan lokaci kafin ya ce, "Idan babu damuwa ki zo na kai ki masaukin da za ki kwana
cikin sirri kafin lokacin mu ga yadda za a y..."

Cikin rawar murya ta ce, "Gobe ne ɗaurin aurena ka sani, ta ya ya zan iya kwana a nan asirina ya tonu idan
aka neme ni aka rasa? Ba zai yiwu ba Adamu, don Allah ka bincika mini idan akwai jirgin da zai tashi ko da
cikin dare ne zan bi sh..."

"Babu inda za ki je ballantana ki yi auren da kike faɗa!"

Ta ji maganar Jamal tsidik a cikin kunnuwanta, cikin hanzari ta juya tana kallonsa, ba ta ankara ba ta ji ya
fisge wayar tare da ɗora ta a kan kunnesa, inda yake ƙoƙarin yin magana amma kafin ya ce wani abu ya ji
muryar Adamu yana faɗin,

"Ki yi haƙuri, zan bincika miki, idan da halin tafiyar a yau sai mu gan..."

"Za ka gani kuwa baƙin munafuki! To ko ubanka ne mijin babu inda za ta je sai da igiyar aurena. Kuma ka
sani wallahi idona idonka sai na nuna maka ba iri na ake ha'inta ba."
Yana ƙare maganar ya ɗora jajayen idanuwansa a kanta, kafin ya fisgo hannunta cikin matsanancin fushi
tana tirjiya tare da buge masa hannun, amma hakan bai hana shi cusa ta cikin mota ba. Hajiya Inno da ke
kallon abin da ke faruwa ta biyo su tana faɗin,

"Ranka ya daɗe ka bi komai a hankali don Allah, ka san tunanin mace ba ɗaya ne da naku maza ba. Kada
ka yanke hukuncin da zai jawo danasani daga baya."

Uffan bai ce da ita ba, illa hannun da ya ɗaga mata yayin da zai bar wurin yana ƙoƙarin hawa kan titi. Nur
da ke zaune gaban motar tsuru-tsuru tana zarar ido, tsabar tashin hankalin da take jin kanta a ciki tamkar
ta fi kowa matsala. Ido ta ɗora a kansa tana faɗin,

"Ban san ina za ka kai ni ba, amma ka sani rashin komawata gida a yau, da abin da rashin gani na zai
haifar ya fi matsalarka girma. Don haka ka tausaya mini kada ka bari rayuwata ta lalace a sanadin biye wa
son zuciyarka."

Kalamanta ba su sa ya ji tausayin ta ba ballantana ya magantu, illa ƙarin baƙinciki da haushin da suka jefa
shi ciki. Gudu ya shiga shararawa a saman titin tamkar wanda zai tashi sama, bai zame ko'ina ba sai a bakin
wani Shopping Mall. A gaggauce ya fice bayan ya saka motar a key gudun ta fice bai sani ba. Shigewarsa ke
da wuya ta ɗaga waya ta kira Adamu, sai dai har ta yi ringing ta gama bai ɗaga ba, cike da jin haushi ta tura
masa saƙo tana faɗin,

'Kada ka tayar da hankalinka a banza, Allah Ya fi kowa sanin gaskiyar abin da ke tsakanina da kai. Don
haka duk matakin da zai ɗauka ka yi haƙuri don Allah kada ka biye shi."

Bayan ta tura saƙon ta yi shiru tana nazari tare da goge hawayen da ya kasa barin idanuwanta. Mintuna
a tsakani ya fito tare da wasu ma'aikatan wurin a bayansa da kayan abinci niƙi-niƙi. Bayan boot ya buɗe aka
gama zuba kayan ya rufe tare da buɗe motar ya shiga. Kuma har lokacin fuskarsa a cure ya tayar da motar
ya juya aguje ba tare da ya ce da ita ƙanzil ba.
Kasancewar ta yi zama garin Kanon tsawon shekara biyu zuwa uku, hakan ya sa ta fahimci inda ya nufa
da ita. Kallon sa ta yi cikin wani yanayi mara misaltuwa kafin wani sabon kuka ya zo mata ta yi magana cikin
raunin murya da zuciya ta ce,

"Me kake nufi da kai ni gidan su Minal?"

Bai amsa mata ba, kamar yadda bai kalle ta ba, gudunsa kawai yake yi da motar har zuwa lokacin da ya
saki babban titin ya gangara cikin layin su Minal. Sai da ya dira a ƙofar gidan sannan ya yi jim yana kallon
gabansa ya ce,

"Ki shiga ciki, idan Baba yana nan ki kira mini shi."

Ba ta fita kamar yadda ya buƙata ba, sannan ba ta ce da shi ƙanzil ba, illa zuƙar majinar kukan da take yi
tare da goge hawayenta jefi-jefi da mayafin doguwar rigar da ke jikinta.

"Ki kira shi na ce!"

Ya sake yin magana cikin ɗaga murya tare da ɗora kallonsa a kan kumburarriyar fuskarta, wadda tsabar
kukan da ta sha ta sauya kala zuwa ja. Ganin ba ta da niyyar fita kuma kukan da take yi ba ƙaramin taɓa
masa zuciya yake yi ba, hakan ya sa cikin zafin nama ya ɓalle murfin motar ya fice. Wasu yara ya yafito suka
zo da gudu, ya buɗe boot ɗinsa yana fito da kayan tare da ba su umarnin su shiga da su daga ciki, kuma
idan Baban yana ciki su yi masa sallama da shi.
Sai da aka shigar da kayan duka sannan ya jingina da motar rungume da hannu kansa a ƙasa yana nazarin
mafita a kan hukuncin da yake son zartarwa. Duk da ya sani abu ne mai matuƙar wahala, amma duk
tsanani gara rayuwa da Nur a wajensa da a ce ya yi rashin ta gabaɗaya.
Jim kaɗan bayan shigar yaran suka fito Innarmu a bayansu lulluɓe da zani tana leƙe, don ta gane wa
idanuwanta mai mutunci da ya gwangwaje su da kayan abinci irin haka. Caraf ta hango Jamal a bakin
motarsa, baki buɗe ta fara rawar jikin gaishe shi tun kafin ya gan ta shi ya fara gaishe ta.

"A'ah! Lale-lale marhabin da zuwanka. Allah Sarki ashe kai ne da wannan tagomashin alheri har haka?"

Sai a lokacin hankalinsa ya dawo jikinsa ya kai kallonsa gare ta yana murmushin yaƙe. Kafin ya bar jikin
motar cikin sanyin jiki ya isa inda take ya rusuna kansa a ƙasa ya shiga gaishe ta, ita kam tuni ta riga shi kai
ƙasa tana godiya ba tare da ta amsa gaisuwar da yake yi mata ba.
"Amm.. Baban yana ciki kuwa?"

Ya yi tambayar kansa a ƙasa bayan ta gama godiyar shi ma ya ce babu komai yi wa kai ne. "Ai ka san
Malam ba ya zama a irin wannan lokacin sai dare ake samun sa a gida. Sai dai idan ya dawo a sanar da shi
ka zo shi ma ya kira ka ya yi maka godiya.
...ai mun gode mun gode sosai wallahi. Allah dai ya biya ka kawai ya ƙara muku zaman lafiya da Amina."

"Amin-amin."

Ya amsa kansa a ƙasa kafin ya ɗago idonsa ya kalle ta cikin girmamawa ya ce, "Tare nake da baƙuwa, za ta
shiga ta zauna kafin zuwa daren sai na dawo mu yi magan..."

"Haba-haba! ai babu komai wallahi an zama ɗaya ta shigo ta zauna gidanku ne kai ma, kuma kana da
ikon kawo duk wanda kake so ya zauna a cikin gidan kamar yadda Amina take da iko da shi."

Har cikin ransa ya ji daɗin furucin Innarmu, hakan ya ƙara masa ƙarfin gwiwar miƙewa ya isa gefen da Nur
take zaune ya buɗe mata ƙofa. Ido cikin ido suka kalli juna tsawon sakon biyu kafin ya nisa, cikin wata kalar
murya ya ce,

"Fito ki shiga ciki, zuwa dare zan dawo mu yi magana."

Sanin Innarmu tana ganin su don ta kasa ɗauke idanuwanta daga kansu cike bin ƙwaƙƙwafin gano wace
ce tun kafin ta iso, don har da leƙawa ta gilashin ta yi da zummar hango ta tun a cikin motar. Sai dai
kasancewar ba a ganin na ciki ta wajen ya sa dole ta bar zura wuyan ta mayar da kallonta ta saman motar.
Dam-dam ƙirjinta ya buga saboda ganin Nur ta fito daga motar, baki buɗe ta ƙura mata kallo har zuwa
lokacin da ta ƙaraso gabanta ta durƙusa har ƙasa tana gaishe ta. Cikin kaɗuwa da zaucewa Innarmu ta riƙe
ƙugu tana faɗin,

"Uban wa ya dawo da ke a cikin gidan nan?"

Nur ba ta ɗaga kanta ba, illa sabon hawayen da ya shiga bin fuskarta. Jamal ne ya yi ƙarfin halin isa
wurin cike da mamaki ya zuba wa Innarmu kallo kafin ya ce,

"Ita ce wadda na kawo ajiya kafin Baba ya dawo mu yi magan..."

"Dakata-dakata yaro! Ko dai ka manta nan gidan iyayen Amina ne matarka wadda kake aure?"

"Ina sane ba mantawa na yi ba. Kuma kin faɗa ina da iko da gidan kamar yadda Amina take da iko da
sh.."

"Amina da kai daban! Sannan wannan tsintacciyar magen daban! Saboda haka ba za ta shiga cikin gidan
nan ta zauna mana ba ko da sakon ɗaya ne. Don ba mu haɗa komai da ita ba, asali ma babu wanda muka
taɓa gani a cikin danginta, shi kansa maigidan da ya ɗebo mana ita daga baya ya gano kuskurensa a kan
riƙon wadda bai san komai a kan asalinta ba. Saboda haka ka kwashe ta ku matar da ita inda ta ɓoye tun
kafin Malam ya dawo ku jawo mana wata sabuwar fitina."

Shiru ya ratsa tsakani bayan maganarta, saboda sabon ɓacin ran da Innarmu ta cusa masa. Bai ce da ita
komai ba tsabar ƙimar Amina da ke ransa, sannan da darajar surukantaka da yake kallo a idonsa.

"Tashi mu je!"

Abin da ya faɗa kenan kafin ya bar wurin ya faɗa matarsa yana ba ta wuta. Nur ta miƙe ba tare da ta ce da
Innarmu komai ba ita ma ta bi bayansa. Hakan ya ƙara rura wutar tashin hankalin da Innarmu take ciki, ta
shiga tsine wa Nur tare da miyagun lafuzza iri-iri, sai wanda bai zo cikin bakinta ba. Har da iƙirarin duk ta
sake ganin ta a ƙofar gidan hukuma ce za ta raba su.

"Kin san shagon Baban ne?"

Nur ta yi banza da shi har suka hau babban titin Jogana suka miƙi hanyar zuwa kasuwar da Baban Amina
yake zama. Saboda ya san kasuwar da yake zuwa tun zamanin yana neman auren Nur, amma bai taɓa
sanin wanne shagon da yake aiki ba.
Sai da suka je bakin titin kasuwar ya samu wuri ya yi parking, sannan ya ɗaga wayarsa ya kira Baban. Sai
dai har wayar ta nemi tsinkewa bai ɗauka ba, cike da jin daɗi Jamal ya amsa sallamar da ya yi masa cikin
mutumtawa bayan ya ɗauka. Suka gaisa tare da sa albarka ga Jamal da yi masa addu'ar ƙarin zaman lafiya
da Amina, bayan ya gama tambayar Hajiya da saƙon gaisuwa gare ta.

"Baba akwai maganar da nake so mu yi da kai."

"To..too babu damuwa. Za ka iya zuwa da dare idan na koma gida sai mu tattauna."

Sosa kansa Jamal ya yi kafin ya ce, "Yanzu haka ina bakin kasuwarku Baba, idan da halin fitowa ka zo mu
tafi gidan tare, saboda magana ce mai matuƙar muhimmanci za mu yi."

"To, babu komai ka jira ni yanzu zan fito sai mu tafi."

Jamal ya katse kiran yana kallon Nur da ta yi tagumi tana kallon mutanen da ke ta zirga-zirga ta gabansu.
Amma zuciyarta ko kaɗan ba ta wurin, don ta tafi duniyar tunanin abin da zai faru idan har aka neme ta ba
a san inda ta je ba. Ga shi ta cire layukanta na Niger, ta saka na Nigeria da niyyar idan ta gama abin da take
yi ta zare shi ta adana kamar yadda ta yi a ranar da ta bar garin.


Akwai kallo🏃


Na gode sosai da addu'o'inku. Allah Ya bar zumunci.

GARE KU MASU TAMBAYA!
Littafin FANSAR ƘAUNA na kuɗi ne. Ku biya ₦500 kacal ga wannan account. 9032685442 Opay. Waɗanda
tura kuɗi ta opay yake bai wa wahala ku tura ta Bank Account; 1230094555 Access Bank Hadiza D. Auta
Ibrahim.


D.
✍🏼 AUTA CE
[2/20, 22:17] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*

*HADIZA D. AUTA*
*AREWABOOKS: Princessdija.*

https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa


*ASHIRIN DA BAKWAI.*

A ɓangaren Minal kuwa, tsawon miniti goma bayan fitarsa tana nazarin yadda ta samu matsayin da ba ta
taɓa tunanin za ta samu a wurin sa ba.

'Ashe ni ma mace ce?'

Ta yi zancen daga ita sai zuciyarta, yayin da ta shiga godewa Hajiya a ranta, da Gwaggo Salame da ke
dannar ta har zuwa kan Innarmu da ke danna mata ashar a kan wajibi ne sai ta zauna.

'Allah Sarki Babana, ka mini nasiha kuma na ɗauka, in sha Allahu zan bi mijina kamar yadda ka ba ni
shawara.'

21 / 29