Author : HADIZA D. AUTA Category : Complete Novels
ƙaƙƙarfar murya ya buga mata tsaya, tare da toshe kunnuwa da
hannuwansa biyu a lokaci ɗaya yana cewa,
"Ki daina! Ba na buƙatar kukan nan...ya isa haka!"
Idanuwansa a rufe yana jujjjya kai alamun ba ya cikin nutsuwarsa, hakan ya ƙara dagula mata lissafi, cikin
matsanancin tsoro da firgici ta sake yin wani ihun da ya saka shi dawowa cikin hayyacinsa babu shiri.
Saboda abin da ta faɗa ta iya ƙarfinta a lokacin da ta fahimci sabon tashin hankalin da yake ƙoƙarin afka su
ciki.
"Innalillahi Jannnnn! Wayyo Allah za ka yi kisa!"
Ta ƙare maganar ido zare saboda motar ta ƙwace masa kuma tana hangen aika-aikar da yake ƙoƙarin
aikatawa. Don saura ƙiris ya taushe mutanen da ya ture daga kan mashin, cikin azama ya ja mugun birki,
ikon Allah ya tsayar da motar cak tana wani irin ƙugi.
Nan take mutane suka janye mashin ɗin cikin sauri, bayan waɗanda ya ture sun yi hanzarin tashi an ja su
gefen titin, sannan aka shiga dudduba inda suka gurje a jikinsu, tare da son tabbatar da babu abin da ya
same su bayan gurjewar da suka yi.
Nan take zage-zage ya fara tashi a bakunan waɗanda Jamal ya tunzura, ganin ya so yin kisa amma kuma ya
ƙi fitowa daga cikin motar ballantana ya ce a yi haƙuri. Yayin da wasu ke tunanin ko dai shi ma ya samu
matsala shi ya sa bai fito ba.
A cikin motar kuwa birkin da ya ja ya saka shi buga goshinsa saman sitiyari, ita ma ta faɗa bayansa babu
shiri ta ruƙunƙume kujerar direban da yake kai tana salati idonta a rufe tsabar ya gama kiɗima 'yan
hanjinta.
Mintuna kaɗan bayan tsayuwar motar, ta ji yana ƙoƙarin ɓanɓare ta daga jikin kujerar, ranta a ɓace ta
rufe shi da maganganun da ya kasa ɗauke kallonsa daga kanta, tsabar mamakin da ta ba shi da tunanin ita
ce ko wata ce aka sauya masa. Saboda ta yi yunƙurin buɗe motar ta fita da niyyar bai wa mutane haƙuri,
sai tunaninsa ya tafi a kan cewa fushi ne ta yi kuma ta tafiyarta za ta yi ta bar shi, saboda ganin yanayin
fuskarta.
Don haka ya yi hanzarin saka wa ƙofofin lock fuskarsa a haɗe yana aika mata harara tamkar bai taɓa yin
dariya ba. Haushin hakan ya sa ta shiga yarfa masa maganganu cike da gayya don kawai shi ma ya ji
haushin ya bar ta ta fice, ko kuma zantukan su sa ya shiga taitayinsa gudun ya jawo musu wata matsala
kafin su isa inda za su je, garin zafin kansa.
"Idan kai ka gaji da zaman duniyar ni ban shirya zuwa lahira a wannan lokacin ba! Don haka ka buɗe mini
na kama gabana tun kafin ka yi wa dangina asara."
"Danginki ko?"
Ya yi maganar cikin wani kalar sautin da ya sa dole ta kalle shi da raunanniyar fuskarta. Hawayen idonta ya
sake dawowa shaa yana sauka a kumatunta, tare da kai kallonta a gefenta tana ƙoƙarin share hawayen da
gefen hannunta. Saboda fahimtar ba ya cikin yanayi mai daɗi, kuma don ƙarfin hali ba ya iya sauka daga
dokin zafin kan da yake kai. Don tana da labarin ciwon da ya same shi a sanadin guduwarta. Kuma jikinta
ya ba ta wataƙila ciwon ne ya motsa masa amma tsabar ƙarfin hali ba zai iya rusunawa ba.
"Kina so ki koma a aura miki wanda kike so ko? Shi ya sa ba kya son mutuwa a wannan lokacin. Haka
n...?"
Ya yi maganar cike da ƙarfin hali dafe da kansa da ke sarawa babu ƙaƙƙautawa. Kafin ta ba shi amsa suka
fara jin ƙwanƙwasar gilashin motar ta kowace ƙofa, don mutane sun yi wa motar rumfa har an fara
shawarar idan ba a buɗe ba a samu abin bugu a buge gilasan domin a ga halin da mai tuƙin motar yake
ciki.
Da rawar baki Nur ta yi magana cikin dusasshiyar murya tana cewa, "Ka buɗe zan ba su haƙuri ne..." Hannu
kawai ya saka ya cire lock ba tare da ya motsa ba.
Cikin sauri ta ɓalle murfin tana ƙoƙarin ficewa, waɗanda ke jikin ƙofar suka yi hanzarin janyewa suka ba
ta wuri ta fito.
Dam-dam ƙirjinta ya shiga bugawa, ganin idanuwan mutanen wurin gabaɗaya suna kanta. Mayafin rigar
da ke jikinta ta ja ta goge hawayen fuskarta, kafin ta gyara tsayuwarta ta zuƙe majinar kuka ta ce,
"Don Allah ku yi haƙuri, wallahi ba ma cikin yanayi mai daɗi ne, saboda mai tuƙin motar ma bai da
isasshiyar lafiya asibiti za mu je da shi yanzu haka. Ƙarfin hali ne ya saka shi yin tuƙin nan, aka yi rashin
dace kuma jiri ya ɗebe shi tsautsayi ya saka shi yin wannan aikin..."
"Mu ma ba ma cikin yanayin mai daɗi ba ku kaɗai ba ne!"
"Wai sai an cuci mutum a dawo cewa ya yi haƙuri."
Zancen wasu 'yan bani-na iya kenan tun kafin ta sauke numfashin maganarta.
"Babu damuwa tun da uzuri ne, ku je kawai babu komai Allah Ya ba shi lafiya."
Ɗaya daga cikin waɗanda aka ture a kan mashin ya yi maganar yana ƙoƙarin yarfe jinin da ke fita daga
bayan hannunsa.
Wani sanyin daɗi ya ratsa zuciyarta. Cikin rawar jiki ta buɗe motar da nufin komawa su tafi, don ta matsu
su bar wurin gudun idon sani su kai wa Hajiyar Jamal rahoton an gan su tare.
Amma dole ta dawo jikinta yana ɓari ta buɗe jakar hannunta ta ciro kuɗi ba tare da ta tsaya ƙirgawa ba
ta miƙa wa mai raunin tana cewa,
"Ga wannan ku yi haƙuri da su, kuma don Allah ku yafe masa har cikin zuciyarku, saboda shi ma ba da
gangan ya aikata ba."
Ta sake yin maganar a marairaice saboda ganin halin da mutanen suke ciki, don ɗayan da aka ture su tare
zaune kawai yake dafe da kansa ba tare da ya ce komai ba. Amma saboda lafazin da wani da ke cikin
dandazon jama'ar ya yi mata cikin ɗaga murya, inda ya yi maganarsa kai-tsaye a lokacin da take yunƙurin
shigewa motar yana cewa,
"Ku dai biya su kuɗi su je a duba lafiyarsu chemist! Don gaskiya ba za a yafe muku kuɗin ba ko da an yafe
muku laifin."
Ba su kuɗin ya sa ta kulle bakin kowa, cikin rawar jiki ta zagaya ta gaba tare da tsayuwa bakin motar
fuskarta a haɗe tana faɗin, "Ka fito zan yi drinving, ba na son a sake samun wata matsalar."
Jim ya yi kamar ba zai fito ba, yana yi mata wani kallon tsakiyar ido. Fuska ta ƙara tsukewa tana kallon
gefe alamun babu wasa a tattare da ita, tsawon sakonni yana kallonta ƙur da lumsassun idanuwansa, kafin
ya sauke nannauyar ajiyar zuciya ya ɓalle murfin ya fice dafe da kansa da ta sarawa.
Cikin sauri ta ba shi wuri ya wuce, sannan ta shiga mazaunin direba ta zauna cike da jarumta ta tayar da
motar. Sai da ta bari ya daidaita zamansa gaban sannan ta ja tana ɗaga wa masu yi mata Allah Ya tsare
hannu suka wuce.
Gudu take shararawa a saman titin idanuwansa ƙur a kanta duk da gudumar da yake ji ana kwaɗa masa a
cikin kai. Sai da ta yi tafiya mai nisa kafin ya yi magana cikin ƙarfin hali saboda jijiyoyin kansa da yake jin
kamar an ɗaure shi da su.
"Ina za ki kai mu?"
Ba tare da ta kai kallonta gare shi ba ta ce, "Asibiti za mu je a duba ka."
Wani kallo ya yi mata kafin ya ce, "Kin maƙala mini ciwo a can kuma yanzu kina son na ga likita. Tafiyar
kike so a fasa ko rabuwa da ni ne ba kya so?"
Dam ƙirjinta ya buga, hakan ya sa ta basar da shi kamar ba ta ji abin da ya ce ba. Bai sake ce mata komai
ba har ta sha wata roundabout tana ƙoƙarin kama wani titin ta miƙe ya sake cewa,
"Idan kika samu wuri ki tsaya zan karɓi tuƙin."
Ba ta ce masa komai ba har ta samu wurin tsayuwa ta ja gefe tana cewa, "Kana fama da ciwo amma kana
ƙoƙarin shiritar da zancen zuwa asibiti. Me ya sa kake wasa da lafiyarka?"
"Ina da magani zan sha idan muka je."
Daga haka ya ɓalle murfin ya fice, tare da ba ta umarnin ta fito. Babu musu ta fita ta koma mazaunin baya
ta zauna. Har ya zauna yana ƙoƙarin tayar da motar, ganin ta a bayan ya saka shi waigawa yana ƙare mata
kallo cike da ɓacin rai. A haka ya tayar da motar suka ci gaba da tafiya babu mai cewa komai. Sai dai
yanayin yadda yake bugun motar ya sa ta gano ta ƙara ɓata masa rai. Tsam ta yi da ranta saboda ko kaɗan
ba ta farinciki da abin da zai taɓa lafiyarsa. Haka kawai ta ji babu daɗi, amma a ranta tana jin ba za ta iya
bin ra'ayinsa ba.
Sai da ya tsaya ya yi musu sayayya sannan ya wuce inda ya yi niyyar su nufa. Cike da mamaki ta kai kallonta
gare shi a lokacin da ta gan su cikin gate ɗin wani babban Hotel.
HOTEL
Abin da ta karanta kenan a lokacin da ta yi arba da saman allon fuskar ginin Hotel ɗin.
"Fito mu je."
Ya faɗa yana riƙe da murfin motar idonsa a kanta. Jiki a sanyaye ta fito bayan ta aika masa harara, rufe
motar ya yi tare da zagayawa ya fiddo jakar kayansa da ke bayan boot ya rataya, hannuwansa biyu ɗauke
da ledodin siyayyar da ya yi musu. Kai-tsaye Reception ya nufa har ya yi nisa ya waigo, saboda bai ji alamun
tana biye da shi ba. Kallon da ya aika mata ya sa ta yi fuskar shanu ta biyo shi tana jin wani ɗaci a tsakiyar
zuciyarta.
Tana tsaye rungume da hannuwa a ƙirji har ya gama karɓar ɗaki aka ba shi kati, ya yi sama cikin sassarfa
yake taka matakalan benen, wanda zai sada su da ɗakin da aka ba su. A wannan karon babu ko ɗar ta bi
bayansa duk da saƙe-saƙen da zuciya take yi mata. Bakin ɗaki ya ja ya tsaya, bayan ya zube ledodin
hannunsa ƙasa, saita katin ya yi jikin na'urar da ke bayar da umarnin buɗe ƙofar. Sai da ta yi wata ƙara ƙirrrr
sannan ƙofar ta buɗe ya shiga da sallama, bayan ya ɗauki ledodin ya ajiye a saman bedside durowa.
Ƙin shiga ɗakin ta yi, har sai da ya leƙo bayan ya sauke jakar kayansa yana faɗin,
"Ko kin ji labarin ina kasuwancin kawunan mutane ne?"
Wani kallo ta yi masa kamar ta yi dariya, amma dole ta fuske. "Malama ki shigo ba na son harkar
ƙauyanci."
Yana maganar ya raɓe gefe ta wuce tana aika masa harara. Rufe ɗakin da ya yi ta ji tamkar an daki saitin
zuciyarta, yatsun hannunta ta shiga kallo hawaye yana bin fuskarta ganin yana ƙoƙarin rage kayan jikinsa.
Toilet ya faɗa tsawon minti biyar bai fito ba, amma har ya gama kwarara wa kansa ruwa ya yi wanka ya fito,
ba ta ɗaga daga inda take tsaye ba. Bayan tsiyayar kukan da take yi ko dogon motsi ba ta yi ba.
Mamaki fal ransa, ganin tana inda ya bar ta, sallaya ya fiddo a jakar kayansa ya shimfiɗa idonsa a kanta ya
tayar da sallah. Sai da ya gama sannan ya kalle ta ya ce,
"Malama ki shiga ki yi wanka ki yi sallah."
Baki ta turo bayan ta yi masa wani kallon ido cikin ido hawaye yana zuba a kan fuskarta ta ce, "Ba zan iya
zama ɗaki ɗaya da kai ba, saboda ni ba muharramarka ba ce kuma ka fi kowa sanin hakan."
Wata guntuwar dariya ce ta suɓuce masa kafin ya ce, "Kina nufin na kawo ki nan ne don na yi wani abu
da ke?"
Shiru ta yi masa tana kallon gefe tare da ƙoƙarin share hawayenta. "Ni ɗan iska ne kin sani, amma ko
wani na ga zai keta miki haddi ba zan taɓa bari ya ƙarasa aniyarsa ba, don dole ne ɗayan biyu ya faru, ko na
kashe shi ko kuma na datse masa abar ya rasa ta gabaɗaya....ke ko ni ne na haiƙe miki babu aure ba zan
taɓa yafe wa kaina ba. Saboda na san abin da nake yi, kuma na san darajar haƙƙi da girman amanarki da ke
hannuna. Ko aurenki na yi ba iya saduwa ce kawai amfaninki gare ni ba, ke ɗin dai nake so kuma komai
naki mai daraja ne a wuri na."
Har cikin zuciyarta kalamansa sun ƙayatar da ita matuƙa. Kuma sun zare mata tsoro da fargaban da ya
lulluɓe ta. Saboda sanin wane ne shi da kalolin jarabarsa, jiki a sanyaye ta nufi toilet ya bi bayanta da kallo
har ta shige, sannan ya koma sauke ajiyar zuciya wata bayan wata tsikarsa tana tashi, a ƙoƙarin danne abin
da yake ji a ransa ya furzar da iska mai zafi a cikin bakinsa. Wanda ya yi silar jefa shi takaicin iyakar da
Hajiya ta yi masa a kanta, saboda tuno zafafan kalamanta.
Shiru ya yi dafe da kansa da ke ta sarawa har jijiyoyinsa suna harbawa. Tsam ya miƙe ya fiddo robar
takeaway da ke ɗauke da abinci, pepper chicken, ice cream da gwangwanin maltina da ruwa, ya ajiye gefen
sallaya sannan ya fiddo rigar baccin da ya siyo mata ita ma ya ajiye a bakin gadon. Ya kwanta gefen gadon
jiri yana kwasar shi ya runtse ido cikin wata kalar murya ya ce,
"Ya Salam!"
Tsam ta yi da ranta a lokacin da ta fito idonta a kansa, saboda ganin yanayinsa ya sa ƙirjinta bugawa, amma
hakan bai hana ta isa saman sallayar ta tayar da sallah ba. Cikin minti biyar ta kammala sallar ta ja lokaci
tana addu'a, wadda fiye da rabinta a kan nema wa Jamal sauƙi a kan ciwon da ke damunsa ne.
"Ki ci abinci."
Ya yi maganar idanuwansa a runtse cikin wata kalar murya, ido ta kai a kan kayan da ya jera kafin ta cira kai
ta kalle shi ta ce,
"Maganinka fa! Ko ka manta ba ka sha ba."
Shiru ya yi mata bai ce komai ba, har sai da ta maimaita maganar sannan ya miƙe yana wani irin nishi ya
jawo jakarsa ya zuge zif. Wata farar leda ya ciro yana faɗin,
"Ki ci abincinki na san kina jin yunwa, don shan maganin ba zai hana ni mutuwa ba."
Yarrr! Tsikar jikinta ta miƙe, tsabar shiga jikin da maganar ta yi wa gaɓoɓinta. A diririce ta zabura jikinta
yana rawa ta jawo ledar maganin tana faɗin,
"Ba yanzu za ka mutu ba. Don haka ka ma daina irin wannan maganar. Allah ba zai taɓa kashe ka ya bar
ni b.. dole ma tare za mu mutu a rana ɗaya kuma a lokaci ɗay...."
"Shiiiih!"
Ya yi hanzarin ɗora hannunsa a saman bakinsa dafe da zuciyarsa yana cewa, "Kina da gata, ba zan so
danginki su yi asarar ki b...."
Ya ƙare maganar da ƙyar yana ɗauke numfashi, saboda tuno ɗaya daga cikin kalamanta da suka tsaya
masa a zuciya. Jikinta yana rawa ta isa gare shi cikin muryar kuka ta riƙe hannunsa tana cewa,
"Don Allah...don girman Ubangiji Jaaan ka daina ba na so! Kada ka bari ciwon nan ya cuce mu a banza
musamman a irin wannan lokacin! Ka yi haƙuri mu je asibiti yanzu don Allah Jaaannn.."
"Babu abin da zai faru, matuƙar za ki daina yin abin da ke dawo da ciwon baya zan samu lafiy.."
"Na yi alƙawari ba zan sake yin abin da zai ɓata maka rai ba. Ka sa a ranka idan har ni ce matsalar daga
yau lafiyarka za ta dawo in sha Allah."
Wani kallo ya yi mata ganin yadda hawaye yake zarya a kan fuskarta. Fuskar da yake gani a mafarki tana
yi masa murmushi, fuskar da yake gani a ko'ina tana yi masa gizo. Amma a yau ga ta gabansa tana gani a
cikin yanayin da ba ya masa daɗi, don gabaɗaya fuskar ta gama zama ja tsabar kukan, bayan jan ido da
kumburin suka yi luhu-luhu tamkar wadda ke ciwon ido. Ƙur ya yi mata da ƙwayar idonsa yana kallon ta
tsawon mintuna suna kallon juna, kafin ya yi wata ajiyar zuciya mai ƙarfi, saboda tuno tarnaƙin da ke
gabansu, tare da zallar tausayin ta da ke taɓa ransa, duk da yana ƙoƙarin kawar da abin a zuciya saboda
tunanin da ke kansa a kan cewa ba ta son sa.
"Ke da za ki auri wanda kike so, me kike yi wa kuka?"
Ya yi maganar cikin raunanniyar murya yana sauke numfashi a sama. Ba ta ce da shi komai ba ta karɓe
ledar maganin ta hau buɗewa ƙirjinta yana bugawa fat-fat. Tsabar tashin hankalin ganin halin da ciwon ya
ƙara saka shi.
Gaba ta saka shi ya ci abinci kaɗan ba don ya so ba, bayan haka ta ɓallo magungunan kamar yadda ta
gani a rubuce jikin kwalayen.
Yana nuna ba ya so a haka ta matsa sai da ya sha maganin, da kanta ta gyara masa kwanciya a kan gadon
tare da ƙara wa Ac gudu. Kafin ta dawo bakin gadon ta tsaya rungume da hannnuwa a ƙirji idonta a kansa
tana zuƙar majinar kuka. Shi ko sai lumshe idanuwa yake yi yana buɗewa zuciyarsa cike da hasashen
washegarin ranar a irin wannan lokacin tana tare da wani a matsayin matarsa shi kuma mijinta. Zuciya mai
ɗora wa mutum matsala har da hango hotonsu a kan gado suna raya sunnar aure.
Salati ta fasa iya ƙarfinta ta yi kansa tana kiran sunansa, saboda nan take wani kalar tari ya turnuƙe shi ya
shiga aman jinin da ya sa ta rungume shi jikinta, a firgice ta dinga cakumar sa tana zunduma ihu da
kururuwar kiran jama'a su kawo mata ɗauki a cikin zaucewa.
Next page.
33.
Kwanƙwasar ɗakin da aka yi ya sa ta zabura da nufin buɗewa bayan ta yi ƙoƙarin raba jikinta da nasa. Caraf
ya riƙe hannunta da jajayen idanuwansa ya dinga girgiza mata kai saboda ganin abin da take son aikatawa.
Tsaye ta yi turus tana kallonsa hawaye yana zarya a kumatunta har ya dafa ta ya miƙe. Hannunta ya ja duk
ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin da ake yi, haka ya nufi toilet riƙe da ita cikin ƙarfin hali ya fara wanke bakinsa tare
da fuskarsa, kafin ya tara kai a showa tana bugun kansa tsawon mintuna yana ta sauke ajiyar zuciya. Sai da
ya kwashi minti huɗu a toilet