Advertisements
Chapter 96 Reading A Duniyata Book 2 Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Duniyata Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Huguma Category :  Complete Novels

Chapter   96 / 119

285K to 288K   out of 356.9K words

da wuri haka ba shi yasa ya bude wayar.

"BB ba'a ga amna ba tun daren jiya......ga musaddiq nan ya rikice mana,kaman yanason rasa nutsuwarsa,ka sanar da hamma don Allah" Abinda saddiq ya fada kenan yana katse Kiran.

Innalillahi yakeso yaja,amma kuma bayaso yayi abinda zai tashi hankalin fannah daga wayewar garinta a rana ta farko,ballantana yasan mata da rudewa qwarai,dan qanqanin abu sai su maidashi babba,don haka ya miqe tsam da wayar a.hannunsa yace.

"Ina zuwa" Ya soma takawa yana fita a dakin. Tadan bishi da kallo kadan,sai kuma ta miqe tana ninke abun sallar da suka idar.

Wani dakin daban ya bude ya shiga,sannan ya fara qoqarin kiran fu'ad yana kuma laluban kayan da zai sauya a jikinsa,idanunsa akan agogo yana duba qarfe nawa.

Su dimma rufe alqur'aninsu kenan,don a yanzun shine malaminta. Tayi sauka tun kafin rasuwar mahaifinsu,tana da tilawa a kanta,amma sai yanayin karatunsa da qira'arsa suke mata dadi,wannan ya sanya ya zame mata malami duk bayan sallar asuba suke tilawar abinda ya sawwaqa tare.

Wani lokaci ido take zuba masa idan yana karatun. Komai Allah ya bashi,duk wata baiwa da take nuna cikar dan adam ya sameta,abu guda daya ne ya masa cikas da naqasu shine MAHAIFIYA.

Kashingidar da yayi da wannan damar ta samu ta zame jikinta zuwa kitchen. Wata irin mahaukaciyar yunwa take fama da ita a dan tsukinnan,ko cikin dare ta tashi abinci takeci,ba jimawa kuma take rasa komai,cikinta yake yayewa tasss kaman an mata yasa.

A tsaitsaye ta hada oats ta madara tasha,kafin sannan saiga ma'u ta shigo.

A mutunce suka gaisa,zuwa sannan ta fara gane inda sabreen tasa gaba na bawa mijinta kulawa da karan kanta.

"Me zamu dafa?"

"Ummm.....bari muga.....bari na fara dafa masa paw paw tea tukunna" Ta fadi tana nufar tsararren store dinsu.

Duk kusan ganyayyakin da yakesha akwai a ciki,busassu anyi packaging nasa cikin wani leda ta musamman da ake kawowa daga china. Packet na Paw paw leave din ta dauko ta dawo,ta wankeshi da kyau ta tafasa ta juye masa cikin wani Traditional English tea set sannan tace da ma'u.

"Ki fiddo naman kai bari naje na dawo".

Ta shiga daidai sanda ya fito daga toilet yana goge ruwan alwala. Idanunsu suka gauraya waje daya,kowannensu ya sakarwa dan uwansa lallausan murmushi.

"Barka da tashi sleepy head" Ta fada cikin salon tsokana. Fadada murmushinsa yayi har fararen jerarrun haqoransa suna fitowa.

"Barka kade my super girl" Ya bata amsa yana karbar tea tray din yana ajiyewa saman drawer. Hannunsa ya miqa mata yana jawota cikin jikinsa,saidai kuma sulalewa tayi ta tsugunna tana gaidashi. Amsa mata yayi cikin murmushi kafin ya miqa hannu ya sake jawota ya rungumeta tsam,fitinannen qamshin kabbasarta na incense by kabo daughter daya hautsina har cikin gashinta da kuma lab lab dinta suna tashi da wani sassanyan qamshi daya manne a fatarta.

"Fatan shalelena ta tashi lafiya.....addarmu.......matar babban yaaya" Yadda ya fadi maganan ya sanyata tuntsirewa da dariya,ya sake kamota yana qanqameta a jikinsa.

"Ina yara na?,fatan sun tashi lafiya?" Ya furta yana qoqarin dage rigar baccin jikinta. Da sauri ta damqe hannunsa tana duban tsakiyar idonsa,sai ya dage mata dukka girarsa yana tambayarta why?,da wannan kallon nasa.

"Ba bra a jikina".

" Good" Ya fada da hanzari yana daukanta cak ya azata saman drawer din,sannan yasa hannunsa ya dage rigar har zuwa inda yakeso.

Da cikin nata ya fara wanda ya fara turo kansa,ya aza dukkanin hannuwansa akai.

"Good morning my Angel's" Dubansa tayi.

"What?" Yatsansa ya dora saman lips dinsa

"Shshshsh" Ya fadi sannan ya maida hankalinsa kan cikin.

"Eheeennnnn......hope you're doing well......am eager to meet you my life.......have a nice and great day" Sai ya sunkuya yayi kissing na cikin. Sama ya komar da fuskarsa tsakanin ababen dake matuqar janye hankalinsa,qanqameshi tayi sanda yake cusa kansa a tsakiyar su,sannan ya sakar mata wani kiss din me sanyi kafin ya janye fuskarsa da idanunsa suka fara canza launi.

"Mun gama gaisawa.....me kike cewa?. Fuska ta bata.

"Son kai hamma.....son kai"

"Name?" Ya tambaya yana ware hannayensa.

"Angels hamma?......ni nafison baby boys.....masu kama da kai.....masu quality dinka". Ta fada tana tura baki gaba. Kyau sosai lips dinta sukayi masa,yasa hannu yana taba lips din murmushi na qwace masa,ya motsa bakinsa cikin nutsuwa.

"Nafison baby girls masu tausayi irin naki......masu tsananin zumunci irin na ummansu......masu qaunar 'yan uwansu.....kinsan ma haihuwar diya mace falala gareta me girma fiye dana d'a namiji?" Kai ta girgiza

"Na sani,idan aka haifi uku aka musu tarbiyya aka aurar dasu zasu zama sanadin shigar mahaifansu aljanna,sannan haihuwar d'iya mace tamkar shigowar haske biyu ne cikin gida,saboda zata jawo wani namijin shima ya zama naku". Tafi sosai ya sakar mata yana murmushi

"Bravo alaiki...." Ya furta yana kissing tafin hannunsa ya aike mata dashi.

"Duk da wannan?,duk da wannan my world kikeson boys?" Kai ta gyada.

"Na rigaka addu'a fa hamma......inaji a jikina Allah ya amsamin.......ina buqatar photocopies din muffin dina" Ta fada tana tsiyaya masa ruwan gwadar ta miqa masa.

Karba yayi yana dubansa,sai daya qare masa kallo sannan ya kalleta da lallausan murmushi

"Ya akayi kikasan ina sonsa?". Dukka girarta ta dage masa tana nade hannayenta a qirji,hakan ya qara mata kyau sosai.

"Kana tunanin idan nace inasonka ina sonka ne da wasa?......duk wanda nace ina sonsa......ina sonsa da gaske.....ballantana kai...." Ta qarasa fadi tana nunashi da yatsa daidai sanda kira ya shigo masa.

"Farouq?" Ya fada a mamakance,farouq dinne da kira haka da sassafe?,cikin jikinsa yaji tabbas akwai wani abu daya faru,ya miqa hannu yana daga kiran



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862



𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 144


*_NACE BA......._*🧏🏽🧏🏽

*_Hajjaju a ina kike siyan turare?....._*

*_NACE A INA KIKE SIYAN TURARE?_*

*_Ga wani fa........TASTED AND TRUSTED ne.......mun gwada munga ingancinsa_*

*_Da yardar Allah saikin godemin_*

*_KUNSAN DUK INDA QAMSHI YAKE ZAKA SAMENI A GURIN,MAGANAR GASKIYA KENAN AHTO_*πŸ˜‚πŸ˜‚

Golden oud
Hawi
Sandal balls
Sandal flakes
Cotton bakhoor
Kabbasine mix
Khumra(alba,alsuma,ebony,monarch,musk)
Deep crush (luxury khumra).
Signature oil
Kuleccham
Kabbasine spray

*_YA SUBHANALLAH.....hajiyata dukka wadannan zaki samesu a_*

*_PRIME SCENTS(the scents of royalty_*

*KE DAGA JIN SUNAN KINSAN ZA'A ZUBDA QAMSHI ME AJI DA DAUKAN HANKALI*

*SUNA NAN A*

*_No 3,kabiru sani lawan street,farawa layout,Maiduguri road kano_*

*BA'A KANO KIKE BA?*

*_karki damu,tuntubeta ta nan,TABBAS kayanki zasu iskeki a duk inda kike cikin aminci da yardar Allah,NA BAKI TABBACIN HAKA_*

*DANNA RUBUTUNNAN DON YIN MAGANA DA ITA KAI TSAYE*πŸ‘‡πŸΎπŸ‘‡πŸΎ
wa.me/+2348103155915

KO KI KIRATA TA NAN

08103155915



144


Shuru kawai yayi yana sauraren farouq har ya gama gaya masa abinda zai fada din. Satar kallonta yayi sanda take qoqarin zuba masa wani tea din.

"Ka kula please dude.....banaso adda taji maganar nan ko don lafiyarta.....itama fanna din ban gaya mata ba,zan wuce gidan yanzu"

"In sha Allah" Ya fada yana sauke wayar daga kunnensa.

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" Shine abinda yaketa maimaitawa can qasan zuciyarsa kafin ya samu ya miqe tsaye yana duban ta.

"Adamamin tea din nan,abba ne ya kirani yanzunnan wai ya kusa sauka yanason nazo". Har ga Allah bata kawo komai ba,kawai mamakinta shine abban ke nemansu da safe haka?,kuma shida farouq?. Ba huruminta bane zafafawa kan sanin meye asalin ainihin kiran ba,don haka ta taimaka masa ya sauya kayansa ya fice zuwa ma'ajiyar motocinsa,inda ya taso jordan suka fice tare.

"La haula wala quwwata illa billah" Shine abinda yake maimaitawa kawai akan hanya yana murza goshinsa. Wani irin tashin hankali ne yaji yana lullubeshi,duk irin tsaron da ya saka.....duk yadda yake kaffa kaffa amma daga gefe akwai wanda yake fakonsu?.

"Su waye?.....su waye?" Ya furta a dan zafafe yana jinjina hannunsa yana duban titi,yana jin kamar ya tariyo daren jiya komai ya wakana a idonsa.

"Waye ya rage?,waye yayi saura?" Ya fadi yanason tunawa ko akwai wani abu daya bari wanda ya kamata yayi baiyi ba.

Wayarsa ya fiddo ya fara qoqarin gwada number amna da kanshi,amma switched off ake gaya masa.

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" Ya koma maimaitawa. Anni kawai yakeji.....ko musaddiq zai biyo bayan anni ne wajen shiga rudani,saidai ita anni ta fishi dauriya da dakiya.

Tun daga harabar gidan daga kan fuskokin masu tsaron gidan ya karanci tashin hankali b'aro b'aro. Jordan na fakashi ya sauka da dan sassarfa ya wuce cikin gidan.

Da batulu ya soma cin karo,shugaban ma'aikatan gidan.

"Ina anni?" Ya tambayeta ba tare daya damu da amsa gaisuwarta ba.

"Tana sama sir"

"Okay.......Inaso kowanne baqo a gidan nan a kula dashi yadda aka saba,a kuma sallamesu ba tare da kowa yasan halin da ake ciki ba......a shaida musu an soke walimar saboda annin batajin dadi,likita kuma yace a barta ta kwanta ta huta sosai,saddiq zai sallami kowa,masu tafiya a jirgi da masu tafiya a mota,inaso nan da azahar gidan ya zamana daga mu sai mu,na tabbata ku kudai kukasan abun.....daga haka banaso labarin ya qara gaba"

"In sha Allah yallabai za'ayi duk yadda kace" Ta fada cikin girmamawa.

Yana shirin haurawa saman yaji muryar farouq,waiwayawa kawai yayi ya kalleshi yana amsa sallamar saiya juya yana haurawa saman. Hankalinsa duka yana kan anni,don haka ita ya fara gani a sanda ya bayyana a parlor din saman.

Kallo daya tak yayi mata yaga wata irin rama ta bayyana saman fuskarta,daga daren jiya zuwa yau?,idan kuma abun ya shallake haka kuma fa?,fu'ad ya tambayi kansa da kansa hankalinsa a tashe.

Sauke dubansa ya sakeyi ga huda,wadda ke cure waje daya taci kuka har ta soma jin ba dadi,saddiq na zaune kusa da ita,da alama qarfin gwiwar lallashinta yake neman tattarawa kuma bai samu hakan ba.

Musaddiq kuwa yana zaune kaman zane,ramarsa har taso wuce ta annin da wani taqi na musamman.

Kallon da yayi musu dukkaninsu a lokaci daya sai yaji zuciyarsa na nufin karyewa kaman yadda ta anni ta karye. Ganinsu sun biyun sai takejin dukka qarfinta ya tattara a nan....kaman sune duk wani hope nata a yanzun.

Fu'ad ne ya lura da yadda jikinta ya soma rawa,ya qarasa da sassarfa ya riqeta yana zaunar da ita. Komawa yayi gabanta ya zauna sosai yana tanqwashe qafafunsa.

"Kece qarfin mu anni.....don Allah ki sake bamu wannan qwarin gwiwar koda karo na qarshe ne....koda shine alfarmar qarshe da zaki mana mu 'ya'yanki". Duk yadda taso tsare hawayenta sai daya zarto,saidai tayi qoqarin saurin daukeshi,banda su farouq da fu'ad din ba wanda ya gani.

"Allah shine qarfinmu muhammadu.....shine kuma zai tsaya mana" Ta fada tana tattaro jaririyar dauriyar data rage mata. Saidai shigowar abba a daidai lokacin ya sanya qwarin gwiwar nata ya sulale yabi ruwa,don nufarsa tayi hawaye yana tsinke mata,fu'ad ya yiwa saddiq alama daya sauko da huda ya juya yana sauka da sassarfa.

*_BAYAN MINTI TALATIN_*

Dukkaninsu suna falon daya dauki shuru bayan gama tattaunawarsu akan al'amarin.

"Nayi alqawarin muddin ina numfashi......tsakanin yau da gobe.....idan yayi tsanani zuwa jibi,tabbas da ikon Allah,da kuma girman zatinsa amna zata dawo cikin ahalinta.....inason kowa a cikinku ya ajiyemin wayarsa.....BB harda kai,kubar security code dinku akai basai kun cire ba.....abu na biyu kowa inaso ya sanya ido akan motsinsa,da motsin duk wani mutum da yake mu'amala dashi komai qanqantarta.....anni ki saka taki wayar a ciki.....abba zanyi connecting kowanne kira da wayata basai ka bayar da taka ba.....but kowanne saqo ko.kiran duk da nayi connecting ka kula sosai yayin dagawa......zamuyi aiki da team dina na kwana biyu zuwa uku in sha Allah" Yadda yace din duka hakan akayi,har zai fita ya dubi huda.

"Bani taki wayar" Saboda wani tunani da yayi. Throughout yau bayason yau sabreen tasan komai ko taji komai,idam ta yuwu ma har zuwa sanda zaa kammala abun,saidai yasan abune me wahalan gaske,karbe wayar hudan zai rage shigarta tashin hankali.

Wunin ranar gaba daya bai zauna ba,dukkaninsu shi da farouq dinma,zirga zirga ce kawai ake yinta a sirrance. Hankalinsa dukka yana kan wayoyin daya karba,wai ko zaiga wani baquwar number ya shigo,saidai ko gilmawar saqo bai gani ba.

Zuwa yammaci saqo da kiran sabreen ya cika masa waya,sai daya idar da sallar la'asar ya ciro wayar sannan ya tuna tunda ya fita a gida bai kirata ba. Da sauri ya maida kiran nasa zuwa ga wayarta,bugu daya ta dauka,muryarta duk tayi wani laushi sosai.

"Am so sorry my world.....ayimin afuwa,munyi busy yau sabgogi sun riqe muffin sosai".

"Hamma na dauka ka manta dani ne yau?,yau Walmar anni,ga lokaci yana shirin kufcemin,na gama shiryawa ban sameka ba,kasan bazan fita ba kuma bada izininka ba,still kowa a gidan na kira number dinsa bai daga ba,hadda huda ma,lafiya kuwa hamma?". Yadda tayi maganar ya tabbatar jikinta ya soma raya mata akwai matsala,muryarta tayi wani laushi.

"Na saka an tsaida walimar nan sabrrr...zazzabi ne ya saukarwa anni,kinsan kuma tana da asthma.....so kiyi zamanki a gida.....i will tray my best naga na dawo gida da wuri". Dan jim tayi kadan kafin tace.

"Anya baka boyemin wani abun hamma?,ko wani abunne ya samu annin?". Murmushi ya saki me dan sauti na qarfin hali.

"Ba komai my world.....karki damu.....ki kulamin da kanki,ki gaidamin yarana". Ya fadi yana katse kiran.

Lamo kawai tayi saman gadon zuciyarta na wani bugawa,bugun sam ba daidai take jinsa ba,hakan yana sake bata tabbacin akwai abinda yake tafiya ba daidai ba.

Tayi juyi saman gadon har batasan adadinsa ba,a nan sallar magariba ta sameta taje ta bada ita,tayi isha'i ta sake dawowa ta kwanta.

Indai ciwon anni baiyi tsanani ba ai ya kamata ace ta samu koda mutum daya ya daga kiranta,bawai kowa ta kira wayarsa zata yita ringing bai daga ba.....ciki harda fuad din kansa.

Sanda tara na dare yayi sai taji hankalinta ya soma tashi,kiransa ne ya bata relief dan kadan.

"Am sorry....on my way dear,karkiyi kewata da yawa". Maganan da sukayi kenan a taqaice.

Yana ajiye kirannata wayar farouq ta dauki ruri. Da hanzarinsa ya ajiye tasa wayar y kuma daga wayar farouq din yana kallon screen din.

Baquwar number ce da babu ita a jerin lambobin kan wayar,baiyi jinkiri ba yayi hanzarin hada abinda zai hada ya kuma daga kiran.

"Farouqu hamza kibiya haka ne?"

"Shine" Fuad ya furta kansa tsaye yana fatan hirar tayi tsahon da yakeso.

"Yauwa......mune wadanda muka dauki qanwarka amna a jiya........saidai kafin mu tattauna komai daku muna buqatar kudi naira billon goma". Idonsa ya lumshe ya sake budesu,wani fushi yana taso masa yana lullube zuciyarsa. Ashar yakeso ya fara sake musu a matakin farko,to amma kuma har yanzu ba'azo gurin ba.

"Ba matsala.....zamu saka muku......amma idan munyi hakan zaku sakar mana qanwa salin alin?".

"Me yuwuwa....duk da bamu keda wannan hukuncin ba,wanda keda ikon fadin a saki ko a kashe daban.....wannan din ladan aikinmu ne muke buqata daga gareku". Bakinsa yaji yana motsi,amma sai yayi qoqarin danne zuciyarsa.

"Zamu biya mun amince......ku fadi inda za'a saka kudin".

" Zamu saka" Ya fada yana datse kiran.

"Oh shirt" Fu'ad ya fada yana dukan seat din motar. Qiris ya rage mintunan su cika.....baici nasara ba......

Bayajin wannan daren yana da nutsuwar gyangyadi ko bacci komai qanqantarsa.....maganar kisa suke fa idan ta kama?. Baiko jira Jordan ya gama tsaida motar ba ya bude ya dira daga ciki yayi cikin gidan.

Baiko tsaya tantance wanda yake parlor din ba ya ketashi ya wuce hallway,wannan qofar dake a kulle kullum ya danna ya budeta yana kutsa kansa ciki.

Ajiyayyen gurinsa ne dake dauke da tarin na'urori,ba kuma kasafai ya fiya shiga wajen ba sai ta baci ko kuma yana da babban aiki irin haka.

Gaba daya qwayayen ya kunna ya kuma kunna kowacce na'ura ya saitata kan aiki,ba dadewa komai ya daidaita,ya fidda gaba daya wayoyin ya zubesu ya riqe ta farouq a hannunsa yana kwafe numbers din zuwa allon screen din dake gabansa.

Tiryan tiryan ya soma kurdawa cikin bincikensa,saidai kaman yadda ya zata komai ya tsaya daidai iya mintuna daya kashe kiran.

"Ya salam" Ya fadi yana jin wani zafi da fusata.

"Da gaske dai wani abu ya faru" Muryar sabreen ta ratsa kunnensa. Da sauri.ya daga kai yana dubanta. Tana tsaye daga bakin qofa,sanye da night wear baby pink masu daukan idanu masu hawa biyu,gashinta ta sakeshi saman kafadarta,yayin da jaririn cikinta ya bayyana sosai ta cikin rigar kasancewar ta lafe mata sosai a jikinta.

Duk da yanayin da yake ciki na tashin hankali hakan bai hanashi hango kyawunta ba......hakan bai hanashi ganin wani kwantaccen kyau daga gareta ba.

"Listen sab....."

"Karka rufemin hamma.....na roqeka" Ta fada jikinta da muryarta dukka suna rawa.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE

96 / 119