Author : Maryam Category : Complete Novels
*KULUWA*
(Ƴar bala'i)
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*
Channel 👇
https://whatsapp.com/channel/0029Vb6Kd5SFnSz8T3XpQ22g
Group👇
https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT
*ALLAHUMMA SALLI ALA SAYYADINA MUHAMMAD WASSALIM*
Marubuciyar
RAYUWAR MU
MA'EESHAT
WANI SHARRIN
YAUDARA ZALLAH
Bismillahir Rahamanir Raheem.
Written by ✍️
Jagabar Jajirtattu
(Ta Batulu)
Chapter 1️⃣
Yara ne wajan guda goma sha biyar suna sanye da uniform green and white na primary school, kowace da duwatsu manya manya a hannunta yana tafe suna bin bayansa shima yana sanye da uniform irin nasu, sai da suka bari ya shiga lungu ɗaya daga cikin yaran mai suna Kuluwa ta fito ba zata wuce shakara goma sha huɗu ba, sauran harda ƴan mata suna da yawa dan za su iya fin sha biyar.
Kuluwa ta ɗaga dutsen hannunta tana cewa.
"Labbaikallahumma labbaik." Ta jefa mishi sauran ma suka fara jifanshi suna faɗin.
"Labbaikallahumma labbaik."
Ruwan duwatsu suke yi tako ina da ƙyar wani tsoho ya tare su yana musu faɗa.
"Wallahi kaci albarcin baba." Kuluwa ta faɗa tana nuna tsohon da ya hana su.
Tayi ƙwafa ta tafi sauran suka take mata baya kamar ƙudaje.
Har ta nufi hanyar gida ta dawo da baya gidan Asabe dilalliya ta nufa, kamar mutumiyar kirki tayi sallama ta duƙa ta gaisheta sannan ta ce.
"Baba lami ce ta aiko ni ki bata wake mudu biyar zata aiko miki da kuɗin jibi idan Allah ya kaimu."
Asabe kamar ba zata bayar ba amman tayi shahada ta auna ta bata waken cike da gargadin kar ya wuce jibin.
"Ta ce idan bata aiko miki dashi ba wai kizo da kanki, zata iya mantawa." Kuluwa ta faɗa tana ɗaukar waken ta fita tana dariya.
Tana tafe tana tunanin inda zata ɓoye waken, tazo wucewa shagon wani mai siyar da hatsi kawai ta yanke shawarar ta siyar ta amshi kuɗin ko ba zata yi komai da kuɗin ba, aiko ta shiga shagon ta duƙa har ƙasa ta gaishe shi sannan ta fara hawaye tana cewa.
"Dan Allah ka taimaka mun ka sai waken nan in samu in kai, mahaifiyata asibiti." Mai shago yaji tausayinta, yanda yake siyarwa a shago haka ya siya, ta amsa tayi godiya ta nufi hanyar gida tana shiga zauren gidan, ta cire jakan makarantar ta wurga tsakar gida ta koma.
Gidan Fatu ta nufa tayi mata gaisuwa cike da mutunci sannan ta ce mata.
"Mama ta ce ki bata shinkafa mudu uku zata aiko miki da kuɗin, idan Baba ya dawo anjima."
Fatu ta fara masifa ita bata san bayar da bashi, Kuluwa ta lalaɓata har da cewa.
"Anjima idan bata kawo kuɗin ba tazo ta amsa komun dare."
Fatu ta bayar da shinkafa mudu uku Kuluwa ta ɗauka ta fita.
"Na rantse da Allah Mama da Baba lami kun shiga uku, tunda kuka shigo sabgata shegu munafukai."
Kuluwa ta nufi gida tayi sallama babu kowa a tsakar gida, ta lalaɓa ta shiga kitchen ta yi mishi mugun ɓoyo, sannan ta fito ta shiga ɗaki ko sallama ba tayi ba.
"Kakus iyayen jaraba." Kuluwa ta faɗa tana hararan tsohowar dake kaɗa, lagwanin risho.
Kaka tayi banza da ita Kuluwa ta fara buɗe kwanoni ganin bata samu komai ba, ta miƙe ta fita tayi sallama tana tura baki, kaka ta amsa sallamar tana cewa.
"Kowa ya tuba dan wuya ba lada."
Kuluwa ta zumɓura baki tana hararanta kaka ta janyo kwanon kusa da ita Kuluwa bata lura dashi ba ɗazun, dambune yasha mangyada da wake Kuluwa sai da taci ta ƙoshi sannan tayi sallah, ta sanja kaya ta kalli kaka ta ce.
"To zamu fita neman na kai, zaman gida bana masu isashen lafiyar ƙafa bane."
Kaka tayi banza da ita Kuluwa tayi hanyar waje tana tafiya tana buɗe ƙafa.
Har ta fice daga gidan kaka bata daina kallanta ba, ta yanko kwanan gidan su Ummi ta haɗu da wata budurwa taci kwalliya tana tafe tana yanga haka kawai Kuluwa taji ranta ya ɓaci.
"Shegiya mai ƙatan kai da leɓe kamar na alade." Kuluwa ta faɗa tana ɗauke kai budurwan ranta ya ɓaci, ta nufi Kuluwa tana zuwa gab da ita Kuluwa ta kauce budurwan ta faɗa kwata mai warin tsiya.
Kuluwa dariya harda hawaye tana ta tsokanar mutane har ta ƙarasa gidan su Ummi, tana zuwa ta buga ƙofar gidan babu jimawa Ummi ta fito suka yi gaba.
"Ina muka nufa.' Ummi ta faɗa.
"Gidan su Maimuna." Kuluwa ta faɗa tana dariya.
Suka shiga gidan suka gaishe da mahaifiyar Maimuna, suka zauna suna tunanin yanda zasu janyo Maimuna waje su daka.
Aka zuba musu shinkafa da miya suka zauna suka cinye tas, da zasu tafi Maimuna ta rako su waje Kuluwa ta rufe mata baki da ƙasa suka yi mata dukan tsiya, sannan suka ruga da gudu Kuluwa tana cewa.
"Gobe ma ki ƙara gulma ta a hadda wallahi sai kin fi haka dakuwa, kuma ki cewa babarku bata iya abinci ba."
Kuluwa sai bayan magrib ta dawo gida tayi sallah sannan ta fara kuka.
"Kuluwa zan ci mutuncin ki wallahi, kinje kin gama yawon neman magana zaki zo ki ta sani a gaba kina kuka."
"Yanzu kin daina ƙaunata kakus Allah sarki Mamana." Kuluwa ta faɗa tana yiwa kaka gwallo.
"Yi shiru dan Allah ki faɗa mun waye ya taɓa ki a daren nan, wallahi sai naci mutuncinshi dan Allah ki daina kuka haba kululun kakanta."
Kuluwa ta share hawayen ƙaryan data ƙirƙiro ta ce.
"Baba na nake san gani dan Allah ki barni inje."
"Kuluwa dare ya yi." Kaka ta faɗa cike da rarrashi.
"Shike nan kaka idan na mutu a daren nan dan Allah ki ce mishi ya yafe mun, kema ki yafe mun dan Allah." Kuluwa ta faɗa tana fashewa da kuka babu hawaye.
"Mutuwa kuma tashi maza kije, Allah ya kiyeye hanya amman ko zan rakaki ne saboda dare ya yi." Kaka ta faɗa tana fatan Kuluwa ta amince suje tare.
"Gwara muje tare dake yanda bom ɗin zai fi tashi da sauri." Kuluwa ta faɗa a hankali.
"Mai kike ce." Kaka ta faɗa ganin bakin Kuluwa yana motsi.
"Babu komai kakata dan Allah ki yi sauri mu tafi, kar mutuwar tazo a daren nan banga Baba na ba."
Da sauri kaka ta saka hijjab ta karkace ba tare data lura ba, Kuluwa ta kulle ƙofar gidan suka nufi gidan mahaifinta.
Dalilin da yasa Kuluwa take san zuwa gida, saboda tana san tayi kallan rigima tsakanin Fatu da Mama, domin ta san yau akwai gagarumin yaƙi a gidan mahaifinta, shi ya sa take san zuwa ta yi kallo ƙarin abin farin ciki kaka data biyota.
Banyi alƙawarin typing kullum ba, sannan bana typing ranar juma'a.*KULUWA*
*(Ƴar bala'i)*
Group 👇
https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT
Channel 👇
https://whatsapp.com/channel/0029Vb6Kd5SFnSz8T3XpQ22g
*ALLAHUMMA SALLI ALA SAYYADINA MUHAMMAD WASSALIM*
Written by ✍️
*Jagabar Jajirtattu*
(Ta Batulu)
Chapter 2️⃣
Tun daga zauren gidan take jin hayaniyya Kuluwa tayi dariya, Mallam Sani yana zaune ya dafe kai Mama da Fatu suna zagin juna, Kaka tayi sallama Kuluwa ta nufi gurin mahaifinta.
"Alhamdulillahi gwara da Allah ya kawo ki, ɗazun ubanwa ya aiko ki karɓan shinkafa mudu uku." Fatu ta faɗa a fusace.
Babu tsoro ko shakka Kuluwa ta ce.
"Bani bace wallahi." Fatu ta saki baki da hanci tana kallanta.
Tashin hankali Mama ta mumulo zagi ta maka ta nufo gurin Kuluwa, Mallam Sani ya dakatar da ita yana cewa.
"Akwai ƙamshin gaskiya a maganar yarinyar nan, saboda ni ba shinkafa na ce ki dafa ba amman saboda neman masifa irin naki, kinje kin ciyo bashin jama'a to wallahi ba zan biya kuɗin ba."
Kuluwa tana lafe ajikin mahaifinta tana yiwa Mama gwallo a fakaice.
"Ku dai wallahi ba zaku taɓa hankali ba, mutane babu Allah a ransu, yaushe Kuluwa tazo gidan bansaniba?." Kaka ta faɗa rai a ɓace.
Baba lami dake ƙunshe dariya ta ce.
"Nima yau kwatakwata banga Kuluwa a gidan nan ba, hasalima ta kwana biyu bata zo gidan ba."
"To baƙar munafuka nayi magana dake ne.?" Mama ta faɗa kamar zata dake ta.
"Daga faɗar gaskiya sai ki dawo kaina, to Allah ya baki haƙuri yanzu sai ki fito musu da kuɗin shinkafar da kika dafa." Baba lami ta faɗa tana dariya.
Fatu dai tayi tsaye tana jiran a bata kuɗin ta.
Ƙarshe yaron Mama ya biya kuɗin yana hararan Kuluwa domin ya san halinta.
"Wallahi sai kin yi nadamar abinda kika aikata mun, munafuka mai baƙin hali irin na uwarta."
"Inalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Mallam Sani gidanka ya haramta a gareni." Kaka ta faɗa tana fashewa da kuka.
Mallam Sani ya dakawa Mama tsawa ta bar gurin tana yin ƙwafa.
"Yanzu a gidanka har matattu ake zagi kuma kana gani ka kasa ɗaukar mataki, wallahi ka zama taɓaɓɓe wanda bai da iko a gidansa." Kaka ta faɗa tana share hawaye da gefen zani.
Da ƙyar Kaka tayi shiru Mallam Sani ya rakasu har gida yana ƙara bata haƙuri.
Lokacin da Kuluwa tazo kwanciya ta ringa ihu tana cewa.
"Dan Allah ki yi haƙuri ba zan ƙara ba." Kaka a zaune ta kwana tana yi mata addu'o'i, Kuluwa idan taga Kaka ta fara gyangyaɗi sai ta zabura tana cewa gata nan zata kamani.
Zuwa ƙarfe biyu bacci ya ɗauke Kuluwa daga nan Kaka ta samu ta kwanta, cike da tunanin irin rashin mutuncin da zata yiwa Mama gobe.
Ƙarfe shida Kuluwa tayi sallah Kaka ta miƙa mata Qur'ani ta ce.
"Maza Kulun majadun ƴar gatan Kaka, fara mai farar aniya zinariya mai haska gida."
Kuluwa da farko ta fara ɓata fuska tana tunanin abinda zata aikata, wanda zai hana ta zuwa hadda amman jin kirarin da take mata.
Yasa ta karɓa Qur'anin tana rausaya jiki tana fari da ido kamar mai tashin aljanu.
"Maza kije ƴar albarka bana so ki makara." Kaka ta faɗa tana miƙa mata hamsin kuɗin wata.
Kuluwa ta amsa ta tafi tana rangwaɗa gata babu ƙiba 😂
Tana zuwa taga an tare makara ta ƙarewa mallamin kallo yana sanye da babbar riga, kuma gashi mallamin mugune bai da mutunci, ya tsani Kuluwa saboda rashin jin maganarta akwaita da ƙoƙari neman magana tsokana, babu wanda ta ƙyale harta mallaman sun san da zamanta, gashi bata ƙaunar abinda zai taɓa mata lafiyar jiki.
Wani tsumma ta gani a kusa da ita ya dunƙule kamar maciji, tayi murmushi ta ɗauka ta ɓoye a cikin hijjab ganin layin yaƙi zuwa kanta yasa ta yanke shawarar ta watsa gurin kawai kowa ya yi ta kansa.
"Wayyo Allah maciji maciji." Kuluwa ta faɗa tana jefa musu tsumman data ɗauka, tashin hankali gaba ɗaya kowa ya watse Mallam yazo guduwa babbar rigarsa ta yarda dashi.
"Mallam maciji a bayanka." Kuluwa ta faɗa tana zurawa da gudu cikin makarantar, Mallam ya fara rarrafe yana raba ido ya kasa tashi.
Koda ta shiga makarantar abinda take faɗi kenan.
"Maciji jama'a akawo ɗauki." Gaba ɗaya ta har gitsa makarantar, yara suna ta ihu wasu suna haurawa ta window suna guduwa, wasu kuma toilet ɗin makarantar suke shigewa.
Ummi ta dafa Kuluwa ta ce.
"Daman ina tunanin yanda zan watsa makarantar ne sai gaki kin zo."
"Dallah rufa mun baki munafuka matsoraciyya kawai." Kuluwa ta faɗa tana hararan Ummi.
Ganin akwai sauran mutanen da suke zaune acikin aji yasa ta fashe da kuka ta buɗe murya ta ce.
"Inalillahi wa'inna ilaihir raji'un macizan sun ƙara yawa." Haka ta ringa bin ajujuwa tana dirawa ta window, ƙarshe dai kowa ya yi takansa daman mallamai huɗu ne kuma kowa ya yi takansa, Mallam da rarrafe ya fita get ɗin makarantar duk ya haɗa zufa.
Suka nufi hanyar gida yara taga suna dambe ɗaya jibgegiya ɗaya siririya mai ƙibar tana ta dukan siririyar, ta miƙawa Ummi Qur'ani ta shiga tsakiyar su ta ɗibo ƙasa ta raba biyu, hagu dama ta kallesu ta ce.
"Gana tsiya gana arziki." Yarinyar da ake duka ta zubar dana arziki ɗayan kuma ta cakumi hijjab ɗin Kuluwa.
Kuluwa ta kwace hijjab ɗinta hamsin ɗin da Kaka ta bata shi ta miƙawa siririyar ta ce.
"Na sai faɗar." Yarinyar tasha ƙasa ta daku tana dafe hamsin ta zura da gudu.
Kuluwa taji anyi sama da ita.
Ta Batulu ce........ ✍️
Likes comments sune ƙwarin gwiwar marubuci.*KULUWA*
*(Ƴar bala'i)*
Group 👇
https://chat.whatsapp.com/EEiLcD9ZnpbFRLSjSOZozT
Channel 👇
https://whatsapp.com/channel/0029Vb6Kd5SFnSz8T3XpQ22g
*JAJIRTATTUN MARUBUTA WRITER'S ASSOCIATION*
Ban yarda a juya mun labari ta kowace irin siga ba, duk wanda na samu ya juya mun labari ba zan lamunci hakan ba.
Chapter 3️⃣
Mai ƙibar ta buga Kuluwa da ƙasa Kuluwa ta kwaso ƙafafunta, suka haɗu da Ummi suka yi mata duka sannan suka tafi Kuluwa ta ɗaga murya ta ce.
"Fankan fankan bata kilishi."
Suna tafiya suna tsokanar mutane da zasu rabu Kuluwa ta cewa Ummi.
"Ki shirya da wuri anjima ki biyo ta gidan mu."
Kuluwa ta karɓi Qur'anin ta nufi gida kaka tana zaune tana jan charbi, taci abinci ta ɗau allo kaka ta bata hamsin.
Kuluwa ta karɓa ta nufi makaranta an biya mata karatun, ta zauna cikin yara haka ta ringa tsungulin ƴaƴan mutane tana faɗin.
"Duk kun cika mana kunne."
Ƙarshe dai Mallam ya sallami Kuluwa domin kullum haka suke yi.
Tazo wucewa taga Sa'idu yana gyaran wuta daman ranar ya mareta, ta janyo tsanin ya faɗo tayi gaba tana dariya ta nufi gidan mahaifinta.
Babu kowa a tsakar gidan ta lallaɓa ta shiga kitchen, tukunya, ta gani a wuta ana dafa wake ta ɗauko gishiri mai yawa ta zuba ta lallaɓa ta fito.
Tayi sallama.
"Baƙar jaraba tauraruwa mai wutsiya." Mama ta faɗa tana hararanta.
Kuluwa tayi kamar bata ji abinda ta faɗa ba ta nufi ɗakin Mallam kamar yanda yara suke kiranshi.
Har zata shiga ta juyo ta kalli Mama ta ce.
"Dan Allah ina jin yunwa."
"Wallahi sai dai ƙamshi ya kasheki amman baki da rabo acikin abincin nan mayya kawai." Mama ta fada tana shiga kitchen.
Kuluwa tayi murmushi ta shiga ɗakin Mallam yana zaune yana karatun Qur'ani, ta duƙa ta gaishe shi sannan tayi shiru tana wasa da hannu.
"Lafiya.?" Mallam ya faɗa yana ajiye Qur'anin hannunshi.
"Daman kayan abincin mu ya ƙare shi ya sa nazo in faɗa maka." Kuluwa ta faɗa tana kallanshi.
"Lami bata aika muku da shinkafa ba.?" Mallam ya faɗa cike da mamaki.
Kuluwa ba tayi mamakin hakan ba domin ta jima da fahimtar matan mahaifin nata makirai ne.
Kuluwa tayi ƙasa da kai Mallam ya kira Baba lami ta shigo tana raba ido.
"Ina shinkafar dana bayar ki aikawa Kaka.?"
Baba lami ta fara kame kame data ga babu wani mafita sai ta ce mishi.
"Na aika mata dashi."
Kuluwa tayi karaf ta ce.
"Eh tabbas ta aika dashi, sai yanzu na tuna."
Mallam ya yi mata faɗa akan ta rage shiririta, Baba lami tana tsaye tana ƙarewa Kuluwa kallo domin bata yarda da wannan maganar data faɗa ba.
"Yunwa nake ji."Kuluwa ta faɗa tana kallan mahaifinta.
Mallam ya ce.
"Kije gurin Mama ta baki abinci."
Kuluwa ta miƙe tayi sallama da Mallam ta fita, babu kowa a tsakar gidan ƙasa ta ɗiba da yawa ta buɗe tukunyar ta samu an zuba shinkafa ya kusa dafuwa ta barbaɗa a sama, tayi gaba tana dariya tana barin unguwar taga wata yarinya tana siyar da awara.
"Zoki bani ala koro kasuwa."
Yarinyar tayi banza da ita Kuluwa ta janyo robar, gaba ɗaya awarar ya zube ta ɗibi guda huɗu ta ce.
"Wannan sun ishe ni, ki kwashe sauran Allah ya koro kasuwa ƴar baƙa." Yarinya ta fashe da kuka.
Kuluwa ta gama cin awarar sannan itama ta fashe da kuka, mutane suka fara taruwa suna tambayar abinda ya faru, Kuluwa tafi mai awarar kuka.
"Saboda ta ce in bata ala koro naƙi, shine ta zubar mun da shi." Kuluwa ta faɗa tana cigaba da kuka.
Mai awara ta saki baki tana kallanta aka taru anata bata haƙuri, Kuluwa ta samu leda ta zuba awarar ta saka yaji ta miƙawa mai awarar ta ce.
"Da na san zaki zubar mun da shi wallahi dana baki, amman kije bakomai Allah ya mayar mun da alkhairi."
Mutane suka ringa yaban Kuluwa suna saka mata albarka, mai awara makircin Kuluwa ya sumar da ita a tsaye.
Kuluwa tayi gaba tana tunanin abinda zata yiwa Baba lami, baba ya bata kayan abinci ta basu shine ta ɓoye kamar yanda ta saba, wallahi wannan lokacin bata ci banza ba sai ta biya harda riba.
Kuluwa taje gida ta ɗauko shinkafar data karɓo gurin Asabe dilalliya, ta shiga ɗakin Kaka ta na faɗin.
"Mallam ya bayar da shinkafa a kawo muku."
"Ina kika baro Qur'anin naki.?" Kaka ta faɗa tana tsareta da ido.
"A ɗakin Mallam." Daga haka ta zauna ta janyo kwanon data gani a rufe, kwaɗon zogale yasha tumatur yana ta ƙamshi.
Ta cinye tasha ruwa sannan ta kwanta tana tunanin irin abinda zata aikatawa Baba lami, wanda zai girgiza duniyarta.
A haka bacci ya kwasheta har akai sallar azahar bata farka ba, Kaka ta yayyafa mata ruwa daman Kuluwa akwai nauyin bacci.
Ta miƙe tayi sallah ta zauna tana hararan Kaka, ganin zaman ba zai fisheta ba yasa ta miƙe ta ɗibo ruwan zafi a kitce ta shiga tayi wanka ta fito.
Riga da zani tasa zanin dai dai gwiwa ta ɗaura aka samu powder ta shafa, ta zauna ta ɗauko gazal ta zana tun daga gira ta haɗe da kunne, ta ɗauko kwalli ta shafa a baki sannan ta ɗaura da lipgloss.
Ta shafa turare ta ɗau madubi, ta fashe da dariya tana yi tana gwallo.
"Oh ni Kulun majadun daman haka nake da kyau kamar, sarauniyar Ingila."
"Sai dai sarauniyar mahaukata amman bana ƙasar waje ba." Kaka ta faɗa tana hararan ta.
"Kakus maine ne abin baƙin ciki dan Kuluwa ta fiki kyau, kin ci zamaninki kina neman kici na wasu."
Kaka tayi banza da ita, Kuluwa ta ɗauko babban madubi ta ajiye a gabanta, ta fara tafiya tana lanƙwaye jiki kamar zata karye.
Ummi tayi sallama ta shigo itama da kwalliyar hauka, irin na Kuluwa suka haɗu a gaban madubi suna waƙa, suna yi suna fari da ido yanda kasan gayyar mahaukata.
Kaka duk yanda tayi banza da ita sai da suka sakata dariya.
Har la'asar suna waƙa a gaban madubi Kaka