Author : Maryam Category : Complete Novels
ta ƙwace madubin ta kora su, suje suyi sallah.
Suna idar da sallah Kuluwa ta ce.
"Kakus ina jin yunwa."
"Ki duba abinci a kitchen." Kaka ta faɗa tana shiga bedroom.
Daga cikin kitchen Kuluwa ta kira Ummi, tana cewa.
"Yau gidan mu babu abinci, zo mu tafi bara tun dare bai yi mana."
Kuluwa ta yafa gyale suka nufi hanyar fita Kaka ta kirata tana cewa.
"Ki zo in gyara miki ɗaurin zanin nan kamar za a tsallake wuta."
"Ai yanzu haka ake ya yin ɗaura zani a sama." Kuluwa ta faɗa tana yin waje da gudu Ummi ta rufa mata baya.
"Ubangiji ya nuna mun ranar da Kuluwa zata yi hankali, yarinya kamar kwancen aljanu."
Banyi alƙawarin update kullum ba, likes and comments sannan kuyi sharing.
Ta Batulu ce........ ✍️*KULUWA*
*(Ƴar bala'i)*
Group 👇
https://chat.whatsapp.com/HDAsWBYpkZP5YJSNFPR5I8
Channel 👇
https://whatsapp.com/channel/0029Vb6Kd5SFnSz8T3XpQ22g
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*
Written by ✍️
*Jagabar Jajirtattu*
*(Ta Batulu)*
Chapter 4️⃣
Sai da suka fita ƙofar gida Ummi ta ce.
"Yanzu ina muka nufa.?"
"Akwai gidajen da akayi biki shekaran jiya, zo muje cin kayan gara." Kuluwa ta faɗa tana tafiya.
Suna tafe suna yarfe hannu kamar masu lalura, idan kayi musu kallo ɗaya zaka ɗauka ƴaƴan aljannu ne fuska yasha powder ana tafe ana fari da ido.
Zun zo wucewa majalisar matasa Kuluwa ta gyara tafiya ana tafe kamar za karye, mai rake yazo wucewa Kuluwa ta tsayar dashi tana tambayarsa nawa nawa.
Mai rake yaga ciniki ya washe baki ya faɗa musu kuɗin, Kuluwa ta kwashi guda huɗu manyan ciki tayi mishi fari da ido.
Mai rake ya tsaya yana kallan ikon Allah suka yi gaba suna mishi fari da ido, ganin za su yi nisa ya tura keken raken yasha gabansu.
"Kuɗin rake na."
Kuluwa ta kalleshi sama da ƙasa ta watsar ta ce.
"Ka godewa Allah yau kasuwar ka zata yi albarka, tunda har ka haɗu damu wallahi yau sai ka siyar da raken nan duka."
Mai rake ya ƙura mata ido shi sai yanzu ya ƙare musu, gabansa ya faɗi lokacin da suka haɗa ido da Ummi kwalliya ne yanda ka san na mutanen ɓoye.
Mai rake yaji tsoron ko aljannu ya haɗu dasu gashi gari ya fara duhu, ya duƙar da kai Kuluwa ta ƙara diɓo guda biyu, Ummi data fahimci ya tsorata ta kalli Kuluwa tayi mata alama.
"Idan na koma duniyar mu zan cewa Baba na ya ƙara maka jari." Kuluwa ta faɗa tana gwallo manyan idanunta, ma sha Allah gashi idanun yasha kwalli.
Shi dai mai rake ya sunkuyar da kai ya ƙasa ya kasa motsawa, gaba ɗaya jikinsa rawa yake yi.
Kuluwa ta daka mishi tsawa.
"Bamu guri zamu wuce, idan kuma zaka bimu bismillah."
Mai rake ya faɗi ya fashe da kuka yana ta rarraba ido, ya kasa magana domin gaba ɗaya ya gama tsorata.
Kuluwa tayi gaba da rake a hannu, suna tafe suna shan rake har suka ƙaraso inda za suje, gidan yasha penti da gani saban gidane suka shiga suna rafka sallama.
Babu kowa a tsakar gidan suka shiga suna cigaba da sallama, wata mata ce ta leƙo tana tambayar su waye, taci kwalliya tana ta zuba ƙamshi, daga gani ka san amarya ce.
Kuluwa ta harareta sannan ta ce.
"Daman yaya ne ya matsa sai mun zo mun gaisheki."
Amarya ta yamutsa fuska tana faɗin.
"Ku shigo."
Kuluwa tayi dariya tana cewa.
"Zaki ci ubanki yarinya Kuluwa ce yau a gidanki."
A saman kujera ta zauna ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya suka zauna a ƙasa kamar munafukai, suka gaisheta da ƙyar ta amsa tana tauna cingom.
"Aunty zamu sha ruwa."
Kuluwa ta fada tana tunanin abinda zata yi.
"Aiko ruwan gidan ya ƙare." Amarya ta faɗa cike da jan aji.
Kuluwa ganin amarya ta hanasu cin cin ranta ya ɓaci.
"Aunty wannan da kike gani ƙanwar budurwan yaya ne." Kuluwa ta faɗa tana na nuna Ummi.
Amarya ta zabura ta mulmulo zagi ta maka,
Ummi ta fashe da kuka tana cewa.
"Yanzu haka yana gidan mu gurin yayata, shi ne na samu ƙawata na faɗa mata lokacin ta gama shiri zata zo nan gidan, sai ta roƙeni in rakota domin ta faɗa miki, kuma wallahi auranta zai yi ni kuma yanda ki kai mana sai naji kin burgeni ba zan yarda aci amanarki ba."
"Inalillahi wa'inna ilaihir raji'un, dan Allah dagaske kuke yi.?" Amarya ta faɗa tana wurgar da cingom ɗin bakinta.
Kuluwa zata yi magana ta fara shaƙuwa tana dafe ƙirji.
"Na shiga uku." Ummi ta faɗa tana jijjiga Kuluwa.
"Mai ya sameta.?" Amarya ta faɗa gabanta yana faɗuwa.
"Tana da laluran aljannu kuma idan suka taso mata sai taci kaza, kuma wallahi idan bata ci kaza ba duk mun shiga uku." Ummi ta faɗa cikin kuka.
Amarya ta shiga kitchen kamar zata faɗi, plate ta fito dashi ta koma drinks ta kwaso guda huɗu ta ajiye, Kuluwa ta miƙe zuruf ta buɗe plate ɗin ta fara cin kaza hannu baka hannu ƙwarya daman yunwa take ji, kana ganinta ka san babu sukuni amarya tana raɓe a gefe tayi tagumi.
"Aunty babu cin cin ne.?" Ummi ta faɗa amarya ta koma kitchen.
Ummi ta ɗauke rabin kazar ta naɗe a zaninta, drink ta ɗauka guda ɗaya ta shanye ta ajiye robar.
Amarya ta fito hannunta ɗauke da plate cike da cin cin dublan alkaki, cike da mamaki take kallan Kuluwa ta cinye kazar ansha lemu guda biyu, ta kalli Ummi ta ganta a zaune a inda ta barta.
Kuluwa ta maƙale murya ta ce.
"Aunty mungode da kika taimaki goɗiyar mu, munji daɗi kuma zamu taimaka miki."
Amarya tayi shiru tana tunanin yanda mijinta yake ce mata daga ita babu ƙari.
"Tabbas mijinki yana da budurwa kuma sai kinyi da gaske zaki iya raba su, lallai ki bincike kayansa zaki samu bayanan da kike nema." Kuluwa ta faɗa tana fari da ido, idan kaga yanda take yi zaka rantse aljannun gaske ne.
"Karki faɗa mishi goɗiyar mu tazo gidan nan, domin zai hanata taimakonki." Kuluwa ta faɗa tana zaro ido, amarya tayi baya da sauri.
Tayi atishawa sau uku sannan ta kalli Ummi tana faɗin.
"Tashi muje gida ana kirana."
Ummi tayi murmushi ta ɗauko leda a saman fridge, ta juye duka abinda basu ci ba ta kalli amarya ta ce.
"Karki manta da abinda aka faɗa miki."
"Mai ya faru.?" Kuluwa ta faɗa tana ɗaure fuska.
"Babu komai." Ummi ta faɗa tana ƙunshe dariya, amarya ta ƙara musu cin cin tayi musu godiya suka tafi.
Sai da suka yi nisa da gidan suka ringa dariya kamar mahaukata.
"Kin samu kaza kamar wata mayya." Ummi ta faɗa tana dariya.
"Ai dalilin da yasa nayi mata haka saboda na fahimci marowaciyya ne, kin ga data ji maganar kishiya harda kaza ta bayar." Suna tafe suna dariya.
Duk da yamma tayi basu fasa zuwa gidan ɗayan amaryan ba.
Ummi tana riƙe da leda Kuluwa ita ce a gaba.
Banyi alƙawarin typing kullum ba.
Ta Batulu ce............✍️*KULUWA*
*(Ƴar bala'i)*
Channel 👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaBJBOr8vd1H4qb9rd1a
Group 👇
https://chat.whatsapp.com/HDAsWBYpkZP5YJSNFPR5I8
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*
Allahumma salli ala sayyadina Muhammad wassalim.
Chapter 5️⃣
Suka samu guri suka zauna amarya ta fito suka gaisa, Kuluwa ta ce.
"Da kawu Nuhu da mahaifiyata uwarsu ɗaya ubansu." Daman kafin su ƙarasa gidan sai da suka tambayi sunan angon.
Amarya tayi musu fara'a sosai ta zuba musu abinci da lemu suka zauna, bayan sun gama da za su tafi ta ɗauko leda babba da ƙarami ta zuba musu cin cin dublan, babbar leda su kaiwa mahaifiyarsu ƙaramin nasu.
Suka amsa suna washe baki da za su tafi ta basu ɗari biyar su hau mashin.
Suna fita suka sai babbar leda suka zuba kayan aciki, suka tsaya suka sai farar powder suka shafa gaba ɗaya fuska, duk wanda ya gansu sai ya furgita idan kuma yara ne sai su hau gudu.
Wani yaro yana haɗa ido dasu ya fashe da kuka yana gudu yana faɗin aljannu, kamar da wasa mutane suka fara gudu Kuluwa Ummi suma gudu suke yi suna faɗin.
"Maraba daku bil'adama."
Abu kamar wasa matasa yara tsofaffi gudu suke gashi babu huta nepa, kuma gari ya yi duhu farar powder kawai kake hangowa da idanu.
Duk wannan gudun Kuluwa na riƙe da leda akai, ta bayan gari suka yi yanke ƴan mata da samari ana ta zance, sun biyo ta bayan gidan mai gari suka ga Sa'ida yarinyar mai gari tana rungume da wani namiji, Kuluwa tayi baya gonakin da suka baro suka koma.
Kara ta ɗibo masu yawa ta dawo har yanzu suna rungume da juna ta ƙara shafa farar powder.
Ta miƙawa Ummi kayan hannunta Ummi ta amsa ta ɓuya a bayan gurin ta yanda babu wanda zai ganta.
Sa'ida da saurayinta Ahmad sun jima suna aikata kuskure, babu wanda ya sani har ciki sun taɓa zubarwa sau ɗaya.
Sa'ida tana ƙaunarshi da gaskiya wannan dalilin yasa, daya nemi ta bashi kanta babu wani tunani ta amince, shi kuma ba ƙaunarta yake yi ba sha'awarta yake yi.
(Kuskuren da ƴan mata ke aikatawa kenan a wannan zamanin, kuma wallahi duk namjin kirki wanda yake ƙaunarki da gaskiya, ba zai nemi taɓa jikinki ba ballantana har ya nemi yin lalata dake Allah ka tsarkake mana zuciya)
Kawai suka ji an daka musu tsawa, zasu gudu Kuluwa ta maƙe murya ta ce.
"Duk wanda ya ƙara taku ɗaya sai na shanye ruwan ƙoƙwan kansa."
Saurayin harda fitsari a wando.
"Wato ku ƴan iska koh.?" Kuluwa ta faɗa tana zaro ido.
Suka zube a ƙasa suna bata haƙuri.
"Ina can bangon duniya yarana suka kirani, suka faɗa mun iskancin da kuke aikatawa, daman sun jima suna bibiyarku amman baku daina ba, yau gani da kaina zan yi muku hukunci dai dai da abinda kuka aikata." Kuluwa ta faɗa tana hararan su, da manyan idanunta masu ƙyalli.
Sun kasa magana sai kuka suke yi Kuluwa ta ce.
"Duk wanda ya ƙara buɗe baki sai na tsayar da bakin." Kamar anyi ruwa an ɗauke, kuma gurin mutane basu cika bi ta hanyar ba.
Zan gindaya muku sharaɗi kuma idan kuka ƙi bin umarni na, sai na mayar daku alade da aladiya.
Suka fara kaɗa kai gashi babu halin magana.
"Lallai kuyi aure da gaggawa idan kuma ba haka ba, zakuji ana cewa maraba da zuwa duniyar aladu."
"Ina so ki yi mishi bulala goma yanzu." Kulawa da faɗa tana miƙawa Sa'ida dorina, a gurin ta tsinta dorinar mai gari ce yara suka jefo gurin.
"Wannan shine hukuncin iskancin da kuke aikatawa." Kuluwa ta faɗa tana zaro ido.
Sa'ida tana ƙaunar saurayinta ba zata iya dukansa ba.
"Hhhhhhhhh wato ke sarkin soyayya lallai zaki yi nadamar hakan." Kuluwa ta faɗa tana ƙara maƙale murya.
"Karɓa kayi mata bulala talatin." Ai kafin Kuluwa ta rufe baki har ya ɗau dorinar ya fara tsuga mata a jiki.
Sa'ida ta fara ihu tana neman taimako Kuluwa ganin asiri zai tonu yasa ta ce.
"Ka cigaba da dukanta har sai na ce ka tsaya."
Tana gama faɗa ta riƙo hannun Ummi suka bar gurin da gudu.
Daga haka suka raba kayan kowace ta nufi hanyar gida.
Abinda ya faru bayan su Kuluwa sun gudu, Sa'ida ihu take kamar ana yanka namar jikinta, shi kuma ƙara zabga mata dorina yake daga ƙarshe ihun ya yi yawa mutane suka taru, da ƙyar aka riƙe Ahmad yana ƙoƙarin sai ya koma ya cigaba da dukanta.
Sa'ida sai kuka take yi tama kasa tashi ƙarshe mai gari ya shiga da ita gida, Ahmad kuma ya saka a kulle shi zuwa gobe da safe.
Kuluwa tayi sallah ta wanke fuska kitchen ta shiga, tuwo ta gani tun na rana da alama ba a ɗaura girki a gidan ba.
"Kakus mai ya hana baki yi girki ba." Kuluwa ta faɗa tana zama kusa da ita.
"Saboda gantalallen ubanki bai kawo cefane ba." Kaka ta faɗa cike da jin haushi.
Kuluwa ta janyo ledar data shigo dashi ta fito da komai na cikin ledar sannan ta ce.
"Gidan Maman Ummi muka je shi ne ta bayar da wannan a kawo miki."
Kuluwa ta san halin Kaka shi ya sa take bin ta a hankali, kuma idan taji yanda aka samo wannan kayan to ba zata ci ba.
Kuma da gaske ne babu kuɗin cefane kayan abincin ne kawai, suka zauna suka ci sauran suka ajiye Kaka ta fara yi mata faɗa kamar yanda ta saba a kowace dare.
"Wai dan Allah Kaka bakin ki baya yin zafi idan kina magana." Kuluwa ta faɗa tana juya ido.
Kaka tayi alwala ta hau darduma Kuluwa ta kwanta tana tunanin bom ɗin da zai tashi gobe a gidan Mallam, Baba lami ga Asabe dilalliya lallai za a sha kallo.
Da sassafe za taje gidan domin taga yanda komai zai wakana a haka bacci ya ɗauketa cike da farin ciki da burin gari ya waye.
Dajine mai cike da tsoro da furgici tana tsaye da ƙwarya a saman, tana sanye da jajayen kaya, tana kiran sunan Samad Samad Samad sai da ta kira sau uku ƙwaryan ya fashe yana kamawa da wuta.
Daga bayanta taji an ce.
"Lallai ki nemo ta a duk inda take domin ita ce cikar muradinki, idan babu ita har abada burinki ba zai cika ba ki nemotahhhhhhhhhh." Cike da amoh maganar ta ɗauke. Hajiya Falmata kenan muguwar mace, makira kuma mace mai fuska biyu.
Karku ruɗe ƴan amanata muna cikin Kuluwa har yanzu.
Yawan likes ɗinku yawan typing ɗina
Ta Batulu ce............✍️*KULUWA*
*(Ƴar bala'i)*
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*
Channel 👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaBJBOr8vd1H4qb9rd1a
Group 👇
https://chat.whatsapp.com/EEiLcD9ZnpbFRLSjSOZozT
Written by ✍️
Jagabar Jajirtattu
(Ta Batulu)
6️⃣
Hajiya Falmata mace mai duniya taƙama izzah rashin mutunci zalunci duk ta haɗa, matsafiyyace mai neman ɗaukaka da suna sai dai har yanzu burinta bai cika ba.
Tana zaune a Kano unguwar ɗan ladi na sidi, mijinta Alhaji Hashim ya rasu tana da ƴaƴa guda uku mata, Sakeenat Salma Sa'adatu, sannan tana da yarinya Fatima, da ita tazo gidan sai ɗan kishiyarta Samad.
Babban burin Falmata ganin bayan Samad sai dai duk yanda zata yi abin yaƙi, domin Samad mutum ne mai addini kuma ya riƙe azkar da karatun Qur'ani.
Mahaifiyar Samad ita ce uwar gida bayan haihuwar Samad Alhaji Hashim ya auro Falmata, lokacin da mahaifiyar Samad Hauwa'u ta samu cikin na biyu Falmata ta sadaukar da ita da jaririn cikin.
Babban burin Falmata Samad ya auri Fatimah, domin dukiyar ta dawo hannunta gaba ɗaya Alhaji Hashim ta sadaukar da jinisa, yanzu Samad kawai ya rage kuma yana yi mata biyayya kamar ita ce ta haifeshi, tayi nasarar haɗashi aure da Fatima amman har yanzu bata cika burinta ba, dodo ya tabbatar mata da cewar akwai jinin da zata samo wanda shine cikar burinta da muradanta.
Sai dai duk inda za aje ba a samo irin wannan jinin ba, kuma har yanzu bata haƙura ba Fatima tana da kirki Samad yana jin daɗin zama da ita, amman itama bata da kirki ƴan aikinta suna kuka da ita, kuma duk cikin da take samu an riga an sadaukar dashi, ba tare da sun san dalilin hakan ba sun yi magani har ƙasar waje amman ba a dace ba.
Kuluwa da sassafe ta tashi taje hadda ta dawo, ta zauna Kaka ta dama koko Kuluwa taje siyo ƙosai, gidan akwai mutane ta fita can ta ƙara dawowa ta cewa mai ƙosan.
"Inji Baban Abba ya ce ki bashi ƙosai na ɗari biyar."
Mai ƙosai taji an ambaci sunan mijinta ta karɓa ta zuba, Kuluwa sai data kai bakin zaure sannan ta ce.
"Wallahi babu wani Baban Abba daya aiko ni, hasalima ban san shiba sunanshi na tambaya." Tana gama faɗa ta zura da gudu.
Sun gama karyawa ta biya gidansu Ummi ta kirata suka nufi gidan Mallam, girkin Baba lami ne a can suka yini kuma aka hanasu abinci, ƙarshe Kuluwa ta ɗauke abincin Mallam ta fita dashi gurin mai sayar da nama suka nufa.
Suka gaisa Kuluwa ta ce.
"Baba lami ta ce ka bata nama na dubu biyar, anjima zata aiko maka dashi idan Ya Salis ya dawo aiki."
Mai nama ya zuba mata Kuluwa ta amsa, suka nufi gida a zaure suka zauna sannan ta fito da abincin Mallam suka cinye tass, ta raba namar gida biyu suka cinye ɗaya suka sha ruwa sannan ta lallaɓa ta mayar da kwanon.
Ta fita suka shigo da Ummi lokacin Baba lami tana ɗaura alale, daman tana yin na saidawa Kuluwa ta zauna tana taya ta bayan sun gama, ta fito da nama ta yiwa Baba lami bismillah, aiko kamar jira take yi babu kunya ba tsoran Allah ta gyara zama, duk da cewar ta hanasu abinci amman haka ta zauna aka cinye namar da ita.
Mama tana ta leƙe domin wallahi ta saka rai, Baba lami har da jefa mata takarda bakin ƙofa.
Bayan la'asar Asabe dilalliya tayi sallama suka gaisa da Mama, sannan ta kalli Baba lami ta ce.
"Yaune cikar alƙawari, zan wuce na ce bari in tsaya in karɓi kuɗin wake."
"Bangane kuɗin wake ba.?" Baba lami ta faɗa tana dakatawa da tsame alale a wuta.
"Kin ga bana san rainin hankali da rainin wayyau, ki ɗauko mun kuɗina ki bani cikin ruwan sanyi." Asabe ta faɗa tana cire mayafin kanta.
Baba lami tayi banza da ita sai data kwashe alalen a wuta zata shiga ɗaki, Asabe ta riƙota.
"Zaki bani kuɗi na, ko kuma sai na kira masu ƙwatar mun.?"
"Kije ki kira duk uban da zai karɓan miki, ina jiranshi."
Dambe ya kaure tsakanin Asabe da Baba lami.
Mama ta ringa dariya tana tafi, daman tana jin haushin hanata nama da suka yi.
Asabe dilalliya ta yiwa Baba lami duka sannan ta ɗebo mata ƴan sanda, ko da aka tambayi Asabe dilalliya ta faɗi abinda ya faru, ta zayyano duk abinda ya faru, Baba lami ta mulmulo zagi tana tsinewa Asabe.
Koda Baba yazo belin Baba lami sun hana domin ta yiwa DPO rashin kunya, kuma ya rantse sai ya yi maganinta Kuluwa duk abinda yake