Author : Maryam Category : Complete Novels
gudu, Mallam Usman shi ne na ƙarshe Kuluwa ta caf ko shi, Mallam Usman ya fara ihu yana neman taimako, Kuluwa ta ringa kai mishi yakushi da ƙyar ya ƙwaci kan shi.
Ta fito filin makarantar gaba ɗaya Mallaman sun gudu, Ummi ta nufi sauran ajujuwan tana cewa.
"Kowa ya yi ta kansa." Duk ajin data je sai ta bigi ƙofar sai tayi gaba, duk ɗalibin da ya fito suka haɗa ido da Kuluwa sai ya nufi bakin get.
Bayan kowa ya watse Kuluwa ta miƙe tana riƙe baya, gurin data birne kayan marmari ta nufa ƴan group suna take mata baya.
Aka raba kowa ya kama hanyar gida Kuluwa da Ummi suka nufi gidan Mallam, suna tafe Kuluwa tana tsintar duwatsu.
Babu kowa a tsakar gidan ta lallaɓa ta shige daman akwai safayar key a hannunta, shinkafa harda nama da alama yau girkin Baba lami ne, Kuluwa ta juye abincin ta jera duwatsu ta fito.
Sai da suka yi nisa sannan suka zauna babu ruwansu da mutanen dake wucewa, suka kwance ledar abinci suka cinye suka sha ruwa.
"Yau fa bana jin komawa gida." Kuluwa ta faɗa tana gyara zama.
"Ina zamu je.?" Ummi ta faɗa tana neman ƙarin bayani.
"Muje kasuwa." Kuluwa ta faɗa tana tafiya, Ummi ta bi bayanta.
Sunje guri yafi biyar amman basu sai komai ba, suka je wani shago za su sai farin powder babba.
Suka tambayi kuɗin powder, mai shago ya faɗa musu kuɗin shi dubu daya.
Kuluwa ta ce.
"Ɗari uku."
Ya ƙwace kayan shi ya yi banza da ita, sun kewaye kasuwa basu sai komai ba, a shagon ƙarshe Kuluwa ta ce.
"Wallahi duk nacin mai shagon nan sai ya siyar mun da kaya."
Sun fara siyayya kamar abin arziki Kuluwa ta ce.
"Ka bamu bashi zuwa bayan sallah sai mu biyaka kuɗinka."
Mai shago ya zuba musu ido yanda suke fari kamar masu tashin jinnu.
"Dan Allah ku tafi na fasa siyar muku."
"Wallahi sai mun siya." Kuluwa ta faɗa tana miƙa mishi dubu ɗaya, kayan da suka kwasa yafi karfin na dubu uku.
Juyin duniya sun ƙi ƙara mishi ko sisi kuma sun hana shi kayan, da ƙyar suka ƙara mishi ɗari biyar suka yi gaba suna godiya.
Sun zo tsallakawa titi mota ya kusa taka su Kuluwa ta rufe ido cike tsoro, a hankali ta buɗe ido ta ƙare musu kallo motar tana tsaye gab da ita kuma babu wanda ya fito daga ciki.
"Allah ya haɗaku da masifa da bala'i tsinannu dangin mugunta." Kuluwa ta faɗa tana riƙo hannun Ummi domin su bar gurin.
Hajiya Falmata tana zaune a bayan mota hasalima ita ce ta hana driver fitowa, kamar an ce ta kalli hannunta taga zoben ta yana haske.
Da sauri ta buɗe ƙofa ta fito, sai dai Kuluwa ta ɓace mata babu ita babu alamarta.
Ta ringa tambayar mutanen gurin inda tabi, su kuma tsoro ya hanasu faɗa mata domin suna tunanin ko zata hukunta ta ne saboda zaginta data yi.
Kamar tayi hauka ta shiga mota har tana hawayen baƙin ciki, tana ji tana gani suka bar gurin.
Kuluwa gida suka nufa Kaka tana bacci ta ɗauko raguwar namar kaza, suka zauna suka ci sannan suka sha ruwa.
Wanka suka yi aka zana fuska da kwalliya, bayan sun sanja kaya suka tashi Kaka.
"Yau kuma ina zaku tafi.?" Kaka ta faɗa tana tsare su da ido.
"Zamu tafi neman mijin aure." Kuluwa ta faɗa tana shafa farar powder a fuska.
"Ikon Allah." Kaka ta faɗa cike da mamaki.
Kowacen su tana sanye da doguwar riga an ci ɗammara da ɗankwallin kayan, an yafa gyalle fuska yasha farar powder, anyi ɗige ɗige da kwalli.
"To Allah ya ki ya ye hanya." Kaka ta faɗa tana ƙunshe dariya.
Akwai wani takalmi da Kuluwa ta siyowa a gwanjo, yana da tsini sosai kamar fensir ta ɗauko zata saka.
"Kuluwa kar ki saka wannan takalmin dan Allah."Kaka ta faɗa cike da rarrashi.
"Gaskiya ki yi haƙuri amman sai na saka wannan takalmin, idan ban saka takalmi mai kyau ba ta ya ya zan samu miji mai kuɗi, in kai ki Saudiyya da umara." Kuluwa ta faɗa tana ɗaure igiyoyin takalmin.
Duk maganar da Kaka zata faɗa Kuluwa bata jita ba, ƙarshe ta dafa Ummi suka fice tana yarfe hannu.
Kuluwa gidan mai gari suka nufa kana ganin yanda take tafiya, ka san bata iya tafiya da takalmin ba Ummi duk kafaɗarta ya gaji, amman tana tsoran masifar Kuluwa.
Suna zuwa ƙofar gida suka samu cike da mutane kamar biki ake yi a gidan, Kuluwa ta duba mai gari bata ganshi ba ta shiga cikin ƙawayen amarya ita da Ummi, bikin Sa'ida ake yi.
Kuluwa faɗuwarta uku da wannan takalmin, bayan sallar la'asar angwaye suka zo ɗaukar pictures da amare.
Daman tun zuwan Kuluwa Sa'ida take musu gani gani, Kuluwa ta janyo Ummi suka shiga ana shirin ɗauka Sa'ida ta lura dasu.
Ta yiwa ango magana aka ware su a gefe Kuluwa ta samo ƙadangare manya masu jajayen kai guda biyu ta haɗasu guri ɗaya ta ɗaure ta ajiye ta koma, ta samo kananan ƙadangaru da yawa ta zuba su a kwano, ta rufe tana zuwa ta ɗau wanda ta ɗaure ta riƙe a hannu ko tsoro babu, tana zuwa ta wurga ma Sa'ida ɗaya ita da ƙawayenta ango ma shi da tawagarsa.
Sanna ta buɗe kwanon ta watsa musu ƙananun,
Gaba ɗaya suka watse kowa ya yi takan sa, ango babu kunya ya cire babbar riga ƙawayen amarya kuwa tsirara suka nemi yi, amarya ta fashe da kuka tana faɗin ango ya taimaka mata, gaba ɗaya sun samu tsarabar ƙadangaru Kuluwa tana tsaye tana dariya, Ummi tana raɓe a gefe cike da tsoro.
Da sauri aka sanarwar mai gari abin da yake faruwa, ya sa aka shiga da matan cikin gida gaba ɗaya sun cire ɗankwalayen su, suna neman cire riga Kuluwa ta watsa taron ango daga shi sai best da gajeran wando.
Aka kulle ƴan matan a ɗaki suna ta ihu suna cire kayan jikin su amarya har da suma.
Kuluwa tana shirin tafiya taji ana magana ta bayanta.
"Baiwar Allah mai yasa zaki jefa musu ƙadangaru." Wata tsohuwa ta faɗa tana riƙe da kwano a hannunta, itama tana sanye da ankon biki.
"Saboda sun hulaƙantani." Kuluwa ta faɗa tana yin murmushi.
"Gaskiya baki kyauta ba." Tsohuwar ta faɗa tana kallanta.
"Ai na haƙura tun da na rama abin da su kai mun." Kuluwa ta faɗa tana shirin barin gurin.
Tsohuwar ta ce .
"Wannan naki ne.?"
Kuluwa ta kalli gurin zobe ne mai kyau yana ta ƙyalli, Kuluwa ta karɓa ta zura shi a ɗan yatsa, zata tafi tsohuwar ta ce.
"Kar ki taɓa rabuwa da wannan zoben ƴata, domin ya yi miki kyau."
"Ni bani da uwa a duniya, dan haka ni ba ƴarki bace." Ta faɗa tana murguɗa mata baki.
Ta Batulu ce ✍️