Author : Mamuh geee Category : Complete Novels
Kai zubair Maya matsalarka da hakan?
Nima aurenta nakeso nayi kuma ni tuntuni ita nakeso.
Qara jinjina abun yayi sbd zancen yayi kamari.
LAILAHH,,yafada da kakkausar murya.
Na'am tace kai tsaye dan ita gaba daya zancensu bai shigetaba bare yadaga mata hankali.
Lailah cikinsu akwai Wanda yayi miki maganar yana sonki?
A'a.
To akwai Wanda kikeso acikinsu?
A'a
Toku dukkaninku kunji dan haka na soke wannan maganar daga yau kuma nabaku qanqanin lokaci kowa ya fiddo mata a hada aurenku dana ayshat.
Abban jabeer ne ya gyara zama yace,
Alh inaga mai zai hana abawa jabeer din lailah tunda shine babba kum......
Kallon da alhajin ya wurgo masane ya sanyashi hadiye sauran zancen nasa.
Kwana biyu lailah bata saka ko dayansu a idontaba sai yau.
Zaune take a kujerar dake balcony dinta tana fira da sabuwar friend dinta dasuka hadu a school itama kamar lailah take yar hutu da ji dakai.
Siyamace ta ukunsu dan ayshat bata cika shiga cikinsuba dan ta dan girmesu.
Red three quarter jeans ne ajikinta da farar top fara ta shaking material ko dankwali batada sai gashinta data sako Danko dauresa yau batayiba.
Fira suke cikin nishadi tsautsayi yasata kallon saitin dakinsa gabanta ya buga da qarfi sbd hangosa tayi daure da towel a qugunsa yafito wanka
Tsikar jikintace ta tashi sbd gabaki daya murdaden jikinsa daya bayyana ga farar fatarsa dake sheqi.
Lumshe idonta tayi ta rufe ruf
Abu daya data lura dashi shi mutum ne maison iska sbd kullum windon dakinsa na gadi a bude yake.
Da qawarta maryam zata tafi ta sauko dan rakata a Palo suka tarar da Anty basma na waya suka wuce bayan sun gaisa.
A harabar gidan ma saida suka tsaya fira kafin maryam tana motarta ta fice.
Tana shirin juyawa motar jabeer tasako kai
Yana pakawa ya iso gabanta ya tsaya yana watsa mata wani shegen kallo da ba qaramin kyau tamasa a kayan jikintaba dako gyale bata doro a kayan jikintaba.
Gaisawa sukayi yafara qoqarin kawo mata zancen soyayya tayi saurin katsesa da cewa,
Pls Yaya jabeer nafada maka banada wannan a cikin agenda na
In fact inada salman dina and I think I'm ok wit him.
Baiji haushiba yacigaba da janta fira hardasu darawa.
Hannu yakai zai tabo dimple dinta daya burgesa datana daria
Ba xato yaji an riqe hannunsa tareda ingizasa baya da qarfi.
A hasale ya dago sai yaga zubair na huci
Tsabar baqin cikin shima baisan sanda ya wazgawa zubair mari ba.
Zubair dama yanada haushin wancan Marin ga kuma wani
Shima hannun yadaga ya wazga masa nasa.
Dambe ne ya kaure tsakaninsu
Lailah kuwa ko ajikinta saima juyawa datayi ta shigewarta
A Palo tasamu Anty basma ta zauna suka hau fira kafin takira dad dinta suka hau fira tana zuba masa shagwaba sbd baya qasar yayai tafiya.
Duk abinda yafaru a idonsa yafaru
Har shigewarta
Sai dai abun qara basa mamaki yayi yanda har wai ake fada akan wacan silly girl din.
Shima qyalewarsa yayi acewarsa qarfi sukeji tunda harsuna iya fada akan mace, macen ma wadda shi bai dauka tanada abin burgewaba bare abin so.
UNBELIEVABLE,
yace ahankali ya yamutsa fuska.
Ayshat ce tafito tafara gani dan tuni abun yafara muni
Ihu tasaki tana kiransu umma.
Ummans jabeer CE tafara fitowa rude aiko itama tahau kuruwa tana qoqarin rabasu.
Umman zubair na fitowa tahau ihun
Wayyo jabeer zai kashe mata 'da
Kallonta umman jabeer tayi tace,
Amma dai hafsatu kinji kunya,
Shi zubair din da kike fada duk bashi ya kawo wannan balain ba.
Eh dolece tasa tunda Yaya za'a masa qwacen mata
Sa'insa ta kaure tsakaninsu suma saida Anty basma tajiyo hayaniya tafito tashiga tsakani amma ina tuni gurin ya hautsune da tashin hankali.
Motar Abba nasir ce tashigo harabar gidan sun dawo shida alh tsoho daga gurin sallar juma'a.
A hanzarce Abba nasir din yafito mota amma daqyar ya raba tashin hankalin dan kuwa daga jabeer din har zubair babu Wanda baiyi jina jina ba.
Shigowar motar baba abdlkrm ne yasa su umma tsaida nasu haya niyar barema sai alokacin suka lura da alh tsoho.
Kowa taitayinsa yashiga
Qofar Palonsa ya shiga kowa ya rufa masa baya dan sauraren hukunci.
M & Z
[3/4, 14:04] +234 818 350 7088: 🌕🌕 AUREN RABA GARDAMA🌕🌕
Na
MAMUH GEEE🌕
And
ZINNIE SMART
46~50
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM.
Tsit palon yayi bakajin motsin komai sai kukan a.c dake tashi ahankali.
Batareda tsohon ya dagoba yace,
Ayshat jeki ki kiramin lailah.
Miqewa tayi jiki a sanyaye tafice.
Minti uku saigata sundawo tareda lailah.,
Zama sukayi
ayshat a qasa ta zauna
Ita kuwa lailah kusada antynta basma ta zauna.
Rai a tsananin 6ace yafara fadin,
Yau koma bayar takai acikin zuriar nan ana fada harda duka,
Kuma qarin abin haushin harda Ku manyansu duk akan dalili daya.
Nayi baqin ciki sosai akan wannan sabon alamari,
To yau zanyi maganin wannan matsalar
Ke lailah inaso ki zabi daya daga cikinsu yanxu anan gurin.
6ata fuska tayi tareda turo baki tace,
Nifa gaskia banda time din wani soyayya ko aure dan haka ba Wanda nakeso acikinsu.
Umman zubair tayi saurin katseta da cewa,
Lailah kidaina fadar haka mana ki duba kiga yanda zubair ke....
Kunji tsiyar ai
Sbd ke kullum hafsatu ke kike kawo matsalar....
Abba nasir ne ya katsesu cikin 6acin rai yana cewa,
Ku kunzama mutanen banza tunda bazaku iya hana 'yayanku ba sai dai kuma ku hau naku abin kunyar.
6acin ran alh tsoho ya qaru iya matuka ya miqe tsaye tareda basu baya ya fara magana cikin kakkausar murya.
KE LAILAH nabaki nanda sati daya ki fitar da daya daga cikinsu su biyu idan ba hakaba wani satin nakuma zagayowa zan raba gardama na aurar dake ga duk Wanda naga dama.
Yana gama fadar haka yashigewarsa dakinsa yabar baya da qura.
What"
Tace da qarfi cikin rawar murya kafin ta kalli Anty basma cikin wani irin yanayi.
Saurin kama hannun lailar tayi suka bar palon.
Da dai dai suka bar palon cikin zullumin ya zata kaya.
Suna shiga Palo tayi wurgi da wayarta a kujera tana wani fidda numfashi.
Dafata Anty basma tayi tace,
Lailah pls take it easy komai zaiyi daidai.
Anty kinajin abinda tsohon nan yafada,
Wlh ni banason kowa acikinsu in fact ni ban tashi wani aure ba,
Danasan wannan shirmen zan tarar a Nigeria daban dawoba.
Da qarfi ta kwala kiran safiya mai aikinsu
Aiko da sauri tazo dan tasan abu kadan ke hasalta lailar.
Bani ruwa mai sanyi yanxun nan.
To,, tace tareda juyawa da sauri. Lailah Waya ta dauka ta danna kiran daddynta Yana dauka ta fashe masa da kukan shagwaba tana koro masa bayani.
Lallashinta yahauyi tareda tabbatar mata da yananan dawowa jibi.
Suna gamawa ta kira mum dinta itama tana dauka ta fara zuba mata abinda ke faruwa..
Lailahna kwantar da hankalinki ba abinda zai yiyu bane yi miki auren dole,so jst calm ur self okey my love.
Nidai mum dan Allah kizo idan bakaba da dad yadawo zan tahowata america.
Kadaki damu my girl dazarar dad dinki yadawo baice komaiba zanzo nataho dake.
OK mum I love you.
I love u too my girl.
***********
Kwana biyu kenan da faruwar abin Sam lailah bata ko fitowa Palo sbd bata buqatar ganin kowa abincinta ma saidai safiya takawo mata daki.
Yau tun safe ta shirya Cikin Morocco gown blue sai dan siririn gyale data daura.
Hand bag ce kawai ahannunta sai key din motar ta fito a Palo ba kowa
Dan haka bata tsaya shiga dakin Anty basma ba ta fice.
Zaune yake bakin gate yana hangota ya dauke kai sbd daga gani yau rashin mutuncin a kusa yake.
A zazafe ta figi motarta ya bude mata gate ta fice.
School ta tafi suna fitowa lectures suka yi gurin shopping itada maryam dagacan
Bata dawo gidaba sai maraice.
A gajiye tadawo tun a gate ta bar motarta tareda jefawa yaseer mukullai tace yashigo da motar ciki.
Karo taci da jabeer ta ra6asa zata wuce yayi saurin shan gabanta yana cewa,
Sis kwana biyu kinqi bari kowa yaganki,kin kuwa San yanda nayi kewar.....
Ya jabeer pls stop all this drama,
For god sake meyasa bazaku barni ba tunda nariga da nafadi ra'ayina.
Toh let me make sumtin very clear to u again,
Ni lailah banason kowa da aure acikinku so pls stay away,okey.
Dariyar zubair Ce tasasu waiwayowa dan basusan da zuwansaba.
Matsowa yayi zaiyi magana tayi saurin daga masa hannu tace,
Pls ya zubair you just heard what I huta,bana buqatar ko 'dayanku so kubarni na huta pls.
Juyawa tayi kan yaseer daya zo gurin a hasale tace,
And you what do you want?
Key yamiqa mata tareda juyawa.
M & Z
[3/4, 14:04] +234 818 350 7088: 🌕🌕 AUREN RABA GARDAMA🌕🌕
Na
MAMUH GEEE🌕
And
ZINNIE SMART
51~55
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM.
Hankalinta bai qara tashiba saida dad dinta yadawo taga baice komai gameda hukuncin da tsoho ya yanke saima lallashinta daya hauyi akan ta daure tazabi daya daga cikinsu.
Yau sati yacika dan haka tana sane taqi zuwa gaida kowa dan kowa gidan haushi yake bata.
Kwanciyarta tayi adaki tanaji wayarta na ringin taqi dagawa sbd tasan cewa xa'ayi take ana kiranta.
Har bacci yafara janta Anty basma tashigo dakin tareda zama bakin gado tace,
Lailah ana kiranki a palon alh babba.
Ba Indi zani ni sbd gskia ni bansan dalilin dayasa ake son shiga life dinaba.
Yi hkr lailah muje kiji koma meyene kadaki manta daddynki na wajen.
Miqewa tayi tana 6ata fuska suka tafi.
Zama tayi tana yatsinar fuska sbd kowama batason gani.
Gyara murya yayi yafara fadin,
Lailah inason ki sanar damu wa kika zaba akan zancenmu na last week.
Turo baki tayi tace,
Nifa gaskia nafada banason kowa acikinsu barema wani aure.
Jinjina kai yayi yace,
To kisani kinyi wasa da damarki dan kuwa bazan janye zancenaba na aurar dake ga duk Wanda naga damaba matuqar baki fidda daya acikinsuba.
Dan haka kowa ya shirya ranar juma'a zan aurar da ita ga duk Wanda nasama,
Haka kuma jabeer da zubair Ku fiddo da mata tare duka za'a hadaku Dana ayshat.
Da gudu tabar palon tana fasa ihu
Sauran jama'ar palon ma da dai dai suka fita sbd hukuncin baima kowa dadi ba bama kamar dad dinta dayakeso tafara gama karatunta.
***************
3 days later,
Lallashin dunia dad da Anty basma sunyi mata amma taki daina kuka.
Yau maryam tazo tasamu ta lallabata dakyar suka fita yawo.
Sosai taji dadin yawon sbd tamanta matsalarta kuma maryam ta tabbatar matada wasace tsoho ke mata dan ba yanda za'ayi ayi mata auren dole
Hakan yasa ta sake suka hau chilling dinsu.
Ta 6angaren su zubair kuwa sunga ba kowa sai Allah sun fidda matayensu har ankai komai anfara shirye shirye.
Gida yacika maqil da 'yan biki domin kuwa hidima tayi nisa
Su lailah da siyama tareda maryam ba abinda ya damesu sbd lailah tuni tayi watsi da komai dan tasan ba abune mai yiyuwaba auren dole agareta.
Duk gyaran da akewa ayshat amarya itama sai anyi mata nata bare ma Anty basma data dage gurin gyaranta.
Anyi kamu da walima ana gobe daurin aure suka fita itada maryam da siyama harda ayshat zasu karbo sauran dinkunan ayshat.
Basu dawo gidaba sai maraice.
Agajiye suke dan haka suna shiga daki ta fada toilet tayo wanka sbd tana period ne.
Doguwar sleeping dress tasaka baqa sbd black shine best colour dinta.
Cornflakes tasa safiya takawo mata tasha tana gamawa saiga hayat brothern zubair yashigo dakin.
Zama yayi akan stool yana cewa,
Lailah kunada baqo a qofar gida tun dazu yazo yaseer maigadi ya hanasa shiga yace saiya kiraki yace yanata kira baki dagaba.
Wat" tafada da qarfi tana miqewa sbd tasan bilal ne brothern maryam Wanda shi take dating 'yan kwanakin.
Miqewa tayi ta 'Dora gyale akanta ta fito.
Tana isa bakin gate ta tarar dashi yana alwala fizge butar tayi tareda wankesa da ruwan.
Dagowa yayi yana mata kallon ido cikin ido wayar hannunta ta jefesa da ita tana nunasa da yatsa tace,
Kai ko acikin dabbobi bansan kai wayeba sbd daqiqancin yayi yawa.
Wani wawan kallo ya jefeta dashi
Hannu ta 'daga zata kai masa mari
Hannunta taji anriqe riqon daya razanata sbd taji maza.
Kallonsa tayi tareda fizge hannunta tafara zazzaga masa rashin mutunci agaban mutane har hkr ake bata amma bata saurara masaba.
Daga qarshe dai shigowar alh tsoho daga masallaci yasa kowa watsewa.
Kallon yaseer yayi yace......
M & Z
[3/4, 14:04] +234 818 350 7088: 🌕🌕 AUREN RABA GARDAMA🌕🌕
Na
MAMUH GEEE🌕
And
ZINNIE SMART
56~60
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM.
Yaseer ina tsananin jin kunyar cewama kayi hkr sbd yau 'da ne ka haifesa amma baka haifi halinsaba,
Nayi baqin cikin ganin abinda lailah tayimaka yanxu a bainar jama'a,
Haka zalika tun ba yauba ina lure da sane da rashin mutuncin datake tafka maka.
Qara kallon yaseer din yayi cikin wani nazari daya shigesa yanxun yace,
Yaseer kadaka damu insha Allah zanyi maganin abin nasan matakin dazan 'dauka.
Cikin qoqarin danne 6acin ransa yace,
Alh basai ka mata komaiba sbd ni ban dauki abin da mahimmanciba.
Girgiza kai yayi cikin qara tabbatar da tunanin da yayi ya wuce.
Cikin tsananin 6acin rai da wani irin tiririn zuciya ya shige dakinsa na gate din yana fidda wani irin huci.
Rigarsa ya farke daga jikinsa yayi wurgi da ita tareda kaiwa bango duka,
Duk baimasaba saida yasa qafa yayi ball da laptop dinsa dake charging.
I hate her,
I hate her so very much,
I despise her,
Infact I hate this house and every one in it.
Wayarsa yaciro yana huci ya danna kira.
Ringing biyu aka dauka tareda cewa,
Barka da yini sir.
Bar tsaya amsawaba yace,
Lawal ka sanar da isowata office gobe sbd na rufe case din binciken alh naseer modibo,
Sannan kayimin booking ticket gobe zan wuce Miami.
Cikin son cika umarnin ogansa yace,
Yes sir but.....
No buts just did wat I said.
OK sir.
Wurgi yayi da wayar tareda fadawa toilet din dakinsa.
******************
WASHE GARI
Qarfe goma za'a daura aure dan haka tuni gida ya kaure da hayaniyar jama'a.
Kowa ka gani ya shirya sai shirin daura aure ake.
Qarfe Tara da Rabi kowa ya shirya banda lailah dan har lokacin barci take bata tashiba
Hattasu maryam da siyama harda amarya ayshat sungama shiryawa cikin ado na musamman.
Anty kubra ce tashigo dakin da kaya a hannunta tana cewa,
A'a maryam harkun shirya Baku tada mutuniyar takuba ta shiryaba har an fara daurin auren.
Janye bargon da lailar ke ciki tayi tana cewa,
Daughter maza tashi kiyi wanka ga kaya na musamman nakawo miki.
Tashi tayi tana duba agogo kafin ta kalli su siyama dake faman daura dankwali ayshat kuwa turare take fesawa taci ado sai qyallin amare takeyi.
Lallaima 'yan Matan nan shine kuka shirya Baku tadani ba.
Tura toilet Anty tayi tana cewa,
Bari anjima kya musu wannan.
Tana fitowa wanka tahau shiri.
Dark blue lace ne Anty basma takawo mata Wanda daddynta ya siyo matasu cikin tsadadden lefen dayayo mata kasancewar alh tsoho ya sanar dashi wazai aura mata.
Mai makeup na gama mata makeup ta suka sauko qasa gaba dayansu.
Palon cike yake da mutane anata hidima.
A gurin daurin aure kuwa ba qaramin tashin hankali da mamaki jama'a sukayiba jin an daura auren LAILAH ALI MODIBO da YASEER.
Iya kaduwa su zubair da jabeer sun shiga sai dai sunsan akwai rigima da tashin hankali gurin lailah.
Ana gamawa batareda kowa yashigo gidanba aka 'dunguma zuwa gurin 'dauro nasu jabeer da zubair gidan matayensu.
Ana watsewa bilal yakirata yace,
Bby gani nazo daurin aure amma ba kowa har an watse inaga nayi latti.
Ok Ai ba damuwa bari nazo ko fira muyi kaga adon danayi.
Ko gyale bata yafaba sbd rigar jikinta fitted gown ce data kar6i jikinta ta zauna mata sosai gashi rigar Nada tsawo sosai amma heels din qafarta sun taimaka gurin rage tsawon rigar.
Tun daga nesa ya kafeta da ido yana hade yawu da qyar yana ayyana kota halin qaqa sai ya mallaki lailarsa.
You luk fabulous.
Thank you my.....
Bata qarasaba taji qarar wurgi da kaya tareda wani irin hucin 6acin rai mara misaltuwa na tasowa daga 'dakin yaseer.
Gabantane ya buga da qarfi haka kawai amma saita daure zata kuma magana motocinsu dadynta dasu alh tsoho dasu abbah tareda angwaye suka parker.
Qarar lasifikar maroqi ce tasayi firgifit amma ga babban tashin hankalinta saita taji yana fadin,
Yau dai min shaida 'daurin auren 'yayan gata da aka 'daura na,
JABEER DA SALMA,,,
ZUBAIR DA KHULSUM,,,
AYSHATU DA ANGONTA AHMAD,, SAINA GIMBIYA LAILAH ALI MODIBO DA ANGONTA YASEER.
Kasa tantance mezatayi tayi saita qurawa daddynta ido don son tabbatarda abinda taji..
Sunkuyar da kai yayi cikin jin wani irin yanayin tausaya mata.
Yanayinsa ya tabbatar mata da hakan gaskiyane.
Juyawa tayi gurin alh tsoho ta 'daga hannu ta.........
M & Z
[3/4, 14:04] +234 818 350 7088: 🌕🌕 AUREN RABA GARDAMA🌕🌕
Na
MAMUH GEEE🌕
And
ZINNIE SMART
61~65
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM.
Hannu ta 'daga ta dora akai tareda kurma wani mahaukacin ihu daya ratsa ko ina cikin gidan Wanda hakan yajawo hankalin kowa yayo harabar gidan.
Ganinsu Anty basma da kowa na