Advertisements
Chapter 1 Reading MUGUN FURUCI Fushin Uba by Ameenatu Sani ce BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

MUGUN FURUCI Fushin Uba by Ameenatu Sani ce

Author :  Ameenatu Sani ce Category :  Complete Novels

Chapter   1 / 7

1 to 3K   out of 19.4K words

๏ปฟ706 650 5625: *๐Ÿ‘„MUGUN FURUCI*๐Ÿ‘„


*WRITING BY AMEENATU SANI*


*_Wannan labarin kirkirarran labari ne banyarda a juyaman shiba ta kowace siga_*


*JIGWAN LABARIN*_:Akan mahaifin da yayi *MUGUN FURUCI* Akan budurwar d'an shi inda kuma tsautsayi ya fada mashi, shikuma d'an yazama lauyan mahaifin yarinyar_.


*SADAUKARWA ga my friend DARMA*

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alฦ™alaminmu ฦดancinmu._* }}

https://www.facebook.com/103637491942644/

๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ *{{N W A}}* ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ


ุจูุณู’ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู…ู ุงู„ู„ู‘ู‡ู ุงู„ุฑู‘ูŽุญู’ู…ูŽู†ู ุงู„ุฑู‘ูŽุญููŠู’ู…



PAGE 1_5


"Haba Habeeb in baka fadaman damuwar kaba waye zaka fadamawa?, kasandai ni mahaifinka ne duk duniya babu Wanda yakaini sanka amma ace Abu na damunka kaki sanar dani haba barrister"


daga kwancen da Habeeb yake ya dago ya kalli mahaifin nashi yace "Abba saidai katayani da addu'ah amma ni inaji ajikina mutuwa, zanyi Abba Santa shine zaiyi ajalina Dan Allah kayafeman"

da sauri Abba ya matso kusa da Habeeb din yace "my son Dan Allah ka fadaman wacece kake so, kuma kake cewa Santa zai kashe ka itadin yar gidan ubanwa ye agarinnan?"

Habeeb yace "Abba zuciyata ta kaini da nisa salma bata sona tace har abada ba zata soni ba!"
atsawace Abba yace "Habeeb wacece salma nace"
Habeeb yace "y'ar gidan Alhaji Lukuman Wanda kuke Neman kujerar chairman kaida shi".


Hular kanshi Alhaji Muhammad yacire yayi fifita da ita kana yaja ajiyar zuciya yace "lallal zuciya batada kashi, Habeeb gaskiya zuciyarka batayi maka adalci ba da har taso diyar abokin karawata, kasani sare koda ace Yarinyar tana sanka Alhaji lukuman bazai taba yarda ka aureta ba, nidai amatsayina na mahaifinka inamai baka shawarar. kayi hakuri da ita kaci gaba da addu'ah Allah yabaka wadda tafita"

tashi yayi yafita Yaja mashi kofar,
Karo sukaci da Hajiya Fadeela dake kokarin shiga dakin Habeeb da sauri tace "Alhaji lafiya dai, ko jikin Habeeb din ne ya matsa?" Girgiza kai yayi yace "wato Hajiya akwai matsala babba"
tire din Lemon da ta dauko ta saki kasa ya tar watse ta buga salati tace "Alhaji Dan Allah karka ceman Habeeb ya mutu, innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!" zata kwasa da gudu zuwa dakin Habeeb din Alhaji Muhammad ya dakatar da ita yace "Hajiya bai mutu ba amma lalle yana dabda mutuwa Wanda nikuma bazanbar hakan ya faruba indai ta sanadiryar yarinyar nan zai mutu".
Hajiya tace "wace yarinya kuma Alhaji?"
Alhaji Muhammad yace "wato Habeeb duk ciwon nan da yakeyi Ashe saboda yarinyar gidan Alhaji lukuman ne Santa yakeyi ita kuma bata sanshi".


Hajiya ta zaro ido tace "Alhaji lukuman dai danasani Wanda kuke Neman kujerar chairman?"
Alhaji yace "itafa, kuma kinsan dai yanda Alhaji lukuman ya tsaneni bazai taba bari Habeeb ya auri y'arsa ba".


Kan kujera Hajiya Fadeela ta zauna ta dafe kai tana addua akan Allah ya sausautama Dan nata.


Bayan kwana biyu Habeeb bayaci baya asha rarrashi na gidan duniya iyayenshi sunyi amma yaki yaci duk yabi ya ramai kullum cikin fadin sunan Salma yake.

Yanzu haka Alhaji Muhammad ya dawo daga office yashigo ya sami Hajiya Fadeela sai magiya takema Barrister Habeeb akan ya daure yaci kada ciwuka su tarar mashi.

Jin gina kai Alhaji Muhammad yayi ajikin kofa can ya dago yace "Habeeb nalura kana san yarinyar nan dayawa,shikenan bari naje na roki Alhaji lukuman da yataimaka yabaka auranta koda kuwa bata sanka ne, ai ita macece zata soka wata rana"
Da sauri Habeeb ya tashi daga kwancen da yake yace "Abba mutafi tare kodan naganta na roketa ta tausayaman ta soni".
Kai Abba ya girgiza yace "Habeeb jikinka babu kwari kabari ninaje insha Allah komi zaitafi daidai"
Habeeb yace "Abba Dan Allah mutafi tare wlh ko ganin ta nayi nasan zansami sauki".

Da sauri Hajiya Fadeela tace "Alhaji kuje tarai din wata kila a dace"

Haka kuwa suka tafi tare sai gidan Alhaji lukuman...

*_Yawan comment yawan typing, masoya wannan salonshi na da banne๐Ÿ‘Œ๐Ÿป_*

*Ameenatu Sani ce*
08065522770
[4/18, 5:10 PM] +234 706 650 5625: *๐Ÿ‘„MUGUN FURUCI*๐Ÿ‘„


*WRITING BY AMEENATU SANI*


*_Wannan labarin kirkirarran labari ne banyarda a juyaman shiba ta kowace siga_*


*JIGWAN LABARIN*_:Akan mahaifin da yayi *MUGUN FURUCI* Akan budurwar d'an shi inda kuma tsautsayi ya fada mashi, shikuma d'an yazama lauyan mahaifin yarinyar_.


*SADAUKARWA ga my friend DARMA*

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alฦ™alaminmu ฦดancinmu._* }}

https://www.facebook.com/103637491942644/

๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ *{{N W A}}* ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ


ุจูุณู’ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู…ู ุงู„ู„ู‘ู‡ู ุงู„ุฑู‘ูŽุญู’ู…ูŽู†ู ุงู„ุฑู‘ูŽุญููŠู’ู…



PAGE 11_15


Wani kallan ukku saura kwata yayi mashi kana yace "kaga malam tashi kaficeman daga gida please" yafada yana nuna mashi kofa
Alhaji Muhammad yace "nifa zuminci nazo mu kulla tsakani na dakai, domin 'Dana yaga y'ar ka yana so".
Sai a wannan lokacin Salma ta d'ago ta kalli alhaji Muhammad da Habeeb, dayake tunda suka shigo bata dago kai ta kalli kowa ba.
Shiko Habeeb yama shagala da kallanta kacokam hankalinshi na garaita jiyake kamar ya dauketa daga gidan yamaidata gidansu da gashi sai ita yanuna mata tsantsar qaunar da yake mata.
Salma idanunta ta tsayar kan Habeeb nan take taji wata wutar tsanarshi taqara ruruwa a zuciyarta da sauri ta taso daga inda take tana nuna shi da yatsa tace "waikai mayan inane?,dady miyakawo wannan marar zuciyar gidammu?nace bana sanshi bana kaunar shi amma dayake wawa ne yaki ya fahimta."
Wani shi'umun murmushi alhaji Lukuman yasaki tare ta murza gashin bakinshi haryaji sanyi aranshi daya kasance Salma batasan Habeeb.
Yace "kinga daughter yishirunki banni dasu"
kallan Alhaji Muhammad yayi da ya daskare a tsaye tun jin irin kalaman da Salma ke jifar d'anshi dasu yace"kai kana tunanin har akwai ranar da zan iya hada jini dakai? To inkana tunanin haka kama daina tun wuri Dan zaren ba irin yadin bane,Dan haka ja d'anka kubarman gida konasa afitarman daku"
Alhaji Muhammad yabuda baki zaiyi magana Salma ta qaraso gaban shi tace "dama Kaine mahaifin shi? Haba shiyasa Ashe naji nakara tsanar shi Dan haka kajama d'anka kunne koshi mayene ni nafi karfin shi wlh kuma bazantaba sanshi ba koda zai mut......saukar mari taji akumatunta Alhaji Muhammad ya kasheta da qwararan maruka har biyu ya d'aura da cewa " kedin y'ar gold ce ko lu'ulu'u da Habeebu bazai rabu dake ba?,marar tarbiya kawai" qarar Habeeb yaji ya fadi qasa dafe da zuciyarshi yasa bai qarasa maganar shiba yayi kan Habeeb din ya tallaboshi yace "Habeebu bude idanunka Dan Allah Ashe dama yarinyar batada tarbiyya kaketa wahalar da rayuwar ka a kanta?" Wani tari Habeeb yayi sai gudajin jini yabiyo baya daqyar yabuda baki yace "Abba mutafi gida".
Alhaji Lukuman da wani baqin ciki yarufe zuciyar sakamakon marin da akaima y'arsa yace "kaini zakazo har gida kadakarman y'a, aiko wlh sainayi shari'a dakai koda wa kake takama".
Afusace Alhaji Muhammad yace "andaka din kaje kayi abunda zakayi" yanuna Salma da hannu yace "ke kuma wlh inbakiyi wasaba sainayi Ajalinki Dan akan 'Da na babu abinda bazan iyaba"
kama Habeeb yayi yace "muje habeebu"
Fita sukayi daga parlorn Alhaji Lukuman sai bala'i yake yanakiran "Muhammad in baka kashe man Salma ba kaiba Dan sunna bane kuma wlh kajira sammaci akan Marin dakayima y'ata"




Afusace Alhaji Muhammad yace ma isah driver yaja motar zuwa hospital aiko batare da bata lokaci ba suka isa medical hospital cikin kankanin lokaci likitoci suka hau duba Habeeb ganin babban 'Dan d'ansiya babu lafiya
Kusan awa daya kana likita yafito daga dakin yasamu Alhaji Muhammad dake tsaye sai safa da marwa yake awajan yace " yella6e muje office mana" Alhaji Muhammad yace yajikin habeebun doctor?" Likita yace da "sauki ranka yadad'e muje office" kana yayi gaba Alhaji Muhammad yabi bayan shi

Zama sukayi su duka kana doctor Auwal ya cire farin gilas din dake makale ga idanunshi yamiqama Alhaji Muhammad hannu yace "barka ranka shidade" musabaha sukayi kana doctor Auwal yayi gyaran murya yace "wato Alhaji, Habeeb Sam yakasa cire damuwa a zuciyar shi bayan nasheda maku zuciyarshi tanadab da kamuwa da ciwo amma ankasa daukar mataki akai" Zazzafar iska Alhaji Muhammad ya huro kana ya muskuta yace "nidai doctor Dan Allah ayi abinda ake ganin yadace wajan ganin Habeeb yasamu lafiya"

To "insha Allahu Alhaji indai za abi dokokin da za'a gindaya masa , kana ayi kokarin ganin ansa dashi da abinda yake so insha Allah zai samu sauki" takarda yajawo yayi Dan rubutu akai kana yamikama Alhaji Muhammad yace "ga wa innan magungunan za'a samosu saiyayi amfani dasu"
Karba yayi ya duba kana ya zaro kudi yamiqa mashi yace "doctor ayi amfani dasu wajan siyan duk abinda ake bukata"
Karba yayi yayi godiya kana yace "da ruwan da akasa mashi yaqare zaku iya tafiya gida"
Shima Alhaji Muhammad godiya yayi kana yabaro office din jama'ar dake bisa barandar sai gaisheshi suke domin sunganeshi dakin da Habeeb yake yashiga, yananan kwance lokaci guda harya qara wata irin rama bacci yake ga qarin ruwan da akasa mashi sai tafiya yake ahankali, wayar shice tayi qara zarota yayi ganin Hajiya Fadeela ce ya daga abangaran Hajiya Fadeela yana dagawa tace "lafiya dai Alhaji inata kira baka daga ba?" Numfashi yaja kana yace "inafa lfy gamu nan hospital Habeeb babu lafiya" arikice Hajiya Fadeela tace wace asibiti Alhaji!?"
"Medical hospital" kett ta datse wayar ta nufo asibitin.....

*_tofa kunadai ji yanzu akafara wasan,innaga comment yanda nake so zancigaba, gamai bukatar document din YANAR GIZO complete saiya tuntubi number ta๐Ÿ‘‡_*

*Ameenatu Sani ce๐Ÿ‘Œ*
08065522770
[4/18, 5:10 PM] +234 706 650 5625: *๐Ÿ‘„MUGUN FURUCI*๐Ÿ‘„


*WRITING BY AMEENATU SANI*


*_Wannan labarin kirkirarran labari ne banyarda a juyaman shiba ta kowace siga_*


*JIGWAN LABARIN*_:Akan mahaifin da yayi *MUGUN FURUCI* Akan budurwar d'an shi inda kuma tsautsayi ya fada mashi, shikuma d'an yazama lauyan mahaifin yarinyar_.


*SADAUKARWA ga my friend DARMA*

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alฦ™alaminmu ฦดancinmu._* }}

https://www.facebook.com/103637491942644/

๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ *{{N W A}}* ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ


ุจูุณู’ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู…ู ุงู„ู„ู‘ู‡ู ุงู„ุฑู‘ูŽุญู’ู…ูŽู†ู ุงู„ุฑู‘ูŽุญููŠู’ู…



PAGE 26_30

Wata irin tafiya Isah driver keyi a saman titi kamar yana tsoran kwaltar Alhaji Muhammad dake bayan mota hakimce yana duba jarida yadago yace "wai Isah mike faruwane kakejan motar kamar baka so?"
Bai kulashi ba yaci gaba da tukinshi, cike da mamakin shirun da Isah yamashi yakara magana "wai Isah hala bakaji minace ba ne?" Daidai lokacin kuma motar su Salma tawuce ai da sauri Isah driver yace "wlh Alhaji kaina ke ciwo" parking yayi a gefen hanya yace "Dan Allah Alhaji kaja motar nan wlh bazan iya tukinba yanzu juuwa nake gani" dayake Alhaji Muhammad sauri yake batare da wata damuwa ba yafito ya zauna wajan driver shi kuma Isah driver yakoma wajan mai zaman banza Alhaji Muhammad yaja motar da karfi suka tafi
Isah driver kamar bashine ya lankabeba yace kanshi na ciwo ba sai baza idanu a titi yake can yaga sunkusa taddo motar su Salma aiko ya fakaici idanun Alhaji Muhammad ya taka giyar motar da karfi jikake kuuuuuuuuuuuuuuuu gammmmm daki motar su Salma cikin minti daya wani mummunan hadari ya afku a titin domin ko motar su Salma tayi wani raga raga mutane suka taru sai sallallami ake ana San fito Dana cikin motar.
Alhaji Muhammad salati ya dauka tunda motar ta fizgesu shiko Isah driver kira yake Alhaji zaka kashemu to adaidai wannan lokacin motar ta daki tasu Salma motar na tsayawa Alhaji Muhammad yafito yana salati innalillahi wa'inna'ilaihir raji'un agigice yanufi wajan motar mutane sun taru dayawa aka Ciro Salma da driver ko kadan ba wanda ke motsi da sauri aka sasu motar Alhaji Muhammad akatafi asibiti mutane sai kira suke "masu kudi basuda imani jibafa Dan yana Dan siyasa irin gudun dayake a titi"zagin Alhaji Muhammad kawai ake mutane dayawa suka bi motar zuwa asibiti
Isah driver irin cikin irin yarude din nan kira yake "Alhaji saida nace karkayi kisa karkayi" Amma kakijin maganata, innalillahi wa'inna'ilaihir raji'un muyau munbani!"
emergency aka shigar dasu cikin yan muntuna likitoci suka taru akansu dayake a kusa da junction abin yafaru akwai yan Sanda a wajan ba asha wahalar ansar suba
Alhaji Muhammad duk yarude tunda yake tuki tsautsayi baitafa fada mashi ba sai yau kira yake "Dan Allah doctor's karku bari sumutu wlh bada gangan ba" mutane sai kira suke Alhaji da gangan fa kature su irin gudun da kakeyi kamar titin ka".
Shikuwa Isah driver fakar idanun jama'ah yayi yabar wajan,wata number yakira ana dagawa yace "Alhaji mai afkuwa fa ta afku muna medical hospital yanzu haka ketttt" yakashe wayar yadawo cikin jama'ah.
Wajan minti goma saiga motocin Alhaji Lukuman sun shigo harabar asibitin cikin sauri ya sauko daga cikin motar yashige emergency din daidai da likita ya fito nan yadakatar da shi cikin hausar dabata ida bin harshenshiba yace "yi hakuri mana muje ana dubasu" kira yake "doctor kataimaka itace diyata kwal a duniya karta barni Dan Allah"
da 'kyerdai aka fito dashi daga ciki doctor yace "Kaine mahaifin yarinyar?"
Alhaji Lukuman yace "eh wancan kuma driver ne"
Da sauri Alhaji Muhammad ya matso yace "doctor ya jikin nasu?" Ai wata irin juyowa Alhaji Lukuman yayi nan suka hada ido da Alhaji Muhammad aiko yakaimashi wata cabka a wuya yace "Ashe Kaine ka bankeman Salma? haba Muhammad minayi maka a rayuwa da kake Neman rayuwar Salma Ashe da gaske kake saikaga bayan ta haba Muhammad".
shidai Alhaji Muhammad baiyi tunanin Salma ce ya bankeba sai da yaga Alhaji Lukuman.
nan jama'ah sukayo caaaa anaba Alhaji Lukuman hakuri da 'kyardai yasaki Alhaji Muhammad dayaji matsa a hannun Alhaji Lukuman
Nan doctor yace "yanzu dai Ku biyoni office nayi maku bayanin abinda ke faruwa"
Office din doctor sukaje waje yanuna masu su zauna kamun yafara koro masu bayani "to Alhaji saifa hakuri"..nan take gaban Alhaji Muhammad yafadi da sauri yace "innalillahi wa'inna'ilaihir raji'un don Allah doctor karka ceman sun mutum" shiko Alhaji Lukuman wani shu'umun murmushi yayi cike dajin dadin kudurunshi yakusa cika.
Zaman glass din shi doctor ya gyara ganin yanda Alhaji Muhammad ya rude kana yace "cool down Alhaji babufa Wanda ya mutu Duk kanninsu suna numfashi saidai sunji jiki harkarama namijin da sauki buguwa ce yayi akai sai glass daya yanke shi a fuska ita kuma macen gaskiya tabugu sosai domin hannunta na dama yakare glass ya shigarmata a fuska saikuma kananun ciwoka Amma gaskiya bata farfado ba haryanzu mundai yimata allure Wanda zasusa ko tafarka ta farka a cikin hayyacinta shi kuma namijin ya farfado maybe ma zuwa anjima a sallamaishi because jikin shi da sauki.
Wata sassanyar ajiyar zuciya Alhaji Muhammad yasaki yace "alhamdulillahi Allah nagodai maka da katsareni da yin kisan kai!".
Shi kuwa Alhaji Lukuman kaidagani kasan baiwani ji dadin labarin ba yanayin fuskarshi ta nuna hakan Amma inkagani saikace duk cikin jimami ne.
Alhaji Lukuman yanuna Alhaji Muhammadda yatsa yace "kuma wlh inasan kasani jinin diyata bazai tafi abanza ba dama kace saikaga bayanta to shine yanzu kanemi ka aikata ko?, to Wlh sainayi shari'a dakai koda kuwa zanyi yawo tsirara, yo anfada maka siyasa haukace Dazaka nemi kasheman diya?"
Cikin kwantar da murya Alhaji Muhammad yace "kayi hakuri Alhaji Lukuman wlh wancanma Dana fada *MUGUN FURUCI* ne nayi wlh bada gangan nabigeta ba tsautsayi ne yafada kaina wlh am...."dakata malam Adana kalaman ka ko kasamu nafada gaban alkali dannan bazasuyi wani tasiri ba" Alhaji Lukuman ne yakatse Alhaji Muhammad da karfi...


_gaskiya nakusa daina typing din book din nan_


*Ameenatu Sani ce*
08065522770
[4/18, 5:10 PM] +234 706 650 5625: *๐Ÿ‘„MUGUN FURUCI*๐Ÿ‘„


*WRITING BY AMEENATU SANI*


*_Wannan labarin kirkirarran labari ne banyarda a juyaman shiba ta kowace siga_*


*JIGWAN LABARIN*_:Akan mahaifin da yayi *MUGUN FURUCI* Akan budurwar d'an shi inda kuma tsautsayi ya fada mashi, shikuma d'an yazama lauyan mahaifin yarinyar_.


*SADAUKARWA ga my friend DARMA*

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alฦ™alaminmu ฦดancinmu._* }}

https://www.facebook.com/103637491942644/

๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ *{{N W A}}* ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ


ุจูุณู’ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู…ู ุงู„ู„ู‘ู‡ู ุงู„ุฑู‘ูŽุญู’ู…ูŽู†ู ุงู„ุฑู‘ูŽุญููŠู’ู…



PAGE 16_20




Batare da bata lokaci ba Hajiya Fadeela ta iso hospital din alokacin Habeeb yasamu bacci sakamakon allurar da akayi mashi,cikin kujerun da aka tanada Dan masu dubiya suka samu suka zauna.
Bangaran gidan Alhaji Lukuman kuwa koda barin Alhaji Muhammad gidan sai ya koma yanata zagayan parlorn tare da buga hannu Hajiya Mariya ta muskuta daga zaunan da take tace "wai Alhaji wannan abun da yafaru duk miyaka woshi harda yake maganar zaiyi ajalin Salma?
Nisawa Alhaji Lukuman yayi kana yace " banni dashi wlh danshi ko zai mutu bazai taba auran ya taba koda kuwa ita Salma tana sanshi bare ma bata sanshi".


*______________________________*

Napep ce tayi parking gaban wani Dan karamin gida madaidaici mai karamin get wata kyakkawar budurwa ce tafito daga ciki hannu ta rike da jikka sai rigar lauyoyi sallamar mai napep din tayi kana ta fara tafiya cike da natsuwa kauran get din ta tura tashiga gidan bayada hayaniyar komi acikin shi amma gidan yahadu daidai na masu rufin asiri.
A parlor tayi sallama wata kyakkawar matace zaune a kan kujera ta fa dada murmushi a fuskarta tace "oyoyo ga *MEENAL* barka da dawowa!".
Itama MEENAL murmushi tasaki tace " thanks you Ammi" zama tayi a kan kujera tace washhhhh Ammi nagaji dayawa wlh"
Ammi tace ai MEENAL sai kin daure tashi zakiyi ki watsa ruwa ga abinci can na tanadar maki yau abinda kikafi so na girka a gidan" baki MEENAL tawashe tace kai amma wlh naji dadi sosai Ammina Bari naje ciki mikewa tayi ta kwashi jikkarta da kayanta ta shige dakin ta

Da kallo Ammi tabita harta shige cikin Dan madaidaicin dakin nata,da shigarta kayanta ta hau cirewa kana ta shige toilet takai 20mint da shiga kana tafito tana tsane ruwan kanta da Dan karamin towel basilin da kwalli kawai ta shafa tasa wata doguwar Riga baka da pink din hula yar

1 / 7