Advertisements
Chapter 2 Reading MUGUN FURUCI Fushin Uba by Ameenatu Sani ce BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

MUGUN FURUCI Fushin Uba by Ameenatu Sani ce

Author :  Ameenatu Sani ce Category :  Complete Novels

Chapter   2 / 7

3K to 6K   out of 19.4K words

yayi parlorn ta shigo a lokacin Ammi harta kawomata Abincin a tsakiyar daki zamatayi kana ta soma cin danwaken tana yima Ammi santi gami da bata labari.



______________________________

Kwanan Habeeb 3 asibiti jiki yayi sauki alhmdlh lillahi domin har ansalla maishi yana dakin shi shida abokin shi Hisham suna fira hisham yace "nikau barrister nabaka shawara mana!" Habeeb yadan muskuta kana yace "Inajinka",Hisham yace " Naga duk ka daura damuwa akan lamarin nan daya faru barrister yakamata kasanya hakuri da dangana a lamarinnan Salma dai ba ita kadai bace mace a duniyar nan ga mata nan k...... "Dakata Hisham shawara kace zaka bani koko umarni ne?"
Hisham yace "aikaga matsalar ka Habeeb kai ba'ataba fada maka gaskiya imdai akan wannan yarinyar ne, Salma tafito ta nunama duniya bata sanka ubanta ma ya nuna baya sanka Amma ka like mata why Habeeb?".
Tashima Habeeb yayi daga kwancen dayake yashige toilet yace " saikuma kayi da Wanda kagani"
Kai kawai Hisham ya girgiza ya haye gadon yayi kwanciyar shi


Alhaji Lukuman ne zaune a office din shi murmushi kawai yake saki yana sauraron labarin da Alhaji Bala ke bashi, saida ya gama tsab kana Alhaji Lukuman yace "Bala ka ganni nan wlh komi nasama gaba a rayuwata sainaga nasa maishi barai wata kujerar chairman, taibur din gabanshi ya buga hadi da mikewa tsaye yace kalleni nan Alhaji Bala badai su Alhaji Nabadi da Alhaji Sabo sun yi saranda da Neman kujerar ba? Hmmmm Alhaji Muhammad shi mai kunnen kashi yace ya nanan akan ba kanshi ba nasan zama chairman ba? To albishirinka yau saura sati naya zabe?"
Alhaji Bala yace "3"
Alhaji Lukuman yayi murmushi hadida zagayowa yafara taku daya bayan daya a office din kana yace "nanda Lokacin saina sanya Alhaji Lukuman nadamar shigowa gonata saina nuna mashi ruwa ba a San kwando bane domin kuwa kila kamun lokacin har mala iku sunyi mashi tambayoyin kabari".

Idanu Alhaji Bala ya zaro kana yace "kana nufin kashe shi zakasa ayi kenan?, tonidai banbaka goyon bayan aikata hakaba domin mutane dayawa sai anyi zarginka ka ka daganan kujerar da kake so zaka iya rasata Ku.....hannu yadaga mashi yace " babu Wanda zansa ya kashe shi sai hukuma da kanta". Alhaji bala yace "taya kenan kuma zata kashe shi ?"
Alhaji Lukuman yace "wannan tambayar yakamata ace tunfar ko kayiman amma katsaya zaka bataman lokaci,kawo kunanka kaji shirin danayi amma zan fada maka ne saboda nayarda dakai banida wani amini daya wuce kai shiyasa"
Kunnanshi Alhaji Bala yakayo,rada Alhaji Lukuman yayi mashi daga bisani suka sheke da dariya Alhaji bala yace "kai Amma wlh dole aji tsoranka Lukuman wato kai akan dukiya babu abinda bazaka iya aikatawa ba ko?"
Alhaji Lukuman yakoma mazauninshi yace "kware kuwa Bala ciki ko harda salwantar da rai..........


________________________________


*TALLA! TALLA!! TALLA!!!*


*Assalamu Alaikum*

*Ina yan'uwa masu sha'awar shiga kungiya ta online writer? To albishirinku😊 kakar tayanke sa'ka👌 Kuma damace agare Ku sabuwar kungiyarmu mai suna 💫💫NASARA WRITER'S ASSOCIATION💫💫 tana maraba da kowa da kowa duk mai sha awar shiga kungiyar kinada damar shiga bako sisin ki👌*


*Ina tsofaffin hannu da sababbin hannu wa inda basuda kungiya? Maza hanzarta domin kasan cewa daya daga cikin members din cikin ta💃💃 domin a dama dake*


*Ina masu San gwada basirar su wajen fara fadakar da Al'umma ta hanyar rubutun Hausa novel? Kungiyar mu tana maraba da ke yar uwa indai kina da sha awar zama online writer*


*Domin neman Karin bayani saiku tuntubi daya daga cikin number's din nan*👇
08065522770
08104335144


*NASARA WRITER'S ASOCIATION*
💫💫 _*{{Nasara abin so ga kowa ,domin marubuta da cigaban rubutu al'kalaminmu y'ancinmu.}}*_💫💫

*Ameenatu Sani ce*
08065522770
[4/18, 5:10 PM] +234 706 650 5625: *👄MUGUN FURUCI*👄

*Writing by Ameenatu Sani*

PAGE 31_35

Bayan komi yadaidaita Alhaji Muhammad yabiya duk wani kudi da aka bukata na asibiti, haryanzu dai hankalin shi baiwani kwanta ba addu'ah kawai yake Allah yatashi kafadunsu lafiya, waya yabugama iyalanshi yasanar dasu halin da ake ciki Amma ba a sanar da Habeeb ba.
Shimadai Alhaji Lukuman yasanar da Hajiya Mariya aikuwa ba karamin dadi taji ba jin cewa Salma bata mutu.
Asibitin duk suka shiryo suka zo duba su.

Alhaji Lukuman ne zaune a motar shi shida Alhaji Bala dubanshi yayi a fusace yace "wlh yanzu haka Isah beyi aikin nan yanda yakamata ba mswwww yanzu yatsira kenan?"
Wata dariya Alhaji Bala yayi yace "wlh harka bani dariya Alhaji Lukuman, ainasa duk tantirancin ka ya zarce duk yanda nake zato Ashe baikai ba? Ainasa yanzu wata maganar ake ba wannan ba".
Wani kallo Alhaji Lukuman yayi mashi yace "kaga Bala karka tunzurani wlh kasandai halina ko? To shikenan cigaba da dariyar kagani".
Alhaji bala yace "aidole nayi dariya, waima jira kai baso kake Salma ta mutu ba kuma laifin ya rataya akan Alhaji Muhammad ba?, Kuma sai aka samu akasi yarinyar bata mutu ba?" Alhaji Lukuman yace "aikasan burina kenan duniya naga an wulakanta Madu an mashi kisan wulakanci kamun kuma yamutu zuciyar shi ta buga,aini wannan shine babban burina wlh".
Wani murmushi Alhaji bala yayi yace "to kwantar da hankalin ka burinka zaicika yau basai gobe ba". Alhaji Lukuman yace "tayaya kenan?"
Alhaji bala yace "ai ida kasheta za ayi kawai tunda kace haryanzu bata farfado ba kaga daganan kowa yasan shine yakasheta koba haka ba?"
Alhaji Lukuman yace good haka ne Amma tayaya zata mutu?"
Alhaji bala yace "ta hanyar yimata allurar guba doctor ko nurse kawai zaka cika da kudi kace sokake ta mutu wlh da gudu zasu aika ta bakaga duk arna bane kuma kasandai arna da kudi".
Hannu ya miko mashi suka kashe yace "wlh aikin ka nakyau bala kai babban shegene kasan takan duniya wlh, ai kuwa haka za ayi yanzu bari naje komi kenan zamuyi waya"
"Ok normal saina Jika"
kana ya sauka daga motar

Baiyuce ko inaba sai gida
Akan daya daga cikin kujerun parlorn ya zauna sai zuba murmushi yake yace "Madu (Muhammad) kabani indai da sharrina ne yanzu wasan yafara wlh sainaga ankashe ka har lahira kana hankalina zai kwanta"
Kiran number Hajiya Mariya yayi dayake tanacen asibiti tana d'agawa yace yi sauri dawo gida ina jiranki"
yanke wayar yayi ya cigaba da sambatun shi

Mintuna kadan saiga motoci sunyo mata rakiya tana shigowa parlorn tace "lafiya kuma?"

Wani murmushin yakara yi yace "zauna mana tana zama ya fara fada mata duk yanda sukayi da Alhaji bala saida ya ida fada mata kana ta zubamashi wata uwar harara tace "Amma wlh daga kai har bala bakuda imani ainasa tunda har Salma ta tsallake tarkon Ku nasa tatsira, to bari kaji wlh ko duniya za'abani bazan taba yarda a kashe Salma inaji ina gani ba, ai wannan maganar banza ce wlh karama Ku canza shawara".
Wani naushi ya kaima kujera yace "waini miyasa banida sirrine? Miyasa komi zanyi saina fada maki? Da ace ban sanar dake ba aida baki isa kifada man magana ba to bari kiji wlh yanda na tsara shirin nan babu ubanda ya isa ya dakatar dani kuma yau basai gobe ba Salma zata mutu".
Hajiya Mariya dataga yanda yake tada jijiyoyin wuya kuma tasan tabbas zai aikata komi yace saita Dan sabko tace "naji Salma zata mutu Alhaji Amma ba mutuwa ta har abada ba zadai ta mutu a idon duniya Amma mu agaremu bata mutu ba".
"Kamar ya" cewar Alhaji Lukuman "kamar dai yanda kaji nafada inasan Salma bazan juri rashin ta ba Amma yau dinnan zamu fitar da ita kasar waje sai muhada baki da doctor yasamo wata gawa mai irin jikin Salma sai a rufeta kar mubari kowa ya bude gawar muce Salma ce ta mutu kaga ko yansanda zasuyi bincike basusan Salma ba saidai karmu bari Wanda yasanta yaga gawar ai shikenan ko?"

Wani banzan kallo yayi mata yace "Amma wlh Mariya bakida hankali taya hakan zata faru? ke wannan shawarar taki batayi ba ki canzata tun wuri".
Nan dai Hajiya Mariya taita kawo mashi misalai harya gamsu da bayabinta yace "to bari naje su hadu da doctor
Din".
Bayan yaga doctor sunyi magana nan danan doctor ya amince da bukatar Alhaji Lukuman Amma saida ya tura mashi makudan kudi ta account kana yace yanzu cikin dare zasu canza ita salmar Amma lalle yanzu su naimi jirgin da zai tashi zuwa anjima tana fitowa su wuce haka Alhaji Lukuman yabi shawarar doctor yaje ya kammala komi na tafiyar Salma nan da d'ayan dare jirgin zai tashi.

6:00am
"Innalillahi wa'inna'ilaihir raji'un wayyo Allah ni Mariya Salma Dan Allah kitashi wlh bazan iya rayuwa babu keba wayyo Allah na!" Doctor kira yake "kiyi hakuri Hajiya kiyi hakuri"

Alhaji Muhammad yana shirin zuwa asibiti sai yaji ana buga kofa Hajiya Fadeela tace "daure Alhaji kayi break din bara naduba kowaye" kofar ta bude security din gidan tagani tace "lfy dai office?"
Cikin rawar murya yace "Hajiya babu Lfy ga police's can bakin get sun tare ko ina yanzu haka gidannan zagaye yake da police's kowa kaga fuskar shi kasan babu imani Hajiya kum....bai ida maganar ba saiga wasu police din su shigo wajen Hajiya Fadeela tace "yallabe Lfy ko" daya daga cikin police din yace "matsa babu hanya" suka shige ciki Alhaji Muhammad yadago yagansu zaiyi magana suka ce "yu a onda aress" Alhaji Muhammad ya zaro ido yace "Lfy!?"
"Alhaji anbamu umarni damuzo mutafi dakai In munje can kaji mikayi" Alhaji Muhammad yace "Toni miye hadina da police? Amma muje"
keyarshi suka tusa hajiya Fadeela tace "innalillahi wa'inna'ilaihir raji'un miyayi maku Dan Allah?" Alhaji Muhammad yace "Hajiya nima nan kaina bansan minayi ba Amma in munje naji ai ciki da gaskiya wuka bata hudashi"
har ciki mota suka shiga kana sukabar unguwar da jiniyi.......


_Turkashi_

*Ameenatu Sani ce*👌
[4/18, 5:10 PM] +234 706 650 5625: *👄MUGUN FURUCI👄*

*Writing by Ameenatu Sani*


*NASARA WRITER'S ASSOCIATION*


36_40


Alhaji Lukuman ne gaban gawar Salma sai zabga kuka yake da sambatu kamar wani zautacce likitoci da yan sada sai hakuri suke bashi yayinda Hajiya Mariya take a wani gadon kwance wai suma tayi bayan angama duk abinda za ayi aka fito da gawa zuwa gida domin ayi mata sallah akaita makwancinta da kyar suka fito suka shiga mota sukabar harabar asibitin.
Ana fita da Alhaji Muhammad sai Hajiya Fadeela tai sauri ta dauko wayar ta kiran number Habeeb tashiga yi Amma Sam bata shiga wayar abokin shi Hisham takira yana dagawa tace "Hisham kuna tare da Habeeb?"
Hisham yace "a'a mummy bama tare yanzu dai ya fita".
Hajiya Fadeela tace Dan Allah Hisham kace mashi komi yake yi yau ya baro Kaduna yazu gida"
"Lafiya dai mummy? Cewar Hisham?".
"Hisham babu lafiya" kettt takashe wayar itama tabi bayan su


________________________________________


"MEENAL wai yau bazaki fita bane?" "Ammi wlh yau Sam banajin dadi kuma yau munada wata shari'a banajin fitane kawai".
Ammi tace "lalle agajiye kike MEENAL yanda nasanki baki wasa da aiki to 'kara ki huta Amma kitashi kiyi break saiki koma baccin"
"to shikenan Ammi".
Fitowa daga cikin bargon tayi tashige toilet wanka tayi kana tayi brush ta fito shiryawa tayi kana ta samu Ammi a parlor tana kallo tace "Ammi kallo kike?"
"Eh ai kinsan shike debeman kewa da kin tafi aiki" murmushi MEENAL tayi tawuce tana cewa "aiko Ammi yakamata asamo mai tayaki fira because TV tana iya gundurar ki"
Kitchen tashiga ta dauko break din ta zauna kusa da Ammi suna kallo.
Tace "gaskiya Ammi yakama a nemo mai aiki a gidannan kinga ta tayaki fira ko yakika gani?"
Ammi tayi murmushi tace "aa yar albarka nikad'e ai zan iya zama kuma kinga y'ay'an y'an uwa suna zuwa duk suna debe Mani kewa".
"Allah Ammi banaso kina kad'eci shiyasa nace haka"
"a,a MEENAL to lokacin da kikayi aure fa? Aikin gani dole na saba".
Fuska MEENAL tarufe tace kai Ammi".
Ammi tace "waike MEENAL miyasa duk lokacin da zanyi maki zancen aure sai kin nuna jin kunya Da alamun baki so? Kuma ni gidannan bantaba ganin inda yau wani saurayi yazo wajen kiba mike faruwa? ya kamata nasani domin yanzu kinkai lokacin da za ace kinyi aure Amma naga Sam baki da ra ayin hakan"
MEENAL ta aje cokalin hannunta takalli Ammi tace "wlh Ammi Sam banasan nayi aure nabarki kita wahala ke daya saidai in tare zamu".
Baki Ammi tarike tace a ina akataba haka MEENAL?"
Baki ta tura gaba tace "abar maganar Dan Allah Ammi,bari nabaki labarin sari'ar da mukayi jiya".....


Alhaji Muhammad zaune a gaban dpo
" Dpo yace "Alhaji Muhammad fatan kasan laifin mi kayi aka kawoka nan?"
Alhaji Muhammad yace "ranka ya Dade ni bansan mi nayi ba".
Dpo yace "yazaka rainama hukuma wayau kace bakasan mikayi ba, to kisan kai kayi"
Zaro idanu Alhaji Muhammad yayi yace "kisankai kuma wana kashe".
Dpo yace "yanzu dai mu umarni akabamu mu kamoka yanzu kotu za amika ka inkaje cen saikayi bayani"
"Innalillahi wa'inna'ilaihir raji'un kisan kai kuma ni? haba yallabe ni din nayi kisa?"
Dpo yace "kai sajan" wani Dan Sanda ya shigo Dpo yace "Ku shiga dashi ciki ku rufe"
"Yes sir" kana ya cema Alhaji Muhammad "tashi muje".


Ankammala hada gawa har an wuce da ita domin sadata da makwancinta
Yayin da mata sai rike Hajiya Mariya ake ana bata hakuri nan ko da tashiga cikin hijabi dariya take tayanda shirunsu ke tafiya daidai.

A gaggauce Habeeb ya dawo tunda ya duro garin yaji mike faruwa hankali tashe yanufa gida Amma mai gadi yamashi bayanin "ai babu kowa gidan anwuce da Alhaji police station Hajiya ma kila can tanufa".aiko kiran Hajiya yayi ya tambayeta "wace station ce suke" nan tafada mashi ya wuce can shida Hisham....


*Ameenatu Sani ce👌*
[4/18, 5:10 PM] +234 706 650 5625: *👄MUGUN FURUCI👄*


*WRITTEN BY AMEENATU SANI*

*NASARA WRITER'S ASSOCIATION*

41_45

Da isarsu station din yaga Hajiya rakube a bango ta zabga uban tagumi hawaye sai zubar mata a fuska suke da sauri ya karasa gateta yace "mommy miyasa kike kuka ina Daddyn?" Hajiya bata iya cewa komiba illah hawaye da ke zarya akan fuskar ta Hisham ne yace "Habeeb Mommy bazata iya magana ba yakamata muga dpo" aikuwa haka akayi suka nemi aimasu iso wajan dpo batare da bata lokaci ba suka shiga bayan sun gaisa Habeeb yace "ranka yadade Sunana barrister Habeeb Muhammad *HM*".
Dpo yace "ai nagane ka" Habeeb yace Ok to nazone akan maganar mahaifina bana garin ne akakirani miyayi yallabe?" Wani murmushin takaici dpo yayi kana yace "gobe case din zaikoma kotu kaji komi ya aikata" Habeeb yace "nidai nasan mahaifina bazai aikata wani mugun abuba yallabe adai sake bincike kamun akai kotu" dpo yace "ai laifin nashi a bayyane yake wannan ma basai an wahalar da shari'ah ba za ayanke mashi kukunci daidai da abinda ya aikata na kisanka"
murmushi Habeeb yayi yace "badai mahaifina ba gaskiya"
kafad'a dpo ya daga yace "Ok ainaga kai babban lauyane maizaman kanshi kuma ka kware wajan zakulo mai gaskiya da marar gaskiya nasan tabbas zaga gano gaskiya don haka zaka iya fara bincike wajan gano gaskiya kamun alkali ya bukaci hakan" kai Habeeb ya jinjina yace "insha Allahu yanzu don Allah ina bukatar ganin shi" dpo yace "gaskiya barrister kayi hakuri bazaka ganshiba a yanzu" murmushin takaici yayi kana yace "to shikenan".

Bayan sun fito ne ya lallashi Hajiya akan sukoma gida komi zaizo da sauki insha Allah haka suka koma gida cike da jimamin abun..


Alhaji Lukuman kuwa bayan an rufo gawar da akakira da sunan Salma yanufo gida jama'ah sai gaisuwa suke mashi shikuwa sai share hawanyen munafurci yake yabukaci ganin dpo akan adaga kai karar kotu harsai an gama zaman gaisuwa amma acigaba da tsare shi.

Bayan kwana biyu da mutuwar, Alhaji Lukuman suka haduda Alhaji bala Alhaji Lukuman yace "to Bala kagadai shirina yanata tafiya daidai yanda na tsara babu matsalar da aka samu ko?"
Alhaji bala yace "hakane Lukuman nikaina ina mamakin yanda shirin ke tafiya daidai" wani murmushi yayi kana yace "to yanzuma wani shirin zan sake kullawa kuma nasan zaitafi yanda nake so"
Alhaji bala yace "to wane kuma shiri zakayi bayan gashi burinka zai cika nasan ganin bayan Alhaji Muhammad?"
Wani murmushin Alhaji Lukuman yakara yi yace "ai bazaka gane bane bala nifa wlh har abada bazan so ace Ahalin Alhaji Muhammad sunyi farin ciki ba, wai ko kanada labarin Alhaji Muhammad dan uwa nane ubammu daya dashi?"
Idanu Alhaji bala yazaro yace "Dan uwanka kuma? Taya yazama Dan uwanka?"
Alhaji Lukuman yace "manta da wannan, ni yanzu burina shine bayan an kashe Alhaji Muhammad sai kuma duniya ta zagi danshi Habeeb uwarsa ta tsine mashi kana daga baya itama uwar nasan yanda zanyi da ita"
Alhaji bala yace "taya kuma hakan zata faru?"
Alhaji Lukuman yace "ta hanyar yima Habeeb asiri a daran yau yazama shine lauyana kuma yayi tsaye tsayin daka harsai yaga nayi nasara alkali ya yankema Muhammad hukuncin kisa,
Kaga duniya zata zageshi akan yana lauya amma yagaza kare mahaifinshi uwar shi zata tsine mashi ta dalilin haka kila intaji za'a kashe Muhammad zuciyar ta ta buga nan take ta mutu kagani nayi nasara shikenan burina na shekara da shekaru yacika".

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°′°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Shiri take a gagauce tomin ta makara da hanzari tafito daga dakin ta tashiga dakin Ammi zaune ta isketa tana lazimi jiranta tayi hartakai karshe kana tace "Ammi Nina shirya zan wuce" Ammi ta dubeta tace "to ga break din ki can ki dauko ki karya kamun ki tafi"
"Aa Ammi wlh banada isasshen time lokaci na kurewa yanzu barrister umar yakirani ni ake jira zamu shiga meeting karfe shabiyu munada wata shari'ah kuma kinga Tara takusa"
Ammi tace "waike MEENAL miyasa bakisan karyawa ne inzaki fita? Tun dazufa nake tashinki daga bacci Amma kinki tashi dama nasan karshen ta bazaki karyaba zaki fita"
mikewa tayi tace "ayi hakuri Ammi bari natafi dashi can naci"
Ammi tace "to hakan yayi" tana kokarin mikewa MEENAL ta dakatar da ita tace "haba Ammi sha zaman ki bari na zuba"
Da sauri ta

2 / 7