Author : Ameenatu Sani ce Category : Complete Novels
da take fada ya sashi fitar da wayar shi transfer yayi mata ta one million kana yace "duba wayar ki in kingama bala'in".
Hawaye shabe shabe a fuskarta ta jawo wayar ganin uban kudin da ya tura mata sai kukan da take ya koma dariya tace " kai Alhajina wlh harkasa naji dadi ngd sosai "
Alhaji Lukuman yace "ainan bama sallamarki bace sai komi ya daidaita zan maki alert mai fasa waya" wani ihon dadi tayi ta ma'kal'kalai Alhaji Lukuman...
_Shegiya naira😎_
*TALLA! TALLA!! TALLA!!!*
*Assalamu Alaikum*
*Ina yan'uwa masu sha'awar shiga kungiya ta online writer? To albishirinku😊 kakar tayanke sa'ka👌 Kuma damace agare Ku sabuwar kungiyarmu mai suna 💫💫NASARA WRITER'S ASSOCIATION💫💫 tana maraba da kowa da kowa duk mai sha awar shiga kungiyar kinada damar shiga bako sisin ki👌*
*Ina tsofaffin hannu da sababbin hannu wa inda basuda kungiya? Maza hanzarta domin kasan cewa daya daga cikin members din cikin ta💃💃 domin a dama dake*
*Ina masu San gwada basirar su wajen fara fadakar da Al'umma ta hanyar rubutun Hausa novel? Kungiyar mu tana maraba da ke yar uwa indai kina da sha awar zama online writer*
*Domin neman Karin bayani saiku tuntubi daya daga cikin number's din nan*👇
08065522770
08104335144
*NASARA WRITER'S ASOCIATION*
💫💫 _*{{Nasara abin so ga kowa ,domin marubuta da cigaban rubutu al'kalaminmu y'ancinmu.}}*_💫💫
*Ameenatu Sani ce👌*
08065522770
[4/18, 5:17 PM] +234 706 650 5625: *👄MUGUN FURUCI👄*
*Writing by Ameenatu Sani*
56_60
Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR Call 08066268951*
Da Isar Hisham police station ya nemi ganin Dpo batare da bata lokaci ba ya ganshi bayan sun gaisa ne dpo ke sanar dashi "ai yanzu haka anjima wajan goma za akaishi gidan yari domin bazasu cigaba da rike mai laifi kamar Alhaji Muhammad ba a wajan su"
Da sauri Hisham ya kalleshi "haba yallaba miye na gaggawar kaishi gidan yari? Dan Allah abani bailing shi"
Dpo yace "kataba ganin anbada bailing din mai laifin kisa?, kaga gata daya zakuyi mashi kuje Ku binciko bayanan da zaku karaishi duk da yanada kwararran louya amma ina tabbatar maku shari'ar zuwa daya za ayanke mashi hukunci"
Ai Hisham ko sauraran shi baiyi ba yabar office din kiran wayar Habeeb yayi amma no answer haka Yakama hanyar zuwa gidan Alhaji Lukuman "
Da isarshi security din bakin gate suka tabbatar mashi baya gida, jiki a sanyaye yabar wajan gidansu Habeeb ya koma amma bai iske Habeeb ba da mamaki yabar dakin wajan Hajiya yaje yafada mata duk yanda sukayi da dpo bakaramin rudewa Hajiya tayi ba amma Hisham yashiga kwantar mata da hankali.
Shikuwa Habeeb bayan fitar Hisham da Kad'an wayarsa takama ringing wata number ce akakirashi da ita cike da bacci idanunshi ya daga wayar jin an ambaci sunan Alhaji Lukuman yasa ya wartsake daga bacci yace "Ok ganinan zuwa"
Bayan mintuna goma saiga Habeeb ya iso a wajan shakatawar Alhaji Lukuman cike da girmamawa ya gaishe su, inda suka bashi wajan zama bayan ya zauna Alhaji Lukuman yaci gaba da koroma shi bayanin dalilin kiran da a kayi mashi....
Daran ranar lahadi Hisham ne yazo wajan Habeeb amma Habeeb Dan nar waya kawai yake a tsawace Hisham yace "waikai Habeeb ya ina maka magana mai mahimmanci amma kayiman banza?" Kunnewa Habeeb ya dade kana yace "wai miye haka Hisham? Kana Neman kasheman dodan kunne"
Hisham yace "magana fa nake maka haryanzu bakace komi ba akan kotu da za'a shiga gobe"
Habeeb yace "to Dan za a shiga kotu gobe sai akayi yaya malam Hisham?" cike da murmushi a fuskar shi ya ida maganar amma in ka kireshi da ido zakagano hawaye kwance a cikin idanunshi
Kai Hisham ya girgiza tare da zama kusa da Habeeb yace "nifa barrister na kasa gane maka kwana biyunnan mike faruwa ne kake wasu abubuwan?"
Habeeb yace "hauka kaga inayi komi?"
Hisham yace "niba wannan ba ga magana mai mahimmanci danake maka Habeeb kodai bakasan insan ainihin shirin da kakeyi ne gamai da shari'ar?"
Habeeb yace "Ashe dai kagane" Hisham yace "Ok ai ba matsala nasan duk cikin aikine na kwararraran barrister bai kamata kabudeman gaskiyar da ka gano saboda ni barene" yana gama fadar haka ya fice daga dakin.
Yana fita Habeeb yabishi ya rufe dakin ya dawo zama yayi kan gado yace "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" haka yayta maimai tawa saiga hawaye sun fara zuba a idanuwanshi, shikanshi ya rasa gane mike damunshi miyasa yake aikata wasu abubuwan, haka yaita sambatu a daranma baiyi bacci ba...
Washe gari tunsafe Habeeb yabar gidan haka Hajiya tazo bata samaishi ba kiran wayarshi tayi nan ma a kashe tajita Hisham takira ta tambayeshi ko suna tare, ya tabbatar mata basu tare Hajiya tace "to kayi sauri Hisham ina jiranka time na tafiya".
Wajan Tara da rabi saiga Hisham bayan sun kara gaisawa tace " wai ina shi Habeeb yace maka zayane?" Hisham yace "wlh Hajiya baifada man ba nima tun safe nake kiranshi wayarshi bata shiga"
Hajiya tace " ok to yanzu ina kuka tsaya ina fata Habeeb yasamo cikakkiyar amsar da zaiba alkali har ya saki Alhaji?" boyayyar ajiyar zuciya Hisham yasaki kana yace "ai Hajiya kinsan Habeeb jarumi ne ba a taba kadashi a shari'a ba Dan haka ki kwantar da hankalinki insha Allah yau sai daddy ya dawo gida"
Hajiya tace "Allah yasa, ni Habeeb ne naga yanzu gaba daya ya canza wlh" Hisham yace "karki damu komi zaikoma dai dai, Hajiya tashi ki shirya mutafi kar lokaci ya kure" Hajiya na mikewa wasu mata su hudu sukayi sallama sosai Hajiya tayi farin cikin ganinsu, sisters dinta ne yayyenta biyu sai kannanta suma sunzo ganin shari'ar ne...
Kotu....
Ameenatu Sani ce👌
08065522770
[4/18, 5:17 PM] +234 706 650 5625: *👄MUGUN FURUCI👄*
*Writing by Ameenatu Sani*
*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
________________________________
https://www.facebook.com/103637491942644/
💫💫 {{N W A}} 💫💫
بِسْـــــمِ ٱاللَّهِ ٱلرَّحْمَنِ ٱلرَّحِــيــمِ
61_65
Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp ORCall 08066268951*
Cike kotun take makill da mutane kuma manyan mutane Harta da sugaban jam'iyya yazo, ga lauyoyi ciki harda barrister Habeeb Muhammad *HM*, kotun tayi tsit ana jiran shigowar alkali bayan wasu yan mintuna saiga shi yashigo, gaba daya a ka tashi domin girmama alkali bayan an zazzauna maga takarda ya fara karanto kara kamar haka..
"A yau ishirin da biyar ga watan daya shekara ta dubu biyu da ashrin da biyu Alhaji Lukuman yana karar Alhaji Muhammad da kisan y'arsa ta hanyar banketa da mota".
Tsittt kotun ta dauka bayan alkali yagama rubuce rubucen shi ya dago kai yace "kotu na bukatar ganin Alhaji Muhammad a gabanta".
Bayan anzo dashi kana yakara fadin " in da kwai lauyoyin mai kara da Wanda ake kara su tashi su gabatar da Kansu".
Hajiya da Hisham da sauran magoya bayan Alhaji Muhammad kowa hankalinshi ya karkata zuwa ga Habeeb basu an karaba sukaji yana gabatar da kanshi.
"SUNANA BARRISTER HABEEB LAUYEN MAI KARA"
Dayawa daga cikin mutanan kotun sunyi mamakin jin furucin Barrister Habeeb musamman magoya banyan Alhaji Muhammad saboda sun San Dan sane
Hajiya Fadeela tace "Habeebbbbbb, bakada hankali ne?" Cikin tsawa ta fadi hakan.
Alkali ya buga gudumar kotu alamun a saurara amma Hajiya Fadeela taki yin shiru saboda rudewa tama manta gaban alkali take.
alkali yace "inbazakiyi mana shiru ba kifita domin nan ba kasuwa bace".
Kukan da ta rushe dashi ne yasa alkali bada umarnin a fita da ita waje, kuma kowa yayi shiru.
Bayan an sakeyin shiru ne alkali yace "ina lauyan mai kare Wanda ake kara?"
Shiru babu Wanda ya Mike Hisham da bakaramin haushin Habeeb yaji ba yana mamakin taya Habeeb ya sauya lokaci daya harya kasa taimakon mahaifinshi? "Allah sarki daddy Allah ya fitar dakai daga wannan iftila'in da yafada maka!".
Shikuwa Alhaji Lukuman da Alhaji bala suna daga gefe tare da sakin wani mugun murmushin jin dadi, shikanshi daddy yayi mamakin Habeeb.
Alkali yace "barrister Habeeb zaka iya fara tambayar ka ga Alhaji Muhammad"
A sanyaye Habeeb ya fito da zaka kurama kwayar idanunshi ido da ka ga kwanciyar hawaye a gurbin idon, agaban Alhaji Muhammad ya tsaya tare da gyara gilashin idanunshi yace " zamuso ka bayyanama kotu cikakken sunanka".
Alhaji Muhammad yace " kamar yanda kowa yasani sunana Alhaji Muhammad ".
Habeeb yace " zamuso kafada mana alakar da ke tsakanunka da Alhaji Lukuman "
Alhaji Muhammad yace "ni babu wata alaka tsakanina dashi".
Habeeb yace "inbaku da alaka amma aikuna takara tare ko?"
Alhaji Muhammad yace "dan muna naiman kujera a tare ba shine zaisa munada alaka ba"
Habeeb yace "Ok to miye Alakarka da ita mariganyiya Salma da harka yi ikirarin saika kashe ta kuma sai gashi ka kasheta da mota"
Alhaji Muhammad yace "ni ban kashe taba kuma da ranta na kaita asibiti, kuma ni banta ba wannan ikirarin ba"
Habeeb yace " kafadama kotu gaskiya domin wannan laifin naka a bayyane yake"
Alhaji Muhammad yace "ni ban kashe ta ba tsautsayine kawai da inya yini baikwana amma ni wlh bada niya na bigeta ba"
Habeeb ya kalli alkali yace "yamai girma mai shari'a Alhaji Muhammad yana so ya wahalar da shari'a ne har yanzu yaki amsawa shiya kashe Salma dan haka nake rokon wannan kotu da a bani dama in gabatar da sheduna domin tabbatar da Alhaji Muhammad da gangan ya kashe Salma"...
_Tofa ikon Allah muje zuwa🤭_
*Ameenatu Sani ce👌*
08065522770
[4/18, 5:17 PM] +234 706 650 5625: *👄MUGUN FURUCI👄*
*Writing by Ameenatu Sani*
_Ina godiya da Addu'o'inku sosai kuma masu magana akan bana typing akan lokaci kuyi hakuri Dan Allah ba zaune nake ba amma insha Allah komi zai daidai ta karkuji komi masoya🥰_
66_70
Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR Call 08066268951*
______________________________
Alkali yace "anbaka dama"
Juyawa yayi ya kalli jama'ah yace in Isah driver yana kusa ya fito batare da bata lokaci ba sai gashi ya fito.
Habeeb yace "isah zamuso kafadama kotu ko kawai waye d kuma shedar da zaka banda yanzu".
Isah driver yace "sunana Isah kuma ni driver ne a gidan Alhaji Muhammad, shedar danazo badawa itace, Lokacin da abun yafaru muna tare da Alhaji ya buge ita yarinyar kuma saida nace mashi kada ya bugeta amma ya bugeta".
Alkali yace " kana driver miya hada shi Alhaji da driving?"
Nan Isah Yakama zare idanu kana yace "ai ai lokacin ni kaina ke ciwo shiyasa ya amshi tukin".
Alkali yayi yan rubucece kana ya kalli Alhaji Muhammad yace " Alhaji Muhammad haka akayi ysakaninka da isah driver?".
Alhaji Muhammad yace "kusan hakan mukayi amma lokacin shike driving din wucewar motar yaceman kanshi na ciwo bayan kuma lfy lau muka taho, kuma batun da yace wai yaceman karna kasheta ya mai shari'a inaso ka tambaye shi tsakaninshi da Allah in munyi wannan maganar, kuma ni abunda na lura shine ya takaman Giya da kafarshi wlh".
Wata uwar zuface ta shatatowa Isah gabanshi ya kama faduwa nan alkali ya kalli Isah yace "tokai Isah kaji tsakaninka ga Allah kace mashi haka?"
Isah yace "wlh munyi haka dashi ya mai shari'a".
Nan Alkali ya yi yan rubuce rubuce kana ya dago yace " wannan kotu mai adalci taji bayani daga bakin kowa kuma ta gamsu saidai za'a dage wannan Shari'a harzuwa nan da 5-2-2022 kuma kotu na bukatar lauyan da zaikare shi Alhaji Muhammad din, za acigaba da zare shi babu batun balling shima Isah driver kotu na bukatar yansanda su bincikeshi".
Nan ya buga guduma alamun antashi.
Alkali ya tattara kayanshi ya fice kotun tacika da hayaniya shikuwa Alhaji Lukuman da Alhaji bala ba haka suka soba sun so ace yau anyanke hukunci amma ai akwana atashi babu wuya, nan suka bar kotun rai bace.
Shikuwa barrister Habeeb da sauri yabar kotun danjin yanda mutane suka fara zaginshi hakan yasa kanshi fara jujjuyawa.
Hisham a fusace yabi ba yanshi.........
*Ameenatu Sani ce👌*
[4/18, 5:17 PM] +234 706 650 5625: *👄MUGUN FURUCI👄*
*_By Ameenatu Sani_*
*_Masoya ina dai dad'a Baku hakuri, kuma inajin dadi da nuna kulawar Ku akan buk dina insha Allah zaku dunga jina ba 'kak'kautawa😂mun kusa 'kar'karewa kuhuta da jirana_*
71_75
Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===150
1GB@=====270
2GB@=====550
3GB@====800
5GB@====1,350
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR Call 08066268951*
____________________________
Koda Habeeb ya hau motar hawaye kawai yake yi wani irin tukuki yakeji a zuciyarshi ga wani zafi da take mashi, da'kyar dai yakai gida wani mahaukacin hon ya dunga dannawa da sauri mai gadi yazo ya bude mashi gate ya danna motar da karfi ko parking din kirki baiyiba ya fito da gudu ya nufi dakin shi kulle kofar yayi ya fada kan gado wani irin kuka ya saki kamar wani karamin yaro yace "innalillahi wa'inna'ilaihir raji'un, wai maike faruwa dani ne?,mai na aikatawa daddy na haka? Why why why haka kakeyi Habeeb?" Ya ida maganar da wani irin kuka.
A fusace Hisham ya shigo parlon murda kofar dakin Habeeb yayi yajita a rufe da karfi yace "Habeeb!!! Bude kofar nan" jin shiru ya kara cewa "na fada maka ka bude kofar nan inba so kake na karyata ba!"
Y'an uwan Hajiya ne suka shigo gidan 'ban garan dakin Hajiya suka shiga samunta sukayi tana kuka Hajiya badariyya tace "wlh Fadeela bansan asararran da kika Haifa ba sai yanzu wlh Habeeb yayi asara duniya da lahira" Hajiya Saude tace "Kenifa inaga Habeeb ya haukace ne Dan wlh abida yayi ba mai hankali ne zaiyishi ba,ace mutum ya dauki d'awainiyar ka har ka kawo wannan matsayin amma ace ka kasa taimakon shi"
Hajiya Umma da tabuga uban tagumi tunda suka shigo tace "Kai jama'ah wai haka Habeeb yakoma?,wlh danasan irin takaicin da zan kwasa kenan da banje ba , ai Fadeela ki godaima Allah dayasa baki kalli shari'ar nan ba inaji da zuciyarki ta fito waje Dan bakin ciki".
Hajiya badariyya tace "yo ni kinji yanda zuciyata tayi? Wlh kamar ta fado naji, kaini yau Habeeb yaban mamaki wlh".
Kuka Hajiya Fadeela ta kara rushewa dashi tace " Dan Allah ya isa haka kubarni naji da wannan damuwar!".
Sallama Hisham yayi dakin Hajiya Umma ce ta amsa mashi Hisham ya samu waje ya zauna yace "Dan Allah Hajiya kuyi hakuri da abinda Habeeb yayi wlh ba acikin hayyacinsa yake ba"
Hajiya Fadeela nuna kofa tace "Hisham tashi kabar nan, ai duk halinku daya dashi duk munafurcin tare kuka kullashi zaka wani zoman nan simi simi tashi kaban waje nace" tafada cikin tsawa.
Cikin sanyin jiki Hisham yatashi yana kiran "ayi hakuri Dan Allah" yabar dakin
Hajiya badariyya taja tsoki tace "aikin banza kawai, kinga Fadeela bawai kuka zaki zauna yiba mafita ya kamata ki nema indai kina san mijinki".
Bangaran Alhaji Lukuman kuwa tafiya sukeyi a mota shida Hajiya Mariya da Alhaji bala Allah Lukuman yace " ya kukaga wasan nawa?, duk da dai aikin baitafi yanda ake so ba amma da alama da nasara"
Wata dariya Alhaji bala yayi yace "gaskiya Lukuman ka iya lalata, to waini abinda ya keban mamaki rannan kaceman babanku daya da shi Alhaji Muhammad din to taya kuka zama haka?"
Wata dariya yayi kana yace "yaudai bari nabaku labari dama itama Hajiya ta isheni da tana so taji".
*Baya Kad'an*
Alhaji Mukutar shahararran Dan kasuwa ne yana safarar man faitur da fiton shinkafa da man Olga da manja turaila turaila ake fito mashi da su , shidin mazaunin kasar Niger ne, yatara kudinda koshi kanshi baisan iya adadinsu ba, matanshi biyu Hajiya binta da Hajiya Sakina, Hajiya Binta itace uwar gida shekaran su shidda da aure amma ko batan wata bata ta'ba yiba hakan yasa Alhaji Mukutar ya auro Hajiya Sakina shekara guda ta Haifa mashi Da namiji Wanda yaci sunan mahaifinshi Muhammad sosai Alhaji Mukutar ya dauki Son duniya ya daurama Muhammad hakan ba karamin bakanta ran Hajiya Binta yayi ba tana tunanin duk dukiyar Alhaji zata koma ga Hajiya Sakina shiyasa ta shiga yawon bin malamai da bokaye amma duk inta taje ace bata haihuwa tasha wahala sosai da 'kyar tasamu bokan dayace zai taimaketa amma saidai cikin aljani zai turo yasa matashi kuma zata haifi da marar jin magana kuma indai tanaso taci kudin Alhaji to yaran shine zai kashe alhajin da hannunshi, haka Hajiya Binta ta yarda bayan shekara daya Hajiya Binta ta haifi danta yaci sunan Lukuman duk da irin murna da haihuwar da Alhaji Mukutar yayi sam baiji yanasan Dan ba ko Kad'an murnar ma ba wani sosai yayita ba hakan yasa Hajiya Binta kara tsanar Muhammad da uwarsa.
Muhammad Nada shekara shidda shikuma Lukuman hudu Allah yayima Hajiya Sakina rasuwa kuma kisan Hajiya Binta ce sularshi bayan shekara daya da mutuwar itama Hajiya Binta ta mutu wajan zuwa wurin boka Dan yakashe Muhammad motar tayi accident ta mutu _(Dama ita rayuwa haka take duniya juyi juyi)_.
Haka Muhammad da Lukuman ke