Advertisements
Chapter 3 Reading MUGUN FURUCI Fushin Uba by Ameenatu Sani ce BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

MUGUN FURUCI Fushin Uba by Ameenatu Sani ce

Author :  Ameenatu Sani ce Category :  Complete Novels

Chapter   3 / 7

6K to 9K   out of 19.4K words

zuba abincin a kula tayima Ammi sallama tafita
abakin titi take tsaye tana tsaida mai napep bayan ya tsaya tafada mashi inda zata tashiga suka wuce
Da saukarta kawarta jiddah ta iso tace "kai Amma wlh MEENAL nawarki tayi yawa tunfa dazu nake tsaye wajannan ina jiranki Amma sai ceman kike gaki a hanya" dariya MEENAL tayi tace "sorry besty wlh Ammi ce tamatsa sainaci abinci bamma Ciba kinganshinan nazubo" karbar kular tayi tace "kai Amma Allah yasakama Ammi da alkhairi wlh kinsan kuwa yunwa nakeji tunda matsa maki akayi kawonan ninaci" kular MEENAL ta sakarmata tace "aidama ke a cici ce wlh saikita kaya, dazu Brs.Umar yakirani wai ni ake jira naga kuma kamar ba ashiga ba ko?"
Jidda tace "to aidai kinsan halin umar burinshi yazo ya ga kema kin iso shiyasa Amma yanzu za'a shiga" kai kawai MEENAL ta girgiza sukaci gaba da tafiya
Karfe shadaya suka fito daga meeting din suna zaune Jidda nacin abinci MEENAL ko waya take latsawa umar na gefansu sai surutu yakema MEENAL tana dariya sama sama can umar yace "wai madam ya maganar mu don Allah? haryanzu kinki bani amsa ta" MEENAL tace "ayya Barrister don Allah abar maganar nan kagadai yanzu akwai aiki gabana"
Barrister umar yace "to shikenan madam kardai kimanta Ina sonki! koba yanzuba ina jiran amsarki please" Jidda tace "lalle Barrister kaima sai wahalar da kanka kake akan wannan y'ar ba'kar" MEENAL tace "eh aba'kar kuma ya nace ko?" dariya sukayi su duka daidai da lokacin Jidda tagama cin abincin kuka tashi domin gabatar da shari'a



*_Ameenatu Sani ce๐Ÿ‘Œ_*
[4/18, 5:10 PM] +234 706 650 5625: *๐Ÿ‘„MUGUN FURUCI๐Ÿ‘„*


*Writing by Ameenatu Sani*

51_55

Da sauri ya karasa gareshi jijjigashi ya hauyi yana kiran "Habeeb! Habeeb!!" Amma Sam Habeeb baya motsi da kyar ya fito dashi daga toilet din kan gado ya shimfidar dashi yaciga ba da jijjigashi amma har yanzu shiru da sauri Hisham ya dauko ruwa masu sanyi a firiji ya shafama Habeeb a fuska wani dogon numfashi yaja kana ya sauke ajiyar zuciya amma baibude idanshi ba Hisham yace "Habeeb bude idonka mana" zuciya Habeeb ya dafe murya na rawa yace "ba..ni.....maaa...gaaani na". Hisham yace "to, sannu Habeeb bari naje nakawo maka ko tea ne nasan bakaci komi ba tun jiya". Baijira cewar saba ya bar dakin kasancewar ansan Hisham sosai a gidan shiyasa kai tsaye yanufi parlor mai aiki ya gani tana goge goge nan yamata magana "tayi sauri ta hadoma shi tea mai kauri" da "toh" ta amsa kana ta shige Kitchen mintuna Kad'an ta kawo tea din Hisham ya karba, kwance ya samaishi ya dafe kai da kyar Hisham ya lallabashi yayi kurba ukku da tea din kana ya ballar masa maganin da yake sha dayake akwai maisa bacci cikin kankanin lokaci ya kama bacci.
Bargo Hisham ya ja ya rufeshi da shi kana yabar dakin parlor ya fito yaga mai aiki yace "tayi mashi magana da Hajiya", bayan mintuna Kad'an saigata tana saukowa Kaida ganinta kasan tasha kuka
zama tayi akan kujera Hisham yace "ina kwana Hajiya?"
Hajiya tace "lafiya lau"
Hisham ya gyara zama yace "am Hajiya Dan Allah kiyi hakuri akan maganar da Habeeb yayi, wlh baida lafiya wannan abun daya faru duk ya rudar dashi yarasa nutsuwar shi,yanzu haka na ba shi magani harya samu bacci insha Allah daya farka zaidawo normal"
Hajiya tadanyi murmushi tace "bakomi Hisham Allah yabasa lafiya"
"Amin Hajiya" cewar Hisham kana ya kara da "fadin Hajiya nazone akan maganar daddy to da muyi maganar da Habeeb amma nasamu baida lafiya yanzu ya kike ganin za mu fara bullo da maganar?"
Hajiya ta fashe da kuka tace "wlh Hisham Alhaji bai kashe wannan yarinya ba kawai ajalinta ne ya biyo ta hannunshi" nan tacigaba da kuka kamar ranta zaifita
Hisham yace "kiyi hakuri Dan Allah Hajiya insha Allah babu abinda zai faru da daddy, yanzu bari na je station din naji ina akatsaya inma takama naje har gidan Alhaji Lukuman din sai naje"
Hajiya tace "to Hisham an godai Allah yasaka da alkhari"
Hisham yace "amin Hajiya ai duk yima Kaine"
Nan yasa kai ya bar gidan..


Dariya suketa shekawa a mota Alhaji bala yace "gaskiya Lukuman kai din bakaramin shu'umi bane hahahahaha" Alhaji Lukuman murza gashin bakinshi yayi yace "waikai Bala haryanzu baka ida Sani naba ko? To bari kaji da wannan hannun nawa na kashe mahaifimmu Dan kawai na mallaki dukiyar sa kaga kuwa ai babu Wanda bazan iya kashewa ba, Muhammad ne kawai bazan iya kashe shi da hannu naba nafiso a yimashi kisan wulakanci a gaban idanu na"
Alhaji bala yace "wai to Alhaji Lukuman jiya kace man shi Muhammad din mahaifinku daya to taya hakan ta faru?"
Kamun Alhaji Lukuman yayi magana wayarsa tafara ringing dagawa yayi ya amsa wayar kana bayan ya gama yace "Bala taka mota muje"...


Ameenatu Sani ce๐Ÿ‘Œ
08065522770
[4/18, 5:10 PM] +234 706 650 5625: *๐Ÿ‘„MUGUN FURUCI๐Ÿ‘„*


*Writing by Ameenatu Sani*


46_50


Da mugun zabure Alhaji Bala ya kalli Alhaji Lukuman yace "wai da gaske kunne na yaji mikace kuwa?
Wani muskilin murmushi Alhaji Lukuman yayi yace " wato kana wasa dani ko? To nafada maka sharrina ya wuce duk yanda baka zato, yanzu bari nashiga ciki gobe tunda asuba saimu hadu karakani wajan malamin"
Shi dai Alhaji Bala haryanzu yana cike da mamakin Alhaji Lukuman, haka sukayi sallama yatafi.
Washe gari tun hudu na Asuba Alhaji Lukuman yayi ma Alhaji Bala waya akan yafito sauri zasuyi tunkamun Jama'ah sufara zuwa .
A bangaran Barrister Habeeb kuwa a daran ranar baiyi bacci ba tunani kawai yake taya har mahaifinshi zai iya kashe Salma? Shin da ganganne ko kuwa 'bacin rana ce? Saikuma ya tuna da wani *MUGUN FURUCI* da mahaifin nashi yayi akan Salma _"Ke kuma idan bakiyi wasa ba sainayi ajalinki Dan akan d'ana babu abinda bazan iya ba"_ Da sauri ya Runtse idanuwanshi yace "nooooo daddy!!!, Nasan baka aikata haka ba, bakai bane, ajalinta ne ya biyo ta hannuka". Dafe kai yayi domin yanda yaji yana sassara mashi da 'kyar ya isa kan katafaran bed dinshi ya sulale ya kwanta amma tunani ne cike da kwanyar shi ta gefe daya yanajin zafin mutuwar Salma tunda duk duniya babu Wanda ya kaishi Santa, dayan ban garan kuwa ya kasa gasgata shin tsautsayine ko da gangan ka 'kagare yake gari ya waye ya binciko gaskiya. Yanda yaga dare haka yaga sapiya
Tunda gari ya waye Hisham yazo wajan Habeeb daya kasa fitowa Kwance yasa maishi cikin bargo saurin karasawa gareshi yayi yace " Barrister ashedai da gaske baka fito ba?, gashi har tara ta wuce" tashi yayi daga kwancen da yake yace "to ai zuwanka gashi na tashi" Hisham ya zauna bakin gado yace "yakamata ka hanzarta tashi ka shirya muje station din nan domin magana da daddy daga can din sai mu biya gidan shi Alhaji Lukuman din muji"
Wani kallo Habeeb yamashi yace "mizamuyi Station kuma?"
Batare da wata damuwa ba Hisham yace "muyi magana da daddy mana muji yanda Accident din ya faru".
Mikewa Habeeb yayi yace "kaga Hisham ni yanzu banda lafiya, gaskiya babu wata station din da zani tun jiya fa nake tunanin kisan da Daddy yayima Salma kuma a iya binciken da nayi an tabbatar shine ya daki motar ta, baya ga haka a can baya inba zan manta ba akwai wani *MUGUN FURUCI* da daddy yayi akan Salma duk saiyanzu abin ya fadoman a rai wlh" tassssss sukaji saukar fashewar pilet Hajiya Fadeela ce tazo kawoma Habeeb breakfast taji wannan *MUGUN FURUCIN* abakin Habeeb da sauri suka juya suna kallonta Karasowa tayi gabansu da sauri ta wanke Habeeb da maruka harbiyu hannunta na rawa ta nunashi da ya tsa tace "Habeeb bakada hankali ne? Mahaifin naka ka yarda yayi kisan kai?" Kumatun shi ya shafa ya zagayeta ya shige toilet, da shigarshi ya sulale kasa wasu zafafan hawaye na biyo kun cinshi ya rasa miyasa yayi wannan *MUGUN FURUCIN* ga mahaifinshi zuciyarshi ce tafara bugawa da sauri ya dafeta a cikin toilet din ya kwanta yana nishi.
Shi kuwa Hisham mutuwar tsaye yayi tunda Habeeb yafara maganar saida Hajiya tashigo kana ya motsa a sanyaye yace "am Hajiya kiyi hakuri Habeeb baida lafiya ne ya damune da tsare daddy da akayi harya fara Sambatu amma aikinsan yanda Habeeb ke kaunar daddy bazai taba aikata haka agare shiba, ki kwantar da hankalinki Dan Allah".
Juyawa tayi ta fice daga dakin jin wasu sabbin hawayen na kara sauko mata itama Sam jiya bata iya wani bacci ba.
Tana fita Hisham ya isa kofar toilet din ya buga yace "Habeeb yi sauri kafito" jin shiru sai ya saurara jin nishin Habeeb a toilet din da sauri ya murda kofar toilet din ya shiga a kwance shamai shamai ya samu Habeeb.....

Ameenatu Sani ce ๐Ÿ‘Œ
[4/18, 5:10 PM] +234 706 650 5625: *๐Ÿ‘„MUGUN FURUCI*๐Ÿ‘„


*WRITING BY AMEENATU SANI*


*_Wannan labarin kirkirarran labari ne banyarda a juyaman shiba ta kowace siga_*


*JIGWAN LABARIN*_:Akan mahaifin da yayi *MUGUN FURUCI* Akan budurwar d'an shi inda kuma tsautsayi ya fada mashi, shikuma d'an yazama lauyan mahaifin yarinyar_.


*SADAUKARWA ga my friend DARMA*

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alฦ™alaminmu ฦดancinmu._* }}

https://www.facebook.com/103637491942644/

๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ *{{N W A}}* ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ


ุจูุณู’ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู…ู ุงู„ู„ู‘ู‡ู ุงู„ุฑู‘ูŽุญู’ู…ูŽู†ู ุงู„ุฑู‘ูŽุญููŠู’ู…



PAGE 6_10


Da isarsu gidan parking sukayi abakin get, Alhaji Muhammad yacema Isa driver yaje yayi magana da security's din bakin get din, aiko haka akayi isa yaje yasanar da daya daga cikin security's din nan security din yace "amma koma waye kesan ganin boss baisan yau ranar weekend bane? "

Isa yace "to ai inajin baisan da tsarin bane amma Dan Allah kayi mashi iso da Alhajin inaga babbar magana ce ta kawo shi wajanshi".

Dan nisawa security din yayi kana yace " to ina zuwa" wajan sauran yace dayake security's ukku ne abakin get din sukayi magana kana daya daga cikinsu ya bude karamar kofar get din yashiga.


Gidan katon gidane don ko get din gidan ukku saboda girmanshi ga katan parking space a wajan manyan motoci ne kusan shidda awajan, atakaicedai gidan Alhaji Lukuman ya hadu iya haduwa.

Zaune suke a babban falo su ukku ne Alhaji Lukuman sai matar shi Hajiya Mariya sai y'arsu Salma, suduka da ka kalli fuskarsu suna cikin farin ciki, karamin table ne agaban Alhaji Lukuman samanshi da katon plate mai dauke da kayan fruit Hajiya Mariya na yayyanka mashi yana duba jarida, Salma ko katuwar wayace a hannunta ta toshe kunnanta da earpiece tana taunar chin gum.


Security din ne ya turo kofar gami dayin sallama acikin su babu Wanda ya amsa mashi to dayake sun saba da hankan baiwani damuba yace "boss kanada bako awaje".
Ko kallanshi Alhaji Lukuman baiyiba yace " kaje kace koma waye yakoma " security din yatashi zaije yasanar da sakon sai muryar Hajiya Mariya yaji tace "jeka shigo dashi".
Da sauri Alhaji Lukuman ya dago ya kalleta yace " wai Mariya miyasa kike man wannan abun? Kobakiji amsar Dana bada bane zakiyi man eyayi kuma?"

Hajiya Mariya tace "haba Alhaji kasan kowayene kesan ganin ka? zakace ace yakoma ai inaga koma waye bakone baisan tsarinka ba shiyasa" Alhaji Lukuman zaiyi magana sai akaturo kofa security din ne agaba sai Alhaji Muhammad sai Habeeb abaya, sanar dasu yayi ga bakinnan kana ya koma.

Alhaji Lukuman yakai dubanshi wajan wa inda akakira da bakin idanunshi suka sabka afuskar Alhaji Muhammad

Kallashi yayi da alamun mamaki saikuma yayi wata munafukar dariya gani da taba hannuwa ya nuna Alhaji Muhammad yace "aidama nasan zakazo koba yauba nasan da wannan yo Alhaji Muhammad anfada maka siyasa wasane ko anfada maka Lukuman na wasane? To inbaka saniba kasani ni Alhaji Lukuman nafi karfin innemi Abu kuma ace ban samuba balle wata banzar kujerar chairman,yo Allah natuba ko kujerar Governor nanema ai saina samu bare ta chairman Dan haka basai kasanar dani ka janye ba nasan ai dama haka kazo kasanar dani ko? To badamuwa ngd" sai ya nuna mashi kofa yace "bi inda kafuto ba sai anyi wani dogon turanciba hutawa nake"
Tunda yafara maganar Alhaji Muhammad da Lukuman dama sauran wa inda ke falon suka bishi da kallo har ya dire maganar kana yace "Haba Alhaji Lukuman nifa bakone a wajanka koba komi kabamu wajan zama" wani irin kallan raini Alhaji Lukuman yayi mashi kana yace "wajan zama kuma? Naga ai mungama magana ko tunda nasan makasudun zuwanka nan Dan haka katashi katafi"
Batare da wata damuwa ba Alhaji Muhammad yanemi daya daga cikin kujerun parlorn ya zauna kana yace "Alhaji Lukuman zauna muyi magana ni yanzu ba maganar siyasa takawoni wajanka ba magana ce mai mahimmanci...

Manage please๐Ÿ‘

*Ameenatu Sani ce*๐Ÿ‘Œ
08065522770
[4/18, 5:10 PM] +234 706 650 5625: *๐Ÿ‘„MUGUN FURUCI*๐Ÿ‘„


*WRITING BY AMEENATU SANI*


*_Wannan labarin kirkirarran labari ne banyarda a juyaman shiba ta kowace siga_*


*JIGWAN LABARIN*_:Akan mahaifin da yayi *MUGUN FURUCI* Akan budurwar d'an shi inda kuma tsautsayi ya fada mashi, shikuma d'an yazama lauyan mahaifin yarinyar_.


*SADAUKARWA ga my friend DARMA*

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alฦ™alaminmu ฦดancinmu._* }}

https://www.facebook.com/103637491942644/

๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ *{{N W A}}* ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ


ุจูุณู’ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู…ู ุงู„ู„ู‘ู‡ู ุงู„ุฑู‘ูŽุญู’ู…ูŽู†ู ุงู„ุฑู‘ูŽุญููŠู’ู…



PAGE 21_25

Bala yace "lalle Alhaji Lukuman bakada sauki akan abinda kake so" Alhaji Lukuman yasha mur da fuska yace "Alhaji Bala saurareni nan! kagadai kaikade kasan sirrina to Dan Allah kada naji kada nagani please! "
Baki Alhaji Bala ya washe yace "bakada matsala dani kai kasani, to amma miye kasona aciki?"
Alhaji Lukuman yace "kada kadamu da wannan yanzu dai zaka iya tafiya ni zan karasa cike wasu takardu nan".
"Ok" abinda Alhaji bala yace kenan yabar office din.

To bangaran Alhaji Muhammad duk ya bar rarrashin Habeeb tunda yace yarabu da son Salma Amma shi yanace ita yake so shiyasa yanzu ya daina kulashi ya maida hankalinshi a kan aiyikan da suka sha mashi kai ga siyasa ta taho babban abinda ya kara bashi tsoro shine yana zaune a office wasu yan daban yara suka shigo sukayi mashi gargadin ya hanzarta janye kudurinshi nasan kujerar chairman in bahaka ba zasu kawar dashi daga doron duniya, shikuma yanuna masu Sam baya tsoronsu nan suka kira waya suka fad'i yanda sukayi dashi kana sai suka fita d'aya daga cikin su haryana fadin Allah ya tai makeka da yanzu lahira tayi bako.
To irere ireren wa innan abubuwan sune suka daukema Alhaji Muhammad hankali daga Habeeb.

Shima dai Habeeb momynshi ta lallabashi harya koma aiki

Bayan sati daya

Zaune suke Hajiya Mariya ta dafe 'kirji tace gaskiya Alhaji banyarda ba wlh saidai kasami wata hanya badai wannan ba" Alhaji Lukuman yace "kinga saurara mana Mariya nagadai Yarinyar nan bake ce kika haifeta ba ko? Kana kuma duk abinda taci ta sha tasa nine nabata ko? To Dan haka bakida hurumin da zaki hanani iko da ita".

Hajiya Mariya tace "naji koma mizaka fada to Amma aini naci kashinta da fitsarinta ko? Kuma nice na kula da tarbiyyarta da kake maganar banice na haifeta ba".


Ganin Hajiya Mariya ta inda take shiga batanan take fitaba sai ya kwantar da murya kuma a zuciyar shi yana nadamar shigo da ita cikin shirinshi, shi 'kwalwarsama ta dode a lokacin da yake sanar da ita.
Cewa yayi "haba my love Mariya kinsan ko wace magana zan fada maki kinsan saida nayi tunani a kanta kana Salma dai matsayin 'ya take a gareki Amma inasan kisani ko itace ta samu wannan damar zata iya rabuwa damu".

Da "kyardai Alhaji Lukuman yashawo kan Hajiya Mariya tare da alkawarin kudi masu tsoka to dayake idonta idon kudi ai tuni ta amince da bukatar shi.

Amma kuma gefen zuciyar ta na jimamin rabuwa da Salma don ita ko kad'an batajin ba ita ta haifeta ba.
A daran yasami Salma yake fada mata gobe in Allah yakaimu ta shirya zataje g.r.a wajan takwas zai aiketa itada driver.

To gidan Alhaji Muhammad shima yasamu kira daga wani abokin su yasheda mashi gobe sunada meeting wajan takwas a nan g.r.a batare da bata lokaci ba yace "Allah ya kaimu Lfy"

Washe gari

7:30 sauri kawai Alhaji Muhammad yake Dan yakusa makara
Hajiya Fadeela tanata taimaka mashi wajan ganin ya kammala shirin ko break fast baiyi nakirki ba ya tafi Isah driver yajashi suka dauki hanya.

Salma ce ta shid'o daga kan matattakalar bene taji shashshekar kukan mom dinta da sauri ta je gabanta tace "subuhanallahi mom miyafaru kike kuka?" Hajiya Mariya ta dago idanuwanta jawur tace "please Salma Dan Allah ki yafeman wlh bada niyata hakan zata faruba".

Ainan Salma ta rud'e itama sai hawaye ya wanke mata fuska tace "mom mikika yiman? Ni wlh koma minene nayafe maki Dan Allah kidaina kuka please mom".

Rungumaita Hajiya Mariya tayi tana "nidai kiya feman kiya feman Dan Allah Salma!"
suna cikin wannan yanayin Alhaji Lukuman ya sauko 'kasa ya gansu haka nan ya had'e fuska cikin wata mummunar murya yace "Mariya!!!"
A firgice ta dako kai yace "miye haka kike shirin aika tawa? Ke Salma tashi ki tafi lokaci na kurewa tun dazu ya kirani yana wajan yana jiranki".

Tashi Salma tayi tashare hawayenta ta fita mota tashiga driver yajata sukabar harabar gidan.

Kallan Hajiya Mariya yayi yace " waiku miyasa 'kwalwar kifaye gare Ku? Yanzu Mariya duk yanda mukayi dake sai kin rusaman shiri? Nibanma San gigin dayakaini harna sanar dake abinda na shiryaba wlh".

Itama Hajiya Mariya cikin daga murya tace 'wlh Kaine mai 'kwalwar kifi in baccin rashin imani Salma zakasa a kashe? To wlh nima nayi nadamar haduwa da kai a rayuwata Lukuman ".

Jin irin maganganun

3 / 7