Advertisements
Chapter 11 Reading Hauwa Kulu Book 4 Complete Hausa Novel Hausa Novels
Advertisements

Hauwa Kulu Book 4 Complete Hausa Novel

Author :  Takori Category :  Complete Novels

Chapter   11 / 12

30K to 33K   out of 34.5K words

kawai sai taji wani mugun amai ya yunkuro mata.
Ta tsugunne a wurin tana kakari amma aman yaki fita kamar zuciyarta zata fito ta bakinta ga goyon Safiyya a bayanta. Da sauri Sarham ya bar maganar da suke yi da Madinah a falo ya karso kitchen din, ?kai kakarin me nake ji haka?? Dai dai lokacin ta samu aman kore fatau dashi ya biyo makogaronta don azumi take na alhamis bata ci komai ba shirin buda baki suke yi. Da sauri ya sauri ya ida gareta ya daga bayan ta yana shafawa har ta samu ta amayar da komai dake cikin hanjinta. Madina ta gifta zata wuce dakin ta kallo daya ta yi mata tasan ciki ne da ita ana mata amai a kitchen ta wuce daki cikin gigicewa.
Ita kuma Hauwa haka take da Haihuwa cikin lalura Allah mai girma!
Ya kamo Hauwa zuwa dakinta yace Mardhiyya ta gyara wurin. Suna shiga ya soma checking dinta har fitsari tayi ya saka masa PT strip. Wata wawuyar runguma da Sarham yayiwa Hauwa saida ya kayar da ita a saman gadon aurensu. Tana tambayarsa cikin tsoro da fargaba ko meye yakewa murna haka? Kuma me sakamako PT strip ya nuna? Amma bai saurareta ba sai sukuwa yake cikin rawa da waka yana narkewa cikin jikin Hauwa;
 Gimbiyar mata kike a zuciyata HAUWA?.
Da za?a bani biro na baki maki HAUWA?
To zaki haura lambar da za?a baki HAUWA?.
In za?a tara mata wa zata fi ki HAUWA?.
To addu?a nake... Allah ya taimakeki HAUWA?.
**** ***** *****
Aikin da ba?a yiwa Hauwa ba enan a wannan shekarar amma dai tayi borin zuwa makaranta duk da haka. Bayan ta ci kukanta ta gode Allah na gwarne da take ganin wahala ne. Shima kuma da yake lallabata yake ya yarda ta fara zuwa DAAR AL HEKMAH UNIVERSITY a wannan shekarar duk da yaron cikin, ya kuma dauki alhakin kaita lacca da daukota da kansa kullum.
Haka Hauwa-Kulu ta soma karatunta karkashin BLaw (Bachelor of Law) wanda zai dauketa tsayin shekaru hudu a jami?ar ?Daar Al Hekmah, Jeddah, KSA?.
Cikin Hauwa wata takwas ta haifi ?yarta ta uku a duniya wadda ta rokiSarham Allah da Annabi ya saka mata sunan aminiyarta Sumayyah.
Sumayyah wadda har lokacin ake ake kai ruwa rana akan maganar aurenta, don Hajja Ramlah ma tabi bayan su Madinah tace ya nemo wata, bata ga dalilin sai wadda ke kin ?yar uwarsa zaice zai aura ba. Baban su kuwa wato Ahaji Attahiru tun karin auren Sarham dama basa ga maciji shi da Sarham don yaji ciwon abinda yace masa a asibiti lokacin da za?a yiwa Madina tiyata. Don haka ma da yaji wai kanwar Sarham ce Usman yake so bai saka baki ba kuma bai yi adawa ba ya dai ce sai abinda suka shawarta shi da ?yar uwarsa.
Shikuma Usman ya dage baiga dalilin da za?a ce Madinah ce zata yi masa deciding matar da zai aura ba tunda gaba yake da ita. Don haka ya kai karar Madinah gun Kakar su Haj Laila kan tana bata masa zancen aure ta karkashin kasa a gurin iyayensu. Haj Laila sai kawai ta tada waliyyai suka tafi gun Abba suka kai kudin aure, Abba bai karba ba yace sai yayi magana da Sarham tukunnah tunda shi yasan Usman fiyeda kowa.
A karshe dai Kakar saida ta tafi har Jeddah ta samu Alh. Attahiru ta gyara komai tsakaninsa da Sarham, tace ita bata ga dalili ba da don suna son autar su Madinah zasu ce baza?a yiwa Madina kishiya ba tunda ba alkawari sukayi a rubuce ba na cewa daga kanta Sarham ba zai kara aure ba, kuma wulakantata yake yi ba sannan polygamy al?adar mutanen Kano ce. Itama da suk ganin ba?ayi mata ba harsuke reference da ita to bari ta gaya musu gaskiya Alkalin Alkalai ya so yi ita ke lalata zancen duk inda yaje neman aure har ya gaji bari, tace tayi nadama lokacin da ?ya?yanta mata biyu suka ki auruwa har bayan digiri na uku suna gabanta. Don haka su bar Usman ya auri wadda yake so ?yar gidan mutunci wato gidansu Sarham su bi su da addu?a. su daina biyewa kishin Madinah sauda dama tana gyara gidanta ne shi Usman ta saka shi a matsala don ta san suna matukar sonta.
Da waannan Haj Laila ta gyara zancen auren Sumayya da Usman. A wata asabar, a masallacin jumaa na tsohuwar jami?ar Bayero aka daura auren SUMAYYAH SHANONO da USMAN SORONDINKI. Kasancewar duk suna birnin Jeddah daga angon har amaryar kuma Sumayyah na tsakiyar karatu dole iyayen da kakannin ne sukayi yinin bikinsu sukadai. Sumayyah ta koma gidan Bhaiya dakin Hauwa acan aka shafa mata lalle dole Madinah ma ta saki ranta albarkarkacin Sarham da Usman da yae ta mata hidima don ta sa hannu a aurensa. Ita taje ta shirya musu kasaitaccen gidansu a Jeddah ta tsara komai dama dai Madinah ba daga nan ba. yayinda Hauwa k??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????e kula da yaranta da danyen jegonta da kawayen Sumayyah da ke cike a gidan kowa nata sha?awar yaran Hauwa da yadda take sabgar kula dasu musamman wajen breast- feeding. Sarham dole ya daga kafa a gidansa sabida hidimar da akeyi kuma shi Abba Prof. ya turowa kudi ya hada da abinda ya tara musamman don auren Sumayyah ya baiwa Madinah ta zabar mata kayan daki daidai karfinsu. Duk da cewa Usman yace baya bukatar komai amma saida suka yi wanda zasu iya kasancewar Usman yana ISDB ne tareda Babansu.
Watan Hauwa uku kenan da haihuwar Sumayyah yarinyar tayi bul-bul gwanin sha?awa haka kamanninta da Sumayyah yayi yawa, a lokacin Hauwa na shekararta ta biyu a (BLaw) Sarham ya gama duk wasu shirye-shiryensa na yiwa Hauwa aikin ido. Ya saka ranar Litinin 5/5 a matayin ranar da zai shiga da Hauwa tiyata, ya kuma kira waya ya gayawa gida, nasa iyayen dana Hauwa, sannan ya gaya musu itada Madinah.
Ya roki Madinah wata alfarma data sanyaya mata jiki.
?Na san a policy dinki Munawwarah, babu taimakawa ?kishiya?, amma ina rokon ki ki taya Mardhiyyah kularmin da ?ya?ya na, har Allah yasa ayi aikinnan na mahaifiyarsu lafiya a gama, kuma idan Waheedah ta shiga wajen su ki daina cewa Mardiyyah ta daina goya mata su bazata iya daukar su ba sabida girman jikinsu, in ma ta tika su da kasa babu ruwanki ?yan uwanta ne, kinji ni ko??.
Mama dama tayi shirin zuwa Umrah a wannan shekarar kasancewar watan Ramadhan ya kama. Don haka ta hau shiri don tuni ta samu visar Umrah. So take ta isa Jeddah kafin ranar da za?a yiwa Hauwa aikin.
Dr. Madinah ta kai gwauro ta kai mari ana I gobe za?a yiwa Hauwa aikin idanunta, tana fafatawa da zuciyarta da kuma shaidan, a karshe ta rinjayi shaidan din, da taimakon Ubangiji.
Ta fuskanci maigidanta Dr. Sarham da ke fitowa daga toilet cikin fararen kayan barci, ya yi wanka ruwa na yarari daga kansa yana yarfewa da santala-satalan hannayensa.
 Babansu Waheedah, please ina so ka bani dama in shiga cikin  team din ku, wato likitocin da za su yi wa Hauwa aiki gobe. Albarkacin musulunci. Ina so a yi wannan aikin ladan da ni. I mean it?.
Hawaye ya digo daga kwayar idonta. Ta tuno tarin rashin kyautawarta garesu shida Hauwa, da tarin gorinta ga nakasar Hauwa, yau ga HAUWA-KULU-MISKINIYA-MUSAKA ta cikawa SARHAMU da gayu gida da ?ya?ya, don ita ta fahimci abinda su duka hankalinsu ma bai kai ba, a matsayin ta na mace kuma cikakkar likita cewa Hauwa-Kulu wani cikin ne da ita, tana boyewa Sarham wannan karon kada ya kara fasa yi mata aiki. Duk abin da zai dawo mata da Sarham dinta na baya (very jovial) domin ya dan canza mata tun dawowarta gidan, saboda yadda take ja baya da duk wata harka ta iyalinsa, tana so ta dawo dashi yadda yake a baya kuma mai yarda da ita, don haka duk abinda tasan zai faranta masa shi ta ke son yi yanzu. Duk da ta san ba?a bari a kwashe daidai.
Ya kama hannunta suka zauna tare a bakin gadonta, ya ce,
?Ni na dade da sanin Madinah-Munawwarahta mai kirki ce, mai imani ce kuma mai tsoron Allah ce. KISHI ne mara amfani yake sarrafa min ita a baya.
Ina rokon Allah ya albarkace mu bakidaya ni da ku iyalina, ya hadamin kan ?ya?yana ko bayan raina.
Ni na san ba za ki iya alaka ta jiki da Hauwa?u ba, sabida kina mata kallon tasgaro ga soyayyarmu, kuma  barrier ga cikar farin cikinki, wanda ko daya in kin duba ba haka ba ne.
Ki sa a ranki aurena da Maijiddah rubutaccen al?amari ne daga Allah (S.W.T) wanda ni ma ban taba hasashensa ba, sannan ba gazawarki ce ta wani bangare tasa na yi shi ba.
Haka nake so duk mata irinki su saka a ransu, sai a samu zaman lafiya da fahimtar juna tsakaninsu da mazajensu.
Komai Ubangiji ya nufeka da yi, ko Ya rubuta yana cikin kaddararka, hakika sai ya same ka. Addu?a ba ta canza kaddara amma tana rage tasirinta.
Don haka ban auri Hauwa ba sai da na yi addu?a da istikhara cewa, idan ba alkhairi bace a gare mu, ni da ke kada Allah ya ba ni ikon aurenta.
Madinah ki yarda ba ki gaza da ni ta kowanne bangare ba, sannan rashin gazawar taki baya nufin shikenan bani da hurumin auren kowa kuma. Hudu Allah ya halattamin. Bayan Hauwa ma Allah Ubangiji ya halatta min wasu biyun sai in ban yi ra?ayi ba, ko ba sa cikin kaddara ta.
Allah Ubangiji ya yi umarnin a kyautata wa MISKINI da MARAYA a cikinAl?qur?ani, wannan rubutacciyar ayar Ubangiji ce.
Don haka kyautatawarki ga Hauwa ko akasinta yana cikin mizanin ayyukanki na alkhairi da na sharri. Na gode da kika fara karkata mizanin don ya koma na alkhairi .
Madina ta yi maza ta rungume shi tana kuka, ta ce, ?Wallahi daga yau na tuba da duk abin da nake yi a kanta. Ka bani dama in shiga cikin likitocinta in yi  repenting kuskurena ko Allah Ya dube ni ya yafe mini.
Amma ka sani KISHI da kishinka Sarham wani abu ne da har abada ba zan daina ba, saboda ba ni nake sawa raina ba, halitta ne. Alkawari daya iya yi maka shine; zan koyi rike linzaminsa& in dinga controlling dinsa ta hanya mai kyau?.
?In ki ka yi hakan, ni kuma na daga miki kafa, ki shige aljanna ba ja?in?ja Madinah?.
?Ya subhanallahi?. In ji Madina tana kara kanainayewa a jikinsa.
?Amma wani hanzari ba gudu ba, bana bukatar taimakon kowanne likita a aikin da zan yi wa Hauwa, ni kadai nayi nazarina kuma nikadai na gano kan matsalar, don haka nikadai zan yi in kika cire (perioperatives) dina da masu allurar tafi da ranka (anaesthethians). It?s a ONE MAN JOB!!!
**** **** ****

ASIBITIN SAUDI-GERMAN
RANAR AIKIN IDON HAUWA-KULU
(KARO NA BIYU)
Dr. Sarham, da sauran masu taimaka maa a yayin tiyata sun zama ready a dakin tiyatar da za?a yiwa Hauwa aikin ido, haka masu allurar anaesthesia. Dr. Madinah Attahiru, ta turo ?yar uwarta Hauwa Bilyaminu a kan gadon marassa lafiya tana sanye da korayen kayan aiki na wanda za?a yiwa tiyata, haka shima likitan korayen kayanne a jikinsa da hularsu. Bisa umarnin likita Sarham, masu allurar tafi da ranka suka fara, daga nan suka shiga aikinsu ba ka jin tashin komai sai tashin yaren likitanci a yayin surgery na idanu. Kalmomin da su kadai suka san me suke nufi da fadarsu. Da yake sun dade da gano matsalar Hauwa-Kulu tuntuni sun kuma dade da tsara komai daga binciken da suka dade suna gudanarwa akan idon Hauwa nada nan aka gama phacoemulsification surgery din, cikin abinda baifi mintuna 45 ba.
Ana fatan kwancewa nan da awanni biyu masu zuwa. Zukatan su Mama, Madinah, Sumayyah, Usman, da Mardhiyyah dake gefe goye da baby Sumayyah, ga  yan biyu suma a hannunta na hagu da dama tana lallashinsu kamar su fita daga cikin kirazansu with so much high anticipation.
**** **** ****

KOFAR DAN?AGUNDI (KANO)
C
ikin rikicewa da tsananin tashin hankali yake ta trying kiran wayar Dalha ana cewa bata shiga, sai ya koma kiran dansa Jamilu cikin hada uban gumi. Baba zakari kenan cikin gigicewar rasa Dalha babban yaronsa daya tattarawa dukkan jarinsa ya tafi Cotonou domin shigo da atamfofi. Ba wannan ne karo na farko da suka fara wannan sana?ar shida Dalha ba sun fara da yi kadan kadan ne har Dalha ya tabbatar Zakari ya gama amincewa da shi kafin yace suyi babban sari na atamfofi da shaddoji kasancewar karamar sallah ta matso.
Amma yau kwana goma sha biyar ya kasa samun layin Dalha wato tun tafiyarsa. Da ya kasa samun Dalha sai ya koma kiran Jamilu, Jamilu ya daga ya tabbatar masa motarsu Dalha ta kife a bisa binciken da yasa aka yi masa kuma ba abinda ya tsira a motar, kamar yadda babu wata rai data tsira.
Tsananin gigicewa (bata mutuwar dalha daya shekara kusan 10 yana wahalta masa ba, a?ah ta kafatanin dukiyarsa da ya tattatara ya damka masa ya tafi da ita ne) tasa ya kama hanyar Singa a kafa, yana tafe yana sambatu, duk nisan kofar Dan?agundi zuwa kasuwar Singa bai ganshi ba, saboda tashin hankali.
Bai yarda da abin da Jamilu ya fada ba shi ya sa ya taka sayyadarsa har Singa, don ya san yana zuwa zai ga Dalha a shago yana fama da kwastomomi yadda suka saba kullum.
Tun daga nesa yake hango hayakin dake tashi kamar bakin hadari a kasuwar SINGA. Ya kara daga kafa yana fadi a ransa lallai damuna ta zo ba shiri a watan da ba nata ba. irin wannan hadari haka?
Yana kara matsowa yaga dafifin mutane suna darawa ?yan kwana-kwana suna wucewa da motar su bayan already wutar tagama cinye rabon sa, ciki har da sashen ?yan atamfa. A kusa da shi yaji daya daga cikin yaransa yaa gaya masa.
 Baba Zakari sai hakuri. Haruna ne jiya da yamma ya jona heater a shagonmu, sai ya manta ya tafi gida, kuma a kofin roba ya jona, shi ne heater ta cinye kofin ta kama shagon da wuta .
Abinka da wutar dare, ko kafin masu gadin kasuwar su ankara wutar ta lashe shagon Alh. Zakari mai atamfa har ta soma laso makwabtansa.
Baba Zakari sai kwasar shi akayi a wheel-barrow zuwa gida saboda sumewa yayi a wurin aka tattakeshi a wurin ba?a sani ba sabida dafifin al?umma da kokarinsu na kashe wutar shikuma sai kara kutsawa yake yi har karfin sa ya kare jininsa ya hau, ya fadi a wurin ba?a kula ba aka yi ta bi ta kansa ana tuntube ana wucewa saida wasu suka daga shi da kyar suka saka a wheel-barror yaran da suka san shi a kasuwar suka tura shi zuwa gidan sa a dan agundi.
**** **** ****

Tundai da suka fahimci ya tsiyace yau kafin sati ya zagayo nbiyu daga cikinmatan da ya auro zawarawa masu kuruciya suka kama gabansu don tunda ya fadi yake jinya har inda nan ke motsi. Biyu sun zauna sabida yaran su da rashin muhalli wato Zainaba da Alto, don ko da yake cikin daularsa aai su baya tsinana musu komai su suke ci da kansu da yaran nasu ta hanyar ?yan sana?o?in cikin gida.
Jamilu ne kadai yake jigilar kai Baabn nashi asibiti amma duk sauran yaran sun fantsama cikin ganuwa suna sana?ar daba, wasu sane wasu kwace, matan kuwa sai addu?a don sun ki zaman aure sun dabbi maza a unguwar dan agundi.
Abinci wannan babu a gidan Zakari don matan in sun dafa basa bashi, sunce sanda yana da shi su ya basu? ?ya?yana kuwa babu mai lokacinsa. Kashi da fitsari duk akan gadon sa yake yin abinsa don faduwar da yayi ta sabbaba masa lalurar  stroke .
Jamilu dake tsaye a kansa ma?aikacin banki ne da in ya tafi aiki kullum sai kusan dare yake dawowa, nan zai shiga hidimar gyarawa uban jiki da wani yaron makwabtansu da yake biya yana kula dashi in baya nan.
Da Jamilu yaga abin ya kazanta sai ya dauke shi ya mayar asibitin murtala ake kula da shi a bangaren ?physiotheraphy?.
Da jimawa can Salele ya gaya masa Hauwa tayi aure da Likita Sarham suna kasar Saudi Arabia.
Sannan bada jimawa ba sun kara haduwa yake gaya masa Malam Bilyaminu da Inna sundawo gidan su na Badala.
Haka kawai jikin sa ke gaya masa ciwon mahaifinsa bana tashi bane don haka akwai bukatar ya hada shi da dan uwansa ya nema masa gafara a wurin sa don da karkataccen bakin sa ya gaya masa shi ya kori Bilyaminu daga Kano don ya cinye gonar gadonsu shikadai.
Haka ya gaya masa shi ya rushe gidan su bayan ya saya biya shi kudin a gaban shaidu da mai unguwa.
Ba don kuma komai ya rushe gidan ba sai don kada shi Jamilu ya auri Hauwa itama kuma Innar da Hauwan su rasa matsuguni.
Da Jamilu ya tambayeshi cikin takaici ko meye dalinlinsa na yin duk wannan ta?asar a ma tsayinsa na musulmi gad an uwansa na jini? Cewa yayi saboda tun suna yara ya lura Bilyaminu ya fishi tauraruwa mai haske ya kuma fishi kashin arziki, duk abinda ya sakawa hannu sai yayi albarka, sannan ana yawan cewa ya fishi kyau a duk inda suka shiga tare.
Jamilu kuka riris ya rika yi saida

11 / 12