Advertisements
Chapter 4 Reading Hauwa Kulu Book 4 Complete Hausa Novel Hausa Novels
Advertisements

Hauwa Kulu Book 4 Complete Hausa Novel

Author :  Takori Category :  Complete Novels

Chapter   4 / 12

9K to 12K   out of 34.5K words

yake ji a halin yanzu akan kowacce mace kafin yau ba. don ya san in soyayya tana kisa a yau zata kasheshi ne kowa ya huta Mama ta huta Hauwanma ta huta Madinar ma ta rasa?

Al?amarin da ya tsoratar da Hauwa don ta dauka Sarham suma yayi, amma jin yana gab da samun abinda yake hari da zafin da taji ya ankarar da ita abin da ke shirin faruwa a lokacin.
Janyewa ta soma yi cikin kokarin dawowa hayyacinta, Sarham kuwa a wannan lokacin ba ka jin komai a bakinsa sai  janye kalamansa na baya , wani ma in ka ji sai ya ba ka dariya ya ce, ?Na ce miki I am not your brother, I?m your loving husband, ki barni in nuna miki hakan yanzunnan, na rantse na fi ki shiga wahala a shekara dayan nan, ba mantawa na yi da ke ba, tunanin hanyar da zan nema miki lafiya nake yi?.
Hauwa ta rikice da kuka da razanar al?amarin da ke shirin faruwa da ita. Ta ce,
?Don Allah Yaya Doctor ka bar ni in koma wa Mama lafiya wallahi wani abu ya same ni za ta gane. Ni ban taba yin wannan rashin kunyar ba. Ka rufa min asiri yadda Allah ya rufa maka?.
Jikinsa ya yi mugun sanyi ganin tana neman shidewa don kuka da razana. Ya kifa kai a kan kirjinta ya yi shiru, kuzarin jikinsa ya ragu, ya daina duk abin da yake yi. Ya soma maida mata sitturun jikinta.
Ya kama hannunta ya dago ta ya dora ta bisa cinyoyinsa, fuskarsa a saman kafadunta ya sumbaci dogon wuyanta a hankali ya ce,
?Does this make a difference? Daga yau za ki daina ce min Yaya Doctor??
Hauwa kamar ta ce kasar wajen ta tsage ta shige haka ta sa tafuka tana rufe fuska, shi kuwa ya kara rungume ta tsaf a jikinsa.
Sun dauki lokaci a haka, ba ka jin komai sai bugun zuciyoyinsu a kirjin junansu.

Karar wayarsa ce ta dawo dasu daga wata duniya mai ban mamaki da suka samu kawunansu cikin abinda bai gaza mintuna talatin ba. Yana dubawa ya ga Abba ke kira.
Kasa dagawa yayi, sai ga kiran Mama ita ma. Itama bai daga ba ya sauke Hauwa daga jikinsa bayan ya sumbaci kirjinta son ransa, ya kuma sake fidda su a hayyacinsu. Karar kiran wayar akai-akai duk ya dagawa Hauwa hankali, amma shi ko a jikinsa. Da kyar da lallashi da kalaman yarda da daukar alkawarin cewa,
?Ni Hauwa na yarda Yaya Doctor ba Yayana ba ne, mijina ne na sunnah, kuma na janye kalmar a SAKE NI!?.
Sarham ya kyale Hauwa yana murmushi da godiyar Ubangiji a fili, ya ce,
?Saura mu je gaban Mama ki canza magana, wallahi sai kin san sauran, don a gidanta za?a yi komai kuma a dakin ?yar ta, don wallahi na gaji da bata hakuri, inyaso in ta ganki da ciki a gabanta ta janye kalmar saki, ta yarda auren Sarham da Hauwa;
?Mutu ka raba ne?.?.
Hauwa ta ce cikin dimuwa da tsoron wai zai iya irin wannan a dakin Sumayyah a gidan Mama, da sauri tace ?Na yarda, wallahi in ta ce ko inaso a yi saki? Zan ce a?ah?.
Shi har dariya Hauwa ta ba shi, ya dara sosai yana bubbuga bayanta, domin ba karamin tsorata da al?amarinsa ta yi ba.
Ko break fast din da ya sayo musu ba ta yarda ta ci ko loma daya ba, shi kuwa sai da ya ci abinsa cikin kwanciyar hankali kamar bashi ake ta kira a waya ba, sannan ya yarda suka fito.
Suna shiga mota ya yi reverse ya hau kan titi, sai a lokacin Hauwa ta ji wani irin kukan kunyar Mama ya zo mata.
Ta rasa da wace fuska za ta je wa Mama yau? Gani ta ke duk abin da suka yi din nan da Yaya Doctor is written on her forehead (a rubuce yake a kan goshinta). Sarham tuki yake yau wani irin tuki cikin nishadi. Kamar tayar motarsa ta samu matsala, ya dora hannunsa bisa nata, ya ce,
?Cry more! It?s all in LOVE! Wani kukan ma yarinya sai an je Jeddah?.

Hauwa ta ce, cikin kuka ?Ni kam na shiga uku yau, Yaya Doctor ka jawo min nayi rashin kunya nayi rashin gaskiya na yi butulci, za ka jawo Mama ta daina tattalina, ka shiga tsakanin Uwa da ?yar ta?.

?My dear Jeddah, in ta daina tattalinki, ni zan yi kin ji??

Da sauri tace ?wallahi ba irin nata ba, dame zaka yi tattalin nawa? In dai irin wannan tattalin na rashin kunya ne wallahi ni na yafe?. Dariya kamar ta kashe Sarham ya kara manne hannunsa cikin taushin fatar hannunta.
Suna isowa gidan dankam da ?yan daurin aure don nan ne meeting point inda daga nan za?a wuce Kofar Gadon kaya, sabida an cika kofar gidan su ba hanya sai ta kofar kitchen suka zaga ya bi da Hauwa zuwa cikin gidan, nan ya hadu da Nancy a hanya ya damka mata ita, ya ce ta kai ta dakinta. Sannan ya ce,
?To Maijidda sai na zo zancen dare?.
Ta yi saurin daga kafa tana gode Allah da Nancy ba ta jin Hausa. Kuma da ita suka fara haduwa
Jama?a kam sun dauke hankalin Mama, don haka har suka kai dakin Hauwa Mama tana falonta da kawayenta ?yan chamber dinsu, sau biyu tana shiga neman Hauwa, Mardiyyah na cewa tana wanka. Har a shigowa ta biyu Mama tace ?to wannan wankan na sake fata ne kenan??
Aka yi daurin auren Surayyah aka zarce da reception a  Ni?ima Guest Palace?, so sai ya zamanto har dare gidan ana kai kawo Mama uwar amarya kanta ya dinke da hidimar bakin da suka gayyato daga bangarenta dana Abba Prof. da suka zo daga Shanono.
Mardiyyah ce ta je ta karbo musu abinci, sai Mama ta ce mata ta je ta zo da Antinta ta gaida su Barr. Hannatu.
Hauwa ta sauke wata wahalalliyar ajiyar zuciyar hayewa tudun muntsira, bayan ta ji ta kwance a kan gadon dakinta ba tareda Mama ta san dawowarta ba, sannan ta biyo Mardiyyah suka fito.
Falon cike yake kuma duk manyan lauyoyi mata ne kawayen Mama.
Mama ta ce, ?Hauwa, yau wane irin wanka ki ke tun dazu kamar mai wankan jego? Shigata biyu ana cewa baki fito ba .
Cikin in-ina ta ce,
?Yi?yi hakuri Mama?.
Mama ta kada kai, ta ce, ?Kawayena ne na ce ki zo ku gaisa?.
Suna ta kallon Hauwa da mamaki ban da Barr. Hannatu, tunda ita ba yau ta san Hauwa ba. Hauwa ta tsugunna tana gaishe su cikin ladabi ba tare da ta kalli sashen da kowacce ta ke ba. wannan ya tabbatar musu da cewa surukar Maishari?ah din bata gani.

Barr. Shafa?atu ta kasa shiru, ta ce,
?Ita ce second wife din Sarham da aka ce ba ta gani ko??
Barr. Habiba ta ce, ?So beautiful masha Allah, and so pathetic!?.
Mama ta san halin ?yan kayanta, tuni Hauwa har ta fara kumburowa, ta ce da Mardhiyyah, ?Mardiyyah maza ku je falo cikin ?yan Shanono, ku daina kulewa a daki ku kadai bayan ga ?yan uwa duk sun zo, ki kai ta ta gaida kowa ki gabatar da ita kinji kafin nazo??.
Suna fita ta kama hanyar komawa daki wato bazata gun ?yan Shanonon ba. Mardiyyah ta ga Antinta na share hawaye. Yau an tabo ta, tunda an mata gorin ido. Cikin ikon Allah suna shiga dakin Sarham na shigowa. Ta kifa kai a jikin gado tana rusa kuka.
Ba karamin kaduwa yayi ba ya iso gareta da sauri, ya manta da Mardhiyyah a wajen yayi maza ya rungumota barin jikinsa na dama.
?Mardiyya lafiya? Me aka yi mata? Ko kin fadawa Mama mun fita ne?? Ya tambaya a dan rikice da damuwa.
Mardiyyah ta ce, ?Yaya Likita ba abinda aka yi mata, Mama kawai ta ce in raka ta ta gaida ?yan Shanono, kada ka dada kada ka rage shikenan fa!?.
Hauwa ta dago ido tana hararar inda Mardiyya ta ke tsaye, ta ce, ?yi min shiru. Ba a kunnenki aka yi min GORIN IDO ba? Har tana ce mun abun tausayi, wani so pathetic??
Sarham ya zauna a gefen gadon yana hadiye dariya ce, ?nagode, je ki abinki Mardiyyah?.
Ita dai bata ga abin kuka ba tunda ba da tozarci suka fada ba. Dukkansu manya ne. haka Mardhiyyah ta sa kai ta fita tana ?yar dariyar shagwabar Antin nata.
Ya sake kankameta yace, ?Kin ga Mardiyya ma dariya ta ke miki?.
?Eh, da yake ba ita aka cewa ?MAKAUNIYA? ba?.
?To karya suke? Ina idon yake??

Ai kuwa Hauwa ta balle da sabon kuka riri-ririiiiii.
Sarham ya sa hannu a kwibinta yana mata cakulkuli, ta zame da mugun zafin nama.
?Tashi ka fita, kafin a ce maka mijin makauniya kaima?.
Sarham ya lumshe ido ya nuna kansa da dan alinsa kamar Hauwa na ganinsa, ya ce, ?Sai in ba su amsa da ?ni na makantar da matar tawa saboda rashin iya aiki na, daga cire hakiya?. Ya kara rungumo ta ya manne bakinsu wuri guda yana sumbata hungrily, ta haka ya hana sautin kukan fitowa.

?Ya salamu sallim, Ya jamilal Munzar (Ya mafi kyawun masu gani)?.

In ji Mama Maishari?ah da ta sawo kai dakin da zummar bai wa Hauwa hakuri, donta san an mata abinda ba ta so. An mata GORIN IDO (ta bakinta).
Da sauri Mama ta koma da baya har tana tuntube da dokin kofa. Dukkansu kuma ba wanda ya san da shigowarta, Hauwa ce ta yi maza ta janye tana fadin,
?Hasbunallah! Motsi nake ji. Tare da dafe goshinta don tabbas taji motsin mutum a kofa.
Sarham ya yi murmushi idanunsa a lumshe, ya ce, ?Yarinya tun ba a je ko ina ba ta fara sanin dadin kiss din miji?.
Hauwa sai ta dau filo ta rufe ido da shi tana fadin, ?Ni wallahi ba ruwana, ni ban san wannan abin ba, duk kai ka koya min yau kuma sai Allah ya saka mini in wani ne yazo ya gani, ai kasan gidan cike yake mutane, ni bana so ma ka daina dakin nan don Allah, kuma ba zan kara binka ko?ina ba?.
Har ya kai bakin kofa ya juyo. Ya kanne mata ido kamar tana kallonsa. Cikin kankanuwar murya yace.
?This is light kiss, ki shirya  hot kiss later tonight!?.
Hauwa ta danna kai cikin cinyoyinta tana rokon Allah ya sa kasar ta tsage ta shige yau ta huta.
Mama tana kallon wucewarsa zuwa dakinsa ta baro jama?a ta dawo dakin Hauwa. Gaba daya dakin Hauwan yanzu kamshin Sandalia ko Oud-Abyad din Sarham yake yi, wato turarukansa na dindindin (Non-alcoholic Arab perfumes).

?Hauwa?u!?
In ji Mama tun daga bakin kofa.
?Ashe ni tufka nake kina min warwara??
Hauwa ta kidime iyaka, ta fara mazari na rashin gaskiya murararn. Kada dai motsin data ji Mama ce? Yau da ta kade har ganyenta.
Mama ta ce cikin takaici,
?Ban taba ganin sakarar mace irinki ba, kai jama?a, Allah wadaran rashin wayo?.
Sai Hauwa ta soma hawaye nan take kamar an balle famfo. Fadi ta ke,
?Wallahi Mama babu ruwana, sai da na ce masa ba zani ba??. Ta kifa kai a cinyoyinta tana rizgar kuka.
Mama ba ta san da zancen fita ba, rikicewa da rashin sabo da karya tasa Hauwa ta fallasa komai.
?Wallahi Mama ban yarda ba, bai yi komai ba? nan? nan? (ta nuna bakinta), kawai na bari, kuma shi ma din fin karfina ya yi?.
Mama takaici kamar ya kashe ta, ta mike tsaye tana cewa, ?Na kuwa daina tada hakarkarina a kan a sake ki, don ki auri mai sonki da gaskiya, tunda naga kina son abinki duk rashin kirkinsa, hada kayanki kafarki kafarsa, kafin a kara yi min abin da yafi karfin idona?.
Haba! Hauwa ta rushe da kuka tana, ?Na tuba Mama, na tuba na bi Allah na bi ki, wallahi ba inda zan iya zuwa in barki?.
Mama ta yi kwafa ta ce, ?ji min munafurcin Hauwa-Kulu, yau da kika sa kafa kika bishi kika barni ma na sani? Ni a wa? Bi mijinki a sha soyayya lafiya, da ma tare na ganku.
Na so ki bari mu wujijjiga shi yadda zai kara sanin darajarki, to kin kwashi jiki kin bi shi kun sha soyayya ko? Bayan ya kwashe shekara bai neme ki ba, da yake ke sakarya ce wadda ta rako mata, kiss din abun banza ne da ki ka barshi ya samu a arha??.
Hauwa kuka kawai ta ke na nadama da kaka-nikayi ta kasa magana, duk sai ta bai wa Mama tausayi.
Ta sassauta ta kama hannun Hauwa, ta ce, ?Ba ki yi min laifi ba Hauwa kin ji, kuma ba ki yi wa Ubangijinki ba.
Karewa ma lada ki ka samu kinji.
Ni na san Sarham yana sonki duk abin da nake yi kuma ina sane. So nake in sa shi ya gane da kansa yana sonki ba auren jihadi da taimako ya yi da ke ba. So nake ya furta min da bakinsa ya janye kalaman kanwar nan da yake jifanki da ita, It does hurts me a lot!
Karshen kaskancin da namiji zai miki kenan, ya tari gaban idon ki yace, ba ya miki so na soyayya. Sarham ba shi da saiti, ki bar ni in saita shi yadda ko wani ya ji ya ce ke kanwarsa ce zai musa da bakinsa yace ?a?ah matata ce abar so na?.
Hauwa na kuka da sharbe ta ce,
?Insha Allah Mama ba zan sake yarda ba?.
Tausayi ya kama Mama don kuru-kuru ga soyayyar lelen Abba nan ta fito yau a idonta, da ko gani ba sa yi, ina ga suna ganin cool kamanninsa da kyakkywan sajen sa da murmushinsa mai daukar hankalin mata?
Mama ta tashi ta fita kwallar tausayi fal idonta.
Mardiyya ta dawo dakin tana cewa,
?Anti ba ki ci abinci ba, Anti don Allah ki daina kuka yana daga min hankali?.

Ta hau share hawayen da gefen mayafi ta ce, ?Na daina Mardi!?.
Ta ce, ?To abincin fa??
?Sai an jima, ki kulle mu ta ciki, ko Yaya Doctor ne ya buga kada ki bude kin ji? Muraji?ar karatuna zan yi?.
Taje ta dauro alwalla, sai ta ga cewa ba za ta iya alwala a haka ba, dole sai ta yi wanka don abin da ba ta taba gani ba ne ta gani a tare da ita yau.
An gaya mata kuma da jimawa wankan iri daya ne da na sallah.
Ta yi sallah ta dora da nafila ta zauna tana muraji?ar karatun da Mama ta kara mata jiya.
Cikowar ?yan uwansu da abokan arziki a gidan ma bai barshi ya iya sake shigowa da daddaren ba balle ya tadda kofar tasu a kulle da mukulli bisa umarnin ko ya buga kada Mardiya ta bude.
Dangin mijin Surayyah suka ce su a wannan ssatin zasu dauki amarya zuwa Ikko don haka dole aka zarce da bikin maimakon sai sati mai zuwa da mama ta saka. Don haka a washegari aka yi wunin Surayya a Gadon Kaya, da daddare dinner sai shirin kai amarya gidan su Engnr. Aliyu a Dorayi washegarin ranar.
Hauwa ba ta je dinner ba ta kulle kanta a daki, amma Mardiyya ta je. Mama ta sameshi har dakinsa ta kora masa  warning din kada ya kara shiga dakin Hauwa sai ya zo mata da hukuncin da ya yanke wa zamansu.
Shi ma kuma yana ta nasa shirin duk don ya wanke ran Mama, ya kuma yi  repenting kuskurensa, tuni ya karbo passport din Hauwa ya kai gun visa.
?Yan biki duk sun watse bayan an kai Surayya family house din su mijinta. Yau kwana uku kenan Mama na gadin Hauwa, ta hana shi kebewa da ita. Ta hanashi rawar gaban hantsi. Iyakar tsaka mai wuya Sarham ya shige ta don sosai yake cikin bukatuwa da Hauwa, don haka ya maida hankali wajen sakin kudi a yi a gama visarta. Ga Abba ya ki shiga maganar, ya ce shi a bayan mai shari?a yake.

*** *** ***

MUTANEN JEDDAH

Sumayyah ce kadai zaune a falon gidan Yayanta tana karatu da gilashi a idanunta, aka danna kararrawar son shigowa, Sumayyah ta mike ta aje littafin da ke hannunta tana fadin, ?Na?am, ina zuwa?. A zatonta Madinah ce ta dawo daga unguwar data tafi.
Tana budewa suka yi tozali da wani sardidin saurayi son kowa. Amma kuma fuskarsa looks so familiar to her.
Ya yi mata murmushi, ya ce, ?Salam, how are you? Tana ciki ne matar gidan? Na kasa kama ta a waya .
Sumayyah ta kasa magana, don gayen ya kai makura wajen kyau, ga tsafta ga sanyin murya.
Da kyar ta iya cewa, ?Ba ta nan!?.
Sai ya mika mata wata leda ya ce, ?ok. Please ga shi ki bata, kice in ji Hajja Ramlah?.
Hannun Sumy na rawa ta karba sai ya ce, ?Ke bakuwa ce suka yi halan daga Nigeria??
?Eh?. Kawai ta ce.
Ya ce, ?Ok, toh. Ki gaya mata zan dawo bayan magriba. Sunana Usman Attahiru, yaya sunan malamar??
?Oh! Are you? Usman??
Ya ce, ?Yeah?.
?Anti na yawan zancenka, ina ji kullum. Nice meeting you?.
Ya ce, ?Na gode, kin san sakuwata ce. Kullum fada muke a baya, ina cin zalinta in more, shiyasa yanzu nake kyautata mata, na maida kaina ma direbanta at times, don in wanke kuruciya mara dadi da muka yi nida ita?.
Duk suka yi dariya mai sanyi.

Ya ce, ?Ya sunanki??

?Sumayyah Abbas?.

?Oh-oh! Ko ke ce Sumayyah kanwar Baban Waheedah??
?Eh ni ce?.
?By the way, nice to meet you too Sumayya, I love the name?.
Cikin murmushi Sumayya ta ce, ?Na gode Uncle Usman. A gaida gida?.
Bayan tafiyarsa Sumayyah ta adana sakon, amma sai ta kasa zaune ta kasa tsaye, Usman Sorondinki da muryarsa ya tsaya mata a rai farat daya, irin yadda wani namiji bai taba shiga ranta ba.
Madinah na dawowa Sumayyah ta bata lokaci ta kintsa, kafin ta kai mata sakon har dakinta, karonta na afarako da sanya kafarta a dakin Madinah tun zuwanta gidan. Ita kanta Madinah ta sha mamaki.
?Ya zo nan kadan kafin dawowarki, yace shi Yayanki ne, wai Osman sunansa?.
?Oh! Zai dawo an jima, mun yi waya na manta da zuwansa ne na fita?.
Sumayyah ta ci gaba da shiru a tsaye, ta kasa tafiya, Madinah ta ci gaba da sabgoginta

4 / 12