Advertisements
Chapter 5 Reading Hauwa Kulu Book 4 Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Hauwa Kulu Book 4 Complete Hausa Novel

Author :  Takori Category :  Complete Novels

Chapter   5 / 12

12K to 15K   out of 34.5K words

ta manta da ita. Ganin haka ta ja matattun kafafunta ta fito daga dakin.
Ko da ya dawo kamar yadda ya ce zai dawo, Sumayyah ya cimma a falo Madiah tana daka tana sallah don haka suka balle da hira shi da Sumayyah, kan kace meye wanan sabo ya fara shiga tsakanin Usman da Sumayyah, bini bini ya zo gidan bayan ada sai in Madinah ce ta kira shi ko Hajjah Ramlah ta aiko shi, ya zama suna dasawa sosai har ta kai su ga karbar lambar wayar juna.
Kafin ka ce me? Madinah ba ta ankara ba aka soma yi mata ?midnight call a gida. Sumayyah har mantawa ta ke Usman Attahiru Yayan Anti Madinah ne, gabadaya ta rufta nan take, kafin dawowar Sarham.

Ranar da Madinah ta fahimci wai soyayya ake tsakanin Sumayya da Usman ta sha mamaki, at the same time a take anan ta nuna wa Usman rashin goyon bayanta, da hujjarta na cewa Sumayyah tun fil azal ba ta kaunarta, kuma an gaya mata ita ce ta hannun daman matar wulakancin da sarham ya auro mata.
Usman kuma ya ce mata, a gaskiya shi bai son gutsiri tsoma irin na mata ba, ya ga Sumayyah ta yi masa, komai nata ya yi masa ba ruwanshi da shirmensu, Sarham kawai yake jira ya dawo ya gabatar da kansa.
Madinah ta lashi takobin ita kuma sai bayan ranta Usman zai auri makiyarta???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?. Ko mata sun kare a duniya bazata bada goyon baya ba, dama dai Surayyah ce kuma tayi aure ita.
**** **** ****

KANON-DABO
A
ka kawo masa visa din Hauwa a wayewar garin litinin, bayan an gama bugawa. Mama na shirin fita office sallamar Sarham ta dakatar da ita. Ya shigo dakin da karfin gwiwarsa yau dai, da kallon marairaita da karbar laifi, suka gaisa shi da Mama ba yabo ba fallasa.
Cikin brown envelope ya mika mata abu,
?Ga shi Mama na karbo!?.

Mama ta amsa ba tare da ta san meye a ciki ba, tana kokarin budewa ta gane passport ne.
Za ta fara fadan har yaushe aka je aka yi passport din ita bata sani ba, ta tuna subutar bakin Hauwa na cewa, sun fita da Sarham kwanaki. Ta yi kwafa kawai ta aje a gefe ko bude visar ba ta yi ba balle ta ga wace iri ce ko ta wata nawa ce. Murya fal ladabi Sarham ya dukar da kai yace,
?Mama kin yi izni za mu iya tafiya tare? Already na yi mana booking jibi ne tashin namu insha Allah?.
Mama ta yi shiru, ya ci gaba da roko, da ban hakuri da ban baki da alkawarin bazai kara maimaita kuskurensa ba kuma zai kula da Hauwa tsakaninsa da Allah. Da kyar Mama ta ce,
?To karatunta fa??
?Ma yi wannan shawarar daga baya in mun je naga yadda abubuwa zasu kasance?.
Mama sai ta kasa musantawa, tunda abin da ta ke rokon Allah dare da rana ne yau Ya amsa musu. Sarham ya dawo kan hanya kuma ya fahimci kansa. Ko bai fada ba ta ga  seriousness a kan Hauwa wannan karon a tare da shi sosai.
Duk da haka ta kawo nata kalubalen na cewa, ya zai tafi da Hauwa babu Mardiyyah?
Wa zai dinga taimaka mata?
Sarham ba tare da tunanin komai ba, ya ce, ?I will take care of her, my self Mama, for the mean time, kafin in yi deciding akan ko zan iya daukar Mardiyyar a gaba. I will do everthing to undo the hurt I caused you Sweet Mum?.
Mama tayi ajiyar zuciya a karshe, ko bata ce ba hakan na nufin amincewarta.

Hankalin Mardiyyah ba karamin tashi ya yi ba jin Mama ta ce ta hada wa Antinta kaya za su tafi Jeddah.
Mardiyyah tana kayan Hauwa a jakar matafiya tana kuka wiwi, amma ta danne bakin da dankwalin ta kada Hauwa taji kukanta, amma saida taji sheshsheka. A kwance take amma saida ta tashi zaune tace ?Mardhiyya lafiya?? Ta gaya mata abinda aka ce da ita. Hauwa kanta jikinta yayi wani irin sanyi. Mama ta alkawarta ma Mardhiyyah tafiya Saudiyyah tare da ita duk lokacin da za ta je umrah, kuma ba za ta mayar da ita Shanono ba ko ba Hauwa a gidan, za ta ci gaba da zama tare da ita ne har aurenta.
Hauwa kanta na kasa, ko dagowa ta kasa yi sabida nauyin Mama da damuwar data cika ranta. Mama lakca guda ta hau yi mata a kan ta zauna lafiya da kowa da zama ya hada ta da shi, kuma ta girmama Madinah tunda ko a girme ta girme ta, ba a aure kawai ba.
Ta ce, ?Na san ba ki da matsala ko kadan a kan girmama na gaba da ke Hauwa?u, amma zaman mata biyu karkashin inuwar miji daya sai an daure an kai zuciya nesa ba kusa ba. in ba haka ba duk zaku taru ne ku kai junanku wuta. Ki sa a ranki ibadah ki ka je yi domin zaman aure ibada ne Hauwa, balle wanda ya zamo ku biyu ne a wurin mijin?.
Jikin Hauwa bakidaya ya yi la?asar ta soma hango babban kalubalen dake gabanta, nan take ta ji kamar ta ce da Mama babu inda za ta je, amma ganin yadda Mama ke ta kai da komowa wajen yi mata shirin tafiyar, da bata magungunan da bata san ma kona menene ba da yadda Sarham din kansa ya dauki komen nata Jeddah da matukar muhimmanci sai ta kasa magana, duk da Mama ba ta kara bari sun kebe ba, ta maida Hauwa dakintama kwata-kwata ana saura kwana biyun su tafi, tana ta yi mata kyakkyawan shiri da tsumi kala-kala da tukudi.
Ita kanta Hajiyar Abba, wato Hajiyar Gadon Kaya cewa tayi ba ta ga dalilin zaman Hauwa tare da su ba, in makaranta ce ai babu inda babu ita. Kada su sake su bata mata rai su tattara mishi Hauwa ya dau kayarsa. In don rashin ido ne ya sa Mama ajiye ta shekara guda a daki ai ya fi kowa sanin ba ta da idon ya je ya auro ta.
Ranar sun sha fadan Hajiya Kulu wadda ta yi tattaki har gida ta sille Mama da Abba don Sarham ya gaya mata takunkumin da Mama ta saka masa na saki, da yaki kuma ta kuma hana shi ko magana da Hauwa.
Shi ya sa ma ranar da ya kawo visa mama ba ta yi dogon ja?in?ja ba, don Abba ya ce a daina yin duk abin da zai saka Hajiya Kulu yin fada, saboda BP dinta.
**** **** ****

Duk wani shiri na tafiyar hauwa Mama ta gama sbhi cikin lokaci, komai da tasan zata bukata ta tanadar mata. Kuma ita da kanta ta kai su filin jirgin Malam Aminu a ranar tashin nasu. Bata dawo gida ba sai da aka kira fasinjoji domin shiga jirgi.
A daren ranar duk kokarin Sarham na samun Madinah a waya bai yiwu ba, ko network ne ko wayar tata a kashe take? Ya so tun a daren ya gaya mata cewa tareda Hauwa zai dawo. Ta shirya mata daki daya cikin dakuna biyun da bata amfani dasu. A zuciyarsa baabu fargabar komai, don yarda zuwa yanzu dole ya kara zama namijin duniya a tsakanin matan nasa kuma ya zauna da Hauwa cikin iyalinsa cikin adalci, bai yarda da raba gida ba shi ra?ayin sa shine samar da kyakkyawar mu?amala ta fahimta da taimakekeniya tsakanin Jiddah da Madinah kasancewar Hauwa nada lalura. Ba zai kaita wani gida ta rayu ita kadai ba.
Yana fatan wannan din ya hada kan iyalin sa da samar da zaman lafiya da kaunar juna a tsakanin su. Don shi wai bai yarda da hargagin Madinah na cewa ita Madinah tafi Hauwa komai ba, wai don tana takama da tanada zurfin ilmi da iyaye masu kudi yen-yen-yen to shi ina ruwansa da wadannan din, tunda dai shi ko wani nasa bai taba aikawa gun Daddy neman taimako daga ISDB ba, itama ba su ne dalilan da suka yi mujazar auren shi da ita ba.
Dr. Sarham Abbas ne rike da hannun matarsa Hauwa Bilyaminu, suna taka matattakalar jirgin  emirate wanda zai tashi da su zuwa kasa mai tsarki a daren yau.
Hauwa kankame ta ke da hannun Sarham cikin tsoro na rashin sabo take taka matattakalar, shi kuma ba tare da damuwa da kallon da ake musu ba ya rike hannun nata sosai yana gaya mata cewa,
?Mind the stairs (ki kula da matattakalar)?.
Lokacin da jirgin ya karci kasa zai tashi, Hauwa ba ta san sanda ta saki salati ta kara damqo Sarham ba. Wasu Larabawa mata da miji a kusa da su, sai da suka yi mata dariya, don sosai ta ke cikin gigita da karar tashin jirgin. Wani hargagi ne da bata taba ji ba mai barazanar buga dodon kunnenta.

A cikin jirgin, shi ya sanya hannu a kwibin Hauwa ya daura mata belt, lokacin da larabawan na kusa da su suka fahimci cewa matarsa ce kuma bata gani ba karamin burgesu Sarham yayi ba sabida yadda yake kula da duk wani motsinta. Ga idanun nata a bude tar masha Allah dasu. Sai da matar ta karbi adireshin su na can Jeddah suka ce su kuma a Ta?if suke zaune In sha Allah suka shigo Jeddah Sayayya watarana zasu kawowa Hauwa ziyara har gida.
Ba su tsaya a ko?ina ba wato babu transit sai a airport din Sarki Abdul?aziz.
Hannun Sarham still cikin na Hauwa, a lokacin da suke (passing immigration checks) na shiga kasar Saudiyyah har suka kammala. Taxi (Ajrah) suka hau, mai Ajrah ya ja mota zuwa hanyar gidanshi da ke cikin gidajen likitoci na Saudi-German.

Tunda suka hautiti Hauwa ta cire yatsunta daga cikin na Sarham. A lokacin shi yanata kokarin saka layin shi na Saudiyyah a wayarsa. Ta mika cikin tunani. Ba kuma tunanin komai take ba face tunanin irin tarbar da matar likitan nata zata yi mata. Da kuma irin zaman da zasu yi tare, duk da cewa na dan takaitaccen lokaci ne wato hutun ta na semester inji Mama.
Shikuma ya sa a ransa Hauwa ta zo Jeddah kenan, wato bazata koma Najeriya ba. tun a cikin motar ya soma browsing din makarantu a cikin birnin Jeddah don nema wadanda ke hada karatun su da speciality na masu bukata ta musamman wato makarantun da ke yin (Inclusive Education).
**** **** ****



KAFIN SAUKAR SU DA AWANNI BIYU

S
umayyah na goye da Waheedah tana goge dining, Madina na daki tana waya da Usman cikin zafin rai, sai Allah ya baiwa kunnuwan Sumayyah damar zuqowa.

?Wallahi sai dai ka daina alaka da ni din Ussy, da dai in bari ka auri Sumayya, kai ne ba ka san irin halinta ba, wallahi annamimiya ce zuciyarta bata da kyau bata kauna ta?.
?Sai kin gaya min me ta yi miki na rashin kauna, sai kin gaya min me tayi na annamimancin, alhalin ita din ba kishiyarki ba ce, kanwar mijinki ce, uwa daya uba daya?.
Madinah ta kara hassala ta ce, ?Yaya Usman ban yi niyyar gaya muku ba sam, nikadai na binne abun ina fama dashi a raina don kada Daddy ya kashe min aure, amma yau tunda ka dage a kan Sumayyah zan gaya maka, Hajjah Ramlah ma zan gaya mata. Sarham ya kara aure a Kano, itada uwarsu sun baiwa yarinyar masauki, tun fil?azal Sumayyah bata taba sona ba, na rasa laifin da na yi mata.
Ko don in rama abin da Sumayyah tayi min na kiyayyar babu gaira babu dalili na rantse ba za?a yi auren nan ba, don na lura ita ma munafukar tana ra?ayinka, har da yi min wani sabon ladabi yanzu, ba ta san kar nake kallonta kamar takarda ba.?.
Sumayyah ta yi mata gyaran murya daga bakin kofa, Madinah ta kashe wayar ta tsuke fuska, sai ta karasa shigowa dakin ta kwantar da Waheedah a gadonta hannunta rataye da jakar kayanta, kamar ba ta ji me Madinah ke fada a kanta ba, ta ce,
?To Anty Madinah da alkhairi, zan koma hostel, tunda Yaya Sarham ya ce yau zai dawo, nagode da zumuncin ki?.
Madinah ta harareta kasa-kasa, ta ce,

?A gaishe su!?.

Sumayyah ta juya cikin bacin rai za ta bar dakin tana fadi a ranta, ko son Usman zai kashe ta itama ta hakura ba za ta aure shi ba, ko da gold aka kera shi.
Har ta kai kofa zata fita Madinah ta ce, ?Umh! Ji mana Summy???
Sumayyah ta dakata ba tare da ta juyo ba, idonta fal kwallah don har ga Allah tana son Usman Sorondinki. Ba ta san me ya sa zuciyarta ta yi mata wannan rashin adalcin ba, tunda Yayan Madinah ne da baasa ga maciji.
Madinah ta ce, ?Makauniya ba ta da Yaya ne? I mean? ita kadai ce a wurin iyayenta babu dan uwa babba namiji haka?
Cikin rashin fahimta Sumayyah ta juyo tana kallonta.
Madinah ta ware mata fararen idanunta sosai, ta kwance ribbons din data daure gashinta dashi ya zubu a wuyanta ta girgizashi sannan ta kara daure shi cikin  hairbound din, ta ce,
?Eh, ai ba za ta rasa dan uwa ba, I mean makauniyar gidanku, ina ga shi zai fi dacewa da ke, dangin ?yar Badala ?yan cikin gari ba nawa dan uwan ba haifaffen Saudiyyah?.
Sumayyah ta saki kwallar idonta, ta fice ba tare da ta ce da Madina komai ba, tana tsoron tayi abinda za?a ce tayi fitina a gidan Yayanta amma data baiwa Madinah amsa, ta so ta ce da ita  dadin abun ma mun san asalin balbela, kowa ya san SORONDINKI a Kano, nan ma cikin Badalar ne ?yar rainin wayo kawai hankaka maida gidan wani naka?.
Wannan da ?yar sarkin Kano ce watakila ko daga ido ba za ta rika yi tana kallon mutane da kima ba.
Shin me ta maida yaran cikin badala ne? ?Yan kauye ko? Za kuwa ta ga kauyanci ganin idonta, sai ta kilar da HAUWA, duk da haka ma Mama tana yawan gaya mata irin ci gaban da Hauwa ke samu a jami?ah tun dawowarsu.
Daga karshe kuma tana tafe a hanya don komawa hostel ta canza shawara, ta sa a ranta rashin mutuncin Madina a kan alakarta da Usman ba zai sa ta fasa son Usman ba, kuma ba zai sa ta barshi ba, don kam tana matukar sonshi. Gara ma ta rike abinta tayi ta gumawa Madina haushi. Ai Usman gaba yake da ita ba shine kanin ta ba da zata saka shi ko ta hana shi ba, bakin cikin ta daya yadda ta gama bata ta gun mahaifiyarsu Hajjah Ramlah.
Ko awanni biyu Sumayya ba ta yi da komawa hostel ba, Ajrah ta sauke Dr. Sarham da maidakinsa, wato amaryarsa Hauwa?u a kofar flat dinsu. Watakila Sumayyah da ta san cewa da Hauwa ya taho da ba ta tafi ba.
Shi kuma bai gaya wa kowaccensu cewa tare zai zo da Hauwa ba. Ita Madinah bai samu wayarta ba ita kuma Sumayyah surprising dinta yaso yi.
Usman ne ya yi mata waya cewa su hadu a jami?arsu don Madina ta masa iyaka da zuwa gidanta, shi ya sa ta bar gidan, da kuma maganganun data ji Madinah nayi da Hajjarsu a kanta sun tsoratata.
Dr. Sarham ke danna kararrawar shiga kofar falon gidanshi, Hauwa na daga dan bayansa ta sha glass da shudiyar abaya, harde da hannuwanta biyu a kirji.

Dr. Madinah wadda a lokacin take shilla Waheedah cikin lilonta cikin murnar ta kori Sumayyah at the same time tana waya da Hajja Ramlah, korafin dai taci gaba da kai mata iri-iri kan kanwar mijinnata wadda ta tabbatar ba tun yau ba ba ta kaunar ta bude ido ta ganta tare da dan uwanta.
Ta ce ma Hajja Ramlah,
?Ban taba gaya muku ba don bana son ki ce in dawo gida Hajjah, Sarham ya dade da kara aure, kuma sun baiwa yarinyar masauki a gidansu.
Hajjah ke shaida ce kan cewa raina ne kawai ban cire na bai wa Sarham da uwarsa da kannensa ba don so da kauna, duk wata kulawa da mace ke yi wa dangin mijinta babu irin wacce ban yi musu ba??. Ta karasa cikin karyewar murya.
Hajja Ramlah bata san sanda ta yi wani ashar mara dadin ji ba, lokacin da Madinah ta idasa gaya mata irin macen da Sarham ya aura da irin nakasarta.
?Idan dai ni na haife ki Madinah, to tattaro kayanki ki ajiye masa ?yarsa ki dawo gida, martabarki da ajinki bai yi wannan lalacewar ba.
Bari Daddy ya shigo in ma kin ki tahowa ni da kaina zan zo in fito da ke tunda Sarham ba shi ne autan maza ba?.
Madinah ta ce, ?Abin da na guda kenan da yasa tun farko na ki gaya muku Hajjah, Sarham ba zai taba sakina ba, don haka ina amfanin in tafi gida da dakon aurensa watarana in dawo?
Besides na lura yanzu baya ta yarinyar, for as long as a year bai je inda ta ke ba, sai yanzu da ya tafi daurin auren kanwarsa ta farko?.
Ta ci gaba da dannar mahaifiyarta ta roke ta kada ta daga wa Daddy hankali a kai saboda Sugar (diabet) dinsa yayi tsanani, taroketa tayi shiru kawai, za ta iya da rayuwa da Sarham a duk yadda ta same ta.

Hajja Ramlah ta san cikin yaranta, Madina ce kadai mace amma Allah ya azurtata da hankali. Sau tari ita ce mai yi mata fadan tayi ba daidai ba in ta kuskure wa mahaifinta. Hajja Ramlah ta samu kanta da cewa,
?Ke dai ki ka kawo yaron nan ki ka ce kina so Madinah, kada ki tilasta

5 / 12