Advertisements
Chapter 6 Reading Hauwa Kulu Book 4 Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Hauwa Kulu Book 4 Complete Hausa Novel

Author :  Takori Category :  Complete Novels

Chapter   6 / 12

15K to 18K   out of 34.5K words

kanki zama da shi in akwai wulakantarwa da tozarci, abu ne da daga ni har mahaifinki ba za mu lamunta ba, wato ya wulakanta ki ko ya kaskantaki ko ya hada matayinki da makauniya?.
?Hajja kada ki damu, I can handle everything, I can take care myself, amma babu batun  yaji a policy dina. Yau in Sarham ya sake ni zan bar masa gidansa, amma ba zan taba yin yaji da aure a kaina ba?.
Karar kararrawar shigowa ta sa ta yi wa Hajja Ramlah sallama, ta dauki Waheedah da ta fara kuka a kan kafadarta, ta isa ga kofar bayan ta amsa da cewa,
?Ina zuwa?.

Ko da ta bude ita ta san ko kowa bai gaya mata ba, wannan din da ya rike hannunta cikin nasa, na nufin ?HAUWA-KULU?.
To amma a yadda Surayyah ta fasalta mata ita ba a hakan ta ganta ba, wato irin ?yan tallan abincin Tashar cikin gari, talauci sama da kasa, ?yan babu cin yau babu na gobe, almajira, musaka.
Wannan din da ke tsaye a gabanta wata  classy yarinya ce da idanu ne kawai ba ta da su, amma za ta goga da kowacce irin macen kasar Najeriya.
Sakamakon cewa fuskarta fes, babu ko digon pimples, idanunta cikin gilashi mai duhu ainun don haka ba ta samu ganin kalar kwayar idanunta ba.

Da farko Madinah gabanta faduwa ya yi, amma haka ta daure ta basu hanya. Wani irin makoko na yunkuro mata, ji ta yi kamar suna shigewa din, ta fita a guje kawai ta bar gidan. Muryar Baban Waheedah ta dawo da ita tunaninta, yana fadin,
?Come on Waheedah?.
Ya mika hannu ya karbi yarinyar da ke ta mika masa hannu tana zillo daga jikin Madinah.
Madinah ta ba shi hanya, cikin kauda ido, hannunsa daya rike da Waheedah, daya rike da hannun Hauwa suka shiga cikin falon.
Sai da ya tabbatar Hauwa ta zauna a daya daga cikin kujerun falon, ya mike ya bi bayan Madinah wadda ta yi wucewarta daki ba tare da ta ce musu ko ci kan ku ba. ko ta nuna ta san tare yake da wata halitta, mutum din ma dan adam mai daraja. Wannan abu ya bakantawa Sarham ba da kadan ba.
Tana shiga yana shiga, ya tura kofar. Da ta daga ido ta dube shi bai iya gasgata cewa kwayar idon Madinah ba ce, sabida yadda ta rine da bacin rai da wani zazzafan kishi mai barazanar fasa mata ido.
?Kin kyauta kenan Madina? Ai ko ni ba ki yi min sannu da zuwa ba, kya yi wa Maijidda wadda ta zo bakon wuri, ta tadda ke a gidanki??.
?Dakata don Allah Baban Waheedah!
Ka gaya min za ka zo min da wannan yarinyar?
Kana tsammanin ni Madina zan iya zama gida daya da kishiya ne? Kishiyar ma irin wannan musakar??
Sarham ya yi kokarin kama hannun Madina, ta yi maza ta ja da baya,
?Don?t dare touch me again, bayan ka gama tattaba makauniya?.
Maganar sai da ta yi amsa kuwwa a kunnen Hauwa sabida yadda ta ware makogaro ta fadeta.
Sarham kuma ya kai wa Madinah wani wawan mari, sai dai kafin hannun nasa ya sauka a lafiyayyar fuskar Madinah tayi maza ta kare da hannunta, ta kuma yi saurin ja da baya kada ya illata mata fuska.
Nashi idon har ya fi nata rinewa da bacin rai, ya ce, ?Munawwarah, ke ce kuwa? Yau ina hankalinki da tunaninki ya je ki ke ma wani dan Adam gorin halitta?
Are you not a medical personnel?
Ni kike dagawa murya kamar wani dan ki? Anya ke ce ko sauya ki aka yi kafin naje na dawo??
Tsaki Madinah ta yi, ta juya ta bar masa dakin tana cewa,
?A?ah, ba ni ba ce, ko kuma kawai kace daga turu na fito. Ka sa a ranka ba zan taba zama gida daya da wannan musakar ba, balle in hada shimfidar miji da ita. Ko ta fita yanzunnan ka kama mata wani gidan ko ni in fita in bar muku gidanku, amma tareda takardata don bazan yi yaji a dawo dani ba?.
Ta yi maza ta shige toilet ta saka key, ganin yadda maganganunta ke kaskanta shi, ba?a fuskarsa kadai ba har a jikinsa dake mazari kamar ana kada masa gangi.
?Ka fita a dakina Sarham, don Allah, saboda wallahi bakidaya ka koma min wani musaki& ?.
Kwafa Sarham ya yi ya juya ya fita daga dakin ba tare da ya dauki Waheedah da ya ajiye a gado tana tsala kuka ba.
Dakin Sumayyah ya nufa, sai ya tarar da dakin a kulle. Wato ita kuma ta tafi ba izninsa. Ya fiddo waya ya kira ta,
?kina ina ne dakinki a kulle??
?Wa? Ni? Bhaiya ai na tsufa a hostel, ba ni ba kara kwanan gidanka?.
Sarham ya kara hassala fiye da farko, ya ma fasa gaya mata cewa ya zo da Hauwa don bai ga amfani ba, ya ce,
?In na kara cewa ki zo gidana Summy ki ce shege ne ni ba haihuwar Maishari?a da Prof. ba. Na yafe miki zuwa gidana daga yau har gaban abada?.
Jikin Sumayyah ya yi sanyi, ta ce, ?Bhaiya??
Ya yi maza ya kashe wayar, jikinsa yana tsuma da bacin rai, ba tare da ya saurare ta ba, ya koma falo ya tadda Hauwa.
A yadda ya bar Hauwa a haka ya same ta a zaune a kan kujera ita ma ta kumbura tayi fam, kiris ta ke jira ta fashe. Don bata taba jin cin mutunci akan lalurarta rabin wanda ta ji a bakin Madinah yau ba. Hakika makanta abu ce mai saka karfin ji!
Ya yi kamar bai ga kumburin da ta ke yi din ba, ya dauki jakar kayanta ya kama hannunta ya ce,
?Taso ki biyo ni mu je ki huta?.
Ta ja tunga a inda ta ke zaune ko motsawa ba ta yi ba. Ta kuma warce hannunta.
?Yaya Doctor ni gida zan koma!?.
Idanuwanta suka yi narai-narai cikin kwalla, wadda ba ta idasa zubowa ba.
Ya dube ta a matukar hassale itama, ya ce,
?Ga hanya nan ki koma din, idan ba ku hadu ku ukun kun haukata ni ba, ba ku ci sunanku na mata tumakai ba!?.
Ya dauki jakarta ya nufi wani daki da ke rufe wanda ke kallon dakin Madinah, ta shirya dakin ne don bakinta ?yan gidansu na Sorondinki in sun zo aikin Hajji su kan shigo su kwana, shi kuma nan ya ga nan ya dace Hauwa ta zauna don girmansa daya da dakin Madina.
Dakin a gyare yake tsaf babu abinda babu na bukata, ga sabon bayi (toilet) makale a cikinsa. Ya ajiye jakar Hauwa ya fito.
Daidai fitowarsa ya ga Madinah tana kwashe warmers din abincin da ta girka daga kan dining table. Ta kwashe komai ta juye a leda ta saka a freezer.
Tana kallon Hauwa a zaune tana tsane ido da gefen mayafin abayarta, ta wutsiyar ido ta harare ta, bayan ta gama kwashe komai ta shige dakinta ta kulle ta ciki.
Sarham ya dawo ya zauna daf da Hauwa, ya rasa ta ina ma zai bullo musu su duka. Hauwa jin zamansa a kusa da ita sai ta kara sautin shesshekar kukanta, wai ita kawai ya maida ita wurin Mama bazata kwana a gidan ba.
Ga gajiya, ga yunwa, ga bacin rai da suka tarun masa don haka bai kula ta ba. Ya fiddo waya ya kira Abbansa yana maida fushinsa, ya gaya masa sun sauka lafiya, haka Mama ma. Bai ja hirar da tsayi ba kuma ya kama hannun Hauwa ya soma janta ta karfi zuwa dakin da ya zabar mata.

A gefen gadon dakin ya zaunar da ita, ?This is your room, in kin ga dama kuma ki kama hanyar Kano a kafa daidai ne. zan je in yi sallah, muje ga toilet in nuna miki yanda yake ki gane komai, ko kina son shiga?.
Wannan karon ta bashi amsa cikin share ido jin yace su je kuma bai kama hannunta ba.
?Idan na fadi fa, tunda ban san hanyar ko?ina a gidan ba??
Tausayi ne mai tsanani ya kama shi, kawai sai Hauwa taji Sarham ya dauketa yana tafiya da ita zuwa toilet din a hannayensa.
Kunya taji soai ta hau sunne kanta a kirjinsa. ?Daka barni na tafi da kafata don in gane hanyar ko?ina?.

Dr. Sarham bai yarda ya direta ba sai a toilet din, ya nuna mata yadda za ta yi amfani da komai na bandakin, ta hanyar dora hannunta akan komai yana bayani. A karshe ya nuna mata (shower) ta wanka da yadda zata dinga kunnawa da rage zafin ruwan daga famfon kada ya kona ta, ya nuna mata kunna (water heater) wadda yace in ta kunna ba sai ta kashe ba don tana kashe kanta automatically.
Ita ba ta san dalilin yawan taba hannayenta da yake yi ba wai yana nuna mata abubuwa, nan kuwa ba ya gajiya da touching dinsu ne sabida taushin fatar hannunta.
?Na gane, ka je zan yi wanka!?.
?Kin fasa komawa gun Maman?? Ya tambaya cikin gatse, yana janyota yana makalewa.
Hauwa ta tsuke fuska da baki, ta ce, ?Ya danganta da sunan da aka kara kirana da shi a gidan nan. Ni duk duniya ba wanda ya taba ce min musaka. In ma musakar ce shin miskini ba mutum bane? Ni dai na san;

?Inna Akramakum Indallahi Atqakum?.

Ta hakan ne ya gane cewa ta ji me Madina ta fada a kanta. Ita makanta da ma sanya karfin ji ne da ita. Ya kuma san ba abinda ta tsana a duniya irin sunan da Madinah ta kira ta da shi, yau mafi muni, don haka ya sassauta murya ya sake makalkaleta a jikinsa yana shafa gadon bayanta, yace.
?Ki yi hakuri, ki kara yin hakuri, ki kuma koyi karbar  labelling na sunan lalurarki, hakan ne zai sa ki zauna lafiya ko da wani ya fada ki daina damuwa irin haka da shiga bacin rai, ba lallai ne kowa da niyyar gorin ido yake ce miki makauniya ba, wani kuma bada isgilanci bane, a?ah suna ne da Malam Bahaushe ke kiran duk wani mai lalurar gani dashi don banbance lalurarsa.
Ki koyi kauda kai a kan hakan muddin kina so ki rabu da bacin rai?.
Ya kara sassauta murya, ya ce,
?Ki gama wankan kiyi sallah mu je tare mu sayo abinci?.
Saboda ya ga sanda matar gidan ta fito ta kwashe nata bakidaya, (amma bai fadi hakan ga Hauwa ba ya barwa ransa).

Wannan ya sa Hauwa ta dan saki ranta, jin cewa za su fita su mike kafafunsu. Don dama sai mutsuka suke mata na zaman jirgi.
?To ka fita zan yi wanka?
?Allah ya yarje min inga komai na jikin matata Hauwa?
Ya fada yana sirka mata ruwan wanka.
Saida ta hada da rokon shi Allah Annabi ya bata waje sannan ya fita ya rufo mata kofar.
Ta yi wankanta da kyau da ruwa mai zafi domin warware gajiyar da zaman jirgi ya haddasa mata, tana wanka tana tunanin yadda zamanta da Maman Waheedah dinnan mara kirki zai kasance a gidan, wadda a zahiri ba ta marabci zuwanta ba, kuma ba ta shirya zama tare da ita ba, kafin maigidan ya kawo ta meyasa bai gaya mata matarsa bata da kirki ba, kuma bai nemi yardarta ba ya daukota ya kawo mata gida?
Wannan ya nuna shi Sarham mutum ne mai yin abin da ya sa kansa a gidansa ba tare da shawara da mata ba. Ita dai ta san za ta yi  tolerating komai, za ta yi wa Madinah biyayya kamar yadda Mama da Inna suka nusarsheta, abu daya ne ba za ta lamunta ba, Madinah ta keta rigar mutuncinta ko ta ci gaba da kiranta da duk sunayen wulakancin da ta ga dama
Wata doguwar rigar atamfa Hauwa ta sanya Chiganvy da aka yi wa wani ubansun dinki wanda ya fiddo kyakkyawar surarta sosai ba tare da ta san yadda kayan suka karbi jikinta ba, ta dauki mayafin da Mardiyyah ta manna a cikinsu ta yafa.
Tana cikin fesa turare Dr. Sarham ya shigo sanye da farar sabuwar jallabiya mai matukar tsada, sai tashin nasa kamshin na musamman yake yi.
?Oya lets go, kin gama ai ko??
Idonsa ya kai ga dressing dinta ya kankance ido, ?Me-ji! Cire wadannan kayan maza-maza, kin manta a Saudi-Arabia ki ke? Ko ba a can ba ne in aka ce ki fita da wannan dinkin jikinki na juyawa a cikinsa sai ki fita don hankali ya wadace ki ko??
Hauwa ta hau shafa dinkin jikin nata wai ta ji me ye laifinsa.
?Ka yi hakuri, ka san dai ba na gani?.
?Umh! Da wani ne ya fada da yanzu cibi ya zama kari, canza su maza-maza ina jiranki?.
Ya ci gaba da tsayuwa kuma bai fita ba.
Hauwa ta rausayar da kai gefe, ?To a gabanka zan canza ne Yaya Sarham??
Ya yi wani dan murmushi cikin rashin jin dadi ya juya ya fita yana cewa,
?Na ba ki wuri, Mrs., matsayina na Yaya har yanzu yana nan bai canza ba kenan ko??
Bai kuma tsaya sauraron amsarta ba ya juya zai fita tayi maza ta riko shi.
Za ta so kwarai ta ga fuskar likita Sarham a yau, ta tabbata wanka ya dauka ko daga ni?imtaccen kamshin da yake zubawa a dakin.
Hauwa ta yi ajiyar zuciya tana ji a jikinta lalurar makantarta ta har abada ce ba ta da magani, don ba ta taba ji ko ganin makahon da idonsa ya bude ba.
Don haka fatanta na ganin fuskar likita Sarham zai ci gaba da kasancewa ?fata? (hope) irin wanda har dan Adam ya koma ga Ubangijinsa bai samu cikarsa ba (actualizing of dream) dinsa.
Ta hau lalubar fuskar Dr. Sarham ta saka fuskar shi a tsakanin tafukanta biyu, tana shafa tattausan sajen gefe da gefen fuskar tasa, ta ce ?You are my HUSBAND, not a brother, and my everlasting dream is to see you with my naked eyes?.
Sarham yayi maza ya hade bakin su wuri guda, yana sakar mata mata wata irin zazzafar sumba mai tsayi da zurfi kusufa-kusufa lungu lungu sako sako a cikin bakinta.
Hauwa sai ajiyar zuciya take yi, kwalla ta taru a idonta, ta yi maza ta rike shi gamgam itama, nan ya idasa rikitata ta hanyar kai bakin shi saman kirjinta, daga wannan lokacin suka lula a wata duniyar ma?aurata mai ban mamaki da shiga rai. Hauwa na neman shidewa Sarham ya dauketa a hannunsa zuwa gadon dakin, har da wata irin sheshshekar fita hayyaci yake yi a jikin Hauwa kai kace bai taba rike mace ba, yana kiranta da sunayenta kala-kala. Wadanda take so (Hauwa?u-Jiddah-Maijiddah) da wadanda bata so (Kuluwa ta, Kulun-Majadun dina, ni ina ganin ki kuma ina son ki a hakan, ko baki ganni ba) .

Tunda Madinah ta kulle kanta a daki ba ta kara ko lekowa falo ba, sai kukan Waheedah ka ke ji yana tashi a gidan, wadda da alama ba ta samu lallashin uwa ba. Wannan kukan na Waheeda har cikin kwakwalwarsa yake tabawa, kukan Waheedah shi ya ceci Hauwa a hannun Dr. Sarham yau kuma, ba don haka ba da tuni ta amsa sunan sauran mata ?yan uwanta.
Taimaka mata yayi ta canza kayan zuwa bakar abaya da mayafinta. Ya san da gayya ta kyale Waheeda take jiniya don haka ya kama hannun Hauwa suka fito ya rufe dakin suka bar gidan.
Madinah na jin rufe kofarsa ta leka waje ta tagar dakinta. Nan ta hange su suna takawa a kasa gwanin ban sha?awa, ya rike hannun Hauwa cikin nasa. Ba ta san dai ina za su je ba, amma jikinta ya ba ta  mud?am (restaurant) da ke cikin estate din nasu za su je, wato wajen cin abincin likitocin Saudi-German.
Wani abu ne da za ta iya cewa tunda suka yi aure rabon Sarham da shi wato cin abinci a ?Mud?am?, don ko ba ta dafa abinci ba zai wa cikinsa ?yan dabaru ne ya zauna lafiya. Sai ta shiga tambayar kanta shin abincin da ta dafa ta kwashe don kar su ci ta kyauta? Lallai kishi mai maida babba yarinya mai juya hankalin mai hankali. Kyabe baki ta yi, ta ce,
?Ba hakkina ne ciyar da su ba daga shi har matar tasa.
Shi da ya ga zai iya wahala da makauniya sai ya fara tunda wuri, kafin wankin hula ya kai shi dare don in yana zaton ni zan kula masa da mata ya yaudari kansa?.

Suna tafe cikin tsanaki a gefen titi, Sarham na tausar zuciyarta a kan kalaman Madinah.
Ya ce, ?Ki daina damuwa don wani ya ce miki makauniya, ko mara gani. Makaho bai isa ya hana al?umma kiransa makaho ba, haka kurma bai isa ya hana al?umma kiransa kurma ba. That?s the same with gurgun mutum (physically challanged) bai isa ya hana a kira shi gurgu ba, but accept it, like it, appreciate it. Accept your disability, enjoy it sai ta zame miki ?unique identification? ba tare da ranki ya baci a banza ba.
Ni idon nan da ana musanye da mun yi na huta da wannan bacin ran na GORIN IDO tunda ban isa hana mutane kiran Hauwa-Jeddah makauniya ba?.
Hauwa, ta daga manyan idanunnan farare kal, tayi ?harr!? Dasu a kan Sarham da wani irin murmushin jin dadi a fuskarta. Sarham ya shafa kansa zuwa keyarsa jin wani ?ignition? na fizgarsa, yace ?kada ki kashe ni da idanunnan Hauwa, I loved them, ina son daren yau in samu Safiyyah ko Maimunatu mai irin su, daga daren farko mai albarka?.
Hauwa ta kai tafukanta ta rufe fuska cikin jin kunya da karuwar Son Sarham mai tsanani a zuciyarta.
Daidai lokacin da suka isa ?mud?am? din suka shiga. Akwai tsirarun mutane, amma ba su da yawa, ya samar musu waje can nesa da kowa ya zaunar da ita, sannan ya je ya yo musu order din zazzafar kazar nan ta (Kentucky Fried Chicken) da aka fi sani da KFC da Chips, aka hado da zazzafan coffee mara sugar aka kawo musu.
Yau Hauwa sai ta samu kanta da jin kunyar cin abinci a gaban likita Sarham, ba su taba cin abinci tare ba sai yau. Shi kuwa bai lura wai kunya ta ke ji ba ya dinga dauko tsokar kazar da chicken nugget yana saka mata a baki ko ya tula mata tsokar a gabanta.
?Ki ci ki koshi fa, kada ki ji yunwa cikin dare?.
Ta soma ci a yangance ya ce, ?Maijiddah ni saurayinki

6 / 12