Author : Boss Bature Category : Complete Novels
soma yi masu addu'a suna tofa masu ajikinsu,Bayan sun Ja masu lallausan blanket dinsu,ta Kashe masu hasken ɗakinsu,Hannunsu ruƙe dana juna suka koma bedroom ɗinsu,Saman katafaren gadonsu suka kwanta,yayi hugging ɗinta tighly,then Ya Janyo lallausar blanket ɗinsu Ya lullu6esu,
Bayan komawar Hosana ɗakinsu,a zaune ta samu marshal daga shi sai short,
"Ae dama saida na faɗa maki,"
Murmushi tasaki"ashe yana acan,Yaron nan yaci ka wayau,"
Dariya yayi yana girgiza kai,Saman Gadon ta hau,Suka gyara kwanciyarsu rungume da juna,
"Ya Omar"Ya amsa mata"Na'am My baby"
"Kayi mun kalaman Soyayya mana kafin muyi bacci".
Gyara muryarshi yayi cike da zolaya yace"Yake akuyar dake cin ciyawar zuciyata"gaba ɗaya suka tuntsire da dariya,
*JunHad*
Tayi mamakin ganinshi zaune saman gadon,Ya jingina bayanshi jikin headboard ɗin gadon hannunshi ruƙe da hoton abbansu,ya ƙura mashi ido yana kallonshi ko ƙyaftawa baiyi,
"My romeo,"ta ambaci sunanshi,batare daya juyo ba,Ya amsa mata"My juliet,"
"Meyasa ka barni ni kaɗai"?
Murmushi ya ɗansaki"Am sorry,Yanzu nake shirin kwanciya,ina kallon Sanyin idaniyata ne"
Miƙewa tayi ta zauna gefenshi,hannu takai tare da shafa fuskar Abba mai ɗauke da murmushi"Allah sarki Abba,we really missed you Ni da babyna,tayi maganar tana shafa sumar kan Junaid,
"My Juliet"ya ambaci sunanta
" na'am My romeo,"
"Idan su babban Yaya suka ajiye aiki zamu koma nigeria da zama,Ni nafison can,"
"Nima nafison mu koma Nigeria,ba don bana jin daɗin nan ba,sai dan saboda ƴan uwanmu"acewar Jahad,
ɗaura hoton yayi a ma'ajiyarshi saman drawer,
"Yaushe zamu ƙara samun baby"?
"Duk lokacin daka shirya,My doctor"
"Ae ni kinsan koda yaushe a shirye nake,ko yanzu ma,ko kina ganin wasa"?
A'a,Na yarda da maganarka,Ae kai ɗin bana wasa bane tayi maganar tare dakai hannu ta ɗan bugi ƙirjinshi,murmushi yasaki"duk da haka bazan ƙyaleki ba,'tana ƙoƙarin buɗe baki tayi magana,Yayi saurin haɗe bakinsu wuri guda,Ba halin Yin magana,Sosai ya ruƙota ajikinshi,Romancing ɗin juna sukayi kafin daga bisani ,Suka gyara kwanciyarsu rungume da junad,A ƙanƙame,
Wuraren sallar asuba,yana cikin bacci Yaji shessheƙar kuka acikin kunnanshi,Gabanshi ne ya faɗi,A hanzarce yakai hannu yana shafa gefenshi saman mattress,Jin wayam babu ita Yasa ya ware idanuwanshi,Yayi mamaki Ganin babu Sehrish asaman gadon,Ga kuma shessheƙar kukan da yake ji acikin kunnanshi,saukowa yayi daga saman gadon,kaitsaye ƙwayar idonshi ta sauka akan ɗigon jinin dake a ƙasan tiles ɗin ɗakin,A jere jinin yake har zuwa toilet ɗinsu,Lokaci guda Hankalinshi Ya ƙara ɗunguma,A gigice Ya miƙe ya nufi toilet ɗin Yana faman ƙwala mata kira"Reesh!reesh!where are u"?Hannu yasa ya tura ƙopar toilet ɗin,Sai dai kash adatse take,ƙwaƙƙwaran naushi yakai ma ƙopar,ta buɗe Ya afka ciki a haukace,tuni idanuwanshi sun ciko tab da ƙwalla,Kwance ya hangota acikin bathtub ruwan dake acikin kwamin wankan ya gauraya da jinin dake ajikinta,Alamu sun nuna cewa ta jima Da mutuwa,hawayene suka wanke mashi fuskarshi,Sam Ya kasa ƙarasawa cikin toilet ɗin,Zubewa Yayi asaman guiwowinshi,sosai ya fashe da kuka,fuskarshi tayi jaga jaga da hawaye,sam bazai iya jure rashinta ba,Zuciyarshi barazanar harbawa take yi,Jiya jiyan nan suka sha soyayya da daddare gashi yau Ya wayi gari batare da ita ba,ashe dama na bankwanane sukayi"?
Runtse idanuwanshi Yayi sosai,Kafin Ya buɗesu a hankali,zurfin tunani ya shiga,Ƙura ido yayi yana kallon ɗagon jikin dake a gabanshi,Yatsanshi yakai tare da dangwalo jinin Yana kallonshi,Kokwanto ya shiga Yi Kamar ba Jini ba,Sam babu ƙarnin jini Ajikinshi,Azafafe Ya miƙe ya ƙarasa shiga Toilet ɗin,Ya tsaya gaban Bathtub ɗin yana kallonta,cike da saran abunda yake zargi,
Muryarshi na kerma Ya ambaci sunanta"Reesh...."shiru bata motsa ba,Almost 3 times Yana Calling Name ɗinta bata amsa mashi ba,jikinshi yayi sanyi sosai,dagasken dai ta mutu,Ya rasa reesh ɗinsa
Girgiza kanshi ya shiga yi la66ansa na kerma Ya shiga faɗin"Reesh why kika barni,Meyasa mutuwa zatayi mun yankan ƙaunane,wlh bazan Iya rayuwa batare dake ba,Zan kashe kainane,"A hanzarce Ya juya Ya fito daga toilet ɗin,jikinshi Na kerma Ya nufi bedside drawer ya ɗauko bindiga,cikin kunnanshi Ya saita bingidar Tare da rufe idanuwanshi,yana karanto kalmatusshahada,Sam batayi tunanin Sgr zai Iya aikata abunda Ya faɗa ba,da gudun gaske Ta fito daga cikin ƙwamin wankan daga ita sai undy data ja har zuwa saman ƙirjinta,tana ƙoƙarin buɗe ƙopar toilet ɗin Tajiyo ƙarar fitar bullet,Wata irin gigitacciya ƙara Sehrish tasaki,tana fitowa Ta same shi baje a ƙasa,jini duk ya wanke fuskarshi,Fashewa tayi da matsanancin kuka,A sukwane ta zube saman guiwowinta
"Innallallahi wa'inna ilaihirraji'un!!Ya rafayet!ka tashi!Nifa wasa nake maka Wlh ban mutu ba Wayyo Allah nashiga uku,Na bani Na lalace,gaba ɗaya tabi ta rikice Ta ruɗe,hannunta duk ya 6aci da jininsa,jijjiga shi tadingayi tana kuka kamar ranta zai fita,a ƙarshe ta rungumeshi tana kuka,ta tsorata sosai,daga wasa tayi silar mutuwar masoyinta,sai da ta jigata sosai,duk ta fita cikin hayyacinta,Sautin dariyarshi data dinga jine yasa ta yin saurin ɗagowa Tana kallon fuskarshi,Zazzare idanuwanta tayi akan fuskarshi,Ganin Yana ta faman tiƙar dariya,ya buɗe idanuwanshi sosai,
Daƙyar ya samu ya tsagaita da yin. Dariyar yace"Reesh ke kika iya tsara drama irin wannan balle ni da nake soja?I can do better than u,'
Fashewa ta kumayi da matsanancin kuka Cikin shessheƙar kuka take faɗin"Meyasa kayi mun haka Ya rafayet!Nifa wasa nake maka,"
Jifa mata harara yayi"haka ake wasa a gidanku?waya gaya maki ana wasan mutuwa?ko shima duk cikin Soyayyarne?da ace tunfarko ban gane so6o bane kika sanya me kike tunanin zai biyo baya,Zuciyata har kusan bugawa tayi lokacin da naganki kwance cikin jini,
Kowannansu Yaji jiki,
Sosai take kuka"Wlh bazan Yarda ba,Ya rafayet Ka tsoratar dani"tayi maganar muryarta na kerma,
"So6on da kikayi amfani dashi kika ajiye bottle ɗin Saman fridge dashi nayi using na kwararama Kaina," Still hawaye basu daina zuba akan fuskarta ba,har wani zazza6i take ji ajikinta,
Kafeta da ido yayi yana kallonta,Kamar wata ƙaramar yarinya,kowa ya bata shawarar tayi mashi irin wannan wasan,
"Naji tsoran na rasaka,"tayi maganar ashagwa6e,
"In har zaki cigaba dayi mun irin wannan wasan to kuwa tabbas wata rana zaki rasa nine,"
Fashewa ta kuma yi da wani kukan Sosai ta sanya mashi rigima,tana faɗin Wlh bazan yarda ba,Ae ni ba haka nayi maka ba,ka tayarmun da hankalina......"
Cikin sanyin murya Ya bata hakuri"Am really sorry,"
Girgiza kai tayi"a'a Bazanyi haƙurin ba,"miƙewa Yayi daga zaune"Yanzu me kikeso nayi maki?wanda zaisa ki yafe mun,"
"Frog jump"ashagwa6e ta bashi Amsa,
Zaro Eyes ɗinshi Yayi "Frong Jump"?Ya maimaita abunda tace,
Ɗaga mashi kai tayi"Eh shi nakeso kayi mun,"
"Zanyi kneeling agabanki,In baki haƙuri"
Bubbuga ƙafafunta Tayi"idan ba zakayi Tsallen kwaɗi ba,ni bazan haƙura ba......."
Ganin Ya tsareta da ido Yasa ta Fashe da wani sabon kuka Hawaye duk suka wanke fuskarta,A ruɗe Sgr ya Zuƙunna tare da kama kunnuwanshi,
"Can zaka tafi,idan kakai saika dawo nan,"da hannu take nuna mashi inda zaije,Bakinta ƙumshe da dariya,Sam bai kawo komai aranshi ba,Ya soma Yin tsallen kwaɗi ya nufi inda ta nuna mashi Ya juyo Ya nufo inda take,
Tuntsirewa Sehrish tayi da dariya Tare da buga tsalle Tana faɗin"Na rama !Na rama!"
Abun ya ɗaure mashi kai,Sakin kunnuwanshi Yayi tare da miƙewa tsaye yana kallonta,Tsantsar farin ciki Ya gani akan fuskarta,Kamar wadda akayi ma Albishir da gidan Aljanna,A ruɗe yace"Reesh are u ok"?
"bakaine kake sanyani Yin tsallen kwaɗi ba,lokacin da muna a gida?Yau nima Na rama,Na sanya Surgeon General Rafayet Tsallan kwaɗi,",tana kai ƙarshen Maganar,Ta watsa da gudu Ta faɗa saman faffaɗan ƙirjinshi Tana dariya,
"Ke ko"?ya faɗi hakan fuskarshi ɗauke da ƙayataccen Murmushi,Abun ma dariya ya bashi,Wai ta rama,Ashe abun ya tsaya mata aranta,kamar zautacciya Haka taci gaba da dariya tana faɗin "I luv u Ya rafayet!Mijina nakaina"
"I luv u too,matata takaina,"ya amsa mata cikin so da ƙauna..............."
💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃*HAPPY ENDING*
*💋Boss Bature💋
*Alhamdulillah!* *Alhamdulillah!!* *Alhamdulillah!!!💃💃💃💃💃💃💃*
*A nan na kawo karshen littafin Abban sojoji wanda na dau tsawon lokaci ina rubutawa😍*
_Dukkan godiya da yabo sun tabbata ga Allah subhanahu wata'ala,the most compassionate and the most omniscient,da ya bani ikon kammalawa cikin ƙoshin lpy kaman yadda na fara,to him be all the glory🙏,tsira da aminci su tabbata ga fiyayyen halitta Annabi muhammad(S.A.W)😍Darussan dake ciki Allah ubangiji yasa mu amfana dasu🙏 ya sadar da ladan gareni da mahaifana da yan'uwana da malamai na da dukkan masoyana a duk inda suke a faɗin duniya🥰kura kuren ciki Allah ubangiji ya yafe man🙏_
_Gaisuwar ban girma ga mahaifiyata Hajiya Rabi'atu Yahaya,she is my first luv and my everything💘,Allah ya ja da rai ya kara maki lafiya my sweetheart😘,My beloved Siblings💞waɗanda littafin nan Sadaukarwa ne a garesu,Nafisat,Aisha,Zainab,Khadija,maimunatu,Abdul'azeez,Fatima,Maryam,Ameenatu,I luv you so,so much,kune ni,in baku bani,I really appreaciate ur Encouragement💪,prayers and all-round support👍,Allah ya kara haɗa kawunanmu ya jiƙan mahaifinmu,Ameen_
_Special thanks to,Fadeela Lamiɗo,sadeeq Abubakar Ceo Lafazi writers,Abubakar Sadeeq AlQuramy,Maisalati,Kamala Kabeer,My Editor Aunty Zainab Laluh,whose contribution in no small measure serve as spices to this work,ina matukar godiya a gareki🙏da ƙarfafa man guiwa da kika rinka yi har zuwa kammaluwar wannan littafi ina rokon Allah kema ya baki ikon kammala littafinki lafiya Asanadin Maƙwabtaka😍and My P.A Munah Bature,ansha gwagwarmaya dae😂,ina matukar godiya agareki my other half😘_
To My Novel's Fans
Ba zan manta da yadda kuka rinƙa karfafa man gwiwa tsawon lokaci ta hanyar daɗaɗan Comment ɗinku,Summayer khutubi,Princess Bahilot,Meenarly Al'ameen,Oummi Sudeis,Asma'u Sani,Amjad (Mrs Rafayet),Maman shureim,ummu khaleel,maman aminu,Aunty hadiza,Xahra haroun,Hamida Yahaya ghandy,Asmieybash,Sadeeya attahuru kaoje,Zahra da sauran waɗanda bansamu na lissafo sunayensu ba,ina sane daku,ina matukar godiya a gareku ur comments means a lot to me,
Members of Comment Section 1&2,bansan da wane kalmomi zanyi amfani wurin gode maku ba,sai dae ince Allah ya barmu tare don ku din kun wuce fans kun zama yan'uwana agareni,
*JINJINA Ta musamman Ga dukkan Masoyan Littafin Abban Sojoji waɗanda suka Cire ƙyashi suka Biya kudin littafin Donsu karanta,ina magana akan Members Na paid group ɗina💃*
(1) Abban Sojoji
(2)Abban Sojoji Vip
(3)Junaid Romeo(Takun ƙarshe)
(4)Father Of Soldiars
*Allah Ya bar zumunci daga nan har Gidan Aljanna,Allah Yabiya maku dukkan bukatunku,Allah ya baku ikon Yin amfani da darussan dake acikin Labarin nan,Ina matuƙar godiya,Da irin haƙurin da kukayi,da kuma uzirin da kukayi mun har Allah ya bani Ikon Kammala Littafin nan,Yanzu gashi komai Ya wuce,Sai in Allah Yasa ina da rabon yin wani littafin kuma Ina fata zaku kasance A biye dani😰Zanyi missing dinku sosai*
*Littafin nan Ya ƙunshi darussa daban daban Na rayuwa,Ya ilmantar,Ya faɗakar,Ya kuma nishaɗantar damu💃💃💃*
*Wai ina mutanan dake cewa idan littafi yayi yawa ƙarshen shi baiyin daɗi😂da waɗanda kecewa Yayi tsawo yen yen yen Suka ishi mutane da surutu😂mahakurci mawadaci Yau dai Surutu akan Littafin Abban Sojoji Ya ƙare,No more Tsegumi No more Complain,No More typing No more Tension Boss Zatayi bacci hada minshari🥱🥱🥱*
*Hafsat Bature Muh'd*
*Boss Bature*✍️
*Ga masu Buƙatar Karanta Book na Abban Sojoji daga Book One zuwa 3 Complte Suyi mun magana ta whatsapp dina 0810388440*
********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.
Visit > https://www.aihausanovels.com.ng
Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.
Email > aihausabooks@gmail.com
******* FOLLOW US ******
Facebook: Ai Hausa Novels
Twitter: Ai Hausa Novels
Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels
WhatsApp Number: 08138873799
Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.
********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************
*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*
*🔥The Father Of Soldiers🔥*
ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ ﺭﺍﻓﻴﺖ❤🔥💞💘💖
*Story & Written by*
*Hafsat Bature Muhammad*
~💋BOSSLADY💋~
_Sabuwar Marubuciya, mai tafe da sabon salo💫_
*Abban Sojoji part 2*
*EPISODE 1*
Meaning Of Name *AMANI* means *wish* arabic name ne na mata🌹ina faɗin ma'anarsu ne saboda masu tambaya, sunaye ne masu kyau mutun zai iya amfani dashi in yana so wa baby girl ɗinsa😍
Ruwan sama ake yi sosai garin, yanayin yayi wani irin daɗin gaske, ga wata irin ni'imtacciyar iska wadacciyar da ta gauraye ko'ina, wurin ƙarfe 5 na marece ne amma sai kayi tunanin dare ne sosai saboda Lullumin da garin yayi, a wannan yanayin kowa na ƙumshe a bedroom ɗinsa saman gadonsa, lullu6e da bargo, baka jin hayaniyar komai ko'ina tsit a cikin gidan 😊
zaune suke acikin mota suna tattaunawa su biyu, Hafsat ce tare da wata Hamshaƙiyar mata wadda bansanta ba, jikinta na sanye da tsadadden leshi Ash colour, fara ce kana ganinta kasan taji hutu Over ya zauna mata, ita ce a mazaunin driver yayin da hafsat ɗin ke gefen ta suna tattauna wa,
Hafsat ta natsu tana sauraronta " Naci sa'a da nasamu address ɗinki kuma na same ki cikin sauƙi, kuma ina fata zaki taimaka mun wurin cimma burina,' matar ta faɗi tana kallonta,
Hafsat tace "ina sauraronki me kike so inyi miki ne "?
Murmushi matar tasaki kafin tace "Kafin na faɗa miki abunda nakeso, pls ina so ki fara bani acct number ɗinki,"
Bin ta da kallo hafsat tayi cikin mamakin jin abunda matar tace,
Amma batayi musu ba, ta shiga karanto mata numbar acct ɗin, ita kuma tana kwashe wa a wayarta dake hannunta,
Bata jima da gama karanta mata numbar ba sai ga Alert ya shigo a wayarta ƙirrrr!
Cikin sauri hafsat tasa hannu ta ɗauki ƴar purse ɗinta dake asaman Laps ɗinta ajiye, ta zugeta ta ciro wayar jiki na rawa ta duba, gabanta ne taji ya faɗi rass !! Ganin Alert na 6millions abun kamar a mafarki take ganinsa
Cikin tsananin mamaki ta ɗago ta kalli matar tare da cewa "Wannan fa? Na menene?
dariya matar tayi kafin tace " akwai wasu tagwayen Yara da Marshal Omar ya kawo gidan nan, Sunan su Hosana da Jahad,'
Jin sunan da ta ambata yasa hafsat kallonta cikin mamaki,.
Taci gaba da cewa "Ba wani aiki bane mai wahala, so nake subar gidan nan ! Suyi nesa da Marshal Omar..........'
Cike da mamaki hafsat ke kallonta , babban abunda ya ɗaure mata kai shine yadda akai tasan cewa Marshal Omar ya kawo yara acikin gidan,.
Daker ta iya cewa "Saboda Me za'ae hakan?
"Saboda basu da amfani," matar ta bata amsa a taƙaice,
Shiru hafsat tayi tana kallonta acikin zuciyarta tana Was wasi akanta,
"Wacece ke? Taya akai kikasan sunan Tagwayen tare da kuma sunan Omer?
"Ba buƙatar wannan, Kawai kiyi mun abunda nace in aikina yayi kyau nayi maki alƙwarin zan ninka miki abunda na baki har sau uku,
Hafsat tace "To shikenan ni zan wuce ciki sai kin jini"
Murmushi matar tasaki tare da cewa "sai mun sake haɗuwa,"
fito wa hafsat tayi daga Motar ta rufe mata sannan ta wuce cikin gidan da hanzari saboda ruwan dake sauka ajikinta,
Yayin da ita kuma Matar taja motarta ta fuce daga gidan fuskarta ɗauke da murmushin nasara,
tana shiga cikin babban falon ba kowa kai tsaye bedroom ɗinta ta wuce, cire kayan jikinta tayi shaf shaf ta canza izuwa riga da wando, ta ɗaure gashin kanta a baya, tana tsaye gaban Mirror tana tunanin maganar Matar nan data kawo mata ziyara sai ga Aunty Babba ta faɗo ɗakin tana faɗin "Hafsat wacece waccan matar da tazo wurinki yanzu"?
Juyowa hafsat tayi tana kallonta tace "Nima bansanta ba address ɗina aka mata shine tazo da buƙatarta,"
"Wace irin buƙata kenan"? Aunty babba ta tambaya tana kallonta,
Hafsat tace "Tayi mun magana akan cewa tana so in raba twins ɗincan da Omar ma'ana subar gidan nan gaba ɗaya, Suyi nesa dashi"
tsoki aunty babba taja tare da cewa "Ita kuma wacece ita isasshiya? halan Omar take so ne shiyasa ta biyo ta wurinki?.
"Bana tunanin hakan, Nafi tunanin Tasan Yaran ne shiyasa take son azubar dasu,"
"To ke kuma kin amince da buƙatarta kenan"?
Murmushi hafsar tasaki tare da cewa "eh mommy na amince da hakan, saboda anan take ta bani miliyan shida kuma tace muddin aikinta yaci ka zata ninkamin abunda tabani ynx,"
tuni aunty babba ta haɗe fuska rai a6ace tace "Amma ke shashashar ina ce? Kawai daga zuwan mata sai ki amince mata da buƙatarta? matar nan fa Omar take so shiyasa takeson a salwantar mata dasu,"
"Koma dai menene Mommy ni bazan bari kuɗin nan su wuce ni ba, saboda ina cikin buƙatarsu, daddy baya sakarmun kuɗi yadda ya dace ke kuma tanadin ki na zuwa wurin bokane kema fa bakya bani ko sisi Burinki akan hayaam da Abrah ne," .
Matsawa Aunty babba tayi kusa da ita tana cewa "Hafsat Anya kina cikin hayyacin ki kuwa? Ni kike faɗama haka"?
"Na faɗi wani abune daba dai dai ba? ta tambaya tana kallon mommyn nata, Ido cikin Ido
Sassauta Murya Aunty babba tayi a ƙoƙarinta nata fahimtar da hafsat tace "duk wannan tanadin da nake saboda kanmu ne fa ! Ƙaruwar mu ce, in har naci nasara akan burina Hayaam tasamu RAFAYET ita kuma Abra tasamu MARSHAL OMAR mune zamu ji daɗi, don haka am commanding u ki tattara kuɗin da tabaki ki mayar mata dasu yanzun nan !!!! ta faɗi a tsawace
Dariya hafsat ta kwashe da ita hada tafa hannu bayan ta tsagaita tace "Mommy kenan !! nima fa lashe Money ce kamarki, bazan bari garabasar nan ta wuce ni ba!! Akace da arziƙi a gidan wasu ƙwara agidanku, kai agidan nakuma kwara a ɗakinku, a ɗakinku ɗin ma ya faɗo akan ka, don haka ni baxan mayar mata da kuɗinta ba!!!!!!!!!
Gaba ɗaya hankalin aunty babba ya tashi don alamu sun nuna cewa Hafsat fa kamar bata cikin hayyacin ta, cikin ruɗi tace "Hafsat anya kina cikin Hayyacinki kuwa"?
Shu'umin murmushi hafsat tasaki sannan tace "Kwarai kuwa! nice dae ƴarki Hafsat ɗiyar general ishaq, jika ga Abban sojoji"
Jinjina kai aunty babba tayi tabbas an samu matsala, domin kuwa tasan Hafsat bazata ta6a fasa abunda tayi niya ba,
Huci kawai take yi tana jinjina kanta a ƙarshe ta fuce daga ɗakin,
Duk wannan suratan da Hafsat su kayi da aunty babba a kunnan Hosana wadda ke la6e a ƙopan ɗakin, jin Takon tafiyar Aunty babba yasa ta gudu izuwa cikin