Author : Boss Bature Category : Complete Novels
yayi alamar eh,
"Okey ka koma daga waje,kasha kallo kawai,"
Wani irin farin ciki ne ya rufe junaid cikin sauri ya fuce tare da komawa wurin sehrish dake tsaye,sam bata ji zuwanshi ba saboda idonta na akan Sgr dake acikin filin wasan,
Hannu yasa tare da ɗan bubbuga kafaɗarta,a firgice ta juyo tana kallon fuskarshi,
"Ko tausayina ma ba kiji ba,kina tsaye kina kallon yarda suke ta wahalar dani,maimakon ki shigo ciki ki ramamun,".
dariya sehrish tayi tare da cewa"junaid nifa nasan ciwon kaina,taya zaka shige cikin waɗancan garadan masu fuskar shanu kace wai zaka buga ball dasu,ae sunfi ƙarfinka,gayanan duk sun wahalar dakai abanza,
ɗaure mata fuska yayi yana murguɗa mata baki,
girgiza kai kawai tayi tana dariya kafin daga bisani suka mayar da hankalinsu kan filin wasan,
Tashin hankali,ƙananun namun dawa sunyi arba da zaki,
Sai faman mazurai suke yi suna kalon shi,kusan su shida ne acikin ragar,in aka haɗa da sgr sun zama su Takwas kenan,gaba ɗaya duk sun sha jinin jikinsu saboda sun san mai zai biyo ba,dama tun alokacin baya idan yazo nigeria da zarar yaji hannunshi nayi mashi ƙaiƙayi,sai ya tara duka acikin ragar suyi Boxing,ba ƙaramin bugu yake yi masu ba,duk yawansu haka zai tarwatsa su,
Hannu yasa tare da cire rigar jikin shi nan take ƙirar nan mai tsoratarwa ta bayyana,wurga ma junaid rigar tashi yayi cikin sauri yasa hannu ya cafke ta,
"Junaid bani na ruƙe mashi rigar,"acewar sehrish,
Miƙa mata rigar junaid yayi hankalin shi na a field din,hannu tasa ta kar6i rigar tare da kaita saitin hancinta tana shinshina ƙamshin turaren jikinta,rungume rigar tayi sosai ajikinta,sannan ta mayar da idanunta akan wasan nasu,
Tunda suka ga Sgr yakai hannu tare da ɗaukar kwallon yana bubbugata ƙasa tana dawowa cikin tafin hannunshi,yayin da kyawawan idananuwan nan nashi ke binsu ɗaya bayan ɗaya yana kallonsu,hakan ba ƙaramin tsoratasu yayi ba,
Wani daga cikinsu ne yace"Wlh kwara kowa yayi ta kansa da alama watan cin ubanmu ne ya tsaya,"
Yana ƙarasa maganar tashi ya nufi hanyar fita daga cikin ragar da gudu zai tsere,sai dae ina kafin ya ƙarasa fita,Sgr yasa ƙafarshi tare da buga ball ɗin da ƙarfin gaske kai tsaye ta sauka a tsakiyar goshin shi,wani irin jiri ne ya ɗebe shi sai gashi ƙasa a baje yana faɗin"la'haula wala ƙuwata illa billah ,'
.gaba ɗaya Sehrish da junaid suka shiga 6a66aka mashi dariyar mugunta hada dafe ciki,
Ganin haka yasa sauran suka yi hanzarin ɗaukar ball ɗin don ayi wasan dagaske,gaba ɗaya suka kacame suna ƙoƙarin ganin sunci nasara akanshi,ba ƙaramar wahala sukaci a hannun Sgr ba,domin kuwa da mugunta ya dinga buga masu kallon da wasa da wasa sai da yayi masu jina jina a hancinansu,dama ba wasan yakai shi cikin ragar ba,ganin yarda suke nuna ƙarfi wurin junaid yasa shima ya shiga don ya nuna masu cewa gaba da gabanta fa,
a nan yabarsu baje ƙasa saman grass carpet ɗin sai faman wash wash suke yi,gaba ɗaya sai da ya tabbatar da cewa ya gama raunata ga66an jikinsu sannan ya fito daga cikin ragar,
da gudu junaid ya ƙarasa wurin shi tare da rungumo shi ta baya fuskarshi ɗauke da dariya yake faɗin"My hero man,u did a good job,naji daɗi da ka ramamun nasan daga yanzu bazasu sake gigin ta6ani ba,"
Hannu Sgr yasa tare da janyo junaid ya dawo ta gabanshi suna fuskantar juna sannan yace"junaid,u ave to be ur own hero,wannan ne burina,banason kana abu tamkar ba namiji ba,kai fa jini na ne!"
murmushi junaid yayi tare da ɗan sunnar dakai cikin jin kunya yace"insha Allah babban yaya zan zama kamar yarda kakeso,"
"Yawwa,haka nakeson ji,ina rigata ne"? Ya tambaya yana kallon shi,
juyawa juanid yayi yana kallon Sehrish dake rumgume da rigar sgr a hannunta,
Murmushi yayi tare da cewa"Tana a wurin sehrish,ita tace na bata ta ruƙe maka bari na kar6a maka,"
Juyawa yayi zai tafi,cikin sauri Sgr ya ruƙo rigar jikinshi tare da cewa"zan amsa dakaina,wuce ka shiga cikin gida banason ganinka haka,kayi wanka sannan ka huta sosai,'
Amsa mashi yayi da toh sannan ya kama hanyar zuwa cikin gidan da dan gudu² kamar yarda ya umarta,
A natse ya soma tafiya har ya isa inda sehrish take atsaye ƙanƙame da rigarshi a hannunta,sam batasan meke wakana ba,ta manna rigar a hancinta idonta a rufe tana shaƙar kamshin turarenshi,da alama ba ƙaramin yanayi ta shiga ba,
koda ya ƙarasa inda take tsaye,idonshi na akan rigar shi dake rungume ahannunta,hannu yakai tare da ruƙo rigar zai janyeta daga hannun sehrish,ae kuwa cikin rashin sani sehrish ta ƙara ƙanƙame rigar alamar bazata saki ba,duk a tunaninta junaid ne zai kar6i rigar,batasan cewa mai rigar bane yazo dakan shi,
a karo na biyu ya ƙara kai hannu zai ruƙo rigar,cikin sauri sehrish ta cafke hannun shi tare da yin wurgi dashi gefe guda,fuskarta tamkar zatayi kuka tace"dan Allah junaid menene haka,bana ce kabarmin rigarba,zan kai mashi ita dakaina,"
Sai da takai ƙarshen maganar,sannan taso ma tunanin wai hannun wanene ma ta ruƙo!tabbas wannan ba hannun junaid bane akwai bambanci sosai ko ta wajen girman hannun,
A hanzarce ta Buɗe idanunta tare da sauke su akan ƙafar Sgr dake tsaye agabanta,wata irin zufa ce ta soma kartomata a fuskarta,nan take ta soma haɗiyar yawu,sai faman mazurai takeyi tana zazzare idanu,
Ja da baya ta ɗanyi murya na rawa a hankali ta shiga ambaton"nashiga ukuna!ashe shine da kanshi,wayyo Allah na wlh nayi tunanin junaid ne........'
Bai bari ta ƙarasa maganar ba,yasa hannu tare da kar6e rigarshi,sannan ya wuce izuwa cikin gidan batare da ya zura rigar ajikin shi ba,
ajiyar zuciya sehrish tashiga saukewa hannunta na dafe da saitin zuciyarta,a haka ta nufi cikin gidan tana zullumin karsu haɗu dashi,bakomai tafi ji ba fa ce yarda tayi wurgi da hannunshi cikin rashin sani,tabbas a lokacin da bai kai zuciya nesa ba,Mari zata sha zazzafan gaske,amma sanin cewa ba da gangan tayi bane yasa baiyi mata komai ba,
_💋Boss Bature💋_
Ba ƙaramin bacci hossana da Omar suka sha ba ahaka,har lokacin jahad na a cikin bedroom ɗinsu kwance saman gadon bacci yayi awon gaba da ita,hannunta na rungume da zanen fuskar junaid da tayi,ta ƙanƙame shi a ƙirjinta kamar wani yace zai ƙwace mata shi,
wuraren ƙarfe ɗaya,Omar ya farka a hankali ya buɗe eyes ɗinshi yana faman sauke ajiyar zuciya,mayar da idanunshi yayi akan hossana dake ƙanƙame dashi,gaba daya ta zura hannayenta tare da ruƙo waist ɗinshi,kanta kuma na akwance saman kafaɗarshi sai sharar bacci takeyi abunta,gashin kanta ya zuba harya rufe side face ɗinta,
A hankali yasa hannunshi tare da ruƙo curly hairs din nata,yayi gefe dashi izuwa saman bayanta,hakan ya bashi damar kallon fuskarta da kyau,ba ƙaramin kyau tayi mashi ba,musamman yarda lips ɗinta ke motsi,dama jazamun ne hossana bata iya bacci batare da la66anta na motsi ba,haka zalika yatsun hannunta kullum cikin kerma suke saboda sabo da 6arna,
Hannu yasa tare da shafa gefen fuskarta,kafin ya mayar da fingers ɗinshi a saman brownish lips dinta,a hankali yake shafa tausasan la66an nata da hannun shi,dan tunani yayi hakan yasa ya fara ƙoƙarin janye yatsan nashi yaji ta cafke shi da bakinta,sucking ɗinshi ta shiga yi batare da saninta ba,
Murmushi Omar yayi yana kallon yarda ta ƙankame mashi yatsanshi acikin bakinta,tana tsotsa kamar wata jinjira,
Da farko ya ɗauki abun wasa,amma daga bisani sai ya dinga jin wata irin kasala na rufe shi,lokaci guda ya soma shiga yanayi na son kasancewa da ita,hakan yasa cikin sauri ya zame yatsanshi daga mouth ɗinta gudun karya jefa kanshi cikin matsala,
Lalla6awa yayi tare sanya hannunshi ya janyeta daga saman kafaɗarshi ya kwantar da ita saman sofa ɗin,sannan ya miƙe tare da ruƙo ƙafafunta ya haura dasu saman kujerar,
Sannan ya dawo tare da zuƙunnawa adai² saitin fuskar hossana yana kallonta,
A hankali yace"Me zan buƙata bayan wannan arayuwata?na mallaki komai da nake buƙata a duniyar nan,nagode ma Allah daya haɗani da ƙaddarata cikin sauƙi batare da nasha wahala ba,tana sona sosai,kuma insha Allah bazan karya mata zuciya ba,a shirye nake dana mallaka maki kaina....duk da takasance mai ta6in hankali,a haka nake ƙaunarta,shi so babu ruwan shi da wannan,burina nasamu wacce take sona tsakani da Allah badan wani abu dana mallaka ba,gashi kuma nasamu,ita wannan bata da cikakken hankalin da zata iya sona don wani abu,burinta kawai Ya omar ɗinta ya kasance atare da ita ko da yaushe....zanje kawai na sanar ma Abbana cewa,Nifa na isa aure,kuma na samu wadda ta dace da rayuwata,yarinyar ta kwanta mun araina sosai tun ranar dana fara ganinta,ashafa fatiha kawai Abba akaimun ita ɗakina,me ya fi wannan?
ya ƙarasa maganar cike da zolaya yayin da fuskarshi ke ɗauke da ƙayataccen murmushi,
yunkurawa yayi tare da miƙewa sannan ya juya cikin sauri ya fuce daga palourn saboda kiran salla da ake ta faman yi,
sam ƙafafunta sun gaza ɗaukarta,jikinta ba ƙaramin sanyi yayi ba,ashe tun lokacin da Omar yake zukunne agaban hossana yana furta waɗannan daddaɗan kalaman nashi take a tsaye tan sauraron shi,
Bata jima da farkawa daga bacci ba,fitowarta kenan tayi arba da wannan tashin hankalin,
Allah sarki jahad,sosai tayi kuka daga tsayen da take,tama rasa kukan me take yi,shin na farin cikin cewa Omar yana son ɗaya daga cikinsu ne,ko kuma na baƙin cikin cewa Hossana yake so ba ita ba?
Jiki asanyaye ta ƙarasa cikin falon,adai dai inda Omar ya zukunna saitin fuskar hossana dake kwance saman 3 seater ɗin, itama adai dai nan taje ta zuƙunna tana kallonta,sai faman sharar bacci takeyi,
Cikin shessheƙar kuka jahad ta soma magana da wannan sanyayyiyar muryartata,
"Ho..hos...sanah....ni bazanyi baƙin ciki dake ba,sam banji kishi ba da Ya omar ya bayyana soyayyarshi agare ki ba,duk da naso ace ni na mallake shi ba don komai ba sai don burin da nake dashi na ganin cewa na saka mashi da irin kyautatawar da yake yi mana,wannan ita kaɗae ce hanyar da zamu iya faranta mashi,idan har ya auri ɗaya daga cikin mu ni ina da tabbacin cewa bazai ta6a danasani ba,kawai abunda nake tunani shine,banda tabbacin cewa Hossana zata iya kyautata mashi sosai amatsayinta na wadda take da ta6in hankali,bansani ba ko hossana zata iya faranta mashi ba,idan har ya aureta taya zata iya ɗaukar dukkan wata buƙata tashi,taya zata iya?that's the reason why naso ya aure ni kenan saboda ni ina da cikakken hankalin da zan iya yi mashi komi yakeso,zanyi mashi biyayya sosai,zan bishi sau da ƙafa,amma sai dae kash ni ban samu wannan damar ba,hossana ke kika samu wannan damar,hossana you're among the most lucky women in the world,ina tayaki farin ciki sosai,ki tashi kiyi godiya ga ubangijinmu Allah subhanahu wata'ala daya mallaka maki kyakkyawar zuciya irinta ƴa' Omar,that's the most greatest gift hossana,"
jiki asanyaye jahad ta ƙarasa maganarta,sannan ta miƙe a kasalance tana ja da baya da baya,yayin da idanunta ke ci gaba da zubar da hawaye,
"Shi kaɗaine namijin da nake da burin na aura aduniyar nan,akan shi ne nafara jin so,na kuma son ya raɗaɗinsa yake,a duk lokacin da mutun ya rasa abunda yake so,"
juyawa tayi da gudun gaske ta koma cikin bedroom ɗinsu tare da faɗawa saman gadon nasu,tana ci gaba da kukan da takeyi,
Cikin kuka take faɗin"na rasa first love ɗina,Ya Allah ka bani makamancinshi duk da nasan cewa zaiyi wuya nasamu kamar shi," hannu takai tare da janyo drawing book ɗinta,ɗago da kanta tayi ta zuba ma zanen fuskar junaid ido tana kallon kyakkyawan murmushin nan nashi,
Nan take taji wani irin sanyi ya ratsa zuciyarta,hannu tasa tana shafa zanen,tana ci gaba da kallon shi,kamanceceniyar su da Marshal omar har taso tayi yawa,saboda junaid fuskar Abbansu ce sak,kuma marshal omar yana ɗaya daga cikin masu kama da abban nasu sosai,hakan yasa kamarsu ta fito sosai,
(Tashin hankali,son maso wani,junaid nason sehrish,ita kuma Rafayet takeso,yayin da shi kuma rafayet har yanzu baisan menene So ba,ga kuma jahad tafara faɗawa tarkon junaid,Ya kenan?)
A ƙarshe Ina taya Hossana murna,dama bai cancanta tasha wahalar soyayya ba,kasancewarta mai ta6in hankali,in har bata samu abunda takeso ba,to fa acan dawanaun kano zamu tsinto ta,amma duk da hakan kuna tunanin cewa Zasu samu Juna cikin sauƙi ita da marshal Omar!???????????
Tuni su Hayaam sun jima da barin maid suna kan hanyarsu ta zuwa Abj,kafin ta bar gida sai da Mamynsu ta haɗata da magungunan data amso mata a wurin bokansu,kala kala wanda zata yi amfani dasu na mallaka,akwai na shafawa ajiki,da wanda akeyin turarensa,da kuma na zubawa acikin abinci ko abunsha wanda za ta zuba ma Sgr,tsaf ta kammala shirya komai saura aikatawa kawai ya rage,
(Nace ba, Allah ya ba mai rabo sa'a)
jin shiru babu kowa acikin gidan ya ba Amal damar tashi daga saman katifar da take kwance tana jinya tun jiya,ba ƙaramin jiki taji ba baiwar Allah,tazama abun tausayi ga yunwa ga ciwo ga kuma rashin wanka,
dakyar ta iya fitowa daga cikin ɗakin adaddafe take tafiya,tsayawa tayi tana tunanin mai yakamata tayi,
Babu kowa a tsakar gidan,tun bayan da Sofwan yazo ya ɗauki Hayaam,Mammynsu da Abra suka fita rakiyarta daga can kuma suka wuce gidan makwabtansu,gidan da suka saba zuwa zaman kashe buje,daga kaga mata sun taru agidan toh fa tsegumi ne da gulma yakaisu,tun daga kan sunan matar gidan zakasan cewa ba ƙaramar guyababba bace,suna kiranta tsigai acan suke kai Amal wurinta in Amani tazo,su rufe ta aɗaki don karsu haɗu da ƴar uwarta,
Shiru Amal tayi tana tunanin abunda ya dace tayi tunda babu kowa agidan yanzu lokaci ne da yakamata ta yanke shawarar yarda zata haɗu da ƴar uwarta,
Cikin sauri ta nufi ɗakin Mammynsu abrah gabanta na faɗuwa tsoranta karsu shigo su tarar da ita,a hankali tasa ƙafa ta shiga cikin ɗakin nata,tsayawa tayi tana faman waige waigen inda zata samu koda waya ce,
Karaf idonta suka sauka akan kuɗaɗen dake baje saman gadon Mammynsu,sabbin ƴan dubu dubu,da alama mantasu tayi a wurin bata kwashe su ba,
nan da nan tunanin Amal ya kasu kashi biyu,
"Amal kina buƙatar kuɗin da zaki je wurin Auntynki!wannan dama ce agareki,yakamata kiyi hanzarin kwashe kuɗin nan kafin su dawo,ki tattara kibar masu gidan,Amal kada ki bari damar nan ta wuce ki!!!ki je ki ɗauka!ki ɗauka mana!Amal ki tafiiiii!!!!!!!"
zazzare ido tayi lokacin da taji abunda zuciyarta ke sanar da ita,
Wani tunanin kuma ya sake zuwa mata
"Amal kada ki ta6a kuɗin nan!wannan sata ce,in kika ɗauke su Allah zai kamaki!ki hanzarta barin ɗakin nan tunkafin kiyi danasanin zuwan shi!kiyi haƙuri kibarma Allah komai mai wuce wa ne,"
Runtse ido Amal tayi yayin da idanunta ke fitar da hawaye masu zafin gaske,
"Ni ba 6arauniya bace,bazan ɗauka ba,saboda bana son Allah ya kama ni da laifin sata," cikin shessheƙar kuka ta furta hakan abayyane,
Sannan jiki asanyaye ta kama hanyar fita daga ɗakin,har tasa ƙafa zata fita daga cikin ɗakin,kwatsam kwakwalwarta ta soma tariyo mata wani abu daya ta6a faruwa,a lokacin Mammy tayi ma Amani ƙaryar cewa za'a je nemo Amal,amma ana buƙatar kuɗi saboda za'a haɗa da manyan malamai domin suyi addu'ar neman dace wa,jiki na rawa Amani ta turo da kuɗi kusan dubu ɗari uku acikin acct ɗin Abra da niyyar akaima malam kuɗin don suyi addu'a akan lamarin,A ranar da abra ta ciro kuɗin a banki,tunkafin tadawo gida ta wuce kasuwa tayi masu siyayar kaya masu yawan gaske,
ƙiri-ƙiri suka hana Amal ko sisi acikin kuɗin nan,kuma ita mammy da kanta ta kira Amal tare da jan kunnanta ta janyota har cikin ɗaki ta nuna mata kuɗin da Amani ta turo da kuma kayan da suka siya saboda rashin imani, aranar Amal tasha kuka sosai,
Cike da ƙwarin guiwa Amal tace"Bazan bar kuɗin nan ba!haƙƙina ne su!nima sunci mun kuɗina,"
Cikin sauri ta juya tare da nufar cikin ɗakin,kai tsaye ta tunkari gadon Mammyn tasu,hannunta na kerma zufa na tsastsafo mata a fuskarta,haka tasanya hannu tare da tattara kuɗin gaba ɗaya ta haɗesu guri guda acikin hannunta,a ƙalla sunyi dubu hamsin,
kamar daga sama taji motsin wani ya faɗo acikin ɗakin,a wani irin firgice Amal ta watsar da kuɗin tare da juyawa tana kallon bakin ƙopar shigowar idonta azazzare~~~~~~~~~~
Wannan kenan
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku
It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining.
Snack
Awarah
Farah
Zobo
Samosa
Cup cake etc
Contact me 09063302182or 09012179727.
Kada abaku labari
********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.
Visit > https://www.aihausanovels.com.ng
Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.
Email > aihausabooks@gmail.com
******* FOLLOW US ******
Facebook: Ai Hausa Novels
Twitter: Ai Hausa Novels
Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels
WhatsApp Number: 08138873799
Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.
********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************
_💋Boss Bature💋_
Join this link to follow my tiktok acct👇