Advertisements
Chapter 161 Reading Abban Sojoji Takun Karshe complete by Boss Bature BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Abban Sojoji Takun Karshe complete by Boss Bature

Author :  Boss Bature Category :  Complete Novels

Chapter   161 / 231

480K to 483K   out of 690.9K words

da cewa "naga missed Calls ɗinta, na manta nabi kiran nata that's why,"
Jinjina kai Omar yayi kafin ya kuma cewa "Har yanzu baka yanke shawara bane game da ita? Pls bro kodan saboda Uncle Donald yakamata ka sassauta mana....'
Wani irin kallo Sgr yake binsa dashi kafin yace "Uncle ya riga da yasan tsarina, ko shi kansa ya tsawatar mata akaina amma taƙi ji so ni banson ya zanyi na fahimtar da ita ba,"
Omar yace "matsalar kenan, ni abunda yafi damuna taurin kanta, in banda ƙarfin hali irin nata taya zata ce dole sai kai zata aura? a ƙalla EVA ta baka kusan 10years aduniya, har yaushe ne zata daina wannan mafarkin? ya tambaya yana kallonsa,
Sgr yace "Omar da ace zan iya canza ra'ayi na akan mace ,to ina mai tabbatar maka da cewa ita ce mace tafarko da ta cancanta ta mallake ni, saboda kusancin dake a tsakani na da ita..................."
Karaf!! Maganar Sgr ta sauka a kunnan Sehrish wadda fitowarta kenan ta nufo cikin babban falon, har ta kammala shiryawa tsaf, ta zumbula jalbaba ajikinta har ƙasa maroon colour, hannunta na ruƙe da hand bag, ƙafarta kuma na sanye da flat shoes launin hijab ɗinta, fuskarta sam babu makeup ƴar hoda ce kawai ta shafa sai ta murza man baki a la66anta, amma ba ƙaramin kyau tayi ba, tsayawa tayi jiki amace tana sauraron firar tasu sam tagaza motsi, har sai da Marshal Omar ya ɗago da idonsa ya kalle ta, gabansa ne yaji yayi mugun bugu sam yagaza ganewa wannan ruɗanin dake a fuskar yarinyar nan, Sehrish bata lura da kallon da Omar keyi mata ba, juyawa Sgr yayi don yaga me Omar yake kallo ne karaf idonsa suka sauka ana sehrish wadda itama idon nata na akanshi, from up to down ya kelle ta kafin yace "Ke zonan," gabanta ne taji ya faɗi rass tayi firgit tana kallonsu, hankali atashe ta tunkare su gabanta na ɗarr!ɗaarr ta ƙarasa inda suke dab da Babban yayan nasu daya kira ta, Hannu yasa tare da ruƙo jalbabar dake ajikinta, saboda tsananin tsoro sai da sehrish ta kusa sakin fitsari tuni jikinta yasoma kerma kaf!kaf !!kaff!
cikin sanyayyiyar muryar nan tasa ta natsastsu yace "Menene wannan haka ajikin ki,"? Ya tambaya in serious matter batare da ya aza idonsa akanta ba,
Murya na rawa sehrish tace"hi..hij..hijabi ceeee...'
"Masallaci zaki je ne"? Ya tambaya yana jiran amsa,
"A'a fita zamu tare da aunty azmee,"
Cire hannunsa yayi tare da nuna mata hanya yace"maza ki koma, ki cire wannan abun, bana son sake ganin shi," cike da mamaki Omar ke kallon sgr har dai yagaza yin shiru yace "Rafayet nan fa ba Us bane Nigeria ce, kuma wannan shine best outfits da yace mace musulma tayi, Domin rufe surar jikinta daga jan hankalin mutane akanta saboda tsaro,'
girgiza kai sgr yayi tare da cewa "ban yarda da wannan shigar ba, shin Omar taya mutun zai iya motsi acikin wannan abun"? Ya tambaya yana nuna hijabin jikin sehrish,😂
Fashewa da dariya Omar yayi kamar kamar me, ganin yarda Sgr ya haƙiƙance akan hijabin dake ajikin yarinyar, shi a ganinsa takurace kuma mutun bazai iya motsi acikinta ba, daƙer ya dakatar da dariyar tasa ya kalli sehrish tare da cewa "Ki faɗa masa yarda kike motsi acikinta may be ya fahimta,"
ɗan murmushi sehrish ta saki ita kanta abun ya gama ɗaure mata kai, ɗagowa da hannayenta tayi tare da cewa "Ga hannun hijabin nan, tun da na fiddo da hannun acikinsa lafiya lau nake motsi acikinta," ta ƙarasa bayanin tana kallonsa
Jingina bayansa yayi ajikin sofa ɗin tare da cewa "Its Okey, u can go,' har ta juya zata tafi Omar yace "Ya Sunan ki ne?
Juyo wa tayi ta kallesa da murmushi a fuskarta tace"SEHRISH"
Omar yace "masha Allah suna mai daɗi, amma menene ma'anarsa? ya tambaya yana kallonta,
*kyawawan halayyu na mutun,"
ta bashi amsa,
*ina fata zaki nuna mana waɗannan kyawawan ɗabi'un acikin gidan nan, har ma ki zama alkhairi agare mu," omar ya faɗi da ɗan murmushi a fuskarsa, duk Sgr na sauraronsu duk da ya ci gaba da dannar wayarsa,
Sehrish ta amsa masa da cewa "Insha Allah," sannan ta wuce
Sai lokacin Sgr yace "Ashe kana surutu har haka Omar?
Kallonsa Omar yayi tare da cewa"Yarinyar ce tana tattare da wani abun al'ajabi a fuskarta shiya sanya Na sake mata,"
"Ba kowace baƙuwar fuska yakamata ace kana sakemawa ba irin haka ba, Mata Basu da tabbas they're trouble makers," acewar Babban yaya,
ƴar dariya Omar yayi batare da cewa komai ba,
Sehrish kuwa kitchen ta wuce ta zubo musu coffee tare da snacks a plate Cikin tray sannan tadawo inda suke tare da ajiye masu saman Table, Omar yace "thank u miss Sehrish,"
Murmushi tayi masa sannan ta juya ta nufi ɗakin azmee tunkan ta ƙarasa ɗakin nata sai ga Azmee ta fito itama ta kammala shiryawa cikin atampha ja, ta aza babban mayafi milk colour launin takalminta ƙafarta, atare suka fuce suna jiran isowar junaid,
Ba da jimawa ba sai ga junaid ya fito daga upstairs yana saukowa down sai faman zabga murmushi yake yi, jikinsa na sanye da haɗaɗɗiyar shadda gezner blue colour mai maiƙo sai faman ɗaukar ido yakeyi kai kace wani sabon ango ne, shaddar tasha aiki a wuyanta tsantsararre, hannunsa na ruƙe da wayarsa haɗe da key ɗin motarsa,
Lokacin daya ƙarasa saukowa daga saman stairs ɗin, gaba ɗaya Marshal Omar da Sgr suka bishi da kallo,
Zagayawa yayi inda babban yayan nasu yake yana isa ya manna mashi kiss agefen fuskarsa sannan yace "Zan fita, saina dawo," ko amsa bai jira ba cikin sauri ya lalla6a ya fuce yana cewa "yaya Omar kayi masa bayani, mu mun wuce ,"
Girgixa kai kawai SGR yayi sam ya kasa magana, wato junaid yasan cewa zai iya dakatar dashi daga fita shine yayi dabarar tserewa,
Murmushi Omar yasaki tare da cewa "Junaid kenan ! komai nasa na burgewa, ya cika ƙiriniya ga shegen wayon tsiya, saboda kada ka hana shi fita shiyasa ya gudu bai jira amsarka ba," yayi maganar yana kur6ar coffee ɗin da sehrish ta kawo masu a cup,
"Ina zasu je ne"? Sgr ya tambaya yana kallonsa, Omar yace "Gidan Uncle Abusufyan na aikesu, inaso zanyi amfani da gidan ne akwai wasu marayune da zan zuba acikinsa kwanan nan,"
Sgr yace "Omar kenan, meyasa baka sanarmun ba? ko ni ba'a buƙatar gudummuwata ne? ya faɗi yana kallonsa,
Murmushi Omar yasaki dama sun saba indai irin haka ne, muddin akace aikin lada yasamu, to har rububi suke yi wurin bada taimakonsu, kowa burinsa ace da dukiyarsa za'ayi amfani wurin bada tallafi sam basa gajiya da irin wannan (Kaji masuyi don Allah) Shiyasa dukiyar tasu kullum hau hawa takeyi kamar kamar me, a ƙalla su kansu basu son adadin gidajen marayun da suka buɗe ba a kasashe daban daban kuma suke ɗaukar ɗawainiyarsu da komai, Manyan asibitoci kuwa da suka buɗe ba iyaka, wanda suma duk kyauta ne ake duba marasa lafiya acikinsu, ga makarantu na marayu da marasa hali da suke dasu ba adadi, wannan ba komai bane ba, kaɗan ne daga cikin abubuwan da suke yi na taimako, Ya Allah ka bamu arziƙi mai albarka wanda zamu amfana dashi kuma ƴan uwanmu musulmai suma su amfana dashi, ba irin arziƙin da mutun zai mallaƙe ba, ka ga ko cikin gidansa fama ake dashi basa ciyuwa balle na waje su samu😧

*****GIDAN ABUSUFYAN*******

Haɗaɗɗiyar daula, Aljannar duniya tun daga kan Tanƙameman gate ɗin gidan Golden colour & brown sehrish ta saki baki tana kallo Ikon Allah, Ba don daga gidan Abban sojoji ta fito ba da sai tace wannan gidan a dubai yake, tsayar da motar junaid yayi abakin gate ɗin sannan ya fito daga cikin Motar, ya nufi jikin gate ɗin, tunkan ya isa ya danna madannin da ke ajikin key ɗin gidan a hankali gate ɗin ya soma zugewa da kansa daker daker yake tafiya saboda gidan ya jima ba'ayi amfani dashi ba tunda Abusufyan yabar Nigeria a fusace gidan yake ahaka garƙame, ganin zai 6ata musu lokaci yasa junaid sanya hannunsa yana ƙoƙarin turasa da ƙarfinsa don yayi saurin f
Buɗewa, aikuwa nan take zufa tasoma wanko masa kamar wanda aka watsa ma ruwa a fuska dama jiki bana wahala ba, muryarsa kamar zaiyi kuka yace "Aunty Azmee wai bazaku fito ba mu tura, Wlh ban iyawa ni kaɗai,"
Jin hakan yasa su fitowa daga cikin motar suna faman tikar dariya, azmee tace"Haba junaid wannan fa ƙaramin aiki ne, sai kace ba Namiji ba haba karka ban kunya mana, Be a Man,'
Kallon azmee yayi yana faman sauke haƙi yace"In dai saina tura wannan jibgegen gate ɗin zan zama namiji, to Allah abarni a jinsin mace yafi mun,"
Fashewa da dariya sehrish tayi har tana dafe ciki jin abunda junaid yace, harara ya watsa mata yana hura hanci,
Azmee na isa jikin gate ɗin tace"Matsa ka gani junaid, ni bari in zama Namijin, ni kaɗai zan tura sa,"
Jin haka yasa junaid matsawa suka bata wuri don ta jaraba, gefen Sehrish ya tsaya suka zuba ido suna kallon azmee,
Hannu tasanya sannan ta soma tura gate ɗin nan take ya tafi da gudun gaske ya ƙarasa zuge kansa,
Zaro ido Junaid da sehrish su kayi cikin tsananin mamakin ƙarfi irin na AZMEE,
A ruɗe junaid yace"Aunty azmee taya hakan ta faru? Ni nakasa turasa amma ke kina aza hannu gate ɗin ya buɗe,"
Murmushi azmee ta saki tare da nuna masa damtsen hannunta tace "Tsohon ƙashi kenan! ba irin naku ba na ƴan shila,"
Fashewa su kayi da dariya su duka kafin daga bisani suka koma cikin Motar, junaid ya shigar da ita cikin gate ɗin kai tsaye yayi parking ɗinta a harabar gidan

*Shin Kuna tunanin Cewa Omar zai samu damar ɗauko su hosanna da Jahad daga gidan Aunty babba*?😟

Ku hanzarta yin payment 300 ne ga acct 3196407426 Bature Hafsat Muhammad first bank, sai aturomin shaidar biya ta numberta 08103884440, idan kuma recharge sai ayimun magana ta numberta,👍👏*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*
•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
──────────────EPISODE 19-20

ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ
ﺭﺍﻓﻴﺖ💋❤️

*Mallakin Hafsat Bature Moh'd*
~BossBature~
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•

Remain 3 pages Only free ya ƙare👏

bayan sun fito daga motar kai tsaye suka nufi hanyar da zata sadaka da babban falon gidan, Sehrish sai faman bin ko'ina take da kallo aranta tana cewa"tab ! Mace ta samu wannan amatsayin gidan aurenta, ae kawai ta bi mijinta sau da ƙafa, tabi da addu'a don ni gaskiya na mallaki wannan hamshaƙin gidan amatsayin gidana, ko ƙofar gida bana leƙawa sai in ta kama,'
sai faman zancan zuci take yi har suka ƙaraso wurin wani bene mai kanannaɗa, hawa junaid yayi sannan azmee tabi shi, itama sehrish tabi bayansu, sai faman jinjina kai take yi tana cewa"lallaine Aljanna ta mai rabo ce,"
daker take tattaka matattakalar benen saboda gajiya don yana da ɗan tsayi, bayan sun kai ƙarshensa, wata haɗaɗɗiyar ƙopa ce wadda kai tsaye in ka bi ta zata sauke ka upstairs inda main falo ɗin gidan yake,
key junaid yasanya yabude ƙopar sannan suka shiga cikinsa,wurin ya haɗu an ƙawata shi ahaka ma wai ba furnitures acikinsa, to inaga ansanya mashi kujeru da sauran abubuwan ƙayatarwa,
Batare da 6ata lokaci ba, sehrish ta buɗe handbag ɗinta, memo ta ciro tare da biro, junaid da azmee suka dunga dudduba falon suna karanto mata abunda za'a buƙata acikinsa, ita kuma tana rubutawa acikin memo ɗin hannunta, bayan sun gama da falon kaf sun lissafa duk wani abu da za'a sanya mashi,
Sannan acikin babban falon akwai bedrooms guda biyar ƙofofinsu na acikin falon, ciki suka shiga suna dudduba ɗakunan masu girman gaske, nan ma azmee ta faɗa ma sehrish duk abunda za'a buƙata na furnitures ta rubuta, daga nan kuma suka sauko downstairs stairs shima bene ne zai biyo dakai ƙasan,
Agajiye sehrish ta kalli junaid tare da cewa "dan Allah wannan wane irin gidane haka junaid? Nafa rikice wlh, mun shigo ta Upstairs yanzu kuma ga mu a downstairs yanzu ta ina zamu bi mu fita? Ba dai sai mun koma upstairs ɗin ba don wlh ƙafafuna a sanƙare suke hawa stairs ko wahala,
Junaid da fuskarsa tayi jawur ya gama cika ya 6atse saboda uwar yunwar da yake ji, ga gajiya duk ta baibaye shi, daker ya iya cewa "wannan ne damuwarki, Ni ta cikina nake yi yaushe har muka kammala muka koma gida ni daga nan ma, ba abunda zan ƙara yi Allah, ku je ku ƙarasa sauran aikin in kun kammala kuyimun magana,"
Wuri yasamu a sitting room ɗin dake a downstairs saman wani benci ya zauna, da alama tun lokacin da akayi ginin gidan aka barsa, don akwai tarkacen kayan aikin da aka bari acikinsa,
Acikin sitting room ɗin akwai ƙofofin bedrooms guda biyu, sai kitchen mai girman gaske, sunsha aiki kaf sai da suka zagaye gidan bayan sun tabbatar sun bincika ko'ina sun dudduba abunda ya dace duka kaf sehrish ta rubuta a memo ɗinta, Ana cikin kiran Sallar magrib suka bar gidan kowa agajiye,
Suna ƙarasawa gida daga babban falon kowa ya wuce ɗakinsa, shaf shaf junaid ya tu6e kayan jikinsa ya faɗa toilet donyi wanka, haka itama sehrish tana shiga ɗakin nata bayan tayi wurgi da handbag ɗinta saman gado tare da memo da biron duka, kai tsaye ta tu6e Jalbab ɗin dake ajikinta, ta cire rigar jikinta, cikin sauri ta faɗa toilet wanka tayo tare da Alwala, tana fito ta ɗaure da towel ta bude wardrobe ta ciro wata doguwar rigar mara nauyi ta zura, daker tasamu tayi sallah bayan ta kammala ta baje saman gadonta, bata ƙara sanin meke faruwa ba sam ta manta da batun jera abinci adining, gana babban yaya da zata kai mashi bacci kawai take kwasa,
Azmee ce kawai tayi ƙoƙarin fitowa bayan ta canza kayan jikinta, tunda ta leƙa tasamu sehrish na jan minsharin wahala, bata tashe ta ba kitchen kawai ta wuce ta shirya masu abincin dinner ɗinsu ta dunga kaiwa a dining tana jerawa harta kammala,
Daker junaid yasamu ya fito sai da yaci ka cikinshi sannan ya wuce masallaci yin sallah,
Sai bayan sallar isha'i sannan sehrish tafarka tana faman zazzare ido, agogon bangon ɗakinta ta duba kusan ƙarfe goma da rabi cuf, arazane ta miƙe tana faman dafe ƙirji tuna cewa bata kaima SGR dinner ɗinsa ba, cikin sauri ta ɗauko mayafi a wardrobe tayi lagensa a kanta, sannan tafito dakin azmee tafara wuce wa don taji ko takaimasa, kwankwasawa tayi sannan ta jira ta buɗe mata,
A lokacin azmee bacci takeyi jin bugun ƙofar sehrish yasanya ta, farkawa daga baccin nata, tasowa tayi ta buɗe mata ƙofa,
Ganin sehrish yasa ta cewa "ashe kin tashi daga baccin? Lafiya naganki ko akwai wani abune?
Sehrish tace "dama babban yaya na manta bacci yaɗauke ni ne, bankai masa ɗina ɗinsa ba, shine nazo na tambaya naji ko ankai masa,"
Azmee tace "Ae basu kai ga dawo cikin gidan ba Shi da Omar, pls kada ki koma bacci ko kuma ki sanya alerm na wayarki in sun dawo ki tabbatar kin kai masu abincinsu, sannan kada ki manta ki bama Omar list din da mukayi masa acikin memo dinki,'
Sehrish ta amsa mata da cewa "to shikena insha Allah zan bashi, mu kwana lafiya,"
Tayi ma azmee sallama sannan ta fito ta wuce nata ɗakin, gefen gado tasamu ta zauna sannan ta miƙa hannu ta ɗauko handbag ɗinta, wayarta ta ciro daga ciki sannan ta shiga dannata, Tunawa tayi da maganar Azmee da tace mata in zatayi amfani da data, wi-fi kawai zata kunna, Cikin sauri tasanya yatsanta ta janyo top of the screen din wayar ta, danna wi-fi ɗin ya kunnu, tsayawa tayi tana tunanin me zata fara yi da wayar yanzu, tana cikin tunanin nan taji ƙarar shigowar motocinsu cikin gidan kusan ƙarfe 11-30 na dare, mayar da wayar tayi saman bedside drawer ɗinta ta ajiye asamanta, miƙewa tayi tana jiran su kammala shigowa sai taje ta kai masu, sai da tabari 12 tayi dai-dai a lokacin tasan sun kimtsa kowannansu na a bedroom ɗinsa,
Sannan ta fito ta wuce kitchen ba ƙaramin daɗi taji ba ganin azmee ta kammala zuzzuba musu komai na dinner ɗinsu, a cikin tray guda biyu ta jera masu asaman table na kitchen ɗin,
Hannu kawai tasanya ta ɗauki tray ɗaya ta wuce dashi sashen marshal Omar sallama da ƙarfi tayi saboda yaji ta da kyau, kasancewar yana acikin bedroom ɗinsa bayan tajiyo Muryarsa yana amsa mata sallamarta ta, sai ta shiga cikin falon nasa ta ajiye masa tray ɗin asaman table, sannan ta fita cikin sauri tunawa da Memo ɗin da azmee tace ta bashi, bedroom ɗinta ta shiga ta dauko memon data bari asaman gadonta, sannan ta koma part ɗin nasa a lokacin har ya fito jikinsa sanye da jallabiya ash, wuri yasamu yazauna saman sofa fuskarsa ɗauke da ɗan murmushi ganin Sehrish,
Ƙarasawa tayi inda yake tare da gaishe shi "Yaya Omar barka da dare, ya gajiyar aiki," ?
"Alhamdulillah miss Sehrish, ya maganar aikin dana saku? Ina fata komai ya tafi dai-dai, sannan ya gajiya nasan kun kwaso ta ko?
Murmushi tasaki tare da miƙa masa memo ɗin hannunta tace"Gashi nan, mun dudduba gidan duka kuma mun rubuta duk wani abu na furnitures da za'a buƙata acikinsa,"

161 / 231

Chapters