Author : sophieG Category : Complete Novels
[7/4, 8:23 PM] Şɧą'ąɯą 💞: [5/9, 3:21 PM] Babee Feeya: *Y'AY'ANA (Abin alfahari na)*
_labari da rubutawa_ _sophieG_
_A very heart touching story 2017_
*bismillahir rahamanir rahim*
_ina rokon ubangiji Allah dayabani ikon farawa lafiya da kammalawa lafiya yasa mu amfana da
darussan dake tattare acikin littafin_
_sadaukarwa ga dukan masoyana_
Page 1
Gidan Majid acike yake da yan barka kowa se kallon babyn yake ana Allah yaraya amma me jego
tayi shiru daga gefen gado take zaune dakaganta kaga me damuwa da alama ma kuka tayi ga dan
karamin akwati agabanta kayan baby kala hudu nata kuma kala biyu,
Jitayi an riko hannunta datayi tagumin dashi,yayartace asama'u janta tayi har dakin yaranta kafin
tafara magana,
Haba badi'a duk abinda zakiyi kibari se an watse kiyi abinki sekin nunawa mutane kina cikin wani
hali,
Cikin muryar kuka tace Yaya dole inyi kuka abin yafara isata majid fa ba talaka bane amma kiga
wulakancin dayai mana nibama kaina nake jiyewa ba dan jinjirinnan dabesan komai ba haka
zetaso yabi layin yayyensa dasuke cikin ukubar rayuwa kamar ba gidan ubansu ba kinsani bantaba
magana ba bantaba nuna damuwata akan duk abinda yakemin shida mahaifiyar saba da kuruciyata
zasusa hawan jini yakamani,
Dukda dahaka badi'a hakurinnan shi zakici gaba dayi kodan yaranki suyi koyi dake kuma komai
na rayuwa me wucewa ne kiga kala biyunnan dayai miki wallahi sedan wane da wane hakama na
yaron wasu kalar designers ne dabantaba ganin suba kuma daga gani masu tsada ne kicigaba da
rungumar kaddarar ki kinji,
Shikenan Yaya inaga bawata walima da zamuyi kawai dai ayi snaks dakayan rabo nasiyo bucket
dozen takwas masu marfi anyi sticker da hoton yaron sukadai gareni kudin zobo ne danaketarawa,
Allah yasa musu albarka zamuyi snacks din nida Yaya muktar farida kuma tayi memo tace zatayi
fried rice da kunun aya su Hajiya kuma zamu Tara wani Abu mubasu suhada gara,
Yaya na gode sosae Allah yabar zumunci kuma su Hajiya subar zancen gara ai wayanda za ayiwa
ba kirki garesuba,
Kedai babu ruwanki susukace zasu iya,
Shikenan Allah yataimaka,
Dakyar tayi bacci ranar saboda masifar mijinta ga yaronta da azabar kuka tarasa inda zata sa
kanta,
Ranar suna yaro yaci suna jabir dakyar ta riqe kukan datakeji har en biki suka watse wani
yankwanannen rago ya yanka kamar ma jaririne befi wata huduba da iyayenta sunsan kalr
wulakancin da ake mata dasun kashe auren batason mijinta yasaketa saboda tanason sa matsalarsa
kawai rashin son haihuwa ne,
Washe gari tagama gyaran gidan yaran su uku sunyi makaranta biyune kusa da ita se jaririnta jabir
biyun basu isa akaisu makaranta ba kuma tasan babansu baze kaisuba shiyasa takeso kafin su isa
zuwa makarantar ta tanadi wani Abu dantasakasu makaranta medan kudi kodan rayuwarsu ta
inganta,
Sallamr mahaifiyarsa taji Hajiya rabi azahiri ta tsorata sanin duk zuwan Hajiya rabi to da cin
mutunci take zuwa,
Gaisheta tayi ta amsa ciki ciki mama kizauna mana,
Bazama nazo yiba inabanda nuna isa dankun rainani yaushe zaku aikamin danama kamar abinda
na roka toga tsiyarku nan nakawo muku banaso wannan abin zanraba nida en uwana,
Hajiya kiyi hakuri ragon ne bayida girma,
Ohh sannu munafuka wato duk abinda Dana yake miki bakya gani harkin raina girman ragon to
wallahi bari yadawo kicenasa ina nemansa senaji idan shine yake daure miki gindi kina wannan
iskancin kuma ga namanan idan ba akarominba kuriqe tsiyarku,
Dama badi'a bame magana ceba hakan yasata shiga kitchen ta kawso sauran naman tahada mata
tamiqa mata tana bata hakuri,
Babu godiya ta karbe sema kara raina naman datayi tatafi tana fadin bafi'a duk ta kwashe tabawa
en uwanta dan munafurci,
Komawa tayi tazauna tamakasa yin kuka kallon jabir take dayketa tsotson mamanta amma
bakomai aciki sbd bakinciki tunjiya takasa cin komai ga yaron bashida madara tana tsoron taba
abincin data ajiyewa yaranta suzo suci basu koshiba dan tasan ubansu baze bada kudin cefane
dasu ba,
Ahaka jabir yagaji yayi bacci sauran yaranma duk sunyi bacci shnifidesu tayi tafito daniyyar
wanke wanke Sega majid yashigo,
Binta yayi damugun kallo ko amsa sannu dazuwan datake masa beyiba,
Ledar data gani ahannunsa taje zata karba Dakatar Da ita yayi yabude ledar yanuna mata,
Kinganusu nan kayan miya ne kuma wallahi nakwana biyu ne daga seke se abdulrahim karki sake
kibawa wayannan Yayan naki jeka inbiki haihuwar rurrutsa,
Muryarta na rawa tace...,
Allah kabamu hakuri da juriya azaman duniya
Ameen.
[7/5, 8:05 PM] Babee Feeya: *Y'AY'ANA (Abin alfahari na)*

Feeyah😍
[7/5, 8:05 PM] Babee Feeya: *Y'AY'ANA (Abin alfahari na)*
*N!$@ online writers*
_written by sophieG_
_A very heart touching story 2017_
_wannan shafin nakune ummeejay,ummeekhaleel,zeenaseer,husaina ubandiya,Sha'awa
ibrahim,jidda(dota),shukrah,adama maifata,bilkisu,meera Dan fodio,ddss. Nagode sosae da
addu'arku agareni Allah yabar zumunci ameen_
Page 2
Yanzu don Allah majid haka zamu cigaba da rayuwa Yayan cikinka nefa amma ace abincin
dazasuci yana musu wuya agidan ubansu,
Magana take kamar zatayi kuka,
To naji malama bazan basu abinciba se randa naga dama kintashi kin haifo yaya jeka inbika
saboda kawai ki karyemin tattalin arziki don kinga Allah yasamin hannu to babu ruwana
dacinsuko shansu ai seda nanuna miki banida muradin ki haife cikin dukansu bayan abdurrahim
kika ki Dan haka dole kece zakiyi dawainiya dasu babu ruwana,
Bata cika sonyin maganaba balle wannan maganar Mara dadi datakejinta
Daga bakin mutumin daba jahiliba Dan boko me tarin dukiya amma se bala'i da makon masifa,
Kije ki hadamin ruwan wanka munada meeting yau akasuwa,
Batace dashi komaiba tabi hanyar dakinsa bayan tahada mai ruwan wankan tazauna zaman
jiranshi yafito,
Kallonta yayi bayan yafito yace,
Lafiya dai badee'a?
Don Allah jabir zaka siyowa madara naringa hada mishi da ita,
Saboda? Yatambaye ta yana shafamai a hannunsa,
Shiru tayi tana nazari kafin tace,
Saboda ni banasamun isasshen abincin dazanci har ruwan nonon sukawo su isheshi wuni daya,
Bari kiji babu ruwna da jabir nabaki abinci kici banason tsegumi don kisani tunyanxu yashiga
layin su abduljabbar,
Takasa cewa komai Dan takaici idan tayarda taci abincin saboda jabir to sukuma su abduljabbar
mezasu CI dama abincinta take basu itakuma idan anyi cinikin zobo setasan yadda zatayi taci
takara musu,
Dakinta tashi ga tazauna bakin gado tana kallon yayanta tana kuka,
Kuyi hakuri *y'ay'ana*nasani wantarana zanyi *alfahari*daku zancigaba da Neman nakaina don
na inganta rayuwarku saboda babanku bashida niyyar sakamin hannu a lamarinku,
Dahaka rayuwarsu taci gaba yau dadi gobe wuya ga yaran duk halinta suka gado basu cika
magana ba haka suketa Jan hanji ga ramarsu tarashin wadata tafara bayyana badi'a ma duk tayi
zuru zuru damuwa tayi mata yawa takasa sanar da mahaifanta ko babban yayansu besan Halin
datake cikiba Yaya asama'u kadai tasani itama kusan halin su daya da badee'a zurfin ciki yayi
musu yawa,
Suna zaune jugum ta kammala abincin rana ta hada da nata Dana abdurrahim kallon abincin take
abdurrahim,abduljabbar,abdulkadir,abdul'aziz, abincin baze ishesu ba ga jabir yafara cin abinci
gashi duk yarame kwanaki yai rashin lafiya amma ko kudin adaidaita sahun zuwa asibiti bebasu
ba,
Tazaunar dasu duka harsun faraci Sega majid yashigo,
Sallallamin dayakene yasata dago tana kallonsa,
Yanzu badee'a cin amanata kike kisatar min abinci kiba yayanki sannan kuma ki hadasu da dana
salon kar yakoshi?
Nikam bansatar maka abinciba nawa dana abdurrahim na hada musu,
Ina ruwana dayaranki kibasu naki daban mana suci karki sake kikara hadamin su da yarona inaso
yaci yakoshi maza zoki raba musu,
Majid don Allah karmu raba kan yayanmu,
Nace kixo kiraba musu abincinan tun raina be baci ba,
Kamar zatayi kuka haka taraba musu abincin nasu abduljabbar befi suyi loma shida shida ba
yakare,
Ta dago tana kallonsa da fuska a maraice hannunta kawai yaja yana fadin,
Abdurrahim kaci abinci sosae kaji,
Yaran suka bisu da kallo har suka bacema ganinsu,
Abdurrahim yakoma kusada en uwansa sunaci atare har aka cinye nasu yadauko nasa sukaci atare
har jabir ma dayake rarrafe,
Bangaren su badi'a kuwa a Palo ya tsaya yacire rigarsa dagashi se singlet da dogon wandon shadda
akan kafafuwansa yazaunar da ita yada kallon bakaken lips d'inta dasuka sha lipstick sunata kyalli
ga sky blue din jallabiya takama jikinta tayi mata kyau,
Kinyi kyau badee'a,
Batama jinshi hankalinta yatafi tunanin yayanta ko sun koshi,
Dan kwalin kanta taji yazame yana kara rungumeta ajikinsa,
Watoshi bashida damuwa ko ga yayansu can yunwa zata halaka su batasan lokacin da kuka ya
kwace mata ba kamar wata jaririya,
Majid kuwa dama ya kwaso jarabarsa bema saurari kukan datakeba seda ya sauketa,
Taso tahanashi sekuma tayi tunani hukuncinta agurin Allah gakuma tsoron karta kwashi wani
cikin dan jiya tafara sallah kuma tasan yanayinta,
Dakinta takoma tasamu yaran a apalo dikansu sunyi bacci gyara musu kwanciyarsu tayi tashi ga
uwar dakin,
Bayan kwana biyu tashirya zuwa gidansu tagaida su Hajiya ta kwana biyu batajeba,
Yace ta shirya yakaita taji dadi sosae,
Ke dawayannann yaran orututu da otonyo zaki,
Eh ta amsa tana kallonsa,
Bazasu shigarmin motaba dama da abdurrahim kadai zaki se wannan jabir din dasena dan matse
nakaiki,
Dasu duka zani danbansan wazan barwa suba kasan kuma sunyi kankanta abarsu sukadai agida
kabarshi kawai zan hau napep,
Kallonta yake cikeda masifa,
Ke kinma fasa tafiyar senagani inkece kike iko dakanki nizaki gaywa wannan banzar maga.......,
Bata jira yakarasa maganarba tana yaranta suka shiga gida,
Shirunta yana masa ciwo danhaka yabita yana balbaleta da fada amma har yakaraci surutunsa
batacemasa uffan ba cikida takaicin abinda taimasa yabar gidan.
*kwanaki a wani group wata takawo topic akan cikin biyunnan wanne ne zaka zaba*
*1 uwar miji bata sonkine*
*2 mijin ki baya sonkine*
*kowa yafadi albarkacin bakinsa but ni awurina banason kodaya acikin biyunnan sbd in uwar miji
batasonki to maganar jin dadi bata tasoba karshema sekun rabu hakama idan mijin bayasonki
karma kikawo maganar kwanciyar hankali a gidan sedai idan Allah ne yayi ikonsa*
*Allah ya dubemu da idon rahma*ameen
[7/5, 8:05 PM] Babee Feeya: *Y'AY'ANA (Abin alfahari na)*
_by sophieG_
*N!$@ onlin€ writ€rs*
_A very heart touching story 2017_
_this page goes to you Sha'awa Ibrahim_
Page 3
Abdulmajid kasim asalinsu en garin sokoto ne akaramar hukumar kware duka en uwansu suna
kware mahaifinsa ne kadai yke zama a sokoto shikadaine gun mahaifiyarsa shiyasa yake sheke
ayarsa yadda yakeso,
Badi'a kintabbatar ba matsala banaso adawo ana dana sanin wannan auren naku,
Babanta ne yasata agaba yana tambayarta don yasan Halin uwar majid batada kirki kokadan,
Abba babu matsala insha Allah,
Banaso kibari sonda kike masa yasa kikasa ganin laifinsa kije kikara tunani nabaki kwana biyu,
Tashi tayi cike da kunya tashi ga daki,
Bayan kwana biyu abba yasake tambayarta ta shaidamasa da babu matsala,
Tana tsananin son sa hakane shima agurinsa yahanata sauraren kowane saurayi inko yaga abu
basetace tanaso ba komai aka kawo musu a kasuwa indai namata ne dazasu siyar seya kawo mata
amma abbansu betaba bari ta karba ba sedai yakoma dasu ya ajiye,
Yayyenta zama sukayi akayi maganar auren muktar yace abarta tunda tana sonsa shima yanasonta,
Bayan kwana biyu iyayen majid suka turo an saka ranar bikin wata me shigowa,
Lokacin bikin yaxo akayishi cikin kwanciyar hankali gidan amarya yayi kyau komai daidai irin na
mutane masu wadata,
Bayan wata biyu da auren badee'a tafara laulayi sunje asibiti aka tabbatar musu datana dauke da
ciki wata biyu sunyi murna sosae kamar su fadawa duniya,
Gata da kulawa ba amagana har mahaifiyarsa ttanaji da cikin tun daga gidanta take zuwa
takaimata kayan kwadayi,
Shikansa majid idan yafita aiki ko kasuwa seyazo saubiyar kafin lokacin tashinsu office ko kuma
kasuwa yayi,
Asibitin da yayarta take aiki acan take zuwa awo,
Tayi masa zancen komawa makaranta yanuna mata bashida ra'ayin komawarta makaranta be rage
tada komaiba kuma yafiso kullum yana tareda ita,
Ba ayi yarjejeniyar cewa zebarta tayi karatuba kafin auren dan haka besamu matsala daga gunta
ko iyayenta ba se aka share batun,
Cikinta yashiga watan haihuwa zuwa lokacin komai ashirye yake kayan babyn dasuka Tara
sukansu basusan adadinsu ba siya kawai suke suna ajiyewa,
Ranar da badee'a ta tashi da naquda da safe a gigice sukayi asibiti hankalin majid duk atashe
yakasa kiran kowa yafada suna asibiti,
Ko awa daya ba ayi dazuwan suba Allah yasauki badi'a lafiya tasamu da namiji murna gurin
abdulmajid ba amagana anan yakira mamansa yafada mata kafin asallamesu asibiti tacika da
dangi,
Ranar suna kuwa anyi barin kudi abinci a ko'ina yaro yaci suna abdurrahim sedai ace Allah yaraya
abdurrahim,
Mahaifiyarsa ta umarcesa daya dawo gidanta har badi'a tayi arba'in tadawo dan babu kyau mutun
yana kwana shikadai agida,
Bemusa mata ba yayi yadda tace sedai kwana kadai ke kaishi gidan kullum yana gurin badi'a da
babynsu,
Ganin haka abbansu yace ranar data cika kwana arba'in takoma gidanta bayason wannan zaryan da
mijinta keyi masa agida,
Ana gobe zata koma majid yafito da safe yashiga dakin mamansa,
Umma nafita zamuje asibiti da badi'a,
Batada lafiyane tatambayesa,
A a za adorata kan maganin family planning ne,
Family me?ta tambayesa tana miqewa tsaye,
Planning umma,
Bakuda hankali wallahi kunyi kadan kaikadai na Haifa inaso naga gida yacika da yara babu wani
planning banyarda daga haihuwar da daya zaku wani ce planning kusake tunani bada yawun
bakinaba,
Umma ai ba wani abubane kuma bawai munce abdulrahim kadai ne zamu Haifa ba,
Banason iskanci kanajina kodan kaga duk abinda kake ina daure ma gindi?tobanda wannan zancen
sena Daura zanina naje har gidansu badi'a nayi rashin mutunci,
A a umma base anyi hakaba kiyi hakuri,
Dayafi dai tafada tana zama tacigaba da mita,
Fita yayi yana tunanin yadda zeyi da wannan zencen.
*duk kalar jin dadin dakake arayuwar duniya dazarar katuna da mutuwa zakaji jindadin yaragu
amma masu imani ne kadai ke tuna mutuwa maras a imani kuwa harkarsu tqduniya kadai sukasa
Agaba wannan babban kuskurene duk yadda kayi niyyar aikata mummunan aiki katunada mutuwa
hakan zesa katuna haduwarka da ubangijinka mezakacemasa ranar tonon asiri? Zakaji tsoron
wannan ranar dataimakon Allah sekaga kakasa aikata wannan aikin Allah kasa mudace ameen*
[7/5, 8:06 PM] Babee Feeya: *Y'AY'ANA (Abin alfahari na)*
_by SophieG_
*N!$@ onlin€ writ€rs*
_A very heart touching story 2017_
_this page goes to you Anty badee social_
Page 5
Baby meyake damun badee'a ne naga ta rame kuma fuskarta da alamun akwai damuwa kuma gasu
Abdul kamar yayan riqo suma duk sun rame,
Mijin yaya asma'u ne ke tambayar ta Dan lokacin daze fita ya hadu da badee'a zata shigo anan
yalura da ramewarta yadda idonta sukayi zuruzuru,
Shiru tayi nadan lokaci tana tunanin tafada masa koze taimakawa kanwar ta ta,
Kiran sunanta yayi kafintadawo daga duniyar tunanin data shiga,
Mahmoud badee'a nacikin damuwa uwar miji da mijin sunsata atsakiya suna gasa mata gyada a
tafin hannu,haihuwa take babu tsari uwar mijin tayi rantsuwa bazatayi family planning ba
shikuma mijin bayason wannan haihuwar datake babu kai babu gindi duk cikin yayannan babu
shekara biyu a tsakaninsu yanzu halin da ake ciki tundaga kan abduljabbar har jabir itake cida su
yace wallahi tunda take haifarsu kamar awaki baze dauki nauyin komai nasuba danshi baze yadda
tacinye masa tattalin arziki itada yayanta ba,
Shiru yayi yana jinjina jahilci dakauyanci irin Na abdulmajid,
Baby yanxu su Hajiya basu dauki wani mataki ba aka zuba masa ido yana wahalar da yar mutane?
A'a itace bataso afada musu basusan halindatake ciki ba Dan tunfarko basuso aurenba saboda
sunsan uwarsa batada kirki batasan girman kowa ba,ganin badee'a tadage shitakeso yasa suka
barta ta aureshi dakunya kuma yanxo daje kai kararsa gurinsu, ga yahanata komawa makaranta
kuma babu wata sana'a mekyau dazata kawo kudi zobo takeyi lokacin sanyi ba asiya sosai sbd
babu k'ishi tausayinta nake konamiji ya yakara da ciyadda mutun uku bare mace, kuma har yanzu
tace tanason abinta,
Dariya yayi yace so hana ganin laifi ai
Uhmm narasa abinda take tsinta agurinsa wallahi,
Allah ya sauwaqe gobe sekishirya dasafe kafin kitafi gurin aiki zanbaki sako ki kaimata,