Author : sophieG Category : Complete Novels
inaso Na taimaka miki,
Ahankali tabata labarin rayuwrta Wanda taji zata iya fada,kuka take kamar ranta ze fita Anty
Zainab narasa kowa da komai nikadai nasan me nakeji azuciyata idan da soyayyar mijina kadai ta
zaunar dani gidanan datuni Na tsufa gidanmu inaso abbana yafahimci abinda nake gudu dayasa
ban bishiba kiga yayana gasunan duka mazane babban shekarr shi shida wazan barwa su?
Wazemin tarbiyarsu? Kakarsu data hanani yin planning yanzu tabi bayan danta batasonsu kokadan
duk lkcn Dana kaimata su dukansu take kamar jakai kiga danta bashida tarbiya kokadan babu
abinda yasawa gaba irin Neman kudi abincin dazamuci wuya yake mana inba yanzu daya yadda
yake bani komai dakansa ba dukda dagishiri dazansa amiya shine yake debarmin adadin dayakeso
kuma idan abincin beyi dadiba ya balbaleni da masifa, Allah yasoni hawan jini bekamaniba kigafa
duka en uwana sun gujeni inason ganin mahaifiyata amma banida iko,haihuwa nayi amma
bayanke dani bawanda yataba ganin babyn bakuma alamar za azomin barka yayata Dana tura mata
hoton babyn ko reply Na Allah yaraya batayimin ba abdulmajid yajanyomin bakin jini agurin en
uwana😭,
Dakyar Zainab tasamu ta rarrasheta,ki godewa Allah badee kin samu haihuwar shekarata goma sha
uku da aure ko bari bantabayiba dagani har mijina lpyr my qlw babu yadda zanyi inason mijina
bazan iya rabuwa dashiba nasan yanason haihuwa amma betaba chanjamin fuska ba ganin idan
bansashi yayi aureba awaje abokanansa kokuma mahaifiyarsa zata sashi yayi auren kuma akwai
en zuga inagudun su zugashi yajuyamin baya ganin nayi shekara bakwai ba haihuwa nace yakaro
aure kila za adace matar ta haihu, yacemin shi bashida ra'ayin mata biyu nikadai yakeso zezauna
dani saboda Allah kuma ga yayan yayyensa nan aisun ishemu har kararsa nakai gdnmu babanmu
yakirashi amma zancen dayane baze iya karo aureba nikadai yakeso haihuwa ta Allah ce koda
yakaro auren idan Allah besa yanada Rabin haihuwa ba bazetaba samun taba,
Badee inason yara sosae shiyasa nace zan koma makaranta nayi skul of nursing bayan nakammala
degree Na seban nema aiki dashiba najira har nzama nurse nasan zanyita ganin yara a asibiti,
Yanzu matsalar danake fuskanta itace mamansa tasoma sauyamin bakamar da ba,yaranki sun
burgeni sosae kuma Na tausayawa rayuwarki shekarunki sunyiwa damuwarki kadan,
Kema abin atausaya miki ne Anty idan haihuwar alkhairi CE agareki Allah yabaki,nikaina
inaganin idan nakara shekaru biyu awannan halin to matsalolina kasheni zasuyi bansan wazan
tunkara zuciyata tayi sanyiba damuwa tamin yawa bama kaina nake jiyewa ba yayana rkar
rayuwarsu ta gurbace ina iyakar kokarina nagrayuwarsu ta inganta Anty don Allah kitaimakeni da
maganin planning bawai nagaji da haihuwar bane inaso ne nadan huta har wayannan yaransu kara
girma nasan insha Allah watarana zanyi alfahari dasu,
Amma kekam anyi sakarar mace sauna kuma Allah wadaran wannan mugun halin naki yanzu
matar dabaki saniba kika zauna kina zubewa sirrinki?,
Basusan dazuwan hajiyaba sejin muryarta suakyi,gaban badee ba karamin faduwa yayi ba.
Nikaina nafirgita amma nadake sbd jarumta😎
En uwa semun hadu wani lkcn
[7/5, 8:08 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfahari na)
By sophieG
A very heart touching story 2017
This page goes to u Anty billy❤
Page 14
Kekuma munafuka kinzo zaki hure mata kunne ko? Tun wuri ki kwashi kafafuwanki kibar
gidannan irinkune sarakan zuga kinzo kikashe mata aure,
Zainab batace komai ba tamiqe tana murmushi,badee se anjima kinji nagode sosae,badee kam ba
bakin magana se hawaye zuciyarta kuna take sosae anwulakanta mata bakuwa batasan yazatayi ba,
Bayan fitar Zainab hajiya takaaraso ta zauna itada wata fitsararriyar mata da alama daga kware
tazo se kallon gidan take tana yatsina fuska irin kallon datakewa badee yayi kamada harara,
Munzo ganin jaririyane tunda ban isa akaimin itaba ninazo ganin ta dakaina,
Kiyi hakuri umma wallahi yau nakeda niyar idan yadawo daga office mukawo miki ita,
Harseda aka kwana? Aitunjiya yakamata akaimin ita amma dayake ban isaba seda ninabiyota
dakaina safara'u karbomin ita nagani natofeta da addu'oin tsari tunba asa tabi sahun yayyenta ba
yaranann dakike gani basa kaunata insunganni kamar sunga azara'ilu(wayannan mutanen basuda
alkibla ko kadan inace ita take hantararsu harda duka?🤔).
Arnyi mata huduba ne?
Kanta akasa tace eh yayi mata jiya dadaddare yace sunanta Lubna,
Yadda hajiya ta zaro ido seka zata cewa akayi sunan babyn shegiya,
Yanzu sabon salo aka samu baza anemi shawarataba akasawa yarinyar suna? Lallai akwai abinda
kikayiwa Abdul wannan karon dole Na tashi tsaye karki rabani dashi, da alaamr mamaki take
kallon umman (metake nufi?),
Eh kikalleni dakyau bakar munafuka wacce tazabi namiji akan iyayenta aiba abinda bazata
iyayiba,
Safara'u dake gefe tace wai dama mama wannance matar yaya Abdul? Eh itacefa kingantanan
kamar diyar roko wannn aise zaman hakri tashi mutafi Allah yaraya tunda kinyi son ranki,
Nan wurin ta zauna ta hsarbi kukanta harta koshi kafin ta janyo wayarta tayi Kiran Zainab kalar
hakurin databaa harseda yaso kular da Zainab din Anty kiyi hakuri kuma ban fasason maganin ba
inda yadda zaki taimakeni kikawo min don Allah,
Babu komai kibari se jininki yadauke zansan yadda zanyi kuma akulamin da Lubna sosae kinji,
Insha Allah nagode sosae se anjima,
Har ranar suna babu wani chanji agurin majid danshi yace bayason taron suna dakyar yana share
gumi yayanka rago daya ranar sunan bawani abin azo agani sukayiba sukadaine agidan daga
yaranta se en uwansa daga kware basu wuce su shida suma banda habaici ba abinda suke mata
agidan itadai iyakacinta dasu ido da aka shigo da naman kadan ta diba tamiqa musu sauran
sukaiwa hajiyarsa batason fitina,
Daga haka rayuwarsu take babu wani ci gaba jiya iyau kalar ramar datayi kadai ya isa yanuna tana
cikin damuwa gun Zainab kadai take samun taimako shima Zainab ta daina zuwa gidan sbd
haukar da majid yai musu wai be yadda da itaba,
Yanzu lubna tana wata bakwai kome take taji muryar babanta zata rufe ido kota fara kuka lokuta
dayawa yakeson daukarta amma bata taba yadda dashiba inkaga dariyarta to gun yayyenta ne ko
mamanta,
Ba ita kadaiba har manyan tsoron babansu suke abdulrahim ne kadai yakedan jin sanyi tagefensa
kuma har yanzu sunanan da yunwarsu abinci ba lallaine yake basu Wanda ze ishesu ba maganar
aci nama batamazo kusaba sedai shi yasiyo yashige daki yaci abinsa badee batada halin Tara kudin
sana'arta tasiyamusu abin marmari idan tayi ranar setayi regretting ga uban jaraba musamman
yanzu dayaga andau lkci bataace ciki gareta ba se abin nasa yaakra kaimi,
Kuka kuwa yazama abincinta babban bakincikinta bewuce rasa en uwanta datayi ba har gidan
yaya muktar ta tafi amma ko kallonta beyiba gashi tanason ganin mahaifiyarta amma abin
yafaskara,
Tura abincin kawai take badon tanajin dadinsa ba sedon ganin Lubna tana rama sbd rashin samun
isashen abinci damuwarta ta tashafi diyar bayan ta kammala dura abincin tasawa Lubna nono
abaki harta kama sekuma ta gantsara mata cizo dasauri ya yakiceta tace,
Yaushe kika zama muguwa harda cizo haka kallon uwar tayi tabingire da dariya su abdulrahim
suka kama mata sunata dariya batasan lkcn da dariyar ta kwacemata b tace Amma yarannan sedai
nace Allah yashirya minku 😂😂.
[7/8, 2:15 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfahari na)
By sophieG
A very heart touching story 2017.
A rayuwata ta duniya babu abinda Na tsana irin wulakanci wallahi ko wanda muka fito ciki daya
yaimin wulakanci yanzunnan senayi sahur dashi nadau azumin shiga harkarsa Na tabbata babu
writer dinda take yin yadda nakeyi wata sekiyi mata magana setai kwana biyu ta amsa shima se
idan taga damar amsaki ne amma ni kowa yazo jikin nabari nake kulashi dankar ace nai wulakanci
amma dukda haka ban tsallake ba seyanzu nagano abinda yasa ake cewa writers Nada jijjidakai🤔.
Akace shiru shiru......?😕.
Page 15
BAYAN SHEKARA 5
Tun lokacin da safara'u ta zo gidan bayan anhaifi Lubna tamaida gidan digan zuwa ba'a wata daya
batazo sokoto ba kuma tana zuwa se gidan Abdulmajid take sauka intazo kwarkwasa da iyayi
bawanda badee bata gani ga yaran tayita hantarar su duk lkcn da tazo basa sakewa,
Kusan sau uku ana kawo kudin aurenta setace ta fasa kuma hajiyar majid ke daure mata gindi
acewarta da ayi taki zama gwanda kar ayi tunda tace yanzu tfasa dole akyaleta babanta kuma Na
kamar hoto haka yake,
A haka har Lubna tai shekara biyar babu wani chanji duk yadda badee tayi Dan ta shirya d en
uwanta da mahaifanta Abu yakiya amma dukda haka batayi kasa a gwiwa ba haka ta shirya taje
gidan kasancewar yaran duk suntafi makaranta,
Mukhtar tasamu akofar gidan yafito tunkafin takaraso yafara magana,
Kin tabbatar kinbaro gidan mijin nakine Dan wallahi matsaawar bakin baro gidansa bane karki
kara zuwa nemanmu,
Don Allah yaya kasaurareni kutausayamin kodan yaya na bazan iya barinsu ba don....saukar Marin
da taji ne ya katse ta,
Tun wuri ki kama kanki kibar kofar gidannan wallahi,
Ko abinda majid ke mata betaba bata mata rai irin haka ba ita da gidan ubanta idan shine bayason
ganin ta bazataje gidansa ba amma sbd me ze hanata sasantawa da iyayenta suma da laifinsu kusan
shekara nawa basu taba nemanta ba amma daga yau tadau Alukawarin bazata kara nemansuba
sedai idan sune suka nemeta,
Tfiya take dakafa harta isa gida sbd yadda zuciyarta kekuna bazata iya magana ba ko sallama
batayiba ta shiga gidan wunin ranar akwance tayishi dakyar tasamu ta daidaita kkanta,
Kwata kwata abinda yake damun majid be wuce yadda Lubna ke kin yadda dashi ga besan ya
akayiba yakesonta sosae ba tun tana karama sosae yakesn daukarta amma yana zuwa kusa da ita
zata kwalla ihu yanzu kuma datake tafiya kowasa take daga tagansa take guduwa ko yadda take
ganin yayyenta nayi idan yadawo baba sannu da zuwa ita idan yadawo kokallonsa batayi guduwa
ma take,
Ikon Allah kawai take kallo yadda majid ya Dora tsararren gini daga gefe tanamamaki sosae,
Yauma kamar kullum yagama sauke mata jarabarsa take tambayarsa ko en haya zesaka asabon
ginin,
Babu ruwanki banason tambayoyi ki zubamin ido kiga yadda zanyi komai sekin sanine,
Shiru tayi batace komaiba,
Shima bangarensa mamaki make shekara biyar bawani mataki bawani ciki amma dai shiyafison
haka Dan wani haushi yakeji idan yashigo gidan yagansu gasunan bi da bi,
Tunda ta tashi yau takejin gabanta na faduwa addua kawai take hartadan samu sassauci bayan isha
karfe tarada hartadan gota taji shigowar motoci bata kawo komai arantaba tana zaune seji tayi
anata rangada guda sekawai ganin mutane tayi a palonta da mace agaba tarufe fuska da mayafi,
Shiru kawai tayi tana saurarensu badan tana fahimtar me suke fada ba,
Wata tsohuwa er kili bibi tace to badee'a ga amarya nan munkawo bawai munbaki amanarta bane
sedan mufada miki kikama kanki sannan tafi karfin asiri yadda kikaso kiyiwa majidu manta uwa
Allah be yadda ba yakubutar dashi to wannan ma tamiki yawa sedai kiyiwa wasu bakar muna
fuka,wata mata dake gefe ta takalleta sheqeqe tace,uhm kuga mace har mace amma se mugun hali
ko kula damiji ba a iyaba duk Wanda yasan majid da baze yadda shine yanzu ba ga haihuwar
kamar tunkiya keko er soyayyar nan da miji damata ke kwasa bakyayi sbd kincika gida da yaya
kamar gidan reno gasunan jeka inbika to yanzu dai ga wacce zata kula dashi nan munkawo se kibi
ahankali,
Kukan ma kin zuwa yayi har suka gama cin zarafin su suka fita bata Ankara ba,
Batun majid yashigo bema tasoba yadda taga dare haka taga rana, ita kanta batasan metake
tunaniba, washe gari ta shirya yara taturasu islamiya tun karfe takwas tana nan zaune a apalo Sega
majid,
Rana ta farko dataji bata kaunar abinda zesa ta kalli fuskar majid batason ganinsa gaba data,
Nace ki hada mana abinkari kinsan amarya ga gajiyar biki ga gajiyar jiya,har yakaraci surutunsa
ko kallonsa batayi ba,
Seda yazo saubiyu kafin tasamu bakin magana,
Majid menai maka Dana cancanci wulakanci irin wannan?koda ace mata uku zaka auro baynni
yakamata kafadamin bazan taba hanakaba balle nace zan tashi hankalina akanka dan nasani yanzu
banida wani gurbi azuciyarka bawai kawai INA zaune azomin da amaryarkaba ko musulunci be
lamunci hakaba anya majid zaka iya da haqqina kuwa?zancen nagirka muku breakfast bema taso
ba inace bauta tazoyi? Tunda tayi ta jiya dadare aitafara kenan Dan haka seta fito da kanta tayi
girkin ninayi nawa tundazu kuma nagaji duk abinda zakayi bazan hanaka ba akwai ranar kin
dillanci,
Tabarshi tsaye agurin tunda yake bata taba gayamai magana ba seyau dole yadauki mataki.
Babu yadda zasuyi dole amarya tafito tayi girki a gefanta dakyar ya lallasheta tafito wai ita tagaji,
Badee bata gane wacce amaryaba Seda takwana biyu tafito rakiyar miji badee taganta wato
safara'u aka San yadda akayi aka Liqa mai.
Kuyi hakuri da wannan yau dakyar Anty bily tabarni nayi wannan😏
[7/10, 2:02 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfahari na)
By sophieG
A very heart touching story 2017
Wannan shafin nakine Sha'awa Ibrahim(wai yaushe zaki cigaba mana da safiyyah ne? Wasu
harsun manta dashi🤔).
Abin duniya ya ishi badee tarasa inda zata saka kanta majid seda yai sati biyu dakin amarya ko
raba musu kwana beyiba tun tana zuwa dakinsa takwnta zaman jiran zuwansa harta dena Dan
yatattara yakoma dakin amarya yanzu amaryar tafi wata a gidan amma kokallon gefen ta bayayi
sedai ta hango fitarshi shikadai kokuma da amarya babu yadda zatayi sedai tasha kukanta ta koshi,
Yau abdulrahim ya tashi ta ciwon kai ko makaranta bejeba, kaje gun babanku kila ya saurareka
danni konaje ba kulani zeyiba, jiki a sanyaye ya yafara tafiya yana tunanin yadda zeyi ko jiya
dayaje korosa suka yi wai yashigo da kazaman takalminsa alhali babu komai a palon se wasu
kalar kujeru da ba mahadi ma Dana mamansa kuma palon ko shara babu amarya an iya gyaran jiki
amma ba a iya gyaran muhalli ba,
Tun kafin ya kwankwasa kofar aka bude babansa yagani cikin shirin zuwa office,
Baba ina kwana?,lpy lau ya akayine? Kudin magani nazo kabani kaina keciwo,waikai yaushe
zakuyi lpy kuda uwarku?kullum cikin matsala?Kodai ita ta turoka da gangan baakayi kamada
Mara lpy ba,hannunsa yasa yazaro nera goma gashi kasiya paracetamol kasha,karba kawai yayi
yana mamakin yadda yabashi nera goma kokunya babu, yakasa tafiya se kallon kudin yake
maganar safara tadawo dashi daga tunanin dya tfi,
Strong ya maganar kudin damukayi bakace komai bafa se shirin fitarka kake kuma nafada ma yau
ankeso natura mata,irin yadda take maganar kamar zatayi kuka tana kara shigewa jikinsa shikam
Dan yaro kallonsu kawai yake,
Sweety kinsan bazan hanaki ba kibari bazan dadeba zandawo sena Ciro daga banki,Na wane kudin
ma kikace?
Dubu hamsin dabiyar ne, OK sena dawo maza kikoma daki wannan kyau haka ina kishin yadda
bishiyar nan yazo take kallonki, Seda taimasa bye bye sannan tashige ciki baban ma gaba yayi
sukabar abdulrahim tsaye agurin,
Koda yaje yakaimata kudin bakin ciki yahanata magana, sekaje kasiya maganin yafi kaita zama
daciwon kai gashi kun kusa fara exam (yana jss1),
Shigowarsa gida kenan yasami Lubna tana wasarta tunda ga nesa yatsaya yana kallonta sosae take
burgeshi bayason taganshi tagudu Dan baya tuna ranar da suka hada ido ta tsaya kokuma taimasa
magana,
Jikawai tayi an dagata sama Seda tatsorata ta kwalla kara,
Lubnatyn baba ninefa yafada yana juyo da Ita,
Cikin hausarta dabata gama fita tace nika sauke ni kaiba babana bane kuma ni sunana Lubna,
Meyasa kikace niba babanki bane? Yadda take ihu seya sauketa yasa shi ajiyeta agabansa,
Kawata ramla kullum ina ganin babanta yakawota da mashin dinsa kuma yazo daukarta amma ni
sedai mamana ta rakani da kafa ita tana sona,
Yadda take maganar babu alamun tsoro kokuma shakka atareda ita cikin idonsa take kallonsa tana
fadamai abinda ke ranta,yajima tsaye yana kallonta wasanta tacigaba tana jira yazo ze tabata
tabballa dagudu sbd tga yadda ko takalmansa su Abdul suka taba yana jibgarsu abdulrahim kadai
yake dagawa kafa,
Tana zaune a palo tana goge kayan yaran gasunan dayawa da alama tajima tana gugar,
Kalli tarin tulin kayan yara nan amma duk sun soma kodewa abdulrahim kayan ma sunsoma
yimasa kadan bansan yazanyiba ubansu bashida kula kalli yadda yaimasa wulakanci kwanaki
maganin nera goma haryaushe yaro zefadama bashida lpy kabashi kudi awulakance? Nidai Allah
yataimkeni da yarannan dole nasan....
Matsalarki kenan rashin godiyar Allah duk abinda nake miki keda yayanki bakya gani dankinga
nadan sassauta miki ko?,
Azahiri yakona mata rai sosae hakan yasa taso gasa masa magana se wata zuciyar tace ta kyaleshi,
To Allah dai yakawomin me sharemin hawayena kwata kwata banida damuwa safara'u ta kiyaye
komai akaina amma ke duk ranar Dana rabeki sekin bata min rai seki zauna dakeda yayanki
kukarata kuma daga yau karki kara turamana yaranki suna damunmu dannasan da gayya kikeyi,
Wannan karon idan tayi shiru ya shammace ta shiyasa ta shirya fadamai magana amma kuka yazo
mata ga bakin cikin kishiya miji yawulakanta ta agabanta,
Abdul ni inada damuwa sosae nakeda Ita,harkanada bakin budewa kace ina samaka damuwa
kasani kalar damuwar danake ciki babu adadinta kuma kaida mahaifiyarka ne sila,
Mahaifiyata tafita abaknki,yaushe zata fita majid kaima se idan kaki gaskiyane Hajiya itace silar
komai sonkai yamuku yawa kanku kadai kuka sani bakwa tunanin halin dazan shiga ko yarannan
shiyasa kukayi wasa da rayuwata yadda kuke so kun rabani dakowa nayi mamaki dahar yanzu
bakin cikin dakukasamin kaida Hajiya....
Tasss taji saukar mari,badee rainin haka yakai tsakanina dake? Zankuwa dauki mummunan
mataki akanki wallahi,
Betaba dukantaba seyanzu da yasamu jarababbiya irinsa duk kalar rashin kunyar dayake yiwa
hajiyar seyanzu yasan yahana a galaifinta,
Bakin cikin dakuka samin be kasheniba shine harda duka majid?babu komai rayuwa ce kuma
Allah yana nan yana kallo danshi ba azzalumin sarki bane akwai ranar kin dillanci ranar da zanyi
alfahari da y'ay'ana kuma lokacin nayi maka nisa nisanda gani kusa dakai.....sekuma tai shiru
basena karasaba inda rai da lafiya zaka ganewa idonka,
Lubna tashigo tagudunta mama kidaina kuka kema wannan baya sonki ko kamar yadda baya sona
nida su yaya abdulrahim ko?dazu Na fada masa ai kuma kice yadaina shigo miki daki tunda baya
sonki,
Hawayen idonta tagoge tanajan hannun Lubna,zokiga yadda ake guga domin kikoya ki hutar dani
watarana,har lokacin yana tsaye kuma Lubna batabar zancenba sosae tagyara zamanta tace,
Ki kyaleshi mama muma BAMA SONSHI tafada tana kallon cikin idonsa,
Sosae yafirgita dajin kalamanta,wannan kodai aljanu gareta yafada azuciyarshi yalura wannan ba
kamar uwarta da yayyenta takeba.
🤔🤔🤔 (akwai matsala kenan),
Kuyi hakuri dajina shiru kwana biyu nima ba ason raina nake hakaba.nagode
[7/12, 10:01 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfahari na)
By sophieG
A very heart touching story 2017.
Wannan shafin nakine maryam Yusuf Ina miki fatan Alkhairi arayuwarki❤
Page 16
Baby nikam wai bazakaje kwana dakin maman Lubna ba? Tunda fa nazo baka taba kwana dakin ta
ba,
Zaune ya tashi yana kallonta,bakiga yadda ta Tara yaya ba yaza ayi nakwana dakinta?,
Amma dai kasan babu dadi kar ace nice nahanaka kaje koda yaune kadai ne,
Nifa jarabar nan tata ce bazan iya da itaba kuma dayara zamu kwana adaki?
Ai kanada daki kuje can mana,seda yadan yi shiru kafin yamiqe yana kwasar wayarsa yarufe
system dinsa,seda safe yafada fuskarsa a hade,
A zahiri bayason ma kallon fuskar badee amma azuciyarsa yana azabtuwa darashinta besan
meyake damunsaba ga wani tsanar yaran maza daya tunkaroshi jiyake kamar yakamasu yaita jibga
sekuma tsoron Lubna dayake wani kalar Abu yake hangowa a idonta dabesan komeye ba amma
komenene yatabbatar da me girma ne,
Tsaf tayi shirin kwanciya tagyara yaran ta abdulrahim da abdul'azeez sune manya ta bude musu
dakin dake cikin palonta daban ta gyara musu dukda bashida wani girma amma baze matsesu ba
lkc yayi daza araba musu makwanci,kullum seta saka su sunshare dakin sbd batason kazanta
kokadan,
Sauran yaran kanana tayi musu shimfida adakinta bayan takaisu sunyi fitsari,
Ita takwanta da Lubna akan gado suna hiransu Dan Lubna badai surutu ba har bacci yadauke ta
tana jikin mamanta,
Ke kisame ni adakina inajiranki,shinen kawai abinda ya iya fada yafice,
Bin bayansa tayi da kallo,wannan mutumen wani show