Advertisements
Chapter 3 Reading YA YANA by sophieG BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

YA YANA by sophieG

Author :  sophieG Category :  Complete Novels

Chapter   3 / 13

6K to 9K   out of 36.4K words

ABIN ALFAHARINA don Allah kutausayamin Ku hango abinda nake hangowa,



Zuciyar baba takawo wuya mikewa kawai yayi yace duk abinda yataso koyasameki ko yayanki
karki sake kinemeni bejira su kawuba yafi ta,



Yaa mukhtar yamiqe shima idonsa yayi ja sosae zefita tariqo kafarsa tana roqonsa tana kuka
kokallonta beyiba sbd tawulkanta su aganinsa yajira tasake masa kafa yasakai yafi ta kawukam
yaga kowa yafi ta shimexeyi seyabi bayansu,

Gun asama'u taje zata fara mata magiya ta daga mta hannu tana miqewa tsaye kafin tace ba
kinzabi mijinki akanmu ba aiseki zauna gashinan kuma kisa aranki bakida er uwa asama'u aduniya
tana gama fdar haka tafita.



Kuka sosae badeea take batasan INA zata sakantaba en uwan datake takama dasu sungujeta harda
mahaifinta .



Nikaina kuka nake😭



Anty badee Gashinan kisakemin Mara nayi fitsari😏
[7/5, 8:06 PM] Babee Feeya: *Y'AY'ANA (Abin alfaharina)*

_by SophieG_

_A very heart touching story 2017_



Inajiran goron sallah na 😎.



Page 10




A gaskiya ta matukar bashi tausayi musamman dayaga tana kuka sosae kuma yasan tanada hakuri
fiye da tunanin sa tabar iyayenta da en uwanta ta zabeshi yana fatan kada wannan yazama babban
kuskure da zatayi arayuwar ta sedai fa yarannan nata idan yagansu jiyake kamar ya sheqesu sunyi
masa yawa dayaso kada yayan su suwuce biyu haka amma ummansa takawo matsala na rashin son
tsarin haihuwa.....



Jin an riqo masa kafa yasashi dagowa yana kallon yadda take kuka kafin tfara magna,



Abdulmajid don Allah katausaya min da yaranmu kar rayuwar mu tashiga garari kasani auren
soyayya mukayi abinda kake mana be dace ba koba don komai ba haqqinmu ne daya rataya
awuyanka ka kula mu,



Wannan haqin data ambata shiyasa shi jin haushi Dan haka tausayinta daya faraji yasoma
gushewa,



Abdul nasan bakason yarannan sbd bakaso haihuwarsu ba ammakasani yayanka ne kataimake ni
koda da abincin dazasuci ne don Allah ba....



Numfashinta sama sama yake har idonta yafara kafewa kafin yayi wani yunkuri tazube agurin,



A rikice ya sungumeta yana zuwa kofar fita da korido yaga su Abdul awajen take karamin cikinsu
yasa kuka ya rasa yadda zeyi dasu dole yasa ka su agaba sukaje asibiti,



Takaici ya isheshi ganin yadda suka cika masa mota kamar wata nursery skul bus,bayan sun isa ya
cewa abdulrahim ya kakula karyabari sufita daga motar kuma karsu taba komai aciki,



Bayan awa biyu likita yagama dubata harta farfado tana kwance yana gefenta se Harar ta yake,

Muryarta harta soma dashewa tace abdulmajid,



Cikin jin haushi yace menene?

Talura da yanayinsa batasan meyasa yakehakaba yanzu, a hankali tace kataimake ni da yayana
don Allah hawayene masu zafi suka zubo mata,



Naji zanyi tunani Kuma menene harda suma? Nace zan sakeki ne kokuma nayi sakin ?
Bakasan yanakeji ba shiyasa iyayena fa suka gujeni,



To ba ganiba ai inakusa yanzu gashi kinjamin nakashe kudi dayawa kuma ga kudin wankin mota
wayannan yayan naki duk sun batamin mota ke kin cika rigima wallahi kinjmin hasara yau
kudinnan wani Abu daze kawo kudi nasoyi dasu,



Idan tanabiyewa majid seciwon zuciya ya kasheta,

Majid a sallamemu mukoma gida banason asibitinnan,



Fita yayi yadawo da Dr aka dubuta yabata magunguna kafin ya sallamesu,



Bayan kwana biyu bata chanja zaniba dn majid baya wuni a gidan Sam balle Taji inada maganarsu
ta kwana se ranar data ristashi tun asuba take tambayarsa kan maganar babu yadda zeyi koba
komai tbar iyayenta sbd shi,



Kiringa dafa abinci dasu ama wallahi kar naga abinci anraga ko an zubar ina ganin haka za asamu
matsala bani key din store,



Damamaki take kallonsa mezakayi dashi? Ina ruwanki ki bani key nizan ringa dibar kayan abincin
dakaina yawan danakeso,

Bataso tayi gardama yace yafasa ta samu ya yarda Dan haka ta miqa masa yayi yadda yakeso
fatnta dai Allah yasa yabasu Wanda ze ishesu zata ragewa kanta damuwa sbd batada kowa kusa
yanzu Dan jiyama takira kanwarta farida awaya taimata rashin kunya kamar ba kanwarta ba,

A can gidansuma Hajiya Taji kwana biyu ba lbrn yasukayi da badee'a Dan haka seta tambayi
abbansu yadda ya amsa mata yasa takama kanta Dan cewa yayi intanason knta da arxiki karta
kuma yimasa zancen badee kuma bebata izinin nemanta ba,



Dahaka rayuwarsu tacigaba da tafiya duk ranar da yaga dama seya basu kadan koyaki dawowa
dawuri balle yabasu na rana wahala suke itada yaran Dan yanzu makaranta me kawai be chanjawa
Abdul rahim ba amma bakin jinin yayanta a idonsa yajawa abdulrahim haushi baya samun abinci
sesanda baban yadawo yadebo musu daga store kafin tagama girkawa itada yaran sun tagayyara
musamman ita datakeda ciki gashi yakai wata takwas yayi girma naban mamaki kana ganin ta
kaga damuwa cikin kadai ke girma kodan kumburin damasu tsohon ciki sukeyi ita batayi komai
yinsa kawai take bata wanidamu da sana'ar taba sbd duk ranar datayi wani abinci kafin yadawo
dakudin ze haukacemata yace yadaina ciar dasu shagonsa yayi kasa ma sbd ciyarda yaranta
dayake shiyasa duk yadda tatara kudin sedai tayi tanadinsu tayiwa yyanta lalurar makaranta, kona
asibiti,




Tana zaune a korido itada yaranta Dan yau babu islamiya yunwa natacinsu har karfe hudu da rabi
be dawoba Sega sallamarsa yashigo ta amsa masa tana hamdalan dawowarsa,



Hada ido sukayi Taji gabanta yafadi kwata kwata batason abin yanzu ga yunwa tanaji su abdul
bame iya kwakkwaran motsi sbd yunwa,

Majid don Allah kabari nabawa yarannan abinci tukunna,ohhh yaranki sunfini kenan inace nine
me bada abincin? Tona fasa sekinzo muntafi inbazakiba seki nemi abinda yayanki zasuci,semi
zauna da tsinuwar Allah data mala'iku (besan Allah ba se anan)



Dakyar tamiqe tana dafa bango ta cewa abdulrahim kaje da kannenka palona kucigaba da kallon
cartoon yanzu zan dawo damurnarsu suka wuce itaam taigaba gogan yabi bayan ta,

Dakyar tayi sallah magriba sbd tsananin gajiya,yana kwance tace Abdul muje kabani abincin na
dafa mana,kibari nahuta mana Nagaji baccima nakeji,daga haka yagyara kwanciyarsa,

Ranar dai se 9 sukaci abinci yaranma har sun fara bacci ta tashesu tabasu kafin taci nata ta kwnta,




Ranar alhamis dasafe bayan tadwo daga awo tace bari ta leqa gidan su kafin taje gdnsu majid
daukar yaranta ta tsaida adaidaita tashiga gdn gabanta ne yafadi ganin baban su zaune tunkan
taaraso yasamata stop,



Kifitar min daga gida kuma kar kafarki tayi tunanin sake dawo min gida bude baki tayi zatayi
magana yace bana bukatar jin komai daga gareki kikoma gun yayanki da mijinki masoyanki kuma
kifita da Sauri,



Tana kuka tabar gidan ga ciki dakyar take takawa tayi danasanin abinda tayi dma tayarda ta bisu a
ranar daga baya ta lallabasu ta dawo gdn mijinta,



Har ta isa gidan su majid kuka take kafin tasamu kakarsu ta lakadawa Abdul'aziz duka yamata
banna,
To muna fuka.....



Nagaji😳anty badee
[7/5, 8:06 PM] Babee Feeya: *Y'AY'ANA (Abin alfaharina)*

_by SophieG_

_A very heart touching story 2017_

This page goes to u my sister,my frnd anty shukra(Zainab yakasai)ILY.

Page 11



Daga bakin kofar ta tsaya tana sauraren kalar cin zarafin da Hajiya ke yimata yau tasaba zuwa
gidan Hajiya tayimata wulakancin da bata zato amma nayau yafi kona mata rai,



Ki karaso mana kiga kalar bannar da danki yaimin Nagano dalilinki nakawo minsu duk lkcn
dazakije asibiti sbd kawai ki takurawa rayuwata Dan kinga bana hanasu abinci bakyaso kiga
cigabana dani kike kishi Dan Dana yana kula dani to wallahi daga zan dau mataki zo ki kwashi
yayanki kubarmin gida tun bankaraa daukar zafiba na illata daya daga cikinsu,



Batareda ta musa ba cikin karfin hali ta dauki abduljabbar daketa kuka yasha duka ta gargada
sauran tayiamata se anjima memakon ta amsa se cewa tayi,

Aikam dai dole atafi mace ba control daga antaba ta seciki ke bakya gajiya da haihuwa ne kiketa
zubo Yaya haka kamar wata akuya?,

Idan ta tsaya sauraren wannan zancen tsaf naquda zata kamata Wanda ze iyasakata haihuwa akan
hanya kirjinta taji yayi nauyi sosae,

Adaidaita ta Tara duka kudin hannunta dasuka saura 90 naira ne da bata biyo gdnsu bane kudin ze
isa akaita gd me adaidaitan dayaji kudin data ambata se kallonta yayi sheqeqe, amma malama ina
ganin bakida hankali ko? Yoke konace kikawo kudin nakaiki zaki shiga? Ga Yaya rututu? Nikam
ba bakin uwa gareniba,shiru tayi tana kallonsa kafin daga baya yaitafiyarsa hakan yasa taja
hannun sauran suka fara tafiya akafa seda sukayi nisa sosae ta tari wani adaidaitan dayake sunci
Rabin tsfiyar yasa yadaukesu,
Wai Hajiya haryanzu bamu iso bane? Eh seka wuce wannan sabon masallacin kadan, ashar ya
lailayo bejira tayi magana ba yace kibani kudina malama ki sauka irinkune basason ganin cigaban
mu kinsan har nan zan kawo ki baki tsaya yimin bayani ba,kudinsa tamiqa masa dn tasan yau in
batayi ahankaliba zuciyarta fashewa zatayi,



Dakyar taga sun isa gida da zuwanta tasamu abdulmajid yana gida batabi ta kansaba tashige
dakinta wanka tayi tayiwa yaranta suka kwanta,

Yaran duk sunyi bacci sbd gajiya itakam takasa baccin ma tunani take EDD dinta saura kwana
biyar sotake ta sauke cikin nan sbd ya isheta sosae ba kadan ba bata taba yin ciki me
kwatankwacin rigima irin wannan ba fatanta dai Allah yasauketa lpy dole tfara shan magani tsarin
haihuwa aboye sbd tagaji sosae ga yayan bawani gata garesuba ita kanta tarasa nata
gatan,murmushin dyaafi kuka ciwo tayi tace a fili yaushe rayuwata zata dawo daidai kamar ta
sauran mutane?nasani abune me wahala asamu wata me irin matsalata arayuwa uwar miji da miji
sun sakani a tsakiya sun dauran laifin dabanawa ba sunkasa gano laifin daga garesu ne shi mijin
bayason haihuwa yanaso nayi family planning uwar mijin tana son jikokai tahana ayi family
planning gashi yanzu tasoma goyan bayan danta bayan dakomai yagama lalacemin, hawayeni
suka zubo daga idonta amma abin mamaki hawayene masu sanyi kuma daidai lkcn babyn dake
cikin ta yayi kicking ahankali tashafa cikin tasa hannu daya tana goge hawayen fuskarta,



Sallamar majid yasa tadawo daga tunanin datake se cewa yayi badee zokiga wani Abu yana gama
fadar yafita rigarta tadauko tasaka tabi bayan sa A gefen gado tasameshi dasaurinta takarasa
yazauna gefensa sbd kafafuwanta dasu kayi tsami sbd tafiyar kasa,



Gani me Zan gani Abu abdulrahim? Bata ga komaiba illa jin bakinsa kan nata😳,

Bayan lafawar komai tashiga sheqa amai batasan dalili ba, gefen gadon ta kwanta tanajin mararta
nadan ciwo shiru tayi kafin tafarajin abin yana Neman yafi karfin ta,



Batayi zaton abin zekai haka ba segata adurqushe dakyar ta ke numfashi,ganinta awannan yana
yin yasashi rikicewa yafara tambayarta menene?

Abdul muje asibiti inaga haihuwace,
Haihuwa ya maimaita,kuma a asibiti? Nibazan iya Da wannan kashe kudinba ki kira Yaya asama'u
mana,



Batasan me zataceba kada tayi magana ya tunzura,a wahale tace don Allah majid kakaini asibiti
kasani Yaya bazata zo ba don Allah karna mutu bakasan me nakeji ba,
Dakyar suka isa asibiti bayan ankarbeta yawuceda yaran yakaisu Inda Hajiya seda ya lallabata ta
karbesu,



Kusan awa uku tana fama kafin tahaihu tasamu baby girl yarinyar wata kalar katuwa Dan seda
akai mata sbd girman babyn,

Wallahi badi'a Nagano babu abinda yake burgeki irin kiga tattalin arzikina ya dakushe kalli bill
dinda akayomin fa? Sekisann yadda zakiyi dashi yafada yana jifanta da papern,



Binbayansa tayi dakallo seda tadaina ganinsa kafin tadawo da kallonta kan nurse dinda ke dakin
tazo cire mata cannula juyawa tayi tana ajiye babyn agefe tafara kuka,

Matar zatayi sa'an Yaya asama'u durqusawa tayi ta dauki papern tafita,

Batasan iya adadin lkcn data dauka tana kukaba seji tayi andafata ta dago tana kallon matar,

Matar ta sakar mata murmushi,
Hajiya badi'a ansallameku sbd keda babynki kunanan lpy Dan haka seki tashi kitafi gida ana
bukatar gadonnan,

Shiru tayi tana tunanin bata fito dawayanta ba Waze kaita gida ga babyn ko kayan sawa batada su
adankwalinta aka nado ta,

Kitashi mutafi zan saukeki gida tundazu dutyna yakare ganin kina wahala yasa ban tafiba najira
har naga me Allah zeyi kiyarda dani bazan cutar dakeba sunana Zainab Muhammad,



Godiya sosae tayi mata har zata fita daga motar Zainab tace, dafa tan kinada me kula dake naga
tafiyama dakyar kikeyi,



Babu kowa nikadaice se yayana kuma duk mazane kanana,



Batareda ta amsataab tajanyo waya da alama mijinta takira tana Neman izinin zata taimakawa
wata baiwar Allah a gidan ta kuma be hanataba,



Turus tayi tana kallon....
Nayi kokari yau tun asuba nake typing😜🙈
[7/5, 8:07 PM] Babee Feeya: *Y'AY'ANA (Abin alfaharina)*

_by SophieG_

_A very heart touching story 2017_

Abinda duk ka tsarawa rayuwarka ba shine tsarinka ba domin tunkan kazo duniya Allah yagama
tsara yadda rayuwarka zata kasance tun ranar da aka haifeka har zuwa ranar dazaka koma garesa,
duk abinda kaga Allah yayimaka shine daidai dakai semuyi imani da kaddara me kyau ko Mara
kyau wanda yayi haka shine cikakken musulmi kuma me imani,ina rokon Allah da ya tabbatar
mana da alkhairi arayuwar mu ameen.



Anty badee wannan shafin nakine kekadai kaunar dake tsakanin mu ta dabance ina rokon Allah
yabarmu tare yakuma bawa ustaz lafiya ameen.❤



Page 12



Turus tayi tana kallon su Abdulrahim su kadai awaje ga kofar korido abude da alama babansu
yananan dasaurinta cikin karfin hali takarasa kuSadasu,



Abdulrahim mekukeyi anan?

Hajiya ce takawomu wai fita zatayi bakowa a gidan bamu gankiba munata kuka babanmu yadawo
yabude gida shine yace nazo mukwanta muyi bacci amma karsu Abdul'aziz sushigo zasu damemu
shine nace banajin bacci yai fushi yace inmuka shigo seya zanemu kuma munajin tsoro,

Yakarashe maganar yana kuka batasan lkcn data janyosu jikin ta ba tafashe dakuka yaran ganin
uwarsu nakuka se hankalinsu yatashi suka biye mata,

Zainab dake kallon su ta lura daga yaran har mamansu sunada damuwa sosae kusa dasu ta matsa
tace maman baby kina bukatar wanka ki huta ki ajiye damuwarki gefe yanzu kinga magriba ta
kusa inaso in koma gida dawuri tun safe nafito,



Murmushi nadole badee tayi tace kiyi hakuri nabarki a tsaye,
Bakomai ai,



Ruwa tahada mata tai wanka tahada mata tea tasha seyaba kyaun gidan take talura mijin ne bashi
da hali amma gdnsa ya tsaru ta tabbata gidan ta baze fi wannan ba duk dukiyar mijinta da baban ta
kuma ga alama mijin Dan gayune sbd talura kamar sbd fenti yayi kamar ba yara a gidan,

To maman baby se abawa baby abincin ta tunda ke kin koshi,

Murmushi kawai tayi taakrbi babyn takalleta sosae sekuma ta share hawayen dasuka zubo mata
tana cigaba da kallon yarinyar ahankali tace,

Barkarki dashigowa duniya me tattare da abubuwa naban takaici abubuwa naban tausayi abubuwa
na jin dadi, kuma ina miki barka dashigowa gidan babanki dabaya kaunarki baya maraba dake
barka da zuwa hannun mamanki me cike da kaunarki Barka da zuwa hannun yayyenki masu sonki
insha Allah ina adduar Allah yabaki juriya da hakurin zama wannan gidan mecike da bakinciki ina
miki Barka......

Zainab ta rufe mata baki da hannunta, haba maman baby kada bacin rai yasaki furta abinda ba
shikenan ba ki yadda wannan rayuwar taki d yayanki kaddara ce kuma kiyi imani da ita kikasance
me hakuri kuma irin hakurinda baya karewa kinji,



Gyada mata kai kawai tayi tace kitashi anty Zainab kitafi gida dare nayi kilama kin barwa
megidanki hidimar yara,

Murmushi me ciwo Zainab tayi tace megidana ba shida matsala koda zan kwana nanne kuma
banida yara koda ya,

Ganin yadda badee kekallonta yasa tace kibari gobe zan dawo idan na dawo Zan baki lbari bani
numbernki zankiraki kiga tawa sekiyi savin idan da Marsala ki kirani, bayan fitarta badee taga
transfer na Dari biyar tayi murna sosae sekuma tayi shiru tunawa da kotakira ba daga wa zatayiba
data ta siya tabude watsapp dinta kai tsaye tanemo sunan yaya asama'u tatura mata massage
kamar haka...

As salamu alaiki

Yaya Allah yasaukeni lpy yau nasamu baby girl kitaimakemu koda da addua ne kadai na gode.

Tatura mata hoton babyn gatanan dake take kama har bakinku iri dayane.



Kwanciya tagyara musu kafin tashiga tunanin abdulmajid yana gidan amma bezo yadubasu ba
hakan yasa tanufi dakin sa dauke da babyn,dasallamarta tashiga dakin zaune ta samesa yana
signing wasu takaddu, zaunawa tayi kusa dashi tayi shiru,



Ya akayi? Yatambayeta yana cigaba da aikinsa,
Yarka nakawo maka naga ko daukarta bakayi ba,banida bukatar daukarta naganta ahannunki ai,

Bata karayin magana ba tayi shiru kusan mintuna goma sha Biyar kafinnyadago yakalleta se
idonsa suka sauka kan babyn dake ta sharar bacci abinta,

Ka taimakeni Abdul koda hudubane kayi mata kasamata duk sunan dakakeso don Allah tafada
cikin rawar murya,



Shiru yayi yafafda kogin nazari,yakamata yashare mata hawayenta kardamuwa taimata yawa ga
babyn data Haifa kyakkyawa yaji yarinyar tashiga ransa fiyeda abdulrahim dole yaimata suna da
sunan dayafiso aduniya,



Taga kamar ba shida niyyar yin abinda ta roqa seji tayi ya sunkuci yarinyar yana murmushi harda
bisimillah,

Bayan yagama abinda yadace yamiqa mata babyn yace sunan ta LUBNA(I'm in love with this
name❤),




Murmushi ne ya kwace mata lkn data tuno hirar dasu kayi auren su saura sati biyu,



Baby badee wane suna kikafiso asawa yarki ko danki? Idan nahaifi namiji nafiso asamishi
abdulrahim ko abubakar sadeeq inkuma macece nafison Fatima ko safiyya🙈 ,

Murmushi yayi yace nikuma nafison sunan babana Abdul'aziz idan macece nafison Lubna❤,

Kai amma baby bantaba jin sunan ba idan nasamu baby girl zakasamata Fatima tabiyun kuma
sekasa Lubna din ko?,

Badee kije ki kwanta kingaji yafda yana mikar da ita,



Wani kalar dadi taji daysa dole seda tayi hugging dinsa sosae irin sosae dinnan 😂😍



Wanna page din Na gobe ne lol. Luv u oll😘
[7/5, 8:07 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfahari na)

By sophieG
A very heart touching story 2017



Wannan shafin nakine meela adeel(meelolo mekan giginya😂😜).



Page 13




Shifa ko period take becika son cin abincin data girkaba sbd kyankyami kawai dai ta iya girki ne,



Badee meye haka kisakeni mana bakyajin karninda kike keda babyn😣,shiyasafa banason
haihuwar nan karnin nono da jini duk su dame mutun dauki babyn ki kutafi se dasafe,



Tasani sarai bawai don yanason babyn yasa mata sunaba kawai dai yanada wata manufa ne talura
da yadda yake kallon yarinyar ko abdulrahim baya kallo haka,



Bayan fitar ta daga dakin yasoma tunani, akwai matsala babba indai ba umma ce ttaadawa en
uwansu Na kwareba baze fada musu haihuwarnan ba kauyawa suzo su cika masa gida acinye mai
abinci subata mai gida,



A bangaren yaya asama'u kuma tana zaune tana tunanin halin da er uwarta take ciki kila yanzu
tanachan da cikinnan yasata agaba ba lpy ga yara,tsaki tayi bayan tuno yadda badee tayi agaban
mijin tanuna ta mato akansa dole yaji dadin kara wulakanta ta kuma tawatsa musu kasa a ido
amatsayinsu na en uwanta da mahaifanta, wayarta ta janyo tanaso tadaina tunanin badee tashiga
WhatsApp da sauri tannufi number ganin anturo hoto kodai hotonsu ne tafada afili har zata wuce
se kuma ta dawo,



Sosae take kallon hoton har batason kyafta idonta, masha Allah tafada tana shafa screen din
wayarta ga yarinyar kyakkyawa me kamada ita amma babu halin kulawa da ita bazata taba
shiryawa d badee ba se lkcn databar gidan Abdul majid sbd jityi ko sunansa batason tunawa balle
taji wani yafade shi hartakai ga ganin mesunan,



Amma setayi kokarin ganin zuciyarta tahanata zuwa ganin babyn karta ruguza komai,
Washe gari Zainab tana off nakwana biyu hakan yasa ta kammala komai Na gidanta bayan ta
sallami mijinta yatafi aiki ta shirya komai tanufi gidan badee, a korido ta sameta tana bacci tun a
tsakar gida take sallama bataji an amsaba, Allah sarki ta fada a fili,gdn angyarashi komai tsaf tayi
wanka tayiwa babyn sunata bacci abinsu ga alama ma yaran basa gidan,



Farkawa tayi idonta sekan Zainab da sauri tatashi zaune,lahh Anty yaushe kika shigo? Inata baccin
gajiya nasha aiki,



Ainaga alama kam keda kikeda Dinki ajikinki meye naki Na wannan urban aikin,




To idan nabarshi Waze yimin? Banidakowa akusa,

Baganiba inji Zainab tana murmushi, bani babyn a huda mata kunne kafin tagama sanin zafin
jikinta,

Bayan angama huda mata kunnen Zainab ta tattara nutsuwarta ta fuskanci badee,

Inaso kibani labrinki kumabawai don inason sanin sirrinki bane sedan

3 / 13