Author : sophieG Category : Complete Novels
ta kyale shi,
Inba zaki shigo ba zan kira baba Wallahi, Dan murguda baki tayi tashiga motar tana jin takaicinsa
sosae tasan idan tayi rashin kunya yanzu majid yaji kan mamanta ze sauke kuma batason abinda
zetaba badee danma kwanakinnan tana ganin ta se a slow ko baccin kirki batayi,
Zama tayi tabar kafafuwanta awaje tajuya masa baya,kishigo mana kinsa AC yanata bin iska yace
yana kallon bayanta,
Babu abinda na tsana irin kallon fuskarka, na tabbata ashekarar nan baza asamu Wanda zeyi kalar
danasanin dazakayiba idan kayi gangancin bari aka Daura auren nan,
Hango majid tayi yasa dasauri tasakafafuwanta tana rufo kofar,
Murmushi yayi yajuyo sosae yana kallon fuskar ta dake a tamke kamar an aiko mata Manzon
mutuwa,
Dan matsowa yayi ganin majid yashige gida yana Dora hannunsa kan shafaffen cikinta me aka
sawa cikinnan?
Dagowa tai dasauri ta kalleshi da idanunta dasuka soma chanja kala zuwa ja,
Kadauke hannunka daga jikina kuma karka kara wannan kuskuren,
Jikinki aina wane kwana nawa yarage?daga nadan Dora hannuna abinda zan mulka son r...
Mari ta wanka mai shine sanadin tsayawar sauran kalamansa,
Dan iska la'ananne wallahi ka gaggauta fadawa mutanen nan kafasa auren nan Dan zakayi
danasani fiye da tunanika,
Fitowa tayi tashigewarta gida tana zuwa tabawa badee labari atake badee taji batada lpy,
Addua kawai tasa agaba Allah yakawo musu mafita,
Washe gari koda suka tashi majid yakawo wani shirgegen kato wai gadin lubna zeyi karta fita,
Duk basu tabbatar da abinba seda suka ga lallai fa auren zemata haryaraba invitation card duk
masifar Hajiya al'amura sun tsaya,
Kuka lubna take kamar ranta ze fita yanzu gobe za auramata mijin dabataso,
Yayyanta duka suka zauna adakin mamansu suna jajanta all al'amarin ganin kawai sukayi
abdulrahim yafita bababu jimawa segashi yadawo,
Wardrobe dinsu ya warware wata katuwar jaka yahau zuba kayan su lubna aciki,
Saboda bacin rai har inner wears seda ya zuba a ciki se kallonsa suke,kusan duka kayan su ya
kwashe dama kayan bawani yawa garesuba,
Badee tace abdulrahim mekake shirin yi?
Gidan zamu bari Wallahi bazaku kwana gidannan ba harmuma,
Yajuyo yana kallon kannensa yace,Ku shirya fada zamuyi megadin can ymzamuyiwa dukan tsiya,
Abdul'aziz ya kwashe da dariya kai yaya idan kakaimu can Waze bamu abinci,?
Allah zebamu kamar yadda yasaba bamu,
Kutashi mu tafi,aidasauri lubna ta tashi Dan duk wata hanya dazata sa afasa aauren sonta take,
Suna zuwa gate megadin yataso yana kallon lubna,
Ke koma megida yace kar abarki ko gate ki l....
Kyakkyawan naushi yasamu daga Abdul'aziz sauran suka riqe shi,
Kabarta ta fita inkayi gardama jikinka yayi tsami,inji abduljabbar,
Itadai badee wani dadi takeji ganin yadda yayan ta suka soma zama abin ALFAHARINTA,
Abdul'aziz yaja hannunta Dana lubna suka sasu a adaidaita yakaisu gdn hajiya,
Zuwa yai yace kusakeshi kuzo mubi bayan su gobe zamuzo adebi kayan shimfiida Dan babu
makwanci a gidan,
Me gadi kam bakinsa yatoshe daya sha haushi,shima Barin gidan zeyi dama anbashi Rabin
kudinsa,
Hajiya har kuka tayi data gansu rayuwar majid nacikin hadari batasan ta ina zata faraba yanzu
sunbarmai gidan Siya cinye shida safara'u,
Majid da safara'u dasukaje kware sun dawo suka samu bangaren badee a rufe ga megadi baya nan
dakinsa ma bakomai,
Sosae suka firgita ganin har suna shirin kwanciya basu dawo ba, safara'u takafe mai kafafuwa baze
iya zuwa gidan hajiyarsa ba seya tuna can kadai su keda mafaka hankalinsa ya Dan kwanta,
Wani kalar nishadi safara'u takeji yanzu tarabashi dakowa saura dukiyar sa dama Dan ita kadai
take tare dashi burinta Dana mahaifiyarta yakusa cika,
Danhaka ta zage damtse taiwa majid tarba me kyau yau,
Washe gari yakira baban Mubarak yace amarya tagudu tunjiya yake nemanta babu labari,
Yanzu alhaji kasan yarinarnan bataso zata tursasata?nidai ko anganota yarona yafasa danbanason
tashin hankali,
Be jira majid yamasa bayaniba yakashe wayarsa.
Daga nan auren ya lalace,
Saura kuma muji yadda safara'u zatayi da babyn ta.
Kuyi hakuri da Dan Wannan pls.😍
[7/30, 9:28 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfahari na)
By sophieG
A very heart touching story 2017.
Page 27
Rayuwa tayi musu dadi a gidan hajiya domin basuda wata damuwa sosae su Abdul ke kula da
gidan dakyar ne zasu wuni su kwana dayunwa tun safe suke fita idan babu makaranta inbasu bar
abinda za aciba Dayansu ke dawowa yakawo sana'ar su gyaran waya ne kuma suna siyan wacce ba
sabuwa ba su kuma siyar Dan haka basuda matsala sosae suke fahimtar juna koda sun samu
sabani,yanzu hakama sun siyawa lubna keken Dinki datafara koyo kuma tana Dan kokari dukda
bata kware sosae ba kuma en unguwar basu sansuba sosae sedai ma mutanen hajiya ne dake kusa
sosae suna mutunci shiyasa suke kawo dinkin,lubna ma daga ankawo style taga me wahala ne take
cewa ki chanja me sauki kokuma ki kai wani gurin karna bata miki,dinkin yara idan tayi seyafi
kyau doguwar Riga kamar akanti kika siyo,zaman banza ya kare,
Bangaren majid kuwa sati daya da tafiyar su badee abubuwa suka soma sauyawa kwata kwata
hankalinsa ba akwance yakeba duk tunaninsa yakoma kan badee da yayanta ya kama hanyar gidan
hajiya har besan iyakaba amma seya kasa zuwa daya matsa dabi hanyar sedai yaga tarin traffic
dabesan daga inda yafito ba harseyagaji ya sauya hanya damuwar tai masa dawa har rama yayi,
Safara'u tazama gagarumar me mulkar gida se yadda takeso za ayi kwata kwata yanzu bata zama
gidan en aiki tadebo ta zuba tafita lokacin da takeso tadawo lkcn dataga dama idan yayi magana
seta balbaleshi da masifar kamar uwarsa karshema shine zebata hakuri,
Mamana ta kaina kinga abinda nace yana shirin tabbata ko?sannu sannu bata hana zuwa....
Sedai adade ba akaiba er gaban goshi,
Kusan shekara goma shabiyar muna fama seyanzu hakarmu ke shirin cimma ruwa,kai amma fa
munsha jira,
Safara'u da mahaifiyarta ke magana Dan har kware taje sbd yanzu da motarta da driver intafara
yawo se indai mai yakare mata,
Yaya asama'u yau takudura aranta duk yadda za ayi seta shiga gidannan tagano kanwar ta seyanzu
take hango kalar da girman kuskuren dasuka yi ido a rufe,tashafe sati biyu tana yawon hanyar
gidan kowani daga cikin su badee da yayanta ne tagani kozataji sassauci aranta,
Mamaki sosae yakamata ganin bangaren badee'a arufe sedai hankalinta yadan kwanta dan taga
sabon apartment daya sha gyara kila kuwa badeen ce aciki dasauri takarasa tana buga kofar,
Kallon mamaki takewa matar data fito tana wani yauki ga kiba duk ta hade ta zama shapeless,
Lafiya dai kika bugamin kofa na bude kuma kin kuramin ido?
Hmm...tasauke ajiyar zuciya,Dan Allah nanne gidan Abdulmajid me mata badi'a?
Ita safara'u se yanzuma ta lura da matar tana kama da badee'a sedai da matar da lubna kamar an
tsaga kara ko ince tamkar yaya asama'u tayi kaki,
Eh nanne amma yanxu nice matar sa badee'a bata gidan yau kimanin wata biyu data gudu itada
yayanta annemesu an rasa danhaka seki kara gaba kuje zuwa nemanta,takarashe maganar tana
yatsina fuska,
Idon yaya asama'u yacika da hawaye,daga ganin Wannan matar ta majid er bariki ce ta karshe
kokuma tantiriyar Mara kunya duk yadda akayi masifartace ta ishi badee'a yasa tabar gidan,
Muryarta araunane tace sakinta majid din yayi?,
Bakiji nace guduwa tayiba?be saketaba mugun halinta de yasa tagudu wayasanima ko yawon
barbada ta tafi?,
Ran yaya asama'u yabaci sosae danhaka juyowa kawai tayi tana goge kwallar fuskarta basuga ta
zamaba dole su tashi tsaye Neman er uwarsu tabar gidan miji karta fada mugun hannu kokuma
mummunan yanayi itada yayanta,
Zama tayi a mota tayi kuka harta gode Allah tana Dora duka laifin akanta ma koda su baba sunyi
fushi da ita yakamata ace sun saurareta ita macece kuma tasan kalar abubuwan da ita badee take
facing kuma ma akan gaskiyarta take me raba da da uwa irin haka se Allah balle ace tabar su gdn
da agaban idonta ma basuda wata daraja kuma ace tabar su to hannunwa?Waze mata tarbiyarsu?
soyayya ta shafe komai dukda zata iya hakuri amma yakamata ace sun mata uzuri,
Ganin babu sarki se Allah yasa ta share hawayenta tan tunanin gunwa ma zata fara zuwa?yaya
mukhtar kam baze saurareta ba,
Gidan farida tayanke zataje dukda faridan batada mutunci amma dole zuwa yanzu tanemi er
uwarta Dan koba komai tana sonta,
Bangaren badee kuwa hankalinta kwance sedai jin kusancinta da iyayenta yasa taji duk hankalinta
yakoma can dan unguwarsu daya da hajiya sedai layi ne ba daya ba sedai kuma babu wani nisa a
tsakaninsu,tafara tuno moment dinsu da en uwanta,
Afili tace koyaya su ummu suke nasan dai sunanan araye, inaso naga farida nasan itama zuwa
yanzu yayanta sun girma,
Allah kadawo da hankalin en uwana da iyayena Agareni, ameen inji lubna dake tsaye tana
kallonta.
Kuyi hakuri da wannan don Allah banida lafiya kuma dakyar nayi typing sena samu ya
goge,Tnx😍
[7/31, 9:11 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfahari na)
By sophieG
A very heart touching story 2017
This page goes to you my everlasting momma Zainab inuwa #aka Anty sis👌🏻,may Allah's noor be
wit u now and forever😍.
Page 28
Sosae badee takejin batada lafiya zuciyarta ke mata ciwo tafi 2weeks ahaka sedai bata fadawa
kowa ba,
Batasan tana kaunar mijinta ba seyanzu, yanzu dayai mata nisa,badan faricikin y'ay'ana ta ba
bazata baro gidanba kodan giftawarsa datake gani yana rage mata damuwa dayawa duk wayannan
abubuwan dayayi daga auren safara'u zuwa yanzu bata Dora laifin akansa sedai akan safara'u
aganinta duk ba acikin hankalinsa yake aikata hakan ba,
Sosae take jin tanason ta kusantu da mijinta amma yayi mata nisa irin nisanda batasan lokacin da
zasu sake haduwa ba tadade bata ji irin wannan yanayin ba ga ciwon da zuciyarta yana dad'uwa
batason fada ne kada hankalinsu yatashi,
Addu'a take Allah yakawo mata saukin wannan ciwon kodan taga iyayenta taji sanyi kuma tanaso
taga farin cikin y'ay'anta,kuma dole idan tanaso taji sauki a zuciyarta to seta cire Abdulmajid
aranta Wanda take hango dinbin aiki agabanta,
Washe gari tunda sassafe takejin babu dadi jikinta har rawa yakeyi har gurin sha biyu tana kwance
hajiya batanan ta tafi kware da Abdul'aziz zata karbo amfanin gonarsu lubna ce kadai a gidan
itama yau aiki take tun asuba take wanki kayanta na badee Dana hajiya se 11:30 tagama se kawai
tayi wanka ta Dora abincin rana dakin tashiga tadan kwanta tahuta kafin ruwan shinkafar data
Dora yatafasa,saukar numfashin mamanta taji yana fita ba daidai ba dasauri takarasa kusa da ita,
Mama menene?bakida lpy ne?amsa ko daya badee bata bataba illa hannunta data riqo tana
dumtseshi sosae saboda ciwon datakeji a zuciyarta,
Dasauri badee ta fito waje a daburce,dakinsu Abdul tanufa sekuma ta tuno bakodayansu a gidan ga
hadari har anfara yayyafi hijab dinta kawai ta dauka ta kwaso uwar tata dakyar take tafiya,
Babu kowa akan hanyar balle tayi tunanin zasu samu abin hawa,
Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un kawai take maimaitawa a lokacin kuma aka tsuge da ruwa,
Afili tace shine amfanin waya dayanzu nakira yaya Abdulrahim,
Tsayuwa ta gagari badee Dan haka tasulale akasa ta kwanta bata damu da yanda ruwa ke dukanta
ba ko magana takasayi lubna take tunani Dan tasan mura bata mata da kyau,
Wata bakar mota ta hango kirar Benz baka tana tafiya slow saboda ruwan da ake,
Mus'ab dake tafiya yana danna wayarsa soyake yaji ya lafiyar matar sa dukda yasan koya kira
rashin mutunci zatayi masa amma a condition dinta yakamata ace yasan yadda take dukda bejima
da baro gidan ba dago kansa yayi yaga er yarinya budurwa tana tsaidashi ga mutun yana gani
yashe akasa Dan haka yai saurin yin parking daga gefe yafito da sauri,
Ke lafiya meyake faruwa?
Dakyar take magana numfashinta nayin sama sama tace,
Mama na kataimakeni zata mutu don Allah,
Hanzarin kwasar badee yayi yasakata abayan mota dasauri lubna tashiga bayan tana rungumo
mamanta dake ta juyi ajikinta,
Baze iyayin gudu da motar ba sbd ruwan da ake ga asibitin dayakeso yakaisu dadan nisa domin a
can yake aiki yanaso yadubata Dan ga alama tanajin jiki kuma yagansu lyk they are helpless,
Bayan sun isa asibtin yafito dasauri yadauki badee ya nufi emergency lubna na biye dashi abaya
tana sharar kwalla, yakai kofar da ze shiga wayarsa ta fara Neman agaji,
Gado yasamu a gefe ya Dora ta kafin yadaga wayar ganin sunan mahaifiyar matarsa,
Sannu isashshe yanzu kabar matar ka a gd naquda ta kamata munzo asibiti baka nan danhaka duk
inda kake kazo muna labour room,
Wani Dr yahadasu dashi Dan duk yarikice yanufi gun matarsa,
Bayan mintuna goma da shiga da badee Sega Dr din yafito yamiqawa lubna wata paper yai mata
kwatancen chemist,kiyi sauri kikawo muna bukatarsu yanzu,
Kallon paper take taga tarin abubuwan bukata batada ko kobo take hawaye suka fara zubowa da
idonta kusa da chemist din taje tazauna akasa,
Mus'ab kuwa kafin yakarasa labour room har matar sa ta sauka, shiga yai yasamu ana gyara su
sedai babyn kamar tazo da mura Dan haka dasauri yasauka siyan magani,
Dasaurinsa yakarasa kusa da lubna shiya manta ma dayazo dawata saboda murnan babyn sa da
tazo atake kuma yatuno da fuskar lubna aransa yace itace wacce naketa burin Allah yasa ke hadani
da ita Alhmdllh,
Baiwar Allah ya akayi?mekike yi anan?,
Cikin Muryarta data soma dashewa tace,abubuwan buqata zan siya kuma ban fito da kudi ba don
Allah kataimaka ka aramin kudin,
Amsar takardar yayi yasiya abubuwan dasauri har ya juya ya hango matar sa da mahaifiyarta suna
zuwa yanayin fuskarsu yasa jikinsa yayi sanyi,
Karbi inji matar sa me suna jameela tana miqa masa babyn,
Kasa amsa yayi yatsaya yana kallonta yana marairaice fuska,
Kasani nafada maka daga ranar Dana haife maka danka ko yarka zamana dakai yakare kuma
bazan taba shayar ma da itaba danhaka gatanan tafada tana ajiye babyn a kasa,
Lubna dake kallon ikon Allah tayi saurin zuwa ta dauke babyn daga kasa,
Don Allah jameela ki taimaka kishayar da ita konawa kikeso zan baki,
Batareda ta amsashiba tajuya itada uwarta dake zugata suka fice,
Kallon lubna kawai yayi yace mutafi aduba jikin mama,
Yadda yayi duk setaji tausayinsa,
Ki tsaya anan zan dubata sedai karki bari ta kwashi sanyi,
Gyada masa kai kawai tayi tana kallon babyn datayi bacci a hannunta,
Bangaren jameela kuwa a zuciyarta tana jin soyayyar yarta sosae sedai abinda mahaifiyarta tafada
mata bazesa ta iya kula da yarinyar ba.
😂😂wasu Na cewa wahalar tayiwa badee yawa yakamata tafara jin dadi yanzu Dan Allah kuyi
hakuri kubari yatafi yadda na tsarashi I promise u a very happy ending insha Allah har Dan luv za
a tabo ammafa niban iyaba saboda banayi😜
[8/1, 11:09 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfahari na)
By sophieG
A very heart touching story 2017
Masu karatu sekunyi hakuri dani Dan sosae nake mistake agurin sunayen yarannan danasan zasu
rikitar dani haka daban saka suba amma zanyi kokarin ganin Na kiyaye nagode.
Page 29
Komai jiki asanyaye yake yinsa haryagama duba badee tayi bacci yasa akai kaita daki annex Shiga
dakin yasamu lubna azaune ta Goya babyn dake bacci da alama yarinyar batada rigima,
Kawo ta nakai ta gida idan da wata matsala seki kirani,yafada yana tsaya wa bayanta Dan ta
kwance zanin goyon,
Banida waya itama mama batada waya shiyasa kaga ina Neman taimako kasancewar duk yayyena
basa kusa,mun gode sosae Allah yasaka da mafificin alkhairi kudin ka kaga gidan mu adaidai inda
kadaukomu zuwa next week insha Allah zanyi kokarin hada maka kazo ka karba,
Kallonta kawai yake yadda take magana cike da manyance seduk yaji ta burgeshi dama tun
lokacin yake rokon Allah yasa ke hada su, murmushi yai mata kafin yace zandawo zuwa anjima
idan ma dasauki sosae za asallame ku,
A hanya tunani yake Waze bawa yarinyar nan reno mahaifiyar sa bata gani ga kanwarsa akwance
komai se an mata ba magana sedai ido kawai larai ke kula dasu duka ayyuka sun mata yawa amma
bashida yadda zeyi yanzu dole ze gwada zuwa lallashin jameela kokuma yasamu wata wacce zata
kula masa da ita ,amma zeyi matukar bakin ciki idan er ta girma a hannun me Reno zefi kyau ta
girma a hannun mamanta,
Huci yafitar daga bakin sa me zafi yana shafa fuskarsa da duka hannayensa bayason hayaniya
kokadan segashi rayuwar sa tazo da kaddara me tarin yawa damuwa Na nema tayi masa yawa,
Bayan la'asar su hajiya suka dawo sunsamu babu kowa agidan kuma ga gidan abude basu yi
tunanin komai ba suka zauna zaman jiran dawowarsu kila basu yi nisa ba,
Wasa wasa har kusan magrib basu dawoba Dan haka suka fito kofar gidan Abdul'aziz yakira
abdulrahim yafada masa su lubna basa gidan a rikice yadawo,
Hajiya tashishshiga makota nakusa dasu amma sunce basu shigo ba hankalinsu yakara tashi
sunanan tsaye akakira sallah danhaka suka shiga gidan suyi sallah,
Bangaren badee kuwa kusan magrib dinnan ta farka garau taji jikinta danhaka tace a sallamesu
dakyar lubna ta rarrasheta tabari suyi sallah,
Mus'ab yadawo asibitin Dan yaduba jikin wayannan mutanen dabesan kosuwayeba soyake
hankalinsa yakoma gu daya irin yadda hankalinnasa ya karkasu bayaso yanaso yai focusing akan
damuwa daya,
Azaune yasamesu har kasa ya durkusa yagaisheda badee yamata yajiki ta amsa tana cewa, naji
sauki don Allah a taimaka asallamemu mukoma gida bawanda yasan inda muke kar hankalin su
yatashi,
Mama bakyajin komai ne yanzu?
Babu abinda nakeji mungode sosae Allah yabiyaka yaimaka albarka,
Ameen ya amsa yana murmushi, fita yayi babu jimawa yadawo da paper hannunta da ledar
magani ahannunsa,
A kofar gidan suka sami su Abdul cirko cirko suna jimami fitowa sukayi nan lubna tai musu
bayanin shine yataimake su sosae suka masa godiya daga baya sukabi badee Lubna kuma yake
mata bayanin yadda badee zatasha maganin,
Har yajuya ze tafi yajiyo muryar lubna tana magana,
Yanada kyau muyi hakuri dakomai da ze riskemu a rayuwar duniya dolene ajarabcemu Dan dolene
a gwada imaninmu wannan jarrabawace ta duniya idan muka cinyeta zamu ga daidai idan kaddara
tazo mana semu karbeta da hannu bibbiyu mekyauce kokuma sabanin haka nalura kamar kanada
damuwa kuma yau naga daya da idona ina rokon Allah daya raya babyn nan akan tafarkin addinin
musulunci yakuma albarkaci rayuwar ta,duk yadda rayuwa tazo maka sekayi godiya ga Allah
domin idan kaji ta wasu sekaga taka bama komai bace, idan ka koma gida ka shafa min kanta don
Allah,
Takarashe maganar muryarta na rawa da alamun kuka takeso tayi,
Duk abinda hakuri be bayarba rashinsa baze bayarba,dabana hakuri dabansan iya cutukan dazasu
sameni ba damuwa taimin yawa inaso tarage min kozansamu sassauci,
Ina rokon Allah daya kawo maka mafita,baka fadamin sunanka ba,
Sunana Mus'ab Muhammad Sharif, nikuma sunana lubna Abdulmajid tafada tana murmushi shima
murmushin yayi kafin yai mata sallama yawuce,
Yarinyar tashiga zuciyarsa sosae dole yanemi kusanci da ita amma tayaya?
Bari nasan yadda zanyi damatsalolin gabana kafin nakama wannan tunda nasan gidansu kuma
bamuda nisa sosae hankalina akwance yake kusan unguwar mu daya ma,
Bangaren majid kuwa komai ya gagareshi albashinsa se yadda tayi dashi idan anyo cinikin kasuwa
da kasonta aciki ita kanta batasan iya adadin dukiyar data Tara ba,
Hajiya nifa plan dina yanzu bewuce asakomai ciwo ba ahankali Wanda zegagara yin komai se
yakai stage dinda shikanshi yagaji da duniyar sena kwashi dukiyoyina nabarshi banida matsala,
Eh kuma shawarar ki tayi Dan haka kibari wani satin kizo muje dakanki ayi maganar kuma kizo
dakudi sosae domin aikin yayi saurin ci,
To shikenan hajiya sekin jini,(wa'iyazubillah Allah ka kallemu da idon Rahama ameen),
Yaya asama'u ta fadawa farida yadda sukayi da safara'u yaya asama'u bamuga zamaba tashi mutafi
dole munemeta muje gida a fadawa su alhaji don Allah,
Sun samu ummansu da alhaji suka zayyane musu komai atake ummansu tafashe da kuka,
Dama irin wannan ranar nake so tazo....
Masoya littafin matsayina anty billy tace nabaku hakuri dajinta shiru kwana biyu insha Allah gobe
ko jibi zakuji ta,mun gode ❤
[8/2, 5:05 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfaharina)
Na
SophieG
A very heart touching story 2017
Idan nabaku