Author : sophieG Category : Complete Novels
Ameen tace murna fall aranta datasan mijinta ze taimaka wa yar uwarta batareda wani tunaniba
aida tuni tasanar dashi, godiya tayi masa dukda batasan mezaiyiwa badee'ar ba,
Washe gari motarsa yabata yace sakon yana ciki se kuma kudi yabata kuma tacigaba da hakuri
insha Allah zata ga ribar yinsa,
A palonta tasamesu abdulrahim kadai yaje makaranta,
Bayan sungaisa Yaya tace
Yanaga yaran basuje makaranta ba?
Babu abincin dazan basu sutafi dashi kuma lesson suke se 3:00 suke tashi kinga ko bazan turasu
haka ba da idan banida abinda zan basu nakan Debi nashi idan nasamu nabiya to yan zuma
koshinkafa yadaina kawo buhu awo yake duk bayan kwana biyu,
Hmmm shikenan Mahmoud ne yabani sako nakawo miki mijinki dai bayanan ko?
Bayanan ta amsa tana kallonta,
Hanyar fita tadosa tana cewa kizo mu kwaso kayan,
Abu biyu take ji axuciyarta murna kuma da takaici yadda mijin yayarta ytaimaketa haka amma
mijinta abin kaunarta yakasa taimakonta,
Kayan abinci ne masu Dan yawa balaifi sekuma kudi dabansan konawa bane,
Yaya asma'u tace sekuma nawa taimakon duk abinda ake so amakarantarsu kifada min insha Allah
zan taimaka kafin muga yadda za ayi achanja musu makaranta,
Cikeda murna tayi godiya kuma zatazo har gida tayiwa mahmoud godiya,
Tundaga wannan lokacin mijin asma'u yake taimakonta dukda watarana takan tashi cikin rashi
mijinta kuwa besan meke gudana ba yana ganinta dai tarage damuwa da al'amuransa amma acikin
zuciyarta itakadai tasan damuwar datakeda game da abdulmajid,
Kwana biyunnan bata jin kanta daidai fargaba take Allah yasa ba abinda take zargi bane,jiya batayi
bacci ba zazzabi takeji ajikinta yadda gabanta ke faduwa yahanata bacci,
Yau kusan sati daya kenan tana fama duk abinda zataci baya zama tayanke shawarar kiran Yaya
asama'u,
Kinga bari idan nataso daga aiki Zanbiyo da abin awon ciki mugani kibar kuka,
Yaya asma'u tace bayan tagama sauraren badi'a data kirata awaya,
Karfe uku agidan tayimata,
Karbi badee shiga kiyo fitsari anan inkin gama ki kirani nazo,
Wani kalar dokawa da zuciyarta tayi lokacin da Asmau tafada mata ciki ne da ita,
Yaya muxubar dashi wallahi bazan iya ba wahalar tayimin yawa,
Kice kintuba badeea wasu sunacan suna Neman haihuwar kamar zasuyi hauka amma basu samuba
kigodewa Allah tunda rabon wannan yazo zaki haifeshi sedai idan kin haihu zamu dauki mataki
kuma kifadawa mijinki kinadauke da cikinsa karki boye masa komai,
Shikenan Yaya nagode Allah yabar zumunci tafada hawaye nabin kuncinta,
Bayan tafiyar asma'u tazauna tayi koka har bata gajiba ba abinda ke daga mata hankali irin....
[7/5, 8:06 PM] Babee Feeya: *Y'AY'ANA (Abin alfahari)*
_by SophieG_
_A very heart touching story 2017_
*Abu nabiyu dayake janyowa mutun bakin jini shine wulakanci sekaga wani ba abinda yake burge
shi irin yawulakanta dan adam,ko dabba kake wulakantawa zata nisance ka balle kuma mutun me
hankali,idan kana wulakantarwa sekowa yaguje ka bawanda yakeson kusantarka*.
*kutuna ita zuciya tanason Wanda yake kyautata mata kuma tanakin Wanda yake musguna mata
saboda haka mukiyaye*
Page 7
11:36pm abinci take bawa jabir dukda yadda yake nuna baya so amma dole zatabashi yaci koda ze
Harar ne magani takeso tabashi inyai bacci se taje gun jarababben ubansa,
Yadanci kadan paracetamol tasake bashi ko zazzabin ze sauka tasamu yayi bacci,
Babu jimawa kuwa bacci ya dauke shi,doguwar rigar bacci tasaka ta zauna yiwa yaranta addua,
muryarsa taji yana cewa,
Kinyi rantsuwa senayi miki kira nabiyu zakizo ko?,
Batace dashi kokaiba seda tagama yimusu addua,hannunsa takama sukabar dakin dan bataso
yadaga murya yatashi jabir,
Shikadai yai kidansa kuma shikadai yai rawarsa,
Kallonta yayi ta lumshe idonta tana hutawa,
Wannan wani sabon salone badee?
Tagano sarai meyake nufi amma bata tankasa ba sema shigewa bayi tayi tabarshi dabaki asake,
Rigarta tamayar jikinta takwanta dan jiri ma takeji,
Shima wankan yayo yahawo gadon cike da masifa azuciyarta tace bari kayi masiifa me dalili,
Yabude bakinsa zeyi magana tace,
Inada ciki!
Ci me?
Yatambaya yana miqewa zaune,
Ciki bansan wata nawa bane amma zekai wata uku,
Waike bakida hankali ne bakya gajiya da haihuwa ne?
Dani da kai se aga Mara hankali,
Yasan gaskiya tafada dan haka yayi kasa da murya,
Wai badee babu yadda zakiyi ki abinnan ko dole seda family planning ake wannan din?
Zaune ta tashi sbd abin yamatukar bata mamaki,
Kadaina jarabar nan shine family planning bayan na asibiti kabari se sanda kaji kanason asake
haifama da ko ya nabiyu Wanda zakaciyar kakaisu makaranta dakanka kadauko su sukuma sauran
shegu ne,
Fuska yahade,
Badee ni kike gaywa magana?,
Banason damuwa Abdul kasan condition dina yanzu ina bukatar Hutu,
Kwata kwata yakasa bacci duk laifin hajiyata ne wallahi,
Washe gari har yaran suka tafi makaranta jabir yana bacci se karfe goma yatashi da zazzabi ga
kansa ya dan kumbura,hankalinta yatashi Sosae addu'a take Allah yabashi lafiya, (nace ameen)
Wasa wasa karamin Abu ya zama babba dan ciwon jabir se gaba gaba yake kansa yayi wani irin
kumburi mahaifiyarsa duk ta gigice,
Abdul jabir fa balafiya kalli yadda kansa ya kumbura,
Uhm nagani Allah yabashi lafiya,yana gama fadar haka yajuya ze fita dasauri takarasa kusa
dashi tana rokonsa yakaisu asibiti dafarko soyai yashare ta sbd yau yanada abubuwan dazeyi kuma
kudi zasu shigo amma ganin ta zauna kasa tana kuka yasa yace tazo sutafi,
Dole aka kwantar dasu amma bill kodaya babu Wanda abdulmajid yabiya acewarsa yarontane
intaga dama tabiya,
Dan Allah abdulmajid kayi hakuri kaceci rayuwar danka kaji ance ma se anmasa aiki,
Karki kara cewa dana danki dai tunfarko seda nafada miki kiyarda azubar dashi kika ki kuma seda
nafada miki duk dan dakika Haifa bayan abdulrahim toki shiryawa dawaiyarsa,
Dagowa tayi tana kallonsa kafin tamaida dubanta ga mutanen gurin kusan dukansu suke kallo
cigaba yayi da surutansa cikin daga murya,
Yaya gasunan jeka inbika ko shekara takwas ba ayi da aurenmu ba amma Yaya biyar gana shida
nan kan hanya mace babu control kana tabata se ciki gida Yakoma kamar makarantar naziri
(tik'ek'en jahili),
Juyawa kawai tayi tanufi dakin da aka kwantar da jabir kukanma yaki zuwa seyau take danasanin
auren abdul bata taba tunanin jahilcinsa yakai hakaba,
A gida kuwa yaran sundawo se kuka suke basuga mamansu ba abdul nacikin daki yafito yadaka
musu tsawa atake suka hadiye kukan,
Anacikin haka Sega mahaifiyarsa tazo unguwar barka shine tabiyo gidan,
Bataga uwar yaran ba ta tambaye sa yafada mata suna asibiti tattara kan yaran tayi tace dasu zata
tafi har kaninsu yaji sauki sudawo gida,
Har bayan kwana biyu gidan su ba asaniba seda Yaya asam'u takirata take fada mata suna asibiti
da jabir,
Yaya tayi mata fada sosae dan bata fada ba har ankwana biyu,
Alokacin kuwa badee zaune kawai take tana jira taga abinda Allah zeyi.
[7/5, 8:06 PM] Babee Feeya: *Y'AY'ANA (Abin alfahari)*
_by SophieG_
_A very heart touching story 2017_
_this page goes to you baby nurse(fatima zarah)_ ILYSM
*Abu na uku dayake janyowa mutun bakin jini shine munafurci*
*munafiki betaba farin jini ba, munafiki annobane idan ana zaune dashi babu abinda yakeso irin
yaga ya tarwatse zaman*
*munafurci yana kunshe da abubuwa ne guda uku*
*abubuwannan guda uku idan mutun yakasance acikin daya dagacikinsu to yatabbata munafikine*
*na daya shine duk yadda zefada magana to baze fadi gaskiya ba cikin kaso Dari bazaka samu
kaso daya dayakasance gaskiya ba acikin maganarsa wannan shine makaryaci zakuga daga yazo
za afara sulalewa saboda ansan indai yazauna ya ringa zuba karya kenan and the worst part of
zama makaryaci shine duk yadda yazo da gaskiya baza'a taba yarda ba koda kuwa ze hadiye
Qur'an yana kashin ayoyi ne baza'a yarda ba saboda kasaba zama kana sharara karya watarana
zaka iya zuwa kayi magana akan abinda kai ko waninka yake bukatar taimako alokacin amma
kowa seyai buris dakai saboda bakada gaskiya kunga kuma tun anan ansamu matsala kenan*
*munafurci babbar cutace don Allah mukiyaye*
Page 8
Yaya asma'u ta firgita sosae dan ganin yadda kan jabir yakumbura sosae se kuka yake batun atada
shi zaune bema tasoba ga uwarsa ma akwance wani kalar jiri take gani idan ta miqe gani take
dama takoma hagu (abin tausayi),
Dasauri anty asma'u takira yayansu mukhtar tafada masa halin da ake ciki ba bata lokaci ya iso
asibitin,
Yayi mata fada sosae ganin yadda jikin yaron yayi tsanani amma ace har kwana biyu bata fada ba,
Hakuri tabasu wallahi ita batasan mema zatayiba abubuwa sunmata yawa itama batada lafiya,
Yanzu ina baban sa? Ya mukhtar yatambaya,
Tun ranar damukazo ko awaya bekara kiran mu ba kuma yace kar akara tambayarsa koda kudin
maganine aranar ma bebiya kudin komai ba yayi tafiyarsa,
Magana take tana kuka da alama ma batasan maganar nafita ba ganin yadda idonta suke a rufe,
Bari kuga naje naga Dr daga baya mayi maganar yaronnan yanajin jiki idan aiki za aimasa
senakira babansa muji yadda za ayai yana gama fadar haka yafita daga dakin,
Shiru tayi tana kallon yadda jabir yakura mata ido ko k'iftawa bayayi ahankali ta riko hannunsa
kara riqe hannun yayi yana lumshe idonsa bayan dan lokaci taji yasauke ajiyar zuciya kuma ya
dan saki riqon dayayiwa hannunta, gyara masa kwanciyarsa tayi dan yaji dadin baccin,
Asma'u nagefe tana kallonta atake taji zufa nakaryo mata,
Mukhtar ne da Dr suka shigo dakin ze duba jikin jabir susaka lokacin da za aimasa aiki,
Yaya asama'u tana gefe tanajira taga yadda Dr zeyi bayan yagama bincikensa,
Dagowa yayi yna kallon badee dan yasan itace uwarsa besan taya zefara fada mata jabir ya rasu ba
se kawai yaja hannun mukhtar suka fito,
Se hakuri yace yana kallon mukhtar,
Allah yajikan sa yasa me ceto ne wannan yaron yafi 30mnt darasuwa kuyi hakuri yana gama
fadar haka yajuya dan ganin yadda mukhtar ya qame,
Dake wayayi yashiga dakin kokallonsu bebiye ba yashiga nado jabir acikin zani yamaida kallonsa
ga badee,
Ku tattaro kayannann mutafi gida,
Dasauri tadago tana kallonsa atake tagano jabir mutuwa yayi ganin yadda mukhtar yarufesa ruf
har fuska da zani,
Batasan lokacinda takai jikin bangoba dakarfi ta rufe idonta kafin tabudesu atake idonta sukayi ja
kuka takeso tayi amma yaki zuwa,
Asmau ce tashi ga hada kayan cikin karfin hali tanason yaron sosae amma yakamata ace akwai
Wanda ze karfafawa badee gwiwa kodan lafiyarta da abinda ke cikinta,
Har yanzu tana gurin takurawa kofar da mukhtar yabi yafita da gawar jabir ido,
Hannunta Asmau taja suka fita binta kawai take batama ganin gabanta,
Yaron ya kwanta mata sosae azuciya tanasonsa yanada sanyin hali tasaba dashi shine Abokin
hirarta,
Yasan yasaka hannunsa yana share mata hawayen fuskarta duk lokacin dayaga tana kuka se
lokacin taji hawaye masu zafi sun zubo mata batayi kokarin hanasu zubowa ba,
Tanaso sucigaba dazubowa kozataji sanyi azuciyarta.
_kuyi hakuri da wannan wallahi yau se a slow nasamu deepcut ne dan yatsata_ILVY oll.
[7/5, 8:06 PM] Babee Feeya: *Y'AY'ANA (Abin alfahari)*
_by SophieG_
_A very heart touching story 2017_
_wannan shafin naki ne anty bilkisu (maman nu'aym)_
*kada mudauki rayuwar duniya abakin komai domin ba komai bace*
*Arayuwar duniya mutun uku ne sukafi kowane mutun bakin jini*
*mutun nafarko shine mutun me girman kai yanajin kansa so high idan yashiga mutane seya ringa
d'age d'age yanajin yafi kowa,to wannan mutun zakuga kowa bayason haduwa dashi domin zuciya
tafison Wanda yake kyautata mata semu kiyaye wannan idan munshiga mutane semu kyautata
mu'amalar mudasu saboda mutane Rahama ne*
*Allah yabamu hakuri Ameen*
Page 6
Yaran dukansu suna makaranta daga ita se jabir suna zaune a corridor yana ta wasan sa miqewa
tayi tashiga daki dan jin karar wayarta,
Bata fito ba seda tagama wayar dasauri tadaga labule tana fitowa danjin karar wani abu,
Tsayawa tayi tana kallon abdulmajid kafin ta maida dubanta ga jabir dayake kuka haryana shidewa
ga gefen fuskarsa yayija harya soma kumbura dauke idonta tayi daga kallonsa takarasa kusada
abdulmajid tanayimasa sannu dazuwa cikin karaji yafra magana,
Banason sannu dazuwanki munafuka nahanaki zama dayaranki duk inda nake ajiye kayana amma
dan wulakanci shine zakibar wannan yaron yataba min takalmi yau dasafe nabawa me shoeshiner
ya gogesu kalli yadda danki yasaka musu kura bayan hakama kinsan ko nawa nasiye su?,
Kallonsa kawai take kafin tamaida dubanta ga takalmin babu alamar kura kokuma antabasu,
Wanine yataboshi awaje shaine yazo yasauke hannunsa kan dan bawan Allah kobadan komaiba
kodan yarintarsa ze masa uzuri,
Batace komai ba tasamu guri ta zauna kallon jabir din take da wahala tasakashi bacci gashi
balafiya gareshiba yauma da zazzabi yatashi,
Bin bayansa tayi da kallo yadda ya daki kofar dakinsa yashige tabe baki tayi,
Azuciyarta tace yau nayi niyyan fadamaka ina dauke da cikinka Na shida amma naga kanka Na
hayaki batason hayaniya yau shiyasa zanbari harka huce komai zakayi sekayi,
Adaki kuwa mamakin hali irin na badee yake ko yaki ake bisa kanta inbataso tankawa ba bazata
tanka ba shikuma abinda ya tsana kenan yafiso tabiye mai suyita yi amma betaba samun haka ba,
Fama take da kanta gakuma jabir yatashi da zazzabi me zafi dan ko zama yakasayi se
mak'alk'aleta yake dakyar tasamu tashirya yayyensa suka tafi islamiyya,
Paracetamol tabashi na yara Allah yataimaketa akwai shi goyashi tayi tashi ga kitchen dukda
tanajin badadi jiri takeji gakuma zafin jikinta yana haduwa da nasa seta ringajin wani iri,
A daddafe tasamu ta kammala abincin takoma daki ta kwnatarda jabir dayayi bacci,
Se bayan isha tasamu kanta yaran duk sunyi bacci saboda wahalar wuni amakaranta,
Kallon fuskqr jabir dake gefenta take shatin yatsun babansa da ya kwandara masa mari dazu
gasunan radorado wurin ya kumbura tausayinsa yakamata batasan lokacin da hawaye ya zubo
mataba dasauri tasaka hannunta ta goge hawayen fuskarta jin abdulmajid ya kwallah mata kira
tashi tayi kafin ta amsa da muryarta can ciki,
Yawwa badee nace abdulrahim yaci abinci kuwa naji shiru kamar yayi bacci,
Gyada masa kai kawai tayi danjitake bazata iya magana ba,
Bakida bakin da zaki amsamin ne?
Eh yaci tayi maganar dan batason hayaniya,
Janyota yayi jikinsa yana tambayarta,inafatan kema kinci?
Eh tace tadora da fadin,
Kayi hakuri yau bazan kwana adakinka ba saboda jabir bayida lafiya tunsafe yake fama da
zazzabi,
Nikuma ina bukatar ki,
Yafada yana harde hannayensa akirji yazuba mata idanuwansa,
Kauda kanta tayi gefe dan batason irin wannan kallon kafin tace,
Kasani bazan bar yarana sukadai adakiba kuma daya cikinsu babu lafiya ze iya tashi cikin
dare shisa nace kayi hakuri yau kadai,
Banyaddaba inkuma kin yadda ki kwana cikin tsinuwar Allah da mala'iku ne karkizo,(wai kuti ke
cewa kaza k'azama)
Kayadda nazo dashi dakinka? Ta tambayesa cikeda gajiya da maganar,
Banyadda ba nafada mini,
Yafada tareda ficewa daga wurin yana barinta atsaye,
Takasa koda motsi dangaskiya bazata iya barin dantaba ga bayida lafiya.
[7/5, 8:06 PM] Babee Feeya: *Y'AY'ANA (Abin alfahari)*
_by SophieG_
_A very heart touching story 2017_
Assalamu alaikum
Dafatan munyi azumi da sallah lpy? Allah yakarbi ibadunmu ameen.
Inajiran goron sallah na 😎.
Page 9
Badee'a tayi lkuka harta gode Allah sotake taga laifin mijinta nakin kulawa da lalurar data sami
dansa har yakai ga ajalinsa,
Majid mugune Dabadan se lkcn mutun yayi yake mutuwa ba da ta dauki kaddarar mutuwar jabir
rankatakaf ta rataya awuyan majid sekuma wannan yaci karo da abu biyu sonda takeyiwa
mijinnata dakuma albarkacin yayan dake tsakaninsu,
Bangaren majid kuwa mutuwar ta dan tabashi sbd betaba kawowa yaron mutuwa ba gashi badi'a
ko kallonsa batayi tunjiya bayan dawowarsu daga asibiti dyasani yake dabe kula yaronba lkcn
dayake bukatar taimako kobadan kasancewar sa dansa ba kodan mahaifiyar yaron dayake matukar
so tawani bangaren kuwa abincin da yan tsirarrun mutane masu zaman amsar gaisuwa en uwansa
da nata keci shine yakeji kamar naman jikin sa ake cira gani yake kamar tattalin arzikinsa suke
cinyewa gsky akwai matsala baze iya yin wani yunkuri na hana zaman ba amma yana ftan daga
Gobe arufe zaman makokin (wannan ko dai Dan iska ne🤔),
Dahaka rayuwa take tafiya har akayyi wata biyu da rasuwar jabir babu abinda ya sauya a al'amarin
majid da gidansa badia wahala take ga wannan karon batayi sa'ar cikin ba yana bata wahala sosae
sana'ar da take bakullum takeyi ba yaranta duk sun fita hayyacinsu,
Yauma kamar kullum ta tashi se a hankali dakyar ta hadawa mijin breakfast yafita aiki ga yunwa
Dan kadan tahada danata bayawa Dan haka yaran kawai sukaci tace zata jira abincin rana lkcn
cikinta yana wata shida kenan,
Bayan azahar yadawo gida yasameta kwance a korido zazzabi yahanata sukuni ga jiri,
Yaya asma'u ta taso daga aiki tace zatazo taduba kanwarta tundaga waje take sallama bataji an
amsaba,
Maganar majid taji yasa ta tsya awaje,
Zma yayi kusa da ita en mata abani abinci na debo yunwa garinnan rana tayi yawa,
Don Allah kayi hakuri wallahi yau banajin dadi banyi girki ba,
Miqewa kawai yayi ya soma fada,
Dan bakyajin dadi sena zauna da yunwa kullum seki lafe kice ba lpy amma kin iya yin sna'ar ki
seni zaki zalunta kibarni da yunwa? To wallahi kinyi kadan yanzunnan kitashi kidafamin abinci
inajiranki Dan Nagano nema kike kizama muguwa,
Batason masifar nan shiyasa ta miqe zuwa kitchen tasan idan ba girkamasa tayiba masifa zetayi,
Yaya asma'u wni abune ya tsya mata awuya zuciarta tadau zafi Tajuya tabar gidan dole sudau
mataki baze yiyu sunaji suna gani a kashe musu er uwa ba tafiya take tana kwalla sbd tausayin
kanwarta mijinta takira tafada masa tana hanyar zuwa gdn ya mukhtar zasuyi magana ne yasan
batada yawo Dan haka ya amince,
Tayi Sa'a yayan yana gida yadawo da wuri tazauna ta labarta masa komai datasani tun bayan
haihuwar abdulrahim har zuwa yau,
Yayi masifa kamar ze cinyeta danme tayi shiru seyanzu tafada masa yabashi hakuri yace tawuce
gida zeyi tunanin me zasuyi,
Washe gari tunda sassafe yaje gidansu yazauna da iyayensa cikin kwamciyar hankali yafadamusu
yadda sukayi da Yaya asama'u yakuma cekarsu daga hankalinsu baba yashirya ranar asabar zasuje
gidan dole sudau mataki mahaifiyarsu har kuka tayi sbd tausayin erta da halin datake ciki,
Sunyi sa'ar samun majid a gida Dan sammako suka yi idonsa zuru zuru domin be taba ganin alhaji
a gidan ba sama sama suka gaisa Yaya mukhtar yanemi akira masu badi'a Gabanta yayi
mummunan faduwa dataji lbrn babanta ne da kawunta se Yaya mukhtar harda asama'u aka zo,
Tass suka zube masa sunsan halin da badi'a takeci Wanda sune shida mahaifiyarsa suka sanyata
ciki atake ya kidime zufa yafara karyo masa,
Alhaji ne yafara magana
Abdul bana bukatar sulhu Sakar min yata zakayi yanzu base anjimaba sbd itama haifarta akayi ba
jaka nakawo maka ba kuma tanada gata gaba da baya kuma inaso kasani Yaya dakake cewa
bakaso naka ne kokaki kokaso Dan kasanima yanzu idan zamu tafi iya kadai zan dauka nabar
maka yayanka shima wannan cikin wallahi daze yiyu nabar ma ka shi baze taka kafarsa gidana ba
sekaje can kasamu wacce batason Yaya irinka ka aura,
Seyanzu yasan yana cikin tashin hankali Dan harya fara hango rayuwarsa babu badeea ya hango
rashin kwanciyar hankali tsintsarsa aciki yatafi duniyar tunani kukan badee ne yadawo dashi,
Ta kama kafar alhaji,
Baba don Allah kayi hakuri karka rabani da yayana da mijina wallahi inasonsu kubarni dasu kodan
tarbiyar yayana,
Garama kidaina rokona bazan juri ana wulakanta ki ina kallo ba kobana raye bazan yadda ba,
Baba wallahi inkuka rabani da majid zan iya mutuwa wallahi inason uban yayana ,idonta yarufe
da soyayyar mijinta bata gani bata hango abinda magabatan ta ke hango mata duk baba har aransa
baso yake yarabata damijinta Ba yaso ace tabashi hadinkai ya hora majid amma takawo cikas,
Akaro na uku baba yasa ke umurtarta data tattaro kayanta kuma bayaso tadauko yaro ko daya
acikinsu abdul ,
Idonta arufe tana kuka tace baba kayi hakuri bazan iya barin yayana ba nasani wata rana zasu
zama